SARAUNIYAR RUWA
Love and adventure
story
*******written by
abdul king article*******
------- A honour to
Firdausi queen article--------
Together with prince and princess of article
.....naxeer $ meenat....
Dedicated to: bigboy isah The author of----
-----MIJIN AJANNA-----
:::::::::The king of arewabookstories:::::::
##### mujittapha muhd####
"""""""" FARKON LABARIN""""""""
Anyi wata yarinya mai suna humairat, kyakkyawa abar
kwatance, son kowa kin wanda ya rasa, saboda wannan baiwar
da ALLAH yayi mata, sai samari sukayi ca akanta, duk da
yawan wadannan samarin nata, bata kulasu ko kadan, domin
ita a ganinta ba wanda ya kwanta mata a cikinsu, sai jan aji da
walakanci take musu a kowane lokaci, lokutta na wucewa,
shekaru na shudewa, amma duk da hakan bata damu da yin
aure ba, @@@@@ tambaya anan itace, kome takeso ta
mallaka kafin ta zabi miji????@@@ sannan kuma wane irin
saurayi takeson?????
H-MAIRAT 1
"CIYON SO"
Haka abbanta ya kirata da fada yana mai cewa "ashe ke
mutuniyar banza ce ban sani ba, yaron da kika cima mutunci a
jiya yarima ne dan dan sarkin garin nan, kuma ki sani cewa
sarki zai dauki mataki domin irin hakan bata taba faruwa ga
dansa ba."
Cikin rawar murya ta amsa da cewa, " haba abba, kayi hakuri
mana, ai wannan ya farune cikin rashin sani, kuma ni zaginsa
kawai nayi,"
anan ya gyada kai yana mai cewa, "iyee lalle yarinya
kin girma, wato zaginsa ma kikayi, to gayamin a cikin samarin
naki wa kika zaba?"
Daga nan humairat tayi shiru ba tare da sanin takamammiyar
amsar daya kamata ta bashi ba, cikin mintuna kadan sai
dabara ta fado mata, cikin sauri tace
" na samu sairayin da
nakeso a yanzu, sunansa BILAL"
Tana rufe baki kawai sai ga wani yaro ya shigo gidan, " salamu
alaikum, wai ana kiran humairat."
"Gaya masa ganinan tafe!" Injita.
" Ki sani cewa idan naji ance kin masa walakanci, to kashinki ya
bushe a gidannan."
" Haba abba ya kana irin wannan maganar, ai
hakan bazai faru ba." ba tare daya tsaya saurararta ba ya wuce
abinsa.
H-MAIRAT 2
To bayan humairat ta tagama shiryawa, kawai saita fita waje
domin ganin ko waye ke nemanta, a zaune yake kusa da wata
itaciya amma da ganin humairat ta nufo shi, sai ya mike tsaye,
humairat taji mamakin ganin wannan saurayin domin bata taba
ganinsa ba, kuma baya cikin samarin dake nemanta, to bayan
sun gaima gaisawa, sai ya fara magana kamar haka:
" Wato ki sani cewa so makaho ne, so shi kesa mutum ya rabu
da yan uwansa, so shi kesa mutum ya dawwama cikin
gurbattaciyar rayuwa, haka so shi kesa mutum yayi tafiyar ba
zata, saboda haka nazo wurinki domin in bayyana miki sirrin
dake raina."
Humairat taji mamakin wannan maganar, domin a cikin
samarinta ba a taba samun wanda yayi mata irin wadannan
dadadan kalamai ba, batasan lokacin data masa murmushin
farin ciki ba, tana tambayar sa daya gaya mata sunansa.
"Ni sunana BILAL" injishi.
Yana fadin haka gaban humairat ya fadi, anan ta tuno da karyar
data ma mahaifinta na cewa tanada saurayi mai suna bilal, to
kada dai ace wannan karyar ce ke shirin zama gaskiya.
Daga nan humairat ta fara ganin juwa, bata kara sanin inda
take ba. Farkawa kawai tayi ta ganta cikin daki kwance
mahaifiyarta na mata fita, sai kawarta a kusa da ita, daga nan
sai ta tambayesu " ina bilal?"
" Wane bilal kuma?" Inji mahaifiyarta.
" Kawarki ce meena ta ganki a sume kusa da icce ( bishiya) daga
nan ta dauko min ke ko motsi bakya yi, saboda haka ina
umartarki daki gayamin abunda ke faruwa domin baki taba
suma ba sai ayau." anan humairat ta done kanta kasa hawaye
na zuba a idanunta ba tare data kallesu ba.
H-MAIRAT 3
To bayan kwana uku da faruwar hakan, wata rana da la asar
sai ga mahaifin humairat ya dawo ya sameta tayi zaune
jugum, da alamar ta shiga duniyar tunani, bayan ya karaso
kusa gareta, sai ya fara yi mata magana da cewa:
" Wai me ke damunki, sai inga kina yawan tunani ba tare da
fuskantar muhimman abubuwan yau da kullum ba."
Cikin jin kunya ta amsa "ba kome abba."
" karya kikeyi, shi bilal din da kika yimin maganarsa fa?"
Cikin sauri humairat ta dago kai ta dubeshi tana mai cewa:
" Wallahi abba ban sanshi ba! Kuma yanzu haka banida
labarinsa."
Wannan magana ta humairat ta harzukasa, daga nan ya fara yi
mata fada, " ke bakida hankali bansan kome ke damunki ba!"
wannan fada da yakeyi ya tayar da mahaifiyar humairat wadda
keta sharar barcinta, nan take ta fito daga dakin.
Wai hala meke faruwa a gidan nan? ta tambaya.
Sai ya amsa da cewa "kina ganin wannan wawuyar yarinya, a
cikin wadannan kwanakin ta gayamin cewa tanada saurayin da
takeso waishi bilal, to ayau ne na tambayeta game dashi, wai
shine take cewa bata sanshi ba."
Daga nan sai mahaifiyarta ta fara magana " wato dama kina
sonshi, shi yasa daga farkawarki kika fara tambayarshi ko?"
" Daga farkawarta kuma? A yaushe ta tambayeshi?" abba ya
tambaya. Daga nan sai umma ta fara basa labarin abunda ya
samu humairat na daga suma har zuwa lokacin da meenat ta
kawota gida, wannan labari ya mutukar bashi mamaki, daga
nan sai ya kalli humairat yana mai cewa " wannan tunanin da
kikeyi na menene? Kuma saboda me kika cemin baki sanshi
ba, bayan daga farko kin fada da bakinki cewa shine
saurayinki?"
" Ka gafarceni abba, amma na gayama hakane saboda kada
ranka ya bace, amma a hakika ba da gaske bane, sai dai a
ranar kuma wannan abun dana gayama ya zama gaskiya,
domin fitar danayi domin ganin ko waye ke bidata sai na
ganshi, anan ya fada mun sunansa bilal, daga nan ban kara
sanin abunda ke faruwa dani ba sakamakon wata juwa dana
fara gani wadda kuma bansan sanadinta ba." wannan magana
taba uwayen humairat mamaki.
H-MAIRAT 4
Bayan mako daya, sai humairat tayi shiri domin zuwa ganin
kawarta meenat, to akan hanyarta ne ta gamu da ita, itama da
shirin zuwa gidansu, anan suka fara tadi, humairat ta kwashe
duk abunda ya faru tsakaninta da bilal ta fada mata.
Cikin mamaki meenat tace, "wato yanzu dai kicemin kina sonshi
ko?" Daga nan sai humairat ta amsa da cewa, "a gaskiya ban
sani ba, ni abunda keban mamaki shine a kullum tunaninsa
nake, mafarkinsa nake, kuma yanzu haka ganinsa nake a
idanuna, kuma tun ina yarinaya ban taba jin ina kaunar da
namiji ba, hasali ma kyamarsu nakeyi."
Cikin murmushi meenat fara magana, " kada ki damu kawata,
wato ki sani cewa dole akwai wani boyayyen al amari game da
wannan yaron, amma idan kika bishi a hankali to da sannu zaki
san ko da wacce yazo."
" E hakane, cewar humairat, amma abun mamaki shine yau sati
daya daga ranar da muka hadu, gashi har yau ban kara
ganinsa ba."
" Kada ki damu humairat, zai dawo wataran." inji meenat
Daganan sukayi sallama, kowace ta kama hanyar gidansu.
H-MAIRAT 5
A cikin wannan dare uwayen humairat suka farka da abun al
ajabi, humairat ce ke mafarki tana fadin wasu kalamai marar
ma ana:
"bai isa ya raba mu ba, ina sonka bilal, ya hasken idona, sanyin
zuciyata, kuma annurin rayuwata, bazan iya rayuwa idan bada
kaiba, ka juyo ka kalleni mana, bai isa ya raba muba."
Haka humairat ta cigaba da maimaita wadannan kalamai
uwayenta na tsaye suna kallonta, daga nan sai mahaifiyar
tace " kana ganin wannan mafarki na lafiya ne kuwa?" Cikin
natsuwa ya amsa da cewa " abun daban mamaki, domin tun
tana yar shekara biyar idan taga namiji to runtse idanu take
domin kada yayi mata magana, amma a yau itace CIYON SO
ya kama, harda buda baki ta ambaci kalmar so ga yaron da
yazo daga sama, wannan abu dame yayi kama." haka suka
cigaba da sake sake ba tare da sanin abunda ke gudana
tsakanin humairat da bilal ba.
H-MAIRAT 6
A zaune yake yana huci da alamar wani ya bata masa rai, to a
dai dai wannan lokaci ne mafaifinsa ya shigo dakin.
" Haba yarima, ya kana huci kamar wani ya bata maka rai, nine
fa sarkin wannan gari, kuma nasha alwashin hukunta duk
wanda ya saba ma, saboda haka yanzu ka gayamin meke
faruwane?"
A lokacinne yarima ya dago kai ya dubi abbansa yana mai
cewa " wato ka sani abba bazan iya rayuwa idan bada ita ba,
kuma a duk lokacin da na mata magana sai tayi banza dani,
hakan kuma na mutukar bata min rai."
Wannan magana taba sarki dariya," haba yarima, wannan wace
yarinya ce daka furta mata tayi banza dakai, bako shakka zata
dandana kudarta saboda wannan laifi data shuka."
"To menene abunyi abba? "Yarima ya tambaya.
Daga nan sai sarki ya fara magana, " inaso ka binciko min
hanyar da mahaifiyarta ke takawa."
"Wannan ba matsala bace, amma meye amfanin yin hakan?"
Yarima ya tambaya.
"Wato ka sani yarima, yin hakan shi zai bani damar shirya wani
sihiri da zai sa ka mallaki wadda kakeso, amma gayanin meye
sunanta?"
"Sunanta humairat."
H -MAIRAT 7
Humairat na tare da kawarta meenat suna zance,
"wai in
tambayeki meenat, a lokacin da kika ganni a bakin bishiya
sume, kina nufin baki ga kowa a tare dani ba?"
" A gaskiya banga kowa ba,"inji meenat, " amma daban mamaki
abun, domin a wannan lokacin ina cikin magana da bilal kawai
sai naji juwa, to daga nan na fadi ba tare da sanin abunda
nake ciki ba," inji humairat. Cikin mamaki meenat tace " to
amma ya akayi ya sanki kuma yasan gidanku alhali ke baki
taba ganinsa ba? Sannan kuma me yasa kika suma a lokacin
daya fada miki sunanshi? Kuma me yasa bai tsaya ya
taimakeki ba a lokacin da kika suma, kawai sai ya tafiyarsa?"
Anan dai sukayi shiru ba tare da sanin amsoshin wadannan
tambayoyi ba.
H-MAIRAT 8
" BABAWO, BABAWO, BABAWO, "yarima ne ke kiran wani
bafadensa, aguje sai ga babawo yazo, " kai ina fatan ka binciko
min aikin dana baka?"
" E na binciko ranka ya dade"
Anan yarima yayi dariya, wani kulli ya dauko cikin leda ya
mikawa bafade, kaje ka turbude wannan kullin a hanyar da take
takawa.
"To an gama ranka ya dade, inji bafade."
*********************
Humairat na zaune kawai sai taga mahaifiyarta ta shigo cikin
yanayin rashin lafiya, dakyar take takawa, to bayan ta zauna,
sai ta fara bayani kamar haka " banda lafiya, yau bazan iya kai
haja kasuwa ba, wai daga na kawo hanyar nan dake shigar
dani kasuwa kawai sai kaina ya fara ciwo."
" To ALLAH ya sauwaka," inji humairat, abu kamar wasa saiga
ciyo yayi tsanani.
H-MAIRAT 9
Meenat na cikin gidansu, kawai sai taji anyi sallama, to bayan
ta fita sai taga ashe yarima ne tare da bafadensa, ganinsu ya
tayar mata da hankali amma hakan ta daure ta gaishesu.
Anan yarima ya fara magana:wato ki sani meenat nazone
domin ki taimaka min da abu daya.
"TO ALLAH yasa zan iya!" injita
"Zaki ma iya, inaso ki samomin gashin kan humairat,nasan da
cewa kawarki ce", inji yarima.
" A gaskiya bazan iyaba, domin bansan abunda zakuyi dashi ba,"
inji meenat.
Anan take yarima ya dauko kudi masu yawa ya mika mata, to
kasan wasu matan akan kudi ba abunda ba zasu iyaba, cikin
rawar jiki tasa hannu da nufin karbar kudin, kawai sai taga
yarima ya mayar da kudin. Bazani baki wadannan kudi ba har
sai in kin samomin gashinta, daga karshe dai meenat tayi musu
alkawarin taimaka musu.
H-MAIRAT 10
" Ki tashi ki tafi hanyar da mahaifiyarki kebi a kasuwa, ki turbude
sihirin da aka yimata, " humairat ce taga bilal a mafarki yana
mata wannan magana, firgigit ta tashi, cikin sauri ta fara shirin
zuwa hanyar domin ganin in mafarkinta gaskiya ne
A lokacin data isa wurin, kawai sai taga meena taba yarima
wani abu a leda, anan tayi mamakin ko menene? Daga nan ta
fara fada:
" Ashe ke meenat haka kike, dake za a hada kai a cuceni, anan
Meenat da yarima sukayi tsuru tsuru domin sun san asirinsu ya
tonu, cikin sauri yarima ya duka a inda aka turbude maganin, a
cikin zuciya ya fara fadin wasu kalmomin sihiri irin nasu, daga
nan sai yasa hannunsa na hagu ya bugi kasa sau uku, to yana
gama bugawa, sai humairat taji bata iya magana.
Daga nan sai yarima da meena suka kyalkyace da dariya," haka
zaki tabbata har abada bazaki iya magana ba, yadda ko wani
yace yana sonki bazaki iya yi masa bakar magana ba, kuma ni
kadai ne zan iya kare wannan sihiri, amma bazan kareshi ba
sai a ranar da kika aminta zaki aureni." inji yarima.
Humairat naji amma ba damar magana, harararsa tayi daga
nan ta kama hanyar gida cikin bakin ciki.
To bayan ta isa gida, daga nan sai mahaifinta yayi ta
tambayarta domin ta gaya masa meke faruwa, amma ba bakin
magana, daga karshe dai mahaifinta ya gano cewa bazata iya
magana ba saboda wasu alamomi da ta nuna masa, haka
bakin ciki ya dabai bayeshi, ga matarsa ba lafiya, haka kuma
diyarsa ma ba lafiya.
H-MAIRAT 11
Da sakaliyar la asar sai abban humairat yaji ana sallama, take
ya fita domin ganin ko waye, anan yayi arba da wani saurayi.
" Hala wa kake nema?" Ya tambayeshi.
" Sunana bilal, ina neman humairat."
Daga nan abban humairat ya fara fada, inda yake shiga ba nan
yake fita ba, " wato kaine kayi mata magani domin ta dinga
sonka ko,kuma da kaga baka samu nasara ba shine ka koma
ka yi mata magani ta daina magana."
To anan bilal ya fara bashi hakuri, " haba abba, ya za ayi nayiwa
yarinyar da nakeso magani, ni banida masaniyar wannan al
amari."
"Ka fita ka bani wuri, idan na kara ganinka a kofar gidana to sai
na yima dubun rashin mutunci," inji abban humairat.
Haka bilal yayi tafiyarsa cikin rashin jin dadi.
*******************
Ba afi minti uku da faruwar hakan ba saiga meenat ta shigo
gidan, anan ta fara yiwa abban humairat dakin baki sai kace
mutuniyar kirki.
Humairat tayi kokarin bayyana masa cewa itace sillar wannan
abun amma ina, saboda rashin baki dole ta hakura, haka
Meenat ta gama maganganunta ta tashi ta fita.
Humairat tayi dana sanin kin bin umarnin uwayenta a lokacin
da suke turata makaranta tana kin zuwa, domin da ace yanzu
ta iya rubutu, da sai ta rubuta duk abunda ya faru.
H-MAIRAT 12
Bayan wasu shekaru, wata rana kawai saiga meenat ta fado
gidansu tana rusa ihu, anan mahaifiyarta ta tareta tare da
tambayarta meke faruwa, anan meenat ta bayyana mata cewa
wai an koreta daga makarantarsu, maimakon mahaifiyarta ta
tausaya mata, kawai saita hauta da fada:
" Oho, ai ba korarki akayi ba ko kasheki akayi ke kika ja, kin
manta abun kunyan da aka sha kamaki kina aikatawa, kuma an
sha kawomin kararki daki daina amma kinki, CIYON SO ya
kamaki, kowane namiji kika gani shawarsa kikeyi, abu har yakai
ga malaminku, yanzu gayamin yara nawa kika lalata a unguwar
nan.
Anan dai meenat tayi shiru domin tasan duk abunda ummarta
ta fadi gaskiya ne.
To dama abbanta na zaune yanaji, daga nan sai ya kado
bakinsa," ai bari ta kananan yara hatta da ni da nake mahaifinta
shawata takeyi, domin wani kallo take min wanda bansan ma
anarsa ba, sannan a cikin wadannan kwanakin na lura da cewa
masifu na yawan farmata, bako shakka akwai laifin da kika
yiwa ALLAH, saboda haka kije ki gyara da ubangijinki.
Wannan magana ta tayar da hankalin meenat domin itama ta
lura da cewa masifu na zo mata ta kowane bangare, kuma duk
abunda tasa gaba to bata samun nasara, haka ta shiga daki
sukuku, anan ta shiga duniyar tunanin kowane laifi tayi.
H- MAIRAT 13
A cikin wannan dare ne meenat tayi yunkurin kaima yarima
ziyara domin bayyana masa wani muhimmin abu daya dade
yana damunta, to bayan ta isa masarautar, take ta fada ma
bafadensa daya kirawoshi da gaggawa, anan yarima ya bada
umarni data shigo ciki, to bayan ta shiga ne, take ta fara
magana:
" Wato ka sani yarima, cikin wadannan kwanakin a gaskiya bana
cikin jin dadi, domin masifu ke samuwata ta kowane fanni,
kuma inaga yanada nasaba da sharrin da muka yiwa humairat,
saboda haka zanso mu kare wannan maganin."
Daga nan sai yarima ya fara magana " na dade inason in
tuntubeki da wannan maganar, domin ni wani CIYON SO ne
ya kamani, duk matar dana gani to dole sai na biya bukatata
da ita, idan kuma ba haka ba to zan zauna cikin rashin jin dadi.
Ai nima haka, duk namijin dana gani to dole sai na biya
bukatata dashi," inji aminat.
"To meye abunyi yanzu?" meenat ta tambaya.
Daga nan sai yarima ya dauko wata takadda mai dauke da
wani ributu ya bata, kije ki karanta wannan takarda a wurin da
muka turbude maganin, sai dai idan kina tafiya kada ki juya
baya, kuma kada kiji tsoro, kuma ki tabbatar da cewa wurin da
muka turbude maganin anan zakiyi adduar, idan kin gama ki
jira zanzo sai mu turbude maganin tare, anan meenat ta amshi
takardar, fitilar kwai ta dauka( kerosene lamp) tare da ashana,
bayan ta kunna saita fita gidan sarautar domin ta cika aikin
yarima.
H-MAIRAT 14
To a wannan lokaci hadari ya taso, ana walkiya da tsawa mai
tsoratarwa, saboda haka kafa ta dauke baka ganin kowa, haka
Meenat ta cigaba da tafiya daga ita sai fitilar kwai cikin wannan
dare.
Tafiya takeyi gabanta na faduwa saboda tsoro, tana cikin
wannan tafiya sai demuwa ta kamata.
------DEMUWA: wani abu ne dake tasoma mutum sai ya rasa
hanyar da yake)
To bayan demuwa ta kama meenat, cikin rashin sani saita shiga
makabarta, haka ta cigaba da tafiya har tayi nisa bata sani ba,
to daga nan sai ta ga wani kabari, wannan kabari kuma sai yayi
mata kamada wurin da suka turbude maganin, take ta fara
karatun wannan takardar, farawarta keda wuya sai fitilarta ta
mutu, ashana ta dauko ta kunna itama ashanar ta fadi, daga
nan sai taji kamar an riketa mata kafafu, daga nesa taji muryar
wani kamar yarima, juyowa tayi domin taga ko waye, daga nan
sai ta fadi, bata kara sanin inda takeba.
H-MAIRAT 15
"LAMBUN TSAFI"
A hankali take bude idanunta domin ganin ko ina take, firgigit
ta farka, anan ta ganta cikin wani katon lambu, shi wannan
lambu zagaye yake da wata gina doguwa, ita wannan gina ba a
ganin iyakar tsawonta, kuma abun mamaki shine ba kofar fita
a cikin wannan lambu, shin wai wa ya kawota wannan wuri?
Meenat ce ke mamaki, anan ta fara zagayen lambun a
hankali tana kallon yadda tsuntsaye ke shawagi, tana cikin
wannan yawo kawai sai ta zo wani wuri inda taga maza da
mata suna wani aiki na tsintar yayan itatuwa, suna ganinta sai
suka daina, anan suka tsura mata ido suna kallonta, haka
itama sai ta fara kallonsu, to ana cikin wannan kallon kallo sai
kawai taga wasu katta cikin shigar yaki sun zo sun kamata,
anan ta fara ihu tana tambayarsu me ta musu, cikin sauri su
kuma wadannan mutanen suka cigaba da aikinsu, to bayan an
kama meenat, ba a tsaya da ita koina ba sai wata fada, anan
aka gurfanar da ita ga wani shirgegen mutum, wanda da gani
shine shugaban lambun, tasowa yayi daga saman kujerarsa,
gashinta ya fara shafawa a hankali tare da sunsuna shi, cikin
zafin nama meenat ta kubce, kafin kaceme ta kabra masa mari,
maimakon ya rama kawai sai yayi dariya, daga nan ya bada
umarni aje a daureta.
H-MAIRAT 16
To bayan an daureta, sai tagane cewa ashe hadda yarima
shima an daureshi, kuma kusa da ita yake, to anan ya fara yi
mata magana, " gaskiya kin tafka babban kuskure, na gaya miki
kada ki karanta wannan takardar har sai in kin kai wurin da
muka turbude maganin, amma bakiji ba, sai gashi kin shiga
cikin makabarta wai kina karantawa," anan aminat ta fara
magana: " ina ganin demuwa ce ta kamani, domin ban ma san
da cewa na shiga makabarta ba sai yanzu daka fada min,"
" to
amma menene ya kawomu wannan wuri?"
"Bako shakka aljannu ne, domin a lokacin danaji muryarki a
cikin makabartar, sai nayi kokarin in shigo in tsayar dake,
amma kafin na karasa kawai sai na fadi daga nan ban san inda
nakeba, farkawa kawai nayi na ganni a cikin wannan lambun."
"To yanzu ya za ayi mu fita?" meenat ta tambaya.
Wata mata dake kusa dasu tana jinsu sai ta kado bakinta cikin
maganarsu," ai ku sani cewa ba hanyar fita a wannan
lambu,duk wanda ya shigo to ya shigo har abada."
H-MAIRAT 17
" Ku sani cewa shi wannan mai lambun matsafi ne na gaskiya,
kuma shi da kansa ke tafiya farautar mutane yana kawosu a
ciki, kuma a duk lokacin da aka kawo sabon bako to sai an
shekara ana masa buloli, a kowace rana akan yimasa bulala
hamsin, saboda haka kuma yanzu sai an muku wadannan
bulolin," anan hankalin yarima ya tashi, shida yake sai dai yasa
a bugi mutum amma yau ace shi za a bugu, ai wannan bazai
yiwuba.
Suna cikin wannan tadin ne aka zo aka kwace yarima da Meenat, wasu katta ne rige da buloli, anan suka fara jansu sai
da suka kaisu wani fili, daga nan suka fara shirgarsu kamar
bazasu barsu ba, har saida suka yimusu bulala hamsin hamsin,
ana gamawa yarima da meenat suka fadi sumammu, ba wanda
ya kulasu, wannan matar kawaice tazo ta tadasu, daganan
tajasu zuwa makwancinsu.
H-MAIRAT 18
Washe gari da sassafe, ihu da kuwa su yarima sukaji, anan
suka farka firgigit, daga nan suka gane cewa dakarun wannan
mutumin ne ke tada mutane da buloli, duk wanda bai farka ba
to kashinsa ya bushe, cikin sauri suka shirya suka nufi wani
wuri inda ake bin layi ana amsar abinci, wannan layi ya
mutukar fatawa yarima rai, a lokacin daya tuno sai dai akawo
masa abinci a lokacin da yana garinsu.
To bayan kowa ya amshi abinci, anan suka zauna suna ci, suna
cikin cin wannan abinci aka jawosu, wato yarima da meenat,
cikin wani fili aka kaisu daga nan aka sauke musu bulala
hamsin, anan suka kara faduwa sumammu.
To bayan sun farka ne sai suka gansu kusa da kawarsu, wato
wannan matar data taimakesu daga farko, anan suka tambayi
sunanta, daga nan ta amsa da" sunana ZULAIHAT
Sato ni yayi daga gidanmu, domin abbana ya kasance attajiri,
wata rana da marece ina tare da kawayena kawai sai muka ga
wani katon maiki dauke da wani mutum, daga nan ban kara
sanin inda nakeba, farkawa kawai nayi na ganni a nan wurin."
" To wai me yakeyi da mutanen daya sato? "Meenat ta tambaya.
"Ai cin naman mutane yakeyi, zulaihat ta amsa mata, a duk
bayan wata daya sai an yanka masa mutum, za a dafa masa
ayi masa romo, daga nan ya samu abun kalaci, kuma duk
wanda layi ya cimmasa, to a ranar karyarsa ta kare, a nan
yarima da meenat suka kalli juna suna tunanin irin zaluncin da
suka yiwa HUMAIRAT ga irin abunda ya jawo musu.
H-MAIRAT 19
Haka aka dinga yiwa yarima da meenat bulala hamsin a
kowace rana, tun suna kidanyar kwanakin da sukayi a lambun
har suka manta.
To wata rana da daddare, kawai saiga mutumin nan yazo da
dakarunsa, anan suka tara duk matan gidan suna kallo daya
bayan daya domin su zabi daya wadda zata kwana da
Gulmanu wato shi matsafin mutumin.
Anan gulmanu yazo kan meenat, kallon tsaf yayi mata, daga
nan yasa aka kamota da karfin tsiya, yarima da zulaihat na
kallo amma ba damar taimakawa, haka aka wuce da ita suna
kallo.
Anan suka zarce da meenat zuwa wata kasaitacciyar fada, daga nan
akasa wasu mata suka yi mata wanka tare da gyarata, sannan
aka sa mata wasu tufafi masu kyau, daga nan aka turota
turakarshi, yana ganinta sai ya tashi, meenat na ganinsa saita
matse jikinta da bango tana makarkata domin batason ya taba
ta, dariya gulmanu yayi sannan ya jawo hannunta, gashinta ya
fara tabawa a hankali, daga nan sai tayi tsaye ta kasa motsi
sai kace wadda ta mutu, daga nan sai ya daukota ya aza
saman kafadarsa ya fara tafiya domin shiga da ita wani daki,
yana cikin tafiya ne sai ga wasu dakaru sun shigo dakin a guje,
wani yare suka yi masa, daga nan bai tsaya wata wata ba sai
yayi jifa da meenat can gefe, daga nan yayi shigar yaki, anan
suka fita a guje, fitarsu keda wuya, saiga yarima da zulaihat
sun shigo, anan suka tallabeta suka fita da ita.
H-MAIRAT 20
A cikin wannan dare yarima na cikin fushi, saboda haka sai ya
mike tsaye domin ya gabatar da wata magana ga mutanen
dake wurin, ai ko suna ganinsa sai kowa yayi tsit, daga nan sai
yarima ya fara da cewa " yaku wadanan jama a, ku sani cewa
idan zamu shekara anan, to wannan azzalumin mutum zai
cigaba da kashe mu daya bayan daya har sai yaga bayanmu, to
yanzu ku kun yarda mu zauna a haka, ku tuna cewa kunada
iyali, kuma sunacan suna jiranku, saboda haka dolene a
garemu mu tashi mu bidarma kanmu yanci."
Daga nan mutane suka fara magana: lalle wannan hakane,
kowa na fadin albarkacin bakinsa, to a wannan lokaci kowa
yaji dadin maganar, saboda haka sai kowa yasa baki, yarima
ne ya kawo wata dabara wadda a ganinsa idan suka bita, to
zasu cimma nasara.
H-MAIRAT 21
Wata rana bayan an kamo su yarima da nufin za ayimusu
bulala kamar yadda aka saba, a wannan lokaci da daddare ne,
cikin zafin nama yarima ya kubce, anan ya amshe takobin wani
daga cikin dakarun, daga nan ya aika shi lahira, to sauran jama
a suna ganin abinda ke faruwa, daganan sai suma suka farma
wadannan dakarun da bugu, kafin kaceme wuri ya tarwatse,
ana cikin wannan dauki ba dadi ne saiga gulmanu ya iso tare
da wasu dakaru masu yawa, anan ya zaro wani sihirtaccen
takobi, saida ya saita da wuyan yarima sannan ya jefo masa
shi, ashe yarima na kalle dashi, cikin sauri ya kauce, anan
takobin yasha bangon lambun, take bangon ya fara girgiza yana
watsewa sanadiyar wannan sihirtaccen takobin, mutane na
ganin haka sai suka fara bi ta wannan bangon daya tsage suna
tserewa, anan gulmanu ya rasa abunda ke masa dadi, runtse
ido yayi yana ambatar wasu kalamai na tsafi, kawai sai ga
wasu tsuntsunye sun bayyana a gaban su, dashi da dakarunsa
suka hau wadannan tsuntsaye suka bi bayan su yarima.
H-MAIRAT 22
To bayan su yarima sun fito a cikin lambun, sai suka gane
cewa ashe a cikin kungurmin daji suke, daga nan suka fara
gudu ba sassauci, suna cikin wannan gudune sai sukaji
tahowar dakarun gulmanu, anan suka hau saman itace sukayi
zaman su, koda wadannan dakaru sukazo wurin sai sukaga ba
kowa, ashe su yarima sun tanadi itace masu tsini, daga nan
sai suka fara jifarsu da itacen, duk wanda aka jefo ma iccen
sai dai ya fadi matacce, ana cikin wannan artabu ne saiga
gulmanu ya hango yarima, anan ya nufo yarima da nufin
rabashi gida biyu, kafin ya iso kawai sai yaji saukar wani icce a
cikinsa, har saida iccen ya shige ciki, ashe meenat ce ta
jefoshi, daga nan gulmanu ya fadi, wata kara yayi kafin daga
bisani yace ga garinku.
To daga nan ne hankalin kowa ya kwanta, ahaka suka cigaba
da tafiya har suka kawo wani katon teku, wani katon jirgin ruwa
ne suka iske a gabar tekun, daga nan suka hau, kowa na fadin
inda yakeso a ajeshi, daga nan sukayi ban kwana da juna,
domin sun san bazasu kara haduwa ba.
H-MAIRAT 23
"MACIJIN RAMZA"
To an fara tafiya kenan, kawai sai wani allo ya fado ma yarima,
anan ya dauki allon yaga an masa zanen wani katon maciji,
daga nan sai yarima ya tuno da wani labari da mahaifiyarsa
sarauniya ta taba fada masa a lokacin da yake karami:
Akwai wani sarki da ake kira RAMZA, shi ramza yana bauta
ma wani katon maciji, kuma wannan maciji mutum ne
matsayin abincinsa, saboda haka duk shekara wannan sarki
kanzo da katon jirgin ruwa ya faka shi a gabar teku, duk fasijan
da bai sani ba idan ya shiga wannan jirgi to bako shakka ya
zama abincin macijin.
Anan gaban yarima ya fadi domin irin wannan hoto daya gani
na maciji irin wanda mahaifiyarsa ta nuna masa ne, to anan ya
tashi domin ya bada umarni a tsayar da jirgi, sai dai kash, a
wannan lokaci jirgi yayi nisa, kuma a mamakinsa sai yaga
baiga kowa ba cikin jama arsa, anan ya fara dube dube, wata
karamar hayaniya ya jiya a kasan jirgin, daga nan sai ya tattaka
ya fara zuwa kasan jirgin, shigarsa keda wuya sai yaga an
daure duk mutanensa, anan yayi niyar fitowa domin gudu sai
dai kash wasu zaratan mazaje yaga sun fito da kwari da baka,
anan suka fada masa cewa yana gudu zasu halbeshi, anan aka
kama yarima aka daure da wata kaca.
H-MAIRAT 24
Haka suka cigaba da tafiya ba kakkautawa, sai da suka shafe
kwanaki arba in suna tafiya sannan suka iso wani katon birni
da aka gina da duwatsu, su wadannan duwatsu an musu
zanen macizzai kala kala, to anan aka bude kofar shiga garin,
anan aka jawo yarima tare da tawagarsa, meena da zulaihat na
kusa dashi, anan suka jero sahu suna tafiya, su kuma mutanen
garin sai kallonsu kawai sukeyi suna musu sowa tare da jefa
musu furanni.
A haka suka cigaba da tafiya ana biye dasu har sai da suka
kawo wata katanyar rijiya dake a tsakiyar garin, to anan
mutanen garin kowa yayi tsit sai kace wadanda aka yiwa
mutuwa, daga nan sai wasu barade daga cikin dakarun garin
sukazo wurin rijiyar, cikin zafin nama suka bude rijiyar, sautin
budewar marfin rijiyar sai da ya ciga garin baki daya, daga nan
sai kowa yaja da baya, a wannan lokaci sarkin garin na can
saman bene yana hangen duk abunda ke faruwa tare dashi da
dakarunsa masu tsaron lafiyarsa.
Su yarima basu san abunda ke faruwa ba, iyaka dai sunga
mutanen garin naja da baya a tsorace, da alama akwai wani
abu a cikin rijiyar, wani karaji ya fara fitowa daga cikin rijiyar,
daga nan sai ruwan rijiyar suka fara fantsamowa waje, wannan
al amari ya dan girgiza yarima.
H-MAIRAT 25
Cikin rashin tsammani saiga wani kataragen maciji ya fito cikin
rijiyar, wannan maciji dai idan aka gama kabrinsa da tsawonsa
bako shakka zai kai itacen dabino, wannan maciji kai uku
gareshi, kuma yakanyi amfani dasu yadda yaso, nan da nan sai
duk mutanen garin sukayi sujjuda ga wannan maciji, daganan
sai macijin ya ratso ta cikin mutanen garin yana tafiya, a haka
har yazo kusa ga tawagar yarima, anan macijin yayi tsalle ya
dauke meenat, daga nan meenat ta fara ihu tana neman
taimako, mutanen garin najin ihunta, sai suka tashi daga
sujjada suka fara murna suna kade kade da bushe bushe, wai
sabuwar shekararsu ta zagayo.
Yarima na ganin haka bai san lokacin da yayi wani ihu ba, cikin
zafin nama ya amshe takobin wani daga cikin dakarun, daga
nan ya katse kacar da aka dauresu da ita, to a wannan lokaci
macijin ya kusa kai meenat a bakinsa, cikin sauri yarima ya fara
taka jikin macijin da matsanancin gudu yana kokarin kaiwa
inda bakinsa yake, kingin kiris ya dura meenat cikin
wangamemen bakinsa, kawai sai yarima yayi wani tsalle ya
saita dakan macijin, ji kake kimis.
Wata kara macijin yayi kafin ya saki meenat, daga nan sai jini
ya fantsama, kafin kaceme macijin ya koma cikin rijiyar a guje
yana wata irin kara, da ji kasan an yi masa rauni, kafin meenat
ta fado kasa sai yarima yayi alkafirra sama ya cabeta, daganan
ya sauko da ita kasa a hankali, daganan mutanen gari suka
bishi da kallo suna mamakinsa, domin a tarihi ba a taba
samun jarumin da yayi irin wannan abu ba, ka hatta da sarki
ramza abun ya bashi mamaki, anan ya kura masa ido ko
kyaftawa bayayi.
H-MAIRAT 26
Daga nan sai wasu dakaru suka zagayeshi da nufin kamashi, to
anan aka fara kallon kallo, can sai suka rikice, haka yarima yayi
ta zubar dasu, amma saboda yawa ko karewa basuyi, anan
wani ya mamayeshi ya lallabo ta bayanshi, wani irin karfe ya
kwada masa a kai, daga nan sai yarima ya fadi sumamme,
anan aka kama shi tare da jama arsa aka wuce dasu kurkuku.
****************
Yarima ne ke gudu wasu zaratan zakuna na biye dashi, gudu
yake iyakar gudu, yana cikin wannan gudu sai ya cimma wata
masarauta, anan ya shiga yana bidar taimako, mace ce
sarauniyar garin, tana ganinsa sai tasa aka kamashi, anan aka
daure, wadannan zakuna suna zuwa suka fara cin naman
jikinsa, ita kuma sarauniyar sai dariya takeyi, anan yarima ya
duba domin ganin fuskar wannan sarauniya, ba kowa ce
wannan sarauniyar ba in banda HUMAIRAT.
Firgigit yarima ya tashi, ashe mafarkine yakeyi, wannan mafarki
ya bashi mamaki da kuma tsoro, anan yarima ya done kansa
kasa yana tunanin irin zaluncin da suka yiwa humairat, baisan
lokacin da hawaye suka zubo masa ba, anan ya fara dana sani.
To duk wannan abun da yakeyi zulaihat na kallonshi, anan ta
matso kusa gareshi tana lallashinsa, ita kuwa meenat ta riga
tasan abunda yakema wannan kuka.
H-MAIRAT 27
Haka yarima da jama arsa suka cigaba da zama wannan
kurkuku, wata rana anzo kawo masa abinci, sai yaga mace ce
maimakon namiji, anan ta bayyana masa cewa sunanta halirat,
kuma tazone da albishirin taimaka musu, domin tanason taga
bayan sarki ramza dashi da macijinsa, domin sun mata
sanadiyar rabuwa da iyayenta.
" Kada ki damu yake wannan mata, na miki alkawarin cewa a
duk ranar dana fito zan hallaka sarki ramza tare da macijinsa,
kuma zan nadaki sarauniyar wannan gari." Inji yarima.
Daganan sai wannan mata ta dauko wani makulli ta bashi,
daganan sai ta tashi ta fita.
Fitarta keda wuya sai yarima ya bude kofar kurkukun da
makullin, daganan sai ya tada sauran jama arsa, anan suka
lallabo suka kashe dakarun dake tsaronsu, daga nan suka
dauki makamansu, daganan suka fito a guje, to fitowarsu keda
wuya sai wasu dakaru da suka ga fitowarsu suka buga kugen
yaki, kafin kaceme dakarun garin sun fara fitowa cikin mugun
shiga ta yaki.
H-MAIRAT 28
To a wannan lokaci hadda sarki ramza yayi shigar yaki, domin
a fusace yake, ba abunda yakeson gani sai ganin gawarsu,
fitowar su yarima keda wuya sai dakaru suka taresu, anan aka
fara dauki ba dadi, daganan kuma sai aka bude wannan rijiyar,
kafin kaceme macijin ya fito, wadanda suka budeshi su yafara
kashewa, daganan sai ya shiga kashe mutane, ganin haka yasa
sarki ramza yin dariya, cikin sauri ya hau dokinsa ya nufo
yarima, haka shima yarima ya tareshi, daganan suka rincabe da
yaki mai tsanani, meenat da zulaihat sai faman kashe dakarun
sarkin sukeyi.
To ana cikin wannan yakine macijin ya nufo su yarima, sai dai
a wannan lokaci sarkin bai ganshi ba, wani tsalle yarima yayi
ya bugi sarki ramza, kamar an daga sarkin sama sai a kusa ga
macijin, anan macijin yayi ma sarki wawan riko, anan ya fara
ihu yana neman taimako, macijin bai sake shiba sai da ya
tabbatar da cewa kowane kashi nashi ya kare, daga nan saiya
hadiyeshi, shi kenan, karshen sarki ramza ya zo, to a wannan
lokaci mafi yawancin dakarun sun mutu, wasu kuma sun tsere,
daganan sai wannan maciji ya tasoma yarima, to kafin macijin
ya cimma yarima, kawai saiya ga yana kara, ashe su meenat ne
a can bayan sa suna yanka sa gunduwa gunduwa, kafin
kaceme macijin ya fadi matacce.
H-MAIRAT 29
Halirat ce ta sheko a guje ta rungume yarima tana masa
godiya, daga nan yaja hannunta har zuwa karagar mulki, shi da
kansa ya zaunar da ita, daga nan saiga wani saurayinta yazo
waishi amar, daga nan sai yarima ya tara mutanen garin ya
sanar dasu cewa amar shine sabon sarkin wannan gari, ita
kuma halirat itace sarauniyarsa, wannan magana ta musu dadi
domin sun gaji da zaluncin sarki ramza, anan suka fara shagali
sunama yarima da mutanesa godiya, daga nan sai akaba su
yarima dawakai da guzuri mai yawa.
Bayan safiya ta waye sai yarima da mutanensa suka hau
dawakansu suka fita garin, anan suka kama hanya sai cin gudu
sukeyi
H-MAIRAT 30
SARAUNIYAR RUWA
A lokacin da yarima da tawagarsa suka bar wannan gari, sai ya
zamana cewa ba abunda sukeyi in banda tsala wani
matsanancin gudu a cikin daji, haka suka cigaba da wannan
gudu har rana ta fadi, to a wannan lokaci sun fara gajiya,
saboda haka sai suka yi shawarar tsayawa sai gobe da safe,
suna cikin wannan hutu ne sai suka fara jin gurnani, cikin rashin
tsammani sai sukaga wasu manyan zakuna sunyi fitar burgu
sun nufoso, kafin kaceme kowa ya tattara kayansa, anan suka
watse kowa yayi ta kansa, to bayan sunyi nisa da wurin ne sai
zakunan suka bar binsu, to anan suka hango wani wuri mai
damshi, daga nan suka yanke shawarar tsayawa a wurin domin
su huta.
Wurin da suke kusa da wani katon teku ne, to suna cikin
wannan hutu ne sai suka hango wani makeken gari a tsakiyar
tekun, wannan abu ya basu mamaki, ko ya akayi aka gina gari
a tsakiyar ruwa, to akwai wata gada a gabar tekun, wadda
itace zata kaisu cikin garin,
H-MAIRAT 31
Cikin son muradin ganin garin suka mike gaba daya domin
shiga a cikin wannan gari, to bayan sunyi nisa akan gadar, sai
suka fara ganin kassan mutane birjik, wannan abu ya basu
mamaki, amma haka suka daure suka cigaba da tafiya, to
bayan sun iso kofar garin ne, anan suka ga kofar ta bude da
kanta, cikin rashin tsoro suka fada ciki, shigarsu keda wuya
kofar ta kulle kanta, wannan kullewa da kofar tayi yadan
girgiza su, amma haka suka daure suka cigaba da dube duben
garin.
Abunda ya kara basu mamakine shine ba kowa a cikin birnin,
kamar anyi shara, to suna cikin dube dube ne sai suka hango
wani doki fari sol yana ta shawagi shi kadai, shi wannan doki
yasha banban da sauran dawakai domin yanada fuka fuki, da
kuma kahoni biyu a kansa, yarima na kallon wannan doki sai
gabansa ya fadi, anan ya tuno da wani labari da mahaifiyarsa
ta taba bashi a lokacin da yana karami:
H-MAIRAT 32
Akwai wani gari a tsakiyar wani teku, shi wannan gari ba a
ganinsa da rana sai da dare, idan mutum yazo tekun ga rana to
bazai ga garin ba, amma idan dare yayi, to garin zai fito yadda
kowa zai ganshi, masana sun bayyana cewa idan rana tayi to
gain zai shige cikin ruwan tekun yadda bamai ganinsa, amma
dare nayi saiya fito, shi wannan gari wata sarauniya ce ke
mulkinsa, ita wannan sarauniya dai ba mutum bace tare da
jama arta gaba daya, domin daga kansu zuwa cubiyarsu duk
na mutane ne, amma daga cibiyar zuwa abunda yayi kasa to
duk kifi ne, kuma duk wanda rashin sani yakai shi wannan gari
to kashinsa ya bushe, domin saidai wani ba bashi ba, kuma
takan hau wani doki mai fuka fuki a yayin tafiya mai nisa, shi
wannan doki yanada kahoni biyu a tsakiyar kansa, wannan
sarauniya ita ake cema SARAUNIYAR RUWA kuma itama
sunanta HUMAIRAT
H-MAIRAT 33
Yarima na gama wannan tunani gabansa ya kara faduwa,
domin yasan bako shakka a cikin garin ne suke, anan yabada
umarni suyi sauri subar garin, sai dai kash, juyowarsu keda
wuya da nufin gudu sai sukayi arba da dakarun sarauniyar sun
zagayesu, kowane rike da kwari da baka, anan aka kama
yarima tare da jama arsa sai fada wurin sarauniya, abunda ke
basu mamaki shine duk da kasancewarsu rabi mutum rabi kifi
amma suna gudanar da ayyukansu ba kasala.
To bayan an kaisu wurin sarauniya, tana ganinsu saita sauko
saman kujerarta, duk da kasancewarta kifanya amma gata
kyakkyawa abun kallo.
H-MAIRAT 34
Anan ta fara tabin fuskar yarima a hankali tana masa wani
kallo marar ma ana, daga nan ta bada umarni akai sauran
gidan yari amma shi yarima a bar mata shi, haka ko akayi, to
bayan sarauniya ta kadaita da yarima, anan ta fara magana:
" Inaso ka zauna tare dani, zan baka duk abunda kakeso na
daga tarin dukiya tare da jin dadi marar karewa."
Sarauniya na gama wannan magana sai yarima ya shiga wani
tunani mai zurfi, fuskar humairat ce ta bayyana a gareshi cikin
wata shiga ta kasaita, tana tafiya tana masa rangwada,
kyakkyawar surar jikinta ta kara girgiza shi, cikin wannan tunani
baisan lokacin daya ce ya aminta ba, sarauniya najin haka
anan ta sheko da gudu ta rungumeshi, rungumeshi keda wuya
saiya farka daga tunanin da yake, anan ya gane cewa
sarauniya ce ke masa rangwada ba humairat ba, cikin wata
murya ya amsa da "BAN AMINTA BA"
H-MAIRAT 35
Yana fadin haka sarauniya ta taga shi sama da hannu guda
cikin fushi, anan idanunta suka juya zuwa ja tamkar wuta, daga
nan sai wasu zaratan zakuna suka fito suna yakar baki, su
wadannan zakuna sunada kahoni biyu a kansu, anan suka fara
gurnani suna jiran sarauniya ta saki yarima domin su samu
abun kalaci, daga nan saita kalleshi tana mai cewa "me kake
cewa?"
Cikin tsoro yarima ya amsa da" NA AMINTA"
Daga nan saita sakeshi tana murmushi, su kuma zakunan sai
suka bace bat, daganan yarima ya mata kallon tsaf, anan ya
gane cewa kamarsu daya da humairat kamar an tsaga kara,
wannan abu ya tuno masa da mafarkinsa, kuma duk abunda
aka nuna masa ya faru, kenan wannan itace sarauniyar da aka
nuna masa mai kamada humairat, kuma da ace bai aminta da
bukatarta ba to da zata ba wadannan zakuna umarni dasu
cinyeshi, amma saboda ya aminta, hakan bata faru ba.
H- MAIRAT 36
A haka yarima ya cigaba da zama da sarauniya cikin wannan
birni, a duk lokacin da tayi kokarin biyan bukatarta daga
gareshi sai yau kauce cikin wayo yadda bazata ganeba, sannu
a hankali dai har ya fara sanin sirrikanta, to wata rana sai ya
nuna mata yanason yaga yan uwansa da tasa aka daure, anan
ta aminta, tare da ita suka shiga gidan yarin, to anan yaga
Meenat tareda zulaihat, haka ma sauran mutanen duk lafiyarsu
kalau, zasu fitowa gidan yarin kenan, sai wata dabara ta fado
ma yarima, rungume sarauniya yayi tare da janta surutu, anan
ta shiga kyalkyatar dariya, bata sani ba kawai sai ya dauke
makullin gidan yarin, anan ya faki idonta ya jefa ma su meenat.
To bayan sun dawo cikin fadar sai sarauniya ta shiga turakarta
domin ta huta, cikin rashin tsammani sai bacci ya kwasheta, to
a wannan lokaci yarima najin wata hayaniya a waje, anan ya
leka, take ya gane cewa su meenat ne suka fito, cikin sauri
suka nufi kofar fita garin, suna bude kofar, to karar budewar
kofar ya tada sarauniya tareda wasu dakaru, anan suka sheko
a guje domin ganin ko meke faruwa, to kafin su iso su yarima
har sun wuce, anan sarauniya ta fara wani ihu tana jin bakin
cikin rabuwa da yarima domin tana tsananin sonsa.
H-MAIRAT 37
Yarima da sauran jama ar dake tare dashi gudu suka farayi ba
sassauci har sai da suka kawo wurin zamansu na farko wato
inda suka tsaya hutawa, to anan sukaga dawakansu, to kafin
su hau sai sukaga ayarin mutane sun zo wurinsu, daga karshe
dai sun gane cewa fatake ne kuma a birnin su yarima zasu, to
daga nan suka hada kungiya suka fara tafiya.
Kwanci tashi har suka iso, daga nan gari ya dauka yariman da
ake tsammanin ya mutu ya dawo, kuma tare da meenat,
uwayen meenat naji basu tsaya koina ba sai fada, anan yarima
ya tarar da cewa abbansa sarki bayada lafiya, tun tafiyarsa sai
dai a kwantar a tayar, saboda haka mahaifiyarsa ce ke
gudanar da mulki, amma ana cewa yarima ya dawo, daga nan
sarki ya warke, shi da kansa ya zo fada da kansa, to anan
yarima yasa aka kira humairat tare da uwayenta, to a wannan
lokaci kuma bilal na tare dasu, haka kuma fada ta cika makil,
to a nan ne yarima ya tonama kansa asiri tareda meenat irin
zaluncin da suka yima humairat, da kuma balain da suka shiga
tun a lokacin da aljannu suka sacesu shida meenat suka kaisu
wata nahiya daban.
H-MAIRAT 38
Anan yarima ya fadi gaban humairat yana bata hakuri, abunda
ya bashi mamaki shine a wannan lokaci tana magana, kuma
mahaifiyarta ta samu sauki, daga nan sai mahaifin humairat ya
fara bashi labari yadda akayi suka samu sauki:
" Wato bayan bacewarka tare da meenat sai wata rana wani
makwabcina yazo ya gayamin cewa a gabansa kuka turbude
wannan maganin, kuma mahaifiyar humairat na tsallakawa sai
yaga ta kamu da rashin lafiya, to anan ya bani shawara da
muje wurin wani yaro mai magani, wannan zuwa kuma yayi
amfani, anan ya nuna masa bilal, wannan shine ya karye
wannan maganin duk suka warke, kuma nayi dana sanin
walakancin dana masa a farko, domin a tsammanina shine
yayi maganin,bako shakka wannan magana haka take, saurin
fushi shi ke kawo dana sani, kuma zato zunubi ne koda ya
zama gaskiya, to amma yanzu a tsakaninka da bilal ban san
wanda za a baiwa humairat ba," daga nan sai bilal yayi farat
yace " ai ni bazan yi jayayya da dan sarki ba, ni na bar masa
humairat, amma inaso a bani kawarta meenat maimakonta."
" TO AN BAKA!" Inji mahaifin meenat, anan fada ta rude da
shewa, daga nan sai sarki yace bazai iya cigaba da mulkin
garin ba, saboda haka zai ba dansa yarima kujerarsa, wato ya
zama shine sarkin garin,shi kuma bilal ya zama wazirinsa, aiko
haka akayi anan aka nada yarima matsayin sarkin garin, shi
kuma bilal waziri, humairat tayi dana sanin walakancin data
yiwa samari tun daga farko, wanda shine yasa ta shiga cikin
kunci, haka yarima shima yayi dana sanin kin yin hakuri a
lokacin da humairat ta masa walakanci, wanda hakan yasa ya
dauki mataki, wanda daga karshe matakin ya zamar masa
fitina, haka itama meenat tayi dana sanin hada kai da akayi da
ita aka cuci kawarta, wanda daga karshe taga abunda ta
shuka.
Daga karshe dai an daura auren yarima da humairat, shi kuma
bilal da meenat, an kuma basu dukiya mai tarin yawa tare da
iyayensu,su kuma su zulaihat da sauran jama ar dake tare da
ita,yarima yasa an basu dukiya mai yawa sannan kuma yasa
an maida kowanensu garinsa.
Anan muka kawo karshen wannan labari.
ALHAMDULILLAH
THE END.........
.....for more novels, search and joint our facebook group:
"KINGARTICLE NOVELS OF ABDUL$BAFFERH"
OR
"KINGARTICLE.NOVL"
Written by
Abdul King Article
0 Comments