REZA

 





REZA

                               AUTHOR: ABDUL KING ARTICLE


                                                 PAGE 1


           Kai da ganin unguwar kasan akwai masu kudi saboda jerin gidajen da aka gina naji da gani. A bakin titi ne wata yarinya sai tafiya takeyi ta dauko bokiti a kanta. Shigar datayi kansa ka bayyana daga gidan data fito. Bako shakka su madaidaita ne: Ba rashi ba kudi. Haka ta cigaba da tafiya cikin sauri ba tare da shakkar komi ba. Da rana ne tsaka saboda haka ba kowa a saman hanyar domin mafi yawan mutane kan samu wurin hutu a wannan lokaci. Tana cikn tafiya ne sai wata mota bugagga ta wuceta. Motar tafiya take a hankali sai duma ke tashi sama sama. Har motar tayi nisa sai tayo baya har saida ta tsaya gab da wannan yarinyar mai dauke da bokiti. A hankali aka fara sauke gilashin. Caraf sai wannan yarinyar tayi ido hudu da wanda ke cikin motar. Ai kuwa tana ganinsa gabanta ya fadi duuumm. Da sauri ta juya da nufin komawa inda ta fito. Shi kuwa da sauri ya fito yana kiranta. 
   " Yasmin, yasmin,  ke magana fa nake. "  
    Tanaji amma haka ta kyaleshi kamar bataji ba. Shi kuwa sai ya dada kara matsawa wurinta. " Yasmin Wai meke faruwane?" 
    " To ba ita bace."  haka yarinyar ta fada tana sauri. Shi kuwa da sauri yaci gabanta. To anan ya mata kallon tsaf.
    " Hahahhh! Au dama haka kike? Shine kike boye boye don kada na gane. To naga kome kuma nasan kome. Ta ALLAH ba taki ba,nan gani nan bari yarinya. Hahhhhhh." Haka ya cigaba da dubanta yana dariya ba kakkautawa. Kai da gani kasan shekarun su daya.
     " Wa ma kikace ne abbanki, hhhhhhh. Yau dai na kama diyar commssioner na dibar ruwa." Haka wannan yaron ya ci gaba da tsangwamarta. Ita kuwa ta riga tasan asirinta ya tonu. Saboda haka ta kyaleshi sai tafiyarta take. Shi kuwa sai ya bita sai magana yake yana dariya tare da shammatarta saboda karyar data masa na cewa ita diyar commissioner ce tare da nuna masa cewa gidansu akwai hali domin abbanta nada mukami sosai a gwamnati. Shi kuwa kai tsaye ya aminta saboda irin yadda take shigar kece raini tare da hawan manyan motoci. Amma sai gashi yau ya kamata ta dauko bokitin nika saman kai.

                                              PAGE 2

     Haduwarsu ta farko itace a wani wurin shakatawa na kiyon dabbobi wato ( Amusement park) 
   Yarinya ce santaleliya ke zaune saman wata kujera ta alfarma sai murmushi take. Kai da ganin shigarta kasan nan gani nan bari. Wato mai kudi ya wuce raini. Wani table ne kusa da ita sai kayan marmari a samansa  irin su dangin inabi. Tanaci tana kallon jama a dai dai. Tana cikin wannan hali ne sai ta hango wata jeep baka. Wani hadadden gayene ya fito ba wasa. Ya buga wanka over sai bouncing yakeyi. Yan matan dake wurin sai kallonsa suke wai a tsammaninsu ya zabi daya a ciki. Anan yayi banza dasu ya nufi wata hanya. Har ta debe tsammanin bazata kara ganinsa ba kawai saita hango shi ya nufota. Wani dadi ne ya lullube ta domin yau tasan batayi fitowar banza ba. Cikin murmushi da sakin fuska ya karaso wurinta yana taku dai dai. Kallon shigarta ya farayi daga sama har kasa. Daga nan sai ya fara magana
    " Amincin ALLAH ya tabbata a gareki yake wannan gimbiya mai farin idanu da hasken fuska." 
    Anan ta dago kai ta kalleshi cikin dariya har saida hakoranta suka fito. 
     " Ko zan iya zama kusa dake?" ya tambaya.
     " A a!" Ta fada cikin murmushi.
     " To me yasa?" 
     " Saboda ba kai nakeso ka zauna ba."
     " Hhhh. Yan mata kenan! To fadamin wa kikeso ya zauna a gurin?" 
     " Dadadan kalamanka sune suka cancanci zama a wannan kujerar ba kaiba." 
     Anan ya tuntsire da dariya har saida ya gincira da bangon dake kusa dashi. Cikin sauri ya zauna yana duban fuskarta. " Indai dadadan kalamai ne to kin samu. Ki dauka cewa daga yanxu zakijisu har sai kin gundura. To amma kafin nan ya kamata nima kiban wani abu kinga daganan sai mu amfani juna." 
    " Tab. To fadi me kakeso kenan?" ta tambaya.
    " Zuciya, zuciyarki nakeso ki mallaka min." 
    " A a bazan baka zuciyata!" 
    " To me yasa?" Ya fada cikin mamaki.
    " Saboda kafi karfinta. Sai da na mallakama jikin gaba daya." 
     

                                                  PAGE 3

      Anan ya kara barkewa da dariya kamar bazai bari ba. Sai da aka jima sannan ya daina. " Amma fa akwaiki daban dariya. To ni sunana huzaifa kefa?" 
     " Zaka iya kirana da yasmin." Ta bashi amsa.
     " Gaskiya naji dadin haduwa dake. Kuma bako shakka indai zakiban hadin kai to zamuci duniyarmu da tsinke. Da farko dai nasan kin san alhaji garba mai zinari ko?"  
     " E mana. Wannan shahararren dan kasuwa ai kowa yasansa a wannan gari. Duk fa wata mota sabuwa shi yake kawota." Yasmin ta fada. A cikin zuciyarta kuma sai murna take tana fadi cewa ( yau dai banyi fitowar banza ba. Na samu gara dan dan mai kudi) 
      " Yauwa. To madalla da kika sanshi. Bako shakka shine mahaifina. Kuma yanzu haka motar dana shigo tasace. Bai dade da yimin kyautarta ba." Huzaifa ya fada bayan ya tura wani inabi a bakinsa.
       " Amma fa naji dadi sosai. Kada kaso kaga yadda zuciyata ke muradin tarbarka. Bako shakka nayi dace. Kuma nasan nafi kowace mace sa ar saurayi." Haka ta fada tana kallonsa fuskarta cike da annuri. " Kamar yadda nace sunana yasmin. Haka abbana shine commissioner ilimi na wannan jahar. Nasan zakaji ana fadinsa wato alhaji sama ilan baka." 
       " Tab lalle ke babba ce. Ai abbanki sananne domin shima a wurin kasuwanci ba a barshi baya ba. Ga kuma tarin ilimin da yake dauke dashi tunda saboda hakane aka bashi commissoner ilimi." Haka ya fada. Can a cikin zuciyarsa sai murna yake yana cewa( Yau banyi fitowar banza ba. Na samu sakarya diyar masu kudi.) 
  Tun daga wannan lokaci sai suka kulla soyayya mai karfi. A duk lokacin da zaixo wurinta takan yi kokari ta aro kayan kawayenta kuma ta yini a gidan don kada ya gane cewa ita diyar talakawa ce. A haka ta cigaba da cutarsa kasancewarta wayayya. Takan iya aro mota ta kawo masa ziyara har inda yake. yasmim tana yin hakane badon komi ba sai don ta koyama maza masu bin matan banza hankali yadda idan ta samu saurayi dan masu hali zataci kudinsa saukake. Domin tasan cewa wasu mazan sai a hankali, Sai dai abunda bata sani ba shine da ita da huzaifan duk shegiyar darin ce.

                                                PAGE 4

    Haka huzaifa ya ci gaba da bin yasmin yana dariya har saida suka kawo dai dai wani katon gidan sama. A wannan lokaci ta fara gajiya da shammatar da yake mata sai dai ba yadda ta iya. Haka ta cigaba da tafiya da bokiti saman kanta shi kuwa sai faman kyalkyatar dariya yake. To suna cikin hakane saiga wata budurwa ta fito daga gidan. Ai kuwa huzaifa na ganinta sai ya juya yabar bin yasmin. Da sauri ya fara tafiya da nufin komawa inda ya fito. Ita kuwa budurwa cikin sauri ta kwala masa kira. Da taga bayada niyar tsayawa sai taci gabansa. Shi kuwa dole ya tsaya kansa a done da alama akwai wani abu. Ita kuwa yasmin na ganin haka sai ta karabo wurinsu cike da mamaki.
   " Ishat ya haka? Dama kin sanshi ne?" Yasmin ta tambaya.
   " Ai kedai bari kawata. Shine fa almajirin da nake baki labari yana mana wanki. Tun wancan satin ya ari motata amma sai yanxu dana ganshi.!" Cewar ishat.
     Ai kuwa huzaifa najin an tona masa assiri sai ya fara fadace fadace.
    " Haba ishat ya zakiyimin haka. Nifa zaki dubi idona kice...." Haka ya cigaba da fadan inda yake shiga ba nan yake fito ba. 
    " Au, wai don na fadi gaskiya shine kake wannan abu?" Ishat ta tambaya.
    " Nifa ban ganeba ke almajiri kikace?" Yasmin ta tambaya cikin mamaki.
    " E mana, ke a tunaninki shi waye? Almajirin ne nan da kin zagaya makarantar malam dan guntu." Ishat ta bata amsa.
    Ai kuwa yasmin najin haka take ta barke da dariya har saida bokitin da take rike dashi ya soma kubcewa. Ajiyeshi tayi gefe sannan ta cigaba da yiwa huzaifa dariyar keta irin wadda ya mata da farko. 
    " Amma gaskiya ishat nifa kin dai cuceni wallahi. Yanzu ki rasa wanda zaki fadawa wannan abu sai...."
   To kafin ya iyar da maganarsa ne ishat ta tsayar dashi. " Kai dakata! Ina fada kana fada. To daga yau an sallameka bazaka kara aiki a gidan ba." 

                                                   PAGE 5

    " Haba ishat nifa wasa nake. Yanxu dai ga makulin motar." Anan ya mika mata makullin motar. Juyawa tayi da karfi zata wuce shi kuwa caraf yaci gabanta. " Kiwa ALLAH kiyi hakuri. Wai ke dama bakisan wasa ba?" 
    " YIHAHAHAHAHAHAHA." Anan huzaifa ya duba yaga waye ke dariya. Ai kuwa anan yayi arba da yasmin harda faduwa takeyi saboda dariya.
    " Ke, ubanwa kikewa dariya?" 
    " An yimaka dariyar sai me, kai dakayi taka me ya faru?" 
    " Ke na fiki tashanci fa ALLAH zanci mutunki."
    " To bismilla shege ya fasa.!" 
    " Ni zaki fadawa haka?" 
    " An fada!" 
    " Ke ni zaki fadawa haka." 
    " Nace na fada." 
    Ji kake tassssss. Saukar mari. " La la la la la la. Ka mareni?" 
    " An mareki ko zaki rama ne?" Ai kuwa kafin ya iyar da maganarsa ne yasmin tayo cikinsa. Kasancewarta doguwa kakkarfa anan ta cafko kwalarsa. Kafin kaceme ta rankwada masa mari sai da ya fadi. Anan huzaifa ya tashi yana huci. Tashinsa keda wuya sai yasmin ta raina tsawonta domin ya fita tsawo nesa ba kusa ba. Anan yaxo daf da ita yana huro mata iskan hanci. Yasmin  bata jira yayi komi ba take ta kamasa da kokawa. Shi kuwa gogan ba kiba ce dashi ba. Anan ishat ta sheko aguje tana rabo amma ina yasmin taki saki. Kunnensa ne ta cije sai faman ihu yake. Da huzaifa yaji tana shirin hallaka shi sai ya jawo kanta ya gwabra da nasa kamar yadda raguna keyi idan suna dambe. Ai kuwa cikin sauri yasmin ta sake sa saboda zafin da taji. 
    Anan huzaifa ya tashi da nufin tserewa domin ya gano cewa yasmin dai tafi karfinsa bazai iya fada da ita ba. To kafin yayi nisa ne ta cafko shi. Anan ya fadi kasa yana bata hakuri amma ko saurarensa batayi ba. Bokitin ta dauko wanda cike yake da nikan attarugu. 

                                                 PAGE 6

     Anan ta zurma kansa ciki sai faman buntsile buntsile yake yana ihu.
A guje ishat ta sheko ta tureta don kada ta jimasa. A wannan lokaci idanunsa sunyi jawur kai kace wanda ya fito daga wutar makera. Ai kuwa huzaifa na jin an fito dashi take ya sha kwana a guje. Anan ya manta da yan takalmansa. Ita kuwa yasmin anan ta dauki bokitinta sai faman zage-zage take. Anan ta kama hanyar gida ita kuwa ishat ta koma cikin gidansu dama bayada nisa da wurin da wannan abu ya faru. 
    Ladi mai kunun zaki ce a kusa ga turminta sai faman surfe take. Daga can nesa ta fara jiyon ihu kamar ana kuka. Da farko bata damu ba domin a tsammaninta wasu ne. Sai daga baya sai taji abun sai matsowa ake a kusa ga gidan.  Bata ankara ba sai taji an banko kofar gidan da karfi. Kawai sai ga yasmin ta sheko a guje tana kuka. 
   " Laaaa diyata! Wane banzan ne kuma ya taba min ke." Yasmin bata amsa ba sai faman sheshsheka take. Can sai ga abba daga ya shigo yana tangadi rike da bell. Abba ba karamin mashayin daga bane kuma shine yayan yasmin haka ya kasance yana da yamin baki wato maganarsa bata fitowa dai dai. Anan yayo cikinta da nufin ya cigaba da dukanta. Ita kuwa ladiyo bata yarda ba. Anan ta amshe bell tare da fara xaginsa. " Wai kai yaushe zakayi hankali? Yarinya ta girma amma bakasan ta girma ba sai dukanta kake sai kace karamar yarinya." 
     Anan abba ya fara magana cikin maye. " Wai umma wai ni  wannan yayinyar jata yiwa fuya uba. Wayayi wayayi she naci uuuubanta.
    " Haba abba kanwarka cefa. To yanzu idan ka kasheta waye zaiyi tallar abincin tunda kai ba zuwa kake ba?" 
     " To ni umma she ta yaina min da wayo. Wai tun daju ina jiya tajo da dafa inci amma she yanju ta dawo." Cewar abba cikin fushi.
     " To yanxu dai kayi hakuri shi kenan. Ni zan dafa da kaina." Inji umma.
     " Wayayi kin kuyu." Anan ya nuna yasmin  da yatsa. " Kuma idan na dawo na ishko baki fita ba wayayi she na jimiki ciwo. Shejiya mai kan goyiba." Anan ya fita yana huci ita kuwa yasmin cikin sauri ta shiga daki. Anan umma ta bita tana lallashi.

                                                 PAGE 7

     Wazajen la asar ne wata mota ta nufo wannan titi wanda akan shine gidan su yasmin. yake. Direba ne a gaba sai mutum biyu a baya. Sai da motar ta kawo daf da gidan su yasmin sai ta tsaya. Abba daga ne ya fara fitowa. Daga nan sai wani alhaji ya fito yana tafiya cikin takama. Jerawa sukayi suna tafiya. Wata magana sukeyi a hankali tare da abba yadda ba mai ji. Sai da suka dau lokaci suna wannan tattaunawar kafin su kyalkyale da dariya. Hadda taba hannu. Shi kuwa abba sai ya shiga cikin gidan yabar alhaji a tsaye. Bai wani dadewa ba sai gashi ya fito da yasmin. Wani wanka ne tayi kai kace sarauniya. Kayan sun yi dai dai da ita ba karya. Alhaji na ganin fitowarta sai ya kyalkyale da dariya yana buga kafa a kasa. Kallon siffar jikinta ya fara yi cikin jin dadi. Ita kuwa yasmin na ganin haka take ta fara tafiya tana rangwada. Sai kararraye jiki take tamkar wadda batada kashi a jiki.
    Abba da kanwarsa yasmin su kadai sukan san abunda suka shirya. Anan alhaji ya matso kusa da ita sai tsalle tsalle yake. 
   " Tab. Amma fa yau kasuwa tayi kyau. Kai abba wannan haja da nake gani ai ko a london iyaka kenan!" Cewar alhaji bayan ya tsura mata ido.
     " Ai ina fadama kasha kuyiminka. Komi ka tauka kamal an gama." Cewar abba bayan ya mata wani signal da idanu. Ai kuwa take yasmin ta nufi motar da nufin shiga. Shi kuwa alhaji sai ya tsura mata ido ko kyaftawa bayayi har saida ta shiga motar. Anan yayi sallama da abba bayan ya danka masa wasu yan canji. 
    " Bismillahirrahmanir rahim." Haka alhaji ya fada bayan ya zauna cikin motar. Ita kuwa yasmin sai murmushi take fuskarta cike da annuri. Anan direba ya tayar ya fara tafiya ba kakkautawa. Shi kuwa alhaji matseta yayi sai da ya zauna gab da ita. " Ai yarinya ki kwantar da hankalinki. Indai muna tare to shi kenan sai abunda kika ga dama. Kudi kuwa ba matsalarki bane domin inada rumbuna rumbuna makil da kudi. Kuma zan baki dama ki shiga ciki ki dulmiya ki wataya iya yinki yadda kikeso."

                                                  PAGE 8

    "Da gaske alhaji?"yasmin ta tambaya. 
    " E mana. Kin aza ina wasa ne? Ai ni bana magana biyu. Dana fadi to shi kenan. Duk abunda na fada shin din daine ba makawa sai anyi." Alhaji ya bata amsa.
    Anan yasmin ta dan sumbaci goshinsa cikin murmushi. " Shi yasa nake sonka sweetheart." 
    Shi kuwa alhaji wani dadi ne ya lullube shi. Bai san lokacin da yayi dariyar farin ciki ba. " Yanzu fa muka hadu. Har na zama sweetheart dinki kenan?"    
    " Kana nufin baka sani ba. Ai idan akwai abunda yafi sweetheart matsayi to kafishi a wurina. Nima yanzun nan ji nake kamar mun dade da haduwa. Banaso wani abu ya takura mana." Haka yasmin ta fada bayan ta matseshi. Shi kuwa alhaji dama abunda yakeso kenan. Take ya jawota da nufin afka mata. Ai kuwa tana ganin haka sai tayi sauri ta janye jikinta. " Haba alhaji ya kana haka. Ka bari mu isa gidan mana." 
    " To to to to to. Ai a ganina da gidan da cikin mota duk daya ne. Balantana mufa manyan mutane a cikin mota muke wannan abu domin yafi gidan sirri." Cewar alhaji.
     " Ni dai gaskiya banaso ka bari sai mun isa mana." Haka yasmin ta fada cikin shagwaba.
     " Hahhhh. To yayi ai har mun iso." Inji alhaji. 
     Anan direba ya shiga da motar cikin gidan bayan mai gadi ya bude musu gate. To bayan sun fitone sai yasmin ta gane cewa gidan ba karamin kato bane. Sai shuke shuke koina. Kai da gani kasan an zuba naira wurin ginasa. Gidan ya kasance na sama abun burgewa. Anan alhaji ya mata iso ciki. Ai kuwa tana shiga falon sai ta zama bakauya. Da farko santsin tiles ne ya kwasheta data fadi. Anan ta debe takalma da taga alamar cewa suna shirin tona mata assiri. Duk da kasancewarta wayayya amma yau sai gashi ta zama bakauya. Domin falon an kawata shi da kayan alatu iri iri. Anan ta shagala sai kallonsu take daya bayan daya.

                                                  PAGE 9


     " Hahha. Hala me kike kallo haka?" 
     Da sauri yasmin ta juyo, anan tayi arba da alhaji ya canza kaya ba irin waccan ta farko ba da yasa manyan kaya ba. Wannan karon kananan kaya ne yasa sai gajeren wandon daya rufe masa guiwa. 
    " Laaaaa alhaji har ka dawo." Anan ta fada jikinsa cikin murna. Shi kuwa sai ya dada kankaneta sai kyalkyatar dariya yake.
   " Zo muje in nuna miki abubuwa naban mamaki." Anan ya jawo hannunta suna tafiya suna tadi. " Ki kwantar da hankalinki ba kowa a gidan. Ni kadaine a ciki." 
   " Amma fa inajin tsoro. To ina matarka take?"  
   " Ki kwantar da hankalinki ai ba a wannan gida take ba. Shi wannan  gida na tanadeshi ne saboda hutawa kawai."  
   " Yauwa sweetheart har kasa naji dadi." 
   Haka suka cigaba da tafiya suna tadi har saida suka kawo wani gidan kasa. Wato ( underground) Anan suka taka steps wanda zai shigar dasu ciki. Sai da suka danyi nisa sannan suka kawo wani wuri mai ban mamaki. Shi dai wurin koina glass ne har inda mutum zai taka. A cikin glass din kuwa ruwa ne sai halittun ruwa kala kala a ciki suna sha anin gabansu. Anan yasmin ta kurawa wurin idanu sai kallo take domin tunda take raye bata taba ganin wannna abu ba. Haka alhaji ya cigaba da zagayawa da ita yana nuna mata wadannan halittu. Ita kuwa sai kallo take tana mamaki. To bayan sun gama da wurin ne sai alhaji yace ta jirashi. Anan ya shiga wani dan lungu. Sai da ya jima sannan ya fito da wata yar jaka. Daga nan sai ya umarceta dasu su koma ainahin cikin gidan. 
    A cikin wani dakine suka shigo mai cike da kayan kwalliya na zamani. " To albishirinki." 
   " Goro" 
   " Fari ko ja" 
   " Fari tas tas tas." 
    To anan alhaji ya bude mata jakar. Ai kuwa tana lekawa sai tayi arba da kudi cike. Anan ta tayi ihun farin ciki take da rungumeshi.
 
                                                  PAGE 10
 
     " Amma fa da sharadi. Idan zaki bayar to shi kenan ga kudi sai ki dauka." Cewar alhaji yana murmushi.
    " Haba alhaji ai wannan ba komi bane. Yanxu ma bari ka gani." Anan ta cire lullubin datayi. Alhaji na ganin haka sai ya kyalkyale da dariya. " To amma kafin nan ya kamata mu dan yi nishadi kadan." Inji yasmin.
     " Nishadi fa kikace. Bayan wanda zamuyi akwai wanda yafishi?" Alhaji ya tambaya.
       Bata tsaya bashi amsa ba. Jakarta ta dauko. Daga nan sai ta jawo wani dan yoghurt a ciki. " Wannan shine nishadin da nake cewa." Ta fada cikin murmushi.
      Shi kuwa alhaji na ganin haka sai ya balle da dariya. " Lalle yarinya kin cika yar duniya." Anan ya nufi fridge dinsa. Wani dan cake ne ya dauko ya ajiye gaban yasmin tare da cups biyu. Cikin murmushi yasmin ta xuba masa sannan ta zubama kanta. Anan suka kafa kai kowa ya fara sha. Take alhaji ya shanye nasa ya ajiye kofi. Ita kuwa yasmin ko digo daya bata bari ya shiga bakinta ba. Iyaka dai tayi kamar tanasha. Ai kuwa yana ajiye kofi sai ya fara hamma. Ita kuwa yasmin sai ta jawosa a jikinta kamar da gaske. 
    " Yauwa sweetheart bari mu fara tunda mun sha yoghurt ko." Anan taji shiru ko motsi bayayi. Kura masa ido tayi sai taga sai faman hansari yake. Anan tayi ihun jin dadi. Cikin sauri tasa kayanta ta dauko jakar daya bata ta kudi. A nan ta nufi underground. Da sauri ta shiga lungun dataga ya shiga. Ai kuwa shigarta keda wuya sai taga kudi a sarkafe koina kamar library na kudi. Anan ta fara diba kai kace bazata bar suba. Haka ta cigaba da dibar kudin sai da ta cika jakarta dam sannan ta fito. Anan ta tarar har yanzu alhaji bacci yake bai farka ba. Anan ta masa kallon keta domin tasan ta gama dashi tunda ta samu damar yi masa reza. 
   Glass dinta baki ta sanya kafin ta dauko takalmanta. Sai wani agogo in banda walkiya ba abunda yakeyi. Anan ta nufi kofar fita cikin murmushin samun nasara tare da yiwa kanta kirari. To kafin takai ga kofar fita ne sai taga wani ya shigo a guje yana kiran alhaji. Kuma a wannan lokaci ne ta fara jin tarin alhaji wato da alamar cewa ya farka.


                   Me zai faru?

                        Zamu cigaba.........


                                                      REZA

                                     AUTHOR: ABDUL KING ARTICLE

 
                                                     PAGE 11

 
        Da sauri yasmin ta labe bayan wani katon fridge. Mutumin na wucewa saita nufi hanyar fita falon. A guje ta nufi bakin gate kuma sai akai sa a mai gadi na cikin dakinsa balantana ya tambayeta abunda takema gudu. Ai kuwa tana fita gidan sai ta samu adai daita sahu. Kai tsaye ta shige. A cikine ta fada masa inda zai kaita.
      Da isha i ne sai abba daga yaji ana sallama. Anan ya fita yana tangadi kai da gani kasan yasha. Ai kuwa anan yayi arba da alhaji tare da direbansa. " Kai wallahi kayi kadan, ba harka ba kudi to ina lfy. Ya zaka turo yarinya ta wawasheni. Kai ni zaku cuta?" Anan alhaji yaci kwalarsa cikin fushi. " Kai nace ni zaku cuta, kai nifa ni zaku yiwa keta. Wallahi kunyi kadan kuyimin reza sai dai wani ba niba." 
    " Ai bani na taukal ma kuti fa. To yanju me janyi ne hala?" Cewar abba.
    " Ubanka nakeso kayi. Nace ubanka nakeso kayi. Ka ganar min shege mai wasu idanu sai kace kwararu. Wai don ubanku ni zaku yiwa reza. Ni zaku cuta ko? To bari ka gani." Anan alhaji ya tankwahe rigar hannunsa. Sai daya dunkule hannu sannan ya fara dibar abba ga ciki. Anan abba ya fara ihu yana kubce kubce amma gam alhaji ya rikeshi. 
     " Zakayi magana ko bazaka yiba?" Alhaji ya tambaya. 
     " Wayyo alaji kayimin yai." 
     " Inyima rai? Ai kuwa zakaci ubanka."
     A haka alhaji yaci gaba da dibar abba saida direbansa yaxo yayi magana. " Ni a ganina alhaji me zai hana mu shiga cikin gidan idan yaso mu duba ko zamu ga jakar."
     " Lalle wannan shawara ce mai kyau, to muje mu gani." 
     Anan alhaji yaja abba har cikin gidan shi kuwa direba na biye dasu. To a wannan lokaci ladiyo bata nan wato innar abba da yasmin. Domin a lokacin da yasmin ta dawo gidan alhaji ita aka ba kudi ta kai banki ta ajiye musu. To har yanxu bata dawo ba, yasmin kawai aka bari a cikin gida. Ita kuwa yasmin tun daga nesa takejin ana dibar yayanta. Saboda haka alhaji na shigowa gidan ashe ta labe da kulki tana jiransa. Ai kuwa yana shigowa dama shine gaba kawai sai ta fito. Sai da ta saita da tulun cikinsa anan ta aza masa kulki ji kake timmm. 
    

                                                  PAGE 12

    Anan alhaji ya fadi yana ihu saboda zafin da yakeji. " Wayyo awazata ta hagu. Mande kayi agaji sun kasheni." 
  Ai kuwa tana ganin alhaji ya fadi batayi wata wata ba anan ta sheka a guje ta nufi katanga. Dama katangar batada tsawo sosai. Kamawa tayi da nufin direwa shi kuwa direba sai ya dahota. Anan ya rike mata kafafu da nufin jawota. Fizge fizge ta kamayi domin ta tsira tasan cewa idan alhaji ya tashi baza a yi mai kyau ba. Ba yadda batayi ba amma ta kasa shi kuwa direba sai kokarin jawota yake. To kafin ya ida jawota ne sai ta tuno cewa yau fa taci wake. Anan ta nisa sai da ta saita da hancinsa sannan ta sako masa wata tusa mai shegen doyi ji kake buuummm.  
    Da sauri direba ya saketa saboda doyin da yaji. To anan ne yasmin ta samu damar dirowa amma cikin rashin sa a sai ta diro cikin ramen kwata ji kake tsunbul. To a wannan lokaci alhaji ya samu damar tashi. anan ya jawo abba dake shirin hawan katanga. " Kai don ubanka ni zaka bugawa tabarya ko?" 
   " Wayayi wayayi bani bane!" Inji abba.
   " To uban waye idan ba kai bane?" Alhaji ya tambaya. 
    " Wayayi ka ganta can." Anan abba ya nuna katanga. Shi kuwa alhaji yana dubawa baiga kowa ba sai yayi tsaki.
     " Ni zaka yiwa karya ko?" Anan aka sa abba cikin hammata sai dibarsa ake yana ihu. Da dai abba yaga alamar cewa kasheshi za ayi sai ya kirkiro dubara wadda zata fidda shi.
     " Wayyo ka shaya jan fatama gashkiya." Inji abba.
     " To fadi inaji." Alhaji ya tsaya.
     " Dama kutin shuna can amma...." Anan abba ya nuna wani daki. " Bayi naje na dauko muku." Anan ya fara tafiya kamar zai shiga dakin. Kafin su ankara sai gashi ya balla aguje ya nufi katanga. Koda su alhaji suka duba kura kawai suka gani da alama ya dade da direwa basu ankara ba. Anan suka duba gidan amma ba jaka balantana alamar kudi.  

                                                     PAGE 13


        " To alhaji sai kayi hakuri tunda kudin ga dai kafi karfinsu. Kanada dubbansu a gida." Inji direba.
       " Ko inada su ai akwai haushi. Ba harka ba kudi." Haka alhaji ya fada yana sheshsheka.
      " To alhaji ya aka iya tunda bakin kwadayinka ne na son mata ya jawo maka. Gashi wurin bincike binciken ka ka binciko reza. Yanzu shi kenan ta yanke ka ta debe maka dukiya." A haka dai alhaji yabi shawarar direbansa. Dole ya hakura ya koma gida. A wannan rana yasmin da yayanta abba ba wanda ya kwana a gidan saboda tsoron abunda ke iya faruwa. A gidan abokansu suka yi bacci sai da safe suka dawo. To yau ma kamar kowace rana sai jidali ya barke tsakanin yasmin da yayanta. 
      " Wallahi kayi kadan ka hanani neman abunda zanci, ai wannan rainin wayo ne. Kai har ka isa." Cewar yasmin tana ciccika.
      " Ke wayayi ina ji miki. Ni kike fatawa aka. To ki fita in ke cegiya ce." Haka abba ya fada bayan ya tare kofar gidan. Can sai ga ladiyo ta fito wato innarsu domin taji abunda yake faruwa. 
      " Ya inajin hayaniya, wai me yake faruwa a gidan ne?" To a wannan lokaci abba ya daga hannu da nufin ya mari yasmin. " Kul kul kada ka marar min diya. Me tayi maka?" 
     " Wai umma ni jata yiwa ishkanci, jiya fa shaida awajata ta tashi kayewa shaboda bugu. Wai kuma yanju fita jata kayayi." Inji abba cikin fushi.
      " To idan ta fita miye ruwanka a ciki. Ai jiya kai kajawa kanka saboda kai ka kawoshi. Ko kana nufin saita ki fita ne neman abinci. To bazan yarda da hakan ba. Sai ka canza dubara." Inji umma ladiyo.
      " Kin gani umma ke kike tauye mata shi yasha ta yaina ni. Ai hakan yainin wayo ne. Yaja ace kayamal yayinya iyin wannan tana fati muna fati." 
     " Ai kai ka jawa kanka. Da ace ka kiyaye girmanka ai da hakan bata faruba. Idan kanaso ta girmamaka saika bar shiga sha aninta. Kome tayi ka kyaleta." Inji umma ladiyo.
     " To umma idan kikace aka shifa abincin waje sayar dashi?" Inji abba.
     " Sai ka bari na fita da abuna in sayar tunda kai baka zuwa. Yanxu kaje ka kiramin mai taxi mu wuce kasuwa." Inji umma. 

                                             PAGE 14

     Anan abba ya fita yana gunguni ita ma yasmin haka ta fita. Kowanensu ya kama gabansa. 
    Wurine na shakatawa an kawata shi da furanni koina. Sai ga mutane maza da mata saman kujeru na alfama. Dan table ne a kusa da kowace kujera. Sai kayan abinci kala kala a sama. A can gefe kuma wurine na musamman da aka kebanci shi ba don komi ba sai domin sayen abinci. Wato da mutum yaje wurin sai ya bayyana musu irin kalar abincin da yakeso. To yana xaune za a kawo masa bayan ya biya kudi daga can. 
     Yasmin ce ke tafiya a wurin sai rangwada takeyi tana taku dai dai. Kai daganin shigar kasan tayi ado na babbar yarinya. Tana cikin tafiyar ne sai ga wani mutum yazo a guje wurinta. " Assalamu alaikum." Haka ya fada.
    " Wa alaikassalam." Ta bashi amsa.
    " Idan bazaki damu ba wai oga ne yakeson ganinki da gaggawa. Kuma ina fatan cewa zaki bada hadin kai." Haka ya fada yana dubanta.
     Anan yasmn ta dubeshi da murmushi. " To amma shi ogan naka yasan koni waye da zai aika a kirani? To ka fada masa bazan zoba. Idan ya damu sai yazo da kansa." Anan ta juya ta tafiyarta. Bayan ta danyi tafiya sai ta samu wata kujera ta zauna. Ai kuwa bata dade da zaunawa ba saiga abimcinta ya iso. Saman table aka ajemata shi. Daga nan sai ta fara ci tana kallon mutane daya bayan daya. Tana cikin hakane sai taga wasu mutane su uku sun nufota. Wanda ke tsakiya shine yasa wata farar suit sai sauran duk bakaken suit ne. Cikin annashuwa suka karaso wurinta. Daga nan sai sauran suka tsaya daga can nesa shi kuwa mai fararen suit din sai yazo daf da ita yana dubanta. 
     " Nayi mamaki cewa wai a wannan gari namu har akwai wanda zan aikowa sako inason ganinsa amma yaki amsa katin gayyata ta. Bako shakka ko waye shi ya cancanci hukunci dai dai da laifin da yayi."  
     Anan yasmin ta dago kai tana dubansa cike da murmushi. Fuskar nan sai wani sheki take. " Au wai magana kake?" 

                                                PAGE 15

     " Wato bakima sani ba kenan?" Ya tambayeta.
     " Amma fa ina maka jaje. Gaskiya ko wacece bata kyuata maka ba. To amma ka tambayeta ko me yasa tayi maka haka kuwa?" Yasmin ta fada cikin natsuwa.
     Anan mutumin ya kyalkyace da dariya yana dubanta. Daga nan sai ya zauna kusa da ita. Wani apple ne ya dauka daga cikin kayan marmarin da takeci. Sai da ya dan gutsira kadan kafin ya fara magana.
   " Ina fatan dai banyi laifi ba bisa ga wannan zama da nayi ba?" 
   " A a bakayiba." Yasmin ta bashi amsa.
   " Kuma ina fatan banyi laifi ba bisa ga wannan apple dana dauka?" 
   " A a baka yiba." Yasmin ta bashi amsa. 
   " To zanso naji daga gareki ke a ganinki wane dalili ne yasa na aika taki zuwa?" 
   " E to. Amma fa kasan gwamnati ta hana aikin banza. Sabida haka bazan fada kyauta ba. Amma idan zaka biya to komi zai dai daita." Ini yasmin.
    Anan mutumin ya kyalkyace da dariya harda buga kafa da kasa. " Ai a tsammanina manyan mata irinki sunfi karfin su amsa daga namiji. Sai dai su bayar kodan wata rana." 
    " Haka dai ka fada. Ai duk yadda ka tara kana son kari. Wannan shine dalilin da yasa nakeson kari a wurinka." 
    " To naji na yarda kuma zan biya ko nawane. Yanxu ke nake saurare sai ki fada." 
    Anan yasmi  ta dan karkada idanu sai da sukayi fari fat kafin ta fara magana. " Ni a ganina babban dalilin da yasa bata amsa gayyatarka ba shine. Tana ganin cewa ita a matsayinta ya za ayi ta zubar da girmanta har wani ya kira ta amsa. Kara dai ko waye ya kawo kansa."
   " To amma zanso naji ko wacece ita da kuma matsayin nata da take takama dashi?" Mutumin ya fada.
   " Ai kuwa bazata iya fadi ba kai tsaye. Sai dai mai son ji ya fara bayyana nasa." Cewar yasmin.

                                                PAGE 16

      Anan ya danyi murmushi kafin ya bata amsa. " Kina magana da manir tukur ci-rani. Nine dan dan tukur ci-rani idan kinji ana fadinsa. wato sanata na babban birnin tarayya abuja. Wannan shiine ID card dina."  Anan ya miko matashi domin ta tabbatar da matsayinsa da kuma inda yake aiki.  
    Bayan yasmin ta duba saita bashi abunsa tana tunanin karyar da zata fesa masa. Can saita fara. " Kana magana da gimbiya aishat abdullahi jelani. Ina fatan ba saina fadi abbana ba domin kasan shine sarkin wannan jaha ga ba daya." 
    " Da kyau. Amma fa naji dadi sosai. To ko zan iya ganin ID card dinki?" manir ya tambaya. 
    " au kayi hakuri fa yana cikin mota. Amma ba matsala sai muje in nuna maka." 
    " Okay ba matsala muje mana." Cewar yasmin
   Anan suka tashi suna tafiya suna hira. A wannan lokaci gaban yasmin sai faduwa yakeyi domin tasan irin wannan karya dakyar a fita. To kafin sukai ga motar ne sai dabara ta fado mata. Suna kaiwa ga motar sai ta fito da makulli. Anan ta bude ta shiga. Yar karamar jakarta ta dauko tana bincike bincike. Can sai tayi salati da karfi tare da sakin ashar. " Kwal uba." 
   " Lafiya kuwa?" Cewar manir
   " Inafa lafiya? ID card din ne ban gani ba." 
   " Baki ganshi ba? Amma daban mamaki. To ko kin yarda shi a wani wurine baki sani ba?" Manir ya tambaya. 
    " Okay sai yanzu na tuna kafin nazonan saida na shiga wani shago na cosmetics. Inaga kamar na baroshi a can."
   " To in hakane me zai hana muje mu gani watakila ma dace." Inji manir.
   " E ba matsala. Ina fatan dai zaka rakani." Inji yasmin.
   " E mana muje kawai." Injishi. Anan ya umarci yaransa da su wuce da motarsa gida shi kuwa sai ya shiga ta yasmin. Anan ta tuka ta nufi shagon cosmetic din. Suna tafiya kan hanya sai labari yake bata har suka iso shagon. 

                                                   PAGE 17

         Bayan tayi parking ne sai suka fito suka shiga shagon. Daga shiga kai tsaye ta nufi wurin wani mutum. " Ina fatan dai ka ganeni?" Yasmin ta tambayeshi.
        " E na ganeki. Dazu kamar kinxo nan yin sayayya ko." Cewar mutumin. Anan yasmin ta kalli manir dama abunda takeso shine yasan cewa da gaske take ta zo wurin. Sai gashi kuwa cikin sa a ta samu abunda takeso.
       " Wani ID card ne nawa ya bata. To ina ganin kamar anan na barshi shi yasa nazo ka tayani bincike ko zamu ganshi." Inji yasmin.
       " ID card? Ai kuwa banga wanda ya tsinci ID card a wannan shagon ba. Amma bari na duba ko zamu gani. Kuma sai ku zagaya ko zaku dace." inji mai shagon bayan ya mike tsaye. Anan ya fara dubawa. Haka shima manir sai hankalinsa ya dauku dubawa kawai yakeyi koina. Ita kuwa yasmin na ganin haka sai ta fito waje tana waya.
   " Hello princess, don ALLAH kiyi hakuri yanxu zan dawo miki da motar. Amma fa kada ki samu damuwa zanzo da bako a gidanku. Yanzu haka muna kan hanya sai munzo. Bye." Tana gamawa sai ta koma cikin shagon inda ta tarar har yanzu basu ganshi ba. 
    " Amma wai kin fito dashi kuwa?" Manir ya tambaya. 
    " Nima abunda nake tunani kenan. Inaga muje gida watakila yana can." Inji yasmin. A nan suka yiwa mai shagon sallama daga nan suka fita. Haka yasmin ta fara tukawa bata tsaya koina ba sai gidan sarki wato inda kawarta take.  Kai da ganin gidan kasan ya ginu iya ginuwa. Kai tsaye yasmin ta shigar da motar ciki. Daga nan saita yiwa manir iso ciki. Basuyi wani nisa ba sai sukaji an kwala musu kira.
    " Laaa. Shegiya yasmin tun dazu fa nake jiranki. Ni dai ALLAH kasa baki karar min da mai ba." Anan cikin yasmin ya bada kulululu domin a ganinta assiri ya tonu. Tana juyawa saita yi arba da kawarta aishat. Wadda itace gimbiyar asali data ari sunanta ta yiwa manir karya dashi. 
   " Kai, dama yasmin ne sunanki ba aisha ba?" Manir ya tambaya.
  " Haba  sweetheart har ka yarda. Ka manta kawai dama muna irin wannan wasan da ita." Cewar yasmin.

                                                PAGE 18 

    To a wannan lokaci aisha ta karaso wurinsu cike da fara a. Kafin su fara magana ne saiga wani bafade ya sheko a guje wurinsu. " Allah yaja zamanin gimbiya aishat. Wai mai martaba ne keso ganinki da gaggawa." 
   " Okay fada masa gani nan tafe." Cewar aisha.
   " Kai, wai kina nufin aishat biyune a gidan?" Manir ya tambaya. 
   " Haba sweetheart nifa banason irin wadannan tambayoyin. Gaskiya na fara gajiya. Wannan fa duk a cikin wasa ne take magana. " Inji yasmin.
   " To ALLAH ya huci zuciyarki. Kema kin san banason inga abunda ya bata miki rai." Inji manir 
   Anan aisha ta fara kallonsu cikin mamaki domin batasan abunda suke tattaunawa akai ba. " Amma wannan shine bakon ko?" Aisha ta tambaya.
   " E kwarai kuwa shine. Sunanshi manir." Yasmin ta bata amsa.
   " To. Kice mai babban suna ne. To ina maka barka da xuwa. Da fatan kazo lafiya." Cewar aishat. 
   " Lafiya kalau nake ina fatan kema haka." Cewar manir cikin fara a. 
   " Okay ku shiga falon ganinan zuwa. Bari naje naga ko me abba yake kirana akai." Anan aishat ta ruga da gudu ta shiga wani lungu. Ita kuwa yasmin take taja shi zuwa cikin gidan. Anan ta kaishi falo. Bayan sun zauna ne sai hira ta barke tsakanin su. A wannan lokaci manir ya fara yarda cewa yasmin yar sarki ce domin daga zuwansu sai ta bude fridge ta dauko masa lemun kwalba. To suna cikin firar ne sai ga hajiya balkisu ta shigo falon wato mahaifiyar aishat. Ai kuwa suna hada ido sai balkisun ta fara yi musu magana. 
   " Iyeee. Yau diyata ce a gidan. Amma yasmin bakida kirki shine ko lekomu bakya yi ko?" 
   Anan gaban yasmin ya fadi domin tasan fa akwai matsala. Shi kuwa manir baice kome ba sai kallon su yake cikin mamaki. " Au. Wai tare kike da bako. To sannunku da zuwa. Ku dan jirani zan dawo." Anan hajiya balkisu ta fita da sauri da alamar cewa akwai wani abu a gabanta.

                                                 PAGE 19

  
      " Ke nifa ban gane ba. Ki fadamin gaskiya ke waye kuma meye sunanki na gaskiya. Ke kince aishat ita waccan tace yasmin. To wane kikeso in dauka?"  
     " Haba dear ka saurara kaji mana." Anan yasmin ta matse shi cikin murmushi tana karkada masa idanu. " Kuskure kawaine tayi amma nice aishat. Kasan sufa wadannan tsofaffin sunada rudu da yawa. Yanxu haka ta manta ne shi yasa kaji tace yasmin.
     " To idan hakane waye yasmin din? 
     " Itace wadda ka gani da farko mana. Ita kuma wannan ta biyun ummar mu ce." 
     " To amma idan hakane ya za ayi uwa ta mance sunan danta?" 
     Manir na fadin haka sai ga hajiya balkisu ta dawo. " Ke aishat zo ki taimaka mun mu dauko wancan bahon." Ai kuwa yasmin najin haka saita tashi tabita. To anan ne manir  yayi ajiyar zuciya domin a tsammaninsa gaskiyane abunda yasmin ta fada masa. Wato kuskurene hajiya balkisu tayi na kiranta da yasmin. Bai san da cewa abunda ta fada shine gaskiya ba, yanzu ma data kirata da aishat tayi subutar bakine. Can saiga aishat ta shigo falon da sauri. Anan ta duba ga mamakinta bataga yasmin ba iyaka dai taga manir shi kadai. Buda baki tayi da nufin yi masa magana cewa ina yasmin take. To anan tayi subutar baki maimakon tace ina yasmin ta shiga ne sai tayi kuskure tace: " Ina aishat ta shiga ne?" 
    Shi kuwa manir sai ya nuna mata lungun data shiga ne. Anan aishat ta shiga da sauri. To a wannan lokaci manir ya tabbatar da cewa sunanta aishat saboda haka bai damu ba sai ya gyara zama yana kallon talabijin jiran dawowar yasmin wadda yake gani a matsayin aishat. Ai kuwa ba a dau lokaci ba saiga yasmin ta dawo tare da aishat sai kyalkyatar dariya suke. Anan aishat ta fita tabar yasmin tare da manir. " Yauwa. Kaga ID card din nan. " Anan ta miko masa duk da cewa gabanta faduwa yake domin ba hotonta bane a ciki ba. Shi kuwa yana gani sai yayi murmushi yana cewa.
   " Ai ki barshi kawai domin na yarda da duk abunda kika fada. Yanxu bari na koma dama ke nake jira." 
     

                                                  PAGE 20

  
   Anan yasmin ta masa rakkiya har waje. To kafin ya ida wucewa ne ya amshi numbarta tare da bata dubu hamsin. Anan tayi godiya ta koma cikin gidan, daga nan saita ba aishat ID card dinta ta fito waje. adai daita sahu ta tare. Da sauri ta shige ciki tare da fada masa inda zai kaita. 
   Tun daga wannan rana sai yasmin taci gaba da cutarsa tana amsar kudi. A duk lokacin da yayi mata maganar banza domin shi jikinta yakeso ta bashi ba aurenta zaiyi ba. ita kuwa sai ta fara kwanaye kwanaye har sai ya manta da maganar. Takan yi amfani da salo irin nata tana juyashi yadda takeso yadda duk abunda ta fada take xai mata. Duk da kasancewar shima manemin mata ne amma ya kasa cimma burinsa saboda wayo irin nata. A duk lokaci da zaizo ganinta yakan sameta a gidan kawarta aishat. Saboda haka sai yayi tsammanin cewa ita diyar sarki ce.  Babban abunda yasa ya cigaba da kulata shine ganinta kyakyawa kuma wayayya. Kuma a ganinsa tunda diyar sarki ce idan ya samu damar yin abunda yakeso da ita to zai yi samu sosai kuma zata soshi. Dama shi abunda yakeso shine: Da yayi amfani da ita sau daya sai ya tafiyarsa yadda baxata kara ganinsa ba.  Sai gashi cikin rashin sa a ya hadu da reza wadda iyaka tayi masa halinta na reza wato cuta. 
   To kamar yadda mutane sukace yau gareka gobe ga dan uwa. Wato kwanaki casa in na barawo kwanaki goma sune na mai abu. Wannan magana haka take domin wata rana a cikin kasuwa yasmin na cikin rumfa ita da ummarta suna toya waina.  Kai daganin shigarta kasan daga gidan data fito domin tayi datti sosai ko alamar wanka babu a jikinta. Kayan datasa duk sun rine da bakin tanda sai zufa take saboda zafin daya isheta. Su kuwa mutane sun cika rumfar sai ciniki ake ba kakkautawa. Idan kaga wannan shigar datayi zakayi mamaki ace wai ita ke yiwa mutane reza domin zaka zata daga cikin wani daji ta fito. Ana cikin hakane saiga wata mota ta faka a wurin. Su yasmin basu damu da wanda ya fito ciki ba domin a ganinsu shima yazo sayen waina ne. Ai kuwa haka ya nufosu a tsanake har ya iso wurin da suke.
    " Ga kudina a zuba min wainar dari biyu sai naman dari da man goma." Anan ya miko dari biyar. Yasmin ce tasa hannu da nufin ta karba. Ai kuwa tana amsa sai suka hado ido da Manir Wai ashe shine yazo sayen waina.

                   Me zai faru?

                        Zamu cigaba.........


                                                   REZA

                                     AUTHOR: ABDUL KING ARTICLE


                                                 PAGE 21


      " Aishat," Haka ya fada ita kuwa sai tayi da dai duniya batasan dashi ba. Juyawa tayi tana ayyukanta. Shi kuwa manir sai mamaki ya kamashi. Anan ya matso kusa da ita yana dubanta cike da mamaki. " Wai kada fa ince gimbiyar ce da kanta na gani ko kuwa?"  
      " Haba malam wai meye hakane sai wani matseni kake. To na fada ba ita bace sai ka matsa ka bani wuri ko!" Inji yasmin cikin fushi. Anan ta tashi tsaye tana ciccika. 
      " Amma ban taba tsammanin haka a gareki ba. Dama ashe ke mayaudariya ce. Shine harda cemin ke diyar..." To kafin ya karasa maganarsa ne sai umma ta tari numfashinsa.
      " Haba dan danga. Ai ko maye akace yayi hakuri ya dangana. To balantana kai da ba mayen ba tunda tace ba ita bace sai kayi hakuri ka tafi mana." 
      " Au, wato dama duk abunda take da saninki kenan. Dama kece ke daure mata tana yadda taso ko. To bari kuji. Koda sama zata hadu baxan yarda ba. Alkur an sai kun ban kudina." 
       " To kudin naka nawane da har kake ikirarin su. Dan neman marassa kunya ka fadi muji." Inji umma.
       " To idan zaki biya sai ki biya domin 3.6 million ne."  Inji manir
        Ai kuwa umma naji haka sai cikinta ya bada wani kulululu. Anan tayi shiru domin tasan da cewa yau fa karyarsu ta kare assiri ya tonu. Can sai ta nisa ta fara magana." Ni a ganina kayi kuskure domin ita wannan da kake gani daga gida sai gida. Ko fita batayi balantana har ta gamu da wani can." 
      " Ai wannan magana dagaji nasa babu kamshin gaskiya a ciki. To idan abunda kika fadi gaskiya ne ta jiyo ta kalleni mana." Inji manir.
      Anan yasmin tayi shiru kuma taki juyowa. " Wato kyaleni zakiyi kenan. To wallahi kinyi kadan. Ba moriya kuma ba kudi. Wato tunda kin samu damar amsar kudin shine kika gudu daga ranar ban kara ganinki ba sai yau ko. To yau karyarki ta kare kome  zai faru sai dai ya faru amma sai kin ban kudina." 
     " Au, wato dama kaima mutumin banza ne ko. Kune kwadayi manema mata. Idan an biya bukata sai a gudu. To gashi baka samu nasara ba ita ta samu. Kuma data biya bukatarta saita gudu. Har shine kake ganin laifinta don ta amshi kudinka. To wayace ka bata ai kai ka bata. Da ace ka samu nasarar yi mata juna biyu ai da shikenan ko duriyarka bazamu kara jiba. Shawaraki kawai." Inji umma ladiyo cikin fushi.
    
                                                       PAGE 22

        " Nifa ba ruwana da duk a abunda zaku fada ku fada kawai. Amma kudi dole sai sun fito yanxun nan a wurina nan. Barima ku gani."  Anan ya tankwahe rigar hannunsa. To a wannan lokaci masu sayen waina sun fara ragewa saboda wasu duk an sallamesu. Wato a cikin rumfar dai su uku ne ke tada jijiyoyin wuya. Anan ya jawo yasmin da karfin tsiya da nufin lahanta ta. Ita kuwa tana ganin haka saita rankwada masa mari. To kafin kaceme sai suka kaceme da kokuwa. Ita kuwa umma ladiyo maburkaki ta dauko tana dukansu don su bari amma ko saurararta basayi. Manir ne ya takarkare shi a ganinsa tunda yasmin mace ce zai iya kaita kasa cikin sauki amma sai gashi abu ya gagara. Daya turata sai yaji kamar ya tura kato domin ko motsi batayi. Suna cikin hakane yasim ta samu nasarar tallabosa kamar yadda masu tallar dawo ke rike roba. Sai da tayi hajijya dashi sannan ta jefa shege cikin kwandon wanke wanke ji kake kimissss.
      " Wayyo cikina." Anan ya tashi yana gurmanta. " Ke don ubanki ni zaki yiwa..." Anan yayo cikin yasmin ita kuwa tana ganin haka saita juya ta dauko bokiti mai cike da kullu. Juyewa manir kullun tayi sannan tayi jifa da bokiti tana jiran isowarsa. 
     " Kam bala in nan da rayuwa!, ke ni zaki zubawa kullu?" 
     " An zuba kome zakayi ka dade baka yiba." 
     Anan manir yayo cikinta da nufin lankwasheta ita kuwa umma ladiyo sai tasha gabansa. " Kul kada ka taba min diya!" 
    " To hala bakiga abunda tamin bane. Ai kome xai faru sai dai ya faru saina hallakata." Anan ya miko hannu da nufin ya jawo yasmin ita kuwa saita jawoshi sai ga manir a kasa ji kake timmm hakoransa na cizon kasa. To kafin ya tashine saita tallabosa kamar ta dauki dan yaro. Sai da ta nunashi a sama sannan ta makashi saman tanda. Kuma a wannan lokaci tandar ta dauki zafi sai tiriri take. To da aka jefa manir saman tanda duwayyunsa ne suka fara sauka saman tandar kafin jikinsa. Anan yayi wani ihu sannan yayi tsalle sama. " Ayihuhu." Da karfi ya fadi hakan bayan ya fado yana soshe soshe. Da sauri ya cire wandonsa bai damu da mutanen dake kallonsa ba. A guje ya nufi wani bokiti shi a tsammaminsa ruwa ne amma kash ba haka ba. Sai da yayi tsalle sannan ya dunguma a ciki. Anan yayi ihu wanda yafi na farko sannan ya fita cikin rumfar a guje ba wando. Wai ashe ruwan xafine tafasashshi wani mai shayi ya kawo a ajiye masa. To a cikinsu ne ya fada. Haka manir ya fita a guje ba wando bai tsaya ta motarsa ba balantana daukar wandonsa.

                                                       PAGE 23

     Su kuwa su yasmin da ganin haka sai suka taro adai daita sahu. Anan suka tattara kayansu suka nufi gida. Su kuwa mutane sai mamaki suke na faruwar wannan abu ba tare da sanin abunda ya kawosa ba. 
     Da la asar ne sanya sanya sai ga wata mota ta faka a kofar gidan sarki. Manir ne ya fito tare da bodyguard dinsa guda biyu. Ai kuwa suna fitowa cikin sa a sai ga gimbiya aishat ta fito. Anan manir ya nufi wurinta. " Sannunki yasmin dama tambaya zanyi." 
   " Yasmin kuma? Nifa sunana aisha ba yasmin ba." Injita.
   Anan manir yayi shiru cikin mamaki. " To idan hakane waye yasmin?" ya tambaya.
    " Ya kana wannan tambaya. Yasmin ai itace wadda kaxo da ita a ranar har na iske kuna wata rigima." Anan manir yayi shiru domin ya gano cewa yasmin yaudararsa tayi da cewa sunanta ashat kuma  ita diyar sarki ce ashe ba haka ba.
    " To yanzu ko zaki iya nuna min inda gidansu yake?"  
    " Gaskiya bazan iya ba domin ban taba zuwa ba. Dama a wurin talla ne na hadu da ita domin ni ma abociya waina ce. Daga nan sai muka kulla kawance." Inji aishat. " 
     " Talla fa kikace, dama tana talla? Nifa cemin tayi ita diyar sarki ce!" Manir ya fada yana mamaki. 
      " Laaaaaa diyar sarki?" Anan aishat ta kyalkyace da dariya. " Babanta mahaucine sana ar nama yake." 
      " Nama?" Manir ya dafe kai.
      " To amma hala wani abune ya faru tsakaninku?" Aishat ta tambaya. Anan manir yayi shiru domin yasan idan ya fadi iyaka tace ala gwai kara da tayi masa haka tunda manemi mata ne. 
      " A a ba kome dama inaso najine?" Anan ya nufi motarsa yabar aishat cikin mamakin wadannan tambayoyi haka. A cikin ransa kuma sai tafarfasa zuciyarsa take domin yasan cewa yasmin ta gama dashi tunda ta amshi mukudan kudi a wurinsa kuma bata biya masa bukatarsa ba. Dole ya hakura ya kama harkokin gabansa. Dama maganin manema mata shine reza.
      Da daddare ne wani kazamin fada ya hargitse tsakanin yasmin da yayanta abba akan kudi. Umma ladiyo na ciki dole ta fito rabo.
      " Ke wayayi shai kin ban kudi. Inba fuya uba ba. Ya ja ayi kiban naiya tayatin don kin yaina ni." Haka abba ya fada cikin fushi yana dubanta.
  
                                                        PAGE 24

     " Don ma ka samu na baka naira talatin shine kake wannan abu. To baxan kara ba sai kayi yadda zakayi." Cewar yasmin.
    Anan umma ladiyo ta shiga tsakani. " Wai dama akan kudine kuke wannan abu. Ke meyasa kikeda mutukar son kudi wai? Ba a dade ba kin amshi miliyoyan kudi ga wani sakarai amma ace wai kiba yayanki naira talatin a ciki."
    " To wai umma shi me zaiyi da kudi? Iyaka fa shaye shaye." Inji yasmin.
    " Ke, ni kike cewa ina shaye shaye. Bayi ki gani." Anan yayo cikinta da nufin maketa ita kuwa sai ta koma bayan umma a guje ta labe. Ita kuwa umma rike shi tayi tana lallashinsa kada ya buge mata yar diya. Anan ta juyo kan yasmin tana mata fada. 
     " Kefa nasan halinki bakya jin magana. Yanzu yayan naki zakice me zaiyi da kudi. Ai wannan rainin hankali ne ki dubi tsabar idonsa ki fada masa haka." 
    " To umma ai abunda na fadi gaskiya ne. Kuma shima ya sani." Inji yasmin. 
    " Ke. Dani kike?" Anan abba yayi cikinta a guje da nufin maketa. Ita kuwa yasmin sai ta fara bode bode a bayan umma bata bari ya kamata. Shi kuwa sai ya cigaba da binta idan yayi nan tabi nan. Ita kuwa umma sai lallashinsa take amma ina bai saurare. Can sai ya kamo hannunta. To kafin ya jawota ne ta kubce ta nufi kofar gida a guje. Shi kuwa dafota yayi da nufin kamota. Tana cikin gudun ne sai tayi tuntube da wata tukunya. Anan yasmin ta fadi rikicaaa.
    " Wayyo umma na mutu. Hancinaaaa, hancina ya karye jama a ayi agaji." Haka ta fada sabida zafin da takeji. Shi kuwa abba sai ya matso kusa da ita yana bankar dariya. Hannunsa yasa ya dauki yar karamar jakar wadda kudin suke ciki. Yana cikin kyalkyatar dariyar ne sai yaji magana a waje ana " KU TARE KU TARE." To kafin abba ya ankara sai ga wani katon sa ya shigo gidan. Anan san ya jawo abba. Sai da yayi waliliya dashi sama sannan ya makashi saman ginan ji kake kicibis. Anan masu san suka shigo suka wuce da abunsu basu tsaya duban abba ba balantana su bashi hakuri. 
    A wannan lokaci abba sai mulmule mulmule yake yana ihu sabida zafin da yakeji. " Umma a kiya liman!" Inji abba.
    " Idan aka kira liman me zaiyi ma." Umma ta tambayeshi.

                                                       PAGE 25

     " Ni dai nace a kiya liman." Abba ya kara fadi.
    " To sai ka fadi idan aka kirashi me xaiyima?" Umma ta tambaya.
    " Umma na mutu. Akiya liman yayimin shalla ya kaini makabalta. Wayyo kunkuyuna. Umma banida kunkuyu." Haka abba ya fada yana mulmule mulmule. Ita kuwa umma sai ta matso kusa dashi ta dauke yar jakar da kudin ke ciki. 
   " ALLAH ne ya kamaku kaida ita. Yanxu zan dauki kudin kuma ba wanda zanba a cikinku." Anan ta nufi hanyar dakinta ta kyalesu suna ihu. Yasmin da abba na ganin haka sai suka fara bata hakuri ta dawo a raba kudin amma ko saurarensu batayiba. 
    " Wayyo umma ki dawo hancinaaaaa." 
    " Yiiiiiiii. Umma ki dawo kunkuyuna. Wayayi banida kunkuyu." 
    Washe gari ne yasmin tayi wanka da nufin zata kaiwa wata kawarta ziyara. To tana cikin taxi ne saita hango wata mata a gefen titi tayi zaune jugum. Kai da gani kasan tana cikin damuwa. Anan tasa mai taxi ya tsaya duk da ba nan xata sauka ba amma haka ta sallemeshi. Takowa tayi har saida taxo wurin matar. Daga nan saita mata sallama. Ita kuwa matar ta amsa. To bayan yasmin ta zauna kusa da ita ne sai tayi mamaki domin matar yarinya ce irin shekarunta. Abunda ya bata mamaki shine me wannan yarinya take tunani haka tayi zaune ita kadai. Kuma kayanta tsaf tsaf balantana tace talaucine ya mata yawa. 
    " Kiyi hakuri na zauna kusa dake wannan ya farune sanadiyar wadansu tambayoyi da nakeso na miki. Ina fatan zakiban hadin kai. Nasan ko kadan bai kamata in tsunduma kaina a cikin abunda bai shafeni ba sai dai sabida hausawa sunce ciwon ya mace na ya mace ne shi yasa na yanke shawarar cewa dole sai na tuntubeki domin naji labarinki da kuma abunda kike tunani wanda yasa har kikayi zaune a gefen titi ke kadai." 
    Anan matar ta dan nisa kafin ta fara magana. " Abunda nake tunani bai shafeki ba domin ko na fada miki ba abunda zaki iya yi akai. Sabida haka inaga da kin matsa anan da zaifi." Inji matar.
   " Wannan tunaninki ne amma ai bakida tabbaci akan abunda kika furta. Kafin nan dai sunana yasmin kefa?" 
   " Xaki iya kirana da maryam." Matar ta fada. 

                                                    PAGE 26

    " Da kyau, ina fatan dai zaki sanar dani abunda ke damunki a yanzu." Inji yasmin.
    " Kai wannan mata akwaiki da son sanin labarin mutane. Amma tunda kin matsa ba matsala zan fada miki. Bako shakka mu mata mayaudara ne kuma macuta wadanda basa tunanin gaba balle baya. Bako shakka mu mata bamuda nazari balle lissafi wanda sanadiyar hakan ne yasa muke fadawa cikin dana sani. Sai kuma shegen kwadayi da muke dashi na abun duniya. Nasan ba kowace mace keda irin wadannan halayya dana fadi ba amma kuma akasari suna dashi. Na kasance ina soyayya da wani yaro waishi tanimu. Tanimu ya kasance kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa. Sabida hakane mafi yawan yan mata ke mutukar nuna kauna a garesa amma ya dage sai ni. Mun fara soyayya ne tun da kuruciya har girma kafin na fara sauya masa sabida kudi da suka budemin idanu.Kwatsam wata rana sai ga wani alhaji mai kudi yaxo nemana. Shi wannan alhaji ya kasance duk shekara sai ya canza mata. Wato idan ya aureki wannan shekarar. To wata shekara zai sakeki ya auro wata. Ba yadda su abbana basu yiba domin fahimtar dani akan halaiyarsa amma naki na gane saboda haka suka zuba mini ido."
   " Tun tanimu bai gane ba har ya fara dagowa sabida alamomin dana fara bayyanawa a garesa. Sabida wannan dalili sai ya sauwakemin ya shafamin lafiya. Shi kuwa alhaji murna yayi mutuka dayaji cewa tanimu yayi fushi. A lokacin da zaa yi auren iyayena basu yimin komi ba sabida ba da son ransu zanyi auren ba. Alhaji ne yayi komi. Ni a ganina zan tabbata a matsayin matarsa amma kash ba haka ba. Shekara daya da tarewa sai ya bani takadda. Yanzu nayi kwatakyas. Bani ga kudi bani ga saurayina na ainahi mai sona son gaskiya. Babban abunda keban haushi shine bai bari na fita dako allura ba domin cewa yayi kome nasane saboda shi yayamin kome. Haka kuma a ckin wannan shekarar ba wani dadine najiba domin shi mashayi ne. Ba ruwansa da hakkin aure. Nayi dana sanin abunda nayi kuma naso ace inada dama in hanashi wadannan ayyuka nasa domin nasan nan bada jimawa ba xai auro wata. Bayan ya maida ita bazawara sai ya saketa kamar yadda yakeyi."

                                                  PAGE 27

    "Gaskiya kinyi babban kuskure da kika tafka wannan mummunar barna. Wannan shi zai zama darasi ga sauran matan. To amma shi wannan alhaji ko zaki iya fadamin address dinsa?" Yasmin ta tambaya.
   Anan maryam ta dauko wata yar karamar takadda ta bata. "Wannan shine address dinsa. To amma me zakiyi da address dinsa?" 
   " Kada ki damu kawata ki zuba ido ki gani amma ni sai nayi maganinsa."Inji yasmin. 
   "Ta yaya zakiyi maganinsa?" Maryam ta tambaya.
   "Ai ba saina fadi ba. Zaki jiya da kanki. To amma ban tambayi shi tanimun ba. Yanxu ko kin san inda yake?" 
   "Aa." Inji maryam.
   "To gaskiya ya kamata ki bido duk inda yake domin shi masoyinka kullum masoyinka ne. Idan kika nemi gafara wata kila ya duba miki."Inji yasmin.
   "Wannan hakane. Amma ni har yanzu inajin tsoro domin ji nake kamar ya manta dani gaba daya. Kusan shekara fa kenan da rabuwarnu."Inji maryam. 
   "Kada ki damu kawata, ai shi namiji kamar guga yake. Zaki iya jifa dashi yadda kikeso kuma a duk lokacin da kikeso sai ki jawoshi. Kina jawowa zakiga ya biyoki yana miki abunda kikeso. Kinga kuwa har yanxu tanimu a hannunki yake sai dai idan baki so ba. "Cewar yasmin.
    Anan maryam ta danyi murmushi har saida hakoranta suka fito waje." Gaskiya kawata akwaiki da hausa sai kace wata marubuciya. Wannan hausa haka sai kace yar jarida."
   "Haka dai kikace ai ni ba wani iya hausa nayiba."Inji yasmin.
   "To yanxu dai meye abunyi akan wannan magana taki?" Maryam ta tambaya.
   " Yanzu dai tunda na gano abunda ya sakaki a cikin wannan tunani zanyi yi iya kokarina na ganin cewa na kwato miki yancinki ga wannan alhaji. Ba ke kadai ba harda duk matan dayama irin wannan abu wato daya aura sai ya saki. To amma kafin nan bari mu fara kammalawa da matsalar tanimu domin shine a gaba. Inaga idan saurayinki ya dawo hannunki to shi kenan komi zai dai daita kafin mukai gana karshen wato alhaji." 
   " To yanxu ya za ayi ya dawo hannuna kenan?" Maryam ta tambaya.
   
                                                      PAGE 28

     "Ai wannan abune mai sauki. Sha kuruminki domin kamar an gama ne. To amma shi wannan alhaji meye sunanshi na ainahi?" 
     "Sunanshi alhaji sadi mai katifa. Shahararren dan kasuwa ne kuma sananne."Inji maryam. 
    "To yanxu sai ki tashi muje naga unguwarku." Inji yasmin. 
    " To. Ke baiwar Allah ina fatan dai ban bata miki lokaci ba. Naga kamar wadannan ayyuka da yawa gashi kuma kamar zaki wani wuri."Inji maryam.
    " A a kada ki damu da inda zanje domin wurin bayada muhimmanci sosai. Kinga kuwa kona fasa ba matsala bane. Yanzu dai yi maza ki jamu muje." Inji yasmin. Anan maryam ta jata suka gangara wata yar hanya. Sai da suka danyi tafiya mai nisa sannan suka cimma wata unguwa kowa sai sha anin gabansa yake. Tun daga shigowarsu aka tsura musu idanu sai kallonsu ake. Wasu kuma sai hararar maryam suke kai da gani kasan kowa yasan abunda tayi. Yasmin ce ta kula da hakan amma kuma sai tayi kamar bata kula ba domin ba abunda zata iya yi akai. 
  To bayan sun iso gidan ne sai maryam ta mata iso har ciki. Daga shigarsu gidan yasmin taga yanayi ya canxa domin duk abunda mutanen waje kema maryam haka suma yan gidan sai harararta suke suna mata kallon banza. Kai da gani kasan akwai masu jin haushinta sosai. Anan maryam ta nuna mata dakin da zata shiga. Ai kuwa tana shiga sai ga wata mata tayo kan maryam da fada. Kai da gani kasan mahaifiyarta ce.
    "Ke in banda rainin wayo  shine kika fita wai ki barni da tulen wanke wanke ko. To ga yacan yana jiranki sai kiyi maza ki fara kafin ranki ya bace."
    " Haba umma nifa ko karyawa ban yiba amma kuma yanxu kice inyi wanke wanke."Inji maryam.
    "Iyeeeee. Lalle yarinya kin girma. To ki fadamin kice bazaki yiba ko. Nace ki fadamin cewa bazaki yiba in sani. In banda shashanci irin naki ke har kinada bakin magana wai baki karya ba to ni na hanaki karyawa ne. Ai da sai kije wurin wancan alhaji sadi ya baki abinci mana tunda kin fifitasa akan tanimu. A haka dai umma taci gaba da jijini ba sassautawa.
    "Yanxu dai umma kiyi hakuri bari naje na wanke."Inji maryam. Anan ta nufi wurin plates din domin ta wankesu

                                                         PAGE 29

   Yasmin fitowa tayi ta kama mata har suka wanke plates din gaba daya. Daganan sai suka koma daki. Ita kuwa maryam fitowa tayi ta xuba musu abinci ta shiga dashi dakin. Anan suka faraci suna tadi.
    "Amma fa kawata naji dadin wannan taimako da kika yimin. Da ace bakyanan da yanxu haka ban isa gama wannan wanke wanke ba." Inji maryam. 
    " Ai ba kome yima kaine."Yasmin ta fada cikin murmushi. " Amma kuma mutanen wannan gida naku ko ince unguwar gaba daya basa sonki. Na fahimce hakan ne ga kallon da suke miki na rainin wayo. Amma kuma banga laifinsu ba domin abunda sukayi yanada alaka da barnar da kika tafka a baya na yaudarar tsohon saurayinki tanimu.
     "Wato kema kin goyi bayansu kenan?" Maryam ta tambaya.
     "A a bana goyon bayansu. Amma inaso ki gane cewa da ace baki kawo yaudara ga al amuran rayuwarki ba da hakan bai faru ba." Cewar yasmin.
     "To yanxu sai ki fadamin wane abu zanyi na karkare wannan bakin suna dana jawowa kaina?" Maryam ta tambaya.
     " Yauwa to yanxu kikayi magana. Da farko dai idan kinaso wannan bakin suna naki ya karkare to sai kin shirya da saurayinki tanimu. Shi kuma alhaji sadi mai katifa sai kinyi yadda zakiyi ya dawo kasanki ya zamana cewa kina juyashi kamar tanda a cikin waina."Inji yasmin.
    " Tab. To ai wadannan abubuwa da kika lissafo bazasu yiwuba. Shifa tanimu kada ki manta yanxu haka yana fushi dani saboda yaudarar dana masa. Shi kuwa alhaji sadi mai kudine sosai yadda yafi karfin ya zauna a kasan mutum sai dai mutum ya zauna a kasansa."Inji maryam. 
    Anan yasmin ta kyalkyace da dariya tana dubanta. "Duk wadannan abubuwa masu sauki ne a wurina. Amma yanzu tashi muje ki nuna min gidansu tanimu."Inji yasmin.
    Anan suka fito gidan sai tafiya suke. Sai da suka danyi tafiya mai jayawa sannan suka cimma gidan. Ai kuwa karasowarsu keda wuya sai sukayi arba da tanimu ya dawo daga wurin yawonsa. Anan ya xuba musu idanu yana jiran isowarsu yaga abunda ke tafe dasu. Kai da ganin yadda yake kallon maryam kasan ba lafiya domin ji yake kamar ya yanketa sabida haushi.
 
                                                      PAGE 30

       "Ke don ubanki me ya kawoki kofar gidanmu. Bana miki kashedi da xuwa nan ba. Zan balla kifa,  zaki wuce ko sai na nuna miki koni waye." Anan ya fara tankwahe hannun rigarsa. 
     " Haba tanimu ka saurara kaji mana. Yanxu munzone domin ayi sulhu nasan cewa maryam bata kyauta ba amma kuma hakan ba shi zaisa ka tsaneta ba. Ka tuna cewa kaima fa kana sabama ubangiji kuma ka nemi gafararsa. Kaga kuwa yanxu ya kamata ace ka saurari abunda tazo dashi." Inji yasmin.
     "Ke saurara. Nifa ba ruwana da wani wa a xi naku. Inba hauka ba sulhun uban me kukeso. Bayan ta riga ta kaini ta baro shine wai ku dawo sulhu. To saurara kiji. Ni ba guga bane da za ayi jifa dani a lokacin da akaga dama sannan kuma a jawoni a lokacin da akaga dama. Sai kujecan ku samu ire iren wadanda kuke nema domin ni bana daga ckinsu. Anan ya kama hanyarsa da nufin shigewa gida. To kafin yakai ga shiga ne sai yasmin ta kwala masa kira. Juyowar da xaiyi sai yayi arba da ita rike da kudi masu mugun yawa a hannunta. Ai kuwa yana kallon kudin idanunsa suka wani budewa sai kace maxuru. Anan ya sheko a guje wurinsu. "Au hajiya magana kike? Bari na dauko tabarma sai mu zauna!" 
      "Wace tabarma kuma? Ai mu ba zama xamuyi ba. Yanxu dai rike wadannan."Anan yasmin ta mika masa kudi. " Abu daya mukeso dakai. Muna so ka yafewa maryam abunda tayima kuma kaci gaba da zuwa gidansu kuna hira wato tsohuwar soyayyarku ta dawo." 
       " Indai wannan ne abu mai sauki. Ai ku dauka kamar komi ya wuce." 
       Anan sukayi sallama ya nufi gida. Ai kuwa yana wucewa suka kyalkyace da dariya. " Ai dama na fada miki cewa shi namiji kamar guga yake. Zaki iya jifa dashi yadda kikeso kuma a duk lokacin da kikeso sai ki jawoshi. Kina jawowa zakiga ya biyoki yana miki abunda kikeso." Inji yasmin.
      " Ai kuwa na yarda da wannan magana taki. Wai yanzu har ya aminta kenan."Inji Maryam.
      " To yanzu mun gama da wannan saura mai wuyar wato alhaji sadi mai katifa. Zan nuna masa cewa duk wanda yayi sata gidan barawo to rance ne ya karba. Bazan zauna ba har saina tabbatar da cewa alhaji sadi mai katifa ya walakanta kuma ya dawo kasan mata. Ba wai kasan mata kadai ba bawan mata."
   "Ta yaya kenan?" Maryam ta tambaya.
   "Ki xuba ki gani." Yasmin ta bata amsa. Anan ta dauko bakin glass dinta ta kafa. Daga nan tayi sallama da maryam. A haka maryam ta bita da kallo tana mamakin yadda za a yi ta mayar da mai kudi kamar alhaji sadi walakantacce kuma bawan mata. 

              Me zai faru?

                        Zamu cigaba.........

                                                          REZA

                                        AUTHOR: ABDUL KING ARTICLE



                                                    PAGE 31

       Bayan sati uku da haduwar yasmin da maryam. Wata rana maryam na cikin dakinta ita kadai tana kallon labarai na NTA ga talabijin kwatsam sai taga wani labari mai firgitarwa kamar haka.  " Innalilahi wainna ilaihir rajiun. Ayau ne muka samu labarin cewa mashahurin dan kasuwar nan mai suna alhaji sadi mai katifa ya samu karayar arziki har takai da cewa abinci ma roko yake a basa. Babu wanda yasan dalilin wannan jaraba iyaka dai malamai sunce yine na ALLAH. Saboda wannan dalili ne yasa sarkin malamai na wannan jaha yayi umarni da asa wannan labari ga media yadda duk wanda ya gani sai ya taimaka masa da addua." Daga nan sai aka nuno vedio dinsa duk ya canza yayi wani baki. Kayan jikinsa sun rine saboda datti. Wasu mutane kuma sai bashi sadaka suke naira biyar naira goma shi kuma ya dage sai amsa yake yana godiya. Wannan labari ya mutukar tayarwa da maryam hankali domin ko da dai rana bata taba tsammanin cewa irin hakan kan iya faruwa ga mai kudi irin alhaji sadi ba domin ko kyauta zaiyi to daga dubu darine zuwa sama yake bayarwa.  
     Batasan lokacin data saki remote din ta fada duniyar tunani akan abunda ya kawowa wannan mai kudi bala i haka ba. Tana cikin wannan tunani sai taji an yi sallama a dakin. Tana dubawa sai taga yasmin ta shigo. Anan maryam ta sheko a guje suka rungume juna cikin farin ciki. " Har na debe rai daga ganinki. A tsammanina bazan kara saki a ido ba."  Haka maryam ta fada bayan ta jawota sun zauna. 
     "  Kiyi hakuri kawata na dade inaso inaso naxo wurinki amma lokacine ban samu ba. Kin san harkar tamu ta kananan mata." Inji yasmin.
     " Wai kanana. Ai ku manya ne mudai ne yara. To ya kike ya hutawarki?" 
     " Duk lafiya kalau."
     " Kawata yanzu fa naga abun mamaki. Wai kinji cewa alhaji sadin dana fada miki cewa yana auri saki ya samu karayar arziki. Yanzu ma abinci roko yake a basa. Ni abunda ya dauremin kai shine ya akayi ya talauce a cikin sati uku." Inji maryam.
      Anan yasmin da kyalkyace da dariya. "Maryam kenan. Ai wannan kadan ne daga cikin ayyukan mu. Shi kadan ma ya gani."
     " Wai ko kina nufin kin san abunda ke faruwa ne. Dama alkawarin da kika dauka na cewa sai kin maida shi walakantacce kuma bawan mata ashe da gaske kike. To fadamin ya akayi kika samu damar yi masa haka?" Maryam ta tambaya. 
      To anan ne yasmin ta fara bata labari.
            Wata rana a a cikin wata unguwa............

                                                   PAGE 32



    Dan saurayine ke tafiya a saman titi yayi wanka kai kace wani dan minister. Sai ga yarinyarsa a gefe suna tafiya sai tadi suke cikin annushuwa. Suna cikin hakane saiga wata mota baka ta wuce a kusa dasu. Motar na wucewa sai ta yo baya har saida ta tsaya kusa dasu. Daga nan sai wata yarinya ta fito daga cikin motar. Ai kuwa tana fitowa sai suka hada ido da wannan saurayin da yayi wanka. Shi kuwa yana ganinta saiya juya baya.
       "Haba sweetheart ya naga ka wani juyawa baya?" Inji yarinyar.
       "E wallahi ina dan tunani ne. Amma yanxu na tuno wani abu. Kin gane ko bari mu koma gidanku inaga kamar na manta wani abu."Cewar yaron.
       "Okay ba matsala muje mana." Inji yarinyar. 
       To kafin su yi nisa ne sai wannan yarinyar data fito cikin mota ta fara kiransa. "Huzaifa, Huzaifa,Huzaifa." 
      "Laaaaa sweetheart naji kamar ana kiranka!" Inji yarinyar.
      " Manta kawai bani bane wani ne can ke magana." Inji huzaifa.
      " Nifa kamar muryar mace nakeji tana kiranka." Cewar yarinyar.
      "Haba dear ki yarda dani mana. Kin fasan banida kowa in ba keba."Cewar huxaifa.
      Anan yarinyar ta danyi murmushi. " To yayi na yarda mu tafi kawai." 
     Suna cikin tafiyar ne sai yarinyar nan data fito cikin mota taci gabansu. " Haba huzaifa ya kana guduna. Ka saurara kaji mana." Injita.
    "Ke mahaukaciya ki rabu dani. Kin san fa na miki kashedi akaina ko." Inji huzaifa.
    "Haba huzaifa ya kana fadin haka. Niface yasmin dinka ko ka manta." 
    "Nifa ban gane ba shin wai wannan wacece data tsayu a gabanmu?" Yarinyar ta tambaya. 
    " Manta da ita kawai mahaukaciya ce zo muyi tafiyarmu." Inji huzaifa bayan ya jawo hannuta. Ita kuwa yarinyar buge hannunsa tayi cikin fushi tana cewa:
     " Ni ba zanje ko ina ba sai ka fadamin ko wacece ita." 
     Cikin fushi huzaifa ya nuni yasmin da yatsa. " Ke idan baki shiga taitayinki ba zan cimiki mutunci fa. Na fiki tashanci fa. Yanxu zaki bacemin da gani ko saina debeki ne." 
     " Haba huzaifa ya kana fadar haka nifa yau ba da fada naxo ba. Alheri ne na kawoma kuma inda ka saurareni duk zamu karu." Inji yasmin.
     " Ke nifa ba wani alheri tsakanina dake. Ke ni har zaki dubi idona...." Anan ya kalli yarinyarsa. " Sweetheart zo mu tafi kawai"


                                                       PAGE 33

   " Kai nifa ba inda zanje idan baka fadamin ko wacece ba." 
   "Haba dear wannan fa ba kowa ceba in banda yasmin diyar ladi mai kunun zaki. Kema fa kin santa."
   " Ni ban santa ba. Sannan ma wai meye hadinka ne da ita?" 
   " Ba wani abu. Dama jiya ne nasha kunun zakin naira hamsin ne inaga kudin ne taxo karba." Anan ya dauko naira hamsin ya mikawa yasmin tare da mata wani signal don ta karba. Shi a ganinsa wannan karyar da yayi zata fiidda shi daga fita kunya don kada yarinyarsa ta gano koshi waye. 
    " Ni ba zan karba ba domin tuni muka bar sayar da kunu. Kuma idan za a yi magana sai a fadi gaskiya banda takulen karya." Inji yasmin.
     Anan cikin huzaifa ya wani murdawa domin yasan asirinsa na gab da tonuwa. " To kada ki karba sai meye. Dama ke ai diyar ladiyo ce mai waina ta unguwarmu. Haka zaki kare a cikin tsiya." 
     " E naji. Kaida kaka almajiri fa a makarantar malam da guntu kai har kanada bakin magana." Inji yasmin.
     " Kai, sister almajiri fa kikace?" Yarinyar ta tambayi yasmin. 
     " Au dama bakisan koshi waye ba shine kike wani kishinsa?" Yasmin ta bata amsa. 
     " Haba yasmin meye wannan abu. Ni zaki yiwa karya a gaban sweetheart dina. Dear kada ki dauki abunda tace zo mu tafiyarmu kawai. " Ai kuwa yana fadin haka sai ga wata mata tazo wucewa tare da diyarta yar karama. Ai kuwa yarinyar na ganin huzaifa saita sheko a guje wurinsa.
     "Laaaa mama dubi almajirin daya mana wanki ya tsere mana da canji."Haka yarinyar ta fadi da karfi shi kuwa huzaifa sai ya cije fuska domin yasan yau karyarsa ta kare. Ita kuwa yarinyar tasa sai ta fara harerensa.
     " Ashe dama kai almajirine shine kamin karya wai kai dan minister ne ko. Kullum sai ka yita amsar min kudi da zimmar zaka bani ko. To ALLAH ya isa tsakanina da kai." Anan yarinyar ta tafiyarta. Shi kuwa sai kwala mata kira yake.
     " Sweetheart ki tsaya kiji mana karya fa take." Haka ya fada yana tafiya yana binta don ya ciyo kanta amma ko saurarasa bata yiba. To yana cikin tafiyar ne sai yayi karo da wani abu. Anan ya fadi rikicaa. Ai kuwa yana tashi sai yaga ashe matar nan ce da yayiwa wanki ya tsere da kudinta. Ashe itace ta tsayu gabansa shi kuma bai sani ba yaci karo da ita.
    
                                                       PAGE 34

    Matar ta kasance katanya doguwa kakkarfa. Kai da gani kaga kato. Anan huzaifa ya mata kallon tsaf a tsorace. Matar bayarraba ce irin wadanda basajin hausa sosai. Anan ta fara yi masa magana da hausa. Amma dakaji hausar kasan ba bahaushiya bace. 
    " Amma kaji kunya shege kawai mai kamada rakumi. Na baka kudi shine ka tafi kaki dawomin da canji ko. To yau  ALLAH ya kamaka. Wawa kawai."
    " Ke nifa ba ruwana duk abinda zakice kice kudine kuma an cinye sai miye." 
    " Kai kada ka fadamin magana fa walayi zanshi uba naka." Inji bayarrabar.
    " Sai kiyi abunda zakiyi mana. To meye ruwana a ciki."
    Ai kuwa bayarrabar najin haka saita hasala. Anan ta debe hijabi tayar. Shi kuwa huzaifa na ganin haka saiya ja da baya saboda tsoro. Kirar jikinta ne ya gani kamar basamudiya. Ka tsawo ga kiba. Kirjin nan ya bulbulo sai kace yar dambe. Shi huzaifa da nufinsa shi arce a guje ai kuwa kafin ya tayar ne ta shako wuyan shege. Anan ta sashi cikin hammata sai dibarsa take. Ita kuwa yar karamar yarinya sai ta fara tsalle tana murna. " Mumy ci uba nashi. Mumy ci uba nashi."  Ita kuwa yasmin tsaye tayi tana kallon ikon ALLAH.
    " Zaka bani kudina ko saina kara shi ubanka."  
    " Wayyo hanjina zasu fito, kiwa ALLAH kiyi hakuri. Wallahi rabona da in rika naira biyar an fi wata uku." Cewar huzaifa yana ihu.  
    "  Wato bakada kudi amma shine kana cutar mutane ko. Bari zaka gani ai." Anan bayarrabar ta dagashi sama. Saida tayi koli koli dashi sannan ta makashi saman titi. Anan ya fara ihu yana mulmule mulmule. Har da bata hakuri yake amma ko saurararsa batayi. Wani tsalle tayi sannan ta fada saman cikinsa sai dukansa take ba kakkautawa. To da yasmin taga abun yayi yawa saita sheko ta rabasu. Dakyar ta samu ta banbare matar daga jikinsa. Daga nan sai yasmin ta bata hakuri. Anan matar ta dauki hijabinta taja diyarta suka wuce. To bayan sun wucene sai yasmin taxo gab dashi tana dubansa. 
     "Hahhhh. "Anan ta kyalkyace da dariya.
     " Wato dariya ma zakiyin bazaki ko tausaya min ba akan abunda yasameni."Inji huzaifa.
     " In tausayama saboda me? Ai kai ka jawa kanka. Ni iyaka nace ala gwai." Anan yasmin ta kara kyalkyacewa da dariya wadda tafi ta farko.

                                                     PAGE 35

    " Au haka ma zakice. To shi kenan nima zan rama." Anan ya mike tsaye da niyar tafiyarsa.
    " Ai ban kammala ba naga zaka tafi." Cewar yasmin.
    " Oh nifa kina damuna to wai meyene haka kina wani tsaida ni."  
    Bata bashi amsa ba sai da ta matso daf dashi. Daga nan sai ta fara zancenta." Wannan abu da nazo dashi mai muhimmnci ne kuma nasan idan ka bani hadin kai to zaka samu riba sosai yadda nima zan sama. " Anan huzaifa ya gyara tsayuwa yana saurarenta. Ita kuwa sai taci gaba da bayaninta. " Wato ka sani cewa idan barowa ya hada kai da dan uwansa barawo zakaga sana ar tasu ta sata sai habaka take saboda sun san abun dafawa. Saboda wannan dalili ne naga idan muka hadai kai ni da kai to xamu samu garabasa mai tarin yawa wadda bazamu iya kirgata ba domin ni da kai halinmu daya kuma kowa yasa halin kowa. " 
     " Yanzu ba wannan ba ki fadi abunda ke cikin ranki sai naji idan harka ce na tsaya in kuma akasin haka kin gane." Inji huzaifa.
      Anan yasmin tayi murmushi kafin ta cigaba da bayaninta. " Ai nasan dole ka tsaya idan kaji abunda nazoma dashi. Yanxu dai ga dubu hamsin nan ka fara tabawa kafin mu tsunduma ga fara aiki." Anan ta miko masa  bandur din kudi shi kuwa jiki na rawa ya karba cikin murna.
      "Kai, raboda da inga irin wadannan ai na manta. Tun wata karya dana shararawa wa wata diyar sanata cewa ni dan gwamna ne amma inason aron dubu hamsin kafin gobe. Tun daga ranar bata kara ganina ba har ila yau." Inji huzaifa. Anan yasmin ta bangale dariya har saida ta tashi fadawa kwata. 
      " To adaiji tsoron ALLAH. Almajiri sai shegiyar karya." Inji yasmin.
      " Nadai ji, aini ko cikin almajirai senior boy ne domin bana bara kuma banasa kaya masu datti. Ke in fada miki tun daga ranar da aka kawoni na tattara kayana na koma shagon da ake saida wee wee. Daga ranar malam bai kara sani a idonsa ba har yanxu. Kinga kuwa ni na daban ne domin almajirancin suna ne amma a zahiri ni ba almajiri bane." Anan yasmin ta kara barkewa da dariya. 
     " Lalle yaro ka zama dan iska. Wato kune bata gari masu saida wee wee, daga, cocaine, rochi kai harda ma giya ko. Ai bari asirinku na gab da tonuwa idan na zama gwamna." Inji yasmin.

                                                       PAGE 36

      "  Ke ubanwa zai zabeki gwamna dubarta tana fama da wata fuska sai kace kwado. Ai ko kwado inaga yafiki kyawo idan ana batun kyau ne." Inji huzaifa.
     " Au nice kwadon?" Yasmin ta fada cikin murmushi.
     " E mana to ke wacece in ba kwado ba, wadannan hakora naki dai abu kamar rakumi a cikin motar nan marsandi." Ya fada a cikin wasa. 
     " Hakama zakace ko? To yayi kyau zan rama." Inji yasmin. 
     " Wai ke in tambayeki. Yama akayi kikasan wadannan kayayyakin maye haka ko kema kina lasawa ne?" Huzaifa ya tambaya.
     " Kajimin mugun abu. To meye ruwanka a ciki idan ina lasawa kai kaban kudin siya ne?" 
     " Ai ko ban baki kudin siya ba nasan satosu kikayi ba naki bane." Inji huzaifa.
     " E na daiji. Aini satar da nakeyi dai dai ce domin bana cutar namiji  kome kudinsa sai idan mutumin banza ne mai son matan banza. Ko kuma mai shaye shaye da auri saki." Yasmin ta bashi amsa. 
     " Ab to ai nima haka nake. Bana cutar mace kome kudinta kuma ko diyar wacece in ba yar iska ba mai bin maza ko kuma yar shaye shaye. Idan na gano tana bin maza sai in lallaba in amshe kudin da take takama dasu." Cewar huzaifa.   
     Anan suka kyalkyace da dariyar keta tare da kallon juna domin sun gano halinsu daya. " Shegen yaro bani mu tabe bani mu tabe." Anan suka taba hannu suna dariya. " Ahayye rass." Yasmin ta danyi sowa.   
     "Yauwa to yanxu sai ki fada mana  wai menene kika hango mana?"  Huzaifa ya tambaya. 
     " Da farko dai kamar yadda na fadi inaso mu hada kai domin ganin mun samu abunda mukeso domin na gano cewa halinmu daya. Kai makaryaci ni nima makaryaciya ce. Kai mayaudari ne nima mayaudariya ce. Haka zalika kasan takun sharri iri iri kamar yadda na sani. Ka iya cuta nima na iya cuta. Wato reza kenan. Kai reza ne nima reza ce. Kaga kuwa idan muka hada kai to ba wanda ya isa ya tari gabanmu domin duk wanda ya tunkaremu iyaka muyi masa reza mu tafiyarmu." Inji yasmin.
      " Nifa bana gane wannan hausa taki wai reza. Shin kicemin cuta yadda zan gane. " Inji huzaifa.
     " Ya kana wannan abu sai kace ba bahaushe ba. Ai ma anar reza shine cuta, zalunci ko kuma keta.  Kaga ga kai azzalumi ne nima azzaluma ce saboda haka ni da kai mun zama reza. Inji yasmin tana murmushi. " Yanxu sai kaxo muje cikin mota in fada maka abunda zamuyi." Anan ya bita suka shiga motar suka wuce. 

                                                         PAGE 37

            Wani katon kamafani ne na motoci mutane suka taru kai da gani kasan akwai wani abu da sukeyi mai muhimmanci. Sunyi sahu jeri jeri a kusa ga wasu mutane dake zaune. Su kuma mutanen dake zaune saman kujeru sai latse latsen computer sukeyi suna kiran wadannan mutane daya bayan daya ana musu tambayoyi. A haka aka yita kira su daya bayan daya har saida kowa ya watse akabar mutum daya kadai. To bayan an kirasa sai ya zauna. Daga nan sai aka fara masa tambayoyi. 
    " Kai meye sunanka?" 
    " Sunana huzaifa!" 
    " To meye sunan mahaifinka?" 
    " Reza." 
    " Kai reza fa kace? Ka kosan ma anar reza? Reza fa na nufin zalunci!"
    " Ai nasan da hakan. Kasa huzaifa reza mana. Wannan shine sunana." 
    " To wane quaification gareka. Dagree ne, N C E, H N D ko kuma secondary?" 
     " Ni ko daya banada." Inji huzaifa.
     " Ko daya bakada kuma shine kazo bidar aiki a kamfanin motoci. To baza a baka ba sai kaje ka samo kwali." Inji mutumin.
      " To in banda wauta irin taku me ya hada kamfanin motoci da wani kwali" Inji huzaifa.
      " Kai malam tashi ka bani wuri ba za abaka ba." Inji mutumi. Anan suka fara sainsa idan wannan ya fadi wannan ya fadi. Can sai ga wata jeep ta xo dai dai wurin da su huzaifa ke wannan hayaniyar. Wani alhaji ne ya fito ciki daga nan sai ya zo wurin domin yaga meke faruwa.
       " Kai kai ku saurara shin wai meke faruwane?" Alhaji ya tambaya.
       " Yauwa alhaji ka ganshi nan wai bayada ko wane kwali amma kuma so yake a bashi aiki." Anan mutumin ya nuna huzaifa.
       Shi kuwa alhaji sai ya matso kusa ga huzaifa." To kai dan samari meye sunanka?" 
     " Sunana reza." Huzaifa ya bashi amsa.
     " Reza! Amma ban taba jin wannan suna ba. To meye sunanka na gaskiya?" Alhaji ya tambaya.
     Anan huzaifa ya washe baki kafin ya bashi amsa. " E to ana kirana da huzaifa reza. " 
    " To ba matsala za a baka aiki dama kaine na karshe a nan. Duk wadanda muka dauka masu degree da N C E zamu kaisu kamfanina na yoghurt suyi aiki a can domin mun fison yan boko. Ku kuma da bakuyi bokon ba zamu ajeku wurin motoci. Amma kai huzaifa aikinka daban ne. Domin da gani kai wayayye ne saboda haka zan daukeka a matsayin speaker na. A duk lokacin da mukaje meeting idan za ayi magana da hausa kai za a kira ka wayar da kan mutane."

                                                         PAGE 38

    " Saboda haka ka tafi daga yau an baka aiki kuma za a dinga biyanka duk wata." Inji alhaji. Anan huzaifa yayi godiya daga nan ya kama hanyar tafiya da zimmar gobe xai dawo ya fara aiki. To kaji jan magana kafin ya tafi sai da yayiwa wannan da sukayi fada dashi gwalo sannan ya wuce. Bayan sati daya da faruwar wannan abu. Wata rana.......
       Wasu motoci ne su uku jeep jeep haddadu sai wani walkiya sukeyi. Kai da gani kasan babban mutum ne a ciki domin yadda yan jarida ke gudu sun kafa kamerori suna jira ya fito su fara daukarsa hoto tare da yi masa tambayoyi. 
A kusa ga wani katon hall ne motocin suka tsaya daga nan sai bodyguards dinsa suka bude masa mota. Ai kuwa yana fitowa mutane sukayi caa akansa kowa na fadin albarkacin bakinsa. Yan jarida sai watsa masa tambayoyi suke amma ko kallansu bai yiba sai tafiya yake ana take masa baya har ya shiga cikin hall din. Ai kuwa yana shiga sai mutanen dake ciki suka tashi tsaye suna masa tabi saboda girmamawa. Shi kuma speaker sai ya fara magana kamar haka: 
       " Godiya ta tabbata ga ALLAH mai kowa mai kome wanda ya hadamu a wannan taro ba don komi ba sai domin mu taya alhaji sadi mai katifa murnar bude sabon kamfaninsa na motoci tare da shaida ma mutane cewa bako shakka ya dauki aniyar fitowa takarar gwamna a zabe mai zuwa."Mutane najin haka sai suka fara tabi da shewa su kuwa yan jarida sai recording sukeyi domin bayyanawa duniya abunda ke wakana. " A tare dani akwai mai girma gwamna wato alhaji harisu iyantama sai kuma mataimakinsu wato malam hamza fullatan. Dukkaninsu suna taya alhaji sadi mai katifa bude wannan sabon kamfani. Saboda haka yanxu zan kira Dr. Ahmad babangida wanda zai yi mana darasi akan motoci. A cikin wannan darasi zamu san mutum na farko daya fara kera mota da kuma abunda yasa ya kerata. To bismillah malan." Anan Dr. Ahmad yaxo ya fara darasinsa. Su kuma mutane sai saurare suke suna nishadi. Masu raba abinci da abun sha sai suka fara zagayawa suna rabawa.     
    To bayan Dr. Ahmad ya kammala bayaninsa ne sai speaker yazo domin ya kira dan wasa na gaba. Wannan speaker ba kowa neba in banda huzaifa wanda aka dauka aiki. Su kadai sukasan abunda suka shirya shida yasmin.
     " To yanxu zan kira shararriyar mawakiyar nan domin ta cashe ta nuna mata bajintar ta.  Saboda haka jama a sai muyi tabi ga yasmina reza." 

                                                         PAGE 39

       Anan mutane suka fara tabi suna ihu jin cewa za ayi wake. Shi kuwa huzaifa jayewa yayi domin yabasu wuri. Wasu makadan zamani ne suka fara wani kidan laushi mai jan hankali. Anan wurin yayi tsit kamar anyi mutuwa. Filin rawar zagaye yake da wani labule yadda baka ganin ganin wanda ke ciki. Wata fitila ce aka hasko daga sama saida ta zagaye filin rawar su kuma makadan sai kara kaimin kidin suke. A hankali aka fara jaye labulen har saida aka jayeshi gaba daya.  Daga nan sai akaga wasu yan mata sun fito daga ciki sai wani tafiya suke suna rangwada. Anan yan kallo suka fara ihu suna tabi na nuna jin dadinsu. Daganan sai suka fara wata rawa mai jan hankalin masu kallo. Yasmin ce a tsakiya kuma kayanta duk sunfi haskuwa bisa ga sauran. Rawar suke kidi mai dadi yana tashi wanda yayi dai dai da rawarsu. Anan yan kallo suka kara kidimewa sai ihu suke suna tabi. Su kuwa samarin wurin gigicewa sukayi da ganin siffar yasmin domin kayan da tasa duk sun matseta yadda ana ganin abubuwa.  
    Shi kuwa alhaji sadi tuni ya manta da abunda yake ciki wurin kallon yasmin. A wannan lokaci ya matsu a kammala taron domin ya kira huzaifa su tattauna game da wannan yarinya daya gani. Abunda bai sani ba shine: saura kadan ayi masa reza. Haka yasmin da abokanta wadanda ta dauko haya suka cigaba da rawa mai jan hankali kuma abun burgewa ga masu kallo. Sai da suka dau lokaci suna tallar jikinsu kafin su kammala. To bayan sun kammala ne sai speaker yayi maganar karshe wato sanar da mutane cewa biki ya kammala. Daga nan sai kowa ya tashi ya koma gidansa.  
    Akan hanyar huzaifa kafin ya kawo gidan alhaji sadi dama sunyi dashi ne ya shiga ciki ya jirashi. Kadan ya rage ya kawo sai yaga wasu mutane sun biyo wata mata mai aljannu suna kokarin kamata. Sai ihu suke. " Ku tare ku tare." Shi kuwa huzuifa yana ganin haka sai yaji duk mutanen sun bashi haushi. Irin yadda yaga matar yar karama batada wani kiba sosai, kuma ga katta sunfi goma amma ba wanda ke iya kamata. Anan yayi ta maza ya tare hanyar da zata bi wai shi a tunaninsa zai iya tareta. Ita kuwa tana ganin haka saita yi wani tsalle ta katso reshen bishiya dake kusa da ita. Huzaifa bai tsorataba da ganin ta katso bishiyar domin a tunaninsa tunda batada kiba ai ba wani karfine da ita ba. Saboda haka zai iya yi mata kamun kaji ya bada ita.
     Anan matar ta saita mummuken shege sannan ta aza masa icce ji kake timmmm. A haka ta wuce tabar huzaifa cikin kwata yana nishi dakyar. Su kuwa wadanda suka biyota ko kallonsa basu yiba. Wucewa sukayi suka kyalesa.


                                                         PAGE 40

   Haka ya dade cikin kwatar sai da kyar wasu masu wheel barrow suka taimaka suka azoshi ciki sannan suka kawoshi gidan alhaji sadi suka ajiye. Suma sunyi hakane saboda sun sanshi. Ba a fi minti uku da ajiyesa ba saiya farka.Anan ya tashi ya shiga cikin gidan yana nishi. Bayan ya wanke kwatar ne saiya shiga falon yana jiran dawowar alhaji.  Ai kuwa yana cikin hutawar ne sai yaji an banko kofa da karfi. Anan ya tashi a guje ya shiga wani daki, a karkashi gado ya boye saboda tsoro domin shi a tunaninsa mai aljannun ce ta dawo wurinsa.  
   "  Kai fito. Ya kana gudun oganka." Huzaifa naji wannan muryar sai ya gano cewa alhaji ne. To anan ya fito yana tafiya dakyar. " Kai ya naga ka canza hala dawa kayi fada." Anan huzaifa ya kalli alhaji ba wando iyaka wata yar karamar riga ce ya sanya kamar mahaukaci. Anan ya kece dariya harda faduwa. " Kai, uban meye kakema dariya?" Alhaji ya tambaya. 
    " Alhaji naga bankin ne a bude!" Inji huzaifa. Ai kuwa alhaji na dubawa sai ya ganshi ba wando wato shi bai ma sani ba. " To alhajin wurin kaka hakan ta faru?" Huzaifa ya tambaya.
     " A wurin wannan bikin ne naga wata yarinya. Inaga saboda kallonta ne wandon ya fadi." Alhaji ya bashi amsa.
     " To amma dai ina fatan cikin mota ka dawo ko?" Huzaifa ya tambaya.
     " Inafa mota. Kasa na tako tun daga can har gida." Inji alhaji. 
     " To dada alhaji ka tona mana assiri. To sufa motocin ya akayi dasu?" Huzaifa ya kara tambaya. 
     " Duk sunyi datti dole nace aje a wankesu." Inji alhaji. Can sai alhaji ya kece dariya shima yana kallon huzaifa. 
     " Alhaji ya hakan kana dariya kai kadai kamar mahaukaci?" Huzaifa ya tambaya. 
     " Ashe bani kadai bane na tafka barna ba. Ai kaima naka bankin a bude yake." Inji alhaji. 
     Ai kuwa huxaifa na dubawa sai yaga ashe shima bashida wando. Wato a lokacin da masu baro suka tallabosa sun debe masa wando cikin rashin sani. " To aini nawa mai saukine tunda ba wanda ya ganni." Inji huzaifa.
     " To yanzu dai ba wannan ba. Nifa wannan yarinyar mawakiyar ta kwanta min fa. Yanzu sai kayi yadda zakayi ka kawomin ita a nan." Inji alhaji.
     " Gaskiya alhaji bazai yiwuba." Inji huzaifa.
     " To me yasa?"Alhaji ya tambaya. 

                                                        PAGE 41

    " Haba alhaji kaima fa kasan cewa yarinyar tauraruwa ce kuma iri irensu taurari suna wuyar gani fa. Ni kaina kafin wannan biki nasha mutukar wahala kafin na sameta." Inji huzaifa. 
    " Ka. To ai wannan ba komi bane indai kudine bakada matsalarsu domin zan baka ko nawane.  Ni abunda nakeso kawai shine ka kawomin ita." Inji alhaji. 
     " To alhaji ba matsala zan duba. Amma fa kasan tauraruwa ce kafin ka samu abunda kakeso dole sai ka bita sau da kafa. Duk abunda tace kayi sai kayi." Inji huzaifa.
    " Ai wannan ba matsala bane. Kadai ka kawota ka gani. Anan alhaji ya wani gyara tsayi wai shi saurayi. " Ya kaga wannan tsayin. Nayi kuwa?" 
    " Haba alhaji ai ka hadu. Ko baturiya ta ganka ai dole ta yarda balle bahuasa." Inji huzaifa. A cikin xuciyarsa kuwa in banda shammatar alhaji ba abunda yake:
    ( Kaine dadi mata ko? Zakaci ubanka nan bada jimawa ba. Ka aza wani katon ciki sai kace kwarya)  haka huzaifa yake fadi cikin zuciyarsa amma a xahiri ba abunda yakeyi in banda yi masa kirari. 
    " Wato alhaji zamuyi sabuwar bakuwa a gidan nan kenan!" Inji huzaifa.
    " E mana bani mu tabe." Cewar alhaji. Anan suka taba hannu suna wata rawa mai ban dariya. Daga nan kuma sai alhaji ya jashi wani daki inda ya bashi kudi masu yawa. 
     Bayan kwana biyu da faruwar wannan abu. Sai huzaifa yayi niyar kaiwa abokiyarsa xiyara wato yasmin domin su sun tayi. A cikin darene ya shigo wani restaurant sai dube dube yake. Ai kuwa bai wani bata lokaci ba ya hango wadda yake nema zaune tana jiransa. Cikin fara a ya nufi wurinta. Anan ta tarbe shi cikin murmushi da karamci. Tun kafin ya xauna ne ya fara mata kirari:
     " Reza muguwar uwa, ke ka haihuwar diya ki kashe abarki. Reza muguwar uwa, ko uwarki baki ragama ba balle uwar wasu. Reza muguwar uwa, idan ba a soki don ALLAH ba sai an sonki don kaifinki. Reza muguwar uwa, ba dai mutum ba ko aljan yana shakkunki. Reza muguwar uwa, nan gani na bari yayan magori.Reza muguwar uwa, ke kadai ka gashi ki soye ki dafe kuma ki zauna lafiya. Reza muguwar uwa, ta kano tumbin giwa kodame kazo an fika " 
     Anan yasmin ta kyalkyace da dariyar farin ciki." To yanzu meye labarin?" Ta tambaya.
    " Ai mun gama da alhaji sadi. Inaga sai dai wani ba shiba." Cewar huzaifa.
    "  Da kyau. Dama abunda nakeso naji. Yanxu taso muje kaga abunda na tsara." Anan ta jawo hannunsa har suka fito daga cikin restaurant din.

                Me zai faru?

                        Zamu cigaba.........

                                                           PAGE 42

      " Yasmina reza, yasmeeeeena. Yasmeeena rezaaaaa." Haka alhaji ke tafiya yana wakarsa cikin jin dadi  har ya shigo wani daki inda ya iske yasmin zaune tana jiransa. " Tab, ALLAHU AKBAR. Lalle huzaifa yayi aiki mai kyau ai yanxu ya fadamin cewa wai kina jirana. To lale marhaba ya sahibata." Anan alhaji ya zauna kusa da ita sai faman kallonta yake. " Amma fa naji mutukar dadi bisa ga wannan ziyara da kika kawomin. Kuma ina fatan ya bayyana miki komai." 
    "  E mana ya fadamin. Amma kuma kaima ina fatan ya fadama game dani domin inada tsada sosai idan zaka iya siya to." Inji yasmin. 
     Anan alhaji ya kyalkyace da dariya. " Haba yan mata ai ni ko nawane zan biya indai kudine to bamatsalarki bane. Yanzu sai ki fadamin miliyan nawa zan bayar?" 
     " Alhaji miliyan fa kace?" Yasmina ta tambaya cikin mamaki.
    " E mana ko sunyi kadan ne?" Inji alhaji.
    " A a basu yiba. Ai ni alhaji wannan gida naka ya burgeni. Ace ma nice dashi dana huta." Inji yasmin.
    Anan alhaji ya kyalkyace da dariya. " Ai kada ki damu yan mata indai gidane zan iya gina miki irin wanda kikeso. "
   "Laaaa alhaji da gaske? "
   " E mana ai gida ba kome bane. Ke har kamfani idan kinaso kin san fa inada kamfanona da yawa. Zan iya baki duk wanda kikeso." Inji alhaji.
   " Alhaji kai babban mutum ne kace kanada dukiya sosai." 
   " Ke, ai ina fada miki bazan iya kirga dukiyata ba ni kaina." Alhaji ya bata amsa. Daga nan sai yasmin ta matse shi domin ta jawo hankalinsa. 
    " Shi yasa nake sonka alhaji." 
    A haka yasmin ta yita bugun cikin alhaji don taji tarin dukiyarsa shi kuwa yayita fada mata. Sai da ta tabbatar tasan dukkan dukiyarsa tare da inda yake ajiye takaddun mallakar kamfanoninsa da gidajensa. Haka tayi kokari wurin matsarsa da dadadan kalamai har saida ya fada mata inda yake ajiye kudinsa a cikin gidansa. Kai harda pin dinsa na ATM sai da ta sani da kuma inda yake ajiyesa. Daga nan sai tayi kara jawo hankalinsa wurin nuna masa jikinta domin ya rude. Sai da ta bari ya kosa dasu fara harka sai taki bashi. Takaddun gidajensa dana kamfanonansa ta dauko. Daga nan sai tayi rubutu kamar haka:
   " Ni alhaji sadi mai katifa na sadaukar da kamfanona da gidajena da kuma waa harin dukiyata ga yasmin akan tiriliyan arba in. Kuma ta bayar da kudin har na karba." Anan ta mika masa tace idan yayi signing zata bashi abunda yakeso. Shi kuma cikin gaggawa yayi signing ya mika mata ba tare da sanin abunda ta rubuta ba saboda rudewar da yayi wurin kallon jikinta.


                                                    PAGE 43

    Anan yasmin ta jawoshi jikinta kamar da gaske shi kuwa sai dada kankaneta dama abunda yakeso kenan. Gashin kanta kawai ya sunsuna sai ya fadi ba tare dayasan inda yakeba. Anan yasmin ta kira huzaifa. Duk wani kudi dake cikin gidan sai da suka sace shi. Sannan suka dauke masa ATM da takaddun kamfanonansa da gidajensa kafin su fita su bar gidan. Wannan abu ya faru da misalin karfe goma na safiya ranar talata. Amma alhaji daya fara bacci shine bai farka ba sai ran larba da misalin karfe biyu na rana. Koda ya farka sai hankalinsa ya tashi ganin halin da yake ciki. Dakyar ya samu yayi wanka yana tunanin inda yasmin ta shiga domin shi a ganinsa har yanzu talata ce. Wayarsa ce ya dauko domin ya kira huzaifa. Ai kuwa yana buda wayar sai yaga alert cewa duk kudin dake cikin account dinsa an ciresu. Anan alhaji ya rude. A guje ya nufi inda yake ajiye ATM card dinsa amma a mamakinsa bai ganshi ba. Anan ya shiga motarsa ya nufi kamfaninsa na motoci da nufin yagani ku huzaifa yazo. Ai kuwa yana shiga ya tarar da yan sanda. Anan suka kawo masa wata takadda tare da yi masa izni yayi signing. 
   " Alhaji munaso kayi signing a wannan takardar domin mu tabbatar da signing dinka na gaskiya saboda wani abune ya faru mai rikitarwa." 
    " Wannan wane abune a fadamin naji." Alhaji ya tambaya. 
    "  A a bazamu fadama ba sai ka fara yin signing din." Inji yan sandan.
    Ai kuwa yanayin signinig din sai suka dauko takardar da yasmin tayi rubutu kamar haka:
    Ni alhaji sadi mai katifa na sadaukar da kamfanona da gidajena da kuma waa harin dukiyata ga yasmin akan tiriliyan arba in. Kuma ta bayar da kudin har na karba. Anan suka duba sai sukaga signing din da yayi a yanzu yayi dai dai dana cikin wannan takardar da yasmin ta kawo musu. Ma ana kenan maganar dake cikin takardar gaskiya ce kuma shi ya fadeta tunda signing iri guda ne a ciki duka takaddun. 
    " To alhaji daga yanzu wannan kamfani ba zamanka yake ba saboda mun gano cewa ka sayar dashi ga wannan yarinyar wato yasmin. Wannan dalili shine yasa mukace kayi signing domin mu tabbatar da cewa idan kaine kuma sai gashi kai din daine. " Inji shugaban yan sandan.
    Anan alhaji sadi ya dafe kai yana sallallami. " Ranka shi dade amin afuwa amma wallahi bani bane nayi wannan rubutu ba. Cuta ta akayi dole akasa nayi signing ba tare dana sani ba."
  
                                                         PAGE 44  

       "  To mudai ba ruwanmu wannan matsalarka ce. Tunda ka amsa cewa sign dinka ne komi yayi. Saboda haka yanxu duk ribar da za a samu a wannan kamfani bazai shiga account dinka ba. Sai dai ya shiga account din wadda ka sayarma wato yasmin." Anan yan sandan suka tafiyarsu. Shi kuwa alhaji sadi binsu yayi domin ya tabbatar musu da cewa reza akayi masa amma ina ko saurarensa basayi. Saboda haka ya kyalesu ya nufi sauran kamfanonansa. To duk inda yaje irin wannan maganar ake fada masa cewa kamafani ya fita hannunsa. Haka suma gidajensa duk inda yaje sai yaji ance sun fita hannunsa. Kai saida takai alhaji sadi yakai bayada gida nasa nakansa. Duk motocinsa kuma saida takai sun zama duk banasa ba. A haka alhaji sadi ya koma abun tausai domin ko abinci sai yayi bara a basa. Su kuma matan dayake aura yana saki duk wadda taji labari iyaka tace ala gwai.
    To anan ne yasmin ta tsaya ga wannan labari da takeba maryam. " Amma fa kawata kin yi kokari sosai yadda kika samu nasarar yi masa haka." Inji maryam." To amma sauran dukiyarsa me zakiyi dashi naga kamar ya miki yawa."
   Anan yasmin tayi dariya. " Ai har na tsara abunda zanyi da dukiyar tasa. Da farko dai ki sani nayi hakane domin nasa masa nadama akan abunda yayi na banzatar da dukiya wurin aure saki da kuma neman matan banxa wanda akan hakane ya rasa dukiyarsa. Nasan yanzu duk inda yake yayi nadama akan hakan kuma daga yanxu bazai kara yarda da kowace mace ba domin zaiga kamar kowace zata iya cutarsa kamar yadda nayi. Kinga kenan dole yabar bin matan banxa kuma ya daina auri saki don kada ya kara haduwa da irin wannan matsalar."
   " Wayyo, har ya bani tausai. Amma kuma abunda kikayi shine dai dai domin idan ba haka akayi masaba to bazaina halinsa ba." Inji maryam.
   " Yauwa ashe kin gane kenan. Ai sabida hakane na yanke shawarar cewa zan mayar masa da dukiyarsa kamar gidajensa, kamfanoninsa da motocinsa. Amma kudinsa bazan mayar ba domin ina so ya koyi darasi akan hakan. Su kudin nasa zan rabasu kashi uku. Kashi daya zan kai gidan marayu. Kashi biyu zan samo duk matan daya aura yana saki in raba musu. kashi na uku kuma namune nida ke sai mu raba." Anan yasmin ta miko mata wata yar jaka." Duk wadannan abubuwa dana fadi na riga na yisu abunda ban yiba shine mayar masa da sauran dukiyarsa na daga dangin kamfanoni da gidaje.

                                                      PAGE 45

   " Na riga nakai kashin farko a gidan marayu. Shi kuma kashi na biyu na bayar dashi ga matan da yake aura yana saki. Shi kuma kashi na uku har na raba shi kashi biyu. Kuma rabin ne na baki a cikin jaka. Sai dai kamfanonansa da gidajensa bazan bashi suba sai nan da sati daya domin inaso ya kara fahimtar rashi da kunci na rayuwa." Inji yasmin. 
   " Ai kuwa kinyi dai dai domin yanxu ji nake na debe haushinsa." Inji maryam.
   " Yauwa to bari na tashi na wuce."  Anan yasmin ta mike tsaye.
   " Au kawata tun yanzu zaki wuce?" Maryam tambaya. " To sai yaushe kenan?" 
   " Hmm. Maryam kenan. Ai daga yau bazaki kara ganina ba." Inji yasmin.
    " Wannan magana fa taki marar dadi. Amma dai wasa kike ko. " Inji maryan.
    " Ba maganar wasa a cikin wannan magana." Inji yasmin.
    " To amma ina ne zaki da baxan kara ganinki ba?" Maryam ta tambaya. 
    " Wurine mai nisa kuma idan na tafi bazan kara dawowa a cikin wannan gari ba." 
    " To amma meye makasudin wannan tafiya?" Maryam ta tambaya. 
    " Saboda inaso in bar halina na reza. Yanzu lokaci yayi daya kamata in yi rayuwa kamar kowace mace."  Yasmin ta bata amsa. 
    " To dake dawa zaki rayuwar. Kinada sauryine?" Maryam ta tambaya. 
    " Kwarai kuwa ni keda saurayi."
    " To meye sunanshi?" 
    Anan yasmin ta danyi murmushi har saida hakoranta suka fito. " Gaskiya baxan fada miki ba!" 
    " To! Wato abun ya zama na boye boye ko." Maryam ta fada.
    "  A a ba haka bane. Wato target   daya ne ya ragemin a cikin wannan gari. Kuma dana samu damar yiwa wannna target nawa reza to xan bar garin in koma can wata duniya daban yadda zan ci gaba da gudanar da ayukana a saukake." Inji yasmin.
     " To ya maganar reza din? Kenan bazaki bari ba ko?" Maryam ta tambaya. 
     " Au wai ke a tsammaninki na daina kenan? Ai ina nufin zan tafi hutu ne temporary amma ina shiga sabon birni ai iyaka na daura daga inda na tsaya." Inji yasmin.
     " Ahayye, rassss." Anan suka taba hannu suna dariya. Daganan sai sukayi sallama yasmin ta kama hanyar gida.

                                                       PAGE 46

           Yasmin ce da huzaifa a cikin daki sai murna suke suna rawa saboda samun nasarar yiwa alhaji sadi reza. " Ayyihuhu. Kudi kudi kudi. Kudi abokan tafiya. Idan baku ba zaman lafiya." Haka huzaifa ya fada bayan ya dauko wani bandur na kudi yana kallo. Ita kuwa yasmin zaunawa tayi domin ta dan huta." Wai in tambayeki. Hala ina sauran mutanen gida naga kamar ke kadaice?" 
        " Su umma ne kuma sun fita yau ni kadaice a ciki." Inji yasmin.
        " Iyeee, kice yau akwai alagwagwajiya." Huzaifa ya fadi yana dariya.
       Ita kuwa yasmin bata amsa ba kallonsa tayi tana murmushi."Ina fatan dai ka kammala aikin dana saka?" 
      " Kwarai kuwa tun yaushe na kammala. Yanzu jira kawai nake ki bada umarni mu fara aiki. Kuma kin san wani abu. Inaga zamuyi samu sosai fiye dana alhaji sadi domin.... Kai kada in baki labari ki rude bari sai mun zauna. To shi alhajin yawai kin mayar masa da dukiyarsa kuwa?" 
      " Tshohuwar magana tun yaushe!" Inji yasmin. 
      "To yanzu yaushe zamu fara aikin kenan?" Huzaifa ya tambaya.
      " Yau." Inji yasmin.
      " Yaufa kikace?" Huzaifa ya tambaya.
      " E mana ai dole mu fara da wuri kada ka manta wannan shine last target dinmu kuma da mun kammala shikenan sai wani jikon in ALLAH ya kaimu. Yanxu ka tafi gida ka adana ajiyarka sai gobe mu hadu da misalin karfe goma na safe." 
      " Ba cewa kikayi yau zamu fara ba?"  Huzaifa ya tambaya.
      " A a ina wasa ne sai gobe kome zai dai daita." Anan sukayi sallama huzaifa ya kama hanyarsa. Ai kuwa bai dade da fita ba saiga umma ta dawo tare da abba. A guje abba ya shigo dakin ya tarar da yasmin tana kirgar kudi. Anan ya bude baki yana kallon kudin harda wani hadiyar yawu kamar wanda yaga nama.
       " Wato ke don bakida kilki shine jakiba wani kato kuti mashu yawa amma ni a mashayin yayanki kin kyaleni ko. To shai an yabasu taye dani!" Haka abba ya fada cikin yamin baki sanidiyar maganarsa bata fitowa dai dai. Anan ya jawo jakar kudin. Ita kuwa yasmin bata yarda ba domin rikesu tayi gam yaja taja.
       " Ka sakar min jaka."
       " Ba ja a shaki ba." Inji abba.
      Can sai ga umma ta sheko a guje. " Wai me yake faruwa ne daga dawowarmu?" 
     " Wai umma wannan yayinyal ce mayal ladabi. Yanju fa taba wani kato kuti amma ni ta kyaleni." Inji abba.
     " To kai ya akayi kasan haka kuma ina kaga shi wanda taba kudin?" Umma ta tambaya.

                                                      PAGE 47

      " Haba ya kina fadal haka ai kina kallo mukaga wani ya fito da jaka yana kilgal kudi." Inji abba.
     " To da kake wannan magana ai bance ban baka ba balantana ka wani sani a gaba kana tada jijiyoyin wuya." Inji yasmin. 
    " To yanxu kai abba ka bari ta kirga sai ta baka naka." Inji umma.
     Ita kuwa yasmin najin haka sai ta dauko bandur uku a cikin jakar ta mika masa." Yanxu dai ga wannan kayi maneji." Anan ya karba yana murna.
    " inhin. Ko kefa yal kanwata. Yanju naji magana. To bani mu tafe." Anan suka taba hannu suna dariya. Daga nan suka lakama juna suna murna tare da rawar farin ciki. Ita kuwa umma kura musu ido tayi tana mamaki. Abun ya kasance gwanin ban sha awa kuma abun ban dariya yadda suke rawar suna wani girgije girgijen duwayya. 
     Washe gari da misalin karfe goma na safiya yasmin ta hadu da huzaifa a wani wuri kebantacce. Saida suka dau lokaci suna magana kafin su tari a dai daita sahu. Ko ina zasu dai oho!"
    Wani makeken gida ne kai da gani kasan naira ta zauna a ciki. Oda akayi daga waje saiga mai gadi ya fito a guje ya bude gate din. Wata motace hadadda ta shigo daga ciki. Daganan saiga wani mutum ya fito daga ciki kai da gani kasan shine mai gidan. " Alhaji sannu da zuwa!" 
    " Yauwa tanko ya aiki."
    " Alhamdulillahi alhaji." 
    Anan alhajin ya shiga gidan. Ai kuwa daga shigarsa uwargida ta tarbeshi cikin fara a. To bayan sun zauna ne sai ya fara magana kamar haka: 
    " Wato ki sani zainaba gobe warhaka zan wuce england kuma inaga zan dau lokaci kafin na dawo amma idan zan dawo zan bugo miki." 
    " Haba alhaji gaskiya nifa na fara gajiya da wannan tafiye tafiye naka kullum bakanan baka can." Haka ta fada domin alhaji yaji kamar ta kula dashine amma 
zahiri ba haka ba. A cikin zuciyarta sai murna take tana cewa: ( Yauwa, ai dama abunda nakeso kenan ka tafi ka bani wuri na sakata na wala na bararrake yadda nakeso da yan samarina.) 
     " Ke ko zainabata ai wannan tafiya ba kome bace tunda abunda mukaci ne zan tafi nema saboda haka kada ki samu damuwa zan dawo insha ALLAH." Anan ya danyi tari sannan ya kurba juice dake cikin wani kofi kafin yaci gaba da magana. 

                                                             PAGE 48

   " Naji korafinki na cewa kinaso a canza  yar aiki to amma hala wani abune takeyi?" Alhaji ya tambaya.
   Anan zainab tayi shiru domin tasan ba wani laifi da zata iya fadi mai aiki tayi mata. Dama abunda yasa takeso a canzata shine mai aikin bata biya mata bukatunta yadda takeso domin ita zainab tafison wadda zata dinga nemo mata samari idan alhaji yayi tafiya ita kuwa waccan tsohuwar mai aikin bata iyawa saboda ustazanci. Wannan shine dalilin da yasa zainba takeso a canxata.
    " E to alhaji gaskiya nidai ta isheni domin kazamace kuma bata iya abinci ba da kuma....." Haka zainab ta yita kushe yar aikin har saida alhaji ya gamsu. 
    " To yayi ba matsala dama ai dazune dazan fita ne gamu da wata yarinya a kofar gida tacemin tanason yin aiki. Yanzu haka tana cikin motata idan kin yarda sai in kirata domin ku shirya." Inji alhaji.
    " Yauwa ko kaifa. Kirata mana da sauri." Haka zainab tace cikin jin dadi tunda ta samu abunda takeso. Ai kuwa ba a wani daukar lokaci ba saiga alhaji ya shigo da wata yarinya. 
    " To ya kikaga wannan?" Alhaji ya tambaya. 
    " E kamar zatayi amma fa da gani kazama ce irin wannan shigar datayi." Haka zainab ta fada bayan ta kura mata ido.
    " Amma yan mata kina wanka kuwa?"  Zainab ta tambaya.
    " Ina wanka? Kambu. Ni nan da kika gani nama fiki wanka." Haka yarinyar ta fada.
    " To." Inji zainab bayan sun hada ido da alhaji. " To sau nawa kike wanka a kullum?" 
    " A kullum fa kikace. Haba sai kace wani kifi! Daga jumu a sai jumu a nake wanka!" Inji yarinyar. 
     Anan alhaji da zainab suka kalli juna suna mamakin wannan yarinyar. (  Kai amma fa da gani wannan sakarya ce zata iya yin abunda nakeso kuwa?) Haka zainab ta fada cikin zuciyarta. " To naji amma nifa banason wannan kazanta naki domin yayi yawa saboda haka zan kaiki kiyi wanka kuma ki canza wadannan kaya dake jikinki kisa sabbi. Daga yanxu kin zama yar aiki a gidan nan kinji ko. To yanxu fadamin meye sunanki?" 
    " Sunana? Sunana fa kikace? To sunana kande mai albasa." Haka yarinyar ta fada amma a zahiri ba haka ba: yasmina reza ce ke shirin yi musu reza. 

                                                      PAGE 49

    Anan zainab ta jata suka shiga toilet. Saida ta gyarata tsaf sannan ta fito da ita. Jiki sai wani kyalli yake. A nan ta dauko kaya masu kyau  ta bata tare da fesheta da turare, daga nan sai suka dawo falo inda alhaji yake. 
   "  Kande mai albasa dan tashi bamu wuri zamuyi wata magana." Inji alhaji. 
   " Har sai ta tashi. Wannan sakaryar da kome bata iya ba yanzu fa nice na mata wanka. Kai da fadi abunda zaka fadi ai wannan komi bata sani ba." Inji zainab.
    " Da gaske? To ba matsala." Anan alhaji ya fara maganarsa a ganinsa abunda matarsa zainab ta fada gaskiyane na cewa yasmin batasan kome ba bai san kuwa kar take kallonsu ba. " Wato dama wasu kudine na ma aikata aka bani ajiya to so nake na ajiyesu a wurinki har saina dawo. Amma fa ki sani kada ki yarda wani abu ya tabasu domin ba nawa bane. Kuma aikina kan iya samun matsala akansu. Kin gansu nan biliyan talatin ne." Anan ya bata wata babbar jaka. 
    " Ai kada ka damu alhaji, inaga har ka dawo to ba abunda zai tabasu domin a cikin dakina zan ajiyesu inda ba mai gani." Cewar zainab. 
     "  Yauwa zainab. To yanzu bari na tashi na fita." Anan alhaji ya fita ita kuwa zainab sai takai kudin a dakinta ta ajiye. Daganan sai ta dawo wurin yasmin wadda take gani a matsayin kande. Hira suka farayi cikin annashuwa ita kuwa yasmin sai ta nuna mata kamar batasan kome ba. 
      " Yauwa dama abunda nakeso ki sani shine inhar zakiban hadin kai kiyi duk abunda na umarceki to shi kenan zamu zauna lafiya dama abunda ya kori waccan tsohuwar mai aikin kenan kin bin umarnina." Inji zainab.
       " Ai hajiya ki kwantar da hankalinki kome kikeso to ki dauka kamar an gama." Inj yasmin. 
       " Yauwa ashe kin gane. Dama ban damu da kin iya dafa abinci ko baki iyaba domin ba shine matsalata ba koni zan iya dafawa kaina. Abunda nakeso dake shine kiyi kokari ki samo min saurayi santalele kyakkyawa hadadde kuma dan bariki wanda zai maye gurbin alhaji idan bayanan. Kin san fa auran wadannan masu kudin matsala ne domin ba wani kyau ne dasu balantana shi yayi min tsufa in ma banda kudinsa me zanyi dashi." Inji zainab.
       " Indai wannan ne ai ba matsala ke hajiya. Ai samun saurayi yafi kome sauki gasunan zube har sai nayi yanga wurin zaba miki." Inji zainab.
       " ALLAH ko kawata?" zainab ta tambaya.
       " E mana ai kisha kuriminki indai saurayi ne kamar an samo. Ai ni inama ganin kokarinki hajiya. Gaki kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa amma ki auri wannan abu. Haba me zakiyi dashi." Inji yasmin.

                                                           PAGE 50

    " Ai kedai bari kande. Ai ni naji dadin wannan haduwa dake domin zamuci duniyarmu a saukake." Inji zainab. 
    " Hajiya da gaske?" Yasmin ta tambaya.
    " Au kin aza ina wasane?" Inji zainab. Anan suka taba hannu suna kyalkyatar dariya. 
      Washe gari bayan alhaji ya tafi saiga yasmin ta shigo da wani saurayi a cikin gidan. Hajiya zainab na cikin falo sai taji shigowarsu. Ai kuwa tana ganinsu ta mike tsage. Kura masa ido tayi ko kyaftawa batayi. Yaron ya kasance dogo fari kyakkyawa dan shala irin wanda takeso. Wata bakar suit ce yasa ta masa kyau sosai. Anan zainab ta sheko a guje ta rungume yasmin cikin murna. " Ba sai an fada ba nasan yayi." Haka zainab ta fada bayan ta matso kusa dashi. " Dan saurayi cire glass din na gani." Injita.
     Anan ya cire glass din a hankali cikin murmushi. Ai kuwa tana ganin irin kyawonsa sai ta rude. Fadawa jikinsa tayi ta wani kankaneshi sai fara a take. Anan yasmin ta tsayu tana kallonsu duk da taji kishi sosai domin itama fa..... Amma haka ta daure domin tasan zasuyi samu. Zainab din ta kasance katanya mai kiba amma ba sosai ba. Anan ta jashi daki a guje suna shiga tasa sakata kome zasuyi dai oho. To bayan shigarsu dakin kafin a fara abun sai yar hira ta barke tsakaninsu. " Dan saurayina...umyun." Haka ta fada cikin shagwaba tana karkada idanu wai ita kyakkyawa. " Au bazaka matso kusa dani ba? To bari nazo." Anan ta xauna kusa dashi ta wani jawoshi a jikinta. " To fadamin meye sunan?" 
    " Zaki iya kirana da audu." Haka ya fada mata amma a zahiri ba haka bane: huzaifa ne abokin yasmin reza. 
     " Amma fa ka hadu." Anan ta fara taba fuskarsa. Shi kuwa sai ya fara jayewa.
    " Haba ya kana kaucewa kaxo mu fara mana" Inji zainab. 
    " Nifa kin san bana aiki kyauta. Yanxu sai ki fadamin ina kika ajiye kudin?" Inji huzaifa.
    Anan zainab tayi shiru domin batasan kudin da zata nuna masa ba. Can saita tuno da wadanda alhaji ya bata. Kawai sai ta jawosu ta nuna masa." Ga wadannan muna gamawa shi kenan sai ka dauka." Ai kuwa huzaifa najin haka sai ya rungumeta kamar da gaske. Ita kuwa kyalkyatar dariya ta farayi dama abunda takeso kenan. Haka huzaifa yayita nunnugarta sai da ya bari ta kamu sannan ya saketa ya mike tsaye.

                                                       PAGE 51
    
  " Ya naga ka tashi. Zo mana dan saurayina." Inji zainab.
   " Hajiya kiyi hakuri wani abune na tuno dashi,, yanxu haka jirane ake nakai wani sako amma na manta nazo nan. Ki bari kawai gobe xan zo nan sai mu cigaba. 
    " Haba kai kuwa ya zaka yimin haka. Sai da ka bari na farajin dadi sannan zaka tashi.' Inji zainab. 
    " Hajiya kada ki samu damuwa gobe warahaka zan dawo." Anan ya juya da nufin fita ita kuwa sai ta fara gyra kayanta.
    " Bazaka tsaya na raka kaba." 
     To bayan ya fita ne sai ya tarar da yasmin tana jiran fitowarsa." Ina fatan dai ka gano inda kudin suke?" Haka ta fada cikin karamar murya don kada hajiyar taji.
    " E mana tun yaushe." Ya bata amsa.
    "  To yanxu ya kenan?" Ta tambaya.
    " Kada ki damu sai gobe zamu kammala." 
    Suna cikin maganar saiga hajiya zainab din ta fito. " Muje na takama kofar gida." Injita. Har sun fara tafiya sai ya tuno akwai maganar da yakeso ya fadawa 
yasmin. Anan ya juyo gunta.
     " Yasmin ji mana!" Injishi. Ita kuwa yasmin saita juyo tana saurarensa. Ita kuwa zainab sai tayi mamaki domin tasan cewa sunanta kande amma gashi yana cewa yasmin kuma sai gashi ta juyo. 
      " Au dama sunanki yasmin?" Zainab ta tambaya.
     " A a ba haka bane sunanta, nine nayi subutar baki." Inji huzaifa don kada ta gane.
      " Kai audu nifa a ganina kamar baka santa ba." Inji zainab.
      " Injiwa ya fada miki? Ni ko na santa sosai " 
      " To idan ka santa meye sunanta wanda muke kiranta dashi a wannan gida?" Anan huzaifa yayi shiru domin bai san irin amsar da zai bata ba. Can sai dabara ta fado masa. Anan ya dauki wayarsa yayi kamar an bugo masa.
      " Hello. Reza ya kike ya makarantar. Ina fatan dai kin shiga sabon gidan tare dani. Domin yanzu haka ina tare dake da hajiya kuma tana bukatar sanin password dinki. Saboda haka sai ki gaggauta fadamin da sauri." Yana fadar haka sai ya juya ya kalli yasmin, ita kuwa tana ganin haka saita gano cewa da ita yake. Daganan itama saita daga waya tayi kamar an kirata. 
       
                                                   PAGE 52

    " Hello, e ai komi lafiya lau domin har na samu aikin a gidan. E kwarai kuwa ai yanxu ina tare dakai ko? To ka saurara kaji domin sako zan fadama. Idan ka shiga gidan sai ka fadaawa hajiya cewa kande mai albasa ce ai shine password din. Ok to sai an jima ka gaida hajiya." Anan ta kashe wayar.
     Ita kuwa hajiya zainab kallonsu take ba tare da tasan abunda sukeyi ba domin ita a tsammaninta da gaske kiransu ne akayi. " Wai kai wannan wacece kake waya da ita?" Zainab ta tambaya.
     " Ai wannan da kika gani wata sister ce nake waya da ita. A germany take karatu fa. Kin san ban dade da kammala degree naba a can." Injishi.
      " To, kace kai babban mutum ne." Injita.
      "Okay to bari na wuce sai gobe." Inji huzaifa.
      " To haka zaka tafi baka fadamin sunan nataba. Shin wai koda gaske baka santa ba?" Zainab ta tambaya.
     "Shin wai da gaske kike sai na fadamiki sunanta? To bari na gani ko zan tuno." Anan ya done kai yana tunani kamar bai sani ba. Sai da aka dau lokaci sai ya dago." Yauwa na tuno. Sunanta kande mai albasa." 
     " Au ashe ka sani." Inji zainab cikin dariya. Anan sukayi sallama ya fita.
      Ai kuwa yana fita sai aka bugoma zainab waya.Tana dauka sai taga alhaji ne. Anan sukayi maganar da sukeyi ta ajiye waya. Ai kuwa tana ajiye waya sai ta fara tsuki. Anan yasmin ta matso kusa da ita domin tasan ko meke faruwa. " Hajiya ina fatan dai lafiya naga kina tsuki." Inji yasmin.
      " Ina fa lafiya. Wai alhaji ne ya fadamin cewa ya fasa tafiyar. Gobe yana nan dawowa. Ni abunda nake jima haushi shine gaba daya ya bata min tsari." Inji zainab.
      " Haba hajya kada ki samu damuwa ai akwai mafita. Yanzu sai ki buga masa ki tambayeshi a wane lokaci zai dawo goben." Inji yasmin.
      Ai kuwa cikin sauri ta buga masa.Yana fada mata saita ajiye wayar tana murna." Cewa yayi sai da daddare. Kinga kuwa kafin ya dawo ai mun gama bararrakewa nida dan saurayina." Anan suka taba hannu suna dariya. "Yauwa kande dama inaso muyi magana. Tunda gobe audu zai dawo inaga kiyi zamanki a gida ki huta ba sai kinzo ba. Kya iya bari sai banda gobe." 
      "Ab. To indai hakane ai wannan ba matsala bane hajiya." Inji kande.

                                                          PAGE 53

      Washe gari saiga huzaifa ya dawo yaci kwalliya sosai wadda tafi ta jiya. Ai kuwa zainab na ganinsa ta sheko a guje ta kankaneshi cikin murna. Itama haka taci ado ba wasa. Wasu kayane tasa kome a fili. Anan ta jashi zuwa cikin daki. Ai kuwa suna shiga ta kwabe kayan ta koma daga sai buje da bra. 
   " Nifa hajiya ina tausaya miki domin nasan yau sai kinyi laushi kamar burodi." Inji huzaifa.
    " Hahhh, kai yaro, ire irenka fa sun ja dani sun barni. Saboda haka ko kai dai dai nake dakai. Inba tsoro ba kazo mana." Anan ta koma saman gado tana jiran isowarsa sai wani kyalkyatar dariya take.
     " Kikace ko? Ai bari ki gani yanxu zaki gane kurenki." Anan ya cire wandonsa domin ya nuna mata kamar da gaske yake. A guje ya sheko wurinta ita kuwa ta wani bankare kafafuwa sai faman dariya take. Jawoshi tayi da karfin tsiya shi kuwa yana ganin haka sai yayi sauri ya dauko wata hoda. Anan ya huro mata ita. Ai kuwa hodar na shiga hancinta sai wani bacci mai karfi ya saceta. Anan yasa kayansa daga nan sai ya dauko jakar kudin da alhaji ya bata ajiya wato biliyan talatin. Ai kuwa yana fita gidan sai ya tari a dai daita sahu ya tafiyarsa. 
Ita kuwa zainab bata farko ba sai da aka dau lokaci mai tsawo. To bayan ta farko ne sai ta fara sallallami ganin ba kudi ba kuma saurayinta. Anan ta fito aguje tana ihu. Shi kuwa mai gadi naji sai ya sheko ya gani ko lafiya.
      " Hajiya ya naga kina kina kuka lafiya kuwa?" 
      " Inafa lafiya. Gashi wurin bakin kwadayina nayi biyu babu. Bani ga saurayi bani ga kudin da alhaji yaban ajiya." Inji zainab
     " Saurayi kuma? Amma kuma ke hajiya ai ni banga shigowar kowa anan ba."
Injishi.
     " Ai nasan bazaka gane ba, ka barshi kawai bazaka gane ba." Haka zainab ta fada cikin kuka.
     " To amma ke hajiya kudin har nawane da kike kuka akansu?" Mai gadi ya tambaya.
     " Kusan fa biliyan talatin ne." Zainab ta bashi amsa.
     " Biliyan talatin? Lalle hajiya sunanki gawa." 
      Suna cikin maganar sai sukaji ana musu sallama.Ai kuwa suna dubawa sai sukayi ido hudu da alhaji. Wai ashe shine ya dawo......

                                                   PAGE 54

              Shi kuwa huzaifa daya hau adai daita suhu bai tsaya koina ba sai bayan gari. To bayan ya sallami mai adai daita sahu sai ya hau titi shi kadai sai tafiya yake. Tun daga nesa ya hango wata mota baka an fakata tsakiyar titi. Mace ce tayi wanka tasa kaya bakake da glass baki. Kai shigar da tayi gaba daya baki ne. Anan ya kyalkyace da dariya domin yasan cewa yasmin ce a tsaye tana jiransa. Ai kuwa yana karasowa sai suka kyalkyace da dariyar farin ciki. 
     " Haba wai meya tsayar da kaine tun daxu fa muke jiranka. Ko ka manta ummana na cikin motar da ita xamu. Kai hadda yayana abba duk suna ciki." Inji yasmin
     " To wai yanxu a ganinki wane gari zamu inda zamuci duniyarmu da tsinke?" Huzaifa ya tambaya. 
     " Ai kada ka damu tafiya ai kamar an gama ne. Muna tafiya zan ginawa yayana abba da ummana shago babba wanda a kullum sai sun samu ribar dubu goma. Daga nan zan siya musu katafaren gida."
     " Au to mufa?" Huzaifa ya tambaya.
     " To ai ni da kai muna tare kuma kasan gidanmu daban ne da nasu." Inji yasmin.
     " To ai ba wannan ba shi wancan gidan naku fa?" Huxaifa ya tambaya. 
     " To ai dama ba gidanmu bane hayace muke. Kuma tun jiya na sayarma wasu sakarkaru shi da takaddun bogi kuma har sun ban kudi. Inaga yau mai gidan zai xo amsar kudinsa na shekara domin bamu biya ba. Kaga kuwa idan yazo sai sun yadda zasuyi dashi." Inji yasmin.
      Anan huzaifa ya kyalkyace da dariya. " Amma fa reza bakida mutunci. To amma ita wannan mota ina kika sameta?" 
    " Au shin ban fadama ba ko. Ai siyota nayi!" Inji yasmin.
    " Hmm. Sawota kikayi kodai reza kika yiwa wani?" Huzaifa ya tambaya. 
     Anan suka kyalkyace da dariya suna kallon juna. Daga nan sai sukasa jakar kudin a bayan boot. Tare suka shiga motar cikin farin ciki. Yasmin ce ke tukawa sai huzaifa a kusa da ita. Ita kuwa umma ladiyo da abba suna a baya. Anan yasmin ta tuka motar ta nufi hanyar fita garin. 
      Daga karshe dai sun samu nasarar fita garin inda suka shiga wani birnin. Anan duniya ta koma musu sabuwa sai bushasha sukeyi yadda sukaso. Dama wannan magana haka take. Duk namijin daya sawa rayuwarsa mata to karshens hasara. Haka zalika duk macen data sawa rayuwarta maza to itama karshenta hasara. Saboda haka samari da yan mata sai mu kiyaye don kada wataran ayi muna reza.
 
                                                           THE END














































Post a Comment

0 Comments