Darasin rayuwa a cikin labari




Labarin: Garin Da Maza Ke Shayar da Jarirai
_Abdul King Article_

*More books*
https://www.kingandqueenbooks.com.ng/

*Group*
https://chat.whatsapp.com/EJyDTUGRuWoCSv2hvGEPB3

 Akwai wani ƙaramin gari a gaɓar dajin Kanyami mai suna Tutsuru. Wannan gari yana da wata baƙuwar doka da ta daɗe tana janyo cece-kuce: "Idan mace ta haihu, sai mijinta ya ɗauki nauyin shayar da jaririn na tsawon makonni biyu kafin ta fara."

Eh, haka kake ji. Maza ke shayar da jarirai. To, yaya ake hakan? Wannan ya samo asali ne tun bayan da wata mata, Uwani Gwangwan, ta shayar da 'ya'yanta goma sha biyu ita ɗaya, har cikin wata shida na ƙarshe ta haihu a tsakar gona, ta miƙe ta kama noman shinkafa.

Tun daga lokacin, mata suka tashi tsaye suka ce "to yanzu sai maza su ɗanɗana". Alkalin gari, Alhaji Funtu, wanda ake kira "Mai Rantsuwa", ya zartar da doka: “Dole maza su sha wahala kamar mata. Idan ba za su shayar da jarirai ba, to sai su neme musu nonon roba su rika jan kwalba!"

Shi kuwa Bahi u  Mai Tsawo, wanda ba shi da haƙuri ko da kaɗan, ya ce, “ni gaskiya ba zan iya kwana da jariri yana kuka ba!” 
To, anan ne rigima ta fara. Jariri yana kuka, Bahi u yana kuka. Ya rasa lokacin da ya shiga kicin, ya yi romo, ya kunna garwashin shayi, yana haɗa madara. Amma kullum sai an samu matsala a wurin girkin, ko gishiri yayi yawa ko kuwa ruwa suyi kaɗan.
“Na shiga uku! Wannan ai ba aikin maza ba ne!” Bahi u ya ce yana shafa fuskarsa da bargo.

Sai wani tsoho mai barkwanci, Mallam Dan Lami, ya ce masa, “To yanzu ka gane me yasa muka ce ‘ka riƙe mace da daraja’? Ai duk tsawon rayuwarta, haka take wahala don jin daɗin mijinta da ’ya’yanta!”

A karshe, bayan Bahi u ya kammala sati biyu da jariri a goyo, sai ya tsaya a gaban jama'a a kasuwa ya ce:
“Wanda ya ce mace ba jaruma ba ce, to bako shakka bai taɓa gyara kwalbar nono ba!”

_Darasin labarin_

Kada mu raina wahalar da wasu ke fuskanta har sai mun gwada.

Mata na da matuƙar haƙuri da jarumta, kuma su ne ginshikin rayuwa.

Yayin da muke nishadi, mu tuna da darasi a ciki—koyi da juriya, ka daraja wanda ke wahala don jin daɗin ka.

Post a Comment

0 Comments