Page 1
Kamar kowane dare idan zatayi bacci wajibi ne ta toshe kunnenta da earpiece tana mai sauraren music 🎶 haka kuwa ya kasance a cikin wannan dare mai tattare da rudani da kuma ban tsoro, tun da gari ya waye takejin jikinta duk ya rikice, sai kuma tunane tunane marassa amfani da suka dabaibaye mata zuciya, gidan makekene tamkar wata masarauta 🏯 iya tsaruwa ya tsaru amma abun mamaki shine mutum uku kawai ke rayuwa a ciki, ita, abbanta sai mumcy, ba yadda mumy bata yiba domin abba ya aje musu mai gadi amma yaki, domin shi bai yadda da kowa ba, kai ko mata masu aikace aikace bai yadda a ajiyesu gidan ba, hakane yasa mafi yawan aikace aikacen gida mumy ce da kanta ke daukar nauyinsu, kasancewar abba mai yawan tafiye tafiye ne baa fiye ganinsa ba, kai abun haushi ma shine gina wannan makusudin gidan sama a jagwalgwalallen kauye irin wannan, ba nepa balantana ayi maganar fanfo, 🚰 kai ko hanyar mota babu, aduk lokacin da abba zai fita sai yayi zagaye a cikin jeep dinsa na akalla minti talatin kafin ya iso titin gaske, titin kuwa kamar anyi ruwa an dauke, sunan wani gari ihunka banza gudunka banza, haka titin yake tsit, ko tsuntsu baya giftawa balantana ayi maganar mota. To abun tambaya anan shine wai me yasa motoci basa bin wannan titi? Titin yanada wani camfi ne ko kuwa? Yadda wannan titi yake haka tsarin kauyen yake, gidaje daya daya, can da nan, kuma tsakanin wannan gida da wancan gida akwai tazara sosai, kasancewar gidajen na laka ne, mafi yawan masu gidajen manoma ne da mafarauta amma kowa sha anin gabansa yake, ba ruwan wani da wani, ita dai Humaira🚺tunda ta taso ta ganta a cikin wannan gida, gidan ya mata amma rayuwar kauyen bata mata ba, batada aboki ko daya a cikin wannan kauye, to yama za a yi tayi aboki da bakauye kasancewarta wayayya, in ma banda kaddara ya za a yi ta zauna irin wannan kauye? A haka Humaira ta cigaba da gyangyadi tana sauraren music daya taushe mata kunne, dare ya raba sosai 🌃 tanaso ta shiga daki amma ji take tamkar idan ta shiga dakin baxata iya baccin ba, gashi mumy da Abba sun yi tafiya, yau ita kadaice a gidan, tana cikin gyangyadi ne sai taji karar wani abu ratsatsss tamkar an fashe glass, firgigit ta mike tana dube dube, bata ga kome ba in banda kyanwowi data gani a can gefe suna guje guje, tsuki taja mai karfi daga nan sai ta kishingida da nufin ta cigaba da baccinta amma abu ya faskara.
Page 2
Fita tayi harabar gidan tana kallon flowers,🌼🌿🍁 ga karar generator daya cika mata dodon kunne, a nan ta zauna zaman plastic chair tana danne dannen waya, ta fara buga game na Zuma kawai sai ta fito, kome taji kawai sai ta tashi ta nufi cikin gida, to kafin ta karasa ne sai tayi tsaye baki bude tamkar wadda taga mutuwa, a hankali ta fara tafiya tana duban wani abu daya tayar mata da hankali, hawaye ne ya fara fitowa daga idanunta daga nan sai ta sheka a guje a wurin kyanwar 🐆 data gani jina jina, abunda ya tayar mata da hankali shine wane abune ya shigo gidan har yayi sanadiyar mutuwar kyanwar ba tare data sani ba, dazu fa ta ganta tare da sauran kyanwowin suna guje guje amma yanzu ace wai ta mutu, abunda yafi bakanta mata rai shine tun kyanwar na yar kankanuwa take kiyonta amma yanxu a wayi gari ace wai ta mutu, tsintsiya ta dauko tare da abun kausar shara, daga nan sai ta dauki gawar kyanwar ta ajiye a cikin kwandon shara, 🚮dakyar ta iya ajiye tsintsiyar daga nan ta nufi cikin gidan, ai kuwa daga shigarta sai taja da baya tana nishi dakyar, wani tiririn hawaye ne ya fara kwararowa a idanuwanta sanadiyar ganin daya kyanwar a mace, anan Humairat tayi shiru a cikin jimami tana tunanin ko meyene yayi sanadiyar kashe wadannan kyanwowi, tsintsiya ta dauka kamar dazu ta ajiye gawar kyanwar a kwandon shara, daga nan sai ta tsunduma a cikin gidan tana mai yawaita tunani barkatai.
Tafiya take tana ganin juwa har ta shigo dakinta, ai kuwa tana shigowa sai ta fadi rikicaa tana nishi dakyar, dakyar ta iya tashi tana dafa gina har ta mike, ai kuwa daga mikewarta ta kara faduwa sanadiyar ganin wata kyanwar a mace, wannan abu daban mamaki, kyanwowi uku duk su mutu a lokaci daya! To wai me yake faruwa ne? Meye ne sanadiyar wannan mutuwa tasu? A haka Humaira ta dauki tsintsiya ta ajiye gawar kyanwar a kwandon shara dakyar, tana dawowa tayi jifa da tsintsiya ta haye gado tana nishi dakyar, batayi ta kan wayarta ba domin ciwon ya tsananta gashi ba kowa a gidan balantana a kawo mata dauki, tana cikin wannan hali ne sai taji gidan yayi tsit tamkar makabarta, daga nan kuma sai generator ya daina aiki wanda hakan yayi sanadiyar daukewar wutar gidan gabaki daya, a wannan lokaci ta fara jin karfin jikinta, katanyar lamp ta lalubo ta kunna daga nan sai ta fita domin ganin meke faruwa da generator ne, tafiya takeyi tana tangadi domin har yanxu da sauran ciwo a jikinta.
Page 3
Koda takai bakin kofar fita sai taji ana kwankwasa gate din, gabanta ne yayi mugun faduwa domin tasan batada aboki a kauyen kuma su Abba zasuyi kamar sati daya kafin su dawo, a hankali ta fara tafiya tana makarkata har ta iso ga gate din, hannunta ta sanya ta bude sakatar amma mamaki wayam ba kowa, har zata juyawa sai taji an rikota ta baya, tana juyawa sai tayi murmushi cikin jin dadi, a lokaci guda sai taji duk ciwon dake jikinta ya saki ta dawo kamar ba ita ba.
” Gambo bakada mutunci, ni har kaban tsoro,” Haka ta fada tana nuni da hannunta da nufin ya shigo, ai kuwa yana shigowa sai ta rufe gidan da sakata, tana rufe gidan sai generator ya kunna kansa ya cigaba da aiki, abun ya bata mamaki amma kuma sai ta nuna kamar bata damu ba, Gambo shine mutum na farko daya fara approaching din Humaira a cikin wannan kauye, sau da dama tana mantawa dashi wannan dalili yasa idan aka tambayeta zata iya fadi cewa batada aboki domin har yanxu bata yi masa daukar aboki a wurinta ba, ita bata masan yadda akayi yasan gidan da take ba domin a cikin wani dare ne da matsanancin ciwo ya kama abba, to akan hanyarsu na fita asibiti ne ta hadu dashi, to anan ya nuna mata hanyar fita kauyen domin a lokacin ba wani fita take ba, daga nan taci gaba da tuka motar 🚗 har ta fita kauyen, bayan kwana uku da faruwar hakan bayan abba ya samu lafiya sai gashi kwatsam har gida, sun dade suna fira, kuma sun dade da shakuwa amma abunda ke bata mamaki shine duk da dadewar da sukayi suna mu amala bai taba fada mata kalmar so ba, to ko me yake bukata a wurinta ne, kayan jikinsa da kalaman bakinsa duka na kauyawa ne amma kirar jikinsa na yan birni ne,da yake shi wankan tarwada ne, yafiye sa kaya farare riga kamar vest 🎽 da wando, sai cover shoe dinsa na roba da wata yar hula kube, amma hular ba kullum yake sanyawa ba sai yaga dama.
Wasu lokuta yakan bata haushi wasu lokutan kuma ya burgeta, yau kan da gani ya burgeta domin yadda take kallonsa cikin murmushi da sakin fuska abun ba a cewa komi, jan sa tayi ga plastic chairs, anan suka zauna suna kallon juna, Juice na Happy Hour da ta rage dazu ta dauko, da yake glass cups na a wurin, batayi wani wahalar shiga cikin gidan ba, tsiyaya masa tayi sai da cika cup din dam dam sannan ta mika masa, ai kuwa Gambo yana kafa kai kafin kaceme ya zuke juice din tas, anan ya ajiye cup din yana gyatsa, ita kuwa Humaira bin sa da kallo tayi cikin murmushi.
Page 4
Abun ya bata dariya amma kawai sai ta kanne tana dubansa. Ba karamin dadi ta jiba domin bako shakka ta samu abun debe kewa da yake shi mutum ne mai ban dariya da nishadi.
” Kin tsura min ido kina kallo sai kace baki taba ganina ba.” Haka ya fada yana kara tsiyaya juice din a cup.
” Kayi hakuri dama… ”
” Dama me?” Anan ya kafa kai ga cup din, ji kake kulum kulum kulum kulum, sai da ya shanye tas sannan ya ajiye yana dubanta, duk yadda Humaira taso ta boye dariyarta abun ya faskara, batasan lokacin data dafe ciki tana zuba dariya ba tamkar baxata daina ba, shi kuwa gogan naka bude baki yayi yana dubanta har sai da ta daina.
” Humaira bakida mutunci, yanxu ni kikewa dariya.”
” Kayi hakuri.”
” To nayi! Hala wai ina kawayenki kyanwowi, yau banji shawaginsu ba!” Anan Humaira tayi shiru domin batasan abunda zata ce masa, har yanxu bazata iya fadin abunda yayi sanadiyar mutuwar wadannan kyanwowi ba!
” Am inaga suna nan, wata kila sunyi bacci.” Anan Gambo ya kalleta cikin wani kallo wanda bai taba yi mata irinsa ba, da alama akwai abunda yake tunani amma ko meye ne?
” Da kyau, to ni zan koma saida safe.” Anan ya tashi ya nufi hanyar fita. Ita kuwa bin sa da kallo tayi, ji take tamkar ta tashi ta hanasa fita amma kuma baxata iyaba, ji take tamkar ta kira sunansa amma kuma baxata iyaba, ji take tamkar tayi tsalle ta rufe gate din domin kada ya fita amma baxata iyaba, to wai me yasa baxata iya hanasa fita ba alhali tana mutukar son ganinsa a kusa gareta, haka tayita dubansa har ya fita gate din, daganan ya hau donkey 🐎 dinsa ya saki linzami ya mika a guje, yana fita sai yanayin humaira ya canxa gaba daya, har yanxu tanajin sukuwar jakinsa a nesa amma kuma bazata iya fita ta kirasa ba, tashi tayi ta nufi cikin gida tana taku dai dai tamkar mai ciki, tana shiga bedroom ta yashe a saman gado tamkar gawa, sai nishi take daya bayan daya su kuwa idanunta sun mata wani nauyi, da yake duk fitillun dakin a kashe suke wanda hakan yasa dakin ya gauraye da wani mummunan duhu, arzikin da tayi shine lamp a kunne take, takan iya ganin haske amma kalilan, generator ne ya kashe kansa da kansa wanda hakan yayi sanadiyar janyo wata bakar kewa a gidan gabaki daya.
Page 5
. King Article-Queen Teei
Anan jikinta ya fara makarkata kamar mai jin sanyi, daga nan sai ta fara ganin dishi dishin wani abu kamar duhu gum ya hade dakin gaba daya, a wannan lokaci ta fara fita hayyacinta sabida tsananin ciwon daya addabeta, idanunta ne suka fara karkarwa suna rufewa a hankali, a hankali, a hankali, kafin daga bisani su rufe ga baki daya…….
BEFORE……….
♈♈♈KAFIN FARUWAR WANNAN ♈♈♈️
Nasir Ahmad mutum ne mai sa a ga kuma kwazo, yana kammala degree dinsa ya samu schorlarship a India, New Delhi, a can yayi masters dinsa, a wannan tafiya ne ya hadu da wata yarinya Bilƙisu Ahmad, tun daga farkon ganinta yaji ta kwanta masa a rai sabida haka sai yayi ta daukin su isa domin ya samu damar aiyana mata abunda ke cikin ran sa, 💟 ai kuwa suna isa sai yaga a jamia daya zasuyi karatu wato University of Delhi, babban abunda ya faranta masa rai shine a department daya suke, Department of Philosophy, ko kadan bai sha wahala ba wurin amso zuciyar yarinyar kasancewarsa kyakkyawa kuma hadadden gaye, a wannan lokaci ba yada wani clothing da yafi jeans, short shirt, long sleeve da sauransu, soyayyar da suka kulla ta kasance abun sha awa, domin dukkaninsu gwanaye ne a fannin kalamai. Suna kammalawa suka dawo Nigeria, anan suke fara lecturing a wata jami a, soyayyarsu ta kara kaimi domin a wannan lokaci sun fara shirye shiryen aure, to a cikin wannan shirye shirye da sukeyi ne wani scholarship ya fito, ba yadda Nasir bai yiba domin Bilƙisu ta cika amma ta kekasa kasa taki, shi kadai ya cika form din kuma cikin sa a ya samu, a nan aka ingizasa a University of Cambridge, United Kingdom, domin yayi Phd dinsa, da yake dan kwanya ne bai sha wani wahala a karatun ba, yana kammalawa ya dawo da kwalinsa, bai wani jima da dawowa ba aka fara shirye shiryen aure, Nasir mutum ne mai tsatstsauran ra ayi, shifa ko kadan bai yadda da kowa ba domin gani yake ako yaushe za a iya cutar dashi, a bisa wannan dalili ne da zai gina gida sai ya samu wani irin jagwalgwalallen kauye da ko titin kirki babu balantana ayi maganar jin dadi na rayuwa, a wannan kauye yaxo ya gina gida naji na fada, kai da gani kasan naira ta zauna, ana daura aure bayan an kammala shagulgula na biki sai aka kawo masa amaryarsa Bilƙisu, sun ci moriyar juna dai dai gwargwado a cikin wannan aure, bayan shekaru uku ne suka samu haihuwa, 🚼anan aka radawa yarinyar suna Humaira, Humaira ta taso sangarce bata ganin darajar mutane balantana kimar dan adam duk da kasancewar iyayenta masu mutunci ne dai dai gwargwado.
Page 6
Amma kuma duk da wannan shakiyanci da takeyi bata bari su Abba su sani domin tasan idan suka san da cewa tanawa jama a daukar uku saura kwata tofa kashinta ya bushe, ita kadaice ga iyayenta, wannan dalili shine ya bata damar yin duk wani abu da takeso cikin walwala ba tare da tsangwama ba, Abba da ummy suna mutukar sonta tamkar su hadiyeta, ita kuwa ba wani damuwa tayi da hakan ba, a kullum gurinta shine taci tasha taji dadi na rayuwa, su kuwa jama a tamkar kiyashi haka take daukarsu……
” Humee Humee, Humee .” bacci takeyi amma tanajin murya kasa kasa ana kiranta, da hamma ta farka tana bude idanunta.
” Shegiya baby, wai yaushe kika zo nan.”
” Ki tashi kiyi wanka mana, kada fa ki manta yaune ranar convocation amma kinyi wani kwance lame lame sai sharar bacci kike.”
” Ni har na manta.” Anan Humaira ta shiga ciki, da sauri ta watsa ruwa ta dawo dakin.
” Wai ina su Mamee ne?” Humaira ta tambaya.
” Ke ba kowa fa, duk sun wuce Convocation Hall, nima sabida ke kawai na tsaya.” Cikin gagggawa Humaira tayi kwalliya daga nan ta dauko long gown dinta ta aza saman wata ratsatstsiyar atamfa, heel shoes 👠 ta sanya mai kwas kwas wanda yayi matching da atamfarta da kuma gown din, sai wata yar pursue 👜 ta yan mata data rayata. Tare suka fito dakin daga nan suka kamo hanyar fita hostel din suna tafe suna hira.
” Ikon ALLAH, wai yanxu mun kammala degree, mun zama graduate, 🎓 baby mun zama graduate.” Haka Humaira ta fada cike da murmushi cikin zumudin ganin cewa sun isa hall din.
” Haka duniya take, komi yayi farko zaiyi karshe.” Inji baby.
” Ai dole mu cashe wannan biki da za a yi mana, bikin kammala makaranta.” Inji Humaira.
” Casu ai dole ne.” Inji baby. Suna shiga hall din kawayenta suka fashe musu da sowa da tabi, da yake Humaira ce star a wurin, selfie suka fara kashewa kafin daga bisani big boys masu ji da kansu su fara tururuwa a wurin. A nan aka hargitse masu hotuna nayi masu hira nayi, ba a fi minti biyu ba Vice Chancellor ya karaso tare da jama arsa, anan Mr. Speaker 🎤 ya gabatar dasu daya bayan daya daga nan kuma ya fara kwararo turanci kamar ruwan sama.
Page 7
Anyi shagali sosai ba kama hannun yaro, an ba students da dama award, Humaira ta karbi award na (Best in Poet📚) bayan an kammala taron ne sai wasu daga cikin yan department din su Humaira suka shirya wani kasaitaccen party a cikin wannan dare, kuma da yake sun san abunda za a yi a wurin ba mai kyau bane sai basu bari hukumar makaranta tasan da party ba domin kada a hanasu, wani daji ne nesa da makarantar suka kebe domin yin wannan shagali, a cikin wata hadaddiyar jeep 🚙 ta Humaira suka kebe domin yin wannan tafiya, da yake su Humaira sunyi lattin zuwa domin koda suka fara shirye shiryen tafiya da yawa daga cikin abokanta duk sun wuce, ita kadai ta rage sai baby da mamee, sai kuma abokanta maza biyu wato Nabil da Mujahid, saida su Humaira sukayi sallar Isha i sannan suka miki hanya ba sassauci, Nabil ne ke tuka motar sai Mujahid a kusa dashi, su kuma su Humaira a baya, Humaira ce a tsakiya sai baby gefen hagunta ita kuma mamee a damanta.
” Nabil ka sanya mana music mana.” Inji Mamee.
” Bakida matsala yan mata.” Anan ya bata amsa. Wayarsa ya dauko yayi connecting daga nan sai ya sanya wani waka na larabci wanda Mishary Bin Rashid Alafasy ya rera.
” Minene wannan abu, waka fa akace ka sanya mana shine zaka sa mana wasu larabawa can.” Mamee ta fada cikin tsawatawa.
” Wannan wakar itace nakeso, kuma banda abunki hala baki san da cewa waka haramun ce ba.” Inji Nabil.
” Au, kasan waka haramun ne to me yasa ka kunna wannan?”
” Ai banda irin wannan, waka mai kidi itace haram, amma marar kidi ba laifi kinga kuwa wannan dana kunna ba laifi a ciki.” anan Mamee tayi shiru domin batasan amsar da zata bashi ba, ita har yanxu bata gamsu da wannan zance nasa ba amma kuma a cikin ranta ta sanya cewa da sun koma gida zata tambayi malaman addini hukuncin shan waka mai kida da marar kida.
Page 8
Bayan sun iso ne sai sukaga ashe kallo ya barsu baya, maza da mata ne an hade sai rawa akeyi ana nishadi, wani dogon table suka nufa, anan suka zauna saman kujerun dake manne a table din, wasu kayayyakin abinci ne iri iri a sama, anan suka fara ci suna hira, a can gefensu kuwa duk irin wadannan table din ne da yawa ga kuma abinci yadda da mutum ya zauna iyaka ya fara ci, a wannan lokaci wurin ya gama cikewa da jama a, wasu na zaune saman table suna cin abinci wasu kuma sai tikar rawa suke, wasu kuma sai shige da fice suke.
” Mamee shiga xenda ki turomin hotunan da mukayi a school.” Inji Humaira.
” Okay dan bani minti biyu ina WhatsApp zan masa replie, amma ki shiga sai kiyi receiving.” Mamee ta fada tana typing da sauri. Bayan Humaira tayi receiving ai kuwa cikin kankanin lokaci sai hotunan suka fara shigowa, suna gama shigowa sai ta fara dubansu daya bayan daya tana murmushi. Tana cikin dubawa ne sai taci karo da wani, ai kuwa tana dubansa sai gabanta yayi mugun faduwa, ganin kanta tayi tare da wani saurayi an musu hoto su biyu, to abunda ya bata mamaki shine bazata iya tuno lokacin da aka dauki hoton ba, gashi kuwa fuskar saurayin tayi wani dishi dishi balantana ta iya ganesa, haka kuma kayan jikinsa duka basu fito da kyau ba, bazata iya tantance ko wadanne iri clothing ne ya sanya ba, a haka taci gaba da duban hotunan tana ganinsu tare wasu ma harda kawayenta.
” Wai Mamee kin san ko waye wannan saurayin?” Anan mamee ta dubi hoton cikin natsuwa, kafin ta bata amsa.
” Gaskiya ban sani ba, amma wata kila friend dinki ne ko!”
” Aini bama wannan ba, abunda keban mamaki shine bazan iya tuno lokacin da aka dauki hoton ba.”
” Kut! Gashi kuwa wasu hotuna bani na dauka ba balantana nace ga yadda akayi, amma wannan ai ba abun damuwa bane koma wanene ai zamu sani nan gaba.” Shiru sukayi suna kallon masu rawa, bayan dare ya raba sosai suka karayin hotuna da yawa daga nan suka dawo hostel, dukkansu sun amshi result amma kuma bazasu koma gida ba sai sun gama sharholiya, yau ne Day 1, saura Day 2 and 3. Tun da asuba Humaira take mikewa tayi shirye shiryenta, to yauma kamar kullum bayan ta tashi, brush ta farayi sai ta dauro alwala tazo ta fara salla, bayan ta tofa addu a ne sai ta dauko wayar Mamee.
Page 9
Cikin my pictures ta shiga ta fara dube duben hotunan domin ta tura wadanda sukayi jiya da dare, jiya din wayarta ba charge shi yasa bata samu damar turawa ba tun daga wadanda ta tura daga farko, su kuwa kawayenta Mamee da baby sai sharar bacci sukeyi abunsu, tana lalubo hotunan sai ta turosu gaba daya, daga nan sai ta ajiyewa Mamee wayarta. Fara kallon hotunan tayi cike da nishadi, cikin rashin tsammani kuwa sai ta kara ganin hotonta tare da wannan saurayin na jiya wanda taga hotonsu tare, anan Humaira ta kidime domin daren jiya gaba daya batayi hoto da namiji ko daya ba. Abunda ya kara tayar mata da hankali shine ko yanzu hoton bai fito clear ba, dishi dishi ne dashi yadda baxata iya gane saurayin ba kuma bazata iya gane clothing na jikinsa ba, wasu hotunan kuma sai ta gansa da ita da kawayenta. Anan Humaira tayi shiru domin bazata iya cewa komi ba, ita dai batasan lokacin da akayi hotunan ba. Risho ta dauko daga nan sai ta daura musu break fast, bayan ta kammala ne tayi nata kalacin sai taji bari ta fita domin tasha iska, wani corridor ne tabi sai tafiya take tana murmushi, yau dai cike take da farin ciki kuma batasan dalilin wannan farin ciki ba, iska sai bugawa yake da karfi domin a wannan lokaci safiya bata ida wayewa ba, akwai dan duhu ba sosai ba. Bayan ta kawo gab da kofar fita sai taji kamar an rike mata kafafuwa, wani irin ciwo ne wanda bata taba jiba, tun daga cinyoyinta har zuwa kasan kafafuwanta sai taji tamkar ana zuba mata ruwan sanyi a ciki, anan tayi tsaye tana dafa gina domin bazata iya tafiya ba, dishi dishi ta fara gani a gabanta daga nan kuma sai ta shiga wani yanayi tamkar mafarki.
” Nine dai wanda kike tunani.” Inji wani bakin abu mai kamada inuwa.
” Kaine wa?” Humaira ta tambaya.
” Kina nufin baki san koni waye ba?” anan ya kara tambayarta.
” Gaskiya ban san ko kai waye ba.” Humaira ta kara basa amsa.
” To yanxu zan miki wata tambaya kuma ina fatan zaki ban amsa.”
” To idan da damar hakan.”
” Wane suna zaki kira wanda ke yawan baki kulawa kuma yana kawo miki ziyara?”
” Masoyi ko kuma aboki!”
” Toni miye matsayina a gurinki, ma ana ni masoyinki ne ko kuma aboki.”
” Gaskiya ban sani ba, amma meye amfanin wannan tambayar?”
” Sabida ya kamata kisan matsayina a gurinki.”
Page 10
Queen Teei-King Article
” Bakada wani matsayi a gurina, ni dai ka rabu dani, ka rabu dani mana, ka rabu dani kawai” A hankali Humaira ta bude idanuwanta tana kallon Mamee a kusa da ita, ita kuwa Mamee ta tsura mata ido, ita kuwa baby kwance take a can gefe tamkar gawa.
” Hala me ya faru?” Humaira ta tambaya.
” Ai ke zan tambaya me ya faru, tare da baby na dauko ku a sume a kofar fita.” Inji Mamee, Sai da Humaira tayi shiru tana tunani, abunda ya fara fado mata a rai shine ciwon data fara ji a cinyoyinta daga nan kuma bata kara sanin inda take ba.
” Ki fadamin menene ke faruwa?” Mamee ta tambaya.
” Nima ban sani ba.”
” Ban gane baki sani ba, to idan bakiyi magana ba ya za ayi mu taimakeki?”
” Ni inaga kamar nayi mafarki ne!” Inji Humaira.
” Mafarki fa kika ce! To me kika gani a cikin mafarkin?”
” Bazan iya tuno dukkan abunda na gani ba, amma inaga kamar nayi magana da wani abu.” Humaira ta fada tana duban yatsunta.
” Wani abu kuma, kina nufin ba mutum bane?”
” Mamee nima fa ban sani ba, bazan iya tuno siffarsa ba kuma bazan iya fadin abunda muka tattauna akai ba, iyaka dai nasan nayi magana da wani abu.” Tarin da sukaji Baby nayi shi ya maida hankalinsu a wurinta, firgigit ta farka tana kallonsu.
” Hala me ya faru kun tsuro min ido kamar baku taba ganina ba.” Baby ta fada a tsawace.
” Ba a sani ba.” Inji Mamee.
” Oho miki.” Anan baby ta mike da nufin shiga toilet, haka Mamee ta bita da kallo har ta shiga, ai kuwa tana fitowa Mamee ta cikata da tambayoyi.
” Da safe da kika tashi ina kika tafi?” Mamee ta tambayeta.
” Wai miye ruwanki dani, kajimin mace!” Inji baby tana murguda baki.
” Ke jaka ce, shegiya, don ubanki idan bakiyi magana ba ya za ayi musan halin da kuke ciki, tare da Humaira na dauko ku a sume ni nama aza kun mutu!” Anan Baby ta fara tunani, dazu da safe tana farkawa sai ta fara jin wata yar murya kasa kasa kamar namiji da mace, abun yabata mamaki domin tasan da cewa security basu bari maxa su shigo hostel dinsu to me ya kawo namiji a ciki?”
Page 11
Daga nan sai ta fita domin taga ko waye, tun da ta fito take ganin dishi dishi, tafiya takeyi amma ji take kamar ta fadi, wani wuri ma sai ta rike gina kafin ta cigaba da tafiyar. Tana isowa bakin kofar sai taga wata mace mai kamar Humaira, amma baxata iya cewa Humaira ce ba domin har yanxu dishi dishi take gani, a gefen ita matar kuma wani abune a tsaye kamar inuwa suna magana, sai dai shi abun baxata iya fadin siffarsa ba, namiji ne mace ne koma dai minene ita dai bata sani ba. To daga nan sai ta fadi rikicaa shi kenan bata kara sanin inda take ba. Baby na zuwa nan ga tunaninta sai ta labarta wa Mamee shi farko har karshe ba tare data rage komi ba. Ai kuwa Mamee najin haka sai ta juyo kan Humaira.
” Kikace mafarki ne kika yi?”
” Har yanxu ban tabbatar ba, ni ina ganin abun kamar mafarki kuma ina ganin abun kamar da gaske.” Inji Humaira.
” Nima haka nakeji, kamar mafarki kamar da gaske.” Inji baby.
” Wannan al amari naku daban mamaki, yanxu dai kunga Magrib ta gabato sabida haka ku tashi ku shirya domin yau ne Day 2, iyaka dai kuci gaba da addua kuna rokon ALLAH yayi muku tsari akan duk wani mugun abu.” Anan ta tashi ta fita.
” Ni cikin addu o i ayatul kursiyu kadai na iya.” Inji baby.
” Hmm, ke har kin samu kin iya, ni ko fatiha na karanta ai dole sai an cini kuskure.” Haka Humaira ta fada tana janyo phone nata domin tasha music.
” Ke Humee bakida mutunci, yanxu karatun kur ani ma……” Baby ta fada tana kyalkyatar dariya.
” Ke ba maganar wasa ba ni ban ma taba jin ayatul kursiyu ba, shi aya ce ko sura?”
” Lallai akwai jan aiki, bari na shiga na watsa ruwa.” Anan baby ta shiga toilet tana dariya. Da misalin karfe 7:00 PM 🕖, a wannan lokaci Humaira da baby na zaune saman carpet suna cin abinci, shinkafa da miya ce wadda taji carbage ko ina, sai tiririn kamshi ke tashi na danyen kifin dake ciki, ita kuwa Mamee da sauri ta shigo tana murmushi da alama tayi waya dashi ne.📱
” Nayi waya dasu Mujahid, sunce mu wuce kawai zasu iskomu a can.” Tana fadar haka sai ta sa charge ta fita. Su kuwa cigaba sukayi da cin abinci suna kallon Indian film na (Hello) a laptop. Da yake sun dade da kallon film din, abunda kawai ke burgesu shine songs da akeyi a ciki masu dadi.
Page 12
Haka suka cigaba da hira kamar baxasu daina ba, basu fita ba sai da suka yi Isha i, Mamee ce ta tuka motar sai Humaira a kusa da ita, ita kuwa baby a baya, sai da suka fita daga cikin makarantar gaba daya sannan suka kunna fitila, dalilin haka kuma shine an sa musu ido sosai, ai kuwa Mamee na hawan titi ta fara murzar taya ba sassauci, dama gwana ce a wurin driving, sabida tsananin gudun da take zubawa basu wani daukar dogon lokaci ba sai gasu a gun da ake bikin. An kawata wurin sosai ba kamar jiya ba, kuma a yau anfi taruwa fiye da jiya. Abun ba kama hannun yaro, ita dai Humaira tun da suka iso wurin take ganin dishi dishi da juwa, a cikin ranta tasan da cewa mugun abu nagab da faruwa, dama duk lokacin data farajin irin wannan yanayin tofa ba lafiya. Basu dade da zaunawa ba sai ga Nabil da Mujahid, ai kuwa suna zama hira ta barke tsakaninsu, duk abun nan da akeyi ita dai Humaira tsit take domin ji take tamkar ta fashe da kuka, da sauri ta tashi domin ta fitar da urine, sai da tayi tafiya mai dan nisa kafin ta samu wuri kebantacce, dukawar da zatayi haka sai ta fara ganin dishi dishi, anan jiri ya fara daukarta kai kace wadda tayi bori, daga nan sai ta jita dulum batare da sanin inda take ba.
” Wai kai me ya kawoka wurina, bana fada maka ka rabu dani ba.” Inji Humaira cikin tsawatawa.
“Kiyi hakuri yan mata, amma bazan daina zuwa wurinki ba har sai nasan matsayina a wurinki.” Inji wani bakin abu mai kamada inuwa.
” Bakada wani matsayi a guna, ni inaso ka rabu dani kawai.”
” Zan kara baki lokaci ki kara tunani, amma ki sani a kullum ina tare dake.”
Hayaniyar jama a da yawan motsin takalma sune sukayi sanadiyar tashin Humaira, a hankali ta bude idanunta tana duban mutanen da suke zagaye da ita, duban gadon da take kwance shine ya tabbatar mata da cewa a asibiti take kwance, tunani ta farayi akan abunda ya faru jiya da dare, a lokacin data samu kebantaccen wuri domin tayi fitsari, to kafin ta fara ne sai ta fara ganin dishi dishi tare da juwa, daga nan bata kara sanin inda take ba, amma kuma idan aka tambayeta zata iya cewa kamar tayi magana da wani abu wanda batasan ko minene ba, bazata iya tuno maganganun da sukayi ba kuma bazata iya fadin siffar shi wanda tayi magana dashi din ba. Saukowa tayi saman gado a hankali tana tambayar Mamee hanyar toilet. Ai kuwa Mamee na fada mata ta mika da sauri ta shige. Su kuwa sauran abokan nata sai sukayi cirko cirko suna kallonta.
Page 13
Bayan Humaira ta fito daga toilet ne sai Mamee ta sanya ta a gaba da tambayoyi.” Humaira dole fa ki fada muna abunda ke faruwa, shin wai meye ne ke sanyaki wannan suma, ki duba fa tun daren jiya da muka kawoki a nan baki farka ba sai yanxu da rana tsaka, kinga kuwa ba lafiya.”
” Gaskiya ya kamata ki fada mana ko menene!” Inji baby.
” Hakane.” Inji Nabil da Mujahid. Anan Humaira tayi shiru domin bata ma san inda zata fara ba, ita dai har yanxu bata san dalilin da yasa take fita hayyacinta ba, kuma shi wanda tayi magana dashi ji take kamar da gaske kuma kamar mafarki.
” Gaskiya ni ban san ko menene ba.” Inji Humaira. Anan sukayi tsit suna kallonta. Baa fi minti biyu ba sai ga wata nurse ta shigo a wurin da suke, a nan tayiwa Humaira tambayoyi daga nan ta basu list na maganin da zasu siya tare da shaida musu cewa zasu iya tafiya domin ga dukkan alamu Humaira din batada wata matsala. Tare suka fita, Nabil yaja motar yana tafiya a hankali kamar bayason tuki, su kuwa yan matan a baya sai Mujahid a kusa dashi, sai da sukayi tafiya mai nisa kafin su iso ga wani chemist, a nan Nabil ya karbi list din ya siyo magun gunan da aka rubuta, yana dawowa ya mikawa Humaira, daga nan ya buga motar yanufi hanyar makaranta. A wannan lokaci titin tsit yake domin dai daikun motoci ne kawai a sama, su kuwa mutane kamar anyi ruwa an dauke, dukkansu sunyi shiru ba wani mai magana, sai da suka shigo gate sannan Mamee ta iya cewa.
” Ya karfin jikin naki.”
” Alhamdulillah.” Humaira ta amsa.
” Allah ya kawo sauki.”
anan ta amsa da “Amin.” Nabil faka motar yayi kusa ga hostel din mata, daga nan yaja Mujahid suka nufi nasu hostel, su kuwa su Humaira suka tsunduma ciki. Daga shigarsu Mamee ta dora musu indomie, dama kifin jiya data siyo ta rage shi a fridge, dashi ta hada ta musu cooking mai kyau, bayan ta kammala ne ta zubawa kowa nasa a plate. A saman carpet suka zauna suna ci suna hira, da yake ba nepa balantana suyi kallo gashi kuwa ba a kunna generator ba. Suna gama cin abincin sukayi salla, daga nan Mamee tace zata fita shan iska, ita kuwa baby yar son yawo ta lake mata, anan sukabar Humaira ita kadai a dakin tana tunane tunane.
Page 14
Tashi tayi ta shiga toilet domin tayi wanka, tana gama wankan ta dawo ta dauki brush domin ji take bakinta ba dadi, bayan ta gama ne sai ta dawo daki ta zauna, yar wayarta ta dauko ta like kunnenta da earpiece tana sauraren music. Sai da akayi kamar minti goma tana cikin wannan hali kafin daga bisani taji tana so tayi bacci, anan ta cire earpiece din, tana ajiye phone din sai ta juya gefen dama da nufin yin bacci, ai kuwa cikin rashin tsammani sai taci karo da wani hoto, anan ta dauki hoton tana dubawa, abunda ya bata mamaki shine itace a cikin hoton tare da wani saurayi, amma kuma ba zata iya tantance siffar saurayin ba domin hoton yayi dishi dishi, bazata iya ganin siffar saurayin ba ko kuma clothing dake jikinsa, anan ta kurawa hoton idanu, ji take kamar ta taba ganin irin wannan hoton, phone nata ta dauko tana duba my pictures, ai kuwa cikin sa a sai taci karo da irin hoton kamar an tsaga kara. Abunda ya dore mata kai shine wane wuri akayi hoton kuma ya akayi batasan wurin ba, kuma yaushe ne aka dauki hoton, kai bama wannan ba waye yayi printing din hoton domin ita tanada tabbacin cewa ba ita bace, anan ta sa a zuciyarta cewa wai ko abokanta ne Nabil da Mujahid ke mata wasa da hanakali, ko kuma dai su Mamee ne keson raina mata hankali. Fita tayi da sauri da shiga motarta.
Anan ta nufi hostel din maza, tana zuwa bakin kofar sai ta kira Nabil tace yaxo tare da Mujahid, ai kuwa suna zuwa ta fara bugun cikinsu domin taji ko sunada sa hannu da wannan hoton, abun ya kara daure mata kai data gano cewa basuda wata masaniya game da wannan hoto, anan ta sallamesu daga nan ta buga motarta ta koma hostel dinsu na mata. Tun daga bakin kofar take jin dariyar Mamee da alama cewa tare take da baby, kuma tanaji a jikinta kamar basu dade da dawowa ba. Tana shiga dakin ta cika musu kunne da surutu sai da ta samu tabbacin cewa suma basuda masaniya game da wannan hoton sannan ta sassauta musu.
” Humee kin san wani abu? Ni inaga wannan saurayin da kike gani a cikin hoto kamar shine ke zo miki a mafarki,” Haka Mamee ta fada tana dubanta. Anan Humaira tayi shiru domin maganar kamar akwai kamshin gaskiya a cikinta.
“To amma idan hakane me yasa nake fita hayyacina idan na gansa?” Humaira tambaya.
Page 15
King Article-Queen Teei
” Wata kila yana zo miki ne da wata siffa mai ban tsoro wadda ke razanar dake har ta kawo miki silar fitar hayyacinki!” Inji Mamee.
” Ni a ganina wannan abu dake faruwa ba wai mafarki bane, abun yana faruwa da gaske ne amma sabida tsananin tsoron dake cikin zuciyarki shi yasa baxaki iya tuno komi game da al amarin ba.” Inji Baby.
” Kuma ni a ganina kamar akwai wani sako da yake son ya isar a wurinki.” Inji Mamee.
” Wannan wane irin sako ne?” Humaira ta tambaya.
” Baxan iya fadar wani abu game da wannan al amari ba, amma ina baki shawara idan kika kara samun kanki a cikin wannan yanayin kiyi kokari ki tuna dukkan abunda ya faru kada ki manta da kome.” Inji Mamee. ” Bari na tashi nayi wanka, kun san fa yaune Day 3, daga yau shi kenan an gama biki domin gobe tun da safe zamu tafi gida.” Anan Mamee ta shiga toilet. Yauma kamar kullum basu fita ba sai da sukayi Isha i, Nabil da Mujahid sun riga sun tafi gida domin har sun kwashe kayayyakinsu, da yawan student sun tafi gida, suna isowa wurin da ake party sai sukaga wayam ba kowa, kamar ba a taba yin wani shagali a wurin ba, abun ya basu mamaki domin basu sani ba shin an canza location ne ko kuwa? Can daga nesa sai suka hango wani saurayi a gefen hanya. Anan Mamee ta tayar da motar har saida ta iso wurin da yake, ai kuwa tana isowa sai dukkansu sukaji gabansu yayi mugun faduwa har sai da tsikar jikinsu ta mike. Humaira bata san lokacin data saki phone dinta ba, sai dakyar ta iya lalubo ta. Anan Mamee ta sauke gilashi domin tayi masa magana.
” Dan saurayi Don ALLAH ko kasan location da aka canxa na party?”
” E na sani.”
” To idan baxaka damu ka shigo mana sai mu tafi tare.”
” To yayi ba matsala.” Anan suka bude masa kofar baya ya shiga, ai kuwa yana shigowa gaban Humaira ya kara faduwa da yake ita kadaice a bayan, ita baby nacan gaba tare da Mamee. Anan Mamee tayi ribas ta ja motar da karfi kamar zata tashi sama. Tun da suka hau saman titi basu kara sanin inda suke ba, sai farkawa sukayi sukaga ana musu sannu, kwance suke a gefen titi, motarsu a can gefe duk fitillu sun fashe, kai da gani kasan cewa anyi mummunan hatsari, abunda ya basu mamaki shine wannan yaron da suka dauka, ta ina ya shiga, ya akayi ya fitar cikin motar?
Page 16
Dukkaninsu sunada tambon jimuwa a jikinsu amma ba sosai ba. ” Don ALLAH malam a lokacin da kuka fito damu a cikin motar bakuga wani saurayi a ciki ba?” Humaira ta tambayi wani.
” Gaskiya bamuga kowa ba, ku uku kawai muka gani a cikin motar.” Ya bata amsa. Wannan al amari ya basu mamaki sosai, godiya suka yiwa jama ar wurin daga nan suka shiga motar, da yake motar bata wani jin jiki sosai ba, a wannan lokaci baby ce ta tuka motar domin itace batada rauni sosai. A hankali ta lallaba tana tafiya saman titi, duk da ba wani gani takeyi ba domin fitillun sun fashe ba haske sosai, wannan yaron da suka dauka bako shakka akwai wani abu a tattare dashi, gashi basu yi masa kallon tsaf ba balantana su iya gane siffarsa, kai ko kayan dake jikinsa bazasu iya fadin colour dinsu ba domin a cikin duhu ne abun ya faru. Suna shiga hostel sukayi tsit tamkar wadanda aka aikowa sakon mutuwa, sun tsorata ainun daganin wannan al amari, haka sukayi bacci suna tunanin wannan abu, tun da sanyin safiya suka shirya kayayyakinsu, Humaira ce ta tuka ta kaisu tasha, daga nan sukayi sallama bayan ta musu kashedin cewa kada su kuskura su fadawa kowa wannan al amari daya faru, anan sukayi bankwana, suka hau motar da zata kaisu garuruwansu ita kuwa ta tuka motarta ta nufin nata kauyen……
♈♈♈CIGABAN LABARIN♈♈♈️
Humuira na farkawa sai ta ganta saman gado lame lame, anan ta fara tunanin abunda ya faru jiya da dare, zata iya tuno lokacin da gambo ya mata sallama ya tafiyarsa, tana kallonsa amma baxata iya kiransa ba, tana so tace kada ya tafi amma baxata iyaba, haka ta tsura masa ido har ya fita tana kallonsa, bayan ya fita ne sai ta shiga cikin gida tana ganin dishi dishi, tana hawan gadonta sai ciwon ya kara tsananta, daga nan bata kara sanin inda take ba. A hankali ta sauko saman gadon tana kallon jikinta domin yanxu ji take garau tamkar babu wani abu daya taba faruwa da ita, dan motsi taji a waje, daga nan sai ta fita domin taga ko waye, ai kuwa tana fita sai taci karo da Mumy na hada musu break fast a dinning table, a guje ta sheka ta rungumeta tana murna.
” Mumy nayi missing dinki!”
” Nima nayi missing dinki daughter.”
” Ba kunce sai kunyi sati daya ba kafin ku dawo?”
” E hakane, amma mun canza maganar, abbanki na can shine zaiyi sati daya.”
Page 17
” Da kyau Mumy, bari na kimtsa nazo naga miye kika dafa mana.” Mumy kallonta kawai tayi tana murmushi. Da gudu Humaira ta shiga daki, bata fito ba sai da ta kimtsa sarai, koda taje dining table abincinta kawai ne a wurin domin Mumy har taci nata ta tafi. Cikin nishadi ta fara cin abincin tana danne dannen waya, bako shakka tasan da cewa da dare mumy ta iso a cikin gidan, a lokacin ita kuma bata san inda kanta yake ba, dama idan ba kowa gidan bata damu da kulle gate din ba, haka take kwanciyarta domin ba a samun barayi a kauyen. Dawowar mumy ya mutukar sanyata farin ciki domin tasan cewa zata bar rayuwar kadaici. Tana gama cin abinci sai ta nufi falo, Plasma TV din a kunne yake, Ta dan fara kallo ne sai taji duk jikinta ya mutu, anan ta fara ganin dishi dishi, tashi tayi da nufin ta kashe TV din, ai kuwa tana mikewa sai ta ganta a cikin duhu, daga nan bata kara sanin inda take ba.
” Wai me yasa kake bibiyata?” Inji Humaira.
” Sabida baki ban amsar tambayar dana miki ba!” Inji wani bakin abu tamkar inuwa.
” Wace tambaya kuma?”
” Wato har kin manta ko?”
” Kwarai kuwa na manta, dama abubuwa masu muhimmanci su kadaine nake iya tunowa dasu a rayuwata.”
” Kina nufin wannan tambayar dana miki batada muhimmanci?”
” Kwarai kuwa batada muhimmanci.”
” To inaso ki wasa kwakwalwa, ki gano amsar tambayar dana miki idan har kinaso in daina bibiyarki!” Humaira Sai farkawa tayi ta ganta saman gado Mumy na mata fifita.
” Mumy me ya faru?”
” Ai ke zan tambaya me ya faru, ganinki fa kawai nayi kusa ga TV a sume.” Anan Humaira tayi shiru tana tunani, bako shakka zata iya tuno lokacin data fara ganin dishi dishi, daga nan sai ta nufi wurin TV domin ta kashe, to daga nan baxata iya tuna abunda ya faru ba, amma kuma ji take kamar tayi mafarki, abunda batada tabbaci shine mafarki ne tayi ko kuwa da gaske ne taga abun, ita dai tasan cewa tayi magana da wani abu amma kuma batasan ko menene ba, kuma bazata iya fadin siffar jikinsa ba ko clothing nasa.
Page 18
Kuma bazata iya tuno maganganun da suka yiba, wannan abu ya bata haushi sosai domin Mamee ta bata shawara cewa ta ringa tuno abubuwan daya fada mata wata kila hakan zai mata amfani nan gaba.
” Yanxu kije kiyi wanka ki shirya zan sameki.” Haka Mumy ta fada daganan sai ta fita dakin. Ita kuwa Humaira tashi tayi ta nufi toilet, sai da ta watsa ruwa daga nan ta fito, a saman gadonta ta samu abincinta a shirye, ai kuwa tana kammala ci sai ga Mumy ta shigo dakin rike da Kur ani.
” Inaso ki buda wannan domin da tanada ai daka fada da kur anin ki karanta min Ayatul kursiyu.” Anan Humaira tayi shiru domin ita fa ko alifun ba un bazata iya karantawa ba.” Abunda yasa nace ki karanta Ayatul Kursiyu sabida neman tsari, sabida haka yanxu ki fara a gabana.” Anan Humaira tayi shiru domin batasan abunda zata ceba. ” Naga kinyi shiru kina kallona, ki dauka mana.” Anan Humaira ta dauki kur ani amma bata buda ba domin tasan baxata iya karanta komi a ciki ba. ” Kina nufin baki iyaba ko me kike nufi? To idan baki iyaba sai ki karanta wani abu a ciki naji!” Anan Humaira ta kara kidimewa. ” Ke don ubanki magana fa nake kin kyaleni.”
” Mumy ni ban iyaba!” Haka ta fada tana zub da hawaye.
” Baki me ba? Ina malamin da muka dauko ya dinga koya miki karatun addini, me ya faru dashi?”
” Mumy korarsa na……” kafin ta iyar da maganarta sai taji saukar mari a fuskarta.
” Yanxu kina nufin malamin kika kora da kanki, to ubanwa ya baki damar ki koresa, idan wani laifi ya miki baxaki iya fada muna ba sai kawai ki zartar da hukunci da hannunki.” Anan Mumy ta shako wuyanta da karfi.
” Fadamin wane laifi ya miki.”
” Mumy nifa na gaji da karatun ne kawai shi yasa na sallamesa.”
” Iyee, lallai wannan yarinya kin kai shegiya, yanxu karatun addinin shine kike cewa kin gaji dashi, ai kuwa kinji kunya kina diyar musulmi amma ace baki iya karatun kur ani ba, to idan kikazo yin salla ya kikeyi, kuma duk hukunce hukuncen addini nasan ba kowane kika sani ba.”
” Mumy nifa na iya salla.”
” To fadamin idan akazo ruku i ya ake cewa?”
Page 19
Anan Humaira tayi shiru tana dube dube, ” Fadamin idan akazo sujjada me ake cewa? Kin gani ko, duk bakisan wadannan ba, Humaira kin cuce mu, yanxu in banda kike muguwa ace addininki baki san kome a ciki ba, yanxu da handout ne aka baki da kinci ubansa amma tunda kur ani ne baki iyaba. Muguwa kawai.” Haka Mumy ta tashi tana fadace fadace. A wannan rana Humaira yini tayi tana tunani wannan abu, bata taba ganin bacin ran Mumy kwatankwacin wannan ba, a cikin dare ko abincin ma bata samu damar ci ba, haka ta kwanta da yunwa tana sake sake har bacci yayi awon gaba da ita. Tun da kulun kulun safiya aka fara buga mata kofa, tana budewa sai taga Mumy a tsaye rike da School Bag.
” Ki saka kala uku a cikin wannan jakar, kuma ki tabbatar kin dauki wasu abubuwa da kike bukata.” Mumy juyawa tayi ta fice daga wurin. Anan Humaira ta amshi jakar tana tunanin abunda ke shirin faruwa, shin Mumy korarta ne xatayi daga gidan ko kuwa? Cikin sauri ta kimtsa domin kada tayi laifi. Ba a fi minti biyu ba sai ga Mumy ta watso mata kira, anan Humaira ta fito a guje rike da jakarta. Mumy na tafiya tana bin bayanta har suka iso harabar gate din.
” Ki shiga cikin motar ki jirani.” Inji Mumy. Anan ta juya ta rufe gidan gaba daya daga nan ta dawo cikin motar, sai da ta ba motar wuta sannan ta tayar ta cilla a guje, dama shi gate basu fiye rufeshi ba idan zasuyi tafiya. Bayan Mumy tayi xagaye ta fito daga cikin kauyen sai ta hau babban titi, anan ta fara cin taya, Kai da gani wannan gudu da take zubawa kasan cewa professional driver ce, sai overtaking take da karfi ba sassauci. Dama a duk lokacin da Mumy zatayi tafiya mai nisa to irin wannan motar take dauka wato Tayota land cruiser, dama ita motoci jeep suna burgeta. A wannan lokacin da suke azababben gudu titin ba motoci sosai sabida har yanxu safiya bata gama wayewa ba. Wannan shi yaba Mumy damar yin overtaking a saukake kuma tana sharara gudu a saman titin yadda taga dama. Da yake ba a fiye samun motoci a saman titin ba amma kuma yau sai gashi suna ganin motoci har da ma overtaking, abun yaba Humaira mamaki domin ita tasan wannan titin tsit yake tamkar makabarta.
” Kin yi break fast kuwa?” Mumy ta tambayeta.
” A a,” Humaira ta amsa.
Page 20
Queen Teei-King Article
” Ki duba can baya zakiga flask da cups biyu, sai wata kula ma dauke da wainar kwai, ki zubawa kanki daga nan sai ki zubo min nawa tea din.” Anan Humaira tayi yadda Mumy ta umarceta, tanaso ta tambayeta wurin da zasu tafi amma kuma tana tsoron taji saukar mari a fuskarta, dole tayi shiru tana shan tea tana kallon titi, a nan Mumy ta kunna waka na larabci amma marar kida, abun yaba Humaira mamaki domin ta lura cewa Ita Mumy a duk lokacin da zata kunna waka to tafison irin wadanda basuda kida, to wai ko abunda Nabil yace gaskiya ne, wai shan waka mai kida haramun ne! A haka ta cigaba da shan tea tana tunanin abun, sun dauki lokaci mai tsawo suna wannan tafiya domin salla kadai ke tsayar dasu, bayan tafiya tayi tafiya sai Mumy ta fara rage gudu da alama cewa sun karaso, ita kuwa Humaira bude idanunta tayi domin taga abunda ke shirin faruwa, a wannan lokaci rana ta fadi likis, wata yar hanya mai cike da yashi mumy tabi dasu, suna shigowa wannan hanyar gaban Humaira ya fara faduwa, kai da ganin wurin kasan daji ne makeke abun tsoro, abun tambaya anan shine wai za a iya samun mutane a ciki kuwa?
Sai da suka dauki lokaci suna zagayar dajin sannan suka iso wata yar tunga, yan bokkoki ne kalilan a wurin, ita dai Humaira bataga alamun mutane a wurin ba, bukkokin ma da tagani ji take tamkar ba kowa a ciki. Mumy na faka motar sai ta fito, ita ma Humaira biyo bayanta tayi, suna gab da isowa ga bukkokin sai ga wata mata ta fito a ciki, matar fara ce mai kiba zata kai shekarun Mumy din.
” marhaba marhaba, marhaba marhaba.” Haka matar ta fada daga nan sai ta sheko da gudu suka rungume juna. Ita kuwa Humaira tsaye tayi tana kallonsu, bayan sun gama farin ciki na haduwa ne sai suka fara magana da wani yare wanda Humaira bata taba jin Mumy ta yisa ba, abun ya daure mata kai sosai, shin wai dama Mumy ba Pure Bahausa bace? Kuma wannan wane irin yare ne? kuma wace magana ce sukeyi? Kuma me zasuyi a wannan wuri? Kuma ita wannan mata wacece? Haka wadannan tambayoyi suka rikirkita Humaira suna mata yawo saman kai, sai da su Mumy suka dau lokaci suna magana sannan matar ta jiyo ta kalli Humaira, to anan ne Humaira ta tabbatar cewa suna magana ne akanta. Matar kusanto Humaira tayi sai da tayi tsaye daf da ita, daga nan sai ta riko yatsunta tana dubansu daya bayan daya kamar mai binciken wani abu, daga nan sai ta kalli Mumy ta mata wata magana a cikin yaren. Daga nan kuma sai ta kalli fuskarta tana tattabawa da hannunta, ita dai Humaira tsaye take tana kallon wannan abun mamaki domin batasan ko minene matar ke aikatawa ba.
Page 21
Bayan matar ta gama binciken da zatayi a kanta sai ta ja hannuta suka nufi bukkar, ita kuwa Mumy shiga motar tayi ta bata wuta, daga nan ta cilla a guje ta nufi hanyar data fito, wannan abu yaba Humaira mamaki, to ita Mumy ina zata tafi ne ta barta cikin wannan daji tare da bakuwar fuskar da bata sani ba. Gashi ko school bag dinta bata fito da ita ba! To Mumy zata dawo ne ko kuwa? Bayan sun shiga dakin sai suka zauna saman wata local carpet, dakin ya tsaru amma da gani ba sai an fada ba kasan local room ne, an kawata shi da kwallaye da tasoshi irin na can da din nan.
” Kada kiji tsoro Humaira domin nima a matsayin mahaifiyarki nake.” Humaira tayi mamakin jin wannan magana daga bakin wannan matar domin batayi tsammanin cewa zata iya fadar kalma daya ta hausa ba domin ko irin shigar datayi bata hausawa bace domin wata atamfa ce ta sanya mai wani zane zane, ita irin wannan atamfa ba aciga ganin matan hausawa da ita ba. Ita abunda ke kara bata mamaki game da matar shine yadda akayi tasan sunanta. ” Sanin koni wacece bayada amfani a wurinki amma zaki iya kirana da Umma kuma idan zakiban hadin kai zan so na miki tambayoyi game da rayuwarki.”
” Kina yawan fita hayyacinki, hakane koba haka ba?”
” Hakane!” Inji Humaira.
” To amma ya akayi kikasan da hakan?” Humaira ta tambayeta.
” Sabida mun tattauna hakan tare da umminki.” Inji matar.
” Ko kin taba tunani akan abunda ke haddasa miki wannan yanayi?”
” Aa ” Inji Humaira. ” Amma ke a ganinki menene?”
” Ni a ganina wata alaƙa ce dake tsakaninki da wani mai bibiyarki kuma ita wannan alaƙa itace ke haddasa miki fita hayyacinki.”Inji matar.
” wannan wace irin alaƙa ce, kuma waye yake bibiyata?” Humaira ta tambaya. Matar shiru tayi ba tare data bata amsa ba. Daga nan sai ta fara kara kallon yatsun Humaira kafin ta cigaba da magana.
” Inaso ki fadamin wane irin ilimi kike dashi?” Inji matar.
” Inada ilimi na sarrafa harshe, zan iya lankwasa harshe na rubuta abubuwa masu ma ana da muhimmanci amma kuma mutum baxai iya gane kan rubutun ba sai idan naso ya gane sannan yake iya ganewa.” Inji Humaira.
” Kamar yadda kike da wannan ilmi nima inada kwatankwacinsa, ni kuma inada ilimi na yin alaƙa da shaidanu.” Inji matar.
” Shaidanu fa kikace?” Inji Humaira.
” Kwarai kuwa!” Cewar matar.
Page 22
” To ya za ayi na tabbatar da hakan?” Humaira ta tambaya. Matar tashi tayi ta dauko wata yar tukunyar laka mai dauke da kasa. Wasu yan duwatsu ne a saman kasar gefe gefe. Wani zane matar tayi saman kasar daga nan saita goge, karayin wani tayi ta kara gogewa, daga nan sai ta cewa Humaira ta sanya hannunta a cikin tukunyar. Humaira na sanya hannunta a ciki sai taji kamar ta sanya hannunta a cikin ruwa alhali kuma tukunyar kasa ce a ciki.
” Me kikaji kin taba?” Matar ta tambayi Humaira.
” Ruwa.” Inji Humaira.
” Ruwa fa kikace?” Matar ta fada tana murmushi.
” Kwarai kuwa ruwa na taba.” Inji Humaira.
” To wannan kadan daga cikin ilimina kenan, idan kika dubi tukunyar zakiga kasa ce a ciki amma kuma idan kikasa hannunku sai kiji kin taba ruwa, to abun tambaya anan shine kin san ko wadanne ruwa ne wadannan?”
” A a.” Inji Humaira.
” Wadannan ruwan sune tushen alaƙarki da abunda ke damunki kuma sune karshen alaƙarki da abunda ke damunki!”
” Me kike nufi da wannan zance naki?” Humaira ta tambaya.
” Ma ana a cikin wadannan ruwan ciyon dake jikinki yake kuma a cikinsu ne maganin ciwon yake.”
” Nifa ban fahimta ba.” Inji Humaira. Anan matar tayi murmushi tana dubanta.
” Taso ki gani.” Inji matar. Anan matar ta jata suka fita wajen bukkar. Daga nan sai ta nuna mata gefen dama tace ta duba ta gani.
” Umma ni banga kome ba sai duhun daji.”Inji Humaira.
” Kada ki damu da duhun dajin kuma kada kiji tsoro, inaso yanxu kin runtse idanunki daga nan sai ki nufi wannan hanyar dana nuna miki, kada ki yadda ki canza hanya ko ki lankwasa, kici gaba da tafiya a hankali kina fadan YA ALLAHU, idan kika cigaba da tafiyar zaki cimma wasu ruwa, da kin shiga cikin ruwan zaki fita hayyacinki, da kin fita hayyacinki wani abu zai faru, to inaso duk abunda ya faru ki dawo ki fadamin kuma kada ki manta da kome.” Inji matar.
” To wai meinene zai faruwa?” Humaira ta tambaya .
” Nima ban sani ba amma idan kinje zaki gani.” Inji matar.
Page 23
” Bayan kin dawo daga hayyacinki sai ki bude idanunki, kina budewa zaki ganki a gabar ruwan, to kada ki juya ki kalli ruwan, inaso kiyi gudu iya karfinki kina fadar YA ALLAHU kiyita gudu har sai kin iso a nan, amma akwai sharadi, sharadin shine kada ki yadda ki juya baya da nufin kallon ruwan, kuma kada ki yadda kiyi kuskure akan abunda na fada miki, da kinyi kuskure daya akan abunda na fada miki to dani dake duk zamu halaka.”
” Amma umma babu wata hanya sai wannan?” Humaira ta tambaya.
” Wannan ita kadaice hanyar da zamu yanke wannan alaƙar dake tsakaninki da shi mai bibiyarki.”
” Umma wai waye yake bibiyata”? Humaira ta tambaya.
” Kada ki damu Humaira, da sannu zaki gano ko waye yake bibiyarki, amma yanzu inaso kiyi duk abunda nace da sannu zamu samu mafita.” Anan Humaira ta runtse idanunta daga nan ta fara tafiya batare da sanin inda ta nufa ba. Gabanta ne ke mugun faduwa sai ji take dum dum, gashi duhu ya fara dabaibaye dajin sai kukan tsuntsaye akeji gaba da baya. Haka taci gaba da tafiya da runtsen ido ba tare da fuskantar wata matsala ba, bayan tayi tafiya mai nisa sai ta farajin kasala, haka dai ta daure tana tafiyar har sai da ta fara jin ta shigo cikin wasu ruwa, a nan ne gabanta yayi mugun faduwa, gashi batada takalma, haka ta tako zubudum zubudum, koda ta fara tafiya cikin ruwan sai jikinta yayi sharkaf da zufa, a nan kasala ta kara dabaibayeta, kafin kaceme ta fadi rikicaa, daga nan ta fita hayyacinta bata kara sanin inda take ba.
” Amma kunyi kokari sosai da kuka gano inda nake zama.” Inji wani bakin abu tamkar inuwa.
” Au, ashe dama nan kake zaune!” Inji Humaira.
” Kwarai kuwa ai nan aka haifeni.” Inji bakin abun.
” Wai kai me yasa kake bibiyata ne?” Humaira ta tambaya.
” Sabida inaso in kulla alaƙa tsakani na dake!” Inji bakin abun.
” Wace alaƙa kuma?” Humaira ta tambaya.
” Kada ki damu yan mata, da sannu zakisan alaƙar da nake nufi, amma inaso in baki sako ga wurin wadda ta aiko ki, ki fada mata cewa ta fita harkata, idan kuma ba haka ba zan dauki mataki da kaina.” Haka tacigaba dajin maganar na mata yawo a cikin kunne ba kakkautawa, firgigit ta farka, ai kuwa tana farkawa sai ta ganta bakin gabar ruwa, wurin yayi tsit tamkar ba halittar data taba wanxuwa a wurin, tana mikewa sai ta mika a guje ta nufi cikin dajin dake gabanta, gudu take iya karfinta amma ji take tamkar batayin kome, kasa da ciyayi take takawa amma kuma ji take kamar tana taka ruwa, tana cikin gudun ne sai ta rage ta dawo sassarfa sabida kafafuwanta da suka wani saki, wani sanyi takeji marar dadi tun daga cinyarta har zuwa kasan kafafuwanta, tana cikin sassarfar ne kuma sai ta dawo tafiya, wannan lokaci kasala ce da gajiya suka fi karfinta, cikin rashin tsammani sai taji kamar wani abu na janta yana kokarin mayar da ita ga ruwan. Anan ta fadi tana nishi daya bayan daya.
Page 24
Itatuwan da ke kusa da ita ne ta rike, amma kuma ji take tamkar wani abu na kokarin banbare hannuwanta akan rikon data yiwa itatuwan, tanaso tayi ihu amma baxata iyaba, domin ji take idan tayi ihu wani abu zai iya faruwa da ita, da karfin tsiya aka banbare hannayen nata akan rikon data yiwa itatuwa, amma abun mamaki shine bata ganin abunda ya banbare hannayen nata, daga nan aka fara mirginowa da ita da tsananin karfi tsiya ana kokarin mayar da ita cikin ruwan, haka ta daure ta kara rike wani itace amma kuma sai ji take ana janta da karfi, tanaso ta juya domin taga abunda ke mata wannan tu a sar sai ta tuno kashedin da aka yi mata. Da karfi ta fara kiran YA ALLAHU, ai kuwa faruwar hakan keda wuya sai taji komi ya lafa, iskan dake kadawa ya bari, ba tajin kome in banda kukan tsuntsaye sai kuma duhun daya dabaibaye dajin gabaki daya, dakyar ta samu ta mike tana nishi, daganan ta fara gudu a hankali domin har yanxu kasala takeji, tana cikin gudun ne sai taji kamar an kara cafkota, faduwa tayi da karfi sai da kanta ya gwabru, daga nan sai ta fara rarrafe tana kokarin rike wani itace dake kusa da ita amma ji take kamar ana fisgota a baya, tana fadar YA ALLAHU sai taga komi ya lafa, bayan ta mike sai ta cigaba da gudu tana fadar YA ALLAHU, anan ta riga ta gano cewa da zaran bata fadi kalmar ba to wannan abun dake binta zai cigaba da samun nasara a kanta. Haka taci gaba da gudu tana fadar YA ALLAHU har ta fita daga cikin dajin, tun daga nesa take hango bukkukin, a can gefe kuma matar ce wato umma a tsaye tana jiran isowarta.
Anan Humaira ta kara kaimin gudu har ta isa wurin matar, tana isowa sai ta fada jikinta tana sheshsheka. Ita kuwa matar wato umma janyota tayi har suka iso cikin bukar, suna shiga Humaira tayi kwance tana nishi, kai da gani kasan taci wuya. Bayan ta huta ne sai ta fita waje domin tayi alwala, tana gamawa sai ta fara salla, tana sallamewa abincin dake gabanta ta janyo sai da taji cikinta yayi dam sannan ta ajiye.
” Ina fatan zaki iya tuno abunda ya faru?” Matar ta tambayeta.
” Zan iya tuno wasu abubuwa amma ba duka ba, a cikin maganar naji kamar yana fadar…..” Anan Humaira tayi shiru tana tunanin maganar, sai da aka dauki lokaci kafin tace, ” alaƙa, amma ban san ko wace alaƙa yake nufi ba, sai kuma….. Inaga mataki yace, Amma dai ban san abunda hakan ke nufi ba. Ni abunda keban mamaki sai naji abun kamar a mafarki kamar da gaske, bako shakka inaji a jikina cewa nayi magana da wani abu amma kuma ban san ko menene ba kuma ban san ya siffarsa take ba.” Murmushi matar tayi kafin ta fara magana.
” Wannan alaƙar da kikaji ya fada itace wadda ke tsakaninku ke da shi, mataki kuma da kikaji yana nufin idan har bamu fita harkarsa ba to zai dauki mataki da kansa.”
Page 25
King Article-Queen Teei
” Umma to wai shi wannan wanene, kuma yaya kamanninsa yake?” Umma shiru tayi tana nazarin maganar, ga dukkan alamu batason fadawa Humaira gaskiyar al amarin domin kada ta tsoratar da ita. Duk da cewa ita Humaira ta dade da sanin cewa wadannan abubuwa dake faruwa da ita dole akwai shaidanu a ciki, ko yanxu tayi tambayar ne kawai domin taji abunda umma din zata fadi.
” Kada ki damu yata, ai wannan al amari ba wani abun tashin hankali bane, kome zai wuce insha Allah.”
” To umma inada tambaya.”
” Ina saurarenki.”
” Umma wai wane yare ne naji kinayi tare da Mumy na?”
” Shi ake cewa Kanuri, ki sani Mumy dinki Kanuri ce abbanki shine bahaushe, kuma a ganina bata fada miki hakan bane domin kada kiyi fushi da ita, dani da Mumy dinki abokai ne tun muna yara haka muka taso kuma har girmanmu bamu rabu ba.”
” Da kyau Umma, to yanzu meye mafita akan wannan al mari dake gabanmu?” Humaira ta tambaya.
” Yanxu tashi zakiyi ki kara shiga wancan dajin dana nuna miki, sai dai yanxu bake kadai zaki tafi ba, zaki hau kan jaki ( Donkey) shine zai shigar dake cikin dajin, amma fa ki sani da kinji yayi ihu to ki sauka kicigaba da tafiya da kanki, kina cikin tafiyar zaki iske wasu ruwa masu tsananin yawa, daga nan sai ki shiga cikin ruwan, kina shiga cikin ruwan zaki fita hayyacinki, kina fita hayyacinki wani abu zai faru, to inaso kada ki manta da abunda zai faru, sabida idan kika dawo zaki fadamin.”
” Ta yaya zan fito daga cikin ruwan?” Humaira ta tambaya.
” Da ikon ALLAH zaki fito, kawai zaki farka ne sai ki ganki a bakin gabar ruwan shi kuma jakin a kusa dake, daganan sai ki hau saman sa, idan kin hau bazai yi gudu ba tafiya ce zai yi, kuma kada ki takura masa yayi gudu komi rintsi komi tsanani, kuma kada ki yarda ki sauka samansa domin yin hakan janyo masifa ce akanki.”
” Na fahimta.” Inji Humaira. Daga nan sai ta tashi ta fita waje, tana fita sai taga jakin yana jiranta. Umma ce ta rike mata shi har sai da ta hau, daga nan sai ta sakesa ya fara tafiya. Tun da Humaira ta fara tafiya saman wannan jakin gabanta ke faduwa, ji take tamkar ta juya baya amma kuma bazata fara yin haka ba, duhuwar dajin shine ya kara kaimin tsoron daya dabaibayeta.
Page 26
Jakin bai wani dade yana tafiya ba sai taji yayi ihu mai tsoratarwa tamkar yana ganin wani abu, ita kanta Humaira sai da zuciyarta ta sosa sabida ganin tsoratar da jakin yayi, anan ta sauka shi kuwa jakin ya koma a guje inda ya fito. Haka Humaira ta bisa da kallo har ya bace mata da gani, ji take tamkar ta kirashi ya dawo amma ba dama, haka ta daure ta nosa cikin dajin tana tafiya cikin mugun tsoro da dimauta, bako shakka ta nuna jarumta da juriya domin ba kowace mace ke iya wannan kasadar ta shigowa cikin wannan daji a cikin dare ba, yar fitilar kwai 🔥 dake rike da hannunta ta fara tangal tangal kamar zata fadi, sai dakyar ta samu ta iya rikota, iskan dake bugawa shi yake barazanar kashe fitilar, ita kuwa Humaira sai faman boye boyen fitilar take kada iskan ya kasheta, sai da tayi tafiya mai nisa kafin ta iya cimma wasu ruwa marar iyaka, sai da ta hanga iya ganinta amma bataga karshen suba, a hankali ta fara shiga ciki tattare da wasi wasin abunda zata iya gani a ciki. Tana samun kanta a cikin ruwan sai ta fara jin kasala tare da ganin dishi dishi, dib bata kara sanin inda take ba.
” Wato baku saurari kashedin dana muku ba ko!” Inji wani bakin abu tamkar inuwa.
” Wane kashedi kake magana akai?” Humaira ta tambaya.
” Kada ki damu ai zaku gani…” Firgigit Humaira ta farka, ganinta tayi a bakin gabar ruwa sai ga jakin a kusa da ita, bako shakka tana ji a jikinta cewa tayi magana da wani abu amma batasan ko menene ba kuma bazata iya fadin siffarsa ba, cikin sauri ta haye jakin domin ta matsu tabar wurin, ai kuwa tana hawansa ya fara tafiya cikin sauri da kuzari, wannan sauri da yake ba karamin burge Humaira yayi ba domin ta matsu tabar wurin. Suna shigowa cikin dajin sai abubuwa suka canxa, jakin rage sauri yayi sai kuma yawan tuntube da yakeyi kamar yana cikin galabaita, ita kanta Humaira dishi dishi take gani domin tunda suka shigo dajin takejin wani kasala, gashi tayi jifa da fitilar kwai dinta balantana ta samu ganin hanya, shi kuwa jakin sai kara shigowa yakeyi a cikin duhun dajin yana tafiya tunkus tunkus, Humaira ji take tamkar ta sauko tayi gudu da kanta domin ta raina tafiyar jakin amma kuma data tuno kashedin da aka yi mata na cewa komi tsanani kada ta sauka samansa sai ta fasa, wani dan karamin iska ne ya fara bugawa daga nan sai itatuwan suka fara motsawa a hankali, Humaira na ganin wannan yanayin tasan ba lafiya ba, da farko dai jakin tsaye yayi ya kasa tafiya, daga nan sai taji tamkar ana janyon jakin ta baya, sai da rike shi sosai da kadan ta fadi, shi kuwa jakin ihu yayi mai firgitarwa daga nan sai ya fara kubce kubce tamkar wani na rike dashi, can sai ya bari, tafiya yaci gaba dayi tare da Humaira a samansa, sai da sukayi nisa kafin jakin yayi turjiya yana huci, kai da gani kasan akwai wani abu dake damunsa to amma menene? Ita kuwa Humaira kidimewa tayi gashi ba damar ta sauka balantana ta gudu.
Page 27
Jakin tangal tangal ya fara kamar zai fadi, wanda sanadiyar hakane yasa Humaira ta samu raunuka a fuskarta domin akan itace yake gogata. Sai da kyar jakin ya tsaya, daga nan yaci gaba da tafiya yana huci ita kuwa Humaira tana fadar YA ALLAHU, daga nan basu kara fuskantar wata matsala ba har suka fito dajin, tun daga can nesa take hango bukkukin amma kuma abun mamaki Umma bata fito ba kamar yadda tayi dazu, a can gefe kuwa zata iya ganin katanyar jeep wanda hakan ya tabbatar mata da cewa Mumy ta dawo kuma watakila dawowarta ne ya hana Umma fitowa tarbarta, watakila tana can tana hira da Mumy. Bayan ta iso ga bukkokin sai ta sauko saman jakin, tana shiga cikin bukkar sai ta iske Umma a kwance tana nishi dakyar, ita kuwa Mumy a kusa da ita sai faman addu a take mata.
” Mumy me yake faruwa ne?” Humaira ta tambaya
” Nima ban sani ba yanxu na shigo!”Inji Mumy. Dakyar Umma ta iya daga hannunta ta yiwa Humaira nuni data dauko mata wata jakar fata a rataye, Humaira na daukowa sai Umma ta amsa, a hankali ta bude jakar daganan sai ta dauko wani garin magani, shaka maganin ta farayi da karfi kamar baxata daina ba, atishawa tayi kamar sau uku kafin ta dawo hayyacinta. Daga nan sai tayi zaune ta fuskancesu da zimmar yin magana.
” Fiye da shekaru ashirin ina alaƙa da shaidanu amma ban taba fuskantar irin wannan matsalar ba sai yau.” Haka Umma ta fada tana duban Mumy. ” Wannan ciwo na Humaira ya tsananta sosai domin abun yafi karfina, idan na cigaba da gudanar da aikin zan iya rasa rayuwata, sabida haka ina baku hakuri akan gazawata.” Haka ta fada tana maida idonta akan Humaira. ” Amma zan hadaku da wata kawata ta gwada sa arta ko aikin zai yi.” Daga nan sai ta canza yare, Kanuri suka cigaba da magana dashi ita da Mumy, ita kuwa Humaira zuba musu ido tayi domin batasan abunda suke fada ba, bayan sun kammala maganar ne sai Mumy tace su tsaya suyi sallar Isha i, suna gama sallar sai sukayi sallama da Umma, ita kuwa Mumy jan motar tayi da karfi ta nufi hanyar fita kauyen. Humaira dake zaune kusa da ita sai faman kallon dajin take a madubin mota. Suna hawan babban titi Mumy ta fara cin taya ba sassauci, wani mahaukacin gudu ne take zubawa wanda tunda Humaira take bata taba ganin wani wanda yayi kwatankwacinsa ba, ga duhun dare daya dabaibaye sararin samaniya amma ko kadan mumy bata damu da wannan ba, gudu take zubawa tamkar mai shirin tashi sama.
” Mum don ALLAH ki rage gudu kada mu halaka.” Haka Humaira ta furta a cikin tsoro, ita kuwa Mumy abun dariya ya bata.
” Wannan yarinya akwaiki da mugun tsoro.” Haka Mumy ta fada cikin murmushi.
Page 28
” Wannan titin da kike gani yanada hatsari sosai shi yasa nake wannan gudun.” Inji Mumy. Anan Humaira ta kalli titin cikin tsoro domin ta lura cewa tunda suka fito kauyen su Umma basu hadu da wata mota ba a saman titi, sai daji suke wucewa mai duhuwar itatuwa abun gwanin ban tsoro. ” Ko zaki iya tuno labarin dana baki na Aunty Maryam?” Anan Humaira ta fara tunanin Aunty Maryam. Aunty Maryam itace kanwar mahaifiyar Humaira wadda suke uwa daya uba daya, wayayya ce ta karshen karshe domin bata dauki driving kome ba, a duk lokacin da zata tafi wani gari sai dai ta tuka motarta ta fita, a haka ne wata rana a cikin dare ta dawo daga workshop sai ta biyo ta wannan titin, a wannan lokaci ana iska mai karfi ga kuma duhun dare daya dabaibaye sararin samaniya, ita kuwa sai tuki take domin ta isa gida, tana cikin tukin ne sai taji tamkar ta taka wani abu, tayarta ce ta fashe akan haka dole ta tsaya, bayan ta fito ne sai taga tayarta ta fashe kamar an fatattaketa, bataga abunda ta taka ba amma dai taji kamar ta taka wani abu, boot ta bude ta dauko sabuwar taya tare da kayan aiki na sanya tayar wato jack da lug wrench, anan ta duka ta fara aiki tana dube dube cikin tsoro, tana cikin aiki ne sai taji ihun mace daga can nesa a cikin dajin, da gudu ta koma cikin motar daga nan sai ta bugawa saurayinta dan gayu domin yaxo ya dauketa, tana gama waya dashi ta kashe wayar, ba a fi minti biyu ba sai ta kara jin ihun mace, anan taji bazata iya hakuri ba sabida haka ta dauko torchlight dinta, a hankali ta fara tafiya har ta shiga dajin tana dube dube amma bataga kowa ba. Shi kuwa saurayinta wayar da yayi da ita ta karshe itace a lokacin data fada masa cewa ta shiga cikin dajin domin ta jiyo ihun mace, koda ya iso wurin sai yaga motarta a can gefe, yana ajiye motarsa sai ya dauko torchlight dinsa ya tsunduma cikin dajin yana kiran sunanta, daga karshe bai ga kowa ba in banda torchlight dinta, wayarta sai takalmanta, anan ya tsorata, da gudu yaja motarsa yabar wurin, daga nan ya kira yan sanda ya fada musu abunda ke faruwa, a cikin daren kuwa suka fito suka zagage dajin gaba da baya amma ko gawar aunty maryam ba a gani ba, yanzu fiye da shekara goma kenan da batan aunty maryam amma har yanzu ba a sake jin labarinta ba kuma ba a san abunda ya faru da ita ba.
Anan Humaira ta tsayar da tunaninta tana kara kallon dajin, bako shakka wannan daji abun tsoro ne, ita kuwa Mumy sai ta fara rage kaimin gudunta, daga nan sai tasha wata kwana ta tsunduma a ciki da gudu, ita dai Humaira kallon wurin kawai take amma batasan inda Mumy zata kaisu ba, shima wurin daji ne sosai gaba da baya, yar hanyar da motarsu ke takawa cike take da hakukuwa, bayan sun yi nisa ne da tafiyar sai suga hango wasu mutane maza da mata zigidir, a cikinsu ba mai kaya suna rawa suna zagayar wuta, sai ihu suke suna fadar wasu kalmomi marar ma ana. tunda Humaira ta gansu jikinta yayi wani sanyi.
Page 29
” Mumy su waye wadannan?” Humaira tambaya.
” Mayyu ne ke rawar maita.” Inji Mumy. Anan Humaira hankalinta ya tashi ganin Mumy ta nufi cikin wadannan mayyu gadan gadan.
” Mumy ina zaki kaimu, bazaki tsaya a nan ba izuwa gobe muci gaba da tafiyar!” Inji Humaira.
” Ki kwantar da hankalinki ba abunda zai faru.” Inji Mumy bayan ta iso gab da mayyun, anan Humaira ta bude ido tana kallonsu daya bayan baya cikin wata mummunar siffa marar kyan gani, mayyun tsaye sukayi suna kallonsu Humaira amma basuda niyar yin wani abu, abun yaba Humaira mamaki.
” Mumy wai ke faruwa ne? Naga sunyi tsaye suna kallonmu amma kuma kamar basuda mugun nufi akanmu.” Inji Humaira. Ita kuwa Mumy murmushi tayi kafin ta bata amsa.
” Humaira kenan, ke a tunaninki a banza zan yarda mu shigo mugun daji irin wannan? To ki sani wadannan mayyun bazasu iya ganin motar da muke ciki ba balantana su ganmu, sai dai suji kukan motar. Shi yasa kikaga sunyi tsaye suna duban inda sukejin motsin amma wayam bazasu iya ganin kome ba. Ko hasken motar bazasu iya gani ba. Iyaka suji kukan motar.”
” Mumy tsafi haramun ne!” Inji Humaira.
” Ai wannan ba tsafi bane, karfin addu a ne da kuma IKON ALLAH.” Haka Mumy tayi overtaking wadannan mayyun ba tare da sun ga motar ba balanatana su kai musu farmaki. Bayan sun yi tafiya mai nisa sai suka cimma wasu bukkoki. gaban bukkokin Mumy ta faka motar daga nan sai ta fito, ita kuwa Humaira biyota tayi. Suna zuwa bukka ta farko sai sukaga wata mace fara marar jiki sosai ta fito dauke da murmushi. Anan ta gaisa da Mumy cikin yaren kanuri, daga nan suka cigaba da magana da yaren, sai da suka dauki lokaci suna magana kafin matar tayi musu iso a cikin gidan wanda ya kasance ginin laka. Wata yar bukka matar ta nuna musu, a ciki zasuyi bacci kafin gobe. Dakin gyare yake tsaf tsaf dashi, wasu local beds ne guda biyu a gefe sai jeren tasoshi da akayi, sai kwaryoyi ( calabash) da aka ajiye a can gefe nesa dasu. Tun da Humaira ta kwanta bata kara sanin inda take ba, sai da asuba taji Mumy na tayar da ita akan ta tashi tayi salla, school bag dinta ta buda ta dauko kayan da zata saka, bayan ta kimtsa ne ita da Mumy sai matar ta shigo, da yaren kanuri ta gaisa da mumy daga nan sai ta fita, bata dawo ba sai da rana ta fara fitowa, shigowa tayi dauke da tray, a saman tray akwai wani local jug mai dauke da kunu, sai wata langa cike da cin cin, can gefen tray kuma wasu local cups ne biyu aka ajiye, matar na ajiyewa sai ta fita. Mumy jawo jug din tayi, sai da cika cup dinta da kunu sannan ta kafa kai, cikin kankanin lokaci ta tayar dashi daga nan ta ajiye cup din tana gyatsa, abun yaba Humaira dariya amma kawai sai ta kanne domin tasan idan mumy ta gano cewa dariya take mata tofa zataci ubanta.
Page 30
Queen Teei-King Article
Ita Humaira mamaki takeyi kasacewar Mumy wayayya amma wai tasha irin wannan kunun, bag dinta ta buda ta dauko juice na Exotic, daga nan sai ta dauki cin cin tana ci tana kurban juice dinta. Tana cikin hakane sai ga matar ta shigo rike da allo da tawadda a cikin wata kwalba.
” Humaira inaso ki rubuta min Ayayul Kursiyu kafa uku ga wannan allon.” Inji matar, Humaira tayi mamaki yadda akayi matar tasan sunanta, amma sai taga wannan ba wani abun mamaki bane watakila Mumy ce ta fada mata. Anan Humaira ta rasa irin karyar da zatayi domin kada taji kunya domin tasan fa bata iya rubutun larabci ba, can sai ta nisa tace.
” Ai kuwa jiya na samu rauni ga hannuna inaga bazan iya rubutun ba.” Haka Humaira ta fada tana mai hada ido da Mumy, done kanta tayi kasa domin tasan halin Mumy ba karamin aikin ta bane ta tonawa mutum asiri gaban jama a ba ruwanta sai dai duk abunda zai faruwa ya faru.
♋♋♋♋♋♋♋♋
” Karya takeyi kinji ko, bata iya rubutun bane gaba daya.” Inji Mumy.
” Laaaa Humaira, da gaske baki iyaba?” Inji matar.
” Wallahi ni Mumy bazan yarda ba wai ke kulum kulum….” Haka Humaira ta fada cikin sakuwa tana turo baki
” Ke wa kikewa sakuwa, kin san halina fa bakaramin aikina bane naci ubanki a nan, a lokacin da ana karatun ubanwa ya hanaki kije ki koya, ai wannan shine matsalar rashin ilmin addini.”
♋♋♋♋♋♋♋♋
Anan tunanin Humaira ya katse, tana dago kanta sai tayi ido hudu da wannan matar wadda ta kawo musu break fast dazu. ” Humaira inaso ki rubuta min Ayayul Kursiyu kafa uku ga wannan allon.” Inji matar. Humaira shiru tayi kafin daga bisani tace.
” Ai kuwa jiya na samu rauni ga hannuna inaga bazan iya rubutun ba.” Haka Humaira ta fada tana noke noke kada Mumy ta tona mata assiri matar ta gano cewa bata iya bane.
” E lallai jiya ta dan samu rauni a hannu, amma ki kawo na rubuta miki.” Inji Mumy.
” Aa ba matsala barshi kawai.” Haka matar ta fada daganan sai ta juya ta fita, cikin murna Humaira ta fada jikin Mumy sabida yau ta rufa mata asiri kuma tunanin da tayi bai zama gaskiya ba.
” Mumy naji dadi yau kin rufa min asiri.” Inji Humaira.
” Kibar jin dadi fa, yau kawai ne, next time idan hakan ya kara faruwa kema kin san abunda zai biyo baya, sabida haka kije ki koyi karatu da rubutu na Qur ani, idan kunne yaji jiki ya tsira.” Anan Humaira tayi shiru cikin dana sanin bata lokacin da tayi ga boko ba tare da taba ilmin addini muhimanci ba.
Page 31
Gashi tayi bokon ta kammala amma kuma da anzo ga addini batasan kome ba, wannan abun kunya ne sosai a wurinta domin ita kanta batason mutane su san da cewa batada iimin addini, anan ta kudurta aranta cewa in har zasu koma gida sai ta janyo wancan malamin data kora domin ya cigaba da koya mata darasi akan addini. Matar ce ta kara shigowa dauke da wani cup mai dauke da ruwan tawadda, da alama cewa an wanke rubutu ne.
” Ki shanye wadannan ruwan.” Haka matar ta fadawa Humaira. ” Idan kin shanye zaki fita hayyacinki, idan kin fita hayyacinki wani abu zai faru dake kuma inaso kiyi kokari ki tuna abunda zai faru dake. Ke kuma zaki bini mu fita tare domin ita kadaice za a bari a dakin.” Haka matar ta fadawa Mumy, daga nan sai suka fita sukabar Humaira a dakin. Humaira na shan wadannan ruwan sai ta fara ganin dishi dishi, kafin kaceme ta baje kwance.
” Ke a tunaninki akwai wani mahaluki da zai iya rabani dake?” Inji wani bakin abu tamkar inuwa.
” Wai me yasa kake bibiyata ne?” Humaira ta tambaya.
” Ina bibiyarki ne sabida wannan abun da kika aikata.
” Wane abu na aikata?”Humaira ta tambaya.
” Wato har kin manta kenan?”
” Kwarai kuwa na manta amma ka tunatar dani.”Inji Humaira.
” Banada lokacin tunatar dake, amma ki tunatar da kanki idan kinada bukata.”
” To zaka iya fadamin maganin ciwon dake damuna?”Humaira ta tambaya.
” A a, amma zan iya kwatanta miki!”
” To kwatanta mini!” Inji Humaira.
” kiyi tunani ki gano wane abune kikeyi kullum, kuma wane abune baki iyaba, to idan kika hada wadannan abubuwan sune zasu baki maganin ciwonki. Kuma kiyi duba zuwan hannunki na hagu da hannunta na hagu zakiga canji, ku sani idan na kara dawowa abun bazai muku dadi ba, sabida haka kuji tsoron dawowa ta.” Anan Humaira ta farka firgigit, dakin ya gauraye da duhu ta koina, tanajin a jikinta cewa tayi magana da wani abu wanda bata san ko menene ba, amma kuma yau tana iya tuno maganganun da sukayi daga farko har karshe. Dakyar ta mike tsaye ta nufi kofar fita, tana budewa sai taga ashe rana ta fadi dubun magrib ya gabato, Mumy ce ta shigo tare da matar, daga nan sai suka umarci Humaira ta zauna, bayan ta zauna ne sai ta bayyana musu dukkan abunda ya faru da ita iyaka dai bazata iya tuno siffar abunda tayi magana dashi ba.
” Yanxu sai ki fada mana wani abune kikeyi kullum?” Inji matar. Anan Humaira tayi shiru tana tunani to wane abune takeyi kullum in banda cin abinci da magana.
Page 32
” Ni inaga cin abinci ne!” Inji Humaira.
” Ko kadan bashi bane, cin abinci ai kowa nayinsa, ki dai kara tunani ki gani.” Inji matar. Anan Humaira ta kara tsundumuwa kogon tunani, can sai ta nisa tace.
” Shan music ne, domin a kullum sai nasha music!”
” To wane abune baki iyaba?”
” Karatun kur ani.” Haka Humaira ta fada cikin jin kunya.
” To kinga a cikin maganar ance abunda baki iyaba da abunda kikeyi kullum sune zasu samar da maganin ciwonki, ma anar wannan zance shine idan kinaso ki warke daga wannan larura da kike cikinta to dole ne ki daina shan music gaba daya, kuma dole ne ki koyi karatun kur ani domin shine zai taimaka miki wurin yaki da wannan ciwo.” Inji matar. Anan Humaira tayi shiru tana kara tunanin maganar da sukayi da wannan abun wanda batasan ko menene ba.
” Kuma kiyi duba zuwan hannunki na hagu da hannunta na hagu zakiga canji, ku sani idan na kara dawowa abun bazai muku dadi ba, sabida haka kuji tsoron dawowa ta.” Cikin sauri Humaira ta kalli hannunta na hagu, anan taga fatar ta canza kala, ta koma baki kirin ba kyan gani, sai kuma wasu zane zane a sama. Anan ta duba hannun matar taga itama tanada wannan alamar, Mumy kadaice batada, Humaira fadawa matar tayi wannan abu da aka gaya mata game da hannunsu na hagu, abunda ya kara tayar musu da hankali shine tsananin ciwon da sukeji ga hannayensu.
” Bako shakka dole mu tsayar da wannan aiki idan ba haka ba zamu iya halaka.” Haka matar ta fada tana duban hannunta, amma zan hadaku da yayana, insha Allah za a samu waraka. Anan matar ta juya baki ta fara magana da Mumy a cikin yaren Kanuri. Sai da suka dade suna magana sannan sukayi sallama. Kafin su fita ne sai matar ta tambayi Humaira cewa.
” A lokacin da kina makaranta, baki taba cin alhakin wani ba kuwa?”
” Gaskiya ban taba cin alhakin wani ba domin banada abokin fada.” Inji Humaira.
” Kidai kara tunani akan wannan maganar, a ganina akwai wani abu da kika aikata shi yasa wannan ciwo ke bibiyarki.” Inji matar. Daga nan suka fita. Mumy taja motar ita kuwa Humaira zaune kusa da ita. Haka Mumy ta dau hanya har suka fita daga kauyen, daga nan ta hau babban titi tana rusa wani irin namijin gudu. Sai da duhu ya fara shigowa sannan suka iso wani makaken daji, Mumy kwana tasha ta cigaba da gudu ba kakkautawa, bayan sunyi tafiya mai nisa ne suka cimma bukkoki. Mumy na faka motar sai ta fito ita kuwa Humaira ta biyo bayanta, wata mace suka gani a kusa ga bukkokin tanaba shuka ruwa, bayan ta gaisa da Mumy sai suka cigaba da magana a cikin yaren Kanuri.
Page 33
” Gaskiya bazai dawo ba sai gobe, amma ku shigo zamu baku masauki sai ku jirasa.” Haka matar ta fadi daga karshe a cikin harshen hausa. Daga nan sai ta musu jagora har cikin gidan, wata yar bukka ce aka ajiyesu daga nan aka ajiye musu duk wani abu da zasu bukata. Dakin tsare yake tsaf tsaf dashi, an kawata shi da local decorations tun daga dangin tasoshi zuwa kwaryoyi sai local bed a gefe.
” Yau ba batun bacci a gareki domin zan koya miki yadda ake karatun kur ani kafin shi wanda muke jira ya dawo zuwa gobe, sabida haka sai ki mayar da hankali akai, kuma inaso ki daina shan music gaba daya, waka mai kida haramun ce, ina fatan kin fahimta.” Inji Mumy. Anan ta fara koyawa Humaira alifun ba un, da yake Humaira mai kai ce cikin kankanin lokaci ta iya, haka tacigaba da gwada mata yadda ake tada harafi da harafi su bada kalma, bata kyale Humaira ba sai da ta gamsu cewa ta iya karanta baki kuma ta iya wasu surori daga cikin kur ani gami da addu oi. Tunda sanyin safiya suka farka, suna gama kimtsawa suka cigaba da karatun daga inda suka tsaya. Haka suka cigaba da karatun basu daina ba sai da rana ta fadi bayan shi wanda suke jira ya dawo. Kai da ganisa kasan babban mutum ne, hula da rawani ke zube a kansa sai cover shoes dinsa na roba, alkyabba ce a saman kayan jikinsa sai sheki take. Da sallama ya shigo dakin yana musu barka da isowa, bayan sun natsu ne sai Mumy ta bayyana masa abunda ke tafe dasu da kuma wannan ciwo dake damun Humaira wanda kesa ta fita hayyacinta ba tare data sani ba.
” Alhamdulillahi tunda har kun gano maganin wannan ciwo dake jikin ita wannan yarinya, dama irin wannan ciwo shafuwar shaidanu ce, kuma ita wannan shafuwar itace ta haddasa alaƙa tsakanin ita wannan yarinyar da kuma shi shaidanin dake bibiyarta, kuma ita wannan alaƙa tafi faruwa ga wadanda ke yawan shan kida kuma basuda ilmin addini ma ana ko kadan basu damu da yin addu a ba. Ita wannan alaƙa tanada hatsari sosai domin komi na iya faruwa ga wanda ciwon ya shafa, amma insha Allahu yanzu zamuga abunda zamuyi.” Inji mutumin. Wani lungu ya shiga a cikin dakin, wata tukunyar laka ya dauko mai dauke da kasa sai duwatsu a sama gefe gefe, wani zane yayi a saman kasar daga nan sai ya goge, karayi yayi ya goge sai yace Humaira ta saka hannunta a cikin tukunyar.
” Me kikaji?” Inji mutumin.
” Naji na taba ruwa.” Haka ta fada tana mai duban tukunyar cikin mamaki domin a ciki kasa ne amma kuma ji take tamkar ta sanya hannunta a cikin ruwa.
” Wadannan ruwan sune tushen alaƙarki da abunda ke damunki kuma sune karshen alaƙarki da abunda ke damunki!” Inji mutumin.
Page 34
” Kuma inaso naji tushen wannan alaƙa taki kafin na cigaba da aiki.” Inji mutumin.
” Me kake nufi?” Humaira ta tambaya.
” Ma ana inaso kiyi tunani a lokacin da kina makaranta baki tabayin wani abu a cikin ruwa ba?” Anan Humaira ta farayin tunanin rayuwarta a lokacin da tana jami a, a wannan lokaci Humaira ta kasance sangartacciya, bata ganin darajar mutane balantana kimar dan adam duk da kasancewar iyayenta masu mutunci ne dai dai gwargwado, amma kuma duk da wannan shakiyanci da takeyi bata bari Abba da Mumy su sani domin tasan idan suka san da cewa tanawa jama a daukar uku saura kwata tofa kashinta ya bushe, batada aiki sai shan music, a kullum da marece takan tuka motarta ta nufi wurin wasu ruwa masu tsananin yawa, takan zauna a bakin gabar ruwan daga nan sai ta kunna music ta cika volume sosai, daga nan sai ta dauki duwatsu tana wasa dasu tana jefawa cikin ruwan, bata barin wurin sai duhu ya fara dursasowa, to wata rana bayan ta ajiye motarta a gefe, sai ta kunna music kamar yadda ta saba, yan duwatsun ta tsinta tana jefawa a cikin ruwan tana bin wakar datake sha kamar ita ta rerata. tana cikin nishadinta ne sai ta jefa wani dutsi, ai kuwa yana shiga cikin ruwan sai taji kamar anyi ƙara, ko kadan bata damu ba domin a tsammaninta wani ne ke iyo a ciki, to watakila ta jefesa cikin rashin sani. Jira tayi taga ko wani zai fito amma ba wanda ya fito, daga nan sai ta dauka ba kowa a cikin ruwan wata kila kunnuwanta ne sukaji kamar anyi ƙara. Cigaba tayi da jefe jefenta, tana cikin jifar ne sai ta karajin wata ƙara a cikin ruwan, saurarawa tayi amma shiru ba abunda ya faru, daga nan sai ta dauko wani dutse ta kara jefawa domin ta gani ko zata karajin ƙarar. Ai kuwa tana jefawa sai ruwan sukayi wani zabura suna kadawa da karfi tare da wani sauti a ciki marar ma ana. da sauri Humaira ta nufi motarta domin taji tsoro sosai, ai kuwa tana bude motarta sai ta fadi a sume daga lokacin bata kara sanin inda take ba. Sai farkawa tayi ta ganta a saman gado, kawayenta Mamee da Baby suna mata fifita.
” Hala me ya faru?” Humaira ta tambayesu.
” Ai ke zamu tambaya me ya faru, mun sameki wurin ruwa a kusa da motarki a sume!” Inji Mamee. Anan Humaira ta tuna lokacin data nufi motarta a tsorace bayan taga ruwa suna zabure zabure kamar su hadiyeta, tana bude motar sai taga wani abu amma batasan ko menene ba, daga nan bata kara sanin inda take ba.
Page 35
Tun da wannan abu ya faru Humaira bata kara samun lafiya ba, mafi yawan lokuta idan tana tafiya sai taji kamar an rike mata kafafuwa, ko kuma taji bata iya tafiya. Ko kuma kawai ta fita hayyacinta har sai an tayar da ita. Anan Humaira ta tsaya daga tunaninta, fadawa mutumin wannan labari tayi tun daga farko har karshe.
” Gaskiya Humaira kinyi kuskure da kika tafi wannan wuri ke kadai, kuma kinyi kuskure da kika jefa duwatsu a cikin wadannan ruwan, bako shakka shaidani ne kika jefa a cikin ruwan kuma wannan shaidani shine yake bibiyarki yana kokarin lahanta ki.” Inji mutumin.” Dama idan magrib ta gabato ba a fiye son kusantar ruwa ba, walau a rijiya, gulbi, tafki ko kuma rafi, sabida haka yanxu dole ki tashi ki yaki wannan shaidani da kanki, inaso kiyi imani cewa ALLAH zai taimakeki kuma yana tare dake, yanxu inaso ki fita a cikin wannan gida, idan kika fita sai kibi hannun dama, kici gaba da tafiya kina karanta Ayatul Kursiyu. Idan kika cigaba da tafiya zaki cimma wasu ruwa, da kin shiga cikin ruwan zaki fita hayyacinki, amma idan kika cigaba da karanta Ayatul Kursiyu to insha ALLAH zaki samu nasara akan wannan shaidani, kuma da kin samu nasara akansa to alaƙar dake tsakaninku zata yanke gaba daya daga nan sai ya rabu dake, rabuwa ta har abada, sabida haka yanxu ki tashi ki fita.” Inji mutumin. Humaira fita tayi daga gidan ta kama hanyar dama wadda zata kaita cikin kasurgumin dajin, a wannan lokaci magrib ta gabato domin har duhu ya fara zagaye sararin samaniya, sai tafiya takeyi tana tunanin shakiyanci data yiwa mutane, bako shakka wannan shakiyanci shine ke bibiyarta gashi har ta yiwa shaidani laifi cikin rashin sani. Haka ta tsunduma cikin dajin tana karanta Ayatul Kursiyu, a duk lokacin da kafarta ta taki kasa sai taji kamar ana mata ambaliya da ruwan tsoro a cikin zuciyarta, haka ta daure ta cigaba da tafiyar har ta cimma wasu ruwa marar iyaka, ai kuwa tana shiga ciki sai ta fadi cikin rashin sanin halin da take ciki.
” Amma kin kuru da kika zo da tsari a wannan wuri.” Inji wani bakin abu tamkar inuwa.
” Me kake nufi dani ne?” Humaira ta tambaya.
” Nayi niyar lahantaki amma yanzu naji bazan iyaba!”
” To me yasa bazaka iyaba?” Humaira ta tambaya.
” Sabida kin iya abunda baki iyaba, kuma kin daina yin abunda kikeyi kullum.”
Page 36
” Ka kyaleta hakanan, kazo mu tafi kawai.” Inji wani bakin abu mai kamada inuwar mace.
” Nayi hakuri zan kyaleta, zan rabu da ita rabuwa ta har abada….” Humaira sai farkawa tayi taji ana janyota a cikin ruwan, muryar Mumy takeji tare da wani mutum a saman kanta.
” Yi sheda, kiyi sheda.” Haka aka cigaba da janta ana kokarin fitar da ita a cikin ruwan. Idanuwanta kuwa sai budewa sukeyi da rufewa. Kamar daga can gefe tana iya ganin dishi dishin mota, ji kawai tayi an dauketa an jefa a bayan motar, a cikin glass kuma tana ganin dishi dishin mumy tana magana da wani mutum, tana gama maganar sai ta dawo cikin motar, da karfi taja motar ta nufi hanyar fita dajin, cikin matsananci gudu ta fito daganan ta kama hanyar fita kauyen, bata wani daukar lokaci ba ta iso ga babban titi, ana ta fara cin taya ba sassauci. Har yanxu Humaira dishi dishi take gani domin ji take kamar a mafarki. Zata iya tuno dukkan maganar da tayi da wannan abun wanda har yanxu batasan ko menene ba, babban abunda ke sanyata farin ciki shine jinsa da tayi yace.
” Nayi hakuri zan kyaleta, zan rabu da ita rabuwa ta har abada….” Wannan abu ya mutukar sanyata farin ciki, yanzu shi kenan bazata kara samun irin wannan matsalar ba, wannan alaƙar dake tsakaninta dashi ya yanke gaba daya, kuma shi zai rabu da ita rabuwa ta har abada. ahaka Mumy tacigaba da driving har ta iso ga kauyen nasu wanda gidansu yake. Tana shigar da motar sai ta rufe gate din. Humaira bata farka ba sai da safe, anan taji karfin jikinta ya dawo, sallolin da ake binta ta rama daganan tazo dinning table domin tayi break fast.
” Ya karfin jikinki?” Mumy ta tambayeta.
” Da sauki sosai,” Inji Humaira.
” To idan kin gama yin breakfast ki fita waje akwai wanda ke jiranki.” Inji Mumy. Daga nan sai ta tashi ta shiga dakinta. Cikin gaggawa Humaira tayi breakfast ta fita waje domin ta ga wanda ke bidarta. wata mota ce hadadda a bakin gate din ta gani, tana karasowa ga motar sai taga wani hadadden gaye ya fito a ciki, jeans ne irin pencil trouser din nan sai long sleeve tare da cotton jacket a jikinsa, agogonsa sai wani sheki yake su kuwa takalmansa galesh shoe ne. Kura masa ido tayi tana kallonsa domin ji take kamar ta taba ganinsa…….
” Gambo.” Haka ta fada cike da mamaki.
Page 37
” Kin yi mamakin ganina ko?” Haka ya fada yana murmushi. Abun ya bata mamaki yadda akayi bagidaje irin wannan ya iya dressing haka. Kuma wai bama wannan ba hala motar waye ya aro?
” Kai gambo waya ara maka mota kuma ina ka koyi tuki?” Abun dariya ya bashi sosai amma sai ya kanne, dan guntun murmushi ya sako mata kafin ya fara magana.
” Ai wannan motata ce!” Haka ya fada.
” What? Shin wai mafarki ne nake kuwa?”
” Bari na baki surprise, can you guess what?” Anan mamaki ya kara kasheta wai bakauye irin wannan ya iya turanci. Motarsa ya bude daga nan sai ya janyo wani wedding card ya mika mata. Bayan ta karanta ne sai ta fara magana.
” Shin wai wace Humaira kake magana za a daurawa aure, kuma wane gambo?” Tuntsurewa yayi da dariya kamar bazai daina ba.
” Wace Humaira kika sani kuma wane gambo kika sani!”
” Kana nufin ni da kai?” Injita.
” Kwarai kuwa ni da ke!” Inji shi.
” Ayyu ruru ru rui.” Da karfi Humaira ta juyo domin taga wacece tayi wannan gudar.Tana juyowa sai taga Mumy a bakin gate tana rangwada guda, anan abun yaba Humaira mamaki, dama duk abunda yake faruwa Mumy ta sani ne, da gudu ta shiga gidan domin taji abunda ke faruwa, to anan ne Mumy ta fara labari kamar haka:
” Gambo da kike gani ba bakauye bane, dan boko ne cikakke kuma iyayensa masu hali ne sosai, yana shigowa wannan kauye ne domin ya kawowa yan uwansa ziyara, shi kuma dama irin dress dinsu yana burgeshi shi yasa yake irin shigar su amma kuma a zahiri ba haka ba. Sabida haka yanzu idan kin aminta dashi za a daura muku aure dama gashi gobe abbanki zai dawo.”
” Mumy na aminta na aminta.” Haka Humaira ta fada tana kyalkyatar dariya. A cikin wannan rana kuma ta samu invitation a wayarta cewa za a daura aure Mamee da Nabil, sai baby da Mujahid, ba karamin farin ciki Humaira tayi ba najin cewa za a daura aurenta tare da kawayenta a rana daya. A haka akayi shagali aka kai amare a gidajensu, ita kuwa Humaira ta dukufa wurin koyan addini sosai, wancan malamin data kora shi ta kira ta bashi hakuri domin ya cigaba da koyar da ita kuma cikin sa a ya aminta, daga wannan rana Humaira ta dawo yarinyar kirki, duk wani shakiyanci data keyi dainawa tayi ita da abokanta, shi kuma wannan ciwo dake damunta na shafuwar shaidanu bai kara dawowa ba, haka suka cigaba da rayuwa cikin jin dadi da annashuwa na har abada.
The end.
Written by Abdul King Article and Queen Teei
Subscribe to our Youtube Channel:
Abdul King Article Novels TV
0 Comments