JARUMAN MATA

JARUMAN MATA
Written by:
abdul king article
A zamanin baya, an yi wani gagarumin sarki, mai karfin mulki
da karfin iko, ga dukiya wadatatta marar iyaka, wannan sarki
ana kiransa da suna marzuk, duk wannan dukiya daya samu
takan zamo a banza, domin ba a binda bai yi ba domin samun
da, amma abu ya gagara.
Sarki marzuk na da mata daya, ana kiranta da hamlat, sarki na
mutukar ji da wannan matar, saboda irin kyawonta, da kuma
iya zancen, sannan kafin ya aureta ya fuskanci kalubale marar
iyaka, domin sai da ya goga da mutum dubu, a cikin dubu din
ya zama zakara, a nan ya samu damar aurenta.
Wata rana da dare, tsakiyar dare a lokacin da kafa ta dauke,
baka jin taku ko motsi, sai sarki marzuk yayi shiri, shirin da bai
fada wa kowa inda zashi ba, a saman doki ya hau, a nan ya
kada linzamin dokin, doki yayi haniniya sannan ya soma wani
namijin gudu kai kace walkiya, take ya bazama cikin daji, gudu
kawai yake ba kakkautawa, ahaka ya ci gaba da gudu har
tafiya tayi nisa, to daga nan sai ya dan rage gudun dokin,
alamun cewa ya kusa kawowa inda yake son xuwa.
Wani burki dokin yaci sai da kura ta tashi, to anan sarki marzuk
ya sauko saman dokin, anan ya kalli dajin ya gane cewa
wannan daji ne mai ban tsoro, domin itatuwansa dogayene
cike da ganyayyaki, sannan ga tsananin duhun daya kara tafke
dajin gaba daya, duk da kasancewar sarki marzuk jarumi, anan
kam sai da ya dan sosu.
Ana cikin haka, kawai sai yaga wasu halittu bakake suna
kokarin zuwa wurinsa, anan hankalin sarki ya tashi, take ya
kidime, da gudu sarki ya kamo dokinsa da nufin komawa gida,
anan doki ya haukace masa, daga karshe dai dokin ya
dungujeshi ya nufi daji, shima yayi takansa, anan sarki ya gane
cewa wadannan halittu bako shakka tsimin bala i ne, domin
dokinsa bai taba yi masa haka ba, anan sarki marzuk ya fara
kallon gefen da wadannan halittu suke, kadan ya rage su kawo
sai yaga wani iska mai karfi ya lullube sararin samaniya, anan
sarki ya koma gefe domin iskan ya wuce, bayan wani dan
lokaci, sai sarki ya tashi, anan yaga iskan ya wuce, kuma dajin
yayi tsit kamar ba kowa ciki, anan ya fara tafiya guda guda,
yana cikin tafiyar ne sai ya tsaya kyam, ko motsi baya iya yi,
anan jikinsa ya fara makarkata, zagayarsa yaga anayi, kuma
baya ganin mai zagayen, maimakon haka sai dai yaga innuwa
tana zagayensa, kuma ba innuwa guda ba, ahaka sarki ya fara
kallon wadannan innuwowi marar iyaka, ba abunda sukeyi sai
zagayensa.
Ana cikin haka ne, sai sarki yaji wata murya tana magana, nice
milat, sarauniyar iblisai ta duniya, sarauniya mai mulkin
dabbobi da tsuntsaye, sarauniya mai mulkin mutane da
aljannu, kowane sarki a kasana yake, haka duk mutumin da
yazo nan to a bayana yake, to daga nan muryar ta tsaya.
Anan sarki ya bude baki da nufin yin magana, cikin tsawa ya ji
an dakatar dashi, kada ka damu yakai wannan sarki, nasan
abunda ke tafe dakai, kuma nasan yadda zan tafiyar dashi,
anan sarki yaga wadannan inuwowin dake zageyensa sun fara
hada kansu wuri guda,haika suka yita hadewa har sai da suka
zamo guda, to gudar ce ta rikede ta zama mace guda
kyakkyawa, sarki bai taba ganin mace mai irin wannan kyau ba.
Daga nan sai wannan matar ta yi nuni da hannunta, take sarki
yaga wani katon gizo gizo ya fito, wannan gizo gizo dai yafi
daki girma, cikin sauri wannan gizo gizo ya dauke sarki ya aza
saman bayansa, haka itama wannan sarauniyar take ya azata
saman bayansa, a guje ya fara gudu da nufin kaisu wani wuri,
anan wannan sarauniya ta gane cewa hankalin sarki marzuk a
tashe yake, domin bai taba ganin wannan abun mamaki ba,
daga nan ta fara yi masa magana da cewa, kada ka damu
yakai wannan sarki, wannan gizo gizo da ka gani shine
matsayin dokina, kuma yanzu haka yana akan hanyarsa ne ta
kaimu fadata, to anan hankakin sarki marzuk ya kwanta daya ji
manufarta, cikin zuciyasa kuma yana mamakin abun, tare da
cewa, gaskiya wannan sarauniya takai hatsabibiya, wato ita
hadda dabbobi take sarrafawa, wai yanzu saman gizo gizo ne
muke, abu sai kace mafarki, haka dai sarki marzuk ya cigaba
da wannan sake sake har suka kawo.
Wata kasaitacciyar fada ce da aka gina saman dutsi, ko ina
kyal kyali yakeyi sai kace zinari, haka sarki marzuk ya bi
wannan masarauta da kallo, anan ya gane cewa shi ba kowa
bane in banda talaka. to bayan sun shiga masarautar ne shida
milat, anan ya kara tabbatar da cewa bako shakka shi ba kowa
bane, anan sarauniya milat ta masa umarni daya zauna saman
wata kujera, haka ko akayi, to bayan sun fuskanci juna, take
suka fara magana, milat ce ta fara magana, wato ka sani
marzuk, naji dadin wannan ziyarar daka kawomin, domin dani
dakai duk muna cikin wata bukata, wadda kuma sai mun hada
karfi da karfe muke iya samunta, wato zaka taimakeni in
taimakeka, anan mamaki ya kashe sarki marzuk, to wane irin
taimako ne take so yayi mata,haka ya fada cikin ransa, yana
cikin wannan tinani sai yaji an aje kwannan abinci a inda yake,
anan ya duba domin ganin ko waye ya aje abincin, ba kowa ya
gani ba in banda wasu zakuna mata guda biyu, wai sune ke
dafa mata abinci, anan mamaki ya kara kashe sarki marzuk,
amma a wannan karon bai nuna alamar a fuskarsa ba.
Daga nan sarauniya milat ta ci gaba da cewa, nasan da cewa
ka samu labarina ne ga babban abokinka,wanda ya baka
shawara cewa kazo wurina, xan taimaka ma ko, a nan sarki
marzuk ya gyada kai, domin abunda ta fadi gaskiyane, daga
nan ta cigaba da cewa, shekaru da dama da suka gabata,
mijina yayi kokarin samun sihirin da zai mulki mutanen duniya
da aljannun duniya, sai dai a wannan lokacin bashi kadai ne
mai neman irin wannan sihirin ba, akwai wani sarki da ake kira
amru, shima yana akan bakarsa ta neman wannan sihiri, ina
gayama cewa amru sai ya zama makiyin mijina, wanda
sanadiyar hakan suka shirya yakar juna, to a wannan yaki ne
amru ya samu nasarar yin wani tsafi ga mijina, anan ya maida
shi dan tsito, dashi da duk ragowar mutanensa, yanzu haka
mijin nawa na nan tare da mutanensa na kullesu a cikin wani
daki, to bayan na fahimci irin ta addacin da amru yama
mutanena tare da mijina, ni kuma sai na fita bidar wannan
sihiri, cikin sa a kuma na samo.
A sakamakon binciken da nayi, na gano cewa sarki amru nada
diya, wato wasu JARUMAN MATA UKU, suhailat, suhaimat, da
nabilat, kowacensu nada mutukar amfani a wurinmu, domin
jikinsu na dauke da wanni sirri da har yanzu ban gano ko
menene ba, wato ka sani cewa, matarka ba zata taba samun
haihuwa ba face tasha jinin daya daga cikin wadannan yan mata, idan har ta samu shan jinin daya daga cikinsu bako shakka  zata haihu, sai dai a cikin
wadannan yan matan uku, ban san kowa cece ya kamata ka
a samu jininta ba. kaga sai mun ganota kenan, ni kuma na gano
cewa mijina da mutanensa bazasu taba komawa yadda
sukeba, face an yanka daya daga cikin wadannan yan matan
uku, sannan an basu jininta sun sha, sai dai ban san wadda ya
kamata mu yanka a cikinsu ba, kaga sai mun ganota kenan,
sannan kuma ba zamu taba samun nasarar yakar sarki amru
ba, face cikin wadannan diyan nasa yan mata uku, wata
cikinsu ta bamu hadin kai domin tayamu yakarshi, domin a
cikinsu akwai wadda tasan sirrin fada da shi, itama ban san kowa
cece ba, kaga sai mun ganota kenan.
To bayan milat ta tsaya nan, sai sarki marzuk ya fara magana,
wato ki sani yake wannan sarauniya, wannan abu da kika fadi
mai mutukar wuyane, domin jinsa nake kamar mafarki, tun da
kince dole sai cikin diyansa wata ta bamu hadin kai kafin mu
samu nasara akansa, nako san wannan bazai yiwuba, yama za
ayi diya da yaudari babanta, ni inaga mu tara mayakanmu
kawai mu kai masa hari, daga nan mu kasheshi, in yaso sai
mu dauki diyan nasa mu biya bukatunmu.
Wannan magana tasa milat tayi wani murmushi, har sai da
hakoranta suka fito, to anan sarki marxuk ya kara ganin surar
jikinta, anan ya gane cewa bako shakka kyakkyawa ce ta
gaske, cikin sanyin murya ta fara magana, wato ka sani shi
sarki amru daban yake da sauran sarakuna, domin fiye da shekara
talatin, ba a taba cin garinsa da yaki ba, haka kuma shi mutum
ne mai tsagwaron tsafi da sihiri, wanda idan kana fada dashi,
yakan yi amfani da wannan sihiri ya kasheka nan take, kai ko ni
nan a matsayina na sarauniya mai juya mutane da aljnnun duniya  ina tsoronsa, saboda haka dolene mu samo hanyar da
zamu sace wadannan yan mata a sirrance ba tare daya sani
ba, cikin gamsassar murya sarki marzuk ya amsa da cewa,
wannan shawara taki tayi, yanxu zan koma gida domin tunanin
mafita, in yaso wani lokaci sai in dawo domin mu kara
tattaunawa, daga nan sukayi sallama da sarauniya milat, yana
fita yaci karo da dokinsa, anan yayi mamaki yadda ya gane
wannan wuri, take ya hau dokin ya nufi hanyar komawa.
Haka sarki marzuk ya cigaba da gudu har ya kawo garinsa, to
bayan ya shiga cikin masarautar, take ya wuce zuwa dakinsa,
shigarsa keda wuya sai ya tarar da matarsa hamlat na gyaran
gashi, anan yayi mamakin ganinta, kome takeyi har yanzu
batayi bacci ba, daga nan sai ta fara yi masa magana, wato ka
sani xuwa wurin milat bashi kasa ka samu nasara ba, anan
sarki marzuk yayi mamaki, ya akayi tasan inda yaje, amma duk
da hakan bai nuna mata ba, kawai sai ya tambayeta, to
menene ya kamata inyi domin in samu nasara, anan tayi
dariya, wannan dariya taba sarki mamaki, domin hamlat bata
taba yin irin wannan dariya ba, anan ya fara tunani, wai ko
itace hamlat ta gaskiya.
Yana cikin wannan tunani kawai sai yaga idanun hamlat sun
canza kala sum koma ja, take maganarta ta canza, SAI MUN
KASHEKA, KUMA BA ZAKA SAMU NASARA BA. kawai sai yaga
ta rikeda ta zama wani tsuntsu mai fika fuki,, a guje tabi ta
taga ta tsere, daga nan sai ya nufi dakin hamlat din gaskiya,
anan ya isketa tana bacci, wannan ya tabbatar mai cewa,
wadda ya gani da farko ba mutum bace.
Dasanyi safiya sarki ya fara mamakin abunda ya faru jiya, to a
cikin wannan dare sai ya kasa bacci, kamar motsi ya jiya , anan
ya tashi domin ya duba, anan ya gane cewa hamlat ce ta fita
garin,to anan ya bita da nufin ganin ko me zai faru, haka
suka cigaba da tafiya har suka kawo bakin gulbi, kawai sai
yaga ta canza yare, anan ta fara fadin wasu kalmomi marar ma
ana, daga nan sai yaga wata katanyar halittar ruwa ta fito, ita
dai wannan halitta kamada doki gareta, sai dai tanada fika
fikai, kuma tafi doki girma sau goma, anan hamlat tayi
magana da wannan halitta, har zuwa kare maganarsu sarki
marzuk bayajin abunda suke fadi, to daga nan hamlat ta nufi
komawa fada, haka sarki ya cigaba da bin bayanta ba tare
daya bari ta ganshi ba, daga karshe kuma sarki yasha alwashin
sanin abunda hamlat ta gudanar tsakaninta da wannan halittar
ruwan.
A zaune yake saman kujera yana huci, ba kowa bane in banda
sarki amru, wasu YAN MATA UKU ne a zagaye dashi, bako
shakka wadannan yan matan diyansa ne, cikin wata murya mai
razanarwa ya fara magana, ku fada mun abunda ke tafe daku,
anan suhailat ta fara magana, wato ka sani abba mafarki nayi,
a cikin mafarkin naga wasu innuwowi tare da kibiyoyi suna
bina, gudu nake kamar raina zai fita, amma daga karshe saida
suka cimmin, to suna tabani sai na tashi daga bacci, wannan
mafarki ya bani tsoro mutuka.
Kufa meke tafe daku, inji sarki amru, tare sukayi magana,
suhaimat da nabilat, muma irin wannan mafarki mukayi.
Anan mamaki ya kama sarki amru, koya akayi mafarkinsu ya
zama iri daya, daga nan sai ya fara magana, wato ku sani
cewa wannan mafarki naku yana tattare da rudani, da farko dai
ku sani cewa rayuwarku na cikin hadari, domin wadannan
inuwowin da kuka gani na wata sarauniya ne, sai dai bazan iya
ganeta ba domin itama ba karamar hatsabibiya bace a fagen
sihiri, su kuma wadannan kibiyoyin da kuka gani na wani sarki
ne, shima bazan iya ganeshi ba, amma ku sani cewa, mutum
biyu ke farautar ku, kuma a koda yaushe zasu iya kamaku,
bansan abunda yasa suke farautarku ba, saboda haka yanzu
zan aike ku wani daji mai hadarin gaske, a cikin wannan daji
akwai wasu halittu kakkarfa dogaye, komi nasu irin na mutane
ne, sai dai sunada ijjiya guda a gaban goshinsu, da kuma
kahoni biyu, wadannan halittu ana kiransu da guzmar, sarkinsu
nada wata sarka ta sihiri, wadda ke rataye a wuyansa a ko
yaushe, to inaso kuyi dubara ku satomin wannan sarkar tasa,
domin akwa wani shiri da zamu hada da ita, amma sai kun
dawo zan gaya muku wannan shirin, rashin samun wannan
sarkar kan iya haifar da matsaloli a wurinmu, saboda haka kuyi
duk yadda zakuyi ku samota, wannan daji da nake gayamu, ba
a cin itatuwansa, kuma ba a shan ruwansa, akwai fitintunu da
dama a ciki, a nan sarki amru ya dauko wata tsuntsuwa ya
basu, wannan tsuntsuwar itace zata nuna muku hanyar wannan
daji, injishi, nan da sati biyu idan baku dawo da sarkar ba, to
rayuwarmu na cikin hadari babba, anan sarki amru ya tashi ya
tafi abinsa, su kuma su suhailat anan suka dulmiya cikin
duniyar tunani da kuma tsoro, ko ya za ayi su samo wannan
sarkar?

JARUMAN MATA 2
written by:
abdul king article
A tsaye yake yana kai komo cikin daki shi kadai sai kace
mahaukaci, yana cikin haka ne sai yaji an bude kofar dakin, da
sauri ya duba domin ganin ko waye, anan ya gane cewa
matarsa ce hamlat, rungumeshi tayi tana sumbatarsa, daga
nan sai ta fara magana, duk yinin yau baka ci abinci ba, ina
fatan dai lafiya, anan sarki marzuk ya mata wani kallo na zargi,
daga nan sai ya gyada kai yace ba komi, dama akwai wasu al
amurra da nakeson kammalawa, shine nake tunanin yadda zan
gudanar dasu.
Murmushi tayi, sannan daga bisani ta soma magana, kada ka
damu yakai mijina, nasan da cewa kana zargina akan fitar da
nayi a cikin dare ba tare dana gayama ba, yadda nima ina
zarginka akan tafiyar da kayi wurin sarauniya milat ba tare daka
gayamin ba, amma ba matsala, dani da kai duk abu guda muke
farauta, saboda haka idan lokaci yayi zan sanar dakai game da
wannan halittar ruwan da ka gani ina magana da ita, da kuma
abinda muka tattauna, anan hamlat ta juya ta fice daga dakin,
mamaki ne ya kama shi, wanda hakan yasa ya bita da kallo har
zuwa bacewarta, ko ya akayi tasan inda yaje? sannan ya akayi
tasan sarayniya milat? haka ya ci gaba da tunanin wadannan
amsoshin ba tare da sanin amsarsu ba.
Biki ne ya kaceme ciki da wajen masarautar, ko ina sai shagali
akeyi, sarki marzuk ya rasa dalilin wannan shagali, sannan
abunda ke bashi mamaki shine matarsa hamlat sai kaida komo
takeyi, anan ya tashi yasha gabanta, wai meke faruwane, ki
gayamin abunda kike shirin yi, injishi.
Haba hasken idona, ta ambata a cikin murmushi, tafiya takeyi
tana taku dai dai cikin rangwada, wato ka sani masoyina, yau
wani bako ne zamuyi wanda na gayyato daga birnin ansari, shi
wannan bako yanada abubuwan ban mamaki, sannan gashi
jarumi a filin daga, wannan ne yasa na gayyato shi domin ya
bamu kariya daga harin makiyanmu, domin rayuwarnu na cikin
hadari a ko yaushe, sunan wannan bako Ahlan, anan sarki
marzuk yayi dariya domin jin dadin kalaman da tayi, bako
shakka ke mai tunani ce, na dade dajin sunan wannan
mutumin, amma ban taba tunanin gayyayo shi ba, cikin wata
rangwada da ta soma yin tasiri akan sarki marzuk hamlat ta
fara magana, wannan ai ba wani abu bane, duk wannan bikin
daka ga na shirya na tarbonsa ne, a wannan lokacin jikin sarki
marzuk ya fara makarkata, saboda ganin surar hamlat, bai
tsaya ta gama magana ba kawai ya finciko ta da hannu daya,
cikin sauri ya wuce da ita daki, da karfi ya makata saman
gado, daga nan ya fara shirye shirye, haba masoyina ka tsaya
muyi ahankali mana, hamlat ta fada, to kafin su fara
gudanarwa kawai sai sukaji shewa da guda, take wuri ya kara
kacamewa, sai kida da busa ke tashi, wannan ya tabbatar
musu da cewa bakonsu ahlan ya iso, cikin sauri sukayi shiri, a
guje suka fita domin tarbarsa.
A wannan lokaci fada ta cika makil, a cikin wannan taro suka
shigo, jama a na ganinsu sai suka fara jayewa ana basu wuri
domin su samu damar shigowa, anan wasu dakaru suka tsaya
bayansu domin basu kariya, zaunawarsu keda wuya sai suka
hangoshi, tafe yake tare da jama arsa, shine a gaba, yaci ado
mirar misaltuwa, kayan sai kyalkyali sukeyi, to bayan ya karaso,
take aka nuna masa wurin zama tare da jama arsa, anan wasu
kuyangi mata kyakkyawa suka fara raba musu kayan abinci da
abinsha, to daga nan sai hamlat ta mike ta fara magana, muna
maka maraba da shigowa wannan birni namu mai albarka
yakai wannan bako ahlan, mun yi farin cikin zuwanka, tare da
amsa gayyatarmu dakayi, wannan ya nuna mana cewa kai mai
karamci ne, kuma bako shakka da sannu zamu kasance masu
adalci a gareka, saboda haka yanzu muna gayyatarka domin ka
nishadantar damu kafin mu fara shagali.
Anan ahlan ya mike, cikin kasaita ya karaso gaban jama a,
daga nan sai ya fara magana, ina mutukar godiya ga
sarauniyata hamlat, tare da mijinta mai girma marzuk, bisa ga
wannan tarba da kuka yimin, kamar yadda sarauniya ta fada, ta
umarceni da in tsayu a nan domin nishadantar daku da
abubuwan ban mamaki, bako shakka zanyi kamar yadda
sarauniya ta fada, yana gama fadin haka, sai kallo ya koma
wurinsa, anan jama a suka tsura masa ido domin ganin
abubuwan ban mamakin da xaiyi.
Taku ya fara yi dai dai cikin salon rawa, anan jama ar dake tare
dashi suka dauko wasu ganguna suna wani kidi mai dadin
sauraro, take suka zagayeshi suna irin takun da yakeyi, take
wannan salo ya canza zuwa rawa mai ban al ajabi, ita dai
wannan rawa a sama suke yinta, kuma ba sama can sosai ba,
iyaka mutane  sunga ahlan da jama arsa sun tashi sama
kamar tsuntsaye, daga nan suka fara tikar rawa mai ban
shawa, wannan rawa tasa mutanen fada suka fara shewa tare
da jinjina, sarki marxuk take ya fara dariyar farin ciki tare da
hamlat, anan mutane suka ci gaba da yi musu tabi.
Bayan sun dauki lokaci suna rawar, sai suka dawo kasa, suna
dawowa, duk sai suka rikede suka zama manyan tsuntsaye,
ahlan kawai ne ya tsaya da siffarsa da mutane, anan mutane
suka fara mamaki, ana cikin haka, kawai sai ga wasu manyan
macizzai suna shigowa fadar, anan mutane suka fara jin tsoro,
daga nan ahlan ya katsa musu tsawa da cewa, kowa ya tsaya
inda yake, macizan na gama shigowa, kawai sai suka fara
rikedewa zuwa mata kyakkyawa cikin shigar yaki, mutane na
ganin haka, take suka fara tabi da shewa, daga nan sai yaki ya
kacame tsakanin wadannan yan matan da mutanen ahlan da
suka zama tsuntsaye, amma ahlan bai shiga cikin wannan fada
ba, wannan yaki dai ya kasance gwanin ban shawa, duk
tsuntsun da suka sara sai ya rikede ya koma siffarsa ta ainahi,
haka wannan wasa ta cigaba da gudana cikin jin dadi, ana kare
wannan sai ayi wannan, haka ahlan da mutanensa suka yita
nishadantar da mutane har zuwa lokacin da bikin ya kai karshe,
to daga nan sai mutane suka watse, su kuma su ahlan aka
nuna musu masaukinsu.
Kwance take tana faman minshari, firgigit ta tashi saboda
yadda taji ana kwankwasa mata kofa da karfi, nabilat ce, to
bayan ta bude kofar sai ta ci karo da suhailat da suhaimat,
haba, a cikin wannan kulu kulun safiya kuke tayar dani, hala me
ya faru?inji nabilat.
Iye, wato kin ma manta da tafiyarmu ko, to yau zamuje
wannan dajin domin sato wannan sarkar ta sarkin guzmar, inji
suhailat, anan nabilat ta fara shiri suna kallo, bayan ta
kammala take suka hau dawakansu, anan suka fita daga garin,
suna fita suka saki wannan tsuntsuwar da abbansu ya basu,
kuma ya gaya musu cewa itace zata nuna musu hanya, anan
suka fara bin wannan tsuntsuwa, duk inda tabi nan sukebi.
Ahaka suka ci gaba da tafiya kwanci tashi har tafiya tayi nisa a
cikin daji.
Acikin wannan daji da suka samu kansu, bako shakka sun
galabaita, amma duk da hakan sun daure, dakyar suke takawa
cikin rashin kuzari da walwala, suhailat ce ta fara magana,
gaskiya ya kamata mu dakata da wannan tafiyar sai gobe, dubi
yadda muka gaji, kuma yan ruwan da mukayi guzuri dasu duk
sun kare, wannan magana ta suhailat tasa jikinsu yayi sanyi,
saboda haka suka dakata da tafiyar sai gobe.
A cikin wannan dare dai ba wadda tayi bacci a cikinsu, saboda
irin abubuwan al ajabi da suka faru a garesu, sai suna cikin
bacci suna ji kamar ana tashesu, da sun farka sai suga ba
kowa, ko kuma suji ana kiran sunansu daya bayan daya, kuma
basu ganin mai kiran.
Ana cikin haka nabilat taji ana kiran sunanta, anan ta kaikaici
idon su suhailat don kada su hanata xuwa, cikin sanda take
tafiya har ta kawo wani kogo mai girma, ciki duhu waje duhu,
amma haka ta daure ta shiga, tana shiga kofar kogon ta rufe
kaf.
Da sanyin safiya su suhailat suka tashi suna neman nabilat,
amma ko duriyarta babu, ahaka suka fara nemanta har suka
kawo bakin wani gulbi, basu dade da zuwa wurin ba sai suka
fara jin takun wani abu, anan suka labe domin ganin ko meye.
Wata halitta ce da basu taba gani ba, ashe dama akwai
samudawa har yanzu?inji suhailat, wannan halitta dai kirar
samudawa gareshi, kuma ijjiya guda gareshi a gaban goshinsa,
da kuma wasu kahoni biyu, tsawonsa ko yakai iccen dabino,
rike yake da wata kwalba, a nan suka kurawa kwalbar idanu,
take suka gane nabilat ce a ciki,kuma da ranta, tana kokarin
fitowa amma ba hanya.
Anan suhaima ta kurawa wannan dodon basamude idanu,
daga nan ta fara magana, bako shakka wannan na daya daga
cikin jinsin da ake cema guzmar, sune abba yace mu sato
sarkar sarkinsu, anan suhailat ta amsa da aa, ai ba wannan
dajin bane, in shine to ina tsuntsuwarmu.
Tare suka daga kai sama, anan suka ga tsuntsuwar tana
shawagi, hakan ya tabbatar musu da cewa wannan shine dajin,
anan suka yanke shawarar bin wannan basamude domin ganin
inda zai kai nabilat,  haka suka cigaba da binsa har ya
shigo wata masarauta da aka gina da dutse, to bayan sun
shiga masarautar ne, sai suka ga wadannan dodannin
samudawan da yawa, a nan suka ga wannan dodon dake
dauke da nabilat ya kai ta cikin wani daki ya tafi abinsa, anan
suka shiga cikin dakin suna faman bude kwalbar, wani gatari
suka dauko suka maka ma kwalbar, anan ta fashe, to karar da
kwalbar tayi ashe wasu dodanni sun jiya. anan suka sheko
domin ganin ko meke faruwa, a wannan lokaci su ukun sun
fito sun nausa cikin masarautar, suna cikin wannan gudu sai
sukaci karo da bataliyar dodanni a gabansu, anan su suhailat
sukayi cirko cirko domin ba wurin gudu, sarkinsu ne a gaba,
rataye da wannan sarkar da suke bida, basutsaya wani abu ba
sai suka zare makamansu, wani tsalle sukayi tare da finciko
sarkar da karfi, suna daukar sarkar sai suka juya baya da karfi,
suna fita sai suka ga wasu dakaru mutum dubu, anan
shugabansu ya umarci su dasu kawo sarkar, ko kuma a
kashesu, a bayansu kuma dodanni ne, suna bukatar sarkar
suma.
WAYE ZAI AMSHI WANNAN SARKAR?
ZAMU CIGABA...

JARUMAN MATA 3
written by:abdul king article

Suhailat cike take da mamaki ita da kannenta, a wannan lokaci
dai ba wurin gudu, a gaba ga dakarun dakeson sarkar, a baya
kuma ga dodanni nan, to bayan wani dan lokaci, sai dakarun
nan suka fahimci cewa wadannan dodannin suma sarkar suke
so, to anan shugaban dakarun ya bada umarni a fara yima
dodannin ruwan kibau, kai kace ruwan sama, haka ko akayi,
take wuri ya rincabe, cikin sauri su suhailat suka samu wurin
fakewa, anan suka gane cewa basu tsira ba domin dodannin
na kai musu hari, daga nan sukayi shawarar zare makamansu
domin afka ma wadannan dodanni, shugaban dakarun yaji
mamakin ganin yadda su suhailat ke fada, a cikin wannan yaki
sai shugaban dakarun ya fahimci cewa an kusa karar da
mutanensa, saboda haka yabada umarni kowa yayi takansa, to
suna cikin wannan gudu domin tsira sai suhaimat ta fadi, a
wannan lokaci kuwa dodanni kusan goma ne ke biyarta, cikin
sa a ashe shugaban dakarun ya hangota, saboda haka ya fara
yi musu ruwan kibau, dakyar dai ya cetota, to bayan sun samu
wurin hutawa, wadanda suka samu raunuka ana musu magani,
a ciki ko hadda suhaimat sai karaji takeyi, a nan shugaban
dakarun yazo wurinta rike da kyalle fari, ciyon da take dashi a
kafa ya fara shafawa yana addu a, nan take tayi shiru, alamar
ta daina jin ciyo, daga nan ya tashi ya tafiyarsa.
A cikin wannan dare shugaban dakarun ya dawo yana
tambayarsu ya jikin suhaimat, a nan sukace taji sauki yanzu
haka tana wurin motsa jiki, daga nan sai ya umarci su fada
masa inda take, a nan suka shiga gaba yana binsu har suka iso
inda take, a nan yaga tana koyon fada ita kadai, daga nan sai
ta tambayeshi wai wace addu a ce ya mata? A nan ya bata
amsa da cewa wannan itace addu a irin ta addinin musulunci,
wadda idan mutum yayi bako shakka zai samu saukin abunda
ke damunsa, a nan suka fara mamakin wannan ko wane irin
addini ne, daga nan sai nabilat ta masa magana da ko zai iya
fada musu takaitaccen tarihinsa, a nan ya fara da cewa sunana
amil, ni dan sarkin tanya ne, wannan sarkar da kuka amso
asalinta ta mahaifiyata ce, kuma sarkar kariya ce ga duk
wanda ya mallaketa, a shekarun da suka wuce wadannan
dodanni suka kawo muna harin sumame, a nan suka kashe
jama armu, kuma suka dauke wannan sarkar, saboda haka
yasa na fito domin ramuwar abunda suka yi muna.
Yana tsayawa nan sai sukaji guguwa ta zagaye wurin, to a cikin
guguwar sai sarki marzuk da sarauniya milat suka fito, hahah,
dama ku muke nema, inji milat. Ai nasan abinda ke tafe daku,
cewar amil, wato ku sani cewa wadannan yan mata uku
bazasu iya warkar da lalurar dake damunku ba, addua ce zata
iya, kai waye, kuma ya akayi kasan haka?inji sarki marzuk,
cikin murmushi amil yace idan baku yarda ba ku kaini wurin
iyalan naku in musu addu a, sai dai idan suka warke to zaku
gasgata addini na kubar bautar rana da tsafi, to anan sarki
marzuk da sarauniya milat sukayi shiru, bayan wani dan lokaci
sai sukace sun yarda, to anan suka fara tafiya domin zuwa
birnin sarki marzuk, domin shi za a fara yima addu ar, to akan
hanyarsu suka gamu da sarki amru, wato baban su suhailat,
anan amil ya masa bayanin kome, take sarki amru ya yarda zai
bisu domin ganin yadda zata karewa. Haka suka cigaba da
tafiya har suka kawo garin sarki amru, take amil yayi addu a
kuma ya amshi sarkar daga hannun su suhailat ya jikata ga
ruwa, sannan ya bada umarni a ba hamlat ruwan, wato matar
sarki marzuk, daganan suka wuce garin sarauniya milat, yayi
ma mijinta da mutanensa addu a, daga nan ya jika sarkar ga
ruwa,ya bada umarni a ba shi ruwan ya sha tare da mutanensa,
to ba a fi kwana biyu da hakan ba, sai ga hamlat ta samu ciki,
shi kuma mijin sarauniya milat sai gashi siffarsa ta ainahi ta
bayyana, da shi da mutanensa, wannan abu da amil yayi yasa
sarki marzuk da sarauniya milat suka musulunta, tare da jama
arsu, shima sarki amru da diyansa yan mata uku duk sun
musulunta, daga nan zumunci ya kullu ga wadannan sarakuna
da diyansu, da jama arsu gaba daya, wannan shine karshen
wannan labari. Alhamudullilah.
.
Written by: abdul king article

Post a Comment

0 Comments