Part (1) kashi na farko
Written by
Abdul king article
DEDICATED TO :
KING BOY ISAH
AND
HUSNA BALA.
A cikin duhun dare na wata rana mai ban tsoro da kuma
bayyana tsintsar rashin jin dadi ga wani mutum wanda yake
daure tamau da kaca. Kai daga nin fuskarsa kasan baya cikin
hayyacinsa domin duk jikinsa tambon duka ne. A saman kujera
yake zaune yana nishi dakyar. Ko laifin me yayi aka daureshi da
wannan kacar??
Kai da gani kasan wannan bugu da aka yi masa na haukane
domin bako shakka wanda yayi sa baida imani ko tausayi. A
cikin wani kungurmin daji gidan yake. Duk da kasancewar
gidan na samane amma an masa tsinkar ban tsoro sai kuma
dajin daya tafke da wata kewa sanadiya tsit din da akayi.
Bakajin kome sai kukan tsuntsaye. Mutumin na a gidan sama
sai wata yar karamar fitila marar haske a cikin dakin da mutum
kan iya hangowa a tagar wajen dakin.
Kowa ya kawoshi wannan gida? Sannan laifin me yayi aka
kawoshi a gidan? Haka dai mutumin ya cigaba da nishi cikin
radadin ciyo da rashin jin dadi. Yana cikin haka sai ya daina
nishin. A wannan lokaci ya tsorata ainun domin kamar yanajin
tafiya an tunkaroshi. To anan jikinsa ya fara makarkata domin
ya fara tuno irin wahalar dayasha. Anan yaga mutum lullube da
fuska yazo wurinsa rike da takubba biyu. Yana tafiya yana goga
takubban ga kasa. Mace ce! To a mamakinsa me tazoyi
wurinsa? Dariya ta farayi daga nan sai ta fara
Goga takubban ga fuskarsa a hankali yadda bazai ji ciwo ba.
Wannan abu ya bashi mamaki ko me take shirin aikatawa???
Can sai ta debe mayafin daya rufe fuskarta. To anan wannan
mutumin da aka daure ya kalleta tsaf.
" ke. Raliyat kece haka? Dama kece sanadiyar wannan abu
daya saneni amma kin ban kunya yanzu duk soyayyar da
mukayi ashe zaki iya cuta ta?" maimakon ta bashi amsa kawai
sai tayi dariya sai kace mahaukaciya. "hmm! A da kenan."
injita. Wata yar karamar yuka ta zaro take ta daba masa a
cinya. Anan ya fara kururuwa saboda zafi.
"kiyi hakuri ki taimakeni. Na miki alkawari zan baki duk abunda
kikeso." ko saurararsa bata yiba anan ta zaro takobin ta fara
yankan hannunsa. Tun yana ihu har takai yayi shiru saboda
azaba. Anan ta tara roba domin jininsa ya shiga ciki. Daga nan
sai ta fara lasar jinin cikin annashuwa da walwala. Tana gama
shan jinin sai ta kama hannunsa guda tayi masa kamar yadda
tayima na farko. To a wannan lokaci sai ta tube kayanta ta
koma zigidir. ( naked) daga nan sai ta shiga cikin robar tana
wanka da jinin nasa. A haka ta wanke jikinta tsaf da jini daga
nan sai ta fito.
Wani murmushi ta masa na mugunta daga nan sai tasa
takobinta a cikin wuyansa. Da karfi taja. Daganan sai kansa ya
fadi rikicaa. Anan ya mutu ko shurawa bai yiba. Wata dariya ta
farayi na shaidanun mata.
" Sunana kenan raliyat. Wannan alkawari ne duk namijin da yayi
yunkurin yin soyayya dani to sunansa gawa!"
====================
Hamir, yazid, najib. Abokan juna ne kuma rayuwarsu iri dayace
wannan yasa abotar tasu tayi kwari. A kullum sukan yi yawo
tare da kuma sauran abubuwa na yau da kullum duk a taren.
Yauma kamar kullum hamir ya tashi firgigit daga barci
sanadiyar jifar tagar dakinsa da yaji anayi. Mika yayi sannan ya
tashi to anan ya dan leka tagar domin ganin ko meke faruwa.
Cikin rashin tsammani sai yaci karo da abokansa wato yazid
da najib ashe sune ke jifar tagar a kokarinsu na tasheshi. Yana
ganinsu sai yayi musu wata alama da hannu wai yana nufin su
bashi minti biyu zai fito. Cikin sauri ya kammala ya fito to anan
yaci karo da mamarsa a cikin falo (sitting room) tana bacci.
Wani tunani ne ya fado masa a lokacin da take masa wata
magana:
" Hamir kaji tsoron Allah ka daina zuwa night club domin a can
a kan hadu da hatsarin rayuwa. Sannan kuma shan waka da
kida (music) haramun ne kuma zama wurin da ake yinsu
haramun ne kaga kenan zuwa night club haramun ne."
"Haba ummi ya kina fadin haka? Nasan bakida tabbacin hakan
amma ji abunda kike fada." injishi.
Anan tayi murmushi ta kankaneshi a jikinta. Wato ka sani dana
duk abunda zan fadama banyin hankan sai na tabbatar da
abunda nake cewa. Ka sani cewa a cikin suratul luqman aya ta
shidda Allah na cewa: a cikin mutane akwai wasu da zasu siyo
maganganu na banza marar amfani wadanda zasu nisantar
dasu daga hanyar Allah. Wannan kalmar da ake cema (Lahwal
hadith) ibn mas'ood tareda halifofi guda hudu da kuma
sahabbai abun girmamawa da kuma tabi een, tare da imams
hudu da kuma yardaddun malaman musulunci tare da kaidodin
musulunci sun yarda cewa ana nufin (al-ghina ) ko kuma
music.
A wannan lokaci jikin hamir yayi sanyi anan ya kara kasa kunne
yana sauraronta: a cikin sahihul buhari vol 7, littafin mashaya
number ta 5590 abu malik al ashari ya bayyana cewa: akwai
wasu daga cikin mutanena dasu halasta zina, shan giya da
kuma amfani da ma'aazif ma ana kayan kida(musical
instruments) suna son su halastasu ma ana ba halas bane.
Kaga kenan daga ayar da kuma hadisin imams hudu sun yarda
da cewa shan waka haramun ne.
Annabi muhammad S A W yace yin waka da saurarenta
haramun ne. Kuma annabi S A W ya kulle kunnuwansa domin
yana tafiya yaji sautin kida na tashi. Annabi fa kenan. To ina ga
kai banza wanda ba kowaba??
Anan hamir ya kalli umminsa. A wannan lokaci idan mutum ya
kalleta kan ce yarinya ce sanadiyar an yi mata saurin aure.
Daga yau na miki alkawari bazan kara shan waka ba kuma
bazan kara zuwa night club ba. Injishi. Anan ta kara
rungumeshi cikin jin dadi.
" Da kyau dana. Haka nakeson ji"
To anan tunanin hamir ya katse, gashi yama mamarsa alkawari
na cewa bazai karaba. Yana cikin hakane sai yaji karar wayarsa
wato sako ya shigo ciki. anan ya duba sai yaga a cikin
whatsapp ne aka turo sakon. Wai ashe ya manta da zaiyi bacci
yabar data dinsa a sake. Yazid ne ya turo sakon:
" Haba hamir kayi sauri muna jiranka mana kafin lokaci ya kure"
Cikin saurin sai hamir ya masa replie: "ok ba matsala ganinan
fitowa"
Anan hamir ya kalli idanun umminsa ya gane cewa lallai bacci
takeyi saboda haka sai ya fara tafiyar sanda a hankali domin
kada ta jiya ta hanashi zuwa. A haka cikin rashin sani ya ci
karo da wani plate na tangaram dake saman dining table Wani
gangarowa plate din yayi da nufin fashewa cikin sauri hamir ya
rike sa da hannu daya. Anan yayi hamdala. Daga nan sai ya
aza sa a hankali. Juyawa yayi da nufin tafiyarsa kawai sai yaji
wani motsi. Ashe wasu plate biyu ne ke gangarowa da nufin
fadowa. Cikin himma hamir yayi hanzari da nufin taresu sai dai
kash ya makara. Ji kake tangarangasssssss. Duk sun fashe.
Anan ya juyo domin ganin ko umminsa ta tashi. Yana juyawa
sukayi ido hudu da ita. Anan gabansa ya fadi
duummmmmmm.
Wani murmushi yayi na jin dadi. Ashe tashin da tayi
idanuwanta a kulle suke ma ana tana a cikin bacci. Ta tashi ne
domin ta juya makwanci. Cikin sauri hamir ya fita a guje ya
manta daya kwashe plates din.
Fitarsa keda wuya sai yaga babu kowa. To anan ya fara dube
ko zai gansu amma ko alamarsu babu. Anan yayi kneel down
cikin rashin jin dadi. Can sai yaji kamar kukan mota daga nesa.
Anan ya mike da sauri. Tunaninsa ya bashi cewa kamar basu
dade ba barin wurin ba saboda haka ya fara gudu na tashin
hankali domin ganin cin musu. A haka yake gudun a saman titi
sai kace mota. Gashi titin tsit ba kowa saboda a tsakiyar
darene. Can sai yaji kamar motar ta tsaya. Daga nesa sai suka
fara kiran sunansa domin yayi sauri su wuce ashe sun
hangoshi ta bayan madubi.
Yana isa suka bude masa motar ya shiga. "Haba mun aza ka
fasa!" inji yazid. Anan yadanyi murmushi ba tare daya tanka ba.
Najib ne ke tuka motar. Haka suka nausa saman titi sai tsala
gudu sukeyi.
Zuwa wani dan lokaci sai suka iso wata unguwa mai yawan
gidajen sama. Kai da gani kasan unguwar masu kudice.
Mutane sai shagalinsu sukyi kamar ba dareba. To daganan
suka faka motar. A wani gida ne suka nufa wanda daga saman
kofar ansa rasiya night club. Tun daga nesa sukejin kida na
tashi sai kuma wasu yan mata da suke shawagi a wurin suna
wasanninsu. Yan matan na ganinsu sai suka tsiro musu idanu
sai kace sun sansu. A wannan lokaci su hamir ko kulasu basu
yiba iyaka sun bude kofa gidan sun shiga. To kafin su ida
shiga cikine wasu katti suka taresu. Anan suka fara cazasu
domin ko sun shigo da makami. Bayan an tantancesu sai aka
basu dama su shiga. A wannan lokaci maza da mata an game
wuri daya. Kowa ya kama gwaninsa. Masu rawa nayi masu cin
abinci nayi. Wuri ya gume bakajin kome sai sautin kida.
Cikin annashuwa su hamir suka fara kallon wurin daga nan
kuma sai suka samu wurin zama. Wani tebur ne a tskiyar sai
kujera uku a gefe. Anan suka zauna suna kallon yadda rawar
ke gudana. Kowane saurayi da yarinyarsa yake rawa cikin jin
dadi. Daga nan sai aka kawo musu ababan ciye ciye da shaye
shaye.
Ba a dau lokaci ba sai sukaga yan matan nan da suka gani a
bakin kofar shigowa gidan sun shigo. A nan suma suka samu
wuri suka zauna.
To a wannan lokaci hamir ya shagala da dube dube. Yana cikin
hakane sai ijiyarsa ta hango wata tauraruwa a cikin taurari.
Tafiya take tana rangwada kai kace jikinta ba tsoka. A haka ya
kura mata ido ko kyaftawa bayayi. Can ya ji saukar mazga a
kafadarsa kimisss. Ashe najib ne yayi haka domin ya karkato
da hankalinsa. "Amma kai banzane, me zakayi da bafulatana?
Yanzu idan ta gane kana kallonta ai kaja mana raini."
To anan hamir yayi murmushi tare da kara kallonta. "Wato ka
sani abokina wannan yarinyar ta hadu. Nasha ganin mata kala
kala amma ban taba ganin wadda ta kwanta a raina ba irin
wannan."
Daganan sai suka kyalkyace da dariya suna kallonsa "shegen
yaro wa daga ganin bafulatana har ta burgeshi!" inji yazid.
To anan ne yazid ya dan kalli yarinyar. "Kai ashe da gaskiyarka
ta hadu. Injishi." daga nan sai suka kura ma yarinyar idanu
domin ganin inda zata. A haka yarInyar ta cigaba da tafiya taku
dai dai cikin mamaki sai sukaga ta nufi wurin da yan matan
nan da suka gani a waje suke. To anan ne suka samu damar
kallon yan matan. "wow ahe sun hadu!"injisu.
Daga nan sai yarinyar ta samu wuri ta zauna kusa da yan
matan. Dukkaninsu sun hadu domin kowace fuska sai kyalli
takeyi. Anan suka fara hira irin tasu gashi kuma akwai dan
jayawa tsakaninsu da su hamir saboda haka basajin abunda
suke fadi. Can sai yarinyar ta tashi da nufin zuwa wani wuri to
anan hankakin hamir ya tashi domin baya gajiya da kallon
fuskarta. Cikin sauri ya mike ya bita su kuma su yazid sai suka
bishi da kallo. Tafiya takeyi yana binta cikin rashin tsammani
sai ta bace masa. Anan ya rasa inda ta nufa. Gashi karar music
duk ta cika masa kunne su kuma mutane sai faman rawa
sukeyi. Anan ya fara dube dube ko zai daice ya ganta. Yana
cikin hakane sai ya bugi kafadar wata yarinya to anan ya jiyo
suka hada ido da ita. Wani kallo ya mata naban mamaki domin
itace yake biya. Sai da suka jima suna kallon juna sannan sai
ya daure ya fara magana:" kiyi hakuri na bugeki cikin rashin
sani."
"Au ba matsala kada ka damu" injita. Anan ta sakar masa wani
murmushi mai dauke da alamar tambaya. Buummmmm.
Anan sukaji karar wani abu. Da karfi suka juyo domin ganin
abunda ke faruwa. Ashe yan sanda ne suka shigo kuma da
alamar akwai wanda suke hako. A mamakin hamir yarinyar na
ganinsu sai gabanta ya fadi. " Yi hakuri ina sauri sai wata rana"
injita. To anan ta fara gudu. Daga nan sai yaga yan sandan su
bita sai halbinta suke kamar suna son kasheta. To anan club ya
watse kowa ya ranta a guje domin tsira da rayuwarsa. To daga
nan shima ya fara bidar su yazid domin su tsere gida. To anan
ya gane cewa ashe ba ita kadai yan sandan ke halbi ba. Hatta
da abokaninta. Amma ko kadan a cikinsu ba wadda aka sama
domin gudu suke tamkar doki tare da bode musu.
Mamaki fa ya rufe hamir. Ko me wadannan yan mata sukayi
ake kokarin kashesu? To bayan ya fita club din ne sai yaci karo
dasu yazid suna kokarin tada motar. Anan ya bisu a guje. Suna
shiga motar suka tayar da kura.
A haka suka hau titi a tsiyace. Haka suka yita faman zazzaga
gudu har suka kawo unguwarsu. Daga nan suka aje hamir a
kofar gida suka juya zuwa nasu gidajen.
Da sauri hamir ya shiga gida. Yana shiga dakinsa ya kulle don
kada ummi ta gane cewa ya fita.
Kwan kwan kwan kwan kwan. Can sai hamir ya tashi wai ashe
safiya ta waye umminsa ce ke buga masa kofa. To bayan ya
bude sai ta shigo ciki. "Menene ya faru jiya?" ta tambaheshi. To
anan gaban hamir ya fadi domin a tsammaninsa ta gano inda
yaje.
Bakinsa na makarkata ya fara magana: "dama mun.........
To kafin ya iyar sai ta katseshi "jiya naga kamar an fashe min
plates kuma jiya kaine kaci abincin karshe to ya haka?" Can sai
sukaji kwas kwas kwas alamun tafiya na takalman mata. Anan
suka fara kallon kofar domin ganin ko waye zai shigo. Ashe
husnat ce kanwar hamir.
"Mama inaga mussa ce ta fashe plates din domin yanzu na
ganta a saman dining table kamar tana bidar abinci"
"Kinada gaskiya nima haka nake tsammani. Muje in gani" inji
ummi. Anan suka fita dakin.
To anan hankalin hamir ya kwanta domin yasan ummi bata
gano komeba. Wani brush ya dauko kirar (Oral-B) da maclean
dinsa. A hankali ya zuba maclean din sannan ya shiga toilet
domin goge baki.
To bayan hamir ya kammala shirinsa sai ya zo dining table
domin yin break fast. A wannan lokaci abincin gyare yake
sannan kuma su ummi jiransa kawai suke ya fito domin su
fara. Sai kannensa mata su biyu wato husnat da labnat. To
bayan sun fara cin abincin kawai yaji jikinsa yayi wani tsam.
Anan su husnat suka kyalkyale da dariya. Wai ashe wurin cin
abincin ne ya zuba tea a rigarsa. Anan ne kuma ya lura da
ummi na kallon hannunsa. Hakan ya bashi mamaki daga nan
sai ya kalli hannun nasa. To anan ne ya gano cewa wai ashe
ya samu rauni jiya da dare a wurin gudu a lokacin da suke
night club.
"Menene ya samu hannunka?" ummi ta tambaya.
Anan hamir ya bata amsa "na dan samu rauni ne jiya da
mukaje amusement park"
Anan ummi ta dan yi murmushi. To bayan sun kammala cin
abincin ne sai hamir ya hau bike dinsa domin zuwa wurin
shakatawa. Wannan wuri dai wani katon tekune wanda mutane
kan zauna a gabar ruwan suna shakatawa (beach) to anan
hamir ya fara gudu ba sassauci. Yana cikin hakane sai ya gamu
da wani abokinsa wai shi anasko. To anan anasko ya bayyana
masa cewa shima zaije beach din. Daga nan sai ya goya shi
domin suje tare.
To bayan sun isa wurin ne sai suka faka mashin din. A wannn
lokaci wurin cike yake da yan mata sai sha aninsu sukeyi. Daga
nan ne su hamir suka samu wurin zama suna kallon yadda
ruwan ke zallo suna yakatawa. Hira ce ta barke tsakaninsu
hadda dariya irin na abokantaka. Suna cikin hakane sai sukaji
an yi musu sallama. Bayan sun amsa sai hamir ya duba domin
ganin ko waye. Cikin mamaki ya mike tsaye. "Ke..... Wadda
muka gamu a night club ko?" ya tambaya.
"E nice, ko zan iya zaunawa?" "hmmm! Har sai kin tambaya.
Zauna mana"
To bayan ta zauna sai suka fuskanci juna. To a wannan lokaci
shi kuma anasco ya hango wata class mate dinsa da suka
dade basu hadu ba saboda haka sai ya tashi yabar hamir da
wannan yarinyar. Anan ya tafi wurinta domin su gaisa.
"Bayin tsammanin zamu kara haduwa ba."inji hamir.
Anan tayi murmushi " to me yasa kace haka?"
"Kafin nan dai zaki fadamin meye sunanki?"
Cikin dariya tace " meya kawoka wannn wuri?"
" To ai baki ban amsar tambayar dana miki ba. Amma duk da
hakan ni na kasance mutum mai son nishadi saboda haka
nakan zo nan domin shakatawa."
" wow! Kusan halinmu daya kenan." ta fada. "Sai dai yanzu ina
sauri zan koma gida"
"Haba keko. Tun yanzu? Amma xanso kiban hadin kai ko mayi
abota."
Anan tadan yi murmushi tare da kallonsa. Ba tare data tanka
ba kawai ta mike ta fara tafiya. Cikin sauri yasha gabanta.
"Haba yan mata ki tsaya mana. Ni a ganina don na roki
amincewarki a gareni ai ba komi bane. Amma yanzu idan
bazaki damu ba kiban numbarki. Idan yaso sai muyi magana a
waya tun da kina sauri."
"Haba malam ya kana wannan magana. Ni fa ban san kaba.
Kaga kuwa bazai yiwu ba kai tsaye na janyoka a jikina ba."
"E nasan da hakan amma kiyi hakuri ki fadamin koda sunanki
mana"
" Suna fa kace? Ba matsala tun da ka roka. Ni sunana raliyat.
Amma ka sani duk namijin da yayi yunkurin sayen zuciyata to
kamar yana kokarin sayar da ransa ne ga mahauta. Amma kai
ban san irin naka shirin ba. Ko kana da kudin sayen zuciyar
tawa tare da kariyar ran naka don kada mahauta su mar barna."
To anan hamir ya kalleta cikin mamaki " amma da zaki kara
bayani domin ban fahimci inda dosa ba"
Murmushi tayi tana mai cewa" kada ka damu dan samari zaka
gane nan gaba" Daga nan sai yaga ta nufi wata katanyar mota
jeep mai bakin glass. Anan ta shiga. To sai bayan tafiyarta ne
sai ya tuno da babbar mantuwar da yayi na kin tambayarta
dalilin da yasa yan sanda ke kokarin kamasu a jiya??
Daga nan sai yaji an kyalkyale da dariya. Yana jiyowa sai yayi
arba da anasko. "shegen yaro wai ina ka samo wannan fine girl
din? Ko dai itace wai bamu sani ba?" injishi.
Anan dai hamir yayi dariya tare da kara kallon motar su raliyat.
Daga nan sai suka hau mashin da zimmar dawowa gida.
To bayan sun dawo ne tunani ya rufe hamir. Anan ya rasa inda
zai sa kansa. Kyakkyawar fuskar raliyat ce ke bayyana a
gabansa a ko yaushe. Da abun ya dameshi sai ya dauki laptop
dinsa ya fito da ita waje ko zai dan sake. Yana cikin hakane sai
yaji an faka mota a kofar gidan. To anan ne yayi duba sai yaga
wani mutum ya fito daga cikin motar. Daga nan sai mutumin
ya nufoshi.
Bayan ya isone sai ya mika hamir hannu domin su gaisa. Bayan
sun gaisa sai mutumin ya zauna a kusa dashi.
" Sunana khalid. Ni detective ne a ofishin yan sanda na wannan
jahar wato police department. Daga nan sai ya nuna masa ID
CARD dinsa. Nasan zakayi mamakin ganina a wurinka amma
kada ka damu. Ba kamaka nazo yiba domin bakayi laifi ba
kuma bazanso ace kayi laifin ba. Amma ka sani kana gab da
yin laifin saboda wata mu amala da kakeson jefa kanka a ciki."
Anan hamir dai ya kara kassa kunne domin yaji ko me ke tafe
da wannan dan sanda.
"Inason in maka kashedi game da wannan yarinyar da kakeson
fadawa tarkonta. Bako shakka idan ka harda ka kai kanka ga
mahalaka to ba abunda zamu iya in banda addu a. Sannan
kuma ka sani cewa abokin barawo ta barawone saboda haka
ako yaushe zaka iya komawa irinta."
Anan hamir ya tari numfashinsa"ranka shi dade ni har yanzu
ban gane inda ka dosa ba!"
"Kada ka damu ai zaka sani." Daga nan sai fito da wani
kunshin nama a cikin leda." Kasan ko menene wannan?"
"E nama ne" inji hamir.
To dama akwai wasu kyanwowi a kusa dasu. Daga nan sai ya
jefa musu naman. Ai ko yana jefawa sai sukayi farat suka
danne naman kowa na dibar rabonsa.
"Kamar yadda kaga kyanwowi nan sun cinye naman nan to
haka kaima naman jikinka zai koma idan ka cigaba da mua
mala da ita. Saboda haka na barka lafiya."
Anan ya juya ya tafiyarsa yabar hamir cikin mamaki. Ko
meyasa yakeson in rabu da ita. Inaga shima yana sonta. To
menene take aikatawa da har bayason inyi mu a mala da ita?
Sannan ya akayi ya gano cewa ina sonta??
Haka dai hamir ya cigaba da tunani ba tare da sanin abun yiba.
Bayan sati daya faruwar hakan wata rana a night club. A
wannan lokaci hamir shi kadai ne yaje badon kome ba in
banda raliyat. Yana nan zaune yana kallon yadda ake cashewa.
Ga kidi duk ya cika masa kunne. A wannan lokaci fuskarsa ta
fara bayyana alamun damuwa saboda rashin ganin raliyat.
Can har ya yanke tsammani sai kawai yaga wasu kyawawan
mata. Watace a tsakiyarsu wadda duk ta fisu hadewa da
kwarjini. To anan hamir yayi murmushin farin ciki domin ta
tsakiyar itace wadda yakeson gani wato raliyat. A wannan
lokaci bata gansa ba domin hira ta dauke mata hankali. Daga
nan sai ya cigaba da shan lemunsa na kwalba tare da satar
kallonta.
Ana cikin hakane sai raliyat ta wani juyowa kamar an kyafatota.
To anan sukayi ido hudu da hamir. Murmushi ya mata amma a
mamakinsa sai yaga tasha toka ba alamun farin ciki a tattare
da ita. Daga nan sai tayi kamar bata ganshi ba kawai ta cigaba
da magana da abokanta. Wannan abu ya girgiza hankalin
hamir. Anan ya fara tunani kada dai ace raliyat bata sonsa.
Ana cikin hakane kuma sai ya nemeta sama ko kasa amma ya
rasata. Anan ya fara dube dube amma ko alamunta babu. To
daga nan ne ya dimauce. Wadda yazo don ita ta tafiyarta ta
barshi! A cikin bakin ciki ya mike da nufin komawa gida. Ya
fara tafiya kenan kawai sai yaji an zuba masa ruwa a riga. Da
karfi ya juyo domin cin mutunci ga wanda ya masa wannan
aika aika. To anan yayi arba da raliyat. Har zai yi magana sai
tayi wani shssssssss. Wai tana nufin yayi shiru. Daga nan sai ta
masa nuni daya biyota. A haka hamir ya bita. Suka yita wuce
mutane har saida suka kawo wani dan tebur mai kujera biyu.
To anan suka zauna. Daga nan ne ta fara magana:
"Bazan so in bayyana maka koni wacece ba amma da ace
kasan koni waye da bazakaso kayi mu a mala dani ba. Nasan a
dalilina kazo wannan club din. Wato ka sani yakai wannan
saurayi duk namijin da yayi yunkurin soyayya dani to bako
shakka rayuwarsa na cikin hatsari saboda haka ina baka
shawara da ka gaggauta janye wannan nufi naka kafin mai
aukuwa ta auku."
Murmushi hamir yayi tare da duban kyakkyawar fuskarta.
"Kada ki damu raliyat. Kome wahala kome rintsi ni ina tare
dake. Nasan da cewa wani ne ya miki barazana cewa idan
kikayi soyayya da wani to zai kasheshi. Amma wannan ba komi
bane idar har zaki ban hadin kai."
Anan ta dan kallesa "Kai kyakkyawa ne!" injita.
Wannan magana tadan sosa inda kema hamir kai kai domin ji
yake kamar an basa duniyar. Daga nan sai ya kara saurarawa
domin jin abunda zata fada.
"A cikin samarin danayi zamantakewa dasu ba irinka. Saboda
haka bazanso ace ka rasa ruhin kaba a kaina. Kasani cewa
idan ka cigaba da tunkarata to kome zai iya biyowa baya." anan
ta tashi ta tafiyarta.
Wannan magana fa ta girgiza hamir domin bai san abunda take
nufi dashi ba. A haka ya daure ya fita domin komawa gida.
====================
Kwanaki na shudewa lokuta na wucewa. Wata rana hamir na
zaune a falo yana kallon talabijin. Kawai sai yaji an nufoshi a
guje. Wai ashe kanwarsa ce labna ta yi wani laifi shine husnat
ta biyota. Tana zuwa wurinsa sai ta fada a jikinsa. "Yaya ka
gani ko" injita.
To anan ya tsayar da husnat wadda ta dauko bulala da nufin
zaneta. Saurarawa yayi domin yaji korafin kowace daga
cikinsu. Dariya yayi domin ya gane abun na yarane. To bayan ya
hukuntasu sun tafi kawai saiga yazid ya shigo gidan.
Cikin dariya suka kalli juna kafin yazid ya zauna. "Kai baba
akwai shagali agaban mu fa" inji yazid. To anan ya labarta
masa cewa yayarsa zatayi aure saboda haka yana gayyatar sa
bikin. Basu dau wani lokaci ba sukayi sallama.
Sati daya kafin biki ummi ta aiki hamir kasuwa domin a ranar
ne abbansa zai dawo daga malaysia. To bayan shigarsa
kasuwa ya gama duk abunda aka aikeshi siya. Kawai sai yaci
karo da raliyat a gabansa tana tafiya. To anan ya fara sauri
domin cimmat. To abunda ya bashi mamaki shine ita sassarfa
takeyi kamar bata son ya cimmata.
Sai da kyar yasha gabanta. "Haba raliyat ya kina gudu bazaki ko
tsaya mu gaisa ba?"
Anan ta kalleshi. "Nayi kokarin kubutar dakai daga halaka
amma kaki. Bako shakka lokaci yayi kira zuwa gareka saboda
kasancewarka mai taurin kai. Ina maka bushara da cewa daga
yanzu bazaka kara ganina ba sai ranar da zamuyi ban kwanan
karshe."
Wasu yan mata kawai yaga sun zo wurinta. Wani kallo suke
masa mai nuna alamar tambaya. Daga nan sai raliyat a bisu
suka tafiyarsu.
Wannan magana ta raliyat ta bashi mamaki domin tafiya yakeyi
yana tunaninta. (INA MAKA BUSHARA DA CEWA DAGA YANZU
BAZAKA KARA GANINA BA SAI RANAR DA ZAMUYI BAN
KWANAN KARSHE) to abun tambaya shine wace rana ce ta
karshe. Kuma ban kwanan menene zasuyi? A haka dai hamir
ya koma gida cikin mamaki.
Ana nan saiga ranar bikin tazo. Sai dai su hamir sai da dare
zasu shiga. To a cikin darene yazid ya dauko motar abbansa
domin zuwa da ita. Daga nan sai hamir ya kwace makullin
domin shi keson tukawa. To a wannan lokaci duk sun hadu
harda anasko da najib. Daga nan ne hamir yaja ragamar tukin
mota suka nausa.
Hamir na tuki cikin mamaki domin wata mota ce ke binsa
takiyin over taking sai binsa kawai take. Haka dai hamir ya
cigaba da tuki har suka iso wurin bikin. To anan ne yazid yasa
aka yi musu goma ta arziki domin an wadata su da dukkan
kayan ciye ciye da lamshe lamshe.
To bayan an gama biki akan hanyarsu na dawowa mai faruwa
ta faru. Wasu dawakai ne ke biyarsu mutanen dake saman
dawakan sai faman halbinsu suke da kibiyoyi. A haka hamir ya
rike matukin mota sai faman gudu yake a tsorace. Gashi basu
san ko su waye ke binsu ba. Suna cikin haka sai sukaji wata
oda. Ashe wata babbar mota ce ke shirin far musu. Anan hamir
yayi sauri ya juya motar anan ta fada daji a guje. Hakanan
motar ta cigaba da gudu har sai da tasha bishiya sannan ta
tsaya. A wannan lokaci hayaki kawai ne ke fita a motar. Daga
nan su hamir suka fito kowanensu sai tari yakeyi. To anan suka
duba suka ga bako shakka a cikin dokar daji suke. Ba yadda
basu yiba domin motar ta tashi amma ina taki. Suna cikin
hakane sai sukaji dawakai sun nufosu. To anan suka dauri
niyar gudu. A haka suka yita gudu ba ji ba gani kamar ransu zai
fita amma da sun tsaya su huta sai suji saukar kibiya.
Suna cikin wannan gudu ne anasko ya fadi saboda gajiya.
Hamir ne ya tsaya taimakonsa. Anan ya juya domin tallabosa.
Yana juyawa sai yayi ido hudu da wani daga cikin masu
dawakan dake biyarsu. Wannan mutumi lullube yake da wasu
kaya wadanda mutum bazai iya cewa mace ne ko namiji ba.
Sannan kuma fuskarsa a lullube take da wani rawani yadda
idanunsa kawai ake gani. To anan hamir yaji mamaki domin
kamar ya taba ganin wadannan idanun. Amma bazai iya tuna
ko wanene ba. Anan wannan mutumin yaja kibiya. Saitawa yayi
da wuyan anasko. Ji kake timissss. Sai da kibiyar ta fito ta
bayansa. Anan anasko ya mimmike jini na fita a bakinsa. Hamir
na ganin haka yaci taya ko juyawa bai yi.
A haka ya cigaba da gudu amma a mamakinsa bai ga
abokansa su yazid da najib ba. Yana cikin wannan gudu sai ya
ci karo da wani abu. To anan yayi wani tsalle sannan ya fado
kasa kansa ya bugi bishiya.
Yana tashi tsaye sai yaga dawakan sun zagayesa. Su kuma su
yazid an dade da kamasu. To anan wani mai doki yazo daf
dashi. Daga nan sai ya debe rawanin dake a fuskarsa. Anan
hamir ya ganeta. Ashe raliyat ce yarinyar da yakeso. Anan yaga
tayi shigar fulani.
"Ke... Raliyat!... Me kike shirin aikatawa haka?" inji hamir.
Anan tayi dariya kafin ta fara magana " Dama na gayama.
Hakan zai faru gareka idan ka cigaba da bibiyata. To wannan
rana itace nake gayama wato ranar da zamuyi ban kwanan
karshe." anan ta fito da kibiya ta saita dashi.
"kafin nan ke wacece. Kuma me yasa zaki aikata hakan?" inji
hamir.
Dariya tayi kafin ta bashi amsa. " Mune wadannan na cikin daji.
Dajin Mutuwa mai razanar da kowa. Kuma mune FULANIN
DAJI, fulanin da ba abota dasu balantana zamantakewa.
Sunana kenan raliyat. Wannan alkawari ne duk namijin da yayi
yunkurin yin soyayya dani to sunansa gawa. Saboda haka
kaima yanzu sunanka gawa.
FULANIN DAJI
Part ( 2 ) kashi na biyu
Written by
Abdul king article
TO PRINCE AND PRINCESS:
NAXEER HR
And
AMINA ABDULLAHI
RECALL:
A cikin na farko mun bayyana labarin wani saurayi waishi
hamir tare da abokansa da kuma kazamar dabi arsu ta zuwa
night club. Wanda akan hakane suka gamu da raliyat wato
yarinyar dake kashe duk saurayin daya ambaci kalmar so a
wurinta. A cikin na farko mun tsaya a inda raliyat ta kama
hamir dashi da abokansa a cikin daji domin kashesu.
THE BEGINNING:
A wannan lokaci idanun hamir sun fito waje domin yasan bako
shakka sunansa gawa. Raliyat ce ta dano kibiyar sannan ta
saita dashi. To kafin ta aiwatar da nufinta kawai sai taga
mutum ya fado a guje wurinta yana ihu. Lullube yake da rawani
shima. Sai dai nasa rawanin mai kaloli ne. "ku taimakeni mana.
Zasu kasheni." injishi.
To anan raliyat ta dakatar da halbin hamir. A wannan lokaci
hankalinta ya dawo ga wannan mutumin. " Suwaye kuma ina
suke?"ta tambaya.
To anan mutumin ya nuna mata hanyar daya fito. Dubawarta
keda wuya sai ta yan sanda marar iyaka a cikin kakinsu. Tun
daga nesa suke halbo musu albarusai ( bullets) domin hallaka
su. To anan raliyat ta gane cewa plan ne aka shirya da wannan
mutumin domin kamata. To anan ta kalli hamir tana mai cewa:
"kada kayi tsammanin ka tsira. Zan dawo. Kuma ka guji
haduwarmu dakai nan gaba. " to anan suka saki linzamin
dokinta da ita da mutanenta anan suka nausa cikin daji domin
tserema yan sanda. Su kuma yan sandan sai suka cigaba da
binsu suna halbinsu domin kamasu. To anan aka fara tsere.
Daga nan sai wannan mutumin ya debe rawaninsa. To anan ne
hamir ya ganeshi. Ashe khaleed ne. Wato detective wanda ya
iskoshi gida yana bashi shawara domin ya rabu da wannan
yarinyar raliyat. Mamaki ya kama hamir. Koya akayi yasan da
cewa suna cikin wannan bala i har yazo ya taimakesu? Daga
nan ne sauran yan sandan da basu bi su raliyat ba suka
kwance su yazid. To anan suka hau motar yan sandan aka kai
kowanensu gida. A wannan dare kowanensu bai runtsaba
saboda tunanin wannan abu. Daga nan kuma suka bar abun
cikin ransu tare dayin alkawari bazasu fadawa kowa ba. Shi
kuma anasko anan yan sandan suka wace dashi asibiti domin
duba lafiyarsa. Anan aka tabbatar musu da cewa yanada rai
sai dai ya samu rauni mai yawa. A haka khalled yayi jira iyakar
daren domin jiran farfadowar sa. To bayan ya fardado sai
khaleed ya bayyana masa cewa yanason yabar wannan abu
cikin sirri kada ya fadama uwayensa ya bari tukuna har sai sun
gama bincike. Anan ko anasko ya yarda da abunda yace.
***************
Tun da sanyin safiya yayi shiri domin fita office. A cikin wata
motarsa irin ta zamani ya fito A C sai hurasa yake. To bayan ya
iso ma aikatar sai ya wuce kai tsaye zuwa ofishinsa. Detective
khaleed ne. Xamansa keda wuya sai ga wani dan sanda ya
shigo.
Bayan ya sare mashi sai ya fara magana: "Yallabai jiya mun
samu damar kama daya daga cikin wadannan mutanen da
mukabi. Sai dai mace ce. Kuma bata magana ba yadda bamuyi
ba."
"ok ba matsala ka kaita dakin ganawa zan zo in ganta" inji
khaleed.
Ba a jima sai khaleed ya tashi domin zuwa wannan daki na
ganawa. Shigarsa keda wuya sai yaga macece bahillata
kyakkyawa ba abunda takeyi in banda dube dube a cikin
shigarta ta FULANIN DAJI. To anan yazauna daf da ita saman
kujera. Wani tebur daya shiga tsakiyarsu.
Wani kallo ya mata kafin ya fara magana. " Zanso kiban hadin
kai domin samun cikakken bayani game daku. Yin hakan shi zai
bamu damar sassauta hukuncin da zamu yanke miki. Yanzu
inaso ki gayamin ke wacece. Sannan a ina zamu ga yan
uwanki?"
Anan khaleed yayi tsaye yana sauraronta domin ta bashi amsa
amma sai yaji tsit. Haka ya ci gaba da magana har sai da yayi
mini talatin amma ko kallonsa bata yiba. Wannan abu ya
bakanta masa rai. To anan ya tashi fusace. Fuskarta ya duba
sannan ya shareta da mari har sau uku. " ke wace irin
mutuniyar banzace. Zakiyi magana ko sai na cigaba da dukan
ki."
Daga nan sai ta juyo ta kalleshi. Maimakon tayi magana kawai
sai ta kyalkyace da dariya. A haka ta cigaba da dariya sai kace
mahaukaciya. Wannan abu yaba detective khaleed mamaki
yanzu ace duk marin da tasha amma dariya takeyi. Gaskiya
akwai alamar tambaya game da wannan al amari. Daga nan
sai ya fita ya kyaleta.
Bayan yan kwanaki kadan sai hankalin hamir ya dawo domin
ya fara samun natsuwa da kwanciyar hankali.
Zaune yake a falo shi kadai yana kallon wani indian film saiga
labnat tazo wurinsa. Wai assigment aka bata na english shine
ta kawo masa ( write a story with the title he who give shall
never lack)
Anan hamir ya kalli wannan assignment cikin mamaki. Ba
turancin ke bashi tsoro ba sai dai yadda xa ayi ya kirkira labarin
ne aiki. To anan ya fara tunani domin yasan idan zai shekara
bakwai bazai iya hada wannan labari ba. " Hala yaushe akace
kuyi submitting? " ya tambaya.
" wai gobe da safe" kuma shine matsayin test. Ta bashi amsa.
Suna cikin hakane saiga yazid ya shigo tare da najib. To bayan
sun gane abunda ke wakana sai najib ya fara magana. " ai ko
inada wani aboki marubuci sai dai yanzu zaiyi wuyar gani. Na
kosan dana fada masa to yanzu zai hada wannan labari ya
aiko muku."
"To yanzu ya kenan?" hamir ha tambaya.
"kada ka damu bari in baka sunan page dinsa na facebook da
kayi searching ka danna like daga nan sai ka aika masa
message. Da kafada masa kai abokina ne zai gane domin ya
sanni sosai. To daganan sai ka fada masa irin labarin da
kakeso. Bako shakka zai yi sannan sai ya turoma."
" Amma muna godiya fa. To ya sunan page din?" hamir ya
tambaya. To anan najib ya bashi amsa. "Kayi seaching
(KINGARTICLE.NOVL) "
Daga nan sai hamir ya sallami labnat da zimmar cewa an jima
zai tuntubi marubucin.
To bayan fitarta ne yazid ya fara magana " kai baba akwai
matsala fa dazu ne muka fita shakatawa wurin ball. To akan
hanyar mu ne wasu mata suka fara binmu kuma gashi
bamusan ko suwayeba."
Hamir najin haka gabansa ya fadi duuummmmmmm.
Anan ya tuno da maganar raliyat: KADA KAYI TSAMMANIN KA
TSIRA DOMIN ZAN DAWO KUMA KA GUJI HADUWATA DAKAI
NAN GABA!
Hamir hamir hamir. Ashe najib ne ke jijjigashi domin ganin yayi
shiru sunata magana bai tanka ba. Cikin rashin sanin cewa
tunani ne ya rufeshi.
Can sai wayarsa tayi kara alamun cewa an bugo. Yana dauka
sai yaji muryar mace. To anan yazid da najib suka saurara
domin sanin ko meke faruwa. Kuma abunda ya kara daure
masa kai shine baya ganin numbar domin an sa no number
A cikin wayar aka fara magana: Nasan zakayi mamakin wannan
kira a wannan lokaci sai dai kash wannan ba komi bane. Dama
na bugone domin mu gaisa.
"ke wacece?" inji hamir
Dariya akayi kafin a fara magana: har ka manta dani kenan,
koda yake banga laifin ka. Dan adam da mantawa.
"Ko zaki gayamin inda kika samo numbata?"
E kwarai kuwa amma kafin nan ka sani cewa a shekara sau
daya nake buga waya. Kuma duk wanda ta fadama shine
abokina.
"Wace irin abota kike magana?"
Abota ta farauta. Idan ka nemoni kaine ka cinye. Idan na
nemoka to nice na cinye.
" kafin nan wace farauta kike magana?"
Dariya akayi kafin a bashi amsa: FARAUTAR RAYUWA!
Daga nan sai aka kashe wayar. To anan hamir ya kara rudewa
kafin kaceme gumi duk ya keto masa. Wannan wace irin
farauta ce ake cema farautar rayuwa. Haka hamir ya fara wasu
wasi a cikin zuciyarsa. Su najib sunyi kokarin sanin halin da
yake ciki amma ko kadan bai amsa ba. A haka ya kyalesu
daga karshe sukayi sallama.
*********************
Halayyar hamir ce fita tun da safe domin yin gudu a matsayin
motsa jiki. Yauma kamar kowace rana ya fita sai faman abinsa
yake a saman titi. A duk lokacin da yake wannan motsa jiki
wani farin cikine yake lullubeshi. Saboda haka bai damu da
kowa ba duk masu kallonsa suyi.
Yana cikin hakane sai yaji wani motsi bayasa. Da karfi ya juya
domin ganin ko meke faruwa. To anan yaga ashe wata motace
tsiyace ta ratso wurinsa tana masa oda domin ya jiye. Sai dai
kash..............
A cikin wata super market ta shigo sai faman sayayya take.duk
da cewa kayan masu tsada ne amma ko kadan bata damuba
sai aikinta kawai takeyi. Kai da ganin shigarta kasan mai
kudice. To bayan ta gama lissafa mata ta biya daga nan sai ta
fito.
Fitowarta keda wuya sai taji oda a saman titi. Juyowa tayi da
karfi domin ganin ko meke faruwa. To anan taci karo da hamir.
A guje motar take da nufin bangajeshi.
Firgigit ta farko. Wai ashe ummi ce ke mafarki. Wannan
mafarki ya tayar mata da hankaki saboda haka sai ta wuce da
sauri zuwa dakin hamir domin dubo lafiyarsa to a mamakinta
bayanan. Daga nan sai ta koma dakinta. Bata jima da zaunawa
ba sai taji ana bugo mata. Cikin sauri ta daga wayar domin jin
ko waye ya kirata. Anan taji muryar mace:
"Ana so kiyi gaggawar zuwa asibitin...... "
Daga nan sai aka fada mata asibitin da akeso taje da kuma
dakin. Ba yadda ummi bata yiba domin a fadamata ko meke
faruwa amma anki. Daga karshe dai haka ummi ta yi shiri
sannan ta hau motarta domin zuwa inda aka umarceta.
Aiko shigarta keda wuya taci karo da hamir ana faman sa
masa akwatin oxygen. To anan gabanta ya fadi. Take ta tuno
da mafarkin da tayi. To anan ne wata nurse ta karaso wurinta
tare da bayyana mata cewa hamir ya samu accident a wurin
gudunsa na motsa jiki. Haka kuma ta samu numbarta ne a
cikin wayarsa.
To anan ne ummi ta tsaya har saida aka kammala masa aiki.
Daga nan saita bugama daddy domin yasan halin da ake ciki.
A lokacin da daddy ya shigo tare yake dasu husnat. " sannu
hamir" inji labnat. Bai amsaba saboda raunin dake kansa yana
masa ciwo sosai. Iyaka dai yayi mata alama da hannunsa na
cewa da sauki. To daga nan ne abokinsa anasko ya shigo
dubashi. To bayan ya gaisa dasu ummi sai ya fara yi musu
hira:
"Gaskiya daban mamaki wannan abun daya faru domin a titi
guda muke gudun amma shi kadai ne abun ya sama. Amma ni
a ganina har da gangancin mai motar. Domin da gangan ya
bankeshi kuma ko tsayawa bai yi ba balantana ya bada hakuri."
haka dai su ummi suka cigaba da saurarensa suna mamakin
ko waye ke kokarin kashe musu da? To bayan hamir yayi yan
kwanaki a asibiti sai aka sallamoshi.
===========================
A zaune yake saman wata kujera mai juyawa dashi yadda
yakeso. Rike yake da jaridar (aminiya) da ganin fuskarsa kasan
ba lafiya ba domin ta nuna alamar damuwa a tattare da ita.
Farkon shafin jaridar an yi hoton wasu gawawwaki da aka
tsinta ba kyan gani gashi kuma ba a san ko su waye suka
aikata hakan ba. Detective khaleed yasha ganin irin wadannan
matsalolin amma na wannan lokaci sun fi hirgitashi. To yana
cikin wannan tunani sai ga wani dan sanda ya shigo office din.
"Sir mun gano kamal. Ashe ba a kasheshi ba. Sai dai yana cikin
wani mawuyacin hali domin baya gane kowa. A jiya muna cikin
patrol muka tsince shi an yadda shi a walakance."
" Ka kaishi dakin ganawa zanzo in ganshi" inji khaleed. To anan
dan sandan ya juya ya fita.
Bayan mintuna kadan sai ya shiga dakin ganawa to a wannan
lokaci dan sandan na ciki. Khaleed na ganin kamal tausayi ya
kamashi. Domin duk ya canza ba kamar yadda ya sanshi ba.
Bayan yazo daf da shi sai ya zauna.
"Kamal ko zaka iya fadamin ko su waye suka yima wannan
aika aikar?" anan kamal ya kalleshi cikin rashin sani. Maimakon
ya bashi amsa kawai sai ya fara dariya. To anan khaleed yayi
mamaki domin duk abunda yakeyi shine wannan yarinyar da
suka kama ta farko takeyi.
"JINI. JINI. JINI" inji kamal.
Anan khaleed yayi mamaki ko me yake nufi da jini? Ahaka
khaleed ya cigaba da tambayarsa amma baya fadin kome sai
jini. Kuma wannan abu shine itama wannan yarinyar ke fadi.
Wato jini. Duk abunda aka ce musu sai dai su amsa da jini.
To anan detective khaleed tausayi ya kamashi. Ko waye
sanadin yi musu wannan abu? Ya tambayi kansa. Amma ko
menene dole yanada nasaba da wadannan matan da suka
kama su hamir. Anan ya fara tunani. To amma su waye
wadannan matan kuma me yasa sukema mutane haka? Anan
dai ya cigba da tunani shi kadai.
Daga nan kuma sai ya tuno labarin kamal a lokacin da yana
lafiya lau:
Kamal dai dan sanda ne mai kwazo da hikima kuma shine
babban abokin khaleed domin a kullum suna tare. A kowane
lokaci ana yawan tsintar gawawwakin yara samari. Saboda
haka wannan ya mutukar bakantawa kamal rai. To anan yayi
shawara da abokinsa wato kamal domin yana so ya fara
bincike ne akan al amarin. Anan kamal ya bashi kwarin gwiwa
dari bisa dari. To daga nan ne sai kamal ya fara zuwa wazajen
da samari ke taruwa suna sheke ayarsu. Hakan ya cigaba dayi
har wata rana yaje night club. To zuwansa night ckub yayi
mutukar amfani domin anan ya samu kadan daga cikin abunda
yake nema.
Wata yarinya ce bahillata fara kyakywa. Tun a farkon ganinta
kamal yaji bai yadda da ita ba. Saboda haka sai ya fara daukar
ta hotuna a sirrance batare data sani ba tare da abokanta.
To wata rana zai je night club din. To a wannan lokaci yana a
cikin motarsa kawai sai ya fara jin ana nishi a can gefen daji.
To anan ya faka motarsa. Fitowa yayi ya nufi inda yakejin
wannan nishi. To bayan ya labe sai ya gano cewa ashe wani
saurayine aka daure tamau da kaca. Wadannan yan matan
fulani da yake gani a night club wadanda yama hoto sune ke
tsaye gewaye da mutumin. Koina jikinsa dukane. Daga nan sai
yaga wata wadda duk tafisu kyau ta zo wurin mutumin.
Kallonsa tayi tare da yi masa dariyar kyeta. Daga nan sai ta
fara magana " Sunana kenan riliyat duk namijin da yayi yunkurin
yin soyayya dani to sunansa gawa. Saboda haka kaima yanzu
sunanka gawa" anan tasa takobi ta debe masa kai. Daga nan
sai ta tara roba jininsa na shiga ciki.
Wannan abu ya bashi mamaki. Wato ita duk namijin da yake
soyayya da ita sai ta kasheshi to amma me yasa? Daga nan sai
yaga sun hau dawakansu sun nufi daji. To bayan tafiyarsu ne
kamal ya koma ofishinsu na yan sanda. Anan ya bayyana musu
abunda ya gani tare da hotunan yan matan daya dauka. To
anan ne khaleed ya bada umarni zasu dinga zuwa night club a
duk lokacin da suka gamu dasu to zasu kamasu. Daga nan
kuma sai khaleed ya dauki aniyar yima duk wanda ya gani da
wannan yarinyar wa a xi domin ya rabu da ita kafin ta
hallakashi.
To wata rana bayan an gama night club din sai kamal yaga yan
matan sunja wani mutumi sai tafiya suke cikin annashuwa. To
anan ya fara kallo ina zasu. Kawai sai yaga sun shiga mota
sunja. To anan shima ya shiga motarsa ya bisu. Gudu sukeyi ba
sassahci to anan yaga sun nufi hanyar da zata fitar dasu daga
garin wadda daga ita sai daji. To anan ya bugama khaleed ya
sanar dashi inda yake domin ya turo yan sanda. Haka ya
cigaba da binsu har suka shigo wani kungurmin daji. To bayan
sunyi nisa cikin dajin sai suka kawo wani katon gida. Bayan sun
bude motar. Abunda ya bashi mamaki shine wannan mutumin
daya shiga motar lafiyarsa kalau sai yaga sun tallaboshi kamar
gawa. Ko me suka yi masa? Ya tambayi kansa.
To anan ya bisu har cikin gidan domin ganin abunda zasuyi ga
wannan mutumi. To anan ya kara kiran khaleed ya sanar dashi
inda yake. Yana cikin wayar ne sai yaji an rike shi rikon
kwarai.yana juyowa sai yaga ashe yan matan ne suka ganshi to
anan suka damkeshi. Ba yadda bai yi ya kubce ba amma ya
kasa. Daga nan sai shugabarsu taxo. "Hala dawa kake waya?
Ta tambayeshi.
Anan ya tofa mata miyau a fuska.
Anan ta mulmule hannunta. Ji kake gibbbbbbbbb.
To daga nan kamal bai kara sanin inda yakeba. Amma a cikin
wayar khaleed duk yaji abunda ke faruwa saboda haka yasan
an kama kamal. Anan aka turo dubban yan sanda domin su
duba wannan gida amma sama ko kasa gida ya bace bat ba a
san inda yake ba. Tun daga wannan ranar da aka kama kamal
basu karajin duriyarsa ba sai yanzu da aka ce an ganoshi.
To anan tunanin Khaleed ya katse. Daga nan sai ya tashi ya
koma office dinsa ya cigaba da ayukansa.
Hamir hamir Hamir. Abba ne ke kiransa. Kamar akwai wani aiki
da zai sa shi. Bayan yazone sai abba ya mika masa kudi. Don
ALLAH yi sauri ka siyomin maltina kwali daya. To anan hamir
ya hau mashin dinsa ya nufi kasuwa.
Bayan ya gama xai dawo kawai sai yaji mutane na direwa suna
ihu. Wasu kibiyoyi ne su biyu jere da juna suka nufoshi. Cikin
sauri ya wani kaucewa. To anan yaga wani mai doki ya nufoshi.
Sai faman sako masa kibiyoyi yake. To anan hankalin hamir ya
tashi bai ma tsaya ta kayan da aka aikeshi siya ba. Juyawa
kawai yayi ya taar. To anan mai dokin ya cigaba da binsa.
Mutane sai kallon ikon Allah suke.
A haka suka cigaba da gudu har takai shi mai dokin ya sauko
ya fara binsa da kafafu. To anan suka hau saman runfunan
kasuwa. Fada nan yanki nan. A duk lokacin da hamir ya duba
sai yaga ana binsa kuma kibau ne ake halbo masa ba
sassauci. To suna cikin hakane sai ya hango wata katanyar
mota. To anan hamir yayi wani tsalle ya fado saman motar. Shi
kuma wanda ke binsa sai yayi tsaye domin bazai iya dirowa
ba.
To anan ne ya gane cewa mace ce keson kasheshi. Amma
fuskarta a lullube take bazai iya gane ko wacece ba. To bayan
ya isa gidane ya bayyana ma abba abunda aka yi masa naban
mamaki.
Ba a dede ba kuma yana zaune a dakinsa shi kadai sai aka
bugo masa. Anan yaga an rubuta (no name)
Bayan ya dauka sai yaji muryar mace ta fara magana. " slm
matsoraci. Ya akayi dazu ka gudu baka tsaya kaji sakon daya
kamata kajiya ba?"
Wane sako kuma? Ya tambaya.
Sakon soyayyarmu mana. Kasani cewa duk wanda ya ambaci
kalmar so ga dan uwansa ya kamata yaji amsa mai kyau. To
amsar ce nakeso in baka. Injita.
Ke wacece wai?
Anan tayi dariya kafin ta fara magana: " kada kayi tsammanin
cewa wai don ka samu nasara shine karshen farautarmu. To
farauta yanxu aka fara. Idan har bamu sameka ba. To xamu
samu nakusa gareka.
Daga nan sai aka kashe wayar. A wannan lokaci hamir ya fara
dana sanin kin bin maganar mahaifiyarsa a lokacin da take
masa wa azi akan ya daina zuwa night club. Gashi abunda ya
jawoma kansa.
Bayan kwana uku da faruwar hakan saiga wani biki yazo. To a
wannan lokaci kanwar mahaifiyar hamirce zatayi aure. Yazid
da najib basu samu damar halittar wannan biki ba saboda wata
larura. Sai dai abokinsa anasko yazo.
To bayan anyi shagali an watse sai hamir da bidi anasko sama
ko kasa amma bai gansa ba. Gashi dare yayi kuma yanason
yazo gida. Anan yayi tsammanin kila ya tafiyarsa. Saboda haka
ya tuko mota ya kama hanya shi kadai. To yana cikin tafiya ne
sai ya kawo ga wani junction inda yan sanda ke duba motoci.
To anan ya parka domin shima su duba tashi. Bayan layi ya
kawo garesa sai aka umarci daya bude bayan motar. Aiko yana
budewa sai yan sanda sukayi caa akansa. Anan suka fitto dashi
da karfin tsiya kafin daga baya su sa masa yankwa. Wai ashe
gawar abokinsa anasko suka gani a bayan motar.
Kowa ya kasheshi? To anan aka kama hamir da zargin cewa
shi ya kashe anasko. Kafin daga bisani labari ya watsu a gari
su kuma yan jarida dama sun samu abunda sukeso. Yazid da
najib basu yarda da zancen ba ko kadan sai dai ba yadda suka
iya domin zancen naga hukuma. Haka itama ummi.
To bayan sati daya da daure hamir domin yin bincike akanshi.
Sai kuma wani sabon al amari ya kullu wai wasu da ba a san
ko su waye ba sun shigo har gidan yari sun sace hamir sun yi
tafiyarsu dashi. To abun tambaya shine su waye suka sace
hamir? Kuma su waye keda sanadin kashe anasko?
TO BE CONTINUE......
FULANIN DAJI
Part ( 3 ) kashi na uku
Written by
Abdul king article
TO THE ROYAL QUEEN:
FIRDAUSI MUHD
AND BESTY:
UMAR D UMAR
Domin ganin farkon labarin yi searching wannan page:
( kingarticle.novl )
RECALL:
A cikin na biyu mun bayyana yadda raliyat tayita kokarin kashe
hamir domin biyan bukatarta. Sai kuma sharrin da aka yi maaa
na sa masa gawar abokinsa anasko a cikin mota wanda daga
karshe akace shi ya kasheshi. Mun bayyana yadda aka kaishi
gidan yari da kuma yadda aka saceshi a gidan. Ko su waye
kedasa hannu a wannan aika aika?
THE BEGINNING:
A zaune yake bisa wata kujera sai ayyukan yau da kullum yake.
Yana cikin hakane sai ga wani dan sanda ya shigo office din.
Wannan ba kowa neba in banda detective khaleed.
" ranka shi dade kayi bakuwa" inji dan sandan.
" ok gaya mata ta shigo" inji khaleed
To bayan ta shigo ne sai khaleed yaga sabuwar fuska wadda
bai saba gani ba. Hakan ya bashi mamaki amma bai damu ba
domin yasan da cewa kome ya kawota ai zata bayyana. To
bayan sun gaisa ne sai ta samu wuri ta zauna. Mace ce
kyakyawa abun kallo sanye da wani gilashi fari fat. Daga nan
sai ta fara magana:
"Nasan da cewa bakasan koni wacece ba kuma dole hakan ya
baka mamaki ganin na shigo office dinka. To da farko dai
sunana hajiya zubaidat, nice mahaifiyar hamir wato yaron da
case dinsa na hannunka. Gaskiya banga laifin kuba a
matsayinku na yan sanda da kuka kamashi domin hukunta shi.
Wannan yayi dai dai domin duk wanda yayi barna
sakamakonsa shine hukunci.
Amma ka sani cewa hamir baya daya daga cikin jerin
mabarnata wadanda hukunci ya dace dasu. Kada kayi
tsammanin ina fadin hakane domin son zuciya. Wannan
gaskiyace nake fada domin inada tabbacin abunda nake
cewa."
Anan khaled yayi murmushi kafin ya fara magana " idan na
fahimci abunda kika fada wato kinaso ki bayyana mana cewa
hamir bashi ya kashe anasko ba. To amma wannan daban
mamaki to idan bashi bane me ya kawo gawar cikin motarsa?
" Ba motarsa bace! Mota tawa ce. Kuma gawa da kake
magana akai shi bai san ta inda ta shiga motarba." inji
zubaidat.
"Na yarda da zance ki. Inji khaled. Sai dai ki sani cewa bazamu
gasgata hakan ba har sai in mun kammala bincike akanshi.
Kuma abun bakin ciki shine shigowar da akayi har gidan yari
aka sace shi bayan an illata mana yan sada da dama. Gashi
bamusan ko su waye ba haka kuma bamusan halin da
rayuwarsa take ciki ba. Saboda haka a yanzu bazamuyi amfani
da maganarki ba har sai mun ganoshi. Sannan mun gano
wadanda suka saceshi da kuma dalilinsu na yin hakan idan
yaso sai mu baki gaskiya."
Daga karshe dai sunyi sallama sannan kowanensu ya kama
harkokin gabansa.
Wata mota ce kirar hilux tare da wata karamar mota sai faman
gudu suke a cikin dajin nan mai ban tsoro. To a cikin hilux din
wani saurayi ne a daure tamau. Wannan ba kowa neba in
banda hamir. A hankali ya fara farfadowa daga dogon suman
da yayi. To bayan ya farka ne sai abun ya bashi mamaki ko me
ya kawoshi cikin wannan mota? Abunda kawai yake iya tunowa
shine:
A zaune yake cikin gidan yari (prison) to a cikin wannan dare
ba dadi yaji sosai ba domin detective khaleed yayi masa
tambayoyi akan gawar abokinsa wato anasko da aka gani cikin
motarsa. Harda ikirarin idan bai fadi gaskiya ba to hukunci mai
tsanani zai hau kansa.
To da misalin karfe biyu na dare ne ya fara jin koke koke a
cikin gidan. Wannan abu ya tayar masa da hankali domin ji
yake kamar an kawoma yan sandan dake gadinsa hari. Ana
cikin hakane sai yaga wasu mutane sun bude dakin nasa. Anan
suka zuba masa wasu ruwa to tun daga wannan lokaci ba kara
sanin inda yakeba sai yanzu daya farfado.
To anan ya duba motar yaga ashe wadanda ke cikinta duk
mata ne.
To bayan an tashi daga office ne sai khaleed ya shiga motarsa
domin komawa gida. Bayan ya isa gidan sai matarsa zeenat ta
kawo masa ruwa mai sanyi domin ya jika makoshi kafin ta
kwashe abinci. To anan ta zauna daf dashi domin ta debe
masa kewa amma a mamkinta yau ba kamar kullum ba domin
fuskarsa kwabe take ba alamar farin ciki a tattare dashi. To
anan ne ta nemi ya sanar da ita damuwarsa aiko bai yi
gardama ba ya bayyana mata abunda ke damunsa. Daga nan
sai ta fara bashi shawara:
" wato ka sani mai gida wannan case ne babba. Kuma idan
bakuyi wani abu ba to komi kan iya faruwa ga wannan yaro da
aka sace. Saboda haka ina baka shawara da ka dauki runduna
domin kawo karshen wadannan yan ta adda."
"Wannan hakane zeenat. Na dade ina wannan tunani saboda
haka yanzu lokaci ne da wannan magana taki zatayi amfani
domin gobe zan dauki rundunar yan sanda zamu fantsama har
sai mun ganosu.
===================
Haka wadannan motoci suka cigaba da gudu ba kakkautawa.
Can sai suka tsaya. To bayan tsayawarsu ne sai aka fito da
hamir domin yasha iska. Can wata dabara ta fado masa. Daga
nan sai ya fada musu cewa zai yi fitsari. To anan suka kwance
shi. Daga nan sai ya zagaya domin biyan bukatarsa.
Kamar da gaske. Zagayawarsa keda wuya sai ya balle anan
yace kafa me naci ban baki ba haka hamir yayita gudu ba ji ba
gani domin tsira daga halaka. Yana cikin wannan gudune sai
yaji an kai masa wani naushi a fuska ji kake gibbbbbb. Saboda
karfin naushin sai da ya fadi yana dubawa sai yaga raliyat a
gabansa tare da wasu mata sun lullube jikinsu baka ganin
kome sai idanunsu. Anan mamaki ya kamashi koya akayi suka
cimmasa?
"Wawa. Kai tsammaninka zaka iya guduwa domin mun kwance
ka? To ka sani cewa xaka kasance tare damu har sai lokacin
da muka ga dama muka kyaleka." inji raliyat. To anan ne ya
gano cewa ashe su raliyat ne suka saceshi a gidan yari. Daga
nan sai suka iza keyarsa gaba bayan sun daureshi tamau.
Al amarin detective khaleed kuma kamar yadda yace ya samu
damar tara rundunar yan sanda daga nan sai suka cika wasu
motoci biyar sannan suka nausa domin neman barayin da suka
sace hamir. Ba kowace hanya suka nufa ba sai dajin nan da
kamal ya misalta musu a lokacin da yana lafiya lau.
Hamir kanyi mamaki wadannan mata domin sun kasance duk
abunda namiji keyi sukan yi kwatan kwacinsa. To a wannan
lokaci dare ya fara rabawa saboda haka kowa censu ta samu
wuri domin kishingidawa. Anan hamir yaji dadi domin yasan
da cewa wannan dama ce ya samu ta kara guduwa. Sai dai
kash yana cikin wannan farin ciki sai ya koma akasinsa domin
raliyat ce ta zauna daf dashi.
Anan ta dauko tuffa(apple) daga nan sai ta faraci. Ko kallonsa
batayi ba balantana ta masa tayi. Gashi kuma a wannan lokaci
yunwa ta kawo masa har ga makoshi. Cikin sauri ya fizge
apple din sannan ya fara ci. Kallonsa tayi ba tayi cikin
murnushi ba tare da ta tanka ba. Sai da ya gama ci sannan sai
yaga ta hankada jakarta sannan sai ta dauko wani ta fara ci.
Abun ya fara shi mamaki. (wato dama akwaisu da yawa) ya
fara tunani. Daga nan sai ya amshe jakar. Anan yasa hannunsa
har kasa amma bai ji kome ba.
Kallonsa tayi cikin dariya daga nan sai ta amshe jakarta. To a
wannna lokaci ta gama cin apple din. Daga nan sai ta sa
hannunta a jakar. To a nan hamir ya kura mata ido yaga
abunda zata fikkai domin yasan ba komi ciki. Cikin mamaki sai
yaga ta fito da wani apple. To anan abun ya bashi mamaki
domin a lokacin da yasa hannunsa kome bai jiya ba. Daga nan
sai ya amshe jakar ya laluba amma wayan kome babu.
Cikin dariya ta fara yi masa magana " kabar wahalar banza.
Idan zaka kwana kana lalube kome bazakaji ba. Ni kadai ne
nake da ikon da zan laluba wannan jakar in dauko abunda
nakeso.
"Wannan wace irin jaka ce?" ya tambaya.
" wannna jaka ce mai tarihi. Ummita ce taban ita a lokacin da
tana raye. " daga nan sai ta jeho masa apple biyu sannan ta
tashi ta nufi wata yarinya data nufosu. A wannan lokaci ta
tsayu da wannan yarinyar sai wata magana sukeyi can ciki
kamar basa son kowa ya jiya.
Anan hamir ya fara tunanin wannna ko wace irin jaka ce?
Haka rundunar detective khaleed ta cigaba da gudu na tsawon
lokaci kafin daga bisani su yadda zango a wani wuri. To anan
ne suka kafa tantuna domin bacci a ciki. To bayan kowa ya
shiga nashi tanti sai khaleed ya fito waje kamar akwai inda
yakeson zuwa. Ya fara tafiya kenan sai yaji an masa magana.
"ranka shi dade ina zaka a cikin wannna dare?"
To anan ya juyo sai yayi arba da abokiyar aikinsa wato sakinat.
Murmushi yayi kafin ya fara magana "ai bazan iya bacci ba zan
so na duba wannan dajin tukuna."
"E to muje na raka ka!" inji sakinat.
"Aa, kada kice haka, kije kiyi bacci mana. hala ina su balkisu?
ya tambaya.
"Wadannan kasan ragwayene duk sun dade dayin bacci. Injita.
Ba yadda bai yi ba don kada ta bishi amma ta dage sai dai suje
tare saboda haka ya kyaleta.
Kamar yadda hausawa sukace tafiya da aboki tafi dadi.
Wannan bako shakka haka yake domin su khaleed sunyi tafiya
mai nisa amma ko kadan basu sani ba. Gashi darene iyakar
dare amma ko tsoro basaji sai kusa kai suke cikin daji.
"Ahhh na gaji bari na dan huta kafin mu karasa." inji sakinat.
Anan ta zauna bisan wani dan icce daya bargace. Daga nan sai
khaleed ya zauna shima.
ALLAHU AKBAR. Wannan magana haka take duk inda namiji da
mace suka kadaita to na ukunsu shine shaidan. Zamansu keda
wuya sai sakinat ta fara yi masa wani kallo. Wanna kallo bana
komi bane in banda shawa. Shawa mai tsanani domin a
hankali jikinta ya fara girgiza sai kace mai jin sanyi. Sai wani
nishi da takeyi can ciki kamar mai jin zawo.
Wato ki sani cewa sakinat idan har muka samu nasarar kama
wadannan barayin to zanji dadin da ban taba jiba domin a
yanxu haka cikin rudani nake. Daga nan sai khaleed yayi ta
zazzaga surutu amma a mamakinsa bai ji ta amsa ba. Daga
nan sai ya juyo domin yaga lafiya. To anan ne ya lura da kallon
da take masa. Daga nan sai jikinsa yayi wani sanyi. Cikin
mintuna kadan shima yabi layi.
Anan sakinat ta tashi tsaye. Hular dake kanta ta cire ta yar.
Daga nan sai ta ajiye fitillun da take dauke dasu. Can kuma sai
ta cire rigar daje jikinta ta tsaya daga ita sai yar ciki. To a
wannan lokaci kafufuwan khaleed sun fara cika saboda ganin
surar sakinat.
Tana zuwa wurinsa jikinsa ya kara mutuwa domin ko magana
bazai iyaba. Gashinsa ta fara shafawa kafin daga bisani tayi
wani kwanto kasan kafafuwansa. To kafin a fara warwasawa
sai wani dan karamin tunani ya fado ma khaleed:
A wannan lokaci yana tare da matarsa zeenat. Khaleed wai
wace mace ce kafiso a duniya?" ta tambaya.
"E to matan da nakeso gaskiya sunada yawa." injishi.
To anan zeenat ta bata fuska.
Haba sweetheart ya naga kin bata fuska harda kuma juya min
baya. Ya tambaya.
"Ai kaima kasan bai kamata ka fadi haka ba."
"Haba sweety tambayata fa kikayi kuma na baki amsa.
To yanzu sai ka gayamin matan naji. Inji zeenat.
" Ta farko dai itace wadda jiya ma saida na kai mata ziyara
domin duk abunda namiji keso ga mace sai da na samu a
wurinta."
Zeenat najin haka sai ta tashi da nufin tafiyarta. Anan khaleed
yasha gabanta. " Ina xaki kuma? Ai ban kare ba."
"to gayaamin wacece ta biyun kuma?"
"Ita kuma ta biyun mun hadu a facebook ne daga nan sai na
amshi numbarta har muka kulla soyayya da ita!" injishi
Dungujeshi zeenat tayi da nufin ta bar masa dakin saboda
bakin ciki. Anan khaleed yayi ta lallashinta har ya ciyo kanta.
Daga nan sai ya goyota har xuwa inda gadonta yake.
Ajiyeta keda wuya sai ta fara fada. "Ni bazan iya zama da kai
ba. Yanxu inaso ka gayamin matsayina a wurinka kuma
wadannan matan su waye?"
Anan khaleed yayi dariya kafin ya fara magana.
"Au dariya ma kakeyi kenan?" injj zeenat.
"Wato ku mata kushinku yayi yawa. Shi yasa ciyon zuciya ke
illata ku da kuma yawan tunani. Da farko dai kin tambayi
matsayinki. To matsayinki a wurina shine har yanzu kina nan
matata. Ita kuma wannan matar dana gaya miki ta farko ke
tunaninki waye keda wannan matsayi. Na fifita wannan mata
da kowa saboda itace mahaifiyata. Ita kuma ta biyu wadda
muka hadu a facebook ai kece. Idan zaki iya tuno farkon
haduwarmu ai a facebook ne. Daga nan sai muka kulla
soyayya."
Zeenat najin haka sai ta kyaljyale da dariyar farin ciki anan ta
rungumeshi suka cigaba da dariyar tare.
"Khaleed zaka yimin wani alkawari?" ta tambaya.
"E fadi bukatarki inaji"
Xaka iya daukar min alkawari cewa bazaka kulla kowace
macce in ba niba?
E na miki.
Kuma zaka iya daukar alkawari cewa baza yimin kishiya ba?
E na miki.
Kuma zaka iya yimin alkawari cewa bazaka taba cuta ta ba har
wata mace ta baka shawa ka auka mata?
E na miki.
Daga nan sai suka rungume juna cikin soyyaya irin ta ma
aurata.
To anan tunanin khaleed ya tsaya. Daga nan sai ya mike tsaye.
Subhanallah me nake shirin aikatawa haka?"ya fada.
Anan sakinata ta kara matseshi domin samun galaba akansa.
Haba ya ka mike ka tsaya ka jiya mana.
Ke matsa baya. Injishi. To anan ne ya kara tuno alkawurran
daya daukar ma matarsa.
"Da ace kinsa na aikata wannan abu danayi dana sanin da
bayada amfani. Bako shakka wannan magana haka take.
( IDAN NAMIJI YA KADAITA DA MACE TO NA UKUNSU SHINE
SHAIDAN) Komi imanin mutum idan ya kadaita da mace to
shaidan xai yi rinjaye akansa. Sannan kuma ya jagorance su
wurin aikata alfasha." inji khaleed.
To a wannan lokaci hankalin sakinat ya fara dawowa jikinta.
"Kayi hakuri khaleed. Ni ma bansan abunda yasa nayi kokarin
yin hakan ba. Shawa ce ta tasomin wadda na kasa hakuri.
"Ba matsala tun da bamu aikata ba. Domin da ace munyi dani
ta shafa domin hukuncina shine jifa tunda inada aure." ya fada.
Yanxu sa kayanki sai mu koma masaukinmu domin idan aka
san muna nan to zargi xai iya shiga tsakani. Daga nan sai
sakinat ta fara shirya kayanta.
Bayan sun gama shirye shiryen su cikin rashin tsammani sai
sukaji ana sako musu ruwan kibau. Anan suka labe bayan itace
tare da mayar da martani. Wata yar karamar bindiga ce suke
halbin da ita (pistol) abun mamaki kuma basu san kowaye ba.
Suna cikin hakane sai khaleed ya nufi wurin da kibau din ke
fitowa a guje tare da halbin wurin. To kafin yakai ga wurin sai
yaji an yi kara wato kamar ya sami mai halbinsu. Daga nan sai
ya rage karfin gudunsa. A hankali ya fara tafiya har yakai wurin
amma kowa bai gani ba. To a wannan lokaci itama sakinat ta
fito daga maboyarta. To a nan suka fara mamaki ko wanene ke
kokarin kashesu. Daga nan sai suka juya suka nufi hanyar
komawa masaukinsu.
Suna cikin tafiya sai sukaji kamar tabi daga sama. To anan
suka daga kawunansu domin ganin ko waye ke musu tabi. To
anan sukaci karo da suhailat saman wani icce.
Suhailat yar sanda ce. Kuma itace mataimakiyar khaleed a
wannan tafiya tasu.
Bayan suhailat ta diro saman iccen sai ta fara magana:
Nayi vedio record na duk abunda kuka aikata a wayata. Kuma
da sannu zan tona muku asiri. Anan ta nuni khaleed da yatsa.
Dama na gayama idan har bakayi abunda nakeso ba to da
sannu sai naga bayanka.
Daga nan sai khaleed ya fara magana "Haba suhailat ya kina
wannan magana, mufa ba abunda muka aikata hasalima larura
ce tasa kika ganmu tare.
"hmmm. To idan baku aikata kome ba me kukeyi a cikin
wannan dare ku kadai a cikin daji. Kai kada ka raina min
hankali naga kome kuma yanzu zaka gani. Injita.
Cikin mamaya ta masa wani naushi a fuska ji kake gibbbbbbb.
Anan khaleed ya fadi sumamme.
Ke kuma karuwar banza. Anan ta finciko sakinat ta makata a
itace. Daga nan sakinat bata kara sanin inda takeba. Wata
yankwa (handcuff) ta fito daga nan ta dauresu sannan ta fara
jansu da kasa domin kaisu masaukinsu domin ta tona musu
asiri.
FULANIN DAJI
Part (4) kashi na hudu
Written by
Abdul king article
A FRIEND IS A BROTHER:
1. SAFREEN AUWAL
2. HAMATULLAH ABDULMAJID
3.LAWAL JNR
4.AISHA DUHU
THANKS FOR YOUR SUPPORT.....
RECALL:
A cikin na uku mun bayyana yadda detective khaleed ya tara
runduna domin fuskantar barayin da suka sace hamir. Sai
kuma wata sabuwar guguwa data bayyana wato suhailtat
wadda ke kokarin bata masa suna shida sakinat akan laifin da
basu aikata ba. Shin ko zata samu nasara kuwa??
THE BEGINNING:
Wani iska ne mai dan karfi hade da yar karamar kura ke yawo
a saman wani titi yana tayar da ledodi. Da ganin unguwa kasan
ta hadu.
Kwas kwas kwas. Takun takalman mace. Wata yarinya ce
kyakkyawa taci ado sanye da uniform na makaranta daga nan
sai ta nufi wani madaidaicin gida. To kafin ta shiga gidan ne
sai iskan ya daga hijabinta dakyar ta samu ta tsayar da hujabin.
Shigarta keda wuya sai wata yarinya tazo a guje ta rungumeta.
Maryam maryam maryam. Haka yarinyar ke fadi cikin murnar
ganin yayarta. To bayan sun zauna ne sai sukaji tari a cikin
daki. Alamun cewa abba yana gida. Ba a dau lokaci ba sai
gashi ya fito:
"Laaaaa. Ke maryam ya akayi kika dawo gashi lokacin
dawowarku makarantar bai yi ba?"
"E abba matsala aka samu kasan bamu biya kudin wannna
term ba shine aka koroni."
Anan abba ya rike baki " kaji matsalata da makarantar kudi
( private school) da ba a biya ba sai su koro yara. gashi kuma
gwamnatin tamu suna kawai ta tara. Yau fa goma ga wata
amma albashi tsit. Kada ki damu jeki abinki gobe kya koma
tunda ba kullum suke korar ba. Daga nan sai ya koma cikin
dakin. A haka maryam ta rike yar kanwarta wato nusaibat suka
fara tadi cikin nishadi.
Wazajen la asar ne sai ga nusaibat ta sheko a guje wurin
maryam.
Yaya ga al ameen nan yazo.
Daga nan sai maryam ta fara shirye shirye zuwa wurin lover
dinta. A wannan lokaci sun dade basu hadu ba domin yana
karatu ne a wata university to yanzu suka samu hutu shi yasa
ya dawo.
A guje ta fito domin ganin fuskar da idanuwanta keda muradin
son gani. Daga nan sai ta dauko kujerun nan plastic chairs ta
fakasu a kofar gidan to bayan sun zauna sai suka tadin duniya
irin na masoya.
" da ka tafi shine ka manta dani ko har flashing ma bakayi."
"Aa keko ya za ayi na manta dake. Ai idan zan manta
kafafuwana masallaci to zan manta dake. Kinga kuwa ba rana
kenan."injishi.
To anan ta dan dunkule cikin hijabi wai ita kunya.
A kullum nakan yi tunanin wannna kyakkyawar fuskar taki duk
da ban san abunda yasa bakyason in ganta ba. A kullum sai ki
dunkuleta cikin hajibi.
Maryam najin haka sai tayi sauri ta kware hijabin. Daga nan sai
ta fuskance shi domin yaci gaba da maganarsa.
"Wai maryam kina sona kuwa?" ya tambaya.
"Haba al ameen ya kana min wannan tambayar kaima kasan da
cewa ba nida wani in ba kaiba." ta amsa.
Anan yayi dan murmushi saboda jin dadin kalaminta tare da
kara kallon fuskarta.
" Da kyau maryam. Zan so na kasance tare dake har abada
amma a kullum akwai wani tunani dake durkusar dani game da
wannan al amari."
" wannna wane tunani ne kuma?" maryam ta tambaya.
Sai da ya dan ya gyara murya kafin ya fara magana: Nakan yi
tunani cewa akwai wata rana da wani mai kudi wanda ya fini
matsayi zai zo ya sace zuciyarki ya mantar dake soyayyar da
muka gina shekara da shekaru.
" Haba al ameen. Wannan tunani naka kayi saurin furza shi
waje domin bana ganin akwai ranar da wani da namiji zai zo
har ya burgeni komi matsayinsa da kudinsa kuwa. Ni kudi baya
gabana. Hakanan bana kula matsayi. Ni kai na gani kuma kai
nakeso kuma in ba kaiba sai dai rijiya.
Anan wani murmushin farin ciki ya cika fuskar al ameen kafin
ya fra magana:
" bako shakka zanji dadi idan kika yimin wannan alkawari
domin ni nasan cewa a cikin zuciyata ba ko masakar tsinke da
zan iya baiwa wata ta zauna in ba keba. Kin mamayeni tamkar
yadda jini ya mamaye jijiyar dan adam.
Anan maryam ta masa kallon nan mai kara dankon soyayya
tare da daga girar sama da kasa sannan ta girgiza su. A haka
suka cigaba da tadi har wazajen magrib. Daga nan sai yayi
niyar komawa gida. Saboda haka sai ya fito da wata yar
tsaraba cikin leda ta shiga da ita. Daga nan sai sukayi sallama
ya wuce.
Tun da sanyin safiya tayi shirin zuwa makaranta. Daga nan sai
ta rataya jakarta ta fara tafiya. Tana cikin tafiya ne sai taci karo
da al ameen saman wani mashin roba roba. Cikin sauri ya faka
sannan suka gaisa.
" Makaranta zaki zo in rage miki hanya mana." ya fada.
Ai ko batayi gardama ba ta hau.
"Au wato mashin ka Siya mana ko?" inji maryam
"Haba waninan sayen mashin. Wannan na abba ne kin san
motar tasa ba lafiya to shine ya aikeni da mashin in masa
sayayya.
Haka suka cigaba da hira har suka kawo makaranta daga nan
sai ya ajiyeta bakin gate sannan ya tafiyarsa. To bayan ta
shigane gabanta ya fadi domin an gama assembly. Kuma da
an gama assemnly to duk wanda ya shigo yayi latti kuma
akwai horo mai tsanani. Daga nan sai ta fara tafiya tana dube
dube don kada wani malami ya ganta. Cikin dace ko ba wanda
ya ganta har ta shiga aji. Duuuummmmm.
Gabanta ne ya fadi domin ganin wata malamarsu a cikin aji
mai koya musu english. Sukan kirata da aunty jennifer
"You maryam always coming late. I have warned you several
times not to make it in my class if you come late. But your
strong head defy my order huh?" inji malamar.
Sorry ma! It will never happen again. Maryam ta bada hakuri.
Anan malamar tayi tsaki. " You are always repeating the same
words filled with apologized. Today i will not take it. I will
make sure i deal with u seriously so that i will send away the
jinns disturbing you up.
Anan malamar ta dauko bulala. Go and kneel down you rascal
child. Sorry ma please. Inji maryam.
Malamar ko kallonta bata yiba gata kuwa katanya ce. Irin
inyamuran ne da basa ragama diyan hausawa. Cikin fushi ta
nufi maryam da nufin cakwademata.
To kafin ta fara dukanta sai taji magana a bayanta.
Excuse ma!
Malamar na juyowa sai taga kyakkyawan saurayi ne keson
magana da ita. Saboda kallonsa yasa malamar tayar da bulalar
cikin rashin sani. What do you want? Inji malamar.
I am very sorry to interrupt your action. Anan saurayin ya fara
magana. The girl you wanted to purnish is my sister of course.
And so i will like to apologized on behalf of her. I know it was
wrong to come late but hers own is due to our mother's
sickness. She was redeploy to hospital today after maryam
took some times caring about her. And that making her to
come late. But i am sorry ma it will never happen again.
Anan malamar tayi murmushi tare da kallon fuskarsa. Yin
hakan yasa maryam ta dan ji kishi kadan domin ta fahimci
cewa duk yan matan ajin sun shagaltu sai kallonsa suke suna
kus kus. Wannan saurayi ba kowa neba in banda al ameen.
Duk da dai mamaki ya kashe maryam na ganin dawowarsa.
Ok no problem but i am asking you to advice her so that she
will come late no more. Now go and take your sit. Inji
malamar. Anan maryan ta nufi kujerarta tare da mayarma al
ameen wani kallo mai daukar hankali. Haka shima ya mayar
mata da martani sannan ya tafiyarsa.
To bayan an tashi break fast ne sai maryam ta tsayu da
abokanta sai hira suke. Amma kin kuru. In badan yayanki yaxo
ba dayau kin niku. Inji safiyat: wata abokiyar maryam
Anan saura suka kyalkyace dariya daga nan suka fara
tsangwamar ta. Shegiya kunji muryarta sai kace wata kyanwa :
sorry ma plsss.
Inji aishat.
Haka dai suka yita tsangwamar ta wasu ta rama wasu tayi
shiru. To suna cikin hakane sai maryam ta tsinkayi wani
bafilatanin daji sai kallonta yake baya ko kyaftawa. Maryam taji
mamakin abunda ya kawo wannan bahillace cikin
makarantarsu. Kuma wannna kallo da yake mata ko lafiya?
Haka dai tacigaba da hira da abokanta har lokacin shiga aji
yayi.
Haka sukayi karatu har lokacin tashi yayi. To a wannan lokaci
abba yazo da motarsa domin daukarta.Bayan maryam ta shiga
motar sai taga wannna bafilacen na dazu yanata kallonta.
Wannan kallo naban mamakine domin tunda take bata taba
ganin wani ya mata shi ba.
Bayan sati daya da faruwar hakan sai abun ya karu domin
maryam tana yawan gamuwa da wannan bafillacen wazaje
daban daban kuma a duk inda ya ganta sai ya kalleta.
Wata rana abban maryam zai fita.
To maigida Allah ya kiyaye. Inji ummin maryam.
Abba ka siyo min chololate! Inji nusaibat.
Anan yayi murmushi. Kada ki damu nusaibat tunda nace
wallahi ai dana dawo zan baki duk abunda kikeso.
Haba maigida ya kana cewa wallahi. Kaifa yanzu ka wuce
rantsuwa. Amma zai fi kace insha Allah.
Anan ya kalli matarsa. Ke kuma matsalata dake kenan. To ko
nayi rantsuwa sai meye tunda nasan zan dawo lfy kuma kina
wannan magana sai kace wanda bai iya mota ba.
To ai maigida kaddara ake gudu!
E da wannan kuma. Yanzu dai sai na dawo. Haka ya fita bai ce
insha Allah ba.
Bayan minti talatin da fitarsa sai gashi ya dawo gigice yana
sallallami. To anan umma ta fito domin ganin ko meke faruwa.
Yau karyata ta kare. Gashi ba a yi albashi ba ko sisi banda
cikin account na cefane kawai suka rage.
Maigada meke faruwane?
Yau kaddara ta rutsa dani. Wani katon sa na buge da motata
kuma ya mutu yanzu haka yan sanda na can waje suna jirana
wai in fito in biya kudin.
To anan umma ta rike baki domin tasan akwai matsala. Suna
cikin hakane sai ga yan sandan sun shigo. Har sun sa masa
yankwa (handcuff) sai sukaji an katsa musu tsawa.
Wani bafilatanin daji ne ya shigo gidan anan ya musu umarni
dasu kwanceshi. Anan ya fara magana:
Sa dai nawane kuma nasan tsautsayi ne yaja aka kade shi har
ya mutu saboda haka na yafe. Daga nan sai abba ya fara yi
masa godiya. To suna cikin hakane saiga maryam ta dawo
makaranta. Gashi kuma ba lokacin dawowarta neba. Tana
shigiwa gidan gabanta ya fadi rassssssss. Saboda ganin
wannan bafilacen dake mata wani kallo a makaranta wai yau
gashi gidansu. Ko me ya kawoshi?
Ahmm ji mana. Amma ke yanzu kuke dawowa kuwa? Bafilacen
ya tambayi maryam.
Aa. Wai akan school fees suka koromu. Ta amsa.
To ya haka. Kai alhaji baka biya kudin yara ba. Inji bafilacen.
E wallahi kasan ba ayi albashi ba. Garin yayi zafi ba kaya.
Yadda za ayi bani account number dinka zan san yadda nayi. A
gaskiya bana son ganin yara sun zauna a gida. Daga nan dai
sai abba yayi masa godiya mai yawa tare da mamakin wannan
abu. Ji fa an kashe masa sa. Amma ko damuwa bai yiba.
Wannan ko wane irin mutum ne?
Ba a fi minti goma ba sai abba yaji alert a wayarsa. Ai ko yana
dubawa sai yaga an turo masa dubu dari biyar. Anan abba ya
rude saboda murna. Daga nan sai ya gwada ma matarsa
abunda wannan bafilace ya masa haka dai suka yita maamaki
suna sa masa albarka.
Ita kuwa maryam ko kadan abun bai burgeta ba domin ji take
akwai abunda yasa yayi musu wannan kyuata taban mamaki.
Amma menene?
Bayan sati daya da hakan wata rana bayan an tashi daga
makaranta sai maryam tayi jiran abba domin yazo ya dauketa
amma abun mamaki ko duriyarsa babu. Daga nan sai ta samu
wuri ta zauna. To tana zaune kawai sai taga wata mota kirar
jeep ta faka wurinta. A wannan lokaci kuwa yan makaranta sun
fara watsewa. A hankali taga an bude gambun motar. Daga
nan sai ta natsu domin ganin wanda zai fito cikin motar. A
mamakinta sai taga wannan bafilacen ya fito. Cikin murmushi
ya mata sallama. To bayan sun gaisa sai ya fara tambayarta
hala me take yi anan. Daga nan sai ta bashi amsa cewa abba
take jira har yanzu bai iso ba. To anan ya umarceta da ta shiga
motarsa zai rage mata hanya. Anan maryam ta ki amincewa.
Ba yadda bai yi ba amma taki.
Wata ran maganar mutane kan zama gaskiya. Kuma bako
shakka duk wanda ya riga bacci dolene ya rigaka tashi.
Hakanan magana jari ce. Idan ka iya sai ka mallaki abunda
kakeso a lokacin da kakeso.
Haka wannan bafulatani ya mata dadadan kalamai domin
ganin cewa ta aminta kuma daga karshe sai ya samu nasara
domin ta aminta zata bishi ya kaita har gida.
====================
Wani ihun mazaje ke tashi kamar akwai abunda yasa su hakan.
Suhailat ce a tsakiya sai kora bayani take su kuma abokan
aikinta sai tabi da dariya suke. Detective khaleed ne a daure
tare da sakinat.
Wannan shine vedio record na shaidar abunda nake gaya
muku. Anan ta mika wayarta ga wani dan sanda domin ya gani.
Yana budawa sai ya fara kallo. Farkon vedio sakinat ce ta debe
riga ana ganin kome na surar jikinta. Bai ko tsaya gama kallo
ba ya ba wani wayar domin ya kalla. Kafin kaceme wuri ya rude
sai zagin su detective khaleed ake tare da jifarsu sai da wata
yar sanda balkisu ta tsawata.
Balkisu tana daya daga cikin wadanda basu yarda da wannan
vedio ba. Domin tasan da cewa akwai hamayya tsakanin
detective khaleed da suhailat. Haka zalika wasu daga cikin yan
sandan basu yarda ba sai dai ba bakin magana saboda tsoron
suhailat domin ba karamar jaruma bace a filin daga.
Haka balkisu ta cire tsoron dake zuciyarta daga nan sai ta fara
magana:
Wannan vedio bana gaskiya bane. Domin idan gaskiya ne ai sai
a bari muga karshensa wato muga abunda suka aikata kafin
mu hukuntasu.
Daga nan sai suhailat ta jiyo da karfi ta kalleta:
Kada ki raina mana hankali kinji. Ko kiso ko kada kiso to dole
mu hukuntasu domin sunyi laifi babba.
Daga nan sai wani dan sanda ya fara magana:
Abunda balkisu ta fadi gaskiyane. Bai kamata muyi hukunci ba
tare da sanin laifin da aka aikata ba. Daga nan sai yan sandan
suka fadi ga baki daya: (wannan gaskiyane)
Anan suhailat ta fara dube dube domin da alamu suna shirin
juya mata baya. Cikin fushi ta cafko wannan dan sanda da yayi
magana. Sai da ta saita da kumatunsa sannan ta masa wani
naushi mai karfi. Anan ya zube kasa sumamme jini na fita a
bakinsa. Daga nan sai sauran yan sanda sukayi tsit domin
ganin abunda ya faru ga dan uwansu. Dukkaninsu suna
tsoronta domin an mata kirar jarumai. Irin matan nan ne ga
tsawo ga kiba.
Duk wanda ya kara yin magana to sunansa gawa. Dolene kubi
umarnina domin nice shugabarku a yanzu. Kuma ku sani cewa
wannan yaron da muka fito nema wato hamir daga yanzu na
soke wannan tafiyar. Ba zamu nemesa ba. Nan da sati daya
zamu kashe wadannan biyun wato sakinat da khaleed. Daga
nan sai mu koma muce sun mutu a wurin yaki. Shi kuma hamir
bamu gansa ba. Ina muku kashedi akan shiga al amurra na.
Duk wanda yayimin shishshigi a wannna tafiya to zan kasheshi.
Anan taba wasu yan sanda umarni daau shigar dasu khaleed
cikin tanti.
A cikin darene khaleed ya rasa abunda ke masa dadi. A duk
lokacin daya tuno matarsa wato zeenat suna ban kwana gashi
yanzu saura sati daya a kasheshi ga laifin da yasan bai aikata
ba. Haka ya barke da kuka har saida sakinat ta fara lallashinsa.
Kayi hakuri mana Allah zai fitar damu daga wannan karangiya
da muka samu kanmu. Tunanin da yake shine wato da ace
basu kadaice shida sakinat ba da hakan bata sameshi ba. A
haka dai yayi dana sani.
Daga nan sai ya fara bata labarin shu u mancin suhailat kafin
suyi wannan tafiya:
wato suhailta ta kasance marar kamun kai domin duk wanda
ya taya takan bashi indai da riba. Saboda wannan abu yasa
bama shiri domin nakan mata wa azi ta daina.
Akwai lokacin data nemeni na hanata to tun daga ranar ta
kudurta kulla min abunda zanyi dana sani tunda naki bata
hadin kai. Wannan duk yana cikin dalilin da yasa tayimin haka.
A haka dai suka cigaba da hira har bacci ya fara daukarsu.
Can sai sukaji ihun mutane kamar ana kawo hari. Kafin
kaceme sai suka fara ganin tantuna na kamawa da wuta. Ihun
mutane ya yawaita. Suna cikin jin wannan abu kawai sai
sukaga an shigo cikin tantin nasu. Suna dubawa sai sukayi
arba da hamir.
Kai she kana raye? Detective khaleed ya tambaya. To anan
sukaga ashe ba shi kadai bane. Tare yake da raliyat.
Cikin sauri ya kwancesu tare da yi musu umarni dasu biyoshi.
Ina zaka kaimu? Kuma meye hadinka da wannan muguwar
yarinyar mai kashe jama a?
Ba muguwa bace. Kuma jama ar da take kashewa laifi bane.
Abunda tayi shine dai dai. Yanzu ka biyomu idan muka tsira sai
kasan labarinta. Inji hamir.
Anan detective khaleed ya fara mamaki to kada dai ace hamir
shima ya koma makashi irin raliyat.
Ya akayi kuka cemu? Kuma wa ya gaya muku muna nan? Inji
sakinat.
Saboda munyi bincike kafin mu zo nan. Inji raliyat.
Anan suka fita a guje da nufin tsira. Suna fita sai sukaji ana
musu tabi. Suhailat ce tasa an zagayesu ga baki daya yadda ba
wurin gudu. Ko ina yan sanda ne tare da bindigarsu Ak47 cikin
shirin yaki.
Kuna ga zaku iya gudu. To ku gudu mana. Anan tayi wata
dariya mai ban tsoro. Tare da dubansu daya bayan daya.
Can sai taba yan sandan umarni: kuyi ma namansu gunduwa
gunduwa.
FULANIN DAJI
Part ( 5 ) kashi na biyar
Written by:
Abdul king article
THE FIRST LADY / THE LADY OF ALL TIMES:
( HUSNA BALA)
I regard my salute.........
RECALL:
A cikin na hudu mun bayyana labarin wata yarinya maryam da
yadda ta hadu da wani bafillacen daji. Sai kuma hamir wanda
yazo tare da wadda ta saceshi wato raliyat domin su kubutar
dasu detective khaleed daga harin suhailat.
THE BEGINNING:
Husnat na labnat ( kannen hamir) a kofar gida suke sai
wasansu suke irin na yan mata cikin nishadi. Suna cikin hakane
sai suka daina sanadiyar wata mota data faka a kofar gidan.
Anan suka fara kallon wannan mota domin ganin wa zai fito a
ciki.
Yazid da najib ne suka fito a cikin motar ( abokan hamir) da
sauri su husnat suka sheko tare da rungumesu. Daga nan sai
suka jasu zuwa cikin gida. A wannan lokaci hajiya zubaidat na
zaune a cikin falo ita kadai ( mahaifiyar hamir)
Bayan sun shigo ne sai ta tashi ta musu maraba tare da kawo
musu lemon kwalba.
Yazid ne ya zuki dan kadan kafin ya fara magana: wai umma
har yanzu ba maganar hamir?
Hmm kai dai bari. Ai sai dai dua i. A can da idan na bugama
detective khaleed nakan sameshi amma yanzu tsit bana samu.
Injita.
Amma umma ki rage tunani insha Allah za a gansa. A gaskiya
naga duk kin canza ba kamar da ba. Mu kanmu nan muna iya
kokarin mu dayin addu a. Domin rashin hamir babban rashine
a wurin mu baki daya. Inji najib.
Anan dai ta dan yi murmushi. To bari mu koma umma. Inji
yazid. Anan sukayi sallama daga nan suka fita.
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
A cikin wani katon gidan samane dake tsakiyar daji wata
hayaniya keta fitowa.
Haba rumaisat yana kina wannan magana. Kece fa sarauniya ta
ciki da wajen wannan daji ba wata in ba keba. Ina fada miki ki
yarda da abunda nace. Idan har baki dau mataki ba to mulkin
ki zai rushe kuma sarautarki zata fadi.
Anan rumaisat ta sauko daga saman kujerarta. A hankali take
tafiya cikin rangwada har ta iso wurinsa. Daga nan sai ta fara
shafa fuskarsa. Kai kyakkyawa ne. Wato ka sani Amil na yarda
da kai amma kafin nan yanzu zan baka wani dan karamin aiki
da nakeso ka cikamin.
Daga nan sai ta dauko wata kwarya. Wasu kalamai ta fara fadi
marar ma ana sannan sai tayi nuni da kwaryar. Anan wani
hayaki ya fito daga cikin kwaryar sai da amil yaja da baya a
tsorace.
Can sai fuskar wasu samari uku ta fito cikin kwaryar.
Wadannan su kadai jininsu zai yi. Saboda haka ina umartarka
daka kawosu cikin gidan nan.
Anan amil yayi dariya. Ai wannan yafi kome sauki domin
wadannan biyun abokaina ne. Guda sunansa yazid dayan kuwa
najib. Amma abunda nakeson sani shine idan na kawosu
bukatata zata biya kuwa?
Anan rumaisat tayi murmushi. Ai ni bana magana biyu.
To sai dai dayan ne ban sani ba. Inji amil.
Anan rumaisat tayi murmushi. sunansa hamir. Bazaka sanshi
ba. Domin ba kai ya kamata ka kawoshi ba. Ita yakamata tayi
amma sai tayi sakaci har soyayyarsa ta rufe mata idanu. Bako
shakka da sannu zata dandana kuskurenta.
Hala wacece? Amil ya tambaya.
RALIYAT!!!! inji rumaisat.
==================
To bayan maryam ta shiga motar wannan bafilacen. Daga nan
sai ya fara tuki da nufin kaita gida. Haka yayita janta da surutu
har suka iso gidan. Daga nan sai ta masa godiya. To kafin ta
fito motar sai ya fito da wani ice cream ya bata. Batayi niyar
amsa ba amma don kada yace ta masa walakanci sai ta amsa.
Daga nan sai ya tuka motarsa ya tafi.
Tana fitowa sai tayi ido hudu da al ameen wato masoyinta.
Anan ya mata wani kallo na alamar tambaya. A kofar gidansu
yake zaune sai wasansa yake da nusaibat wato kanwar
maryam. Anan maryam ta zauna kusa dashi ta fasa shiga
gidan.
Wancan kuma wayeshi?? Ya tambaya.
Anan maryam ta bayyana masa kome dangane da wannan
mutum.
A gaskiya banji dadi ba domin ina gudun kada in rasaki. Domin
duk wannan alheri da yayi muku ba don Allah yayisa ba. Da
alama ke yakeso. Inji al ameen.
Anan maryam tayi murmushi. Haba kai kuma ai duk yadda
yake maitar sona sai dai in na aminta ko. To kada ka sama
ranka damuwa domin ba zan aminta da kowane namiji ba in
bayan kai.
Anan al ameen yayi murmushi na nuna jin dadin wannan
kalami. Haka dai sukayi zance daga karshe sukayi sallama.
To sai bayan ta shiga gidan ne sai abba ya gaya mata cewa
motarsa ce ta lalace. Kuma a saman hanyarsa ya gamu da
wannan bafilacen wanda shine ya kara taimakonsa ya kai
motar wurin gyara. Anan mamaki ya kara kasheta. Wato da
gaskiyar maganar al ameen.
To a cikin wannan darene saiga bafilacen ya dawo anan ko ya
tarar da abban maryam shi kadai a saman tabarma yana shan
iska. To bayan sun gaisa sai ya fara bayani:
Da farko dai sunana alhaji sulaiman. Ni manomi ne. Kuma a
gaskiya yanzu abunda ya kawoni wurinka abune mai girma
wanda har inajin tsoron furta shi domin ban sani ko zan iya
samu.
Anan abban maryam yayi dariya. Haba alhaji ai yanzu mun
zama yan uwa. Ko abuna ka dauka bazance kandil ba domin
nakane. Saboda haka kada kaji tsoron furta duk abunda ke
ranka.
Daga nan sai alhaji sulaiman ya fara magana: wato ya ta
wurinka na gani kuma gaskiya inaso. Wannan shine babban
dalilin da yasa nazo wurinka.
Anan abban maryam yayi dariya: Haba kaiko dan uwa ai
wannan ba wani abu bane don ka ambaci kalmar so ga yata.
Wato ka sani cewa duk abunda na mallaka to kamar nakane
saboda haka ka kwantar da hankalinka yanzu bari inje in
kirama ita. Anan alhaji sulaiman yayi godiya mai yawa.
To bayan abba ya shiga gidan sai ya tarar da maryam a cikin
falo sai kallo takeyi. Anan yazo wurinta:
Ki saurara kiji abunda zan gaya miki domin mai
muhimmancine. Akwai wani bako sunansa alhaji sulaiman
yana nan waje yana jiranki. Inaso kiyi masa biyayya kamar
yadda kikemin. Kuma kada ki kuskura ki bari rashin jituwa ya
hadaku dashi. Daga nan sai ya juya ya fita. Maryam tayi
mamaki domin batasan ko wanene yazo wurinta ba. Cikin sauri
ta yafa wani karamin hijabi sannan ta fita.
Fitarta keda wuya gabanta ya fadi duummmm.
Anan taga bafilacen nan daya rage mata hanya daga
makaranta. To kada dai ace shine abba keson hadata dashi.
Sallama ta masa daga nan sai ya amsa cikin murmushi tare da
mata izni ta zauna. A wannan lokaci unguwar ta haskake
sanadiyar wutar nepa da aka kawo. Saboda haka maryam ta
riga ta masa kallon tsaf.
Daga nan sai ya fara magana: a gaskiya naji dadin ganinki
maryam domin a yanzu idan ace a bude miki zuciyata kiga irin
farin ciki da nake ciki da abun zai baki mamaki domin wannan
itace mafi soyuwar rana a cikin ranakun rayuwata.
Maryam tayi mamaki yadda ya ambaci sunanta koya akayi ya
sani? Inaga abba ya fada masa! Ta fada a cikin zuciyarta.
Wato ki sani maryam a lokutta daban daban ina yawan ganinki
a wazaje daban daban wanda hakan yasa na samu kwarin
gwiwa na ganin cewa na binciko tarihin zuriarku. To bayan na
samo abinda nake nema sai kuma na gano cewa bako shakka
na yaba da hankalinki saboda haka nazone domin samun
amincewarki.
To anan yayi shiru domin yaji abinda zatace. A gaskiya ni ban
gane inda ka dosa ba. Inji maryam.
Haba maryam da hausa fa nake magana ya zakice baki gane
ba. To tunda kin fison sai na fito karara. Abunda nake nufi ina
so ki bani hadin kai domin mu raya sunnar manzo S A W.
Anan maryam ta dubeshi ta dafe kirji. Haba malam ya zaka
zomin da wannan sabuwar magana kai tsaye. To gaskiya kayi
hakuri domin idan har na aminta da abunda kake bukata
tamkar nayi zaluncine saboda akwai wanda ya rigaka a wurin
saboda haka ni na barka lafiya. Anan maryam ta tashi tabar
malam sulaiman rike da baki. A haka ya bita da kallo har ta
shige gida.
Tun da sanyin safiyar laraba ummin maryam ta farka saboda
wata hayaniya da takeji anayi a cikin gidan. To bayan ta fito
daga dakin sai ta tarar da mijinta sai fada yake inda yake shiga
banan yake fita ba. Maryam ce a gefensa da alama kamar da
ita yake.
In banda kike banzar yarinya ya za ace wai bakyason alhaji
sulaiman. To meye gareshi? Ke haka zaki karewa kin fison ki
auri dan matsiyata jikan matsiyata in banda abinki me zakiyi da
al ameen yaron da yanzu yake karatu nasan ko rantsuwa nayi
bazan yi kaffara ba yakan yi shekara bai rika naira biyar ta
kansa ba.
A haka dai abba ya cigaba da yiwa maryam fada yana fifita
alhaji sulaiman akan al ameen.
Bako shakka ciwon so ya kamata domin duk da fadan da ake
mata sai tunanin al ameen take. Suna cikin hakane sai sukaji
sallama bayan sun amsa sai sukaga wani mutum ya shigo to
anan abban maryam ya tareshi da karamci domin direban
alhaji sulaiman ne kuma kamar ya aikoshi da sako. Anan yasa
wasu yara su shigo da buhuhuwan abincin da aka aikoshi dasu.
Buhu biyar na shinkafa. Biyar na gero, biyar na dawa biyar na
masara tare da tukuicin dubu hamsin duk inji alhaji sulaiman.
Anan abban maryam yayi godiya mai yawa tare da rakiyarsu
har waje. To bayan ya shigo gidan ne sai ya fara magana:
Kinga harkar ya kamata ko. Yarinya ki tsaya kici kudi kibar kudi
inda suke. Yanzu ki gayamin al ameen ya taba yi miki irin
wannan kyautar?
A haka dai tayi shiru tana saurarensa domin kamar kalaman
nasa na ratsata. To bayan wani lokaci sai tayi shirin zuwa
makaranta.
Karfe biyu cif aka buga karaurawa wato lokacin tashi yayi. To
bayan ta fitone sai taci karo da al ameen a saman mashin roba
roba na abbansa. Anan ya rage mata hanya ya daukota. Suna
cikin tafiya sai suka kawo wurin da ake saida kaji soyayyi. To
anan kamshin ya ratsata.
Sweetheart bazaka tsaya ka siya mana kaza ba? Injita.
Anan yayi murmushi. Haba maryam ai kema kin sani. Wannan
aljihun nawa wayam yake ko naira baza a samu ba. Ya fada.
Anan maryam ta bata rai: kai kullum haka kake cewa!!
A haka dai yayita lallashinta har ya samu suka kawo gida. To
bayan ya sauketa sai ya tafiyarsa.
Wazajen la asar sakakiya ne alhaji sulaiman yazo bidarta. Da
tayi niyar taki zuwa amma saboda tsoron abba ta tafi.
Tana isa wurinsa ya mata umarni data shigo motarsa zasu
yawon shakatawa aiko ba tare da gardama ba ta shiga. Haka
yayita zaga gari da ita yana gwada mata wazajen da bata taba
zuwaba. Suna cikin tafiya sai suka iso wurin nan da ake saida
kaji. To anan ya tsaya domin ya saya. A wannan lokaci ba
karamin dadi taji ba wato abunda al ameen ya kasa siya mata
sai gashi wani ya siya mata.
Wazajen magrib ne suka nufi hanyar gida. Yana ajeta ya juya
ya tafiyarsa. Da shigarta gida su umma suka fara kallon ledar
sanadiyar kamshin daya cika musu hanci. Anan ta zauna sai da
kowa ya debi rabonsa sannan ta shiga da sauran dakinta.
A haka dai alhaji sulaiman ya dingi zuwa a kowane lokaci daga
nan kuma ya bude mata idanu da kudi. A cikin zuciyarta
tafison al ameen amma saboda sabon yanayin data tsinci
kanta a ciki sai ta fara bin son zuciya. Tun haduwarta da al
ameen bai taba kashe mata makudan kudi irin wadannan ba.
Amma shi alhaji sulaiman bai dauki naira kome ba. Ga kuma
iya zance sai kace marubuci ko kuma dan gidan rediyo.
Daga nan sai tarayyata da al ameen ta fara samun tangarta
domin ta fara cije masa. A kowane lokaci al ameen kanyi
abubuwa da dama domin ganin ya burge maryam amma kash
alkalami ya bushe ko kadan bayada matsayi a cikin kundin
zuciyarta. Hakan ya bata masa rai daga nan kuma sai ya
zurfafa domin ganin cewa ya gano kishiyarsa.
Ummin maryam batason yadda maryam ke walakanta al
ameen domin itama tafi aminta dashi. a kullum takan mata
fada cewa kada ki manta da tsohon masoyinki saboda ganin
sabo yazo miki. Domin takan yiwu tsohon masoyin shine na
gaskiya. Amma ko kadan maryam bata saurara. Domin wannan
zance kamar gatana yake a cikin kunnuwanta. Shi kuwa abba
abunda yakeso kenan wato yaga tana kula alhaji sulaiman.
Domin ko kadan bayason harkar tsiya shi yasa ya tsani al
ameen.
Nepaaaaa! Yarane sukayi kuwa sanadiya wutar da aka kawo to
anan maryam taji dadi domin batada chargi. To kafin tasa
charge din sai kawai taji an kirata. Tana dauka sai taga al
ameen ne.
"Ok ganinan fitowa" ta fada.
Daga nan sai ta tashi cikin mamakin kome ya kawoshi cikin
wannan tsohon dare. Tana fita sai taci karo dashi, da ganin
fuskarsa kasan cikin wani yanayi yake na kaka nikayi.
Haba maryam yanzu abunda kikayi ya dace kuwa wai ace
saboda wani katon banxa sai ki manta dani kada fa ki manta
munyi alkawarin aure kuma iyayenmu sun san da hakan.
Amma naga ko kadan abun bai dameki ba sai sha aninki kawai
kikeyi.
Wani murmushi ta masa na rainin wayo kafin ta fara magana:
Aini a ganina mace rigar kowace. Duk wanda yasa dole a kalla
idan kuma bai yi hankali ba a kwace. Saboda haka ni a ganina
tunda abun yazo haka kara kowa ya kama kabansa ka bidi dai
dai dakai haka nima.
Haba maryam nifa ban gane inda zanceki ya dosa ba. Kada ki
manta nine fa al ameen dinki. Mun taso tun muna yara a cikin
turbar kaunar juna amma a cikin kwanakin nan sai ki canza sai
kace wadda aka yiwa sammu.
Ba wani sammu da aka yimin. Ni malam kamaga tafiyata!
Anan ta juya da nufin shiga gida. Cikin sauri al ameen ya sha
gabanta.
Maryam ki tsaya kiji mana. Yanzu kiyi hakuri duk abunda na
fada cikin rashin sani ne. Ni a ganina bai kamata ace mun
samu sabani ba nida ke domin yin hakan babban kuskure ne
kuma yakan iya haifar da matsala babba. Sannan yanzu ki tuna
fa duk unguwar nan an san mu tare amma ace yanxu kwarma
mun bata. Kinga za a yimana dariya kenan a daukemu
mahaukata.
Anan maryam tayi tsaki. To idan an mana dariya zata lake
mana ne a jikinmu? Ni bazan iya auren matsiyaci ba wanda
bayada gabas bayada yamma. Kuma inama kashedi da zuwa
gidanmu daga yau sai yau.
Ni kike cewa matsiyaci? Al ameen ya tambaya.
E na fada matsiyaci talak talak. Ko zanji saukar aradu ne?
Daga nan ta nufi gida tabar al ameen cikin bacin zuciya.
A cikin wannan dare al ameen ko bacci ya kasa. Haka
umminsa ta shigo dakinsa bai ko sani ba. Kayi hakuri al ameen
Allah zai baka wata. Dama ita duniya haka take. Kana bida abu
yana gudunka. Suna cikin wannan zance sai sukaji sallama.
Kamar muryar mace.
Daga nan sai ta shigo dakin. Suna dubawa sai sukaga ashe
hajarat ce wato mahaifiyar maryam. Anan al ameen ya duka ya
kwashi gaisuwa. Daga nan sai ta samu wuri ta zauna.
Kayi hakuri al ameen banji dadin abunda ya faru tsakaninka da
maryam ba. Anan ta fara magana.
Ba yadda banyi da ita ba ta domin ganin ta dawo cikin
hayyacinta amma abu yaci tura. Yanzu haka da ita naso muzo
amma taki.
Daga nan sai ummin al ameen ta dan yi tari kafin itama ta fara
magana: ai ba kome ke hajarat indai dan wannan abu ai ba sai
kinzo ba. Kin san dama idan Allah bai nufi ayi ba to duk yadda
mutum ya kokarta domin cikar burinsa to abun bazai yiwu ba.
Dama an rubuto cewa ba matarsa bace.
Wannan hakane! Inji Hajarat.
Haka suka danyi maganganu kafin daga karshe suyi sallama
hajarat ta koma gida.
Bayan sati daya da wannan al amari sai alhaji sulaiman ya
kadaita da abban maryam domin su tattauna wata magana mai
muhimmanci. A cikin maganar dai sunyi tsokaci akan cewa ya
kamata a fara shirye shiryen aure tunda yarinya ta aminta.
Saboda haka alhaji sulaiman zai turo magabatansa nan da sati
biyu domin su tattauna zancen. Daga nan sai sukayi sallama
kowa ya kama hanyarsa.
Bayan an tashi daga makaranta ne maryam ta fito. Anan tayi
arba da al ameen saman mashin. Kiranta yayi domin tazo ya
rage mata hanya. Ko kallonsa batayiba. Anan ta kwada masa
wata muguwaar harara daga nan sai ta nufi wata mota jeep ta
shiga.
Bako shakka wannna shine wanda ke sonta! Al ameen ya fada
cikin zuciyarsa. Daga nan ya buga mashin ya nufi gida.
So hana ganin laifi! Wannan magana haka take, wai duk
walakancin da maryam ta yiwa al ameen sai da ya dawo
bidarta a cikin wannan dare.
Tana fitowa batayi wata wata ba ta kwada masa mari
tassssss.
Kai wane irin mutum ne banza soko marar zuciya. Na fada ma
kada ka kuskura ka tako nan da zimmar bidata amma saboda
taurin kai irin naka sai da kazo. Shegen nacin tsiya sai kace
abu yar kwari.
Kika mareni??
E na mareka ko zaka ramane? Anan ta nufi motar alhaji
sulaiman domin taga ya kusanto ta.
MARYAM
Anan al ameen yayi kiranta da karfi. Daga nan sai ta tsaya
domin saurarar abunda zai fada. A hankali ya fara tafiya har ya
kawo wurinta.
Yanzu kina ganin abunda kika yimin ya dace. Nine fa al ameen
dinki amma kalli yadda kike walakantani. Bazan iya rama kome
kika yimin ba domin na cancanci haka sai dai ki tuna cewa
Allah na gani kuma yasan niyata. Ni bazan iya cutar dake ba ko
kuma in yaudareki amma sai gashi yau kedin da nakeso kece
kemin haka.
To a wannan lokaci hawaye sun fara kwarara daga idanun al
ameen. Haka itama maryam ta natsu tana saurarensa tare da
yi masa wani kallo mai alamar tambaya.
Daga nan sai ya ci gaba da magana:
Hausawa sunyi gaskiya da sukace son maso wani son wahala.
Bako shakka wannan magana haka take. Saboda haka ina
godiya da karamcin da kika nuna min. Sai da ki tuna cewa duk
wanda yaci amanar wani to kul ajima kul a dade sai yaga tasa
sakayya. Kuma duk abunda mutum ya shuka shi zai girba in
hairan hairan in sharran sharran.
Saboda haka da wannan magana nake miki sallama kuma na
miki alkawarin cewa zan rabu dake rabuwa ta har abada.
Kuma zan nisance ki nisanta mai nisa. Kuma daga yau bazaki
kara ganina ba. Domin zanyi tafiya wurin dazan manta dake in
yaso daga baya sai in fara sabuwar rayuwa. Daga nan sai al
ameen ya tafiyarsa hawaye na kwarara a idanunsa.
To a wannan lokaci ne maryam ta bishi da kallo kamar tace ya
dawo. Duk idanunta sunyi ja kamar ba ita ba. To anan ne taji
an mata sallama. Tana juyowa sai tayi arba da alhaji sulaiman.
Anan ya lura da kallon da take ma al ameen kamar tana cikin
damuwa.
Hala wancan wayeshi?? Ya tambaya.
Anan maryam ta yi murmushi ba tare da bayyana masa abunda
ya tambaya ba. Daga nan sai alhaji ya kyale yajata da surutun
wani abu.
Zaune suke cikin mota kaza a gabansu amma abunda yabashi
mamaki shine duk surutun da yake zubowa iyaka ta amsa da
E. Kamar dai yau ba lafiya ba. Haka dai sukayi hira suna
karewa maryam ta fito ta nufi gida.
Shigarta keda wuya sai umminta ta tareta da fada:
Wallahi kiji tsoron Allah ke kina ganin abunda kikayi ya dace
kuwa? Wai ki rabu da tsohon masoyinki saboda kin samu mai
kudi. To duniya ce duk abunda kayi shi akema. Akan wani
kodadden bafilacen daji sai ki yiwa saurayinki na gaskiya
walakanci.
Daga nan sai abba ya fito dakinsa. Haba keko ya kina haka.
Kodan kinga ta samu cigaba shine kike kishi? To yarinya ta
zabi wanda takeso kuma kamar an bashine. In banda abunki
ina ita ina al ameen. Ai ko kadan basuyi dace ba domin ita
matar mai kudice ba talaka ba. Anan abba yaja hannunta suka
shiga daki suka bar ummin maryam tsakar gida.
Wazajen azzuhur ne sukaji sallama. Wasu mata ne su biyar
suka shigo gidan. Kai da ganin shigarsu kasan da cewa
FULANIN DAJI ne.
Anan abba da ummin maryam suka taresu cikin girmamawa
domin sun gano cewa jama ar alhaji sulaiman ne.
To bayan sun kadaita sai suka tattauna abunda ya kawosu
wato maganar sadaki da kuma shirye shiryen biki. Anan abba
ya fada musu dukkan abunda ya shirya tare da fada musu
farashin sadaki. Daga nan sai sukayi sallama tare da alkawarin
kawo sadaki. Sai kuma bikin wato nan da sati za a fara shirye
shirye.
To bayan tafiyarsu ne ummin maryam ta fara fada:
Ya za ayi da ganin mutane bakasan daga inda suka fito ba sai
ka basu mata. Ko bincike kayi a kansu?
Anan yayi murmushi. Wannan ba abunda ya dameki bane
domin ni na riga na yarda dashi kuma nasan ba zai cuceni ba.
Tsaki ummin maryam tayi. Yin aure ba tare da bincikeba
matsala ce babba domin ya kamata asan koshi waye sannan
daga ina ya fito kuma wace sana a yake? Sannan ni ban ma
taba ganin inda mata sukaxo bidar aure ba. Maza aka sani da
hakan. To meye wannan abu. Gaskiya ni ban yarda da wannan
aure ba domin ba gaskiya a ciki.
To yayi idan kece mai iko da gidan sai ki hana auren ni kuma
zan gani. Inji abba. Anan yasa hularsa ya nufi masallaci.
Bayan sati daya shagali fa ya matso na biki. Domin an kawo
lehe kuma anyi duk abunda ya kamata. A ranar da za a daura
auren anyi shagali mai kayatarwa domin an kashi naira kuma
yan uwa da abokan arziki na ko ina sun zo.
To a cikin darene ya jeren daki da yan kai amarya sukayi zaune
jugum suna jiran abba yazo domin a yi magana. Abunda basu
sani ba shi kansa abban bai san gidan da za a kaita ba. Bai ma
sani ba shin a cikin wannan garin da suke cikine ko kuma a
wani?oho. Shi bai sani ba domin bai taba tambaya ba kuma
baiso ya sani ba. Wannan abu ya farune sanadiyar rufe masa
baki da akayi da kudi. Ya zama sai yadda akace yayi zai yi.
Karfe goma cif na dare sai ango yazo shi kadai a ciikin
motarsa. Anan ya musu umarni da cewa ba sai anyi jere ba
domin gidansa shirye yake kuma ya tanadi duk wani abu da
amarya ke bukata. Kuma bayason yar rakiya shi kadai zai dauki
amaryarsa ya tafi da ita.
Ummin maryam bataji dadin haka ba ko kadan sai ba yadda ta
iya domin an ci karfinta. Haka yan uwa da abokan arxiki suka
ringa guda har amarya ta shiga motar angon. Daga nan sai ya
tuka tun suna hangen dushi dushin motar har ta bace bat basa
ganin kome. Daga nan sai suka juya kowa ya kama hanyar
komawa gida.
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
A lokacin da suhailat ta bada umarni da a kashe su hamir.
Take yan sandan suka gyara rikon bindigogi. To kafin su
aiwatar kawai sai raliyat tayi shewa da karfi. Yin hakan keda
wuya sai suhailat taga yan sandanta na zuba kasa domin wasu
kibiyoyi ne ake jefo musu wadanda basu san ko daga ina suke
fitowa ba. Saboda haka suhailat ta fara gudu tana bidar
maboya haka suma dakarun nata wato yan sanda.
To anan ne su hamir suka samu damar gudu dama sun hada
kai da wasu mutanen raliyat cewa idan har sukaji shewa to ana
bukatarsu da gaggawa.
Mata ne fulani su uku kowace rike take da kwari da baka sai
faman halbin su suhailat suke. To bayan su hamir sun tsere sai
suka nufi dandalin su raliyat.
A wannan lokaci sun gaji likis. To bayan sun huta sai detective
khaleed ya fara magana: a gaskiya ina godiya da irin wannan
taimako da kuka yimin domin ko kadan banyi tsammanin
hakan a wurinki ba domin a ganina bakida imani ko kadan.
Anan raliyat ta kalleshi tayi dariya. Haba ya zakace banda
imani. Yanzu haka fa nafika!
Anan yayi murmushi. To amma zan so ki fadamin labarinki da
kuma dalilin sace hamir? Sannan kuma me yasa kike kashe
duk namijin da ya furta kalmar so a wurinki?
A wannan lokaci tayi murmushi har hakoranta sun bayyana:
wannan labarine mai tsawo kuma bazan iya fadama shi yanzu
ba amma ka sani cewa ba sace hamir nayiba taimakonsa nayi
domin rayuwarsa na cikin hadari.
A wannan lokaci hamir na rike da tuffa yanaci( apple) bai san
lokacin daya yadda shiba jin cewa rayuwarsa na cikin hadari.
Ko zaki bayyana abunda kike magana akai? Inji sakinat.
A a bazan iyaba domin ba lokaci amma ku tashi domin inaso
ku rakani wani wuri? Inji raliyat.
Wane wuri kuma? Khaleed ya tambaya.
Ba sai kun sani ba. Ku biyoni kawai. Injita
Anan su hamir suka rufa mata baya ita kuma ta shiga gaba
domin kaisu wurin.
FULANIN DAJI
Part ( 6 ) kashi na shidda
Written by:
Abdul king article
DOMIN GANIN FARKON LABARIN KAYI SEARCHING:
(KINGARTICLE.NOVL
TO ALL MY FANS
LOVE U ALL
RACALL:
A cikin na biyar mun bayyana yadda maryam ta yaudari tsohon
saurayinta wato al ameen tare da bin alhaji sulaiman saboda
kudinsa. Sai kuma su detective khaleed da suka samu damar
kubuta daga harin suhailat sakamakon zuwan su hamir. Sai
kuma amil wato yaron da rumaisat taba kwangila cewa ya
kawo mata yazid da najib.
THE BEGINNING:
Wani kayataccen fili ne cike da jama a sai kuma wani dogin titi
mai tsawo a tsakiyar filin. Mutane sai ihu suke kamar da alamu
cewa za a yi wasan tseren motoci a wurin.
Yazid da najib sai dariya suke domin wani abokinsu ne a
tsakiya sai faman basu labari yake. Suna cikin hakane sai mai
gabatarwa ya mike ya fara magana:
Muna maku barka da isowa, a yau ne za a gabatar maku da
wata gagrumar wasa wadda baku taba gani ba. Domin dukkan
jaruman yanzu sun gabato. Daga nan sai ya fara kiran
sunayensu su kuma jama a sai tabi suke da ihu. Yazid da najib
suna cikin wannan wasa da kuma abokinsu. Wannan aboki ba
kowa neba in banda AMIL.
Anan aka tamburan fara wasa kafin kaceme fili ya dauke da
ihun jama a domin a wannan karon an tara kwararri a cikin
wasan to kowa naso yaga waye zai zama zakara. Cikin sauri
kowane jarumi ya tada mota kafin kaceme sun fara cin taya. A
haka kowanensu ya wanzama domin ganin cewa ya buge
abokan karawarsa. A wannan karon yazid ya dage sai ya dauki
na daya domin a wancan karon bai ji dadin wasan ba. To anan
amil ya gane nufinsa saboda yadda yaga ya dage. Kafin
kaceme shima ya kara giya don kada a barshi baya. Daga nan
sai fili ya kacame da ihu yadda mutane sukaga najib ya wani
dago mota da nufin wuce abokan karawarsa. To anan yazid da
amil suka raina kansu don sunga wanda ya fisu kasada.
A haka kowane dan wasa ya wanzu yana style daban daban
domin burge yan kallo. Saura minti biyar sukai ga inda akaeso
su tsaya to duk wanda yayi saurin kai wurin to shine zakara. To
a wannan lokaci kowanensu a tamanin yake domin ganin ya
cimma burinsa.
Najib ne a gaba sai faman dariya yake domin ganin cewa ya fi
kowa gudu kuma ya kusa kaiwa inda akeso. Shi kuma yazid
ransa a bace yake domin fa idan ba na daya yayi ba to yanaga
bazai kara yin wasan ba. Suna cikin hakane sai tunani ya fado
masa. To anan yazid ya fizgi mota a guje. Ga motocin yan
kanana ne na irin na wasan tsere.
Kadan ya rage najib yakai ga wurin kawai sai yazid yasa gefen
mota ya wani bugun motarsa. Kafin kaceme motar najib ta
kama wata hanya daban anan ta kubce masa. Shi kuwa yazid
sai ya dawo na daya.
Dole najib ya faka yana tsaki domin an wuceshi. Dauriya dai
yayi ya tayar ya cigaba. Sai dai kash yayi latti. Kafin yakai ga
wurin sai yaji ana sanarwa cewa yazid ne na daya sai kuma
amil na biyu. Dakyar shima ya samu ya wuce sauran daga nan
akace shine na uku.
To anan fili ya rude. Dama wadannan ukun sune jaruman
wasan kuma a cikinsu ne yan kallo ke tsammanin cewa zakara
zai fito. Anan aka fito da kyaututtuka ana raba musu wato na
daya dana biyu dana uku.
To bayan an gama rabon kyaututtukan ne sai kowa ya watse
anan su yazid suka shigo motar amil domin ya rage musu
hanya. Tunda suka shigar motar basu kara sanin inda sukeba.
Iyaka dai sun farka sun gansu daure a cikin wani gida.
WANNAN SHAFIN NAKANE KAI KADAI:
******* KING BOY ISAH********
NA YABA DA NAMIJIN KOKARINKA AKAN LITTAFIN
( ALJANNAR FATIMA) NAYI KARATUN LITTAFAI DA DAMA
AMMA BAN TABA KARATUN WANDA YA TSARANI BA IRIN
WANNAN. ALLAH YA KARA BASIRA AMEN.
=================
A lokacin da su yazid suka farka sun razana sosai domin
abunda kawai suke iya tunowa shine lokacin da suka shiga
motar amil. To ya akayi suka zo wannan gida? Kuma ina amil
din. Suna cikin wannan tunani sai suka jiyo ihun wata mace.
Anan hantarsu ta kada domin ji sukayi kamar su tsere amma
ba dama domin a saman kujera suke zaune kuma an dauresu
da kaca tamau yadda ko motsin kirki basayi.
Fitilar dake dakin bataci sosai domin haskenta dushi dushi
yake. Can sai suka farajin tafiyar wasu kamar sun nufosu. Anan
yazid da najib suka fara kallon juna a tsorace domin basu san
abunda ke faruwa ba. A mamakinsu sai sukaga wata mata
tsaye da amil sunzo kusa garesu. To anan suka fara magana
da fillanci yadda su yazid bazasu iya gane abunda suke cewa
ba. Amil ko kallonsu bai yiba balantana ya kulasu iyaka dai
sunga yana washe baki da alamar yana cikin wani farin ciki
marar misaltuwa. To bayan sun gama maganarsu sai suka juya
suka tafi. Anan su yazid suka fara kwala masa kira domin yazo
ya cecesu amma ina haka ya tafi ya kyalesu.
::::::::::::::::::::::
A lokacin da raliyat tace su hamir su rakata wani wuri. Bayan
sunyi tafiya mai nisa sai suka iso wani katon kogo. A haka
suka nausa ciki sai tafiya suke. To bayan sunyi tafiya mai nisa
sai suka kawo ga wani kabari. To abunda ya basu mamaki a
wurin shine ganin kasan mutane matattu. A haka suka yita taka
wadannan kassa har suka iso ga kabarin. Suna isowa wurin sai
sukaga raliyat ta fadi tana kuka. Daga nan suka fara lallashinta
suna bata hakuri tare da tambayarta dalilin wannan kuka. To
anan ta fara basu labarinta:
Ni ba muguwa bace. Kuma ko kadan banada ra ayin kashe
mutane sai dai ba yadda na iya domin yin hakan shine mafita a
gareni.
Abbana da ummina sun kasance a cikin jin dadi kuma sune ke
mulkin wannan daji saboda haka duk fulanin dake ciki kan
basu matsayi babba. Abbana ya kasance attajiri a dalilin
hakane ya gina wani katon gidan sama shi kadai a cikin
wannan daji domin shi mutum ne wanda bai damu da sha anin
mutane ba. Ba yadda ummina batayi dashiba akan ya koma
inda mutane suke amma yaki.
Haka muka cigaba da zama cikin annashuwa ba tare da
tunanin kome ba. Wata rana sai wata bakuwa ta shigo wannan
daji namu. Mun dade muna jin labarinta amma bamu gasgata
ba.
Wannan bakuwa ta kasance da ban mamaki domin takan bada
magani kuma yadda mukaji ana fada idan taba mutum magani
to duk abunda ke damunsa zai warke sarai. Sai dai da anyi sati
daya shi kuwa mutumin zai canza domin wata tsaguwa ce zata
fitoma mutum a hannu. To duk wanda wannan tsaguwa ta fito
masa zai zama ba abunda ke burgeshi in banda shan jinin
mutane. Saboda haka dolene ya kashe mutum idan yasha jinin
sai ya kawowa wannan bakuwa gangar jikin domin tayi
tsibbacenta.
To anan ne muka gano cewa wannna bakuwa ba magani
takeba. Domin duk wanda tama magani sai ya zama bawanta
sai abunda tace yayi sannan zaiyi. To kafin mu dauki mataki
sai muka gano cewa mafi yawan fulanin dake wannan daji sun
zama bayinta. Kuma gawawwaki sun yawaita domin a kullum
sai an turbude jama a.
Anan abbana yayi yunkurin daukar mataki a matsayinsa na
shugaban wannan daji. Abunka da matsafi to ashe ita wannan
bakuwa tasan da zuwan abban na. To anan tayi shiri ta zo ita
da mabiyanta. Bayan sun zagaye gidan kawai sai mukaji an
banko gambun gidan da karfin tsiya.
Anan tasa aka daure abba na da ummina. Ni kuma a wannan
lokaci ina yar shekara takwas. A gabana tasa aka yi musu
kisan gilla. Sannan aka kawosu cikin wannan kogon aka
turbude.
Anan ta nuna musu kaburbura guda biyu. Wadannan sune
kaburburan ummina da abbana. A wannan lokaci kwalla ta cika
idanun raliyat.
To bayan nan sai ta komo kaina:
Ke bazan kasheki ba sai dai zan sihirceki yadda duk namijin da
yace yana sonki to sai kin kasheshi. To tun daga wannna ranar
na zama baiwarta sai abunda tasa ni. Bani kadai ba. Mafi
yawan mutane dajin idan ta kashe iyayensu haka take mayar da
yayan.
Bayan na girma na mallaki hankalina sai abu ya daukaka. Bana
tausayawa mutum ko wayeshi idan dai ya furta kalmar so a
kaina to bazai kwana duniya ba.
Wannan sihiri da tayimin ya karye wata rana dana kaima wani
dattijo hari a cikin wannan daji domin kasheshi. To anan ya
kamani ya dura min wani magani a baki. To tun daga ranar naji
baxan iya kashe kowa ba kuma bana bukatar shan jini. Sai dai
a wannan lokaci kuma ta nuna min hoton hamir kuma tana
bukatar in kawo matashi. Anan na dinga binsa kamar zan
kasheshi domin kada ta gane cewa sihirin ya karye. Har
lokacin dana samu damar saceshi a cikin prison. Shi kuma
abokinsa anasko bani kashe shiba. Ita da kanta ta kasheshi
sannan tasa gawarsa a motar hamir. Wato plan din data hada
shine idan yan sanda suka kamashi a zatonsu shi ya kashe
abokinsa to in bi dare in saceshi sai in kai matashi. To ni
kuma dana saceshi sai naki kai mata shi. Su kuma sauran
abokaina dole subi umarnina domin nice shugabarsu. Zan iya
nuna muku recording din danayi a lokacin da take bani umarni
in kamo mata shi. Da kuma wasu vedios inda take cin naman
mutum danye.
Anan raliyat ta fito da wayarta ta basu domin su gani. Anan
detective khaleed ya rike baki yana mamaki irin wannan
zalunci.
Sunan wannan matar RUMAISAT. Inji raliyat.
Bako shakka mun samu abunda mukeso saboda haka yanzu
muje ki nuna mana wannan gida naku domin nasan a ciki take.
Inji khaleed.
Wannan hakane inji balkisu.
Daga nan sai suka mike da nufin fita kogon. Aiko suna kaiwa
kofar fita saiga suhailat ta shigo tare da yan sandanta. To anan
aka fara kallon kallo. Mamaki ya kashe hamir koya akayi tasan
inda suke?
Anan aka kama su hamir tare da detective khaleed aka daure.
Daga nan sai suhailat ta bada umarni da a wuce dasu
masaukinta.
==================
Al ameen ne rike da jaka yana ban kwana da mahaifiyarsa. Can
sai ga abbanshi ya shigo gidan.
Kwanaki nawa zakayi kafin ka dawo? Inji abba.
Zan yi sati daya. Al ameen ya fada.
To Allah ya kiyaye. Inji ummansa.
Daga nan sai al ameen ya fita. Mai mashin ya tara sannan ya
fada masa cewa ya kaishi tasha. Tunda aka ajeshi tasha ya
kula da wasu fulani mace da namiji sai kallonsa suke suna kus
kus. To anan ya fara bidar mota amma duk inda yaje sai yaga
ance motar ta cika.
A haka yayita dubawa amma ko kadan ba sa a. Saboda haka
sai ya samu wuri ya kishingida yana jiran ko zai dace.
Can sai yaga wata mota ta faka wurinsa. Yana dubawa sai ya
ashe fulanin nan ne dake kallonsa.
Maigida ai kaduna zakaje ko? Namijin ya tambaya.
Anan mamaki ya kashe al ameen koya akayi suka san inda
zaije?
E can zan tafi! Ya fada. To kazo mu rage ma hanya mana
domin muma can zamu. Anan al ameen yayi godiya daga nan
sai ya dauko jakarsa. To kafin ya shiga ne sai wani tunani ya
fado masa a lokacin yana hira da mahaifiyarsa:
Dana kada ka yarda da motocin da bana tasha ba domin a
cikinsu akan samu marar gaskiya. Inji umminsa.
Anan wata zuciya tace kada ya shiga. Can sai ya canza ra
ayinsa saboda haka ya shiga. Daga nan suka fara tafiya baji ba
gani kai kace masu tashi sama. Tafiya tayi tafiya saboda haka
sai dadin mota yasa shi bacci. A haka aka cigaba da tafiya ba
tare dayasan inda akeba.
To bayan anyi nisa da tafiya sai ya farka. To abunda ya bashi
mamaki ba saman titi sukeba a cikin wani kungurmin daji suke
sai wuce bishiyoyi suke. Kuma a wannan lokaci duhu ya soma.
Anan ya fara magana yana tambayarsu inda zasu kaishi amma
a mamakinsa ko juyowa basu yiba balantana su tanka masa.
Duummmm. Gabansa ne ya fadi saboda ganin wani makeken
gida da fitilar mota da yado. To kada dai ace a cikin wannan
gida zasu kaishi. Da dai yaga bazasu tsaya ba. To abunka da
city boy dama ya iya mota. Matukin motar ya rike daga nan sai
ya canza hanyar da karfin tsiya. To anan motar ta kubce ta
kama daji a guje. Ita kuma matar tumanyo masa tayi ta afka
masa da kokuwa. Anan suka hargitse. Gata mace amma kamar
maza take naushinta yake amma sai yaga ta hadiye kome
bataji. Suna ciki haka ya samu damar maka ca can gefe. Shi
kuwa namijin sai faman tuki yake yana kokarin komawa hanyar
gidan. To anan al ameen ya shakeshi ita kuma motar ta kama
yin gefe gefe har sai da tasha wani icce sannan ta tsaya. Daga
nan sai yayi yunkurin bude motar domin fitowa amma ganbuna
a kulle suke.
To a wannna lokaci macen ta farfado kuma ta gane abunda
yake shirin yi. Anan ta kara afko masa. Bai yi wata wata ba ya
maka mata wani uban naushi a wuya a nan ta fadi sumamma.
Daga nan sai ya fara fashe gilashin motar da nufin fita. Yana
cikin hakane shima namijin ya taso. To a wannan lokaci har al
ameen ya diro ta tagar motar. Shi kuma namijin sai ya fito da
bindiga ya fara halbinsa. Anan al ameen yaci taya shi kuma ya
dafa masa.
Karar bindigar ce ta tayar da yarinyar. Anan itama ta dauko
tata bindiga tabi bayansu.
====================
A lokacin da alhaji sulaiman ya dauki maryam. Anan suka fara
tafiya da matsanancin gudu. Tun maryam na iya ganin gari har
suka fito suka kama hanyar daji. Ai ko basuyi nisa ba wani
bacci mai nauyi ya dauketa. Ita ab bata farka ba sai da taji
motar ta rage gudu. To anan ta farka domin ganin inda suke. Ai
ko tana bude idanu sai ta rike baki domin a wani daji ne suke
mai duhu ko me ya kawosu anan?
A haka dai suka cigaba da wuce manyan itatuwa har suka iso
wani makeken gida. To anan ne ya mata iso da cewa ta fito.
Daga nan sai ya shiga gaba tana binsa. A haka ya shiga da ita
cikin gidan. Gidan makekene ga kuma siffar ban tsoro da akayi
masa sai kace GIDAN FATALWA
Daga nan sai ya zagaya da ita gidan tare da nuna mata
wurinta. Wani katon falone cike da kayan alatu sai kuma
dakinta a can gefe. Duk abunda take bukata na abunci
akwaishi cikin store. A haka dai ya nuna mata gidan tare da yi
mata kashedin cewa kada ta kuskura ta shiga wani wuri in
banda wurin daya nuna mata.Maryam bataji dadin wannan abu
ba domin a ganinta bai kamata ace ya hanata shiga wasu
wazaje a cikin gidan ba.
Kwana da kwanaki maryam taci gaba da rayuwa cikin wannna
gida sai abunda ke bata mamaki mafi yawan lokutta takan ji
kuwa a cikin gidan kuma idan ta tambayi mijin nata sai ya fada
mata cewa ba kome. To wata wata rana a cikin dare ta tashi
domin tayi fitsari sai taga mijin nata bayanan alhali kuma kafin
tayi bacci yana nan. Anan ta fara dube dube amma ko
alamunsa babu.
Wata fitila ce yar karama ta dauka daga nan sai ta fara yawo
cikin gidan tana bidarsa. A inda take upstairs ne ga wurin ya
kafle da duhu. A hankali take tafiya a tsorace domin wata yar
karamar kara takeji daga downstairs. Daga nan sai ta nufo
hanyar da nufin takowa. A mamakinta sai taga mijinta tsaye da
wata mata suna wata magana a can kasan bene. Anan mamaki
ya kamata domin bata taba ganin wani a cikin wannan gida ba.
Saurarawa tayi domin taji abunda suke fada amma kash
batajin kome. Daga nan sai ta hango wata mace a daure
saman kujera. Wannan abu ya mutukar tayar wa maryam
hankali domin jini ke fita a jikin matar da gani kasan tasha
wuya. Sai kuka take amma ko saurararta basayi. Ita kuwa
macen ta tsaye kara bakinta tayi tana shan jinin dake kwarara
daga jikin matar.
Anan gaban maryam ya fadi duummm. To kada dai ace ta
kawo kanta gidan.....
Bata iyar da tunanin ba fitilarta ta fadi. Anan taga mijinta ya
juyo da karfi saboda karar faduwar fitilar. Amma a mamakinsa
bai ga kowa ba. Abunda bai sani ba shine maryam dukawa tayi
don kada ya ganta.
Bayan ta dauki fitilarta kawai sai taga mijin nata ya cigaba da
magana da wannan matar ita kuwa sai faman shan jini take.
Wannan ba kowa ceba ij banda rumaisat. To bayan sun gama
maganarsu kawai sai taga mijin nata ya dauko wani takobi.
Anan ya datse kan wannan matar da ake shan jininta.
Saboda tsananin tsoro daya dabai baye maryam batasan
lokacin datayi karaba. To a wannan lokaci alhaji sulaiman yaji
wannan karar.
Anan maryam ta jiyo a guje da nufin komawa sama domin ta
gano cewa mijin nata dan mafia ne. Juyowarta keda wuya sai
ta ganshi gabanta. Anan tayi mamaki ko ya akayi yayi saurin
hawan benen har ya fado gabanta?
A bayanta kuma rumaisat ce rike da yuka. Anan maryam ta
rasa abunda yi. Kuka ta farayi kafin ta fara magana:
Sulaiman ashe haka kake ban sani ba. Ka cuceni ka rabani da
maisona na gaskiya. Kuma ni bazan iya zama dakai ba a
yanzu.
Anan yayi dariya: ai kin makara yarinya. Daga nan ya kwada
mata mari tassssssss. Anan ta fadi gigice. Daga nan ya cafko
ta tana ihu ya wuce da ita kasa. Sai da yayi tafiya mai nisa
sannan ya kawo wani daki mai shegen duhu. A ciki ya jefata
sannan ya kulle da kwado.
A wannan lokaci bakin ciki ya turnuke maryam domin ji take
itama kamar kasheta za ayi. Saboda haka sai ta fara kuka tana
tunanin tsohon saurayinta wato al ameen. Anan tayi dana
sanin cutarsa datayi. Tashi tayi tana kallon dakin. Anan ta gane
cewa daki ne babba ne. Sai dai matsanancin duhun daya
zagaye dakin shi ya hanata gane wadanne kaya ne a ciki.
Hakan maryam tayi kukan bakin ciki daga karshe ta hakura
domin ta gano cewa ba mafita.
A haka taga safiya har faduwar rana ba abunda tasa abakinta.
To anan ne ta gano cewa wato za ayi mata horo da yunwa har
ta karasa. To anan ne ta fara tunanin mafita. Tashi tayi ta fara
kalle kalle dakin. To anan ne ta fara jiyo wani kugi can kasan
dakin. Da karfi taja da baya tare da mannewa ga bango. Anan
tsoro ya kara dabai bayeta. Daga nan sai ta fara tafiya a
hankali domin gano ko ina wannan karar ke fitowa.
Taku hudu tayi sai taji karar wadda tafi ta farko har sai da ta
fadi tare da like kunnuwanta da hannuwanta. A hankali karar ta
fara lafawa har ta bace. Daga nan sai maryam ta mike tsaye.
Can kuma sai taji rugugi a kasan dakin. Cikin tunaninta sai taga
kamar wannan karar a kasan dakin yake fitowa. To dama
akwai wata katuwar carpet a tsakiyar dakin. Daga nan sai
maryam ta fara yunkurin jayeta gefe. Haka ta kama kici kici
dakyar ta jinyeta. Aiko tana janyeta sai taga wani katon rame
an rufe da marfi. Kai da gani kasan underground ne.
Anan ta fara tunani ko ta bude? To tana cikin wannan tunani
ne sai ta hango wata yar karamar torch-light. Anan dadi ya
kumeta. Cikin sauri ta dauki fitilar. Tana haskawa taga haske
ya fito anan taji dadi.
Baammm.Dummmm. Gibbbbbb.
Anan taga ana bugun kofar dakinta da karfi kamar ana son
shigowa. To anan tsoronta ya dawo domin ta fahimci cewa
mai bugun rike yake da gatari kuma dashi yake bugun kofar.
Mannewa tayi ga gina tana kukan tsoro anan jikinta ya dau
karkarwa. Can sai ta fahimci cewa kukan da take bazai amfana
mata ba domin kofar dakin ta kusa ballewa. Anan ta yake
shawarar shiga underground din duk da har yanzu bata daina
jin kara na fitowa ciki ba.
Da karfi ta jawo carpet din. Tana shiga underground din sai ta
jawo carpet tasa don kada asan inda ta shiga. Anan ta ga wani
tsame (Ladder) daga nan sai ta fara taka tsamen har ta shigo
gidan kasan (underground) saukowarta keda wuya taga kassan
mutane birjik ko ina. Sai gawawwakin mutane wasu duk sun
bushe. Anan ta fara tafiya tsorace tana kalle kalle.
Sai da tayi tafiyar kusan minti talatin amma bataga kowa ba.
Kuma bataga wurin fita ba. Tana cikin tafiyar ne sai taji karar ta
dawo. Anan maryam ta like kunnewanta. Tana cikin hakane sai
tayi tsaye kikam kamar wadda tayi mutuwar tsaye. Wata
yarinya ce ta gani jini sai zuba yake ga jikinta. A tsorace
maryam ta rasa abun yi. A hankali taga yarinyar tana tafiya
kamar tana shirin tunkarota. Daga nan sai maryam ta fara ja da
baya a tsorace. Tana cikin hakane sai taci karo da wani abu
anan ta fadi. Daga nan sai maryam ta ci gaba da rairafe ganin
ta tserewa wannan yarinyar. Caraf taji an damke hannuta. Ashe
yarinyar har ta cimmata.
Jini. Jini. Jini. Haka yarinyar ke fada.
Daga nan sai tasa wasu manyan akaifu nata da niyar yankan
fuskar. To anan maryam ta turata da karfi ta kuma tashi tsaye.
Tashinta keda wuya sai taji wannan karar ta dawo. Daga nan
kuma sai taji kamar ana dirowa daga kasa. Dubawarta keda
wuya sai taci karo da wasu fulani maza da mata ba kyan gani.
Daga wanda baida kafa daya sai wanda baida hannu. Su kuma
wadanda ke lafiya lau sai tangadi suke kamar mashaya gida.
To anan ta gane cewa sune keyin karar. Kuma tare suke yinta
kamar hadin baki.
A mamakinta sai taga suna lasar baki kamar mussa taga
nama. Anan suka nufota gadan gadan da niyar yakusata. Wani
icce ne ta hango a can gefe. To anan ta daukoshi da niyar
kariyar kariyar kanta. Aiko suka gewayeta da nufin yankata
gunduwa gunduwa ita kuwa duk wanda ya matsota sai dai ta
makeshi da icce. A haka maryam tacigaba da fada da wannan
mutane masu ban mamaki amma ko karewa basayi. Maimakon
haka sai karuwa sukeyi. To da taga ba kanta sai ta bidi hanyar
gudu domin tsere musu. Aiko su kuma suka dafa mata. A haka
ta cigaba da gudu duk wanda taga ya kusa cimmata sai ta
makeshi kafin ta cigaba da gudun.
Tana cikin gudun ne sai ta hango wata hanya yar karama da
zata kaita waje sai da hanyar an liketa da wasu karaffa. To
anan ta rasa abunyi gashi kuma wadannan fulanin sun kusa
cimmata. Daga nan sai dabara ta fado mata. Iccen ta saka tayi
ta bugun karafan har saida suka lankwaahe yadda zata iya bi ta
wuce. Aiko tana shiga suna kawowa. Anan wani yasa hannu ya
kamo kanta da nufin janyota. To ashe batayar da iccen taba.
Anan ta saita da mummuken shege. Ji keke duummmmm.
Anan ya saketa saboda zafin bugun. Da karfi ta wani wucewa
sannan ta mayar da kofar ta rufe. Anan wadannan fulani sukayi
tsaye suna kuka miyau na dalala saboda bakin ciki basu samu
namaba.
To bayan maryam ta fito anan ta gane cewa cikin kungurmin
daji wannan gida yake. A guje ta fara gudu ba ji ba gani. Aiko
batayi nisa ba sai ta hango al ameen a tsaye kamar yana
jiranta. Anan dadi ya cika zuciyatta. Ashe bai manta dani ba.
Duk irin zaluncin dana masa sai da ya biyoni domin ya ceceni?
Haka maryam tayi magana a cikin zuciyarta ita kadai. To
amma ya akayi yasan inda nake? Abunda ta fara tambayar
kanta kenan. Ai ba matsala ko menene zanji. To anan ta kara
kaimin gudunta domin cimmasa. Haka shima sai ya bude
hannuwansa. Aiko tana zuwa ya rungumeta.
Masoyina ashe baka manta dani ba? Ta fada.
Anan taga yayi dariya. To anan tsoro ya fara kamata. Can sai
taga ya rikida ya koma mijinta wato sulaiman.
Yarinya in kinsan wata ai baki san wata ba! Ya fada yana
dariyar keta. Tabin jikinta kawai yayi sai gasu sun shigo gidan.
Anan maryam ta fasa wata kara mai tsanani saboda bakin ciki.
FULANIN DAJI
Part (7) kashi na bakwai
Written by:
Abdul king article
RECALL:
A cikin na shidda mun bayyana yadda su hamir suka kara
komawa tarkon suhailta bayan da raliyat ta bayyaa musu
abunda yasa take kashe duk namijin da yace yana sonta. Sai
kuma yazid da najib wadanda amil ya yaudara ya kawosu ga
rumaisat. Maryam da saurayita al ameen duk suna cikin wani
mugun hali na shigowa wannan bakin daji. Shin ko maryam
zata kubuta daga sharrin mijinta sulaiman?
THE BEGINNING:
Wani katafaren gida ne sai sauti ke tashi kai da gani kasan ana
ceshewa. Wata mota ce aka faka a gidan. Daga nan sai wani
kyakkyawan saurayi ya fito ya shiga gidan. Wannan saurayi ba
kowa neba in banda KING BOY ISAH.
To bayan isah ya shiga gidan kawai sai wasu yan mata suka
fara shewa da juna jin dadi. Kai da gani kasan shine sarki a
wurin. Shigar da yayi ta haskaka sa saboda haka kowace
yarinya sai kallonsa take tana kokarin shishshige masa. A haka
ya cigaba da tafiya yana bouncing cikin takama da nuna isa.
Kamar shi ake jira yana zaunawa sai aka fara party.
Abincuccuka ne kala kala marar adadi. Maza da mata a can
gefe sun game sai rawa ake irin ta xamani. Wata yar
bafulatana ce ke tafiya hade da rangwada. Kai da gani kasan
wanda takema wannan. King boy ne yayi dariya domin ganin
yarinyar ta nufoshi. Wani chewing gum ne take tauna kai kace
shaidaniya.
Xaunawarta keda wuya tayi masa irin kallon nan mai daukar
hankali. A wurin kallonta ne king boy ya kifar da fanta dinsa
cikin rashin sani.
Ohhh my dear ya kana haka? Sai kace makaho. Ta fada.
Anan yayi murmushi tare da kara dubanta. Wata shigace tayi
matsatstsa yanda duk ana ganin surar jikinta. To anan king boy
kara kidimewa. Tashi tayi kamar zata sumbace shi kawai sai ta
fasa. Handkerchief ta dauko daga nan ta fara goge masa masa
fanta din da ta zuba a jikinsa.
Kallonta yake ko kyaftawa bayayi. Tana juyowa sai ya done
kansa. Yar kunya ce ta dan kamasa a haka wani digon fitsari
ya fito masa ba tare daya sani ba. To bayan ta zauna sai suka
fuskanci juna. Anan ta fara magana:
Yau a cikin farin ciki nake marar misaltuwa domin da za a
tsaga zuciya kaga abunda ke ciki. Nasan baza kayi bacci ba.
Kuma ina godiya marar adadi da zuwanka wannan birthday
nawa.
Anan isah yayi dogon numfashi kafin ya fara magana:
Haba mufeedah ya kina wannan magana. Kema kin san dolene
inzo wannan birthday domin shi zai kara mana dankon abunda
muka gina.
Dariya tayi kadan har hakoranta suka fito. A gaskiya king boy
kai gwarzon marubuta ne. Jiya fa na karanta littafin nan daka
rubuta wato ALJANNAR FATIMA. Ba kaga yadda nayi dariya ba
har cikina yayi ciwo. Iyaka dai muce Allah ya kara basira.
Anan isah yayi murmushi saboda jin wannan kalami nata. Daga
nan kuma sai ya amsa da ameen. Can sai ya tashi tsaye.
Toni zan wuce naga dare yay. Inji shi.
Anan mufeedah ta rike hannunsa. Ba inda zakaje yau a dakina
zaka kwana. Ta fada.
Dadine ya lullube king boy sai dai ga fili ya nuna kamar bai
aminta ba. A haka sai da sukan danyi mahawara ta minti biyar
kafin daga bisani ya aminta.
Wazajen assalatune malam hashimu ya tashi domin bautar
ALLAH madaukakin sarki. To dama a tsakar gida yake yawan
ibadar tasa. Kabbartawarsa keda wuya sai yaji kamar an diro ta
saman gate. To anan ya sallame ya zuba a guje cikin gida.
Tafiya yaji anayi kamar an nufosa. To anan malam hashimu ya
kara kidimewa daganan sai ya fadi yana salati domin shi a
tsammaminsa barayi ne suka shigo.
Kuwa ALLAH kuyimin rai. Wallahi ko sisi banida.
Can sai yaji an tallaboshi. Haba abba ya kana haka nine fa!
To anan tsoron malam hashimu ya gushe. Kaine ubanwa?
A cikin zuciya kamar yace nine ubanka.
Nine danka isah.
Isahhh. Daga ina kuma? To kafin ya bashi amsa.
Tassssss. Tassssss. Saukar mari biyu a kuncin isah.
In banda kake tafki me yasa baka kwana inda ka jeba. Bana
hanaka yawon dare ba. Kai zama wani irin yaro na daban. A
kullum kana wurin party. Baka ga waccan baka ga wannan. A
haka dai alhaji hashimu yayi ta masa fada ba sassauci.
To wannan fada ne ya tada saratu wato matar malam
hashimu.
Wai me nakeji a gidan. Lafiya kuwa? To bayan ta matsone sai
ta fahimci abunda ke faruwa.
E to saboda ya fita yawo wurin budurwarsa shine zaka tsareshi
da fada. Toni kada ka sabatta mun da. Domin har yanzu ina
son abana. Ai idan fada ne kanka ya kamata ka yiwa. Dama
ance kyaun da ya biyo uba. To saboda ya biyoka shine zaka
damu mutane da surutu. Injita.
Au wato haka ma zakice? Inji malam hashimu.
E haka zance. Kai a lokacin kuruciyarka meye bakayi ba. Ko
kana tsammanin na manta? Yan matan garin nan hatta da
matan aure sun san da zamanka. Dama ance abunda kayi shi
ake ma. Wannan abun da isah keyi shine ka yiwa da abba da
umma. Ka manta lokacin daka kayar da abbanka gabana.
Kuma ka tura umma cikin kwata wai don tama fada. Gaskiya
kada ka kara yiwa dana haka domin banaso.
To anan malam hashimu yayi tsuru tsuru domin asirinsa ya
tonu.
Anan ne saratu ta lura da cewa king boy ya fara tankwahe
hannun rigarsa. Hala me kake shirin yi? Xan rama marin da
yayi min! Ya bata amsa.
Au wato marinka yayi. Kada ka raga masa dana ci kwal
ubansa. To anan hankalin malam hashimu ya tashi. Bai ko
tsaya ba a guje ya nufi gate. Kamawa yayi da nufin direwa. To
anan king boy ya jawo kafar shege. Haka ya fado tuiii. Sai da
wata yar karamar tusa ta fito saboda xafin da yaji. Fusssss.
Kafa king boy yasa da nufin takashi. To abunka da tsohon
kashi. Cikin sauri ya make shi can gefe. Kafin kaceme ya kama
gate ya dire. Anan yaci taya ko taka kasa bayayi saboda tsabar
gudu. A haka shi kuma isah ya rarumi icce ya bishi a guje.
=================
To bayan maryam ta tsinci kanta cikin wannan gidan data gudu
anan ta rasa abunda ke mata dadi. Gani kawai tayi wasu
samari su biyu a daure sai faman ihu suke domin rumaisat ce
rike da yuka sai faman dadara masu ita take. Daga nan sai
taga wasu fulani su uku yan mata cikin shigarsu ta fulani
kowace rike da kwarya. Anan suka ajiye kwaryar kusa ga kusa
wadannan samarin. Suna bude kwaryar sai taga wasu macizzai
manya su uku. Sun fito. To anan macizzan suka fara lasan
kafafun wadannan samarin su kuma sai faman ihu suke
saboda tsoro.
Anan ne sulaiman ya jawota ya zaunar saman kujera. Daga
nan sai ya daureta sannan ya kawota kusa ga wadannan
samarin. To a wannan lokaci rumaisat sai faman magana take
da wadannan fulani. Amma da fillanci suke maganar saboda
haka su kadai sukasan abunda suka tattauna akai. Suna gama
maganar sai fulanin suka dauki macizzan suka mayar cikin
kwarya daga nan sai suka fita waje. To a wannan lokaci ne
rumaisat da sulaiman suka fuskanci juna. Anan suka rungume
juna suna sumbatar kansu(kiss) don kawai maryam taji haushi.
Daga nan sai suka nufi wani daki domin cikawa junansu
bukata.
To anan ne maryam ta lura da wadannan samarin. Tambayarsu
sunayensu tayi. Anan suka fada mata. Yazid da najib ne. A
haka itama ta fada musu nata. Daga nan sukaba juna labarin
abunda ya shigo dasu gidan. To anan suka tausayawa juna tare
da hada baki domin ganin sun gudu tare.
A cikin wannan darene suke sa ran cikar burinsu na tserewa
domin sun hada plan. Suna zaune saiga rumaisat ta shigo da
yukarta kamar yadda ta saba zata fasa jikinsu tasha jini. Wani
murmushin mugunta take domin ganin su uku ne. Gashi
maryam nada yar kiba saboda haka zata fisu mai. To anan
rumaisat ta kusanto ta. Kee. Miye sunanki?
Miye ruwanki da sunana? Maryam ta bata amsa. Anan
rumaisat tayi dariya har saida hakoranta suka fito wadanda
duk sun lalace saboda shan jinin mutune. Yukar ta aza a
wuyanta tana gogawa a hankali. Can sai ta turnuke fuska. Anan
ta dallawa maryam mari mai kyau tasssss. Da karfi ta daga
yukar da nufin datsa mata. Aiko kafin ta iyar da nufinta tuni
yazid ya wani dunguzata da kafarsa. Anan ta fadi tayar da
yukar. Da karfi ya dauke yukar sannan ya fara kwance daurin
da aka yi masa. To a wannan lokaci kan rumaisat ya bugi
kasa. Saboda haka ta fadi sumamma. To bayan yazid ya
kwance kansa daga nan sai ya fara kwance su maryam.
Bayan ya kwancesu sai suka nufi kofar fita a guje. Ba yadda
basu yiba amma kofar taki budewa. To anan maryam ta tuno
cewa akwai wani abu da ake latsawa sai kofar ta daga sama.
Cikin sauri ta latsa wannan abun. Anan kofar ta fara dagawa a
hankali. To a wannan lokaci rumaisat ta farfado domin jin
karar kofar. Su kuma su maryam a guje suke gudu. Maryam ce
ta fara fita domin itace a gaba. To anan ne rumaisat ta latsa
abun rufe kofar. Aiko nan kofar ta farayin kasa. Su kuma su
yazid a lokacin sun kara kaimin gudu domin kada kofar ta rufe
dasu. Aiko suna kaiwa kadan ya rage su fita kofar ta rufe
gamm.
Bayan fitar maryam bata tsaya ba gudu ta farayi kamar ranta
zai fita. Sai da tayi tafiya mai nisa sannan ta tsaya tana
sheshsheka.To anan ta fara tafiya tana tangadi sabida gajiya
kamar ranta zai fita. Tafiya take amma tunanin cutar data yiwa
al ameen take. A wannan lokaci tayi dana sani domin da ace
bata cuceshi ba da duk wannan fitina bai sameta. A haka
tacigaba da tafiya tana tunani. Tana cikin tafiya sai taci karo
da mutum tsaye. Anan tasha jinin jikinta. Dubawarta keda
wuya sai taga ashe al ameen ne. To anan ta tuno da yaudarar
da mijinta sulaiman ya mata. Ya mata shigarsa tana xuwa
wurinsa ya kamata. Anan taja da baya a tsorace. To a wannan
lokaci shima al ameen ya ganta. A guje ya nufota saboda
tsananin murna da nufun rungumeta. Ai kuwa tana ganin haka
tace kafa me naci ban baki ba. Anan maryam taci taya bata ko
duban kasa. Dajin cike yake da kayoyi amma bata ko jinsu
saboda gudu.
A haka al ameen yayita gudu amma ko alamun cimmata bai
da. Daga nan sai ya fara kiran sunanta. MARYAM nine fa al
ameen ki tsaya kiji mana. Kwal uba. Maryam najin haka a nan
ta kara giya fuuuuu.
=============
Saratu ce tare da mai gidanta malam hashimu a cikin wani
falo na alfarma. Can sai ga king boy isah ya shigo. Mama inaso
kiban kudi inyi shaye shaye? Anan tayi dariya. Haba dana
wannan ai ba kome bane. Yanxu zan baka dubu hamsin kaje ka
rungumi mata kayi abunda kakeso. Domin duniyar takuce
samari. Kuma kasha abunda kakeso na daga dangin shisha,
daga, sholi, totlin, emzolyn, fenecillin. Amma banda giya kaji
dana.
E naji! Ya amsa.
Anan ta shiga daki. Bata dade ba ta fito da kudi ta mika masa.
Rungumeta yayi yana murna. Sai mumy na. Yauwa dana kaje
ka dawo lokacin da kakeso kuma idan mutum yama magana
to ka yanke ma shege labba. To anan suka hada ido malam
hashimu. Done kansa yayi domin yasan dashi take. King boy
isah buga motarsa yayi sannan ya tafiyarsa.
Haba saratu yanzu abunda kikayi ya dace kenan? Kece fa kike
lalata wannan yaron. Yanzu ji yadda ya shashince. Hauka
kawai yakeyi to wa ya gayamar haka ake gayu. Yaje yayi wani
aski sai kace zabo wai shi bajatoli.
Wai kai meye ruwanka a ciki inaso in gayama ka fita harkar
dana fa. Domin na gano cewa kai dan adawa ne. Haka dai
tayita shaka masa bakaken maganganu. A haka yayi shiru ya
kyaleta dama indai da sabone to ya saba da walakancin da
take masa.
Shi kuwa king boy isah bai tsaya ko ina ba sai club. Anan ya
dauki yarinyarsa mufeedah tare da wata kawarta. A haka suka
yita yawon banza har dare yayi. Daga nan sai mufeedah ta
amshi tukin motar wai zata kaisu wani wuri. A guje suke gudu
tun suna ganin gidaje har suka daina. Bayan wani lokaci sai
gasu wani kungurmin daji. King boy yayi mamakin abunda ya
kawosu wannan daji amma kuma bai damu ba. Bayan sun faka
motar sai mufeedah ta fito. Anan ta fada jikin shi da nufin zai
biya mata bukatarta. Har ya aminta zasu fara kenan sai tace ya
fara da kawarta zataje da dawo. To anan mufeedah ta tafiyarta
ta bar su cikin mamaki. Ko ina zata acikin wannan daji?
Cikin sauri king boy ya finciko kawar mufeedah din. Bai ko
tsaya ba yayyaga kayanta yayi saboda sauri. Kafin kaceme sun
fara nishi.
Can bayan abu yayi nisa sun dade sunayi sai sukaji kamar
tafiya bayansu. To anan suka mike daga nan sai suka fara sa
kayansu. Suna cikin hakane sai isah yaga wata kibiya ta xo kai
tsaye ta shiga cikin wuyan yarinyar har sai da bullo. To anan
yarinyar ta fadi jini na fita fa karfi. Anan king boy ya kurma
uban ihu amma bai ga kowa ba. Can sai yaga mufeedah tsaye
tare da wasu jama a kowane rike yake da kibau. To anan ya
fahimci cewa sune suka kashe wannan yarinyar.
Cikin shigar fulani suke kai da gani kasan basada imani. To
anan aka fara kallon kallo tsakaninsu da king boy isah. Zaburo
masa sukayi da nufin yin gunduwa da namansa to anan shi
kuma ya cika wandonsa da iska.
::::::::::::::::::::::::
Al amarin maryam kuma tunda ta fara gudu bata tsayaba sai
da ta tabbatar da cewa ta yiwa al ameen nisa yadda bazai iya
cimmata ba. Ita a cikin ranta ji take kamar mijinta ne sulaiman
ya kara yin shigarsa domin ya kamata. Haka tayita ta tafiya har
dare yayi mata. A wannan lokaci tsoro ya fara kamata domin
bakajin kome in banda kukan tsuntsaye. To tana cikin tafiya ne
sai ta hango wata yar bukka. Anan farin ciki ya lullubeta. Kai
tsaye ta kutsa kai ciki. Shigarta keda wuya sai taga wata yar
bafulatana tsaye kikam kamar tana wani abu. Gabanta ne ya
fadi rassssssssss.
Idanun matar suka bata tsoro domin ba wadanda ta saba gani
bane. To anan tayi mata sallama tare da fada mata bukatarta
nata barta ta kwana a gidanta idan yaso gobe zata tafiyarta.
Matar najin haka sai tazo gab da maryam ta tsaya. Rungumeta
tayi cikin murna amma abunda ya bata mamaki shine matar
kamar bata magana. A nan dai bafulatanar ta nunawa maryam
wurin baccinta. Daga nan kuma sai ta kawo mata wata kwarya
ta a jiye a gabanta. Maryam na budawa taci karo da nono
zalla. A haka ta fara shan nonon duk da yaminsa saboda
yunwar da takeji. To bayan ta koshine sai ta ajiye kwaryar gefe
tare da yiwa matar godiya amma bata amsa ba. Hakan ya
daure ma maryam kai amma sai tayi kwanciyarta bata damu
ba.
To a tsakiyar darene sai taji kamar wani abu na tabin jikinta.
Firgigit ta farka. To anan ta kurma uban ihu saboda abunda ta
gani. Wani katon maciji ne wanda bataga iyakar tsawonsa ba.
Cikin kwaryar da tasha nono yake fitowa zai fita dakin.
Anan ta duba zuwa ga gadon wannan matar domin ta tayar da
ita. To anan ta kara kidimewa domin maimakon taga matar sai
kawai taga katon maciji cikin shigar matan fulani sai sharar
barcinsa yake. Da gudu ta juya da nufin fita dakin to anan taji
an cafkota an makata ga gina. Ashe matar ce ta farka cikin
siffar macijin. A haka ta gangaro saman gadon. Ita kuwa
maryam jikinta sai karkarwa yake domin bata taba jin tsoro irin
wannan ba. Macijin sai huci yake yana fitar da harshensa. To
kadan ya rage ya cimmata sai maryam ta dauki wata adda
dake rataye a bangon dakin. Ai ko macijin na isowa ta ishi ishi
ta dura mai ita. Anan macijin ya fara wulle wulle yana kuka
cikin muryar mace. Da gudu maryam ta fita ko juyowa batayi.
Sai da tayi nisa sai ta tsaya tana sheshsheka.
Anan wani kukan dole ya kubce mata. Daga nan sai ta fara
tunanin rayuwar datayi da al ameen cikin jin dadi to da ace
bata yaudareshi ba da hakan bai faru gareta ba. A wannan
lokaci maryam tayi dana sani yadda tayi sakaci kudi suka rufe
mata ido har ta yarda ta yaudari masoyinta na gaskiya. To
tana cikin kukan ne sai taji kamar magana daga bayanta. Tana
juyowa sai tayi arba da wani dattijo. Anan maryam ta tashi
tsaye tsoro ya kara kamata.
Diyata me kikewa kuka a cikin wannan dare? Ya tambaya.
Anan maryam taja da baya a tsorace domin a wannan lokaci
batayarda da kowa ba. Kada ka taba ni. Haka take cewa
dattijo.
Da dai dattijon yaga bazata yarda dashi ba. Kawai sai ya fara
wata waka mai dan karen dadi da fillanci. To abunka da
mutanen dori basa zama banza. Aiko maryam najin wannan
wakar sai wani bacci ya xomata. To anan ta fadi batasan inda
takeba. Shi kuma dattijon sai ya tallabota ya kawota a cikin
bukkarsa.
Sanyin safiya ne ya tayar da ita. Aiko tana farkawa sai ta fara
duban dakin da take ciki. Can sai taci karo da dattijon nan na
jiya. Anan ta fara kuka tana rokonsa: don ALLAH kada ka cutar
dani.
Haba diyata kada ki damu. Ni ba macuci bane kuma bazan iya
cutar dakeba. Ni taimakon ki zanyi. Daga nan sai maryam taji
idanuwanta sunyi nauyi kuma jikinta ya fara canzawa. Wani
shauki ne ya fara shigo mata domin ji tayi ba abunda takeso
sai tasha jini. To anan ta tashi tsaye tana wani zallo. Kafin
kaceme ta fadama dattijo da nufin kasheshi tasha jininsa.
Wani gocewa dattijon yayi sannan ya dauko wani magani cikin
jakarsa. Anan ya danne maryam sannan ya zuba mata maganin
cikin bakinta. To anan ta fara kakarin amai. Daga nan sai ta
fara amai sai da ta amaye duk nonon da tasha. Tana gama
amaye nonon sai ta dawo cikin hayyacinta. Anan taji bata
bukatar shan jini.
Abunda ya bata mamaki shine ganin tayi nonon ya hade kansa.
Daga nan sai ya koma dan karamin maciji. Wato kenan maciji
ta sha a matsayin nono. Anan dattijon ya kama macijin. Wani
siddabaru yama macijin sai macijin ba zama ruwa ya mutu.
Daga nan sai dattijon ya fara yi mata magana:
Yarinya kin kuru domin da ace baki zonan ba da nan da kwana
uku zaki zama mayya. Haka zaki dinga kashe mutane kina
shan jininsu. Kuma ki sani wannan nono da kikasha ba nono
bane domin nonon maita ne. Wanda mayyun FULANIN DAJI
kesha. Kuma duk wanda ya bakishi shima mayene. Saboda
haka yanzu inaso kiban labarinki.
To anan maryam ta bashi labarinta tun daga farko har karshe.
Anan dattijon ya tausaya mata tare da yi mata nasiha akan
yaudarar datayi. Ai kinyi wauta yarinya domin ba a auren
mutum idan ba a san daga inda ya fito ba. Kuma ba a auren
mutum ba tare da bincike ba kome matsayinsa kuma kome
kudinsa. Amma nasara na tare dake domin na hango taimako
akan hanyarki. Saboda haka taso ki gani.
Anan maryam ta tashi ta bishi. Bayan sun fita cikin bukkar sai
ya nuna mata wata hanya. Inaso kibi wannan hanyar kiyita
gudu domin anan ne zaki gamu da nasara.
Haba baba ai da kaxo sai mu tsere tare don kada su kasheka
kaima! Inji maryam.
Anan dattijon yayi dariya: kada ki damu yarinya koda zan
shekara dubu ne a wannan daji to ba abunda zai samani
domin kar tasan kar. Nasha nayi wanka. Amma ke nake jima
tsoro domin rayuwarki na cikin hadari.
Anan maryam tayima dattijon godiya daga nan ta nufi hanyar
daya nuna mata a guje
================
Su kuma su hamir bayan suhailat ta rutsa dasu cikin kogo. Sai
tasa aka kamasu. A nan ta jagoranci tafiyar zuwa masaukinsu.
To suna cikin tafiyar ne sai suka hango wani hayaki na tashi a
wuni wuri can da nisa. To anan suhailat ta bada umarni aje
wurin da hayakin ke fitowa a duba a gani.
Caraf raliyat ta fara magana: idan kinason mu rayu to kada ki
kuskura kisa muje wurin wancan hayakin domin duk wanda
yaje wurin to sunansa gawa.
Hala miye ruwanki? Ai nice shugaba ba keba! Inji suhailat.
Anan ta tursasasu don dole su tafi. To bayan sun isa wurin sai
suka isko wasu bukkoki da yawa kamar dai wani dan karamin
gari. Anan suka yita tafiya cikin wannan gari abun mamaki tun
da shigowarsu basuga kowa ba. Sai da sukayi nisa sannan
suka fara ganin fulani yan kwarori kuma duk wanda suka yiwa
magana baya tankawa sai dai ya tsura musu ido yana kallonsu.
Raliyat tasan kome dangane da wadannan fulani sai dai tasan
ko tayi magana suhailat bazata yarda ba saboda haka taja
bakinta tayi shiru.
Wata mata sukaga ta zo wurinsu. Anan ta gaidasu tare da basu
umarni su zauna wurinta kafin safe. Sun ji mamakin wannan
tarba domin basu san wannan matar ba. To anan suka fara
tunani cewa ashe mutanen garin na magana da gan gan suka
kyalesu.
::::::::::::::::::::::
A lokacin da maryam ta fara gudu. Sai da tayi tafiya mai nisa
kafin ta tsaya hutawa. Aiko tsayawarta keda wuya sai taji ana
kiranta. Tana juyawa sai tayi arba da al ameen. To anan tace
kafa me naci nan baki ba. Haka shima ya dafa mata. To a
wannan lokaci maryam ta gaji. Tana cikin wannan gudu sai ta
fadi rikicaa. Anan shi kuma al ameen ya fado saman jikinta
rigingine sai kace wanda ya hau gado.
Ba yadda maryam bata yiba domin ta turashi gefe amma ta
kasa.
To anan ta fara bashi hakuri don kada ya hallakata. Anan ne ya
nuna mata shine al ameen dinta. Maryam bata yadda ba ko
kadan. Anan tayita tabin fuskarsa domin sanin gaskiya. Daga
karshe dai ta yadda da cewa shine al ameen dinta na gaskiya.
To anan ta kara kankaneshi a jikinta tana kuka:
Kayi hakuri masoyina na yaudareka. Anan ta bashi labarinta
tun lokacin da sulaiman ya aurota ya kawota wannan daji har
ta gano cewa shi dan mafia ne. Anan shima al ameen ya bata
nashi. tare suka tashi da godema ALLAH da ya sake hadasu. A
wannan lokaci son al ameen ya kara shiga zuciyarta. Saboda
haka sai ta matse a jikinsa haka shima ya lakamota. Daga nan
suka fara tafiya suna hira cikin annashuwa. Suna cikin hakane
sukaji an nufosu a guje. A tsorace maryam ta zabga a guje sai
da al ameen ya cafkota da karfi. Wani saurayi ne sukaga ya
fado gabansu yana ihu su taimakeshi. Anan a ameen ya zo gaf
dashi. Su waye a bayanka?
To anan ya fara basu labarin yadda aka kawoshi cikin dajin tare
da fada musu sunansa wato king boy isah.
Anan al ameen ya bayyana masa cewa suma yaudararsu akayi
aka kawosu saboda haka yanzu tare suke. Daga nan sai suka
fara tafiya su uku.
::::::::::::::::::::::::::
A cikin wannan dare su hamir suka tashi da abun al ajabi
domin fulanin ne sai kawo musu farmaki suke da niyar
kashesu. Saboda wannan dalili fada mai tsanani ya hargitde
domin kowane dan sanda rike yake da bindigarsa sai faman
diba yake.
A nan balkisu ta kaikaici idon suhailta daga nan sai ta kwane
su hamir domin suyi ta kansu. Su kuma wadannan fulani kamar
basa karewa domin kashesu akeyi amma wasu sai zuwa suke
kuma duk wanda yayi sakaci sukaci karfinsa to zasu filla filla
da naman jikinsa daga nan sai su shanye masa jini. Da dai su
detective khaleed suka ga ba kanta sai suka arce kowa ya fara
gudu.
Su kuma su aminat suna isowa wurin suka ga abunda ke
faruwa. To anan suka fara gudu suka bi bayan su khaleed. A
haka su hamir suka yita gudu har suka iso wani katon gida.
Anan gaban aminat ya fadi domin shine gidan da aka kawota.
Daga nan sai raliyat ta fara magana:
Wannan shine gidanmu da rumaisat ta kwace. Amma yanxu
idan muka samu damar kasheta to duk sihirin data yiwa
wadannan fulani zai karye. Daga nan sai khaleed ya bada
umarni a shiga gidan. A wannan lokaci suhailat bata da ikon
kome tun da khaleed ya dawo. Da farko maryam bata yarda ta
shiga gidan ba amma da aka fada mata cewa zasu hada karfi
da karfe su yaki rumaisat sai ta yarda.
Shigarsu keda wuya sukayi arba da ita saman kujera sai
kallonsu take.
Sannunku da zuwa fa. Na dade ina jiranku sai yanzu! Injita.
Anan maryam tayi arba da mijinta. Haka shima king boy isah
yaga yarinyarsa. Wasu fulani suka fara fitowa da kwarya suna
ajiyewa. Su fulanin yan mata ne su uku. Ajiye kwaryar keda
wuya sai kwaryar ta fara girgizawa da karfi. Kafin kaceme ta
fashe. Anan wasu manyan macizai suka fito suka nufi su
hamir. Haka suma yan matan. Daga nan sai aka kacame da
yaki. To anan suka lura da fulanin fitowa suke ta koina cikin
gida domin su kawo musu hari. Haka itama rumaisat. Wasu
takubba biyu ta dauko ta dako tsalle. To anan raliyat ta tareta
daga nan suka kacame. Ana cikin wannan yakine hamir ya
hango abokansa a daure wato yazid da najib. Cikin sauri ya
nufi wurin domin cetosu. To anan wani saurayi yasha gabansa.
Wannan na kowa neba in banda amil. Anan suma suka fara
nasu yakin
Daga karshe dai sun samu nasara domin an kashe rumaisat
tare da duk mabiyanta. To kasheta keda wuya sai sukaga
fulanin dake yakarsu sunyi tsaye wuri daya. Anan hayaki ya
fara fitowa bakinsu. Duk wanda hayakin ya fito bakinsa sai yayi
atishawa ya fara tambayarsu meke faruwa. To anan suka cewa
wato rumaisat duk itace sillar wannan abu. Ta sihircesu tare da
mayar dasu mayyun karfi da yaji.
Anan suka fahimci cewa yanzu kowane bafulatani dake dajin
zai koma dai dai tunda an kashe shugabar wato rumaisat
To anan suka yi shirin komawa gida. Bayan sun isane khaleed
ya gano cewa kamal yaji sauki haka itama wannan yarinyar ta
murmure domin yanzu suna magana lafiya kalau. To anan suka
sallameta.
Shi kuma king boy isah yayi dana sanin yawon da yakeyi na
dare wanda shine sanadin shigowarsa a cikin wannan balai.
Haka itama maryam tayi dana sanin yaudarar da ta yiwa al
ameen.
Hamir yayi alkawari bazai kara shan waka ba kuma bazai kara
zuwa night club. Ita kuwa raliyat a gidan su hamir ta dawo da
zama domin abbansa ya daauke mata kome. Idan sun gama
karatu za a daura musu aure.
Itama maryam haka taci gaba da soyayyarta da masoyinta na
gaskiya wato al ameen. Wannan shine karshen wannan labari
ALHAMDULILLAH
THE END
KINGARTICLE.NOVL
0 Comments