ATU BUDDARA

11/10/2022 à 14:16 - Les messages et les appels sont chiffrés de bout en bout. Aucun tiers, pas même WhatsApp, ne peut les lire ou les écouter. Appuyez pour en savoir plus.
11/10/2022 à 14:16
12/10/2022 à 08:33 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU🍂BUDDARA🍂

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

              NA

       AMIRA SAMINOU
      ( Zauja🍂Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

               *A*

Zaune suke a tsakar gida tana zaunar rake duk Ido suka zuba suna kallon ikon Allah basu ankara ba suka ji ta sanbado masu wata uwar tusa ji kake burrrrr har ukku lafiyayu amma ba damar magana sabida yanzu za su ga rashin mutumci sai da ta shanye rakenta tass sannan ta dubi Jamila ta ce'' ke ta so ki kwashe wanan abin .''

Hararenta ta yi, kasa kasa kafin tata shi ta fara kwashe wa kyalci ta yi, ta ce'' wallahi zaki san ni Kika harara dama na kula kanki rawa yake .''

Mikewa ta yi, ta shiga daki Jim kadan tafito wayarta ta dauko mai touch kirar itel ta kunna waka sannan ta dawo kan tabarman ta zaune ta ce'' Ohh yeah Inna ke ce zaki yi rawa yanzu nan .''

Jin ta ambaci sunanta ya sa gaban Inna faduwa tana duba gefe da gefe tsawar data daga mata ne ya sa ta mike rike da yar sandarta nan tafara juya gefe gefe kallon kin rainani ta yi, mata ta ce'' Haka ake rawa garinku bara kiga yanda zaki yi.''


Tsaye ta mike nan tafara karya kugu tana nuna mata yanda zata yi Haka Inna ta shiga juya kugu tana karya shi zaune ta yi, tana sheke dariyarta har da su rike ciki ta ce'' a'a Inna Ashe kin iya rawa haka to sannu da kokari koma ki zauna .''

Haka tafara dan gwala yar sandarta ta koma wajen zamanta sai wuci take Haka ta yi, ta kiransu suna taka rawa tana shekewa da dariya sai da ta gaji dan kanta sannan ta ce'' ke Jamila ta shi ki kawo min ruwa zan sha .''

Haba wai ke Marfu'atu duk wajen nan ba wanda kike raina sai ni ina matsayin Matar yayanki amma sam baki min ladabi.''

Iyeeehhh lallai kam wannan matar nayi dariya kin ga haura na shi yasa kike min rashin kunya ko yasin zaki san kin min rashin kunya .''

Yaya Nura ne ya shigo ai kuwa ta fashe da Kuka tana harba kafafu da sauri ya kariso wajenta ya ce'' Atu lafiya kike Kuka?"

Yaya ba wanan matar ba ce ta yi, min rashin kunya sai zagina take har da duka na fa ,tafada cikin gunguni da yar shagwafa .''

Ki hakuri Atu na ki barni da ita zan dauki mataki .''

Ganin bata samu abin da take bukata ya sa ta yi kaylci a zuciya ta ce tun da ba zai dauki mataki ba nasan abin zan yi a badimi kuma ta ce'' laifi na farko ko a dau mataki koni na dauka wanda yarinya zata yi Kuka .''

Daki Jamila ta shige ,ita Habiba wacce suke Kira da Habi ta kama gabanta Inna ma daki ta koma ganin lokacin dandali yana kara kusantowa ya sa ta mike ta nufi kewaye Bata wani jima ba tafito kai tsaye dakin Habi ta shige ta dauko kayan kwaliyarta tare da baza mata su cikin daki nan tafara shefe shefenta tana gamawa ta yunkura zata tashi Kenan wata tusarr ta sake zuwa mata tsaf ta sauke ta a bakin Habi dake shirin yi mata magana tana gamawa ta kakafe zanne tafito daga dakin ta nufi dakinsu ita fa Inna ta saka kaya zane daban riga daban sai dan kwali Irin na kauye tanyani shika ta d'aura a kanta sannan ta dubi Inna ta ce'' zan tafi dandali sai na dawo .''

Da a dawo lafiya Inna tabi ta da shi tana hamadalla da fitarta tana fitowa Habi tana kofar daki tana jiranta ta ce'' Ke Atu yanzu ke ko kunya baki ji ki gama zabga tusarki sannan yanzu kice zaki je neman samari .''

To ai ko saurayin ya min rashin kunya Al kur'an tsaf zan watsa masa ita kuma in yi gaba abina kuma.kisan da bashi kike ci sai na dauki mataki a kanki .''

Wallahi an dai ji Burr saura sirr ."

Hhhh to ai baki sani ba abin kunya gaba na bashi ba baya ba .''

Tana gama fadan haka tafice daga gidan a Kofar gidan ta ci karo da balki da Hasiya mugun tsoranta suke amma basu iya rayuwa idan Bata nan sabida tsokanarta kawai dan su ci dariya hararensu ta yi, ta ce'' To su Hasiya an zo cinye mana abinci gida Aka tarar na fito ,hmm ku tafi Muje kar ayi Bamu .''

Haka suka bi bayanta suna tafiya dan tsabar mugunta Irin tata sai zagba masu tusa take kuma tana cika su da Surutu ba damar magana ta ci ma yarinya uwa har suka karisa wajen da shigarsa mai kidin kalangu yafara tadi yana mata kirari sabida kowa shakarta yake ga ka Marfu'atu kyakyawa fara mai farar zuciya farar Macé alkyabar mata yarinya ta wajen Inna ina bada gaisuwa Babbar yarinya .''

Wani hamshakin murmushi ta saki tare da fito da kudi ta masa like nan fa ta shiga filin rawa yafara takawa nan sauran suka take mata bayan sai bayan sallah isha'i sannan suka Kamo hanyar gida Suna cikin tafiya suka ji alamun ana biyarsu ta baya har zasu yi gudu Atu ta ce'' karku damu muje cikin watsen kogon daga nayi magana zaku kece da dariya kun dai gane su iro ne kuma kusan manufarsu a kanmu .''

Da to suka amsa mata Sannan suka ruga suka fada cikin wanan kogon kuma amsa amo ya ke ta yar wuda suke lekonsu ganin sun nufi inda suke ya sa Atu rangada wata iriyar dariya ta ce'' yaku bil Adama me kuke yi a wanan yankin namu da dare ya yi, duk wanda ya sake bi a tanan sai shanye masa jini .''


Hahahaha su Balki suka fara sai na halaka ku kuma yau zan shanye jininku a hankali kafin ku karisa gida suka kara gagafewa da wata dariya.''


Tun da su Iro suka fara jin saukar muryar jikinsu yafara rawa a nan take Iro ya sa fara sakin fitsarin kuma yaki karewa Abbas kuma Ya tsule da zawo sai biyar kafafuwansa yake Ashiru kuma kashi mai tauri kuma ya lake ya kasa fitar da shi sai matsar kwalla yake .''

Cikin razananiyar muryanta ta ce'' Zaku fice daga wajen nan ko sai na bayyana gare ku ne .''

Haba ai suna jin suka fida takalmi hula a hannu iro yana gudu yana fitsari ,Abbas kuma zawon da ya yi, duk ya Bata shi , Ashiru kuma kashin yaki fitowa Yana kugu hawaye na zubar masa .''

Suna ganin sun tafi Haba suma suka fito kafa me na ci ban baki ba suka antaya da gudu sai kofar gidansu Atu kallon juna suka yi suna gagafewa da dariya suna tafawa harda rike ciki ita Balki harda faduwa kasa tsabar dariyan keta sai da Suka ci mai isarsu sannan Atu ta ce'' ya ka mata ku tafi gida dare ya yi, kar ku hade a hanya fa .''

Haba ai Hakan bama zata faru ba muna murna ta koma ciki cewar Balki.''

Hasiya ta ce'' ai bama zamu hadu da su ba sabida yanda suka razana burinsu su samu wajen buya .''

Wallahi kuwa hakane yanzu dai sai da safe insha Allah ina zamu hadu cewar Balki.''

Mu hadu wajen mai koko da yamma .''

Da Tom suka amsa sannan suka kama hanya ita kuma ta shige gida .''

WASHEGARI 

Kofa ta bude lokacin a na kiraye kirayen Sallah kai kewaye ta shiga tana fitowa ta daura Alwala sannan ta zo tafara buga kofar dakin Jamila da kuma Habi ,suna fitowa Jamila ta ce'' Lafiya .''

Ita ce ta yi, yawa .''

Na ga Alama tun da gashinan tafara saka ki hauka .''

2 Kenan yanzu dai lokacin sallah ya yi ke kwara ke Yaya Nura yana gida ba kamar waccen mai cikin kashin ba .''

Tana gama fadan haka ta shige dakinsu nan ta tarar da Inna ta kabarta sallah tana nafila da yake ita ce tata she ta ita ma nafila ta yi, tana gamawa Aka tayar da sallah nan suka yi sannan ta yi addu'a ta koma ta kwanta nan ta bar Inna tana Azkar .''


Tun da uwar Safiya tafito daga daki tana buga ma ko wace kofa amma Jamila ta ki budewa Inna da Habi sune suka fito tare da neman wajen zaman ganin ba zata daina dukan kofar ba ta ce'' Wai ke Atu me ya sa kin cika naci ki rabu da ita mana Yayanki yana ciki fa .''

To ni ina ruwana ai dama shi nake nema ba ita ba sabida yunwa nake ji kuma nan kawai huskewa Kuka yi .''

Shiru ta yi, bata kuma magana ba ganin basu da niyar fitowa ya sa ta nutsa kai cikin dakin ai da gudu tafito ta nufi kofar gida sannan ta dawo da gudu tafara zagaye gidan a guje Inna ta ce'' Wai ke me yasa Kayan kuruciya basu Kare maki ne yarinya kusan Shekara 14ans(year) a ce Bata fara Mallakar hankalin kanta ba .''

Sai a lokacin ta tsaya ta ce'' Inna wallahi Yaya da Jamila ne .''

Habi ta ce '' me suka yi kuma ?"

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' wallahi yan Iska ne .''

Dariya suka saka Inna ta ce'' gulmar data aike ki ita Kika gani .''

Amma dai sun ji kunya  wallahi .''

Ai sai da na ce ki kyale ta zata fito Kika ga abin da Kika gani .''

Ni dai ban yafe ba Alkur'an sun zama yan Iska amma wallahi sun ji bakin haushi..............


Ya Kuka ji wanan Idan ya yi maku zam zam in ga ruwan comment 💃💃
12/10/2022 à 08:34 - Mom Star ✨: 🍂🍂 ATU 🍂 BUDDARA🍂

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


           Na 

       Amira saminou
      ( Zauja 🍂Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

              *B*

Hankalinta yana kan wayarta turo kofar da aka yi ya sa ta daga dara daran idanunta ta sauke su kan Lantana ranta a bace ta ce'' Wai ke sakarar wani gari ce ne zaki shigo ko sallama ba za ki yi .''


Yi hakuri Hajiya mantawa na yi .''

Idanunta tafido ta ce'' to tun da kin manta ki fita idan ki tuna sai ki dawo .''

Fita ta yi, ita kuma haushi ne ya turnine ke ta taci gaba da Abin da take ta jima sosai kafin ta dawa ta turo kofar ta fado ciki a guje ta ce'' yawa Hajiya na dawo .''

Menene kuma ?" 

Sai da ta wangale baki hakora duk waje ta Sosa keya ta ce'' Wai dama dan in ce na tuna abin da na manta da zun .''

Oyeehh to fadi na ji .''

Assalam alaiki .''

Murmushi ta yi, ta ce'' To ya yi , kyau Zaki iya tafiya .''

Amma kinsan me .''

Ina jinki ,'' Nifa wajen Mama na tafi tafada min dan kaine baya ja sosai .''

Kinga ta kanki tun da har sallama mantawa kike .''

A'a ita fa ina tuna ne da ita kawai kaine nane baya ji lokaci a kauye aji na farko sai da nayi Shekara 11 ina maimaita shi kuma har yanzu ban ci gaba ba .''

Tashin hankali wai dagaske ko shirmanki ne .''

Allah ma kuwa tafada cikin garancin nan sannan ta ci gaba cewa shi yasa Abba ya ce zai min aure ni kuma nake yi ta rizgan Kuka .''

To Lantana ya isa haka ina tea din yake.''

Hehehe Hajiya ai kin ga tsiyar kenan mantawa nayi .''

To yanzu je ki doramin .''

Fita ta yi, ita kuma ta girgiza kai ,ta koma kan wayarta ta .''

★★★★★

Fitowa ya yi, cikin shirin zuwa gonna tun da suka fito take kallonsu dariya ta arce da ita tana tafawa tana kara shekewa da wata sabuwar dariya Hakan ya sa Nura daure fuska ya ce'' ke Lafiya ?

Langwafar da Kai gefe ta yi, tana sake yin wata dariyar har da rike ciki su Kaka da Habi ma biye mata suka yi sabida dariya tata tayi yawa Hakan ya sa ta ja ra'ayinsu suka yi ta dariya, tsoki Nura ya ja  , ya jefa masu kudin kalacensu yafita yana kwafa Jamila da jikinta ya yi, sanyi ta nufo su ai kuwa dama ita Atu take jira ta zaune ta mike tsaye har ta Bude baki zata yi, magana ta ji, saukar tuso shi zaune radam a cikin bakinta Bata Kai ga rufe bakin ba ta dauko ruwa ta kwarara mata ta ce'' yawa ki sha magani mai kara lafiya .''

Tun da tafara Sakarma Jamila tusa ta yi, mutuwar zaune ta kasa rufe bakin sai lokacin da ta zuba mata ruwa da sauri ta kalle ta ta ce'' Atu me nayi kuma Zaki kwada min tusa a baki da sasafe ko kalaci ban yi ba .''

Hade fuska ta yi, ta ce'' wanan ai magani mai kara lafiya ake kiransa .''

To Bana so ke me ya sa baki barsa a cikin ki ba .''

Ke kimin shiru karki kara kwasar wani laifin Yan Iska kawai ke da mijinki .''

Tana gama fadan haka ta ce'' Inna ta idan kin ji shiru na reta wajen mai koko .''

Allah ya kiyaye hanya Jikale ta .''

Anya ba cutata za'ayi ba wanan sunnan baya fitowa sai in ana bukatar wani Abun wajena .''

Dama wai nace ki debo min ruwan wanka.''

To kaji fitowa zaki yi , ki ce na debo maki ba sai kin hada da cuta ba .''

To ayi hakuri a debo min ruwa .''

Sai na sha koko dan Allah ki bani na kosai sai na hada .''

Yawa yar Albarka duba Karka shin pillow .''

Babu musu ta danna Kai dakin tana daukowa ta yi, gaba abin ta a wajen mai koko suka hadu da su suna ganinta suka Washe baki Balki ta ce'' Atu dama ke Muke ta jira .''

Idan ba koko Zaki saya min ba lafiya ake nema na.''

To ai kece Kika ce mu hadu anan .''

Ai zan zo ko na ce bazan zo bane .''

Allah ya baki hakuri .''

Ki biyo dare ki karbe idan ya bani .''

Shiru suka yi ita kuma ta Mika ma mai koko kudinta a dole Aka yi tsalaken layi Aka bata wajen ko sai ma Haka dan ba karamin aikinta bane ta zubar da kokon ko ta watsar da kullun kosai kowa ma ya rasa 


Comment and sharhi pls🙏🏻🙏🏻🙏🏻
12/10/2022 à 08:34 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA🍂

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


           Na 

       Amira saminou
      ( Zauja 🍂Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

4&5

Suna nan zaune su Iro ,Ashiru da kuma Abbas suka zo wajen cike da washe baki Abbas ya ce'' A'a mutuniyar Ashe yau ana wajen mai koko .''

Yi ta yi ,kamar ba da ita yake ta mike tsaya tare da kakafe zanne ta ce'' Ke Balki ku tashi mu tafi .''

Da sauri Iro ya ce'' haba mana kyakyawa da kin ga mutuman shine zaki tafi baki ji Yana magana bane .''

Wata uwar harara ta balla masa ta ce'' kaga ina kula Yara ne .''

A'a,'' '' to ka fita idona na rufe ko yanzu na shiga kwalwarka na dame maka kudin kubewa a ciki .''

Da Sauri ya dafe kansa ya ce'' ah sauka lafiya Atun Abba .''

Murmushi mugunta ta yi, ta ce'' To ga sadakar kirarin da kayi min ai kuwa nan ta banka da masa tusa mai wari kamar mushe ya mutu daga mai koko har mai kosai da Wanda suka zo saya suka watse shiko Iro ya yi mutuwar tsaye Ashiru kuma déjà ya zarce da gudu shi da Abbas su Hasiya da Balki kuma suna biya da ita baya suna jera mata sannu suna mata kirari ita kuma sai kara dage kafada take tana Doro sai ka ce wata yar Sarki har kofar gidansu suka raka ta ganin zasu tafi ta ce'' ina Zaku tafi kuma ?"

Wai zamu tafi karki ce zamu cin ye maku abincin gida .''

Ai karku damu da wasa nake fa dama zamu debo ma Inna Ruwan wanka kuzo mu dauki jarka duk matar da ta maku magana kada ku kula ta .''

Jinjina mata Kai suka yi sannan suka shiga daga ciki da sallama a bakinsu babu kowa tsakar gidan Hakan ya basu damar daukan jarka suka nufi bakin Pompo .'''

★★★★★

Cikin shirinta tafito na zuwa shcool Riga da wando ne jeans Sun dan kama ta duk da ba wata make-up ba ce ta yi, amma ta hadu sosai litafin makaranta suka hannunta sai jaka karama da wayarta dake hannunta wajen da Mama take ta zaune a shagwafe ta ce'' Mama nafito shine ba zaki tashe ni ba har na soma makara .''

Sorry yar gidan dady Bana son na tashe ki kina tsaka da baccinki .''

Har zata yi magana suka tsinkayo muryan Lantana tana fadin Iyeehhh dama Aunty Haka Kika zama yar Iska ban sani ba .''


Dan hade fuska ta yi, ta ce'' wanan wace Irin banzar magana ce nice nake maki kama da yan Iska Kuma.''

Cikin Irin maganar mararsa wayo ta ce'' To ki ga Kayanki Kuma a Haka Zaki fita idan da a kauyenmu ne ihuu zasu yi maki .''

Tsaye ta mike ta ce'' ko kema ihun da zaki min ne.''

Wace ni shegiya in ji dan daudu sai kin dawo .''

Mtsss taja tsoki tana fitowa daga falo motarta ta nufa tana shiga tafice daga gidan ta dauki hanyar UNIVERSITÉ dake cikin ADS .''

★★★★ 

Wai Hajiya ni ko nace yaushe Malam zalumu zai dawo gidan nn ne .''

Murmushi Mama ta yi, ta ce'' kin matsu ya dawo ne .''

A'a kawai dan naji ne idan bai da mata kawai sai ki aura masa ni.''

Kallon baki da hankali ta yi, mata ta ce'' To ba damuwa bara na Kira maki shi sai ku fara zan tawa kafin ya dawo .''

Ai da gudu ta yi, dakinta sai sauke ajiyar zuciya take kamar wacce Aka koro .''

Haka kawai ina zaman zamana na tsaye sauraren wanan azalumin mutuman yafada min magana da zan kasa cin abinci dan wallahi in ban ci abinci akwaye matsala .''


★★★★★

Suna isa bakin Pompo babu jimawa suka dawo gida nan Inna da sauran Yan gidan suka yi wanka Aka samu na d'aura girki sai da su Balki suka ci abinci sannan suka tafi gida .''

Wani Irin uban ihuu suka ji Atu ta buga tana tsale kallon wajen da take suka yi ganin lawan mijin Habi ya dawo da gudu ta nufe sa tare da fadawa jikinsa ta ce'' Yaya lawan nayi kewanka sosai kullum sai Nura da Matarsa Sun min munafurci .''

Rabu da su yar kanwata dama halinsu day .''

Murmushi ta yi, abokin shirme ya dawo ta ce''. Yaya an fara saka mana Ido ya kamata kafara wuta wa sannan kazo ka sha labari.''

Haba to an jima zamu tafi bakin ruwa ki daki duk uban da kike so kuma ya taku .''

Girgiza Kai Habi ta yi , tare da shigewa daki amma nan murna ce fal a zuciyata abin kaunarta ya dawo gida sai da idan ta tuna masifar da zasu rin ka kunno masu sai taji babu dadi .''

Comment and sharhi pls🙏🏻🙏🏻
12/10/2022 à 08:35 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA🍂

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


           Na 

       Amira saminou
      ( Zauja 🍂Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

6&7

Tana shiga kai tsaye classe ta shiga sabida ta yi retard cour din Histoire suka yi bayan sun fito Nihal ta dube ta ta ce'' Yasmine lafiya yau naga kin shigo classe a late .''


Ba komai bacci ne ya dauke ni shi ya sa kin ga ni yunwa nake ji ina son zan ci donot ne .''

Tab ai wanan sai Plaza zamu same sa .''

Ba damuwa ta shi mu tafi dan ko break ban yi ba .''

To idan Hajara ta zo Bamu nan fa .''

Idan ta Kira sai ta isko mu a tsan din .''

Mikewa suka yi suka nufi motar Yasmine suna shiga ta dauki hanya da yake babu wani nisa sosai hakan ya sa suka Kariso cikin kankanin lokaci tana shiga suka tsaya nan suka saya donot din sannan suka shiga daga ciki nan ta yi, masu oder shawarma da fritte sai juis de mil babu Bata lokaci aka kawo masu suna tsaka da ci ne Nihal ta ce'' Ni ko Yasmine ina Lantana mai aikin ku ne nayi missing din ta kwanan biyu nan.''

Murmushi ta yi, ta ce'' tana gida wanan shirmanta ya yi ta afki wallahi" wai kinsan me ta ce min yau ne ?" 

A'a sai kin fada bani in sha .''

Ce min ta yi, wai yaushe na zama yar Iska .''

Dariya ta kyalkace da ita ta ce'' To me Kika yi na zama yar Iska kuma .''

Hmm ki barta da shegentakarta kawai wai dan na saka wanan Kayan .''

Sosai ta ci dariya ta ce'' daga yanzu sai kinsan irin Kayan da zaki saka idan tana gidan .''

Ke zan maki rashin mutumci fa me kayana suka yi kuma .''

A'a wanan amsar tana wajen Lantana ai .''

Shiru ta yi, Bata kuma cewa komai ba Kiran da ke shigowa kan Wayar Yasmine ya sa ta kallon screem din ganin sunnan Hajara ya sa ta kalli NIHAL ta ce'' Hajara ce .''

Daukan wayar ta yi, ta ce'' Yanzu dan rashin mutumci ina Kuka shiga Kuka barni ina ta faman neman ku .''

Muna Plaza muna jiranki a dazun baki fito ba shine muka zo ga abincinki Yana jiranki .''

Amma Nihal kinsan fa an kusa komawa aji gaskiya idn kun gama ku tawo min da nawa .''

Baki da matsala yanzun zamu tawo insha Allah .''

Wai ina Yasmine ne banji motsinta ba .''

Gani ta samu ne ,'' tafada tana sauke cokali daga bakinta .''

A'a yau ban ji sautin muryan kawata ba shi yasa na tambaya ko lafiya .''

Murmushi kawai ta yi, sai Nihal da ta ce'' gamu nan zuwa ki tsaya bakin etager din da  muke zama .''

Ok sai kun kariso .''

Katse Kiran ta yi, ita kuma ta zauna zaman jiransu sai da Suka koshi sannan suka koma Université a inda suke zama nan suka same ta nan Nihal ta Mika mata abincinta tana gamawa aka buga karaurawar shiga aji nan suka tashi suka shiga .''


★★★★★

Hello Son yanzu ka manta da ni ko kirana ma ka daina kwana biyu .''

Sorry Mamaaa wallahi karatu ne ya boye ni amma ai ke ba zaki taba mantuwa a zuciya ta da rayuwa ta baki day .''

Hmm kafa iya dadin baki yanzu dai ka karatu .''

Alhamdulilah Mama ina yar amana ta .''

Tatafi école sai karfe 1h30 zata dawo .''

To a gaishe min da ita nayi missing rigimarta 2day .''

Idan ka dawo sai ku d'aura daga in da kuka tsaya .''

Hakane Mama ina dadyna .''

Kafini labarinsa sabida kusan kullum sai kun yi magana wai ya baka tambaya mutuniyar taka ba .''

Hmm wake nan Mama .''

Zan ci gidanku amaryarka mana ko dazun nan sai da ta ce idan baka samu mata ba kawai ka dawo ayi da kai.''

Idan ransa yafi dubu to ya bace game fuska ya yi, kamar tana gabansa ya ce'' duk na rasa wacce zan aura sai wanan kazamar kin ga Allah tun wuri ki samo min wata yar aikin dan wanan yarinya ko hmm.''

Ina laifin mai sonka wai yaushe ma zaka dawo .''

Alkur'an nasan auren dole zaku man kwara ma na zauna a nan din .''

Dariya Mama ta yi, sosai ta ce'' Tom ya yi maka kyau tun da gudunmu kake yanzu dai ba wanan ba ka kula da kanka da karatun ka sai an jima .''

Tom Mama a gaishe min da yar amana ta kafin na dawo .''

Insha Allah sannan Lantana ma zata ji sakon ka .''

Murmushi kawai ya yi, ya ce'' ita ma ki gaida ita .''

Munafiki ana so ana kaiwa kasuwa Tom zata ji ita ma .''

Tana kaiwa nan ta katse kiran nasan ta mike tare da shigewa daki .''

★★★★★

Sai da ya yi, wanka sannan ya ci abinci ya samu waje ya kwanta sai bacci mai dadi ya yi, gaba da shi ,Atu kuma tana waje ta saka matan gida Suna taka rawa wasu tana dariya wani gurin kuma ta gyara masu tana Bata fuska sai da Suka gaji sosai Sannan ta shafa masu lafiya nan ta saka Habi ta kawo mata abinci ta Shaka sannan ta dubi Jamila ta ce'' ke taso ki kawo min ruwa zan sha kuma ki debo min na wanke hannu .''

Babu musu ta mike ta yi mata Abin da take so sabida LAWAN ya dawo gida tana gama sha nan ta shiga sambada masu tuso shi motsi kadan zaka ji Burr kuma babu damar magana bare a tashi zuwa daki kwarya ta samu nan tafara kida tana fadin ni Atu na sama rumbun Kaya sai ta Bada Burr da turare na mai kamshi da lafiya sai ta kara sakin kirrr kai kai tusa ji kake turrr burrt kirrr Kitt ,wanan tusar kam sai da ta saka Inna suman zauna Jamila ta sulale kasa tana danne hancinta Habi kuma sai tofin yawu take a kasa zuciyarta tana jera Allah ya isa ita kuma Atu ko a jikinta kawai sakin kayarta take hankali kwance zuciya zaune tana ci gaba da kidan ta tana aikin jera masu tusa kusan lokaci guda ganin zata kashe su a banza ya sa Jamila cewa dan Allah Ranki shi dade ki daina sako tusar nan wallahi kamshin ya Bade ko ina .''

Sai da ta gyara zama tare da kara sakin wata tusar har da su daga kafa ta ce'' yau nishadi nake ji shi yasa zan nishadantar dan ku da sanyanyar tusa ta .''

Muna godiya da wanan nishadi amma a daina Haka ni kinga shara daki ma zan yi.''

Habi ta wuff ta ce'' ni kuma Yayanki Yana daki zan dubo idan bai tashi ba .''

Inna ganin suna shirin barinta cikin masifa ya sa ta ce'' wayoo bayana  dazun a bayi na fadi dan Allah ku taimaka min ku kaini dakina .''

Dariya mugunta ta sheke da ita ta ce'' lokacin da kuke tikar rawa baki tuna da gurdewar da Kika yi ba sai yanzu to Alkur'an babu inda zaku tafi duk wacce mijinta ke son ganinta ya zo nan wajen Marfu'atu buddara ya tambaya izini selon ace na kyale ku kun lalace ko.''


Amma wanan yarinya kina cutar mu wallahi kuma a Haka kike tafiya wajen samari kuna shan fira .''

Dariya ta yi, hade da tafi ta ce'' ban baki kashin labari ba ai dazun wajen mai koko na sakamar Abba da abokansa lafiyayar tusa mai kara lafiya da kwanciyar hankali.''

Shiru suka yi jin ta kara sakin wata uwar tusa mai masifar wari .''


Comment and sharhi pls 🙏🏻🙏🏻🙏🏻
12/10/2022 à 08:35 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

8&9


Tun 12h da Suka shiga sai wajen 13h30 sannan suka fito duk a gajiya mota ta nufi ita da kawayenta sai da Suka fara ajiye Hajara sannan ta ajiye Nihal a hanyarta ta zuwa gidane motarta ta tsaya da alama tana bukatar gyara ga shi anguwar babu kowa ta jima nan tanan tsaya sannan wasu hamshakan motoci suka biyo ta hanyar da gudu har sunyi nisa sannan kuma suka dawo wata bakar mota ce babba ta fito sai kyalli take tana ganinsu ta sauke ajiyar zuciya fitowa ya yi, yana bin ta da wani Irin kallo ita kuma sherewa ta yi , kamar Batasan akwaye mutane a wajen ba ganin Bata da niyar tanka masu ya saka shi sauke girman kansa ya ce'' sannu yan mata me kike yi a nan ke day ga shi babu kowa baki tsoron wani abu yafaru da ke .''

Sai a lokacin ta kallesa hadaden saurayi ne kyakyawa kyaunsa ya wuce tunanin mai karatu sunkuyar da kai ta yi ,sabida kwarjinin da ya yi , mata ta ce'' bansan miye matsalar motarta ba tsayawa ta yi, ina cikin tafiya .''

Kallonta ya yi, a Karo na biyu Yasmine tana da kyau amma ba tsan ba fara ce tana da tsayi sannan akwaye iya daukar wanka ya ce'' kin ga yanzu akwaye zafin rana sosai bai kamata tana dukan wanan baby girl din ba Muje driver na ya Kai ki gida idan an gyara maki motar zata isa gidanku lafiya .''

Dan hade fuska ta yi, ta ce'' Haka kawai sai na shiga motarka ka sa ce ni ,tana maganar tana hadawa da hararen Wasa .''

Murmushi ya yi,wanda ya tafi da rabin tunaninta ya ce'' ba sace ki zan yi kanki zan yanke idan baki shiga ba .''

Make kanta ta yi, ta ce'' bani zuwa ka Kira a gyara min idan kayi niyar taimako.''

Dariya ya yi, ya ce'' na ji shiga zai kai ki gida zata iso daga baya .''

Ganin duk ta gaji ga yinwa da ke mata duka ya sa ta shiga nan ya ja suka tafi nan ta shiga nuna masa gidan na su Yana ajiye ta ya tafiyarsa .''

Tana shigowa gidan babu kowa a falo Hakan ya Bata damar shigewa dakinta kai tsaye toilet ta wuce ta watsa ruwa tana fitowa ta saka Kayan shan Iska sannan ta fito falo neman abinci .''


★★★★★★

Tana gama cika su da tusa ta mike ta nufa toilet ta yi, wanka tsabar tusar tana aiki hakan ya sa Habi da Jamila suka kumbre motsi kadan sai Sun leka toilet ji kake kurrr zukuttt Haka suka yi shiga kafin wani ya fito har day tafara sakin cikin wando ita kuma muguwar sai dariya take bin su da ita dakin Habi ta wuce ta shirya tsaf tare da watsar mata da Kaya ko ina sannan ta nufa dakin Inna ta saka kaya kallon Inna ta yi, ta ce'' ni zan fita !!

Ina zuwa Atu?" 

Dan bata fuska ta yi, ta ce'' nifa Bana son tambaya ai dai kinsan zan dawo gidan ba tsan zan kwana ba ko .''

Allah wuci zuciyarki Atun Inna .''

Murmushi ta yi,ta ce'' gidansu Hasiya zan tafi .''

Tom a dawo lafiya .''

Sosai suka yi farinciki da fitar da ta yi, sabida ko ba komai za su shakata .''



Tana fitowa kai tsaye gidansu ta wuce dama Balki tana gidan nan suka tsaya bakin kofa suna ganin masu wuce wa kawai dan su ja fada ai kuwa Aka ci sa'a wasu saurayi da budurwa Sun zo za su wuce da alama daga birni suka fito ta saka Riga da riket na kanta Sun matse ta sosai dan da kyar take tafiya murmushin mugunta ATU ta yi , ta ce'' je ki dauko min donko yanzu .''

Ko da suka ji hakan Sun san abin da zata yi , babu musu Hasiya ta shiga gidan ta dauko guda ukku suka samu dutse nan suka sai ta a tare sai a mazaunan wanan budurwan ,da sauri ta saki kara tare da dafe wajen saurayin ne ya jiyo yana tambayar lafiya ta sakar masa murmushin yake da yafi Kuka ciwo ta shiga wasa da hannunta a baya ta ce '' a'a Karka damu ba komai wani lokaci dama haka nake ina tafiya sai nayi ta sakin kara .''

Jinjina kai ya yi, sannan suka ci gaba da tafiya nan ma Bata ankara ba ta je saukar wasu duwatsun a mazaunanta wanan Karon kasa daurewa ta yi, har da Kuka ya ce'' Wai Samiha lafiya wanan ihun haka duk kin riki ce lokaci day.''

Wasu ne suke shana da danko wallahi da zafi sosai .''

Dariya ma ta so ba shi yanayin yanda ta yi, maganar juyowar da zai yi ai kuwa shima ana same shi a keyarsa ji kake kwal kwal har guda ukku da sauri ya dafe kansa su kuma suka gagafe da dariya har da rike ciki ganin Sun nufo su ya sa ATU kwasar duwatsu ita da su Balki suka fara yi masu ruwansu ai ba shiri suka fara gudu suna biyarsu suna dariya sai da Suka yi nisa sannan suka dawo gidansu Hasiya Kai tsaye dakinta suka wuce suna ci gaba da dariyansu Sun jima zaune a wajen suna firansu suka ji sallama dan lekowa Balki ta yi , ganin Arafat ne da Samiha ya sa ta ruga da gudu tafada ma Atu ,sosai hankalin Hasiya ya tashi kar Kaka tata shi daga bacci nan Atu ta ce'' je ki dauko min Igiya ukku .''

Babu musu ta fito da sauri ta dauko sannan ta kaima Atu wajen manya manyan Shanu kosa shi suka nufi nan suka d'aura igiyar a kugunsu tare da d'aura ma saniyar a hankali suka fito daga gidan suna fitowa waje suka ja igiyar da karfi nan Shanun suka fara gudu ganin dagaske wajensu zasu nufa ya sa Arafat da Samiha gudu sosai suka sha gudu nan Samiha tafadi kasa ta gaji nan ya duka ya goya ta sabida su Atu na nesa da su amma sabida Samiha Irin jibga jibgan matan nan ne ya sa da kyar yake gudu duk ya gaji har suka Iso wajen ganin fa idan bai yi ta rayuwarsa ba wanan Shanun a banza zasu hallaka shi nan ya saki Samiha tafadi dumm kake ji ya sako ta daga Bayansa wata kara ta saki bai tsaya ta kanta ba ya tsere abin sa ganin fa shannun Sun kusa cin mata ya sa ta daure tafara gudu da kyar .''

Ganin Sun basu wahala sosai ya sa su dawowa hanyar gida Suna tintsirewa da dariya musanman faduwar da Samiha ta yi, nan ta kwance Shanun daga kugunta ta mika ma Balki ta ce'' rike wanan zan yi gyara dan kwalina .''

Tana Mika mata Kenan ta jiyo ta ji da bugu wani abu mai taushi ga kamshin turarensa sai dokan hancinta ya ke kallon kallo suka shiga aika ma juna hannunta day Yana kirjinsa shi kuma ya zagaye nashi da kugunta yana Kare mata kallon Yana yin yanda yake kallonta sosai ya shiga zuciyarta take gabansu ya shiga faduwa har suna iya jiyo sautin bugawar zuciyar dayansu ganin kallon ba mai karewa bane ya sa shi wura mata iska a idanunta da sauri ta lumshe su tare da dan ja baya ta sunkuyar da kai .''

A dan fusace ya ce'' ke baki da hankali ina kike kallo zaki wani zo ki fadamin a jiki sai kin mani fyade .''

Jikinta a sanyaye ta fito da idanunta ta ce'' dan Allah ka yi hakuri nima bansan Hakan tafaru ba.''

Yanayin yanda take magana dan karamin bakinta pink yana dan motsawa a hankali Hakan ya yi matikar birge sa a hankali ta dago lumshasun Idanunta tana kallonsa .''

Murmushi ya sakar mata ita ta mayar masa nan ta wuce tafara tafiya jiki ba kwari sai da Suka yi nisa sannan MARWANE suka tafiyarsu dan da alama wajen daurin aure ya kawo su garin .''


Hmm yanzu Atu baki ji abin da mutuman nan yake fada kanki fa ce maki ya yi baki da hankali me yasa baku Nuna masa kallar naki ba .''


Haka kawai ta saki murmushi musanman idan ta tuna Irin yanayin da suga shiga ga wani kallo mai kama da love sannan ta ce'' kar ki damu ai da gani bako ne ni kinga na tafi gida ki gaishe min da Kaka tun da bacci take .''

Sosai abin ya basu mamaki amma sabida abar bala'i ya yi sleep ya sa suka ce insha Allah yau zaki tafi Dandali ne .''

E'e idan kun shirya kuzo sai mu wuce .''

Ba damuwa insha Allah .''

Tana gama fadan hakan ta juya ta nufi gida suma suka kama hanyar gida Balki Bata jima ba ita ma ta nufi na su gidan.''


Idan babu comment bazan sake typing ba Alkur'an🙄🙄🙄
12/10/2022 à 08:35 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

Wanan page din sadaukarwa ne gare ki Mama Farhane ina godiya Sosai da kokarinki  kiyi yanda kike so da ita 

10&11

Kai tsaye danning tanufa ta zuba abinci dai dai cikinta sannan ta zuba jus tana ci tana danna waya Lantana ce tafito tare da rike baki tana kallonta jin alamar ana kallonta ya sa ta jiyo tana kwada mata harara ta ce'' ke lafiya kika sakani a gaba kina kallo baki taba ganina bane ko menene .''

Hmm ranki shi dade wani sabon salo na gani a wajenki .''

Na me fa ?"

Kin saka kayan yan Iska baki ko tsoro sweety na ya shigo ya ganki haka ko Dady kuma baki mai da niya ki ce abinci sai latsa waya kike da ni ce Hajiya hmm tafada tare da Jumke hannunta na dama ta buga shi da dayan .''


Iyeehh ,Yasmine tafada tare da sakin baki ta ce'' waye sweetyn naki .''

Sai de ta rufe idanunta ta ce'' Malam zalumu mana .''

Kina kiransa Malam zalumu din ne zai so ki ashe bazaki kula da shi .''

Haba ai yanda na ke sonshi har cikin birgin bangon zuciya ta kinsan me zan yi masa idan muka yi aure .''

A'a sai kin fada .''

Da kaina zan yi masa wanka sannan in saka masa pampos in goya sa Ya yi bacci .''

Dariya Yasmine ta tintsire da ita ta ce'' A'a lanle yaya Irfan zai sha Soyyaya tom Allah ya kaimu lokacin .''

Turo baki gaba ta yi, ta ce'' kina min dariya ba fa da wasa nake ba .''

Tom ai nima dagaske nake din Lantana ta Irfan a'a bara ya dawo musha shagali .''

Dan fari ta yi da ido tare da murmusawa tana kwafe fuska tare da rufe fuskanta da dukan hannayenta ta wanka da gudu dakinta wai ita a dole ta ji kunya .''

★★★★★

Jiki a sanyaya take takawa har ta kariso gida da sallama ta shiga ,Habi dake waje tana wanke Kayanta ta amsa bata tanka ta ba ta huce dakinsu ta tarar Inna tana Ninke kaya zaune ta yi, dan nesa da ita ta ce'' Inna ina son zamu yi magana dake.''

Tom ina saurarenki Atu .''

Meye soyayya ne ?"

Tom soyayya kuma me yasa kike tambaya .''

Ki fadamin kawai idan zaki fada .''

Idan kina son wani zaki din ga jinsa a ranki kaunarsa ya shigarsa kina son ganinsa a ko wane lokaci yawon shaukinsa kyauta mai birgewa da wajensa ki ji duk duniya babu abin da kike muradin kasancewa da shi zuwa cikar burinku wato aure sannan a duk lokacin da Kuka hadu musanman idan bai fitar maki kalmar so ba zaki din ga jin zuciyarki tana bugawa da sauri kunyarsa tana kara kama ki da kyar zaki iya dagowa ku hada Idanu sai de ki satar kallonsa kuma shima hakan.''

Idan baya Sonka fa ?"

Tsanarsa ce zata kama ka ko wane lokaci Zaki ji kamar yana ta kura ki baki son dai dai da sauraren muryansa bare ki kalli fuskansa har kiji wani Abun yana birge ki a game da shi dan zaki dauke sa da shi da Banza duk day suke .''

Uhmm Inna ta godiya nake sosai bara nayi shirin zuwa dandali Allah ya sa shima ya tafi .''

Girgiza kai Inna ta yi, ita kuma ta wuce toilet tana wanka tana sakin murmushi harta fito yau daga ka gane ta kasan babu tsokana a tatare da ita dakin Jamila ta shiga ta yi kwaliyarta tana gamawa tafito sannan ta saka kayanta ta shirya tsaf sannan tafito daidai lokacin su Balki sun kariso nan suka kama hanya babu maia hanya har suka karisa sabida Sun kula Atu ba su gabanta ba sai murmushi take saki ita ka dai suna isa nan mai kida kalangu yafara tadi yana mata kirari ita kuma ta chanza salon tafiyarta ta karisa cikin fili tafara yi masa liken kudi sosai take rausayawa hakan ya bama Marwane daman kallon yanda take takawa Abin gwanin birgewa sun jima sosai sai daf da Mangariba sannan Atu ta ce'' su tafi gida .''

Nan su Balki suka mara mata baya tana tafiya mazaunan na kadawa shap din ta yafito gwanin birgewa sai ya yi forme coka cola ta dan gantsara kadan gata kyakyawa Irin ta bugawa a jarida fara ce Bata da tsayi kuma ba gajera ba ce yanayin tafiyarta hakan yakara birge Marwane suna dan taba fira yanda suka rakashe nishadi har suka isa gida .''


Washegari tana fitowa daga daki Inna ta ce ta debo mata ruwa babu musu ta dauki jarka uku sai da ta biya ta gidansu Hasiya sannan suka tafi gidansu Balki nan suka dauki tulu su biyu ita kuma tana rike da jarkan a bakin Ruwa suka tarar da su Marwane suna wutane share su suka yi amma rabin hankalinta yana wajensa suna gama di ban ruwan da gangan ta watsa ruwa sai a saman fuskanka,da sauri ya lumshe Idanu sabida sanyin ruwan har farkwon zuciyarsa ,a hankali ya fara bude su ya sauke a kanta hannu ta hade waje guda ta ce'' dan Allah kayi hakuri bansan nayi ba zan daukar jarkan ne .''

Mikewa ya yi , tsaye tare da nufo in da take da sauri ta rufe idanunta sabida duk tunaninta sharara mata mari zai yi sai ta tsinci dadadar muryansa yana fadin miye sunnanki .''

Marfu'atu amma amfi Sanina da Atu .''

A ina gidanku yake ?" 

Kai ni fa banason tambaya me zaka yi da gidanmu haka kawai bansan ka sai ka din ga jera min tambayoyi to bansani ba idan zaka yi hakuri kayi idan kuma ba zaka yi ba Kai ta shafa .''

Tun da tafara magana yake kallon dan karamin bakinta shi birge sa ta kara yi yanayin Maganarta kuma nishadi yake bashi ,daukan Jarkanta ta yi, sabida ranta har ya bace zata tafi Kenan ya riko hannunta ya ce'' Marfu'atu sunanki yana da dadi sosai amma me yasa kike da fada ne .''

Bansani ba ai kaine ka fara .''

Daga tambaya shikenan .''

Tom Banaso .''

Murmushi ya yi, ya ce'' Tom shikenan ni ban hakura ba sai na rama .''

Tab ai sai de ka rame dan bazan taba yarda ba, ta karishe maganar tana murguda masa baki tare da sambada masa tusa tafi kala biyar ta kakafe zanninta suka kama hanya .''

Tsananin rudewa Marwane yafara cikin ruwan sabida wani dishi dishi yake gani sauran Abokan nasa kuwa mutuwar tsaye suka yi dama Salman ya san halin Atu dan ko ranar farko haduwarsu da Marwane ya yi mamakin da bata yi masa wanan iye shegen ba .''

A hanya kuma su Balki sai dariya suka bin Atu da ita Hasiya ta ce'' Gaskiya Balki baki da kunya wai nan kina son shi ne kika buga masa wanan uwar tusar wallahi koni kusan sikewa nayi sai da ta sake wata sannan na dawo dai dai .''

Hmm ai ke Hasiya baki da kunya ko kadan yanzu idan kun saké haduwa ya Kenan .''

Mtsss aikin Banza kune kuka san kunya ai ni Tuni na kasa ta a Katon plate ina tallarsa a hanya duk na rabe ta .''

Ya yi ,matar dan birni wanan kamshi mai dadi haka.''

To Allah zan ci uwar mutume idan bai man shiru ba naje nayi tusar idan akwaye wanda ya isa ya hanani .''

Ganin fa da gaske ta dauki zafi Hakan ya sa suka kame bakinsu sai jera mata sannu suke kamar ta yi wani uban aiki .''
12/10/2022 à 08:36 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*


12&13

Tana gama cin abinci ta mike ta nufi falo tare da kunna T.V tana nan zaune taji ana Horn fitowa ta yi,duk a tunaninta Dady ne ko Irfan tana fitowa ta ga motarta tasha wanka sosai har da kwaliya da Murmushi ta kariso wajen ta ce'' sannu da kokari ina mutumen yake ne .''

Ajiyar zuciya ya sauke tare da mika mata makullin motar ya ce'' bayanan ya yi , tafiya wani abokinsa yake aure shine suka tafi kauye sabida a tsan magabatan angon suke .''

Eyaah naso mu hadu sabida nayi masa godiya amma duk hakan bata bace ba ka Kira min shi .''

Ba damuwa insha Allah , Yana gama fadan hakan ya fara kiran MARWANE babu Bata lokaci ya dauka cike da girmamawa ya fara gaida shi bayan ya amsa ya ce'' yallabai na ce ga motar na kawo mata ta ce na kiraka ta yi maka godiya .''

Ba damuwa bata wayar.''

Mika mata wayar ya yi ta Karba tare da karawa a kunnanta bayan sun gaisa ta ce'' sannu da kokari hakika farinciki sosai shi yasa bansan ko dame zan saka maka ba sai ta wanan hanyar dan Haka na gode sosai.''

A'a karki damu babu komai insha Allah idan na shigo gari zan saka ya kawoni gidanku sai mu gaisa ko .'''

Amma da naji dadi Allah ya dawo da ku lafiya .''

Amin yafada ita kuma ta Mika masa wayarsa ta ce'' na gode da kokari fa .''

Karki damu babu damuwa bara na wuce ana jirana a waje .''

Tom shikenan .''

Yana gama fadan haka ya juyawarsa ita kuma ta shige ciki tana shiga ta tarar da Momy a falo kallonta ta yi, ta ce'' ke kuma daga ina kike da wanan kayan .''

Turo baki gaba ta yi, ta ce'' motata ce aka kawo min .''

A'a har ta iso Masha Allah amma Allah ya ma yaron nan Albarka .''

Gaskiya dai kam Amin sabida ya tseratar dani daga shairin yunwa .''

Ohh ke yanzu ba ta kanki kike ba ta ciki kike .''

Tom Momy ba sai ciki ya dauka ba kake gudun ka tsira .''

Shiru Momy ta yi , ita kuma ta ce'' Momy wai yaushe Malam zalumu zai dawo ne .''

Murmushi Momy ta yi ta ce'' kin ci bashi sai na fadamasa kema zaki biye ma lantana din ko.''

Rufamin asiri karki saka ya ballamin kafa ba shiri .''

Har Momy zata yi magana Lantana ta shigo falon kamar an jefo ta a hasale Yasmine ta ce'' wai ke me yasa baki da hankali ne Zaki wani fado mana haka .''

Wallahi hankalin ne nake ta biya amma yaki Bari na kama shi sannan kuma haihuwa aka yi ba daga sama na fado ba .''


Mtsss sai ki ta biyarsa tun da cizon kwalta kike .''

Ai kuwa dai shi yasa hakorana suke kara kaifi sosai sabida duk kwalta da ta fashe da hakorana nake gyara ta .''

Ke ta shi bace min da gani .''

Mikewa ta yi, tare da dauko mata magani da ruwa ta kawo mata kallonta ta yi, ta ce'' na miye wanan din .''

Na ga kina ta game fuska na zata kanki yake ciwo .''

Ohhh na gane mahaukaciya Kika daukeni ko lanle Lantana .''

Dariya Momy ta gumtse ita kuma Lantana ta juya tana fesa tata dariya .''

★★★★★

Tana shiga ta kwala kiran Jamila tana fitowa ta ce'' ke je ki kawo min abinci yunwa nake ji .''

Hararenta ta yi, ba damar ta ce bata kawowa ta ga rashin mutumci ganin idanunta mikewa ta yi tare da tafiya ta zuba mata abinci ,ke Habi kema fito Banason shashanci kina jini kin ma mutane shiru .''

Shiru ta yi mata kamar bata jin ta hakan ya sa tanufa dakin zata shiga Jamila ta ce'' ke Atu karki shiga Yayanki yana gidan nan fa .''

Kin ga Malama shimfida min Tabarma ki kawo min ruwa sannan wanki na yana jiranki kuma wallahi idan ba kiyi mai kyau ba sai kin yi sau dari takwas .''

Kame baki ta yi, tana kallonta ita kuma tana gama rufe baki ta nufa dakin ai kuwa tana shiga ta sanya kai ba sallama ta ga Habi na kwasar naman kaza .''

Iyeeehhh munafuka shi yasa kika shiru Kika sharara ma Jamila karya Kika ce Yayana yana ciki amma kin ji bakin haushi .''

Shiru Habi ta yi, sai labta zufa da take ,ganin bata da niyar magana ya sa ATU karban Plate din tafito da shi waje ta zauna ta ci sai da ta koshi sannan ta ce'' Jamila kin ga Habi munafuka ta shige daki sabida ta cinye kazarta wallahi Yaya ma baya ciki .''

Ai dama gulma ce ta kaiki dakin .''

Turo baki ta yi,ta ce'' ke fa yar rainin hankali ce dama daga ke har ita duk bakake ne ta ya za'ayi zuciyarku ta zama fara .''

Shiru ta yi, mata bata ko tankata ba ke munafuka ta cikin daki sai ki fito ko .''

Ke wanan yarinyar ta kula ke yar bana bakwaye ce .''

Dariya ta gagafe da ita ta ce'' sai de yar bana sha bakwaye .''

Da haukan yafi maki yawa .''

Wai dama mahaukaciya Kuka daukeni ko .''

Mikewa tsaye ta yi, tare da nufi wajen Jamila ita kuma tana duke tana wanki ai kuwa Atu ta shiga kida da bayanta daga ta buga hannu day sai ta saki tusa burr daga ta kara sai ta Bada futtt ,har ma sai ta Karka ta gefe sai dariya keta take yi mata .''

Jamila kuwa tuni ta yi, suman duke ta kasa motse sabida dauyin tusar ga masifar wari Tuni kanta yafara sarawa ta sa ci gaba da wankin .''

Sai da Atu ta gaji dan kanta sannan ta kyale ta ta shige daki Jamila kuwa sai da ta yanki uwar da aiketa fadama Atu magana buni buni ta shiga toilet sabida cikinta da ya rikice
12/10/2022 à 08:36 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*


14&15


Ita kuwa muguwar dariya  keta kawai take mata daga cikin daki sai da ta gama cin dariyarta sannan tafito ta kalli Jamila da har yanzu bata gama dawowa dai dai ba ta ce'' ina Inna ta ne .''

Habi ce dake shirin fitowa ta ce'' tafita tun dazun tatafi bayan gidan mai gari .''

Tabe baki ta yi, sannan tafice daga gidan .''


Tana fitowa ta wuce gidansu Hasiya lokacin Balki Batanan dan haka suka wuce wajen mai koko da kosai wajen cike yake da jama'a birjik suna ganin Atu ta Faso gari ai kuwa suka fara bata hanya daga masu gudu sai masu dan matsawa nesa da ita wajen mai koko ta ta zauna ta ce'' ke zuba min koko ni da kawata yunwa nake ji .''

Shiru mai koko ta yi, kamar Bata jin Atu ta ci gaba da Abin da take fuska a hade kamar bata taba dariya ba ,Hasiya ce ta ce'' Wai ba kiji a nan maki magana bane kin wani share mutane .''

Kinga Malama dan Allah tashi ki ban waje bazan iya Bada koko na ba ko ana dole .''

Murmushi mugunta ATU ta yi , ta ce'' To Alkur'an yanda bazan sha sa ba haka kowa ba ya rasa .'''

Tsaye ta mike tare da Karka mazaunanta dai dai so din koko ta buga masa wata iriyar Shaharariyar tusa sai ta saki biyar à take sannan ta mike tsaye ta ce'' Wai Alhamdulilah cuta tafita .''

Tun da mai koko ta saki baki tsabar kidimewa da rudewa hakan ya sa tafara Kuka tana fadi kasa tana birgima tana fadamin wayo wayoo wayo koko azo a sayi kokona Atu ta buga masa tusa , dariya Atu ta tintsire da ita ta ce'' ku sha koko me rai da lafiya sai anjima .''

Hannun Hasiya ta ja wace kanta ke juya mata tun lokacin da Atu tafara sakin tusarta ai kuwa mai koko ta biyo su sai Sun biya ta gudu suke shararawa ita ma tana biye da su sunyi gudu mai tsayi sai hutai take yi ganin fa wanan yarinyar ba fasa biyarsu zata yi ba hakan ya sa suka shiga gidansu Balki tare da kwanto karan gidansu ai kuwa mai koko bata Ankara ta ji Kare a bayanta yana zuba haushi Haba kafa me naci ban baki ba gudu take bankadawa shi kuma karan yana biye da ita .''


★★★★★

Marwane kuwa tun lokacin da Atu ta sakar masa tusa yake kwance gidan me gari dan ya kidime sosai har yafara sambatu tsabar tusar ta shige sa da kyau mai gari ya zata shafar Aljanun ce hakan ya sa ake ta bashi Rubutu ana masa addu'a ,sai da ya samu sati day sannan ya dawo garas dan haka mai gari ya ce'' su tatara su koma gida hakan kuwa Aka yi a hanyarsu ta komawa gida ne suka tsinkayi Atu da kawayenta su biyu suna kwasar dariya ga Kare Sun kwanto ma diyar mutane sakawa ya yi a tsayar da motar sannan yafito tare da nufa inda take tana ganinsa ta hade fuska shima tashi a murtike hakan ya sa ta sha jinin jikinta kallonta ya yi, ya ce'' ke wace iriyar dakikiya ce zaki sakar mata Kare idan ya cije fa .''

Kallon gefe da gefe ta shiga yi taga wai dawa yake magana ne ganin daga ita sai su Balki ya sa ta ce'' ku dakikai ana yi maku magana .''

Ai ba da su nake ba dake  nace yanzu Atu ya dace abin da kike yi kuwa wanan ai mugunta ce.''

Karka damu jana fada ta yi fa.''

Kina yar firit dake haka kike tsokana wai bama ki cin abinci ne .''

Sai da ta yi masa kallon nafika zama yar Iska sannan ta ce'' ai kuwa dai a haka nake tsone ma mutane Idanu sabida kullum gidanmu sai Sun kwashi ruwan jikina Sun yi girki ci nake amma baya fitowa kai harta sabulu ya rainani yana nan kwance a jiki daga na shiga wanka sai de nayi ta kwarara ruwa kumfa na fitowa .''

Ke karki raina min hankali .''

Ina yake na kamo shi dan kar na Raina shi .''

Hmm kaji da shi kin ga ni yanzu tafiya zan yi birni kuma bazan sake dawowa ba .''

To me yasa zaka tafi dan birni .''

Sabida tusar da kika min ta rikitani kamar mai kamun Aljanu shi yasa mai gari ya ce nayi tafiya ta .''

Haba dai ashe lafiya ce ta kara samuwa to a gaida mutanan birni .''

Insha Allah sai wata rana kuma zan yi missing din ki sosai Atu ina son wanan dramer taki sosai Falalu ya bani labarin ki kuma hakan ya yi matikar birgeni kalma day zan fadamaki shine I love you sannan insha Allah wata rana zan dawo gare ki .''

Jin yafadi kalmar Missing da I love you ya sa tafashe da dariya ta ce'' idan ma zagina kake ba komai nima I love you ba shikenan na rama ba .''

Murmushi ya yi, tare da girgiza kai ya ce'' sai wata Rana .''

Ba zaka karfi tusar ban kwana ba .''

Da sauri Falalu ya ja hannunsa suka bar wajen .''

★★★★★

Tsabar Sun kulleta ya sa ta mike tanufa daki ,kwancin ta keda huya Lantana ta shigo ta ce'' Ranki shi dade gani .''

Karanki nayi wai ke me yasa kike takura ni wallahi kika cika ni korarki zan yi a gidan nan .''

Kame baki ta yi, tare da daura hannunta saman kanta ta ce'' na shiga ukku na bani na lalace wayo Allah .''

Ke menene hakan Kuma ?"

Dan Allah karki mayar dani kauye idan na koma tuwon dawa da hatsi shine zan ta fama da shi ki tausaya min .''

Kuma shine kika takurawa rayuwa ta .''

Wallahi ba haka ba na zata kirana kika yi shi yasa .''

Naji je ki kawo min tea na sha .''

Hé hé hé Ashe ina da Rana .''

Filo ta dauko tare da biyo ta da shi ai kuwa zuba a guje tana fita ta rufe dakin tare da sauke ajiyar zuciya tana fizgar da Iska wai Allah fitinar Lantana ma ta isheka Riga da wando
12/10/2022 à 08:36 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

16&17

Ranar da ya shigo gari babu ko wutawa ya kira Yasmine tare da shaida mata an jima zai zo gidansu sosai ta ji dadi ita dai wanan mutumen yana birge ta sosai tana jin dadi muryansa idan suna Waya kamar karya katse .''

Wanka ta mike ta yi tare da daukar wanka Riga da wando jeans sun dan kame ta sai de ba sosai ba ta sha wanka turare dama ta saka Lantana ta hada masu abinci mai rai da lafiya sai da aka gyara dakin baki sai kamshi yake sannan Aka kai abubuwan tabawa Lantana ta baro dakin wajen Yasmine ta dawo ta ce'' Aunty hajiya Ranki shi dade na Kammalla komai .''

To sannunki da kokari .''

Wai yanzu da wanan shigar yan Iskan zaki tafi wajensa ni dai babu ruwana idan ya yi maki wanan ab.... Da sauri ta daga mata hannu ta ce'' ke banason shashanci fice daga daki .''

Juya mata baki ta yi, ta ce'' Haka Kika yi ko a School din nasan fice min daga daki fice daga daki ka dai kike rubutawa a Book din.''

Wata iriyar harara ta balla mata babu shiri tafice daga dakin suna karisowa ya yi kiranta ya shaida mata yana harabar gida da ok ta amsa sannan ta katse kiran Lantana ta Kira ta ce'' ki tafi bakon yana waje ki kai sa ma saukinsa ganina nan tafe .''

Aikin Banza sai ki yi korana amma kuma daga abu kadan ya taso Lantana ! Lantana je ki yi .''

Bata tankata ba ta katse kiran dan ta kula Lantana taga wajen baccinta .''

★★★★

A hanyarta ta komawa gida taga yan samari suna zaman fada sai tikar rake suke suna zantawa wajensu suka nufa ta ce'' Iro lafiya kwana biyu baka tafiya zance na jima bansha rake ba .''

Atu Ashe har yanzu kina Sona ai Abbas ne da Ashiru suka ce kada na sake tafiya wajenki tunda ke buddara ce .''

Karka ce kai ta yi, Irin na rashin mutumci tare da kashe idonta tana masu kallon zan ci uwarku ta ce'' Yanzu bani raken idan na gama sha akwaye labari .''


A'a Bismillah ga waje ku zauna .''

Babu musu suka zauna nan Balla mai rake ya yanka masu rake ita da kawayenta sai da Suka koshi dan kansu sannan Balki da Hasiya suka mike sabida sun sa labarin da zata bama su Iro ,kallonta ya yi, ya ce'' Atu sai ina kuma .''

Tambaya ko neman sani .''

Ko day kawai na damu da inda zaki tafi ne .''

Yanzu dai kaga bani da yan canji ka aramin idan na samu zan baka.''

Babu musu ya dauko jaka biyar ya Mika mata ya ce'' wanan su kadai a aljihuna bani ko ASI.''

To na tambaye ka ne .''

A'aa to me yasa kake fadamin .''

Dan karki ce in kara maki .''

To Sun wadatar shiknan ga Atu mayyar kudi ko .''

 Ba haka nake nufi ba fa,sannan ina labarin da zaki bani din.''

Sai da ta faki idanunsu sannan ta karkata kugu ta mayar dashi gefe guda ai kuwa tafara sakin bama bamai masu masifar kara da bala'in wari .''

A take duk suka zube a kasa Ashiru cewa ya ke wayoo Umma ta Allah ya isa wallahi .''

Iro kuwa fadin yake a kaini Rana Banason inuwa ku bani ruwan sanyi nasha zan mutu 

Abbas kuwa harshensa a waje ya yi suman kwance babu damar magana .''

Dabzar raken ta diba tare da tusa kowa a baki tana saké shekewa da dariya su Balki ma dariya suke Balla mai rake tun lokacin da aka sako ta farko ya saki rakensa ya yi gaba da gudu duk Wanda ya gane sa yana gudu sai yabi bayansa Haka ya samu mutane diyawa bai tsaya ko ina ba sai a Kofar gidansa sai huci yake sai a lokacin mutanan suka ce wai Balla me kake ma sharara ma gudu hakane .''

Atu buddara tana tsan ta somar da su Iro wajen da nake zama.''

Duk tsoki suka ja tare da juya wa Suka yi tafiyarsu shi kuma ya karisa shigewa gida .''

Suma su Balki sabida basu samu wantsan kamshi Al'ul din ba ya sa suna tafiya tana fadi dim dim chass sai ta bada burrrr farrr duk karar tusa ce haka suke daurewa Hasiya ta hango wani bisa Katanga tana leke ta nuna ma Atu murmushi ta yi ,ta ce'' oh yeah kuzo mutafi .''

Suna isa wajen dama kowa ya dauki kankaru ai suka fara aika masa jifat shedan suna sakin dariya a tare shi kuma mutumen sai kwarara ihu yake yana a taimake sa ganin ba fasa jifar zasu yi ba yaje saukowa daga katangar da yake tana da tsayi ai kuwa ji kake tummm garamm yafadi kasa sake kyalkacewa da dariya suka yi sannan suka zuba a guje sabida karya biyo su sunsha gudu sosai Sannan suka hango wani yana saman wani dan siririn Ice da alamar mai jego sai tsikoma ayi mata wanka jego da shi wajen icen suka karisa suka fara girgiza shi ai kuwa ya makale sosai amma basu fasa ba da karfi suke girgiza sa har mutuman yafadi ,kira yake ku taimaka min ni ba mahaukaci bane aikoni aka yi Sun cucuni wayo Allah bayana ya karye kafata ta goce ku kaini asubiti ,dariya suka ci gaba da yi masa sabida tsabar rudewa ce ta saka shi sambatun nan sauran abincin da ya ajiye suka dauka tare da watsa masa shi a fuska suka kwasa a guje kasa ta shi ya yi, bare ya biyo shi amma ya sha Alwashin wajen mai gari zai tafi .''

Sosai suka sha tsokana yau sun gaji dan haka Atu ta ce'' kun ga sai da safe Mangari ba ta gaba to ni nayi gida m mu rabu a nan .''

Cike da tsoro Balki ta ce'' idan su Iro suka tare mu fa .''

Hahaha ashe ku matsorata ne Muje sai Kubi ta kofar gidanmu .''

Suna tsaka da tafiya suka hango wani Kare kawai dan jan fada suka nufesa tare da taka wutsiyarsa ai kuwa Kare yayo kukan kura sai gantarama Atu cizo ta yi saurin watsa masa kasa Balki ma haka Hasiya ba Haka kafin ya warware suka zuba a guje kowa kansa ya sani .''


Suna isowa gida Atu ta ce'' ku ci gaba da gudu kafin ya iske ku dan wallhi ko gidanmu ba zaku shiga ba .''

Kamar su yi kuka sabida gudun da Suka sha yau haka suka sake kwasar wani suka yi gidajensu .''

Kare kuwa sai haushi yake yana birgima idanunsa duk cike da kasa .''

Tana shiga gidan babu kowa a tsakar gida har zata shiga daki ta ji ana rafka sallama har zata tafi sai ta tuna da Abin da Suka aikata ai kuwa ta shiga dakin ajiyar kaya ta rufe Inna ce ta fito tare da amsa sallama tafita waje yaran me gari ne suka zo neman Atu ,ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' hala tsokana ta yi,.''

Kwarai dagaske har su uku ma wallahi mai gari ya kamata sai ya yi dambunta a garin nan .''

Ai Bata dawo gida ba Tun dazun tafita .''

Idan ta dawo ki bata sako .''

Atu kuwa tana cikin wanan dakin sai sharara zufa take tana goge wata wani na sake zubowa jikinta sai rawa yake .''
12/10/2022 à 08:36 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*


18&19


Cikinta ne ya yi mata wata iriyar juyawa ai kuwa tuni tafasa ihu tana Kiran sunnan Inna dake shirin shiga daki taji ihun Atu da sauri ta shiga dakin ganin ta dafe cikinta ya sa ta ce'' Atu lafiya me ya faru ?"

Hankalina a tashe yake fadamin mutanan Sun tafi sai na Sanar dake abin da yake damuna .''

Murmushi Inna ta yi , ta ce'' dama nan kika buya tun da kun yi tsokana ba .''

Dan Allah fadamin me mutanan suka fadamaki ne .''

Sun zo su tafi dake mai gari ya aiko su wai kun karya ma wani mutume baya sannan kuka watsa masa abinci .''

Cikinta yakara juyawa ai kuwa ya saki wata iriyar kara sabida tsabar firgice ji kake kurrrrr sai ga lafiyayar tusa ta sanyo Kai tana sakin tusar cikinta ya daina ciwo ta ce'' Alhamdulilah barin cuta a ciki babban tashin hankali .''

Kallon Inna ta yi dake dafe da hanci ta ce'' bara na tafi wajen me garin naji da wata uwar suka tawo Nifa na zata wani Abun Ashe wanan karamar matsalar ce bara na kira yayana mu tafi tare .''

Mikewa ta yi, tare da fitowa ta.fada toilet ta yi wanka ta shirya tsaf sannan tafara dukan dakin Habi tafara kwadama Lawan kira .''

Da sauri yafito ya ce'' kanwata lafiya dai waye ya tabamin ke naga duk fuskanki a hade .''

Tsokana nayi fa shine mai gari yake nema na.''

Mtsss jirani na dauko rigata mutafi karki damu .''

Dakin ya koma babu jimawa yafito tare da jan hannunta suka dauki hanya zuwa gidan me gari dama Tuni har an kai su Balki sai tambayarsu ake Sun ki suyi magana sabida Sun san idan Atu tazo magana ta kare.''

Suna isowa Balki da Hasiya suka saka shewar dadi tare da fadin mu munfi karfi ayi mana iskanci a garin nan wallahi sannu da zuwa uwar dakinmu Atu ta kowa idan kaki kuma ta yi ma rashin mutumci.''

Da sauri mai gari ya daka masu tsawa ya ce'' A'a to to dama ashe kuna magana mune kuka dauka yan Iska din.''

Zaune Atu ta yi , tare da hade fuska ta ce'' Lafiya ake nema na .''

Ke bamusan rashin kunya miye hadinku da wanan mutumen da kuka kada shi daga saman ice.''

Ka tambaya sa mana .''

Bamusan shashanci to tun da hakane zaki biya sa tarar jaka talatin kuma ta zauna .''

Dariya ta tintsire da ita sannan kuma tafashe da Kuka tana harba kafafunta da sauri mai gari ya ce'' kai Lawan kashe wutar kanwarta ka karta ta'azara .''

Hannunta ya kamo tare da murza dan yatsanta gudu shikenan ta yi duf tare da mikewa tsaye ta Sakarma kawayenta Murmushi Sun san me zata yi dan haka suka nufi bayan me gari Balki ta rike kunne guda itama Hasiya Haka ita kuma Atu ta taka kafarsa sannan tafara Kukan mashine burr burum su kuma suna murda kunnansa tare da jansa wai Sun mayar da shi mashin ihu yake babu wanda ya kawo masu dauki yana tsaka da wanan ihun Atu ta takarkare ta bumsuma ma masa rangadediyar tusa tafi a kirga sannan suka saka ma kowa kaikayi sannan suka wanka da gudu .''

Mai gari yana a Sosa fadawa suna a Sosa daga ana cikin Sosa ma mai gari daga na fadawansa sun motsa sai Sun ce wayo a Sosa asosa Sun dan yi nisa sannan suka tsaya suna masu dariya ganin duk Sun rikice ya sa su koma kowa rike da biredi a hannunta daga mashin din su suka koma murdan kunnen me gari daga ya Budé baki zai iya ihu sai Atu hahaha biredi zaka ci sai ta jefa masu cikin baki Lawan tsabar dariya har faduwa ya yi kasa daga Sun murda masa kunne yafasa kara sai ta ce'' hahahaha biredi zaka ci tana yi tana sankama masa da tusa sai da Suka yi dan kansu sannan suka baro wajen mai gari yafi kowa galabaita wanan tusosun da Atu ta yi , ta antaya masa suka kara kumbra masa da ciki shima ya shiga sakin tasa tusar daga ya motsa sai ya saki burrr duk motse gudu Yana da tusa biyu ,a hanya a Atu ta ce'' Allah kuyi ta kanku sabida mai gari yana watsakewa mun shiga tamanin .''

Dariya suka kuma saki sannan Balki ta ce'' wanan aikin kuma nawa ne dan kwal ubansa sai ya shafamana lafiya ko bai ma Allah .''

Kashewa suka yi sannan Lawan ya ce'' Idan ma idée din ku ta Kare kumin magana kera kudi Muke da zasu ce mu basa jaka talatin satarsu zamu yi .''

Sosai suke tautaunawa bisa kan yanda zasu billo ma mai gari .''

Washegari kamar yanda ta saba sai da ta yi alwala sannan tafara dukan kofar su Jamila babu shiri duk suka fito Lawan da Nura Sun tafi Masallaci ganin Habi bata fito ba ya sa ATU bin bayanta ganin tana kirga kudi masu uban yawa ya sa ATU lalafawa a hankali ta kwato kudi da sauri Habi ta tsora ta duk a tunaninta Lawan ne sai taga Atu da Sauri ta ce'' ke ban kudi na.''

Tab idan kin isa uwata bazan bayar ba.''

Fitowa ta yi, tare da kwalama kowa kira Jamila idon kudi tana gani ta ce'' A'a Atu daga ina kike da wanan kudin .''

Dakin wanan munafukar dama kwana biyu bamuci kaza ba yau zamu ci shinkafa da miyar kazaaaa taja maganar tana yatsine fuska ta ce'' ke Jamila zo ki mana cefane sannan idan miyar nan Bata yi dadi ba Alkur'an wanka zan yi maki da ita .''

Haka Habi tana ji tana gani Jamila tana gama sallah tafita kasuwa Aka yi cefane sannan suka yi lafiyayen girki mai dadi suka zuba ita da Inna Atu sai Jamila Lawan da kuma Nura amma suka hanama Habi kamar bakinciki zai kashe ta ganin fa da gaske ba Bata zasu yi yasa tatafi tsakiyar su Inna ta zauna da sauri Atu ta ce'' Habii lafiya kika zauna anan .''

Nima ci zan yi mana ko kalaci ban yi ba sannan da kudina ace bazan lasa ba .''

Sosai suka buga Loma ya yi sauran dan kadan Atu ta yi tsaraf da kafar kaza Inna ma haka Jamila Haka ya yi sauran babu komai a ciki sai sauran abinci Habi kuwa dauke plate din ta yi , ta koma gefe .''

Sai da ta yagi kaza sannan ta ce'' ke Habi lafiya Zaki daukar masa abinci .''

Kudinki ne ko nawa .''

Ohoo dai musha rabaje kudin matar Yayana ce .''

Mtss aikin Banza .''

Menene banza shinkafa Banza mijinki Banza kema Banza .''

Nice Banza to kema Banza ce .''

Barauciyar kudi Allah ya Toni asirinki .''

Ni ce barauciyar a hasale ta mike tare da buga ma Atu Plate din ta yi cikin daki da gudu .''

Dariya suka tintsire da ita sannan Atu ta ce'' munci shinfaka da kudin wata min hada da kaza da kudin wata kuma zamu hauda da lemon kwalba su Oh ho sai de haushi .''

Babu yanda Habi ta iya ta shige daki tana Kuka tana kiran kudi Sun tafi shikenan Sun suntseni kudi sosai take kwarara ihu babu abin da suke yi mata sai dariya .''

Da yamma kuwa Haka suka saké girka abinci ko lashe Habi bata yi ba suna tsaka da hakane mai gari yafado cikin gidan tare da mutanansa an sake Kamo su Balki Atu na ganinsu ta mike tsaye ta ce'' kun ji kanshin miya shine ka wani shigo ma mutane gida sabida a sammaka ko to wallahi kwalele .''

Wallhi idan baki man shiru ba zan sharara maki mari .''

Da sauri ta dafe kuncinta ta ce'' Mari a yeeehh huuu sai bayan sati biyu.''

Kai ku kama mani ita .''

Ganinfa da gaske tunkaro ta suke kuma idan Sun kamata a mari zasu sakata da sauri ta yi kasa tare da fara ma mai gari kirari tana kida katon budo dake gabanta ai Tuni yafara rawa har dasu juyawa yana karya kugu sai da ta shagalar da shi sannan ta  kashe ma Lawan Idanu ya tafi ya debo masu ruwa ya kawo masu tsaida kidan ta yi ta ce'' wanan babbar ziyarar da mai gari ya kawo mana ya kamata ya sha ruwa sai mu tafi ko sabida ta kwaso tafiya .''

Washe baki ya yi har kuda suna biya ya ce'' hihihi haka shine ya dace kaga yarinya mai hankali .''

Zaune suka yi duk aka zuba masu ruwa suka sha har da su fadin ruwan da dadi suke fa .''

Murmushi ta yi , ta ce'' ruwa ne kadai babu komai fa .''

A'a wallahi da dadi suke kara min .''

Haka sukayi ta zuba masu ruwa sai da Suka shanye su tass ai kuwa nan ciki yafara murdawa da sauri suka tashi dafe da ciki shi mai gari dauriya ya yi , bayason fadawansa Susan yana jin zawo su kuma sai murda ciki suke wani Irin Juyin waina cikin mai gari ya yi , da sauri ya ce'' kai Haba ina wallahi zawo nake ji .''

Kafin ya kai kofa har ya cika wandonsa da zawo hakama fadawansa da gudu suka fice daga gidan .''

Atu da Lawan sai su Hasiya suka yi tafi sannan suka fara sambada dariya , Nura ne ya kallesu ya ce'' me kuka yi masu n .''

Tana cikin dariya hannunta rike da cikinta ta ce'' abar bala'i ya yi sleep yaya .''

Nabi bala'in da gudu ba takalmi me kuka yi masu ne .''

Maganin zawo muka fara saka masu .''

Daga zaunan da yake ya bingire tare da fashewa da dariya ya ce'' A'a mai gari da zawo jama'arsa da zawo Allah Sarki har Sun ban tausayi .''

Inna kuwa girgiza kai ta yi , ta ce'' yau gani ga gidan yan Iska duk n'a tarasu babu day na gari daga Mazan har matan .''

Tana gama fadan hakan ta shige daki .''
12/10/2022 à 08:39 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

20&21

Nura ya ce'' kai Jama'a sigari haraka wiwi kuma duniya ce amma wanan yaran kun iya iskanci wallahi .''

Wanan maganar da ya yi ya kawo ma Atu idée ta saki murmushi ta ce'' saura shirinmu na gaba.''

Wato dai ba zaku daina wahalar da tsowon mutane ba ,cewar Nura .''

Idan yafasa ya ci uwarsa yanda bazai rabu damu ba haka shima Bamu rabuwa da shi .''

Mikewa su Hasiya suka yi suka ce Atu ina ga zamu tafi yamma ta yi ,sosai .''

Gaskiya dai kam bara na zuba maku abinci mu ci sabida yau miyar kifi zamu shashafa hhh abin ka da ba sabon ba .''

Washe baki Hasiya ta yi ,ta ce'' kamar kinsan shigiyar yunwa Irin sosai din nan .''

 To yanzu Zaki kwashi girki na kudin Banza .''

Zaune suka yi ta saka Jamila ta zuba masu abinci suka kwashi girki sannan suka hauda da ruwa ta yi masu rakiya suka tafi gida.''

Ke yanzu Hasiya daga ina kike ne .''

Daga gidansu su Atu .''

Ban raba ki da wanan marar kunyar yarinya ba amma shine Kika yi kunnen uwar shegu dani Kika watsar bakin hanya ko .''

Turo baki ta yi, ta ce'' wallahi Mama karki kuskura ta ji ki ni babu ruwana tohhh .''

Iyeeehhh kema ta baki kason Nata na rainin wayo wallahi ta saki ta zo gidan nan da kafa day zata fita .''

Mikewa ta yi, daga zaunan da take ta ce'' ni dai babu ruwana Idanuna kallo ne nasu dan ko raba ku bazan yi .''

Tana gama fadan haka ta shige daki tabar Mama saki da baki .''

★★★★

Da sallama ta shiga falon nan suka amsa shida abokinsa Bayan Sun gaisa ta zauna tare da fadin Malam Marwane ya hanya kuma .''

Tom alhamdulilah Allah ya yi nufi min shigo garinku lfiya .''

Ashe kun karisa bikin .''

A'a sai ana saura kwana biyu zan koma sabida wata yarinya na hadu da ita ,hade fuska ta yi, tun kafin taji me zai fada kallonta ya yi ya ce'' lafiya dai ko .''

Kankaro murmushin yake ta yi , ta ce'' uhm babu komai ya sunnanta .''

Marfu'atu sunnanta to yarinya bata ji ko kadan nan ya kwashe labarin komai ya Bata .''

Wata iriyar dariya ta gagafe da ita har da su rike ciki ta ce'' lanle ka ce kasha turaren Al'ul mai dadin kamshi gaskiya kwara da mai gari ya koro ka tun kafin a saké na biyu .''

Ohh dariya ma zaki man ko.''

Ba haka bane wallahi yanayin yarinyar ne ya min kama da Lantana sai de ita bata tusa amma akwaye kulle mutume wai dama duk yan kauye Haka suke .''

Hau haba kice kuna da Atu ta biyu kuma .''

Hmm a yanzun ma saura kiris ta batamin rai sai da na kora ta ..'

Kwara dai sabida yanda wanan kyakyawar fuskan ta sha kwaliya bazan so ganinta cikin bacin rai ba .''

Murmushi ta yi ta ce'' Abokinmu baka magana tun da kuka shigo baka ce komai sai labarin daya baka ya sakaka dariya.''

Azumin magana nake .''

Hhhh wanan lokacin kuma ai kwara kayi buda baki .''

Haba dai barni na ci gaba .''

To ai ya Riga da ya karye sai de wani .''

Kuma fa hakane .''

Sosai suka sha fira nan ta yi masu tayin abinci suka ci suka sha sai bayan sallah Mangariba suka tafi bayan Sun gaisa da momy Lantana da tatafi kwaso kayan abinci sai ta kwaikwaye kashin da Suka Bari sai da ta yi nake sannan tafito tana zuba masifa har ta kariso falon Momy ta ce'' ke lafiya kike ta zuba kamar an kunna radio .''

Hmm Momy wanan mutanan ne fa wai Sun kama komai sun tsanye su ga dangin mayu .''

Harara Yasmine ta d'Allah mata ta ce'' basu komai ba Momy yanzu haka ita ce ta cinye sa Kenan kece dagin mayun.''

Kaji jan shairi sai de idan Aljanu ke cikin dakin .''

Aljanu masu bakin tauna da kwadayi ba .''

Sosa keya ta yi tare da mikewa ta nufi kithchen da kayan Yasmine ta mike tare da biyan bayanta ganin ta baje a kasa tana sake aikama cikinta abinci ya sa Yasmine ta ce'' su acici mala'ikun tauna me kike yi a yanzu .''

Turo baki gaba ta yi , ta ce'' wanan matar Allah ya zuba maki sa'ido to bani ke ci ba Aljanuna ne .''

Hakane naga alama .''

Tana gama fadan haka ta dawo falo.''

★★★★★

Suna isa gida kai tsaye part din sa ya wuce ya saké watsa ruwa tare da kayan shan iska ya kwanta kan gado yana tunanin kyakyawar face din Atu da yanda take murmushi a natsu idan zata yi mugunta cikin wayo da dubara take yin ta Murmushi ya yi, ya ce'' ina sonki kuma Insha Allah sai na mallake ki a matsayin Matata Sosai yake tunaninta musanman lokacin da suke yin ban kwana da ta furta masa kalmar I love you gskiya zai yi anfani da sakarcinta har ya nemi sabo da ita jin ana kiran icha'i y sa mikewa ya zura jallabiya ya tafi masallaci yana dawowa ya wuce part din su Mama.''


★★★★★

Mai gari kuwa sai fama yake da murdawan ciki yau ko zaman shugabanci babu wanda yafito sabida suna fita daga gidansu Atu kowa hanyar gidansa ya kama hunin ranar nan haka mai gari ya kare da zawo duk yafita hayacinsa .''

BAYAN SATI 1

Zaune suke a fada suna tautauna yanda zasu kora su Atu daga gari wasu suce a kyalesu wasu kuma su ce a kore su dan Haka mai gari ya saka a Kira masa yan gidansu Atu da kawayenta Haka ko akayi duk suka halara nan mai gari yafara jawabi Atu najin zancen kora ta mike tsaye ta ce''' kai mai gari haka zamu yi da kai jiya nan fa ka kirani na tafi gidanka ka ce min idan na amince zaka min dukan abin da nake so shine da ka gama cin moriyar ganga shine zaka yada koranta .''

Saki da baki yake kallonta tun da tafara magana ya ce'' yaushe muka yi kiji tsoron Allah.''

Dama ai ba kai nake tsoro ba ku dan Allah ba haka Aka yi ba .''

Hakane har Liman sai da ya ce'' yana Sona ,cewar Hasiya.''

Kaji yara Yan shairi .''

Fashewa da kuka Atu ta yi ta ce'' wallahi baka isa ba sai na tafi gidan radio na fadamasu dukan abin da kamin sunnanka ya jima bai bace ba mudan ka kora mu daga wanan garin.''

To to to naji kuyi zamanku amma no tsokana .''

Idan an Jani koma wanene Alkur'an bazan daga masa kafa ba .''

Idan hankalin me gari yafi dubu to ya tashi kyauta kawai ya shafama yaran nan lafiya tun kafin sauran mutumcinsa ya karisa watsewa a idanun mutane .''

Ana gama magana kowa ya watse suka yi gida a hanya kuma Mamar Hasiya sai bala'i take zubawa har suka kariso kofar gidansu Atu har zata shiga ta dawo ta ce'' ke Hasiya ki ma wanan BBC din magana ta rage zuba kamar ruwa Allah Karta kulleni mantawa zan yi da ita ko wacece wajenki sai de abotarmu ta lalace.''

Tana gama fadan haka ta shige gida .''

Mama kuwa bata kuma magana ba sabida lamarin Atu yana bata mamaki sosai .''

Yau ta kama juma'a yau ne Marwane zai shigo garinsu Atu sabida ranar Asabar ake bikin suna shigowa gari dama akwaye wani hadaden gida da akayi wanda Jabir ango zai zauna a amaryarsa sabida yana aiki koyarwa a kauyen kuma a nan aka yi masa transfere shi yasa ya gida gidansa ya saka komai Harta da kayan kallo duk akwaye to a bayan gidansu Atu yake tun da taga wanan hadaden gidan kullum sai ta yi, addu'a Allah ya sa mai gidan ya zama mijinta za'aga rashin mutumci da ruwa ruwansa Haka suka yi ta hidima inda duk rabin hankalinsa yana kan Atu ta ina zai fara ganin har su hadu tunowa ya yi da Falalu ya Santa kasa jurewa ya yi ,ya ce'' Falalu ina ne gidansu Atu .''

Me zaka yi a tsan din .''

Ina son zamu yi magana da ita ne ka taimaka ka kaini.''

Kaga dai yanzu muna aikin kula da baki kayi hakuri zuwa yamma ko.''

Haba Idanuna suna son ganin abincinsu yau kimanin sati day Kenan ban sakata a idanuna ka taimaka .''

Girgiza kai ya yi ,ya ce'' Allah ya sa tana gidan sabida shegen yaro da neman rigima Irin tata shi yasa Bana shiga harakarta sabida idan ka tsokane ta sai fa ta rama babu wanda take daga ma kafa .''

To sannunka da kokari tashi mu tafi .''

Babu yanda ya iya haka ya mike suka tafi suna isa kofar gidan ita kuma tayo tsokana bata kula ba kawai tafada jikinsa da yake shima bai Ankara ba ai kuwa suka fadi kasa tana samansa gashin kanta ya rufe masa fuska dan karamin bakinta pink saman goshinsa hannunsa ya dago tare da janye gashin a hankali suna aikama junansu da kallo so Sun dauki lokaci a hakan sannan ya yi gyaran murya sai a lokacin ta dawo hayacinta ta mike tsaye da sauri jiki a sanyaye wata kunyarsa ce ta kamata a take ta dukar da kanta kasa tana wasa da yatsan hannunta ,wata naunauyar ajiyar zuciya ya sauke ya ce'' Marfu'at barka da yamma.''

Da karfi gabanta yafadi ta kara sunkuyar da kai ta ce'' kayi hakuri dazun Kare ne ya biyoni shine nake gudu har na buge ka .''

Karki damu babu abin da ya yi maki dai ko.''

Cikin sanyin murya ta ce'' Bai min komai ba kayi hakuri.''

Babu komai yakk ,'' lafiya lau harka dawo .''

E'ee yau na shigo shine nace nazo na ganki ko Zaki kara cemin I love you.''

Murmushi ta yi , ta ce'' dan Allah menene haka .''

Zan fadamaki amma sai ranan da zan yi tafiya ta .''

Bata damu ba dan Haka ta ce'' Babu damuwa Allah ya kaimu .''

Zaki zo bikin ko .''

A'a ,'' me yasa to?"

Sabida idan aka batamin rai zan iyayin komai dan haka asha biki lafiya fatan Zaman lfy da ango da kuma amarya .''

Amin muna godiya .''

Babu komai tafada tana shirin shiga gida ya yi saurin cewa baki ji ba .''

Tsayawa ta yi, tana kallonsa , ajiyar zuciya ya sauke tafi sau ashirin ya ce'' dama wajenki nazo ina son zamu yi magana ta fahimta sharadi Banason kiyi magana har sai na karisa sannan banda tusa bare shashanci.''

Tom naji Allah ya sa muji Alkairi .''

Marfu'atu dama ni bako ne amma ba ko ina ba sai a zuciyarki zuciya ta ta yi min mumunan kamu bisa kan kaunarki .''

Kallon baka da hankali ta yi masu tare da daukan dan dariya ta ce'' lanle baka da hankali sai yau na tabbatar to Allah ya sawake maka abin da yake damuka ni kaga tafiya ta .''

Har ta juya ta tsinci muryansa yana fadin tabbas ni mahaukaci ne amma a soyayyarki Atu wata Rana Zaki fahimci Irin yanda nake ji a kanki ,Zaki fahimci gaskiya mafarkin da nake yi a wane dare sannan kuma zaki fahimci Irin matsanancin son da nake yi maki a zahiri amma a lokacin zai zamo babu wata sauran dama da ta rage a tsakanina dake babu komai na gode ni dai ina sonki har abada .''

Turo baki ta yi ,tare da fadin naji sai an jima ni yunwa nake ji .''

Tana gama fadan haka ta shige gida jiki ba kwari suka juya suka bar kofar gidan .''
12/10/2022 à 08:39 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

22&23


A hanya kuwa Falalu ya ce'' To yanzu miye anfanin haka katafi amma babu biyan bukata yarinyar da kafi karfi ta dauke ka awon igiya .''

Babu komai ni ko Haka ya wadatar tun da nagani farinciki rayuwa ta wallahi ina masifar son yarinyar nan .''

Tom Allah ya yayemaka abin da yake damunka kamar yanda tafada .''

Kaga yanzu ni bani bukatar dogon surutu .''

Shiru ne ya ratsa su Haka suka ci gaba da tafiya babu mai magana har suka karisa .''

Atu na shiga gida tafasa Kuka da sauri Lawan yafito ya ce'' ke lafiya waye ya taba ki.''

Cikin kukan munafurci ta ce'' Ashiru abokin Iro ya mareni tare da sako mani kare saura kiris ya cije ni nayi gudun famfalaki na guje masa.''

Wani kukan kura ya yi, tabb ashe za'ayi bila'i a garin nan me kika yi masa ne .''

Wai dan nace banason Iro shi yasa  .''

Rabu da shi yau zan ci uwarsa .''

Murmushin mugunta ta yi , ta ce'' yawa Yayana idan ina gabanka ni ba kowa ba ce .''

Kai Lawan ka kuskura ka daki yaron nan sai na Saba maka .''

Inna auta fa ya daka shine zaki hana na rama mata .''

E'eee ai nasan duk ta kare ita ce tafara tsokanarsa zuba mata Idanu zasu yi tana iskancin da taga dama a gari harta mai gari bata ragama ba.''

Haba Inna miye haka tun da ke ba zaki shigar min fada ba shine zaki hana .''

E'eee din na hana kada na kuskura naji hakan.''

A hankali tafara yi masa kus kus ta ce'' Yaya anya Inna Bata sha wani abun ba yau ta rude abin ba mutumci .''

Dariya ya fashe da ita ya ce'' ko dai Yaya Nura ya bata wiwi tun da ya ce duniya ce .''

Gaskiya tafara gila ta sosai muyi ta kanmu karta duka.''

Gulmar me kuka yi ne ..'

Gaskiya Inna kina takura mu wanan sa'ido har ina Nifa ba tsoronki nake dan haka go daki kona hada ki da masuburbudar wari na .''

Ai ba shiri Inna ta yi hanyar daki ta ce'' ban shirya zuwa asubiti ba .''

Saké kwashewa da dariya suka yi sannan Lawan yafada mata kalar muguntar da zata ta rama dukan da Ashiru ya yi mata .''

Jinjina kai ta yi ,alamar gamsuwa dakinsu ya koma ita kuma ta yi waje sai kofar gidansu Balki tana shiga Kaka tana waje gaishe ta ta yi , tare da tambayar ina Balki take .''

Tana daki yanzun ta shiga .''

Tom Kaka bara nazo na tayaki aiki .''

Atu ni ba wanan aikin nake so ba dan Allah ku daina tsokana kinji sosai ta yi mata nasiha amma Atu saurarenta kawai take idan ta shiga ta kunnen dama sai ta fita ta hagu tana kammalla yi mata nasihar kamar ta dauka ta ce'' Tom insha Allah Kaka ba zamu kuma ba bara na wuce dakin Balki na gode sosai .''

Yawa Allah ya yi maki Albarka .''

Amiiiin kakuss dinmu .''

Ohh Allah ni Indo yau naga abu Allah ya shirya mana ku yaran nan .''

Tana shiga nan ta labarta ma Balki abin ya faru shewar dadi suka yi sannan suka taba fitowa suka yi suka nufi gidansu Hasiya ai kuwa Sun ci sa'a zata fito nan suka hade wani kwango suka nufa inda ke da majijiya( wanan jan cinnaka  nan suka Kamo mai yawa suka zuba a leda sannan suka nufi majalisar su Iro ,Ashiru yana ganinsu ya mike tsaye ya ce'' gani nasan ni kika zo nema Kika kuma buga mana tusa sai na dame maki kunnun kubewa a a kwakwalwarki .''

Ladabi ta yi wanda hausawa suka fadi fadin ladabin kunama ta ce'' haba mana Ashiru hakuri nazo baku fa shine zaka rufeni da masifa .''

Cike da kasaita yana aza doro ya ce'' kun ga nayi maganinta ko .''

Idanu Atu ta kashe ma Balki ai kuwa tabi ta bayan su Iro tare da sakawa kowa majijiyar ai a take ta lake a jikinsu nan suka fara ihu daga gefe suka koma suka fara antaya dariya sannan Atu ta ce'' su Ashiru manya an fadamaka ana taba Atu a kwana lafiya yanda ka sakani Kuka da gudun famfalaki kaima gashi na rama .''

Kashewa suka yi tare da kawayenta ji kake ramm sannan a tare suka furta babban magana kato hannun mata sai ga su Iro da Kuka .''

Kamar wanda aka sakama kaikayi sannan suka yi kirtan fatarsu ita kuma majijiyar sai tsalarsu take tako ina Kuka suke tsakaninsu da Allah babu mai taimakon wani ga zafi haka haka yakarama wajen zafi sosai Haka suka fara cire kayansu daga su sai culotte ( karamin wando) suka ci gaba da Susa su kuma uwayen muguntar suka juya tare da tafiyarsu zuciyarsu fess cike da murna suka rabu .''


Gani zasu halaka kansu a banza nan suka watse Kuka nufi hanyar gida Ashiru yana isa ya fada toilet yana zubawa jikinsa ruwa ai kuwa wani bala'in zafi ya rufe sa da karfi yafasa kara wanda hakan ya janyo hankalin yan gidansu ihu yake kwarara yana a miko masu soson karfe babu shiri ya fito waje da gudu ina tsale yana ihu kamar ba namiji ba .''

Iro kuwa yana shiga Yana fadi kasa yana kowa yafito ku Sosa min wayoo ku Sosa min dan yayan Iro da yaga abin da ke faruwa ya ce'' la kawu yafadi kasa yana dariya yana kwaiwayon yanda yake yi yana kara kecewa da dariya duk abin da ya yi sai ya biya masa .''


Abbas kuma tun daga kofar gidan ya mayar da asosa waka yana yi yana rawa .''


A hanyarsu ta komawa gida Atu ta ce'' na manta ban baku labari ba tsabar Raina a bace yake .''

Tom a yanzun fa ?"

Ya yi fari fesss tun da na rama .''

To Bamu labari musha .''

Wanan saurayin da nayi ma tusa a bakin ruwa yazo gidanmu fa .''

Haba me ya fadamaki ne .''

Wasu Irin masifafun dadaden kalamai ne wai yana Sona .''

To me kike jira kema ki so shi mana .''

An fadamaki bani da aji ne kodan ina yar kauye ba wanan maganar sai na gilasa sannan zan yarda amma kalaman Sun tafi da zuciya ta babu wanda ya iya soyayya kamar shi muryansa ma abar dubawa ce ga kyau wace zata ce bata son shi Nifa tun ranan haduwa ta da shi na kamu sosai .''

Munafuka Ashe ana so ana kaiwa kasuwa ne tom Allah idan baki saurin amincewa ba idan har ya ce yana Sona tsaf zan bada kai bori ya hau .''

Wallhi da nayi kwallo dake har sai na mayar dake agwaluma .''

Dariya suka fashe da ita sannan Balki ta ce'' Atu kishi ko wanan akwaye aiki duk ranan da taga saurayin nan da budurwa .''

Tab uwarta zan ci babu wani daga kafa ranan koni ko ita .''

Allah ya shirya ki .''

Ai bani kadai nake bukatar shiriyar ba harda ku .''

Yanzu ya kamata mu tafi gida kin ga ni Mama bata san nafito ba fa.''

Ya kamata kam dama yamma ta yi kar ayi mana fada cewar Atu .''

Haka suka watsa kowa tabi hanyar gidansu .''

★★★★★

Zaune ta yi tare da fadin Momy wai yaushe yaya Irfane zai dawo wanan jarabation din ta dameni .''

Tun da ta dameki ki dame ta kema .''

Dama Momy kice kike daure mata kugu tana rainani Allah wata rana farfesunta zan yi .''

Kira shi kiji yaushe zai dawo nima ta fitine ni da fitinarta wallahi .''


Habibi nurulqalbi sahibi zai dawo rawa rawa ,Haka tafito tana taka rawa tare da waka tana murna sosai ta ce'' Malama Aunty Hajiya Ranki shi dade gaskiya ke din ta dabance tafada tare da rumgume ta .''

Kamar zata kurma ihu tsabar takaici ta ce'' ke wai baki da ta idone a gaban surukar taki kike wanan shashanci a haka yaya Irfane din zai aure ki .''

Dafe kai ta yi,duka da hannayenta biyu ta ce'' kashh kaji tsiyar Kenan Allah ya zuba min mantuwa .''

Baki manta soyayya sai surukarki .''

Kin ga karki ja min shairi bafa Haka nake nufi ba .''

To koromin bayani naji .''

Dama mantawa ne nayi shi yasa nayi rawar sabida sahibul qalbi zai dawo .''

Idan ya dawo zaki gani kurenki kwara ma ya dawo mu huta da fitinarki .''

Tabe baki ta yi, ta ce'' Lantana ta zama kwali ta zama ciwon da kai har da na hanji babu wanda ya tsone maki Idanu a gidan nan sai ki day ina shirin zama Auntynki.''

Allah zan kwada maki tafi idan baki fice min da gani ba ba dai Aunty ba aunto .''

Ohoo dai yawa Momy me za'a dafa ne .''

Lantana Kona fada ai yi zaki yi ki tafi ki mana abinci mai dadi kawai .''

Sannan banda shirme dan Allah yau Habibinki zai dawo , cewar Yasmine.''

Ehooo dadi kasheni in dawo bara na gudu kithchen na hada abinci na musanman .''

Tana gama fadan haka ta yi kithchen a guje .''

Me yasa kika fadamata hakan.''

Sabida yau zan ci girkinta da yafi na kullum dadi .''

Allah ya shirya mani ku musanman Lantana.''

Tana shiga kithchen tafara hada girki kala daban daban masu shegen dadi ga kanshi dake tashi ta jera a danning ranan harda drink ta hada kala uku sannan tafito ta je ta rangada wanka tafito falo kallon juna suka yi tare da tsintsirewa da dariya ,turo baki ta yi, ta ce'' lafiya kuke min dariya kuma ko banyi kyau ba.''

Irin wanan haduwa ai ko kasar larabawa sai hakan  kin Kammalla girkin .''

E'eee ina Habibi nawa yake .''

Yana hanya Sun kusa karisowa ni kinga yunwa nake ji bara na rage masa dadi .''

Mikewa Yasmine ta yi , ita da Momy suka nufi danning tare da fara kwasar girki tabbas abincin yafi na kullum dadi sabida kawai na tafi yan jaraba take yi masu amma wanan kuma sai de Masha Allah .''

Sai da Suka koshi sosai Sannan Yasmine ta mike ta ce'' Yanzu ya kamata nayi wanka bacci mai dadi ya yi gaba dani .''

To Nurulqalbi zai dawo shine zaki yi bacci .''

Hhhhh ai da wasa nake maki yaushe rabon ki mana Irin wanan dadaden girkin tun Shekara biyu da Suka wuce lokacin tafiyar Yaya Kenan .''

Kenan dama kema kin iya wanan abar ko.''

Hade fuska ta yi , ta ce'' me na iya kuma .''

Ina nufin karya mana.''

Lanle Lantana yau zaki kwashi kashinki a hannu ni zaki ce ma ina karya
12/10/2022 à 08:40 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*


24&25

Zagaye falon suka shiga duk Sun hargitse wajen tsabar yanda Yasmine ta hasala ta ce'' ke zo nan tun kafin Raina ya bace .''


Allah ya banzo ki daka ni a turmi ba Tun ban ga aure na da Malam zalumu ba .''


To zan ga ta yanda za'ayi ya aure ki sabida sai na amince zai zaba budurwan da ta yi mani sannan zai yi aure a hakan zai aure ki baki min ladabi.''

Tana jin haka ta durkusa har kasa sai ka ce dagaske sabida yanda ta yi ladabi tare da sunkuyar da kai ta ce'' Kanwar mijina na ce dan Allah ki yarda Yaya Irfane ya aure ni .''

Har ga Allah Yasmine ta dauka dagaske Lantana take ,yatsine  fuska ta yi , ta ce'' ba fa zan yarda ya aure ki ba.''

Tsaye ta mike tare da yin dariya ta ce'' ke idan aka ce maka Lantana ta yi hakan ko a mafarki zaki yarda Kenan hmm idan yatafi neman aure na ki Hana sa .''

Tsabar ta kulle ta ta dauko filo bata Ankara ba ta jefe ta da shi ai kuwa a guje ta yi waje tana yi mata dariyar keta ta shige daki .''

Momy ta ce'' idan baki hankali da wanan yarinyar ba Allah sai hawon jini ya kamaki .''

Ki barta Allah zata gane kuranta .''

Haka kike fada kullum ni dai bakina dariya ce kawai .''

Hmm Allah sai na kira na fadamasa ya dawo wanan fitina da me ta yi kama .''

★★★★★

Sosai suke hidimar biki sai kida yake ta shi sabida yau ne ranan daurin auren Jabir Mustapha da amaryarsa Safiya Abba bisa sadaki dai dai yanda shari'a ta gindaya ango baki har baka mutane suna ta taya shi murna ganin bai ga Marwane ya ce'' Kai Falalu ina Abokina .''

Sai da aka d'aura sannan ka kula bayanan ai tun dazun ya tafiyarsa ganin wanan kwailar ta sa .''

Kenan yau baka masa rakiya ba .''

A'a bani zuwa sabida kar ta yi mana abin da zai bata min rai .''


Falalu ohhh baka da dama .''

A'a barni kaga laifina.''

A'a ko kadan ban gani ba .''

Haka suka ci gaba da hidimarsa Marwane kuma yana fita daga wajen ya nufi gida tare da fadawa kan bed ya yi kwanciyarsa sabida gajiya ga tunani ya yi masa yawa .''

★★★★★

Suna isa gidan Mama ta hade fuska gaida ita suka yi ta amsa ciki ciki sannan Atu ta ce'' Mama wai ina dan waken ne Allah kuwa yunwa nake ji.''

Hannu ta mika tare da fadin ban ajiye da ku ba dan haka ku face min daga gida ta karisa fada tare da fizgan roban yajin da karfi ai kuwa sai a idanunta wani wawan ihu ta saka hade da tsale ta ce'' idona a taimaka min ku kawo min ruwa .''

Dariya suka sakata gaba suna yi sai da taga ba su da niyar kawo mata ruwan ta nufi hanyar Randa tana lalabe kamar makauniya .''

Dariya Balki ta yi ,ta ce'' iko sai rabbi Allah Hasiya da Mamanki makauniya ce Irin masifafun nan za'ayi .''

Hade fuska ta yi, ta ce'' To Bana son iskanci wasan ta tsaya iya nan .''

Ni marainiyarki da Atu ce ta yi maki magana da ta zauna sabida kina tsoronta .''

Da sauri Atu ta yi karaf ta ce'' wayo ni Atu masifa Atu bala'i Atu ciwon kai Allah idan kuka kuskura Kuka yi fada sai na cire maku idanu.''

Tsab suka ja bakinsu suka yi shiru a hankali Hasiya ta lalaba ta bayan Mama tare da shiga dakin girki ta zuba masu dan wanke mai isarsu sannan tafito lokacin suna fita har ta karisa wanke idanunta ai da gudu suka bar gidan sai faman kiransu take tsabar haushi kamar ta kama da wuta ta ja kwafa ta ce'' zaki dawo gidan tun da ba gidansu Atu zaki bacci ba.''

Suna fitowa sai da Suka yi gudu mai tsayi sannan suka tsaya suka sauke ajiyar zuciya wani wajen suka samu sannan suka fara cin dan waken suna kammallawa suka mike tare da tafiya suka wanko hannusu sannan Balki ta ce'' Atu yau ne za'a kawo amaryan wanan mutumen fa .''

To ni ina ruwana ko  tafiya zaki yi ne .''

A'a na zata mun reta tsan sabida muyi tsokana ta ban mamaki .''

Dan Jum ta yi sannan ta ce'' wanan kuma hakane yanzu ku tafi gida ku dauki wanka sai kuzo mu huce ko .''

Munafurci Banza munafurci wofi babu inda zaki tafi sai na hada maki jini da majina cewar mai koko .''

Murmushi mai ciwo Atu ta yi, ta ce'' me kike jira to .''

Ganin fa dagaske farmata zata yi ai kuwa ta yi saurin cewa kin ga anan wani zai iya ganinmu ya rabamu fada amma mu tafi filin Kaci uwarka kin ga sai mu daku dan son ranmu.''

Dan tana gaja ta juya zasu tafi ai kuwa Atu ta janyo kafafunta ta baya tafadi kasa à take bakinta yafarshi jiyo da ita ta yi sannan Atu ta samu bulala ta ICE tafara zabgarta da ita sai da tayi mata lis sannan Balki tafara yi mata Susan kadangare a tafin kafafunta Hasiya kuma tana mata tsakulkuli Atu kuma tana jan kumatunta kuka me hade da dariya take yi tana fasa kara suma dariyan suke mata tsabar dariya har Kuka yafara zuwa ma mai koko Sun jima sosai Sannan suka rabu da ita kowa ta yi hanyar gidansu da kyar mai koko ta mike ta ce'' Allah bazan yarda ba sai na rama nima kawayena zan Kira komai tafanja ma fanjam .''


Dukansu suna isa suka fara shirin zuwa wajen bikin Jabir suna kammallawa suka nufi gidansu Atu sai da suka jira ta yi sallah Mangari ba sannan suka tafi suna fitowa suka ci karo da Marwane shi da ango .''

Murmushi dauke a fuskanta ta ce'' I love ina huni ,ango kasha kamshi .''

Murmushi ya yi jin yanda ta Kira kalmar I love you din ajiyar zuciya ya sauke ya ce'' lafiya lau yakk sarauniya ta Masha Allah kin sha kyau ina zuwa haka.''

Wajen biki zan tafi ya jikin naka .''

Alhamdulilah da sauki tun da har na ganki ya maganarmu ta ranan ne .''

Wani Irin kallon kauna ta aika masa wanda bata san ta yi ,ba ta ce'' ai zaka bari sai nayi tunani .''

To zuwa yaushe matar Marwane .''

Murmushinta ya kara fadada ta sunkuyar da kai ta ce'' kaji kuma wai matarka yaushe ka bada sadaki ne .''

Idan kin amince ko yau sai na bada na dauke ki mu tafi birni .''

A'a ba yanzu ba sai na gama cin duniya da tsanke .''

To ki din ga tsinka a hankali karta ritsa da ke .''

Ina da kai ai nasan bazaka so hakan ba .''

Gaskiya ne amarya ta yanzu zamu tafi daukan amarya lokaci yana ja bara mu huce tun da na ganeki hankalina ya kwanta .''

Wai kaji amaryarsa sai ka ce dagaske aure na zaka yi .''

Idan da har da wasu zasu tambayeni wacce nake son aura ,amsa ba zata wuce ke ba ,domin ke ce wacce zuciya ta ke son kasancewa tare da ke har abada .''

Hmm Tom na gode bara na barku ku wuce ko.''

Baki gamsu da magana ta a gareka ba ko.''

A'a wallahi dan naga kuna sauri karna batamaku lokaci .''

Hakane to sai anjima kawayenmu da kuma sarauniya .''

Ok sai an jima ango Allah ya bada zaman Lafiya .''

Amin suma amin na gode sosai Atu .''

Yana gama fadan haka suka yi tafiyarsu .''


Bayan Sati day kwance take kan Tabarma hannunta rike da waya ta saka eapice tana sauraren musique tana girgiza kai tana biyar wakar Inna ta ce'' sabon Salo dama Atu kina gidan nan yau na jisa tsite .''

Inna Kenan bara kiga me zan yi zuwa an jima .''

Waya ta baki ne ?"

Wani abokin Marwane ne wallahi sai nayi masa abin da ba zai sake fadamin magana ba .''

Hmm Allah ya shirya ki.''

Amin .''

Tana nan kwance har rana tafara kawo mata ta chanja waje kiran Marwane dake shigo wa ta daga bayan sun gaisa ya ce'' Atu gani a Kofar gidanku nasan zuwa yanzu kin shirya ko.''

Nasan gidan fa Allah kayi tafiyarka tare da kawayena zan tafi .''

Tom shikenan sai kin zo karki jima dan Allah .''

Naji nace .''

Jin maganar tafara isarta ya sa ya katse kiran. Mikewa ta yi ta shirya tsaf tare da dauko wani Abu ta daure zanninta da shi sannan tafita zuwa gidan Hasiya daga tsan suka yi gidansu Balki sai da ta shirya sannan suka fito suna shiga gidan kai tsaye falo suka wuce nan suka tarar da Amarya a ranan suka yi sabo da Atu ganin babu fita bare ya shigo ya sa ATU zubawa terras din wajen mai tana gamawa ta koma daki kamar Bata yi komai Falalu da shigowarsa Kenan bai Ankara ba ga wajen da sulfi sai da ya ji an kwashe sa ya yi sama sama sannan ya dawo timmm da kasa kamar an jefo kayan wanki
12/10/2022 à 08:40 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

26&27


Momy ! Momy ! Momy Allah ki ma wanan yarinyar magana ki ce mata tafita idona in rufe tun tafi nayi kwallo da ita .''

A hankali ta dago da kanta ta ce'' to kusu da mage miye kuma da baku da aiki sai fada .''

Momy ce min take fa ita Auntyna ce Allah ki fadamata zan ci yan garinsu .''

Da abun bai yi dadi ba kin cinye yan garinsu yanzu kira min ita .''

Ciki ta shigo ta ce'' gani sai ba an kirani ba .''

Girgiza kai Momy ta yi , sabida lamarin Lantana yana bata mamaki kallon ta ta yi a nutse ta ce'' ke Lantana kifita idanun Yasmine kafin ranki ya bace .''

Sai da ta kare mata kallo ta ce'' Momy ta fada min ta ina zan fito .''

Fito ta tsakiyar kaina .''

Tabe baki ta yi , ta ce'' Ohoo dai Malam zalumu yana dawowa gidan nan ni ce matarsa dan dole ki bani girmana .''

Mtsss Yasmine ta ja sannan ta shige dakinta ,kallonta Momy ta ce'' Lantana dama ki tafi dakin Irfane ki gyara sa insha Allah cikin satin nan zai dawo.''

Wani uban tsale ta buga kamar zata tashi sama ta ce'' yaushe Kenan Momy .''

Bansani ba ya ce surprise din mu zai yi .''

Cike da murna ta ce'' Allah ya dawo min da shi lafiya ashe mun kusa shan biki a gidan nan .''

Shiru Momy ta yi, mata har ta gama zuba ta yi gaba abin ta .''

Tana shiga daki ta fada kan bed tare da janyo wayarta haka kawai taji tana son jin muryan Marwane dan haka tafara kiran layinsa sai da ta kusan katsewa sannan ya daga tare da sallama a bakinsa .''

Amsawa ta yi ,ta ce'' Manyan gari baku neman mutane sai sun neme ku.''

Afuwan ina busy ne shi yasa .''

Haka kake fada kullum yakk .''

Lafiya yakk kema .''

Alhamdulilah gani ina ta aikin tunaninka .''

Murmushi ya ce'' amma naji dadi .''

Kenan kai baka tunani kenan ka manta dani ko.''

A'a idan na zauna babu abin da nake yi sai aikin tunaninki.''

To miye tunaninka a kaina ?"

Sabida kina da kirki sannan yan gidanku suna da karamci da son mutane .''

Sai me kuma ?"

Ina ga babu komai sabida haka kike birgeni .''

Dan fuskanta hade kamar yana kusanta ta ce'' Marwane ni wace iriyar macece a wajenka.''

Me ya sa kika yi wanan maganar.''

Ina son ka bani amsa kafin na amsa taka tambayar.''

Ina maki kallon kanwata kuma kawata .''

Daga wanan ba komai , '' kusan haka dai .''

Gaskiya ne Marwane so diyawa uwayen da muke so basu ne suke son mu ina son fadamaka wani Abun koda ba zaka saurare a kansa amma ka bani 1mnt a natsu dan saurare ne .''

Ina jinki .''

Gaskiya kai din mutumen kirki ne sosai kuma ban taba haduwa da wanda yake kulawa dani ba sama da iyayena gaskiya kai din jarumi ne sannan kuma sadauki dan autan Maza hakan ya saka zuciya ta kamuwa da Abin da ta san yafi karfinta ba zata iya samunsa ba amma kuma tana min Babbar barazanar duk randa na rasa ka nasan nima bazan iya rayuwa ba Marwane ina Sonka sannan ba kebe wani kebeben waje wanda kaine ka dai zaka mulke sa na baka makullin zuciya ta dan Allah Karka yi sake ya samu tangarda sabida ina ma son so Bana fatan rasaka ina son ko kadan ne ba kaba ta waje ta samu sallama a zuciyarka .''

Tun da tafara magana yake jin sautin muryanta da kalamanta a matsayin Atu ce take furta su har sai da ta kai karshe sannan ya tuna da wace yake magana Murmushi ya yi ,ya ce'' hakane hakika naji dadi da kulawanki a gareni da kuma soyayyarki amma sai de bazan boye maki cewa ina da wacce nake so amma bana gabanta amma kuma ita ce a zuciya ta .''

Sosai jikinta ya yi sanyi muryanta ta kariya ta ce'' ka bani dama nima na gwada nuna maka kallar tawa soyayyar dan Allah Karka Rabu dani .''

Kansa ya shafa zuwa sajensa ya ce'' ba damuwa sai an jima ina hada kaya zan koma gida ne .''

Tom ba damuwa Allalh ya kawo ka lafiya ya kiyaye hanya .''

Amin na gode sosai addu'a mai kyau .''

Murmushi ta yi ,ta ce'' matsayinka ya wuce na godiya a gareni sai an jimaaa.''

Tafada tare da katse kiran janye wayar ya yi tare da kallonta Yana nazarin maganar Yasmine ajiyar zuciya ya sauke tare da ajiye ta yafara shirinsa yana gamawa yafito tare da nufa gidansu Atu .''

Yaro ya Tura nan ya Kira masa ita tana fitowa ta washe baki ta ce'' I love you ashe kaine .''

E'ee bani so nazo wajenki sabida baki Sona ko.''

Sunkuyar da kai ta yi sabida kwarjinin da yake yi mata ta ce'' A'a dama ina son ka zo ban yi tsamanin ganinka a yanzu ba .''

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce'' Atu gobe insha Allah nake son komawa garinmu .''

Gabanta ta ji yafadi dasss ta ce'' gida kuma me yasa zaka tafi kuma .''

Ba komai dama biki ya kawo ni kuma an gama shi yasa zan tafi .''

Zuciyarta ta kariya idanunta har Sun kawo kwalla amma ta kasa magana wajenta ya matso tare da daura hannayensa biyu a fuskanta ya saka babban dan yatsansa yana share mata hawaye da suka fara gangarowa saman fuskanta ya ce'' Atu ki amince da soyayya ta idan kika watsi da bukatata ta Samar min gurbi a zuciyarki ,zaki sa na shiga zargi kaina karki sa zuciya ta tafara kallon so a matsayin wani Abu marar daraja Abun gujewa da rashin cancanta ga rayuwa ta Zahiri linzamin farinciki na na a hannunki a yanzu  ina sonki ki aminta dani hasken idaniya ta .''

Kukanta ya tsananta ta kara fashewa da wani sabon kuka ta ce'' duk wanan da ka fada kake tunanin tafiya ka barni cike da kewarka sai da na fara sabo da kai shine zaka gujemin .''

Hannuwansa ya sauke daga fuskanta sannan ya kamo hannuwanta ya fara murzasu a hankali ya ce'' a dukan lokacin da muka nisanta da juna zuciya ta na zama kamar kwalbar da babu komai a cikinta mai kyau gani a Ido amma marar amfani a zahiri Atu ki ce kina Sona ko hakan zai sa naji san yi a raina.''

Lumshe idanunta ta yi ta ce'' Menene I love you ka fadamin a irin wanan ranan zaka fahimtar dani abin da take nufi .''

I love you yana nufi ina sonki .''

Murmushi ta yi ,sai da ta shafi sajensa mai birgewa da daukar hankali ta ce'' ina son wanan kyakyawan fuskan da ma mallakinta ina masa so marar masultuwa sannan ina kaunarsa fiye da tunaninsa bana fatan rasa shi bare har ya yi nisa dani ina Sonka Marwane .''

Tsabar dadi da farinciki bai san lokacin da ya rumgume ta tsam a jikinsa tare da sakin wani hadaden Murmushi Balki da isowarsu Kenan suka kama baki Hasiya ta ce'' Atu yaushe kuka zama yan Iska ne .''

Da sauri ta janye jikinta da nashi ta ce'' ba iskanci bane Soyyaya ce idan farinciki ya mamaye zuciya ta rasa inda zaka saka kanka kake yaushe kika zo.''

Yanzu nan wani kallon kauna ta aika ma sa ta ce'' I love you zan yi kewarka sosai yaushe zaka dawo.''

Duk lokacin da kike bukata zan zo .''

Amma da naji dadi sosai .''

Karki damu matsayinki ya wuce hakan bara na wuce naga kawayenki Sun tawo sai wani lokacin idan mun sake haduwa bye bye .''

Ita ma hannu ta shiga daga masa har ya bace ma ganinta kallonsu ta yi, ta ce'' Aikin Banza kawai ina tsaka da shan soyayya ta kun wani zo kun koramin I love you dina wai uwar me zan yi maku.''

Allah ya huci zuciyarki Kawarmu .''

Kwafa ta yi sannan ta ce'' idan kun ga dama ai sai mu shiga daga ciki.''

Bayanta suka bi suna isa a tsakar gida suka zauna nan ta shiga basu labarin abin da yafaru tsakaninsu da Marwane ,cike da shaukin so Balki ta ce'' Ohh Allah Allah ka Bamu masoya musha lubaya Irin wanan love haka har na matsu mu tafi birni biki .''

Hmm ranan wanan mawakin zan a kiramin wanda yake tashe da wakokinsa .''

Ashe zamu gwangwaje ranan , cewar Hasiya.''

Sosai suke taba fira musanman bisa kan maganar bikin Atu .''
12/10/2022 à 08:44 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

28&29

Sosai suka sha fira sai bayan sallah isha'i sannan suka tafi gida sai ta yi masu rakiya tana dawowa tafada toilet ta yi wanka sannan ta saka yan kayan shan iska sannan ta yi sallah ta ci abinci su Yaya Nura na dawowa suka daura fira sai dare sannan suka watse Atu na shiga daki tafada kan yagagiyar katifarta nan tafara tunanin kalaman Marwane wani sihirtaciyar kaunarsa na kara shigarta dariya ta yi hade da tafi ta ce'' Inna ! Inna ! Inna! Sannan ta kara fashewa da wata sabuwar dariya Inna da ta zuba kunne tana jiran ta ji cewar Atu sai ta ji ta kara kwashe da dariya ta kamar zautaciya haka ta yi ,ta zuba sambatu har bacci ya yi gaba da ita a asuba Inna ta tashe ta nan tafito waje tare da kwasar kankara tafara jefawa a Kofar dakin Jamila da Habi babu shiru duk suka tashi Habi na jin an fara jefen dakinta Ta ce'' Fitinaniyar yarinyar tsan tatashi dan jaraba ko baccin kirki baza'a barka ka yi ba .''

Lawan ne ya buge mata baki ya ce'' me kike fada yanzu .''

Fashewa ta yi da Kuka ta ce'' naje na ce jarababiya'' kara buge bakin ya yi cikin Kuka ta kuma fadin an fadama jarababiya''  nan ma yakara buge bakin haka ta yi ta fada yana mata baki a nan karshe cikin sautin Kuka ta ce'' wallahi Allah na fada kuma na kara fada Jarababiya'' wani kyakyawan naushi ya kai mata a baki babu shiri ta yi gumm da bakinta shi kuma ya ja tsoki ya fito waje Ita kuma Jamila tana jin bugun kofar ta Budé sabida batason abin da zai shiga tsakaninta da Atu sabida ta kanta take tana dauke da jaririn ciki shi yasa ta daina tsokanarta dan tasan karamin aikin Atu ne ta sakar mata tusar da ko ajiyar zuciya ba zata sauke ba cikinta ya bare Alwala ta d'aura sannan ta yi dakinta dama Tuni Lawan da Nura Sun tafi Masallaci ita ma Atu alwala ta d'aura sannan ta koma daki sai da ta karisa sallah sannan wata kibiyar soyayya ta soke ta a take ta saki wani hadaden murmushi ta ce'' Inna ta kinsan me .''

Dama tun jiya Atu ta kulle Inna da haushi a hasale ta ce'' kin ga Allah Kika kuma kiran sunana sai na Saba maki .''

Tsaye ta mike tare da wulli da hijjab din ta dauke darduman sannan ta kama saman katifarta wani uban tsale ta buga tafadi kwance kan katifar ta ce'' Allah sarki soyayya Allah ya bar ma kowa nashi wanan kalaman love Sun hadu sosai wallahi I love you dina ya iya shayar da zumar soyayya wayoo Inna I love you dina ya bani giyar soyayya .''


Habi dake shirin hucewa ta ji abin da Atu take fada ya sa ta ce'' hmm su soyayya manya amma an ji jiki .''

Daga murya ta yi ta ce'' Aunty matsala Allah ya shiryeki da shegiyar gulma to ayi fitsari a kwanta sabida kalar tamu soyayyar ba kalar taku bace .''


Tabe baki ta yi sannan ta yi gaba abin da .''

Inna kuwa tun da Atu tafara sambatunta take ta yi kasake tana kallon ikon Allah wato kwannan da taga tana Sanya Kenan tunanin so take hmmm Allah ya fida wanan mutuman karta kore sa da tusar sa .''

Tana tsaka da tunani taje Atu ta kwallara kara tana fadi wayoo masoyi har na fara kewanka tabbas idan ka tafi zan sha wahala da karfi ta kira sunnan Inna ta ce'' na sha giyar soyayya .''

Tana gama fadan haka ta rufe idanunta bacci ya yi gaba da ita .''


Cike da murna Jamila ta d'aura abincin break babu Atu yar masifa bare a addabe rayuwarta sosai ta ji dadin hakn tana kammallawa ta zuba ma kowa sannan ta dauki nasu ta yi dakinta suka ci abincinsu cike da so da kauna ita da mijinta 

Bangaren Habi kuma sai hade fuska take tana turo baki yana mata magana tana watse sa a kasuwa ganin Bata da lokacinsa ya sa shi cin abincinsa ya yi shirin fita gona ,ita kuma ba haka ta so ba Irin dan rarashin nan ta so ya yi mata amma ganin yafita hasala kallonsa ta yi ,ta ce'' Wai fita zaka yi ne ?"

A'a kwance zan yi idan zaki tafi aikin gonar.''

Turo baki gaba ta yi ,Bata sake cewa komai ba shi kuma yafice daga gidan .''

Ita ma Jamila suna gama break ta shirya ita da mijinta suka fita sabida zata tafi gidansu ziyara .''

Sosai take sharar baccinta ganin har 11h ta yi bata ta shi ba Inna tafara tashinta cikin magagin baccin ta Karka ce kugu ta bada burrrr Inna bata Ankara ba sai saukar Tusa ta ji ya ratsa ta da sauri ta mike tsaye tana fitowa ita kuma Atu ta bude idanunta tare da karanta Addu'a tashi daga bacci ta mike tana zuba mika hade da hamma waje tafito kai tsaye ta fada toilet wanka ta yi, ta shirya sannan ta yi break ta kalli Inna ta ce'' Alhamdulilah Inna ta Marwane bai zo nema na ba .''

Waye MARWANE kuma ?"

Ohh na manta ashe baki sanshi ba ho ho Inna nasha giyar soyayya .''

Tana gama fadan haka tafita waje ta ce'' na tafi gidansu Balki sai na dawo .''

Rike baki Inna ta yi sabida lamarin Atu sai dua'i ta ce'' To karki jima gidan nan babu ruwa .''

Tana fita ta nufi gidan lokacin suna bakin kofar gida ita da Abbas sai Hasiya ita da Ashiru wajensu ta kariso Ashiru yana ganinta yafara neman hanyar boya da sauri cike da ladabi ta ce'' Yaya Ashiru ,da Yaya Abbas ina kwana .''

Cike da mamaki suke kallonta cikin rashin yarda suka ce lafiya lafiya lau Atu ashe kin fito .''

Ita ko ya da son ranka .''

Babu ,ke wajenku nazo fa .''

Balki ta Dube ta ta ce'' Wai wanan mutuman Sun zo wai suna son mu da aure amma sai mun rabu dake sabida karki lalata mana tarbiya.''

Hade fuska ta yi, tare da kashe Ido day ta saki baki kafin ta rufe ta ce'' wato ni yar Iska bani da tarbiya kuke nufi ko .''

Dan Allah ki hakuri Atu ba Haka Muke nufi ba .''

A'a karku damu zaku ga rashin tarbiya ganin idanunku ,Balki bara na huce gida duk yarinyar da ta kuskura ta zo sai na ci uwarta alkur'an.''

Da sauri Hasiya ta ce'' haba Haba Atu ai kema kinsan ko da kowa zai juya maki baya ban da ni a ciki Ashiru din me me zan yi da shi Allah na tuba me na sama ya ci bare ya bama na kasa ni fa Bana son sa wallahi .''

Haka Balki ma ta ce'' ke kuma miye na daukar zafi me zan yi da wanan Allan kwankwan din wanda babu komai a jikinsa sai tsofafin Kaya kinsan burina ni sai ma mota dan birni .''

Murmushi Atu ta yi ta ce'' haba masoyi baya zama makiyi Yaya Ashiru ka yi hakuri ku Bamu lokaci zan shawo maku kansu yanzun nan ku bani 2mnt .''

Washe baki suka yi a tare suka ce muna godiya Sosai Atu gskiya mun yi maki rashin fahimta amma ba zamu sake ba.''

Karku damu ai ni yanzu babu ruwana sabida nasha giyar soyayya I love you dina ya iya lubaya sosai .''

Kallon juna Abbas da Ashiru suka yi amma babu bakin magana ,hannun su Balki taja suka shiga ciki wajen wani Katon rame suka nufi da alama na kwalbati ne ( kwata) suka rufe hancinsu sannan suka kwaso wanan kwatamin sai doyi yake sannan suka nufi waje cike da dubara Atu ta takarkare a tare suka watsa masu dai dai Ashiru ya bude baki kawai ya ji saukar katon kashi ( bahaya ) a bakinsa babu shiri suka bi hanyar gida babu abin da suke sai wari masifa .''

Dariya suka sheke da ita sabida sannan suka koma gida suka wanko hannayensu suka fito waje a hanyarsu ta tafiya Atu ta ce'' ku tsaya ana maganar duniya ake ta lahira mu tafi gidansu Marwane naga ko ya tafiyarsa .''

A haka zaki tafi kina warin kasshi .''

Kuma fa hakane amma ina son ganinsa ne sabida nasha giyar soyayya.''

Ohh Allah ya bamu hakuri ya kawo mana masu son mu su Bamu giyar soyayya .''

Yanzu ya za'ayi Kenan .''

Mu tafi gidansu Hasiya kiyi wanka ki shirya sai mu tafe .''

Allah ya sa bai tafi ba .''

Da Amin suka amsa sannan suka nufi gidan wanka ta yi ta chanza Kaya sannan suka nufi ma saukin su Marwane a ci sa'a basu tafi ba tana ganinsa da gudu ta nufe sa tare da fadawa jikinsa bai Ankara ba har sai da ya ji tsoro ganin Atu ce ya sa shi sakin murmushi ya ce'' Cutie na ashe kice na yi tunanin ba zaki neme ni ba .''

Kara matse sa ta yi, ta ce'' tun jiya nake ta tunaninka ina ta addu'a Allah ya sa baka tafi ba .''

Ashe kin damu dani haka Cutie  I love you.''

Murmushi tare da raba jikinsu ta ce'' nasha giyar soyayya tafara haukatani sai sambatu nake dan Allah idan katafi ba zaka manta dani ba .''

Hannunta ya kamo tare da daurawa sai tin zuciyarsa ya ce'' Cutie ke din ta musanman ce a gareni kina cikin nan ,'' yafara tare da nuna mata zuciyarsa .''

Dan dukan wasa ta kaima wajen ta ce'' bansan wane hali zan shiga duk ranan da naga wata a tare da kai ina da kishi sosai kasan da wanan I love you dina .''

Insha Allah ke ce tafari kuma ta karshe .''

Turo baki ta yi , tare da juya masa baya , murmushi ya ce'' Cutie na gode menene kuma .''

A shagwafe ta ce'' uhmm uhmm ba nayi maka kwaliya ba amma baka ce nayi kyau .''

Juyo da ita ya yi, ya ce'' Atu na aike ko baki kwaliya dama ke kyakyawa ce ajin farko wace ko wane namiji yake burin samu kuma ya mallake ki a matsayin mata sabida kuyi rayuwar farinciki kina haske tamkar hutar lantarki idan kin fito dole kowa ya kalle ki kina da kyawawon Idanu masu fari tamkar madara ga hancinki har baki dan siriri dai ke ga dan karamin bakinki mai kyau a samansa baki baki ne daga kasa kuma pink me kyau ga hadaden murmushinki mai daukar hankali duk wanda ya ajiye idanunsa a kanki Abu na karshe idan kin yi dariya tsarin hakoranki kamar masara ga haske har kaina zan iya hagowa a ciki .''

Cike da kunya ta ajiye kanta a kirjinsa ta ce'' uhmm uhmm ai kaima duk abin da ka fada Haka yake a naka bangaren I love you dina zan yi kewarka sosai .''

Tafada cikin raunataciyar murya kamar zata yi Kuka .''

Da sauri ya dago fuskanta ya girgiza mata kai alamar kar ta yi kuka ya ce'' kina son idan na tafi a hanya na kasance cikin damuwa .''

Girgiza masa kai ta yi alamar a'a .''

Tom ki sakarmani kyakyawan murmushinki idan na tuna na kasance cikin farinciki .''

Babu musu tafara Murmushi sai da ya tabbatar babu wata damuwa a tatare da ita sannan ya dauko kwalin waya ya Mika mata ya ce'' ina son zaki din ga amfani da wanan wayar sabida da ita zamu din ga magana .''

Amma bn iya amfani da ita ba ko fa makaranta Boko ban yi ba .''

Murmushi ya yi, ya ce'' ba dole sai kayi makaranta kake rike Irin wanan wayar ba yanzu zan nuna maki komai kin ji daga zarar mun yi aure zan sakaki a makaranta .''

To ka nuna min magana .''

Babu musu suka zauna nan ya shiga nuna mata komai da kyar da wahala ta gane abin da yake nuna mata Sannan ya Mika mata tare da yi masu alkairin kudade ita da kawayenta amma sam taki amsa sai da ya nuna mata ransa ya bace sannan ta saka hannu ta Karba sannan suka yi tafiyarsu Balki ta ce'' yau naga yanda shan Zumar soyayya Allah ji nake kamar na bankade ki na tsaye a wajensa .''

Banason iskanci fa kina hadamin kanki da Marwane .''

Allah ya baki hakuri gashi yanzu min samu 20mille ( dubu ashirin ) 

Kadan daga aikinsa Kenan .''

Har suka isa gida Suna zantawa kan maganar Marwane da yanda take jin kaunarsa a zuciyarta
12/10/2022 à 08:44 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*


30&31

Dakin da yake mallakin Irfane ta shiga nan ta shiga gyara shi tsaf har toilet sai da ta wanke ta feshe ta da Airfreshh sabida ta san mutuman Nata akwaye son kamshi sannan tafito daga dakin a gajiye ta shigo falon babu kowa a ciki hakan ya Bata damar shiga dakin Yasmine tana shigowa babu ko sallama baki abin magana ta ce'' Anty Albushirin din ki .''

Sai da ta tsora ta sabida Bata ji shigowarta kawai muryanta ta ji tsoki ta ja ta ce'' haka na koya maki shigo min dakin .''

Ki hakuri na fadamaki mantuwa gareni dama abin da ya kawoni wajenki shine ,da sauki ta daga mata hannu ta ce'' idan ba zaki min sallama ba fitar min daga daki.''

Mikewa ta yi tare da kwaikwayon yanda Yasmine ta yi maganar ta sannan ta ce'' Sallama alaikum .''

Wa'alaikum salam tafada tana banka mata harara .''

Ohh na zata bazaki saurare ba .''

Shiru ta yi mata ganin bata da niyar bata amsa ta ce'' Anty wajenki fa na zo .''

Sako naji .''

Dama dan kiji Habibi na ya kusa dawowa har na gyara masa dakinsa .''

Sai kuma me ke tafe dake .''

Ina cikin farinciki sosai sabida nasan yana dawowa za'ayi aurenmu.''

Uhmm sai kuma me.''

Zamu sha shagalin biki sabida bikinmu zai fita layin ya'ya'yan sarauta.''

Sai me kuma .''

Zamu sha soyayya sannan na kula da masoyi na .''

Sannan me kuma.''

Ke Malama kin isheni baki kulani sai tambaya ta kike wanan ai bakin ciki kike man sabida kin ga zan auri Big boy hadaden saurayi wanda yafi naki ko dan kin ga zan riga ki aure shi yasa kike man hasasa .''

Lantana yanzu ni ce nake maki hasada .''

Dariya ta tsintsire da ita ta ce'' hoo duniya ashe kina magana kika cika ni da sai kuma me kin ga yanzu na fadamaki magana kamar yanda kika kulleni dan haka sai an jima Malama Aunty Hajiya Ranki shi dade Yasmine.''

Tana gama fadan haka tafice abin ta tana ci gaba da dare ta .''

Girgiza kai ta yi , tare da jan tsoki wayar Marwane tafara kira sai da ta kusan katsewa sannan ya daga cikin sanyanyar muryanta ta ce'' Amincin Allah su tabbata a gare ka mahadin rayuwa ta .''

Murmushi ya yi tare da sauke ajiyar zuciya ya ce'' tare da ke yan matana yakk.''

Hmm normal dai wato dai idan bani na kira ka ba zaka taba kirana ba ko.''

A'a ina hanya ne zan dawo gida .''

Masha Allah Ashe kace zan din ga bama idanuna abinci duk randa suka Bukaci gani .''

E'ee insha Allah nima zan so haka.''

Hmm sai ka ce ka wani damu dani .''

Na damu dake sosai mana yan mata .''

Murmushi ta yi, ta ce'' dama Yayana zai dawo daga tafiya shine nace idan ya zo dan Allah ko zaku gaisa .''

Babu damuwa idan ya dawo zan yi kokari insha Allah naje .''

Idan ko kayi hakan zan ji dadi sosai.''

Kiji dadinki sabida shine farinciki na .''

Dagske masoyi.''

Sosai ma .''

Tom bara na kyale ka sabida kana hanya idan ka sauka lafiya sai mu karisa zantawa .''

Ok ba damuwa ki kula da kanki .''

Insha Allah kaima hakan .''

Katse kiran ya yi , ita kuma ta mike tafito falo.''


★★★★

Atu na Isa gida ta kwala kiran Jamila da shigowarta Kenan zazafi ya koro ta Inna dake zaune ta ce'' Atu dan Allah ki rabu da Jamila zazafi yake damunta .''

Murmushi ta yi , ta ce'' eyyahh ai ban samu labari ba bara na kira watsan munafukar ''

Kai tsaye dakin Habi ta nufi tana ganinta ta ce'' karyar iskanci dan ina kiranki shine zaki fara bacci karya tom shikenan jirani Ina zuwa .''

Labulan dakin ta saki sannan ta zo ta debo ruwan dauda wanda suka kwana biyu a wajen sai tsami suke suna wari haka ta nufi dakin Habi da su saman gadon ta haura tare da banbare bakin Habi ta saka ma kwarari tafara tsiyaya ruwa suna shiga ta bakinta ganin da gaske Atu kashe ta zata yi idan bata Farka ba hakan ya sa ta bude idanunta ganin ruwan da suka shiga bakinta ya sa ta kwarara ihu tana fadi wayoo na shiga uku a kaini asubiti cutar Ebola zata Kamani wayoo na bani na bani na lalace Atu muguwa Allah ya isa wallahi mikewa tsaye ta yi ta ce'' hmmm ashe karyar banza kike na zata baccin Zaki ci gaba da yi .''

Harara ta balla mata tana ci gaba da kukanta .''

Kika ce ke shigaya ce Allah nafiki zama yar daba idan baki hankali ta hanci zan Tura maki su .''

Da sauri Habi ta sauke idanunta sabida ta daina hararen Atu sauran ruwun ta karisa watsa mata ta ce'' kiji da wanan sannan ki gyara dakinki ki fito ki girka mana abinci kafin cikina yafara jin yunwa .''

Tana gama fadan haka tafice daga dakin .''

Sosai Habi ta sha kuka har ta gode ma Allah sannan ta nufi toilet tafara brush din bakinta yafi sau ashirin sannan ta haye saman abin kashi tafara yunkurin yin kashi amma sam Yaki fitowa sai kuka ta ci tana zagaye cikin toilet ...
12/10/2022 à 08:44 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*


32&33

Ba ita tafito daga toilet din ba sai da ta samu ta yi zawo babu abin da yake fitowa sai kararsa kana shigowa zaka ci karo da karar zawon Habi tana yi tana matsar kwalla har sai da ta kammalla sannan tafito a tsakar gida ta samu Atu zaune tana aikin jera mata dariya Irin ta ketar nan harara ta watsa mata ta ce'' muguwa Allah ya sa wanan mutuman ya dauke ki ki bar mana gidan nan ko zamu Sarara.''

Tabb ai in akwaye wanda ya isa to wallahi ya ci karya ya kwana da yunwa ai a gidan nan za'a bani daki mu din ga shan soyayyarmu a ciki har sai haushi ya kashe ki .''

Kaji karyar Banza waya fadamaki idan aka yi aure a na zaunawa gida yanda muka Baro gidanmu haka kema zaki fita ko baki so yar rainin hankali.''

Ohoo dai Allah ko da dakin ki ne sai mun zauna .''

Mtsss ke waini ba matar yayanki ba ce .''

Dan maimaita ban ji me Kika ce ba .''

Sabida ke kurma ce .''

A'a karki ga laifina idan warhaka ta yi Bana ji sosai shi yasa .''

Inna dake saurarensu a daki tafito ta ce'' Wai yanzu Atu ina ruwan da nace ki debo min .''

Hmm Inna Kenan yau ruwa ya ci dan Sarki ina fita wanan Karen sai ya cije ni.''

To miye hadinki da shine .''

Jansa nayi kuma na watsa masa kasa a Idanu kinsan ko idan ya rike ni Allah sai de Habi ko Jamila su Sama maki wata jikar amma bani ba .''

In ta karema Kare cizo yake Bari ya koma tunni ke yanzu ki rasa da wa zaki fada sai da kare .''

Maganar kike so Allah Inna Habi tatafi danni ina son rayuwa sabida ina son muyi aure ni da I love you dina .''

Girgiza kai Inna ta yi , ta ce'' Habi je ki debo min ruwa .''

Yawa Inna na ce yau kin ga babu in da zan tafi ki barni zan yi mana girki Irin na Yan birni.''

Tabb Allah sawake waye zai baki girki kisa mu kwana da yunwa .''

Ke yi man shiru ko na cire maki baki ina ruwanki shiga shara ba Shanu rabu da ita Atu yau ke ce zaki yi girki karki yi kuka haka kawai yarinya ta ce zata yi abu sai ku Hana ta , cewar Nura''

Dama Nura kana gidan nan ,cewar Inna .''

E'eee dama haka kuke takura min yar kanwata to wallahi ko ba dadi sai kun ci abinci nan sabida ai baku koya mata ba .''

Murmushi ta yi ta ce'' kuma yaya Irin na yan birni wanda muke kalla a gidan Amaryar Jabir irinsa zan yi mana .''

Yanzu karfi kudin cefane ki sayo abin da kike da bukata .''

Cike da murna ta karfi kudin tayi hanyar waje .''

Shine Nura ficewarsa ya yi ya nufa gona .''

 Yana fita Habi ta dubi Inna ta ce'' Yanzu sabida Allah girkin wanan yarinyar zamu ci a gidan nan me ta iya Alkur'an ko tantama babu yau sai kewaye ya yi manya baki wato Alhaji zawooo.''

Ai wanan yarinyar tana abin da taga dama tana kwaruwarmu sai hakuri bara muga abin da zata girka din.''

Tulo Habi ta dauka sannan ta fita dan debo ruwa .''


Atu tana dawowa ta wanke tukunya sannan tafara zuba ruwa a ciki sannan ta saka gishiri da Magi sai da Suka taso ta saka Albasa ta banka tattasai jajirr da shi sannan ta kawo gari tuwa na hatsi ta saka da garin shinkafa sannan ta saka tumatir danye shikenan ta rufe sai da tuwon yafara dawuwa sannan ta dauko muciya tafara tukawa da kyar har wani daka tsale take idan zata juya muciyar tana gamawa ta dauko mai ta saka sannan ta kada miyar Kuka a cikin tuwon shikenan Aka sauke sannan ta d'aura tukunyar miya kawai ruwa ne sai Maggi da attarugu da gishiri da tumati na kwanko ta hada waje guda ta rufe tukunyar shikenan ta kammalla dauko kwanoni ta yi tafara zubama kowa sannan ta kashe wutar murna kawai take ta iya abincin yan birni sai da dare ya yi Nura da Lawan suka shigo sannan ta zuba masu abinci ta zuba ma Habi da Jamila sannan ta zuba ma Inna suna zaune saman tabarma duk ta ajiye sannan ita ma ta zuba nata ta zauna .''

Habi ce ta kwaso tuwo tare da yamutse fuska ta aika cikin baki ai wani uban gishiri da Attarugu da Suka yi yawa ga garin tuwon bai dafu ba yamutse fuska ta yi kamar zata yi Kuka amma Bata yi magana sabida tsaf Atu zata sauke masu kwadon rashin mutumci Haka bangaren su Nura yana kaiwa baki ganin Atu na kallonsa ya saka shi murmushi ya ce'' A'a kanwata wanan abinci mai masifar dadi ina kika iya shi .''

Washe baki ta yi , ta ce'' gidan Jabir abokin I love you a t.v din matarsa .''

A'a ya yi dadi amma karki ci ki ajiye min an jima sai na cin ye.''

A'a to ni me zan ci yunwa fa nake ji .''

Tafiya zaki yi wajen mai doya ki sayo mana har da kifi sai ki ci ko .''

Tana jin haka ta dauko abincin tare da turo masa shi gabansa sannan ya Mika mata kudin karfa ta yi amma taki tafiya sai Sun cinye abincin nasu kuma shi ya yi hakan ne sabida su samu su zubar .''

Inna ta ce'' Jamila ta shi kitafi daki ki dauko min wanan sakon kin ji.''

Babu musu ta mike dama Nura ya yi mata alama kar ta ci sabida shi de na cikinta yake .''

Inna ta ce'' Wai Atu miye sunnan wanan girkin ne .''

Heheheyeee yan birni suna kiransa da sakwaran doya shine na hada maku.''

Lanle kam ya yi dadi ba laifi amma ki tafi ki sayo naki abincin ko .''

A'a fa bazan tafi ba sai kun cinye sa .''

Habi dake sharfan zufa tana ci tana hade fuska tana murmushin yake daga sun hada Ido da Atu Lawan kuwa ci kawai yake yana hadewa da kyar dan sai yafito da Idanu waje yake shiga a cikinsa .''

Inna kuwa da yake ta bama Atu baya haka take ci tana Kuka duk zufa ta jika ta sai da taga Sun kusa cinyewa sannan ta mike ta ce'' bara na tafi saye cikina sai kukan yunwa yake .''

Tom sai kin dawo cewar Nura dake matsar kwalla tsabar attarugun dake cikin girkin .''

Suna ganin fitarta dukansu suka mike a tare suka nufi shara suka fara zubar da abincin sannan Habi tafara Karirin Amai Lawan kuma ruwa yake bankama bakinsa Lawan kuwa sai kasa yake sakawa a bakinsa Inna kuma Tuni ta kumbre sai sakin tusa take ba'a 1mnt ta bada furrr ko tafiya take tana burrr ratatatata zukuttt farrr .''

Haka ta cika su da sakin Iska in banda dariya babu abin da Jamila take har da su faduwa tsabar ta kulle Habi ya sa ta dauko Katon ICE ta biyo ta da shi ai kuwa ta shige daki tana ci gaba da dariya .''
12/10/2022 à 08:45 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*


34&35

A hanyarta ta dawowa ta hadu da Falalu hade fuska ta yi , tare da canza hanya ya yi sauri tare ta a hasale ta dago ta ce'' Alkur'an ka bani hanya tun kafin na saka rigar rashin mutumci na hada kwalin bankada .''

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce'' Atu ni fa banada tsokana na zo gare ki ba dama Marwane ne ya bani sako na kawo maki .''

To amma dazun ai mun yi waya amma bai fadamin zai bada sako a kawo min ba .''

Karki damu dama wanan sakon sai de mu ce ki hada da hakuri.''

Bangane me kike son fadamin ba .''

To dama ce min ya yi in fadamaki cewa kiyi hakuri bisa kan bata maki lokaci da ya yi sabida yana da wacce yake so kuma a gidansu a Sonta dan cikin satin nan zai yi aure bai san ta yaya zai fara Sanar dake hakan bane shi yasa ya ce na zo .''

Tun da yafara magana gabanta ke faduwa kwalla suka cika idanunta ta ce'' Falalu dan Allah ka fadamin gaskiya abin da kake fadamin hakane .''

Wallahi kuwa haka ya ce min .''

Fashewa da kuka ta yi ,tare da wankawa a guje ta yi gida ba ko sallama tafada jikin Inna dake sambada tusa jikinta har rawa yake tsabar tashin hakanli.''

Nura ne ya kariso wajenta ya ce'' ke Atu lafiya me ya faru kike Kuka ne ?"

Yaya shikenan nima rayuwa ta ta zo karshe bazan sake koda 1 mnt a nan din ba ashe dama cin amana ta zai yi ya auri wata ya barni da dakon soyayyarsa Yaya me yasa maza basu da amana .''

Atu babu in da zaki tafi ke waye ya fadamaki cewa zai yi aure ne .''

Falalu neee wanan abokin nasa wallahi idan ban auri I love you dina ba mutuwa zan yi .''

Kuka take kamar ranta zai fita tana Kiran sunnan I love you dina wayo wayooo wayo a i love you dina a kaini wajensa wallahi ina masifa da bala'in da jafa'in da tashin hankalin kaunarsa wallahi gidan nan zan Bari idan ban aure sa ba .''

Inna ce ta ce'' ki ajiye hankalinki Atu insha Allah ke ce ka dai Marwane zai aura kin ji jikale na.''

Mikewa ta yi, ta shige daki duk zafin da ake kwadawa tana zufa tana Kari amma tana ciki ta kulle sai kuka take shi Lawan babban tashin hankalinsa rashin cin abinci da bata yi ba ga kukanta yana daga masa hankali haka wajn Nura ma dan babu abin da yafi kauna sama da Atu sai dan uwansa Lawan .''

Shi kuma Falalu yana ganin tafiyarta ya bushe da dariya ya ce'' yar wahala kawai kina tunanin zan bar Marwane ya mallake ki kina dalleliyar yarinya son kowa kin wanda ya rasa ai wallahi dole ki aure ni domin ina sonki shi munafiki daga zuwansa har ya son hanyar da ya nema ya fadamata abin da ke ransa ka je ka kari ta da Yasmine din.''

★★★★

Kwance take tana ta sharar baccinta ta daura girki ta kyale shi ya yi baki kamar bakin tukunya wani uban naushi taji an sakar mata da sauri ta mike tsaye ta ce'' yess sir .''

Hade fuska ya yi, ya ce'' ke dan iskanci tun dazun na shigo gidan nan ina jin kafurar yunwa shine zaki wani zo ki baje kiyi ta sharar baccinki ni ko Ohoo ko to na baki 3mnt ki kawo min abinci .''

Da sauri Lantana ta nufi kofar fita tana waiwayensa tana sakin murmushi shi kuma in banda harara babu abin da yake banka mata tana nufa kithchen din ta yi sauri sakin salati tare da kashe gaz din jiki na rawa tafara d'aura simple abinci tana gamawa ta zuba tare da kai masa dakinsa da sallama a bakinta ta shiga tana wani fari da Idanu tana gwale baki wai ita birge sa take son yi ,karfa ya yi da karfi tana fadi ke banason iskanci ni sa'an kine zaki din ga mani wani Haka Haka ya fada Yana kwaikwayon yanda ta yi ya ce ki fita idanuna Banason iskanci .''

Turo baki gaba ta yi ,ta ce'' Wata wutar kaunarka da zafin ciwo radadin Sonka suke kullum suke kara haduwa da zuciya ta sai ta aika ma jinin jikina idan ina gabanka sai na rasa natsuwa ta .''

Zaki fice min daga daki ko sai na yi ball dake ke yanzu dan baki kunya ni kike kallo ki ce wai kina Sona .''

Ciwon sone babu ruwansa da kunya .''

Dan biyo ta ya yi, ta dan matsa kadan ya ce'' ki kalleni kin ga nayi maki kalar wanda zaki kalla ki ce kina son shi Banason iskanci wallahi ki fita harakana .''

Sai da ta kai bakin kofa sannan ta ce'' Ina sonka Sweety darling beby dina .''

Takalmin kafarsa yafito zai jefeta  ta wanka a guje tana fadin ina sonka ina sonka beby na .''

Murmushi ya yi, sabida dramer Lantana tana birge sa girgiza kai ya yi ya koma ciki ya zauna yafara cika tumbinsa .''


★★★★

Kusan sati ukku Kenan Marwane yana kiran Atu amma bata dagawa hakan yana matikar bashi mamaki Kenan rashin daukar wayarta sannan ta yi Banza da lamarinsa dan yanzu idan kaga Atu zaka dauka ta yi hankali sabida ta daina shiga harakar kowa duk ta rame kamar bata da lakka ta dan yi haske idanunta sun fada kwance take kan kafafun Inna sai faman kuka take sai rarashinta suke kan ta dauki wayar amma taki dagawa sabida duk gani yake zaginta zai yi ya fadamata magana mararsa dadi .''

Sallama suka ji ana kwadawa da sauri ta mike zaune ta ce'' Inna wanan muryan I love you dina ce dan Allah yaya ka tafi kuyi magana idan dagaske shine din.''

Ajiyar zuciya Lawan ya sauke dan Tuni Nura yafita waje yafito bayan Sun gaisa Marwane ya ce'' dan Allah Atu nake nema .''

Hararensa Lawan ya yi , ya ce'' dan Allah Malam me ya kawo ka kofar gidanmu kazo ka fadamata cewa baka Sonta ko me ka saka mana kanwata cikin tashin hankali Bata ci abinci sai mun yi da gaske .''

Na shiga ukku me ya sa mu Atu din.''

Ciwon Sonka Falalu ya same ta yafada mata wai tafita harakarka sabida kanada wacce kake so kuma aurenta zaka yi dan haka Atu ta yi hakuri da bata mata lokaci da kayi .''

Innalilahi wallahi ban yi haka da Falalu ba ko maganar Atu bama yi tsakaninmu sabida ta tsane sa shi yasa tun yaushe ya fadamata hakan ne .''

Yanzu kusan sati ukku kenan.''

Wallhi yaya dagaske ina son Atu kuma ina kaunarta idan kana tunanin Bana Sonta yanzu mu tafi masallaci a daura mana aure da ita .''

Cike da mamaki yake kallonsa ya ce'' lanle naga kafara shan kwaya kaga Malam bace mana daga kofar gida tun kafin nayi garinka yanzu .''

Haka Marwane ya juya ya yi tafiyarsa ransa a jagule .''
12/10/2022 à 08:45 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

36&37


Ransa a face ya yi gidansu Falalu yana isa yafito ko marfin motarsa ya rufe ba ya shiga gidan yana kiran sunan Falalu tun da ya ji muryarsa ba a yanda ya saba jin ta ba ya sa shi fitowa a tsora ce da sauri ya cakumi huyan rigarsa a zafafe ya ce'' Falalu ni zaka nuna ma cewa Kai dan kunama ne ni zaka yi ma rashin mutumci na dauke ka abokin na gari shine ka mayar da kanka dan iska .''

A'a in dai iskanci ai karamin abu ne a gareni sabida daure yake da kuguna sabida haka da shi nake yawo me nayi maka zaka shigo har gidanmu Kaci min mutumci .''

Ai ni banga mutumcin da zan ci maka ba Banza dan Akuya miye hadinka da Atu me ka Sanar da ita ne .''

Kasan lokacin haihuwa ta da Mamar mu ta gaji sosai da nakuda shine ta bawa akuyar ta karisa fito dani kaga ai dole ta zama uwata .''

Ai naga alama sabida cikin dabbobi kayi wayo .''

Sosai suka yi ta sa'in sa har ta kai ga Marwane ya naushi Falalu nan take bakinsa yafashe ganin haka ya dauko gishiri ya watsa masa a baki ai take Falalu ya kara wata iriyar kara sai ga fitsari mai hade da kashi mai tauri yafito lokaci gudu .''

Mtss Marwane ya ja sannan yafita ya kama hanyar garinsu rai a bace .''

★★★★

Atu kuwa tana ganin shigowar Lawan ta mike tsaye ta ce'' Yaya ina I love you din yake ne naga ka shigo kai day.''

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce'' ni na kore shi sabida ya bata ran kanwata .''

Ai kuwa take tafashe da kuka tafadi kasa tafara birgima duk ta bade jikinta da kasa har gashinta kanta wallahi Allah bazan yarda ba sai ka dawo min da I love you dina wayo na shiga hamsin na fito 60 wallahi ni birni zan tafi idan bai dawo ba .''

Nan Inna ta mike tare da sharara mata mari ta ce'' ke baki da hankali kin san me kike fada .''

Daina Kukan ta yi , ta ce'' na fadi kasa ina birgima babu wanda zai rarashe ni shine za'a buge da mari na hmmm to ga naku sakon .''


Wata mahaukaciyar tusa ta sarkamasu mai zafi da shegen wari ai take duk suka fadi kwance suna neman in da zasu shaki Iska ,Dariya tafashe da ita ta ce'' idan Ba'a rarasheni ba Alkur'an zan kuma yin wata.''

Da sauri Inna da Habi suka dafa kafafunta suna bata hakuri tare da rarashin Nata .''

Ohh duniya huya ba dadi dan kun ga na daga maku kafa kwana biyun nan ina cikin damuwa shine za'a mari ne .''

Nan wata sabuwar tusar ta sake sambada masu ,ai kuwa gida ya riki ce daga Atu ta yi , tusa sai Jamila ta yi tusa sabida tusar da Atu tafara yi farko ta saka cikin Jamila rudewa ganin zasu kashe su a banza ya sa duk suka yi waje da gudu .''


★★★★

Da gudu ta shigo falon kamar wacce aka koro ta nufi bayan Momy da sauri ta mike tana tambayar Lantana ko lafiya .''

Ajiyar zuciya ta sauke tafi ashirin ta ce'' Malam zalumu ne ya biyoni sabida na ce masa ina son shi wai .''

Mtsss Allah idan baki bace min daga wajen nan zan zabga maki mari.''

Turo baki gaba ta yi ta ce'' kema kora ta zaki yi bara na tafi wajen kanwar mijina .''

Har ta nufi hanyar dakin Yasmine sai gata tafito cikin shirinta na zuwa shcool da kallo Lantana ta bita tana rike kasan baki ta ce'' kanwar mijina har kin fito ina zuwa haka Kika sha wanan shiri Irin na Yan Iska .''

Aike ne kika yi ne da zaki tambayeni.''

Wai na zata ko da rikon Jaka ne nayi maki .''

Dama kanki kama yake da Jakar .''

Kin ga tun da gidanmu day kanunmu Irin day ne Kenan .''

Hararanta ta yi ta ce'' kanki ake ji .''

Lantana ta karashe da harare ba mari ba sai de ruwan Ido su tarare ,tsan naga wani mahaukaci ya ce kyaleni kyaleni wanka nake yi .''

Girgiza kai Yasmine ta yi, ta ce'' Momy na fita sai na dawo .''


Ni da ba Momy din ba a dawo lafiya .''

Dariya kawai Momy take biyarsu tana yi masu tare da shigewa dakinta .''

Ita ma Yasmine tafice daga gidan .''
12/10/2022 à 08:45 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*


38&39



Tun a hanya ke Kiran wayarta amma taki dagawa sabida tana waje tana sakin bama bamai ita da Jamila sai da suka dauki lokaci sannan ta kalli jamila ta ce'' fice min daga wuri mai fuska kamar mage mai yanayin angulu .''

Turo baki ta yi tare da hararenta ta mike tare da shigewa dakinta ,ita ma dakin Inna ta shiga nan taga miss call din sa ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' Alkur'an kiransa zan yi wanan shawaran da Habi ta bani cutata kawai take tana shan soyayya da mijinta ni kuma ta hanani soyayya da I love you dina.''

Daukan wayar ta yi , tare da danna masa kira kamar jira yake nan ya yi dauka yana fadin Cutie na ashe har zaki iya mantawa dani haka sabida kin daina sona ko .''

Hmmm ango kenan sai da ka gama shan amarcin naka zaka wani ce min na manta da kai .''

Waye fadamaki nayi aure Cutie?"

Hmm Falalu mana amma Kaci amana ta kuma daga yau bazan kuma daukan Kiran ka ba Tun da kana da mata ni kuma banason wanda ya taba aure .''

Iyeeehhh lanle Cutie to kiyi hakuri amma ni bani da budurwa sai ke ka dai nake yi ma son so marar masultuwa wallahi Falalu karya ya yi maki ce min ya yi yana sonki shi yasa ya hadani fada dake .''

Idan ko gaskiya ka fadamin wallahi Falalu zai gane ba shi da wayo yanzu muka so ma wasar baisan wacece Marfu'atu Buddara ba .''

Me zaki yi masa ?"

Har zata yi magana cikinta ya murda da karfi da alama gudawa ke damunta ajiye wayar ta yi sannan ta nufi toilet ta yi fida cutar cikinta sannan ta dawo ta dauki wayar suka ci gaba da firansu daga haka suka koma ta soyayyarsu kamar basu yi fada ba .''

Suna Kammalla wayar kamar jira take nan tafito daga gidan ganinsu Inna kamar an shanye kayan wanki ya sa ta sheke da dariya ta ce'' ai sai ku kuma ciki sabida warin tusar ya wuce nina tafi yau Falalu sai nayi masa rashin mutumci .''

Tafiya tafara yi Inna nayi mata magana amma ta yi Banza da ita ta yi tafiyarta ,Ohh Allah ni Inna Allah ya shirya min wanan yarinyar .''

Hanyar kare ta nufa ganinsa kwance ya sa ta karisa wajensa tare da sunshina masa takalmin Falalu ai kuwa nan ta har besa da ciki suka fara gudu kan hanya sai gidansu Falalu tana shiga ta ganshi zaune sai kuka yake fitsari na zuba masa dariya ta sheke da ita sannan ta nuna ma karen Falalu ganin fa dagaske wajensa zaya nufa ya sa shi mikewa Sun yi zagaye yafi sau ashirin a cikin gidan sai ihu yake yana bama kare hakuri amma a banza sai haushi yake karawa waje yafita da gudu yana ihu yana jama'a ku taimaka wayo zata kasheni wallahi bana sonki na daina soyayyar muguwa wayo Atu Allah ya isa haka yake gudu yana maimaita maganar Kare sai biyarsa yake ya gaji sosai ruwa kawai yake bukata amma Karen masifar yaki ya rabu da shi ganin zai kashe kansa a banza ya sa ya haura kan Katanga nan karen ya tsaya yana masa habshi ya ce'' zaka ci uwarka idan baka fice min daga nan din nan mugu kawai .''

Saké wani Habshin ya yi ,shi ma ya sake fadin mugu shi ya zo ya cijeni ya barni da wahala to na fika wayo .''

Sake wani Habshin Karen ya yi ,shi ma ya sake fadin ai sai kayi tafiyarka sabida na fi karfinka dan iska kawai .''

Wani Habshin ya yi mai karfi nan Falalu da kadan yafado kasa ya yi sauri rike katangar yana yi ma Karen gwalo .''


Dariya dake boye tana sake shirya masa wani tarkon ta ce'' Mahaukaci kawai sai magana yake shi ka dai wanan gidan mahaukata kawai ya dace da shi.''

Yana nan sama shima Karen yake tafiya Haka rana ke gasa Falalu sai zufa yake shararawa ga kishirwa ta dame sa .''


Wani Katon dutse de ya dauko tare da sai tawa zai kwadama Karen ai ya zabga da gudu , a galabaice ya ce'' amma wannan karen Allah tsine maka Albarka yanzu kasan da dutse zai sakawa ka gudu shine ka kyaleni ina shan wahala sauke ya yi ya biyo ta wata katuwar bushiwa nan ya taka wani zare farar foda ta bade masa fuska sama ya daga kansa nan aka watso masa ruwa masu zafi zafi ai da sauri ya tatare doguwar rigansa ya kwasa a guje yana tsaka da gudu ta jefo masa ICE ya fadi kasa ji kake tummm har ya fashe baki amma haka bai sa ya daina gudu ba da kyar ya karisa gida ya shige daki tare da kullewa .''

Gani ya ci azaba ya sa ATU komawa gida cike da farinciki fal a fuskanta .''


★★★★

Da sallama ya shigo falon Lantana dake shara ta amsa tana fadi Nawan harka shigo .''

Hade fuska ya yi kamar bai taba dariya ba ya share ta ,ganin bai da niyyar magana ya sa ta ci gaba da cewa ni dai ko barkono mutume zai sha wallahi bazan bi tsoransa ba sabida so mugun ciwo ne .''

Tabe baki ya yi bai ce da ita komai ba sannan ta duka ta ci gaba da shararta har ta kariso wajen kafarsa ta ce'' Masoyi hau in goya ka .''

Ajiyar zuciya ya sauke Irin ta addabesa din nan a hasale ya sakarmata zazafen Naushi a baya da sauri ta yi kasa tana fadi wayoo soyayya ta kasheni zai farke min bayana Hajiya ina son shi wallahi wani ya sake sakarmata nan ta zube a kasa tafara kuka sabida yanda dukan ya shiga jikinta sosai .''

Mtss ya ja sannan ya fita tare da shigewa motarsa ya bar gidan .''

Ranta a bace ta mike ta ce'' zaka san ka dakeni wallahi Allah ba Irin Lantana ake zalumta a zauna Lafiya zaka dawo ka sameni .''

Part din sa ta nufa ta share ta tsaf tare da zuba masa mai ta goge terras din da shi tana yi tana sakin murmushi har ta karisa sannan ta dawo part din Momy babu Yasmine nan bare ta ja fada dan haka ta yi zamanta a falon har barci barawo ya yi gaba da ita .''
12/10/2022 à 08:46 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*


40&41


BAYAN SHEKARA 20 

Asalam alaikum yaron yake ta kwada sallama ,fitowa Inna ta yi, daga daki tana hamma tare da amsawa ta ce'' yaro daga ina haka .''

Murmushi ya yi ya ce'' Wai Atu ta zo ana sallama da ita .''

Tun kafin Inna ta kirata tafito cikin shirinta tsaf da ita ta waye ta kara kyau ta kara zama Big girl ta kara haske ka dirinta ya kara fitowa abin gwanin birgewa kalllon Inna ta yi ta ce'' sai na dawo din .''

Jamila ce tafito da yarinyarta a hannu ta ce'' Atu dan Allah idan zaki dawo ki tawo min da comme din nan .'''

Murmushi ta yi , ta ce'' pomme 🍎ake cewa ba comme ba ke har yanzu baki waye ba .''

Hmm ai sai ke amaryan dan birni .''

Ina dangin gulma kice da ita na tafi sai na dawo ki .''

A dawo lafiya suka yi mata Sannan tafita ta bar gidan tana fita kofa ta tsaya yana jingine da motarsa ya dauki style ya hadu sosai ta ce'' kyakyawa na a lokacin da na fara ganinka sai da na sake rumtse idanuna dan tabbatar da cewa ,shin a zahiri nake ganinka ko gifta ne ta cika tunani na lanle Kai din na daban ne ,I love you dina kana da wata baiwa da ba kowa zai iya gane hakan ba ,daga ciki akwaye ta zazakar murya da kuma tattausan murmushi Kai din na daban ne angon Marfu'at ,barka da zuwa .''


A lokuta da yawa kalmomi sukan gagari furtawa ,domin bayyanar maki da addadin yanda sonki yake kara mamaye zuciya ta a kullum ,Bana fatan zuwan ranar da zan gaza wajen nemo kalmomin da zan firta maki cewa ina sonki ,hmm karda ki manta dani a cikin zuciyarki .''

Da akwaye wani da nake gani ko jin muryansa ke zamomin maganin dake warkar da dukan nin damuwa ta ,ba kowa ban face kai hasken idaniya ta.''

Insha Allah zan kasance dake kullum dan ganin farinciki Yana wanzuwa kullum a fuskanki zamu iya tafi matar Marwane .''

A duk inda zaka je ka tabbatarwa kanka cewa ina biye da kai ,ko da banzo a zahiri ba to zan zo maka a cikin bacci ,kai ma zaka zo min à cikin mafarkina ,mu kasance a tare da juna cikin wani kayatatacen lambu mai dauke da furanni mabambantan kaini ,begen ka shine abin yi a kullum , mu tafi hasken idaniya ta .''

Marfin motar ya bude mata Sannan ta shiga ya rufe sannan ya zagayo ya bude mazaunin driver ya zauna tare da jan motar suka dauki hanyar Maradi suna tafe suna firarsu cike da so da kauna har suka isa .''

Tun a kofa Atu ta so nuna halinta na rashin kunya nan ya yi rarashinta yana mata huduba sabida mai gadi daya Bata mata ran, da kyar ya shawo kanta suka shiga daga ciki tun daga shigarsu tafara ganin karamci da nuna kulawa a gare ta musanman kanwarsa Safiya sosai take kulawa da Atu a nan ta huni sai yamma ya zo ya dauke ta da zasu tafi ta sha kayan arziki sannan ta fito suka kama hanyar kauye gudu yake shararawa ita kuwa sai surutu take zubawa tana fadamasa dukan abin da yafaru a gidan wani ya yi dariya wani kuma murmushi har suka Iso lafiya ,tun a hanya da Hasiya da Balki suka hangota ai kuwa suka fara biyar motar da gudu har ta tsaya kofar gidansu Atu suna isowa suka bude marfin motar suna fadin oyoyo ga Atu ta dawo wallahi yau garin ba dadi sabida ba kyanan .''

Shine daga zuwa na zaku wani budé min kofa ba zaku jira I love you din nawa ya bude min ba kun ga dazun da zamu tafi kamar wata yar Sarki ko mai gari haka ya Budé min kofa sannan ya rufe kuma da naje gidansu kanwarsa Safiya sai da ta saya min wani Abu fari mai sanyi da dadi sannan na ci abinci mai masifar dadi .''


Kallon Marwane ta yi, ta ce'' I love you ni fa bansan sunansa ba ka fadamasu .''

Murmushi ya yi, a ransa ya ce'' wato shi dan kauye duk in da yake sai ya nuna halinsa ajiyar zuciya ya sauke a fili ya ce ICE crème .''

Tsale ta yi , ta ce'' yawa iya crème shine ta saya min kin ji dadi kamar zumaa

Dariya ta bashi sosai Sannan ya ce'' Atu ni zan tafi a gidan Sadik zan sauka zuwa safe insha Allah zan dawo.''

Turo baki gaba ta yi , kamar zata yi kuka ta ce'' shine zaka tafi ka barni kasan yau ba muyi zan ce ba .''

Sorry matar Marwane zamu yi insha Allah a waya kin ji yan matana .''

Zaka fara ko menene sholly kuma ?"'

Ina nufin kiyi hakuri ..''

Washe baki ta yi , ta ce'' Tom shikenan sai ka dawo ka kula da hanya sannan ka gaishe min da Sadik din.''

Ok ya fada tare da shigewa mota ya yi gaba abin sa , tun a kofa suke bude kayan atamfofi ne tsadadu masu kyau sai turare da kayan shafa takalmi da dai sauransu Haka suka shiga gida ba ko sallama tafara rafka ma mutanan gidan kira .''

Sosai suka yi farinciki da dawowarta da godiya bisa kan abin Arzikin da iyayen Marwane suka yi ma Atu nan tafida atamfofin ta bama Habi gudu ,Jamila ma haka Inna ta bata biyu sannan ta bama Balki da Hasiya cike da farinciki suke yi ta godiya sai turare kuma ta bama Jamila da Habi ta ce'' su ajiye ma mazajensu baki har kunne sai saka mata Albarka suke mikewa tsaye ta yi ta ce'' Habi ke da Jamila tun da nake a gidan nan baku taba yi man godiya ko sakamin Albarka ba sai yau sabida an karu dani ba .''

To ai dole mu saka maki albarka kanwar mijinmu Allah ya barki ke da I love you din ki .''

Amin tafada tare da shigewa dakin ita da su Balki suka ci gaba da firansu .''

★★★★

Kwanci ta shi babu huya wajen Allah Lantana ta waye Irfane ya saka ta Makaranta ta kara ilimi ta zama Macé wanan shirman duk ta daina yin sa sai shan love suke tun daga lokacin da ta yi masa gugar terras ya fadi ya ji ciwo a kafarsa take kulawa da shi hakan ya saka masa kaunarta suka fara shan love dan yanzu har Dadyn Yasmine ya dawo an fara maganar aure Yasmine kuwa tafara saduda da lamarin Marwane sabida ta kula baya Sonta ga Dady ya matsa kan tafito da mijin aure lokaci day za'a yi da su Lantana .''

Dan Haka ta yanke shawaran kiran Marwane tana kiransa bayan Sun gaisa ta ce'' Marwane nawa ni ka dai ya soyayya ta .''

Murmushi ya yi , ya ce'' sai godiya yakk .''

Alhamdulilah dama dady ne ya ce na fito da miji ganin babu wanda ya dace nayi rayuwa da shi sai kai shi yasa na tuntube ka .''

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce'' Yasmine idan nace bana sonki nayi maki karya sabida ke macece abin son ko wane namiji amma sai de nasha fadamaki ina da wacce zan aure kuma wallahi ta ce min in dai zan yi mata kishiya to bazata aure ni ba yanzu haka cikin satin nan zan Tura magabatana a gidansu a yanzu haka ina garinsu yau na shigo na kai ta wajen Hajiyarmu gobe da safe zan dawo .''

Tun da yafara magana take ji kamar ana watsa mata ruwa masu masifar zafi ta ce'' Marwane ya zaka yi min haka sai da na gama shagala da cewa kaima kana sona zaka iya aure na shine zaka ce min zaka Tura iyayenka gidansu Atu dame tafini ne yar kauyen .''

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce'' ina mai fargaban fadamaki cewa koda bata fiki da komai ba tafiki a zuciya ta bare ma babu abin da zaki nuna mata ki yi hakuri zan kashe kirana .''

Fashewa da kuka ta yi, ta ce'' shikenan Marwane na gode sosai da kalar taka soyayyar a gareni zan rumgumi ka'ddara ta ni a haka ta zo min amma ka sani a duk in da nake ko zan kasance Sonka yana cikin zuciya kuma ina Sonka .''

Tana gama fadan haka ta katse Kiran ta ci gaba da kukanta Lantana ce ta shigo da sallama dauke a bakinta ta ce'' kanwar mijina lafiya kike Kuka me ya faru .''

Lantana Ashe a wanan rayuwar zaka iya neman Abu mafi soyuwa a zuciyarka ka rasa shi ban taba tunani ko da da rana gudu Marwane zai ce baya sona sai da ya Bari na kamu sosai Sannan zai guje min .''.


Zaka iya rasawa sabida masoya da dama Sun rasa cikar burinsu wani matsalar daga iyayensu ,wasu kuma ta hanyar auren wanda basu so wato auren dole ko auren hadi da dai sauransu  duk Irin yanda suke son juna dole su rabu ko da basu taba neman Abun a tsawon rayuwarsu suka rasa ba .''

To yanzu ya zan yi dady ya matsa min da maganar aure .''

Shawara day ce idan zaki dauka .''

Menene fadamin?''

Wanan dan kanin Momy dake sonki ki amince kawai tun kafin Dady ya maki zafin da baki so .''

Hmmm kuma fa hakane zan yi tunani na gode Lantana kawar fada na .''

Murmushi ta yi, ta ce''bara na wuce kithchen ina girki ne kafin Yayanki ya dawo dan ke na rantse sai de girkin ya Kone .''

Da ko kin kashe mu me zamu ci to .''

Ohoo dai zan yi kokari na ja abuna mu tafi restaurant idan ya koshi ba matsala .''

Amma baki da kirki naki kawai kika sani ko.''

Sosai ma ,tafada tana ficewa daga dakin .''
12/10/2022 à 08:46 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*


42&43




Kwance yake ya yi nisa cikin tunaninsa Sadik ne ya shigo kawo masa abinci sallama ya yi masa kusan sau uku amma bai amsa ba sai da ya taba shi ya ce'' Haba abokina wanan wane Irin tunani ne da zai sa ina maka sallama amma baka ji na.''

Ajiyar zuciya yaja tare da fuzgar da Iska ya ce'' wallahi Yasmine ce ta dagula min lissafi nan ya fadamasa maganar da Suka tattauna .''

Tom yanzu ya zaka yi da ita ne .''

Hmm Abokina Kenan la vie d'aujourd'hui la ,il faut s'occuper de soi-même 

( Wanan rayuwar da kake gani wa iya ka iya da kanka ) Allah ba zan yi abin da zan takura ma kaina ba Atu nake so ba Yasmine ba kuma ita ma na sha fadamata hakan dan haka ta rumgume ka'ddara kawai .''

Gaskiya dai kam sabida idan ka ce ka auresu su biyu duk Randa ka fada wata matsala personne ne te fera rien ,ni la famille ,ni te proche ou bien tes amis( babu wanda zai yi maka wai ko wasu dangi ,ko yan uwa , ko abokai ba zasu yi maka ba )

Hakane abokina wanan tunanin shine fal a Raina amma yanzu ka d'aura ni hanya zan tsaya wajen Atu dama c'est elle dan ma vie( dama ita ce a cikin rayuwa ta ) 

Sosai suka tattauna sannan Sadik ya dawo wajen matarsa shi kuma Marwane ya ci abinci tare da mikewa ya shiga toilet .''


Atu na fitowa rakiyarsu Balki ,Hasiya ta ce'' ina da sai mun biya wajen Balla na karfo ma Mama gishiri da Magie .''

Babu musu suka nufi wajensa suna isa bayan Sun gaisa Hasiya ta ce'' Malam balla Mama ta ce wai ka bata gishiri da Magie sai ka hada da wantsan ka yi lisafi.''

Iro dake gefensa ya ce'' kai gaskiya Abokina kana fama diyawa fa D'ailleurs fait attention à mauvaise client's.''
(Kuma.kayi hankali fa dan jarin dake gareka duk sai abu a cinye sa )

Atu ce ta dube sa da yake ita ma Marwane yana koya mana ta France din ta ce'' kafin ka yi gulmar mutume ka tsaya ka yi nazari da suna da shi ai ba zasu zo cin bashi ba Kai idan ba rafe rafe ba me ya kawo ka nan mu zaka yi Karyan iskanci dan ka tafi birni karatu ga ka nan kamar wani dolo ba kama jiki mtsss aikin Banza sai gulmar asara kadai ka ajiye .''


Mamaki ne ya kama shi ta yaya aka yi Atu da Bata yi karatu ba ta san abin da ya fada Anya wanan yarinyar da ba aljanu take yawo ba tsaye ya mike ya ce'' ina ruwanki ai ba dake nake yi ba .''

Mtsss ka dai ji bakin haushi kai Malam balla idan zaka bada ka miko mana muyi gaba idan kuma kaima kabi layin ya'ya'yan Banza masu gulma da sa'ido sai mu ware .''

Karyan iskanci ai dole ki ce Haka cikin garin nan waye bai san cewa ina sonki ba amma sabida kin ga mai kudi kike man hulakanci sabida son abin duniya .''

Cike da isa da gadara tafara ta kawa zuwa wajensa tare da juyawa ta ce'' kai yanzu ka kalleni da kyau ka gani nayi maka da Irin macen da ta dace da kai ai duk wanda ya gani yasan cewa matar manya ce kuma shima mai kudi da kake magana ganin dacewa da cancanta ce a gare sa shi yasa ya bani so ni kuma na bashi kauna .''


Tana gama fadan haka tafito da kudi ta mikewa Malam balla ta ce'' ku gani da kyau ku kara sani ni Atu buddara nafi karfin wulakanci bare wanda nake tare da shi kai BALLA ka fida bashin da kake biyarsu sauran kuma ka kara ka ja jari .''

Tana gama fadan haka ta juya ita da kawayenta suka yi gaba abin su .''

Cike da masifa da tsabar takaici da bakinciki Iro yafara zazaga masifa amma ina ta yi nisa shi kuma Balla dan kudinsa aljihu ya yi , ya kama Iro ya ce'' Iro assois toi d'abord je vais te raconter une histoire.''
( Iro zauna in baka wani labari ) 

Mtss aikin Banza gaba ya yi bai tsaya sauraran Balla ba .''

Dariya Balla ya kwashe da ita ya ce'' pourquoi tu t'inquiètes cette fille de ta famille .''
( Kai ina ruwanka da ita yar gidanku ce ko yar uwarka ce ) 

Komawa ya yi kan tebir din sa ya zauna .''

★★★

Kai amma Atu kin birgeni yanzu kika tabbatarwa da Iro cewa na gaba ya yi gaba , cwar Balki .''

Ai ki barshi wai ni zai Raina ma hankali sakarai kawai .''

Suna isa gidansu Hasiya nan suka bama Mama sakon sannan Hasiya tafara Labartama Mama abin da ya faru ,kallon Atu ta yi , ta ce'' ynzu duk ke kika biya kudin nan suna da yawa fa .''

Murmushi ta yi , ta ce'' karki damu ku uwayene gare mu kin ga dole muyi maku idan muna son ci gaba .''

Cike da kunya da farinciki ta ce'' hakane na gode sosai dan Allah ki hakuri ki yafemin tsanar da nayi maki a baya .''

Karki dama Mama raina bai taba baci akan abin da kike man ba kawai ina mayar da magana ne sabida musha dariya .''

Ja'irar agwagwa kawai Allah ya kara shirya mana ku.''

Da Amin suka amsa sannan Atu ta mike ta ce'' Hasiya ina ga zan koma gida mangariba ta gabato .''

Gskiya ne Mama bara na taka masu yanzu zan dawo .''

Bata ce da su komai ba suka fito ta dan yi nisa sosai Sannan ta ce'' bara na koma zan yi miyar da zamu yi kalaci da ita gobe insha Allah.''

Amma Hasiya da kin bari Mama ta yi ai tasan idan mun fita sai wanda Yaga dawowarmu .''

Wallahi gabana yake faduwa Bana jin dadi kwara na tafi kawai .''

Tom Allah ya sawake sai da safe Kenan .''

Ba damuwa , tana gama fadan haka ta juya su kuma suka ci gaba da tafiya .''

A hanyarta ta komawa gida nan su Iro ,da Ashiru ,Abba suka tari gabanta hade fuska ta yi ta ce'' Iro lafiya zaka tare ni a hanya .''

Wani wawan mari ya sharara mata ya ce'' dazun a kanki watsan buddara ta min rashin mutumci a cikin mutane dan haka yanzu zaki girbi abin da kika shuka .''

Ban gane me kake son fada ba ,ni me nayi kuma ai ban kula ku .''

Wanan kuma ke ta shafa taba Atu garin nan babban tashin hankali ne sabida ita kanta bala'i ce amma yau zamu yi maki fyade shine abin da zaki girba ina fatan kin gane .''

Baya tafara yi gabanta na tsananta faduwa tana kallon hanyar da su Atu suka bi ko da zata hango su amma babu alamarsu ''kaga Iro Karka tabani wallahi zan yi maka rashin mutumci .''

Dukansu suka tarar mata suka mata shegen duka sannan duk suka yi mata fyade a some take sabida ta sha duka na fitar hankali batasan me suke yi mata ba Tun shigar da Iro ya yi , mata cike da mugunta ,sai da Suka gama sannan suka bar wajen da gudu .''

Jin shiru ya sa Mama fitowa tana dubawa ina Hasiya ta jima ita da ta ce ba zata jimawa shine zata kai har wajen karfe 9h wanan wane Irin iskanci ne Haka take tafe tana fada nan suka ci karo da Malam tsalha dake bayan layinsu ya dauko Hasiya duk jini a zaninta ga fuskanta duk ta kumbra .''

Cike da fargaba ta ce'' Malam lafiya na ganka da Hasiya haka me ya same ta ne .''

Tom wallahi ban sani ba nima nazo wucewa ne na ganta kwance bata ko motsi .''

Tom dan Allah ka shigo min da ita daga ciki idan ba damuwa .''

Juyawa suka yi suka koma gidansu Hasiya har cikin daki ya ajiye ta sannan Mama ta yi ,masa godiya ya yi tafiyarsa kallo day Mama ta yi mata ta fashe da Kuka mai cin rai da tafiyar da zuciya mai saurare ruwa ta debo tare da yayafa mata su nan ta farka da ihu tana Kiran Iro dan Allah kayi hakuri Karka tsutar dani .''


Kallon Mama ta yi , ta ce''dama Iro ya yi maki hakan ?"

Fashewa ta yi da kuka nan suka rumgume juna suka ci gaba da Kukan babu mai rarashin dan uwansa .''

Garin nayin haske ta gyara jikin Hasiya sannan ta fito ta nufi gidansu Atu nan tafada mata Hasiya Bata da lafiya tana son ganinta .''

Babu musu tafito suka tafi suna isa ta fada dakin Hasiya ta ce'' Ashe baki jin dadi shi yasa jiya kika dawo gida me yake damunki ne sai mu tafi Asubiti .''

Fashewa da kuka ta yi , tana kallon Atu cike damuwa ta ce'' lafiya kuke kuka Hasiya dan Allah ki fadamin?"

Cikin Kuka ta ce'' Atu ke ba wacce zan boye ma abin da ya faru dani ba ce sabida kin wuce abikiya ta ke yar uwa ta jiya Bayan mun rabu da ku su Iro da suka dake ni sabida sabanin da kuka samu da shi wajen Balla Hakan bai ishe su ba sai da Suka hada da yi min fyade yanzu shikenan nima bazan kai labari gidan mijina ba ko saurayi bani da shi bare na san me iya daukar ka'ddara ne ko akasin hakan.''

Cike da kariyar zuciya Atu ta ce'' Sabida fadan da muka yi shine zai huce haushinsa a kanki ni uban ya ce ba zai zo ya neme ni ba sai ke wallahi sai ya gane bashi da wayo.''

 wayarta ta janyo tare da kiran Marwane bugu biyu ya dauka a take tafashe da kuka ,cikin damuwa ya ce'' Cutie lafiya kike Kuka gani a Kofar gidanku yanzun na kariso .''

Ina gidansu Hasiya kawao tafada tare da katse kiran .''

Cike da tashin hankali ya shiga mota tare da nufa gidansu Hasiya yana isa ya kirata ta ce zai iya shigowa ,da sallama ya shiga nan ya ci karo da Mama bayan Sun gai sa ta ce'' yaro ka wuce suna ciki.''

Shiga dakin da ta nuna masa ya yi , Atu na ganinsa tafada jikinsa tare da kara fashewa da wani sabon kuka shima matsata ya yi gam a jikinsa dan tunaninsa wani abun ne ya samu Atu ganinta cikin koshin lafiya ya sa shi jin dadi,ajiye kansa ya yi sannan gashin kanta ya ce'' Cutie pourquoi pleure tu,(me yasa kike Kuka) ?"

Cikin kuka ta ce'' I love you su Iro ne .''

Cike da damuwa ya ce'' me suka yi maku ne ki yi magana Cutie ?"

Raba jinkinsu ta yi ,sannan tafara bashi labarin abin da yafara har izuwa fyaden da Suka yi Hasiya .''

A fusa ce ya ce'' sabida kin fada masa gaskiya kuma shine yafara tsokanarku zai yi mata hakan wallahi Allah ya rufa masa asiri da ba Kece ya taba ba amma wanan ma zai zama izina da mai Irin halinsu dan iska kawai .''

Wayarsa ya fito da ita tare da kiran wani yaronsa ya ce'' ina son ku turo min da motar police ina nan kauyen Madarumfa .''

Ok sir ,ya fada sannan ya katse kiran ,cike da bada umarni nan suka shiga mota bayan ya fada masu Oga yana son ganinsu nan suka kama hanyar Madarumfa .''


Suna shigowa cikin garin suka kirashi nan Atu ta bashi adresse din wajen da su Iro suke zama da gidajensu .''

Haka ko aka yi duk a gida a kamosu nan suka yo gidansu Hasiya tun da Iro ya ganshi kofar gidan ya san abin da Suka aikata ne za'a hukunta su a kai .''

Atu da Hasiya sai Marwane ne suka fito cike da kallon kaskanci Atu ta wanke Iro da mari ta ce'' tirr da halin Iro ka ji kunya dama ba tun kuke bukatar irin wanan damar dan kun lalatamana rayuwa idan ba zaka manta ba kun taba biyomu bayan mun dawo daga dandali to mune Aljanun da muka kora ku sabida tun farkon haduwa da kai na gane nufinka a kaina ni da kawayena dan Haka Muke taka tsan tsan daku amma duk da hakan sai ka aikata abin da nake gujemaka Faruwa hakan a rayuwarka wallahi sai ka gane kowa da kalar nasa iskancin sannan iskancin wani yana gaba dana wani .''

Kallon Marwane ta yi , ta ce'' I love you ina son idan kun tafi da su sunsha duka na fitar hankali sannan hannayensu da Suka yi anfani da su ta hanyar dukanta a yanke ma kowane yatsan hannunsa biyu sannan duk wata azaba ta duniya wace zata wahalar da su a saka su idan ka yi min haka shine zai kara tabbatarmin da shaidar cewa dagaske kana sona .''

Karki damu matar soja Marwane wanan umarnin ki dauka kin samu .''

Kallon Sharif ya yi , ya ce'' ku tafi da su zuwa an jima zan zo insha Allah .''

Daukan su Iro Aka yi a wulakance aka saka su a mota nan suka bama mota huta zuwa Maradi .''

Cike da farinciki da jin dai Mama da Hasiya suka rumgume Atu suna mata godiya ita da Marwane .''

Daga Hasiya daga jikinta ta yi ,ta ce'' ki daina kuka kawata bansan miye abota ba sai da na hadu dake kice abokiyar da bani da tamkarta a rayuwa ta sabida ke din ta musanman ce a gareni taya kina cikin damuwa zan barki a cikinta ni miye anfani na .''

Ina godiya Sosai matar I love you kuma Soja .''

Sosai ta kwantar mata hankali ta ce'' ki koma ciki ni zan tafi gida an jima zamu zo ni da Balki .''

Tom shikenan sai an jima , cike da farinciki suka koma gida ita da Mama suna shiga Hasiya tafadi kasa jini ya balle mata .''

Da gudu Mama tafito ganin su Atu ba su kai ga tafiya Ba ta ce'' Atu jini dan Allah ki taimaka min .''

Da gudu suka koma tare da déjà har ta suma nan suka kwaso ta suka zuba a mota nan suka yi Asubitin dake cikin gari babba mai tsadar gaske suna shiga nan aka karfe ta sabida Sanin Marwane ko wanene ya sa suka fara Bata taimakon gagawa Sun jima sosai a ciki sannan Doctor yafito ya ce'' Marwane ya shigo Yana son ganinsa .''

Babu musu ya bi bayansa bayan Sun zauna Doctor ya yi , yan rubuce rubucensa sannan ya dago tare da kallon Marwane ya ce'' Yallabai miye halakarka da yarinyar nan .''

A takaice ya ce'' yar uwa ta ce lafiya dai?"

Sakamakon binciken da muka yi shine an yi mata fyeda na mugunta da son zuciya sannan ayi amfani da reza wajen tsatsaga wajen sannan kafarta ta goce sannan yau tatashi Bata ci komai ba hakan ya haifarmata da zubar jini sabida tsatsagata da Suka yi .''

Cike da kariyar zuciya ya cire hulansar yana fizgar da Iska daga bakinsa ya ce'' wato kashe ta suka so yi hmm .''

Takarda Doctor ya mika masa ya ce'' a soya mata wanan maganin zuwa an jima idan ta farko zamu Bata su sabida Alluran bacci da muka yi mata .''

Godiya ya yi masa sannan yafito jiki a mace yana fitowa Atu ta Dube sa ta ce'' I love you lafiya me yafaru da ita .''

Hannunta ya ja suka fita cikin bacin rai ya ce'' wanan Iron dan iska ce mugunta ya yi ma Hasiya fa nan ya kwashe komai ya fadamata sannan ya ja kunnenta kan karta kuskura tafada Mama .''

To yanzu ina zaka tafi beby .''


Police station yau da kaina zan yi masu hukunci .''

Murmushi ta yi, ta ce'' bara mu kyauce yau an taba zuciyar yan maza .''

Shi ma murmushin ya yi, mata bai ce komai ba yafada mota ya yi gaba .''

Ita kuma ta shiga daga ciki Mamma na ganinta ta ce'' Atu miya faru da Hasiyar ne .''

Karki damu Mama bubu komai jini kawai ya balle mata amma Likitoci Sun shawo kan lamarin yanzu haka ma Marwane din yatafi sayo mata magani .''

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' har hankali ya kwanta ina godiya da kulawa .''

Babu komai Mama .''

Suna nan zaune har tsawon Awa 5 sannan wata Norse tafito ta ce'' wacece Atu ?"

Mikewa ta yi, ta ce'' gani .''

Marar lafiyar nan ce take son ganinki .''

Har ta Farka ne .''

E'ee tabata amsa bayanta ta bi suka nufi dakin da sauri Atu ta nufi wajenta tare da kama hannunta tana zama daga gefenta cikin Kuka Hasiya ta ce'' Atu ha Kika nayi farinciki ganin Allah ya sa an kama su Iro ta sanadiyarki naji dadi sosai akan jajircewarki sannan ina Alfahari da ke sannan ki kara rike Marwane sabida masoyi ne na gaskiya sannan samun irinsa sai an dage a madadin kauna da abotar da ke tsakaninmu dan Allah karki rabu dashi koda me zai maka sannan karki bata masa rai na jima ina burin nayi aure na rayu da mijina cikin farinciki da kulawa amma sam hakan ba zata yiyuwa a sabida Haka nake neman yafiya a gare ki ke da Balki da Mama ko da d wanda nayi ma ba dai dai dan Allah ku gaffartamin .''

Haba mana Hasiya wace Irin magana kike hakan ai baki mana komai hakika ma ke yar amana ce sannan nayi maki Alkawarin duk rantsi duk wuya ina tare da Marwane .''

Naso ganin aurenku sabida naga gidanki da rahar da zamu din ga yi idan mun tafi gidanki da yaranki amma Hakan Bata faru ba ina maki fatan alkairi da zaman lafiya a gidanki .''

Zaki gani insha Allah Zaki warware ki dawo kamar kowa ciwo ai ba mutuwa ba ce .''

Wani tari ta yi ,mai hade da jini da sauri Atu tafita ta Kira doctor nan suka shigo suka fara Bata agajin gagawa Atu da ta fadama Mama halinda Hasiya take nan suka yi ta Kuka .''

★★★

Marwane suke yana fita Office din su ya nufi yana isa ya cire doguwar rigarsa daga shi sai karama sannan ya bude office din sa ya dauko centure da wata karamar akwati ya saka aka bude masa wajensu Iro nan ya shiga tare da yaransa biyu kulle kofar Aka yi nan ya gansu a yashe ayi masu azababen duka babu neman shawara ko wata magana Marwane ya shiga jibgarsu yana dukansu suna suma yana kwarara masu ruwa suna sake farfadowa sannan suna komawa suman sai da ya yi masu lis sannan ya ce'' uban waye ya bada shawaran ayi ma Hasiya fyade .''

Da sauri Ashiru da Abbas har hade baki suke a tare suka ce Iro ne wallahi Iro ne .''

Jinjina kai ya yi , ya ce'' waye ya bada shawaran tsagatsaga a kasanta ne .''

Iro da Abbas suka ce Ashiru ne sabida mun nemi hanyar shiga Bamu samu ba .''

Ohh shine suka nemi kashe yar mutane idan baku da ilimin kan lamarin uban da ya aike ku yi mata fyade .''

Wani tsautsayi ne da karar kwana .''

Idan kun tafi Kotu zaku fadamasu tsautsayi ne .''

Yana gama fadan haka yafito daga wajen wayarsa dake ta ringing ya dauka ganin kiran Atu ya sa shi dagawa cikin kuka ta ce'' I love you ,Hasiya babu ita .''

Cikin tashin hankali ya ce'' ta mutu .''

E'eee dan Allah ka zo .''

Jifa yayi da wayarsa sannan ya yi rubutu ya bama Kamilu suka tafi kotu da ita bisa kan maganar kisa da fyaden da su Ashiru suka yi ma Hasiya .''
12/10/2022 à 08:46 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*


44&45



Yarane na gani a harabar gidan da manyan mutane suna kai kawo a cikin gidan dan gidan makil yake da jama'a mutane arziki daga cikin falon kuwa ko hanyar da zaka bi ka fito babu dakin da amare suke ciki na leka naga sai wasa da dariya suke tsakaninsu da kawayensu sai shegentaka suke ma Lantanar da yanzu ta kara kyau ta yi fresh da ita gwanin birgewa shagali ake sosai a gidan har aka daure auren Lantana ita da sahibinta Irfane Alhaji Habibu bisa sadaki dai dai yanda shari'a ta gindaya ,sai na Yasmine Alhaji Habibu da Abin kaunarta Moctar Haruna bayan an d'aura Abokan Arziki na ta Taya ango murna su kuma amare wanka aka yi masu sannan Aka jasu zuwa dakin kanin mahaifinta inda aka daura auren suka yi masu nasiha mai ratsa zuciya sannan aka fito da su nan aka nan fa aka mai dasu dakin da kawayensu suke nan aka  shiga daukar hoto dare nayi aka dauki amare day Aka yi gidan Irfane da ita day kuma gidan Moctar .''

★★★

Marwane na Isa ya fito tare da shiga ciki Mama ka dai ya gani nan ya shiga tambayar ina Atu take .''

Tana watsan dakin suma ta yi ,lokacin da kuka karisa waya .''

Mama sannu ki hakuri Allah ya jikanta da Rahama dama duk me rai sai ya dandana zafin mutuwa .''

Hakane Dana na gode sosai Allah ya biyaka.''

Amin ya fada sannan ya shiga daga ciki nan aka shirya gawar sannan suka fito da ita bayan ya duba Atu har yanzu bata Farka ba dan haka ya sa wata Norse ta kula da ita tare da sécurité d'Anna suka tafi kauye suna shiga nan aka kai ta gidan mai gari nan aka tara mutane aka yi mata sallah sannan aka tafi kai ta makwancinta na gaskiya sosai mutuwar Hasiya ta bama kowa mamaki musanman Balki da ta rabu da ita basu wani jimawa kuka kasa zuwa mata ya yi tsabar mamaki gidansu Hasiya ta nufi ganin dagaske fa babu Hasiya ya sa tafashe da wani mahaukacin Kuka ta ce'' Mama ina take ina kika kai min Hasiya ta ne dan Allah ki ce min tana daki .''

Mama ma fashewa ta yi , da kuka tana rarashin Balki ita kuma sai kuka take .''

Atu na farkawa ta shiga dube Dube nan wata Norse ta ce'' Sannu Madame yanzu yallabai Marwane zai dawo ya ce na kula dake .''

Kulawar ta ci uwarta munafuka kawai .''

A tsora ce Norse din take kallon Atu da duk ta rikice ta fita hankalinta ta nufi hanyar waje da sauri Norse din ta ce'' Madame ina zaki tafi .''

Harara ta balla mata ta ce'' idan zan tafi ki Hanani fita .''

Tabe baki ta yi, sannan ta kyale ta tana fitowa taga sécurité har biyu da sauri suka tare hanya day daga cikinsu ya ce'' Ranki shi dade ina Zaki tafi ne?"

Wajen Hasiya zan tafi nasan yanzu tata shi bata aiko kirana ba .''

Ranki shi dade ai Sun tafi da ita dan yanzu ina kyautata zaton a Kaita makwancinta.''

Kallon baka da hankali ta yi masa sannan ta takarkare zata gudu nan suka yi saurin rike ta ihu yake su saké ta amma Sun ki gantsara ma day daga cikinsu cizo ta yi, nan ya ji zafi ya sake ta nan ta yi waje da gudu kamar sabon kamu dai dai Marwane ya shigo sabida dama Sun hanya Norse ta kira sa tafada masa abin da Atu take yi shine suka tawo asubitin nan ya yi ram da abarsa ya rike ta gam kankame sa ta yi, tana Kuka sosai .''

Cutie sorry ki natsu mana kin ji matata ina tare da ke .''

Daina kukan ta yi ,sannan ya ja hannunta suka shiga mota nan ya dauki hanyar gida da ita sabida nemanta da ake yi dan sai da ya sanar da gidan halin da ake ciki sannan hankalinsu ya kwanta tana kwance jikinsa har bacci ya dauke ta ,kamshin gashin kanta yake Shaka sai lumshe Idanu yake yana saka abubuwa da dama a ransa har suka kariso Marfin motar aka bude masa sannan ya dauko ta kamar baby suka shiga daga ciki Nura da Lawan suna ganinta suka nufito da sauri sajent ya tare su tare da girgiza masu kai baya suka koma sannan Inna ta shimfida Tabarma ya ajiye ta sannan ya gyara zamansa ya ce'' Inna gatanan yanzu haka mutuwar nan ta tabata sai kun kara hakuri da ita yanzu na samu ta yi bacci dan Allah karku takura ta sabida hakan zai sa tata shi da wani ciwo sabida katse mata baccin da kuka yi sannan insha Allah ganin wanan damuwar tafita a kanta zan yi kokari na turo da magabatana ayi maganar aurenmu cikin satin nan sabida rabata da garin nan shine zai taimake ta dawo kamar yanda take a baya.''

Nura ne ya ce'' wallahi idan zata kwantar da hankalinta sabida yanayin shakuwarsu da Hasiyar zai iya tabata Kenan daga zarar anyi sadakan uku ka turo a saka Rana ku tafi Allah ya kiyaye hanya .''

Hakane maganarka Yaya dan kwanciyar hankalinta shine namu idan ta samu natsuwar daga baya Tazo ganinmu .''

Mikewa Marwane ya yi, ya ce''tom shikenan bara na koma dan Allah a kula da ita sabida zan tafi bisa casse din su Iro sai zuwa jibi zai muzo tare da iyayen nawa sabida nazo mata da labari mai dadi .''

Insha Allah babu damuwa zamu kula da ita .''

Fita ya yi ,ita kuma Atu Bata Farka ba sai wajen karfe 14h lokacin duk mutanan gidan suna nan Sun saka ta gaba suna kallo kallon Inna ta yi , ta ce'' ina I love you din yake ne?"

Yatafi Kotu ake nemansa zai dawo idan ya samu lokaci .''

Tsinani Allah Ubangiji ya tona ma duk mai Irin halinsu Iro asiri idan masu shiryuwa ne kuma Allah ya shiryesu .''

Da Amin duk suka amsa sannan ta mike ta nufi toilet wanka ta yi , sannan tafito shiryawa ta yi tafito waje kallonta Inna ta yi , ta ce'' Ina zuwa Atun Inna ?"

A takaice ta ce'' gidansu Hasiya zan tafi .''

Tom bara mu tafi tare dan dama ina jiran ki Farka ki ci abinci sannan .''

Kamar zata yi kuka ta ce'' Bana ci Inna bana jin zan iya tauna wani abu sabida komai ya fita a Raina .''

Habi da Jamila ma hijjab suka dauko nan suka nufi gidansu Hasiya suna isa wajen Mama da Balki ta nufi tsabar Kukan da Atu ta sha har idanunta da fuskanta Sun kumbra wajen ya yi jajir Balki tana ganinta ta ce'' Atu ya muka ji hakuri kuma .''

Idanunta ne suka kawo ruwa nan ta kalli Mama ta yi mata alama da kar ta yi ,duke kanta ta yi ta ce'' sai hakuri sai de mu ce Allah ya mata rahama kabarinta .''

Haka suka sha zama wanan gudun hunin kasancewar Atu bata sallah sai su Balki kawai ke tashi sallah .''

★★★

Marwane yafita yanufi Kotu nan shigar da kara tare da shaidar da za'a gabatar sannan yafita zuwa gida nan yake Sanar dasu abin da yake Faruwa .''

Shiryawa suka yi suma suka tafi kauyen su Atu tun da sasafe ,shi kuma ya tafi kotu sabida kallon karar da za'a gabatar .''

Tsabar dukan da Suka sha bama ka iya gane fuskokin su Iro ga tsoron Marwane daya mamaye zukatansu hakan ya sa suka Bada kai bori ya hau suka zayyane gaskiyar abin da yafaru nan Kotu ta yanke masu hukunci kisa tare da tarar 1millions ga dukansu sannan aka tashi cike da farinciki Marwane ya dawo gida sabida ko ba komai ya cika burin Hasiya da Atu sabida jin dadinsu gida ta koma ya samu  wutu sannan ya kira Hajiya suka shai da masa Sun zo lafiya sannan ya ce'' su yi baccinsu a tsan sabida gobe zasu tawo shida su Abba sai su koma tare .''

Duk da Atu ta kasance cikin damuwa hakan bai hana ta nuna kulawarta kan Hajiya da Safiya kanwar Marwane kuma Sun yaba da jajircewarta dare nayi suka dawo gidansu Atu a nan suka yi bacci ,tun da sasafe su Marwane suke zo sabida su samu addu'a kuma alhamdulilah ayi ta da su dama a masallaci ne nan aka daura aurensu shi da Marfu'atu duk da tana cikin damuwa mai tsanani hakan bai hana ta farinciki ba amma ta danne sa sosai Mama ta Taya ta murna ita da Balki da Kaka sai mutanan arziki Hajiya kuwa sai kulawa da Atu take tana kara shagwafata .''

Sai da Suka yi sati Cif sannan suka tawo da Atu a nan gidan Hajiya ta zauna inda ta saka aka fara gyara ta ciki da waje Marwane kuma ya matsu satin nan ya tawo a kawo masa amaryarsa .''

Tun da Atu tatafi gidan ya yi shiru babu dadi musanman Habi da Suka fi yin dramer har kukan rashinta sai da ta yi.''
12/10/2022 à 08:46 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*


46&47




Tun da Atu ta bar gidansu Habi ta dasa sabon iskanci sabida cikin da take dauke da shi bata girki Bata shara sai kwanci tare da rashin kunya tana ci tana sakin Iska wato tusa tana waka tana Burr burrr burrrrr sai ta karka ce kugu dama zuwa hagu take sakin tusar abin har ya zama kar waka take rerawa ganin haka ya sa Jamila fara yi mata kida dan Jamila yana rawa ita kuma Habi tana bankada tusa sai da ta gaji ta mike tsaye ta ce'' wato na kula ke Jamila bakin ciki kike man taya ina tusa ba zaki hanani ba kar yarona yafito ta tsakiyar kai tsabar wari shine zaki tayani da kida .''

Tabe baki ta yi, ta ce'' zancen burr inji tusa da karki daina tusar ai ni dadi ta yi min idan kin samtalo yaronki ya koma dan Habi Buddari ba shikenan kin ga ya yi gadon uwarsa Atu buddara .''

Fashewa da kuka Habi ta yi , ta ce'' Amma Jamila baki kirki kin san da hakan shine zaki kyaleni kullum nayi ta sambada tusa .''

Dariya Jamila ta buge da ita ta ja hannun danta suka yi daki tana yi ma Habi gwalo .''



★★★★★

Kwance take saman 3st tana latsa waya wata hadadiyar yarinya na gani wacce ba zata wuce 21 ba kyakyawa ce ta sha gyara jikinta sai sheki yake fatarta ta kara haske hade da masara kadan sai ya kara mata kyau fatar jikinta sai taushi da daukar hankali da sallama ya shigo bata dago da kanta ba ta amsa karisa shigowa ya yi daga wajenta kanta ya dafa kujerar da take kwance ya dan yi mata rumfa ya ce'' wato Cutie kin manta dani ko baki kulani kuma bakisan ki tare a gidana ni ka dai nake kewar muryanki murmushinki da ma ke kanki .''

Tana daga kwancen bata daina abin da take yi a wayarta ba ta dago ta kalleni ya yi masifar kyau cikin wani yadi pink shara shara dinkin da gani ya sha aiki sannan an sauke masa Money murmushi ta yi tare da sauke idanunta ta ce'' I love you a duk in da nake dole na kasance cikin tunaninka nima ina kewarka sosai Hajiya ce ta ce karna sake kula ka da kuma daukan wayarka har sai ta kammalla abin da take .''

Shine zaki kyaleni in ta shan wahala a kanki uhmm uhmm ni dai kizo mu tafi gidanmu .''

Ka tambayi Hajiya idan ta amince kayana a shirye suke .''

Amma yau fa sati day Kenan dan Allah ki rarashe ta ki dawo gareni .''

Tabb Allah bazan iya ba haka kawai ta ce min bani da kunya.''

Murmushi ya yi sabida yanda Atu ta karashe maganar kamar wato yar fari dakin Hajiya ya nufa bayan ya gaida ita ya ce'' Hajiya wai yaushe Atu zata tare ne.''

Tambaya kake ko neman sani ?"

Babu ko day kawai nazo ki fadamin ne .''

Yaushe zaku yi tafiyar wajen aikinku ne .''

Yanzu hajiya sai na dawo zata tare amma fa ina shan wahala sosai Hajiya nan da wata day ne .''

Kallon dan Nata ta yi duk ya dan rame ya yi baki kadan sannan ta ce'' To ka tashi idan ka dawo daga tafiyar sai kazo ka dauke ta .''

Cikin ransa bai ji dadi ba amma haka ya mike yafita jiki ba kwari yana fitowa ya nufi hanyar fita ganin bai kulata ba ya sa ta bi bayansa da gudu tare da rumgume shi ta baya ta ce'' I love you shine zaka fita ba zaka ka ce min na yi maka rakkiya ba .''

Dawo da ita ya yi gabansa cikin sanyayar murya ya ce'' idan na kiraki kin rakani ba tare zamu tafi ba haka zan juya na kyale ki cike da kewarki zan tafi ina tunanin wane hali kike ciki kuma ke naga kamar baki damu dani ba shi ya sa zan yi tafiya ta .''

Hannayanta ta d'aura kan fuskansa ta ce'' haba mana I love you dina Allah zuciya ta cike take da muradinka tunaninka da kewarka me yasa zaka hukuntani ta hanyar kyaleni kasan Irin damuwar da zan shiga ne .''

Hannayenta ya sauke kan fuskansa ya ce'' na makara aiki sai na dawo ki kula da kanki .''

Ganin zai tafi bai bata ajiyar da ya Saba sauke mata ba ya sa ta fashe da Kuka juyowa ya yi ya ce'' Menene kuma Cutie na ?"

To ai zaka tafi baka min kusss din nan ba .''

Murmushi ya yi , tare da share mata hawaye ya ce'' kiss ake cewa matar Marwane .''

Ohoo ni ina ruwana inda zaka min ba sai nasan sunnansa .''

Rigimamiya kawai yafada tare da danna mata lafiyayen kiss .''

Murmushi ta yi , sannan ta yi ciki a guje .''

Girgiza kai ya yi hade da murmushi sannan ya yi gaba abin sa .''




★★★★

Lantana kuwa sai zuba hau din ta take tun Irfane na hakuri har ya kai ya yi mata magana zata daura girki ta kyalesa wani lokacin har sai ya Kone wai bacci take sannan idan tatashi zata zabga masa uban gishiri wai ita ramuwa take kan abin da yake mata a gidansu .''




★★★★

Yasmine kuwa Masha Allah zamansu gwanin birgewa babu wata matsala sai shan soyayyarsu suke duk da bata jin son shi har yanzu amma tana koya ma zuciyarta dan samun zaman lafiya mai daurewa
12/10/2022 à 08:48 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

48&49




Marwane yana tafiya Hajiya tafito ganin Atu Bata falo ya sa ta leka Window duk abin da suke a gabn idanunta Hakan ya sa ta yanke shawarar kwara su tafi tun kafin su yi abin kunya a gaban idanunta da sallama Atu ta shigo ganin Hajiya zauna a Falo wata kunya ta kamata haka ta wuce sum sum zata huce daki Hajiya ta ce'' Marfu'atu ki hada kayanki Bayan Mangariba zaki tare a gidanki karku tsinye soyayyar a waje .''

Babu kunya ta daga tsale sosai tare da sakin tusa burrr ta ce'' gaskiya Hajiya naji dadi bara na tafi na fara shiri dan har na kagara Mangariba ta y i.''


Da mamaki Hajiya take kallonta hancinta a rufe sabida tun da Atu ta zo gidanta Bata taba Sakarma Hajiya turare ba sai yau ai baki day falo ya karade da shi ganin Kamshin Al'muski na shirin kashe Hajiya ya sa ta koma daki tana sauke ajiyar zuciya .''


Atu na shiga daki Safiya dake kwance tana sharar baccinta ta zubama naushi tare da kyauta tusa dai dai bakinta da hancinta wata iriyar karar neman taimako ta kwala ta danne hancinta ta ce'' Aunty lafiya kike kuwa wanan surnanin tusar da kuka min laifin me nayi maki ne .''


Ina cikin farincikine ita ma tazo tayani murna ne .''

To sai ta hada da cuta gaskiya bazan iya zama dakin nan ba .''

Kara sakin wata tusar ta yi,ta ce'' Ke yau zan koma wajen I love you dina fa .''

Gaskiya ai kwara ki tafi idan kika zauna kina min wanan zazafar tusar taki zaki kumbra min ciki in tsule da bahaya .''


Wata uwar sahihiyar tusar ta saki mai mugunta warin masifa ,Safiya kamar an koro ta ko taga dodo hakan ta bankada da gudu jin falon shima da kalar nashi kanshin ya sa ta shigewa dakin Hajiya dake zaune tana sauke ajiyar zuciya tun da ta shigo dakin dan ji take dakinma warin tusar tana sauke ajiyar zuciya ne sabida ta ji ko baya yi  da gudu tafado dakin tana kiran Hajiya ! Hajiya ! Hajiya! Wanan matar zata kasheni da tsamin tusa .''

Hajiya ta mike tsaye Kenan suka ci karo da Safiya tana shigowa a guje ai kuwa suka ci karo goshinsu ya bada karar garamm à take Hajiya tafara tana Kiran A'aaaaaa ta kasheni ta fadi kan gado tare da dafe kanta , ita ma Safiya hannunta yana dafe da dai dai idan suka bugu .''


Atu kuwa hankalinta kwance bata 1mnt ta saki tusa har ta gama hada Kayanta da duk abin da zata bukata sannan ta yi dakin Hajiya tana shiga da sallama tusa na mata amshi ai Hajiya bata warware ba ganin Atu ta sanyo kai ya sa ta yi ta Garauhu tare da samun hanya ita da Safiya suna rigagin fita sai waje Atu kuwa shekewa ta yi da dariya tana fadin kai duniya fida cuta a ciki akwaye dadi sakin iska musanman nawa akwaye kara lafiya bara naga ina zasu nufi .''.


Cike da mugunta ta yi waje ai Hajiya batasan lokacin da tafada dakin mai gadi ba ,Safiya kuma tafada Toilet din mai gadi  ba ko takalmi ga wajen duk tsami amma tusar Atu tafi gigita mutume hakan yasa bata Ankara da wajen da ta shigo ba bare ta ji warin toilet din .''

Me gadi kuwa sama ya haura sabida tunaninsa wani abun ya biyo su Hajiya .''

 
Ita kuma zaune ta yi tsakar gida tafara kida tana sausayawa sai da ta gaji sannan ta koma cikin dakinsu kusan Mangariba tana shiga daki tafada toilet ta d'aura Alwala ta tafara sallah .''


Hajiya dake daki sai zufa take sai yanzu ma tafara jin warin daudar dakin mai gadi da kayan daudarsa da sauki tafito tafara sauke ajiyar zuciya Bata hutawa ba na bin wata haka take jera su .''

Safiya kuwa sai a lokacin ta kula da wata katuwar tsutsa dake tunkaro kafarta da sauri ta kwallara kara tafito waje tana kakafe kakafe kamar mahaukaciya ai daganan tafara sheka amai sabida tsamin da kewayen yake zubawa Hajiya ce ta shiga ciki dar dar ta dauko ruwa a frige ta zabga a guje sai wajen ta mikawa Safiya sai da ta gama shan ruwa sannan suka yanka a guje suka.fada tsohon sashin Marwane suka rufe ruf .''

Atu kuma tana kammalla sallah ta koma toilet din ta yi wanka tana fitowa ta dauki wanka ta yi wanka turare sai zuba kanshi take mai dadi fitowa ta yi ,sai da ta leka dakin Hajiya babu kowa sannan tafito waje ganin basunan ya sa ta tambayar mai gadi ya ce suna part din Marwane wajen ta nufa tare da fara nocking Hajiya ta ce'' waye ?"

Hajiya nice na Kammalla shirina shine nace kizo ki kaini gidan mijina.''

To naji zan fito amma dan Allah karki man wanan tusar take dan har yanzu yan cikina rawa suke .''

Tom idan dai zaki kaini Allah bazan yi maki ba .''

Jin haka ya sa Hajiya fitowa a tsora ce tanufi part din su nan tafara hada ma Atu Kayan shafa da sauran kayan baccinta da turaruka har da na huta sannan ta hada mata da kayan gyaran jiki sannan ta zuba a wata karamar akwati ta dauke gyalenta suka fito Safiya sai Hajiya sai Marfu'atu Buddara nan suka nufi gidanta tun kafin su shiga cikin gidan Atu tafara santinsa tana murna suna shiga kamar ta haukace masu tsabar yanda gidan ya tsaru ya hadu sosai sai da Suka karisa gyara mata gidan Safiya kuwa ta nuna mata yanda ake tafiyar da komai har Sun fito zasu shiga mota ta yanka a guje ta ce'' Hajiya baki jibi.''

Duk fitowa suka yi daga motar suna jiran abin da zata fada ta ce'' ba komai bane dama kyautar aikin da kuka yi min zan baku .''

Jin hakan ya sa su Hajiya juyawa da karfi amma kafin su karisa shiga Atu ta takarkare ta sambada masu tusa tana gamawa ta ce'' Wai Alhamdulilah sai da safenku .''

Karisa shiga motar suka yi hanci a tushe nan driver ya jasu a tsiya ce sabida shima warin tusar ya kai masa .''

Tana shiga dakin ta baje kan kujera ta janyo wayarta tafara latsawa ta jima nan zaune har wajen 22h00 amma Marwane bai shigo ba dan haka ta mike ta nufi dakinsa ta kwanta nan bacci ya yi gaba da ita .''

Sai wajen 00h00 sannan ya dawo gidan a gajiya nan ya ga an gyara waje ya fito fess da shi dakin Atu ya shiga amma babu kowa sai de ga gyara nan shima ya sha sai kanshi yake murmushi ya yi, ya ce'' Wata kila da safe zata dawo wayoo dadi kasheni in dawo in ga diyana da jikokina .''

Dakinsa ya nufa bai kula da ita ba ya fada toilet ya yi wanka yana fitowa ya yi shirin bacci sannan yazo yafara kan bed da sauri ya mike ita ma ta bude idanu nan suka saki ihuuu a tare ita idanunta a rufe sai kwala kara take  shiru ya yi , yana kallonta sannan ya ce'' Cutie ashe kece ?"

I love you Ashe ka shigo ?"

Dariya suka yi a tare duk idanun Atu a rufe sannan tafadi kan gado ta ci gaba da baccinta .''

Cike da farinciki shima ya kwanta tare da janyota jikinsa har bacci ya dauke sa .''


WASHEGARI

Suna karisa sallah asuba Bayan sun yi addu'a mikewa tayi ta nufi kithchen ta dafa masu indomie da yake da ta zauna gidan Hajiya duk suke nuna mata wani abun sai de Bata kware ba tana kammallawa ajiye saman dan madaidaicin table din dake zagaye tsakiyar falon sannan ta koma daki lokacin ya fito daga wanka nan ta taya shi ya shirya sannan suka fito ta suka ci abinci sai uban mai da tattasai haka yake daurewa yana yi yana hadawa da ruwa har ya karisa amma ta yi dadi ba laifi ya yi mata sallama ya fita yana shiga mota ya saka tishu yafara durzan bakinsa idanunsa sun yi ja ganin hakan ba zai daina ba ya sa shi jefa chuigwom a bakinsa lokacin ne ya ji saukin abin .''

Yana fita ta gyara komai sannan tafada toilet wanka tana fitowa ta shirya sannan ta dawo tsakar gida ita da me gadinta suka fara zazaga fira kamar Sun yi sabo
12/10/2022 à 08:48 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*


50&51




Tun da yafita har ya dawo tana nan zaune jin Horn din motarsa ya sa ta wanka a guje kai tsaye tafada kithchen tana kokarin hada jallof din shimkafa sabida ita take tunanin zata fi sauri da sallama ya shigo bata falo kai tsaye daki ta wuce ganin Batanan yafara Kiran Cutie na nazo ba zaki zo ki tarbeni ba tana jin yafara kiranta ta yi ,saurin Tura komai tare da kunna gaz ta rage wutarsa sannan tafito ganinsa tsaye kamar me neman wani Abu a shagwafe ta ce''  I love you shine zaka dawo baka Sanar dani ba gashi yanzun na d'aura girki.''


Murmushi ya yi, ya ce'' ina kika taba ganin amarya tana girki abinci na sayo mana an jima da yamma sai na fita .''

Washe baki ta yi ta ce'' shi yasa nake Sonka wallahi dama banaosn yin girkin bara na kashe hutar .''

Murmushi kawai ya yi ,ita kuma ta koma kithchen tafara masifar kai yanzu wanan yar banzar jallof din shimkafa ba sai ki ce min ba yanzu zan ci ki ba gashi kin sani wahala mtsss ta karishe tare da dukan tunkuyar wani zafi ne ya daki hannunta da sauri ta fasa kara yana falo ya ji kararta hakan yasa shi shiga kithchen din Kuka ya tarar tana yi ya rike hannunta da yaga tana yarfa hannu ya ce'' Cutie lafiya me ya samu hannunki ne kuma kike Kuka?"

Cikin Kuka ta ce'' I love you wanan tukunyarce daga ina mata fada shine ta konani .''

Murmushi ya yi ,ya ce'' Kema ban da abinki Atu ina ke ina fada da tunkuya uhmm gashi yanzu kin ja ta Konamin hannunki .''

Ohh ni zaka yi ma fada ba tukunyar da ta konani ba tafada tana kara fashewa da sabon kuka.''

Rumgume ta yi tsam a jikinsa ya yi ,ya ce'' Sorry Cutie na zan yi mata fada Muje na saka maki crème ya daina ciwo .''

Kara labewa jikinsa ta yi ,a haka suka dawo falo sannan ya zaunar da ita ya tafi daki ta dauko crème din ya shafa mata Sannan ya dauko plate ya zuba masu abinci sannan ya shiga bata a baki sai suka kusa cinyawa ta ce'' Ashe haka aure yake da dadi ni wallahi naji dadi da tukunyar nan ta konani gashi yanzu I love you dina yana bani abinci a baki .''

Toh Cutie me kike fada ai ko baki Kone ba zan baki ai ke din Matata ce fa .''

Hmm zan gani idn na warke ko zaka bani .''

Haka dai ta yi ,ta cika sa da Surutu har suka gama sannan ya jata daki suka yi wanka suna fitowa ya ce'' Cutie zo muyi bacci ?"

Tab Allah bani zuwa sabida kai dan iska ne haka na taba ganin Yaya Nura da Habi a daki wallahi tsoro suka bani fa .''

Cutie ai wanan ba iskanci bane zo kiji wani Abin .''

Babu musu ta nufesa tare da kwantawa a kirjinsa hannunsa ya daura kan gashin kanta yana shafawa a hankali kanshinsa sai tashi yake hakan yasa shi lumshe Idanu ya ce'' Cutie kina son baby mai kyau kuma ta yi kama dake ko dan kuyi ta Wasa .''

Da sauri ta ce'' ina so mana lokacin da Jamila ta haihu ni fa nayi mata renon bebynta wallahi ina so zamu je a sayo mani ne .''

Murmushi ya yi , ya ce'' wanan ba siya ake ba Allah ne yake kawowa dan Haka idan kin shirya karfa kin ga sai na baki .''

Na yarda in dai zan samu kyakyawar baby mai kma kai I love you ai yi ta santinta maza na Sonta ni kuma ina saka tana masu rashin mutumci .''

A'a ba haka za'ayi ba idan ta samu miji na gari bazamu kore sa ba zamu bashi ita sai a sake mata dani kanin ko .''

E'eee hakane kuma ka kawo shawara fa .''

Tana tsaka da mugun duminta yafara.......


Hannunsa ya kai zai tabata ta buge hannun idanunta duk Sun jiki tsabar kuka da tasha sai fadin wayo Allah na zafi na mutu na lalace wallahi yanzu I hate you kake ba I love you ba .''

Murmushi ya yi , ya ce'' Baby fa kike so daga yau shikenan ba zaki kara jin zafi ba .''

Ba wani nan ai sai da nace kar kayi kar kayi amma sai da kayi gashi yanzu ka maidani yar Iska ko kazar amarci ban ci ba .''

Dariya ta yafashe da ita sosai har da rike ciki ya ce'' ai zan kawo maki tun da munyi sallah mun gode Allah ai duk kaza mai sauki ce .''

Ni ka rabu dani kuma sai ka biyani kaza ta wallahi ko na fara kiranka I hate you .''

Da ko na shiga tamanin Kika kuma kirana haka in dai kaza ce bara na kara sai na gyara maki jikinki Muje ki ci ko .''


Wallahi Allah ka kuma tabani sai na kwarara ihu idan mai gadi ya ji zaka ji kunya kuma ni ka dai zan cinye kazar Allah ko dandane ba zaka yi ba .''


Naji Allah ya huci zuciyar Cutie na kuma my Suger dina.''

Murguda masa baki ta yi tare da turo sa har zai kama shi ta yi sauri rufewa suka saki dariya a tare mikewa ya yi ,ya sungume ta sai toilet ya wanke ta tsaf amma ya sha shagwafa sai rakki take masa yana gamawa suka yi wanka sannan suka tsarkake kansu suka fito kaya ya tsanza mata Sannan yajata suka fito falo ledar kazar ya janyo tare da bude mata ledar ai ba musu ta fara kwasarta tana zabga ma cikinta kazar ko kallonsa ba tayi ba tun da ta sunkuyar da kai sai da ta kai ta kararkaf ba komai sannan ta dago ta ce'' bani ruwa I love you .''

Dariya ta so bashi amma sabida gudun rigimarta ya sa shi gumtse bakinsa ruwan ya kawo mata sannan tasha tare da yin gyatsa ta ce'' sai yanzu yan cikina suka dawo dai dai sabida na ci kaza amma fa ta ji dadi ba laifi .''

Sosai ma ai tana da dadi .''

Haba ni fa nayi mamaki shi yasa ka dauki dazun Ashe karfin kaza ne wai baka gaji ba kuwa .''


Murmushi ya yi ya ce'' Atu kenan ai kamar na dauki wayata haka kike .''

To nima dan Allah ka din ga kawo min Irin kazar nan dan nayi karfi .''


Tom shikenan nima sai idan zaki rinka bani wanan labarin sai na din ga sayo maki .''

Hararensa ta yi , sabida ta gano abin da yake nufi ta ce'' ina son kaza amma Banason baka wanan labarin .''

Tom shikenan ashe Kenan baki son ki ci dan kiyi karfi .''

Ina so na yarda tun da ka ce har da baby zan samu .''

Yawa kin gani shagali biyu Kenan kika hada ko.''

Mikewa ya yi , ya ce'' bara na koma office an yi sallah La'asar karna makara .''

Tom Karka mance da kazar nan tawa fa .''

Insha Allah matar Marwane i love you so soo much.''

Hmm I love you too mijina .''

Fita ya yi ,ita kuma ta sha magani sakamakon zazafi da ke son kamata sannan ta kwanta bacci ya yi gaba da ita .''


★★★★

Habi kuwa Masha Allah ta kara kyau sabida cikin jikinta zaune suke a harabar gidan ita da Jamila sai Inna ,Habi ce ta dubi Inna ta ce'' Surikata wai in tambaya ki ?"

Ina saurarenki Habi .''

Yawa dama nace wai me yasa Atu take yawon tusa ne kuma me mugun wari kamar mushe kuma idan tafara bata gajiya.''

Hmm jiya ina jinki keda Jamila ita ma Atu ai Bada shi aka haife ta ba lokacin da Mahaifiyarta tana raye ta aike ta debo mata ruwa shine suka tafi garin tsokanarsu ita da su Balki da Hasiya suka jefi wata tsohuwa Sun Bata hakuri amma taki hakura hakan ya sa ATU ta yi mata rashin kunya sannan suka yi tafiyarsu tun da wanan lokacin tana tashi daga bacci tatashi da wanan tusar yanzu abin ya yi sauki lokacin yana sabo musanman idan tana cikin bacin rai har cikin bacci sambada abarta take yi idan tana tafiya tana surbubuda tusarta hakan ya sa ake ce mata buddara yanzu ne da girma ya zo mata take masifa kan buddara da ake ce mata ya sa babu mai fada sai de ace Atu sabida babu wanda bai san masifarta ba shi yasa ake tsoranta cikin anguwa .''

Tom yanzu Inna kunsan da hakan kuka kyale ta Shekara da Shekaru gashi har ta mallaki hankalin kanta tana gidan aurenta kinsan ba mai jurewa sai mu din nan .''


Tun Mamarta tana raye Muke nema mata magani na gargajiya har da aji GARAUHU  muka din ga dirkata mata amma a banza .''

Ai da shawara kuka yi kyauta gidan Malam ya kamata a kai ta zai fi wanan jike jiken .''

Ai abin da ya sa ya yi sauki sabida addu'ar da Mahaifiyarta take yi ne tana Bata tana sha shi yasa wallahi a da ko second 1 Bata yi ta barka mana tusa .''


Tom Allah ya kawo saukin lamarin kafin ta haihu dan wallahi a dakin nakuda kafin babynta ta fito sai ta rumtume wajen da kanshi,cewar Habi .''

Hararan da Nura yake dalla mata da shigowarsa Kenan ya sa ta sauke idanunta har ya huce dakinsa ita ma Jamila Bayansa tabi .''

★★★★

Masha Allah yau Atu ta cike wata biyu a gidanta ita take dauke da jaririn ciki tun da ta samu cikinta laulauyin da yazo mata dashi shine tusa wacce warinta yafi na dana tun Marwane na hakuri har ya yi magana ya ce'' Cutie me yasa idan zaki yi tusa ba zaki fita ba kinsan Allah idan kika yi ta sai tafi Awa 1 Bata tafi ba .''

Kara lafiya ne fa muke yi ni da babyna .''

To shikenan sai kuyi ta aika min da sansami .''

Wallhi bansan tana zuwa ba kawai tafito ni kuma in takarkare in sambada ta .''

To me yasa kike wanan abin Atu dan Allah ki fadamin me yasa ake ce maki buddara ne ?"

Tsaf ta kwashe labarin komai ta bashi kallonta ya yi Bayan ta karisa ya ce'' me yasa kika yi mata rashin kunya ne?"

Mun fi Awa 3 muna bata hakuri dana gaji kuma ga rana shine ya sa nace idan taga dama ta yi hakuri idan kuma ba dama ni nayi tafiya ta shine fa ta jefeni da wanan kamar tana jirana .''

To karki kuma kin ji matata .''

Na daina tsokana fa amma idan aka tsokane ni Allah bazan iya hakuri ba .''

Girgiza kai ya yi , tare da mikewa ya ce'' tashi mu tafi gidan Hajiya tun ranar da kika tare rabonki da su .''

Hmm kamar kasan nayi kewarsu sosai wai yaushe zamu tafi kauye ?"

Sai kin haihu .''

Marairaice fuska ta yi kamar zata yi kuka sai ya tuna a labarinta idan ranta ya bace ko tana cikin farinciki matika to zata yi ta sakin tusa da sauri ya ce'' karki yi dan Allah zuwa jibi sai mu tafi .''

Da sauri ta mike ta ce'' bara na shirya tom.''

Zaune ya yi , yana jiran fitowarta Bata wani jima ba tafito nan suka nufi gidan Hajiya suna isa suka shiga da sallama amsawa Hajiya ta yi ganin tare da Atu yake ya sa ta mike tsaye ta ce'' Marfu'atu yau har dake a gidan nan kuma ?"

E'eee Hajiya nace bara nayi maku huni sai yamma na koma gida .''

Murmushin yake ta yi , ta ce'' Tom shikenan ki tafi Safiya tana daki yanzu ta dawo daga School .''

Tom shikenan tafada tare da mikewa ta nufi dakin tun Bata karisa sallama ba Safiya tafito a guje ta fada jikin Hajiya tana Hajiya zata kumbra min ciki da tusa.....
12/10/2022 à 08:48 - Mom Star ✨: 🍂🍂ATU 🍂 BUDDARA 🍂


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

                  NA

         AMIRA SAMINOU
        ( Zauja 🍂 Zaujuha)

*Bismillahir Rahamanir Rahim*



52&53




Rike baki Atu ta yi ganin Safiya tana gudunta hakan ya sa ta ce'' jar uba ni za'ayi ma iskanci to wallahi da sake ba dai ni kuke gudu ba ai baku ga komai ba yanzu ma aka fara wasan .''

Falon ta dawo tana fadin tohh ke kuma Safiya lafiya guduwa daga ganina .''

Dan Allah Yaya ka dauke matarka ku tafi gida wallahi tusa take mana masu warin gaske .''

Dariya Atu ta yi ta ce'' Allah bazan yi maki ba ki tambayi I love you ai na daina yanzu ko .''

Jinjina kai kawai ya yi , ta ce'' Safiya je ki taya ta fira mana yanzun zamu tafi .''

Cike da tsoro hakan suka nufi dakin Hajiya ta kallesa ta ce'' Wai yanzu Haka zamu zuba Idanu muna kallonta tana sakin wata mahaukaciyar tusa wallahi ba ko Shaka duk ranar da ta haihu wanan warin idan bai kashe abin da ta Haïfa ba to zaka saka mashi cuta .''

Ai maganin matsalar ce ya sa muka zo nan din yanzu Malam zaki kiramana Muje ta in da zamu fara shaho kan matsalar .''

Tom shikenan bara na Kira sa Allah ya sa yana gari .''

Amin ya fada .''



Suna shiga daki Atu ta kulle kofa ta ja hannun Safiya suka nufi toilet dubara ta yi mata ta saka ta kwanciya sai ta Haye saman kanta tafara zafafaka mata tusa masu uban warin masifa suma take tana dawowa amma taki daga ta kuma ba bakin magana kar tusa ta shiga ta bakinta .''

Sun dauki lokaci kafin Malamin ya shigo sannan Hajiya ta zo kiransu jin ihun Safiya ya sa tafara nocking tana kiran sunanta amma tsabar mugunta ATU sai dariya take Safiya kuma har ta sare kawai ita ma ta zama buddara sai da taga dama sannan ta daga ta ganin Atu ta daga ta ya sa ta fito daga toilet da wani Irin wawan gudu ta bude kofa Hajiya dake bakin kofa tana nocking tafada jikinta tana jan Maganarta cikin sigar wahala ta ce'' Hajiya wallahi wanan matar zata kasheni gskiya a kaini asubiti kar ya'yan cikina su fashe tsabar bala'in warin da Suka sha a wajenta .''

Har Hajiya zata yi magana suka ga fitowar Atu daga toilet ai a guje suka bar wajen sai falo bayan Marwane suka buya hankalinta kwance tafito kamar Bata yi komai ba suna hada Idanu da Malam din nan ta fido Idanu gabanta ya shiga faduwa da sauri ta juya zata koma daki Marwane ya yi kukan kura ya damko ta ihu ta shiga yi tana kokarin kwatar kanta amma ya mata riko mai kyau har sai da ya kawo ta wajen Malam din fuska a hade ya buga mata tsawa ya ce'' ke zauna a nan ,yafada cikin Bada umarni .''

Babu musu ta zauna tana kallon Marwane ta ce'' Yanzu shine duk ka rasa wanda zaka kawoni wajensa sai wanan dan Allah ka ce ya tafiyarsa .''

Juya mata kai ya yi ,ya ce'' Idan kun karisa zan fida shi .''

Gyara murya Malam ya yi , sai da ta zabura ya ce'' Me kike yi a jikin wanan baiwar Allah ne?"

Babu komai dan Allah Kar kayi man komai zan fita .''

Me yasa Kika shiga jikinta ne .''

Rashin kunya ta yi man shi yasa .''

Kinsan mun taba haduwa bisa kan Irin wanan lamarin ko .''

E'eee tafada cikin dumauta .''

Ya ce'' To ina son ki fita tun kafin na fara kona ki.''

Dan Allah Karka konani Allah zan fita bazan saké shigowa rayuwarta ba na yafe mata .''

Tom ba ma ita ba kika kuskura muka sake haduwa bazan Sarara maki ba ina fatan kin gane .''

Na yarda ,sannan na gode .''

Wata uwar atishawa ta yi ,tare da bankada wata uwar tusa har wani tsanwa ke fitowa a mazaunanta ai ba shiri duk suka danne hancinsu  ita kuma tafadi kwance bacci ya yi gaba da ita .''

Sosai suka yi ma Malam godiya sannan suka mashi abin Alkairi ya yi tafiyarsa .''

Tana nan kwance ba ita ta Farka sai bayan sallah La'asar tana tashi taji kanta ya yi mata nauyi sannan jikinta gashinan kamar Bata da lakka wani uban Amai ya zo mata da sauri ta mike ta nufi toilet tafara kwarara amai kamar zata amayo yan hanjinta bayanta suka biyu suna jera mata Sannan Hajiya kuwa ta hada mata tea mai kauri ta bata ta sha kadan sannan ta kwanta sabida zazafi da take jin yana shirin kamata har dare suna gidan dan har Doctor yazo ya duba ta ya tabbatar masu da lauyayi ne take irin na masu ciki nan ya rubuta mata magani ya yi tafiyarsa .''


Sai da Suka kusa raba dare a gidan Hajiya ta taso Atu ta yi zamanta amma taki hakan yasa ta rabu dasu suka yi tafiyarsu .''


Bayan kwana biyu cikin shirinsu suka fito tsaf na tafiya kauye yanzu Atu ta daina tusa da yawon tsokana dan yanzu batason rigima ko abin da zai daga mata hankali shi yasa Bata shiga sabgar kowa mota suka shiga tare da daukar hanyar kauye suna tafe suna taba fira har suka karisa shigowa kauyen kai tsaye gidansu Hasiya suka huce suna shiga Mama na zauna tana aiki da sallama a bakinta ta Karisa tana fadin Mamana barka da gida ya aiki .''

Alhamdulilah Atu mutanan birni yau kune a garin namu .''

E'ee wallahi Mama gamu dai Allah ya nufa mun shigo shine nace bara nazo na ganki fatan dai komai dai dai ko .''

E'ee to bana ce ba sai godiyar ubangiji .''

Masha Allah ya yi kyau .''

Sai a lokacin Marwane ya shigo tare da wasu samari suna shigowa da kayan abinci sai da Suka karisa sannan ya fido kudi ya basu godiya suka yi sannan suka tafiyarsu cike da murna ta ce'' Atu har da Abin Arziki Ashe tare da mai gidan kuka zo .'' 

Karki damu ba komai ko ba Hasiya ai kina da ni sabida ita din yar amana ce .''

Hakane Allah ya maku Albarka dana ina godiya Allah ya jikan magabata na gode kaji .''

Babu komai Mama ina kwana.''

Lafiya lau .''

Mama ya kamata mu huce shigowarmu Kenan muka zo nan .''

A'aa to ba laifi ki gaishe min da Innar taki .''

Insha Allah zata ji tafada sannan tafita ,shima Marwane kudi ya sauke ta mata na cefane sannan ya yi tafiyarsa suka kama hanyar gidansu Atu babu wani nisa dan haka basu wani bata lokaci ba suka kariso a Kofar gidan ya yi parking sannan tafito tana shiga da sallama a bakinta su Inna dake zaune suna fira suka kallo wajenta tare da amsa sallama cike da farinciki suke fadin oyoyo ga Atu amarya ,ga Atu mutanan birni a'a kunsha hanya zo ki zauna .''

Zaune ta yi , tare da gaishe da su ,suka amsa suke da mamaki ,da a baya ne tana shigowa ganin wanan zaman da Suka yi zata ce wace gulmar kuke sannan ba zata jira a ce ta zauna ba bare ta gaishe da su Habi cikin ladabi hmm lanle an samu chanji sosai .''

Atu kun kwaso gajiya fa bara a kawo maki ruwa .''

Inna da kin barshi a gidansu Hasiya mun sha ruwan ai .''

A''a madallah a tsan kuka fara zuwa Kenan .''

E'ee ta ce ma a gaishe ki .''

Wai Atu ba zaki ce ke Habi tashi dauko min abinci ke Jamila kawo min ruwa Allah munyi missing din dramer ki .''

Insha Allah mun daina ai yanzu lafiya ta samu alhamdulilah .''

Masha Allah garin yaya Kenan ?"

Marwane ya buda baki ya ce'' Sakamakon jinjinrin cikin dake gare ta ya sa take yawon tusa ko second ba'ayi ta saki wata shine na tambaye ta bisa kan Lamarin ta bani labari cikin ikon Allah muka samu Malami ya rabasu da matarnan lafiya tun daga wanan lokacin ta daina shirma wata tusa da kula mugunta duk da tun da muka yi aure Bata taba min laifi ba sai de barkwancinta .''

Masha Allah muna godiya Sosai kaji dan nan Allah ya maka Albarka ya biyaka da gidan aljannah .''

Amin Inna bara na huce gidan Sadik Abokina zuwa yamma zan dawo sai mu tafi gida .''


Ba damuwa Allah ya kaimu .''

Fita ya yi , baya ya sauke masu nasu kayan abincin biyu uku na shinkafa ,karton Makaroni hudu ,mai manya bidon biyu da Maggi da dai sauransu sai kudi da ya sauke masu sannan ya yi gaba abin sa .''


Sosai suka sha firan yaushe gamo sannan Atu ta Kiran yaron wajen Jamila ta ce'' Muhsin je ka gidansu Balki ka kira min ita .''

Babu musu ya mike ya fita a guje sai gidansu Balki babu jimawa suka shigo tare cike da murna suka rumgume juna sannan ta gaishe da su Inna ta zauna suka shiga fira sallah kawai take tada su har Aka yi La'asar bayan Sun yi sallah suka shiga dakin Inna sabida su dan zanta zamnsu ke da huya Balki ta ce'' Kawata kin ga yanda Kika yi kyau kuwa daga ni ansan gidan hutu kika fito Masha Allah kin ga yanda fatarki ke sheki kamar kina wanka da ruwan madara .''

Hmmm kawata Kenan ciki ne dani fa shi yasa kika ga hakan.''

A'a Masha Allah da alama yanda kika yi hakan abin da ke cikin sai ya yi kyau sosai.''

Hmm Allah ya sa ya ake ciki kn maganar aurenki ne .''

Ke dai Bari cikin satin nan za'ayi bikin ai zaki zo ko?".

Me zai hana kawata ai dole na.''

Amma zan sha soyayya a gidana.''

Sosai ma sabida aure daban ne hakurinsa yafi yawa amma kuma dadinsa yafi saka farinciki .''

Allah ya bamu ikon hakuri da juna .''

Karshen maganar Kenan amin.''

Sun dan taba fira suna taka da firan Muhsin ya shigo ya ce'' Aunty wai kawu ya zo .''

Tom ina zuwa yanzu .''

Fita ya yi ,su kuma suka kara shan firansu sannan suka fito nan ta shirya ta yi masu sallah har kofa suka rakata sannan suka dawo bayan tatafi .''


★★★

Alhamdulilah Lantana yanzu ta daina shirmanta dan yanzu tana dauke da ciki suna gudanar da rayuwarsu cike da farinciki da jin dadi dan cikinta ya girma sosai da alama haihuwarta tana kusa 


★★★★

Yasmine ma haka sai shan soyayyarsu suke dan yanzu ta kammalla karatunta har ta samu aiki a gidan radio suna gudanar da rayuwarsu cike da tsafta gwanin shawa'a ita ma tana dauke da cikin wata takwas dan har ta dauki hutu a wajen aikinta sannan tana samun Kulawa a wajen mijinta Kuma Yayanta .''

★★★★

Suna isa gida wanka suka yi suka ci abinci suka daura fira tare da tsara yanda zsu saye kayan baby dan ita kanta Atu cikinta ya dauki girma sai ka ce mai ya'ya goma a ciki ga wani uban ci dake gare ta sam bata ragama abinci wani lokacin kamar ta yi ,kwace Haka take ja da cikinta har satin bikin Balki ya zagayo haka ta yi karfin halin tafiya Aka ci biki da ita sannan ta yi mata akwati biyu gudunmawarta da kudi sai yamma suka dawo tun suna hanya take jin bayanta yana rike mata amma ta daure bata yi magana ba suna isa gida wanka ta yi , ta saka yan kayan shan iska ta fito falo abinci ya kawo mata amma sam baya birge ta sabida azabar da take ji a bayanta da mararta da kyar ya samu ta yi loma biyu nan tafara mutsu mutsu da sauri ya kira Hajiya suka tawo gidan nan ta Bata wasu magunguna gargajiya ta sha sannan ta gyara ta suka hada kayan roba aka tafi Asubiti tun da aka shiga da ita dakin labour ba wanda yafito Hajiya da Safiya suna zaune shi kuma sai zagaye yake yana ambatar sunnan Allah a zuciyarsa Hajiya tana jan tarbi Safiya na addu'a a zuciyarta tun da sasafe har dare ya raba sai de Suka doctos din fitowa suna komawa sai da Atu ta yi kwana da huni day sannan ta haifi yan biyu mace da namiji dumur damur da su Masha Allah gasu da daukar Idanu da gwanin birgewa haka aka fito da su bayan an shirya su hmmm murna ba'a magana tun da Marwane ya karfe su ya masu huduba ya rike yar macen mai kama da Atu yake ta kallonta kamar ya mai da ita a ciki tana rike a hannunsa yake kiraye kirayen abokansa ya kira Sadik yafada masa ya ce ya sanar da iyayen Atu babu musu bayan fito ya shaida masu ai cike da murna suka fara shirin tafiya sai Habi ta ce babu in da Zaku tafi à take nakudarta ta taso nan suka yo kanta suka nufi asubiti ita ma suna tafiya da yake ta ci nakudarta a gida bata jima ba ta santolo yar baby girl bai kyau sai ka ce Atu ta haife ta sabida yanayin fuskanta sak farinciki ba'a magana ga ahalin su Atu bayan a sallamo su Habi daga asubiti Mamar Hasiya ta dawo kula da ita sabida Habi a yar garin ba ce Maman Hasiya tafara tsaronta ne kafin danginta suzo Inna kuwa da Jamila suka tafi birni lokaci har an sallamo su Atu daga Asubiti a nan Jamila ta huni sai santin yaran take sai yamma sosai ta koma gida dan tana shiga ana kiran Mangariba .''

Sosai mutane da Abokan Arziki na nesa dana kusa suke zuwa ganin Baby's din Atu dan yau ne suka cika sati day Yara sun ci sunnan Farhanat da Farhane sosai aka shagaji na gani kuma na fada sosai aka yi shagali da shinkafa sannan aka yi wanka da lemu suka Karkafa baza da Nerori har dare sannan kowa ya watse mai jego ta samu ta wanka ta ci abinci ta shiga shayar da yan biyunta wata kaunarsu tana shigarta .''


★★★★

Bangaren Lantana ita ma Masha Allah ta haifi yaronta mai kyau sannan kato da su sai de Masha Allah shima ranan sunansa ya ci sunnan ,Shuraime shima ba laifi an sha shagali .''

★★★★


Yasmine kuwa yan mata ta Haïfa sak ita sannan itama taga Abokan Arziki Sun zo Taya ta murna a ranar biki idan yarinyar ta ci sunan Hanane an sha shagali babba sabida yarinya yar gatan Yasmine da Saifulahi ce .''

★★★


Sosai yaran Atu suke shan kulawa Kota ina musanman idan Hajiya ta zo sai su fara rigima ita fa Inna kan yaran ita Hajiya ta ce Bata rike kishiya a bata miji ita ma Inna ta ce wanan auren sai anyi sa da Alhaji Haka zasu yi ta wasa da dariya har Atu ta yi arba'in ta samu kulawa sosai a hannun Inna bayan tatafi suka sha soyayyarsu sannan suna zaune lafiya cikin kwanciyar hankali sannan yarnsu sun kara girma Sun murmure.''

Bayan yan watanni 

Yara Sun girma Sun fara iya rarafe Atu na dauke da wani cikin Haka take kulawa da yaranta babu abin da Suka nema suka ra sa haka shima Marwane yana kokari wajen kulawa da su duk aikinsa yana da hatsari amma hakan bai sa ya kyalesu ko Sun Bukaci abu basu samu ba har Allah ya sauke Atu lafiya ta saké haihuwar beby boy in da ya ci sunnan Rushdane su Farhanat kuwa Sun kara girma da wayo dan yanzu har tafiya suke a haka har ta yi arba'in dan haka suka shirya suka kai ma Hajiya ziyara .''


Yaran sai guje guje suke Hajiya ta damko Farhanat ta ce'' ke yanzu kawai zaune ki zan yi sabida bani son ki aure min miji .''

Cikin yanayin maganarsu ta yarda ta ce'' ni da ma banison tsoho .''

Ja'ira ai yafi kyau .''

Turo baki gaba ta yi, ta ce'' A'a fa shi fa ya tsufa har da furfura yake da ni kuma mai kyau ce dan mijin Atu Aliya zan aura .''

To ai mijina yafi na Aliya kanwata zama dan saurayi .''

Hmm ba wani nan idan kinason nace ina son sa sai kin bani chocolat .''


Bakinta taja ta ce'' Farhanat asha dadi to shikenan zan baki .''

Bata fuska Farhane ya yi , ya ce'' zan ce na fasa auren fa .''

Haba rabu ita da kai zan fara bama chocolat mai gidana .''

Gwalo ya yi ma Farhanat ita kuma ta jefe sa da fillo nan suka shiga zagayen falon .''



Alhamdulilah duka duka anan na kawo karshen wanan littafi mai suna Atu buddara kuskuran dake ciki Allah ya gafatarmana idan nayi dai dai Allah ya bani lada sannan Allah ya sai muyi anfani da Abin da muka fada a ciki na Banza muyi watsi da shi na gode sosai masoya makarantan littafina da masu saurare ina maku godiya sannan Allah ya hada mu a gidan aljannah firdaussi ina godiya Sosai da hadin kanku ..........bussalam 


Kema baza taba mantawa dake ba Aïsha ina godiya da karfin gwuiwa da kike bani da shawara sannan Ina godiya godiyarma ta gode Allah ya kara daukaka AMNAH NOVELS T.V sannan yakara zakin murya 


Daga taku har kullum Mom Star ✨

Post a Comment

0 Comments