Written by
abdul king article
A lokacin da matsanancin duhu ya zagaye ciki da wajen birnin,
wasu halittu kan farka domin gudanar da ayyukansu na yau da
kullum, wannan farkawa tasu ya haddasa wata kakkarfar
guguwa, wannan guguwa ta fara tsiri sama tana wani irin karaji
mai amo, da karfi wannan guguwa ta fara gudu tana buge
abubuwa, haka ta cigaba da shiga lungu lungu na garin tana
bannata kayayyaki.
Tafiya takeyi tana rangwada da taku dai dai sai kace marar jini
da tsoka, juyawa tayi da karfi sakamakon karar wani abu da
taji, wannan abu data gani ya tayar mata hankali, saboda haka
ta fara gudu domin samun mafaka, amma ina, haka wannan
guguwar ta cimmata, a nan guguwar ta daga ta sama, ita kuwa
sai ihu takeyi tana neman taimako, amma ina, haka guguwar ta
mata guntu guntu, wato kai daban, hannaye saban, kafafuwa
daban, anan matar ta fadi matatta.
Daga nan sai guguwar ta cigaba da tafiya har ta cimma wata
mota, saurayi da budurwa ne a ciki, yana shafa gashin kanta a
hankali, ita kuwa yarinyar sai wani nishi takeyi tana murmushi,
suna cikin haka ne sai sukaji kamar motarsu na tashi sama,
anan suka leko ta taga domin ganin abinda ke faruwa, kuwa
suka farayi domin guguwa ce ta daga motar sama, anan
guguwar ta jijjiga motar, daga baya kuma ta makata ga
katangar wani gida, take wadanda ke cikinta sukace ga
garinku, a haka wannan guguwa ta cigaba da keta gidaje tana
gudu, saurayi da budurwa ne a saman titi, sun rungume juna
suna tafiya, budurwar bata ankara ba sai jin tayi saurayinta na
kuwa, anan taga guguwa ta daga shi sama tana juyawa, akwai
wani dogon mashi mai tsini soke a saman wani gida, take
guguwar ta jefa shi saman mashin, a nan ya fadi matacce jini
na fita a bakinsa, ita kuwa budurwar gudu ta fara yi tana
neman taimako, a cikin wannan gudu ne guguwar ta cimmata,
daga nan ta tsaga kanta gida biyu, daga nan itama ta fadi ba
rai.
A haka wannan guguwar ta ci gaba da tafiya har ta cimma
wani matsakaicin gidan sama, tsiri tayi sama da nufin shiga
wata taga.
FARKON LABARIN
Meenat na cikin dakinta tana wasa da laptop, kawai sai taji
iska na damunta, da sauri ta tashi da nufin kulle tagar dakin,
cikin rashin tsammani sai taga an dagata sama an jefata
saman gado, wata guguwa ce ta shigo dakin, anan ta fara
zagayar gadon meenat, ita kuwa meenat take jikinta ya dau
rawa, ba a dauki lokaci ba sai guguwar ta nufi kasan bene, to a
wannan lokaci duk fitilar dake dakin ta mutu, anan meenat ta
fara lalube, dakyar ta lalubo madubin idonta "eyeglass"
Bayan ta sanya, anan ta tashi domin fita daga dakin, tafiya taji
ana tako benen da nufin shigowa dakinta, anan ta rasa abunda
zatayi, cikin tsoro ta koma saman gado tana makarkata, a
haka ta cigaba dajin wannan tafiyar, ana cikin haka ne sai taji
tsit, kamar an daina tafiyar, daga nan sai ta tashi tana laluben
kofar dakin, tana ciki haka ne sai taji an banko kofar da karfi,
wata fitilar hannu aka cinna mata ana kiran sunanta, MEENAT,
MEENAT, MEENAT, ke aunty ce ke magana, wai ina kike?
Meenat najin haka take ta sheko a guje ta rungume aunty
balkisu, lafiya naga idanunki sunyi ja?
lafiya lau aunty, meenat ta amsa,
A haka aunty ta jata suka yi kasan benen domin cin abincin
dare "dinner"
Meenat na cikin wani hali, duk da dai ta boye abunda ke
damunta a lokacin da aunty balkisu ta tambayeta, wannan
abun ban mamaki ba shine na farko ba a wurinta, tasha ganin
ire irensu tun tana karama, abunda ke daure mata kai shine
batasan abunda yasa hakan ke faruwa a gareta ba, gashi kuma
bata taba gayawa kowa ba.
Ummi wai me kikeyi ne haka? duk kin bata mana wuri da
abinci, aunty balkisu ta tsawata mata, anan ummi ta done kai
alamar jin kunya, suna cikin cin abincin, kawai sai sukaji an
bude kofar falon, ashe bafferh ne ya shigo, bafferh dai shine
saurayin meenat, wannan soyayya ta samo asali tun suna yara,
saboda haka iyayensu sun san da hakan, kamar dai kowane
lokaci bafferh kan shigo gidan yayi abunda yakesko kamar
gidansu.
Ummi ce ta tashi da sauri ta rungumeshi, to bayan ya kusanto,
cikin girmamawa ya gaida su, anan meenat ta masa wani kallo
mai bayyana tsintsar so, haka ya mayar mata da martani kafin
ya zauna, wow, amma wannan abinci yayi dadi, inaga bako
shakka gimbiyata ce ta dafa shi!!! ya fada, anan meenat tayi
murmushi tana kallonsa.
uhmm, aunty balkisu tayi kaki tana mai cewa, wace gimbiya
kuma, gimbiyar taka dako shayi bata iya hadawa ba, wannan
magana tasa su dariya gabaki daya, haba aunty... inji meenat,
gaskiya nifa..... anan ta juya musu baya tana ciccika cikin fushi,
bazan ma ci abincin ba........ta fada.
anan aunty balkisu ta fara lallashinta, haba yan mata, wasa fa
nakeyi, gimbiya uwar gimbiyoyi, kyakkyawa son kowa kin
wanda ya rasa, to yi murmushi mana, anan meenat ta dan yi
murmushi saboda jin dadin wadannan kalamai, haka su kuma
sauran mutanen gida sai suka fara mata tabi da jinjina, anan
gida ya kable da sowa.
Tun da safe tayi wani wanka, bayan kammala break fast sai ga
bafferh ya shigo gidan, cikin jin dadi suka nufi mota, bafferh ne
ke tukawa, to anan hira ta barke tsakaninsu, yau kasan munada
"EDS 201" inji meenat, anan bafferh ya kalleta, banason
wannan course din ko kadan, ni in badan keba dayau ko
makarantar bazanjeba, anan meenat tayi dariya tare da gyran
madubin idonta, haba to idan kace haka mu muce kaka? inji
meenat, juyawa yayi da nufun bata amsa, amma cikin sauri ya
juya matukin motar, anan suka fara ihu shida meenat, a
tsakiyar manyan motoci suke, sannan ga wata mota a gabansu
tana shirin afka musu, cikin sauri ya kara giya yana kokarin fita
tsakiyar motocin, wani irin gudu ne yake naban mamaki, yana
fita babbar motar na kawowa, cikin ilimi ya murza matukin
motar yana kaucewa, wannan bajinta da yayi taba meenat
mamaki, anan ta fara yi masa tabi, yaushe ka iya mota haka?
murmushi yayi ba tare daya amsa ba, haka suka cigaba da
tafiya har suka iso makarantar, bayan sun faka motar, kai
tsaye suka shiga aji.
Bayan awa biyu da kare lecture, kawai sai suka fito suka nufi
gida, to a wannan lokacin tare suke da kawar meenat wato
nabilat, itace a bayan motar, sai surutu kawai take rafka musu,
a haka suka cigaba da tafiya har suka zo wurin dazasu ajeta,
daga nan suka nufi gida, tun daga bakin gate sukejin hayaniyar
mutane a gidan, da sauri suka shiga domin ganin ko me ke
faruwa, ashe daddy ne ya dawo, cikin murna meenat ta fada
jikinsa, ahaka ya riketa sai kace karamar yarinya, to bayan sun
natsu, sai ya fara tambayarsu ya makarantar, daga nan suka
fara bashi amsa da cewa lafiya lau.
A cikin wannan dare dai meenat ta kasa bacci, saboda haka
sai ta shigo falo domin ta sarara, anan taci karo da daddy yana
ba aunty balkisu labari, a gefe guda kuma kaka zuwaira ce a
kishingide, gaskiya akwai matsala a wannan gari, inji daddy,
hala meke faruwa? kaka zuwaira ta tambaya, wato jiya mutum
dari biyar suka mutu sakamakon wata guguwa ta anoba data
bayyana, anan ya gwada mata labarin rubuce a jarida, ga kuma
hotunan wadanda suka nan birjik, meenat najin daddy ya fadi
wannan guguwa, take hankalinta ya tashi, domin kai tsaye sai
ta tuno da abinda ya faru da ita a baya na guguwa, a lokacin
data fara zagayar gadonta.
Kaka zuwaira ta nisa kafin daga bisani ta fara magana, ai kaine
sanadin kome, kasa daruruwan mutane cikin halaka, kuma ka
cuci muhibbat, ALLAH zai isar mata.
Haba kaka, ya kina irin wannan magana, ai abunda ya wuce bai
kamata ace kina tunashi ba, tunda yanzu dai komi ya wuce.
Wannan magana tasa meenat cikin rudani, anan ta fara tunani
wacece muhibbat? sannan kuma da gaskene mahaifinta shine
sanadin mutuwar mutuwar mutum dari biyar din da guguwa ta
halaka, to yaya akayi haka? meenat ta cigaba da wannan
tunani har daga karshe bacci yazo mata, saboda haka ta tashi
ta nufi daki.
Cikin wani kwaroro take mai duhu, gudu take iyakar gudu,
tamkar wani abu na binta, tana cikin wannan gudu sai taci karo
da wata mata, juyawa tayi da nufin komawa inda take, daga
nan sai matar ta mata magana, haba meenat, ya kina gudun
mahaifiyarki, ai nice na haife ki da cikina, daga nan sai matar
tace ki shiga dakin mahaifinki,zaki ga wani akwati baki boye,
inaso ki dauko akwatin ki duba abinda ke ciki, daga nan sai ta
nuna mata wata hanya, idan kikabi wannan hanyar ba mai iya
cutar dake.
Firgigit, meenat ta farka, wai ashe mafarki ne takeyi, wannan
mafarki ya bata mamaki, anan ta fara tunanin wacece
mahaifiyarta ta gaskiya, domin ita a tunaninta, aunty balkisu ce
mahaifiyarta.
Bayan safiya ta waye, sai meenat ta wuce kai tsaye cikin dakin
aunty balkisu, haka zaki shigo ko sallama babu, wai yi hakuri
aunty, meenat ta amsa, bayan sun fuskanci juna, daga nan sai
meenat ta fara magana, dama inaso in miki wasu tambayoyi
ne, wai don ALLAH me kika sani game da maganar da kaka
zuwaira ta fada jiya? gama fadin haka keda wuya sai taga
hawaye sun zubo a idanunta, kiyi hakuri aunty, ban fadi
wannan magana ba da nufin bata miki rai.
Ai ba shi nakema kuka ba, sai dai ina tunanin wani abu daya
daya faru shekaru da yawa, wato ki sani meenat, wannan
tambaya taki sirri ce, kuma mahaifinki bazai so in gaya miki
itaba, saboda haka kiyi hakuri, to aunty wai da gaske bake kika
haife niba? injiwa, ni na haifeki da cikina in baki sani baki sani,
to wacece muhibbat? meenat ta kara tambaya, haba meenat,
wadannan tambayoyi sunyi yawa, ya kina haka, to kiyi hakuri
aunty zan fita, daga nan sai meenat ta fita daga dakin, ita
kuwa aunty balkisu ta bita da kallo har ta bace.
To bayan meenat ta fita ne sai taji ana busa sarewa, juyowa
tayi taga ko su waye, anan taga bafferh tare da kawayenta
suna mata tabi, HAPI BIRTHDAY MEENAT, a guje suka sheko
wurinta suna tayata murna, daga nan sai ga daddy ya shigo da
wani katon cake, cikin gaggawa aka bata yuka ta yanka, daga
nan sai suka fara shagali da murna.
Bayan an gama wannan shagali kowa ya watse, sai daddy yayi
kiran meenat domin ta gyara masa daki, anan taji dadi domin
zata bincika ta gani in mafarkinta gaskiya ne, a haka ta shiga
dakin tana bincike maimakon gyara, lungu lungu sako sako,
cikin wannan kazamin binciken ne ta gano wani akwati karami,
cikin sauri takai akwatin dakinta, hakan ya tabbatar mata da
cewa mafarkinta gaskiya ne, a cikin wannan dare ta bude
akwatin, ga mamakinta sai taga littafi, da wani zobe, sai kuma
wasu kayayyaki wadanda batasan kansu ba, a makarin littafin
an rubuta MUHIBBAT, daga nan sai ta bude ciki, hoton wani
gida ne ta gani mai ban tsoro, domin anyi hoton a ciki dare, sai
kuma ga hoton daddy da wata mata, sai kuma gata a
tsakiyarsu a lokacin da tana yarinya, wadannan hotuna sun
bata mamaki, ko wane irin gida ne wannan, it kuma wannan
matar ko wacece, daga nan sai ta kara bude littafin, a nan taci
karo da wani labari, amma abunda ke bata mamaki shine, tana
fara karatun labarin sai taga wutar dakin ta dauke gaba daya,
da sauri da kulle littafin tana lalube, kulle littafin keda wuya, sai
taga wutar ta dawo, anan cigaba da karatu, kuma sai taga
wutar ta kara daukewa, tana kullewa kuma sai ta dawo, sau
biyar tana haka, daga nan sai ta gane cewa littafin bai
karantuwa, sabida haka ta aje shi saida safe.
Tun da sanyin safiya ta buda littafin, amma mamaki ba kome a
ciki, daga nan ta buga ma bafferh, shi kuma ya bata shawara
cewa suje wani wuri mai nisa su karanta littafin, to a cikin dare
suka shiga mota, anan sukayi tafiya mai nisa har suka shigo
daji, daga nan sai suka bude akwatin, a hankali suka dauko
akwatin, sunna budewa sai suka ga rubutun littafin ya dawo,
anan suka fahimci cewa lalle wannan littafin sihiri ne, zasu fara
karatun littafin kenan kawai sai suka ga ya tashi sama kamar
tsuntsu, anan suka fara binsa da nufin rikeshi, amma gudu
yake tamkar mai kafafu, haka wannan littafi ya ci gaba da
jansu har sukayi nisa cikin dajin, cikin wani kogo nai
matsananin duhu littafin ya shiga, anan sukayi cirko cirko
domin suna jin tsoron shiga kogon, juyawa sukayi da karfi
saboda wata kara da suka ji, anan sukaci da karo da itacen
dajin na tafiya, suna kokarin kawo musu hari, sannan a cikin
wannan kogon wani gurnani ke fitowa.
MEYE KARSHEN WANNAN LABARI?
ZAMU CIGABA...............
ABDUL KING ARTICLE
MU HADU A KASHI NA BIYU....
GIDAN FATALWA 2
kashi na biyu
Written by
abdul king article
TUNATARWA DAGA NA FARKO:
A cikin na farko mun tsaya a inda meenat da bafferh ke
kokarin karatun littafin sihirin da suka sato, cikin hakane littafin
ya tashi sama kamar mai fuka fuki, daga nan suka fara bin
littafin har ya shiga wani kogo, daga nan kuma sai suka fara jin
gurnani na fitowa a cikin kogon, haka zalika sai kuma ga wasu
itace suna tafiya da nufin kawo musu hari.
CIGABAN LABARIN:
Hankalin meenat yayi mutukar tashi ganin wannan abun ban
mamaki, shi kuma bafferh tsaye yake domin tun farkon
rayuwarsa bai taba ganin itace na tafiya ba, wani irin narkeken
reshen bishiya ya fado gabansu, ji kake duuum, anan suka fara
gudu tsorace, su kuma wadannan itace suka cigaba da jefa
musu bishiyoyi, a cikin wannan gudu ne meenat ta fadi, nan da
nan wani reshen bishiya ya laulayeta, kuwa ta fara yi tana kiran
sunan bafferh, cikin sauri ya juyo, a guje ya sheko da nufin
kawo mata dauki, gudu yake yana kaucewa itatuwa na fadowa
gabansa, a wanan lokaci ba karamar bajinta ya nuna ba, domin
a lokaci guda sai kaga icce goma sun fado suna shirin
makeshi, amma cikin jarumta sai kaga ya kauce, da sauri ya
riko hannunta, sannan ta tashi dakyar, daga nan suka cigaba
da gudu, a haka har suka kawo wata gada, wannan gada dai a
kasanta akwai ruwa, wasu zaratan kadodi ne a ciki, jira kawai
suke mutum ya fado su sami na kalaci, gashi gadar kuma
tsohuwa ce, domin wasu katakayyan da aka yita dasu duk sun
fara bantalewa, meenat ce a gaba bafferh na biye da ita, tana
aza kafarta a saman gadar take wane katako ya balle, a nan
ya fada cikin ruwan, wasu kadodi ne su bakwai suka fito a cikin
ruwan suna rigangan daukarsa, domin a tsammaninsu mutum
ne ya fado, a nan meenat taja baya tsorace, gaskiya bazan iya
hawa wannan gadar ba, injita, haba meenat, ya zaki fadi haka,
idan har baki hau wannan gadar ba, to dani dake duk zamu
rasa rayukanmu, inji bafferh, suna cikin wannan magana sai
sukaji saukowar wani abu duum, wani icce ne ya fado
gabansu, a tsorace basu san lokacin da suka hau wannan
gadar ba, meenat ce a gaba, saboda gudu bata ko duba inda
take takawa, saboda yawan takun da sukema gadar take ta
fara zaftarewa tana fadawa cikin ruwan, wannan ya tayar ma
da bafferh hankali domin shine a baya, kafin kaceme ya kara
giya, meenat ji kawai tayi ya wuceta shuiii, sai kace walkiya,
wannan abu yabata mamaki, a nan ta tsaya kallonsa, cikin
rashin sani sai kafarta ta fada cikin wani rami, a nan wani
katako mai tsini yayi tsalle ya fado mata a cinya, wata kara
tayi domin katakon shigewa yayi gaba daya, a nan jini ya
fantsama, wani irin radadi takeji sai kace wuta, ko tafiya ta
kasa yi, a nan ta fara tangal tangal kamar zata fada cikin
gadar, dakyar ta samu ta rike gadar da hannu daya, su kuma
kadodin sai faman tsalle sukeyi suna jiran ta fado su samu
abun kalaci, bafferh na can ganga, wato ya tsallake gadar,
wannan abu daya gani ya faru ga meenat yasa ya sheko a guje
da nufin taimaka mata, yana cikin wannan gudu ne sai ya
hango wasu halittu bakake a saman bakaken dokuna, su
halittun ba a ganin jikinsu domin komi nasu baki ne, su kuma
dawakan basuda idanu, domin wurin idanun like yake, amma
sai faman gudu sukeyi suna kokarin cimmusu, haka kuma
wadannan itatuwan suma biye suke da halittun, anan meenat
ta kwala ihu domin bafferh yayi sauri, bako shakka a wannan
lokaci halittun sun kusa cimmata, bafferh gudu yake iyakar
gudu, anan ya gane cewa idan yayi wasa fa meenat zata rasa
rayuwarta, wani irin tsalle yayi cikin gwaninta, da karfi ya jawo
meenat ta mike tsaye, anan ya dauketa ya aza saman
kafadarsa, gudu ya fara yi domin tsallake gadar, ita kuma
gadar ta fara ruzgawa, su kuma wadannan halittu su kusa
cimmusu, daga nan sai wadannan halittu suka fara jifar su
bafferh da itace masu ci da wuta, haka bafferh yayi ta
kaucewa yana gudu, kuma ga meenat saman kafadarsa, wato
nauyi saman nauyi, dakyar ya kawo bakin gabar, to a wannan
lokaci gadar ta kusa fadawa cikin rawa, domin rabinta duk ya
zabtare cikin ruwan, wani irin tsalle bafferh yayi sannan ya
tsallake gadar, yana tsallakawa ita kuma gadar ta fada cikin
ruwa gaba daya.
ZAINAB KING ARTICLE:
Bazamuyi labarin page zuwa page ba, sai dai zamu takaita shi
yadda zaku gane, zaku iya aiko mana sakonni zuwa wannan
email " abdulkingarticle@gmail.com" via zainab@novel.twitter,
frm the kingdom of article, the king of article, and the
legendary wizard of writting," neena novela.abdu
SAI KUN ZO
CIGABAN LABARIN:
To bayan bafferh ya tsallake gadar, kawai sai yaga wadannan
halittun dake binsu sunyi tsaye cirko cirko saman dawakansu,
wato kamar bazasu iya tsallako gadar ba tun da ta fada cikin
ruwa, a wannan lokaci ya ajiye meenat a kasa, sun tsayu suna
kallon ikon ALLAH, anan suka fahimci cewa,wadannan haliitun
basuda siffar mutane, haka kuma dawakansu, domin lullube
suke da wasu bakaken kaya yadda ko fuskarsu baxaka iya gani
ba, ko ka kalla sai dai kaga duhu, anan wadannan halittun suka
yi wani irin kuka, daga nan suka juya da dawakansu suka bar
wurin, to bayan tafiyarsu keda wuya sai su meenat suka nausa
cikin dajin suna tafiya domin samun hanyar da zata fidda su,
meenat gurmunta takeyi saboda raunin da ta samu a cinya,
suna cikin wannan tafiya sai sukaji kukan mota a gabansu, a
nan mamaki ya cikasu, to bayan motar ta kawo wurinsu, a nan
ta tsaya, cikin razana sukayi tsaye kikam suna jiran me zai
faru, wani mutum ne ya fito a cikin motar sanye da malfa, ku
meyaku cikin wannan daji mai hadarin gaske? ya tambaya,
cikin sauri meenat ta fara yi masa bayani, ai mu dalibai ne
daga state university ta wannan garin, kuma munzo wannan
daji ne domin gudanar da bincike "reseach"
Anan wannan mutumin ya girgiza kai, toni sunana ali sarkin
baka, Kuma nine shugaban wannan daji, haka zalika ni
mafarauci ne, to amma ya naga kamar kun galabaita, daga nan
sai meenat ta bayyana masa irin bala in dasuka hadu dashi, a
nan wannan mafaraucin ya tausaya musu, daga nan sai yazo
wurin meenat, hannunsa ya aza saman raunin data samu a
cinya yana fadin wasu kalmomi a cikin zuciya, wasu ruwa
kawai suka gani suna fitowa a hannunsa, ruwan na tabin raunin
sai kawai fata ta fito a wurin, take tambon ya bace, sai kace
bata taba jimuwa, kuma tabar jin ciyo, a anan suka gane cewa
lalle wannan mutumi ba kanwar lasa bane a wurin sihiri.
To bayan da meenat ta warke sarai, kawai sai suka hango wani
katon gida, a nan ta gane gidan, domin shine taga hotonsa a
wannan littafin da suka sato, a nan ta umarci bafferh dasu je
gidan, shi kuma mafaraucin sai ya fara yi musu bayanin akan
gidan, ai ku sani, bala in dake cikin wancan gidan, to yafi
wanda kuka sha a baya, a nan ya shiga motarsa ya tafi, bafferh
fada ya fara yi mata, duk laifinki ne, gashi kin masa karya ya
tafi ya barmu, kinga da bai tafi ba da sai ya nuna muna hanyar
fita wannan daji, anan meenat tayi murmushi tana mai cewa,
ai tafiyarsa nada amfani garemu, kaga yanzu sai mu cigaba da
binciken wannan littafin har sai mun ganshi, anan bafferh ya
harareta, ya za ayi muga wannan littafi, bayan mun barosho
cikin kogo, kuma hanyar da zata kaimu wurin ta lalace
balantana mu bita. inji bafferh.
To naji, yanzu sai kazo muje wancan gidan da muka hango,
domin shine naga fotonsa a cikin wannan littafin, daga nan
suka fara tafiya xuwa wannan gida, suka manta da gargadin
mafarauci.
To bayan sun kawo gidan, sai sukaga an ajiye motoci kala
kala, bayan sun zo gaf da motocin, sai sukaga mutane na
fitowa cikin motocin, daga ciki harda aunty balkisu da daddy,
anan mamaki ya kamasu meenat, koya akayi sukazo wannan
daji?to me ya kawosu?
Aunty balkisu ce ke tafiya cikin rangwada har ta kawo wurinsu,
marin meenat tayi har sau biyu, sannan ta jawo kanta ta buga
ga glass din mota, har sai da glass din ya fashe.
KU DAURE MIN SU!!!
Taba wasu samudawa umarni, anan aka daure meenat da
bafferh, wata kaca ce aka dauresu da ita yadda ko motsi basa
iya yi, daga nan sai ta fara tambayarsu, ina littafin da kuka
sace?
Anan meenat ta kalli bafferh, daga nan suka done kai kasa ba
tare da cewa uffan ba, cikin fushi aunty balkisu ta amso wata
karamar bindiga daga hannun masu tsaronta, "pistol" halbawa
tayi sau uku domin ta nuna musu cewa akwai harsashi ciki
"bullets" daga nan sai ta aza bindigar saman kan bafferh, zakiyi
magana ko sai na fasa kan saurayin naki!!! inji aunty balkisu,
shi kuma daddy kallonsu yake ba tare daya ce kome ba, daga
nan sai meenat ta fara magana, haba daddy ka taimake mana,
kana ganin abunda aunty ke shirin yi? daga nan sai daddy ya
fara magana, bazan iya taimakwanki ba meenat, face idan zaki
fada muna inda kuka aje wannan littafin, domin nima ina bayan
auntin ki.
Wani kallo aunty balkisu tama meenat, ke, ki sani ni ba
mahaifiyar ki bace, kije can ki bidi mahaifiyarki ta gaskiya,
wannan magana tasa hawaye sun zubo a idanun meenat, haka
shima bafferh tausayinta ya kamashi, to wacece mahaifiyata ta
gaskiya? meenat tambaya, yauwa, kinga sai ki fadamin inda
kuka ajiye littafin kafin na baki wannan amsar, inji aunty
balkisu.
Kusan minti sha biyar meenat batayi magana ba, daga nan sai
daddy ya bada umarni a kaisu cikin wannan gidan a kulle, hako
ko akayi, ita kuma UMMI sai kallonsu take, wani matsiyacin
duhu ne a cikin gidan, daddy da aunty balkisu na a cikin daki
daya, haka suma mutanen da akazo dasu duk an basu
masauki.
To bayan kowa yayi bacci a cikin gidan, meenat ita kadai ce
cikin wani wuri mai mugun duhu, gashi ba wuri guda ne aka
ajesu tare da bafferh ba, saman kujera take daure da kaca,
kawai sai taga an bude kofar dakin, ashe ummi ce rike da
yuka, anan ta bada yukar tana mata umarni data yanke kacar
ta gudu, anan meenat ta shiga yanke kacar, ita kuma ummi sai
ta fita a guje domin kada a ganta, to bayan meenat ta yanke
kacocin, sai taga duhu yayi yawa, saboda haka sai ta fara kiran
ummi domin ta kawo mata mata fitila.
UMMI,UMMI, UMMI, wai ko batanan, anan taji shiru, cikin sauri
meenat ta mike,a hankali ta fara takowa kasan benen domin
ganin ko meke faruwa, tsoro ya dabaibaye zuciyarta, kuma
matsanancin duhu daya mamaye wurin gaba daya, takawa
takeyi guda guda cikin tsoro, tana cikin wannan tafiya sai ta
hango wani abu kamar mutum, a lullube cikin bakaken kaya,
anan jikin meenat ya dau rawa, ta rasa abunyi, juyawa tayi da
nufin komawa, cikin mamaki sai ta kara ganin irin wannan
halittar a bayanta, to a wannan lokaci tsoron dake jikinta ya ya
harzuka mutuka,batasan lokacin data fadi ba, a haka ta cigaba
da mirginowa kasan benen har ta kawo kasa, a wannan lokaci
dakyar take nishi, to bayan ta tashi, abunda ya daure mata kai
shine bataga wadannan halittun bakake ba.
Anan ta cigaba da tafiya a hankali tana kiran ummi, tana waige
waige saboda tsoro,bata ganin ko tafin hannunta, sannan
abunda ke ke damunta shine me yasa duk fitillun gidan sun
mutu? kuma ita ummi inata shiga ne? a haka ta cigaba da
tafiya har ta shigo wani daki, shogowarta keda wuya sai taga
fitila, anan ta kunna, jin dadi tayi saboda ganin wani fanfo,cikin
sauri takunna fanfon domin shan ruwa, ihu tayi domin jini ne
ke fitowa maimako ruwa, juyawa tayi da nufin fita, kawai sai
taci karo da karamar yarinya, laa ummi, ina kikaje ina neman
ki, anan taji shiru, kuma gata rike da wani gatari, kuma
idanunta duk sun juye zuwa ja, da karfi meenat ta kaucema
saran data kawo mata, anan ta fitabdakin a guje, cikin wannan
gudune sai taci karo da wani abu, anan ta fadi, ahankali ta
dago kanta domin ganin ko meye, anan ta gane cewa
wadannan halittun ne bakake data gani dazu, ihu tayi sannan
ta nufi wani daki a guje, kullewa tayi tana nishi, shigarta keda
wuya sai ta kara ganin wannan halittar baka kirin, a guje ta
nufo kofa da nufin guduwa, to kafin ta kawo ga kofar, sai taji
anan bugunta da gatari, wato anaso a ballata da karfin tsiya a
shigo ciki, taga ta leka da nufin guduwa, sai taga duk itatuwan
dake dajin sun zagaye gidan yadda ba wurin gudu, a wannan
lokaci wannan halittar ta kusa cimmata, haka kuma kofar
dakin ta kusa karyewa saboda bugun da tasha da gatari, anan
ta hango watarijiya a cikin dakin rufe da marfi, kawai sai taga
an budeta, ashe bafferh ne, to anan ya mata umarni da ta
shigo ciki, rijiyar kamar hanya take, wai ya akayi ka kubuta
bayan da suka daureka anan, inji meenat, anan ya bata amsa
da cewa ai ummi ce ta kawomin yuka domin in taimaki kaina,
anan taji mamki to meyasa ummi keson kasheta? suna cikin
gudu sai suka hadu da aunty balkisu tare da jama arta, wato
kunaso ku gudu ko, to ku sani bazaku tona sirrin da muka
binne shekaru da dama ba, anan ta bada umarni da aka masu,
to kafin a aiwatar, kawai sai kasa ta fara girgiza, tana tsagewa,
anan wadannan mutanen suka fara fadawa ciki, sai kuma wasu
kibiyoyi da ba asan inda suke fitowa ba suka fara kashe
jama.a, idan kibiyar ta shiga jikin mutum, sai dai aga yayi
kunburi ya fashe.
MEYE KARSHEN WANNAN LABARI?
ZAMU CIGABA....
MU HADU A KASHI NA UKU..
ABDUL KING ARTICLE
GIDAN FATALWA 3
kashi na uku
Written by
abdul king article
TUNATARWA DAGA NA BIYU:
A cikin littafi na biyu, mun tsaya inda bafferh da meenat suka
hadu da aunty balkisu tare da jama arta wato matsu tsaronta a
cikin wannan rijiyar mai kamar hanya, a inda ta bada umarni a
kamasu, to kafin a aiwatar sai kasa ta fara girgiza, haka kuma
wasu kibiyoyi da ba asan ta inda suke fitowa ba suka shiga
kashe jama a, wanda idan kibiyar ta shiga jikin mutum, sai dai
aga yayi kunburi ya fashe.
CIGABAN LABARIN:
Bala i yayi bala i, domin ta koina kibiya fitowa take, saboda
haka hanjin mutane sun yawaita a kasa, jini sai malala yake
tamkar ruwa, to a wannan lokaci aunty balkisu ta rude, domin
mafi yawan masu tsaronta sun mutu "security agents" to ana
cikin haka sai wasu daga cikin mutanenta suka zo da wata
shawara, cikin sauri suka fito da garkuwa domin kare
wadannan kibau, "protector" cikin dubara suka hada wani
sahu, daga nan sai su aunty balkisu suka koma bayansu,
meenat ko magana bata iya yi saboda tsoro, haka suka cigaba
da tafiya cikin wannan sahu, duk kibiyar da tazo sai dai ta
tsaya ga garkuwar, an dauki lokaci wadannan kibiyoyin na
fitowa kafin daga bisani su dauke gaba daya, to bayan kibiyoyin
sun dauke, sai dakarun suka aje garkuwowin, suna duban inda
kibiyoyin ke fitowa, basa ganin kome face tsananin duhun daya
karwade wurin gaba daya, anan wasu daga cikinsu suka fara
yadiya da fitila " torchlight" sai dai fitilar batada haske sosai,
saboda haka duhun ya rinjayi fitillun, daga nan sai suka fara jin
wani ruri marar dadi, wanda hakan yasa kowa ya like
kunnuwansa, kuma abun mamaki basa ganin mai yin rurin, da
sun haska wurin sai dai suka ga duhu, gaskiya ni bazan iya
zama a wannan gida ba, tsoro nakeji!!! inji meenat.
Yi shiru, banza, ai duk kece kikaja, yanzu zamu cigaba da
tafiya domin mu samu hanyar fita, aunty balkisu ta fadi cikin
fushi, to daga nan sai suka cigaba da tafiya cikin wannan rijiyar
"underground" suna waiwaye waiwaye, kowanensu idanunsa
sun fito saboda tsoro, domin ji suke a kowane lokaci za a iya
kawo musu hari, to suna cikin tafiyar sai suka kawo wani wuri
da anyi zane zane a bangon wurin, anan suka fara kallon zane
zanen domin da fenti ja aka yishi, wasu kwarangwal din
mutane ne aka zana, sai kuma wata mata mai siffar dodanni
tana kalaci da naman mutum, anan suka cigaba da kallon
wadannan zane naban mamaki, shi kuma bafferh kome ya
kaishi, hannunsa yasa ya shafi wani zane, yin haka keda wuya,
sai suka fara jin wani rugugi, kamar ana magana amma basajin
abunda ake cewa, cikin rashin tsammani sai sukaga wani abu
mai kamada maciji, sai dai jikinsa dauri gareshi, kuma bayada
kafafu balantana idanu, cikin sauri wannan abu ya laulaye daya
daga cikin dakarun aunty balkisu, haka wannan mutumi ya fara
ihu yana neman taimako, amma ba mai iya zuwa wurinsa,
kafin kaceme wannan abu ya wuce da wannan mutumi, cikin
minti biyu sai aka jefo musu gangar jikin wannan mutum, kai
daban, hannaye daban, kuma kafafuwa daban, duk an masa
guntu guntu ba kyan gani, wannan abu ya mutukar tayar musu
da hankali, anan suka fara gudu, kowa na ta kansa, aunty
balkisu ce ke basu umarni inda zasu shiga sai kace tasan
gidan, wannan abu yaba meenat da bafferh mamaki, anan suka
fara tunani wai ko batada nasaba da wannan gida?
To suna cikin wannan gudu ne sai wannan abun ya dawo, cikin
sauri ya kara laulaye wani daga cikinsu ya wuce dashi, abokin
wanda aka laulaye ya kasa hakuri, saboda haka ya bi shi domin
cetoshi, anan su aunty balkisu suka rikeshi suna bashi hakuri,
amma ina ya kasa jurewa, sai kuka yakeyi yana kiran sunansa,
AL AMEEN, ihun al ameen din sukaji tare da ganin guntattakin
jikinsa, anan suka tashi kowanensu yacigaba da gudu, suna
cikin gudu sai suka kawo ga wani wuri mai matattakala, a can
saman wurin akwai wata kofa wadda zata fiddasu daga cikin
rijiyar, cikin sauri kowanensu ya fara tattakawa yana kokarin
fita, turanni in tureka suke, suna cikin wannan hali sai wannan
abun ya kara dawowa, wani ya laulaye sannan ya wuce dashi,
ganin haka yasa kowanensu ya kara himma ganin cewa ya fita
daga wurin, cikin kuzari meenat ke kutsa kai ganin cewa ta fita,
amma a duk lokacin data tunkaro wurin sai wani yasha
gabanta ya wuce, haka meenat ta cigaba da kokari amma duk
a banza, kafin kaceme kowa ya haye ya barta, anan ta fara
kokarin hawa cikin tsoro tana waige waige, fara takawarta
keda wuya sai sukayi ido biyu da wannan halittar mai kashe
mutane, anan jikin meenat ya dau rawa, sukuma wadanda suka
samu damar hawayewa sai suka fara yi mata magana, suna
bata umarni da tayi sauri, haka meenat ta cigaba da takawa
jikinta na rawa, shi kuma wannan halittar kokarin cimmata
yake, anan yayi wani tsalle ya riko rigar meenat, to a wannan
lokaci tana gab da fita, shi kuma bafferh yana ganin abunda ke
faruwa sai ya zaro wata karamar yuka, rigar meenat ya fara
yankewa har sai da katse wurin da wannan halittar ya rike rigar,
daga nan sai ya jawota da karfi, tana fitowa suna kulle kofar, ji
kake baaaam.
Anan sukayi tsaye suna nishi, kai da gani kasan sun gaji, daga
nan sai suka cigaba da tafiya har suka shigo wani daki, inda
sukaga daddy da ummi na bacci, wannan abu yaba meenat
mamaki, anan ta tuno lokacin da ummi ke binta tana kokarin
kasheta, kuma gashi yanzu ta sameta tana bacci, to ya haka?
Aunty balkisu ce ta matsa da bugunsu har sai da suka tashi, ku
bakuji abunda ke faruwa damu neba? anan suka amsa da
basuji komeba, anan meenat taja ummi gefe tana tambayarta,
ke da kika bani yuka nida bafferh ina kikaje? meenat ta
tambayeta, anan ummi ta amsa da cewa, bayan na baku yuka
domin ku kwance kanku keda bafferh, anan dakin na shigo na
tarar da daddy na bacci, daga nan sai na kwanta nima na fara
bacci, daga nan ban dan abunda ke faruwa ba sai yanzu da
kuka tasheni, inji ummi, anan meenat ta shiga mamaki, kenan
waccan ummi data gani tanason kasheta bata gaskiya bace,
wannan itace ta gaskiyar.
Bayan kamar minti goma, sai aunty balkisu ta dauki fitila da
niyyar zuwa ban daki, anan ta fita, cikin tsoro take tafiya tana
waige waige, kamar ana tafiya bayanta takeji, anan tayi tsaye
cif ta kasa motsi, rike take da fitila jikinta na makarkata, kuma
ta kasa juyawa baya balantana taga ko meye, ana cikin haka
sai taga jini na zuba ga kafafunta, anan ta juyo a hankali, ihu ta
buga, wani hannu ta gani duk kassa, ba tsoka a ciki, a guje
tayar da fitilar ta nufi dakin data baro, anan ta fara kwankwasar
kofar domin a bude mata, amma ina basaji, can kuma sai ta
hango wani haske, wata mata ce a cikin hasken sai dai bata
ganin matar da kyau, domin dushi dushi take gani, anan ta
cigaba da kwankwasar kofar domin a bude mata, shi kuma
wannan hasken mai dauke da matar ya cigaba da nufota, wata
juwa ta fara gani, kafin kaceme ta fadi, batasan inda take ba.
Mutane ne kewaye da wani gado, a saman wannan gado aunty
balkisu ce, fita ake mata domin ta farfado, daganan sai ta fara
bude idanu a hankali, can sai ta budesu gaba daya, da karfi ta
tashi.
INA TAKE? abunda ta tambaya kenan.
HALA WACECE? daddy ya tambayeta, anan aunty balkisu ta
kankane jikinsa tana kuka, ashe bata mutu ba, dama tana raye,
ta fadi cikin kuka, ki gayamin wacece mana?
MUHIBBAT!!! inji aunty balkisu.
Ina bazai yiwu ba, inji daddy, domin ni na turbudeta da kaina,
kuma yanzu an fi shekara goma da mutuwarta, anan dai aunty
balkisu ta kara kankane jikinsa tana kuka, nidai na tuba, kuma
yanzu inaso ka nemo muna hanyar fita cikin wannan gida.
Wannan magana taba meenat mamaki, domin kaka zuwaira ta
taba yin magana akan muhibbat, a lokacin da daddy yazo mata
da labarin cewa guguwa ta kashe mutum dari biyar, kuma ta
taba ganin an rubuta sunan MUHIBBAT a wannan littafin data
tsinta cikin akwati, to tambaya anan shine wacece muhibbat?
haka wannan tambaya ta cigaba da damun meenat, anan ta
kasa samun sukuni sai da ta gabatar da ita gaban daddy.
Wato ki sani meenat bazan iya amsa miki wannan tambaya ba,
sai yanzu zan kira kaka zuwaira domin ta bayyanar dake
abunda ke damunki na daga wannan tambayar, anan daddy ya
dauko laptop dinsa, kunnawa yayi, daga nan sai ya kira aunty
zuwaira, fuskarta ce ta bayyana ga screen din laptop din, daga
nan sai daddy ya fada mata abunda meenat ke son sani,
murmushi kaka zuwaira tayi, su kuma sai kallon fuskarta suke,
daga nan sai ta fara labari kamar haka:
Tun kafin a haifeki meenat, babanki wato daddy ya sayi
wannan gida da kuke ciki a yanzu, domin yasa amaryarsa a
ciki, wannan amarya tasa itace mamarki, kuma itace ake kira
MUHIBBAT, na masa fada a lokacin da ya sayi wannan gida,
domin gidan ya kasance tilo a tsakiyar daji, amma haka
babanki ya kanne akan yanason gidan, to bayan an daura
aurensa da muhibbat, bayan wani lokaci, sai ya hadu da aunty
balkisu, wadda suka far soyayyar boye da ita, ita kuma balkisu
batasan yanada mata ba, wata rana sai ta kawo masa ziyara, a
wannan lokaci kuma bayanan, to anan taci karo da muhibbat,
daga nan ta gane cewa yanada mata, rikici ne ya kullu
tsakaninsu harda buge buge, to a cikin wannan fada ne balkisu
ta samu nasarar buga ma muhibbat tangaram, anan muhibbat
tace ga garinku, to bayan daddy ya dawo, anan ya rasa abunda
ke masa daddy, ke kuma lokacin kina jaririya, domin kwananki
hudu, to anan daddy ya yi kokarin turbude muhibbat a cikin
wannan gidan, haka ko akayi, a nan ya gina mata kabari cikin
gidan, daga nan kuma sai ya auri aunty balkisu, to wannan
shine takaitaccen labarin muhibbat, inji kaka zuwaira, wannan
labari yasa meenat ta mutukar bayyana haushinta ga aunty
balkisu, domin ji take kamar ta kasheta.
To menene ke bamu tsoro a cikin wannan gida? meenat ta
tambaya, daga nan sai kaka zuwaira ta bata amsa da cewa,
idan aka rufe gawar mutum a gida, to hadari ne zaman wannan
gida, domin ruhin mutumin kan iya zamar muku matsala,
sannan wannan gidan da kuke gani, na dade inajin labarinsa,
yafi shekara dari gine, asalinsa na wani mai kudi ne, shi ya
gina shi, amma saboda yawan tsoron da ake bashi, dole yabar
gidan, haka wani ya saishi, shima dakyar yasha, dole yabar
gidan, daga nan sai mahaifinki shima ya saya, kinga tun asali
wannan gidan ba mai kyau bane, daga nan sai laptop din ta
dauke saboda rashin caji, daga nan sai daddy ya basu umarni
dasu tashi su samu hanyar fita daga gidan, gaba dayansu suka
tashi, anan suka fara tafiya cikin tsoro, basuyi nisa ba sai
wannan halittar ta dawo, cikinsu ta dauke wani, yana karaji ta
wuce dashi, to a wannan lokaci sun kawo daf da kofar fita,
amma kuma taki budewa, to anan aunty balkisu tayi tsintuwar
wata takadda wadda aka yi rubutu da jini kamar haka: SAI NA
KASHEKI.
hankalinta ya tashi, amma haka ta daure, wani irin mugun bugu
daddy yama kofar, daga nan sai ta bude, budewar kofar keda
wuya sai wannan halittar ta fito, anan ta laulaye mutum biyar ta
wuce dasu, wato saura daddy, aunty balkisu,ummi,bafferh, da
meenat, sauran security agents duk sun mutu, kusan su
hamsin.
Suna fitowa daga gidan, sai wani haske ya bayyana a kofar
gidan, wata mata ce a cikin hasken, kawai sai aunty balkisu ta
tsaya tana kallon hasken, a wannan lokaci wannan halittar ta
dawo, kafin kaceme ta laulaye aunty balkisu, ita kuma ummi ta
fasa wata irin kuwa ganin mahaifiyarta cikin wani hali, anan ta
sheka a guje da nufin kai mata dauki, meenat ce ta riketa don
kada taje ta halaka, kiyi hakuri meenat, bazan iya rayuwa ba
idan bada momina ba, injita, daga nan ta kubce ta nufi wurin
halittar, aiko tana zuwa itama aka laulayeta, shi kuma bafferh
zuciyarsa ta kawo, anan yayi wani tsalle da nufin kai dauki,
halittar ce ta cabe shi, daga nan sai halittar ta shiga dasu cikin
gidan suna ihu, ita kuma wannan matar a cikin haske
murmushi tama meenat kafin daga bisani ta bace, anan
meenat ta gane cewa matar tayi kamada wannan data gani
cikin littafi, bako shakka itace muhibbat, wato mahaifiyarta,
anan meenat ta nufi gidan a guje, tana zuwa kofar gidan na
kullewa, haka ta duka tana kuka, gashi kuma tanajin ihun su
bafferh a ciki, anan daddy yazo wurinta yana lallashinta, daga
nan sai yaja hannunta suka shiga cikin mota, wato su biyu
kawai suka rage cikin taron jama a, a haka daddy ya fara tuka
motar yana fita kokarin fita daga dajin, to bayan sun isa gida
ne, sai kaka zuwaira ta fara lallashinta, su bafferh basu mutu
ba, kada ki damu meenat, anan meenat ta fara kallonta cikin
mamaki, daga nan sai kaka zuwaira ta cigaba da bayani,
wannan littafin da aka rubuta labarin muhibbat ta dauko, laa ya
akayi kika sameshi? meenat ta tambaya, ai ali sarki baka ya
kawo min shi, wato ki sani meenat, a binciken da nayi da nayi,
na gano cewa mahaifiyarki muhibbat bata mutu ba, domin a
lokacin da a lokacin da aka turbudeta, ashe wannan hakittar
ce ta tona kabarinta ta cinyeta, saboda haka sai ruhinta ya fita
daga gangar jikinta, to wannan ruhin ne ke baku tsoro, kuma
shine kuke gani matsayin haske, akwai wasu ruwa da ake
cema RUWAN SIRRI, da zaran an ba halittar wadannan ruwan,
to ba ko shakka zata amayo duk abunta ta hade, to a cikin
wannan amai ne zamu gansu, sai dai ruwan basu cikin wanan
duniyar da muke takawa, suna can wata duniya daban, aiko
duk inda suke sai na nemosu, inji meenat, daga nan sai kaka
zuwaira ta bata wata sarka, wannan sarkar tsari ce, ki riketa
sosai, kuma da itace zaki iya dawowa wannan duniyar, daga
nan sai kaka zuwaira ta bude wannan littafi, anan ta fara
karanta wadansu kalmomi marar ma ana, wani bacci ne mai
nauyi ya dauki meenat, daga nan kuma sai wata guguwa ta fito
ta dagata sama, anan wannan guguwar ta cigaba da tafiya da
meenat sama domin kaita wannan duniyar da zata nemo
RUWAN SIRRI. kaka zuwaira da daddy sai daga mata hannu
suke har ta bace suka bar ganinta.
WANNAN SHINE KARSHEN LABARIN GIDAN FATALWA, SAI
DAI ZAMU HADU A WANI LABARI MAI SUNA ( RUWAN SIRRI )
WANNAN LABARI SHINE CIGABAN GIDAN FATALWA, KUMA A
CIKINSA NE ZAMUJI GWAGWARMAYAR DA MEENAT TASHA
DOMIN SAMO RUWAN, DA KUMA YADDA SU BAFFERH ZASU
TASHI, MUNA BAKU HAKURI DOMIN LITTAFIN BAZAI FITO BA
SAI BAYAN SALLAH, AMMA YANA FITOWA ZAMUYI POSTING
DINSA, MUNA GODIYA.
abdul king article
To be continue in ( RUWAN SIRRI)....
0 Comments