TAFIYAR DARE ( MAYYUN JINI )






TAFIYAR DARE 
MAYYUN JINI
AUTHOR : ABDUL KING ARTICLE
EPISODE 1
PAGE 1
Dare mahutar bawa, idan lokacin ka yayi dole a tareka, dare
mahutar bawa, idan kazo dolene komi ya samu akasi. Dare
mahutar bawa, duk wanda bai zauna wuri daya ba to bayada
banbanci da matacce.
Wannan magana haka take ba tantama, nasan dolene kayi
mamaki yadda na fadi wadannan zantuttuka masu rudani da
tafarfasa zuciya. Amma wannan ya farune sanadiyar wani
bakin al amari daya taba faruwa a gareni shekaru da yawa,
wannan al amari ya farune a cikin dare kuma ya kare a cikin
dare. Sanadiyar hakane naga ya kamata in bayyana kadan daga
faruwar wannan abu ba don komi ba sai dai domin kaima ka
kiyayi dare domin gudun watarana.
Sunana anisa, amma akan kirani da baby, a wannan lokaci ba
abunda na rasa na jin dadi daga gidanmu domin abbana ya
tanadar min duk wani abu na jin dadi da annashuwa, amma
kuma duk da hakan ko kadan ban damu ba. Babban abunda ke
batamin rai shine abba baya bari na fita ko kofar gida, idan
kaga na fita to makaranta zanje domin duk wani abu da ake
bukata akwai masu aiki. Saboda haka su ake sawa aikace
aikacen gida.
Inada waya babba ipone x, sai kuma laptop dita HP, kai in
takaicemaka labari harda mota tawa inada amma ko kadan
bana moriyarta sanadiyar bana yawo, daga makaranta sai
makaranta, kai ko biki idan zan fita sai abba yayi min nasiha
cewa in kiyaye, wannan abu na mutukar batamin rai sai dai ba
yadda xanyi, a duk lokacin danaga kawayena suna
sharholiyarsu abun kan mutukar burgeni, sai naji dama ace
inada wannan damar ai da shikenan.
Bako shakka uwaye sun cancanci yabo, godiya, karamci, da
kuma girmamawa. Duk wanda bai girmama uwayensa ba to
yayi asara tun a nan duniya. Duk abunda abbana ke horar dani
gaskiyane, ni a tunani na yana cutar dani amma daga baya sai
na gano ba haka ba. Bako shakka abba na mutukar sona so na
hakika son da duk wata ya mace zataso ace abbanata na
mata. Na gano hakan ne sanadiya wata tafiya data kama mu a
cikin dare nida kawayena. Saboda haka bari in baka labarin
wannan tafiya da kuma makasudinta.
PAGE 2
Anisa ce ke zaune cikin wani katafaren falo cikin jin dadi,
fuskarata cike take da annashuwa da walwala. Kai da gani
kasan diyar masu hali ce tun daganin shigar ta. Dan lemon
tane exotic a kusa da ita sai wani cup na glass rike da
hannunta, idan tadan kurba lemon sai ta fincike wani cake
dake kunshe a cikin wata leda. Idanunta ko kyaftawa basayi
sanadiyar ta kurawa tv idanu sai kyalkyatar dariya take kai kace
mahaukaciya.
" Laaaaa, shegiya baby hala miye kikeci haka kina dariya sai
kace aJmaryar da za a kai gobe? "
Anan anisa ta daga ido sai tayi arba da kawarta. A guje ta
sheko suka rungume juna cikin murna. " Amma zee bakida kirki
ko kadan,wai ace kinyi graduating amma ko flashing ba za
ayimuna ba." Haka anisa ta fada tare da jawota.
" Haba kawata kiyi hakuri mana, ai da kin san abundan ya faru
da bakice haka ba." Cewar zee tana murmushi.
Anan anisa ta wani karkada idanu tare da yi mata kallon uku
saura kwata. " Humm, dama haka kike, ai dama nasan dole ki
manta damu tunda kin samu kawaye a can ko. Mutuniyar
banza." Anan anisa ta fita falon. Bata jima ba sai gata ta dawo
da wani cup. " Yauwa, bari na zuba miki lemon kema kisha ko
kyaji gardi." Anan anisa ta zuba mata lemon ta bata. " Saura
kuma kice mun bazaki shaba."
" Au, har na isa." Inji zee bayan ta karbi lemon. " Kedai kinason
exotic, ni kodan bai yimun ba, balantana yanzu fa akwai drinks
na yayi amma ke kullum ancient ce. Bakauya kawai."
" Iyee, kina nufin ni bakauya ce?" Anisa ta tambaya.
" Tab, to ke a tsammaninki yar birni ce? Mai bleaching da garin
kwaki irinki." zee ta bata amsa.
Dariya sukayi tare da kallon juna suna taba hannu. " Keda ko
waya bakida, amma ni kike cema bakauya." Anisa ta fada cikin
wasa.
" E naji dai, ai waya nice banso samu ba, kema kin san ruwa
ba sa an kwando bane, zan iya sa samarina su siya min duk
wadda nakeso." Inji zee cikin daga murya.
" Samari kuma? Yaushe kika fara bin maza ban sani ba?" Inji
anisa.
" Au, dama baki sani ba? Ai karuwace kike kawance da ita."
Xee ta fada cikin bakar magana.
PAGE 3
" A a ni dai kada ki kaini inda yan kuda ke salati, nifa ba haka
nake nufi ba. " Anisa ta fada cikin lallashi.
" Ko ma me kike nufi ke acciki, nidai nasan duk yadda goma ta
lallace tafi biyar albarka. Ke da kike daure sai kace tunkiyar
masar. Idan ba tsoro ba mutum ya fita mana, kinzo kin hakince
cikin gida bakya ko tunanin aure, ko kina nufin samarin a cikin
gida zasu ganki suce sunaso?"
" Kema fa kin san ba laifi na bane laifin abba ne." inji anisa.
" To cigaba da jira sai abba yace ki fita sannan zaki fita, aiko
yarinya inaga zaki tsufa gidanku, domin nan da shekaru kadan
zaki yi expiry. Kinga da ganan sai mu kaiki bola tunda kinyi
wari." Haka zee ta fada tana hamma. Cikin rashin tsammani ta
banko wata tusa mai shegen doyi ji kake buuuuuuuummmmm.
" Haba zee bagirman kibane, yanzu fa da ace su al-ameen na
nan da sunyi dariya." Cewar anisa bayan ta toshe hancinta.
" Wai har kin sa gabana ya fadi, hala ina suka jene?" Zee ta
tambaya.
" Tare suka fita da abba, inaga harda mumy ta bisu wai zasuje
kasuwa." Anisa ta bata amsa.
" Kice ke kadaice a gidan yau?" Zee ta fada.
To kafin anisa ta bata amsa sai ga wata tusa wadda tafi ta
farko kara da wari. Anan zee ta mike da sauri." Wayyo cikina,
inaga exotic din nan da kiban ya bata mun ciki. Nifa zawo
nakejiiii." Anan zee ta nufi toiltet a guje. Anisa ce ta danyi
dariya saboda kallon data yiwa zee a lokacin da take gudun.
Wato kayan data sa ne suka matseta sosai yadda gudun take
amma ana ganin kome na siffar jikinta. Anan anisa ta kara
fanka domin warin yadan rage. To bayan ta zauna ne sai
tunanin maganar zee ta taso mata.
To cigaba da jira sai abba yace ki fita sannan zaki fita, aiko
yarinya inaga zaki tsufa gidanku, domin nan da shekaru kadan
zaki yi expiry. Kinga da ganan sai mu kaiki bola tunda kinyi
wari.
Bako shakka abunda zee ta fada gaskiyane fa, to yanzu idan na
cigaba da zama a nan to yaushe zanyi aure, burin kowace ya
mace shine tayi aure ta kuma haifafa. To amma ni ko kadan
banada wannan gatan. To yanzu yama za ayi samari su ganni
suji na burgesu idan ban fita ba? Bako shakka dolene na dauki
mataki sosai game da wannan al amari. Anan tunanin anisa ya
yanke sanadiyar fitowar zee daga toilet.
PAGE 4
" Wai, har naji dan sauki." Cewar zee bayan ta kishingida kan
kujera.
" Duk kin cika mana wuri da shegen doyi." Inji anisa cikin wasa.
" Ai ba laifina bane, ai dana sani da ban sha ba." Inji zee. Anan
ta mike ta dauki jakarta." Bari na koma gida magriba ta kusa."
" Tun yanzu zaki fita?" Anisa ta tambaya.
" Hmmm, ni dai sai anjima kada ki bata min lokaci, gashi ba
yawo kikeyi ba balantana nace ki rakani." Haka zee ta fada
kafin ta fita.
Anisa binta tayi da kallo cikin zurfin tunani na wannan maganar
data yi mata. Haka zee ta fita cikin rangwada kai kace jikinta
ba jini da tsoka bane. To a wannan lokaci tunanin anisa ya
zurfafa har takai ta kashe tv saboda ji take kamar ana
damunta. Gaskiya dole na dauki mataki akan wannan al amari,
abu har yakai an fara yimin gori akan rashin fita. Gashi kuma
na girma amma har yanzu ace banada yancin kaina. Haka dai
anisa ta cigaba da tunani daga nan kuma sai ta koma dakinta
domin ta dan yi bacci.
Kida ne ke tashi mutane sai rawa akeyi kowa ya kama
gwaninsa, maza da mata an cankude sai bushasha akeyi.
Anisa ce ke tafiya tana waige waige a cikin filin rawan. A haka
ne tayi kicibis da wata budurwa tsaye. " Yauwa, dama ke nake
jira." Haka yarinyar ta fada kafin daga bisani ta dauko yuka da
zimmar yanka ta. Anisa ce ta kwala uban ihu daga nan ta farka
firgigit. Ashe mafarki ne takeyi. To a wannan lokaci mumy ce
ta shigo taga lafiya. Anan anisa ta fada jikinta tsorace.
" Me ya faru haka kike wannan ihu sai kace mahaukaciya, to fa
kada ince dai mafarkin ne kika karayi?" Mumy ta fada bayan ta
rungume ta."
" E wallahi mumy, a wannan karon dakyar nasha da ta sokamin
yuka." Anisa ta fada a tsorace.
" Kinga abunda nake fada miki ko? Idan akayi la asar ba a
bacci amma kinki. Ko yaushe sai kice wai yafi karfinki." Mumy
ta fada bayan ta tayar da ita." To yanzu sai kije kiyi salla ga a
can ana magrib."
PAGE 5
Da misalin karfe 8:30 PM ne su anisa suka nufi dinning table
domin daukar dinner. A wannan lokaci kowanensu yayi sallar
isha i. Al ameen ne da husna suka fara zaunawa saman
kujerun. Abunka da yara basa ko bari sauran jama ar su karaso
domin aci abincin tare. Cikin gaggawa suka fara tura loma
suna kyakkyatar dariya.
To bayan kowa ya zauna ne sai aka fara cin abincin tare. " Nifa
wannan mafarki na anisa kan mutukar ban mamaki domin ban
taba jin wanda ya taba yin irinsa ba. Kuma ace abu ya kici yaki
cinyewa." Haka daddy ya fada yana kallonsu daya bayan daya.
" Hmm, kai dai bari, ai abu ya tsananta yanzu. Tunda har da
fizge fizge take yi idan tana bacci." Haka mumy ta fada tana
kallon anisa.
" Haba mumy fizge fizge fa kikace." Anisa ta fada cikin rashin
jin dadi.
" E to zan miki karyane?" Mumy ta tambayeta.
" Yanzu dai ya isa sai ku saurara muci abinci." Daddy ya
tsawatar.
A haka dai suka cigaba da cin abincin, to bayan sun kammala
ne kowa ya nufi dakinsa domin ya sarara. Haka anisa ta shiga
dakin cikin rashin jin dadi. A yau dai jikinta ba karfi sai kace
wadda aka zane. Laptop da dauko da nufin kallo kuma saita
ajiyeta gefe saboda tunanin daya dameta. Tana cikin hakane
sai ga husna ta shigo aguje rike da littafinta na islamiya
( MUKARRAT TAUHID)
" Shegiya har kin ban tsoro, wai uban me ya kawoki dakin
nan?" Anisa ta fada cikin jin haushi.
" Wayyo sorry baby, wani fa assignment ne aka bamu kuma
gobe akeso mu bayar." Husna ta fada cikin tausayawa.
" Ina fatan dai english ne?" Anisa ta tambaya.
" A a, amma duba ki gani."
Anan husna ta miko littafin. Anisa na kallon littafin gabanta ya
fafi. " Kwal uba." Ta fada da karfi tana kallon husna. Anan ta
fara tunani yadda zata bulloma al amarin domin ko kur ani
daga shekara sai shekata take karatunsa a lokacin azumi.
Gashi kuma bataso ace bata iya ba.
PAGE 6
" Baby ya naga kinyi shiru?" husna ta tambaya cikin natsuwa.
" E ina dan tunani ne ai kema kin san cewa wannan littafi na
dade da kammala shi. Yanzu bari na biya miki."
Anan anisa ta rika mukarrat tauhid ba tare da sanin abun cewa
ba. Ita kuwa husna kallonta take tana saurare taji me zatace.
" An karbo daga.... Ummm......" Muryar anisa ta fara rawa.
" Laaaaaa, bafa hadisi bane ji yadda take....." Husna ta fada
cikin dariya.
" Ke ubanwa kikewa dariya?" Anisa tasha toka.
Anan husna tasha jinin jikinta domin tasan data motsa zataji
masga.
" Wane wurine za a biya miki?" Anisa ta tambaya.
Anan husna ta buda mata dai dai shafin da takeso ta karanta
mata. Cikin rashin tsammani sai sukaji an banko kofar da karfi.
Juyawa sukayi da nufin ganin ko waye. Ai kuwa ba kowa ceba
in banda halina wato kawar anisa.
" Me kuke karatu haka?" Ta fada tana taku dai dai. Basu amsa
mata iyaka dai sun bita da murmushi har ta karaso wurinsa. To
anan suka taba hannu cikin jin dadi. Batayi wata wata ba ta
fizge littafin tana dubansa. " Anisa, yaushe kika zama ta
kwarai, wai kece da wanan littafi kuwa?" Halina ta tambaya
cikin mamaki.
" Hmm, ai kema kin sani ba saina fadaba. Nifa rabona da
arabic tun..... " Anan anisa tayi shiru bata iyar ba don kada
husna ta gane halin da ake ciki na cewa bata iya karatun ba. "
To yanzu tun da Allah ya kawoki ai shi kenan kin hutar dani sai
ki fada mata." Cewar anisa cikin murmushi.
Kasancewar halina mai ilimin addini ce, cikin kankanin lokaci
ta karbi littafin ta fashema husna shi har saida ta fahimci
abunda ake magana akai. Daga nan kuma ta taimaka mata
wurin amsa assignment din da aka bata. Anan husna ta karbi
littafinta ta nufi waje bayan tayi godiya. Wannan abu da halina
tayi ya mutukar burge anisa domin tasan cewa idan da bata
zoba. Tofa yau da kunya ta kasheta.
PAGE 7
" Amma fa kawata kin ceceni, yau inaga da baki zoba da
sunana gawa." Anisa ta fada cikin dariya.
" Au wai kina nufin bazaki iya karanta wannan littafin na yara
ba?" Inji halina.
" Wai na yara! Kajita da wata magana." Anisa ta fada tana
kallonta.
" Wai ya akayi kikasan ina nan?" Anisa ta tambaya.
" Daga shigowata na iske su mumy a falo, to bayan mun gaisa
ne saita fadamin cewa kina nan daki." Halina ta amsa.
" Gaskiya ilimin addini yayi, yanzu ke halina bakida matsala ko
kadan."
" Haba wa? Ni har ilimi gareni, ai idan kikaga wasu sai kin rike
baki."
Anan su anisa sukayi tadi har saida dare ya raba sannan sukayi
sallama halina ta koma gida.
Tunda kulu kulun safiya anisa ta farka domin yau akwai al
amurran da takeso ta gabatar, a haka ta shirya jikinta tsaf,
daga nan ta dauko wayarta ta fara wasa. Da misalin karfe 8:30
AM, sai ta farajin ana kwankwasa kofar dakinta. Bai jira an
budeba kai tsaye ya shigo.
" Anisa, wai kece a farke?"
" E mana daddy tun dazu fa na tashi."
" Tab, kina nufin har kinyi sallah?"
" E mana tun dazu."
" Mamaki, Keda bakya asuba sai karfe goma sha biyu na rana
amma yau har kin samu asuba. To Allah yayi miki abarka yata."
Anan ya juya ya fita.
Da misalin karfe 11:30 AM, anisa ta fito da makullin motarta, a
yau fa cikin jin dadi take saboda tafiyar da zatayi. Rabonta data
fito waje har ta manta. Gate man ne ya mayar da kofar bayan
ta fita da motar. To anan ta nausa aguje ba sassauci. A haka ta
miki hanya duma na tashi a hankali yadda ita kadai keji. Bayan
tayi tafiya mai dan nisa sai ta cimma wani makeken gida. Sau
biyu kawai tayi oda aka bude mata gate din. Ciki ta nausa kai
da gani kasan cewa ba bakuwar gidan bace.
" Hajiya sannuki da zuwa." Anan mai gadi ya sheko a guje
wurinta.
" Yauwa barka, ina fatan dai tana ciki.?" Anisa ta tambaya.
" Gaskiya batanan, amma taban wannan takardar cewa idan
kinzo in baki."
PAGE 8
Anan anisa ta karbi takardar tana karantawa, " Ai kuwa daka
fadamin da bazan shigo ciki ba, kaga yanzu aiki ya sameni wai
ba a nan zamu hadu ba." Haka anisa ta fada cikin rashin jin
dadi domin ji take kamar duk ta wahala.
" Hajiya ayi hakuri, anan na tafka babban kuskure." Haka mai
gadi ya bata hakuri. Daga nan kuma ya bude gate din ta fita.
To bayan ta fita ne saita nufi inda zata hadu da kawarta. Anan
taci taya sai banka wuta take. Bata tsaya koina ba sai kusa ga
wani restaurant. Aiko tsayawarta keda wuya sai taji an shigo
cikin motar. Tana dubawa sai tayi arba da zee. Wato kawarta.
" Tun dazu fa nake jiranki amma sai yanzu." Zee ta fada cikin
murmushi
" Yanxu dai ba wannan ba, muje muci abinci nifa yunwa
nakeji." Anisa ta fada bayan ta fito daga motar. Daga nan sai
zee ta biyota. Bayan sun zauna ne aka kawo musu abincin da
sukeso. Daga nan sai suka faraci suna tadi. To cikin hakane
anisa ta lura da wani zane ( Tattoo) dake a hannun zee, hoton
maciji ne akayi a hannun nata. Anan anisa ta kurawa wannan
zane idanu cikin mamakin ko me yake nufi. To da zee ta lura
da kallon da takewa zanen, sai tayi sauri ta juyar da hannunta.
Anisa tayi mamaki sosai domin bata saba ganin irin wannan
zaneba. Tayi niyar ta tambayi zee game dashi amma kuma sai
wani abu ya tauke mata hankali har ta manta. To bayan sun
kammala cin abinci sai zee ta karbi makullin motar domin ta
tukasu zuwa wurin da zasu.
" Kikace walimar aurece zamu ko?" Anisa ta tambaya.
" Koma dai miye ai zaki gani." Zee ta bata amsa.
A haka suka yita shiga lungu lungu sako sako wasu unguwanni
anisa bata masan dasuba. Sai wazajen la asar sannan suka
kawo wani gida shi kadai a rabe. Anan zee ta mata umarni
dasu shiga ciki. To bayan sun shigo ne sai anisa taga ba
abunda ake in banda casu. Katon filine wangameme mutane
maza da mata sai sharholiya akeyi. Daga shigowar anisa aka
tsura mata ido, anan kowa ya bita da kallo wasu ko kyaftawa
basayi.
PAGE 9
" Wai dama ba walima ce mukazo ba?" Anisa ta tambaya.
" Hmm, wai walima. Kada ki damu kawata na fadi hakane
yadda idan kika fadawa su mumy kai tsaye zasu yarda kije.
Domin idan ba walima kikace zakiba nasan bazasu bari ki fita
ba." Xee ta bata amsa.
Anan sukayi dariya, " Lalle kin cika yar duniya. Wato har kin san
halin da gidanmu yake ciki kenan." Inji anisa.
Anan suka zauna suna kallon yan rawa, to abunda yaba anisa
mamaki shine mafi yawancin mutanen dake wannan wuri suna
dauke da irin zanen zee akan hannunsu, katon macijine baki
kirin aka zana musu. Wannan abu yaba anisa mamaki, to anan
ta fara ganin cewa duk yadda akayi wannan zane na maciji
akwai abunda yake magana akai, kuma bako shakka dole
abokan juna ne domin bazai yiwuba ace duk daukakin
mutanen dake gidan sunada zane iri daya a hannunsu.
" To amma wai me yasa kika kawoni wannan wuri?" Anisa ta
tambaya.
" Saboda inaso in taimake ki, nasan da cewa gida ba a bari kiyi
yawo, amma yanzu wannan yawo da mukayi don Allah bakiji
dadi ba?" Zee ta fada cikin fara a.
" E kwarai kuwa, kamar kin san abun na yimin zafi wai ace
banda ikon fita, kenan fa ko yanxu da ace banyi wannan karyar
ba da bazasu bari na fita ba." Inji anisa.
" Kada ki damu kawata, ai daga yau kukanki ya bushe, wannan
wuri fa dana kawoki nan za a share miki hawayenki. Kuma za a
baki yanci na kiyi duk abunda kikeso a lokacin da kikaga
dama." Xee ta fada cikin harzukawa.
" Allah ko kawata? To amma wannan wane wurine kuma ya za
ayi ku sharemin hawaye?" Anisa ta tambaya.
" Ki kwantar da hankalinki kawata. Yanzu zan gabatar dake ga
sauran members namu. Amma fa duk abunda sukace kiyi
zakiyi." Inji zee.
Daga nan saita tashi ta nufi wani lungu. To anan ne anisa ta
kalli wurin taga yadda aka kawata gidan abun gwanin ban
shawa. Ga mutane iri iri kowa sai sha a nin gabansa yake.
Kowane saurayi yaja tasa budurwa sun fake a gefe daya. Abun
ya mutukar burge anisa duk da cewa batada saurayi.
PAGE 10
A wannan lokaci duhu ya farayi amma kuma mutane sai
tudadowa sukeyi sai kace yanxu aka fara cin kasuwa. Tana
cikin wannan hali sai taji an shafi kanta. Da karfi ta juyo domin
taga ko waye. To anan tayi arba da wani saurayi dan shala.
Anan suka hada ido da anisa. Gabanta ne ya fadi duuuumm.
" Yan mata ko kinada karas ne? "
Anan anisa ta kalle sa ba tare da cewa komi ba sanadiyar
rashin sanin abunda yake magana akai. " Ya ina magana kin yi
shiru. To idan bakida ni zan baki." Anan ya fada yana dubanta
daga sama har kasa. Can sai ga zee ta dawo. To a wannan
lokaci shi kuwa ya mike hannunsa da nufin ya kara shafa
kanta. Caraf yaji an cafke masa hannu.
" Haba zalo kawata cefa!" Zee ta fada cikin laushi.
" Iyeee, dama kawarki ce, to nifa koma wace na siya. Saboda
haka yanzu sai ki fada mata."
" Kai kuma kana wannan magana kofa register ba a yi mata.
Yanzu dai kayi hakuri idan ta zama yar gari zan tuntunbeka.
" Tab wai ke nufinki bata taba haduwa da karas ba. Amma fa
tayi girman banxa. Ga kyau amma ko kadan bata more masa."
Anan ya fada yana mai tafiyarsa. Daga nan sai zee ta jawo
hannunta suka nufi wani lungu.
" Wai me yake nufi da karas? Ko yana nufin carrot wanda na
sani?" Anisa ta tambaya.
Anan zee ta kyalkyace dariya. " Ke sabuwar zuwace bakisan
kome ba. Ga kuma shegen ustazanci da kike fama dashi.
Yanzu dai muyi sauri suna jira."
Saida sukayi tafiya mai dan nisa kafin su shigo wani katon daki
cike da mutane kowa sai sha anin gabansa yake. Ai kuwa
mutanen na ganin sai suka fara tabi da shewa suna kallon
anisa. Ita kuwa batason abunda akeyi ba iyaka dai ta kura
musu idanu. A haka suka cigaba da tafiya ana musu tabi har
suka kawo wurin wani dogon table mai fadi an lullubeshi da
carpet.
PAGE 11
To anan wani mutum yama anisa umarni data tube kayanta ta
kwanta saman teburin. Da farko taki yarda sai da kyar zee ta
shawo kanta sannan ta yarda ta debe dan kwali shi kadai.
Amma sauran kaya taki cirewa. Daga nan sai mutumin ya kura
mata idanu. Sai da ya kallace surar jikinta tsaf sannan sai ya
kyalkyace da dariya. Can kuma sai ya taba hannunsa sau uku.
Ai kuwa saiga wani kato ya fito daga shi daga shi sai dan
guntun wando duk ana ganin kome nasa. Ai kuwa mutanen na
ganinsa sai suka fara ihu suna masa jinjina ka da gani kasan
sananne ne a wurin. A haka ya cigaba da tafiya yana taku dai
dai su kuwa yan matan gurin sai kallonsa suke suna kyalkyatar
dariya.
A haka wannan katon ya nufo wurin anisa. Daga zuwansa sai
ya dauko wata kwarya dake jicce a wurin. Wata katanyar
fanteka ya bude ya debo wani abu jawur. Daga nan sai ya
mikowa zee domin ta ba anisa.
" Wannna zobo ne ko meye jawur?" Anisa ta tambaya.
" Kedai sha kawai." Xee ta fada.
Ai kuwa anisa na kafa baki mutanen suka dau ihu. Bata wani
jimawa ba ta amayar da abun tana tari sai da zee ta kwantar
da ita. Daga nan sai mutumin ya kusance ta. Ai kuwa sai kaji
wurin yayi tsit sai kace anyi mutuwa. To anan kowa ya kuro
musu idanu yana kallonsu. Da farko mutumin sai ya fara shafa
gashin kanta. Ai kuwa nan take jikin anisa ya mutu. Daga nan
sai ya sauko da hannunsa ga dukkanin jikinta koina shafawa
yake. To anan anisa ta fara girgiza sai kace marar lafiya. Can
kuma sai ta fara nishi sai kace mai jin kashi. Sai da ya dau
lokaci yana shafa jikinta daga nan kuma sai ya bankare
kafafuwanta da nufin warwasawa.
Caraf sai ga anisa ta mike zumbur. A wannan lokaci duk
abunda takeji ya kau. Da karfi ta ture wannan katon dake shirin
afka mata daga nan ta mayar da dankwalin ta.
" Dama kin kawoni ne domin a cimin mutunci?" Anan anisa ta
kama hanyar fita tana zub da hawaye. Da gudu zee ta biyota
tana lallashinta.
" Haba baby ya kina fadar haka sai kace ba wayayya ba. Nifa
taimakonki xanyi domin ki zama daya daga cikinmu. Kuma ina
tabbatar miki da cewa da ace kin tsaya to da yanzu an gama
kome."
Anan anisa ta finciko hannunta da karfi tana kallon zanen
maciji.
" Wannan macijin da aka zana a hannunki me yake nufi, kuma
me yasa duk daukakin mutanen dake wannan gidan sunada
shi?" Anisa ta tambaya
PAGE 12
" Wannan zane na maciji dake hannuna an yi shine da wuta
yadda bazai taba gogewa ba har abada. Kuma wannan macijin
da kike gani shine uban gidanmu. Kuma kema kafin ki shiga
kungiyarmu dole sai an miki shi." Zee ta bata amsa.
" Maciji shine uban gidanku, to meye ya hadaku da maciji inba
maita ba. Kuma menene nasha a cikin kwarya? Kada fa
kicemin jini ne. Ashe ku mayyu ne. Mayyun jini. To idan ba jini
bane menene nasha?" Anisa ta fada tana xub da hawaye. " Ni
yanzu kinga tafiyata." Anan ta juya ta nufi kofar gida.
Caraf sai zee ta rike hannunta. " Haba kawata ya zakiyimin
haka. Wai kuwa kin san irin kunyar da kika jefani a yau din nan.
To bari na fada miki wani abu. Bazaki zo kiga sirrinmu ba
sannan ki fallasa mu a gari kowa yaji. Ga kaida duk wanda
yazo nan to dolene yayi mana biyayya. Saboda haka dolene ki
shiga kungiyarmu ko kinaso ko bakyaso. Yanzu kije duk inda
zaki. Nasan ke da kanki zaki kawo kanki har wurinmu. " Anan
zee ta koma cikin gidan ta kyaleta.
Daga nan ne anisa ta nufi motarta. Dakyar take tukin har ta
samu damar fita daga unguwar wadda ba gida gaba balle baya
in banda wannan na su zee. To bayan takai gida ne ta tarar su
mumy har sunyi bacci. A haka ta kishigida saman gadonta
tunanin duniya ya dabaibayeta. Cikin hakane bacci ya dauketa.
" Anisa, anisa, anisa." Anan ta sheko a guje wurin daddy. "Ban
taba aika ki wani wuri ba tunda nake. Yau ma lalura ce shi
yaza zan aikeki domin yan aikin duk basu zoba. Anan ya bata
kudi tare da fada mata abunda yakeso ta siya masa.
A cikin motarta ta shiga bata tsaya koina ba sai wani katon
shago da ake siyar da shaddodi. To bayan ta siya ne kafin ta
fito sai tayi kicibis da wani saurayi. Suna hada ido gabanta ya
fadi. Anan ya mata kallon tsaf. Done kanta tayi ta fita shi kuwa
sai ya biyo bayanta.
" Don Allah yan mata idan bazaki damu ba ko zan iya sanin
sunanki."
Anan anisat ta kalleshi cikin mamaki. " Kai kuwa daga ina
haka? Daganin mace sai ka noce."
" Haba don Allah fa nace, yanzu kiyi hakuri ki fadamin sunan
kawai."
PAGE 13
" Kai ni kaga tafiyata banada lokaci." Inji anisat. Anan ta juya ta
cigaba da tafiyarta. Shi kuwa bai damu ba sai ya fara binta
yana lallashinta. Kajifa mata da yanga. Tun da ganinsa fa taji
ya kwanta mata amma saboda jan aji irin na mata haka ta
cigaba da juyashi sai kace waina a cikin tandu. To sai akayi sa
a yaron mai baki ne, saboda haka cikin kankanin lokaci ya
shawo kanta. Kafin kaceme ya samu abunda yake nema.
A cikin sati daya kacal soyayya mai karfi ta shiga tsakanin
wannan yaro da anisat. Yakan kawo mata ziyara akai akai har
gida tare da fita da ita yawo har dai a cikin dare. Ba yadda su
daddy basuyi ba domin ganin sun hanata fitar dare amma taki.
Wata rana suna chat a whatsapp:
Hamir: Slm
Anisa: wslm
Hamir: ya kk ne.
Anisa: lfy lau kaifa.
Hamir: Akwai inda nakeso muje yau da dare ina fatan ba
matsala.
Anisa: Nifa na fara gajiya da night club din nan kaji kuwa yadda
su daddy ke fada.
Hamir: Haba sweety,yanzu ke matsayinki na big girl ace gida
ana miki haka. To ai munada yawa domin da kawayenki za a.
Anisa: Da gaske? To yanzu ya kenan.
Hamir: Kada ki damu zan zo har gidanku da dare.
Anisa: Ok ba matsala.
Hamir: Bye dear ki kulamin da kanki.
Anisa na ajiye wayar sai ga mumy ta shigo cikin dakin. Anan ta
zauna kusa da ita. " Anisa wai kece kuwa? Nifa sanina yata
mai ladabi da biyayya ce kuma bata saba umarnina. Amma sai
aka wayi gari kin canza. Kece yawon dare, shaye shaye, fadace
fadace. To wai ina tambayarki yaushe zakiyi hankali ne?"
" Haba mumy shaye shaye fa kikace."
" E na fada kinayi, sau nawa kike shigowa a cikin maye
bakisan inda kanki yakeba."
Anan mumy ta dauko wata yar karamar jaka ta anisa dake
rataye a bango. Ai kuwa tana budawa sai tayi salati. " Wato
nan kike boye magungunan ki ko?"
PAGE 14
Anan anisa tayi shiru domin tasan batada gaskiya. " To Allah
ya shirye ki." Anan mumy ta dauki jakar ta fita. Bayan minti biyu
da faruwar hakan sai ga abba ya shigo gigice.
" Ke, ashe bakida hankali ban sani ba. Yaushe kika lalace
haka?"A haka daddy ya sameta da fada inda yake shiga banan
yake fita ba. A hakan anisa tayi shiru domin tasan halin abba
idan yayi zuciya. Inda sabone ai ta saba da fadansa. Can kuma
sai ga mumy ta shigo aguje tana bashi hakuri domin shi
nufinsa ya doketa. Anan dai ta lababa shi ya hakura ya fita. Ita
kuwa anisa abun ko a jikinta bata damu ba jira kawai take dare
yayi hamir yazo.
Da misalin karfe 8: 30 PM hamir yazo. To anisa ta riga tasan
yau fa idan akaga fitarta to karyarta ta kare saboda haka saita
diro ta taga. A hankali take tafiya sai kace hanwawa. To bayan
ta fita gidan ne saita tarar da wata jeep a fake. Ai kuwa kai
tsaye ta shiga domin tasan ko su waye a ciki. Da shigarta ta
tarar da kawayenta wadanda take haduwa dasu a night club.
Matan su biyu ne sai ita cikon ta uku. Sai hamir da abokansa
biyu.. Gaba daya dai su shidda ne a motar. Wato mata uku
maza uku: hamir, safyan, da najib. Sai anisa, mamee, da kuma
ruky.
Hamir ne ke tuka motor domin shi ne yasan inda zai kaisu. A
wannan lokaci kowanensu cikin jin dadi yake sanadiyar tafiyar
dare ce zasuyi. To anan suka yanki titi sai tafiya ake ba
kakkautawa.
" Hahhhha. Sheri mamee har kin ban dariya." Haka ruky tace
sanadiyar wani labari da mamee ke bata.
" To idan kece ya zakiyi?" Mamee ta tambaya.
" Me zan yi kuma. Guduwa mana." Ruky ta bata amsa.
" Ai ko kin gudu zasu iya binki fa. Bakisan matsafa neba." Inji
mamee.
" Wai menene kuke tattaunawa haka sai dariya kukeyi?" Anisa
ta tambaya.
" Ai ina gaya miki kawata wannan yarinya ce mamee da
shegiyar karya. Wai labarin wasu ne takeban masu amfani da
jinin mutum." Inji ruky.
" Ke waya fada miki karyane. Duk abunda na fadi da gaskene."
Cewar mamee.
PAGE 15
" To nidai a dawo farko inaso naji farkon labari." Inji anisa.
" To yanxu idan abunda mamee ta fada ya zama gaskiya ya
kenan?" Hamir ya fada.
Anan suka kyalkyace da dariya su a ganin su ya za ayi wnan
abu ya faru. A haka suka cigaba da tafiya suna ratsa
dazuzzuka a guje. To suna cikin tafiyar ne sai hamir ya faka
motar.
" Wai menene ya faru?" Najib ya tambaya dama shine a gaba
kusa dashi.
" Zan dan yi larurane, fitsarin ne ya matseni." Anan hamir ya
fita ya bar su a cikin motar. Su kuwa sai suka cigaba da firarsu
kafin ya dawo.
" Wai hala wane wurine zai kaimu?" Anisa ta tambaya.
" Tab, wai kema bai fada maki ba kike nufi?" Najib ya fada.
" E mana. Tsamanina ya fada muku ai." Anisa ta bashi amsa.
" Kada ku damu inaga baxai wuce club ba." Cewar safyan.
" Amma fa yakamata ace ya dawo yanzu. Bari na fita na duba."
Anan safyan ya fito cikin motar yana kiransa amma ko
alamarsa babu. Saboda tsananin duhu dakyar ya dawo cikin
motar ya dauki yar karamar torch-light. Anan ya fara tafiya
yana haskawa amma ba hamir ba alamarsa.
" Inaga fa akwai matsala kada fa ace hamir ya bata." Cewar
ruky.
" Hahahha. Kufa mata tsoro fa ya muku yawa. Wai bata. Hala
an fada muku shi mace ne da za a saceshi." Najib ya bata
amsa.
" To kufa kada muyi zaune a nan wani abu ya samemu. Ni har
na fara jin tsoro." Inji mamee cikin wasa.
Anan suka kyalkyace da dariya suna kallonta. " Ashe dama kina
tsoron tafiyar dare?" Najib ya tambaya.
" E mana. Idan muka haddu da mayyun jini fa." Mamee ta fada
cikin kashe idanu.
" Wannan labari fa ba da gaske bane. Wai kun taba ganin inda
mutum yaci mutum?" Najib ya kara tambaya.
" Au dama baka sani ba. To sau nawa akayi. Na taba jin labarin
wani gida dake cikin......"
To kafin mamee ta iyar da maganar sai sukaga safyan ya shigo
gigice. Anan suka fara kallonsa a tsorace. " Lafiya kuwa. To ina
hamir din." Anisa ta tambaya.
PAGE 16
" Kai. Ku bani makullin mota. Ni bazan xauna a nan ba. Yanzu
gida zan wuce. Ku bani makullin motar na tuka." Anan ya mike
da nufin komawa gaba. Su kuwa su anisa sai suka rikeshi suna
tsammanin ko ya zautu ne. Kubce kubce yayi tayi domin su
barshi ya tafiyarsa amma sukaki.
" Ku sakeni in tafiyata. Ni bazan mutu a nan ba. Bazan mutu a
cikin wannan tafiya ba." haka safyan ke fada yana fisge fisge
su kuwa suka rikeshi gam. To bayan yaga bazasu sakeshi ba
sai ya fara zub da hawaye.
" Haba safyan, wai wannan kuka fa. Yanxu dai ka fada mana
wai meke faruwane?" Anisa ta tambaya.
" Nasan zakuga kamar na haukace ko? To da hankalina. Kuma
duk abunda nake ina sane. Idan har kunaso mu rayu to dole
mu bar wannan wuri yanxu idan ba haka ba to nan bada
jimawa ba zamu zama gawawwaki." Cewar safyan.
To anan hankalinsau ya tashi gaba daya. Kowanensu ido ya
fito sai kace mazuru. " To yanzu sai ka fada muna menene ka
gani kuma ina hamir yake?" Anisa ta tambaya.
" Hamir ya yaudaremu. Ya cucemu. Ni dana sani da ban
bijirewa iyayena ba. Dana sani da banyi tafiyar dare irin wannan
ba. Yanxu shi kenan haka zamu mutu." Anan safyan ya cigaba
da kukansa. Ba yadda basuyi dashi ba ya fada musu kome ya
gani amma ya kasa.
" Tunda bazaka fadaba ni bari na fita na gani." Inji anisat. Anan
taja ganbun motar da nufin budewa. Ai kuwa kafin ta bude
kawai sai taji saukar gatari akan ganbun. Anan tayi wani ihu ta
kulle ganbun.
" Wayyo Allah. Gasunan fa." Inji safyan a tsorace. Anan suka
farajin sara ta koina. Cikin karfin hali najib ya kunna motar da
karfi ya wani juyawa kafin kaceme ya fizgi daji. Ai kuwa sai
motar ta kubce, shi kuwa ya kasa controlling dinta. Daga nan
sai suka fara ihu ganin mutuwa a fili. Sai da motar tayi tafiya
mai nisa kafin ta bugi wani icce. Daganan saita tsaya hayaki
sai fita yake. Cikin sauri su anisa suka fito sai tari suke da
sheshsheka. A wannan lokaci kowanensu ya tsorata sosai
domin basuyi tsammanin cewa zasu rayu ba.
PAGE 17
" To yanxu meye abunyi kenan?" Mamee ta tambaya.
" Bako shakka dole mu bar wannan daji yanzu idan har munaso
mu rayu." Cewar ruky.
" To amma su waye wadannan dake son kashemu?" Najib ya
fada.
" Wannan itace amsar daya kamata mu gano." Inji anisa.
Haka suka cigaba da tattaunawa ta yadda zasubar wurin amma
ba wani nagartaccen tsari da suka hango. Ba yadda basuyi ba
motar ta tashi amma taki. A haka suka hankura domin sun san
cewa sun kawo kansu ga mahalaka. Suna cikin hakane sai
suka farajin gudun wasu mutane kamar sun nufosu. Ai kuwa su
anisa najin haka sai suka rantama a guje. Kowanensu sai gudu
yake kamar ransa zai fita. Sai da sukayi gudu mai nisa kafin su
tsaya sanadiyar sunji kamar an daina binsu. To anan suka fara
tafiya suna waige waige. Kai daganin tafiyarsu kasan sun gaji
mutuka. Amma saboda tsoro haka suka daure kamar basa
gajiya sai shiga suke a cikin dajin.
" Nifa na gaji. Gaskiya bazan iya tafiya ba." Anan ruky ya
zukunna tana sheshsheka. Ganin haka yasa kowanensu ya dan
gincira kusa ga itace domin su samu sarari. Can sai anisat ta
mike da sauri. Cikin fushi ta ci kwalar safyan.
" Ka fada mana menene ke faruwa damune. Su waye ke
kokarin kashemu. Kuma dazu daka fita me ka gani?"
Anan safyan ya fara nishi guda guda saboda matsar daya sha.
" Duk abunda mamee ta fadi gaskiya ne. Bako shakka hakane
batayi karya ba." Anan anisa ta sakeshi domin ya cigaba da
bayaninsa. " Bako shakka hamir yana daya daga cikin wadanda
muke zargi domin fitar danayi saina ganshi yana........" To kafin
ya iyar sai suka farajin halbin kibau. Ai kuwa cikin sauri suka
mike. Shi kuwa safyan kafin ya gyara sai yaji saukar kibiya a
bayansa. Anan yayi ihu ya fadi yana fizge fizge saboda zafin da
yakeji. Najib ne ya dauko shi daga nan sai suka cigaba da
gudun. Sai dai najib shine baya saboda daukar dayawa safyan.
A wannan lokaci sun san cewa da an kamasu to sunansu
gawa. Saboda haka suka takarkare wurin kariyar kansu.
PAGE 18
Sai da sukayi gudu iya ransu kafin su kawo wani wuri mai
ramuka da kwazazzabai. To anan suka boye a cikin wani
kungurmin rame. Sun dade a wurin ko matsi basayi kafin su
fara ganin wasu halittu suna isowa a wurin. Kai da gani kasan
su ake nema. Tufafin jikinsu bakake ne sai wasu muggan
makamai da suke rike dasu. Ba a ganin fuskarsu domin sun
rufeta da bakin kyalle. Abun mamaki kuma shine tafiyarsu
daban ce. Domin sunada mutukar sauri sai kace iska. Kai da
ganinsu dole ka girgiza saboda kasan a buge basa buguwa.
Anan su anisa suka sandare cikin rame ko shaida basa son yi
saboda tsoro. Sai da wadannan mutane suka zagaye wurin tsaf
basu gansu ba daga nan sai suka nufi wata hanya suka wuce.
To anan ne suka fito suna haki kamar ransu zai fita. Shi kuwa
najib a lokacin ya ajiye safyan a gefe sai zubar da hawaye
yake. Su anisa ne suka zo suna girgiza shi amma ko motsi
bayayi. A nan mamee taxo tana girgixa shi. " Haba safyan ka
tashi mana. Nasan ba zaka tafi ka barni ba. " A haka ta cigaba
da girgiza shi amma ina. Daga nan sai ruky ta tayar da ita
domin sun san cewa rai yayi halinsa. Mamee ta durkusa sai
zubar da hawaye take saboda rashin safyan.
" To yanzu haka zamu mutu kenan? Su waye wadanna
mutane? Kuma me yasa suke son kashemu. Gaskiya bazai
yiwu ba, ni yanzu sai na gano ko su waye tare da daukar
fansa." Anan mamee ta nufi hanyar da suka fito. Ai kuwa
mikawarta keda wuya sai ga wadannan mutanen sun fito. Su
anisa na kiranta amma ina ko jinsu batayi. A haka wadannan
mutane suka kamata suka wuce da ita. Su anisa kuwa na ganin
haka suka runtuma basa ko juyawa. A haka suka ci gaba da
gudu cikin bakin ciki domin sun san cewa mamee sai dai Allah
yaji kanta. Yanzu sun koma su uku kenan: Anisa, ruky da najib.
Shi kuwa hamir ba duriyarsa tunda ya fita. Abunda basu sani
ba shine wai yasan halin da suke ciki kuwa. To idan ya sani ina
yake kuma me ya fitayi. Gashi dama safyan ne yaga wani abu
a tattare dashi kuma gashi ya kare balantana ya fada musu
abunda ya gani.
PAGE 19
A haka suka cigaba da gudu har saida suka iso wani katafaren
gida. To anan suka fara jin dadin domin a ganinsu zasu samu
taimako. Da karfi suka shigo gidan suna dube dube. Basuga
kowa ba inbanda wata mace kan kujera sai dubansu take.
Anan ta musu sannu da zuwa tare da zaunar dasu kan kujeru.
" Ki taimaka mana. Wasu ne keson kashemu gashi bamusan ko
su waye bane. Idan kinada waya ki bamu akwai wadanda zamu
kira." Najib ne ya fadi cikin sheshsheka. Anan matar ta kalleshi
cikin murmushi.
" Da ace zan iya taimaka muku..." Daga nan sai matar ta tashi
tsaye. Taku uku tayi daga nan saita juyo. Ai kuwa juyawarta
keda wuya sai sukaga ta rikida. Anan gaban anisa ya fadi
domin ba kowa ceba in banda kawarta zee. " Ke a ganinki zaki
iya tsere mana ko? To duk inda kikaje muna ganinki." Xee ta
fada tana kallon anisa. " Dama na fada miki cewa keda kanki
zaki kawo kanki har wurinmu. Ai kuwa gashi kinzo da kanki."
Anan tayi shiru saboda shigowar wani a gidan. Su anisa na
juyawa sai sukayi arba da hamir. Ba yadda basuyi ba domin su
tashi daga saman kujerar da suka zauna amma sun kasa. Zee
na ganin haka sai ta fashe da dariya." Ai kubar wahalar da
kanku domin idan zaku shekara a nan bazaku iya tserewa ba
sai yanda naso nayi daku." Daga nan saita kalli hamir. " Da
kyau hamir aikinka na kyau. Zo matso kusa gareni." Anan suka
fara sumbatar juna suna kyakkyata dariyar mugunta. Daga nan
sai hamir yazo kusa ga ruky. Wata yar karamar yuka ya dauko
daga nan sai ya fara dasasawa a makwogoronta. Ai kuwa nan
take jini ya baltsu. Shi da zee suka tara bakinsu sai sha suke.
Su kuwa anisa da najib sai zub da hawaye suke saboda
tausyawa ga yar uwarsu. Hardai najib yayi mutukar bakin ciki
domin shine ke sonta. " Nan bada jimawa ba za a gabatar daku
ga uban gidanmu." Inji zee. Daga nan sai aka kaisu wani daki
mai duhu aka kulle.
Anisa ce ta shiga cikin tunani, ko wane uban gida zee take
magana akai. Kada dai ace wannan macijin data gani an zana
a hannunta.
PAGE 20
Ba a wani dadewa ba saiga xee ta shigo dakin tare da wasu
samudawa. Da ganinsu anisa ta ganesu. Wato sune wadanda
suke binsu a lokacin da suke gudu cikin daji. To anan aka fito
dasu cikin gidan. Wadannan mutanen dake binsu sun tsayu sai
buga ganguna sukeyi. Anan aka ja su anisa sai tafiya akeyi
dasu kamar an koro shanu. Sai da akayi tafiya mai nisa sannan
aka kawo wani wuri cikin dokar daji. Anan aka kunna wuta. Su
kuma wadannan masu bakaken kayan sai suka fara zagayen
wutar suna fadin wasu kalamai da su anisa basajin abunda
suke fadi. Wasu kuma sai kada ganguna sukeyi.
Ana cikin hakane sai ga wani irin zabgegen maciji ya ratso ta
cikin jama a. Shi dai wannan maciji abun kallo ne domin
girmansa jikinsa yafi daki. Ai kuwa suna ganinsa sai suka
durkusa saboda girmamawa. Shi kuwa macijin sai wangame
baki yake tamkar an bude kofa. Anisa na ganin wannan maciji
sai ta tuno da zanen data gani a hannun zee. Bako shakka
wannan macijin ne suka zana.
Wasu samudawan ne suka janyo anisa da karfin tsiya. Anan
najib ya kura musu idanu yaga me zasuyi. Ai kuwa sai yaga sun
dukar da ita gaban macijin. Daga nan sai hamir ya dauko wani
takobi da nufin datse mata kai. To kafin ya iyar da nufinsa ne
najib yayi kukan kura ya zubar da mutanen dake rike dashi.
Wani naushi ne yama hamir sai da ya fadi rikicaa. Daga nan sai
ya tallabota da nufin su gudu. Kawai sai anisa taga jini na fita a
bakinsa. Anan ya saketa. Dubawar da anisa zatayi haka sai
taga ashe zee ce ta sokama najib takobi har sai da ta bullo ta
cikinsa. " Kada ki damu dani ki gudu. Ki gudu nace." Inji najib.
Anan najib ya fadi yana nishi dakyar. Ita kuwa anisa sai taci na
kare ai kuwa sauran jama ar sai suka rufa mata baya da nufin
su kasheta.
Daganan sai aka fara tsere. A wannan lokaci anisa da karfin
tsiya take gudu domin tasan da sun kamata to sunanta gawa.
Ba yadda basu yiba domin ganin sun cimmata amma taki. A
duk lokacin data waiga ta gansu sai ta kara kaimin gudu. Haka
ta cigaba da gudun har tabar dajin ta kawo bakin titi. Anan ta
hau titi ita kadai a cikin wannan dare sai gudu take. Gashi ba
mota ba kowa balantana ta koma gida. A haka ta cigaba da
gudu saman titi har saida wasu yan sanda masu patrol suka
risketa. Anan ta fada musu abunda ya faru. To bayan yan
sandan sunje wurin sai sukaga gidan ya bace bat ba a ganinsa.
Saboda haka dole suka dawo. Daga nan kuma sai suka taimaki
anisa tare da mayar da ita har gida........
PAGE 21
Dare mahutar bawa, idan lokacin ka yayi dole a tareka, dare
mahutar bawa, idan kazo dolene komi ya samu akasi. Dare
mahutar bawa, duk wanda bai zauna wuri daya ba to bayada
banbanci da matacce.
Wannan magana haka take ba tantama, nasan yanzu ka samu
nagartacciyar fahimta akan abunda nake nufi. Bako shakka
nayi dana sanin kin bin umarnin iyayena. Domin da ace nayi
abunda sukeso da irin hakan bata faruba. Ni kadaice na dawo
cikin mu shidda, sauran kuwa duk sun kare. Zee da hamir suna
raye. Saboda haka nasan wannan gwagwarmaya bata kareba.
Maita gaskiya ce. Kuma koina akan samu mayyu. Sai dai har
yanxu ba a san mafarinta ba, da kuma yadda ake gane masu
fama da ita ba
Ba kowane abokine na kwarai ba. Wani kanyi abota dakai
domin wani abu da yake bukata a wurinka. Wani kuma kanyi
abota dakai domin ya juya maka ra ayi. A duk lokacin dana
tuno rayuwar danayi a baya nakan yi nadama sosai domin
nasan tabargazar dana afka a baya. Bako shakka zama da
madaukin kanwa shi kasa gira tayi toho. Wannan magana haka
take. Domin mutum abun tsoro ne. Indai kana tare da mai
mugun hali to fa dakyar bai shafa ma ba. Ni na tabbatar da
wannan domin naga an shafa min. Ban taba tsammanin cewa
halina zai sauya ba. Amma sai gashi ina cikin wadanda ake
kwatance dasu akan aikata barna.
Nayi kuka sosai kuma nayi bakin ciki sosai amma ba yadda na
iya dole na hakura. Na rasa abokaina wadanda bazan taba
mantawa dasu ba. A hakan nayi nadama tare da yin abunda ya
kamata. Iyayena basu gujeni ba. Haka sauran kannena. Sun
rungume ni tare da share min hawaye. Babban abunda ke
damuna shine makiyana suna raye. Wato hamir da zee. Kuma
nasan kul a jima kul a dade sai sunyi kokarin yin wani abu a
gareni. Saboda haka saina zurfafa domin in gano hanyar da
zan kare kaina daga sharrin su. A yanxu na gama bincikena
kuma nasan abunda zanyi. Wannan farawa ce ba karshe ba to
amma me zai faru a karshen?
The story continues on the second version of the new
episode.......


TAFIYAR DARE 
MAYYUN JINI
AUTHOR: ABDUL KING ARTICLE
EPISODE 2
PAGE 22
A cikin duhun daren wata rana, wata mota kirar sienna ta
samu kanta a saman titi sai tafka wani namijin gudu take.
Mutum biyar na a cikin motar sai ihu suke saboda music dake
tashi duk ya cika musu kunne. Basu damu da hakan ba sai
faman nishadi suke suna fira.
Aswad da namil sune gaba. Sai nabilat,humairat, saudat a
baya. Kai da gani kasan sun yi tafiya mai nisa. Kuma yanzu
hakan suna kan hanyarsu ta zuwa wani gari domin yin al
amurran yau da kullum.
" Hahhh.Wai yaushe zamu isa ne?" Saudat ta fada cikin dariya.
" Hmmn, yan mata kenan. Ai inaga ko yanzu akwai awa goma
a gabanmu." Aswad ya bata amsa.
Anan sauran suka kyalkyace da dariya. " Haba aswad ai
wannan ba girmanka bane. Kana abu sai kace faisal." Nabilat
ta fada cikin wasa.
" Wai dama ke bakisan halinsa ba. Ai wannan kurun da kike
gani ba makaryaci kamarsa." Namil ya fada bayan ya dan doki
aswad a ciki.
" Yanzu ke dear har kin yarda da abunda yace. Ki rabu dashi
kawai ni zanyi maganinsa." Cewar aswad bayan ya rike sitari
gam saboda shigowar wasu ramukka. Hanyar ba kyau motar
sai gwaram gwaram takeyi. To bayan sun wuce gadar ne sai
fira ta koma sabuwa. Domin a wannan lokaci saida kowa ya
fadi albarkacin bakinsa harda humairat wadda ke latse latsen
waya. Suna cikin firar ne sai mota ta fara rage gudu.
" Ya naga haka wai lafiya kuwa?" Namil ya tambaya.
" Bazance mai neba domin munyi full tank tun a gida. " Aswad
ya fada yana dube dube.
Can sai motar ta tsaya cak wuri daya. Sa ar da suka samu
shine sunyi parking me kyau a gefen titi. To anan suka fito
cikin mamaki abunda yasa motarsu ta tsaya.
" To yanzu meye abunyi kenan?" Saudat ta tambaya.
" Kada ku damu bari na kara gwadawa ko zamu dace." Inji
Aswad. Anan ya shiga motar ba yadda bai yiba amma taki
tashi. Anan namil ya taimaka masa suka bincike motar tsaf
komi dai dai amma kuma taki tashi.
PAGE 23
" Amma fa wannan abu daban mamaki to wai meke faruwa da
motar nan ne. Gashi kuma harda full tank akayi." Nabilat ta
fada cikin rashin jin dadi
" Ai kedai bari. Ni yanzu haka wani abu nakeji. Mu kadai cikin
dokar daji sai kace mayyu." Humairat ta fada tana kalle kalle.
Ita kuwa saudat bata damu ba. Wayarta ma ta dauko wai
hotuna zatayi. " Kuzo muyi pic mana." Ta fada cikin yanga.
" Pic kuma? Lalle saudat kin haukace, ke yanzu bakya ganin
halin da muke ciki har kina maganar hoto." Namil ya fada cikin
takaici.
" Kai kuwa miye ruwanka a ciki. Ai ba da kai nake magana ba,
zaka iya bari sai idan na ambace ka." Saudat ta rama.
" E to zagarni tunda na fada miki gaskiya." Cewar namil.
" Aiko ban zageka ba kasan abunda kayi bai daceba. Shi yasa
akeson mutum yayi tunani kafin yayi magana. Mtssss. Aikin
banza kawai." Saudat ta fada cikin takaici.
Shi kuwa namil sai ya kyaleta bai tanka ba. Anan suka cigaba
da gyaran mota shida aswad ko zasu dace amma ina ba
abunda ya faru.
" Ni inaga me zai hana mu shiga cikin wannan dajin wata kila
ko zamu iya cimma gari idan yaso sai mu kira bakanike yazo
ya duba." Inji nabilat.
" Wannan tunani ne mai kyau. Inaga sai ku jiramu nan. Ni da
namil sai muje." Inji aswad.
" Aa, bazaku tafi ku barmu a cikin wannan daji mai ban tsoro
ba. To amma me zai hana muje tare.?" Inji saudat.
" To yayi ba matsala muje din." Inji aswad.
Anan suka raba titi suka shiga cikin dajin mai cike da dogayen
itatuwa sai furanni koina. Aswad da saudat su kadaine keda
torch-light. Daji ne iya daji mai ban tsoro. Koina ka duba sai
itace. A kasa kuwa ciyayi ne masu sarkako. Aswad shine
jagoran tafiyar sai namil a gefensa. Su kuwa yan matan sai
binsu suke kowace jiki na karkarwa kamar ace kyat su ruga.
PAGE 24
" Wai kuna ganin zamu iya cimma gari anan kuwa? Naga tafiya
muke amma ko alamar gona babu. Koina sai itace da
ramukka." Inji aswad.
" Gaskiya nima fa abunda nake gani kenan. Ai yanxu inaga
kamar munyi minti talatin muna tafiya ko." Cewar saudat.
" Miye minti talatin? Ai munfi. Mun dade fa a wurinnan."
Nabilat ta bata amsa.
" Ke dubi gabanki." Humairat ta tsawatar.
Ita kuwa saudat bata jiba sai firarta take. Ai kuwa kafin
kaceme sai tayi tuntube da wani kututturen icce. Sai da tayi yar
karamar kara kafin ta juya da nufin faduwa. Shi kuwa namil da
jin ihunta sai yayi sauri ya juyo. To kafin ta fadin ne yayi saurin
rikota.Anan ya tallabota har saida ta mike tsaye. " Wai,na kuru.
Nafa gode dan uwa." Cewar saudat.
" Kada ki damu saudat ba kome." Inji namil.
Anan saudat ta kalli humairat da nabilat. " Ku kuma da kuke
tumaki kuna ganin zan fadi amma a cikinku ba wadda zata iya
taimaka min." Injita.
" To miye ruwanmu a ciki. Ai naso ace kin fadi kin karkarye
muga yadda zakiyi." Cewar humairat.
" Iyeee. Ni ko?" Saudat ta tambaya.
" To idan akace kedin me zakiyi?" Nabilat ta fadi cikin wasa.
" Yanxu dai ya isa ko kuwa sai naci uban mutum ne?" Saudat ta
hasko musu fitila.
" Ahayye. Rassss." Tare suka fadi nabilat da humairat. Daga
nan sai suka taba hannu suna dariya.
" Shegiya ke har wani karfi ne dake. Dubarta. Yar ramamma ba
jiki sai tsangwama." Cewar humairat bayan ta kulle idonta
saboda hasken fitilar da aka hasko mata.
" Ji yadda take tafiya burtum burtum sai kace agwagwa. Wai
damu zatayi fada." Inji nabilat.
Anan dai sukayita tsangwamar saudat tun tana iya ramawa har
saida tayi shiru saboda abun yayi yawa. Su kuwa su aswad
saurare kawai suke suna dariya.
PAGE 25
Saboda wannan fira da suke sai da sukayi tafiya mai nisa ba
tare da sun sani ba. Duk da kasancewar dajin mai tsananin
duhu ne amma haka suke tafiya sai kace ba mutane ba. To
suna cikin tafiyar ne sai fitillun su suka fara billin bilin. Wato su
kawo su dauke. A wannan lokaci kuma suka fara jiyo ihun
wasu daga can nesa. Ai kuwa daga jin haka sai hankalinsu ya
tashi. Anan suka fara gudu domin ganin ko su waye. Sai da
sukayi gudu mai dan nisa kafin su kawo inda abun yake. To
anan suka labe bayan itatuwa suna ganin abunda ke wakana.
Wasu mutane ne masu kirar samudawa sanye da bakaken
kaya. Ba a ganin fuskarsu domin sun rufeta da bakin kyalle.
Kowanensu ya rike kwari da baka tare da sauran makamai
masu ban tsoro na dangin takubba. Wasu mutane ne suka
kamo su biyu mace da namiji sai ihu suke. A gaban idonsu
wadannan samudawan suka kashe macen da namijin. Daga
nan kuma sai suka ja gangar jikinsu suka wuce da ita wani
wuri. Bayan wucewar su keda wuya sai su aswad suka fito
daga maboyarsu a tsorace.
" Bako shakka dole mu bar wannan dajin. Domin wadannan
mutane da muka gani na taba jin labarinsu da dadewa. Sai
gashi kuma kaddara tasa munxo wurinsu. Kamar yadda naji
ance suna...."
To kafin nabilat ta iyar sai sukaji ihu a bayansu. To anan sukayi
cirko cirko suna tunanin abunyi. Ai kuwa sai ga wata mata a
guje tazo wurinsu. " Don Allah ku taimakeni. Kasheni zasuyi.
Gasunan tafe." Haka matar ke fadi tana kuka. To anan sukazo
wurinta suna lallashinta tare da tambayarta abunda ke faruwa.
Amma saboda tsoron daya dabaibayeta sai ta kasa bayani
iyaka dai abunda take fadi shine su taimaketa. Wannan abu ya
mutukar tayarwa su aswad hankali domin sai suka rasa abunyi.
" Gaskiya baxan iya zama a wannan wuri ba. Ni inaga kawai
mu koma bakin titi inda motarmu yafi mana sauki." Humairat
ta fadi cikin tsoro. Ai kuwa take ta nufi hanyar da suka fito wai
ta tafiyarta. Cikin sauri aswad ya jawo hannunta.
PAGE 26
" Wai kinada hankali kuwa? Hanyar da muka fito itace wannan
matar ta fito kuma tace sun biyota ne don su kasheta. To idan
kikaje kika tarar dasu fa. Ni inaga kawai mu manta da komi
muyita gudu har mu kure dajin mu gani ko zamu samu
taimako." Inji aswad.
" To ai ko yanzu bamu tsira ba. Domin hanyar da kakeso mubi
itace mukaga sun shiga tare da gawawwakin mace da namijin
da suka kashe." Inji Humairat.
To anan suka rude suka rasa abunyi. Gaba kura baya hayaki.
Wato idan sukaje gaba basu tsira domin zasu iya haduwa dasu
haka ma idan suka juya baya inda suka fito shima basu tsira
ba.
" Ni inaga kawai mubi shawarar humairat cewa mu koma inda
muka fito wurin motarmu. Inaga zamu iya bacci a can kafin
gobe da safe sai musan abunyi." Inji namil.
" Wannan gaskiya ne ina bayanka." Inji nabilat.
" Nima haka." Saudat ta fada
Daga nan sai suka amince cewa xasu koma ta hanyar da suka
fito saboda gudun kada su hadu da wadannn miyagu masu
kashe mutane. To anan suka juya tare suna tafiya da sauri cikin
tsoro ba mai yarda a barshi baya. Ita kuwa wannan matar da
suka gani sai tayi shiru ta cigaba da binsu. Ai kuwa basuyi wani
nisa ba suka farajin hargowa. Wasu kibiyoyi ne aka fara sako
musu cikin rashin tsammani. Ai kuwa sai kibiya ta shiga
wannan matar bakuwa. Anan tayi kara ta fadi. Su kuwa saura
suka runtuma baya a guje. Aswad kawaine ya tsaya taimakonta
shima da yaga abun yafi karfinsa dole yayi ta kansa. Gudu yake
suna binsa sai halbi kakeji ta koina. Yana cikin gudun ne yaji
karar matar. Anan yasa a ransa cewa sun kasheta. A haka
aswad yayi gudu iya karfinsa. Sai dakyar ya cimma abokansa.
To daga nan ne suka tsaya suna haki bayan sunji cewa kamar
an daina binsu.
" Wai yanzu meye abunyi kenan. Ku a ganinku haka zamu
cigaba da gudu da mun gansu kenan? Gaskiya inaga ya kamat
muyi fito na fito domin musan abunda suke nema a gunmu."
Cewar saudat.
" Bama shiba. Ya kamata musan ko su waye, kuma me yasa
suke kashe mutane, kuma idan sun kashe to me sukeyi da
sauran gangan jiki." Cewar namil.
PAGE 27
" Duk kunada gaskiya, amma maganar fito na fito dasu bata
tasoba domin sun fimu kome, da farko dai sun fimu yawa, ga
kuma makamai, to ya za ayi mu yaki wadannan. Ni a ganina
kawai mu cigaba da gudu har zuwa karshen wannan daji wata
kila ma samu taimako." Inji aswad.
" Da gaskiyarka aswad, wannan itace kawai mafita." Cewar
humairat.
" To amma yanzu me zai hana mu samu wuri a nan muyi bacci
zuwa gobe sai musan tayi." Cewar nabilat.
" Hmm, to ke in banda abunki ai yanzu ba wanda zai iya bacci
a cikinmu saboda wannan tashin hankali da muke ciki." Inji
aswad. " Inaga dai mu daure mu cigaba da gudun kafin su iso
nan." Ya kara fada.
Duk da kasancewarsu sun gaji, amma haka suka daure suna
tafiya da sauri don gudun wadannan mugaye masu farautar
mutane. Cikin wannan tafiya ne wani dan reshen bushiya ya
fado duum. Ai kuwa nan saudat ta ci taya sai da suka tarota
domin ita a zatonta sune suka kawo musu harin ba zata.
" Wayyo kafata, ni gaskiya na fara gajiya." Cewar nabilat bayan
ta zauna.
" Wai me kike nufi ne, ki tashi mana mu cigaba." Inji aswad.
" Kai mu hutu zamuyi, idan kana iyawa to ka tafi kai dai." Inji
humairta bayan itama ta zauna.
Ai kuwa nan suka yi zamansu suna nishi dakyar. Suna cikin
hutun ne bacci ya sacesu amma banda aswad domin yana
nesa dasu. Saidai duk abunda ke faruwa yana kallo. Kai da
ganin fuskarsa kasan yana cikin rashin jin dadi. To anan ya
tashi da nufin tayar dasu sai dai abunda ke damunsa shine
kishin dake busar da makwogoronsa. To anan ya fara shawara
ko ya tayar dasu ko kuwa ya fara samo ruwan da zaisha. Can
sai yaji kishin ya damesa. Saboda haka baiyi wata wata ba sai
ya fara bincike ko zai samu tafki a wurin. Sai da yayi tafiya mai
dan nisa kafin ya cimma magudanar ruwa masu tafiya. Anan
ya duka ya kwankwada har saida yayi hamdala. Mikewarsa
keda wuya sai ya fara jiyo ihun wasu. Ai kuwa a guje ya juya
domin ganin ko su waye.
PAGE 28
Cikin kankanin lokaci ya isa wurin daya bar su namil na bacci.
A mamakinsa baiga kowa ba. Anan ya tsorata, to kada dai ace
wadannan miyagun sun zo sun wuce dasu. Anan ya fara kiran
sunayensu daya bayan daya amma ba wanda ya amsa. Can
kuma sai ya cigaba da jin ihun. Daga nan ya runtuma a guje a
inda yakejin sautin na fitowa. Yana cikin gudun ne sai ya tarar
da wasu gungun miyagu sun farauto wasu mutane sai jansu
suke da kasa. Anan ya fara tafiya sannu sannu domin ganarma
idonsa. Kicibis sai yayi arba dasu namil. Wai ashe wannan ihu
da yakeji sune bayan da aka rutsa dasu suna bacci. To anan
aswad ya rasa abunda ke masa dadi. A buge dai wadannan
miyagu basu buguwa balantana shi ko makami bayada.
Cikin bakin ciki da rashin jin dadi ya cigaba da tafiyar sanda
yana binsu a hankali domin ganin inda zasu kaisu. Su kuwa su
namil sai faman kururuwa suke suna neman taimako. Haka
wadannn miyagu suka cigaba da jansu a kasa har saida suka
riski wani makeken gidan sama mai ban tsoro. Anan aswad ya
labe bayan itace har saida suka gama shiga gidan. Daga nan
sai ya lababo domin bude kofar amma gam ya kasa. Ba yadda
bai yi ba amma daya tura sai yaji kamar kara rufeta ake. A
haka ya hakura ya fara zagayen gidan ko zai samu hanyar
shiga. Ai kuwa cikin sa a ya dace domin wata katanyar
makwarara ce ya hango manne a kasan gina. Ba abunda ke
fitowa ciki in banda wani abu jawur. A haka ya kurawa
makwararar idanu yana tunanin ko menene ke fitowa ciki
jawur. Daga karshe dai sai ya fara tunanin cewa jini ne domin
jan yayi yawa.
Cikin makwararar ya shiga bayan ya durkusa. A haka ya cigaba
da tafiya a durkushe yana tsallake sassan jikin mutane. Wasu
har sun fara wari saboda dadewa. Ai kuwa sai banko jini akeyi
a ciki. Kafin kaceme kayansa sun koma jawur. Haka dai aswad
ya daure ya cigaba da tafiya har saida ya dau lokaci kafin ya
kawo karshen makwararar.
PAGE 29
Daga nan sai ya diro a cikin wani wangamemen daki. Ba kome
a ciki dakin in banda gawawwaki. Anan ya fara dube dube.
Wasu gawawwakin sun bushe. Wasu kuma danyu ne da gani
kasan ba a dade da kawasu ba. Wasu kuma a can gefe zigidir
ba mai ko kyalle a jiki. An hade maza da mata a wuri daya ba
kyaun gani. A haka dai aswad ya cigaba da kallon dakin yana
kallon abubuwan ban mamaki. Sai kuma sassan jikin mutane
dake sarkafe a gina. Irin su kai, hannaye, kafafuwa kai harda
cinyoyi. Sai kuma wani katon gatari a kusa ga makwararar. Kai
da gani kasan dashi ake ma mutane kisan gilla. Haka aswad ya
karema dakin kallo tsaf daga nan kuma sai ya nufi kofa da
nufin fita. Murda ganbun yayi a hankali da nufin budewa amma
sai yaga ko alamar girgizawa bai yi ba. Daga nan sai yasa
karfinsa amma duk a banza. Da dai yaga ganbun na shirin bata
masa lokaci sai ya dauko gatarin dake rataye saman gina.
Cikin karfi ya fara dibar ganbun ba sassauci. Ai kuwa yana cikin
hakane sai yaji tahowar wasu. Anan yayi jifa da gatarin. Daga
nan ya tube kayansa ya koma zindir. Cikin sauri ya shafama
kansa jini sannan yayi kwance cikin gawawwaki sai kace
matacce. Yana nan kwance ne sai yaga wasu mutum biyu sun
shigo mace dana namiji sun ajiye wasu gawawwaki. Daga nan
sai suka fara wata magana. To a mamakinsa ba hausa ce
sukeba. Wani yarene suke wanda bayaji. Anan ya kurawa
namijin idanu kamar ya sansa. Da karfi yayi magana. " Hamir!"
Ai kuwa sai namijin ya juyo inda yake kwance. To anan
hankalin aswad ya tashi don kada asirinsa ya tonu. Ita kuwa
maccen sai ta hanashi domin a ganinta ba kowa a wurin.
Saboda haka yaji dai kamar an kirasa ne. Daga nan sai namijin
ya fasa zuwa wurin gawawwakin. Iyaka ya bincika makwarara
daga nan suka tafiyarsu.
Shi kuwa aswad cikin sauri ya fito, anan yasa kayansa ya fita
dakin cike da mamaki wannan abu. Bako shakka yasan wannan
namijin. Abokinsa ne kuma dan makarantarsu. To amma kuma
ya akayi ya shigo wannan kungiya? Wannan itace amsar da
aswad ya kasa ba kansa.
PAGE 30
Tafiya yakeyi cikin tsoro da fargaba. Sai juye juye yakeyi domin
a ganinsa ana iya kawo masa hari ta ko ina. Gidan ya kasance
da lunguna masu ban tsoro. Haka dai ya cigaba da tafiya sako
sako kwana kwana amma baiga abokansa ba. Wannan abu ya
mutukar tayar masa da hankali wanda daga karshe sai ya fara
tunanin ko an kashesu. Yana cikin tafiyar ne sai yaji ana
magana cikin wani daki. To anan ya labe yana lekon ko su
waye a ciki. Idansa ya kafa a huduwar dake ganbun. Anan ya
ga abokinsa hamir da wannan matar da suka shigo dakin
gawawwaki tare. Wasu bokitayya ne cike da jini. Su kuwa su
hamir din sun tube kayansu sai wanka suke da jinin. Yana cikin
lekensu ne sai matar ta juyo. Anan sukayi ido hudu da aswad.
Ai kuwa bai yi wata wata ba ya watsa a guje.
Yana cikin gudun ne yaci karo da wata mata, a nan ya fadi
saida kansa ya bugi gina. Da sauri ya mike domin ganin ko
wacece. Ai kuwa yana ganinta sai ya ganeta domin itama yar
makarantarsu ce tare sukayi jami a. " Laaaa. Zee me kikeyi
anan? Kema sun kamoki ne?" Anan ya fadi saboda rashin
karfin jiki. " Ki taimake ni zee. Zasu kasheni."
Anan ita kuwa zee din ta tallaboshi. " Haba aswad ya kana
wannan magana. Kayi shiru kaji ba wanda zai taba min kai."
Anan ta rikoshi suka fara tafiya har saida suka iso wani daki.
Daga nan ta taimaka masa ta azashi saman wata kujera. A
wannan lokaci jikin aswad ba karfi ko kadan saboda wahalar
daya sha. Jikinsa duk tambo ne na jimuwar da yayi. Anan zee
ta zauna kusa dashi tana tabin fuskarsa. Daga nan kuma saita
rungumeshi cikin murmushi. Kasancewar aswad cikin rauni ko
kallonta baya iya yi. Hannu tasa da nufin kwance masa bell.
Sai dakyar ya samu ya tsayar da ita.
" Haba aswad ya kana haka. Nasan kafi kowa son wannan abu
da zamuyi." Inji zee.
" E amma banda yanzu." Cewar aswad.
Daga nan saita mike tsaye. Rigarta ta debe ta koma daga ita
sai wata yar shame wadda ta matseta sosai kana ganin kome
nata. Anan tayi tafiya ta rangwada domin ya gani. " Ina fatan
dai zakaso abunda ka gani. Kome na nan yadda ka barshi ba
abunda ya canza." Zee ta fada tana murmushi.
PAGE 31
Can sai ga hamir ya shigo dakin shi kadai. Ai kuwa aswad na
ganinsa sai ya mike yana tangadi. " Me ya kawoka nan. Macuci
azzalumi. Ashe dama kai dan kungiya ne." Haka aswad ke fadi
a lokacin daya tunkari hamir cikin fushi.
" Haba aswad ya kana fadar haka, ka kwantar da hankalinka ba
abunda zai faru." Anan ta jawo aswad saman kujerarsa.
Daga nan saita yiwa hamir wani signal da idanu. Ai kuwa yana
ganin haka sai ya fita. " Waike in tambayeki, hala me kikeyi a
cikin wannan gida na marassa imani? Aswad ya tambaya.
" Na marassa imani fa kace?" Cewar zee.
" E mana, ai naga abunda na gani. Kuma nasan cewa kema a
cikinsu ki...." To kafin ya iyar ne zee ta masa wani mugun bugu
fuska. A nan ya zube kasa sumamme. Daga nan saita jawoshi
ta kaishi wani karamin daki ta kulle.
Bayan kamar minti ashirin, sai ga zee ta dawo tare da hamir.
Anan suka bude dakin da aka kulle aswad amma a mamakinsu
ba kowa ciki. A nan suka fara dube dube amma ko alamunsa
basu gani ba. Juyowa sukayi da nufin su tafi. Ai kuwa
juyowarsu keda wuya sukuyi arba dashi a tsaye. Anan ya jawo
kawunansu ya buga da juna. Ai kuwa nan suka fadi sumammu
jini na fita ta hancinsu. Daga nan sai ya fita dakin a guje. A nan
ya nufi wani lungu mai tsananin duhu. Gashi bayada fitila
domin ya dade da jifa da ita tun a lokacin da aka biyosu.
Saboda haka sai ya fara tafiya a hankali don gudun kada yaci
karo da wani abu. Fitillun dake gidan basaci sosai. Wasu kuma
sun lalace sai dai su kawo su dauke. Haka dai aswad ya ci
gaba da tafiya cikin duhu yana lalube. Can sai ya farajin nishin
wani. A nan ya nufi inda yakejin sautin na fitowa. Ai kuwa yana
cikin tafiyar ne sai yaji gudun wasu samudawa sun nufo wurin
da yake. Cikin sauri ya boye kusa ga ganbun wani daki. To
bayan sun wucene sai ya shiga dakin dama a cikine yakejin
nishin na fitowa.
PAGE 32
Ai kuwa shigarsa keda wuya ya like hancinsa da hannuwa
saboda tsananin doyin da yakeji. Anan ya fara dube dube
amma baiga kowaba. Kuma baisan ko menene ke wari ba. Can
sai ya hango wani daki. To anan ya nufi ciki. Ai kuwa shigarsa
keda wuya sai ya tarar da kwarangwal na mutane ( skeleton)
tare da wasu gawawwaki duk sun rube. Dakyar ya samu ya
shiga har kuryar dakin. Ai kuwa shigarsa keda wuya sai ya tarar
da nabilat kwance tana nishi. Sun tube mata kaya ta koma
zigidir. Sai kuma bayanta duk an zaneshi da yuka. Anan aswad
yazo kusa da ita cikin tausayawa. Tallabota yayi yana
tambayarta inda akaje su namil amma bata iya magana.
Goyata yayi ya fito da ita dakin. Daga nan sai ya cigaba da
gudu yana bincikar inda aka aje sauran abokansa. To yana
cikin gudu ne sai ya hango wasu samudawa a gabansa.
Kowanensu sanye da bakaken kaya. Bako shakka kai da ganin
wadannan mutane dole ka girgiza domin tafiyarsu ma ta daban
ce. Anan ya juya baya da nufin tserewa kuma sai yaga wasu
irinsu.
Sun rike kwari da baka kai da gani kasan basada imani. Aswad
a tsorace yake domin yasan dasun iso gunsa to sunansa
gawa. Kawai sai ya hango wani daki a kusa dashi. Ai kuwa a
guje ya kutsa kai ciki. To kafin ya shiga ne wani daga cikin
miyagun ya halbo kibiya. Ai kuwa kai tsaye ta shiga bayan
nabilat. Sai da ta danyi wata kara daganan bata kara cewa
komi ba. To bayan ya shiga dakin ne sai yaga ashe hanya ce
doguwa irin wadda ya baro. Cikin sauri ya kutsa kai ciki sai
faman gudu yake. To bayan yayi tafiya mai nisa sai ya tsaya
domin yaga halin da nabilat take ciki. Anan yaga ta sandare ko
motsi batayi. Girgizata ya farayi amma ina rai yayi halinsa.
Anan ya rungumeta yana kuka cikin bakin ciki ya rasa babbar
abokiya tun suna yara. Ya dade zaune kusa gareta yana
jimami. Bayan wani lokaci kuma sai ya tashi ya nufi hanyarsa
yana tafiya dakyar. Haka ya cigaba da tafiya yana tangadi sai
kace wanda yasha giya. A wannan lokaci kome nasa ciwo
yake. Yana cikin tafiyar ne ya fadi galabaice ba tare da sanin
inda yake ba.
PAGE 33
A haka aswad ya kasance cikin wannan hali na suma ba tare
da sanin inda yakeba. Sai da aka dau lokaci mai tsawo kafin
surutun wasu miyagu ya tadashi. Cikin sauri ya tashi firgigit.
Labewa yayi cikin wata kwana mai duhu. Bayan sun wuce ne
sai ya fito yana bin bayansu domin yaga inda zasu. A haka ya
cigaba da tafiya yana binsu. Idan yaga zasu jiyo sai ya boye
don kada su ganshi. Sai da sukayi tafiya mai nisa duk a cikin
gidan kafin su shigo wani irin makeken daki. Duk mutanen
dake cikin dakin a tsaye suke suna sanye da kaya jajjaye masu
ban tsoro. Wani mutum ne yayi tsaye a tsakiyarsu sai wata
magana yake da wani yare. Kasancewar aswad baya jin abunda
suke fadi sai ya boye a cikin labule. Dakin gaba daya an
zagayeshi da jan labule ta ko ina. A haka aswad ya natsu yana
kallonsu domin yaga abunda ke gudana.
Yana cikin kallon ne sai yaga mutumin ya daina magana.
Daganan sai wasu mutum biyu suka shigo da wani namiji a
daure. Saman wani benchi aka daureshi tamau. Daga nan sai
mutumin ya dauko wata yuka. A gaban idonsa aka yanke
wannan mutumi. Yukace aka darara masa a wuya kamar
yadda ake yankan rago. Cikin kankanin lokaci jini ya kama
kwarara kamar fanfo. Anan mutumin wanda da gani kasan
shine shugaba ya dauko wata tasa ya tara yadda jinin zai zuba
a ciki. Shi kuwa mutumin da aka yanke sai ya kama fizge fizge
sai da wasu suka rikeshi. To bayan jinin ya gama zuba ciki sai
shugaban ya dauki tasar ya kafa kai. Sai da yasha sannan yaba
na kusa gareshi. A haka aka fara zagaye da wannan tasar. Idan
wannan yasha yaba wannan har saida kowa yasha. Shi kuwa
na karshe dasha sai ya ajiye tasar a kusa ga shugaban.
Anan aswad ya lura cewa mutanen maxa da mata ne. Shi
kuwa shugaban sai ya nuni tasar da yatsansa. A nan ya fara
fadin wasu dalassammai na tsafi. Ba a wani jimawa ba sai
yaga innuwar mutumin da aka kashe ta fito cikin tasar. Anan
shugaban ya kama innuwar ya turata cikin wata kwalba. Daga
nan sai ya rufe ya ajiye ta wani wuri cikin dakin. Can kuma sai
aka shigo da wata yarinya zigidir. Anan aka azata saman
benchin da aka kashe wannan mutumin na farko.
PAGE 34
Bayan an daureta tamau sai shugaban ya tube kayansa ya
koma zigidir. Anan ya fuskanceta da nufin keta mata haddi. Shi
kuwa aswad da karfi ya dago kansa domin ganin ko wacece
wannan yarinyar. Ai kuwa yana dubawa sai yaga ba kowa ceba
in banda humairat. Jikinta duk jini ne kai da gani kasan ta
galabaita. Anan ya fara tunanin meye abunyi kafin wannan
mugun mutumi ya iyar da nufinsa akanta. Wasu samudawa ne
sanye da bakaken kaya ko fuskarsu ba a gani saboda sun
rufeta da bakkin kyalle. Rike suke da muggan makamai sai
kaida komo kawai suke a cikin dakin domin tabbatar da tsaro.
Hankalin aswad ya mutukar tashi domin yasan idan suka
ganshi to karyarsa ta kare. Haka ya cigaba da wasi wasi sai
daga baya dubara ta fado masa.
Cikin sauri ya fito daga maboyarsa ya kalli shugaban. " Ni zanyi
duk abunda kukeso indai kunyi alkawari bazaku taba wannan
yarinyar ba."
Anan mutanen dake cikin dakin suka tsura masa ido ko
kyaftawa basayi. Daga nan sai shugaban ya fara magana da
wani yare yana kallonsa. Haka ya cigaba da maganar har saida
aswad yayi zaton cewa kamar bayajin hausa. Mutum biyu daga
cikin samudawan ne suka rikoshi. Anan suka gurfanar dashi
gaban shugaban. Daga nan sai suka dauko wani benci suka
axa shi sama. Basu daureshi ba iyaka dai sunyi tsaye gabansa
sai maxurai suke. Bako shakka aswad yayi wautar bayyana
kansa ga wadannan miyagu. Sai daga bayane wannan tunani
ya shiga kwakwalwsarsa.
Shi kuwa shugaban kai tsaye ya nufi wurin humairta da nufin
biyan bukatarsa. Aswad yayi kokarin tashi domin ya hanashi
amma sai suka rikeshi. Daya ya dafe kafafunsa dayan kuma
hannaye. A gaban idonsa wannan mutumi ya taka bencin a
inda humairat take. Take ya jawota a jikinsa. Ba yadda aswad
bai yiba domin ya hana wannan abu amma ina sunfi karfinsa
domin sun rikeshi gam. Yana kallo ana warwasawa amma ba
yadda ya iya. A haka ya fara zub da hawaye na bakin ciki
domin humairat itace yarinyarsa tun kafin suyi wannan tafiyar.
Sai kuma nabilat wadda itace babbar kawarsa tun suna yara.
PAGE 35
Saida aka dau lokaci ana warwasawa da humairtat ba
kakkautawa. Su kuwa sauran yan kungiya sai kallo suke domin
abun gwanin ban shawa ne a wurinsu. Ita kuwa humairat tanaji
sai dai bazata iya komeba domin a daure take tamau. Bayan
an gama ne sai shugaban ya dauko wata karamar yuka. Anan
yasa aka juya masa ita. A saman bayanta ya fara wasu zane
zane. Saboda radadin da takeji dole ta fara ihun wuya. Anan
aswad ya gane cewa irin wannan zanen da aka yiwa humairat
bako shakka shine ya gani ga bayan nabilat kafin ta mutu. To
kenan indai hakane itama sai da shugaban yayi amfani da ita
kafin ayi mata wadannan zanukkan. Bayan an gama zane
bayan humairat da yuka sai aka dauketa aka wuce da ita wani
wuri. Shi kuwa aswad sai suka daureshi tamau da kaca aka
barshi a nan. Yana kallo kowa ya fita dakin ya barshi a nan.
Ba a wani jimawa ba saiga zee ta shigo dakin. Cikin rangwada
ta shigo cike da murmushi sai taku take dai dai. " Kai a ganinka
ka samu nasara ne ko?" Daga nan saita fara kewayensa tana
masa kallon keta.
" Kai kyakkyawa ne" Ta fada a lokacin data karo bakinta domin
ta sumbaceshi. Ai kuwa da karfi ya tofa mata yawu. A nan taja
da baya tare dayin dariya. Halshenta ta janyo tana lashe yawun
daya tofa mata. Bata damu ba ko kadan da kazantar dake
tattare dasu ba. Wata karamar yuka ta dauko tana lasawa a
halshenta. Anan aswad ya kura mata idanu domin yaga ko
meye take shirin yi. Kusa ga kafafuwansa ta tsaya. Anan ta fara
soka masa yukar a hankali ga ciki. Datasa sai ta fitar, a duk
lokacin data fito da yukar sai yayi kara saboda tsananin zogin
da yakeji. Kafin kaceme jini ya fara kwararowa ga kasa. Ita
kuwa sai murmushin keta takeyi. Tana cikin yi masa wannan
lahani sai wani ya shigo dakin. Tana ganinsa saita tsaya.
Daga nan sai suka fara wata magana da wani yare. Aswad naji
amma bai san abunda suke fada ba. Daga nan kuma sai tayi
jifa da yukar tabi mutumin. Aswad na kallo suka fita dakin. To
anan ne ya fara tunanin abunyi kafin ta dawo. Domin yasan
idan ta dawo to lahanin da zata yi masa sai ya ninka na daxun.
PAGE 36
Yukar data jefar a kusa gareshi take. Sai dai matsalar itace ko
motsin kirki baya iya yi balantana ya tabuka wani abu. A haka
dai ya daure yana mike hannayensa ko zai iya daukar yukar.
Dama an ce mai nema na tare da samu ai kuwa cikin sa a ya
dauko yukar. Dakyar ya lankwasa ya yanke kacar dake
hannunsa na hagu. To kafin ya yanke na daman ne saiga zee
ta dawo. Shi kuma yana ganinta cikin sauri ya boye yukar a
jikinsa. Daga shigowarta ta kura masa idanu ko kyaftawa
batayi. Ai kuwa batayi wata wata ba ta afka masa sai
sumbatarsa take. Shi kuwa aswad dama yasan abunda ya
tanadar mata saboda haka bai damu ba sai ya bata hadin kai.
Saida suka dade suna sumbatar juna amma bata gano cewa
ya yanke kacar da aka daureshi da ita ba. A haka abu yayi
kamari zee sai nishi take, shi kuwa ya dada kankaneta a jikinsa
kamar da gaske. Suna cikin yini ya fito da yukar ya soka mata
a kirji.
Anan ta fadi tana kururuwa shi kuwa jini ya fallatso. Da sauri ya
yanke dayar kacar ta hannunsa na dama. Daga nan ya kara
soka mata yukar a dayan kirjin. Sannan ya tallabota ya daura
saman bencin da aka daureshi. Anan ya daureta tamau sannan
yayi tafiyarsa ya barta tana ihu. A guje ya fita dakin don gudun
kada wasu su shigo. Yana cikin gudun ne sai ya lura cewa inda
yake takawa akwai digon jini. Saboda haka sai ya yanke
shawarar bin sawun jinin domin yaga mai shi. Ai kuwa haka ya
cigaba da tafiya guda guda har saida yakai wani daki. Shigarsa
dakin keda wuya sai yayi arba da humairat tana nishi daya
bayan daya. Cikin sauri yazo wurinta duk jikinta ya rine da jini.
Sunkuyawa yayi kusa gareta yana zub da hawayen tausayawa.
Tana ganinsa sai tayi murmushi duk da cewa cikin ciwo take.
A nan ta jawo kansa har saida jikinsa ya hade da nata. " Ka
kulamin da kanka. " Haka ta fadi cikin kunnensa daga nan bata
kara cewa kome ba. Iyaka dai yaji kalmar shahada wadda
itace kalmarta ta karshe. Aswad yayi kuka sosai domin a cikin
ransa ba yarinyar da yakeda muradin aure irin humairat. Sai
kuma gashi ta tafi ta barshi. A haka ya rungumeta a jikinsa
yana kuka cike da tausayawa. Saida ya dau lokaci a hakan
kafin ya saketa ya fita dakin.
PAGE 37
A haka aswad ya fito dakin cikin jimamin rasa humairat. Tafiya
yake dakyar kai da gani kasan ya gaji sosai. To anan ne ya fara
bidar hanyar fita daga gidan domin a ganinsa namil da saudat
sun mutu. Gidan ya kasance katon gaske sai kace gari. A haka
aswad yayi ta kalwade amma ya kasa gane hanyar fita. Duk
inda ka duba lungu ne cike da dakuna birjik. Sai dan neman
duhun daya mamaye gidan gaba daya. Ga fitilllu amma basaci
sosai saboda haka mutum ba ko ina yake gani ba. Kuma
kasancewar lokacin a cikin darene. To sai duhun ya karama
gidan ban tsoro. Shi kuwa aswad sai tafiyarsa yake yana
tuntube da gawawwakin mutane. To yana cikin tafiyarne sai
yaji gudun wani kamar an biyo shi. Anan ya labe domin yaga ko
su waye. Ai kuwa suna wucewa ta wurinsa sai yaga wadannan
samudawan ne masu bakaken kaya suka biyo wani da nufin
kasheshi.
A guje ya bisu da nufin yin taimako. Koda ya cimmusu sai ya
tarar sun kama mutumin zasu sareshi. To kafin su aiwatar da
nufinsu ne ya taresu da fada. Gawawwakin mutane ya rinka
dauka yana dukansu dashi. Shi ma mutumin na ganin haka sai
ya samu damar kubcewa. To anan aka fara bata kashi tsakanin
wadannan miyagu dasu aswad. Saida suka dau lokaci suna
fadan kafin su samu damar kai mutum biyu kasa cikin su
goma. To da sukaga fadan ba mai karewa bane balantana
gashi sun fara gajiya. Cikin wayo suka runtuma a guje su kuwa
miyagun suka bisu. Ba inda wadannan miyagu basu duba ba
lungu lungu sako sako amma basu gansu ba. Saboda haka
suka juyo da nufin komawa.
Su kuwa su aswad sai suka fito daga maboyarsu. To anan
aswad ya gane cewa namil ne ashe dama bai mutu ba. Cikin
jin dadi suka yiwa juna barka tare da cigaba da binciken gidan
ko xasuga saudat.
" Amma fa naji dadin ganinka abokina, ina fatan dai ka gano
inda su nabilat suke?" Namil ya tambaya.
Anan aswad yayi shiru bai tanka ba.
" Lafiya kuwa ya naga kayi shiru?" Ya kara tambaya.
" Yanzu dai muje mu nemi saudat, domin nabilat da humairat
sai dai muyi musu addua." Cewar aswad.
PAGE 38
Anan namil ya done kansa cikin jimamin wannan magana.
Daga nan sai suka mike hanya suna tafiya suna juyawa don
tsoron kada a kawo musu harin ba zata. Sai da sukayi tafiya
mai dan nisa kafin su fara jiyo ihu a cikin wani daki. A hankali
suka bude dakin. Ai kuwa shigarsu keda wuya suka tarar da
saudat a daure saman kujera. Wani mutum ne fuskarsa a cabe
sai kace dodo. Da wasu dogayen hakora da yake fama dasu
marar kyan gani. Yankan sassan jikinta kawai yake da yuka
tana ihu. Mutumin na juyowa sai yayi arba dasu. Cikin sauri sai
ya dauko gatarinsa yayi cikinsu. Namil ne ya tare shi suka
kaceme da azababben fada. Shi kuwa aswad sai ya nufi wurin
saudat da nufin kwanceta.
Bako shakka mutumin yafi namil karfi nesa ba kusa ba amma
duk da hakan bai yarda an kaishi kasa ba. Wani takobi ne ya
dauko dake rataye a bangon dakin. Dashi yake kare harin
wannan mutumi mai siffar dodanni. Shi kuwa aswad yana
kwance saudat sai ya turata waje domin ta jirasu. Yana
dawowa sai yaga mutumin ya kai namil kasa yana neman
hallaka shi. Da sauri da dauko wata kwalba ya makama
mutumin da kai. Ai kuwa dole ya saki namil. Anan aswad ya
tallabo namil suka fita dakin. Fitarsu keda wuya sukaci karo da
miyagun sai nemansu suke. Shi kuwa namil baya iya gudu
domin akwai rauni a kafarsa. Haka dai aswad ya rika shi suka
cigaba da gudun su uku. Su kuwa miyagun sai halbo musu
kibiya suke.
Suna cikin gudun ne sai sukaji namil yayi wata kara. Anan suka
duba sai sukaga ashe yuka ce ya taka har ta huda kafarsa ta
fito. Ba yadda basu yiba su fitar da yukar amma suka kasa.
Gashi kuma yukar a kasa take idan ba a fito da itaba to bazai
iya tafiya ba.
" Ku tafiyarku wata kila ku tsira da ranku. Ku barni nan domin
nasan lokacina yazo." Haka namil ke fada yana zub da hawaye.
A wannan lokaci kuma miyagun sun kusa cimmusu. Duk da
hakan aswad bai saurari maganarsa ba. A haka yayita kokarin
fitar da yukar amma abu ya faskara. To anan ne suka kyaleshi
domin miyagun na gab da cimmusu.
PAGE 39
A guje suka shiga kwana sai kace motar da ba burki. Bayan
sunyi nisa kadan sai suka jiyo karar namil. Anan suka fara
zubar da hawaye domin sun san cewa an kashe shi. A haka
aswad da saudat suka cigaba da mugun gudu sai kace ransu
zai fita. Cikin gudun ne suka samu kansu cikin wani daki. Sai
wata katanyar makwarara lake a kasan dakin. Aswad yayi
mamakin ganin wannan makwarara domin tayi kamada wadda
ya shigo cikin gidan. Amma kuma yasan ba ita bace domin shi
wannan dakin ko alamar jini babu. Kamar an dade ba a yi
amfani dashi ba. Cikin makwararar aswad ya shige ita kuwa
saudat ta bishi a baya. A haka suka cigaba da tafiya har suka
samu damar fitowa daga gidan. To bayan sun diro ne sai suka
kalli juna cikin jin dadi suna mamaki har yanxu cikin darene
duk dadewar da sukayi a gidan.
Tsayuwa sukayi na dan lokaci suna ma gidan kallon tsaf. Wato
makeken gidan sama ne mai ban tsoro. Haka shima dajin cike
yake da dogayen itace sai furanni ko ina. To suna cikin
wannan dube duben ne sai sukaji motsi a bayansu. Dubawarsu
keda wuya sukaci karo da wadannan miyagun suna fitowa ta
makwararar da suka fito. Ai kuwa cikin karfi su aswad suka
ranta a guje ba sassauci. Gudu suke suna tsallake ramukka sai
kace doki. Saida suka dau lokaci suna gudun sannan suka fara
hango dishi dishin titi. To anan suka kara kaimin gudunsu
domin su cimma titi su gani ko xasu samu mota. Su kuwa
wadannan miyagu sun rufa musu baya sai halbinsu suke da
kibiya.
Cikin gudun ne saudat ta fada wani kwazazzaben rame mai
shegen zurfi. Anan aswad ya tsaya yana tunanin yadda xai
daukota ta. Ita kuwa sai ihu take domin tasan da sun zo wurin
to karyarta ta kare. Da sauri aswad ya katso bishiya mai dan
kwari. Anan ya tura mata, cikin sa a kuwa ta rike. A hankali ya
cigaba da jawota har saida ya fito da ita. To anan ya juya da
gudu da nufin ta biyoshi. Sai da ya dan yi nisa sai yaji tsit
kamar bata biyoshi ba. Ai kuwa yana juyowa sai yaga ashe
miyagun ne suka halbo mata kibiya har ta nutse a cikinta. Yayi
nufin ya taimaka mata amma dole ya fasa domin suna gab da
karasowa. A haka ya kyaketa suka isar da ita shi kuwa yayi ta
kansa.
PAGE 40
A wannan lokaci hasken alfijir ya fara fitowa. Haka aswad ya
cigaba da gudun har saida ya kawo bakin titi. Anan ya hango
wata yar karamar mota ta yan sanda. Hannunsa ya fara dagawa
yana nuni cewa su tsaya. To bayan motar ta tsaya ne sai yaga
ashe mace ce yar sanda ita kadai a ciki. Anan ta kalleshi
taganshi jina jina.
" Malam lafiya kuwa?" Ta tambaya.
" Ba lafiya ba. Don ALLAH ki tamikeni. Kasheni zasuyi."
" Su waye?" Ta tambaya.
Bai tsaya amsa mata ba iyaka ya bude motar ya shigo. " Muje
kawai zan miki bayani." Ya fada.
Anan ta tayar da motar tana dubansa cike da mamaki. " Hala
meye sunanka?"
" Aswad."
" Ni yar sanda ce kuma zan taimakeka idan har mun isa cikin
gari." Haka ta fada tana juya sitarin. " Kada ka damu sunana
anisa." Ta fada bayan ta kama hanyar fita daga cikin dajin.
A haka aswad ya samu damar tsira daga sharrin wadannan
miyagun mutane bayan ya hadu da anisa. Maita gaskiya ce.
Kuma koina akan samu mayyu. Sai dai har yanxu ba a san
mafarinta ba, da kuma yadda ake gane masu fama da ita ba.
Aswad ya tafi da zimmar cewa kul a jima kul a dade sai ya
fanshi kisan gillar da aka yiwa abokansa. Haka itama a anisa,
wannan dalili shine yasa ta yanke shawarar zama yar sanda
domin ta fadada bincike domin ganin bayan wadannan mayyu.
A duk lokacin daka tsinci kanka cikin daji, kada kayi
tsammanin cewa irin hakan bazai iya faruwa ba. Ka dauka
cewa fiye da hakan kan iya faruwa.
Wannan ba labari kawai neba. Gaskiyace, da gaske akwai
mayyu masu irin wannan dabi a can a wani gida. Gidan yana a
cikin daji. Sai dai har yanzu ba a san inda dajin yake ba
balantana a gano gidan. Aswad da anisa zasu hada kansu
domin ganin sun cika burinsu na ganin cewa wadannan mayyu
sun kare, to abun tambaya anan shine ta yaya zasu cika
wannan buri tare da daukar fansar kisan da aka yiwa
abokansu?
The story continues on the third version of the last
episode........


TAFIYAR DARE 
MAYYUN JINI
AUTHOR : ABDUL KING ARTICLE
EPISODE 3
PAGE 41
Ni anisa, a kullum idan nayi tunani nakan yi mamakin wannan
duniyar da muke ciki, yadda al amurra suka tabarbare ba mai
tausayi balantana hakuri. Na gano hakan ne sanadiyar wani
lamari dana gani ya faru akan idona. Wato hakuri shine
maganin zaman duniya. Saboda haka duk wanda bai yi hakuri
ba, to bazai ga hakuri ba. Talauci masifa ce, fitina ce kuma
bala i ne, wannan dalili shine yasa akace kowa ya tashi ya
nemi nasa ba don komi ba sai don kariya daga wannan masifa
ta talauci. Bari in fada maka wani labari na wata yarinya wadda
wanna masifa ta rashi ta faru akanta. Sanadiyar hakan yasa al
amurran rayuwarta suka lalace sabida kin yin hakurin da tayi.
Sunanta khadija, akan lakanceta da dije, haka ta kasance cikin
wannan sababi na talauci ita da iyayenta. Abbanta Dan shago
ne dashi sai kuma noma da yakeyi duk shekara. Wataran sukan
yini basusa hatsi a baka ba saboda masifar rashin da suka
tsinci kansu a ciki. Wannan rayuwa da khadija samu kanta a
ciki ya jefata halin kaka ni kayi. Wanda daga karshe ta kasa
jurewa da jarabawar da aka yi mata. Anan kuma ta fara dana
sanin abunda ta aikata.
Kafin dai muje ga labarin bari mu waiwayi abunda ya faru a
baya. Bako shakka na gama binciken da nake gudanarwa.
Kuma a yanzu hakan ina kan bakana na daukar fansar kisan
gillar da aka yiwa abokaina. Sai dai har yanxu akwai abunda
nakeso na tabbatar kafin na fara aikin. Zee da hamir sune
manyan makiyana. Amma da sannu zasu gane kuskurensu.
Kuma da sannu zasuyi dana sanin abunda suka aikata.
Yanzu bari muje ga labarin khadija da da kuma makasudin
faruwarsa. Tare da jin yadda muka kare da wadannan miyagun
makiya nawa masu farauntar mutane. A duk lokacin dana tuno
abunda ya faru nakan yi bakin ciki sosai. Amma duk lokacin
dana tuno abunda na shirya sai nayi dariya mai yawa. Nasan
cewa kul a jima kul a dade assiri zai tonu. Kuma karshen alewa
kasa. Haka kome nesan jifa kasa xata dawo.
Wata rana a cikin wani kauye...........
PAGE 42
" Wallahi ni umma yunwa nakeji."
" Haba dije, yanzu kiyi hakuri kije rafi sai ki debo mana ruwa.
Idan malam ya dawo maga abunda ya samo mana ko."
" To ni kullum sai na yini ba abunda naci, kuma abincin ko dadi
babu."
" Yanzu dai kiyi hakuri diyata ta kaina. Sheka maxa ki debo
mana ruwan."
Haka dije ta karbi tulun badon tasoba. Tafiya take tana gunguni
cikin takaici. " wani shegen tuwo kamar kanacin dussa. Da
wata banzar miya ko gishiri babu. Mtsss." Haka ta fada cikin
gunguni bayan ta kai kofar gida.
" Laaaa dije, dama yanzu nake cewa in biya miki sai gashi kin
fito, yanzu dai taka muje nasan rafin nan ya cika." Inji kawar
dije wato mairo.
A haka dai dije ta daure ta sakar mata dan guntun murmushi.
Daga nan sai suka kama hanyar zuwa rafi. Ita kuwa mairo ta
kasance mai surutu sosai. Tafiya suke sai zuba take ba sauki.
Tun dije tana iya amsawa har takai sai dai tace to. Sai da suka
kai bayan gari sannan suka iso rafin. Mutane maza da mata
kowa sai sha anin gabansa yake. Masu dibar ruwa nayi masu
wanki nayi. Wannan lokaci marecene sanya sanya domin
magrib ta gabato. Dije ta kasance kyakkyawa abun kallo,
saboda haka daga isowarsu duk samarin dake wurin suka tsura
mata ido kowa sai fadin albarkacin bakinsa yake. Ita kuwa dije
bata damu ba domin ta saba da irin wannan kallon da ake
mata. Kai da ganin tafiyarta kasan ba lafiya. Domin yinin yau
komi bata ciba tun da safe.
A cikin shagon nasu kome babu domin duk sun cinye abunda
ke ciki. Tun da safe abba ya fita nemo abunda zasuci amma
gashi har marece bai dawo ba. Dije ta kasance mai tarbiya,
ladabi ga kuma kunya. Sai kuma tarin ilimin addinin da take
dauke dashi.
Dakyar ta sunkuya tulunta a cikin ruwan. Ai kuwa tana janyowa
sai santsi ya kwasheta cikin ruwan. Ita kuwa mairo dama a
kusa gareta take. Cikin sauri ta ajiye tulunta ta shiga cikin
ruwan domin ceto dije. Anan ta tallabota tare da tulunta.
PAGE 43
" Sannu dije." Wasu yan mata da suka kewayeta suna mata
jaje. Can kuma sai ga gungun samari sun iso wurin.
" To ita ya jikin nata." Babba daga cikin samarin yayi magana.
" E to da sauki." Mairo ta amsa.
" To ALLAH tsare gaba." Ya kara fada.
A haka aka yita zuwa ana ma dije jaje. Ita kuwa kwance take
sai nishi take dai dai sabida ruwan da tasha. Bayan wani dan
lokaci ne mutane suka fara watsewa aka bar mairo da dije. Ita
kuwa mairo sai fita take mata dai dai domin ta farfado. Duhu
ya farayi a wurin sai kuma iskan dake hurawa mai shiga jiki.
Ita kuwa mairo sai karkarwa take tare da dube dube cikin
tsoro. Suna cikin wannan hali ne sai taga an hasko musu wani
haske. Anan mairo ta juya a mamakinta sai taga mota na xuwa
wurinsu. Tayi mamaki sosai da ganin motar domin a kauyen
nasu ko mai mashin babu. Ita kanta rabonta da taga mota an
fi shekara.
Anan ta kurawa motar idanu har ta iso wurinsu. Ita kuwa dije
sai ta fara farfadowa. To bayan motar ta iso gab dasu sai
sukaga wani mutumi ya fito daga ciki. Shigarsa ba irin ta
mutane bace domin kayan nasa dai abun tsoro ne. Haka siffar
jikinsa domin kirar samudawa ce dashi. Dije na ganinsa sai ta
tashi da karfi. Hannunsa ta kalla daga nan sai ta ja da baya.
Anan ta juya da nufin barin wurin.
" Ke baki dauki tulunki ba." Mairo ta fada amma ina dije bata
amsa ba sai tafiyarta kawai take. Anan ta dauko tulunan ta ba
dije nata daga nan suka fara sauri domin su bar wurin. Shi
kuwa mutumin sai ya bisu da kallo har suka bace masa da
gani.
" Dije yau naga abun mamaki." Mairo ta fada tana waige waige
ta gani in bai biyosu ba. " Wai ko kinga hannunsa?" Ta
tambaya.
" Hmm, ni ban taba ganin wanda aka yiwa zanen maciji ba a
hannu." Mairo ta fada cike da mamaki.
" Maciji fa kikace?" Dije ta tambaya.
" E mana, wai kina nufin bakiga hannunsa ba. Ai zanen maciji
ne aka yi masa a hannu kuma irin wannan zanen da baxai
goge ba har abada." Cewar mairo.
PAGE 44
" To kuwa indai hakane abunda na gani ya zama gaskiya." Inji
dije.
" Hala me kika gani?" Mairo ta tambaya.
Anan dije tayi shiru bata amsa ba. " Abunda nakeso dake shine
idan munje gida kada ki fadawa kowa abunda ya faru." Inji dije.
" Kada ki damu kawata an gama." Mairo ta fada.
Haka suka cigaba da tafiya har suka iso cikin gari. Daga nan
suka yi sallama kowa ya kama hanyar gida. Ai kuwa da shigar
dije a gida sai ta tarar dasu umma sunyi zaune zugum sai kace
wadanda aka yiwa mutuwa. Dan kanenta ne a kusa ga umma
ya gincira sai cizon baki yake sabida yunwa. Shi kuwa abba ya
debe hular sai zufa ke kwarara a jikinsa.
" Umma kada dai kicemin yauma ba a samo ba." Dije ta fada
bayan ta ajiye tulun.
Anan suka jiyo suna kallonta amma ba wanda ya tanka mata. "
Innalillahi wainna ilaihir raji un. Gaskiya ni na fara gajiya
wannan abu dame yayi kama. " Anan dije ta shiga dakinta sai
rusa kuka take. Tana cikin kukan ne abba ya shigo yana
lallashinta.
" Haba dije kiyi hakuri mana, shi rashi na Allah ne kuma samu
na Allah ne, kuma nasan Allan nan daya jarrabemu da wannan
rashi bai manta damu ba. Iyaka dai...."
" Iyake me?" Dije ta katseshi. " Kana zama da mutum kullum
babu. Ni nayi dana sanin kasancewa a cikin wannan gida. Da
ace mutum yana zabar inda yakeso da bazan yarda na fito ta
wannan zuri a ba." Haka dije ta fada cikin kuka.
Shi kuwa abba sai ya matso kusa gareta yana shafa gashin
kanta. " Haba diyata ya kina wannan magana. Sai kace wadda
bataje arabiya ba. Ni a ganina kome nufin Allah ne. Kuma Allah
yasan abunda yasa ya jarrabemu da wannan rashi. Tana iya
yiwuwa ya gwada mu ne ya gani ko zamu iya hakuri da masifar
da muke ciki. To kinga kuwa idan bamuyi hakuri ba bazai taba
yaye mana wannan masifa da muke ciki ba.
" Jarabawa? Ai wannan jarabawa tayi yawa kome hakurinka
dole ka gaji." Cewar dije.
" Haba dije kada kiyi sabo fa."
" To idan nayi sabo sai me?"
PAGE 45
Anan dije ta tashi da karfi. " Ni tafiyata zanyi bazan iya zama
cikin wannan talauci ba."
Shi kuwa abba sai yabita yana lallashinta. To anan ne umma ta
shigo da taji hayaniyar tayi yawa. " Haba dije yanzu idan kika
fita to ina zaki. Mu fane iyayenki kuma bakida wasu wadanda
suka fimu." Umma tace bayan ta riko hannunta.
" Ni bazan zauna bakin talaucin ku ya kasheni ba. Baci ba sha
Kullum haka."
" Kibar daga murya kada makwabta suji." Umma ta tsawatar.
" To idan sunji sai me? Ai abunda na fadi gaskiya ne ba karya
ba."
Anan dan kanenta ya sheko ya rungumeta. " Yaya kada ki tafi
ki barmu mu kadai a nan."
Anan dije tayi shiru tana duban kanenta daga nan kuma sai ta
koma dakinta tayi kwance ruf da ciki. A haka sukayi bacci
basuci kome ba cikin rashin jin dadi.
Tunda kulu kulun safiya umma ta farawa bugawa dije kofa
domin ta tashi. Cikin magagin bacci ta bude kofar sai hamma
takeyi. " Yaufa ki tashi akwai aiki a gidan nan. Yanzu nan koje
ya kawowa abbanki sadakar dawa tiya uku. "
" Laaa, dawa. Hehehehe." Anan dije ta fada jikin umma ta
kankaneta cikin murna. Tun bata wanke baki ba ta nufi dakin
umma a guje. Dawar ta dauko tiya uku ta fara durawa cikin
bakinta sai da umma ta jinye bokitin.
" Wai dije lafiyanki kuwa. Kinacin dawa danya idan ta halakaki
fa. Yanxu yi maza ki shirya akwai inda zan aikeki. "
Bayan dije ta kimtsa ne sai ta shiga dakin umma domin taji
sakon da zata bata. Bayan an mata bayanin abunda akeso tayi
sai ta fito daga gidan. Tafiya takeyi tana taku dai dai. Yau dai
fuskarta cike take da annuri ba kamar jiya ba. Wani lungu ne ta
shiga inda gidaje dai dai kune. Haka dije ta cigaba da shiga
lunguna lunguna tana dan wakenta na yan mata. Bayan tayi
tafiya mai nisa ne sai ta kawo gonar abba. Anan ta gyara
daurin kallabinta kada ya fadi.
PAGE 46
Ai kuwa tana kutsa kai ciki sai ta farajin nishi na fitowa a bayan
wata bukka. A hankali ta fara tafiya domin taga ko waye. Tana
kaiwa wurin sai ta tarar da mairo na fesa wani irin zawo. Da
karfi mairo ta mike tsaye saboda tsoro. Batasan lokacin fa
fitsari ya fara fita daga tsaye ba. " Shegiya dubi gabanki." Dije
ta tsawatar.
" Wai na manta." Cewar mairo bayan ta dauko zanenta.
" Ashe dama kece ke mana xawo tun da safe ko?" Dije ta
tambaya.
" Haba kawata yau fa dai ne. Kuma yau din ma matsiyata yayi."
Inji mairo cikin kunya.
" To meye kika zoyi nan?" Dije ta tambaya.
" Au, har kin manta cewa muna fitowa tsintar kara? Yanxu haka
fa girki ne za ayi shine aka tadani naxo tsintar karan." Mairo ta
fada. " Hmm, yar kawata kenan." Mairo ta fada bayan ta matso
kusa ga dije da nufin rike hannunta. Ai kuwa da karfi dije taja
da baya tana like hanci.
" Gaskiya wari kikeyi sosai, yanxu dai muje ga gulbi can ki
wanke wannan kazantar dake jikinki." Inji dije.
" Ni din ke wari?" Mairo ta tambaya.
" E mana, koda yake ance gwalo bayajin warin jikinsa." Dije ta
fadi cikin yanga.
" To yayi zan rama ai, yanxu dai muje gulbin ko bazaki rakani
ba?" Mairo ta fada cikin murmushi.
" Allah zance baxan jeba." Inji dije
" To yanzu dai kiyi hakuri muje." Mairo ta fada cikin wasa.
Haka suka cigaba da tafiya suna fira har suka kai bakin gulbin.
Da zuwa mairo ta nufi wurin da nufin shiga. Kafin ta kai sai taji
an katsa mata tsawa.
" Kai, uban waye ke lekena?"
Anan sukaga nana ta fito daga cikin gulbin wai ashe wanka
takeyi a ciki. Nana ba karamar shakiyiya ce a garin ba domin
har maza suna shayinta. Ta kasance katanya kakkarfa mai
siffar karfi. Anan ta fito daga cikin gulbin zigidir tana duban su
dije. " Wallahi ni zanci uban yaro. In banda iskanci me ya
kawoku nan ne?"
" Kiyi hakuri nana bamusan kina ciki ba." Mairo ta fada bayan ta
done kanta.
PAGE 47
Anan nana ta matso kusa dasu. Su kuwa kowane jikinsu sai dar
dar yake kada suji mazga. Sun san da cewa nana bata buguwa
a garesu. A wannan lokaci sun mata kallon tsaf. Bako shakka
nana ba karamar katanya bace. Damatstsan nan cike suke kai
kace yar dambe. Zanenta ta dauko ta yafa. " Wallahi kun kuru
yau banajin fada da sai naci ubanku. Shegu masu kan goriba."
Anan nana ta bangajesu ta wuce.
" Hmm, shegiyar ji tafiyarta. Kato kenan." Mairo ta fada cikin
karamar murya.
" Ke me kikace?" Nana ta juyo.
" Haba nana ai badake takeba. Wannna magana fa tsakaninmu
ne." Dije ta bata amsa.
" Au, kin kuru." Nana ta fada bayan ta cigaba da tafiyarta.
Bayan nana ta wucene sai mairo ta shiga gulbin. Anan ta
tsaftace kanta daga nan suka nufi wurin tsintar karan. Suna
gamawa suka nufi hanyar gida. To akan hanyarsu ne suka
gamu da ummar dije.
" Wai me ya tsayar dakene tun daxu?" Umma ta fada.
" Ba kome umma." Dije ta bata amsa.
" Tun daxu nakejin tsoro,akan hakan yasa nace dole naxo na
duba ko lafiya." Umma ta fada bayan sun fara tafiya tare.
A haka suka cigaba da tafiya suna fira su uku, sai da suka
kawo wata mararraba sannan suka rabu. Dije da mamarta suka
nufi hanyarsu daban itama mairo haka. A haka mairo ta cigaba
da tafiya ita kadai, kasancewar tun da safene ba kowa kake
gani a hanya ba. To anan hanya tabi da ita ta wannan rafin da
dije ta fada jiya. Ai kuwa tana kaiwa wurin sai ta tarar da wata
mota. Bayan ta kusa cimma motar ne sai taga wata mata ta
fito daga cikin motar ita kadai. Anan aka fara kallon kallo. Can
sai matar tayi magana ta kirata. Bayan mairo tazo wurin sai
matar ta fara bayyana mata ko ita wacece.
" Sunana anisat, ni yar sanda ce mai binciken manyan laifukka
kuma yanzu haka akwai abunda nake bincike a wannan kauye
naku saboda haka inaso ki bani hadin kai dari bisa dari." Anan
ta nuna mata ID card dinta. Ita kuwa mairo batasan ko meye ID
card ba iyaka dai ta karba tana kallon foton anisa dake ciki.
PAGE 48
" Wai ko kun taba yin bako a wannan gari naku?" Anisa ta
tambaya.
Anan mairo tayi dan tunani mai zurfi, cikin kankanin lokaci sai
ta tuno da mutumin da suka gani jiya a wurin rafi. Daga nan sai
ta amsa da cewa. "E kwarai kuwa."
" Ina fatan dai zaki iya bayyana min ko shi waye!" Anisa ta
fada.
Anan mairo ta fada mata wannan mutumin da suka gani jiya
wurin rafi tare da zanen dake hannunsa na maciji. Haka anisa
ta cigaba da yiwa mairo tambayoyi ita kuwa sai bata amsa
take. Daga karshe sukayi sallama anisa kuwa sai ta dauko cake
ta bata. Mairo ta karba cikin mamaki domin tunda take bata
taba ganinsa ba. Da anisa ta fahimci hakan sai ta fada mata
cewa abinci ne. Haka anisa ta shiga motarta ta manta ta karbi
ID card dinta. Ita kuwa mairo a tsammaninta an batane kyauta.
Anan ta kama hanyar gida tana tafe tana tsalle tsalle.
Bayan magrib ne mairo ta kaiwa dije ziyara. Anan ta bayyana
mata yadda ta gamu da wannan yar sanda anisa. Da kuma
kyautar data bata na hotonta. Sai kuma dan cake din data
bata. Da karfi dije ta karbe cake din ta bantali dan kadan. Ai
kuwa tanajin dadi sai ta finciko shi iyakar hannunta. Daga nan
kuma saita amshe ID card din ta rataya a wuyanta kamar
sarka. Ita kuma mairo bata damu ba anan ta barta shi. Haka
sukayi sallama mairo ta koma gida.
Bayan sati daya da faruwar hakan, yar dawar da akaba su dije
sai ta kare. Sabida haka sai rayuwar da ta dawo. A kowane
lokaci dije kanyi bakin ciki sosai idan taga yadda rayuwarsu
take. Ba jin dadi balantana walwala. Saboda wannan dalili sai
ta yanke shawarar cewa bari ta gwada zuwa rafin nan wata kila
ko zata gamu da yar sandan nan. Idan ta gamu da ita ta mata
tambayoyi kila ta bata irin abunda taba mairo wato cake.
Da daddare ne amma ba sosai ba. Sai dije ta fita ita kadai da
nufin zuwa rafin nan. Haka ta kama hanya tafiya take da sauri
kai kace wadda aka yiwa busharar wani abu. A wannan lokaci
yunwa ke damunta sosai domin rabonta da abinci har ta
manta. Babban abunda yasa ta yanke wannan shawarar na
tafiya rafi shine ko wata kila ta dace ta gamu da wannan yar
sandan wato anisa.
PAGE 49
Idan ta gamu da ita wata kila ko tamata tambayoyi yadda tama
mairo. To idan aka yimata tambayoyin kila ta samu cake ko ta
rage yunwar dake damunta. A haka ta cigaba da tafiya ba
sassauci. Sabida tsabar yunwar dake damunta ko takalma bata
dauko ba. A kasa take tafiya bata damu ba. Bayan ta isa rafin
ne sai ta tsaya tana duban ruwa amma kowa babu. Wurin yayi
tsit sai kace makabarta. Anan dije ta duka cikin bakin ciki.
Cikinta ne ke wani murdawa saboda yunwa. Cikin rashin
tsammani sai taga an hasko mata haske. Tana dubawa sai
taga mota tafe wurinta. Anan dije ta mike cikin jin dadi domin
a zatonta yar sandan ce. Kaji wani abu, da takardar cake din
tazo.
Anan ta falfala da gudu saida sukayi gab da gab sannan ta
tsaya. Kawai sai taga namiji ya fito a ciki. Dubawarta keda
wuya sai taga ba kowa bane in banda wannan namijin da suka
fara gani a ranar da santsi ya kwasheta ta fada rafi. Anan ta
mika masa takardar dake hannunta na cake. Shi kuwa
mutumin yana karba sai yayi murmushi. A nan ya jawota inda
motarsa. Yana bude motar sai dije ta leka ciki. Ai kuwa a guje
ta shige ciki domin ba kome in banda abinci kala kala tare da
irin cake din da takeso. Kwance tayi ruf da ciki sai diba take
tana kaiwa baki. Abinka da sakarya batasan ko waye shi ba
iyaka dai daga ganisa ta shige motarsa. Koda yake ba laifinta
bane, tsananin yunwa ce ta jawo hakan.
Shi kuwa mutumin da ganin hakan sai ya tsaya cak yana
kallonta. Haka dije tayi cin hauka har saida tayi tatil. Daga nan
sai ta fito daga motar tana gyatsa. Fitowarta keda wuya sai
kunya ta kamata ganin mutumin na kallonta.
" Amma fa na gode sosai." Ta fada tana dubansa.
Shi kuwa murmushi yayi ba tare daya tanka ba. " Wai a wannan
gari kake?" Dije ta tambaya amma shiru bai tanka ba. " Ni
sunana dije kaifa?" Anan ya kara yin murmushi baice kome ba.
Anan dije ta fara tunani wai ko baya magana ne. Can sai taga
ya shiga motarsa. Anan ya juya ya nufi inda ya fito. Haka dije
tabi wannan mutumi da kallo har ya bace mata da gani. Ita
kuwa sai ta dawo gida cikin mamaki. Haka kuma taja bakinta
ta tsuke ba tare da fadawa kowa ba harda mairo da take
kawarta.
PAGE 50
A yau dije tayi bacci mai dadi domin tunbinta a cike yake. Taji
mutukar dadi na ganin wannan mutumi domin ya bata abunda
takeso.Iyaka dai abunda ke damunta shine wai kuwa yana
magana? To idan yana magana me yasa ya kyaleta a ranar. A
haka dai ta cigaba da tunanin cewa kila baya magana. Saboda
wannan abu daya faru sai dije ta maida rafi wurin zuwanta a
duk lokacin da takejin yunwa. Sai dai bata zuwa sai a cikin
dare domin mutumin a lokacin ake ganinsa. Bata fadawa kowa
halin da take ciki ba domin ganin take idan ta fadawa su umma
sukan iya hanata zuwa. A kan hakan ne ta tsuke bakinta ko
babbar kawarta mairo bata fadawa ba.
A duk lokacin da taje yakan bude mota ta shiga har sai tayi
tatil da abinci. Kuma a duk lokacin da tayi masa magana baya
amsawa sai dai murmushi. A kwana a tashi har suka fara
sabawa da juna. Wataran idan tazo yakan rungumeta yana
mata wasa amma kuma baya magana. Dije bata damu da duk
abunda zai mata ba in har zata cika cikinta. A wannan dalili
takan bashi hadin kai suyi wasansu daga nan kowa ya kama
gabansa.
Wata rana a cikin dare bayan dije ta iso wurin. A mamakinta
bata ganshi ba. Sai da tayi tsayin kusan minti talatin sai gashi
ya zo. Ai kuwa kai tsaye ta shiga motar. Shigarta keda wuya
sai ya kunna ya tayar. Dije tayi mamaki ko ina zai je da ita.
Taso ta tambayeshi amma data tuno baya magana sai ta tsuke
bakinta. Iyaka dai ta jawo kayan abinci sai kalaci take cikin jin
dadi. A duk lokacin da suka hado ido sai yayi mata murmushi
saboda hakan dije bata damu ba iyaka dai a tunaninta yana
yawon shakatawa ne da ita. Abu kamar wasa sai ga tafiya tayi
nisa har suka fita cikin garin dije bata ankara ba sai faman
shagali take da su cakes. Anan suka hau titi sai gudu yake a
tamanin. Sai da sukayi tafiya mai nisa sannan dije ta dawo
cikin hayyacinta. Anan ta gane cewa ba cikin garinsu ne ba.
Saman titi ne suke tafiya sai dazuzzuka masu ban tsoro dake
a gefen titin.
PAGE 51
Anan dije ta fara damunsa daya tsaya amma ina ko kallonta
bayayi. Tuki yake iya karfinsa. Ita kuwa sai ta fara ihu tana
bugunsa amma yakiji. Da dai taga bazata fita ba kawai sai ta
rike sitarin. Anan motar ta fara kalan keluwa sai da kyar ta
tsaya. Ai kuwa motar na tsayawa dije ta fito a guje. Anan tayi
arba da wasu mutane masu kirar samudawa. Kowanensu
sanye da bakaken kaya sun lullube fuskarsu da bakin kyalle.
Can sai ga mutumin shima ya fito. Dije na ganinsa sai ta sheko
ta rungumeshi a tsorace. Shi kuwa hannunsa yasa ya bugeta
can gefe. Anan taga an miko mishi takobi. Shi kuwa cikin sauri
ya nufota. Dije na ganin haka sai ta rantama a guje cikin dajin.
Su kuwa masu bakaken kayan sai suka dafa mata. Anan aka
fara tsere tsakanin dije da wadannan mutane. Sai halbota mata
kibiyoyi suke amma duk a banza domin bata samunta.
Suna cikin gudun ne sai suka tsaya wuri daya suna dube dube.
Wato dije ce ta bace musu da gani basusan inda ta shiga ba.
Sai da suka dade suna binciken wajen amma ko duriyarta
babu. Daga nan sai suka nufi wata hanya suka tafiyarsu. Can
sai ga dije ta fito. Ashe dama cikin wani rame ne ta shiga sai
ta sanya ganyayyaki a sama yadda ba kowa zai gane akwai
mutum a wurin ba. Cikin dajin ta kara shiga sai faman gudu
take tana mamakin irin wadannan mutane da kuma abunda
yasa sukeso su kasheta. Bako shakka akwai ban mamaki a
tattare dasu domin gudunsu daban yake da sauran mutane.
Idan suna gudu kai kace akan iska ne suke gudu.
Haka dije ta cigaba da gudun a cikin daji sai da tayi nisa
sannan ta tsaya tana haki. To anan ne ta kara duban dajin taga
irin bishiyoyin dake ciki. Wato dajin ya kasance wangameme
mai ban tsoro. Ko ina itace ne dogaye masu furanni. Haka dije
ta cigaba da tafiya tana sauri ko zata samu taimako. Sai da
tayi tafiya mai nisa amma ko kadangare bata hadu dashi ba.
To anan tsoro ya fara dabai bayeta domin duhun ya tsananta.
Dakyar take ganin inda take takawa.
PAGE 52
Dije tayi mutukar dana sanin kin yin hakuri halin gidansu na
talauci wanda ta tsinci kanta a ciki. Gashi yanxu ta jefa kanta
ga mahalaka. Babban abunda ke damunta shine can a gida ba
wanda yasan inda take balantana a kawo mata dauki. Tana
cikin tafiyar ne saita hango an kunna wuta a wani wuri. Da
sauri ta nufi wurin inda ta isko mace da namiji a zaune sai
firarsu suke. Tana isowa sai ta fara yi musu bayyani cewa su
taimaketa za a kasheta. To abunda ya bata mamaki shine
suma wadannan mutane basajin hausa kamar wancan
mutumin daya daukota. Wani yarene suke wanda batasan
kome suke fadi ba. Koda sukaga dije a galabaice ta zube kasa
sai nishi take dai dai. Sai macen ta tallabota tana mata fifita.
Dije najin suna magana amma batasan abunda suke fadi ba.
Anan suka kashe wutar dakeci. Ita kuwa macen na rike da dije
har saida suka kai wata yar bukka. A cikin bukkar an gyarata
sosai da kayan alatu. Anan ta kishingida dije saman gado sai
fita take mata. Ana cikin hakane sai ga wata mace ta shigo
bukkar. Anan ta kurawa dije idanu bata ko kyaftawa. Daga nan
kuma sai suka fara wata magana da wannna matar dakema
dije fita cikin wani yare. To bayan sun kare sai matar ta juya ta
fita. Haka shima namijin sai ya bita. Anan aka bar dije da mai
mata fita.
Bayan wani dan lokaci sai dije ta farfado. Hankalinta ya fara
dawowa. Anan ta kalli matar amma batace kome ba. Ita kuwa
matar sai murmushi take mata. To anan ne ta lura da zanen
macijin dake hannunta irin na wancan mutumin data hadu
dashi a rafi. Anan dije taja da baya a tsorace. Ita kuwa matar
na ganin haka saita rungumeta tana sumbatar ta. Tun dije na
kokarin ta kubce har takai ta tsaya wuri daya saboda abunda
takeji yana shiga. Anan ta mimmike kafafuwanta saman gado
sai wani nishi take. Ita kuwa matar sai matsar jikinta take duk
inda taga dama. Daga nan dije bata kara sanin abunda ya faru
ba.
PAGE 53
Firgigit ta farka. Anan ta ganta cikin wani daki mai duhu an
daure kafafuwanta da hannayenta. A mamakinta ba a cikin
bukka bane. Hasalima shi wannan daki kamar a cikin gida
yake, sai dai shi wannan wane gida ne kuma ya akayi tazo
nan? Anan dije ta rasa abunda ke mata dadi domin a halin
yanzu tana tsaka mai wuyar sani. Batasan inda takeba kuma
batasan abunda ke iya faruwa da ita ba. Bako shakka hakuri
shine maganin zaman duniya, duk wanda bai yi hakuri ba to
bazaiga hakuri ba. Wato da ace dije tayi hakurin talaucin da
suke ciki da irin hakan bai faru ba. Amma sai gashi kwadayinta
na son abun duniya ya kaita ya baro.
Bude dakin akayi a hankali. Can sai aka hasko mata fitila.
Tanaji sai taga an tallabota an azata saman kujera mai tayu.
Ita wannan kujera da an turata sai ta fara tafiya. Ai kuwa anan
aka fara tura dije saman kujerar sai ihu take tana neman
taimako. " Waye kai? Me kakeso a gareni?" Haka ta cigaba da
fadi amma ko jinta bayayi. Da sauri ya nufi wani lungu da ita.
Sai da yayi tafiya mai nisa sannan ya tsaya a kofar wani daki.
Anan dije ta tabbatar da cewa lallai yanzu a cikin wani gida ne
ba bukka ba. To amma ya akayi taxo gidan?
Bayan sun shiga dakin ne sai ta ga cewa ashe mutumin nan ne
wanda yayi sanadiyar shigowarta dajin. Anan ta kura masa ido
sai harararsa take. " Macuci azzalumi me kake shirin yi dani,
kuma nan inane ka kawoni." Haka dije ke fadi cikin bakin ciki
amma shi ko damuwa bai yiba iyaka kallonta jikinta yake yana
murmushi. Anan yazo yana shafa fuskarta a hankali. Yana cikin
hakane dije ta gatsa masa cizo. Sai da yayi kara sosai sannan
ya fadi. Ai kuwa tashinsa keda wuya ya gabza mata mari sai da
ta kife saman kujerar. Daga nan ya jawota ya aza saman
kujerar. Cikin fushi ya kara gabza mata wani marin. Daga nan
kuma sai ya dunkule hannu yana dukanta kamar bazai barta ba.
Fuskarta ya nunnuga sai da ya mata jina jina kafin ya fita dakin
cikin fushi. Anan yabar dije cikin rauni mai yawa jini sai tsiyaya
yakeyi. Kai da gani kasan taci wuya domin gaba daya fuskarta
ta canza ko ina sai jini ke fita.
PAGE 54
Haka dije taci gaba da zama a wannan daki sai nishi take dai
dai. Saida aka dau lokaci kawai sai ga matar nan data gamu
da ita cikin bukka ta shigo. Anan matar tazo kusa da ita.
Hannuta rike yake da wani karamin akwati. Cikin murmushi
matar taxo kusa ga dije. Daga nan saita bude akwatin ta dauko
wani kyalle. A hankali tabi fuskar dije tana shafe jinin dake
tsiyaya a fuskarta har saida ta tsanar da ita tsab. Tana
kammalawa sai ta fita. Fitarta keda wuya sai ga wannan
mutumin na farko ya shigo. Cike da murmushi ya shigo yana
duban ta. Anan dije ta done kai ko kallonsa batason yi. Shi
kuwa sai ya tallabo fuskarta ya kura mata ido. Can kuma sai ya
kyaleta. Wata yar karamar yukace ya fito daga jikinsa. A kirji ya
soka mata sai da tayi kara sannan ya fito da yukar. Anan ya
jawo yukar a gefen jikinta har saida ya keta mata riga yadda
ana ganin kome a fili.
Jifa yayi da yukar sai kallonta yake kai kace mussa taga nama.
Hannunsa ya dora saman jikinta sai shafawa yake ko ina. Kafin
kaceme sai ya jawota jikinsa. Ita kuwa dije ba yadda ta iya
domin a daure take. Da mutumin yaga kamar idan tana daure
bazai iya yin abunda yakeso ba sai ya dauko yukar ya
kwanceta. Anan dije ta kyaleshi sai da ya shagala yana
warwasawa kafin ta manna masa cizo a kunne. Ihu ya kurma
yana dukanta ita kuwa taki sakinsa. A haka suka fara mulmule
mulmule cikin dakin amma dije taki sakin kunnen saida ta
guntule shi. Daga nan saita tashi ta dauko kujerar nan mai
tayu. A kai tayita rafka masa har saida ya suma. Anan ta fita
dakin a guje ta barshi cikin jini.
Gudu take iyakar gudu amma ta kasa ganin karshen gidan
domin ko ina lungu ne. Tana cikin gudun ne saita jiyo ihun
wasu a cikin wani daki. Sai dai ba damar shiga domin wasu
samudawa ne rike da makamai a kofar dakin sai kai da komo
suke. Anan dije ta labe tana tunanin yadda za a yi ta shiga
dakin domin ganin ko su waye ke ihu. Can sai taji kamar an yi
magana a cikin dakin. Kawai sai samudawan suka shiga ciki
dama su biyune. Ita kuwa dije sai ta bisu jikinta na karkarwa.
PAGE 55
Labewa tayi bayan wata kujera tana duban abunda ke faruwa.
Wasu mata ne biyu aka sarkafe a gina jikinsu duk jini ne. Sai
wani mutumi mai siffar ban tsoro rike da gatari yana magana
da wadannan samudawan da suka shigo ciki. Wadannan mata
duka yan garinsu su dije ne. Dayar itace nana wadda suka
hadu da ita a gulbi tana wanka. Dayar kuwa abokiyar nana ce,
akan kirata da ladiyo. Anan mamaki ya kashe dije koya akayi
sukazo wannan gida? Tana kallo sai taga mutumin ya ajiye
gatarin yabi wadannan samudawa biyu suka fita tare. Fitarsu
keda wuya sai dije ta fito bayan kujerar ta nufi wurin su nana.
Ai kuwa nana na ganinta sai ta fara ihu a tsammaninta
mutumin ne ya dawo. " Kiyi shiru mana kada suji. Bari na
kwanceku." Inji dije.
Anan nana ta jiyo tana kallonta. " Dije, me ya kawoki nan?"
Nana ta tambaya." Yanzu ba lokaci bayani bari sai mun fita."
Dije ta bata amsa. Anan ta dauko gatari ta sare kacar da aka
dauresu da ita. Sai gasu sun fado kasa timmm. Saida yar
karamar kura ta tashi saboda nana mai jikice sosai. Ita kuwa
ladiyo ko motsi batayi saboda ta dade da suma. Anan nana ta
goyata. Ita kuwa dije sai ta dauki gatari ta jagoranci tafiyar.
Gudu sukeyi dakyar suna lalube a cikin duhu. Gidan ya kasance
katon gaske sai kace gari. Ga lunguna birjik. Dakuna kuwa ba a
magana domin ko ina sune hagu da dama.
Suna cikin gudun ne sai suka iso wani wuri da mutane sunyi
sahu sai tafiya suke suna waka. Dukkaninsu sun sanya kaya
jajjaye. Ba a jin abunda suke fadi cikin wakar domin wani
yarene suke fadi. Kayan da sukasa sun lullube dukkan jikinsu
yadda ba a ganin kome in banda fuskarsu. Anan su dije suka
labe suna kallon ikon ALLAH. Mutanen hade suke maza da
mata sai tafiya suke a cikin sahu. Shi kuwa shugaban tafiyar
shine a gaba yana jagorantarsu. Mutanen bari biyu ne. Rabi a
gefen dama rabi kuwa a hagu. Sai shugaba a can gaba. To a
tsakiyar wani irin makeken maciji ne wanda tsawonsa yafi a
kirga. Haka kuma fadinsa sai kace daki. Macijin na tafiya cikin
kasaita yana wangame baki.
PAGE 56
Anan dije ta gane cewa wannan macijin shine aka zanawa
wannan mutumin da ya kawota dajin. Kuma irinsa ne ta gani a
hannun wannan matar ta cikin bukka. To indai hakane kenan
wannan maciji alama ne na cewa kungiyarsu daya. Bayan
wadannan mutane sun wuce sai su dije suka bi wata hanya sai
faman gudu suke ba kakkautawa. Basuyi wani nisa ba sai nana
ta gaji. Anan ta ajiye ladiyo domin ta huta. Ita kuwa dije sai ta
kasa zama ta kasa tsayi. Iyaka taje ta dawo gabanta sai
faduwa yake. Kai da gani kasan a cikin tashin hankali take.
" Wai meye wannan abu? Ke bazaki zauna ba?" Nana ta
tambaya.
" Ai bazan iya kome ba a yanzu har sai mun fita daga wannan
gida." Dije ta bata amsa.
" To wai ke yama akayi kika shigo wannan bala i alhali bakya
yawo?" Nana ta tambayeta.
" Hmm. Da kenan. Yawo yanzu kam......" Anan dije tayi shiru
domin jin wata mata ta fito daga wani daki sai tafiya take
kwas kwas kwas. A haka matar tabi ta wurinsu ta wuce amma
bata gansu ba domin sun manne jikinsu a bango. Gashi kuwa
wurin tsananin duhu ne dashi. To bayan matar ta wucene sai
suka tashi suka nufi wata hanya. A wannan lokaci ba gudu
sukeyi ba. Sassarfa ce sukeyi domin sun fara gajiya da gudun.
Har dai nana da take da jiki baya bari ta motsa sosai.
" Gaskiya na gaji da goyon nan fa." Nana ta fada.
" Ki daure mana tun da bazamu yar da ita ba. Mucigaba da
zaga yawa watakila mu samu hanyar fita." Inji dije.
Suna cikin maganar sai ladiyo ta fara tari. Anan suka ajeta gefe
suna girgizata ko zata mike. Ai kuwa cikin sa a sai ta bude
idanu.
" Kai, meke faruwa ne?" Ladiyo ta tambaya.
" Yanzu dai ba wannan ba. Tashi mu cigaba da tafiya." Inji
nana.
"Hala ina su lami?" Ladiyo ta tambaya.
" Bamu sani ba. Amma mu bincika ko ma gansu." Nana ta kara
fada.
" Au, ashe baku kadai bane. Kunada yawa kenan?" Cewar dije.
" Ai su biyu kawaine bamu gani ba. Wato lami da rabi." Inji
nana.
" To me zai hana mu bincika ko zamu gansu?" Inji dije.
" Nima abunda nake shirin cewa kenan." Cewar nana.
PAGE 57
Anan suka tashi su uku sai faman sauri suke ba mai yarda a
barshi baya. Suna cikin tafiyar ne sai sukaji motsin wasu a
gabansu. Anan suka manne a gina suna jira suga ko su waye.
Can sai ga wasu samudawa sun tallabo wasu mata biyu akan
kafada. Matan ko motsi basayi kamar matattu. Bayan sun
wucene sai su dije sukabi bayansu domin suga ko su waye.
Haka suka cigaba da tafiya cikin sanda idan sukaga kamar
zasu juyo sai su labe. Cikin wani daki suka ajiye matan daga
nan suka fito suka tafiyarsu. Su kuwa su dije da karfi suka fada
cikin dakin. Cikin sa a suka tarar da wadanda suke nema wato
lami da rabi. Sai dai ita lami rai yayi halinsa domin har sun
yanke wasu sassa na jikinta. Anan nana ta fara kuka na
tausayawa zuwa ga abokiyarta. Su kuwa su dije sai faman
lallashinta suke. Sai da kyar suka ciyo kanta.
" Hamir ya cucemu, ya cucemu daya kawomu wannan gida."
Nana ta fadi cikin dana sani.
" Hamir kuma? Wai har yanzu baku daina wannan sana a taku
tabin maza ba? Kenan a can kuka hadu dashi." Dije tace tana
dubanta.
Anan nana tayi shiru batace uffan ba. Ita dai tasan abunda ta
aikata ita da kawayenta wanda shine yayi sanadiyar kawosu
wannan gida. Anan suka tallabo rabi sai fifita suke mata. Sai
da suka dau lokaci sunayi sannan hankalinta ya dawo jikinta.
Suna ganin ta mike sai suka nufi hanyar fita daga dakin. To
kafin su fita ne sai sukaji takun wani kamar yanason shigowa
ciki. Cikin sauri suka lallabe suna jiransa. Ai kuwa yana
shigowa suka yi masa taron dangi. Mai bugu nayi mai cizo
nayi har suka kaishi kasa. Anan suka fita dakin suka barshi
kwance cikin jini.
A wannan lokaci tafiya suke kamar wadanda aka yiwa charge
domin duk wanda suka hadu dashi to sai sun masa jina jina.
Sai dai idan sukaga mutanen nada yawa to sai su labe har sai
sun wuce. Amma daga mutum uku zuwa kasa duk wanda suka
hadu dashi to sai sun ji masa rauni. Haka suka cigaba da gudu
a cikin gidan amma ko alamar karshe basu gani ba. Duk inda
suka duba lungu ne. Haka kuma dakunan gidan sun kasance
daki cikin daki har ba adadi. Wannan abu kan mutukar rudasu
sai su rasa shin wai gaba sukeyi ko baya.
PAGE 58
Wani lungu ne suka shigo. Tafiya sukeyi amma kamar a cikin
ruwa suke tafiyar. Sai daga baya suka gane cewa jini ne ya cika
lungun gaba daya kamar anyi anbaliyar ruwa. Suna cikin tafiyar
ne sai suka fara jiyo karagin wani abu. Kai dagaji kasan wannan
abu zaiyi ban tsoro domin wani gurnani ne yake marar dadi.
Suna cikin tafiyar ne sai sukaji ladiyo na ihu. Anan ta fadi
kwance. Wani abune ya laulaye kafarta sai janta yake iyakar
karfinsa. Anan su dije suka kai mata dauki suna jawota amma
abun yaki sakinta. Saboda tsabar karfinsa ya janyeta. Anan
sukayi tsaye a tsorace kowane sai kalle kalle yake. Can sai
sukaji an jefo musu wani abu. Ai kuwa suna dubawa sai
sukaga sassan jikin ladiyo an yankata guntu guntu. Kai daban,
kafa daban. Kome daban. Ganin wannan abu ya mutukar
tsorata su. Ita kuwa dije batasan lokacin data yar da gatarin
data dauko ba. Anan suka juya baya da nufin gudu. Kafin suyi
nisa sai sukaji suma an laulaye kafafuwansu.
Anan aka fara jansu suna ihu sai faman rike gina suke. Ba
yadda basu yiba domin su tsira amma ina sai da abun ya
janyosu. Ai kuwa suna kawowa gab da abun sai dije ta gane
cewa wannan macijin ne da suka gani dazu shine ke jawosu
da halshensa. Anan ya wangame baki da nufin suna fadawa
yayi musu cin gyada. To kafin su kai ga bakin nasa ne dije ta
wankala ta dauko gatarin data yar, saida ta saita da bakin
shege ji kake kimissss. Anan macijin yayi kururuwa ya balla a
guje. Daga nan sai suka tashi suna nishin wuya. Wata hanya ce
suka nausa suna tafiya dakyar. Bayan sun dan yi nisa sai suka
kai ga wata katanyar kofa. Anan suka daga kai sama amma
basuga karshen tsawonta ba. Kofar ta kasance mai karfin
gaske domin karfe ne aka narka kafin ayita.
Ba yadda basu yiba domin ganin sun bude kofar amma gam
taki budewa. Saboda haka sai suka yanke shawarar su hau
samanta. Ai kuwa nan take suka dane dama tanada
matattakala. Sai da sukayi nisa saman kofar. Kadan ne babu su
kai ga karshe sai ga masu bakaken kaya sun iso wurin. Ko
wane rike yake da kwari da baka. Sun lullube fuskarsu da bakin
kyalle ba a ganin kome. Anan suka fara sakar musu ruwan
kibau su kuwa su dije sai suka kara kaimin saurinsu.
PAGE 59
Duk da kasancewar nana mai jikice amma haka ta takarkare
bata yarda an barta bayaba. Ita kuwa rabi a wannan lokaci ta
fara gajiya sai nishi take dakyar. Wasu daga cikin masu
bakaken kayan sai suka dane kofar suna bin sawun su dije. To
a wannan lokaci ne aka sako wata kibiya. Cikin rashin sa a ta
shige hannun rabi. Anan tayi kara ta saki kofar amma kafin ta
fado sai nana ta rike ta da hannu daya. Anan nana ta nuna
mata data daure su ci gaba. Can kuma sai aka kara sako mata
wata kibiya. A wannan lokaci fadowa kawai tayi domin kibiyar
ta huda wuyanta. Su dije na kallo amma ba yadda suka iya.
Haka suka tsallake suna jimamin rasa abokiyarsu. Anan suka
yo kasa sai taka matattakalar sukeyi har suka kawo kasa. Daga
nan suka diro. To bayan sun diro ne sai suka tabbatar da cewa
yanxu sun fito daga gidan. Anan suka fara gudu baji ba gani
kai kace mahaukata. Haka suma masu bakaken kaya suna
dirowa sai suka bisu a guje.
Sai da gudu yayi gudu sannan suka fara hango dishi dishin titi
tare da jin jiniyar motar yan sanda. Anan su dije suka kara
kaimin gudu domin su cimma motar yan sandan ko xasu samu
taimako. Gudu suke suna ihu ko yan sandan zasuji. Suna cikin
gudun ne sai sukaga wasu mutane sun diro saman itace a
gabansu. Mace da namiji ne idanuwansu sunyi wani baki
bakyan gani. Kuma a wannna lokaci ne masu bakaken kaya
suka cimmusu. Anan nana ta gane namijin. Shine saurayinta
hamir wanda yayi sanadiyar kawota wannan gida itada
abokanta.
" Ke a tsammaninki kinsha ko? To yanxu zakibi yan uwaki
dama suna can suna jiranki."
Anan ya bude hakoransa marar kyan gani yayi cikin su dije. To
kafin ya karasa ne sai sukaga ya fadi. Suna dubawa sai sukaga
yan sanda biyu mace da namiji ashe sune suka halbeshi. Dije
na kallon macen yar sandan saita ganeta. Itace anisa wadda
mairo ta bata labarinta. Kuma har ta karbe ID card dinta daga
hannun mairo. Anan anisa ta juya zuwa ga macen wato
abokiyar hamir.
" Sannunki zee, sai gashi yau mun kara hadewa. Kuma sai
gashi na kamaki a lokacin da nakeso." Inji anisa.
" To daga nan fa?" Zee ta tambaya.
" Sai zuwa lafira." Anan anisa ta bindige zee kasa.
PAGE 60
Su kuwa masu bakaken kaya na ganin haka sai suka rantama a
guje. Anan anisa da abokin aikinta suka rufa musu baya a guje.
Sai da su masu bakaken kayan gudunsu daban yake. Suna
gudu sai kace iska. Kafin kaceme sun ba su anisa tazara mai
yawa. Suna kaiwa ga gidan. Taba kofar kawai sukayi sai suka
bace bat ba a ganinsu. Haka shima gidan sai ya bace bat wurin
ya koma fili. Anan anisa ta fara cizon hannu domin wannan
shine abunda ya faru a lokacin da yan sanda suka taimaketa
bayan ta fito daga gidan. Yan sandan suna zuwa gidan sai
sukaga ya bace ba a ganinsa. Haka anisa ta dawo tare da
abokin aikinta wurin su dije. Anan dije ta bata ID card dinta tare
da fada mata yadda akayi ta sameshi da kuma labarinta.
" Kada ki damu dije. Xan taimakeku keda iyayenki. Daga yanzu
bazaku kara zama cikin wannan hali na talauci ba. Zan mayar
dake birni inda zaki samu ilimi na zamani wato boko keda
kanenki. Shi kuwa abbanki zansa a nema masa aiki mai tsoka."
Anan anisa tayi gyaran murya kafin ta cigaba. " Wannan namiji
da kike gani sunansa aswad. Abokin aikina ne. Kuma shima ya
taba shiga irin halin da kiki tsinci kanki. Ba shi kadai ba har ni
nan na taba fadawa ciki."
Haka suka cigaba da tafita suna hira har suka kawo bakin
motar. To kafin su shiga ne dije da nana suka kalli juna cikin
farin ciki. Daga nan sai suka shiga motar su anisa. A wannan
lokaci hasken safiya ya fara fitowa amma ba sosai ba. Aswad
ne ke tuka motar sai anisa kusa dashi. Dije da nana a baya.
Anan aswad ya mika ya nufi hanyar fita dajin.
Daga karshe dai anisa ta taimaki dije sosai itada iyayenta. Ta
basu gida a cikin birni. Shi kuma abba an samar mashi aikin
gwamnati. Dama yanada qualification na N C E aikine bai
samu ba. Dije da kanenta sun zama yan birni gadan gadan
domin a gidan anisa suka tare ita ke daukar dawainiyarsu.
Iyaka dai idan ta samu dama takan kaiwa abokanta na kauye
ziyara. Haka ta riki zumunci batayi watsi da su mairo ba. Da su
nana.
PAGE 61
Ni anisa, a kullum idan nayi tunani nakan yi mamakin wannan
duniyar da muke ciki, yadda al amurra suka tabarbare ba mai
tausayi balantana hakuri. Na gano hakan ne sanadiyar wannan
lamari dana gani ya faru akan idona. Wato hakuri shine
maganin zaman duniya. Saboda haka duk wanda bai yi hakuri
ba, to bazai ga hakuri ba. Talauci masifa ce, fitina ce kuma
bala i ne, wannan dalili shine yasa akace kowa ya tashi ya
nemi nasa ba don komi ba sai don kariya daga wannan masifa
ta talauci.
Wato da ace dije tayi hakurin talaucin data tsinci kanta a ciki.
To da bata shiga wannan masifa ba. Haka shima karuwanci
fitina ne. Domin da ace nana batabin maxa to bazata hadu da
hamir ba har ya kawota wannan gida na maita ba. Maita
gaskiya ce. Kuma koina akan samu mayyu. Sai dai har yanxu
ba a san mafarinta ba, da kuma yadda ake gane masu fama
da ita ba. Da gaske akwai wannan gida. Kuma ba abunda akeyi
a ciki in banda yankan mutane. Sai dai har yanxu ba wanda ke
iya cewa ga inda gidan yake saboda an asirceshi.
Zee da hamir sun mutu. Amma kuma shugabansu bai mutu ba.
Haka ma macijin da suke bautama yana raye. Kai in takaice
maka labari da yawa daga cikin mayyun suna raye. Kaga kenan
labari bai kare ba. Domin zasu cigaba da gudanar da miyagun
ayyukansu har abada. Wannan labari ba shirme bane gaskiya
ce. Kuma yakan iya faruwa gareka, gareki, ko kuma garemu.
Ka tsaya kayi tunani, ka hanga, kuma ka auna sai ka rubuta
abunda ka gani a cikin wannan labari idan ba kamshin gaskiya
a cikinsa. Sanina ne cewa duniya ta canza daga yadda muka
santa zuwa akasin haka. Duk abunda baka tsammamin ya faru
shi yake faruwa, kuma duk abunda kake ganin zai faru shine
baya faruwa. Addu a itace takobin mumini kuma duk wanda ya
riketa to bazai tabe ba har abada. ALLAH ka tsaremu, ka
karemu daga sharrin duk wani mugu na boye dana zahiri.
Ameen.
THE END
Based on the novel by abdul king article.

Post a Comment

0 Comments