“cigaban gidan fatalwa”
= part ( 1 ) kashi na farko=
Dedicated to
Firdausi queen article
RECALL BACK……
A cikin littfin “GIDAN FATALWA” mun bayyana irin
gwagwarmayar da meenat tasha domin sanin mahaifiyarta ta
gaskiya, wanda hakan yasa ta tsinci littafin sihiri wanda a
cikinsa ne ta samu dukkan bayanan da take bukata, sai kuma
gidan fatalwa, wato gidan da aka turbude muhibbat mahaifiyar
meenat, wanda hakan yasa ruhinta ya tashi yana basu tsoro,
sannan kuma mun yi bayanin abunda yasa aunty balkisu ta
kashe muhibbat, daga nan kuma bayan bala in da suka hadu
dashi a gidan fatalwa mutane da yawa sun rasa ryokans.
A cikin haka ne meenat da daddy su kawai ne suka tsira tare
da fita gidan lafiya lau. Bafferh, ummi da aunty balkisu duk
suna a cikin gidan sakamakon wannan halittar data cinyesu,
wanda hakan yasa kaka zuwaira ta bayyana cewa basu mutu
ba, amma sai in an samo wasu ruwa wadanda ba a cikin
duniyar mutane suke ba, saboda haka meenat tayi shiri domin
samo wadannan ruwa, wato “RUWAN SIRRI”
THE BEGINNING OF RUWAN SIRRI
Bayan da kaka zuwaira ta karanta wannan littafin na sihiri, take
sai bacci ya kama meenat, anan wata guguwa mai karfi ta fito
ta dauke meenat ta wuce da ita sama domin kaita duniyar da
zata samo wadannan ruwa na sirri.
Bako shakka a cikin bacci take, saboda haka batasan abunda
ke faruwa da ita ba, haka wannan guguwa ta cigaba da tafiya
da ita har sai da ta iso wani wuri mai ban mamaki, ita dai
meenat batasan abunda ke faruwa ba, daga nan sai guguwar ta
ajiyeta a hankali, tana ajeta sai ta bace bat. Shi dai wannan
wuri gaba daya sahara ne wato koina yashine.
Wata yar karamar hayaniya taji wanda hakan yasa ta tashi
firgigit to daga nan sai ta ga wasu halittu masu ban mamaki a
gewaye da ita suna kallonta, su dai wadannan haliitu mutane
ne, sai dai yan guntaye, sannan kuma sunada manyan kunnuwa
haka idanunsu kwala kwala, halittarsu dai ta banbanta da ta
sauran mutane, to bayan meenat ta mike tsaye sai taga ta fisu
tsawo domin kowanensu a bakin cibiyarta yake tsayawa, a nan
meenat ta fara kallon wannan wuri tana mamakin ko ina ne.
Daganan sai taga mutanen na jayewa da alamar wani ya ratso
yana son zuwa wurinta, wani saurayi ne ta gani saman doki,
wasu dakaru na take masa baya, wani kallo ya mata cikin
natsuwa, daga nan sai dakarun suka diro mata, kafin kaceme
sun daureta, daga nan sai suka jata zuwa wani babban birni
nasu……
Written by
Abdul king article
To bayan wadannan halittun sun shiga da meenat cikin brnin
sai ta gane cewa lallai wannan birni nasu ya tsaru, su kuma
sauran jama ar garin sai faman kallonta sukeyi, ita dai meenat
abun ya daure mata kai domin bata taba ganin irin wadannan
halittu ba, cikin wani gidan yari aka daureta.
Ba a fi minti goma da yin haka ba kawai saiga wannan
saurayin da ta gani da farko yazo wurinta shi kadai, bayan ya
bude gidan yari take ya shiga ya zauna kusa da ita, tambayarta
ya fara yi.
Ke wacece? Daga ina kike?
Murmushi meenat tayi domin ganin takeyi in ba don tana
daure ba da hannu guda ma ya isa ta makeshi.
Hala meya dameka da sanin koni wacece!!! Ta fada.
Kiyi hattara yan mata domin kina magana da yarima lamras.
Inji wani badakare, cikin fushi meenat ta amsa to koda shine
sarkin ma gaba daya oho, anan wadannan dakaru suka fusata,
kafin kaceme sun zagayeta, to anan suka fara dukanta sai da
suka tabbatar da cewa bata iya ko motsawa daga nan sai
yaruma lamras ya bada umarni da akawo masa ita dakinsa.
Da daddare ne iyakar dare, mika ta fara yi tare da yin hamma,
kawai sai ta farka, anan ta ganta saman wani gado na kasaita,
dariya kawai taji an yi mata, dubawa tayi kawai sai taga ashe
yarima ne ke kallon surar jikinta, daga nan sai yayi wani tsalle
da nufin ya fado saman jikinta anan meenat tasa kafa ta maka
shi can gefen gina, ji kake guuumm, anan kansa ya bugi gina,
kawai sai yarima ya fadi sumamme.
Anan hankalin neenat ya tashi domin tasan idan dakaru suka
gani to bako shakka kashinta ya bushe, domin zasu iya kasheta
saboda haka sai ta dauko yarima ta aza saman cinyarta tana
masa fifita jo zai tashi, ana cikin haka sai ga wasu dakaru biyu
sun shigo dakin, to a tsammaninsu yarima lafiyarsa kalau irin
yadda suka ga meenat ta kankameshi a jikinta, anan suka fita
dama muradinsu su gani in lafiyarsa lau, bayan fitarsu keda
wuya sai meenat ta aza sa a gado ba tare da sanin abuda
zatayi ba, bayan wani dan lokaci sai taga yayi atishawa anan ta
sheko a guje batasan lokacin data rungumeshi ba saboda
murna. “wato kin aza na mutu ko?” inji yarima.
Bako shakka na aza ka mutu. Ta amsa
Anan yarima ya gyara murya tare da dubanta sama har kasa,
wato ki sani yake wannan yarinyar, tun da nake ban taba ganin
matar da naji ta kwanta min ba irinki, saboda haka me yasa
bazaki ban hadin kai ba muyi aure. Meenat dariya tayi tare da
dubansa, ka dubi surar jikinka ka dubi nawa, jika wani dan
cukul dakai, sai kace in hadiye, me zanyi da wanda nafi kome.
Wannan magana fa ta sosa ran yarima, anan ya fara tunani,
wato saboda tana ganin ta fini girman jiki dani da mutanena
shine take yimin yadda taga dama, to yayi zata gani. Juyawa
meenat tayi da nufun fita daga dakin, cikin sauri yarima ya
tsayar da ita, zan so kiyimin alfarma tada.
Wace alfarma juwa? Ta tambaya, idan bazaki damu ba zan so
ki zauna a wannan garin namu nasan bako shakka dole akwai
abunda ya kawoki wannan duniya tamu, domin ko kadan
bakida kamada irin mutanenmu. Anan meenat ta gyada kai
cikin alamun yarda, wani dadi ne ya lullube yarima domin
yasan irin makircin dazai kulla mata wanda zai sa ta soshi,
anan yarima yaja hannunta tare da nuna mata dakinta.
To bayan yarima ya koma dakinsa take wata dubara ta fado
masa saboda haka sai yayi shiri domin tafiya wurin wani
babban amininsa domin su tattauna wani muhimmin al amari,
su kadai suka san abunda suka tattauna a wannan haduwa
tasu ta musamman, daga nan dai sai yarima yayi shiri ya
dawo.
Tun da sanyin safiya yarima lamras yazo tadata, anan ya samu
sa a ba tare da bata lokaci ba ta tashi, anan ya mata umarni da
yanaso yakaita wurin babansa sarki domin ta gaida shi, haka
ko akayi, anan meenat ta amince ba tare da gardama ba, cikin
jin dadi yarima yaja hannunta suka fara tafiya fada, wannan
tafiya tasu daban mamaki, ita dai meenat ta kasance doguwa
kuma kyakkyawa abar kwatance, shima yariman kyakkyawa ne
sai dai yanayin jikinsa tare da na mutanensa duk yan kanana
ne, haka suka cigaba da tafiya, duk inda suka wuce sai kaga
ana kallon meenat domin gaba daya garin ba wanda yakai
tsawonta, haka kuma kirar jikinta daban yake dana matan
garin. To bayan sun isa fada, anan kallo ya koma sama, anan
kowa ya tashi tsaye yana kallonta hadda sarki domin basu
taba ganin irin wannan halittar ba, anan dakaru suka fito da
makaman yaki domin a tsammaninsu wani naman daji ne ya
kamo yarima.
To bayan fadar ta natsu, sai yarima ya tako har zuwa wurin
babansa wato sarkin garin, anan ya fara gabatar da meenat a
gaban kowa tare da bayyana musu inda suka tsinceta, anan
mamaki ya kama mutanen fadar gabaki daya.
Yake yan mata ko zaki bayyana mana ko a ina kike? Sarki ya
tambaya. E ranka ya dade, ni na fitone a wani wuri mai nisa
kuma nazo wannan gari naku domin bincikar wani abu mai
muhimmanci, inji meenat. Anan sarki yayi tabi har sau uku,
dakyau, amma zanso sanin ko wane irin abune wannan idan
yaso ko zan taimaka, cewar sarki. Ina godiya ranka ya dade sai
dai wannan abun mai muhimmancine, bazanso fadinsa a
gaban mutane ba.
Anan mutanen fada suka cika da mamaki, wannan ko wane irin
abune take bida? To bayan wani dan lokaci sai sarki ya jawo
yarima anan suka tattauna kus kus yadda bamai jinsu daga nan
sai akaba meenat umarni data koma masaukinta. To bayan
meenat ta fito daga cikin fadar bata tsaya koina ba sai a wani
wuri na shakatawa da aka killace, anan ta samu wuri ta zauna
tana kallon yadda tsuntsaye ke shawagi, anan wani tunani ya
fado mata na duniyarta inda ta baro, anan ta kalli sarkar dake
rataye ga wuyanta, maganar kaka zuwaira ce ta fado mata
inda take gaya mata cewa idan bada wannan sarkar ba to
bazaki iya dawowa a duniyarmu ba sai dai ki tabbata a can
saboda haka ki kula da wannan sarkar kada ki yarda ta
salwanta.
Kafadarta taji an taba wanda sanadiyar hakan yasa tunanin da
take ya yanke, juyowa tayi domin ganin ko waye anan taci karo
da yarima lamras, cikin annashuwa ya zauna kusa da ita, anan
ya dubeta yana mai cewa wai me yasa bazaki aminta daniba,
cikin dariya ta dubeshi tana mai cewa haba yarima hala ka
manta abunda da na gaya ma a baya, ka dubi jikinka ka dubi
jikina, nifa ba irin jinsinka bane, saboda haka ba yadda za ayi
ka samu abunda kakeso, anan ta tashi ta nufi masaukinta
tabar yariama cikin cizon yatsa, to duk abunnan dake faruwa
ashe sarki ya kulla, kuma shima ya gane cewa bako shakka
meenat bata son dansa, anan yazo ya dafa kafadar yarima,
haba dana kada ka damu, ai idan tasan wata batasan wata ba,
indai saboda girman jiki yasa bata kulaka, to cikin kwanaki
kadan zakaga ta dinga kulaka domin zamu sauya mata
kammani itama ta dawo yar karama irin jinsinmu, yarima najin
haka take ya bushe dariyar farin ciki, domin a wannan lokaci
ba yarinyar da yakeso irin meenat.
A cikin wannan dare meenat tayi shiri domin fita ko zata dace
da abunta fa fito nema wato “RUWAN SIIRRI” haka ta fito cikin
fada ta kama hanyar shiga cikin garin, anan ta cigaba da tafiya
tana waige waige, domin yanayin gidajen garin ba irin wadanda
ta saba gani bane haka ma yanayin al adun mutanen sun
banbanta da wadanda ta sani, tana cikin wannan tafiya bata
sani ba sai taci karo da wata yarinya, a wannan lokaci yarinyar
da dauko wasu kayayyaki a saman kanta, take wadannan kaya
suka zube gaba daya. Ke hala bakya gani dazaki bugeni??? Inji
yarinyar. Anan meenat ta duko kanta kasa domin ganin ko
meke faruwa, daga nan ne ta gane cewa ashe barna tayima
wannan yarinya. ” yan mata kiyi hakuri ban gani ba” inji meenat
Ba matsala na hakura. Inji yarinyar. To anan ne suka hada ido
da meenat, anan meenat ta gane cewa yarinyar ba karamar
kyakkyawa bace, to kafin su rabu meenat ta tambayi sunanta,
anan ta amsa mata da ( RUMAISA)
Haka meenat ta cigaba da yawace yawace amma bataga
wanda ya kamata ta tambaya game da wadannan ruwa ba,
saboda haka tayi hakuri ta dawo a cikin masarautar. A wannan
lokaci a gajiye take, saboda haka shigarta daki keda wuya sai
bacci ya saceta, to a cikin wannan darene sarki da yarima
lamras sukayi shiri domin gudanar da aikinsu ga meenat, cikin
taku suke tafiya har suka iso gaban dakin, a hankali suka bude
dakin daganan sai suka shigo, wata yar kwalba ce sarki ya fito
da ita, shi kuma yarima sai ya dauko wani dan karamin surunji,
anan yasa wannan surunji cikin kwalba, ko menene a cikin
kwalbar oho, to bayan yarima ya jawo ruwan kwalbar, take ya
nufi gadon meenat da nufin dura mata ruwan, isarsa keda
wuya sai meenat tayi wata irin atishawa mai karfi wadda tasa
hankalin yarima ya tashi domin a tsammaninsa ta farka, cikin
natsuwa ya zuba mata ruwan, sai ko a bakinta dalalalal, anan
yarima yayi dariya tare da sarki, cikin sauri suka fice dakin su
kadai sukasan sharrin da suka yimata
Tsunstsaye ne ke shawagi a sararin samaniya tare dayin kuka
irin nasu wanda sukadai suka san abinda suke cewa, wannan
shawagi da sukeyi shi zai tabbatar ma mutum cewa sun fito
neman abinci kamar yadda idan safiya ta waye ko wane
mahakuki zai tafi bidar abinda yaci, sai dai wannan shawagi da
sukeyi bana lafiya bane domin sun cika tagar dakin meenat da
koke koke, saboda wannan kokawa tasu yasa meenat ta tashi,
anan ta gane cewa wai safiya ta waye, su wadannan tsuntsaye
kome sukeso? Anan tadan yi tunani bayan kallon da tamusu.
Mika tayi tare da aje kafafuwanta a kasa da nufin tashi tsaye,
anan mamaki ya kasheta, siffar jikinta taga ta canza, anan ta
zo daf da madubi domin ganin ko meke faruwa da ita, wani
uban ihu ta gabza tare da faduwa kasa sumamma.
Haka meenat ta kasance cikin wannan yanayi na suma ba tare
data farfado ba, sai da ta dau lokaci mai tsawo kafin daga
bisani ta farka firgigit kamar an tada ita, to anan ne ta kara
kallon madubin dakin domin ganin siffar jikinta, hawayene ya
zubo a saman kumatunta, ita datake kyakkyawa doguwa
amma dubi yadda jikinta ya koma, saffar jikinta ta koma irin ta
mutanen garin, ta zama yar guntuwa, ga kwala kwalan idanu,
manyan kannuwa da kuma katon kai, anan meenat ta fara
tunani domin tasan wannan makircine aka yimata, amma ko
suwaye??? anan dai tayi shiru ba tare da sanin takamammiyar
amsar wannan tambaya ba. Tana cikin wannan tunani sai ga
yarima lamras ya shigo a dakin, laaaaaaaa. Cikin mamaki ya
fada, hala meke faruwa dakene? Ya fada cikin tausayawa,
anan meenat ta rasa amsar da zata bashi, hawayene suka kara
dilmiyowa a idanunta, anan yarima ya fahimci halin da take
ciki, saboda haka sai ya rungumeta yana lallashinta, abun ya
bashi mamaki domin yanzu tsawonsu guda da meenat, a fili ya
nuna kamar ya tausaya mata, gaskiya idan muka gano ko
wanene ya miki wannan aika aikar bako shakka zai fuskanci
hukunci mai tsanani. Ya fada. Amma a cikin zuciyarsa ko
kadan bayajin kome. Haka dai ya lallasheta daga baya kuma ya
jata domin suci abinci.
A wannan lokaci mutanen fadar sun cika da mamaki, koya
akayi meenat ta koma da irin siffarsu?? Haka dai suka cigaba
da kallonta cikin rudani da kuma alamar tambaya.
A kwana a tashi bata bar komeba, tun meenat na ganin
muninta a cikin wannan siffa har ta daina, amma tadau
alkawari kul a dade kul a jima sai ta gano musabbabin
sauyawar halittarta ta ainahi, wata rana meenat na tare da
yarima a cikin filin shakatawa na masarautar, kawai sai ya zo
da maganar soyayya, anan meenat tayi shiru kamar bata jishi
ba, murmushi yayi tukun, haba hasken idona, dakefa nake
magana amma kinyi shiru sai kace kurma, anan meenat ta dan
dago ta kalleshi batare da cewa komeba, to a wannan lokaci
duhu ya dan fara, daga nan sai wata daga cikin masu aikin
gidan ta dauko kwannan abinci ta ajiye a gaban su yarima,
anan meenat ta dago kai domin ta kallli ko wacece, anan ta
gane yarinyar, ” rumaisa” ce. Wannan yarinyar data buge cikin
rashin sani a kasuwa, anan meenat taga rumaisa na mata wani
kallo wanda batasan ma anarsa ba, ajiye abincin keda wuya
kawai sai sukaji karar mutane, anan sukaji garin ya bice da
ihun mutane, wannan ihu bana lafiya bane, cikin sauri suka
mike tsaye, anan yarima ya zare takobinsa, “inaji cewa kamar
an kawo mana hari” injishi, daganan sai ya fara gudu domin
zuwa kofar garin, haka itama meenat ta binshi domin ganin ko
meke faruwa, a guje rumaisa ta shige cikin masarautar domin
isar da sako cewa an kawoma garin yaki.
To bayan su meenat sun isa kofar garin, anan suka tarar da
gawawwakin mutane birjik, wasu irin tsuntsaye ne ke feshin
wuta ga mutanen garin, sai kuma wasu zaratan dakaru dake
can waje suna bugun kofar garin domin su samu damar
shigowa su ci garin da yaki.
Su kuma dakarun wannan gari na su yarima sai kokarin dafe
kofar garin sukeyi, ana cikin hakane saiga sarki qamar wato
baban yarima lamras, a bayansa wasu dakaru ne kimamin
mutum dubu, anan yayi wani ihu take da basu umarni, cikin
sauri suka fito da kwari da baka anan suka fara harbin
wadannan tsuntsaye, to a wannan lokaci kofar garin ta kusa
karyewa sanadiyar dukan da tasha, daga nan sai wadannan
dakaru dake kokarin shigowa wannan birni suka dauko tsame
(LADDER) wannan tsame nasu na karfe ne, anan suka azashi
saman katangar garin, take wasu daga cikinsu suka fara
hawansa domin shigowa garin, to anan ne dakarun sarki
qamar dake saman katangar suka fara halbinsu da kibau, to a
wannan lokaci ne meenat tayi wuf ta amshe takobin wani
badakare, anan tayi wani ihu wanda yasa duk dakarun suka jiyo
suna kallonta, a guje take, take ta nufi katangar garin, anan
mutane suka fara kallonta suna mamakin ko ina zata, wani
tsalle tayi daga nan ta tsallake katangar, anan mutane suka
cika da mamakin wannan jarumta tayi, to bayan ta fita garin
ne, anan ta fara yakar wadannan dakarun da suka kawo musu
hari, wannan yasa suma sauran dakarun garin sukayi koyi da
ita, anan suka fara fita garin domin tayata wannan yaki, a cikin
wadanda suka bita harda yarima lamras tare da babansa
qamar. To a wannan lokaci meenat ba karamar jarumta ta
nuna ba a haka yasa yarima lamras ya karajin sonta ya shiga
zuciyarsa, basu dau lokaci ba suka tarwatsa rundunar
wadannan mayakan da suka kawo musu hari, anan ne yarima
ya shego a guje ya rungume meenat, anan ta kankaneshi a
jikinta tana dariyar farin ciki, sarki qamar na ganin hakan sai
yayi murmushi, wani tunani ne ya zo masa a lokacin da yana
cin tashi kurciya, anan dakarun garin suka fara yimata karari
suna kiran sunanta cikin farin ciki. “MEENAT MEENAT
MEENAT”
Daga nan sai aka bude kofar garin domin su shigo ciki, anan
meenat ta fara tambayar yarima. Wai hala waye keda sa hannu
cikin wannan hari da aka kawo muku??
Anan yarima ya gyada kai, daga nan sai yace, gaskiya bazan
iya cewa ga kowanene ba. Domin wannan ba shine karo na
farko ba, an sha yimuna haka, amma muna ganin cewa wasu
makiyanmu ne masu son dukiyar birninmu. anan dai suka shige
birnin ba tare da furta komai ba.
Bayan sati daya da faruwar hakan, wata rana meenat na cikin
dakinta kawai sai taji ana kwankwasawa da alamu anaso
anaso a shigo a ciki, anan ta tashi domin ta bude kofar,
budewarta keda wuya sai tayi arba da rumaida. Ko zan iya
shigowa ciki?? Ta tambaya.
E shigo mana, meenat ta bata amsa, to bayan sun zauna sai
rumaisat ta fara magana, nasan zakiyi mamakin ganina a
wannan lokaci duk da cewa ban taba kawo miki ziyara ba. To
ki sani cewa nazone domin sanar dake wani muhimmin sako,
yake wannan jaruma kina tare da abubuwa naban mamaki, idan
zaki iya tuna cewa a lokacin da kika shigo wannan birni namu
ai ba haka halittar ki take ba, amma daga baya sai komi naki
ya sauya zuwa irin jinsinmu, nasan zakiyi mamaki game da
wannan, daga nan kuma sai kika fara tambayar kanki wai waye
keda hannu wurin wannan juyawar halitta taki? To inada amsar
wannan tambaya taki. Kuma inada maganinta.
Mafi yawancin mutane wannan gari suna mamkin abunda ya
kawoki wannan duniya tamu kasancewarki ba irin jinsinmu ba,
to ni nasan abunda ya kawoki, kuma nasan abunda kike bida,
kuma nasan inda za a samu wannan abun da kike bida. Anan
meenat ta kura mata idanu domin ta sosa mata inda ke mata
kai kai.
Ki sani yake wannan ma a bociyar kyawo, zan fada miki duk
abunda kike bida amma da sharadi daya!!! Wane sharadi
kenan?meenat ta tambaya. Anan rumaisa ta kalli sarkar dake
rataye ga wuyan meenat. Inaso kiban wannan sarkar dake a
wuyanki.
Anan meenat ta mata wani kallo, daganan sai ta fara yin
tunani, wata magana ce da kaka zuwaira ta mata game da
sarkar kafin ta shigio wannan duniyar.
“KADA KI YARDA WANNAN SARKAR TA BACE MIKI, DOMIN
DA ITA KADACE ZAKI IYA DAWOWA DUNIYAR MUTANE IRIN
JINSINKI, IDAN KUMA HAR TA BACE, TO ZAKI TABBATA A
WANNAN DUNIYAR HAR ABADA”
Wannan magana ta tayar wa da meenat hankali, domin ko
kadan bazata iyabada sarkar ba, daga nan sai rumaisa ta tashi
tsaye, bazan tilasta da ki bada abunda kikeso ba, amma zan
baki wuri domin kiyi tunani, daga nan sai ta fita tabar meenat
cikin tunani, babban abunda keba meenat mamaki shine koya
akayi ita matsayinta na mai aiki amma har tasan wadannan
abubuwa, gaskiya akwai alamar tambaya game da wannan
yarinya, haka dai meenat tayi ta sake sake ba tare da sanin
mafita ba.
Ranaku na wacewa daya bayan daya, wata rana meenat tazo
wucewa a kusa ga dakin yarima, sai ta farajin nishi, anan tayi
tsaye tana tunani domin kwanakin nan sai ganin yarima take a
birkice, idan ya shigo da wannan yarinya dakinsa gobe sai kaga
wata, daga nan dai ta wuce ba tare da tace komeba. Bayan
rana ta fadi sai meenat tayi shiri domin shiga filin shakatawa
na masarautar, shigarta keda wuya sai taci karo da yarima a
zaune saman kujera yana kallon tsuntsaye na shawagi, anan
tazo ta zauna kusa dashi.
Daga nan saita fara yi masa magana, zan so in baka shawara
a matsayina na abokiyarka, wato ka sani yarima abunda kakeyi
bai daceba a matsayinka na dan sarki, wadannan matan da
kake harka dasu ba abunda zasu jama in banda zubar mutunci,
da kuma cututtuka marar magani, saboda haka ina baka
shawara ka daina.
Anan yarima lamras yayi wata irin dariya, daganan sai ya tashi
tsaye, ai ba bukatar shawara nakeba, yanzu dai bama wannan
maganar ina gayyatar ki kasaitaccen bikin da za ayi a mako
mai zuwa na murnar sabuwar shekara, sai kin zo. Daga nan
yarima ya wuce cikin masarautar ya bar meenat cikin mamaki.
:::::::::::::::::::::::::::::
A cikin wannan nahiya da meenat ta sauka, akwai wani gari da
ake kira GARWA, sarkin wannan gari sunansa habar, habar ba
karamin mayaki bane dashi da jama arsa haka kuma a kullum
yanada burin da yake son samu.
A cikin wani lambu take tare da wani saurayi kyakkyawa, a
zaune suke suna nishadi, amma abunda ke bata mamaki shine
batasan wannan saurayin ba, kuma bako shakka sonsa ya
kamata, suna cikin wannan hira ta nishadi kawai sai taga wani
barde a saman doki anan ya nufo wannan saurayin da take hira
dashi, wannan barde yana rike da mashi, wani tsalle yayi da
nufin soka ma saurayin mashi, anan tayi wata kara cikin
takaicin rabuwa da wanda takeso, anan ta tashi firgigit, wai
ashe mafarkine takeyi, wannan mafarki kan bata mamaki
domin tana yawan yinsa, kuma bako shakka a cikin zuciyarta
tana jin son saurayin na ratsata, sai dai kash gashi batasan ko
wayeba sannan kuma wannan da ke kokarin kasheshi ko
waye? Kuma me yasa yake kokarin kasheshi, haka dai
wadannan tambayoyi suka cigaba da damunta ba tare da sanin
amsar suba.
Gimbiya kulsum ce ke wannan mafarki, wato diyar sarki habar,
to anan tayi mika daga nan ta tashi tayi wani wanka, bayan ta
kammala sai ta nufi fadar babanta sarki domin amsa kiran da
yayi mata, shigarta keda wuya fadar sai ta iskeshi yana
tsawatawa dakarunsa: ku ragwayene, ya za ace kun kasa
yankamin kan wannan sarkin tareda dana dansa ku fita ku bani
wuri anan ya koresu. To bayan gimbiya kulsum ta karaso, anan
ta zauna kusa dashi saman wata kujera da aka yiwa ado da
zinari, daga nan sai ya sallami dukkan dakarun dake tare dashi
domin yanason yin sirri da diyarsa.
Wato ki sani gimbiya, inada wani buri da nakeson kammalawa
amma bazan iya ba dole sai kin ban hadin kai, to anan gimbiya
kulsum ta kashe kunne domin taji abunda babanta zai ce. Daga
nan sai ya cigaba da bayani, akwai wani birni da ake kira
YAMLA wannan birni sunada albarkacin kasa tare da tarin
dukiya marar iyaka, sunan sarkin wannan gari qamar, yanada
da mai kwarjini da ake kira lamras, a cikin masarautarsu,
akwai wasu tarin lu u lu u dake cikin wani akwati, su wadannan
akwatayya sunfi su dubu, to fiye da shekaru goma na ta tura
mayakana domin su satomin wadannan akwatayya amma sun
kasa, kuma ki sani cewa idan muka mallaki wadannan
akwatayya, to arzikin birninmu zai kara kasaita fiye dana da, to
yanzu abu daya nakeso kiyi, nan da sati daya zasuyi bikin cikar
sabuwar shekararsu, to a cikin wannan biki nakeso ki tafi ki
satomin wadannan akwatunan domin a ranar hankalin
mutanen garin naga bikin, shi kuma yariman garin wato lamras
bayada aiki sai son matan banza, saboda haka zan tura masa
wata aljanna wadda zata dauke masa hankali, to da yayi lalata
da ita zai kamu da wata cuta, kinga daganan sai ki dauko
akwatunan cikin sauki.
Wannan magana dai ta girgiza hankalin gimbiya, daga nan sai
tayi tambaya, to amma meyasa kakeson illata yariman gashi
kuma bazai tare komeba, daganan sai sarki ya fara bata amsa,
wato shi yariman shike rike da makallin dakin da akwatunan
suke, kuma shi ke gadinsu, kinga kuwa dole sai an masa haka,
bayan kin shiga masarautar ita wannan aljannar da zan turo ita
zata baki makullin dakin tareda nuna miki inda yake, saboda
haka kiyi saurin tattarasu ki dawonan, sannan kuma zan hadaki
da wasu dakaru masu yawa wadanda zasu tayaki kwasar
akwatunan. Kuma yau da dare zaki rakani wani wuri. Daganan
sai ya bata umarni data koma ta cigaba da ayyukanta, haka
gimbiya kulsum ta shiga dakinta tana tunani, ko kadan batason
yadda babanta ke zalunci amma kuma bata iya hanashi.
A cikin wannan dare ne sarki habar tareda gimbiya kulsum
suka hau dawakai, anan suka saki linzami suka fara wani
namijin gudu sai kace iska, sarkin ne gaba gimbiya na binsa,
haka suka cigaba da wannan gudu har suka kawo wani katon
teku, daga nan sai suka sauko saman dawakansu, tafiya suka
farayi har suka kawo gabar ruwan, daga nan sai sarki ya fara
ambaton wasu kalamai marar ma ana, cikin abunda bai fi
kiftawa ba sai sukaga wani haske ya fito a cikin ruwan,
daganan sai hasken ya rikede ya zama wata mace mai
tsananin kyau, ita kanta gimbiya kulsum sai da ta yaba da
kyawon wannan mata to ina ga namiji, lallai karyar yarimar
lamras ta kare domin ba yadda za ayi yayi arba da wannan
mata ba tare da yayi shawarta ba, gimbiya kulsum ta fadi a
cikin zuciya.
Daganan sai sarki habar ya fara magana da wannan mata cikin
wani yare na daban wanda gimbiya batajin abunda suke fada,
to bayan sun gama maganar, sai matar ta koma haske daganan
sai ta shige cikin ruwan ta bace bat, wata dariya sarki yayi ta
alamun samun nasara, daganan sai ya kalli gimbiya, wannan
matar da kika gani itace zan turama yarima, kuma itace zata
baki makullin bayan ta gama da yarima. Cikin murmushi
gimbiya ta fara magana, amma zanso ganin fuskar wannan
yarima! Daganan sai sarki yayi nuni da yatsansa zuwa ga ruwan
yana ambaton wasu kalamai a cikin zuciya kawai saiga fuskar
yarima lamras ta bayyana a ruwan, gimbiya na ganin wannan
fuska take gabanta ya fadi rasssss, anan ta tuno da mafarkinta,
bako shakka wannan saurayin shine ta gani a mafarki, kuma
shine wanda take muradi ace ya zama mijinta, daganan sai
suka hau dawakai suka nufo hanyar dawowa, haka suka iso
masarautar gimbiya bata masan sun kawo ba, wannan abu fa
ya rudata, gashi idan ta fadawa sarki tanason yariman ko
kasheta zai iya yi, anan gimbiya ta kwanta tana tunanin hanyar
da zatabi ta taimaki yarimanta wato lamras.
A cikin birnin yamla wato birnin su yarima lamras, a yau ne ake
bikin cikar shekara, saboda haka manyan jaruman birnin sun
shigo fadar sai wasanni ake gudanarwa kala kala, haka meenat
tayi wata kwalliya to zo ka gani, ana cikin wannan bikine sai
taga wata bakuwar fuska, yarinya ce kyakkyawa abun kallo,
wata rawace takeyi mai daukar hankali, a tsakiyar wasu yan
mata take sai tikar rawa suke, anan meenat ta lura da idanunta
kamar ba irin wadanda ta saba gani bane, daga nan dai sai
meenat taji bata yarda da wannan yarinya ba, sannan abunda
ke bata mamaki shine tunda yarinyar ta fara rawa yarima sai
kallonta yakeyi ko kyaftawa baya yi, bayan wani dan lokaci, biki
yaci baki,kawai sai meenat ta hango yarima lamras tareda
wannan yarinya a cikin wani lungu suna wata magana, daga
nan sai taga yarinyar taja yarima hannun yarima suna nufin fita
wurin bikin, to anan ne kuma ta hango wata yarinya a guje tana
kiran yarima lamras kamar akwai wani abu da takeson
gayamasa, anan meenat taj mamaki domin batasan ko wacece
ba, wannan yarinya ba kowa ceba in banda gimbiya kulsum,
itace ke kiran yarima tanason ta gaya masa sharrin da aka
shirya masa, sai dai kash ta makara, ahaka ta fita tana bidarsu
amma ko duriyarsu bata gani ba, daga nan sai gimbiya kulsum
ta fashe da kuka, anan ta fara tunani irin balain da zai samu
yarima lamras.
To bayan an gama biki kowa ya watse, anan mai faruwa ta
faru, koda yarima ya koma dakinsa bai da lafiya, meenat ce ta
gano hakan bayan da ta shiga dakin domin yi masa wasu
tambayoyi to anan ta kira mahaifinsa wato sarki qamar domin
ganin abunda ke faruwa, cikin kankanin lokaci jikin yarima ya
kunbure, wasu kurajene suka fara fitowa a jikinsa suna
fashewa, sannan kuma suna fidda wasu ruwa, gashi yarima
nason yin magana amma bai iyawa domin ciyon yayi tsanani,
to anan hankalin sarki ya tashi ya rasa abunda ke masa dadi,
anan meenat ta tuno da wannan yarinyar data gani a wurin
bikin. Daga nan sai sarki ya fada mata cewa tun da dare yayi
sai gobe a kira masu magani domin su duba lafiyar yarima,
daga nan sai meenat ta wuce dakinta.
Meenat na cikin tafiya kawai sai taga ansha gabanta, anan
taga wannan yarinyar data gani tana kiran yarima a wurin biki.
“kiyi hakuri nasha gabanki, amma akwai wata magana mai
muhimmanci da nakeson yi dake” inji yarinyar
Daga nan sai meenat tajata zuwa dakinta, anan yarinyar ta fara
magana: ni sunana gimbiya kulsum diyar sarki habar na birnin
darwa, daga nan sai ta fara bata labarin sharrin da abbanta ya
shiryawa yarima lamras domin ya samu damar sace wadannan
akwatunan na lu u lu u da kuma yadda ta bugi cikinsa har ya
fada mata maganin da zai warkar da yarima da kuma inda za a
samo shi, daga nan sai meenat tayi shiru cikin mamaki, to
bayan gimbiya kulsum ta fada mata kome, daga nan sai ta fita.
Tun da sanyin safiya meenat ta isko sarki qamar ta bayyana
masa abunda ta sani game da wannan cuta ta yarima, daga
nan sarki ya rike baki yana mamkin abun, cikin kankanin lokaci
sarki yasa aka tara masa dukkan jaruman garin. Daganan sai
ya fara yi musu bayani kamar haka:
Yaku sadaukan wannan birni ku sani cewa idan mutum ya fita
a cikin wannan birni namu yabi hanyar yamma zai yi tafiya ta
kwana dari cif kafin ya isa wani birni dake a saman wani katon
dutsi, sunan wannan birni askandariya. Wannan birni wani
sarkine ke mulkinsa, sunan wannan sarki gamza, sarki gamza
tare da jama arsa suna bautar wani iccene dake a cikin wani
kogo, ko kadan basa bari wani ya debi iccen, saboda haka ya
tanadi wasu dakaru su dubu sabain wadanda basa cin abinci
kuma basa shan abinsha, kuma basa bacci, a kullum gadin
wannan icce suke ko kuda basa bari ya hau kansa, su
wadannan dakaru an sihircesu da tsumin tsafi irin na shi sarkin
wato gamza, saboda haka karfinsu ba irin na mutane bane,
kuma yakarsu sai an shirya, a binciken da mukayi mun gano
cewa wannan icce shi kadai ne maganin da zai warkar da
cutar dake damun yarima.
Sai dai ku sani cewa a cikin wadannan kwanaki dari da mutum
zai yi kafin ya isa birnin, akwai bala i nau i nau i har kala dubu,
kuma cikin wadannan masifu uku kawai muka sani saura sai
idan mutum yaje, a saman wannan hanya akwai wani karamin
gari na wasu dodanni masu kalaci da naman mutum, bayan
mutum ya wuce garin akwai wasu kwari da har yanzu ba asan
inda suke fitowa ba, su wadannan kwari kan shiga jikin mutum
daga nan sai suyi masa gunduwa gunduwa, to idan mutum ya
wuce kwarin sai ya iso wani wuri inda ba a takawa, domin idan
mutum ya taka wurin take zai nutse ya halaka, to kunji fa.
Saboda haka nasa kyautar zinari dubu, azurfa dubu, lu u lu u
dubu, rakuma dubu da kuma dawakai dubu ga duk wanda ya
yarda zai sadaukar da rayuwarsa yabi wannan hanya har ya
shiga wannan birnin askandariya ya debo ganyen wannan icce
(bishiya) saboda haka waye zai iya yin wannan tafiya??? Sarki
ya tambaya.
Anan fada tayi tsit, jarumai kowanensu idonsa ya fito don
tsoro, anan aka rasa wanda zai yi magana, wannan yanayi na
jaruman garin ya tayar ma sarki hankali, anan ya rasa abunda
ke masa dadi.
Ana cikin wannan yanayi kawai sai meenat ta tako tsakiyar
fadar, anan jarumai suka kura mata idanu suna tunanin me
zatace. Cikin murmushi ta fara magana: Ni zan iya, na yarda
zan sadaukar da rayuwata in debo wannan icce. Anan jaruman
gari suka done kai saboda kunya, ya za ace mace tayi wannan
tafiya gasu.
To anan sukaji tabi, rumaisa ce ke ma meenat tabi saboda jin
dadin kalamin da tayi, daga nan sai sarki ya tayata, kafin
kaceme fada ta rude da tabi da kuma shewa, to anan sarki ya
sallami kowa.
Meenat na cikin daki saiga rumaisa ta shigo, gaskiy kin nuna
bajinta domin ban aza xaki iya haka ba, amma wai kuwa kin
san irin balain dake wannan hanya? Anan meenat tayi
murmushi ba tare datace kome ba. To ya maganar dana miki
game da sarkar, ina fatan kin yanke hukunci yanzu? Wannan
sarkar tanada muhimmanci a gareni, inji meenat, anan ta fada
mata sirrin sarkar da kuma kashedin da aka yimata na badata
ga wani. Daganan sai rumaisa ta dauko wata riga doguwa ta
bata, wannan itace gudunmuwata a gareki, anan meenat ta
karba tayi godiya ba tare da sanin muhimmancin wannan riga
ba.
Daga nan sai rumaisa ta fara magana, wannan tafiya da zakiyi
mai hadarin gaskece inada wasu yan uwa da suka taba bi
wannan hanyar, fiye da shekaru da dama amma har yanzu ba
duriyarsu, kanwata tare da abbana ne, shi yasa yanzu ni kadai
nake tare da mahaifiyata. Daga nan sai rumaisa ta tashi ta fita
dakin.
Tun da sanyin safiya meenat gama shiri, anan ta dauki guzuri
mai yawa, daga nan tayi bankwana da mutanen garin, anan ta
hau doki ta kama hanyar nan mai hadari domin samo wannan
icce.
SHIN WAI MEENAT ZATA SAMO WANNAN ICCE KUWA?
WANNE IRIN BALAI ZATA GAMU DASHI A WANNAN HANYA??
YA MAGANAR RUWAN SIRRI?
SHIN KO MEENAT ZATA KOMA ZUWA GA HALITTARTA TA
AINAHI?
ITA KUWA GIMBIYA KULSUM ZATA CIKA BURINTA NA GANIN
CEWA TA MALLAKI YARIMA LAMRAS???
TO BE CONTINUE………
PART 2 COMING SOON INSHA ALLAH.
abdul king article
for more novels:
SEARCH AND JOINT OUR FACEBOOK GROUP:
KINGARTICLE.NOVL
OR
KINGARTICLE NOVELS OF ABDUL$BAFFERH
RUWAN SIRRI
“cigaban gidan fatalwa”
part ( 2 ) kashi na biyu
Dedicated to:
Firdausi queen article
RECALL BACK……………
A cikin ruwan sirri littafi na farko mun bayyana yadda meenat
ta tafi wata duniya ta daban domin samo wadannan ruwan na
sirri wadanda zasu tada bafferh, aunty balkisu da kuma
mamarta wato muhibbat, a cikin wannan duniya ta gamu da
kalu bale iri daban daban, sannan kuma mutanen data isko na
wannan duniyar ba irin wadanda ta saba gani bane domin
halittarsu daban take data sauran mutane, wanda hakan yasa
suka yi mata sharri suka juya halittarta izuwa tasu, sai kuma
gimbiya kulsum wadda ta bayyana sihirin da aka yiwa yarima
lamras tare da inda za a samo makarinsa, yanzu dai meenat na
kan hanyarta na zuwa samo wannan iccen na sarki gamza.
THE BEGINNING:
Wani santamemen fili ne mai cike da yauki ga kuma ban tsoro,
a haka wani iska mai kara tare da wata karamar guguwa ya
fara kai kamo a cikin fili. Daga nan sai ga wasu tsuntsaye dake
sararin samaniya suna kalwade a cikin filin, kome ya faru cikin
rashin tsammani kawai sai tsuntsayen suka fara wani kuka
kamar basada lafiya, take sai wannan iska mai dauke da
guguwa ta jawosu, tsuntsayen na kara suna ihu amma haka
guguwar ta jawosu har sai da shige dasu cikin kasan wannan
filin mai yauki, kafin kuma ta shiga dasu sai da ta yayyanka su
gunduwa gunduwa wato kai daban kafafuwa daban, ma ana ko
mutum ne yabi ta filin haka wannan guguwar zata yi masa ta
shige dashi ciki kasa tayi masa gunduwa gunduwa . To abun
tambaya shine meke kawo wannan abu???
Written by
Abdul king article
A cikin wadannan tsuntsaye da wannan guguwa ta kashe akwai
guda wanda ya tsira, ma ana kenan ko a cikin mutane masu
biyar hanyar akwai masu tsira daga sharrin guguwar, to abun
tambaya shine idan guguwar ta nutse da mutane a karkashin
kasa wai me suke iskowa a can?
Daki ne gyararre wanda aka tanadar ma kowane alatu na
kawa, wani gado ne a tsakiyar dakin sai daukar kyalli yake,
yarinya ce budurwa kyakkyawa a sama sai sharar barcinta take.
Firgigit ta tashi, anan ta dubi kafadarta ta dama, wani
murmushi tayi, wai ashe wani tsuntsu ne ya fado mata shine ta
tashi, ko ta ina ya shigo? Anan ta tambayi kanta cikin zuciya.
Kallon tsuntsun tayi sai taga bai da alamar tashi ya tafiyarsa to
anan taji shawarsa saboda haka kawai sai ta ajiyeshi a saman
gadonta ta cigaba da baccinta.
Firgigit ta kara tashi, a wannan lokaci kamar akwai abunda ke
damunta, gashi dakin ya kable da duhu koina, ko meke faruwa,
ya akayi fitillu suka mutu?? Anan ta fara lalube amma ko
duriyar fitila babu, to anan ta fara jin tsoro kadan, kada dai ace
wannan abun dake damunta shine zai dawo mata a cikin
wannan daren. Ta danyi tunani.To abun tambaya shine ko
menene ke damunta??
Anan ta mike tsorace, tafiya takeyi gabanta na faduwa, tana
cikin hakane sai ta taji kamar ana tafiya bayanta, da sauri ta
juya tsorace amma bataga kowa ba, anan ta cigaba da tafiya
amma daga baya sai tayi tsaye wuri daya ta kasa motsawa, a
cikin duhun take ganin wani abu kamar yana matsowa kusa
gareta, anan ta fara ja da baya amma abun sai matsota yakeyi,
tana cikin wannan ja daba ne taci karo da gadonta anan ta fadi
rikicaaaa. Daga nan sai ta yanke shawarar bari ta kwanta
hakanan, juyawa tayi da nufin bacci amma ina anan ta kasa
domin a tsorace take. Kuma sai taji kamar ana tasheta. Anan
wannan budurwa ta kara mikewa a tsorace, to a wannan lokaci
abun yayi kamari sosai, domin ba abunda takeso irin ta fita
daga dakin. Cikin wata yar karamar murya tata irin ta yan mata
ta fara magana:ABBA ABBA ABBA anan taji shiru ba wanda ya
amsa. Hakan yasa hankalin ta ya kara dugunzuma domin
batasan halin da abbanta yake ciki ba.
Firrrrr cikin rashin tsammani sai taga ana tafiya gabanta anan
taja da baya ta rasa abunyi, wani uban ihu ne mazga daga nan
ta fadi sumamma. A guje sai ga wani dattijo ya shigo dakin
sanadiyar ihun dayaji tayi. Fitilar dake hannunsa ya ajiye
sannan sai ya dago ta yana kuka saboda tausayawa anan ya
fara fadin sunanta: ILHAM, ILHAM, ILHAM. Ko motsowa batayi
ba balantana ta bashi amsa, anan ya kara kankaneta a jikinsa
yana kuka, cikin kukan yana fadin wasu kalamai: wannan gida
na sharri da aka kawomu bama ganin kome sai tashin hankali
da masifa. Daga nan sai wannan dattijon yaji kamar wata
murya tana magana dashi:
Kada ka damu abba, da kai da yarka ilham lokaci ya kusa da
zaku fita daga wannan gidan”
Anan dattijon ya dubo domin ganin ko waye amma sai yaga
babu kowa, anan ya dubi diyarsa ilham yaga har yanzu bata
farka ba, bai ga komeba in banda wani tsuntsu da ya fito yabi
ta tagar dakin ya tafiyarsa.
===================
Haka meenat ta cigaba da tafiya kwanci tashi ba tare da ganin
wani tasku ba har ta fara tunanin cewa wai ko da gaske akwai
balain da aka ambata a wannan tafiya.
Wata rana da dare sai ta iso wani mai ban tsoro, wurin make
yake da duwatsu, anan ta fara kallon wurin tana mamakin
duwatsun dake wurin, wani iska ne mai laushi ya dan bugi
fuskarta, anan sai ta dago kai ta dubi sama, dubawar da zatayi
kenan sai tayi arba da wani gari da aka gina da duwatsu anan
ta fara mamakin wannan gari domin bata taba ganin irin ginin
ba. Cikin hanzari meeenat ta jawo dokinta ta nufi wannan gari,
abun mamaki shine kofar garin ma dutsi ce, domin da dutsi
aka yita. Daga nan meenat ta kutsa kai ciki tare da washe baki
tana kalle kalle, a cikin zuciyarta ta fara tunani, ” shi wannan ko
wane irin garine, basama tsoron harin makiya, wato kofarsu
bude.
Anan dai meenat ta cigaba da zaga garin lungu lungu amma ko
kuje bata gani ba. Garin yayi tsit, tana cikin wannan tafiya sai
taji kamar motsi, da alamar wani na ihu yana son a taimakeshi,
anan meenat tayi sauri ta labe domin ganin ko meke faruwa.
Anan taga wasu halittu wadanda bata taba gani ba, wasu
samudawan dodanni ne ta gani, ijiya daya garesu a goshinsu,
anan taga sun dauko wani mutum da suka daure, yana ihu
amma basu damu ba anan suka jefashi cikin kegi. Daga nan
sukayi tafiyarsu, wannan abu yaba meenat mamaki, kada dai
ace ta shigo garin nan na dodanni da ake bata labari masu
kalaci da mutum. Anan gaban meenat ya fadi rassssssd. A
guje ta sheko ta nufo hanyar fita garin, abun mamaki shine sai
gashi ta isketa a kulle. To waye ya kulleta? Ta fada a cikin
zuciyarta, gashi kuma a lokacin da zata shigo garin a bude ta
iskota. Anan hankalin meenat ya kara dugunzuma, kada dai
ace cikin dodanni nan akwai wanda yaga shigowarta, daga nan
sai tayi kokarin bude kofar da hannunta, anan meenat tasa
hannu taja iyakar karfinta amma kofar ko gyangyadi bata
yiba.haka meenat ta cigaba da kokartawa amma daga karshe
dole ta hakura domin kofar batada alamar budewa.
To anan meenat tazo wurin wannan mutumin na farko da aka
sa cikin keji, anan ta fara kallon kejin tana tunanin yadda zata
taimaka masa, tana cikin hakane sai taji kamar ana huro mata
iska. A hankalin ta juya domin ganin ko meke faruwa, anan tayi
arba da wani jibgegen dodo rike da kulki, take meenat ta zare
takobinta, wani ihu tayi sannan ta soka masa shi a kafa, cikin
mamaki sai taga dodon bai damu ba, domin a tsammaninsa
kusace aka soka masa, anan ya debe takobin ya yar, daga nan
sai ya cafko meenat da hannu guda. Ji kake kimissssssssss.
Anan ya maketa, daga nan bata kara sanin inda takeba.
TANK U VERY MUCH:
1.SAFREEN AUWAL
2.AMINA ABDULLAHI
3.ABUBAKAR ABUBAKAR AHMED
4 NAXEER HR
5.AISHA DUHU
6.JAZXY-INDIAN
7. MUFEEDAH MUHD
8. HUSNA BALA
9. ZUBAEDAH LAWAL
10.HUSSAINA UTHMAN LAMIDO
11.UMAR D UMAR
12. AND ALL THE LOVERS
///// I WILL ALWAYS REMEMBER U/////
=================================
Wani ihu takeji gashi tanason bude idanu amma kiwiyar bude
su takeji, a haka dai ta bude dakyar, daganan sai ta tashi
firgigit. Anan taga abunda ke faruwa gareta, a daure take
tamau da kaca tare da wasu. Anan ta fara mamaki domin
abunda kawai take iya tunowa shine a lokacin da soka ma
wani dodo takobi, haka dai meenat ta fara kalle kalle a
tsorace, ga mutane nan ba kyan gani cikin tausayawa, anan ne
ta gane cewa dodanni rike suke da buloli suna zanarsu, wai
ashe aiki suka saka su yi na fashin dutsi. Anan meenat ta dauki
guduma ta fara fashin dutsin itama.
Zuwa wani dan lokaci sai aka kaisu wani wuri domin su huta,
anan aka jerosu layi ana basu abinci cikin wani dan koko, anan
meenat ta kalli wannan koko domin tasan ita sai taci hamsin
da irinsa kafin ta koshi saboda kankantarsa. Anan meenat ta
amso nata abincin tana kallon ya za ayi ya isheta, loma guda
kawai tayi ta amayeshi saboda rashin sabo, anan ta fara kallon
wadanda suka saba suna cin abincinsu lafiya lau. A haka ta
ajiye ta hakura.
To bayan da dare yayi meenat na cikin bacci sai taji kamar ana
kiran sunanta a hankali, anan ta tashi, daga nan sai ta fara bin
sautin inda muryar ke fitowa, haka ta cigaba da tafiya har ta
kawo wani wuri daga nan sai ta tsaya.
Hucin iska ta jiya kamar yana fitowa a bayanta, juyawa tayi
anan taci karo da wata halitta ta daban, mutum ne mai fuka
fuki kuma yakan tashi kamar tsuntsu yadda yakeso, sai dai
halittarsa yar karama ce. Murmushi yama meenat daga nan sai
ya fara yi mata bayani:
Ni sunana zulyan, kada kiji mamakin halitta ta domin haka
mutanen garinmu suke maza da mata kowa nada fuka fuki, da
farko dai taimako daya nakeso kiyimin wanda inda kikayimin to
zan iyabaki duk abinda kikeso, anan meenat ta kashe kannu
tana saurare, nasan da cewa kin fito neman iccen gamza
wanda zai warkar da cutar yarima lamras. Zan iya taimaka miki
ki samu abunda kikeso a cikin sauki. “Gayamin me kakeso nayi
maka????meenat ta tambaya.
Anan ya bata amsa, akwai wasu mutane guda biyu da suka
taba taimakona bisa ga wata lalura dana shiga.sai dai a yanzu
suna cikin wani hadari, to nasan ke kadaice zaki iya fiddasu
daga wannan hadarin, saboda haka naxo wurinki ki sauke
wannan nauyin, anan meenat ta harare shi bata jira ya karasa
maganarsaba.
Nauyi fa kace. To bazan iya ba, inada abubuwan dana keso na
kammala. Anan ta juya ta tafiyarta, haka zulyan yata binta yana
bata hakuri domin ta sauraresa amma taki daga karshe haka
ya hakura ya tafiyarsa.
Tun da sanyin safiya meenat ta farka sanadiyar wani ihu da
taji, mikewarta keda wuya sai taga wadannan dodannin ne ke
kama wasu daga cikin mutane suna kaisu wani wuri, anan
meenat ta tambaya wata dake kusa da ita. Hala ina ake
kaisu?? Yankesu za ayi daganan sai a dafasu domin dodannin
suci, wannan abu ya mutukar bata mata rai, kenan wataran
itama haka za a yi mata. Tana cikin wannan tunani saiga
zulyan ya shigo, sai dai ita kadai ke ganinsa.
“idan kika ban hadin kai zan taimakeki yadda zaki fita wannan
gari kuma ki kubutar da duk wanda kikeso” injishi
Gayamin hanyar da zan kubuta yanzu?ta tambaya.
Anan ya bata amsa: da zaki baro garin yamla, akwai wata riga
da rumaisa ta baki, to wannan rigar itace zata kubutar dake
daga fita wannan gari, meenat taji mamaki ya za ace riga itace
zata kubutar da ita, daga nan sai ta umarceshi daya debe mata
kacocin da aka daureta dasu, nuni kawai yayi da yatsansa take
kacoci suka wargaje.
Anan meenat ta fara gudu tana kokarin isa inda take ganin ta
ajiye kayanta tun farkon shigarta wannan gari, tana ko zuwa ta
iskosu lafiya lau,to anan ta dauko rigar cikin sauri tasa, abun
mamaki shine ai taga ta bace ba a ganinta. Wato amfanin rigar
shine idan ta sata to bamai iya ganinta har sai lokacin data
cireta, to anan tayi shiga ta yaki daga nan ta fito ta fara yanke
kacocin da aka daure mutane dasu, kafin daga bisani wasu
daga ciki suka nufi kofar garin suna bugunta da karfin tsiya, to
anan ne dodanni suka gane cewa wannan bugu bana wasa
bane daga nan suka fara fitowa. Ita kuwa meenat tare da
wadanda ta kwance suka far ma dodannin da yaki, anan
meenat ta cigaba da kashesu domin basa ganinta sanadiyar
rigar da tasa.
Suna cikin wannan yakine sai sukaji karar wani abu buuuuum.
Ashe kofar garin ce ta tsage sanadiyar bugun da tasha. Anan
meenat tare da tawagarta suka yita bi suna wucewa har saida
kowannensu ya fita, daga nan suka samo wani makeken dutsi
suka kulle kofar don kada dodannin su fito, wannan rana dai ta
farin ciki ke, haka suka yita murna sunajin dadi.daga nan kuma
sai suka cigaba da tafiya domin subar wurin gaba daya.
Kwanci tashi har sukayi nisa da tafiya.
Wata rana meenat tana zaune ita kadai tana kallon sararin
samaniya, cikin rashin tsammani sai taga zulyan ya diro a
gabanta, ko kallonsa bata yiba balantana ta kula da zuwansa.
Haba yar uwa, wurinki fa nazo amma ji yadda kika juya baya
sai kace wadda taga makiyinta. To me kake so nayima????
Wannan abun dana gaya miki na farko, wato ki sani meenat
idan kika taimakeni, nima zan taimakeki, sannan kuma a cikin
wannan tafiya da kukeyi zaku hadu da wani balai wanda ya
nika na dodanni sau goma, amma idan kikayi alkawari zaki
taimakeni to zan gaya miki hanyar fita daga wannan balain.
Anan meenat ta tashi tsaye, bama bukatar taimakonka, kuma
abunda kakeso bazan taba yiba, anan meenat ta juya ta
tafiyarta, haka zulyan ya tashi ya kada fuka fukansa ya
tafiyarsa. Daga nan ne meenat tare da mutanen da suka samu
damar fitowa daga garin dodanni suka cigaba da tafiyarsu.
A cikin darene suka kawo wani wuri, to anan suka yadda zango
da nufin su kwana kafin gari ya waye, daga nan sai daya daga
cikinsu ya zagaya, a wannan lokaci meenat zaune take hankali
kwance cikin nishadi, basu wani jima ba sai sukaji kara, anan
suka tashi tsaye gaba daya, daga nan sai suka nufi inda sukaji
wannan kara, wannan mutumin daya tafi zagayawa shine ke
ihu, wasu kwari ne manya bakake sai shiga jikinsa suke, anan
meenat da tawagarta sukayi tsaye suna kallon wannan abun
mamaki, daga nan sai wannan mutumin ya fara kunburi kafin
kaceme ya fashe tussssssss, hanji daban, kafa daban kai
daban, anan su meenat sukaja da baya tsorace, can kuma sai
sukaji wani daga cikinsu shima kwarin sun far masa, cikin
kankanin lokaci shima yayi kamar yadda na farko yayi, to anan
suka fara gudu kowa na bidar mafita, anan meenat ta tuno da
maganar da zulyan ya gaya mata, wato da ace ta bashi hadin
kai da hakan bata faruba.
Ana cikin hakane sai meenat ta tuno rigar da rumaisa ta bata
wadda idan tasata bamai ganinta, cikin sauri ta daukota ta
sanya, amma abun mamaki shine sai taga kwarin sunyi
tururuwa suna shirin afka mata, wato su suna ganinta kenan to
anan meenat ta rasa abunda zatayi, can sai taji kamar ana
mata magana:
Wannan riga da kikasa batada amfani a wannan lokaci domin
su wadannan kwarin suna iya ganin kome.
Anan meenat ta juya domin taga ko waye ke mata magana. To
anan tayi arba da zulyan. Idan kikayi alkawari zaki taimakeni ni
kuma yanzu zan fitar dake daga kangin wadannan kwari.
Anan dai meenat ta gane cewa idan dai bata bashi hadin kai
ba to bako shakka zata rasa rayuwarta. Cikin sauri tace na
amince. Tana fadin haka sai zulyan ya jawota ya aza saman
bayansa, daga nan ya daga fuka fukansa ya tashi sama, to a
wannan lokaci meenat na ganin yadda kwarin suka mamaye
wurin, sai kashin jama a suke, gashi ba damar ta tsaya tayi
taimako domin itama ta kanta take.
Haka zulyan ya cigaba da gudu da ita har sai da yayi nisa, daga
nan sai ya sauko, a hankali ya ajiyeta.
Wai in tambayeka, hala me yasa wadannan kwari suke kashin
mutane sannan kuma daga ina suka fito??? Ta tambaya.
Anan zulyan yayi murmushi kafin ya bata amsa, wannan labari
ne mai tsawo, kuma bazan iya baki shiba a yanzu domin ba
lokaci amma dai zan fada miki hanyar da zaki taimakeni.
Wato ki sani meenat akwai wasu mutane da suka taba
taimakona wanda a yanzu suna cikin wani hadari saboda haka
yasa nakeso in taimakesu da taimakonki, wadannan mutane
mace da namiji ne, uba da diya, sunan uban ahnab, ita kuma
diyar sunanta ilham, wata rana yaki ya barke a garinmu
tsakanin kabilu biyu, wato da kabilunmu dana wasu amma duk
gari daya muke. Sanadiyar wannan yaki shine wata kanwata ce
wani shugaban ya gani to anan yaji yanaso, to dayazo nema
sai ahaka hanashi domin ba dan kabilar mu bane, to wannan
ya tayar da cece kuce, daga nan sai yayi niyar yin yaki domin
ya saceta da karfin tsiya, to a cikin wannan yaki sun kashe
jama armu da yawa, daga nan sai suka biyoni da niyyar
kasheni, to anan na fara gudu har na iso wani gari waishi
yamla. Anan na samu wani gida, shigata gidan keda wuya sai
naga basuji tsoro ba duk da kasacewata ba irin halittarsu
gareni ba, wannan gida dana shiga ba gidan kowa bane in
banda su ilham. To anan suka boyeni zuwa wani dan lokaci
kuma suka nuna min hanya na tafiyata.
Meenat taji mamaki ya ambaci yamla, domin shine garin data
fito wato garin su yarima lamras, to kada dai ace ilham da
babanta sune dangin rumaisa wadanda ta gaya mata cewa sun
bace shekaru da dama sanadiyar bin wannan hanya mai
hadari.
Can sai zulyan ya cigaba da bayaninsa: ilham ta kasance
yarinya mai son kida tun tana karama, ba yadda mahaifinta
yayi ya hanata amma taki, to wata rana da dare sai taji ana
kidi, saboda haka sai ta tashi domin taje tayi kallo, anan tafiya
mai nisa ba tare data sani ba, kuma a cikin wannan tafiya
bataga masu kidin ba iyaka dai tanajin kidi. Saboda haka sai
tayi niyyar dawowa gida, to tun daga ranar data dawo gida
bata kara lafiya ba domin sai ta fara ganin abubuwa naban
mamaki, kuma ana yawan bata tsoro har dai da dare. Akan
binciken da mahaifinta yayi sai ya gano cewa bazata warke ba
har sai an samo iccen sarki gamza an hada da ruwan sirri
wato ruwan da kike bida, da an hada an bata tasha zata warke.
Sanadiyar haka abbanta yayi shirin bin wannan hanya mai
hadari domin ganin cewa ya samo iccen sarki gamza tare da
ita, to akan hanyarsu ne suka hadu da wani balai, wata guguwa
ce ta taso mai daukar mutane, to anan guguwar ta jefasu
karkashin kasa a cikin tarkon ” NAMIL”
Namil ya kasance matsafi kuma gawurtaccen sadauki wanda
sanadiyar hakan yasa ya gina makeken gida a karkashin kasa,
dashi da mutanensa kawai ne ke zama gidan, namil ya
kasance yana amfani da mutane domin aiwatar da
siddabarunsa na tsafi, sanadiyar hakane ya tsafance hanyar
dake tare da gidansa yadda duk mutumin da yazo wucewa
guguwa kan daukeshi da karfin tsiya ta kawoshi gidan,ita
wanna guguwa wataran idan ta tashi takanyi tafiya har zuwa
duniyarku, kuma tayi barna ta kashe jama a. gidan kuma an
tsafance shi yadda duk wanda ya shigo bazai iya fitowa ba har
abada, gidan ya kasance yanada matsanancin duhu saboda a
karkashin kasa yake, kuma yanada kofofi kala kala har kwara
dari. Kowace kofa mutum yabi domin fita daga gidan zata
dawo dashi a cikin gidan.
Cikin wadanna kofofi dari guda kawai ce ta gaskiya wadda
idan mutum ya bita to bazata dawo dashi gidan ba, shi kenan
ya fita. To a cikin wannan gida nakeso ki shiga ki kubutar da
ilham da abbanta ahnab. Inji zulyan
To idan na shiga gidan ta wace kofa zan fita kenan?? meenat
ta tambaya.
Gaskiya nayi bincike da yawa amma har yanzu ban gano kofa
ta gaskiya wadda ake fita gidan ba!! Inji zulyan.
Anan meenat ta kalleshi cikin mamaki, yanzu zan kaiki hanyar
da zata kaiki a gidan. Inji zulyan. Daga nan sai ta hau bayansa
anan ya bude fuka fukansa ya tashi sama.
Basu dade suna tafiya ba sai ya tsaya anan ya ajiyeta tare da
yi mata nuni inda zata hadu da guguwar. Daga nan shi kuma
sai ya tashi ya tafiyarsa, to anan meenat ta tunkari wannan
hanya tana tafiya cikin rashin tsoro, tun kafin tayi nisa da
tafiyar sai taga kasa na tsagewa tana ruzgawa, to anan taga
wata guguwa ta zo aguje ta dagata.daga nan sai ta nutse da
ita cikin kasa.
Sai da akayi tafiya mai nisa a cikin kasa da meenat kafin a
jehota a wani wuri, anan ta fara mulmule mulmule tana
gangarowa sai can ta tsaya wuri daya, daga nan sai ta tashi. A
mamakinta a cikin wani makeken gida take mai ban tsoro,
anan ta fara tafiya tana dube dube, a haka ta yita karo da
kassan mutane da kuma gawawwaki barkatai wasu duk sun
bushe. Haka tayita cikin wani dogon kororo sai da ta dade tana
tafiya kafin ta kai ga karshensa. To anan taga wata kofa, kai
tsaye ta bude kofar ta kutsa kai ciki, shigarta keda wuya sai
taci karo da wasu katta su bakwai a saman kujeru, wani dogon
teburine a tsakiyar dakin sai ga kwannan abinci a sama, amma
a mamakinta a cikin kwannan ba kome cikin in banda naman
mutane, da naman wadannan kattan suke kalaci, to anan suka
kurawa meenat idanu, ko dubansu bata tsaya yiba kai tsaye ta
wuce daki na gaba
Anan meenat ta tuno da wata babbar mantuwa da tayi, ta
manta ta tambayi zulyan ya nuna mata hoton ilham tare da
abbanta yadda idan ta gansu zata ganesu. To tana cikin
wannan tafiya kawai sai taji ana wata magana a wani daki, to
anan ta nufi dakin domin ganin ko meke faruwa. Shigarta keda
wuya sai ta isko wani dattijo tare da wata yarinya sai hira suke
abinsu. To anan aka fara kallon kallo.
Ko zamu iya sanin koke waye? Dattijon ya tambaya.
E, ina bidar wata yarinya ilham tare da abbanta ahnab.
Anan sai meenat taga sun tashi tsaye gaba daya. Lafiya
kuwa?? Anan suka tambaya.
E lafiya kalau.meenat ta basu amsa.
To nine ahnab, wannan kuwa yata ce ilham.inji dattijon.
Anan meenat taji dadin wannan kalami, daga nan sai ta zauna
ta fada musu abunda ke tafe da ita. Wannan abu yasa dattijon
ya fara yi mata kallon marar hankali. Haba yarinya ai wannan
gida da kike gani sihirtaccene, kuma batun fitarsa bai ko
tasoba saboda haka kima manta da wannan.
Murmushi meenat tayi daga nan sai ta fara tambayrsa. Wai duk
tsawon shekarun nan da kukayi ya akayi kuka rayu, tun da naji
ance duk wanda ya shigo wannan gida sunansa gawa!!
Anan dattijon ya fara bata amsa, ai duk wanda ya shigo gidan
bai kai tsaye suke kashe shiba, idan mutum ya shigo zasuyi
maraba dashi harda daki zasu bashi su dinga kulawa dashi, sai
dai daga baya sai su zo da wasu kaidodi barkatai wadanda
idan mutum ya saba guda zusu kasheshi, da farko dai ba a fita
da dare, to idan mutum ya fita sunansa gawa, To idan sukaga
mutum kan iya bin wadannan ka i dodin daga nan sai su
kasheshi ba sai yayi laifi ba, amma mu abunda ya kubutar
damu shine shugaban gidan wato namil ya kamu da son
ilham, saboda haka mu ba a yi mana komai, mukanyi yadda
mukeso, amma baya gamu duk wanda ya shigo dolene ya
mutu.
Suna cikin wannan hira sai sukaji an bude kofar, wasu mutane
ne su hudu sanye da bakaken kaya a jikinsu, daga nan sai daya
daga cikinsu ya fara magana:
Sannu da zuwa meenat, muna maki barka da isowa kuma
muna fatan zaki kiyaye da sharuddanmu, kuma muna maki
albishir da cewa wadannan mutanen biyu da kikazo dominsu
to bazaki taba samun damar kubutar dasu ba, anan yayi dariya,
daga nan sai ya fita ana suka rufa masa baya.
Wannan shine namil!inji ahnab.
Anan meenat ta girgiza kai, lalle wannan ba karamin hatsabibi
bane, wato yamasan abunda ya kawoni. Ta fada a cikin zuciya.
Haka dai meenat tayi kwanaki a cikin wannan gida har ta saba
da ilham tare da abbanta ahnab. To wata rana da dare sai kisa
ta kama meenat gashi kuma ruwansu sun kare, anan ta bude
daki da niyar fita. Cikin sauri ilham ta jawo hannunta. Kiyi
hakuri ba a fita da dare!! Injita. Murmushi meenat tayi, ai ni ba
ruwana da ka i dodinsu, dole ne na fita na samu ruwa domin
bazan zauna kisa ta kasheni ba. Anan ta bude ta fita.
Haka meenat ta fara tafiya tana kokarin zuwa wata rijiya data
sani domin dibar ruwa, tana cikin tafiya kenan sai taji jikinta
yayi wani tsam duk ba dadi, anan dai ta daure ta cigaba da
tafiya, can bayan tayi nisa sai taji tahowar wani iska mai karfi a
wurinta, iskan na zuwa dab da ita sai ya tsaya can kuma sai ya
tafiyarsa, wannan abu yaba meenat mamaki amma bata damu
ba kawai sai ta cigaba da tafiya.
Tana isa wurin rijiyar kawai sai taga ilham a tsaye idanunta
duk sun juye, anan gaban meenat ya fadi domin tasan ta
barota a daki, ilham din data gani sanye take da wasu kaya
dogaye kuma jini ke zuba a jikinta, anan meenat ta kara
dubawa ta gani shin wai ilham din ce kawai sai taga bataga
kowa ba, to anan meenat ta tsorata, anan ta fasa dibar ruwan
saboda tsoro, juyawa tayi domin komowa dakinsu kawai sai ta
kara ganinta. Fasssssssssssss gabanta ya fadi.
Daga nan sai aka fara kallon kallo, kawai sai taga wannan
yarinyar mai kamada ilham ta zaro wata yuka tana gurnani, to
anan meenat ta fara ja da baya domin bata fito da komi ba.
Wani tsalle wannan yarinyar tayi da nufin kaima meenat sara,
anan meenat ta wani kaucewa. Tana juyowa kuma sai taga
bataga yarinyar ba. Daga nan dai sai meenat tayi sauri ta nufi
hanyar dakinsu.
Tana shiga sai ta fara magana dasu ilham, ku shirya yanzu
zamu bar wannan gida! Anan gaban dattijo ahnab ya fadi.
Yanzu fa kikace?
E yanzu domin damun dau lokaci to sunannu gawa saboda
haka ku biyoni baya.inji meenat.
Anan ta shige gaba tana gudu suna binta. Suna cikin wannan
gudu a hankali sai sukaga wata mace a gabansu, itama jini ke
zuba a jikinta. Anan su meenat sukayi tsaye cirko cirko, matar
sai wani gurnani takeyi, can sai sukaga matar ta rikida ta koma
namil, anan ya fara yi musu dariya ku kuna ganin zaku iya
tserewa??
Da karfi suka juya sakamakon wani gurnani da sukaji, wasu
zaratan damisoshi ne suka gewayesu, sai wani miyau ne ke
dalala a bakinsu. Daga nan sai aka fara kallon kallo. Can kuma
sai sukaga damisoshin sun bace. Anan namil yayi dariya
sannan ya kalli meenat. Wannan yaki ni dake ya kamata
muyishi idan yaso sai kuyi abunda kukeso.
Daga nan sai ya zaro wasu sihirtattun takubba guda biyu ya
rike, wani tsalle yayi daga nan sai ya diro ma meenat, anan
itama ta tareshi take suka kaceme, wannan namiji yaki daya
barke tsakanin meenat ta namil ba karamin tayar wa da ahnab
hankali yayi ba, domin namil a kasance jarumin gaske.
Meenat ta wanzu tana kare kanta daga mugayen harin da
namil ke kawo mata duk da ya kasance yanada tsananin sauri
da iya yaki, hakan yasa meenat ta raina kanta domin tasan ta
gamu da gamonta. Sai da suka dau lokaci suna wannan artabu
amma ba alamun nasara ga meenat domin ta fara gajiya, shi
kuma namil kamar a lokacin ake baki abinci yanaci. Ya
kasance yana juya wadannan takubba yadda yaso kamar
walkiya saboda sauri, cikin hakane ya mamayi meenat ya kai
mata naushi a fuska, anan ta danyi tangal tangal kamar zata
fadi, can kuma sai ta tsaya dai dai.
To daga nan ne meenat ta farfado anan ta fara kai masa sara
da suka cikin gwaninta da iyawa ba sassauci, hakan yaba
namil mamaki kamar ba itace ya gajiyar ba, daga nan dai yaki
ya cigaba, namil yayi kokarin gajarce wannan yaki domin a
zatonsa zai mata kwaf daya, daga nan sai ya canza shawara,
anan ya fara aiki da siddabarunsa na tsafi. Suna cikin wannan
fada kawai sai meenat taga ya bace takobinsa kawai ake gani.
A haka yayi ta kawo mata mugayen hare hare domin samun
nasara amma ya kasa. Daga nan sai ya batar da takobin nasa
ya zama hadda shi ba a gani. To a wannan lokaci meenat ta
rude domin batasan yadda zata kare harinsaba. Anan ta fara
dube dube, can sai taji takunsa anan ta nufi wurin da nufin
yakar shi, ai ko tana zuwa wani naushi ta jiya a fuska
gibbbbbbbb. Anan ta juyo da baya ta tsaya tana kalle kalle, can
sai taji hucin wani iska a bayanta, anan ta juya domin a
tsammaninta shine tana juyawa sai taji wawan sara a kafada.
Anan jini yayi tsargi, meenat sai da tayi ihu saboda zogin da
taji, anan ta fadi tana, namil na ganin haka sai ya fito da
siffarsa yana dariya domin shi a tsammaninsa ya samu nasara.
Yana cikin wannan dariya sai meenat taga ya fadi, ashe ilham
ce ta soka mishi wata karamar yuka, anan meenat ta jawo
takobinta ta katse masa kai, anan ya fadi matacce.
Daga nan sai sukaga gidan ya fara girgiza kamar zai fadi, can
kuma sai sukaga duk kofofin gidan sunyi wani ja.
Guda kawaice haske ke fitowa a ciki, daga nan sai meenat tayi
musu umarni dasubi wannan kofar mai haske, haka suka fara
gudu domin fita daga gidan, anan kuma gidan ya fara rushewa
yana faduwa, haka dai suka yita gudu har suka iso wannan
kofar, a cikin wannan kofa suka yita gudu har suka samu
kansu waje, daga nan sai sukaji gidan ya rushe gaba daya.
Fitarsu keda wuya sai meenat tayi arba da dokinta, anan farin
ciki ya kamata, su uku suka hau dokin daga nan suka nausa a
guje. Sai da sukayi tafiya mai nisa sannan suka tsaya domin
hutawa.
To a wannan lokaci meenat na gyara kayanta dake saman
doki, kawai sai rigar da rumaisa ta bata ta fado, anan ahnab ya
tambaya. Wannan riga fa waya baki ita?? Anan meenat ta
bayyana masa asalin wadda ta bata ita. Daga nan sai ahnab ya
rike baki hawaye na zuba a idanunsa. Ashe rumaisa na raye! Ya
fada. Anan ya bayyana ma meenat cewa ai rumaisa diyarsa ce.
Ita kuma meenat sai ta gane cewa lalle sune wadanda rumaisa
ta taba bata labarunsu cewa sun bace ba a san inda suke ba.
Suna cikin hakane sai ga zulyan a guje, cikin farin ciki ya sauko
da fuka fukansa, anan yama meenat godiya marar iyaka daga
nan kuma sai ya umarcesu dasu hau bayansa domin ya kaisu
masarautar gamza inda zausu debo iccen. Cikin kankanin
lokaci suka hau bayansa. Anan yayita zabga gudu dasu har sai
da ya wuce wanna wuri mai hadari. Daga nan sai ya nufi
hanyar birnin askandariya wato birnin sarki gamza
Haka yayita gudu dasu amma basu isa masarautar ba sai da
dare, to anan ya sauko dasu gab da kofar shiga birnin. Ku sani
cewa sarki gamza ba karamin hatsabibi bane saboda haka sai
kunyi hankali. Ya fada. Anan ya daga fuka fukansa ya tafiyarsa.
Daga nan meenat ta shige gaba suna binta, anan suka yita taka
matattakalar kofar har suka diro a cikin garin. Daga nan sai
suka fara tafiyar sanda sannan suka nufi wani mashahurin kogo
inda suke tsammanin nan iccen yake, bayan sun shiga cikin
kogon sai da sukayi tafiya mai nisa sannan suka isko katuwar
itaciyar, cikin farin ciki suka debi ganyayyakin itaciyar sannan
suka boyesu a jikinsu. Daga nan suka juya da nufin fita kogon.
Juyawarsu keda wuya sai sukayi arba da dakaru sama da dubu
a zagaye dasu, wasu kacoci ne aka jeho musu anan aka
dauresu tamau. Can sai wani narkeken kato yazo gabansu,
anan ya fizge sarkar dake wuyan meenat. Wata dariya yayi
sannan ya fara magana: sannuku da zuwa masarautata ni sarki
gamza, dama na dade ina jiranku, gashi kuma kun zomin da
abunda nakeso, shekarata ashirin ina bidar wannan sarkar sai
yanzu na samu.
Meenat najin haka gabanta ya fadi, to me zaiyi da sarkar??? Ta
tambayi kanta. Anan ta tuno da maganar kaka zuwaira na
cewa udan bada wannan sarkar ba to bazata iya komawa
duniyarsu ba, wato sai dai ta tabbata a wannan duniyar har
abada.
ME ZAI FARU???
SHIN KO MEENAT ZATA SAMO RUWAN SIRRI?
YA LABARIN GIMBIYA KULSUM?
HALITTAR MEENAT TA AINAHI ZATA DAWO KUWA??
YA LABARIN YARIMA LAMRAS??
MEYE SARKI GAMZA ZAI YI DA WANNAN SARKAR?
MU HADU A KASHI NA UKU DOMIN JIN CIGABAN LABARIN
TO BE CONTINUE……….
abdul king article
FOR MORE NOVELS:
SEARCH AND JOINT OUR FACEBOOK GROUP:
KINGARTICLE.NOVL
OR
KINGARTICLE NOVELS OF ABDUL$BAFFERH
RUWAN SIRRI
“cigaban gidan fatalwa”
Part ( 3 ) kashi na uku
Dedicated to:
Firdausi queen article
RECALL BACK:
A cikin littafin ruwan sirri kashi na biyu, mun bayyana yadda
meenat tayi gwargwarmaya domin samo iccen sarki gamza,
wanda a cikin wannan tafiya ne ta hadu da wata halitta mai
ban mamaki, gashi da jikin mutane amma yanada fuka fukai,
wai shi zulyan, inda yayi mata bayani cewa idan har ta
taimakeshi to shima zai taimaketa, tayi kokarin taimakonsa
wanda hakan yasa ta gamu da yan uwan rumaisa wadanda
suka bace ( ilham da ahnab) a yanzu dai sarki gamza ya
kamata tare da su ilham sannan kuma ya kwace mata sarka
sakamakon wani abu da yake son yi da ita.
THE BEGINNING:
Wasu jaruman sadaukai ne a saman dawakai sai gwabza wani
irin nagartaccen gudu sukeyi sai kace masu tashi sama. Wani
saurayi ne kyakkyawa a tsakiyarsu saman nasa dokin shima
sai da ganinsa anga yaron manya tun a shigar da yayi.
Haka suka cigaba da gwabza wannan gudu har suka kawo
askandariya. Wato birnin da sarki gamza ke mulki. Anan aka
bude musu kofar garin daga nan suka shigo ciki. Da alamu
wadannan samari sunyi farauta domin wata katanyar dabba ce
suka sauko da ita daga nan sai suka shiga gidan sarautar. Shi
kuwa saurayin duk inda ya wuce sai kaga dakaru na gaida shi
cikin girmamawa.
Sunanshi yarima munib da ga sarki gamza, anan yarima munib
kama hanya da nufin shiga masarautar, to a wannan karron an
fito da fursunoni ma ana wadanda aka tsare a gidan yari
domin suyi wasu ayyuka na yau da kullum, yarima munib ko
kulasu bai yiba balantana ya kallesu. Haka ya cigaba da tafiya
domin isa wurin daya nufa. A saman hanyarsa ne kafin ya kai
ga shiga masarautar cikin rashin sani yayi karo da wata
budurwa, anan suka ja da baya, daga nan ne yarima yayi mata
kallon tsaf ko kyaftawa baya yi. Can sai sukaba juna hakuri
sannan kowa ya kama hanyar gabansa. To anan ne yarima ya
fara tunani domin tun tashinsa bai taba ganin yarinyar data
kwanta masa ba irin wannan. Sai dai abunda ke damuwarsa
shine ita yar fursuna ce, kuma dolene laifi tayi kafin a kawota,
to zata yiwu yarima ya auri yar fursuna mai laifi?? Anya kuwa
mahaifinsa zai yarda da wannan aure?? Kuma koda mahaifinsa
ya yarda to ita zata soshi kuwa?? Sannan daga ina take kuma
wane laifi tayi aka kawota gidan yari?? Haka wadannan
tambayoyi suka cigaba da damun yarima ba sassauci. Daga
nan ya hankure ya shiga gidan masarautar cikin rudani.
Written by
Abdul king article
To bayan yarima ya shiga gidan masarautar, take ya wuce
bangaren mahaifiyarsa. Yana shiga ko ya tarar da ita zaune
kuyangi sun gewayeta sai faman nishadi ake. Suna ganinsa sai
suka tashi cikin girmamawa suka fita. anan yarima yazo gab da
mahaifiyarsa ya zauna. Cikin murmushi ta fara magana: sannu
da zuwa dana, nasan kana cikin farin yadda nima haka cike
nake dashi, nasan da cewa kana sane da bikin aurenka kai da
gimbiya marsiyya nan bada jimawa ba domin yanzu haka komi
gyare yake.
Tana fadin haka gaban yarima ya fadi rasssssssssssss,
kyakkyawar fuskar yarinyar da yaci karo da ita ta fado masa a
rai, anan ya fara tunani wai wacece wannan gimbiya
marsiyya?? Shifa ko ganinta bai taba yiba, sannan shi koma ya
ganta bazai iya soyayya da ita ba a yanzu.
Tassssssssss. Saukar mari. Ya ina magana dakai kayi banza
dani sai kace ina magana da dutsi, ka tsaya kana tunane
tunanen banza. Yanzu gayamin me kake tunani??
Anan yarima ya fara magana, umma kiyi hakuri ayyuka ne suka
yimin yawa shi yasa wataran zakiga bana majin maganar
mutane sosai.
Wadanne ayyuka kuma? Kai gayamin gaskiya. Injita.
Umma ki yarda dani mana, saninki ne cewa duk abunda yake
farin ciki a gareki bako shakka zan rugumeshi a matsayin farin
ciki a wurina, kinga kuwa ba yadda za ayi in yarda in bata miki
rai.
Anan tayi murmushin farin ciki tare da rungumeshi, da kyau
dana, haka nekeso naji, saboda haka yanzu tashi ka tafi sai na
bideka kuma.
Anan yarima ya tashi cikin damuwa gashi bayason gimbiya
marsiyya amma bai son ya bayyana don kada ya bata ma
mahaifiyarsa rai, haka ya cigaba da tafiya baya ko gani sosai
saboda bakin ciki. A cikin wannan dare dai yarima ya kwana
yana tunanin wannan yarinyar daya gani gashi bai sani ba ko
zasu kara haduwa.
Cikin wani irin gidan yarine suke mai duhu da ban tsoro, haka
su meenat ke zama a wannan wuri cikin kadaici da rashin inci,
a wannan lokaci duk bacci sukeyi, wata yar karamar hayaniya
data fara shigowa ta taga yasa ilham ta tashi, to anan ta gane
cewa safiya ta waye, anan ta kafa idanunta ga tagar domin
ganin ko meke wakana, murmushi tayi ganin wani kyakkyawan
saurayi tare da wasu suna wata magana, anan ta fara tunani ko
ina tasan wannan saurayin, ba a dauki lokaci mai tsawo ba sai
ta tuno. Ashe shine wanda suka taba buge juna cikin rashin
sani.
Basu dau lokaci suna maganar ba sai taga sun kaceme da
wani azababben yaki, wannan yaki fa ya tayar wa da ilham
hankali domin tana gudun ta rasa wannan kyakkyawan saurayin
da take kallo, amma daga baya sai ta gano cewa yakin gwaji
ne sukeyi bana gaskiya ba, daga nan sai hankakinta ya kwanta
to anan ta natsu tana kallonsa ko kyaftawa batayi.
Gibbbbbbbbb. Wani naushine aka kai masa. Anan yasa hannu
ya tare naushin tare da mayar da martani, haka dai ilham ta
cigaba da kallon wannan yaki nasu cikin natsuwa da
annashuwa har zuwa wani lokaci mai tsawo da meenat da
abbanta ahnab suka farka.
Hubair da yazid abokan juna ne. Kuma sun shigo birnin
askandariya domin kammala wani buri da suka dade suna
muradin ganin sun samu. Tabi sukayi da yiwa juna murmushi
domin ganin irin yadda aka kawata masarautar birnin. Da
alamun cewa suna tare da nasara ga wannan zuwa da sukayi.
To a cikin darene bayan kafa ta dauke duk gari anyi tsit, daga
nan sai su yazid suka durfafo wannan masarauta ta
askandariya, wani karfe ne mai hade da kaca suka dauko, anan
suka jefa karfen can kololuwar gidan saman masarautar, daga
nan suka fara taka kacar suna kokarin kaiwa a saman
masarautar. Basu dade suna wannan aiki ba suka diro saman
masarautar, wata taga ce suka fashe da karfin tsiya daga nan
suka fada ciki. Daga nan suka fara bincike shiga wannan daki
fada wancan da alamun akwai abunda suke bida, haka suka
yita wannan bincike har suka kawo ga dakin sarki gamza, to a
wannan lokaci dakarun sun farayin bacci domin basa
banbance wanda ya shigo da wanda ya fita.
Saboda haka kai tsaye su yazid suka kutsa kai cikin dakin.
Anan suka fara bincike, can sai suka gano wani karamin
akwati, to anan suka dauko shi, budewarsu keda wuya sukayi
arba da wata sarka sai kyalli takeyi. Anan sukayi dariyar farin
ciki, daga nan suka dauka suko nufo waje.
LABARIN LABEENA:
A wani lokaci can da kafin sarki gamza ya zama sarki. A
wannan lokacin babansa ne ke mulkin birnin askandariya wato
sarki nayib. gamza ya kasance cikin zababbun sadaukan garin
wadanda ake ji dasu. To wata rana sai tafiya ta kama
mahaifinsa zuwa birnin mihad domin kai ziyara ga abokinsa
sarki najmad dake mulkin birnin.
To ga kaidar sarauta a wannan lokaci dolene dan sarki ya auri
diyar sarki, saboda haka wannan ziyara tanada nasaba da
alakar aure tsakanin diyan wadannan sarakuna biyu. Wato
yarima gamza da gimbiya halirat.
Tun da aka fara wannan tafiya hankalin yarima a tashe yake
domin ko kadan babu wadda ya tsana a duniya irin gimbiya
halirat, kuma ace wai ita zai aura!!
Tun kafin ayi wannan magana ta aurensa da gimbiya halirat, ya
kasance yana soyayyar boye da wata yarinya labeena, sunyi
mutukar shakuwa tun suna yara. Duk da kasancewarta diyar
talakawa amma yarima bai kula da hakan ba ko kadan.
Wannan dalili yasa labeenat ke mutukar ji dashi. Ba yadda sarki
nayib bai yi ba domin warware wannan soyayya amma abu ya
faskara, saboda haka ya kafa masa doka cewa a duk lokacin
daya gano yana soyayya da ita to kashinsa ya bushe.
Maimakon wannan magana ta tayar da hankalin yarima sai ya
kara jajircewa na cewa ba wata inba labeenat ba. Cikin rashin
tsammani sai ga wannan magana ta bijiro ta aurensa da
gimbiya halirat.
To bayan sun iso masarautar mihad. Anan sarki najmad ya
taresu tarba ta karramawa. Wani dogon teburine aka girke a
wani daki na musamman, sai ga abinci kala kala a samansa.
Wasu kujeru na alfarma ne suka zagaye teburin. Daga nan sai
sarki nayib tare da mutanensa suka zauna domin kyakashewa.
To a wannan lokaci shima sarki najmad na zaune tare da
mukarabansa. Haka kuma gimbiya halirat na zaune daf da
yarima gamza. Sai dai ko abincin baya iyaci saboda bakin cikin
daya yi masa yawa. Ita kuwa gimbiya a farin ciki take domin
sai satar kallonsa take tana murnushi.
To bayan an gama cin abinci an watse. Sai sarakuna biyu suka
kadaita domin ganawa ta musamman.
A gaskiya naji dadin zuwanka birnina domin wannan shi zai
kara tabbatar min da amincewarka game da auren ya yanmu.
Inji sarki najmad.
Wani murmushi sarki nayib yayi kafin yayi magana: ai wannan
zuwa nawa dai dai yake da daura auren domin bazan bar
wannan gari ba har sai magana ta kafu.
Anan sarki najmad yayi wata bahaguwar dariya. Haba ya kana
fadin haka sai kace baka yarda dani ba. Ai duk abunda kace
dai dai ne. Domin diyanka ne, kuma kanada iko akansu.
Wannan gaskiya ne. Inji sarki nayib. Amma kai kafi cancanta
kayi magana domin kafini kusanci dasu.
Haka dai suka cigaba da wannan tattaunawa wanda daka
karshe sukasa ranar da za a daura auren. Daga nan sai sarki
nayib ya dawo birninsa domin jiran wannan rana.
A kwana a tashi sai ga wannan rana tazo. Kar kaso kaga yadda
bakin ciki ya dabaibaye zuciyar yarima gamza. Haka akayi
shagali aka watse daga nan akabar yarima da gimbiyarsa. Tun
a wannan rana yarima ya fara halinsa na tsanar gimbiya halirat.
A hankaki a hankali tun bata ganeba har ta fara ganewa. Daga
nan abu yayi tsamari da farko gimbiya tayi tsammanin zata iya
jure walakancin da yake yi mata amma daga baya sai ta gane
hakan bazai yiba. Domin itama fa diyar sarki ce. Duk da cewa
ba wani namiji daya kwanta mata irinsa.
To anan ne gimbiya halirat ta tsananta bincike domin gano
musabbabin wannan walakanci da yake yi mata. To a cikin
binciken ne ta gano cewa akwai wadda yakeso wai ita
labeenat. Wannan ya mutukar tayar mata da hankali domin ko
kadan bata son kishiya. To anan ne gimbiya tayi alwashin cewa
sai taga bayan labeenat.
Wata rana labeenat na zaune ita kadai a cikin wani lambu tana
nishadi kamar yadda ta saba. Cikin rashin tsammani sai taga
wasu mazaje su biyar a saman dawakai.fuskokinsu a rufe suke
yadda idanuwansu kawai ake gani. Anan suka rufar mata da
sara har sai da suka tabbatar da cewa tabar motsi. Daga nan
suka dauki gawar suka jefa a cikin ruwa. Daga nan suka juya
domin isar da sako ga wadda ta aikosu.
To a lokacin da suka isar da sakon ga gimbiya halirat sai akayi
rashin sa a yarima gamza yaji duk abunda suka fadi. To anan
hankalinsa ya tashi domin bai san inda zai sa rayuwarsa ba. To
anan yayi yunkurin kashe gimbiya amma sai mahaifinsa ya
hanashi. Haka suna kallo ta koma birninsu.
To bayan da aka jefa labeena a cikin ruwa ashe bata mutu ba,
daga nan sai ruwa suka yita janta har suka kawota wani dan
karamin gari a kusa ga teku, to anan ne ta hadu da wani mai
sana ar su wanda ya tsinto ta a cikin ragarsa ta kamun kifi.
Anan yayi mata goma na arziki sannan ya sanyota a jirgin ruwa
domin ta dawo birnin askandariya.
A wannan tafiya sun gamu da cikas domin manyan kifayen
dake tekun suka fara damunsu suna bugun jirgin da karfin
tsiya, a haka wannan al amari ya cigaba da wakana har zuwa
lokacin da jirgin ya fara tangal tangal yana shirin kifewa a cikin
ruwan. Daga nan ne kifayen suka wangame bakunansu suna
jiran jirgin ya kife su fara cin mutane, to anan hankalin labeenat
ya tashi domin bata taba ganin irin wannan abu ba.
Anan ta hango wani dan karamin kwale kwale (canoe) mai
daukar mutum daya. Cikin sauri ta cafko shi ta diro daga
saman wannan katon jirgin da suke ciki(ship) anan ta fara tukin
kwale kwalen iyakar karfinta. Shi kuma wannan katon jirgin
take ya nutse. Anan kifaye suka samu ganima.
Haka labeenat ta cigaba da tuka wannan jirgi har sai da ta kai
bakin gaba. To anan ne ta hanga iyakar ganinta amma ba
abunda take hangowa sai wani katon birni, daga nan sai ta
nufin birnin. Shigarta keda wuya sai ta tambayi wani ya fada
mata sunan garin. Anan gabanta ya fadi jin an ambaci mihad.
Domin tasan shine birnin su gimbiya halirat.
Juyawa tayi da nufin fita garin, juyawar da tayi kenan sai
sukayi ido hudu da gimbiya halirat tana saman doki dakaru na
take mata baya. Anan labeenat tayi tsaye ko motsi ta kasayi.
Haka ta cigaba da kallonsu har suka iso wurinta. Daga nan sai
halirat ta fara yi mata magana: ke bakuwa ce a garin nan naji
kina tambayar wani game da garin! Idan kinason aiki ki biyoni
zan baki.
Anan hankalin labeenat ya kwanta domin tasan bata ganeta
ba. Amma abunda ke bata mamaki shine ko ya akayi ta baro
birnin askandariya ta dawo garin su. Babban abunda yasa
labeenat ke wannan tunani shine har yanzu batasan ko su
waye sukayi kokarin kasheta ba, kuma batasan wanda ya
aikosu balantana sanin makasudin yi mata hakanan.
Haka dai labeenat ta gurfana cikin girmamawa: na gode ranki
shi dade. Ina bukata. Daga nan sai ta bita. Haka suka yita
tafiya har suka iso masarautar. To anan halirat tayi mata iso a
ciki.
Inaso ki gayamin sunanki da kuma ina kika fito??
Anan labeenat tayi shiru domin batasan irin amsar da zata bata
ba,can sai dabara ta fado mata.
Sunana ihsan, kuma na fito ne a birnin Liyana.
Da kyau! Inji gimbiya halirat. To menene ya fito dake daga
gida??
Anan gaban labeenat ya fadi, to kada dai ace gimbiya ta
ganota.
E na fito daga gidane domin samun abun dogaro!
Daga nan sai gimbiya tayi murmushi, zan so in ajeki a cikin
masu yimin hidima, domin ke kyakkyawa ce kuma ina bukatar
irinku. Amma me kika gani??
Ba matsala ranki shi dade duk yadda kikayi dai dai ne. Inji
labeenat.
Daga nan sai gimbiya halirat ta nisa kafin daga bisani ta fara
magana: kina yimin kamada wata makiyi yata, sai dai yanzu
bata duniya domin na dade dasa akasheta. Daga nan sai
gimbiya halirat ta bata labarin sharrin da tasa ayi mata cikin
rashin sanin cewa ita din dai ce bata mutu ba. Daga nan ne
labeenat ta gano cewa kenan wadanna da suka tareta da nufin
kasheta ita ta turosu. Saboda haka sai taci alwashin cewa sai
ta rama abunda tayi mata.
Haka gimbiya halirat ta mayar da labeenat a cikin masu yi
mata hidima ta yau da kullum cikin rashin sanin cewa itace
babbar makiyi yarta. To wata rana da dare sai labeenat tayi
shiri domin kashe gimbiya halirat domin tasan kul a jima kul a
dade a duk lokacin da gimbiya halirat ta gano ko ita wacece to
bako shakka kasheta zatayi, saboda haka bari ta fara kasheta
kafin hakan ya faru.
Haka labeenat ta riko wata karamar yuka tana tafiyar sanda har
ta shigo dakin gimbiya. Anan ta daga yukar da nufin daka mata
a zuciya. Firgigit sai gimbiya halirat ta tashi, to anan aka fara
kallon kallo.
Ke wacece? Gimbiya ta tambaya.
Nice wannan labeenar da kika sa a kashe, sai dai baku samu
nasara ba domin na tsira daga sharrin ku.
Daga nan sai labeenat ta fara kawo mata mugayen hare hare
da nufin kasheta . Anan gimbiya halirat ta fara kaucewa cikin
salo irin nata na iya yaki. Sai da suka dau lokaci amma ba
alamun nasara ga kowa. To a wannan lokacin dakarun garin
sun fara jin hayaniya kamar akwai wani abu dake gudana a
dakin gimbiya. Saboda haka suka sheko a guje domin gani. To
a cikin wadannan dakaru har da sarki najmad wato baban
halirat wanda shine kan gaba yana jagorantarsu.
Gimbiya halirat ta gano cewa idan ta cigaba da wannan fada to
zata iya rasa rayuwarta. Saboda haka ta nufi kofar dakinta a
guje da nufin tsira, to a wannan lokaci sarki najmad ya bude
kofar da karfi. Ita kuwa labeenat sai ta jeho wannan karamar
yukar dake hannunta domin kashe gimbiya. Daga nan sai sarki
najmad yayi sauri ya kade gimbiya ta fadi can gefe. To anan
yukar ta shiga jikinsa. Labeenat na ganin wannan tsautsayi sai
tayi sauri tabi ta tagar dakin. Anan tayi tsalle ta diro domin fita
garin gabaki daya. To anan dakarun suka rabu gida biyu. Wasu
suka bita domin kamata. Wasu kuma suka dauki sarki najmad
domin duba lafiyarsa.
Daga karshe dai labeenat ta samu nasarar fita garin. Shi kuwa
sarki najmad ya samu mummunan rauni wanda daga karshe ya
rasa rayuwarsa. Wannan al amari yayi mutukar batawa gimbiya
rai saboda haka tayi niyar yakar birnin askandariya. To a
wannan yaki ne ta samu nasarar kashe mahaifin labeenat
wanda shine sarkin yakin birnin askandariya. Ba karamin farin
ciki tayi ba duk da cewa bata samu nasarar kashe makiyi yarta
ba.
A haka dai ta cigaba da kawowa birnin askandariya hare hare a
lokuta daban daban domin samun nasara. Amma abun takaici
shine a duk lokacin da suka kawo harin ba nasara, haka suke
komawa da kunyarsu. To daga karshene gimbiya halirat tayi
fushi mutuka, saboda haka sai ta shiga duniya domin samun
ilimi na tsafi. Anan tayi alkawari cewa zata dawo ta halaka
mutanen garin ga baki daya, sannnan kuma ta dauki fansar
mahaifinta kuma ta kashe labeenat.
Ba a dau lokaci da wannan al amari ba sai sarki nayib ya
kwanta rashin lafiya. To anan yayi wa dansa gamza wasiya:
Ka sani dana rayuwarka tana cikin hadari da kaida mutanen
wannan gari domin a duk lokacin da gimbiya halirat ta dawo
bako shakka zata aiwatar da abunda ta fada. Saboda haka
inaso kayi kokari ka kiyaye martabar wannan birni namu da
kuma wannan yarinya labeenat.
Anan ya cigaba da bayanina: shekaru dubu da suka shude,
akwai wata sarka da sarkin aljannu na duniya ya kera da
hannunsa. Shi wannan sarki na aljannu ya kasance yana bin
wani addini wai shi musulunci. Dalilin da yasa ya kera wannan
sarka shine saboda kariya daga makiyinsa. Sai da ya shekara
dari takwas yana rokon ubangijinsa daya kare duk mutumin da
sarkar ta dawo hannunsa.
Daga nan sai ya dulmiya ta a cikin wasu ruwa da ake cema
“RUWAN SIRRI” su wadannan ruwan sun kasance suna
maganin cututtuka kala kala har kala dubu. Sai da wannan
sarka ta shekara dari takwas a cikin wadannan ruwa sannan ya
fito da ita.
Wata rana sai yayi wani mafarki. A cikin mafarkin sai aka nuna
masa wata mata mai suna muhibbat wadda zatazo karshen
zamani. Ita wannan mata zata hadu da balai kala kala wanda
daga karshe zata rasa rayuwarta tabar wata karamar diyarta.
To a cikin mafarkin sai aka nuna masa cewa wannan diyar tata
itace zatayi amfani da wannan sarkar. To a tarihin wannan
sarki yanada baiwa domin duk mafarkin da yayi kan zamo
gaskiya. Saboda haka sai ya kera wani littafi da kansa, anan ya
debi jininsa ya rubuta labarin wannan mata da kuma wasu
abubuwa naban mamaki daya gani a mafarkinsa. Cikin kuwa
hadda taswirar wannan mata da iyalanta(drawing) daga nan
sai ya dauki sarkar da littafin ya kaisu wata duniya can daban
inda wani jinsi na bil adama ke rayuwa ba irin mu. Domin jiran
wannan lokaci na wannan matar muhibbat tare da diyarta.
Anan sarki nayib ya nisa kafin ya cigaba da bayaninsa. Akwai
wani lokaci da diyar wannan mata zata zo wannan birninmu
domin dibar wannan icce namu mai albarka. To idan har ka
samu nasarar kwace sarkar bako shakka ba wani tsafi da zai yi
tasiri akanka saboda haka zaka huta da barazanar gimbiya
halirat.
To bayan wannan wasiya, sarki nayib bai dau lokaci ba ya rasa
rayuwarsa. To anan aka nada gamza a matsayin sarkin garin.
Shi kuwa gamza kai tsaye ya auri masoyiyarsa wato labeenat.
To a cikin wannan aure ne aka samu cikin yarima munib.
Bayan wani dan lokaci sai labeenat ta fara mugayen mafarkai
akan gimbiya halirat. Saboda haka hankalinta ya tashi mutuka.
Domin tasan a duk lokacin data dawo garin to bako shakka
itace zata fara mutuwa. Saboda haka labeenat tayi shiri zata
shiga duniya domin ta samo sirrin tsafi wanda zatayi dogaro
dashi domin kariya ga harin gimbiya halirat. To anan labeenat
tabar danta yarima munib ta fita domin cikar burinta. Ba yadda
sarki gamza bai yiba domin ta zauna amma taki.
To bayan tafiyarta ne da wasu shekaru sarki gamza yayi
tsammanin ta mutu, saboda haka sai ya kara aure. To anan ya
auri wata kyakkyawar yarinya mai suna amisat. Haka amisat ta
dauki yarima munib a matsayin danta tun yana karami har
girmansa. Kuma shi yarima a tsammaninsa itace mahaifiyarsa
domin babansa bai taba bayyana masa gaskiyar lamarin ba.
=========================
Wata karamar gajeriyar dariya ke fitowa a cikin wani kogo mai
duhu, dagajin muryar kasan da cewa mace ce ke yinta. Sanye
take da wasu kaya na manyan mata masu ji da kansu. Kai
daganin shigar kasan da cewa yar sarauta ce.
Wasu manyan jarumai ne su biyu ke tsaye a gabanta suna
saurarar aikin da take shirin sasu.
Hubair da yazid nasan kune jaruman da kuka san kan
masarautar askandariya ciki da wajenta. Saboda haka ku kuka
fi cancanta da kuyi wannan aiki mai mutukar wahala. Injita. Sai
dai idan kukayi kuskure to zaku rasa rayukanku domin sarki
gamza ba zai kyalle kuba.
To anan ne yazid ya fara magana: haba gimbiya halirat, ya kina
wannan magana sai kace bakisan kanmu ba. Ai mu bama
kuskure shi kansa kuskure tsoronmu yake saboda haka ki fadi
bukatarki yanzu zakiga aiki da cikawa.
Murmushi tayi kafin ta fara magana: ku sani cewa akwai wata
sarkar sihiri da sarki gamza ya amshe ga wata hatsabibiyar
yarinya da ta shigo garinsa domin dibar iccen da suke bauta.
To wannan sarkar nakeso ku satomin domin nasan dole tana
wurinsa.
Wannan ba komi bane ranki shi dade. An gama. Inji
hubair.daga nan suka tashi suka fita. To wannan shine dalilin
da yasa hubair da yazid suka shigo birnin askandariya domin
kammala wannan aiki da gimbiya halirat ta basu.
:::::::::::::::::::::::::::::::
To bayan da hubair da yazid sun samu damar sato wannan
sarkar anan suka fara kokarin fita masarautar don kada
asirinsu ya tonu. To kafin suyi nisa da tafiyar ne suka farajink
ana buga kararrawar garin wato alamun cewa kowa ya tashi
domin akwai masifa tafe.
Gurnani da gudun dakarun garin ya ba su yazid mamaki. To
anan suka gane cewa ashe wani katon tsuntsu ne a sama sai
aman wuta yake ma mutanen garin, wata mata ce a sama ba
abunda take in banda jefo kibiyoyin sihiri ga dakarun garin
masu kokarin kare birnin.
Wannan abu yabasu mamaki amma basu damu ba, haka suka
cigaba da gudu suna kokarin fita masarautar. A cikin wannan
gudu ne nasu sukaci karo da wasu dakaru to anan suka tsayar
dasu suna tambayarsu ko su waye. Maimakon su basu amsa
kawai sai suka fara yakarsu. Taron yawa yafi taron karfi kafin
kaceme an kai su yazid kasa. Can sai yazid ya tuno maganar
daya gayawa gimbiya kafin ya fito.
( mu bama kuskure, kuma shima kuskure tsoronmu yake)
Anan yaga bazai yiwuba, kafin kaceme ya kubce. Anan
gumurzu ya koma sabo, daga karshe dai su yazid sun samu
nasarar fita garin lafiya lau domin suna gamawa da wadannan
dakarun kawai sai sukaga wannan tsuntsun ya kamasu ya aza
saman bayansa. Anan ya daga fuka fukansa yayi sama dasu.
Tun da sanyin safiya sarki gamza ya farka yaga irin barnar da
aka yiwa mutanen garinsa, gawawwaki koina ba kyan gani.
Daga nan kuma ya gano cewa an sace masa sarka, wadda ya
kwace wurin meenat. Sarki gamza yayi mamakin wannan hari
na ba zata. To kada dai ace gimbiya halirat ce ta dawo!!!!
Bayan sati daya da faruwar hakan, sai ga gimbiya marsiyya ta
kawo ziyara garin wato yarinyar da akeson aurama yarima
munib. Wannan ziyara ta musamman ce domin ganin yarima
saboda haka iyayenta basu zoba maimakon haka sai suka
hadota da dakaru wadanda zasuyi gadin lafiyarta. Sarki gamza
ya karramata mutuka tare da dakarunta daga nan kuma ya
basu masauki. To a wannan lokaci gasar shekara ta matso. Ita
wannan gasa duk shekara ake yinta. Saboda haka akan tara
sadaukai suyi fadan gwajin karfi duk wanda ya fito zakara kan
samu kyauta mai tsoka.
Akwai wani abu da sarki gamza ke nufi dasu ilham domin ya
umarcesu dasuyi shirin shiga wannan gasa mai hadari amma
kuma sai ya debe meenat. Wato bada ita za ayi gasar ba. Iyaka
dai ilham da abbanta kawai ne za ayi dasu. Wannan abu ya
mutukar ba yarima mamaki domin bai taba yiwa yan fursuna
haka ba. Kuma ita wannan gasa maza aka sani da yinta, domin
duk macen da taje sunanta gawa. Kuma me yasa debe
meenat? Ko yana nufin ya yarda da jarumtakarta. Haka dai
yarima ya cigaba da wannan tunani, daga karshe dai ya yanke
shawarar horar da ilham tare da abbanta domin su samu
damar kare kansu ga harin makiya.
To a wannan lokaci sadaukan garin sun fara kimtsawa domin
fuskantar wannan gasa saboda haka duk yan fursuna an basu
dama su fito suyi kallon gwajin gasar kafin a fara ta ainahin. To
a wannan lokaci meenat na zaune ita kadai tana kallon yadda
yarima ke horar da ilham tare da abbanta. Sai kuma wasu
mazaje dake bayansu suna horar da kansu, filin dai ya cike da
sadaukai sai horar da kansu sukeyi.
Ana cikin wannan horo ne sai ahnab wato abban ilham ya gaji,
saboda haka sai ya komo wurin meenat yayi zamansa ya kyale
ilham da yarima suci gaba dayi.
A duk lokacin da yarima ya hada ido da ita sai yaga ta done
kai, anan ya rasa gane abunta take nufi.
Gyaran murya yayi kafin ya fara magana: inaso ki rike takobinki
da hannu biyu sannan ki fara kawomin mugayen hare hare, to
anan ilham ta dan kalleshi. Wannan kallo ba karamin sosa ma
yarima zuciya yayi ba.domin wani dadi ne ya lullube shi.
Taku yayi uku sannan ya gyara mata rikon takobi. To anan ta
fara kawo masa sara yana kaucewa. A hankali har ta fara gane
yadda ake kai hari. To daga nan ne shi kuma ya fara kai mata
tana karewa. To suna cikin hakane saiga gimbiya marsiyya
tazo giftawa. Anan abun yabata shawa irin yadda sadaukai ke
horar da kansu. Tana cikin waige waige ne sai ta hango yarima
tare da wata yarinya suna fada. Anan ta fara mamaki ko
wacece wannan?? Babban abunda ya bata haushi shine irin
yadda yarima ke kallonta. Kuma itama da alama tana satar
kallonsa kuma a duk lokacin da suka hada ido sai taga sunyi
murmushi. Kamar dai akwai wani abu dake gudana tsakaninsu.
Cikin sauri gimbiya marsiyya ta isa wurin.
Sannunki, ai da kin bani takobin sai kije ki huta ko, da alamar
akwai gajiya a tattare dake.inji marsiyya. Ilham batayi gardama
ba ta mika mata takobin. Anan ta nufi wurin su meenat domin
zaunawa. Haka yarima ya bita da kallo har sai da gimbiya
marsiyya ta kyafatoshi.
To anan suka fara kallon kallo, cikin murmushi yarima ya fara
magana: nasan ke jaruma ce saboda haka ki shirya ma
fuskantata, domin bazan raga miki ba ko kadan.
Anan gimbiya tayi dariya tana mai bashi amsa. Haka kace,
aiko yau kayi gamo da gamonka domin ko kadan bana
shakkunka. Kuma yanzu zan nuna maka cewa ni ba kanwar
lasa ceba. Wannan magana da sukayi ta janyo hankalin
sadaukan ya koma a kansu. To anan suka natsu suna kallonsu.
Wani kukan kura tayi sannan ta fara kawo masa sara da suka
cikin bajinta irin ta manyan jarumai. Da farko yarima bai daukin
abun komai ba amma daga baya sai ya gane cewa idan baiyi
da gaske ba zaiji kunya. Anan ilham ta fara kallon wannan fada
nasu tana tunani” dama ace nice keda wannan jarumta ai
dana futa” ta fada.
Fadan nasu ya kasance abun debe kewa da nishadi, ita dai
gimbiya ta kasance ba abun da take yi in banda kai masa sara
cikin salon yaki, cikin hakane ta lankwasa takobin ta masa
wata bulala a baya anan yarima ya fadi timmmm. Kafa tasa da
nufin takashi, daga nan sai yayi wani tsalle yana juyawa har ya
mike.
Daga nan sai yarima ya canza salon fadan, haka ya fara kai
mata hari cikin sauri har ya samu damar yar da takobinta. To
anan ya kayar da ita ya aza mata takobi a wuya ma ana shi ya
cinye. Dariya gimbiya tayi daga nan sai ta mike. Juyawa tayi da
nufin tafiyarta kawai sai tayi karo da meenat a gabanta. Anan
meenat ta fara magana. Kinyi kokari, amma banji dadi da kika
yarda ya kaiki kasa ba, domin irin wannan kanja ma mata raini.
Hhhhhhhh. Yarima yayi dariya. Ko zaki gwada ne kema?? Anan
meenat ta juyo wurinsa. Ai ni bana fada da yara. Wannan
magana ta meenat tasa sadaukan suka fara kallonta, ita
wannan ko mi take takama dashi?? Wai yarima zata cewa
yaro!!
Anan meenat ta juya da nufin komawa inda take. Cikin rashin
tsammani sai taga yarima a gabanta. Ai da kin bari mun gwada
domin a banbance waye yaro waye babba. Cikin murmushi
meenat ta bashi amsa, kamar yadda na fada ma bana fada da
yara. Anan ta cigaba da tafiyarta.
Cikin wata murya mai karfi yarima ya fara magana: ai ni ban
san da cewa a cikin mata akwai matsorata ba, masu tsoron
karawa da mazaje.
To anan meenat ta tsaya wuri guda tana saurarensa. Kuma a
wannan lokaci duk hankalin sadaukan ya dawo kansu. Daga
nan meenat ta dawo wurinsa, anan ta amshe takobin dake
hannun gimbiya marsiyya. Daga nan sai sadaukan suka
zagayesu domin kallon wannan fada.
Kallon kallo aka farayi tsakanin yarima munib da meenat. Kai
da gani kasan kar tasan kar. Cikin wani salo na manyan barade
ta kawo masa wani kakkarfan sara. Saboda karfin saran sai da
yarima yaja da baya. Sai can ya turje wuri daya. Anan yayi
mamakin irin wannan karfin sara domin a tsammaninsa wani
kato ne ya fado masa.
Cikin gwaninta irin na manyan jarumai suka kacame da wani
azababben yaki. Wannan yaki ya kasance mai ban tsoro domin
da farko yan kallo sunyi tsammanin na gaskiya ne. Sai daga
baya suka gano ba haka ba. Cikin kowace dakika meenat ta
kasance takan kai ma yarima sara fiye da goma a lokaci guda.
Hakan ya tabbayar ma da yarima cewa lallai jarumar gaskiya
ce. Domin yayi karo manyan jarumai masuji da kansu amma
bai taba haduwa da irinta ba. Wannan sauri na meenat ya rudar
yarima domin ya rasa hanyar da zaibi ya kare saran domin
sunyi yawa. Haka wannan yaki yaci gaba da gudana har takai
yarima bai iya mayar da martani sai dai kariyar kansa.
Cikin hakane meenat ta samu nasarar yimasa yanka uku a
kafada sai da yayi ihu domin zogin da yaji. A haka yan kallo
suka wanzama suna kallon wannan fada tare da mamakin
meenat.
Can sai meenat tayi wani tsalle, anan yarima ya dago kai
domin ganin inda zata. Cikin rashin tsammani sai yaga ta dawo
bayansa. Kafin ya juyo tuni ta masa wani naushi a fuska ji kake
fussss. Karfin wannan naushi yasa yarima ya yar da takobinsa.
Daga nan sai ta kara masa wani mai karfi wanda yafi na farko.
To anan yarima ya fadi rikacaaa kamar gawa.
Wannan faduwa ta yarima ta tayar da hankalin yan kallo.
Domin a tarihinsa ko a cikin gasar ta gaskiya bai taba faduwa
kasa war was ba. Amma sai gashi yau mace ta kaishi kasa
kuma wurin gwaji bama wurin gasar ba. To ina ace a gasar
ne???
Anan fili yayi tsit tamkar anyi mutuwa. Can sai yarima ya fara
dan tari. To anan meenat ta miko masa hannu, anan ya rika
hannun nata har ya tashi tsaye. Mikewarsa keda wuya sai fili
ya kacame da shewa. Anan aka fara yiwa meenat tabi da
jjnjina. Haka itama tayi ta kallon jama a tana daga musu
hannu. Wannan jarumta da meenat tayi yasa sunanta ya
bazama a garin. Haka shima yarima sai da ya jinjina mata. To
anan ya gane cewa wato saboda jarumtakarta ne abbansa ya
hanata shiga gasar. Don kada ta yiwa sadaukan garin barna.
Domin bako shakka karo da irin wadannan kiran ruwa ne.
Da ganin fuskarta kasan cikin annashuwa take. Gimbiya halirat
ce a zaune tana kallon sarkar da su yazid suka kawo mata.
Wannan matar dake saman wani katon tsuntsu dake aman
wuta a birnin askandariya gimbiya halirat ce. Kuma itace ta
dauke su yazid a lokacin da suke kokarin fita garin.
Anan ta fara magana: bako shakka kunyi namijin kokari da kuka
samo min wannan sarka. Domin ban aza zaku iya ba. Sai da
har yanzu akwai wani aiki daya da nakeso ku cika min.
Ku sani cewa akwai wata gasar fada da akeyi a birnin
askandariya a duk shekara saboda haka inaso ku shiga wannan
gasar domin ku kashe yarima munib. Idan kuka yimin wannan
to zan baku kyauta wadda zata isheku har zuwa karshen
rayuwarku.
Cikin murmushi hubair ya fara magana: gimbiya ni a ganina tun
da har kinada ikon juya wadannan kwari na sihiri yadda kikeso.
Me yasa ba zaki aika masa suba. Ko kuma ki turasu su kashe
mutanen garin gabaki daya. Kuma nasan akwai wata halitta
wadda har yanzu bamada masaniya akanta. Amma nasan
itama tana karkashin ikonki. Ita wannan halitta kanyi kalaci da
mutum yada taso wanda hakan yasa wasu daga cikin halittun
suka koma wata duniya ta wasu bil adama daban suna
kashesu. To ni inaga kosu kika tura ai zaifi sauki.
Dariya gimbiya halirat tayi, duk abunda ka fadi gaskiya ne,
wannan shine dalilin da yasa na shiga duniya nayi shekaru ina
bidar sirrukan tsafi. saboda wannan dalili ne yasa na tanadi
wadannan kwarin, kuma na sihircesu yadda suna jin kamshin
mutane, akan hakan yasa duk mutumin daya gifta ta wannan
hanya sunansa gawa. Domin bako shakka wadannan kwari
zasu kasheshi. Sai dai yanzu banason nayi aiki dasu, ku
nakeso. Saboda haka ina umartarku dakuyi shiri domin nan da
kwanaki kadan za a fara gasar. An gama ranki shi dade. Inji
hubair.
A cikin birnin askandariya. Yarima munib na tare da
mahaifiyarsa amisat sai kuma sarki gamza. Fada kawai suke
masa.
Dolene ka auri gimbiya marsiyya ko kanaso ko bakaso! Inji
amisat
Can sai ga gimbiya marsiyya ta shigo dakin. Ku gafarceni na
shigo ba tare da neman iznin kuba. Amma abunda ya kawoni
shine game da wannan magana da kuke yita nanatawa.
A gaskiya idan kuka yiwa yarima haka bakuyi adalci ba.
Daganan sai ta kalli sarki gamza. Abbana ya ban labarin
labeenat. Da kuma gwagwarmayar da kasha saboda bakason
gimbiya halirat. Daga nan sai hawaye suka fara zubowa a
idanunta. Dalilin haka yasa nake rokonku daku bar yarima ya
auri wadda yakeso, idan kuma ba hakaba to labarin labeenat
daya faru a can da shine zai kara maimaita kansa. Idan na
koma masarautar mu nasan yadda zanyi da iyayena. Saboda
haka gobe zan koma garinmu. Anan ta juya ta fita dakin.
Anan mamaki ya kama yarima. Ko ya akayi tasan baya sonta??
Sannan wacece labeenat??
Bayan sati daya da wannan al amari. Sai ranar wannan gasa
mai hadari tazo, wani fili ne aka tanada domin yinta, kujeru
wasu saman wasu, kuma sai aka jerasu yadda na gaba bazai
kare ma na baya ba. A haka wannan fili ya cika makil. Daga
nan sai aka fara buga tambarin fara wasa.
Ga kaidar wannan gasa sadaukai biyu ne ake hadawa fada da
juna duk wanda aka kayar to ya fadi. Haka za ayita hadasu har
sai an samu wanda ya rage. Ma ana ya rinjayi kowa.
Tunda aka fara wannan gasa hankalin ilham a tashe yake.
Domin a nan ta raina kanta. Ganin yadda sadaukai ke jajircewa
domin kai matakin karshe.
Hubair da yazid suna cikin wadanda za a kara dasu a wannan
gasa, sai dai sun lullube fuskokinsu da wani kyalle don kada a
gane. Kallo guda ilham ta musu taji bata yarda dasu ba.
Wani ihu taji mutane sun kwala. Anan tayi saurin duba zuwa ga
filin gasar sai ta gano cewa wasu sadaukai ne ke fada da juna
shine mutane ke ihu domin ganin yadda suke nuna bajintarsu.
Sun kasance suna juya takubba yadda sukeso cikin salon yaki
irin nasu. Ana cikin hakane sai aka kai ga yarima, tun daga
fitowarsa mutane ke masa kirari domin sun san da
jarumtakarsa a filin gasar. To a dai dai wannan lokacine su
yazid suka natsu domin kallon irin salonsa na fada. Wasu karti
ne su goma zai kara dasu. To anan aka sako wasu damisoshi
biyar daure da kaca. Abunda yasa aka sako wadannan
damisoshi shine don su karawa gasar wahala. Wato koda
mutum na karawa da abokin hamayyarsa to dole yayi taka tsan
tsan don kada ya fada wurinsu.
A tare wadannan sadaukai goma suka jero sahu suna kai ma
yarima sara da suka. A cikin salo irin nasa yake kare saran tare
da mayar da martani. Su kuma wadannan damisoshi sai
gurnani sukeyi suna jiran wanda zai fado wurinsu.
A wannan lokaci ilham na tare da meenat kafin a kirata. Anan
meenat ta gane cewa shima yarima ba kanwar lasa bane
domin cikin salon yaki yake yakarsu ba sassauci. Haka wannan
fada ya cigaba da gudana sai daga karshe yarima ya tarwatsa
su gabaki daya. Anan mutane suka fara yi masa tabi da jinjina.
Daga nan sai aka kira yan wasa na gaba. Wato ilham da
abbanta zasu yaki wasu sadaukai biyu. Anan gabanta ya fadi
rasssssssss. To kafin su shiga filin gasar ne yarima ya taresu.
Inaso ku jajirce a wannan gasa kada kuji tsoro ko karaya. Anan
ilham ta kalleshi tare da yimasa murmushi.
To bayan sun shiga filin gasar ne sai aka fara kallon kallo.
Daga nan sai suka rikece tare da kaima juna sara. Ahnab ya
kasance dattijo, amma ko kadan baya shayin wadannan
sadaukai domin yakarsu yake da zuciya daya. Sai da suka
dade suna wannan fada sai ilham ta fara gajiya. Har takai
abbanta ahnab shike kareta daga harin wadannan sadaukai.
Bayan wani lokaci sai ahnab shima ya fara gajiya, to a wannan
lokaci ita kuma ilham ta dawo hayyacinta. To daga nan ta
canza salon fadan. Anan ta fara yin wani fada da yarima ya
koya mata. Idan ka gani sai kace marar lafiya amma nan duk
salon fada ne. Cikin sa a kuwa takai wadannan sadaukai biyu
kasa. Anan aka yi musu jinjina sannan suka fito filin.
Yan wasa na gaba sune hubair da yazid suma zasu yaki
sadaukai biyu. Anan ilham ta kura musu idanu cikin rashin
yarda. Har suka gama fadansu ilham bata ida yarda dasuba.
Anan ta nunawa meenat tasu tana fada mata cewa bata taba
ganinsu a filin gwaji ba.
Haka aka yita hada sadaukai suna yakar junansu har sai da
aka kai matakin karshe, wadanda suka kai wannan mataki sune
yarima da ilham sai kuma hubair da yazid, shi kuwa ahnab ya
samu rauni sakamakon wani sara da wani barde yayi masa a
cinya saboda haka aka fiddashi filin gasar.
Hubair da yazid sun samu abunda sukeso. Anan suka kalli juna
kafin fuskantar su yarima. To wannan matakin karshe kowa
nasan kallonsa. Domin su hubair sun taka rawar gani kuma ana
ganin kamar sune zasu cinye wannan gasa. Saboda haka
hankakin yan kallo ya dawo kansu.
Kukan kura sukayi sannan suka tasoma juna cikin son ganin kai
abokin karawa kasa. To anan suka rincabe ba sassauci. To
anan yarima ya lura da irin saran da suke kawo masa kamar
sunaso suyi masa kwaf daya. Bako shakka yarima ya hadu da
gamonsa domin duk salon da yayi na yaki sai yaga sun sanshi
har sunfi shi iyawa. Haka itama ilham abun ya daure mata kai.
Daga nan yan kallo suka fara tabbatar da abunda suke tunani
akan cewa su yarima yau ba sa a.
A cikin wannan yaki yarima ya gaji mutuka haka itama ilham,
to daga nan ne suka buge ilham anan ta fadi gefe guda ko
motsi bata iyayi. Shi kuwa yarima a wannan lokaci takobinsa
ya fadi. To anan ne yazid ya dauko wani karamin mashi da
nufin soke yarima.
To anan dakaru suka fara tsawata masa domin ga kaidar
wannan gasa ba a kashewa amma sai sukaga ko jinsu bayayi.
Gashi dakarun suna nesa da filin balantana su hana. Kuma idan
sukace zasu hana to kafin su shigo filin mai afkuwa na iya
faruwa to anan suka rasa yadda zasuyi. Anan yarima ya bude
idanu yana kallon mutuwa a fili su kuma su yazid anan suka
durfafe shi. Anan yarima ya fadi. Runtse idonsa yayi domin
yasan da cewa yau sai wani bashi ba. Haka itama ilham tana
kallo za a kashe mata yarima amma ba abunda take iyayi.anan
hawaye suka fara zubowa a idanunta domin tasan yarima shi
kenan.
Yarima na cikin mamaki domin bai san abunda yasa wadannan
sadaukai keson kasheshi ba. To anan ya fara yima ilham kallon
ban kwana. Gashi bai cika burinsa na bayyana mata irin son da
yake yi mata ba.
To kafin hubair da yazid su aiwatar da nufinsu. Kawai sai akaji
haniniyar doki ya shigo filin gasar. To anan yan kallo suka bude
ido suna kallon abun mamaki wanda basu taba gani ba. Wata
mata ce a saman dokin. Sannan dokin baya taka kasa domin a
saman iska yake gudu.
Tun daga nesa wannan mata ta fara yiwa su hubair ruwan
kibau. Koda ta karaso wurinsu sun dade da mutuwa. Anan ta
dauki yarima munib da hannuta tana sumbatarsa. Daga nan
kuma sai ta jawo ilham ta gamasu dare. To anan ne dokin yayi
haninya sannan ya sauko kasa. To a wannan lokaci dakaru sun
shigo filin haka shima sarki gamza ya fito domin ganin ko
wacece ta ceci dansa daga halaka.
Labeenat!!!!!! Sarki gamza ya fada da karfi da ganin wannan
matar. Anan ya sheko a guje, haka itama wannan matar. To
anan suka rungume juna cikin farin ciki. Daga nan yan kallo
suka fara kallonsu suna mamakin abunda ke faruwa.
To ana cikin hakane sai akaga wata bakar guguwa ta durfafo
filin gasar. Hankalin meenat yayi mutukar tashi da ganin
wannan guguwar domin ta taba ganin irinta.
Wasu kwari ne manya manya a cikin guguwar. Anan meenat ta
gane wadannan kwarin, sune wadanda bayan ta fito garin
wadannan samudawan dodanni da ita da wadanda suka tsira.
Akan hanyarsu suka gamu da wadannan kwari. To anan
wadannan kwarin suka yita kashin mutane. Wanda daga karshe
zulyan ne ya ceceta daga harinsu.
Can sai akaga wadannan kwari sun koma wata mata. Wannan
ba kowa ceba in banda gimbiya halirat. To anan mamaki ya
kashe meenat. Kada dai ace wannan mata itace keda
wadannan kwarin!!!
Cikin tafiya ta kasaita gimbiya halirat ta tako gaban su sarki
gamza. Wata harara ta banka wa labeenat kafin ta fara
magana: kada kiyi tsammanin ganin kin ceci danki daga
sharrina komi zai lafa. Wannan kadan ne kuka gani. Kuma
inaso ku saurari abunda zai biyo baya. Anan ta rikida ta koma
wadannan kwarin, daga nan sai guguwa ta dauketa ta bace da
ita bat.
Yan kallo wannan gasa sun cika da mamakin ganin abunda ke
faruwa. Daga nan dai akayita watsewa har kowa ya koma inda
ya fito. To bayan yarima ya farfado daga dogon suman da yayi,
anan sarki gamza ya bashi labarin abunda ke faruwa tun daga
farko har karshe. To anan ne ya gano cewa amisat ba itace
mahaifiyarsa ta gaskiya ba.
Bayan sati daya da faruwar hakan, wata rana sarki gamza na
cikin fada. Kawai sai yaga dakaru sun shigo da wata mata. Wai
tanason yin magana dashi.
Ni sunana marliyat. Ina nan a wani karamin gari dake
makwabtaka da birnin ka waishi dimana. Mun kasance cikin
wata anoba domin wasu kwari ne ke damunmu wadanda bamu
san kansu ba. Su wadannan kwarin kan shiga jikn mutum daga
nan sai su kunbura shi, daga karshe kuma sai su fashe mutum
yadda zai yi gunduwa gunduwa wato kai daban kafa daban.
Wadannan kwari sun kashe jama a wadanda basa kirguwa.
Saboda haka na gudo domin in fadama tun da kaine babban
sarki. Idan yaso sai kayi wani abu akai.
Kada ki damu zan dau mataki game da al amarin! Inji sarki
To anan marliyat ta juya da nufin fita fadar. Kadan ya rage ta
fita sai sarki gamza yaga ta juyo ta fara kallonsa. To anan yaga
idanunta sun juya sunyi wani ja. Wata magana ta farayi wadda
daga sauraro kasan da cewa ba marliyat gaskiya ce ke wannan
magana ba.
Anan ta nuneshi da yatsa. Bazaka taba samun nasara ba.
Kuma da sannu sai naga bayanka da kaida duk mutanenka.
Anan yaga jikin marliyat ya fara kunburi. Kafin kaceme ta fashe
fasssssss. Anan sassan jikinta sukayi gundu gundu. Daga nan
sai yaga wadannan kwari sun fito jikinta. Haka kuma sai ya
fara jin dariyar gimbiya halirat kamar daga nesa. Daga nan
kuma sai wadannan kwari suka bace bat.
Cikin sauri sarki gamza ya shiga gidan sarautar. To anan ya
tara matansa biyu wato amisat da labeenat sai kuma dansa
yarima munib. Anan ya labarta musu abinda ke faruwa. Wato
ku sani cewa rayuwarmu na cikin hatsari domin ako yaushe
wadannan kwari kan iya zuwa wannan birni namu suyi mana
barna, saboda haka dolene mu dauki kwakkwaran mataki akan
hakan. A dalilin wannan yasa na yanke shawarar kiran duk wani
fursuna dake gidan yari zai fito ayi wannan tafiya dashi domin
ganin an dakile wannan matsala. Cikin wadannan fursunoni
namu duk wanda ya tsira daga cikinsu game da hadarin
wannan tafiya. Zamu bashi yanci ya tafiyarsa.
Cikin kankanin lokaci aka sanar da yan fursuna wannan zance
na sarki. Saboda haka suka fara shirye shirye.
A cikin wannan tafiya harda labeenat za a tare da sarki.
Saboda haka sai aka debi dakaru masu yawa. Anan aka bar
amisat domin ta kula da garin har lokacin da su sarki suka
dawo.
Daga nan suka kama hanyar wannan gari wato dimana.
Kwanci tashi har tafiya tayi nisa.
Wata rana ilham na zaune ita kadai tana shakatawa kawai sai
ya yarima munib yazo wurinta. Daf da ita ya zauna.
Ya kinyi zaune ke kadai sai kace wadda aka yiwa mutuwa.
Anan ta juyo ta kalleshi. Ina tunanin wani abune daya dauremin
kai.
Amma zanso inji wannan abu daya daure miki kai!
Murmushi tayi kafin ta fara magana: kada ka damu zan fadama
idan lokaci yayi. Anan ya dan gyada kai. Wai ban taba
tambayarki ba hala a wane gari kike??
A birnin yamla!!! Ta bashi amsa
Ita kuma meenat na tare da abban ilham sai faman shan hira
suke.
To bayan dare ya raba sai kowa ya samu wuri domin yin bacci,
ita kuwa meenat a wannan lokaci batajin bacci, saboda haka
sai ta tashi domin ta zagaya wurin. To a cikin yawonta ne taga
wadannan kwari sun jero sahu suna tafiya, to anan meenat ta
yanke shawarar binsu domin ganin inda zasu.
Haka taci gaba da bin wadannan kwari har suka iso wani kogo,
anan taga suna shiga ciki. Abun mamaki shine sai taga zulyan
na magana da gimbiya halirat, to kada dai ace shi ke mata aiki.
Haka dai meenat ta koma mafakarsu. Daga nan kuma sai ta
sanar dasu sarki abunda ta gani. To anan sukayi shiri domin
shiga wannan kogo.
Cikin sanda suka fara tafiya har sukayi nisa cikin kogon to
bayan sunyi nisa ne sai suka farajin dariyar gimbiya halirat.
Cikin rashin tsammani sai ta bayyana a gabansu. Wasu dakaru
ne a bayanta wadanda duk jikinsu karfe ne.
To anan aka fara kallon kallo,can sai aka kacame da wani
namijin yaki, sudai wadannan dakaru na gimbiya halirat basajin
sara ko suka, haka kuma duk wani abu mai tsini baya tasiri
akansu. Wannan abu ya mutukar rudar dasu meenat domin sai
suka rasa hanyar da zasu yakesu. Ana cikin hakane sai gimbiya
halirat ta hango labeenat. To anan suka sheko a guje suka fara
nasu fadan, sai dai su nasu yakin na daban ne domin suna
amfani da tsafi.
Anan meenat ta hango zulyan ya shigo. Cikin sauri ta nufeshi.
Ashe kai munafiki ne. Wato dama shine ka labe wurinta domin
cutar damu.
Haba meenat ya kina wannan magana. Ya fada, ni ba aiki nake
mata ba, abunda yasa kika ganni wurinta shine domin inason
in taimakeku, ku sani wadannan dakaru da kuke fada dasu
bazaku taba samun nasara akansu ba face kun kashe………..
Labeenat bata dau lokaci tana yakar gimbiya halitat ba sai
gashi ta kaita kasa. Anan labeenat ta fara magana. Banason
kasheki. Sai dai ki sani cewa inaso ki fita harkata dani da
mutanena. Idan kuma ba haka ba to zakiga abunda zai biyo
baya. Anan labeenat ta juya da nufin ta kyaleta. Juyawarta
keda wuya sai ta hango yarima munib ya nufota rike da takobi.
Anan tayi tsaye tana kallon mai yake shirin yi.
Wani tsalle yayi sannan ya jefo takobin. Anan labeenat ta juya
domin ganin inda takobin ya nufa.
To ashe bayan data juya da nufin ta yafewa gimbiya halirat.
Ashe ita gimbiya bata yarda ba, shine ta tashi domin ta kashe
labeenat. Ashe shi kuma yarima munib ya hango abunda take
shirin aikatawa. Daga nan ne ya jefo mata takobinsa. Haka
wannan takobi ya shiga cikin gumbiya halirat. Anan ta fadi ko
shurawa batayiba.
To daga nan ne maganar zulyan takai karshe: ku sani
wadannan dakaru da kuke fada dasu bazaku taba samun
nasara akansu ba face kun kashe….. Gimbiya halirat.
Yana idarwa sai yaga gimbiya ta fado gabansa matatta.
To anan sukayi dubo zuwa ga dakarun kawai sai sukaga suna
ci da wuta. Anan meenat ta debe sarkarta daga wuyan gimbiya
halirat.
To daga nan sai sukayi shirin fita daga kogon.
Daga karshe dai sun fita lafiya saboda haka sauran yan
fursuna da suka rayu a wannan yaki an basu yanci su tafiyarsu,
to anan su meenat sukayi ban kwana dasu sarki gamza. Daga
karshe kuma yarima yayi alkawarin kai musu ziyara.
Anan su meenat suka kama hanyar komawa birnin yamla. To a
cikin wannan tafiya ne meenat ta bayyana musu abunda ya
kawota wannan duniya tasu wato”RUWAN SIRRI” to daga nan
ahnab yayi alkawin taimaka mata domin shi ke gadin
wadannan ruwa.
A lokacin da sarkin aljannu ya kera wannan sarka ta meenat.
To a wannan shekara akwai wata cuta data bayyana wadda ta
shafi mutane da aljannun duniya. A dalilin hakane sarkin
aljannu ya tara malaman birninsa domin su roki Allah akan
saukin wannan cuta.
Wata rana sai yayi wani mafarki. To a cikin mafarkin ne aka
nuna masa wani gida wanda komi nasa farine. A cikin gidan
akwai wata rijiya. To a cikin wannan rijiyar ruwan sirri suke, su
wadannan ruwa suke maganin wannan cuta data addabi
mutane da aljannun duniya. Har zuwa lokacin da sarkin aljannu
ya mutu ba a san wanda ya kera wannan gida ba, haka kuma
ba a san asalin ruwan ba.
A dalilin haka yasa sarkin aljannu ya bukaci danka ruwan ga
hannun mutane domin su taimaki junansu. To a cikin
bincikensa ne ya gano wani mutum mai amana a wata duniya
can daban. Wannan mutumi sunansa sanim. Sanim shine
kakan ahnab na dari da sha biyu. To anan sarkin aljannu ya
bayyana masa sirrin wadannan ruwan da kuma yadda ake
dibarsu. To kafin sanim ya mutu sai ya danka sirrin ga dansa,
haka shima dan dan ya ba dansa har abun ya kawo ga ahnab.
To bayan su meenat sun isa birnin yamla sai sukaga ba a
zaune lafiya domin an kawowa garin hari, yaki kawai akeyi.
Anan meenat ta yanke shawarar shiga cikin birnin domin ta
kaima yarima wannan icce data debo. Su kuwa su ilham anan
suka shiga cikin yakin aka fara damawa dasu.
Kai tsaye ta shiga dakin yarima lamras anan ta isko babansa
sarki qamar a tsaye jugum, tana shigowa ya zare takobinsa
domin a tsammaninsa wani ne ke kokarin kawo masa hari.
Yana ganinta sai ya mayar da takobinsa. Cikin sauri meenat ta
jika wannan icce a cikin ruwa. Daga nan taba yarima ya
shanye. Shanyewarsa keda wuya sai ya mike sai kace wanda
bai taba rashin lafiya ba. Anan sarki qamar ya rungumeshi cikin
farin cikin ganin dansa ya farka.
To anan ne yarima lamras yayi shrin yaki da nufin fita. Ba
yadda sarki bai yi dashi ba akan ya zauna amma yaki. Daga
nan sai meenat da sarki suka bishi. To bayan sun shigo filin
yaki an fara damawa dasu kenan. Sai kawai akaga yarima ya
yar da takobinsa. Wata yarinya ce ta sheko a guje wurinsa.
Wannan ba kowa ceba in banda gimbiya kulsum. To anan
abbanta yayi tsaye yana kallonta wato sarki habar.
Suna haduwa suka rungume juna. Anan mamaki ya kama
meenat ko ya akayi ya santa. Wannan abu yasa dukkanin
dakarun dana sarki habar dana sarki qamar suka yarda
takobinsu. Anan suka fara ihu suna murna. Kafin kaceme an
shirya.
A lokacin da yarima lamras na yaro. Mahaifiyarsa ta taba zuwa
dashi wani gari domin shakatawa. Wannan gari shine garwa
wato garin su gimbiya kulsum. To anan yarima ya kulla soyayya
da gimbiya kulsum, sai dai matsalar iyayensu basa shiri.
Saboda haka soyayyar batayi karfi ba.
To tun daga wannan lokaci basu kara haduwa ba sai yanzu.
Daga karshe dai sarki qamar da sarki habar sun shirya saboda
haka sarki qamar ya shirya wata liyafa ta musammam saboda
warkewar yarima.
Manyan sarakuna sun kawo masa ziyara saboda warkewar
dansa. A cikin hadda babban abokinsa wato sarki arma tare da
dansa yarima zayyad. To a wannan liyafa ne yarima zayyad
yaga rumaisa wato yayar ilham anan yaga tayi masa, saboda
haka ya bayyana mata sirrin dake ransa, daga nan ta aminta.
Haka shima yarima munib tare da iyayensa sun kawo ziyara a
birnin. To anan ne ya bayyana soyayyarsa ga ilham, haka
shima yarima lamras tare da tasa wato gimbiya kulsum. To
anan aka shirya ranar bikin aurensu Wanda za ayi tare.
Daga nan kuma sai ahnab ya bayyana ma meenat yadda ake
dibar wadannan ruwa na sirri. Daga nan kuma sai ya kaita
gidan wanda keda nisa daga garin. Meenat batasha wahalar
diban ruwan ba domin tana tare da ahnab wanda yasan sirrin
gidan. Tanashan ruwan sai taga jikinta na canzawa. Anan taga
halittarta ta ainahi ta dawo. Daga nan sai shima ahnab ya dibi
ruwan domin kaima ilham don a kare ciyon dake tare da ita.
Wata yar karamar gora meenat ta samu ta dura ruwan a ciki.
Daga nan sai suka dawo birnin yamla.
A ranar da ake bikin su yarima lamras a ranar ya duka shida
mahaifinsa ya bayyana wa meenat cewa juyawar halittarta
sune sanadi, anan ya bayyana mata yadda suka yi mata sharri.
Daga karshe dai meenat ta yafe musu.
To anan ne meenat tayi shirin barin wannan duniya. To anan
jama ar garin suka taru domin yi mata bankwana. A wannan
lokaci zulyan na tare da ahnab. Daga nan ne meenat tama
sarakunan tayin addinin musulunci. Anan suka karba suda
mutanensu.
Wai yaushe zaki dawo??? Inji zulyan.
Anan meenat ta masa murnushi ba tare data amsa ba. Daga
nan sai ta murza wannan sarka da kaka zuwaira ta bata.
Cikin rashin tsammani sai ga wata guguwa ta fito. To anan
wani bacci ya kama meenat. Kawai sai wannan guguwa ta
dagata sama.
A haka sauran jama a suka yita dagama meenat hannu suna
mata bankwana.
Daga nan sai aka daura auren yarima lamras da gimbiya
kulsum, shi kuma yarima munib da ilham, sai yarima zayyad da
rumaisa. Haka akayi shagali aka watse sannan kowa ya koma
garinsa.
Haka wannan guguwa ta yita tafiya da meenata har tabar
wannan duniya, to daga nan ne aka shigo da ita duniya irin
jinsinta(earth)
A hankali wannan guguwa ta ajiye meenat daga nan sai ta
bace bat.
Bayan ta shiga gidansu ne su kaka zuwaira sukayi maraba da
ita to daga nan ne kaka zuwaira ta fara magana: bayan tafiyarki
meenat mun gano cewa koda an ba wannan halittar wadannan
ruwa da kika samo to muhibbat wato mahaifiyarki bazata tashi
ba domin tayi mutuwar gaskiya, kuma fatalwarta ne ke baku
tsoro a cikin wannan gidan. Haka itama aunty balkisu bazata
tashi ba sanadiyar wannan halittar data cinyeta, saboda haka
ta mutu. Yanzu ruwan ko an ba halittar iyaka bafferh da ummi
kawai ne zasu tashi.
To anan hawaye ya zubo idanun meenat kan cewa ta rasa
mahaifiyarta. Daga nan ne suka shiga mota daddy na tukawa
har suka kawo wannan gida na fatalwa. To anan meenat ta
xuba ruwan sirri a wani tire sannan ta shiga gidan. Tana ajiye
ruwan sai ga wannan halittar ta fito. Anan halittar ta zuke
ruwan gaba daya. Tana gamawa sai ta fadi tana shure shure,
anan halittar ta mutu, to kafin ta mutu ne tayi aman su bafferh
da ummi, anan su meenat suka daukesu. Duk jikinsu yayi wata
lamniya.
Bayan sun kaisu gida ne aka wankesu tas. Sai da sukayi wata
guda kafin jikinsu ya samu sauki har su fara gane mutane.
Ba a dau lokaci ba kuma aka daura auren meenat da bafferh.
Daga nan suka zauna cikn jin dadi marar iyaka.
THE END
ALHAMDULILLAH.
FOR MORE NOVELS:
SEARCH AND JOINT OUR FACEBOOK GROUP:
KINGARTICLE.NOVL
OR
KINGARTICLE NOVELS OF ABDUL$BAFFEEH.
====abdul king article====
0 Comments