A WANI LOKACI

     
    
              By
  Abdul King Article                              
   Halima Bala Wakili
  Queen Nasmah
                                                                         Episode one

(The finding)
                         
  King and Queen Writing
 Chamber

Page 1 
 Duk da tsananin duhun da ake gwabzawa a cikin wannan dare mai ban tsoro bai hana wata mota samun kanta a saman titi ba, yarinyar dake tuƙa motar sai sharara namijin gudu take ba tare da tunanin abunda ke iya faruwa ba, da yake ƙaramar mota ce ladies car Honda Brio mai gambu huɗu, sa ar da yarinyar ta samu shine titin ya kasance highway kuma akasarin mutane basu cika bin hanyar ba sabida tsoron abunda ke iya faruwa, haka wannan yarinya ta cigaba da gudu ita kaɗai tana kallon dogayen bishiyoyin da suka gwaraye dajin gabaki ɗaya. A cikin hakane sai ta fara rage gudu wanda ke nuni da cewa kamar ta iso destination ɗinta, wata hanya ta ɗauke marar titi daga nan tacigaba da tafiya a hankali, rufe glass tayi sanadiyar ƙurar dake tashi tana mayar da idanunta akan hanya. Sai da tayi tafiya mai nisa kafin tayi parking dai dai wani gida upstairs, gidan ya kasance narkeke abun tsoro, a nan wannan yarinyar ta fito sanye da Arabian Gown sai kuma dark glasess  daya rufe mata idanu. Yar mini bag 👜ɗinta ta ratayo daga nan ta nufi wannan gida tana tafiya tana gurmanta, a cikin  tafiyar gurmanta  ta iso wannan gida, sai da ta kalli falon gidan sosai domin mafi yawan karkacen dake ciki tsofaffi ne, hakama gidan da gani ya jima sosai, a nan taci gaba da gurmanta tana mai taka stairs cases  ɗin har ta isa  sama, a nan ta kalli hallway na gidan kafin taci gaba da tafiya a ɓangaren hagu, motsin data jiyo yana kusantowa shine ya ƙara mata ƙwarin gwuiwa akan cigaban tafiyarta domin da alama waɗanda take nema suna kusa, sai da ta iso dai dai ɗakin sai ta murɗa ƙofar ta shiga ciki.
" Da kyau Anisa, dama ke muke jira domin yanzu zamu fara." Anan Anisa ta kalli wanda ya mata magana kasancewarsa a tsaye sanye da  long sleeve da jeans, sai cover shoe dinsa dake sheƙi, daga nan sai ta maido idanunta ga mutanen dake cikin ɗakin, a zazzaune suke saman plastic chairs su huɗu, namiji biyu mace biyu. Su matan da ganin dress ɗinsu an san yan duniya ne, atamfa ce a jikinsu sai long gown data rufe jikin nasu, hakama mazan, shirt ce a jikinsu da jeans sai normal cover shoes.
" Au, sannunku." Haka Anisa ta faɗa amma a cikinsu ba wanda ya amsa mata.
Page 2 
Anan ta zauna saman plastic chair tana jiran abunda zai faru ya faru.
   " Ina muku barka da zuwa wannan ƙungiya tamu mai taken Musakkai Association," Haka wannan mutumin dake tsaye ya faɗa yana mai kallonsu ɗaya bayan ɗaya. " Da farko dai sunana  Uzaim Sharim kuma nine shugaban wannan ƙungiya ta Musakkai. Kamar yadda muka sani dukkaninmu mun haɗu online, kuma ga online ne na fitar da address na wurin da zamu haɗu da kuma dalilin kafa wannan ƙungiya wanda a haka yasa dukkaninmu muka halartu a nan, kuma ina muku jinjina sosai bisa  ga rashin tsoron da kuka bayyana domin ba kowane mutum zai iya ganin abu online ya yarda dashi ba, kuma ba kowane mutum zai iya ganin address online ya ɗauka cewa gaskiyane, wani kan iya tunanin cewa zai iya rasa rayuwarsa idan yabi address ɗin, amma ku kun bada haɗin kai tunda gashi kun samu damar halarta kamar yadda muka tsara, gaskiya na jin jina muku, yanzu zan ƙarayin bayani akan wannan ƙungiya tamu domin mu ƙara sanin dalilin kafata." Anan aka tsurowa Uzaim idanu ana jiran abunda zai faɗa. " Kalmar musaki kamar yadda muka sani tana nufin mutum wanda ya rasa wani ɓangare na jikinsa ta dalilin ciwo ko kuma hatsari, to haka abun yake a wurinmu, kuma inada tabbacin cewa dukkaninmu a nan munada wani aibi a jikinmu, na kafa wannan ƙungiya ne domin mu baiwa juna labari akan yadda wannan larura ta faɗa muna da baiwa juna shawara akan yadda rayuwarmu ta yau da kullum zatayi kyau. Sabida haka yanzu zamu fara da sanin junanmu kafin muje ga darasi na gaba. Yanzu dukkaninmu zamu tashi mu faɗi sunanmu ɗaya bayan ɗaya. Zan fara dake ta gefen dama."  Anan Anisa tayi ƙaramin tsaki domin tasan da ita yake, ko meye na tambayan sunana bayan daga shigowata sai daya ambaci sunan da kansa, kuma fa sai da nayi waya dashi bayan na faɗa masa sunan nawa a lokacin da nake son karin bayani akan address din daya faɗa, kai abun haushi harda chat nayi dashi kuma na tura masa pics domin ya ganeni cikin sauki."  haka ta faɗa a  cikin zuciya daga nan kuma sai ta mike tsaye,
    " Zaku iya kirana Anisa, kuma ina mai farin cikin kasancewa a cikinku domin wannan ba ƙaramar nasara bace mutum ya haɗu da jininsa." Anan ta zauna daganan sai wata ta miƙe domin ta gabatar da kanta. 
    " A taƙaice sunana Haulat, nima ina mai farin cikin kasancewa a cikinku." Anan ta zauna. 
    " Ni kuma sunana Milam, ina mai yi muku barka da warhaka."  Haka ta fada sai ta zauna, Daganan sai namijin farko ya tashi domin ya gabatar da kansa.
     " Zaku iya kirana da Haris, ina taya kowa da kowa zuwan wannan ƙungiya."
     " Ni kuma sunana Jalim, barkanmu da zuwa wannan ƙungiya." 
Page 3   
Anan ne Anisa ta tabbatar da cewa bako shakka su shidda ne wato maza uku mata uku idan aka haɗa da uzaim wato shugaban ƙungiyar. Bayan kowa ya gabatar da kansa sai Uzaim ya fara magana kamar haka:
    " Yanzu ba tare da ɓata lokaci ba zan so na kira Anisa domin ta bamu labarinta da kuma bayyana mana irin nakkasar dake jikinta." Anisa najin haka sai tayi sauri ta miƙe ta nufi wurinsa, wata magana ta faɗa masa a cikin kunne daganan sai ta dawo ta zauna. Zaunawarta keda wuya sai Uzaim yaci gaba da magana. " A bisa wasu yan dalilai Anisa bazata samu damar bamu labarinta ba sai dai zuwa wani lokaci, sabida haka zan juya zuwa ɓangaren maza kuma ina kyautata zaton cewa Jalim kaine zaka maye gurbin Anisa." Jalim najin haka sai yayi murmushi, " wannan murmushi dake fuskarka shine ya furta muna cewa ka aminta da abunda muke buƙata." Inji Uzaim. Anan Jalim ya ƙara sakin murmushi tare da alamar cewa ya aminta. " To kafin Jalim ya fara bamu labarinsa inaso mu sani cewa duk wanda muka kira anan to zai bamu labarin nakkasar dake jikinsa da kuma yadda akayi ya zama musaki mu kuma sai muyi ƙoƙarin ganin cewa mun basa shawarwari ta yadda rayuwarsa zata dai daita, ina fatan mun fahimta. Sabida haka yanzu Jalim fili nakane zaka iya farawa." Uzaim komawa yayi gefe ya samu kujera ya zauna, shi kuwa Jalim miƙewa yayi yana tafiya har ya iso dai dai tsakiyar ɗakin ta yadda kowanensu zai iya kallonsa. Murmushi ya saki kafin ya nuna musu yan yatsunsa wato (fingers) anan suka gane cewa bayada ƙaramin finger na hannun hagu, yatsansa na ƙarshe wanda yake ƙarami wato the last smallest finger dake hannun hagu to an fince shi. Anan Jalim ya ƙurawa wannan yatsa idanu kafin ya fara labarinsa kamar haka :
A wani lokaci, na taɓa tsinta kaina a cikin matsanancin halin rayuwa, a wannan lokaci wanda bazan manta dashi ba na kasance tare da iyayena a cikin wani irin baƙin talauci, bamuda abinci balantana abunsha, yar sana'ar da abba keyi ta kasuwanci komi ya tsaya tun lokacin da supermarket ɗinsa ta ƙone ƙurmus, ni kuma a wannan lokaci na kammala degree amma ba aiki gaba da baya. Yan uwa da abokan arziƙi da muke tsammanin suyi mana agaji amma a cikinsu ba wanda ya nuna damuwarsa,  a cikin hakane sai nayi wa Umma magana akan mafita.
   " Umma wannan zama da mukeyi haka bazai amfane mu da kome ba, a bisa wannan dalili nakeso na fada miki nifa na ɗau niyar shiga duniya domin neman nakai." Inji Jalim.
   " Haba Jalim, kada ka manta ku biyu kawai na haifa daga kai sai ƙanwarka, kuma kaine keda ƙuzarin fita kayi aikin ƙarfi ka nemo muna, to yanzu idan ka fita wa zai bamu." Inji Umma.
  " Kada ki damu umma  a cikin kuɗin da nake tarawa na aiki zan ciro dubu goma."Inji Jalim.
Page 4     
       "Zan baiwa Suhaila dubu biyar ta ajiye idan yaso ta sayi dankali tana toyawa a waje kinga a nan sai kuyi amfani da ribar, ni kuma sai nayi manejin biyar har naje na dawo."
       " shin wai kai Jalim dake wannan maganar hala wane wurine zaka tafi?"umma ta tambaya.
       " umma zan ƙetara ne duniyar sahara, kin san course dinmu Geology yana dealing da mineral resources wato albarkatun da aka samu a cikin ƙasa irin su zinari azurfa da dai sauransu, a cikin hakane muka yanke shawarar shiga duniyar sahara tare da wasu abokaina domin mu nemo zinari, idan mun samu nasarar samun zinarin sai mu tattara shi mu sayar idan yaso ribar da muka samu sai muyi sana a da ita." Inji Jalim. Anan umma tayi gyaran murya kafin ta fara magana kamar haka:
     " Bazan hanaka neman arziƙi ba domin talauci abun gudu ne ga kowane mutum, amma ka sani wurin da zaka tafi wuri ne mai hatsari domin da yawan mutane suna rasa rayukansu a irin wannan sabga. Daga ƙarshe dai inaso ka riƙe gaskiya da addua a duk halin daka tsinci kanka a ciki. Yanzu idan Abbanka ya dawo zan faɗa masa idan yaso sai naji tasa shawara. " Anan Jalim yaci gaba da baiwa umma  labarin yadda tafiyar zata kasance da kuma ainahin wurin da zasu tafi, daga nan kuma sai ya faɗa mata wasu abokan nasa waɗanda zasuyi tafiyar tare, babban abunda ya ƙayatar da umma shine mafi yawan abokan nasa da zasuyi tafiyar tare duk ta waye su domin yan asalin unguwar ne, bayan sun gama fira ne sai Jalim ya shige ɗakinsa yana jiran dawowar Abba, babban abunda ke tayar masa da hankali shine Abba zai iya kwafsa masa, amma duk da hakan bai yi ƙasa ƙasa da addu a ba, a cikin darene har bacci ya fara ɗaukar sa sai yaji Umma na ƙwala masa kira, cikin hanzari ya diro saman gado ya durfafi falon gidan, daga zaunawarsa sai Abba ya fara magana :
     " Jalim an faɗamin cewa kanada muradin son shiga duniyar sahara tare da abokanka domin neman zinari, gaskiya naji daɗin wannan zance domin sana ar zinari ba ƙaramar sana a bace kuma ina yi maka fatan nasara."
    " Ina godiya Abba." Inji Jalim.
    " Hala yaushe ne zakuyi tafiyar?"Abba ya tambaya.
    " Gobe gobe ne domin yanzu haka na shirya kayana tsaf, ina jirane safiya ta waye." Inji Jalim. Daga nan sai Jalim ya fizgo kuɗi a cikin aljihunsa, "  Waɗannan dubu biyar ne, gobe da safe sai a baiwa Suhailat domin ta sayi dankali tana toyawa a waje idan yaso sai kuyi amfani da ribar, idan kuma batada buƙarar hakan to sai tayi wata sana a  ta yadda riba zata fito." Anan Jalim ya miƙawa Abba kuɗin daga nan ya tashi ya nufi ɗakinsa. Daga shigarsa yayi ta sharar bacci shine bai farka ba sai da Asuba, cikin sauri ya kimtsa ya rataya jakarsa (school bag)
Page 5   
Short shirt ce a jikinsa mai kwala da jeans 👖 sai facing cap daya aza domin kariya daga rana, cover shoe ne a ƙafarsa 👟👟 sabida kiyaye hatsarin dake cikin sahara, yana gama kintsawa sai yaji oda a waje, a nan ya tabbatar da cewa abokansa ne a mota kuma suna jiransa ne. Cikin hanzari yayi bankwana dasu umma daganan ya fita waje. Yana fita ya tarar da abokansa na gyran kayansu a cikin boot, mota ce Toyota Hilux, kasancewar motar modern design ce to boot ɗinta ana kulleshi kuma ana rufewa ba kamar sauran Hilux ba. Wata ƙatanyar tasa ce da marfinta cike da cin cin suka jefa a cikin boot domin yin guzuri, daga nan sai wata jarka babba cike da ruwa itama suka ajiyeta. Daganan suka ajiye plates da cups  da sauran abubuwan buƙata duk a cikin boot ɗin. Jalim na ganin haka shima sai ya jefa yar jakarsa a cikin boot ɗin daga nan suka rufe. Anan Jalim ya juyo yana kallon gidansu a lokacin suma su umma tsaye suke suna kallonsa. Gidan nasu ya kasance gidan alfarma, a bakin gate ɗin gidan an shuka flowers gwanin ban sha awa, idan mutum ya kalli gidan bazai yi zaton cewa masu gidan suna ciki talauci ba. Da yake a wancan lokacin na baya kafin supermarket ɗin Abba ya ƙone sun kasance a cikin jin daɗi, akwai motoci kusan huɗu a gidan domin kowane da motarsa, Abba yanada motarsa haka umma tanada motarta, Jalim yanada motarsa daban haka itama Suhailat tanada motarta, amma a cikin lokaci sai da duk aka sayar da motocin sabida tsananin talauci,  daganan kuma aka sayar da sauran abubuwa jin daɗi na gidan tun daga fridge, tv da sauransu, tashin hankali daya addabesu shine koda sun ajiye kudi domin yin sana a sai wani abu ya faru wanda zai yi sanadiyar ƙarewar kuɗin, babban abunda ya kawo musu matsala shine ƙonewar supermarket ɗin Abba tare da manyan shagunansa domin shi kasuwanci ne a gabansa, da yake shi Abba bai damu da aikin gwamnati ba domin yana kammala Diploma sai ya faɗa kasuwanci, kuma a makaranta ne wurin Diploma ya haɗu da umma wadda ta kasance class mate ɗinsa,   anan suka ƙulla soyayya mai ƙarfi wadda ta kaisu ga yin aure. Kuma a cikin wannan aure ne aka samu Jalim da ƙanwarsa Suhailat, daga nan haihuwa ta tsayawa umma, sa ar da Jalim ya samu shine a lokacin da supermarket ɗin Abba ya ƙone tuni ya kammala degree ɗinsa amma ba aiki, ita kuwa Suhailat tana 100 level, sabida rashin kuɗi dole ta tsayar da karatun domin Abba ba zai iya biyan kuɗin registration ba.........
" Kai, wai tunanin me kake." Cikin sauri Jalim ya juyo yana kallon abokinsa Faruƙ, sauran abokan nasa su buyu suma sun karkata zuwa gareshi. Anan ne Jalim ya tuno wai dama tafiya zasuyi.
" Wai dama mu huɗu ne zamuyi tafiyar ko?"Jalim ya tambaya." Aa mu hamsin ne!" Faruk ya bashi amsa cikin takaici.
Page 6   
Anan Jalim ya ƙara kallon abokan tafiyarsa wadanda suka haɗa da faruƙ, Safyan da yazid, shine cikonsu na huɗu. Dukkaninsu sun yi irin shigar Jalim wato jeans da  t shirt sai cover shoe domin kariya daga hatsarin sahara, kowanensu sanye da dark glasses.
     " Kome yake tunani dai oho!" Inji Safyan.
     " Wata kila yarinyarsa yake tunani!" Inji Faruƙ
     " Yarinyarsa, wai kana nufin Tumba?" Safyan ya tambaya
     " Wace Tumba, Kande mai fura dai ko."  Inji Yazid. Anan suka ƙyalƙyace da dariya suna kallon Jalim, Haka Jalim yayi shiru yana sauraren abokansa na masa tsiya kuma ba yadda zai yi. Daga nan sai suka shiga mota bayan sun yi bankwana dasu umma. Faruƙ ne a gaba kuma shine driver sai Safyan a kusa dashi, Yazid da Jalim su kuma a baya. Cikin gwaninta Faruƙ ya tada mota daga nan ya fara tuƙi. 
     " To kafin muyi nisa fa duk mai jin zawo yayi magana domin idan munyi nisa bazamu tsaya ba." Inji Faruƙ cikin jan magana. Anan suka ƙyalƙyace da dariya suna kallon Jalim domin sun san cewa dashi Faruƙ yake.
     " Tabɗijan." Inji Safyan.
     " Hala me ya faru?" Faruƙ ya tambaya.
     " Wata tusa ce Jalim ya saki a ranar da zamuyi project defence."  Anan suka ƙyalƙyace da dariya suna sauraren Safyan. " Ina faɗa muku jin abunan kake ɓarrrrrrr sai da hall ya amsa." Anan suka ƙara ƙyalƙyacewa da dariya suna kallon Jailm. 
     " Kasan gogan naka mayen wake ne." Inji Yazid. 
Shi kuwa Jalim shiru yayi da yake ba mai yawan magana bane, mafi yawan lokutta idan suna tsiyarsu sai dai yayi shiru yana saurare. Haka suka yita hira cikin nishaɗi, shi kuwa Jalim yana saurarensu wani lokaci ya amsa wani lokaci kuma ya sharesu. Wasa wasa sai gashi tafiya tayi nisa, a wannan lokaci kowanensu yayi tsit sabida gajiya, shi kuwa Faruƙ sai cin taya yake ba sassauci, haka suka yita ratsa dazuzzuka har rana ta fadi liƙis, sa ar da suka samu shine a kowane checkpoint basu shan wahala domin nan take ake basu umarni su wuce, duk da rana ta faɗi basu tsaya ba sai gudu suke domin salla ce kawai ke tsayar dasu. Sai da duhu ya fara shigowa sa anan suka shiga border wanda zai sadasu da destination ɗinsu. A cikin wanan border da suka shigo sun sha wahala sosai domin sojojin dake aiki a checkpoint ɗin basujin Hausa, daga French sai English suke speaking kuma gasu da tsanani.
Page 7      
Sa ar da suka samu shine Faruƙ yanajin French, Faruƙ ne yayiwa sojojin magana har suka shawo kansu, sai da ƙyar sojojin suka basu umarnin wucewa domin sai da kowanensu ya nuna National I D Card daganan kuma suka faɗi maƙasudin tafiyarsu. Bayan sun shigo wannan sabon yanki sai  kowanensu ya buɗe idanu yana kalle kalle domin sun san da cewa sun shigo sabon wuri. Faruƙ yana cikin tuƙi ko me ya hango  sai ya taka burki da ƙarfi, anan motar tayi wani juyawa daga nan kuma ta kauce hanya, cikin tsananin firgita Safyan ya farka da yake ya fara angaje, motar na tsayawa sai kan Faruƙ ya bugu daga nan bai ƙara sanin inda yake ba.
Anan su Jalim suka fito gigice daga nan suka yo kan Faruƙ wanda har yanzu a done yake da alama bai san inda yake ba.
    " Wai meye ya haddasa wannan hatsari?" Yazid ya tambayi Safyan.
    " Gaskiya ban sani ba domin angaje nake." Inji Safyan. Jalim ne ya fito da Faruƙ daga nan sai suka riƙa masa suka fito dashi tare, a gefen titi suka ajiyeshi suna masa fifita da yake motar tayi wrong park ne a gefen titi.
     " To yanzu meye abunyi?" Yazid ya tambaya.
     " Mu kaishi asibiti mana..." Inji Safyan.
    " Kada ku manta mu baƙi ne a wannan yanki sabida haka ba inda muka sani, kuma idan mukace mu kaishi asibiti zasu iya zabga mana kuɗin da bazamu iya biya ba. Kunga kenan abunda ya kamata muyi shine muyi masa addu a daga nan mu haɗa masa da irin magungunanmu na gargajiya. " Inji Jalim. Anan suka gyaɗa kai cikin alamar aminta. Safyan ne ya fara yi masa addu a shi kuwa Yazid sai ya tsinto furen itatuwa yana shafawa kan Faruƙ domin jini ne ke fita ga hancinsa. Shi kuwa Jalim sai ya shiga motar yana tayarwa domin ya gani ko zata tashi, sai da ya ɗau lokaci yana wahala amma mota ba alamar tashi. Anan Jalim yayi tsaye yana tunanin mafita, gasu dai a tsakiyar daji kuma a cikin dare, ko mota bata giftawa saman titin balanata su nemi lift.  Suna ciki hakane sai suka jiyo sautin mota a can nesa, tashi tsaye sukayi domin ganin ko wace irin mota ce, a haka sautin motar ya cigaba da kusanto su har sai da takai ga motar suna gani a saman titi. Mota ce Lorry mai dogon body, irin motar nan da ƙauyawa ke amfani da ita idan zasu shigo birni, sai kaga mutum uku a gaba kusa ga direba su kuma sauran mutane a can baya tare da shanunsu da sauran komatsansu. Ita wannan mota da suka hango ba passengers a ciki, direba kawai ne ke tuƙi shi kaɗai. Jalim ne ya tsaya tsakiyar titi yana yiwa direba alamun ya tsaya, kuma cikin sa a direban na zuwa daf dashi sai ya tsaya. A nan Jalim yayiwa direban bayani akan ko zai iya rage musu hanya ya ajiyesu a wani ƙauye idan yaso zuwa gobe sai su dawo su duba motarsu.
Page 8     
Da yake direban yanajin Hausa a nan ya aminta daga nan sai suka shiga motarsa bayan sun  tallabo Faruƙ, Jalim ne ya shiga gaba kusa ga direban su kuma su Safyan a bayan body ɗin motar suka hau bayan sun aza Faruƙ wanda yake nishi daƙyar.  A haka direban yaci gaba da mulmula motarsa yana keta dazuzzuka har ya iso wani dan ƙaramin ƙauye, kai tsaye ya nufi gidan sarkin ƙauyen dasu inda ya gabatar dasu daga nan ya tafiyarsa. Sarkin ƙauyen mai suna Lamitu yayi murna sosai da ya yaji labarin su Jalim da abunda ya fito dasu daga gida. Jalim ba ƙaramin ƙoƙari yayi ba wurin baiwa Lamitu wannan labari, Anan Lamitu ya basu masauki kuma yayi musu alƙawarin cewa gobe zai basu bakanike wanda zai duba motarsu.
   " Da yake mu yan ƙabilar Tubu ne amma munajin Hausa." Inji Lamitu bayan ya gyara rawaninsa dake shirin faɗuwa. " Asalinmu shine a cikin Sahara amma sabida wasu dalillai shine muka dawo anan muka kafa ƙauye domin munada muradi na son yin noma da sauran buƙatu, amma har yanzu akwai ƴan uwanmu dake cikin Sahara." Inji Lamitu. A wannan lokaci da Lamitu ke bada labari su Jalim   zaune suke a saman tabarma a cikin masaukin da aka basu, shi kuwa Lamitu ya shigo ne ya ƙara yi musu barka sai fira ta ɓarke tsakaninsu. Faruƙ ya fara samun sauƙi  domin daga zuwansu  Lamitu ya shafa   masa magani a wurin daya samu rauni, da yake kansa ne ya bugu wanda yayi sanadiyar sanya jini fita hancinsa.
 " Akwai wasu ƴan uwana da zasu fita neman zinari gobe, kunga kun samu abokan tafiya iyaka kubi bayansu. " Lamitu yana faɗar haka sai ya zaro watta takadda a cikin aljihunsa, ita wannan takadda map ce.   Anan ya aza finger ɗinsa ga wani point a cikin map ɗin, " Wannan shine taswirar Agadez, zakubi ta cikin Agadez daga nan sai kubi wannan hanyar." Anan ya aza finger ɗinsa ga wani layi dogo, " Wannan hanya itace zata kaiku a cikin saharar da zaku nemi zinari. Amma kada ku manta kafin ku shiga Agadez ɗin dole sai kun ratsa garuruwa daban daban. Da yake akwai garuruwan dake makwabtaka da Agadez  irin su Mayahi, Bouza da sauransu. " 
" To Niamey fa?" Safyan ya tambaya. " Na aza ko zamu ratsa yankin Niamey kafin mu shiga cikin saharar!" 
" Aa ba ruwanku da Niamey!" Inji Lamitu. " Amma ban sani ba watakila abokan tafiyarku subi hanyar, iyaka dai ku tabbata kuna biye dasu domin sune suka san hanyar." Inji Lamitu yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya. A wannan lokaci Faruƙ ya fara farfaɗowa domin duk bayanin da Lamitu ke faɗa to yana akan kunnensa. 
" Inada tambaya." Inji Faruƙ. Anan suka maido hankalinsu a wurinsa domin suji abunda zai faɗa. " Waɗanne irin ƙabilu ne ke rayuwa a cikin sahara?" Inji Faruƙ.
Page 9    
" Kasani kowa zai iya rayuwa a cikin sahara domin abun ra a yine." Inji Lamitu, " Amma ƙabilun da ake kyautata zaton cewa mafi yawansu za a iya samunsu ga sahara sune ƙabilar Buduma, ƙabilar Zarma, ƙabilar Songhai da sauransu, ina fatan ka fahimta."
" E na gane." Inji Faruƙ.
        " Ku jirani zan tafi na dawo." Inji Lamitu, cover shoes ɗinsa ya sanya daganan ya fita ɗakin bayan ya bar musu map ɗin suna dubawa. Cikin ƙanƙanin lokaci ya dawo ɗauke da tray cike da dambu sai jug mai ruwa da kuma cups. " Yanzu kuci kusha zuwa gobe sai mu tattauna." Yana faɗar haka sai ya fita ɗakin. Ai kuwa kamar ya san da cewa sunajin yunwa domin daga fitarsa suka yiwa dambun nan dirar mikiya harda ture ture wurin kai loma. A nan Safyan ya fizgo wata loma wadda ko ba a faɗa ba kasan tafi ƙarfinsa, ai kuwa yana dannata sai fitar tusa kakeji randam, a nan suka ƙyalƙyace da dariya suna kallonsa, a na cikin hakane sai ga Faruƙ ya fizgo tasa lomar, ai kuwa tana shiga shima yana sakin tasa tusar, a haka dai sukayi ta wazgo tusoshi harda Yazid, Jalim kawai ne ya tsira bai yi tusa ba. Ai kuwa Jalim na ganin haka sai ya juyo kansu, a nan ya fara zabga musu tsiya, duk tsiyar da suka yi masa a cikin mota sai da ya rama tsaf ba tare da rage komi ba. A nan sukayi shiru cike da tunani, wai dama haka duniya take, idan kaga mutum yana aikata laifi  to kayi masa addua da wa a zi ya shiryu, idan bazaka iyaba to kada kayi masa gori domin baka sani ba ko zaka iya aikata irin laifin daya aikata. A lokacin da suna University Jalim ne mai tusa domin al adarsa ce idan yanacin abinci to dole ne yayi tusa, kuma tusar tana fita ne ba tare da son ransa ba domin duk yadda ya matse tusar sai sound ya fita. A bisa wannan dalili yasa abokansa su Safyan, Yazid da Faruƙ ke masa tsiya a ko yaushe, amma sai gashi yanzu abun ya dawo kansu har takai cewa shi kaɗai ne ya tsira daga wannan masifa. A haka suka yita cin abincin suna fira har kowanensu ya gundura, duk da yawan haɗamarsu sai da suka rage abincin da kuma ruwan shan. Daga nan suka juya bacci har safiya ta waye.  Masifar ƙarar dake tattare da tusar da Safyan ya Mazgo dai dai kusurwar hancin Jalim shine yayi sanadiyar tashin Jalim a gigice sabida azabar warin daya  keta masa haddin hanci. A guje Jalim ya fito ɗakin yana tsaki cikin fushi, daga nan kuma sai ya ƙara shiga ɗakin inda ya tarar da Safyan din a zaune.
   " Amma kai doki ne, ya zakiyimin tusa a cikin baki ni da farko nama aza bindiga ce aka halba shi yasa na tashi gigice, ko kaɗan irin wannan bai dace ba." Inji Jalim.
  " Kayi hakuri aboki kaima kasan lalura ce." Haka Safyan ya fada cikin murya mai laushi.
  " Lalura, wace irin lalura kuma, a can shekarun da suka wuce nima haka nake faɗa muku amma baku sauraren na." Inji Jalim.
Page 10 
" Idan nace muku lalura ce sai kuce ƙarya ne da gan gan ne nake sakin tusa duk inda naga dama, Sabida haka idan zakayi tusa Ka duba girman ALLAH ka koma gefe idan ka gama sai ka dawo. " A nan Safyan ya done kansa cikin jin kunya domin yasan bai kyauta ba duk da shima ba akan ransa abun ya faru ba, a nan ne ya fara dana sanin tsarguwar da sukewa Jalim  a lokacin da yake cikin irin wannan lalurar ta tusa. A wannan lokaci Faruƙ da Yazid sun farka kuma kowanensu tusar yakeji iyaka dai suna matsewa ne domin kada su cutar da Jalim. A cikin hakane dai abun yafi ƙarfinsu, a nan suka tattake iya ƙarfinsu suka halbo wata irin guduma mai tsananin ɗoyi. Shi kuwa Jalim daya fito a guje sai da Lamitu ya tarosa yana tambarsa lafiya. Anan Jalim ya faɗa masa ba lafiya ba. Shi kuwa Lamitu daga jin haka sai ya nufi ɗakin, a lokacin da Lamitu ya taka ƙafarsa zuwa cikin ɗakin a wannan lokaci ne wata tusa ta kubcewa Faruƙ, cikin sauri Lamitu ya fito yana nishi daƙyar. 
" Kuyi sauri ku kimtsa domin waɗanda zakuyi tafiya dasu suma suna can suna shiri." Inji Lamitu. Yana faɗar haka sai ya juya. Daga nan sai Jalim ya koma ɗakin ya faɗama abokansa saƙon Lamitu, ai kuwa sunajin haka sai suka ɗau himma, suna gama kimtsawa sai ga Lamitu ya dawo ɗauke da tray cike da soyayyen dankali sai kuma kunu a cikin jug da kuma cups, yana ajiyewa sai ya juya ya fita ɗakin, a nan su Jalim suka hau wannan dankali cikin rashin mutunci har saida suka cinyesa gabaki ɗaya tare da kunun. Suna ajiye cups ɗin sai ga Lamitu ya shigo cikin sauri. 
" Kuyi hanzari gasucan sun shirya yanzu ku suke jira." Anan su Jalim suka   fito ɗakin shi kuwa Lamitu sai ya jagorancesu zuwa wani ɗaki, daga shigarsu ɗakin sai ya ɗauko Shovel shovel da hoe da scythe yana rarraba musu, ba ƙaramin jin daɗi sukayi ba domin basu tanadi kome dangane da mining ɗin da zasuyi ba amma sai gashi yanzu sun samu kayayyakin cikin sauƙi. Daga nan sai ya ɗauko wata leda ya miƙawa Jalim.
" Wannan tanti ne kuma amfaninsa shine kuyi rumfa dashi idan dare yayi yadda zakuyi bacci cikin natsuwa, idan kuka walwalesa zaku gansa kamar ɗaki." Lamitu yana faɗar haka sai yaji ana bubbuga masa ƙofa. Anan ya fito tare dasu Jalim, mutum ne namiji suka gani a tsaye sanye da rawani da riga doguwa, sai wasu cover shoes dinsa. Lamitu yana ganinsa sai ya canza yare, anan suka fara magana a cikin halshen Tubu, su kuwa su Jalim kallonsu kawai suke domin basu san abunda suke faɗa ba. Bayan sun gama maganar ne sai Lamitu ya juya wurinsu.
" Wannan shine Dohori, kuma shine bakaniken da zai gyara muku mota kuma yana cikin waɗanda zakuyi wannan tafiya dasu. Zaku shiga motar Dohori dashida abokan tafiyarsa domin na riga na faɗa musu inda motarku take."
Page 11  
      " Da kun isa wurin zai fito ya gyara muku mota kuma kada ku basa komi domin na biyasa kuɗin aikinsa, bayan an gyra motarku sai ku shiga motar kuna bin bayan motar Dohori har ku isa cikin saharar dana faɗa muku. Kuma ina tunanin jiya na bar muku taswira ko." 
     " E gatanan." Anan Jalim ya fito da map ɗin.
     " Ku ajiye wannan taswirar kuyi amfani da ita" Inji Lamitu. Anan Lamitu ya nuna musu yadda ake haɗa tantin da kuma yadda ake naɗesa daga nan kuma ya basu torclight  ɗaya  ɗaya.
    " Yanzu sai kubi Dohori domin shine zai muku jagoranci a wurin da zaku tafi." Inji Lamitu. Anan suka yi masa godiya daga nan sukabi bayan Lamitu. To anan suka gane cewa gidan babba ne duk da kasancewarsa ginin laka amma kuma ya tsaru. Bayan sun fito gidan ne sai suka fara kallon yanayin garin. Gidajen dake garin duk na laka ne kuma da ganin sutarar mutanen garin zaka iya gane cewa sunada nasu al adu. Mazan garin na sanye da doguwar riga da wando da kuma rawani wanda ya rufe fuska idanu kawai ake gani, sai wasu cover shoes masu ban tsoro. Haka suma matan sun rufe jikinsu kaf yadda ba a ganin kome, mafi yawan matan garin sukan  rufe fuskarsu ta yadda idanuwansu kawai ake gani. Haka su Jalim suka cigaba da kallon mutanen wannan gari suna karantar halayensu. Language ɗin da mutanen ke furtawa shine Tubu, haka tunanin su Jalim ya kasance. Bayan su Jalim sun  iso motar Dohori, sai Dohori ya faɗa musu cewa su hau bayan body su zauna. Da yake motar lorry ce kuma akwai wasu mutane a saman body  ɗin kowanensu ya rufe fuska da rawani, su waɗannan mutane dake saman lorry  tare suke da bag bag  ɗinsu da kuma shovel shovel, anan su Jalim suka taka suka hau, shikuwa Dohori a can gaba ya zauna kusa ga direba dashi da wasu abokansa. Da yake motocin uku ne kuma duka lorry ne, motocin iri ɗaya ne domin har colour ɗinsu iri ɗaya ne, motar Dohori itace a gaba, sauran motocin biyu suna biye. A nan aka tayar da motocin aka fara tafiya. Shi kuwa Lamitu sai faman ɗaga musu hannu yake yana musu bankwana. Anan su Jalim suka lura sabida haka suka ɗaga masa nasu hannun. Sai da sukayi tafiya mai ɗan nisa kafin su cimma titi. Daganan aka fara cin taya ba sassauci. Da yake mutanen dake cikin wannan mota tasu Jalim yan ƙabilar Tubu ne sabida haka sai suka yita hira da yarensu. Su Jalim sai ji suke ana gwalabniya amma ba damar su tanka. Sai da sukayi tafiya mai nisa kafin su cimma dai dai wurin da motar su take. Tun daga can nesa su Jalim suka hango motarsu, ba karamin daɗi ne ya lulluɓesu ba ganin cewa ba abunda ya faru da motar. Suna isa wurin sai duka motocin sukayi parking. Dohori ne ya fito riƙe da yar jakarsa ta kanikanci, su Jalim na ganin haka sai suka diro suka biyo bayansa. 
Page 12      
" Ina makullin motar?" Dohori ya tambaya. Anan Faruƙ ya mika masa makullin. Shiga yayi cikin motar ya kunna amma bata tashi ba, yana ganin haka sai ya dawo gaba ya fara taɓe taɓensa. Yana gamawa sai ya dawo ya kunna motar, kai tsaye ta tashi. Daganan sai ya dubesu cikin murmushi.
" Zaku iya shiga ciki. Yanzu motarku itace ta huɗu a cikin jerin motocin da ake wannan tafiya dasu, sabida haka zaku biyo bayanmu daganan har mu isa wurin." Dohori yana faɗar haka sai ya juya ya nufi motar da yake. Faruƙ na ganin haka sai ya nufi motar da nufin tuƙawa. Cikin sauri Jalim ya tarosa.
" Kada ka manta bakada lafiya kuma da alama gajiyar jiya na nan a tare dakai, to me zai hana kaban motar na tuƙa." Inji Jalim. Anan Faruƙ ya aminta da maganar Jalim, sabida haka sai ya dawo baya tare da Safyan, shi kuwa Jalim sai ya tuƙa motar, Yazid a kusa dashi. Cikin kwanciyar hankali Jalim ke tuƙa motar yanabin sahun motocin da suke tafiyar tare, a haka suka cigaba da tafiya ba sassauci ko hutu, basu tsayawa inba wani abune mai muhimmanci ba. Tafiya dai dakai tafiya domin sai a cikin dare suka isa Bouza, a bisa wannan dalili sai suka yanke shawarar yin bacci a nan idan yaso zuwa gobe sai suci gaba da tafiyar, a nan suka faka motocinsu a gefen titi daga nan kowa ya diro yana sha anin gabansa, su kuwa su Jalim zamansu sukayi a cikin motarsu daga nan suka  ɗebo cin cin ɗinsu  tare da soft drinks, a nan suka zauna suna ci suna fira har suka gamsu. Daganan suka kishingiɗa kafin kaceme bacci yayi awon gaba dasu. Anan suka yita sharar bacci ba tare da sanin abunda yake faruwa ba. Jalim ne ya fara farkawa sanadiyar tusar dasu Faruƙ suka fara mazgo masa. Anan ya tayar dasu daga nan ya fita motar, dubawar da zai yi haka sai yaga sauran motocin su Dohori su uku babu ko ɗaya. Anan ya dafe kai domin yasan sun tafi ne kawai, to amma wannan wace irin rayuwa ce idan har zasu tafi me zai hana su tayar dasu? Anan su Faruƙ suka diro suna mamakin wannan abu.
" Yanzu mu fara kimtsawa idan yaso sai mu tattauna wannan maganar zuwa an jima." Inji Jalim. Anan suka gyaɗa kai cikin alamar yarda daga nan sai kowanensu ya fara sha anin gabansa, sai da suka kimtsa sarai sa anan suka yi tsaye a gaban mota suna tunanin mafita.
" Ni a ganina idan mukayi amfani da wannan map ɗin da Lamintu ya bamu to zamu iya shiga cikin saharar ba tare da mun sha wahala ba." Inji Safyan.
" Hakane amma ai kasan irin wannan map ba kowa ke ganeta ba sabida wasu rubutun da French aka yisu." Inji Jalim.
 " To ai Faruƙ yanajin French kaga kenan zai iya jagorantarmu." Inji Yazid. 
Page 13      
Dukkaninsu dawo da hankinsu sukayi ga Faruƙ domin suji abunda zai ce. Shi kuwa Faruƙ gyaran murya yayi kafin ya fara magana:
    " Zan iya jagorantarku amma ku sani a cikin map ɗin sun bada warning akan wata masifa da ake cema Black Storm wato baƙar guguwa, a cikin karance karance da nayi na littafai masu bincike sun bayyana cewa ita wannan baƙar guguwa har yanzu ba a san mafarinta ba  kuma idan ta taso to tana haɗiye mutane ne kamar yadda mutum ke haɗiye abinci. To kunga wannan masifa ce babba amma idan kun yarda mu tafi shi kenan."
   " Amma kai Faruƙ ban taɓa sanin bakada tunani ba sai yanzu." Inji Safyan. " Kada ka manta mun fito neman arziƙi ne ba wai neman tsiya ba. Kuma yanzu  idan muka koma gida me zamu faɗawa iyayenmu tunda sun dagora damu ne. Sabida haka kabar maganar wata baƙar guguwa kawai idan zaka jagorancemu to mu tafi kawai." Safyan yana zuwa nan a zancensa sai sukaji oda a bayansu. Mota ce Jeep ta tsaya daga nan sai wani bature ya fito a ciki, tattakowa yayi zuwa wurinsu bayan ya gaida su da kalmar " Hello."
   " You have stayed here for a long time, is everything okay?" Inji baturen. 
   Ma ana :(Kun jima sosai a wannan wuri ina fatan dai ba wata matsala)
  " Everything is alright sir, we were only discussing on our personal issues."Inji Jalim
 Ma ana:(Komi yana lafiya lau ranka shi daɗe iyaka dai muna tattauna ne game da alamurran rayuwarmu)
" Okay, My name is Jack Willow from United States, actually I am Archaeologist, and I came here for the purpose of research and study."
( Sunana Jack Willow daga Amurka. Kuma ni gwani ne akan sashen binciken tarihin mutanen da suka gabacemu, kuma nazo wannan wuri ne domin nayi bincike kuma na kara samun ilimi."
" I am Jalim and this is my team, and yes we are here for mining."Inji Jalim.
 (Sunana Jalim waɗannan kuma sune mabiyana kuma munzo wannan wuri ne domin mu binciko albarkatun dake cikin ƙasa)
" Oh! This is good, but what are you going to find during your mining process." Inji baturen.
(Hakan yanada kyau to amma menene kukeda muradin  bincikowa a cikin ginar da zakuyi)
" Our ambition is to find goals and diamond and if there is then precious ornament." Inji Jalim
( Burinmu shine mu nemo zinari da kuma damon kai harma da ƙarafuna masu tasiri  idan akwai)
" And this is our map, I don't know if you can help us out." 
( Wannan itace taswirarmu kuma ina fatan zaka iya taimaka muna) Inji Jalim bayan ya miƙawa baturen taswirar da Lamitu ya basu. Anan baturen ya kalli map din cikin natsuwa kafin ya fara magana kamar haka:
Page 14      
   " I can Lead you to your destination, but you have to be aware of the Black Storm, our intelligence are still making research upon it, and immediately they were done I can update you about it. Now give me your phone number." Inji Baturen.
   ( Zan iya jagorantarku har zuwa wurin da kuke nema, amma fa kuyi hattara da baƙar guguwa, masu dauko muna bayani har yanzu suna akan aikinsu na bincike akan wannan guguwar kuma idan sun kammala zan iya sanar daku abunda suka gano sabida haka yanzu kaban numbarka." Anan Jalim ya baiwa baturen numbarsa daga nan sai baturen shima ya basa tasa inda sukayi saving.
   " I will give you my camera, and I need pictures and vedios of the places you are going." Inji baturen
    (Zan baka kamera, kuma inaso ka ɗaukomin hotuna da kuma bidiyon wurin da zaku tafi) 
Anan baturen ya fito da ƙaramar kamera a cikin motarsa ya baiwa Jalim. Daga nan sai ya nuna masa yadda zai yi amfani da ita, yana gama nuna masa sai ya umarcesu dasu biyo bayansa. Anan baturen ya shiga jeep ɗinsa  su kuma su Jalim suka shiga tasu motar Hilux. Jalim ne ke tuƙi sai Yazid a kusa dashi, Faruƙ da Safyan kuma a baya. Cikin matsanancin gudu Jalim yaja motar ba sassauci. Haka suka dinga wazga namijin gudu sai kace walƙiya. Sune basu iso border Agadez ba sai da rana ta fadi liƙis, anan baturen yayi parking daga nan sai Jalim yayi nasa parking a kusa ga jeep ɗin baturen.
   " I will stop here, now it's your turn to continue your journey alone." Inji Baturen.
    (Anan zan tsaya, sabida haka yanzu lokaci ne da zaku cigaba da tafiyarku ku kaɗai) Anan baturen yayi musu kwatancen saharar da suke nema sai da ya tabbatar sun fahimta sa annan ya juya motarsa ya tafiyarsa. Shi kuwa Jalim taka motar kawai yayi ya figzi motar da matsanancin gudu daga nan ya faɗa cikin Agadez din, haka Jalim yabi kwatancen baturen yana sharara gudu kuma yana bin map ɗin, sai a tsakiyar dare suka fara hango dishi dishin saharar a can nesa dasu, Jalim ƙara gudun motar yayi dai dai gwargwado, a wannan lokaci Jalim yasha wahala sosai domin su Faruƙ in banda zuba tusoshi ba abunda suke, bacci suke amma tusa ke fita kai dagani kasan ba lafiya ba. Tafiya tayi tafiya sai gashi Jalim ya shiga cikin saharar, a wannan lokaci dukkaninsu sun yi bacci in banda Jalim dake tuƙin motar, sai da yayi tafiya mai nisa kafin ya iso dai dai wurin da baturen ya faɗa masa. Anan ya taka burki da ƙarfi wanda hakan yasa su Faruƙ farkawa. Duban saharar sukayi iya ganinsu basuga ƙarshenta ba. Daganan sai suka fito daga cikin motar, tantin da Lamitu ya basu suka ɗauko suka buɗasa kamar rumfa, daga nan sai suka shiga ciki da nufin gobe da safe zasu fara aiki.
Page 15     
Sabida baccin dasu Faruƙ sukayi a cikin mota sai abun ya kasance a wurinsu cewa basuda muradin yin bacci a wannan lokaci, shi kuwa Jalim sabida gajiya tuƙin motar ba abunda yakeso in banda baccin. Babban tashin hankali a wurin Jalim shine daya fara baccin sai warin tusar su Faruƙ ya tayar dashi, ba yadda bai yiba domin ganin yayi bacci amma abu ya gagara, dole hakanan ya kishingiɗa yana tsaki cikin tsananin takaici. Bayan safiya ta waye ne sai su Faruƙ sukayi tunani sosai akan abunda ya faru jiya, bako shakka sunada masaniyar cewa basu kyauta ba domin sun hana Jalim bacci sabida tusoshin da suke duk da cewa lalura ce ba wai son ransu bane. A wannan lokaci Jalim na waje yana goge baki.
      " Idan Jalim ya shigo ya kamata mu basa haƙuri akan abunda ya faru domin gaskiya bamu kyauta ba." Inji Faruƙ.
     " Nima haka nakeso na faɗa," Inji Safyan. " Amma kafin nan inaso wannan abu daya faru a wurinmu ya kasance darasi, ma ana idan mukaga mutum a cikin wata lalura to kada muyi masa gori tunda yanzu idan zan tuna a can da Jalim ne keda wannan lalura ta tusa amma gashi yanzu abun ya dawo a wurinmu. To kunga kenan duk halin da mukaga wani a ciki mu ɗauka cewa ƙaddararsa ce kada mu musguna masa." Inji Safyan.
   " Abunda ka faɗa gaskiyane." Inji Yazid. Jalim na shigowa cikin tantin sai suka tada maganar, anan suka basa haƙuri akan dukkan abunda ya faru. Kasancewar Jalim mai haƙuri sai yace ba matsala ya yafe musu, to abunda ya baiwa su Faruƙ mamaki shine tunda Jalim yace ya yafe musu sai tusar ta tsaya gaba ɗaya. Daga wannan lokaci basu ƙarayin wata tusa ba.  Anan suka janyo cin cin ɗinsu tare da bottle drinks ɗinsu. Bayan sun karya kumallo sai suka naɗe tantin suka mayar dashi a cikin motar, shovel shovel da hauya suka janyo domin fara aikin, a wannan lokaci sauran mutanen da suka fito neman zinari sun kasu ƙungiya ƙungiya kowanensu sai faman gina yake, mutanen lulluɓe suke da rawani sai doguwar riga da cover shoes masu ƙarfi sai faman gina suke, anan Jalim yaja mabiyansa, sai da suka zagaya, anan suka samu wuri dai dai yadda baturen ya kwatanta musu cewa zasu samu zinari, Jalim ne ya faɗawa kowanensu ta inda zai ginawa daga nan suka fara aiki. Suna cikin aikin ne sai Faruƙ ya daina, ajiye shovel ɗinsa yayi yana kallon wata yarinya dake zaune a can nesa dasu, lulluɓe take da rawani hakama jikinta ta lulluɓe shi ta yadda ba a ganin kome, fuskarta kawai ake hangowa. Anan su Jalim suka mayar da kallonsu a wurinsa.
    " Kai lafiya kake kallon matar mutane?" Inji Jalim, anan ne Faruƙ ya dawo da hankalinsa a wurinsu.
   " Kaga wannan matar da nake kallo." Inji Faruƙ.
Page 16       
" E na gani." Inji Jalim
" Idan zaka tuno a lokacin da ina tuƙa mota kafin muyi nisa sosai ai sai da muka samu hatsari ko?" Inji Faruk.
" E hakane." Inji Jalim.
" To wannan matar ce na gani a saman titi kuma a wurin kauce mata ne muka samu hatsari, to abunda yaban mamaki shine ko me takeyi a nan!"Inji Faruƙ. Anan su Jalim suka mayar da hankalinsu ga wannan matar suna kallonta cikin mamaki. Bako shakka kyakkyawa ce duk da cewa ta lulluɓe jikinta sarai. Shi kuwa Faruƙ nufarta kawai yayi da alama yanada muradin yi mata magana, tun daga nesa yake tunani da wane yare ya kamata yayi mata magana, matar ta kasance fara sol, kirar jikinta kuma thick slim. Faruƙ na zuwa wurinta sai yayi magana da yaren French.
" Bonjour." Inji Faruƙ.
Ma ana ( Ina kwana) Matar ɗago kanta tayi ta masa kallon tsaf kafin ta amsa masa kamar haka:
" Bonjour comment vas-tu." Inji matar
Ma ana ( Lafiya lau ya kake) Murmushin jin daɗi Faruƙ ya saki jin tana tambayarsa lafiyarsa. Daga nan sai faruƙ yayi mata wata magana kamar haka:
     " Il semblait que je te connaissais."
Ma ana( amma fa kamar na taba ganinki a wani wuri!) Daga nan sai matar ta kallesa cikin natsuwa kuma har yanzu tana zaune a inda take shi kuma a tsaye, daga nan sai ta tambayesa:
      " où m'as-tu connu?"
     Ma ana ( Wane wuri ka taba ganina)
     "  Je t'ai vu une fois quelque part sur la route." Inji Faruƙ.
     Ma ana( Kamar na taɓa ganinki a saman titi)Daga nan sai matar ta amsa masa kamar haka:
   " Sincèrement je ne suis pas celui."
   Ma ana ( Gaskiya bani bace) Ba yadda Faruƙ bai yiba domin ta faɗa masa gaskiya amma taƙi duk inda ya ɓullo sai ta tokare wurin, daga ƙarshe dai ta faɗa masa sunanta Hassina. Kuma tana tare da ƴan uwanta ne, sun shigo wannan saharar ne domin neman zinari.
Page 17     
 A cikin wannan hirar da sukayi ne Faruƙ ya gano cewa tanajin Hausa sosai, daga nan sai suka cigaba da hirar tasu da Hausa, ba yadda bai yiba ta faɗa masa ƙabilarta amma taƙi faɗa. Daga nan sai ya daina tambayarta bayan ya ƙulla abota mai ƙarfi da ita. Su Jalim na kallonsu kawai sai sukaga matar ta biyosa. Anan Faruƙ ya jeru da ita yana tafiya yana mata hira ita kuma tana murmushi. Su Jalim sun yi mamaki sosai yadda akayi Faruƙ ya saye wannan matar cikin ƙanƙanin lokaci, basu ankara ba sai ga matar a gabansu tare da Faruƙ. Anan Faruƙ yabisu ɗaya bayan ɗaya yana faɗa masa sunayensu da kuma wasu bayanai game dasu duk a cikin yaren Hausa. Bayan ya gama gabatar dasu a wurinta sai ta faɗa masa cewa zata koma wurin ƴan uwanta suci gaba da aiki amma zata kawo musu ziyara a cikin dare. Daga nan sai Hassina ta tafiyarta su kuma suka cigaba da aikin tono ƙasa, kowanensu sanye yake da facing cap dinsa sabida kariya daga rana. Haka dai suka cigaba da aiki har rana ta faɗi, da yake kowanensu yana rataye da yar jakarsa, duk wanda ya tono zinari sai ya jefa a cikin jakarsa.
A cikin darene sosai su Jalim sukayi shimfiɗa a waje domin a wannan lokaci basuda ra ayin bacci a cikin tantin sabida iskan da ake kaɗawa mai daɗi sun fiso su tsaya a waje. Suna cikin hira ne sai ga Hassina ta faɗo musu kamar daga sama tare da wata ƙawarta.
" Na aza bazaki shigo ba." Inji Faruƙ.
 " Gashi kuwa na baka mamaki tun da nazo tare da ƙawata Zamana." Inji Hassina bayan ta zauna tare da ƙawarta.
 " Sannunku dai." Inji Zamana.
 " Yauwa sannunki dai." Su Jalim suka amsa tare.
 " To yanzu wane irin labari zaki bamu." Inji Faruƙ.
 " To wane iri kukeso?" Hassina ta tambaya.
 " Mun fison ki bamu naban al ajabi." Inji Faruƙ.
 " To ku saurara yanzu zan fara." Inji Hassina. Anan su Jalim suka kasa kunne suna saurare wane irin labari ne zata bayar. Ita kuwa Hassina sai ta fara labarinta kamar haka:
A wani lokaci, an taɓayin wani ɗan sarki dayace bazai auri ko wace mace ba sai wadda gira ( Eyelashes) bata fito mata. mafi yawan mata sun yita aske girarsu amma da sun zo sai yace a jira bayan mako daya idan girar bata fito ba. Wasu da sun jin haka zasu tsere wasu kuma sai sun gwada sa arsu. 
Page 18      
Abunda yasa yarima yace bazai auri ko wace mace ba sai marar gira  shine, wata rana yana yawo a cikin daji saman dokinsa sai ya hango wasu yara mata suna faɗa, dayar sai ta sanya faratta ta yage girar dayar, ai kuwa yin hakan keda wuya sai ga gira ta cire gaba daya. Anan yarima ya kalli ita wannan yarinyar da aka cirema gira sai yaga a yanzu da batada gira tafi kyau bisa ga can da. Anan yayi tunani dama ace zai iya samun mace wadda gira bata fito mata da shi kenan. To a bisa haka ne sai yayi sanarwa cewa duk yarinyar da gira bata fito mata shi zai aureta. Ana cikin hakane wata rana sai ga wata yarinya kyakkyawa ta fito wadda batada gira, anan ta faɗawa yarima zatayi shekara daya dashi kuma idan har gira ta fito mata a cikin wannan shekarar to yayi mata duk hukuncin dayaga dama. Haka kuwa akayi, sai da aka shekara ɗaya amma gira bata fito mata ba. Anan yarima ya tabbatar da cewa yanzu kam ya samu irin yarinyar da yakeso wadda gira bata fito mata. Daganan sai yarima ya tuntuɓi yarinyar da maganar aure ita kuwa tace ta aminta amma kafin nan tanaso ya rakata wani wuri amma su biyu kawai zasu tafi, kasancewar yarima jarumi sai ya aminta. Sai da sukayi tafiya mai nisa  sa' annan suka iso wani ƙatafaren kogo. Anan suka shiga ciki, bayan sun shiga ciki sai yaga ashe kogon masarauta ce babba, anan ta zaunar dashi saman kujera ta alfarma daga nan sai ta kawo masa kayan itatuwa domin ya motsa bakinsa. Ba tare da tunanin kome ba ya fara ci, ai kuwa yana cikin cin itatuwan sai yaga duk gashin dake jikinsa yana faɗuwa kasa, yarima da yake kyakyawa sai gashi ya dawo mummuna ba kyan gani. Anan yarinyar ta kyalkyace da dariya tana kallonsa.
" Kai a tunaninka wace mace zatayi shekara ɗaya gira bata fito mata kuma ka yarda ita?" Inji yarinyar. " To ka sani ni ba mutum bace kuma nayi wannan shiri ne domin na samu galaba akanka, kamar yadda ka wahalar da mata wai bazaka auri ko wace mace sai marar gira  haka kaima zan wahalar dakai domin babu macen da zata iya aurenka a haka. Kuma idan ka koma masarautarku baza a yarda dakai ba domin kammaninka sun canza."  Yarima najin haka sai ya faɗi yana rokonta ta tausaya masa. Daga nan sai ta dubeshi cikin tsana tace. " Zan baka mafita daya, idan har kanaso wannan sihiri ya karye to sai ka koma can masarautarku ka nuna musu cewa kaine yarima ɗan sarki, kuma koda ka faɗi cewa kaine yarima sihirin bazai karye ba sai gaba ɗaya mutanen garin sun yarda da cewa kaine tsohon yarimansu."
Page 19     
   " Kuma inaso ka sani cewa duk wani wanda yasan dakai a masarautar baya nan domin ya mutu. Kuma yanzu sarautar ta fita daga gidanku zuwa wani gida daban. Sabida haka idan tafiya zakayi to ka tafi amma ka sani cewa jikinka ya canza gaba daya, haka muryarka ta canza, tafiyarka ma ta canza, komi naka ya canza to yama za ayi mutanen masarautar su yarda da cewa kaine tsohon yarimansu? Anan ta ƙyalƙyace da dariya daga nan ta ɓace ɓat, shi kuma yarima ya tsunduma cikin duniyar tunani." Hassina na zuwa  anan sai tayi shiru su kuwa su Jalim tsura mata ido sukayi domin suji abunda zatace. " To yanzu alal misali ace kaine wannan yarima dake cikin wannan masifa, wace hanya zakabi domin ka tabbatar wa mutanen masarautarku cewa kaine tsohon yarimansu kuma har su yarda da cewa kaine?" Hassina na faɗin haka sai gardama ta ɓarke tsakaninsu. Anan kowanensu ya bada hujja abunda zaiyi ita kuwa Hassina sai saurare take tana ƙyalƙyatar dariya tare da ƙawatarta Zamana. Haka suka cigaba da wannan gardama har dare ya raba daga nan kowanensu ya nufi makwancinsa haka suma su Hassina komawa masaukinsu sukayi.
      Tun da sanyin safiya su Jalim suka fara aiki, a wannan lokaci ba ƙaramin daɗi suka jiba domin kowanensu ya samu abunda yake buƙata, sun yi gina mai zurfi kuma ciki sa a sun samu zinarin tare da wasu abubuwan buƙata. Suna cikin aikin ne sai Jalim yaga wayarsa na bugawa, yana dubawa sai yaga Jack ne wato wannan baturen daya kwatanta musu wannan saharar.
   " Hi dude how was the finding!"Inji Jack.
   Ma ana( Yane maza, wai ya binciken naku) Daga nan sai Jalim ya amsa masa kamar haka:
   " The finding is good, we just found what we were after."
  Ma ana( Bincike lafiya ne kuma har mun gano abunda muke nema)
" Alright, so what about my camera, hope you did the right thing." Inji baturen.
Ma ana( To ya kamerar dana baku ina fatan dai kayi abunda na gaya maka)
" Yes I did it." Inji Jalim.
Ma ana(E nayi abunda ka fada)
" Alright bye." Inji baturen.
Ma ana ( To yayi sai an jima) Anan baturen ya katse wayar.
Page 20         
Shi kuwa Jalim ɗauko camerar  yayi yana ɗaukar vedios da hotuna da yake tun ranar da suka shigo cikin saharar ya fara aikin. Bayan ya gama amfani da camera ɗin sai ya mayar da ita cikin motar inda ya dawo aikinsa. Bai daɗe da fara aiki ba kawai sai sukaji ihu, anan sukaga sauran mutane masu ginar zinari suna hawan motocinsu suna barin saharar cikin matsanancin gudu, haka masu raƙuma sai dai su haye su zabga a guje. Su Jalim basu ankara ba sai da sukaji ƙarar bindiga, cikin sauri suka mayar da kayansu cikin mota, da matsanancin gudu Jalim ya fizgi motar ya shige wata hanya. Da yake cikin sahara ne motar bata gudu sosai. Bayan sun bar wurin ne sai suka hango mutanen dake riƙe da bindigogi a saman mashuna suke, irin mashunan da ake cema Desert Motorcycles, kowanensu ya lulluɓe fuska da rawani, sai halbin mutane suke ba tare da dalilin kome ba. Sai da Jalim yayi nisa sosai sa annan ya samu wani wuri kusa ga wani tsohon birni.  Anan yayi parking, kai daganin birnin kasan ba kowa a cikin birnin domin wasu katangu sun fara ragargajewa. Jalim nayin parking sai yaga wasu daga cikin masu ginar zinari suna isowa wurinsu a cikin motocinsu, cikin ƙanƙanin lokaci mutane da yawa suka halarta a wurin kowa na fadin albarakacin bakinsa akan abunda ya faru. Su kuwa su Jalim kowanensu yayi shiru sai tunanin mafita suke. Suna cikin wannan hali ne sai sukaga sama tayi baƙi ƙirin kamar hadari, anan wani iska mai ƙarfi ya fara bugawa, Jalim ne yaga wayarsa na ƙara yana dubawa sai yaga jack ne. Anan ya ɗauki wayar ya kara ga kunne.
   " Hi dude, you have to leave that desert now, our intelligence told us the Black Storm is coming on your way right now." Inji Jack.
   Ma ana( Yane maza, inaso na gaya muku cewa ku gaggauta barin wannan saharar domin waɗanda ke bamu bayani sun faɗa mana cewa Baƙar Guguwa tana akan hanyarta na zuwa wurin da kuke yanzu yanzun nan."
  " So what do you want us to do?" Jalim ya tambaya.
  Ma ana ( To me kakeso muyi kenan?"
  " I want you to leave that place now, and you have to give warning to your friends that are in there." Inji Jack.
  Ma ana ( Inaso kubar wannan wurin yanzu, kuma ku gargaɗi sauran abokanku dake a cikin saharar) Jalim yaji abunda baturen ya faɗa amma cikin ransa bai yarda ba. Gani yake kawai yana faɗin ra a yinsa ne, sabida haka sai ya tsinke wayar.
Page 21    
Ai kuwa yin hakan keda wuya sai sama ta ƙara rinewa da wani irin baƙi, wani irin ƙaƙƙarfan iska ne ya fara kaɗawa, daga nan sai iskan ya cigaba da bugawa da tsananin ƙarfi. Sarahar ce ta fara tsagewa tana ruftawa da mutane a ciki, anan mutane suka fara ihu suna guje guje cikin tunanin wannan wace irin masifa ce. A wannan lokaci Baƙar Guguwa ce ta taso tana fizgar mutane da karfin tsiya tana jefasu a cikin ramen da sahara ta zaftare, tashin hankalin shine guguwar ba wai mutane kaɗai take janyowa ba domin hadda motoci da raƙuma janyo su take da karfin tsiya tana jefa su cikin ramen,  a can ƙasan ramen kuwa wuta ce keci irin ta volcano, da yawan mutane kafin su isa ƙasan ramen zasu ragargaje, wasu kuwa guguwar na fizgo su zata fige su ɓalli ɓalli wato kai daban hannuwa daban. Da yawan mutane suna ƙokarin gudu a cikin motocinsu amma da motar ta fara gudu sai saharar da zaftare anan motar zata faɗa cikin ramen, ko kuwa guguwar ta janyo motar da ƙarfin tsiya tayi mata gunduwa gunduwa, hakama raƙumi guguwa idan ta janyosa to tana fige shi guntu guntu ko kuwa raƙumin na cikin gudu sai ya nutse cikin saharar, da ƙyar da suɗin goshi su Jalim suka samu damar shiga motar su, da ƙarfi Jalim ya fizgi motar a guje amma kuma guguwar ta ƙazanta domin baya ganin hanya, sai kuma zaftarewar da saharar keyi ta kowane gefe, wani birki yaja sakamakon hango dishi dishin rame a gabansa, ribas yayi da ƙarfi cikin rashin sanin cewa akwai wata mota a bayansa, ai kuwa yana juyowa sai motar taci karo da waccan ɗayar motar, anan guguwa ta fizgi motar su Jalim tayi jifa da ita a can gefe, daga nan kuma sai guguwar ta fara janyo motar da ƙarfin tsiya tana ƙoƙarin jefata a cikin ramen inda saharar ke zaftarewa, da tsananin firgici su Jalim ke ihu a wannan lokaci da sukaga motarsu na shirin gangarawa a cikin wannan rame na halaka, ba abunda ke fitowa a cikin ramen in banda wani sauti marar ma ana sai kuma ihun mutanen da guguwar ke fizgowa tana jefawa a ciki. Da ƙarfi su Jalim ke bugun glass ɗin motar domin su samu damar fitowa amma duk a banza, shi kuwa Jalim yana ganin motar ta nufi ramen sai ya gangara da nufin rike stirring, ai kuwa kafin ya isa ne sai wani ƙarfe ya yanke ya faɗo masa ga ƙaramin yatsansa na hannun hagu, anan Jalim yayi ihu mai firgici domin ƙaramin yatsansa ya guntule gaba ɗaya, amma duk da haka sai da yayi ƙoƙari wurin riƙe stirring ɗin kuma yana mai taka burki, a wannan lokaci motar a jicce take kuma ta nufi ramen gadan gadan domin guguwar ce ke ingizata da karfin tsiya. To kafin motar ta faɗa ramen ne sai kawai su Jalim sukaga kamar an cira motar daga sama, motar tashi sama tayi kamar tsuntsu daga nan sai ta dawo dai dai. Su Jalim duba sukayi a cikin tagar motar daga nan sai suka hango wani ƙaton jirgi a can sama, ashe Jack ne tare da abokansa turawa suka kawo musu agaji, wasu ƙarafuna ne suka jefawa motar, a nan ƙarafunan suka laulaye motar daga nan sai jirgin ya tashi sama da motar.
Page 22      
Ihu taɓi da jinjina ba wanda su Jalim basuyiwa Jack ba domin ya basu gudummuwa sosai. 
   " A wannan rana naga tashin hankali irin wanda ban taɓa gani ba." Inji Jalim yana kallon su Anisa, Uzaim da sauran mutane. " Da yawan mutanen da sukazo neman zinari sun rasa rayukansu ta dalilin wannan Baƙar Guguwa wato to The Black Storm, har yanzu bamusan meya haddasa wannan guguwa ba kuma bamusan abunda kesa saharar na zaftarewa ba, an rasa dukiyoyi marar iyaka tun daga raƙuma, motoci da sauransu. Wutar da keci a cikin ramen da saharar ke zaftarewa bako shaka tayi kamada na Volcano, kuma ina gani masu karatun Geology zasu iya bada haske game da abunda Volcano ke nufi, Jack ne ya shigo damu yankin mu, a cikin wani daji suka ajiye motarmu daga nan muka basa kamerarsa, bayan mun gyara motar sai muka kama hanyar dawowa kuma nine na ɗauki ragamar tuƙin motar duk da cewa banada ƙaramin yatsa na hannun hagu, har muka iso gida bamu tuntuɓi labarin Lamitu ba ko kuwa Hassina da kawarta Zamana, nasarar da muka samu a wannan tafiyar shine ba wai zinari kaɗai mukai nemo ba. Mun nemo diamond diamond da kuma precious ornaments, Jack ne yayi muna hanya muka sayar dasu akan miliyoyan kuɗi, daga wannan ranan mukayi bankwana da talauci nida abokaina domin duk wani jin daɗi da muka rasa sai da ya dawo. Wannan shine labarina kuma sanadin yadda na rasa ƙaramin yatsana na hagu kuma ina fatan zamu ɗau darasi a cikin wannan labari nawa kuma idan akwai mai shawara da zai bayar to ƙofa buɗe take." Jalim na zuwa a nan sai su Uzaim suka fara masa taɓi cikin jin daɗi shi kuwa sai ya koma saman kujerarsa ya zauna. Daga nan sai Uzaim ya miƙe tsaye domin ya fara jawabi.      
  " Muna godiya sosai Jalim akan wannan ƙayataccen labari daka bamu mai cike da abubuwan al ajabi, bako shakka wannan tafiya taku ta zamo darasi gareku kuma garemu. Kuma a cikin wannan labari na ɗauki darasin cewa kada kayiwa mutum gori idan kaga yana cikin masifa, tunda munga su Faruƙ suna tsarguwar Jalim akan lalurar dake damunsa na tusa amma sai gashi abun ya dawo wurinsu. Haka kuma na ɗauki darasin cewa kada kayi saurin ƙaryata mutum kome ya faɗa maka, kunga kamar yadda muka gani a cikin wannan labari ai Jalim yayi saurin ƙaryata Jack domin bai yarda da cewa akwai Baƙar Guguwa ba, amma kuma sai ga guguwar ta faru, to ace tun farko ya yarda da maganarsa, ace sun yi saurin barin wurin wata ƙila a samu sauƙi. To wannan kenan yanzu sai na saurara idan akwai mai wata shawara sai ya faɗa kafin naci gaba. Anan akayi tsit. " Tunda anyi shiru wannan shine ke nuni da cewa ba mai shawara sabida haka yanzu zamu watse sai kuma wata friday mu dawo a nan cikin irin wannan lokaci domin inada tabbacin cewa Anisa ta gama shirya labarin da zata bamu."Inji Uzaim. Anan Anisa tayi guntun murmushi. Daga nan sai  kowanensu ya hau motarsa  ya nufi wurin shaaninsa.
                                                                    
 A WANI LOKACI
                                                                                By
  Abdul King Article                                
   Halima Bala Wakili    
    Queen Nasmah
                                                                         Episode two
 (The Spirit)
   King and Queen Writing Chamber
Page 23             
Uzaim, Jalim, Haris, Haulat, Milam. Dukkaninsu zaune suke saman plastic chairs sun yi shiru. Su mazan gaba ɗaya sun yi dress na yan kanti jeans and long sleeve sai cover shoes, su kuwa matan kamar haɗin baki dukkaninsu arabian gown ce, Suna cikin wannan hali ne sai ga Anisa ta shigo da sauri tana tafiya tana gyran long gown ɗinta sanadiyar tayi dress da atamfa.
   " Kuyi haƙuri abubuwan ne." Haka ta faɗa cikin murmushi.
    " Kema kin san baki kyauta ba amma dai ba matsala zaki iya farawa." Inji Uzaim. Anan Anisa ta kalli tagar dake kusa da ita, bako shakka cikin darene sosai domin in banda kukan tsuntsaye da rurin iska ba abunda akeji. Daga nan sai ta maida kallonta zuwa garesu bayan tayi tsaye a tsakiyar ɗakin yadda kowa zai iya ganinta. Anan ta cire dark glasses dinta wanda hakan yasa dukkaninsu suka maida idonsu a kanta, eye dinta na hagu ya kasance dan tsito sosai domin na daman yafi girma amma kuma duk da haka tana gani dashi, daga nan kuma sai ta dubi ƙafarta ta hagu wadda ta kasance bata iya taka ƙafar yadda ya kamata domin gurmanta takeyi. Anisa kyakkyawa ce domin farace sol.
   " Zan baku asalin labarina, kuma a cikin wannan labarine zakuji abunda yasa idanuwana na hagu ya kasance dan tsito, kuma a cikin wannan labarine zakuji abunda yasa nake gurmanta." Inji Anisa. Daga nan sai ta fara labarinta kamar haka:
      A wani lokaci can da daɗewa, na taɓa tsintar kaina a cikin tsananin son zagaya duniya ba don komi ba sai don naga yadda rayuwar yau da kullum ke gudana, abbana da ummina larabawan Khartoum ne, abbana ɗan kasuwa ne kuma yakan shigo yankin Hausawa domin yanada manyan shaguna tare da yara larabawa masu masa tsoro a wazaje daban daban, wannan hulɗa da abbana keyi da Hausawa yasa mukaji Hausa sosai nida ummina, da yake ni kaɗaice ga iyayena sabida haka ina samun gata dai dai gwargwado, abbana ya kasance mai yawan tafiye tafiye kuma ta wannan dalili na kamasa hannu a ƙwarya a kan wata tafiya da zai yi.
  Page 24     
" بصدق أنا لن أذهب معك "
 Inji Salman wato abban anisa a cikin halshen larabci.
Ma ana: (Gaskiya bazan tafi dake ba) 
Ita kuwa Anisa jin cewa abbanta yace bazai tafi da ita ba sai ta ɓata fuska, shi kuwa abban nata yana ganin haka sai ya janyota a jikinsa yana lallalashi domin baya son ganin ɓacin ranta.
" لا تقلق يا أميرتي أنا ذاهب معك " 
Cewar abban Anisa a cikin murmushi
Ma ana( Kada ki samu damuwa gimbiya zan tafi dake) 
Anisa najin haka sai ta juyo zuwa ga mahaifinta cikin jin daɗi.
" شكرا جزيلا لك أبي "
Inji Anisa
Ma ana ( Ina godiya sosai abbana)
A wannan lokaci abban anisa yana sanye da babbar rigarsa ta larabawa da rawani, ita kuwa Anisa arabian gown ce doguwa a jikinta sai kallabi a saman kanta. A cikin falon ne suke zaune amma duk abunda suke ummin Anisa dake goge fridge tana kalle dasu, bayan ta gama goge  gogenta sai tazo gab dasu Anisa ta zauna.
" اسمع يا أميرتي ، لا تتبع والدك ، دعه يذهب وحده " 
Cewar ummin Anisa
Ma ana ( Ki saurareni dakyau gimbiyata, kada ki kuskura kibi abbanki, ki barshi yayi tafiyarsa shi kaɗai ) Abban Anisa najin haka sai ya juyo ya kalli matarsa da nufin yin magana :
" لا تقلق أنا ذاهب معها  "
Ma ana ( Kada ki samu danuwa zan tafi da ita)
" لكنك تعلم أنه أمر خطير "
Ma ana ( Amma kasan da cewa akwai hatsari)
Haka ummin Anisa ta faɗa cikin fushi daga nan sai ta tashi ta tafiyarta. Sai da ƙyar da suɗin goshi ummin Anisa ta yarda ayi  tafiyar da Anisa. Ummin Anisa ce da kanta ta tanadar musu duk wani abu da ake buƙata kafin ayi tafiya a cikin jirgin ruwa, tun daga biyan kuɗi amsar takaddar shaida da sauransu, Kuma a ranar da zasuyi  tafiyar itace ta tuƙa mota ta kaisu wurin da zasu shiga jirgin ruwan wato ship. Kasancewar Anisa bata yawo a wannan lokaci sabida haka ba koina ta sani ba, sai kalle kalle take tana kallon jiragen dake cikin ruwan. Bankwana sukayi da juna, Anisa ce ke rike da yar karamar jaka domin kayansu a haɗe suke ita da abbanta.
Page 25      
Takaddar shaida suka nuna daga nan suka shiga jirgin, ita kuma ummin Anisa sai faman ɗago musu hannu take a cikin motarta har suka ɓace mata da gani. Bayan su anisa sun shiga jirgin ne sai aka nuna musu cabin ɗinsu.
  ( Menene Cabin? Cabin yana nufin ƙaramin ɗaki a cikin babban jirgin ruwa kamar ship, shi wannan ɗaki an tanadesa ne domin yin bacci ga kowane passenger )
 Anisa tanada nata cabin hakama abbanta yanada nasa cabin, da yake cikin jirgin akwai wurin da ake sayar da abinci da kuma abinsha sabida haka ba wata matsala. Ba karamin daɗi Anisa tajiba kasancewarta a cikin babban jirgin ruwa, ƙabilar larabawa ne keda yawa a cikin jirgin, wasu sunyi dress ɗinsu na larabawa wasu kuma English dress, sai da masu English dress ɗin akasari maza ne, Anisa sai kalle kalle take tana bin abbanta duk inda ya taka, ko kaɗan batasan wurin da abbanta zai tafi ba kuma batasan abunda zai yi a wurin ba kuma bata damu data tambayesa ba. Hakama me yasa zasuyi tafiyar a cikin jirgin ruwa bata sani ba! Wata babbar kujera abban Anisa ya zauna inda yake hango ruwan sosai da sosai bayan jirgin ya fara tafiya, haka itama Anisa a kusa dashi ta zauna tana kallon yadda ruwan ke ambaliya.
" ما هو طعامك المفضل؟ "
Ma ana( Wane abunci kika fiso)
Inji Abban Anisa
" طعامي المفضل هو لسان الحمل واللحوم  "
 Ma ana( Abincin dana fiso shine plantain da nama)
Inji Anisa
Daga nan suka cigaba da hira cikin nishaɗi, suna cikin hirar ne sai ga wani yaro ya nufosu sanye da suit, tun daga nesa yaron ke satar kallon Anisa, daga zuwansa sai ya gaida Abban Anisa. Shi kuwa Abban Anisa daga kallonsa ya ganesa domin yaron bahaushe ne kuma ɗaya daga cikin masu sayen hajarsa. Sunansa Ahnab, kasancewar Ahnab yanajin larabci sosai shi yasa yake shiga yankin larabawa domin sayayya ta yau da kullum. Kyakkyawa ne wankan tarwaɗa irin wanda wasunsu suke buƙata kasancewarsa dogo, zaunawa Ahnab yayi daga nan suka cigaba da hirar tare, kuma a cikin wannan hirar ne yayi sabo da Anisa sosai, Ahnab yana  cikin waɗanda sukaba Anisa gudummuwa akan koyon halshen Hausa. Haka dai wannan babban jirgi yaci gaba da gudu a cikin ruwa, idan ya isa wannan tsibiri ya wuce wannan tsibiri, a ko yaushe su Anisa basuda matsala domin suna samun duk abunda suke buƙata, ita kuwa Anisa ko gangancin tambayar wurin da zasu tafi bata taɓa yiba, haka kuwa abbanta da Ahnab ba wanda ya faɗa mata inda zasu tafi.
Page 26      
Iyaka dai tafiya jirgin keyi ba dare ba rana ita kuwa sai kallon ruwan teku take tana nishaɗi, a wani lokaci da wannan jirgi ya ɗauka yana gudu ne su Anisa sukayi gamo da mummunan tashin hankali, ƴan fashin ruwa ne wato pirates a saman ƙananan jiragen ruwa wato boats, ƴan fashin sunada yawa kuma kowanensu a saman boat yake, su waɗannan boats sun kasance marar girma kuma kamar yadda ake tuƙa mota haka ake tuƙasu sai tsananin gudu. Cikin ƙanƙanin lokaci yan fashin suka zageye jirgin su Anisa, a wannan lokaci rana ta faɗi liƙis, kacoci suka jefama jirgin su Anisa daganan suka fara hawan kacocin zuwa cikin jirgin, ƴan fashin sanye suke da babbar riga ta larabawa sai kuma rawani wanda ya rufe musu fuska yadda idanu kawai ake gani, ɗauke suke da bindigogi ababen tsoro, ƴan fashin sun samu amsar dukiya mai tarin yawa daga nan kuma suka tafi da Anisa domin ta ɗebe musu kewa, sai bayan tafiyarsu ne Salman ya gano yayi kuskure.
  " Bazai yiwu ba, dole nabi bayansu." Inji Salman wato abban Anisa a cikin halshen Hausa. Ahnab kallon Salman yayi ganin Hausar tasa ta tsaya dai dai ba kuskure.
  " Zan taka maka mu tafi tare." Inji Ahnab. Searching ɗin jirgin nasu suka farayi har suka gano boat, da sauri suka jefa boat ɗin cikin ruwa daga nan suka durfafi bayan yan fashin. Salman ne ke tuƙi iya ƙarfinsa, jin ihun yan fashin a can nesa shine ya kwantar masa da hankali domin durafafar inda suke yayi, haka yayita binsu da baya har suka iso wani wuri mai yawan duwatsu, anan yan fashi sukayi parking  na boats daga nan suka nufi wani kogo, shi kuwa Salman da Ahnab sai binsu suke da baya da baya. Bayan Salman da Ahnab sun shiga cikon kogon sai sukaga ashe daga ciki an gyara wurin sosai kamar wata masarauta. Salman murmushi yayi ganin Anisa a can ɗaure da kaca, wani garin magani ya ɗauko a cikin jakarsa daga nan ya zuba shi ga ƙasa. Ashana ya ɗauko ya kunna saman maganin daga nan sai yayi wata addua a cikin bakinsa yadda ba wanda zaiji yana tofawa ga maganin. hayaƙi ne ya fara tashi sama, to abunda yaba Ahnab mamaki shine hayaƙin shiga kawai yayi cikin yan fashin, duk wanda ya shaƙi hayaƙin sai ya faɗi yana bacci ba tare da sanin inda yake ba. Haka duk ƴan fashin sukayi bacci in banda Anisa, kuma gata a cikin hayaƙin amma bata bacci, haka shima Salman  da Ahnab gasu a cikin hayaƙin amma basu bacci. Ahnab yayi mamaki sosai ganin wannan abu da Salman yayi amma kuma sai ya nuna kamar bai damu ba, Cikin sauri Salman ya yanke kacar dake ɗaure da anisa da wani gatari na ƴan fashin. Da ƙarfi ya janyota suka fito kogon, daga fitowa suka shiga cikin boat ɗinsu, da ƙarfi abban anisa yaja jirgin ya fara gudu, ai kuwa yana barin wurin sai ƴan fashin suka farka daga baccin, anan suka gane abunda ya faru, bindigogi suka ɗauko daga nan suka yo waje da gudu.
Page 27   
Cikin sauri suka hau boats ɗinsu suka biyo bayan su Anisa. Abban Anisa na tuƙin jirgi sai ji yayi ana halbo musu bindiga, gudun jirgin ya ƙara daga nan kuma ya fara kaucewa albarusan da ake jefa musu, ba yadda abban anisa bai yiba domin ya tsallake wannan hari na ƴan fashi amma duk da haka sai da wasu albarusan suka fasa masa jirgi, anan jirgin ya fara tangal tangal sabida ruwan dake shigowa a ciki, daga karshe dai jirgin kifewa yayi dasu, sa ar da suka samu shine a wannan lokaci sun iso bakin gaɓar ruwan, su kuwa ƴan fashin suna ganin jirgin ya kife sai suka juya domin a tunaninsu su Anisa sun mutu. Cikin sauri su Anisa suka fito daga cikin ruwan suna tari sabida tsananin sanyi. A wannan lokaci duhu ya fara shigowa, kamar daga sama sai abban anisa yaji an masa magana cikin halshen larabci :
" اهلا وسهلا بكم في مصراتة  "
Ma ana( Barka da zuwanku Misrata)
Abban Anisa juyowa yayi daga nan sai yaga abokinsa ne Fahad wanda shima balarabe ne a nan Misrata  ɗin cikin shigarsa ta larabawa wato jallabiya fara da rawani fari.
" شكرا لك فهد  "
Ma ana ( Ina godiya Fahad )
Inji Abban Anisa
" Tunda ka iso lafiya muje kawai ka fara aiki." Inji Fahad cikin halshen larabci.
" Ba matsala mu tafi kawai." Inji Salman wato abban Anisa. Daga nan sukabi bayan Fahad suna tafiya yana musu hira a cikin halshen larabci. Haka suka cigaba da binsa har suka iso  gidansa, suna shiga kofar sai suka samu kansu a cikin wani kwaroro, sai da sukayi  tafiya kafin su iso ga falon gidan, matar Fahad ce a zaune tayi jugum sanye da arabian gown ɗinta sai  ɗan kwali, bayan su Anisa sun gaisa da ita ne sai Fahad ya jogorancensu zuwa wani ɗaki, tun da suka nufi wannan ɗakin Anisa kejin gabanta na faɗuwa ba tare da sanin dalili ba, sai tunanin dake damunta shine cewar Fahad " Tunda ka iso lafiya muje kawai ka fara aiki." To wane irin aikine Fahad ke nufi abbanta zai aiwatar, kuma dama abbanta yazone yayi wani aiki? To wannan wane irin aiki ne? Haka waɗannan tambayoyin suka dinga yiwa Anisa yawo a cikin zuciya har suka iso ɗakin, ɗakin yanada girma sosai, gado ne a gefen ɗakin sai wata yarinya balaraba kwance ɗaure da kacoci, tana sanye da riga doguwa hakama gashinta lullube yake da ɗan kwali amma da mutum ya kalle ta yasan batada lafiya domin idanuwanta sun yi wani juyawa,  hakama fuskarta ta canza kamar ba mutum ba, daga shigowar su Anisa yarinyar ta fara jifarsu da wani irin kallo marar ma ana 
" Wannan itace yarinyar da nake baka labari." Inji Fahad cikin halshen larabci.
Page 28     
Shi kuwa abban Anisa najin haka sai ya kalli yarinyar irin kallo na natsuwa, sabida duhun daya fara shigowa sai abban Anisa ya umarci Fahad daya kawo musu abun kalaci su kimtsa tukuna. Anan Fahad ya jagorancesu zuwa wani ƙaramin ɗaki, a cikin ɗakin darduma ce zalla shimfide, sai plates plates na abinci kala kala, can gefen ɗakin kuwa modern toilet ne domin idan zasuyi alwalla, sai da su Anisa suka  kimtsa sosai sa anan suka koma zuwa wancan ɗakin na wannan yarinyar, abban anisa ne ya musu jagora har zuwa ciki yana mai rike da jakarsa, ai kuwa suna shiga ɗakin sai ga Fahad da matarsa suma sun shigo ciki. Ɗakin ya kasance mai tsananin duhu duk da cewa akwai fitillu a ciki, wani ɗan ƙoƙo abban anisa ya fito dashi daga cikin jakarsa, daga nan sai ya zuba garin magani a ciki, ashana ya kunna ya jefa cikin ƙoƙon daganan yayi wata addua yadda ba wanda zai ji, yana tofa adduar sai hayaƙi ya fara fitowa daga cikin ƙoƙon, anan hayaƙin ya fara shiga hancin wannan yarinyar ta saman gado, ai kuwa yin hakan keda wuya sai yarinyar ta zauna tana kallon abban anisa a cikin fushi, idanuwanta sun wani juyawa abun tsoro. Magana ta farayi cikin halshen Portuguese,  maganar dake fitowa ga bakin yarinyar mutum bazai iya tantance ko waye mai maganar ba, namiji ne mace ce mutum bazai iya ganewa ba domin sautin muryar ya banbanta dana sauran mutane, cikin fushi yarinyar ta fara magana kamar haka :
 " Quem é você para me acordar em meu sono!"
Ma ana( Kai waye da zaka tayar dani daga bacci)
Abban Anisa najin haka sai ya mayar da martani kamar haka:
" Não se preocupe, eu vim aqui em paz "
Ma ana ( Kada ka damu, nazo ne cikin aminci)  
Wani duhu ne ya  gauraye wurin da yarinyar take, idanuwanta ne suka canza zuwa yanayin tsoro, da ƙarfi ta girgiza kacar da aka ɗaureta da ita, da yake kacar an janyota ne yadda ta ɗaure hannayenta biyu wato na dama dana hagu, zata iya kwanciya saman gado ko kuwa tayi duk abunda takeso amma bazata iya kwance kacar ba domin an mata mugun ɗauri.
 " Não há paz aqui "
Ma ana( Babu aminci a nan) 
Haka yarinyar ta faɗa tana mai kallon abban Anisa cikin fushi. Shi kuwa abban Anisa najin haka sai ya buɗa jakarsa daya aje a can  gefe, kwalba ya ɗauko daga nan ya buɗata, wata addu a ya karanta a cikin zuciya yadda ba wanda zai ji daga nan sai ya tofawa yarinyar, ai kuwa yin hakan keda wuya sai jikin yarinyar ya fara girgizawa da matsanancin ƙarfi, sai da ta ɗau lokaci a cikin wannan hali kafin daga karshe ta fara magana kamar haka :
Page 29         
" Hoje você ganha, mas amanhã eu vou ganhar "
Ma ana ( Yau ka samu nasara, amma gobe nine zan samu nasara ) 
Yarinyar na faɗin haka sai wani baƙin hayaƙi ya fara fitowa daga bakinta, shi kuwa abban anisa juya kwalbar yayi gefen hayaƙin, anan hayaƙin ya fara shiga cikin kwalbar, sai da ya gama shiga gaba ɗaya daga nan sai abban Anisa ya kulle kwalbar, ai kuwa faruwar hakan keda sai wannan yarinyar dake saman gado ta dawo cikin hayyacinta, idanuwanta sun dawo lafiya lau hakama jikinta, da gudu mahaifiyarta ta nufota, cikin murna suka rungume juna,shi kuwa Fahad sabida murnar ta masa yawa sai ya kasa magana, abunda kawai ya iya faɗa shine :
" شكرا لك شكرا لك شكرا لك  "
Ma ana ( Ina godiya ina godiya ina godiya)
Haka Fahad ya faɗa  a cikin halshen larabci, shi kuwa abban Anisa baiwa Anisa kwalbar yayi yace ta riƙe kuma ta biyo bayansa. Anisa bin abbanta tayi, sai da sukayi tafiya mai nisa sa annan suka iso wurin wata tsohuwar rijiya, anan abban Anisa ya umarceta da cewa ta buɗe marfin rijiyar ta jefa kwalbar, idan ta jefa kwalbar tayi sauri ta dawo gida, daga nan sai ya tafiyarsa ya bar Anisa a wurin rijiyar, Anisa na ganin abbanta ya tafiyarsa sai ta tunkari wannan rijiyar da nufin jefa kwalbar a ciki, tafiya takeyi amma sai tunani take kamar ta buɗe marfin kwalbar taga me zai faru, haka taci gaba da wannan tunani har daga ƙarshe dai tayi tunanin bari ta buɗe kwalbar,  ai kuwa tana buɗe kwalbar sai taji wani sauti ya fito daga can nesa. Anan ta dubi kwalbar amma bataga kome ba, tsaki tayi daga nan ta jefa kwalbar cikin rijiya, tafiya ta farayi har ta iso gida, tana isowa sai ga abbanta da Fahad sun fito daga cikin gidan. Abbanta kallonta yayi cikin alamar zargi kafin yayi mata magana kamar haka a cikin halshen larabci :
" ماذا فعلت بالزجاجة التي أعطيتك إياها؟  "
Ma ana ( Wane abu kikayi da kwalbar dana baki)
Anisa najin haka sai gabanta ya faɗi amma daga karshe sai taga bari ta faɗa masa  gaskiya. Daga nan sai ta masa magana kamar haka:
" أنا آسف يا أبي ، لكنني فتحت الزجاجة  "
Ma ana ( Kayi haƙuri abba, amma na buɗa kwalbar)
Tun kafin Anisa ta iyar da maganarta abbanta ya gwabra mata wani wawan mari, ɗaga hannu yayi da nufin ya ƙara mata wani sai da Fahad ya riƙesa yana basa haƙuri, a wannan lokaci Anisa tayi dana sanin abunda ta aikata domin abbanta ba karamin hasala yayi ba domin shi nufinsa yayi mata wawan duka in banda Fahad ya hanashi.
Page 30        
 Anan ne Anisa ta fara tunani ashe wannan dalili yasa abbanta bayason tafiyar da ita domin kada tayi masa wawanci, ai kuwa gashi ta masa wawanci shi kuwa ya bata wawan mari, da ƙarfi abban Anisa ya janyo hannuta ya nufi cikin gidan da ita shi kuwa Fahad na biye dashi, sai da suka iso ɗakin da wannan yarinyar take sai Anisa ta gano tayi kuskuren buɗe wannan kwalbar domin yanzu yarinyar ta dawo yadda take, idanuwanta sun juya kuma hankalinta ya ɓace, gata balaraba amma bata magana da larabci sai da halshen Portuguese. Ahnab ne da mahaifiyar yarinyar ke ƙoƙarin sanya mata kaca. Abban Anisa sakin hannun Anisa  yayi daga nan sai ya fara magana kamar haka : 
" انظر إلى ما أحضرته  "
Ma ana ( Dubi abunda kika janyo)
" أنا آسف يا أبي ، لقد أخطأت  "
Ma ana ( Kayi haƙuri abba, nayi kuskure )
Haka Anisa ta faɗa cikin dana sani.
Abban Anisa juyawa yayi gefen Fahad daga nan sai ya fara magana dashi kamar haka a cikin halshen larabci:
" Wane wuri ne Maryam ta samu wannan matsalar?"
" Maryam ta samu matsala ne tun lokacin dana tafi Portugal da ita domin na buɗa sabuwar supermarket a can, kuma banada raa yin tafiyar da ita domin naso na barta gida wurin mahaifiyarta,  itace ke damuna sai nayi tafiyar da ita, ni kuma ganin cewa ita kaɗaice ɗiyata kuma banason ranta ya ɓace sai nayi tafiyar da ita, to tun a can ta fara abubuwa marassa ma ana amma abun bai tsananta ba sai da nawo nan." Inji Fahad cikin halshen larabci.
" To a tunaninka menene ya janyo mata wannan ciyo?" Inji abban Anisa.
" Gaskiya ban sani ba amma dai Maryam tana wasa da addu a kuma bata baiwa addini muhimmanci." Inji Fahad. 
" A cikin me kukayi tafiyar?" Inji abban Anisa.
" A cikin babban jirgin ruwa."  (ship)  Inji Fahad
Abban Anisa najin haka sai ya nufi wani lungu ita kuwa Anisa tabi bayansa, haka sukayi tafiya har suka iso wannan ɗakin da sukaci abinci a ciki, anan suka zauna tare suna kallon juna.Daga nan sai Anisa ta fara magana da larabci kamar haka :
" Zan sadaukar da kaina domin na gyra wannan kuskure dana aikata sabida haka yanzu ka faɗamin menene abunyi!" Inji Anisa.
Page 31      
Salman najin Anisa ta faɗi haka sai ya ɗauko takadda da biro, wani rubutu yayi kamar haka a cikin halshen Portuguese : 
( Jissu Jissu, venha aqui e case comigo, não posso viver sem você) Daga nan sai ya buɗa jakarsa ya ɗauko irin wannan kwalbar daya bata farko, ita kwalbar ta kasance baƙa yadda mutum ba zai iya ganin abunda ke ciki ba kuma kwalbar  tanada girma sosai domin ta glass ce, anan ya bata kwalbar kafin ya fara magana kamar haka : 
" Zaki tafi wannan rijiyar dana nuna miki, da kin tafi sai ki karanta wannan abun dana rubuta miki a cikin takadda sau uku, kina karantawa zakiga baƙin hayaƙi yana fitowa daga cikin rijiyar, daga nan sai kiyi sauri ki buɗa kwalbar, kina buɗa kwalbar zakiga hayaƙin na shiga ciki, da hayaƙin ya gama shiga ciki sai kiyi sauri ki kulle kwalbar ki jefata cikin rijiyar daga nan kuma ki rufe marfin rijiyar, amma fa ki sani cewa wurin rufe marfin kwalbar sai kin yi da gaske domin wanda ke ciki zai yi ƙoƙarin fitowa,  kuma idan kika barshi ya fito to shi kenan zai dawo kanki, amma idan kika kulle marfin kwalbar kuma kika jefa kwalbar a cikin rijiyar to shi kenan wanda ke cikin kwalbar zai tafi inda bazai ƙara dawowa ba. Kuma ke kaɗaice zaki tafi domin ba wanda zai rakaki a cikinmu." Haka Salman ya faɗa yana kallon ɗiyarsa Anisa kafin ya cigaba da magana. " Inaso ki sani cewa wanda kike nema yana cikin rijiyar amma kuma zamansa a cikin rijiyar bazai iya hanashi yin mugunta ba, wannan dalili yasa Maryam har yanzu batada lafiya domin bai rabu da ita ba, idan har kinaso Maryam ta samu lafiya kuma shi wannan baƙin abu ya daina cutar da mutane to dolene sai ki sanya shi a cikin wannan kwalbar, daya shiga cikin wannan kwalbar bazai iya fita ba kuma kwalbar bazata iya fashewa ba, sabida haka yanzu ki tashi ki tafi." Kafin Anisa ta tafi ne Salman ya bata padlock da makulli yace idan ta rufe marfin rijiyar to ta sanya padlock ta rufe marfin, shi kuwa makullin padlock  ta tabbatar cewa ta jefashi cikin rijiyar tare da kwalbar.  Anisa najin haka sai ta tashi ta fita waje, tafiya takeyi  cikin tsananin tsoro har ta isa bakin rijiyar, a hankali a hankali ta buɗe marfin rijiyar tana mai kallon tsananin duhun dake ciki, rijiyar ta kasance tsohuwar rijiya mai tsananin zurfi da faɗi, Sai da Anisa ta ɗau lokaci cikin fargaba kafin ta ɗauko takardar da abbanta ya bata, a hankali ta buɗa takardar daga nan ta fara karanta abunda ke ciki.
 " Jissu Jissu, venha aqui e case comigo, não posso viver sem você." Anisa batajin halshen Portuguese, iyaka dai ta karanta waɗannan kalmomin kamar yadda abbanta yace ba tare da sanin abunda suke nufi ba kuma ita bata damu da tambayarsa ma anarsu ba, ai kuwa tana karantawa sau uku sai taga baƙin hayaƙi yana fitowa daga cikin rijiyar.
Page 32         
Da sauri ta buɗe kwalbar inda shi kuwa hayaƙin ya fara shiga ciki, hayaƙin na gama shiga sai ta sanya marfin kwalbar da nufin rufewa, anan aka fara kokuwa tsakanin Anisa da kwalba, ita Anisa tana ƙoƙarin rufe kwalbar amma sai ji take kamar wani abu yana ƙoƙarin fitowa a cikin kwalbar.A cikin wannan kokuwa ne tayi muguwar faɗuwa har sai da ƙashin ƙafarta na hagu ya karye, kuma a cikin wannan kokuwa ne tayi muguwar faɗuwar da idanunta na hagu ya bugi dutse, sai da ƙyar da suɗin goshi ta rufe kwalbar daga nan ta jefa kwalbar tare da wannan makulli da abbanta ya bata a cikin rijiyar, da rarrafe ta rufe marfin rijiyar daga nan ta sanya padlock ɗin, ai kuwa tanayin haka sai ta faɗi sumammiya sabida tsananin wahalar datasha. Koda Anisa ta farka sai ganinta tayi cikin falo abbanta yana mata fita, a nan ne Fahad ya fara bata bayani domin shi likita ne kuma ɗan kasuwa. Fahad ya faɗa mata cewa sabida wannan faɗuwar datayi bazata iya taka ƙafarta ba, zatayi tafiya amma da gurmanta, haka kuma idanunta na hagu zata cigaba da gani dashi amma zai kasance ɗan tsito sosai. Da sanyin safiya ne Salman ya fito tallabe da Anisa domin bata iya tafiya,  Fahad yayi musu goma na arziƙi daga nan kuma ya raka su  a cikin motarsa inda zasu shiga jirgin ruwa, shine yayi musu kome, daga nan sai Ahnab ya shiga babban jirgin ruwan da zai kaishi yankin Hausawa su kuwa su Anisa suka shiga nasu jirgin ruwan wanda zai kaisu Khatourm.
" Maryam dai ta warke sarai tun a lokacin dana jefa kwalbar a cikin rijiya, wannan shine labarina." Haka Anisa ta faɗa tana kallon su Uzaim, " kuma wannan shine dalilin dayasa nake gurmanta idan ina tafiya, kuma wannan shine dalilin da yasa nake sanya baƙin glass domin na ɓoye idanuwana na hagu." Tana faɗar haka sai ta nufi wurin kujerarta. Su kuwa su Uzaim taɓi suka fara yi mata har ta zauna. Ai kuwa tana zaunawa sai Uzaim ya tashi tsaye domin ya fara bayani :
    " Bako shakka wannan labarine mai ɗauke da darasi, darasin dake cikin labarin kuma shine muhimmanci yin addu a da kuma muhimmancin ɗaukar addini da muhimmanci, idan mukaga abunda ya faru ga Maryam zamu iya cewa ƙaddara ce amma kuma abbanta yana zarginta akan rashin baiwa addini muhimmanci da kuma sakacinta a wurin yin addua, sai kuma bin zuciya, idan muka tuna Anisa tabi son zuciyarta wurin buɗe kwalbar da aka bata wanda ta dalilin haka ne  ta jefa kanta cikin masifa har daga ƙarshe ta kasance gurmuwa kuma idanunta na hagu ya samu matsala." Uzaim shiru yayi yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya kafin yaci gaba da magana. " Zan tsaya anan idan akwai mai tambaya ko ƙarin bayani zai iya." 
  Page 33
 " Gaskiya inada tambaya." Inji Jalim." Kuma tambayata shine Anisa ta faɗi wata Jimla a cikin halshen Portuguese wadda bata faɗa muna ma anarta ba, sabida haka ya kamata ta faɗa mana ma anarta yanzu."
  " Jimlar itace kamar haka :  Jissu Jissu, venha aqui e case comigo, não posso viver sem você." Anisa tashi tsaye tayi da nufin bashi amsa :
  " Kamar yadda na faɗa a wancan lokacin banajin halshen Portuguese, amma daga baya abbana ya koyamin har na kasance zan iya magana da halshen, kuma ma anar wannan jimlar shine : Jissu Jissu, ka fito nan waje ka aureni, bazan iya rayuwa idan bada kai ba." 
  " To waye Jissu ɗin?" Inji Jalim.
  " Jissu shine sunan shaiɗanin dake damun Maryam, wato Maryam Ibn Fahad." Inji Anisa.
  " Wato kina nufin The Spirit." Inji Jalim.
  " Yes The Spirit." Inji Anisa. Anan su Uzaim suka yi musu taɓi da alama labarin ya burgesu. Daga nan sai Uzaim yaci gaba da bayani kamar haka : 
  " To anan zamu dakata sai wata friday inda Haulat zata bamu labarinta." Daga nan sai kowanensu ya tashi ya nufi hanyarsa ta fita.

   A WANI LOKACI
                                                                                By
  Abdul King Article                              
   Halima Bala Wakili
  Queen Nasmah
                                                                         Episode Three
   (The Kingdom)
   King and Queen Writing Chamber
Page 34
   " Jissu Jissu, don ALLAH kiyi shiru duk kin cika muna dodon kunne da surutu." Haka Uzaim ya faɗa yana duban Anisa shi kuwa a lokacin yana tsaye.
   " Kai kuma abun ya isheka hakanan," Inji Anisa a cikin wasa.
   " Amma wannan yarinya baki kyauta ba, yanzu gudan shugaban namu zaki faɗawa haka?" Inji Haris.
 " Kai kuma idan an faɗa masa haka meye ruwanka  a ciki!" Haka Anisa ta faɗa tana binsa da hararar wasa." Su kuwa su Jalim, Milam da Haulat murmushi kawai sukayi da alama wannan wasa yana burgesu. Daganan sai kowanensu yayi shiru, anan suka mayar da hankalinsu ga Uzaim domin jin abunda zai faɗa, shi kuwa Uzaim ganin sun yi shiru sai ya cigaba sa bayaninsa kamar haka :
   " Ba tare ɓata lokaci ba zan gayyato Haulat domin ta bamu nata labari, sabida haka Haulat yanzu fili nakine zaki iya farawa " Anan Uzaim ya samu kujera ya zauna, ita kuwa Haulat miƙewa tayi ta nufi tsakiyar ɗakin, daga nan sai ta janye mayafinta yadda zasu iya kallon ɓangaren fuskarta na hagu, anan suka gane cewa a ɓangaren fuskarta na hagu yanada tambon ƙuna domin kamar an  sanya wuta an cire fatar. Haulat kallonsu ta farayi ɗaya bayan ɗaya kafin ta fara bayaninta kamar haka:
    " A masarautarmu, mafi yawan ƴan uwana maza da mata basu damu da baiwa ilimi da sana a muhimmanci ba domin a tunaninsu mulkin duniya mai ɗaurewa ne, ga dokar sarautar gidanmu idan babba ya hau karaga, to mutuwa ce kawai ke rabasa da mulkin, kuma a duk lokacin da wannan ƙaddarar ta faru, to baza a baiwa ƴa ƴansa sarautar ba, sai dai a baiwa wani ƙanensa karagar mulki, kuma hakane ya faru ga masarautarmu, bayan mutuwar Abba wato sarki, mune ƴa ƴansa amma a cikinmu ba wanda aka baiwa sarautar, wani ƙanensa aka baiwa karagar mulki.
Page 35
Abun takaici a wannan lokaci shine a cikin mu huɗu ba wanda ya tanadi wata sana a mai muhimmanci, kai ko mai  diploma babu, nice ƴar auta kuma ni kaɗaice keda degree in Nursing kuma ina aiki a asibiti, maza biyu mata biyu, haka muke. Ba ƙaramar masifa muka shiga ba domin duk wani jin daɗi da muke ciki sai da ya ƙare, hasalima gidanmu aka bamu daban domin bazai yiwu muci gaba da zama a gidan sarautar ba, ni kaɗaice ke aiki kuma ina ƙoƙari wurin ganin cewa muna samun na yau da kullum nida ƴan uwana da kuma mahaifiyata, matsalar dana samu shine hassadar data fara ruruwa a tsakanin ƴan uwana ganin cewa ni kaɗaice ke aiki harda ƴar ƙaramar mota Honda, kuma wannan hassadar da suka bayyanar itace sanadiyar rasa ɓangaren fuskata na hagu, kada na jaku da surutu zan fara da abunda ya faru a can baya :
   A wani lokaci, ƴa ƴan sarki Salim sun taɓa fuskantar rayuwa mai tsanani kuma hakan ya faru ne akan rasa mahaifin nasu da sukayi wato sarki Salim, ga dokar wannan masarauta idan sarki ya mutu to baza a baiwa ƴa ƴansa sarauta ba sai dai a baiwa wani ƙanensa sarautar, haka kuma ya kasance domin ƴa ƴan sarki Salim sunaji suna gani aka baiwa ƙanen  mahaifinsu sarautar su kuma aka fitar dasu daga gidan sarautar, adalcin da aka musu shine an basu gidan zamani nasu na kansu domin suci gaba da rayuwa, sarki Salim yanada ƴa ƴa huɗu wato maza biyu mata biyu, Hanib, Anib, sai  Aulat da Haulat, Hanib ne babba sai Anib mai bi masa, sai Aulat, Haulat itace ƙarama kuma ƴar auta, a wannan lokaci da wannan abu ya faru ƴa ƴan sarki Salim ba mai wata sana a, kai ko mai Diploma babu domin basu ɗauki karatu da muhimmanci ba, ba abunda suka sama gaba in banda jin daɗin rayuwa domin ga tunaninsu sarautar mai ɗorewa ce, sai gashi abun ya canza musu tun ga mutuwar mahaifinsu sai rayuwa ta tsananta a wurinsu, sa ar da suka samu shine Haulat tayi karatu har zuwa matakin Degree in Nursing, kuma tana aiki ne a asibiti, da wannan aiki da takeyi ne take kulawa da ƴan uwanta da kuma mahaifiyarsu, tun a lokacin da Haulat ta sayi ƙaramar mota Honda ƴan uwanta suka fara canza mata domin a tunaninsu wasu maƙudan kuɗi take samu.
   " Umma gobe  night duty zanyi wato aikin dare kuma idan na tafi bazan dawo ba sai gobe da safe." Inji Haulat.
  " To ALLAH ya tsare ya miki albarka." Inji umma wato mahaifiyar su Haulat.
Page 36
Aulat ce ta shigo gidan tana harare harare, Ummi ce ta dubeta cikin mamakin wannan sabon yanayi data fara gani ga ƴarta.
  " Wai Aulat lafiyarki kuwa kwanakin nan naga kin canza gaba ɗaya kamar wadda aka yima wani laifi." Inji Umma
   " Umma nifa ban ce ga wanda yamin laifia ba iyaka dai circumstances ne." Inji Aulat.
   " Kin jita da wani turanci ni ina nasan wani sakamtansin, ai naso ace nayi boko na rama wannan tsiyar da kuke min." Haka Umma ta faɗa cikin jin haushi domin tun ba yau ba ƴa ƴan nata kan buga mata turancin duk da cewa sun san bata iyaba.
   " Umma ki bar jin haushi akan yarinyar da bata gama secondary ba, da ace kinajin turanci da zaki gane cewa duk turancin da takeyi ita dasu Ahnab da Anib ba dai dai bane, yau kaɗaine tayi turancin kirki kuma shima ɗazu taji na faɗi kalmar shine ta riƙe." Haka Haulat ta faɗa cikin rashin sanin cewa Aulat ta jiyota, da har Aulat zata shiga ɗakinta sai ta dawo baya.
  " To ƙadangaruwa, jaɓa mai baƙar aniya me kike faɗa ne?" Haka Aulat ta faɗa cikin fushi. Ita kuwa Umma jefo mata takalmi tayi da ƙarfi, da gudu Aulat ta shige ɗaki tana gunguni. Can sai ga Ahnab da Anib sun shigo tare sanye da ƴan kanti wato jeans and tshirt, tafiya suke suna rera waƙar turanci harda wani bouncing suke, dariya da mamaki ne ya kashe Haulat ganin yadda ƴan uwan nata suka dage akan wannan waƙar ta turanci alhali basu iyaba domin ba abunda suke faɗa in ba shirme ba.
  " Ke ina makulkin motarki!" Haka Hanib ya faɗa cikin wata murya mai razanarwa.
  " Bazan bayar ba, jiya haka kawai kuka ƙarar min da mai alhali kun san da cewa man ya tashi." Haka Haulat ta faɗa tana murguɗa baki.
  " Ƙwal uba, ke! Zan takaki a wurin nan." Hannu Hanib ya ɗaga amma kafin ya iyar da nufinsa ne sai ya tsaya sanadiyar kallon da yaga Umma  na  jifansa dashi.
  " To gatanan sai ka daketa na gani." Inji Umma.
  " To amma Umma ai kin san bazai yiwu wannan yarinyar tana faɗawa yaya magana ba." Inji Anib cikin fushi.
  " Kai kuma ƙadangaren gobara ba da kai nake magana ba, haka kawai sai ƙatta suyima yarinya taro batasan hawa ba batasan sauka ba, to ku daketa na gani." Anan su Hanib suka fara kallon juna jin Umma ta kirasu da ƙatta.
Page 37
  " Umma ƙatta fa kikace." Inji Hanib.
  " E to meye marabinku da ƙatta ko akwai wani abu da kuke tsinana min ne? ita wannna yarinyar da kuke rainawa itace cinku itace shanku, amma duk da hakan baku damu ba domin a kullum burinku shine kuci mata mutunci." Haka Umma ta faɗa cikin fushi.
  " Umma degree ne fa kawai tayi da ace mun so da zamu iya." Inji Anib 
  " To yanzu sai ka faɗamin meya hanaku yin digrin, nace meya hanaku." Anib shiru yayi domin bai san amsar da zai bata ba.
  " Wa kike kallo ke zan takaki a wannan wurin." Haka Hanib ya faɗa yana shirin tunkaro Haulat, ita kuwa Umma na ganin haka sai ta rarumo taɓaryarta dake can gefe, Hanib da Anib suna ganin haka sai suka bar wurin domin sun san ba ƙaramin aikin Umma bane ta fasa musu kai kuma ba abunda zai faru.
 A cikin dare ne Haulat tayi shirin zuwa asibiti, uniform ɗinta na nurses ta sanya farare dagana ta hau motarta domin zuwa asibitin wato wurin aikinta, tuƙi take iya ƙarfinta domin tayi latti sosai, tana shiga da motar cikin asibiti sai ta fakata gefe, da sauri ta nufi Female Ward, tana isowa bakin ƙofar sai ga abokiyarta Ramlat ta fito.
  " Nayi tsammanin bazaki shigo ba har zan tafi." Inji Ramlat.
  " Yi haƙuri ƴar uwa abubuwan ne, amma tunda yanzu na shigo ai zaki iya tafiya." Inji Haulat.
   " To yayi ba matsala sai gobe." Haka Ramlat ta faɗa daga nan ta nufi motarta. Ita kuwa Haulat da sauri ta shige ward ɗin, wani ɗan kwaroro ta ɗauke mai tsayi, sai da ta ƙuresa kafin ta shigo wani lungu, ƙaramar tafiya tayi daganan ta iso ga wasu gadaje na marassa lafiya masu yawa, kallon gadajen Haulat tayi ganin babu kowa samansu domin duk majinyatan an sallamesu, mamakin da Haulat keyi su ga dokar wannan asibitin dole ne mutum ya shigo aiki koda babu masu jinya domin a tunaninsu ako yaushe za a iya samun majinyata. Wata ƴar kujera plastic chair ta janyo, zaunawarta keda wuya sai ta tuno cewa bata kulle ƙofa ba, da sauri ta nufi ƙofar domin ta rufe, tana aza hannunta saman ƙofar sai taga an turo ƙofar da ƙarfi, cikin razana Haulat taja baya domin ganin ko waye, wani ƙato ne taga ya shigo mata sanye da ƴan kanti jeans and short shirt, makeken glass baƙi  ya sanya sai cover shoe ɗinsa abun tsoro.
  " Malam lafiya?" Haka Haulat ta faɗa cikin rashin yarda.
Page 38
  " Banida lafiya inaso kimin allura." Haka ƙaton ya faɗa yana dubanta.
  " Haba malam in banda abunka ai ba nan ya kamata kazoba, kada ka manta nan female ward ne kuma muna duba mata marassa lafiya, male ward ya kamata kaje domin akwai maza a can sune zasu yi maka allura." Inji Haulat.
  " Ni dai kawai nace kiyimin allura." Haka ƙaton ya faɗa cikin sauri.
  " Malam kanada hankali kuwa! wace mace kake tsammani zata yima gardi irinka allura? ai yadda tsarin wannan asibitin yake shine maza suyima maza allura mata kuma suyima mata allura, kuma koda inaso nayima allura taya zanyi allurar tunda banga abun a rubuce ba kuma ban san ko wace allura kakeda buƙata ba tunda allurorin sunada yawa, yanzu dai ina baka shawara kaje male ward akwai maza sune zasuyi maka allura idan ka nuna musu abun a rubuce." Inji Haulat.
   " Haka kikace?" Inji ƙaton a cikin fushi. 
   " E haka nace." Ita kuwa Haulat ta bashi amsa. Da ƙarfi ƙaton ya kulle ƙofa ita kuwa Haulat ganin wannan abu sai ta kulle ƙofar daganan ta nufi wurin zamanta. Zaunawa tayi tana tunanin wannan al amari domin abun ya kwance mata kai. Bayan wani ɗan lokaci sai taji ana ƙwanƙwasa mata ƙofa, da farko kamar bazata buɗe ba domin a tunaninta ƙaton ne ya dawo, can kuma sai taga bari ta buɗe, miƙewa tayi tsaye daganan ta nufi ƙofar, ai kuwa tana buɗewa sai taci karo da H.O.D wato (Head of Department)Haulat tayi mamakin ganin HOD a cikin wannan dare domin ba kasafai ake ganinsa a cikin dare ba.
  " Ina yini ranka shi daɗe." Haka ta faɗa cikin girmamawa.
  " Lafiya." Inji HOD yana mata wani kallo.
  " Haulat ki faɗamin meye aikinki a wannan asibiti!" Inji HOD ɗin. Haulat tayi mamakin wannan tambaya domin  da ɗan rainin wayo a ciki.
  " Ranka shi daɗe ai a tunanina kafi kowa sanin amfanin aikina a wannan asibiti tunda da yawan staff ɗin ba kowa ke iya night duty ba amma ni haka nake hanƙuri dashi." Inji Haulat.
  " Ba ina magana akan duty bane," Haka HOD ya faɗa yana gyara babbar rigarsa tare da hula kafin yaci gaba da magana  " Inaso ne ki faɗamin ayukkan daya kamata ace kina aiwatarwa a cikin wannan asibiti."
Page 39
  " To ba matsala ranka shi daɗe zan yi bayani." Inji Haulat. 
Ɗagowa tayi daga kallon da takema cover shoe ɗinsa kafin ta fara magana :
  " Ayyukana sun haɗa da duba marassa lafiya, ɗaukar ɗawainiyarsu, basu magani harma da allura inda buƙatar yin hakan."
   " Da kyau, to inaso ki sani cewa waɗannan ayukka da kika lissafo ba mata kawaine zaki baiwa suba, harda maza idan da buƙatar hakan." Inji HOD.
   " Haba ranka shi daɗe kada ka manta sai da fa akayi general meeting kafin daga bisani Director ya bada command cewa maza su duba maza mata su duba mata amma kuma yanzu naga ka ɗauko wata hanya ta daban."
  " Ke dakata," HOD tsawa ya daka mata yana mai ɗaga mata hannu. " Kada ki manta mune muka baki aiki kuma ako yaushe zamu iya sallamarki." HOD na faɗar haka sai ga wannan ƙaton ya shigo. " Gayanan, inaso ki masa allura yanzu a gabana." Inji HOD ɗin. Shi kuwa ƙaton yanajin haka sai ya fara banye belt ɗinsa.
   " Menene kake shirin aikatawa haka!"  Haulat ta faɗa tana mai duban ƙaton.
   " Zan cire wandona sai kiyimin allura kamar yadda ake buƙata." Inji ƙaton yana mata murmushin ƙeta.
    " Kam bala i." Haka Haulat ta faɗa cikin rashin sanin cewa kalmar ta fito daga bakinta.    
    " Ranka shi daɗe a matsayinka na HOD inada yaƙini cewa ka ƙware wurin yin allura to me zai hana kayi masa da kanka."
    " Ke banason shashanci dani dake waye babba, babba ya kamata yayi aiki ko ƙarami?Sabida haka ki shiga taitayinki." HOD na faɗar haka sai ga wani abokin aikin Haulat ya shigo mai suna Ƙasim sanye da lab coat ɗinsa, Haulat na ganinsa sai tayi ɗan gajeren murmushi, shima ƙasim jifarta yayi da murmushin kamar yadda ta masa.
  " Tunda ga Dr. Ƙasim nan sai yayi masa allura. " Inji Haulat.
  " Okay allura za ayi, to ba matsala." Anan Dr. Ƙasim ya fara gyran hannun rigarsa shi kuma HOD yana ganin haka sai ya amshe maganar.
   " Kada ka damu Dr.Ƙasim da yake shi wannan da kake gani rashin lafiyarsa mai zuwa ce da tafiya, kaga kuwa bazamu biyewa hakan ba." HOD na faɗar haka sai ya nufi ƙofar fita, da sauri ƙaton ya gyara wandonsa ya nufi bayan HOD.
Page 40
Shi kuwa Dr.Ƙasim janyo wata kujera plastic chair yayi ya zauna, itama Haulat zaunawa tayi saman kujera  daganan sai suka fuskanci juna.
  " Nayi mamakin ganin HOD a cikin wannan daren domin ba kasafai ake ganinsa ba, da yake nazo giftawa ne sai naga office ɗinsa a buɗe, ina shiga sai sakatiryarsa Maryam ta faɗa min ya fita. To akan hanyata ne na dawowa sai naji hayaniya na tashi a cikin ward ɗin nan, to ina shigowa sai naga ashe kune a ciki." Shiru Dr. Ƙasim yayi na wani lokaci kafin yaci gaba da magana: " Wai wace magana ce na tarar kuna tattaunawa akai?"
  " Wai allura yakeso nayima wannan ƙaton!" Inji Haulat.
  " Allura kuma, to ai Male Ward akema maza allura kuma shi me zai hana yayi masa allurar da kansa!" Inji Dr. Ƙasim.
   " Hmm kai dai faɗi." Haulat ta faɗa cikin mamaki.
   " To kiyi hankali dai kin san yanzu ba kowa ake yarda dashi ba." Dr.Ƙasim na faɗar haka sai ya miƙe tsaye ya tafiyarsa, Haulat cigaba tayi da tunanin wannan abu daya faru domin tanaji a jikinta cewa dole akwai wani abu da HOD yake nufi da ita amma kuma wannan abu ko menene?
   Ƙarfe takwas na safe Haulat ta nufi gida bayan isowar wadda zatayi duty a lokacin, har ta shiga ɗakinta amma sai tunani take, tana hawa saman gado bacci yayi awon gaba da ita domin daren jiya bata samu bacci ba sanadiyar tunanin daya dabaibayeta mata zuciya akan abunda ya faru, itace bata farka ba sai da rana liƙis, tana gamawa kimtsawa sai ta fito tsakar gida inda ta tarar Umma ta dafa jollof rice, abunda yaja hankalinta ga abincin shine cabbage da kifin data gani a ciki domin ita mace ce mai son cabbage da kifi, da sauri ta janyo plate da nufi kitchen inda Umma ke faman sauke abincin.
   " Kiyi hankali kada gasi koka ya ƙona ki." Inji Umma tana dubanta.
   " Umma gas cooker fa ake cewa ba gasi koka ba." Inji Haulat cikin ƴar ƙaramar dariya.
   " To shaiɗaniya hadda ke ko!" Inji Umma tana dubanta.
   " Ai gas ɗin ma ya kusa ƙarewa zuwa anjima zan siyo kamar litre biyu." Inji Haulat.
   " To ƴar albarka ALLAH ya miki albarka."
   " Amin amin Umma." Inji Haulat, anan ta fita riƙe da plate tabar Umma na gyaran table ɗin da gas cooker ɗin yake. 
Page 41
A saman tabarma Haulat ta zauna tana cin abincinta, can sai ga Aulat ta shigo tare dasu Ahnab, dubansu Haulat tayi tana tunanin ko daga ina suke.
  " Ke tashi ki zubo muna abinci." Inji Hanib cikin muryarsa mai razanarwa.
  " Hala bakada ƙafafu ne, kaje kitchen ka ɗiba mana." Inji Haulat cikin rashin tsoro.
  " Lallai ma yarinya." Haka Hanib ya faɗa yana mai walƙato hannunsa da nufin yanka mata mari, ita kuwa Haulat tana ganin haka sai ta rarumo plate ɗin da take cin abinci, ga fuska ta yaɓa masa abincin, da sauri Hanib yaja baya yana mai susar idanu sabida zafin da yaji, ita kuwa Aulat wani tsalle ta dako da nufin haɗiye Haulat, cikin tsananin sauri Haulat ta caɓeta daganan ta makata ga ƙasa, can gefe kuma sai ga Anib kamar an jefoshi, tun kafin Anib ya diro Haulat ta mayar dashi inda ya fito da wani bagidajen naushi, anan ya faɗi yana nishi domin jin yake kamar cikinsa zai fashe. Daga can baya kuma sai Haulat taji an janyo mata hannu da ƙarfi, tana juyowa sai taci arba da Hanib, kubcewa tayi akan riƙon daya mata daganan ta gwabra masa mari kamar yadda yake nufi da ita, da gudu ta nufi kitchen inda taci karo da Umma zata fitowa, sa ar da taci shine Umma bata riƙo komi ba.
  " Ke lafiya kuwa?" Umma ta faɗa da ƙarfi. Shi kuwa Hanib sai faman ciccika yake ganin Haulat ta tsaya bayan umma domin yasan cewa bazai samu daman dukanta ba.
   " Menene yake faruwa ne?" Umma ta faɗa tana kallon Hanib. Hanib shiru yayi domin bai san amsar da zai bata ba, ita kuwa Umma taƙi jinin rashin gaskiya, Hanib hararar Haulat yayi kafin ya fara magana:
  " Situfat gil, zamu haɗu ai."
  " Ƙaton takkwali kawai, stupid girl ake cewa ba situfat gil ba." Inji Haulat cikin aji. Hanib ya ɗan ji kunya akan wannan gyara da Haulat ta masa, abunda yafi baƙanta masa rai shine ƙaton takkwali data kirasa, a matsayinsa na ya yanta shine ya kamata ace yana mata gyaran turanci amma sai gashi itace ke masa, bazai zargi kowa akan wannan yanayi daya tsinci kansa ba na rashin ilimi domin yasan da cewa laifinsa  ne, da ace ya tsaya yayi karatun tun ƙuruciya da hakan bai faru ba.
   Juyawar da Hanib da zai yi da nufin tafiyarsa sai yaci karo da Anib da Aulat tsaye suna dubansa wanda hakan ke nuni da cewa sunji abunda ke faruwa. Da sauri Hanib ya tafiyarsa ba tare daya juyo ba, daganan sai Anib da Aulat suka rufa masa baya.
Page 42
Bayan fitar su Hanib daga gidan sai Haulat da Umma suka zauna saman tabarma.
  " Sai ƙaryar turanci alhali komi basu iyaba, dukkaninnsu fa secondar ce kawai suke taƙama da ita." Inji Haulat cikin takaici.
  " Hmm, su har sunada takaddun sakandarin nida ko firamare ban tafi ba." Inji Umma itama cikin takaici. Anan Haulat tayi shiru tana nazari maganar Umma domin tanaji a jikinta cewa abbansu wato sarki Salim yayi mutuƙar ƙoƙari daya auri Umma duk da cewa batada ilimin boko, a matsayinsa na sarki ya kamata ya auri mace wayayya ƴar gidan manya amma ko kaɗan bai duba hakan ba, daya tashi aure sai ya auro wacce gidansu baa  boko sai dai kasuwanci. Abunda ya baƙantawa  Haulat akan wannan tunani da take shine wai mazan yanzu kuwa zasu iya auren mace don ALLAH ba don wani arziƙi da take ɗauke dashi ba!  Murmushi Haulat tayi kafin ta juyo kan Umma.
  " Umma ki godema ALLAH tunda kinada ilimin addini, ai ilimin addini ake buƙata bana boko ba." Anan Umma tayi murmushin jin daɗi jin Haulat ta faɗi haka.
  " ALLAH ya miki albarka ƴata, abunda kika faɗa gaskiyane." Cewar Umma.
  " Amin amin Umma." Inji Haulat. Tun daga wannan rana sai hassada mai tsanani ta shiga tsakanin Haulat da ƴan uwanta, haka abu ya tsananta har ta fara ganowa. A wani lokaci a cikin dare, bayan Haulat ta samu kanta a cikin asibiti, zaune take saman kujera tana angaje domin bacci mai nauyi ke damunta, tana cikin wannan angaje ne sai taji an banko ƙofa da ƙarfi, firgigit ta miƙe tsaye cikin tsoro, HOD ne taga ya shigo sanye da babbar rigarsa sai cover shoe ɗinsa.
  " Ki biyoni mu tafi waje ga wata marar lafiya can a cikin mota." Inji HOD yana gyran hularsa. Anan Haulat tabi bayansa, suna fitowa sai taci karo da wata ƙatanyar jeep baƙa mai baƙin glass.
  " Yi sauri ki buɗe motar ki fito da ita tana ciki " Inji HOD yana gyran hularsa. Da sauri Haulat ta nufi motar da nufin buɗewa, ai kuwa tana buɗewa sai taji an janyo ta ciki da matsanancin ƙarfi, daga wannan lokaci Haulat bata ƙara sanin inda take ba. 
    kamar ji take ana huro mata iska, kamar dishi dishin wani abu take gani, firgigit Haulat ta farka tana nishi daƙyar, anan ta samu kanta cikin wani ɗaki mai duhu, zaune take saman kujera ɗaure tamau da kaca.
Page 43
Bazata iya faɗin lokacin da aka shigo da ita wannan ɗaki ba, anan takalli ɗakin kallon tsaf. Bako shakka ƙaton ɗaki ne mai karikitai a ciki, bazata iya ganin karikitan dake cikin ɗakin ba sabida tsananin duhu. Ba yadda bata yiba ganin cewa ta kubce amma abu yaci tura, ƴar ƙaramar fitila ce a rataye wadda ke haskawa, tafiya ta faraji an nufota, ba ƙaramin tsoro ne ya cika mata zuciya ba, sai daga baya ta gano cewa akwai wata ƙofa a can bayanta, wannan ƙaton ta gani yayi tsaye a gabanta sanye da jeans and short short, sai cover she ɗinsa abun tsoro tare da baƙin glass, kallon ƙeta ya fara yi mata wanda hakan ya tabbatar mata da cewa yanada masaniya akan abunda yake faruwa, can sai ga Hanib da Anib sun shigo ɗakin suma sanye da ƴan kanti da cover shoes, amma su basu sanya glass ba, Haulat shiru tayi tana tunani ace wai da sanin ƴan uwanta aka yi mata wannan aika aika, abunda ya ƙara tayar mata hankali shine ganin shigowar Aulat a ɗakin, wato kenan sun haɗa kai domin ganin bayanta, anan suka keɓanta da ƙaton suna wata magana sannu sannu, bazata iya jiyo abunda suka faɗa ba amma tana tunani cewa suna magana ne akanta, suna gama maganar sai suka juya suka tafiyarsu suka bar ƙaton anan. Ƙaton yana ganin sun tafiyarsu sai ya fara binta da wani irin kallo, ita kuma Haulat tana duban idanunsa ta gane abunda yake nufi da ita domin a wannan lokaci ba hijabi ne a tare da ita ba, riga da wando na uniform ne a jikinta, sa ar data samu shine basu cire mata ɗan kwali ba. Haulat na ganin nufinsa sai ta fara binsa da murmushi cikin alamar cewa ta aminta, shi kuwa gogan yana ganin haka sai hankalinsa ya tashi, da sauri ya kwance ta yana mai kallonta, da yaga abun bazai yiba sai ya fara kwance bell ɗinsa da sauri, ita kuwa Haulat sai da ta bari ya hankaltu ga kwance bell sai ta janyo wani ƙarfe data hango gefen ɗakin, kafin ƙaton yayi wani abu tuni ta makeshi, anan ya faɗi sumamme, da gudu ta fito ɗakin tana duban hanya, anan ta gane cewa a cikin dare ne kuma gida ne ƙaton gaske mai lunguna lunguna, anan Haulat ta fara gudu iya ƙarfinta amma duk inda ta shiga sai taga lungu ne kamar babu hanyar fita, ba yadda bata yiba domin gano hanyar fita amma abu yaci tura, tana cikin dube dube ne sai ta fara jiyo maganganu a can gefe, laɓewa tayi domin ganin kosu waye, can sai ga HOD tare da wasu ƙattan samudawa, anan ta kalli waɗannan samudawan domin da ganinsu tasan ba mutunci, kowanensu sanye da ƴan kanti sai baƙin glass, suna wucewa sai Haulat ta fito tabi bayansu, haka taci gaba da binsu har ta samu damar fitowa a cikin gidan.
Page 44
Anan ta gane cewa narkeken gidan sama  ne abun tsoro a cikin daji, HOD da samudawa komawa gefe sukayi suna tattaunawa ita kuwa Haulat tana ganin haka sai ta juya da gudu ta shige daji cikin rashin sanin cewa samudawan sun hangota, anan suka biyota ita kuma jin haka yasa ta ƙara ƙaimin gudunta, abu ga mace kuma mai rauni sai ta faɗi sabida tsananin gajiya, HOD ne ya karaso wurinta tare da ƴan uwanta su Hanib, wata kwalba wani basamude ya baiwa HOD, shi kuwa HOD buɗa kwalbar yayi daganan yayo kan Haulat wadda ke faman rairafe tana nishi daƙyar, Aulat ce ta tsayar da ita daganan sai HOD ya fara zuba mata ruwan dake cikin kwalbar, tun da HOD ya fara zuba mata ruwan ga fuska Haulat bata ƙara sanin inda take ba.
   " Sannu sannu." Firgigit Haulat ta farka tana kallon Umma a gefenta tana jera mata sannu, anan tagane cewa kwance ne take a asibiti, an sanyama fuskarta  plaster a hannun haggu " Kada ki damu Haulat domin waɗanda suka yi miki wannan ɗanyen aiki asirinsu ya daɗe da tonuwa, ƴan sanda ne masu patrol ɗin dare suka tsinto ki a cikin daji kuma suka kawoki asibiti, daganan sai ƙawarki Ramlat ta bugo ta faɗamin, yanzu haka da nake magana HOD yana kotu domin an kamasa  hannu dumu dumu cikin ƴan fashi da makami baya ga kuɗin asibiti daya cinye, ita kuma Aulat ta rasa idanunta na hagu, itama a cikin daji aka tsinto ta kamar yadda aka tsinto ki, har yanzu ban san abunda ya sameta ba iyaka sai kuka take tama faɗin ki yafe mata," Anan Umma ta nuna ma Haulat gadon Aulat a can gefe, " Hanib da Anib sun zama musakkai domin halshensu ya kare ta yadda basu iya magana, kuma sun rasa ƙafafuwansu na hagu,  suma tsinto su akayi a cikin daji jina jina kuma har yanzu ba a san abunda ya faru dasu ba." Umma na zuwa nan sai ga Dr.Ƙasim yazo.
    " Haulat sannu." Haulat ɗaga masa hannu kawai tayi ba tare dayin magana ba. " Umma nazo ne na faɗa miki cewa gobe ne zamu tafi India domin ga binciken da mukayi mun gano cewa mummunan acid ne aka zubama Haulat ga fuska kuma mun samu tabbacin cewa asibitin da zamu tafi sunada ƙwararrun kayan aiki."
   " To ba matsala ɗana ALLAH ya sakama da alheri wannan ɗawainiya da kakeyi haka." Dr.Ƙasim ajiye wata leda yayi mai cike da kayan abinci daganan ya tafiyarsa. 
Page 45
Mun samu damar tafiya India, an yi aiki sosai kuma na samu sauƙi, HOD ƙaryarsa  ta ƙare domin an yanke masa hukuncin Life in Prison tare da sauran waɗanda aka kama masu sa hannu ga wannan laifi, Tun anan duniya Hanib da Anib da Aulat sunga abunsu domin duk sun walaƙanta, halshen su Hanib ya buɗe wanda hakan yasa suka cigaba da magana, sun nemi na yafe musu, da farko ban yi nufin yafewa ba amma sabida wasu dalillai sai na yafe musu, Hanib da Anib sun samu aikin share share a wata asibiti dake kusa, ita kuma Aulat sai ta auri wani bakanike mai ijiya ɗaya. Ni kuma Dr. ƙasim ne da kansa ya faɗamin cewa idan har na aminta zai aiko da manya ayi maganar aure. Kuma hakan yamin dai dai domin na aminta, har yanzu da nake bada wannan labari Hanib, Anib da Aulat basu fadi yadda akayi suka zama musakkai ba, kuma a cikin ransu basu son maganar domin da an fara sai su tashi. Wata rana sai aka aiko mana saƙo cewa ƙanen mahaifinmu da akaba sarauta rai yayi halinsa sabida haka sarauta zata dawo gidanmu sabida shi bayada ƙane kuma bayada ƴa ƴa masu girma. Hanib ne ya kamata aba sarauta tunda shine babba amma kuma hakan bazai yiwu ba tunda bayada ilimi kuma ga tulin laifin  daya aikata wanda mutane bazasu so ace shine sarki ba, hakama Anib, ni aka tambaya idan inada miji wanda na aminta dashi za a iya bashi sarautar, Dr.Ƙasim na kira  kuma cikin sa a ya aminta, anan aka baiwa Dr. Ƙasim sarauta daganan kuma akasa rana idan al amurra sun kwanta za ayi shagalin bikinmu. Wannan shine labarina kuma labarin masarautarmu." Inji Haulat.
   " Tofa matar sarki, wannan labari ya ƙayatar amma inada wata tambaya." Inji Jalim. " Inaso ki fadamin hala wane dalili ne yasa kika yafema ƴan uwanki alhali daga farko bakiyi  niyar yafe musu ba!" Inji Jalim. Anan Haulat ta kallesa  kafin ta bashi amsa.
   "  Wannan dalili shine, mu mutane mun kasance masu aikata laifi ako yaushe, sabida haka ya kamata idan wani ya muna laifi kuma ya nemi mu yafe masa to mu gaggauta yafe masa domin muma mu samu gafara ga ALLAH maɗaukakin sarki."
" ALLAHU AKBAR." Haka su Uzaim suka faɗa tare cikin jin daɗin kalamin da tayi. Daganan sai Haulat ta samu wuri ta zauna. Shi kuwa Uzaim saiya miƙe ya tsayu tsakiyar ɗakin domin yin bayani :
" Wannan labari da Haulat ta bamu ya karantar damu cewa ita mugunta mai ƙarewa ce, kuma duk wanda ya zartar da ita ga wani to sai yaga abunsa."
Page 46
" Kamar yadda muka gani ƴan uwan  Haulat sun haɗe mata kai wanda hakan yasa suka cutar da ita amma sai gashi daga ƙarshe abun ya dawo kansu tunda har sun walaƙanta, hassada guba ce, kuma duk wanda ya hau jirgin wannan guba to sai ta aikasa ga aikata ashsha kamar yadda ya faru gasu Hanib, hassadar da suka bayyanar ga ƴar uwarsu itace silar rushewar duk wani jin daɗi da suka gina, rashin  ilimin addini hasara ce, aikata mummunan laifi kuskure ne babba tunda gasu Hanib sune ya kamata a baiwa sarauta amma sabida rashin iliminsu da kuma ɗanyen aikin da suka takfa sai aka fasa basu sarautar.  Kuma ya kamata mu sani cewa riƙon mutum har zuciya bayada amfani, abun nufi anan shine idan mutum ya maka laifi kuma ya nemi ka yafe masa to ka amsa, wato ka yafe masa, haka kuma idan mutum zai zaɓi matar aure, to kada yace sai ƴar boko, kamar yadda muka gani shi marigayi sarki Salim matarsa ba ƴar boko bace amma kuma mai ilimin addini ce, ga ladabi da sanin ya kamata. A nan zamu dakata sai wani sati idan ALLAH ya kaimu ran friday zamu ƙara haɗuwa a nan domin cigaba da tattaunawa." Anan suka tashi suka fara fita ɗaya bayan ɗaya da zimmar cewa sai ran friday zasu dawo domin cigaba da tattaunawa.

  A WANI LOKACI
                                                                                By
  Abdul King Article                                   
   Halima Bala Wakili    
    Queen Nasmah
                                                                          Episode Four
               (Dark and Darkness)
   King and Queen Writing Chamber
Page 47
Haris ne a tsaye yana duban abokansa dake cikin  ɗakin, sanye yake da jeans and t shirt kamar yadda su Uzaim suka yi dress, sai dai shi a ko yaushe zaka ganshi da wani handkerchief, yakan lauya wannan handkerchief ga fuskarsa yadda idanuwansa kawai ake iya gani, su kuwa su Uzaim a wannan lokaci sun tsuro masa ido domin jin abunda zai faɗa, ajiye handkerchief ɗin yayi a gefe yadda kowanensu zai iya ganin fuskarsa, to a nan suka gane cewa hancinsa yana da tsaguwa mai girma a tsakiya domin an rataya wata yar ƙaramar roba wadda ta manne hancin dai dai ba ragi ba ƙari.
   " Na taɓa tsintar kaina a cikin duhun rashin tunani da kuma duhun rashin zaɓi," Haka Haris ya faɗa yana mai kallon su Anisa, " A wannan lokaci banada ra a yin kaina domin duk abunda abokaina suka faɗamim ina ɗaukarsa a matsayin gaskiya cikin rashin sanin cewa wasu kan faɗi ra a yinsu ba tare da tunanin abunda zai biyo baya ba, wannan duhu dana tsinci kaina a ciki shi ne sanadin rasa hancina har takai cewa bana iya sheɗa ba tare da wannan robar da aka aza min ba, kada na jaku da surutu bari na faɗa muku abunda ya faru:
A wani lokaci inada shekaru sha takwas a duniya, na kasance yaro mai tarin abokanai kuma duk abunda suka umurce ni shi nake yi ba gargada dan gani nake yi banida wasu masoya sama da su.Wata rana ina zaune akan motar yayana da ya aje ƙofar gidanmu, na ɗora ƙafata ɗaya kan ɗaya ina ta shillo da ita, sai ga su Abeer sun zo wurina, da murnata na diro daga kan motar muka gaisa da su, sannan na ƙara hawa kan motar dan a lokacin babu wanda ya kai ni rashin ji a wannan garin namu.Duk suka haye kan motar kasancewar su biyu ne, sai ya kasance mu uku ne muka zauna bayan motar, muna ta labari, sai ga wata yarinya mai suna Aleesha ta zo wucewa.
Page 48
“Ina ma ace ta so ni "na faɗa, Adam wanda suka zo tare da Abeer ya ce “wallahi ka je ai ba za ta ƙi ka ba", kafin in yi magana Abeer ya ce “idan ta ƙi amicewa ka watsa mata mari ", ina kallonsu cikin gamsuwa da maganar su na ce haka za a yi bari na je.Dirowa nayi daga motar cikin isa da ƙasaita nake tafiya ina jin ni na isa, na nufe ta, jimana ƴam mata, na kira ta amma bata juyo ba, da sauri na tari gabanta, ina saka hannuna cikin aljihu na ce “ Haba Baby Aleesha magana nake yi fa " nayi maganar ina shafa gefen sajena da ya kwanta luf da shi ya bi fatar jikina, “matsa min a hanyata," ta faɗa tana kaucewa. Kin ko san da wa kike magana, Haris ne fa na faɗa ina ci gaba da shafa gefen sajena. “Eh Haris ne sai me in kai ne, ƙaramin yaro da kai har ka iya tare mace, mtswww."  ta ja wani dogon tsaki, bata kammala yin tsaki ba, ta ji tassss saukar mari a kuncinta.Ina huci kamar mayunwacin zaki na ce who the hell do u think u are, har kina da bakin gaya min magana, to hell with u and ur fucking life, useless maggot. Galala Aleesha ta saki baki tana kallona yayinda na juya ina tafiya, ashe duk abunda ke faruwa akan idon yayana ne Hasheem wanda ya fito da niyar jan mota.Ina isa gaban motar yaya Hasheem ya fara min faɗa “Dama ashe kai wawa ne ban sani ba, miyasa kullum sai kayi abunda zuciyarka ke so ne, dama an daɗe ana faɗa min baka jin magana ashe maganar da gaske ce," sosa ƙeyata na shiga yi ina jin shi yana faɗa amma sai na karkace kaina kamar ba da ni yake ba.Su Abeer kuwa ƙasa suka diro suna gaida yayana da basu san ya zo ba sai da suka ji yana min faɗa, can ciki-ciki ya amsa musu sannan ya buɗe motar ya bata wuta ya wuce abun shi.Abeer ya matso kusa da ni yana tambaya “wannan shi ne babban yayanku," na ce" Eh shi ne."  " I don't like him ya fiye faɗa," dariya suka tare Adam ya ce “Don't mind him shi ma lokacin da suna yara haka yayi". Murmushi nayi na ce “let's go in, am sure mama is done with our lunch ".Tare muka shiga cikin gidan suka nufi part ɗina ni kuma na nufi ɓangaren su Mama. Ta backyard na zagaya dan na samu na shiga kitchen kai tsaye. Tsaye Mama take tana rufe food flasks ɗin mu, " Hello my beautiful mom, " na faɗa Ina waving hannuna, murmushi ta mayar min tana shafa gefen fuskata ta ce “ my handsome son is growing, someone should congratulate me plss,"

Page 49
 Ina jujjuya ido na ce " Congratulations for having someone as handsome as I am, I hope my lunch is ready." Tana murmushi ta ce “yes my son, hope su Adam sun zo."  " Yes Mama suna side ɗina." Murmushi tayi kasancewar Mamana akwai far'a idan kayi magana da ita sau dubu zata maka murmushi sau dubu, “oya kar ka bar su da yunwa ku je ku ci abinci " tayi maganar tana miƙa min tray mai ɗauke da kuloli guda biyu, karɓa nayi sannan na wuce. Ɗaki na dawo na sami su Abeer sun baje suna ta kallo, zama nayi gefe na ce, " guys Kuna ganin abunda Aleesha ta min ya dace, na zubar da ajina na tunkare ta amma ta watsa min ƙasa a ido," Adam ya ce “u can take revenge my dear worry not about it," "How?" na karɓi zancen, Abeer yayi saurin karɓar zancen “gobe zata je School, mu tare ta a hanya mu mata dukan tsiya". Murmushi nayi irin na mugunyar nan na ce " Oh yesss haka shi ne dai-dai, I will teach her a great lesson of her life, she will regret knowing me in her life, mu ci abinci. " Haka muka gama cin abincin nan muka tattara muka fita wurin ƙwallo. Ba  ni na dawo ba sai dare , ko da na dawo jikina yayi liƙis ga wata muguwar gajiya . Ko wanka ban yi ba na faɗa kan gadona sai barci. Washe gari da safe su Abeer suka tashe ni daga barcin nan, wanka nayi na shirya ko breakfast ban yi tsabar Ina jin masifa, haka muka nufi hanyar makarantar da Aleesha take . Aka yi sa a kuwa muna zuwa sai gata ta ɓullo sanye da kayanta na makaranta da suka sha guga, nan take muka mata zobe dan yau mun ƙara yawa mu biyar ne, karkace kai nayi cikin isa na ce, " Kin yi tunani yanzu zan iya samun amsa," cikin kallon tsana ta ce “I hate u , and I will never love u, never in my life. " aiko su Abeer suka yi cikinta da bugu ni kuma nayi tsaye ina kallonsu. Mutanen da dama tun ɗazu suna wurin zaune hankalinsu ya dawo kanmu dalilin kukan da Aleesha ke yi,  da sauri suka nufo mu gadan-gadan. Da ƙyar suka ƙwace ta hannun su Adam. Tun daga wannan lokacin na ɗaura aniya da fitsara kala-kala, tun Momy bata yarda ba har ta fara yarda, gashi a lokacin duk wanda nayi ma laifi bai isa ya rama ba dan Daddy zai tsaya a case ɗin. So da yawa ansha ɗauko min ƴan sanda da zummar kama ni amma Yaya Hasheem zai shiga zancen a kashe case ɗin idan komai ya lafa ya min faɗa kamar idonshi da bakinshi zasu faɗo. Ko kaɗan hakan bai sa na ji a raina zan daina ba, dan gani nake yi ina kan hanyar daidai.
Page 50
Kwatsam sai lokacin zagayowar haihuwata ya zo, a lokacin zan cika shekara 22 a duniya, ni da abokanaina muka shirya bikin cika shekaruna ashirin da biyu, muka gayyato mutane maza da mata aka sha biki, an ci ansha an gode ma Allah. A wurin wannan taron ne na ƙara ƙyalla ido akan wata yarinyar kyakkyawa, dana tambayi Abeer wanda ku san duk shi ya gayyato waɗannan mutane sai ya ce min sunanta Hibbatullahi. Ba wai ina sonta ba ne sosai amma dai yarinyar ta min, kuma tunda idona suka yi tozali da ita ganin wayewarta yasa nake ganin dole sai na yi soyayya da ita. Bayan an watse wannan taron da safe na bibiyi gidansu. Ina zuwa na sa aka mata sallama ta fito, tana zuwa na faɗa mata abunda ke zuciyata kai tsaye ba wata kwana-kwana, amma sai taƙi amincewa da ni. Sosai abun ya min ciwo ganin har gida na bita, da yake a lokacin ɗabi'ar bugun mata ya same ni aiko na daddage na kwashe ta da mari, ta ɗaga hannu zata rama na riƙe hannun na sake kai mata wani marin. Da kuka ta shige gida. Ni kuma na kunna sabon machine ɗina da Daddy ya siya min as birthday gift na wuce. Ina zaune gida ina cin abinci na ji ana buga gate ɗin gidanmu kamar za a ɓalla shi, yayana mai bi min Hamza ya je ya buɗe dan daga ni sai shi ne a ɗakin. Yana buɗewa ya ga ƴan daba  rututu sun shigo cikin gidanmu, wanda a cikin ƴan dabar har da yayan Hibbatullahi. Ina jiyo muryoyinsu suna magana da Hamza amma na ƙara gyara zamana .“Ina wannan mara kunyar ƙanin naka?" Yayan Hibbatullahi wato Habibullahi yayi magana cikin muryar ƴan daba. Hamza ya ce “ya fita " , “Ga saƙo ka faɗa mishi idona idonshi sai na sauya mishi halitta "  Habibullahi yayi maganar, Ina zaune ina saurarensu Hamza ya shigo cikin ɗaki ya kwanta, kallonshi nayi na ce su waye . Hamza ya ce “Ban sani ba," na ce "Daga tambaya," Hamza ya ce “Kai ka sani tunda baka jin magana, abun da yasa ka shiga gonar Habibullahi shi zai maka bayani idan ka ci ɗan banzan duka u will get back into your senses," ɗage kafaɗu  nayi irin ko a jikina duk da a zuciyata tsoro ne fal a raina dan ranar yini nayi ɗaki ban fita ba. Washe gari ina Ƙofar gida sai ga su Adam sun zo. Sun lura da yanayina gaba ɗaya na canza saboda tsoron da yayi tasiri a raina. Ahmad ya ce " Wai Haris lafiya dai," 

Page 51
numfashi na sauke dan gani nake yi maganin matsalata ya zo na ce " Yayan Hibbatullahi ne ya zo gidanmu jiya ya buge min warning akan ƙanwarsa Hibbatullahi," Adam ya ce “hala me ka mata," "yo kuma ai kun san dukanta zan yi. Marinta nayi har sau biyu." Na faɗa musu, Faruk ya ce “yanzu ma tashi zaka yi mu je bikin da ake yi unguwarsu mu buge mata warning." aiko cikin jin ƙwarin guiwa na ɗauki mutum huɗu a machine ɗina muka tafi wanda kowa yasan mun mishi yawa. Muna zuwa ko muka tarar ana ta rawa,har da ita Hibbatullahin, muka shiga aka yi rawa da mu, sannan muka ja ta gefe, na ƙara mata barazana idan har bata sa yayanta ya fita harka ta ba sai na sauya mata kamanni, har aka yi kwana huɗu Habibullahi bai ƙara zuwa gidanmu ba, mun sha haɗuwa da shi a hanya amma sai ya ɗage kai ya wuce, haka yasa na sakankance akan ya bar zancen, Na ƙara zuwa wurinta, ina tsaye ina jiran zuwanta kawai sai ga Habibullahi da tawagarshi sun zo a buge suna layi. Wani abokinshi ya ce “Kai wannan ba Harissss ba neeeh?" cikin wata murya ta maye. Aiko nan suka yi cikina da bugu suka mini liƙis, a daddafe na dawo gida dan ko da na ja machine ɗina bana gani da kyau kawai dai na ja shi ne dan ba ni da mai kawo ni gida, a ranar ikon Allah ne ya kawo ni gida dan ko da na iso ban gane ina nake ba, Hamza na zaune ƙofar gida ya ganni cikin jini da sauri ya nufe ni tare da saurin tare machine ɗin ya riƙe shi gam duk yadda ya kai ga riƙe machine ɗin sai da ya buge gate da ƙarfinshi, ni kuma jini ya buge ni na faɗi tim a ƙasa, Hamza ya tashi ta ɗaya yana ɗingishi dan ƙafar tashi ta bugu sosai ya shiga cikin gida ya kira Mommy, hankalinta ya tashi sosai ganin yadda fuskata tayi dameji, idan ba an faɗa maka ni ne ba to ba za ka yarda ba, tana kuka ta kira yaya Hashim, yana zuwa aka ɗauke ni zuwa asibiti, nan aka ba ni taimakon gaggawa, wanda da farko sai da aka ƙi karɓa ta akan cewa sai jami'an tsaro sun saka hannu, Yaya Hashim ne yayi tsaye har suka amince aka shiga dani ciki, sosai aka shiga binciken lafiyata musamman yadda aka ga ciwon.Bayan gwaje-gwaje da bincike-binciken da likitoci suka gudanar sai suka gano hancina ya samu matsala, suka yi min aiki a hanci, sannan aka maida ni ɗakin jinya, ni kuma a ranar na sa wa Mommy rigima sai an sallame ni, yaya Hashim ya dinga faɗa.
Page 52
amma mommy ta dage sai an sallame ni, dole ba yadda ya iya ya bi umurnin mommy suka wuce, aka bar Hamza da mommy ta lura yana ɗingishi sanadiyyar buguwar da yayi da mashin,  Yaya Hashim ya bashi dubu biyar ya biya kuɗin magani ya same mu gida, muna dawowa Mommy ta fara tambayar abunda ya faru amma fir na ƙi sanar da ita ƙarshe ma da ta dame ni da tambaya tashi nayi na shige ɗaki.
BAYAN KWANA BIYU
Na tashi da safe da mugun ciwon kai wanda ya sanya na gagara leƙa koda waje ne, ga shi zugin da nake ji ya gauraye ko ina na fuskata, musamman hancina da nake ji ko wane lokaci zai iya watsewa tsabar raɗaɗin da nake ji. Mommy ta buɗe ƙofar ɗakinmu ta shigo, cike da mamakin ganina kwance tana kallona, dan ta san jiya na fita. “Dama kana nan ?" ta tambaya tana mamaki, da ƙyar na iya ɗaga baki na ce “eh,"  jikina ta taɓa ta ji shi rau da shi yayi zafi, da sauri ta ɗauke hannunta daga jikina tana faɗin “Haris are you okay," cikin ƙarfin hali ina ɗan cije baki na ce “not really " juyawa tayi ta nufi labulen ɗakinmu, ta ɗage labulen windown ɗakinmu yadda zata ganni da kyau, sannan ta dawo ta tsaya gabana, ware ido tayi ganin yadda fuskata ta kumbura “Haris this is serious, Bari na kira Abbanka. " Ta ƙarasa maganar tana taɓa wayar hannunta, girgiza mata kai nake yi ina mata hani da kar tayi hakan, da yake mommy mutum ce mai son farincikina sai ta fasa kiran Daddy, ta kira Yaya Hashim, da yake gidansa da gidanmu ba wani nisa, bai yi cikakken minti bakwai ba sai ga shi ya zo. Da ƙyar nake tafiya idan mommy ta yi yunƙurin kamani sai in kauce dan ko kaɗan bana so a ga ni raggo ne. Motar yaya Hashim muka shiga ya kai mu asibiti. Muna isa aka yi ƴan cike-ciken takardu, sannan aka aje mu a waiting room, Sai da muka kai ga layi sannan muka shiga wurin likita, muna zuwa likita ya min tambayoyi sannan ya sanar da Mommy za a min hoto a hanci. Ɗakin X-ray aka shiga da ni, nan aka ɗauki hoton ƙashin hancina,  sannan aka ce na jira waje har hoton ya fito, muka jira na kusa awa ɗaya, dan sai da aka yi ta yawo da hoton ƙashin, sannan aka kai ma likitan da muka fara gani da muka zo, nan yayi ta dube-dube da karanta sakamakon hoton, sannan ya ɗago ya kalli mommy ya ce “Hajiya dole sai mun shiga da yaronki surgery room yau ɗin nan. "  
Page 53
 ido mommy ta zaro waje ta ce “likita yi min bayani yadda zan gane." likitan ya ce “ hancinshi zamu yanke domin ciwon ya fara kama gefen fuskarshi, idan ba a cire ba kawai yuyuwar ya shafi duk ilahirin fuskarsa, kafin matsalar tayi yawa ya kamata a yi saurin ɗaukar mataki tun abun bai fi ƙarfinmu ba."  Sosai hankalin mommy ya tashi, dole ta kira Daddy ta faɗa mishi abunda ya faru. Haris yayi shiru yana kallon su  Uzaim da tun ɗazu suka yi shiru suna sauraren labarin sa. Uzaim ya ce “Amma Haris ya mommy tayi da Daddy?" Numfasawa Haris yayi ya ci gaba da magana.“A nan ta sanar da shi halin da ake ciki, nan ya nemi a bashi likitan suyi magana da shi, likitan ya mishi bayani sosai fiye da yadda ya ma mommy, nan daddy ya karɓi account number likitan ya tura mishi 30 million, ba wani ɓata lokaci aka shiga da ni ɗakin tiyata, aka min allurai  daga nan ban sake sanin inda nake ba sai farkawa nayi na ganni da wannan robar a hancina. " Uzaim ya ce tabbas rashin jinka ya janyo maka, amma wani mataki aka ɗaukar ma su Habibullahi?" “Daddy ne ya hana mommy ɗaukar mataki a cewarshi, wanda ya jawo ruwa shi ruwa ke ci. " Haris ya faɗa. Uzaim ya ce “haka ne kam."  “ Kuma tun daga wannan ranar na rabu da duk wani mugun aboki nawa." Haris ya faɗa yana yana kallon su Uzaim. " Wannan shine ƙarshen labarina." Cewar Haris bayan ya nufi kujerarsa domin ya zauna, ai kuwa yana zaunawa sai Uzaim ya miƙe tsaye ya nufi tsakiyar ɗakin ta yadda kowanensu zai iya ganinsa daganan sai ya fara bayani kamar haka :
  " Darasin da zamu duba a cikin wannan labari da Haris ya bamu shine, kada ka sakankance cewa duk abunda aka faɗa maka zaka yarda, duk abunda aka faɗa maka kafin ka aikata ya kamata kayi tunani akai, kasance mai ilimi na addini dana boko kuma ka kasance mai amfani da ilimin ta hanyar daya kamata, sai kuma inaso nayi muna tuni da cewa kada mu yarda duhun rashin tunani da duhun rashin zaɓi ya dabaibaye mana zuciya, a nan zamu dakata sai kuma wani makon idan ALLAH ya kaimu zamu ƙara haɗuwa ran friday a irin wannan lokaci domin cigaba da tattaunawa." Uzaim na faɗar haka sai kowanensu ya miƙe da zimmar fita waje.

    A WANI LOKACI
                                                                             By
  Abdul King Article        
   Halima Bala Wakili    
    Queen Nasmah
                                                                         Episode Five
                                                                       (Black Blunder)
   King and Queen Writing Chamber
Page 54
  " Milam ce ya kamata ta bamu labarinta amma sabida rashin zuwanta zan maye gurbinta." Haka Uzaim ya faɗa yana duban su Anisa. " Da farko dai..." Kafin ya iyar da maganarsa ne sai ga Milam ta shigo ɗakin da sauri.
   " Babies kuyi haƙuri fa nayi latti." Haka Milam ta faɗa tana dubansu cikin murmushi.
   " Ke su waye babies?" Inji Anisa tare da masga mata harara.
   " Ke kuma Jissu ba ruwanki." Haka Milam ta faɗa tare  da murguɗa baki. Ita kuwa Anisa abun dariya ya bata, tun a lokacin data basu labarinta shi kenan sun mayar da ita Jissu.
   " Jissu Jissu, venha aqui e case comigo, não posso viver sem você." Haka Jalim ya faɗa cikin tsokana. Ita kuwa Anisa dubansa tayi cikin mamakin yadda ya faɗi jimlar ba tare da kuskure ba sai kace yanajin halshen Portuguese ɗin. Su kuwa sauran dariya ce ta kubce musu sai da Uzaim ya tsawatar sa annan suka dakata.
  " Tunda Milam ta iso zamu bata fili domin ta bamu labarinta sabida haka Milam fili nakine." Inji Uzaim. Ita kuwa Milam da sauri ta matso kusa garesa, wani abu ta faɗa masa a cikin kunne daga nan sai ta zauna. Shi kuwa Uzaim cigaba yayi da bayaninsa kamar haka : " Sabida wasu ƴan dalilai Milam bazata samu damar bamu labarinta ba sai dai zuwa wani sati, a bisa wannan dalili ni kuma zan maye gurbinta na bada labarina." Tsuro masa ido sukayi domin jin abunda zai faɗa. " Bakinsa ya buɗe ya janyo haƙoransa, anan suka gane cewa ashe haƙoran roba ne yake sanye dasu, haƙoransa na gaskiya ƴan ƙalilan ne. Bayan ya nuna musu haƙoran sai ya fara bayaninsa:
    " Idan zan tuna rayuwar danayi a baya to zan kasance mai yin nadama akan abubuwan da suka gabata, bako shakka na kasance mutum mai baƙar aƙida, kuma wannan baƙar aƙida itace silar jefani a cikin aikata kuskure, kuskuren daya kasance abun kunya a gareni, inaso ku kusance masu saurare domin yanzu zan fara da abunda ya faru.
Page 55
A wani lokaci, ina da ƙananun shekaru na, baƙar aƙidar da na ɗaukar wa kaina itace shaye-shaye. Mahaifina Malan Barau babban malami ne na Muhammadiya a rugar mu ta Ƴar tugu fa dake cikin ƙauyen Bunguɗu, ɗai daga cikin ƙaramar hukumar Jahar Zamfara. Mahaifi na yana da ɗiya biyar, huɗu mata, sai ni kaɗai namiji kuma babba a cikin su. Faɗin tarbiya da kulawa da iyayen mu suka bamu bata lokaci ne, sun yi tsayin daka akan mu na ganin mun zama abun ƙauna da alfahari ga al'umma, sai Allah ya jarabce su akaina, a matsayina na babba, kuma namiji wanda suke fatan ko bayan ransu zan riƙe ƴan uwa na da aminci. Kwatsam, komai ya canza a rayuwa ta, na koma sabon mutun kamar ba niba. Ance komai ze faru yana da sila, to zan iya cewa silar lalacewar rayuwa ta ya fara ne daga bin wani abokin banza mai suna Gazali. Shi kuma Gazali ɗalibi ne a makarantar baba na, to wataran muna zaunawa muyi karatu a tare, kuma umurnin baba na ne, yace in dinga taimaka mashi gurin karatu, saboda baya gane karatu ko kaɗan, wataran har azo a tashi Gazali bacci yake a aji. Ranar da bazan manta ba, naje gidan su Gazali dan in dubashi kwana biyu bai zo makaranta ba, koda naje na iske shi a cikin maye, nasan shaye shaye haramun ne kuma ɗabi'a ce wadda kowa ke guje mata, ina kallon shi ina mamakin mai zai kai mutun mai hankali shan wannan ƙazantar, na duƙa na ɗauki wata kwalba na buɗe na shaƙi abunda ke ciki, a take na rufe na a jiye kamar inyi hauka saboda warin da naji, na kalle shi nace mashi,
" Gazali miye amfanin wannan rayuwar, daɗin mi kake ji idan kana shan wannan abun, shiyasa kullum cikin aji baka mai da hankali sai bacci, miye ribar wannan ƙazamar rayuwar dakasa kanka,?"
 Gazali ya ɗago ya kalle ni yana wata dariya, sannan yace,
"Kai Uzaim bazaka gane ba, ita fa wannan harkar daɗi gareta, sam babu wata damuwa aciki, kai ma kaɗan gwada mana, zaka san abunda nike nufi," 
Ya ƙare maganar yana miƙomin kwalbar abunda yake sha, ni kuma nasaka hannu na buge kwalbar sai da ta faɗi ƙasa ta zube, sannan na nuna shi da yatsa nace,
Page 56
" Ni bazan ta ba irin wannan rayuwar taka ba, kuma kai ma ina maka addu'ar shiriya da dik masu hali irin naka, kuma Inshallah idan baka bari ba sai na gayama baba salihi ( cewa da baban Gazali ɗin )",
Ai ban rufe baki ba Gazali ya fara babbaka dariya kamar mahaukaci, hakan ne yasa na ɗago ina kallonshi da mamaki kafin yace,
" To kaje ka faɗa mana, an gaya maka banda lasisin akan abunda nike aikatawa ne, Allah ya kiyaye, ko in kira maka shi ?yana cikin gida,"
   Fahimtar renamin da wayo zeyi yasa kawai na juya na fita ɗakin ina mamakin wannan abu.. a cikin rai na kuwa inaji banga abunda za'a bani da zai sani aikata ɓarnar shaye-shaye ba. Sai na ma kaina alƙawari zan kama baki na mu cigaba da karatu kawai tsakanina da Gazali.
   A duk iya ƙoƙarina na ganin Gazali ya bar bacci a aji ya kuma mai da hankali ga karatu abu yaci tura, malan na Lura da yanda nike iya ƙoƙarina akanshi, wataran ban iya karatu na ba, amma haka zan dage dan inga ya iya nashi. To randa akaci sa'a yazo da kanshi, dan mafi akasari yayan shi ke taso ƙeyar shi da bulala, to ranar kam karatu zeyi ba sauƙi, har mamaki nike da na gaya mashi da ya riƙe kuma ranar bazai yi bacci ba. Anan na gane cewa Gazali har ma ya fini basira kawai dai be amfani da ita ne yanda yada ce.
   A haka muka yi sabo sosai dashi, duk inda zaka gan mu atare muke, mafi akasari in zanje gidan su zan iske shi yana bacci, inyi ta mamakin hali irin na Gazali, tunda na riga nasan dalilin yin baccin sai kawai in wuce ba tare da ma yasan nazo ba. 
  Ranar mun gama karatu da wuri, saboda yana cikin hayyacin shi shiyasa mukayi saurin gamawa, sai yace inzo in rakashi wani guri, atake nace mashi bazan je ba, dan tausayi ne kawai yasa nake kulashi badan inaso ba, nan ya fara min daɗin baki da cewa ai ba jimawa zamuyi ba zamu dawo, ba dan rai na yaso ba haka nan na bishi. Tafiya muke naga beda niyar tsaya wa yace mun kawo inda zamu, inason inyi mashi magana kuma dai na share dan inga iya gudun ruwan shi. Wani kongon gida mukaje, tun daga bakin ƙofar zaka fara cin karo da kwalayen sigari, kuma ga hayaniyar mutane nan acikin gidan kamar ana buki.
Page 57
nidai ina biye dashi kamar jela inga mi muka zoyi anan. Koda muka shiga samari ne guda goma masu jini ajika, majiya ƙarfi waɗanda ya kamata ace suna makaranta ko kuma gona suna biɗar na kansu, amma ko wane a cikinsu daka kalleshi zaka san babu natsuwa a tare dashi. Zubomin ido sukayi, da alama sun gane ni baƙuwar fuska ce a cikin su, wani daga cikin su da ya ke kwance gefe guda, kamar shine shugaba ya ɗago ya kalleni, sannan ya kalli Gazali sai yace,
"Gaza( sunan da suke Kiran Gazali kenan) waye wannan kazo muna dashi a nan, kuma miye manufar ka tayin haka",?
"Jagaba aboki nane, shi ma yana son ya shigo hulɗar ne, shine nace bari in kawo shi tunda yau oga zai yi aike sai asanar mashi mun samu ƙaruwa a cikin tawagar tamu, nasan zeyi alfahari da hakan.," 
   Da sauri na ɗago ina kallon Gazali dake Shirin binne ni da raina, kafin inyi magana, wanda ya Kira da jagaba ya cigaba da cewa,
" To ai haka mukeso, lallai Oga yau zai ji daɗin abunda ka aikata, dan ko jiya da mukayi waya yace yanason ƙarin mutane saboda campaign ɗinnan dake tafe, kuma kasan yafi son irin haka, mutun yayi ra'ayin shigowa dakan sa gudun samun matsala, to yanzun shi abokin naka kayi mai bayanin yanda abun yake ko kuwa?,"
  "Aa jagaba ban yi mashi ba, tunda naga yau oga zai shigo shine na bari ya ganema idon sa". "To ai duk fine ne, nasan ko wane lokaci yanzun oga na iya zuwa".
 Ni dai da ido nabi Gazali ganin ya kunna sigari yana zuƙar abarshi hankali kwance. Bamu kai minti talatin da zuwa ba naji hayaniya ta ƙaru daga waje ana shelar ga oga nan yazo. Kowa ya miƙe tsaye ana tattaro natsuwa. Ni kuwa zuba ido nayi inga wannan oga. Ga mamaki na wani ɗan siyasa ne da na shaida fuskar sa saboda yawan fastocin shi dake yawo a gari. Mamaki ya kama ni matuƙa ina kallon yanda suke mashi kirari kamar zasu haɗiye shi. Aka kawo mashi kujera ya zauna sannan yafara tsara masu abubuwan da yake so ayi idan ana campen ya kuma ciro maƙudan kuɗi ya bawa jagaba cewa su sai duk kayan aikin da suke buƙata. bayan sun gama magana ne jagaban ya gabatar dani a matsayin wanda keson yin aiki tare dasu. 
Page 58
ya kalleni na wasu mintuna sai kawai ya tashi yace jagaba yasameshi a waje.
  Bayan kamar minti goma jagaba ya dawo yamun alama da hannu cewa inzo, ban musa ba na tafi na tsaya gefen shi dan warin sigarin da yake sha yana damuna. Sai da ya zuƙi hayaƙin ya fesar sannan ya fara magana.
     "Oga yace in sanar dakai cewa, yaga huskar ka da rauni, to a wannan tafiya tamu dai indai kashigo ba gudu ba ja da baya, saboda kamar ka riga kasan sirrin mu wanda kuma saɓa muna ko bijirewa tamkar kiran ajalinka ne da kuma na iyalinka. Dan haka kashigo cikin mu kenan sai idan mutuwa ta raba", sai ya dan dakata yasa hannu a aljihun shi ya ciro leda biyu ya miƙomin a inda nike tsaye kamar ruwa sun cinyeni, a hankali na tako nazo inda ya ke nasa hannu na karba, "wannan leda kyauta ce daga oga yace a baka somin taɓi ne, wannan kuma kayan aiki ne ( ƙwayoyi da kayan shaye shaye ), nasan zaka buƙa ce su, dan haka ka kula sosai, bijirewa na nufin rasa ranka dana ahalinka". Yana kai wa aya ya juyo ya kalli sauran yaran yace, "ku zo musa ƙafa", haka nan suka bishi suka fita suna tangaɗi kamar zasu faɗi. Suna fita naga Gazali yayo inda nike kawai na juya na fita abuna dan bansan kuma mi zai gayamin ba bayan ya gama lalatamin rayuwa. Duk da kiran sunana dayake kuwa baisa na juyo na kalleshi ba har na isa gida ina tunanin wannan bala'i da Gazali yasa ni a ciki.
    Kwana biyu ina kwance ina zazzaɓin wannan al'amari, ba abunda yafi tadamun hankali kaman yanda jagaba ke faɗin su kasheni su kashe ahalina. Nasan kuma ba barazana bace tabbas zasu iya dan a ranar da abun ya faru Gazali ya iske ni gida ya ƙara tabbatar min da cewa zasu iya halaka ni indai na saɓa masu dan sun taɓa aika wani barzahu dagashi har iyalin shi domin kawai yace yabar aiki tare dasu. Ni ya zanyi kenan? na tsinema Gazali yafi cikon carbi. Tun lokacin da abun ya faru bacci ya ƙaura cewa ido na, yanda naga rana haka zanga dare ko ƙiftawa banayi. Tunawa nayi da kayan da jagaban ya bani dan nasan yanda suke saka Gazali bacci kamar wani matacce. Da sauri naje na ɗauko na buɗe, banyi wata wata ba na kwankwaɗe kwalba guda duk da wari da ɗaci da nakeji. Na maida ledar na saka a jikkata. Banyi cikakken minti biyar ba bacci mai nauyi ya daukeni.
 Page 59
Shikenan ya zamana sam ban iya bacci sai nasha ƙwaya ko wani abu da zai bugar dani. To dama ansan banda lafiya a gida, ko bacci bansamun yi, to ganin kwana biyu ina bacci sukayi murna cewa lallai sauƙi yasamu.
  Randa mahaifiya ta, inna ta fara ganina a buge, bayan na dawo gida na wuce ɗaki na dake zaure, ta zo duba ni taganni ina shan ƙwaya, da farko ta dauka magani ne, sai da ta tunkaro cikin ɗakin gadan gadan warin kayan maye suka daki hancinta, da kallo ta bini na mamaki da son ƙarin bayani, ganin haka yasa nayi zumut na miƙe ina son inyi magana, to ƙwaya ta fara aiki ajikina, atake na zube ƙasa na fara jin kaina na saramin, inna naganin haka ta furta "innalillahi wainna ilaihi rajiun, mi zan gani haka? uzaim miyaka kai ga wannan halaka?," da sauri ta juya ta fita, ba jimawa sai gata ta dawo tare da malan. Tsaye yayi akaina yana kallo na yanda gaba ɗaya hankali na ya fita kaina. "Allah ya shiryeka Uzaimu", yana faɗar haka ya juya ya fita inna nabiye dashi.
   Haka rayuwa  tacigaba da tafiya, mamaikon samun sauƙi ma sai ƙara lalacewa nayi saboda na riga nayi sabo da sha barin shi zai min wahala. A ƙwauyen mu yanzun babu wanda besan halin da nake ciki ba, saboda wata rana da dare ina tare da Gazali mun gama shaye shayenmu sai nakama hanya zan tafi gida ina tangaɗi. saboda gushewar hankali kawai na faɗa gidan wani mutun, ranar kuwa nasha duka da tsinuwa, daga nan gari ya ɗauka cewa ɗan malan ya lalace yana shiga gidan mutane ya zama kwarto, har anamin kirari da "ɗan malan yaƙi halin malan". Jin haka yasa malan yanke shawarar aurar dani tunda ba'a shaye shaye kawai na tsaya ba harda kwartanci. A tunaninshi ƙila yin auren zai sa nadaina abun da nakeyi. Haka ya sami ɗiyar ƙaninshi larai ya nema min auren ta wanda daƙyar da suɗin goshi akayi auren, wanda ni sai ranar ɗaurin auren nasan wainar da ake toyawa dan sai inyi sati ban kwana a gida ba. Aikuwa auren nan shine ya sani danasani wanda har a yau inayi. Larai mai haƙuri ce da juriya, sam duk wulaƙancin da zan mata bazata taɓa damuwa ba kuma bazata kai ƙarata wa iyayenmu ba. Babu abunda nadaina sai ma wanda na ƙaro. Ana haka larai tasamu juna biyu, aikuwa ƴan uwa da abokan arziki suna ta murna da farinciki a cewar su aure yayi albarka tunda suna ganin sauyi a halayya ta. 
Page 60
Larai ce kawai tasan kan lamarin dan ita keshan baƙar azaba ta, ni kuwa na iya takuna a gaban mutane. 
   Watanni sunja, yanzun cikin larai wata tara haihuwa yau ko gobe. Kullum sai tamun nasiha tun randa tasamu cikin nan, " Uzaim kaji tsoron Allah ka daina abunda kakeyi, ni matar ka ce kuma haƙƙi akanka, ko bakayi domin ni ba kayi domin yaran da zamu haifa anan gaba, ina tsoron tabon da zakayiwa ƴaƴanka a dinga jifar su da kalmomi marasa daɗi, tabbas kana da lokaci, ka natsu ka gyara rayuwarka tunda hali ne na wasu ka aro ba naka ba, kafin lokaci ya ƙure maka.", a duk lokacin da zatamin waɗannan kalamai duk kuzarina mutuwa yake, amma dana fita waje na haɗe da abokan banza zanyi watsi da abun a raina incigaba da abunda nakeyi. Ranar da zata haihu ne ta na cikin naƙuda sama sama nashigo gidan abuge, tana ganin haka kamar kullun tabani hanya nashige ɗaki tana bina da addu'a. Ina cire rigata na kwanta sai gata ta shigo ɗakin ahankali ta zauna a gefe na, kamo hannuna tayi ta ɗaura a bisa cikin tana shafawa ahankali tana murmushi kafin ta fara magana,
 "Nasan ko wane uba yanason ɗansa, amma tabbas nasan kai bakasona kamar yanda baka son abunda ke cikina, ƙaddarar muce ahaka, har yau da muke zaune ban taɓa jin sonka ko kaɗan ba a raina, kawai zaman biyayya da jihadi nakeyi kuma na tabbata lada ta agurin Allah mai yawa ce. Yau inshallah nake sa ran zan haihu saboda alamun da nakeji a jikina, ina roƙon ka kayafemun idan nayi maka laifi, abunda kuma zan haifa, idan ya rayu ina neman alfarmar ka zame masa uba duk da nasan baka sonsa baka son uwarsa, nagode ina maka fatan alkhairi", ta miqe ahankali ta fita.
   Idan nace maganganunta basu tsayamun a rai ba to tabbas nayi ƙarya, kalma bayan kalma nake fassara su ina fahimtar su. Da naga tunanin zai hanani sukuni yasa na fito daga ɗakin ko riga babu sai singlet na fita waje. burina kawai inje shago in sayi abunda zan sha ya kaudamun da tunanin maganganun ta a kai na. Ina kuwa samun shago na saya masu ƙarfi nasha, a take naji duniyar na juyamun ban gane komai kuwa, koda za'a tambayeni miye sunana bansaniba a lokacin. Ina tafiya ina buga surutu a hanya ana kallo na, yau ma gidan wasu na shiga, 
Page 61
yana zaune da matar shi suna fira na faɗo masu, duk suka tashi a zabure suna kallo na, mutumen ya tsuramun ido ni kuwa ina ƙoƙarin shiga ƙuryar ɗaki sai yace, 
"wai wannan ba ɗan gidan malan bane, yau kenan kwarton cin a gida na ya sauka, to ai kuwa zan maka illar da daga yau bazaka sake marmarin yin wannan baƙar ɗabi'ar ba," Yana kaiwa aya ya fita, ni kuwa da banma san abunda yake faɗa ba nasamu kujera na zauna abuna. Da ƙatuwar sanda yadawo, baiyi wani tunani ba ya bugamin ita a baya, take na miƙe tsayi dan sosai bugun ya shigeni, kafin ingama tantancewa ya ƙara bugamun a ƙafa bansan lokacin da nafaɗa kan sumintin ɗakin bakina ya bugi suminti take hauru biyu suka fita, hannu yasa ya jawoni kamar kayan wanki ya kawoni ƙofar gidan ya zubar, nidai gaba ɗaya na rikice saboda azabar da nake ciki. Shiga yayi maƙota ya kira wasu samari ukku yace sumin dukan kawo wuƙa, ina ganin sun nufeni na ari ta kare, na fara gudu suna biye dani kamar nayo satar kayansu. Ina cikin gudu na kawo gab da wata falwaya ban lura ba nayi kanta ji kake tim! bakina da kaina suka bugeta, atake wasu haurun suka ƙara fita, ni kuwa saboda bugun da kaina yayi, da tsananin azabar da nake ciki yasa na faɗi agurin a sume.
    Koda na farka safiya ce, haske ya buɗe ko ina. Ahankali na buɗe idona na ɗan yunƙura na zauna ina bin ɗakin da kallo. A gadon malan na tsinci kai na an ɗaura mun wani abu kamar ganwo akai, banda ciwo ba abunda kai na keyi, bakina kuwa yayi suntum saboda girma. malan ne yashigo cikin ɗakin ɗauke da jariri, wanda sai a lokacin na tuna na bar larai tana naƙuda a daren jiya. Miƙomun yaron yayi sannan yace, "Ga yaronka, jiya aka haifa maka shi lokacin da katafi wurin iskancin ka kabar yarinyar mutane cikin wahala, ta gama galabaita koda innarka ta leƙa gidan, ta haifar ma yaro ita kuma tace ga garinku nan, ka kashe larai, Allah ya shiryeka!",
malan na kaiwa nan ya fashe da matsiyacin kuka ya juya ya fita 
"Na kashe larai?, larai ta mutu?, innalillahi wainna ilaihi raji'un, kai chona, kai con wannan rayuwa tawa, Allah na tuba ka yafemin, Allah kaji ƙanki matar kirki ya maki rahama, lallai na cuci kaina na cuci rayuwar larai, Allah ya waddan kalar rayuwata, haƙiƙa nayi danasani wanda bayada amfani, Allah ka yafemin kajiƙan larai da rahama.
Page 62
Tabbas matar kirki ce Allah kasan ban roƙi yafiyarta ba, Allah ka yafemini, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un",  Kuka nake kamar raina zai fita ina rungume da yarona a ƙirji inajin ƙaunar shi nashiga cikin raina. Ahankali nayiwa yarona huɗuba kuma nasa mashi suna Abdallah. Tun a wannan rana rayuwa ta ta sauya gaba ɗaya. Nabar duk wani abun da bai dace ba nakoma roƙon Allah da yayafemun kuma ya raya mun ɗana Abdallah. Ahaka wani lokaci gwamnati tana ɗaukar mutane zuwa ƙasar waje karatu Allah yasa nasamu kuwa zamuje ƙasar Sudan karatu. Daƙyar malan ya amince da nanuna mashi amfanin yin hakan kodan gujewa su Gazali. Ahaka na tattara na tafi Sudan na barwa inna Abdallah tana kula dashi. Zan iya cewa rasuwar larai itace silar barin shaye shaye na har nazama abunda nake a yanzun." Uzaim na zuwa a nan sai ya tsaya yana dubansu ɗaya bayan ɗaya kafin yaci gaba da magana : " Haka na rasa haƙorana a wurin shashanci, akan haka ya zama dole na siya haƙoran roba domin na ɓoye giɓin dake bakina domin a wannan lokaci haƙoran da suka rage a bakina basuda yawa, idan muka dubi darasin wannan labari zamu gane cewa wasu abubuwa dake faruwa ga mutane to daga laifinsu ne, duk da cewa akwai ƙaddara amma kuma muma a matsayinmu na masu hankali ya kamata muyi tunani kafin mu aikata dukkan kome, idan zamu tuna a lokacin da Gazali yamin ƙaryar cewa inaso na shigo a cikinsu ya kamata na nuna masa kuskurensa kuma a nan wurin da abun ya faru, amma sabida rashin tunani sai nayi shiru kuma yin shiru ɗin ne ya jefani a cikin halin dana samu kaina a ciki, abun nufi anan shine ba kome ake yin shiru ba, wani abu dole sai kayi magana ko sabida ka samu damar kare kanka daga faɗawa halaka. Sai kuma adduar iyaye, adduar iyaye tanada muhimmanci sosai domin idan zamu tuna mahaifina mutum ne mai yimin addu ar shiryuwa koda kuwa na aikata ba dai dai ba, kunga kenan ya kamata iyaye su duba ba wai da yaro yayi laifi sai a hausa da tsinuwa ba, idan yaro yayi laifi ayi masa, yin addua ɗin sai ya kasance alheri a wurinsa.  Anan zamu tsaya sai kuma wani sati ran friday zamu ƙara haduwa domin cigaba da tattaunawa." Daga nan sai kowanensu ya miƙe da nufin fita.
  
     A WANI LOKACI
                                                                                By
         
  Abdul King Article      
  Halima Bala Wakili    
   Queen Nasmah
                                                                         Episode Six
                                                                     (Princess Milam)
     King and Queen Writing Chamber
Page 63
    " Nifa kun isheni da surutu kowanenku jissu Jissu wai me yasa kukemin hakane!" Haka Anisa ta faɗa tana mai dubansu cikin fushi. Ɗan ƙaramin rikici ne ya ƙullu tsakaninsu daga nan kuma sai ga Uzaim ya shigo cikin ɗakin.
   " Kuyi haƙuri fa yau nine nayi latti." Inji Uzaim.
    " Bazamu yiba, idan wani ne a cikinmu yayi lattin ai sai kayi ƙorafi." Inji Anisa.
    " Ke Jissu amma bakida mutunci yanzu abunda zaki faɗa kenan?" Inji Uzaim.
    " E an faɗa ɗin, koda wani abu ne?" Haka Anisa ta faɗa tana mai tsura masa ido.
    " Ai ba ke kaɗai ce ba kuma inada yaƙini sauran sun yafe." Haka Uzaim ya faɗa cikin murmushi.
    " Gaskiya bamu yafe ba kuma nima ina bayan Jissu." Haka Milam ta faɗa tana mai duban Uzaim cikin murmushi.
   " Ke Milam yaufa ranarki ce amma kina faɗar haka." Inji Uzaim
   " To sai me idan na faɗa wayace kayi latti!" Cewar Milam.
   " To yanzu naji sai ku faɗamin nawa aka cini tara?" Inji Uzaim. 
Milam najin haka sai tayi murmushi tare da miƙewa tsaye, " Lokaci na tafiya bari na fara." Anan Uzaim ya samu wuri ya zauna ita kuwa Milam tsayuwa tayi a tsakiyar ɗakin yadda kowanensu zai iya ganinta daga nan sai ta janye mayafinta ta yadda zasu iya ganin kunnenta na hagu, anan suka gane cewa kunnenta na hagu yanada wata tsaguwa mai girma domin tambon tsaguwar ya fito sosai kamar  yankan takobi, sai kuma can ƙasan kunnen an guntule ɗan ƙire, rufe mayafinta tayi daga nan sai ta fara labarinta kamar haka :
 A wani lokaci, yankin Amhara ya taɓa kasancewa ɗaya daga cikin manyan yakunan da babu kamarsu sabida tsagwaron cigaban da suka samu ta fannin harkokin yau da kullum, sai dai duk da wannan cigaba  da suka samu.
Page 64
Basu manta da mulkinsu na  gargajiya ba, akwai garuruwa daban daban a cikin wannan yanki na Amhara amma babbar masarautar itace ta Amhara domin itace ke juya yankin gabaki ɗaya, sarkin dake mulkin wannan masarauta ana kiransa da Bamlak, halshen da mutanen wannan yanki ke magana dashi shine Amharik, shi wannan halshe na Amharik yanada nasa haruffa waɗanda ake amfani dasu a wurin yin rubutu kamar haka: (  ለ ሐ መ ሠ ረ ሰ ሸ ቀ በ ቨ ተ ቸ ኀ ነ ኘ ) masarautar Amhara sun kasance a kan tafarkin rashin addini domin a wannan lokaci suna cikin duhu wanda yayi nasaba da mutanen zamanin baya. Sarki Bamlak yanada ƴa  mace da ake kira Solyana, mahaifiyar Solyana ta mutu a wurin haihuwarta, sabida wannan dalili sai Bamlak ya auri wata mace mai suna Amnen, Solyana ta taso ƙarƙashin kulawar Amnen, ita kuma Amnen ta kasance muguwar mace domin ko barorin gidan suna shayinta kada ta kwafsa musu domin ba ƙaramin aikinta bane, ana nan ana nan sai ga wani baƙon mutum ya shigo garin, shi wannan baƙo ya shigo ne da sabon lamari domin maƙasudin shigowarsa shine ya tallata musu wani sabon addini, Sarki Bamlak ba ƙaramar fusata yayi ba sabida haka sai yasa dakarunsa suka kama wannan baƙo, gidan yari aka jefa wannan baƙo da niyar cewa gobe za a fille masa kai, ita kuwa gimbiya Solyana ba ƙaramin tashin hankali ne ya sameta ba domin tun a lokacin da wannan baƙo ya fara bayanin wannan sabon addini  sai taji tana gane abunda yake faɗi sarai, cikin darene ta ɗau zimmar taimakon wannan baƙo, dokinta ta hau bayan tayi shiri sosai, anan ta durfafi wannan gidan yari da matsanancin gudu, tun daga nesa dakarun dake gadin gidan yari suka fara jefo mata ruwan kibau ita kuwa sai kaucewa take tana ƙara ƙaimin gudunta, haɗuwarta da waɗannan dakaru batayi kyau ba domin hatsabibin yaƙi ne ya ɓarke tsakaninsu, ta koina sara da suka fitowa yake ita kuma ta wanzu tana mai kare kanta tare da mayar da martani, da ƙarfin tsiya ta kutsa kanta cikin gidan yarin, tana shiga wani lungu sai ta diro saman dokin, riƙe takobinta tayi tana shiga lungu lungu neman wannan baƙo, a cikin wani ɗaki ta hangosa, da ƙarfin takobinta ta ɓalle gambun daganan sai taga baƙon yana nishi daƙyar, mayafin data rufe fuskarta  ta yaye daganan sai ta fuskanceshi. Ya jigata sosai domin koina a jikinsa tambon duka ne, taimaka masa tayi inda ya miƙe tsaye, anan ta riƙa masa suna tafiya tare, tafiya yake da gurmanta rike da Solyana wadda ta riƙesa gam domin tana sakinsa zai iya faɗuwa, bayan sun fito gidan yarin ne sai ta taimaka masa inda ya hau saman dokinta.
Page 65
Daganan sai itama ta hau dokin kuma ta riƙe mutumin kada ya faɗo, to kafin ta saki linzamin dokin ne sai taji an kira sunanta a cikin halshen Amharik.
   "  li‘iliti " - ልዕልት
  Ma ana ( Gimbiya)
Anan Solyana ta juyo domin ganin ko waye ya ambaci sunanta, anan ta gane ba kowa bane in banda sarkin yaƙin garin wato Addis, mamakin da Addis keyi shine ya akayi gimbiya Solyana ta iya faɗa haka? kaɗa linzamin dokinta tayi, shi kuwa dokin fizgarta yayi da matsanancin gudu daganan ya durfafi ƙofar fita garin, riƙe wannan mutumin tayi gam kada ya faɗo daganan taci gaba da gudunta, da karfin tsiya dokin ya bangaje ƙofar daganan ya fita, shi kuwa sarkin yaƙi Addis tsaye yayi yana dubanta tare da sauran dakarunsa cikin tsananin mamakin wannan abu daya faru. Anan gari ya ɗauka cewa gimbiya Solyana ta yaudari mahaifinta domin ta ƙetare umarnin daya bayar, Sarki Bamlak ba ƙaramar fusata yayi ba wai ace ɗiyarsa ta cikinsa itace tayi wannan aika aika, dakaru ya baza tare da umarnin cewa su dawo masa da kan Solyana da kuma baƙon data taimaka, ita kuwa Solyana tunda ta bar masarautar Amhara sai ta cigaba da kutsa daji tana gudun mutuwa a saman dokinta domin tasan da cewa dolene sarki ya turo dakaru su kamata, kuma da an kamata kasheta za a yi domin ga ƙaidar masarautar Amhara duk wanda ya fitar da ɗan gidan yari to hukuncinsa shine kisa, sai da tayi gudu sosai sa an nan ta samu maɓoya a cikin wani kogo, a cikin kogon ta ɗaure dokinta daganan kuma ta shimfiɗe wannan mutumi a gefe, fita tayi waje ta kamo kifaye a cikin ruwa, da yake wurin mai albarka ne ta koina za a iya samun kifi, bayan ta dawo cikin kogon ne sai ta kunna wuta da duwatsu, ƴan itatuwa ta jera saman wutar yadda zata iya gasa kifayen, bayan kifayen sun gasu ne sai ta ajiye nata a gefe daganan ta baiwa wannan mutumi nasa, tayar dashi tayi daganan sai ta gincira shi, ɗan tsiton kifi ta finciko ta jefa masa a baki,  taunawa ya farayi yana yamutsa fuska da alama bayajin daɗin kome sabida rashin lafiyarsa, da Solyana taga bayada ra a yin kifin sai ta koma gefe taci gaba dacin nata. Tana kammalawa sai ta fara angaje domin bacci yafi ƙarfinta, gashi tanaso tayi baccin amma bazata iyaba domin ji take a ko yaushe dakarun da sarki ya izo zasu iya kamata, haka dai taci gaba da tunani tana angaje har bacci yayi awon gaba da ita.
Page 66
Tun da sanyin safiya Solyana ta tashi firgigit sanadiyar sautin wata ƙara data jiyo, duba wannan mutumin tayi taga yana nan ƙalau, daganan sai ta janyo takobinta, tafiyar sanɗa ta farayi tana dube dube har ta fita cikin kogon, ai kuwa tana fita sai ta hango wani babban jirgin ruwan ya rabe gida biyu kuma yana nutsewa a cikin ruwa, da gudu ta nufi wannan jirgi domin ta gani idan akwai mutun a ciki tayi taimako, tsundumuwa cikin ruwan tayi daganan ta fara iyo, sai da tayi iyo sosai kafin ta cimma ɓallin jirgin, da sauri ta riƙe ɓallin jirgin wanda ke shirin nutsewa cikin ruwa, da ƙarfi tayi alkafira sama daganan ta diro saman jirgin, tafiya ta farayi a hankali domin kada nauyinta yayi sanadiyar nutsewar jirgin  domin a wannan lokaci ruwa sun fara shigowa cikin jirgin, tana cikin dube duben ne sai ta jiyo nishin mutum a can nesa, da gudu ta nufi wurin, ai kuwa tana isa sai ta tarar da namiji kwance cikin rashin lafiya, abunda ya bata mamaki shine shi wannan mutumi ba irin mutanen yankin Amhara bane domin mutanen Amhara akasarinsu sunada fata wankan tarwaɗa, amma shi wannan mutumi fari ne sol gashin kansa kuwa sai sheƙi yake, sai da Solyana ta kallesa sosai kafin ta taimakesa ya miƙe tsaye, a wannan lokaci jirgin saura ƙiris ya nutse domin ruwan sun fara rinjayar jirgin, ita kuwa Solyana tana ganin haka sai ta tallabi wannan mutumi da ƙarfi ta diro saman jirgin, ai kuwa tana dirowa jirgin na nutsewa, anan ta riƙe wannan mutumi tana iyo dashi har ta iso gaɓar ruwan, tana isowa sai ta janyo mutumin, tallabarsa tayi da hannuwanta har ta iso kogon da take, bayan ta shiga kogon ne sai ta ajiyesa a gefe kusa ga wannan baƙon mutumin data fito dashi gidan yari, daganan sai gimbiya Solyana taci gaba da jinyar waɗannan mutane su biyu ba dare ba rana, a hankali a hankali har suka fara samun sauƙi, shi dai wannan baƙon ya kasance mai surutu domin cikin ƙanƙanin lokaci ya sabu da Solyana kasancewarsu suna magana da halshe ɗaya, kuma a cikin wannan hirar ta gano cewa sunansa Sador kuma shi yarima ne a masarautar Selam, kalmar Selam -ሰላም 
ta fito ne daga halshen Amharik kuma ma anarta shine aminci, tushen kalmar shine wasu mafarauta daga masarautar Amhara sun fito yawon farauta sai suka samu wani wuri mai laushi da albarka, daga nan sai suka yanke shawarar kafa gari a wannan wuri, to suna cikin shawara ne sai wasu ƴan fashi  suka fito daga maɓoyarsu suka zagayesu kowanensu riƙe da kwari da baka, daga nan sai shugaban waɗannan mafarauta ya fara magana kamar haka :
Page 67
" wedezīhi beselami inimet’aleni " - ወደዚህ በሰላም እንመጣለን
Ma ana ( Mun zo wannan wuri ne cikin aminci) Anan ƴan fashin suka ƙyalƙyace da dariya daganan sai suka ƙyale mafarautan kuma sukayi musu laƙabi da Selam, koda aka kafa garin sai aka dinga kiran garin da Selam ma ana aminci. Shi kuma ɗaya mutumin wanda Solyana ta fito dashi a cikin ruwa ya kasance bayajin halshen Amharik, halshen da yake magana dashi shine English, to sa ar da Solyana ta samu shine Sador yanajin halshen English domin ƙabilar turawa da kuma larabawa suna shiga birnin Selam domin tallata hajarsu kuma ta wannan dalili mutanen birnin Selam suka koyi halshen larabci da kuma turanci, ba ƙaramin sabo ne ya shiga tsakaninsu ba domin sai wannan baturen ya fara koyon halshen Amharik daga Sodar ita kuma Solyana sai Sodar ya fara koya mata English ɗin, kwanaki na shuɗewa har takai cewa dukkansu sun iya abunda suke koyo, to anan ne baturen ya fara basu labarinsa bayan ya faɗa musu sunanshi Miller, kuma sai labarinsa yayi shige dana Solyana domin ya baro garinsu ne sabida ya amshi a wani baƙon addini ga wani balarabe, kasancewarsa shima ɗan sarki ne daga nan sai mahaifiyarsa sarauniya ta turo a kamashi shine ya tsere a cikin jirgin ruwa, shima balaraben da ya shigo da addinin a cikin garin daƙyar yasha, Miller ya fito ne daga birnin London kamar yadda ya faɗa, sannu sannu sai soyayya ta fara shiga tsakanin Solyana da Miller, daganan sai Sodar ya basu shawara me zai hana su bishi zuwa birnin Selam idan yaso sai a ɗaura musu aure, haka kuwa ta kasance domin Solyana da Miller sun aminta zasu bishi, su uku suka hau dokin Solyana daganan sai suka nufi hanyar zuwa birnin Selam, Sodar ne a gaba sai Miller a kusa dashi, ita kuwa Solyana itace baya, kwanci tashi har suka iso birnin Selam, Solyana da Miller sun samu karɓuwa sosai ga sarki da sarauniya wato iyayen Sodar, anan akasa rana ɗaurin aurensu wanda kuma ya kasance tare dana Sodar domin zai auri amaryarsa mai suna Katina. An samu nasarar ɗaura auren Solyana da Miller sai kuma Sodar da Katina bisa tsarin addinin Islam. Solyana da Miller sun sheƙe soyayyarsu sosai domin sai da Sodar ya samar wa kowanensu aiki, shi Miller ya kasance a cikin maƙera domin ya iya ƙira sosai kuma anan aka basa babban matsayi domin shi ke bada umarnin yadda za a ƙera makamai da sauran abubuwan amfani, ita kuwa Solyana sai ta kasance mai dafama sarauniya abinci kuma sai aka bata babban matsayi domin ita ke bada umarnin yadda za a dafa abincin.
Page 68
Solyana da Miller sun samu kwanciyar hankali sosai domin an basu gida a cikin masarautar Selam, a cikin wata hira da Miller, Solyana ta tambaye shi inda sunansa ya samo asali, shi kuma sai ya fara bayani kamar haka:
   " The word miller is related to mill, miller stands for someone who works at mill, and mill could be refer as machinery that process materials by grinding or crushing."
 Ma ana ( Kalmar miller tana da dangantaka da mill, kalmar miller tana nufin mai yin niƙa, shi kuma mill yana nufin injimin da ake niƙa dashi.)
   " And why were you named Miller?" Solyana ta tambayeshi.
 Ma ana ( Me yase ake kiranka da Miller."
   " Miller is our family name, and the origin of the name was that our great great grand father was a miller, I was given his name as a remembrance to him and one funny thing about is I grew and turned to a miller," Inji Miller.
 Ma ana ( miller shine sunan danginmu, kuma asalin sunan shine kakan kakanmu ya kasance mai yin niƙa, daganan sai aka laƙamin sunanshi domin a dinga tunowa dashi kuma nima dana girma sai na kasance mai yin  niƙa.)
   " Assume we have a daughter, what do you think we should name her?" Solyana ta tambayehi.
Ma ana ( Yanzu idan muka samu ƴa mace, wane suna kake ganin ya kamata mu sanya mata)
Sai da Miller yayi tunani kaɗan kafin ya bata amsa kamar haka : " I think we should name her Milam."
Ma ana ( Inaga mu sanya mata suna Milam) Wannan suna da Miller ya faɗi ba ƙaramar dariya yaba Solyana ba, ana nan ana nan abu kamar wasa sai ga Solyana da ciki, lokaci na tafiya sai ga Solyana ta haifi santaleliyar budurwa, anan aka sanyawa yarinya suna Milam, ba a fi sati da wannan haihuwa ba sai ga wata wasiƙa ta shigo hannun sarkin Selam, ita wannan wasiƙa an aiko tane daga masarautar Amhara, anan magatakarda ya fara karatun wasiƙar wadda aka rubuta cikin haruffan Amharik kamar haka :
( ይህ ደብዳቤ ከአማራ ንግሥት አምነን ወደ ሰላም ንጉሥ እየመጣ ነው፣ እኔ የማደርገው ትዕዛዝ የልዕልት ሶልያናን መሪ ከልጃችሁ ከሶዳር ጋር ፀሐይ ከመጥለቋ በፊት ፈጥናችሁ አምጡ፣ ይህን ሥራ አለመጨረስ ከተማችሁን እንድትሠሩ ያደርጋችኋል። እስከመጨረሻው ይጠርጉ። መልካም እድል ተመኘሁላችሁ። )
Page 69
Ma ana ( Wannan wasiƙar ta fito ne daga Amnen sarauniyar Amhara zuwa ga sarkin Selam, inaso ka gaggauta yankomin kan gimbiya Solyana da kuma ɗanka yarima Sodar kafin faɗuwar rana, gazawa akan wannan aiki dana baka zai yi sanadiyar bajewar birninka a doron ƙasa, na barka lafiya) ba ƙaramar hasala sarki yayi ba jin cewa wai anaso ya kashe ɗansa na cikinsa da kansa, abunda ya bashi mamaki shine ya akayi sarauniya Amnen ta san da cewa Solyana ta Sodar sun shigo garin, bako shakka  dole akwai wanda ya faɗa mata, kuma idan hakane to waye ya faɗa mata? cikin tsananin fushi yasa aka kawo masa fatar damisa, tawadda aka ajiye masa a gefe sai wani alƙalami na ƙarfe, ba yadda magatakarda bai yiba domin sarki ya bari ya rubuta raddin wasiƙar amma yaƙi, sarki ne da kansa ya rubuta raddi mai zafi daganan ya baiwa wanda yazo da wasiƙar farko, ai kuwa wanda aka baiwa wasiƙar yana tafiyarsa sai sarki ya bada umarni a fara shirye shiryen yaƙi domin a kowane lokaci zasu iya ganin dakaru.
  " nigišiti āmineni gezhi sitihoni niguši bamilaki inidīhu t’a‘oti newi  "  Haka sarkin yaƙi Tedros ya faɗa a cikin halshen Amharik
Ma ana ( Sarauniya Amnen ita ke mulki, shi kuwa sarki Bamlak ya zama gumki kawai.)
" lerejimi gīzē iyegezachibeti noralechi፣ bezīhi gīzē gini negeru yekefa hone." -Inji sarki
Ma ana ( Ai tuni itace ke juyashi yanzu dai ne abun ya tsananta)
Miller ba ƙaramin ƙoƙari yayi ba domin sai da ya tabbatar cewa an ƙera makamai naji na faɗa marar iyaka waɗanda ba a taɓa gani ba. Sarkin yaƙi Tedros yayi mutuƙar ƙoƙari sosai wurin ganin cewa an tabbatar da tsaro domin jera dakaru akayi a saman katangar garin suna hangen abunda ke waje, kowanensu riƙe da kwari da baka waɗanda Miller ya ƙera, sai da akayi sati ɗaya ba abunda ya faru, a cikin sati na biyune suka wayi gari da sabon al amari domin dakarun sarauniya Amnen sun fito sun yi cirko cirko a ƙofar garin, Tedros ne ya hango hakan ai kuwa cikin sauri ya buga ƙugen yaƙi, anan dakaru suka fara fitowa a guje cikin shiri, kafin kaceme gari ya ɗauka gaba ɗaya cewa dakarun sarauniya sun iso. Dakarun sarauniya Amnen sahu suka jero rike da dogayen masu da kuma garkuwa, ita kuwa sarauniya Amnen tare da sarki Bamlak a can gefe nesa da filin yaƙi aka ajiyemusu kujerun alfarma yadda zasu iya kallon abunda ke gudana, sai dakaru sama da dubu sun zagayesu suna basu tsaro. Sarauniya Amnen ce rike da wani ƙaho tana kallon dakarunta cikin murmushi, busa ƙahon tayi da ƙarfi wanda yin hakan na nuni da cewa a fara yaƙi, anan dakarun suka nufi birnin Selam da matsanancin gudu.
Page 70
su kuma dakarun birnin Selam dake saman katangar garin suna  ganin  haka sai suka fara zubo musu ruwan kibau, anan dakarun sarauniya suka fara zuba ƙasa, ba yadda dakarun sarauniya basu yiba ganin cewa sun cimma katangar birnin Selam amma abu ya faskara domin duk wanda ya nufi katangar sai da wani ba shi ba, sai da aka ɗau lokaci ana wannan gumurzu sarauniya Amnen ta busa ƙaho wanda ke nuni da a tsayar da yaƙin, anan sarkin yaƙi Addis yayo kan sarauniya da nufin yin magana.
  " የኔ ንግሥት ይቅር በለኝ በዚህ ጦርነት ድል የለም "
yenē nigišiti yik’iri belenyi bezīhi t’orineti dili yelemi
Ma ana ( ki gafarceni sarauniya, amma babu alamun samun nasara ga wannan yaƙi,)
Sarauniya Amnen kallonsa kawai tayi kafin ta bashi amsa.
" ስለዚህ ምን ዓይነት ውሳኔ ማድረግ አለብን "
silezīhi mini ‘ayineti wisanē madiregi ālebini
Ma ana ( To yanzu wane mataki kake ganin ya kamata mu ɗauka kenan?)
"የለንደን ንግስት እንድትረከብ ማሳወቅ ያለብን ይመስለኛል"
yelenideni nigisiti iniditirekebi masawek’i yalebini yimesilenyali " Inji Addis
Ma ana ( Inaga kawai mu faɗawa sarauniyar London ta turo dakarunta domin bazamu iyaba)
"   ይህ ጥሩ ምክር ነው "
yihi t’iru mikiri newi    " inji sarauniya
Ma ana ( Wannan shawara ce mai kyau) 
Anan sarauniya Amnen ta yanko fatar damisa, tawadda da alƙalami ta yanko daganan ta fara rubutu cikin halshen English, tana gamawa sai ta baiwa sarkin yaƙi Addis, shi kuwa Addis dokinsa ya hau daganan ya nufi wata hanya, shi kuwa sarki Bamlak sai kallonsu kawai yake ba tare da yayi magana ba. Haka Addis yacigaba da gudu saman dokinsa har ya cimma wani wuri inda wasu turawa ke ƙera hanyar jirgin ƙasa, a can nesa dasu babban jirgin ruwa ne wanda da alama a cikin jirgin ruwan suka zo wurin. 
  " Give this letter to your queen " Inji Addis 
Ma ana( Ku danƙa wannan wasiƙar ga sarauniyarku.) Anan turawan suka amsa daganan suka cigaba da aikinsu . Shi kuwa Addis dawowa yayi daganan ya faɗama sarauniya Amnen abunda ya faru. A cikin dare ne wani sauti ya tayar dasu sarauniya, anan suka fito cikin tantinsu domin ganin abunda ke faruwa, anan sukaga jirgin ƙasa a can nesa dasu ya tsaya, murmushi sarauniya Amnen tayi tana mai duban sarkin yaƙi Addis domin da alama sarauniyar London ce ta iso, ƙofar jirgin aka buɗe daganan saiga sarauniya ta fito dakarunta na take mata baya rike da manyan bindigogi, cikin walwala sarauniya Amnen ta tari sarauniyar London, anan suka rungumen juna cikin farin ciki.
  " We are going to launch our first attack now."Inji sarauniyar London.
 Ma ana ( Yanzu zamu gabatar da harin farko)
Page 71
Anan dakarun sarauniyar London suka fara fitowa da wasu makaman yaƙi da sarauniya Amnen bata taɓa gani ba, hakama sarkin yaƙi Addis bai taba ganinsu ba, daganan sai dakarun suka jero sahu sahu suna jiran umarnin shugabansu wanda ke tsaya a gabansu.
  " Release the explosives at the count of two." Inji shugaban dakarun.
Ma ana ( ku halba nakiyoyi bayan ƙida biyu.) 
Anan dakarun suka janyo wansu manyan makamai suna girkesu a ƙasa, su waɗannan makamai sun kasance masu tsananin girma domin kowane makami ɗaya dakaru goma ke turashi, a can ƙasan makaman an musu tayar ƙarfe yadda idan an turasu zasuyi tafiya, nakiyoyi aka fara ɗurawa a cikin makaman daga nan aka saita su yadda suna kallon ƙofar birnin Selam.
  " One, two, release." inji shugaban dakaru.
Ma ana( Ɗaya, biyu, ku halba) 
Anan dakarun sarauniyar London suka fara halba waɗannan nakiyoyi kamar bazasu daina ba, duk nakiyar data shiga birnin Selam sai ta fashe, kuma tana fashewa sai kaga mutane suna bajewa ga ƙasa, nakiyoyin sun kasance masu tsananin ƙarfi domin da sun fashe to duk wanda ke kusa dasu shima zai fashe, sai dai aga ƙafafuwa daban hannaye daban,  anan  mutane suka fara guje guje domin ƙauracewa wannan masifa data tunkarosu, su kuwa dakarun birnin Selam cikin firgici suka farka domin ɗaukar mataki amma kuma sun makara domin dakarun sarauniyar London har sun ɓalle ƙofar birnin, anan dakarun suka shigo garin suka hau kan mai uwa da wabi.
" ānichī be’inya layi t’ifati neshi kebalishi gari huneshi t’ifati āmet’ashibini "       Inji sarauniyar Selam.
Ma ana ( Zuwanku a wannan gari ba alheri bane, duk wannan masifar da muka shiga to kece sanadinta da keda mijinki ) 
Haka sarauniya ta faɗa tana mai duban Solyana, daga nan sai ta hau dokinta ita da mjinta sarki shima ya hau nasa doki, sarkin yaƙi Tedros ne tare da sauran dakaru suka zagaye su daganan suka nufi wata hanya wadda zata fitar dasu daga garin, haka suma sauran mutanen garin da yawansu sun samu damar kuɓuta, ita kuwa Solyana riƙe take da ɗiyarta Milam sai faman neman mijinta Miller take, lungu lungu take shiga amma babu alamarsa, ita kuwa Milam  sai faman kuka take, har yanzu dakarun sarauniya London basu daina halbo nakiya ba, duk da cewa yanzu sun ci ƙarfin garin domin sun samu damar shigowa, duk wannan gumurzu da ake sarki Bamlak bai farka ba, har yanzu yana cikin tantinsa yana sharar bacci. Ita kuwa Solyana sai faman guje guje take tana kaucewa halbin nakiya tana neman mijinta, tana cikin gudun ne aka halbo wata nakiya, duk yadda Solyana tayi domin ta ƙauracewa nakiyar abun yaci tura domin sai da wani iska mai ƙarfi yayi jifa da ita a can gefe 
Page 72
Anan idanun Solyana suka fara buɗewa da rufewa, a can gefe zata iya ganin dishi dishin  ƴarta Milam sai faman kuka take, dakarun London ta gani sai faman ɗaure mutane suke, anan ne ta fara tunani ko ina Miller ya shiga? Kuma ina Sodar ya ɓoye tare da matarsa Katina? har yanzu Solyana dishi dishi take gani sabida idanunta dake buɗewa da rufewa, wata kaca taga an jefo mata daga nan aka ɗaureta tamau, a can gefe kuma wani badakaren London taga ya ɗauki Milam, haka taci gaba da kallonsa har ya ɓace mata da gani, daganan sai idanunta suka rufe gam bata ƙara sanin inda take ba.
Tun da sanyin safiya sarki Bamlak ya farka yana hamma, matarsa Amnen ya duba wadda ke sharar bacci abunta, a can waje kuma yakan jiyo muryar sarkin yaƙi Addis da alama yana baiwa dakaru horo ne, anan Bamlak ya fito daga cikin tantin domin ya sarara, ai kuwa yana fitowa sai yayi kiciɓis da birnin Selam, anan ya ƙura ma garin idanu yaga sai hayaƙi ke faman fitowa, ga katangu sun rushe ba kyaun gani, anan ya zuba da gudu ya shiga cikin garin da sauri, daga  shigarsa  sai ya fara zub da hawaye domin gawarwaki ne birjik ba  kyan gani. Kai da ganin garin kasan an yi tashin hankali domin da yawan gidaje sai ci suke da wuta, wasu katangu sun rushe wasu sun rugurguje ba kyan gani. 
  " inesu solīyana ina mīlerini bicha iyefelegu bīhonimi lemini inidīhi āyineti firidi benit͟s’uhāni sewochi layi yifets’imalu "
 " Inji sarki Bamlak cikin fushi.
Ma ana ( Me waɗannan mutane sukayi da za a zartar musu da wannan hukunci bayan Solyana da Miller kawai ake nema)
Daganan sai yaci gaba da zaga garin yana kiran sunan Solyana.
  " soliyana፣ lijē solīyana yeti nati? " 
Ma ana ( Solyana, ina ƴata Solyana) 
Sarki Bamlak yana cikin hakane sai yaga an taɓa shi a baya, yana juyowa sai yaga sarkin yaƙi Addis shi kaɗai, anan Addis ya fara masa magana kamar haka:
" yelenideni nigisiti yezīchini ketema zēga yiza ābirwati hēdalechi kiburinetiwo yik’irita " 
Ma ana ( Kayi haƙuri ranka shi daɗe amma sarauniyar London ta kama akasarin mutanen wannan birni domin tafiya dasu can inda take)
 " beyazechachewi sewochi mini litaderigachewi newi?" 
   Inji sarki Bamlak
  Ma ana( Su waɗanda ta kama me zatayi dasu?)
 " kibirihini ālawik’imi "
 " Inji sarkin yaƙi Addis
Ma ana ( Nima ban sani ba ranka shi daɗe)
"   sile soliyana ፣ tegedilalechi weyisi teyazechi? "
   Inji sarki Bamlak.
Ma ana ( Itafa Solyana an kamata ne ko kuma an kasheta?)
Page 73
" kibirihini ālawik’imi " 
  Inji Addis
Ma ana ( Ban sani ba ranka shi dade )
"āmineni bemameni tet͟s’et͟s’ichalehu፣ lijēni yat’ahuti be’iswa mikiniyati newi "
  Inji sarki Bamlak
Ma ana ( Nayi dana sanin yarda da Amnen da nayi gashi yanzu na rasa ƴata Solyana) 
Wata ƙara sukaji a can waje, cikin sauri suka fito garin domin ganin ko menene, ai kuwa suna fitowa sai sukayi arba da jirgin ƙasa a can nesa dasu yana shirin tashi, anan suka fara kallon jirgin domin bazasu iya cewa akwai mutane ciki ba ko babu.
 " solīyana inidet’efachi፣ āmimēni laderegechiwi negeri iniditikefili āregagit’alehu። "
  Inji sarki Bamlak.
Ma ana ( Kamar yadda Solyana ta salwanta haka itama Amnen zan salwantar da ita) 
Anan sarkin yaƙi Addis ya kalli sarki Bamlak cikin tashin hankali domin yasan da cewa sarki zai iya ɓatar da Amnen kamar yadda ya faɗa, to abun ruɗanin shine da sarauniya Amnen da sarkin yaƙi Addis sun kasance ƴan uwan juna domin uwa ɗaya uba ɗaya, ita sarauniya Amnen itace ƙanwar sarkin yaƙi Addis. Anan sarkin yaƙi ya fara tunani ai kuwa bazai yiwu ya bari a salwantar da ƴar uwarshi ba, babban tashin hankali shine sarki yace zai salwantar da ita amma kuma yaushe zai salwantar da ita kuma a wane lokaci? kuma shi a matsayinsa na ɗan uwanta wane mataki ya kamata ya ɗauka domin ya kareta daga harin sarki? 
    Milam na zuwa a nan sai ta tsaya sanadiyar tsawar dataji ana gwabzawa, wani ƙaƙƙarfan iska ne ya fara bugawa wanda ke nuni da cewa hadari ne ke shirin tasowa. " To sabida zuwan wannan hadari dole na dakata a nan domin mu tafi gida, zuwa wani sati idan mun haɗu sai na cigaba da labarin " Inji Milam
   " Amma gaskiya Milam baki kyauta ba." Inji Jalim. " Kada ki manta baki faɗa mana matakin da sarkin Bamlak zai ɗauka ba kuma baki faɗa mana yadda sarkin yaƙi zai kare Amnen daga harin sarki ba, kuma ina labarin Sodar da matarsa  Katina?  Shi kuma Miller wane wuri ne ya ɓoye, kuma ita Solyana ta mutu ko kuwa tana nan da ranta? Kuma a cikin dakarun London waye ya ɗauki Milam?Sai kuma sarki da sarauniya na Selam da suka bar garin akan tsaron sarkin yaƙi Tedros, shin wane mataki ne zasu ɗauka domin su rama wannan cin mutunci da aka yi musu?  Kuma kada ki manta baki faɗa mana darasin labarin ba kuma baki bayyana mana yadda akayi kika samu rauni a kunnenki ba!"
Murmushi Milam tayi kafin ta bashi amsa. " Kada ka manta wannan labarin dana baku shine kashi na farko, idan muka haɗu wani sati zan baku kashi na biyu, kuma a cikin kashi na biyu zakuji darasin labarin da kuma yadda akayi na samu rauni kai harma da sauran tambayoyin da kake ganin ban amsa ba duk zakujisu a ciki " 
Page 74
Anan kowanensu ya miƙe daganan suka kama hanyar fita ɗakin da zimmar cewa zasu haɗu wata jumu a domin sauraren cigaban wannan labari.



   A WANI LOKACI
                                                                                By
  Abdul King Article                                   Halima Bala Wakili    
Queen Nasmah
                                                                         Episode Seven
                                                                     (Princess Milam 2)
    King and Queen Writing Chamber
Page 75
Milam ce a tsaye tana duban su Uzaim cikin mamaki yadda kowanensu ya tsura mata ido yana kallonta, Anisa ce ta shigo ɗakin cikin sauri daganan ta nufi wata plastic chair domin zaunawa.
   " Su Jissu yaufa anyi latti." Haka Milam ta faɗa cikin tsokana.
   " E ɗin ko kina nufin zaki cini tara ne?" Inji Anisa.
   " To kada ki manta mufa a ƙungiyarmu bamu ɗaukar latti." Inji Milam.
   " To idan anyi lattin me zai faru." Haka Anisa ta faɗa tana mata hararar wasa.
   " Mufa labari mukazo musha ba wai sauraren wannan rigimar taku ba." Inji Uzaim.
Anan Milam tayi murmushi kafin ta fara magana " To ranka shi daɗe a gafarceni yanzu zan fara labarin." 
   " Haka yayi kyau sosai domin labari mukazo musha ba wai sauraren rigima ba." Inji Jalim.
Murmushi Milam tayi daganan sai ta cigaba da labarinta kamar haka :
A wani lokaci, an taɓayin wani azzalumin sarki mai suna Benyam, shi wannan sarki ya kasance yanada mata bakwai, kowace daga cikin matan nasa ɗiyar sarki ce kuma sai da sarki Benyam ya yaƙi garinsu  kuma yaci garin da yaƙi kafin ya auresu da ƙarfin tsiya ba wai don suna so ba, matarsa ta farko ta kasance bata taɓa ruwa ko kaɗan, ba yadda sarki bai yiba domin yasan dalilin da yasa bata taɓa ruwa amma abu yaci tura, matarsa ta biyu ta kasance bata cin abinci, sarki yayi iya ƙoƙarinsa domin ya gano dalilin hakan amma bai gano kome ba, matarsa ta uku ta kasance bata bacci, sarki yayi iya ƙoƙarinsa domin sanin dalilin rashin baccinta amma ya kasa, matarsa ta huɗu bata magana, itama sarki yayi iya ƙoƙarinsa amma bai gano kome ba, matarsa ta biyar ta kasance bata gajiya da aiki domin takan kwana ta yini tana aiki ba tare da gajiya ba, matarsa ta shidda ta kasance bata dafa abinci iyaka duk lokacin da sarki keson cin abinci zata kawo masa irin wanda yakeso, ba yadda sarki bai yiba domin ya gano ko dame take dafa abinci amma abu yaci tura, matarsa ta bakwai ta kasance bata dafa abinci da ruwa.  Ba yadda sarki bai yiba domin ya gano ko dame take dafa abinci amma ya kasa, wata rana sai wani baƙo ya zo wurin sarki, anan baƙon ya faɗama sarki cewa akwai wata masifa dake shirin tunkaro garinsa kuma ita wannan masifa zata fito ne daga matansa.
Page 76
Kuma idan har bai ɗau mataki ba to zai iya rasa sarautarsa. Anan baƙon yaci gaba da bayaninsa da cewa idan har yanaso ya kare kansa daga wannan masifa to dolene ya san sirrin dake tattare da matansa, shi zai iya faɗa masa sirrin matan nasa amma da sharaɗin cewa idan har ya faɗa masa to zai bar masa matan nasa gaba ɗaya  kuma idan yaƙi yarda to matan nasa zasu haɗe masa kai wanda daga ƙarshe zasu tanƙwarar dashi kamar yadda ya yiwa iyayensu. Ba yadda sarki bai yiba domin baƙon ya faɗa masa ko wace irin masifa ce amma yaƙi, anan sarki ya kiɗime domin matan nasa duk kyakkyawa ne kuma ko ɗaya bazai iya bayarwa ba balantana dukkansu, ba a fi kwana uku da hakan ba sai ga mutane sun taru fadar sarki domin yin ƙorafi akan masifar data shigo musu, ita wannan masifa kamar yadda mutane suka faɗa haka kawai sai cikin mutum yayi kumburi ya fashe, anan mutum zai mutu, kuma ana duba cikinsa sai aga wasu ƙwari manya manya masu tsananin girma suna fitowa a cikinsa, ba wanda zai iya faɗin yadda akayi ƙwarin suka shiga cikinsa iyaka dai anga fitowarsu, anan sarki yasa a kira baƙonsa domin ya faɗa masa cewa ya aminta da buƙatarsa, anan aka duba gabas yamma kudu arewa amma baƙo ya ɓace haka kuma matan sarki sun ɓace, anan sarki ya kiɗeme domin bai san ma anar hakan ba, shin baƙon ne ya sace matan nasa ko kuma matan tserewa sukayi da kansu? Idan tserewa sukayi da kansu to wane wuri zasu tafi kuma wane mataki ne zasu ɗauka akan zaluncin da sarki ya aiwatar akansu? Idan kuma baƙon ne ya sacesu to meye ƙudurinsa akansu? Kuma ita wannan masifa data shigo gari menene ya haddasata kuma ya za a maganceta?
   Firgigit Solyana ta farka tana kallon mutanen dake cikin jirgin ƙasan, dukkansu ɗaure suke tamau da kaca. Gyra zamanta tayi a saman kujerar tana kallon wajen tagar jirgin, bako shakka sun shigo wani yanki na daban duba da irin yanayin wurin, tunani ta farayi ko menene ya tayar da ita? daganan sai ta tuno lokacin da kakanta wanda ya haifi mahaifiyarta ke bata labarin Gimbiya Bakwai, wato labarin sarki Benyam da gimbiyoyi bakwai daya aura, ko wane hali Sodar da matarsa Katina suke ciki? sarki da sarauniya na Selam sun samu  damar kuɓuta kuwa? ya labarin mahafinta Bamlak da sarauniya Amnen? hawaye ne ya fara zubo mata a lokacin data tuno da mijinta Miller da kuma ɗiyarta Milam, babban tashin hankali a wurinta shine rashin sanin inda zataga waɗannan mutane da take tunani, lulluɓinta ta gyra tana mai kallon tagar jirgin ƙasan a lokacin da yake zabga namijin gudu, sauran mutanen dake cikin jirgin duk sunyi tsit kai da gani kasan akwai abunda suke tunani, mafi yawan mazan sun kasance sanye da rawaninsu, su kuma matan  sanye da lulluɓi, jirgin ne ya fara rage gudu ita kuwa Solyana sai ta mayar da hankalinta wuri ɗaya domin tanada yaƙini cewa sun iso wurin da za a kawosu, har yanzu batasan dalilin da yasa aka kamasu ba kuma batasan abunda yasa aka zo dasu wannan wuri ba.
Page 77
Jirgin ƙasan tsayawa yayi cif daganan sai Solyana taga wasu dakarun London sun fito cikin wata ƙofa, da ƙarfi suka tayar dasu suna ingizasu waje. Bayan an fito dasu ne Solyana ta gane cewa lallai wannan wani birni ne wanda tun farkon rayuwarta bata taɓa ganin irin saba, dube dube ta farayi tana kallon gine gine garin domin iya tsaruwa sun tsaru. Wata mata ce ta nufosu dakaru na take mata baya cikin shigarta na turawa da hula mai malfa a saman kanta, Solyana ƙura mata ido tayi domin matar takan mata kamada wata fuska data sani, bako shakka itace sarauniyar wannan birni .  Haka Solyana ta faɗa cikin zuciyarta.
   " You are welcome to London city." Haka baturiyar ta faɗa tana kallon su Solyana.
Ma ana ( Barkan ku da isowa birnin London) Daga nan sai baturiyar taci gaba da bayainta:
  " You will be giving food, shelter and job."
Ma ana( Za a baku abinci, wurin zama da kuma aiki.)
Wani daga cikin mutanen Amhara ɗebe rawaninsa yayi da ƙarfi ya jefashi sama kuma ya caɓe, cikin wata kakkausar murya yayi magana.  " We need our family back."
Ma ana ( Munaso a dawo muna da iyalinmu ) Sauran mutane na ganin haka sai suka fara jefa rawaninsu suna caɓewa suna faɗin " We need our family back." Haka maza da mata suka yita faɗi cikin hargowa. Ita kuwa baturiyar na ganin haka sai ta daka musu tsawa.
  " Keep quiet." 
Ma ana ( Ku saurara) Bayaninta taci gaba dayi kamar haka:
" We brought you here as slaves not free men."
Ma ana( Mun zo daku wannan wuri a matsayin bayi ba wai masu ƴanci ba)
" I am your queen, I ruled the entire London, you have to do what I said or you will be punished accordingly."
Ma ana ( Nice sarauniyarku, kuma nike mulkin ɗaukacin London, sabida haka dole ne kubi umarnina ko kuma ku fuskanci horo kamar yadda ya dace) 
Sarauniyar London juyawa tayi ta kama hanyar zuwa masarautar su kuma dakaru suna take mata baya. Sauran dakarun kuwa ingiza su Solyana sukayi inda suka nuna musu masaukinsu, ƙaton ɗaki ne wanda girmansa ya wuce tunanin mai tunani, a cikin ɗakin ƴan ƙanana gadaje ne a ciki, can gefen ɗakin kuwa an jero wurin ba haya masu yawa, anan aka haɗe maza da mata kowa ya kama gadonsa, a cikin bahayan  kuwa basuda matsala ta ruwa domin akwai fanfuna  da kuma shower masu yawa, idan lokacin cin abinci yayi iyaka a buga musu ƙararrawa daganan sai su biyo layi suna amsar abincin da kuma abun sha, sarauniyar London sai da ta tabbatar da cewa an rabasu ƙungiya ƙungiya kuma an basu ayyuka.
Page 78
Masu share share da goge goge daban, masu wanke wanke daban, hakama masu aikin gona daban, kuma kowane yasan inda yake aiki da kuma lokacin da akeso ya tafi aikin, ita kuwa Solyana a lokacin da sarauniyar London tazo kanta, sai ta dubeta cikin natsuwa kafin ta fara magana.
  " She's beautiful and... clean as well, with regard to this I will sacrificed her to work with the cookers." 
Ma ana( Ita kyakkyawa ce kuma mai tsafta, sabida wannan dalili zan sadaukar da ita tayi aiki tare da masu dafa abinci)
Sa ar da Solyana ta samu kenan domin sai aka jefa ta a cikin waɗanda ke dafama sarauniya abinci, ita kaɗaice daban a cikin masu dafa abincin domin sauran sun kasance matan turawa ne, mafi yawan lokutta idan matan turawa  suna aiki da ita sukan tambayeta.
  " Are you Indian?"
Ma ana ( ke ƴar Indiya ce)
 " Nop actually I am Ethiopian." Inji Solyana.
Ma ana ( Aa, ni ƴar Ethiopia ce)
" Really! So which language do you speak?" 
Ma ana ( Da gaske! to hala wane halshe kike magana dashi)
" To tell you the truth, my tribal language is Amharic." Inji Solyana.
Ma ana( In faɗa muku gaskiya halshen da nake magana dashi shine Amharik) 
Solyana takan yi mamaki idan suna mata waɗannan tambayoyi domin tanada masaniyar cewa matan indiya fatarsu fara ce, ita kuma ba fara bace domin wankan tarwaɗa ce, kuma mafi yawan mutanen Amhara fatarsu wankan tarwaɗa ce, Solyana ta samu matsayi sosai ga wannan aiki da take sabida kasancewarta kyakkyawa sai ta samu farin jini, duk inda ta wulga sai an kallo, mafi yawan lokutta abokanta turawa kan yi tsammanin ba abunda ke damunta cikin rashin sanin  cewa ta ciki na ciki, yau ma kamar kullum bayan ta kaiwa sarauniya abincinta na dare sai ta fito masarautar ta kama hanyar zuwa masaukinta. To akan hanyarta ne taji an kira sunanta cikin halshen Amharik.
   "  li‘iliti " - ልዕልት
Ma ana ( Gimbiya)
Da ƙarfi Solyana ta juyo domin ganin wanda ke kiranta, mace ta gani tsaye tana mata murmushi, ai kuwa Solyana na dubanta sai ta ganeta, yarinyar sunanta Arsema kuma ta kasance mai yiwa Solyana hidima kafin ta dawo birnin Selam.
Page 79
Bayan Solyana ta bar birnin Amhara, sai matan da take mata hidima  kowace ta kama gabanta, ita Arsema a lokacin tanada ƴan uwa a Selam sabida haka sai taga bari ta koma can wataƙila ta samu aikin yi, bata jima da zuwa wurin ƴan uwan nata ba sai ga sarauniyar London ta kawo hari a garin, kuma cikin rashin sa a tana cikin waɗanda aka kama a matsayin bayi. Da gudu Arsema ta nufo Solyana, anan suka rungume juna cikin farin ciki kafin su fara magana da halahen Amharik
  " Gimbiya ban yi tsammanin zan ƙara ganinki ba." Haka Arsema ta faɗa cikin halshen Amharik.
  " Zan so ki faɗamin dame dame ya faru bayan tafiyata!" Inji Solyana itama a cikin halshem Amharik.
  " Ba abunda ya faru bayan tafiyarki in banda damar da sarauniya Amnen ta samu wurin juya mahaifinki sarki kamar yadda takeso, sai kuma tsananta zalunci da tayi wanda hakan yasa mafi yawan barorin gidan suka canza sheƙa kuma nima wannan dalili yasa na koma Selam ko zan samu aiki sai kuma gashi kinga abunda ya faru." Inji Arsema. " Abunda yafi baƙanta min rai shine hadda  mahaifina yana cikin waɗanda aka kama, sai da shi ba cikinmu yake ba domin an kaisa ne a wani gidan yari na ƙarƙashin ƙasa tare da wasu mutane kuma ban san dalilin da yasa sarauniya tayi haka ba."
   " To amma ya akayi kikasan da cewa yana can?" Solyana ta tambayeta 
   " Sabida a gabana sarauniya ta bada umarni a tafi dasu can." Inji Arsema.
   " Ko kin san inda gidan yarin yake?" Solyana ta tambayeta.
   " Na sani amma fa ki sani wuri ne mai hatsari domin dakaru suna bada tsaro sosai ba dare ba rana." Inji Arsema.
    " Mu tafi ki nunamin inda wannan gidan yari yake." Inji Solyana.
    " Meye ma anar hakan?" Arsema ta tambaya.
    "  Zan fito da waɗanda aka kama ne ba tare da laifin kome ba." Inji Solyana. Arsema najin haka sai ta ƙura mata ido cikin mamaki kafin ta fara magana:
 "ልዕልት ይህን ማድረግ አትችልም "
li‘iliti yihini madiregi ātichilimi
 Ma ana ( Gimbiya bazaki iyaba)
" Kada ki manta akwai dakaru masu bada tsaro a wurin, to taya zaki kuɓutar da mutane?" Inji Arsema.
 " Mu tafi kawai ki nuna min gidan yarin." Inji Solyana. Arsema shiru tayi tana tunanin abunyi sai da Solyana ta daka mata tsawa sannan hankalinta ya dawo. Anan Arsema ta shiga gaba Solyana na biye da ita, sai da sukayi tafiya mai nisa kafin su fara shiga lungu lungu cikin birnin.
Page 80
wata ƙofa ce Arsema ta buɗa daganan taja baya. 
  " Wannan itace ƙofar da zata saɗaki da gidan yarin da kike nema amma gaskiya bazan iya shiga ba, zan jiraki a nan waje." Inji Arsema. Solyana dubanta kawai tayi daganan sai ta shiga ƙofar mai cike da tsananin duhu. Anan Solyana ta samu kanta cikin kwaroro mai tsananin duhu, sai da tayi tafiya mai nisa kafin ta fara jiyo sautin mutane a can nesa, samun kanta tayi a wani wuri mai tsananin faɗi, gefe gefe na wurin ɗakuna ne wanda da alama ƴan fursuna ne a ciki, daga can ƙarshen wurin kuma wata matattakala ce wadda zata jefa mutum wani gida dake can ƙasa, kallon tsaf Solyana ta yima wurin tana mai tunanin hanyar da zatabi domin cimma wannan matattakalar da zata kaita ƙasan gidan. Murmushi tayi mai nuni da cewa ta samu mafita, bin gina ta farayi tana mai tafiyar sanɗa kuma sabida duhun dake wurin dakarun dake gadin wurin basu samu damar ganinta ba, cikin sauri ta shige ƙofar da zata saɗata da mattakalar, ai kuwa tana shiga sai taga cewa mattatakala ce doguwa wadda zata kaita can ƙasan gidan, a hankali ta fara tafiya tana mai dube dube har takai can ƙasan, to anan ne ta gane cewa ɗakuna ne birjik a wurin kuma kowane ɗaki akwai ƴan fursuna ciki, a can gefe kuma wasu makullai ne ta hango a sankarfesu, da sauri ta ɗaukosu daganan ta fara buɗe ƴan fursuna ɗin, ai kuwa da gudu suka fara fitowa suna guje guje, wani sauti ta juyo wanda bazata taɓa mantawa da mai wannan sauti ba, a hankali ta juyo, anan tayi arba da wani dattijo riƙe da Milam ya nufota.
"  li‘iliti " - ልዕልት Inji tsohon.
Ma ana (gimbiya)
Miƙo mata Milam yayi wadda keta faman kuka, kuma a dai dai wannan lokaci ne Arsema ta shigo wurin kamar an jefota, ai kuwa Arsema tana hango wannan dattijon sai ta sheƙo da gudu, suna haɗuwa suka rungume juna cikin farin ciki.
  " Bazan manta da wannan karamci ba, domin ba wai mahaifina kawai kika taimaka ba, kin taimaki mutanen Amhara gabaki ɗaya." Inji Arsema cikin halshen Amharik. Anan Arsema ta janyo mahaifinta suka kama hanyar fita ita kuwa Solyana rungume da Milam cikin murmushi, a wannan lokaci dakarun dake gadin wurin sun ankaro abunda ya faru sabida haka sai su Solyana suka fara gudu domin kada asirinsu ya tonu, ai kuwa suna cikin gudun ne sukayi arba da dakarun London riƙe da bindigoginsu.
  " One move and you are dead." Inji ɗaya daga cikin dakarun.
Ma ana ( Motsi daya zai yi sanadiyar mutuwarku.)
Page 81
Ita kuwa Solyana tanajin haka sai ta baiwa Arsema Milam.
" Ki kulamin da ita." Haka ta daɗa cikin halshen Amharik. Cikin salo Solyana ta janyo ɗaya daga cikin dakarun, sai da tayi majaujawa dashi kafin ta jefama sauran shi, ai kuwa suna haɗuwa ya bangajesu suka faɗi ƙasa, daganan Solyana ta fara ɗauki ba daɗi da waɗannan dakaru, suna ƙoƙarin su halbeta amma bata yarda domin dataga wani na shirin halbinta sai ta janye da sauri, su kuwa ƴan fursuna ɗin cigaba sukayi da gudu kuma a haka ne Arsema ta samu damar gudu tare da mahaifinta, ba yadda Solyana batayi ba domin ta samu damar gudu amma abu yaci tura, kasancewar taron yawa yafi taron ƙarfi sai aka kamata, da kaca suka ɗaureta tamau daganan sai aka gurfanar da ita gaban sarauniya.
  " You have broke the rule of your queen." Inji sarauniya.
Ma ana( Kin karya dokar sarauniyarki)
" You freed them and thinking you will go free huh?"
Ma ana ( Kin basu ƴanci kuma ke a tunaninki zaki samu ƴanci ko?) 
" You will be punish accordingly." 
Ma ana ( Za a baki horo kamar yadda ya dace) Anan dakaru suka ingiza Solyana waje, a cikin wani gidan kaso aka jefata aka rufe. Tun da sanyin safiya aka fito da ita, da ƙarfi ake ingizata, ita kuwa Solyana sai binsu take cikin rashin sanin abunda zasu aiwatar. Bayan dakarun sun fito gidan sarautar da ita sai suka nufi wani fili wanda ke cike da mutane, har yanzu ingiza Solyana akeyi da ƙarfi wadda ke ɗaure da kaca, wata matattakala aka hau da ita, anan Solyana ta samu kanta saman wani wuri mai tudu, duk mutanen dake wurin tsuro mata ido sukayi suna kallonta, da yawansu sun kasance mutanen Amhara ne wasu kuma turawa ne, a cikin waɗannan mutane kuwa harda Arsema da mahaifinta, Arsema na rike da Milam sai zubar da hawaye take, ita kuwa tun a lokacin da ta ƙyalla ido taga mahaifiyarta, sai ta fara kuka kamar bazata daina ba, akan haka ne Arsema ta tako saman tudun ta baiwa Solyana Milam domin ta lallasheta, abun mamaki Solyana na ɗaukarta  sai tayi shiru, Solyana rungume Milam tayi kamar bazata saketa ba, ita kuwa sarauniyar London dake can gefe, a fusace ta fisge Milam tayi wulgi da ita, cikin sa a kuwa sai Milam ta faɗo jikin mahaifin Arsema, ita kuwa  Arsema tana ganin haka sai ta sauko saman tudun. Sarauniyar London duban mutane tayi kafin ta fara magana a cikin halshen turanci:
   " Ta yaudaremu, kuma ta zubar da ƙimar wannan birni, ta kuɓutar da masu laifi sabida haka dolene ta fuskanci horo mai tsanani." Wasu dakaru ne suka janyo Solyana da ƙarfi, ɗaureta akayi yadda hannuwanta biyu sun ɗaga sama, daganan sai wani mutum yazo, shi wannan mutumi ya  lulluɓe fuskarsa da baƙin ƙyalle yadda ba a ganin kome.
Page 82
Riƙe yake da bulalar kaca mai tsananin girma, anan ya ɗaga wannan bulala yana zubama Solyana, bulala ɗaya yayi amma sai da bayanta ya fashe, anan jini ya fara tsargowa saman tufarta, Arsema ba ƙaramin tashin hankali ta gani a wannan wuri ba domin ko namiji akema wannan duka ba hus balantana mace, da yawan mutanen Amhara sai zubar da hawaye suke sabida tausayi, ita kuwa Solyana tunda aka fara dukan nata batayi ko gizau ba, tunani ya dabaibaye mata zuciya daganan sai idanunta suka fara buɗewa da rufewa, dishi dishin mutane ta fara gani suna zubar da hawaye, a can gefe kuma Milam ce saman mahaifin Arsema sai faman kuka take, duk da cewa tana cikin tsananin jin zogin dukan da ake mata amma bai hanata yin murmushi ba ganin cewa kamar Milam na kusa da ita. Tunani ne ya ƙara cika mata zuciya daganan kuma sai idanunta suka rufe gam.
   Sarki Benyam ba ƙaramar fusata yayi ba ganin cewa matansa wato gimbiyoyi bakwai daya aura sun ɓata, zargin da yake shine wannan baƙon da ya shigo birnin shine ya  sace su, sabida wannan dalili sai sarki ya baza dakarunsa su shiga lungu lungu na duniya duk inda yake su kamosa, kuma don ya sauƙaƙa musu aikin sai ya zana taswirar baƙon ga fatar damisa yadda idan sun gansa zasu iya ganesa, anan sarki ya baiwa sarkin yaƙi fatar damisar, shi kuwa sarkin yaƙi sai ya jagoranci waɗannan dakaru domin cika umarnin sarki. Kwanci tashi dakaru sai aiki suke a rassa daban daban na duniya suna neman wannan baƙo, wata rana sai sukayi arba da wannan mutumin da sarki ya zana musu cikin wani rafi yana wanka. ai kuwa yana fitowa sukayi awon gaba dashi, basu tsaya dashi ko ina ba sai gaban sarki, shi kuwa sarki sabida tsananin murna sai da yaba duk dakarun da akayi wannan tafiya dasu dakiya mai tarin yawa, daganan sai aka fara tambayar wannan mutumi shin wai ina ya ɓoye matan sarki kuma menene maganin wannan anobar data addabi gari, anan mutumin yace shi gaskiya bai taɓa zuwa wannan gari ba sabida haka bai san abunda suke magana akai ba. Ba yadda sarki bai yiba domin samun bayani amma bai samu kome ba, tunani ne ya cika cikin sarki, shin wai wancan baƙon da yazo wurinsa yayi shigar wannan mutumi ne ko kuwa shi ɗin dai ne iyaka dai yanaso yayi masa ɓadda kama ne? daga ƙarshe dai bayan an labartawa mutumin anobar dake damun garin sai yace yanada magani amma sai idan sarki ya yarda zai bishi wani wuri, anan sarki ya aminta, shirya musu dawakai akayi suka hau, mutumin na gaba saman dokinsa shima sarki yana biye dashi saman nasa doki, sai da sukayi tafiya mai nisa sa anan suka cimma wani rafi, anan mutumin ya sabko saman dokinsa shima sarki sai ya sabko saman nasa dokin, anan mutumin ya cema sarki ya shiga cikin rafin ya ɗebo duk wani fure daya gani saman ruwa, idan ya koma garinsa sai ya jefa furen a cikin ruwan garin.
Page 83
To duk wanda yasha ruwan zai warke da kowace irin  cuta dake damunsa. Anan sarki ya shiga cikin rafin yana ɗibar furen shi kuwa mutumin yayi tsaye a gaɓar ruwan, to abun mamaki koda sarki ya fito cikin ruwan sai ya nemi wannan mutumi sama da ƙasa amma babu shi, anan sarki ya fara tambayar mutane kuma yana nuna musu taswirarsa daya zana, anan ne wani dattijo ya faɗama sarki cewa ai wannan mutumi daya zana shekarunsa ɗari uku da mutuwa kuma ana kiransa da sarkin rafi sabida bashida wurin zama in ba rafi ba kuma duk wani rafi dake wannan nahiyar to ya san dashi. Anan sarki ya dawo masarautarsa yana mamakin wannan abu. Mutanen garin sun samu sauƙin wannan annobar dake damunsu bayan sarki ya jefa furen cikin ruwan garin, amma kuma duk da haka sarki bai daina damuwa  ba domin har yanzu yana tunanin hanyar da zai bi ya dawo da gimbiyoyinsa guda bakwai da suka ɓace, to abun tambaya shine ta wace hanya sarki zai gano gimbiyoyinsa guda bakwai?
   Firgigit Solyana ta farka, har yanzu takan jiyo sautin kukan Milam a cikin kunnuwanta, har yanzu takan jiyo sautin kakanta wanda ya haifi mahaifiyarta a lokacin da yaci gaba da bata labarin Gimbiya Bakwai wato sarki Benyam da gimbiyoyi bakwai daya aura, motsin tafiya taji wanda ke nuni da cewa an nufo inda take, anan Solyana ta gyra zamanta tana jiran mai shigowa, can sai ga sarauniyar London tare da Arsema da kuma mahaifin Arsema ɗin, a wannan lokaci sarauniyar London ce ke riƙe da Milam sai dakaru ke take mata baya, dakarun suna buɗe gidan yarin sai sarauniya ta shigo tare da Arsema. Anan sarauniya ta miƙawa Solyana Milam.
  " Kiyi mata kallon ƙarshe domin daga wannan rana bazaki ƙara ganinta ba." Haka sarauniya ta faɗa cikin halshen English. Ita kuwa Solyana rungume ƴarta tayi cikin tausayawa da jimami, ga yarinya jaririya amma za a rabata da mahaifiyarta tanaji tana gani. Arsema da mahaifinta sai zubda hawaye suke domin gani suke duk sabida su wannan abu ya faru, bayan daƙiƙu kaɗan sai sarauniya ta fisge Milam daga hannun Solyana, anan ta  damƙa wa Arsema ita daganan dakaru suka ingizasu waje, har su Arsema sukayi nisa Solyana takan juyo ihu da kururuwa na Milam sai kace bazata daina ba, duk da taurin rai irin na Solyana amma a wannan lokaci sai da ta zubda hawaye sabida tausayin ƴarta Milam.
   A birnin Amhara kuwa, tun a lokacin da sarauniyar London ta tafi da mutanen birnin Selam sai sarki Bamlak ya ɗauki dukkan tsana ya ɗora a wuyan sarauniyarsa Amnen domin a ganinsa itace sanadin rabasa da abar ƙaunarsa kuma ƴarsa ta cikinsa wato Solyana, wannan tsana tayi tsanani sosai domin ita kanta sarauniya Amnen tana ganin canji a wurin sarki, shi kuwa sarkin yaƙi Addis da yasha alwashin kare ƙanwarsa wato sarauniya Amnen daga harin sarki Bamlak da yaga abun yana shirin wuce gona da iri sai ya tuntuɓi sarauniya Amnen da maganar. 
Page 84
  " Me zai hana kibar wannan birni ki tafi wani wuri kici gaba da rayuwarki domin ina jin tsoron matakin da sarki zai iya ɗauka akanki, zan baki dukiya mai tarin yawa wadda zata isheki nemawa kanki wani aiki." Inji sarkin yaƙi Addis a cikin halshen Amharik.
  " Kada ka damu ɗan uwana, a yanzu haka ina gab dana shawo kan wannan matsalar domin akwai wani sabon ilimi da nake koyo, kuma wannan ilimi shine zai maye gurbin duk wata ɓarna data faru zuwa alheri sabida haka inaso ka zuba ido kaga abunda zai faru." Inji sarauniya Amnen, haka sarkin yaƙi Addis ya tafiyarsa yana tunanin wannan magana ta ƙanwarsa cikin nazarin cewa wannan ko wane irin ilimi ne take magana akai?
  Shi kuwa sarkin yaƙi Tedros na birnin Selam tun a lokacin da sukabar bar garin ya ɗau ragamar kare sarki da sarauniya na Selam dashida sauran dakaru, ƙalilan daga cikin mutanen birnin ne ke biye dasu kuma a cikinsu hadda Yarima Sodar da matarsa Katina. Yarima Sodar ba ƙaramin farin ciki yajiba a lokacin daya gano cewa uwanyensa wato sarki da sarauniya na Selam suna raye, tanti suka kafa a wani wuri mai nisa, anan suka cigaba da rayuwarsa, sai daga baya Yarima Sodar ya bada shawarar cewa mai zai hana su koma tsohon birninsu na Selam su gyarasa idan yaso sai su cigaba da rayuwarsu a can, cikin amincewa sarki ya yarda da wannan shawara daganan sai suka ɗunguma suka koma birnin Selam, ƴan ƙalilan na mutanen da suka rage sune suka sadaukar da kansu cewa zasuyi aikin garin, anan suka duƙufa ba dare ba rana kullum cikin aiki suke.
   Tun a lokacin da sarauniyar London ta keɓantar da Solyana a cikin gidan yari na musamman, Arsema da mahaifinta basu ƙara jin labarinta ba kuma akan dole suka daina bincike akanta domin babu wani bayani dangane da lamarinta, ta mutu tana raye basu sani ba, kulawar Milam ta dawo kan Arsema ita da mahaifinta, da yake itama Arsema tana cikin masu dafama sarauniya abinci sabida haka ƴan kuɗin da ake biyanta duk wata dasu take hidimar yau da kullum, duk ƙarshen wata sukan taru inda ake biyansu albashinsu, anan za a dinga kiran sunayensu ɗaya bayan ɗaya, bayan an yi bincike akansu domin kada wani ya amsar ma wani kuɗi sai a biyasu. Shi kuwa Mahaifin Arsema yayi ƙoƙarin samun aiki a wani babban shago da ake sayar da ɗanye kifi da kuma daffafe, mahaifin Arsema ya kasance ɗaya daga cikin masu tsaron shagon, kuma shagon ya kasance a ƙarkashin sarauniyar London, suma duk wata ake biyansu kamar yadda ake biyan su Arsema.
  Shekaru na shuɗewa rayuwa na tafiya har Milam ta zamo budurwa, cikar halittarta ya fara fitowa  wanda hakan yasa kyawonta ya ninka kansa ninkin baninkin, Milam ta taso yarinya mai tsananin son nishaɗi da kuma karatu.
Page 85
Sabida wannan dalili kullum a cikin dare sukan haɗu  ita da abokanta mata su huɗu a wani fili domin karatun dare, Milam itace ta biyar ɗinsu, Arsema itace ke koya musu karatun kuma a cikin wannan karatu ne suka samu nagartaccen ilimi akan tushen gaskiya da kuma rayuwa mai albarka. Milam ta kaaance mai tsananin farin jini ga mutanen masarautar London sabida haka sai kowa ya zama nata, hatta dakarun London sukan jata da tsokana kuma akan wannan dalii sai ta laƙe musu har sai da ta samu horo mai tsanani akan sarrafa makamai a filin daga, sabida baki irin nata sai da ta samo hanyar da suka nuna mata maɓoyar da ake aje makaman, a hankali a hankali sai gashi ta iya tuƙa babban jirgin ruwa da kanta, haka shima jirgin ƙasa ba a barta baya ba. Tun a ranar da Arsema ta faɗama Milam labarin mahaifiyarta Solyana sai abubuwa suka canza domin alwashi tasha na cewa kul a jima kul a daɗe sai ta fito da ita duk da cewa batasan ainahin gidan kason da aka ajiyeta ba kuma ita kanta Arsema bazata iya tunawa da wurin ba sabida shekarun da suka shuɗe, babbar matsalar itace rashin sanin cewa Solyana na raye ko kuwa ta mutu.
  Ƙudurin da Milam ta ɗauka shine zata cigaba da binciken masarautar wataƙila ta samu wasu bayanai masu muhimmanci, kuma a cikin hakane ta samu wani littafi mai suna " The Seven Princess " ma ana gimbiyoyi bakwai, sace littafin tayi da zimmar cewa idan ta gama karatu zata mayar dashi, bayan ta gama karatun littafin sai ta yanke shawarar cewa zatayi amfani da taken littafin wurin ceto mahaifiyarta Solyana.
   Yauma kamar kullum bayan Arsema ta shigo domin basu darasi sai Milam ta miƙe tsaye, anan ta karɓi umarni ga Arsema domin yau itace keson bada darasi, tsaye Milam tayi tana dubansu ɗaya bayan ɗaya kafin ta fara magana tana mai riƙe da littafin data sace cikin fadar sarauniya.
  " Wannan shine littafin dana karanta kuma a cikinsa ne zan bada darasi akan rayuwarmu, rayuwarmu ta kasance  cikin tsoro da kuma musgunawa tun a lokacin da aka rabamu da yankinmu na Amhara, bamuda ƴanci amma bamu damu ba, ba a bari mu aiwatar da al adunmu na gargajiya amma bamu damu ba, akwai ƴan uwanmu da aka garƙame a gidan kaso ba tare da laifin kome ba amma bamu damu ba. " Haka Milam ta faɗa cikin halshen Amharik daganan kuma sai ta cigaba da bayaninta. " Sabida wannan dalili sai na nemo muna mafita, kuma mafitar ta kasance a cikin wannan liittafi, a cikin wannan littafi na karanta labarin wani sarki da ake kira Benyam, shi wannan sarki yana auren gimbiyoyi bakwai kuma su waɗannan gimbiyoyi ya auresu ne da ƙarfi ba wai don suna soba amma kuma daga ƙarshe su waɗannan gimbiyoyi sun haɗa kansu wurin ganin cewa sun ƙwaci kansu daga wannan sarki kuma cikin sa a sun aiwatar da nufinsu 
Page 86
To ina kira damu taron matan Amhara cewa mu haɗa kanmu kamar yadda waɗanmam gimbiyoyi bakwai suka haɗa kansu.Domin idan muka haɗa kanmu to zamu samu nasara wadda zata dawo muna da ƴancinmu, sabida haka waye zai tsayu dani ganin cewa mun ƙwatowa mutanenmu ƴanci. " Arsema miƙewa tayi ta ƙaraso wurin Milam, daganan sai ta rike hannunta na hagu tare da cewa:
  " Ina tare dake." Abokan Milam wato ƴan matan huɗu sai suka taso sukayi kamar yadda Arsema tayi.
  " Muna bayanki." Haka suka faɗa tare, can sai Milam taji an rikota ta baya, tana juyowa sai taga abokiyarta ce Liyat.
  " Nima ina bayanki." Haka Liyat ta faɗa.Milam ba ƙaramin jin daɗi tayiba ganin Liyat domin Liyat itace zata nuna musu gidan yarin da suke sa ran zasu ga mutanensu. A wannan lokaci su bakwai ne gami da Milam, anan Milam ta fara zuba musu dubarun data tsara kuma tana jaddada musu cewa idan suka bata haɗin kai to bako shakka zasu cimma matsaya. Tun daga wannan rana sai Milam ta fara basu horo akan yadda ake sarrafa makamai da kuma yadda ake fakon abokin gaba a filin daga, bata barsu a baya domin sai da ta tabbatar cewa kowanensu zai iya tuƙa jirgin ƙasa da kuma jirgin ruwa.
   A cikin wani darene suka kai hari ga masarautar London, gudu sukeyi suna jefa nakiyoyi, duk nakiyar data fashe sai kaga gidaje na rushewa dakaru suna faɗuwa, sarauniyar London ba ƙaramar hasala tayi ba da taji ance ƴan mata bakwai ne ke wannan aiki. Shirin ƙwarai sarauniya tayi daganan ta durfafi gidan yari riƙe da takobinta dakaru na take mata baya. Ita kuma Milam sai buɗe ƴan fursuna take ita da abokanta, Liyat da Arsema kuwa suna can suna ƙoƙarin tayar da jirgin ƙasa wanda zasu gudu dashi, duk ɗan fursunan da aka kwance sai ya fito da gudu ya nufi hanyar jirgin ƙasa domin Milam ta faɗa musu cewa su tafi can akwai jirgin dake jiransu, hakama can masaukin su Milam ɗin mutanen Amhara sai gudu suke suna ƙoƙarin zuwa wurin jirgin sabida suma Milam ta faɗa musu cewa su tafi can, dakarun London sai ƙoƙari suke ganin cewa sun hana mutane zuwa wurin amma abu yafi ƙarfinsu domin mutanen Amhara sai dukansu suke. Sai da Milam ta tabbatar cewa duk ƴan fursuna sun gudu sa an nan ta nufi wani gidan yari na ƙarshe, tana ɓalle ganbun da gatari sai ta shiga ciki, mace kyakkyawa ta gani a ciki sai sharar bacci take, Milam na ganinta sai taji cewa lallai wannan itace mahaifiyarta Solyana da Arsema ke bata labarinta. Anan Milam ta tunkareta, tana isowa wurinta sai ta duƙa, hannunta ta aza saman fuskar Solyana. Ita kuma Solyana tanajin ana taɓa mata fuska sai ta farka amma idanunta suna buɗewa suna rufewa, zata iya hango dishi dishin wata yarinya a kusa da ita.
Page 87
Can kuma sai tunani ya dabaibaye mata zuciya.
Tun a lokacin da sarki Benyam yaga cewa masifar data addabi mutanensa ta kau sai ya fara tunanin hanyar da zaibi ganin cewa gimbiyoyinsa guda bakwai sun dawo wurinsa, a kullum idan rana ta faɗi yakan tafi bakin rafi dake bayan gari shi kaɗai yana tunanin matansa, wata rana bai daɗe da zaunawa ba bayan ya saki dokinsa kawai sai yaga wata halitta mai kamar namiji mai kamar mace a cikin ruwan, sarki Benyam miƙewa yayi tsaye cikin firgici domin baiga lokacin da wannan halittar ta shiga ruwan ba, sanye take da kaya baƙaƙe waɗanda suka lulluɓe jikinta ga baki ɗaya masu tsananin faɗi da girma ta yadda baya ganin kome na jikinta, idan ya kalli fuskarta ba abunda yake gani in ba duhu ba, anan sarki Benyam ya kalli wannan halittar cikin tsoro domin bazai iya cewa namiji ne ko mace amma yafi kyautata zaton cewa mace ce, magana ce yaji tana fitowa daga wannan halittar amma kuma maganar batada asali domin bazai iya cewa namiji ne ko mace ba iyaka dai yafi kyautata zaton cewa mace ce. Anan wannan halittar ta faɗa masa cewa zata dawo masa da matansa amma da sharaɗin cewa duk abunda matan suke buƙata a wurinsa kada yayi musu ko menene, sarki yayi mamakin yadda wannan halittar tasan da cewa yana neman matansa, anan ya aminta, ita kuwa halittar sai ta jefo masa furanni guda bakwai tace yaje ya shukasu a cikin gadinarsa amma kada ya basu ruwa sai gobe da safe, sarki na komawa gida ya shuka waɗannan furanni da aka bashi yana mamakin yadda matansa zasu dawo, a wannan dare bai yi bacci ba domin ya matsu safiya ta waye yaje ya zuba musu ruwa. Tunda ƙulun ƙulun safiya sarki ya nufi gadinarsa ɗauke da battar ruwa, yana zuwa inda furannin suke sai ya zubama fure na farko ruwa, ai kuwa yin haka keda wuya sai fure na farko ya koma mace, anan sarki yayi murmushin farin ciki domin matarsa ce ta farko ta dawo, tana kallonsa sai tace ya bata ruwa tasha, sarki yayi mamaki domin wannan matar tasa bata taɓa ruwa amma yau ita da kanta ke cewa ya bata ruwa tasha, shi kuwa sarki cikin sauri ya miƙa mata battar ruwa tasha sabida ya manta da kashedi  da wannan halittar ta masa, tana gama shan ruwan sai taja baya, anan ya zubama fure na biyu ruwa, yin hakan keda wuya sai ga matarsa ta biyu ta dawo, tana kallonsa sai tace ya bata abinci taci, itama sarki yayi mamaki domin batacin abinci amma yau ita da kanta ke cewa ya bata abinci taci, anan sarki yasa aka kawo mata abinci, tana gama ci sai taja baya, anan ya zubama fure na uku ruwa, sai ga matarsa ta uku ta dawo, tana kallonsa sai tace ya bata wuri tanaso tayi bacci amma da sharaɗin cewa kada ya zubama sauran furanni ruwa sai ta gama baccinta, anan sarki ya aminta yana mamakin wannan abu domin wannan mata tasa ta kasance bata bacci ko kaɗan, anan ta kwanta tana sharar bacci shi kuma sarki yana kallonta, sai ta gama sa annan taja baya.
Page 88
Shi kuwa sarki sai ya zubama fure na huɗu  ruwa, yin haka keda wuya sai ga matarsa ta huɗu ta dawo, tana kallonsa sai ta gaida shi cikin gimamawa tare da basa labarai masu daɗi, sarki yayi mamaki sosai domin wannan matar tasa ta kasance bata magana amma sai gashi yau itace ke basa labarai da kanta. Tana gama basa labarai sai taja baya, anan sarki ya zubama fure na biyar ruwa, sai ga matarsa ta biyar ta dawo, tana kallonsa sai tace ya bata guri ta huta domin ta gaji, sarki yayi mamaki da wannan abu domin wannan matar tasa ta kasance bata gajiya da aiki balanta har ta faɗa da kanta cewa ta gaji amma yau ita kanta ke cewa ta gaji, bayan ta gama hutawarta sai taja baya shi kuma sarki sai ya zubama fure na shidda ruwa, sai ga matarsa ta shidda ta dawo, tana kallonsa sai tace ya kawo mata kayan dafa abinci domin tanaso ta dafa masa abinci, sarki yayi mamakin wannan abu domin wannan matar tasa ta kasance bata dafa abinci, iyaka duk lokacin da yakeso zata kawo masa abinci irin wanda yakeso amma sai gashi yau ita da kanta ke cewa ya kawo mata kayan abinci ta dafa masa, anan sarki yasa aka kawo mata kayan abinci, tana gama dafa masa sai taja baya, daganan sai sarki ya zubama fure na bakwai ruwa, sai ga matarsa ta bakwai ta dawo, tana kallonsa sai tace ya kawo mata ruwa ta dafa masa abinci, sarki yayi mamaki domin wannan mata tasa ta kasance bata dafa abinci da ruwa, amma sai gashi yau ita da kanta ke cewa ya kawo mata ruwa ta dafa abinci, anan sarki yasa aka kawo mata ruwa, tana gama dafa abincin sai taja baya inda ƴan uwanta gimbiyoyi suke, anan sarki yaga sun haɗe kansu wato kowacensu ta riƙe hannun ƴar uwarta, anan suka fara kewaye suna zagaye da sauri da sauri, wata guguwa ce mai tsananin ƙarfi ta ruru a tsakiyarsu, to anan ne sarki ya gano cewa sun haɗa wannan guguwar ne domin su samu damar gudu, da ƙarfi ya kira dakarunsa domin su kamasu amma sun makara, ko kafin dakarun su iso har guguwar ta lulluƙa da gimbiyoyinsa guda bakwai a cikin gajimare, anan sarki Benyam ya duƙufa cikin taskar baƙin ciki, sai a wannan lokaci ya tuno cewa yayi kuskure akan kashedin da aka yi masa na cewa kada ya biya musu duk wata buƙata da sukeso, ashe dama sun haɗa masa wannan tarkon ne domin su samu   damar haɗa kansu kuma su samu damar guduwa, ba yadda sarki bai yiba ganin cewa yaci garuruwan waɗannan gimbiyoyi guda bakwai da yaƙi domin ya ƙara tursasu su auresa amma abu yaci tura, akan dole yayi haƙuri cikin tunanin cewa ba kowane kuskure ke gyaruwa ba sabida shi kam yayi kuskuren da bazai gyaru ba.
  Firgigit Solyana ta farka tana tuno lokacin da kakanta wanda ya haifi mahaifinta ya faɗa mata ƙarshen labarin gimbiya bakwai, kuma a cikin labarin ne ta ɗau darasi cewa duk wanda ya sama kansa mugunta to ƙarshensa wahala da baƙin ciki kamar yadda sarki Benyam ya samu kansa.
Page 89
kuma duk mutanen da suka haɗa kansu akan aikata alheri to rayuwarsu nasara da farin ciki ne zasu lulluɓesu kamar yadda ya faru ga gimbiyoyi bakwai. 
   A wannan lokaci idanun Solyana sun buɗe tangaram, tsura ma Milam ido tayi cikin tunani mai kamada farin ciki, wai jaririyar da take rungumawa itace ta zama budurwa, hawayen farin ciki ne ya ɗigo cikin idanun Solyana domin bazata taɓa mantawa da fuskar Milam ba, rungume juna  sukayi   cikin farin ciki. Sai da suka jima ƙanƙane kafin su saki juna, Milam janyota tayi suka fito gidan yarin daganan suka kama hanyar fita domin a wannan lokaci babu kowa ciki, duk abokan Milam sun nufi hanyar jirgin ƙasa domin kada a barsu baya. Su Milam suna cikin gudu ne sai sukaci karo da sarauniyar London tare da dakarunta. Anan aka fara kallon kallo.
  " You think you can escape!" Inji sarauniyar London.
Ma ana ( Ke a tunaninki zaki iya gudu!)
  " I think I can defeat you only if you battle me alone." Inji Milam.
Ma ana( Ina tunanin cewa zan samu nasara akanki idan har kika yaƙeni ke kaɗai)
  " Let's see." Inji sarauniyar London.
Ma ana( Bari mu gani.) 
Sarauniyar London fito da takobinta tayi daganan ta fara kaima Milam sara da suka, su kuma dakarunta dake riƙe da manyan bindigogi tsage sukayi suna kallon wannan gumurzu, Milam wanzuwa tayi tana kare kanta tare daja baya domin bata fito da gatarinta ba, a cikin wannan gumurzu ne sarauniya ta samu nasarar yankan Milam ga kunne, cikin rashin sa a kuwa ta guntule ɗan ƙire, ita kuwa Solyana dake tsaye ba ƙaramar hasala tayi ba ganin cewa Milam ta samu tsaguwa ga kunnenta kuma can ƙasan kunnen an guntule ɗan ƙire, cikin zafin nama Solyana ta afkama sarauniya, kafin kaceme ta bajeta ga ƙasa, haka suma dakarun da naushi ɗaya ɗaya duk da zubar dasu,  anan Milam ta kalli mahaifiyarta Solyana cikin mamaki, wato abunda  Arsema ta faɗa mata dangane da jarumtakar Solyana gaskiya ne, duk da cewa Solyana tayi shekaru masu yawa gidan yari amma har yanzu ƙarfinta na nan, da gudu Solyana da Milam suka fito gidan yari daganan suka nufi hanyar jirgin ƙasa, bayan tafiyarsu ne sarauniyar London ta farka da ita da dakarunta akan sumar da sukayi, cikin sauri suma suka fito gidan yarin suna durfafar sawun su Milam. Solyana tana cikin gudu ne sai taji an kira sunanta da ƙarfi, tun kafin ta kalli mai muryar ta fara murmushi domin tanaji a jikinta wannan ba kowa bane in banda rabin ranta, ai kuwa tana jiyowa sai taci karo da Miller ya fito cikin wani gini wanda duk ya rugurguje, tafiya yake da ƴar gurmanta domin da alama ya samu rauni ga jikinsa, da gudu Solyana ta nufi wurinsa, ai kuwa suna haɗuwa suka rungume juna cikin farin ciki.
Page 90
Ita kuma Milam tsaye tayi tana dubansu, ko ba a faɗa mata ba tanaji cewa wannan baturen shine Mahaifinta wanda Arsema ke bata labari akai, bayan Solyana da Miller sun gama murnar farin ciki sai suka juyo kan Milam.
  " Wannan shine mahaifinki." Haka Solyana ta faɗama Milam cikin halshen Amharik. Shi kuma Miller janyota yayi ya rungume cikin farin ciki, ƙarar bindiga tasa suka saki juna, suna dubawa sai sukaga sarauniya ce tare da  dakarunta ke halbinsu, da gudu  su Milam suka bar wurin, su kuwa dakarun cigaba sukayi da halbo musu bindigogi, anan aka fara tsere, Su Milam suna gudu suna kaucewa albarusan da ake halbo musu, ita kuwa sarauniya tare da dakarunta sai gudu suke suna halbinsu, sai da suka jima suna wannan gudun sa annan suka fara jiyo kukan jirgin ƙasan a can nesa dasu, su Milam ƙara gudu sukayi suna kiran a buɗe musu ƙofar jirgin, su kuwa dakarun sarauniya sai halbinsu suke domin kada su cimma jirgin. Hargowar ihun su Milam ne ya janyo hankalin mutanen dake cikin jirgin, bayan sun gano abunda ke faruwa ne sai suka shaidawa  Arsema da Liyat cewa su rage gudun jirgin kuma su buɗe ƙofa, ana buɗe ƙofar jirgin su Milam suna isowa, anan mutanen dake cikin jirgin suka taimaka musu suka janyosu ciki, suna gama shiga ana kulle ƙofar su kuwa su Arsema ƙara gudun jirgin sukayi ta yadda dole sarauniya da dakarunta su daina binsu, sarauniya na ganin jirgin ƙasan ya cilla kamar walƙiya sai ta tsaya cikin baƙin ciki ita da dakarunta suna kallon yadda jirgin ƙasan ke narka namijin gudu, abunda yafi baƙanta musu rai shine gaba ɗaya mutanen Amhara sun shige cikin jirgin  domin ba wanda aka samu damar kamawa.
   A cikin jirgin ne Miller ke baiwa Solyana  labari cewa sarauniyar London ta kawo hari ne a birnin Selam domin ta samu nasarar cafkeshi, kuma kafin ta kawo harin sai da ta haɗa kai da sarauniya Amnen, sarauniyar London da sarauniya Amnen sun yi bincike sosai kafin su gano cewa yana birnin Selam tare da Solyana, kuma a cikin binciken nasu ne suka gano cewa Sodar yana tare dasu a cikin birnin. Miller shine na farko da sarauniyar London ta fara cafkewa a lokacin data kawo hari birnin Selam, kuma data tafi dashi London sai ta garƙamesa a cikin wani gini inda bai isa ya fito ba, damar daya samu ta fita shine su Milam sun jefama ginin  da yake ciki nakiya, anan ginin ya ragargaje shi kuma sai ya fito. Solyana shiru tayi tana tunanin wannan batu. Haka suka cigaba da rayuwa cikin wannan jirgi kwanci tashi har suka iso yankin Amhara, a dai dai birnin Selam jirgin ya tsaya, bayan mutane sun fito sai sukasha mamaki domin birnin Selan da suka bari a ragarganje sanadiyar harin sarauniyar London amma yanzu an gyara shi sosai da sosai. Anan gari ya ɗauka cewa waɗanda sarauniyar London ta tafi dasu sun dawo, yara fitowa suka farayi da gudu suna rungume iyayensu cikin murna. 
Page 91
Ita kuma Milam sai godiya ake  zuba mata domin itace sanadiyar fitowarsu daga wannan masifa, sarki da sarauniya na Selam sun yi maraba da zuwan su Milam, hakama Sodar da matarsa Katina sun yi maraba dasu. Shi kuma Sodar ya samu ɗa namiji sa an Milam da kuma mata biyu, bayan kwana uku da zuwan su Milam sai Solyana tayi shirin zuwa masarautar Amhara ita da Miller da Milam, kowanensu hawan doki yayi daganan suka kama hanya, kwanci tashi har suka iso garin, sarki Bamlak ba ƙaramar murna yayi ba ganin cewa Solyana ta dawo da miji da kuma ɗiya mace, ita kanta Solyana tayi mamakin canzawar sarauniya Amnen daga muguwa zuwa matar kirki, gabaki ɗaya rayuwar mutanen birnin ta canza sabida sun yi riƙo da addinin gaskiya. Sarki Bamlak murabus yayi akan karagarsa ya naɗa Solyana a matsayin sarauniyar da zata cigaba da mulkin garin, shi kuma Miller shine sarkinta, hakama a can birnin Selam Sodar ne aka naɗa sarkin garin sabida mahaifinaa yayi murabus, Milam kuwa bata manta da abokanta ba, Arsema, Liyat da sauransu, sai da ta tabbatar cewa sun samu aiki kuma sun samu dukiya mai tarin yawa, kasancewar Miller sarki kuma yanada dukiya mai tarin yawa sai ya buɗa manyan shaguna a yankin Hausawa kuma sabida wannan dalili yasa Milam ta samu damar iya halshen Hausa sabida shige da fice da takeyi a cikin garuruwan Hausawa cikin babban  jirgin ruwa. Bayan wasu kwanaki wata rana Miller yana cikin fada tare da dakaru sai ga wani bature ya shigo da wasiƙa, anan ya miƙawa  Miller takardar daganan ya tafiyarsa, shi kuma Miller yana buɗa wasiƙar sai ya fara karantawa kamar yadda aka rubuta a cikin halshen English:
   [ It was indeed a honour to the crown prince of England that becomes the crown king of Amhara, your queen far above any other says a royal greeting to the son of United Kingdom, perhaps I do not possessed the grace of being a mother as I am supposed to, although the era of my half life, my late king, is always remembered, that moment he died, while I am about giving birth to you. There was something he told me, something I can't dare to forget but ignored. It was now that I realised my mistakes, the Ethiopian girl I locked in dungeon for years was the wife of my son, and the shiny little angel I terrible threw was the daughter of my son, I am not asking for forgiveness as I knew I didn't deserved it,  but in my chest I knew how sincerely I embraced what your father told me, that he also embraced it before his demise, trustworthy lies in the knowledge you learned, and with that I hold it just like your king did. My princess, she might  decide to curse me for my crimes, a grand mother that slit the ear of her grand daughter, this was a shame to the land of whites, but I will remain loyal to Princess Milam, and when ever the king decided, let him come home, if not for his queen then for the grave of his king. Her royal highness the queen of England, to his royal highness the king of Amhara]
Page 92
Ma ana ( Ba ƙaramar girmamawa bace ga yariman England da a yanzu ya samun matsayin zama sarkin Amhara, sarauniyarka wadda babu irinta tana miƙa gaisuwar sarauta zuwa ga ɗan masarauta mai haɗe da juna, wataƙila ban cancanci zama uwa ba kamar yadda ya kamata na zama, duk da cewa har yanzu ina tunanin zamanin da nayi tare da rabin raina, wato marigayin sarkina, a lokacin da mijina kuma sarkina zai mutu ina gab da haihuwarka, akwai wani abu daya faɗamin, wani abu wanda bazan taɓa mantawa dashi ba amma kuma sai nayi watsi da abun sabida rashin ɗaukarsa da muhimmanci, amma kuma sai yanzu na gano cewa nayi kuskure akan abubuwan dana aikata, wai ashe wannan yarinyar ƴar Ethiopia dana garƙame a gidan kaso shekaru da dama da suka gabata itace matar ɗana, kuma wannan jaririyar danayi wulgi da ita ashe itace ɗiyar ɗana. Kada ka ɗauka cewa ina neman gafara  domin nasan da cewa ban can canci hakan ba, amma kuma duk da hakan a cikin zuciyata na karɓi abunda mahaifinka ya faɗamin, kuma shima mahaifin naka ya ƙarbi abun kafin mai rabawa ta rabamu, bako shakka akwai gaskiya a cikin ilimin daka koya, kuma sabida haka yasa nima na riƙe wannan ilimin daka koya hannu biyu biyu kamar yadda mahaifinka sarki yayi kafin ya rigamu gidan gaskiya, gimbiyata, zata iya tsinemin akan laifin dana aikata, kaka mace wadda ta yanke kunnen jikanyarta, gaskiya wannan abun kunya ne ga ƙasar turawa, amma duk da hakan zan kasance mai gaskiya ga Gimbiya Milam, kuma a duk lokacin da sarki ya zartar da hukunci, to ya kawo ziyara gida in har ba don sarauniyarsa ba, to sabida ziyarar ƙabarin mahaifinsa sarki, daga girman karagarta wato sarauniyar England zuwa ga girman karagarshi wato sarkin Amhara)
   Miller na gama karanta wasiƙar sai yayi murmushi, bai yi mamaki ba ganin cewa mahaifiyarsa wato sarauniyar England tasan halin da yake ciki kuma harda matsayinsa daya samu tare da iyalinsa wato Solyana da Milam, da sauri ya nufi cikin gidan  sarautar ya nuna ma Solyana da Milam wannan wasiƙar, ita kuwa Solyana bayan ta karanta wasiƙar sai ta shawarceshi da cewa ya kamata su kaima mahaifiyarsa wato  sarauniya  England ziyara a cikin babban jirgin ruwa, anan Miller ya aminta da wannan shawara kuma cikin kwana biyu suka kimtsa suka nufi England, daga ƙarshe dai sun samu ganin sarauniya kuma sun haɗa kansu tare, haka suma masarautar Selam sun samu kwanciyar hankali sosai, wato sarki da sarauniya na Selam, Sodar da matarsa Katina sai kuma ƴa ƴan Sodar uku wato mace biyu namiji ɗaya, harda sarkin yaƙi Tedros bai bari an barshi baya ba  wurin gane addinin gaskiya tare da mutanen masarautar Selam gabaki ɗaya, ita kuwa sarauniya Amnen tun a lokacin data gane addinin gaskiya sai ta samu kwanciyar hankali ita da sarki Bamlak.
Page 93
Shi kuwa sarkin yaƙi Addis ba ƙaramin farin ciki yayi ba ganin cewa anyi sulhu tsakanin sarki Bamlak da sarauniya Amnen, a haka dai mutanen yankin Amhara da kuma England suka aminta da addinin gaskiya kuma daga wannan lokaci sai aminci gaskiya da wadata suka dabaibaye yankin gabaki ɗaya.
   " Mahaifiyata ƴar Ethiopia ce, mahaifina kuma baturen England wato London," Haka Milam ta faɗa tana kallom su Uzaim kafin taci gaba da magana. " Halshen da muke magana dashi shine Amharik, amma kuma wannan halshe namu bai hanamu koyon wasu harussan da muke buƙata ba, ni ƴar sarauta ce gaba da baya amma ko kaɗan ban taɓa jin ƙyamar mutane a cikin raina ba, bako shakka ni jini biyu ce wato jinin Ethiopia da kuma jinin turawa sabida kasancewar mahaifiyata ƴar Ethiopia mahaifina kuma bature." Milam na zuwa nan sai ta nufi kujerarta domin zaunawa, anan su Uzaim suka bita da taɓi cikin farin cikin akan labarin data bayar har zuwa zaunawarta, shi kuwa Uzaim tashi tsaye yayi ya nufi tsakiyar ɗakin kafin ya fara magana kamar haka:
  " Bako shakka Milam tayi bajinta akan wannan labari data bamu mai haɗe da darussa, kamar yadda muka gani a cikin wannan labari an nuna fifikon addinin Islam akan kowane addini, kuma duk wanda ya riƙi wannan addini da gaskiya to zai samu amincin gaskiya da wadata kamar yadda mutanen Amhara, Selam da England suka samu, kuma yana ɗaya daga darasin wannan Labari akan amfanin taimako, kamar yadda muka gani a cikin wannan labari Solyana ta ɗau zimmar taimakon mutanen Amhara kuma akan hakane itama ta samu damar taimakon kanta tunda sai gashi ta gano ƴarta Milam, sai kuma inaso na faɗakar damu cewa kada muyi saurin yin fushi da mutum idan ya muna laifi domin bamu sani ba wataƙila yayi dana sani, kamar yadda muka gani daga ƙarshe ai sarauniyar London ta gane kuskurenta kuma akan hakane ta aikowa ɗanta Miller wasiƙa. Kuma mu sani cewa duk wanda ya ɗau hanyar zalunci to kul a jima kul a daɗe sai taskar baƙin ciki ta buɗe masa ƙofofinta marar iyaka kamar yadda ya faru ga sarki Benyam wato sarkin daya auri gimbiyoyi bakwai da ƙarfin tsiya ba wai don suna sunada ra ayi ba a cikin labarin Gimbiya Bakwai, kuma a cikin wannan labari na gimbiya bakwai mun ga amfanin haɗin kai kamar yadda gimbiyoyi bakwai suka haɗa kansu kuma yin hakan ne ya basu   damar guduwa akan hannun sarki Benyam. Anan zamu tsaya kuma ina taya mu murna akan nasarar da muka samu akan kammala baiwa juna labarinmu kuma ina mai sanar damu cewa zamu cigaba da haɗuwa kowace friday a wannan wurin domin akwai darussan da zamu fara gabatarwa kuma a cikinmu kowa zai samu darasi wanda zai bayani akai.
Page 94
Kuma a yanzu haka da nake wannan maganar munada new members masu yawa amma sai wani sati zasu shigo su gabatar da kansu, sabida haka ina muna fatan alheri gabaki ɗaya daga nan kuma sai friday mu haɗu a nan." Anan Uzaim ya nufi ƙofar fita haka suma su Anisa sai suka fito, kowanensu ya hau motarsa ya tafiyarsa. Haka wannan Ƙungiya ta Uzaim taci gaba da samun ɗaukaka har takai cewa a duk sati akan  nunasu ga gidajen rediyo da talabijin akan waɗannan darussa da suke gabatarwa.
                      The End
Thanks to our writers:
Abdul King Artice
Halima Bala Wakili    
 Queen Nasmah

Yi searching domin kallon film din A Wani Lokaci a YouTube channel dinmu mai suna " King Article Studio " 
 
Sponsored by King and Queen Writing Chamber

























Post a Comment

0 Comments