*SIRRINA*
*_Khadmah K_shitu🦋_*
_FREE BOOK_
*[2023]*
_Wannan littafin sadaukarwa ne gare ki lishat oum neehal, ina miki fatan Alkhairi._
Ina miƙo gaisuwa ta gare ku Lailat Abdullahi, Gimbiyar AMB, Princess Khadija,Sarauniyar _Jarumai,Nanakhadii duk ina muku fatan Alkhairi._
*_ƊANƊANO_*
*BISMILLAHIR RAHMANUR RAHIM*
Kallo ɗaya Zaka Mata kasan ba chikakkiyar mutum bace! Tsaye take riƙe da madubin tsafin ta, tana hango Yanda Sahash Ke kokarin ƙona Mata fuska duk ta Hada zufa, Wani nurmushi ne ya subuce Mata ta shafo gefen fuskar ta, tare da zama Bisa makeken Gadon ta, Madubin Nata ta ajiye ta nufi ban daki, wanka ta shiga Bata jima ba ta fito sanye da wata Riga Mai Fadi da Alama rigar wanka Ce, gashin ta ta Fara tsanewa, kafin ta shafa Wani Mai Baƙi sai ga gashin ya bushe tana kammala shafa Mayuka kala-kala a gashin, ta Saka wata doguwar Riga milk Kamar gown ta sha adon zinarai, sannan ta ɗauko alkyabba maroon ta Saka Daga Bayan doguwar rigar Na Ja ƙasa.
Tun da ta nufi hanyar fada bayi Ke zubewa cikin tsananin girmamawa Suna gaishe ta, Daga hannu take yi tare da sakar musu murmushi Har ta karasa fadar ba tare da Wani yayi yunkurin yi Mata iso ba ta shige kai tsaye, zaune ta Samu mahaifin Nata Bisa kujera ya hakimce Yana sakar Mata tsadadden murmushi, risinawa tayi ta gaishe sa ya amsa cikin tsatsar kulawa kafin yace “Yake wannan wannan kyakykyawar gimbiyar, Ko akwai abun da kike bukata gurin mahaifin ki?” Dago bulalen idanuwan ta tayi, cikin shagwa‘ba tace "Mai martaba Ina so in fita yawo Kuma nida Risha Kawai Bana son Wani ya buyo mu." Ƴar dariya yayi cike da ƙaunar Yar tasa yace "Toh shike nan Amma Ku Kula." cikin murna ta sumbaci goshin sa, ta fice da sauri sashen ta ta koma ta Kira Sunan Risha Sai gata ta bayyana cikin ladabi ta durkusa, tare da Fadin “Ranki ya Dade umarnin ki nake Kira.” "Ki shirya ina so zamu fita zaga gari yanzu". Cikin girmamawa ta Kuma Faɗin "Ai ranki ya Dade Yanzu ma a shirya nake zamu Iya tafiya, in Har kina bukatar Hakan." Tana Gama Fadin haka Aliya ta fito, Ita Kuma ta biyo ta a Baya Wani Farin doki ne ajiye dai-dai bakin sashen Nata, Sai Wani Farin Shima Dan Dai Bai kai Na gimbiyar ba Aliya ta Hau Nata sannan Risha ma ta Hau, cikin sauri fadawan ta suka taso ta Daga musu hannu, Risha tace "Gimbiya Bata buk’atar rakiyar Kowa". Da sauri suka Bata hanya cikin girmamawa, Daga haka suka Fara tafiya.
_ƘASAR YALAZ_
Ƙasar yalaz ƙasa ce da ta kasance ƙasar mayu, sannnan ƙasar tana da masarautu guda ukku Masarautar Manaaj itace babbar masarauta mai ɗauke da ɗunbin tarihi, sun kasan ce suna da yalwar arziƙi, babu ruwan wani da wani kowa na rayuwa cikin salama mafi akasarin mayun masarautar suna da ƙarfin sihiri sosai, uwa uba kyawu ko wane maye yana chanza suffa, zuwa kyakykyawar suffa saidai yawancin su ƙwayar idanun su blue ce ko yellow sannnan yanayin tafiyar su a lanƙwashe zai tabbatar maka da ba chikakkun mutane bane, sun kasance suna bautawa wani gunki da suke kira da Abin bauta Mihar sannan ga baki ɗaya mayun ɗai-ɗaikun su ne, ke shan jini domin kaso tamanin cikin ɗari basa sha, suna da adalin sarki kuma jarumi jajirtacce, sarki Zahir yana gudanar da mulki cikin adalci da kuma izzar sarauta matan sa biyu Sarauniya sarah ita ce uwar gida sai Sarauniya Kunjam ,kunjam tana da yara mata biyu Sahash sai Sanam sanam nada shekara huɗu aka haifi Aliyaa, tun asali sarki zahir yana zaune da sarah ne, mace mai kirki ga tsananin kyawu Sarah tana da wani matsanancim kyau mai natsuwa tana da manyan idanuwa masu ɗauke da ƙwaya blue, idanuwan ta na matuƙar tafiya da zuciyar mutane.
Sarki zahir ya aure ta ne a dalilin Aminin mahaifin sa Tsoho Arar tun da suka yi aure bata taɓa haihuwa ba hakan yasan ya bayan shekara bakwai aminin sa yayi masa tayin ɗiyar sa kunjam babu ɓata lokaci ya auri kunjam, duk da auren kunjam da yayi bai daina nuna wa Sarauniya Sarah tsananin ƙaunar sa gare ta ba, hakan yasa kunjam ta kasance cikin matsananciyar tsanar Sarah, kullum a koda yaushe burin ta taga bayan sarah sannan taci buri ta samu haihuwar ɗa namiji da zai gaji sarki sai dai abun baƙin cikin ta haifi mace, sai dai tun yarinyar ta sahash nada shekaru biyu ta samu wani cikin farin ciki gun ta ba'a magana, sai dai anyi rashin sa'a a wannan karon ma mace ce ta haifa, jin daɗin ta ɗaya mai martaba na nuna ƙaunar sa gare su, hakan yasa ta rage damuwa sai dai fargabar ta ɗaya sarah ta haifi namiji, ana cikin haka sanam ƴar ta takai shekara biyu, kwatsam sai ga ciki ya bayyanar ma sarah baƙin ciki da tashin hankali kamar kunjam tayi hauka, gashi sarki ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗaura kan sarah da cikin ta kuma ƙarara yake nuna hakan daga lokacin wutar ƙiyayyar sarah ta ƙara kunnuwa zuciyar kunjam har ta yaran ta ta hana su koda shiga sashen sarah, tun lokacin da Sarah ta haifi yarinyar ta Mai martaba ya ɗauki ƙauna da soyayyar duniya ya ɗaura kan aliyaa.
A wannan lokacin kunjam tana fitowa ƙarara ta nuna ƙiyayyar ta gare su, tsoron ta ɗaya sarki dan tasan shi ɗin ba kanwar lasa bane,hakan yasa take shakkar ƙuntatawa Sarah, tun tasowar Aliyaa ƴan uwan ta ke nuna mata tsananin ƙiyayya hakan yasa ta ja jikin ta da su dan kwata-kwata bata zuwa koda inda suke, ita Allah ya yita tun tasowar ta tana ƙaunar rawa dan ta iya sosai, gefe ɗaya mahaifin ta na koyar da ita faɗa a kuma samun ƙarfin ikoh duk da dama tana da wani irin ikoh mai ban mamaki, gashi ta zarce mahaifiyar a kyau an abun ya haɗe mata, ga uwa ga uba hakan yasa su sahash da kunjam kulkum suke ƙoƙarin kai farmaki ga kyakykyawar fuskar ta, kuma basa ita ɓoye matsananciyar ƙiyayyar su gare ta da mahaifiyar ta a koda yaushe tana zuwa gun kakan ta tsoho arar yana ƙara mas sihiri da kuma kariya, shi yasa aka gaza cin galaba kanta.
Sannan Aliyaa na da wani irin ƙarfin iko na wucin gaban misali, kowa na alaƙanta hakan ne sanadin Kakan ta tsoho ARAR, sannan kowa ya san da cewa babu mayu daban-daban masu sheɗanci da tsananin ƙarfin iko kamar na masarautar manaaj, wannan dalilin ya sanya kowa ke burin mallakar masarautar.
Masarauta ta biyu ita ce masarautar Nahaar, masaraurtar nahaar masarauta ce mai ɗauke da mayu kala-kala sannan suna da yalwar arziƙi da ƙarfin iko, sai dai mayun ƙasar suna shan jini suna da wani azzalumin sarki wato sarki Gobrar ga baki ɗaya bashi da burin da ya wuce ya mallaki ga baki ɗaya masarautun da masarautar manaaj da ta Hizaar ya haɗe ya chigaba da mulkar su baki ɗaya gashi kuma yana da ƙarfin iko sai dai bai ma ko kama ƙafar, sarki zahir ba.
Hakan yasa a koda yaushe ya cikin tada fitin-tinu, sai dai duk makircin sa yana shakkar sarki zahir yaran sa biyu, Karan Sai Arman su kan su yaran basa ji a koda yaushe suna zaluntar mayun dake ƙar-ƙarshin su.
Masarauta ta ukku ita ce masarautar Hizaar, masarautar hizaar masarauta mai ɗauke da tarihi, mayun sun kasance masu ƙarfin ikoh, sannan suna da ƙarfin iko da arziki suma, saidai masarautar bata kai sauran ba , suna da sarki Ahal kwata-kwata bashi da maƙiyi kamar sarki zahir bashi da lokacin yin wani mulki, a koda yaushe yana ƙoƙarin kaiwa sarki zahir farmaki kwata-kwata baya ƙaunar sa, sabo da a da yaso sarauniya sarah amma ƙememe tsoho Arar ya hanashi auren ta, ya bawa sarki zahir.
Yana da makirar mata da yara biyu duka maza Razan sai Tazaan yaran sa azzalumai ne sosai sannan mahaifiyar su kullum cikin makirci take wa kishiyar ta dan bata taɓa haihuwa ba.
Duk masarautun ukku ko wace masarauta nada tambarin ta, MANAAJ suna da tambari a hannun su kafin a kai wuyan hannu An rubuta manaaj, kowa dake masarautar yana da shi. NAHAAR suna da tambarin su a tafin hannu, kowa dake cikin masarautar yana ɗauke da tambarin. HIZAAR Suna ɗauke da tambarin su ne a bayan wuya, kuma kowa dake masarautar yana da tambarin.
K_shitu🦋
*SIRRINA*
*_K_SHITU🦋_*
*_SHAFI NA ƊAYA DA NA BIYU._*
*P 1-2*
Gudu suke yi na fitar hankali cikin baƙin dajin, babu abun da kake ji sai kukan tsun-tsaye da na namun dawa. ja sukai suka tsaya dan babu hanya, ruwan dake gaban su tsayin shi yafi ƙarfin suce zasu zagayo, saukowa gimbiya Aliyaa tayi daga bisa dokinta, hakan yasa itama Risha ta sauko. wata bukka suka nufa daga chan gefen dama sai dai a mamakin su bukkar a buɗe take, bayan sun san ko da tsoho Arar yazo a koda yaushe rufe take, babu alamun wani a ciki, hakan ya suka ƙarasa sai dai da alama kamar yana ciki.
Tsayawa Risha tayi ita kuma ta shige ciki, zaune ta tarar dashi yana ta faman bincike-bincike, cikin sauri ta ƙaraso tare da faɗin "Ranka ya daɗe! lafiya kazo a wannan lokacin. bayan nasan sai zamu haɗu ko wani abu ya taso a masarauta kake zuwa, shin ko da akwai wani muhimmin abu dake faruwa ne?"
Cikin damuwa ya dube ta sannan ya furzar da iska yace "Ina kike ƙoƙarin zuwa baki sanar dani ba, ko akwai wani abu dake faruwa dake ne?" da mamaki take ƙare masa kallo cikin nuna Ƴar damuwa tace;
"Babu Abun da yake Faruwa ina so naje nayi wani bincike ne shi yasa".
"Bincike kuma Aliya! akan me?"
"Babu komai ina so na samu wani ƙarfin iko ne nagani ta yadda ake samun sa a wani littafi ko akwai wani abu da ba dai-dai ba." Numfashi yaja yace,
"A safiyar yau wani yayi yunƙurin cutar dake! ko akwai wani baƙon abu da kika gani?" jim tayi kafin tace gaskiya babu kowa sai dai Sahash! ita kaɗai ce tayi yunƙurin ƙona mun fuska". "Aliya! kuma shine baki sanar dani ba?"
"Kayi haƙuri gani nayi ba sabon al'amari bane a garemu."
Jin-jina kai kurum yayi, cikin sigar gargaɗi ya fara mata magana "Ki sani a yau da ban zo nan na dakatar dake ba, da kin rasa dukkanin ƙarfin ikon da kike dashi! wannan littafin baki yi tunani a ina aka same shi ba, baki yi mamakin ganin shi kwatsam a ɗakin ki ba. baki tsoron abun da zai je ya dawo. A cikin y'an kwanakin nan kina wasu abubuwa na gaza gane kanki, ki sani akwai manya-manyan matsalolin dake shirin kunno kai a lokacin da ba ayi zato ba! Mahaifiyar ki Tana cikin matsala sai dai a iya bincike na ban fahimci komai ba, ya kamata kiyi taka tsan-tsan zan saka miki hodar iko a madubin tsafin ki. dan a lokuta da dama idan kina kallon sahash tana ganewa, ya zame miki dole ki kiyaye dan akwai mafarkin da nake yawaita yi akan Naz... masarautar Nahaar akwai wani ɓoyayyen tuggu da suke shiryawa Ki sani kece kece! Aliya kece mgajiyar masarautar manaaj sarki zahir mahaifin ki ya faɗi hakan a gaban kowa, hakan yasa maƙiya suka taso ki gaba ana burin ganin bayan ki". Numfashi ta sauke a hankali jin ya ambaci mahaifiyar ta, sannan tace "Ranka ya daɗe ka ce Naz baka ƙarasa ba" "ina so nace nahaar ne." gyaɗa kai kawai tayi, alamar gamsuwa Sun jima suna tattaunawa kafin daga bisani ya saka mata farar hodar ikon. har zasu rabu ya kira sunan ta "Aliya! ki kiyaye kisani a koda yaushe ba sahash kaɗai ke ƙoƙarin ƙona miki fuska ba, sa'a kawi suke neme kuma jin san cewa babu magajin da zai iya gadon ko wace masarauta in har yan da wata tawaya, ki kiyaye a koda yaushe ana burin ganin bayan ki."
jin-jina kai kawai tayi sanan suka rabu...
Cikin tsananin ɓacin rai take farfasa duk abun da ta gani a ɗakinta, lokaci ɗaya ta fita a hayyacin ta hannuwan ta duk ta tsattsage ga jini na zuba wata kwalba ta ɗauka, ta buga da ƙasa nan take ta tarwatse. jin ana buga ƙofar ya sata nufar ƙofar cikin wani ɓacin ran, sai dai kafin ta ƙarasa ta taka kwalbar da ta fasa, zubewa tayi ƙasa jin wani raɗaɗi na ratsa ta.
Kifewa tayi fasassun kwalaben suka soki jikinta, wani irin ihu tayi hakan yasa Sarauniya kunjam da ke bakin ƙofar ta faɗo ɗakin jikinta har tsuma yake, a gigice ta ɗaga duka hannayenta sama ta ɗauke ta sama, sannan fa jefar da ita kan gado. cikin gigita take faɗin "Sanam! mai kike son mayar da kanki? me ya sameki ko Karan ne?" lokaci ɗaya ta jero mata waɗan nan tambayoyin waɗan da suke barazanar fasa zuciyar Sanam ɗin. cikin ƙaraji da mugun kishi ta fara magana "Na rantse da wannan duniyar tamu! bazan taɓa ƙyale Karan da Sahash ba dole na ɗauki mummunar fansa akan cin amanar da suka aikata min. ya zama dole su biya abin da suka aikata! Ni sanam in har na barsu haka ni ba jinin Masarautar zahir bace!"..... Da wani irin mamaki take duban ta wanda ya kasa ɓoyuwa kwata-kwata sai duban sanam ɗin take wacce ita kuma, wani matsanancin ɓacin rai ne kwanche a kan fuskar ta wanda ya bayyana zata iya aikata komai a halin yanzu dan tana da muguwar zuciya! Ajiyar zuciya sarauniya kunjam ta sauke dan tasan bata da kalmomin da zata faɗawa sanam zuciyar ta tayi sanyi, dan a halin yanzu ta fara karaya da al’amarin su daga sahash ɗin har Sanam ko waccen su idon ta ya rufe mulki take buƙata da ƙarfin ikoh. Sahash idon ta yafi na kowa rufewa tsabar kwaɗayin mulki da ƙarfin iko, jiya sun tattauna sosai da sahash tayi mata bayani akan yanda take ƙoƙarin mallakar karan, dan samu wani ƙarfin iko a tattare dashi saidai bata yi tunanin sheɗancin ya kai haka, sai yanzu zuciyar ta ke hararo mata abubuwan da suka shuɗe a shekarun baya, da waɗan da take a raye abubuwan suka faru da waɗan da mahaifin ta ya sanar da ita tasan itace ta ɗaura su akan wannan turbar amma yanzu ta fara sarewa, tashi tayi ta fice daga ɗakin tana girgiza kai dole ta dakatar da wannan wutar ƙiyayyar da ta hango tana ruruwa a zuƙatan y'ay'ayen nata. ita kuwa tana ganin mahaifiyarta, ta fita bata tausashe ta ba kuma bata nuna ɓacin ranta ba, taji ɓacin ran nata ya ƙara daɗuwa hakan yasa taji ƙarin ƙiyayyar karan ɗin da sahash alƙawari ne wannan dole su biya abun da suka aikata.
MASARAUTAR HIZAAR
Kai kawo kawai take yi a cikin ɗakinta, hankalinta idan yayi dubu to ya tashi mai ke shirin faruwa da Karan ɗinta,....Dole ta dakatar da faruwar wannan mummunan al'amarin, ba zai taɓa yuwa ace ɗan da taci buri a kan sa, ya rasa dukkanin ƙarfin ikon sa wanda ya gada daga gun mahaifan ta, bazai taɓa yuwa ba dan bata taɓa neman abu ta rasa ba, kuma bata taɓa ƙin yin nasara akan abun da take so ba cikin ƙaraji take faɗin "Ya zama dole ka zama ma-mallakin masarautun nan guda ukku! ba zan iya juriyar ganin ba kai ne magajin, masarautar HIZAAR da MANAAJ da kuma NAHAAR! Dole ka rabu da Sahash wannan alƙawari na ne ba zai taɓa tafiya a banza ba dole ka mallaki dukkan ƙarfin ikon da yake da matsanancin ƙarfi, dole nayi zarra! cikin mayun YALAZ da babu wata sarauniya da ta kai ni ƙarfin izza da mashahurin ƙarfin ikon da ya zarce na Riyaad da Nazaar! dole na zama fitacciya!" Zama tayi tana mai kallon tafin hannun ta, ganin karan ɗin ne ya sata sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi wata 'yar ƙaramar aba ce mai kama da ƙarau-rawa tayi ƙara sai gashi ya bayyana.....Matashin saurayi ne da a ƙalla zai kai shekaru, Ashirin da takwas (28) cikin izza ya ƙaraso ya zauna, a fusace ta fara magana;
"Karan! Kai baka isa ka karya ƙudurin da na ɗauka ba. tsawon shekaru aru-aru nayi Alƙawari ko Kunjam bata isa ta dakatar dani ba!" wani ƙasaitaccen murmushi ya saki, cikin ƙasaita yake faɗin; "Sarauniyar manaaj! kin san waye karan! gaba da baya, babu yanda za'ayi na yi wannan shirin kwata-kwata zuciya ta bata gaban sanam ɗin ko sahash dukkanin su ina so nayi amfani dasu ne, dan cimma wani ƙuduri na! hasali ma ni wacce nake ƙauna kuma nake burin mallaka, ta arziƙi ko ta ƙarfin izza ia ce Aliyaa! a lokacin da sarki yayi wani zama na samu sauraron maganar da yayi akan shi aliya ce yake so ta zama sarauniyar manaaj.....Na ɗauki alwashin mayar daje sarauniyar da .ba'a taɓa samun irin ta ba a YALAZ baki ɗaya zamu kasance fitattu."
.
Gudu take yi kan dokinta hankali kwanche. da ka ganta ka san tana cikin nishaɗi. sahash ke nan Tsayawa tayi dai-dai wani kogo, shigewa cikin kogon tayi da baya-baya, wani ƙaton halitta ne zaune baƙiƙ-ƙirin bashi da kyan gani ko kaɗan.......
30-4-2023
_Ma sha Allah....A gaskiya naji daɗin ƙaunar ku da karar da kuka nuna min A kan wannan book ɗin nawa🥰🌛._
Ga masu buƙatar group su min mgn.
09117440993
_INA MASU BUƘATAR FARA RUBUTUN LITTAFI HAUSA? TOH…_
*AMBITIOUS WRITER FORUM* _SUN SHIRYA TSAF DON ƊAUKAR SABABBIN MARUBUTA GA WANDA YA SHIRYA YA TUNTUƁEMU 09117440993_
_#SIRRINA....🦋free-book 2023; haƙƙin mallakar khadmah ne ban yarda wani ko wata su chanza mu littafi na ta ko wace siga ba tare da izini na ba, yin hakan kuskure ne ƴan youtube ku kiyaye._
_In har naji ruwan comments yau zan k'ara sakin update❤️🌛._
*ALLAH KA GAFARTA MA IYAYEN MU DA KAKANINMU.*
_#Khadmah K_shitu🦋_
*SIRRINA*
_*K_SHITU🦋*_
*_SHAFI NA UKKU DA NA HUƊU._*
*P 3-4*
Wata dariya ya fara marar dad’in sauraro ko ina na amsawa cikin kogon, kanta a k’asa ta fara ƙoƙarin magana. tsagaita dariyar yayi sannan ya dakatar da ita, ta hanyar ɗaga mata hannu da faɗin “Ya isa! ba sai kinyi bayani ba komai ya faru a kan idanuna Dan haka ga wannan tashi ki tafi”. miƙa mata wata 'yar wuƙa yayi, ta karɓa tare da ƙara duƙar da kanta alamar girma-mawa, ƙara bushewa da wata dariyar yayi, ita kuma ta fice fuskar ta cike da annuri, babu abin da take so face ta ganta gaban mahaifiyarta.Cikin nishaɗi ta cigaba da gudu bisa dokinta, ƙarasowar ta ƙofar shiga manaaj ɗin ne ya sata tsayawa, ba tare da ta sauko daga kan dokin ba, tayi girgiza ta ɓace sai gata, gaban ɓangarenta.
Saukowa tayi kawai ta nufi ɓangaren sarauniya kunjam, babu wani naiman iso ta bayyana gabanta.
Ganin da tayi tana sassarfa ita kaɗai ne ya bata mamaki, mai kuma ta tuna oho sai ta fara dariya. sai da tayi mai isarta kafin tayi shiru.
Haɗe fuska tayi ba tare da tace komai ba ta zauna bisa ɗaya daga cikin kujerun zinaran dake a ɗakin, Ƙafarta ɗaya ta ɗaura bisa ɗaya ta fara magana cikin isa da gadara.
"Sahash! duk yanda nake kwaɗayin sarautar Manaaj ina tsoron hazarin dake tattare da masarautar. bana so ki kasance ɗaya daga cikin sheɗanun mayun da za'a shafe labarin su!".
Cikin mamaki take kallon ta, sai kuma tayi wani ƙayataccen murmushi tace “Sarauniya! yau kece kike faɗin waɗan nan maganganun da kanki, gaskiya na kasa yarda Bayan nasn kece mutum ta farko da ta fara kwaɗaita mun so da kuma ƙaunar sarautar manaaj.” Zuba mata rikitattun idanuna tayi, ta kasa cewa komai.
"Ni sahash nayi alƙawarin hawa kujerar mulkin sahash! ko ta wace iriyar hanya"
Ajiyar zuciya a sauke sannan ta dubi sahash ɗin, dan yanzu ƙwarin guiwar ta ya fara dawowa.
"Ya kamata kiyi aka tsan-tsan da Sanam domin ita ba mulkin ke gabanta ba, Karan shine wanda afi ƙauna! kuma take son ayuwa dashi me yasa kike ƙoƙarin mallake sa? ki sani abin da kike yunƙurin aikatawa ka iya janyo wata fitina a daban, dan haka ki kiyaye."
Cikin nuna halin ko'in kula tace "Bana yunƙurin raba su kawai ina buƙatar samun wani ƙarfin iko tattare dashi ne, idan yaso daga bisani na rabu dashi....amma a halin yanzu bazan iya barin sa ba."
ta buɗe baki za tayi magana ta tari numfashinta, ta hanyar faɗin "Na sani akwai haɗari a masarautar hizaar amma babu abunda ya same ni a yanzu haka nasan ya san da shiri na amma, bai san taƙamai-mai a wace hanya zan farmake sa ba, dan haka ki zuba ido. na barki lafiya".
Tana ƙarasa maganarta ta fice, da wani mugun murmushi akan fuskar ta.
Jin bayanin da sahash ɗin tayi mata ne ya saka ta, saurin ɓacewa dan samu sanam.
Bayyanar ta ke da wuya taci karo a abin da yayi matuƙar razana ta, zaune ta iske ta zaman daɓas zamn ƴan bori ga wata wus a gaban a idanuwan ta a rufe ta buɗe tafukan hannayenta, waɗan da suke ɗauke da wani abu kamar kacha.
A kiɗime ta fito da dogon harshenta, ta fara ƙoƙarin saka shi a wutar dan kashe ta baki ɗaya, gaba ɗaya ta kasa tayi hakan sau ukku amma da ta kai harshen sai ya kasa shiga, ganin hakan yasa, cikin ƙaraji tace "Sanam ki dakatar da wannan baƙin tsafin!" ko gezau bata yi ba a fusace kuma faɗin “Nace ki dakatar ko!” wannan karon cikin tsawa ta ƙarasa ta ƙarasa maganar, har fuskarta ta fara sauya launi, abun ka ga ainahin farar fata.
Sai da taja kusan mintuna goma a haka, kafin ta buɗe idanunta ta sauje su kan sarauniya kunjam da duk, tsantsar ɓacin ranta ya gama bayyana. miƙewa tayi ba tare da tace komai ba wutar ta mutu murus.
A fusace ta ɗaga hannu da niyyar wanke ta da mari, sai dai kafin ta kai hannunta a kan fuskarta, hannun ya daskare.
Tayi ƙoƙari tayi motsi da hannun amma hakan a gaza faruwa, zama tayi bisa kujera sannan ta murza 'yan yatsun ta, sai ga hannun ya saki, cikin wani irin alhini ta dube ta, tare da faɗin,
"Sanaaam!" murmushi ta saki jin yanda taja ƙarshen sunan kafin itam tace,
"Na'aaaam!"
Bata sake sarewa da lamarin sanam ɗin ba, sai da tace,
"Zan iya keɓewa ni kaɗai ba tare da wani ya dame ni ba?"
Jin tayi shiru taƙi magana ya sanya kawai ta ɓace, ganin idan ta zauna babi abinda zata amfanarwa kanta yasa ita ta ɓace cikin fusata.
MASARAUTAR HIZAAR
Wani baƙin hayaƙi ne ya gauraye dakinta, babu abun da kake ji sai sanbatunsu, Iska mai tsananin ƙarfi ce ta fara ɓannatar da abubuwa, kafin wani haske mai yawa ya bayyana duƙewa suka yi tare da kare idanunsu,dariya ce ta fara tashi mai ban tsoro hakan ya sanya su zubewa ƙasa......
Kuyi manage da wannan, in sha Allahu naji ƙorafin ku zan ƙara yawan typing ɗin.
Khadija Muhammad🦋
Ambitious writers asso...
Duk wanda yake jin daɗin book ɗin yayi sharing🙌
*SIRRINA*
_*K_SHITU🦋*_
AMBITIOUS WRITERS ASSOCIATION📚✍️
_Wannan littafin sadaukarwa ne gare ki *OUM NEEHAL* Ina miki fatan alkhairi da fatan nasarori masu yawa da albarka much luv nd kind care, may Allah reward you with the best nd highest rank in this world, and jannatul_firdaus❤️🌛 *SARAUNIYAR JARUMAI* gaisuwarki ta musamman ce ke ɗin jaruma ce, kuma jajirtacciya fasihiya, mai tarin alkhairi thank you so, much for you kindness, nd prayers. Allah ya taimake ku baki ɗaya. may Allah continue guiding you for ever! dearist.❤️🌛❤️🦋_
*_SHAFI NA BIYAR DA NA SHIDDA._*
*P 5-6*
Wata mummunar halitta ce ta bayyana marar kyan gani, sai da ɗakin ya girgiza basu ɗauki lokaci a haka ba, ta sakar musu wani farin tulu, ta ɓace.....A hanzarce suka shiga rige-rigen ɗauka dan kowa cikinsu yana so ya riga ɗauka, a hanzarce sarauniya Halsha tayi nasarar ɗaukewa, tsuke fuska mai martaba Ahal yayi ya dubi sarauniya halsha, yace "Ya kike ƙoƙarin riƙewa? ai nine wanda ya kamata ki ba ai?".
Wani kallon ukku saura kwata ta watsa masa ta kuma ja dogon tsaki, tace "Kana tunanin zan baka wannan tulun kenan toh kayi kuskure! yaushe ne ma ka fara dawowa natsuwarka kwata-kwata na lura, a da kafi son mu ƙare a hizaar kawai, babu wani ƙarfin iko da DAULA ta musamman to gwara da kayi gaggawar dawowa hayyacinka, duk ƙiyayyar da kake ikirarin kana yiwa zahir ta tsaya a laɓɓa kawai ke nan?". Cikin mamaki yake kallonta kafin yace,
"Yanzu kina nufin wannan masarautar babu DAULA Kenan ya kike so ayi yanzu?".
A kufule ta kuma duban sa tace, "Yanzu Wane shahararren ƙarfin iko! kake dashi na kece raini? kasan yan da Manaaj suke da mayu masu ƙarfin tsafi, bugu da ƙari har yanzu ba'a samu chigaba ba, akan samun sanin wasu duniyoyin mu a koda yaushe a YALAZ zamu ƙare, ka san shahararru kuma ƙwararrun sheɗanun mayu masu ƙarfin sihirin da ya wuce dukkan misali, sun fito ne daga manaaj! AZLA, NAZAAN, RIYAAD, duk daga manaaj aka same su kuma tsatson su zahir, ƙarfin ikon su ka taɓa jin irin shi?".
Cikin samun ƙwarin guiwa yace "A gaskiya babu."
Tafa hannuwanta tayi, dan abun da ta riga ta san zai faru kenan.
"Gaskiya ni bana so ikon mu ya ƙi, kai shaharar da za'a shafe tarihin mu, nafi so mu gagari kowa, masarautun duka su dawo ƙarƙashin ikon mu."
Dariya yayi yace "Shi yasa nake ƙara ƙaunarki a koda yaushe, dan ke ta daban ce kin fini kaifin tunani yanzu so nake ki faɗa min matsayar mu guda! kuma ya kamata mu a dana wannan tulun, har zuwan BAƘIN WATA na ɗaya."
Murmushi ta saki tare da faɗin.
"Yanzu nake jin ina tare da SARKIN SARAKAI amma ba da ba da ka gaza dawowa hayyacinka, kayi tunani akan makomar mulkin ka."
Dariya yayi yace, "Gaskiya ya kamata muyi, shiri na musamman."
"Hahhaha! dama kaine ba'a cikin shiri ba dan a koda yaushe ina cikin shiri, ya kamata ka kira boka filza ya ƙara maka ƙarfin iko! dan kallon nan da kake masa akwai ikuna sosai a tare da shi." tana gama faɗar haka ta fice ɗauke da tulun.
MASARAUTAR JODHAN
Tun daga farkon gate ɗin masarautar zaka fahimci masarautar suna ji da arziƙi iya arziƙi, da tarin dukiya za'a iya kiran wannan masarautar da Aljannar duniya, idan ka shigo cikin masarautar, wani babban round ne kamar na titi dan dai shi wannan yana da girma sosai kuma a jiki akwai tambarin masarautar *JODHAN* Gina-gine dogaye ne masu tsananin girma, da ka kalla kasan an baza wata aba wai ita dukiya, shuke-shuken kansu akwai wani ƙyale-ƙyale a jikin su komai ya haɗu iya haɗuwa, ɓata lokaci ne ma fasalta masarautar jodhan.
Gefen haggu na bi ganin wani titi ya mi‘ke daga gefen wani ’bangare, Wanda da ka kalla kasan akwai abun kallo iya kallo, cin karo nayi da wani katon lambu, iska mai daɗi na kaɗawa ga wasu furanni masu ƙamshi, gefe ɗaya wani sweeming pool ne, idan ka kuma matsawa zaka ga wani fili irin na ƙwallo, tsayawa nayi dan na fara tsorata da lamarin wannan masarautar, komowa nayi na shiga wani ɓangare da yafi na ko ina tsaruwa da haɗuwa wanda ya kasance a tsakiya, sau wasu ɓangarorin bi-biyu a gefen dama da haggu.
Bayi da hadimai ne kai kawai daga ƙofar fadar zuwa ɓangaren sarauniya A'isha, wacce ake kira da Ammah Ko'ina an zuba dukiya ba dai kaga abu yasha ado babu zinari ba, fadar ta ƙawatu manyan fitilun har tsoro suka kusa su bani sabo da farin su sai aka zagaye su da golden ɗin zinari, gasu da mugun faɗi da girma A.C kamar tayi magana masarautar ta kai ƙololuwar haɗuwa, fiye da duk yanda zan yi bayani na.
Wani katafaren ɗaki na kutsa kai, wanda ya kasance na Ammah wato uwar gidan sarki, kwanche take bisa makeken gadonta, kamar gawa tamkar kuma babu alamun a tattare da ita bayi ukku ne ke zaune, shigowar wani matashin saurayi sanye da ƙanan kaya a ƙalla, zai kai shekara 28 dogo fari kuma kyakykyawan gaske, kallo ɗaya zaka mishi ka fahimci bai san wata aba wai ita wahala ba.
Ƙarasowa yayi ya zaune gefen gadon, zubewa sukai suka gaishe shi, yana amsawa duk suka miƙe suka fice. Addu'a ya ara tofa mata, tausayin mahaifiyarsa yana nuƙur-ƙusar zuciyar sa amma ba zai iya aikata wani abu da ba dai-dai yau kimanin wata huɗu kenan, tunda ta kwanta bat sake tashi, ba likitoci sunyi imani da tana nan a raye dan zuciyar ta na bugawa kuma wani sa'in ƙafarta ko hannunta na motsi.
Ya kai kusan mintuna ashirin yana mata addu'o'i kafin ya tashi ya fice cikin tsananin tausayin ta, ya rasa wace ƙasa ma za'a kai ta a dace dan kusan ƙasashe sha....anje ba'a dace ba.
MASARAUTAR MANAAJ
Zaune sarauniya Sarah take tana fuskantar 'yarta, ga baki ɗaya Aliya ta bata dukkanin attention ɗinta.
"Aliya! ki riƙe wannan zoben da muhimmanci kuma ki kula dashi sosai, zai miki amfani sosai a lokacin da baki yi zato ba, mahaifiyata ce nima ta bani."
Murmushi tayi tace, "Kar ki damu da yardar abun bauta, zan yi yanda kika ce, yanzu ni zanje , majami'a."
Gyaɗa kanta tayi tare da sakar mata murmushi, ita kuma ta miƙe ta gyara zoben dake hannunta.
A hankali take tafiya cikin izza, har ta ƙarasa ɓangarenta, wata Riga mai kama da alkyabba ta ɗauka, kalar kore sosai, (army green) ta saka.
Fitowa tayi tana tafiya cikin ƙasaita, da sauri Risha ta nufo inda take ta zube ƙasa tana faɗin; "Ranki ya daɗe! ko kina buƙatar rakiya ta?"
Cikin tsadaddiyar muryarta mai cike da izza tace, "Kar ki damu zan je mujami'a ne, kuma ba zan daɗe ba." Tana gama faɗar haka ta fice, ba tare da a jira cewar Risha ba.
Haka nan taji tana sha'awar hawan wani dokinta, da ta daɗe bata hau ba.
Tun da ta nufi gun da ake ajiye dawakai, hadiman dake gurin sai zubewa suke suna kwasar gaisuwa, ita dai aikin ta murmushin nan dai ne, da ɗaga hannu. ƙarsawa tayi ta hau dokin nata har zata fara tafiya taci kawo da Sahash wacce take tsaye gabanta ta riƙe ƙugu, tana aika mata da wani rikitaccen kallo, ta wutsiyar ido ta kalle ta, abun da ya ƙara ƙular a sahash ɗin kenan, ganin ta dunfaro inda take gadan-gadan ya sata, kaucewa dan sarai tasan Aliyaa zata iya buge ta ta wuce, wani baƙin doki ita ma ta hau, tabi bayan ta a hanzarce.
Gudu take yi kan dokinta a natse, dole idan ka kalle ta ta burgeka.
Ita ma sahash ɗin da gudu take bin bayanta, basu daɗe ba suka isa, a tare suka sauko takalmanta aliya ta cire ta shige ciki ita ma tabi bayanta tana sakin wani makirin murmushi.....
Share pls❤️🌛
GASKIYA INA JIN DAƊIN CMMNTS ƊIN KU, SAN SO FISABILILLAH❤️🙌
IDAN NAJI SHARHI MAI YAWA ZAN ƘARA SAKIN UPDATE, MAI SON GROUP SAI YA MIN MAGANA.
_#Khadmah K_shitu🦋_
09117440993
*SIRRINA*
_*K_SHITU🦋*_
*_SHAFI NA BAKWAI DA NA TAKWAS._*
*P 7-8*
Tun kafin Sahash ta ida shiga wata iska mai ƙarfi ta hanata har tayi tangal-tangal zata faɗi sai kuma bata faɗi ba, komawa tayi bisan dokinta, ba tare da ta fara tafiya ba.
Mayu ne kowa na harkar gabansa, masu addu'a nayi masu gyare-gyare nayi, A natse ta ƙarasa ta fara addu'o'inta, ta kai kamar mintuna sha biyar sannan ta fito, gurin dokinta ta nufa ganin babu sahash ya sata murmushin gefen baki, babu ɓata lokaci ta fara tafiya jij-jiga dokin ya fara kamar zasu faɗi sai yai sama da ƙafafunshi na gaba ya kuma dire su ƙasa da ƙarfi, zoben da sarauniya sarah ta bata ne ya fara haske duhu ne ya mamaye gurin hatta gabanta bata iya gani. bata yi wani yunƙuri ba kawai taga ta ɓace, ita kanta tayi mamaki amma da ta tuna maganar mahaifiyarta sai kawai tayi murmushi.
Kallon ɗakinta tayi haka nan taji tana son zuwa gaishe da mai martaba, ficewa tayi ba tare da jiran iso ba ta shige kai tsaye, Kamar kullum zaune ta tarar dashi bisa kujerarsa, ganinta da yayi ne ya sashi faɗaɗa fara'arsa, ya kuma sallami mutanen dake fadar ƙarasawa tayi ta zauna, cikin shagwaɓa tace "Barka da hutawa!"
ganin yanda ta turo baki sai yayi murmushi ya kamo hannayenta, yace.
"Aliya! kina tunanin haka nan nake ƙyale sahash da kunjam? Nasan duk abin da ke faruwa MANAAJ NAHAAR HIZAAR kawai dai ina mayar da komai ba komai, kuma ina nuna ban san komai ba, ina zuba idanu ne naga ƙarshen shirin ne, Yaƙi kawai ake so a tada, dan haka ki zuba idanu zan kuma sadaukar miki da ƙarfin ikon da nike ji dasu, in har na mutu! dan dama mahaifina yasha faɗamin ni ba mai tsawan ran da zai daɗe sosai bane, amma kisan da sani kamar al'mara haka zaki ga komai, kuma matattun shaiɗanu zasu tashi za'a gwabza baƙin yaƙi na ban mamaki, a yanzu haka laɓen da sahash keyi ina kallonta amma tayi kaɗan a saurari furcina, Aliya daga yau zuwa kwanaki ukku kachal ina son koya miki yaƙi irin wanda na iya da wanda ban iya ba ma duk zan koyar da ke da ƙarfin sihiri, zakiyi baƙin tsafi yau dole! a yau,Kisan da sani cewa kece! dai sarauniyar manaaj babu wani wanda zai mulki manaaj sai ke! ki sami a koda yaushe kece abar farmaki, na san zaki bar wannan duniyar tamu na tsayin lokuta, amma dole zaki dawo ki ɗauki fansar mahaifiyarki, babu mahaluƙin da ya isa ya cutar dake in har ina numfashi, kiyi haƙuri a koda yaushe ki kasance mai kawar da kai, koda kin san abu ki nuna baki sani ba, ki ɓoye ƙarfin ikon ki, koda farmaki aka kawo miki kar kiyi saurin mayarwa da naki ƙarfin ikon! dan akwainmasu san karɓeshi duka kar kiyi kuka, sarauniya jaruma ce ba ragguwa, ki kula da fuskarki dan Idan an nemi ƙona ki ba'a yi nasara ba akwai haske! zai iya miki illah kiyi taka tsan-tsan ina sha'awar irin rayuwar da na bincika naga zaki gudanar a gaba, dan dama mulkin da za kiyi na shekara biyu ne kachal, abun buƙata a guri na shine ki chanza tsare-tsren masarautar nan da mayun cikinta!"
jikinta ya kai maƙurar sanyi bata ce komai ba sai gyaɗa kai miƙewa yayi ya ɗauko, wasu tokobbai suka fara faɗan.
Sahash na tsaye bakin ƙofar shiga fada ta bada baya, sanam ta bayyana cikin wata azama ta saki wata ƴar wuta a dogon gashin sahash ɗin, bata ji wuta a kanta ba ta dai ga gashinta yane kakkarewa, a hanzarce ta jiyo ta sauke idanunta kan sanaam wani ƙayataccen murmushibta sakar mata, tare da kashe mata ido ɗaya kafin tayi wani yunƙuri har ta ɓace.
A razane ta ɓace sai gata ɗakinta baya ta faɗa cikin wani ƙaton abu da alama bahan wanka ne, lokacin da ta kalli kanta a madubi tsananin baƙin ciki fasa mdubin tayi, da sauri ta fito a fusace dan ji take yau ko ita ko sanaam, sai dai ta duba ga baki ɗaya masarutar babu sanaam babu dalilinta, sashen mahaifiyar ta taje sosai sarauniya kunjam ta tsorata da ita, haka dai tai ta tausar ta amma tace ita ko mai martaba bai isa hana ta ɗaukar mataki ba jin ta riga da ta yanke hukunci yasa mahaifiyarta tattara zancen ta watsar gefe.
MASARAUTAR NAHAAR
Zaune yake gaban mahaifiyarshi suna shirye-shirye dan suna jiran nan da kwanaki ukku, komai ya wuce dan sunyi gagaru-min shiri sun baza ƙarfin iko, tsafinsu na maita, sihiri iya sihiri abin si wanda ya gani zai tabbatar, tambaya e watso ma karan ɗin wacce baibyi zaton ta ba.
"Ka kuwa yi nasara kan Sahash?" cikin ɗan diri-ricewa yace
"Tun lokacin da mukai maganar nan, na rabu da ita."
"Amma ita sanaam fa!?"
"Ai tun lokacin da ta samu, labarin ina tare da sahash tayi min wulaƙanci ni kuma nace, har abada kar ta sake nuna tasan karan!"
"Da fatan dai baka yi sakaci da ƙwan zinaren nan ba?"
"Yana nan na ajiye guri mai sirri!"
"Ka kula sosai."
Arman ne ya shigo yana ɓaɓɓata rai, dubanshi mahaifiyarshi tayi tace "wa ya taɓa min yarima arman ɗina?"
"Wai mai marataba ne ke so na aure wata ƴar abokinsa."
A Razane tace "Wane abokin daga ciki?"
"Nima ban sani ba nadai ji yana maganar zasu zo nan."
*ASSLAMU ALAIKUM*
*MUHIMMIN SAƘO DAGA KHADIJA MUHAMMAD SHITU (K_SHITU)*
*WANNAN LITTAFIN NAWA MAI SUNA A SAMA YA KOMA LITTAFIN KUƊI SAKAMAKON ABUBUWAN DA SUKA FARU, MAI BUKATAR SIYA YA MIN MAGANA, ZAN KARA PAGE ƊAYA, SHIKENAN.*
GA NUMBER TA.
+2349117440993
*SIRRINA*
*_K_SHITU🦋_*
*_SHAFI NA TARA DA NA GOMA._*
*P 9-10*
Yau kwana biyu kenan kullum sai mai martaba ya koya mata abubuwa da dama, faɗa kuma dama ta iya yanzu kuma tana ƙara koyo ta ƙware sosai ya bata, kyautar wani zobensa da yake matuƙar ji dashi, sannan yayi mata gamsasshen bayani a kan zoben, Yau rana ta ukku kenan kamar yanda, ya faɗa sunyi faɗa sosai, sannan ya ɗaura mata wata sarƙa mai kyau a wuya, ya kuma faɗa mata a koda yaushe ta kasance cikin shiri, dan gobe ne BAƘIN WATA! ke kamawa.
Haka ta bar sa cikin mamakin to mai zai faru goben, ita dai bat yi wani yunƙuri ba ta kwanta hankalinta kwanche dan har dare ya fara, kuma tana da yaƙini da wani abu ne tsoho arar zai gaya mata.
MASARUTAR HIZAAR
Tsakiyar dare sarauniya halsha ta tashi ta hau shiri gadan-gadan dare da sarki ahal, babu ɓata lokaci suka gudanar da baƙin tsafi, suka nufi babban gate ɗin masarutar, dan ficewa zasu iya, doki ɗaya suka hau suka suka fara tafiya da gudu dan akwai tafiya, sosai sun daɗe suna tafiya har suka yi amfani da ƙarfin ikonsu suka isa da wuri, Wata tsohuwar maƙabarta suka shiga, sun wuce kabarbura masu yawa wasu kabari guda ukku da suka fi sauran suka tsaya, a tare suka ɗaga farin tulu suka fasa a kabarin tsakiya, wata guguwa ce da iska haɗe da hayaƙi suka taso suka rufe kafin wata tsohuwa ta umurce su da su, ɗauki tulun cikin kabarin, ɗauka sukayi suka ɓace fuskokinsu ɗauke da farin ciki.
MASARAUTAR MANAAJ
Cikin sauri-sauri sahash ke shiri tana gamawa ta kama hanyar fita ba tare da kowa ya ganta ba, maƙabarta ta nufa.
Kallo ɗaya zaka mata kasan ba chikakkiyar mutum bace! tafe take tana rangaji cikin maƙabartar, wani ƙaton madubi ne ya bayyana ɗauke da wat matashiyar budurwa wacce take kwanche bisa wani makeken gado, a gaggauce ta fara ƙoƙarin ƙona mata fuska, cikin barci taji kamar ana ƙoƙarin chutar da ita.
a firgice ta tashi tare da ɗaukar madubin tsafinta wani murmushi ne ya suɓce mata ganin yanda sahash keta ƙoƙarin ƙona mata fuska, wani farin haske ne ya fito daga idanunt yayi cikin madubin, sahash na tsaye kawai ta faɗi a kufle ta nutsa cikin masarautar, wani kabari taja ta tsaya, amma shine na farko sai guda biyu kuma, wae wuƙa ta fiddo ta yanka hannunta jini ya zuba saitin kabarin.
a firgice ta fara jera masa tambayoyi, "kaka suwayi waɗan nan?"
"Daman nasan zaki tambaya waɗan nan sune wasu shaharrun sheɗanun mayu waɗan da aka shafe su da daɗewa, amma an tdo su saboda samun sarauta, kuma kowa nason haɗe masarutun ukku a chigaba mulka, amma hakan ba zai taɓa yiwa bai sai anje tekun jazal an samo abunda zai dawo da su, yasa su komo ƙarƙashin iko, saidai kuma duk cikin su babu wanda yasan wace duniya tekun yake."
"Toh amma kai kasan inda tekun?"
"Eh na sani! amma aliya kece kaɗai zaki iya zuwa ki ɗauko kafin su gano dan hana faruwar yaƙin........
PAID BOOK
MAI BUƘATA YA MIN MAGANA NAN NA GAMA FREE PAGE.
09117440993
0 Comments