BASMA

[08/08, 14:11] Miss Green๐Ÿ€: _*๐Ÿ”–BASMA*๐Ÿ”–_ 

๐Ÿ“„Littafi na 1


*UMMU MAHER*
(MISS GREEN)๐Ÿ


*arewa book*
 *PROFILE NAME* Rabiattu0444
๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป

*LINK*
https://arewabooks.com/chapter?id=62d10b94e4924f3d434fb7f9

*Wattpad*
*PROFILE NAME*
Rabiatu333

๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป
*LINK*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_campaign=invitefriends

*Matso kiji*
mu yawaita karatun alqur'ani mai girma don yana wankr cutukan zuciya dana bayyane.
------------------------------
2๐ŸŸข

A hankali Abeed ya zagayo ta gaban mahaifiyarsa ya kalleta sosai sannan ya ฦŠago haษ“arta ya ce"ya ke ma'abociyar ฦ™yau da haiba ina neman gafararki ya ke mahaifiyata abin tinฦ™aho na,ta gaban goshin sarki babu wani a gabanki ko a bayanki,ke ce agaba ke ce a farko babu wani mahaluฦ˜in daya isa ya tsaya a gabanki ya ce bake bace don cikar izza da kuma ฦ˜yau da ฦ˜awa."dun gure kansa ta yi tana dariya ta ce"kai yarima gaskiya ka raina ni sai kace wata matarka?".murmushi ya yi sannan ya ce"ai babu wata mace a guna data fiki ya ke mahaifiyata babu wanda ya isa yaja da ke matuฦ™ar ina wajen ba tare da na cire masa yatsanta guda ba,don haka ni ke ce abar ฦ™auna ta har abada".

 wani irin jin daษ—i ne ya sauka a fuskar sarauniya Jidda don arayuwarta tana matuฦ™ar son taga an yabe ta kuma duk abinda ta ce ayi to ya zama dole a yisa,don tun a masarautarsu ta sudan babu mai ษ—aga mata hannu ba tare da ta saka anyi mata maganinsa ba.sarauniya Jidda tana da izza da kuma mulki bata yadda a kawo wani abu a masarautar ba wanda ba ita ce ta kafa sa ba,don haka kishiyarta fulani Khadija binta ta ke sau da ฦ™afa don aฦ™wai lokacin da ta mari Fulanin akan ta karya mata doka,tun Abeed yana ฦ™arami ta ke sonsa tunda ita alokacin Allah bai bata haihuwa ba sai daga baya ta haifi namiji sai kuma mata 2 ฦดan biyu daga nan bata ฦ™ara haihuwa ba.


Sarauniya Jidda kuwa tana da ฦดara guda5 ษ—aya namiji huษ—u mata ta aurar da biyu matan Hasiya da Husna,yanzu kuma aฦ˜wai Hajara da Bilkisu.


Hajara ce kawai tayo halin Sarauniya Jidda saboda tana da izza da mulki da kuma wulaฦ™anta ษ—an adam babu ruwanta komai girmanka yanzu zata zageka ta saka aci maka mutunci.



Washe gari da sassafe Fulani da kanta ta isa ษ“angaren ษ—anta Yarima Abeed yana ta karatun alqur'ani mai girma ta shigo,ta kalli ษ—an na ta cikin burgewa aranta tana ฦ™ara son ษ—an na ta don aฦ™wai addini sosai kuma kullun ba shida abokin hira irin qur'ani ya yi karatu a turai na shekara 15 amman ko da yaje ษ—in ma bashi da wani aboki sai wani abokinsa Al'amin shima Al'amin irinsu ษ—aya da Abeed don yana da matuฦ™ar taka tsantsan sosai da addininsa.
tsayar da karatun Yarima Abeed ya yi sannan ya gaida mahaifiyarsa cikin girmamawa sannan ta ce"yarima anjima ฦดan matan nan na masarautu daban daban zasu zo gidannan ka zaษ“i wacce ka ke so daga cikinsu kaima ka yi aure ko ns ji daษ—i araina".ransa yaji ya yi masa zafi ammzn saboda mahaifiyarsa taji daษ—i sai ya ce"babu komai mai babbar fada insha'Allah ina nan ina jiran zamansu Allah ya zaษ“a min tagari a cikinsu."

 murmushi ta yi sannan ta ce"Ina alfahari da kai ษ—ana,saboda ban taษ“a baka umarni baka bi ba don haka ina maka fatan alheri a rayuwarka ta duniya ya wanke maka dukksn abinda ke damunka na zuciyarka ya cikamin burina na ganinka a matsayin Yariman ฦ™aisa babu abinda zai sani farin ciki irin ganin wannan ranar".

murmushi ya yi sannan ya ce"ummi na Allah ya kaimu lokacin yasa muna da rai da lafiyar gani".murmushi ta yi ta ce"amin".


tana fita yabi hanyar da tabi da kallo yana masifar son mahaifiyarsa amman kuma aฦ™wai wani mummunan hali irin na mahaifiyarsa wanda baya sonsa,yasha yi mata wa'axi akan hakan amman sai ta nuna masa fushinta don haka yana ji yana gani sai dai ya yi shiru ya ฦ™eleta don mahaifi yafi gaban wasa.

 Kallon ฦ™aton mudubin da ke ษ—akinsa ya yi,ya kalli kansa ya kalli irin halittar da Allah ya yi masa,amman fa sai dai kash ya rasa wani abu a zuciyarsa wanda ya ke ji kamar ba zai taฦa samunsa ba.

Kash nasan masu karatu zasu so suji wannan wata irin matsala ce da Yarima,ku biyo ni ni miss green don kuji wata irin matsala ce haka.
****

Ina kitchen ina girki salimat ta shigo ฦ˜anwar Maryam ta ce"ke kurma har yanzu baki gama girkin bane?yunwaqq muke ji?".ban ma san me take cewa ba na cigaba da girkina kawai sai ta ษ—ebo ruwan zafin dana fara zubawa na shayi ta watsomin a kan kyalkyawar fuskata,tsananin zafin dana ji yatsa na ฦ™wala wani irin ihu ina yarfe hannuwa na don har hannu sai da ya zubar min,abinka da farar fata wajen ya tashi ya yi ja nan da nan,Mama da tazo wucewa ta kitchen ษ—in taji ฦ™ara ta da sauri tayo kaina,tana tambaya ta me ya faru?kasa magana na yi saboda tsabar azabar dana ji na rungume Mama ina kuka mai cin rai.

Da sauri Salimat ta fita don tasan bata da gaskiya da sauri Mama ta janyo hannunta ta ce"ai wallahi babu inda zakije Salimat don wallahi na gaji da abinda kuke wa yarinyar nan,ana cikin hakan Hajiya Saratu ta fito tana cewa"to wata wainar kuma ake toyawa,nasan babu munafukar data haษ—a wannan abin sai kurma.

 Faษ—a sosai akayi ranar agidan don duk da Mama bata ramamin ba amman fa anyi masifa sosai kuma Salimat tasha duka wajen Mama da ฦ™er Hajiya saratu ta amshe ta tana kuka tana tsine mana ni da mama.


 Alhaji Tasi'u ransa ya ษ“aci sosai shine mijin mama yayar mahaifiyata dukanmu ya taramu ya kalli Salimat ya ce"idan na ฦ™ara ganin wani mahaluฦ™i ya hantari Basma baiwar Allah marainiya,ku me yasa baฦ™wa tausayin yarinyar nan ne?da wanne zata ji da kurmanta ko da maraici ko da matsalarku,yarinyar nan a bata taษ“a ganin mahaifiyarta ba ballanta ma taji ฦŠuminta to wallahi bazan yarda a salwantar da rayuwarta ba,ke kuma hajiya saratu ki jawa mutumncinki don wallahi na ฦ˜ara jin wani abu ya faru to tabbas ran kowa sai ya ษ“aci".yana faษ—ar hakan ya yi tafiyarsa,Abubakar ya kalli Basma ya yi mata alama da hannu ta yi haฦ™uri baza a ฦ™ara yin hakan ba".ษ—an murmushi ta yi har ฦ™yawawan dimfil ษ—inta ya lotsa ฦ™yaunta ya ฦ™ara fitowa.

Abubakar ma murmushin ya yi yana ฦ™ara jin son yarinyar acikin zuciyarsa ga ta kurma amman Allah subhanahu wata ala ya yi mata baiwa kala kala.

 Shima faษ—a sosai ya yi wa ฦ™annensa Maryam da Salimat,don su biyu ne yanzu yaran Hajiya Sara mata waษ—anda basuyi aure ba ta aurar da mata uku,Abubakar shi kaษ—ai ne namiji shine kuma ษ—anta na biyu.



*Miss green ce*
[08/08, 14:11] Miss Green๐Ÿ€: _*๐Ÿ”–BASMA*๐Ÿ”–_ 

๐Ÿ“„Littafi na 1




*Ummu maher(miss green๐Ÿ€)*


_Noticed๐Ÿ›:wannan littafin labarine akan wata yarinya wacce ta kasance kurma ce._

----------------------
*matso kuji๐Ÿ‘‚๐Ÿป*
Babu abin ฦ™yama a ha
littar Allah matuฦ™ar shi ya yi halittarsa don haka mu kiyaye don muma bamu fi ฦ™arfin ikonsa ba.

---------------

Bismillahir Rahmanir Rahim


   
     1๐ŸŸ 


. . . .A hankali na ke share ฦ˜aton gidan a zuciyata ina ta istigfari don ban taฦa yin shiru da bakina akan ambaton Allah,shiyasa ko da yaushe zaka ganni cikin nutsuwa da kamala,wata sharar naji an watso min na ษ—ago kaina Maryam na gani a kaina tana ce wa"to uwar shara ga wata ฦ™arin sharar nan".bance mata ฦ™ala ba na koma gefe na zauna don nasan tunda Maryam ta fara haka to tabbas tana son ษ—ebo rigima ne.

 Cikin fushi ta ce"ikon Allah yanzu don na kawo wata sharar ki haษ—a shine zaki koma gefe ki zauna ke ga ki uwar fushi ko?".sunkuyar da kaina na yi hawaye na bin kuncina Allah sarki baki yana da daษ—i wani lokacin,yanzu da ina da baki da tuni ko da wataran banyi magana ba to tabbas wataran zanyi don sha'anin mutanen gidan sai a hankali.

 Ana cikin hakan Hafsat tazo ta sameni ina kuka ta ce"Basma me ya faru ki ke kuka kuma?".tasan halina ba lallai in gaya mata ba don aฦ™waini da haฦ™uri kamar dutse don haka ta juya kan Maryam don taga alamar ni da Maryam ne don ta juya ฦ™eyarta ta yi irin ษ—aurin nan na ture kaga tsiya,don ฦ™arin neman rigima sai ce wa ta yi"to tsigarallahu to da kika zo rama mata zakiyi ko kuwa inji labari?".ran Hafsat ne ya ษ“aci sosai ta ce"kin san ai zan iya rama mata ษ—in saboda kin san Basma kurma ce shine ki ke mata duk abinda ki ke so don ki zalunce ta,to wallahi ba zaiyuwuba sai na tsaya tsayin daka na rama mata duk wani cin kashi banza kawai babbar kwabo".

 Shaฦ™o Hafsat Maryam ta yi ta ce"ikon Allah yanzu Hafsa ni ki ke zagi saboda wannan kurmar banzar ko?ko da ya ke ฦดan ubanci za ki nuna min saboda ita ฦดar ฦ™anwar Mamanki ce dole ki nuna min haka?to wallahi ki maida hankalinki ko kuma inci ubanki hankali ฦ™wance".

 hayaniya sosai su Hafsat suka  fara ita da yayarta Maryam ni kuka babu abinda na ke sai kuka ina rabasu,muna cikin hakan Hajiya Saratu ta fito tana ce wa"ikon Allah ke Hafsat tsabar tsaurin ido ki rasa da wacce za kiyi faษ—a sai sa'ar yayarki?amman ke dai baki da kunya wallahi,ko da ya ke aikin munafukar uwarki ne mai zugaku a kan yi wa mutum rashin mutunci".babu abinda Maryam ta ษ“oyewa mahaifiyarta harda ฦ™arya da sharri duk ta haษ—a ta faษ—a.


 Tafi Hajiya Sara ta farayi tana ce wa"ai ni daman nasan babu munafukar da ta haษ—o wannan faษ—an sai wannan munafukar kurmar.sai ana magana ta yi maka wuฦ™i wuฦ™i da idanu tana kallon ka kallon rainin hankali.


 Ta yo kaina tana ce wa dukan da Hafsat ta yiwa ฦดa ta yasin akanki zan rama,da gudu Hafsat ta yo kaina tana ce wa"wallahi Hajiya babu wanda zai ฦ™ara dukan baiwar Allahn nwn a gidannan,don ita ba jakar ku bace."tana faษ—ar hakan taja hannuwa na muka nufi ษ—akin mama.

 Haryanzu ban daina kukan ba,Hafsat ta buษ—e fridge ta ษ—akkomin ruwa mai sanyi ta ce"gashi kisha Basma,amsa na yi na hau shan ruwan nan sai da na shanyesa duka,Hafsat ta yi dariya sannan ta ce"ki yi haฦ™uri ฦดar uwata kowa da irin ฦ™addararsa kuma indai ina gidannan babu shegen da ya isa ya bugeki wallahi sai na rama miki.

 Wasu hawaye ne masu zafi suka zubomin na kalli Hafsat na yi mata alamun na gode,dariya ta yi sannan ta ษ—akkomin wani hausa book mai suna silar fyaษ—e na marubuciya Ummu maher.

 Sosai naji daษ—in littafin har Mama ta dawo ta sameni ta ce"to uwar karatun littafi sana'ar a ke yi ne?ฦดar dariya na yi sannan na yi mata alama da hannu na ce sannu Mama dafatan kin dawo lafiya,ta ce lafiya ฦ™lau ษ—iyata.

Nan muka cigaba da hirarmu da Mama amman da hannu muke yi don sai kace ma  ina jin maganar gwanin sha'awa.
*****

*ฦ˜AISA PALACE*

abinda kenan aka rubuta a babbar masarautar wacce ta haษ—a abubuwa masu abin sha'awa shuke shuke masu ฦ™yau sanyin idaniya.


A hankali ya ke takawa duk inda yabi sai kaga an zube ana gaishesa,yana amsawa cikin kulawa tsaษ“anin Hajara ฦดar uwarsa don ta haษ—e fuskarta sosai kamar kunun tsamiya.



 Yarima Abeed kenan yana da matuฦ™ar mutunci ga mutane ba shida girman kai ko kaษ—an amman sai dai fa masarautar ta su aฦ™wai lauje cikin naษ—i don aฦ™wai abubuwa sosai waษ—anda suka kasance na zalunci da kuma kitimirmira kala kala.


 Yana da ฦ™yau sosai wanda tsayawa faษ—ar kyaunsa da kuma cikar izzarsa na dabanne,da yawa mata sun kamu da ciwo iri iri saboda shi,sai dai shi sam har yanzu bai ga wacce ta yi masa ba,don mafi akasarinsu ba don komai suke sonsa ba saboda kuษ—i da kuma ฦ™yau don masarautar ฦ™aisu masarauta ce masu ษ—inbin dukiya sosai.

Kai tsaye ษ—akin mahaifiyarsa ya shiga wacce ake ce mata,Jidda amman ana ce mata sarauniya saboda mahaifinta shima sarki ne mai zaman kansa don yana da kuษ—i sosai.


Zagaye ya same ta tana yi a cikin ษ—akin  ya yi sallama ya shiga,ta ce"yanzu abeed abinda ka ke yimin kana jin daฦŠinsa in baka umarni ka ฦ˜i bi,sai abinda kishiyata ta baka umarni shi ka ke yi,to yau na barka na yafe mata kai".

 Cikin fushi ta juya masa baya wannan kuma yana daga cikin tarkon da ta ษ—ana wa Yarima don ayanzu yana da shekara a duniya35 amman ko zancen aure bayayi shiyasa a wannan karen ta shirya yi masa aure ko ma me zai faru sai dai ya faru don ba za ta yadda kishiyarta ta dinga bawa ษ—anta shawara ba don ita bata yadda da kowa ba.





*Miss green ce*
[08/08, 14:11] Miss Green๐Ÿ€: _*๐Ÿ”–BASMA*๐Ÿ”–_ 

๐Ÿ“„Littafi na 1


*UMMU MAHER(MISS GREEN๐Ÿ๐Ÿ€)*

_Noticed๐Ÿ›:wannan littafin labarine akan wata yarinya wacce ta kasance kurma ce._


Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444


*Matso kiji๐Ÿ‘‚๐Ÿป*
yin sallah akan lokaci yana ฦ˜ara kusantamu da ubangiji,sannan Allah yana shiryar da mutum da barin alfasha.
------------------------------

  3๐ŸŸก4

ranar Hajiya Saratu ฦ™wanan baฦ™in ciki ta yi na yadda Alhaji ya ke banbanta su Salimat da kuma ฦดar ruฦ™onsa wato Basma,ji ta ke kamar ta kashe ta ta huta,ko a waje Basma tana da farin jini sosai a wajen mutane don kafin kaga an aiko neman su salimat to sai an aiko neman Basma,abin yana bata mamaki duk da yarinyar tana da ฦ™yau sosai amman kuma ai ba tada baki,to ta yaya zata yi zancen?ai kuwa bazai yiwu tana kallon wannan kurmar ta yi aure tabar ฦดaฦดanta ba,don haka idan sun san wata basu san wata ba.


Kuka sosai na ke yi idan na tuno da mahaifina yana raye amman ban isa yanzu inje gidansa inyi ฦ™wana ษ—aya bama,saboda wani shinge da ya gifta a rayuwarmu,na ษ—aga kaina sama ina tuno wani abu daya shuษ—e a rayuwata.


Mahaifina bai taษ“a ko da ฦ™wana ษ—aya ba tare da ya kawo mace gidansa ba,aฦ™wai Hajiya Tani ita daman ta zama kamar matarsa tun a zamanin mahaifiyata tasan da zaman Tani kuma ba aure sukayi ba,sai dai ba yin kansa bane aikin asiri ne.

 Ban san mahaifiyata ba idan ba a hoto ba ayadda aka bani labari mahaifiyata sunyi auren soyayya da mahaifiyata mahaifina asalin shuwa arab ne dake yankin maiduguri ษ—an gatane sosai awajen mahaifansa,tunda Hajiya Tani taga mahaifina sai ta ฦ™waษ—aitu dashi sosai ta dinga kashe kuษ—inta wajen bokaye amman abin bai taษ“a cinsa ba,da ta gano mahaifiyata ke karya komai ta hanyar addu'ah da kuma magani sai ta saka mahaifiyata sosai a gaba,ita kuma mahaifiyata fulanine na asali da ke yankin yola,don haka iyayensu suj tsuma su sosai da maganin tsarin jiki,sai da mahaifiyata ta yi shekara biyar da aure sannan ta samu cikina,nan fa mahaifina Alhaji Sa'eed ya dinga kula da mahaifiyata tare da tausayinta,don yana sonta sosai ana haka wataran ta fara naฦ™uda sosai aka kaita asibiti,tunda Hajiya Tani taji ankai mahaifiyata asibiti bata yi ฦ™asa a guiwa ba,sai ta nufi asibiti ta saka niฦ™abi a fuskarta ta yadda ba za a gane taba,ta shigo har cikin asibitin ta samu nurse ษ—in da ke duty,ta sakar musu kuษ—i ta basu ragama akan kashe mahaifiyata,saboda kuษ—i suka aikata abinda suka aikata suka shaฦ™e mahaifiyata ta mutu tana halin naฦ™uda,sai dai kash an kashe miciji batare da an sare kansa,ana cikin hakan mahaifiyata ta haifeni,suka ciro ฦดar sannan suka kashe ta,babu wanda baisan Hajiya Tani ce ta aikata hakan ba har ฦ™ara aka shigar bayan likitocin sun tona mata asiri ammanfa Hajiya Tani mutum ce me shegen wayo da sanin makamar aiki na asiri don haka tuni ta kashe bakin kowa,don ko da kayi yunฦ™urin ta yarda maganar to tabbas sai ta kashe ka,yayan mahaifiyata ita ta kasheshi har lahira don ya tayar da maganar,shiyasa babu wanda ya tayar da maganar har iyau,da yayar mahaifiyata ta amshi ruฦ™ona bayan ansha gwagwarmaya da mahaifina akan badani don son mahaifiyata ne ya shafeni,amman fa a yanzu ta manta na yana da wata ฦดa mai suna Basma don tuni ya manta dani don Hajiya Tani ta mallakesa sai yadda ta yi dashi.
Wani guntun hawaye na share don tuno da wannan labarin da Mama ta daษ—e tana bani,tabbas inason in zama lauya amman babu yadda za ayi in zama hakan tunda ni kurma ce,ina yawan kuka akan kasancewa ta kurma ammanfa idan na tuno shima jin wata ฦ™addara ce ta rayuwa sai in share hawayena in cigaba da roฦ™on Allah akan Allah ya banni ma a hakan don wannan ma wani ladane na daban,don duk mutumin da Allah ya haliccesa da wata tawaya yasan abinda yasa ya barshi a hakan,don shi yasan kaษ—ai abinda jin zai haifarwa wannan bawan na sa.


*******
Masarautar ฦ™aisa


Cikin takunsa mai ฦ™yau da kuma tsari ya shigo sashen Sarki Abdulhamid ฦ˜aisa,sarkine mai mutunci da mutunta mutane kana ganin Sarki Hamid kasan shine mahaifin yarima Abeed don kamarsu ษ—aya sosai sai dai yarima Abeed yafi mahaifinsa fari da kuma yarinta.


 "Allah ya ฦ™ara maka lafiya ya Abee,ina gaisheka ina ฦ™ara gaisheka Sarki mai adalci Allah dai ya barmu da kai cikin ฦ™oshin Lafiya".

 ษ—an murmushi ya yi irin na Abeed ya ce"ina sonka ษ—ana,Allah dai ya zaษ“a maka mata salihar baiwa wacce duk zamuyi alfahari da ita a masarautar nan,sai dai har yanzu baka kawo mana gimbiyar ba haryanzu, har mun gaji da zaman jira".

ฦŠan murmushi ya yi yana sosa ฦ™eyarsa ya ce"Abee ka tayani da addu'ah don yanzu samun mata ta gari shine komai". Fatan alkhairi ya yiwa ษ—an nasa mafi soyuwa aransa.

"Abee insha Allah gobe zan koma aikin nan namu atayamu da addu'ah Allah ya bamu nasara".ษ—an ษ“ats fuska Sarki Hamid ya yi don arayuwarsa babu abin daya tsana irin aikin Hamid don aiki ne na hatsari wato aikin soja.

 Ganin hankalin mahaifinsa ya tashi yasa ya zauna sannan ya ce"Abee agurinka kawai na ke samun fatan alheri na wannan aikin nawa,saboda Ammi babu abinda ta tsana irin aikina,kuma babu yadda zanyi ne shiyasa,na tayin addu'ar Allah yasa idan ba alkairi bane aikina Allah yasa inji ya fita daga raina amman kullum ฦ™ara kusanta na ya ke".sai ya yi kalar tausayi don haka Abee ya ce"babu komai Yarima Allah ya dafa maka ya baka abinda ka keso duniya da lahira,ya tsareka da dukkanin wani sharri".murmushi Abeed ya yi don jin daษ—in addu'ar mahaifinsa ya ce"Amin Abee na gode.

 Wannan abinda Sarki Hamid ya saba bawa Abeed yauma shi ya bashi yana ฦ™ara ja masa kunne akan ya kula dashi sosai kamar yadda zai kula da kansa.



*miss green ce*
[08/08, 14:11] Miss Green๐Ÿ€: _*๐Ÿ”–BASMA*๐Ÿ”–_ 

๐Ÿ“„Littafi na 1


*UMMU MAHER(MISS GREEN๐Ÿ๐Ÿ€)*

_Noticed๐Ÿ›:wannan littafin labarine akan wata yarinya wacce ta kasance kurma ce._


Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444


*Matso kuji๐Ÿ‘‚๐Ÿป*

mu kasance masu rintse ganinmu da jinmu yin haka zaisa mu ragewa kanmu zunubi musamman yanzu da mutanen duniyar suka taฦarฦare,Allah ya tsare mana imaninmu amin.

----------------------------

  5⚪6


. . .tafiya na ke cikin nutsuwa na saka hijabina kalar ruwan makuba,kasance wa ta mai hasken fata sai hijabin ya yi min ฦ™yau sosai,dai dai ฦ™wanar makarantarmu wata mota ta shawo ฦ™wana da gudu na yi gefe don saura kaษ—an ta bigeni,tsoro ya shigeni  na kama makyarkyata saboda tsoro bakina yana rawa.

 dai dai lokacin na cikin motar ya fito yana faษ—a na rufe fuskata don tsoro,Salimat ma alokacin sun taho zasu tafi islmiyyar don ita daman sai ta gama biyawa ฦ™awayenta na iska sannan suke tahowa ita kuma Hafsat ba tada lafiya.
 Ai kuwa ganin wannan mai motar yana faษ—a sai itama Salimat ta fara faษ—an ฦ™awayenta na biye ta."Hmm wannan yarinyar ta saba wannan rashin mutuncin da ma ka bugeta ka buge banza don daman musaka ce,bata ji kurma ce don haka ka ga sai ta dawo babu hannu babu ฦ™afafu babu ido musaka sak".

 wani tsananin tausayi ne ya kama Ahmad ya kalli inda Basma take ta takure kanta sosai saboda tsananin tsoro da fargaba,a take yaji yarinyar ta ฦ™wanta masa saboda ko da ganin yadda Allah ya yi ta haฦ™iฦ™a ya yi mata baiwar da ba kowa ne ya santa ba.
 Kasa ฦ™arasa tunanin nasa ya yi ganin fuskar Basma yaji numfashinsa ya kusa ษ—auฦ™ewa.ga ta dai kurma amman Allah ya tsara mata halitta mai ฦ™yau da tsari babu wanda zai ce kurma ce saboda yadda Allah ya tsara baiwarsa.

 Ta kowa ya yi a hankali ya ce"yi haฦ™uri kinji wallahi ban san ba ฦ™ya ji ba".ya haษ—a hannayensa alamar ban haฦ™uri.a take fuskar Salimat ta sauya don ganin mutumin ya biyewa Basma yana ta wani rawar kai,gashi ฦ™yaฦ™ฦ™yawa dashi ษ—an manya don daga ganinsa kuษ—i sun zauna masa sosai.
 Cikin fushi ta yi hanyar makarantar ฦ™awayenta na ta ฦ™ara zuga ta,ita kuma tana ฦ™ara hawa kamar ko gi.
Babu yadda baiyi da Basma ta faษ—a masa inda gidansu ya ke ba amman taฦ™i,ฦ™arshe ma ta yi wucewarta makaranta,jikinta sai rawa ya ke.
  Wani yaro ya samu ya tambayesa ina ne gidansu Basma tiryan tiryan yaron ya rakasa,Ahmad ya zaro kuษ—i ya bawa yaron,cikin murna yaron ya ce"na gode".
 "don Allah shiga nan gidan kace wai ana sallama da maigidan idan yana nan kaji"?cikin murna yaron ya ce "to".sannan ya shiga gidan.
  Allah ya taimaka lokacin Alhaji yana Alwala ya shigo ya ce"wai ana sallama da maigidan".
  
  To Alhaji ya ce sannan ya fito,hango mai danฦ™areriyar mota ya yi yana mamakin wannan waye?donshi babu wanda sukayi dashi zaizo wajensa.

 Bayan sun gaisa Ahmad ya ce"daman Baba zuwa na yi in nemi izininka wajen neman aurar ฦดarka don kada in tsaya da ita ba tare da anyi min ixini ba,idan muka daidaita sai in turo magabata na."

 sosai yaji daษ—in jin maganar yaron don dama haka addinin musulunci ya tanadar mana idan ษ—ayanku zai nemi aurar yarinya kafin ya fara tsayawa da ita to ya nemi ixinin iyayenta.
 
 "Wacce daga ciki ษ—an samari"?.
 "baba yarinyar kurma ce amman ban san sunanta ba?".

 wani murmushin jin daษ—i Alhaji ya yi sannan ya ce"to to Basma zaka ce min yarinyar kirki indai Basma ce na baka izinin tsayawa da ita don kaima na yarda da hankalinka da tunaninka don haka babu komai na yarje maka,idan kuka sasanta sai ka turo iyayenka,amman ni mariฦ™inta ne Babanta yana maiduguri da zama idan cen ษ—in zakuje ma babu komai,mudai fatanmu kariฦ™e mana Basma da amana don marainiya ce".
 
  "Babu komai Baba insha Allah bazan taษ“a tozarta Basma ba ina fatan Allah yasa ta soni kamar yadda na ke sonta".

 fatan alheri Alhaji ya yiwa Ahmad sannan ya ษ—akko kuษ—i a mota ya bawa Baba masu yawa yaฦ™i karษ“a dole ya mayar dasu cikin motar.

 Babu abinda ya ษ“oyewa mama ta dinga murna tana sanya alheri,babu yadda Alhaji ya iya dole ya faษ—awa Hajiya Sara.
 
Ranar ฦ™wana ta yi bata yi bacci ba saboda tsabar baฦ™in ciki da kuma hassada,da sassafe ta fara shirin tafiya ฦ™yauyensu don baza ta yadda tana ji tana gani wannan kurmar ta samu miji ฦดaฦดanta basu samu ba.






*don Allah kuyi haฦ™uri typing ya yi min yawa shiyasa na yi kaษ—an*


*miss green ce*
[08/08, 14:11] Miss Green๐Ÿ€: BASMA:: https://arewabooks.com/book?id=62d10b4de4924f3d434fb605


_*๐Ÿ”–BASMA*๐Ÿ”–_ 

๐Ÿ“„Littafi na 1


*UMMU MAHER(MISS GREEN๐Ÿ๐Ÿ€)*

_Noticed๐Ÿ›:wannan littafin labarine akan wata yarinya wacce ta kasance kurma ce._


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444


*Matso kuji๐Ÿ‘‚๐Ÿป*
Mu rage yawan cin naman mutane domin yin hakan yana haifarwa rayuwarmu tangarษ—a sosai,kuma yana rage maka ฦ™ima har awajen Allah.
------------------------------

   7๐ŸŸข8

. . .Abin tsautsayi Hajiya Sara ta yi hatsari a hanyar garinsu,ina zaune ina yankan salad sai ga Maryam ta shigo kitchen kai tsay,ta shaฦ™o min wuya tana ce wa"shegiya mayya kin lashe mana kuruwar uwarmu yanzu gashinan ta yi hatsari akan hanya wallahi bazamu yarda ba,daman tunda za ta yi tafiya ta ce ta yi mafarkin kin biyota tana gudu kina gudu to wallahu ba zamu yarda ba".kuka na fara yi ina buษ—e bakina kamar zanyi magana duk hankalina ya tashi sosai saboda tsabar masifarsu yanzu duk na koma ฦ™ashi saboda azaba.
 Ga shi babu kowa a gidan,don haka tuni ta fara wanka min mari tana ce wa"shegiya munafuka tunda ki ka zo gidannan baki ษ—aya kin hanamu da uwarmu zaman lafiya saboda tsabar masifarki da kuma maitarki sai anyi magana ace wai ke kurma ce ana jin tausayinki daga haka ki cinye mutane."
 Fuska ta ta yi jawur saboda shan mari ta kumbura ga kuma farar fatata da ta yi ja ษ—au,don kanta ta gaji ta fita badon ta gaji da dukana ba,tunda ni dai ba ramawa zanyi ba.

 Ina zaune a kitchen ษ—ina ina ta kukan maraici,tabbas rashin uwa arayuwa ba ฦ™aramin tasiri ya ke takawa arayuwa ba,to ni banma santa ballanta ma inganta in faษ—a mata abinda ya ke damuna tunda mahaifina ma ya manta yana da wata ฦดa ma.

  Wannan abin ba ฦ™aramin damun zuciyata ya ke ba,duk da mama bata taษ“a barina na yi kukan rashin uwa ba,komai da uwa za ta yi wa ฦดaฦดanta mama tana yimin,wani abinma kafin ta yi wa Hafsat ni ta yi min.

 Ina nab zaune sai ga yaya Abubakar ya shigo hankalinsa atashe don yanzu a ke faษ—a masa hatsarin da ya faru da mahaifiyarsa,sai ya haษ—u dani ina fitowa a kitchen ษ—in fuskata ta yi jawur da ruwan hawaye.bakina ya kumbura har jini ya taru ba tare dana sani ba.

 "Subhanalillah,Rabi'atu me ya faru da bakinki kuma ya yi ja haka?".ษ—an taษ“a bakin na yi naji zafi sosai sai ga hawaye shar.

 "Me ya faru wa ye ya yi miki haka?".ban basa amsa ba yasha gaba sannan ya ce"Rabiatu ni ba yaro bane ki gayamin abinda ya faru da bakinki ko kuma wallahi babu ruwana da ke".
 da sauri na shige ษ—akinmu ina kuka,yabi bayana da kallo yana tausayawa rayuwata,yana shiga ษ—akin Hajiya Sara yaga Maryam ta yi zuru2 na rashin gaskiya ga tsoro fal idanuwanta don tasan Yaya Abubakar dukansa dukan mutuwa ya ke,sosai ya fuskance ya kuma fahimce ce wa ita ce ta yi wa Rabiatu wannan abin.

 Bai ce mata komai ba ya shige ษ—akin yana dariyar mugunta ya je ya kulle ฦ™ofa ya fara jibgarta sai da ya haษ—a mata jini sosai a bakinta sannan ya ce"to dabara ta rage ga mai shiga cikin rijiya ko yau ki ka ฦ™ara yi mata haka nima fa bazan gaji ba,mu zuba mu gani."

 yana faษ—ar hakan ya barta a wajen tana kukan neman taimako,Hajiya Sara ta karye a ฦ™afarta don haka sai da a kayi mata gyaran ฦ™afar sannan suka dawo da ita gida,ganin bakin Maryam duk ya kumbura ta tambayeta me ya faru?ta ฦ™washe ฦ™arya da gaskiya ta faษ—awa Hajiya Sara,ai kuwa da Abubakar yaxo ce wa ra yi"to sallamamme ษ—an gidan hajiya hasiya ni dai yau wallahi na yafewa hasiya da Basma kai,tunda ka nuna a fili wancen kurmar ta fi ฦ™annenka mutunci,idanma wani abin ka ke nufi da wannan yarinyar kasani sai dai ka mutu don wallahi ba zaka auromin kurma agidana ba,daman Maryam duk ta faษ—amin yadda ka ke tsare yarinyar a lungu kana tsara mata xance,kana nan tuzurun ฦ™ato duk ฦ™annen bayanka sunyi aure kai ka zauna gantalewa,ayi dai my gani na yafewa hasiya kai".
 
 babu yadda ya iya haka ya zauna yana ta nunawa mahaifiyarsa yadda zancen ya ke ammanfa sai ta toshe kunnuwanta tana yi mai kallon banza.daga ฦ™arshe dai tashi ya yi ya tafi ransa a ษ“ace da zaluncin da mahaifiyarsa ta ke yi.
Cen ma ษ“angaren mama masifa ta ke sosai na abinda a ka yiwa Rabiatu Alhaji yana dawowa ta fashe mishi da kuka tana faษ—a masa ce wa ya yi musu katanga dasu Hajiya Sara don bayan kurmanta so suke su kashewa yarinyar halitta ta dawo na ฦ™asashshiya,sosai ran Alhaji ya ษ“aci ya bawa Mama haฦ™uri sannan ya yi mata alฦ™awarin kawo ฦ™arshen abin ฦ™wanannan gidan zai raba biyu yaga ta tsiya,sosai mama ta yi murna da hakan don idan da ita kaฦŠai ne ba za ta damu ba don matuฦ˜ar hajiya sara ta yi mata ita ma ramawa ta ke to shiyasa ba za ta yi mata hakan ba.




****
Sosai gaban Yarima ya faษ—i ganin modesta a ฦangarensa,ta matse sosai cikin kayan bacci,ya dafe kansa tunawa da ya yi mukullin ya barsa a wajen mai aikinsa,banza ya yi mata ya shige ษ“angarensa dai gata ta buyosa tana wani rungumarsa,wani irin abu yaji yana yawo a jikinsa ya juya da sauri ya dafa wannan tsarin da mahaifinsa ya basa yana kiran sunan Allah,sai ga Modesta a ฦ™asa wanwar ta bugu sosai,wannan manyan hips ษ—in na ta sun bugu,ta fasa ฦ™ara.





*Miss green ce*
[08/08, 14:11] Miss Green๐Ÿ€: _*๐Ÿ”–BASMA*๐Ÿ”–_ 

๐Ÿ“„Littafi na 1


*UMMU MAHER(MISS GREEN๐Ÿ๐Ÿ€)*

_Noticed๐Ÿ›:wannan littafin labarine akan wata yarinya wacce ta kasance kurma ce._


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444


_MT COLLECTIONS๐ŸŒฟ☘️_
_Ina kuke mata ฦดan ฦ™walisa masu son ado na kece raini๐Ÿ’„๐Ÿ’‹ kiji next year Alhaji yayi mai kyautar ฦดar moton nan ko yace Hajiya na biya Maki kujerar Hajj๐Ÿคช nan dai ko wa ke fatan yagan sa yaje๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿšถ‍♀️๐Ÿšถ‍♀️ Kuzo ga kayan gyarar Aure daga taskar mu MT, matsalar ki yamushewar jiki , rashin ฦ™iba kema so kike duk inda kika je ace ga Hajiya tazo ku bata wuri๐Ÿ˜ , ko matsalar infection ke damunki , rashin ฦ™arfin ษ—a namiji saurin gajiyawa ke Kuzo akwai ingantattun kayan mata dana gyara Suplement wanda zai gyaraki kiyi caras abunki , idan ฦ™iba ne tayi maki yawa kisha kiga kin koma dai dai ษ—aukar oga๐Ÿ™ˆ๐Ÿ‘‡ ._
_Infection na buda gaban mace taciki yabar wajen a tsuke a matse kullum kina zaune kina cewa kefa a matse kike alhalin Mai gidan hkr yake๐Ÿƒ๐Ÿป‍♀️_

_Ina macen da batada shaawa kwatakwata ke bakijin feeling toh wlh kixo Kisha infection set dinmu Dan girman Allah inkinsha kitafasa ma oga infection flusher kibashi ya subhanalillahi Ranan kam saidai kukawomun yarana ajiya๐Ÿ˜… in ana sallah baa magana daga wanan ranan zakisa mene ne wanga Abu kenufi kinji_๐Ÿ™ˆ๐Ÿ™ˆ

_Infection nasa ruwa agaban mace tsinkakken ruwa Wanda shi Sam baida yauki toh wanan fa ba ruwan niima ba ne ruwan niima shine Mai yauki hajaju kizo Kisha infection set kirabu da sharrin infection Dan Allah_

 _infection set dinmu zai wanke miki Mara zai share yakwashe duk wani sanyi na jiki dana mara_
 _ina mai famada ciwon Mara mai tsanani lokacin alada zokisha toilet infection dinmu wannan ciwon yazama tarihi.._
_Ba'anan Mt collections ta tsaya ba , muna sai da liquid soap mayuka na haษ—i , turaruka ,shu'umin humra , colecture shampoo conditioner da dai sauran su ...mayukan Suplement wanda zasu dawo maki da martaban fatar jikin ki yasa jikin ki tayi sumul kiga fata na sheฦ™i yana glowing ,kar ku manta ku biyo mu a shafikan mu na๐Ÿ‘‡_
_INSTAGRAM๐ŸŽฏ #MT COLLECTIONS_
_FACEBOOK #MT COLLECTIONS_
_WHATSAPP๐Ÿช€ 08081202932_
CALL☎️ _09060703187_
_Muna bada sarin kayan mu a ko'ina ษ—aya ko sari... Zaku samu shagon๐Ÿ™️ mu a nan cikin garin Zaria  City babban dodo benen Yahya Aminu #MT COLLECTIONS 015_

_MT COLLECTIONS TAKU CE☘️_


 9๐ŸŸข10

Da ฦ™er modesta ta tashi ranta na matuฦ™ar yi mata suya ta ce"yanzu Yarima saboda na nuna maka so da ฦ™auna shine zaka yimin wannan abin to wallahi zaka san ka yi min haka sai ka zo kana roฦ™ona in soka".
 ษ—an murmushin ฦ™arfin hali ya yi sannan ya nuna mata ฦ™ofar ษ—akin da hannunsa ya ce"ku fita banason in ฦ™ara ganin wannan mummunar fuskar ta ki don Allah,ke ko kunya ma bakiji ba?shin shi addinin na ku bai hanaku zina bane?kin daษ—e kina yaudarata da salonki ada cen baya ma dana biye miki yanzu Allah ya shiryar dani,don haka kada ki yadda in ฦ™ara ganin fuskarki anan."

 yana faษ—ar hakan ya yi shigewarsa ciki ya batta anan,kuka sosai modesta ta yi a wajen gani ta ke kamar ba Abeed ษ—in da ta mayar dashi mayen mata bane,tabbas Abeed mutunne mai mutunci da karrama ษ—an adam,ya ษ—auketa aiki ne ba don komai ba sai don tausayinta da ya ke ji a matsayinta na mace kuma talaka,har yau har gobe shine ya ษ—auki nauyin ciyar da iyayenta,da ya ke suma anan pataฦ™wat ษ—in suke.

 Tun fara aikinta a gidan ta ke matuฦ™ar sonsa da ฦ™aunarsa ta gwadasa ta fanni da dama ba tare da ya taษ“a ko da kallonta ba,rana ษ—aya bosayo wata ฦ™awarta ta bata shawarar yi wa Abeed asiri,da ya ke mutum ne mai tsoron Allah da ki ya ye dokokinsa,a wanan lokacin bai kamasa ba,sai ta koma kan abincin sa anan ne ta samu dama,ta zuba masa maganin mugun sha'awar mace,ai kuwa awannan ranane ranar da Abeed bazai taษ“a mantawa da ita ba,ya fara saษ“awa mahallincinsa suna holewarsu da Modesta,aฦ™wai lokacin da modesta ษ—in taja garinsu kasa haฦ™ura Admiral B.ya yi ya.ษ—akko bosayo wato aminiyar modesta suka tare,aฦ™wai wanda mahaifin Abeed ya ษ—ora wajen kula masa da ษ—an na sa duk da ba yaro bane,amman zama irin wannan babu mata,ga kuma matan da kansu suke kawo kansu,don haka yasa a kula masa da duk motsin da Abeed zaiyi.ai  kuwa wannan mutumin ya gano Abeed yana kawo mata gidansa,lokacin da mai martaba yaji wannan ba ฦ™aramin baฦ™in cikin abin ya yi ba,kuka babu irin wanda baiyi ba yasan halin ษ—an sa da bin dokar ubangiji bazai taษ“a yin hakan cikin hankalinsa ba,dole aฦ™wai wata a ฦ™asa.

 Babu shiri ya kira Abeed ya ce ya dawo gida,ai kuwa aranar ya dawo yadda yaga ran mahaifin na sa ya tashi ba ฦ™aramin ษ—aga masa hankali ya yi ba,babu abinda Mahaifinsa ya ษ“oye masa na daga cikin abinda aka faษ—a masa akansa.

 Sosai Abeed ya yi nadamar abinda duk ya aikata haka kurum dai yaji bazai iya rayuwa idan babu mace ba,kai tsaye ya faษ—awa mahaifinsa abinda ya ke ciki.

 Cikin ษ“acin rai ya ce ai kuwa aure ya kamata ayi maka don bazan yarda ana zubar min da mutunci ba,faษ—in wannan maganar har zazzaษ“i sai da Admiral B.ya yi donshi fa har yanzu baiga macen da ta ฦ™wanta masa ba.

 Ana haka Sarki ya haษ—awa ษ—an na sa maganin tsari da kansa sannan ya koma,sannan sarkin yasa wannan mutumin ya ฦ™ara zuwa ya yi masa ษ“oyen sirri,anan ya gane yanzu Admiral B.ษ—in ya daina bin mata ya nutsu aikinsa ne kawai a gabansa.

 Sosai Sarki yaji daษ—i ya kuma yi wa ษ—ansa fatan alkhairi akan Allah ya bawa ษ—an nasa mata tagari sanyin idaniyarsa.
Duk wannan abin da ake yi Sarauniya jidda bata san me ake ciki ba,ita hankalinta yanzu ya koma kan nemowa ษ—an ta mata ta nunawa sa'a ฦดar sarauta don ita a tsarinta idan ba ฦดar sarauta ba,to lallai ba matar yarima ba ce.



****

Muna dawowa daga makaranta ina bitar karatuna hankalina aฦ™wance na ruฦ™o qur'anina a ฦ™irjina kaina a ฦ™asa,kunya,kamala,hankali,duk kana kallona ba sai angaya maka ba kasan ce wa na tattara duk wannan nasabar.

 Dai dai wata  mota mai ฦ™yau na wuce ko kallon inda take banyi ba sai kawai naga mai motar ya biyoni,yasha gabana,saurin ษ—aga idanuna na yi na kallesa,masha'Allah ฦ™yaฦ™ฦ™yawa ne sosai babu ฦ™arya kuma saurayi ne bazai wuce 28 years ba,gaba ki ษ—aya ya saki hanci da baki da komai yana kallona,ya ce assalamu alaikum duk da bana ji kamar ya sani ya ษ—aga hannayensa ya haษ—a biyu alamar gaisuwa,nima amsa masa na yi da hannuwa na ya ce"yaya sunanki"?.yana maganar yana dariyarsa mai tsayawa arai,ganin ban basa amsa ba ya ษ—akko wani ษ—an littafi a aljihunsa sa bairo,babu yadda na iya na rubuta masa sunana Basma.

 Ya karษ“a ya ce nice name Basma,ya rubuta min sunansa Zaidul abidin,na ษ—aga masa hannu alamar na tafi don tsoro ne fal a zuciyata gashi zuciyata sai bugawa ta ke ban taฦa jin son wani ฦŠa namiji ba,irin abidin kawai lokaci ษ—aya naji ina sonsa.

 Yasha fa gashin kansa ya yi ya shiga motarsa ya biyo Basma har ฦ™ofar gidansu,don abaya ya biyota ba tare da ta sani ba.

 Ya ษ—auki wayarsa yana murmushi ya ce"Ammi na yau dai addu'arki ta amsu ayau na samo miki suruka Basma".

 murna sosai mahaifiyarsa ta yi don aabidin shi kaษ—ai ne ษ—anta aduniya shiyasa ta ke matuฦ™ar sonsa kuma ta ke son ya yi aure da wuri,musamman saboda matsalar da ya ke da ita ta ciwon zuciya.




*Miss green ce*
[08/08, 14:11] Miss Green๐Ÿ€: _*๐Ÿ”–BASMA*๐Ÿ”–_ 

๐Ÿ“„Littafi na 1


*UMMU MAHER(MISS GREEN๐Ÿ๐Ÿ€)*

_Noticed๐Ÿ›:wannan littafin labarine akan wata yarinya wacce ta kasance kurma ce._


Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444


*Matso kiji*

Yin sallah akan lokaci yana da matuฦ™atar tasiri acikin rayuwarmu,na hanamu alfasha da kuma kariya daga ubangiji.
---------------------

    11๐ŸŸก12

Ina zaune ina karatun alqur'ani a cikin zuciyata mama ta nufo inda na ke tana dariya ta ce"Basma anjima zaki yi baฦ™o ya ce wa babanku anjima xaixo wajenki to don Allah Basma kada ki ba da ni,ki bawa mara ษ—a kunya kinga dai halin da muke ciki daga ni har ke,aurenki ayanzu shine zai kawo warwa rewar matsalar gidan nan don daman ke ce basa son gani agidan don haka duk baฦ™in cikinsu sai kin riga ฦดaฦดanta aure muna nan dasu.

 ฦŠaga kaina na yi cikin biyayya,mama ta ce"Allah ya yi miki albarka Basma ya haskaka miki rayuwarki Allah ya baki masu yi miku biyayya ke ma".


 Hafsa ce ta tsantsaramin ฦ™walliya,na yi ฦ™yau sosai kamar ka ษ—aukeni don ni ba ma'abociyar ฦ™walliya ba ce iya ka in saka hoda da lipstick shikkenan,ni adole na yi ฦ™walliya kuma ko ina akace in shiga zan shiga.

 Mama ta ce"Basma baฦ™on fa yaxo har yanzu baku gama ฦ™walliyar bane?yana ษ—akin babanku kinga babu daษ—i yana jiranku fa?".
  Hijabina na ษ—akko a wanke a goge ruwan skye blue na saka,ai kuwa Hafsa ta tirษ“une fuska wai dole sai dai in saka mayafi,duk abinta ฦ™in sakawa na yi na noฦ™e ฦ™eyata alamar ba zanyi ba,dariya Mama ta yi ta ruฦ™o hannu na tana ce wa"ko turare baki saka ba Basma bari asaka miki".
 war na yi da idanu na kamar zanyi kuka ta sani sarai bana saka turare don duk matar da ke saka turare tamkar tana yaษ—a zinane don wani ฦ™amshin kawai zaiji ya ji yana sha'awar mace don haka dole mutum ya kiyaye dokokin ubangiji.
Ina shiga ษ—akin kaina a ฦ™asa na tsugunna na gaishesa ba tare dana kalli fuskarsa ba,ษ—agowa ya yi yana kallona sosai yana jin ninkin son Basma acikin ransa,tabbas auren Basma ayanzu shine babban burinsa na rayuwa,yana sonta da dukkanin gaskiyarsa.

 Na samu guri na zauna a lallausan kafet ษ—in idanuna a ฦ™asa yana wasa da ฦดan yatsun hannuna ya ce"Basma ni sunana Ahmad nasan baki sanni ba,amman na sanki ni na nemi ixinine tun daga wajen mahaifinki kafin inzo,na yi hakanne don kare hukuncin Allah wanda ya horar damu,idan zakuyi aure ku fara neman izinin mahaifin mace ba kawai ka tsare yarinya akan hanya ka ce kana so ba".

 "Basma ina ฦ™aunarki da dukkanin gaskiya ta,ina sonki don Allah badon komai ba,sai don addininki da hankalinki,tabbas duk wanda ya aureki a matsayin matar aure to tabbas ya samu mata tagari,ina fatan yadda na ke sonki ki soni ko da bai kai yadda na ke sonki ba".

 ษ“oye fuskata na yi waini kunya,ya kalleni ya ce"Basma ba zanyi miki dolen so na ba,zan baki nan da ฦดan ฦ™wanaki har ki saba dani.

 Nan dai ya dinga yimin hira ni kuma ina ta ษ“oye fuska ta,don matuฦ™ar kunyarsa na ke ji,da zai barni da tuni na daษ—e da guduwa,don muguwar kunyarsa na ke ji.

 Shima ya fuskanci hakan sai ya tsagaita hirar tamu ya ce"to Basma zan tafi da ฦ™aunarki da kuma sonki,don Allah kimin abinda zan ta tunaki har in ฦ™ara dawowa."

 to fa rasa me zanyi masa na yi,kunya ta isheni na juya fuskata. Ya ce"Basma kenan kunya ta hanaki sakat amman na gode don kunyarma ai tana da daษ—i a wajen mace,don haka ni zan tafi insha Allah wani satin ranar jumma'ah kenan zan dawo".

 yana fita na ฦŠan rakasa ฦ˜ofar gida,nan muka haฦŠu da maryam a hanya har tana neman bugeni,ta saki hanci da baki tana kallon Ahmad wanda bai ma san tana yi ba.

 Mamakin ganina atare dashi ta yi,wani malulun baฦ™in ciki ya tsaya mata a zuciyarta,ta kalli bayan Basma ษ—in ta gallara mata harara ta wuce tana ce wa in kinsan wata ai baki san wata ba,don wallahi bazamu yarda ki yi aure agidannan mu bamu yi ba.

 "Hajiya wallahi da idona na ganta sun fito daga ษ—akin Abba na ฦ™asan bene,wallahi Hajiya sai munyi da gaske kan yarinyar nan don na ga alamar nan ba da daษ—ewa ba za ta bar gidannan ta barmu."

 "ina ai wallahi bata isa ta yi aure a gidannan ba,ke bari ma ingaya miki Basma indai ina raye babu wanda zai so ta don wallahi bama ta Isa ta yi auren ina raye ba".


 muna sallama da Ahmad ya shiga cikin motar ni kuma ina bakin ฦ™ofar motar,sai ga Yaya Abubakar nan na gaishesa ko amsawa baiyi ba ya shige cikin gidan.

 Na koma gidan duk guiwa ta asake,ina ji araina ko na yi masa laifi ne ban sani ba?babu wanda zai bani amsar don haka na shigo cikin gidan.
***

Bayan Yarima Bilal ya samu hutu ya dawo gida,gidan ana ta hidimdimu,duk da yasan duk sanda zai dawo Sarauniya jidda tana gabatar masa da walimu kala kala,amman sai yaga na  yau kamar yafi na kullum,kai tsaye mangaren mahaifiyarsa ya nufa yana zuwa ya rungume ta yana ce wa"Gimbiyata na dawo dafatan na sameki lafiya"?.

 itama cikin farin cikin ganin ษ—an na ta ta ce"lafiya lau ษ—ana yariman gobe,kuma ango".

 da mamaki ya ke kallon Sarauniya jidda da taga mamakin hakan ya ke sai ta ce"jakadiya Ramlat ku fito tare da Khadija".

 ฦ™yaฦ™ฦ™yawar yarinya ce a gabansa ta tsaya wacce tasha ฦ™walliya cikin kayanta na sarauta bayan ta zauna ta gaishesa ya amsa yana mamakin wannan wacece?.

 "na san baka santa ba amman yanzu zaka santa wannan matarka ce ayau aka ฦŠaura maka aure da ita,aฦ˜wai gimbiya abida ma itama matarka ce yau aka ฦŠaura muku aure ita a sudan ta ke ฦณar masarautar mu ce"

 da sauri ya tashi yana mamakin wannan yanke hukunci irin na mahaifiyarsa sarauniya jidda,yaya zaiyi da mata biyu a yanzu kuma?.



*miss green ce*





_MT COLLECTIONS๐ŸŒฟ☘️_
_Ina kuke mata ฦดan ฦ™walisa masu son ado na kece raini๐Ÿ’„๐Ÿ’‹ kiji next year Alhaji yayi mai kyautar ฦดar moton nan ko yace Hajiya na biya Maki kujerar Hajj๐Ÿคช nan dai ko wa ke fatan yagan sa yaje๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿšถ‍♀️๐Ÿšถ‍♀️ Kuzo ga kayan gyarar Aure daga taskar mu MT, matsalar ki yamushewar jiki , rashin ฦ™iba kema so kike duk inda kika je ace ga Hajiya tazo ku bata wuri๐Ÿ˜ , ko matsalar infection ke damunki , rashin ฦ™arfin ษ—a namiji saurin gajiyawa ke Kuzo akwai ingantattun kayan mata dana gyara Suplement wanda zai gyaraki kiyi caras abunki , idan ฦ™iba ne tayi maki yawa kisha kiga kin koma dai dai ษ—aukar oga๐Ÿ™ˆ๐Ÿ‘‡ ._
_Infection na buda gaban mace taciki yabar wajen a tsuke a matse kullum kina zaune kina cewa kefa a matse kike alhalin Mai gidan hkr yake๐Ÿƒ๐Ÿป‍♀️_

_Ina macen da batada shaawa kwatakwata ke bakijin feeling toh wlh kixo Kisha infection set dinmu Dan girman Allah inkinsha kitafasa ma oga infection flusher kibashi ya subhanalillahi Ranan kam saidai kukawomun yarana ajiya๐Ÿ˜… in ana sallah baa magana daga wanan ranan zakisa mene ne wanga Abu kenufi kinji_๐Ÿ™ˆ๐Ÿ™ˆ

_Infection nasa ruwa agaban mace tsinkakken ruwa Wanda shi Sam baida yauki toh wanan fa ba ruwan niima ba ne ruwan niima shine Mai yauki hajaju kizo Kisha infection set kirabu da sharrin infection Dan Allah_

 _infection set dinmu zai wanke miki Mara zai share yakwashe duk wani sanyi na jiki dana mara_
 _ina mai famada ciwon Mara mai tsanani lokacin alada zokisha toilet infection dinmu wannan ciwon yazama tarihi.._
_Ba'anan Mt collections ta tsaya ba , muna sai da liquid soap mayuka na haษ—i , turaruka ,shu'umin humra , colecture shampoo conditioner da dai sauran su ...mayukan Suplement wanda zasu dawo maki da martaban fatar jikin ki yasa jikin ki tayi sumul kiga fata na sheฦ™i yana glowing ,kar ku manta ku biyo mu a shafikan mu na๐Ÿ‘‡_
_INSTAGRAM๐ŸŽฏ #MT COLLECTIONS_
_FACEBOOK #MT COLLECTIONS_
_WHATSAPP๐Ÿช€ 08081202932_
CALL☎️ _09060703187_
_Muna bada sarin kayan mu a ko'ina ษ—aya ko sari... Zaku samu shagon๐Ÿ™️ mu a nan cikin garin Zaria  City babban dodo benen Yahya Aminu #MT COLLECTIONS 015_

_MT COLLECTIONS TAKU CE☘️_



Ga group

Na face book
ak saraki
    &
Ummu maher miss green๐Ÿ€



Ummu maher palace

๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=pfbid02Bi3dtp6ftDQ6vyRa5mVewzSiNsXA6N97Uq2Qeypf7j5g2FpN5XsRjsKqXGi3D2gal&id=100082587072617&sfnsn=scwspwa



Ak palace
๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป


https://facebook.com/groups/943534712916776/
[08/08, 14:11] Miss Green๐Ÿ€: _*๐Ÿ”–BASMA*๐Ÿ”–_ 



   
     Na๐Ÿ’‹
*(UMMU MAHER)MISS GREEN๐Ÿ€๐Ÿ*



_Noticed๐Ÿ›:wannan littafin labarine akan wata yarinya wacce ta kasance kurma ce._


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444



  13๐ŸŸข14


. . . . . Kasa magana Abeed  ya yi kawai ya sunkuyar da kansa don hukuncin da mahaifiyarsa ta yanke akansa ya yi masa tsauri mata biyu alokaci ษ—aya?bai gama tunanin ba ya ji ta ce"babu abinda za ka nema sarkin gobe komai na saka an tanadar maka shi need,shahararren ษ“angaren mai martaba wanda ya tanada saboda kai,don haka part ukune aciki sai ka zauna aษ—aya matanka a biyu."

 kanshi ya kulle sosai ya kasa gane komai don haka bai ฦ™ara ce wa komai ba,ya nufi sashensa yana jin zuciyarsa ta cunkushe sosai,sam baya son auren dole ko kaษ—an amman mahaifiyarsa sai da ta dage ta yi masa,shi fa haryanzu baiga irin macen da ya ke so ba,yana son mace mai ilimi,mai kunya,mai kare dukkanin haฦ™ฦ™oฦ™in ubangiji akanta,waccs bata damu da rayuwa da abinda ke cikinta ba,kuma wacce bata fiye magana ba,infact ma da zai samu kurma da sai ya fi jin daษ—in rayuwarsa sosai.


Don shi ba mutunne mai yawan yin magana ba don haka ya fi son zama shi ษ—aya ma wani lokacin.
 Yana shiga ษ“angarensa ya shiga banษ—aki ya saki shaya tana ฦ™warara a jikinsa,sam bai shiryawa aure yanzu ba,idan ma ya shirya yafi son ya zaฦi matar da hannunwansa.

 Gaban mudubi ya tsaya yana goge jikinsa ya kalli jikinsa sosai,a zahirin gaskiya shi namiji ne mai karsashi,chest ษ—insa yana da faษ—i sosai Allah ya yi masa halitta mai ฦ™yau da haiba,babu macen da zai ce yana so ayau ba tare da ya samu ba,sai dai lalurarsa kawai ya ke tunani.
****


"Hajiya Saratu wallahi na yi mamaki sosai da har ki ka bari wannan yarinyar ta samu saurayi ke baki samu ba,ni dai idan zaki yadda da na baki wata shawara wallahi idan har za ki ษ—auka".

"haba Hajiya Lantai ai kinsan tun muna yara ke aminiya ta ce,don haka ki faษ—i shawararki kai tsaye don na san ba zaki bani shawara mara ฦ™yau ba".

 "idan kin yarda ina son ki binciko gidansu wannan yaran muje mu samu mahaifiyarsa mu gaya mata duk abinda ke wakana,cewar wannan yarinyar kurma ce kuma an taษ“a zubar mata da cikin shege".

 tafa hannu sukayi Hajiya Sara ta ce"kai lantai kin iya mugunta iri iri wato idan Hasiya tasan wata bata san wata ba,wai ita mai ฦดar ฦ™anwa don na ga alamar ma tafi son shegiyar kurmar da ฦดaฦดan cikinta."


 "Hmm ai kuwa dai na gaya miki haka za ayi don kinga ba a bori da sanyin jiki gwara ma musan abinyi tun yanzu". Nan dai suka cigaba da tsinewa baiwar Allah Basma wacce ma bata san wainar da ake toyawa ba,dukkaninsu da zaka tambayesu tambaya ษ—aya ba zasu iya amsa maka ba?me Basma ta yi musu suka tsaneta?ba za su taฦa gaya maka ba,kawai dai hassada ce da kuma ฦ˜iyayya.

 Bayan wannan zuwan sau uku Ahmad yana zuwa,duk zuwan da zaiyi sai ya aikomin da abubuwa sosai har mama tana faษ—an abubuwanda ya ke kawowa sunyi yawa.
****

Gimbiya Bilkisu da kuma gimbiya Abida,sun ci ฦ™walliyarsu irin ta ฦดaฦดan sarauta,suna zaune kan lafiyayyun kujeru waษ—anda suka amsa sunansu kujeru,irin ฦ™irar faransa ฦ™asan ฦ™afafunsu an saka tumtum sun ta ka tumtum ษ—in da ฦ™afafunsu.

Ammanfa ko waccensu hararar ฦดar uwarta ta ke,don mabanbanta yare ne kuma ba ฦ™asa ษ—aya ba sai gashi sun haษ—a miji da juna,ita gimbiya bilkisu balarabiya ce ฦดar ฦ™asar masar wacce mahaifinta aminine ga sarkin ฦ™aisa mahaifin Yarima Abeed,don haka suka ฦ™ulla alaฦ™a tsakanin ฦดaฦดansu don aminintakarsu ta ฦ™ara samun gindin zama don tun suna makaranta a merica suka shaฦ™u da juna gasu kuma ฦดaฦดan sarakai,tun daga nan abota mai ฦ™arfi ta shiga tsakaninsu,kuma haryanzu suna yin amintakarsu don idan ษ—aya abu ya shige mai duhu ษ—aya kan kira ษ—aya don su samu solving ษ—in matsalar.

 Gimbiya bilkisu tun ba yau ba tasan yarima Abeed alokacin da suka je masar shi da mahaifinsa da kuma ฦ™aninsa sufyan ษ—an gidan fulani don shi Abeed ba shida aminin daya wuce sufyan ฦ™aninsa ษ—an gidan fulani khadija,saboda son da mahaifiyarsa ta nuna masa tun yana ฦ™arami har kawo iyanzu,bayan sufyan sai Mohd shi kuma makaranta sukayi tare.

To fa tun anan take matuฦ™ar son Abeed don har ciwo ta yi saboda yarima Abeed anan ne fa Mahaifinta ya ti tsiye ta har ta faษ—a masa gaskiya to tun daga lokacin ya yi wa amininsa magana,ko da ya faษ—a masa ba ฦ™aramin daษ—i yaji ba to shine aka fara shirin auren ba tare da uban gayyan ya sani ba wato Admiral B.

 Sarauniya jidda tana jin hakan ta ti tsallen baษ—ake ta ce itama sai an auri ฦดar ษ—an uwanta,babu yadda sarki ya iya dole ya bata haษ—in kai aka aurawa Yarima mata zankaษ—a zankaษ—a har guda biyu.
***

"Hajiya wallahi abinda muka faษ—a miki babu sharri ko ฦ™age acikinsa idan har ma baki yadda ba to kije unguwar ki tambaya".

 ran Hajiya Salamatu ya ษ“aci sosai don a ganinta duk abinda Ahmad zaiyi bai taษ“a ษ“oye mata ba,sai yau saboda wata lalatacciyar yarinya kuma kurma ya ne mi aure ba tare da ya gaya mata ba?.

 gaskiya ta yadda da maganar waษ—annan mutanen don idan ba haka bane me yasa tunda Ahmad ya fara neman auren bai gaya mata ba?.

 Hajiya Salamu ta ce"ina zuwa bari in hau sama in dawo,ku dai ba gode muku da wannan ฦ™auna da kuka nuna wa ahalina".

 tana hawa Lantai ta ce"Hmm kinji fa wannan gidan dukiya tsububu ace muna ji muna gani mubar yarinyar nan ta ฦ™washi irin wannan daษ—in?".



*miss green ce*

kada kuga bana typing da yawa ina zuwa skull abubuwa sunyi min yawa aษ—an rage da wannan.



_MT COLLECTIONS๐ŸŒฟ☘️_
_Ina kuke mata ฦดan ฦ™walisa masu son ado na kece raini๐Ÿ’„๐Ÿ’‹ kiji next year Alhaji yayi mai kyautar ฦดar moton nan ko yace Hajiya na biya Maki kujerar Hajj๐Ÿคช nan dai ko wa ke fatan yagan sa yaje๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿšถ‍♀️๐Ÿšถ‍♀️ Kuzo ga kayan gyarar Aure daga taskar mu MT, matsalar ki yamushewar jiki , rashin ฦ™iba kema so kike duk inda kika je ace ga Hajiya tazo ku bata wuri๐Ÿ˜ , ko matsalar infection ke damunki , rashin ฦ™arfin ษ—a namiji saurin gajiyawa ke Kuzo akwai ingantattun kayan mata dana gyara Suplement wanda zai gyaraki kiyi caras abunki , idan ฦ™iba ne tayi maki yawa kisha kiga kin koma dai dai ษ—aukar oga๐Ÿ™ˆ๐Ÿ‘‡ ._
_Infection na buda gaban mace taciki yabar wajen a tsuke a matse kullum kina zaune kina cewa kefa a matse kike alhalin Mai gidan hkr yake๐Ÿƒ๐Ÿป‍♀️_

_Ina macen da batada shaawa kwatakwata ke bakijin feeling toh wlh kixo Kisha infection set dinmu Dan girman Allah inkinsha kitafasa ma oga infection flusher kibashi ya subhanalillahi Ranan kam saidai kukawomun yarana ajiya๐Ÿ˜… in ana sallah baa magana daga wanan ranan zakisa mene ne wanga Abu kenufi kinji_๐Ÿ™ˆ๐Ÿ™ˆ

_Infection nasa ruwa agaban mace tsinkakken ruwa Wanda shi Sam baida yauki toh wanan fa ba ruwan niima ba ne ruwan niima shine Mai yauki hajaju kizo Kisha infection set kirabu da sharrin infection Dan Allah_

 _infection set dinmu zai wanke miki Mara zai share yakwashe duk wani sanyi na jiki dana mara_
 _ina mai famada ciwon Mara mai tsanani lokacin alada zokisha toilet infection dinmu wannan ciwon yazama tarihi.._
_Ba'anan Mt collections ta tsaya ba , muna sai da liquid soap mayuka na haษ—i , turaruka ,shu'umin humra , colecture shampoo conditioner da dai sauran su ...mayukan Suplement wanda zasu dawo maki da martaban fatar jikin ki yasa jikin ki tayi sumul kiga fata na sheฦ™i yana glowing ,kar ku manta ku biyo mu a shafikan mu na๐Ÿ‘‡_
_INSTAGRAM๐ŸŽฏ #MT COLLECTIONS_
_FACEBOOK #MT COLLECTIONS_
_WHATSAPP๐Ÿช€ 08081202932_
CALL☎️ _09060703187_
_Muna bada sarin kayan mu a ko'ina ษ—aya ko sari... Zaku samu shagon๐Ÿ™️ mu a nan cikin garin Zaria  City babban dodo benen Yahya Aminu #MT COLLECTIONS 015_

_MT COLLECTIONS TAKU CE☘️_



Ga group

Na face book
ak saraki
    &
Ummu maher miss green๐Ÿ€



Ummu maher palace

๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=pfbid02Bi3dtp6ftDQ6vyRa5mVewzSiNsXA6N97Uq2Qeypf7j5g2FpN5XsRjsKqXGi3D2gal&id=100082587072617&sfnsn=scwspwa



Ak palace
๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป


https://facebook.com/groups/943534712916776/
[08/08, 14:11] Miss Green๐Ÿ€: _*๐Ÿ”–BASMA*๐Ÿ”–_ 



   
     Na๐Ÿ’‹
*(UMMU MAHER)MISS GREEN๐Ÿ€๐Ÿ*



_Noticed๐Ÿ›:wannan littafin labarine akan wata yarinya wacce ta kasance kurma ce._


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444



  15๐ŸŸฉ16


Cikin murna sosai su Hajiya Sara suka dawo suna wa su Basma dariya Hajiya Lantai ta ce"Hmm kin san Allah ni har na fara jin tausayin mutanen nan don wallahi na hango tsagwaran masifa a fuskar wannan hamshaฦ™iyar matar."

 dariya Maryam ta yi sannan ta ce"Hmm wallahi Umma kin burgeni da kuka je gidansu wannan Ahmad ษ—in,ai wallahi idan tasan wata bata san wata ba,wai su sn baza hanci da baki za a wuri ษ—an mai kuษ—i,ai wallahi tallahi sai Basma ta bar gidannan tunda ba gidan ubanta bane."

 Hajiya Sara ta ce"Hmm ai ni dai tunda har suka shigo gona ta sai sun san sunyi da ฦดar halak,haifaffiyar ฦดa haka kwai ina ji ina gani kurma naฦ™asashiya ta riga ฦดaฦดana aure ai ba ma zai yiwuba."


****

har dare Admiral B.yana kaiwa yana komowa a ษ“angarensa ya rasa yadda xaiyi da wannan hukuncin da mahaifiyarsa ta yanke,yana son mahaifiyarsa kuma yana jin maganarta,amman sji baisan ta yadda zaiyi ya zauna da mata har biyu ba".

 kai tsaye ta baya yabi ya isa sashen Fulani Khadija don duk da ba itace ta haifesa ba yana matuฦ™ar sonta,don matar ta yi ta ko'ina don bata taษ“a bashi muguwar shawara ba tun yana ฦ™araminsa har zuwa yanzu da ya yi wayo,ta haษ—a kansa dana ษ—anta sufyan saboda haka kansu ya haษ—u sosai duk da shi bai kai saba,ayanzu yana da shekara ashirin da biyar,don haka ya basa wajen shekara goma don sanda aka haifi Sufyan yana da wayonsa sosai.
Tana zaune da bayinta suna hira,ya tsaya yana kallonsu abin sha'awa abinda tunda yana ฦ™arami bai taษ“a ganin mahaifiyarsa da bayi suna hira ba,saboda mahaifiyarsa tana amfani da sarauta ta ganawa bayinta azaba sosai shiyasa kowa a masarautar tsoronta ya keji,ko da ฦดaฦดanta su Hajara bata hira sji kaษ—ai ne take hira dashi sosai harda dariya sai kuma mahaifinsa Sarkin ฦ™aisa.
Tana hangosa ta kama dariya tana ce wa"oh ango yaushe rabonda na ganka a ษ“angarena har na manta saboda kunya ko?".

 A shagwaษ“e ya fara magana kamar ษ—an yaro"ya ce da kuka yi min auren dole ba".?

mamaki sosai Fulani khadija ta yi ta ce"duk ษ—a nagari baya kaucewa abinda iyayensa suka ce ya yi,don haka bana son in ฦ™ara jin maganarka akan hakan,ka yiwa kanka fatan alkhairi akan wannan auren kada ka duba ce wa kaima yanzu fa ka kawo ฦ™arfi(ma ana ka girma)don haka ka yi a hankali don ka rabu da duniya lafiya.

 "Kada ka taษ“a ษ—aukarwa kanka haฦ™ฦ™in wata ka danne acikinsu kowacce ka ba ta haฦ™ฦ™inta,Allah ya yi maka albarka ya sakawa aurenka ma albarka".

 Sosai yaji daษ—in addu'arta suka yi hira sosai tuni ya ji hankalinsa ya ฦ™wanta,ษ“angaren Abida ya fara nufa tunda ita ce amarya yana jin yadda gabansa ke faษ—uwa,ya taษ“a dai dai saitin zuciyarsa yana jin adadin bugawar zuciyarsa,ya kama addu'ah ba wai tsoron auren ya ke ba,amman rashin lafiyarsa ya ke tunawa ba,don yasan tabbas idan bai samu mace mai mugun dauriya ba ba zata iya zama dashi ba.
    


****

Tun da Ahmad yazo zuwan ฦ™arshe ya yi min alฦ™awarin kawo kuษ—i,ya ce in sanar da Baba ban ฦ™ara ganinsa ba.


*miss green ce*

kada kuga bana typing da yawa ina zuwa skull abubuwa sunyi min yawa aษ—an rage da wannan.



_MT COLLECTIONS๐ŸŒฟ☘️_
_Ina kuke mata ฦดan ฦ™walisa masu son ado na kece raini๐Ÿ’„๐Ÿ’‹ kiji next year Alhaji yayi mai kyautar ฦดar moton nan ko yace Hajiya na biya Maki kujerar Hajj๐Ÿคช nan dai ko wa ke fatan yagan sa yaje๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿšถ‍♀️๐Ÿšถ‍♀️ Kuzo ga kayan gyarar Aure daga taskar mu MT, matsalar ki yamushewar jiki , rashin ฦ™iba kema so kike duk inda kika je ace ga Hajiya tazo ku bata wuri๐Ÿ˜ , ko matsalar infection ke damunki , rashin ฦ™arfin ษ—a namiji saurin gajiyawa ke Kuzo akwai ingantattun kayan mata dana gyara Suplement wanda zai gyaraki kiyi caras abunki , idan ฦ™iba ne tayi maki yawa kisha kiga kin koma dai dai ษ—aukar oga๐Ÿ™ˆ๐Ÿ‘‡ ._
_Infection na buda gaban mace taciki yabar wajen a tsuke a matse kullum kina zaune kina cewa kefa a matse kike alhalin Mai gidan hkr yake๐Ÿƒ๐Ÿป‍♀️_

_Ina macen da batada shaawa kwatakwata ke bakijin feeling toh wlh kixo Kisha infection set dinmu Dan girman Allah inkinsha kitafasa ma oga infection flusher kibashi ya subhanalillahi Ranan kam saidai kukawomun yarana ajiya๐Ÿ˜… in ana sallah baa magana daga wanan ranan zakisa mene ne wanga Abu kenufi kinji_๐Ÿ™ˆ๐Ÿ™ˆ

_Infection nasa ruwa agaban mace tsinkakken ruwa Wanda shi Sam baida yauki toh wanan fa ba ruwan niima ba ne ruwan niima shine Mai yauki hajaju kizo Kisha infection set kirabu da sharrin infection Dan Allah_

 _infection set dinmu zai wanke miki Mara zai share yakwashe duk wani sanyi na jiki dana mara_
 _ina mai famada ciwon Mara mai tsanani lokacin alada zokisha toilet infection dinmu wannan ciwon yazama tarihi.._
_Ba'anan Mt collections ta tsaya ba , muna sai da liquid soap mayuka na haษ—i , turaruka ,shu'umin humra , colecture shampoo conditioner da dai sauran su ...mayukan Suplement wanda zasu dawo maki da martaban fatar jikin ki yasa jikin ki tayi sumul kiga fata na sheฦ™i yana glowing ,kar ku manta ku biyo mu a shafikan mu na๐Ÿ‘‡_
_INSTAGRAM๐ŸŽฏ #MT COLLECTIONS_
_FACEBOOK #MT COLLECTIONS_
_WHATSAPP๐Ÿช€ 08081202932_
CALL☎️ _09060703187_
_Muna bada sarin kayan mu a ko'ina ษ—aya ko sari... Zaku samu shagon๐Ÿ™️ mu a nan cikin garin Zaria  City babban dodo benen Yahya Aminu #MT COLLECTIONS 015_

_MT COLLECTIONS TAKU CE☘️_



Ga group

Na face book
ak saraki
    &
Ummu maher miss green๐Ÿ€



Ummu maher palace

๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=pfbid02Bi3dtp6ftDQ6vyRa5mVewzSiNsXA6N97Uq2Qeypf7j5g2FpN5XsRjsKqXGi3D2gal&id=100082587072617&sfnsn=scwspwa



Ak palace
๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป


https://facebook.com/groups/943534712916776/
[08/08, 14:11] Miss Green๐Ÿ€: ๐Ÿ”–๐Ÿ”–๐Ÿ”–๐Ÿ”–๐Ÿ”–๐Ÿ”–๐Ÿ”–


 *BASMA*




Na Ummu maher
(miss green)๐Ÿ€


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din๐Ÿ‘†๐Ÿฝ.



  
  
   17๐ŸŸจ18


. . . .Abin ya dameni sosai na rasa wanda zan gayawa inji daษ—i,Hafsat tana kallo a tv tana kallona don abin Basma yanzu ya daina ba ta mamaki don ฦ™wana biyun nan tambayar duniya ta yi wa Basma amman ta ฦ™i gaya mata,ina cikin wannan halin ne Mama ta kirani ษ—aki don taji abinda ke faruwa akan maganar Ahmad don ta ga ฦ™wana biyu baizo ba? Nima ban iya ba ta amsa ba don nima ban san abinda ya hanashi zuwa ba.
Hankalin mama sosai ya tashi,ta samu Baba da daddare take faษ—a masa halin da ake ciki,sosai ya yi mamakin abin yana ta murnar Basma ta samu miji kuma sai ga abinda ya faru.


 Har gidansu Ahmad Baba ya je sai dai masu gadin gidan sub hanashi shiga,babu yadda zaiyi dole ya koma sai dai tun kafin yasha ฦ™wanar gidan hancin motar Ahmad ya shaho ฦ™wana Ahmad ษ—in ma yaga Baba don haka ya yi parking ya fito suka gaisa cikin mutunci da mutuntawa Baba ya ce"Mlm Ahmad ko da baka faษ—a ba nasan ba lafiya ba don gashinan na ga duk yadda karame sosai,Allah dai yasa lafiya".

 "Baba ฦ™wana 2 banji daษ—i bane wallahi,amman insha Allah gobe da safe xanzo har gida in sameka aฦ™wai maganar da na ke son muyi."

 gaban Baba ne ya faษ—i sosai duk da bayasan takurawa Ahmad ษ—in amman sai ya ce"Allah ya baka lafiya insha Allah zan jira ka duk da nima gobe tafiya zanyi amman kafin nan Insha Allah zan jira ka".Sallama sukayi cikin mutunci da mutunta wa sannan Baba ya tafi,Ahmad shiru ya yi yana kallon Baba har ya bar get ษ—in layinsu yana kallonsa zuciyarsa tana buga masa da sauri da sauri,baisan abinda zai faษ—awa Baba gobe idan yaje ba?ce masa zaiyi mahaifiyarsa ta hana sa auren Basma?ko kuwa ce masa zaiyi ya fasa aurenta?.

 Haka dai ya gama shawararsa babu mai basa amsa don haka ya shiga motarsa ya yi riverse ya tafi zuciyarsa a tunฦ™ushe fal tunanin Basma yana matuฦ™ar son Basma da zuciyarsa harma da gangar jikinsa,amman mahaifiyarsa ta yi masa katangar ฦ™arfe da ita hawaye ne masu zafi suka zubo masa ya share hawayen na tausayin Basma,ko da ace bai aureta ba yana mata fatan alkhairi a cikin rayuwarta.

 Tabbas yasan Rashin Basma tamkar rasa rayuwarsa ne,don shi da kansa mamakin irin ฦ™aunar da ya kewa Basma ne,don Allah ya jarabcesa da mugun jin tausayinta don lalurarta tana buฦ™atar a tausaya mata sosai a bata kulawa acikin rayuwarta uwa uba kuma ga ta marainiya lada biyu kenen.
Yana shigowa har zai wuce ษ“angarensa yaji Hajiya ta ce"lallai Ahmad yanzu haka ka koma zaka wuce ษ“angarenka ba tare da ka shigo mun gaisa ba?na fuskanci tunda na yi maka maganar wannan shegiyar gantalalliyar yarinyar raini ya shiga tsakani na da kai,saboda na yi maka tsakani da ajalinka shine zaka gujeni,tun yanzu Ma an fara yimin haka ina ga nan gaba kuma?ai sai abinda na gani,tunda ta gama sanin maza idonta ya buษ—e duk an zubar da ฦดaฦดan a ฦ™wararo".

 ษ—an saka hannunsa ya yi ya share hawayen fuskarta jin irin zagi da cin fuskar da mahaifiyarsa ke yi wa Basma,tabbas mahaifiyarsa bata ฦ™yauta masa sam,don ko ฦดaฦดa matan da ta aurar ba ta yi musu auren dole ba,ammanshi ga shi ko bincike bata yi ba anzuga ta ta hau kai,bai ce mata komai ba ya shige sashinta duk jikinsa ya yi sanyi sosai.

 Riฦ™e baki Hajiya ta yi tana ce wa"ikon Allah sai kallo yanzu dai Ahmad saura kaษ—an a bamu fili ka zaneni ko?saboda na yi maka magana shine harda kuka akan ฦดar iska tambaษ—aษ—ษ—iya,wa iya zubillah ji ya yi kamar ta ษ—ana masa wani mashi acikin zuciyarsa yana ji dama ace shi ta zaga ba Basma ba,da wani ne ya zagi Basma da yau sai ya yi ฦ™wanan baฦ™in ciki kamar yadda ya saka Basma aciki amman babu yadda zaiyi don mahaifiya ta wuce gaban komai a rayuwa.

 Cokali ษ—aya biyu ya yi ya cire pork ษ—insa yana goge bakinsa sa tissue yana shirin tashi yaji Hajiya ta ce"ikon Allah abincin ma yau baza kaci ba?tunda na taษ“a ฦดar gwal da gwalagwalai shiyasa zaka caccakamin abinci kabarsa awajen?ni dai yau na ga ฦ™addara wallahi wannan wani irin so ka ke yi wa wannan yarinyar?".

 Fatima ce ta kalleta ita da Afrah suna mamakin yadda ta takurawa yayansu akan abinda bai kai ya kawo ba,Babu yadda ya iya haka ya zauna yana ta turawa ba don yaso ba daga ฦ™arshe ta ce"Ahmad idan ka gama cin abincin ka sameni a sama aฦ™wai magana mai mahimmaci da zamuyi da kai don na ga alama sai na tashi tsaye kamar yadda aka asirceka nima in tashi tsaye muyi yaฦ™i dasu,don ni ba sallamammiya ce irinka ba."
Babu yadda ya iya haka yana ji yana gani ya ajje abincin yana ta juya cokali,ya jiyo muryar Fatima ta ce"Yaya ka yi haฦ™uri da halin Hajiya insha Allah za ta sakko har ta yadda kuyi aure".

 ษ—an murmushi ya yi ya shafa kan Fatima sannan ya tashi yabi Hajiya gabansa na dukan uku uku,yana zuwa ya isketa akan ษ—an wani ฦ™aramin stool ya tsugunna cikin sanyi kamar ba ita ce ta gama masifa ba ta ce"yanzu Babana don na yi maka magana akan wannan watsatsiyar yarinyar shine zaka  watsamin ฦ™asa a ido?kai yarone Ahmad haryanzu baka san abinda ya ke maka ciwo ba,shiyasa za ta haษ—a baki da uwarta su cuceka,wataฦ™il ma da cikin shege za'azo maka kaga wa gari ya waya dole mu karษ“a tunda za ace aure ya ba ka".

 "Hajiya inason ki yi bincike sosai akan yarinyar nan kafin ki yi mata hukuncin wannan ฦ™azafin".sosai Hajiya ta waro idanu tana kallon Ahmad kamar yau ta fara ganinsa,mamaki sosai a fuskarta ta ce"gaskiya Ahmad sai yanzu na yadda ba ka da hankali sam arayuwarka hankalinka da na ke gani ashe duk shirmen banza ne,to ba zanyi binciken ba ka ji?idan kuma ฦ™arat za ka bi kaje duk inda zakaje ka faฦŠa ni dai na ce ba zaka aure ta ba".

 Nan da wata biyu ma masu zuwa ka shirya aure don daman ฦดar gidan ฦ™anwata Hajiya jummai wato Samira ta daษ—e tana sonka kana wulaฦ™anta ta,to wallahi ni dai ba zan yarda ka auri wanman yarinyar ba".

 sunkuyar da kansa ya yi sam baison auren Samira don sam bata da tarbiyya balle kunya,shi sam ko da auren ma zaiyi ba xai iya auren Samira ba.
"Yanzu Aliyu daga dawowarka babu hutu zaka tafi ganin Basma?ina laifin ka huta kaci abinci ko?.ฦดar dariya ya yi sannan ya yi wa Hajiya Meena Kiss a kumatu ya ce dont wait again My ammi na yanzu zanje indawo,don wallahi tunda naje Canada tunanin Basma kawai na ke na kasa komai wallahi."

 babu yadda ta iya da ษ—an na ta abin sonta a kullum duk abinda ya ke so to tabbas ko da ranta baya so dole sai ta soshi,don lalurar Aliyu bata son damuwa dole ta rakasa kawai da addu'ah.

 Yau ma ina dawowa a hanya na ji horn ษ—in mota a bayana,da sauri na juyo ganin Aliyu ban san lokacin da na fara fara'ah ba,don ban san me yasa duk sanda naga Aliyu na ke jin wani abu a game dashi ba,ko akan Ahmad bana jin hakan amman akan Aliyu ina jin wani abu can cikin zuciyata.

 Kuma ko matsanta kaina dana ke yi ฦ™wana biyu da ฦ™arin tunanin Aliyu don tunda muka yi haษ—uwar farko bamu ฦ™ara haษ—uwa ba.

 Murmushi ya yi min sannan ya ce"Basma kenan na rasa me yasa duk lokacin da nazo unguwar nan muke haษ—uwa a ฦ™wanar makaranta?.













_MT COLLECTIONS๐ŸŒฟ☘️_
_Ina kuke mata ฦดan ฦ™walisa masu son ado na kece raini๐Ÿ’„๐Ÿ’‹ kiji next year Alhaji yayi mai kyautar ฦดar moton nan ko yace Hajiya na biya Maki kujerar Hajj๐Ÿคช nan dai ko wa ke fatan yagan sa yaje๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿšถ‍♀️๐Ÿšถ‍♀️ Kuzo ga kayan gyarar Aure daga taskar mu MT, matsalar ki yamushewar jiki , rashin ฦ™iba kema so kike duk inda kika je ace ga Hajiya tazo ku bata wuri๐Ÿ˜ , ko matsalar infection ke damunki , rashin ฦ™arfin ษ—a namiji saurin gajiyawa ke Kuzo akwai ingantattun kayan mata dana gyara Suplement wanda zai gyaraki kiyi caras abunki , idan ฦ™iba ne tayi maki yawa kisha kiga kin koma dai dai ษ—aukar oga๐Ÿ™ˆ๐Ÿ‘‡ ._
_Infection na buda gaban mace taciki yabar wajen a tsuke a matse kullum kina zaune kina cewa kefa a matse kike alhalin Mai gidan hkr yake๐Ÿƒ๐Ÿป‍♀️_

_Ina macen da batada shaawa kwatakwata ke bakijin feeling toh wlh kixo Kisha infection set dinmu Dan girman Allah inkinsha kitafasa ma oga infection flusher kibashi ya subhanalillahi Ranan kam saidai kukawomun yarana ajiya๐Ÿ˜… in ana sallah baa magana daga wanan ranan zakisa mene ne wanga Abu kenufi kinji_๐Ÿ™ˆ๐Ÿ™ˆ

_Infection nasa ruwa agaban mace tsinkakken ruwa Wanda shi Sam baida yauki toh wanan fa ba ruwan niima ba ne ruwan niima shine Mai yauki hajaju kizo Kisha infection set kirabu da sharrin infection Dan Allah_

 _infection set dinmu zai wanke miki Mara zai share yakwashe duk wani sanyi na jiki dana mara_
 _ina mai famada ciwon Mara mai tsanani lokacin alada zokisha toilet infection dinmu wannan ciwon yazama tarihi.._
_Ba'anan Mt collections ta tsaya ba , muna sai da liquid soap mayuka na haษ—i , turaruka ,shu'umin humra , colecture shampoo conditioner da dai sauran su ...mayukan Suplement wanda zasu dawo maki da martaban fatar jikin ki yasa jikin ki tayi sumul kiga fata na sheฦ™i yana glowing ,kar ku manta ku biyo mu a shafikan mu na๐Ÿ‘‡_
_INSTAGRAM๐ŸŽฏ #MT COLLECTIONS_
_FACEBOOK #MT COLLECTIONS_
_WHATSAPP๐Ÿช€ 08081202932_
CALL☎️ _09060703187_
_Muna bada sarin kayan mu a ko'ina ษ—aya ko sari... Zaku samu shagon๐Ÿ™️ mu a nan cikin garin Zaria  City babban dodo benen Yahya Aminu #MT COLLECTIONS 015_

_MT COLLECTIONS TAKU CE☘️_



Ga group

Na face book
ak saraki
    &
Ummu maher miss green๐Ÿ€



Ummu maher palace

๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=pfbid02Bi3dtp6ftDQ6vyRa5mVewzSiNsXA6N97Uq2Qeypf7j5g2FpN5XsRjsKqXGi3D2gal&id=100082587072617&sfnsn=scwspwa



Ak palace
๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป


https://facebook.com/groups/943534712916776/
*Ummu maher ce*
[08/08, 14:11] Miss Green๐Ÿ€: *๐Ÿ”–BASMA๐Ÿ”–*




     NA๐Ÿ’‹
UMMU MAHER(MISS GREEN๐Ÿ)


Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444



   19๐ŸŸก20


. . . .Nima murmushin na yi ina kallonsa duk da bai furta min wata kalma da zan gane ce wa sona ya ke ba,amman na ga so na acikin idanuwansa,sai dai Ahmad ya riga daya shige masa gaba amman ni dai da za'a tambayeni wanda na ke so to tabbas shi zan zaษ“a.

 ฦ™yautar wani ษ—an ฦ™aramin kit ya bani ya gaya min ce wa daga tafiya ya ke yanzu ko hutawa baiyi ba,amman tunda yanzu ya ganni zai wuce gida.

 Waige na ya ke har ya shiga cikin motar ni kuma sai murmushi na ke masa ban san ya ya ake ba so ba,amman tabbas ina son Aliyu so kuma mai tsanani.


 Kallon banza Maryam ta yi min ta saki tsaki ta ce"banza mara kamun kai kawai ko da wani bakin ma ake hira oho?".ko kallonta banyi ba na biyo hanyar gida tana yimin kallon hadarin ka ji baฦ™in ciki fal zuciyarta don arayuwarta idan da wanda ta tsana bai wuce Basma ba,yarinyar ga ta kurma amman aฦ™wai farin jini don ko ta ina ba tada makusa sai dai matsalar baki wanda shima Allah ya ne ya ฦ™addara mata hakan a rayuwarta kuma kowani ษ—an adam da irin ta sa ฦ™addarar.


 "Hajiya wannan yarinyar idon masu kuษ—i gareta yanzu ma haka fa da wani mai mota na ganta a tsaye,wallahi wannan har ya fi Ahmad kuษ—i da komai wallahi,gaskiya Hajiya ni fa ina tsoron yarinyar nan ta yi aure mu bamuyi ba".

 "haba Maryam ni fa bazan taษ“a yarda wannan yarinyar ta yi aure ku bakuyi ba,idan har na bari wannan yarinyar ta yi aure ku bakuyi ba ai na cuci kaina wallahi,don haka kuma daina tunanin komai insha'Allah bazan bari wani ma ya raษ“eta ba,dole in san abinyi tunda an rabata da wancen ta koma wani".

 haka dai sukayi ta ฦ™ulle ฦ™ullensu na yadda zasu kassara rayuwar Basma,ita kuwa Baiwar Allah bata san wainar da ake toyawa ba.


 Abba da kansa ya aika aka kirowoni ya shaida min halin da ake ciki a game da zancen aurena da Ahmad wai ya fasa,sosai naji baฦ™in cikin abin amman babu yadda zanyi haka tawa ฦ™addarar take,ganin halin dana shiga yasa Baba yasa ni a gaba yana ta yimin nasiha mai ratsa jiki.


 Mama ta yi baฦ™in cikin fasa aurena da Ahmad ya yi,ta yi min nasiha sosai da yadda da ฦ™addara,Hafsat ta samu miji wani munir harma ya aiko an kawo kuษ—i,mama tana murna sai kuma ga abinda ya faru.


"Anya Aliyu haka kuwa zaiyuwu ace kana son yarinya amman kamar wani yaro ka kasa gaya mata kuma ka kasa zuwa gidansu ka gaya mata?gaskiya ka canza tsari ka fi kowa sanin yadda banason ษ“acin ranka ko kaษ—an,don Allah ka gaya mata ko kuma ni inje har gidan na su in tona komai don bazanso ษ“acin ranka ba?".

 "Insha Allah zan gaya mata Hajiya ta".dariya ta yi sannan ta ce"gaskiya Babana baka da kirki".nan dai suka saka dariya dukansu abin sha'awa wanda haka ya kamata kowacce uwa ta kasance da ฦดaฦดanta,ko da yaushe ka gansu cikin annushuwa ba wai kaje gida ka gansu kamar gidan makoki ba,kowa yana danna wayarsa kamar gidan karuwai.


****

Babu yadda Abeed ya iya yana ji yana gani ya fara zuwa ษ“angaren Bilkisu gani ya ke kamar zai cuci yaranne don shidai babu yadda za'ayi ya ฦ™wana da mace ba tare da wani abu ya faru ba,kuma shi ga irin lalurarsa yana ganin ba kowacce macece za ta iya auransa ba,idan ba irinsa ba wacce ta kasance mai irin matsalarsa.

 Bayinta suna kusa da ita suna mata fifita ya shigo,tsaษ“ar sarauta ko da ya yi sallamar ma sai da taga damar amsawa sannan ta kori bayin na ta,shima abinda ta yi masa shi ya yi mata ya shige ษ—akin ฦ™wanansa ya barta anan.

 Cixon yatsanta ta yi tabi inda yabi da idanu tana harararsa,ranta yana mata suya shifa namiji haka ya ke idan yaga ana sonsa babu abinda ba zaiyi ba don ya ฦ™untata maka.

 Tuno wani abu da ta yi yasa tabi bayansa badon ranta ya so ba,sai don wannan abin da ta tuno,yana cire kayansa ta samesa sai ta wayance sannan ta amshi kayan ta fara taya sa cirewa,wani abu yaji tun daga kansa har zuwa ฦดan yatsunsa,amman sai ya daure ya cije ya shiga wankan.

 Yana fitowa daga wanka ta nufo inda ya ke ta rungumesa ta baya,yaji wani yar ajikinsa yana nema ya saki layi jin abinda ta ke masa.ya yi saurin janye hannayensa sannan ya ce"ke baki iya gaisuwa  ba ko?".ษ—an turo bakinta ta yi sannan ta ce"ina wuni".?

 "lafiya".

Kawai ya ce mata ya cigaba da saka kayan baccinsa sannan ya umarceta da ta yi alwala suyi sallah,babu yadda ta iya don ita wataran ma sai ta ga dama take sallah don haka ta turo baki sannan ta wuce banษ—akin,yana hangota ta cikin madubi shi kuma lokacin yana shafa body spray ya ce a zuciyarsa yanzu wannan har ita ce mace ta gari?kana saka ta bautawa Allah tana turo baki lallai aฦ™wai aiki a gabansa.

Wanka ta yi sannan ta ษ—auro alwalar tana wani kallonsa kamar mayya,yadda ya yi mata wani mugun ฦ™yau daya saka wata jallabiyya mai sulษ“i ruwan fari mai ฦ™yau da haiba.gashin kansa duk ya ฦ™wanta don kan Yarima Abeed ba ฦ™aramin gyara ya ke sha ba.
 Gashin jikinsa ma duk a ฦ™wance gashinan da yawa kamar ka kitsesa,wani haษ—iyar yawu ta yi aranta tana cebwa gaskiya na yi sa'ar miji,tuna ba ita kaษ—ai ba ce matarsa yasa ta wani turo baki,amman tuna wani abu yasa ta yi murmushin mugunta ta bi sa suka yi isha'i sannan sukayi nafila raka'a biyu.

 Suna idarwa ya ษ—aga hannayensa sama yana addu'ah yana kukan Allah ya yaye masa irin lalurar da ya ke ษ—auke da ita.

 Kallon ฦ™asa ฦ™asa Gimbiya Bilkisu ta ke wa mijinta Abeed daman ya iya wannan addu'ar haka?bata gama mamakin ba ya kama goshinta ya fara yi mata addu'ar da manzon Allah(S.A.W)ya koyar damu idan mutum ya yi sabon aure.
Mamaki sosai Bilkisu ta yi to wannan kuma wacce irin addu'ah ce oho?ni kuwa Ummu maher na ce ikon Allah ita kuwa Bilkisu tana ฦดar musulmi amman bata iya komai na musulunci ba?to Allah ya ฦ™ฦดauta Allah ya shiryar damu Amin.

 Yana gamawa ya janyo naman ษ—awisun daya shigo dashi ya ajje mata sannan ya yi addu'ah ya hau gado ya fara bacci,wani baฦ™in ciki ne ya ษ—arsu a azuciyar Bilkisu ta hararesa tsabar rashin son da ya ke mata shine ya hau gado ya barta anan?wato ita ce za ta shayar da kanta a matsiyanta na amarya.

Tashi ta yi tabar abin anan sanan ta saka wata tsaleliyar rigar bacci wacce da kanta ta siyo ta a ฦ™asar germany.

 Sosai rigar ta yi mata ฦ™yau kasancewarta fara sol,kuma kalar rigar baฦ™ace ta taje gashin kanta ta shafa turaren da Mahaifiyarta ta bata na janyo hankalin Abeed.

 ฦ˜amshin turaren yaji kamar daga sama nan da nan ya gigice ya janyo Bilkisu ya rungume yana addu'ah,sosai ta basa kanta musamman ma da taga Yariman kamar ษ—an hannune don ba dai sarrafa mace ba.

 Sai dai da tafiya tayi tafiya tun talitainin dare ya ke abu ba har safiya kuma bashi da niyyae haฦ™ura,ta yi kuka ta yi magiyar ammanfa abu yaฦ™i ci yaฦ™i cinyewa,har suma sai da Bilkisu ta yi babu yadda ta iya dole ta ฦ™yalesa,amman shiru bai kawo ba,ษ—an sauran ฦ™arfin daya rage mata ta ture sa gefe ta miฦ™e da k'er za ta shiga banษ—aki ya yi saurin wafto ta amman ta zame ta shige banษ—aki ta saka sakata.

 Awajen ya tsaya yana riฦ™e da mararsa wacce ke murษ—a masa kamar zai mutu,anan ya fara murฦ™uฦ™usu yana magiyar ta buษ—e masa ฦ™ofar amman shiru bata buษ—e ba.
Anan ya lallaษ“a ya hau kan gado duk da sanyin A c amman wani zazzafan zazzaษ“ine ya yi gaba dashi ya hau rawar sanyi.












*Miss green ce*
[08/08, 14:11] Miss Green๐Ÿ€: *๐Ÿ”–BASMA๐Ÿ”–*




     NA๐Ÿ’‹
UMMU MAHER(MISS GREEN๐Ÿ)


Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444


*Matso kiji๐Ÿ‘‚๐Ÿป*

yawan istigfari yana kankare mana zunubinmu,yawan istigfari yana ฦ™ara kusanta mu ga ubangiji.
--------------------------


  21⚪22


. . . . .ina ษ—akko kaya acikin sif ษ—ina na hango wannan ษ—an ฦ™aramin kit ษ—in da Aliyu ya bani na ษ—akko ina murmushi na buษ—e ,waro idanuwa na yi ganin sarฦ™ar gold ษ—in da ke cikin ษ—an ฦ™aramin kit ษ—in,duk da ban san gold ba amman ko da ba'a gaya min ba sheฦ™i da walฦ™iyar da ya ke zai shaida maka hakan.

 Hafsat da ke saka kayanta ta waro idanu sannan ta ce"Basma waye ya baki wannan sarฦ™ar haka?".ka sa magana na yi sannan ta amsa tana dubawa ta ce"Basma kinyi shiru fa baki gaya min ba?" A hankali na fara ฦ™watanta mata wanene ya bani da maganar kurame,na rungume hannuwana a ฦ™irji sannan na yi mata alamar zanen heart da hannu na.

 Waro idanu ta yi ta ษ—ala min duka sannan ta ce"lah!lah!! Mutuniyar a ina ya ke kuwa wannan wanda Ya yi dacen Mata Basma".

 dariya na yi ina ษ“oye fuskata waini kunya ta ce"hmm yanzu zamuje gidan anty shamsiya idan yaso sai ki gaya mata tunda na ga kamar kunfi kusa da ita".

ฦดar dariya na yi sannan na ฦ™arasa saka rigata sannan muka haษ—a kayanmu cikin troly guda ษ—aya mukasha hijabanmu har ฦ™asa sannan muka fito.

 Idris ne kawai a farlon ฦ™anin Hafsat sai Mama dake kitchen,ฦ™arasawa kitchen ษ—in na yi sannan na yi mata magana da hannu alamun zamu tafi kenan,mama ta tsame hannunta daga cikin yankan naman da take ta ce"to shikkenan idan kunje kuce ina gaisheta da yaran na ta da maigidan".da to muka amsa sannan muka fito muna ษ—an hirar mu Maryam da Salimat ne suka taho ganinmu da troly sai suka kallemu suka ce"Hafsat ina zuwa kuma?".

 "inda kuka aikemu"?.sosai abin ya basu haushi musamman maryam da ta yi maganar Salimat ta ce"ai kinga Yaya maryam kin janyo ta gaya mana magana ni fa a harkata bana son raini kin san kuma wannan siririyar yarinyar raini gareta,balle yanzu tana ji da kanta waidon an kawo kuษ—inta,ai dole ta dinga ganinmu wasu ษ—ai ษ—ai,in dai aure ne ayi mugani".

 tana faษ—ar hakan taja hannun Yayarta Maryam suka wuce,sosai abin ya damu Hafsat duk da na ba ta baki sosai,saboda haka ma shiyasa bana kulasu sam.

 Muna hanya ina tunanin Aliyu,yanzu dana taho ta ina zai ganni har mu gaisa kamar yadda muka sabayi,tabbas yanzu na yadda ina son Aliyu abinda ban taษ“ayi a rayuwata ba,wai ince inason wani ษ—a namiji.


 Sai dare sannan muka isa garin Abuja gari me daษ—i da ni'ima har tasha Anty shamsiyya ta aiko aka ษ—aukemu har unguwarsu,kallon gidajen unguwar ta su na ke masu ฦ™yau da kuma tsari,har muka iso na su katafaren gida mai ฦ™yau dashi,azuciyata na ce lallai anty shamsiyya ashe gidan da suka canza ษ—in haka ya ke".?
da ya ke adacen ba anan suke ba,kuma rabonmu da zuwa Abuja mun daษ—e sosai,gwarama Hafsa tazo alokacin tana da ciki har ta haihu shekara biyu kenan,Anty shamsiya ita ce ฦดar mama ta biyu Anty Atika ita ce ta farko,Atika itace babba sai Shamsiya sai Iklima sai Hafsat sai idris,Atika tana aure a Bauchi,Iklima kuma tana aure a lagos bata daษ—e da aure ba shekara ษ—aya kenan,sai hafsat sai idris ฦดaฦดanta biyar kenan.


 Har cikin gidan aka shigo damu gidan gwanin sha'awa gidan sashe biyu ne sashen kishiyarta da kuma na ta.

 Ina ganin anty shamsiya na rungumeta ina dariya,ita ma dariyar ta ke tana ce wa"oyoyo ฦดan matan Mama sannunku da zuwa".
 Hafsat ta ce"ikon Allah na ga alama an manta da wata halitta Hafsat don haka wallahi yanzu sai in koma abina tunda ba a son zamana."

 "autar mama ban manta da ke,lale marhabin amarya".ษ“oye fuska Hafsat ta yi sannan ta wuce da sauri tana ce wa"lah anty banga twins ba"?.
 "twins suna skull anjima zasu dawo amman ilham da kausar suna ciki yanzu suka gama drama".

 dariya dukanmu mukayi Hafsat tana cewa"lallai yarannan har yanzu basu daina faษ—an nan ba?ah lallai ki ce yau zan gyara musu zama".ta faษ—i hakan tana dariya ta shiga gidan.
Ai kuwa muna shiga suka taho a guje suka rungumemu ni kuwa mamaki ya kamani yadda na ga dukansu sun zama ฦดan mata,ilham tana da shekara 14 kausar 10,dukkansu suna sona sosai don idan muna hira dasu sai kice da mai jin magana suke don har dariya munayi dasu don su basufi shekara ษ—aya da zuwa kano ba,don haka mun saba dasu sosai.




****

"Ahmad wato dana ce maka kaje kaga yarinyar nan shine ka yi min kunnen uwar shegu ko?ni nan isa in zaษ“a maka abinda ya ke mafi alkhairi a rayuwarka ba ko?".

 "Hajiya wallahi yarinyar nan bata dace dani ba sam bata da kunya balle tarbiyya shiyasa ni banso kika haษ—a aurenmu ba tunda halina da na ta ba ษ—aya bane?".

 "ikon Allah lallai Ahmad na yarda wannan yarinyar ba iya asirin sonta ta yi maka ba,har da haษ—ani da kai ta yi don adacen baya ba ka yimin musun duk abinda na sakaka."

 "Hajiya ki yi haฦ™uri insha Allah zan aure ta in dai hakan zai sakaki farin ciki,amnan ki daina zagin Basma baiwar Allah wacce bat damu da duniya bama ballanta na. . . ."

 "kai shasha rufemun baki dalla,tunda baiwar Allah ce ai mu ba yinka ne?ai insha Allah sain karya wannan mugun asirin da ta yi maka da ina faษ—a kana faษ—a".

 ganin abin ba na ฦ™are bane yasa Ahmad ya tashi ya yi wa Hajiyarsa sai da safe sannan ya tashi ya tafi,harar bayansa ta yi sannan ta ce"zanyi maganinka ne ฦ™wanan nan don na ga alama kuruwarka ma ta cinye shegiya ฦดar matsiyata".nan dai Hajiya ta yi ta zagin Basma wacce bata ji ba bata gani ba.
*****
Sai da Gimbiya Bilkisu ta yi bikin jikinta sosai don ba ฦ™aramar wuya tasha ba,kana ganin tafiyarta kasan me ya faru,shi kuwa Yarima Abeed yana samun sauฦ™i ya fara shirin tafiya,ai kuwa wannan tafiyar anyi tashin hankali sosai don ita Gimbiya Abeeda ce wa ta yi ai Yarima abeed yana sane don ya ga ฦ™wananta yazo shiyasa ya shirya tafiya,don wannan maganar ai har bakin Sarauniya jidda ya je,ta kira Admiral B.tana tambayarsa abinda ya faru,wayo ya yi mata sannan ya ce mata an kirawosa ne agun aiki shima don babu yadda zaiyi ne.

 Fatan alkhairi ta yi masa sannan ta kira Abida ta shaida mata abinda ke faruwa,amman duk da haka gani take ai cin fuska ne me yasa a ฦ™wanan Bilkisu ba a kirawosa ba sai akanta tunda ita aka fi tsana.

 Shi kuwa Admiral B.tausayinta kawai ya ke ji don yadda ya yi wa Bilkisu abin har tsoro ya basa shiyasa ya koma don aฦ™wai likitansa da ya ke gani a yanzu haka kuma akan matsalarsa.

 Bilkisu kuwa murna sosai ta yi da tafiyar mijin na ta don abin ya ba ta mamaki sosai,don ko a tarihi bata taษ“a ganin namiji haka ba.






*Miss green ce*
[08/08, 14:11] Miss Green๐Ÿ€: *๐Ÿ”–BASMA๐Ÿ”–*




     NA๐Ÿ’‹
UMMU MAHER(MISS GREEN๐Ÿ)


Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444


*Matso kiji๐Ÿ‘‚๐Ÿป*

Mu dinga ฦ™yautatawa iyayenmu kula da iyaye yana saka kyakkyawan ฦ™arshe.
----------------


  23๐ŸŸฃ24


. . . .ina duba kayana na ษ—akko wannan kit ษ—in da Aliyu ya bani,na kalli Hafsat ita ma ni take kallo ta ce"au daman dashi ki ka taho?wallahi na ษ—auka a gida ki ka barsa?muna cikin wannan maganar ne Anty Shamsiya ta shigo tana tsokanarmu da ฦดan matan Mama.ฦดar dariya mukayi ni da Hafsat sarฦ™ar da ษ—an kunnen suna hannuna ina juya su.

 "Basma a ina ki ka samu ษ—an kunne da yarin sarฦ™ar gold haka me tsada?".da mamakinta ta faษ—i hakan tana duba sarฦ™ar da yarin.

 Nima kallon sarฦ™ar na ke yadda take ta walwali Hafsat ta ce"Anty itama Basma wani saurayinta ne ya ba ta wai sunansa Aliyu suna haษ—uwa hanyar makaranta,amman dai nima Allah baisa na taษ“a ganinsa ba."

 "idan kun koma Basma ki ce ya turo kinji"?.ta yi min alamar hakan da hannu na ษ—aga mata kai da to.

rannan da yamma muka fita wani super market na ci ฦ™walliyata cikin doguwar riga abaya baฦ™a tasha stone mai ฦ™yau na yafa mayafinta a kaina ban wani yi ฦ™walliya ba amman na shafa hoda da kuma lipstick na yi ฦ™yau sosai Hafsat na ji kawai tana ษ—aukana a hoto da camera ฦ™aras ฦ™aras,ta ce"wow Babyn mama gaskiya kinyi ฦ™yau kin ganki kamar wata half case.

ฦณar dariya na yi na wuce gaba tana dariya itama,mai motar gidan yana tsaye yana jiranmu alokacin ya dawo daga kai Anty Shamsiya aiki da kai yara skull.
 Kallona sosai Hamza ya ke yana ayyanawa aransa,ina ma dai ace ya auri wannan yarinyar da ya caษ“a wallahi yarinya sai ka ce wata matar shuguban ฦ™asa babu abinda ta rasa na mace a cike take ษ“am,shi babu ruwasa da wai kurma ce shi a haka ya ke sonta,amman fa yasan wannan tafi ฦ™arfin ajinsa matar manya ce.

 Ko a mota ina lura dashi kallon tsaf ya ke min,sai in juya in kalli windows ษ—in motar,idanuwanta kawai Hamza ya ke kalla yadda suke a lumshe kamar mai jin bacci,leษ“enta kamar ta shafa jan baki.

 Hafsat ta ce"don Allah Hamza ka yi tuฦ™inka ka daina kallon wani wajen?sai ka saka munyi hatsari"?.
"af Hajiya don Allah ki yi haฦ™uri insha Allah bazan ฦ™ara ba".dariya Hafsat ta yi ta ce"ah to gaskiya dai ya kamata adaina don kada ayar damu.

Muna zuwa katafaren wajen muka shiga hankali fa gaba kiษ— ษ—aya ya koma kanmu yadda kasan sun samu abin kallo,Hafsat ta ce kau gaskiya ni fa mutanen garin nan sun fiya kallo kamar zasu cinye mutane wallahi".
 

 Kallonta na yi bance komai ba na yi dariya don ni tun shigowarmu na ga irin kallon da ake mana amman duk ban kula dasu ba sa yi har su gaji indai kallo ne,don ni dai duk inda na yi yadda kasan talabijin haka suke kallona.
Ko da muka shiga ma masifa Hafsat taks mutane suna ta kallonmu,ita fa dai da tasan haka ne da baza tazo ba,haฦ™uri na dinga ba ta amman fir Hafsat ta ce sai dai fa mu canja wani wajen nan an fiya kallon mutane.


 Muna fitowa shima Hamza ya kafeni da idanuwa Hafsat na lura da hakan,daman Hamza yana jikin motar ya tsaya ya yi face ษ—in ฦ™ofar wajen ta kalleshi ta kalleni ta ce"na shiga uku na wai su mutanen garin nan wasu irin mutane ne kamae mayu suyi ta bin mutum da kallo kamar sun samu talabijin?".

 har muka shiga mota Hafsar tana ta mitarta babu wanda ya ce mata ฦ™ala,shi daman Hamza ba shida bakin magana don kunya ma ya ke ji da Hafsat ษ—in ta kamasa yana kallon Basma.


 To wajen da muka je yanzu daษ—an dama dama don wajen ba wajan kowa da kowa bane sai wanda ya amsa kansa sannan zai je wannan shahararren waje.

 Shuke shuke ne suka cika wajen gwanin sha'awa ga kuma tables na cin abincin mai ฦ™yau da tsari,na kalli wajen ina murmushi Hafsat ta ce"Basma wajen ya yi ko?".ษ—aga kaina na yi alamar eh.

Hafsat ta ce"yauwa ko dai na ji wannsn wajen babu wannan saka idon nan kowa yana harkarsa ne,idan ma da saka idanuwan to fa babu yawa kamar na can".ni dai duk ina jinta bance komai ba ina ta kallon wajen gwanin sha'awa.


 Na hango swimiming pool mai ฦ™yau Hafsat na danne danne a wayarta ba ta kula dani ba na tashi ina zagayen wajen har na iso wajen wannan ruwan,a hankali na janye fararwn ฦ™afafuna na saka ฦ™afata duka biyu acikin ruwan na zauna a bakin wajen ina wasa da ruwan ina jin wani daษ—i a cikin raina.

 Na kalli wani yaro ya yo wajen ruwan mamansa da babansa na binsa da gudu zasu kama sa suna dariya kamar abin wasa,sosai suka bani sha'awa wasu hawaye suka zubomin na gogesu ina ce wa a zuciyata Allah sarki uwa tana da daษ—i duk da ban taษ“a ganin mahaifiyata ba,amman ina matuฦ™ar sonta da ฦ™yaunarta na sha ษ—aukar hotonta inyi ta dubawa ina mata kiss,mace ฦ™yaฦ™ฦ™yawa da ita kamar itace ta yi kanta tsabar ฦ™yau.sam bana tuna mahaifina a rayuwata sam bai damu dani ba bai san ciwona ba ko kaษ—an rabonda inga babana yau shekara 7 kenan alokacin ina da shekara10 mukaje ni da Mama da Hafsat amman har muka je muka dawo sau ษ—aya na gansa baya zama a gidan sam,kullum yana cikin yawo abin ya zauna min sosai a zuciyata,rannan na buษ—e fridge ษ—in ษ—akinsa kawai giya ce ฦ™walabensu manya manya duk da ban iya karatu ba na ษ—auka na nunawa mama.

 Sosai ta yi mamaki don bata taษ“a zata abin na sa ya kai har haka ba,ai kuwa washe gari yana dawowa mama ta ce tafiya zamuyi,to shima daman bai damu ba ta wani ษ“angaren ma gwara mu tafi ษ—in don nun takurawa rayuwarsa,don ya saba ษ—auko mata har suyi ฦ™wanaki a gidansa kamar matansa yanzu kuwa tun zuwanmu komai ya tsaya masa cak.
Kuษ—i ya bamu sosai don yana samun kuษ—in banza wajen Hajiya,don haka muka taho tun daga nan bamu ฦ™ara zuwa maiduguri ba har yau.

Ina son in zauna tare da mahaifina ko don ganin idona wata ฦ™ila zaisa ya ษ—an rage wani abin,ina ji masa mutuwa wacce ako da yaushe take zuwar wa ษ—an adam ko ka shirya ko baka shirya ba.


 Wasu hawaye suka zubomin na gogesu yanzi mahaifina kenan ษ—an wuta ne?kai gaskiya inason in zauna tare da mahaifina don gani na ke tunda na rasa mahaifiyata bai kamata in rasa mahaifiba tunda yanzu a halin da ake ciki tunda ta rasu bai yi aure ba.


 A hankali na tashi na hango Hafsat tana zaune kan tebir ษ—in tana yimin dariya tare da ษ—ago min hannu,nima dariyar na yi cikin ikon Allah silษ“in wajen ya ฦ™washeni luuu na faษ—a ruwan ji ka ke tsundum.

 Da gudu Hafsat ta taso tana kirana tare da nemab taimko,amman kowa ya yi shiru a wajen saboda suma duk basu iya ruwan ba.


 Jiniyar wasu motoci ne ta fara karaษ—e wajen kamar motocin ฦดan sanda sai dai ba na ฦดan sanda bane na sojoji ne.
Hafsat sai kuka ta ke harda majina,duk ta tayar da hankalinta ni kuwa sai facal facal na ke a cikin ruwan.



Dukkansu ฦ™amewa sukayi awajen suna sarawa ogansu ya fito a hankali cikin motar wow,sai da na yadda birona tsabar kallo.

Swiming ษ—in da ya ke zuwa ne duk ranar da babu aiki don yana matuฦ™ar son yin wanka a swiming amman fa kowa sai ya bar wajen sannan.

Rigarsa ya cire daga shu sai boxer amman yana da ษ—an tsayi.


 "Ranka ya daษ—e wai wata yarinya ce ta faษ—a cikin ruwan"?.da sauri ya kalli cikin ruwan ya tsaya kamar wani ba'adare yana kallonta,tunda ya ke aduniya bai taษ“a ganib surar da ta yi masa ฦ™yau kamar ฦดaฦดan lu'u lu'u irin wannan yarinyar ba,yana cen yana tunani shima silษ“in ya ฦ™washesa ya faษ—a.



*Miss green ce*
[08/08, 14:11] Miss Green๐Ÿ€: *๐ŸBASMA๐Ÿ*

BOOK 2๐Ÿ“ƒ


BY
UMMU MAHER(MISS GREEN๐Ÿ€)


Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444



---------
SIRRINKI๐Ÿ‘‚๐Ÿป

ฦณAR UWA KI KASANCE MAI RUFE SUTURARKI AKO DA YAUSHE,RUFE JIKINKI YANA TAIMAKA MIKI WAJEN YIN RIGAKAFI GA MUTANE DA KUMA SHAIฦŠANU.
----------------------------------


*25๐ŸŸข26*

. . . . .numfashin Basma har ya fara ษ—aukewa saboda da ษ—ewar da ta fara yi acikin ruwa,da sauri ya ruฦ™ota ya rungumeta sosai kamar wani zai ฦ™wace masa ita,abin gwanin sha'awa kamar a india,mutane aka fara tafi awajen da sauri Hafsat ta taho ta rungume Basma tana kuka bayan ya ajje ta a gefen wajen,da kansa ya saka hannuwansa guda biyu a ฦ™irjinta,sai da yaji wani shork har cikin ฦ™waฦ™walwarsa ya daure ya fara danna ฦ™irjinta ruwan yana fitowa har dai ya gama fitowa,ya tsira mata idanuwa yana kallon fuskarta,ya shagala sosai da kallonta,ita kuma a lokacin ta buษ—e idanuwanta da sauri ta tashi tana kallon wajen kamar bata san tazo ba.


 Da sauri ya tashi bayan ya dawo daga hayyacinsa ya amshi rigarsa daya cire ya saka yana kallon Basma kamar zai cinyeta,Hafsat ta ruฦ™o hannuwana muka fara tafiya.

 Wani abu yaji mai kamada kishi saboda yadda mutanen wajen suke kalle masa matarsa,don shi har ya yi mata don tunda ya ke zai iya cewa bai taษ“a ganin macen da ta ฦ™wanta masa arai irin Basma ba.

Motar su ta sojoji ya shiga ya kafa glass ษ—insa a fuska wato no respect suma sauran sojojin ganin ogansu ya shiga mota da sauri suka shiga suna sara masa.

Muna fitowa waje Hamza ya taho da sauri yana ce wa"iyayen ษ—akina lafiya me ya faru?naga Basma duk jikinta ya jiฦ™e tana rawar sanyi haka?.shiru hafsat ta  yi masa ganin ya dage da tambayar sai ta ce"Hamza don Allah kaja mu mu tafi Basma ce ta faษ—a ruwa yanzu".

 da sauri ya juyo yana ce wa"subhanalillahi sannu Basma,amman babu abinda ya sameta ko?shiyasa banji daษ—i ba da muka baro wancen wajen tunda na ga cen ษ—in babu irin abubuwa nasu hatsari".
 

 har ya gama maganarsa babu wanda ya ce masa ฦ™ala har ya gaji ya yi shiru,muna zuwa gida Anty shamsiyya ta dinga yi mana faษ—a akan mudinga kula da kanmu,daga cewa zamu super market shine muka tafi wani waje harda swiming pool,ganin ranta ya ษ“aci ne muka bata haฦ™uri tare da yi mata alฦ™awarin ba zamu ฦ™ara fita ba har mu koma kano.


Sosai suke gudu a motar don su gano inda  motarsu Basma take,amman sun duba ko'ina babu su babu labarinsu,dukan sitiyarin motar ya yi ya kifa kansa yana addu'ar da ma yana ษ—ago idanuwansa ya ganta,tabbas babu abinda zaisa yabar Abuja idan har bai ga Basma ba.


****

Yau ake ษ—aura auren Ahmad da amaryarsa,amman fa kana ganin fuskarsa kasan ฦ™wata ฦ™wata baya cikin hayyacinsa don tunda ya rasa Basma gani ya ke tamkar ya rasa komai na rayuwarsa,tunda aka dawo daga ษ—aura auran na sa yaji baki ษ—aya kansa yana wani irin sara masa ya cire kayansa ya shiga wanka bayan ya fito yasha magani ya ฦ™wanta.

 Yana ฦ™wanciya babu da ษ—ewa Hajiyarsa ta shigo ษ—akin nasa,ganinsa ya rufu da blanket sai taji gabanta ya yi mugun faษ—uwa sosai,a hankali ta isa inda ya ke ta zauna a bakin gadon a hankali ta yaye blanket ษ—in ta shafa fuskarsa,wani zazzafan zazzaษ“i taji a jikinsa yana tashi harda huci.
 
 Cikin tashin hankali ta kira sunansa tana haษ—a baki wajen ce wa"Ah.Ah..Ahmad tashi mu tafi asibiti ba  kada lafiya jikinka ya yi zafi sosai.


"Mama ki barshi na fara jin sauฦ™i yanzu".ya faษ—i hakan yana dafe kansa"gaskiya Ahmad bakaji sauฦ™i ba,ga kanka nan har yanzu zafi zau kamar wuta."

 babu yadda ta iya dolenta ta haฦ™ura ganin ษ—an na ta ya dage,tana addu'ar Allah ya bawa ษ—anta abin sonta lafiya,tunda ta takura masa akan wannan auren shikkenan ya shiga ciwo yau lafiya gobe babu lafiya,ita kanta amaryar ta kasa gane kansa sam,don irin wannan zancen da ake zuwa shi ko sau ษ—aya bai je ba,sai dai ita idan har ta matsu tazo da kanta.


***

"Wallahi mama tunda Basma ta yi tafiya na kasa gane kai na baki ษ—aya,hankalina duk yana kanta Mama na rasa wani irin so na kewa Basma a tarihin rayuwata babu yarinyar da ta taษ“a shiga zuciyata irinta".


 "Aliyu kenan ni dai duk wannan tatsuniyar na gaji da jinta idan har kana son yarinya to kaje gidansu kawai ayi komai a gama,don daman a addinance ma idan kaga yarinya kana so to babu abinda yafi sai kaje gidansu ayi maganar aure a wuce wajen,ba azauna kullum ana soyayya ba,iyayen yarinya su gaji har su ba ta wani".

 da sauri Aliyu ya ฦ™walalo manyan ฦ™yawawan idanuwansa ya ce"caษ“ษ“i jan ai wallahi mama idan har aka aurawa Basma wani to fa ki siyo likafa ni ji ajje don tabbas margayawa zanyi".

 dafe ฦ™irji mama ta yi ta ce"to Allah ma ya kiyaye Aliyu kai kaษ—ai fa na ke dashi a duniyar nan?idan har ka mutu ni yaya zanyi da rayuwata,ni dai ina maka fatan akhairi akan Basma don insha Allah ina ji ajikina matarka ce insha Allah."

 ฦŠan murmushi yayi sannan ya sumbaci goshin mahaifiyar ta sa ya fita,yana mata bye bye,ฦŠan murmushi ta yi tana kallon ฦŠan nata sannan ta tashi ta saka myafinta,don taga idan har ta biyewa ฦŠan nata to fa zaiyiwa kansa biyu babu ne gwara taje gidansu yarinyar da kanta ayi komai a wuce wajen.


Tana fitowa direbanta yaja ta sai gidansu Basma,da sallamarta ta shiga har cikin gidan,hjy saratu tana daga cikin ฦŠaki ta ce"Kai wannan wani irin sallama ce tun daga ฦ™ofar gida kamar masu neman gafara".tana faษ—ar hakan ta fito waje ta saman bene tana hango wata hamshaฦ™iyar mata tun daga kan suturarta har kan kayan jikinta babu na banza.

 Da sauri hajiya saratu ta sakko tana ce wa"lale marhabun hajiya".tana washe baki kamar wacce aka yi wa albishir da shiga aljanna.

Kai tsaye ษ—akinta ta kai ta nan da nan ta saka maryam ta kawo mata lemo da ruwa a fridge sannan ta zauna suka ฦ™ara gaisawa,jikin hajiyar Aliyu dai har yanzu ba a sake ya ke ba ta ce"don Allah hajiya  ke ce mahaifiyar Basma"?.

 Wani irin mummunar faษ—uwar gaba Hajiya saratu taji ta ce"eh.eh.amman ba ni ba ce".
 ta faษ—i hakan duk hankalinta ya tashi don arayuwarta ta tsani taga arziฦ™i yana ฦ™etaro Basma ba tare da ya ฦ™etaro ฦดaฦดanta na cikinta ba.

 Hajiya ta gane wani abu a dangane da matar sai ta ce"oky to don Allah a haษ—ani da maman na ta".?

 babu wanda ya yi magana acikinsu don faษ—uwar gaba sai maryam ce ta yi ta maza ta ce"am Hajiya gaskiya ba nan gidan bane ki dai nemi gidansu".

 mamaki sosai ne akan fuskar Hajiyar Aliyu ta kalli Hajiyar Aliyu duk taga yadda idanuwanta ya yi zuru zuru saboda tashin hankali bata ฦ™ara ce wa komai ba ta tashi ta buษ—e labulen ษ—akin a hankali ta fita,tana mamakin waษ—annsn mutanen.

 Hango gilmawar mama ta yi ta shiga kitchen kuma sai taga kamarsu ษ—aya da Basmar Aliyu don yasha nuna mata hotunan Basma awaya don bashi da aiki idan ba kallon hotunan Basma ba.

 da ษ—an sauri ta bi bayan mama kitchen ษ—in,mama taji tsoro don jin mutum a bayanta,da sauri Hajiyar Aliyu ta ce"sannu baiwar Allah nasan baki sanni bako"?.

 ษ—aga kai mama ta yi sannan ta ce"eh amman lafiya kuwa baiwar Allah"?.ษ—an murmushi Hajiyar Aliyu ta yi sannan ta ce"yauwa don Allah ke ce maman Basma"?.ta faษ—i hakan tana kallon fuskar mama duk da ko da bata faษ—a ba kammanin da sukayi zai tabbatar maka da ita ce mamanta.




 *Miss green ce*
[08/08, 14:11] Miss Green๐Ÿ€: *๐ŸBASMA๐Ÿ*

BOOK 2๐Ÿ“ƒ


BY
UMMU MAHER(MISS GREEN๐Ÿ€)


Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444



---------
SIRRINKI๐Ÿ‘‚๐Ÿป
*addu'ar samun lfy ga ko wani irin ciwo*

an rawaito daga Aisha (R.A),tace manzon Allah(S.A.W)ya kasance idan mara lfy yazo wurinsa da kokena rashin lfy ya kan ษ—auka hannunsa na tsakiya ya sanya a bakinsa sannan ya dangwali ฦ™asa sannan ya ษ—aura a inda kewa mutumin ciwo,sai ya karanta wannan addu'ar kamar haka;

"bismillahir turbati ardina biriqati ba'dina yashfa Taqimuna bi'izni rabbina".
------------------------------------


 27๐ŸŸก28


. . .."eh ni ce mahaifiyarta amman lafiya kuwa"?.ษ—an murmushi Hajiyar Aliyu ta yi sannan ta ce"masha Allah daman nazo wajenki ne,amman dana shigo wancen ษ“angaren sai ta ce min wai ba nan gidan bane?".

 ษ—an murmushi maman ta yi sannan ta bawa Hajiyar Aliyu damar shigowa,bayan sun gaisa ne da fara'a hajiya ta ce"yauwa,ฦณar uwa nasan baki sanni ba sunana Hajiya Aisha mahaifiyar Aliyu mai son ฦดarki Basma".
 wani irin sanyi Mama taji tun daga ฦ™afafunta har zuciyarta,sannan ta ce"Allah sarki da ya ke yanzu sunyi tafiya ne,amman bata ko kafin su tafi bata sanarmin da zuwansa ba,amman a hakan ma ina godewa Allah kuma ina gode miki,da har kika iya tattaki ki ka zo gidannan,Allah yabar zumunci".

anan dai sukayi ta hirarsu gwanin sha'awa mama ta faษ—awa hajiyar Aliyu idan har Basma ta dawo taji daga bakinta insha Allah komai zaizo da sauฦ™i sai ayi bincike aturo a wuce wajen.

 Sosai Hajiya Aisha taji daษ—i ta ce"to Hajiya na gode sosai Allah yabar zumunci kuma Allah ubangiji ya dawo mana dasu lafiya".sosai mama taji daษ—in addu'ar ta ce"Amin Hajiya na na gode a kuma gaidamin da surukin na wa,sannan ya kamata yazo mugaisa ".

murmushi Hajiya ta ce"ai in dai Aliyu ne yau ma sai ki ganshi don ba kunya ce dashi ba,musamman ma akan Basma".dukkansu sukayi dariya mama ta rako Hajiya suna ta dariyarsu kamar daman sun san junansu.

 Wani malolon baฦ™in ciki ne ya cika zuciyar Hajiya Sara ta ษ“alla musu harara tare da ce wa"munafuka ita dai duk wanda yazo gidannan sai ta shige masa,Indai wannan kurmar ce insha Allah sai ta janyo muku zaman gidan yari ko kuma ta janyowa kanta zaman gidan kaso,tunda har hulฦŠa take da ฦณaฦณan manya."maryam da Salimat suna taya ta zagin Basma,Maryam ta ce"Hmm ni wallahi wannan matar dana gani duk ta tsolemin idanu so na ke kawau nasan me tazo yi gidannan?don wallahi wannan matar kana ganinta ba sai an gaya maka ba kasan irin mutanan nanne waษ—anda suka gaji kuษ—i gaba da baya,dama Allah zaisa inyi sa'a in auri ko da ษ—anta ne wallahi dana kerewa sa'a."

 ta faษ—i hakan tana dariya,Salimat ta ce"to uwar ja wa kai jaraba idan kuma ฦดar mafiya ce fa"?.banxa maryam ta yi mata ta shige ษ—aki abinta don ba ta son ฦ™anwae tata ta ษ“ata mata wannan farin cikin da take ciki,don tasan tun kafin taga ษ—an na ta tasan shima ฦ™yau zaiyi kamar uwarsa.
Muna ta shirin dawowa kano munyi tsaraba sosai Hafsat ta kalleni sannan ta ce"hmm wai yaya naga kina ta farin ciki ne Basma?kina murna zakiga Aliyu ko?".

 rufe idanuwa na na yi wata kunya ta kamani da yake anty shamsiyya tana wajen ta ce"Hmm bari in tashi kuyi hirarku don ni dai adaina jin kunya ta,amman dai ku shirya Hamxa ya kaiku ku siyo sauran kayan kunji?" amsa mata Hafsat ta yi da "to".sannan muka fito don tafiya.


 Pakistan ne ajikina na yafa mayafin pakistan ษ—in,"Wow"naji Hamza ya ce sannan ya ce"kai gaskiya Basma kinyi ฦ™yau wallahi,amman dai in dai mukaje wajan nan ba zaki fito ba ko?"

 Mamakin maganarsa mukaji dukkanmu Hafsat ta ce"eh da yake mijinta ne kai ko ubanta ai dole ka hana ta zuwa?".ฦดar dariya kawai ya yi sannan ya buษ—e mana murfin motar muka shiga.

Hafsat jibgo kaya ta dinga yi tana ajjewa ni kuwa abu biyu na ษ—auka nawa na karan kaina sannan na ษ—aukarwa mama wanu mayafi mai masifar kyau,ina cikin ajje kayan na hango wani agogo mai shegen ฦ™yau naje na tambayi kuษ—insa na siya sannan na fita ina jiran Hafsat,tana fitowa muka tafi.

 Zuwansa kenan ya hango lokacin da suka shiga motar da sauri sauri ya hau motarsa ya bisu abaya,hankalinsa yana kan inda suke bi,sunzo shan ฦ™wana kenan wata mota babba ta shawo ฦ™wana,da sauri ya yi gefe har yana shirin faษ—awa cikin rami,kansa ya ษ—an bugu da sitiyarin motar,sosai yaji zafin buguwar amman baiji zafin hakan ba ya janyo motar a hankali amman sai ya tarar motar ta rufe wajen baki ษ—aya.

Dukan sitiyarin motar ya yi da ฦ™arfi sannan ya ce"oo shet me yasa bana samunku dream girl,wallahi matuฦ™ae ban ganki ba bazan iya barin garin Abuja ba".

 yana faษ—an hakan yaja motar ya bisu amman bai gansu ba,ko ฦ™asa ko sama babu su babu labarinsu,wasu hawaye masu zafi suka zubo masa ya saka hannunsa ya goge,yaji ฦ™arar wayarsa ya amsa kiran daga cen ษ“angaren Sarauniya Jidda ta ce"lafiyarka kuwa Sadauki me yake damunka"?.

 "babu komai aiki ne ya yi min yawa".babu yadda ta iya dole ta katse kiran tana mamakin abinda ke damun ษ—an na ta.
Babu yadda Anty shamsiyya bata yi damu ba,akan mu hau  jirgi ba amman tsorona ya hanamu hawa ai kuwa Hafsat sai mita take wai da tuni mun keta hazo amman na yi musu baฦ™in ciki,ko da muka hau motar ma faษ—an ta take ta yi na mita,don daman nasan halin Hafsat aฦ™wai faษ—an tsiya.

Tun tana mitar har ta yi baccinta,na shafi gefen fuskarta a zuciyata ina ce wa"Hafsat kenan sarkin faษ—a Allah dai ya bawa Munir haฦ™uri don zaisha mita.


Ni ban iya baccin mota ba haka na kafe idanuwa na ina jan carbina har Allah ya kawomu sai wajen ฦ™arfe 7 na dare sannan mukazo.

Alokacin Hafsat tana bacci ai kuwa ina tashinta daga bacci na ce mata sai yanzu mukazo ai kuwa sai ta hau mita tana miฦ™a,tana ce wa"ai kinga Basma shegen tsoronki ni wallahi yana cutata gaskiya, yanzu ba ga shi ba kin jawo mana tun safe muna tafiya sai yanzu mukazo kano Allah ma dai da yasa bamu haษ—u da ฦดan kidnapping ba?".dafe kaina nayi don wallahi mitar Hafsa har ciwon kai take sakawa.

 "To Allah dai ya tsaremu ko ฦดan mata?".da sauri na juyo don ganin me yi mana wannan maganar
Sosai na yi mamakin ganin bawan Allahn tun da muka shiga motar ya kafa min idanu da kuma mun haษ—a ido sai ya sunkuyar da kansa kamar mai jin kunyata.

Ban kulasa ba sai Hafsat ta ti karaf ta ce"Hmm bawan Allah jirgi fa akace zamu shiga amman wallahi wannan ฦดar uwar ta wa taฦ™i yadda mu shiga saboda tsabar tsoronta wallahi".


 ฦดar dariya ya yi sannan ya ce"hmm ai dole taji tsoro babbar yayarmu".da sauri Hafsat ta juyo ta ce"haba mlm yanzu ni ce babbar yayar ni fa shekarata 18 amman kace min babbar yaya?ai ido ba mudu ba yasan kima ai kowa ya kalle ka yasan ka haifeni a haihuwar kaji".dariya abin ya basa ya kalli Basma wacce ta haษ—e fuska tamau kamar zatayi kuka.

Ya yi murmushi ya taso har inda Basma take ya kalleta sosai sannan ya ce"wai wanan beauty ษ—in ba ta maganane?".

 banza na yi masa ki albarkacin kalli bai samu ba na janyo hannun Hafsat,don na gaji da surutun ta ciwon kai ya ke sakani.

 Tsabar maita wannan bawan Allahn tsabar naci har gida sai da ya  biyo mu,abin mamakin Aliyu na hango a ฦ™ofar gidanmu ajikin motarsa ya kafamin idanuwa,amman ganin wannan bawan Allahn ya biyoni a baya kamar maye sai magana ya ke min.fuskar Aliyu na kalla ya haษ—e girar sama da ta ฦ™asa,ko kafin in ฦ™arasa har ya shige cikin motarsa cikin fushi yabar wajen.






*Miss green ce*
[08/08, 14:12] Miss Green๐Ÿ€: *๐ŸBASMA๐Ÿ*

BOOK 2๐Ÿ“ƒ


BY
UMMU MAHER(MISS GREEN๐Ÿ€)


Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444



---------
SIRRINKI๐Ÿ‘‚๐Ÿป
1
*Yadda ake maganin ฦ™urajen fuska.*


Daga ummu maher


Asamu garin alim da ma'ul wardi cokali biyu a haษ—a arinฦ™a gogawa a fuska abarshi ya kai minti 15.

     
   2
ko kuma a samu zuma da lemon tsami a dinga shafawa idan mutum zan ฦ™wanta bacci idan ya tashi ya wanke.
-----------------------------------


     *31๐ŸŸข32*


Sosai abida tasha wahala a wajen gwarzon mijinta yarima Abeed,shima da kansa yaji jiki sosai don kullum shan magani ya ke amman kuma kullum abin ฦ™ara gaba ya ke,ya sha zama a ษ—aki shi kaษ—ai ya yi kuka sosai,don irin wannan matsalar ba kowacce macece take zama da miji a haka ba,sai wadda Allah yasa lalurarsu ษ—aya.


Abida tasha wuya don haka ko iya motsi ba ta iyayi da ษ—an yatsanta saboda tsabar wahalar da tasha,shi kuwa da wuri ya fice zuwa sashensa don baki ษ—aya jikinsa mugun ciwo ya ke masa.



****

Ta gumi sosai na yi ina tunanin Aliyu yau ฦ™wananmu biyu kenan da dawowa amman sam ya ฦ™i zuwa inda na ke,na yi kuka sosai don na saba da Aliyu sosai har ba na jin zan iya rabuwa dashi.

Mama tana gama wayar da take ta kalleni sannan ta ce"jiya Alhaji sunyi magana da iyayen Aliyu gobe insha Allah za'a saka rana har da sadaki".mamaki sosai na yi na fito da idanuwa waje ina mamakin hali irin na Aliyu.


 "wallahi Basma kinyi dacen mijin aure da kuma dacen uwar miji sai dai inyi miki fatan samun zaman lafiya agidanki,Allah ya tsare gabanki da bayanki".murmushin jin daษ—in addu'ar Mama na yi cikin jin kunyarta na tashi da sauri na shige ษ—akinmu,itama Hafsat tana waya da munir.


ฦ˜wanciya na yi na ษ—aga idanuwa na sama ina tuna wai yau ni ce za'a kawo kuษ—ina harda na sadaki,rufe fuskata na yi ina dariya ni kaษ—ai,Hafsat ta kashe wayar sannan ta ce"ikon Allah Basma me kuma ya faru ki ke dariya ke kaษ—ai"?.biro na samu kusa dani na rubuta mata na miฦ™a mata.

 "Wayyo Allah Basma gaskiya na ji daษ—i wallahi Mama kuma bata faษ—a min ba?na yi murna wallahi Allah dai ya kaษ—e duk wata fitina da za ta ษ“ullo cikin wannan auren".Amin na ce a zuciyata sannan na tashi na shiga wanka don ina da waษ—anda muke karatu tare dasu,karatun mu na kurmaye na ฦ™ware sosai a fannin koyar da karatun ta yadda zasu fahimta sosai kamar masu ji.
 Wannan baiwa ce da Allah ya kewa bayinsa,sai kaga makaho baya gani amman kuma ya iya rubutu da karatu,ya Allah ka sa mu cika da imani amin.


 Washe gari da wuri iyayen Aliyu sukazo a babban farlon gidan Baba ya tarbesu,ko da Baba ya timtiษ“i mama akan sanarwa da mahaifina ce wa ta yi a ฦ™elesa kawai da bai san da ฦดar ba sai yanzu?ya manta da ฦดarsa tilo a duniya ya biyewa sharrin ฦดan bariki suna kaษ—a masa ganga.


 Baba bai ce komai ba ya wuce amman tabbas zai faษ—a masa ko da bayan an kawo kuษ—in sadakinne,an saka rana nan da wata 2 an kawo sadaki naira dubu ษ—ari biyu,suna tafiya Baba ya shigo kana ganin bakinsa kasan yana cikin farin ciki,kuษ—in suna jikinsa ya wuce ษ“angaren Mama.

 Hajiya Sara tana kallonsa ta biyosa tana ce wa"Alhaji lafiya naga kana ta murmushi haka?kamar wanda aka yi wa albishir da gidan aljanna?".murmushin ya ฦ™arayi sannan ya ce"ai dole kiga ina murmushi Saratu kuษ—in wannan yarinya  Basma aka kawo harda sadakinsu tare kuma da tsayar da ranar aure.
Da sauri hajiya Sara ta da fe ฦ™irjinta tana zare idanuwa har ฦ™wallar azaba sai da ta fito mata ta ce"innalillahi wa inna ilaihi raji'un,yanzu Alhaji ina gidannan a rasa wanda zai faษ—a min za a kawo kuษ—in kurma sai da aka kawo sannan za'a faษ—a min?wallahi an zalunceni ai nasan duk wannan munafukar matar ce za ta hanaka to wallahi na ga ta yadda za'ayi wannan auren matuฦ™ar ina raye".

 tana faษ—ar hakan ta taho kamar za ta tashi sama,sosai Alhaji Saminu ya yi mamakin hali irin na matarsa saratu tun tasowarta na ฦ™uruciyarta haka yasha fama da ita don macece mai nuna baฦ™in ciki da hassada akan komai musamman idan taga ya yiwa wani abu ba tare da ya nemi shawararta ba,sam Hajiya saratu ba zaษ“insa bace zaษ“in iyayensa ne kuma tun kafin su mutu sun danฦ™a amanarsu a hannunsa don haka wannan ya ke tunowa ya ke ฦ™eleta a dukkan abinda za ta yi.

 Girgiza kansa kawai ya yi ya wuce don idan da sabo ya saba da halin Hajiya Saratu na mugun hali,muna zaune a farlo kusa da mama tana bamu labari Baba ya shigo,ni da Hafsat muka gaishesa muna shirin ta shi ya ce"a'a ku yi zamanku maganar ai ta shafeku".dawowa mukayi muka zauna kanmu a ฦ™asa.

"Wannan sadakin Basma ne gashinan naira dubu ษ—ari biyu ne,kuma an saka ranar aurenta nan da wata biyu kamar yadda aka saka na Hafsat don haka waษ—annan kuษ—in ki ajjesu a nemi mahaifinta yasan duk halin da ake ciki".

"Alhaji ba wai na ฦ™i ta taka bane amman fa sam a yanzu bazan faษ—a masa ba har sai biki ya taho don wallahi zai iya wargaza duk wani shirinmu don mu kullum so muke muga rayuwar Basma ta yi ฦ™yau ba kamar yadda ya lalata rayuwar ฦดarsa da kansa ba".ta shi Baba ya yi ya ce"to ni dai yanzu bari in fita wajen aiki daman ina shirin fita sai kuma ga su".
Adawo lafiya mukayi masa sannan na shige ษ—aki da sauri wai ni kunyar mama,Hafsat ta bini tana tsokana ta wai ke ki ka ce kina so da baki ce kina so ba da ba'a baki shi ba.



"Wallahi Maryam in dai har ina raye wallahi wannan yarinyar bata isa ta yi aure ba,sai na lalata abin ni Alhaji zai munafinta har a saka ranar aure ni ina gefe?wallahi ayau zanje wajen Hajiya Salamatu ayi duk wacce za'ayi don wallahi sai na saka an lalata wannan auren".

 "hmm ni fa Hajiya kaina baki ษ—aya kullewa ya yi saboda mu an mayar damu ba abakin komai ba shine har za'ayi bidiri a gidannan har haka mu ba tare da mun sani ba?to wallahi bazai taษ“a yi yuwa ba.

 Salimat ta ce"Hmm Hajiya ni jin zuciyata na ke kamar za ta buga saboda tsabar tashin hankali wallahi,Hajiya ko kin san Aliyu ษ—innan dana tayar da hankalina akansa saboda sonsa ashe shine ya ke son Basma?ษ—azu na fita Aisha take faษ—a min wai ta taษ“a ganinsu suna zance hanyar makarantarmu."

"kan uban cen ai wallahi ba zai taษ“a yiyuwa ba,dole ne ma asan duk yadda za'ayi amman aure sai an fasa sa sai dai dukkaninku ku rasa wallahi,kurmar me?kurmar banza da wofi duk ta saka ฦดaฦดana dani kaina acikin matsala,to wallahi ki zanyi yawo tsirara dole ne ma inyi mai yiyuwa a fasa auren nan".tana faษ—ar hakan ta figi mayafinta ta fita.


Aranar Aliyu yazo ansha sosai kamar babu gobe,na bashi haฦ™uri akan mutumin da ya ganmu rannan dashi,kallona ya yi sosai sannan ya ce"Basma a lokacin hankalina ya tashi sosai,ina sonki Basma bana son abinda zai rabani dake sai mutuwa,mutuwarma ina fatan ta ษ—aukemu tare,ayanzu babu wani tunanin da zanyi tunda ko ayanzu na riga dana bada sadakin aurenmu,don haka abinda ya rage mana sai mu cigaba da addu'ah har Allah ya kaimu ranar aurenmu".

ya faษ—i hakan yana kallon cikin idanuwa na,murmushi na yi ina kallonsa
ya yi min wani irin kallo mai tsayawa arai na tashi da sauri zan fita ya janyo bayan mayafina,sai ga Maryam ta zo wucewa ta saki ฦ™ara.




*Miss green ce*
[08/08, 14:12] Miss Green๐Ÿ€: *๐ŸBASMA๐Ÿ*

BOOK 2๐Ÿ“ƒ


BY
UMMU MAHER(MISS GREEN๐Ÿ€)


Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444



---------
SIRRINKI๐Ÿ‘‚๐Ÿป

Mu yawaita yin addu'ar fita daga gida da kuma ta shigowa saboda samun kariyar Allah da kuma ta mala'ikunsa.
------------------------------


29๐ŸŸก30


 . . .wani matsanancin faษ—uwar gaba naji yadda Aliyu ya tafi cikin ษ“acin rai ina addu'ar Allah dai ya kaishi gida lafiya ba tare da wani abu ya sameshi ba don a yadda yaja motar komai zai iya faruwa dashi.

 Hafsat ta kalleshi sannan ta ce"haba bawan Allah yanzu meye amfanin biyomu har gida don Allah?".ษ—an murmushi ya yi sannan ya ce"so ne ya janyo komai ba don so ba da babu abinda zai saka in biyo ku".

 ni kam tsabar haushin korar min masoyin da ya yi yasa na yi shigewa ta cikin gidan ina jan kayan na mu daฦ™er,Allah ya taimakeni har na shiga cikin gidan babu wanda na gani a tsakar gida na yi hamdala sannan na ฦ™arasa shiga cikin farlon mama,tana kitchen ษ—inta na farlo ta hangoni da sauri ta fito tana mana sannu da zuwa.

 Da sauri na tashi na rungume mama kamar na yi shekara ban ganta ba,harda guntun hawaye na mama ta ce"ina Hafsat ษ—in kuma ta tsaya"?.ko kafin in bata amsa sai ga ta ta shigo tana mita.

 Mama ta ce"ke kuma me ya faru ki ke mita haka"?.sai da ta ajje kayan hannunta sannan ta ce"wallahi mama wani mutunne me shegen na cin tsiya ya biyomu mama tun a mota har gida sai da ya biyomu,wai shi son Basma ya ke kuma tunda naga Basma ta zungura ฦ™eya ta tafi cikin fushi wallahi nasan ba ta sonsa."

 sai ta kalli inda na ke taga tuni ma har ma na shigewa ta ษ—aki,mama ta ce"to ni dai wuce kitchen ki ษ—akko abincinku a kula da faranti har kunun aya ma na yi muku yana cikin fridge".da sauri hafsat ta shige ta ษ—akko abincin ta ajje a farlo sannan ta ษ—akko kunun ayar ya yi sanyi sosai ta ajje mana a ษ—aki,tuni ma har na shige wanka Hafsat ta ce"uwar tsoro kawai ai kema gashi nan jikinki ya gaya miki daga saukarmu a mota har kin shige wanka".ta faษ—i hakan tana dariya taji ฦ™arar wayarta ta ษ—auka munir ne ta yi ฦดar dariya sai da ta cire kayanta ta ษ—aura zani sannan ta ษ—auka tana shirin katsewa ta ce"hello".wata ฦดar dariya munir ษ—in ya yi sannan ya ce"amarya ba ta laifi yau shan ฦ™amshinne ya motsa kome? Ya hanya ina fatan kun sauka lafiya"?.

 nan dai suka cigaba da hirarsu ta masoya,ina fitowa daga wanka na ta da sallar isha'i sannan na yi addu'o'in da na sabayi na shafa na buษ—e jarkar kunun ayar na zuba a gora na fara sha sanyin har raina.

Ina cikin sha Hafsat ta gama wayar sannan muka fara cin abincin lokacin Baba ya dawo muka gaisa ya zauna a farlo yana tambayarmu yaya muka barosu da yaranta da maigidan harma da abokiyar zamanta.

 Duk muka amsa masa da suna nan lafiya sannan muka ษ—akko masa tsarabarsa ta jallabiyya har guda biyu masu ฦ™yau da kuma hula guda biyu suma masu ฦ™yau,dariya ya yi sannan ya ce"ikon Allah harda wannan wahala kuma bayan duk wata sai ta aikomin da kuษ—i kamar wani albashi? ina godiya Allah ya yi muku albarka ku dukanku.muka amsa da "amin".

 mama kenan duk ฦดaฦดanta ta koya musu tausayin  mahaifinsu tun suna ฦ™anana,bata koya musu rashin tausayin mahaifinsu ba iyaye da dama sai dai idan ฦดaฦดansu sun yi musu alheri su ฦ™ullesa a bakin zaninsu suฦ™i su nunawa iyayen yaran baki san kanki ki ke cuta ba,ko kuma kaji uwa na ce wa kada ฦดaฦดanta su taimakawa mahaifinsu don wani dalili na ta,to wallahi kiji tsoron Allah domin shima mahaifi yana da nashi haฦ™ฦ™in akan ฦดaฦดansa musamman idan ya manyanta.
*****

Har ya bar Abuja bai sameta ba ya duba duk inda zai ganta amman shiru don haka dole ya koma gida ba don yaso ba,saboda Fulani ta matsa masa sosai akan ya dawo.

Ranar da ya dawo kamar ko da yaushe ya idan zai dawo gidan kamar ana buki yana ana shiga ana fice komai dare kuwa don babu wanda ya isa ya yi bacci agidan idan shalelenta bai dawo ba.

 Matansa ma kowaccensu tasha ฦ™walliyarta gwanin sha'awa kowacce ganin ta take babu ya ita a ฦ™yau da kuma sarauta,sai da ya fara zuwa wajen mahaifiyarsa sannan ya wuce wajen fulani kishiyar mahaifiyarsa ya gaisheta suna gaisawar ta ce"yarima ni kuwa yaya naga duk ka rame haka?ko wani abinne ya ke damunka bamu sani ba?".

 ษ—an murmushi ya yi na jin daษ—in kulawar matar akansa don ko mahaifiyarsa bata tambayesa abinda ya ke damunsa ba,ita dai burinta kawai ya dawo gida.

 "Wallahi ammi ฦ™wata ฦ™wata bana jin daษ—in rayuwata a yanzu,saboda wata yarinya da ta shigo rayuwata a ฦ™wana biyu kawai ta hargitsamin komai na cikin rayuwata,kuma abin takaicin ban san a inda take ba".?

 ya faษ—i hakan kamar zaiyi kuka,sosai fulani ta yi mamakin Abeed tun yana ฦ™arami bai taษ“a saka abu aransa irin wannan yarinyar ba,shi ba ma mutunne mai saka damuwa aransa ba.

 "Ina son mace wacce bata damu da rayuwa ba,wacce bata damu da mai kuษ—i ko akasin haka ba,mai hankali nutsuwa rashin magana da sauransu,amman duk wannan yarinyar ta haษ—a waษ—annan abubuwan a ษ—an zamanda na yi da ita."

 sosai Fulani ta ฦ™wantar masa da hankali sannan ta yi masa alฦ™awarin za ta taya sa addu'ah da kuma taya sa nemanta.jiki babu ฦ™wari ya wuce ษ“angarensa sai da ya yi wanka sannan ya wuce sashen matan na sa ษ“angaren Abida ya fara zuwa tunda a musulunce ษ“angarenta ya kamata  ya fara zuwa tunda har ya tafi bai shiga sashenta ba.

Tana jin tafiyarsa da sauri ta wuce ta zauna akan faffaษ—an gadonta tana gyara zaman haษ—aษ—ษ—iyar rigar baccinta wacce ta gaji da haษ—uwa kusan rabin jikinta duk a bayyane ya ke.
Da sallamarsa ya shiga Abida ta tsura masa idanuwa kamar mayya tana hangota kawai a jikin abeed yaya za ta yi kuwa tsabar murna,bata iya ษ“oye ฦ™waษ—ayinta ba ta isa gareshi ta faษ—a jikinsa tana masa sannu da zuwa,Abida kenan aฦ™wai kissa da kuma kisisina,ita kuwa Bilkisu babu abinda ya shafeta don bata ma iya yadda za ta janyo hankalin miji ba tafi gane tasha maganin mata kawai.wanda kuma rashin ganewa ne hakan a wajen mace wajibine ki iya waษ—annan saboda ki zama star a gidan aurenki ba wai mace ta zauna da ฦ™azanta hammata duk jiki yana wari ba.

 So ya yi ya biye mata amman sai ya basar da ita a daฦ™ile ya ce"ki saka hijabinki ki biyoni sashen bilkisu yanzu".wani malulun baฦ™in ciki ne ya cika mata ciki jin an ambato sunan bilkisu don yadda Bilkisu take wani jijji da kai wai ita ฦดar sarauta itama ฦดar sarautar ce kuma babu abinda masarautarsu za ta nunawa ta su.

 Babu yadda ta iya dolenta ta bishi ba don ranta ya so ba,tana tunanin abinda za ta yi don ta ฦ™ular da Bilkisu.

Haษ—asu ya yi dukkansu ya yi musu faษ—a sannan kowaccensu ta tashi tana wani taฦ™ama da kuma jijji da kai,ya.kallesu ya yi ฦดar dariya sannan ya ce"duk zanyi maganin wannan ษ—agawar ta ku don sai na koya muku menene zaman aure don yaga suna neman ilimi akan hakan.


 Bayan sunyi sallah ne Sarauniya jidda ta aiko musu da farfesu da kuma kayan marmari,kamar ba amarya ba haka Abida ta buษ—e cikinta taci ta ฦ™oshi ya kalleta da gefan idanu,azuciyarsa ya ce Allah ya ฦ™yauta sam shi a rayuwarsa bai son mace mara kunya kuma a hasashensa shine Abida buษ—aษ—ษ—an ido ne da ita sosai don ta fi Bilkisu ma.

 Ko da ya ฦ™wanta har ta fara baccinsa mai daษ—i ya fara mafarkin Basma,kawai sai yaji ana shafa ko ina na jikinsa,sam bai son yin wani abu a yanzu don baya son wahalar da jikinsa da kuma ita amman dole sai da taja ra'ayinsa sai dai fa yana ษ—aukar hanya ta fara gane mutan garinsu.



*Miss green ce*
[08/08, 14:12] Miss Green๐Ÿ€: *๐ŸBASMA๐Ÿ*

BOOK 2๐Ÿ“ƒ


BY
UMMU MAHER(MISS GREEN๐Ÿ€)


Wattpad user name
   Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444


[07/08, 11:59] Miss Green๐Ÿ€: Duk mai son magana dani ga no ษ—ita ta whatsapp sai ka yi save number na inyi ta ka๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป
 07068606171
---------
SIRRINKI๐Ÿ‘‚๐Ÿป

ฦณAN UWA MU RAGE HASSADA DA ฦ˜ETA,DON YANA CIRE MANA IMANIMU BAKI ฦŠAYA.
-----------------------------------  


33 ๐ŸŸข34

"Na shiga uku na ni Maryam iskanci da rana tsaka kuma Basma".sosai na tsorata da jin ihun da maryam ta yi ni da Aliyu,kafin ince wani abu Maryam ta shiga cikin gidan,na kalli Aliyu naga shima ni ya ke kalla ya ce"wai wannan ignorance ษ—in a gidanku take"?.ka sa ce masa komai na yi saboda ban san ma me zance masa ba sai da ya ฦ™ara maimaita wa sannan na ce masa"eh anan gidan take mamanta ita ce uwargida".

"oky i understand na gane Allah ya ฦ™yauta"da Amin na amsa masa muka cigaba da hirarmu gwanin sha'awa,amman fa zuciyata tana dukan uku uku saboda tunanin abinda zaije ya dawo,ai kuwa muna cikin hirar sai ga maryam ษ—in ta fito ita da Salimat.

 Wani baฦ™in kishi ke jan Salimat ji take kamar ta kashe ฦดar kurmannan kowa ya huta,kallon sama da ฦ™asa take min tana wani hararata,sai da tazo dai dai inda muke a tsaye ta ce"Hmm Allah dai ya ฦ™yauta bawan Allah za'a cucesa a maฦ™ala masa masifa sai da aka gama yawan duniya sannan za'a wani liฦ™ewa mai kuษ—i."

 ban san sanda wasu hawaye masu zafi suka zubomin ba na goge hawayen,ganin hawaye a idanuna ba ฦ™aramin baฦ™anta ran Aliyu ya yi ba,ya kalli Salimat cikin fushi ya ce"look ki yi maza kibar wajannan saboda kin fara wuce gona da iri don wannan da ki ke gani a gabana ko me tayi a rayuwarta bazan taษ“a gudunta ba,don haka kada ki ฦ™ara laฦ™abawa matata wannan ฦ™azamin furucin idan kuma ฦ™inki zaki yi nadamar duk waษ—annan maganganun da ki ka yi.

sheฦ™eฦ™e maryam ta kallesa sannan ta ce"hmm to idan aka ฦ™i me mutum zaiyi kuma"?.a zafafe ya kalleta zaiyi magana Basma ta tare gabansa ta kalli cikin idonsa ta girgiza masa kai alamar kar ya yi haka.

 Kallonta ya yi sosai aduk sanda ya kalli idon Basma yana ganin tsananin sonsa acikinsa tare da wani irin sirrin da ba kowa ne ya ke gani ba sai shi kaษ—ai.
 Bai ce komai ba ya shige motarsa Basma ta ษ—aga masa hannu ya tafi yana kallon abar sonsa Basma.

 Itama Basma ษ—in murmushi ta yi tana addu'ar Allah ubangiji ya kawo musu lokacin aurensu lafiya.

Tana juyowa taga Salimat ta tsare mata hanya ta nuna ta da ya tsa ta ce"ke kina ganin kin tsira daga tarkonmu ko?to wallahi bari kiji Aliyu na wa ne shi kaษ—ai ba na wata macen bane don ni kaษ—ai aka haliccesa don haka tun wuri ki fita harkarsa idan kuma ba haka ba?wallahi sai kin raina kanki don gab ki ke da komawa makauniya daman ke ga ki kurma,kinga sai ki zama musakarki tsaf."

 tunda na ke dasu Salimat ban taษ“a ko da yi musu kallon banza ba amman yau ban ma san sanda na yi mata ba,saboda na ga rainin hankalin na ta har ya fi na kullum,mutum da saurayinsa amman ace wai sai ya rabu da ita saboda wata,wannan ma ai ฦ™arfin hali ne.

 "Inye lallai kurman nan wuyanki ya isa yanka yanzu Salimat ษ—in ki kewa wannan banzan kallon"?.cewar maryam wadda take kallona kamar taga baฦ™uwar fuska,bance musu komai ba na yi wucewa ta abina,ban gama shiga gidan ba naji maryam ta ce"ai kin banza aikin hofi ai gidan da ki ke wani gadara har ki ke iya ture mutane kina shiga ai ba gidan ubanki bane,idan gadarar ki ke so ki yi ai sai ki koma gidan ubanki ษ—an caca kuma ษ—an giya".

 cak na tsaya saboda yadda naji maganar kamar saukar aradu,nan da nan idanuwa na sukayi jawur kamar gauta,na juyo na kallesu tsaf hawaye sun fara taruwa i danuwa na,da gudu na shiga cikin gidan ina rufe bakina da hijabina,ina jin zuciyata kamar za ta fito.

 Tabbas rashin ji a rayuwa ba ฦ™aramin abu bane,tabbas yau da ace ina iya mayar magana to babu abinda zaisa ฦ™inฦ™i mayarwa da su Salimat magana.

 Mama tana zaune a farlo na faษ—a kanta ina kuka sosai,hankalinta atashe ta ษ—ago fuska ta tana kallon cikin idanuwa na yadda sukayi jawur kamar gauta cikin alhinin ganina a haka ta ce"Basma me ya faru?me ya sameki?".kukan har yanzu na ke ba tare dana ba ta amsa ba,koda da maganar kuramen ne.

 Hafsat ma da ta gama waya yanzu da munir jin kuka cikin tashin hankali ta fito ta ษ—agoni ta rungumeni tana tambayata lafiya"?.

 ban iya ba ta amsa ba ta zaunar dani a hamkali akan kujera ta ษ—akko biro da takadda ta ce"Basma don Allah ki yi haฦ™uri ki tsayar da kukan ki faษ—amin me ya faru?".

 Karษ“ar abin rubutun na yi hannuwa na suna kakkarwa na fara rubutun cikin kuka hawaye na yana ษ—igowa kan takaddar.mama sai kallona take tana tausayina har cikin ranta.
Da sauri Hafsat ta karษ“a ta fara karantawa,zuciyarta har tafarfasa take wajen karantawa ta tashi da sauri xa ta fita,na ruฦ™o hannayenta duka biyu ina kuka ina girgiza mata kai.

Ko kallon inda na ke bata yi,mama ma da sauri ta amshi takaddar tana karantawa itama zuciyarta tafarfasa kawai take don abinda su Salimat sukewa Basma ya yiwa yawa.

Bankaษ—a labulen ษ—akin Hajiya Sara Hafsat ta yi,ko sallama bata yi musu ba tana shiga ta shaฦ™o wuyan maryam ta yarfa mata maruka har biyu,da sauri Hajiya Sara ta tashu tana ce wa"na shiga uku na Hafsat baki da hankaline zaki shigo mana ษ—aki kamar mahaukaciya ki riฦ™e wuyan ฦดa ta kina duka kamar wata zautatta?to wallahi idan ma munafukar uwarki ce ta aikoki ma ษ—an banzan duka zaki sha wallahi".tana faษ—ar hakan tana ฦ™oฦ™arin cire ni daga jikin Maryam.

Alokacin mama da Basma suka shigo ษ—akin,faษ—a sosai akayi don mama da Hajiya sara suma danban sukayi sosai,Salimat ta shaฦ™oni sosai har sai da na fara ganin wasu taurari,ban san sanda wani ฦ™arfi yazomin ba na shaฦ™eta nima na zauna kan ruwan cikinta na hau dokanta kamar Allah ya aikoni.

Nan da nan bakinta ya fashe har ya ta fara zubar da jini a bakinta,muna cikin hakan ne Yaya Abubakar ya shigo,sosai ya yi mamakin abinda ke faruwa har yana tunanin anya kuwa agidansu ake wannan toya wainar.

Sosai ya yi namijin ฦ™oฦ™ari wajen raba wannan gawurtattan faษ—an,ai kuwa yana rabawa Hajiya Saratu ta fashe da kuka don tabbas yau tasha duka a hannun Hajiya Aisha.

 "Wallahi wannan matar so take ta kasheni ni da ฦดaฦดa na abubakar shigowa kawai sukayi suka fara dukanmu kamar sun samu jakai,wallahi bazan yarda ba sai an ฦ™watomin ฦดanci na".

 kallon mahaifiyar ta sa ya yi ya girgiza kai sannan ya ce"Umma tabbas aฦ™wai abinda ya faru har hakan ta kasance,tunda na ke a gidannan ban taษ“a ganin Mama ta yi magana akan duk abinda su Salimat da maryam suke mata ba,uwa uba abinda sukewa Basma amman yarinyar nan ban taษ“a ganin ta ษ—aga idanu ta kalli abinda suke mata ba ballanta ma har ta iya ramawa."
"To dan ubanka rama mata zakayi ko me?shege wanda bai damu da ฦดan uwansa ba,daman ina lura da yadda ka ke wani shsshigewa wannan shaiษ—aniyar wannan kurmar,ai ko na yi hauka bazan yadda ka ษ—akki mana ire iren ฦดan giya ba tanbaษ—aษ—ษ—u,kun ษ—auka bamu san abinda ubanta ya ke ba?to ko yanzu mutum idan yaje borno ya ce akaisa gidan Abdu ษ—an caca,mai mata mai harka da gudu za a kaika gidansa don haka wallahi bazan taษ“a yadda in haษ—a jinina da gurษ“atacciyar zuri'a ba".

 ko kafin Hajiya Sara ta rufe bakinta mama ta ce"oho ai mahaifinta ne ya ke yi ba ita bace takeyi ba to alhamdulillah,kuma mu haryanzu bamu taษ“a haษ—a Allah da wani ba,ke kuwa ko yanzu idan akaje unguwarku,aka tambayi inane gidan karuwai za a nuna gidan ubanki kinga kuwa mu gidanmu bashi da wannan sunan,don haka idan zakiyi magana ki dinga taunata tunda kema baki san abinda za  a mayar miki ba".mama tana faษ—ar wannan maganar taja hannuna muka fita daga farlon".
Tsabar haushi Abubakar ko tsayawa baiyi ba da sauri ya fito daga ษ—akin ya tafi wajen aikinsa,don yau yana jin zuciyarsa babu daษ—i,tabbas idan mutum ya yi dacen uwa tagari to fa tabbas ya godewa Allah don mace tagari itace tushen al'umma.


"Wallahi Umma bazan yadda da wannan cin mutuncin da Basma ta yi min ba,jiba fa yadda ta fasamin bakina sau jini ya ke".tana faษ—ar hakan ta fashe da kuka sosai.

Zagaye kawai Hajiya Saratu take aษ—akin na ta tunanin kawai abinda xa ta yiwa Hajiya Aisha kawai take,tabbas a wannan karan ba za ta yadda ba dole sai Aisha ta ษ—anษ—ana kuษ—arta akan abinda ฦดar ฦ™anwarta ta yi mata wato Basma.

Mayafinta ta ษ—auka ta fito tana harar ษ—akin Hajiya Aisha tana ce wa aranta in kinsan wata ai baki san wata ba,don saina ษ—auki mummunan mataki akanki da wannab shegiyar kurmar.




****

"Wai Ahmad wannan wani irin rayuwa ne akawo maka mata yau ฦ™wana ษ—ai ษ—ai har ฦ™wana 30 amman  baka taษ“a shiga ษ—akinta ba,kasan laifinka awajen Allah kuwa"?.


 mahaifiyar ta sa ya yi sosai sannan ya ce"Hajiya nima kaina ban san abinda ya ke damuna ba ni dai nasan tunda na rasa Basma sai na ke jin kamar na rasa komai na wa. . .."

 tun kafin ya ฦ™arasa da sauri ta katsesa wajen ce wa"wato akan wannan shegiyar kurmar yarinyar ne ka ke wulaฦ™anta min ฦดar ฦ™anwata?to tabbas idan bata yi da wasa ba saina saka an kullemin shegiya ta rasa me fito da ita daman bata da galihu,ni za ta cinyewa ษ—a saboda tsabar maita na cinta,to wallahi ka fi ฦ™arfinta shegiya karuwa kawai."

 jin maganar mahaifiyar ta sa ya yi kamar ta buga masa wata guduma akansa,gwara ta gaya masa duk maganar da za ta faษ—a masa akan ta  faษ—awa Basma baiwar Allah wacce bata ma san abinda ke faruwa ba.



*Miss green ce*
[08/08, 14:12] Miss Green๐Ÿ€: *๐ŸBasma๐Ÿ*



๐Ÿ“By Ummu maher(miss green๐Ÿ€



   35๐ŸŸข36



. . .kusan mintina talatin kenan Sarauniya jidda tana kan yarima Abeed tan kallon ikon Allah tunani kawai ya ke tunda ya zauna kusan ma za ta iya cewa harda hawaye.a hankali ta kira sunansa ta ce"yarima me ya sameka haka ka ฦ™wana biyu sam mun kasa gane kanka,hatta matanka ma sunce ka yi musu tawaye ba sa ganinka ฦ™wata ฦ™wata idan aฦ™wai abinda ya ke damunka ne ka faษ—a min don Allah".?
 
Ta faษ—i hakan kamar za ta yi kuka,duk taurin rai irin na Sarauniya jidda amman matuฦ™ar taga Abeed a wani hali to fa sai kaga ta zama kamar wata hauka sabon kamu.

"Kai na ke sauraro Abeed".kai tsaye ta faษ—i hakan tana wara idanuwanta akansa,sun kuyar da kansa ya yi a duk tsawon shekarunsa a duniya bai taษ“a jin mahaifiyarsa ta faษ—i sunansa kai tsaye ba,saboda sunan mahaifinta ne sarkin sudan.

 Kunya kawai ya keji akan abinda zai fito daga bakinsa ya furtawa mahaifiyarsa akan mace ya shiga wannan halin macen dama bai san yanzu a inda take ba?ko rufe idanuwansa ya yi to fa fuskar Basma kawai ya ke gani,ya rasa wani irin mugun so ya ke mata hakan da haryanzu aikinsa ma yana barazanar tsayawa cak,saboda tsabar tunanin Basma.

 "Yanzu Yarima ban isa ka gayamin abinda ke damunka ba?shikkenan babu komai amman na tabbatar da Fulani ce waccen munafukar kishiyar tawa da ta fini awajenka yo da yanzu tuni ka faษ—a mata tunda ita ce tayo min naฦ™udarka ai dole ma ka faษ—a ."tana faษ—ar hakan ta kama hanya za ta tafi.

Da sauri ya tashi ya ruฦ™o hannun mahaifiyarta sa duka guda biyu bai san lokacinda ya rungumeta baki ษ—aya ba,ya fashe da kuka sosai kamar wanda akace masa iyayensa duka sun mutu.

 Sosai jikin Sarauniya jidda ya yi sanyi tabbas abinda za kaga ya sa Yarima kuka to fa wannan abin ba ฦ™aramin abu bane,a hankali ta zaunar dashi cikin tausayi irin na ษ—a da uwa ta kalleshi a hankali kamar ษ—an ฦ™aramin yaro ta ce"yauwa ษ—ana yanzu gaya min me ke damunka ฦ™wana biyu da har ka kulle kanka kai ษ—aya a ษ—aki ka ฦ™auracewa matanka"?.

 tabbas yana son gayawa mahaifiyarsa gaskiya kuma baya son ษ“oye mata komai a hankali ya buษ—e bakinsa ya faษ—a komai duk jikinsa a sanyaye ga wata irin muguwar kunyar mahaifiyarsa daya ke ji.

A zafafe ta tashi ta ce"daman akan wata ฦดar iska ne ka saka kanka acikin wannan halin?ita ฦดar uban waye a duk faษ—in ฦ™asar nan da za ta saka ษ—ana mafi soyuwa a raina cikin matsala har haka?Abeed ka daina cin abinci ka daina gayu,wajen aikinka ka daina zuwa?ka ฦ™auracewa matanka?duk a dalilin wannan fitinanniyar yarinyar?wata ฦ™ila ma mayya ce ta kama maka kuruwa to wallahi bazai taษ“a yiyuwa ba sai na ษ—auki mummunan mataki akanta.shegiya wata ฦ™ila ma ฦดar matsiyata ce".tana faษ—ar hakan fuuu ta fita daga ษ—akin ba tare da ta sake ko da kallon inda ษ—an na ta yake ba.
Wasu zafafan hawaye suka taho kamar an buษ—e fanfo ya rasa yaya zaiyi da rayuwarsa tun daga ranar da yaga wannan yarinyar shikkenan ya shiga wani matsanancin hali.




****

"Basma jiya munyi waya da mahaifinki ya ce yana son ganinki kije maiduguri,to ni dai ina tunanin tura ki wannan garin musamman ma gidan mahaifinki daba saitine dashi ba".

 kallon mama na yi na yi wani murmushi har ษ—an dimfil ษ—ina ya lotsa mai matuฦ™ar ฦ™aramin ฦ™yau tabbas addu'ar dana daษ—e ina yi ce akan mahaifina yanzu gashi Allah ya amsa min hankalinsa yanzu ya dawo kaina.

Wannan murmushin dana yi shine ya tabbatarwa da mama ce wa tabbas inason ganin mahaifin na wa,don haka ba za taษ“a iya raba ษ—a da uba ba,don haka abinda yanzu kawao yafi shine ta ฦ™aleta taje ko da sati biyu ne ta yi kafin lokacin bikinta.

 Da daddare Aliyu yazo,nasha adona da wani sabon less ษ—ina ni daman gani da cikar halitta sosai shiyasa ma ban cika saka mayafiba don tabbas zan haษ—a babban go slow idan har na fito haka.

Ta kuramin Hafsat ta yi dole na na saka mayafin pink colour ruwan less ษ—in,na yi irin ษ—aurin zahra buhari,ban saka komai ba daga hoda sai ฦ™walli sai lipstick,idanuwan nan nawa kamar na mage sai sheฦ™i suke,fata ta mai ฦ™yau da haske sai walฦ™iya take,ฦ™yau tsantsa irin na shuwa arab,ga kuma jinin fulanin asali duk sai ya haษ—u ya bada wani irin colour mai masifar ฦ™yau.

"Wow gaskiya Basma kinyi ฦ™yau sosai kamar na saceki wallahi".cewar Hafsat wacce take gogemin takalmina high hill wai adole shi zan saka,ga shi kuma siket ne duk sai na jini a matse.

Babu yadda zanyi don idan naฦ™i sakawa nasan halin mitar Hafsat don haka na karษ“a na saka duk ina jin jikina kamar kowa kallona ya ke.

 A hankali na ke takuna mai matuฦ™ar ษ—aukar hankali,sai ka rantse koyamin tafiyar akayi amman babu ko ษ—aya,kawai dai halitta ta ce hakan muka haษ—u da maryam a kan hanya haushi kamar ya kashe ta ta bugeni ta wuce.

 Nima ko kallonta banyi ba na yi wucewa ta saboda bana son abinda zai ฦ™ara haษ—ani dasu,don tun dukan dana yi wa Salimat yanzu na karษ“arwa kaina ฦดanci don ko gani na ta yi canja hanya take.
tun daga nesa ya kafamin idanuwansa kamar zai cinyeni,a kunyace na ฦ™arasa kusa dashi na gaishesa,amman sai da na yi gaisuwar tafi sau biyu sannan ya dawo cikin hayyacinsa,ya shafa gashin kansa ya kalleni sosai sannan ya ce"gaskiya Basma Allah ya tsaraki sosai yadda ki ka san wata tauraruwa,a gaskiya na yi dacen matar aure,ga addini,ga kunya,ga ฦ™yau,ga ladabi da biyayya,gaskiya na zama autan mata wallahi.

ฦณar dariya na yi cikin kunya na juyar da fuskara gefe ya ce"au rowar ganin ฦ™yaฦ™ฦ™yawar fuskar taki ki ke? gaskiya ni dai ki juyo idan baki juyo ba kuka zanyi".ya faษ—i hakan cikin shagwaษ“a kamar wani yaron goye.

Hirarmu mai daษ—i muka fara anan ne na ke sanar dashi tafiya ta maiduguri,wani irin faษ—uwar gaba yaji ya kalleni idanuwansa taf da hawaye ya ce"yansu Basma sai ki kama hanya ki tafi har maiduguri ai is too easy wallahi yadda rayuwar nan ta zama wata iri"?.ya faษ—i hakan yana kallon na sosai kamar zai cinye ni.

 Tausayi sosai ya bani don daman nasan dole za'ayi haka,amman babu yadda zanyi don bana son dama ta ta kufcemin addu'ar dana daษ—e inayi akan mahaifina Allah amsa,nuna masa na yi babu yadda zanyi ne kuma ba daษ—ewa zanyi ba.

Ranar har ganin mama Aliyu ya yi akan maganar mama ta rarrashesa sosai ta nuna masa muhimmancin hakan tunda yanzu na kusa aure.

Babu yadda ya iya dole ya haฦ™ura ya cigaba da yimin addu'ar fatan zuwa lafiya da dawowa lafiya.




*****
"Yarima aฦ™wai hanyoyi da dama da za'a gane wannan yarinyar a duk inda take,sai dai inason ka ฦ™wantar da hankalinka don Allah,ka rage wannan tunanin ka ji".


ษ—agawa fulani kai ya yi alamar zai daina,yana son matar sosai don tana fahimtarsa aduk halin daya shiga,amman ya rasa me yasa mahaifiyarsa ba ta nuna kulawarta aduk wata damuwarsa,damuwarta dai ita ce damuwa, ko da ma cen  Sarauniya jidda macece mai son kanta sosai balle yanzu da ta ฦ™ara bunฦ™asa.


Ranar yana ษ“angarensa ya fito daga wanka kenan ษ—aure da tawul,sai ga fulani ta shigo ษ—akin suka gaisa ta ce"yauwa ka yi sauri ka shirya k yi baฦ™i"?.ษ—an murmushi ya yi sannan ya ce "to".

yana gama shiryawa cikin kayan meetings ษ—insa coart ce fara da kuma wando baฦ™i,ya riฦ™e necktail ษ—in a hannu ba tare daya saka ba.wani irin ฦ™yau ya yi sosai kamar ka sacesa.

Gaisawa sukayi da mutanen sannan fulani ta gabatar dasu"waษ—anan masu zane ne na kawo maka daga ฦ™asashe da dama duk irun zanen da mutum ya ke so suna zana wa,wala na mutum ko na wani abin daban".

kallonta ya yi sosai sannan ya matsa kusa da masu zanen ya rufe idanuwansa ya fara siffanta musu yadda Basma take.

Su kuwa suna ta baje fasaharsu kamar ba gobe,suna gamawa ya buษ—e fuskarsa sosai akan zanen,na farko sam baiyi kama da fuskar Basma ba,amman na biyun yana ษ—ora idanuwansa kan hoton yaga Basma ras acikin hoton kamar za ta yi magana.


Da sauri ya rungume Fulani yana nuna mata zanen wanda ya yi dai dai da hoton fuskar Basma,ai kuwa a ranar Fulani ta baza hotunan  sosai.

"Hmm Batul wannan yarinyar fa da ake cigiya na santa".inji cewar Hajiya Tani.

"Ai kuwa Tani wannan yarinyar duk wanda ya nemo duk inda take to tabbas babu shi babu talauci".ฦดar dariya Hajiya Tani ta yi sannan ta tashi ta ce "to ni bari in tafi amman gobe zanzo".bata jira abinda Batul zata ce ba ta fita da saurinta.


A gidansa ta samesa ko sallama bata yi ba,mahaifin Basma ya ษ—ago ฦ™yawawan idanuwansa ya kalleta sannan ya ce"Tani ban hanaki zuwa gidannan ba"?.bata kula saba again sai kawai ta fara gaya masa ai ana neman ฦดarsa Basma a masarautar ฦ™aisa.


Da sauri ya tashi ya kalleta sannan ya yi wata dariya ya ce"tabbas talaucin dana ke ciki a yanzu yazo ฦ™arshe,ashe yarinyar dana ke wulaฦ™antawa ita ce silar arziฦ™ina?Allah na gode maka.


Har masarautar ฦ™aisa yaje tafiyar ฦ™wana har uku a mota,yana zuwa ya shine mahaifin yarinyar nan da ake nema,ai kuwa babu ษ“ata lokaci aka kaisa ษ“angaren Fulani don ta ce bata yi shamaki da duk wanda zaizo akan maganar wannan yarinyar ba.


Sosai ta yi murna amnan cikin lokaci ฦ™anฦ™ani ta haษ—e fuska ta tashi tana zagaye a ษ—akin ta kallesa sosai,sannan ta ษ—akko wani ษ—an ฦ™aramin aฦ™wati.ta wannan aฦ™watin kuษ—ine acikinsa ayanzu ba anjima ba za'a ษ—aurawa ฦดarka aure da kuma ษ—ana Yarima."

kamar saukar aradu haka yaji maganar amman cikin dakiya ya amsa mata da to,ai kuwa a ranar aka ษ—aura wannan auren,babu sanin ango da amarya,kai hatta Sarauniya Jidda babu saninta a ciki.




*Caษ“ษ“ijan ana wata ga wata kun san ba ฦ™aramin bidiri za a yi a wannan littafin ba*

*tabbas aฦ™wai chaฦ™wakiya sosai acikinsa*


*ku biyoni don jin yadda littafi na ukunsa dana huษ—unsa zai kasance*


insha Allah anan zan tsaya a free page,zan fara payment kada ki bari a baki labari wannan littafin ban zafafa kuษ—insa ba akan farashi mai rahusa 200 wato naira ษ—ari biyu ne kacal complete ษ—insa katin mtn ki ta acc.

Duk mai son cigabansa wato complete ya yi min magana ta wannan number๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป


07068606171
Ummu maher(miss green)

amman ta whatsapp zakayi min magana.



*Miss green ce*

Post a Comment

0 Comments