GIDAN MATATTU







   GIDAN MATATTU

                                          AUTHOR : ABDUL KING ARTICLE
 

                                                        PAGE 1

        Duniya juyi juyi, yau idan tayima zafi gobe tayima sanyi. Haka idan kana cikin farin ciki to wataran zaka koma bakin ciki, duk abunda ka gani nufin ALLAH ne haka ya tsara kuma haka abun yake kuma dole shi zai faru. Mafi yawan mutane basa tunani kafin su gudanar da ayyukansu wanda hakan shi ke janyo matsaloli na yau da kullum. Kada kayi tsammanin cewa idan ka shuka sharri wai sai a lahira zaka samu hukunci, to wataran tun a duniya za a fara nuna ma abunka kafin kaje can ka hadu da masifa marar iyaka. Haka kuma kada kayi tsammanin cewa idan ka shuka alheri wai sai a lahira zaka samu sakamako, domin wataran akan sakama tun a nan duniya kafin kajecan ka hadu da jin dadi marar iyaka. 
       Jan aji, walakanci, da kuma bin zuciya. Wadannan abubuwa sune suka tattara suka yima yan matan zamani cudanya a cikin zukatansu har takai ba kowa suke ganin girmansa ba. Ba yan matan kadai ba. Har mazan akwai masu irin wannan hali sai daifa na matan ya fiye yawa. Kada kayi tsammanin dukiyarka, kudinka ko kuma wani abu da ALLAH ya baka an bakane saboda kafi kowa. To ba haka abun yake ba. ALLAH yana azurta wanda yaso a lokacin dayaga dama kuma ya tsiyata wanda yaso a lokacin dayaga dama. A duk lokacin da baka samu abunda kake nema ba to ka dauka cewa nufin ALLAH ne kada ka yarsa kabi son zuciyarka. Mafi yawan mutane kanyi fushi idan basu samu abunda suke nema ba cikin rashin sanin cewa kin samunsa shi yafi zama alheri. Duk wanda bai bi maganar iyayensa ba to zaiyi kuka mai yawa hakama duk wanda yabi son zuciyarsa to zai rayu cikin tashin hankali.
       Soyayya gamon jini ce, wanda kakeso ba dole ne ya soka ba, shi kuma wanda ke sonka ba dole ne ka soshi ba. A kullum nakan yi tunani akan wata rayuwa danayi a baya wadda kuma har yanxu abun kan bani mamaki. Mu mutane bama tunani kafin mu gudanar da ayyukan mu kuma mafi yawanmu kan bi shawarar muggan mutane sai daga karshe muyi dana sani. Idan na tuno rayuwata ta baya nakan yi kuka mai tsanani kuma idan na tuna rayuwata ta yanzu sai nayi dariya mai yawa.  Kada na jaka da surutu bari na fadama kadan daga cikin wannan rayuwa tawa kuma kadan daga makasudin wannan kuka da nakeyi da kuma wannan dariya nakeyi.

                                                         PAGE 2

                                                   

          Tafiya takeyi da sauri cikin fargaba da kuma tsoro a saman wani titi ita kadai. Kai da ganin tafiyar kasan ba lafiya ba domin yi take tana juyawa baya kamar ana binta. A cikin darene take wannan tafiyar gashi kuwa dare ya raba saboda ba kowa a saman titin. Wayar dake hannunta ba charge wanda hakan yasa tayo guzurin yar karamar torch-light da take yadawa tana ganin hanya. Mafi yawan gidaje an kulle hakama shaguna. Sama kuwa baki kirin take domin ba alamar farin wata. Haka dai ta cigaba da tafiya tana waige waige a cikin zuciyarta kuwa ji take kamar ta fashe da kuka. Tana cikin tafiyar ne sai tayi tsaye gib kamar wadda aka sokama mashi. Zuciyarta ce ke bugawa da karfi kamar ta tsage daga nan sai torch-light dinta tayi wani lumshi kafin kaceme ta dauke kyaf. Duhun daya dabaibayeta shiya haddasa wani saurayin tsoro a cikin zuciyarta. Kafin kaceme jikinta ya fara karkarwa har ta saki torch-light din cikin rashin sani. Tanaso tayi magana amma ji take kamar an rufe mata baki. Anan zufa ya fara kwarara a jikinta sai kace wadda tayi suraci. 
       Tana cikin wannan haline saita fadi idanunta suna lumshewa, kai da gani kasan akwai abunda take hangowa amma kuma wannan abu ko menene? To kafin ta fita hayyacinta sai ga wata mota ta karaso a inda take. A guje wani saurayi ya fito yana fadin sunanta cikin tausayawa. Haka ya tallabota yana tambayar meke damunta amma ba damar ta amsa sai nishi take dakyar. Hannunta take dagawa tana nuni da wani abu amma shi saurayin bai fahimci hakan ba domin a tunaninsa duk tsananin ciwo ne. Bayan ya kaita cikin motarsa. A guje yasa giya take motar ta wani fizgesu da karfi. Mikewa yayi? santal saman titin sai da yayi tafiya mai dan nisa kafin ya kawo ga wani gida mai kirar zamani.  
        Lakamata yayi daga nan ya shiga da ita cikin gidan,sallama ya farayi bayan ya shigo da ita a cikin falon. A mamakinsa ba wanda ya amsa haka yasa ya fara tunanin cewa masu gidan sunyi bacci. A saman wata babbar kujera ya gincirata daga nan sai ya debo ruwan sanyi a cikin fridge. Kyalle ya dauko yana shafe gumin dake fitowa a jikinta. Daga nan kuma sai yayi addua a cikin ruwan ya bata tasha. Ai kuwa faruwar hakan keda wuya sai ta dawo cikin hayyacinta.
         

                                                            PAGE 3

        
          " To ni zan tafi gida samirat tun da naga kamar kin samu sauki. Amma gobe zan dawo sai naga ya jikin naki." Anan ya tashi da nufin fita. Ai kuwa kafin ya kai ga kofa sai gata ta biyoshi a guje ta rike hannunsa.
          " Haba samir ya zaka fita ka barni a cikin wannan hali, a gaskiya bazan iya bacci a cikin wannan gida ni kadai ba." Inji samira. Anan samir ya kalleta cikin mamaki yadda akayi ta rike masa hannu domin a duniyar nan ba wanda samira ta tsana kuma take kyama irin samir. Saboda tsananin tsanar data yi masa ko a hanya idan ta hangosa juyawa zatayi da baya don kada su gamu. Shi kuwa samir ba macen dayaga ta kwanta masa a rai inba samira ba. Ba yadda bai yiba yaga ya shawo kanta amma abu ya gagara abu sai kara kamari yake amma kuma shi bai damu ba haka yake jure duk walakancin da take masa. Bako shakka akwai alamun tambaya gameda wannan riko data masa. Anan tunanin samir ya katse daga nan sai ya fuskanceta. 
          " To in banda abunki samirat ai kema kin san ba yadda za ayi nayi bacci a gidanku. Yanzu haka fa nasan ummina batayi bacci saboda tunanin ko wani abu ya sameni. Kuma ni a tsammanina ai iyayenki na ciki kinga kuwa ba wani tsoro da zakiji." Inji samir.
           " Su umma basu nan, sunyi tafiya kuma zasu dade kafin su dawo." Samira ta fada cikin karamar murya. 
           " To amma me ya fitar dake a cikin wannan dare? Yanxu fa karfe biyu da rabi." Samir ya fada yana duban agogo. 
           " Kada ka damu da wannan. Yanzu dai abunda nakeso ka kokarta ka tayani bacci a yau idan yaso gobe ka tafiyarka." Inji samirat.
           " Kiyi hakuri samirat amma bazan iyaba. Yanzu haka ummina tana jirana kinga kuwa idan na tsaya a nan kome zai iya faruwa gareta. Saboda haka kinga tafiyata." To kafin ya fita ne sai ta jawosa da karfi. A nan ta rungumeshi tare da kankaneshi tana kuka cikin tausayawa. 
            " Haba samir yanxu idan ka fita ka barni nayi kaka kenan, kada fa ka manta na fadama ni kadaice a cikin wannan gida. Kuma gaskiya ni tsoro nakeji."Injita.
             

                                                          PAGE 4

    Anan samir ya kalleta ciki da mamaki wannan kankanewa data yi masa domin a can da ko kallonsa batada lokacin yi. Idan har ta kallesa to harararsa ce zatayi ko kuma bakar magana ce zata mayar masa. Amma sai gashi yau har ta jawoshi a jikinta. Bako shakka akwai bayani game da wannan abu. Da farko samir yaji dadin kankanewar data yi masa amma daya tuno cewa bawai don tana sonsa tayi masa haka ba sai farin cikin ya koma ciki. Anan ya zurfafa cikin tunani yana hango abunda ya faru a baya a lokacin da suna yara shida ita. 
     Binta yakeyi yana kiran sunanta domin faranta mata amma ina ko kallonsa batayi. A wannan lokaci suna yan primary shida ita. A duk lokacin da aka tashi bread yakan yi kokarin yin wasa da ita amma ita kuwa ko kadan bata yarda ko hannunsa ya taba jikinta domin yana matsota zata canza kwana. To bayan an tashi makarantar ne gaba daya samir ya biyota yana kiran sunanta kamar yadda ya saba kullum, duk da yasan da cewa bazata amsa ba amma kuma bazai iya barin kiran sunanta ba yana mata wake da kuma kirari. Haka suka cigaba da tafiya har suka kawo wani dan kwaroro mai kamar hanya. To a ciki sukabi domin bulla kwanar karshe wadda zata kaisu gida. A wannan lokaci daga shi sai itane a cikin wannan kwaroro tana gaba yana biye da ita. To suna cikin tafiyarne sai kadangare ya fado mata a wuya. Ai kuwa da gudu ya shige cikin rigarta, anan samirat ta kurma uban ihu daga nan ta nufi wurin samir tana rokonsa daya taimaketa. To a lokacin ne ta rungumeshi kuma ta kankaneshi saboda tsoron da takeji har saida ya debe mata kadangaren. Ai kuwa yana debe mata ta nufi gida a guje. A wannan rana tayi bakin ciki sosai data fahimci cewa wai ashe samir ne ta rungume harda kankaneshi saboda tsoro. Daga shigarta gida sai da wanke hannunta da omo domin ji take duk ya samata kazanta. Su kuma uniform din daga ranar bata kara sanya suba domin a ganinta kazantar dake jikin samir duk ta dabaibayesu saboda haka tayi sadaka dasu saida aka siya mata sabbi. Shi kuwa samir yayi farin ciki sosai da wannan runguma data masa duk da yasan da cewa tayi hakane ba wai don tasoba. 
       Anan tunanin samir ya tsaya. Kallonta ya karayi yana sama zuciyarsa cewa wannan itace runguma ta biyu bayan waccan data masa ta farko a lokacin da suna yara. Bako shakka wanan rungumar data yi masa ba don ALLAH tayi masa itaba tunda itama waccan ta farkon bada son ranta ba. Anan ya tureta daga jikinsa saboda haushin daya dameshi.

                                                         PAGE 5

        " Haba samir wai tafiya zakayi?" Ta fada tana matsowa kusa dashi. Rike hannun nasa tayi da alamar bataso ya fita. " Wai da gaske fita zakayi?" Ta kara fada.
        " E to amma...... To yayi yanzu mudai je ki zauna." Anan samir yajata har saida suka zauna a saman kujera. " Nasan da cewa zuciyarki tana cike da tsoro da kuma fargaba kuma wannan abu da kikeji ya farune sanadiyar wannan yawo da kikayi na dare. To yanxu inaso ki fadamin inda kikaje a cikin wannan dare." Inji samir.
        " Haba wai ya kana min irin wadannan tambayoyi gaskiya fa banaso. Kada fa ka manta kaima kana yawon tunda yanxu kai fada me ya fita dakai a cikin wannan dare har ka gamu dani?" Samirat ta tambaya.
         " Aini larura ce tasa na fita domin umma ce ba lafiya anan na tafi gidan wani abokina da yake yanada chemist. A cikin wannan tsohon daren na tayar dashi yaxo ya bani magani yanxu haka suna cikin motar. Kuma yanxu ina fita sai gida domin naga halin da take ciki. To kinji abunda ya fitar dani daga gida saura ke ki fadamin meya fitar dake a cikin wannan dare?" 
       Anan samira tayi shiru batare datace komeba. Can sai aka bugoma samir waya. To bayan ya dauka sai yaga umma ce. Anan ta fara magana kamar haka." Samir kana jina, kada ka yarda ka dawo gida domin gasu nan sunzo kuma da nufin illataka. Saboda haka ka zauna inda kake harda safe kuma kada ka damu dami domin jiki da sauki."Daga nan saita kashe wayar.  
       " Su waye wadannan da suka shigo gidanku da nufin illataka?" Samirat ta tambaya amma samir ko kallonta baiyiba balantana ya bata amsa. " Haba samir magana fa nake " Ta kara fada.
        " Ai tsammanina kamar abun bai shafeki da kike kokarin sanin ko su waye, to koda an fada miki ko su waye zaki iya hanasu aikata abunda sukaga dama?" Inji samir.
         " Ni dai yanzu ka fadamin ka sani wata kila nayi wani taimako." Cewar samira.
         " To ba za a fada ba. Ke in gaskiyane me yasa baki fadamin abunda ya fitar dake a cikin wannan dare ba." Inji samir.
         " Tab, ai kuwa indai hakane sai dai kowa ya rike nasa." Samira ta fada.
         " To shi kenan kowa ya rike mana ai dama ban damu dana sani ba." Inji samir.

                                                            PAGE 6

        " Yanxu dai kin samu abunda kikeso tunda bazan tafi gida ba dole a nan zan tsaya. To dan jirani bari na kulle mota na dawo." Anan samir ya fita da nufin kulle motar. To bayan ya kullene sai ya dawo cikin gidan inda yabar samira. A mamakinsa sai yaga ta canza duk ta fita hayyacinta. Jikinta sai karkarwa yakeyi da alama tana cikin rashin lafiya. Xufa ne ke kwarara a jikinta bakyan gani. Da ka kalli fuskarta kasan da cewa wannan ciyo akwai dai domin bai yi kamada ciyon da aka fi sani ba na yau da kullum. A tsorace take domin kokari take ta tashi amma kuma bata iyawa. Bakinta yana motsi kamar tanason yin magana amma kuma ba a jin abunda take fada. Sai dan yatsanta da take dagawa sama kamar tana nuni da wani abu. Haka samir ya cigaba da bin yatsan nata da kallo domin a tunaninsa wani abune take gani. Amma kuma idan ya duba shi baya ganin kome. Tallabota yayi ya nufi daki da ita. A saman gado ya azata yana mata fifita. Daga nan sai ya tashi ya kunna fanka sanadiyar wutar da yaga an kawo. To a wannan lokaci ta fara dawowa cikin hayyacinta. Shi kuwa ba abunda yake sai addua yana tofa mata. 
        " Ya kikaji da jikin?" Samir ya tambayeta.
        " Da sauki." Ta fada cikin wani murmushi wanda ya tayarwa samir hankali domin tunda yake bata taba yi masa murmushi ba in banda sau daya a lokacin suna yara, sai wannan shine na biyu. Hasalima in banda murgudar baki da kallon rainin wayo ba abunda take masa.  Shi kuma wannan murmushi data yi masa a lokacin da suna yara ya farune wata rana da ummarsa ta kawoshi gidansu samira din yayi bacci sai da safe taxo ta daukeshi sabida a ranar an fada mata cewa abbanta ba lafiya to tanaso taje ta dubashi kuma gashi batason taje da samir din domin tafiyar kwana daya ce. Sabida wannan dalili sai ta yanke shawarar bada ajiyarsa ga makwabtan ta wato gidan su samirat. To bayan ta kaisa gidan ne su kuma sai akayi rashin sa a domin su kuma a wannan ranar wata tafiya ce ta kamasu ta kwana daya. Da suma sunyi niyar kai samirat a can gidansu samir din sai gashi an rigasu an kawo musu shi.  A nan iyayen samirat suka kai samir a dakinta saman gadonta. Daga nan sai suka lullubesu bayan sun tayar da generator yayi aiki har safe don kada yaran suji tsoro. Sai mai gadi da suka bari ya ci gaba da aikinsa kafin su dawo.

                                                             PAGE 7

      Haka samir da samirat sukayi ta bacci a saman gado daya batare da sun sani ba. Sai da tsakiyar dare bayan kowanensu ya farka yin fitsari sai suka kurawa juna idanu. To wannan shine haduwarsu ta farko domin basu taba sanin juna ba sai a wannan ranar. To bayan sun dawo saman gadon ne sai fira mai karfi ta barke a tsakaninsu inda samir ya fara yi mata gatana ita kuwa tana kyakyatar dariya. To a wannan lokaci kankane suke da junansu cikin annashuwa sai labari suke mai dadi. To a cikin hakane samirat ke masa murmushin jin dadi sanadiyar bata taba ganinsa ba. Bayan safiya ta waye iyayen samirat sun dawo, anan suka hada musu karin kumallo. Ai kuwa suna cikin cin abincin ne sai ga mamar samir taxo daukarsa tare da fada musu cewa zasu tashi daga wannan unguwar dama haya sukeyi amma kuma sun gina nasu a wata unguwa can daban. Iyayen samirat basuji dadin wannan bayani ba kasancewar maman samir tanada kirki sosai. To bayan sun tamabayi unguwar da zata koma ne ta fada musu sai sukayi murna domin suma sun sayi gida a can kuma suna gab da komawa. 
        A haka tayi bankwana dasu daga karshe sun koma unguwar. To bayan watanni ne sai iyayen samirat suma suka dawo gidansu. To anan abokantakarsu ta cigaba da gudana. To a wannan lokaci shi kuwa samir ba wata wadda yakeso irin samirat. Ba yadda bai yiba ganin ya ciyo kanta domin ta zama abokiyarsa amma taki. A ko yaushe sonta sai kara shiga yake cikin zuciyarsa kuma a duk lokacin daya tareta da maganar tofa a ranar ya bani domin walakanci sai ya ture. Haka suka cigaba da wannan zama har girmansu.
        To anan tunanin samir ya katse, kara kallon samirat yayi ya gani shin wai itace ko kuwa mafarkine yake. A haka ya kura mata ido yana kallonta tun bata gane ba har ta fahimci yana kallonta.
      " Wannan kallon fa, wai kai in tambayeka, me yasa idan kana kallon mutum baka kyaftawa?" Samirat ce ta tambayeshi shi kuwa shiru yayi domin bai san irin amsar da zai bata ba. " Au wato baza kayi magana ba. To shi kenan." Haka ta fada cikin murmushin dayasa samir ya kara kidimewa sabida dukkan kyawon fuskarta sai da ya fito. 

                                                          PAGE 8

      Daga nan kuma sai ta fara lumshe idanu kamar ciyon nason dawo mata hakan yasa samir yacigaba da tofa mata addu oi. A haka ta aza kanta saman kirjinsa daga nan sai wani bacci mai nauyi ya dauketa. Har yanxu samir bai yarda da abunda yake gani ba domin a tunaninsa mafarkine yake. A haka ya kura mata ido yana kallon siffar jikinta da tunanin cewa inama zata amshi soyayyarsa. Yana cikin tunanin shima baccin ya saceshi. 
     Sai wazajen asalatu samir ya farka. Ai kuwa daga farkawarsa ya tayar da samirat amma ko alamar motsi babu a jikinta saboda bacci yafi karfinta. Dole ya kyaleta yayi sallarsa shi kadai. Da misalin karfe bakwai ta farka sannan ta kimtsa jikinta. Daga nan ta shiga kitchen inda ta dora musu abunda zasu karya dashi. Bata wani jimawa ba a kitchen sai ta kira samir yaxo suje dinning. Bayan sun zauna ne sai ta fashe madara ta zuba masa a cup dinsa. Milo ta jawo tare da sauran kayyayaki har saida ta hada masa tea. A can gefe kuwa wata kula ce cike da kayan soye soye, a plate ta zuba masa nasa tare da yanko masa wani cake mai siffar mangoro. Haka samir ya bita da kallo har ta kammala hada abincin. Daga nan sai ta zauna ta fuskance shi. Tare suka fara cin abincin cikin natsuwa da annashuwa. 
      " Amma fa wannan abinci yayi dadi ashe dama kin iya girki haka!" Samir ya fada yana dubanta. Anan samirat tayi murmushi amma batace uffan ba. " Amma fa kibar ganin kinyi wani kokari domin kema kin san na fiki iya girki. Idan nayi abinci.... Hmmm... Ai ba a magana." Wannan magana taba samirat dariya har saida hakoranta suka fito. Shi ma maganar taso bashi dariya domin ya fada kawai amma a zahiri yasan ko kadan bazai iya cimma kafarta ba. To bayan sun kammala cin abincin ne sai yayi mata sallama daga nan ya nufi waje inda motarsa take. Tuki ya farayi har saida ya isa gida. Yana ajiye motar sai ya kutsa kai sai dakinsa. Laptop dinsa ya dauko yana latse latse. Can sai yaga an banko kofar da karfi. Yana dubawa sai yaga ashe kanwarsa ce labnat. 
      " Yaya, wai kaga wani assignment da aka bamu arabic kuma yau zamu bayar." To anan ne samir ya tuna cewa ashe yau assabar. Karfar littafin yayi yana dubawa.

                                                             PAGE 9

          " Hala ina sabnat?" Samir ya tambaya.
          " Ita har ta wuce makaranta." Sabnat ta bashi amsa.
          " To tayi assignment din kuwa?" Ya kara tambaya.
          " Nima ban sani ba." Labnat ta bashi amsa.
          " To umma fa tana ciki?"
          " Umma tana cafeteria kuma tace ka iskota a can. Yaya in fadama wani abu, yau fa abba zai dawo."
          " To ke ya akayi kikisan yau zai dawo?" 
          " Umma ce ta fadamin."
          " To yayi kawo biro na fara kada ki makara." A haka samir ya fara watse mata assignment din har sai da ya kammala sannan ya bata ta fita. Cikin sauri yayi wanka daga nan ya jawo roba robansa. A nan ya nufi hanyar cafeteria  saman mashin din. Bai wani dadewa ba ya iso dama bayada nisa da gidan. Ai kuwa yana shiga masu aikin suka fara yi masa tsiya kasancewarsu mafi yawa daga ciki mata ne kuma yana wasa dasu. Haka dai yayi banxa dasu ya nufin ofishin first lady wato ummarsa. 
           " Yauwa naji dadin ganinka domin a wannan satin munada aiki sosai. Da farko dai kusan maiakatu hudu suka aiko muna sako mu dafa musu abinci domin sunada meeting. Wanna shine dalilin kiranka domin mu fara shirye shirye tun yanxu. Akwai abubuwan da nake ka siyo yanzu saboda haka ga mukullin mota kayi sauri ina jira." Anan ta miko masa makullin motar da kuma takadda tare da kudi.
           " To amma umma kada fa ki manta yau assabar kuma inaga ai abincin kamar bazasu karba ba sai ranar litinin. To me zai hana mu bari sai a ranar don kada ya lalace." Inji samir.
            " Kajimin yaro dan iya yi. To waya fadama abinci kawaine za a dafa musu, za a hada musu cake, meet-five, cin-cin da dai sauransu to idan bamu fara a yau ba bazamu iya kammalawa a cikin lokaci ba. Saboda haka yanxu kayi sauri ina jiranka." Anan samir ya karbi makullin tare da kudin bayan ya fahimci bayaninta. A nan ya nufi motar daga shigarsa ya tayar sai kasuwa.


                                                      PAGE 10

           Bayan ya shiga cikin kasuwa ne ya sayi duk abunda aka rubuta a list din sai wadanda suka rage dole sai a supermarket za a samesu. Take ya shiga motarsa ya danyi tafiya kadan. A nan ya hango inda yake nema. Fitowa yayi cikin motarsa ya shiga cikin supermarket. 
           Ai kuwa daga shigarsa ta kura masa ido cikin murmushi ko kyaftawa batayi. Sunanta meerat, meerat yar gidan masu halin ce domin abbanta shahararren dan kasuwa ne kuma mafi yawan supermarket dake garin mamallakin ne. Kyakyawa ce fara doguwa son kowa kin wanda ya rasa. Tun suna yara take mutukar son samir amma shi kuwa ba wadda ya tsana a duniyar nan irinta. Domin ko wannan shigowar da yayi ta rashin sanin cewa supermarket dinsu ne. Da ace yasan cewa nasu ne dako kasuwar bazai kara zuwa ba balantana yazo ga titin. 
          Wani dan kwando samir ya dauka inda zaisa kayan. Tafiya yakeyi daya bayan daya yana duban abunda ya masa. To bayan ya gama daukar kayan sai ya nufi wurin da ake biyan kudi. Anan aka fada masa cewa ya tafiyarsa domin har an biya masa. Anan ya fara mamakin to waye ya biya masa saninsa ne cewa bayada aboki a wurin. Juyowa yayi baya da nufin yaga wanda ya biya masa. Ai kuwa cikin rashin tsammani yaci karo da meerat sai murmushi take masa. Yana kallonta sai yaji zuciyarsa na tashi saboda tsanini rashin son da yake mata. Anan ya saki kwandon ya nufi waje a guje. Dukawa yayi ya fara kawaroro amai. Ita kuwa meera a kusa dashi ta tsaya tana kallonsa cikin takaici Idanunta cike da hawaye. 
         Anan ta fara tunanin irin soyayyar da take nuna masa tun suna yara a lokacin unguwarsu daya, makarantarsu daya wato primary kuma ajinsu daya. A duk inda yake tana biye dashi shi kuwa in banda duka da zagi ba abunda yake mata. Tun yana dukanta har yakai ya daina don kada ya illata ta. To abun mamaki a gunsa shine a duk lokacin daya kalleta sai yaji rashin sonta ya kara shiga cikin zuciyarsa. Haka kuma a duk lokacin da yaji wannan rashin son a zuciyarsa to sai yayi amai. Idan sau goma zai kalleta a yini to sau goma sai yayi amai. Wannan amai da yakeyi yasa yaji baya kaunarta ko kadan ita kuwa ko kadan bata taba jin bata sonsa ba duk da walakancin da yake mata. Hasalima sonsa sai kara shiga zuciyarta yake. Saboda wannan dalili yasa ta samu tabarau baki tana sanyawa a duk lokacin da take son ganinsa. Amfanin tabarau din shine ya rufe fuskarta yadda bazai ganta ba balantana yayi amai. 
     
                                                    ME ZAI FARU?

                                  ZAMU CIGABA.....
  
                                                       PAGE 11
     

       A nan tunanin meera ya katse ganin samir ya mike tsaye, cikin sauri ta dauko tabarau dinta baki ta sanya. " Haba samir ka juyo ka kalleni mana."  A cikin murya mai dadi ta fada amma ko kallonta bai tsaya yiba tafita ya farayi. Ita kuwa binsa tayi a guje tasha gabansa. " Haba samir ya kana guduna wai me nayi makane? Yanxu dai ga ruwa na kawo maka sai ka kuskure bakinka ko." Anan ta mika masa swan water. Karba yayi kamar abun arziki ai kuwa yana bude gora sai ya fara kwarara mata ruwan har saida suka kare. Daga nan sai ya nufi wurin wani mai shago ya siya ruwa ya fara kuskure bakinsa. A nan meera ta matso kusa garesa tana masa magana akan yayi hakuri amma ko kallonta bai tsaya yi ba. Yana gama kuskure bakinsa ya nufi motarsa ita kuwa sai faman binsa take tana masa magana. Haka samir ya shiga motarsa ya tafiyarsa yabar meera tana zub da hawaye saboda bakin ciki da takaici. 
     Bayan azuhur ne saiga samir ya dawo cafeteria inda ya iske har sun sawo kayan sun fara girkin. " Haba kai kuwa samir, tun da safe na aikeka amma wai sai yanzu. To wai hala me ka tsaya yine haka."  To kafin ya bata amsa ne sai yaji magana daga bayansa.
      " Dan samari an girma." Anan samir ya juyo domin yaga kowa ke magana, anan yayi arba da kawar ummarsa wato talatu. Lakama shi tayi kamar dan yaro tana murmushi kafin ta cigaba da magana.  " Ai kuwa yau da safe sai naga wani kamar shi yana tafiya wata yarinya na binsa amma kuma ransa kamar a bace. Nace wannan samir dina ne haka." 
        " Inaga bani bane." Haka samir ya fada da sauri don gudun kada ta ganoshi. 
         " Kai samir fadamin gaskiya nafasan halinka da......." Anan ta jawo hannunsa suna tafiya tana masa tsiya. Bayan kome ya kammala ne sai suka watse kowa ya nufi gida. Shi kuwa samir bai dawo gida ba sai sha biyu na dare domin tafiyarsa yayi yawo shida abokansa. Yana shiga dakinsa yayi kwance saman gado yana nishi saboda gajiyar data damesa. To anan ne tunanin samirat ya fado masa a rai kuma sai yaji yana son ganinta tare da tambayarta musabbabin wannan ciyo da takeyi mai ban mamaki. 
      

                                                           PAGE 12

             Yana cikin wannan haline sai yaji ana jifar tagar dakinsa. Anan ya bude tagar yaga ko waye, gidan nasu na sama ne kuma dakinsa a sama yake. Torch-light ya dauko ya haska. Ai kuwa yana dubawa sai yayi arba da samirat. Anan ya rasa yadda zaiyi ya shigo da ita gidan domin ya baro su umma a waje sunata shakar hira saboda abba ya dawo. Wata dabara ce ta fado masa. Igiya ya dauko mai karfi ya daura ga wani karfe. Daga nan sai ya jefa mata tare da yi mata umarni ta hau igiyar zai jawota. Anan samirat ta makalkale igiya shi kuwa gogan naka sai jawota yake har saida ya samu damar cafke hannunta. Anan ya janyota gaba daya. Debe igiyar yayi ya adana daganan sai ya kulle tagar tare da sama dakinsa sakata. 
        " Wai ke me ya kawoki wannan wuri ne a cikin dare haka?" Samir ya tambaya.
        " Kayi hakuri samir bana iya bacci a wannan gidan ni kadai." Ta bashi amsa.
        " To ai mai gadi na nan bai kamata ace kina jin tsoro ba." Inji samir. Anan samirat tayi shiru batace kome ba. Zaunawa tayi daga nan sai ta dauko laptop dinsa ta buda tana lallatsawa. " Kuma in tambayeki. Wai wannan ciyo da kikeyi wane irine domin ban taba ganinki a cikin irin wannan hali ba." 
         Samirat kallonsa tayi ba tare da tace uffan ba. A nan samir ya rasa ma a nar wannan kallon data masa ko tayi fushine dai oho. Daga nan kuma sai ya canza hirar tasu bayan ya fahimci cewa batason yana maganar wannan ciyo dake damunta. 
         " Hala ina ka samu wannan hoto?" Samira ta nuna masa wani hoto a cikin laptop dinsa.
         " A cikin wani group na whatsapp aka turo hoton ni kuma nayi saving, hala ya kikaga yan matan sun hadu ko?" Samir ya tambaya. Murmushi tayi ba tare da tace uffan ba. " Hala kin san su ne?" Samir ya kara tambaya.
         " A a ban san suba. Na dai tambaya kawai." Haka samirat ta fada amma da ganin fuskarta kasan dole akwai abunda yasa tayi wannan tambayar. Haka taci gaba da kallon hotunan wasu ta tambayesa wasu kuma ta wuce kawai. Anan samir ya kishingida kan gadon saboda baccin dake damunsa yabar samirat da laptop dinsa. Bai wani jimawa da fara baccin ba sai yaji an fado masa da karfi.

                                                        PAGE 13

        Yana tashi sai yaga an dauke wuta kuma da alamar cewa ciyon samirat ne ya dawo, yar torch-light dinsa ya dauko yana yadawa sai yaganta a saman jikinsa tana nishi dakyar. Sai ga laptop dinsa a can gefe. A nan ya gyara mata kwanciya daga nan kuma sai ya rufe laptop din ya kaita mazauninta. Samirat sai nishi take da kuma zabure zabure kamar dai akwai abunda take gani. Shi kuwa samir tsaye yayi a kanta yana mata addu oi. Daga farko ya dauka abun zai wuce amma daga baya sai yaga ciyon sai kara habaka yake. Jikinta ke girgizawa da karfi sai kuma idanunta da suka jujjuye bakyan gani. Wani kakaki take marar dadi kamar an shakure mata wuya. Abunda yaba samir mamaki shine hannunta tasa a wuyanta kamar tana kokarin janye wani daya shakure ta. A nan ya duba amma baiga kowa ba ita kuwa sai faman kokuwa take tana kokarin janye abunda ya shakureta. 
         Da sauri samir ya rirriketa ganin tana shirin faduwa saman gadon amma duk da hakan jikinta sai girgiza yake idanuwanta kuma sunyi fari fat ba a ganin bakin dake cikinsu. Abunda ya tsoratar da samir shine budewar tagar bayan kuma ya samata sakata. Da sauri ya taso da nufin rufewa ai kuwa sai wani iska mai karfi yayi jifa dashi can gefe. Yana kallo wannan iskan mai cike da kura ya tallabo samirat da nufin fita da ita wajen tagar. A guje shi kuma yabi ta ya rungumeta. To anan aka fara ja in ja. Rungume yake da samirat yana kokarin mayar da ita a saman gadon amma sai ji yake ana janta da karfin tsiya da nufin fita da ita ta tagar. Abun mamaki idan ya duba baya ganin kome in banda iskan daya cika dakin kamar guguwa. Ita kuwa samirat a wannan lokaci ta dade da suma saboda tsananin bala in da take ji. Gashi ba haske balantana yaga ko menene ke janta. Yar fitilar tasa ta kubce masa dama itace yake takama da ita. To anan ne tsoro ya fara kama samir amma haka ya daure yaja aja sai gumurzu yake da abunda baya gani. 
          Sai da kyar samir ya samu nasara haka kawai ba zato ba tsammani sai yaga an bar janta. Iskan daya cika dakin fita yayi ta taga daga nan sai tagar ta kulle kanta tasama kanta sakata. To anan ne yaga wuta ta dawo. Dakyar ya tallabota ya aza saman gadon domin ya gaji likis. Anan ne yaga jini na fitowa ta bakinta da hancinta. Da sauri ya dauko kyalle ya fara goge mata yana girgizata domin ta tashi amma ina ko motsi batayi.

                                                          PAGE 14

             Anan hankalin samir ya tashi, aza kunnensa yayi ga zuciyarta amma sai yaji bata sheda. Cikin tausayawa ya fashe da kuka. Anan ya rungumeta batare da sanin abunda zaiyi ba. Haka dai ya cigaba da kukan ba kakkautawa kai kace karamin yaro. To yana cikin kukan ne sai yaji ta fara tari. Anan yayi shiru ya jiya shin wai da gaske itace ke tarin. Ai kuwa yana tabbatar da cewa itace anan ya daina kukan. Kara kankaneta yayi a jikinsa yana murna da cewa bata mutu ba. A hankali ta fara bude idanunta har saida ta budesu gab. Daga nan samir ya mata umarni ta shiga baye ta wanke jinin dake jikinta. Mikewa tayi amma ta kasa tashi domin ji take duk jikinta ya mutu. Samir ne ya kaita bayen da kansa. Yana kaita ya jiyo zai fito ita kuwa ta rikeshi domin tsoro takeji. A haka ya juya baya har saida ta kammala sannan ya tallabota ya dawo da ita dakin nasa.  Anan ne ta kwanta saman gado saboda baccin dake damunta. Shi kuwa samir ko kadan bayajin bacci saboda ganin wannan abun mamaki domin tunda yake bai taba ganin irin wannan abin al ajabi ba. A haka ya kishingida amma kuma baya iya baccin. Sai wajen asalatu wani bacci mai nauyi ya daukesa. 
          Samir ne yake gudu cikin wani kogo kamar an biyoshi. Sai da yayi tafiya mai nisa sai ya kawo ga wani gulbi, ruwan gulbin sai tafarfasa suke kamar ana banka musu wuta. " Kada ka yarda ka shigo wannan kogon." Anan samir ya juyo yaga mai masa magana. Ai kuwa yana juyowa sai yaga almajiri ne amma idanunsa fari fat ba baki.
         " Kai kuwa me kake nufi da wannan maganar?" Samir ya tambaya.  
         " Ina nufin kada ka yarda ka shiga gidan matattu kuma ka daina taimakon matattar mace domin in ba don kaiba da tuni na rama musu abunda da tayi musu." 
         " Gaskiya bazan bari ba. Amma ka fadamin su wayene kuma me ta musu.?" Samir ya tambaya. Anan almajirin yayi nuni zuwa ga gulbin. Kawai sai samir yaga mace da namiji sun fito duk jikinsu a kone bakyan gani.
        " Itace sanadin mayar dasu haka. Kuma kaima idan ka cigaba da taimakonta to haka zata mayar dakai. " Inji  almajirin. 
        Firgigit samir ya farka ashe mafarkine yake. Ai kuwa yana dubawa sai yaga samirat a gabansa tana tayar dashi. Anan ya kalleta yaga jikinta ya dawo normal kamar ba itace wadda tayi rashin lafiya jiyaba.
      
       
                                                         PAGE 15

        " Dama na tayar da kai ne na fadama ni zan wuce gida kafin rana ta fito mutane su sa min ido." Injita. Anan samir ya mike ya dauko igiya. Bayan ya daure sai ya mata umarni data hau. A hankali ta hau igiyar tana saukowa kasa har ta dire. Daga nan ta dago masa hannu ta nufi gida. A wannan lokaci da sauran duhu domin safiya bata iyar da wayewa ba. Wannan shi yaba samirat damar komawa gida ba tare da wani ya hangota ba. Shi kuwa samir tsundumuwa yayi cikin tunanin wannan mafarki da yayi domin bai san abunda ake nufi dashi ba. Bayan ya kimtsa ne sai ya nufi dinning inda ya iske har sun fara cin abincin. To anan ne yama abba sannnu da zuwa shi kuwa ya fara tambayarsa ya labarin makarantar. 
        " Yauwa naji dadin ganinka a wannan lokaci domin inaso in tambayeka game da wadannan mutanen dake barazana ga rayuwarka. Wannan fa shine karo na uku suna kawoma farmaki har gida amma cikin kariya ta ubangiji a duk lokacin da sukazo basa iskoka." Haka umma ta fada tana dubansa zaman jiran ya bata amsa.
          " To gaskiya bazan iya fadin ko su waye ba domin nima ban sansu ba. Amma inaga mahassada ne daga makarantarmu suke bibiyata." Inji samir.
          " To amma dai ba banza ba. Dole akwai abunda ka musu ko?" Inji abba.
          " Ni dai zan iya tuno dayan domin sai naji ko suna kiransa da amiru zaki ko kuma waye ma dai bazan iya fadin ya ainahin sunan yake ba." Cewar umma. Shi kuwa samir yana jin ta fadi wannan suna sai ya tuno da gayen domin shine babban makiyinsa a makaranta kuma abunda ya hadasu shine: 
          Samir ne ya ratayo jaka yana sauri domin yanada lecture. Yana cikin tafiyar ne sai ya hango wasu gayu su biyar sun nufosa. Ai kuwa suna isowa inda yake suga zagayeshi sai kallonsa suke cikin harara. Na tsakiyar ne ya matso daf dashi sannan ya fara magana. " Wai kai wane irin mutum ne mai nacin tsiya tace bata sonka ko dolene sai kayi soyayya da ita, hala ita kadaice mace? To wannan shine last warning kada na kara ganin ka fuskanci samirat. Kada ka manta a duniyar nan ba yarinyar danakeso irin meera. Amma saboda sihirin daka mata na kasa mallakarta har yanzu. Don dole na koma kan samirat wadda nake mutukar ji da ita. To ka sani a wannan karon bazan hakura ba. Koni ko kai.  Ni yanzu na bar maka meerat kayi yadda kakeso da ita. Amma ka sani samirat tawace kuma ba kai bata."

                                                 PAGE 16
      
       " wai ko kana nufin duk yarinyar danayi soyayya da ita kaima sai kayi? To kada ka manta nine amiru zaki, kuma ka sani idan na kara ganinka da ita to wannan shine ganin na karshe da zakayi mata domin sai dai mahaifiyarka ta haifi wani." A haka amiru zaki ya wuce tare da yaransa yabar samir a tsaye. 
    Ai kuwa kayi wauta babba domin dama meera ko dauka kabar samirat din domin akan samirat sai dai kayi gunduwa gunduwa da namana amma bazan daina binta ba. Haka samir ya fada a cikin zuciyarsa daga nan ya cigaba da tafiyarsa. 
       To anan ne tunaninsa ya katse yacigaba da cin abinsa. " Inaga ya kamata ka kula sosai domin bada kowa ake fada ba a wannan lokaci." Inji abba daga nan sai ya tashi ya koma falonsa.  A haka dai suka yita watsewa daya bayan daya har saida ya zamo cewa samir kawaine aka bari yana cin abincinsa. Wata cinyar kaxa ce ya dauko da nufin kaiwa baki kawai sai yaga ta fadi. Anan yasa hannu da nufin dauka kawai sai yaga kamar iska ya kara jefata can gefe. Tsuki yayi daga nan sai ya tashi ya nufin wurin da take. Hannu ya kara kaiwa da nufin dauka kawai sai yaga an kara jifa da ita. A nan samir yayi tsaye yana mamaki wannan abu. Can sai ya nisa a guje ya nufi cinyar kazar amma kafin yakai sai yaga an yi jifa da ita wani gefe, haka samir yayita bin cinyar kazar da nufin dauka amma dayaje sai yaga an yi jifa da ita wani wuri. Dole ya hakura ya dawo dinning table ya zauna yana mamakin wannan abu. Can sai ya sa hannu da nufin daukar wata cinyar kazar, ai kuwa kafin yakai ga taba kazar sai yaji an rike masa hannu gam. Ba yadda bai yi ba ya kwace hannunsa amma ya kasa. Kuma abun mamaki baya ganin wanda ya rike hannun iyaka dai yana ji cewa hannunsa ya sadanre a wuri daya tamkar gunki. A haka samir yayita kubce kubce domin ya kwace hannunsa amma ya kasa har daga karshe ya fado saman kujerar.
       To bayan ya fado ne sai aka fara mulmula shi, idan aka kaishi wannan gefe sai akai shi wancan gefe, samir yana kokari ya mike tsaye amma baya iyawa domin ji yake kamar an dannesa. Haka aka yita mulmula shi ba tare da ganin wanda ke masa haka ba. Ana cikin mulmula shi ne sai aka yi jifa dashi can gefe sai da kansa ya bugi gina da karfi. Anan ya dafe kai yana yar kara saboda ciyon da yakeji. Yunkuri yayi daga nan sai yaga ya mike tsaye lafiya lau.  

                                                      PAGE 17

            Anan ya fara kallon jikinsa yaga komi normal yana iya watayawa yadda yakeso, hakama hannunsa ya dawo dai dai. Tafiya ya farayi yana nishi kai kace wanda yasha duka. Yana cikin tafiyar ne sai yaji takun takalma a bayansa. Anan yayi tsaye kikam zuciyarsa sai bugawa take saboda tsoro, yana so ya juya amma kuma bai san abunda zai gani ba. Can sai yayi ta maza ya juya a hankali. Yana dubawa sai yayi arba da labnat fuskarta a murtuke ba alamar farin ciki. 
           " Ke?" Haka samir ya fada cikin mamaki domin baiga lokacin data zo wurin ba. Abunda kawai yake iya tunawa shine tare da ita akayi breakfast daga nan kuma ana kammalawa sai ta tashi ta tafiyarta. " Hala ya akayi kika zo nan?" Ya tambaya.
          " Ai kai zan tambaya me yasa kake shiga hurumin da ba naka ba. Kada ka manta nayima kashedi amma naga kamar baka jiba. To wannan shine na karshe ina fadama ka fita harkata, ina fadama ka fita harkata." 
          Anan samir ya kalli labnat yaga duk ta canza kamar ba ita ba." Wai ke lafiyarki kuwa wane kashedi kuma kike magana akai. Ni a sanina bakyada ciyon hauka amma yau naga...."
          " Kai dakata." Anan ta katsesa. " Kada kayi tsammanin cewa karatu nasa kaci jarabawa. Saboda haka ka cire wannan tunani a cikin zuciyarka na cewa taimako zai sa ta........" 
         Anan samir ya fara jin kansa na sarawa daga nan sai ya fadi ba tare daya ida jin abunda labnat ke fada ba. Daga nan bai kara sanin inda yake ba iyaka ya farka ya gansa a dakinsa sai meera kankane dashi tana kuka. Yana farkawa sai ya fara tunanin abunda ya faru dazu to ya akayi ya shigo wannan daki ita kuwa meera me ya kawota a gidan. " Ke ya akayi kika shigo wannan gidan bana hanaki zuwa wurina ba." Samir ya fada bayan ya murtuke fuska. Ita kuwa meera cikin sauri tasa glass dinta baki kada ya fara jin amai. 
         " Kayi hakuri abun begena wallahi tun a lokaci da wannan abu ya faru na kasa zaune na kasa tsaye sai da nazo nan da nufin na baka hakuri. To a lokacin dana shigo gidan naga ba kowa sai nayita sallama domin a tsammanina su umma na nan. Haka na duba ko ina amma banga kowa ba. Da har zan tafiyata sai naga bari na duba a dinning ko kana nan. Ai kuwa ina zuwa na tarar dakai kwance ko sheda bakayi. Anan ne na kawoka daki duk hankalina a tashe domin a tsammanina ka rigamu gidan gaskiya. Wannan shine dalilin da yasa kaga ina kuka kuma shine dalilin da yasa nazo gidanku. Amma don ALLAH kayi hakuri bana son ranka ya bace." 

                                                           PAGE 18

          Anan samir yayi shiru ba tare da yace kome ba. " Sweetheart ina fatan lafiyanka lau." Haka ta fada shi kuwa maimakon ya bata amsa sai yayi wani murmushi. " Wow samir! Ashe dama kana murmushi?" 
       Haka ta fada cike da farin ciki domin rabonta da yayi mata murmushi tun suna primary 3 wata rana da tazo wurinsa domin ya ara mata pencil. To anan ya dauko ya bata cikin murmushi daga nan kuma sai ya lakamata suna tafiya suna hira har suka shigo  aji. To a wannan lokaci bai fara jin baya sonta ba sai daga baya bayan soyayyar samirat ta rufe masa idanu. 
       Anan tunanin meerat ya katse. Ckin farin ciki ta fada jikinsa cike da murna domin bata taba tsammanin cewa irin wannan rana zata faru ba. Shi kuwa samir kyaleta yayi ba tare da yace kome ba.  " Ko zan iya cire glass din?" Ta tambaya.
      "A a." Samir ya bata amsa. Daga nan sai ya tashi saman gadon ya nufi wardrobe dinsa. Ita kuwa binsa tayi tana rike da hannunsa.
      " Haba samir har yanxu kana nufin baka sona?" Anan ya juyo ya kalleta daga nan kuma sai ya cigaba da binckar kayansa. Bayan ya dauko wadanda zai sanya sai ya xo kan gado. " Wai kai samir me yasa baka son shigar hausawa, tun da nake ban taba ganinka da shadda ba. A kullum jeans da t-shirt sune kayanka wai me yasa?" Meera ta tambaya.  Kallonta yayi cikin dariya ba tare da yace kome ba. " Wato dariya na baka kenan." Haka ta fada. Rigarsa ya dauko da nufin sanyawa ita kuwa meera kankane bayansa tayi." Sweetheart ka hadu fa. I love you." Anan ta sakeshi. Daga nan ta dauki jakarta ta kama hanyar fita. To kafin ta fita ne samir ya kwala mata kira.
      " MEERA! Inaso kiyimin wata alfarma." Anan ta juyo taji me zaice. " Kada ki fadawa kowa halin da kika tsinceni bayan kin shigo wannan gida." Meera najin haka saita sheko da gudu ta kankaneshi.
       " Kada ka damu sweetheart bazan fadawa kowa ba. Amma kuma zanso ka fadamin da bakinka wannan abu daya sumar dakai." Inji meera.
        " Kada ki damu zan fadamiki amma ba yanzu ba." Samir ya bata amsa.
        " To sai yaushe kenan?" Ta kara tambaya.
        " Sai na kammala bincike akan abun domin yanzu nima banada masaniyarsa." 
      
                                                        PAGE 19
      
       Anan meera ta sakeshi tana kallonsa cikin mamaki. " To yanxu kana nufin baka san abunda ya sumar dakai ba?" 
       " A hakikanin gaskiya ban sani ba kuma inaso ki yarda dani."
       " To kayimin alkawari zaka fadamin idan lokaci yayi."
        " Kada ki damu kece ta farko da zata fara sani." Anan sukayi sallama meera ta tafiyarta. To bayan ta tafiyarta ne samir ya fada kogin tunanin abunda ya faru da safe gashi yanxu agogonsa ya nuna masa cewa karfe biyu. Salla yayi yana idarwa ya fara baccin da bai farka ba sai karfe hudu da rabi. Yana farkawa ya kimtsa yayi la asar daga nan sai ya fito waje inda ya iske su umma sun dawo. Sai ga kawarta talatu ta kawo mata ziyara. Ai kuwa tana hangosa ta shiga yi masa tsiya tun yana ramawa har ya kyaleta ya tafiyarsa. Dakin su labnat ya shiga inda ya tarar dasu sai wasa suke abunsu. Dakin duk sun batashi. Gashi kuwa kawayensu sun kawo musu ziyara sai faman guje guje ake. Ai kuwa suna ganin shigowarsa sai sukayi tsit. 
          " Laaa yaya!" Haka suka fada tare wato labnat da sadnaf. Daga nan sai ya jawo hannun labnat ya fita da ita. Su kuwa suna ganin haka sai suka cigaba da wasansu. A haka ya lakamata yana tafiya itama kuwa sai ta lakamoshi duk da tsayinta bai kai nasa ba. Daga nan sai ya nufi kofar gida da ita. 
          " Hala me yasa yau bakuje makarantar arabiya ba." Ya tambaya.
          " Yau ana hutu ne domin barayi sun shiga gidan shugaban makarantar, mafi yawan malamai sun tafi gidansa suyi masa tozanko shi yasa aka bada hutu na yau da gobe." Labnat ta bashi amsa. 
         " To amma labnat lafiyanki kuwa tazu da safe sai naga kin canza harda fadamin cewa wai ko kin yimin kashedi. To kashedin me kike magana akai?" Samir ya tambaya.
          " Kashedi kuma? Bani bace yaya to wane kashedi nake da ikon na baka tunda kaine na gaba gareni hasalima kaine kake da ikon yimin kashedi idan nayi ba dai dai ba." Cewar labnat. Anan samir ya kalli kanwarsa yana mamakin wannan abu.
          " To a lokacin da kika gama breakfast dinki kin dawo a dinning table daukar wani abu ko kuwa tafiyarki kikayi?"

                                                         PAGE 20
    
         " Ina gama breakfast shiga nayi dakinmu nasa uniform daga nan sai na nufi makaranta. To bayan na isa ne aka fadamin cewa barayi sun shiga gidan malam yau ba makaranta. Daga nan na wuce gidan kawayena domin na fada musu to anan na tsaya muka yita wasa. To amma yaya hala wani  abune ya faru?" 
         " A a ba abunda ya faru yanzu tafiyarki gida kawai dama na tambaya ne." Inji samir. Anan labnat ta wuce gida shi kuwa samir hankalinsa kara dugunzuma yayi domin yasan ba lafiya ba. To fa kada ace irin ciyon samirat ne ke shirin illatasa. Babban abunda ke basa mamaki shine labnat din daya gani wadda bata gaskiya ba. To wai waye yamasa shigar labnat kuma wane kashedi ne akeso a fada masa?" Gashi kuwa a zahiri yaga abun ba mafarki yake ba balantana yace ai ba kome. Haka dai yaci gaba da wannan wasi wasin kafin ya shiga gida.
       Yau ne safiyar litinin, mafi yawan dalibai sun cika jami ar domin samun lecture a cikin lokaci. A cikin dandazon dalibai ne wata mota ta keto sai sheki take kai da gani kasan motar ta hadu. Samir ne ya fito a ciki yayi wanka over yan mata sai albarka suke sawa. Bayan ya kulle motar sai ya nufi wani block. To kafin ya karasa ne sai yaji ana masa magana. 
         " Takawarka lafiya kyakkyawa dan mamarsa." Anan ya juyo yayI arba da wasu yan mata su biyu, su wadannan yan mata course-mate dinsa ne. " Matsalarka daya. Baka wankan shadda kullum cikin kananan kaya kake." Haka dayar ta fada daganan suka fara yi masa dariya. Anan ya jirasu sai da suka karaso daga nan suka shiga block din tare.  Bayan sun shiga aji sun zauna. Basu wani dadewa ba saiga lecturer din ya shigo. Lecture akeyi amma hankalin meerat naga samir sai satar kallonsa take. Shi kuma a wannan lokaci hankalinsa naga samirat sai kallonta yakeyi. A duk lokacin da meerat taga ya kalli samirat sai taji kishi sosai domin ji take kamar ana soka mata mashi a cikin zuciya. Ana gama lecture din sai ga amir zaki yazo wurin samirat. Tana ganinsa sai ta kyalkyace da dariya anan suka fara kallon juna cikin yanayin da samir ya kasa fahimtar abunda suke nufi. Saboda tsananin kishi bai san lokacin daya fita ajin ba cikin fushi. Haka ya buga motarsa ya nufi cafeteria. Abinci ne lafiyayye aka kawo masa amma dakyar yake kai loma saboda ganin wannan abu.

                                                         PAGE 21
          
          Da yaji baxai iyaba a haka yabar abincin ya nufi wurin da ake biyan kudi anan aka fada masa cewa an biya masa. Bai ko tsaya tambayar wanda ya biya ba domin yasan ba wanda zai biya masa kudi in ba meerat ba. Ai kuwa yana fita cafeterin din sai yaci karo da ita a gabansa sai murmushi take masa. Yana hada ido da ita sai yaji zuciyarsa na tashi. Anan ya duka ya fara kwaroro amai. To a lokacin ne meerat ta tuno cewa batasa glass dinta ba. Cikin sauri ta daukoshi a jaka ta sanya daga nan ta kawo masa ruwa domin ya kuskure baki. Yana gama kuskure bakin tashi kawai yayi ya nufi wata hanya bai ko tsaya kallonta ba. Ita kuwa sai binsa take tana bashi hakuri amma ko saurarenta baya yi. Sai da yayi yar tafiya mai nisa sannan ya kawo inda motarsa take. To a can gefen motar akwai wata kujera mai fadi. Kujerar ya nufa ya zauna haka itama meerat sai ta zauna daf dashi.
         " Dear don ALLAH kayi hakuri kuskure ne na manta da glass din a jaka tsammanina yana makale a fuskata."
         " Kinga abunda nake fada miki ko ki daina bina, yanzu ji abunda kika sani gaba daya ji nake kamar an yimin duka." Haka samir ya fada cikin fushi yana harararta.  
          " Dear kayi hakuri irin hakan ba zai kara faruwa ba. Indai don ni bazaka kara amai ba." Haka meerat ta fada amma a mamakinta sai taga yana murmushi. Da farko ta aza ita yakewa murmushin Sai daga baya ta gano ashe hankalinsa ne ya karkata ga samirat wadda ko kulasa batayi ba tafiyarta kawai take. Anan ya tashi ya nufi wurin samirat. " Dear ina zaka?" Haka meerat ta fada amma ko saurarenta bai yiba. Wurin ya taro gabanta ne sai yayi kuskure ya bangajeta kadan ab babu data fadi. Ai kuwa tana tashi sai ta hausa da fada.
         " Wai kai samir mahaukacin ina ne, na fadama ka daina bina kaki yanxu ji abunda ka sani da kadan na fadi ajina ya zube. To yanxu me kakeso dani ne?" Haka ta fada tana ciccika sai kallon wani gefe take.
          " Haba abun begena kiyi hakuri mana ai kuskure ne kuma kin san kowa na kuskure. Dama na tasone na rakaki inda zaki kona debe miki kewa koba haka ba." Haka ya fada cikin sakin fuska. Ita kuwa in banda harararsa ba abunda take. Duk abunda yake fada akan kunnen meerat ya zo domin a kusa dasu ta tsaya tanajin abunda ke faruwa. 

                                                      PAGE 22

          Anan ta fara tunanin cewa wannan maganar gaskiya ce wato duk abunda kayi sai an yima. Yanxu ya gama yi mata walakanci sai gashi ba a dade ba shima ya samu wadda ta masa.  
        Haka samirat tayi banza dashi ta tafiyarta shi kuwa sai binta yake yana bata hakuri. Ita kuwa meerat sai ta bishi tana kokarin ta janyo shi wurinta amma ko saurarenta baya yi. Sai da suka dade suna wannan tafiyar amma ba wanda ya samu abunda yakeso. A haka samir ya hakura ya daina bin samirat haka itama meerat hakura tayi ta daina bin samir. To bayan an tashi daga makaranta ne samir ya nufi gida cikin bacin rai haka itama meera ta shiga gidan ranta a bace. Duniya juyi juyi, yau idan tayima zafi gobe tayima sanyi. Bako shakka yau tayima samir da meera zafi domin kowanensu a cikin bakin ciki yake. A yinin wannan rana ko magana basa sonyi har dare yayi. A haka samir ya zauna a tsammaninsa yaga samirat ta kwankwansa masa a taga amma tsit yakeji ba wani alamu. Da misalin karfe goma ne yaga bari ya fita ya dubata watakila ciyon nata ne ya taso. Don gudun kada a kulle gida sai ya daura igiya a tagarsa ya sakota waje yadda idan ya dawo iyaka ya dane ya shiga ciki. Daga nan sai yabi ta kofar dakinsa ya fita. mashin dinsa ya dauka, yana murdawa ya fita a guje bai tsaya ko ina ba sai kofar gidansu sanirat. Kai tsaye ya shiga ciki. To anan ne ya lura da cewa dakin mai gadi kulle yake har an sa masa makulli. Shiga yayi cikin falon yana sallama amma ba wanda ya amsa masa. Sai da ya duba gidan tsaf amma ba kowa saboda haka ya dawo falo yayi zamansa yana jiran dawowar samirat.
          Talabijin a bude take saboda haka yana zaunawa kallo kawai ya fara. Anan yayi gyaran zama iskan fanka na bugunsa sai nishadi yake da talabijin. Yana cikin kallon ne sai ya fara angaje, a haka dai karamin bacci ya saceshi. Firgigit sai yaji kamar an tadashi. Yana tashi sai yaga talabijin a kashe. A nan ya fara tunanin cewa samirat ta dawo. Tashi yayi yana kiranta amma tsit ba wanda ya amsa. Sai da ya zagaye gidan tsaf amma baiga kowa ba. Anan yafara tunanin kila ta shiga makwabta ne saboda haka sai ya nufo falo. Ai kuwa yana shiga falon sai yaga talabijin na aiki da alamar an kunnata. Anan mamaki ya kashe samir domin yasan ba kowa a gidan. 

                                                         PAGE 23

            Daga nan sai yayi zamansa yaci gaba da kallonsa bai damu ba. Yana cikin kallon sai yaji yana bukatar ruwa saboda haka sai ya nufi fridge. Ruwa ya dauko a cikin gora tare da wani cup. Daga nan sai ya dawo yayi zamansa. Bayan ya bude kwalbar sai ya tara cup din yana zuba ruwan. Da karfi ya saki gorar ya tashi tsaye cikin tsoro domin jini ne ke fitowa a cikin gorar maimakon ruwa.  Kara kallon gorar yayi sai yaga ta dawo dai dai wato ruwan sun dawo. Anan ya daga gorar yana mamaki wannan abu. Murza idonsa yayi yaga shi wai jinin ne kodai shine ke ganin haka. Anan ya tabbatar da cewa bako shakka ruwane. Daganan sai ya zauna.  Kara daga gorar yayi yana zuba ruwan a cikin cup kawai sai ya kara ganin jini maimakon ruwa. A wannan lokaci jifa yayi da gorar can gefe saboda tsoron da yaji. Daganan sai ya tashi tsaye da nufin fita gidan. Mace ya gani ta shigo da irin kayan samirat daganan sai ta nufi wata kwana. A guje samir ya bita yana kiranta amma tsit baiga kowaba. Haka yacigaba da duba lungun data shiga amma a mamakinsa kowa babu. 
          Daga nan sai ya nufo falo. Ai kuwa yana shigowa cikin falon sai ya tarar da wannan mace a kusa ga talabijin amma kuma ta juya masa baya. Anan samir yaja da baya a tsorace. Anan ya mata kallon tsaf domin ya gani shin samirat ce ko kaka amma ya rasa gane ko wacece domin ta juya masa baya yadda baxai iya ganin fuskarta ba. A hankali ya fara tafiya yana kiran samirat amma bata juyo ba. Anan ne gabansa ya fadi domin ya tabbatar da cewa wannan mace ba samirat bace. Haka dai yaci gaba da tafiya a hankali yana kiranta har sai da yazo gab da ita. Hannu yasa da nufin tabata, ai kuwa kafin hannunsa ya kai ga jikinta sai yaji an dagasa sama, sai da akayi waliliya dashi sannan aka maka shi a bango. Anan ya fado galaibace yana nishi dakyar. To a wannan lokacin ne wutar gidan ta dauke gaba daya. Dakyar samir ya samu ya mike tsaye. Mikewarsa keda wuya sai yaji an nufosa ana sallama. Anan tsoro ya kara dabaibayeshi domin muryar mace yakeji. Matsawa ya farayi yana lalube saboda duhu amma sai jin takun tafiya yake ana binsa. Yana cikin laluben ne sai yaci karo da wani abu. Ai kuwa yana tabawa sai yaji jikin mace ne ya tabo. A guje ya juya baya ya nufi hanya ba tare dayasan inda yake takawa ba. Yana cikin gudun ne yasha gina anan ya fadi rikibis kai kace gawa domin kome nasa ciwo yake. 

                                                      PAGE 24

                 Ai kuwa faduwarsa keda wuya sai yaga an kawo wuta. Anan ya mike yana tangadi sai kace wanda yasha giya. Tafiya ya farayi yana gurmanta ya nufi kofar fita. To kafin ya kaine yaji an jawoshi da karfi an kara makasa saman gina. Anan ya fado galabaice. Daga nan sai aka yita daukar kayayyakin falon ana jefo masa tun yana kaucewa har sai da takai ya fadi kome baya iyawa. Sai da ya dade a cikin wannan hali kafin ya farfado daga sumar da yayi. Yana bude idanuwansa sai yaga innuwowi ( Shadow ) na yawo ta koina a cikin falon. Mikewa yayi a tsorace ya nufi kofa a guje. Yana kaiwa ga kofar sai yaga an dagasa sama ana shirin dawowa dashi. To anan ya rike kofar iyakar karfinsa. Wani iskane mai karfi sai faman cillo yake dashi amma samir yaki sakin kofar. Cikin rashin tsammani sai yaji an jefoshi da karfi tun daga bakin kofar falon har wajen gate kusa ga mashin dinsa. Yana ganinsa kusa ga mashin dinsa sai ya mike da sauri dama abunda yakeso kenan. Yana hawa yasa giya, a guje yaja mashin din ba tare da sanin inda ya nufa ba. A wannan lokaci ba kowa saman titi sabida haka samir sai kwarara uban gudu yake. Daga nan sai hankalinsa ya fara dawowa a jikinsa. To yana cikin gudun ne sai ya fara hango wani abu a madubin mashin din. Yana dubawa da kyau sai yaga ashe innuwowin daya baro gidan su samirat sune ke binsa........ 
                                                              ********
           A haka meera ta yini cikin bakin ciki domin ko abinci sai da kyar ta tura loma biyu a cikinta. Wazajen karfe tara ne bakin cikin ya fara ragewa saboda wani film data fara kallo. Koda aka buga goma sai taji kawai tanason ganin samir saboda haka sai ta kirasa domin suyi vedio call amma yaki dauka. Gashi tana ringing amma ba answer. Daga nan sai tayi niyar zuwa gidansu. Makullin motarta ta dauko ta fita. Ita da kanta ta bude gate kuma ta mayar dashi daganan sai ta buga motar bata tsaya koina ba sai gidansu samir. A wannan lokaci gidan bude yake amma tanajin kunyar shiga don kada su umma su tamabayeta dalilin zuwanta. Anan ta daga kanta sama cikin mamaki sai ta hango tagar dakinsa  a bude sai kuma wata igiya mai karfi daya jefo anan kasa.  Daukar igiyar tayi sai taga lalle tanada karfi sosai. Daga nan saita dane igiyar tana takawa har ta isa saman tagar dakin. Daga nan sai tayi tsalle ga shigo dakin. Anan ta duba ko ina amma bata gansa ba. Saboda haka sai ta zauna da zimmar jiransa. To a wannan lokaci data shigo dakin shi kuwa samir bai dade da fita ba inda ya nufi gidansu samirat. 
 
                                                          PAGE 25

             Haka meera tayi kwance saman gadonsa sai nishadinta take ita kadai. Tana cikin wannan hali ne sai tagar ta kulle kanta da karfi. Anan meera ta tashi ba yadda batayi ba domin ta budeta amma ta kasa saboda haka ta kyaleta. Kwanciyarta ta karayi saman gadon tana mulmulawa yadda takeso. Tana cikin hakane sai ta hango wani novel an rubuta masa REZA. Daukowa tayi ta fara karatu can kuma sai taji idanunta sunyi nauyi kamar tana jin bacci. Anan tayi jifa da novel din ta kwanta da alamar bacci takeji. Bata wani jimawa ba da runtse idanunta ba sai ta farka. Ai kuwa tana tashi sai taga an dauke wuta. To anan ta shiga laluben wayarta a saman gadon domin ta yadda fitila. To tana cikin laluben ne sai taji ta lalubo wani kamar samir. Ai kuwa cikin farin cike ta rungumeshi sai magaganun soyayya take fada masa. Tana cikin rangwada masa kalamai ne sai aka kawo wuta. Anan ta duba amma wayam ba kowa. Anan ta fara kwalawa samir kira amma ba wanda ya amsa. Kwanciyarta tayi cikin rashin damuwa a tsammaninta ya fita yayi wani abu. 
           Can sai aka kara dauke wuta. Ana dauke wutar sai taji hannayeta sun tabo wani abu kamar mutum. Kara kankameshi tayi domin a tsammaninta samir ne ya dawo. Ana kawo wutar kuma data duba sai taga ba kowa. To anan ne jikinta yayi wani tsam duk gashin jikinta sai da ya mike. Ta dan tsorata amma ba sosai ba domin har yanzu ganin take samir ne ke mata wasa. Daga nan saita dauko littafin da tayi jifa dashi wato REZA. Budawa tayi da nufin fara karatu amma a mamakinta shafukan littafin ba kome a cikinsu duk sun koma fari fat. Anan tayi mamakin wannan abu domin da farko data dauko shi taga rubutu amma kuma yanzu ba abunda ta gani. Haka tayita bude shafukan daya bayan daya har takai ga page na karshe. To anan ne taga anyi wani gwalaje sai kuma zanen wane gida a kasa. A can gefe kuma anyi wani rubutu wanda ta kasa gane abunda ake nufi. Ajiye littafin tayi can gefe.
        Juyowar da zatayi haka sai taga mutum a lullube kusa da ita. Anan ta tashi saman gadon da karfi saboda tsoron dataji. Manne jikinta tayi a gina sai karkarwa take. Sai da aka dau lokaci sannan ta samu jikinta ya tsaya dai dai. Anan ta fara kiran sunan samir amma bai amsa ba kuma wuta bata dauke ba. A hankali ta nufi gadon tana tafiya daya bayan daya sai kiransa take amma tsit.

                                                            PAGE 26

           Tana cikin tafiyar ne sai taji fadowar wani abu rikicaa. Anan meera tayi ihu ta kara manne jikinta a gina saboda tsoron daya dabaibayeta. Tana dubawa sai taga ashe berayene suka kayar da wani plate. Daga nan sai ta dan nisa cikin natsuwa ta nufi gadon. Tana zuwa dab da gadon sai gabanta ya fadi ji kake duuum. Anan ta fara jin tsoro domin har yanzu mutumin a lullube yake cikin bargo. Hannuta tasa a hankali ta jaye bargon. Tana dubawa sai taga ba kowa a ciki. Anan ta samu cikakkiyar natsuwa amma kuma har yanzu tsoro takeji domin ita tasan mutum ne ta gani a cikin bargon to ya za ace tana budewa bataga kowa ba. Hankalinta ne ya bata cewa akwai wani abu a wannan daki to amma kuma menene? Kila ma wannan abun shine yasa samir ya gudu yabar dakin. Daukar wayarta tayi dake saman gadon, cikin sauri ta nufi tagar dakin da nufin ta bude ta fita. To kafin takai ga tagar ne sai taji ana kwankwasa tagar da karfi kamar akwai wani a waje. Hankalinta ne ya dugunzuma sosai domin batasan yadda zatayi ba. Tanaso ta bude amma batasan abunda zata gani ba. Anan ta fara ja da baya cikin tsoro fuskarta kuwa kamar tayi kuka.
       Tana cikin ja da baya ne taci karo da wani abu. Ihu tayi mai karfi kafin ta juya da sauri taga ko menene amma wayam ba kome. Zaunawa tayi saman gadon ta rasa abunda ke mata dadi. Can kuma sai taga an bar kwankwasar tagar. Mikewa tayi tsaye da nufin bude tagar domin ta fice waje. To kafin takai ga tagar ne sai taji an jawota da karfi an azata saman gado. Anan aka bankareta ita kuwa sai ihu take. Wutar dakin ce ta fara billin billin wato ta kawo ta dauke. Anan ta fara kokarin mikewa amma datayi yunkuri sai taji kamar ana mayar da ita. Haka kuma hannayenta da kafufuwanta ji take kamar an dauresu amma kuma bata ganin abunda aka dauresu dashi. Wani abune mai duhu taga ya nufota wanda ta rasa ko menene. Ihu ta cigaba dayi amma duk a banza domin abun sai karasota yake gashi kuwa an daureta bata iya tashi balanatana ta gudu. Abun na zuwa dab da ita sai ta fadi sumamma saboda tsoron daya cika zuciyarta. Haka meerat ta kasance cikin halin suma sai da aka dau lokaci kafin ta dawo cikin hayyacinta. Ji take duk jikinta ya mutu kamar wadda aka zane. Anan taga wutar dakin ta dawo dai dai kuma jikinta ya saki batajin an daureta.

                                                          PAGE 27 

      Mikewa tayi tana tafiya dai dai kamar kafafuwanta na ciyo. Anan ta kalli kofar dakin. Da taso tabi ta ciki amma kuma batason iyayen samir su ganta saboda haka sai ta nufi tagar da nufin fita. Tana karasowa sai taga tagar ta bude kanta da kanta. Anan meera ta dan ja da baya a cikin tsoron ganin wannan abu. Duba tagar tayi amma a mamakinta igiyar data biyo ta cikin dakin ta bace ba kome. Anan meera ta rasa yadda za ayi ta fita. Wani iska ne ya dan fara kadawa har takai fitillun dakin sun fara mutuwa. Cikin rashin tsammani sai taji an turota da karfi ta tagar. Anan meera ta fara ihu domin tasan cewa data kawo kasa to sai dai wata ba ita ba. Cikin sa a sai ta fado saman wata katifa da aka shanya. Meera na mikewa sai ta nufi motarta da sauri. To kafin takai ga motar ne sai ta hango wata yarinya nesa da ita. Saboda duhu bata iya ganin fuskar yarinyar balantana tasan ko wacece haka ma kayanta bata iya ganinsu iyaka dai tasan yarinya ce. Cikin sauri meera ta karasa motarta. Ba yadda batayi ba amma motar taki budewa ita kuwa yarinyar sai ta nufota. Anan hankalin meera ya dugunzuma wurin sauri makullin harda faduwa yayi. Tana dauka ta turasa da karfi anan taga motar ta bude. Da karfi ta shiga taja ganbun ta rufe. Anan ta fara tayar da motar amma itama taki tashi. Ita kuwa yarinyar sai karasowa take. Kadan ya rage yarinyar ta karaso sai motar ta tashi. Anan tayi wani ribas sannan taja motar da karfi ta tafiyarta. Meera sai tuki take hankalinta a tashe saboda wadannan abubuwa data gani. Dubawa tayi ta madubi a mamakinta sai taga wannan yarinyar ce ke biye da ita har yanxu. Anan meera ta kara giya amma a duk lokacin data dubi madubin motar sai taga yarinyar na biye da ita har yanxu.
                                                  ***************
             Shi kuwa samir yana ganin wadannan innuwowi na binsa sai ya fizgi mashin a guje. A haka yayita bi lungu lungu sako sako amma basu daina binsa ba. To yana cikin gudun ne sai ya hango wata mota a gabansa tana gudu a tsiyace kai da gani kasan ba lafiya ba. Da sauri yasa kafarsa ga burki domin rage gudun mashi din amma yaki raguwa maimakon haka mashin din sai kara gudu yake. Anan yasa hannunsa da nufin yayi kwana amma duk a banza mashin din shike controlling din kansa. Anan samir ya fara ihu ganin mutuwa a fili domin yasan idan ya hadu da wannan motar tofa karyarsa ta kare. Kicibis anan mashin din samir ya bugi motar. Jifa akayi da samir a can gefen titi hakama itama motar a can gefe tayi wrong-park. 

                                                    PAGE 28

         Meera ce a cikin motar. Da  sauri ta fito ta nufi wurin samir ba tare da sanin shine ba. Tana tallabosa sai ta fashe da kuka ganin cewa samir dinta ne ta buge. Komawa tayi cikin motar ta dauko ruwan gora. Anan ta dawo wurinsa sai yayyafa masa take amma yaki tashi. Kankanesa tayi tana ihu ko wani zai kawo dauki amma tsit saboda dare ne. Idan ta duba gefen titi bata ganin kome sai daji mai duhu. Anan ta fara jansa da nufin kaisa cikin motar. Tana cikin jansa ne sai taji ya fara tari. Sakinsa tayi tazo gab da fuskarsa tana girgiza shi. A hankali ya fara bude idanuwansa har saida ya farka. Mikewa yayi da sauri yana kallon meera.
       " Meera! Ya akayi kikazo nan?" Ya tambaya.
       " Kada ka damu abun begena yanzu kaxo muje gida kawai domin ka jigata sosai." Meerat ta bashi amsa. Anan samir ya kalli mashin dinsa wanda ya tararratse sai kuma motarta a can gefe. Hankalinsa ne ya basa cewa accident sukayi. Daga nan kuma sai ya tuno innuwowin dake binsa 
        " Shin bakiga wasu....." Haka samir ya fada yana kallon sama.
        " Wasu me? Dear kayi magana mana." Inji meerat. Anan yayi shiru baice kome ba. " Kazo mu shiga mota domin tare nike da labnat." Inj meerat.
         " Labnat, wace labnat kuma?" Anan samir ya fara tunani domin koda ya fito gida tayi bacci. " Hala ina kika hadu da ita?" Samir ya tambaya.
         " A saman titi mana. Yanxu haka tana cikin mota nayi mamaki bata fito ba. Ke labnat, fito ga yayanki samir." Meera ce ta kwala mata kira amma tsit basuga kowa ba. To anan hankalin samir ya tashi domin yasan ba labnat ce ta dauko ba. Daga nan sai ya fara tunanin labnat din daya gani a dinning table lokacin da cinyar kaza ta wahalar dashi. Bako shakka akwai wani abu dangane da wannan al amari. To abun tambaya anan shine waye ke zo musu da siffar labnat domin yanxu ya tabbatar da cewa ba ita bace.
           " Ba labnat ce kika dauka ba." Inji samir.
           " Wannan magana da kake fa. Tama fadamin cewa wai kaje gidansu samirat koba haka bane?" Inji meerat. Anan samir yayi shiru mamaki ya hanasa magana. To amma ya akayi tasan yaje gidansu samirat? 
           " Meerat inaso ki yarda dani cewa wannan ba labnat ce kika dauka ba domin koda na baro gida tayi bacci." Cewar samir. Meerat najin haka sai hankalinta ya tashi. 

                                                      PAGE 29
   
           Anan ta tuno yarinyar data gani kusa ga motarta a lokacin data fito dakin samir dakyar. Da kuma lokacin da take binta a bayan mota. To tana cikin gudun ne sai ta hango wata yarinya a tsakiyar titi. To a lokacin wannan yarinyar dake binta ta daina. Tana haska mata fitilar mota sai taga ashe labnat ce. Daganan saita fito ta kawato cikin motarta. Anan ta tayar da motar ta cigaba da tafiya. 
      Anan tunanin meerat ya katse. To kenan wannan yarinyar dake binta itace ta mata shigar labnat har ta daukota cikin rashin sani. Samir na kallo sai yaga meera na tangadi kamar zata fadi. Anan yayi sauri ya rungumeta don kada ta fadi. Ajiyeta yayi a gefe yana girgiza ta. A wannan lokaci sai nishi take dakyar kamar shedarta nasan daukewa. To anan ne hankalin samir ya tashi. Gashi batada glass amma kuma bayajin amai duk da cewa kallon fuskarta yake. Wannan rashin son da yake mata sai yaji an lullube shi da tausayinta da kuma kaunarta. Rungumeta yayi yana girgizata amma ko motsi batayi iyaka yaga ta sandare. Anan ne ya fashe da kuka yana tunanin walakancin daya yimata tun suna yara. Nadama da kuma hankalta sun bayyana a idanun samir irin yadda yake kukan kai kace mahaifiyarsa ce ta cika. Daganan sai ya saketa. Tashi yayi da nufin duba mashin dinsa idan zai iya zuwa gida domin ya bayyana abunda ya faru. Baiyi wani nisa da tafiya ba sai yaji tari a bayansa. Yana juyowa sai yaga ashe itace ke tarin. A guje ya sheko wurinta ya kankaneta sai murna yake ganin cewa bata mutu ba. Tana bude idanu sai ta yi masa murmushi irin yadda ta saba. 
      Anan mamaki ya cika meerat ganin cewa samir ya rungumeta yana kallon fuskarta ba tare da yayi amai duk da cewa batada glass, shin wai yau wace irin rana ce. Hawaye duk sun cika idanunsa saboda wannan suma da tayi a tunaninsa ta mutu. Shin wai dama samir na sona? Wannan shine tunanin farko daya fara shiga zuciyarta. To amma idan baya sona me yakema kuka saboda na suma kuma me yasa ya rungumeni cikin tausayawa? Anan meera ta kura masa idanu tana tunanin rayuwarsu ta baya a lokacin da suna yara. Bako shakka wannan abun mamaki ne a gareta akan wannan sauyi na samir domin duk rayuwarsa sau daya ya taba rungumeta kuma sau daya ya taba kallonata kallo na tausayi sai wanna shine na biyu,  kuma wadannan abubuwa sun farune a lokacin da suke yara.

                                                     PAGE 30

            
         Wata rana a lokacin da samir da meera suna yara, kamar yadda ta saba takan bi bayansa tana masa magana a duk inda ta gansa. To kamar kullum tana cikin binsa ne sai magana take masa amma yaki kulata. Cikin sauri tasha gabansa taki bari ya wuce, idan yabi nan ta tare in yabi can ta tare. Kawai sai ya hasala. Hannu ya dunkule sannan ya kai mata wani irin duka ga ciki iyakar karfinsa. A nan ta fadi sumammiyar ko motsi batayi. Gashi kuwa ba kowa a wurin, a nan hankalin samir ya tashi daga nan sai ya rungumeta yana dana sanin wannan duka daya mata domin a wannan lokaci ya aza ta mutu. Sai hawaye ke kwarara a idanunsa girgiza ta kawai yake amma taki tashi. Anan ya saketa ya kama hanyar gida domin ya fadawa su umma abunda ya faru. To kafin yayi nisa ne sai yaji ana tari. Yana juyowa sai yaga ashe itace. To anan ya sheko da gudu wurinta yana murna da cewa bata mutu ba. Cikin jin dadi ya rungumeta sai murmushi yake. To bayan meera ta bude idanu sai ta fahimci yadda yake kallonta kallo na tausayawa. Tayar da ita yayi ya kakkabe kurar dake jikinta kai hadda rakata gida. To tun daga wannan ranar koda tazo wurinsa baya dukanta duk da cewa baya sonta. 
        Anan tunanin meerat ya katse daga nan sai ta mike tsaye." Inaga yanxu sai mu wuce gida domin naga dare yayi sosai." Inji samir. Anan suka nufi motar. Sai da suka duba tsaf amma basuga labnat din ba. Samir ne ya shiga sit din driver ya zauna sai meera ta zauna sit na kusa dashi. Anan ya tayar da motar. Gyara tsayuwar motar yayi daga nan yaci hanya. 
      " To mashin dinka fa?" Meera ta tambaya.
      " Kada ki damu gobe zan dauki abuna." Samir ya bata amsa.
      " Yauwa dama tace na tunatar dakai game da kashedin data yi maka." Inji meerat.
      " Hala wacece?" Samir ya tambaya.
      " Labnat mana." Meera ta bashi amsa.
      " Ta fada miki ko wane kashedi take min?" Samir ya tambaya.
      " A a bata fada ba, iyaka dai tace na fadama game da kashedin data yima. Amma ni abunda na fahimta shine kamar akwai wani abu da takeso ka bari." Inji meera.
        " To kamar meye kenan?" Samir ya kara tambaya. 
        " A a ban sani ba, wannan tsakaninku ne kai da ita." Inji meera.

                                                      PAGE 31

            " Kada ki manta na fada miki wadda kika dauka ba labnat bace, saboda haka duk wannan abu da take fadi ban san ma anarsu ba."Inji samir.
            " To amma idan ba labnat bace to wacece ta fitomin da siffarta?" Meera ta tambaya.
            " Wannan tambaya da kikayi ita yakamata mu zurafafa bincike har sai mun gano amsarta domin nima takan fito mun kuma tayi min kashedi sai dai ban san abunda take nufi ba." Inji samir. " Kuma ya kamata ace yanzu hankalinki ya baki cewa ba labnat bace domin idan itace to meyasa a lokacin da kika bugeni da mota bata fito ta agaza ba. Kuma a lokacin da kika kirata ai bata fito ba. Kuma tunda a cikin mota kika barta ai yakamata yanxu mu ganta to ina take?" Inji samir.  
          " Lalle wannan magana taka akwai kamshin gaskiya a ciki. Nima nayi wannan tunani iyaka dai saboda rashin tabbas nayi shiru." Inji meera. Suna cikin tafiya kawai sai sukaga motar na rage gudu. A hankali taci gaba da rage gudu har takai ta tsaya. Anan suka fara mamaki domin cike take dam da mai. Samir fita yayi ya duba amma ba abunda ya gani. Anan ya dawo ya tayar da motar amma taki tashi.  Haka yaci gaba da kokartawa sai da kyar ya samu ta tashi. Ai kuwa tana tashi tun bai taka ba ta fara tafiya. Anan ta hizgesu ta banka a guje. Ba yadda samir bai yiba domin ya rage gudu amma abu ya faskara. Suna cikin gudun ne motar ta nufi wani gini. Da karfi tasha ginin kafin ta tsaya. Su kuwa su samir fitowa sukayi sai tari suke. Anan suka dubi titin amma tsit ba kowa. Kida suka fara ji yana tashi a hankali. Anan suka fara kalle kalle suna son ganin inda ake kidan. Tafiya suka farayi suna waige waige har suka kawo ga wata kofa. Bude kofar sukayi suka fada ciki. Wani dan kwaroro ne mai zurfi. 
         Daga shigarsu sai sukaji kidan sai tashi yake daga ciki. Tafiya suka farayi har saida suka kure kwaroron daga nan sai suka nufi gefen hagu. Basu wani dadewa suna tafiya ba sai suka cimma wani katon fili mutane an hade maza da mata sai rawa ake ana shakatawa. Ga kwalaben giya iri iri su kuwa yan mata ba a magana irin muguwar shigar da sukayi ta bayyana abubuwa ga fili. Anan su samir suka fara mamakin wannan night club domin basu taba jin labarinsa ba.
       " Inaga mu tsaya mu huta anan idan yaso daga baya sai mu nufi gida." Inji samir. Ba tare da gardama ba meerat ta aminta. Anan suka samu kujeru suka zauna. A tsakiya kujerun table ne aka ajiye domin masu cin abinci.

                                                  
                                                    ME ZAI FARU?

                                  ZAMU CIGABA.....
  
                                                    PAGE 32


       Basu dade da zama ba sai ga wani katon mutum ya nufo wurinsu. " Yallabai me za a kawo, beer kukeso ko kuwa roksi, kuma akwai burkutu harma dasha ka tsage."Inji mutumin. Anan samir ya kalleshi.
      " Ai mu bama shan giya, amma idan kunada maltina to ka kawo kwalba biyu."Inji samir.
      " To an gama ranka shi dade. Anan mutumin ya tafiyarsa. Bai wani dadewa ba sai gashi ya dawo da maltina din. Shi kuwa samir kudi ya dauko ya mika masa daga nan sai mutumin ya tafi. Fira suka farayi mai dadi suna kallon yan rawa sai cashewa suke. To suna cikin firar ne sai sukaga amiru zaki ya fito daga wani lungu rike da samirat jikinta sai girgiza yake kai da gani kasan batada lafiya. A haka ya jawota har sai da yakaita wannan kwaroro dasu samir suka biyo. Ajiyeta yayi da karfi cikin fushi. Anan su samir suka bishi. Labewa sukayi suna kallonsa domin ganin abunda ke faruwa.
       " Gaskiya na fara gajiya da wannan ciyo naki domin nima yana tabani. A duk lokacin da nake tare dake bana samun kwanciyar hankali saboda abubuwa da nake gani na ban tsoro. Hakama gidanku. Bana iya shiga gidanku saboda bala in dake ciki, ni a nan zan barki kuma inaga ya kamata mu rabu wato ki nemi wani na nemi wata." Amiru zaki tafiyarsa yayi ya kyaleta cikin ciyo. Ita kuwa sai kokari take ta kirasa amma bata iya magana. Yana fita sai sukaji kukan motarsa da alama shine ya tafiyarsa. A guje suka sheko wurin samirat suga meke faruwa. Samir tallabota yayi ya aza saman cinyarsa ita kuwa sai nishi take dakyar. Anan samir ya fara yi mata addu oi yana tofawa ita kuwa meera tayi tsaye tana kallon ikon ALLAH. 
         " inaga ya kamata mu kaita gida koya kika gani?" Inji samir.
         " A cikin motarwa? Ai tayi kadan ta shigar min mota indan ni ta mutu a nan." Haka meera ta fada sai hararar samirat take saboda haushi. 
          " Haba meera ya zakice haka. Kada fa ki manta yar uwarki ce musulma kuma duk wanda ya taimaki wani ALLAH zai taimakeshi." Inji samir.
          " To bari kaji wannan tsinanniyar la ananniyar wadda batasan kome ba sai jan aji, walakanta mutane da kuma bin zuciya. Har ita kake cewa na taimaka. To ni tunda nake bata taba taimakona ba koda na bidi taimakonta." Meerat.

                                                        PAGE 33

    "Haba meerat nifa ban sanki da irin wadannan kalamai ba. Kuma duk abunda kike fadi ai bakida tabbacinsa iyaka dai kina fadine." Inji samir.
    " To bari na fadama, ni nan da kake gani na fika sanin halin samirat domin kai sonta kawai kake amma bakasan ko waye itaba. Yanxu kai a tunaninka ka taba ganin mace budurwa mai tsoron ALLAH da kuma ilimin addini tazo wannan wuri? Kaima kasan duk macen dake zuwa night club to kingi ce wadda ko aurenta kayi to second hand ce ka aura." 
      " To yanxu ki fadamin walakancin data taba yi miki?" Samir ya tambaya.
      " Ai wannan yafi kome sauki." Inji meera. Daga nan sai ta shiga bashi labari kamar haka:
          Wata rana a cikin dare matsananciyar rashin lafiya ta kama kanwar meera kuma a lokacin abba da umma basa gida. Kusan karfe daya na dare ne meera ta sata cikin mota. Anan ta tuko motar da nufin ta kawota asibiti. To tana cikin tafiya sai ta taka kusa a nan tayar tayi faci akan dole ta tsaya. Anan meera ta fito tana bidar wani mai mota don ya taimakesu ya kaisu asibiti. Sai da tayi kusan minti talatin amma ba kowa saboda tsakiyar dare ne gashi kuwa tayi nisa da gida balantana ta koma. Har ta yanke tsammani sai ta hango wata mota saman titi. Anan meera ta tayi tsaye tsakiyar titi tana taga hannu domin motar ta tsaya. Motar na zuwa dab da ita sai ta tsaya. Samirat ce ta fito a ciki taci ado over kai kace sarauniya. Meera tayi mamakin ganinta a cikin wannan dare. Daga nan sai meerat tayi murmushi ganin cewa tasan samirat domin course dinsu daya a jami a. 
          " Yauwa samirat don ALLAH ki taimaka ki ajiyemu a asibiti kanwata ce batada lafiya kuma gashi mota ta tayi faci." Inji meerat.
          " Mtssss." Samirat tayi tsuki. " Ni nama aza club zaki mu wuce tare dama akan wannan abun kika tsayar dani? To ni kinga tafiyata marar hankali kawai." Anan ta nufi motarta. Ita kuwa meerat da gudu tasha gabanta tana rokonta amma taki. A haka samirat ta shiga motarta ta wuce night club tabar meera cikin bakin ciki. Meera dawowa tayi cikin motarta ta tarar kanwarta sai nishi take dakyar. Haka ta cigaba da zama har uku na dare ko zata gamu da wani mai mota amma ba wanda ta gani.Misalin karfe uku da rabi ne yarinyar ta cika. Meerat tayi kuka mai tsanani saboda mutuwar wannan yarinyar. Duk da tasan da cewa lokacinta ne yayi amma da ace samirat tayi yunkurin yin taimako to watakila za a iya ceto rayuwar yarinyar. To tun daga wannan rana meerat ta tsani samirat sosai har takai tanaji kamar ta murde mata wuya kowa ya huta. 

                                                        PAGE 34
 
       " To kaji abunda ya faru." Meerat ta fada bayan ta kammala labarin. Anan samir yayi shiru domin yasha jin ana fada masa cewa samirat na zuwa night club. Kuma batada kirki ko kadan domin duk namijin dayace yana sonta to bata fitowa karara ta fada masa yayi hakuri har sai ta ci masa mutunci gaban mutane sannan tayi masa korar kare. Sai kuma mafi yawan dalibai dake zaginta domin idan ana jarabawa bata taimako koda mutum ya tambayeta. " Ya naga kayi shiru?" Meerat ta tambaya.
       " Ba kome." Samir ya bata amsa. Daga nan sai ya kara rike samirat domin jikinta sai girgiza yake jini na fitowa a hancinta. Idanunta sun kafe wuri daya kamar akwai abunda take gani. Samir tashi tsaye yayi ya fuskanci meerat.
        " Nasan da cewa samirat bata kyauta miki ba. Amma kada ki manta idan mutum ya bika da sharri to kai ka bisa da alheri domin bakasan ya karshenka zai kasance ba. Zanso ace ki bani dama ki taimakeni sau daya idan yaso daga wannan taimako to kada ki kara taimakona. Wannan taimako shine ki yarda samirat ta shiga motarki muna ajiyeta gidansu sai mu tafiyarmu." Haka samir ya fada yana duban meera kuma a rike yake da kafadunta. Anan meera ta kallesa kallo na hakika daga nan ta rasa yadda zatayi domin ko kadan batason ta taimaki samirat. Duk da cewa son da takewa samir bana wasa bane har takai ba abunda zai nema a wurinta ya rasa. 
          " Koda zan taimaketa sai dai nayi don kai ba wai don nasoba ko kuwa don inada niya. Saboda haka ba matsala mu tafi." Inji meerat. Anan samir ya tallabota suka kama hanyar fita. Suna kaiwa inda motar sai meera ta bude masa ganbun baya. Anan ya ajiyeta ya kulle daga nan sai ya shiga ya tayar da motar ita kuwa meera sai ta zauna sit na kusa dashi. Tafiya sukeyi amma ba wanda yayi magana har suka iso gidan su samirat. Anan samir ya fito da ita. Da har zai shiga gidan sai ya tuno bala in daya hadu dashi a ciki. Tsaye yayi ya rasa yadda zai yi domin yanajin tsoro kada ya shiga ya kara haduwa da irin wannan masifar. 
         " Ya naga kayi tsaye kaje ka ajiyeta mu wuce mana." Inji meerat bayan ta fito daga cikin motar. Samir ajiyeta yayi a gefe sannan yazo gab da meerat. Rike hannunta yayi kafin ya fara magana.
         " Wannan shine taimako na karshe da zakiyimin."
         " Kada ka manta bamuyi haka dakai ba.Taimakon da zan iya yi kenan. Batun na shigar da ita cikin gida bai ma taso ba." Inji meerat.

                                                         PAGE 35

          " Haba meerat nifa zaki yiwa ba ita ba." Inji samir.
          " To kai in banda abunka ya za ayi na dauki wannan katanya ga tsawo ga kiba kanaso na mutu ne?"  Inji meerat.
          " Ai bata fiki kiba ba. Kinga kuwa zaki iya daukarta." Samir ya bata amsa.
          " Kai dai wallahi ka fiye naci da yawa." Inji meerat. Daganan sai ta taimakawa samirat har ta mike tsaye. Anan ta riketa ta shigar da ita cikin gidan. To bayan ta fito ne sai samir ya ganta a hargitse. Da sauri samir ya jawota yana tambayarta lafiya. 
         " Gaskiya ba lafiya ba. Wannan gidan akwai matsala domin daga shigata sai jikina ya fara karkarwa kamar yadda na samirat keyi. Haka kuma inajin muryar yara kamar suna wasa duk da nasan da cewa batada kanne. To abun mamaki wadanne irin yara ne ace har yanxu basuy bacci ba." Anan meerat ta duba agogonta. " Yanxu karfe biyu da rabi na dare fa." Inji meerat. 
           Samir shiru yayi yana tunani domin yafi kowa sanin cewa wannan gida ba lafiya ba wannan shine dalilin da yasa yaki yarda ya shiga. Daga nan sai ya fara tunanin maganar amiru zaki:
      (  Gaskiya na fara gajiya da wannan ciyo naki domin nima yana tabani. A duk lokacin da nake tare dake bana samun kwanciyar hankali saboda abubuwa da nake gani na ban tsoro. Hakama gidanku. Bana iya shiga gidanku saboda bala in dake ciki, ni a nan zan barki kuma inaga ya kamata mu rabu wato ki nemi wani na nemi wata. )
          To kenan indai hakane samirat tasan ko meye a cikin gidan kuma dole tasan sanadin wannan ciyo nata wanda ke taba duk wanda ya kusanceta. Bako shakka amiru zaki ya fahimci cewa akwai wasu abubuwa akan samirat wannan shine dalilin da yasa ya gujeta. To ai kuwa indai hakane nima zan gujeta. 
     Anan tunanin samir ya katse. " Kuma fa kaji wani abu. Ina shiga na tarar da iyayenta a zaune cikin falo sai kallon TV suke duk da cewa a kashe take." Inji meerat. A nan samir ya kara komawa cikin tunanin domin samirat ta taba fada masa cewa iyayenta sunyi tafiya kuma ba yanxu zasu dawo ba. To in dai hakane su waye meerat ta gani a cikin gidan? " Lafiyanka kuwa?" Meerat ta girgiza shi.
      Daga nan sai tunaninsa ya katse. " E lafiya lau ba matsala mu tafi gida." Shiga sukayi cikin motar samir na tunawa har suka iso gidansu.
  
                                                          PAGE 36

        " Amma tunda dare yayi me zai hana ki tsaya a nan sai gobe ki tafi gida." Inji samir. Da har meerat zata amince sai ta tuno bala in data hadu dashi a cikin dakin a lokacin da taxo ganinsa baya nan.
        " Ai kada ka damu ba matsala zan iya tafiya. Mai gadin gidanmu bayada matsala domin da kudi na sayeshi." Meerat ta bashi amsa. Daga nan sai sukayi sallama meerat ta buga motarta ta nufi gida. Shi kuwa samir igiyar daya jefo ya lakane. Anan ya hau yana tafiya har ya isa sama inda dakinsa yake. Tsalle yayi ya shigo dakin. Daganan sai yayi kwanciyarsa, wani irin bacci mai dadi ya saceshi. 
         Tunda sanyin safiya samir ya farka. Yana hamma ya tashi daga nan ya nufi toilet. Bayan ya kimtsa ne sai ya fito ya shiga falo. Daga zaunawarsa sai ya kunna TV ya fara kallo. Ita kuwa umma sai hidimar hada break fast take. Da misalin karfe takwas da rabi umma ta buga kararrawa na cewa azo a fara break fast. Daga nan sai samir ya tashi ya nufi dinning table. Bayan kowa ya hallara sai aka fara cin abincin tare. Suna cikin cin abincin ne sai sukaji sallama. Samir ne ya fara dubawa a nan ya hango meera. Bayan ta gaidasu ne sai umma ta mata umarni data zauna. Anan aka hada mata kayan tea kai da gani kasan an santa sosai a gidan domin su labnat sai fira suke da ita. To bayan sun gama karyawa ne sai samir ya dauko jakarsa ta makaranta ita kuwa meera sai tabi bayansa. To kafin su fita ne sai umma ta kwalawa samir kira. Anan yazo wurinta
yaji me zatace.
      " Wai samir wannan yarinyar ba itace wadda baka...." To kafin umma ta iyar sai samir ya katseta.
       " -Yanxu fa wannan abun ya wuce ke umma ni da ita mun koma abokai." Anan umma ta kalleshi cikin mamaki domin tasan da cewa a duniyar nan ba wadda ya tsana irin meera amma yau gashi har kawo masa ziyara take. 
       " To itafa samirat?" Umma ta tambaya. Anan samir yayi shiru baice kome ba. 
      " Umma ina sauri munada lecture yanzu dai sai na dawo." Anan ya fita yabar umma cikin mamaki.
      " Gashi ko glass din bata saba amma kuma bayajin amai." Haka umma ta fada cikin zuciyarta kafin ta cigaba da ayukanta.
     

                                                      PAGE 37

          Kada kaki makiyinka domin yakan iya zamo masoyinka, kuma duk mai hakuri to yana tare da wadata. Bako shakka wannan magana haka take domin sai gashi a yau wanda yafi kowa kin meera yau shine yafi kowa sonta. Kuma hakurin da tayi na jure walakancin da samir yayi mata sai gashi ya zamo mata wadata domin abun ya zama kamar ba ayiba. 
     Wato a lokacin da suka shiga makaranta sai abun ya zamo gwanin ban shaa wa kuma abun mamaki domin daliban makarantar sun san da cewa samir baya kaunar meerat ko kadan amma sai gashi yau sun fito a mota tare sai murmushi suke suna dariya irin na masoya. Duk wanda ya gansu tare sai ya tsaya ya sosa idanunsa ya gani mafarkine yake ko kaka. Kafin kaceme labari ya watsu akan cewa samir da meerat sun shirya. Wasu shedanu kuwa harda posting sukayi a social network kamar haka:
     ( THE RECONCILLATION OF SAMIR AND MEERAT )
         Daga nan sai suka sa photonsu a gefe a lokacin da suke tafiya suna dariya. Shi kuwa amiru zaki dayaji labarin kuma harda ganin photonsu ga net sai gabansa ya fadi domin fa yasan da cewa karyarsa ta kare domin meerat bazata amshi soyayyarsa ba. To dama yana cikin motar sa ne aka aiko da labarin a chat. Yana dubawa sai ya karanta. Dakyar ya samu ya tuko kansa makaranta saboda tsananin haushi. Ai kuwa yana fitowa daga motarsa sai ga samirat itama ta faka tata a can nesa dashi. To abunda yaba mutane mamaki shine a cikinsu ba wanda ya kula kowa iyaka kowa harkar gabansa yake. To anan mutane suka fara tunanin cewa an samu matsala tsakaninsu. Kafin kaceme an musu hotuna a lokacin da kowanensu yabi hanyarsa. Daga nan aka baza ga net. Daga can  sama sai akayi rubutu kamar haka:
       ( LOVE BREAKAGE OF AMIR AND SAMIRAT )
          To bayan sun shiga aji ne sai abun ya kara canzawa domin samir da meerat a kujera daya suka zauna. Su kuwa su amir da samirat kowanensu shi kadai ya zauna. To wannan shi ya tabbatar wa mutane cewa an bata tsakanin amir da samirat kuma an shirya tsakanin samir da meerat. Kada kaso masoyinka domin yakan iya zamo makiyinka. Bako shakka wannan magana haka take. Dubi yadda samirat da amir suka bata a lokaci daya duk da tsananin soyayyar dake tsakaninsu. Lecture akeyi amma samirat sai kallon samir take tana murmushi. Irin murmushin nan da mace keyi idan tanason namiji. Shi kuwa a wannna lokaci ko kulata bai yiba domin fuskar meerat ce a gabansa. Haka shima amir sai kallon meerat yake amma ko kadan bata kula shiba domin samir ne a gabanta ba shiba.

                                                             PAGE 38

        Bayan an gama lecture ne sai kowa ya fita sha anin gabansa. Samir da meerat ne a can gefe saman wata babbar kujera mai daukar mutane da yawa. Ita wannan kujera an ajiyeta ne domin dalibai idan sunada bukatar hutu. Ba abunda su samir keyi sai fira cikin annashuwa. Suna cikin firar ne sai ga wasu yan mata su biyu sun nufosu.
     " kyakkyawa dan mamarsa, matsalarka daya. Baka wankan shadda kullum cikin kananan kaya kake." Haka dayar ta fadi tana murmushi.
      " To! Kenan abun nan da ake cewa gaskiyane." Haka dayar ta fada itama. Daga nan sai suka taba hannu suka tafi suna kus kus.
       " Wai da gaske kike kin ga iyayen samirat a lokacin da kika shigar da ita gidan?" Samir ya tambayeta.
       " Kwarai kuwa na gani. Kuma abunda ya bani mamaki dasu harna fito ko kallona basu yiba domin daga shigata na gaidasu amma basu amsa ba iyaka dai naga sai kallon talabijin suke duk da cewa a kashe take. Kuma babu wani alamu na cewa suna motsi ni a ganina dakyar idan suna da rai." Inji meerat.
       " Yauwa ai ga samirat can ta nufo nan bari mu tambayeta." Inji samir. Samirat na zuwa dab dasu sai ta tsaya.
        " Sannunku dai." Haka ta fada amma meerat sai harararta take. 
        " Yauwa sannunki samirat. Dama kuwa inaso na tambayeki wai iyayenki sun dawo daga tafiyar da sukayi kuwa?" Samir ya tambaya.
        " A a gaskiya basu dawo ba har yanxu ai na fadama ni kadaice a cikin gidan yanxu. Amma lafiya kuwa?" Inji samirat. 
        " E lafiya lau ba kome." Samir ya bata amsa. Daga nan saita nufi wurin wasu kawayenta dake kiranta su kuwa su samir hada idanu sukayi cikin mamaki  domin sun san da cewa ba lafiya a wannan gida. 
                                                  **************
         Idan dare yayi mafi yawan mutane kan samu wuri su huta hakan yasa samir ya shige dakinsa ya kunna wayarsa sai latse latse yake. To yana cikin hakane sai yaga an fara jifar tagar dakinsa. Yana dubawa sai ya hango samirat na daga masa hannu. Anan ya dauko igiya ya daura daga nan sai ya mata umarni data hau. Hayewa tayi shi kuwa ya fara jawota har ta kawo ga tagar. Hannunta ya jawo sai ta diro cikin dakin. Anan samir ya kalleta ba kamar yadda ya saba ba domin a wannan lokaci fuskarsa dame take ba annuri. 


                                                                PAGE 39

        " Wai lafiyanka kuwa?" Samirat ta tambaya.
        " Gaskiya ba lafiya ba! Wai ke me ya kawoki wurina?" Samir ya tambaya.
        " Haba samir wannan wace irin tambaya ce, niface samirat ko ka manta ni." Injita.
        " Kiyi hakuri samirat amma gaskiya bazan iya cigaba da mu amala dake ba domin a duk lokacin da kika zo a dakina bana samun kwanciyar hankali saboda ina ganin abubuwa naban tsoro sai kuma mugayen mafarkai da nake yawan yi. 
Kuma kada ki manta wadannan abubuwa dana fadi sune sukasa tsohon saurayinki wato amiru zaki ya gujeki. Saboda haka nima inaso ki shafa min lafiya domin bazan iya jure wannan masifa ba." Inji samir. Juyawa yayi da nufin ya koma kan gadonsa kawai sai ta jawo hannunsa. Anan ta rungumeshi sai hawaye ke kwarara a idanunta.
        " Kayi hakuri samir nasan ban kyauta makaba domin ka nuna min soyayya amma na nunama akasinta. A lokacin da kowa ke guduna amma kai a lokacin kake sona. Kayimin rana amma ni nayima dare. Ina nadamar wadannan abubuwa dana aikata domin yanxu haka ina tsanar kaina. Kada kayi tsammanin cewa duk walakancin danake ma wai bana sonka. Ko kadan ba haka bane iyaka dai jan aj ne kuma nayi nadamar yinsa." Anan ta kara kankane samir sai hawaye ke zuba. To anan ne shima ya dan ji tausayinta daga nan sai ya fara lallashinta. Bayan ta daina kukan ne sai ta fara yi masa magana. " Inaso kazo muje gidanmu akwai abunda zan fadama."
       " Gaskiya bazan iya zuwa gidanku ba amma ai ko menene zaki iya fadamin a nan." Inji samir.
      " Ai kara muje can domin inaso ka tayani bacci, kuma ka sani abunda zan fadama mai muhimmanci ne." Inji samirat. Anan samir ya nuna bazai bita ba. Daga nan sai ya fada mata irin masifar daya hadu da ita a lokacin dayaje ganinta. Yana gama bata labarin sai sukaji ana jifar tagar. Yana dubawa sai yaga ashe meerat ce. Anan yayi mata umarni data hau igiyar zai jawota amma taki. Ba yadda bai yiba amma taki shigowa dakin. Daganan sai ya hau igiyar ya sauko wurinta.
       " Kizo mu shiga daki mana ya kinyi tsaye sai kace bakuwa." Inji samir.
       " Kayi hakuri amma bazan iya shiga dakinka ba." Injita.
       " To me yasa?" Samir ya tambayeta. Anan ta bashi labarin irin masifar da ta gani a cikin dakin a lokacin data kawo masa ziyara.

                                                       PAGE 40

         " To yayi dan jira bari na fito." Anan samir ya koma cikin dakin. Can sai ya fito tare da samirat. To bayan sun diro ne sai meerat ta fara harararta.
         " Wai hala meya kawo wannan tsinanniyar a dakinka?" Meerat ta tambaya. 
         " Kada ki damu zan baki amsa dama akwai...." To kafin ya iyar da maganar ne sai sukaji kukan mota a guje bayansu. Da sauri suka kauce da kadan an banke su. Wani burki aka taka sannan aka tsayar da motar. Wani hayaki ne ke fitowa daga cikin motar kai da gani kasan an mata tukin hauka. Ja suka farayi da baya domin basu san wanda zai fito a cikin motar ba. Ganbun motar na kusa ga driver sukaga an balle anyi jifa dashi can gefe. Sai wani gurnani ke fitowa daga cikin motar. Anan suka tsorata sosai domin sun san ba lafiya ba. Wani  wargajejen mutum ne ya fito daga cikin motar ga tsawo ga kiba. Idanunsa sunyi jawur kamar garwashi. Sai wani gurnani yake yana kallonsu. Sai da sukayi masa kallon tsaf sai suka gane cewa amiru zaki ne ya canza. Gaba daya jikinsa ya canza domin ya kara kiba sosai haka kuma tsawo. Akaihun hannayensa ( Finger nails. )ma sun kara tsawo da kauri. Sai wasu hakora nasa da suka koma kamar na zaki saboda tsawo. Gaba daya dai jikinsa ya canza ba kyan gani. Wani gurnani yayi tare da ihu daga nan sai ya nufosu a guje. Samir ne ya taresa da nufin tsayar dashi. Wani buga yayima samir sai da yayi waliliya sau bakwai a sama kafin ya fado saman mota rikicaa. Daga nan ya nufi wurin samirat wadda ke ja da baya a cikin tsoro. Da hannu daya ya shako wuyanta ya daga sama. Akaihunsa ya mimmike da nufin soka mata su a kahon zuci. To kafin ya iyar da nufinsa ne samir yayi wani tsalle ya maka masa wani uban naushi ji kake gib. Anan amir ya saki samirat daga nan ya fadi can gefe. 
        Wani gurnani yayi tare da ihu daga nan kuma sai ya mike tsaye. To anan ne samir ya fahimci cewa wannan ba amir din daya sani bane dole akwai wani abu daya shiga jikinsa domin kamar ba cikin hankalinsa yake ba. Maimakon yayo kan samir su ci gaba da fadan sai ya koma kan samirat yana kokarin kasheta. Shi kuwa samir a guje yabi bayansa ya taresa. Anan suka kacame da azabbaben fada. Kai da ganin fadan kasan cewa amir yafi karfin samir nesa ba kusa ba domin dagasa yake sama sai yayi waliliya dashi sannan ya bugashi saman titi. Kai da ganin karfin nasa kasan bana mutum bane dole akwai wani abu. Idan yayiwa samir wani kaye su meera basa ko tunanin ya tashi amma sai sukaga ya mike sun cigaba da fadan. Kasancewar cikin dare ne ba kowa a wurin balantana a kawo agaji. Suna cikin fadan ne amir yayiwa samir wani naushi. Saboda karfin naushin sai da iska ya dauki samir sannan ya makashi saman wata gina. Anan ya fado jina jina tamkar gawa. A guje meera ta nufi wurinsa sai girgizasa take domin ya tashi. Shi kuwa amir yana ganin haka sai ya nufi wurin samirat yana kokarin soka mata dogayen akaifunsa. Ita kuwa sai ja da baya take a tsorace.

                                                          PAGE 41

      Haka samirat taci gaba daja baya a tsorace shi kuwa amir nufota yayi yana taku da dai. Kai da ganin fuskarsa kasan akwai alamar tambaya. Samirat na cikin ja da baya ne ta fadi. Anan amir ya shako wuyanta kamar ya dauko kaza. Ita kuwa sai wulle wulle take kafafuwanta na lilo. Akaifunsa ya fara tura mata a xuciya. To kafin ya iyar da turasu ne samir ya tashi. A guje ya nufi wurinta daga nan yayi jifa da amir a can gefe. Da sauri ya tallabota ya kawota cikin motar meerat. Anan ya shiga da sauri itama meerat ta shiga. Da karfi yasa giya yaja motar a guje. Shi kuwa amir koda ya tashi sai yayi ihu da gurnani saboda jin haushin cewa samirat ta kubuta. Motar samirat dake kusa dashi ya tallabo ya makata saman wata gina sai da tayi kwatsa kwatsa saboda jin haushin da yayi. Anan yabi su samir a guje wadanda tuni sun yi masa nisa. Gudu yake da kafa tamkar doki saboda karfin dake jikinsa. Ai kuwa bai wani dadewa ba ya fara hango motar su samir anan ya kara kaimin gudunsa. Shi kuwa samir ashe ya hangoshi a cikin madubi a nan wata dabara ta fado masa. Rage gudun motar ya farayi sai da ya bari amir ya matsesu dab sannan ya taka burki. Ai kuwa motar na tsayawa sai ga amir yayi karo da ita da karfi anan ya fadi. To kafin ya samu damar mikewa ne amir yayi ribas ya kara bugesa. Daganan ya takashi da karfi duk a cikin ribas din. Daga nan kuma yayo gaba ya kara takasa. Haka yayita masa har sai da ya tabbatar baya motsi sannan ya buga motar yaci gaba da gudu.   
      A haka samir yaja motar bai tsaya ko ina ba sai gidansu samirat. Tallabota yayi ya shigo da ita a guje cikin gidan ita kuwa meerat na bayansa. Suna shigowa suka kulle ganbuna da tagogi. Anan ya shimfeda saman babbar kujera ta cikin falo. Daga nan ya shiga yi mata fifita har saida ta farfado. Daga nan sai ya samu wuri ya zauna kusa ga meerat. 
       " Ku yafeni, duk laifina ne, nice naja muku wannan abu." Haka samirat ta fada tana kuka. 
        " Laifinki kuma? Ta ina ya zama laifinki?" Samir ya tambaya. 
        " Ai bama wannan ba. Yanzu abunda ya kamata mu sani shine me yasa amir keson kasheta alhali masoyiyarsa ce?" Meerat ta tambaya.        
        " Ai ba amir bane, wannan da kuke gani ba amir bane." Inji samirat. Anan samir da meerat suka kalleta cikin mamaki wannan magana datayi.
        " To idan ba amir bane waye kenan?" Samir ya tambaya.
         " Sune, nasan da cewa sune suka ari jikin amir domin su dau fansar abunda na musu." Inji samirat.
          " Su waye kenan? Kuma me kika yi musu da har zasu dau fansa?" Samir ya tambaya. To anan ne samirat ta fara basu tarihin rayuwarta kamar haka:

                                                          PAGE 42

       Samirat ce a zaune cikin filin gate din gidansu, a saman wata kujera take sai ga wani dan table a gefen ta. Kayan marmari ne iri iri a sama sai diba take tana ci a cikin nishadi. Can sai ga abbanta ya fito daga cikin gidan. Daga isowa wurinya sai ya jawo wata kujera ya zauna a kusa da ita. Kai da ganin yanayin fuskarsa kasan akwai abunda ke tafi dashi a wurinta.
     " A gaskiya samirat banajin dadin yadda kike takurawa yaron nan samir domin inaga duk a cikin wadanda ke sonki babu kamar shi domin shi kadaine ya jure walakancin da kike masa. To inaso ki sani cewa idan har kika bari ya kubce miki to bazaki samu irinsa ba." Inji abba.
        " Haba abba ya kana wannan magana, kaima fa kasan mutum bazai iya auren wanda baya soba. A gaskiya ni bai yimun ba saboda haka ni bazan iya daukarsa a matsayin miji ba." Inji samirat.
        " To idan bai yimiki ba me yasa bazaki fito da wani ba wanda kikeso sai ayi auren kowa ya huta. Kadafa ki manta mafi yawan kawayenki duk sun tare a dakin miji. Ke kuma in banda yawace yawacen banza ba abunda kika iya. Kuma bakya tashi yawo sai a cikin dare na rasa ko uwar ina kike zuwa." Abba ya fada cikin fushi.
        " Haba dad banaso kayi fushi " Anan samirat ta matso daf dashi. " Duk abunda kaga inayi to akwai dalili." 
         " To sai ki fadamin meye dalilin wannan yawo naki na dare kuma ina ne kike zuwa?" Abba ya tambaya. Anan samirat tayi shiru ba tare da sanin amsar bashi ba. "  To daga yau banaso na kara ganinki da wannan yaron amiru, amiru zaki ake ce masa ko amiru kura ko ma dai amirun uban waye ina so ki rabu dashu rabuwa ta har abada domin nayi bincike akansa kuma na gano yaron banza ne domin in banda zuwa night club da bin matan banza ba abunda ya sani. Saboda haka in kunne yaji to jiki ya tsira idan na kara ganinki dashi to duk abunda ya biyo baya ke kika ja." Abba ya tashi yayi ya koma cikin gida yabar samirat a cikin tunani.
         Bai dade da shiga gidan ba saiga kawarta ta shigo wato hafsat. " Kawata ya na ganki cikin wannan tunani lafiya kuwa?" Hafsat ta tambaya.
       " Inafa lafiya." Anan samirat ta labarta mata kashedin da abba ya mata akan tarayyata da amir.
        " To ai ke samirat abunda abba ya fada gaskiyane domin nima inajin labarin amiru kuma nasan da cewa mutumin banza ne ba abunda ke a cikin zuciyarsa sai mata." Inji hafsat.

                                                            PAGE 43

       " To, wato kema kin goyi bayan na rabu da shi kenan?" Samirat ta tambaya.
       " Kwarai kuwa, kara ki rabu dashi ki koma ga samir domin shine mutumin kirki kuma shi ke miki so na tsakani da ALLAH." Inji hafsat.
        " Wato ke kawata ki sani cewa duk wannan hali na amir na dade da saninsa iyaka dai bazan iya rabuwa dashi ba domin irin rayuwar tana burgeni." Inji samirat.
         " Amma dai kinji haushi samirat, yanzu wannan kazamar rayuwar ta bariki itace ke burgeki?" Hafsat ta fada cikin mamaki.
        " Kada ki manta kowa fa da ra ayinsa, shi samir din ba wai sonsa ne banayi ba. Iyaka dai jan aji ne irin namu namu na manyan mata da kuma bin zuciya. A gaskiya bazan iya karbar soyayyarsa ba har sai na gama more rayuwata idan yaso daga baya sai na karba." Inji samirat. 
        " Au, wato sai kin tsufa kinyi expiry kin koma second hand sannan zaki karbi tukuicinsa?" Inji hafsat.
        " To wannan ai ba kome bane, bari na shiga gida na dauko makulli na rage miki hanya dama inaso na kai masa ziyara." Anan samirat ta mike tsaye.
        " Kada dai kicemin amirun zaki kaiwa ziyara?" Hafsat ta tambaya.
        " To inada wani in banda shi, kajita da wata magana." Anan samirat ta shiga gidan. Dakinta ta shiga ta dauko makullin mota. Ta falo ta biyo da nufin fita. Kicibis sai tayi karo da umma. 
          " Hala ina zaki a wannan lokaci?" Umma ta tambaya. 
         " Wata kawata ce ta kawomin ziyara shine zan rage mata hanya na kaita gida." Samirat ta fada.
         " To kidai yi sauri domin magrib ta kusa." Inji umma. Daga nan sai samirat ta fita. Bayan sun shiga motar ne sai mai gadi ya bude musu gate. Ribas tayi har ta fitar da motar waje, daganan sai ta cilla ta nufi unguwar su hafsat. To bayan ta kaita gida ne sai ta wuce gidansu amiru. Dama dakinsa a wajen gate yake. Shigewa kawai tayi ta sameshi kwance saman gado sai latse latsen waya yake.
         " Dear lafiya kuwa? Ke da mukayi dake zamu hadu dake a club karfe daya na dare!" Amiru ya tambaya cikin mamaki.   
         " Kayi hakuri sweetheart amma yau bazan iya tafiya club din nan ba." Anan ta bashi labarin kashedin da abba yayi mata akansa. 

                                                       PAGE 44

     Indai wannan ne ai ba kome bane, yanzu bari na fada miki abunda zakiyi idan yaso sai na fada miki sauran idan mun hadu makaranta gobe. Jawota yayi a jikinsa daga nan sai ya fara fada mata wasu maganganu a cikin kunne domin kada wani yaji.
       " To amma meye amfanin wannan abu?" Samirat ta tambaya.
       " Kada ki damu zan fada miki idan lokaci yayi." Inji amiru. Daga nan sukayi sallama samirat ta koma gida.
        Da misalin karfe daya na dare ne samirat ta tashi ta tube kayanta ta koma daga ita sai sai bra da pant. Sudadawa tayi ta shiga dakin mai gadi dayake baya rufe dakinsa. Tana shiga ta tarar dashi yana bacci daga shi sai guntun wando. Anan ta tayar dashi. Yana tashi ya fara sallallami.
       " Samirat me zan gani haka lafiya kuwa?" Ya tambaya.
       " Gaskiya ba lafiya ba. Don ALLAH kaxo muje akwai matsala a dakina." Haka ta fada da alamar damuwa a fuskarta.      
        " To yayi bari nasa kayana." Inji mai gadi.
        " A a bai sai kasa ba kazo muje yanxu nan." Inji samirat. Hannunsa taja a guje suka nufi dakinta. Ai kuwa suna shiga tasa sakata. Wutar dakin ta kashe daga nan ta mamayesa ta cire masa wando. Rungumesa tayi tare da matseshi yadda bazai iya tashi ba. Daga nan sai ta fara ihu tana bidar taimako wai ga wani nan ya shigo dakinta. Ba yadda mai gadi bai yiba domin ya tashi samanta amma ya kasa saboda ta masa rikon kwarai. Ihun da take ne ya farkar da abba da kuma umma. A guje suka nufo dakinta amma dakin a kulle yake. Da karfin tsiya abba ya balle ganbun ya kutsa kai ciki. Yana shiga ya hasko torch-light dinsa sai ga mai gadi kuru kuru saman diyarsa. Anan abba ya hasala, jawoshi yayi sai dibarsa yake. Mai gadi yanaso ya fada musu abunda ya faru amma abba bai saurare sai dukansa kawai yake. Ita kuwa umma matsawa tayi wurin samirat ta tayar da ita. Ita kuwa samirat sai kukan munafuci take wai ya ji mata ciwo. Daga karshe dai a cikin wannan dare abba ya kori mai gadi. Shi kuwa mai gadin sai kuka yake yana rokonsa domin yanada kusan diya uku sai matarsa daya kuma a wannan sana a ta gadi kawaice ya dogara. Saboda takaicin wannan abu daya faru mai gadi na komawa gida yace ga garinku. A haka ya rassu gaban matarsa da diyansa. Su kuwa sai kuka suke sun rasa mahaifi. Akan hakane iyalan wannan mai gadi suka walakanta suka koma bara domin ba wanda ya kula dasu. Ba a fi sati ba matar mai gadi ta rassu saboda bakin cikin rasa miji. Su kuwa diyan mace biyu namiji daya dole suka koma bara.

                                                            PAGE 45

           Samirat ce ke tafiya a cikin makaranta shi kuwa samir sai faman binta yake yana kiranta amma taki ta juya ta kalleshi. Yana cikin binta ne sai amiru zaki yasha gabansa. To anan ne samirat ta juyo tana duban abunda ke wakana.
          " Wai kai wane irin dakiki ne marar zuciya ta fada maka bata sonka bata sonka amma kaki ka rabu da ita. To ina fada ma ka shiga taitayinka idan kuma kaki zakaga abunda zai faru." Anan amiru ya juyo kan samirat." Dear mu tafi kawai kyale banzan." Amiru tafiya ya farayi a tsammaninsa samirat na biye dashi. Ashe ta tsaya tana kallon samir sai tunani take. 
        ( Kayi hakuri samir, ba wai sonka ne bana yiba amma ba yanzu na shirya ma amsar soyayyarka ba domin nafi sonka sau dubu bisa ga wannan amirun ) Haka ta fada cikin zuciyarta tana kallonsa bayan yayi nisa. To anan ne amiru ya juya sai yaga ashe bata biyo shi ba.
         " Wai me kike kallo haka?" Ya tambaya.
         " Ba kome, muje kawai sweetheart." Daga nan sai suka nufi wasu yan kujeru suka zauna.
          " Ina fatan kinyi abunda na saki?" Amiru ya tambaya.
          " Kwarai kuwa na kammala jiya nasa aka kori mai gadin yanzu haka nasan yana gidansa." Samirat ta fada.
           " Da kyau, to yanzu sai mataki na gaba." Anan ya matso daf da ita ya fada mata wani abu a cikin kunne daga nan kuma ya bata wani garin magani a cikin leda. " Kiyi yadda nace kinji ko." Amiru ya fada.
           " Kada ka damu an gama." Samirat ta fada. Daga nan sukayi sallama ta nufi gida.
          Abba ne a cikin dakinsa sai karatun jarida yake ita kuwa umma ta fita bata nan. Samirat ce ta shigo a cikin dakin dauke da wani faranti. Saman farantin wasu cups ne biyu. A cikin cups din kuwa juice ne ta hada. Cikin fara a ta shigo dakin ta ajiye farantin a kusa dashi.
        " Abba ga juice na hada mana." Injita bayan ta dauki cup daya tanasha. 
        " Wai ke bana hanaki irin wannna shigar ba. Dubi kayan da kikasa kome a waje." Abba ya fada cikin tsawatawa.
         " Kayi hakuri abba bazan kara ba." Haka ta fada. Daga nan sai ya dauki cup din ya fara shan juice din. Ai kuwa yana shanyewa sai ya fita cikin hayyacinsa. Wata irin shawa ce ta kamasa yaji ba abunda yakeso sai saduwa da mace. Kafin kaceme wandonsa ya cika. Ita kuwa samirat na ganin haka sai ta koma zigidir. Shi kuwa abba na ganin haka sai ya kara rudewa.


                                                       PAGE 46

       Saboda ba cikin hankalinsa yake ba to bazai iya gane cewa dariyarsa ceba. Jawota kawai yayi ya fara biyan bukatarsa. To ashe kafin ta shigo dakin ta ajiye camera a sama sai vedio record takeyi na duk abunda sukeyi. To bayan sun kammala ne sai samirat ta tafiyarta. Shi kuwa abba wani bacci ne ya saceshi mai dadi. Koda ya farka bazai iya tuno abunda ya faru ba iyaka dai yasan cewa samirat ta kawo masa juice to yanasha sai yayi bacci. To bayan ya tashi ne sai yaji duk jikinsa ba karfi kamar yayi amfani da mace. Ko kadan bai damu ba domin a tsammaninsa mafarki ne yayi a cikin baccinsa. Bayan yayi wanka ya canxa sai ya koma falo ya fara kallon news. 
       Can saiga samirat ta fito dauke da laptop dinta. Ajiye laptop din tayi daga nan sai ta kunna masa. Anan abba ya rike baki ganinsa saman diyarsa sai aiki yake. Hawayen takaici ne suka fara zobo masa daga nan sai ya tuno da juice din data bashi. Wato kenan wannan juice ta hadashi ne domin ta yaudaresa tasa yayi amfani da ita. To amma meye dalilin da yasa tayi masa wannan abu? Cikin takaici abba ya tashi ya daga laptop din yayi jifa da ita sai da ta warwatse.
      " Amma samirat kin cuceni, yanxu ina matsayin abbanki amma ni zaki yiwa haka." Biyota yayi da nufin ya ballata guntu guntu. Daga nan sai taja da baya tana masa magana.
        " Dukana din dazaka yi ba shi zai fitar dakai daga sharrin dana kulla ma. Saboda haka ka saurereni idan kanaso kada assirinka ya tonu." Cewar samirat. Abba najin haka dole ya tsaya yana saurarenta. " Wannan vedio daka gani inada shi a memory card dina kuma ni kadaice nasan inda na ajiye memory saboda haka kabar ganin watse laptop din da kayi ya bata. Da farko dai yanxu inaso ka fadamin pin dinka na ATM da kuma inda kake ajiye dukiyoyinka. Sai kuma maganar amir, idan har kanaso kada umma taji wannan magana to kayi shiru. Duk abunda ka gani inayi nida amir to kada kace na bari idan kuma kaki to zan bayyana wannan vedio kowa ya gani." Haka samirat ta fada tana masa kallon keta. Anan abba yayi shiru ya rasa abunda ke masa dadi. Ba yadda ya iya dole ya bata abunda takeso. To tun daga wannan rana duniya ta dawowa samirat sabuwa domin sai abunda taga dama takeyi shi kuwa abba yana kallo amma ba damar magana.  

                                                    PAGE 47

           Samirat ce a zaune saman kujera a cikin gate din gidan sai latse latsen waya take. Tana cikin hakane sai taji almajiri na bara. Kiransa tayi ta bashi naira goma ya sawo mata chewing gum.  To bayan ya fita ne can sai ya dawo yana kuka.
         " Lafiya kuwa naga kana kuka?" Samirat ta tambayeshi.
         " Kudin da kika bayar ne suka fadi." Inji almajirin.
         " Ai kuwa kayi kadan yaro ni zaka yiwa sata kace wai sun fadi."Anan ta tashi ta ciyo kwalarsa. Marinsa tayi sai da ya fadi. Yana tashi ta kara masa wani marin sai da ya kara faduwa. Anan ta jawoshi sai duka take kamar tana fada da warinta. Shi kuwa yaron karami ne bai fi shekara goma ba. Sai ihu yake yana neman afuwa amma taki taji. Daga nan sai ta jawoshi cikin gida. Dama ta aza ruwan zafi wadanda zatayi wanka. Debo ruwan zafin tayi sannan ta tubewa almajirin riga yana ihu. Cikin rashin imani ta fara kwarara masa ruwan zafi a baya. Tun yana kuwa yana neman taimako har takai ya fadi kome bai iyawa. Sai jini ke fita ga hancinsa baya nasa kuma duk ya bulce kamar ansa reza an debe masa fata. Anan ne ta tabbatar da cewa almajirin ya mutu kuma gashi tana jin tsoro kada ace ita ta kasheshi. To a wannan lokaci ba kowa a gidan sai ita. Daga nan sai taja gawarsa can bayan gida. Kasancewar gidan babba ne kuma gashi na sama. Gina ta farayi har sai da ta gina rame mai zurfi. Daga nan sai ta jefa gawar almajirin sannan ta rufe da kasa. 
       Tana gama aikin ne saiga abba da umma sunzo wurin. Da sauri tayi jifa da hauyar data rike ta nufi wurinsu. " Tun daxu muka dawo amma bamu ganki ba sai kuma mukaji kamar ana gina wani abu a bayan gida sai mukaga bari muzo muga lafiya." Inji abba.
       " Lafiya kalau abba ba abunda ya faru. Yanxu kuxo mu shiga ciki." Anan ta lakamasu sai labari take basu har ta shiga dasu cikin gidan. To sa ar dataci shine basu kalli wurin datayi ginar ba.
                                                     *********
        A cikin wannan dare samirat ta wuce club. Ai kuwa daga shigarta ta hango amir sai tikar rawa yake yana shan giyarsa. Yana hangota yayi jifa da kwalbar ya nufota. Anan suka zauna saman wasu kujeru sai fira suke cikin annashuwa.
 
                                                       PAGE 48

       " Kai yaufa na kuru?" 
      " Hala menene ya faru?" Amir ya tambaya. Anan ta bashi labarin almajirin data kashe. Tana gama labarin sai yayi tsuki yana kallonta.
      " Amma ke sakarya ce, to don ki kashe almajiri shine zaki wani damar da kanki. Ni nan ina fada miki mutanen dana kashe basada iyaka domin yanzu haka akwai wani dan makarantarmu da nakeso na kashe."
      " Hala waye wannan?" Samirat ta tambaya.
      " Ai kin fi kowa saninsa, wato ki sani samirat duk namijin da yayi yunkurin kusantarki to sai naga bayansa domin son da nake miki ya wuce yadda kike tsammani. Saboda haka bako shakka sai naga bayansa."  Anan suka kyalkyace da dariya daga nan suka nufi wani daki. Daga shigarsu suka tube kayan jikinsu anan suka fara aiki. Bayan su samirat sun gama shakiyancin su. Sai suka dawo gida. Daga shigarta tayi kwanciyarta saman gado sai bacci. 
         Bayan safiya ta waye ne sai ta kimtsa kanta domin yau ba makaranta. Tana gama break fast ta dauki kujerarta sai wajen gate inda ta fara karatun wani novel na hausa ( FULANIN DAJI ) Da misalin karfe goma cif sai taga wata mata ta shigo gidan. Matar almajira ce daga shigowarta sai ta fara bara. To ita matar ta kasance mai murya babba to daga fara baran sai gidan ya rude da muryarta. Ita kuwa samirat hasala tayi daga nan sai ta nufi matar da fada.
        " Wai ke wace irin jahila ce zaki shigo gida ki cika mu da muryarki irin ta jaririn jaki. Idan ba a baki ba ai sai kiyi hakuri. Ku wadannan talakawan kunada matsala fa gashi tsiya ta isheku amma sai damun mutane, ai nasan ba a banza aka barku haka ba." A haka dai samirat tayita zaginta kai harda turata take waje. Da karfi tayi jifa da yar robar matar a waje da nufinta ma ta mareta sai ga abba yazo ya hanata. Anan abba yaba matar sadaka sannan ya juyo kan samirat sai fada yake mata.  
        " Idan kika ga dama ki bayyan wannan vedio duniya ta gani amma ni a matsayina na mahaifinki idan har ina raye  bazan yarje miki ba kinama mutane irin wannan walakanci domin abun yayi yawa. Idan har bazaki bata sadaka ba to me yasa bazakice tayi hakuri ba. Idan ma cewa tayi hakuri ya miki nauyi sai ki kyaleta idan ta gaji da baran ta tafiyarta." Anan abba yayi mata fada hakama itama umma ta fito. Bayan ta fahimci abunda ya faru itama sai ta hauta da fada. Da samirat taga bazasu daina ba sai ta tafiyarta daki ta kulle tayi zamanta sai karatun ta take.

                                                            PAGE 49

      Da misalin karfe goma na dare sai wayar samirat ta fara ringing. Bayan ta dauka sai taji muryar amir, anan ya fada mata wata unguwa da kuma address na wani gida inda zata sameshi. Cikin sauri ta buga motarta bata tsaya ko ina ba sai kofar gidan wanda yake a cikin lungu. Kai da ganin unguwar kasan abun tsoro ce domin ba gidaje sosai kuma wurin ya kasance kamar daji. Bayan ta shiga gidan ne sai ta tarar da amir zaune saman wata kujera sai ga yaransa su biyar a tsaye . Yana ganinta sai ya tareta da murna. 
      " Kamar yadda na fada miki, idan nayi magana bana sabawa, to ki sani na kama wanda nake farauta kuma a yau ne zan aiwatar masa saboda wannan daliline nace bari na kiraki kiga karshensa." Anan ya nuna mata wani daki." Yana a cikin wannan dakin. Yanxu ki jiramu zamu tafi wani wuri mu dawo." Anan amir ya fita gidan shida yaransa. Ita kuwa samirat da karfi ta shiga dakin ta tarar da samir kwance cikin jini. Anan ta rungumesa tana ihu sai tunanin abunda ta masa take." Shi kenan na rasa masoyi na gaskiya mai sona tsakani da ALLAH, samir kada ka mutu ka barni."  A haka ta kankaneshi sai rusa kuka take. To a cikin wannan kuka datakeyi ne samir ya farka to anan yaji tana fadar kada ya mutu ya barta. Anan ya fara tunani shi kuma( Dama samirat na sona kuwa? )
Bayan ya tashi ne sai ta taimaka masa ta kwance daurin da suka yi masa. Anan ta mika masa makullin motarta.
       " Ka shiga motata ka gudu kafin su dawo." Anan samir ya karbi makullin da niyar fita. Ai kuwa yana fitowa dakin sai ga amir ya dawo tare da yaransa.
       " Kai kana tsammanin zaka iya guduwa ne?" Amir ya tambayeshi. Anan wani daga cikin yaransa yayo cikin samir da nufin kaishi kasa. Da sauri amir ya tareshi. " Kada ka damu giwa, ai wannan fada nawane ba naka ba." Inji amir. Anan ya tube riga yana yiwa samir nuni daya zo suyi dambe. Su kuwa yaran nasa sai suka zagayen filin sai kirari sukewa amir. " Zaki, zaki , zaki." Haka suke fada suna tabi. 
        Da karfi amir yayo cikin samir. Ai kuwa suna haduwa amir ya daga samir sai da yayi hajijiya dashi sama sannan ya makashi ga kasa. Anan hankalin samirat ya tashi domin tasan cewa amir ba karamin kato bane kuma bugeshi abu ne mai wuya. Da sauri samir ya mike ya kara takawa. Daga nan suka kara hadewa amma kuma a wannan karon sai da samir ya dan bubbugeshi kafin akaishi kasa. A duk lokacin da suka hade to samir ne ake kaiwa kasa har sai da takai an masa wani kaye da baya ko iya tashi.

                                                              PAGE 50

       " Yanxu xan murde masa wuya ya mutu sai kowa ya huta." Haka amir yace daga nan sai ya nufi wurin samir da nufin halakasa. Ita kuwa samirat gabanta sai faduwa yake domin batason a kashe samir. To kafin amir ya iyar da nufinsa sai dabara ta fado mata. Da sauri ta tsayar da amir daga nan sai ta fara magana.
     " Nasan da cewa kayi kokari kuma ka nuna mana cewa kai zakine." Yaran amir najin haka sai suka fara ihu najin dadin wannan maganar data fadi. " Amma kuma a wurina baiyi kokari ba ko kadan." Daganan sai sukayi shiru suna kallonta. " Kada fa ku manta wannan fada da sukayi na hannu ne, to me zai hana a kawo takubba idan yaso sai su gwada mu gani." Daganan sai gidan ya rude da sowa saboda jin dadin wannan maganar data fadi. Da sauri ta nufi wurin samir tana girgiza shi sai dakyar ta samu ya tashi. " Kada ka bani kunya." Haka ta fada a cikin kunnensa bayan taga ya dawo hayyacinsa. Yana mikewa tsaye sai aka jefo masa takobi. Anan ya kalli samirat ita kuwa sai nuni take masa daya dauka. Yana daukar takobin sai amir yayo cikinsa. Anan suka hargitse da masifaffen fada kai kace bazasu daina ba. Sai da wannan fadan yasha banban dana farko domin amir ne keshan wuya. Duk inda ya kawo farmaki sai samir ya tare ya mayar masa da abunsa. Kafin kaceme an yima amir yanka uku masu kyau. Anan ya fadi yana ihu saboda zogin da yaji. Ita kuwa samirat sai murmushin farin cike take. Yaran amir na ganin haka sai suka zage makamansu sukayo kan samir. Anan aka fara dauki ba dadi ai kuwa cikin sa a samir ya zubar dasu gaba daya. Daga nan ya fita a guje. Su kuwa suka dafo masa. Koda suka kai kofar gida har ya tayar da motar samirat. To kafin su karaso ne yasa giya ya tayar a guje. Dole suka dawo suka fadama amir abunda ya faru.
         " Amma fa ya kuru." Haka amir ya fada bayan yaransa sun tayar dashi.
         " To wai ta yaya ya samu makullin motarki?" Amir ya tambaya.
         " Inaga faduwa yayi sai ya dauka." Samirat ta bashi amsa.
         " Nima haka nake tunani." Inji amir. Anan yaja hannunta suka shiga wani daki. 

                                                             PAGE 51         

            " Gaskiy akwai matsala, har yanxu abba bai kyaleni ba." Anan ta bashi labarin walakancin data yiwa almajira da kuma irin fadan da abba yayi mata.
           " To ai wannan ba kome bane, sai idan yana raye zai iya kin yarje miki to idan baya raye fa?" Amir ya tambaya.
           " Nifa ban gane wannan magana taka ba me kake nufi?"Inji samirat.
           " Ya kamata ace kin gane abunda nake nufi." Amir ya fada yana dubanta.
           " To in tambayeka mana, wai shi wannan mai gadi dakasa na kora to meye amfanin hakan kenan?" Samirat ta tambaya.
           " Saboda akwai abunda nakeso kiyi kuma banaso ya gani shi yasa nasa kika masa wannan sharrin." Inji samir.
            " To wannan abu menene halan?" Samirat ta tambaya. 
            " Kawo kunnenki kiji." Anan ya jawota ya fada mata wata magana a cikin kunne.
            " Haba samir, iyayena ne fa, gaskiya bazan iyaba." Inji samirat.
            " Ke kuma sakarya, da kin yi haka shi kenan komi ya kare domin zamu mallaki kome mucigaba da cin duniyarmu ni dake." 
            " Kayi hakuri amir amma baxan iya wannan aiki ba." Inji samirat. Daga nan sai amir ya tashi cikin fushi.
            " Ina fada miki idan har bakiyi wannan aiki ba to shi kenan zamu rabu kuma rabuwa ta har abada." Anan amir ya nufi kofar dakin da nufin fita. Da sauri samirat ta rikoshi tare da rungumeshi. 
            " Haba sweetheart ya zakayi fushi dani daga wannan magana, to kada ka damu domin wannan aiki kamar an gama ne." Anan ya rungumeta cikin farin ciki.
             " Yauwa dear ko kefa, yanxu dai naji bayani." A cikin motarsa yasa wani yaronsa ya kaita gida. 
             Da misalin karfe daya na dare samirat ta farka tayi shiri sosai kai kace yar dambe. Kaya tasa matsatstsi wadanda suka rufe fuskarta yadda ba a ganin kome. daga nan ta dauko wani gatari da kuma wata karamar yuka. Da karfin tsiya ta balle dakin abba ta kutsa kai ciki inda ta tarar dashi yana bacci shida ummarta. Wani sara ta kai masa da nufin ta datse masa wuya cikin iko na ubangiji sai ya farka. Anan ya tureta can gefe. Tana tasowa sai suka fara fada tana kai masa sara yana kaucewa.

                                                       PAGE 52
   
      Wannan fada nasu ne ya tayar da ummarta, ita kuwa sai tayi yunkurin taimakawa mijinta. To a wurin wannan yunkuri ne samirat ta kasheta. Shima abba kuma sai ta kaishi kasa. To kafin ta kashe sa ne sai ta debe kyallen data rufe fuskarta dashi daga nan kuma ta soka masa yuka a kahon zuci anan yace ga garinku. To wannan fada nasu yayi kamari domin sai da suka fito bakin gate. To a bakin gate din ne ta samu nasarar kashe iyayen nata. Bayan ta kashe abba ne sai taga shigowar wannan almajirar data taba yiwa walakanci. Samirat tayi mamakin ganin wannan almajira a cikin wannan dare amma bata damu ba domin jawota tayi ta kasheta don kada ta tona mata assiri. Daga nan sai ta kira amiru a waya ta fada masa cewa aiki yayi kyau. A cikin motarsa yaxo shi kadai har gidan. Daga nan sai suka dauki gawawwakin suka nufi bayan gida. Sai da suka gina rame sannan suka turbudesu a ciki. 
        Tun daga wannan rana dana kashe iyayena da kuma wannan almajirar ban kara samun sukuni ba. Na kasance a cikin fargaba, tsoro da kuma tashin hankali a ko yaushe. Ina ganin abubuwa naban tsoro kala kala, iri iri, daban daban. Sai kuma mugayen mafarkai da nakeyi naban tsoro a ko yaushe. A kullum banada lafiya. Ga tarin dukiya ta abba bana iya amfani da ita saboda wannan rashin lafiyar. A dalilin hakane dukkan abokaina suka gujeni domin duk wanda ya kusance ni to bashi ba zaman lafiya. Yadda ake bani tsoro da kuma mugayen mafarkan danake shima haka zai dinga ji.  Nasan da cewa sune suke son su dau fansar abunda na musu, nasan da cewa mattattu ne suka farka domin su dau wannan fansar. Wadannan matattu basu kowa bane in banda wadanda na kashe, sune suka shiga jikin amir domin daukar fansa a kaina. Bako shakka nayi dana sanin wannan muguwar aika aika danayi, kuma nayi dana sanin bin shawarar mugun mutum wato amiru. 
        Bako shakka duk wanda bai bi maganar iyayensa ba to bazai ji dadi ba, kuma duk wanda yabi son zuciyars to yana cikin masifa. Nayi dana sanin jan ajin dana yiwa samir, nayi dana sanin walakancin da nayiwa wadannan almajirai, kuma nayi dana sanin bin zuciyar danayi na kashe iyayena. Anan samirat ta tsaya bayan ta gama basu labarin. 

                                                     PAGE 53

               Cikin fushi samir ya tashi tsaye. " Amma ke samirat kin cika macuciya, mayaudariya kuma marar imani, ashe dama ke kika kashe iyayenki shi yasa a duk lokacin dana tambayeki sai kice min sunyi tafiya. Ko kadan banajin tausayinki kuma wannan kadan ne kika gani domin sai kinga abunda yafisa. Yanzu ke ko kunya baki jiba kin yi sanadiyar mutuwar mai gadi shida matarsa. Haka kuma kin kashe almajiran da basu ji basu gani ba. Sai kuma iyayenki da kika kashe saboda son da kikewa saurayinki.Bako shakka dole ne wadannan mattatu su farka domin su dau fansar abunda kika yi musu. Ni kinga tafiyata domin bazan iya zama a wannan gida ba, ni bazan iya zama a GIDAN MATATTU ba.To kafin samir ya fita ne sai suka farajin wani rugugi a saman kwanon gidan. A guje samirat da meerat sukazo suka kankaneshi saboda tsoro. 
       " Wannan rugugi da nake jifa?" Samir ya tambaya.
       " Shine ya taso!" Samirat ta bashi amsa. 
       " Kadai dai kicemin amir ne,  to ya akayi yasan muna nan?" Haka samir ya fada cikin mamaki domin ko takin da sukayi masa a mota ya kamata ace ya mutu. Rugugin sai karuwa yake sai kace giwaye ne a saman kwanon. Daga nan sai wutar gidan ta fara billin billin ta kawo ta dauke. Can sai sukaga an balle kwanon falon da karfin tsiya an yi jifa dashi. Daga nan sai sukaga dirowar wani abu kamar an jefo doki daga gidan sama. Suna dubawa sai sukayi arba da amir idanunsa sunyi jawur. 
        " Ke kina tsammanin zaki iya guduwa daga sharrin da kikayi? To bazaki iyaba, yadda kikaga bayanmu muma sai munga bayanki." Haka amir ya fada cikin wata murya mai rugugi kamar tsawa. Magana yake amma sai kaji kamar mutum goma ne a jikinsa suna magana. 
       " Kai kuma." Anan ya nuni samir da yatsa. " Sai da na fadama kada ka yarda ka shigo gidan matattu kuma ka daina taimakon matattar mace... Amma kaki." Haka amir ya fada cikin muryar dan yaro. To anan ne samir ya tuno da mafarkin da yayi na almajiri wanda yayi masa kashedi akan gidan. Bako shakka wannan almajirin ne ke masa magana.  Daga nan sai amir yayo cikinsu a guje. Su kuwa su meerat na ganin haka sai suka ranta a guje suka nufi upstairs. Anan samir ya taresa da nufin tsayar dashi. Ai kuwa suna haduwa yayiwa samir wani duka sai da ya tashi sama sannan ya bugi gina ya fado. Da sauri samir ya mike ya bishi a guje. To a wannan lokaci ya kusa cimma samirat dama ita yakeson kamawa. Wani tsalle amir yayi sai kace doki cikin kankanin lokaci yasha gabanta. Anan ya dagata sama ya jefa saman gina. Haka ta fado galabaice sai jini ke kwarara a hancinta. Dagota ya karayi da nufin kara makata a gina to anan ne samir ya buga masa wani karfe daya dauko.

                                                          PAGE 54


         Jifa yayi da samirat can gefe daga nan ya fuskanci samir. Anan suka kaceme sai bugun juna suke cikin mugun nufi. Kai da ganin fadan amir kasan ba lafiya ba domin a duk lokacin daya bugi samir. To iskane zai dauki samir yayi hajijiya dashi sannan ya makashi saman gina. Daga nan kuma sai yayi wani tsalle ya diro masa. Suna cikin fadan ne amir yayi kan samirat. Tashi sama yayi kamar tsuntsu sai wani gurnani yake. Duk abunda ya dauko jefo mata yake haka kuma daya bugi gina sai kaga ta zube kasa ta wargaje.  Kafin ya cimmata ne samir yayi kukan kura ya bugosa da wani gatari. Anan amir ya fado kasa sai kace giwa. Yana tashi yayiwa samir wawan duka. Tun daga gidan sama samir ya fado rikicaa. Daga nan amir yaci gaba da binta sai gurnani yake. Ita kuwa samirat tuni ta rikice sai gudu take iya karfinta idan ta shiga wannan lungu tabi wancan shi kuwa amir bantalo gina yakeyi yana jefa mata. Tare take da meerat sai faman gudun suke. Suna cikin gudun ne amir ya jefo wani ballin gina. Anan  ballin yayi waliliya sannan ya fado kan samirat. Take ta fadi cikin ciyo. Amir na ganin haka sai ya bar gudun. Tafiya ya farayi da sauri ya nufota. Ita kuwa meerat janta ta farayi domin ta tashi amma ina ta kasa domin ta samu rauni a kafarta. Yana zuwa wurin yayi jifa da meerat can gefe, da hannu guda ya daga samirat. Daga nan sai ya bude farattansa ( Finger nails ) Da nufin soka mata a kahon zuci. To kafin ya iyar da nufinsa ne meerat ta lallabo ta bayansa ta buga masa wata tukunya.  
        Anan tukunyar tayi guntu guntu, shi kuwa amir na ganin haka sai yayi jifa da samirat yayo kanta. Da gudu tayo downstairs domin tsere masa shi kuwa a guje ya dafota. To tana cikin gudun ne taci karo da samir rike da gatarinsa da wani karfe. Meerat labewa tayi bayan samir daga nan sai aka fara kallon kallo. Maimakon amir yayo cikinsa sai ya juya a guje ya nufi wurin samirat. Ai kuwa yana zuwa ya tarar ba tanan da alama ta boye wani wuri. Anan ya fara dube dube yana tafiya a hankali. Yana cikin hakane saiga samirat ta fito ta bayansa rike da wani takobi. Da karfi ta soka masa takobin sai da ta nutse a cikinsa sannan ta fito ta baya. Anan amir yayi gurnani ya cafke ta da hannunsa. 
       " Ai mutuwa daya akeyi ba biyu ba. Kin riga kin kashemu saboda haka bazamu kara mutuwa ba." Haka amir ya fada cikin wata murya mai ban tsoro kai daka jiya kasan ba shi bane. Daga nan sai ya zage takobin yayi jifa dashi. Farattansa ya kara budewa da nufin barka mata ciki saiga samir a guje ya masa wani mugun naushi. 
                                
                                                     PAGE 55

      A cikin  taga amir ya fada shida samirat sukayo kasa. Shi kuwa samir na ganin haka sai ya biyoshi. Itama meerat bata yarda an barta baya ba domin dirowa tayi. Ai kuwa sai gasu a bayan gida. Cikin sauri amir ya daga samirat sama. Farattansa yasa ya barko cikinta. Daga nan saiga hanjinta a waje. Anan yayi jifa da ita tana wulle wullen mutuwa. Samir da meerat na kallo amma ba yadda suka iya domin abun ya riga ya faru. A guje meerat ta nufi wurinta tana girgizata amma ina rai yayi halinsa. Shi kuwa amir faduwa yayi daga nan sai sukaga wani hayaki ya fito daga cikn bakinsa. Hayakin na fitowa sai amir ya koma dai dai siffarsa ta asali ta dawo. Daga nan sai hayakin ya shiga jikin samirat. Gani sukayi samirat ta tashi. Anan ta karbe gatarin da samir ya rike. Tana zuwa wurin amir sai ta debe masa kai anan shi kuma ya mutu. Faduwa tayi sai hayakin da ya shiga jikinta ya fito. Anan ta koma yadda take wato matatta. Daga nan sai hayakin ya fito ya rarrabu. Kashi biyu na hayakin ya tashi sama wato shine na mai gadi da matarsa. Sai kuma kashi hudu suka koma a cIkin ramensu. Su kuma wadannan kashin hudun sune na iyayenta da kuma almajiran data kashe. 
       Haka samir da meerat suka tsayu suna kallon wannan hayaki, to abunda ya basu mamaki shine idan suka kalli hayakin sai suga kamar mutanen da samirat ta kashe ne a cikinsa suna tafiya. Haka suka yita kallon hayakin har ya bace. Anan meerat tazo wurin samir ta rungumeshi tana kuka. Duk da cewa batason samirat ko kodan amma ta tausaya mata a wannan karon. Haka shima samir din sai zubda hawaye yake. 
        " To yanzu meye abunyi?" Meerat ta tambaya.
        " Abunyi shine muyi gina mu binnesu a wannan wuri tunda suma a nan suka binne wasu. Daga nan kuma zamu bar wannan magana a matsayin sirri bazamu bari kowa ya ji ba." inji samir. Daga nan sai suka fara gina. Sai da ramen yayi zurfi sannan suka dauko gawawwakin suka tura a ciki. Daga nan suka mayar da kasa suka rufe. Lakama juna sukayi daga nan suka nufi hanyar fita gidan. To kafin su fita ne samir ya hango wani kwado ( Padlock) Anan ya dauko kwadon. Sai da suka kulle duk tagogi da kofofin dake gidan. Daga nan suka fita bakin gate din suka sa masa kwadon suka kulleshi. Shi kuma makullin kwadon jifa sukayi dashi don kada wani ya gani ya bude gidan. Daga nan suka tafiyarsu suka cigaba da al amurran rayuwarsu. 

                                                       PAGE 56


                
        Duniya juyi juyi, yau idan tayima zafi gobe tayima sanyi. Haka idan kana cikin farin ciki to wataran zaka koma bakin ciki, duk abunda ka gani nufin ALLAH ne haka ya tsara kuma haka abun yake kuma dole shi zai faru. Mafi yawan mutane basa tunani kafin su gudanar da ayyukansu wanda hakan shi ke janyo matsaloli na yau da kullum. Kada kayi tsammanin cewa idan ka shuka sharri wai sai a lahira zaka samu hukunci, to wataran tun a duniya za a fara nuna ma abunka kafin kaje can ka hadu da masifa marar iyaka. Haka kuma kada kayi tsammanin cewa idan ka shuka alheri wai sai a lahira zaka samu sakamako, domin wataran akan sakama tun a nan duniya kafin kajecan ka hadu da jin dadi marar iyaka. 
       Jan aji, walakanta mutane da kuma bin zuciya su suka sanya samirat cikin halaka, bako shakka duk wanda yabi son zuciyarsa to zaiyi kuka wata rana haka kuma duk wanda yayi hakurin masifar data sameshi to zaiga saka mako mai kyau.  Bazan iya mantawa da samirat ba domin sonta a cikin zuciyata yake, haka kuma bazan iya mantawa da walakancin data yimin ba a lokacin da sonta ya mamaye ciki da wajen zuciyata, sai kuma jan ajin data yimin duk da cewa itama tana sona. A kullum nakan tuno rayuwar da mukayi muna yara da kuma farkon haduwarmu a lokacin da ummina ta kaini gidansu. 
       Bako shakka wannan magana haka take, makinyinka na wata rana shine masoyinka na wata rana kuma masoyinka na wata rana shine makiyinka na wata rana, ban taba tsammanin cewa rana irin wannan zatozo ba har na riki meerat a matsayin masoyiya ba. Amma sai gashi yanxu itace gimbiyata, kuma sarauniyata wadda ta maye gurbin samirat gabaki daya.  
         Wani rashi alheri ne, rashin samun soyayyar samirat alheri ne a wurina wannan shine dalilin dayasa muka kasa jituwa. Mafi yawan mutane kan yi kuka idan suka rasa wani abu ko kuma suka kasa samun abunda suke so cikin rashin sanin cewa hakan shi yafi zama alheri a wurinsu. Nayi kuka mai tsanani na rashin samirat amma daga baya sai na tuna cewa wannan shi yafi zama alheri a gareni domin sai gashi an bani wadda tafi samirat kome, wadda ke sona so na tsakani da ALLAH, haka na rike meerat da zuciya daya wato zuciyar soyayya, kuma wannan soyayyar ce ta kaimu gayin aure bayan mun kammala karatun mu. Shi kuwa labarin GIDAN MATATTU mun yi alkawarin cewa bazamu bayyana shi ba don kada wasu suji suje ganin kwam. A haka muka cigaba da rayuwarmu cikin jin dadi da walwala. Wannan shine karshen labarin samirat, yarinyar data kashe iyayenta saboda saurayin da take so daga karshe itama ta kare a GIDAN MATATTU.

                                                         

THE END



                                                 Written by

                                                                  Abdul king article
                                                               
          
           

    

Post a Comment

0 Comments