HUSNAT

HUSNAT
written by :
abdul king article

A guje take gudu bata ko tsoron faduwa, wannan gudu nata ya
mutukar ba mutane mamaki, saboda haka wasu kan tsayu
domin kallon ta, amma ko kadan bata kulasu ba, iyaka dai ta
tunkari abunda ke gabanta.
Fara ce doguwa, kyakkyawa abar kwatance, amma duk da
wannan kirar da aka yi mata, bata damu da wani abu ba face
famar gudu, shin ko ina zata?
Bayan kamar minti uku sai ta iso masarautar, a wannan lokaci
tayi zufa kamar ranta zai fita, cikin sanyin murya tayi magana,
wanda hakan yasa wani bafade ya bude mata kofar, to bayan
shigarta ne sai taga bafaden na mata wani kallo.
Husnat taso ta karasa, amma daga baya sai ta tsaya domin
tambayarsa, haba ilu, ya kana min wannan kallon, ina fatan dai
lafiya?
Anan ilu ya gyada kai yana mai cewa, ina fa lafiya, sarauniya ta
baki dakika talatin kiyi mata aiki sai gashi kin yi minti uku, ai
ko yau kashinki ya bushe, domin yanzu haka tana ciki tana
jiranki.
Anan gaban husnat ya fadi, haba ilu, dakika talatin fa kace, to
ya za ayi su isheni kuma kasan da cewa wurin da nisa?
oho, ni zaki gayama, kije ki sameta kawai, inji ilu.
Haka husna ta shiga fadar zuciyarta cike da sake sake, daga
nan dai ta wuce turakar sarauniya, to bayan ta shiga ne kawai
sai ta duka cikin girmamawa.
Anan sarauniya ta kalleta, sannu da zuwa, ina fatan baki
wahala ba? husnat tayi mamakin wannan tambaya, domin a
tsammaninta bakar magana ce zata yi mata, daga nan sai
sarauniya ta dauko wata kwarya ta bata, ga ruwa nan kisha,
anan husna ta amsa cikin murna, budewar ta keda wuya kawai
sai taga jini, anan gabanta ya fadi, batasan lokacin da ta saki
kwaryar ba, take sarauniya ta kware da wata dariya tana mai
cewa, wannan jinin wani bawa ne daya saba aikina, saboda
haka kema yanzu jininki zai koma cikin wannan kwaryar.
Cikin hanzari dakaru suka kama husna, aka samata kaca, daga
nan suka shigo da ita a cikin wani fiili suka daure, daga nan sai
ga sarauniya tazo, cikin natsuwa take takawa har ta iso wurin
da aka daure husna, daga nan sai ta fara yi mata magana, na
aikeki, makin kiyi hanzari shine kika tsaya lakwaita, kuma
wannan ba shine karo na farko da nake gargade ki daki daina
hakan, amma kinki, saboda taurin kai, daga nan sai husna ta
fara magana, kiyi hakuri sarauniya, wurin yanada nisa, kuma da
gudu nake har zuwa lokacin dawowata, wannan magana tasa
sarauniya dariya, cikin hanzari ta zare takobi, anan ta saita da
wuyan husna da nufin datsewa, kafin ta aiwatar sai ga wani
bafade a guje yazo wurinta, dagani kasan sako yazo isarwa,
bai bari kowa yaji abunda yace ba, saboda haka sai ya gayama
sarauniya magana cikin kunne, cikin hanzari ta kalleshi, kamar
akwai alamar damuwa a tare da ita, ko wace irin damuwa ce?
Daganan kuma sai ta kara daga takobi da nufin datse kan, a
wannan lokaci husna ta sadaukar, saboda haka ta runtse ido,
to kafin sarauniya ta iyar da nufinta kawai sai taji an rike
takobin, anan ta juyo husace da nufin ganin ko waye, cikin
rashin tsammani taci karo da hamil.
saurayine kyakkyawa dogo, cikin murna sarauniya ta rungume
shi, sai da suka dade kafin su saki juna, daga nan sai ta juyo
kan husna tana mai cewa, amma kin ci sa a, in banda murnar
dawowar hamil dana tsireki, anan taba dakaru umarni dasu
kwance husna, sannan kuma ayi mata duka mai tsanani tare
da aikin wahala, daga nan sai sarauniya ta juyo ga hamil, kawai
sai taga yana kallon husna, kallo na tausayawa, wannan kallo
ya mutukar ba sarauniya haushi, saboda haka cikin fushi taja
hannunsa suka bar wurin.
WAYE HAMIL?
Hamil jarumi ne a wannan birni, saboda haka akwai wata alaka
da sarauniya ke shirin kullawa dashi, duk da ko kadan baya da
ra ayin alakar, sarauniya nason aura masa diyarta, wato
gimbiya hasina, hamil baya da ra ayin hasina ko kadan a cikin
ransa, duk da ta kasancewarta kyakkywa kuma gata gimbiya.
Hamil na zaune saman wata kujera ta alfarma yana kallon
yadda alamurran sarauta ke gudana, to a cikin wannan kallace
kallace da yakeyi sai ya hango wata tauraruwa fuska, wadda ta
dusashe dukkan wadanda ke kusa da ita, cikin hanzari yayi
kallo zuwa ga wannan fuskar, anan ya ganeta, husnat ce, wasu
dakaru ke shibgarta da manyan buloli kamar bazasu barta ba,
wannan duka ya mutukar baiwa hamil haushi, saboda haka ya
tashi, cikin hanzari ya kai wurinsu yana mai katsa musu tsawa,
dole suka daina saboda ganinsa, kowanensu ya done kai kasa
yana mazurai saboda tsananin tsoronsa, anan ya kira wasu
kuyangi mata ya basu umarni dasu dauki husna, haka ko akayi,
to bayan sun wuce da husna, sai ya dawo mazauninsa, a
mamakinsa sai ya tarar da hasina, daga nan sai ta fara yi masa
magana, haba hamil, ina kaje haka inata kewarka, inji hasina,
kawai sai hamil ya mike, daganan sai ya kalleta yace, inason
inje gida domin kaka na nemana, haba hamil, to ai sai na
rakaka ko, inji hasina, rufe bakinta keda wuya sai sukaji wani
kamshi ya dabai bayesu, anan suka juyo domin ganin ko waye,
husna ce taci ado kamar ba ita ba, tafiya take rana rangwada,
tun daga nesa hamil ke kallonta har zuwa lokacin data iso
wurinsu, anan ta duka, daganan ta fara godiya ga hamil da irin
taimakon da yayi mata, na hana dakaru bugunta, anan ya nuna
mata aiba kome, daga nan sai ta tashi da nufin komawa, haka
kuma hamil ya bita da kallo har ta bace, hasina ta lura da irin
wannan kallon da yakema husna, wannan ya mutukar bata
mata rai, domin a tarihinta, ko fuskarta bai taba yima kallon
kirki ba, amma ji yadda yake kallon wannan, ko dame tafini?inji
hasina, haka dai tabar abun cikin ranta ba tare data gayama
kowa ba, daganan suka yi sallama da hamil ya nufi hanyar
gida.
A cikin wannan dare hira ta kaceme tsakanin hasina da
mahaifiyarta sarauniya, wai ya kukayi da hamil? hmm ke dai
umma, ai yau mamaki yaban, kin ga yadda yake kallon husna,
gaskiya akwai alamar tambaya game da wannan al amari,
daga nan sai sarauniya ta girgiza kai, wato bai bar kallontaba
kenan, bako shakka dole sai mun dauki mataki tun kafin abu ya
girma, inji sarauniya, to umma wane mataki zamu dauka?
hasina ta tambaya, daga nan sai sarauniya tayi murmushi tace,
wato ki sani yata, zamu dauki mataki kwakkwara, sai dai
bazanso sarki ya sani ba, daganan sai hasina tace ai bazai sani
ba, domin dubi irin wahalar da husna kesha, ai daya sani daya
dauki mataki, daganan sai suka kyalkyace da dariyar keta,
kawai sai sarauniya tace, ab, nama manta, mun riga mun rufe
masa baki da asiri, ko ya sani bazai iya yin komai ba, haka
suka cigaba da kyalkyatar dariya sai kace mahaukata.
Haka shima hamil, a cikin wannan daren yayi tunani mai xurfi,
a duk lokacin daya runtsa sai yaga fuskar husna, kamar tana
masa murmushi, anan ya fara tunanin wai me yasa su
sarauniya basa sonta, dole akwai wani abu dake gudana, kuma
ya kamata ya san ko meye, daga karshe dai haka ya kwanta
cikin begen husna.
Da karfi ake kwankwasa kofar gidan, sanadiyar hakan ne yasa
hamil ya tashi firgigit, cikin magagin bacci ya mike, cikin rashin
sani da kadan ya buge kakansa zamra, to bayan ya bude gidan,
sai yaga sarkin yaki tare da dakaru, sarki nason ganinka, inji
sarkin yaki, take ya juya ya wuce, hamil yaji mamakin wannan
maganar, saboda haka yana shiga cikin gida, kawai ya sanar
wa da kakansa zamra wannan .maganar, daganan yayi shiri ya
nufi fada, to bayan yaiso fada, take ya wuce wurin sarki, anan
ya fadi yayi gaisuwa, daga nan sai sarki ya dauko wata wasika
ya bashi yace ya karanta, to anan hamil ya fara karantawa
kamar haka:
DAGA SARKIN LUNBIYA, WATO AMNU DAN JANDU, NA
UMARCEKA DAKAYI BIYAYYA KA DAWO KARKASHINA AMMA
KAKI, SABODA HAKA NA DAUKI ANIYAR YAKARKA TARE DA
MUTANENKA, KODA YAUSHE KU TSAMMACEMU.
DAGA MAKIYINKA AMNU.
To bayan hamil ya gama karatun wannan wasikar, sai fada tayi
tsit, kowa ya kasa cewa kome, daganan sai sarki ya fara
magana, wato ka sani hamil, wannan yaki da zamuyi yaki ne
mai mutukar hadari, domin mayakan sarki amnu sun fimu
yawa nesa ba kusa ba, saboda haka yasa nayi kiranka domin
ka bamu irin taka shawarar, daganan sai waziri ya mike, ranka
ya dade inada magana.  an baka izni, inji sarki.
Wato ku sani jama a, inji waxiri, wannan yaki da zamuyi tamkar
tarbar aradu ne, a tarihin dai kun san da cewa sarki amnu bai
taba faduwa yaki ba, sannan kuma yanzu haka yanada
makaman yakin da bamu taba gani ba, bako shakka duk wanda
ya fita wannan yaki ba dolene ya dawo ba, saboda haka ina
mai bamu shawara da cewa da ayi wannan yaki kara mu zama
bayin sarki amnu, wato mu koma mu cemasa zamuyi duk
abunda yakeso damu, daganan mutanen fada sukace lallai
wannan magana ta waziri gaskiyace, haka fada ta hargitse
kowa na fadin albarkacin bakinsa.
Daga nan sai hamil ya mike da nufin magana.Haba jama a, wai
ko kun dubi irin wahalar da kakaninmu suka sha domin ganin
cewa sun assasa wannan gari, wato ku sani cewa shi namiji
bai san tsoro ba, saboda haka duk namijin dake maganar tsoro
ba namiji bane, bazai yiwu ace mu yarda mu tsayu bayan wani
ba, shin wai ku yanzu kunason zama bayi?kunason ganin
yayanku da matayenku a walakance? idan har bama son haka
 to dolene mu fita wannan yaki, mu kare
mutuncinmu, kuma mu tsare dukiyarmu, sannan mu kare
yayanmu da matayenmu, kawai sai hamil yaji ana masa tabi,
dubawar da zaiyi haka sai yaga ashe husna ce, anan ta masa
wani murmushi wanda take hamil yaji kamar an bashi duniya,
tana cikin tabin sai sarki ya tashi ya fara, daganan sai fada ta
dauka aka kaure dayi masa tabi da jinjina saboda maganar da
yayi, ko kadan waziri bai ji dadin wannan magana ta hamil ba,
amma haka ya daure yana tabin dole, to bayan fada ta watse,
sai sarki yasa akayi sanarwar wannan yaki ga mutane, domin
kowa ya kara kama kansa, sannan akasa doka, ba mai shiga,
kuma bamai fita.
Hamil yaji dadin wannan murmushin da husna ta yimasa saboda
haka a yinin duk tunaninta yakeyi, to bayan su sarauniya sun
samu labarin wannan yaki, take suka shirya dubara domin
ganin an tafi da husna wannan yaki, badon komi ba sai don a
kasheta, kuma suka hada kai da waziri domin yasan yadda
zaiyi ya kashe sarki a wannan yaki, idan yaso sai su bashi
sarautar gari. Daga nan ya aminta tare da musu alkawarin abunda 
sukeso.
HUSNA 2
written by:
abdul king article
(zaku iya samun farkon labarin a page dinmu, wato:
kingarticle.novl via fb)
A lokacin da hamil ya koma gida, zuciyarsa cike take da sake
saken wannan yaki, duk da dai a farin ciki yake saboda
murmushin da husna tayi masa, a cikin wannan dare dai bai
samu runtsawa ba, domin a duk lokacin da ya runtsa, to fuskar
husna yake gani.
Al amarin su sarauniya kuwa, dama mun fada muku cewa sun
hada kai da waziri domin idan akaje wurin wannan yaki, yasan
yadda zaiyi ya kashe sarki, domin yana takura musu, sun yi
masa alkawarin kyauta mai tsoka .
kuyangi sunata faman aiki, kawai sai husna taji wani ya
kirata, anan ya gaya mata cewa sarauniya ke kiranta, cikin
hanzari husna ta bishi, to bayan sun isa, kawai sai taci karo da
hamil tare dasu sarauniya, hasina na can gefe sai kace marar
lafiya.
Anan sarauniya ta fara magana, wato ka sani hamil, ba don
komi yasa na kiraka ba sai don in baka wani sako, bako
shakka nasan kasan da maganar wannan yaki da za ayi, duk da
nasan bakuda mayaka masu yawa, saboda haka inason
kayimin al farma kaje da husna wannan yaki, domin ta koyi
yadda ake fada, kuma ta iya kare kanta daga harin makiya,
anan husna ta kalleta da nufin magana, amma saboda tsoron
hukunci tayi shiru, daganan sai hamil ya fara magana, wato ki
sani sarauniya, wannan yaki da za ayi, yaki ne mai mutukar
hadari, wanda ba a taba yin irinsa ba a tarihin wannan gari, mu
kanmu bamuda tabbacin dawowa, to ina ga ita husna, bako
shakka idan akaje da ita wannan yaki, to tamkar an sa takobi
an datse mata kai ne, domin bazata dawo ba, yana gama fadin
hakan, sai yaga hawaye na kwarara a idanun husna, take
tausayinta ya kamashi, sai dai ba halin nunawa don tsoron
sarauniya, cikin tsawa sarauniya ta fara magana, bafa
shawararka nake nema, wannan umarni ne nake baka, saboda
haka dolene husna taje wannan yaki.
To yayi, ba matsala, inji hamil, amma inaso husna ta koma
gidanmu domin in fara koya mata dubarun yaki kafin lokacin
yayi, daganan sai sarauniya da hasina suka kyalkyace da
dariya, wannan ba matsala bane, kaje da ita duk inda zaka,
iyaka dai idan lokaci yayi, to da ita za a.
Daganan hamil ya tashi, yayiwa husna umarni da ta dauko
kayayyakinta, bayan ta kammala hadasu, sai ya azata saman
doki, yaja linzami ya nufi hanyar gida.
To bayan sun isa gidan ne, husna ta shiga mamaki, irin yadda
aka kawata gidan, kuma ga lambu a ciki, cikin hanzari hamil
ya nuna mata dakinta, anan ta shiga, ta iske dakin gyare,
daganan ta fara shirye shiryen kayanta, tana cikin wannan aikin
ne taji murya kamar daga waje, ashe hamil ne ya leko ta taga
yana gaya mata cewa tazo ta gaida kakansa zamra, to anan
tayi sauri ta sanya wata riga doguwa, daganan sai ta fito,
fitowata keda wuya sai taci karo dashi, yana zaune saman
wata kujera, cikin girmamawa ta duka domin gaida shi, cikin
hanzari ya rike mata kafadu yana mai cewa, haba gimbiya
husna, ai matsayinki yafi karfin ki dukamin, anan husna ta hada
ido da hamil, kowanensu cike da mamaki koya akayi yasan
sunanta alhali bai taba ganinta ba, daganan dai sai husna ta
sambaceshi domin girmamawa.
A cikin wannan dare, kawai sai husna taji tanason nishadi,
saboda haka sai ta shigo cikin lambun dake kusa ga gidan,
shigowarta keda wuya, sai taji kamar ana buga karfe da karfe,
saboda haka sai ta fara tafiya guda guda domin ganin ko
waye, ga mamakinta kuma sai taji anyi tsit, tana cikin wannan
tafiya kawai sai taji kamar daga baya an kai mata wani
zazzafan sara, cikin zafin nama ta goce, tana juyawa sai taga
mutum ya rufe fuskarsa da wani kyalle, kai waye? ta tambaya,
maimakon ya bata amsa kawai sai taga yayi cikinta da sara,
gashi rike da takubba biyu, ita ko komi batada.
Anan husna ta shiga gocewa da kai martani sai kace wata
tsohuwar basadaukiya, sai da suka dauki dakika arbain suna
wannan artabu, daga nan sai husna ta mamayeshi ta masa
wani naushi, saboda karfin naushin sai da ya bugu da wani icce
sannan ya dawo, kawai sai husna taji ana mata tabi, juyawar
da zatayi haka kawai sai taga kakan hamil wato zamra, cike
yake da annuri, haka shima wancan data buge sai taji yana
dariya, cikin sauri tazo wurinsa ta debe kyallen daya rufe
fuskarsa dashi, anan ta gane cewa ashe hamil ne, cikin murna
ta rungumeshi tana dariya da mamakin abun, haka shima
zamra ya kusanto wurin, daga nan suka rungume juna su uku
suna dariya, daga karshe suka koma cikin gidan.
Hasina ce a cikin dakinta, kawai sai taji an bude kofar, ba
kowa bane in banda ramat, ramat saurayine mai son cin ado
da kayan kwalliya, kuma shi keson hasina, sai dai tun suna
yara ba wanda ta tsana irinsa, gashi dan dan attajiri.
shigowarsa keda wuya sai yaga hasina bata ko kallon inda
yake, anan ransa ya bace, sai yayi murmushi, taku dai dai yake
har yazo wurinta, tun daga kafarta ya fara tabawa har zuwa
saman kanta, wannan abu ya mutukar ba hasina haushi, take
ta tashi da nufin bar masa dakin, kawai sai ya jawo hannunta
ya azata saman gado da karfi, daga nan sai ya fara magana,
haba masoyiyata, yanzu fa akanki na shigo wannan dakin,
amma ko kulani bakya yi, wai ya kikeso inyi?
Daga nan sai hasina ta zaunar da kanta saman gadon,
fuskarsa ta jawo ta sambaceshi kadan, sannan tace,kada ka
damu, ina wani aiki ne yanzu, ka dawo anjima, wannan
sumbata ta mutukar sa ramat farin ciki. domin bata taba
yimasa haka ba, cikin sauri ya rungumeta yana mai cewa ina
godiya abar kaunata, daga nan ya juya ya fice, haka hasina ta
bishi da wani kallo mai alamar tambaya, abu dai kamar ta
canza ra ayinta.
To bayan tafiyar ramat ne sai sarauniya ta shigo dakin, kuyangi
uku na take mata baya, duk mata ne kuyangin, daga nan sai
hira ta katse tsakanin hasina da ummarta wato sarauniya.
wato ki sani hasina, nazo da wata shawara, inaga zaifi kyau
mu tura a kashe husna a can gidansu hamil tun kafin su wuce
wurin yakin, ko ya kika gani, daga nan sai hasina tayi shiru
kafin daga bisani ta fara magana, umma ina so in miki wata
tambaya, wai wacece mahaifiyar husna, kuma me yasa muke
cutar da ita, cutar da bama yiwa kowa a gidan nan in banda
ita, anan jikin sarauniya yayi sanyi, ta rasa amsar da zata bata,
daga nan kuma sai ta fara magana da cewa, wato ki sani yata,
wannan labari ne mai tsawo, duk da dai sirri ne, bazan so
kowa yasan da wannan magana ba, amma kiyi hakuri, idan na
yanke shawara zan fada miki, daga nan sai sarauniya ta mike
zumbur ta fita, kuyanginta suka rufa mata baya, anan tabar
hasina cikin zullumi, tana mamakin wane irin sirri ne da sai
anyi shawara kafin a fada mata.
Hamil kishengide yake a saman gadonsa, kawai sai yaji husna
ta shigo, a hankali ta maida kofar ta rufe, anan ta zauna dab
dashi, to bayan sun fuskanci juna, sai ta fara yi masa tambaya
kamar haka, ina so ka gayamin ya akayi kakanka yasan sunana,
kuma ya kirani da gimbiya, alhali ni baiwa ce, me yake nufi da
hakan? cikin natsuwa hamil ya fara magana, wato ki sani
husna, wannan kaka nawa yana da abubuwa naban mamaki,
domin yakan iya gayama abunda zakaci gobe, harma da
abunda zakayi, da kuma abunda zai faruwa gareka, ban san
yadda akeyi yana yin wadannan abubuwa ba, amma ni a
tsammanina, baiwa ce kawai ya samu, kiranki da yayi na
gimbiya, bako shakka haka ne, domin idan ba gimbiya kike ba,
ba yadda za ayi ya kiraki da hakan.
Kana nufin yasan labarina kenan?husna ta tambaya! bako
shakka ya sani, cewar hamil, amma idan baki yarda ba muje
wurinsa, nasan zai fada miki koke wacece, da kuma abunda
yasa yakiraki da gimbiya, anan suka mike suka nufi dakin
zamra, shigarsu keda wuya, kawai sai sukaci karo da hasina,
zaune take tare da kakan hamil wato zamra, anan mamaki ya
kashesu, kome ya kawota wannan gidan?
tsoho zamra ya musu umarni dasu zauna, daga nan ya fara
magana, nasan abunda yasa kuka zo nan, kunason kuji labarin
husna ko, da kuma abunda yasa na kirata da gimbiya, to ku
bude kunnuwanku kusha labari.
.ME ZAI FARU?
HUSNA 3
written by:
abdul king article
(zaku iya samun farkon labarin a page dinmu na
kingarticle.novl)
HASINA, HASINA, HASINA, sarauniya ce ke kiran ta amma ko
duriyarta babu, anan ta girgiza kai ta fita fadar.
A lokacin da su husna suke saurarar kakan hamil, wato zamra,
game da labarin da zai fara basu, farkon maganarsa itace:
Kimamin shekaru ashirin da suka shude, sarkin wannan gari
mata biyu gareshi, dayar sunanta hamrat, dayar kuwa
labeenat, sarki na mutukar sonsu, wanda hakan yasa duk
abunda suka nema a wurin sarki sai sun samu komi tsadarsa,
hamrat ta kasance mai tausayi da jin kai, gata kuma jaruma a
fagen yaki, domin a wannan lokaci idan ka debe habar, to ba
wanda yakai jarumtakarta.
waye habar kuwa? hasina ta tambaya!
Kada ki damu, zan gaya muku ko waye, ku dai biyoni kawai.
Ana nan Ana nan, sai rudani ya fara shiga tsakanin matan sarki,
duk da kasancewar hamrat mai hakuri, amma a wannan lokaci
ta kasa jumrewa, ba kowa ke haddasa wannan rikice ba face
labeenat, domin ita mace ce mai ji da kai, ga kuma kin son
gaskiya, abu kamar wasa wasa, sai kiyaya tayi kamari, wanda
hakan yasa labeenat ta fara shige da fice domin ganin bayan
hamrat.
Wata rana sai labeenat ta kirawo habar a cikin turakarta a cikin
sirri, dalilin wannan kira shine tana son ta bashi kwangilar
hamrat, wai ya kasheta, ba yadda batayi ba, amma habar yaki
amincewa, domin shi mutun ne mai son gaskiya, saboda haka,
shima sai ta maida shi makiyinta na gaskiya.
A wancan lokacin, sarkin lumbiya, wato amnu dan jandu yana
da niyar yakar wannan gari domin ya kwashi dukiya, saboda
haka dukkan mayakan wannan gari suna filin daga domin kare
martabar wannan birni, sai dai a wannan lokaci, hamrat da
habar basu samu damar hallartar wannan yaki ba, saboda
basuda lafiya, kuma su kawai ne akeji dasu a wannan birni,
dakyar hamrat ke iya takawa, sarki bayanan, yana filin daga,
wannan tafiya tasa taba labeenat damar yin abinda takeso.
Duk da kasancewar hamrat a cikin rashin lafiya, sai tayi
kokarin fitowa domin zuwa wajena ko zata samu taimakon
magani, to a lokacin data fito ne, sai ta kamajin motsi a wani
lungu na gidan, saboda haka sai ta leko domin ganin ko waye,
tana lekowa sai taci karo da labeenat tare da wani suna
Zina. dukkansu bamai kaya a jikinsa, domin sun dade suna
aikatawa.
Anan labeenat tayi tsuru tsuru don kunya, amma hamrat sai
tayi kamar bata ganta ba, anan ta nufo gidana ta sameni ina
jinyar habar, wato ku sani habar dana ne, to bayan tahowarta
ne na taimaka mata da magani da ita da habar, wanda take
suka mike, sukace sun warke, anan sukayi shirin yaki sukace
zasu je su taimaki mayakan wannan gari, ba yadda banyi dasu
ba don kada su je, amma sukaki.
Ita kuwa labeenat tana jin tsoro kada sarki ya dawo hamrat ta
fada masa abunda tayi, saboda haka sai ta tara wasu jaruman
bayinta su dubu, ta musu alkawari yanta su idan sun kashe
hamrat, to anan wadannan bayi suka nufi filin yaki domin ganin
bayan hamrat.
Na manta ban gaya mukuba hamrat na dauke da juna biyu,
amma ko kadan wannan ciki nata bai hanata komi ba, ana
cikin wannan yakine nakuda ta kama hamrat, saboda haka
dole ta tsaya domin samun sauki, a haka ne kuma wadannan
bayi suka hangota, saboda haka suka nufi wurinta domin cika
alkawarin labeenat, to kafin su kasheta ne habar yasha gabansu, to
anan aka fara dauki ba dadi, shi yana kokarin kare hamrat su
kuwa suna kokarin kasheta, dakyar ya samu damar tauke
hamrat daga filin yakin ya azata saman doki, sannan shima ya
hau dokin, gudu sukeyi amma wadannan bayin halbinsu sukeyi
da kibau, ana cikin haka ne suka fado saman dokin, to a
wannan lokaci hamrat ta fara haihuwa, su kuwa wadannan bayi
sun matso wurin, anan habar ya tare su, to dama habar yanada
mata mai suna lazinat, kuma itama tana a cikin wannan yakin,
saboda haka sai ta biyo mijinta domin ta taimaka masa, anan
ta iske shi yana artabu dasu, saboda haka itama ta shigar
masa.
Bayan zarma yazo nan, sai hawaye suka fara zumo masa, anan
su husna suka fara lallashinsa suna son jin cigaban labarin.
Daga nan sai ya cigaba da labarin, wato a cikin wannan yaki
dai an samu nasarar kashe hamrat, bayan sun dukufar da
habar tare da matarsa, suma aka kashesu, to kafin hamrat ta
iyar da mutuwa ne ta haifi wata jaririya.
Wannan jaririya da aka haifa itace husna, kuma itace akaba
labeenat riko, wato sarauniyar wannan gari, hamrat itace
mahaifiyar husna, kai kuma hamil habar ne babanka,
mahaifiyarka itace lazinat, anan zamra ya kalli hasina yaga tayi
shiru, ke kuma labeenat ce mahaifiyarki.
Tsoho zamra na zuwa a nan, kawai sai husna ta mike fusace,
bazan kara zama a nan ba face na rama kisar gayya da aka
yima mahaifiyata.
Tana gama fadin haka sai ga sarauniya labeenat ta shigo cikin
dakin, ashe dama data bidi hasina bata ganta ba zowa tayi
wannan gidan, to tana shigowa ta tarar da zamra na basu
wannan labari, saboda haka sai ta labe ta taga tanjin abunda
yake fadi.
Daga shigowarta sai ta zare takobi, a yau zan kasheka yakai
wannan tsoho, saboda ka tona sirrin dana dade ina binnewa,
inji sarauniya, cikin sauri hamil ya zare takobinsa domin kare
kakansa, to kafin su fara fadan sai sukaji ihun mutane, anan suka
fita waje domin dubawa, fitarsu keda wuya sai sukaga ashe
sarki amnu ne ya kawo yaki, mayakansa sai kashe jama a
sukeyi.
To anan ne aka buga kugen yaki, kafin kaceme mayaka sun
jero sahu sahu, to anan aka fara dauki ba dadi.
Ana cikin wannan yakine wasu mayakan sarki amnu suka biyo
sarauniya labeena da nufin kasheta, ashe husna ta gansu, cikin sauri ta zaro kwari da baka domin ta tsayar dasu, anan ta sheko a guje domin kareta amma kash kafin ta karaso tuni sun kashe labeenat. Anan hasina ta sheko ta rungumeta tana kukan bakin ciki na rabuwa da mahaifiyarta. To bayan an gama wannan yaki ne, an samu nasarar kashe sarki amnu da mayakansa, anan su husnat suka kadaita.  daga karshe dai sun yafema juna daga nan kuma sai zarma ya labartawa sarki abunda ya faru. Anan sarki ya kankane husnat domin bai taba tsammanin cewa diyarsa ceba. Anan sarki ya ginawa hamil katon gida tare da bashi dukiya mai yawa shida kakansa. sannan kuma aka daura auren husna da hamil, ita kuwa hasina da saurayinta, wannan shine karshen wannan labari.
ALHAMDULILLAHI
written by
abdul king article.

Post a Comment

0 Comments