DOCTA ILHAM

16/02/2022 à 08:36"☘️ typing☘️☘️✍️"
26/02/2022 à 05:42 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

       *DOCTA ILHAM*
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

            *Na*

      *Mom kadija*
1📓
Da gudu take saukowa daga saman step tana Kiran Mama !Mama! Mama! Har ta karisa saukowa ,lokacin Mama ta mike tsaye tana shirin taje ta duba me Inteesar ta kema ihu Haka tana kwalla mata Kira, da sauri ta buya tana hakki tana sauke ajiyar zuciya,lokacin ne *Ilham* tafito ranta a bace tana banka mata harara, juyowa Mama ta yi tana kallon Inteesar ta ce''hala jan fada kika yi shine Kika zo Kika buya Bayana ko, Mama wai fa daga na tashe ta daga bacci shine fa ta biyo ni a guje tana surfa ruwan masifa, Mama Wallahi wanan yarinya ki mata magana ina baccina fa taje ta ta karkare ta sakarmin naushi a baya Wallahi Sai na rama, kin ga Ilham Rabu da ita kije ki shirya kiyi break kitafi wajen aikin ki ,'' ajiyar zuciya ta sauke tace''wallahi ke ko zaki zo hannuna zakuni nayi fa tana ta sharar baccinta gashi tana jinya a asubitinsu shi yasa na tashe ta fa ,to amma Haka ake tachin mutume da duka kuma, to naji Mama bazan sake ba,hmm kamar dagaske Mama tafada tana hararenta 

Ilham na shiga daki toilet ta huce Bata wani juma ba ta fito ta fara shirinta a nutse tana tsaka da saka turare Inteesar ta shigo dakin ta ce''Malama aunty Ilham Dady Yana jiranki za muyi break.''

 Naji Zaki iya tafiya?"

 Haba Aunty kiyi hakuri mana bazan sake ba ta fada tare da kama kunnenta duka biyu.''

wayoyinta da makullin motarta ta dauka se yar sac ta kalleta da kyawawan idanuwan ta tayi murmushi tare da kai mata Dukan wasa ta ce''wanan yar dakikiyar kanwar tawa bata jin magana sosai sai iliman tsokana,''dan turo baki ta yi, ta ce''naji komai Zaki fada nidai kiyi hakuri,Haba kanwata kema kin san bazan iya fushi dake ba burga ce kawai nakeyi, Dariya suka yi a tare suka rumgume junan su,'' Mama ce ta shigo dakin ta gansu sunata raha murmushi dauke a fuskarta ta ce''yanzu ku yaran nan muna kasa muna jiranku ku kuma kune naku yi ,'' dan Sosa keya Inteesar ta yi ta ce''Mama hakuri na bata yanzu zamu fito ai,kanku dai ake ji,'' ta fada sannan ta yi tafiyarta suma bayanta suka bi suna saukowa suka ga Dady zaune Yana jiransu da gudu suka karisa saukowa suka isa inda yake suka fada jikinsa ina kwana Dady suka fada a tare lafiya lau Yaran albarka,''Mama ce tace'' karku fara cikani da surutunku kuzo muyi breakfast tukunan, Inteesar cike da tsokana ta ce''Mama wai baki gajiya da cin abinci ne kuma seki sa kowa ya yi chiru kamar kurame wai se kice babu kyau ana CIN abinci ana magana Haba mana Mama se mu zauna shiru se karar cokula, jan kunnen ta yi tace''ke wanan yarinya bakinki ba zai shiru ne ba,washh da zafi Mama Naji ki yi hakuri ta fada tana jin zafin murde mata kunne da ta yi,zaune sukayi Mama ta yi serving din su, nan suka fara cin break din su 

Suna Kammalla wa Ilham ta mike tsaye tace''Mama zan huce Sena Dawo kuyi min addu'a,Allah ya maki albarka yakare ki daga shairin karfe da Dukan abun ki, amine Mama nagode , sunbatar Dady da Inteesar tayi, bye bye ta masu tana tafiya harda dan gudu take hadawa da shi dan tafara makara, tana fitowa ta fada mota ,tayi Horn ,getman ya Budé mata kofar tafita a nutse tana tunkin ta Harta Kai bakin Titi ta dauki hanyarta ta zuwa asubiti *ATTAGADUM* a tsan take aikinta, tana cikin tafiya wata dalleyiyar mota ta shigo ta hanyar ta , da sawri taja Burki ta kashe motar tare da fitowa,shima tsayawa ya yi yafito, kallonsa tayi rai a face tace'' Kai Malam baka da hankali ne zaka shigo kwana babu Horn kuma bazaka iya jira har motoci su gama hucewa ba inda ka bude ni fa me zaka ce, shi dai kallonta yake tunda ta fara zazaga masifarta shi tama birgesa musanman yanda dan karamin bakin ta dake motsawa da dan sauri sauri, hannunsa ya daura kan bakinsa yama hannunsa kiss tare da aiko shi a Nata bakin, Ido ta fido ta saki baki ta kasa karisa maganan da zata fada, cikin tautausar muryar shi ya ce''Yan mata kina lafiya kuwa zaki zo ki hauni da ruwan masifa.'' ko ha kama zaka ce ah daga gidan mahaukata na gudo iyakar rashin lafiya.''Dariya ma taba shi ya ce''to mahaukaciya kiyi hakuri ni zan huce ko banida Time kin kananen Yara irinki dan ina da aikin yi zan tafi kar haukan naki yata so ki fara ta kaina.'' Yana fadan Haka ya shige motarsa ya yi tafiyarsa, cike da takaici ita ma ta shige motarta kamar ta kurma ihu ko zata ji sanyi a zuciyarta, gudu taf ara shararawa amma bana hauka ba, dan ta makara , tana isa ta yi parking, ta fito tare da dauko Jakarta , tana shiga taga docta Bachir tsaye se zagaye yake, tunda taga Hakan ta san tayi laifi,, cikin Sanda ta shigo dauke da sallama a bakinta, amsawa ya yi fuska a hade cikin harshen frensh yace'' Ilham kinada hankali kuwa zaki je kiyi zamanki a gida ki san kina da marar lafiya kina kulawa da shi amma Kika barshi dazun ba dan nashiga dakin dase dai mu tarar yarasu mi yasa zakiyi Haka, a tsorace cikin french tace'' kayi hakuri docteur wallahi nafito ne a hanya wani yakaho mani Karo Allah ya takai ta abin nayi saurin tsaida mota na amma insha Allah wanan shine na karshe, ajiyar zuciya ya sauke yace''Alllah ya kiyaye gaba yanzu nasaka mashi drip kuma nasa faruk ya gyara masa jikinsa da dakin daya fata , ok docteur zan duba shi yanzu, dakin ta shige ta tarar Yana bacci, murmushi tayi tace''sannu baba Allah yabaka lfy.'' ji tayi ance amine Yan mata.'' juyowa tayi dan ganin ko Waye..........................................................

Se mun hadu a next page✍️
26/02/2022 à 05:42 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

       *DOCTA ILHAM*
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

          *Mom Khadija*

2📓

Ido ta fido ta ce'' Kai ne nan me ya kawo ka sorry?" Yan mata baba na zo du bawa nima ke fa.'' murguda masa baki ta yi ,ta ce'' nike kulawa da shi ai ,''thank you Yan mata Zaki iya Bamu waje muyi magana da shi ne ,''a'a Akan me?" kuma na ga ai bacci yake yi zaka iya jira san da zai Farka ,ajiyar zuciya ya sauke ya ce'' to bazaki bani wajen zama ba ina matsayin bakon ki ,''ba fira na zo yi ba aiki yakahoni ina son zan duba shi zaka 'iya Bamu waje ranka shi dade ,''kallonta yake don shi dai yarinyar tayi mashi'' ,fita ya yi itako tafara duba shi ,sanan takoma office din ta ta dauko wasu takardun tafito dasu zuwa office kin doctor Bachir Nocking tayi yabata izinin shigowa ,a hankali take turo kofar har ta shigo ,ta ce'' docta na duba shi naga bayada wata matsala sai dai shawarwari da za'abawa famille ( familly ) su kula da shi dan yanzu jikinsa Alhamdulilah murmushi ya yi, ya ce'' sannu da kokari doctor Ilham anjima zan je in kara duba shi sai nayi magana da iyalinsa , murmushi ta yi ,ta ce'' na gode doctor tafada tana Mika masa takardun , karfa ya yi, yace'' na miye wanan .''saka makon Alhaji ne ?" jinjina Kai ya yi ,itako tafito dakin Alhajin takoma lokacin ya Farka ,murmushi ta yi ,ta ce" baba sannu ya jikin ,yawa yata ya kokari da hakuri damu ,'' Alhamdulilah baba dama cewa na yi bara nazo.''ya Budé baki zaiyi magana yaji magana ta bayan shi ,juyowa suka yi a tare murmushi Alhaji ya yi ,ya ce "son kai ne ?" e'e baba nazo wata doctor ta ce" bazan ganka ba wai zan ta kura ka ,yafada yana kallon Ilham ,tafe baki ta yi tana ban ka masa harara ,Alhaji ne ya ce" ta yi man dai dai saboda rigiman ka zaka iya ta shi na daga bacci.'' umm umm kai baba seka goyi bayan ta karfa ta raina ni ,kamar yanda baka son raini haka ita ma bata so.'' gyaran murƴa ta ƴi, ta ce" ɓaɓa ni zan huce Allah yakara baka lafiƴa ,''Amine muna godiƴa ƴan mata .''ɓata cema sa komai ɓa ta yi tafiƴar ta 

Ilham nafita Dady shima ya tafi wajen aikin sa ,se Inteesar dake zaune tana ma karan ta kwaliƴa harda su saka masa kaƴa wai zasu tafi motsa jiki mikewa taƴi tana jaƴe da shi Har suka fito haraɓar gidan suka nufa sashin motsa jiki 

Safiya wai kina ina ne Kika barni Inata faman jiran ki idan ba zaki je duba Alhajin ba se na yi tafiya ta ,fitowa ta yi da sauri ta ce'' yi hakuri Ammi wallahi na tsaya dauko abincin ne.''
Bata ce mata komai ba ta shige gaba ta biyo Bayan ta ,driver naganinsu yatada mota suka shiga se hanyar *ATTAGADUM*suna isa 
 suka fito dai dai lokacin da Ilham ta fito zata tafi gida ,kallonsu ta yi , ta ce'' Ammi ina huni.''harara ta banka mata ta ce'' da ban huni ba zaka ganni,'' Hmm ke dai bari Ammi seka ce ta kirki daga ita har uwar ta makirai ne , murmurshi ta yi, ta ce'' baba Yana dakin hutu na baya dan gobe za'a Sallama meshi ,ohhh ni Murja tambayarki na yi ne kaji wani salon gulma ko da yake doli ki iya saboda uwar ki ma ta iya ta ,rufe idonta ta yi, dan taji zafin maganar ta amma sai ta ce'' a gaida mai jiki natafi gida se kun iso ,tafiya ta yi suko suna kananun magangan su ,tana fita tashi ge motar ta zata rufe kofar taji an rike ta fuska a daure yake kallonta hannunsa day a gudun sa ...................
26/02/2022 à 05:42 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

       *DOCTOR ILHAM*
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

          *Mom Khadija*

3📓


Hannunsa day a Kugun sa ya ce'' Yan mata tafiya Za ki yi bako Sallama , Ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' Walahi wanan Mutuman kafara Takura ni Diya fa ni ka Matsa min zan yi tafiya ta , *Musa Abul khair* za ki ce ,'' Dan Allah zan tafi gida ?" Murmurshi ya yi ,ya ce'' Yan mata kuma Kuka Za ki man ,'' Na kusa dai ,''tom Allah ya Huci zuciyarki Yan mata ina sonki Matata ta Gobe ,'' Harera ta ban ka masa ta jenyo kofar ta rufe ,bye bye ya shiga mata 

Da Sallama a bakinsu suka shigo dakin ,amsawa ya yi ,Safiya ta ce '' baba Sannu ya jikin ,'Allhamdulilah?:"Alhaji yanzu Bana ce watsan yar Banzan Yarinya ta bar shigowa nan doli se ita zata na duba ka ,'' wai murja me yasa kike Haka ne gabar Shekara da Shekaru baza ku dai na ba ,"Alhaji in dai na fa ka ce ," e'e ban isa da ke bane ?" ke fa ki Kayi ma uwar ta laifi ta sanadiyar ki Yarinta Inteesar Bata hankali isa she ki saka mahaifarta ta lalace ba ki je kin Bata Hakuri ba ,''Alhaji ni fa Dan Allah Abar maganar nan ,''sabida baki da gaskiya ko na ji ai ke ce Kika so ayi ta daga shigowarki ba ko sannu bare ki ji lafiya ta Kika buge da fadan Banza ,''Shiru ta yi, dan ita kan ta Ta san ba ta da gaskiya ,Safiya ta ce'' Baba dan Allah banaso ku kullum fada ,'' Mama na zamu dai na kin ji ,tom bara na zuba ma Abinci 

A gajiye ta Shigo gidan babu Kowa a falon ,har zata Haye sama ta ji motsi a kithchen ,hanyar tanufa ,da Sallama ta shigo ta ce'' mama sannu da aiki , Wa'alaikum salam A'a Ilham kin Dawo ne ,'' E'e mama ina Inteesar ne , murmurshi  ta yi ta ce'' tana daki wai za ta yi wasa ,girgiza Kai ta yi ta ce'' Inteesar manya ana girma ana cin  kasa Mama zan je in huta kafin an jima Sai na duba ta ,Tom Mama ta fada ,'' ita ko tayi dakin ta rage Kayan jikinta ta yi ta huce toilet wanka ta yi Bata wani juma ba tafito ta saka Kaya Marasa nauyi sanan tafito tanufa dakin Inteesar ,A Hankali turo kofar da Sallama a bakin ta ,Inteesar dake wasa tana tsale tsale tana wasa da miyo duk ta Bata jikin ta ,cikin maganar ta ta kamar masu ko Yan magana ta amsa mata Sallama ,tana danne harshen ta tana magana ta ce'' Aunty Har kin Dawo ,jinjina mata Kai ta yi cike da tausayin kanwar tata, ta ce'' Kin Sha maganinki ne ,A'a Mama ta ce'' Wai harna ci abinci ,''to Me kike jira tun dazun baki ci abinci ba lokaci fa ya huce ,turo  baki ta yi kamar za ta yi Kuka ta langwafar da Kai idanun ta da ba daidai suke ba ta ce'' Mama Bata kara sa girkin ba , murmurshi  ta yi ta ce'' To kar ki yi Kuka ta Gabon goshi na ki wasanki zan zo se muci abincin a tare ko ,Washe baki ta yi har seda yawu suka zubo ta ce'' To Aunty ,cike da tausayin kanwar ta tafito daga dakin ta Dawo falo
26/02/2022 à 05:43 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

       *DOCTOR ILHAM*
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

          *Mom Khadija*

5📓

Shuru ta yi Bata ce komai sai kara hade fuska da take ,Doctor Bashir ne ya shigo da sallama ,amsawa su ya yi , ya ce'' Alhaji ya jikin , Alhamdulilah ,'' babu abin da ya ke ma ciwo ne ,'' E'e babu kafa ta ne kawai ke min ciwon ,Ok gobe In Sha Allah zamu sake duba lafiyan ka Dan muna sa ran gobe ko zuwa ban da gobe zamu sallama me ka , Murmurshi  ya yi ,ya ce''Kai Doctor muna godiya Allah ya biya ka ,Amine ya fada sanan yafita .

*WASHEGARI*

Tun da ta yi Sallah Asuba tafito a kithchen ta samu Mama Nan ta kama su ka hada breakfast suna dan taba fira har suka Kammalla ,Mama ta ce'' Ilham ki je ki shirya zan gyara danning table din ,Toh ta fada sanan tanufa hanyar dakin ta 

Sai da ta yi wanka ta shirya cikin shirin ta na zuwa Asubiti dan Aikin da Za ayi ma Alhaji ,sanan ta je dakin Inteesar da tun da ta yi Sallah ta koma bacci Tashin tafara ta ce'' Inteesar ta shi bacci ya isa Haka ,Bude idonta ta yi ta sauke su kan kyaukyauwar fuskar yayar ta ta ce'' yaya har kin tashi , Murmurshi  ta yi, ta ce'' E'e zan ma tafi Asubiti ,zaune ta yi tareda Mikewa tanufa toilet , Ilham kuma fitowa ta yi ta samu Mama har ta kammalla komai ,ta ce'' Mama ina ga zan huce kar na yi late dan zamu yi Aiki amma yaw da yamma zan Dawo bazan juma ba ,A'a ki hankuri har ki yi breakfast Yanzu Dadyn ki zai fito Inteesar ta ta shi ne ,E'e na bar ta ta shiga toilet , To bara na zuba maki na ki kar ki makara ,A'a Mama an yi Haka bara na yi Serving kin Kai na tafadi Hakan tanufa daning din 

Tana kanmalla CIN abinci lokacin Dady da Inteesar suka fito , gaishe da Dady su ka yi sanan ta Mike tsaye ta ce'' ni zan tafi Sena Dawo ,Allah ya tsare ki yarinyar kirki cewar Dady ,Amine ,ita ma Mama da Inteesar suka mata A Dawo lfy ,fita ta yi Ta fada motar ta ta dauki hanyar Asubiti ,bata juma ba ta iso dan gudu take shararawa dan kar ta huce Time kin da zasu shiga Blooc , parking ta yi tafito ,lokacin Ammi za ta tafo ita da Mussa Abul Khair za ta aike shi ,Safiya ce tafito da gudu tana cewa Ammi nima zan bishi ,Ajiyar zuciya Ilham ta sauke cikin dar-dar ta ce'' Ammi ina kwana ,tafe baki ta yi, ta ce'' da ban kwana ba da kin ga zaa fita da gawana ai , Allah yabaki Hankuri Ya mai Jiki ,da sauri Mussa Abul Khair ya ce'' Alhamdulilah muna godiya Sosai Da kulawar da Baba ya ke Samu a hannun ku ,wani tausasan Murmuchi ta yi masa ta ce'' kar ka damu ba komai , wani  Sanya yen ajiyar zuciya ya sauke ya Washe baki kamar sakarai Yana rawan baki ya ce '' Na gode ,Bata tankasa ba har zata shige ciki Ammi ta ce'' dama ya'yan karya ai doli su iya karuwanci da naga har kiwon karnuka suke ,To Wallahi jinin gida na yafi karfin ki sai dai Abi wani sarkin Anga yaro kyaukyawa ana son sa ce masa zuciya ko , juyowa ta yi ta kalleta tareda girgiza Kai ta yi gaba abin ta ,''Ammi Meyasa ki ke mata Haka ne na lura tun da Muka zo asubitin nan kike ta kurata diya fa wai mi ye tsakanin ku da Maman ta ne ,Hararen shi ta yi ta ce'' uwar ka ce tsakanin mu ka ga Allah ka ki ya ye ni fa ,Ohhh naga ne kallon da ta yi min Yan zu a she signe ta yi ma na ka tambaye ni abin da ke tsakani na da uwar ta ko ,shuru ya yi dan shi tun da yadawo daga *TUNISIE* yarasa abin da ya hada su fada da Hajiya Maryam ( Mama ) , jin bai ce komai ba yasa Ammi cewa ba zaka aiken da na yi ma ba ne ,'' fita ya yi Safiya ta bi ba yan shi ta ce'' Hamma ( yaya) ka yi hankuri nima tun jiya na kasa gane Mike damun Ammi ,Dariya ya yi ya ce'' kar ki damu kan ki rikicin tsufa ne ,ita ma Dariya ta yi ,ta ce'' Kai da Ammi ba ruwa na , Ta fada tana shiga mota ,shi ma shigan ya yi suka nufa *MARADI STORE* Don siyan abin da Ammi ta Aike su
26/02/2022 à 05:43 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

       *DOCTOR ILHAM*
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

          *Mom Khadija*

6📓

A Kofar *Maradi Store*  ya tsai da motar sa suka fito ,Kai tsaye ciki su ga shiga dama sayayar Kayan tea sanan suka fito ,A bakin Mota ya ce'' Sofi ina son zamu yi Magana Sanan za ki so duk abin da na Nuna ina Kauna ,Sosai ma wace Magana zamuyi ,Kin ga yarinyar nan Ta da zun wace Ammi take yawon jan ta fada ,E'e Ilham ka ke nufi ,dama kin san ta ne ,E'e Yar gidan dady Mustapha ce Makautan mu, Ajiyar zuciya ya sauke ya ce'' Sofi banida Abokin shawara da ya huce ke Wallahi Allah ina son Ilham kuma rasa ta tamkar rasa rayuwa ta ne Soyayar ta na Wahalar min da zuciya Amma ina jin tsoran tunkarar ta da Magana kuma ina ta azab-tuwa da son ta ,To hamma ka dauko baban aiki dan da Wahala Ammi ta barka ka Aure ta gaskiya nima ba kaunar ta na ke yi ba amma tun da Kana Son ta nima da ga yanzu zanfara kaunar ta ,To Mi ya sa ba ki sonta ,'' saboda dalilin Ammi da ban san me ya hada su da Maman su Ilham ba , Shiyasa ma na dai na Abota da ita kuma Bana shiga sabgarta ,'' Sofi ki tausayamin kin ji ,To hamma zan yi kokari inga ko za ta yarda dani a Karo na biyu ,'' Na gode Sofi na ,'kar ka damu yaya na zan shawo kanta sai ka inda kari sa sauran aiki.

Ilham nashiga ciki su ka fara shirye shiryen shi ga da Alhaji a daki Sun dan dau ka 1h suna duba shi suka kara dau kan jininsa sanan suka fito da shi ,sanan Ilham ta je ta Kai jinin *Laboratoire*

Dawo da ta yi tanufa office din Doctor Faruk ta turo kofar a hankali tareda yin Sallama,cikin Sakin fuska ya amsa ya ce'' Doctor Ilham yaw ke ce a office Dina ,fuskar ta a hade ta Mika masa takardun hannun ta ta ce'' Gashi D.t Bashir ya ce'' Na kahoma su kuma Yana nemanka nan da 30mnt ,'' takkardun mi ye ,hararen shi ta yi ,ta ce'' Ba gasu a hannun ka ba ,Allah ya Huci zuciyar ki ,ka mani laifi ne ,A'a ,to mi ye na bani hakuri ,Babu ,tafe baki ta yi, ta juya za ta fita har ta Kai kofa ta tsinci Murya shi Yana fadin Ilham ya maganar mu ne na jiki shuru , cike da shakiyanci ta ce'' wace magana fa ,Haba Ilham ki gane ki Amin ce da bukata ta Wallahi zan rike maki Amana , Ajiyar zuciya Ilham ta sauke ta ce'' Faruk Kana ba ni Mamaki Wallahi ka ga na yi kama da Yan Iskan Yan Matan da kuke lala tama rayuwa to Bari ka ji ni na taso ne a gidan Mutumci sanan Iyaye na Sun bani tarbiya ko da ina karama ban yarda na yi bata garin Abokai ba bare Kai Rana tsaka ka ce zaka fatamin rayuwa ba ka kama girman ka kafin ya fice a Ido na ,tana gama fadan Haka ta yi, tafiyar ta ,cike da Mamaki Faruk ya ke bin Ilham da kallon har karisa Maganar ta tafita ,dan A da idan yai mata Maganar za ta yi Kuka ko ta yi shuru tana sawrarensa
26/02/2022 à 05:43 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

       *DOCTOR ILHAM*
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

          *Mom Khadija*

7📓

A hasale ya Daki table din da ke gabansa ya ce'' Wallahi Ilham komai zai faru sai de ya faru Sai na Aika ta Abin da Na yi,Akan ki Yana gama fadan Haka ya fito dan amsa Kiran DOCTOR Bashir 

Tafiya ta ke kamar wacce Kwai yafa she ma a jiki tana tunanin da mamakin faruk Bata Ankara ba taji an bangajeta saura kadan Ta fadi  kasa karfan benan da ke wajen ta yi sauri da fawa amma sai da kan ta ya bugu ,kafin ta yi wani yin Kuri ta ji Mari har uku lafiya yu '' sai da ta ga Stars suna yawo a sama ,Kuka ta fashe da shi ta ce'' Ammi me na yi maki Za ki man wanan cin Fuskan a cikin mutane wai me na yi maki ne kin Ta kurawa  da rayuwa ta ne ,ban sani ba tsanar da na kema uwar ki ita ce ta shafeki Wallahi sai kin yi na dama sani na a rayuwar ki diyar Macijiya maciya Amana , Ajiyar zuciya ta sauke tareda share hawayen ta ta ce'' bazan taba Dana sani ba tun da ban zallumci kowa ba sai de in ga haske Yana haska ka min rayuwa kuma Na gode da sadakar marin da na samu a gare ki , tana gama fadan Haka ta yi tafiyar ta , Mussa Abul Khair da tun da Ammi ta daki Ilham ya ke tsaye Yana kallon  Abin da Ammi ke yi ,ganin tafita a guje yasa shi bin Bayan ta office din ta ta shi ga ta rufo kofar da karfi ji kake garamm ,zaune ta yi ta saka Kuka mai tsuma zuciyar duk mai sauraro ,A hankali ya fara murda handlle din ya shiga da Sallama a bakin sa cikin kuka ta amsa ,ciketa fargaba ya zaune Yana kallonta ya ce'' Yan mata Dan Allah ki yi hakuri Akan abin da Ammi na ta yi maki nasan Bata kyauta ba ,Dan Dago da kan ta ta yi ,ta ce'' Banason hakurin ka ka rike abin ka kuma kafice min da ga office ,Cikin sanyi jiki ya ce'' Na ji zan fita amma ki saurare ni,''babu abin da zan ji da ga gareka Walllahi Abul Khair Na tsan......... Da sauri ya danne mata baki Yana girgiza mata Kai, hannu ta saka ta buge hannunsa ,tafara tatare Kayan ta zata fita ,jenyota jikinsa ya yi Yana kallon fuskarta lumshe Ido ya yi cikin zazakar muryarsa ya ce'' Ilham ,gabanta ta ji Yana bugawa da karfi karma zuciyarta zata fito da ga kirjinta sosai ta ji sunan ya kara kyau daya furta shi daga bakinsa ,kasa ta yi da idonta ,''Yaci gaba da cewa Ilham ki yi hakuri nasan kina da hankali da fahimta nasan kin san  cewa babu kyau gaba bare kuma ni da ban maki komai ba ki tausaya min dan Allah ki yafema Ammi na ,Ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' Na ji Allah gafarta mana baki day ,amine, kallonsa ta yi, ta ce'' ko zaka iya saki na lokacin ta shi na ya yi , bakinsa ya Kai daidai kunnenta ya ce'' Ina Rokon ki wata Alfarma ,Ta me fa , murmurshi  ya yi , ya ce''Ina son kiman murmurshi  dan girman Allah kar ki ce A'a , Murmurshi  ta yi masa badan komai ba sedan ya hada ta da girman Allah,kiciniyar kwatar kan ta tafara yi ,amma ta kasa kallonsa ta yi fuska a hade ta ce'' ka cika ni kafin ran ka yabaci ,Indai zan samu hukunci da ga wajenki na shirya dauka ,a shagwafe ta ce'' dan Allah , Murmurshi  da bai san lokacin daya zo masa ba ya ce'' dan sakeyi nagani ,murguda masa baki ta yi ,ta ce'' Dan Girman Allah ka cika ni ,'' sausauta rikon da yai mata ya yi ,Tai saurin ja baya ,kallon love ya shiga aika mata Ya ce'' ina son........................................

Comment
26/02/2022 à 05:43 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

       *DOCTOR ILHAM*
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

          *Mom Khadija*

8📓
 
Wowww fan's Ina Matikar godiya ,Godiyar ma ta gode ina yinku 💯 

Kowa ta shirya zamu yi Salfie cas cas cas 📸📸



Ya ce, ''Ina son zan Raka ki gida.''Ko?Ba na So Wallahi.''Me ya sa? Ko dai ni ne ba kya so na Kai ki. ''Kusan Hakan.'',''Saboda me ?"Ni Wallahi kaci kani da Surutu ,Ba na so, ana dole ne ?" " Allah Huci zuciyarki yallabiya Bani na kai Zomon ba Rataya Aka bani. ''Fuska ta hade ta ce'' Ni ce yallabiyar ma .'' sorry bazan sake ba my *ALBI*.? ''Shuru ta yi. ? ''tana masa kallon tuhuma ta ce'' Na gode?'' Abul Khair yau ka Faranta min Raina Sosai da motata Nazo ba sai ka rakani ba.'' ''Murmurshi  ya yi ,ya ce'' to Nima Na gode da Kika Ba ni lokacin ki Ilham Babu abin da na ke jin dadi Idan kin fada sai Abul Khair Ban taba tunanin Sunana Yana da dadi Haka ba sai a bakinki Na ji Haka ,"Ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' kar ka damu zaka iya tafiya ,"Dan Sosa keya ya yi, Ya ce'' sai yaushe Kenan ,"To.?"kaji mani wani Mulkin Mallaka Dan Allah ka yi ,tafiyan ka Inason zan duba Abu." sai An jima  Amma yau tun da Aka fito da Alhaji baki je kin duba bashi ba ,''Ba bukatar Hakan Doctor Faruk zai kulla da shi ,'' Dan fata fuska ya yi ,da  sauri ta ce'' Kar ka damu Ina son zama ni ka dai ,'' tom.?yafada sanan yafito daga office din ,Ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' Aikin Banza Ilham kin bani Mamaki wai harda su yima shi shagwafa Ina Aikin me wai nice har da sakarmasa Murmushi ,'' cike da jin haushin kan ta,? "ta gama Abin da za ta yi."Tabaro Office din. 

Duke take tana wanke Kayanta Dana yaran ta gefe day kuma ya'yanta ne Zaune suna cin Abinci sai dan na goyen da yake taya ta.",wankin  tana hanashi  shi kuma Yana Mata Dariya 

Shigowa yayi fuska a hade da ledojin cefane a hannunsa Sallama dauke a bakinsa ,'' Amsawa ta yi ,ta ce'' Mn cœur Bon arrivé ,Bai amsa ba ya ce '' lahiya .?yaran nan basu tafi School ba suke nan zaune.''Yanzun nan suka Daho wai sai An yi Versement,'' wai har Sun yi rabin Shekarar ne ,E'e ga Zahiri ka gani ,Ajiye ledojin ya yi ,ya ce'' Aïsha Ajiye wankin nan ki daura mana girki Yinwa na ke ji sosai , '' karfan ledan ta yi, tanufa kithchen sai da tafara daura girkin sanan Tazo ta ci ,gaba da wankin ta 

''Kwance take kan 3st Écouteur ( eapice) a kunnenta tana sauraran Music Tana buga game.''

Horn yake ta yi.'' a waje amma ina sam Ba ta ji ya juma Yana Horn.''sai tsan.?" yar yarinya ta da bazata Gaza huce 2year ba Tafara bugun ta tana Kiran."Momy ! Momy ! momy ! 

Juyowa ta yi ,ta ce'' Zuci miye ,'' A Lokacin ta ji Horn din sa ,Mikewa ta yi , tafita waje ta bude masa kofar ,Ransa a face ya fara kokarin shigo da Mashin din sa dama Tuni tana Budé masa ta Dawo cikin falon  ta zauna tana ma yar diyar ta wasa ,Da Sallama ya shigo falon ,tsan ciki ciki Ta amsa ta ci gaba da Harako kin gaban ta ,shima daki ya huce yarage Kayan jikinsa ya Dawo falon ya zauna ,Mikewa ta yi ,tafita waje plate din da ta ci abinci Wanda yake ajiye wajen wanke- wanke ta dauko ta wanke sa sanan ta Dawo falon ta duka karkashin Table ta dauko Cokalin da zai ci abinci da ita tafita ta wanke ta ,sanan ta huce kithchen ta Bude Tukunya ta Zuba masa abincin sanan ta kahomasa ta ajiye gaban sa ,Ajiyar zuciya ya sauke yafara cin Abincin ,'' Ya ce'' Basira yanzu kina jina dazun ina ta Horn amma Kika shareki sai da Kika ga dama sanan Kika Budé min kofa ,kamar za ta bugeshi ta ce'' Kamar ya ban gane ba wai kuma da sabon salon Karyan da kazo min da ita ,Cike da Mamaki ya ce''  Basira ni nake maki karya ,Murguda masa baki ta yi, Ba ta ce komai ba ,ya ce '' Kinga abin da yasa Banason son fira da ke Magana mai dadi baki iya yima mijinki ita ba ,''cike da rashin kumya ta ce '' To sai me in baka yi fira da ni ba ina ruwa  na an fadamaka cewa banada Wanda zai Ta yani fira ne ,Shuru ya yi ,bai ce komai ba ya ci ga ba da kwasar girkin sa 

Aïsha Na gama girkin ta ta dauko kuloli ta zuba a ciki ta sanan ta fito ta jera a dan karamin Table din dake Tsakiyar Falon Babu abin da dakin Ke yi se kamshi sai da ta gyara komai sanan Ta shi ge bedroom dan Tashin SaÏfullahi ..................................................
26/02/2022 à 12:14 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

       *DOCTOR ILHAM*
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

          *Mom Khadija*

10📓

Ita ma sai da ta Kammalla Yan danne dannen ta ta nufa daki ta yi baccin ta dama Tuni Khairat ( diyar ta ) ta yi ,baccin ta .'''

WASHEGARI 

Tun da Aka fara Kiraye Kirayen Sallah yake Tashin ta ,''Amma dan tsabar rainin wayo tana jinsa ta kyalesa ganin bata da niyar ta shi ne yasa shi kyaleta sai da ya gama Nafilolin sa Ya nufa Masallaci  jin ya fita yasa ta ta shi ta daura Alwala ta shimfida darduma dan gabatar da Sallah.''' 

Kamar kullum Bayan ta gama Sallah Ta fito dan ta ya ,Mama hada break Bayan Sun Kammalla ne Ta nufa daki Kai tsaye toilet Ta fa da, babu jimawa ta fito Ta fara shirin tafiya Asubiti.''

Fitowa ta yi, ''tsaf da ita duk da ba ta yi wata Makeup Ta yi, ''masifar kyau,wajen da Mama ke zaune Ta nufa a shagwafe ta ce'' Mama wai ina Dady ne? tun jiya ban saka shi a Ido na ba ,'' Ilham Yar gidan Dady Yafita ,'' Kai Mama shine bai je ya dubani ba ,'' To? wanan tsakanin ku ne babu ruwa na.'' Mikewa ta yi ta ce'' Mama zan tafi kiman addu'a ,'' Ilham kullum Ina yin maku ita Amma yanzu dai kin ci abinci ne ,'' A'a Mama ? Ba na jin  yunwa ne ,'' To ? Babar magana Haka Za ki je da yunwa, "Mamaaa zan ci idan Na tafi Asubiti," Hmm Allah yasa da gaske nake ," Ta fada tana cewa Mama sai na Dawo.'' Tana fitowa ta shige Mota ta tafice da ga gidan.''

Fitowa su ka yi a tare, " suka dawo Falo serving nasu ta yi, sanan ta zauna da ga gefensa suka fara cin abincin su. " Suna Kammala wa suka dan tafa fira sai da dare ya ƴi, suka tafi suka kwanta." 

Tana isa Asubiti ta isko," Abul khair zaune suna lalatsa waƴa ," jin kamshin turaren ta yasa shi dago wa  cike Da zolaƴa ya ce" Asalam Alaikum Matata ta gobe ," Wa'alaikum Salam ," Matata ba za ki, man sannu ba, " to? Ba ka da Lafiya ne," A'a na zauna ne ita zaman jiran ki ,girar sama ta da ge ta ce" aikanka na ƴi bare kai min gori , A'a Na ga Tun jiya da kika fita Amma baki dawo ba , Kallon ka Ta kura ni tai Masa, sanan Tafara  Tafiƴa ," ɗa sauri ya sha gaɓan ta  ƴa ce" Haba Matar Ina zaki tafi ga shi bamu yi ,Maganar dana ke so miƴe ," To?  Ce maka aka ƴi ɓa na ɗa ,Aikin  ƴi ne ,Allah huci Zuciƴar ki *Albi* na  idan kin ta shi Dan Allah ki ƴi ,hakuri ki saurare ni yau ne zamu bar asubitin nan kuma ina son zamuƴi Magana mai Mahinmaci ne ,Na gode Allah zai rabani da Takura ," Murmurshi ƴa ƴi , tare da girgiza kai ,Hararan sa ta ƴi, ta shi ga ,da ga ciki ," sai da Ta fara ,huce wa , "wajen  Doctor Bashir ,da  Sallama Ta shi ga , Amsawa ya ƴi ,ya ce" Ilham sai yanzu, E'e, To? Dama dalilin da ƴa sa na ce idan kin shi go ina son magana da ke ,ga wanan ,karɓa Ta ƴi, ta ce" ta miƴe wanan din ," Takadar Sallamar ki da ga Aiki ne ,Cike da Mamaki tsoro da faduwar ga ba kamar za ta ƴi ,kuka ta ce" ...........................................................................

Ku ƴi hakuri da wanan waƴar 2% take 

Comment ✍🏼
26/02/2022 à 12:14 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

       *DOCTOR ILHAM*
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

          *Mom Khadija*

11📓

Cike da Mamaki tsoro da faduwar ga ba kamar za ta ƴi, kuka ta ce" Doctor Menaƴi  Zaka Koreni," Jin dadin ," kara gigicewa ta ƴi ta ce" Amma ɓakamin Adalci ba," Ɗariƴa ya ƴi mai isar sa ƴa ce " Naga Alamar Majinyacin Naki Ƴafara samin sauki shiyasa na Sallama shi Amma Tun da kin ce ba' a maki Adalci ba ,To? Sai a bar shi  Har lokacin da kike ɓukata ," Hawaƴen dake bin kumcin ta ne ta ƴi, saurin  sharewa ta ce" Wallahi Doctor Bashir kabani Tsoro sosai , Murmurshi ƴa ƴi,ya ce" Maganin mai tambaƴa na ƴi , daga yau idan na baki abu ki kara tambaƴa na Haka zan yi maki ,Ɗariya ta ƴi, ta ce" Kasan me ? A'a" Nafasa baka Inteesar sai de ka nemi wata ,mikewa ya ƴi ,ya ce" To? "kin ma isa ai nasan Mama ba za ta hanani ba ,hmmm Tafada ,Tare da ,ficewa daga office din ."

Dakin da Alhaji yake Ta nufa "bakinta dau ke da Sallama ,Amsawa Safiƴa ta ƴi, ta ce" A'a Ilham ke ce? , Murmushi ta ƴi, ta ce" E'e Wallahi sofi nice ina Ammi ko Yaƴanki ," Eeeyah Ammi Ta tafi giɗa Amma yaƴana yana waje ,Ok Ina son ganin sa a office di na , To in sha Allah yan zu, zan kira shi." Juyawa ta ƴi ,Ta fita daga room din takoma office din ta.

Tun da sasafe Ta tashi ,ta ƴi , shara da Mupping ta gyara ko Ina sanan ta dau ra breakfast tana Kammalla  wa ta je ta ƴi,wanka tana fitowa , ta saka wata hadadiyar riga goduwa ce ta fesa turare ma masifar kamshi sanan ta je Ta tashi yaran ta ta gyara masu jikinsu suma sai kamshi suke fitar wa dakin Saïf Ta nufa Ta fara tashin sa Cikin salon so ,A hankali ya fara bude Idon sa ya sauke su Kan Aïsha da ke ta sakar masa Murmushi kamshin turaren ta na kara ratsa hudojin hancinsa ,lumshe Ido ya ƴi , Tare da karanta addu'an ta shi ,daga bacci  sai da ya gama ta ce" ina kwana Mn cœur , lahiƴa lau  Mn cœur, " Da Alama kina son mantar dani in Kasa gane a Duniya na ke ko ,A lahira ,'' Murmushi ta ƴi , ta ce'' in dai muna tare duk inda zaka je ,To a tare zamu je ,'' jenyota jikinsa ya yi, ya ce'' shi ya sa Sonki ke kara Nunkuwa a zuciya ta kullum Bana jin a lokacin dazan wayi gari Inga Bama tare da juna sai de in mutuwa ka dai ,'' Murmushi  ta ƴi, ta ce'' ita ma Mutuwar in Tazo Ta dau ke mu a tare ,'' Mn cœur Time na gudu Kar ka Makara aiki ka tashi ,'' raba jikinsu ya ƴi,ya ce'' ina da Meeting kuwa , ya fada Yana Mikewa tsaye ya nufa toilet ,bai wani juma ba ya fito, ta taimaka mashi ya shirya sann suka fito falo dan suyi breakfast .''

Sai da ta dau ra ci, yakusan shigowa gida da sauri ta gama addu'an ta shafe jikinta sanan ta je Ta fada kan bed Ta jen yo Wayar ta, ta kunna data Ta fara duba sakonin wasu ta mayar wasu ta share su ,jin Alama shigowansa yasa tai saurin Ajiye Wayar ta rufe idon ta kamar mai bacci ,da sallama ya shigo, ganin yan da yabar ta Haka ya isko ta yasa shi kara Tashin ta ,Mtsss taja ta ce '' wai dan Allah lafiya ne ,kin yi sallah ne ,'' Bansani ba Kai nake jira ai ,girgiza Kai ya ƴi, yafito falo ,sai da ya gyara komai ya hada abin break yama dakin turare sanan yaci ya rage mata sauran yatafi daki ya yi, wanka ,Yana fitowa yayi shirin fita office ,yazo ya tashe ta ,tana Budé idon ta ya ce'' kizo fita zan yi ki rufe gidan ,Yana gama fadan Haka ya fita ,ita ma Mikewa ta yi ,ta zo sai da ta tsaya ya fitar da Mashin din sa sanan ta buga kofar da karfi tasaka sakata.'' 

Musa Abul Khair '' Na shiga office din Doctor Ilham da sallama ,Ta amsa fuska a hade ,shigowa ya yi, ta Nuna masa wajen zama ,ta ce'' Bayan binciken da Mu kayi ma Alhaji Mun gano Ba shi da wata Matsala sai de a guje fata masa rai dan ko wane lokaci zai iya samun ciwon zuciya saboda Haka a kiya ye ,sanan wanan Takardan maganin da za'a saya ne dan yaci gaba da shansu  a kan Lokaci ,'' Mika masa ta yi ,ya karfa tare da  yin godiya ,ya ce'' Ilham inba damuwa ina son zamu yi magana , hararen sa ta yi ,ta ce" ina sauraren ka," Cikin sanyin jiki ya ce'' Ilham ? Kin zamo Ta Musamman daga cikin mutane na Musamman   Dana taba haduwa dasu a rayuwa ta ,kin shiga zuciya ta kin zauna ta yadda bazan iya mantawa dake ba har Abada ,ina fata da  burin kasancewarmu a tare a daula mafi tsari da kyawun birgewa wato Aljanna. Cikin nishadi da yalwatuwar murmurshi  fuska nake mai furta maki cewa Ina sonki ina kaunar ki dan Allah ki Aminci da Bukata ta, karki ce A'a dan zan iya shiga wani hali ya kaini ga na rasa rai na ,dummm ta ji kwakwalwa ta ta Bada baki sake take kallonsa maganganansa na saké Daho mata idon ta Sun mata Nauyi dan baza ta taba daga su ta kallesa ba dan tsabar Mamaki , ta ce'' ...........................................................................

Alkur'an idan Ban ga ruwan comment ba Ba zan ci gaba ba.
26/02/2022 à 12:14 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

       *DOCTOR ILHAM*
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

          *Mom Khadija*

12📓

Ta ce'' Abul Khair ? Baka da hankali ne ,'' ina cikin hankali na Ilham ki tausayamin Dan Allah ba dan ni ba badan na isa ba sai dan Darajar Soyyayar mu ,'' To? Ni dama Na fada maka cewa ina Sonka ne kaga Malame ta shi kafice min a office kafin Ranka ya face ,a Marairai ce ya ce'' Ilham Na hadaki da girman Allah ki karfi Soyyaya ta rashin samun ki tamkar shiga hadari ne rayuwa ta zata zama abar Tausayi Ilham nasan ki da tausayi dan Darajar Allah kice kina Sona koda zan ji sanyi a Raina ,Tausayinsa ne ta ji yakama ta ta ce'' Na ji zan yi tunani ta shi ka tafi zan nemeka idan Na gama tunanin ,da karfi ya ce'' dagaske kike Ilham Zaki soni ,zan nemaka  ka tafi ina da aiki yanzu ,'' Ta shi tsaye ya yi , Ta reda Kamo hannunta ya daura kan sai tin zuciyarsa ya ce'' Ilham ki ji Yan da take barazanar fitowa , duk lokacin da Muka hadu Haka zan ta jin sautin ta da karfi ,Dago da fuskar ta ya yi, ya ce'' kalli kwayar Ido na koda ba ki san ,miye so ba nasan kina jin labarin sa kin zama wani bangere daga cikin Sasan jikina ,saurin rufe idonta ta yi ,ta ce'' Dan Allah ka tafi ka ji bani da lokacin wanan shurman ,'' Ilham ba shurme bane sone duk silan Haka ba laifi na bane zuciya ta ce ,'' Murmushi ta yi ,ganin Yana shirin Bata mata lokaci ta daura hannunta a gefen fuskarsa ta ce'' Abul Khair Dina ka yi ,hakuri ka tafi gida idan nazo sai muyi magana kaji ,Ta fada cikin tautausar muryar ta mai dadin saurare ,'' hannunsa ya daura a Nata ya ce'' dagaske ,''jinjina masa Kai ta yi, ta ce'' Na Ta bata ,'' hannunta ta jenye shima ya dauki takardun da ,ta ba shi  ya fita Yana aika mata da kallon so ,'' Naunayan ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' Ohhh ni Ilham naga ta kaina Meyasa Haka ke Faruwa dani ne Mahaifiyarsa Bata kauna ta ,ga danta Yana haukan Sona ,wanan wace iriyar rayuwa zan yi idan na shiga gidan sa ,A'a gaskiya bazan iya Soyyaya da shi ba zauna wa ta yi ,ta rafka uban ta gumi tama rasa meke mata dadi .''

Bayan Sun gama breakfast ne ya Mike Tareda fadin Mn cœur zan huce na makara ,'' ita ma Mikewa ta yi , suka fita a tare har bakin motarsa ta kaishi sanan ta marairaice fuska ta ce'' Mn cœur yanzu Tafiya zaka yi ka barni da kewanka ,Sorry ki yi hakuri ai bazan juma ba ,umm umm nidai gaskiya da ka yi zamanka Bana son katafi ka barni ni kadai gashi yaran nan suma zasu Tafi Islamiya , Jenyota jikinsa ya yi , Ta reda kamo fuskarta suka fuskantar juna ya ce'' Eeyah Mn cœur To ko na zauna ne ? " Da zanfi kowa farin ciki ,amma yanzu katafi tun da ka ce bazaka juma ba ,kiss din ta ya yi ,a goshi ya ce'' Ranki shi dade sai na Dawo ,ita ma kiss tai masa ta ce'' Allah yadawo mana da kai gida lafiya yakare ka da shairin karfi ,. Amine Mn cœur ,a shagwafe ta ce'' Mn cœur Allah ya tsare a Dawo lafiya mijina ina son ka kulamin da kaina da kuma Kai mijina badan ni ba badan na isa ba sai dan Darajar Soyyayar mu ,insha Allah gudaliya ta , Murmushi ta yi, Ta reda Raba jikinsu Haka suka Rabu da juna bada son rainsu ba ,'' bye bye ta shiga yimasa har sai da Taga ficewarsa daga gidan ,sanan ita ma ta shiga ciki.''

Daki ta koma ta dare saman gado Ta reda janyo wayar ta ta hauda data nan ta shiga duba sakonni suna sai da ta gaji dan kan ta taje ta wanka ta fito falo ta zuba  abin break din da Al'ameen ya hada masu ,tana cikin ci ne Khairat ta fara Kuka ,tsoki taja ta ce'' Zuci ta so gani nan ,da Kuka yarinyar Ta fito  daga cikin dakin ta Kariso wajen ta ,kan cinyoyin ta daura ta Ta fara Bata abincin a baki ,'' Wayar ta ce ta fara ringing tana dubawa taga sunan ,kawata ,'' daga wa ta ce'' manyan manya maganin Kanana Kanana ya dai ,Hmm kawata Haka na samu ai indai kuna gari mu ba komai bane ,Dariya ta yi ,ta ce'' ka ji wani salon Kuma kin fada dan jin dadin bakin ki ,A'a Wallahi maganar gaskiya ce ke ba wanan bama ina nan tafe gidanki anjima kadan abban ummi zai kahoni ,To? Allah ya kahoki lafiya ina nan ina jiranki ,ok to abban Khairat ya fita ne ,to ba dolen sa ba me zan masa ,hmm kawata kenan kun yi halin Kenan ,ke dai sai kinzo akwaye labari , in sha Allah ,'' tana gama fadan Haka ta katse kiran.''
26/02/2022 à 22:24 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

13📓

Zaune take tana kallon wani Série a Novelas T.V ,'' taji tana Nocking a waje ,Mikewa ta yi ,Tafita Tareda Budé kofar ,ai da sauri ta rumgume ta Suna Sakarwa juna Murmushi ta ce'' Kawata? '' Ashe dagaske za ki zo ,'' E'e gani kuwa ,'' to? Ina yallabai ,hmm ina ruwanki Fushi ma yake da ke ,'' da sauri ta daura hannunta a kirjinta Tareda fiddo Ido ta ce'' Me ya sa ? '' Na fada Masa cewa fada kike keda Yayana shiyasa kuma ya kira shi dan ya ce '' yagaji da wanan iskancin naku ,Tafe baki ta yi ,ta ce'' kin ga huce ciki kar ki fatamin rai ,ko? To nima zan fara ma yayanki abin da kike ma nawa ya rikice ki ji ,in da dadi , Murmushin kawai ta yi ,bata ce komai ba ,

Suna shiga falon suka zauna nan Basira ta kahoma Nafissa kawar ta ruwa da dan Abin Ta fawa ,sanan ta zauna kan 1st ta ce'' To ya Labari ? "Kawata ,Zaki ji labari idan yayanki ya shigo ,'' ajiyar zuciya ta sauke ta ce''Wai da gaske kin fada Masa muna fada da abban Khairat ,'' Wallahi kuwa keni Na gaji da yawan korafe korafen ki gwara a kawo karshen matsalar nan ,'' gabanta ne ta ji ya yanke ya fadi dan idan dai har Yaya Sadik yasan wanan sai ya ci mutumcinta ,tana cikin wanan tunanin ta tsinci Murya Nafissa ta na cewa ke kar ki damu ba fada zai maki ba sulhutaku kadai zai yi ,'' a Hasale ta ce'' gaskiya Nafissa ba kyauta min ba to? " Dama Na ce maki ina bukatar taimakonki bare Namijinki kin ga kar ki kara mani Haka ," Murmushi ta yi ,ta ce'' To ? Uwa ta Haka za'a zuba maki Ido kina aika ta Barna Meyasa ba ki son gaskiya ne ,'' sai Randa Kika dakeni ,Dariya ta yi ,ta ce'' kin ga wasa na ke maki bai ma san da maganar ba amma Wallahi in dai baki gyara ba to zan Sanar masa sai ya dauki mataki da kansa , Murmushi ta yi, ta ce'' Wai Allah har Naji wani sanyi a Raina ,hmm Allah ya shirye ki ? " Yanzu fadamin Me ya hadaki da shi ne ,'' Sunkuyar da Kai ta yi ,tana kwasa ta Yatsan ta ,'' Hmm ke ce da laifin Kenan ko ,'' gyada mata Kai ta yi ,alamar e'e,'' to Me yasa? " baki ba shi hakuri ba ," kam Lanle kawai sai in ba shi hakuri salon ya Raina ni,'' Iyeehhh?" ya Raina ki fa Kika ce , E'e Sosai ,e'ee lanle Basira kina cikin fata Wallahi da nidai shawara zan baki amma idan Zaki dauka ,'' to? Ina jinki ,'' Basira dan Allah ki san darajan kan ki kisan Mi ye ,duniya wanan sakarcin naki babu inda zai sauke ki sai a tashar wahalla yanzu ke ba za ki gyara halinki ba ke kullum fada da miji ko da ban tambaye ki nasan kan maganar fitar da ya Hanaki ce kike fushi da Mijinki Me ya sa,'' Haba kinsan fa akwaye zafi ka tambayi mutume abu a Hanaka ,'' Dariya ta yi, ta ce'' tabbas a kwaye zafi Musanman fatar da kake da wani muhiman abu, to ? Amma sai ki yi ,hakuri tun da ke kan ki kin san ,kina yawan fita to miye a ciki dan ya Hanaki wanan ,nidai abin da zan ce da ke shine ki bama mijinki hakuri ku zauna Lafiya dan Allah Bamu baki sha'awa Nida Aïsha yanda Muke kulla da gidan auren mu ke baki jin dadi dan Allah kar ki so kan ki ,'' hakane Abun Yana birgeni sosai kawata musanman rayuwar gidan Aïsha, to? Dan Allah mi ya sa ,baki ko yi da ita ne ,zan yi in sha Allah ,Ohoo in ma kinaso kar ki yi ,wanan ya rage naki dan jiya da Na je gidan Momy na ji suna magana tsakaninsu wai zai kara Auré kuma diyar abokiyar Momy ce zai aura amma ba na fadamaki dan ki kara daga ma mijinki hankali bane sabida kishi dan a yanda yake fada mata cewa baki da lokacin sa sai na wayarki baki kullasa idan yamaki magana sai kin ga dama ki Amsa ko ki yi abin da ya sakaki nan Momy ta goyi Bayansa dan yanda ta kulla da yaron ta duk ya fita hayacinsa ,darammm ta ji gaban ta yafadi da karfi ta ce'' ni Sani zai ma kishiya dan Allah wasa kike ko da gaske ,kin tafa jin Namaki Irin wanan maganar sai da na tabatar sanan na kore  maki labari amma idan dan halin da kike masa ne To lokacin fa bai kuremaki ba.''


Ganin zama bazai fisheta da komai ba Hakan yasa ta Mike Tareda dauko wasu takkardun ta fito Ta nufa dakin da Alhaji yake ,da sallama a bakinta ta shigo ,nan Alhaji da Safiya suka amsa amma ban da Ammi sai ma harara da take galla mata ,'' ko a jikin ta dan Bata damu da Abin da take mata ba dan inda sabo ta Saba gwara dai su yi ta ,tafiya ko zata ji sanyi a ranta , Murmushi dauke a Fuskarta ta ce'' Am ga wanan takkardan sallama a Alhaji ne daga Asubiti,ta Mika wa Ammi da karfi ta, karfi takkardan tana watsa mata harara , juyowa ta yi, ta kalli Alhaji tana Murmushi ta ce'' Congratulation Alhaji jiki ya yi ,kyau Alhamdulilah sai de a guje fata maka rai ko abin da zai sakaka damuwa yawon facin rai duk ba naka bane ,'' shima Murmushi ya yi, ya ce'' Ilham Allah yamaki albarka Na gode da kullawarki gareni Allah yabaki miji na gari da yaran da zasu maki biyyaya ,Amine Alhaji Na gode sosai bara na tafi lokacin ta shina ya yi, Murmushin kawai ya yi, amma bai ce komai ba ,ita ta juya ta yi ,tafiyar ta.'' 

Safiya ta Mike ta biyanta da gudu ta sha gabanta ta ce'' Ilham dan Allah ina son magana dake in ba damuwa ,'' gyara Tsayuwar ta ta yi , ta ce'' Allah yasa lafiya ,'' in sha Allah dama maganar Yayana ne ke tafe dani ,shi ya ce'' maki wani Abu na yi masa ne Kika zo daukar fansa ko ,'' Murmushi ta ƴi, ta ce'' A'a ko day babu ,'' to tell me ? Mana ,'' ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' Ilham dan Allah ki yafemani Abun da Na yi maki Wallahi na biyewa shairin zuciya ne Hakan yasa nake maki kallon da Ammi take maki kuma ni ban san miye sirrin da yasa ta tsaneki ba ina son mu Dawo daidai kamar da duk da nasan Hakan da huya ,'' Murmushi ta yi ,Tareda daura hannunta kan kaffadar Safiya ta ce'' Kar ki damu Sofi dama ni ban rike ki a Raina ba Allah yasa Hakan yafi zama alkairi a garemu ,'' amine Aminiya ta na gode ,kar ki damu ,amma nace kin yi magana da yayana ne ,'' cike da zolaya Ilham ta ce'' dama kina da yaya ne ,hararen wasa ta yi mata ta ce'' e'e yaya Musa Abul Khair Wanda ya tafi Tunisie wajen karatu tun muna Yan kusayanmu ,Dariya ta yi , ta ce'' A She ya Dawo ,'' e'e Wallahi kin san ko har yanzu baba ce min yake yar kusanya ,'' Murmushin ta yi ,dan ita har yanzu Bata saké da Safiya dan kar ta saké yarda da ita a Karo na biyu ta juya mata baya ,'' kin ga safiya wanan firar ba mai karewa ba ce sauri nake zan ba Inteesar Maganin ta ,To ? Ki cewa Mama an jima zan shigo na duba Inteesar din , Murmushi mamaki ta yi , ta ce'' in sha Allah sai kin zo din ,ok bye ,'' tana cikin Tafiyar ta a Nutse ta d'aura kafarta bisa bawan banana nan yaja ta da karfi..........................................,............................
28/02/2022 à 01:02 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

14📓

Wani Irin sulfi ne ya ya jata da karfi Ba ta san lokacin da ta kurma ihu ba tana shirin kaiwa kasa ta ji Tafa da jikin Wani Abu ,Ajiyar zuciya ta sauke amma jikin ta sai rawa yake Bude idonta ta shi ga yi,a hankali dan zai da Ta fara Budé Ido day sanan ta Budé su a tare ganin Abul Khair ne yasa ta sauke ajiyar zuciya ,kawai sai taji ta tsinci kan ta da yin Kuka ,sosai ta daga masa hankali bai wani kullata ba yaja ta a Office din ta dan Mutanan da ke za ga ye dasu , kofar ya rufe Bayan Sun shi ga cikin tautausar muryar sa Ya ce'' Ilham ki dai na wanan Kuka dan hawayenki tamkar huta ce ke Tafarfasa a zuciya ta ba na so ,ki hakuri dan wanan hawayen naki suna da matikar tsada a gareni,'' cikin sheshekar Kuka ta ce'' Miye na yi ,ma Ammi da take azabtar dani Irin Haka me na tare mata da take son ta ga ta shi ga, damuwa ko son ganin hawayena a Hakan kake son na aminci da soyayarka kasan dacin da nake ji a zuciya na idan Na tuna wai wacce na dauka a Matsayin Mahaifiya ta ce take kirana da sunan karuwa na yi ,gadon baki hali Me ya sa ,ina mai Rokonka da Girman Allah ka fita a hanya ta Bana sonka Abul Khair , ta kara she ta na Kuka ,'' da karfi ta rufe idonsa jin kallaman da ke fitowa a bakin ta ya ce'' Ilham I cannot leave you down ,because you are my life ,our love like biggest garden in the World, I love you ,'' Sosai take kallonsa hawaye na tsiyaya a idonta ta ce'' Abul Khair ina Bukatar zama ni kadai na fahimta so kake ka karamin ciwon Kai Bana bukatar ganinka a yanzu ,'' wani Yawu ya hadiye mai daci ya ce'' shikenan zan tafi amma kisani zan tafi cike da kaunar ki Ina sonki ALBI na ,'' juyar da Kai gefe ta yi , wasu zafafan hawaye na sake wanke fuskarta ,'' ganin ya fita ne ita ma ta fara Ta tara Kayanta Tafito ,ta shige Mota ,amma ta kara ta buka komai , Nocking ta ji an yi mata ,juyowar da zata yi ,ta ga DOCTOR Faruk ne ,saurin share hawayen ta ta yi, Tareda daure fuska ,ta sauke glass din motar ta ce'' lafiya dai ,'' dan Murmushi shakiyanci ya yi ,ya ce'' Ilham har yanzu ke baki Waye ba Tun ranar da Muka yi maganar nan Kika fara wasan fuya dani ni fa taimakon ki zan yi a matsayina na masoyinki ,'' kallon ba ka da hankali ta yi ,masa ta ce'' da Alama har yanzu iliminka babu amfanin da yake maka sunanka Doctor Faruk Amma da alama sai ka je a duba ka dan kallon mahaukaci na ke maka ko na rasa wan da zai taimake a duniya Wallahi ko inuwar ka bazan kalla ba bare kasa ran zan zo neman taimako wajenka doli ake yi ne ka kalleni ni ba sa'an matan da zaka raba bane koda sadaka na Aka baka dan nafi karfinka Wallahi dan Haka ka je Ka nemi sa'anka , tana gama fadan Haka ta zuge glass din ta ta shi motarta sai gida.''

Tun da Ilham ta fara Ta fiya da motarta Faruk ya yi sakaka Yana kallonta dan ba karamin Mamakinta yake sha a Yan kwanakin nan dan gani yake kamar a mafarki ne Ilham ke fadamasa Irin wanan maganganu masu datsi ,kamar ya kurma ihu Haka yake ji dan Ilham ta gama da shi dan a kalmar da tafi fata masa rai shine ,'' ni ba sa'an matan da zaka raba bane koda sadaka na Aka baka dan nafi karfinka Wallahi,wanan wajen yafi Kona masa rai sosai , jiki ba kwari Hakan ya shi ge motar sa Ya yi ,tafiyarsa .''

Tana shiga ta fara tatare duk inda suka fata ta kwashi plate din ta kai kithchen sai da ta wanke su sanan ta Dawo falon ta kalli Yaranta ta ce'' Ihsane ku tashi ku tafi Makaranta kar lokaci y Huci ,To Umma ? Amma kin ga fadila bacci ta koma fa kuma Malamin Islamiyarmu ya ce'' Mu daina Makara , Murmushi ta yi ,ta ce'' To? Haka ya c e'' Ki ta sheta ku tafi ko ,'' Mikewa ta yi ,tafara Tashin Fadila ,tana ta shi suka tafi Islamiya ,ita kuma Aïsha ta gyara dakinta  ta yi ,Mopping tareda saka turare ta fito dan dora girkin Rana ,'' tana cikin aikin ne Saïf ya kira ta ,da Murmushi a Fuskanta ta dauka tareda sallama a bakinta , amsawa ya yi , ya ce''Matar Saïf ina sonki kuma zan ci ga ba da sonki har na tsawon rayuwata Matata, ni da ke tamkar kashi ne mai gwari da Bana fatan wata Rana ya yi ,targade bare har ya Kai ga ya karye . Ina sonki Yan mata Saïf tunaninki ya adabi rayuwata kullum sonki na dada karuwa a ko wane second na rayuwa ta ke ta Musanman ce gareni Aïsha Bana samun sukuni har sai Na ji Muryanki ko Muna a tare ,'' Murmushi ta yi mai sauti ta ce'' Mijin Aïsha na ta ita ka dai shi so na gaskiya ba ya ta ba duba tsawon lokacin da Aka dauka a na tare ko wani tsanji na rayuwa ,a saboda Haka Sonka ke karuwa a cikin zuciya ta a kowace Rana ,a kullum Kana kara zama saurayi a idanuwana , kuma gwarzo Abun alfahari na Kai ne sanyin idaniyata ina sonka . Allah ya Dawo min da Kai gida lafiya , amine Matar so ki kulamin da kan ki sosai fa ,kar ka damu Mijina ,nima ka kulamin da kanka , Murmushi ya yi ,ya ce'' ina yaran mu ,Sun ta fi Islamiya ,to Allah ya Dawo dasu lafiya ,Amine ,to bara n'a bar ki amma badan na soba na yi baki ne ,umm ummm ni dai bazan yar da ba fa, ina jin dadin Yan da dadan Muryanka ke ratsa kunnuwana su huce duk ilahirin jikina shi ne za ka ce ,wai ka yi ,baki ,Dariya ya yi, ya ce '' Mn cœur uwayan rigima pls ai zan Dawo gidan da na gama da su ,turo baki gaba ta yi , kamar Yana gabanta ta ce'' da gaske za ka zo ,sosai ma kar ki damu kin ji shalele ta Ba na Son,kina saka damuwa a ran ki '' A gafarce ni ranka shi dade tun da zaka Dawo ai bani da wata damuwar ,'' to? Ki man Dariya dan na tabatar da Hakan ,'' dariyar ta masa mai sauti ta ce'' in dai hankalinka zai kwanta zan kasance mai dauke ma daukan damuwar da tafi karfina ba ,thank you gudaliya ta bye ,ok merci Mon amour ,'' tana gama fadan Hakan ta katse kiran ta ci gaba da aikin ga ban ta .'''
03/03/2022 à 12:51 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

15📓

Ilham Na karaso wa ta fito ta nufi cikin ciki falon babu kowa Hakan ya Bata damar shi ga dakinta ,sai da tai wanka sanan ta saka Yan Kayan Zaman gida ta haura kan gado ta kwanta zuciyarta cike da damuwa da tambayar kan ta me ta yi ,ma Ammi ne Me ke tsakaninsu da Mama da suke rufe sirrin basa bukatar mu ji , ajiyar zuciya ta sauke tareda rufe idonta dan bacci ta ke ji amma ina sam yaki daukar ta da ta rufe Ido sai ta hango ga Abul Khair nan Yana mata kallan tausayi Yana rokonta da ta amince da soyayarsa ,Mtss Kai wanan Mutuman ya sha min Kai Wallahi ,'' kamar ta yi Hakan ta zauna tana aikin tunanin yan da zata bulloma soyayar Abul Khair ko ta je ta fadawa Ammi ta masa magana ya kyale ta ne ,nan dai tai ta saka da warwara har bacci ya yi ,gaba da ita 

Sai da ta Kammalla koma sanan ta nufa daki ta yi ,wanka ta tsaya gaban Madubi ta yi ,Make -up sosai tai kyau ta saka doguwar Riga atamfa ta yi mata kyau sosai ta yi, wanka da ruwan turare ,sanan ta Dawo falo ta jaho wayarta Ta kira Saïf ,Yana dauka da sallama a bakinsa , amsawa ya yi , ya ce'' Matar ya dai ,'' a shagwafe ta ce'' Na Kira in ji lafiyar Mijina ne , '' Murmushi ya yi , ya ce''  Alhamdulilah Matar ,'' Mn cœur ina ta jiranka tun dazun shiru baka Dawo ba  ,'' sorry Yar leleta  ina aiki ne ,'' umm ummm shine ka manta dani ko ,'' Aïsha ke wata ta Musanman daga cikin wani bangare na jikina kin zama tamkar zuciyata ce shi ya sa bazaki tafa mantuwa daga cikin ta koda Bamu tare Zuciyoyinmu Suna game da juna ne babu abin da nake yi idan nafito sai aikin tunaninki na zama tamkar wani zautata  ce Haka kawai sai Na tsinci Kai na da yin Murmushi ko Dariya ,'' Murmushi ta yi ,ta ce '' a nawa bangaren ma Haka yake Mijina shi ya sa a ko da yaushe kaunarka ke kara Nunkuwa a zuciya ta ta sanadiyar Hakan ne na ke kiranka da ga birnin zuciya ta *Sanyin idaniyata* ,'' nan dai suka sha firansu cike da shauki da kaunar juna 

To? " Yanzu me kike ganin zan yi ne ki bani shawara kawata ,'' nidai shawaran da zan baki shine ki zauna Lfy da Mijinki yanzu idan gidan ku wani yasamu Labarin Hakan Musanman Yayanki Abul Khair kinsan sai kin kwashi kashinki a hannu dan Haka ki Nitsu ki kula da mijinki wani Fushi ko bacin rai Bana ki bane Aljanah Kika zo nema da rahaman Ubangiji karki fata ladanki mana mijinki ne ko ba aurenki ya yi ,ba ya baki Shekaru da Zaki ba shi girmansa duk lokacin da yai maki laifi ki ba shi hankuri bare kuma kuna da Alaka tsakaninku Wallahi kawata ina fadamaki duk lokacin da Kika Bari Sani ya kubucemaki sai kin Raina kanki saboda Mutume mai hakuri kamarsa bai iya fushi ba ina ganin ya kamata ki ajiye makaman yakinki ki kama mijinki ku rayu ku zauna Lafiya Haka Zaku ta zama babu ci gaba rayuwarki sai de kullum ko ke keda laifi sai kin jira har sai yabaki hakuri Haba wanan ki sake rayuwa kuma Ingani a aika ce daga yau din dan insan matsayina a gareki ,'' To me zan yi ? Ki ba shi hakuri kawai, in sha Allah zan yi ,'' Allah yasa da gaske kike ,'' Wallahi kuwa ,nan dai sukaita tautaunawa kan Yan da za ta yi ,daga bisa suka ta shi dan daura girki .''

Baccinta take hankali kwance ba ita ta Farka ba sai Bayan sallah La'asar ,tana shi ta shiga toilet sai da ta yi ,wanka sanan ta dora Alwala ta zo ta gabatar da sallah ,'' tana gamawa ta zauna kan gadon ta ta dauko Wayar ta Miss call ta gani duk na Safiya ce ,'' Murmushin Mamaki ta yi, dan rabon da safiya ta kirata yanzu Sun Kai kusan Shekara day ,'' Kiran ta maida mata bugu biyu ta da ga ,ta ce'' Aminiya lafiya ina ta kiranki amma baki da ga ba ,'' Cikin Muryan Wanda ya ta shi da ga bacci ta ce'' Wallahi bacci ne ya yi  ,ga ba dani sai yanzun na ta shi ,'' Ahan ok toh gani nan zuwa gidanku yanzu ,'' To? Ba damuwa sai kin zo .'' tana fadin Hakan ta katse kiran tana bin Wayar da kallo ,'' Haka kawai ta tsinci kan ta da tunanin Abul Khair lokacin da ya ke mata rada a kunne da lokacin da yake sakarmata Murmushin sa mai Ta fiyar da ita ,da lokacin da yake Yi mata kiss tana masifar zai buge ta , Murmushi ne ya Bayana shimfide a Fuskarta ,jin ana Nocking ne yasata sakin tsaki tamike dan ganin Waye ,'' tana Budé kofar ta ga Mama tsaye tana karemata kallo ,''' ta ce'' Ilham dama A she kina gidan nan amma shiru baki fito ba lafiya dai ko ,'' Murmushi ta yi , ta ce'' Lafiya lau Mama lokacin dana shigo ba kowa a falon shi ya sa na huce daki na shine bacci ya yi,gaba dani dan na gaji sosai sai yanzu ma na ta shi ,'' To in jin dai an yi sallah ,''E'ee yanzun na gama ,'' to? " ki zo Safiya tana nemanki Lafiya dai ko,'' E'ee Mama zamu yi magana an jima ,dama ta ce '' in ce maki za ta zo ganin Inteesar ,'' To ? Muje ,fitowa suka yi a tare har falon ,ganin Safiya da Mussa Abul Khair yasa ta hade fuska ,kusa da Safiya ta zauna ta ce'' Aminiya A she da gaske Za ki zo ,'' kin dauka da wasa nake ne ,A'a na sanki da cika Alkawari ai ,'' Ina Inteesar din take ne ,'' tana dakinta da Alama wasa take shi ya sa Bata fito ba ,'' ya jikin Alhaji da sauki ko ,'' Baba ya fita koda Muka Dawo ya ce'' zai je ya tataki ,'' A'a lanle jiki ya yi ,kyau Allah yakara ba shi lafiya ,Ameen ,Kallon Mama ta yi ,ta ce'' Mama yinwa fa nake ji , Murmushi Mama ta yi ,ta ce '' ai ina ga ban yi girki ba yau dama ina jira idan Kika Dawo sai ki girka mana ,'' kamar za ta yi Kuka ta ce'' Kai Mama ko kadan bazan samu ba ,'' hmm bansani ba a cici kawai jirani ina dawowa ,'' ta shi Mama ta yi, Ta nufa kithchen Jum kadan ta Dawo da plate biyu a hannunta ,ta mikawa Abul Khair sanan ta huce dakinta ta barsu su kadai ,'' Zaune ta yi kasan Capet ta ce'' Aminiya ta so muci abinci ,saukowa Safiya ta yi, suka fara ci ,a nutse take cin Abincin kamar ba ta son tauna shimkafar ,'' shiko ya kasa CIN ko da cokali day ne sai kallonta yake Musanman sharesa da ta yi,kamar Bata gan shi ba Hakan yasa sai ya ji wani Iri ,'' Sai da Suka Kammalla sanan ta tatare Kayan ta kai kithchen ta wanke plate din sanan ta biyo masu da ruwa Gora uku ta Mikewa Safiya day kuma ta ajiye gabansa ,'' Murmushi ya yi ,ya ce'' Na gode , '' kallonsa ta yi ,amma Ba ta ce komai dan tun da ta kallesa ta ga ya yi, bala'in kyau ga wani kwarjini Daya cika mata Ido sai sheki yake kamar dan larabawa,'' Sai A lokacin ta ce'' Mun Yaris ( ina kwana ) ,''kara gas ( lafiya lau ) ,'' to? Yau abin naku ba hausa sai buzanci to ni na yi waje Mama da Inteesar idan kun gama soyewar taku sai ku mani magana in fito ,'' kallonta Ilham ta yi ,tana banka mata harara ,'' ka she mata Ido ta yi ,tana hayewa sama ,'' wayarta ta dauka ta rubuta texte kamar Haka ,Wallahi Aminiya ki Dawo Kona biyo Bayan ki ,'' stickers din Dariya ta aikomata ,Hakan ya Bata mata rai ta ce'' mata shik ( ubanki ) ,'' kallon ta ya yi ya ce'' wadurtole,( ya kike ) ,kara gas ,shiru ya tsaya wajen na dan sacanni tsan ya ce'' tawasaya ( kyakkyawa ) ,'' Murmushi ta yi, tareda sunkuyar da kanta ,'' Ilham baki ce komai ba Tun dazun ko baki so ganina ba ko da yake kin ce bakyason ganin fuska na ,''A'a ina so da zun ma Bana hankali na Raina a face ya ke ka yi hakuri ka ji ,To? Yanzu kina maraba da zuwa na ,'' gyada masa Kai ta yi ,ta ce '' ai bakonka Annabin ka dan Haka na ji farin ciki da zuwanka dama duk Wanda yataso ya zo gidanmu ,'' to Kenan kina Sona ,'' Murmushi ta yi ,ta ce'' bazan ce Bana sonka ba saboda tun lokacin da ka ce Kana Sona tunaninka ya ka sa fita a kaina ,kullum idan har zan yi bacci to sai ka zo min dan Allah wai ana soyaya dole ne ,'' Alama ne ta kema ki na jin abin da na ke ji a game da ke ,Ilham ke rayuwa ta ce bazan iya daina sonki ba sai de in Nunfashi a duniya ki tausayamin kin ji ,'' Wani Irin Murmushi da Ba ta san lokacin da yazo mata ta yi ,masa ba ta ce'' zan yi tunani ,'' zuwa yaushe ,'' Randa Allah ya ce ? '' to Allah ya Nuna mana ,Amine,'' Mikewa ta yi ,ta ce'' zan je na Kira Sofi ta ,'' Dama ki kyale ta dan banki mu zauna da ga ni sai ke ba dan ina jin dadi wanan ya na yin kin saki jiki munyi fira sabanin yanda kike Disgani cikin Mutane ba ,'' A shagwafe ta ce'' To? '' ai kaine kake fara tsokana ta shi ya sa ,'' kallonta ya tsaya yi, dan ta birgesa sosai ,'' kumya ce ta kamata ganin Irin kallon da yake aikama ta dan ita ba ta san lokacin da ta yi ,masa shagwafan ba ,'' cikin tautausar muryarsa ya ce''...................... ...........................................
03/03/2022 à 22:40 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

16📓

ALBI komai Kika yi Yana kyau kike karawa bazan taba gajiya da furta maki cewa Ina sonki ba ki daure kimin koda kwanta kwacin Wanda nake maki ne , Murmushi ta yi ,ta ce'' Na gode ,'' kallonta ya yi ,ya ce'' in sha Mushmush ( Murmushi) na Lafiya kamar bakyason Magana dani tunda zun sai zuba maki surutu nake amma baki ce komai ba ,'' dan Bata fuska ta yi ,Tare da dafe kan ta ta ce'' yaraf Akami wata ( kaina Kai ciwo ) shi ya sa amma ka yi hakuri ,'' Ido ya fido ya ce '' yarafni ?" Ya tambaye ta Yana kallonta ,'' dan langafe  Kai ta yi, ta ce'' E'e amma yanzu zan je in sha magani ,'' A gulu Isiri ( tai kwanta) ki huta idan kin sha magani ko ," Na gode sosai da kulawarka gareni ,'' Karki damu ALBI kima Safiya magana mu huce gida ,'' ok to? " Sama ta haura Kai tsaye ta yi, dakin Inteesar da suke ta wasa ita da Mama da Safiya ,'' sallama ta masu ,'' su duka a tare suka amsa ,'' kallon Safiya ta yi ,ta ce'' Sofi ya ce'' Wai kizo ,'' To?" Har kun gama shan soyayar ,'' Murguda mata baki ta yi, ta ce'' Ina ruwanki yar sa'ido kawai ,'' A'a ba Ido na saka maki ba hanci na saka ,'' Dariya ta yi, ta ce'' ke Aaa ciki ,'' Hmm Muje karki saka Malam zalumu ya da ke ni ,'' hannu ta dora a bakinta ta ce'' Sofi Mon Halal din nawa ne kike cema Malam zalumu ,'' E'e din ? Wai Naji kamar kin ce Ton Halal kodai kin kamu ,'' sunkuyar da Kai Ilham ta yi , dan ita kan ta ba ta san lokacin da ta furta Hakan ba ,'' Aminiya ta Allah yasa Alkairi a cikin wanan soyayar taku Yayana Yana matikar kaunarki amma kina wahalar masa da zuciya Amma wanan kalmar da Kika fada ta sakani jin dadi sosai dan ba komai kin fara kamuwa ,'' kallon Mama dake saurarn ikon Ilham ta yi , sanan ta mai do dubanta ga Safiya ta ce'' Fassto ( shiru ) ,'' Kallon Mama ta yi ,da gefen idonta tana Murmushi sanan ta kalli Ilham a hankali ta ce '' Naki ?" Kwafa ta yi ,Mata ta ce'' Allaf ( barki ) ,''ka she mata Ido day ta yi , ta ce'' Mama ni zan tafi ,'' da Murmushi dauke a fuskar Mama ta ce'' To?'' Safiya ki gaida Hajiya Murja ,'' zata ji in sha Allah ,'' fita suka yi Ita da Ilham suka sauko kasa Yana nan zaune inda ta barsa ,kallonta ya yi ,ya ce'' Ilham dama baki kwanta ba ,'' A'a Na fara jin ya daina ciwo ,'' To? '' Allah ya sauwake ,'' Amine ,'' har kofar gida ta raka su har ta jiyo zata koma ciki ,Safiya ta ce'' Aminiya ina mai kara baki hakuri dan Allah Komai ya huce tsakanina da ke Na gode da tarban Dana samu daga gareki a yau ,'' La? " Karki damu Sofi Komai ya huce ai ,'' To ? Allah ya sa wai kin san gobe ne bikin Ummulhair ne ,'' ke dan Allah? " Ni kin ga nama manta wanan Kan nawa Allah ya yi ,shi da mantuwa ,'' Dariya ta yi w ta ce'' Hakane har da aiki da ya sha maki Kai shi ya sa ,'' hakane ,'' To ? Zaki je ne ,'' E'e Zani Ai gobe Bazan je ba sai ban da gobe ,'' ki ce kin samu hutu ,kedai bari ,'' Haka za'ayi sai mun hadu ko ,'' E'e in sha Allah ,'' sai da ta ga Sun fara tafiya sanan ita ma ta koma cikin gida.''

Sai da Suka sha love din su sanan ta katse kiran ,'' kwanciya ta yi ,dan ta gaji sosai wani bacci mai dadi ne ya fara di banta  sai ta ji ana Nocking cikin bacci ,Ta shi ta yi , ta je ta Budé kofar ,'' yaranta ne suka Dawo daga Islamiya ,'' kallonsu ta yi ,ta ce'' Nabila har kun ta so ,'' E'e ,'' Kuje ki cire Uniforme din ku sai na zuba maku abinci ko ,'' Wallahi kuwa Momy kamar kin san yinwa nake ji cewar Ihsane ,'' Murmushi ta yi , ta ce'' Kuje yanzu zan duba ai ,'' nan suka shige ciki Kai tsaye dakinsu suka huce ita kuma a falo suka bar ta kafin su huta har ta karisa zuba masu abinci ta jiyar masu kasan Capet ,'' nan suka zauna suka fara kwasar girki,'' ita ko ta ce'' Ihsane zan je na kwanta dan Allah ban da fada kun ji ,'' To? Momy nima dai baccin zan yi ,'' hucewa daki ta yi , ba ta ce mata komai ta je tai kwanciyarta .'' 

 Bayan Sun gama girki ne suka shi ga gyara ko ina a gida a ta kaitse sai da Suka ma ko ina fess sanan Fadjimata ta ce'' Bassira ni zan je gida yamma ta yi ,'' hmm dama ba shi zai zo daukarki ba ,'' E'e ni zan tafi da kaina ,'' Tom bara na Raka ki ,A'a ki Zamanki kin ga ,Yayana bai sani ba ,'' shikenan tun da Hakanan Kika ce  ,Na gode sosai da ziyararki gareni nima zan shirya naje gidan naki ,'' ina jiranki amma in ji samako mai kyau ,'' karki damu kawata ki dauka an gama ,'' Khairat ce ta fito daga daki Waya rike a hannunta tana cewa Mama ayici ( abinci ) ta fada cikin gwarancinta ,'' Daukarta ta yi , ta ce'' To Muje na baki ,'' nan tai ma Fadjimata kyauta mai kyau sanan ta saka yaran makotansu suka taro mata mai Napep har kofar gida ,sosai ta yi, mata godiya sanan ta yi, tafiyarta .'' ita kuma daki ta huce da yarinyarta sai da Suka yi wanka suka shirya tsaf da su sanan Tazo ta zuba ma Khairat din abinci ta zauna ta fara Bata sai da ta tabatar ta ko shi sanan ta kwashe plate din ta yi , kithchen da shi ,sanan ta Dawo falo ta kunna T.V Ta zauna tana jiran shigowar mai gida .''

Ilham mike tsakaninku da Musa Abul Khair ,'' babu komai Mama ,'' To? Miye kaho Safiya gidan nan ,'' Ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' Mama Abul Khair cewa ya yi ,Yana Sona naso yi masa hulakanci ko dan sabida abin da Ammi ta ke min amma na kasa to ana Haka ne sai Safiya ta zo neman gafara wajena kawai nace mata ba komai tun da dama ai bani na fara gaba da ita ba ita ce ta fara kuma ta zo neman sulhu ,'' Ina Kika san Abul Khair dan tun lokacin kuna Kanana keda Safiya ya tafi kasar waje ,wajen karatu ,'' shine Wanda neke fadamaki ya nemi ban kade ni da mota Yana kiss ina cikin yi masa masifa ,Dariya Mama ta yi, ta ce'' To ? Ilham bazan Hanaki soyayyarki ba amma kisani ki yi ,taka tsan tsan dan kinsan Mahaifiyarsa ba sonki ta ke ba  ,'' in sha Allah Mama ,'' Addu'a ta gareki ita ce Allah yasa Alkairi ne ke tafe da shi ,'' Amine Mama ,'' nan dai suka ta zantawa fira tsakanin uwa da yarta. ''
08/03/2022 à 21:03 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

17📓

Sai da Suka sha fira sosai Sannan ta ce'' Mama ina ga zan shiga ciki Na ga kamar an kusa Kiran sallah Mangariba.''

'' gaskiya ne to shi ke nan,'' 

 Har ta fara tafiya sai ta juyo ta ce,''

 Mama da ma ina son Fada maki,'' cewa gobe ne bikin Ummulhair na manta sai yanzu Safiya take Sanar da ni.'' 

Mama ta ce'' A'a ki ce diyar kirki ta kusa aure to Allah ya sa Alkairi ya ba su Zaman Lafiya ya sa gidanta ne.''

amine  Ilham Ta fada.''

 cike da zolaya  Mama ta kalle ta ta ce'' sanan Allah ya kawo na Yan baya Musamman na Musa Abul Khair.''

 cike da kunya ta ce'' Kai Mama ta fada tana haye sama da gudu.'' 

Dariya Mama ta yi, tana Mikewa ta nufi daki don An fara Kiran sallah.''

 sai da ta fara shiga dakin Inteesar ta duba ta ta ce'' Intee na ke dai a zaune tun da zun ,'' cikin Yanayin Maganarta na kamar Yan koyan Magana 

ta ce'' Auntyna ina wasa ne Ba na son hayaniya ,'' 

Ilham ta ce'' To? " Ya yi ,kyau Yanzu ki tashi muyi sallah sai ki sha magani ki kwanta ko ,'' Murmushi Inteesar ta yi ,ta ce'' amma a tare zamu yi ko ?"Ilham ta ce'' E'e ta shi ki Alwala.''

'' Mikewa ta yi , kan ta na langafe a gefe Ta nufi toilet alwala ta daura sannan ta fito Ta nufi dakin Ilham da tun lokacin da Inteesar ta shiga toilet ta fita ,'' tana shigowa lokacin Ilham ta fito nan suka kabarta Sallah a tare .'''


Bayan tashin tane ta yi, sallah sanan ta nufa dakin su Ihsane tashin su ta yi, suka yi sallah sannan suka yi shirin tafiya Islamiya suna fita ita kuma ta fara aiki gidanta sai da ta fara dora girki sannan ta gyara ko'ina ta yi, Mooping tana gamawa ta je ta yi wanka ta shirya tsaf da ita kamar wata matar gwamna ,tana nan zaune Aka Kira Mangariba Hakan ya sa ta shi tai  sallah ta dauko kur'ani ta fara karantawa,'' har Aka yi isha'i sannan ta maida sallah ta ta saké gyara fuskanta ,sai 9h30 ,sannan ta ji Horn din Saïf ,'' Mikewa ta yi ta fita fuskarta dauke da Murmushin tana jiran fitowarsa ,'' su Ihsane ne suka fara fitowa suka rigo suna Momy ! Momy ! Hannu ta saka ta tarbe su tana shafa kansu ta ce'' Ihsane shi ne ba ku sanarwa Kuka tafi gidan Kaka kuma sai yanzu Za ku Dawo.''

a shagwafe Ihsane ta ce''Aunty Salma ce Ta zo daukarsu Muhusine shi ne Muka tafi a tare.''

To?" Shi ke nan ku je ku cire Uniforme dinku ,ku watsa ruwa sai ku fito ku ci abinci .'' 

Nabila ce ta yatsine fuska ta ce'' ni dai ba na jin  yunwa dan Mun ci abinci a gidan Kaka .''

 Murmushi ta yi , ta ce'' Na ji dama ba son cin  abinci kike yi ba ,sai ki kwanta dan gobe akwaye École ko,'' Dakin suka wuce ,'' ita ko ta nufa Motar Saïf ,tana Tafiya Mai daukar hankali har ta karasa ta Budé kofar ,'' wani sanyanyen Murmushi ya yi ,Mata Yana janyo ta , ya daura kan cinyarsa ,'' Kallon ta ya yi, ya ce'' Matar Saïf Irin wanan kyau Haka wanka ya bi jiki yar kwalisa ta .''

 kwanciya ta yi ,a kirjin shi ta ce'' barka da zuwa sanyin idaniyata .'' 

Murmushi saïf ya yi , ya ce'' Yawa Mn cœur ya gida .'' 

A shagwafe Aïsha ta ce'' babu dadi Mijina ,'' Me ya sa ?'' 

Saboda farinciki na Yana yin nisa da ni amma in da Naji dadi Yana kullawa dani har Naji Muryarsa a Waya hankali na ya kwanciya.'' 

cikin dan Yana yin damuwa ya Saïf ya ce'' Sorry kin ji Matar Saïf duk in da nake hankali na kanki Bada son Raina nake barin gidan nan ba ko dan na din ga kallon kyakkyawar fuskarki da sanyayen kamshin turaren jikinki Dana gidanki kina aika min da dadar Maganar ki Irin ta soyyaya mai kwantar min da hankali .'' 

sai da Aïsha ta rausayar da Ido  ta ce'' Mon amour Muje ka huta da Alama ka gaji sosai .'' 

kamar kin sani Amarya ta ,'' dagowa ta yi ,ta kallesa ta ce'' Amarya kuma Haba Mn cœur ,'' Dagaske nake ,'' yar dariya Aïsha ta yi ,ta ce'' an jima idan mun fata ka ce min tsohuwa ko ,''dariya Saïf ya yi , ya ce'' ai da Wasa nake maki .'' 

Ido cikin Ido take kallonsa a shagwafe Aïsha ta ce'' ko? "

 Shi ma kallonta ya ke  ya ce'' Allah ma kuwa ,'' dan hararen wasa Aïsha ta yi , Masa ta ce'' hmm To? ''  Muje .'' 

saukowa ta yi , sanan shima ya fito hannunsa cikin na juna suka shigo falon ,'' yaransu na zaune Ihsane na rike da Book a hannunta tana lesson ,Nabila kuma tana Wasa da Wayar Aïsha ,'' basu damu da ganinsu da Suka yi hannunayensa rike da juna dan sunsa ba da Hakan kuma baya damunsu ,'' daki ya huce yabar Aïsha dan zuba ma su Ihsane abinci kafin ya fito ,'' Ihsane ce tai saurin cewa ,Momy Bafa da yawa Za ki zuba ba ,'' To? '' Aïsha ta fada ta zuba mata daidai yanda zata iya cinye ta ce'' Ajiyar zuciya Aïsha ta sauke ta ce'' ki sauri ki ci abinci ki min récitant lesson din ki kuje ku kwanta ,'' To Momy ?"  Ihsane ta fada Tare da saka hannunta a plate din.''


Horn din Babur din sa ta ji ,cike da kunya da san yin jiki ta fita dan Budé masa kofar ,tana isa ta Budé masa ita duka ,sai da ya kalleta dan Mamaki sanan ya fara kiciniyar shigowa da Mashin din sa .'' 

ajiye zuciya Bassira ta sauke ta ce'' Abban Khairat barka da dahowa .'' 

yawa Ya fada Yana kallonta yanda ta yi ,kyau ta gyara jikinta sai kace sabuwar Amarya ,Mamaki bai bar Fuskar Sani ba ya ji tana kokarin Amsar abin hannunsa Tana sakar masa Murmushi.''

 ta ce'' Abban Khairat yau da Alama ta kwaso gajiya sosai ko Muje ka yi , wanka sai ka zo Ka ci abinci .''

 Kamar Mai koyan Magana Sani  ya ce'' To ?''  Muje ,'' ita ta fara tafiya ta shi go falon sanan shima ya Mara mata baya dan sai da ya parking din Babur din sa ,'' da sallama a bakinsa ya shi go , tana zaune 1st ,ta Amsa masa ,Yana shigowa har zai zauna.''

Bassira ta ce'' A'a ba Haka Muka yi da kai ba fa ,'' Murmushi ya yi, Yana Sosa keyarsa ya Mike ta nufa dakin ,bai wani juma ba ya fito ,nan ta zuba masa abinci ta ajiye gabansa yau kam komai na kan table sai de ta dauko ta zuba masa ta mayar ta ajiye ,ga daki sai kamshi ya ke  shararawa ,ganin Hakan sai ya ji dadi a ransa ya ji abincin yafi na kullum dadi sosai ya kwashi girki kamar Wanda ya yi ,shekaru bai ci abinci ba ,'' Bassira na zaune har sai da ya Kammalla sanan ta dubesa.''ta ce'' Abban Khairat , juyowa ya yi, Yana kallonta,'' kamar zata yi Kuka.''

 ta ce'' dan Allah ka yi hakuri bisa kan abin da na yi maka nasan ni ce ke hadasa komai a gidan nan sabida rashin hakuri na dan ina ganin bai kama ta a ce na tambayeka abin da ya karfinka ba amma kasa yi man shi ,shi ya sa?'' amma in sha Allah zan gyara ,'' wata iriyar sanyanyar ajiyar zuciya Sani  ya sauke wani farin ciki na kara ziyarta zuciyarsa ya ce'' Baseera ki fahimce ni idan har kin ga na Hanaki Abu to kin yi mai isarki ne ki yi , la'akari da cewa kullum sai kin fita kuma ba wani waje mai mahinmanci ba sai biki kullum ke Za ki biki wata ranar ma Haka Zaki fice ban san kin fita ba amma kawai sai in share wasu matan basu isa Sun fita ba tare da izinin Mijinsu ba Ba dan suna tsoronsu ko suna jin kansu wasu Iri daidai da Makauta zasu tafi sai Sun Sanar dasu ,wasu kuma basu sanarwa dan Yana cikin Anguwane amma koda Mahaifiyarsu ba tada lafiya suna tsoron Su hau abin hawa amma gudun samun Matsala sai Sun Sanar da Mijinsu koda suna tunanin baza su bar su fitan ba ,amma ke Hakan Za ki fita cikin anguwa ki yi yawon ki in Za ki fita ma sai kin ga dama kike sanar dani ,shi ya sa ?" 

da Kika tambayeni wanan na ce maki A'a' amma ba nayi Hakan dan Ranki ya bace ba kawai sai da ki samu ki huta da kwanciyar hankali amma hanakin dana yi sai kike ganin fata maki rai na yi. ''

 Cikin Yana yin damuwa Bassira To Na ji ? " Ka yi hakuri ba zan sake ba ta fada a shagawfe .''

 Murmushi ya yi , ya ce'' Ashe zamu sha Soyyaya a yau din nan ko ,'' Murmushi ta yi , tare da sunkuyar da Kai Alamar jin kunya .''

Bayan Sun gama sallah ne Ilham ta ce'' Intee na bara na zuba mana abinci ki ci sai in baki magani.''  

Inteesar ta ce'' A'a ni gaskiya ba zan ci abinci Mama ba a yau Abu mai dadi nake so ,Ta fada cikin yana yin Maganar ta .'' 

Ilham ta ce'' kaji wata sabuwa ,To me zaki ci?" 

Kifi nake son ci kuma idan bansamu ba zan Mutu.'' 


  Ido Ilham ta fido ta ce'' Intee na kin san me kike fada rashin cin kifin ne zai sa ki Mutu.''

 Inteesar ta ce'' wallahi dagaske nake Aunty dan sabida ,Ammi ta zo ta nemi Mama da fada Amma Bata biye tata ba sai ita ka dai tai ta zuba kamar yayan ka danya ,shine na Bata Hakuri ,juyowa ta yi, ta kalleni ta ce'' ke nakasashiya Bada ke nake ba da uwarki nake ina magana masu lafiya ba irinki ba kamar wata Sakarai ,kuma Wallahi Kika kara magana ko Kika nemi Abu Kika rasa koma minene to Zaki Mutu shi ya sa na ce maki Mutuwa zan yi ta Kare she maganar kamar zata yi Kuka ,'' sosai maganar Inteesar ta daga hankalin Ilham.''

 ta ce'' Me ya sa ? "baki Sanar dani ba .''

 Kai Mama ta ce Karna Fadamaki kuma Yanzun ma ki yi shuru kar taji .''

 Ilham ta ce''  To ? '' Na ji bara na je in sayomaki dama ina son zuwa gidansu Ummulhair bara sai Na Kira Safiya Muje a tare .'' 

 Tom ? Amma dan Allah karki juma dan kar in mutu .'' 

cike da tausayin kanwarta ta ta ce'' Intee na babu abin da zai samu bawa idan Allah bai K'ADDARA masa zai faru da shi ba ,babu Wanda ya isa Yaga bayanka sai idan Allah ya yi ,nufi lokacin Mutuwarki ne yazo ba ,sanan Ammi Bata isa ta ka sheki 
Ki ba Tun da rayuwarki ba'a hannunta ta ke ba ki kwantar da hankalinki kin ji bara na ta shi yanzun nan zan Dawo .'''
10/03/2022 à 09:19 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

18📓


Fitowa suka yi a tare in da Suka tarar da Mama zaune Akan 3st tana jan tarbi,'' kallon su Mama ta yi ,ta ce'' Ilham ina zuwa Haka yanzu .''

Mama zan je gidansu Ummulhair ne daga tsan zan huce na siyoma Intee na Kifi dan ta ce'' Baza ta ci abinci kin ba.'''

"Inteesar manya wai kuma da Abin da Kika zo da shi kuma, to ki hanzarta ki yi ,ki Dawo kafin Dadynku ya shigo.''

Kai Mama ki ce ma na Bari ya rigani shigowa da bacci bakin hanya ya kamani doli.''

Mama ta ce'' Ah to ?" Wanan kuma ku ta shafa ,'' har Ilham za ta yi ,Magana Inteesar ta yi sauri cewa Auntyna ki sauri Karna Mutu .''

Kallon ta Maman ta yi, ta ce'' Inteesar Bana Hanaki wanan maganar ba.''

To?'' Mama ai Ammi ce ta ce'' zan Mutu , sai da Mama ta kalli Ilham sanan ta maido duban ta sannan ta ce'' Kar n'a sake jin wanan maganar kin ji ko .''

''Mama dama Ammi Tazo gidan nan ne.''

Kin ga Ilham ki Maza ki je ki dawo Bana son surutun Banza .''

Bata ce komai ba ta fice daga gidan sai da ta Kira Safiya Bayan ta dauka ta ce'' Aminiya Zaki je gidansu Ummulhair ne .''

E'e To?" Yanzu ma na ke son ta fiya , ki fito gani nan zuwa ,'' Ok Aminiya sai kin zo .'' 

katse Wayar ta yi , lokacin da ta iso kusan Motar ,'' shiga ta yi ,tare da yi mata Key , Mai gadi ya Bude mata get din , sai da Tazo Daf da zata fita ta tsaye ta ce'' Baba mai gadi ina Aliyu ya ke ne ,'' Yana dakinsa Hajiya ,'' To? " Ka yi ,masa magana zamu fita tare zai kawo ma Inteesar sako ,'' Ahan yanzu kuwa ,'' dakin Aliyu ya nufa Jum kadan ya Dawo Tare da shi ,sai da ya gaishe da ita Sannan ta masa Izinin shiga Motar ,ya shiga sannan ta tashi ta suka fice daga gidan,''' sai da Suka fara Ta fiya kofar gidansu Safiya sanan suka huce sayan Kifi sai da ta siyama Inteesar ita da Aliyu sanan ta ba shi kudin Napep ya tafi gida su kuma suka huce gidansu Ummulhair ,''sun dan yi ta fiya mai Nisa sanan suka iso gidan parking ta yi ,sannan suka huce ciki Mutane ne barjik a gidan dan har sai ka tsallaka zaka samu har ya hucewa a Hakan har suka Karasa inda su Ummulhair din suke Ita da sauran kawayensu,'' da sallama a bakinsu suka shiga Ummulhair na ganin Ilham ta watso mata harara tana fadin 

Hmm Marar Kirki sai yau Kika ga damar zuwa ne .''

Murmushi Ilham ta yi , ta ce'' Sorry kawata kin san bani da dama kawanan aiki ya sha min Kai sai gobe ka dai nake hutu .''

Kina aikin ne kike hawa on ligne ne .'' 

Niii ?" Ta fada tana fido Ido ta ce'' wallahi Wi-Fi ne na wajen aikin mu kin san ni ke karfan jinyar Alhaji na gidansu Safiya .'' 

Haba ni fa na ce ina ta yimaki Texte Message baki dubawa shi yasa rai na ya kara baci .''

To ? " Ya dai na tun da gani gabanki ko .''

Da'ifa dake zaune gefen Arufa ta ce'' Hmm ai ke Ummulhair kiji dadin ki ma tunda Ilham Tazo bikin ki ni nan ko leke babu bare in sama ran zata zo .''

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' Kai Da'ifa amma kin san na baki Uzuri na ko .''

Arufa dake sauraransu tana cin indomi ta ce'' ai ke dama shiru Kuka yi in dai Ilham ce ba Zaku gaji da jin korafi ba .''

To Allah ya Huci zuciyarku kawayena ina neman Afuwa cewar Ilham din .'' 

shikenan kuzo muyi abin da ya kawo mu ,''

 ta fiya ma zamu yi ai cewar Ilham ,'' Me yasa ?" Hmm ko wajen zama babu  da ga shi gowa Kuka fara mani ruwan masifa na korafinku .'' 

Allah Huci zuciyarki yallabiya ga wajen zama ai cewar Arufa .''

Zauna wa suka yi nan suka fara dasa wata sabuwar fira suna raha sai shewarsu kake ji , suna ciki Hakan ne Abokin Ango ya ya Kira Sayyada bayan ta dauka ne ya ce'' su fito zasu basu kudin damu ,'' to gamu nan fi towa yanzu,'' katse Kiran ya yi,'' ita ko Sayyada ta ce'' Ilham ke da Safiya ku ta so mu je Abokan Ango na waje ,'' 

Kallon ta Ilham ta yi, ta ce'' me zan je in masu ,'' Wallahi sai kin je koda baza ki masu wani Abun ba bare ma Ba'a rasa abin yi ba ,'' Tom ,'' ta shi Mu je ,'' Mikewa suka yi suka fita a tare sai kofar gidansu Ummulhair ,'' wajen wasu hadadin Motoci suka nufa guda biyu da sallama dauke a bakinsu ,'' Amsawa suka yi ,Bayan Sun gaisa ne Kabir ya dauko kudin ya Mika mata amma hankalinsa na wajen Ilham sai kallon ta yake ,'' Sayyada ce ta ce'' ya Haka kuma Kabir ai ba Haka Muka yi daku dan Haka ba zamu Karba ba ,'' To ki karbi wanan zuwa gobe zai mu baku cikon .''

Ko? " Kubarsu a hannunku zuwa goben sai ku Bamu baki day .''

Sun jima suna ta Abu day sai Safiya da ke tayasu amma Ilham ko hmm Bata ce ,'' jin Bata da niyar magana ne ya sa kabir cewa wai ita wanan Bata magana ne .''

E'e kasan jikan kurame ya aure ta me zata baka idan ta yi magana ne.''

Me ya yi ,zafi shi ba huta ba tambaya kawai na yi ,kuma ba wani Abu bane dan nace ta bani zuciyar ta .''

Kallon ta Safiya ta yi, ta ce'' To? " Ke kin ji Ilham ki ba shi zuciyarki .''

Cikin tautausar muryar ta ta ce'' Ni zuciya ta ba sadakan ta nake bayarwa bare ka dauka ai kuma tana tsan shimfide tana bacci a in da ya dace .''

Murmushi ya yi, ya ce'' Ah ina ne ya dace da ita ne.''

Wajen Wanda ta dace .''

Ah ina Kenan ,'' To? " Ka ji wani karfin hali ina ruwanka da Wanda ya dace da ita kuma .''

Tana gama fadan Haka ta shigewar ta ciki ta bar su nan ,'' kallon Safiya ya yi , ya ce'' wallahi kawarku tatafi da ni dan girman Allah ku taimakamin da lambarta ,'' babu ruwan mu me yasa baka Amsa wajen ta ba .''

Kar Kuja wanan zantsen Da girman Allah ai na hada ku ko ,'' to sai ku karasa biyan kudaden zamu bayar ,'' babu musa ya dauko cikon kudin ya basu ,su kuma suka ba shi lambar , sallama suka yi masu Sanan suka shi ga daga ciki ,suma suka yi tafiyarsu .''

Suna Chiga suka tarar dasu sai shakar fira suke hankali kwance ,''safiya ce ta ce'' Ilham Haka sai kije ki kyalemu ki shigowarki ,'' To ? " Ai dama sai da nace ma ku bazan je ba Kuka matsa dan na san babu abin da zan yi ma ku .''

In ji wa ya  ce'' ke ko Kika mana an fani dan lambarki ta taimaka Sun Bamu cikon kudin nan .''

Ban gane ba ,'' za ki gane ai in Kika ji Kira yanzu .'' 

Kin ga ni ta shi Mu tafi 21h40 Dady ya ku san shigowa .'' Muje ai dama dare ya soma yi .''

Sallama suka yi masu suka koma gida sai da ta ajiye Safiya ,'' fi towa ta yi ,tana cewa Aminiya gobe wane lokaci zamu tafi ne .''

Idan na Kammalla abin da nake kafin daurin auren sai Muje ko.''

shi ke nan Allah ya Nuna mana goben lafiya ,'' amine .''

Suna nan suna fira Musa Abul Khair ya fito ganin Shiru Safiya Bata  Dawo ba,'' har zai fara mata masifa sai ya gan ta ,Ashe ita da Ilham lumshe Idonsa ya yi ,Yana karasawa wajensu ,sallama ya masa ,suka amsa yau kam Ilham da sakin fuska suka gaisa ,shima kuma sosai ya ji dadin Haka ,'' kallon Agogon hannun ta ta yi ,

ta ce'' kai Ashe na jima a wajen nan gidan zan fita Dady Yana hanya sai da safe ,tafa da a nutse.''

Gaskiya kam ya kama ga sai da safe .''

***************

Sai da ta karasa cin sanan ta yi ,récitant lesson din ta suka shige dakinsu dan yi bacci kamar yanda Momynsu ta Umarce su ,tana nan zaune Saïf ya fito kusan ta ya zauna Yana jenyo ta jikinsa ,ita ko ta Laye kamar Bata a wajen ,'' cike da Yana yin damuwa ya ce'' Matar Saïf Me ya sa me ki ?" Duk kin yi san yi .''

Babu komai,'' ta fada tana Mike wa ta dauko plate din abinci tazo gabansa ta fara ba shi a baki , hankalinsa na kan ta ya matsu ya ji damuwar ta ,sai da ya Kammalla cin abinci ya sha jus din da ta hada masa sanan ya kalle ta ya ce''  Matar Saïf kina son ganina cikin damuwar ne ." 

A'a Me ya faru ne ?" Bana jin dadi ina ganin ki cikin damuwa ne ki fadamin ita in sha Allah zan yi iya kokari na dan magance maki ita .''

A shagwafe ta fada jikinsa tana Kukan chagwafa ta ce'' Mon Cœur na yi kewa ne .''

Kewar me matar Saïf.''

Gida mana yau kusan Shekara uku Rabo na da garin *Maradi* tun haihuwar Nabila fa .''

Hakane matar Saïf ai kin yi kokari ma ba kamar lokacin da kina Yan mata ba Motsi ka dan sai ki ce Mon Cœur dan Allah zan je Maradi na duba Mama da su Inteesar in ga yanda jikin ta yake ,ya yi , maganar Yana kwaikwayon Yan da take yi .''

Dukan wasa ta kaima sa ta ce'' Yanzu kuma ni tsohuwa ce ko .''

Kai ni bance ba ai ke kullum kara zama kike Yan mata .''

Murmushi ta yi ,ta ce'' To ya za'ayi da karatun su Ihsane .''

Zan je Makarantan su sai Na fada masu zasu yi ta fiya ne .''

Hakan ma ya yi ,to yaushe zamu Dawo ne .'' 

Zaku yi wata day ne dan ku ga gari shima ya Ganku .''

Cike da zolaya ta ce'' Na zata zaka ce wata biyu.''

Kai in kama wa  A'a wallahi wata day ma hakuri zan yi kawai dan kin juma rabonki da gidan .''

Wasa fa nake ma.'' dan kunnenta ya ja Yana cewa bakijin magana ko .Naw

Sorry mai gida na daina ta fada tana dora hannun ta saman n'a shi hannun Wanda ke wajen kunnenta ,'' janye hannunsa ya yi , ya ce'' t shi mu ji mu kwanta bacci na ke ji.''

To Muje tafa da har ta shi tsaye kuma sai ta zauna ta ce'' ni dai kaffafiya na zafi suke man ni goyani zaka yi .''

Babu musu ya duka ita ko ta Haye Bayan suka yi dakinsu sai da ya shimfide a hankali sanan ta kashe hutar ya jama masu bargo suka yi baccinsu .''
15/03/2022 à 00:04 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

{{YAR LELEN NOBLE ce}}

19📓

WASHEGARI

Bassira na tashi sallah Asuba Bata koma bacci ba sai da ta hada abin break sannan ta jera Bisa dan karamin Table din dake Tsakiyar Capet din ta sannan ta je ,ta yi wanka Wata yar doguwar Riga wace da Bata gama sauka har kasa ba ta saka turare sannan ta nufa in da Sani yake cike da ladabi ta fara Ta shinsa lumsasun idonsa ya Bude a hankali .''

Murmushi ta yi , ta ce'' ina kwana Ruhi na ,'' sai da ya sake murza idanuwansa dan tabbatarda da gaske Bassira ce ko dai Mafarki ya ke , gani da gaske ne ya sashi cewa 

Lafiya lau Rahi na.'' to Haka na keso ai ka ta shi na shirya ma break din ka na jiranka a table .''

Wani Irin Murmushi jin dadi ya yi , ya ce''  To? " Na gode ganin zuwa amma ina Khairat ta ke ne .''

Zuci tana bacci ka ga ai jiya Bata yi bacci ta huri ba .'' 

Cewa Za ki yi jiya ta Hana mu shakata sai da ta yi , bacci. ''

Murmushi ta yi , ta ce'' ka tashi mana Bana son ka Makara aiki.'' 

 shi ne kike kawar da maganar da nake maki wai ke kunya ki ji ni da kyau yau Khairat za ta yi kanne ko kanwa .''

Wanan maganar ta ku ce ta manya ni dai ba ruwa na .''

Ni dawa Mike maganar  nan ne .''

Sai da ta wainar da Ido ta ce'' ni da mijina mana .''

Dariya ya yi , ya ce'' To?" Bara mu fara daga yanzu .''

Iyeeh ta fada tana fita daga dakin,'' Murmushi ya yi , Yana cewa Ruhi na ba za ki Dawo ba zo ki ji wani Abu .''

Na kiya idan ka fito sai ka Sanar dani .''

Ganin baza ta Dawo ba ya sa shi tashi ya nufi toilet .'''

Bayan ta gama sallah ne ta sauko ka sa Kai tsaye Kithchen ta shiga Ta tarar da Mama tana hada breakfast ,''da Murmushi a fuskan ta ta ce'' Mama ke dai kike aiki babu sanarwa .''

A'a Ilham Na hutar dake Allah ya maki Albarka .''

Amine Mama amma ki je ki huta zan Kari sa sauran .''

To ?" Amma kar ki gyara danning Inteesar ta rigaki.''

Kai yau wace Rana Inteesar ta rigani ta shi har da su kama jera abinci a danning .''

To Na dai fadamaki in ba so kike ta aza mana Ti jara ba .''

Allah ya sa kar in manta ,'' ni dai ba ruwana tsakaninku ne .''

Murmushi ta yi , Ta fara aikin ta .''

Yau tun da sassafa koda tata shi Saïf bayanan zaton ta ya tafi motsa jiki dan Haka ta fara shirya masu breakfast ,Awaran kuskus ne sai soyayan dankali da kaza sai jus de fruit ,tana Kammallawa ta ajiye a danninga ta huce toilet ta yi ,wanka ta shirya su Ihsane sanan suka Dawo falo zamansu ke da huya sai ga Saïf ya shigo fuskarsa dauke da Murmushi ya nufi inda take ya rumgume tare da yaransu .'' 

Murmushi ita ma ta yi, ta ce'' Mon Cœur c'est comment .'' 

Nasan Kika ji wanan Albichirin din sai kinfi ni jin dadi yau na kara samun Karin girma a office din mu Hakan ya sa kema dan mu ta ya juna farin ciki na nema maki visa yau din nan ma Zaku shi ga jirgi ku je Maradi .'' 

Cike da farin ciki ta ce'' Thank you soo much Mon Cœur ta fada tana kara kankanme shi Na gode sosai wanan baza ta Haka .'' 

Karki damu Matar Saïf indan baki ji dadi ba ke da yarana wa kike son ya ji kina iya bakin kokarinki ganin kin sakani farin ciki ni me zai Hana na Murmushi a saman wanan kyaukyauwan fuskan ta ki matsayinki gareni ya huce ki nemi Abu a waje na kuma na san bai fi karfina ba Amma na ka sa yi maki shi ba .''

Walahi ka sani farin ciki sosai da sosai Allah yakara Bude na Alkairi amma na yi Mamakin daka samu visa a kuraren lokaci.'' 

Amine matar Saïf wani aboki na ne dake airppot na nemi Alfarma wajensa shine yamin shi Na wani Mutume da zai yi ta fiya ya fasa kuma a yau zai yi ta .''

Na gode ban san da wane bakin ma zan ma godiya ba.''

To ?" Ki je ku shirya an jima ka dan zamu ta fiya airppot din.''

To? " Momy ina zamu tafi ne yau kuma cewar Nabila .''

Gidan Mama Ihsane ta fada ta ci gaba da cewa kuma a Maradi ya ke.''

To ? Ina ne Maradi kuma gidan wace Mama .''

Cike da yarinta ta ce'' Kaka ta wajen Mama mana dama aike baki san ta ba kuma in fada maki Aunty Ilham tana da kirki sosai kullum sai ta bani shocolat da biscuit kuma ta kaini *Kalla transa Mall* ta yi ,mani sayaya sosai wani lokacin har *kalla transa couture* Nake Raka ta.'' 

Kai nima zan so in je kodan a siyamani shocolat da biscuit 🍪 din.''

Hmm Yanzu Nabila dama kwadayi zai kai ki ,to? " Zan ce ma Aunty kar ta sai maki .''

Dariya su Saïf suka yi Aïsha na cewa Bana son surutu kuzo ku yi Break mu yi ta ta fiya ko .''

To? " Mama suka fada a tare sannan ta zuba masu abinci su dukansu suka zauna suka ci sanan ta hada masu kayansu da duk abin bukata tare da Saïf duk suka hadasu sannan suka fito daga sai Airppot ,suna isa suka dan zauna kafin lokaci ya yi , sun Kai Awa day da Rabi sanan Aka Kira sunansu suka tashi kamar karsu rabu da juna amma a Haka suka shige jirgi sai da Yaga tashinsu sannan ya koma gida.''

Tana gamawa ta jera bisa daning table ta shirya shi tsaf dan ta manta sam da batun Inteesar ta gamawa tsaf ta nufi wajen Mama ta ce'' Mama na Kammalla .'' 

Kira Inteesar ta gyara danning din ,'' sai da ta fido Ido ta ce'' ai Mama na manta har na gama ai .''

Amma Ilham kin iya shegenta ka babu ruwa ko rabon fada bazan yi ba .'' 

Inteesar ce ta sauko tana fadin Mama wai har yanzu baki karasa girkin ba ne .''
 
Ilham ce ta kalle ta ta ce'' tun dazun an gama Har ma na shirya daning .''

Turo baki gaba ta yi ta kara langabar da kanta tare da fa shewa da Kuka ta ce'' ni Wallahi sai kin biya ni Mama bani na ce zan yi ba .''

To ka ji wata sabuwa Kuma Mama kin ga yanda kike fata ta da shagwafa ko .''

Dariya Mama ta yi, ta ce'' Ilham manya ke a kwaye Wanda ya kamo ki wajen shagwafa ne ni dai na fadamaki babu ruwana daki ma zan shiga .''

Dariyar ta ta gumtse ta ce'' Intee na ta so na girka maki Abu mai dadi naki ne na musanman har da Kifi a ciki.''

Mama ce dan ta kara hasa hutar ta ce'' ai har gulmanki ta yi ,tana cewa wai kin rigata tashi daga bacci yau.''

Ai ko ta fadi kasa ta fara harba kafafu tana birgima a ka sa sai ihu take .'' 

Dariya Mama ta yi ,ta ce'' baza ki hada ta da Dady ba .''

Ilham ko shiru ta yi , dan ta rasa Abun yi ,'' jin Mama ta ce '' Haka ya sa Inteesar kafka ihu tana Kiran Dady ! Wayoo Dady!  

Dady dake dakinsa yana aiki da computer ya ji ihun Inteesar Murmushi ya yi ,  ya ce'' an kwana biyu ba'ayi ba sai yanzu , kashewa ya yi , tare da saukowa ka sa .''

Wajen ta ya nufa Yana cewa Inteesar lafiya Me ya faru .''

Cikin Kuka ta ce'' Dady Ilham ce wai na ce zan yi jere a danning table shine ta je ta yi har da gulma na fa ta ke yi .''

Har Dady zai yi magana suka jiyo sallamar Aïsha ai da gudu Ilham ta nufe ta tare da fadawa jikinta cike da Murna ganin juna suka rumgume junan su .''

Dady da Mama ma fadada Murmushinsu suka yi Dady na cewa Mutane *INGAL* ne tafe.''

 Dady gamu fa ya Mika tarar daku .''

Ah Masha Allah ya gida ya hanya .'' 

Lafiya lau Dadyna nayi missing din ku sosai Mama ta fada a shagwafe .''

Nabila ce ta kalle ta ta ce'' la la la Momy anan din ma sai kin yi Irin abin da kike ma Abbanmu ko.''

Ihsane ne ta ce'' To ?" Uwar surutu tambayarki aka yi me Momy ta yi ,ne .''

Shagwafa mana kullum sai ta yi ,ma Abbanmu .''

Dariya duk suka saka inda Aïsha ke hararan Nabila Wasa ta nufa wajen Mama ganin Irin kallon da Aïsha ke mata .''

Inteesar da ta ga an man ta da Babin ta ya sa ta sake fashewa da wani sabon Kuka .''

Dady ne ya juyo ya ce'' Inteesar kyale ta zan yi maganin ta yanzu kin ji .''

To amma gulmana fa ta yi ,'' Dariya Ilham da Aïsha suka yi mata  Ilham Na yi mata gwalo .'' 

Sake fashewa da Kukan ta yi ,ta ce'' Dady ka gansu suna min Dariya ko kuma Auntyna har da gwalo take man .'' kyale ta autar Dady sai  ta sha duka .''

Saké fachewa suka yi da Dariya ,Mama ta jefe su da Pullo din kujerun falon .'' 

Nan suka yi daki da gudu.''
25/03/2022 à 01:04 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

20📓

Suna shiga suka tsira fira sam Ilham ta man ce da zantsen zuwa gidansu Ummulhair har sai da Safiya ta Kira ta ,tana ganin Kiran ta yi saurin rufe bakin ta tare da daukar Kiran ,

Asalam alaikum Aminiya ya kike .''

Lafiya kalau ya kike kema ina ya jiran ki yanzu Amarya ta kirani wai mu yi sauri kar a barmu zuwa gidan daurin auren.''

To gani nan zuwa kin san Aunty Aïsha ne suka taho yau din shi yasa Kika jini shiru .''

A yoyo ki ce ina mata sannu da zuwa idan mun Dawo daga gidansu Ummulhair zan zo mu gaisa.''

To ba damuwa zata ji in sha Allah.''

To sai kinzo din ,'' tana gama fadan Haka ta katse kiran ,Mikewa Ilham ta yi , ta fada toilet Jum kadan ta fito Ta fara shirya ta dauko yar fondation ta na cikin Murzawa ne ta ce'' Aunty Aïsha ,? Safiya na yi maki sannu da zuwa .''

Wace Safiya Kenan ,'' Kai Aunty ta gidan Ammi Murja .''

To?" Me ya kawo ta ne me take nema wajenki .'' 

Murmushi Ilham ta yi, ta ce'' Alkairi mana Bara dai na Dawo za ki sha labari ta ma ce idan mun Dawo zata zo ta gaishe ki .''

Tafe baki ta yi , ta ce'' Allah ya kaho ta lafiya .''

Amine Ilham ta fada lokacin da take daukar Jakarta da Key din Mota ta ce'' sai dawo ko .''

A Dawo lafiya Aïsha ta fada tana Mikewa suka fito a tare izuwa falo su Dady ne a zaune sai Inteesar dake ta zuba masu shagwafe ita a doli an mata laifi baa Bata Hakuri ba,'' kallon ta Ilham ta yi, ta ce'' Intee ni zan fita me kike bukata .'' 

Hakuri Zaki bani ,'' Dariya Ilham ta yi, ta ce'' shi ka dai kike bukata ,'' gyada mata Kai ta yi ,'' to ?" Allah ha baki hakuri Intee ni zan tafi sai na Dawo .''


 Adawo lafiya suka yi mata Sannan ta fita Kai tsaye motar ta ta nufa Get man ya Budé ma kofa fita ta yi , direct gidansu Safiya ta fara zuwa tana isa ta kirata ,ita ma kamar jira ta ke sai ga ta ta fito ta shiga suka huce.''

Yana fitowa har ta fito masa da kayansa ta goge masa takalminsa da agogo da dai sauransu karasa shirinsa ya yi ,sosai ya yi , kyau musamman da ya samu kullawa fiye da da yake ma kansa komai , fitowa ya yi ,ta zaune a kasan Capet suna wasa ita Khairat ,dan tsugunawa ya yi , irin nasu n'a Maza ya ce''  Ruhina ya Kika ganni .''

Tsaf da Kai kamar yau kafito daga cikin kwalli .''

Wani kayatacen Murmushi ya yi , ta ce'' Zanni gurin daurin auren Abokina daga tsan a dauro nawa.''

Hararen wasa ta Galla masa ta ce'' da baka yi bayani ba ai in dai ka wata a gidan nan to?  " Babu Ni a gidan nan .''

Ina ai ni dake Mutu kara ba takalmin kaza .''

Nima a nawa bangaren sai in mutuwa ce ta rabani da Kai shine ka dai zan amince ka kara aure .''

Allah ya barni ni da yar amana ta .''

Amine mijina ka bar wanan maganar fatamin rai take ka zo muci abinci Zuci yunwa take ji .''

Jenyo Khairat ya yi , ya ce'' Zuci na wai Zaki ci abinci ,'' E'e Papa .'''

Gyara zamansa ya yi , suka fara aika ma cikinsu sakonni .''

Suna isa kofar gidansu Ummulhair ciki suka shiga direct dakin da Amarya take ciki shiga lokacin ne su kuma zasu fita ,'' Ummul ce ta ce'' Ilham sai yanzu da kun iske mun tafiyar mu .''

Wallahi ke dai Bari Aunty ne ta Dawo shi yasa Kika ga na jima ko break ban yi ba na fito .''

To kuje mu tafi ko amma ke a motar da nake Zaki shiga .''

A'a kawata da mota na nazo kuma idan an daura auren gidan zan huce sai kuma da yamma sai na  Dawo .''

To ?" Ba damuwa na zata a daidaita Kika zo yanzu dai mu tafi .''

Fitowa suka yi baki dayansu sai gidan Uncle Mustapha Wanda ya dauka daurin auren.''

Sun dan jima a gidan da yake yau juma'a kuma daurin auren na masallaci ne shi yasa Aka dauki lokaci sai  Bayan an gama sallah ne Aka daura auren aboka arziki sai yima ango barka suke shiko sai Washe baki yake har kunne .''

Ban garan su amarya kuwa tana cikin cin abinci masu yima ta wanka suka zo nan kawayenta suka ta shi tare da rufe kofar  dan boyen amarya suke sai an basu kudi , duk yanda aka yi su Budé Sunki sai da Aka basu 10mille (Jaka goma ) sannan Aka dauki Ummulhair Aka mata wankan turare suka Bata Lafayya ta saka sanan Aka aza mata daran Amare suka yi wajen Uncle Mustapha Wanda ya d'aura auren ta tare da sauran ubaninta suka mata nasiha mai ratsa zuciya da duk sasen jiki sosai abin ya shige Ummulhair har Kuka sai da ta yi , Bayan an gama ne aka fito da ita nan ma uwaye mata suka fadi Albarkacin bakinsu sai da Aka yi Sallah La'asar sanan Aka dauko amarya zuwa gidansu kafin lokacin Kai ta gidan ta ya yi.'' 

Daga gidan Uncle Mustapha Ilham da Safiya suka nufo hanyar gida ,Ilham Muje ki ajiyeni a gida na dauko kayana sai Muje gidanku a tsan zan shirya .''

To? " Babu damuwa amma ki yi sauri ki fito Kar Ammi ta fito ta ganni kema kin san abin da zai biyo baya ai .''

Ke tafi tsan uwar tsoro ,'' E'e Na ji dai Daya ke uwata nake tsoro ba wari ba .''

A lokacin ne suka iso nan ta fita ta shiga ciki ta dan jima kadan sannan ta fito suka huce gidansu Ilham kofar mai gadi ya Budé masu suka shiga sai da ta yi parking sannan suka fito tare da shigewa ciki , babu kowa a falo dan Haka suka huce dakin Ilham nan suka tarar da Aïsha na ta Waya ita sahibinta dan tafkarta a baya Ilham ta yi , ta ce'' To? " Laila & Majnun Wayar ta isa Haka gani na Dawo a katse hakanan.''

Mikewa zaune ta yi , tana banka mata harara ta ce'' rigimamiya kin Dawo dan ki shamin Kai ko .''

E'e Na ji komai Zaki ce a kashe Waya dai .''

To uwar me zan maki ne ,'' fira zamu yi mana.''

Sai in bar wacce nake yi fa mijina dan mu yi daku, to Bazan iya ba ?".

Karban Wayar ta yi da karfi tare da karawa a kunne ta ce'' Yaya Saïf abar soyayyar Hakanan wacce Kuka sha a gida Bata isa ba kuma Tazo nan baza ka Ba ri ta Bamu lokacinta .''

Dariya ya yi , ya ce'' Allah ya huce zuciyarki Amarya ta ke fa na kira ta ce'' ba kyanan kin fita amma ai baki Sanar da ni ba .''

To to zaka fara Kenan ." Ai baka san wani Labari .''

To ba ni in sha ,'' ni yanzu na yi sabon saurayi hadade kyaukyawa Wanda yafika kyau sosai dan Haka ba zan yi auren da Kai ba.''

Tab yo kin ma isa ai ni dake har Abada .'' 

Kai de kaji da tsufanka bazan aure ka ba Kai ta ja da Auntyna .''

Dariya ya yi,sosai ya ce'' Ilham sarakan rigima har yanzu kina nan yanda kike .''

A'a Kai ma ka san Bana baza ta taba zama bara ba kawai dai ina ma mijina shagwafa ne ta fada tana Satan kallon Aïsha.''

Yau wa Amarya ta Ashe dai har yanzu ina cikin zuciyarki ko .''

Da sauri Aïshata karfe Wayar ta tana cewa Bana son Iskanci Ilham .''

Da karfi ta ce'' rabin raina si love you .''

Ita ma Aïsha da sauri ta kashe Wayar ta ce'' ke dai Kika sani Ilham ni yanzu kin bar bani wahala .''

Dariya ta yi, tana mata Chakulkulu ta ce'' ai de yafi sona .''

nan dai su ka yi ta raha tsaninsu har da Safiya tana goyan bayan Aïsha suna cikin wanan ne Wayar Ilham ta yi kara Alamar shigowar Sakko ta wattsapp , dauka ta yi tare da duba wa nan  dukansu suka zauna a saman bed din suna dan tafa fira ita ko Ilham dan tsoma baki take idan ta yi , Replay din Message din.''

Aminci Allah ya tabatar a gareki sinadarin rayuwata ❤️.''

Wa'alaikum salam na gode wake magana .''

Kabir ne Wanda Kuka hadu jiya gidansu Ummulhair .''

Ok banga ne ba Wallahi ko zan iya ganin photo naka .''

To ba damuwa yanzu ko ai girmanki ne ki ne Abu doli ki samu 😍.''

Hmm ina jira😎.''

Har zata ajiyar Wayar taji shigowar Sako duba wa ta yi , tana gani ta bushe da Wata iriyar dariya wacce ta saka su Safiya katse firan da suke suka juyo suna tambayar lafiya ,saké fashewa ta yi ,da wata sabuwar dariyar ta ce'' Wai Wanda Kika basa lambana ne ya min texte Bayan mun gaisa nace ya turomani Photonsa shine ya turo sai na gansa kamar wani jemagen😂 a tare suka sake saka wata Dariya .''

Wallahi ko ai in fadamaki bazan kara mai da masa ba message ba 😂

Wallahi wanan matar kin iya sherance mutume wai kamar jemage 😂wayoo cikina cewar Aïsha.''

Safiya ta ce'' kawai ga lambar shi kisa ma shi  jemage ta fada tana Dariya ta ci gaba da cewa Haba ke ko ki maida masa message din sa mana har Yan kallaman soyayyar nan masu kwantar da hankali .''

Hararen ta yi ,ta ce'' To,? " Wallahi Bana son Iskanci tsiyar me zan ci da lambar shi .''

Taimakonki mana zai yi kin samu santalalen saurayi kina kushesa kuma nake ganin zai fi Abul Khair haduwa 😎.''

Kam bala'i Wallahi Aminiya karki Bari in kamana ki dan sai na maki tsarki da Attarugu.''

Tab da tatasai sai yafi nake gani.''

Aïsha ta ce'' da ko ta kashe ki .''

Allah dai ya shiyeki Ilham cewar Safiya .''

Ya dai shiryemu baki day.'' 

Nan dai su ka yi, ta zuba surutu suna Dariya sosai suke raha .''
25/03/2022 à 09:22 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

21📓

{ƳAR  LELEN NOBLE}


Sun jima zaune suna ta shan fira kafin suka ta shi dan fara shirin tafiƴa gidansu Ummulhair sosai Safiƴa ta ci Make up ta ƴi ,kyau dan ita ma Safiƴa ɓa ɓaya ba wajen iƴa daukar wanka Ilham kuma babu ɓaɓu abin ɗa ta ƴi sai ƴar foda da ta shafa kuma shi ma sai da Safiƴa da Aïsha suka matsa mata sai ɗa suka sha photos sannan suka fita ɗaga gidan bayan sun ƴima Mama Sallama a wanan karon Safiƴa ce ke tukin Motar suna Cikin tafiƴa suna fira Ilham ta ji shigowar sakko Har biyu a waƴar ta na farko Kabir ne wanɗa ta saka mashi suna jemage ,na karshe kuma ɓata nan lamɓar ɓa na kaɓir ta fara duba Murmushi ta yi ,

 ta ce" Ke Aminiya Wallahi wanan mutumen da kika hada ni da shi ya fara ta kura ni  sai ka ce uɓa na wai ƴana jirana In sauki In taho wajen biki kar ƴa ya mutu dan idan bai ƴi to zali da kyukyawar fuska na ba  kwaƴe matsala."

Dariƴa Safiƴa ta ƴi , ta ce" wanan kuma babu ruwa na ."

Ohh haka m zaki ce ko ki hada ni da wanan masifar kike cewa wai babu ruwanki ."

To ? "Ni me zan ce so kike In sake cewa wani abun ki mani tsarki da atarugun." 

Ke nifa matsala ta dake baki da mantuwa wasa fa nake ."

Hmmm Allah ɓa zance komai ɓa fa ." 

Na ji babu damuwa nima zan rama ai ."

Shiru suka ƴi In da Ilham ta duba day message din kamar haka " Asalam Alaikum Matata ta goɓe da fatan kin huni Cikin koshin lafiƴa ."

lafiƴa lau Amma ni a sanina bani da igiyar kowa a kaina ." 

Injiwa ya ce ni ba mijinki bane ?"..

Dan Allah da wa nake magana." 

Ton Halal surelƴ, I realƴ love ƴou ,and I want be your Husband forever , be with me pls." 

Wani kayatacen Murmushi ta ƴi ," barka da zuwa fadar lambun soyayya mai Cike da tarin furenni masu matikar Kamshi da dadi shaka a duniƴar masoya ." Ta fada tare da tura masa ." 

Na gode sosai da tarban da na samu daga abin ɗa nafi kauna a duniƴa zan so ganin wanan kayataciyar fadar dan na kasance tare da Albi ta furanni masu dadi kmashi da sautin kukan tsutsaye daga wanan fadar ." 

Karka damu ai kai din na musamman ne." 

Matsayinki gareni baa iƴa musulta shi , Allah ƴa barmani ke Ilham hakika ina matikar sonki har hakan ya sa bana ji bana gani sai sautin muryarki ta daki dodon kunne na idanuwa na sunƴi to zali da kyukyawar fuskarki ka dai nake dawowa daidai ." 

In ko hakane ka dauka ka samu danni ta kace kamar ƴanda ka fada ." 

Ji ta ƴi , an karbi wayar da karfi daga hannunta juyowa ta ƴi ,ta ce" ke Aminiya me ye hakane , " hmmm wanan wane irin hulakanci ne muna tare kike ta latse latsen waƴa sai Murmushi kike ke ka dai kin ma manta da ni ." 

Dariƴa Ilham ta ƴi ,ta ce" bar ni love na ke sha kin katsemin nishadi na." 

Sai ki bari idan kin tafi giɗa sai ki ƴi lover lover din Naki ." 

Wallahi ki bani ko insa ayi maki horo mai tsanani yau din nan ." 

To Busmillah ?" Ke dama ba sonsa kike ba shi ka ɗai yake Ta shan wahala ."

Da kenan Safiƴa Amma yanzu ƴan rogo sun ƴi rumfa ina son Abul khair fiye da tunaninki ni kai na bazan iƴa musulta yanda son Abul ya shige ni farat day ne har Mamaki hakan nake ." 

Sarautar ubangiji mana Allah dai ya tabatar mana da Alkairinsa musha biki kai ranar ba taushe hannu ko Aminiya ta ." 

Ina mana fatan hakan koda yaushe amma Abu day ke damuna shine Ammi an zata so hadin  nan kuwa ." 

Dan Allah Ilham ki share Maganar Ammi idan Allah ƴa k'addara Abu babu wanɗa ya isa ya sauya shi ruwa da iska guguwa da hadari ba su isa su Hana wanan lamarin tabbatuwa ."

Allah ƴa sa Amma kin san laifin da Muka ƴi mata ne ,A'a amma lokacin da ta ce min In ta sake ganina dake sai ta ci mutumci na dana tambaƴa dalili wai sai ta ce min sabida Mama ne ya sa duk ta tsani duk ƴan gidanku ." 

Babar magana Allah yaba ta hakuri duk da ban san miƴe sila ba ." 

Ilham ni ina son maganar  ki da Musa kuma zan kasance mai Alfahari duk ranar da kika shigo gidanmu karki tafa tunanin zan sake juyamaki baya duk baki nuna min hakan a fili ba me zai hana ku fito da soyayyar ku kowa ma ƴasani ." 

Ni bani da matsala ga kowa a gidanmu dan Dady ne ka dai har bai san wainar da ake tauyawa ba Amma Mama Tun kafin mu wara soyayya da Abul ta fahimta dan Mama Akwaye lura da saka Ido bisa Kan komai sai de ta kyaleki In ta lura ɓaki son ta sani ita kuma sai ta nuna maki cewa ita fa ta haifi ki ." 


Shiru suka ƴi sakamakon isowa gidan bikin da suka ƴi saukowa suka ƴi bayan sun parking sanan suka shiga gidan lokacin har an shirƴa Amarya za'a kai ta wajen Mahaifanta dan su ƴi mata nasu Nasihar." 


********* Suna gama cin abinci suka dan tafa fira sannan ya mike ya ce" Ruhina ina ga zan tafi Aiki lokaci yana tafiƴa." 

A shagwafe ta mike ta ce" ƴanzu tafiƴa zaka ƴi har yanzu ban gama kyasawa ba Idanuna har yanzu suna muradin son kara ganinka a kusa dani ka jiii Ruhina." 

Gefen fuskarta ya shiga shafawa ya ce" Ruhina babu abin ɗa nake matikar so In ganinki a kusani dani shine ke kara mani farinciki da jin dadi badan ina son fitar nan fa nake ƴi ɓa doli ce ta kamani ," 

To?" Sai da wane lokaci  zaka dawo ne ."

Wanɗa ya kwanta maki a rai ." 

Ka ƴi zamanka shine ya kwanta min sosai ." 

Kiss ya mata a goshi ya ce" to ?" Ayi mani uzuri zan je In dawo bazan jima ba ." 

Murmushi ta ƴi , ta ce" karka damu Ruhina Allah ƴa kawo kasuwa mai albarka ka ƴi aikinka Cikin natsuwa koda yaushe kadawo muna maraba da kai ."

Kin tabata," sosai ma papan khairat." 

Sai na dawo ," Allah yadawo mana da kai lafiƴa ya kareka daga shairin karfe ." 

Ameen , ya fada tare da fiɗa mashin din sa ya ƴi tafiƴar sa ."
25/03/2022 à 09:23 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

22/23📓

{{YAR LELEN NOBLE ce }}

Yana fita ita kuma ta koma ciki ta yi ,abin da zata yi ,sanan ta Kira kawarta ,Bayan ta dauka ne suka gaisa ta ce'' Kawata a gskiya samun kawaye Irin ku a halin yanzu a kwaye huya duk dauka na idan Mace ta yi , mijinta laifi ta nemi yafiya wajensa to zubda girma da mutumci ne ta yi a gabansa sai yanzu na gane babu abin da Zaki kara a idonsa sai daraja da mutunci.''

Kawata kenan ai duk wace Kika ga tana Hakan to gaskiya tana cikin matsala wanan ai girman kai ne girma ya huce Wanda ya fiki dashi shi dan me yake baki hakuri dake bazaki iya ba .''

Ai kuwa kawata yanzu idan Kika ganni da Sani Zaki ce Sabin aure ne yanda Muke kulawa da juna Abin baa magana.''

To Allah dai yakara ma kowa hakuri a gidansa?" dan shi iyayenmu suka yi gashi abin nazo kanmu yaushe Zaki zo gidana .''

Amine kawata wanan shine fa zan saka Rana sai nazo ko .''

To ina jira ?" Karfa ki dauki lokaci mai tsayi ,'' karki damu .''

Katse kiran ta yi ,sanan ta janyo Khairat suka kwanta bacci ya yi gaba dasu. ''

Tunda su Ilham suka fita Abul Khair Na kofar gidansu burinshi dai yaganta hankalinsa ya kwanta musanman yau din nan da ta saki jiki suka sha fira tun sakon da ya aika mata Bata mai da ba Motsi kadan ya duba wayarsa yaga koda ta maido wayarsa Bata yi kara ba Hakan yasa ya zauna shida mai gadi a bakin kofa suna dan tafa fira ,..

Ammi ce ta fito da alama fita zata yi ganin Musa Abul Khair kofar gidansu Ilham tasa ta kwalla masa Kira da sauri ya taso Yana isa wajenta ta wanke shi da mari sai da Yaga star uku uku suna yawo a kanshi kafin ya Dawo hayacinsa ya tsinci muryarta tana cewa Musa dan ubanka me ya kaika wantsan matsiyacin gidan ne Bana Hanaka zuwa ba ohh na gane shi yasa yanzu kafara daukar halin Irin na muna fukai ko ,'' tunda ya dafe kuncinsa bai sauke hannunsa ba har sai da ta gama magana cike da ladabi

 ya ce'' Ammi naje wajen Ilham sai na tarar Batanan shine na tsaya jiranta dan Allah ki yi hakuri .''

Uwarka ce wanan shedaniyar yarinya to Wallahi Musa ka fita a idona in rufe tun kafin ka hadu da bacin Raina .''

Ammi ba fa wani Abu ya kawoni ba gaisawa nazo muyi da ita.''

Iyeeeh lanle Musa yanzu ka Nuna mani ka girma ka balaga tunda har ka iya Duban kwayar Ido kake fadamin sunan wanan hatsabibiyar yarinyar.''

Wallahi Ilham Babu ruwun ta ke ce kike mata kallon da kike mata .''

Wani wawan mari ta saké sharara masa Wanda sai da yaga duhu ya mamaye ko ina kunnensa Yana fida sauti suuuuuu ,Hakan yayi daidai da dawowar su Ilham da sai da motarta kenan ta ga ana marin sahibinta, ai tun kafin Safiya ta kara she ajiye motar ta balle Marfin motar ta fito a guje tayo wajensa tare da rikesa tana duba fuskarsa da ta yi , jajir abinka ga farar Fata ai Bata san lokacin da hawaye suka fara wanke mata fuska ba ta ce'' Mon halal me yasa meka me kayiwa Ammi take dukanka Haka ta fada hankalinta a tashe .''

Har zai yi magana yaji anyi jifa da Ilham juyowa ya yi , Yaga Ammi dake cika tana batsewa tana kallon Ilham a wulakance ta ce'' Musa warkama aré ita bare ( Bana sonka da yarinyar nan ) ka fita a harakarta ke kuma utuleri  turakil ( marar kunya ) a gaban nawa sai kin Nuna mani kin iya karuwanci ko,to kijini da kyau daga yau bake ba Musa tunda ba uwar ta haifamin shi ba .''

Cikin Kuka ta ce'' Ammi dan Allah ki yi hakuri idan nayi laifi a rashi Sanina ki yafemin ko zan samu saukin tsanar da Kika mani ,durkusawa ta yi Tare da hade hannayenta wajen guda ta ce'' dan Allah ki fadamin laifi na kike son azabtar dani bisa kan soyayyar Abul Khair rabani da shi tamkar tarwatsa rayuwa ta ne Ammi ki tausayamin .''

Kan kace me duk da dare ne amma Hakan bai Hana mutane zagayesu ba sosai mutane diyawa suka tausayama su Abul Khair da Ilham jin hayaniya ta yi yawa ne yasa Mama da Aïsha fitowa dan ganin abin da ke faruwa ganin Ilham durkushe tana Kuka gaban Ammi yasa ran Aïsha faci dama ko da tsanma da suke ganin mutumci juna ita ba shiri suke yi ba wajen da suke ta karisa tare da mikar da Ilham tsaye tana watsa mata harara tare da kallon Ammi ta ce'' amma Wallahi an daiji kunya kizo cikin kananan Yara kin masifa mi zai sa girmanki a zube a idon mutune ki mana laifi kuma kizo ki daura mana karan tsana dan tsabar bakin ciki Irin naki to bara kiji in fadamaki da manyan bakake sannan ki kwantar da hankalinki aure dai ne tsakanin Ilham da Abul Khair ko to ki dauka an gama kuma in dai basu yi aure kafin na koma INGAL ba to ba sunana *Aïsha Muhamed bista* ba .''

ke Marar kunya dama Ashe kinzo ya yi uwar Abul Khair doli ah ba shakka naga kin Kai tsayina kina da abin da nake da doli ki tsaya kina fadamin magana shugabar yar rashin kunya .''


Har digiri gareni wajen yima irin ki rashin kunya tun da saya Kuka yi da kudinku kuma ni Abul Khair matsayin dan uwana yake ba Dana ba sannan Wanda ya isa dashi to shi ne zai hada aurensa idan kin isa sai ki Hana .''

Tana gama fadan Hakan ta jawo hannun Ilham da karfi take jan ta har suka iso falo ta saké ta ta ce'' Ilham Me ke tsakaninku da Abul Khair ne .''

Babu kunya bare taji wani dar dar ta ce'' Soyayya kuma muna son har  ta kaimu ga aure .''

Sosai ta bawa Mama da Aïsha mamaki dan yanda Ilham ke da kunya da zurfin ciki baka iya gane halin da take ci Ashe har ta kamu diyawa da son wanan yaron yarinyar da bazata iya daga Ido in Kana mata magana ko ita tana baka Amsa sai gashi ita ce babu wani tsoro take furta son Abul Khair take lanle Soyayya daban ce ,'' Ajiyar zuciya Aïsha ta sauke tare da dafa kafadarta ta ce'' Ilham nasan Abul Khair sosai mutuman kirkine duk yaranta ba halinsu day ba ban sani ko Safiya  tunda ban wani san ta sosai ba Amma ko Bassira babu ruwan ta da Abin da bai shafe taba karki damu da duk abin da ta fada in dai Abul Yana sonki Mahaifinsa ka dai zai Sanar dashi Wallahi kafin gobe kin zama amaryarsa .''

Amma Aunty Aïsha me nayi mata take hulakantani cikin jama'a nan ta Bata labari tun daga har duwarsu da Abul Khair jefota da ga saman bene da kuma bawan banana da ta jefar duk dan ta fadi .'' 


Sosai abin ya bawa Aïsha mamaki ?" ta ce'' Mama wane mataki Kika dauka ,'' babu abin da zan yi bisa lamarin Murja Bana iya masifarta duk neman wata rigimarce take kwana diyawa Bamu yi ba Tun daga lokacin data saka mahaifa ta ta lalace abin bai ishe ta Hakan ba bansan me take nema gareni ba .''

Amma Kika Zira Ido kina kallonta tana shika tsiyar ta a gaskiya ni baza'ayi Haka dani ba na tsani rainin hankali tana baba ta kama girmanta amma ta kasa sai kara kaskantar da kanta take Mtss aikin Banza .''

Bayan tafiyar su Ilham ne Ammi ta kalli Musa da Safiya ta antayamasu wani zazafan Harare Wanda yasa suka sha jinin jikinsu ta juya ta shige cikin gidan Safiya ma Key din Motar Ilham ta bawa mai gadi sannan suka bi Bayan Ammi duk jikinsu a sanyaye suka shiga suka ganta zaune ta rafka uban ta gumi tana Karka da kafarta alamar masifa dan nesa da ita suka zauna suna jiran cewarta .''

A tsiyace ta kalli Safiya ta ce'' Wallahi Safiya ban san kin rainani Irin Haka ba Bana Hanaki yawo da watsan lalataciyar yarinyar ba shine Kika nunamin ban isa dake ba ko .''

A'a Ammi ke fa uwa tace kin san Irin yanda nake maki biyaya baki isa kice nayi Abu ba in tsalakesa wanan ma gani Na yi gaba ba kyau kuma ina matikar son kawantsan mu ne shi yasa na je na Bata hakuri Muka koma kaman baya .''

Rashin tarbiyar tata ce ta fara shafarki har Kika iya take magana ta Kika koma wajen karuwa yar tasha .''

Ammi ki daina wanan furicin Akan Ilham Wallahi babu abin da take aika tawa a Irin furicin da kike mata ki kyautata mata zato fa .''

To uwata ? " Wanan umarni naki ya yi, ayi hakuri bazan sake ba .''

Shigowar Alhaji ne ya katse maganar da Safiya zata yi suka amsa masa Salamarsa,'' kallonsu ya yi ,yanda suka yi jigum kamar Wanda suka yi Sata ya ce'' ku lafiya kuke nan zaune kamar Wanda suka yi laifi .''

Da sauri Safiya ta tari bakin Ammi ta ce'' dama akan maganar auren Yaya Musa ne,'' A'a Masha Allah dama yaron nan Kana da wacce kake so ka zauna haka bani labari wacece ita .''

Sai da ya Saci kallon Ammi sannan ya ce'' ita ce Wada ta kula da kai a asubiti,'' Kai ma sha Allah ka ce yarinyar kirki to miye na ganku a nan abin farin ciki ya samu shine kake Hakan kamar ka yi ,Kuka .'''

To ai Baba ?" Ammi ce sam Bata kaunar yarinyar nan dama Yan gidansu cewar Safiya ta fada tana kallon Ammi dake galla mata harara .''

Ban gane ba me Hakan ke nufi ne ?" Mikewa su Abul Khair suka yi sannan Safiya ta ce'' Amsa na hannun Ammi tana gama fadan Haka ta yi ,shigewa dakin ta shima Abul Khair yafita zuwa part dinsa .''

Kallon rashin fahimta Alhaji ya yi , Ammi ya ce'' Wai ke Murja me yasa kike Hakan ne ko akwaye Wanda ya Hanaki Abin da kike so ne dan kin haifeshi sai ki Nuna inkon ki  a kansa kijini ni ba karamin mutume bane abin da Dana yake si shi zan yi masa tun da bai Saba doka ba kuma Allah bai haramta masa ita dan Haka Ilham yarinyar kirki gidansu akwaye tarbiya ta iya girmama na gaba gare ta ga addini da ilimin boko ga aikin ta nayi dan ladabi da biyaya to me zai Hana ko wane Namiji kwadayin Irin wanan matar .''

To Alhaji ko dai kaima son Nata kake,'' Murmushi ya yi, ya ce'' da Dana bai rigani ba to da ita zan aura dan ta zama kishiyar ki , Yana gama fadan Haka ya shige ciki ,'' kamar ta cinye kanta dan tsabar takaici da haushin maganar Alhaji zuciyarta sai Tafarfasa take kamar ta kama da huta🔥🔥.''
25/03/2022 à 09:23 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

24/25📓

Ba ita ta tashi daga bacci ba sai Bayan sallah Azahar tana tashi ta yi Sallah sanan ta dora masu abin da zasu ci ita da Khairat jallof din macaroni ce ta yi masu sannan ta tashi Khairat sai da Suka watsa ruwa sannan suka fito suka fara cin abincin suna gamawa ta tare komai sannan ta hauda data nan fa ta shiga fira ita da kawayenta har sai da akayi La'asar sannan ta sauka ta fara kiciniyar gyara gidan ta dan yanzu su Bassira an iya tsafta sai da ta yi masa turare sannan taja hannun Khairat suka fito waje nan ta dora girki Bayan ta gama ta juye a kuloli ta Kai bi sa dan table din dake Tsakiyar Falon ta sanan ta shiga wanka Bayan ta gama ta shirya tsaf da ita tana jiran shigowar Sani .''

Kwance yake bisa doguwar kujera wayarsa a hannu sai Murmushi yake shi ka dai ganin texte din baza ta yi masa komai ba ya sa Ya kira ta ai kamar jira take ta dauka bayan Sun gaisa ta ce'' Mon Cœur kamar ka sani dama ina son jin muryarka dan nayi missing Nata sosai .'' 

Kai Mon Cœur ni zance Haka kin tafi Maradi kin manta dani ko .''

Wace ni mijina Kenan kamar na manta da kaina nane Kai fa ka san bazan iya mantawa da Kai fa Mon Cœur ta fada a shagawfe .''

Da Wasa fa nake kullum ko da yaushe ina matikar son Naji muryarki na Dukan kunnena ke kuma sai kice Zaki yi man texte shi yasa nace kin manta dani mana .''

Oumh oumh dan Allah ka daina fadan Haka kaji Taya zan kiraka ga su Mama suna nan fa kuma dakin nan bani day ke da shi ba Ilham tana nn yanzu ma har ta yi ,bacci ka san biki suka yi sai yanzu ake huta gajiyar .''

Kai kice Amarya ta ta gaji ko nazo yi mata tausa ne ,'' bara in ta sheta ta baka Amsa da kanta mana .''

Ke ma Zaki iya Bada amsa ai ,'' bisa kan wane dalili fa .''

Kin fini sani ai ,'' Hmm ni sai de in ce ka yi mani ita kuma sai Abul Khair din ta ya yi , mata .''

La Mon Cœur kishi kike Kenan ,'' To ba doli ba ?" Ina zaune Za'a mani wayo Allah bazan yarda ba .''

To shikenan Matar Saïf ina yaranmu tunda Kuka zo banji muryarsu ba .'''

Suna dakin Inteesar a tsan suke baccinsu suna tashi suyita dire dirensu in na masu magana Mama ta yi, fada .''

Dariya ya yi , ya ce'' har da Inteesar din suke wasan ta su ,'' E'e harda ita kasan har yanzu lafiyar nan Bata samu ba sai de abin da baa rasa ba .''

Gaskiya badan wani Abu ba Dana ce wanan matar muguwace yarinya mai kyau ga ilimi da fahimta amma har yanzu ba hankali da yanzu tana da hankalinta da tare da Ilham za'a masu aure dan in ban fadi karya ba Inteesar yanzu zata Kai 19 year .''

Wallahi kuwa hakane mijin aïsha dazun ma fa sai da Muka yi fada da ita dama ina son zaka kara mani kwanaki ko wata biyu nayi dan sai na Nuna mata iyakarta kafin na koma ayi auren Ilham da Abul Khair din in ga abin da zata iya yi da sarautar ubangiji.''

Bani labari me ya faru ?" Hmm ni ban san me ya hadasa fadan ba Tun da nima hayaniya ce ta yi ,Waya muka fito Nida Mama nan dai ta kwashe duk abin da ya faru ta fada Masa .''

Good matar so kin mani dai dai ita wanan matar ko dai rikicin tsufa ne ke damunta .''

Da Alama dai Mn cœur sai na saka Ilham ta mata aiki a kwakwalwarta sanan zata Dawo dai dai.''

Nan sukai ta tautaunawa bi sa kan Lamarin Murja daga bisani suka yi sallama dan dare ya yi ,Hakan suka Rabu badan Sun so ba .''

WASHEGARI 

Ilham tunda Asuba da ta tashi Ba ita ta koma ba sai da Suka yi abin da ta Saba kullum sannan taje ta yi , wanka ta fito cikin shirinta na zuwa aiki tana fitowa kowa ya hallara a danning table dan ta dan ci abinci ka dan sanan ta yi ,masu sallama ta fita , ganin motar ta Bata cikin gida yasa ta fita waje Bayan ta gaishe da Baba mai gadi tambayarsa makulli ta yi , ya ce '' ai dan saurayin nan ne ya karfa ya ce tare Zaku je aiki ,.''

Murmushi ta yi ,ta ce'' Yana ina ,'' ina ga Yana mota ke yake jira .''

Bata ce komai ba tanufa motar Yana ganin ta tinkaro wajen ya fito tare da Budé mata kofar gaba ta kusa da driver shiga ta yi , tare da yi masa godiya shima ya shiga sai da ya fara tafiya ta ce'' Mon halal Mun Yaris ,'' kara gas ,'' wardurtole ,'' Ah kara gas Alhamdulilah ,'' madallah yanzu shine zaka zo Kaini Asubiti kar fa nasa  ka yi late .''

Karki damu nima ai a Asubitinku na koma aiki ,''  dagaske ?.''

Of course ," amma Naji dadi sosai Mn halal kaga yanzu ina tare da Kai bare in baka kusana kishi ya kamani.''

Ai ke kadai babu wata Albi ta ke ce kuma in sha Allah daga ke na rufe kofa .''

Dariya ta yi , ta ce'' ba wani nan zumudin Soyayya ce ke ratsaka ka Bari ka sha magani inka warke sai muyi magana .''

Kai baki yarda ba Kenan ,'' A'a ni me zai Hana inki yarda Mn halal guda ya yi, magana in ce ban yarda ba .''

Barki yau na lura da tsokana Kika fito ,'' Wasa fa nake ni duk gajiya ta ishe ni ma .''

To sai hakuri ? " Ba doli kuna ta yawo wai ku bikin kawa sai da na Hana Safiya Ammi ta fara masifa na gyale ta .''

Kai kake ganin yawo Muke amma mu Sada zuminci muke dan rabona da wasu kawayen mun jima Sosai sai a bikin nan .''

Murmushi tare da satan kallonta ya ce'' ki ce Ana mu idan yazo mutane zasu cika anguwarmu .''

E'e masu shafa Fatiya ba,'' Dariya suka yi tare .''

A dai dai nan ya tsaida mota dan Sun iso har zata Budé kofar ya ce'' ban yarda ba dan Bana son ki batamin aikin gidana ,'' Murmushi ta yi , amma Bata ce komai nan ya fito sannan ya zagaya ya Budé mata kofar Irin kallon love din nan ta yi masa a take ya lumshe Ido dan kallon ya tafi dashi cikin dadar muryarta ta ce'' Thank you soo much Mon halal .''

You are welcome dear Muje ko ,'' gyada masa Kai ta yi , sannan suka jera a tare suka Tafe suna firansu Irin ta masoya.'' 

Tun shigowarsu Doctor Faruk ya Gansu a zatonsa Ilham din ce ita ka dai dan ya dauki Aniyar cewa yau ko halin kakane sai ya Nuna mata illar maganar da ta fadamasa dan har yanzu idan ya tuno Kuka yake fashewa da shi, kwafa ya yi , sannan shima ya shiga daga ciki dan yau suna da meeting à office din Doctor Bashir dan Haka sai da ya nufa office din sa Ya ajiye kayansa sannan ya fito zuwa wajen meeting din a hankali ya murda handlle din tare da sallama a bakinsa ,duk amsa masa suka yi sannan ya nemi waje ya zauna tunda ya shigo Ilham ta hade fuska dan yanzu haushi kawai Faruk ke Bata shi ko wani Irin  kallon  kawai  yake mata Wanda shi ka dai ya san ma'anarshi ,gyaran muryar Doctor Bashir ne ya maido hankalinsa wajensa dan ji me zasu tautauna sai da ya Budé taro da addu'a sannan ya ce'' ina me farin ciki amsa gayata ta da Kuka yi kuna ganin wanan yanuna Musa Abul Khair dan Haka kowa ya maida dubanshi garesa sannan shi kuma yaci gaba da cewa wanan bakon mune an yi masa transfér daga kasashen waje zuwa wanan Asubiti ta mu da fatan kun yi farin ciki da zuwansa .''

Dukansu suka masa da sosai ma Allah yabamu ikon karuwa da Hakuri da juna ,amine sannan suka ci gaba da Abin da yakawo su nan kowa ya watse ya koma office din sa Ilham har office din sa ta raka shi sai da Suka fira sannan ta Mike ta ce'' ina ga zan tafi kar azo nemana fa .''

Tun yanzu Albi ya fada a marairaice ,'' sosai ya bata Dariya ta ce'' Mn halal sorry ka ga aiki Muka zo yi kayi hakuri ai a tare zamu gida ko .''

In dai kin yarda Zaki aure ni sai Muje a tare ,'' a kunya ce ta ce'' Abul Dina Bana da zafi a yanzu amma zuciya ta ta san Kai ka dai take so kuma take burin kasancewa a tare da Kai amma sai in Ka nemi amincewar Dadyna hukuncin da ya yanke, to bisa zan zauna?" Karki damu ALBI in sha Allah zan yi magana da Baba sai ya je ya nema mani izini zuwa fira dan in manya suka shigo lamarin zai fi armashi .''

Ashe ka gano dawan garin ,'' Murmushi ta yi , ya ce'' Ilham Allah ya barmani ke ya sa in mallake ki a matsayin Matata .''

Allah ya amsa?" ta fada  tana fitowa da sauri tanu fa office din ta .''

Murmushi ya yi tare da girgiza Kai ya saka biro a baki Yana tuno farkon haduwarsu wani ya yi , Dariya wani Kuma Murmushi kamar wani mahaukaci.''

Kiran da ake mata ne ya katse mata baccinta tsuki taja sannan ta dauka tare da karawa a kunnunta tana fadin Hello ,a day ban garan Aka masa mata oui cutie yakike , jin muryar da ta daki Dodon kunnenta ne ya sa baccinta ya watse daga idonta sannan ta tashi zaune tana kara cewa Hello Kitty .''

Yes Cutie bacci kike na katse maki shi ko ,'' ai nama ta shi yaushe a gari .''

Jiya na shigo duk gajiya ta dameni ya kwana biyu,'' a shagwafe ta ce'' kafi Sanin kowa halinda kasakani tafiya ba sanarwa Sai da Naji labarin katafi anyi Kitty yanzu Kanayi dani.''

Sorry cutie Wallahi tafiya surprise ne ta zo mani shi yasa kema ai kin san ke din ta daban ce a gurina babu wata.''

Kitty Kenan ya ake ciki ne ?" Yau Zaki leko ne ,'' A'a bazan samu dama ba duk a gajiye nake Wallahi .''

Ban gane ba?"  kodai kinyi sabo ni kin manta dani ,'' A'a Kitty na babu kowa har yanzu Kai kadai zaka sha zumar ka ban hadaka da kowa ba kuma Bana fatan zan fara nan gaba .''

Haba har kinsa Naji sanyin dadi a Raina dan Allah ki samu ki leko ki gane kwana biyu diyawa fa rabona dake Cutie .''

To zan duba? " Idan Ammi ta yarda zaka ganni dan nayi yawo sosai a satinan Kitty .''

Ki dai duba in ba Haka ba akwaye matsala ,'' haba ai din taka ce Kai kuma duk cikin takone Bana son a gane halin da nake ciki yanzu zan ce mata Zani neman aiki Kai kuma ka kokarta ka Samomanshi cikin satin nan kaga sai mu dinga holewar mu ko .''

Kai Cutie gaskiya kina huta wanan shawara ta yi , zan duba maki koda wajen aikina ne .''

Thank you Kitty na Allah yabarmani Kai ni ka dai dan ina kishinka sosai .''

Nafiki Cutie ke wasa ma kike yi ai ,'' Anya dai ?" In dai kina sona in ganki a gidana nan da Awa 2 nan .''

Wanan Haka yake Karka damu yanzu zan zo in sha Allah amma fa bazan jimaba .''

To shikenan ?"Cutie na I love you ,'' love you soo much.''

Sauna ganki ,ok tom katse kin ta yi , tare da ajiye Wayar tana sakin Murmushi ta ce'' haba gwara inje inda za'a debemin kewa ina shan soyayya da in zauna gida bakin ciki ya kashe ni duk kawaye Sun yi aure wasunsu suna bisa hanya amma ni Shekara ta 21 day amma ta Hanani kulla saurayi waini yarinya ce Ammi baki san lokacin ya kuremaki ba sai ma kin ganni da baby Zaki gane tsanina da Ilham wace karuwar ne .''

Sai mun hadu a next page ✍️
25/03/2022 à 09:23 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

{{ YAR LELEN NOBLE ce}}

26/27📓

Mikewa ta yi , sai da ta yi wanka ta shirya cikin wasu kananen Kaya sannan ta saka Lafaya dan kar Ammi ta gane ta fito a falo ta samu Ammi tana yankan farce cike da ladabi ta tsuguna ta ce'' Ammi ina kwana ,'' 

lafiya lau ke kuma ina Zaki je ne ?.''

Zan je neman aiki ne da tsan sai na je gidan Amarya zamu yi mata girki har satin biki ya huce.''

Amma Safiya kin san Bana son yawo ko .''

Ki yi hakuri mana Ammi wata Rana nima fa Haka zata zo gare ni .''

Na ji amma karki jima sanan ki sauri ki dawo.''

In sha Allah da na gama Abin da nake ban zan jima ba .''

A Dawo lafiya .''

Mikewa ta yi ,ta fita cike da Murna tana fita ta tare mai adaidaita ta fadamasa inda zai kai ta kallonta ya yi tare da fadamata abin da zata Bada , shiga ta yi ,suka bar anguwar Sun dan yi tafiya mai tsayi sannan suka iso wani dan madaidaicin gida mai kyau da ga ganinsa kasan Anka she kudi kudinsa ta bashi sannan ta shiga gidan bakinta dauke da sallama ,Yana jin sallamar ta ya taso tare da rumgume Yana fadin Welcome Cutie she dai Zaki zo .''

Ga Zahiri kuwa,'' Murmushi ya yi ,sannan yajata suka shiga ciki 2st suka zauna a tare cike da shagwafa ta ce'' Nifa Kitty fushi nake yi da Kai .''

Yeah nasani ki yi hakuri kin ji Cutie na ,'' amma sai ka barni ni ka dai kuma kasan zan yi kewarka Bana ji dadi Idan baka kusa dani shine ka yi tafiya ko sanarwa babu .''

Sai da ya juya suna fuskantar juna ya sa hannayensa ya tallabo fuskarta suna kallon juna Ido cikin Ido ya ce'' Cutie kin yarda dani ko kin san nima ina jin duk abin da Kika fada a yanzu tafiyar nan Kamani ta yi doli badan naso ba ta kai tsayeni kin san ai ban taba yi maki Haka ba.''

Ka sa ta yi , da idanunta ta ce'' Na yarda da Kai mana amma ai laifinka ne nasha fadamaka ka fito muyi aure mu bar wanan banzar rayuwar da Muke Kitty .''

Nasani Cutie ina sonki kuma zan aure ki Abba nane baya gari amma da zarar ya Dawo zan Tura a gidanku kin ga da kin zama mallakina zan je dake duk in da nake tafiya .''

Kanta ta langafe gefe ta ajiye bisa hannunsa take ka tabbata Kitty Nifa ina Sonka shi yasa na baka rayuwa ta da Dukan komai nawa dan Allah Kar ka juyamin baya ka ji .''

Cike da salon yaudara da iya tsara zance ya ce'' Of course zan Tura yanzu ya ake ciki ne nayi missing naki dayawa fa .''

Murmushi ta yi , ta ce'' ina tsaraba ta take ne ?." 

Muje daki sai na baki ,'' da gaske ta fada a shagwafe .''

Muje ki gani.?"

Mikewa ta yi , suka shiga ciki kallonta ya yi , ya ce'' Cutie na gaji jirani zan yi wanka idan Na fito kimn tausa .''

Dariya ta yi, amma Bata ce komai ba Haka ya shige toilet ya Barta Zaman jiran shi 

Tana shigowa Office din ta ta tarar da miss call har goma dubawa ta yi , taga Kabir ne tsoki ta ja ta ce'' wanan mutuman dan walaha ne Wallahi ...ba ta Kai ga rufe bakinta message ya shigo dubawa ta yi , kamar Haka .

Nayi fushi ?" , Ka yi hakuri .''

Ba damuwa dan kinga na damu dake ne shi yasa kike mani Haka har vidéo call na yi maki amma baki daga ba .''

Ina Asubiti ne Bana kusa da Wayar .''

Kina da kyau sosai Ilham .''

Na gode ?" Zan kiraki yanzu .''

Shuru Bata maida masa ba Haka ya kirata a vidéo call amma taki dagawa dan ta tsani appel vidéo.''

Tana cikin duba takkardun da ta gani a jiye na wata mai ciki ta ji shigowar sako ajiye aikin ta yi dan a tunaninta ko Abul Khair ne amma sai ta ga Kabir dubawa ta yi.''

Ilham insha Allah bazan kara damunki ba dan n'a damu dake ina ta kiranki amma Kika share ni sai an jima .''

Voice ta yi masa ta ce'' ka yi hakuri ni ma kaina Ban san dalilin da ya sa Bana kulla mutane ba amma ina son Dukan Wanda yake Sona .''

Wayoo Allah I even like your voice Wallahi na ji dadi .''

Dariya ta yi dan lamarin kabir mamaki yake Bata yanzun ya yi fushi da ita amma har ya sauko Replay ta yi masa ta ce'' Allah Sarki Kabir din Ilham .''

Na ji dadi kawai So nake Allah ya hadamu wata Rana .''

To Allah ya yarda Kabir din Ilham .''

Wayoo Allah Ilham Zaki kashe ni dis nyt me kyau ina sonki .''

Na gode🥰

Ba godiya nake so ba cewa Zaki yi kina Sona ?" 

Sticker din Dariya ta Turamasa amma Bata ce komai ba .''

E din baki taba cewa kina Sona ba sai de kullum ni ke fadamaki ka wai ki gayamin .''

Kar ka damu ka ji dadi abinka Bana son ka saka damuwa sabida ni .''

Tana Tura masa ta ajiyewar Wayar ta ci gaba da Abin da take ,turo kofar da akayi ne ya sa ta mai do duban ta Fa'iza ce ta shigo ta ce'' Doctor Ilham dama Bashir ne ya ce'' Na zo na fadamaki cewa takardun mai cikin nan ki kawo masa su yanzu dan yanzu Haka Yana labour ne .''

A nutse ta kalle ta ta ce'' ganinan zuwa ina aiki bisa kan su ne .''

To Ranki shi dade ?" .

Tana fita ta rufo kofar Ilham ta dan jima kafin ta Mike ta nufa Office din Bashir tana isa ta yi , Nocking izinin shigowa ya Bata sannan ta shiga Bayan Sun gaisa ne ta ce'' sir ga takkardun nan .''

Karfa ya yi , Yana duba wa ya ce'' Amma yanzu fai'za ta shigo take cemin da alama tana labour ne .''

E'e Haka ta ce , to Muje na duba ta sai ki karasa sauran aikin ko .''

Tom ta fada shi kuma ya Mike suka fito Yana Nuna mata takkardun da ta ba shi Yana cewa yanzu zan huce dakin ke kuma sai kije ki bawa Musa Abul Khair su .''

To sir ta fada cike da zumudin zata je wajensa ,fitowar sa Kenan ya gansu suna Tafe jere da juna suna Ido hudu da Ilham ya hade fuska ya koma office din sa ta na ganin Haka ta karfi takkardan ta nufa Office din da sauri tabi bayansa sam bai kulla tana Bayansa ba ya rufo kofar da karfi Hakan ya sa Yatsan hannunta shiga ya dantse ta ,yar kara ta saki dan tsabar zafi har idonta Sun kawo ruwa ,juyowa ya yi Yaga hannunta Yana zubda jini ,a rikice ya ce'' Albi ki yi hakuri ban san kina bayana ba .''

Ai kamar jira take abin ka ga shagwafafiya ta fashe da Kuka tana yar fa hannun janyota ya yi , sannan ya rufe kofar ya zaunar da ita bi sa chair din dake wajen sannan ya yi tsugunni Irin na Maza ya Kamo hannunta tare da  jawo Kayan dressing Yana mata ya ce'' Mon halal ki yi hakuri ban kula kina bayana ba dan Allah ki yafeman sannan ki dai na Kuka kin san na sha fadamaki cewa tadamin da hankali yake kina son na shiga damuwa ne .''

Hawayenta ta share ta ce'' Na daina in dai Hakan zai sakaka damuwa na bazan sake ba .''

Allah ya barmani Mon halal din ta ki zama Mallakina hankalina ya kwanta in san ni naki ne ke dai .''

To Waya fada?" cewa ba Kai ka dai ne bane a zuciya ta .''

Yanzun fa na ganki da Bashir ,'' Murmushi ta yi, ta ce'' Babu abin da ke tsakanina da D.C Bashir sai mutumci kuma wajenka ya ce'' Na zo in baka wanan takardun ka duba zamu shiga wajen wata mai ciki da take Labour .''

Sorry Ilham ban san Haka abin yake ba kishine yakamani amma zan kiyaye gaba kuma yanzu ba gobe ba idan mun tashi aiki zan je wajen Alhaji in Sanar masa ayi ta ta Kare .''

Sunkuyar da Kai ta yi , ta ce'' ga takardun sannan ni yau anan zan kwana sai gobe zan sauka daga aiki .''

Bai ji dadi da ba tare zasu koma gida ba amma ya ce'' babu damuwa Zaki ji sako wajen Dady .''

Murmushi ta yi , tare da ficewa daga Office din tana cewa Allah ya sa Muji Alkairi.''

Girgiza Kai ya yi , ya ce'' amine sannan ya rufe kofar .''

Dakin da matar take tanu fa sosai ta tausaya mata dan halinda da ta ganta Haka ta yi ta kulla da ita har Allah ya sauke matar Lafiya ta santalo beby boy kyaukyauwa Murmushi Ilham ta yi , ta ce'' Ma sha Allah Congrats ta fada tana Mika mata beby din ,'' sai da matar ta kalla abin da ta Haifa sannan Ilham ta karfe sa ta kawo ma jama'ar da Suka yi raki yi sai santin yaron mutanan suke , ita kuma ta koma ciki ta gyara mai jego sannan suka Kai ta dakin hutu ita da beby din ta kafin da safe su sallama me ta dan tun safe fa Suka zo sai wajen karfe 1h30 na dare matar ta haihu tana gamawa ta koma Office din ta sai da ta tabatar ta rufe kofar sannan ta cire rigarta ta likitoci ta kwanta bi sa dan karamin gadon dake dakin.''

Sai da yamma lis sannan Musa ya Baro Asubitin dan ya so su hadu da Ilham amma ba dama ga shi wayarta a kashe dan Haka ya yi hakuri ya tafi gida sai da ya yi , wanka sannan ya nufi part din Ammi tana zaune tana karatun jarida da sallama ya shigo , ciki ciki Ta amsa ta ce'' Har ka Dawo ,'' E'e Ammi .''

To ka abincin ka tsan a kithchen ka je Ka dauko .''

Cike da Mamaki yake kallonta dan tunda yake da Ammi bai taba tafiya ya dauko abinci ba sai de ta kahomasa cike da sanyin jiki ya nufa kithchen ta dauko sannan ya fito har zai fita ya tsinci Murya ta tana fadin in dai har zaka din ga kin bin umarni na baka gaji da mamaki ba .''

Bai ce da ita komai ba ya fita sai da ya ci abinci sannan ya nufa bangaren Alhaji Yana kwance yana kallon T .V d sallama ya shiga Bayan Sun gaisa ya ce'' Alhaji wajenka nazo ?" 

Ta shi ya yi daga kwancen da yake ya ce'' lafiya dai ko .''

To lafiya lau Amma ba sosai ba?" Har sai na ji amsarka ka dai zan warke .''

Fadi ina jinka?" Hmm dama bisa kan maganar Ilham ce ina son ka je Ka nema mani izinin auren ta .''

Ya fada Yana sunkuyar da Kai kamar tsohon farawo 😂.''

To Musa gaskiya na yi farin ciki da haduwark da yarinyar nan sannan ko ba komai zata kulla da Kai sosai .''

Cike da kunya yake kallon Alhaji amma bai ce komai ba ,shi kuma ya ci gaba da cewa kar ka damu tufa azakare wanansa adakidwaya hura banne ( gobe zan je in nema maka aurenta ) .''

To Baba na Na gode ni zan tafi gyare muzai ( sai an jima ) .''

Fitowar sa Kenan ya hango Safiya ta shigo daga ne sa Ya kirata ta tsaya kamar munafika sai da ya kariso har inda take ya ce'' daga ina kike?" .

Gidan Amarya na je zamu yi mata girkin sati .''

Ke baki gajiya da yawo ne kamar wacce ta ci kafar Kura Karna sa ki naga gobe kin bar gidan nan .''

To ai Ammi ta sani kuma ita ta ce naje ai?" Ni kuma na ce kar ki kuskura kibar gidan nan .''

Turo baki gaba ta yi ,ta huce ciki tana magana kasa kasa har ta shige ciki da sallama a bakin ta .''

Amsawa Ammi ta yi , ta ce'' Har kin Dawo yane an da ce ne .''

A'a Ammi wai sai banda gobe zamu kara ta fiya dan ni na sare tun da na fita sai wajen karfe uku wai muyi hakuri Sun tashi shi yasa na huce gidan Amarya da naga karfe biyar nace bara na Dawo gida .''

To ki shiga ki huta ga abinci sai kice?" Wallahi kamar kin san ina jin yunwa .''

Tafada tana shigewa dakin ta .''

Ilham na bacci aka Budé kofar da yake tana kulle kofar ta cire makullin shi yasa Aka shigar mata Office jin ana shafata ya sa ta gyara kwanciyarta dan a tunaninta mafarki take yi , jin ana daga mata Riga ya sa ta bude idon ta suka yi Ido hudu da shi ,a tsora ce ta tashi zaune gabanta na dukan sha tara tara jikinta na rawa ta ce'' .........................................................................
....................................

Comment ✍️
25/03/2022 à 09:25 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

{{YAR LELEN NOBLE ce}}

28/29📖

Jikinta na rawa cikin rawar murya tace'' Fa..ruk ,'' wani uban mari ya sharara mata Wanda ya sa sai da taga star uku suna yawo a saman kanta sannan ya fincikota da sauri ta gantsara masa cizo tayi wajen wayarta ta dannan lambar Abul Khair ,da sauri ya kwace Wayar Yana buga mata Kai ga bango aiko hannunta ya danna karaurawar dake Nuna a kwaye matsala ,dan ita tama manta da ita tsabar firgici jin ana nufo dakin yasa ta kwarara ihu Hakan Yaba mutanan damar shiga Kai tsaye ,da mamaki kowa yake kallon Faruk Ilham Na ganin ta nufa wajen fa'iza tana Kuka ,'' d.c Bashir ne yanufa wajen Faruk tareda shako huyansa yayi hurgi dashi kamar Kayan wanki ya Kai masa naushi a Ido cike da facin rai dan ubanka iskancin da kake a waje bai isheka ba har sai kazo dan ka batamin sunan asubiti ko asarare kawai Kai de anyi dan iska kuma kasani daga yau Wallahi bazaka kara sha'awar lalata Yan mata ba dan uwarka kallon sécurité din dake wajen yayi yace'' ku fitarmin dashi kuci ubanshi ,cike da girmama umarni suka sungume shi sukayi waje da shi suka fara dumarshi kamar an Sun samu Banza sai da sukayi masa jina jina sannan suka barshi sannan suka daure shi da igiya a wajen asubiti suka koma ciki ,'' kallon Ilham ,Bashir ya yi, ya ce'' babu wata damuwa dai ko ,'' gyada masa Kai ta yi alamar e'e ,'' to ke ?" Fa'iza ki zauna anan idan Allah ya kaimu da safe zai ga abin da zan masa.''

Cike da jin kunya ta ce'' D.C na gode sosai .''

Karki damu babu komai ?.

Ficewa ya yi Ita kuma ta koma ta kwanta amma baccin Yaki daukarta sai de ma Hana fa'iza baccin da ta yi dan sai tafara bacci sai ta ce'' fa'iza bacci kike ne ,'' ita kuma sai ta ce'' A'a a Haka har Asuba ta yi ,Mikewa ta yi, duk da kanta Yana saramata amma Haka ta daure ta shiga toilet ta dora Alawa tafito tareda Tashin Fa'iza ita ma taje ta yi alawa a tare sukayi sallah sannan Ilham tafara har hada Kayanta ,''kallonta Fa'iza ta yi ,ta ce'' Ranki shi dade ina kuma zuwa yanzu .''

A takaice ta ce'' gida zan je mana?"

To amma ai nake ganin gari bai yi hasken da Zaki fita yanzu ba kuma gashi motarki Batanan .''

Ajiyar zuciya ta sauke dan sai yanzu ma ta tuna cewa Abul Khair ya tafi da ita zaune tayi tareda dafe Kai dan sosai kanta ya bugu ga rashin bacci da Bata samu ba Wayar ta janyo tareda Kiran wayar Abul Khair ,sai da ta yi ringing hudu a na biyar ya dauka tareda da sallama a bakinsa amsawa ta yi ta ce''Mn halal dan Allah in ba damuwa kazo yanzu a asubiti ina son ganinka .''

Lafiya dai ko Ilham Me ya faru ?" 

Sai kazo tafada tareda kashe Wayar ta ajiye ta gefe, jin Hakan yasa shi dauko makullin motarta yafito zai fita suka hadu da Alhaji a hanya ,sai da ya gaida shi ,ya amsa Yana fadin ina kuma zaka je yanzu.''

Wajen aiki ne aka kirani amma yanzu zan Dawo .''

To ba damuwa ?"ka kula da hanya sai Dawo ko ."

Insha Allah Baba.''

Baba Yana shiga ciki shima ya yi wajen motarsa ya shige sannan get man ya Budé masa kofa yafice daga gidan sai Asubiti .''

Yana isa ya sauko ko kulle motar bai yi ba ya fito yanufa office din Ilham dan a yanayin da tayi masa magana zaka san tana cikin damuwa ,'' Yana kaiwa ya yi , fa'iza ta Mike tareda Budé kofar da Aka saka ta kullawa da Key ,'' bai tsaya Wata wata ba yanufa inda take tareda ajiye hannunsa a kafadarta ya ce'' rayuwa ta lafiya kike me yasa meki hakane .''

kallonsa ta yi , da idonta da Suka cika kwalla ta ce'' Babu komai .''

Ya Zaki ce babu komai ?" Kin ga tell me hankali duk a tashe yake Waye ta jimaki ciwon nan .''

Fa'iza ce ta ce'' Kar ku na tsoma baki Akan abin da bai shafeni amma jiya kadan ya rage yallabai Faruk ya mata fyade .''

Wani Irin garam gabansa ya buga da karfi idonsa sukayi jajir jijiyoyin Kanchi suka taso ya ce'' ina yake ne .''

A tsora ce Fa'iza ta ce'' Yana Bayan Asubitin nan an jima za'a fito dashi dan nunawa Al'umma sannan a huce da shi police station .''

Fitowa ya yi ,yanufa Bayan Yana isa bai tsaya Wata wata ba yashiga kaima Faruk mazga sosai yake ihu har muryarsa ta dusashe ,da gudu sécurité din dake wajen suka yo kansa da kyar Aka kwace Faruk a hannun abul Khair da sai sauke ajiyar zuciya yake .''

Safiya nayi Alhaji yatafi gidansu Ilham nan ya saka mai gani ya masa magana ,bai wani jima ba yafito nan suka gaisa cike da mutumtawa , Alhaji ne ya ce'' Muhamed dan Allah nazo ne Akan maganar yaron wajena da yar ka Ilham .''

Lafiya dai ko ?" Alhamdulilah dama nazo nema masa auren tane idan Allah ya sa ba'ayi mata mijiba .''

 Washe baki Dady ya yi , ya ce'' Masha Allah to ai Ilham yarka ce babu damawa fairakat ( na baka ita).''

Kai amma Naji dadi sosai nagode Allah ya saka da alkairi ya basu Zaman Lafiya .''

Amine fairaturage ( Allah yasa Alkairi)."

To Na gode Muhamed Inde gyara muzai .''

Nan sukayi sallama sannan kowan nansu suka koma gida ,alhaji Na shiga Kai tsaye part din Ammi yanufa da sallama a bakinsa ,amsawa sukayi dama ita da Safiya ce zaune a falo suna jan tarbi ,'' Baba ina kwana ?" 

Lafiya lau Safiya ana zaune .''

E'e baba .''

Baice da ita komai ba ya duba Ammi ya ce'' Hajiya Ta yau nazo maki da baban Albushir ,'' Murmushi ta yi , ta ce'' To Bani labari in sha .''

Dazun munyi magana da Muhamed Bisa kan maganar Ilham da Musa Abul Khair sosai yafini murna ya ce'' yabamu ita .''

Tunda yafara maganar Ammi ta hade fuska kamar ta makure huyansa ta ce'' bangane me kake nufi ba Kana nufin wanan karuwar yarinyar zata zama Sakakuwa ta Allah ya sauwake kaga Alhaji ni wanan shedaniyar yarinya bazan taba laminta ta shigo mani gida ba Wallahi .''

Kallon bakida hankali ya mata ya ce'' nawa Kika kashe wajen gina wanan gidan ne to ni bazan kaminci wanan iskancin banzan naki ba Wallahi idan har baki dai na abin da kike ba to da alama wata zata shigo wata kuma ta kama hanya dan ni bazaki mai dani karamin mutume ba .''

Yana gama fadan Hakan yafice daga part din ,a hasale Ammi ta ce'' ko da za'a yi auren nan Wallahi sai de wani gidan amma ba nawa tafada tana kallon Safiya taci gaba da cewa munafika ai duk kune Kuka jawo za'a kawo mani diyar watsan mutumniyar banzan ta kara she tana bankada mata Harare .''

Allah yabaki hakuri Ammi .'' tafada tana shigewa daki sabida Kiran wayarta da ake yi .''

Tana shiga ta fada kan bed tareda amsa Wayar tana fadin Hello Kitty na ya kake .''

Lafiya lau Cutie ke jiya kike gudu ba ko sallama .''

Murmushi ta yi, ta ce'' ba doli ba ai naga baka da niyar sallama ta shiyasa gashi mangari ba ta Kurato so kake yau a Hanani zuwa ne.''

Haba in sa Raina ina bacin Baki kusana ni dama Kira nayi inji Zaki zo yau ne .''

Me zai Hana sosai ma zan zo ?" Dan farincikin ka mana .''

Idan fa Amma ta Hanaki ?"..

Haba ina ji koda satan hanya ne sai na fita dan nayi tauri bazan tankwasu yanzu ba .''

Dariya ya yi, ya ce'' my Cutie love kin fa iya soyaya ba dama .''

Ai ban kaika ba ko Kitty na.''

Babu gwani dai to da wane lokacin Zaki zo ne .''

Bayan sallah La'asar in sha Allah .''

To Allah ya kahomani ke lafiya ta kirkin .''

Amine ta fada nan sukayi sallama ta katse kiran .''
25/03/2022 à 09:25 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

{{YAR LELEN NOBLE ce}}

30/31📖

Da kyar suka samu abul Khair ya kwantar da hankalinsa Hakan yasa yayi hakuri ya koma ciki wajenta yanufa ya ce '' rayuwa ta garin yaya wanan dan Iskan ya samu damar shigowa wajenki ,'' nan ta fadamasa abin da ta sani ,iska mai zafi ya fizgar ya ce'' Muje gida ko ?" 

Babu musa ta Mike suka yi hanyar gida babu mai magana kowa da abinda yake sakawa a ransa har suka iso sai da ya shiga da ita har cikin gida sannan suka yi sallama ya tafi gidansu Ilham Na shiga ta tarar dasu Mama suna breakfast Inteesar ta kalleta da karkatacen kanta tana zubar da yawu ta ce'' Aunty na har kin Dawo .''

E'e ?" Kawai ta fada tareda gaishe da su Mama ,'' suma suka amsa sannan ta huce daki babu Wanda ta saké yima magana .''

Tana shiga ta fada toilet wanka ta yi , ta saka Kaya Marasa nauyi sannan ta bi lafiyar gado sai bacci .''

Dady ne da sai da Ilham ta shigo ya tuna da maganar Alhaji ya ce'' Maryam dama dazun ban Sanar dake ba yau da sasafen nan Alhaji yazo gidan nan neman auren Ilham .''

A'a Masha Allah gaskiya nayi farinciki sosai .''

Amma Maryam Ilham ta san abin da ke tsakaninku da Murja ne .''

A'a Bata sani ba kuma Bana fatan ta sani tunda babu anfani Hakan .''

Hakane nasan wata rana dole ne ta sani in dai ana tare kuma ana raye .''

To banki idan lokaci ya yi Sata sani ai .''

Allah yasa Alkairi a cikin wanan hadin da mukayi .''

Amine .''



Safiya ce ta fito cikin shirinta Irin na isanan tana taunar shiwgom ta ce'' Ammi na shirya ni zan fita ko .''

Da Mamaki take kallon Safiya wanan kuma wace Iriyar shiga tayi wai tana nufin a Haka zata fita,'' katse mata tunani ta yi tana fadin sai na Dawo Ammi .''

Fita ta yi , batare da taji cewar ta ba ,dan tsabar Mamaki sosai Ammi take kallonta har ta bacewa ganinta Anya kuwa Safiya ce wanan.''

Da wann tunanin ne Abul Khair ya shigo tareda gaishe da Amma ko kallonsa Bata yi bare yasama ran zata amsa .''

Ina kwana Ammi? '' 

Bansani ba tunda kaine mai Bada lafiyar .''

Shiru ya yi ,n'a dan lokaci dan Yaga yau abin ba sauki Mikewa ya yi ,ya ce'' Ammi zan fita babu abin da kike da bukata ne .''

Ko hmm Bata ce masa ba bare kallon arziki ,'' fita ya yi ,ya koma part din sa Ya kwanta nan ya Kira Wayar Ilham amma ba'a daga ba sai da ya jera mata miss call 3 sannan ya shafamata lafiya tashi yayi ya shirya dan zai fita .''

Janye suke da shi saman  jaki Sun Rataya masa takalmi a huya ko Riga babu a jikinsa sai zagaye gari suke yi da shi kowa ya gansa ya san me ya aika ta Haka sukai ta yawo da Faruk tun safe har yamma sannan suka Dawo da shi nan D.C ya Kira Yan Sanda suka yi gaba dashi.''

Ilham na tashi ta je ta d'aura Alwala ta yi Sallah sannan ta fito falo dan yinwa take ji, babu kowa a falon sai Aïsha wajenta ta zo ta zauna tana fadin Matar Habibi yakk .''

Bansani lafiya dazun Kika shigo kamar da damuwa a fuskarki.''

Sosai ma nake cikin ta Wallahi wani abokin aiki nane ya takurani Aunty yau fa bidar cin zarafina ya yi fa .''

Amma garin yaya Ilham ?" 

Nn ta fada mata abinda yafaru sosai Aïsha ta ce'' dan Iska dama Bari suka yi Wallahi su kashe sa kowa ma ya huta .''

Wallahi kuwa Aunty har yanzu abin Mamaki yake bani .''

Kinga kibar saka damuwa a Ranki Ilham ni kam me yasa ? Kike son auren Musa Abul Khair ne baki tsoron ki fada cikin Matsala dan na lura fa wanan uwar ta shi ba kaunarki take ba me zai Hana ki hakura da sonsa ."

Aunty ?" Hmm ni ba ita zan aura ba dan ta ne mijina baki na da ita biyaya a matsayin ta na uwa ta kuma uwar mijina amma kibar maganar cewa in dai na soyaya dashi dan intatara in damu zulafate( Wallahi ina sonsa kuma zan aure shi .''

To Babar magana ?" Ki kwantar da hankalinki kin kusa zama amaryarsa dan da zun Alhaji yanzu suka yi maganar da Dady .''

Rumgume ta Ilham ta yi ,tana Mikewa tsaya ta ce'' Wai daga gaske kike Aunty Kai gaskiya Naji dadi zan auri jarumina ,dan take rawa tafara tana Waka ,Allah Nagode 🎤daka bani abin kauna Yan uwa kuzo ku tayani farinciki 🎤kwanan zan shige lanle zanje dakin yayana kuma shine angona 🎤Allah ya kaimu ranar musha shagali shoky.''

Dariya Aïsha ta yi , sakamakon su Mama dake tsaye suna kallon Ikon Allah amma ita Ilham Bata ma san suna tsaye ba , cike da izgili Aïsha ta ce'' Ilham Ashe kin iya rashin kunya bansani ba Kenan aure kike so da kin sanar tun huri ai da yanzu kema kina da yaranki .''

Tsaida rawan ta yi , ta ce'' Aunty Kenan ribar soyaya ita ce aure rasa Abul Khair Dina tamkar rasa rayuwa ta ne dan Haka Banason ana mani tangal tangal dashi ina fatan kin gane ko .''

Wata dariya ta saké shekewa da ita ta ce'' ke da Wasa fa nake yi Dady cewa ya yi ,ya maki miji Ali ne dan gidan baba mai gadi .''

Tabe baki tayi ta ce'' To fadama Wanda bai san halinki ba ,'' 

har Budé baki Zatayi magana ta ji Mama na fadin Sannu da kokari Ilham bansan kin iya Waka mai dadi Haka ba.''

Waya kunya ce ta kama ta ai ko ta zuba a guje ta yi sai harabar gida tana sakin Murmushi .''

Suma dariyan suka yi Dady Yana girgiza Kai ya ce'' A'a gwara Musa ya fito idan ba Haka ba akwaye matsala .''

Gaskiya dai kam Alhaji da Alama dai .''

To Mairiri na ni zan tafi sai idan Allah ya Dawo da dani kuma .''

A Dawo lafiya Alhajina Allah ya tsare ya kiyaye hanya .''

Yana fita yanufa motarsa ya bar anguwar baki day ma .''

Safiya na isa kofar gidan Kitty din ta ta yi , Nocking ,nan yazo ya Budé mata tareda rumgume ta jikinsa Yana fadin Cutie kamar kinsan jiranki kawai nake yi .''

To gani Kitty na ai kasan ya huce matsayin ka nemi Abu ka kasa samu a wajena dan Kai fa dan gata ne .''

Murmushi ya ƴi , ya ce'' Mu shiga daka ciki ko .''

Babu musu suka shiga ciki a falo suka zauna sai da Suka sha firansu sannan suka sha shiga soyayarsu a takaice sai yamma sannan ta koma gida badan ta so ba sai dan marice ya yi sosai dan da kyar ma suka Rabu .''

Kwanci tashi babu huya wajen Allah dan yanzu manyan har Sun shigo lamarin Ilham da Musa maganar aurensu Aka tsaida nan da sati uku ,sosai suka ji dadi a kowane bangare amma banda Ammi dake cike da haushin Ilham dama duk me son ayi auren nan dan yanzu Ilham ta Aïsha na kara kulawa da ita Haka Mama dan yanzu har ta dauki hutu aiki .''

Tun randa Safiya ta Dawo gida tafara sheka Amai kamar Yan cikinta zasu fito tun tana daukar abin kamar Wasa har dai sai da yafara sakamata zazaga yau Yana lafiya gobe ba lafiya Haka take murkusan abin ta batare da ta Bari wani ya fuskanci halin da take ciki ba duk da batasan ciki ne da ita ba .''


Bassira ce zaune ta nama Khairat wasa babanta kuma Yana aiki da computer dan Daho da kallonta ta yi, garasa ta ce'' Ruhi na dan Allah inba damuwa ina son zan je gidan kawata gobe .''

Murmushi ya sakarmata ya ce'' Allah ya kaimu Ruhi na dan sosai yaji dadin Hakan dan tunda sukayi aure Bata taba tambayar izini ba Hakan yasa yau babu musu ya yarda ta je din godiya ta yi masa .''

Ya ce'' karki damu babu abin da Zaki in ki yimaki shi sai de in yafi karfina ko banda halin yin sa .''

To Allah ya barmu tare Ruhi na?"

Amine yafada Yana ci gaba da maida hankali bisa kan aikinsa .''

Kwanaki suja kuma suna ta tafiya muna satin bikin Amarya Ilham  sai shirye shiryen biki ake amarya ta sha gyara sosai sai Kyali take tana daukar Ido ta wani kara kyau kamar balarabiya ga gyaran da take sha Kai abin Ba'a magana , Haka Safiya ke daurewa tana zuwa gidan duk da Ammi Bataso amma Haka ta kyaleta sabida Alhaji ya ce'' ta kara shiga sabgarsu Wallahi duk Abi da ya biyo baya to ita ta jawa kanta ,a bangaren ango ma Ba'a barshi a baya ba abin Ba'a cewa komi sai Masha Allah babu wani shagali da sukayi sai Arabian Night sosai nan ma suka rakashe nan naga fan's din *DOCTOR ILHAM* Sun fito sai kwasar rawa suke suna kwaso shoky .''

WASHEGARI 

Yaune Ranar ASABAR kuma yaune Duban mutane suka shaida auren Musa Abul Khair Iliyas and Ilham Muhamed Bista bisa daki duba dari biyar Sosai mutane su kai ta ya ango murna shiko wai Washe baki yake har kunne .''

A cikin gidansu Ilham sai hidima ake kowa Yana harakar gabansa anci ansha anyi shagali san gwangwaje .''

Bangaren gidan Ammi babu walwala dan Mutanan dake gidan sunke hidimarsu sai dangin Alhaji da Suke ta murna suna zolayan Musa sai de yayi Dariya ko Murmushi amma bai tankamasu har dare yayi Aka zo daukar amarya zuwa gidan Musa Abul Khair 

Nima anan nake tsaida Alkalamina ✍️sai da safenku 🤭
27/03/2022 à 10:08 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

{{YAR LELEN NOBLE ce}}

32/33📓

Dare nayi Aka zo daukar amarya da tasha nasiha mai ratsa zuciya sai Kuka take har sai ta baka tausayi har za'a a fito da ita ta kiya tace'' zan yi magana da Aïsha ,kanwar Mama ce ta ce'' ai tareda ita za'aje sai kuyi maganar ,'' Kuka ta saké fashe dashi ,'' kanwar Mama ta ce'' Wai Ilham bazaki shiru ba minene ,'' sai da taja nunfashi ta ce'' yinwa nake ji zanci abinci tafada cikin muryar Kuka ,'' Dariya suka kwashe da ita suka ce Zaki amma Muje mutane mu suke jira ,Haka Aka fito da Ilham suka saka ta a mota sai sai gidanta kowa ya ga gidan sai yayi santinsa ya hadu iya haduwa kuma an tsara shi yayi kyau Haka Aka huce da ita dakin Jahid Bayan an yi Sayan baki kowa ya watse sai Safiya da Da'ifa sai Arifa ,da sauran abokan Ango ,nan su ka yi ta tsula tsiyarsu har suka gama kan Ilham Na duke tana Kuka ango ne ya kallesu ya ce'' Kai dan Allah baku ga dare ya yi ba ku tafi mana dan in samu damar rarashin Amarya mana ,'' Sadik ne Baban Abokinsa ya ce'' To dan Iska zamu tafi Allah Bamu Alkairi amma kabi yarinyar mutane a sannu dan kar ta ji ciwo ,'' Sahib dake gefen Sadik ya Kai masa duka Yana fadin Kai de anyi dan iska ,Haka dai suka yi suka gama ango ya rakasu ya jima waje dan sai da ya saka su Safiya a mota sannan ya Dawo ciki da sallama ya shigo ,a kasan makoshi ta amsa masa nan ya kariso wajenta tareda janyota jikinsa Yana dage Sakalar da Aka rufe ta da ita Yana kallonta fuskar ta a sunkuyi yasa ka hannu Dago ta ya ce'' Ilham din Abul Khair Waye Ya tabamin ke ne ,'' kara sunkuyar da Kai tayi ta ce'' Kai mana ?

Ni kuma Yan mata na me nayi .''

Dan turo baki ta yi amma Bata ce komai .''

To na gane kiyi hakuri nayi laifi amma wajen masoyinki Zaki kwana ko .''

Ni gida zanje fa ?"

Muje na Rakaki ,'' Mikewa ta yi ,tareda mai da Sakalar ta ta fito waje har ta Kai gaban get ganin da gaske take yasa yama mai gadi Alama ,ai ya kulle kofa, da gudu ya kariso ya sure ta kamar baby suka Dawo suna Dariya ,suna shiga dakin ya ce'' Wai har kin Dawo ta gajiyar hanya .''

Babu tafada a takaice .''

To yanzu dai Muje muyi sallah mu godiya Allah Daya gwada mana wanan ranar ta farinciki mai Albarka .''

Babu musu ta Mike suka nufa toilet a tare sai da ta jira ya Kammalla sannan ta saka Key wai dan kar ya shigo sannan ta dora Alwala tafito ,'' tana fitowa dama ya shimfida darduma ya jamasu sallah Bayan Sun Kammalla ne yamasu addu'a suka shafa sannan ya janyo mata kazarta ,da kyar yasa mu ta ci kadan sannan suka je suka kwanta .''

Safiya ce dake zaune ita da Ammi suna dan taba fira taji zuciyar na tashi sabida kamshin abinci dake tashi ai ko tayi waje da gudu tana kwarara Amai kamar Yan cikinta zasu fito musanman ma Bata ci wani Abu sosai ba Hakan yasa ta gallabaita sosai , sai da ta gama ta Dawo falon kallonta Ammi ta yi, tace'' Safiya lafiyarki lau kuwa?"

Lafiya lau Ammi jiya ne naci abinci wajen Arabia Night to ina ganin Zafi ne ya tasomin  .''

Eyahh yaka mata kisha magani .''

To yanzu zanje in sha .''

Tana gama fadan Haka ta shige daki tareda kiran Wayar Kitty Yana dauka babu wani gaisuwa bare kuma soyaya ya ce'' Kitty Kana ina ne .''

Lafiya dai ko ? Cutie da wanan daren Haka .''

To ba zance komai ba ina son za muje gobe asubiti ni da Kai. '

Asubiti kuma wani za muje dubiya.''

A'a ni zaka Kai sabida ina zargin wani Abu .''

Shikenan Allah ya kaimu sai kinzo ki.''

Ok bye Kitty na .''

Katse kiran ta yi , tareda yin kwanciya tana tunanin rayuwarta me ya Aike ta biyewa shairin zuciya ta Bada mutumci wajen wani Wanda ba mijinta me zata ce ma Allah wasu hawaye ne zafafa suka gangaro da kwarin Idonta sai da taci Kuka mai isarta sannan ta share hawayenta kanta dake saramata ta dafe tana karanta Addu'a ta samu yayi dama sannan wani bacci yayi gaba da ita .''

Bayan tafiyar Ilham gidanta ne Mama ta kalli Aïsha ta ce'' Aïsha Wallahi hankali sam bai kwanta da auren nan ba sabida watsan Murja wace baka tsokane ta ba tayi ta surfa ruwan masifa bare kuma an jata kiga fa ko diyarta bassira Bata zo ba sunan ana auran Yayanta .''

Mama ki kwanta da hankalinki kiyi mata fatan alkairi insha Allah babu abin da ta isa ta yi mata in Allah ya nufa yasa me ta ba .''

Hakane maganarki to ina fatan Alkairi ya basu zaman Lafiya .''

Amine Mama ni zan je in kwanta a gajiye nake .''

To yau baza kuyi fira da Saïf bane .''

A kunya ce ta ce'' A'a ya sha kanwa ba zai iya magana ba sai ya sauko.''

Dariya Mama ta yi , ta ce'' lanle dai kam buhu nawa ta bashi ne .''

Mikewa Aïsha ta yi, ta ce'' Yana da yawa ni kaina ban san  yawansa .''

Lanle zamu ci tarar Ilham duk Randa ta shigo gidan nan .''

Dariya Aïsha ta yi tana hayewa sama tana shiga ta kwanta wani baccin wahala ya yi ,gaba da ita .''

WASHEGARI 

Bassira ta shirya tsaf Bayan ta gyara ko ina gidan ta ta yi , gidan kawata a tsan zata huni hunin ranar fira kawai suka sha abinsu har sai da Sani ya Dawo sannan ya dauko ta suka Dawo gida abinci suka ci suka suka shiga firarsu ta masoya .''

Tana ta shi ta yi, sallah ta  sauko suka hada abin break Bayan Sun Kammalla kowa yaje ya shirya sannan suka halara a danning suka fara antayama cikinsu abinci ta Riga kowa fida hannunta dan Bata jin dadin abinci Haka ta tashi ta nufi daki dama ta shirya ta dauko mayafinta ta saka ta dauko Jakarta ta fito, ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' Ammi zan fita .''

Ina zuwa kuma yanzu ?" 

Zan je wajen aikin nan ne mantawa nayi nafadamaki na samu  wanan hidimar ce ta saka na manta .''

A'a Masha Allah Allah yasa Alkairi cewar Alhaji .''

Amine Baba sai na Dawo .''

A Dawo lafiya suka yi mata ta fita mai Napepe ta tare ta fadamasa anguwar da zai Kai ta ya fadamata kudinsa sannan ta shiga Sun dan yi tafiya kafinsu iso ,suna isowa ta bashi kudinsa ta shige gidan ,Yana cikin bacci yaji ana Nocking ta shi yayi yazo ya buge kofar ganin ita ce yasa ka murmusawa Yana rumgumo ta , dan buge hannunsa ta yi ,ta ce'' ka shirya mana kafito mu tafi Kai nake jira , babu musu ya ce'' To Muje ki ta yani wanka .''

Harara ta Ballamasa ta ce'' naki bazan yi ba ?" 

Kai tsaye Haka Cutie .''

Shiru ta yi ,masa Hakan yasa shi tashi ya tafi ya shirya sai da ya kusan Kai Awa day sannan ya fito suka huce Asubiti *CLINIQUE DU KATSINA* suna isa suka shiga ciki nan suka hadu da D.C Mansoor Bayan ya mata wasu Yan Tambayoyi ta amsa masa ne yasa Aka de bi jinin ta da fitsari ya Kira Norse Asiya ta tafi dashi ,Sun dan jima sosai kafin a Kammalla sannan Norse Asiya ta Dawo dauke da résultat ta Mikewa D.C Mansoor sannan ta juya ta yi tafiyar ta ,dubansa ya maido wajen Safiya ya ce'' Félicitation Mdn .''

A dan razane ta ce'' Pourquoi fa ?" 

Kina dauke da ciki wata biyu .''

Da sauri ta mike tsaye tana kallon Kitty da D.C ta ce'' ciki kuma har wata biyu wani marayan Kuka ne yazo mata tareda fadawa jikin Al'ameen ( Kitty ) tana fadin ni dai Banason cikin nan a cire mani shi Bana kaunarsa wayo Allah na bani na bani na lalace nashi ga Tasa'in da tara .''

Jikin Al'ameen da ya yi , sanyi ne ya saka shi daga ta tana bubuga bayanta alamar rarashi cike da damuwa ya ce'' Muje gida za muyi magana .''

Babu musu ta mike tsaya Doctor ne ya kallesu ya ce'' ga wanan Ordonnance din a siyama ta magungunan nan ya zamana tana shan su a kan Lokaci ,kafar ya yi , yaja hannunta suka fita suna fitowa suka shige mota sai rizgan Kuka take tana nadamar abinda ta aika ta har suka iso gidan Kitty Bata dai na Kukan ba ,parking ya yi , yafito tare da zagaya wa ya Budé mata kofa tare da sungumota suka shiga ciki a falo ya dire ta ya zauna kusanta cike da muryar rarashi ya ce'' Cutie gaskiya ban ji dadin Kika aika a asubiti ba sai ka ce bakisan ko Waye uban dan cikinki ba kenan dama ba so na kike ba .''

Ai Kai naga Kana Sona tunda har ka karfi mutumci na ba aure sannan ko maganar baka so ina yi maka Haka kuma zaka gudu ka barni da wanan wahalar kuma in haife gaskiya ni bazan iya ba cire shi zan yi Wallahi .''

Ki gane ina sonki Dady ne baya Yaki ya mani aure shine .''

Gudan balligi da Kai Haka zaka ce wai bazai maka aure ba ba ka dai fito da matar ba .''

Sorry ki yi hakuri karki zubar da wanan cikin zan kula da shi kuma in dauki nauyin komai na shi in sha Allah .''

Mikewa tsaye ta yi, ta ce'' wallahi bazan iya ba Haka kawai sai Na haifi dan shege ina yar sunna sai de kayi duk abin da zaka yi amma sai na zubar da shi .''

Wani uban mari ne ya sharara mata ya ce'' dan nawa ne dan shege Ashe baki da mutumci Safiya Wallahi kibani mamaki .''

Karya na fada ba shegen bane fadamin in ji a aure muka same sa ne kuma ka jini da kyau ko ka fito muyi aure Kona je gidanku da wanan cikin tunda kace kar na zubar da shi nasar da su sai su tsaida ranar aurenmu .''

Tana gama fadan Haka ta yi tafiyar ta fitowa ya yi , Yana kiranta amma ina har ta tsaida mai Napepe ta shige shi ko ya ja suka yi tafiyarsu .''

Ilham da ta tashinta Kenan ta yunkura zata Mike taji duk jikinta Yana mata ciwo wani marayan Kuka ta saka tana komawa ta kwanta ,da sallama ya shigo tareda karisa wa wajenta Yana fadin Albi na barka da safiya a she kin tashi.''

Hararen sa ta yi , tana juya masa Kai baya ,'' wai fushi ake dani bara nazo na kara sai in yi rarashi .''

Wani Murmushi da Bata san lokacin da Zoma ta ta saki tana fadin banaso Wallahi .''

Dariya ya yi Yana kariso wa wajenta ya janyo hannunta ya ce'' Ilham hakika Naji dadi kuma nayi farinciki sosai da Allah ya mallakamin ke a matsayin mata kuma Kika bani Abu mafi tsada a rayuwarki bansan wace Iriyar godiya zan yi maki ba ina kaunarki Ilham Allah ya barmani ke ya Bamu zaman Lafiya da Hakuri da juna abar Alfahari na ke din daban kike da sauran mata ke zinariya ce Ilham bansan ya zan musultamaki Irin baiwar da Allah ya yi, maki ba .''

Murmushi ta yi ,ta ce'' Kamar yanda Allah yabani miji na gari ba nima ina godiya ga Allah Allah yakara mana kwanciyar hankali da Hakuri da junanmu .''

Amine yafada Yana sumbatar ta tareda daukarta ya yi , toilet da ita sai da ya wanke tsaf ta yi, ta tasarkake Kanta sannan suka fito nan ya Taya ta shirya wa Bayan Sun Kammalla ne ya ce'' Rayuwa ta Muje kici abinci ko .''

Bata ce masa komai ba dan ita har yanzu kunyarsa take ji ,'' Murmushi ya yi ,tareda janyo ta da dan karfi ,da sauri ta ce'' wash ?

Dariya ya yi , tareda sungumota suka fito falon tana dire ta a Capet ya je danning ya dauko masu breakfast dinsu suna fara cine har zata yi magana Ammi ta banko masu kofa da karfi tana yi kan Ilham tareda................................................................................
27/03/2022 à 15:38 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

{{YAR LELEN NOBLE ce}}

34/35📓

Tareda tsayawa gabanta ta ce'' ke yar Marasa mutumci karuwa mai lalaci nazo ne Naji Sakamako ko yasa meki a budurwa ko sabanin Haka .''

Cike da Mamaki suke kallonta da Ilham batayi tunanin Ammi ta daka Iskanci ta shanye shi a cikinta wai har ta kalli tsabar idonta tana fadamata Hakan wanan wace Iriyar uwar miji ce ,katse mata tunani ta yi , ta hanyar cewa dake nake kinyi jugume kina saurare na , fashewa tayi da Kuka tana Mikewa tsaye ta ce'' ni bani da amsar tambayarki sai dan ki yake da ita ,tana gama fadan Hakan tafara tafiya da kyar har ta iso daki ta fada kan bed tana ta Kuka ,'' Dan fata fuska ya yi , ya ce''  Ammi me Hakan ke nufi me Kika aika ta yanzu a gaban SURIKARKI Kika fadan Hakan .''

To shanyaye daga aure jiya har ta gama da Kai ko Daya ke su din dangin mayune dole Hakan ta faru .''

Naji Ammi kiyi hakuri bazan Bari ta shanye ni ba zan yi ta zabga Sallolin dare kuma kema ki Taya ni yafada Yana gumtse dariyarsa .''

Banason iskanci Musa ni zaka yi ma rashin kunya ne .''

A'a Ammi ki zaune ki huta an jima na Kai ki gida .''

Banaso Kai ka kawo ni ne kuma ba zama nazo yi ba dan Haka kaga tafiya ta .''

Fita tayi shiko yabi bayanta har sai da yasa ka ta Adaidaita sai masifa take amma ko kyalla bai ce da ita ba bare ya amsa mata tana shigewa suka tafi shima ya Dawo gidan direct dakin da Ilham take ciki ya nufa ya sa meta kwance tana Kuka wajenta ya kariso tareda janyota jikinsa ya ce'' Amarya ta dan Allah kiyi hakuri nasn Ammi Bata kyauta ba nasan ki da Hakuri ki kara da Wanda kike da ba Tun yau Kika Saba ganin Haka ba gashi kuma duk Irin abin da take maki sai da Muka auri juna to a nan ne Zaki Nuna mani kallar naki hakuri Haba ke fa jaruma ce yar Aljanah.''

Shiru ta yi , tana share hawaye ta amma Bata ce komai ba Haka dai yayi ta rarashi har yasa mu ta saki jikinta suka Dawo Wasa da Dariya .''

Haka rayuwa ta yi , ta tafiya in da Ammi kullum sai Tazo dan ta kurawa Ilham har ta samu ciki Haka take rayuwa babu dadi a cikinta sai de in mijinta Yana gida amma Ammi sam Bata raga mata wani ta yi ,Kuka wani kuma mamaki amma Hakan bai sa ta Sanar da gidansu ba dan ta san Aïsha Bata da dadi da hakurin magana shi yasa ma Bata Sanar da ita ba sai de in ta Kira ta suyi Waya bisa kan Abin da ya shafi rayuwa ko yanda zata kara kulawa da mijinta sai ta katse Wayar .''

Aïsha ce kwace akan cinyar Mama yaranta kuma suna wasa da Inteesar ce tsale tsale suke abinsu nan Saïf ya kira ta dagawa ta yi , Bayan Sun gaisa ya ce'' Matar Saïf wai yaushe Zaki dawo Wallahi akwaye matsala fa.''

Dariya ta kyalekyale da ita ta ce'' Sorry sai kanwar da Aka baka ta saké ka .''

Af toh kema sheganta Zaki yi man Irin na Al'hassan wai cemin yake gabro ni dai dan Allah ki Dawo .''

To zan Dawo amma da sharadi sai na bikin Ilham idan ta haihu ka yarda .''

Haba yanzu fa kina cikin wata na biyu Kuma ki Dawo da Watan goma in da rai .''

E'e in ba Haka ba gaskiya sai de in yi zamana ko kazo muga Juna ka koma.''

Gaskiya na yarda da Hakan idan Na jayeki wa zai kulamin da Amarya ta .''

Hmm ba dai zaka Bari ba ko zan fadama Musa fa ya dauki mataki a kanka .''

Dariya ya yi , ya ce'' zan zo nan da jibi sai nayi sati na koma .''

To ba damuwa Allah yahomin Kai lafiya mijina .''

Amine matar Saïf ki kullamin da kanki kafin nazo ta Dawo hannuna .''

Insha Allah Karka damu ka dauka an gama sahibi na.''

Katse kiran ya yi , ita kuma suka ci gaba da firarsu da Mama.''

Tunda daga ranar da Safiya taje asubiti ita da Al'ameen Bata sake ganinsa ba ko ta kira shi bata shiga in ma ta samesa to bazai daga ba duk tabi ta rame ta kanjame ta yi baki ga kuraje da Suka fito mata burma burma Sun Bata mata fuska kullum tana cikin Hijjabi Bata Bari su hadu da kowa a gidan dan tun safe idan tafita aiki sai ta daura ci Ammi ta shiga sallah ko Batanan take shigowa kuma da ta shige dakinta Bata fitowa abinci a sace take cinsa yau de karya ta Kare sabida a tunaninta ba yanzu Ammi zaka Dawo ba dan ta san idan ta fita sai yamma lis take dawowa Sai gashi yau Allah ya Dawo da Ita kwance take sai bacci take sha abin ta babu Hijjabi a jikinta ga cikin nan yakara fitowa dan yanzu watansa uku sabida koshin da ta yi , sai ya kara fitowa ,'' turus Ammi ta yi , tana kallon Ikon Allah me take shirin gani Safiya da ciki duk Irin tsananin da ke yi masu amma a banza shine taji ta zubda masu mutumci da kimar gida ajiyar zuciya ta sauke ta huce daki sai da ta dauko dorina mai Harshe Hudu duk ta sha mai sai kyalli take sannan ta dawo falon tana cikin baccinta mai dadi ta ji saukar bulala har cikin kwakwalwar ta Batasan lokacin da ta tata shi tana kwarara ihu nan Ammi taci gaba da zabga mata ita ita ko sai ihun neman dauki take amma babu kowa a gida sai da tayi mata lis yanda ko yatsan hannunta bazata iya dagawa ba ta kyale ta tareda zaunawa ta Kamo kunnenta tana janyota da shi ta murde shi ta ce'' dan Ubanki sabida kin daukeni yar Iska shine Kika je Kika aika ta faskanci dama tunda ganki da watsan shegiyar yar Asarar yarinyar Ilham nasan kema sai kin yi Irin Nata halin ta koya maki karuwanci ta aure yayanki yanda asirinta zai rufu ke kuma ta tona naki ko walahi sai kin fadamin Waye uban yaron nan .''

Cike da Tsoro da rawar jiki Safiya ta ce'' wallahi ba laifin Ilham a wanan harakar dan tun kafin mu shirya da ita nake yi abu na kuma ita kanta Bata sani ba da ta hanina kuma Al'ameen dan gidan Aunty baraka ne ya mani ciki .''

Al'ameen ?"Ammi tafada ta ce'' zanci uwarki dan kanwar tawa kike son lakama ma laifi ne kuma ina Kika san shi har Kuka hadu da shi .''

Lokacin da yaya ya Dawo daga karatu ranar Muka hadu da shi tun daga ranar muka fara sabawa da shi har ta Kai ni da ina zuwa gidansa idan shi bai zo ba soyayar sa da kaunarsa suka shigeni sosai ta yanda bazan iya hanamasa Dukan abin da yake bukata daga gareni ba mun kai Shekara biyu fa haduwa yane mi da Na bashi kaina in ba Hakan ba Zai iya rasa ransa duk yabi ya damu sai hada gumi yake Ashe abokansa ne suka sakamasa maganin ta da sha'awar kasancewar ranar haihuwarsa ce wai ya more ranar ni kuma bazan iya rayuwa in ba Shiba ganin zai mutu yasa na bashi Kai na har ya samu natsuwa tun da ga wanan lokacin Muka fara rayuwa kamar mata da miji har ta kaimu ga munsamu ladan zinar da Muka ke aikata wa ,sunkuyar da Kai ta yi, tana Kuka sai ta baka tausayi sake lakada mata duka Ammi ta yi , sai da taga tana fitar da jini daga kasanta sannan ta kyale ta shigowar Alhaji Kenan Yaga wanan Tashin hankalin ga Safiya na zubar da jini Ammi ta yi , zaune sai lalatsa Waya take kamar ba uwarta ba Hakan yasa ya sure ta ya yi , asubiti da ita  taimakon gagawa Aka Bata ta hanyar ta karbanta suka yi ciki da ita tareda dakatar da Alhaji .''

Ganin Sun fita yasa Ammi saka Hijjab din ta ta yi , gidan Musa lokacin baya gidan ya fita Ilham take kwance tana jin jiki sakamakon jaririn cikin dake Bata azaba tana shigowa tayi kanta tareda shake mata huya ta ce'' dan Ubanki Irin masikancin da kike yi ne Kika koyawa Safiya dama ta tabata ke karuwar ce mijinki ya rufamaki asiri Wallahi sai nayi Ajalinki uban kowa ma ya huta nan ta shiga duganta hannunta day tana shake da huyan Ilham ta kar ta samu Allah ya taimaka ta tataro Dukan karfinta ganin fa zata Ila tata yasa ta ture ta ta fito daga gidan a guje ita m Ammi ta biyo ta da gudu ta tare mai Napepe ta ta shege sai da Suka fara tafiya ta fadamasa inda zai Kai ta ,ita ko Ammi nan ta yi , ta tsayuwar babu Abin hawa har su Ilham suka bacewa ganinta sosai ta ji haushin Hakan ,su Ilham Na isa gidansu ta fito ta ce wa baba mai gadi ya bawa mai Napepe kudinsa har ta fito ,'' ganin yanda take babu hijab ba mayafi bare takalmi ya sa shi Mikewa ya basa kudinsa ,tana shiga falon Mama ce da Aïsha babu ma kowa a gidan dan tunda yaran Aïsha suka tawo suke tafiya makaranta da Inteesar wani marayan Kuka ta saki tana fadawa jikin Mama ,'' in hankalin Mama da Aïsha ya yi , dubu to ya ta shi nan suka shiga tambayarta ganin Kuka bazai tsaya ba ne ya sa Aïsha janyota jikinta tana shafa bayanta alamar rarashi sai da ta tsagaita kukanta sannan ta ce'' Aunty ba rarashi nake nema ba dubanta ta mai do ga Mama ta ci gaba da cewa Mama ina son yau ba gobe ba ki Sanar min miye tsakaninki da Ammi na gaji da cin fuskar da take min yau fa bidar kasheni ta yi , tana kirana karuwa mai lalasisi me nayi mata bansan hawa ba bare suka ta dauki karan tsan ta daura min Wallahi ta ci mutumci auran dan ta da nake yi da ta gane ruwa ba sa'an kwando bane.''

Tunda ta fara magana Mama take kallonta dan tunda Take da Ilham Bata taba tunanin yi ma wani rashin kunya bare Babar Mace kamar Ammi cike da rarashi ta ce'' Ilham ki daina Kuka kiyi hakuri komai ya huce miye abin mai da shi baya kiyi hakuri kin ji .''

Mama ba hakurin ki nake bukata a yanzu ba ni kawai ki Sanar da ni Bana son jin komai in ba abin da nake son sani ba .''

Kuma Mama ta fashe dashi tana sunkuyar da Kanta sai ta ji abin da ya huce Shekaru masu yawa Yana dawo mata yanzu .''

Ganin Mama baza ta fadama ba yasa Aïsha cewa ki zauna ni zan Sanar da ke ,'' Babu musu ta zauna tana jiran fewar Aïsha Dady ne ya shigo dan yaji komai Ilham ke fada dan tun shigowar ta shima ya danno Kai .''

*TUSHAN LABARI*


Alhaji Muhamed Bisa, baban abokine ga Alhaji Mudanssir wato ( baba ) dan tsananin shakuwar da Suka yi ne yasa har suka zamana ana masu kallon Yan uwa a tare suka Kammalla makaranta su tun basuda ko sisi Haka suka fara aïkin gini kuma suna neman aiki abinci a tare suke cikinsa komai nasu Irin day Hakan Allah ya nufa Muhamed Bisa samin aiki inda Mudanssir har yanzu takardunsa basu fito ba har Muhammad yafara aiki har ya taka baban matsayi ya dauki Mudanssir aiki sosai yaji dadi da farinciki Kuma suka je gaban iyayensu nan suka ta yashi murna inda Mamar Mudanssir ta yi , ta ma Muhamed godiya har da kwallar ta kuma ta je gidansu ta yi ma iyayenshi godiya dan Baban Mudanssir ya jima da rasuwa ana cikin Hakan ne Bista wato Mahaifin Muhamed yafara masa maganar aure shida Mudanssir tareda gargadin kar Wanda ya Dawo masa ya ce'' bai samu mata ba dan duk wace ya ga dama zai hadasu da ita jin Hakan ne ya sa Muhamed saka manajensa ya samosa Yan mata Haka Aka yi Kai masa su Yana cewa a samu wato cikin wadan da Muhamed ya ce'' ba ya sone Mudanssir ya yi kitibus da Murja ita da kawar ta dan Murja ta so Muhamed ya aure kawar ta Hajara amma ina sam yaki yarda har suka fara shan soyayarsu kullum sai ta yi , ma Mudanssir zan tsen Hajara wajen Muhamed Bisa amma shi Bata gabansa wata Rana da marice sunje Shopping shida Mudanssir da Murja shiko Muhamed dan rakiya ne Bayan Sun gama ne suna fitowa Maryam zata shiga ita da familly Nata tunda Muhamed ya hangota yake ta kallonta dan har da budan faduwa ya yi , sosai yarinyar tata fi ,cike da siyasa ta dauki photon ta sannan suka tafiyarsu ,Murja na ganin wacce Muhamed yake kallon yasa tafara kishi da ita sam ta ji Bata kaunar ta a Haka yasa Managen sa nemo masa Maryam har Allah yasa suka gano gidansu Bayan sati day ne su Muhamed zuwa gidansu Maryam suka saka a kayi masu sallama da papanta ya masu ISO zuwa falon baki bayan Sun zauna ne suka shiga gaisawa nan Mudanssir yafara koro masa maganar dake tafe da su ,sosai papan Maryam ya ji dadi dan hanyar da Suka biyo ita ce daidai Hakan yasa ya ce'' tabbas Kuma hakika Naji dadin Hakan da Kuka yi amma bazan yi saurin baku ita ba har sai Naji daga gare ta ina son ku dawo nan da sati day .''

Godiya suka yi masa sukayi sallama suka Baro gidan .''

Papa Yana shiga gida ya samu Momy ya fadama ta abin da ke tafe da su Muhamed sosai ita ma nayi murna dan yanzu ba yawan samari suke neman izinin iyaye ba suke fara soyaya da Yarinya har suzo gidansu ta ce'' to Babu damuwa ?" Zuwa an jima da marice dan Sanar da Maryam din idan Sun dawo daga School .''

Gaskiya dai kam amma ke kina tunanin zata yarda ne .''

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' ina tunanin Hakan dan Maryam bazata taba watsamana kasa a Ido ba .''

Hakane nima Na yarda da Hakan .''

Bayan an yi sallah La'asar Maryam ta Dawo daga School sabida rattrapage suka yi tana shigowa sai da ta watsa ruwa ta huta sannan ta ci abinci nan Momy taje Sanar da ita maganar Muhamed a nutse ciki tautausar maganar ta dan karamin bakinta Yana motsawa hankali tayi kasa da Ido tana wasa da yatsun hannunta ta ce'' To Allah yasa Alkairi a ciki ni bazan iya jayaya da Dukan zafin ku gareni ba dan nasan na gari ne Zaku bani dan Haka bani da Abin fada face Allah ya saka Alkairi ne ke tafe da shi .''

Amine Maryam Allah ya maki Albarka .''

Amine Momy ,'' Bayan Sun gama firar ne ta shiga gyara gida da dora girki tana Taya masu aïki .''

Tun lokaci da Muhamed ya zo gidansu Maryam Papa ke bincike Akan sa ganin babu wani aibu garesa yasa bai yi yinkurin hannashi auren yar sa ba ,'' satin da ya basu nayi suka Dawo nan suka ji Sakamako mai kyau .''

Bayan wasu watanni Aka fara maganar auren Mudanssir da Murja sai kuma Muhamed da Maryam sosai Murja ke jin haushin Maryam dan ta fita da komai ba kyau tarbiya girmama na gaba da ita dama Wanda ta girma dan kar girman ta ya fada sosai take Kare mutumcinta dan har yanzu Bata Bari Muhamed ya taba ko da hannunta ne har Aka daura masu aure ranar biki an sha shagali anyi facaka da dukiya har Allah yasa amare suka tare gidansu day sai de kowa da Nata bangaren babu ruwan kowa da dan uwansa sai ma Maryam ce idan ta gaji da zaman taje wajen Murja amma babu abin da take mata sai habaici Hakan bai sa Maryam ta ji haushi ko ta taki komawa wajenta Haka rayuwa ta ci gaba da zuwa Murja sam Bata kyautata ma Maryam sai mugunta wani lokacin har ta nemi yin dambe da ita amma Maryam Bata yarda da Hakan ba dan ta san Murja ja mata shairi take son yi tunda tana da ciki sai de ta koma part din ta ta ci Kuka idan abin da Murja ta yi ya Bata mata rai musanman Gorin haihuwa da take mata amma duk abin da ake mazajensu basu sani ba dan in a gabansu ne to Murja zata saki jiki Su sha fira da Maryam Bayan Idonsu ne take gallazamata suna Haka har Murja ta haifi dan ta Santatale hadade mai kyau ga daukar Ido dan idan kaga yaron zai baka sha'awa kaji ya birgeka Bayan an sallame su daga Asubiti ne suka koma gida nan Maryam da sauran Yan uwa Murja suke kama aiki kuma har ranar biki yaro ya ci sunansa Musa Abul Khair sosai Aka yi farinciki da murna anyi biki kamar ba gobe anyi kacakaca da kudi ,'' 

Bayan biki kullum Maryam tana wanan Murja amma sam Bata Bari ta dauki dan ta yau ma yaron Yana rike da hannun mai tsaro jego Maryam ta karbesa tana masa Wasa sai Murmushi take sosai take jin yaron kamar ita ta haifeshi Murja da fitowar ta daga wanka taga yaron ta hannun Maryam yasa ta nufe ta da sauri tana kokarin Amsar dan ta tana cewa wai ke dan Allah me yasa baki da zuciya ne Kare ya dauke ke dama kunnen kashi gareki ne .''

Ki yi hakuri Wasa nake masa ne?"

Nabi hakuri da gudu ba takalmi naci uwarta idan Wasa kike son yima yaro to ki haifo naki mana .''

Wani Irin sulaluwa taji zuciyarta ta yi , ta ce'' Allah bai mance dani ba kuma zai bani da yarda sa .''

To ki fice min daga part tunda kema kinsan naki Yana nan zuwa .''

Haka ta tashi ta fice daga part din cike da takaicin halin Irin na Murja .''

Tun da wanan lokaci Maryam Bata saké tafiya wajen Murja ba dan ta fara gajiya da halinta har sai da ta ji Arba'in ranar da koma dan yi abin sadaka dayake Hajara ma tazo nan sukai ta habaicinsu suka gaji ko ci kanku Bata ce ba ta yi , Abin da zata yi Ita da kanwar Ammi ( Mamar Al'ameen) ta yi , tafiya ta.''

Kullum zamansu babu tsanji Hakan yasa yanzu Maryam Bata tafiya wajenta ganin Maryam ta daina zuwa kwana biyu yane yasa Murja fitowa daga part din ta tayo waje ganin Maryam a harabar gida ita ka dai sai karanta litafinta take mai Suna Farhat tana sakin Murmushi dan bakamin Dariya take Shaba tsakanin Farhat da Al'ameen musanman in da yake sharara mata karya sunje gidan rasuwa ya ce'' Wai Abba ya ce'' tayi kwanciyarta wajensa shi bazai samu damar zuwa ba.''

Tana cikin Dariya ne taji ta ta howar Murja tana tafe tana Tulla yaronta tana Waka mu dai Allah ya bamu dana dada Zuci idan fitsari Banza ne kaza ta yi shi mugani .''

Girgiza Kai Maryam ta yi, ta ci gaba da Harakokin gabanta ,'' Haka Murja ta yi , ta gama Maryam Bata ce da ita komai ba .''

Bayan shakara biyar ne Allah Yaba Maryam cikin Haka ta yi, jan Kayanta sam Bata Bari Murja ta sani ba sai ma kyau da cikin yasaka ta ta kara kyau da haske Murja Bata san da cikin Maryam ba sai labarin haihuwarsa ,dan a tare ma suka haihu ta haiho yarinya ta su duka ya'ya mata ne gare su ,dan tsabar masifar sai da ta je ganin abin da Maryam ta Haïfa ta ga kyaukyawa yarinya sabanin tata yar dan yarinyar Maryam sai de godiyar Allah cike da jin haushi da ta kaici ta Baro part din Maryam ta samu yar jaririyar diyarta tana dukanta kamar ta samu Jaka da sauri mai tsaro ta amshe yarinya tana cewa Haba mana Murja miye yasa bakida hankaline me wanan yarinyar ta yi , maki daga zuwanta ki sameta ki yi ta jumga idan Kika kashe ta fa .''

À hasale ta ce'' kin ga iya babu ruwanki ai bake kika haifarmin ita ba taya zata yarda afi ta kyau ita kuma ta fito Haka .''

To kaji wani ikon Allah lanle sai yanzu na yarda cewa baki da hankali Wallahi kishi kike da Maryam ne har yanzu kema kin san ba daga Diya ba ko ke Maryam tafiki kyaun kallo bare kuma abin da zata Haïfa ko da basu yi kyau ta to zasu yi na ubansu kuma shima Musa kibar ganinsa hadaden yaro kyaukyawa wajen ubansa ya gadosa dan indai yaran ki zasu biyoki nasan sai muni kamar buri Haka zasu yi ta yi .''

Shiru ta yi ,sai cika take tana batsewa har zuciyarta ta sauko ,ranar biki ne yarinyar wajen Maryam ta ci sunan Aïsha Humaira , in da yar Murja ta ci sunan Bassira  duk da ba wani shagali Aka yi sosai ba sabida ubannin yaran basu gari amma Alhamdulilah kowa ya wadatu .''

Tunda Murja ta Lura da Musa yafi Shakuwa da Maryam sakamakon yawan jansa da take a jiki shi kuma uwarsa babu abin da take yi sai aiki latse latsen waya hakn yasa duk yaranta suka ja baya daga gare ta zuwa wajen Maryam nan zata biye masu suyi ta guje guje cikin gida da Sun gaji su huta in lokacin Sallah ya yi , su je,su yi suci abinci su dora daga inda suka tsaya .''

Dan shiyasa ta dauke shi ta kaishi wajen yayarta dake tsan kasashan waje da kyar ya Saba da ita kuma yake yarda da ita ,nan ya koma da rayuwarsa sai de suyi Waya da Murja .''

Bayan Shekara uku ne Aka haifi su Ilham da Safiya sune suka sha gata da soyaya musanman yanda Dadyn su Aïsha ke kulawa dasu wannan ma ba karamin haushi yake ba Murja ba ganin duk yanda ta so huce Maryam sai Allah tafita da wani Bangaren mai mahinmanci in da lokacin Bassira da Aïsha suna primaire Ajin na farko suko su Ilham lokacin ko tafiya Bata fara ba .''

Shekaru Sun ja kwanaki Nata tafiya Allah ya saké bama Maryam cikin inda Murja take ta jiran tsanmani dan tunda ta Lura da cikin Maryam yasa ta ke yawan takura ma Mudanssir a doli sai ya Bata 😂wanan Abu tun yanayi da dadin rai har yafara gajiya dan bai san mi yasa take yawan takura shi ba,'' ganin Bata samu ba yasa kullum sai ta nemi Maryam da dambe dan cikin ya zube amma sam Maryam taki yarda da Hakan dan da taga take Taken ta zata gudu part din ta ta saka Key sai da cikin Maryam ya kai wata tara kullum Murja sai taja fada Rana t'ai ta zaginta Hakan yasa Maryam kasa jurar zagin ta ce'' Murja ina baki girmanki amma bakisan Hakan ba ina daraja ki ke kuma kina kasa da kimarki shiru shiru ba tsoro bane hakuri kawai nake dani dan Allah ki fita a hanya ta Bana son kina zagin iyayena dan nasan mutumcinsu kuma suna Dukan komai na rayuwata Banason na fara sa'in sa dake sabida nasan kin bani har Shekara biyu kuma kin rigani shigowa a wanan gidan kafin nashigo duk da ranar day Aka kawo mu amma na lura ke bakasn Ana daga maki kafa ba .''
 
An je an zaga kiyi Dukan abin da zakiyi wani daraja da mutumci ke da iyayenki su wanan yar uwayan tsishine bacin  shara bolla dabbobi jakai .''


jin maganan ganin Sun yi muni yasa Maryam sharar ma Murja mari ta ce'' ilar rashin tarbiyar Kenan da daga gida kinsamu tarbiya babu ta yanda za'ayi ki rena uwayen wasu koda daga sama suka fado kuma Wallahi na rantse da Allah Kika kara zagin iyaye na sai kin gane baki da wayo wahuya kawai shasha .''

Sosai Maryam ta bawa Murja mamaki dan ta dan ji shakarta musanman marin da ta da sharara mata sai da ya tsara jikinta amma tsabar masifa irinta Murja yasa ta kaima Maryam duka da kadan a cikinta nan Maryam ta same ta kamar diyar ta yi ,Bawa Murja shegen duka da yake gaban mai gadi komai yake Faruwa Hakan yasa ya Kira Mazajansu ,'' Bayan Maryam ta gama bama Murja kashi ne yasa ta Mikewa daga ruwan cikinta har ta juya Kenan ta ji Murja ta Kamo kafanta duka biyu ji kake Tum Alamar faduwarwa Maryam Hakan yayi daidai da shigowar S Muhamed kafin su karisa yin parking Murja ta Haye Maryam da ke fita da jini dan kasan Tillas ne mai Sulfi ta fada wani jiri na dibanta amma Hakan Murja ta dage sai Dukan cikin Maryam take babu tausayi bare Imani da ta dauko wani Katon dutse ta dage ta a cikin wata iriyar razananiyar kara Maryam ta saki tareda sumewa amma Hakan baisa Murja ta daina Kafkamata shi ,'' a guje su Muhamed suka yo kanta inda Muhamed ganin jini ga matarsa Bata ko motsi jini sai zuba yake ba kyakyawa ta yasa shi hurgi da Murja ya suri matarsa Mudanssir yabi bayansu suka nufi Asubiti sosai zuciyar Muhamed ta karaya dan har Yaga matarsa ta mutu dan ba ta dan yake cikinta yake ba ta uwar dan yake , da taimakon likitoci Aka shiga da Maryam cikin daki da kyar suka samu tafara nunfashi dan tun safe da Aka kahota sai wajen Karfe 12h na dare ta Farka nan wata sabuwar na kuda ta tasoma amma sai de bazata iya haihuwa da kanta ba sabida karfinta ya Kare ,Hakan ya bama DOCTOR damar fitowa dan à saka hannu za'ayi mata aiki ,ganta ya kwantata ma Muhamed Halinda Maryam take ciki bai yi wata wata ba ya aminci Aka yima ta aiki Aka fido wata kyakyawa yarinya sai de da Alama Bata da lafiya dan komai na jikinta a Karka ce yake ba daidai yake da day bangaren ba har ta kanta ya langafe Sun ajiye yarinyar ne suka fara duba uwar a nan ne suka tabatar da akawy Babar matsala sukayi Dukan abin da ya dace sanann suka dumke mata wajen ita kuma yarinyar Aka fito masu da ita dan su ganta ,Kuka Muhamed ya fashe dashi dan a tunaninsa yarinyar ma bazatayi rai ba sai gashi cikin Ikon Allah ta rayu rumgume diyar yayi wani Sonta na kara shiga ransa dan sai yaji yafi son ta duk cikin yaransa ,dan Dago da kallonsa ya yi , Yana cewa Norse ina uwar yarinyar take ne da fatan dai tana lafiya .''

To Alhamdulilahi ne amma Doctor ya ce'' kuzo Yana son magana da ku ,kallon juna sukayi 
Tsakanin Muhamed da Mudanssir suka bi Bayan norse din ta Nuna masu bureau din Doctor Bayan Sun gaisa ne D.C ya ce'' Waye mijin Maryam a cikinku ne .''

Muhamed da zuciyarsa ta gama karaya ya ce'' ga ni?" Yawa sakamanko Dukan da akayi mata a marar ta Hakan ya sa Mahaifarta lalacewa bazata kara haihuwa ba sai wani Ikon Allah Dan Idan ma Aka bar Mahaifar a jikinta zata iya yi mata kumbri a cikinta Hakan zai iya haifar mata da kansa Hakan yasa Muka cire ta .''

Wani marayan Kuka Muhamed ya saki dan babu abin da yafi kauna sama da iyayan sa sai Maryam dan tsabar biyayarta da hakurinta ga iya kulawa da miji dama shimfidarsa sosai ya tausayamata kallon D.C ya yi , ya ce'' yanzu tana wane hali ne .''

Lafiyar ta lau sai de abinda Ba'a rasana ba dan yanzu ma munyi mata Allura bacci sai munga Tashin ta .''

Sosai D.C da Mudanssir suka shiga kwantar ma da Muhamed hankali yarinyarsa ta rike da hannunsa Yaki Bari kowa ya karbe ta har garin Allah ya waye Maryam Bata Farka ba sai wajen Bayan Sallah Mangariba ta tashi a hankali ta fara Budé idonta ta sauke su bisa kan mijinta dake zaune yaka karema halitarta kallo Yana ganin zan dutsen da Aka Dakar masa mata ,suna hada Ido ta sakarmasa Murmushi shima ya maida mata gani ta farfadone ya sashi Kiran iyayenta dan Sanin halin da take ciki sannan ya Kira Norse Bayan Sun gama Wayar .''

Bayan Bayan da su Maryam Suka je Asubiti Aïsha da gabanta akayi komai lokacin Ilham tana tafiya ita da Safiya amma basuda wani wayo kuma suna School ita ma sabida batada lafiya ne yasa ta ganin abin da yafaru a Idonta sai Kuka take dan ta kasa cin komai tun daga lokacin tafara koyan rashin kunya Bata sararama kowa musanman Murja da tafi tsanarta a rayuwar ta dan a zaton ta taka she mata uwa .''

Ita ko Murja hankalinta kwance zuciya zauna dan tasan ko da Maryam Bata mutu ba to abin da zata Haïfa doli ya mutu dan dama shine har Bata so yazo duniya sosai take more rayuwar ta cike da farinciki da jin dadi musanman da tunda mijinta yabi Muhamed bai Dawo ba har yanzu .''

Sai da Suka yi sati day sannan Aka sallami Maryam daga Asubiti suka Dawo gida inda Mamarta ta Dawo kulawa da ita sosai har takara watsakewa ranar biki yarinta ta ci sunan Inteesar kowa sai santinta yake dan tafi diyan Maryam kyau dan de Halitarta ba dai take da tasu ba amma babu hadi tsakaninsu har Ilham , inteesar tafita haduwa .''

Tun daga wanan lokacin kuma Aka yima mazanjensu transféré zuwa garin Maradi nan ne kowa ya nemi gidansa sai de suna kusa da juna daganan kowa yafara rayuwarsa har Aka aurar da Aïsha ita Bassira amma Ammi bata daina jin haushin su Maryam sabida su kullum abin karuwa suke samu ita Kuma tana komawa baya. Haka kawai Murja zata shigo gidan Maryam tayi ta zagin ta tana ce mata ba dai kin aurar da Aïsha to insha Allah Ilham sai ta zama rikakiyar karuwa kullum idan Sun hadu sai ta furta wanan Kalmar har Ilham suka tasa ita da Safiya suka zama kawayen juna komai nasu Irin day gasu Sun zama Yan mata sosai A lokacin ne Musa Abul Khair ya Dawo in da Suka fara haduwa da Ilham lokacin zata je Asubiti suka bida Buge juna da mota ,Bayan zuwan Musa ne Al'ameen ya shigo suka hadu Safiya nan suka fara aika ta Barnansu asiri a rufe babu Wanda ya sani.''

 Ci gaban labari .''
28/03/2022 à 16:58 - Mom Star ✨: ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
      
*DOCTOR ILHAM*

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

          *Na*

         *Mom Khadija*

{{YAR LELEN NOBLE ce}}

36/37📓

Godiya dubu gareku fan's ina godiya ga kullawarku kuma ina jin dadin comment naku masu kirana kuma ina godiya ga fatan alkairi Allah yabar kauna 🌹 Arakam🌹

Barka sister Meenah barkanki da Kammalla Littafin Wasu kawaye masifa ne) Allah yakara Bassira da Zakin hannu

Sai ke Shafa'atu kema barkanki da Kammalla Littafin Kishin Mace Allah yakara basira da fahimta 🌼 SAHIBAR NOBLE🌼

Kam amma Wallahi wanan matar muguwace yar jaririyar ma Bata ragama ba sabida son zuciya Irin Nata da bakinci Allah ma yakara da yar tata ta dauko mata Abin kunya fatan da take min Allah bai nufa Kai na ba sai cikin data Haïfa Allah yakara kiyaye mu daga shairinta kuma ga dai ta nan duniya Wanda bai zo bama ta ishe sa Riga da Wanda harda zanin daurawa .''

Hakane Ilham Allah yabamu hakuri shiyasa kwata kwata na tsani wanan matar Wallahi Bana ma na kaunar ganinta .''

Wajan Mama Ilham ta zo ta tsuguna gaban ta ta ce'' Mama kiyi hakuri ban san Haka maganar take ba abinne ya dameni kulllum tana zagina tana mani cin fuska cikin mutane kuma fa har yinkurin kasheni ta yi , bisa kan wanan dalilin da ban sani ba Fassto Mama na tuba .''

Hakane gashi ai yanzu furicin da take maki ya koma bisa kan yar ta ta dauko masu abin kunya yanzu bakin ta sai ya yi , shiru ke kuma sai ki zauna tana gallazamaki .''

Kam Allah taiwarail Khair ( Allah ya sawake ) .''

Dariya Aïsha ta yi , ta ce'' ki Rabu da ita dan ta san ba muyi gadan bakin hali Irin Nata ba kinsan ance idan ta karewa Kare cizo yake yabari ya koma tunni.''

Hakane nima naga alama dan gashi kan yar ta .''

Dady da ya yi jigum Yana sauraransu ya ce'' shi yasa ka fadi Alkairi a kan dan mutume ko kayi shiru ko kuma ka bishi da Addu'a amma dayawa basu gane Hakan har ta da Yanayin shigar mutume suka gani sai Sun saka bakinsu bisa kan abin da bai shafesu ba kuma basu ganin aïbu a tatare da su sai a jikin Wani dan Abu kadan idan kayi mutane basu san farko ba zasu Kai ka karshe ko TUSHAN LABARI basu ji .''

Hakane Dady Allah ya kiyaye gaba .''

Amine .''

Inteesar ce ta shigo tareda yaran sai tsale tsale suke da sallama suka shigo suka Ruga a guje cikin daki .''

Girgiza Kai Ilham ta yi, ta ce'' Allahu tuwarate warde Alkair Intee na .''

Amine ya Allah .''

Dady ne ya kalle ta ya ce'' Ilham mijinki ya san kinzo gida ne .''

A'a bai sani ba ina son ya je gidan Yaga yanda ya yi , nasan zai ne meni .''

To ita Ammi ta Sanar da shi baki gida ne cewar Aïsha.''

Na kanne ( An ya dai )."

Haka dai suka yi tautauna maganarsu suna ciki zantawa ne Musa ya Kira Ilham taga ta yi , tareda da sallama a bakinta ,'' amsawa ya yi , sannan ta ci gaba da cewa Wayamin killi ( ina huni ) .''

Lafiya lau arahas zayuwa .''

Arahaz wadurtole ( ya kake) 

Arahaz Agurmi ( ya gari )

Hmm Agurmikus ( gari yayi zafi ) 

Me yasa ?" ta tambaya tana fido Ido .''

Nazo gida ba kyanan duk wajen a ya mutse ina Kika je e ya faru ?"

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' ban san me zan ce da Kai yanzu ba amma kaje ka samu Ammi zaku yi magana da ita idan kazo sai ka buyo Muje gida tare .''

Tom shikenan yafada ? Dan tunda yaji ta ambaci Ammi ya san akwaye matsala .''

Katse kiran ta yi , tana ajiye Wayar gefe .''

Aïsha ce t kalle ta ta ce'' me ya ce maki ne duk jikinki ya yi sanyi.''

Komai kawai dai Inde iniya ( ya bani tausayi )

Dan tabe baki ta yi , tana mata hararen wasa ta ce'' a gaisheku masoya .''

Murmushi ta yi, ta ce'' E'e dan ki fadama mijinki ko Longin sonsa babu dan gata ya dame ya shanye .''

Dariya su Dady suka yi ,Mama ta ce'' Wai Ilham issi Harakta iskanci nan dan yanzu kwata kwata utuleri turakil.''

A kunya ta ce'' Yanzu Mama bani da kunya kenan Aïsha Madami sulmada .''

Da sauri Aïsha ta ce'' Bana son Iskanci fa Ilham ni ce na koyamaki rashin kunyar ma .''

E'e mana ?" Kam Lanle Aïsha isirin darbarardi.''

Dariya suka kwashe da ita Dady ya ce'' kenan Ilham kin yarda ke yarinya ce cewa fa take a kula dake ma'ana utularigris .''

Dan hade fuska ta yi , ta ce'' Mama wai bani da hankali .''

Ba fa Haka nake nufi ba ina nufi ita ke Baba gareki ta kula dake Dadynku Yana son hada fada ne .''

Sai a lokacin ta saki Dariya tana cewa Haba yanzu hankalina ya kwanta .''

Dama ai a tashe Kika shigo a ta shi a koma inda Aka fito Tazo kwarakar tuwo to mun tsaye Kayanmu Agulu.''

Ke ya kamata nace ma ki tafi ba ni ba sabida ni a garinmu nake ke ce zance kinzo tsanye mana abincin gida .''

Suna cikin wanan maganar ne Ihsane ta rigo da gudu tana fadawa jikin Aïsha tareda fashewa da Kuka .''

Hankali a ta she tace'' Ihsane pourquoi pleure tu ?" C'est quoi ton problème.''

Aunty Inteesar ce ta fadi kasa muna cikin Wasa .''

Qu'est que vous allez faire a elle .''( me Kuka yi mata ne)  

Rien Momy kawai muna Wasa ta fadi Haka Kawai .''

Kallon Mama Aïsha ta yi,sannan ta maido Dubanta ga Ihsane ta ce'' Fassto zata ta shi kin ji .''

Tana gama fadan Haka duk suka nufi dakin Inteesar ruwa Ilham ta watsa mata nan ta fara tari tana Aman jiri idanunta duk Sun yi sama jikinta sai rawa yake .''

Ajiyar zuciya Ilham ta sauke ta ce'' Mama Muje mu Kai ta Asubiti ciwan ta ne ya taso kar mu rasata ta fada a dumauce .''

Sungumarta Dady ya yi , suka nufi Asubiti suna isa Aka basu taimakon gagawa.''

Da taimakon Allah da likitoci Inteesar ta samu jinin ya tsaya ta daina komai sai Bacci da ta samu sakamakon Allura da akayi mata ta bacci .''

Fitowa ya yi , ya ce'' Yanason ganin Dady babu musu yabi Bayansa suna shiga ya bashi izinin zama ,ya zauna Doctor ya jima Yana Yan rubuce rubucen sa daga bisani ya Dago yana Mika masa takardar hannunsa ya ce'' wanan Kayan Aïkin da za'ayi ma Inteesar ne a siyosu nan kwana biyu za'ayi aikin Insha Allah dan da Alama jikinta Yana son zama daidai ne .''

Dagaske Doctor ?" A'a ban tabatar ba sabida dazun abin da nagani shi nafada ku dai Taya mu da addu'a Allah yasa muyi a sa'a .''

Amine Dady yafada Yana fitowa daga Office din ya fita ba tareda yama kowa magana ba Pharmacie 17 portes ya tafi ya Sayo magungunan da sauran kayan aiki Yana dawowa ya je wajen Doctor ya Mika masa shi kuma ya bashi takarda ya saka hannu .''

Nan mijin Ilham yazo asubiti sai dare suka koma gida Bayan yaji Ba'asin abin da ya hadasu da Ammi Haka ita ta fada Masa babu abin da ta boye .''

Hakuri ya Bata sannan suka ci gaba da zamansu lafiya .''

BAYAN KWANA BIYU

Inteesar ce saman bed ga su Mama da Aïsha Dady da Ilham kallonsu ta yi , ta ce'' Aunty na me yasa me Nine?" 

Suma kikayi t?" Ta Bata amsa a takaice .''

Nan Mama ta shiga labarta mata Abin da ya faru .''

Murmushi ta yi , ta ce'' Mama wane aiki za'ayi mani nasan bazan taba samun sauki ba kamar ku kashe kudinku a banza.''

Ke Inteesar Fassto dan Allah kina ja da ikon Allah ne .''

Ko kadan Mama Allah ya bani lafiya .''

Amine Haka Zaki ce tun farko .''

Cike da tausayin kanta t ce'' Mama and Dady Aunty's dan Allah idan mun shiga za'ayi mani aikin nan idan Allah ya dauki Raina ku yafamai tafada duk jikinta ya bace da miwo .''

Baki mana laifi ba Inteesar kuma Insha Allah za'ayi aikin nan lafiya a gama shi lafiya.''

Suna cikin firar ne Doctor suka shigo dan za'a tafi da ita Haka nan Aka fita da ita Cike da fargaba kowa da ka gansa kasan Yana cikin damuwa Haka shiga dakin Bayan ta saka rigar bleu ta Marasa lafiya ta kwanta a bed din tareda Tura kanta cikin wata farar na'ura ta daga idonta sama sai haske take gani sai wasu fitulo da Suka haska inda za'ayi mata aikin kallon Ilham Doctor ya yi , ya ce'' Mdn ki kwantar da hankali ki tsaya muyi aikin nan a nutse in sha Allah zamu gama lafiya .''

Ajiyar zuciya ta sauke cikin raunataciyar murya ta ce'' Kai anya zan iya Doctor .''

Zaki iya mana ki sama Ranki bamuda lokaci ku matso mu fara .''

Sai da Ilham ta kalli Inteesar da idonta ke kallon hasken hutar da ke cikin Mashin din tana girgiza Kai sai da Doctor ya kara kwantar mata da hankali sannan ta dan saki jiki suka fara aikinsu cike da iyawa da kwarewa Ilham suna cikin yi tana karanta Addu'a har Allah ya sa suka Kammalla suka gyara komai sannan taje ta wanke hannunta ta cire tsanwar rigarta ta saka fara sannan ta fito tana Murmushi .''

Tunda suka ga hakan Su san Allah ya taimaka Sun gama lafiya tana karisa wa ta rumgume Mama tana fadan Mama ki mana murna Allah ya sa mun kammll.......bata karisa Maganarta wayarta dake gefe ta yi, kara dubawa ta yi , taga sunan Doctor wata iriyar buga gabanta ya yi da karfi kamar zai fasa kirjinta ya fito cike da faduwar gaba ta ga Wayar amma ta kara cewa komai ,sai Doctor da ya ce'' Ilham kizo a kwaye matsala ,hurgi ta yi, da Wayar ta koma dakin a guje tana kallon na'urar da ke Nuna nunfashin Inteesar Yana tafiya daidai sai taga Yana rage karfi , da sauri ta zura rigarta ta nufi wajen tana fito da daga in da kanta yake ciki idonta a lumshe Bata ko kwakwaran motsi gefen shafarta tafara shafawa tana dan bubuga kumatunta da yatsun hannunta biyu ,shi ko Doctor Yana aiki da wata yar karamar na'ura Yana danna mata a gabanta dan nunfashin ya daidai ,ganin sai kara ragewa yake ya sa Ilham ta fashewa da Kuka tana rumgumo Inteesar ta ce'' Intee na dan Allah Kar ki rufe idonki gani ni ce fa Auntyn ki nice Ilham dan Allah ki tashi kar ki tafi ki barni babu abin da nafi kauna a rayuwa sama dake Intee kar ki man Haka dan Allah .'' 

Cikin galabaitaciyar murya ta yi , Murmushi ta ce'' Aunty na ki barmani Kuka Addu'ar ku ka dai nake da bukata nima ina sonki kuma ina maki fatan alkairi Haka Allah ya Gadara ma rayuwa ta ba mai tsayi ba ce ina sonki Aunty na ki ya femin keda su Mama kuma na yafewa dukan Wanda ya yi ,min laifi dama Wanda na yi wani Irin tari ne ya taho mata sai Alan jini Haka Doctor ya kara kaimi wajen dAnna abin amma ina tun nunfashin Yana 99 har ya Kai 20 Yana ganin Haka kamar mahaukaci yakara danna mata Abin daidai ta nunfashin amma ina Sai da ya gansa 5% sannan ya hakuri Yana Dukan wani table dake gefensa da sauri Ilham ta shiga jijigata tana Zuma salati tana Kuka kamar ranta zai fita tana sambatu Intee me yasa Zaki tafi ki barni bacin kince ba zamu taba rabuwa ba me yasa bazaki ciki Alkawari ba Intee na nice fa nice Ilham dan Allah ki tashi Mama zata ji farinciki dama sauran Yan uwa Wallahi zan maki Dukan abin da kike da bukata Intee na sai da nace ki rinka shan magani amma baki sha gashi yanzu Zaki tafi ki barni rabuwa ta har abada Intee na ,'' karar na'urar ta dauke daga sauti da take badawa ya sa Ilham faduwa kasa sumamiya .''

Da sauri Doctor da shima baya hayacinsa dan ya jima da son Inteesar a zuciyarsa dan babu baban burinsa da ya huce ya aure ta yanayin ta ne yake gani kamar baza'a bashi ita ba shiyasa bai Sanar da kowa ba sai Ilham shiyasa ma Ilham Bata barin Inteesar yawan fita ko wani kula samari sabida Doctor amma gashi yanzu ya rasa ta daukar Ilham suka yi suka nufi da ita dakin duba Marasa lafiya nan suka dukufa wajen ce to Nata ran .''

Tunda Ilham ta koma dakin Opération gaban Mama ya shiga lugude Yana bubugawa da karfi karfinsa sosai ta kara shiga damuwa sabida ganin yanda Ilham ta yi , hurgi da Wayarta ta koma dakin a guje ,Aïsha ji take kamar ta shiga dakin da tsabar Tashin hankali ,'' 

Bayan Sun yi nasarar ce to ran Ilham ta farfado sai kuka take tana wasu maganganu da batamasan tana yi ba nan suka mata Allura bacci dan sabida jininta ya hau sosai dan in ba ayi hankali ba cikin ta zai iya zubewa nan bacci yayi gaba da ita ,'' sannan Doctor ya fito Yana goge hawayen da yake boyewa su Mama na ganinsa suka nufosa suna tambayar lafiya dai ko .''

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce'' Mama & Dady Allah yabaku hakurin rashi Allah ya jikanta ku yi mata Addu'a ka dai take bukata ,Aïsha da tunda Doctor ya fara magana ta kara koda motsi dan tayi glass ,Mama kuma sai da Dady ya kireta dan tafiya ta yi, zata faduwa tana rafka Salati nan ta rufe fuskarta da kirjin dady ta fashe da wani marayan Kuka .''

A Haka suka saka hannun Aka basu gawar Inteesar in da Ilham kwata kwata Bata cikin hankalinta sai da ta kwashe Wata day har Aka gama Zaman takabar Inteesar Ilham Batasan wainar da ake toya ba Aïsha ce da Musa sai Safiya suna zaune kowa ya yi , jigum suna jiran farkowar ta Aïsha dake zaune saman gadan da Ilham take wajen kafafunta taji suna tabata kallonta ta yi , taga tana kokarin Budé idonta cike da Murna Aïsha ta ce'' Ilham din Mama kin tashi ne tafada tana Mikewa tsaye nan su Abul Khair suka nufo ta tana kokarin ta shi zaune nan ya kamata tareda gyara mata zama ,'' Kallon Aïsha ta yi , ta ce'' Aunty ina jin yunwa fa ?"

Da sauri ta dauko plask ta hadamata tea mai kauri sosai sannan ta Bata sai da ta shan ka dan ta Mika mata ta ce'' ina Mama da Intee na suke bangansu ba.''

 suna nan lafiya Sun tafi gida yanzu zasu Dawo .''

Fita Musa Abul Khair ya yi , ya sanar da Doctor nan suka shigo tare ya duba ta sannan yaja Musa suka fita nan yafada masa abubuwan da ya kamata Ilham ta samu da Yan shawarwari dan har yanzu jinin bai saura ba sai da Suka yi sati sanan Aka sallama me su lokacin jikin yayi kyau sosai Kai tsaye guda suka Dawo bayan Sun huta ne suka sa taci abinci tasha ruwa sannan ta ce'' Wai ni Mama banga Intee na ba tana ina ne.''

Dady ne ya yi , gyara murna sannan ya fadamata cewa Inteesar ta rasu nan ya masu nasiha mai ratsa jiki ta hakuri jurija da fatan Alkairi ,'' kallon Dady ta yi,ta ce'' shikenan yanzu bazan sake ganinta ba  kuma bazan sake jin muryanta ba Ashe da gaske ta tafi Kenan .''

Dafa kafadarta Dady ya yi , ta kara Bata magana Haka dai ta yi , hakuri amma zuciya ta sosai take soyuwa .''

Bayan sadakara kwana Arba'in na Inteesar Muhamed Bista.''

Nan Ilham ta tara ta koma gidanta shima Saïf bayan kwana kwana biyu yayi tafiyarsa yanzu cikin Ilham da Safiya ya kara girma ya fito yanzu Ammi ko kadan Bata shiga mutane baki ya mutu dan yanzu ko biki tatafi sai anyi gulmanta ana Nuna ta yau ma bikin Babar kawarta take ma diyarta aure ta shirya tatafi amma matar nan ta yi mata tass har zata zauna ta ce'' A'a Murja lafiya dai Waya gayatoki ko nima kin zo kiga Yana yin yar tawa ki kaima yarki ta lalata mata rayuwa ne dan Allah ki fitarmin daga gidan dangin Karuwai kawai .''

Sosai Ammi taji zafin maganar nan dama abin da take ma wani yau gashi anmata Ashe Haka Maryam take ji a zuciyar ta duk lokacin dana ai banta mata yar ta harda Bata taba aika tawa ba amma gashi ni n'a san yar tawa ta yi ,amma na ji zafi gashi har yarinyar da nayi sanadin mai da ita nakasashiya ban je nayi mata ta'aziya ba wani Kukan nadama ta fashe da shi tana cikin wanan tunanin ne mota tayi gaba da ita tareda taka kafarta nan ta fadi kasa somamiya da kyar Aka samu mutanan da zasu daga ta à saka mota a Kaita a subiti Suna isa Aka Kiran Yan Sanda nan suka bincika wayarta Aka samu lambar mijinta suka Sanar da shi a asubitin da suke 

Nan ya kariso Yana isowa Doctor Yana fitowa ya ce'' Kai ne mijin marar lafiyar nan .''

E'e Nine lafiya dai ko ?" 

To lafiya amma ba lau ba matar ta tayi hatsari wajen tsaidar motar wanda ya Budé ta ya sa , ya taka kafarta Hakan yasa kafar ta tatake dole sai an yanke kafar so muna son saka hannunka .''

Girgiza knsa yayi ya ce'' yanzu Doctor sai an yanke kafar babu data dabara .''

Gaskiya nayi iya kacin kokari n'a amma Hakan bai samu ba Kawai yanke kafar shine mafita .''

Haka Alhaji ya saka hannu badan ya so ba nan Aka yi mata aiki Aka yanke kafar ta dan kwana biyu Bata farko ba tana shi ta ganta babu kafa sosai wata nadamar ta sake ziyarta ta tana da Ta Sanin da Allah ya wadai da mai Irin Hali Irin Nata sai da jikinta yayi kyau sosai Sannan Aka sallame su .''

BAYAN WATA TARA 

Ilham ce kwance sai juyi take da Alama tana labour ne Haka ta ci abar ta gida sabida ta sannan Yanayin aikinsu sai da faya ta fashe sannan ta Kira Musa Abul Khair dama Yana cikin anguwar nan ya kariso suka dauki Kayan haihuwa suka huce Asubiti suna isa ya Kira Mama ya Sanar da ita nan suma suna suka zo asubiti nan suka shiga Safa da Marwa suna nan zaune suka jiran Allah ya suke Ilham lafiya ,Aka shigo da Safiya ita ma tana labour da ka ganta sai kafi tausaya mata yanda duk ta Kare bama zaka gane ta ba ,Bayan ta kuma Ammi ce tana ba da kafarta cikin koyan tafiyar guragu .''

Mama na ganta tata shi ta kama ta ce'' haba kema Murja me ya kaiki fitowa yanzu ba ki koda lafiya ki zauna bara sai su karisa da ita ciki mana .''

Tunda Mama tafara magana Ammi ke kallonta cike da Mamaki mutume sai mantuwa babu ruwan shi da lamarin duniya abin da ke gabansa kawai yake yanzu duk Irin abin da ta yi mata Hakan bai sa ta Nuna wata damuwa ba Kai gaskiya Allah ya wadaran mai hali Irin nata ya shiryar da shi .''

Sun dan jima sosai har Aka yi Sallah Mangariba babu Wanda ta haihu Haka sukayi ta rokon Allah suna Kai masa kukansu ,Haka ma Musa Abul Khair tunda yatafi masallaci bai dawo ba har Ilham ta haihu bai dawowa nan ta santolo Yan beby boy dinta Masha Allah da shi bazan iya masulta maku Irin kyau yaron ba dan ya kwaso kyau uwa da uba wai sai de muce Masha Allah ,'' Bata jima ba ita ma Safiya ta haihu ta haifo mace mai kama da ubanta saka wato Al'ameen Haka fito dasu Bayan an fito da iyayen dakin hutu ne Mama ta kalli diyar Safiya ta ce'' gaskiya dole in yi kishi ace sai da ta ga na tsufa ita kuma ta shigo dunya to nima zan je a tsanza min fata .''

Dariya suka saka Dady ya ce'' To ai ko kin tsanza ba zai Kai tata dan ina gama kar Alhaji Mudanssir ya min kwace dan ance da zafizafi ake bugun karfe tun yanzu ma nayi kame .''

Mama ta ce'' To ai da tsofuwar Zuma ake magani dan Haka ko kaje sai ka Dawo .''

Inji wa ya fadamaki bazan dawo ba nayi sabon jini.''

Cike da kunya Ammi ta ce'' ki Rabu dashi mana ke da Kika yi sabon miji me nene na kishi da wanan tsugudidin kishinyar.''

Kuma fa hakane Murja kema kin yi magana .''

Kuka ne ya subucema Ammi dan Bata Masan yazo ba ta durkusa kasa tana Kamo hannun Mama ta ce'' dan girman Allah Maryam ki yafemin ki gafartamin laifina nasan n'a yi maki laifin da har ki Mutu bazaki taba mantawa dani ba ki yafemin dan Allah badan nima kuma badan halina ba .''

Murmushi Maryam ta ce'' Haba mana Murja ya muna murna Zaki daga mana hankalinki dama ni ko tsan ban rike ki a Raina ba kuma na jima da yafeme ki sabida Allah gafirar Rahim mu kanmu muna masa laifi ya yafemana bare kuma mu Yan Adam butulu ki Bari dan Allah ki manta da wanan maganar ta huce Bana son bara tana dawowa Bana .''

Murmushi Alhaji Mudanssir ya yi, ya ce'' Alhamdulilah Mun gode ma Allah kuma muna cikin yi masa godiya hajiya Maryam Allah yasa ka maki da Alkairi hakika ke yar halak ce kuma kinsan Darajar dan Adam a madadin Matata muna godiya Sosai .''

Babu komai Allah yafemana baki dayan mu nan Aïsha da Ilham ,da Safiya suka rumgume Ammi da Mama suna godiya ga Allah Daya kawosu wanan ranar farinciki bisa jindadi .''

Musa dake gefe sosai ya ji dadi Hakan Yana kara yima Allah godiya .''

Doctor ne ya shigo ta duba masu jego Yaga basu da wata Matsala sannan suka sallama mesu Haka Mama ke kulawa da Ilham da Safiya Ammi ma da yar guntuwar kafarta take dan yi wani Abun dama Mama tana hanata har Allah ya kaimu ranar suna Inda dan Ilham ya ci sunan Dady amma za suna kiransa da Najbudeen ,diyar Safiya kuma ta ci Sunan Inteesar sosai kowa ya ji dadi dan wanan Ammi ce tasa Aka saka sunan Inteesar din Masha Allah anci an sha shagali ba ka dan ba kamar basuma san inda dukiyar take fitowa ba Haka Aka Kammalla biki lafiya inda DOCTOR ILHAM Fan's suka zo Taya Ilham murnar karuwar data samu suma Sun Bada gudum muwarsu wajen Taya murnarsu Sunsha rawa ba kadan ba sunsa mu tarba ta musanman .''

Bayan suna da sati day Al'ameen ya samu labarin haihuwar Safiya Haka yazo gidansu Bayan Sun gaisa da Alhaji ne ya ce'' wajen Safiya yazo .''

Babu musu Alhaji ya mashi ISO dan yasan shi kuma jikanyar tasa tana kama da shi shi yasa ma ya shiga da shi ciki da sallama a bakinsu suka shigo .''

Ammi ce zaune ita ka dai karanta jarida Bayan Sun gaisa ne Ammi ta kwallama Safiya Kiran nan ta fito kire da yarinyar ta tana ganin Kittyn ta ta hade fuska tana fadin Ammi gani .''

Dama bani nake nemanki ba uban yarki ne ya zo .''

Sosai Al'ameen ya ji kunya dan a tunaninsa ba susan shine yama Safiya ciki ba .''

Dan sunkuyar da Kai ya yi , ya ce'' Ammi ,Baba dan Allah ki gafartamin ku ya feman a hakika na sakaku cikin damuwa da nayi niyar tafiya ta na bar garin nan na fito Kenan na bi ta gefen wani Masallaci Naji Malamin Yana wa'azi bisa kan aikata zina da ma Dukan me yinta sosai Na yi na dama dan walahi naga masifu dan yanzu komai nawa ya lalace banida komai sai masa'antar da Aka raba mana ta gado Nida Yayana Hakan yasa n'a koma wajen Malam din Dana ji Yana wa'azi ya ce'' Hakan ba zai fasa Faruwa dani ba har sai Na nemi gafaran yarinyar kuma sai ta yafe shine nazo dan Allah ki yafemin Safiya kuma Wallahi na shirya auren ki ko yanzu ma a daura .''

Hararensa Ammi ta yi, ta ce'' ka ci Albarkacin Murja Bata Da bace da ka gane baka wayoo Al'ameen wai Safiya tana yar uwa amma sai ita ka ci zarafinta Hmm tayi mata kyau Allah ya fe mana baki day .''

Hakika Al'ameen kaga jarabawa babu damuwa Allah yafe mana baki dayan mu sannan kuma kaje ka turo da magabantanka sai anyi maganar auren .''

Godiya ya masu Sannan suka barsu daga shi sai Safiya nan ya karfi yarinyar Yana kallonta Dago da kansa ya yi ,Yana aika mata da salon kallonta mai tafiya da ita bata san lokacin dana saki Murmushi nan suka dan taba fira ya yi tafiyarsa .''

Alhamdulilah yanzu dan Ilham ya kara murmujewa ya zama katuwa dan zaka dauka zai Kai Shekara biyu amma nan Shekaransa day da wata takwas dan Harma ta yaye shi yanzu Haka ma tana da wani cikin sosai abul ke kulawa da ita babu abinda ta nema ta rasa sai Wanda yafi karfinsa .''

Kwanci tashi babu huya wajen Allah yau ne auren Safiya da Al'ameen Masha Allah duk da ba wani shagali Aka yi sosai ba Amma Alhamdulilah ciki Rufi assiri Aka yi komai Aka gama lafiya amarya ta tare gidan ta yanzu suna rayuwarsu cikin tsafta ita tana samun Kulawa daidai gwargwado mai rufin asiri .''

Aïsha ita ma ta koma gidanta suna zaune lafiya ita da mijinta da yaranta dan yanzu ma tana dauki da ciki sosai Saïf ke kulawa da ita kamar ya maida ta a cikinsa tsananin lele suna rayuwa cikin farinciki dan yanzu kafin ta Kira Mama sai ta Kira Ammi yafi a kirga .''

Mama da Ammi kuma yanzu Sun zama manyan manyan kawaye kuma abotar mazanjensu Takara dankon karuwa Haka suke rayuwa dan yanzu Ilham Ammi tana ji da ita dan sai de in Bata ce tana son abu ba rayuwa mai kyau mai cike da nishadi suke yi har cikin Ilham ya Kai haihuwa ta santalo baby girl kyaukyawa Haka ma Safiya ta haifo Yan biyu Macé da Na miji ,Aïsha ma ta kara haihuwar dan namiji abin da taji ma tana burin samu sai yanzu Allah yabata ranar sunan Yara sunci manyan manyan sunaye Ilham Nata Ahlam ,'' Safiya nada Rashida da Irshad ,aïsha Dana Ammar .''


Alhamdulilah ! Alhamdulilah ! Alhamdulilah ! 

Masha Allah duka yabo ya tabata ga Allah Subahanahu wata'alla duka duka anan na kawo karshan wanan litafin mai Suna DOCTOR ILHAM inda nayi daidai Allah yabamu lada inda nayi kuskure kuma Allah ya gafartamin .''

Ina godiya Sosai masoyan DOCTOR ILHAM masu comment Allah ya saka da Alkairi ya biya maku Dukan bukatar da ta duniya da lahira Allah ya sa kowa ta Rabu da iyayenta lafiya sannan ta gama da duniya lafiya nagode sosai da fatan Alkairin ku gareni Alkairi ya lulubeki Alfarman Annabi Muhamed (S.W.A) 

Nagode sai mun hadu Bayan Sallah insha Allah 

Nazo maku da tsarabar litafina mai Suna *INA KA SHIGE .'' Dan ta Yaku Munar Sallah ya kaimu ya sa muna da rai da lafiya Allah ya sa mu shiga Watan Ramadan Allah ka kara tsarkake mana zuciyoyin mu ya sa mu aikata aikin Allah Allah ya shirya Wanda basu saman bisa hanyar daidai Amine ya Hayu ya kaiyum ina sonku Fan's fatan alkairi gareku da Dukan kowa ma

Wasalam daga taku Amira saminu kalla transa ✍️ YAR LELEN NOBLE🌼

Post a Comment

0 Comments