SHAWARA ABAR DUBAWA


SHAWARA ABAR DUBAWA
                                                                        By

Abdul King Article 
                          .                                             Asmy_cute
                                                                    Esma'el last born    
                                                     
Zainab Mustapha Musa (Mmn sadig)
                                                                              All in

Zamfara Writers Association
In Conjunction With
King and Queen Writing Chamber

 Babi na Ɗaya
   ( Gaskiya da Amana )

Page 1

      " Muna muku barka da warhaka  tare da sanar daku cewa shahararriyar  marubuciyar nan da aka fi sani da Sarauniya ta ƙaraso sabida haka ba tare da ɓata lokaci ba zamu fara gabatar da wannan shiri namu mai taken SHAWARA ABAR DUBAWA kada ku manta nine naku Kamal Ahmad a nan gidan rediyon Gamji FM akan mita cisin da ɗaya da ɗigo biyar a nan Jahar Zamfara, baƙuwa muna maki barka da zuwa a cikin wannan shiri namu kuma munaso yanzu ba tare da ɓata lokaci ba muji wace irin shawara ce zaki baiwa matasa maza da mata domin su duba kuma suyi nazari akan al amurran dake faruwa na yau da kullum. " Ɗan murmushi  tayi kafin ta fara magana kamar haka: " Da farko dai zaku iya kirana da Ahlam wadda aka fi sani da Sarauniya, ni marubuciya ce a ƙarƙashin ƙungiyar King and Queen Writing Chamber wato Sarki da Sarauniya kuma gaskiya naji daɗin wannan gayyata domin ko ba wani abu  ai mutum zai bada gudunmuwa kuma ya tofa albarkacin bakinsa domin ita shawara abar dubuwa ce, shawarwarin da nakeso na baiwa matasa maza da mata ƙwara shidda ne kacal amma  kuma bazan so na faɗe su kai tsaye ba domin wasu bazasu yadda da abunda nake faɗa ba, zan so ya zamana cewa duk abunda na faɗa to akwai hujja akansa, zan  bada shawarwarin ne a cikin labari sabida haka masu saurare sai ku biyoni da kyau domin jin waɗannan shawarwari da zan bayar.

*Page 2*

Murmushi tayi kafin taci gaba da magana kamar haka: " Shawara ta farko da zan bayar tana bayani ne akan *Gaskiya da Amana*, wato mu sani cewa yanzu zamani ya canza ta yadda bafa kowa ake bawa gaskiya da amana ba, akwai mutane masu daɗin  baki dake amfani da kalamai masu daɗi su janyo mutum a jikinsu sai bayan ka gama amincewa  dasu sai su zalunceka, wannan labari da zan bayar ya faru ne akan wata yarinya mai suna Indo, indo ta kasance mai saurin amincewa da mutane tare da gasgatasu, kuma wannan hali nata shine silar jefata a cikin halin ƙaƙa nikayi, masu saurare sai ku biyoni da kyau domin jin yadda wannan labari ya kasance:

A Ruggar Shehu, an taɓayin wata yarinya da ake kira Indo, Indo yarinya ce mai aji, fasali, ilimi, haɗi da duk wani abu da ake buƙata ga ƴa mace, mahaifinta shine sarkin manoma na wannan rugga kuma ana kiransa da Barau,  Barau mutum ne mai himma da iya muamala a cikin mutane kuma wannan hali nasa shine silar janyo masa farin jini ga  ɗaukacin mutanen wannan rugga, Barau yanada mata ɗaya Lami wato mahaifiyar Indo. 
Indo tana samun gata dai dai gwargwado kasancewarta ita kaɗai ga iyayenta, duk wata tarbiya da yakamata ace uba ya baiwa ƴarsa to bako shakka Barau ya baiwa Indo domin sai da takai ta kawo maƙwabtansa ma suna masa magana akan takurar da yakema indo ya wuce gona da iri. Shi kuwa Barau ko a jikinsa domin a saninsa Indo tanada wani hali wanda bayaso, kuma wannan hali ba kome bane in banda saurin gasgata mutane, duk abunda aka faɗa mata tana yadda ba tare dayin dogon nazari ba shi kuma Barau ba abunda yafi tsana irin wannan hali, yayi mata magana yafi a ƙirga amma ba abunda ya canza domin abu kullum sai gaba yake, ana nan ana nan wata rana Barau yana cikin aikin gona tare da ƴarsa Indo dake taimaka masa yin ƙananan aikace aikace sai yaji sukuwar doki a bayansa, anan ya tsayar da aikin domin ganin ko waye, mutumin namiji ne cikin shiga ta alfarma sanye da rawani a saman kansa, anan wannan mutumi ya nufo Barau gadan gadan, bayan sun fuskanci juna ne sai mutumin ya fara magana kamar haka:

*Page 3*

 " Da farko dai sunana Tanimu, gaskiya ba a wannan rugga nakeba amma kuma ina shigowa yawon sukuwa a saman dokina, kuma a cikin wannan yawo da nake nayi gamo da wata yarinya zata tafi ɗibar ruwa a rafi, da farko naso kada nayi magana amma kuma daga baya sai naji bazan iya cutar da kaina ba, sabida haka sai na gabatar da ɗan ƙaramin bincike, to a cikin binciken dana gabatar sai na gano cewa wannan yarinya dana haɗu da ita ƴarka ce kuma idan har kabani dama to zan so na gabatar da kaina a wurinta na gani ko zan samu ƙarɓuwa." Bayan mutumin yazo nan a zancensa sai ya tsaya yana jiran amsar da Barau zai basa.
  " To gaskiya naji daɗi sosai daka tuntuɓeni akan wannan magana domin wannan shine ya kamata mutumin kirki ya farayi wato ya fara gabatar da kansa ga iyayen yarinya kafin ya fara tuntuɓar ita yarinyar, sabida haka na baka dama yanzu idan mun koma gida zaka iya gabatar da kanka a wurinta idan ka samu karɓuwa shi kenan domin bazan yiwa ƴata auren dole ba." 
  Anan Barau yayi sallama da Tanimu cikin farin ciki cewa Tanimu zai dawo da marece domin ya gabatar da kansa zuwa ga Indo, bayan Barau ya koma gida sai ya labartawa mahaifiyar Indo abunda yake faruwa, ita kuwa Indo tunda mahaifiyarta ta bata wannan labari sai ta shiga cikin wani yanayi na faɗuwar gaba da kuma tsoro, Indo bata ankara ba sai da taji ana mata sallama a waje, cikin sanyin jiki da miƙe tsaye, rarumo mayafi tayi daga nan ta nufi waje, ai kuwa tana fita waje sai tasha jinin jikinta domin  a wannan lokaci ba abunda Indo take tsoro irin doki, wani wawan tsalle ta daka ta juya da gudu, ai kuwa juyawar da zatayi sai ta faɗa jikin mahaifinta Barau. Sai da ƙyar Barau ya shawo kan Indo har ta yarda zata saurari Tanimu. Bayan Indo ta yadda zata saurari Tanimu sai mahaifinta ya tafiyarsa domin basu wuri su tattauna, anan Tanimu ya fara zuba bayani Indo na saurare amma hankalinta baya nan domin duk bayan daƙiƙa sai ta juya ta kalli inda dokin yake ta gani idan bai nufota ba, haka dai tayi sallama da Tanimu ba tare da bashi amsar da yake nema ba. Bayan Indo ta koma gida sai wani tsanar Tanimu ya dabai baye mata zuciya, a cikin zuciyarta kuma tanaji ba wai Tanimu ne ta tsana ba kamar dokin nasa ne ta tsana. 

*Page 4*

Dedicated to: Halima Bala Wakili

Haka dai taci gaba da wannan tunani har bacci yayi awon gaba da ita, tun da sanyin safiya mahaifiyar Indo wato Lami ta damƙa mata tulu domin taje rafi ta ɗebo ruwa, cikin fushi Indo ta karɓi tulun domin ta tsani a mata irin wannan tashin da ƙulu ƙulun safiya, anan ta kama hanya tana haɗuwa da mafarauta ɗai ɗaiku  a saman hanya, har ta isa rafi bacci bai saketa ba, hangawa tayi iyakar ganinta amma babu kowa a wurin, anan ta sanya tulun cikin ruwa sai da ya cika maƙil sa an nan ta fito dashi, ɗaukar tulun tayi da nufin azawa a saman kai ai kuwa sai talallaɓiya da zaftare mata ƙafafuwa, anan Indo ta saki tulu daga nan kuma sai ruwan ya janyota da ƙarfin tsiya, ihu Indo ta ƙwala tana neman taimako domin ji take kamar ana janyota a cikin ruwan, abunda ya tayar mata da hankali shine babu kowa a wurin balantana ta samu agaji, haka dai Indo taci gaba da ihun neman taimako su kuma ruwan rafi sai ƙara ingizata suke da ƙarfin tsiya, tana cikin wannan hali ne sai taji kamar daga sama an janyo hannunta da ƙarfin tsiya, ba ƙaramin daɗi Indo taji ba ganin cewa Tanimu ne ya kawo mata ɗauki, cikin sauri Tanimu ya fito da ita yana mata sannu, a saman dokinsa ya azata kuma ya kawota har gida tare da faɗama mahaifinta abunda ya faru, a wannan rana Lami tasha faɗa domin sai da Barau ya mata tas da yake yasha faɗa mata tabar aikin Indo ɗibar ruwa da sanyin safiya domin ba a san abunda ke iya faruwa ba. Wannan jarumtaka da Tanimu ya aiwatar yasa iyayen Indo suka ƙara bashi girma ita kuwa Indo sai ta sakankance dashi gaba ɗaya. Kwanci tashi har takai Indo tabar tsoron doki gaba ɗaya domin wasu lokutta Tanimu da kansa zai rakata ɗiban ruwan kuma har ya azata a saman dokinsa, duk wannan abu dake faruwa kamar an yiwa iyayen Indo sihiri domin basu nunawa Tanimu cewa mu amalar ta isa hakanan yanzu idan da gaske yake to ya turo manya ayi magana, kuma abun ikon ALLAH basu taɓa tambayar asalin sa ba ko kuma suyi bincike akansa ba. Wata rana sai tafiyar gaggawa ta kama mahaifin Indo, kuma tafiya ce mai muhimmanci domin zai tafi wani gari ne ya sayar da kayansa na gona, kuma garin da zai tafi akwai nisa domin sai an tsallaka ruwa, a wannan lokaci da zai tafi Indo na bacci sabida haka bai samu damar ganawa da ita ba, iyaka dai yayima matarsa Lami sallama daga nan kuma ya kama hanyar da zata saɗashi da jirgin ruwa kwale kwale ɗauke da ƴan buhuhuwansa.

*Page 5*

 " Indo kada ki ɗauki gaskiya da amana ki baiwa wannan yaron Tanimu domin wasu mutane basu tsoron ALLAH sabida haka basu san muhimmanci riƙe gaskiya da amana ba."
Firgigit Indo ta farka tana juyayi, bako shakka mahaifinta ne ta gani a cikin mafarki yana faɗa mata wannan zance, cikin sauri ta nufi ɗakin mahaifinta, anan ta tarar bayanan, ai kuwa tana fitowa sai tayi kiciɓis da mahaifiyarta Lami wadda ta fada mata cewa ai yayi tafiya tun da sanyin safiya. Indo bata faɗawa kowa wannan mafarki ba iyaka dai tabar abun a zuciyarta sai faman saƙe saƙe take.
  Ana nan ana nan wata rana sai Tanimu ya bijirowa da Indo da wata sabuwar magana, har Indo ta shigo gida tana tunanin wannan zance:
 " Wai ke Indo me kikeyi a cikin ƙauye? ki biyoni mu tafi birni muci duniyarmu da tsinke, idan har kin yadda to babu abunda zai faru kuma kada ki manta ni yanzu ai nakai matsayin da zaki iya ban gaskiya da amana domin bazan zalunceki ba." Haka Indo taci gaba da tunanin wannan zance a kullum dako yaushe, shi kuwa Tanimu a kullum idan yazo fira to sai yayi ƙoƙari ganin cewa ya laftawa Indo daɗaɗan kalamai masu taɓa zuciya, a haka dai Tanimu yaci gaba da laftawa Indo lafazi mai laushi har yaci sa a ta aminta dashi tunda kwana ɗaya ne zasuyi.
   Haka Indo ta damƙawa Tanimu gaskiya da amana ba tare dayin tunani ba, ba tare dayin nazari ba kuma ba tare dayin shawara da kowa ba, sai da rana ta faɗi liƙis sa annan Tanimu yazo, bayan Indo ta yiwa mahaifiyarta ƙaryar cewa Tanimu  zai rakata gidan ƙawarta Mairo kuma sai cikin dare zata dawo. Da sauri Tanimu ya aza Indo saman dokinsa yana mai binta da daɗin baki, daganan ya kaɗa linzamin dokinsa yana mai zaburar dokinsa. Tun da suka fara wannan gudu Indo kejin kasala domin jikinta ne ya rufe da wani irin zafi, haka dai Tanimu yaci gaba da gudunsa ita kuwa Indo idanuwanta suna buɗewa da rufewa har takai idanun nata sun rufe gam, daga wannan lokaci bata ƙara sanin inda take ba. Kamar daga nesa tanajin hargowa na mutane, kamar a jikinta tanaji ana zuba mata wani abu, firgigit Indo ta farka tana kallon inda take, abunda ya tayar mata da hankali shine tsananin duhun da tayi tubali dashi.

*Page 6*

Tunani ta farayi a lokacin da Tanimu ya azata a saman dokinsa daga nan ya fara gwabza namijin gudu, ana haka sai kasala ta rufe mata jiki daga nan kuma bata ƙara sanin inda take ba, da sauri Indo ta miƙe tsaye amma a mamakinta sai taji ƙafafuwanta ɗaure suke tamau da kaca ta yadda bata iya tafiya sai dai tsalle, hakama hannuwanta an ɗaure su tamau da kaca, bakinta kuma an saka wani abu an liƙe shi gam ta yadda bata iya magana, hawayen takaici ne ya fara kwarara saman idanuwanta daga nan kuma ta fara tuno mafarkin da tayi:
 " Indo kada ki ɗauki gaskiya da amana ki baiwa wannan yaron Tanimu domin wasu mutane basu tsoron ALLAH sabida haka basu san muhimmanci riƙe gaskiya da amana ba." Wasu hawayen baƙin ciki ne suka dilmiyowa Indo, a wannan lokaci ba ƙaramin tashin hankali Indo ta tsinci kanta a ciki ba, shin wai dama Tanimu yaudarata zaiyi? To amma me yasa? Wane laifi na masa? Kuma wane wuri ne nan? Meye dalilin da yasa ya shigo dani a wannan wuri? Indo na cikin wannan tunani sai taga an banko ƙofa da ƙarfi, anan taga wasu ƙatta uku sun shigo, kai da ganin shigarsu da yanayin jikinsu kasan ba Hausawa bane, da ƙarfi suka janyota suka fito da ita a cikin ɗakin, bayan sun fito ne sai taga ashe ba ita kaɗai bace, akwai ƴan mata da yawa irinta waɗanda aka fito dasu da ƙarfi ana ingizasu da ƙarfin tsiya, abun tambaya ko ina za a kai waɗannan ƴan mata? haka aka yita jan su Indo har aka shigo dasu wani ƙaton ɗaki mai famfuna dogaye birjik, daga nan sai akayi musu zigidir bayan an kwancesu, ba yadda Indo batayiba domin kada a cire mata sutura amma abu yafi ƙarfinta, abun haushi shine wai waɗannan ƙattan sune zasu mata wanka, tanaji tana gani hadda kubce kubce, amma haka suka ɗaureta tamau sa annan suka mata wankan soso da sabulu, a wannan rana Indo taci kuka har ta yafe domin tunda take a rayuwarta irin haka bai taɓa faruwa  ba, jero ƴan matan akayi gaba ɗayansu ana musu kwalliya harda Indo, kuma abun baƙin ciki maza ne ke musu kwalliyar, bayan an gama kwalliya sai akaba kowacensu sutura domin ta sanya, suturar da aka basu bayada ban banci da babu domin jikinsu a fili ana ganin kome, bayan sun gama sanya suturar sai aka fara musu hotuna, cikin daƙiƙu  aka wanko hotunan waɗanda suka kasance masu girman gaske.

*Page 7*

 Anan aka fara kai waɗannan ƴan mata a wasu ɗakuna.Duk wadda aka jefa cikin ɗakinta sai a kulleta daga nan sai a ɗaura hotonta saman ƙofar ɗakin, bayan an jefa Indo ɗakinta sai taga cewa ɗakine gwanin ban sha awa mai ɗauke da bayi, har yanzu Indo tunani take dalilin da yasa aka shigo da ita wannan gida, wai kuwa Tanimu ne ya mata haka ko kuwa dai shima yana cikin irin halin data shiga ne? A kullum da safe, rana dare ana kawo mata abinci da abinsha, haka Indo taci gaba da rayuwa cikin rashin sanin dalilin da yasa aka shigo da ita wannan gida, ana nan ana nan wata rana a cikin dare sai ta farajin wata hargowa a can gefen ɗakin, tafiya ta farayi a hankali har ta iso wurin, anan taga wata rijiya mai tsananin girma, hannu ta sanya ta buɗe marfin rijiyar, da sauri taja baya sabida tsananin duhun data hango a ciki, hargowa taji a cikin rijiyar da alama akwai wani abu a ciki,  dube duben ɗakin ta farayi har ta samu wata ƙaramar fitila, da sauri ta nufo rijiyar inda ta tarar akwai wani tsani na ƙarfe wanda zai shigar da ita can ƙasan rijiyar, hawan tsanin tayi tana takawa a hankali har ta samu kanta ƙasan rijiyar, ai kuwa tana dirowa sai taci arba da wata mace durƙushe sai faman nishi take, da farko Indo ta tsorata ganin matar cikin wani irin yanayi na ƙunci, amma daga baya sai ta mayar da hankalinta wuri ɗaya inda ta fuskanci matar, ita kuwa matar sai ta bata labarinta kamar haka:
  " Saurayi na shine silar shigowata wannan gida bayan na damƙa masa gaskiya kuma na basa amanar kaina, amma bai dubi hakan ba, yake ƴar uwa ki sani cewa wannan gida babu abunda ke ciki in banda masifa, duk yarinyar da aka shigo da ita a wannan gida to za a mayar da ita karuwar ƙarfi da yaji, idan zaki tuno bayan an gama yi muku wanka ai sai da aka muku hotuna, kuma aka ɗauki hotunan aka manna ga  ƙofar kowane ɗaki da akwai mace a ciki, to idan namiji yazo neman mata iyaka a fara nuna masa ƙofofin kowane ɗaki domin ya zaɓi hoton wadda ta masa, duk wadda ta masa zai biya kuɗinta daganan sai su buɗe masa ɗakinta domin yayi lalata da ita, kuma idan bata yadda ba suyi mata dukan tsiya kuma su tilasta mata, haka suke neman kuɗi da mata ba dare ba rana. Duk wadda  sugaka batada lafiya ko kuma ta gaza sai su jefata cikin rijiya domin yunwa da baƙin ciki su kasheta.

*Page 8*

Kuma kowane ɗaki akwai rijiya iyaka da mai ɗakin ta gaza sai a jefata cikin rijiyar a nemo wata. Anan indo ta lallashi wannan yarinyar daganan itama ta bata nata labari, cikin ƙankanin lokaci Indo tayi sabo da wannan yarinya mai suna Mariya kuma sukayi shawara a tsakaninsu cewa zasu nemo mafita a cikin wannan dare, Indo taimakawa Mariya tayi har suka fito cikin rijiyar sabida kasancewar Mariya babu lafiya kuma rashin lafiya ne yasa ta gaza fitowa cikin rijiyar bayan an jefata ciki, bayan sun fito cikin rijiyar sai suka zauna jiran wanda zai kawo abincin dare ya ƙaraso, ai kuwa basu jima ba suka fara jiyo sautin takalmansa, Wani ihu Mariya ta ƙwala mai razanarwa, shi kuwa gogan naka yanajin haka sai ya nufi ɗakin da sauri domin a tunaninsa wani abu ne ya faru, yana shiga Indo ta makesa da wani ƙarfe. su Indo na ganin ya faɗi sai suka fita da gudu, matsalar shine Mariya bata iya gudu da sauri sabida rashin lafiya, indo gudu take amma dole ta dawo baya ta taimakawa Mariya, ga gidan da lungu lungu saƙo saƙo, gudu suke amma har yanzu basuga hanyar fita ba, suna cikin gudun ne suka haɗu da wasu samudawa gandam gandam su bakwai, dole su Indo suka bada haɗin kai aka kamasu, daga nan sai samudawan suka jefasu cikin wani ɗaki da nufin keta musu haddi, to kafin su iyar da nufinsu ne sai Indo taga wata fuska da batayi tsammanin cewa zata ƙara gani ba, Tanimu ne ya shigo ɗakin daganan ya tsawatama samudawan a cikin wani halshe, anan tunani ya cikama Indo ciki, dama Tanimu ba bahaushe bane? to idan bahaushe ne ina yasan waɗannan mutane har ya iya halshensu? Wasu baƙaƙen maganganu Tanimu ya faɗama Indo masu taɓa zuciya har sai da tayi dana sanin haɗuwa dashi. Ashe dama gaskiya ta ƙare! ashe dama babu amana! Dama haka duniyar take! Wanda kake tunanin masoyinka ne ashe maƙiyinka ne, Wato kada mutum ya baiwa kowa aminci kenan! Ko kuwa dai mutum yayi bincike kafin ya bada aminci ɗin! Haka Indo da Mariya suka cigaba da zama cikin wannan sabon ɗaki ba dare ba rana shi kuwa Tanimu iyaka ya shigo ya faɗa musu maganganu son ransa daganan kuma ya tilasta musu saɗuwa dashi, a duk lokacin da Tanimu ya shigo ɗakin to Indo da Mariya basu bashi haɗin kai sai dai ya gaji ya tafiyarsa, ana nan ana nan sai ga Mariya ta warke sarai daga nan kuma sai wata dubara ta faɗo musu yadda zasuyi maganin Tanimu. 

*Page 9*

A cikin wani darene Tanimu yazo musu kamar yadda ya saba da buƙatarsa. A wannan lokaci yayi mamaki domin Indo ta basa haɗin kai, shi kuwa gogan naka yana ganin haka sai ya saki jiki ganin cewa ba abunda zai faru, yana cikin wannan hali ne Mariya ta narka masa wani bagidajen ƙarfe a saman kai, anan ya faɗi yana mulmule mulmule, a cikin rijiyar ɗakin su indo suka jefasa, suna kulle rijiyar sai suka fito waje da gudu, wani azababben gudu suka farayi kai kace walƙiya, lungu lungu saƙo saƙo sukebi kasancewar gidan da tsananin girma, sai da ƙyar da suɗin goshi suka samu damar fita, tsintar kansu sukayi a wani daji, gudu sukaci gaba da yi har takai sun haɗu da wasu ƴan sanda masu patrol ɗin dare, sa ar da suka samu shugaban ƴan sandan bahaushe ne, kuma a cikin ƴan sandan akwai Hausawa, anan su indo suka baiwa waɗannan ƴan sanda labarinsu  daga farko har ƙarshe, anan ƴan sandan suka tausaya musu da musu alƙawari cewa zasu ɗauki mataki game da wannan al amari, kuma a cikin hakane su Indo suka gane cewa ashe a cikin Liberia suke, shugaban ƴan sandan sai da ya tabbatar da cewa Indo da Mariya an dawo dasu Nigeria wurin iyayensu daga nan kuma Indo ta labartawa iyayenta abunda ya faru tare da daukar niya cewa bazata ƙara damƙawa wani mutum gaskiya da amana ba har sai tayi bincike idan ya cancanci hakan.  Daga nan sai Alham tayi shiru kafin taci gaba da bayani,  " bako shakka wannan labari ya karantar damu cewa kada mu baiwa mutum gaskiya da amana ba tare dayin bincike akansa ba, kuma kada ganin cewa mutum yana iya ƙoƙarinsa ganin cewa ya faranta maka ka ɗauki yarda ka damƙa masa, duk abunda zamuyi to muyi bincike mai zurfi kafin mu aiwatar sabida haka ina ba matasa maza da maza shawara kada ku sakankance cewa zaku ɗauki gaskiya da amana ku baiwa mutum wanda bakusan asalin sa ba, bakusan ma inda ya fito ba, yin hakan kuskure kuma munga abunda ya faru ga Indo.


Shawarwarin da zamu duba a cikin labarin sune kamar haka:

(1) Kada ka gasgata mutum ba tare da yin dogon bincike akansa ba, idan muka dubi wannan labari zamuga Indo ta kasance mai saurin gasgata mutane wanda hakan yasa Tanimu ya samu galaba akanta

(2) Ba kowa ake baiwa gaskiya da amana ba, kafin ka baiwa mutum gaskiya to ka tabbatar cewa ya cancanci hakan

(3) Kada daɗin bakin mutum yasa ka dauƙa cewa mutumin kirki ne har ka bashi dama ya illata ka

(4) Duk wani abu da zakayi yanada kyau ka fara tambayar Iyayenka ko ka nemi shawarar na gaba gare ka domin jin irin nasu tunani, da ace Indo ta nemi shawarar iyayenta da bazasu taɓa bari ta biyewa Tanimu ba har ya kaita ga mahalaka


(5) Duk wanda yazo neman ki to ki tabbatar cewa anyi bincike akan asalinsa, sana arsa da kuma iyayen sa domin gudun faɗawa halaka, haka kuma maza ku tabbatar kunyi bincike kafin ayi aure

Anan mukazo ƙarshen babi na farko sai kuma ranar Laraba wato 30( August) 2023 zamu yi posting babi na biyu, kada a manta waɗanda basu son posting zasu iya sayen complete ducument akan 300 kacal, mata zaku iya tuntuɓar Zainab Mustapha Musa +234 814 055 1791 maza kuma Isma'il Abubakar +234 903 740 5690, masu buƙatar posting kuwa kada a manta zamu haɗu a ranar Laraba 30 ( August) 2023, domin jin waɗanne irin shawarwari ne babi na biyu zai zo muna dasu

Zamfara Writers Association
In Conjunction With
King and Queen Writing Chamber


*SHAWARA ABAR DUBAWA*
                                                                        By
                                                                *Abdul King Article*   
                          .                                             *Asmy_Cute*
                                                                    *Esma'el Last Born*    
                                                     
*Zainab Mustapha Musa (Mmn Sadig)*
                                                                              All in

Zamfara Writers Association
In Conjunction With
King and Queen Writing Chamber

*Domin ganin farkon labarin*:
https://www.kingarticlenovels.com/2023/08/shawara-abar-dubawa.html


*Whatsapp Group*:
https://chat.whatsapp.com/Fk1ohCHMdAdHGYh5hHRo1A

*Facebook Group*:
https://facebook.com/groups/1435791047211648/

Babi na Biyu
( Kama Ƙarya a Cikin Soyayya )

Page 10

Shawara ta biyu da zan bayar tana bayani ne akan rashin gaskiyar da wasu ƴan matan ke yiwa maza wato kama ƙarya a cikin soyayya, a cikin wannan labari zamuga illar zaɓar dukiya akan masoyin gaskiya, da yake labarine akan wani yaro Audu wanda budurwarsa ta yaudara bayan ya mata goma da goma na arziƙi, masu saurare sai ku biyoni domin jin yadda wannan labari zai kasance:
Abida yarinya ce kyakkyawa dai dai gwargwado, zaune take akan kujerar ƙarfe tana wasa da tsinken tsintsiya a hannun ta, duka duka shekarun ta bazasu haura sha tara ba, Abida yarinya ce mai yawan tunani, a yanzu haka tayi nisa a tunani sosai amma hakan bai sa ta daina wasa da tsinken da ke hannun ta ba na tsintsiya.  Kiran sunan ta da mahaifiyar ta ke yi yasa ta dawo hayyacin ta, 
"Abida, Abida." amsawa tayi a hankali " na'am inna" 
" Me kike tunani haka?" Inna ke tambayan ta, 
" babu komai." Abida ta baiwa inna  amsa,tashi tayi ta shiga ɗaki ta zauna akan kujera ta zuba uban tagumi.
" Toh ni dai tashi na aikeki gidan Asabe ki ce nace ta bani ƙulin ashirin bashi zan aika mata kuɗin ta idan baban ku ya dawo," amsawa tayi da "toh" amma jikin ta bai bata ta je gidan ba tare da kuɗin ba sabida Asabe bata da mutunci.

*Page 11*

Ta shi tayi ta nufi wajan da ta ke ajiye jakan islamiya ta ɗauko ta buɗe ta na da hamsin da ta ajiye,  hijabi ta sa ta wuce ta siyo ƙuli ta dawo, anan inna ta tayi masu kwaɗon ƙanzo da ƙuli suka ci suka sha ruwa, bayan rana ta faɗi sai Abida tace ma inna zata fita zataje gidan ƙawarta, amsa mata inna tayi da " Sai kin dawo amma ki kula kin san yanzu samari basu da halayen ƙwarai ba kowa ke yi maka magana ba ka amsa, amma kar ki wulaƙanta kowa kinji Abidan inna."  amsawa Abida tayi da " insha ALLAH zan kiyaye inna."
Abida sai faman tafiya takeyi tana tunanin yadda zatayi aure domin ita zaman gida ya ishe ta amma matsala ɗaya ke damunta waye zai so ta kuma ina zata samu wanda ta ke so? Tambayan da ta ke yiwa kanta kenan har ta isa gidan su ƙawarta Lantana, sallama tayi aka amsa sannan ta gaida mahaifiyar Lantana tare da tambayar ta " Lantana na gida kuwa? " Amsa mata mahaifiyar Lantana tayi da " a'a na aike ta kai sirfe amma yanzu zata dawo ki zauna mana ga wuri kafin ta dawo." Cikin ladabi Abida ta zauna suna hira har Lantana ta dawo, ta shi su kayi suka koma ɗaki, lantana ta fara tambayar ta: 
 " Wai lafiya duk kika koma haka duk kin rame kamar wadda bata cin abinci!" 
 " Ai gwanda wanda baya cin abinci da halin da nake ciki!" Inji Abida.
 " innalillahi meya faru?" Lantana ta faɗa cikin mamaki, Anan Abida ta fara bata labarin abinda ke ranta, " Tashin hankali!"  lantana ta faɗa tare da waro idanuwa. " Kina nufin yaudara kenan kike so kiyi?" Lantana ta tambaya.
 " Bangane yaudara ba me kike nufi ne?" Inji Abida.
 " Eh mana yaudara kikeso ki aikata ko tunda  ina samarin ki da ke cikin garin nan duka?" 
Anan Abida ta watsa mata wani kallo tare da faɗin " Dalla ja can wayace miki auran su zanyi?" 
" To shikenan ai sai kiyi mu gani," Inji Lantana, bayan sun taɓa hira sai sukayi  sallama, anan Abida ta nufi hanyar gida, akan hanyan ta ta komawa ta hadu da saurayin ta Sa'idu amma tayi kamar bata ganshi ba, shi kuma kamar wani wawa ya buɗe baki yana kallon ta har ta wuce abunta. 

*Page 12*

Bayan Abida tayi tafiya mai nisa sai taji ana kiran sunanta, anan ta tsaya wuri ɗaya tana jiran ƙarasowar wanda ke kiranta, haka ta ke jin ta ku ɗaya bayan ɗaya har aka ƙaraso wurin ta, sallama akayi mata sannan ta amsa bayan tagama kallon ko waye sai ya fara magana kamar haka
  " ina ce ba ki sanni ba ko?"  
  Amsawa tayi da "eh," 
" To shikenan tunda ba ki sanni ba sai an jima." Anan ya tafiyarsa
Tunani Abida ta tsaya yi wannan waye haka da zai mata  magana kuma yana wani ja mata aji lalle ko ma waye ya ci uwar rainin hankali duk ƙauyen nan wa ya kaita kyau da har yau namiji zai ja mata aji, gajiya tayi da tsayuwa ta wuce gida. Bayan gari ya waye Abida tagama aikin da ta ke taya inna, anan ta fita ko zata ƙara ganin wanda yayi mata magana jiya  amma bata ganshi ba, gajiya tayi da zagaya ƙauyan ta dawo gida. Bayan  anyi  Isha'i sai ta ƙara fita amma bata samu abinda ta ke so ba, tana tafiya akan hanyar ta ta dawowa taji ance "Sunana Audu."  Chak ta tsaya wuri ɗaya 
 " Audu kuma innalillahi waye kai dan ALLAH?" 
  Amsa mata yayi da  "Ɗan Adam mana kamar ke kyakkyawa!" 
  " Meye kuma na zolaya?" Abida ke tambaya.
  " Babu wani zolaya ALLAH ke kyakkyawa ce kuma ina son ki." Inji Audu.
Abida tayi mamaki jin Audu ya ambaci kalmar so kai tsaye babu ko alamun kunya, amma duk da haka sai ta gimtse kawai kamar bata damu ba, da taga dai abun nasa da gaske yake sai tayi dariya daganan ta wuce gida ba tare da faɗa masa kome ba, bayan Abida ta isa gida sai ta samu mahaifiyarta zaune a tsakar gida,
" Wai ke Abida meke damun ki ne yau ba ki da aiki sai yawo ina kike zuwa ne?"
" Motsa jiki nake zuwa shiyasa amma kiyi hakuri bazan ƙara ba idan ba kya so." 
 " Shikenan ki wuce ga abincin ki nan kije ki dauko ki ci."
 Amsawa Abida tayi da " toh inna." Bayan taci abinci ta kwanta ta fara bacci acikin bacci wazajen assalatu ta ke jin ana kiran sunan ta amma ta kasa tashi.
 
*Page 13*

" Shikenan idan bazaki tashi kiyi Sallah ba bara na debo ruwa na zuba miki sai ki tashi..." Inji inna, tashi Abida tayi tana faɗin " haba inna me yayi zafi haka!"
A kwana a tashi dai soyayya me ƙarfi ta shiga tsakanin Audu da Abida amma Abida sam bata son Audu dukiyar shi ta ke so. Kullum sai ya zo gidan su amma da yayi mata maganan aure sai tace ya bata lokaci, bayan sun ɗauƙi tsawon wata shidda suna soyayya sai Abida ta fara tunanin yadda za ayi ta yaudareshi, tana so tayi amfani da kuɗi sosai wajan yiwa kanta hidima, kuma ta na so ta je birni yawon buɗe ido, wata irin dariya tayi sannan ta tashi ta fita neman Audu, tayi Sa'a kuwa ta ganshi sannan ta fara tambayan shi kudi ta ke so dan ALLAH ya taimaka ya bata dubu hamsin tana so tayi siyayya a birni, amsawa yayi da " Toh ai kinsan kinfi ƙarfin komai a wurina insha ALLAH anjima zan kawo miki shalele ta ina ƙaunar ki kyakkyawa ta,"  hira sukayi sosai sannan ta wuce gida bayan an ɗauki lokaci kaɗan aka aiko wani yaro neman Abida, fita tayi tana zuwa taga Audu ne ashe ke yi mata sallama, bayan sunyi hira ya sa hannun shi aljihu ya ciro kuɗi ya ba ta suka yi sallama har yana tsokanan ta da ƴar birni. Bayan ta shiga gida ta samu wuri ta ajiye kuɗin wurin da babu me gani, a kwana a tashi dai Abida ba taje birni ba idan Audu ya aiko kiran ta sai tace aje ace mishi ita ba ajin shi ba ce, bazata zo ba, Audu ya shiga tashin hankali sosai meyasa Abida zata yaudare shi lokaci ɗaya shin dama ba son shi ta ke tsakani da ALLAH ba kuɗin shi ta ke so. Idan kuɗi ne kuwa taci kaɗan wallahi sai na ɗauki fansa. haka yake faɗa acikin ran shi shi kaɗai har bacci ya ɗauke shi. a kwana a tashi dai Abida ta nemi umarni wurin iyayenta cewa tanaso ta kaiwa wasu ƴan uwansu ziyara a birn kuma cikin sa a suka aminta bayan sun bata guzuri mai yawa, Abida a birni tafiya ta ke cikin ƙasaita tana ji babu kamar ta tana ɗauke da naira dubu hamsin a jikin ta,  har ta isa kasuwa zatayi siyayya, bayan ta siye abinda ta ke so zata bada kuɗi wani mutum a gefen ta yace " Haba kyakkyawa kamar ki kalar villah zaki biya kuɗi da kanki ki bar abinki kawai zan biya."  godiya tayi, ya biya ƙudi ta wuce tana tafiya ya ce da ita " Haba malama taya zaki tafi bamuyi sallama ba, amma yanzu abinda za'a yi ki bani number wayanki zan kiraki idan kin isa gida,"  Murmushi tayi sannan tace  " meye kuma waya?" Dariya yayi yana mai cewa : "Bangane meye waya ba dan ALLAH ki bani kinji."

*Page 14*

" Wallahi bansan meye haka ba mu a ƙauyen mu bama da ita." Inji Abida.
 " Shikenan." Haka ya faɗa daganan yace ta ɗan jira shi ya shiga kasuwa, anan ya siyo waya da sim card ya bata,  Bayan ta isa gida ya kirata suka gaisa, sannan yace da ita auran ta yake so yayi nan da sati biyu gobe zai turo iyayan shi ayi magana, tana dariya ta kashe waya tana murna zata zama ƴar birni, bayan gari ya waye ɗan birni ya cika alƙawari ya turo iyayan shi akan maganar auren Abida, aka amince an bashi. Magana tabi gari kowa ya sani, har Audu ya ji da sauri yazo gidan su yana tambayar ta shin da gaske ne abinda ya ji a gari, amsa ta bashi da cewa " Tabbas abinda kaji hakane," kuka ya shiga yi me ƙarfi yana roƙonta, " kar kiyi min haka kinsan bazan iya rayuwa idan babu ke ba, dan ALLAH ki tausayamin."  tsaki tayi ta wuce gida.Tashi yayi ya share hawayen shi yana faɗin " Sai dai kowa ya rasa." Bayan Audu ya koma gida sai tunani ya hanasa sakat domin daya gincira sai maganar Abida ta faɗo masa, " Tabbas abinda kaji hakane," to shi kenan yanzu ya rasa Abida har abada, gaskiya bazai yiwu ba, dole ya ɗau mataki akan wannan cin amana da Abida ta masa. Shi Audu abunda yafi baƙanta masa rai shine kuɗinsa data wawashe bai ji bai gani ba, a cikin hakane Audu ya yanke shawara cewa zai yi amfani da tsumin sihiri ganin cewa ya tarwatsa rayuwar Abida, haka yaci gaba da wannan tunani har bacci yayi awon gaba dashi, to a cikin bacci ne sai Audu yayi mafarkin wani haske a cikin wani wuri mai duhu, shi kuma sai yata bin hasken har ya iso daf da hasken, yana isowa sai ya tarar da mahaifiyarsa a cikin wannan haske fuskarta cike da murmushi.
   " Uwa, dama kina nan?" Audu ya tambaya cikin mamaki da yake yana kiran mahaifiyarsa da Uwa.
   " Aa Audu har yanzu bana nan kuma yanzu ma daka ganni nazone domin na gargaɗeka akan wani kuskure da kake shirin aikatawa."
  " To Uwa wannan wane irin kuskure ne da kike tuhumata akai!" Inji Audu. Anan Uwa tayi shiru na ɗan lokaci kafin ta fara magana kamar haka:
 
*Page 15*

 " Wato ka sani Audu nasan cewa yaudara akwai ciyo amma ka sani cewa wannan tudu da kake shirin hawa babu indai zai jefaka sai cikin rame sabida haka ina shawartarka dakayi saurin janye duk wani makami daka tanada domin gudun faɗawa halaka."
 " To Uwa, sabida dai kinyi magana zan janye amma naso ramuwar wannan ciyo da aka dasamin a ƙirji."
 " Kayi haƙuri ɗana, ALLAH zai saka maka da alheri ka zuba ido zakaga abunda zai faru."
Firgigit Audu ya farka, bako shakka mahaifiyarsa ce ya gani kuma duk abunda ta faɗa masa yana jinsa har cikin zuciyarsa, alwala yayi daganan yayi salla raka a biyu, adduar neman gafara yayiwa mahaifiyarsa daganan yayiwa kansa addua. Tun kafin ya iyar da addua ne baba yazo yana tashinsa su tafi masallaci. Bayan sun dawo masallaci sai baba yayi kiransa domin su tattauna wata magana, koda Audu ya shiga ɗakin baba sai ya tarar dashi kishigiɗe saman buzunsa, anan Audu ya samu wuri ya zauna, shi kuwa baba yana ganin haka sai ya fara bayaninsa kamar haka:
  " Abunda zan faɗa maka ba dolene kaji daɗi ba amma dai ba yadda muka iya dole haka za ayi, wato Audu ka sani inada wani tsohon amini a birni domin tun muna yara muke tare, to ba a daɗe ba yazo wannan ƙauye namu neman mata kuma an bashi, to bayan mun gaisa ne sai yake faɗamin cewa me zai hana ka bishi a birni wata ƙila ka samu abunda yafi nan, a yanzu haka dai da marece zai aiko direbansa da mota Akori Kura domin ta kwashe kayanka, ni muma zan baka buhuhuwan abinci da kuma bisashe domin kayi sana a a can, ni kuma zan cigaba da noma da kuma sayar da kayan abinci, ina fatan ka gane." Tunda baba ya fara magana zuciyar Audu ke bugawa domin shi cikin ransa bayan son tafiya birni a wannan lokaci kuma bazai iya ƙin amsar wannan umarni da baba ya bashi ba, shi Audu abunda yafi tayar masa hankali shine kada ace aminin babansa ne Abida ta aura domin idan hakane gaskiya baza a yi mai kyau ba.
  " Ina magana kayi shiru bakace kome ba!" Baba ya faɗa cikin tsawatawa.
  " Ba matsala baba ALLAH yasa wannan zaɓi daka yanke shine mafi alheri a garemu." Inji Audu.

*Page I6*

" Amin amin Audu, ALLAH yama albarka ya tsareka daga sharrin maƙiyanka, yanzu ka tashi kaje ka huta har zuwa a jima direban ya iso." Haka Audu ya tashi jiki a sanyaye ya nufi ɗakinsa, ai kuwa yana kishingiɗa kai saman gado sai ga amaryar baba ta shigo masa da kunu da ƙosai.
  " Ɗana tashi ka karya kumallo." Haka ta faɗa cikin murmushi daga nan ta fita ɗakin. Sai da tayi nisa sa anan ya iya amsa cewa " Ina godiya amarya." 
Da rana liƙis Audu ya fito waje da gudu samadiyar wata oda dayaji ana babbakawa a waje, da alama direban ne ya iso, ai kuwa Audu na fita waje ya tarar baba yana gaisawa dashi, daga nan sai direban ya kama suka fara jefa buhuhuwan da sauran komatsai a bayan motar, bayan sun gama jefa kayan sai Audu yayi bankwana da  Baba, wasu ƴan kuɗi baba ya damƙa masa kafin ya koma gida, anan Audu yayi godiya daga nan ya shiga mota, shi kuwa direba murza motar ya farayi iya ƙarfinsa domin ya matsu subar wannan ƙauye, sai da sukayi nisa da tafiya sa annan Audu ya tuno bai yi bankwana da abokansa ba, sai da rana ta faɗi liƙis sa annan suka isa birni, anan Audu ya wangale baki yana kallon manyan gine gine naji na faɗa abun gwanin ban sha awa, bayan sun isa gidan ne sai direba ya shigar dashi har ciki, Audu yayi mamaki ganim gidan makeke kuma an tsarashi sashe sashe, anan direba ya nunawa Audu ɗakinsa mai haɗe da baye a ciki daga nan kuma ya wuce dashi kasuwa inda ya nuna masa shagon da aka kama masa, ba tare da ɓata lokaci ba Audu ya fara jera buhuhuwansa na abinci kuma ya ɗaure bisashensa, ba ƙaramin daɗi ne ya kashe Audu ba domin ko babu kome ai zai ƙara sanin jama a, daga nan kuma direban yaci gaba da nunawa Audu abubuwa masu muhimmanci har sai da ya tabbatar cewa Audu ya gamsu, shi kansa Audu yayi mamakin irin wannan jumriya tasa duk da cewa akwai gajiyar tafiya amma haka ya daure yana bin direban sau da ƙafa ba tare da nuna gazawa ba,  da yake tsakanin ƙauyen su Audu da kuma birni babu jayawa sosai. Bayan su Audu sun koma gida sai suka tarar alhaji ya dawo, cikin sauri suka shiga gaidashi inda ya amsa cikin girmamawa yana mai kallon Audu, bayan sun gama gaisawa ne Audu ya koma ɗakinsa inda abokinsa direba ya shigo suka ƙulla sabuwar hira, suna cikin hirar ne Asabe mai girki ta kawo musu abincin dare.

 *Page 17*

Anan sukaci suka sha, sai da dare ya raba sannan direba ya tafiyarsa gida, da yake gidansu a kusa da gidan alhaji yake. cikin ƙanƙanin lokaci sai shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Audu da mutanen wannan gida na alhaji, hakama a cikin kasuwa sai yayi fice domin gwani ne a wurin mu amala da mutane da kuma sanin ya kamata, a haka ya samu abokai da dama, kasuwancin nashi sai albarka yake, kafin kaceme Audu ya sayi mashin roba roba, a duk ƙarshen wata kuma yakan burƙaƙa mashin ɗinsa ya kai ziyara ƙauye wurin mahaifinsa ya kuma musa goma na alheri, haka dai rayuwar Audu taci gaba da gudana har ya yanke shawara cewa zai tara kuɗi ya saye gida idan yaso sai ya dawo da mahaifinsa a kusa dashi, abu ɗaya ke ciwa Audu tuwo a ƙwarya wato wani aiki da alhaji ya bashi na kula da wata mahaukaciya, ita wannan mahaukaciya babu wanda ta yarda yazo wurinta in ba Audu ba domin duka barorin gidan duk wanda ya kusanceta sai dai wani bashi ba, ita wannan mahaukaciya an ƙebeta can ƙuryar gida inda babu kowa, anan aka jefata cikin wani ɗaki aka kulle domin kada ta gudu, da yake ƙofar ɗakin mai tsananin ƙarfi ce hakama tagar ɗakin ta yadda bazata iya guduwa ba, daganan sai aka sanya ma ɗakin kwaɗo aka baiwa Audu makulli tunda shi kaɗai ne ke shiga kai mata abinci, akwai komi a cikin ɗakin harda baye da fanfo yadda zataji daɗin yin aiki, Audu ne ke kai mata abinci safe rana dare, duk da cewa Audu baya son wannan aiki amma ba yadda ya iya, kamar yadda alhaji ya faɗa masa cewa wannan mahaukaciya ce amma shi Audu baiga wani alamun hauka a tattare da ita ba, duk da cewa bata magana kuma a kullum lulluɓe yake iskota, Audu ya ɗauki tsawon lokaci yana bata abinci amma bai taɓa ganin fuskarta ba.
  Kamar kowane dare bayan Asabe mai girki ta kawo ma Audu abincin da zai kaima mahaukacciya, sai ya tashi ya nufi ƙuryar gida inda ɗakin mahaukaciyar yake, tafiya yakeyi hankalinsa kwance ba tare da tunanin kome ba. Bayan ya buɗe ɗakin sai ya kutsa kai ciki, daga shigarsa sai ya ajiye abincin, fitowar da zaiyi haka sai yaji an cafko shi an makashi ga gina, kafin ya ankare sai yaga mahaukaciyar nan tayo cikinsa da tsananin ƙarfi, shi kuwa Audu cikin jarumta ya tareta daganan sai faɗa ya sarƙe tsakaninsu, Audu yayi mamakin irin ƙarfin wannan mata domin tana kai masa hari ne da nufin halakasa.

*Page 18*

Sai da ƙyar Audu ya samu yaci galaba akanta daganan ya ɗaureta da wata kaca mai ƙarfi ta yadda bazata iya kwancewa ba, bayan ya ɗaureta sai yayi tunani bari ya janye lulluɓin dake fuskarta domin ganin yadda take, ai kuwa yana janye lulluɓin sai yayi tsaye wuri ɗaya daganan yayi mutuwar tsaye. 
   " Abida." Haka ya furta cikin tashin hankali.
   " Audu," Haka ta faɗa cikin juyayi.
   " Dama kece mahaukaciyar da ake bani labari?"
   " Dama kaine mai kawomin abinci a kullum?"
Anan sukayi tsit kowanensu da abunda yake tunani. Kukan Abida ne ya dawo da Audu cikin hankalinsa, kallonta yake cikin tausayi domin koba a faɗa masa ba yasan taji jiki, Abida da take kyakkyawa amma yanzu tayi baƙi ta rame ta yakuce, abunda ya ƙara tayar ma Audu hankali shine ganin cewa wasu hakora daga cikin bakinta sun zube kuma hannunta na hagu ya zama dungu domin an cire shi, cikin rashin tsammani sai Audu yaji hawaye na zuba ga idanunsa.
  " Abida wanene ya miki wannan ɗanyen aikin?" Haka Audu ya faɗa cikon damuwa. Ita kuwa Abida jin wannan kalami na Audu sai taji tamkar an yaɓa mata ruwan wuta a cikin zuciyarta, cikin tashin hankali ta fara magana kamar haka:
   " Nayi dana sanin zaɓar dukiya akan masoyin gaskiya, nayi dana sanin akan yin aure ba tare da binciken halayyar wanda zan aura ba, nayi dana sanin yaudarar dana maka Audu." Anan Abida tayi shiru tana sheshsheka, " Audu ka yafemin nasan haƙƙin kane akaina." Shi kuwa Audu shiru yayi domin ji yake tamkar an rufe bakinsa da makulli.
   " Wato ka sani Audu," anan tayi shiru kafin taci gaba da magana. " Alhaji ba mutumin kirki bane, duk wannan aika aikar daya sameni shine sila sanadiyar na gano wani ɓoyayyen sirri nasa shine ya yanke shawara cewa zai mayar dani mahaukaciya kuma abun ƙyama a cikin alumma."
   " Taya hakan ya faru?" Audu ya tambaya.

 *Page 19*

  " Wato ka sani Audu, Alhaji riƙaƙƙen mugu ne, kuma tantirin azzalumi a cikin alumma, idan har kanaso ka tabbatar da abunda na faɗa maka to kada kayi bacci a yau, idan dare ya raba zakaji kukan mota da kuma oda har sau uku, Alhaji yakan fito ya shiga wannan motar su tafiyarsu shida yaransa, to inaso kabi bayansu domin kaga inda suke tafiya." Anan Audu yayi shiru yana nazarin wannan zancen.
  " Ba matsala zan duba duk yadda akayi zan faɗa miki." Anan Audu ya fita daga nan ya kulle ɗakin, tunda Audu ya shiga ɗakinsa bai runtsa ba, dubarar da yayi itace bugama abokansa ƴan sanda tare da faɗa musu abunda ke faruwa, cikin haɗin kai suka amsa masa tare da shaida masa cewa zasu shigo idan dare ya raba, haka Audu yaci gaba da zama bai yi bacci ba har sai da yaji kukan mota da kuma oda kamar yadda Abida ta faɗa masa, cikin sauri ya fita gidan, ai kuwa yana fita sai yaga Alhaji ya shiga wata mota, yana shiga motar sai aka yanki na kare, motar na wucewa sai ga abokansa ƴan sanda su biyar cikin shirinsu a cikin mota, da sauri Audu ya shiga motarsu yana nuna musu inda motar su Alhaji tabi, haka su Audu suka cigaba da bin bayan su Alhaji har sai da suka tabbatar da cewa lallai Alhaji riƙaƙƙen ɗan fashi ne tare da yaransa sabida sun tarar dasu da miyagun bindigogi, ashe dama idan dare ya raba Alhaji yakan fita babban titi yana tare matafiyan dare, abunda ya samu ga matafiyan dare shine yake juyawa yana kasuwanci wannan dalili yasa ba kowa yasan Alhaji yana wannan harkar ba sabida shi baya shiga gidaje kuma a duk dare kafin ya fita sai ya rufe fuskarsa da rawani yadda idanunsa kawai ake gani shida yaransa, su Audu sun samu nasara cafke Alhaji da yaransa bayan sun ɗau lokaci suna artabun halbe halbe, da wayewar safiya ƴan sanda suka tara masu yiwa Alhaji aiki suka faɗa musu abunda ke faruwa sabida haka kowa ya kama gabansa, dama Alhaji ba mata garesa ba ko ɗiya to babu wanda ya damu, direba kuwa da aka faɗa masa haka bai yi mamaki ba domin ya daɗe yana wannan zargin iyaka dai rashin hujja yasa yayi shiru da bakinsa, Audu yayiwa Abida alƙwarin aure tare da yi mata albishir da cewa zai siya mata hannun roba wanda zai maye gurbin dungun hannunta da kuma haƙoran roba waɗamda zasu maye gurbin waɗanda ta rasa.

*Page 20*

Duk alƙawarin da Audu ya ɗauka sai da ya tabbatar ya cikasa, kuma a cikin haka ya dawo da mahafinsa da matar mahaifinsa wato  amaryar baba anan birni daga nan kuma ya siya musu gida, hakama iyayen Abida Audu bai manta dasu ba domin sai da ya dawo dasu birni bayan ya damƙa musu nasu gidan da kuma jari na yin kasuwanci, haka dai Audu da mutanensa suka cigaba da rayuwa cikin jin daɗi na har abada.
     Daganan sai Ahlam tayi shiru kafin ta cigaba da bayani kamar haka: " Idan muka dubi wannan labari zamuga cewa yin ƙama ƙarya a cikin soyayya abune marar kyau, Abida tayi kama ƙarya a cikin soyayya ko nace tayi mugunta a cikin soyayya kuma daga ƙarshe sai ga abun ya dawo a kanta, kuskure ne babba mutum yayi amfani da sunan soyayya sabida yanada muradin gabatar da zalunci, kuma a cikin wannan labari zamuga cewa ba haka kawai ake aure ba, kamar yadda mukaga Abida ta zaɓi dukiya akan masoyin gaskiya kuma sai gashi tayi dana sanin wannan aika aika datayi, duk wanda zai yi aure to ya tabbatar cewa yasan halayyar wanda zai aura da kuma sanaarsa, a bisa haka nakeba matasa maza da mata shawara cewa dokin kama ƙarya a cikin soyayya doki ne makaho, duk wanda ya hau makahon doki to sai dokin nan ya masa kaye in ba a yi hankali ba ƙafa ta karye ko hannu, to haka dokin kama ƙarya a cikin soyayya yake, duk wanda yayi mugunta a cikin soyayya ko kuma ya yaudari abokin soyayyarsa to ya jira nasa lokaci kawai."  A nan zan dakata sai kuma shawara ta gaba da zan bayar." Cewar Ahlam.

Shawarwarin da zamu duba a cikin labarin sune kamar haka:

(1) Kada ki yaudari wanda yace yana sonki, idan har bakida ra ayi dashi to ki faɗa masa tun da wuri domin ya nemo wata, haka kaima kada ka yiwa ƴar mutane wayo ka shanye mata alewar madara kuma daga baya ka yaudareta, alhaki kuikuyo ne, mai shi yake bi

(2) Yarinyar kirki bata roƙon kuɗi a hannun saurayi domin idan wani zai iya baki don ALLAH to wani sai dai ya baki saboda jikin ki, saboda haka ƴan mata a guji roƙon samari kuɗi ki bari sai idan ya baki da kansa sa annan ki karɓa

(3) Kada kuɗin saurayi yasa ki ruɗe kamar yadda Abida tayi, ki bari sai kin tabbatar da cewa kuɗin na halat ne ba wai na sata ba ko kuma makamancin haka

(4) Samari ayi hattara bafa kowace mace zaka dinga ɗaukar kuɗi kana jefa mata alhali ga ƴan uwanka can suna roƙo, ba ana nufin kada ka bata kuɗi ba amma kafin hakan ka tabbatar da cewa aurenta zakayi kuma ka yadda da amincinta, kuma ka tabbatar cewa Iyayenka har ƴan uwanka sun wadata da dukiyarka, idan ka tabbatar da hakan to don ka ba mace kuɗi ba wani abu bane

(5) Mu dinga yafiya ga junan mu, kada mu manta muna saɓo kuma mu roƙi ALLAH ya yafe muna, idan muka dubi wannan labari zamuga cewa ko kaɗan Abida bata kyauta ba amma kuma daga baya Audu ya yafe mata kuma sun samu fahimtar juna akai, duk wanda yama laifi kuma ya nemi ka yafe masa to ka tabbatar kayi hakan, ko bai nema ba idan zaka iya har zuciyar ka ba wani abu bane don ka yafe masa

Anan mukazo ƙarshen babi na biyu sai kuma ranar Juma'a  wato 1st (September) 2023, zamu yi posting babi na uku, kada a manta waɗanda basu son posting zasu iya sayen complete ducument akan 300 kacal, mata zaku iya tuntuɓar Zainab Mustapha Musa +234 814 055 1791, maza kuma Isma'il Abubakar +234 903 740 5690, masu buƙatar posting kuwa kada a manta zamu haɗu a ranar Juma'a 1st (September) 2023, domin jin waɗanne irin shawarwari ne babi na uku zai zo muna dasu

Zamfara Writers Association
In Conjunction With
King and Queen Writing Chamber





SHAWARA ABAR DUBAWA
                                                                        By

Abdul King Article   
                          .                                             Asmy_Cute
                                                                    Esma'el Last Born    
                                                     
Zainab Mustapha Musa (Mmn Sadig)
                                                                              All in

Zamfara Writers Association
In Conjunction With
King and Queen Writing Chamber

Domin ganin farkon labarin:
https://www.kingarticlenovels.com/2023/08/shawara-abar-dubawa.html

*Whatsapp Group*:
https://chat.whatsapp.com/Fk1ohCHMdAdHGYh5hHRo1A

*Facebook Group*:
https://facebook.com/groups/1435791047211648/

 *Babi na Uku*
( Karuwanci  )
*Page 21*

Shawara ta uku da zan bayar tana magana ne akan wata yarinya Kande wadda zata gudo daga gidan iyayenta dake ƙauye ta dawo birni saboda talaucin iyayenta, a cikin wannan labari zamuga illolin rashin haƙuri akan halin da mutum ya tsinci kansa a ciki, da kuma illolin bin son zuciya, ba tare da ɓata lokaci ba zan fara labarin kamar haka:

A wani ƙauye dake cikin garin Gusau wanda ake kira Madogara anyi wasu bayin ALLAH miji da mata da ƴaƴansu uku, mata biyu namiji ɗaya, matan  sun haɗa da Zulai da Kande,  sai namiji daya mai suna Tukur, Malam Shehu mai faci shine mahaifinsu sai  matarsa Harira wacce akewa laƙabi da Asshibi. Kasan cewar ko wane ɗan adam ka gani yanada tasa jarabawar dake damunsa ko ya take,  kamar haka Kande ta zamewa su malan Shehu da matarsa Asshibi ta su jarabawar,  domin kullum safiya da matsalarta suke fara karya kumallo,  duk cikin ɗiyansu itace marar jin magana kuma wacce tafi kowa son jin daɗi sai kace ba wacce aka haifa kuma ta tashi a ƙauye ba, alhali kuwa bata san ko hanyar da akebi aje birni ba. Idan kaga shigarta da maganarta  kasan tana kwaikwayon yan birni ne wadan da take gani a cikin shirin wasannin kwaikwayo, a ƙauyen na su samari tun suna kulata har takai yanzu wasu tsoron yi mata magana sukeyi saboda suna ganin kamar tafi ƙarfin su.


*Page 22*

Wasu kuma suna kama kansu da ita ne saboda kare mutuncin su kar ayi masu wani zargi tunda ansha ganin Kande a ɗakin wa su samari,  wasu suna zargin har ciki an zubar mata, Iyayen Kande sunsha zubar da hawaye akanta,  kusan kullum sai an kawo ƙararta ko kuma ace an ganta a ɗakin wani saurayin har takai yanzu iyayen nata sun daina kuka iyaka su ce ALLAH ya shirya ma su ita sun gama duk abunda za su iyayi dan ganin ta zama mutuniyar kirki kamar sauran ƴan uwanta amma taƙi, haka kawai ta bijirewa iyayenta tabar zuwa tallar dawo tun tana yar shekara sha huɗu amma kuma kullum ana ganinta da kuɗi tanacin abunda ta ke so kuma ta ɗinka kalar kayan da take so, haka dai rayuwa ta ci gaba da tafiya a gidan malam Shehu kusan kullun sai ka jiyo muryar Asshibi tana faɗa da Kande,  tana magana Kande na mayar da martani kamar kishiyoyi,  watarana haka kawai sai Kande ta yanke shawarar zuwa birni domin ta gaji da zaman ƙauyen tana ganin ita yanzu ajinta ya wuce zama ƙauye sai dai birni,  wannan ya sa ta zo wajen mahaifiyarta Asshibi ta ce: " Inaso in fara zuwa birni tallar dawo (Fura) saboda na gaji da maganganun da akeman a ƙauyen nan cewa bana sana'ar komai " kallonta kawai Asshibi tayi bata ce mata komaiba ta ci gaba da fitar geronta,  wannan ya sa Kande ta sakeyin magana " Kina fa jina, " ta faɗi hakan tana wani ɗaure fuska kamar tana hararar innar ta-ta,  sai lokacin Asshibi ta tanka ma ta " To bazaki tafi birni talla ba, idan bazaki iya tsayawa Ƴar Shararra nan ƙauye inda yan uwanki ke tsayawa ba to ki bari, "  shiru Kande tayi sannan ta ce " To shikenan zan tsaya nan ɗin ai yadaifi zaman banzan tunda shi ke sa anaman wani kallo " Asshibi taji daɗin hakan sosai kuma malam Shehu yaji daɗi shima bayan da ya dawo Asshibi ta bashi labarin yada sukayi da Kande,  yayi addu'a ya ce " Mai yiyuwa lokacin shiriya ne ya zo gareta kuma ALLAH ya amshi addu'ar mu. " A ranar wata juma'a ce Kande ta koma tallar sai dai ashe tanada wani nufi na daban a ranta saɓanin abunda ta faɗawa iyayen nata,  inda suna isa Ƴar Shararra ta baiwa ƙawarta Jamila kayan tallar ta faɗa mata cewa idan ta koma gida to baiwa mahaifiyarta Asshibi ta faɗa mata cewa  ita ta wuce birni,  Jamila tayi iya yinta dan ganin ta hanata amma taƙi saurarenta sai da ta tafi.

*Page 23*

Bayan rana ta faɗi liƙis Jamila ta shigo gidansu Kande ta kawowa Asshibi kayan tallar Kande kuma ta faɗa mata abunda ya faru,  Asshibi ta shiga damuwa da tashin hankali nan take ta aika aka kira malam a masallaci ta faɗa masa abunda ya faru,  " Yanzu wa Kande ta sani a birni da zata kwasa taje! Dama duk abunda ta faɗa ƙarya ne kenan yaudarar mu tayi " Asshibi ta katsesa " Malam ka maza kaje ko zaka samu ganinta," anan malam Shehu yayi shiru baice komaiba, sai da yayi tunani na ɗan lokaci kafin  ya jawo kekensa ya kama hanya,  gashi dai marece yayi kuma juma'a ce dai daga cikin ranakun da kasuwannin Gusau ke ci,  wannan yasa ababen hawa sukayi yawa kowa na kokarin komawa gidansa,  bugu da ƙari lokacin da malam Shehu ya iso hadari ya ta so mai haɗe da iska wanda takai har masu ababen hawa sun kunna fitilun motocinsu da mashuna dan kaucewa haɗari, " Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! " Abunda wasu mutane dake kan hanya suka faɗa kenan lokacin da wata babbar mota ta buge malam Shehu, irin motar nan mai tsada da sai manyan alhazzai ke tuƙawa, nan take Malam Shehu ya suma bai san inda kansa yake ba, Kande kuma lokacin da ta fito bisa titin birnin Gusau kana ganinta kasan baƙauya ce,  sai kalle-kalle takeyi kuma hankalinta ya tashi saboda bata taɓa zuwa birni ba kuma bata saba ganin ababen hawa irin haka ba,  ga hadarin da ya taso sai guje-guje takeyi saman titi idan taga mota ko mashin zasu wuce. Kande na cikin wannan yanayi sai ga wata mota babba ta tsaya daf da inda take, ba ƙaramin jin daɗi tayiba domin da ganin motar tanaji a jikinta cewa matafiya ne a ciki maza da mata, direban motar magana ya mata idan tanada ra ayi ta biya kuɗi zai ajiyeta a cikin birnin Gusau, kai tsaye Kande ta aminta daga nan ta biya kuɗin mota, bayan Kande ta samu wurin zama a motar sai ta gano cewa mafi yawan mutanen dake cikin motar tantirai ne na ƙarshen ƙarshe, akan hakane ta ƙulla ƙawance da wasu mata biyu da take gani a tare suke, Kande ta labarta musu cewa ta baro gida ne saboda talaucin iyayenta kuma tanaji a yanzu ba girmanta bane ta zauna a ƙauye ba, anan waɗannan matan suka faɗa mata cewa ai suma abinda ya barosu gidan iyayensu kenan, dayake su waɗannan matan tsofaffin tantirai ne sai suka yiwa Kande alƙawarin cewa in har ta aminta zasu bata masauki domin ta dinga cin gashin kanta.

*Page 24*

Ita kuwa Kande dama abinda takeso kenan saboda haka ta aminta, basu isa Gusau ba sai a tsakiyar dare, suna sabkowa daga motar Kande ta fara dube duben gidaje da sauran albarkatun dake cikin birni kasancewarta baƙauya gaba da baya, a nan ƙawayenta biyu suka jagorance ta har masaukin su domin babu nisa daga inda motar ta ajiye su, wani makeken gida suka iso mai ɗakuna birjik, anan suka kamawa Kande ɗaki da kuma faɗa mata cewa duk wata ake biyan kuɗi ɗakin, ba ƙaramin tashin hankali ya kama Kande ba jin cewa duk wata sai an biya, itace hankalinta bai kwanta ba sai da suka faɗa mata sirrin yadda suke samun kuɗi kuma a haka Kande ta shigo harkar karuwanci gadan gadan.
    A tsakiyar dare Malam Shehu ya farka inda ya samu kansa a gadon asibiti, wanda ya buge Malam Shehu da mota wani attajiri ne ɗan kasuwa da ake kira Alhaji Tanko, Alhaji Tanko na ganin Malam Shehu ya buɗe idanu sai yayi sauri ya kira likita, koda likita ya shigo sai ya fara ƴan gwaje gwajensa daganan kuma yayi rubuce rubucen magungunun da za a siyowa da kuma yadda za ayi amfani dasu, bayan likita ya tafiyarsa sai Alhaji yayiwa Malam Shehu bayani cewa shine sanadin jefasa cikin wannan masifa saboda haka yana neman yafiya, Malam Shehu ko kaɗan bai nuna damuwarsa akan wannan lamari ba kuma a haka ya yafe ma Alhaji cikin lumana, sai da safe Alhaji ya buga ma iyalinsa waya tare da faɗa musu abinda ya faru, cikin gaggawa suka iso asibiti tare da jerin abinci kala kala, anan suka yiwa Malam Shehu sannu da kuma nuna damuwarsu akan faruwar wannan al amari, anan Malam Shehu yaci abinci kuma yasha magungunan da aka siyo masa, kwanci tashi har Malam Shehu ya warke sarai, bayan an sallami Malam Shehu daga asibiti sai Alhaji Tanko ya samar masa aiki a wani kamfani, a hankali a hankali Malam Shehu sai cigaba yake samu saboda kasancewarsa mai yin aiki tsakani da ALLAH, a haka har ya janyo ɗansa Tukur a wannan kamfani, daganan sai Malam Shehu ya siya mashin daganan kuma ya aje sanaar faci iyaka da safe shi da ɗansa Tukur su shigo suyi aiki su koma, a haka har aka fara lissafo Malam Shehu a matsayin ɗaya daga cikin masu kuɗin ƙauyen Madogara domin Alhaji Tanko sakar masa dukiyarsa yayi gaba ɗaya.

*Page 25*

Kuma a hakane gidan Malam Shehu ya canza zuwa makeken gidan zamani mai cike da motoci da barori masu hidima, cikin ƙanƙanin lokaci Malam Shehu ya fara ƙoƙarin gina nasa kamfani a cikin ƙauyen Madogara domin tsayuwa da ƙafafuwan sa.
   Ita kuma Kande a yanzu babu inda sunanta bai zaga ba ciki da wajen birni domin manyan mutane ke zuwa nemanta kuma a hakane ta tara maƙudan kuɗi na tashin hankali, sabida wannan ɗaukaka data samu sai ƙawayen nata suka fara mata hassada domin gani suke sune silar shigowarta wannan harkar amma gashi ta fisu kome, tun a ranar da Kande ta shigo wannan harkar bata ƙara samun kwanciyar hankali ba domin masifar yau daban ta gobe daban, ƙawayen nata sai faman muzguna mata suke wanda hakan yasa suke faman bin bokaye ganin cewa sunga bayanta, mafi yawan lokuta Kande batada lafiya saboda tsabagen baƙin sihirin da suke mata, wasu lokutan takan yi tunani cewa duk masifar data shiga itace ta janyo ma kanta amma saboda baƙin hali irin nata ta kasa gane gaskiya balantana ta shiryu, akan dole Kande ta koma wata unguwa inda ta kama wani makeken gidan haya ita kaɗai bayan ta siyo mota ƴar ƙwalisa domin kece raini, tafiya tayi tafiya ita kuma Kande sai bunƙasa take, wata rana da dare sai taji ana ƙwanƙwasa ƙofa a waje, bayan ta fita ne sai ta tarar da wasu mutane kuma kamar yadda suka nuna mata a buƙace suke kuma idan ta yadda zata bisu to kuɗi ba matsalar ta bane, da daɗin baki suka jata har cikin hamshaƙiyar motarsu, tana shiga suka fizga a guje sai kace bazasu tsaya ba, sai da suka shigo cikin daji sa anan Kande ta gane nufinsu akanta, ashe ƴan mafiya ne bata sani ba, da ƙarfin tsiya suka matseta daganan suka yanke wasu sassa daga cikin jikin ta domin yin siddabaru kuma daga ƙarshe suka yanke mata ƙafafuwa biyu, haka suka bar Kande cikin jini da jimami ga tsananin ciwo dake addabar ta, ihu ta cigaba da rafkawa baji ba gani, sai da ƙyar da suɗin goshi ta samu taimakon wasu mutane inda suka kawota asibiti a cikin motar su, suna ajiyeta suka tafiyar su, anan akaja Kande domin bata taimakon gaggawa, ba ƙaramar wahala Kande tasha ba domin babu mai kula da ita, ƙawayen nata tasan ko an faɗa musu bazasu zoba, dole ta lallashi nas ɗin dake kula da ita akan ta tafi gidanta akwai kuɗaɗen data ajiye.

*Page 26*

Haka wannan ciyo yaci gaba da ragargazar Kande har sai da takai ta sayar da ƴar motarta domin yiwa kanta magani shi kuma gida dole aka koreta tunda bata biya kuɗi ba dama haya take, koda Kande ta fara samun sauƙi to akan keken guramu take, rayuwa kenan, duk wanda bai kiyaye dokokin ALLAH ba to rayuwarsa bazata taɓa yin albarka ba, Kande da take ƴar gata ga aji ga ji da kai amma sai gashi yau ta dawo ba kowa ba, Kande da take mai tsafta da son kwalliya amma sai gashi ta dawo ƙazama aji na farko, babban baƙin ciki a wurin Kande shine yau itace ke bara su kuma waɗannan ƙawayen nata sune ke mata dariya akan wannan masifa data janyo ma kanta. Ƴan kuɗaɗen da Kande ta tara a wurin bara ne yasa tayi tunanin cewa ya kamata ta koma ƙauyen Madogara wurin iyayenta domin ta nemi yafiyarsu kamar yadda take ji cewa haƙƙinsu ne ke bibiyar ta, akan haka Kande ta shiga motar haya har ƙauyen Madogara, daga isowarsu ta fara tuƙa kekenta na guragu har ta iso unguwar su dai dai bakin ƙofar gidan su, abinda ya bata mamaki shine maimakon taga gidan laka na ƙauye kawai sai taga makeken gidan sama na zamani sai mutane ke shige da fice a ciki, sai a lokacin ne ta tuno cewa tun a lokacin data shigo ƙauyen taga cigaba sosai tunda har da tituna an shimfiɗa, sai kuma wasu gine gine da take gani na zamani masu ƙaryatarwa, ga famfuna, rijiyoyi da murtsatse mutane sai ɗiban ruwa suke, a can gefe kuma makarantu ne firamare da sakandire sai kuma asibitoci daban daban, ga kuma wata babbar makaranta ta gaba da sakandare da ake ginawa, sai kuma gidajen mai ababen hawa dangin motoci da mashuna sai shan mai akeyi,  to wai me yake faruwa ne? Wane mai kuɗi ne ya shigo wannan ƙauye har yayi irin wannan taimako haka? Anan Kande ta fara tambayar mutane gidan Malam Shehu mai faci amma duk wanda ta tambaya iyaka yace bai sani ba cikin rashin sanin cewa sunan Malam Shehu ya canza daga Malam Shehu mai faci zuwa Malam Shehu Mai Naira. Hankalin Kande ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yayarta Zulai a cikin wata  makekiyar mota, wata oda ta zabga daganan mai gadi ya fito da gudu ya buɗe  babbar ƙofar gidan, tana wucewa sai ga ƙanenta Tukur shima da fanfaleƙiyar motarsa, anan Kande ta bude ido tana mamakin wannan abu, dama gidansu ne ya koma haka! Da sauri ta nufi motar Tukur, tana isa yana shigewa gidan.

*Page 27*

Shi kuwa mai gadin masga mata wani walaƙantaccen kallo yakeyi, ba yadda Kande bata yiba amma mai gadi ya hanata shiga, suna cikin rigima ne sai ga Malam Shehu ya fito, anan aka fara kallon kallo tsakanin Malam Shehu da Kande, Kande ƙarasowa tayi da nufin magana amma Malam Shehu ya dakatar da ita bayan ya gaya mata maganganu masu rikitarwa akan cewa bata tashi dawowa ba sai da duniya ta fara horarta, ta gujesu a lokacin da basuda kuɗi amma yanzu kuma ta dawo taci banza ko, to bazai yiwu ba saboda haka ta koma inda ta fito, wata juwa ce Kande ta fara gani kafin idanuwanta su fara buɗewa da rufewa, tana cikin wannan hali ne sai ga mahaifiyarta Harira ta fito cikin shiga ta kammala, tun daga nesa Harira ta fara banka mata harara wanda hakan yasa cikin Kande ya bada wani ƙulululu, Kande ce bata samu sauƙi ba sai da ta saki wata tusa mai zafi ji kake abin nan buiiiiiiiiiiiii, anan Kande ta fara zufa gashi ana iska amma zafi takeji, sai da Harira ta tabbatar ta bankawa Kande goma da goma na rashin mutunci kafin taja hannun Malam Shehu, Kande na kallo suka shige cikin baban gidan su na alfarma suka barta a waje cikin takaici saman keken guramu, a wannan rana Kande taci kuka mai isarta amma babu mai lallashi, abinda ya ƙara tayar mata da hankali shine jin wa azin wani malami a kusa da masallacin dake gidan yana bayani akan illolin fushin iyaye akan ƴaƴansu, anan tsoro ya ƙara daburta mata lissafi, Kande bata taɓa sanin tanada imani ba sai yau, malam na gama wa azin sa ya fito zai tafi gida ta taresa, anan ta zayyana masa abinda ya faru tsakanin ta da iyayen ta da kuma roƙarsa alfarma ko zai taimaka ya roƙar mata su yafe mata, anan malam ya tausaya mata ganin halin da take ciki, cikin sauri yayi sallama da Malam Shehu, anan Malam ya fara kwararo bayani akan muhimmancin yafiya har sai da zuciyar Malam Shehu ta karayya, cikin kukan tausayi Malam Shehu ya rungume ƴarsa Kande yana faɗin ya yafe mata, haka itama Harira ba a barta a baya ba da yake duk abinda malam ke faɗa to a akan idanunta ne, Zulai da Tukur suma sun nuna damuwarsu akan wannan al amari, anan Kande ta samu albarkar iyayenta daga nan kuma suka tausaya mata akan halin data tsinci kanta a ciki bayan an mata alkawarin cewa za a fitar da ita waje a sanya mata ƙafafuwan roba domin taci gaba da tafiya kamar yadda take a da.

*Page 28*

Iyayen Kande da ƴan uwanta sun tausaya mata mutuƙa bayan ta faɗa musu labarinta, Malam Shehu kuwa ya mata alƙawarin cewa idan ta ƙara samun sauƙi zai bata hannun jari domin tayi kasuwanci kuma ta koma makaranta domin samun ilmin Addini dana boko kamar yadda ƴan uwanta keyi kuma idan lokaci yayi zai haɗasu yayi musu aure a tare, ba ƙaramin farin ciki ne ya cikama Kande ciki ba ganin cewa ta samu karɓuwa ga ƴan uwanta, abinda ya ƙara faranta mata rai shine ganin waɗannan mutane da suka mata wannan aika aika a akwatin kallo an kamasu ana zarginsu da sace wata yarinya, su kuma waɗannan ƙawayen nata dake mata dariya a lokacin da wannan masifar ta afka mata sai gashi ƴan hisba sun kamasu kuma aka saka ranar da za a tafi dasu kotu domin a musu hukunci, tsalle Kande ta daka da zimmar cewa a ranar sai ta tafi kallon su domin ta rama dariyar da suka yi mata, daga wannan lokaci sai rayuwa Kande ta canza zuwa mutuniyar kirki, a haka taci gaba da rayuwa ita da ƴan uwanta a cikin jin daɗi na har abada.
   Ahlam na zuwa anan sai ta dakata, " Anan nazo ƙarshen wannan labari kuma shawarar da zan bayar itace ƴan uwa mata a guji faɗawa karuwanci, duk yadda iyayenki suke da talauci to kiyi haƙuri kada ki yarda ruɗanin duniya ya rinjayi tunanin ki, hakama maza a guji shiga ƙungiyoyi na assiri domin wannan ba ƙaramar masifa bace ace mutum ya kauce hanya, kamar yadda muka gani a cikin wannan labari Kande itace ta janyo wa kanta duk wata masifa saboda ta guji iyayenta akan talaucinsu kuma data tafi inda take tsammanin ta samu arziƙi sai gashi ta samu tsiya, shi arziƙi daga ALLAH ne, yanada kyau a nemi arziƙi amma idan ba a nufi mutum yayi kuɗi ba tofa duk abinda zaiyi bazai taɓa yinsu ba shi yasa akeson mutum yayi imani da ƙaddara alherinta da sharrinta. Anan zan dakata sai kuma shawara ta gaba da zan bayar. " Inji Ahlam.


Shawarwarin da zamu duba a cikin labarin sune kamar haka:


(1) Ayi imani da ƙaddara alherinta ko sharrinta

(2) Kada ki yadda talauci yasa ki kauce hanya

(3) Duk halin da kika tsinci kanki a ciki to kiyi haƙuri domin shi mahaƙurci mawadaci ne haka kuma maza sai anyi haƙuri da rayuwar duniya

(4) Ayi biyyaya ga iyaye domin samun albarka

(5) A tashi a nemi na kai domin shi talauci masifa ne

Anan mukazo ƙarshen babi na uku sai kuma ranar Monday  wato 4th (September) 2023, zamu yi posting babi na huɗu, kada a manta waɗanda basu son posting zasu iya sayen complete ducument akan 300 kacal, mata zaku iya tuntuɓar Zainab Mustapha Musa +234 814 055 1791, maza kuma Isma'il Abubakar +234 903 740 5690, masu buƙatar posting kuwa kada a manta zamu haɗu a ranar Monday 4th (September) 2023, domin jin waɗanne irin shawarwari ne babi na huɗu zai zo muna dasu

Zamfara Writers Association
In Conjunction With
King and Queen Writing Chamber





SHAWARA ABAR DUBAWA
                                                                        By

Abdul King Article  
                          .                                            Asmy_Cute
                                                                    Esma'el Last Born
                                                     
Zainab Mustapha Musa (Mmn Sadig)
                                                                              All in

Zamfara Writers Association
In Conjunction With
King and Queen Writing Chamber

Domin ganin farkon labarin:
https://www.kingarticlenovels.com/2023/08/shawara-abar-dubawa.html

Whatsapp Group:
https://chat.whatsapp.com/Fk1ohCHMdAdHGYh5hHRo1A

Facebook Group:
https://facebook.com/groups/1435791047211648/


 Babi na huɗu
(Mahaƙurci Mawadaci)

*Page 29*

Shawara ta biyar da zan bayar tana bayani ne akan wani mafarauci da ake kira Ɗan Juma wanda ya kasance marar haƙuri kuma duk abinda ya samu baya godewa ALLAH, a cikin wannan labari zamuga illolin rashin haƙuri da makamantan hakan, ba tare da ɓata lokaci ba zan fara labarin:

A cikin dajin Maɗaci akwai wani ɗan ƙaramin ƙauye da akasarin mutanen wannan ƙauye mafarauta ne, Kamar yadda mutanen wannan ƙauye sukeda zuciyar neman na kai to hakama a wurin al amurran su, sun kasance masu mutuƙar zuciya, duk a cikin waɗannan mutane Ɗan Juma shine mafi rinjaye a ƙarfin zuciya da kuma sanin yadda ake tafiyar da harkokin farauta kuma akan wannan dalili ya samu kambun yabo a matsayin sarkin mafarautan dajin Maɗaci, duk wani abu da mafarautan garin zasu aiwatar sai sun tabbatar da cewa sun nemi Ɗan Juma shawara domin gudun ɓacin rana, hakama sauran mutanen ƙauyen suna mutuƙar girmama Ɗan Juma kasancewar sa gwarzo kuma ɗaya daga cikin garkuwowin wannan ƙauye, matar Ɗan Juma wato Mairo na fuskantar ƙalubale domin Ɗan Juma bayada haƙuri ko kaɗan, abu kaɗan sai ya hauta da faɗa, hakama a wurin farauta duk abinda ya samu baya godewa ALLAH duk da kasancewarsa babban mafarauci da ke iya farauto dabbar da ba kowa ke iya farauto irinta ba.

*Page 30*

A kullum adduar Mairo itace ALLAH ya shirya mata shi amma shi gogan baima san tanayi ba domin a kullum sai ƙara tunzura yake, kasancewar Mairo mai haƙuri bata ko ɓata ranta idan ya fara masifarsa iyaka tayi shiru tana lallashinsa, duk abinda ya nemo bata rainawa kuma duk abinda yace tayi a nan take zata aiwatar dashi, a kullum cikin yin masa hidima take da kuma ɗawainiya dashi ganin cewa ta faranta masa rai amma duk da haka a duk lokacin daya tashi tsula tsiyarsa to baya raga mata ko kaɗan, wasu lokutan hakan yake barinta cikin baƙin ciki tayi kuka har ta gaji ta daina kuma bai wuce gobe taci gaba da ɗawainiya dashi ba tana masa hidima, wayyo baiwar ALLAH, ace ana samun irin waɗannan matan kuwa! ana nan ana nan wata rana sai Ɗan Juma ya dawo gida ya tarar Mairo bata dafa abinci ba, duk da cewa ta masa bayani batada lafiya amma bai raga mata ba, baima damu da jinin dake tsiyaya a ƙafafuwan ta ba haka ya sameta da duka kamar bazai barta ba, bayan ya gama mata lalas kuma ya korata zuwa gida da saki ɗaya, duk da cewa Mairo taji zafin wannan abu daya mata amma bata gaza wurin bashi haƙuri ba sai da taga ba dama sa anan ta tafiyarta, ko kaɗan Ɗan Juma baiyi dana sanin abinda yayiwa Mairo ba domin ganin yake duk abinda ya mata kamar yama banza ne kuma itace ta janyo ma kanta, akan hakan ya ɗau ɗamarar ƙara aure domin ya tusama Mairo baƙin ciki, ba a fi mako ba aka kawo masa amaryarsa Dije wacce zata maye gurbin Mairo, da farko Ɗan Juma yayi farin ciki da ganin sabuwar amarya amma abinda ya baƙanta masa rai shine amaryar tasa ba sabuwar bace domin wani ya rigasa shanye romon, cikin zafi bai san lokacin daya wanke fuskarta da mari ba, anan dambe ya ɓarke tsakanin su, kasancewar dije ƙatuwa ƙaƙƙarfa haka take cira Ɗan Juma tana makawa saman gina cikin rashin mutunci, da Ɗan Juma yaga ba hus sai gashi ya fito a guje kada ta hallaka shi yana mamakin irin wannan ƙarfi na Dije, duk da matsayin sa na Sarkin Mafarauta amma tafi ƙarfin sa, anan ya fara tunanin tsohuwar matarsa Mairo wadda yasan ko kasheta zaiyi bazata rama ba iyaka ta bashi haƙuri koda kuwa ba laifinta bane, amma ita wannan tun a daren farko ta fara gana masa azaba ai kuwa babu lafiya, da gurmanta Ɗan Juma ya nufi ɗakinsa yana tafiya yana waiwaye idan Dije bata biyo shiba. 

*Page 31*

Yana shiga ya kulle ƙofar kada ta shigo yana nishin wahala saboda matsar daya sha a wurin wannan dambe, bako shakka Dije ba ƙaramar hatsabibiya bace, lallai dole ya shirya ma zama da ita, haka yaci gaba da wannan tunani har bacci yayi awon gaba dashi. Tun da sanyin Safiya masifar Dije ta farkar da Ɗan Juma akan ya tashi ya nemo mata abinda zata ci, cikin firgici ya farka ya nufi  daji, tun da safe yake wahala amma sai da ƙyar ya kamo wani zomo, tun a daji ya gyarasa yadda da yazo iyaka ayi girki, daganan ya biya gonarsa inda ya ɗebo kayan miya domin ayi girki dasu, abinda ya ƙara baƙanta masa shine ko kaɗan Dije bata tausaya masa ba duk da wahalar da yasha domin da tayi girkin gaba ɗaya ta tsame naman tabar masa kai da ƙafafuwa a nasa akushin, ba yadda Ɗan Juma ya iya dole ya ƙyaleta domin yasan fa idan ya matsa mata to sai dai suyi dambe, haka dai rayuwa taci gaba da gudana tsakanin Ɗan Juma da matarsa Dije rikicin yau daban na gobe daban, wani lokaci ta dafa masa abinci wani lokaci kuma taƙi dafawa, Duk abinda Ɗan Juma yayi bata gode masa a kullum cikin musguna masa take da wahalar dashi, hakama idan aka je kwanciya bata tausaya masa domin ita bata gajiya kasancewar ta harija,  kamar yadda yake ma Mairo idan sun tafi kwanciya, ita Mairo ta kasance Siririya marar jiki sosai, shi kuma Ɗan Juma idan an tafi kwanciya baya raga mata ko kaɗan, cikin rashin mutunci yake narkar ta sai kace baiwa, to haka itama Dije idan an tafi kwanciya tana ragargazar Ɗan Juma dai dai gwargwado cikin rashin mutunci domin matsesa take iya ƙarfinta yadda bazai iya kubcewa ba har sai ta gama biyan buƙatar ta, cikin kwanaki kaɗan sai ga Ɗan Juma ya fara canza kamanni domin ko farautar sai da ƙyar yake fita domin Dije ta cinye ƙarfin jikin, abinda yafi tayar ma Ɗan Juma hankali shine da zaran abokansa sun samu labarin cewa matarsa na masa wannan aika aika to dole raini ya shiga tsakaninsu inma bai rasa kambun sarautar Sarkin Mafarauta ba, Ɗan Juma yayi dana sanin abinda yayiwa Mairo domin a yanzu ya gano cewa itace masoyiyarsa ta gaskiya, abinda ya faranta masa rai shine saki ɗaya ya mata ba uku ba, akan wannan dalili ya ƙuduri niyar cewa zai sallami Dije ta bashi wuri daganan kuma ya dawo da Mairo ɗakinta, sai da yayi rikici sosai da Dije domin ko bayan ya saketa cewa tayi bazata fita ba domin ita dashi mutu ka raba.

*Page 32*

Sai da dattijan gari da iyaye suka sa baki sa annan Dije ta yadda zata tafi amma ya sani kul a jima kul a daɗe sai ta dawo,ba ƙaramin jin daɗi Ɗan Juma yayi ba ganin cewa Mairo ta karɓesa hannu biyu biyu duk da zaluntar daya mata, hakama  iyayen Mairo basu walakanta shi ba iyaka sun masa nasiha ya gyara halinsa, a haka Mairo ta dawo ɗakin mijin ta wanda a yanzu ya dawo mata sabo hul a cikin leda, duk wata takurawa da yake mata tuni ya kau da ita, a haka ya wanzama yana nuna mata shuke shuken farin ciki daban daban, Ɗan Juma da matarsa Mairo suna cikin cin duniyar su da tsinke sai ga Dije ta dawo tana mai basa haƙuri akan abubuwan data masa da kuma labarta masa irin masifun data shiga bayan rabuwar su, da farko Ɗan Juma bai yi niyar kula taba amma saboda Mairo tasa baki har da bashi ƙwarin gwiwa akan ya mayar da ita ɗakinta indai ta aminta zata kasance matar kirki, Dije ta yadda cewa zata masa ladabi da biyayya dai dai gwargwado kuma akan hakane Ɗan Juma ya mayar da ita dama itama saki ɗaya ne ya mata, daga wannan lokaci sai Dije ta canza zuwa matar kirki da kuma riƙe amanar mijinta ganin cewa ta faranta masa rai, shi kuwa Ɗan Juma sai yau ɗau himma ganin cewa ya riƙe matan sa biyu wato Mairo da Dije a cikin aminci da walwala ba tare da nuna banbanci a tsakaninsu suba, daga wannan lokaci sai Ɗan Juma yaci gaba da samun buɗi na arziƙi kuma ya riƙe matansa a cikin jin daɗi na har abada.
Anan Ahlam tayi shiru kafin taci gaba da bayani kamar haka: " Shawarar da zan bayar itace mu kasance masu haƙuri a dukkan halin da muka samu kanmu kuma mu kasance masu yin addu'a a kowane lokaci, kamar yadda muka gani a cikin wannan labari shi mahaƙurci Mawadaci ne domin haƙurin da Mairo tayi ai bai tafi ga banza ba, tunda wanda ya koreta da kansa shine ya dawo da ita da kansa bayan ya gano muhimmancin ta,  hakama adduar da tayi an samu biyan buƙata. sai kuma mu kasance masu yafiya idan an muna laifi, duk wanda ya nemi ka yafe masa to ka tabbatar ka yafe masa domin kaima kana neman UBANGIJI ya yafe maka, to saboda haka me zai hana idan mutum ya nemi ka yafe masa sai kaƙi? 

*Page 33*

Sai kuma maza kafin ayi aure a tabbatar an fara binciken halin yarinya kada mutum ya auro wadda tafi ƙarfinsa kamar yadda Ɗan Juma ya auro Dije, kuma maza ya kamata a kiyaye ganin cewa ba a ci zarafin mata ba domin duk wanda ya zalunci wani to sai yaga abinsa kamar yadda ya faru ga Ɗan Juma, kuma a tabbatar kafin aure ayiwa mace aune aunen asibiti domin a tabbatar da lafiyarta, haka shima namiji ya kamata a masa aune aunen asibiti domin tabbatar da tasa lafiyar,  sai kuma mata ya kamata ku riƙe mutumcin ku domin mace mai daraja itace wadda takai budurcinta a ɗakin mijinta, kamar yadda muka gani a wannan labari saboda Dije ba cikkakiyar budurwa bace yasa Ɗan Juma ya fara tsanarta tun a daren farko, to haka abun yake a zahiri, namiji yana girmama mace idan ya tabbatar cewa ta kiyaye budurcinta yadda ya kamata, haka suma maza sai su kiyaye mutuncinsu ganin cewa basu raba mace da budurcinta ba, a nan zan dakata sai kuma shawara ta gaba da zan bayar." Inji Ahlam.

Shawarwarin da zamu duba a cikin labarin sune kamar haka:

(1) Mu kasance masu haƙuri domin Mahaƙurci Mawadaci ne

(2) Maza kafin ayi aure a tabbatar an binciki halin yarinya kada mutum ya auro ma kansa kamar yadda ta faru ga Ɗan Juma

(3) Ƴan mata kuma a tabbatar an kiyaye budurci, kada ki yadda wani ya miki wayo ya amshe miki romo domin ita mace mai mutumci itace wadda takai budurcinta a gidan miji

(4) Addu'a ba abar rainawa bace saboda haka mu tabbatar mun riƙe addu'a dai dai gwargwado

(5) Mata  kada kuci zarafin mazanku, haka kuma maza kada kuci zarafin matan ku, aure ba wasa bane ɗaukarsa da muhimmanci shine abu mai kyau


Anan mukazo ƙarshen babi na huɗu sai kuma ranar Laraba wato 6 (September) 2023, zamu yi posting babi na biyar, kada a manta waɗanda basu son posting zasu iya sayen complete ducument akan 300 kacal, mata zaku iya tuntuɓar Zainab Mustapha Musa +234 814 055 1791, maza kuma Isma'il Abubakar +234 903 740 5690, masu buƙatar posting kuwa kada a manta zamu haɗu a ranar Laraba 6 (September) 2023, domin jin waɗanne irin shawarwari ne babi na biyar zai zo muna dasu

Zamfara Writers Association
In Conjunction With
King and Queen Writing Chamber



SHAWARA ABAR DUBAWA
                                                                        By

Abdul King Article   
                          .                                             Asmy_Cute
                                                                    Esma'el Last Born   
                                                     
Zainab Mustapha Musa (Mmn Sadig)
                                                                              All in

Zamfara Writers Association
In Conjunction With
King and Queen Writing Chamber

*Domin ganin farkon labarin*:
https://www.kingarticlenovels.com/2023/08/shawara-abar-dubawa.html

*Whatsapp Group*:
https://chat.whatsapp.com/Fk1ohCHMdAdHGYh5hHRo1A

*Facebook Group*:
https://facebook.com/groups/1435791047211648/

 *Babi na Shidda*
  ( Sihiri da Bokaye )

*Page 34*

Shawara ta biyar da zan bayar tana bayani ne akan wata mummunar rayuwar da wasu matasan suka ɗaurawa kansu ta aiwatar da sihiri da kuma bin bokaye, wannan labari ya faru ne ga wani matashi da ake kira ɓawo wanda zai yiwa wata yarinya sihiri sabida tace bata sonsa, daga ƙarshe sihirin zai dawo kansa har yazo yana neman yafiya ga yarinyar, masu saurare sai ku biyoni da kyau domin jin yadda wannan labari zai kasance:

Can da daɗewa a cikin wani ƙauye, an taɓa yin wani yaro mai suna Ɓawo, Ɓawo wani taƙadirin matashin sauriya ne da ya gagari mutanen ƙauyensu gaba ɗaya ta hanyar shaƙiyanci da taƙadirancin da yake tsulawa a gari, wanda mutum baya da ikon tunkararsa ko zuwa gidansu domin kai ƙararsa, indai mutum ma yayi ƙarfin halin tafiya gidan nasu tofa labarin ne zai sha bam-bam domin kuwa duk abinda mutum ya je dashi dan ya amayar, zaiji kamar an-sanƙamawa bakinsa kwaɗo an rufe ruf, sai dai mutum ya juyo cike da takaici da baƙin ciki. Wannan abu yana ɗaya daga cikin abinda yake ƙara ciwa mutunen ƙauyen tuwo a ƙwarya, Salamarsu ɗaya ne Ɓawo na zuwa cirani a kudu ne dan duk wani shaƙiyanci a can ne ya ƙaro haɗe da kafewar zuciya da  bushe fitilarsa, har yake cin karansa babu babbaka. Duk da ba wani dogon zango yakeyi ba a tafiyar yake dawowa gida. Saboda yafi jin daɗin sheƙe ayarsa a ƙauyen nasu, ta hanyar aikata fasaɗin nashi da duk macen da yaso.


*Page 35*

Ko da kuwa matar aure ce! Mutuƙar sukayi ido huɗu  tofa sai takawo kanta a wajensa ya juyata tamkar waina akan tanda. Kallo ɗaya mutum zai yiwa Ɓawo ya tabbatar da cewa shi ɗin tatacce ne koma cikaken ɗan duniya na ajin farko. Tun daga kan ɗabi'unsa izuwa shigarsa, ɓawo gani yake duk ƙauyensu ba kamarsa da haɗuwa da gayu irin nasu na ƴan duniya, duk da ba wani kyau ne dashi can-can ba, domin kuwa baƙi ne gajere  ƙaƙƙarfa kamar baƙin basamude, sai uban gashin kai da ya tara tare dayi masa ado da shuni, kai tamkar dai busashshiyar gonar da fari ya kama, amma duk da haka jin kansa yake a saman hazo. Ɓawo sam baya da wari ko sa'ah a samartaka a ƙauyen nasu, mafi yawan sa arsa sunyi aure wasu daga ciki har da hayayyafa, domin kuwa shi ba aure ne a gabansa ba tunda yana samu gonakin wasu yana farmaka, Ɓawo ba hayen shaƙiyanci yayi ba kusan gada yayi wajen mahaifinsa, domin shima haka akayi fama dashi a lokacinsa. Sai dai fa kun san ɗan gado wanda yafi na gada, to haka ne saboda Ɓawo ya dame mahaifin nasa ya shanye ata tantiranci, domin shaƙiyancin nasa har da sihiri ta yanda babu mai iya tanka masa. Idan kuwa ya ƙyalla ido ya ga budurwa ko da kuwa macen aure ce sai ya huce ƙishinsa akanta, ta hanya amfani da sihirisa. Arwanatu yarinya ce kyakkyawa  mai cikakken diri da sura, uwa uba hankali da natsuwa, tare da tarin ilmi na addini gata da mutuƙar son ibada, wacce a shekaru bata fi sha-shidda ba, mahaifinta babban malami ne kuma masani akan addini. ƙauyensu yana gabas dana Ɓawo, takan yawan shigowa ƙauyen su Ɓawo kasancewar mahaifiyarta haifaffiyar ƙauyen ce, wacce takan zo wajen kakarta Hajjo hutu, zuwan Arwanatu na da  mutuƙar tasiri a wajen wasu matan ƙauyen, domin kuwa tana ƙoƙari sosai wajen ƙara wayar masu da kai ta fuskar addini kasancewar ta hafiza, inda take ceto wasu da yawa daga duhun jahilci zuwa haske. Kamar yanzu dai da tazo wajen Hajjo domin yimata hutu, sallar La'asar ta idar tare da naɗe darduma, adai-dai lakacin Hajjo ta shiga ƙwala mata kira, da sauri Arwanatu ta fito ba tare ta tsaye cire hijab ɗinta ba tace, "Haba hajjo! Wannan wane irin kiran  ne kika min haka?"


*Page 36*

Ta faɗa cike da natsuwa. Mere baki dai Hajjo tayi cikin sigar tsokanar jikarta tace "Ke dalla tafi can a haka kullum lunƙume da hijabi kamar wata matar liman, bazaki cire ki sha iska ba, ni goro zaki amso  min wajen Tabawa, na duba wanda nake dashi ya ƙare, kin ga maza amshi naira hamsin ne ki siyomin na duka, "  Hajjo tace tana miƙa mata kuɗin. Amsar kuɗin tayi ta fito daga cikin gidan, tafe take cike da natsuwa ta nufi gidan Tabawa, a hankali ba tare da tayi aune ba taji ta daki wani abu kamar icce,
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji un " itace kalmar da Arwanatu ta faɗa cikin amon murya domin kuwa ta firgita sosai wanda saura kaɗan ta zube a wurin, ɗago kan da zatayi tayi ido huɗu da mutum tsaye a gabanta ba tare da yana da niyar gurgusawa ba ko nan da can. Fuskarta a ɗan haɗe tace, " Dan ALLAH kayi haƙuri ban kula da zuwanka ba."
Wani wa-tsatstsen murmushi ya sakar mata haɗe da ɗaga mata girar idonsa ɗaya, irin dai kallon nan  nasu na ƴan duniya, kafin yace: " Ba komai ƴan mata. " Ƙoƙarin raɓawa ta gefensa take ta wuce shi kuma yana shan gabanta, wannan abu da yake mata ba ƙaramin ƙular da ita yayi ba, ba zato ba tsammani taji a hannuwa mutum duka biyu a akan kafaɗunta. Haka kuwa yayi mutuƙar ƙuna mata rai, ido a rufe ta wanke fuskarsa da lafiyayyen mari bayan ta fizge jikinta da sauri tayi gaba cike da takaici da baƙin cikin abin da mutumen da ba ta ko san wayeshi ba yake ƙoƙarin taɓa jikinta. Da wannan mamaki har ta isa gidan Tabawa ta siyo goron, a hanyar ta ta dawowa ne ta  sameshi a in-da ta barshi. Sam ko ta kansa ba tayi ba tai wucewarta. Ɓawo kuwa ganin wucewarta yasa yabi bayanta domin ganin gidan da zata shiga. Dan kuwa duk zagaye-zagayensa da shaƙiyancinsa a ƙauyen nasu bai taɓa cin karo da zuƙeƙiyar yariyar da ta tafiyar da zuciyarsa ba irinta, sai dai  kuma  yayi mamaki ta yanda akayi yarinyar ta tsallakewa ƙaidinsa, saboda wannan shi ne karon farko  da yayi ido huɗu da yariyar  da sihirinsa baiyi tasiri akanta ba, wacce har take da jarumtar saka hannu ta mareshi, lallai kuwa wannan shi ne kuskuren farko da ta aikata ma rayuwarta, dan kuwa ko dame take yawo sai ya mallaki rayuwarta gaba ɗaya. A wannan haɗuwar ne Ɓawo ya lashi takobin sai ya shiga rayuwar Arwanatu ko ta halin  ƙaƙa.

*Page 37*

ƙa-ƙa dan ya mallaketa kamar yanda ya alƙawantama kansa.A haka Ɓawo ya cigaba da zarya gidan su Arwanatu amma tayi  biris dashi, dan kuwa idan da abin da Arwanatu ta tsana a rayuwarta to Ɓawo ne. kusan sati yayi yana faman jewaɗi amma taki bashi ko damar ganinta, da yawa mutanen ƙauyen sun tausaya ma rayuwar Arwanatu na ganin shigowar Ɓawo a rayuwata saboda baƙin nacin da yakeyi kanta. Duk wani ɗan guntun surƙulonsa da sihiri duk ya gwada akanta amma baiyi nasara ba, abin da  ya hasalasa ke nan ya tafi wajen bokansa wanda yake bashi sa'a. ganinsa na farko da boka, ya tabbatar masa da cewa lallai ba zaiyi nasara akan yarinyar ba domin tana da babbar kariya ajikinta na yawan  ibadar da  takeyi, amma yanzu yazo akan sa'a dan kuwa a daren jiya ne ta fara al'adarta wanda aduk lokacin da takeyi tana samun  raunin ibada, to da wannan muma zamuyi amfani dashi muyi aikinmu a kanta, amma akwai kasada, da sadaukarwa a ciki idan zaka iya.Cike da jin daɗin cewa haƙarsa zata cimma ruwa Ɓawo ya  amince da duk abin da boka ya buƙata." Da farko zaka sadaukar da mazaƙutarka ga dodon tsafinmu, idan ka amince to a yanzu zamuyi maka aikinka." cewar boka. A firgice Ɓawo ya ɗago kansa yana kallon boka tare da faɗin " Taya za'ayi hakan." idan  ya sadaukar da ƙarfinsa ga dodo, to shi miye amfaninsa tunda baya da kayan aiki.? Dariya boka ya fashe da ita mai ƙarfi tare da faɗin " Zamu ruɓanya maka ƙarfinka sau ukkun da kake dashi, amma  sharaɗin shine idan aka ɓata mana aiki, to dodo zai zuƙe ƙarfin gabanka shi ne fansa..." Cike da amincewa da yaƙinin haka ba zai taɓa faruwa ba, ɓawo ya faɗi a gaban boka yai sujjada  tare da faɗin " Ai idan ina da kai babu ni ba rusuna a rayuwata." Ruwa boka ya zuba masa a wata ƙaramar ƙwarya yace ya tafi ya wanke gabansa dashi ya kawo mishi.A take duka Ɓawo yayi abin da boka ya buƙata ya bashi ruwan.A gefe boka ya ajiye ruwan   tare da yin wasu surƙullensa, bat! Kamar ɓatan dabo ruwan suka ɓace tare da ajiye  wani ƙullen magani. Ɗaukar maganin boka yayi ya ba Ɓawo tare da faɗin a yau idan dare ya raba, zaiyi turaren kuma ya tabbatar da yarinyar ta shaƙi  maganin.

*Page 38*

Tofa! Aiki ya ƙare domin ita da kanta zata kawo kanta a shinfiɗarsa, aikuwa  kamar yanda boka ya umurci Ɓawo haka ya aiwatar ba tare da ya sha wahala ba kasancewar katangun ƙauyen gajeru ne, da wannan Ɓawo ya tsallaka, hannunsa riƙe da kaskon wuta har izuwa ɗakin da yake da yaƙini tana ciki, dan sai da ya ɗage tagar ɗakin ya leƙa  tukunna domin ya tabbatar idan tana ciki, bayan ya ganta ne  ya barbaɗa garin maganin akan garwashin dake cikin kasko ya tura hannunsa ta tagar ɗakin, sai da ya tabbatar ta gama shaƙar maganin sannan ya fito da hannunsa cike da farin cikin samun nasara. Kai tsaye ƙofar gidansu ya tafi ya zauna jiran Arwanatu, kamar yanda dai boka ya sanar dashi mutuƙar ta shaƙi hayaƙin da kanta zata kawo kanta. Tabbas tsafi gaskiyar mai shi dan kuwa a wannan daren Arwanatu ta kawo kanta ga Ɓawo. Wanda  ba tare da tausayawa ba ko duban yanayin da take na jinin al'ada ba Ɓawo ya afkamata, wanda tsawon sati ɗaya Arwanatu ta kwashe a ɗakin Ɓawo yana morarta ba tare da kowa ya sani ba, a kullum shi ke kawo mata abinci ba tare daya bari wani ya ganta ba, duk da uwar nemanta da ake a gari yana ji yayi biris.  A cewarsa sai ya gama morarta zai ɗauketa ya jefar bakin gari ba tare da kowa ya ganshi ba.Sai dai ance rana dubu ta ɓarawo ɗaya ta mai kaya, awata safiya ne yaron da Ɓawo ya aika siyo masa waina ya ga Arwanatu bayan da ya kawo bai sameshi ba.Dama iyayen Arwanatu duka suna a garin hankali a tashi ana nemanta, sai ga yaro kwatsam yazo masu da labarin ya ga Arwanatu a ɗakin Ɓawo, abin da ya bawa mutane da yawa mamaki, duk da an san Ɓawo zai iya aikata fiye da hakan. A lokacin da iyayen Arwanatu da jama'ar gari suka tafi ɗakin Ɓawo, Arwanatu na ganinsu haka tayi zillo tana batun guduwa, kamar wuta ta ga ruwan kashinta, da ƙyar da suɗin goshi aka fito da Arwanatu a ɗakin Ɓawo. Wanda a yanayin da kakarta ta ga Arwanatu, faɗuwa tayi a sume, domin kuwa kowa ya tabbatar da aikin asiri ne akan Arwanatu, kwana uku mahaifinta yayi yana  faman yimata aiki dan fitar da duk wani sihirin dake jikinta kasancewarsa malami kuma masani akan karya sihiri ko sammu.

*Page 39*

A ɓangaren Ɓawo kuwa kwana ukku nan da akayi yana cikin tsananin musifa da tashin hankali, dan ana karya asirin da ke jikin Arwanatu, gaba gareshi wato sandar aikinsa ta ƙan-ƙance ta koma kamar na yara, wanda idan zaiyi fitsari sai yayi ta zunduma ihu yana buga kansa a ƙasa sannan fitsarin yake fita, tuni ya fice hayyacinsa, inda kowa yake ALLAH wadai da halinsa. Arwanatu kuwa ta samu lafiya ta hanyar kula da take samu awajen iyayenta, Arwanatu da ita da iyayenta suka barma  ALLAH komai, inda suka ɗauki hakan a matsayin tasu ƙaddarar ta hanya ƙyale Ɓawo da ALLAH ga duk abin da yayi masu kansa yaiwa, domin kuwa duniya ce wanda bai zo ma jira take,  kana tafiya sannu-sannu ma kai tuntuɓe ballantana kai  sauri. Ɓawo kuwa haka ya cigaba da zama cikin musifa da  tashin hankali, dama haka duniya take duk abin da mutum ya shuka shi yake girba in hairan imma sharran, babu nasara ga mai bin bokaye sai taɓewa da a sara! Ɓawo baiji kunyar tunkarar Arwanatu ba  da kuma wasu mutan gari neman yafiya ba, ita kuwa Arwanatu kasancewar ta mai tausayi batayi ƙasa ga gwiwa ba wurin amsa masa buƙatarsa amma sauran mutane ko oho, wasu suce sun yafe wasu kuma sai a can, tsabar masifa da tashin hankali ya sanya Ɓawo barin garin da zimmar cewa idan abubuwa sun lafa zai dinga kawo wa ƴan uwansa ziyara, Haka duniya take, duk abinda mutum ya shuka shi zai girba, in hairan hairan, in sharran sharran. Shiru Ahlam tayi bayan tazo nan kafin taci gaba da bayani kamar haka: " Shawarar da zan baiwa samari maza da mata shine mu guji bin bokaye kuma mu guji yiwa mutane sihiri, ba dalili bane saboda mace tace bata sonka kayi mata sihiri, kuma ba dalili bane saboda namiji ya yaudareki ki masa sihiri, idan har mutum yaga ana shirin cutar dashi to yayi ƙoƙarin kare kansa, idan kuma bazai iyaba to yayi addua kuma ya nemi taimakon ALLAH, cutar da jama a masifa ce babba domin idan wasu sun yafe to wasu bazasu iya yafewa ba kamar yadda muka gani ya faru ga Ɓawo. Anan zan dakata sai kuma shawara ta gaba da zan bayar." Inji Ahlam.

Shawarwarin da zamu duba a cikin labarin sune kamar haka:

(1) Kada ka yiwa mace sihiri saboda tace bata sonka haka kema kada ki yiwa saurayi sihiri saboda ya yaudareki

(2) Yanada kyau a ɗauki bautar ALLAH da kuma addu'a da muhimmanci kamar yadda muka gani a cikin wannan labari bauta da kuma addu'ar da Arwanatu keyi shi ya hana Ɓawo samun galaba akanta daga farko

(3) Samari a nemi sana a ta halat kuma idan kunada hali kuyi aure domin aure da sana a sune dawakan mutumci ga ɗa namiji

(4) Duk halin da mutum ya tsinci kansa a ciki to yanada kyau ya koma zuwa ga ALLAH domin samun mafita

(5) Kada ka bari mutane su shaideka da rashin mutunci, kayi ƙoƙari ganin cewa ana shaidar ka ta halin mutane na gari

Anan mukazo ƙarshen babi na biyar sai kuma ranar Juma'a wato 8 (September) 2023, zamu yi posting babi na shidda, kada a manta waɗanda basu son posting zasu iya sayen complete ducument akan 300 kacal, mata zaku iya tuntuɓar Zainab Mustapha Musa +234 814 055 1791, maza kuma Isma'il Abubakar +234 903 740 5690, masu buƙatar posting kuwa kada a manta zamu haɗu a ranar Juma'a 8 (September) 2023, domin jin waɗanne irin shawarwari ne babi na Shidda zai zo muna dasu

Zamfara Writers Association
In Conjunction With
King and Queen Writing Chamber








SHAWARA ABAR DUBAWA
                                                                        By

Abdul King Article  
                          .                                             Asmy_Cute
                                                                    Esma'el Last Born   
                                                     
Zainab Mustapha Musa (Mmn Sadig)
                                                                              All in

Zamfara Writers Association
In Conjunction With
King and Queen Writing Chamber

*Domin ganin farkon labarin*:
https://www.kingarticlenovels.com/2023/08/shawara-abar-dubawa.html

*Whatsapp Group*:
https://chat.whatsapp.com/Fk1ohCHMdAdHGYh5hHRo1A

*Facebook Group*:
https://facebook.com/groups/1435791047211648/

*Babi na Shidda Part 1A*

( Garkuwa da Mutane)

*Page 40*

Shawara ta shidda kuma ta ƙarshe da zan bayar tana bayani ne akan Garkuwa da Mutane, garkuwa da mutane labarine mai ban tausayi akan wata yarinya da zata faɗa hannun masu garkuwa da mutane, a cikin wannan labari zamuga irin mummunan ƙarshen da masu aikata irin wannan laifi keyi da kuma wasu hanyoyi da za abi ganin cewa an magance wannan matsalar, masu saurare sai ku biyoni dakyau domin jin yadda wannan labari zai kasance:

A ƙauyen Ɗan Marke, anyi wani masunci da ake kira Kalla, Kalla mutum ne mai ƙima a cikin wannan ƙauye sabida ko kaɗan baya shiga abunda bai shafe shiba, matar kalla wato Hassi, kusan shekararsu biyar da aure amma ko ɓari bata taɓa yiba. Da sanyin safiyar wata rana bayan kalla ya isa tafkin da yake kamun kifi, zagayawa yayi a can gefe inda ya buɗe ƙyauren wata ƙatanyar bukka, jiragen ruwa ne kwale kwale birjik a ciki, anan kalla ya mulmulo nasa jirgi daga nan ya kulle ƙofar, daga isowarsa bakin ruwan sai ya fara hango dishi dishin wani abu a can nesa, mugun tsoro ne ya dabaibaye Kalla domin a wannan lokaci babu kowa a wurin kuma gashi safiya,  kuma abun sai nufosa yake, haka dai Kalla yaci gaba da kallon wannan abu har sai da takai yana jin kukan jariri a ciki.

*Page 41*

Duk da cewa yayi mamakin wannan abu amma kuma daya tuno cewa wannan tafki babba ne kuma a kan samu manyan jiragen ruwa a samansa masu tafiya daga gari zuwa gari, wata ƙila da gan gan aka yar da jariri, ko kuma hatsari wani jirgi yayi sai jariri ya samu kansa a cikin ruwa, haka dai Kalla yaci gaba da wannan tunani har wannan ƙunshi mai ɗauke da jariri ya iso inda yake, cikin fargaba Kalla ya ɗauki wannan ƙumshi, da zumuɗi ya banye ƙunshin inda ya tarar da jaririya kyakkyawa a ciki, Kalla kasa magana yayi, irin yadda kyawon jaririyar ya tafi da hankalinsa sai nazari yake wannan ko daga wace ƙabila ta fito? Anan kalla ya tsaya jira ko zai ga wani ya fito daga cikin ruwan nemanta, sai da Kalla ya ɗau lokaci mai tsawo kafin ya yanke shawarar tafiya da ita gida tunda baiga kowa ba, da sauri Kalla ya mayar da jirginsa a cikin bukka, yana rufe ƙyauren sai ya nufi hanyar gida ɗauke da jaririyarsa, daga shigarsa gida matarsa Hassi ta tarbesa cikin murna, anan ya labarta mata abunda ya faru tare da faɗa mata nufinsa na barin wannan jaririya a wurinsa tunda bai san iyayenta ba, anan Hassi tayi na am da maganar kalla tare da faɗa masa cewa ta aminta da hakan amma kafin nan me zai hana su tafi tafkin suyi tafiya mai nisa a jirgin ruwa ko wata ƙila zasu iya ganin iyayen wannan yarinyar domin tanaji a jikinta kamar hatsari ne ya rutsa dasu, ba tare da gardama ba Kalla ya aminta da wannan shawara ta matarsa, anan Hassi ta rungume wannan jaririya shi kuma Kalla yayi gaba Hassi na binsa, suna isowa bakin tafkin sai Kalla ya nufi ƴar bukkar da suke ajiye jiragen ruwansu, makulli ya fito dashi ya buɗe ƙyauren daganan ya danna kai a ciki, anan ya mulmulo jirginsa har bakin tafkin, ita kuwa Hassi shiga tayi ta zauna, daga nan sai Kalla ya tura jirgin har cikin ruwa, jirgin na shiga cikin ruwa sai ya haye daga nan ya ɗauko sandar tuƙin jirgi wato baka, anan ya fara tuƙawa a hankali a hankali, sai da tafiya tayi nisa kafin Kalla ya maida hankalinsa sosai akan tuƙin jirgin, haka Kalla da matarsa suka yita tafiya a cikin jirgi ba sassauci, duk wani abu da suke da buƙata sai dai suyi a cikin jirgin, har tafiya tayi nisa amma jaririyar nan batayi kuka ba, tafiya sai ci gaba take har rana ta faɗi amma Kalla da matarsa basuga alamun cewa anyi hatsari ba, hakama kuma basu gamu da kowa ba balantana su tambaya suji Abinda Ya faru.

*Page 42*

Sai da duhu ya fara shigowa sa annan Kalla ya yanke shawara cewa ya kamata su juya akalarsu zuwa gaɓar ruwa domin su huta, akan wannan dalili Kalla ya juya ragamar tuƙin zuwa gabar ruwa dake can gefe, ai kuwa suna isowa sai sukaci karo da wani ƙaramin gida a gefe, daga nan sai Kalla da matarsa Hassi suka nufi wannan gida da zimmar cewa idan masu gidan na ciki zasu roƙesu masauki, suna isa daf da ƙofar gidan sai suka ji wani nishi na fitowa ciki da alama ko waye ke wannan nishi bayada lafiya, da sauri suka shiga ciki inda suka tarar da wani magidanci da matarsa suna jinyar wani mutum, daga kallon fuskar mutumin suka tabbatar cewa wani jinsi ne daban, cikin tausayi suka ƙaraso inda mutumin suna tambayar abinda ya same shi, anan mai gidan ya labarta musu cewa a cikin ruwa ya ceto shi a lokacin da ruwa ke ƙoƙarin cinye sa, gashi da alama ba Hausa yake jiba balantana ya faɗa musu abinda ya faru akan yadda akayi ya samu kansa a cikin ruwa, bayan wani nazari da Kalla yayi akan wannan mutumin sai ya gano cewa duk yadda akayi wannan mutumi yanada nasaba da jinin Larabawa domin yadda jikinsa ke sheƙi kasancewarsa fari tas, gashin kansa kuwa luf luf dashi, a lokacin ne Kalla ya tuno da jaririyar daya tsinto a cikin ruwa, daga nan sai ya labartama mai gidan labarin wannan jaririya daya tsinto da kuma hasashensa na cewa duk yadda akayi wannan mutumin yanada alaƙa da wannan jaririya, abinda ya basu mamaki shine wata yankuwa da suka gani a cinyar jaririyar wanda da alama ko menene ya mata wannan yanka to mai kaifi ne, haka shima wannan mutumin dake nishi daƙyar akwai irin wannan yanka a cinyarsa wanda hakan ya ƙara masa tsananin zogin da yake ji a jikinsa sai kuma jinin dake fitowa a ciki, a wannan lokacin ne suka ga itama jaririyar jini na tsalgowa a cinyar ta, cikin sauri Kalla ya ɗaura ƙyalle saman cinyarta, haka shima wannan mutumin sai suka duƙufa wurin ceto rayuwar sa domin a wannan lokaci yayi nisa, haka dai abu ya kasance a wurin su har suka yanke tsammani da wannan mutumi, cikin aminci wannan mutumin ya cika da kalmar shahada a bakinsa, da gaggawa mai gidan ya zagaya inda ya faɗama Mai Anguwa abinda ya faru, daga nan Mai Anguwa yazo tare da mutanensa inda akayi jana izar wannan mutumi kamar yadda Addini ya tanadar. 

*Page 43*

Tunda ƙulu ƙulun safiya Kalla da matarsa Hassi suka yiwa wannan mutumi godiya akan karamcin daya nuna musu, bayan nan sai suka kama hanyar komawa gida, da sauri Kalla ke tuƙin jirginsa ita kuma Hassi a bayansa rungume da jaririya, sai da sukayi tafiya mai nisa kafin su iso ƙarshen ruwan, bayan Kalla ya tsaya a bakin gaɓa sai Hassi ta fito, shi kuma sai ya turo jirgin zuwa cikin bukka daga nan ya rufe ƙyauren da makulli, Anan Kalla ya shige gaba Hassi na biye har suka iso gida, suna isowa Hassi ta ɗaura sanwa dama akwai kifin data shanya a rana gudun lalacewa, cikin ƙanƙanin lokaci Hassi ta kammala girkin, anan suka ci suka sha, daga wannan lokaci sai Kalla da matarsa Hassi suka cigaba da rainon wannan jaririya bayan an zana mata suna Suhaila, tun Suhaila na ƴar ƙanƙanuwa take raka Kalla kamun kifi, koda ta fara tasawa sai ta zamo gwana a wannan fanni, a duk lokacin da Kalla ya dubi Suhaila sai mamaki ya cika masa ciki domin ko kaɗan batayi kamada matan Hausawa ba, ga tunanin Kalla gani yake duk yadda akayi tanada alaƙa da jinin Larabawa domin siffar jikinta ya banbanta dana sauran matan daya saba gani, hakama tambon wannan yankan dake kan cinyarta bai dushe ba, ciyon ya warke sarai amma tambon yana nan, ƙalubalen da Suhaila ta samu a wannan ƙauyen shine gorin da wasu kan mata na cewa tsintacciya ce marar asali,  a duk lokacin da hakan ya faru Suhaila kan jima tana kukan baƙin ciki, ita kuwa Hassi tana mutuƙar ƙoƙari ganin cewa ta faranta mata tare da ɓoye mata yadda asalin labarin nata yake, haka dai rayuwa taci gaba da tafiya har Suhaila ta zamanto cikakkiyar budurwa, duk da cewa Kalla da Hassi har yanzu basu samu ƙaruwa ba amma ko kaɗan basu damu ba domin sun riƙe Suhaila gam tamkar ɗiyar da suka haifa ta cikin su, matan wannan ƙauye suna mutuƙar kishi da Suhaila domin ta wuce su nesa ba kusa ba ta kowane fanni, akan hakan yasa suke ƙoƙarin ɓata mata suna na rurin jita jitar cewa tsintacciya ce marar asali, da farko abun ya fara baƙantawa Suhaila amma tun a lokacin da Hassi ta faɗa mata cewa ƙarya suke kishi kawai ne ke damunsu saboda ta fisu kyau sai ta janye duk wata damuwa dake ranta, haka shima Kalla ba a barsa a baya ba ganin cewa ya sauke duk wani haƙƙi daya rataya a wuyansa, ana nan ana nan wata rana sai tafiya ta kamma Kalla da Hassi zuwa wani gari kuma a cikin jirgin ruwa zasuyi tafiyar.

*Page 44*

Da yake wani taro za a yi na masu kamun kifi a wani ƙauye, ita kuma Hassi tanada ƴan uwa a ƙauyen kuma sun gayyaceta wani shagalin biki da za ayi na wani ɗan uwanta da zaiyi aure, idan sun tafi ƙauyen shi Kalla zai tafi wurin taron ita kuwa Hassi wurin ƴan uwanta, zuwa kwana biyu bayan sun gama abinda suke sai su dawo. Akan wannan dalili sai kalla ya damƙa mabuɗin bukkar da yake ajiye jirgi ga Suhaila domin taci gaba da sana ar kamun kifi kafin ya dawo, da yake jiragen biyu ne to zai tafi da ɗayan sai yabar wa Suhaila ɗayan, sauran jiragen dake cikin bukkar kuwa na abokan sa ne masu irin sana arsa, da yake duk wanda jirgin sa ke cikin bukkar to yanada mabuɗin ƙyauren. Tunda sanyin safiya Suhaila ta yiwa Kalla da Hassi rakiya har inda ruwan, cikin sauri Kalla ya mulmulo nasa jirgin, Hassi na ganin haka sai ta shige shi kuwa kalla ya tura cikin ruwa, jirgin na shiga ruwa sai Kalla ya fara tafiyar dashi da sandar tuƙin jirgi, haka Suhaila tayita kallon su tana ɗaga musu hannu har suka ɓace mata da gani, anan ta yanke shawara cewa zata kama kifi, shiga tayi cikin bukkar ta mulmulo ɗaya jirgin wanda a cikinsa akwai ragar kamun kifi, koda tayo bakin ruwa sai ta hango wasu ƴan mata suma sun shiga bukkar da nufin mulmulo nasu jiragen, Suhaila tayi mamaki ganin cewa ba ita kaɗaice mace wadda ta iya kamun kifi a cikin wannan gari ba, cikin ƙanƙanin lokaci kowacensu ta fara aikinta na kamun kifi, masuyi da mashi nayi masuyi da raga sunayi, kowace sai tuƙa jirgi take tana ƙoƙarin ganin ta samu nata rabo, haka waɗannan ƴan mata suka yita aiki har sai da kowacensu ta samu nata rabo, suna kammala aikin sai suka cigaba da tuƙin jirgi sai da sukayi tafiya mai nisa sa annan suka iso wani wuri mai damshi domin su huta, anan suka ajiye jiragensu bakin gaɓa bayan kowacensu tayi guzurin kifin da zata gasa domin ci, daga nan suka nausa cikin dajin, ita kuwa Suhaila sai binsu take cikin nishaɗi ganin ta samu ƙawaye sai firarsu sukeyi, bayan sun yi nisa sai suka samu wuri mai kyau suka yadda zango, kunna wuta suka farayi bayan ta ruru, sai suka jera itace daganan suka fara gasa kifayensu, bayan kifayen sun gasu sai sukaci suka sha, da yake akwai ruwan ƙorama a wurin, bayan sun gama kalaci sai sukayi zaman hutu, masu fira nayi masu wasanni nayi.

*Page 45*

Kasancewar mafi yawan ƴan matan iyayensu sun tafi wannan taron na masu kamun kifi shi yasa suka samu damar sakewa ba tare da tunanin kome ba, ita kanta Suhaila ta san idan ta koma gida ba abinda zatayi shi yasa takeji ƙara tayi firanta cikin kwanciyar hankali, haka suka cigaba da nishaɗi har rana ta faɗi liƙis amma basu damu ba, suna cikin hakane sai suka hango samarin garin su a can nesa dasu suna ƙoƙarin isowa inda suke, anan ƴan matan suka fara ihu da sowa domin ko babu kome ai za ayi firar masoya, duk da cewa Suhaila batada saurayi amma bai hanata sakin fuska ba ganin ƙawayenta masu samari suna zaman jiran nasu samarin, abinda ya dakatar da ƴan matan akan wannan ihu da suke shine jin rurin mashuna a gefensu, cikin fargaba suka miƙe tsaye domin ba kasafai ake ganin mashin a ƙauyen ba, kafin su ankara sai ga mashuna masu tsanani yawa sun zagayesu ɗauke da manyan bindigogi, irin mashunan nan da ake kira da Suzuki, kowane mashin ɗauke da mutum biyu, sanye da rawani sun rufe fuskokinsu yadda idanu kawai ake gani, takalmansu kuwa rufaffi ne masu ƙarfi, daga saukowarsu saman mashuna suka fara halbin waɗancan samarin dake ƙoƙarin zuwa wurinsu, su kuwa samarin da yake a cikin su akwai masu ɗauke da kwari da baka, sai suka fara jefo musu kibiyoyi da masuna, su Suhaila sunyi ƙoƙarin gudu amma babu dama domin a zagaye suke, da ƙarfin tsiya aka fara tallabarsu ana azawa saman mashuna, kowace yarinya a tsakiyar mashin maza biyu gaba da baya yadda bazata iya gudu ba, kafin waɗannan samari su ƙaraso tuni waɗannan azzalumi sun yi musu fintiƙau, tunda aka aza Suhaila a saman mashin jikinta yayi sanyi domin idanunta sai rufewa suke suna buɗewa, gata a tsakiyar maza kuma sun riƙeta gam balantana tace zata iya tsira, gashi duhu ya fara ketowa balantana suce wata ƙila a kawo musu ɗauki, wani masifaffen gudu waɗannan azzalumai keyi  sai nausawa suke a cikin daji, ga mashunan da tsananin ƙarfi balantana ace wani abu zai iya illatasu, akan hakan tunanin Suhaila ya haska mata cewa sunyi kuskure da suka shigo cikin daji su kaɗai a matsayin su na mata, bako shakka sun yi kuskure da suka bari dare ya musu a cikin daji, inama ace tasan hakan zai faru da ita da bazatayi ko gangancin fitowa waje ba, inama ace ita mai ƙarfi ce da tuni ta rinjayi waɗannan azzalumi kuma ta kuɓutar da ƴan uwanta mata.

*Page 46*

Babban abinda ke baƙanta mata rai shine yanzu idan iyayenta suka dawo ko waye zai faɗa musu abinda ya faru da ita? wata ƙila waɗannan samarin su yaɗa labarin a gari har labarin ya riski iyayenta! to bayan labarin ya riski iyayenta shin ko akwai wani mataki da zasu ɗauka ganin cewa sun kuɓutar da ita tare da ƙawayenta? To koda ace sunada niyar kuɓutar da ita to ya za ayi su gano wurin da waɗannan azzalumai zasu tafi dasu! ko kuwa dai mutanen ƙauyen zasu haɗa kansu wuri ɗaya ganin cewa sun kawo musu ɗauki, to amma taya za a kawo musu ɗauki tunda babu wanda yasan inda waɗannan azzalumai zasu tafi dasu! Haka Suhaila ta zuba ido tana kallon dajin da suke ketawa cikin rashin sanin ainahin inda za a kaisu, kuma idan an kaisu a wurin ma meye za ayi musu? Baccin wahala ne yayi awon gaba da ita cikin rashin tsammani, itace bata farka ba sai da taji ana daka mata tsawa, firgigit ta farka inda ta kalli wakeken dajin da aka kawosu, daji ne abun tsoro wanda ya amsa sunansa daji, ta ko'ina sai ciyawa da manyan itatuwa gwanin ban tsoro, ga wasu manyan duwatsu da tsaunuka babu kyan gani, da ƙarfi aka fara ingiza su Suhaila, anan suka fara  tafiya suna tangaɗi sabida tsabar gajiya, sai da sukayi tafiya mai nisa sa annan suka iso wani murgujejen kogo mai tsananin duhu, tunda isowarsu wurin Suhaila ta gane cewa akwai matsala domin waɗannan azzaluman da sukayi sanadiyar zuwan su a wannan wuri sai faman kashe manyan macizzai sukeyi haɗi da wasu halittun daji masu cutarwa dake ta faman kawo masu farmaki, wasu halittun ma basu taɓa gani ba, su kunami ba a maganarsu domin tun a lokacin da suka iso wurin sai zubowa sukeyi ta koina sai kace ruwan sama, sa ar dasu Suhaila suka samu shine mutanen sun kunna musu fitillu suna yada musu hanyar da zasu taka, bayan sun iso ƙofar shiga kogon sai sukayi  tsaye cikin tsoro da fargabar abinda zasu iya gani a ciki, sai da aka daka musu tsawa sa annan suka danna kai ciki, bayan sun shigo ne  suka gane cewa lallai wannan kogo mai girma ne, tun a lokacin da suka shigo kogon suka gane cewa lallai wannan wuri mahalaka ce kawai aka jefosu domin sai gawawwaki suke gani wasu sun bushe wasu ma ƙwarangwal. sai da sukayi tafiya mai nisa a cikin kogon kafin a basu umarnin su dakata.

*Page 47*

Daga nan sai suka fara kallon kogon domin ganin yadda yake, a can gefen kogon kuwa mutane ne suka hango maza da mata ɗaure tamau da kaca cikin mummunan yanayi, wasu sun rame sun bushe tamkar ba mutane ba, wasu sabida tsabagen yunwar dake addabar su naman jikin suke zaƙalƙala suna ci domin samun wadata, ɗan jinin dake fitowa kuwa shine matsayin ruwa a gunsu. Daga kallon waɗannan mutane sai Suhaila ta fara zub da hawaye saboda tsabar tausayi domin duk wanda ya kalle su yasan suna cikin masifa, hakama sauran ƴan matan sun tausaya musu mutuƙa, da ƙarfin tsiya aka fara ɗurawa waɗannan ƴan mata wasu ruwa, duk wacce ta shanye ruwan sai ta fita hayyacinta ya zamana cewa duk abinda aka umarce ta dayi sai tayi, duk wacce aka baiwa ruwan sai a ajiyeta a can gefe, ita kuwa Suhaila na ganin haka sai tayi sauri ta shiga layin waɗanda an riga an basu ruwan tare da waɗansu ƴan mata masu wayo irinta, bayan an gama basu ruwan sai aka ɗauresu tamau da kaca daga nan aka jingina su ga bangon kogon, wasu samudawa ne suka fara fitowa a wani lungu na kogon suna kallon waɗannan ƴan mata da aka ɗaure, tunda waɗannan samudawa suka biyo layi suna kallonsu ɗaya bayan ɗaya gaban Suhaila ke bugawa domin tasan babu alheri a tare dasu, duk wanda yaga wadda ta masa sai kawai ya kwance ta ya mayar da ita zigidir, a wannan rana Suhaila taga tashin hankali marar iyaka domin tunda take a rayuwarta bata taɓa ganin gaban namiji mai girman irin na waɗannan mutane ba, ga tsawo ka ƙiba kamar ba mutane ba, Suhaila na kallo wani ya shiga cikin wata yarinya da matsanancin ƙarfi, anan yarinyar ta mimmiƙe tana nishin wahala sabida masifa, haka wannan basamude ya cigaba da ragargazar wannan yarinyar tun ruwan jin daɗi na fitowa a gabanta har takai ruwan sun ƙare yanzu jini ne ke fitowa a gaban nata, koda ya gama biyan buƙatarsa yarinyar bata motsi gaba daya domin halshenta ya zazzalo waje kuma ya karye, saboda tsabar zogin da taji a wurin wannan aibi har ta tamne halshenta ta haƙora wanda yayi sanadiyar rabuwar halshen gida biyu, Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, wannan rashin imani dame yayi kama! Yanzu ana nufin itama haka za a yi mata, kuma suma waɗannan ƴan matan haka za a yi musu? 

*Page 48*

Anan Suhaila ta fara zub da hawayen takaici tana tunanin mafita domin ko ba a faɗa ba tasan cewa wannan yarinyar taji jiki, haka aka cigaba da yiwa waɗannan ƴan mata aika aika cikin rashin imani, wasu matan da amfara suke sheƙawa barzahu saboda masifa, abun nasu har maza basu tsira ba, sai a ɗaure namiji a samu samudawan mata su biyo layi suna saɗuwa dashi har sai gabansa yayi jajur, wani da yayi da mace ta farko anan take zai sume saboda bala i, babban tashin hankali a wurin mazan shine tsananin ɗoyin da gaban waɗannan samudawan matan keyi, ga namiji ɗaure tamau amma liƙe hancinsa yake saboda warin da waɗannan matan keyi, baya ga haka kuma akwai samudawan mazan dake amfani da maza ƴan uwansu, hakama akwai samudawan mata dake amfani da mata ƴan uwansu, haka dai aka cigaba da zabga ɓarna sai da dare ya raba sa annan aka ƙyale su, baccin wahala da takaici ne yayi awon gaba dasu sune basu farka ba sai da safiya ta waye liƙis bayan an fara daka musu tsawa, Suhaila na kallo aka baiwa wasu mazan da aka kamo bindiga, abinda ke bata mamaki shine duk abinda aka umarci mazan suyi sai suyi wanda tasan idan a cikin hankalinsu suke bazasu iya aikatawa ba, bako shakka waɗannan ruwan da aka basu jiya da dare dole akwai wani sinadari a ciki mai ɓatar musu da hankali, hakama suma matan duk wadda akace tayi abu sai kawai ta aiwatar, anan aka baiwa waɗannan maza mashuna daga nan sauran samudawan suka ja nasu mashuna sauran na biye dasu, Suhaila kallonsu tayi cikin takaici domin tasan cewa yawon farautar mutane zasu tafi, su kuwa sauran samudawan dake gadin wurin sai kai da komo suke domin su tabbatar da tsaro, a hakane Suhaila taga wani daga cikin samudawan ya fito da wata na ura yana magana, anan Suhaila ta zuba masa ido domin tasan waya ce yakeyi duk da a ƙauyen nasu ba kasafai ake ganin masu waya ba.
  " Na baka sati ɗaya idan baka kawo kuɗaɗen da ake buƙata ba to zaka tarar da gawar ɗan uwanka." Yana faɗar haka sai yayi dagon tsaki ya shiga wani lungu. 
  " Sannunki dai, sunana Maryam." Inji wata yarinya kusa ga Suhaila.
  " Zaki iya kirana da Suhaila."


*Page 49*

  " Naga kina kallon wancan azzalumin yana waya da wasu, yanzu saura mu a bugama dangin mu a faɗa musu su kawo kuɗi tunda anyi garkuwa damu." Inji Maryam.
  " Garkuwa fa kikace?" Suhaila ta tambaya.
  " E mana, ai duk wanda kika gani a wannan wuri an kawosa ne da ƙarfin tsiya ba wai don ya soba, dama dalilin yin hakan a wurin su shine zasu buƙaci kuɗi ga dangin duk wanda ke a wannan wuri kuma duk wanda ƴan uwan sa basu bada kuɗin da ake buƙata ba to za a kashe sa." Inji Maryam. 
  " Kina nufin anyi garkuwa damu kenan?" Suhaila ta tambaya.
  " E mana anyi garkuwa damu, ai dama aikin waɗannan azzalumai kenan suyi garkuwa da mutane domin biyan buƙatunsu." Inji Maryam. Tunanin da Suhaila keyi ita ƙauyen nasu mutum nawa ke amfani da waya, ita dai tasan iyayenta basuda waya balantana ace a buga musu su ɗauka, hakama idan kuɗi ake buƙata to me suka ajiye balantana har suba wani? Yama za ayi saƙon waɗannan azzalumai ya riski mutanen ƙauyen nasu?
Anan Suhaila da Maryam suka ƙulla ƙawance inda Maryam ke bata labarin cewa ita ɗaliba ce a Jami a amma abun haushi har cikin masaukinsu na ɗalibai inda suke bacci na cikin makarantar aka shiga akayi garkuwa dasu, bako shakka akwai ƙaramcin tsaro ace irin waɗannan miyagu su shiga har wurin da ɗalibai mata ke bacci su tafi dasu, to hala ina masu gadin ne? Kuma masu gadin suna kiyaye aikinsu a cikin adalci kuwa? Hasalima su nawane ke gadin masaukin ɗalibai mata? Kuma da gaske masu gadin sunada makamai naji na faɗa ko kuwa a hannu babu suke? Haka Suhaila taci gaba da wannan tunani mai ruɗani daban tsoro, daga nan kuma itama ta labartawa Maryam yadda akayi garkuwa dasu ita da ƙawayenta, suna cikin firar ne sai sukaga wani daga cikin azzaluman ya janyo wata yarinya da ƙarfin tsiya yana ƙoƙarin keta mata haddi ita kuwa sai faman kubce kubce take, su Suhaila suna kallo wannan mutumi ya kira mutanensa inda suka rike masa wannan yarinya gam, Suhaila na ganin haka tasan cewa ita wannan yarinya ba a bata waɗannan ruwan masu juya hankali ba domin da an bata da tuni ta bada haɗin kai.


*Page 50*

Duk yadda akayi sabuwa ce aka kawo domin ba a ɗaure ta da kaca ba kuma dalilin hakan yasa wannan mutumin ya kira samudawa su riƙe masa ita domin ya biya buƙatarsa,  to amma idan sabuwa ce ya akayi jiya basu ganta cikin su ba? Wata ƙila kuma an bata ruwan iyaka dai ƙarfin addu'a ne yasa sinadarin bai gusar mata da hankali ba, Suhaila na cikin wannan tunani sai taji mutumin na tambayar samudawan dake riƙe da ita:
 " shin wai an bata ruwa kuwa?"  Anan suka amsa da " E an bata."
 " To amma idan an bata me yasa har yanzu hankalinta bai gushe ba?"
 " A kullum akwai adduar da take yi, a tunanina yin hakan yasa har yanzu hankalinta bai gushe ba." Inji ɗaya daga cikin samudawan. Anan mutumin ya girgiza kai yana kallonta tare da umartarsu dasu ƙara riƙeta gam kada ta kubce, a saman wani murgujejen dutse suka ajiye ta inda suka banƙareta bayan sun danne hannayenta da ƙafafuwan ta. Ita kuwa sai faman kubce kubce take ganin wannan mutumi na ƙoƙarin shiga cikinta, da Suhaila taga abun ba sauƙi sai tayi yunƙurin kusantar wannan yarinyar domin ita tama manta da ɗaure take tamau da kaca, sai da ta yunƙura sai taga kacar ta janyo ta da ƙarfi ta manna ta ga bangon kogon, wani daga cikin samudawan dake gadinsu yana ganin haka sai ya nufota yana tambayarta buƙatarta. Bayan ta faɗa masa sai ya kwance tushen kacar da aka ɗaureta daga nan ya riƙa, ita kuwa Suhaila na ganin haka sai ta nufi inda wannan yarinyar take, daga isowarta sai ta fara mata magana kamar haka: 
  " Ki kwantar da hankalinki ƴar uwa kada ki manta wannan abu da zai faru babu son ranki a ciki tunda tilasta miki akayi, sabida haka insha ALLAH bakida laifi, kuma wannan kubce kubce da kikeyi bazai haifa miki kome ba sai ɓarna domin bazaki iya dasu ba kuma idan kika cigaba da haka to iyaka su miki rauni wanda daga ƙarshe zaki iya samun wata matsala, to a nawa shawara ƙara kiyi kuruminki duk abinda zai faru ya faru tunda ALLAH na nan kuma yana kallo kuma tun kafin wannan abu ya faru shine ya ƙaddaro da faruwar sa, kamar yadda duk abinda yayi farko zai yi ƙarshe to wata rana ƙarshen wannan zaluncin dama azzaluman dake gudanar dashi zai zo ƙarshe." Suhaila na faɗar haka sai taga yarinyar ta samu natsuwa.

*Page 51*

Haka shima wannan mutumin tare da samudawan sa sai jikinsu yayi sanyi. Suhaila juyawa tayi ta nufi inda take shi kuma wannan mai riƙe da kacar da take binta yayi domin kada ta gudu daga nan ya nufi wurin bangon kogon daganan ya ɗaureta Kamar yadda take a da, mutumin shiru yayi jim yana kallon Suhaila cikin mutuwar jiki, ita kanta Suhaila tayi mamakin wannan abu, dama da gaske haka abun yake, shi waazi yana amfanar masu imani! Da alama dai maganar da tayi ya ratsa wannan mutumi tare da samudawan sa duba da halin da suka shiga bayan tafiyarta, Abinda yafi ɗagama Suhaila rai shine wai dama musulmi ne amma kuma yake wannan aika aika? To sufa sauran samudawan nasa musulmai ne ko kuwa? Suhaila na kallo mutumin ya suturta jikinsa daga nan ya bada umarni a ɗaure wannan yarinyar kamar yadda aka ɗaure su a bango, tafiyar sa yayi samudawan sa na biye dashi har ya shige wani lungu a cikin kogon. Suhaila da Maryam sun yi mamakin wannan abu haka itama wannan yarinyar tayi mamaki sosai, ashe dama a cikin miyagu akwai masu tsoron ALLAH? Wato duk yadda mutum yake saɓama ALLAH to kada a yanke masa ƙauna ga rahmar ALLAH domin wata ƙila ya shiryu, wato duk yadda kaga mutum na aikata ɓarna to kada ka masa mummunan zato, idan har bazaka iya yi masa addu'ar shiryuwa ba to kayi shiru, Idan kaga mutum na aikata ɓarna to kayi ƙoƙarin yi masa wa azi domin samun shiryuwa, hakama idan kaga mutum na aikata ɓarna to kayi amfani da bakinka, hannunwanka ko jikinka gaba ɗaya domin ganin cewa ya daina aikata wannan ɓarnar da yake aikatawa, haka dai Suhaila taci gaba da wannan tunani har sai da wannan yarinyar ta dakatar da ita bayan ta mata magana da yake a kusa da juna aka ajiye su, cikin ƙanƙanin lokaci sai ƙawance ya shiga tsakaninsu harda Maryam ɗin, anan yarinyar ta faɗa musu sunanta bilƙisu kuma anyi garkuwa da ita ne da ita da sauran fasinjoji da yake sunyi tafiyar dare, haka Suhaila ta ƙawayenta biyu suka cigaba da fira a kullum dako yaushe, a yini iyaka a basu abinci sau ɗaya, wasu lokutan ma ba a basu kome haka suke yini da yunwa, ko kuwa idan an basu abinci sai a hana nusu ruwa, ko kuwa a basu ruwa a hana musu abinci, kuma idan za abada abincin loma ɗaya ɗaya ake bayarwa sai ruwa da mutum ya ƙurba sau ɗaya shi kenan.

*Page 52*

Abincin kuma ba wai na kirki bane domin gari ne busashshe ko kuma busashshen biredi ko kuma su kawo abinda baya ciyuwa gaba ɗaya.Hakama ruwan ko kaɗan babu tsafta cikin su sai dai a sha kawai, mafi yawan lokutan kafin a basu abinci sai an lagude jikinsu an tayar musu da sha awa, akan wannan dalili yasa sha a wa mai tsanani ta kama Suhaila domin ko baya ga wannan a gaban idanunta samudawan nan ke ɓarke mata ko kunya babu, hakama Maryam da Bilƙisu haƙuri kawai sukeyi domin abun ya fara fin ƙarfinsu tare da duk sauran matan dake wurin. A kullum abu sai gaba yake yi domin da samudawan nan sun fita farauta to dole su dawo da gun gun mutanen da suka kama maza da mata, akan wannan dalili yasa a kullum akwai matan da ake ɓarkewa kuma akwai mazan da ake yiwa haka suma, wasu lokutan idan abun ya yiwa Suhaila yawa sai dai ta riƙe mararta tana kukan zuci gudun kada ƙawayenta su gane cikin rashin sanin cewa su kansu wannan matsalar tana addabarsu, wasu lokutan ma idan tsananin sha awar ta tasowa Suhaila a gaban idanun ƙawayen nata take tsiyaya saboda masifa, tunda wannan lalura ta kama Suhaila sai ta kasance cikin tsananin jin kunyar ƙawayen nata domin tasan cewa sun gano halin da take ciki, Suhaila bata samu sakewa ba sai da ƙawayen nata suka kamu da irin wannan lalurar, haka kawai sai su fara tsiyaya ba tare da an taɓa suba kuma ba tare da komai ba, daga nan sai suka sake da junansu da zimmar cewa zasu rufama kansu assiri tunda abun ne yafi ƙarfinsu, iyaka suci gaba da addua ALLAH ya kawo musu sauƙin wannan masifa. sa annan su waɗannan miyagun mutane ba wai jira suke a musu laifi ba haka kawai sai suyi ta dukan mutum ba tare da laifin kome ba, kuma ba ruwansu da mace domin kome ƙarancin shekarunta zasu iya ci mata mutumci, su maza ba a ko magana domin babu tausayi ko kaɗan, wani idan aka fara bugunsa to sai sunga ya mutu suke ƙyalesa, hakama idan mace ce ake bugu itama sai ta daina numfashi ake ƙyaleta, bugun da sukeyi ya wuce hauka domin duk abinda ke gabansu dashi suke amfani, ƙarfe ne, guduma ce, ko menene suka samu iyaka suyita rafkar mutum har sai sunga ya daina numfashi, haka Suhaila da ƙawayenta suka cigaba da adduar neman tsari daga sharrin waɗannan miyagun mutane, wata safiya ta wata rana sai Suhaila ta tsinci kanta cikin matasananciyar shaawa.

*Page 53*

Bata ankara ba sai ji tayi tana tsiyaya. Duk yadda Suhaila taso ta tsuke bakinta kada aji amma abun sai da yafi ƙarfin ta, haka taci gaba da ihun jin daɗi tana murje murje sai kace sabuwar mahaukaciya, sa ar data samu shine ƙawayen nata bacci suke yi Saboda safiya ce. Cikin rashin sani ashe duk abinda takeyi wani basamude nacan gefe yana kallonta, cikin sauri basamuden ya nufo inda take yana mata kallon mugunta,  hankalin Suhaila ne yayi mugun tashi ganin wannan azzalumi ya nufota domin tasan irin rashin imanin da suke wa mata, wani maɗacin tsoro ne ya zaftare mata ƙirji wanda hakan yasa wasu miyagun ruwa ƙara biyowa ƙasan cinyoyinta, itace bata samu sauƙi ba sai da ya iso daf da ita, kacar da aka ɗaureta ya kwance daga nan ya tsura mata ido yana mata murmushin mugunta, surar jikinta ya fara kallon yana tanɗar halshe kamar wanda ya samu nama, ita kanta Suhaila a tsorace take ganin yadda yake kallon ta domin tasan yau kwananta ya ƙare, bata ankara ba sai taji ya zura mata hannu cikin dukiyar fulani yana murzawa wanda hakan yasa wasu gudan ruwa da basu iyar fa fitowa ba sukayi fitar burgu a gabanta, anan Suhaila ta langwaɓe wuri ɗaya domin a wannan lokaci babu wani sauran ƙarfi dake tare da ita, jikin nata ya mutu yayi sanyi gaba ɗaya, shi kuwa basamuden yana ganin haka sai ya ɗauketa ya aza saman kafaɗarsa daga nan ya nufi hanyar fita kogon, Suhaila na kallo ana tafiya da ita amma babu damar ta ƙwaci kanta, gashi tana kallon ƙawayenta na bacci amma babu damar ta musu bankwana domin ji take wannan shine ganin ƙarshe a tsakaninsu, anan ta fara tunanin mahaifinta Kalla da mahaifiyarta Hassi da kuma sauran mutanen ƙauyen su, wasu hawayen takaici ne suka biyo idanunta, haka taci gaba da hawaye har wannan basamude ya fito da ita cikin kogon......

Su waye asalin iyayen Suhaila?

Shin Kalla da Hassi sun san halin da Suhaila take ciki kuwa??

Meye ƙudurin wannan basamude akan Suhaila?

Shin Suhaila zata samu damar kuɓuta daga waɗannan azzalumai tare da sauran mutanen da akayi garkuwa dasu ko kuwa?

Waɗanne irin shawarwari ne wannan labari yayi tsokaci akai?

Anan mukazo ƙarshen Babi na Shidda Part 1A sai kuma ranar Monday wato 11 September 2023, zamu iyar da cigaban labarin wato Babi na Shidda Part 1B

Zamfara Writers Association
In Conjunction With
King and Queen Writing Chamber




SHAWARA ABAR DUBAWA
                                                                        By

Abdul King Article   
                          .                                            Asmy_Cute
                                                                    Esma'el Last Born  
                                                     
Zainab Mustapha Musa (Mmn Sadig)
                                                                              All in

Zamfara Writers Association
In Conjunction With
King and Queen Writing Chamber

*Domin ganin farkon labarin*:
https://www.kingarticlenovels.com/2023/08/shawara-abar-dubawa.html

*Whatsapp Group*:
https://chat.whatsapp.com/Fk1ohCHMdAdHGYh5hHRo1A

*Facebook Group*:
https://facebook.com/groups/1435791047211648/

Babi na Shidda Part 1B
(Garkuwa da Mutane)

TUNATARWA DAGA INDA MUKA TSAYA A WANCAN MAKON:

A wancan makon wato ranar Juma'a 8 September 2023, mun tsaya ne inda Suhaila ta samu kanta cikin matsananciyar sha awa har takai wani basamude daga cikin masu garkuwa da mutane yayi awon gaba da ita domin ta ɗebe masa kewa akan wani hali daya kamata hannu da hannu, a yanzu kuma zamu cigaba da labarin kamar haka: 

*Page 54*

Bayan basamuden ya fito da Suhaila a cikin Kogon, Anan ta ƙara kallon dajin, bako shakka daji ne abun tsoro wanda ya amsa sunansa daji, wasu motoci ne ta gani na yaƙii an jero masu ɗaukar mutane ta baya kamar misalin irin motocin nan da ake azama shanu a baya, sai dai su waɗannan an tanade su ne domin ɗaukar mutane a baya ba shanu ba, Suhaila ba ƙaramin mamaki ya cika mata ciki ba ganin waɗannan azzalumai suna tafiyar da al'amurra su sai kace wasu ƙwararrun jami an tsaro, abunda yafi bata mamaki shine wai yama akayi waɗannan miyagu suka samu waɗannan motoci haka? Kuma ta ina suka samu waɗannan manyan bindigogi masu ƙare dangi? Da sauri basamuden ya jefata cikin motar bayan ya shiga ciki, gilashin motar ya rufe kada aga abinda zai faru, cikin ƙanƙanin lokaci sai wasu daga cikin miyagun suka fara tururuwa suna hawan can bayan motar. Wasu kuma a wasu motocin. Direbobin motocin ne suka fara tuƙi daganan suka kutsa kai cikin daji, Suhaila wani tsoro ne ya ƙara cika mata ciki domin wannan basamude sai kallon surar jikinta yake, tana ji tana gani ya sanya hannunsa cikin dukiyar fulaninta yana murzawa yadda yakeso, gashi tanaji abun na damunta amma ba yadda ta iya domin gaba ɗaya jikinta ya mutu, a wannan lokaci ko kasheta za ayi bazata iya kare kanta ba balantana ma tace ta yiwa wannan basamude musu, haka wannan basamude yaci gaba da murzar Suhaila tana tsiyaya bai ma damu da direba dake kallon abinda ke faruwa a madubi ba, sa ar da Suhaila ta samu shine basamuden bai shiga cikinta ba iya dukiyar fulaninta kawai ya tsaya, sai da sukayi tafiya mai nisa sa annan suka iso wani ɗan ƙauye, suna isowa ƙauyen sai basamuden ya ƙyaleta, wata makekiyar bindiga ya janyo a can gefe daga nan ya buɗe motar ya fita, hankalin Suhaila bai dawo jikinta ba domin ko bayan fitarsa tsiyaya take baji ba gani, ƙarar bindiga ne ya sa ta dawo cikin hayyacinta, a nan ta kalli cinyoyinta da ƙafafuwanta cikin jin kunya domin tasan cewa ko ba a faɗa mata ba to tana buƙatar wankan tsalki, abinda ya ƙara daburtar da ita shine to ta ina ma zata nemi ruwa tayi wankan tsalkin tunda idan za abasu ruwa a baki ake basu su kurɓa sau ɗaya shi kenan, salla ma sai dai suyi taimama domin ko sunce a bari suyi ba a bari, sauƙi ɗaya ake musu shine idan zasuyi bayan gari ana kwance su kuma a basu ruwa su wanke, amma shi kan fitsari wasu lokuta sai dai suyi anan maganar ruwan tsalki kuwa babu, ƙarar bindigogi ne ya ƙara jefa Suhaila cikin matsanancin tsoro, anan ta kallo gilas ɗin motar inda taga ana yiwa mutane kisan wakaƙanci, suna halibi ne kan mai uwa da wabi babu babba babu yaro ba mace ba namiji ba tsoho ba tsohuwa duk wanda suka samu kashewa suke, hawayen baƙin ciki ne da kuma tausayi suka gangaro idanun Suhaila, su waɗannan mutane me sukayi ake musu irin wannan kisan gilla? duk wanda aka halba a kai take kan zai fashe kwanya ta tarwatse.

*Page 55*

Idan a ciki kuma sai cikin ya fashe hanji da kayan ciki su fito.Idan a ƙafa akayi halbin sai ƙafar ta guntule gaba ɗaya, idan hannu ne sai hannun ya guntule gaba ɗaya, wani albarushi idan aka halbo daya shiga mutum sai aga mutumin yayi gunduwa gunduwa wato hannu daban kai daban ƙafafuwa daban, saboda masifa wani albarushin ko akan kuskure ya shiga gina sai gina ta tarwatse idan akwai mutane a kusa iyaka ta faɗo musu ta ragargazasu, haka aka dingi kisan wakaƙanci mutane sai guje guje suke. Wasu kuma a cikin gidajensu ake ɗaure su a kunna musu wuta, haka zasu yita ihu suna neman taimako har sai wutar ta cinye su ƙurmus, Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, wannan masifa dame tayi kama! Suhaila na kallo wannan basamuden daya kawota cikin mota ya janyo wata mace da ƙarfi a bayyanar mutane yana ƙoƙarin keta mata haddi, ita kuwa cikin fushi ta fizgo wata kwalba fasassa ta ɗura masa a ciki, a nan ya faɗi yana nishin wahala domin kwalbar ta fasa cikinsa sai jini ke fitowa, matar zata gudu ne wasu samudawa suka cafketa, a nan basamuden shi kuma ya tashi cikin fushi ya nufi wurinta, Suhaila na kallo ya yiwa wannan mata zigidir sa anan ya danneta da ƙarfin tsiya ya mata fyaɗe daga nan kuma ya janyo wata yuƙa mai kaifi a ƙugunsa ya yanke mata nonuwa biyu, haka yabar wannan mata cikin jini har sai da mutu,  Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, da baƙin ciki yayiwa Suhaila yawa sai ta fara ƙoƙarin buɗe motar amma ta gaza domin an kulle ƙofar da makulli, cikin takaici ta fara bugun gilas ɗin motar amma ko alamar tsaguwa babu sabida tsananin ƙarfin dake tattare da gilas ɗin, anan wata zuciya ta faɗa mata cewa ki daina wahalar da kanki da ace sun san akwai hanyar da zaki fita a cikin motar ai bazasu iya barin ki ke kaɗai ba, done kai tayi tana rusa uban kuka mai ƙuna zuciya, har ta gama kukan da take waɗannan miyagu basu gama cin zalin mutanen ƙauyen ba, sai da suka kashe iya son ransu suka ƙone gidaje sa annan suka kama ƴan ƙalilan da basu samu damar tserewa ba, cikin fushi basamuden nan ya shigo cikin mota bai yi takan Suhaila ba saboda tsananin ciyon dake addabar sa wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya mata ba, bayan motocin sun iso bakin kogon sai ya fito da ita da ƙarfi, shigar da ita yayi ciki ya ɗaureta kamar yadda take a da sa annan ya tafiyar sa, anan ƙawayenta su Maryamu suka fara tambayar abinda ya faru.

*Page 56*

Bayan ta faɗa musu sai ta ƙara musu nasiha da cewa ya kamata su dage akan addu'a. ita kuwa Maryam ciki fushi ta mayar mata da martani kamar haka:
  " Kullum addua mukeyi amma babu biyan buƙata kuma da kin zo sai kiyita damun mutane da cewa ayi addua, yanzu dubi irin abincin da suke ci ma kaɗai abun kallo ne amma mu gamu nan ko ruwa ma sun hana muna." 
Anan Suhaila ta juya inda taga azzaluman nan sunyi gungu zazzaune saman darduma ta alfarma ga abinci kala kala, shi nama ba a ko maganarsa domin sai fizgar abunsu sukeyi suna ci hankali kwance, anan mamaki ya bayyana ƙarara a fuskar Suhaila tana tunanin ko ta ina suke samun wannan abinci mai rai da lafiya bayan kasancewar su  a cikin daji?  Ita dai tasan cewa bazai yiwu ace suke dafa abincin ba domin basuda lokacin dafawa, ga hakan sai dai a dafa musu, to amma idan dafa musu akeyi to su waye ke dafa musu tunda ita dai bata taɓa ganin an dafa abinci a wannan wuri ba, kuma idan akace siyo musu akeyi to waye ke siyo musu tunda ita dai bata taɓa ganin an siyo wani abu ba, hakama idan kawo musu abincin akeyi a wani wuri to su waye ke kawo musu tunda ita dai bata taɓa ganin an kawo komi a wurin ba kuma tanada tabbacin cewa duka waɗanda take tare dasu basuda masaniya game da wannan abu. Murmushin ƙarfin hali Suhaila tayi kafin ta baiwa Maryam amsa kamar haka: " A matsayin mu na musulmai ya kamata muyi imani da ƙaddara mai kyau da marar kyau, kuma wannan hali da muke ciki ai ALLAH ne ya nufi abun zai faru kuma yana sane, ko baya ga haka a duk lokacin da mutum yayi addua indai yayi adduar yadda akeso amma baiga biyan buƙata ba to lokacin biyan buƙatar ne bai zo ba, ko kuma akwai wani nufi na ALLAH akan hakan, kuma Kada ki manta ai addu'ar da Bilƙisu keyi tayi tasiri har ya zamana cewa an bata ruwa masu juya hankali amma hankalinta bai gushe ba, saboda haka ba a fushi da addua koda kuwa mutum baiga biyan buƙata ba, muyi haƙuri muci gaba da addua insha ALLAH wata rana sai labari, kuma sanin mune cewa ALLAH yana jinkirta ma azzalumi amma a duk lokacin da zai kamasa to zai masa riƙo mai tsanani ta yadda bazai iya kubcewa ba. Haƙuri shine maganin zaman duniya saboda haka muci gaba da haƙuri muna roƙon sauki insha ALLAH sauƙi yana nan tafe."

*Page 57*

Wannan nasiha da Suhaila ta musu ba ƙaramar tasiri tayi a cikin zukatansu ba, a haka wata yarinya a cikin waɗanda aka kamo a cikin wannan ƙauyen da aka tafi da Suhaila mai suna Lami  ta nemi tayi ƙawance dasu ganin cewa Suhaila tanada ilimin addini, shaƙuwa ce ta ƙullu tsakanin waɗannan ƴan mata da yanzu sun koma su huɗu wato Suhaila, Maryam, Bilƙisu da Lami. Kwanci tashi abu sai gaba yake, masifar yau daban ta gobe daban, a haka Suhaila ta basu shawara cewa ya kamata suyi ƙaryar bayan gari idan an sake su sai su nemi mafita, duk da cewa ko bayan garin iyaka a sakar musu kacar a ƙafarsu kawai yadda zasu iya yadda sukeso amma ba a kwancewa gaba ɗaya, kuma basamuden mai rakiya zai riƙe kacar ne yace mutum ya tafi gefe yayi bayan garin sa daga nan sai a danƙa masa ruwan da zai wanke. Suhaila da ƙawayenta duka sun aminta da wannan shawara, sai da dare ya raba sa annan suka fara gudanar da shirin nasu, bayan sun keɓanta ne sai suka sanya dutse suna bugun kacar domin ɓallata amma da mamaki ita Lami tsaye tayi tana kallonsu, ba yadda basu yiba domin ta ɓalla nata kaca amma sai kallonsu take tana musu wani kallo marar ma ana, suna cikin hakane sai gani kawai sukayi samudawa sun zagayensu, to anan suka gane cewa ashe Lami mayaudariya ce wato tana yiwa waɗannan miyagu aiki, ashe dama tare dake dasu kuma itace ta sanar musu cewa su Suhaila zasu gudu, Lami ce da kanta ta faɗawa su Suhaila haka tana musu murmushin mugunta, anan samudawan suka kwance Lami suna yabonta akan cewa aikinta yayi kyau, su Suhaila gaza magana sukayi saboda mamaki domin basu taɓa tsammanin hakan zai iya faruwa ba, wato kenan su waɗannan azzalumai sunada mai akata ɓoyayyu ta koina masu sanar dasu akan abubuwan dake faruwa cikin sirri, da ƙarfin tsiya aka ingiza su Suhaila a cikin kogon daga nan aka ɗauresu tamau da kaca, irin ɗaurin nan hannu daban daban ƙafafuwa daban daban, daganan samudawan nan suka ɗauko kaca suna dukan su Suhaila kamar bazasu daina ba, duk inda kacar da buga sai dai fatar ta fashe jini yayi tsalgi, tun farkon farawa su Maryam suka sume, Suhaila kawai ce ta jimre har aka daina dukan nata sai hawayen takaici ke kwararowa saman idanunta.


*Page 58*

Duk wanda ke cikin wannan kogo sai da ya tausaya musu ganin yadda fatar jikinsu ta fashe ta koina sai kace waɗanda wuta ta ƙona, jini kuwa sai kwararowa yake babu kyan gani, sai da aka jima sa annan Maryam da Bilƙisu suka farfaɗo daga suman da sukayi, a wannan dare ko bacci basu samu ba sabida tsabar zogin da jikinsu keyi, safiya na wayewa kuma dai dai rana ta fito sai aka janyo su Suhaila da ƙarfin tsiya aka shanya da rana, haka suka yini cikin wannan ranar sai da dare ya raba aka dawo dasu cikin kogon, bako shakka su Suhaila sun ji jiki, tun a lokacin da aka musu wannan duka rabonsu da abinci ko abin sha, a wannan dare Suhaila da abokan ta suka duƙufa addu'ar ALLAH ya isar musu akan wannan cin zali da ake musu, duk da cewa a cikin rauni suke amma ko kaɗan basu gaza ba wurin ambaton ALLAH, bako shakka haka abun yake, haƙuri shine maganin ko wace masifa, haka kuma mutum mai hankali baya fushi da addu'a koda kuwa baiga biyan buƙata ba domin wata rana fa sai labari, azzalumi ya guji adduar mutanen daya zalunta domin kul a jima kul a daɗe to ranar ƙin dillanci na nan tafe, bacci mai nauyi ne yayi gaba dasu Suhaila, kamar a cikin baccin take jin wani ruri da rugurguji mai ban tsoro, da sauri ta buɗe idanuwanta tare da ƙawayenta wato Maryam da Bilƙisu, anan sukayi arba da azzaluman nan sai guje guje suke suna faman halbin wasu abubuwa dake tunkaro su, a nan su Suhaila suka buɗe idanu war suna kallon abinda ke faruwa, wasu macizza ne masu matsanancin girma ke fitowa ta ko'ina sai kace ruwan sama, duk da girman samudawan azzaluman nan amma sai kaga maciji ya janyo biyar daga cikinsu a lokaci ɗaya ya nannaɗesu kuma ya kakkarya ƙasusuwan jikinsu sa annan kuma ya cinyesu, mamaki ne ya cika su Suhaila, ashe da gaske akwai macizzan nan da ake kira mesa, wasu macizzan kuma idan suka janyo basamude namiji sai su mayar dashi zigidir, kamar yadda samudawan ke saɗuwa da mata cikin rashin mutunci to haka macizzan nan ke saɗuwa dasu cikin rashin mutunci, to anan su Suhaila suka gane cewa a cikin macizzan akwai maza akwai mata domin ita mace macijiya sai ta janyo namiji basamude tana saɗuwa dashi da matsananci ƙarfin tsiya, haka gaban namiji zai miƙe yana fitar da wasu ruwan wahala, maimakon ihun jin daɗi sai dai aga basamude yana ihun wahala.

*Page 59*

Bayan ya gama ihun sa sai macijiyar ta cinye gaban gaba ɗaya daga nan kuma ta kakkarya ƙasusuwansa ta haɗiyesa, ita kuma mace basamudiya idan maciji namiji ya janyo ta, abun na farko da macijin zai farayi shine ya cinye mata nonuwa, yana gamawa da nonon sai ya fara saɗuwa da ita cikin rashin mutunci, saboda tsabar masifa a wurin wannan saɗuwa sai hanji su fara fitowa a baki, tana cikin ihun wahala ne sai macijin ya kakkarya ƙasusuwan jikin ta kuma ya haɗiyeta. Ko kaɗan su Suhaila basu tausaya ma waɗannan azzalumai ba domin kamar yadda sukayi ne ake musu, sai da su Suhaila suka duba da kyau suka gane cewa ba wai macizzai kaɗai bane ke yiwa waɗannan azzalumai wannan aika aika ba, hadda wasu halittun daji da basu taɓa ganin irin suba, haka kawai sai sukaga kogon yana girgizawa da tsananin ƙarfi, basu ankara ba sai sukaga kacocin da aka ɗauresu suna tarwatsewa saboda tsananin girgizar da kogon keyi wanda hakan yasa mutane maza da mata suka fara guje guje suna fita waje, abun ikon ALLAH ga macizzai da sauran halittun daji sai ragargazar waɗannan azzalumai sukeyi amma kuma ba ruwansu da sauran mutane, mutum ɗaya su Suhaila suka tausaya ma bayan sun hangesa a can nesa yana nishi daƙyar da alama a cikin ciyo yake, wannan mutumi ba kowa bane in banda wannan mutumin da yazo yiwa Bilƙisu fyaɗe amma da Suhaila tayi magana sai ya dakata, koda suka isa wurinsa sai nanata kalmar shahada yake, babu wani tambo a jikin sa balantana suce cikin macizzan nan ne ko kuwa wani naman daji ne ya illatasa iyaka dai suna ji a jikin su lokacin sa ne yazo, anan sukaga katin shaidarsa ta aiki a yashe da ƙasa, koda Maryam ta duba sai tayi mamaki domin babban maaikaci ne da ko ba a faɗa ba tasan yana amsar albashi mai tsoka, ko menene yasa ya shigo cikin waɗannan miyagu oho?  hannunsa sukaga yana ɗagawa sai kuma bakinsa dake motsi kamar yana neman gafarar su. 
   " Kada ka samu damuwa mun yafe maka gaba ɗayanmu." Inji Bilƙisu, anan Maryam da Suhaila suka ɗaga kawunansu cikin alamun cewa sun yafe masa, kallon su yayi da idanun tausayi daganan ya sakar musu guntun murmushi da kuma alamar hannu mai nuni da cewa ya gode, kalmar shahada ce ya furta daganan ya daina motsi, Bilƙisu ce ta shafe sa daganan ta ɗauki shaidar katinsa ta aiki ta adana. 

*Page 60*

A nan suka fara tunanin yadda zasuyi da gawar domin basuda niyar barin sa a nan, suna cikin wanan tunani sai girgizar kogon ta ƙara ƙaimi, cikin rashin tsammani sai sukaga wani gefe na bangon kogon ya fashe, wasu ruwa ne masu tsananin yawa suka fara fitowa daga nan suka wuce da gawar mutumin da ƙarfi, anan su Suhaila sukaga waɗannan samudawan na wannan mutumin daya kira su riƙe masa Bilkisu a lokacin da yake ƙoƙarin ɓarketa da yawansu sunyi shahada a cikin ruwa, wato da alama dai a cikin wadannan samudawa akwai na kirki kuma a cikin na kirkin ne wasu suka tsira wasu kuma sukayi shahada, su Suhaila na ganin haka sai suka fara gudun ceton rai, wani masifaffen gudu ne sukeyi shi kuwa kogon sai ruzgawa yakeyi, su kansu mamakin gudun sukeyi domin yadda suke cikin gajiya da kasala ga babu ci babu sha sunada yaƙini cewa wannan gudu da sukeyi daga ALLAH ne, su kuwa macizzai da  halittun daji sai ragargazar azzaluman nan sukeyi cikin rashin mutunci, mamakin daya ƙara cika musu ciki shine a lokacin da waɗannan ruwan suka ɗauki gawar wannan mutumin basuda zafi ko kaɗan, amma ruwan suna ƙarasowa inda samudawan suke sai suka canza zuwa tafassasun ruwan zafi, anan abu ya cakuɗewa waɗannan miyagun mutane, ga macizzai, ga kunami, ga halittun  daji naban tsoro kuma ga tsarabar ruwan zafi da akayo musu guzuri da ita, su Suhaila kuwa sai a wannan lokaci suka gane cewa ashe kogon yanada nisa sosai kafin a fita ciki kuma su waɗannan azzamumai ashe sunada yawa sosai, dukkan waɗanda aka kama maza da mata sun gama tserewa domin su Suhaila kaɗai ne ke faman gudun masifa suna tsallake ramuka da kuma ɓallin kogon dake zaftarowa daga sama yana faɗowa, su Suhaila na kallo kogon na ruzgawa da waɗannan miyagun mutane, wasu kuma ɓallin kogon ke faɗo musu ya ragargazasu wato kai daban ƙafafuwa daban, babu abinda ke tashi in banda ihun azaba da waɗannan azzalumai keyi, suna gab da fitowa ne suka hango wani maciji na cinye nonuwan Lami, basu tsaya kallonta ba domin sun san cewa daya gama da nonon to iyaka ya saɗu da ita saɗuwar rashin mutunci daga nan ya kakkarya ƙasusuwan jikinta kuma ya cinye ta.


*Page 61*

Daga nan kuma Suhaila taga wannan basamuden daya tafi da ita cikin mota yana taɓa mata nono wata macijiya ta janyosa da ƙarfin tsiya tana ƙoƙarin yi masa fyaɗe,  saninta ne da macijiyar ta gama yi masa abinda takeyi iyaka ta hallakashi har lahira,  Suhaila na ganin haka  sai ta tuno da matar daya yanke ma nonuwa kuma ya mata fyaɗe a bayyanar mutane. Haka suma mutanen nasa wasu macizzai sun janyo su sai faman fyaɗe suke musu suna hallakasu.Ko kaɗan Suhaila bata tausaya musu ba domin kamar yadda sukayi ne ake musu, haka suka cigaba da gudu suna kallon azzaluman da suka sani da waɗanda basu sani ba macizzai sai faman  kisan gilla suke musu. Sai da su Suhaila suka fito kogon sa annan sukayi arba da wani irin makeken tafki laƙe da bangon kogon, daga inda suke tsaye zuwa wurin tafkin akwai ƴar tazara, ɗan nazari sukayi shin wai waɗannan ruwan da suka shigo cikin kogon daga wannan tafkin suka fito ko kuwa? wasu dawakai ne farare guda uku suka hango a nesa dasu kamar jiransu suke, da sauri suka nufi inda dawakan. Suna isowa sai suka ji kamar an cirasu da ƙarfi an azasu saman dawakan, sunyi mamakin hakan domin su kansu sun sani bazasu iya hawan dawakan da kansu ba. Wani azababben gudu waɗannan dawakai suka fara hambaɗawa sai kace walƙiya, da ƙarfi su Suhaila suka riƙe dawakan suna mamakin wannan abu domin suna ji a jikin su cewa dawakan gaskiya waɗanda mutane ke hawa bazasu iya irin wannan gudu ba, su waɗannan dawakai ba ruwansu da girman rame ko kwazzabe domin tsallake sa suke tamkar kibiya, hakama itace ko tsaunuka iyaka su raɓa su wuce sai kace guguwa, har yanzu manyan macizzai da halittun daji sai fitowa suke ta koina suna durfafar wannan kogo na waɗancan azzaluman samudawa, dawakan kuwa sai faman gudu sukeyi baji ba gani, macizzan da sauran halittun suke ratsewa dawakan, cikin ƙanƙanin lokaci dawakan suka iso bakin titi, suna isowa sai sukayi tsaya ƙit, kamar daga sama su Suhaila ji kawai sukayi an sabko dasu saman dawakan, daga nan sai dawakan suka juya cikin dajin tamkar walƙiya suka ɓace musu da gani, su Suhaila tsaye sukayi suna mamakin wannan abu, bako shakka ALLAH gwanin gwanaye ne, sarkin sarakai, mamallaki mai mulkin duniya da abinda ke cikin ta, bako tantama ALLAH gwanin basira ne, gwanin hikima.

*Page 62*

Gwanin tausayi, gwanin jin ƙai, gwanin rahma, gwanin iyawa, gwani wanda babu kamarsa kuma babu irinsa,kuma baza a taɓa yin kamar saba kuma baza a taɓa yin irinsa ba, bako shakka ALLAH shine na farko kuma shine na ƙarshe, kuma shine mabuwayi kuma  shine marinjayi, wato duk wanda bai yi imani da ALLAH ba toya taɓe kuma yayi hasara duniya da lahira, Suhaila da ƙawayenta gaza magana sukayi domin sun san cewa wannan abun daya faru daga ALLAH ne. Suna cikin wannan hali ne sai suka ji kukan mota a can nesa, tsakiyar titi suka dawo suna ɗaga hannu domin mai motar ya tsaya, koda motar ta iso sai ta tsaya, ƙatanyar jeep ce abun kallo, anan suƙa ƙurawa mai motar idanu wanda shi kuma hankalinsa ya karkata ga kallon Maryam, da sauri ya buɗe motar ya fito ita kuwa Maryam na ganin haka sai ta sheƙo da gudu ta rungume sa cikin kukan farin ciki, sai da suka samu natsuwa ne sa annan Maryam ta faɗa musu cewa abban ta ne da yake shi ɗan kasuwa ne mai yawan tafiye-tafiye, anan Suhaila da Bilƙisu suka shiga bayan motar inda suka tarar da larabawa namiji da mace, anan Abban Maryam ya faɗa musu cewa waɗannan larabawa abokan sana'arsa ne, ita kuwa Maryam gidan gaba ta shige tana labartawa abban nata abunda ya faru, tunda Suhaila ta kalli larabawan nan gabanta yayi wani mugun faɗuwa, a haka aka fara kallon kallo ita dasu, a cikin jikinta tanaji kamar akwai wani abu amma ko menene? haka suma waɗannan larabawa da ganin yadda suke kallonta da alamar tambaya, basuyi tafiya mai nisa ba ƴan sanda suka tare su suna yiwa Abban Maryam tambayoyi, anan ya faɗa musu abinda ya faru ita kuwa Bilƙisu ta danƙa musu katin shaidar aiki na wannan mutumin domin su kaiwa iyalinsa kuma su faɗa musu abinda ya faru, cikin ƙanƙanin lokaci ƴan sanda suka bugu ma ƴan uwansu domin su hallaro su shiga dajin tare wurin bincike, anan ƴan sandan suka amshi adireshin Abban Maryam da numbarsa domin idan sunada buƙatar kawo masa ziyara domin samun ƙarin bayani akan wannan labari, ƴan sandan na sallamarsa sai ya buga motarsa ya nufi gari, sai da yayi gudu mai nisa sa annan ya iso cikin birni, anan ya fara shiga lungu lungu saƙo saƙo domin zuwa unguwar su, ita kuwa Suhaila buɗe baki tayi tana kallon manyan manyan gine gine domin tunda take bata taɓa shigowa birni ba.

*Page 63*

Duk da cewa a cikin dare ne amma tasan cewa birnin ya tsaru, tsayawar da yayi ne a wani makeken gidan sama suka gane cewa sun iso, anan ya yace su fito su shiga cikin gidan, Maryam na buɗe gate ɗin sai wasu mutane suka fito mace da namiji, anan Suhaila ta ƙura musu idanu tana tunanin inda tasan su, hankalin ta bai dawo ba sai da taji wannan matar ta rungume ta tana kukan tausayi. 
  " Suhaila ashe da rabon zamu ƙara ganinki." Anan ne hankalin Suhaila ya tabbatar mata cewa wannan mata ba kowa bace in banda mahaifiyarta Hassi. Kalla shima matsowa yayi yana duban ƴarsa yadda ta canza gaba ɗaya sabida wahala, tare suka shiga gidan gaba ɗaya inda Kalla ke bata labari cewa wani abokinsa ne ya masa hanya idan ya kama kifi sai ya shigo birni ya sayar domin an fi samun riba kuma a hakan ya haɗu da Abban Maryam, yau kuma daya kawo musu kifin dare yayi gashi kuma tare yake da Hassi, sai ya nemi ya kwana a gidan kafin gobe sai gashi wannan abu ya faru, tun kafin su shiga cikin gidan masu gadi suka kai labarin cewa Maryam ta dawo, akan hakan ƴan uwanta suka tashi daga bacci domin tarbonta. Koda suka shiga falon gidan sai murna ta koma sabuwa, a cikin waɗannan mutane ne ita kuwa Bilƙisu ta hango iyayenta, da gudu ta sheƙo ta rungume su, anan ne ta gane cewa da mahaifinta da mahaifin Maryam aminan juna ne saboda kasancewar su manyan ƴan kasuwa, kuma sun shigo gidan ne da nufin zasu kwana domin da safe akwai wata tafiya da zasuyi mai muhimmanci tare da Abban Maryam, murna gun Bilƙisu ba a magana, ga mahaifiyarta ga mahaifinta a tare da ita, haka itama Maryam ga mahaifiyarta ga mahaifinta, itama Suhaila haka, bayan an natsu ne ana firar yaushe rabo sai Maryam ta faɗa musu labarin su tun daga farko har ƙarshe akan yadda akayi garkuwa dasu da kuma masifar da suka fuskanta bayan anyi garkuwa dasu dama sauran abubuwan da suka faru dasu har zuwa lokacin da suka samu damar kuɓuta daga hannun waɗannan azzalumai, anan falo yayi tsit ana mamakin wannan al amari, sai da aka ɗau lokaci ba mai magana  sai waɗannan larabawan suka durfafo inda Suhaila take, anan suka zauna suna dubanta kafin matar ta fara magana, yadda take magana Hausar ta bata zauna tangaram ba domin wasu lokutan sai ta surka da Larabci ko Turanci.

 *Page 64*

  " Zan so ka faɗamin labarin wannan yarinya taka!" Inji matar, Kalla najin haka sai jikin sa yayi sanyi, daga nan sai ya fara basu labarin lokacin daya tafi ruwa shi kaɗai kamun kifi har zuwa lokacin daya tsinci Suhaila da kuma tafiyar da yayi tare da Hassi ko zasuga iyayen ta, matar najin haka sai tayi sauri ta janyo yuƙa, da ƙarfi ta yaga suturar Suhaila dai dai cinya, anan matar taga  tambon  tsaguwa. Itama balarabar nuna musu cinyar ta tayi inda sukaga irin wannan tsaguwar ta cinyar Suhaila, shi kuma Kalla na ganin haka sai ya tuno cewa a lokacin da Suhaila na jaririya tanada tsaguwa a cinyar ta kuma irin wannan tsaguwar ce ya gani ga wannan balaraben daya cika a gabansa bayan ya samu masauki a wani gida bayan ya fita neman iyayenta tare da Hassi, anan matar ta rungume Suhaila cikin kukan farin ciki. Haka shima balaraben sai hawaye ke zuba idanunsa. Kalla tsura musu ido yayi domin yanason yaji labarin wannan tsaguwar dake cinyarsu da kuma yadda akayi Suhaila ta fita hannunsu, to anan ne matar ta fara basu labari kamar haka: " Mu Larabawan Sudan ne mata da miji kuma ƴan kasuwa masu yawan tafiye-tafiye daga ƙasa zuwa ƙasa domin saye da sayarwa da kuma tallata hajarmu, a hakane wata rana a cikin dare mun shigo yankin Hausawa a cikin ƙaramin jirgin ruwa wato kwale kwale sai hatsari ya rutsa damu, wata mummunar gugguwa ce ta taso tare da wasu ruwan sama masu tsananin ƙarfi wanda hakan yasa jirgin ya fara tangal tangal kuma yana ɓallewa gunduwa gunduwa, a wannan lokaci Suhaila na jaririya kuma tana akan hannun ƙanen mahaifinta, wani katako ne mai kaifi ya ɓalle daga nan guguwa ta janyo sa sai saman cinyar Suhaila, ƙara ta saki mai firgitarwa, shi kuma a wurin ƙoƙarin cire katakon ne akan cinyar ta wani katako ya faɗo masa a cinya inda ya fasa masa cinya har ya zamana cewa wurin ya kwakware ana ganin ƙashin sa, saboda tsabar masifa bai san lokacin da ya saki Suhaila ba ita kuwa tana cikin wani ƙumshi lullube, ni kuma a wurin riƙota kafin ta faɗa cikin ruwa sai wani katakon ya faɗomin kuma ya fasa min cinya, anan Suhaila da ƙanen mahaifinta suka faɗa cikin ruwa, dani da Abban Suhaila da sauran mutanen dake cikin jirgin bamu tsira ba domin jirgin kifewa yayi, da yawan mutane sun halaka, wasu kuma da suka ƙware a wurin iyo sun tsira, da yake Abban Suhaila ya ƙware a wurin iyo.

*Page 65*

Shi ya taimaka min har muka iso bakin gaɓa tare inda muka samu taimakon wasu mutane, ita kuwa Suhaila da ƙanen mahaifinta anan muka rasa su. Abinda ya faranta min rai shine tun lokacin da muka haife ta aka sanya mata suna Suhaila, kuma abun ikon ALLAH kuma Suhaila kuka sanya mata a lokacin da kuka tsinceta. "
" Bako shakka ALLAH gwanin hikima ne daya rabamu da ƴar mu a lokacin da muke buƙatar ta kuma ya saɗamu da ita a lokacin da bamuyi tsammani ba. " Anan sauran mutanen dake cikin wannan falo suka tsura ma wannan matar idanu tare mijin ta wato Abban Suhaila, ita kanta Suhaila kallon ta sukeyi domin labari nasu yanada ruɗani a ciki, shi kuwa Kalla sai ya tuno cewa a lokacin daya fita neman iyayen Suhaila tare da matarsa Hassi a cikin jirgi, da dare ya musu sun tafi wani gida a kusa da ruwan domin neman masauki kafin safiya ta waye. To a cikin gidan sun jiyo nishin mutum, kuma da suka shiga Kalla ya dubi mutumin sai yaji a jikinsa cewa wannan mutumin yanada nasaba da jinin larabawa tun daga yanayin jikinsa, abunda ya ƙara tabbatar masa da cewa wannan mutumin shine ƙanen mahaifin Suhaila da ummar Suhaila ke bada labari shine mutumin yanada wata mummunar tsaguwa a cinyar sa haka itama Suhaila tanada irinta kuma tun a lokacin yaji a jikin sa cewa da Suhaila da wannan mutumi sunada alaƙa domin raunin su iri ɗaya kuma a cinya, sai dai a wannan lokaci ita Suhaila jaririya ce balantana ta faɗi abinda ke faruwa shi kuma mutumin yayi nisa a cikin magagin mutuwa, anan Kalla ya ƙara jaddada musu wannan labari da kuma yadda akayi jana izar wannan mutumi wato ƙanen mahaifin Suhaila. Abban Suhaila ya tausaya ma ƙanensa mutuƙa jin yadda ya cika, haka itama Ummar Suhaila ta tausaya masa sosai, sai da suka jima suna nanata wannan labari sa annan suka nufi wurin bacci, tunda ƙulun ƙulun safiya suka tashi suka kimtsa, Abban Maryam da abokan sa su Abban Bilƙisu da Abban Suhaila akan dole suka janye maganar tafiyar da zasuyi taro saboda murnar ganin ƴa ƴansu,  anan Abban Suhaila yayiwa Kalla kyautar gida a cikin wannan birnin da kuma mota, sa annan kuma ya masa alƙawarin cewa zai buɗe musa babban gidan sayar da kifi yadda zai ɗauki ma aikata yana biyansu.

*Page 66*

Maryam da Bilƙisu a jami'a ɗaya suke, sabida haka sai Abban Maryam yace zai sa a yiwa Suhaila jarabawar kammala Sakandire da kuma duk takardun da ake buƙata domin nemo mata gurbin shiga jamia, daganan kuma Abban Suhaila yace zai zauna a wannan birni yaci gaba da kasuwancin sa sai dai idan yanada buƙata sai ya kaiwa ƴan uwan sa ziyara a Sudan.Haka shima Kalla zai cigaba da zama a birni sai dai ya dinga kaiwa ƴan uwan sa ziyara a ƙauye, duk da cewa yanada niyar ɗauko ƴan uwan nasa suma su dawo birni idan ya tsayu da ƙafafuwan sa. Kamar yadda ƴan sanda sukace zasu tuntuɓi Abban Maryam idan sunada buƙatar ƙarin bayani akan abinda ya labarta musu, haka kuwa abun ya kasance domin sun kawo ziyara tare da yan gidan rediyo da talabijin inda akayi fira dasu Suhaila akan wannan al amari shima Abban Maryam da sauran abokansa wato Abban Bilƙisu da Abban Suhaila an musu tambayoyi, shi kansa Kalla da matarsa Hassi basu tsira ba domin sai da akayi fira dasu kuma aka musu tambayoyi, ƴan sanda sun shaida musu cewa sunyi bincike a cikin wannan kogon da akayi garkuwa dasu Suhaila amma babu abinda suka gani domin akasarin kogon ya rushe, in banda gunduwa gunduwar jikin waɗannan miyagun azzaluman to babu kome a ciki, ƴan sanda sunyi alƙawarin cewa zasu cigaba da gudanar da bincike domin tabbatar da tsaro ga al'umma, daganan kuma aka yaɗa labarin ciki da waje birnin. Daga ƙarshe dai Kalla ya samu arziƙi har takai ya dawo da ƴan uwansa da kuma ƴan uwan Hassi a birni kuma ya nema musu sana a tare da basu kyautar kujerar makka da kuma gidajen zama, ita kuwa Suhaila ta samu gurbin karatu a jami'ar inda ta haɗe da ƙawayenta wato Maryam da Bilƙisu, kuma a cikin jami'a ne suka haɗu da samari ƴan arziƙi da suka musu alƙawarin aure idan sun gama karatu. A haka waɗannna mutane suka cigaba da rayuwa cikin jin daɗi na har abada. Daganan sai Ahlam tayi shiru na ɗan lokaci kafin taci gaba da magana kamar haka: " anan nazo ƙarshen wannan labari kuma ba tare da ɓata lokaci ba zan fara bayanin darasin labarin haɗe da shawarwarin da zamu dubawa a ciki, darasin farko da zamu duba a cikin wannan labari shine kada mutum ya jefa kansa cikin damuwa idan yayi aure amma bai samu yara ba, wasu lokutan haihuwar ba alheri bace kuma ko baya ga haka ita haihuwa nufin ALLAH ne.

*Page 67*

Idan ALLAH bai ƙaddaro mutum zai haihu ba to ba makawa sai dai yayi haƙuri, amma kuma yanada kyau a tafi asibiti a duba ko wani rashin lafiya ne ya hana haihuwar ga waɗanda basu samu ba, idan muka dubi wannan labari zamuga Kalla da matarsa Hassi basu haihu ba, amma kuma ALLAH ya basu ɗiya Suhaila wadda akan dalilin ta sun samu arziƙi yadda mutum baya tsammani. Sai kuma darasi na biyu da zamu duba a cikin wannan labari shine muhimmanci addua, kamar yadda akayi bayani a cikin wannan labari ai adduar Bilƙisu ce ta hana waɗannan ruwan masu juya hankali su samu galaba akanta, kuma adduar su Suhaila ce ta janyo afkuwar masifa ga waɗannan azzalumai, abun nufi anan shine kada mutum yayi fushi idan yayi addua baiga biyan buƙata ba domin ita addu'a lokaci gareta, indai lokacin addu'ar yazo to take buƙatar mutum zata biya indai mutum yayi adduar yadda ake akeso, shi yasa yanada kyau a tambayi malamai yadda ake addu'a kafin ayi. Sai kuma shawara ta farko da zan bayar wadda zan so ace gwamnati ta duba sosai ga lamarin to tayi nasaba da waɗannan mutane masu garkuwa da mutane, a wannan zamani da muke ciki an samu cigaba yadda ba a tsammani har takai cewa idan kana waya da mutum za a iya bibiyar numbarsa sa a gano ta inda yake wanda a turance ake kira da tracking, to me zai hana a kowane sashe na jami'an tsaro a tanadi gefen computer da kuma ma aikan da zasu dinga gudanar da waɗannan ayyuka a sirrance yadda duk wanda akayi garkuwa da ɗan uwansa iyaka yakai rahoto ga jamian tsaro daganan sai a tura rahoton ga sashen masu computer, daganan sai a jira waɗanda sukayi garkuwa ɗin su kira neman kuɗi, da sun kira sai ayi amfani da numbar da suka kira ayi tracking ɗinta, kuma koda ace sun ɓoye numbar wato sun yi hiding ɗin numbar to ana iya bayyanar da numbar wato ayi reveal na numbar  kuma ayi tracking ɗinta, idan an samu nasarar gano wurin da suke wato location ɗin su to sai jami'an tsaro suyi shirin kamasu domin ayi musu hukunci yadda ya kamata. Shawara ta biyu kuma ya kamata a baiwa jamian tsaro makamai naji na faɗa domin hakan shi zaisa su samu ƙarfin gwiwa akan aikin su, kuma ya kamata a gudanar da bincike mai tsauri tunda su waɗannan azzalumai sunada waɗanda ke aika musu rahoton abubuwan dake faruwa wanda hakan yasa akan samu nakassa a wurin kamasu. 

*Page 68*

Kuma idan jami'an tsaro sunyi maganganun sirri bai kamata su bari maganganun su fita waje ba domin cikin rashin sanni akan iya samun masu aikawa waɗancan azzalumai rahoto. Shawara ta uku kuma ya kamata idan waɗanda aka kama sun samu nasarar kuɓuta daga waɗannan azzalumai to a binciki su a gani idan ba a basu wani abu mai cutarwa ba a jikinsu, kuma a musu awon cututtuka domin tabbatar da lafiyarsu tunda akan samu wasu daga cikin waɗannan azzalumai su yiwa mata fyaɗe abun nasu wasu lokuta har maza basu tsira ba kamar yadda muka gani a cikin wannan labari. Kasancewar mata sunada kunya ba kowace yarinya ke iya faɗin aika aikar da aka yi mata ba saboda haka da mace ta samu kuɓuta daga wurinsu to a tabbatar an binciki lafiyarta koda kuwa batayi magana akan hakan ba, kai ko namiji ne shima a tabbatar an binciki lafiyarsa. Kuma ya kamata a samu jamian tsaro da zasu dinga yawon sintiri a ciki da wajen ƙauyuka da birane saman tituna da dazuka ba dare ba rana domin tabbatar da tsaro. Kamar yadda muka gani a cikin wannan labari su waɗannan azzalumai suna iya haɗa kai da mutanen da ba a tsammani domin biyan buƙatunsu, zaka iya samun abokin ka wanda su yakema aiki kuma zaki iya ganin ƙawarki wadda su take ma aiki kamar yadda ya faru dasu Suhaila bayan sun gano cewa ƙawarsu Lami tana tare da waɗannan azzalumai, kada ka yarda da kowa kema kada ki yarda da kowa, ba kowane sirrin zuciya ake faɗama abokai ba, wani sirri ɓoyesa ake ɓoyewa ta har abada kuwa. Duk abinda kaga baka yadda dashi ba to ka tabbatar ka kai rahoto ga jami'an tsaro domin su ɗau matakin gaggawa. Sai kuma binciken maiakata ya kamata ayisa domin a tabbatar da cewa sune ba wasu ba kuma a tabbatar sun riƙe aikinsu da gaskiya. Anan nazo ƙarshen waɗannan shawarwari kuma ina fatan ba a manta waɗanda na faɗa a baya ba a cikin labaran dana bayar, idan za a tuna labari na farko dana bayar mai taken *Gaskiya da Amana* yana magana ne akan wata yarinya Indo mai saurin gasgata mutane wanda a dalilin haka ne wani azzalumi ya samu nasarar saceta har ya ƙetara da ita wata ƙasa inda aka tilasta ta zama karuwar ƙarfi da yaji, darasin dubawa na wannan labari shine ba kowa ake baiwa gaskiya da amana ba, kuma mutum ya kasance mai tunani kafin ya aikata dukkan kome, sai kuma labari na biyu mai taken *Kama Ƙarya a cikin Soyayya.*

*Page 69*

Wannan kuma labari ne na wata yarinya Abida da zata yaudari saurayinta Audu daga nan taje birni ta auri wani mai kuɗi cikin rashin sanin cewa ɗan fashi ne ta aura. Wannan labari yana bayani cewa yaudara a cikin soyyaya babu kyau ko kaɗan tunda sai gashi Abida ta haɗu da masifar wannan mugun mutum data aura har takai ta rasa wasu sassa na jikinta. Sai kuma labari na uku mai taken *Karuwanci,* wannan kuma labari ne akan wata yarinya Kande da zata gudo daga ƙauye saboda talaucin iyayenta ta shiga birni da harkar karuwanci, a cikin wannan labari an faɗakar da mutane akan illolin karuwanci da kuma rashin haƙuri domin Ƙande zata faɗa hannun ƴan mafiya  kuma a dalilin haka zasu mayar da ita musaka. Sai kuma labari na huɗu mai taken *Mahaƙurci Mawadaci*, Mahaƙurci Mawadaci labari ne akan wani mafarauci Ɗan Juma daya kasance bayada haƙuri kuma duk kyautatawar da matarsa ta masa baya gani, akan haka zai saki matar tasa saboda wani ƙaramin laifi sai bayan yayi sabuwar amarya ne zai gane cewa lallai yayi kuskuren rabuwa da tsohuwar matarsa domin wannan daya auro batada mutunci ko kaɗan, a cikin wannan labarin anyi bayani akan abinda rashin haƙuri ke janyowa da kuma makamancin hakan. Shi kuma labari na biyar mai taken *Sihiri da Bokaye* yana magana ne akan wani hatsabibin yaro ɓawo mai yiwa mata sihiri domin biyan buƙatar sa wanda akan hakane zai yiwa wata sihiri, bayan buƙatar tasa ta biya sai sihirin ya wargaje ya dawo masa ita kuwa ta warke sarai, daganan zai walaƙanta yabi duniya, a cikin wannan labari ana bayani ne akan illolin yin sihiri da kuma matsalolin da waɗanda suka yadda da sihiri suke fuskanta, sai kuma labari na shidda wato *Garkuwa da Mutane*, shine labarin Suhaila da ƙawayenta da suka faɗa hannun masu garkuwa da mutane, a cikin wannan labari an faɗi amfanin addu'a ga mumini da kuma mummunan ƙarshen da masu irin wannan harka keyi da kuma wasu shawarwari akan yadda za a magance wannan matsala, dukkanin labaran nan shidda da aka ambata wato *Gaskiya da Amana, Kama Ƙarya a Cikin Soyyaya, Karuwanci, Mahaƙurci Mawadaci, Sihiri da Bokaye da kuma Garkuwa da Mutane* to shawarwari ne ababen dubawa ga samari da ƴan mata, kuma akan hakane na kawo ƙarshen waɗannan shawarwari ina fatan ALLAH ya bamu ikon yin amfani dasu amin." 

*Page 70*

   " Muna godiya sosai marubuciya Ahlam da waɗannan zaratan shawarwari da kika bayar kuma muna roƙon ALLAH ya saka miki da alheri duniya da lahira, to masu saurare anan mukazo ƙarshen wannan shiri namu mai taken *Shawara Abar Dubawa* tare da baƙuwar mu marubuciya wato  Ahlam daga ƙungiyar *King and Queen Writing Chamber* wato *Sarki da Sarauniya Writers,* Ahlam ta bamu gwarazan  shawarwari har guda shidda a cikin labari, anan kuke sauroron gidan rediyon Gamji FM akan mita cisin da ɗaya da ɗigo biyar a nan Jahar Zamfara, nine naku Kamal Ahmad nake cewa anan zamu naɗe tabarman shirin sai kuma wani satin idan ALLAH ya kaimu zamu ɗaura daga inda muka tsaya." Daga nan sai Ahlam ta fita waje ta nufi wurin motarta haka shima Kamal motarsa ya nufa domin zuwa gida.

    ALHMDULILLAH

Anan mukazo ƙarshen littafin *Shawara Abar Dubawa* kura kuran da mukayi a cikin wannan littafi ALLAH ya yafe muna, anan zamu dakata sai kuma wani jiƙon idan ALLAH ya yadda


Zamfara Writers Association
In Conjunction With
King and Queen Writing Chamber





























Post a Comment

0 Comments