ZUCIYA ƊAYA





[8/3, 2:19 AM] Ummeeta❤‍🔥❤️: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA DAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin qirqirar shi nayi,idan yayi daidai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 1*

        A hankali ta tab'a ƙanwar ta dake zaune a reception ɗin asibitin tana kuka,ɗagowa tayi ta tashi tsaye tare da rungume ta tana cigaba da kukan ta,da ƙyar tayi shiru

Sannan tace "dan Allah Sister kar ki bari Ummina ta mutu dan Allah"wani kukan ne ya sake kwace mata 

"Kiyi shiru Siyama insha Allah Ummi bazata barmu ba" 

"Amma ai ɗazu kinji Dr yace idan ta wuce yau ba'ayi aikin ba zata iya mutuwa kuma har yanzu bamu samu kuɗin ba" 

"Insha Allah zan samu,Yuhanees na nan zuwa da wasu kuɗin sai mu hada da wannan mu bayar sai su bimu saura mu biya a hankali" 

Wani kukan Siyama ta sake fashewa dashi,cikin damuwa tace "Siyama kukan nan naki yana tayar mun da hankali dan Allah kiyi shiru" 

Wata nurse ce tazo tace "HANAN,Dr Yusuf na kiran ki" 

Ɗaga mata kai kawai 
tayi sannan ta kalli yar uwar ta Siyama data zauna sannan sai ta wuce

Duk abunda suke yi tun ɗazu akan idon shi,a hankali ya maimata sunan "Hanan,nice name"

 Sannan ya juya wurin da ake biyan kuɗi dan a wurin yake tsaye

 Yace "Mubarak kasan wadancan?"ya tambaye shi tare da nuna wurin da Siyama ke zaune

"Eh yallabai,kwanan su huɗu kenan sun kawo mahaifiyarsu tana fama da ciwon ƙoda,za'a mata aiki ne amma har yau sun kasa biyan kuɗin,wlh tausayi suke bani"

 "Nawa ne kuɗin aikin?”

"1.1 million ne yallabai"

 A hankali ya girgiza kanshi sannan yace "wane Dr ke kula dasu?"

"Dr Yusuf ne" 

Kallon Siyama ya sake yi sannan ya hau upstairs ya wuce

A bakin office ɗin Dr Yusuf suka yi clash dan ta fito shi kuma zai shiga sai ta buge shi

A razane tace "dan Allah kayi haƙuri"

"Ba komai" ya amsa a taƙaice tare da kallon ta ya mata murmushi ita ma murmushin ta mayar mishi duk da tana cikin damuwa

Sannan ta wuce,shi kuma ya shiga office ɗin da sallama

Da sauri Dr Yusuf ya tashi haɗi da bashi hannu suka gaisa sannan suka zauna

Dr Yusuf yace"yallabai ashe ka shigo?"

"Eh tun ɗazu ma na zo"

 "Allah sarki,to ya jikin Hajiyan?"

"Alhamdulillah tana gida ma, wani na zo dubawa"

"Ok to Allah ya ƙara lafiya"

 "Ameen...yawwa nace wace yarinya ce ta fita yanzu?"

"Oh Hanan?"

"Umm"

"Mahaifiyarsu suke jinya aiki za'a mata" 

"Yaushe kenan za'ayi aikin?"

"Yau ya kamata ayi amma har yanzu sun kasa biyan kuɗin" 

"Nawa ne?"

"1.1 million"

"Ka je kayi magana a fara shirin yi mata aiki yanzu,zanje in biya kuɗin"

"Masha Allah,Allah yasa ka gama da duniya lafiya,nayi murna sosai wallahi dan ba ƙaramin tausayi yaran ke bani ba wallahi" 

"Ameen"

A haka suka fito office din tare da Dr Yusuf kai tsaye ya wuce wurin biyan kuɗi

Wata mata ce na ga ta tsayar da Dr Yusuf

Tace "Dr me wancan ya zo yi nan kuma yau? "tana maganar ne tana kallon shi har ya b'ace musu hakan yasa Dr ya gane wa take nufi

 "Ya zo dubiya ne" 

"A office ɗin naka?"

"A'a Hajiya,yazo office ɗinane dan neman information akan wasu"

 "Su wa kenan?"

"Wasu yara ne da za'ayi wa mahaifiyar su aiki basu da kuɗi shi ne...."

 Katse mishi zance tayi da "shine ya biya?"

"Eh"

Ajiyar zuciya ta sauke tare da zaro wayar ta daga cikin jaka sannan ta juya ta wuce,shima Dr Yusuf ya wuce domin ayi shirin shiga theatre.

A bangaren Hanan kuwa,bayan ta koma reception ta tarar da Yuhanees tazo,zama tayi kusada ita sannan tace

"Ya ake ciki ne rabin rai?"

 "Hmm,200k kawai aka samu"

"Karki damu nagode sosai Allah ya barmun ke,yanzu ki kawo saimu haɗa da wannan 400k ɗin sai mu kai musu,tun da sun wuce rabi may be zasu taimaka mana"

 "Haka kike tunani hayatee?"

"Muje mu jarraba dai"

"To Allah ya sa mu dace"

"Ameen"

Yuhanees ce ta kalli Siyama tace "Sisto bari mu dawo kinji"

Kai kawai ta iya daga mata sannan suka wuce




 "Hanan ai an biya kuɗin aikin da na duk wani magani da za'a bukata"

"Cikin mamaki tace "an biya kuma...?" 

"Eh yanzu ma ya bar nan"

Kamin tace wani abu sai taji muryar Dr Yusuf "Hanan kuzo kuyiwa mahaifiyar ku addu'a dan yanzu zamu shiga theatre da ita" bai jira komai ba ya wuce suma suka bi bayan shi

A ɗakin suka tarar da Siyama dan ita ya fara kira,suka mata addu'a sosai sannan aka shiga da ita

Dr Yusuf zai shiga theatre room ɗin kenan Yuhanees tace "amma Dr dan Allah muna so musan waya biya kuɗin"

A taƙaice yace "AAJ" sannan ya shige

"AAJ!!!" Suka maimaita sunan a tare cikin mamaki

Hanan tace "amma ya akayi har AAJ ya biya mana kuɗi,ko ganin shima bamu taba yi ba"

 Yuhanees tace"kar kiyi mamaki da ikon Allah hayatee,kin san ubangiji yana taimakon bawan shi ta hanyar da baiyi tsammani ba,Allah dai ya saka mishi da alkhairi"

Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "ameen"

 Siyama kuwa tace"ina roƙon Allah ya tsare shi daga makiyan sa,kuma Allah ya nuna mun shi face to face"

Murmushi sukayi sannan sukace ameen.

Mubarak ne yazo dauke da wasu reciepts ya ba Hanan yace "ga reciepts dinku nan yace a baku,may be zai dawo gobe dan an kira shi yana sauri ne"

"Allah ya kaimu lafiya,mun gode"

Daga haka suka zauna suna tayin addu'ar samun nasara.


 Driving yake a hankali cikin natsuwa da ƙwarewa karatun qur'ani kawai ke tashi a motar,suratul maryam daga bakin hafizin qur'anin nan Sudais,yana bin karatun  shima a hankali

Wayar shi ce ke kara hakan yasa ya rage muryar sannan ya ɗauka

"Ammi ina hanya,gani nan zuwa yanzu in few minutes"

Bata ce komai ba ta kashe wayar 

"Oh Allah,yau kuma waya tab'a mun ita"

Wani gajeren tunani yayi sannan yace "a'a bazata sani ba dan ba wanda zai gaya mata...koma dai menene Allah yasa da sauki"

Daga haka ya ƙara volume ya cigaba da sauraren karatun.....



Ummeeta🥰.......📝

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

          *ZUCIYA DAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
[8/3, 2:19 AM] Ummeeta❤‍🔥❤️: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
*ZUCIYA DAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰

        
🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙
http://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''
بسم الله الرحمن الرحيم
  ~~~~~~~~~~~~~~

Wannan littafin na ZUCIYA DAYA ƙirƙirarren labari ne,idan yayi daidai da rayuwar ka/ki,a mun uzuri akasi aka samu👏👏👏



 *Page 2*


           Dai-dai wani tangamemen gate naga ya tsaya tare da danna horn,da sauri naga an buɗe mishi gate ɗin

Wani madaidaicin titi ya bi wanda bazai  wuce na mota ɗaya ba, sai gefe-gefen shi dake cike da flowers masu matuƙar kyau da ƙamshi

Tafiya kaɗan yayi ya taradda wani ɗan ƙaramin roundabout wanda idan ka bi right handside zai sada ka da wani garden mai kyau komai akwai ciki,idan kuma kabi left handside swimming pool ne tare da rumfunan turawa nashan iska

Sai ya miƙe ya sake yin horn a gate na biyu,nan ma buɗe mishi gate ɗin akayi

Wani tangamemen fili ne masha Allah yasha interlocks,nesa da wurin kuma wani ƙayataccen building ne mai kyaun gaske wanda kusan rabin shi na glass ne

Left hand naga yabi direct sai parking lot,yayi parking ɗin motar cikin jerin motocin dake wurin,a ƙalla zasu kai takwas,sannan ya fito

Kai tsaye building ɗin ya nufa tare da danna door bell

Wata kyakkyawar yarinya ce ta buɗe kofar bazata wuce 17 yrs ba

Rungume shi tayi ta ce ”welcome Sweet Bro"peck ya mata a goshi

Ya ce "yawwa Sweetie....ina Ammi?" 

"Tana ɗakin ta kuma tun ɗazu take ta jiran ka,yau ma kayi abun ko?" ta ƙarasa maganar da tambayar shi tana nuna shi da ɗan yatsa tana buɗe ido

Murmushi yayi tare da ɗaga kai ya ce "but how did she knows"

Ɗaga kafaɗa tayi ta ce"no idea,amma dai ina zaton Hajiya Karime ce,dan ta kira ta"

Ajiyar zuciya yayi sannan ya wuce yana faɗin"let me go and meet her"

(Tashin hankali,faɗin girma da tsaruwan palourn ƙauyanci ne,just imagine it urself,abunda kawai zan iya gaya muku,komai na palourn maroon ne da milk)

Upstairs ya hau,kai tsaye ya shiga ɗakin Ammin shi tare da sallama,bata cikin palour,hakan yasa ya gane tana cikin ɗakin,sai kawai ya zauna jiran ta

Kyakkyawar dattijuwa ce ta fito,daga ganin ta ka ga naira da hutu shiyasa fuskar nan tata kamar wata yar 30yrs while she's 47.

Zama tayi kan kujera tana kallon shi

A hankali ya ce "sannu da fitowa Ammi"

 "Yawwa" ta amsa ba yabo ba fallasa

Buɗe baki yayi zai yi magana ta ɗaga mishi hannu "dakata,ina ka tafi daga office?" 

"Asibiti na tafi Ammi"

 "Ai ina da sauran magani,me kaje yi a can?"

"Aminu naje dubawa,wannan cleaner ɗin da yayi accident"

Wani kallo ta bishi dashi tace "sai kuma kayi me?"

Ya fahimci abunda take so ya gaya mata,bai saba da yiwa Ammin shi ƙarya ba koda hakan zai b'ata ranta,dan haka kai tsaye ya bata labarin abunda take so taji

"Ammi naje duba shi sai naga akwai kuɗin da ake buƙata domin treating ɗin shi kuma beda su,sai na biya 150k sannan na bashi 200k domin ya kashe matsalar gidan shi kamin ya ji sauƙi ya dawo bakin aikin shi....ina wurin biyan kuɗin ne kuma na ga wasu yara suma mahaifiyarsu na buƙatar a mata aiki ko kuma ta rasa ranta shi ne suma na biya musu 1.2 million na aikin da kuma kuɗin abubuwan da za'a buƙata saboda su ma......"

"Dan Allah kayi mun shiru ubansu,sarkin iyayi,kana nufin million ɗaya da dubu dari biyar da hamsin ka kashe a banza?"

"Ammi ba a banza bane  tunda mabuƙata na ba"

"Mabukata ko? to mu gaya maka akayi bamu bukata ne ko me?"

Palourn ya bi da ido yana ƙara kallon girman shi da kayan more rayuwar dake ciki,a ranshi yace 'me wannan daƙin me kuma yake buƙata a rayuwa banda gamawa da duniya lafiya..!?'

Katse mishi tunani tayi da faɗin "kullum ina raba ka da wannan halin,a banza ko?...to bari kaji kar in sake jin wannan shashancin"

"I'm sorry Ammi,zan kiyaye"

A taƙaice tace "better"

Cikin takaicin wannan halin na mahaifiyar shi ya tashi ya fita,duk da ya saba da wannan halin nata amma kullum ƙara jin haushin halin nata yake

Main palour ya koma,wata ce zaune kan kujera ta harɗe ƙafa tana shan fruits tana kallo,kamannin ta sak irin na wacce ta buɗe mishi ƙofa,sai dai wannan tafi kaurin jiki

Jin ƙamshin turaren shi yasa ta juyo ta ce "welcome big Bross"

 "Yawwa sannu...ina Yasna?"

"Kaman ta na part ɗinka"wucewa yayi ba tare da yace komai ba

Direct sai part ɗin nashi,(Masha Allah,shima wannan part din ba baya ba wurin haɗuwa,komai na ciki navy blue ne da fari)

Zaune ya same ta a palourn shi tana kallon cartoon,suna haɗa ido ta sakar mishi  murmushi shi ma murmushin ya mayar mata sannan ya shiga ɗakin shi,ita kuma ta fita.

Bayan kamar 25mins,sai gashi ya fito sanye da three quater da singlet baƙaƙe,sunyi masifar mishi kyau dan farar fatar shi ta sake haskawa

Kyakkyawa ne ajin farko wanda ya amsa sunan shi namiji,sexy eyes ne dashi wanda suke ɗauke da baƙaƙen eyelashes masu tsayi,ga dogon hanci masha Allah,da pink lips ɗinshi,gashin kanshi tubarkalla baƙi siɗik wanda yasha gyara da kyakkyawan aski kamar wani ba'indiye,ga sajen shi da ya kwanta kan kyakkyawar fuskar shi,Gsky da ace kyau ke sa a shiga aljanna da wannan yayi sa'a

Zama yayi kan 3seater,hakan yayi dai-dai da shigowar Yasna hannun ta riƙe da plate

Kusa da shi ta zauna,ta ɗora plate din kan center table,sannan ta kalle shi,ya jingina da kujera ya lumshe idanu

Ta ce "Sweet Bro ga abincin ka nan"

Ɗaga mata kai yayi sannan ya gyara zama ya ce "Sweetie ina mamakin yanda akayi su Ammi suka san da zuwa na asibiti"

"I'm very sure Hajiya Karime ce ta ganka,dan shekaran jiya da ta zo,ta gaya wa Ammi yau zata je check-up"

Jinjina kai yayi tare da sauke ajiyar zuciya

"Ni wallahi na tsani wannan matar,dan munafuka ce"cewar Yasna

"Quiet Sweetie..,kar na sake jin wannan kalmar,kinsan dai ta haife ki ko?!....i wonder why Ammi behave like this wallahi"

"Ai ita ke zuga ta"

"Allah ya kyauta"

"Ameen"

Jawo plate ɗin tayi dake kan center table ta buɗe

Wani daɗi yaji ganin favorite ɗinsa ne,fried spaghetti wanda yasha kayan lambu da ƙoda,

Ya san itace tayi mishi,kallon ta yayi ya ce "tnx Sweetie"

"You deserve more than that Sweet Bro"

Tashi tayi ta ɗauko mishi hollandia youghurt cikin fridge ta zauna ta cigaba da kallon ta




  *ASIBITI* 

Around 6:25pm aka fito da Ummi daga ɗakin theatre zuwa aminity room

Siyama ce kawai a ɗakin kasancewar Hanan da Yuhanees sun koma gida suyi abinci

A hankali ta fara buɗe idonta tana karanto "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN"

Ta sauke idanun ta kan Siyama dake ta faman kallon ta tana murmushi ita ma murmushi tayi ta ce "Siyama na"

"Na'am Ummi na,ya jikin ki?"

"Da sauƙi,ina Hanan?"

Kafin ta ba ta amsa sai gasu sun shigo ɗakin da sallama

Ai kuwa da sauri suka ƙarasa shiga ɗakin

Hanan tace "Ummi ashe kin farka...ya jikin?"

"Alhamdulillahi Hanan"

Kallon Yuhanees tayi tace "zo mana Yuhanees"ita ma cike da murna ta isa bakin gadon ta durƙusa ta ce "Ummi ya jiki?"

Alhamdulillahi,Yuhanees na gode Allah ya saka muku da alkhairi"

"Haba Ummi meye kuma abun godiya,ai dole ne mu miki,fatan mu kawai Allah ya baki Lafiya"

"Ameen Allah ya muku albarka"

"Ameen"

Nan Hanan ta tashi ta je kiran Dr Yusuf dan ya ce idan ta farka su kira shi

Tare suka shigo da ita da wata nurse,nan yayi yan gwaje gwajen da zai yi yayi rubutu

Sannan ya ce  "Alhamdulillah,anyi nasarar aiki kam dan naga da sauƙi,yanzu ku haɗa mata lipton ku bata tasha kar taci abinci,Allah ya ƙara lafiya"

"Ameen mungode"

Haɗa mata lipton ɗin sukayi kamar yanda yace,suka taimaka mata ta zauna tasha,su kuma suka shimfiɗa tabarma suka fara cin abinci

Bayan sun gama ne Ummi ke tambayar su yanda akayi suka samu kuɗin aikin

Yuhanees ta ce "Ummi kinsan AAJ?"

 "Ai duk garin nan ba wanda besan AAJ ba,in baka sanshi a fuska ba to zaka san sunan shi"

"To shi ya biya"

Cikin mamaki tace "shi ya biya?!"

Hanan ta ce "eh Ummi,muma Dr Yusuf ne ya gaya mana shi ya biya" 

"To Allah ya saka da alkhairi"

Siyama ta ce "ameen,ai ba ƙaramin taimakon mu yayi ba,dan da ace be biya ba,banajin zasu iya mana uzuri su karb'i rabi su bi mu saura"

Ummi ta kalle su ta ce "to a ina kuka samu rabin kuɗin"

Kafin Siyama tayi magana Hanan tayi saurin cewa "a'a Ummi bamu samu ba,dama shawara mukayi idan Allah yasa mun samu ko da rabi ne sai mu basu su bi mu sauran"

"Allah sarki,Allah ya na tare da bayin sa ai" 

Wani kallon mamaki Siyama da Yuhanees suka bi Hanan dashi

Ita kuma ko kallon su batayi ba dan kar Ummi ta fahimci wani abu

Haka suka cigaba da hira da ita har wani baccin ya sake kwashe ta

Tashi sukayi suka yi sallah sannan Yuhanees ta tashi zata wuce gida,Hanan ta fita ta rakata

Fitowar su daga ɗakin,Yuhanees ta kalli Hanan ta ce "Hayatee meyasa kika b'oyewa Ummi maganar kuɗin nan?"

"Kema kinsan wurin da na aro kuɗin nan,idan Ummi tasan wurin da na karb'o su ranta zai b'aci ne,dama saida ta ja mun kunne"

"Yanzu kina nufin Ummi bata so hakan ba?"

"To rabin rai ya zanyi?..,dole ya zamar mun dan bazan zauna ina kallon Ummi a haka ba"

"Hmm to Allah ya kyauta,yanzu yaushe za'a mayar musu da kuɗin?"

"Hutun sati biyu na ɗauka,idan na koma zan kai musu,ke kuma gobe idan kin shigo sai mu mayar da wanda kika samo"

"A'a ki barsu wajen ki,dan mallaki nane ba arowa nayi ba"

"Ina kika samu?"

"Sarƙa ta na sayar wacce kawuna ya kawo mun daga saudiyya"

Wasu hawaye ne suka zubo mata tana jin son aminiyar ta na ƙara shiga ranta

Ta rungume ta ta ce "nagode rabin rai,Allah ya saka miki da alkhairi"

"Haba hayatee,ai komai na wa naki ne,Allah ya ba Ummi lafiya kawai"

"Ameen"

Nan suka ƙarasa bakin titi ta tarar mata napep ta wuce,ita kuma ta koma cikin asibitin

Ummi na bacci har yanzu,hakan ya bata damar jan Siyama waje ta mata bayani akan cewa kar ta yarda ta gaya wa Ummi ta aro kuɗi,kawai dai zasu gaya mata kuɗin da Yuhanees ta bada




     *8:34pm* 

Yana zaune a palourn shi wayar shi tayi kara,dauka yayi ganin abokin shi ne

"Hello my Man,ya kake?"

Daga ɗayan bangaren aka ce "normal Super...ɗazu bayan tafiyar ka Mr Joseph ya zo akan maganar kayan nan"

"Ai na gaya musu ba wani kayan da zasu samu indai ba su gama biyan sauran kuɗin ba"

"Na dai gaya mishi ya dawo gobe domin hurumin ka ne ba nawa ba"

"Shikenan Allah ya kaimu" 

"Ameen...amma Super meke damunka na ji ka wani iri" 

"Bari kawai my Man,abunda kasani ne dai"

"Halin ammi wai?,ka rage sa damuwa a ranka,addu'a kawai za muyi mata insha Allah zata gane gaskiya"

"Allah yasa hakan" 

"Ameen,saida safe"

"Yawwa ka gaida mun da Hajiya"

"Zataji" daga haka suka kashe wayar

Telephone ɗin da ke kan ɗan ƙaramin table kusa da kujera ta dau ƙara

Ɗauka yayi tare da yin sallama,muyar Ammin shi yaji ta ce

"Kazo main palour"

Bata jira komai ba tayi hanging,wayar shi ya ɗauka ya fita zuwa main palour

Zaune take kan resting chair da system a gaban ta

Yasna da 'yar uwar ta Yasmin kuwa suna kallo(Kallo daya zaka musu ka gane 'yan biyu ne saboda kamar da suke da shi)

Zama yayi kan two seater fuska a daure ya ce "sannu da aiki Ammi"

Kallon shi tayi ta nuna mishi kusa da ita da alamar ya zo ya zauna

Ba musu ya koma wurin da ta nuna mishi

Shafa kanshi tayi ta ce "haba son,dan kawai na maka faɗa shine tun ɗazu baka zo nan ba"

Shiru yayi bece mata komai ba tace "to yanzu dai kayi hakuri,kasan raina b'aci yake yi ne wallahi idan naga kana banzatar da kuɗi shiyasa nake maka fada,kayi ƙoƙari ka daina kaga daga nan baza'a sake jin kan mu ba tunda shine kadai abunda ke hada mu" 

Ɗaga kai kawai yayi dan baya son ya jawo wani dogon surutu ta ce "yawwa my son,yanzu tashi muje muci abinci" 

Tashi yayi ya nufi dinning area 

"Sarakan kallo kuma ku tashi"cewar Ammi tana kallon su Yasmin

Haka suka bi bayan Ummi wacce ta zauna kusa da kujerar AAJ,ai kuwa da gudu Yasmin ta zauna ɗayan gefen shi,

Kuka Yasna tasa tana faɗin "wallahi na riga ki ƙarasowa...Sweet Bro kace ta tashi mun" 

Yasmin ta ce "baza'a tashi ba ɗin" 

Kuka Yasna keyi tana kallon yayanta shima ita yake kallo yana murmushi 

Ammi kuwa sai faɗa takeyi wai tayi shiru ta zauna wani wuri

Da ya ga kukan ba mai ƙarewa bane sai ya tashi daga wannan kujerar yace Yasmin ta zauna a wurin shi,kuma sai ya zauna kan wadda Yasmin ta tashi

Ya nuna ma Yasna kujerar dake gefen shi yavce "to zauna nan ke kuma"sannan fa ta zauna,ya kasance sun sashi tsakiya 

Yace "hope that's all" 

Ɗaga kai tayi kawai taja plate ta fara serving ɗin shi

Ammi ta ce "kai kaji zaka iya" 

Nan suka ci abincin su cikin kwanciyar hankali.......






WANENE AAJ?????

Ku biyo ni a next page insha Allah zaku ji ko shi waye





🥰UMMEETA🥰...........📝
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

            *ZUCIYA DAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
[8/3, 2:19 AM] Ummeeta❤‍🔥❤️: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA DAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
              🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰


🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙
http://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/


'''We are the moonlight writers we shine all over the samu👏👏👏

بسم الله الرحمن الرحيم
 ~~~~~~~~~~~~~~


Wannan littafin na ZUCIYA ƊAYA,ƙirƙirarren labari ne,idan yayi dai-dai da rayuwar ka/ki,a mun uzuri akasi aka samu👏👏👏

Wannan page ɗin sadaukarwa ne ga C.E.O ta moonlight writer's association QUEEN NASMERH🥰,ina matuƙar godiya akan yanda kike bani gudummawa akan littafina da kuma taimakon da kike mun,Allah ya saka miki da mafificin alkhairi, Ameen



 *Page 3*

     WANENE AAJ????

Cikakken sunan shi ARSHAD AHMAD JALAL,sunan mahaifin shi AHMAD JALAL,mahaifiyar shi kuma RUƘAYYA MANSUR

Ƴan asalin jahar Adamawa ne kuma fulani,auren zumunci aka musu dan iyayen su uwa ɗaya uba ɗaya suke,sai dai Ahmad su biyu ne a wurin iyayen su,shi da ƙanwar sa Fatima,Rukayya kuma ita kaɗai ce

Bayan rasuwar iyayen Rukayya ne mahaifin Ahmad wato Jalal suka yanke shawarar haɗa auren su shi da matar shi Inna Shatuwa,sai dai  an jinkirta auren zuwa lokacin da Ahmad zai tsayu sosai akan kasuwancin sa

Ahmad ya tashi da sha'awar harkar kasuwanci shiyasa da ya kammala karatun shi bai tsaya neman aikin gwamnati ba,Baffa ya haɗa shi da wani abokin shi dake kasuwanci shima dan ya haɗa shi da mutane

Yana son abun shiyasa ya jajirce sosai,Allah kuwa ya taimaka mishi yana ta samun nasara har ya haɗu da wani wanda ya kasance mishi amini dan komai tare suke yi

Arziki ya fara taruwa,nan yayi ƙoƙarin biyawa Baffa da Inna Makka,bayan dawowar su suka tarar ya rusa gidan ya sake mishi samfari,ya kuma siyawa ƙanwar sa kayan ɗaki dan an kusa bikin ta a lokacin,ba ƙaramin farin ciki suka yi

Anyi auren Fatima cikin wadata da kwanciyar hankali ita da mijinta Yusuf

Daga nan Baffa ya fara damun Ahmad akan maganar auren su da Ruƙayya,amma yace yafi so a haɗa auren su da aminin shi Abdul,ganin irin shaƙuwa da amincin da ke tsakanin su yasa Baffa ya ƙyale shi akan a jira Abdul ɗin

Abdul kuwa baida ma wacce yake so shiyasa ya gaya wa Ahmad yayi haƙuri ayi auren shi dan baida tsayayya kuma su Baffa sun matsu suga auren shi

Da ƙyar Ahmad ya yarda,ya ce "kai dai kace kawai baka so ka auri ƴar garin mu,kafi so sai ka koma gida"

Dariya Abdul yayi ya ce "ai kasan matar mutum kabarin sa,duk inda take ai zan aure ta"

Haka dai akayi auren Ahmad shima,kowa yayi farinciki da auren,Abdul kuwa ba ƙaramin gudummawa ya bada ba akan auren kamar shine angon

Bayan wata ɗaya da auren suka fara fita maƙwabtan jihohi suna sarin kayayya ki kuma har Nijar da Cameroon ma suna zuwa

Shekara ɗaya da wata uku da auren su Ahmad,Ruƙayya ta haifo santalelen ɗanta,son kowa ƙin wanda ya rasa,duk wanda ya ga yaron sai ya ji kamar ya sace shi ya gudu,ga shi kamar ka tab'a jini ya fito,sai dai ace Masha Allah

Kowa yayi murna sosai,ran suna kuwa an kashe naira musamman Abdul dan shi ya siya shanu da ragon da aka yanka,sannan ya ɗauki nauyin duk wani abunda za'a buƙata a ranar sunan,kama daga abinci,abun sha da makamantan su,bayan kuma kayayyakin sawa da ya haɗa jiririn da su

Ahmad cikin tsananin son aminin shi ya ce "i'm speechless Abdul,bansan ta inda zan fara ba,nagode nagode Allah ya saka maka da mafificin alkhairin sa"

"Haba Ahmad,kana so ka nuna mun ɗanka ba ɗana bane ko me?,abunda zan iyayi ma ɗana ne fa na mishi,ai ɗan halak baya manta halacci,kai da su baffa kun riƙe ni tamkar ɗan uwa har bana ma kaina kallon maraya,sannan duk wani abunda na samu ta dalilin ka ne,dan da ni kaɗai zanyi kasuwancin nan da yanzu ban kai haka ba dan ka fini experience,sannan idan zan tafi ganin dangin mu sai ka haɗa musu sha tara na arziki sannan mu tafi tare,kuma....."

Rufe mishi baki Ahmad yayi ya ce "ya isa haka nan sharhabilu,meye kuma na gay mun wannan abun"

Dariya suka yi,Ahmad ya sake cewa "yanzu dai mu tafi ana jiran ka sanar da sunan da za'a sa ma ɗanka"

Murmushin jin daɗi yayi ya ce "Allah ya raya mana ARSHAD kuma yasa mai taimakon addini ne da al'ummar Annabi MUHAMMAD S.A.W"

"Ameen ya Allah"

Haka kuwa akayi,yaro ya ci suna Arshad,su Baffa ma sun sa ma Abdul albarka sosai dan sunji daɗin abunda yayi

Wata biyu da sunan Arshad,Baffa ya ce ga garinku,sakamakon ciwon cikin da ya kama shi cikin dare,mutuwar ta girgiza mutane dan an kwanta da shi ne amma ba'a tashi da shi ba
To Allah ya jiƙan Baffa

  
Haka rayuwar ke ta tafiya Ahmad da Abdul suna ƙara samun cigaba sai dai har ynx Abdul bai samu matar da yake ganin ta dace da shi ba,lamarin da ke ci ma Ahmad tuwo a kwarya,dan ya matsu shi ma ya ga jinin Abdul

Wani zuwa ne da Abdul yayi garin su shida Ahmad,Allah ya haɗa shi da wacce yake so,Ahmad yayi murna sosai kuma yace sai an kawo ta ta ga Inna da Rukayya

Ai kuwa aka kawo ta tayi musu wata biyu dan ita ma marainiya ce,cikin wata biyun nan kuwa ba ƙaramin shaƙuwa ya shiga tsakanin ta da su Inna da Ruƙayya ba,ga Arshad kuma bacci kawai ke raba ta dashi sai kuma idan zai sha mama,sun shaƙu sosai har suna ji kamar kar su rabu
Farincikin su ɗaya,wata rana za su rayu tare tunda idan akayi auren nan garin zata dawo wurin mijinta
 
Ran da ana gobe zata koma,Abdul ya kai ta kasuwa,nan ta ga wata ƴar ƙaramar sarƙa ta fashion mai matuƙar kyau,wani ƙololo ne a jikin ta yana walƙiya,a tsakiyar ƙololon kuma akwai harafin *R* a rubuce,nan ta takurawa Abdul akan tana so zata saiwa Ruƙayya,haka ya cire kuɗi ya biya

Ruƙayya kuwa tayi farinciki da wannan ƙyautar kuma taji tana girmama kyautar,hakan yasa ita ma ta dauko mata wani zobe wanda Ahmad ya kawo mata daga Makka,shi da kanshi ya bada design ɗin zoben,shiyasa har yau bata b'a ganin wanda ke da irin shi ba,ta bata a matsayin kyautar ta

Inna kam kallon su kawai take yi ta ce "wannan irin abu kamar waɗanda akace baza su sake haɗuwa ba"cikin so da ƙaunar juna suka rabu kowa na marmari ɗan uwan shi,Abdul ya mayar da ita garin su ya dawo sai kuma nan da wata shida idan anyi aure sai ta dawo




Tafiya ce ta kama su zuwa garin Kaduna amma Abdul yace Ahmad ya wakilce shi kawai dan yana so ze tafi garin su,dan tunda ya mayar da matar da zai aura bai koma ba yau wata biyu kenan

Ahmad ya so yayi hakuri su tafi tare idan sun dawo amma yace bazai iya jira ba,ya tafi kawai,ba dan ranshi ya so ba ya yarda

"To amma kasan akwai maganar siyan gida da za muyi a Kadunan kafin lokacin auren ko?"

Dariya yayi ya ce "na baka wuƙa da nama,idan kaje ka duba mun gidan nima,sai dai kasan Inna tace bata so ta bar jahar ta,ya za'ayi kenan?"

"Munyi magana ai,tace mu koma can kawai tunda munga can ɗin ya fi mana sauƙin kasuwancin,inya so sai mu riƙa kawo mata ziyara tunda anan ɗin ma ba ita kaɗai bace,Fatima na nan"

"To Allah yasa mu dace"

 "Ameen"

A rana ɗaya suka bar jihar Adamawa,Abdul ya wuce garin su Ahmad kuma ya wuce Kaduna

Tun bayan tafiyar su,kullum sai sunyi waya,Ahmad na ba shi update akan abunda yake yi can,kuma ya gaya mishi ya siya musu gida

Abdul ya gaya mishi yana tunanin zai daɗe dan haka kawai idan yayi sallama da Inna za su iya komawa Kadunan kafin ya dawo,zai zo idan ya dawo

Ahmad yayi mamakin wannan maganar dan yasan be saba daɗewa ba,amma be nuna mishi ba yace ba komai

Haka kuwa akayi,sun koma Kaduna da shi da Ruƙayya sai jaririn su Arshad lokacin yana da watanni sha ɗaya

Inna ma kanta tayi mamakin dadewar Abdul amma kuma tayi tunanin ko akwai wasu dangin sa da yake so ya ziyar ta dan ya gaya musu maganar auren shi tunda yanzu saura wata uku da sati biyu


A kwana a tashi,tun Ahmad da Abdul suna waya,yanzu har ta kai ko ya kira sai dai yaji switch off,yau wata uku kenan kuma auren saura sati biyu,yana so su fara shiri kar lokaci ya ƙure musu

Hakan ya sa ya shirya dan zuwa garinsu Abdul ɗin dan Inna ma ta bashi wannan shawarar

Abun da ya ba Ahmad mamaki,lokacin da ya isa garin na su Abdul,kai tsaye family house ɗin nasu ya wuce amma aka ce mishi wai sun tashi tun wata biyu da suka wuce,kuma basu gayawa kowa inda za su koma ba

Kwanan Ahmad goma a garin ya cigiyar Abdul duk inda yasan suna zuwa tare idan sun zo garin,amma amsar ɗaya ce ba wanda yasan inda suka koma

Haka ya tattaro ya dawo Adamawa wurin Inna,ya gaya mata komai,tayi mamaki sosai kuma ta ji haushin rashin ganin shi

Ahmad kuwa ya fi kowa baƙinciki da hakan dan yayi kuka sosai kamar ba babba ba,dan har ƙaramar jinya yayi kamin aka samu ya dai-dai ta ya dawo Kaduna

Ya gaya wa Ruƙayya,tayi mamaki sosai kuma tayi bakinciki itama kullum kuka take dan ita ma dai sun shaƙu da Abdul ɗin dan ganin shi take kaman yayan ta dan ƙanwata yake kiran ta,ga kuma shaƙuwar su da matar da zai aura ɗin,har tana tantama idan ba wani laifin Ahmad ya mishi ba amma yace lafiya ƙalau suka rabu

 *BAYAN SHEKARA  HUƊU* 

Duk da cewar kwanaki sun ja dan yau shekara huɗu kenan rabon shi da Abdul,amma duk bayan wata biyu yakan tafi garin su ko Allah zai sa ya samu labarin shi,amma shiru ba amo ba labari

Sai dai a harkar kasuwancin sa cigaba yake ya samu kamar yanda ya saba dan ya bude shoprite kashi biyu a nan kaduna masu suna ABMAD SHOPPING STORE,ma'ana dai sunan shi da na Abdul ya haɗa,bayan ƙananan shaguna da yake da su a kasuwanni na sayar da kayayyaki,su ma dai duka da sunan ABMAD

Ya haɗu da wani abokin shi Mus'ab,sai dai kowa nashi kasuwancin daban,wanda matar shi ta kasance ƙawa kuma aminiya ga Ruƙayya,wato Karime


 *BAYAN SHEKARU SHA ƊAYA* 

Ruƙayya na fama da ƙaton cikinta wanda haihuwa yau ko gobe,su na son cikin,saboda har sun cire rai da samun  wani haihuwa saboda shekarun da ta dauka ko b'ari bata sake yi ba

Sannan har yanzu dai ba abunda Abbi ya fasa akan neman Abdul(Ahmad,Abbi sunan da Arshad ke kiran shi kenan),sannan kuma suna yawan ziyartar Hajjo(Inna,ita ma Arshad ke kiranta da hajjo tun lokacin da yakai shekara biyar har yanzu,har su Ahmad da Ruƙayya su ma sun ɗauki sunan) da Anty Fati(Fatima,ita dai Arshad ke kiran ta da hakan)

Ko yaushe suka tafi,idan suka dawo sai Ammi(Ruƙayya) da Abbi sunyi faɗa,saboda kawai taimakon da yake ba ƴan uwa da abokan arziki,kuma daga baya ta ɗauko wannan halin dan da ba haka take ba

Wannan karon ma haka ta kasance bayan dawowar su,faɗan su keyi

"Wai kai meyasa kullum cikin rabar da dukiya kake ne"

"Saboda dukiya ba tawa bace,Allah ne ya bani aron ta,kin ga kuwa dole in ba bayin sa"

"To wallahi bari kaji,idan har ka zama sanadiyyar talaucewar mu Allah ya isa"

"Kina cikin hankalin ki kuwa? Wai meke damunki ne yanzu"

"Tsana,da kuma ƙin talaka da talauci,shi ke damuna"

"To sai dai ki dawwama cikin damuwar,amma bazan tab'a daina taimako ba,kuma ko bayan ba rai na sai ɗana ya ɗora daga in da na tsaya,duk da ba wanda yasan gawar farko"

Juyawa tayi ta kalli Arshad dake tsaye ya naɗe hannu a kirji yana binsu da ido,ta ce "Arshad,wannan ba halin kirki bane,kar ka kuskura inga ka ɗauko wannan halin,dan kuɗin ƙarewa za suyi mu koma cizon yatsa"

Sai dai kash,ta makara,dan tun Arshad na da shekara biyar,duk hirar da za suyi da Abbin shi sai ya nuna mishi amfani taimako kuma yayi ta kwaɗaita mishi aljanna da abunda ke cikin ta,sannan kuma lokacin da aka sa shi islamiya,kusan kullum sai an gaya musu falalar taimako,dan tun yana 7yrs,ya haddace ayar da malamin su ke yawan karanta musu,wacce Allah yake cewa
 من ذالذى يقرض الله قرضاحسنافيضاعفه وله اجراكريم
 MA'ANA:
Wanene wanda zai ranta wa Allah rance mai kyau,domin Allah ya ninka masa shi(a duniya) kuma yana da wani sakamako ma karamci/mai girma(a lahira)

Nan kuwa ya ce "Ammi ai taimako ba karya arziki ya ke yi ba ƙara shi yake yi,kawai kiyi hakuri muyi ta yi,ko Abbi?" ya ƙarasa maganar da tambayar Abbi

"To kinji ma abunda ƙaramin yaro ya faɗa"

Da wa aka haɗa ta kuwa ba da su ba sai faɗa take tayi,tana matuƙar son Arshad,sai dai she can't control her temper idan aka zo maganar taimako ko kuma talaka,saboda mummunar huɗubar da aminiyar ta Karime ta mata kuma tabi

Faɗa take tayi har ta buge jikin kujera bata lura ba da yake irin na royal din nan ne

Faɗuwa tayi tana ihu da sauri yayo kanta sai ihu take tayi,ya ruɗe ya rasa abunda zai yi

Karime ce ta shigo nan,ta kama aka kaita ɗaki dan taga nakudar tazo mata dab,idan akace sai anje asibiti to zata haihu a mota

Kasancewar ta tsohuwar ungozoma yasa ta taimaka mata har ta haifi kyawawan twins ɗinta mata masu kama da juna kuma suna kama da Arshad

Murna a wurin su ba'a ko magana dan har sun manta da ma batun faɗa,Nan ya kira mutanen Adamawa ya gaya musu

Sai tururuwa ake yi zuwa ganin yaran,dan sune first twins ɗin a aka fara haifa a familyn su

Ranar suna anyi hidima sosai kamar ba gobe,Hassana aka sa mata Yasmin,Husaina kuma Yasna


Wata irin ƙauna ce Arshad yake musu tun suna jarirai har yanzu..........











Mu hadu a next page dan jin ƙarashen tarihin AAJ,sannan mu dawo cikin ainihin labarin mu
Naso ace a page ɗinnan na gama baku tarihin shi,amma na gaji gsky,dan haka kuyi haƙuri zuwa next page insha Allah



Gaisuwa ta musamman zuwa ga editors ɗin Moonlight Writers Association
Queen Nasma❤️
Queen Maryam❤️
Aiimar❤️
Mrs FH❤️
Jidda Umar❤️
Allah ya saka da alkhairi ya ƙara daukaka



🥰UMMEETA🥰.......📝



♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

          *ZUCIYA ƊAYA* 

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
[8/3, 2:19 AM] Ummeeta❤‍🔥❤️: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA DAYA*
[8/3, 2:19 AM] Ummeeta❤‍🔥❤️: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA DAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin qirqirar shi nayi,idan yayi daidai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


A last page, nasa bayan shekara sha daya instead of bayan shekara shidda,dan Arshad na da 11yrs aka haife twins
Ina fatan zaku mun uzuri,tnx❤️🥰


Ina miki fatan samun lafiya Mrs F.H🥰🌹,Allah yasa kaffara ne👏




 *Page 4*

   Arshad na da 13yrs,Yasmin da Yasna kuma na da 2yrs Allah yayi wa Abbi rasuwa,mutuwar da har yau basu san dalilin mutuwar ba,ya dai fita aiki sai gawa kawai aka kawo musu

A lokacin Abba(Yusuf,mijin Anty Fati) yaso ayi bincike kasancewar yana da aboki lawyer,amma Hajjo tace b'ata lokaci kawai za'ayi da kuɗi kuma,dan haka a bar maganar kawai,Allah ya gafarta mishi dai kawai

Kowa yayi jimamin mutuwar Abbi,saboda yawan taimakon da yake dashi,maganar kowa daya "Allah ya bishi da kyawawan halayenshi,Allah yasa ɗanshi ya gaje shi"

Haka rayuwar su ke tafiya bayan rasuwar Abbi,Hajjo ta so su Ammi su koma Adamawa,amma ta ce tafi son zama a Kaduna,ba dan ta so ba ta ƙyale ta,sai dai kamar yanda suka saba,suna zuwa Adamawan idan su Arshad suka yi hutu,ita ma Hajjo taka zo wani lokacin,haka ma Anty Fati

Abba ɗan kasuwa ne shima,hakan ya sa ya riƙe ragamar kasuwancin Abbi har zuwa lokacin da Arshad zai yi wayo,duk da Ammi ba haka ta so ba,dan ƙanin Karime ta so ya cigaba amma Hajjo ta hana

Tun lokacin da su Yasmin suka kai 6yrs Arshad ke gaya musu abunda Abbi ke gaya musu akan taimako,sai dai Ammi takan nuna musu illar hakan kamar yadda Karime ke gaya mata,kuma tana nuna musu cewar talaka abun ƙyama ne

Yasna ta tashi da shegen surutu,duk abunda akayi a bayan idon Arshad idan ya dawo sai ta gaya mishi,sai ta riƙa gaya mishi abunda Ammi ke faɗa,shi kuma sai yayi ƙoƙarin gaya mata hakan ba gaskiya bane

Ya so ya fahimtar da Yasmin ita ma,sai dai ta fi ɗaukar maganar Ammi,daga ƙarshe ma ta kai idan taji maganar da zai mata kenan,sai tayi ta kawo mishi excuses,kodai za ta yi fitsari ko za ta sha ruwa,har ta sulale ta gudu wurin Ammi

Hakan yasa ya fi shaƙuwa da Yasna sannan kuma halinsu ya zama ɗaya,Yasmin kuwa halayen Ammi ta ɗauko

Bayan Arshad ya kammala secondary school yana da 18yrs su kuma su Yasmin su na da 7yrs lokacin suna primary 1,Ammi ta ɗauki Arshad ta tura shi Australia dan ya ƙarasa karatun shi a can

Sai dai abun mamakin shi ne Hajjo ko kaɗan bata so tafiyar Arshad wata ƙasar karatu ba kuma shi kaɗai saboda tana tsoron kar halayensa na kirki su canza,amma kuma ta gagara hanawa dan ko maganar bata yi ba,cikin ikon Allah kuwa har ya kammala karatunshi ya dawo bai ɗauko ko wane mugun hali ba

Sakamakon wani abokinshi da suka haɗu acan ɗin SAJJAD,tare yake da da iyayenshi sai suka buƙaci ya zauna tare da su,sun basu kulawa sosai kuma sun kula da tarbiyyarsu,duk da lokaci zuwa lokaci Ammi ba tura mishi kuɗi sosai,amma hakan besa ya lalace ba

Arshad ya kammala karatunshi lafiya shi da Sajjad,sun karanci Business Adminstration,suka tattaro suka dawo Nigeria dukan su hadda iyayen Sajjad ɗin,suma ƴan Kaduna ne

Arshad mutum ne mai sakin fuska,ga taimakon na ƙasa dashi,duk abunda yake so to zai ɗauke shi da muhimmanci,yana son Ammi sosai da kuma ƙannen shi

Ga son zumunci,dan sometimes shi kaɗai yake zuwa adamawa wurin su Hajjo wani lokacin ma shi da Sajjad,sai dai yana da saurin fushi da zuciya,shi ne kawai matsalar shi

Yana da 25yrs,Abba ya damƙa mishi dukiyarsu gaba ɗaya,dan yana da tabbacin zai iya kulawa da komai yanzu,kuma dukiyar ta ninku yanzu tayi yawa fiye da da

Hakan yasa ya yanke shawarar bude company na shi na kanshi,Ammi kuwa taji daɗin hakan

Sannan kuma ya ƙara faɗaɗa ABMAD SHOPPING STORE ɗin duka biyu,da sauran dake cikin kasuwanni

Mutanen Turkey suka mishi zanen company ɗin kuma da taimakon su aka gina shi,hakan yasa har yau babu haɗaɗen company a Kaduna kamar AAJ IMPORT AND EXPORT COMPANY LIMITED

Cikin sauki ya samu ma'aikata suka fara kasuwancinsu,ba wata matsala,yayi ƙaurin suna a Kaduna hadda ma maƙwabtan garin,sannan suna mu'amala da kamfanoni daban-daban daga wasu ƙasashen kamarsu Turkey,Australia,Malasia,Singapore,India,har ma da China,da wasu ƙasashen kuma

Sajjad shi ne MD a company ɗin AAJ,Arziki kam alhamdullahi a wurin kyakkyawan matashin nan Arshad

Lokacin da aka mishi zanen company ɗin shi,ya sa aka mishi zanen gidansu kuma aka gina shi,gida ya haɗu ƙarshen haɗuwa ma

Tun lokacin da Hajiya Karime ta ƙyalla idon ta akan Arshad taji tana buƙatar ya zama surukinta,wato ya auri ƴar ta FARHA

Tayi wa Ammi magana,kuma tayi matuƙar farin ciki da hakan,sai dai shi Arshad ɗin 
kwata-kwata baya ƙaunar ta saboda rashin kamun kanta amma ita kuma kullum manne take dashi sai dai idan bata zo gidan ba

Sannan baya jin zai iya haɗa alaƙa da Hajiya Karime dan sam bai yarda da ita ba,kuma ita ke ƙara zuga Ammi akan ƙin talaka da kuma hana taimako

Kullum tunanin shi yanda zai raba ta da Ammi,amma baya tunanin hakan zai yiwu,saboda yanda Ammi ke bata muhimmanci a rayuwarta
 


 *WANNAN SHINE ASALIN AAJ* 






 _CIGABAN LABARI_ 

 ~Washe Gari da Safe~ 

Arshad ya kammala shirin shi ciki suits ash colour,da cover sheos baƙaƙe agogo ma baƙi,sai wani daddaɗan ƙamshi ke tashi a jikin shi,ya fito


A balcony suka haɗu da Yasna ta fito cikin shirin ta na uniform ɗinsu masu kyau

Ta ce "Morning Sweet Bro"

"Morning.....ina zaki ta fi haka,ko har kun gama zaku wuce?"

"A'a,Ammi ta ce na kira ka,ta kira ka baka ɗaga ba"

"Wayan na palour ne"

Riƙe hannunta yayi suka shiga ciki,dinning area kawai suka wuce dan suna can

Jan kujera yayi ya zauna sannan ya ce "morning Ammi"

"Ka tashi lafiya"

"Alhamdulillah"

Yasmin ta ce "Morning Big Bross"

"Morning"

Yasna ta ɗauki plate ta zuba mishi irish,plantain da ƙwai,ta ajiye mishi,ta sake ɗaukan wani bowl zata zuba mishi farfesun kayan ciki

"Sweetie wai ni kike zuba mawa?"

Ta ce "eh mana Sweet Bro"

"A'a coffee kawai zaki haɗa mun,ina sauri ne"

Ammi ta ce "saurin me kake yi"

"Ina so zan biya asibitin ne kafin in wuce company"

"Au,kenan jiya ɗin ma a banza nayi magana ko?....baka ji ba kenan"

"Na ji ki mana Ammi"

"Amma baka ɗauka ba"

Coffee ɗin ya karb'a daga hannun Yasna,ya ɗan sha ya ajiye sannan ya tashi tsaye ya ce "Zan ɗauka Ammi,but i'm sorry to say, bansan ko yaushe ba....sai na dawo" sha fa kan Yasmin da Yasna yayi ya ce "take care twins,bye" bai jira komai ba kawai ya fita

Ammi da ta bishi da ido tun ɗazu,sai daya bar palourn sannan ta iya ƙyafta ido ta ce "be san ko yaushe ba?!!....ikon Allah,lallai zanyi wa tubkar hanci"

Yasmin ta ce "gwara dai kiyi kam Ammi,dan ba ya da ranar dainawa"

Yasna ta galla mata harara ta ce "yenyenyenyen,ji bakin ta,to idan bata yi ba ai ke sai kiyi"

Yasmin zata yi magana kenan,ta ga Ammi ta ɗauki gwangwanin madara zata jefawa Yasna ɗin dan akwai tazarar kujera uku tsaƙaninsu,sai dai bata samu nasarar samunta ba,dan Yasna ta lura da hannun Ammi,da gudu ta bar wurin ta yi ƙofar palourn ta fasa breakfast ɗin

Ammi na huci ta ce "da kin tsaya ai,in fasa shegen bakin....masu mugun hali kawai,ai har ke zanyi maganinki tunda halinku ɗaya"

Yasmin ta tashi ta ce "sai mun dawo Ammi"

"Allah ya kiyaye"

"Ameen"

Palour ta tsaya ta ɗauki jakarta da na Yasna dake kan cushion sannan ta fita










🥰UMMEETA🥰.......📝



♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

          *ZUCIYA ƊAYA* 

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA DAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirar shi nayi,idan yayi daidai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 5*

Bayan fitar Arshad daga palourn,kai tsaye parking area ya nufa,ya shiga motar shi ƙirar VENZA fara mai baƙin tinted sai sheƙi take yi,ya ja ya fita direct sai asibitin

Sai da ya fara zuwa duba cleaner ɗin su sannan ya wuce office ɗin Dr Yusuf suka gaisa,sannan ya ke tambayar shi

"Dr ya aikin da kuka yi jiya,na mahaifiyarsu Hanan"

"Aiki kam alhamdullahi,da sauƙi sosai ma,ɗazu ma da asuba na shiga na sake duba aikin,ba wata matsala"

"To masha Allah,ina so zan duba ta"

"To yallabai,amma akwai wani patient da zan duba yanzu,sai dai ka tafi kai kaɗai"

Kai AAJ ya ɗaga mishi,sai Dr Yusuf ya ce "su na aminity,room six"

"Ok,nagode"

"Aa ba damuwa"tashi yayi ya fita office ɗin

Kai tsaye ya wuce aminity ɗin dan an tab'a kwantar da Ammi wurin ita ma

Sai da ya ɗan tsaya bakin ƙofar sannan yayi knocking

Siyama ce ta bude mishi ƙofar,su na haɗa ido,ta wani saki baki tana kallon shi,tana yaba irin kyaun shi,a ranta take ce wa 

'Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin wannan hallita....kai!!!! Ai tunda nake ban tab'a ganin namiji mai kyaun wannan ba a Nigeria,ai ko a India ma sai an tona.....Lahaula Fii Shi'ati Allah...." maganar Hanan ce ta dawo da ita cikin hayyacin ta

"Siyama wai ke da waye ne haka,ba ki bari ya shigo ba kuma ba ki fita kin sa me shi a can ba"

Hanan ba ta ganin ko waye,sai murya kawai taji mai daɗi,sak irin muryar da ta kwana da ita a kunnen ta,dan jiya ta fara jin irin muryar

"Just leave her,may be sai ta haɗiye ni sannan zata bari in wuce"cikin wasa yayi maganar ya na murmushi

Wata irin kunya Siyama ta ji,tayi dariya ta ce "haba dai malam,taya za'ayi in haɗiye ka,ai baka da wurin zama a cikina"

"Allah ko!"

"Eh mana"

"To bani hanya in wuce"

Wata dariyar ta sake yi sannan ta matsa ya shiga,ta rufe ƙofar

Hanan ya fara kallo yana mata wani killer smile,ita ma bata san lokacin da ta dan yi wani guntun murmushin da ya fito da dimples ɗin ta ba,sakamakon sake ganin fuskar nan da tayi karo na biyu.

AAJ ya tsugunna har ƙasa ya ce ma Ummi "ina kwana"

Kallo ɗaya Ummi ta mishi ta ji ya kwanta mata,ta ce "lafiya ƙalau  ɗan nan"

"Ya jiki?"

"Alhamdullahi,da sauƙi sosai....ta shi ka zauna ga kujera nan mana"

Tashi tsaye yayi ya ce "a'a wurin aiki zan tafi,ina sauri ne"

"Ayya,Allah ya bada sa'a,nagode sosai" kallon Hanan tayi ta ce "ke baki iya gaisuwa ba ne?"

A hankali ta ce "ina kwana"
 
Wani kallo ya mata mai ɗauke da saƙonni kala-kala,sannan ya ce "ba na son gaisuwar tunda sai da aka roƙa mun,kawai kora da hali ne kike so ki mun kamar yadda wannan ta hanani shigowa,to ku kwantar da hankalin ku yanzu fita zanyi,da ma mahaifiyata na zo gaidawa"

Murmushi Ummi tayi ta ce "ai kuwa naji daɗi Allah ya saka da alkhairi"

"Ameen"

Siyama ta ce "kaiii!!!yanzu Ummi kina nufin goyon bayan shi zaki yi?"

Dariya yayi ya ce "gashi kuwa kin gani,ko an gaya miki Ummin ta ku ce ku kaɗai?"

Huci ta ke yi tana mishi wani kallo mai kama da harara,shi kuwa dariya ta ba shi,ya juya wurin Ummi ya ce "Ummina sai anjima,may be zan dawo"

"To shikenan,a dawo lafiya"

Ya ce ma Siyama "ya ma sunan ki?...yawwa Siyama da Hanan sai anjiman ku" sai ya fita bai tsaya jiran jin me zasu ce ba

 Hanan taja kujera ta zauna ta ce "to,Ummi dai ta samu ɗa"

Dariya Ummi tayi ta ce "to ba ke kika gayyato mun shi ba?"

"Ni???,wlh Ummi ban san shi ba,jiya dai na ganshi ya fito office ɗin Dr"

Siyama ta ce "wurinki ɗin dai ya zo"

Sallamar Dr Yusuf ce ta katse musu maganar

"Sannun ku,ya mai jiki?"

Hanan ta ce "da sauƙi sosai"

"Masha Allah......AAJ ya shigo kuwa?"

Kallon kallo suka yi,Siyama ta ce "AAJ kuma?"

"Eh mana,na gaya mishi room number ɗin ai"

Siyama ta Kalli Hanan ta ce "sister ko shi ne ya fita?"

"To ta ya zan sani"

Dr yusuf ya ce "ikon Allah,ya sa suits fa,ash colour"

Da sauri Siyama ta ce "wallahi shi ne"

Ummi ta ce "wai kana nufin AAJ ne ya shigo ɗakin nan?"

"Eh shi ne"

"Amma mun yi abun kunya,ko godiya fa bamuyi mishi ba"

"Kenan dukan ku baku san shi ba?"

"Sunan shi kawai muke ji"inji Ummi

Dariya yayi ya ce "to ai rashin sani ne,may be zai dawo anjima ai"

Nan dai ya sake duba ta sannan ya fita ya bar su da mamaki,Siyama kam daɗi take ji yau ta ga AAJ




Daga asibiti,company ya wuce,dan ana ta kiranshi yana rejecting tun yana asibitin

Katafaren gate ne wanda motoci uku zasu iya jerawa su shiga a tare ba wata matsala,horn yayi,da gudu gateman ya buɗe mishi

Fili ne mai girman gaske da ya sha haɗaɗɗin interlocks da wasu flowers ta kowane kusurwa,da itace masu kyau jifa-jifa

A tsakiyar company ɗin,akwai wani zagayayyen wuri mai kamar roundabout,ƙasan wurin ruwa ne ke fitowa suna watsi kamar ana huro su,sai dai ba jiƙa mutane suke yi ba,hasali ma flowers ɗin dake zagaye da roundabout ɗin suke ba ruwa

A saman roundabout ɗin still,anyi wani building me harafin *A* ,ga wani allo na glass transparent a kanshi,mutum zai ga kamar akwai ruwa cikin glass ɗin,da wasu ƙananan flowers da aka manna a ciki masu sheƙi da ƙyalli,daga tsakiyar glass ɗin rubutu ne ke wucewa kamar haka:
AAJ IMPORT AND EXPORT CO. LIMITED
Kuma anyi rubutun da wani style mai ɗaukar hankali,da daddare kuma glass ɗin wuta yake fitarwa multi-colours.Gefe ɗaya kuma masallaci ne shi ma ya sha kyau har ya gaji.

Parking ɗin motar yayi a wurin da aka tanada dan parking ɗin motar shi,shi kaɗai

Tun da ya fito ma'aikata ke ta gaida shi a tsatsaye dan ya hana kowa durƙusa mishi

A haka har ya zo floor na farko,dan 3 floor ne a company ɗin,ya shiga,nan ma gaida shi ɗin ake tayi,private elevator ya nufa,wanda shi kaɗai ke bi,floor na biyu ya tsaya,ya shiga wani office

Mutumin da ke cikin office ɗin ya tashi yana gaida shi "ina kwana yallabai"

"Lafiya ƙalau....Mansur ina file ɗin da nace ka haɗa mun jiya?"

"Gasu nan yallabai,akwai waɗanda ke wurin Abida ne,idan na haɗa zan kawo maka office"

"Shikenan,ka yi sauri"

"Ok sir"

Ya juya ya fita,elevator ɗin ya sake shiga zuwa last floor 

Wani bangare ya shiga,ya tura wani glass door wanda yake transparent ne,haka shi wannan office ɗin yake,gaba daya glass ne kuma transparent

Wata ma'aikaciya ce a zaune kan table ɗinta tana aiki cikin computer,ganin shi da tayi ne ta tashi tsaye ta ce "welcome sir"

"How are you doing"

"Fine,sir"
Zai shiga wata ƙofa dake wurin tayi saurin cewa "sir,MD have been looking for since morning"

"Don't mind,i will call him"

Isa yayi bakin ƙofar dake wurin ita ma dai duk glass ce,amma wannan kuma ba'a ganin cikin office ɗin

Wani wuri naga ya danna jikin ƙofar kamar fingerprint sannan tayi sliding ta buɗe,yana shiga ta mayar da kanta ta rufe

Babban office ne mai kamar wani palour,akwai cushions a gefe navy blue,an zagaye su wuri ɗaya da center table a tsakiyan su,wani gefe kuma fridge ne,gefen shi kuma wurin haɗa coffee,da jugs da cups a jere,daga can ƙarshe kuma table ɗinshi ne na aiki mai girma sosai da tarkacen files,an kimtsa su gefe ɗaya,da globe a gefe,da wurin sa birurruka,sai wani shi ma mai kamar globe yana juyawa,yana ɗauke ne da tambarin company ɗin,an rubuta AAJ CO.LIMITED

Gefe ɗaya kuma wani abu ne mai kamar show glass,na glass ne,shi kuma daga ƙasa har sama duk awards ne,sai flowers dake cikin wasu vases masu kyau,a kowane lungu dake office ɗin

Zama yayi kan kujerar shi ya rufe ido yana juyawa a hankali,sannan ya zauna da kyau ya ɗauki wayar shi,numbern Sajjad yayi dailing,har ta yanke bai ɗauka ba,murmushi kawai yayi ya ajiye wayar yana kallon ƙofar shigowa

Abun mamaki,daga ciki ana ganin duk wanda ke waje

Hango Sajjad yayi ya shigo ƙofa ta farko wurin da secretary ɗinshi take,sai ya sa hannun shi ƙarƙashin table ɗin,ya danna wani abu,sai kawai ƙofar shi tayi sliding ta buɗe,Sajjad ya shigo ta sake rufewa

"Wannan wai wane irin iskanci ne kake ji haka yau,ina kiranka ka wani kashe mun waya"

Murmushi yayi ya ce "haba my Man i'm really sorry,ina wurin suruka ta shiyasa"

Cikin mamaki ya ce "suruka kuma???"

"Eh mana,yanzu dai yi haƙuri ka zauna"

"Ba za'a zauna ba"

Dariya AAJ yayi,Sajjad ya ce "wai ma yaushe ka fara son Farha ɗin har ka fara zuwa gidansu tunda safe?"

'Bata fuska AAJ yayi ya ce "dan Allah My Man karka canza mun mood mana,kai kasan ko mata sun ƙare bazan so Farha ba"

"To kayi mana new catch kenan"

"Ban sani ba"

"Ka fasa bani labarin?"

"Eh.......nidai neman me kake mun"

"Hmm,na ba Khairat,zata gaya maka,ka ga tafiya ta"

Ya juya ya fita,kasancewar daga ciki mutum zai iya buɗewa ya fita sai in shi ya dannan wani madannin daban ƙofar ta rufe,to sai in shi ya buɗe maka

Bin shi kawai AAJ keyi da ido,sannan yayi murmushi,ya ɗauki telephone ya kira Khairat,ya na kallon ta ta ɗauka,ya ce "ki zo" bai jira ta ba ya ajiye wayar,ya danna,ƙofar ta buɗe ta shigo

Zuwa tayi gefen shi ta tsaya tana miƙa mishi wata takarda "MD ne yace wai na baka inji Mr Joseph"

Karba yayi ya karanta sannan ya ce "mutumin nan fa na wasa dani,he thought i'm joking ko!?"

Ajiyar zuciya yayi ya ce "you can go"

Tana buɗe ƙofar Mansur ya shigo

"Yallabai ga files ɗin na haɗa"

"Ka tabbatar gaba ɗaya ne?"

"Eh insha Allah"

"To ka ba ma Khairat tayi signing sai ta kawo mun"

"To yallabai"ya juya ya fita

Computer ya kunna ya fara aikin shi cikin natsuwa da kwarewa.........











Jinjina a gare ku ƴan group ɗin Zuciya Ɗaya Fans♥️,ina jin daɗin comments ɗinku sosai🥰
Allah ya saka da alkhairi





🥰UMMEETA🥰.......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

          *ZUCIYA ƊAYA* 

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
[
[8/3, 2:19 AM] Ummeeta❤‍🔥❤️: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA DAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirar shi nayi,idan yayi daidai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 6* 

       _ASIBITI_ 

"Amma abun nan akwai mamaki,mafi yawancin mutane suna tunanin zaiyi girman kai duk da dai yanada taimako" cewar Yuhanees

Wacce zuwanta kenan suke bata labarin yanda suka yi da AAJ

Hanan ta ce "Bari kawai rabin rai,wallahi ban ta6a tunanin yanada sauƙi haka ba"

Ummi ta ce "shiyasa ake so ka riƙa kyautatawa mutum zato"

Hanan ta ce "haka ne wallahi,jiya ma fa har buge shi nayi,yace mun ba komai"

Yuhanees ta ce "ashe ma ke yau ne karo na biyu da kika gan shi!"

Hanan ta ce "amma kuma ban san shi ne ba"

Ummi tayi ajiyar zuciya ta ce "Allah dai ya kyauta"

Suka haɗa baki wurin cewa "ameen"

Nan suka fara breakfast,kasancewar Yuhanees ta kawo musu





Around 1:30pm AAJ ya fito daga office ɗin shi da niyar zuwa masallaci,wurin Khairat ya tsaya

"Umm Khairat"

"Na'am yalla6ai"ta amsa tana miƙewa tsaye

"Ki duba e-mail ɗinki na turo miki wani saƙo,sai kiyi printing ɗinshi out ki kai ma MD yayi signing kuma ya ajiye wurinshi"

"To yalla6ai"

"Yawwa kuma i'm going out,if possible may be i'm coming back,if not kuma sai gobe in Allah ya kaimu"

"Ok sir,safe journey"

"Tnx" daga haka ya fita

A first floor ya haɗu da Sajjad shi ma zai tafi masallaci,sai suka wuce tare

Bayan fitowar su daga masallacin ne AAJ ya ce "Man ni fa daga nan gaba zan ƙara"

"Ina kuma?" ya tambaye shi cikin mamaki dan yasan bai saba fita daga company ba sai huɗu,idan ma aiki ya musu yawa sai magrib"

"Wurin surukata mana"

Wani irin kallo Sajjad ke mishi,daga bisani ya ce "a dawo lafiya,idan ka dawo kuma sai ka gaya mun wace me sa'ar ce haka"

"Ba zaka gane ba man,ai ni nayi sa'a ba ita ba,bara na dawo dai" 

"To shikenan" suka yi musabaha,sannan Sajjad ya shiga ciki,shi kuma ya wuce wurin da yayi parking motarshi ya wuce




Da sallama ya shiga ɗakin bayan Yuhanees ta buɗe mishi ƙofar

Gaisawa suka yi sannan ya gaida Ummi yana ƙara tambayar ya jiki

"Alhamdullahi ai har naci abinci ma ɗazu"

"Amma mara nauyi ne ko?"

"Eh kafa ce aka siyo"

"Allah ya ƙara lafiya"

"Ameen"
 
"Nagode sosai AAJ,Allah ya saka maka da alkhairi,ashe kai ne ka biya mun kuɗin aiki bamu maka godiya ba ɗazu,dukan mu ba wanda ya sanka a fuska"

"Ayya Ummi,ke fa mahaifiyata ce,akan me za ki gode mun,albarkarki kawai nake buƙata"

Wani daɗi taji a ranta ta ce "Allah ya maka albarka ya sa ka gama da duniya lafiya"

"Yawwa,ameen Ummina"

Kallon Yuhanees yayi ya ce "amma ke ban ganki ba ɗazu ko?"

Ɗaga kai tayi ta ce "eh haka ne,mun gode Allah ya saka da alkhairi"

"Ameen" 

Yana shirin tambayar su Siyama sai kawai ya ga sun turo ƙofa sun shigo su na ta dariya

Haɗa idon da suka yi da shi ne ya sa su yin shiru

Siyama ce ta matso kusa da shi ta ce "ina wuri yalla6ai"

Ɗaure fuska yayi ya ce "je ki nemi yalla6ai"

Murmushi tayi ta ce "to ai sunanka ne"

"Haka aka gaya miki?"

"Haka dai naji ana kiranka"

"Ke tamkar ƙanwata ce Siyama,ki kirani da Sweet bro kamar yanda Yasna ke kirana,ko Big Bross yanda Yasmin ke kirana,idan kuma duka bazaki iya ba,sai ki kirani da ARSHAD"

Wani kallon mamaki suka bishi da shi dukansu

Sannan dai Siyama ta ce "ina wuni Yayana"

Murmushi yayi ya ce "lafiya ƙalau ƙanwata"

"Mun gode sosai da taimakon da kayi wa Ummina"

"Umminki kuma?"

"Au yi haƙuri,Umminmu"ta faɗa tana dariya

Hanan ma buɗe baki tayi zata mishi godiya ya katse ta

"Mun go......"

"Haba mana dan Allah,zaku sa inji wani iri mana"

Murmushi kawai tayi bata ce komai ba

Ummi dai kallonsu kawai take yi,Yuhanees ma kallon mamaki take mishi yanda ta ga yana fara'a ba kamar yadda tayi tsammani ba

Hanan ce ta katse ta dga kallonshi ɗin da take yi ta ce "rabin rai mu tafi ko"

"Uhmm,muje"

"Ummi mun tafi,Siyama ki kula"

"Sai kun dawo" cewar Ummi

AAJ kuwa ya ce "ko zan iya yin rakiya?"

Kallon juna Yuhanees da Hanan suka yi,sannan Yuhanees ta ce "ba matsala"

"Ummi sai gobe,Allah ya ƙara lafiya"

"Ameen,nagode"

Kallon Siyama yayi ya ce "ƙanwata sai gobe"

"To Yayana Allah ya kaimu lafiya"daga nan suka fita shi da su Hanan

Buɗe musu booth yayi dn su saka basket ɗin dake hannun Hanan,sai ya koma mota ya zauna,ita ma Yuhanees ta buɗe back seat ta shiga

Hanan da ta sa basket ɗin sai ta rufe,ita ma ta buɗe back seat ɗin ta shiga

A ranshi ya ce 'tirƙashi,driver kenan'
Kwantar da seat ɗin shi yayi ya kwanta,ya kunna musu karatun ƙur'ani

Da mamaki suka bi shi da ido suna kallo,sun kusan 7mins a hakan sannan Hanan ta ce "mun shigo fa"

Ya ce "ai na gan ku"

Sakin baki suka sake yi suka ce "ka gan mu?"

"Eh,na ga baku tashi tafiya bane shiyasa"

Hanan ta ce "mun tashi fa"

"To wa kuka maida driver"

Sai a lokacin suka gane me yake nufi,Yuhanees tayi ma Hanan alamar ta koma gaba,girgiza mata kai Hanan tayi,Yuhanees ta sake 6ata fuska

Kamar yasan me suke yi,sai ji suka yi ya ce "Hanan ki dawo gaba"

Shiru ta ɗan yi ta na kallonshi sannan ta fita ta koma gaban

Gyara zama yayi ya kunna motar suka ɗauki hanya,Hanan ke directing ɗinshi har suka iso ƙofar gidansu

Yuhanees ta fara fita,sannan Hanan ta kai hannu zata buɗe ƙofa bayan ta mishi godiya

"Hanan" ya kira sunanta,a hankali ta juyo tana kallonshi sannan ta ce "na'am"

Sai da ya gama kallonta sannan ya ce "ina tunanin bazan samu zuwa duba Ummi ba gobe,dan inada aikin da zanyi"

Kallonshi take yi cikin rashin fahimta,ganin haka yasa ya miƙa mata wayarshi ya ce "your number,sai in kira inji jikin Ummi"

Sai da ta gama kallonshi sannan ta kar6a ta sa mishi 
Ya ce "tnx"

A hankali ta ce "mun gode" ta buɗe ƙofar ta fita,sai da ya ɗan yi 5mins sannan ya tada motar ya wuce

Ƙarfe 3:04pm,hakan yasa ya wuce gida kawai,part ɗinshi ya wuce kai tsaye

Yayi wanka,ya shirya cikin ƙananan kaya,jeans blue black da t-shirt sky blue sai ƙamshi ke tashi,ya fito ya wuce main palour

Waɗanda ya gani a palourn ne yasa shi murtuƙe fuska ko kallonsu bai yi ba ya wuce dinning area ya ɗauko ruwa a fridge sannan ya sake dawowa palourn

Sai a lokacin suka gan shi,ya ce "ina wuni Ammi"

"Lafiya ƙalau.....yau ka dawo da wuri"

"Ba aiki ne da yawa"

Juyawa yayi kamar zai fita,Ammi ta ce "baka ga Hajiya Karime ba ne?"

Wani irin kallo ya mata ya ce "ban lura da ita bane,sannu da zuwa"

Murmushi ta yi ta ce "yawwa my boy,ya aiki?"

A taƙaice ya ce "lafiya" ya juya ya fita,binshi kawai suka yi da ido

Yana fita Farha ta tashi da sauri ta bi shi,a balcony ɗin part ɗinshi ta isko shi ya zauna,ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya,yana shan ruwan da ya ɗauko,a lokaci ɗaya kuma yana dannan wayarshi

Jawo ɗayan kujerar tayi ta zauna ita ma tana kallonshi,bai ma nuna yasan da mutum wurin ba,ya sa waya a kunnenshi

"Yasna kina ina?"

"Ina gida"

"Ke dalla nasan kina gida,gida a ina?"

Dariya tayi sannan ta ce "oh sorry,ina ɗakin mu"

"Ki kawo mun snacks part ɗina,kiyi sauri kuma dan inaso inci kamin a kira sallah"

"Laaaa ashe ka dawo,to gani nan zuwa"

Kashe wayar yayi ya cigaba da dannawa

Farha da ke ta aikin kallonshi,ta ce "my dear baka ganni bane?"

Ko ɗaga kai baiyi ba bare ya mata magana,hannunta ta kai zata ta6a shi,a tsawace ya ce "don't you dare touch me,or else i will break the useless hand into pieces"

Wani kallon shagwa6a ta ke mishi kamar zata yi kuka,ya ce "stupid"

Ya tashi ya shiga palour ya barta nan,ta ce "ina tausayinka duk randa ka shigo hannuna,ba dai ni kake wulaƙantawa ba ko"

Ta tashi ta wuce,a  kunnen Yasna duk abunda ta faɗa dan basan ta iso wurin ba,saboda ta bata baya

"Mahaukaciya kawai,sai na gani da ke da Sweet Bro waye abun tausayi,dani kike zancen ai" ta raka ta da harara,dan ta bi hanyar parking area,tayi tsaki sannan ta shiga palourn Yayan nata........... 








🥰UMMEETA🥰.......📝



♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

          *ZUCIYA ƊAYA* 

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
[8/3, 2:20 AM] Ummeeta❤‍🔥❤️: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA DAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin qirqirar shi nayi,idan yayi daidai da rayuwaru wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 7*


Kwance ta isko shi kan kujera, fuskar nan ba annuri, ta ajiye plate ɗin snacks ɗin sannan ta zauna gefen shi ta ce

"Sweet Bro!"
Buɗe idanunshi yayi sannan ya tashi ya zauna

Jan center table ɗin yayi gabanshi ya fara ci a hankali, sai yaji gaba daya ma baya jin daɗinshi

"Bani fresh milk" ya faɗa yana kallon Yasna, wacce ita ma shi take ta kallo

Tashi tayi ta ɗauko mishi tare da cup, ta zuba ta ba shi

Sai da ya gama sha sannan Yasna ta ce "Sweet Bro,dan Allah ka saki fuska mana, i hate to see you in this condition"

Kallonta yayi sannan yayi wani guntun murmushi ya ce "i'm sorry dear, waɗancan mutanen ne suka canza mun mood wallahi"

"Ai idan da sabo ya kamata ace mun saba, yau ma wani munafurcin ne ta zo tayi"

"Ni gaba daya ma i don't have any idea on how to deal with them, i don't know what to do,more especially Farha, i hate that girl wallahi" ya faɗi maganar cikin jin haushi da 6acin rai

"Hanya ɗaya ce zata maka maganin Farha"

"Wace hanya kenan?" ya faɗa cikin neman ƙarin bayani

"Kawai wata budurwa zaka samu ka kawowa Ammi a matsayin wacce kake so"

Dariya yayi, ya ce "idan kuma nace bakya kawo wuta sai kice na raina wayonki ko?" 

Cikin muryar shagwa6a ta ce "but this is a good idea Sweet Bro"

"Na sani, it's a good idea,amma kinsan Ammi, kinsan abunda zata ɗauka da wanda ba zata ɗauka ba"

"Kamar ya?"

Ajiyar zuciya yayi ya tashi tsaye yana duba wrist watch ɗinshi, ya ce "zan wuce masallaci, idan kin shiga ki gayawa Yasmin ku shirya after magrib zamu tafi gidansu Sajjad, okay?!"

"Yawwa Sweet Bro, kaman kuwa kasan yau Intisar bata zo makaranta ba, kuma wayarta switch-off"

"To naji, yanzu dai you should get ready before i come back"

"Ok"

Tattara kwanonin tayi ta bi bayanshi suka bar part ɗin

Kitchen ɗin da ke main palour ta nufa da kayan, Inna Asabe ce a ciki tana haɗa girkin dare, sai ta miƙa mata snacks ɗin "Inna Asabe ga wannan sai ki haɗa da sauran ki kaiwa su Hafsa"

"To Yasuna mun gode kinji, Allah yayi albarka"

"Ameen,Inna na fa gaya miki Yasna ba Yasuna ba" ta ƙarasa maganar tana dariya, dan kullum sai sunyi drama da Inna Asabe akan sunanta

"To ai ke sunan naki ne ba irin na mu ba"

Dariya tayi ta ce "kedai kawai kice ba ki iya ba"

Ita ma Inna Asaben dariya tayi, sannan Yasna ta kai cup ɗin cikin sink ta fita

Ammi ta gani da Hajiya Karime suna fita daga palourn, da alama wucewa Hajiya Karime zata yi

"Gwara dai ki wuce dan kin takura mun ni da gidanmu" daga haka ta haura upstairs ta shiga ɗakinsu

Babban ɗaki ne shi ma daya ji kayayyaki ciki, kallo ɗaya zaka ma ɗakin ka gane cewar na mata ne, sannan komai da ke cikin ɗakin purple ne da baby pink

Kan gadonsu ta hau da gudu tana dariya, wani mugun kallo Yasmin ta mata wacce ke kwance kan gadon tana game a laptop

"Wai Yasna yaushe za kiyi hankali ne for God Sake?"

"Ke dalla can fitinanniya, wani albishir na zo miki da shi"

"To sai aka ce idan kinzo ki mun hauka?"

"Kaiiii.....ni ce mahaukaciya ma ko? To na fasa gaya miki ma" zata sauka daga kan gadon kenan Yasmin ta tashi zaune da sauri ta riƙe ta

"Haba twinny i'm sorry, gaya mun kinji"

Tana wani turo baki ta ce "mutum sai son gulma ga rashin haƙuri.....to Sweet Bro ne yace after magrib zai kaimu gidansu Intisar"

Da sauri ta ce "are you serious?"

"Yeah"

"Yeeeeyyy.....love you Big Bross"

Wani kallo Yasna ta mata sannan ta ce "to sai ki tashi kiyi sallah ai"

"Ba za'a yi ba, ina ruwanki da ni"

Sai da ta sauka kan gadon sannan ta ce "kar Allah ya sa kiyi, wallahi Allah ya ƙona ki ba ruwanmu" ganin tayi Yasmin ta taso kamar zata biyo ta, da gudu ta bar ɗakin

"Matsoraciyar banza kawai" ta tashi ta shiga toilet







Hanan da Yuhanees ne suka shiga ɗakin da sallama, Siyama ce kawai a zaune tana karanta wata jarida dake ɗakin

Sai da suka ajiye kwandon abincin sannan Yuhanees ta ce "sisto ina Ummi?"

"Tana toilet alwala take yi"

Hanan ta ce "Alhamdulillah, jiki ya fara sauƙi"

Yuhanees ta ce "ai sai dai mu gode ma Allah"

Ummi ce ta fito daga toilet ɗin, tana tafiya a hankali, Siyama ta tashi da sauri ta shimfida mata carpet, Yuhanees kuma ta riko ta har ta hau carpet ɗin

"To sannunku,Allah ya muku albarka"
suka haɗa baki wurin cewa "Ameen"

Hanan ta ce "Ummi a zaune zaki yi sallah ko?"

"Haka dai aka ce,amma ai zan iya yi a tsaye"

"To shikenan"
Haka kuwa tayi sallanta a tsaye, dan ba laifi anyi nasarar aikin, ba wata matsala

Bayan ta gama, suka zuba mata taliyar da suka kawo taci,su ma suka zuba na su suka ci

Bayan sun gama ne mahaifiyar Yuhanees ta shigo ɗakin

Da gudu Siyama ta faɗa jikinta "Sannu da zuwa Umma"

Da fara'a ta amsa "yawwa Sima ya jikin Umminki?"

"Da sauƙi sosai"

"Masha Allah"

Zama tayi akan kujerar da Hanan ta bata ta, gaisawa suka yi da Hanan da Yuhanees, sannan ta gaida Ummi

"Ummin Siyama ya jiki"

"Alhamdulillah, jiki sai dai a gode ma Allah"

"Allah ya ƙara sauƙi, Allah yasa dai ba kiyi fushi ba, ban samu zuwa ba sai yau"

"A'a wallahi ba komai, ai kuna ƙoƙari, kullum Yuhanees na asibitin nan tun safe sai dare, ai kema nasan akwai uzuri"

"Haka ne ai an zama ɗaya kuma, Allah dai ya ƙara lafiya"

"Ameen ameen"

Wata nurse ce ta shigo ɗakin ta sake duba jikin Ummi, ta bata wasu magungunan kuma sannan ta fita

Suma Hanan da Yuhanees fita suka yi harabar asibitin suka zauna

Hanan ta tsura ma wuri ɗaya ido tana kallo, sai tunani kawai take yi, Maganar Yuhanees ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta faɗa

"Hayatee tunanin me kike yi haka ina ta magana shiru? Ummi dai taji sauƙi bare in ce jikin Ummi ne ke damunki"

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "rabin rai zuciyata ce ke son jawo mun abunda ba zai ta6a yiwuwa ba"

Cikin rashin fahimta Yuhanees ta ce "ban....bangane me kike nufi ba, kamar ya?"

"Zuciyata tana hango mun abunda ya fi ƙarfina, kiyi hakuri bazan iya gaya miki ko menene ba yanzu, amma zan gaya miki wani lokacin"

"Idan har abunda take hango miki alkhairi ne, Allah ya ba ki, idan kuma ba alkhairi Allah ya cire miki shi gaba ɗaya ko ma menene"

"Ameen rabin rai, nagode"

Daga haka suka cigaba da hirarsu ta duniya, sai wurin ƙarfe 6:36pm sannan suka koma ciki dan suyi sallar magrib

Bayan sun idar ne, Umma da Yuhanees suka yi shirin wucewa, har titi Hanan ta rakasu sannan ta dawo

Hanan ta ce "Ummi, ɗazu sai da muka tafi kasuwa muka yi siyayyan kayan abinci da sauran abubuwan da bamu da su, sannan na ware 22k na makarantar Siyama, on monday zamu tafi tare sai a biya dan naga gobe friday ba lallai a sa me shi ba"

"To ai ni Hanan kin bar ni cikin duhu, duk ina kika samu waɗannan kuɗaɗen haka?"

"Yuhanees ce ta bada dubu ɗari biyu lokacin da muna neman na yi miki aiki, kuma da AAJ ya biya sai ta ce muyi amfani da su kawai, shi ne ɗazu ta raka ni muka shiga kasuwa"

"Allah sarkin sarauta, mai kyauta da ƙari, Allah yayi albarka, mun gode sosai wallahi"

"Ameen, shi ne dama abunda nake ta so in gaya miki.....ke kuma Siyama ki shirya, monday za ki koma makaranta"

Cikin farinciki Siyama ta ce "kai alhamdulillahi,naji daɗi sosai...ai ma za'a sallame kafin monday ko?" ta ƙarasa maganar da tambayar Hanan

"To may be, ban sani ba dai"

"Allah ya sa su sallame mu ma"

"Ameen"



***************


"Wai ina Yasna?" 
AAJ ke tambayar Yasmin, tun ɗazu suke zaune palour suna jiranta

"Bata gama kwalliya ba" cewar Yasmin

Ammi ta ce "sai in rasa wace irin kwalliya take yi, kamar wacce zata canza fuska!?...kuma da daddare ma wa zata yi wa kwalliya?"

AAJ yayi dariya ya ce "Ammi kika sani ko zata samo miki sutuki ne"

"Sai dai idan Sajjad ɗin ne suruki na"

"Haba dai, Sajjad kam yana da budurwa ai"

"Na ba shi yayi ta biyu"

"A'a sweetie na first lady ce"

"Hmm" Ammi ta faɗa tana ta6e baki

Da sauri ta sauko daga stairs ɗin "i'm so sorry Sweet Bro, i kept you waiting"

"Ni dai wuce mu tafi" ya faɗa yana miƙewa tsaye shi da Yasmin

"Ammi sai mun dawo"

"Allah ya kiyaye, ka gaida mun Hajiya Sumayya"

"Zata ji"





Horn yayi a bakin gate ɗinsu Sajjad, da gudu gateman ya buɗe dan ya san shi, ya tsaya suka gaisa ya ba shi kuɗi sannan suka ƙarasa ciki

Direct palourn gidan suka shiga, Intisar ce kawai a ciki tan kallo, tana ganinsu ta tashi tana ihu, sai da suka rungume juna, sannan Intisar ta samu damar gaida AAJ

 "Ina wuni Ya Arshad"

"Yanzu kika ganni?"

"I'm sorry" ta faɗa tana dariya

"Ina Mujaheed da Hajiya?"

"Mujaheed na gidan Anty, Hajiya kuma na ɗaki bara na kirata"

Sama ta haura, bayan minti uku sai ga su sun fito tare

"Arshad ashe kai ne da waɗannan fitinannun yaran ko?"

Dariya yayi ya tsugunna ya gaida ita, yana gaya mata saƙon Ammi cewa tana gaisheta

Yasmin ta ce "yanzu Hajiya mune fitinannu?"

"Eh mana, ni dai ku wuce ɗakin Intisar gaisuwar ma na yafe"

Dariya suka dukansu su uku suka wuce abunsu

"Hajiya Sajjad fa?"

"Yanzu ya bar nan, yana ɗakinshi"

"Ok" sai ya wuce zuwa ɗakin Sajjad ɗin, ita ma Hajiya komawa tayi ɗakinta

Da sallama ya shiga ɗakin, zaune yake kan cushion ɗin dake ɗakin yana waya

Zama yayi kan gado yana kallonshi, sannan yayi tsaki ya ce

"Mtwss....ji be shi kaman na kirki, sai wani kashe murya yake yi"

Kashe wayar Sajjad yayi yana dariya bayan ya ce "i will call you later baby"

"Su baby anji jiki"

"Daɗin abun dai kaima ka ɗau hanya, zaka fara kashe naka muryan"

"Mtwss ni dai ba wannan ya kawo ni ba, magana ce akan Farha, yarinyar nan ta fara shiga gonata da yawa fa"

Gyara zama Sajjad yayi ya ce "to ai kaine baka so yin maganinta ba Super"

"Kamar ya ban so yin maganinta ba?"

"Kawai wata zaka kawowa Ammi a matsayin wacce zaka aura"

"Hmm Ammi ba zata yarda ba, saboda wacce nake so ba masu kuɗi bane, talakawa ne"

"Wacce ka ce mun kai kayi sa'ar samunta ɗazu?"

"Eh"

"Tirƙashi....amma kar ka tada hankalinka,zan samo mana mafita insha Allah"

"To Allah yasa mafitar tayi aiki"

"Ameen.....yawwa ɗazu Khairat ta kawo mun takarda"

"Eh, ina fatar an kaiwa Mr Joseph"

"Eh an kai mishi"

"To kayi ƙoƙarin fitowa da wuri gobe, dan ina so a fara meeting ɗin da kai"

"Insha Allah, kaima kar ka biya wurin surukarka sai idan mun gama ka tafi" ya ƙarasa maganar yana dariya

Shi ma Arshad dariyar yayi ya ce "ai gobe bazan tafi ba ma saboda wannan issue ɗin"

"To da ya fi kam"
Daga haka suka cigaba da hirarsu, sai ƙarfe 9:43pm sannan suka fito suka wuce, bayan sunyi ma Hajiya sallama.............







🥰UMMEETA🥰.......📝




♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
[8/3, 2:20 AM] Ummeeta❤‍🔥❤️: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA DAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin qirqirar shi nayi,idan yayi daidai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏



 *Page 8*


     _Washe Gari_


Dr Yusuf ne ke duba Ummi, wata nurse na tsaye daga gefenshi, bayan ya gama dubata, yayi rubutun da zai yi, sai ya ce

"Hanan ina tunanin yau ɗinnan za'a sallameku, dan naga jikinta alhamdulillahi"

Hanan cikin farinciki ta ce "to Dr mun gode"

"Amma sai da yamma"

"Ba matsala Allah ya kaimu"

"Ameen" 

Fita suka yi shi da nurse ɗin.Hanan komawa tayi ta zauna kan kujera tana ƙara yi wa Ummi sannu, Siyama kam na kan tabarma tana ta bacci

Wayarta ce ke ƙara hakan yasa ta duba agogon wayar Ummi, ƙarfe 7:02am 

"Ikon Allah,wa ke kirana tun da safe haka?"

Ummi ta ce "to ki ɗauka mana"

"Ai number ce, ga ta kuma special ce"

"Umm, kiyi bismillah kawai ki ɗauka kar ki tayar mun da yarinya"

Dariya tayi ta kai hannu zata ɗauka sai kiran ya tsinke, kafin tayi wata magana wani kiran ya sake shigowa

Ɗauka tayi ba tare da tace komai ba, sai da aka kusan 3mins sannan daga ɗayan 6angaren aka ce

"Kina tsoron kar a sace ki ne?"

Wani guntun murmushi tayi dan ta gane mai muryar, sai yanzu ma ta tuna da ta ba shi numbernta

"A'a ba tsoro nake ji ba"

"Kuma shi ne kika yi shiru?"

Wani murmushin ta sake yi ta ce "kawai dai na rasa me zan ce ne, kar nayi sallama ya kasance ba musulmi bane"

"Ok ta nan ki bullo kuma?.....to shikenan dai, kin tashi lafiya?"

"Lfy qlw"

"Ya jikin Ummi"

"Da sauƙi sosai"

"Allah ya ƙara sauƙi, ki gaisheta pls"

"Za ta ji insha Allah"

"Yawwa bye, take care"

"Uhmm"

Katse wayar suka yi a tare, sannan ta kalli Ummi da ke kwance abunta, ta ce

"Ummi AAJ ne, yace yana gaida ke"

Ba tare da neman wani ƙarin bayani ba ta ce "ina ansawa"

Ba wanda ya sake magana cikinsu, sai dai kowa da tunanin da ke ranshi



****************

AAJ ne ya fito daga office ɗinshi, wurin Khairat ya tsaya wacce ita ma a tsaye take tana haɗa wasu takardu cikin sauri

"Ya dai Khairat?...ki yi a hankali mana, ba su ƙaraso ba ma ai"

Da sauri ta kalle shi dan bata ma san yana wurin ba

"Oh God" ta faɗa tana dafe ƙirji haɗi da sauke ajiyar zuciya tana rufe ido

Wani kallo ya mata yana ɗaga gira ɗaya sama ya ce "have i scared you?"

Kai ta ɗaga mishi kawai, ya ce "sorry, you should meet us at the meeting hall when you're through, but you have to hurry up"

"Ok sir" 
Ya bude ƙofar kawai ya fita, a hanya suka haɗu da Sajjad, shi ma meeting hall ɗin za shi, sai suka ƙarasa tare

Suna shiga sai ga Mr Joseph shi da wasu mutane biyu, gaisawa suka yi sannan suka zauna, Khairat ita ma ta shigo ta zauna

Sun ɗauki kusan awa ɗaya da rabi suna abu ɗaya, kafin daga bisani suka yi concluding kowa ya wuce inda za shi


Office ɗin AAJ Sajjad da Arshad ɗin suka koma, zama suka yi kan cushion ɗin da ke office ɗin, dukansu fuska ba annuri

Sun kusan 10mins a zaune, sannan Sajjad ya ce "wai super meyasa ka dage akan hana musu kayan ne?"

"Ba na gaya maka muna binsu kuɗi bane"

"To wai har nawa ne da har ka ƙi yarda a ƙara musu wasu, ga shi kaya masu yawa suke so, zamu samu riba sosai fa"

"Almost 33million ake binsu, sannan muhimmin abunda ma ya hanani basu kayan, akwai abunda nake zargi ne shiyasa"

"Zarginsu kake yi?"

"Sosai"

"Amma ai mun daɗe muna harƙalla da su"

Gyara zama yayi ya ce "Sajjad mutum na iya canzawa ko wane lokaci, haka ma kuɗi na iya sauya mutum, kawai a bar maganar"

"Shikenan tunda haka kace, Allah ya kyauta"

"Ameen"

Cikin kawar da zancen Sajjad ya ce "to mun sallame ka, tashi ka tafi"

Kallon rashin fahimta ya mishi ya ce "ina?"

"Wurin surukarka mana"

Murmushi mai kama da dariya yayi ya ce "a'a yau bazan tafi ba, ai na kirata"

"To wai yaushe zamu je in ganta ne"

"Very soon insha Allah, bari su koma gida"

"To Allah ya bata lafiya......bari in wuce, akwai aikin da zanyi" ya faɗa yana miƙewa tsaye

Shi ma Arshad tashi yayi tsaye yana faɗin "nima dai inada abunyi, we shall meet later"

Gyaɗa kai Sajjad yayi ya fita daga office ɗin, shi ma AAJ sai da ya fara haɗa ma kanshi coffee sannan ya wuce kan kujerarshi ta aiki 






**************


Da misalin ƙarfe 5:22pm aka sallami su Hanan suka koma gida

Maƙwabta sai shigowa suke yi su na mata ya jiki, Hanan da Yuhanees kuwa sai ƙoƙarin haɗa musu abincin dare suke yi, Siyama kuma na wurin wata ƙawarta nan maƙwabtansu

Suna bakin murhun zaune, wayar Hanan tayi ƙara, kallo ɗaya tayi ma numbern ta gane ta

Ɗauka tayi haɗi da yin sallama, sannan ta ce

"Ina wuni"

"Lafiya ƙalau, ya kike" ya amsa mata

"Lafiya"

"Ya jikin Ummi"

"Da sauƙi, mun dawo gida ma"

"An sallame ku ne?"

"Eh, bamu daɗe da dawowa ba ma"

"Masha Allah, ban daɗe da na dawo gida ba, na gaji sosai, may be dai gobe zamu zo, tunda saturday ba da wuri nake fita ba wani lokacin ma ban zuwa"

"To Allah ya kaimu"

"Ameen.....me kike yi?"

"Abinci" ta ansa a taƙaice

"Ashe dai kin iya abinci, nayi sa'a kenan"

Cikin rashin fahimtar inda maganarshi ta dosa ta ce "hmm"

Murmushi yayi dan ya san bata gane me yake nufi ba, ya ce "we'll talk later, take care"

"Nagode"

Kashe wayar tayi tana sauke ajiyar zuciya, Yuhanees dake ta kallonta tun da ta fara wayar ta ce "Hayatee wa kika samo mana kuma haka?"

"Ke malama AAJ ne fa, jiya ya kar6i number na dan ya ji jikin Ummi"

Wani kallo Yuhanees ta mata, irin ta ma raina mata wayo, sai dai ta ce "Allah ya tabbatar da alkhairi"

Harararta tayi ta ce "ke dai kika sani"

Dariya Yuhanees tayi ba tare da tace komai ba suka cigaba da aikinsu



 

A 6angaren AAJ kuwa, bayan ya kashe wayar, ya ce ma Yasna dake zaune tana ta kallonshi, dan su na main palour, ita Yasmin gaba ɗaya hankalinta na wurin kallon da take yi

"Ke don't swallow me mana"

Dariya tayi ta ce "who's she?"

"To shugaban magulmata, antynki ce"

"Serious?"

"Zan miki ƙarya ne?"

"A'a" ta faɗa cikin murna "to kira mun ita mu gaisa"

"A'a ba yanzu ba, sai nan gaba"

"But why?" ta faɗa cikin  shagwa6a66iyar murya

"Ba yanzu ba na ce"

Gudun kar ya mata faɗa ya sa tayi shiru kawai

Tashi yayi ya ce "Yasmin"

"Na'am"

"Ku tashi lokacin magrib yayi, Yasna ke ma ta shi"

Ansawa suka yi, lokaci ɗaya suka tashi suka hau sama, shima fita yayi ya wuce masallaci



*********************



"Ta ya za'ayi ace an taya mishi irin wannan ribar amma ya ƙi amincewa"

"Yalla6ai ina tunanin ko ya gane wani abu ne"

"Bana tunanin haka gaskiya, dan AAJ mutum ne mai saurin yarda kuma be cika zargin mutane ba, musamman waɗanda ke tare da shi"

"To yanzu ya zamu yi kenan?"

"Ai idan ya san wata bai san wata ba.....zan canza salo, dan hankalina bazai ta6a kwanciya ba indai burina bai cika ba"

"Burinka ma zai cika yalla6ai, nasan halinka kuma na yarda zaka iya"

**************








🥰UMMEETA🥰.......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirar shi nayi,idan yayi daidai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri akasi aka samu👏👏👏


 *Page 9*


Da daddare bayan su Arshad sun gama cin abinci, kowa ya wuce ɗakinshi

Kwantawa yayi kan Italian bed ɗinshi bayan yayi wanka yayi alwala, yayi dailing numbern da yayi saving da Hanny, sai da ta kusa katsewa sannan aka ɗaga

"Haba your highness, wayar ma sai kin ga dama za ki ɗauka?"

Cikin jin kunya da mamakin sunan da ya kirata da shi ta ce "a'a ba haka bane, shigowata ɗakin kenan"

"Ai na ɗauka duk cikin mulki ne"

"Mulki ai sai a gidan sarauta"

"To ai kema sarauniya ce"

Buɗe manyan idanunta tayi kaman yana ganinta ta ce "sarauniya...!!!, a ina?"

"Ba ki sani ba?"

Girgiza kai tayi ta ce "a'a bansani ba"

"Shikenan zan gaya miki, amma ba yau ba"

Murmushi tayi sannan ta ce "to ba damuwa"

"Yawwa ya jikin Ummi"

"Da sauƙi sosai ma, tayi bacci"

"To ke ma je ki kwanta, sai da safe.....yawwa, kar ki manta zamu zo gobe"

"Allah ya kaimu, amma kai da waye?"

"Ƙanina" ya faɗa yana murmushi

"To Allah ya kaimu"

"Ameen, sweet dreams, bye"

"Same to you"

Kashe wayar suka yi, kowa na jin wani yanayi cikin ranshi

Ta ƙara gyara katifarta ta je tayi alwala ta kwanta, ƙarar shigowar saƙo taji, numbern AAJ ne, da sauri ta duba, wani Goodnight message ne ya turo mata mai daɗin gaske, sau uku tana karantawa sannan ta iyayin reply da "tnx" dan bata ma san me zata tura mishi ba da ya wuce hakan

Harafi uku kawai ta tura mishi, amma ya tsinci kanshi da jin daɗin reply ɗinta, sai da yayi nafilolin da yake yi sannan ya kwanta, wani daddaɗan bacci ya ɗauke shi


***************

"Farha!!!" sai a yanzu ta ji kiran da ƙawarta ke mata, kallonta tayi ta ce "ya aka yi?"

"Tunanin me kike yi ne haka wai? Ina ta magana amma kin yi shiru"

Cikin damuwa ta ce "Samira wai dan Allah ba na da kyau ne?"

"Wannan wace irin tambaya ce?....ai ko munafuki ba ze ce ba ki da kyau ba Farha, ba abunda kika rasa"

"To meyasa Arshad ke wulaƙanta ni ne?"

"Mtwss, har kin bani haushi wallahi, yanzu akan namiji ne kika shiga wannan damuwa haka?"

"AAJ ne fa"

"To ai naga kuɗinshi kike so ba shi ba ko"

"Da AAJ da kuɗinshi nake so, ba wai kuɗin kaɗai ba"

"Hmm, ke kika so wahalar da kanki, amma da tuni an wuce wurin"

Cikin 6acin rai ta ce "dan Allah Samy ki kyaleni, i hate nonsense kin sani......idan kin gama shirin ki tashi mu tafi, past 11 yanzu" ta ƙarasa zancen tana fita daga ɗakin

Kallo Samira ta bi ta da shi ta ce "iska na wahalar da mai kayan kara" daga haka ita ma ta ɗauki wani ƙaramin gyale ta bi bayanta

****************

2:14pm
Arshad ne da Sajjad tsaye a bakin ƙofar gidansu Hanan, sun jingina jikin motarsu

Siyama ce ta fito, suna haɗa ido da AAJ ta washe baki, ta ƙaraso kusa da su

"Sannu da zuwa Yayana"

"Yawwa ƙanwata, ya gida?"

"Lafiya ƙalau" kallon Sajjad tayi ta ce "ina wuni"

"Lafiya ƙalau ƴammata"

"Wai ku shigo inji sister"

"Ok"

Bin ta suka yi zuwa cikin gidan, a bakin zauren gidan suka tsaya, dan anan aka musu shimfiɗa

"Ku zauna" ta faɗa, ta wuce cikin gidan, zama suka yi kan tabarmar su na ƙara bin wurin da kallo

Hanan ce ta yi sallama ta ƙaraso zauren, hannunta ɗauke da tray da ruwa a ciki da drinks

Tun da ta shigo idanunsu ke kanta musamman AAJ shi da yake jin wani irin yanayi

Ajiye tray ɗin tayi, sannan ta gaishesu, Sajjad kawai ya ansa mata, kallon AAJ yayi ya ga ita yake kallo, a hankali ya kai hannunshi kan ƙafar Arshad ya muntsile shi

Wani wawan kallo yayi ma Sajjad, shi kuma sai danne dariyarshi yake yi, ya ce "ina gaida kai"

Kallonta suka yi suka ga tana murmushi kanta a ƙasa, tana ɗaga kai suka haɗa ido da AAJ, ba shiri ta miƙe ta yi cikin gida

Dariya Sajjad ke yi sosai yana kallon Arshad da ya wani ɗaure fuska

"Haba, irin wannan kallo haka?"

"To ina ruwanka, sa idon banza kawai"

Dariya ya sake yi ya ce "amma fa in dai ita ce Hanan, to kayi sa'ar samun kyakkyawar mace, sai kace shuwa arab!....ina fatan yadda fuskarta take da kyau haka ma zuciyarta ta ke"

A hankali AAJ ya ce "ameen" dan har yanzu fuskar nan a ɗaure ta ke

Siyama ce ta shigo zauren riƙe da wani tray da cups a kai, Hanan na bayanta, nan tsakiyar tabarmar ta ajiye

Sannan suka zauna suka sake gaisawa

Arshad ya ce "ya jikin Ummi"

Hanan ta amsa "alhamdulillahi, tace ma ta na gaida kai"

"Ina amsawa"

Siyama ta kalli Sajjad sannan ta kalli Arshad ta ce "Yayana meyasa ba ka zo da ƙannenka mata ba ka zo da ƙaninka"

Kallon Sajjad Arshad yayi yana ɗan dariya, ya ce "matsawa yayi akan lallai sai ya biyoni"

"Ke waye ƙaninshi, da wa kike" Sajjad ya faɗa ya na wani kumburo fuska

Kallonshi tayi ta ce "kai mana"

"Wa ya gaya miki haka, ni ba ƙaninshi bane, don't repeat that rubbish"

Hanan ta ce "amma ai ce mun yayi da ƙaninshi zai zo"

"May be yan da wani ƙanin ban sani ba" tashi tsaye yayi ya ce "idan kun shiga ina gaida Ummi, kai kuma idan ka gama ina jiranka a mota" ya fita bai sake cewa komai ba

Hanan ta ce "dan Allah ka ba shi haƙuri, wallahi ba mu san ba ƙaninka ba ne"

Yana ƴar ƙaramar dariya ya ce "just forget about him, haka muke ni da shi, munyi one one ne ai......shi aminina ne kuma ɗan uwana, ni da shi kamar twin brothers muke, so don't bother yourself, i know how to calm him down,okay!?" ya ƙarasa maganar yana ɗaga gira

Girgiza kanta kawai tayi tana murmushi

Shi ma tashi yayi yana duba agogon hannunshi ya ce "zamu wuce"

"Amma ko ruwa ba ka sha ba"

Kallon Siyama yayi ya ce "je ki ce ma ƙanina ya ba ki saƙo injini" sai da suka yi dariya ita da shi sannan ta fita, ya mayar da kallonshi kan Hanan ya ce 

"Kar ki damu da rashin shan ruwana, wani lokacin abincinki ma zanci"

"To shikenan" ta amsa ba tare da fahimtar ainihin abunda yake nufi ba

Shi ma dai murmushi yayi dan ya san bata gane nufinshi ba

Siyama ta shigo ɗauke da wasu manyan ledodi a hannunta, ta ce "ga shi Yayana"

"Ki kai ciki, na ku ne"

"Mun gode Yayana, Allah ya saka da alkhairi"

"Ameen ƙanwata"

Har ƙofa Hanan ta rakashi, ya ce "ina zuwa"

Zuwa yayi ya buɗe motar ya ɗauko wata leda madaidaiciya ya bata, ya ce "this is for u"

Sai da ta gama kallon ledar sannan ta kar6a ta ce "nagode"

"Ki gaida Ummi sosai sosai, sai na kiraki"

"Zan gaya mata, Allah ya kiyaye, mun gode"

"Ameen, sai anjima" ya juya ya shiga mota ita kuma ta shiga gida

Kwance ya tarar da Sajjad a gefen mai zaman banza, kamar wani mai bacci

Ba abunda Arshad yace mishi, ya tada motar kawai ya ɗauki hanya, shi ma tun da ya shiga motar yana sane amma ya share shi


Trays ɗin ta kwashe bayan ta shiga gida ta wuce dasu, Siyama kumata dawo ta naɗe tabarmar...........


*******************

"Malam, ni fa so nake kawai wannan karon ayi aikin nan direct akan Arshad"

"So nawa zan maimaita miki bazan iya yin ko wane irin aiki akanshi ba,...Arshad fa mutum ne da sam baya wasa da addini, ba zamu ta6a samun galaba akanshi ba, mu haƙura kawai"

"Mu haƙura fa kace!?...lallai baka san burina bane har yanzu shiyasa, amma ba komai, idan kai ba za ka iya ba, ni na san me zanyi" tashi tayi a fusace ta fita daga cikin ɗan ƙaramin ɗakin malamin ta na huci

Bin ta da ido Malamin yayi, ya ce "ni dai ba zan wahalar da kaina ba akan abunda nasan bazan iya ba, Allah ya raka taki gona"
Daga haka ya cigaba da jan carbin hannunsa yana wasa da ƙasar dake cikin tray a gabanshi...............








Manage this pls👏🥰


🥰UMMEETA🥰.......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         *ZUCIYA ƊAYA* 

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirar shi nayi,idan yayi daidai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri akasi aka samu👏👏👏


Wannan page ɗin naku ne Feeza Ƴar India🥰 da Hussaina Usman🥰, kuyi yanda kuke so da shi😘🥳💃
Na ji daɗin comment ɗinku sosai, Allah ya saka da alkhairi🥰❤‍🔥

 *Page 10* 

Waya Hanan ke yi da Yuhanees da daddare, tana gaya mata AAJ ya zo, sakamakon a yau ɗin nan suka yi tafiya zuwa ƙauyensu ita da Ummanta, ƙanin babanta ya rasu

"To me ya kawo miki?"

"To nima ban buɗe ba, amebo kawai"

Dariya Yuhanees tayi ta ce "to shikenan, tun tafiya ma ba tayi nisa ba kin fara 6oye mun abu ko"

"Tafiya kuma da wa?"

"Da AAJ mana"

"Ke dalla malama banson shirme"

"Oh shirme ne ma kenan!"

"Kin ga sai da safe, gidan mutuwa kike kina ta surutu, ki gaida Umma"

"To idan ya kiraki ina gaidashi"

"Haka na gaya miki?"

"Ai ba sai kin faɗa ba"

"Hmm, bye" kashe wayar tayi ba ta jira jin me za ta ce ba, dan ta san idan ta biye mata ba kashewa za ta yi ba

Zuwa tayi ta ba Ummi maganinta sannan ta dawo ɗakinsu, Siyama sai faman gyara litattafanta ta ke yi

Zama tayi bakin katifar ta ce "oh Allah Siyama, gobe Sunday fa ba Monday ba"

Dariya tayi ta ce "wallahi nayi missing ɗin makarantar ne, 3weeks fa ban tafi ba"

"To ai in da rai kamar gobe ne"

"Allah ya kaimu to"

"Ameen, yanzu ki tashi kiyi alwala, ki je ki kwanta, yanzu Ummi ke cewa ba ki zo kin kwanta ba"

"To"
Tattare litattafan tayi, ta je tayi alwalan sannan ta wuce ɗakin Ummi, dan can take kwana


Ita ma Hanan alwala tayi sannan ta zo ta zauna kan katifarta, ta jawo ledar da Arshad ya bata, ta buɗe

Turaruka ne a ciki guda huɗu na manyan mutane masu ƙamshin gaske

Ɗaya bayan ɗaya ta buɗe su tana jin ƙamshinsu, sannan ta jawo wani ɗan ƙaramin kwali da ya rage cikin ledar, ta buɗe, ƙaramin akwati ta gani mai shape ɗin heart, ta daɗe tana kallonshi sannan ta buɗe, bracelet ne a ciki silver colour, sai sheƙi yake yi mai masifar kyau, daga tsakiyanshi heart ne wanda aka rubuta _BE MY LOVE_ a ciki

Gaba ɗaya ɗan hannun ya tafi da imaninta, sai kallo take yi ta gagara ɗauke idonta.Wayarta tayi ƙara, hakan ya haddasa mata faɗuwar gaba, tana jin haka ta gane mai kiranta, dan ta fahimci in dai ta ganshi ko ya kirata sai gabanta ya faɗi wanda ta rasa dalilin hakan

Jawo wayar tayi da sauri dan ta kusa tsinkewa, ta ɗaga

"Assalamu Alaiki" ya faɗa a hankali

"Wa'alaikas salam"

"Ƴan mata, ya kike"

Dariya tayi a hankali ta ce "lafiya ƙalau"

"Dariya na ba ki?"

Shiru tayi ba ta ce komai ba, ya ce "to ya jikin Ummi?"

"Alhamdulillahi, taji sauƙi"

"Allah ya ƙara mata lafiya"

"Ameen.....mun ga saƙo, Allah ya saka da alkhairi"

"Ameen, amma ki daina gode mun dan Allah"

"Ta ya hakan zai faru?"

"Ni dai na gaya miki"

"To shikenan, ka yi haƙuri"

"Ai dole, yawwa in tambaye ki?"

"Eh, Allah ya sa na sani"

"Kin sani ma,.....ina saurayinki? Ya zo duba Ummi kuwa?"

Jin tambayar tayi bambara-ƙwai, dan bata yi tsammanin wannan tambayar ba, ita ina ta ga saurayi? Idan ma har tana da shi, meye na shi na tambayarta?

"Kin yi shiru?" maganarshi ta dawo da ita

Ta ce "um...a'a ban...babu"

Murmushi yayi jin yanda take bada amsa, ya ce "bangane ba, meye babu?"

"Saurayi"

"You mean you're single?"

"Yes" ta faɗa a kunya ce

Ajiyar zuciya ya sauke, ya ce "alhamdulillah" a ranshi, dan shi kaɗai ya san yanda zuciyarshi ke bugawa kafin ta ba shi amsa, daurewa kawai yayi

A zahiri kuma ya ce "Allah ya kawo mafi alkhairi"

"Ameen"

"Akwai wani abu?"

"A'a"

"To sai da safe ko"

"Allah ya tashe mu lafiya"
Suka yi hanging wayar a tare

Kamar jiya dai, hakan ta kasance yau, ta gama gyara wuri ta kwanta, message ɗinshi ya shigo, Goodnight message ne yau ɗin ma, yau reply ɗinta "tnx, same to u"
Ya ji daɗi sosai fiye da yanda ya ji jiya
Daga haka ko wannensu ya kwanta



 ```Asuba ta gari``` 


****************


"Baby, na yi ƙoƙari na bi duk hanyar da zan bi, na samo miki aiki a kampanin AAJ, dan ina tunanin za ki mun aiki yanda ya kamata"

Ajiyar zuciya tayi tana kallon matashin dake zaune ya wani 6ararraje akan 3seater, ba zai wuce 30yrs ba

Ta ce "haba darling, kai kasan bazan ba ka kunya ba, na gaya maka ban san dalilin da yasa yaƙi amincewa da su ba, amma by God grace, burinka zai cika"

"Kullum haka kuke faɗa ke da Gboy, burina zai cika, burina zai cika, but when?" ya faɗa a tsawace

"Calm down darling" ta faɗa ta na zama kusa da shi, "i have a great plan, wanda idan muka yi aiki da plan ɗin, i'm very sure za ka ga AAJ yanda kake da burin ganinshi"

"Plan?, wane irin plan kenan?"

"Zan gaya maka, amma samu bi plan ɗin ne step by step, if not abun zai dawo kanmu, na san halinka da garaje"

"Hmm, shikenan, tell me"

Gyara zama tayi, ta zayyana mishi yanda plan ɗin nata yake, dariyar mugunta yayi, ya ce "that's why i love you baby"
Tashi tsaye yayi ya sa hannu aljihu, ya haɗe fuska kamar bai ta6a dariya ba ya ce "i will destroy you AAJ"

Murmushi tayi tana wani jujjuya idanunta saboda jin daɗin abunda ya faɗa







Ƙarfe uku da rabi, Yuhanees ta sauka gidansu Hanan, kasancewar ita kaɗai ta dawo, Yayanta, Umma da Babanta duk suna ƙauye, ta dawo ne saboda gobe zasu fara exam a makarantar da take karatu

Zama suka yi wurin Ummi suka ci abinci tare, suka yi ta hira, dan jikin Ummi kam alhamdulillahi kamar ba'a mata aiki ba

Sai kusan ƙarfe biyar sannan suka tashi suka koma ɗakin Hanan ɗin, ta nuna mata abunda AAJ ya bata sannan ta gaya mata wai yana tambayarta ko tana da saurayi

Wata irin dariya Yuhanees tayi ta ce "wallahi Hayatee wani lokacin kanki baya ja, yanzu me kika fahimta da hakan?"

"Kyautatawa"

"Kyautatawa ko soyayya?"

"Ban gane soyayya ba?"

Gyara zama Yuhanees tayi, ta ce "bari in gaya miki gaskiya, since from the first time na san AAJ yana da wata manufa a ranshi game da ke, kuma manufar ta soyayya ce, kowa ya san AAJ mutum ne mai taimako, ke na ki ya banbanta da sauran, use your number six and think, meyasa ya ce Siyama ta kirashi da Yayanta?, meyasa zai kar6a numbernki dan kawai ya ji jikin Ummi?, meyasa zai sake biyoki gida shi da abokinshi harda baki kyauta naki na daban?, ina ruwanshi idan kina da saurayi ko babu?, he just want to know weather he can have a place in your heart or not, everything is clear my dear, ki sake karanta abunda ke cikin bracelet ɗin nan, _BE MY LOVE_, ko har yanzu ba ki fahimta ba?" 

Tun da Yuhanees ta fara magana take kallonta tana nazarin abubuwan da ta faɗa

Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke, sannan ta ce "kenan abunda zuciyata ke neman jawo mini, haka ne?"

"Menene?"

"Tun ranar da na fara ganinshi a bakin office ɗin Dr Yusuf, na ji zuciyata na bugawa, da tunaninshi na kwana a raina, amma a rana ta biyu da na fahimci shi ne AAJ, sai na ji gaba ɗaya ban dace da shi ba, dan matsayinmu ba ɗaya ba"

"Hayatee, addu'a za ki yi, Allah ya za6a miki abunda ya fi alkhairi, amma ai soyayya ai ba ruwanta da matsayi"

"Hmm, Allah ya kyauta"

"Ameen,......yanzu dai tashi mu je mu taya Siyama haɗa abinci, mun barta da aiki, zamu ƙarasa maganar anjima"

"To shikenan"
Tashi suka yi suka fita dan yin aikin abincin



********************


Farha ce zaune ita da Hajiya Karime a palournsu, su na shan fruits

"Mummy, wai dan Allah yaushe za ki share mun hawayena?, na gaji da jin very soon"

"Farha, da ace kinsan ƙoƙarin da nake yi akan ki samu Arshad, da ba kiyi wannan maganar ba, Yaron ne yaƙi da shi sai an shirya"

"Mummy hanya ɗaya za ki bi, Ammi tana jin maganarki, why not ba za kiyi mata magana ba asa ranar aurenmu kawai"

"Nima na yi wannan nazarin, amma karki damu, komai zai zo ƙarshe, dan nasan abunda zanyi"

"You better do something gaskiya, idan ba haka ba ni zanyi wani abun"

"Haba Daughter, ai wannan aikin nawa ne, kwantar da hankalinki kawai"

"Much love Mumcy" ta rungumeta haɗi da mata peck a kumatu

"Bari in haɗa ma Daddaynki abincinshi kafin ya shigo"

"Ok Mum"

Tashi tayi ta wuce kitchen, ita kuma Farha ta gyara kwanciyarta kan kujerar ta na danna waya













Ina ƙara baku haƙuri na rashin yin update jiya, nagode sosai da ƙaunar da kuke ma novel ɗin nan💓
Much love🤍✨





🥰UMMEETA🥰.......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

      *ZUCIYA ƊAYA* 

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirar shi nayi,idan yayi daidai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri akasi aka samu👏👏👏



 *Page 11* 

Monday ranar aiki, masu tafiya makaranta sun wuce, masu exam ma sun wuce, ma'aikata ma kowa ya wuce wurin neman halal ɗinshi



Hanan ce a ɗakinta, gaba ɗaya ta yamutsa ɗakin sai addu'o'i kawai ta ke karantowa

Ummi ta shigo tana kallon ɗakin cikin tsananin mamaki, ta ce "Hanan lafiya kike kuwa?"

Da sauri ta juyo tana kallonta, dan ba tayi tsammanin ta tashi ba, dan ta barta ta na bacci

Cikin rawar murya ta ce "Umm...Ummi...kin..ashe kin tashi"

"Na ce me kike yi? Me kike nema?"

"Ummi na..na abun nan, ehm..yawwa ID card ɗina nake nema"

"ID card kuma? Na wurin aikin?"

"Eh"

"To ina kika ajiye shi?"

"Na manta inda na ajiye"

"Kin duba jakarki?" ta faɗa ta na ɗaukan wata jakar Hanan dake ƙasa, dan ta hargitsa komai

Kafin ma tayi magana, har Ummi ta buɗe jakar, rufe ido kawai tayi, dan ta san yana nan cikin jakar

"Kai Hanan, ba za ki iya kwantar da hankali ki nemi abu ba? Ba shi ba ne wannan?" ta nuna mata

Murmushin ƙarfin hali tayi, dan ta san ba shi take nema ba, ta ce "yawwa Ummi, shi ne kuwa, nagode" ta ƙar6a

"To je ki sa kaya ki zo ki wuce, zan gyara miki ɗakin, kar ki makara"

"A'a Ummi bari zan gyara yanzu ai, abun karyawanki na kitchen"

"To kiyi sauri, kin san halin mai gidanku"

"To Ummi"

Fita Ummi tayi, ita kuma ta ja wani stool ta zauna ta na goge zufa

"Na shiga uku ni Hanan, yanzu ta ina ma zan fara?...lahaula wala ƙuwata illa billah" addu'a take tayi kaman zata yi kuka

Tashi tayi ta kimtsa ɗakin jiki a sanyaye, dan ta san zama bazai mata magani ba.Ta na gamawa ta je ta sake yin wanka saboda gumin da tayi, ta zo ta shirya cikin riga da skirt na  atampa, red in colour ta sa hijab ɗinta ja da flat shoes baƙi, ta ɗauki jakarta ma ja sannan ta fito

Ummi na tsakar  gida ta na shan kununta

"Ummi na gama zan wuce, maganinki na nan gefen katifarki"

"To Hanan Allah ya kiyaye, ki kula dan Allah"

"Insha Allah, kuma dan Allah kar kiyi abinci, Maman Nana(maƙwabciyarsu) ta ce zata kawo miki"

"To Mama Hanan" dariya suka yi dan ta san yanayin mganar da tayi ne yasa ta ce mata mama

"Sai na dawo" ta tashi ta fita




***************


Arshad ne cikin office ɗinshi sai faman aiki yake tayi, wayarshi tayi ƙara, ganin numbern yasa yayi murmushi ya ɗauka

"Uwargida ran gida" ya faɗa ya na dariya

"Dalla yi mun shiru sarkin daɗin baki, ka kyauta kenan ko?" aka faɗa daga ɗayan 6angaren

"Haba Hajjo, kiyi haƙuri, wallahi yau nake so dama zan kiraki"

"Ai dama haka za ka ce"

"Kin san me Hajjo, satin nan da ya kamata ace na zo, sai aiki ya mun yawa wallahi"

"Sannu agogo, ko dai kishiya ka mun, shiyasa ka gagara zuwa ganinmu?"

Wani murmushi yayi har cikin ranshi, ya ce "Kaman kin sani kuwa Hajjo, son kowa ƙin wanda ya rasa"

"Da gaske?"

"Eh mana"

"To yaushe za ka kawo mun ita, ga shi jiya Nabeel(ɗan aunty fati)ya kawo mun wacce yake so ya aura, ka ga sai a haɗa auren ko?"

"To ai sai anyi auren Ya Nabeel sannan nima zan yi, ai shine babba"

"To duka shekara nawa ne a tsakaninku?"

"Yanzu dai Hajjo i'm busy, i will call you back"

"Biziyo, ɗan turancin ƙaniya kai"

Dariya yayi ya ce "to zan kiraki, ina aiki ne"

"Allah ya bada sa'a, ka gaida ƴan biyu da Ruƙayya"

"To matas, bye" ya kashe wayar kawai, ya cigaba da aikinshi


****************

Hanan ce a makarantarsu Yuhaness zaune, kallo ɗaya zaka mata ka gane tana cikin tashin hankali

Wayarta ta dauka ta sake kiran Yuhanees a karo na shidda, sai a lokacin ta ɗauka

"Hello Rabin rai"

"Na'am Hayatee, kina ta kirana muna exam, yanzu muka fito, lafiya kuwa?"

"Kina ina Rabin rai? Wallahi ina cikin tashin hankali"

"Kina ina ke?"

"Ina nan bakin department ɗinku"

"To gani nan zuwa"

Zaman minti goma tayi ta na jiranta sannan ta ƙaraso ita da wasu ƙawayenta guda biyu

Sai da suka gaisa da Hanan sannan suka wuce

Zama Yuhanees tayi kusa da ita, ta ce "Hayatee menene?, gaba ɗaya kin tsorata ni"

"Rabin rai ban ga kuɗin nan ba"

"Wane kuɗi?" ta faɗa a razane

"400k ɗin da na kar6o"

"Ina kika ajiye?"

"Na ka sa tunawa wallahi"

Shiru suka yi na wani ɗan lokaci, sannan Yuhanees tayi ajiyar zuciya ta ce "to yanzu ya za muyi kenan?"

"Kaina ya ƙulle, bansan ya zanyi ba, ko wurin aikin ma ba zan iya zuwa ba"

"A'a, kar ki ce ba za ki tafi ba, tunda shi ogan na ku bai san kin kar6a ba, sai ki tafi kiyi ma Mu'azzam ɗin bayani, ki gaya mishi za ki samo kafin ya samu labari"

"To amma Rabin rai ina zan samu?"

"Allah zai ba mu mafita, zan duba idan akwai abun da zan siyar, sai mu kai kuɗin"

"Amma haka za ki yi ta sayar da kayanki?"

"Kar ki damu Hayatee, you deserve more....yanzu muje in raka ki titi ki tafi, kina ƙara makara"

Tashi tayi ba dan ta so ba, ta rakata ta shiga napep, ita kuma ta koma cikin makarantar dan suna da wata paper

A bakin gate ɗin wani ƙaton company aka ajiye ta, mai suna MK INVESTMENT LIMITED

Shiga tayi tana karanto addu'o'i daban- daban, har sai da ta kai office ɗin Mu'azzam, tayi sallama ta shiga

"Malama Hanan, yau kin shigo kenan"

"Eh wallahi, ai hutun da aka bani ya ƙare"

"Allah sarki, to ya jikin mahaifiyarki ɗin"

"Ta ji sauƙi, alhamdulillahi"

"To madallah"

"Mu'azzam dama wata magana ce nake so zan gaya maka" ta faɗa gabanta na dukan uku-uku

Ya ce "to....to ina jinki"

Cikin ɗar-ɗar ta gaya mishi komai, har ta gama kallonta yake yi, ita kuma ta kasa ɗaga kai ma ta kalleshi

Can ya nisa, ya ce "Hanan na yarda da ke, amma ke kin san waye yalla6ai, amma dai still zan miki uzuri har ki samu, sai dai ki sani, cikin satin nan za'a haɗa mishi kuɗin nan a mishi transfer zuwa account ɗinshi"

Da sauri ta ce "in sha Allah zan kawo kafin ma ya buƙata"

"To Hanan, Allah ya sauwaƙe"

"Ameen, nagode"

Tashi tayi ta fita zuwa reception dan nan take na ta aikin



****************

Ammi ce zaune tare da Hajiya Karime suna hira, su Yasna kuma na zaune su na kallo

Gaba ɗaya haushin Hajiya Karime ya cika Yasna, hakan yasa ta tashi ta koma ɗakinsu

Tana wucewa kuwa Hajiya Karime ta ce "Hajiya Ruƙayya dama magana ce ma ta kawo ni"

"To Hajiya Karime ina jinki"

"Wai me zai hana a sa ranar auren yaran nan kowa ma ya huta"

"Haka ya kamata gaskiya, amma ai kin san sai anyi magana da su Hajjo"

"To ayi musu magana mana"

"To wai saurin me kike yi?"

"Bana so ne Arshad ɗin ya ga wata kuma ya fasa da Farha"

"Haba dai, har ya isa?, ai baida wata mata a duniyan nan da ta wuce Farha"

"To Allah ya sa, amma kin san halin Arshad...."

Ta katse ta "hali? Ai bai isa ya tsallake maganata ba, ki kwantar da hankalinki kawai"

"To Hajiya Ruƙayya, nagode"

Haka suka cigaba da hirarsu har Hajiya karime ta tashi ta wuce

Bayan Ammi ta dawo daga rakata, ta zauna ta ce ma Yasmin

"Yasmin!"

"Na'am"

"Kar ki kuskura ki gayawa waccan maganaɗisu maganar da muka yi akan Arshad yanzu, kin san za ta iya gaya mishi, and he can take any action, tunda ba sonta yake yi ba"

"Ammi ai ba zan gaya mata ba, dan ni ina son aunty Farha, kuma ina so ya aure ta"

"Yawwa ƴar albarka, haka nake son ji"

"Bari in shiga ciki kafin ya dawo"

"To Ammi"

Haka ta tashi ta wuce sama, zuwa ɗakinta.........










🥰UMMEETA🥰.......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi, idan yayi daidai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏

Ina godiya masu comment, Allah ya saka da alkhairi🥰🤗

Wannan page ɗin sadaukarwa ne ga dukkan ilahirin members ɗin Moonlight Writers Association🌙✨
Ina matuƙar alfahari da ƙungiyar nan da shugabannin ƙungiyar da sauran members gaba ɗaya, Allah ya ƙara ɗaukaka, Allah yasa mu cigaba haskawa duk duniya, kowa yayi alfahari damu💪🥰🌹

We shine all over the world, and we will continue to shine forever and ever insha Allah🌍✨❤️




 *Page 12*

Saukowarshi kenan daga kan stairs, kowa ya tashi tsaye da sauri, suna sunkuyar da kai ƙasa

Wani kallo ya bi su da shi ɗaya bayan ɗaya a wulaƙance, har ya zo gaban wani cleaner, tsoho, da sauri ya ja da baya dan ya ba shi hanya, amma cikin rashin sani ya ture wani flower vase da ke bayanshi, a nan take vase ɗin ya fashe

Cikin faɗuwar gaba ya juya ya kalli vase ɗin sannan ya kalleshi, zai yi magana kawai ya ji saukar mari a kumatunshi, duk wanda ke wurin sai da ya razana

A tsawace ya ce "kai mahaukacin ina ne,eh?, ba za ka iya abu a hankali ba? Kun fi so kuyi ta ja wa mutum asara, yanzu kalli 6arnar da kayi mun, ka san nawa ne kuɗinshi?,......matsiyacin banza kawai, to wallahi ba zan yi asara ba, a cikin albashinka zan cire kuɗin vase ɗin nan, wawa kawai ƙazami" daga haka bai tsaya jin komai daga gareshi ba ya fita

Da sauri ma'aikatan da ke wurin suka yo kan tsohon da ya durkusa a ƙasa yana kuka

Hanan ta ce "dan Allah baba kayi haƙuri ka daina kukan nan"

Tsohon ya ce "ai dole inyi kuka, dan kawai ba ka da shi, sai ka zama wulaƙantacce? Yaron da yayi sa'ar ɗana shi ne zai gaya mun waɗannan maganganu haka hadda mari?"

Wani ne ya ce "kayi haƙuri Baba Kabiru, in sha Allah MK sai ya haɗu da dai-dai shi"

Baba Kabiru ya ce "hmm, ba komai, nagode, ku cigaba da aikinku kar ya dawo kuma, Allah ya shirya shi"

Haka kowa ya koma bakin aikinshi, gudun kar ya dawo ya same su a nan, shi kuma Baba kabiru yayi ƙoƙarin gyara wurin da ya 6ata


Tunda Hanan ta koma wurin zamanta, take ta nazari, gabanta sai faɗuwa yake ta yi, a ranta ta ce 'MK kwata-kwata baya wasa da kuɗinshi komai rashin yawansu, yanzu yayi wannan masifar akan vase ɗin da bai wuce 5k ba,  to ya zata kaya tsakanina da shi idan ya buƙaci kuɗinshi kuma ban samu ba fa?....400k,ai ban san ma wane irin mataki zai ɗauka ba, oh Allah....Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan, wa anta taj'alil hazni iza shi'ita sahla'

"Hanan!!!" kiran da wata abokiyar aikinta ta mata ya dawo da ita

"Me kike tunani haka?"

Murmushin yaƙe tayi ta ce "ba komai Zulaihat"

"To na ga kin ajiye mutum anan, tana ta tambayarki amma shiru" ta faɗa tana nuna wani mutum da ke tsaye gaban table ɗin Hanan

"Ayya,i'm really sorry, ban ganka ba ne" 

"Ba komai, dama office ɗin accountant na ke nema"

Haka dai ta nuna mishi, ta cigaba da aikinta amma sam ba ta da sukuni

********************

Tunda Hajiya Karime ta koma gida take ta murna, Allah ya dawo da Farha ta gaya mata yanda suka yi da Ammi

Ai kuwa tana dawo ta zayyana mata komai

"Yawwa Mummy, ni na san Ammi zata yi wani abu, kinsan kuma baya tsallake maganarta"

"Sasai ma kuwa Farha,kin ga kamar wacce ke jira in mata maganar!,...yanzu tsorona ɗaya kar waccan tsohuwar ta hana"

"Taya za ta hana?, idan ma ta nuna za ta kawo mana matsala ai maganinta kawai za muyi"

"Bari dai mu gani, everything will be easy"

"I hope so Mumcy"

"Don't bother yourself my dear"

Ɗaga kai Farha tayi ta kwanta kan cinyar Hajiya Karime




********************

Ƙarfe huɗu Arshad ya dawo gida, hakan ya sa ya tsaya masallacin da ke jikin gidansu yayi sallah sannan ya ƙarasa gida

Part ɗinshi ya wuce yayi wanka, ya shirya cikin wando three quater navy na jeans da riga armless an mata manyan rubutu navy blue

Main palour ya wuce, ya gaida Ammi da ke nan zaune tana duba wasu kaya a laptop, zama yayi kusa da ita shi ma yana kallon kayan, ya ce

"Ammi wai waɗancan kayan basu iso bane?"

"A'a na fasa sayen waɗancan ne saboda an gaya mun basu da quality, kuma ka san shi ɗan kasuwa ya fi son abunda ke da quality, shi ne nake duba waɗannan"

Kallon kayan yayi da kyau, ya ce "amma Ammi ai irin waɗancan kika saba saye, sai yanzu ne ba su da quality?...ko customers ɗin na ki ne suka gaya miki haka?"

"A'a, Hajiya Karime ce dai ta gaya mun ai ba su da quality"

Tsaki yayi wanda bai ma san lokacin da ya fito ba, ya ce "wai Ammi duk abunda matar nan ta gaya miki sai kin ɗauka?, ni da kaina fa na tafi pakistan ɗinnan, sai da na nemi companyn da kayansu ya fi na kowa quality da kyau, sannan na haɗaku, amma shi ne wacce ko Nijar ba ta ta6a zuwa ba za ta gaya miki wai kaya basu da kyau kuma ki yarda?"

"Wai me matan nan ta tsare maka ne Arshad?!, kwata-kwata na fahimci ba sonta kake yi ba, ka tsaneta"

"Ni ba haka na faɗa ba, kawai dai naga kin yarda da ita ne sosai, amma Allah ya baki haƙuri"

Tashi yayi ya wuce dinning area ya zauna, Zulai mai aikinsu ita ma, ta zo da sauri za ta yi serving ɗinshi, sai ga Yasna da gudu tana saukowa daga stairs, ta ce "a'a Anty Zulai, ai ina nan, zanyi serving ɗin Yayana"

Kallonta kawai tayi tana murmushi, ta ce "to yi haƙuri, ban ganki a palourn bane shiyasa"
Sai kawai ta wuce, dan Yasna in dai tana gida, bata yarda kowa yayi serving ɗin Arshad ba sai ita

Tan gama zuba mishi ta miƙa mishi ya fara ci, ita kuma ta zauna gefenshi, ta ɗauki wayarshi tana kallon pictures

Yasmin ita ma da saukowarta kenan, ta zo ta zauna suka gaisa da Arshad

Ya ce "Shiyasa nake cewa kin fi wannan hankali, dan ke kina gaida mutum, ita kam saidai aukin ɗura ma mutum abinci"

Dariya Yasmin tayi, ita kuma Yasna sai turo baki take yi ta ce "ai abinci ya fi gaisuwa"

"Wa ya gaya miki?"cewar Arshad

Yasmin ta ce "kyaleta Big Bross......yawwa dan Allah Big Bross idan ka gama cin abinci, mu tafi swimming pool pls"

"Dan kar in huta?"

"A'a Big Bross"ta faɗa tana dariya

Yasna ta ce "ai inda bai ci abinci ba da zan ga ta yanda zai je swimming pool ɗin ai"

Dariya dai Arshad yayi da Yasmin, dan sun san magana ce ta mayar musu

Ya ce "to shikenan, kuje shirya"

Da sauri suka wuce ɗakinsu, skin tight suka sa three quater pink colour da t-shirt ƴar picika ita ma pink dan Arshad ya hanasu sa vest in dai ba ɗakinsu suke ba, ko wacce ta ɗauko after-dress ta ɗora, sannan suka fito

A palour suka tarar da shi yana jiransu, Ammi kam ta ma wuce ɗakinta

Suna isa swimming pool ɗin suka cire after dress ɗin, dan wurin a killace yake, nan suka fara swimming, suna ta wasa ruwa, abun gwanin burgewa, sai dariya kawai suke tayi

Sai ƙarfe shida sannan suka koma cikin gida, suka yi wanka suka zauna jiran a kira sallah, shi kuma wucewa yayi masallaci



*******************

Su Hanan ne zaune a ɗakin Ummi dukansu, Siyama sai gaya musu abubuwan da ya faru a makaranta take yi, dan Siyama akwai surutu kamar aku, Ummi da Yuhanees kawai ke jinta dan Hanan hankalinta ma baya jikinta, Yuhanees ta lura da hakan tun lokacin da Hanan ɗin ta dawo wurin aiki ta ganta jiki ba ƙwari

Duba lokaci tayi ta ga ƙarfe shidda da rabi, sai ta ce ma Siyama ta tashi ta sa ma Ummi ruwan alwala, sannan ita ma ta tashi, ta ce ma Hanan "ke ma ki zo kiyi alwalan ko?"

Sai data ta6a ta sannan ta gane me ma take cewa, tare suka fito ɗakin har Ummi, suka yi alwala, Ummi da Siyama suka shiga ɗakin Ummi, Hanan da Yuhanees suka wuce ɗakin Hanan ɗin

Sai da suka gama sallah sannan Yuhanees ta ce "wai dan Allah Hayatee ba za ki rage damuwa ba?"

"Ai dole ne rabin rai, yau ba ki ga yanda MK yayi ma wani tsoho ba akan abunda bai kai ya kawo ba a irin arzikinshi, to ni ya kike tunanin zai mun akan 400k?"

"To gaya miki akayi zamu bari ya sani ne ba ki biya ba?"

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Rabin rai ni fa nasan ba wani abunda za oi sayar da zai kai 400k, dama abunda kike da shi mai tsada, sarkarki ce, kuma kin sayar da shi"

"Hayatee ko ta wane irin hali ne, za mu biya MK, ki daina damun kanki pls, ko so kike yi Ummi ta fahimci wani abu?"

"Dama sai da Ummi ta ce kar in je neman komai a companyn nan dan tana tsoron halinshi amma na ƙi ji"

"Ni dai ki daina wannan maganar, pls"

Wayar Hanan ce tayi ƙara, tsab ta gane mai kiran nata, saboda yanayin da ta saba ji a ranta, kasa ɗauka tayi, sai da y sake kiranta a karo na biyu sannan Hanan ta dauka

"Kina so li wahalar da ni ko?" abunda ta fara ji kenan

Sai da ta daidaita muryarta ta yanda ba zai fahimci wani abu ba, sannan ta ce "a'a, bana kusa ne"

"Ba rashin daukar wayarki ba ne ma matsalar, yau gaba ɗaya ban kiraki ba, kuma ba ki damu ki kirani ba ko?, ko da ace ma mutuwa nayi ba ki da labari"

Da sauri ta ce "wannan wace irin magana ce haka?, dan Allah ka daina" ita kanta ba ta san lokacin da ta faɗi hakan ba, sai bayan ta faɗa ne ta tsaya nazarin wai me ma tace

Wani irin daɗi ya ji ya ce "ba ki so in mutu ne?"

Shiru tayi bata ce komai ba, sai murmushi kawai ta ke yi, ya ce "cigaba da murmushinki, sunnah ne, sannan kuma yana yi ma kyakkyawar fuskarki kyau"

Wani murmushin ne ya sake ƙwace mata ba ta shirya ba, Yuhanees kam kallonta take yi cikin mamaki, kamar ba ita ba ce take ba haƙuri yanzu, tashi tayi ta fita ita kam

"Kin gama murmushin?"ya tambaye ta

"Eh na gama"

"To, dama na ɗan shigo anguwarku ne yanzun nan, shine nake so inji, ko zan iya ganinki?"

Sai da ta ɗan ɗauki lokaci sannan ta ce "to shikenan"

"Yawwa, nagode"

Daga nan ta tashi ta tafi ɗakin Ummi, ta gaya mata AAJ zai zo, ta ce "Allah ya kawo shi lafiya"

Ba ta fi minti biyar da gayawa Ummi ba, ya kirata, yana ƙofar gida, tashi tayi ta shiga ɗakinta, turare kawai ta ƙara fesawa duk da ƙamshin da take yi amma sai ta ji ya mata kaɗan, dan Hanan na mugun shiri da turare, ta sa hijab ɗinta ta fita

Yana cikin motar bai fito ba, ita ma sai ta buɗe motar ta shiga, ƙamshin turarenta ya daki hancinsa, lumshe ido yayi a hankali sannan ya amsa sallamar da ta mishi

"Kiyi haƙuri, na zo ba tare da na sanar da ke ba ko?"

"Ba komai ai"

"Godiya nake sarauniya"

Murmushi tayi ta ce "na gaya maka ni ba sarauniya ba ce"

"Ke sarauniya ce, a cikin........" hannunta da ya kalla ne ya hanashi ƙarasa maganar

Kallon hannunta tayi ita dan ta ga me yake kallo, amma ba ta ga komai ba, sai kawai ta bi shi da ido

Ya ce "Hanan kyautar ba ta miki ba ne?"

"Na me?" ta tambayeshi cikin rashin fahimta

"Be my love" abunda kawai ya faɗa kenan 

Nan take ta gane bracelet ɗin da ba ta sa ba ne, sai tayi shiru kawai

A sanyaye ya ce "Hanan, nasan abu ne mai matuƙar wuya a gareni in iya za6en abu mai kyau  na mata, dan ban ta6a ba, may be shiyasa bai miki ba, amma ki sani, it will means alot to me idan na ganshi a hannunki, Hanan ban so gaya miki abunda ke raina ba yanzu, amma sai naga it's better ki sani yanzu ɗin, Hanan ban san soyayya ba,  ban san ya mutum ke ji ba idan ya fara son wani, amma kin zama sanadin da na san hakan, i just love you since from the first time i set my eyes on you, na san za ki ji abun wani iri saboda ko sati ɗaya banyi da saninki ba nake gaya miki haka, amma hausawa sunce, a bari ya huce yana kawo rabon wani, duk wani abu mai kyau kowa na burin ya sameshi"

A hankali ta ce "kyau?"

"Eh Hanan, ke kyakkyawa ce, ba wai kyan fuska kawai nake nufi ba, harda kyan hali, i wish to have you as my wife Hanan, please don't say no"

Duk da ta san da cewar yana sonta, tun lokacin da Yuhanees ta fahimtar da ita, amma sai ta ji kalamanshi sun mata nauyi, ta rasa wanda ma za ta ɗauka

"Ba zan takura ki ba Hanan, if youvdon't love me just let know, zan na ki lokaci kiyi tunani, okay?!"

Har yanzu dai ta kasa cewa komai, sun kusan 6mins ba um ba um um, sannan yayi ajiyar zuciya ya ce "dare na yi Hanan, ki shiga gida, sai na kiraki, just take your time and think, daga nan har kwana biyu"

"Hmm, sai da safe, nagode"

"Ki gaida Ummi da Siyama"

"Za su ji" jiki a sanyaye ta shiga gida, shi ma haka ya ja motar jiki ba kwari, ganin yanda ta mishi yasa shi yin la'asar, kar ya kasance ba ta sonshi, da wannan tunanin ya isa gida, ko main palour bai koma ba ya wuce 6angarenshi


Ita ma Hanan dai ta zauna wurinsu Ummi, ba wai dan tana jin daɗin hirar ba, har ta gaji ta koma ɗakinta, tayi sallar isha'i ta kwanta, sai juyi take yi, dan idan wannan 6angare na zuciyarta ya kawo mata maganar AAJ, tayi tunani kala-kala a kai, sai kuma wani 6angare ya kawo mata tunanin kuɗin MK da ba ta gani ba, haka tayi ta waɗannan tunanin har bacci yayi awon gaba da ita



******************

MK ne zaune a palournshi na guest house ɗinshi, shi da wani suna shan lemun kwalba da shisha

Mutumin ya ce "yalla6ai, wai ya maganar wannan contract ɗin?, naji kayi shiru"

"Ina tunanin ai zan barwa abokin abbana shi, dan yanzu ba contract ba ne a gabana, abunda ya fi damuna bai wuce in ga nayi destroying ɗin AAJ ba, kuma ka sani"

"Yalla6ai, na sha gaya maka, we should kill him kawai a wuce wurin"

"A'a Gboy, bana son kasheshi da kai na, na fi son miserable life ɗin da zan jefashi ya kasheshi, ai duk wanda ya ci tuwo dani, miya ya sha, ban san asara ba, ban kuma gaji asara ba, dan haka ba zanyi asara ba ko ta naira biyar kuma a zauna lafiya"

Gboy ya ce "haka ne yalla6ai, ina rokon Allah ya cika maka wannan burin naka, amma me za ka yi to?, wace hanya za ka bi?"

"Plan ɗin babyna za mu bi"

"Wane plan kenan?"

Karanto mishi yanda plan ɗin yake yayi, kamar yanda ta gaya mishi, dariya Gboy yayi, ya ce "tabbas idan aka yi haka, wannan matsiyacin bai da hanyar fita, dole tarkonmu sai ya kama tsuntsu"

Dariya suk sake yi, suka cigaba da tattauna yanda plan ɗin na su zai kasance..............









🥰UMMEETA🥰........📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

       ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        A Hot Love Story
     🥰🥰🥰

         Created and Written
           BY
 🥰UMMEETA🥰

🌙MOONLIGHT WRITERS ASSOCIATION🌙
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/


"'We are the moonlight writers we shine all over the world."'
بسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~~~


Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi, idan yayi daidai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏



 *Page 13* 


Yau tsawon kwana huɗu kenan da Arshad ya tafi gidansu Hanan, bai sake komawa ba sai dai sukan yi yawa kullum, na safe daban na dare daban, a koda yaushe idan ya kira ta sai ya ji kamar ya tambaye ta amsar maganarsu ta ranar nan, amma sai yake ganin kaman idan ya tambaye ta to takura mata zai yi, shiyasa yayi haƙuri har sai ya ji daga bakinta




Yau jumma'a, misalin ƙarfe tara na safe, Arshad na zaune a office ɗin shi yana ta faman aiki, ya hango wata matashiyar budurwa ta shigo wurin secretary, sun ɗauki lokaci su na magana, sannan Khairat ɗin ta kirashi ta wayar telephone

"Hello yallab'ai"

"What's going on Khairat?"

"Wata ce ta zo wai tana son ganinka, kuma na gaya mata ba za ta samu ganinka ba tunda ba ta da appointment da kai, amma shi ne ta ce wai magana a zo da ita mai muhimmanci"

"Magana? Kuma mai muhimmanci?"

"Haka dai ta ce"

Sai da ya ɗan numfasa sannan ya ce "shikenan, let her in"
 Sai kawai ya ajiye wayar, ya danna mata ƙofar, ta buɗe

Shigowa tayi da sallama a bakinta, shi ma ya amsa yana bin ta da kallo har ta ƙaraso bakin table ɗinshi, nuna mata kujera yayi, ya ce "Have a seat"

Zama tayi, sannan ta ce "nagode.....ya aiki?"

"Alhamdulillah, wace magana ce ta kawo ki?"

"Yallab'ai, ni ba kowa ba ce a garin nan, kuma ba ƴar kowa ba ce ni, shiyasa ba na so in je fa kai na cikin wani matsala, amma duk abunda ya dangance ka, ba zan iya kyalewa ba"

Wani kallo yake mata, ya ce "har yanzu ban fahimci inda maganarki ta dosa ba"

"Za ka gane...,ko ka san cewa kana da maƙiya?"

"Hmm, ai dama duk yanda mutum yake a rayuwa, dole sai ya samu maƙiya da kuma masoya"

"To ina so ka sani, daga cikin maƙiyanka, akwai waɗanda suke so su lalata maka background, so suke yi sai sun 6ata maka suna"

"Kamar ya?" ya tambayeta cikin mamaki

"Nima ban san ko ta ya za su aikata hakan ba, amma tabbas su na da wani ƙwaƙƙwaran shiri akanka"

"Su waye?"

"Ba za ka ji daga bakina ba, dan na gaya maka ba na son shiga cikin matsala, na dai gaya maka haka, dan ka kwana cikin shiri". Tashi tsaye tayi tana faɗin "na bar ka lafiya" ta juya ta fita

Kallonta kawai yake yi har ta fita, sai tunanin maganarta yake ta yi, ya rasa abun da ma zai yi, hakan ya sa ya ɗauki wayarshi ya kira Sajjad, bugu ɗaya ya ɗauka

"Hello Super"

"My man idan ba wani aiki kake yi ba, ka ɗan zo mana dan Allah"

"To ina zuwa, ba ni 5mins"

Kamar yanda ya faɗa kuwa within 5mins ya shigo office ɗin AAJ

Zama yayi yana faɗin "lafiya?, na ga mood ɗinka ya canza ba kamar yanda na bar ka ba"

Tas ya kwashe yanda suka yi da yarinyar nan ya gaya mi shi

Sajjad ya lura maganar ta tsaya mishi, hakan yasa ya ce "haba Super, ina ikhlasin na ka ya tafi kuma? Ka manta kai ne kake gaya wa mutane faɗar Manzon Allah SAW? Wanda ya ce koda ace duniyar nan za su taru domin su amfanar da kai wani abu, ba za su iya ba, face abunda Allah ya rubuta a gareka, haka kuma, da za su taru domin su cutar da kai, ba za su iya ba, face abunda Allah ya rubuta a gareka.....ko kana so ka ce mun ka manta ne?"

A hankali Arshad ya girgiza kanshi

Sajjad ya ci gaba da cewa "to akan me wannan ɗin zai dameka? Allah na tare da bayinsa masu tawakkali, Allah na tare da kai Arshad, meye abun damuwa? Wannan ai usual thing ne, so nawa maƙiyanka ke kallon cikin idonka su maka barazana, amma su gagara yin komai? Ba abunda suka isa suyi maka sai kallo, i'm very sure su na so ne ka janye maganar wannan contract ɗin da muka samu wurin ƴan italia ɗin nan"

Kusan 4mins AAJ bai ce komai ba, yana ta nazari, sannan ya nisa ya ce "thanks alot My Man, ka tunatar dani abunda nabai kamata ace na manta ba"

"Amfanin zaman tare kenan ai"

"Haka ne"

Cikin sigar zolaya Sajjad ya ce "ni da na ji yanayin maganarka har na tsorata, dan na ɗauka ko Hanan ce ta kiraka ta gaya maka bata sonka, so nayi fa in kira ambulance kafin in shigo"

Harararshi yayi ya ce "wa ya hanaka kiransu to"

"Tunanin na yi kuma gwara in fara ganin halin da kake ciki" ya ƙarasa maganar yana ƴar dariya

"Sajjad you think i'm joking ko? Na gaya maka idan ban samu Hanan ba anything can happen to me amma kana ganin kamar wasa nake yi"

"Ni!!!!....ni na isa ince wasa kake yi? Fatana ɗaya Allah ya sa ta amince ta kar6i soyayyarka"

"Ameen.....ina tunanin zuwa gidansu ma anjima, za ka rakani?"

"A'a, nima wurin ta wa gimbiyar za ni"

"Kar Allah ya sa ka rakani ɗin"

Miƙewa yayi yana faɗin "ameen, bye"

Ya fita ya bar shi nan zaune, gaba ɗaya ya cire maganar waccan yarinyar daga cikin ranshi, sai kawai ya mayar da hankali ya ci gaba da aikinshi




********************


A 6angaren Hanan kuwa, tana office ɗin Mu'azzam, dan ya buƙaci ganinta, tun da ya kirata hankalinta yake a tashe, har yanzu da take zaune a gabanshi

"Hanan na ga kaman ki na cikin damuwa ko?"

Kallonshi tayi ta ce "dole ne Mu'azzam, dan na san cewa za ka yi MK yace a tura mishi kudinshi ko?"

Murmushi yayi ya ce "a'a ba haka zan faɗa ba, dama ina so ne ki kwantar da hankalinki ki nemi kuɗin, dan ba na ma tunanin zai kar6i kuɗin nan wani sati ma, tun da kin ga satin nan ya ƙare yau friday, to zai iya kai upper week ma"

Duk da ta ji daɗin maganar, amma hakan bai sa tayi farinciki ba, dan burinta kawai ta samu kuɗin nan su sauka daga kanta, ko da kuwa zaivkai upper year ma sannan ya kar6a, dan Allah ya gani tana masifar tsoron MK, dan bai da mutunci ko kaɗan

"Na ji kinyi shiru" cewar Mu'azzam

Murmushi ta ƙirƙira ta ce "na ji daɗin zancen ne shiyasa, Allah ya ba ni ikon biya kafin upper week ɗin, nagode sosai Mu'azzam"

"Ameen, ba komai Hanan"

 Haka ta tashi ta fita daga office ɗin

********************

Hajjo ce zaune a palournta, tana waya da Ammi

"Ruƙayya ashe Yaron nan ya samu mata, shi ne ba ki mishi magana ya kawo mana ita ba?"

Shiru Ammi tayi tana mamaki, sannan ta ce "a'a Hajjo, zai kawo ta mana, dama muna jira ne sai sun gama fahimtar junansu da kyau, ai dole sai ya kawo ta"

"To wane fahimtar juna kuma ya rage? Tun da nake ban ta6a jin yayi maganar budurwa ba sai wannan karon,to tun da har ya iya gaya mun ya samu budurwa, to tabbas sun fahimci junansu"

"To Hajjo, in sha Allah idan su Yasna suka yi hutu, in za mu zo, to tare da ita za ko ganmu"

"To madallah, Allah ya kaimu"

"Ameen Hajjonmu, ya su Fatima?"

"Lafiya ƙalau, jiya ma tana nan ai, yanzu ma ga su Nabeela nan"

"Kina ta fama da rashin jinsu kenan"

"Wallahi kuwa"

Dariya Ammi tayi ta ce "to ki gaishesu"

"Za su ji, ki gaida ƴan biyu"

"To sai anjima"

Suka kashe wayar gaba ɗayansu

Nabeela ƴar 18 years, dake ta sauraren Hajjo tun ɗazu ta ce "Hajjo korarmu za ki yi?"

"Eh mana, ina zan iya da fitinarku? Ai sai dai Ummanku"

"Ni dai Hajjo ba inda za ni"

"Sai na gani idan gidanki ne ai, mijina kawai za'a bar mun, sai ki zo ran lahadi ki ɗauke shi"

"Mijin nake bai fi kowa rashin ji ba ma?!"

"Eh ba ruwanki"

Tana rufe baki, sai ga wani yaro ɗan 5years, da gudu sai kan kafar Hajjo, wata kuma na bayanshi da gudu ita ma,ƴar 11years, tana faɗin "wallahi sai na zane ka"

Hajjo ta ce "lafiya? Me ya miki?"

Cikin fushi ta ce "wai Hajjo ya taradda ni ina wasa, sai kawai ya takani ya wuce, hadda cewa ya taka ya taka" ta karasa maganar tanakoyon maganarshi, shi kuma ba abunda yake mata sai dariya

Hajjo ta ce "yi haƙuri takwara, na san akwai ki da haƙuri" ta kalli yaron ta ce "kai kuma Adnan ka bata haƙuri, kuma kar ka sake"

Cikin shagwa6a66iyar murya Adnan ya ce "Hajjo ƙarya fa take yi"

"Nace dai ka bata haƙuri ko, idan ba haka ba kuma za ka bi su ne ku koma tare"

Da sauri ya kalli Meerah ya ce "kiyi haƙuri to"

Bata ce mishi komai ba kawai ta juya ta koma inda ta fito

Nabeela da ke kallonsu tun ɗazu ta ce "kin gani wanda kike cewa a bar miki, wata rana sai ya karya miki ƙafar ai, dama ya lafiyar kura"

"Ba ruwanki dai, ni dai je ki duba girkin nan, idan su Larai sun gama"

"To ai shikenan"

Ita ma ta tashi ta nufi kitchen ɗin, ta bar Hajjo da Adnan anan, Hajjo ma ja moshi kunne akan ya riƙa jin magana






Ita kuma Ammi tunda ta kashe wayar take ta nazarin ya akayi Hajjo ta san da maganar Farha? Kuma dai ta san Arshad ba zai gaya ma Hajjo ba tunda ba sonta yake yi ba, haka ma su Yasna da Yasmin ba za su gaya mata ba tunda ba ta sa su ba, "to ko dai wata budurwar yayi ne??...kai impossible, dan da zan ji ko da a wurin Yasna ne, amma dai zan zauna da shi inji"

Haka dai tayi ta surutunta ita kaɗai har ta gaji ta tashi ta fita, dan da ma za ta je duba kayanta ne da suka iso yau din nan

*******************Hanan ce zaune a tsakar gida ita da Ummi, da yamma, Siyama kuma na wurin ƙawarta a nan maƙwabtansu, ta je aron note ɗin da aka yi ba ta nan, Yuhanees kuma ta koma gida dan iyayenta sun dawo tun kwana biyu da suka wuce

Hanan ta ce "yawwa Ummi, AAJ zai zo bayan magrib"

"To Allah ya kawo shi lafiya"

Hanan ta sake cewa "Ummi dama akwai wata magana da nake son muyi, ko ma ince shawara"

"Ina jinki"

Rasa ta inda zata fara ma tayi, sai da ta taushi zuciyarta, sannan ta iya fara magana a sanyaye "Ummi dama AAJ ne ya zo mun da wata magana"

"Wace irin magana?"

"Wai...wai cewa yayi yana sona, ni kuma Ummi sai nake ganin matsayina da na shi ba ɗaya ba, shi ne kawai nake tunanin ƙin amincewa, gara kowa ya nemi dai-dai da shi"

Sai da Ummi ta gama kallonta tsab, sannan ta ce "Hanan, kina sonshi?"

Shiru tayi ba ta ce komai ba,Ummi ta sake maimaita tambayar, sannan a kunyace ta ce "gaskiya Ummi ina sonshi, amma ina....."

Ummi ta katse ta "Hanan, na san kina gudun wulaƙanci ne, shiyasa kike fara kawo matsayinki da na shi ba ɗaya ba, amma ina so ki sani, Allah ne ya haɗa ku, kuma ya sa muku son junanku, to meyasa ba za ki roƙi Allah ya tabbatar muku da alkhairi ba? Kar ki cuci kanki bare kuma zuciyarki, ni na daɗe da fahimtar yana sonki kuma ki a sonshi ke ma, dan haka nake roƙon Allah ya tabbatar muku da abun da ya fi alkahiri"

Jin kalaman Ummi ya sa ta ɗan rage jin abunda take ji a ranta tsakaninta da AAJ ɗin, ta ce

"To shikenan Ummi, nagode"

Suka ɗan yi shiru, kafin daga bisani Ummi ta jawo musu wata hirar, har akayi magrib sannan suka tashi ma sallah,  Siyama ma lokacin ta dawo, sai ta ɗauki buta ita ma




Bayan magrib ɗin kuwa, sai ga Yuhanees ta zo, dan Hanan ta buƙaci ganinta

Su na nan cikin zauren gidan suna ƙara jera kulolin da ke wurin, dan sun gama shiryawa tsab kowacensu da hijab ɗinta, AAJ ya kirata dan ya sake tunatar da ita yana hanya fa, dan kar ta manta da yace yana zuwa

"Eh ban manta ba, idan ka zo ma za ka iya shigowa zauren"

"To malama"

Murmushi tayi ta ce "malama kuma?"

"Eh mana"

"Hmm to nagode"

"Yawwa, sai na zo"

Daga haka suka kashe wayar

Yuhanees tayi ajiyar zuciya ta ce "Hayatee yanzu da Ummi ba ta miki wannan bayanin ba, da haka za ki cuci kanki kina ji kina gani?, Hayatee duk wanda ya san yadda kike mu'amala da AAJ, to wallahi kallo ɗaya zai miki ya gane kina sonshi"

"Rabin rai kenan, na san ko da ace kowa bai fahimta ba, to tabbas ke da Ummi za ku fahimta, Allah ya gani tun ranar da na fara sa shi a idona naji ina masifar sonshi, ban ta6a tunanin zanyi ma wani ɗa namiji kallo ɗaya inji ya shiga raina irin haka ba"

"Ni na sani ai, shiyasa ma ban ba ki shawarar yaudarar kanki ba"

"Rabin rai ba wai zan yaudari kaina ba, ina tunanin abunda mutane za su faɗa a kaina ne, za'ayi tunanin meyasa ina ƴar talaka amma bazan nemi dai-dai ni ba, sai dai shi? Wasu kuma za su yi tunanin ko kuɗinshi nake so ba shi ba, kinsan........"

"Mutane kike so ko kuma ni?, ko kuwa mutane za su zauna da ke?" muryar AAJ kawai suka tsinta cikin kunnuwansu, dan ba su san da shigowarsa ba, hatta ƙarar motarshi ba su ji ba

Juyawa suka yi suna kallonshi, takowa yayi har gaban Hanan ɗin ya tsaya, ya ce "why do you worried yourself about what people would say? Ni kin san matsalolin da ke gabana idan har na nuna ki a matsayin wacce nake so? Amma ban damu da matsalolin ba, domin in dai har zan same ki, to komai mai sauƙi ne....Hanan ina so ne ni da ke mu kasance masu ZUCIYA ƊAYA, kar mu ta6a tunanin wani abu zai iya shiga tsakaninmu, domin idan kika biye ta mutane, to har abada ba za ki ta6a yin abunda kike so ba, dan wani abun idan kika yi za ki burge wasu, sannan kuma za ki ba wasu haushi komai ƙoƙarinki, just think about it pls Hanan"

Shiru Hanan tayi, domin ta gamsu da maganarshi, Yuhanees ta ce "Hayatee ba ƙarya a maganarshi, ki cire tunanin mutane, ki ba zuciyarki abunda ta ke so"
Daga haka ba ta tsaya ba, ta wuce cikin gida ta bar su nan a tsaye kamar haƙori............









Idan muka haɗu a next page, za ku ji idan sun samu sun zauna,ko kuma ci gaba suka yi da tsayuwar kamar haƙori😂😂😂


Ina yinku over ƴan grp ɗin zuciya ɗaya fans♥️dan comments ɗinku na ba ni nishaɗi💃🥰


🥰UMMEETA🥰........📝



♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

      ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
🔥❤️: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirar shi nayi,idan yayi daidai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri akasi aka samu👏👏👏


 *Page 14*

Tun da Yuhanees ta shiga cikin gida, ba wanda ya sake magana cikinsu, har tsawon mintuna goma

Sannan Hanan tayi ajiyar zuciya, ta ce "ka zauna"

Kamar ba zai zauna ba, sai dai kuma ya zauna ɗin kamar yanda tace, tsugunnawa tayi, ta ɗauki cup, ta tsiyaya mishi juice ɗin abarba da kwakwa da suka yi, sannan ta miƙa mishi

Kallonta kawai yake yi, bai ansa ba kuma bai ce komai ba, sai da ta kalle shi ta ce "ga shi"

"Hanan ba zan iya ansar komai daga gareki ba, dan har yanzu ba ki aminta da ni ba, Hanan why do you hate me pls ?"

Cikin sauri ta ɗaga ido ta kalle shi ta ce "hate??....akan me?"

"Akan dalilai irin na ki, sannan da ace kina so na ko kaɗan  ne, za ki so abunda na ba ki, amma kin ga har yanzu kin gagara sa wa"

Ƙoƙari tayi ta cire wannan kunyar ta ce "I don't hate you Arshad, I love you, I love you with all my heart, meyasa kake tunanin zan ƙi ka?, na gaya maka dalilina na rashin amincewa da kai at first, amma yanzu na cire wannan, amma promise me one thing"

Tun da ta furta 'I love you' ya tsinci kan shi cikin farincikin da ba ya misaltuwa, shi kan shi yasan ba zai iya tuna when last da abu ya faranta mishi rai irin na yau ba, ji yake yi kamar ya ɗauke ta ya goya dan ta fahimci irin murnar da yayi

Ya ce "just tell me Hanan, ko menene zan ɗauka"

"Ka mun alƙawari, ba za ka tab'a cuta ta ba, ko kuma ka yaudare ni, whatever difficult the situation is, promise to be by my side, promise not to leave  me when i'm in need of you, idan har ka mun haka, nayi maka alƙawarin ba za ka tab'a dana sanin so na da kai ba a rayuwa"

"This is the easiest thing i can do to you Hanan, ba zan tab'a barinki ba, duk wuya duk rintsi"

Wani sanyayyan murmushi ta saki, wanda ya ƙara fito mishi da ainihin kyaunta, dimples ɗinta duka sai da suka lotsa, sannan ta ce

"To yanzu za ka sha juice ɗin ko na mayar?"

"Haba dai, in dai rowa za ki mun, shikenan"

"Har na isa?"ta faɗa tana murmushi ta miƙa mishi ya sha, yana zuba mata santi, wai juice ɗin ya mishi daɗi

Ya kai kusan one hour sannan ya samu ya wuce, bayan ya haɗa ta da ledodin da ya kawo musu, kuma ya aika saƙon gaisuwarshi ga Ummi.




Tana shiga gida, ɗakin Ummi ta wuce, dan suna can har Yuhanees ɗin

Ajiye ledodin tayi, sannan ta cire hijab ɗinta ta sa kan ƙofa, ta zauna

Yuhanees ta ce "sannu juliet, ta shi za kiyi ki rakani, tun ɗazu nake son wucewa gida amma kun wani manne sai hira kuke ta sha, kun tare ma mutane hanya"

Harararta tayi, ta ce "ba ki so wucewa ba, tun da ba mamaye ƙofar gidan muka yi ba"

Yuhanees ta saki baki tana kallonta, sannan ta ce "Ummi kin ga sakayya ko?, kirana fa tayi, na zo ƙafa da ƙafa na taya ta aiki, amma kin ji abunda take gaya mun"

Ummi ta ce "ai kin san halin ɗan adam Yuhanees, kyale ta, kina zaman-zamanki za ta sake dawowa nemanki"

Murmushi tayi ta ce "to Ummi, nikam sai da safe, Sima bye" ta faɗa tana sa hijab ɗin ta ta miƙe tayi waje

Da sauri Hanan ta tashi tana dariya,vta figi hijab ɗinta ta fita tana cewa "haba Rabin rai, i'm sorry mana, in babu ke babu ni"

Ummi ta ce "ai kin saba"

Siyama kan dariya kawai take yi, dan tana jin daɗin ta ga su na haka



*****************

A b'angaren AAJ kuwa, tun da ya isa gida, yana part ɗinshi, ya kira Sajjad ya gaya mishi cewa Hanan ta amsa tana son shi, ba ƙaramin murna Sajjad ya taya amininshi ba, dan shi ma tun lokacin da ya ga Hanan ɗin, yake ma Arshad kwaɗayin samunta, kuma ga shi ya samu, fatanshi kawai Allah ya sanya alkhairi a tsakaninsu

Ko bayan da ya gama waya da Sajjad, ya daɗe zaune kan gadonshi, ji yake kamar duk duniyar nan ya fi kowa farinciki yau

Yana nan zaune, sai ya ji sallamar Yasna, ya amsa mata, tare da ba ta umurnin shigowa, kallo ɗaya ta mishi

Ta ce "Sweet bro, lafiya?, na daɗe ban ganka cikin mood ɗin nan ba fa"

Kyakkyawan murmushi ya mata ya ce "wurin auntynki na fito"

"Auntyna?, wacce nace ka kira ta mu gaisa ka ce a'a?"

"Yeah"

"To me ta ba ka da ya sa ka farinciki haka?"

"Kawai cewa tayi tana so na"

Dariyq tayi ta ce "lallai Sweet Bro, zan so ganinta wallahi, dan ta tafi da imaninka da yawa"

Shi ma dariyar yayi ya ce "za ki ganta very soon"

"To shikenan,.....dama Ammi ce ke son ganinka, ta kira telephone amma baka ɗauka ba, haka ma wayarka"

"Ba daɗe da na bar palourn ba kuwa, wayoyin ma na can, ki gaya mata ga ni nan zuwa, wanka kawai zanyi"

"Ok"
Ta fita, shi kuma ya wuce bathroom yayi wanka, ya sa jallabiya, maroon da pencil ɗin wandon shi baƙi, shigar ta mishi kyau sosai, sannan ya wuce main palour

Kallo suke yi dukansu hadda Ammi, sai da ya kalli TVn sannan ya ce "yawwa a gaida indiyawa, aikin kenan ai"

Dariya dai suka yi da Yasmin da Yasna ɗin, dan ba su so su ma juya kallonshi ayi wani abu ba su gani ba

Wucewa yayi ya zauna kusa da Ammi, suka gaisa, sannan ta ce

"Arshad in tambaye ka mana"

"Ina jinki Ammi"

"Wai yaushe ka gaya wa Hajjo maganar Farha"

"Farha kuma? Wace Farha?" yayi maganar cikin rashin fahimta

"Ban son rainin hankali, wace Farha ka sani?"

Shiru yayi sannan ya ce "ni banyi maganarta da kowa ba ma bare Hajjo"

"Ah'ah, to ya akayi Hajjo take ce mun wai ka samu mata?"

Nazari ya ɗan tsaya yanayi, sannan daga bisani ya tuna ya tab'a ce ma Hajjo ya samu budurwa
'Oh ni, Hajjo akwai surutu wallahi, yanzu ɗan wannan zancen har ta samu abun bada labari?' ya faɗa cikin ranshi, muryar Ummi ta dawo da shi

"Kayi shiru"

Ajiyar zuciya yayi ya ce "akwai ranan da cikin wasa nake gaya mata na mata kishiya shiyasa kwana biyu ban kira ta ba, may be ta ɗauka ko da gaske ne"

Sai yanzu Ammi ta ji ta samu natsuwa, dan tana ta tsoron kar ya ce mata ya samu wacce yake so, dan sai ta yi da gaske sannan zai aminta da auren Farha, ko ma ya ce zai haɗa su, amma idan ba kowa a ranshi to cikin sauƙi zai amince

Dariya tayi ta ce "kai Hajjo, ka san tana masifar so ta ga kunyi aure kai da Nabeel, ga Jafar nan shi ma ya kusa fara neman mata"

Dariya ya ƙirƙira shi ma, ya ce "ai na gaya mata sai an fara auren Ya Nabeel sannan ayi na wa, tun da dai shi ne babba"

"Idan anyi magana ka ce shi ne babba, to duka shekara nawa ne a tsakaninku? Shi 30 kai 28"

"Whatever dai, kin ga shi yana ma da mata, ni kuma nema nake yi"

"To idan kuma na ce na samo maka fa?"

Wani kallo ya mata, dan ya san maganar Farha za tayi, kasancewar bai so ta b'ata mishi mood, ya sa yayi dariya kawai ya ce "ko da ace ina da matar ma a hannu, to sai an fara yin na shi......ni bari ma in je in kwanta, na gaji yau"

"Tun da nayi maganar aure ko?"

Dariya kawai yayi, har ya kusa kai ƙofa, Yasna ta ce "Sweet Bro yau kam ba za ka ci abinci ba ko?"

"Eh na ƙoshi"

Dariya tayi ta ce "ai dole kam"
Sai lokacin ya gane inda maganarta ta dosa, murmushi kawai yayi ya fita, Ammi dai tana jin su amma ba ta damu ta gane ba, Yasmin kam ba ji ba gani, sai kallo take ta yi




Da daddare kuwa, Arshad da Hanan sun daɗe suna waya, sannan suka kashe, Arshad kuma ya sake biyo ta da Goodnight message,  ita ma sake tura mishi tayi mai daɗi

Yayi mamakin ganin message ɗin, dan bai yitunanin za ta turo mishi ba, sannan fa suka kwanta bayan sun yi alwala, shi dai Arshad sai da ya haɗa da nafilolin da ya saba


********************
Washe gari da safe, Arshad na gida bai tafi ko ina ba, sai ma bacci da yake tayi, har kusan ƙarfe tara da rabi

Ammi kuma na zaune palournta da Hajiya Karime, suna ta hira, hirar kasuwancin Ammi suka fara, inda ta ce zata haɗa ta da ƙaninta dan ya san kaya masu quality, daga baya kuma suka dawo kan maganar Arshad da Farha, ta tabbatar mata cewa Farha ta kwantar da hankalinta dan in dai ita ta haifi Arshad, to dole ne sai ya auri ta


Farha kuma na main palour ita da su Yasmin, amma da Yasmin kawai suke hira dan Yasna ba ta ma da lokacinta

Can dai Farha ta ce "wai Yasmin ina Arshad ne?"

"Yana part ɗinshi, kin san yau saturday, ba fita yake yi ba"

"Kaii!!! Na ma manta ai, amma shi ne baku tafi islamiya ba?"

"A'a sai 12 sannan mu dawo 6"

"Ok, to bari in je in gan shi"

Ta tashi ta fita, Yasna ta rakata da harara, tana fita ta ja tsaki ta ce "Wai dan Allah Twinny me suka zo yi gidan nan tun da safe?"

"Fita za suyi mana, da Mummy da Ammi"

"Fita kuma? Ina?"

"A'a, ban sani ba"

"Hmm, shi ne waccan mai kama da aljanar za ta tafi tayar da Sweet Bro?!, Allah ya sa ya koro ta"

"Umm, Allah ya shirya ki, ban san me ta tsare miki ba"

"Ai ba za ki sani ba"






Farha na isa part ɗinshi, tayi sa'a kofar a buɗe take, dan tun da ya dawo sallar asuba bai rufe ba, wucewa tayi cikin palourn, yana nan kwance ko akan kujera dan bai koma ɗakin ba

Zama tayi kan kujerar da ke kusa da shi, ta sa mishi ido sai kallonshi kawai take yi, tana saƙa abubuwa daban-daban a ranta

Ji yayi kamar ana kallonshi, hakan ya sa ya fara buɗe idonshi a hankali, ya kuwa sauke su a kanta, tashi yayi da sauri ya zauna, ya ce

"What the hell are you doing here?" ya tambaye ta a tsawace

Cikin sanyi ta ce "haba darling, laifi ne dan na zo ganin mijina?"

"Mijinki?, as how?"

"Eh mana mijina, dan Ammi ta tabbatar da cewa ni matarka ce"

"A gidan uban wa aka ɗaura aurena da ke da har kike referring kanki as my wife?"

"Ba'a ɗaura ba, amma za'a daura"

"You are just decieving yourself, ko mata sun ƙare duniyar nan, ba zan auri ƙazama irinki ba"

Kallon kanta tayi da kyau, ta ga irin shigar da tayi, ita dai a wurinta ta haɗu, dan wando ne a jikinta baƙi, sai t-shirt fari, sannan ta ɗora top baƙi akai, sai wani ɗan ƙaramin gyale fari da tayi rolling kanta

Ta ce "ƙazama fa kace darling!"

"Eh ƙazama, to bari kiji, ni ba mijin ƙazama ba ne, matata ta fi ki da komai sau ɗari, dan haka ki kama kanki" yana gama faɗar haka ya miƙe, ita ma tashi tayi da sauri ta ce "mata?, wacece ita?"

"Ina ruwanki?, ina so ne dai ki sani, ni ina da wacce nake so kuma zan aura, kamila ba irinki ba watsatstsiya, hope you get me right?.....idan kin gama za ki fita ki rufw mun ƙofa da kyau"

Ya kwace wayoyinshi ya wuce bedroom ya bar ta nan

Ta ce "tashi hankali, kenan Ammi ƙarya tayi ma Mummy wai ni ce matarshi? Ko kuma Mummy ce ta mun ƙarya?, hmm ƙazama, watsatstsiya, ni?, to wallahi da sake, sai kasan ko da wa kake"

Ta juya a fusace ta bar palourn, ƙofar ma ba ta tsaya rufewa ba, bare ma wai har ta rufe ta da kyau..................










🥰UMMEETA🥰......📝

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

       ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
: ♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA DAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin qirqirar shi nayi,idan yayi daidai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 15*

Bayan fitar Farha daga part ɗin, direct main palour ta nufa tana kuka, ko kallon su Yasmin bata yi ba, ta haura sama

Yasna ta kyalkyale da dariya ta ce "Allah ya ƙara, ba ke uwar iyayi ba! To kaɗan kika gani in dai Sweet Bro ne"

Yasmin ta ce "wai me yasa kike haka ne? Kuka fa take yi"

"Ta yi na jini, ina ruwana"

Farha ce ta sauko da sauri, har yanzu tana share hawaye, ta ce ma Yasmin "ina Mummy?"

"Ai kina barin palourn nan suka fita"

Ba tare da ta ce komai ba ta fita

Tsaki Yasna tayi ta ce "kya kai su in kaya ne, kin ga Twinny, ni zan je inyi shirin islamiya, idan kin tashi sai ki zo ki shirya kema" daga haka ta haura sama abunta



Farha kuwa na barin palourn, parking area ta wuce, ta ɗauki motarta, dan da motar gida su Ammi suka fita, driver ya kai su


Wani hotel ta tafi, kai tsaye ta wuce room 102 tayi knocking, wani matashin saurayi ne ya buɗe, bata bi ta kanshi ba ta shiga cikin ɗakin

Samira na zaune kan gadon tana shan shisha, sai wani saurayin kuma dake kwance kan gadon yana danna waya

Wanda ya buɗe mata ƙofar ne ya dawo ya zauna kan kujerar ɗakin, ya ce "haba star girl, sai yanzu za ki zo?"

Ko kallonshi ba ta yi ba, ta ci gaba da shan shishar da ta kar6a hannun Samira, ya sake cewa "wai meke damunki ne?"

Samira ta ce "dalla kyale ta KB, tana ta faman wahalar da kanta akan wani"

KB ya ce "waye wannan shi ɗin da har ya isa ya canza ma star girl mood haka?"

Samira ta ce "wannan dai Arshad ɗin, gidansu ta je ai"

Wanda ke kwance kan gadon ya ce "waye kuma Arshad? Har ya kai namijin da zai tayar miki da hankali haka?"

Wani wawan kallo Farha ta mishi, Samira ta ce "Jabir ka kuwa san waye Arshad?, AAJ fa"

Miƙewa yayi zaune ya ce "AAJ!!!, wannan gayen?"

"Kwarai kuwa"

"Lallai dole ki haukace akan shi"

Farha ta kalle shi ta ce "tabbas na haukace akan shi, amma dole ne shi ma sai ya haukace a kaina"

KB ya ce "ta ya?, kin san fa irin su ba wani kula mata suke yi ba"

Ta ce "baya kula mata, amma an samu ya kula wata daban, wacce ba ni ba, kuma na ɗauki alwashin raba su"

Samira ta ce "wacece wannan da har ta samu damar kula Arshad, har ta samu lokacinsa?"

"Ban san ta ba Samy, kuma bana son saninta, amma for sure sai na raba su"

Jabir ya ce "ka ji mun sakarci, ta ya za ki raba su bayan ba ki ma san ta ba?"

Sai da ta galla mishi harara sannan ta ce "ko ma dai ya zanyi, ba ruwanka"

Tsaki yayi shi ma, ya gyara kwanciyarshi, ya ce "aiki ya same ki kuwa"

Bata tanka shi ba, ta ce ma Samira "Samy, tashi za muyi ki rakani, dan ban ga ta zama ba"

"Zuwa ina kuma?" cewar Samira

"Gidan Malamin Mummy za muje"

KB ya ce "ku dai mata kun yarda da Malamai ko?"

Farha cikin fushi ta ce "KB kar ka gaya mun ba daɗi, ai naga kuma mazan yanzu ba'a bar ku a baya ba"

"Allah ya ba ki haƙuri star girl"

"Ameen" ta amsa tana tashi tsaye, ta ɗauki jakarta da mukullin motarta, ta ce "ke kuma idan za ki rakani ki tashi mu tafi"

"Abu dole" cewar Samira, ta juya tayi ma Jabir da ke ta danna wayarshi peck a kumatu, ta ce "i will be back dear"

"Safe Journey" kawai ya ce mata

Har sun kai ƙofa, KB ya ce "star girl haka za ki tafi ba kuɗin abar? Ta ƙare fa"

Tsaki tayi, ta buɗe jakarta ta fiddo kuɗi ta ba shi, bata ma san nawa bane, dan ta matsu ta kai wurin Malam

"Yawwa ƴar gari, a dawo lafiya" inji KB yana kallon kuɗin yana murmushi, fita  kawai suka yi ita da Samira 

********************

Hanan ce zaune a gidansu Yuhaness, a tsakar gida, Yuhanees ɗin tana tsintar shinkafa

Yuhanees ta ce "Hayatee, nayi nazari, na duba, gidan nan gabaɗaya ban san me zamu sayar ba wanda zai kai ko da 100k ne, amma wallahi ban samu ba, shiyasa na fara tunanin ko zamu nemo rance ne?"

"A ina, Rabin rai?, ni dama na gaya miki, na san ba wani abunda za'a samu na siyarwa, kawai dan ki kwantar mun da hankali ne, amma zamu samu ko tayaya ne"

"Ba wai za'a samu ba, kin ga yau da gobe muke da, jibi Monday, kuma kinsan Mu'azzam yayi tunanin zai kar6a kuɗin satin nan da ya ƙare amma bai ansa ba, to kin ga kuwa ina kyautata zaton farkon satin nan da zamu shiga zai iya buƙatarsu"

"A'a, Mu'azzam ya tabbatar mun sai upper week sannan zai kar6a, amma dai duk da haka na fi so kuɗin su bar hannuna before then"

"Nima dai abunda na gani kenan, we will think about it dai.....amma wallahi al'amarin MK na matuƙar ba ni mamaki, ace cikin millions of naira, amma ana tsoron gaya maka babu 400k, saboda tsabar son kuɗi?"

Hanan tayi ajiyar zuciya ta ce "Rabin rai, duk yanda za'a ba ki labarin MK akan kuɗi, ba za ki gane ba, in dai ba kina tare da shi ba, ke dai Allah ya bamu mafita kawai"

"Ameen to"

Tashi Hanan tayi ta ce "bari in wuce ni dai, wurin Bala mai kayan miya fa za ni ammana biyo ta nan, na san yanzu idan Ummi ta ga na daɗe za ta ce za ta ɗora abincin"

"Ba Siyama na nan ba?"

"A'a tana islamiya"

"Oh eh haka ne, to ki gaida Ummi, sai munyi magana dai"

"Yawwa, ina gaida Umma idan ta dawo"

Suka yi sallama ta fita daga gidan, ta wuce ta siyo kayan miyanta sannan ta wuce gida


Kamar yanda ta faɗa kuwa, Ummi na zaune a tsakar gidan tana koƙari hura wutar gawayi

"Dama ai na faɗa, to Ummi na dawo, ta shi inyi"

"Ai naga rana nayi, shiyasa na ce to bari in hura wutar, ko ruwa ne in ɗora miki"

Cire hijab ɗin ta tayi, ta rataye shi kan igiya, ta kar6i ashanar daga hannun Ummi, ta ce "gidansu Yuhanees na biya shiyasa, kuma kin ga Umma bata nan, ai da ta koro ni har sai mun gama abinci sannan" ta ƙarasa maganar tana dariya

Ummi da ta koma kan tabarma ta zauna, ta ce "ai ta san idan ba ta koro ki ba, to haka zaku yi ta hira, ba wanda zai yi aikin cikinku"

Hanan dai dariya kawai take yi, Ummi ta sake cewa "yawwa, anyi ta kiran wayarki ma, ashe ba da ita kika tafi ba"

"Eh na barta ɗaki ne"

"To yanzu ma tana ɗakin, idan kin ɗora tukunyar sai ki duba mai kiranki"

"To Ummi"

Sai da ta ɗora tukunyar sannan ta wuce ɗaki, ta duba ko wa ya kira ta

Numbern Arshad ne dan har yanzu bata yi saving ba

"Kaiii....Allah ya sa lafiya, 13 missed calls"

Kiran shi tayi, bugu ɗaya ya ɗauka kamar wanda ke jiranta

"Dan Allah Sarauniya hukuncin nan ya mun tsauri" abun da ya fara faɗa kenan yana ɗaga wayar

Murmushi tayi ta ce "ai kafi ƙarfin in maka hukunci, sai dai kai ka mun"

"Akan wane dalili zan hukunta ki?"

"Akan na ƙi ɗaga wayarka mana"

"Tab, ai ba zan iya ba, amma gaya mun, me ya hana ki ɗaga wayar"

"Na je siyan kayan miya ne"

"Da kan ki?"

"Eh, Siyama na islamiya"

"Ok, yanzu ma na kai su Yasna islamiyar, saboda kawai kar na huta, each saturday and sunday wai ni suke so in kai su"

Ƴar dariya kawai tayi ta ce "amma ba suyi latti ba? Na ga yanzu 12:03pm"

"Ai ƙa'idar makarantar 12-6 ne"

"Oh, su Siyama kuma 8-2 ne"

Murmushi yayi ya ce "su Hanan da Arshad kuma fa?"

Dariya tayi ta ce "24hours"
Shima dariyar yayi, ya ce "dama muryarki nake ao inji, ko za'a amfana da ni yau, kin san you are my strength, so yanzu fita zanyi"

Murmushi tayi ta ce "to Allah ya kiyaye mun kai, ya tsare ka daga sharrin mutane da aljanu, da......"

"Da me?"

"Da sharrin idanun mata mana"

Dariya yayi ya ce "just calm down my angel, i'm only yours, and i will be yours forever and ever, no matter what"

"Thank you"

"I love u dear"

"Love u too"
Suka kashe wayar cike da so da ƙaunar juna, jin kan su suke yi kamar sunyi shekaru tare, gashi ko wata basu yi ba

Ta fito waje, Ummi ba ta kan tabarmar, ta leƙa ɗakinta, ta ga tana bacci, sai ta fito ta gyara kayan miya, dama jollof ce za tayi

********************

Farha da Samira ne zaune a gaban Malamin su na ta kallon shi, sai wai wasa da ƙasa yake tayi

Can ya nisa, ya kalli Farha ya ce "yawwa ƴar gidan Hajiya, ya akayi? Ina saurarenki yanzu"

Gyara zama tayi, ta ce "Malam, wannan zuwan kaina ne, ba Mummy ta aiko ni ba kamar yanda kake tsammani"

"To ina jinki"

"Yawwa, Malam ai ka san Arshad ko"

"Kwarai kuwa, ai na sha yi wa Hajiya aiki akan Mahaifiyar shi Arshad ɗin"

"To, ko ma dai menene, ni dai zuwa nayi domin ka sa shi ya so ni, sannan akwai wata wacce yake so, ina so ka cire mishi sonta gaba ɗaya daga cikin ranshi, sannan ina so ya dawo tafin hannuna, domin in riƙa juya shi son raina, yayi mun biyayya fiye da yanda zai yi wa mahaifiyarsa"

Ajiyar zuciya yayi, sannan dai ya bubbuga ƙasar da ke gabanshi, yana wasu surutan da shi keɗai yake jin abun shi, sannan ya kalli Farha ya ce

"Ƴar gidan Hajiya, ina so ki sani, Hajiya ma da kanta ta zo nan kwanan baya, akan in mata aiki kwatankwacin wannan, sai dai ita ba so take yi ya rabu da wata ba, so take yi ya aure ki sannan kuma ya dawo ƙarƙashin ikon ta, ta yanda zata sa shi ya mayar da duk abunda ya mallaka a duniyar nan da sunanki, sannan a kashe shi daga baya"

Da sauri ta ce "kisa kuma Malam? A'a ni dai bana so a kashe shi, amma dai ayi yanda ta ce ɗin"

"To ai abunda nake so ki gane shi ne, ni ba wani aiki da zan iya yi akan shi, domin a tsaye yake, sam ba ya wasa da ibadah, sannan ga yawan adhkar, duk wasu addu'o'in tsari da kika sani, da ma waɗanda ba ki sani ba, ba wanda ba ya yi, safe da yamma, ga yawan nafila cikin dare, dan haka duk wanda zai gaya miki cewar zai iyayin nasara akan shi ta wannan hanyar, to ƙarya kawai ya miki domin ya ci kuɗinki, abu ɗaya kawai na gano miki yanzu, ita yarinyar ƴar talakawa ce, dan haka idan kina son samun shi, shawara ɗaya zan ba ki, kiyi amfani da kisisina da makirci irin yanda wasu matan ke yi, dan ki cimma burinki, amma ta wannan hanyar, ba zai ta6a yiwuwa ba"

Kallon juna suka yi ita da Samira sannan ya kalle shi, ta ce "to Malam ya zanyi kenan?

"Ki na mace, amma ba ki san yanda za kiyi ba?, ki je kiyi shawara da ƙawayenki"

Shiru tayi kusan mintuna uku, sannan tayi ajiyar zuciya, ta buɗe jakarta ta ƙirgo kuɗi ta ba shi, sannan ta ce "nagode Malam, sai anjima.......Samy tashi mu tafi"
Haka suka taso suka bar ɗakin

Zaune suke cikin motar, tsawon wani lokaci, sannan Samira ta ce "to wai yanzu Farha, meye abun yi? Kin ji dai abunda ya faɗa"

"Hmm, Samy nima abunyi nake tunani anan, kuma yanda zai so ni ne yafi damuna, dan tunda naji yarinyar ƴar matsiyata ne, to na san Ammi ma ba zata ta6a yarda ba, shiyasa na ajiye maganarta gefe ɗaya, zanyi wa Mummy magana, zamu nemo mafita"

"Shikenan, kiui mata magana, amma kar ki yadda ki ce kin share maganar yarinyar ita ma"

"To meyasa"

"Na dai gaya miki"

"To shikenan naji......yanzu dai ina zan kaiki? Gida ko wurinsu KB za ki koma?"

"Kai ina!!! Kai ni gida kawai"

Tayar da motar tayi suka ɗauki hanyar gidansu Samira

********************

Ku san lokaci ɗaya Ammi da su Yasna suka dawo, ƙarfe 6:42pm

Arshad na gama parking, ya fito suka gaisa da Ammi, sai ya wuce masallaci, dan ana dab da fara kiran magrib, su kuma su Ammi suka shiga gida, dan su Ammi sun aje Hajiya Karime gida


Ammi ta wuce ɗakinta, su ma su Yasmin suka wuce ɗakinsu, suka cire uniform suka yi wanka sannan suka yi sallah

Ba su fito ba sai da suka yi sallar isha'i, sannan suka dawo palour.Saukowarsu yayi dai-dai da shigowar Arshad, suka gaisa, sannan ya gaida Ammi, suka wuce dinning area, suka fara cin abinci

Arshad ya ce "yawwa Ammi, wai ina kika tafi ne yau tun safe?"

Kallon shi tayi sannan ta ce "ABMAD store na tafi, na duba kayan da za'a ƙaro ne dan inyi ordern su"

"Wane ABMAD ɗin Ammi?, supermarket ko na kasuwa?"

"Na kasuwa mana, supermarket ai shekaran jiya aka kawo kaya"

"To ai na ga na kasuwan ma akwai kaya, ba na gaya miki lokaci ɗaya na duba su ba da supermarket, amma ba wasu kayan da ake buƙata"

"To me kake nufi? Ban da ikon zuwa in duba abunda ke gudana a kasuwanci na sai kai?"

"A'a Ammi ba haka nake nufi ba, shikenan a bar maganar, kiyi haƙuri"

"Amma idan ba rainin hankali ba, yaro ya tsare ka kamar shi ya haife ka?"

"Nace i'm sorry Ammi na"

"Ya wuce ai"

Basu sake cewa komai ba, suka ci gaba da cin abincinsu, Yasmin da Yasna dai ba su ce komai ba

Suna gamawa, Arshad ya musu sai da safe ya wuce part ɗin shi

Wanka yayi, yayi alwala, sannan ya kira Hanan, sun daɗe suna waya, gwanin burgewa, ji suke yi kamar su kwana a haka suna wayar

Arshad ya ce "yawwa my angel, ranan kin ta6a gaya mun kina aiki, amma baki gaya mun wane irin aiki bane"

"Aikin company ne"

"Kaiii....ashe dai matar tawa babba ce, me kika karanta ne?"

Dariya tayi ta ce "Business Admin"

"Da gaske?"

"Eh, akwai wani abu ne?"

"A'a, kawai ina mamakin yanda muke da ZUCIYA ƊAYA tun ma kafin mu haɗu, kin san nima abunda na karanta kenan"

"Amma ni na karanta shi ne, saboda na so na zama kamar mahaifina, amma na fahimci banda experience irin na shi akan business, tun da har yanzu a ƙarƙashin wani nake"

"Haba my angel, kina da experience tunda har kika karanta Business Admin, da kaɗan-kaɗan ake fara komai, wata rana za ki kasance tamkar mahaifin naki, wataƙila ma har ki fi shi"

"To Allah ya nuna mun wannan ranar"

"Ameen, amma a wane company kike aiki?"

"MK Investment Limited"

"MK......Investment???"

"Eh, ka san shi ne?...ko da yake ma za ka san shi"

"A'a ba wai sanin shi nayi ba, dama ina tunanin kaman da shi ne muka ta6a haɗuwa a china, kin san akwai wani MI a kano ne ko? To na gane da wannan MK ɗin ne muka haɗu"

"Oh, ai na ɗauka ko ka san shi ne"

Ƴar dariya kawai yayi ya ce "a'a i don't know him,.......za ki fita on monday?"

"Eh"

"Ƙarfe nawa?"

"9:00am"

"To zan zo in kai ki, sai ma in gaida Ummi, dama kwana biyu ban ganta mun gaisa ba"

"To na ka aikin fa?"

"Ko ƙarfe nawa zan iya zuwa ai, in dai ba wani aiki ne mai muhammanci ba, dama ina zuwa da wuri ne saboda hakan ya kamata, kuma aikinki ya fi zuwa company"

Dariya tayi ta ce "amma kuma bana so ka zama zauna gari banza, it's better ka tafi ɗin"

"To naji zan tafi, amma sai na kai ki"

"To Allah ya kaimu, kace zaka haɗa ni da Yasna mu gaisa fa"

"Yau da alama bacci take ji, amma gobe in sha Allah zan haɗa ku, kema yanzu ki kwanta, sweet dreams"

"To Allah ya kaimu, sai da safe"

"Yawwa my angel....kin san me?"

"A'a sai ka faɗa"

"I so much love you" ya faɗa cikin wata irin murya mai sanyi ga daɗi

Murmushi tayi ta ce "love you too dear"

Shi ma murmushin yayi, sai suka kashe waya, sai da yayi nafilolin nan dai as usual, yayi addu'ar bacci, sannan ya kwanta

Ya ɗauki wayar da niyar tura mata message, sai ya ga har ta riga shi, yaji daɗi sosai, sannan shima ya mayar mata da reply ya kwanta



 ```ASUBA TA GARI``` 







🥰UMMEETA🥰......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA DAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin qirqirar shi nayi,idan yayi daidai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏

Ina ƙara miƙa saƙon ta'aziyya ga ɗan uwan mu na Moonlight Writer's Association, EXCELLENCY ISA HAMZA, Allah ya gafarta mata yayi mata rahama, Allah yasa mutuwa hutu ce a gare ta, Allah ya sa aljanna ce makomarta
Allah ya ƙara muku haƙurin rashinta
Allah ya gafartawa sauran musulman da suka riga mu gidan gaskiya, Allah ya haskaka kabarinsu baki ɗaya, Allah ya kyautata ta mu idan ta zo.Ameen

Na jinjina muku ƴan ZUCIYA ƊAYA FANS GROUP❤️ Allah ya saka muku da alkhairi da irin addu'oin ku, Allah ya bar zumunci🥰🤗






 *Page 16*

Hajiya Karime ce ke breakfast ita da Farha, kasancewar Mahaifinta, Alhaji Mus'ab, yayi tafiya

Hajiya Karime ta kalli Farha, da tunda ta taso daga bacci ranta a 6ace yake, ta ce

"Daughter wai me ke damunki ne? Yau gaba ɗaya ban ga annuri a fuskarki ba"

Wani irin kallon shaƙiyai tayi mata, sannan ta kai abinci bakinta, ta ce "akwai abunda nake so zan tambaye ki tun jiya, amma lokacin da na dawo kinyi bacci"

"Nima ai ina so zan tambaye ki, ina kika tafi ne jiya? Har kusan 11:30 ina jiranki, amma har nayi bacci ba ki dawo ba, kar dai yawon nan da na hanaki shi kike so ki ci gaba?! Kin san dai Arshad ba zai ta6a son mace mai yawon banza ba ko!?"

A fusace ta ce " pls hold on Mum, ni ba wannan nake son ji ba, Arshad ɗin da kuke nema ku raina mun hankali a kanshi!"

Cike da mamaki Hajiya Karime ta ce "ban gane ba Farha, me kike nufi? Kamar ya raina miki hankali?"

Cikin fushi, kuma a tsawace ta sake cewa "rainin hankali mana Mummy, duk irin wulaƙancin da yake mun ina shanyewa dan nasan wata rana zan rama, bai isa ba? Amma kun san yana da wata wacce yake so, shi ne ba za ku gaya mun ba" ta kai karshen maganar hawaye na zuba kan fuskarta

Da sauri Hajiya Karime ta dawo kusa da Farha ta zauna, cikin sigar lallashi ta ce "kin ga daughter calm down mana, ki mun bayani, wa ya gaya miki yana da wacce yake so? Wanda ko cikin wasa ban ta6a ji ance ya kula wata ba?"

"Mummy kina so kice mun ba ki ma san yana da budurwa ba?"

"Haba Farha, kamar ba ki san mahaifiyarki ba? Ai kin san inda na sani, da tuni nayi wa tubkar hanci"

"Hmm, to yana da budurwa, kuma a kanta jiya ya mun zagin ƙasƙanci, yace mun ƙazama ya ce mun watsatstsiya" ta sake fashewa da kuka

"Dan girman Allah kiyi shiru, kin san na tsani kukanki......amma ya akayi Hqjiya Ruƙayya ba ta gaya mun yana da budurwa ba"

Cikin sheshsheƙar kuka Farha ke cewa "raina mana hankali ne take yi Mummy"

"A'a Farha, ina da tabbacin bata sani ba, dan ba ƙaramin aiki nayi a kanta ba"

"To kenan shi ne bai gaya mata ba?"

"Haka nake tsammani, amma kar ki damu, zan kira ta"

"Dan Allah Mummy kiyi ƙoƙari kiyi wani abu"

"Don't worry daughter, je ki shirya kawai ki tafi inda za kije"

"Yawwa Mumcy na" ta rungume ta sannan ta wuce ɗakinta

********************

Ƙarfe 12:40pm, Ammi na zaune a balcony tana shan iska, dan ita kaɗai ce a gidan, tun da Arshad ya tafi kai su Yasna makaranta bai dawo ba

Wayarta da ke ƙara ne ya katse mata karatun da take yi

"Hello, Hajiya"

"Na'am Mummyn Farha, ya lafiya yau na ji ki shiru tun safe?"

"Lafiya amma ba lau ba"

"Toooo.....me ya faru kuma? Ba dai matsala aka samu ba ko?"

"A'a ba wannan maganar ba ce, wai Hajiya kina da masaniyar Arshad kuwa yana da budurwa?"

Zaunawa tayi da kyau, da sauri ta ce "ban gane yana da budurwa ba, wacece ita?"

Cikin lumana Hajiya Karime ta ce "a'a Hajiya, ai ba abun tashin hankali bane, dama ina so ne in gaya miki, zan yi ma Farha bayani a tsanake, domin tayi haƙuri kawai da yaron nan, kin ga dama ba sonta yake ba, tunda har ga wacce yake so, kar a tauye moshi haƙƙinshi"

"Dan Allah Mummyn Farha ki daina wannan magar dan ba zata ma yiwu ba, ai wallahi ko ƴar gidan uban waye sai ya rabu da ita"

"A'a dan Allah Hajiya...."

"Kin ga Hajiya Karime, kima daina zancen rabuwa tsakanin Farha da Arshad, kinji na gaya miki, ki barni da shi kawai"

"To shikenan Hajiya, mu wuni lafiya"

"Yawwa, sai anjima"

Suna kashe wayar, Ammi ta sauke wani ajiyar zuciya ta ce "lallai ma yaron nan, kenan ni ce zai yi wa ƙarya?, nayi mamakin yanda akayi Hajjo tace mun yana da budurwa, no wonder......hmm za ka zo ne ka same ni"


Ita kuwa Hajiya Karime tana kashe wayar, ta ce "ka ji banza, hadda wani ƙwalailaicewa wai in daina maganar rabuwa, aivba wannan maganar, dan idan ana ɗaura aure da gawa, to ko da gawar Arshad ne sai anyi.......ko dai kiyi maganin abun ko kuma ni inyi"

********************

Nabeel ne gaban Hajjo suna wasa da dariyar da suka saba, irin ta kaka da jika

"Gaskiya fa Hajjo kin ga duniya, irin wannan daɗewa haka?, kinyi lokacinki, kinyi na iyayenmu, ga na mu nan kina so kiyi" Nabeel ya faɗa yana dariya

"Kuma har na ƴaƴanku ma sai nayi" ta faɗa tana harararshi

"Haba dai Hajjo, mu da har yanzu aurenmu maba rana?"

"Ai gwara kai, ina sa rai za kayi, amma ka ga wancan ɗayan, aikinshi kawai yasa a gaba"

"To Hajjo so kike ya zauna ba aiki ne?"

"A'a, kai ba ga shi kana aikin ba, amma ka samu lokacin samo mata?"

"Ai aikinmu ba ɗaya ba, shi ne boss a wurin aikinshi, dole komai sai da shi, ni kuma ina da lokacin hutu"

"Umm, ko ma dai menene, tun da baka son gaskiya"

"Ba fa gaskiya ne bana so ba......to wai nikam ba ma kin gaya mun yace yana da budurwa ba?"

"Haka dai ya faɗa, amma na ka sa gasgatawa, dan ban ji Ruƙayya ta amsa mun zancen da ƙwarin gwiwa ba"

Tashi tsaye yayi, ya ce "that's how you always behave(haka kike yi koda yaushe ai), sai mutum ya gama ba ki labari, sai ki ƙaryata shi"

"Fatima kayi wa turanci dan ƙaniyarka, kuma na ƙaryata ku ɗin"

Dariya yayi, ya ce "haba Hajjo, hadda zagi? Allah ba ki haƙuri, sai anjima"

"Allah ya raka taki gona"

Ya fita kawai bai ce komai ba, ban da dariyar da yake yi

"Anjima dole in sa a kira mun radion can mai aiki da jini, Husaina, zan ji gaskiyar ai, dan komai da ya shafi Arshad, ita ke fara sani"

Ta jawo wani bowl da mai aikinta ta ajiye mata kan table, zogale ne wanda ya sha haɗi har ya gaji, ta fara ci, tana kallon sunnah tv

********************

Sajjad da Arshad ne zaune cikin wani wurin shan iska, around 5:30pm, sai hira suke tayi

"Gaskiya Super ka tsinci dami a kala, irin wannan soyayya haka?!" Sajjad ya faɗa yana kallon Arshad da ya gama waya da Hanan

Murmushi yayi ya ce "ai Man, ina mamakin irin wannan so da nake yi mata, lokaci ɗaya fa ta shiga raina, sai ka ce wani magani?"

Dariya Sajjad yayi ya ce " ba wani magani, kawai dai haɗuwar jini ne, kuma ina fatan shi ne za6in Allah, wanda ka daɗe kana roƙo"

"Ameen my man"

"Amma ka san me yake ɗaga mun hankali Super?"

"A'a menene?"

"Ina tsoron ranar da Ammi zata san wacce kake so, dan ba budurwar ba ce tashin hankali, idan ta gano ba masu kuɗi ba ne, shi ne matsalar"

Ajiyar zuciya yayi, ya ce "nima shi ne kawai abunda yake bani tsoro Sajjad, sai dai kuma as long as na tuna Hanan, sai inji i can face any problem(zan iya fuskantar ko wace irin matsala) in dai zan same ta"

"Ta ya kake tunanin za ka auri wacce mahaifiyarka ba ta aminta da ita ba?"

"Sajjad, akan Hanan, i can do anything(zan iya yin komai), idan ta kama ma mu bar garin nan, muje wani wuri muyi aure sannan mu dawo, zan yi"

"A'a Super, meye kuma abun barin gari? Ni da nake so auren AAJ ya zama auren da duk duniya kowa zai ji!, sannan a daɗe ana labarin auren a jahar KD da kewaye, to idan ka gudu kayi auren sirri, ai ka rusamun plan"

Dariya AAJ yayi, ya ce "wai kuwa duniya....to AAJ ɗin har wani ne?"

"Ai kai ƙarami kake ɗaukan kanka, amma Allah ya nuna mana auren nan lafiya, kuma yasa da amincewar Ammi, za ka sha mamaki, dan ni da Yasna zamu tsara komai"

"Ai haukarku ɗaya kai da Yasna, shiyasa ta ku tazo ɗaya"

Dariya Sajjad yayi, ya ce "kana wasa kenan, just pray kawai Ammi tayi supporting ɗin auren nan"

"To shikenan, Allah ya sa"

"Yawwa, ameen"

Arshad ya duba agogon hannunshi, ya ce "ya kamata in je in ɗauko yaran nan, kasan na gaya maka zan biya da su gidansu Hanan"

"To shikenan, safe journey"

"Aha, bye" ya faɗa yana kwashe wayoyinshi da mukullin motarshi, sannan ya wuce

********************

Tun da ya ɗauke hanyar gida, Yasna ta ce "Sweet bro, Allah ya sa yau ma ba zuwa za kayi ka ajiye mu ka tafi sha'aninka ba, yanda ka mana last week"

Yasmin dake gaba, ta ce "ke wawuya ce wallahi, kin manta da ya ajiye mu, abunda ya bamu?, ai na fi son haka ma"

"Kaiii......ai kuwa na manta, muje kawai Sweet bro, ba komai"

Sai a lokacin yayi dariya ba tare da ya ce musu komai ba



A bakin ƙofar gidansu Hanan yayi parking, wayarshi ya ɗauka ya kira Hanan, tana ɗauka ya ce "gamu a ƙofar gida"

"To su shigo mana"

"Ok" sai ya kashe wayar

Kallon Yasmin yayi ya ce "Yasmin, gidan nan za ku shiga" ya faɗa yana nuna gidan

Wani wulaƙantaccen kallo Yasmin tayi ma gidan, sannan ta kalle shi ta ce "me kuma zamu yi a ciki?"

"Idan kika shiga za ki gani"

Ita dai Yasna ba ta ce komai ba, ta ajiye jakarta ta fita, kallonshi Yasmin ta sake yi ta ga ya 6ata fuska, sai ita ma ta ajiye jakarta ta fita

A zauren gidan suka tsaya, Yasna sai kwala sallama take yi, sai ga Siyama ta zo cikin fara'a ta ce "sannunku da zuwa, ku shigo mana"

Murmushi kawai Yasna ke yi, ita kuma Yasmin fuskar nan a kwa6e, sai wani harare-harare ta ke yi, har suka shiga cikin gidan

Kan tabarma suka zauna, inda Ummi take zaune, suka gaisa, Yasna ce kawai ta saki fuska har suka gama gaisawa da Ummi da Siyama

Siyama ta ce "dama Ya Arshad yace you look alike" ta nuna Yasna tace "ke ce Yasna ko? Wannan kuma Yasmin"

Murmushi Yasna tayi ta ce "haka ne, to amma ya akayi kika gane?"

"Ai yace Yasna kamar bulala take bata da jiki, sannan ta fi sakin fuska"

Shagwa6e murya Yasna tayi ta ce "ni ce kamar bulala?"

Siyama ta ɗaga kai tana dariya, ta ce "Ya Arshad ya faɗa, ba ni ba"

Yasna ta wani ƙara marairaicewa, Ummi tayi dariya ta ce " kin ga, kyale ta, ai ba ke kaɗai ce me kama da bulalar ba, hadda ita, da me ta fiki?"

Ai kuwa Yasna tayi ma Siyama gwalo tana dariya, Yasmin kam banda harara da yatsinar fuska ba abunda take yi

Ummi ta ce "Siyama , shiga ki gaya wa Hanan sun shigo, naga har yanzu bata fito ba"

"To, may be kaya take sawa, kin san yanzu ta fito daga wanka" cewar Siyama tana miƙewa tsaye ta shiga ɗakin Hanan ɗin

Yasna ta kalli Ummi, ta ce "ke ce Ummi?" ta tambaye ta cikin mamaki

"Eh, ni ce" Ummi ta amsa mata

"Laaaaa.....Ummi ya jiki? Wallahi kwata-kwata ban gane ba, sai yanzu da na ji kin ce Hanan"

Murmushi Ummi tayi, ta ce "ai naji sauƙi sosai Yasna"

"Kiyi haƙuri Ummi, wallahi da farko ba gane ba, kawai dai nayi shiru ne"

"Ba komai ai Yasna"

Yasmin sai wani kallon mamaki take bin Yasna da shi, a ranta ta ce "kenan ta san su?......ko dai labarinsu ta sani?.....oh God, Big Bross da Yasna akwai shegen kwashe-kwashen tsiya, ko ina suka haɗu da waɗannan kuma, oho? Hadda wani ya jiki?, kar Allah yasa ta ji sauƙin, ina ruwan mu, mtwsss"

Hanan ce ta fito, sanye take da jallabiya sea green, tayi ma farar fatarta kyau sosai, ba abunda ta shafa ma fuskarta banda mai, ko kwalli bata sa ba, amma sai wani kyalli take tayi, dan Hanan masha Allah, in dai maganar kyau ne kam, abun a'a magana, dan ta haɗu ta ko ina, ga madaidaitan idanu masu ɗauke da dogayen eyelashes, sannan baƙin idonta blue neda ratsin baƙi-baƙi a ciki, ga hanci, ga ɗan mitsitsin bakinta mai two colour, red and brown, sai kace ta zana shi da eye pencil, maganar gashi kuma ko a garinsu feeza ƴar india take, za'a sara mata, a india kenan, dan gashinta akwai tsayi, ga santsi sannan baƙi ne sosai, Hanan dai ta ciri tuta, in dai kyau ne

Da sauri Yasna ta miƙe tsaye tana kallonta har ta ƙaraso kusa da ita, kan tabarmar, Yasna sai yaba irin kyaun Hanan kawai take yi a ranta, da farko Siyama take ta yabawa amma sai ta ga ashe kyaun Siyama ba komai bane in dai ga Hanan, kamar yanda ta san duk irin kyaunsu ita da Yasmin, in Arshad ya zo, to su ba komai bane a kyau

Maganar Hanan ce ta dawo da ita, "ki zauna mana Yasna, na san i made a mistake(nayi laifi), i kept you waiting(na bar ku kuna jira), so sorry dear"

Zama suka yi tare, sannan Yasna ta ce "a'a aunty Hanan ba komai ai.....ina wuni"

Murmushi tayi, sannan ta ce "lafiya ƙalau, ya Ammi"

"Tana lafiya"

Hanan ta kalli Yasmin da hankalinta gaba ɗaya yana kan kallon gida, ta ce "malama Yasmin, ba gaisuwa?"

Sai lokacin ta ma kalle ta, tabbas ta yaba kyaun Hanan, amma shegen halinta bai bari ta fahimci hakan ba, a hankali ta ce "ina wuni?"

"Kin wuni lafiya?"

Ɗaga mata kai kawai tayi, Hanan ta ce "to ga ruwa nan ku sha, sai ku tashi muyi sallah, dan na ji kamar an fara kira ko?"

Yasna ta ɗauki ruwa ta sha abunta, Yasmin kam mamakin Yasna take tayi, wai yau ita ke shan ruwan leda? Tirƙashi, hmm.Ita fa komai ƙyamarshi take ji na gidan, ba wai dan gidan nada ƙazanta ba, tsabar wulaƙanci ne kawai, gidan madaidaici ne dai-dai ƙarfinsu, amma ba wanda zai shiga gidan ya ce ya ga wata ƙazanta ko ƴar kaɗan ce, dan tun daga kan Ummi, Hanan, har zuwa Siyama, dukansu suna da tsafta sosai, kuma kullum gidan cikin ƙamshin turare yake kamar dai yau 

Tashi suka yi, kowa yayi alwala sannan suka shiga ɗakin Hanan, Ummi ce kawai ta shiga ɗakinta

Sun idar da sallar, suna ta hirarsu banda Yasmin dake bin su da ido, wayar Hanan tayi ƙara, ta ɗauka tana murmushi

"Gimbiya shanyar da kuka yi ta bushe, ki ce su fito mu tafi" abunda ta ji ya fara faɗa kenan

Dariya tayi, ta ce "we are so sorry dear, ga su nan zuwa" sai ta kashe wayar

"Yasna, ku tashi,ya ce wai ku fito haka nan" cewar Hanan ɗin

Tun kan ta rufe baki, Yasmin ta tashi da sauri ta bar ɗakin, tayi waje.Rakata suka yi da ido, ba wanda dai yace komai

Yasna dai ba wai dan ta gaji da su ba ne ta taso, sai dole, sai da suka shiga tayi ma Ummi sallama sannan suka fito ita da Hanan, dan Siyama daga bakin zaure ta koma

Arshad na tsaye jikin mota shi da Yasmin, da alama dai magana suke yi, shiru suka yi da su Hanan suka fito

Yasna ta tsaya kusa da shi ta ce"Sweet Bro ka bari sai munyi sallar isha'i mana, ni dai ban gaji da su ba"

Yasmin ta watso mata wani mugun harara, duk da bata ma ga ta harare ta ba, tunda duhu ya sauko, sai hasken glubs ɗin gidajen mutane kawai da ya haska wurin, ta ce "ai sai ki kwana a nan ɗin, idiot"

Arshad ya ce "zan kwaɗa miki mari wallahi, kin san ni, da ke take?"

Shiru Yasmin tayi  tana wani huci, tana ƙara hararar Yasna da Hanan ɗin

Hanan ta ce "mai yayi zafi? May be dai ta matsu taje ta ga Ammi ne, that's why(shi ya sa)......sorry dear, you will soon meet your Mom(za ki haɗu da Ammin ki nan ba da jimawa ba)" ta ƙarasa zancen tana kallon Yasmin da ko kallon arziki bata yi mata ba.

 Ta sake kallon Arshad, ta ce "cool down dear, sorry"

Wani murmushin gefen baki yayi, ya ce "ai dole za ki ce sorry, tun da na kawo miki waɗanda suka fi ni muhimmanci, sai kika manta da ni ko?"

Shafa fuskarta tayi tana murmushi, ta ce "ai wanda zai fi ka muhimmanci wurin Hanan sai ya shirya, kawai dai ɗaukin ganinsu nake yi"

"Ai kuwa na gani, ba ki ma damu ki zo mu gaisa ba, ko ki bani ruwan sha, ko kuma ki bani ruwan alwala ma"

Ɗan buɗe ido tayi tana dariya, ta ce "na manta wallahi, kayi sallah?"

"Ban sani ba, ai wacce ta damu da ni ta zo mun gaisa, kuma ta kawo mun ruwa, har masallaci sai da ta nuna mun sannan ta koma cikin gida"

"Wacece?" ta tambaye shi tana ɗan 6ata fuska

Dariya yayi ya ce "ke dalla malama ba fa wata ba ce, ƙanwata ce, Siyama"

"Oho, ai na ɗauka ko wata ce"

Dariyar ya kuma yi, ya ce "ashe dai kina so na"

Tayi dariya kawai tana rufe fuska, Yasna tayi gyaran murya ta ce "to romeo and juliet, mun gaji da tsayuwa fa, ka buɗe mana mota mu shiga mu zauna kafin ku gama love" ta ƙarasa tana dariya

Su ma dariyar suka yi, sannan Hanan ta ce "yi haƙuri kinji, ku tafi kawai, sai da safe, ina gaida Ammi"

Arshad ya ce "ban gane sai da safe ba!"

"Eh mana, we'll talk through the phone(za muyi magana ta waya)"

"To shikenan, ki gaida Ummi.....love u"

Murmushi tayi ta ce "love you too, safe journey"

Ta juya kawai ta shiga gida, shi kuma ya zagaya ya buɗe musu motar suka shiga

Yasmin ta zauna backseat, sai saƙa abubuwa take yi a ranta, musamman idan ta tuna ɗan conversation ɗin nan da Arshad da Hanan suka yi yanzu, ji take yi da ace tana da dama a wannan lokacin sai tayi mata shegen duka (sai kace zata iya.....Lol)

Yasna kuwa sai labarin yanda aka tarbe su take ta ba Arshad, ya ji daɗi sosai, dama yayi expecting ɗin hakan, ga shi sai yabon Hanan take yi, shi kuma sai ji yake yi yana ƙara sonta, da haka har suka isa gida............








🥰UMMEETA🥰......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA DAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin qirqirar shi nayi,idan yayi daidai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 17*


Tun lokacin da suka isa gida, ba su haɗu da Ammi ba dan tana cikin ɗakinta, su kuma ɗakinsu suka wuce suka yi wanka, suka yi sallar isha'i sannan suka fito palour suka zauna zaman jiranta

Yasna ta kalli Yasmin ta ce "dan Allah twinny ya kika ga Aunty Hanan?"

Yasmin ta gane wa take nufi, amma sai ta wayance, "wacece haka nan kuma?"

Kallon mamaki ta mata sannan ta ce "wacce muka fito gidansu yanzu mana, za6in Sweet Bro"

"Za6in Sweet Bro kuma?!  Ban gane ba, za6i a ina?"

"Mtwss, wai me yasa kanki baya ja ne for God sake, to budurwar Sweet Bro"

"Budurwa?,.....yawwa dama zan tambaye ki, wai su waye waɗannan? Gida sai kace keji!?"

Cikin jin haushin maganarta, Yasna ta ce "Keji???....Keji fa kika ce......dan kawai kin ga Allah ya rufa miki asiri ya kawo ki cikin wannan mansion ɗin, shi ne har kika sami bakin da za ki kira muhallin bayinsa da keji!?, To wallahi ki daina, dan ko wane lokaci Allah zai iya jarabtarki da zama cikin irin wannan gidan ko ma wanda ya fi shi ƙanƙanta"

A hasale Yasmin ta tashi, tana nuna Yasna da ɗan yatsa, ta ce "God forbid(Allah ya kiyaye), ni kike yi wa irin wannan fatan? To sai dai aniyarki ta bi ki, kuma kar ki kuskura ki sake danganta ni da gida makamancin wancan kurkukun, akan me?" ta juya kawai ta wuce

Sama ta haura, bata tsaya ko ina ba sai ɗakin Ammi

Tana nan zaune palournta, gaba ɗaya ta rasa abunyi, jiran dawowar Arshad kawai take yi, dan bata ma san sun dawo ba

Yasmin ta turo ƙofa ta shiga ɗakin, ranta a 6ace

Kallonta Ammi ke yi, har ta zo kusa da ita ta zauna, Ammi ta ce "lafiya? Yaushe kuka dawo?"

"Mun kai 15mins da dawowa"

"Ina shi Arshad ɗin?"

"Bai shigo ba, yana part ɗin shi"

Har Ammi zata tashi, sai kuma ta zauna tana kallon fuskar Yasmin, ta ce "lafiya kuwa? Kin wani 6ata rai haka!"

"Hmm....Ammi, bari in gaya miki gaskiya, wallahi ki taka wa Big Bross birki, idan ba haka ba kuwa, zai ɗauko miki abun kunya"

Cikin rashin fahimta Ammi ta ce "ban gane abun kunya ba Yasmin"

"Ammi, me Aunty Farha ta rasa da har Big Bross ya ce baya sonta, ya koma can wata ƙazamar anguwa, ya ɗauko wata ƴar gidan talaka, wai ita yake so"

Cikin ruɗu, Ammi ta ce "yanzu kina nufin  da gaske ne Arshad yana da budurwa?"

"Wallahi Ammi, sai ma kin ganta kin ga gidansu, gidan sai kace wani akurki, da ƙyar na ga na fito gidan"

"Da ya ce mun zaku biya wani wuri, ashe gidansu zai kai ku dama?"

"Eh"

"Tirƙashi......hmm, ina zuwa"

Fita tayi daga ɗakin a fusace kamar za ta tashi sama, Yasna na zaune a parlour tana game da wayarta, tana jiran masu aiki su gama jera musu dinner sannan ta kira su, sai ganin fitar Ammi kawai tayi daga palourn

Ajiye wayar tayi tana kallon ƙofar, ta ce "Ammi!!!!.....to lafiya take wannan sauri haka? Ina za ta je to? Mts" tayi gajeren tsaki, ta tashi da gudu ta fita daga palourn ita ma, ta bi bayanta

Arshad na kwance kan cushion, sai waya yake tayi cikin farin ciki, da alama da Hanan yake waya

Wani wawan bankaɗo ƙofar ɗakinshi ya ji anyi, sai da ya firgita, dan tun da yake ba wanda ya ta6a bankaɗo mishi ƙofa haka

Da sauri ya tashi zaune, yana cewa "I'll call you back(zan kira ki)" bai jira ta amsa ba, ya kashe wayar, ganin yanayin Ammi ya tsorata shi

Har ta ƙaraso gabanshi yana kallonta, sannan ya miƙe tsaye, ya ce "Ammi lafiya?"

"Ban sani ba!" ta faɗa a tsawace, tana huci

A lokacin ne Yasna ta shigo ɗakin da gudu, tana kallonsu cikin mamaki

Ammi ta ce "Arshad yaushe ka fara mun ƙarya? Iye?"

"Ƙarya kuma Ammi?" ya tambaye ta cikin mamaki

A tsawace ta ce "kar ka raina mun hankali Arshad, taya zan nemo maka mata kamar Farha, amma kace baka sonta, kuma ka rasa wacce za ka so sai ƴar talaka, jinin matsiyata?"

"Ammi....."

"Rufe mun baki" ta sake yi mishi wata tsawar, "wallahi ka kiyaye ni, ba kai ba wannan fitsararriyar, hadda wani kwashe mun yara ka kai su, dan kawai a goga musu tsiya ko!"

Sunkuyar da kai yayi kawai, yana ji ranshi na 6aci, Yasna na kallonshi ta ji gaba ɗaya bataji daɗi ba, ta ƙaraso kusa da Ammi ta ce "haba Ammi, waɗannan kalaman fa basu dace ba a matsayinki na mahaifiya, kin......"

Nuna ta Ammi tayi da yatsa tana girgiza kai, ta ce "don't you ever interrupt(kar ki yadda ki sa baki), ai duk abunda yayi kina sane, amma da yake kina da shegen hali irin na shi, sai baki gaya mun ba, to ki kama bakinki kafin in 6alla ki a gidan nan..........kai kuma ka buɗe kunnenka da kyau ka saurare ni, Wallahi in dai nice na haife ka, in ni ce mahaifiyarka, ba tsinto ka nayi ba, to ka sani, baka da mata a duniyar nan da ta wuce Farha, kar in sake jin ka ta wata ƴar iska, and that's my final say(shi ne magana ta ta ƙarshe)" tana gama faɗar haka, ta kalli Hanan tana watsa mata wani mugun harara, ta ce "and you....., behave yourself(ki kiyaye ni)" ta fita ba tare da ta rufe ƙofar ba, sai Yasna ce ta je ta rufe ƙofar ta dawo

Zubewa yayi kan kujera, ya rufe ido, yana fitar da numfashi a hankali, yana karanto addu'o'i dan ya samu ya rage jin abunda yake ji a ranshi

Yasna sai aikin kallonshi take yi, sannan ta tashi ta ɗauko ruwan sanyi a fridge, ta zuba a cup, ta ba shi

Ƙar6a yayi yana sipping a hankali, har ya shanye, ya ba ta cup ɗin ta mayar, ta zo kusa da shi ta zauna

"Sweet Bro dan Allah kayi haƙuri, na san Ammi ba ta kyauta ba"

Murmushin takaici yayi, ya ce "Sweetie, na san hakan zai faru, kuma fiye da hakan ma zai iya faruwa tun da har nace bana son Farha, sannan kuma na ɗauko wacce ba ƴar masu kuɗi ba nace ita nake so, abunda ke ba ni haushi bai wuce wai mahaifiya ta ce ke da irin wannan hali na ƙyamar talaka, i'm always missing Abbi at this moment Sweetie, da ace yana nan, duk wannan abun zai zo da sauƙi"

Cikin muryar kuka Yasna ta ce "kayi haƙuri Swwet Bro, nima nakan yi irin wannan tunanin, amma in sha Allah komai zai zo da sauƙi, ina ji a jikina, kai da Aunty Hanan you're made for each other, kuma you will be together forever(zaku kasance tare har abada)"

Wannan maganar ta tayi, sai ya ji ta kwashe mishi kusan 50% of his worries(ku san ka shi hamsin na damuwarsa)

Ya ce "thank you dear" ya rungume ta

Sun kai 5mins a haka sannan ya ce "tashi ki tafi ɗakinku ki kwanta"

"Amma ai ba ka ci abinci ba"

"Ke kin ci me?"

"A'a, amma ina zuwa" ta tashi ta fita daga palourn

Main palour ta koma, Ammi na nan zaune tana waya, ko ba'a gaya mata ba, ta san da Hajiya Karime take wayar

Bata ko kalli gefen da take ba, ta wuce dinning area, Yasmin na zaune wurin tana cin abinci, ita ma ko kallonta bata yi ba

Ta ɗauki plate ta zuba abincin, fried rice ne, sai ta ɗauki wani bowl ta zuba coslow a ciki, sannan ta ɗauki wani bowl ɗin kuma, ta ɗibi pepper chicken, sannan ta ɗora su kan tray, ta ɗauki spoons guda biyu fa forks biyu, sai ta wuce

Duk abunda take yi Ammi na kallonta, ta ƙyale ta bata ce mata komai ba har ta fita

Tana gama wayar, ta tashi, har ta fara hawa stairs, sai ta tsaya ta ce

"Yasmin"

"Na'am"

"Idan kin gama ki rufe mana ƙofar"

"Ammi, Yasna ta sake fita ai"

"Na ganta, ba dawowa zata yi ba, kema kin sani"

"To shikenan"

Ammi ta wuce ɗakinta




Lokacin da Yasna ta koma wurin Arshad, har ya koma ɗaki ya sa pyjamas ɗin shi baƙi masu stars fari, ya dawo palour

Aje tray ɗin tayi kan center table, ta haɗa musu komai, ta sa spoons, sannan ta matso da table ɗin gabanshi, ta ce

"Sweet Bro bismillah"

Murmushi yayi, ya ce "yau ranar hijira ce kenan"

"Eh, ba zan kwana a can ba, dan na san Ammi za ta iya duka na"

"To yanzu da kika tafi, ba ta palourn ne?"

"Tana nan, amma waya take yi"

Ajiyar zuciya yayi, sannan ya ɗauki spoon ya fara cin abincin, ita ma ta ɗauka tana ci, haka har suka gamacin abincinsu tare, suka sha ruwa sannan ta kife kayan cikin tray ta je ta ɗora kan ftidge, dan babu kitchen a wurin

Yasna ta wuce ɗakin Arshad ta kwanta bayan ta yi alwala, shi ma ya shiga yayi alwala sannan ya dawo palour, sai da ya gama sallolin shi sannan ya hau kan 3seater ya kwanta, dan haka suke yi duk ranar da Yasna ta ƙi kwana ɗakinsu, sai ya bar mata bedroom ya dawo palour

'May the dark winds be the smoothing breeze that pampers you,May the shiny sky form a blanket of warmth on you, May you have the sweetest dreams, and all your dreams comed true Ruhi.Good night'

Saƙon da ya tura ma Hanan kenan sannan ya kwanta





Ƙarfe 5:00 na asuba, Arshad ya farka, ya shiga bathroom yayi alwala, sannan ya fito ya tayar da Yasna, ba dan bacci ya ishe ta ba ta tashi tana tangaɗi

"Ki zo na wuce dake part ɗinku kafin in wuce masallaci"

"Hmm...kaje zan zo"

"Ina?"

"Masallacin"

Dariya yayi yana kallonta, sai ya koma toilet, ya ɗibo ruwa a hannunshi, ya zo ya watsa mata a fuska

A firgice ta buɗe ido tana cewa "Ammi na tashi fa" tana kallon Arshad, ta ga yana dariya, sannan ta tuna ashe nan ta kwana

"To tashi ki wuce, ƴar gidan Ammi"

Turo baki kawai tayi ta sauko daga kan gadon ta fito palour, shi ma ya fito suka wuce, sai da ta tsaya ta ɗauki tray ɗin da ta ajiye kan fridge jiya

Sai da ya kai ta har ƙofar palourn, ya danna bell, Ammi ta zo ta buɗe ta wuce ko kallonsu bata yi ba, sai da Yasna ta kalle shi, sai yayi mata murmushi ya ce "just go in(ki shiga kawai)"

Ɗaga mishi kai tayi sannan ta shiga, shi ma ya wuce masallacin


Ƙarfe 7:30am Arshad ya gama shirin shi, ya fito main palour, dinning area ya isko su dukansu, su masu Yasmin sun gama shirin makaranta

Gaida Ammi yayi, ta amsa mishi da "lafiya"

Bai ce komai ba ya ja kujera ya zauna, Yasna da Yasmin suka gaida shi, sannan Yasna ta haɗa mishi na shi breakfast ɗin

Breakfast ɗin kurame yau suka yi, dan har suka gama ba wanda ya ce komai, sai da ya duba agogon hannunshi, 7:51am, sannan ya tashi, ya ce ma Ammi "Ammi na wuce"

"A dawo lafiya"

Ya ce ma su Yasmin "take care(ku kula)" sai ya fita




Yana hanya ya kira Hanan

"Kin shirya?"

"Eh"

"I'm on my way(ina hanya)"

"To, Allah ya kiyaye"

"Ameen" ya kashe wayar

Agogon ɗakin ta kalla, takwas saura minti biyu, "bari inyi wanka, may be 15mins za su kawo shi nan"

Ta tashi ta shiga wanka, dan Siyama kam ta wuce makaranta ma, shiryawa tayi cikin less ɗinta peach da golden, ɗinkin riga da skirt dai-dai jikinta, ya mata masifar ƙyau, ta sa hijab mai hannu, peach colour, tasa kwalli sai lipstick, ko hoda bata shafa ba, sannan ta ɗauki jakarta ƴar fashion golden colour, bayan ta sa ma jikinta turare kaɗan, mara ƙarfi, dan ta san haramun ne mace ta sa turare mai ƙarfi ta fita waje, both ƴan mata da matan aure

Ɗakin Ummi ta shiga ta zauna zaman jiranshi, suna hira ita da Ummi har ya ƙaraso

Yau kam izini ya nema ya shiga har tsakiyar gidan, dan su gaisa da Ummi, addu'o'i tayi ta jero mishi sannan suka wuce, yana ta mata godiya
 




MK na office ɗinshi, shi da Gboy, dan shi ma a nan yake aiki

"Yalla6ai, maganar da muka yi kwana ki, naji kayi shiru, ko ka fasa aiwatarwa ne"

"Haba Gboy, ai kasan waye MK, bana yafiya, and you knew with"

"Haka ne, amma na ji baka sake magana akai bane"

"Kasan idan mutum zai yi sana'a, dole sai ya zuba kuɗi sannan zai samu riba,to wannan ma haka yake, dole sai na sa kuɗi na cikin wannan tsarin, sannan zan samu yanda nake so"

"Amma kana ganin idan ka zuba kuɗinka, zaka samu riba?"

"Sosai ma kuwa, bana kai kaina wurin da ba zan ci riba ba, tabbas zan mayar da kuɗi na, sannan kuma zan samu mu irinsu kusan ninki biyu ko uku, ka ga kenan, zan jefi tsuntsu biyu da dutsi ɗaya, ga kuɗi ga tarwatsa AAJ"

"That's good my guy(yayi kyau mutumi na), shiyasa kake burge ni wallahi....amma yaushe kenan"

"Akwai wasu kuɗi da zan kar6a wurin Mu'azzam, so ina tunanin da su zanyi amfani wurin wannan harkar"

"Amma da kace sai kuɗin wancan contract ɗin sun shigo sannan zaka haɗa ka kar6a gaba ɗaya"

"Ka manta na sallama contract ɗin wa abokin mahaifina?"

"Oh, haka ne"

Jawo wayar telephone MK yayi, ya kira office ɗin Mu'azzam sau biyu amma bai yi picking ba, tsaki yayi ya ajiye wayar, ya tashi ya fita yana faɗin "wai ni zan kira sau biyu ba'a ɗaga ba" shi ma Gboy tasowa yayi ya biyo shi

Office ɗin Mu'azzam ya tafi, amma ba ya ciki, sai ya fito, wata ma'aikaciya ya gani, ya ce "ke Mu'azzam ya shigo?"

"Eh yalla6ai, yana ƙasa wurin reception"

Bai ce mata komai ba suka sauko shi da Gboy dake biye da shi

Mu'azzam na tsaye wurin wani table yana magana da wani ma'aikacin, ya ji an kwala mishi kira

"Mu'azzam" ba shi da aka kira ba, duk ma'aikatan dake wurin sai da kowa ya natsu ya mayar da attention ɗinshi kanshi

"Na'am yalla6ai"

"Har ka fara yawon naka ko?"

"A'a yalla6ai, wani aikin ne na zo yi nan"

"Mtwss, come on mu tafi ni ka mun transfer ɗin kuɗin nan" sai ya juya ya wuce

Har zai hau stairs, sai ya juyo, ya ga Mu'azzam ko ɗagawa daga wurin da yake bai yi ba, dan tun da ya ambaci transfer ɗin kuɗi ya ji kunnuwanshi sun toshe

"Mu'azzam!!!" ya sake kiranshi, amma bai ji shi ba sai da wani ya tab'a shi

Sannan fa ya dawo cikin hayyacinshi, ya bi bayan MK, gabanshi sai faɗuwa yake tayi har suka kai office ɗin shi Mu'azzam ɗin

Zama yayi kan kujerarshi ta aiki, MK kuma ya zauna kan kujerar dake gaba table ɗin, Gboy kuma na tsaye

Alert ya ji ya shigo wayarsa, sai ya duba

"Saura fa" ya tambayi Mu'azzam ɗin

Dakewa yayi, ya ce "basu cika ba?"

"What a silly question!(wannan wace tambayar banza ce!)....miliyan ashirin da dubu ɗari huɗu ya kamata in gani, me ya ci four hundred thousand ɗin?"

Shiru yayi yana wasu muzurai, MK ya mishi tsawa "ina 400k?.....kaima ka fara cin amanata kenan"

Tashi yayi daga kujerar, da sauri Mu'azzam ya taso shi ma ya zo gabanshi ya tsaya ya ce "dan Allah kayi haƙuri yalla6ai, wallahi ba ni na ci su ba"

"Ni na ci su kenan?"

"A'a, aro.....aro na...."

A tsawace ya ce "kamun magana mana, aro me?"

"Aro na bada" ya faɗa cikin tsarƙaƙƙiyar murya

"Tashin hankali!!! ka bada aron kuɗina ba da izini na ba?"

"Kayi haƙuri dan Allah"

Shiru MK yayi sannan ya ce "wa ka ba?"

"Hanan"

"Hanan? Wace Hanan?"

"Ta reception"

Kama hanyan barin office ɗin yayi yana cewa "zo mu je"


Suna sauka ƙasa, ya tambayi ina Hanan, aka ce mishi ai bata ƙaraso ba tukuna




Sai da Arshad ya shigo cikin company ɗin sannan ya ajiye ta

"My first time to enter this company(yau ce rana ta farko da na fara shiga kampanin nan)"

"Are u serious?(da gaske kake?)"

"Allah da gaske"

"Ashe nayi ƙoƙari da na kawo ka"

Dariya yayi ya ce "yanzu dai ki shiga, kin ga nima zan wuce office"

"To nagode Allah ya kiyaye mu kai"

"Ameen wifey"

Murmushi tayi sannan ta fita, shi kuma yayi reverse ya fita

Har ya fito daga cikin company ɗin, sai ya lura ta manta da wayarta, sai kawai yayi parking gefen hanya, ya ɗauki wayar ya fito



Tun kafin ta tura ƙofar, ta ji muryar MK yana faɗa, ta ce "yau kuma wane mai tsautsayin ne? Allah ya kyauta" sannan ta tura ƙofar shiga

Tana shiga, Gboy ya ce "yalla6ai ai ga ta nan"

Tana jin hakan, gabanta ya faɗi, musamman ma da ta ga Mu'azzam gaban MK yayi tsuru-tsuru

Takawa MK yayi har gabanta ya tsaya, ta duƙar da kai, gabanta na dukan tara-tara

"Ke" ya kira ta amma ko motsi bata yi ba, sai da ya ƙara cewa "ke!!!!" a tsawace, sannan ta ɗago, idanunta sunyi ja, tana shirin kuka

"Ke kika kar6i kuɗina?" tayi shiru

"Ba da ke nake magana ba?" 

Sai ta ɗaga mishi kai, sannan cikin muryar tsoro ta ce "mahaifiya ta ce bata da lafiya a lokacin, shi ne sai......"

Katse ta yayi da faɗin "mahaifiyarki uwata ce? Ina ruwana da rashin lafiyarta, ta mutu mana"

Ɗaga ido tayi da sauri ta kalle shi, ta ce "ta mutu fa kace yalla6ai" ta ƙarasa maganar hawaye na ciko idanunta

"Haka na faɗa, idan ba wahalar da rayuwa ba, me zata zauna yi cikin wannan duniyar ku na fama da talauci, meye amfanin rayuwarta cikin tsiya?  Kuna matsiyatan banza shi ne har kuke wahalar da kanku wurin tattalin rayuwar wata, kuma da kuɗi na, yarinya amfanin rayuwa shi ne kayi ta cikin dukiya da wadata, ba irin ta ku ba, ta ƙasƙantattun matsiyata......"

Cikin jin zafin maganganunshi, hawaye na bin fuskarta, ta ce "enough MK, enough(ya ishe ka MK, ya isa)" ta faɗa a tsawace

Buɗe ido yayi, ya ce "kan uban can.....MK kike wa tsawa?"

Ai kuwa ya ɗaga hannu a hasale zai kwabta mata mari, sai ji kawai yayi an riƙe mishi hannu da ƙarfin tsiya

Ba Hanan da ke jiran saukar mari ba,  hatta ma'aikatan duk dake wurin sai da suka saki baki cikin mamaki suna kallonsu

Juyawa MK yayi cikin mamaki dan ganin wane isashshen ne ya riƙe shi, sai ya ga wanda baiyi zaton gani ba a wannan lokacin kuma a companyn shi

"AAJ!!!"














Mu haɗu a next page🤗😉
  
🥰UMMEETA🥰......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA DAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin qirqirar shi nayi,idan yayi daidai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 18*


Kallon-kallo suka tsaya yi na kusan 3mins, sannan MK yayi ƙoƙarin ƙwace hannunshi da ƙarfi yana ma AAJ wani irin kallo, sannan ya ce 

"Uban wa ya baka izinin shigo mun cikin company, har ina magana da ma'aikaciya ta ka shiga tsakani"

Kallon cikin idanunshi AAJ keyi, ya ce "da ace magana ce kawai, da ba zan shiga ba, amma babban kuskuren da ka so ka aikata a rayuwarka, shi ne da ka bari ƙazamin hannunka ya ta6a ta......hmm!" sai yayi shiru kawai yana mishi kallo mai wuyar fassara

MK ya ce "to da me za ka yi?......wai ma kai a wa da har zaka damu idan na mare ta, ai ina ganin a ƙarƙashina take aiki ko?"

"Gaya maka abunda zanyi 6ata lokaci ne, kuma dan tana aiki a ƙarƙashinka, ba shi ke nufin zaka iyayin duk abunda ka ga dama ba, coz i won't tolerate that(ba zan jure hakan ba)"

"Oh, really!(da gaske!)" ya faɗa yana mishi wani shaƙiyyin kallo " ita wannan banzar har tana da wani matsayin kenan a wurinka? Just look at her, ƙazamammiyar matsiyaciya, wawuy.........."

Bai sauke zancen da ke bakinshi ba, ya ji saukar lafiyayyen mari a kumatunshi, duk ma'aikatan da ke wurin sai da suka rufe baki da hannuwansu, Hanan kam ji tayi ma kamar ita aka mara, dan sai da ta dafe kumatunta, ta rufe ido da ƙarfi

MK ya kusan minti biyu riƙe da kumatunshi, yana mamakin yau shi aka mara a cikin companynshi kuma gaban ma'aikatanshi, maganar AAJ ce ta dawo da shi

"Marwan Kabeer! Ina so ka sani, idan kana cin ƙasa, to ka kiyayi ta shuri, akwai wurin da za kayi rashin kunya ka ci riba, wani wuri kuma sai dai ka kwashi kashinka a hannu.....na daɗe da sanin baka da mutunci, amma zan nuna maka kai ƙaramin mara kunya ne.....ban san me kake taƙama da shi ba da har kake kiran wasu da matsiya ta, kai a tunaninka, yawan dukiya shi ne arziki da wadata?...you're wrong(kayi kuskure), wadata a cikin zuciya take, kai ne matsiyaci domin ba ka da wadatar zuciya, Hanan ta fi ka arziki dan tana da wadatar zuciya, kuma i'm advicing you( ina ba mka shawara) ka daina wannan halin naka na wulaƙanta mutane, dan baka san irin ranar da za su maka ba, and i'm warning you at the same time(kuma a lokaci ɗaya, ina maka kashedi)kar ka sake kwatanta irin abunda kayi yau akan Hanan, saboda she's part of my life, she's my happiness(ita ɗin, wani yanki ne daga cikin rayuwata, ita farincikina ce), idan kuma ba haka ba, hmm.......ina tausaya maka"

Yana gama faɗar haka, ya ciro wallet daga aljihunshi, ya ɗauko cheaque, yayi signing ɗin naira million ɗaya, ya ninke shi, sannan ya jawo hannun MK ya ɗora mishi

"Ban san nawa kake bin ta ba, amma na san ba za su wuce haka ba, idan kuma sun wuce, let me know, in ma basu kai ba, to ka riƙe gaba ɗaya, dan kai ne matsiyaci"

MK ya gama daskarewa a wurin, ko motsin arziki ma ya kasa yi, ya rasa gane dalilin hakan, shin kunyar kallon ma'aikatan na shi yake ji shiyasa ya kasa motsawa? Ko kuma mamakin abunda AAJ ya mishi ne yake yi? Ko kuwa lissafin yanda zai rama wannan wulaƙancin ne yake yi? Shi kanshi ya rasa wannan amsar, bare kuma sauran mutanen da ke wurin

AAJ dai yana gamawa ya juya ya fita, ba tare da ya damu da yanayin MK ɗin ba

Hanan na ganin ya fita, ta kalli MK ta ga yana mata wani kallon da duk wanda ya kalli idanunshi sai ya tsorata, dan idanun nan kaman wanda akayi wa turaren barkono, sai huci yake tayi

Bata sake yadda sun haɗa ido ba, ta juya da sauri ta fita ita ma

Lokacin da ta fita, har ya kai gate, da gudu ta ƙarasa wurinshi, sai bakin mota sannansuka haɗu

Kallonta yayi, sannan ya ce "lafiya?....koro ki yayi?"

"A'a, amma na san zai kore ni"

"To meyasa kika fito?"

Kallonshi take cikin mamaki, ta ce "dole in fito, dan haɗuwa ta da MK ba zai yi kyau ba, shiyasa na kori kai na"

"Ni kuma ban goyi bayan ki kori kanki ba"

"Amma meyasa"

"Ke matsoraciya ce?" ya tambaye ta, amma shiru tayi dan bata da amsar ba shi

Ya sake cewa "ki ci gaba da aikinki, nothing will happen by God grace(ba abunda zai faru in sha Allah), amma idan ya kore ki da kanshi, sai ki daina zuwa"

Ajuyar zuciya tayi, ta ce "hmm.....naji, amma dai yau kam, ba zan koma ba"

Kallonta yayi, yayi murmushi, sannan ya ce "to muje in mai da ke gida"

Sakin baki tayi ta zaro ido, ta ce "idan na koma gida me zan ce wa Ummi ya dawo da ni yanzu? Gidan su Yuhanees zan tafi"

"Ai duk abu ɗaya ne to......ko za ki bi ni company?"

Shiru ta ɗan yi sannan ta ce "alright(shikenan)"

Buɗe musu motar yayi suka shiga, sannan ya tayar, suka ɗauki hanyar companyn shi




A 6angaren MK kuwa, tun da Hanan ta fita, ya saki cheaque ɗin ya wuce, ya hau upstairs, bai tsay ko ina ba sai office ɗinshi

Gboy ne ya ɗauko cheaque ɗin ya bi shi da sauri, sauran ma'aikatan dake wurin kuwa sai a lokacin ne suka samu damar tofa albarkacin bakinsu, kowa sai Allah ya ƙara ya ke faɗi, musamman Baba Kabiru da ya ce "ai in sha Allahu yanzu ya fara ganin irin haka"


A office ɗin kuwa, MK ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai yawo yake tayi, ya rasa abunda ke mishi daɗi har Gboy ya shigo

Ganin yanayin da yake ciki ne yasa Gboy cewa "kayi haƙuri yalla6ai, tabbas AAJ ya aikata babban kuskure akan abunda yayi, dole ne mu gaggauta aiwatar da tsarinmu saboda ya zama hukunci gare shi akan abunda ya aikata, ita kuma waccen Hanan ɗin sai a kore ta"

MK bai ce mishi komai ba, banda takawar da yayi a hankali zuwa kujerarshi, ya zauna yana ɗan jujjuyawa a hankali, sannan ya ja numfashi ya ce 

"Wannan abun da AAJ yayi, ya aikata kuskure, dan ba MK ake wa irin haka ba, sai dai hakan ba shi zai sa in gaggauta yin abundanake shirin yi ba, sai dai ma zan jinkirta ne, domin ya bani wata hanya sabuwa da zan fara musgunawa rayuwarshi da ita, kafin in kai ga tarwatsa rayuwar"

"Kamar ya kenan?"

"Ba za ka gane ba Gboy, har sai ka ga na fara buga wannan wasar"

"Hmm, to ita kuma Hanan ɗin fa, ka kore ta domin ta je can ta ci gaba da rayuwar talaucinta"

Kallonshi yayi yana yamutsa fuska, ya ce "Gboy meyasa kanka ba ya kawo wuta ne? Idan na kore ta ma aikin banza ne, ba wani talauci da zasu yi fama da shi, ka manta ya ce ita farincikinshi ce? Ka ga kuwa ba yanda za'ayi ya bar ta su wahala idan na kore ta, kuma ma idan na kore ta, ta ya zanyj yan da nake so bayan da ita zanyi amfani wurin cimma buri na!? Kau dai kawai ka zuba ido, sai na tabbatar da AAJ yayi dana sanin mari na da yayi"

Gboy dai ba abunda ya fahimta daga cikin abubuwan da MK ya faɗa, ya dai yi shiru ne kawai

MK ya ce "je ka kawai, zan neme ka"

"Ok sir, na bar ka lafiya" ya tashi ya fita daga office ɗin

**********************


"Hajjo nace maganar auren Arshad ne ya tashi" cewar Ammi da ke zaune a ɗakinta tana waya da Hajjo

"To alhmadulillahi, kamar kuwa kin san jiya muka gama maganar nan da Nabeel, yake cewa ai bai da lokacin nemo mata" cewar Hajjo

Ammi ta ɗan yi dariya ta ce "to ba ya gaya miki ya samo mata ba?"

"Ya gaya mun, amma yanayin yanda naji kin amsa mun ne ranar da na tambaye ki, ya sa na ɗauka ko wasa yake mun"

"A'a Hajjo, da gaske ne"

"To madallah, ya sunanta, kuma ƴar gidan waye?"

"Sunanta Farha, ƴar gidan abokin marigayi ce, Alhaji Mas'ud"

Cikin murna Hajjo ta ce "Masa'udu dai abokin nan na shi na nan Kaduna? Mijin ita wannan baiwar Allah.....um Karime?"

"Eh, ita"

"Masha Allah, abu yayi armashi, yaron nan akwai son zumunci wallahi, kin ga idan ya aure ta, ai zumunci ba zai lalace ba sai ma ya ƙara ƙulluwa"

"Sosai kuwa Hajjo.....to yanzu yaushe za'a zo ayi maganar auren?"

"To nima dai da ace za su bi ta tawa, kar a wuce wata uku, to amma kin san yana cewa shi ba zai yi aure ba sai anyi na Nabeel, to ina ganin zanyi ma shi Yusuf magana, dan a samu ayi na Nabeel akan lokaci sai azo ayi na Arshad ɗin"

'Bata rai Ammi tayi, sannan ta ɗan murmusa ta ce "Hajjo kar a biye maganarshi mana, a haɗa su kawai ayi lokaci ɗaya"

"Nima zan fi farinciki da haka, amma dai zanyi magana da Yusuf muji, ai karki damu, tunda dai har ya samu mata, ai an gama mai wuyar"

"To shikenan Hajjo, na gode, Allah ya ƙara lafiya"

"Ameen, Allah yayi albarka, ki gaida mun da ƴan biyu, sannan ki gayawa Husaina ina da faɗa da ita, dama ina so zan kira ta"

Dariya Ammi tayi ta ce "ai kun fi kusa, in dai mutumiyar ce"

Ita ma Hajjo dariyar tayi, sannan suka kashe wayar a tare

Ammi tayi ajiyar zuciya ta ce "in sha Allah Arshad ba za ka bani kunya ba, aure ne kai da Farha, kamar an gama.....dole ne shi ma Abban Nabeel ɗin in kira shi, in zuga shi akan a haɗa auren Nabeel da Arshad kuma kar ya wuce wata ɗaya ma"

Haka dai tayi ta saƙawa tana warwarewa, yanda za ayi auren nan na Arshad da Farha ba tare da matsala ba

**********************

Farha na kwance tana chatting a ɗakinta, kiran waya ya shigo, sai da tayi tsaki sannan ta ɗaga

"Hello!"

"Sweetie ya kike?"


"Ƙalau.....ya aka yi?"

"Haba, ya daga gaisawa za ki ce ya aka yi?"

"Ai na san ba ka nema na sai kana da buƙata da ni"

Dariya yayi, ya ce "ba haka bane, kin san idan rai na ya 6aci, kece kawai za ki iya kwantar mun da hankali"

"Ai dama na sani"

"Sorry dear"

"Hmm.....kana ina?"

"Ina wurin aiki, amma yanzu guest house zan tafi, mu haɗu a can kawai"

"Shikenan.....amma akwai inda zan biya, sannan in zo"

"Ba damuwa hot lady, sai kin zo"

"Ok, bye"

Tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka, sannan ta dawo gaban mirror ta zauna, ta kusan minti talatin tana ta kwalliya, sannan ta shirya cikin jallabiya purple, tayi kyau sosai, ga shi ta kama jikinta, sannan ta ɗauki fashion bag ɗinta purple da wayarta da mukullin mota, ta fito

Mai aikinsu ce a palour tana ta goge-goge, tana ganinta ta durƙusa ta gaishe ta, bata amsa ba, ta ce

"Idan Mummy ta sauko, ki gaya mata na fita"

"To Allah ya kiyaye"

A yatsine ta ce "ameen" sannan ta fita

Bata tsaya ko ina ba sai AAJ IMPORT AND EXPORT COMPANY LIMITED, a parking lot ta ajiye motarta sannan ta fito

Wayar ta dake ƙara ta kalla, sannan ta ɗauka

"I've been waiting for you Farha" aka faɗa daga ɗayan 6angaren

"Daɗina da kai gajen haƙuri MK, ina zuwa nan da 30mins"

"Har 30mins?"

"Eh, ina wurin wanda zan aura ne"

Ƴar dariya yayi, ya ce "amma ina tausaya wa wanda za ki aura kuwa"

'Bata rai tayi, ta ce "me kake nufi?"

"Ba komai, sai kin zo dai"

"Bye"
Suka kashe wayar a tare sannan ta ƙarasa cikin company ɗin


Arshad na zaune kan kujerarshi ta aiki, yana ta aikin gabanshi, Hanan kuwa na zaune kan ɗaya daga cikin cushions ɗin dake office ɗin tana karanta wani magzine da ta ɗauka kan center table ɗin

Wayar telephone ɗinshi tayi ƙara, ya ɗauka

"Hello Khairat"

"Yalla6ai wata ce ta zo, wai tana son ganinka"

Sai a lokacin ya ɗaga, ya hango Farha a tsaye sai tauna chewing-gum take yi

"Ki sallame ta kawai"
Har zai yi hanging, sai kuma ya ce "Khairat"

"Na'am"

"Bar ta ta shigo"

"Ok sir"

Yana ajiye wayar, ya ce "Hanan"

"Na'am" ta ɗaga tana kallonshi

"Help me with water please(ki taimake ni da ruwa dan Allah)"

"To" 

Tashi tayi ta ɗauko ruwan cikin fridge sannan ta zo gaban table ɗinshi ta zuba a cup, ta miƙa mishi

Kallon ƙofar yayi sannan ya ce "Hajiya zagayowa za kiyi ki bani"

Dariya tayi sannan ta zagaya, sai a lokacin ya danna mabuɗin ƙofar, Farha ta shigo

Juyawa Hanan tayi da sauri tana kallon ƙofar, dan ta tsorata

Farha kuwa sakin baki tayi tana kallon Hanan, jikinta har wani 6ari yake yi...........







Manage this pls🤗
  
🥰UMMEETA🥰......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 19*

Farha shigowa office ɗin tayi da sauri idanunta na kan Hanan har ta ƙaraso kusa da ita

Jawo ta tayi baya da ƙarfi, ta ce "mahaukaciyar ina ce ke da za ki wani zo kusa da miji na? Daga nan ai za ki iya miƙa mishi ruwan ba sai kin kawo har nan ba"

Kallonta Hanan ke yi cike da mamaki, musamman da ta ji ta ce wai mijinta, ta juya tana kallon Arshad, ta ga shi ma ita ɗin yake kallo

"Dalla Malama ki fita daga nan, ni zan ba shi ruwan da kaina, dan haƙƙina ne" maganar Farha ce ta dawo da ita daga kallon da take ma Arshad


Riƙe hannunta tayi da nufin janta zuwa waje, amma sai ta dake, ko motsawa Hanan ɗin ba tayi ba, harararta Farha tayi ta ce "ki wuce mu tafi ko! Ai hadda kai darling, akan me za ka bari wannan ta zo ta ba ka ruwa ma fisabilillahi" ta ƙarashe zancen tana kallon Arshad

"Ke! Ki sakar mun hannu, idan ba haka ba kuwa za ki sha mamaki" cewar Hanan da ta gama cika da haushi

"Iyeeee!!! Su kulu anyi kallabi, ke ki na matsayin ma'aikaciyarshi, ni ina matsayin matarshi amma shi ne har kika samu damar gaya mun haka?"

"Mata? Ai kuwa ke kam anyi sakaryar mata wallahi, ta ya har za ki bari ma'aikaciya ta fi ki matsayi a wurin mijinki?"

"Ke har kina ganin kin fi ni matsayi?"

"Ga shi kuwa kin gani! Tun da kike da shi, ya tab'a cewa ki ba shi ruwa?"

Shiru Farha tayi tana kallonta, Hanan ta ci gaba da faɗin "bai tab'a ba ko? Kin ga kenan na fi ki matsayi"

Farha ta kalli Arshad da ya tsura musu ido yana murmushi, sai kace ya samu TV, ta ce "amma kana jin abunda take gaya mun, wai ta fi ni matsayi? Kuma shi ne ba za ka ce komai ba?"

Ƙara faɗaɗa murmushinshi yayi, ya ɗan sa hannu cikin gashin kanshi yana sosawa, yana juyawa kan kujera, ya ce "to ai Farha sai nake ganin kamar ba ƙarya a maganarta, ta fi ki matsayin, kuma idan ba ki manta ba, na gaya miki cewar ina da wacce nake so, kuma ga ta nan a gabanki, ba ma'aikaciya ta bace kamar yanda kike tsammani, but....my wife to be(matar da zan aura)"

Nan take Farha ta ji gabanta ya faɗi, jin cewa ita ce wacce yake so ɗin, dan a tunaninta aiki take yi a ƙarƙashinshi

Nuna Hanan ɗin take yi da yatsa tana faɗin "yanzu dama akan wannan ka gaya mun magana rannan?"

Ɗaga mata gira yayi yana murmushi, ita kuma sai kallonsu take yi daga shi har Hanan ɗin, tana jin wani ɗaci a bakinta, zuciyarta kamar za ta fito

Hanan ta zagaya kusa da kujerar Arshad ta tsaya, ta ce "na ga kina mana wani irin kallo, ya kika ganmu, perfect match ko?" ta ƙarasa maganar tana kashe mata ido ɗaya

"Na gani, perfect match ko?! Ai kun wuce perfect match.....zan yi maganinki" Farha ta faɗa a hasale, sannan ta juya da sauri ta bar office ɗin

Kallo suka bi ta da shi har ta gama fita daga office ɗin gaba ɗaya, sannan Arshad ya ɗaga kai ya kalli Hanan yana murmushi, zai yi magana ta ɗaga mishi hannu

Ta ce "Dakata! Me yasa ka mun ƙarya?"

Ɗan haɗe gira yayi yana mata kallon mamaki, ya ce "ƙarya kuma? Wace irin ƙarya?"

"Eh ƙarya, ka san kana da wacce za ka aura amma shi ne ka bari na fara sonka? Kuma har kake wani iƙirarin za ka aure ni?"

"Kin ga Hanan, kar maganar da ta faɗa ya sa ki ji wani abu a ranki"

"Kamar ya! Cewa fa tayi matarka, which means aurenta za ka yi"

"Oh Allah My Hanny!" cewar Arshad yana miƙewa tsaye, sannan ya kalle ta ya ce "zo nan" sai ya fara tafiya

Juyawa yayi ya ga tana nan tsaye wurim da take, yayi murmushi ya ce "zo mana"

Sannan ta biyo shi, wurin cushions ɗin ya nufa, ya zauna kan one seater, ya nuna mata 3seater dake kusa da shi yace ta zauna, ba musu ta zauna

Sannan ya gyara zama yana fuskantarta da kyau, ya ce "Hanan, akwai maganar da nake so zan gaya miki da daɗewa, bansan yanda za ki ɗauki maganar ba shiyasa nake tsoron gaya miki, dan bana so ki canza ra'ayinki a kaina, saboda ina sonki sosai Hanan, son da ko a mafarki ban tab'a tunanin akwai macen da zan yi ma irin shi ba bayan mahaifiya ta, sai ga shi ji nake idan ba da ke ba, bazan iya rayuwa ba, zan iya yadda in rasa duk abunda na mallaka a duniyan nan, amma ba zan iya jure rashinki ba, dan Allah kar abunda zan gaya miki ya tsorata ki"

Tunda ya fara magana, Hanan ke jin gabanta na faɗuwa, sai tunanin take to menene zai gaya mata haka? Shi kanshi ya fahimci hakan, sai ya ce 

"Ba wani babban abu bane zan gaya miki ba, sai dai ban san yanda ke za ki ɗauke ta ba ne"

Ajiyar zuciya tayi, ta ce "gaya mun menene, Allah ya sa zan iya jurewa"

A hankali ya ce "ameen" sannan ya ci gaba da magana

"Hanan, wannan yarinyar da ta zo yanzu, sunanta Farha, ƴa ce a wurin wata ƙawar Ammi, wacce ta ɗauke ta tamkar ƴar uwa, haka ma mahaifinta abokin mahaifina ne kafin rasuwarsa, Ammi da mahaifiyar Farha sun daɗe suna so in auri Farha, sai dai ni kwata-kwata bana sonta, ba ta burge ni, a lokacin munyi shawara da Sajjad akan in samo wata in kawo ma Ammi a matsayin wacce nake so, wataƙila zata haƙura da zancen Farha, sai ga shi kuwa Allah ya ba ni ke, amma matsalar da kenan, ba za ku jitu da Ammi ba"

Ɗagowa tayi tana kallonshi, ta ce "meyasa to? Nayi mata wani laifi ne?"

Rufe ido yayi a hankali yana girgiza mata kai, sannan ya buɗe ya ce "ba abunda kika yi mata Hanan, sai dai Ammi na, ta tsani talaka, ba ta son su kusance ta ko ta kusance su, na daɗe ina so in kai ki gidanmu, amma tsoron irin tarbar da za ta miki ne yasa ban kai ki ba, bana so Ammi ta miki wani abu kiji gaba ɗaya a ranki kin tsaneni Hanan, mahaifiya ta ce, na fi kowa tsanan wannan halin na ta, sannan kuma ga shi Yasmin ma tana ƙoƙarin ɗauko halinta, ko ma in ce ta ɗauko"

Kallonshi take yi, sai ta ji gaba ɗaya ya ba ta tausayi, shi ma kallonta yake yi yana jiran ya ji me za ta ce

"Kin yi shiru Hanan, ko har kin karaya ne? Kin fara tunanin rabuwar mu ko?"

Girgiza mishi kai tayi ta ce "ko ɗaya, ina roƙon Allah ne akan ya shiga wannan lamarin na mu, idan har akwai alkhairi a tsakaninmu Allah ya bamu ikon jure duk wani abunda zai faru kuma ya sassauto da zuciyar Ammi, idan kuma ba alkhairi, Allah ya mana abunda ya fi dacewa da mu, amma ina sonka Arshad"

Ya ji daɗin kalamanta sosai, ya ce "ameen, ban tab'a mafarkin rasa ki ba Hanan, in sha Allah kuwa ba zan rasa ki ba a zahiri"

Murmushi tayi ta ce "ina fatan haka"

*********************

Farha kuwa tun bayan fitar ta daga companyn, ta wuce guest house kamar yanda suka yi da MK, sai dai kafin ta isa ta kira Samira, sai suka haɗu a can

"Haba hot lady, gaskiya kin daɗe, kun sha love kenan" cewar MK

Farha dake zaune gefenshi ta watsa mishi harara, ta ce "wane irin love? Mtwsss" ta faɗa gaba ɗaya ranta a b'ace

"Cool down babe, meya faru?"

"Ba abunda ya shafe ka bane, Samy, ki san yanda za kiyi da shi, ni daga nan ina da wani uzurin" ta ƙarasa ta a kallon Samira dake gefe a zaune

Kallon Samira, MK yayi, ya ce "kin san fa ke nake buƙata Farha"

"Ai kuwa haƙuri za kayi da ita, idan kuma ba haka ba kayi two zero" inji Farha

Ita ma Samira cewa tayi "ai ni Farha ba ki kyauta mun ba, na ɗauka ma wani serious issue ne kika kira ni ina hutawa, ashe haɗa ni za kiyi da wani?"

Farha ta ce "dan Allah kar ku ƙara b'ata mun rai, wanda nake ciki ma ya ishe ni......ni kun ga tafiya ta, ku yi yanda kuka ga ya dace da ku" 

Ta figi jakarta da mukullin motarta ta fita ta bar su nan a zaune

******************

Misalin ƙarfe 3:32pm, Yasna na garden a zaune, ta kunna waƙa tana bi tana kallon tsuntsayen da ke shawagi a wurin, da dukkan alamu tana jin daɗin wannan yanayin

Wayarta da tayi ƙara ne ya katse waƙar da ke tashi a wayarta, FAV COUSIN aka rubuta, hakan yasa tayi murmushi sannan ta ɗaga haɗe da yin sallama

"Ya Umma da su Meerah?" Yasna ta tambaya bayan sun gaisa da Nabeela

"Lafiya ƙalau suke, ya su Ammi da Yasmin, da babban yaya"

"Kowa lafiya ƙalau, ina fitinannen Hajjo?"

Dariya Nabeela tayi, sannan ta ce "yana gida ai, ni ina wurin Hajjo, daga makaranta nake, shi ne na biyo ta nan ɗin"

"Ayya, kin zo shan fura ba da ni ba!" tayi maganar kamar za tayi kuka, cikin shagwab'a

"Ke ni kinsan wannan shagwab'ar ta ki ba ɗaukanta nake yi ba, sai su Ya Arshad da Ya Nabeel da suka ji za su iya"

Dariya suka yi tare, Yasna ta ce "sai kuma Ya Jafar"

Dariya Nabeela tayi, ta ce "yarinya kina ruwa, tsab zai karya ki kin sani"

"Kin san mun kusan sati ɗaya bamu gaisa ba? Wallahi ni tsoron kiranshi nake yi, ko Ya Nabeel da yake babba fa bana tsoronshi kamar Ya Jafar"

"Ke ma kenan da ba kwa kusa, to mu kuma fa?"

Muryar Hajjo ta ji tana cewa "wai Nabeela za ki bani wayar nan ko sai kin ƙarar da kuɗin kuma?"

Nabeela ta ce "kai, wannan tsohuwa akwai jaraba, ni dai ga ta" ta faɗa tana miƙa mata wayar, Yasna sai dariya take ta yi

"Yawwa, Assalamu alaikum" cewar Hajjo

 "Wa'alaikissalam my kakus"ta amsa tana dariya

"Ke ni ba shashanci za ki mun ba, tambayarki zanyi"

"To Hajjo, Allah ya sa na sani" ta faɗa cikin natsuwa, jin muryar Hajjo da tayi ta san wannan maganar arziki ce

"Na sanki, na san halinki, na kuma san yanda kike son yayanki, ba za ki so abunda zai cutar da shi ba, kin san maganar aure ana so ayi bincike a kai, na san Abbanku(baban su Nabeela) zai yi ƙoƙari wurin yin bincike, amma ina so inji daga bakinki kuma, tunda kin santa, to dole kin san halayenta, dan haka ki gaya mun, ita wannan yarinya da Arshad yake so, Farha, ya ɗabi'unta suke?"

Gyara zama Yasna tayi, ta ce "Farha kuma Hajjo?" 

"Eh mana, haka Amminku ta gaya mun sunanta"

"Kuma ta gaya miki yana sonta?"

"Ban son rainin hankali wallahi, idan ba ta gaya mun ba zan tambaye ki ne?"

"Allah ya huci zuciyarki Hajjo, amma maganar gaskiya, Sweet Bro ba ya son Farha, hasali ma Ammi ce ke ƙoƙarin haɗa wannan auren, shi kuma yana da wacce yake so, sunanta Hanan"

"To! Amma meyasa Ruƙayya za tayi haka?....Ba ta san da zancen Hanan ɗin bane?"

"Ta sani Hajjo, sai dai kin san yanda Ammi ba ta shiri da talaka, kuma ita Hanan ɗin ba masu ƙarfi bane"

"To ke kin san ita Hanan ɗin?"

"Eh na santa, ya kai mu gidansu, a yanda na fahimta, bata da wata matsala, daga ita har mahaifiyarta da ƴar uwarta, su na da fara'a sosai, kuma sun san darajar ɗan adam"

Ajiyar zuciya Hajjo tayi, ta ce "to shikenan, kar ki gaya ma ita Ammin ta ku mun yi wannan maganar, zan yi nazari a kai, idan da yiyuwar ya aure su ne dukansu su biyu, kin ga idan aka gama bincike a kan su, sai kawai ya haɗa su, tunda yana da dukiyar da zai iya riƙe mata sama da biyu ma"

"Amma Hajjo ban katsi hanzarinki ba, kar ki manta, duk wanda zai riƙe mata sama da ɗaya, ba wai abunda zai ciyar da su kawai ake dubawa ba, za'a bincika ne shin zai iya yin adalci a tsakaninsu kuwa? Na gaya miki kwata-kwata baya son Farha, Hanan yake so"

"Meye aibin ita Farha ɗin, da ba zai so ta ba?"

"Tana da shi wallahi Hajjo"

"To na ji, wannan ba maganarki bace, naji abunda nake son ji daga gare ki, sauran kuma za muyi magana da su Fatima ko menene ma za ku ji"

"To shikenan, Allah ya sa muji alkhairi"

"Ameen, ki gaishe su"

"To za su ji, sai anjima"

Daga nan suka kashe wayar

Yasna ta ɗan yi shiru, sannan ta ce "i think i have to talk to Sweet Bro about this(ina tunanin sai na gaya ma Sweet Bro wannan maganar)"

Duba agogon hannunta tayi, ƙarfe huɗu saura mintuna huɗu, ta ce "na san yanzu yana hanyar dawowa"

Sai ta wuce cikin gida da nufin yin sallah, ta zauna jiranshi

*******************

Hanan ce tsakiyar gidansu tana alwala, dan bata daɗe da Arshad ya ajiye ta ba shi ouma ya wuce, Ummi na ɗakinta tana bacci, Siyama kuma tana ɗakin Hanan ɗin tana sallah sannan sai ta wuce islamiya

Yuhanees ta shigo gidan da sallama, sai dai akwai alamar damuwa a fuskarta

Yanayin yanda Hanan ta ji shigowarta da sallamarta yasa ta ɗago da sauri tana kallonta

"Rabin rai lafiya?"

"Hayatee ni wallahi na tsorata, aka ce mun yau MK ya nemi kuɗinshi, wai har faɗa kuka yi, na ɗauka ko ya miki wani abu, ga shi nayi ta kiran wayarki amma not reachable"

"Ki kwantar da hankalinki rabin rai, ba abu da ya mun, waya kuma may be dai network ne"

"To kin ce ba abunda ya faru, bayan an gaya mun har faɗa kuka yi fa!"

"Haka ne, Allah ne ya taimake ni AAJ bai wuce ba, kin san na gaya miki yau shi zai kai ni wurin aikin.......wai ma, wa ya gaya miki?"

"Hmm, Zalihat ce, amma ni ba wannan ba, gaya mun ya aka yi?"

"Bari in ƙarasa alwala, mu shiga ɗaki in gaya miki"

"Idan kin gama sai alwalan, sai ki zo ki gaya mun, me ya haɗa ki da MK" abunda suka ji Ummi ta faɗa kenan

Gaba ɗayansu a tsorace suke, dan Hanan ba ta san ta tashi ba, ita kuwa Yuhanees ta ɗauka ba ta nan ne

Yuhanees tayi ƙoƙarin cewa "Ummi ba fa wani abu ba ne"

Ɗaga mata hannu Ummi tayi, ta ce "yi mun shiru, ni na haife ku, ba ku kuka haife ni ba, dan haka ba wani salo da za ki zo mun da shi, dan haka idan ta gama, ku isko ni ɗaki"

Tana gama faɗar hakan ta koma cikin ɗakinta

Hanan da Yuhanees sai wani kallon juna kawai suke yi, sannan dai daga bisa ni Hanan ta ci gaba da alwala, tana yi tana tunanin irin faɗan da Ummi za ta yi, har ta gama

Sai da Ummi ta bari Hanan tayi sallah, sannan ta zaunar da su a gabanta, ta tambaye ta akan ta gaya mata komai, ban da ƙarya

Tun daga aron kuɗin har ranar da ta yamutsa ɗaki wurin neman kuɗin, har zuwa abunda ya faru yau, ba abunda ta b'oye ma Ummi, tana gamawa ta ce "amma dan Allah Ummi kiyi haƙuri, wallahi ban karb'i kuɗin dan sab'awa maganarki ba, sai dai dan ba zan iya jure wani abu ya same ki ba, sannan kuma na b'oye miki ne dan bana so ranki ya b'aci Ummi, dan Allah kiyi haƙuri"

Jan numfashi Ummi tayi, ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce "na haƙura Hanan, sai dai ina so ki sani, ban ji daɗi ba da kika b'oye mun wannan zancen, yanzu da Allah bai kawo Arshad ba, ina za ku samo wannan kuɗin? Sannan kin san abunda zai aikata miki? Ke kin fi ni sanin halinshi, ba sai na gaya miki ba, na hana ki aro kuɗi wurinshi ne, dan in kare miki mutuncinki da kuma tsoron irin haka"

Yuhanees ta ce "kiyi haƙuri Ummi, duk abunda tayi da sa hannuna, dan ta gaya mun ba so kike yi ba, ammavna bata goyon baya akan ta ƙarb'o, kiyi haƙuri ba za mu sake aikata wani abu ba, ba tare da mun shawarce ki ba"

Kallo ta bi su da shi sannan ta ce "to shikenan, na haƙura, Allah ya tsare gaba, Allah ya muku albarka"

"Ameen Ummi mun gode" suka haɗa baki wurin amsawa

Ummi ta ce "amma dai ba za ki koma wurin aikin ba ko?"

"Nima haka nayi tunani, amma Arshad ya ce kar in kori kaina har sai in shi da kanshi ya ce ya kore ni"

"Amma kuwa komawarki ba matsala ba ne?"

Yuhanees ta ce "tunda har ya ce ta koma, in sha Allah ba abunda zai faru"

Ummi ta ce "kin san zuciyar maza da ta mata ba ɗaya ba fa, ina tsoro kar ya mata wani abu"

Yuhanees ta ce "Ummi as long as tana addu'a kamar yanda ta saba, sannan ke ma kika ci gaba da mata addu'ar, ba abunda zai same ta sai alkhairi"

Ummi ta ce "hmm, haka ne kuma, addu'a makamin mumini ce, Allah ya tsare ta ya tsare ku baki ɗaya"

Nan ma amsawa suka yi tare da "ameen"


Sannan suka tashi suka koma ɗakin Hanan

Hanan ta gaya mata abunda ya faru tsakaninta da Farha, da kuma maganar da Arshad ya gaya mata akan mahaifiyarshi

"To ammi dai rabin rai, kina tunanin alaƙar mu za ta ɗore kuwa? Kin san duk abunda ba yardar uwa fa, yana da matsala" Hanan ta ƙarasa zancen ta da hakan

"Haba Hayatee, me yasa kike da saurin losing hope akan abu ne wai? Ni fa da ba haka na sanki ba"

Kallonta kawai Hanan ke yi, Yuhanees ta ce "ni fa a ganina, idan mutum zai tsare sallolinshi guda biyar, sannan kuma duk lamarinki za ki riƙa sa Ubangiji, sannan ki na addu'a kuma ki na yawaita salatin manzon Allah SAW da istigfari, to za ki ga komai na ki ya zo da sauƙi, ki daina jin tsoro, ni ina ji a jikina ke matar Arshad ce, sai dai ban sani ba ke kaɗai ce ko kuma ke da wata, amma Allah ya zab'a mana abunda ya fi alkhairi"

Hanan tayi murmushi ta ce "ameen rabin rai, nagode sosai Allah ya saka miki da alkhairi, Allah ya bar mun ke har mutuwa"

"Ameen Hayatee"

Suka rungume juna suna farin ciki, sannan suka ci gaba da hirarsu ta duniya

********************

"Tabɗijam, ai wallahi ba zai yiwu ba, ya ina nan ina saƙa, amma shi kuma yana ƙoƙarin kwancewa? Yanzu har tayi matsayin da za ta riƙa zuwa office ɗin shi?" cewar Hajiya Karime dake zaune a balcony ita da Farha

Farha ta ce "Bari kawai Mummy, ni gaba ɗaya kaina ya ƙille, ban ma san irin matakin da zan ɗauka ba, ga shi Malam ya ce ba wani aiki da zai yi tasiri a kanshi"

"Ai ki kwantar da hankalinki daughter, kin san hausawa sun ce, idan hagu ya ƙi sai a koma dama, Allah ya kaimu gobe, zan ɗora mahaifiyarshi akan wata hanyar da nake ganin za ta yi aiki"

"Wace hanya kenan?"

"Ai zai ci gaba da hulɗa da ita yarinyar ne idan har ita da iyayenta suka ba shi fuska ko?"

Ɗaga kai Farha tayi tana sauraron Mummynta

"To gidansu yarinyar ya kamata muje, ayi mausu barazana ita da iyayen na ta, ina ce kin gaya mun talakawa ne, to kin san talaka akwai tsoro, za mu cusa musu tsoro ne, ta yanda ko da ita yarinyar tayi taurin kai, to iyayenta za su taka mata birki, su hana ta kula shi, shi kuma tunda ba ƙuda bane sarkin maita, dole ya rabu da ita, daga nan sai a hanzarta maganr aurenku"

"Woww!!! Good idea Mummy, ina sonki my super hero.....sai dai matsalar ba mu san gidansu ba"

"Neman gidansu ba zai yi wahala ba, kawai dai ta amince da shawarar, ki ga aiki da cikawa"

Dariya Farha tayi, ta ce "ai dole ma za ta amince, kin san yanda take ɗaukar maganarki, ko maganar waccan tsohuwar, Hajjo, bata ɗauka haka nan"

Dariya suka yi tare, hadda buga hannu sai ka ce wasu ƙawaye..............











Dan Allah ina barar addu'arku, gobe in sha Allah zan fara exams, plssss😔💓

Sannan kuma dan Allah ku taya mu da addu'a, anyi garkuwa da antyn CEO ɗin Moonlight, Queen Nasma, Allah ya tsare su a duk inda suke, kuma ya bayyana su cikin aminci, da sauran ƴan uwanmu musulmai da aka ɗauke
Dan Allah ku taya su da addu'a, dan ba a san bakin wanda Allah zai karb'a ba👏




🥰UMMEETA🥰......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏

Ina matukar godiya da irin addu'o'in ku, naji dadi kuma nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi🥰😍

Naji sauƙi yanzu kam, in sha sai kuma typing.....🖊️🖊️🖊️


 *Page 20* 
Yau kusan kwana biyu kenan da faruwar faɗan AAJ da MK, kullum Hanan cikin fargaba take zuwa company ɗin, da sa ran jin kiran MK, amma ko ta kanta baya bi, kowa yayi mamakin yadda MK ya kyale ta, amma ita tana ji a jikinta akwai wata a ƙasa, sai dai ta daure ne kawai

Haka ma Yasna tana ta so tayi ma Arshad magana akan maganar da suka yi da Hajjo, sai dai kwana biyun nan tana bacci da wuri, lokacin da zai dawo tayi bacci, da safe kuma lokacin da zai fito sun wuce makaranta

Sai yau Allah ya sa ya dawo da wuri, da daddare kuwa ta isko AAJ part ɗin shi, ta sanar da shi duk maganar da suka yi da Hajjo 

"Wai meyasa Ammi ta dage akan sai na auri Farha ne?" Arshad ya faɗa a hasale bayan Yasna ta gama zayyana mishi komai

"Ni ma dai na rasa gane me Ammi ta gani a tattare da ita wallahi"

"Yasna akwai matsala in har Ammi ta riga ni tunkarar Abba akan wannan maganar"

"Shiyasa nima nayi gaggawar gaya maka"

"Dole ne in tafi Adamawa kwanan nan"

"Amma da ka fara kiranshi dan har yanzu ban ji tayi magana da shi ba"

"Zan kira shi da safe ai, amma kuma ina so na ganshi"

Ajiyar zuciya Yasna tayi, ta ce "to, Allah dai ya kyauta"

"Ameen"

Daga nan ta mishi sai da safe, sannan ta koma part ɗinsu

********************

Washe gari da safe, bayan AAJ ya fita wurin aiki, ya kira Abba suka gaisa, sannan ya ci gaba da cewa

"Abba dama magana ce akan wacce nake so"

Cikin kulawa Abba ya ce "to Arshad, nima maganar da nake ta so in maka kenan, dan Hajjo ta mun maganar"

"Eh Abba, dama akwai wata wacce nake so sannan kuma akwai wacce Ammi ta nace akan sai na aure ta, kuma Abba bana sonta wallahi"

"To ai ni wannan abun ma yana ɗaure mun kai, aka ce ita wannan da Amminku ke so ɗin ƴar gidan Alhaji Mas'ud ce"

"Eh amma dai bata da ɗabi'u masu kyau, kuma ma dai ni bana sonta ko kaɗan"

"Hmm, to shikenan dai, zan duba in gani sai in kira ka"

"To Abba, nagode"

"Allah ya maka zab'i mafi alkhairi"

"Ameen Abba"

Sai suka yi sallama suka kashe wayar

Rufe ido Arshad yayi yana ta tunani kala-kala ta yanda zai gujewa auren Farha, har dai ya gaji ya ci gaba da aikinshi

*******************
Da rana Ammi na zaune palour ita da su Yasmin dake cin abinci, dawowarsu kenan daga makaranta, suka ji an danna doorbell, Yasmin ce ta je ta buɗe ƙofar, murmushi tayi ganin su Farha ne da Hajiya Karime, sai da suka gaisa sannan suka ƙarasa cikin palourn

Kusa da Ammi, Farha ta zauna tana ta fara'a, sannan suka gaisa da ita

Ammi ta ce "Hajiya ku ne da rana haka?"

Murmushi Hajiya Karime tayi, ta ce " wallahi kuwa, daga unguwa muke, shi ne ta takura akan lallai sai mun biyo ta gan ki"

Ammi ta kalli Farha tana washe haƙora, ta ce "Allah sarki ƴar Ammi, nima ai nayi kewarki"

Dariya kawai Farha tayi, Ammi ta ce "Yasna, tashi je ki ce ma Asabe ta kawo ma su Hajiya abinci"

Hajiya Karime ta ce "a'a alhamdullahi, mun gode, mun ci abinci ai"

Ammi ta ce "in ke ba za ki ci ba, ai ƴa ta za ta ci"

Farha ta ce "Ammi ai ba zan iya cin abincin ba, bare ma ba na jin yunwa"

Yasna dama can ko motsawa daga wurin da take ba tayi ba ma, dan tun da suka shigo ɗakin ta wani haɗe rai, ban da gaisuwar da tayi ma Hajiya karime shi ma can ciki tayi, ba ta sake mayar da hankalinta kan su ba

Ammi ta ce ma Farha "abincin gidan na mu ya daina yi miki daɗi ne?"

"A'a Ammi , amma yanayi da nake ciki ne yasa ba zan iya cin abincin ba"

"Wa ya tab'a mun ke Farha?"

Turo baki tayi, ta ce "Arshad mana"

Ammi da ta wani b'ata rai, ta ce "me ya miki?"

Hajiya Karime tayi saurin amsar zancen, ta ce "wai Farha ba mun gama wannan maganar da ke ba?"

Ammi ta ce "kyale ta mana Hajiya, gaya mun kin ji Farha"

Tattaro hawaye ta fara yi, ta ce "Ammi wallahi Arshad baya so na, ba zai aure ni ba"

Ammi ta ce "ai bai isa ba, na sha gaya miki ki kwantar da hankalinki, ke ce zai aura"

"Amma Ammi taya hankalina zai kwanta, bayan waccan matsiyaciyar budurwar ta shi har company take isko shi"

Ammi ta ce "what!? Company kika ce?"

"Kwarai kuwa Ammi, ranan na je wurinshi kawai na taradda ita cikin office ɗin shi ma"

A hasale Ammi ta ce "kenan dai da nace ya rabu da ita, ƙi yayi ko? To bari ya dawo, kiyi shiru kin ji"

Hajiya Karime ta ce "a'a Hajiya, ba fa zai yiwu ki lallashi ƴarki sannan ki riƙa yi wa na wa ɗan faɗa ba"

Ammi ta ce "ba ya jin magana, dole kuwa in mishi faɗa.....akan me?"

"To Hajiya, ina da shawara, ba shi ya kamata kiyi ma wannan faɗan ba"

Ammi ta ce "to wa zanyi ma idan ba shi ba?"

"Ai ba shi da laifi, ita wannan yarinyar da ta maƙale mishi ya kamata a ja ma kunne, amma kullum ki tsare mun yaro kiyi ta mishi faɗa?"

Shiru Ammi tayi tana nazari, sannan ta ce "kin kawo shawara kuwa, zan shirya gobe in tafi gidan na su, zan mata wankin babban bargo kuwa"

"Haba Hajiya, ai ba ke ya kamata ki tafi ba, ki bani address ɗin gidan kawai, yau ɗin nan ma sai in tafi"

"Hakan ma yayi, amma nima ban san address ɗinta ba, ga dai su Yasna nan sun san gidan, sai su raka ki"

Yasna da tun lokacin da suka fara maganar take musu wani irin mugun kallo, tana jin haushinsu, ta ce 

"Ammi wace Yasna!!? Wallahi ba inda za ni, haka kawai zan raka ku gidan mutane ku je cin mutunci!!!"

Tana rufe baki, Ammi ta tashi ta kai mata duka, ta ce

"Ni nake miki magana kina cewa ba za kiyi ba?"

Hajiya karime da ta riƙe Ammi ta ce "yi haƙuri mana Hajiya, ai yarinya ce"

"Wannan da kike gani ba wani yarinta, tsabar rashin kunya ne da ya cika mata kai......kuma zanyi maganinki a gidan nan" tana maganar ne tana dangwarin kan Yasna dake dunƙule kan kujera

Hajiya Karime ta ce "kiyi haƙuri dan Allah"

Yasmin ta ce "Ammi kiyi haƙuri, ni zan kai su har ƙofar gidan"

Takowa Ammi tayi gaban Yasmin ta shafa kan ta, ta ce "yawwa ƴar albarka, je ki shirya ki sauko ku tafi"

"To" cewar Yasmin, sannan ta haura sama
Su Ammi kuma suka koma suka zauna, sai faman aikawa Yasna harara take yi, ita kuwa Hajiya Karime murmushi tayi ma Farha a fakaice, ganin plan ɗinsu ya tafi dai-dai yanda suka tsara shi


Ita ma Yasna tashi tayi ta bi bayan Yasmin ɗin

A bakin drawer ta tararda ita tana fito da kayan da za ta saka

Zama tayi kan gado, ta ce "yanzu kai su za kiyi?"

Ba tare da ta juyo ta kalle ta ba, ta ce "eh"

Yasna ta ce "amma kin san ba girma da arziki zai kai su ba, yanzu kina goyon bayan ki kai su su ci musu mutunci?"

Ba abunda Yasmin ta ce mata, sai ma wucewa da tayi dressing room ta sa kaya, tana gamawa ta fito

Har ta kai ƙofa, Yasna ta riƙe ta, ta ce "dan Allah twinny kar ki kai su, wallahi idan kika kai su Sweet Bro ba zai ji daɗi ba, kuma ba kiyi mishi adalci ba"

Harararta Yasmin tayi, ta ce "kamar ya ban mishi adalci ba!? Ai adalcin kenan, a raba shi tsiya, ke baki da hankali wallahi"

"Ke har kin isa ki raba ɗan adam da tsiya ne? Infact, kar ki ƙara kiran Anty Hanan da tsiya, kin ji na gaya miki" Yasna ta faɗa cikin fushi

"Au, duka na za kiyi?...To na maimaita, tsiya, kuma ba abu da zai hanani kai su har gidansu"

Kafin ma Yasna tayi wata magana har Yasmin ta fita daga ɗakin, shiru tayi tana mamakin wannan abun

Zuwa tayi bakin window ta tsaya, nan ta hango su sun nufi parking area, tana kallonsu har suka shiga motarsu Farha ɗin, Farha ce ta ja motar

"Damn it! Da gaske fa zuwa za suyi kenan, i can't let that happen"

Sauka ƙasa tayi ta ɗauko wayarta, sannan ta dawo ɗakinsu, Ammi dai ko kallonta ba tayi ba






Arshad na office shi da Sajjad, Sajjad ya ce "wai super wannan kiran gaggawa fada kamun dan Allah?"

"Man, wallahi na manta gaba ɗaya wai yau mutanen Lagos zasu zo"

"Mutanen Lagos kuma?"

"Eh mana, na daga kampanin Mr Phillip"
 
"Amma baka gaya mun ba"

"Shekaran jiya muka yi magana akan zai turo da manajojinshi za muyi magana da su, amma i don't know what comes over me, wallahi na manta"

"Ai kai ne kullum cikin tunani......yanzu suna hanya ne ko me?"

"Dama nayi ma Sagir magana, akan yau baƙin da zamu yi shi zai ɗauko su daga airport, to yanzu ya kira ni wai ya gansu, su na ma hanyar company ɗin nan, dan yau suke so mu gama komai su koma"

"Tab, ashe kenan dole mu shirya urgently, dan ya zamana kafin su ƙaraso mu shirya komai"

"Haka ya kamata, yanzu ka je ku fara shiryawa, zan tattara wasu files ne nan sai in zo, kayi magana da Khairat idan ka fita"

"To shikenan"

Sannan Sajjad ya fita, shi kuma zaunawa yayi ya haɗa wasu files, yayi rubutun da zai yi sannan ya tashi, ya ɗauki files ɗin da wayarshi, ko tunanin me yayi?, sai kuma ya maida wayar ya ajiye ya fita


Fitarshi ke da wuya, kiran Yasna ya shigo wayar, har ta gama ringing ta yanke, tsaki Yasna tayi sannan ta sake kiran wayar, amma shi ma har ya yanke ba'a ɗauka ba

"Ya salam, ina Sweet Bro ya ajiye wayar kuma?" tsaki ta sake yi, ta ci gaba da kiran wayar amma a banza bai ɗauka ba, ta kira shi ya kai sau goma sha biyar, sannan ta haƙura da kiran, sai dai ranta duk ya b'aci

********************

A ƙofar gidansu Hanan Farha tayi parking, sai wani kallo suke bin gidan da shi

Hajiya Karime ta ce "kin tabbata nan ne gidan?"

Yasmin ta ce "eh Mummy, nan ne"

"To ku fito mu shiga"

Yasmin ta ce "a'a Mummy, ni bazan shiga ba, ku dai ku shiga ku fito, ina jiranku"

Farha ta ce "amma meyasa?"

Hajiya Karime ta ce "kyale ta kawai, mu shiga ɗin"

Ɗaga kafaɗa tayi ta ce "ok Mum"
Sannan ta fito, suka shiga.



Yuhanees da Siyama na ma Ummi wanki a tsakar gidan, kasancewar zuwan Yuhanees ɗin kenan ta ga Siyama na wankin sai ta taya ta, duk da cewar Ummi ta hana ta amma ta dage akan sai tayi, Ummi kuwa na gefe kan kujera sai hira suke tayi, Hanan kuma na ɗaki tana sa kaya, dan ita ma bata daɗe da dawowa ba sai ta shiga tayi wanka

Bankaɗo ƙofar gidan suka ji anyi, sai suka mayar da hankalinsu su na kallon hanyar zauren, su na jiran ganin waye haka

Hajiya Karime da Farha suka shigo ko sallama babu, tsakiyar gidan suka yi tsaye su na wani harare-harare, ba wanda ya ce musu komai sai kallon mamaki suke musu

Farha ce ta kalli su Yuhanees ta ce "ina Hanan?"

Yuhanees ta ce "ta je koyon sallama"

"Karki gaya mun magana" cewar Farha

Yuhanees ta ce "ki ɗauki mataki mana" ta faɗa tana harararta

Ummi ta taso ta ce "yi shiru Yuhanees,  baiwar Allah lafiya?" ta tambayi Hajiya Karime

Murmushin isa Hajiya Karime tayi ta ce "nan ne gidansu Hanan?"

"Eh nan ne" cewar Ummi

" Good, ina son ganinta"

Kafin suyi magana, sai ga Hanan ɗin ta fito tana faɗin "lafiya nake jin magana?"

Tsayawa tayi cak, ganin Farha da tayi, dan tsab ta gane ta

Farha ce ta taka zuwa gabanta, ta ce "lafiyar kenan, na zo ne in miki kashedi akan ki rabu da mijina"

Yuhanees ta ce "miji kuma?" cikin mamaki

Farha na kallon Hanan, ta ce "kwarai kuwa, idan ke ba ki san shi ba, ita tasan shi"

Ummi ta ce "yarinya, ki bari mu zauna, kiyi mun bayani yanda zan fahimta, naji kina magana ne akan mijinki"

Hajiya Karime ta ce "ke kin ga munyi miki kama da waɗanda suka zo wannan gidan domin su zauna?" ta faɗa tana wani hararar gidan ta ko ina

Ummi ta ce "hmm, baiwar Allah, bai kamata ki biyewa yarinya haka ba, kamata yayi mu zauna muyi magana ta fahimta"

Yuhanees ta ce "dan Allah Ummi ki kyale su, kar Allah ya sa su zauna, ke ki gaya mana wanene mijin na ki da har kike zargin Hanan na bibiyarshi"

Hanan ta ce "rabin rai wannan ba matar aure ba ce, tana magana ne akan Arshad"

Yuhanees da Ummi suka haɗa baki wurin cewa "Arshad???"

Hajiya Karime ta ce "eh Arshad, ina so ki ja wa ƴarki kunne akan ta rabu da shi, domin shi ba sa'an ta ba ne, ya fi ƙarfin ya auri talaka, domin kin san hausawa sun ce babban goro sai magogin ƙarfe"

Yuhanees ta ce "oh, ai yanzu ne gane, kenan wannan abun ita ce Farha dama? Iska na wahalar da mai kayan kara, amma kun bani kunya wallahi, ai an wuce zamanin da ake yin faɗa akan saurayi, kowa baje irin ta ta basirar za tayi a fagen kula da shi da kuma nuna mishi soyayya, daga nan ne mai rabo za ta ɗauka, amma ke" ta nuna Farha "dan ki na daƙiƙiya, shi ne kika ɗauko mahaifiyarki kika zo dan ta taya ki yaƙi......"

Ɗaga mata hannu da Ummi tayi ne ya sa ta yin shiru

"Ya isa Yuhanees.......Hajiya, ina so zan tambaye ki" ta mayar da kallonta kan Hajiya Karime

"Dan Allah Arshad ɗin ne ya aiko ku?"

"Ji mun wata tambayar banza, ina da haƙƙin zuwa ne shiyasa na zo, na ga waccan ƴar ta ki(ta nuna Yuhanees) tana so ta ja wo muku masifa, dan bata san wacece ni ba shiyasa ta cika kaifin baki, amma ba da ita zanyi ba, ke zan gayawa, kiyi gaggawar raba Hanan da Arshad domin kuwa Arshad mijin mace ɗaya ne kuma ƴa ta ce Farha, idan kuma ba haka ba, to wallahi ina miki albishir da cewa daga ke har ƴaƴanki zaman Kaduna sai ya muku wuya, dan duk abunda yake na wa, to na wa ne, duk abunda yake na ƴata, to na ta ne, ba ma sharing, idan kunne ya ji......kin san sauran"

Farha ta ce "ai dole ma ne ta sani....."

Hanan ta b'alla mata ƴan yatsunta ta ce "kulll yarinya, kar ki kuskura ki ɗau wannan hanyar, nayi shiru ne coz i can tolerate ur madness, amma idan haukarki ta nuna miki yi wa mahaifiya ta rashin kunya, to wallahi sai dai a fitar da ke daga cikin gidan nan, dan bugun kawo wuƙa zan miki wallahi, ki mutunta mahaifiya ta kamar yanda na mutunta ta ki bance mata komai ba, wannan tsakaninmu ne ni da ke, kuma na ri ga da na miki bayani tun a wancan lokacin"

Shiru Farha tayi, ganin yanda Hanan ke mata magana, sai ta ji ta bata tsoro 

Hajiya Karime ta ce "wannan ba maganar ku bane ku kaɗai, kar ki ɗauka barazana ce na muku, wallahi bani da kyau, dan haka ki shafa ma kanki lafiya, dan ku zauna lafiya ke da ƴan uwanki"

Yuhanees ta ce "ba wanda ya isa ya canza abunda Allah ya rubuta akan mu, kuma mun dogara da shi"

Hajiya Karime ta mata kallon yarinya ba ki sanni ba, sannan ta ce "to shikenan, mu zuba mu gani"

Ta jawo Farha da nufin su wuce, amma sai da Farha ta sa ƙafa ta shure bokitin da suke wanki da shi, da ruwan da kayan da ke ciki duk suka zube, Yuhanees ta tafi da niyar jan Farha, amma Ummi ta riƙe ta, tana girgiza mata kai, tsaki Farha tayi sannan suka wuce

Ajiyar zuciya Ummi ta sauke, ta kalli Hanan dake tsaye gaba ɗaya ranta a b'ace, Hanan za tayi magana Ummi ta ɗaga mata hannu kawai, sai ta wuce ɗakinta

Siyama da ta zama hoto, ta ga abunda ya fi ƙarfinta, ta duƙa ta ɗauke bokitin, ta sake ɗibo wasu ruwan, sannan ga kwashe kayan ta sa tana ɗaurayewa

Yuhanees ta matsa kusa da Hanan, ta riƙe mata hannu, ta ce "calm down Hayatee, ki bar ma Allah komai"

Hanan ta ce "rabin rai Ummi fa...."

"Kiyi shiru wannan maganar ba ta yanzu ba ce, je ki ɗibi abinci ki ci, kar ki sa komai a ranki"

Shiru ta ɗan yi, sannan ta ɗaga kai kawai ta shiga kitchen, ita kuma Yuhanees ta dawo wurin Siyama suka ci gaba da ɗauraye kayan

********************

Kusan meeting ɗin awa ɗaya da ƴan mintuna su Arshad suka yi da baƙinsu na Lagos, sannan suka wuce

Office ya dawo, ya duba agogon bango dake office ɗin, 4:21pm, yayi ɗan tsaki, ya ce "lokacin sallah har ya wuce wallahi, ga shi ban so na kai time ɗin nan ba a company yau"

Ɗaukar wayarshi yayi, ya ga missed calls kusan ashirin, yayi mamaki a ce cikin ɗan lokacin nan da baya kusa har ya samu waɗannan kiran haka

Dubawa yayi, kira biyu na Jafar ne(shi yake bin ya Nabeel), uku na wasu abokananshi ne guda biyu, sauran sha biyar kuma na Yasna ne, cikin mamaki da kuma fargaban irin wannan kiran, yayi dailing numbernta

Bugu ɗaya kuwa ta ɗauka, kamar tana jira

"Sweetie lafiya na ga missed call ɗinki haka? Ina Yasmin da Ammi? Kina ina?" ya faɗa cikin ruɗu

"Sweet Bro lafiya ƙalau muke"

Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya ce "to lafiya?"

"Ai lokaci ya ƙure kuma Sweet Bro, dama zan gaya maka ne su Farha da Mummynta sun tafi gidansu Anty Hanan wai su ja mata kunne akan ta rabu da kai"

"Ban gane me kike faɗa ba" ya faɗa yana haɗe gira yana girgiza kai

"Kamar dai yanda ka ji, haka nake nufi Sweet Bro, kuma Yasmin ce ta kai su sannan kuma Ammi ce ta bada goyon baya, na so a ce ka riga su zuwa gidan, amma baka ɗaga ba" ta faɗa a sanyaye

Ranshi in yayi dubu to ya b'aci, abunka da farin mutum har wani ja yayi, jijiyoyin kanshi suka wani tashi, ba abunda yace mata, sai kashe wayar kawai yayi, ya ɗauki mukullin motarshi ya fito office ɗin, ba abunda ya tsaya tattarawa

Khairat ta miƙe tsaye ta bishi da ido ganin yanda ya fito, Sajjad ma da ke ƙoƙarin shiga office ɗin, da sauri ya matsa mishi, dan da kaɗan ya banke shi, yana kiranshi amma ko jinshi ma ba yayi

Ko bayan da ya sauka ƙasa ma, duk ma'aikatanshi sunyi mamakin yanda suka ganshi, dan basu tab'a ganinshi a haka ba

Figar motarshi yayi, ya ɗauki hanyar gidansu Hanan, wani tunani kuma yayi, sai ya sake juya akalar motarshi izuwa gida..........
🥰UMMEETA🥰......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥




        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 21* 

Yana zuwa gida bai tsaya ko ina ba sai main palour, Inna Asabe ce kawai a palourn tana gyarawa

Ko kallonta bai yi ba, sai ihun kiran Yasmin da yake yi

"Yasmin!....Yasmin!.....Yasmin!!!"

Inna Asabe tayi tsaye tana kallonshi, kamar za tayi magana, sai ta ga su Yasmin ɗin ma suna saukowa

Yasmin ce a gaba, Yasna na bayanta, sai sauri take yi, tana ƙarasowa kusa da shi ta tsaya

"Big Bross ga...." ba ta kai ƙarshe ba, ya ɗauke ta da mari, hakan yayi dai-dai da saukowar Ammi dan ta ji shigowarshi

Sake marinta yayi, sai dai wannan karon bai samu fuskarta ba, dan ta rufe fuskar da hannunta, sai ya same ta a hannu, Ammi ta zo da sauri ta ja ta zuwa bayanta

Yasna ce ta riƙe ta, dan ta tausaya mata saboda ta maru musamman marin farko, haka ma Inna Asabe ta tausaya mata, ba ta dai ce komai ba

Ammi ta ce "Arshad kanka ɗaya kuwa? Marinta fa kayi, Yasmin ka mara!"

Shi ma cikin fushi ya ce "na sani Ammi, ta ma gode ma Allah ita ce, wallahi da sai na kusan karya ta a gidan nan, amma yanzu ma ki jira dawowa na, wallahi idan naji abunda bai mun dai-dai ba, sai na ba ki mamaki" ya ƙarasa zancen yana nuna Yasmin dake ta faman rusa kuka a kafaɗar Yasna, ita kuma sai shafa mata baya take tayi kamar wata jaririya

Ammi da tayi wani sororo tana kallonshi, ta ce "Arshad?"

Ko kallonta bai yi ba, ya juya ya bar palourn, haka tayi ta kiranshi, amma har ya fita ko juyowa bai yi ba

"Arshad! Arshad!.......tabɗijam"

Juyawa tayi ta ja Yasmin suka koma kan kujera suka zauna, ta kalli wurin da ya mare ta, ga shatin hannunshi nan ya kwanta, fuskar nan tayi ja

"Yi shiru ya isa haka, kyale shi, dani yake zancen ai"

Kallon Yasna tayi za tayi mata magana, ta ga hawaye shane-shane a fuskarta, sakin baki tayi ta ce "hadda ke ya mara?"

Girgiza kai tayi tana share hawayen, Inna Asabe ta ce "bai mata komai ba Hajiya, kawai dai kin san abunka da jini ɗaya"

Ammi ta ce "hmm, to ya isa kema, je ki ɗauko mata ruwa ta sha"

Yasna ta wuce ta ɗauko ruwan ta bata, sai da ta sha sannan Ammi ta ce ta ja ta su koma ɗakinsu, ta ɗan kwanta kafin a kira sallar Magrib

Yasna ta ce "amma Ammi ba kyau baccin bayan la'asar fa"

"Ba bacci nace tayi ba ai, uwar iyayi, kuje ta ɗan kwanta ne"

Ba ta ce komai ba, ta kama ta suka wuce ɗakinsu

Bakin gadonsu suka zauna, Yasmin sai share hawaye take tayi, Yasna ta kalle ta ta ce "kin gani ko twinny, sai da nace miki kar ki tafi amma kika ƙi, yanzu ai ga abunda kika ja wa kanki"

Yasmin ta ce "dalla malama ki kyale ni, ina ruwanki da ni, munafuka kawai, kuma wallahi ba zai tab'a aurenta ba"

Sakin baki Yasna tayi tana kallonta, wato ma har yanzu ba za ta canza ba

"Yasmin ni ce munafuka? To shikenan kar ki daina, kuma ki daina rantsuwa akan abunda ba ki da tabbas"

"Akan menene ban da tabbas ɗin! Auren Hanan? To na maimaita wallahi ba zai aure ta ba"

Yasna ta miƙe tsaye ta ce "Ashe kuwa ki shirya ma azumin kaffara"

Ba ta tsaya jin komai daga gare ta ba kawai ta fita daga ɗakin, ita ma Yasmin rakata tayi da harara, sannan tayi tsaki ta kwanta

********************

 Arshad kuwa tun bayan da ya fita daga palourn, ya wuce part ɗinshi

Zama yayi kan kujera, ya sa hannu biyu ya riƙe kanshi ya rufe ido, sai faman furzar da iska yake yi lokaci zuwa lokaci

Sallamar Sajjad ce ta sa shi ɗagowa, suna haɗa ido ya sake komawa yanda yake

Sajjada ya zo kusa da shi ya zauna yana kallonshi, sannan ya ce "Super lafiya?" ya tambaye shi cikin damuwa

Sai da yayi kusan minti uku sannan ya ce "Ina zuwa Man" ya tashi kawai ya shiga bedroom ɗin shi, Sajjad kuwa sai roƙon Allah ya ke yasa lafiya

Wanka yayi, sannan yayi alwala, ya fito ya shirya cikin wani yadi milk colour, yayi masifar yi mishi kyau, ya feshe jiki da turare sannan ya ɗauko wasu takalmanshi baƙaƙe ya sa suka yi kyau ma farar ƙafarshi, ya shace gashin kanshi sannan ya ɗauko sallaya ya fito palour wurin Sajjad

Kallonshi Sajjad yayi, sannan ya ce "yau laraba, kuma yanzu karfe biyar, bare ince ko masallaci zaka tafi, ina zuwa haka?"

Murmushin da bai kai cikinshi ba yayi mishi, sai ya cire takalminshi can wurin ƙofa sannan ya dawo ya shimfiɗa sallaya ya fara sallah, sai da ya gama yayi addu'a sannan ya gyara zama ya fara zayyana ma Sajjad duk abun da ya faru

Shiru ya ɗan yi na wani lokaci sannan ya ce "amma Yasmin ta ba ni mamaki wallahi"

Arshad ya ce "banyi mamaki ba ni, dan na san wacece Yasmin"

"Hmm, amma kai ma baka kyauta ba da ka dake ta"

Wani wawan kallo yayi mishi, yayi tsaki ya ce "ni ba wannan ne ya dame ni ba, yanda ma zan tunkari gidansu Hanan nake ji"

"Ka kwantar da hankalinka, insha Allah ba wani abun da zai faru"

"I hope so"

"Yanzu ka bari idan muka yi sallah, sai mu tafi"

"To shikenan"

**********************

"Mummy wallahi na ji daɗin wannan plan ɗin na ki, kin ga yanzu, dole ne ma ta rabu da shi" cewar Farha

Hajiya Karime ta ce "yaro dai yaro ne, ba ki fahimci abunda na fahimta ba kenan"

Farha ta ce "Mummy me kika fahimta?"

"Yarinyar nan Hanan, ban ga alamar tsoro a tattare da ita ba, bare kuma wai har tayi tunanin rabuwa da shi, sannan kuma kin ga wannan ɗayar, ban san sunanta, ita kanta za ta iya hana Hanan rabuwa shi"

Murmushi Farha tayi, ta ce "kai Mummy, ai ni na fi so in ga sauyi a fuskar mahaifiyarta, dan ita ce take da ikon hana ta da kuma sa ta, to kin ga kuwa duk yanda take son shi, in dai mahaifiyarta ta raba su dole ne ta kyale shi, ke ba ki ga yanda ran mahaifiyarta ya b'aci ba?"

Ɗan ƙaramin nazari Hajiya Karime tayi, ta ce "tabbas, maganarki akan hanya take, amma duk da haka ba za muyi sake ba, dole ne in ƙulla wani abu"

"Me kenan Mummy?"

"Zan gaya miki nan gaba"

"To shikenan, bari inje inyi wanka"

"Yawwa ƴar Mummy, ina tunanin ma friday Daddynki zai dawo"

Wani tsalle tayi ta ce "wow, wallahi i really missed him alot"

Murmushi tayi, ta ce "to je kiyi wanka kafin a kira sallah"

Wucewa tayi ɗakinta tana ta fara'a

********************

A ƙofar gidansu Hanan, Arshad yayi parking, suka fito suka tsaya jikin motar.Wayar Hanan ɗin ya kira har ta tsinke ba ta ɗauka ba, ya sake kira na biyu, sai Siyama ta ɗauka

"Hello Ya Arshad"

"Na'am Siyama, ina Hanan"

"Ba ta nan, ta je ta raka Anty Yuhaness"

"To zo kiji, ina ƙofar gida"

"To, gani nan zuwa"

Sai suka kashe wayar, ba ta fi minti biyu ba, sai ga ta ta fito

Sai da suka gaisa da Sajjad sannan ta mayar da hankalinta kan Arshad

"Siyama, ɗazu wasu sun zo gidan nan?"

Shiru ta ɗanyi, sannan ta ce "eh"

"Su nawa?"

"Su biyu, ɗayar kusan shekarunsu ɗaya da Sister, ɗayar kuma dattijuwa ce"

"Kika ce su biyu?"

"Eh su biyu ne"

Hamdala yayi cikin ranshi, dan hakan ya nuna mishi cewar ba su san tare da Yasmin suka zo ba, sannan ya ce "me suka yi da suka zo?"

Ai kuwa yayi sara akan gab'a, dan ya tambayi radio, labari ta ba shi tun daga farkon shigarsu gidan har fitarsu, duk abunda suka faɗa ba wanda ta manta, hatta gwallo da bokitin da Farha tayi sai da ta gaya mishi

Shiru suka yi daga shi har Sajjad ɗin, sannan suka kalli juna, Sajjad ya mayar da kallonshi kan Siyama ya ce "Siyama, ki shiga ki ce ma Ummi dan Allah muna son ganinta"

Arshad yayi saurin kallonshi ya ce "Man!?, taya kake tunanin zan iya fuskantar Ummi?"

Siyama ta ce "may be za ta saurare ka Ya Arshad, amma tun ɗazu su Sister ke son yin magana da ita amma ta ƙi ba su fuska, yanzu ma kafin Anty Yuhaness ta wuce sai da suka shiga dan su mata magana amma ta ce idan maganar ce su kyale ta kawai"

Arshad ya dafe kai ya ce "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un, Man ka ga abunda nake tsoro ko?"

Sajjad ya ce "haba Super, to idan ba ka fuskance ta ba ka ba ta haƙuri, me za kayi?"

Siyama ta ce "haka ne Ya Arshad, in sha Allah za ta saurare ka"

Sha fa fuskarshi yayi, ya ce "to shikenan, shiga ki mata magana"

Komawa tayi cikin gida, Ummi na ɗaki ta isko ta, ta gaya mata Ya Arshad na son magana 

Ta ce "ɗauko tabarma bayan ƙofa, ki shimfiɗa tsakiyar gida, sai ki ce ya shigo"

"Su biyu ne, da abokinshi"

"Su shigo mana"

"To"

Ɗaukar tabarmar tayi ta shimfiɗa kamar yanda Ummi ta ce, sannan ta fita ta gaya musu su shigo, sannan suka biyo bayan Siyama har cikin gidan, suka zauna kan tabarmar

Ummi ce ta fito sanye da hijab ɗinta, ta jawo kujerar dake gefen ɗakin ta zauna, sannan suka risina suka gaishe ta, cikin sakin fuska ta amsa musu tana tambayarsu ya aiki

Shiru suka yi na kusan ƴan mintuna, sannan Arshad ya fara magana kan shi a ƙasa

"Ummi dan Allah kiyi haƙuri abun da ya faru ɗazu, wallahi ban san da zuwansu ba sai daga baya Yasna ta gaya mun, amma in sha Allah na miki alƙawari zan ɗauki mataki amma dan Allah Ummi kiyi......"

Ummi ta katse shi "Arshad!"

Shiru yayi amma ya kasa ɗaga ido ya kalle ta, ta sake kiranshi

"Arshad!"

Da ƙyar ya iya ɗagawa ya kalle ta ya ce "na'am"

"Ka na son Hanan?"

Jin tambayar yayi wani iri, ya kasa cewa komai, sai da ta sake tambayarshi

Sannan ya ce "Ummi ina son Hanan, kuma tsakani da Allah nake son ta" hakan yayi dai-dai da shigowar Hanan

Tana ganinsu sai da gabanta ya faɗi, wucewa tayi bakin ƙofar kitchen kan turmi ta zauna

Ummi ta ce "ka tabbata?"

"Eh Ummi, ina sonta wallahi, dan Allah kiyi haƙuri"

"Waɗannan ɗin su waye?"

"Yarinyar tana so na ne amma ni bana sonta, to shi ne ta biyo ta wannan hanyar dan kawai Hanan ta rabu da ni"

Ummi tayi ajiyar zuciya, ta ce "Allah ya kyauta, dama ba ta ɗaga mun hankali ba, tunda ba kai ka aiko ta ba sannan kuma ba mahaifiyarka ba ce, ina so ne dama in sake tabbatar da irin son da kake mata....ba damuwa Arshad, Allah ya mana mai kyau"

Ɗagowa yayi da sauri ya kalle ta, ya ce "Ummi kin haƙura?"

Murmushi tayi ta ce "Arshad ai ban yi fushi ba dama, haƙurin me kake bani? Ba ka yi mun komai ba"

Wani irin farinciki ne ya baibaye zuciyoyinsu, Arshad da Hanan, dan dukansu tsoro ɗaya ne a ransu kar Ummi ta raba su

Sajjad da bai ce komai ba tun bayan da suka gaisa, sai yanzu ya ce "mun gode sosai Ummi"

Nan ma murmushin tayi, ta ce "ba komai, ya sunanka kai"

Ya ce "Sajjad"

"Masha Allah, suna mai daɗi"

Arshad ya wani kalli Sajjad dake murmushi, sannan ya kalli Ummi ya ce "to Ummi ni kuma fa?"

Dariya tayi ta ce "kai ma haka ai Arshad"

Sannan suka yi dariya, nan dai Ummi ta koma ɗakinta wurin Siyama, ya rage da ga su Arshad sai Hanan

Tashi yayi ya koma kusa da ita ya tsugunna ya kallon fuskarta, duk da ya kasance dare ne, amma bai sa gidan yayi duhu ba kasancewar akwai wuta

Ƙoƙari yayi ya fara tattaro zance, sannan ya ce "i'm really sorry for what happen"

Kallonshi kawai take yi da kyawawan idanunta masu ɗaukar hankali

Rufe ido yayi yana girgiza kai, haɗi da yin wani killer smile, sannan ya sake buɗe ido ya kalle ta, ya ce "dan Allah ki daina mun irin wannan kallon, wani iri nake ji, kiyi haƙuri dan Allah"

Ita ma murmushin tayi, ta ce "haƙuri akan me?"

"Abunda su Farha suka yi"

"Farha daban Arshad daban, Farha ce tayi laifi, meyasa Arshad ke ba da haƙuri?"

"Saboda shi ya san darajar abunda aka tab'a mishi"

Murmushi ta sake yi, ta ce "meyasa ba ka gayawa Ummi cewar Ammi ba ta so na ba?"

Kallon ƙofar ɗakin Ummi yayi, sannan ya ce "dan Allah kar ki gayawa Ummi wannan maganar please"

"Amma meyasa?"

"Daga maganar da tayi ɗazu, na fahimci idan har mahaifiya ta ba ta sonki to lallai raba mu za tayi, kuma Hanan banajin zan rayu ba tare da ke ba"

"Amma ka san dole ne wata rana sai ta sani!"

"Na sani, amma ina fatan kafin wannan lokacin Ammi ta gyara halinta"

"Kenan za mu ɗauki shekaru a hakan?"

"A'a"

"Amma yanayin maganarka haka ya nuna"

"Ba haka nake nufi ba Hanan, ina so zan tafi wurin kakarmu, anan ne na san in sha Allah komai zai yi dai-dai"

"To ina fatan haka"

"Yawwa your highness haka nake son ji.......har yanzu MK bai ce miki komai ba?"

"Eh ba abun da yace mun, but i know he's up to something"

"Nima ina jin hakan, amma kar ki ji tsoro, Allah ya na tare da ke, ba abunda MK zai iya yi miki"

"Shikena , Allah ya sa"

"Ameen, kinga bari mu wuce kar Ummi ta ce bani da kunya"

Dariya ne ya sub'uce mata, ta ce "na yaushe kuma?"

Shi ma dariyar yayi, sannan ya juya da niyar yi m Sajjad magana, amma ya ga tabarma wayam ba kowa akai

"To shi kuma wannan ina ya tafi?"

Dariya ta kuma yi, ta ce "kana nufin kace ba ka ga lokacin da ya fita ba?"

Girgiza kai yayi, ta ce "ai kuwa ya daɗe da fita"

Murmushi yayi ya ce "ai ba laifi na bane, ke ɗin ce idan ina kallonki bana ganin kowa"

"Hadda Ummi dake bayanka?"

Da sauriya juya amma bai ga kowa ba, ya juyo yana kallonta sai faman dariya take tayi, ba ƙaramin kyau ta mishi ba

Sai da ta gama dariyarta sannan ta tashi ta raka shi har wurin mota, Sajjad ya fito, ta ce "malam tafiya ba sallama?"

Dariya yayi ya ce "kin san ni tsoron masoya nake ji musamman wannan, dan ba ko da yaushe yake gane kan shi ba"

Dariya tayi ta ce "ai kuwa"

Arshad ya haɗe rai ya ce "to idan kun gama sai ki koma gida kai kuma ka shiga mu tafi"

Dariyar suka sake yi, sannan ta ce "to yallabai, Allah ya kiyaye"

Yayi murmushi ya ce "ameen madam, sai na kira ki"

"Bye" 

Sannan ya shiga motar suka wuce, sai da suka bar layin sannan ta koma cikin gida..........









🥰UMMEETA🥰......📝



♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 22* 

Yau tsawon kwana biyar kenan da faruwar wannan abu, ba abunda ya sauya a soyayyar Arshad da Hanan sai ma abunda ya ƙaru, dan yanzu ma idan ya zo wurin Hanan ɗin, yakan shiga har cikin gidan su zauna suyi hira da Ummi da Siyama, sun ɗauke shi tamkar ɗan gidansu

Farha kuwa tunda ta samu labarin yanda Arshad yayi ma Yasmin take shakkar haɗuwarsu, dan tana da tabbacin tunda har ya iya marin Yasmin to ita zane ta ma zai yi, duk yanda Hajiya Karime ta so su tafi gidan, amma ta ƙi yarda

Sai dai sun tafi wurin wani malamin daban, akan ya raba Arshad da Hanan, kuma ya tabbatar musu da hakan zai yiwu, sai dai yana buƙatar kuɗi da kuma lokaci, inda suka ba shi naira dubu ɗari da ashirin, su na jiran tsammani

Ammi kuma ta kira Abba akan maganar Arshad ɗin da Farha

"Abban Nabeel na ji kayi shiru akan maganar auren nan na Arshad, lafiya dai?"

"Haka ne, amma kin san komai yana buƙatar bincike, musamman sha'ani na aure, so zanyi bincike akan ita yarinyar"

"Amma wane bincike za kayi Abban Nabeel!? Ina ce yarinyar nan na gaya maka ƴar aminiya ta ce, sannan kuma ka san mahaifinta, Alhaji Mas'ud, to me kuma ya rage?"

"Tabbas mun san iyayenta, amma ba mu san ainihin halayenta ba, kuma kin ga ita zai aura ba iyayenta ba"

"Amma ai......"

"Kiyi haƙuri ayi binciken dan Allah, in Allah ya rubuta matarshi to sai ya aure ta" ya katse ta

Ba dan ta so ba ta ce "to shikenan, nagode"

Daga hakan su kayi sallama, sai zulumi ta ke yi, anya kuwa ba wani abu bane a ranshi
Shi kuma ba wani bincike da ya fara akanta, kawai dai yana so ne sai Arshad ɗin ya zo sun yi magana sannan ya san abun yi

********************

Yau Hanan na zaune a reception, su na hira ita da Zulaihat, sai ga wani Shehu ya zo wurinsu

"Hajiya Hanan da Zulaihat, sannunku da hutawa"

Murmushi tayi ta ce "Hajiya Zulaihat ɗin dai, ni kuma Hanan"

Ya ce "meyasa to ba za'a kira ki da Hajiya ba?"

"Saboda banyi kama da su ba"

Zulaihat ta ce "ai ko kin yi kama da su, ki na matar AAJ"

Bugun wasa Hanan ta kai mata, sannan ta ce "ba AAJ ba, ƴar rainin hankali"

Dariya Shehu yayi, ya ce "ni dai duk ba wannan ba ma, kun ga kun mantar da ni, Hanan MK na kiranki"

Ras, ta ji gabanta ya faɗi, Zulaihat ma kanta sai da ta zaro ido

Hanan ta ce "lafiya yake nema na?"

"To ta ya zan sani? Ki je ki gani"

Zulaihat ta ce "ki je kawai Hanan, in sha Allah ba komai"

Sai da ta ɗan ɗauki lokaci tana tunani sannan ta wuce

Ta kusan minti biyar a bakin ƙofar office ɗin shi sannan tayi knocking ya ce ta shigo

Bata yarda suka haɗa ido ba har ta kai kusa da table ɗin shi ta tsaya

"Ki zauna mana" ya faɗa cikin murya mai sanyi

Tayi matuƙar mamakin jin yanda ya mata magana, hakan ya sa ta kalle shi, sai ta ga yana mata murmushi, sakin baki tayi tana kallonshi

Ya ce "ya dai Hanan? Feel free and get seated (ki saki jikinki, ki zauna)"

Haka ta ja kujera ta zauna, sai da ya gama abunda yake yi cikin system ɗin gabanshi sannan ya mayar da hankali kanta

"Hanan"
Ya kira sunanta, ba ta amsa ba sai dai ɗaga kai da tayi ta kalle shi

"Na san kina jin haushi na akan abunda na miki sannan kuma kina jin tsoro kar inyi miki wani abu, ko ba haka ba?"

A hankali ta ɗaga mishi kai, ya sake yin murmushi ya ce "to ki kwantar da hankalinki, na kira ki nan ne saboda in ba ki haƙuri akan abunda ya faru, kullum ina so in ba ki haƙuri amma ban san ya za ki ɗauki maganar ba, ban sani ba Hanan za ki yafe mun ko kuma a'a"

Kallon mamaki kawai take mishi, dan ba ƙaramin mamaki ya ba ta ba

Da ƙyar ta ce "ba komai yallab'ai, komai ya wuce"

"Da gaske kike yi?"

"Eh, komai ya wuce"

"Nagode Hanan, saura kuma wata alfarma ɗaya"

"Ta me?" ta faɗa tana kallonshi

"Ina so ki saki jikinki da ni, duk wata matsalar da ta shafe ki ina so ki sanar da ni, idan  ina da halin taimaka miki zan taimaka miki, na san za kiyi tunanin banda abun taimaka miki da shi saboda kina tare da AAJ, amma karki manta kowane mutum da irin baiwar da Allah ya mishi, na koyi wannan zancen ne a wurinki, dan Allah kar ki ce a'a"

"Kamar ya yallabai?"

"Na san kin gane me nake nufi Hanan, amma zan ƙara miki haske, ina so ne in zama tamkar ɗan uwanki, na fahimci duk wanda yqyi mu'amala dake zai ci riba, ina so in canza halaye na su koma tamkar na ki halayen, na sanin darajar ɗan adam, ki amince mun, za ki samu lada Hanan, sannan ina so ki taya ni ba AAJ haƙuri kafin nima in samu damar ba shi haƙurin da kaina"

Shiru tayi na ƴan mintuna, sannan ta girgiza kai ta ce "ba komai, Allah ya ƙqra ganar da mu baki ɗaya, kuma in sha Allah zan mishi magana"

"Nagode sosai Hanan" ya faɗa yana ta mata murmushi

"Zan iya tafiya?"

"Eh Hanan, tafi kawai"

Tashi tayi jiki a sanyaye ta fita, bin ta yayi da ido har ta fita, sannan ya jingina da kujerarshi yana jujjuyawa, ya saki wani irin dariya, ya ce

"I pity you Hanan(na tausaya miki Hanan), a tunaninki MK na bada haƙuri ko? You're wrong, i will definately make you cry(kinyi kuskure, tabbas sai na sa ki kuka)" ya ci gaba da murmushi

*******************

Bayan sallar magrib Arshad ya zo wurin Hanan sai dai yau ko gidan bai shiga ba, su na cikin mota

Sun daɗe su na hira sannan Hanan ta gaya mishi cewa MK ya bata haƙuri ɗazu sannan kuma ta gaya mishi ya ce ta ba shi haƙuri shi ma, sai dai bata gaya mishi ɗayan maganar ba na cewa ta saki jikinta da shi kamar yanda Yuhanees ta ba ta shawara

"Yanzu ke kin yarda da haƙurin da ya ba ki?"

"Eh to, alamun shi sun nuna mun kamar da gaske yake yi"

"To shikenan, Allah ya sa" ya amsa mata da hakan ne kawai dan ya ga kamar ta yarda da tuban MK, amma shi ya san ba banza ba, baya son dai yasa mata shakku ne

"Ameen"

"Yawwa kin san me?"

"Sai ka faɗa"

"Ina so zanyi tafiya ne gobe, zanyi kwana biyu"

'Bata rai tayi ta ce "tafiya fa kace"

"Eh, amma ai kwana biyu nace miki zanyi, ba daɗewa zanyi ba"

"Ko ma dai yini ɗaya ne, ai za ka tafi ko!"

Murmushi yayi ganin yanda take yi kamar za tayi kuka, ya ce "to ke in banda abun ki, ai idan na tafi ba wai shikenan ba za ki sake ji na ba, za muyi waya mana kamar yanda muka saba"

Shiru tayi kawai tana wani yamutsa fuska, kallonta yake yana murmushi sai wani sonta dake ƙara shiga ranshi

"Shikenan baby doll, idan ba kya so in tafi ai sai in kira Abba in ce mishi na fasa zuwa"

Da sauri ta kalle shi ta ce "a'a, akan me?"

"Na ga ai ba kya so ne"

"Amma ai kiran Abbanka ya fi nawa"

"Abbana kuma? Ban da ke kenan?"

"Ba fa haka nake nufi ba" ta faɗa a shagwab'e

Dariya kawai yayi, sai ya duba agogon hannunshi, ya ce "kin ga dare yayi, ki shiga gida kawai, ni zan wuce"

"To, Allah ya kiyaye ya kai ka lafiya"

"Ameen Hearty, ki gaida Ummi da radio" ya ƙarasa yana dariya

Ita ma dariya tayi ta ce "ba ruwana ni dai"

Sannan ya ɗauko wasu ledodi a backseat ya bata, ya nuna mata ledar ta da na Ummi da na Siyama da na Yuhanees

Sakin baki tayi ta ce "amma ai sunyi yawa dear"

"Idan kin fita ki zubar da su"

"Allah ya baka haƙuri, mun gode Allah ya saka da alkhairi ya ƙara arziki"

"Ameen, sai da safe"

"Allah ya bamu alkhairi, i will miss u so much(zan yi kewarka sosai)"

"I will miss u too(zan yi kewarki nima)"

Sannan tayi murmushi ta fita daga motar, sai da ta shiga gida sannan ya ja motar ya wuce

********************
Washe gari da safe ya gama duk wani shirin da zaiyi na tafiya, wata ƴar ƙaramar jaka mai kyau navy blue, ya sa kayanshi a ciki, sannan ya fito palour, in da Yasna take zaune, kasancewar yau ɗin asabar ba makaranta sai islamiya 12pm

Tashi tayi ta karb'i jakar sannan suka wuce main palour, Ammi na zaune a kan cushion Yasmin ma haka, ya zo kusa da Ammi ya zauna sannan suka gaisa, Yasmin ma ta gaida shi, ya amsa mata da "lafiya", haka yake amsa gaisuwarta tun lokacin da su ka samu matsala, abun yana matuƙar damunta, duk yanda take da Arshad tana son shi sosai dan ko mutum bai da hankali in ya ga irin yanda yake kyautata musu yake tarairayarsu dole ne ya burge ka bare kuma su da yake yi ma

Ammi ta ce "wai har ka fito tafiyar kenan?"

"Eh Ammi, ina so in isa da wuri ne shiyasa"

"Ni wannan tafiyar ta ka ma da rana ɗaya na rasa dalilin yin ta wallahi"

"Ammi na gaya miki ina son ganin Hajjo da Anty Fati shiyasa, kuma kin ga kwana biyu kawai zanyi"

"To company kuma wa ka bar ma?"

"Sajjad mana, ko kin manta da shi? Sannan yau saturday, monday zan dawo"

"Hmm to shikenan, Allah ya kiyaye hanya, ka gaishe su.......Yasmin je ki ɗauko saƙon da nace zai kaiwa Antynku"

Yasmin ta tashi ta wuce ɗakin Ammi. Shi kuma ya fita Yasna ta bi bayanshi.A parking area Yasmin ta taradda su, Yasna na ta gaya mishi abunda zai dawo mata da shi

Ta buɗe backseat ta sa saƙon, sannan ta dawo gabanshi, ta ce "Big Bross na san har yau kana fushi da ni, dan Allah kayi haƙuri, bana so ka tafi da haushi na Bross, i'm really sorry" sai hawaye kawai suka biyo kumatunta

Fitowa yayi daga cikin motar, ya riƙe mata hannu, sannan ya sa ɗayan hannunshi ya share mata hawayen, ya ɗaga fuskarta yana kallon cikin idanunta, ya ce "stop crying sweetie(ki daina kuka sweetie), na haƙura ai, kuma bazan iya yin fushi da ƙanwata ba, kawai dai ban ji daɗin abunda kika yi ba"

"Ba zan sake ba bross"

"Shikenan ya wuce, ki kula da kanki kinji"

Murmushi tayi ta ɗaga kai, Yasna dake gefe ta ce "ni kuma fa Sweet Bro?"

Murmushi yayi, ya jawo su ya rungume su tare, kusan munti biyu sannan ya sake su suka yi sallama ya shiga mota ya wuce

Yasna na murmushi, ta ce "ko ke fa twinny, amma ke ki ce ba ki son abunda Sweet Bro yake so!"

"To yanzu ma wa ya gaya miki ina sonta ne? Kawai ina jin wani iri ne yanda bross yake fushi dani amma ba wai dan na haƙura ya auri wata Hanan ba"

"Kina nufin tuban muzuru ki kayi kenan?"

"Na gaskiya ne nayi, amma ai ba cewa nayi ina sonta ba ko?"

"Hmm you won't change twinny(ba za ki canza ba twinny) Allah ya shirye ki" bata sake kallonta ba ta wuce cikin gida

Yasmin ta ce "ameen in da gaske kike yi" ta fita daga wannan second gate ɗin, ta wuce wurin swimming pool ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun da ke wurin


Ammi kuwa bayan fitarsu, ta ɗauki wayarta ta kira Hajiya karime

"Hajiya kin ga kuwa tafiyar nan ta Arshad da gaske yake yi"cewar Ammi bayan sun gaisa

"Ya tafi ne?"

"Bai daɗe ma da ya fita ba"

"To Hajiya meye wai abun ta da hankalin? Ya ce Hajjo yake so ya gani sai Antynshi, kin ji bai ma yi maganar Abbansu ba"

Ammi ta ce "ba za ki gane ba ne Karime, yaron nan da kike gani wayon tsiya ne da shi, na tabbata ko da ba Abban Nabeel ya je gani ba, to tabbas maganar Hanan ce za ta kai shi Adamawa, amma in ba shi ba, wata nawa ya rage ayi hutun makaranta sai mu tafi gaba ɗaya?"

"Haka ne kuma da maganarki, amma dai kar ki ce komai yanzu, mu bar komai wurin Malam, kin san na gaya miki ya ce zai iya raba su, kuma na yarda da shi"

"Haka kike gani?"

"In sha Allah komai zai tafi yanda kike so"

"To ba damuwa, nagode"

"Ai an zama ɗaya, ba komai"

"To ki gaida Farha, sai anjima"

"Za ta ji"
Suka yi sallama kowa ya kashe wayar

Farha dake gefe tana sauraren Mummynta, ta ce "Mummy ya tafi ne?"

"Eh, ya tafi"

"Mummy ko za mu koma wurin Malam ne wai, mu ji ya ake ciki?"

"Kar ki samu damuwa, nasan zai iya raba su"

"Amma ni ina shakku akan wannan aikin Mummy, saboda ance yi wa Arshad aiki ba abu bane mai yiwuwa"

"To ai ya ce ba ainihin Arshad ɗin zai yi ma ba, zai yi ma wanda yasan zai iya hana aurensu ne kuma ya hanu ko yana so ko baya so"

"To Allah ya sa"

"Ameen daughter, ai ki kwantar da hankalinki, ba dai aikin da zai karkata gare ki bane ba zai yiwu ba? To idan akayi wanda zai aure ki ko da baya son ki ne ai dole za ki samu chance ɗin wawuro mana kuɗinshi hankali kwance, tunda kin zama matarshi"

Farha tayi dariya ta ce "wa ya ga Farha a matar AAJ, tab, za'a shuka tsiya Allah" su ka sake yin dariya

Hajiya Karime ta ce "idan ana sallah ai ba'a magana daughter, Allah dai ya nuna mana wannan ranar"

"Ameen Mummy"

Suka ci gaba da hirarsu................







🥰UMMEETA🥰......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 23* 

Kusan ƙarfe 4:20pm ya isa gidan Hajjo, bakinta kuwa har kunne, tana ta jin daɗin ganinshi

Tarba ta musamman aka mishi, dan ta sa an dafa mishi tuwon shinkafa da miyar zogale wanda ya ji nama da ƙashi, sannan aka mishi farfesun cow tail da pepper chicken, sannan an haɗa mishi haɗaɗɗen kunun aya, ga fura da aka sa ma kindirmo wanda bai da surki da komai, ya sha sanyi dai-dai sha. Daga gidan Anty Fati kuwa, Nabeela ce ta aiko mishi da favorite food ɗin shi, fried spaghetti da banana smoothie.

A tsakiyar palourn Hajjo aka baza mishi komai sai wanda ya zab'a

Ɗakinshi da ya saba sauka ya fara shiga, yayi wanka ya sa ƙananan kaya, farin wando da riga army green, yayi sallar la'asar sannan ya dawo nan palour wurin Hajjo ya zauna a ƙasa kusa da ita ya naɗe ƙafa

"Sannu, ka kwaso gajiya kam" cewar Hajjo tana kallonshi

"Bari kawai matas, har jiki na ke ciwo" ya faɗa yana wani b'ata fuska

"To wani ya sa ka biyo mota? Ina ce jirgi kuka saba biyowa"

"Ai ka ji irinta kuma, ke maimakon ki tausaya mini shi ne kike cewa haka!...anya matar nan kina so in ɗaga miki ƙafa ki shiga Aljanna kuwa?" ya faɗa cikin sigar wasa irin wanda suka saba

Harararshi tayi, ta ce "dan gidanku idan kai ke bada aljannar ka hana ni"

Dariya yayi, ya ce "ba zan hana ki ba, amma ke ce ta ƙarshen shiga"

Larai da ta shigowarta ɗakin kenan, dariya ya sub'uce mata, Hajjo ta aika mata da zagi ta ce "Ladingo kika yi wa dariya"

Larai da kama bakinta tana ƙara ƙumshe dariyar, Arshad yayi dariya, ya ce "abun har da zagi?"

Bata ce mishi komai ba dai sai harara da take aika mishi, yayi murmushi ya kalli Larai ya ce "kyale wannan tsohuwar kinji"

Ita ma murmushin tayi, ta ce "to yallab'ai.......Me za'a zuba maka?, ina so zan wuce gida ne, na gama aiki na na yanzu"

"Je ki kawai, matata zata zuba mun"

Murmushi tayi, ta ce "to yallab'ai, a huta gajiya....Hajjo na tafi, sai na dawo" bata jira amsawarta ba ta wuce dan ta san ba lallai ta amsa mata ɗin ba, haka kuwa aka yi, har ta fita bata ce mata komai ba

Arshad ya ce "Hajjo ki zuba mun mana"

"Wa? Ni!!, ai wanda ya ce ka bari Larai ta wuce, shi zai zuba maka abincin"

"Ba za ki zuba ba kenan"

"Eh" ta faɗa tana ƙara gyara pilon da ta kishingiɗa da shi

"To Allah ya shirya mun ke"

Turo ƙofar palourn da akayi ne ya sa ba ta samun damar cewa komai ba, Adnan ne da gudunshi, sai kan jikin Arshad, sai dariya yake ta yi

Arshad ma dariyar yake yi, ya ce "my brave bro(jarumin ƙanina)"

Adnan ya ce "Ya Arshad yaushe ka zo?"

"Yanzu na zo"

Meerah ma da gudu ta ƙaraso, ta zauna gefenshi ta rungume shi "sannu da zuwa Ya Arshad"

Peck ya mata a goshi ya ce "tnx dear"

Sai yanzu ma ya lura da Nabeela da Jafar da suka zauna kan kujera, cikin fara'a Nabeela ta gaida shi tana tambayarsu Ammi

Sannan Jafar ya cire bluetooth ɗin da ke kunnenshi ya ce

"You're welcome Bross(sannu da zuwa Bross)" 

"Na same ku lafiya?"

"Lafiya ƙalau"

Kallonshi Arshad ke yi ganin yanda ya sake toshe kunne ya ci gaba da danna wayarshi, Ya ce ma Nabeela "wai shi wannan har yanzu bai daina wannan banzar ɗabi'ar ba?"

Nabeela ta kalli Jafar da hankalinshi ba ya ma kansu, ta ɗaga kai ta ce "haka yake kullum"

"To Allah ya kyauta....sauko ki zuba mun abinci"

"Wai har yanzu ba ka ci abinci ba?"

"To ba ta bani ba" ya faɗa yana kallon Hajjo da ta wani rufe ido kamar mai bacci, yana dariya

Dariya ita ma tayi, dan ta san tana jin su, tayi shiru ne kawai dan yanda suka mayar da hankalinsu wurin Arshad suka kyale ta

Fried spaghettin ta zuba mishi kamar yanda yace, anjima sai ya ci tuwon, sai fura da ta zuba mishi, sannan ya sa ta zuba musu abunda suke son ci, Jafar kunun aya kawai ya sha, su kuma suka ci gaba da bidirinsu

Meerah da Nabeela suka kwashe kayan bayan sun gama cin abincin, sannan suka dawo suka zauna, ya ba su tsarabar da ya zo musu da shi

Sai da aka fara kiran sallar magrib, sannan kowa ya wuce wurin sallah, su na dawowa Jafar ya wuce, Arshad kuma ya kwashe su cikin motarshi suka wuce gidan Anty Fati, duk yanda ya so Hajjo ta biyo su, ƙi tayi ta ce sai ya dawo dai


A palour suka tarar da Anty Fati, zaune tana kallo

"Aaaa, maraba da mutanen Kaduna"

Yana murmushi ya zauna kusa da ita, ya ce "Anty ina wuni"

"Lafiya ƙalau ɗan Anty, ka zo lafiya?"

"Lafiya ƙalau....Anty ina Babban Yaya?"

Muryar Nabeel suka ji daga bakin ƙofar palour yana shigowa "ka ga Mr.AAJ, sardaunan samarin arewa"

Miƙewa Arshad yayi, suka yi musabaha sannan suka rungume juna suna dariya

"Wannan kirarin duk ni kaɗai Babban Yaya?"

"Ai ka wuce hakan ma"

"To na gode"

Suka zauna kan two seater, Nabeel ya ce"saukar yaushe? Ni ɗazu Umma ke gaya mun wai kana hanya"

"Wallahi kuwa, da yamman nan na iso"

"To ya su Ammi, ina su Yasmin?"

"Lafiya ƙalau, su na gaishe ku"

"Muna amsawa"

Nan dai suka yi ta hira har sai da suka yi sallar isha'i suka dawo, sannan Arshad ya duba lokaci, ƙarfe tara, ya ce "Anty wai sai yaushe Abba zai dawo ne?"

"Yau su na da meeting ƙarfe takwas da rabi, ina tunanin ba su gama ba"

"Tab,ba dawowan yanzu ba ne kenan, kuma Hajjo na san tana jira na, sai dai mu haɗu gobe"

"Lallai dai kam, gobe ma da rana in sha Allah za ka iya samunshi"

"To Allah ya kaimu"

Sallama suka yi dukansu, sannan ya wuce

Lokacin da ya dawo Hajjo kam ta ma yi bacci, sai kawai ya wuce fridge ɗauko kunun aya ya wuce ɗakinshi, dan ji yayi ba zai iya cin abinci ba, ba abunda yake buƙata yanzu sama da ya ji muryar Hanan cikin kunnenshi, dan tun da ya iso ba su sake yin magana ba

Wanka ya fara yi, yayi alwala sannan ya sa kayan bacci, ya zauna ya kira ta, kusan minti arba'in suka yi suna waya, sannan suka kwanta

*******************

Tun da safe, Hajiya Karime da Farha suka shirya suka nufi gidan malam domin jin inda aka kwana

"Tabbas yaron nan yayi tafiya ne dan ya samu gyara yanda zai auri Hanan"

Farha ta ce "dama na faɗa, to yanzu Malam ya za'a yi kenan?"

"Ai ni nace ku kwantar da hankalinku, ban tab'a yin aiki ba tare da na samu nasarar wannan aikin ba, nayi muku alƙawari sai na raba shi da ita, ba zai tab'a auren ta ba"

Hajiya Karime ta ce "na yarda da aikinka Malam, mun ba ka wuƙa da nama, kar ka bamu kunya"

"Ba ki da matsala Hajiya"

"Yawwa" ta buɗe jakarta ta ciro kuɗi ta ba shi sannan suka fita daga gidan

********************

"Hanan ina so ne za ki raka ni company ɗin AAJ" cewar MK dake waya da Hanan

"Ayya, ai baya nan, yayi tafiya" inji Hanan

"Tafiya kuma? Lafiya?"

"Lafiya ƙalau"

"To ba damuwa, idan ya dawo sai mu haɗu ɗin"

"To shikenan"

"Yawwa, gobe kiyi ƙoƙarin fitowa da wuri, akwai aikin da zan sa ki"

"In sha Allah zan fito da wuri"

"Aha, sai anjima"

Kashe wayar suka yi, Hanan ta ce "yau kuma aikin ta kaina ya biyo kenan!"

Yuhanees dake gefenta, ta ce "ba wani ta kanki ya biyo, dan kawai ku ƙara shiryawa ne"

"Hmm, da alama kam, dan bai ta'a sa ni wani aikin ba bayan wanda nake yi"

"Ke dai ki kula, Allah ya kyauta"

"To ameen......kiyi sauri ni dai ki gama wannan kwalliyan na ki, mu je mu dawo da wuri"

"Ni wallahi dan kin takura mun ne, amma Allah ya gani ban so zuwa wurin bikin nan ba"

"Na dai ji, ai ba'a biye ma halin mutum"

"To malama, ni dai tashi mu tafi" ta miƙe ta ɗauki mayafinta suka fito

********************

Abba ne zaune a palournshi, Arshad kuma na zaune ƙasa, kusa da ƙafarshi

Abba ya ce "ya gajiya Arshad?"

"Alhamdulillahi, ya aiki?"

"Alhamdulillahi, jiya Antynka ta ce ka jima kana jira na, muna can muna meeting ne"

"Haka ta gaya mun ai"

Murmushi Abba yayi, ya ɗan nisa, sannan ya ce "yawwa, ina jinka, gaya mun ya maganar da muka fara da kai?"

"To Abba, dama kamar yanda na gaya maka, akwai wacce nake so Hanan, to sai kuma ita wannan Farha ɗin, Ammi ke so in aure ta, sai dai wallahi Abba bana sonta ko kaɗan"

"Arshad ban tari hanzarinka ba, amma abunda nake son ji shi ne, dalilin da ya sa baka sonta"

Shiru Arshad ya ɗan yi, sannan ya ce "Abba, ka ga dai ba ta da kamun kai, bata da natsuwa, ga rashin tarbiyya.....ni dai kawai Abba ba ta mun ba"

Sauke ajiyar zuciya Abba yayi, ya ce "Arshad, wane irin rashin natsuwa take da shi? Tana bin maza ne? Ko kuma ya ya?"

"Abba gaskiya bana ce ba, dan banda tabbas, amma dai wallahi...."

"Dakata da rantsuwar haka, Arshad! Zanyi bincike akanta sosai, idan har ban samu wata matsala a wurinta ba, to sai dai kayi haƙuri ka bi abunda mahaifiyarka ta ke so"

Ɗagowa yayi da sauri ya kalle shi, ya ce "Abba kana nufin in aure ta?"

"Eh Arshad"

"To Hanan kuma fa? Kuma na gaya maka bana son Farha..."

"Arshad, ka kwantar da hankalinka ka ji bayani na, idan Farha ba ta da wata matsala, to za ka aure ta dan ka farantawa mahaifiyarka, kar ka manta idan ka sa mahaifiyarka farinciki, to zaka samu lada, sannan kuma zata iya yiwuwa idan ka bi umarninta, ya zame maka alkhairi nan gaba, dan sannu a hankali Allah zai iya sa maka sonta. Sai kuma maganar ita Hanan ɗin, ƴar asalin ina ce? Su waye iyayenta?"

Fuskar nan ba annuri, ya ce "nima ban sani ba, amma dai na san ba ƴan asalin Kaduna ba ne, kuma mahaifinta ya rasu"

"To ba damuwa, ita ma zanyi binciken, idan bata da wata matsala, sai ita Amminku ɗin tayi haƙuri ka haɗa su su biyu"

"Amma Abba ni mijin mace ɗaya ne, bani da ra'ayin mata biyu"

"Allah kuma ya halatta maka auren har huɗu, kuma ina da tabbacin in dai ka aure su, za ka iya kwatanta adalci ai"

"Abba ni......"

Ɗaga mishi hannun da Abba yayi ne ya sa shi yin shiru

"Iya adalcin da zan iya yi kenan a wannan maganar, dan ina maka kallon da nake ma Nabeel ne, fatana Allah ya maka zab'in da ya fi alkhairi"

Shiru yayi bai ce komai ba rai a b'ace, sai kuma ya tashi ya fita ba tare da ya mishi magana ba, shi ma Abba rakashi yayi da ido har ya fita, sai ya girgiza kai kawai ya ce "Allah ya kyauta"



Tunda Arshad ya fita, bai tsaya ko ina ba sai gidan Hajjo, dan ko Anty Fati bai tsaya yi ma sallama ba

Tura ƙofar palourn yayi ba tare da yin sallama ba, ya je kusa da Nabeel ya zauna, kasancewar su na palourn tare da Hajjo da Ja'afar

Hajjo ta ce "iskancin ya tashi ko? Ka shigo mana gida kamar gidan arna!"

Ko kallonta bai yi ba, kanshi na ƙasa, shi kaɗai yasan irin tunanin da yake yi

Nabeel ya kalle shi da kyau, ya dafa kafaɗarshi ya ce "me ya faru ne AAJ?"

Girgiza kai yayi ya sauke ajiyar zuciya, Nabeel ya ce "ka gaya mun mana, ya ku kayi da Abba?"

Ɗagowa yayi, a sanyaye ya ce "Ammi has ruin everything Big Bro(Ammi ta lalata komai BabbanYaya)"

"Meyasa ka ce haka?"

Duk yanda suka yi da Abba ba abunda bai gaya mishi ba, ya ƙara da cewa "ta ya kake tunanin zan iya auren mata biyu dan Allah?"

Hajjo tayi karaf ta karb'e zance da "to meye dan ka auri mata biyu? Baka isa auren ba ne ko me? Har kake wani b'ata rai haka"

Tsaki Arshad yayi dan bai ma da lokacinta, Nabeel ya ce "haba Hajjo, Arshad ɗin guda nawa ne da har za'a ce ya auri mata biyu? Da ma ace yana son su ne dukansu ɗin"

Arshad ya ce "ba ma zai yiwu in so mata biyu lokaci ɗaya ba, kuma da sunan aure, sai dai ɗaya ta haƙura, infact ma ni ba zan iya haɗa Hanan da wata ba wallahi"

Hajjo ta ce "toooo!!! Sannu Majnoon uban soyayya"

Murmushi Nabeel yayi, ya ce mishi "take it easy dear"

Ja'afar da ke saurarensu tun ɗazu ya ce "look Ya Arshad, i have an idea(ka ga Ya Arshad, ina da shawara)"

Kallonshi Arshad yayi da alamar ina jinka

"Ka ce baka san asalinsu ba ko? To kayi ƙoƙari kayi binciken asalinsu da kanka, idan har aka samu yanda ake so, kar ka damu da matsalar Farha, i know how to deal with, there's no way you can marry her, because i so much hate that lady, infact i don't trust her and her parents(na san ya da zanyi maganinta, ba yanda za'ayi ka aure ta, saboda na tsani yarinyar nan, kai ban ma yarda da ita ba ita da iyayenta)" ya ƙarasa zancen da turanci saboda baya son surutun Hajjo

Arshad ya ce "what will you do then?(me za kayi to?)"

"Just trust me, i will never let that marriage happen between you and that foolish girl ( ka yarda da ni, ba zan tab'a barin wannan auren tsakaninka da waccen wawuyar yarinyar ya faru ba)"

Hajjo dake ta harararsu ta ce "to munafukai, shi ne kuma koma yaren nasara ko? To ko me zaku ce dai duk yanda muka yanke hakan za'ayi, dan ba ku kuka haifi kanku ba"

Arshad ya ce "kanki ake ji dai, ni na shiga inyi wanka, dan ƙanina ya sa na ɗan samu natsuwa, dan na yarda da irin ƙwaƙwalwarshi"

"Kan Ruƙayya dai ake ji, ɗan rainin wayo mara kunya kawai"

"Gobe dai zan bar miki gidan ai sai kiyi ta masifar ke kaɗai" ya tashi kawai ya wuce ɗakinshi

Shi ma Nabeel tashi yayi, haka ma Jafar, suka yi mata sallama akan zasu wuce

"Dama ba wanda na gayyata" abunda kawai ta amsa musu da shikenan, a su kula ta ba dai suka fita..........










Manage this pls❤️



🥰UMMEETA🥰......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 24* 

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" abunda Hanan ta faɗa kenan a razane bayan farkawar da tayi daga bacci a firgice

Bin ɗakinta tayi da kallo, ta ga tabbas ita kaɗai ce a ciki kamar yanda ta saba kwana ita kaɗai

Sannan ta ɗan sauke ajiyar zuciya, tayi shiru tana sake tuna abunda ta ji da wata irin murya da ta kasa gane mace ce ko namiji

'Hanan!!! Tabbas soyayyarku ke da Arshad abun burgewa ce, duba da yanda kuke son juna tsakani da Allah, amma ina miki albishir da cewa ke ɗin ba za ki tab'a zama matarshi ba, dan haka ki cire shi a ranki tun wuri, sannan kuma ina so ki sani, wani al'amari zai iya kasancewa akanki ko akan Arshad kuma mummuna, ina nufin ɗaya daga cikinku zai ji rayuwa ta daina mai daɗi, har ma ya gwammaci mutuwarsa, sai dai bansan taya hakan zai faru ba, amma dai ku shirya.....Hahahaha" haka aka ƙarasa zancen da dariyar mugunta, mai firgitarwa

Wayarta ta ɗauka, zuciyarta na dukan uku-uku, ta shiga neman numbern da tayi saving da HEARTBEAT, ta daɗe tana ringing sannan ya ɗauka

"Hello" ya faɗa cikin muryar bacci

Ajiyar zuciya ta sauke da taji muryarshi, "hello" ita ma ta sake maimaitawa

"Lafiya dai Jasmine? Kin ga time ɗin da kika kira kuwa?" ya faɗa yana hamma yana ƙara murza idanunshi dake ta rufewa saboda bacci

Sai a lokacin ta tuna ma dare ne, wayarta ta duba, karfe 2:39am na dare, sai ta ɗan rufe baki "kayi haƙuri dan Allah, wallahi na manta ne"

Tashi yayi ya zauna, ya ce "ba mantawa kika yi Angel, a ruɗe kike ne lokacin da kika kira ni, ko ba haka ba?"

"Ya aka yi ka sani?"

"Na san lafiya ba zata sa ki kira ni cikin wannan daren ba, dole akwai matsala, kuma wannan matsalar ce tayi forcing ɗin zuciyarki ta kira ni ba tare da kin duba agogo ba, dan haka ki gaya mun menene, jikin Ummi ne?"

"Hmm, a'a"

"To mafarki kika yi?"

A hankali ta ce "eh"

Murmushi yayi ya ce "kin yi mafarkin na mutu ne ko kuma zan mutu gobe a hanya?"

Ji tayi gabanta ya faɗi, ta ce "meye haka kuma dan Allah?"

Dariya ta ba shi saboda yanayin yanda tayi maganar kamar zata yi kuka

"To i'm sorry (kiyi haƙuri)" ya faɗa yana dariya

Ƙaramin tsaki tayi, ta ce "sai da safe"

"Don't hang up please (kar ki katse dan Allah), na ce kiyi haƙuri wasa nake yi"

"Wasa da mutuwa?" ta faɗa tana b'ata rai

"To bazan sake ba your highness, kinji"

Shiru tayi ba ta ce mishi komai ba, ya sake ce wa "dan Allah kinji"

"Shikenan, naji"

"Yawwa, to gaya mun menene"

"Kawai mafarki nayi, amma ka bari sai ka dawo sannan zan gaya maka"

"Meyasa ba za ki gaya mun ba yanzu"

"Ka dai bari sai ka dawo, yanzu ka kwanta, dama muryarka nake son ji shiyasa na kira"

"To shikenan, lafiya ƙalau nake, kuma zan dawo lafiya in sha Allah, kinji ko!"

"Allah ya dawo da kai lafiya to"

"Ameen Hearty, matar AAJ" ya faɗa cikin daddaɗar murya

Ta ji daɗin abunda ya faɗa, sai dai ta tuna da mafarkinta, a ranta ta ce 'ina fatan hakan Chubby', a zahiri kuma ta ce 

"Sai da safe dear"

"Bye" sai suka kashe wayar tare

Ta daɗe a zaune, sannan dai tayi addu'a ta kwanta, shi kuma sai da yayi nafila sannan ya sake kwantawa

********************

Da safe bayan su Yasmin sun gama shirin makaranta sun yi break-fast, Ammi ma ta shirya cikin swiss less ɗinta mai kyau, ta sa gyale 3 in 1, sai suka fito tare

Da gudu driver ya zo, ya durƙusa ya gaida Ammi, ya tashi zai buɗe mata mota, sai ta ce

"Bani mukullin kawai, zan kai su da kai na dan akwai wurin da nake son zuwa"

"To Hajiya, Allah ya kiyaye" ya faɗa cikin girmamawa yana bata mukullin

Buɗe motar suka yi suka shiga, sannan ta ja su suka wuce. A bakin gate ɗin makarantar ta ajiye su, sannan ta wuce, bata tsaya ko ina ba sai ƙofar gidan Hajiya Karime, aka buɗe mata gate ta shiga

A palour ta taradda Hajiyar, ta zauna suka gaisa

Ammi ta ce "ina Farha? Ko bata tashi daga baccin ba?"

Hajiya Karime ta ce "ta tashi har ma ta fita ai"

"Ok....Hajiya kin ga na miki zuwan safe ko?"

"Nima dai shi ne nake ta mamaki ai, Allah ya sa lafiya"

"Lafiya ba amma lau ba, dan wallahi Hajiya na kasa natsuwa akan yaron nan, kin san yau zai dawo, to ban san da wane irin zance zai dawo ba, ina fargaba kar su amince mishi da auren Hanan fa"

Ajiyar zuciya Hajiya Karime tayi haɗi da yin murmushi, ta ce "yanzu kina nufin ɗan wannan abun ne ya taso ki da safe haka?....Hmm to yanzu ya kike so ayi?"

Gyara zama tayi, ta ce "yawwa, ina maganar Malamin da kika ce ya tabbatar miki zai iya raba mana su! To ya ake ciki?"

"Shekaran jiya mun tafi, kuma ya ce aiki na tafiya yanda ya kamata"

"To alhamdulillahi, amma dai ina so ki tashi yanzu mu tafi sai mu ji"

Dariya tayi ta ce "kin dai tsorata da maganar zuwa  Adamawan nan da yayi"

"Bari kawai, ni na san ba zuwan Allah da Annabi ba ne, kin san yanda na ƙi jinin talaka wallahi, ke ni da ya aure ta gwara ya sake shekaru biyar ba aure"

"Har biyar! Kar fa ayi abun kunya" Hajiya Karime ta faɗa tana ƴar dariya

"Yo da ya ɗauko mun tsiya kuma fa?"

"Allah dai ya kyauta, amma ba zai aure ta ba kuma ba zai ƙara ko da shekara ɗaya ba tare da ya auri Farha ba"

"Allah ya sa" cewar Ammi

"Ameen, amma yanzu kin ga 8:32am, mu bari zuwa 10 sai mu tafi"

"To ba damuwa"

Sai suka ƙara zama suka ci gaba da tattaunawa

********************

Duk wani shirin tafiya Arshad ya gama shi, ya je gidan Anty Fati su yi sallama da ita da sauran ƙannenshi kafin su wuce makaranta, dan fitar safe yayi dan ya same su gida

Ya gama sallama da su sai ya wuce palourn Abba, kamar yanda Anty Fati ta gaya mishi cewa yana son ganinshi, kasancewar sun gaisa, sai kawai Abba ya fara maganarshi dan kar ya tsayar da shi

"Arshad, na san abunda na gaya maka jiya bai maka daɗi ba kasantuwar saboda wannan maganar ce ya sa ka zo garin nan, ko ba haka ba?"

Ɗaga mishi kai Arshad yayi, sai ya ci gaba da cewa "to ina so ka sa ma zuciyarka tawakkali da haƙuri, na san kana da su, amma akan wannan yarinyar sai naga kana nema ka cire su a ranka, to ka sani, duk jajircewar da za kayi, matuƙar ba matarka ba ce, ba za ka tab'a samunta ba, idan kuma matarka ce, ko ana muzuru ana shaho sai ka aure ta, kuma ni kai na zan so ace ka auri yarinyar da kake so ɗin"

Kallonshi Arshad yayi ya ce "to Abba idan haka ne, ka taimaka mun dan Allah kar ka bari in rasa Hanan, wallahi Abba ina sonta, bana jin zan amfana a duniyar nan idan har ba same ta ba"

Shiru Abba yayi saboda yayi mamakin yanda Arshad ya iya kallonshi ya ce wai yana son wata, duk da ba shi bane mahaifinshi, amma ya san Arshad na da kunya, kuma bai yi tunanin zai iya gaya mishi haka ba, sai ya ce "Arshad kayi haƙuri, ka riƙa yin addu'a ba abunda zai same ka ko da ace ka rasata, amma ba na fatan haka, ka je kawai in sha Allah nan da sati ɗaya zan aiko wani tare da Jafar dan ayi bincike ƙwaƙwara akansu"

"To Abba, nagode sosai, Allah ya ƙara lafiya"

"Ameen, Allah ya kai ka lafiya"

"Ameen, na bar ka lafiya"

Sai ya tashi ya fita ya bar Abba zaune yana tunani

A bakin motarshi ya taradda Jafar, dan shi kaɗai ne bai fita ba sai anjima

Jafar ya ce "ya dai Ya Arshad?"

"Hmm, maganar ɗaya ce dai, wai za'ayi bincike, amma ka san wai hadda kai cikin masu binciken"

Gyara tsayuwarsa Jafar yayi ya ce "da gaske Ya Arshad?"

"Eh, amma meye abun jin daɗi haka?"

"Ai dole ne mu ji daɗi dan har da kai, ba dai da ni za'a yi bincike ba! To ka sa ma ranka ba za ka tab'a auren Farha ba, dan wallahi binciken ƙwaƙwaf zan mata"

Murmushi Arshad yayi ya ce "Jafar idan baka son mutum ya shiga uku wallahi, mutum ya ji tsoron Allah ya ji tsoron miskilin mutum"

Wani murmushin gefen baki Jafar yayi, wanda duk wanda ya gani ya san na mugunta ne, ya ce "Allah dai ya kai ka lafiya Ya Arshad, sai mu zo"

"To shikenan, Ameen", suka rungume juna sannan Arshad ya shiga mota shi kuma Jafar ya wuce part ɗin su

Sai da ya ƙara komawa gidan Hajjo ya ɗauki kayanshi, suka sake yin sallama bayan sun yi halinsu kamar yanda suka saba, sannan ta rako shi har bakin mota, tana jin ba daɗi, har da ɗan hawayenta

Dariya ma ta ba shi, ya ce "Haba matas, kar ki damu, zan sake dawowa ai nan ba da daɗewa ba, sai dai ni da kishiyarki za mu zo dan ta gaishe ki"

Tana share hawayen ta ce "ai ba zan bari ma sai ka zo ba, ni da kaina zan zo ganin wannan kishiyar ta wa"

Mutmushi yayi, ya ce "to Allah ya kawo mana ke ƙalau"

"Ameen, A sauka lafiya"

Ya shiga mota ya wuce sannan ta koma cikin gida

********************

Zaune yake kan kujerarshi ta aiki yana ta aiki cikin laptop ɗin shi, lokacin da Gboy ya shigo tare da wani mutum

Tashi yayi suka yi musabaha da mutumin sannan ya ba shi damar zama, suka zauna tare, Gboy ma ya ja ɗayar kujeran ya zauna

"Alhaji Zayyad manya ƙasa" cewar MK yana dariya

Shi ma Zayyad ɗin dariya yayi, ya ce "idan ba ku nan kenan MK"

Dariya yayi ya ce "haka dai ka faɗa"

"Haka ne ma"

"To shikenan, yanzu dai taimakonka nake nema shiyasa na buƙaci ganinka"

"Ai ka fi ƙarfin ka nemi taimako, ka gaya mun kawai me kake so"

"Zayyad, harka ce ta samu, waɗannan kayayyakin ne nake so za'a shigo mun da su"

"Kai kuma?" Zayyad ya faɗa da mamaki

"Ƙwarai kuwa, sai dai ba da sunan company ɗinnan ba"

"To da wane company kenan?"

"Zan gaya maka dan cikin sirri nake so ayi, kamar yanda muka tab'a yi a Katsina"

Murmushin mugunta Zayyad yayi, ya ce "kenan dai akwai wanda ya shiga gonarka"

"Ƙwarai kuwa, kuma fita zai mishi wuya ba"

Dariya Zayyad yayi ya ce "wallahi kai dai mugu ne, waye wannan ɗin"

"Abokin mugu ma mugu ne, dan haka ni da kai muna tare"

"Amma ai kai ne babba, yanzu dai duk ba wannan ba, wanene wannan da fitina ke shirin ƙwanƙwasa mishi ƙofa?"

MK ya buɗe baki zai yi magana, sai dai bai samu furta zancenshi ba, aka ƙwanƙwasa ƙofar office ɗin, kallon ƙofar suka yi a tare, sannan MK ya ce "come in (shigo)"

Hanan ce ta turo ƙofar ta shigo, sai da ta kai tsakiyar office ɗin sannan ta tsaya, ta gaida su, suka amsa mata, MK ya ce ta ƙaraso.Kusa da table ɗinshi ta tsaya daga gefe

Kanta a ƙasa, ta ce "Yallab'ai gani, ina fatan ban makara ba"

Agogo ya duba, sannan ya ce "a'a Hanan, kin zo a lokacin da ya dace, nagode da cika alƙawari"

Murmushi kawai tayi, sai ya ci gaba da cewa "Hanan dama aikin da nace miki zan sa ki, ba wani babban aiki bane, kin ga wannan" ya faɗa yana nuna Zayyad, wanda tun lokacin da ta shigo har yanzu idanunshi na kanta, har ta gaji da wannan mayen kallon

Ba tare da ta kalle shi ba, ta ce "eh na ganshi"

"Sunanshi Zayyad Abdallah, ƙwararre ne wurin iya shigo da kayayyaki masu ƙarko da inganci daga ko wace ƙasa, ya kawo mun wani contract ne (kwangila) dan inyi signing, sai dai na akwai waɗanda aka kawo mun kusan guda uku, idan na haɗa da na shi za su mun yawa, to shi ne yake so yayi da wani babban company, kuma na san ba wani babban company a garin nan sama da na AAJ"

Kallonshi take cikin rashin fahimtar inda zancen na shi ya dosa, ta ce "sai dai yallab'ai ban san me kake so ni inyi ba, ai irin wannan ba aiki na bane"

"Tabbas ba aikinki bane, amma anan ya zama aikinki, kin san na san AAJ na cike da haushi na, duk da kince kin ba shi haƙuri, amma ina shakkar tunkararsa, sai nake ganin kamar ba zai yarda da ni ba......abunda dai nake so ki mun shi ne, ina so kiyi mana jagora izuwa wurin AAJ dan in ƙara ba shi haƙuri sannan kuma in gabatar mishi da contract ɗin"

Shiru tayi tana nazari, sannan ta ce "amma taya ni zan maka jagora, bayan ni ba secretary ɗinka bace?"

"Za ki wakilce ta"

"To amma....."

"Dan Allah Hanan, kar ki manta kince za ki ɗauke ni tamkar ɗan uwanki, kenan ba za ki iya taimaka ma ɗan uwanki ba?"

"A'a ba haka nake nufi ba......shikenan dai, zan raka ka, amma a matsayin ma'aikata zamu tafi ba wai a matsayin wacce ke da alaƙa da AAJ ba"

"Ba damuwa, godiya nake, gobe sai mu tafi ko?"

"Allah ya kaimu"

"Ameen, za ki iya tafiya"

Haka ta ja jiki, ba ƙwari ta fita, dan tunani ne ke zuwa kanta kala-kala

Tana fita MK yayi murmushi, ya ce ma Zayyad "kana tambaya akan wanda fitina ke tunkara ko?"

Zayyad ya ɗaga kai, MK ya ce "to AAJ ne da wannan yarinyar, sai dai kowa da irin na shi fitinar"

Zayyad ya ce "AAJ dai!?"

"Ƙwarai kuwa"

"Kana nufin waccen asarar da ya saka shekarar da ta wuce shi ne har yanzu baka ɗauki mataki ba?"

"Eh, amma yanzu hukuncin biyu ne, dana asarar da ya sa ni da kuma na tozarta ni da yayi gaban ma'aikata na"

"Lallai ashe ya ɗebo ruwan dafa kansa......amma ni fa wannan yarinyar kar ka mata komai, ka bar mun ita mana"

"Ta maka kenan?"

"Sosai ma kuwa, ai irinsu ake kira hot ladies"

Dariya MK yayi, ya ce "ai shikenan, kayi yanda kake son yi da ita, dama budurwarshi ce, kuma ya ce wai she's his own happiness (ita ce farincikinshi) ina so ka lalata mishi wannan farincikin"

"Ba ka da matsala MK, ka san ni, ba ni da dama ai" ya ƙarasa yana wani murmushi

"That's good (yayi kyau)......Gboy, ka raka Zayyad, daga nan sai ka ƙarasa mishi bayanin da ya rage"

Gboy dake zaune tun ɗazu bai ce komai ba sai faman gyara wasu takardu yake yi, ya ce "to Yallab'ai"

Suka tashi shi da Zayyad suka fita.MK yayi murmushi yana girgiza sannan ya ci gaba da aikinshi

********************

Ammi da Hajiya Karime ne zaune a gaban Malam yana ta jan carbi yana zane da ƙasar dake cikin tray

Sannan ya kalle su ya ce "Hajiya, wannan aikin an gama shi, domin tabbas naga ranar rabuwar Arshad da Hanan"

Fara'a fal a fuskokinsu, Ammi ta ce "alhamdulillahi, ɗa na zai rabu da tsiya, sai dai a bi wani bokan"

Hajiya Karime ta ce "ƙwarai kuwa Hajiya"

Malam ya ce "sai dai kuma, na fahimci ɗanku yana da tarin maƙiya, ma su son ganin bayanshi"

Hajiya Karime ta ce "ai dama duk inda mai arziki yake yana da maƙiya, daga cikin maƙiyansa ma ai hadda wannan matsiyaciyar Hanan ɗin"

Ammi ta ce "tabbas, kuma in Allah ya yarda ya fi ƙarfinsu wallahi"

Malam ya ce "to shikenan, za ku iya tafiya ai, ina da baƙi waje" ya faɗa dan ya fahimci duk yanda zai musu bayani ba fahimtarshi za suyi ba

Ammi ta ciro bandir ɗaya na ƴan dubu-dubu guda ɗaya ta ba shi sannan suka fita su na ta murnar samun wannan labari

********************
Sai da yamma sannan Arshad ya iso gida, yana ajiye motar ya wuce part ɗinshi, wanka yayi, yayi sallah, sannan ya dawo main palour

Yana shiga, Yasmin da Yasna suka zo da gudu suka rungume shi su na ta jin daɗi

Ammi dake zaune ta ce "to kuyi sauri ku yadda shi, mutum ya dawo da gajiya ku wani riƙe shi haka"

Yasmin ta ce "ai Big Bross ɗina jarumi ne, ba zai faɗi ba, ko?" ta ƙarasa tana kallon Arshad

Murmushi yake tayi, ya ce "sosai ma kuwa, ba kiyi ƙarya ba ta Big Bross"

Suka yi dariya, Ammi ta ce "au haka ma ka ce"

Yasna ta ce "ai gaskiya ne Ammi"

"To ai shikenan, sai ku bar shi ya ci abinci"

Suka yi dariya, sannan suka wuce dinning area dan haɗa mishi abinci, shi kuma ya ƙaraso wurin Ammi suka gaisa tana tambayar su Hajjo

Yasna ta zo ta ce "Sweet Bro mu tafi ga abincin can"

"Yasna ba yanzu ba, sai anjima"

Ammi ta ce "haba! Tun ɗazu fa nake bibiyarsu su ci abinci suka ce sai ka dawo ku ci tare"

"Oh! To kuyi haƙuri, mu tafi"

Ya ja su suka je suka ci abincin, yana basu labarin su Nabeela da Hajjo

Yasmin ta ce "wallahi nayi kewarsu"

Arshad ya ce "ai zuwa next week in sha Allah Jafar na nan zuwa"

Yasna ta zaro ido, ta ce "me!!??"

Dariya Arshad yayi sosai, dan ya san Yasna ba ta son abunda zai haɗa ta inuwa ɗaya da Jafar, saboda tsoronshi take ji, ya ce "eh, kuma sati biyu ma zaiyi"

Kamar za tayi kuka, ta ce "shikenan watan kuka na ya tsaya"

Arshad ya ce "ai dan ba kya jin magana ne yasa ba kwa shiri, amma kin ga ai Yasmin ba ruwanshi da ita"

"Ina jin magana fa, kawai dai baya so na ne"

"Wa ya gaya miki! Yana sonki sosai Sweetie"

Turo baki tayi kawai alamar dai ba ta yarda ba, Ammi da zuwanta kenan taji ana maganar Jafar, sai ta zauna, ta ce

"Zuwa zai yi ne?"

"Eh Ammi, amma sai next week" cewar Arshad

"Lallai, ashe muna da babban baƙo a gidan nan, ni ya zo ma ya mun maganin wannan fitinanniyar kafin ya koma"

Yasmin da Arshad suka sa dariya, Yasna kuwa ta shagwab'e ta ce "Ammi har da ke? Autarki ce fa"

"Ayya yi haƙuri, na ɗauka ai Yasmin ce, yi haƙuri autar Ammi"

Sai ta jawo ta ta rungume kasancewar su na kusa, sai murmushi take tayi, Arshad kuwa in banda aikin kallon Ammi ba abunda yake yi, ya gaza haƙuri, sai da ya ce 

"Ammi tun da na dawo na fahimci kamar kina farinciki sosai, na kwana biyu ban ga fara'arki haka ba"

Yasna ta ɗaga daga jikin Ammi, ta ce "wallahi nima yau mamakin Ammi nake tayi, Ammi ki gaya mana menene?"

Ƙara faɗaɗa murmushinta tayi ta ce "ina farinciki ne saboda wani fitina dake tunkaro gidan nan, na kau da shi"

Yasmin ta ce "fitina kuma?"

Ɗaga mata kai tayi, Arshad ya ce "wace irin fitina kuma Ammi?"

"Kar ku ɗaga hankalinku, zan gaya muku amma ba yanzu ba, sai na tabbatar da mun rabu da fitinar"

"To shikenan, Allah ya tsare mu daga wannan fitinar da sauran fitintinu na duniya da lahira" cewar Arshad

Suka haɗa baki wurin amsa mishi da "ameen"

Ammi kuwa a ranta cewa tayi 'na ji daɗin wannan addu'ar da kayi da kanka, kuma in sha Allah wannan fitinar Hanan, sai ta rabu da kai kwanan nan'...........









MUJE ZUWA DAI, AI YANZU AKA FARA🤩




🥰UMMEETA🥰......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 25* 

Bayan sallar magrib, Arshad ya tafi gidansu Sajjad, a harabar gidan suka haɗu, Sajjad ɗin na ƙoƙarin shiga mota, sai ya rufe motar ya fasa shiga har Arshad ya gama parking ya fito

Rungume juna suka yi cikin murna sai ka ce waɗanda suka yi wata ba su haɗu ba, Sajjad ya ce
"Shi ne ka zo ba ka jira ni ba, dan fitowar nan da nayi wurinka za ni"

Arshad yayi murmushi ya ce "yau fa Monday, na san ka gaji da aikin company shiyasa kawai na ce zanzo"

"To mu shiga daga ciki" ya faɗa yana murmushi

Palourn gidan suka shiga, Hajiya(mahaifiyar Sajjad) tana shirya abinci kan dinning, ganinsu da tayi ne ya sa ta sauko tsakiyar parlourn da fara'arta

Ta ce "mutanen Adamawa, an dawo lafiya?"

Sai da suka ƙaraso cikin parlourn suka zauna, sannan Arshad ya ce "lafiya ƙalau Hajiya, ya gida"

"Lafiya ƙalau" ta amsa bayan ta zauna

Ya ce "ina Inti da Mujaheed?"

"Su na gidan Zainab, mijinta yayi tafiya, shi ne suke taya ta kwana"

"Allah sarki"

Daga nan suka yi ta hira su uku, har aka yi isha'i, Alhaji (mahaifinshi) ya dawo, sai suka wuce masallaci, su na dawowa suka wuce part ɗin Sajjad su ka ci gaba da hirarsu

Sajjad ya ce "yawwa Super, na ma manta ban gaya maka ba, ɗazu Mr Joseph ya zo tare da manager ɗinsu, sai dai na gaya musu su dawo gobe"

"Eh Directornsu ya kira ni ina hanya, mun yi magana, ya turo mun da waɗancan kuɗin, yanzu kayan da suke so ɗin ne za'a basu idan sun zo goben"

"Da yawa suke so fa"

"Kayan 5billions ne ya ce"

"Amma kana ganin ba matsala idan aka basu? Ka san fa yanda muka yi da su a waɗannan fa!"

"Zamu yi yarjejeniya da su gobe ɗin"

"To a damuwa, Allah ya kaimu lafiya"

"Ameen, bari in wuce, ka ga har ƙarfe goma ta wuce"

"To shikenan, nagode sai mun haɗu goben"

"Yawwa"

Har bakin motarshi ya raka shi sannan ya koma cikin gida

Sai kusan goma da rabi sannan Arshad ya isa gida, part ɗinshi ya wuce dan ya san sunyi bacci, shi ma yana shiga wanka yayi, yayi alwala yayi shafa'i da wutri sannan ya kwanta ya tura ma Hanan  night message mai daɗi dan yana tunanin tayi bacci ita ma, yana gama turawa ya kwanta.

********************
Washe gari da safe Arshad na office ɗin shi tare da Khairat, tana mishi bayanin abubuwan da akayi da ba ya nan, Sajjad ya shigo tare da su Mr Joseph su uku kasancewar ƙofar a buɗe take, umurtarsu yayi da su zauna ka cushions ɗin, sannan ya sallami Khairat shi kuma ya zo wurinsu ya zauna

Sai da suka gaisa sannan suka fara gabatar da abunda ya kawo su, sunyi yarjejeniya akan nan da wata huɗu za su biya shi kuɗin, suka yi signing sannan ya umurci Sajjad da yasa a ba su kayan

Bai jira su ba ya tashi ya koma kan kujerarshi ta aiki, su ma suka tashi suka fita, a bakin ƙofar office ɗin suka haɗu da su MK za su shiga, Mr Joseph yayi ma MK murmushi, shi ma MK murmushin ya mishi a fakaice kamar yanda ya mishi

MK, Zayyad, Gboy da Hanan suka ƙarasa cikin office ɗin yayin da su Sajjad suka fita bayan ya gama kallon MK cikin mamaki

AAJ bin su yake da ido, fuska a turnuƙe kamar bai tab'a jin kalmar fara'a ba a rayuwarshi, har suka ƙaraso bakin table ɗinshi

Gboy da Hanan suka tsaya daga bayan kujerun da ke wurin, Zayyad da MK kuma suka ja kujerun da niyar zama

A tsawace AAJ ya ce "are you insane?(ba ku da hankali ne?)" yana bin su da mugun kallo, su kuma suka yi tsaye su na kallonshi

MK ya ce "what happen?(meya faru?), kayi haƙuri wurinka muka zo kuma da alkhairi"

Ƙara haɗe rai yayi, ya ce "da ku ka zo wurina sai kuma akace kar ku nemi izinina kafin ku shigo? Har kuke ƙoƙarin zama?"

Zayyad ya ce "amma ai munyi magana da secretary ɗinka"

"Ita ce AAJ ɗin ko kuma ni?"

Kallon-kallo MK da Zayyad suka shiga yi, Gboy ya ce "kai ne yallab'ai, amma kayi haƙuri tunda mun shigo"

Wani kallo ya aika ma Gboy ya ce "ba da kai nake magana ba, da ubangidanka nake yi"

MK ya ce "to kayi haƙuri, ko dan albarkacin Hanan, wani aikine ya kawo mu"

Ko kallon gefen Hanan baiyi ba, ya ce "aiki ka zo yi nan ko nuna mun mace? To ban ganta ba, ku koma ku nemi izini sannan ku shigo"

Wannan karon hadda Hanan sai da ta kalle shi cikin mamaki, dan ji take yi  bata tab'a jin tana tsoronshi ba sai yau, dan kamar ba Arshad ɗinta da ta sani ba

MK ya ce "amma ai......."

A tsawace ya katse shi da "ai me?? Dallah Malam ku fita idan na baku izini sai ku shigo, ko kuma ku koma inda kuka fito"

MK zai yi magana, Zayyad ya dafa shi yana girgiza kai, sai suka fita, MK sai huci yake

Gboy yayi ma Khairat magana, sannan ta shiga office ɗin AAJ ta barsu a nan

Zayyad ya raɗa ma MK cewar "ka kwantar da hankalinka mutumina, wannan fushin ba naka bane, ka barshi ya shigo hannu kawai, zai yi bayani, kyale shi yayi iskanci da ya ga dama yanzu, lokacinshi ne, muma namu na zuwa" daga jin haka sai kawai MK yayi murmushi, ya ji ya manta da wulakancin AAJ

Khairat ce ta fito sannan ta ba su izinin shiga, sai da suka sake neman izininshi sannan suka zauna suka gaisa

Haƙuri MK ya fara ba shi akan abunda ya faru kwanan baya, sannan ya gabatar mishi da Zayyad da kuma ƙudirinsa

Shiru AAJ yayi, ya ce "i can't accept this contract (ba zan iya yarda da wannan kwangilar ba)"

Zayyad ya ce "meyasa?"

"Sabida ban tab'a harƙalla da kai ba"

"Amma ya kamata ka yarda dani, nima ina so na shiga jerin waɗanda suke harka da kai, kana burge ni yanda kake tafiyar da kasuwancinka"

"Duk da haka dai, zanyi tunani"

MK ne ya kalli Hanan da alamar ta sa baki

Cikin fargaba ta ce "dan Allah ka yarda yallab'ai, muna son yin harka da company ɗin nan shiyasa takanas muka zo ba muyi aike ba, dan Allah"

Kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke ido, ya ce "ban amince ba, nace zanyi tunani akai"

Ta ce "tunanin m......"

Katse ta yayi da "ban son takura, nace  zan duba, dan haka you can leave pls(zaku iya tafiya dan Allah) akwai aiki a gabana" ya faɗa rai a b'ace, sai dai a zuciyarshi yana jin ba daɗi saboda yanayin da yake mata magana

MK ya ce "shikenan, mun ba ka lokacin, mun gode"

Sai suka tashi suka wuce, Hanan jiki a sanyaye dan tana ji kamar ta ba shi haushi, shi ma binta yake da ido har suka fita, sannan ya nisa ya ci gaba da aikinshi


Kusan minti talatin da wucewarsu MK sannan Sajjad ya shigo ya zauna

Ya ce "Man me MK ya zo yi nan kuma na ganshi tare da Hanan, ko wani abu ne"

Sai da ya jingina bayanshi jiki kujerarshi sannan ya ce "ba wani abu bane, wai abokinshi ya kawo mun yana so muyi aiki tare"

"Sai ka ce me? Ka amince?"

Murmushi yayi, ya ce "ban amince ba, sai dai ina tunanin amincewa saboda Hanan"

"Ban gane saboda Hanan ba!" Sajjad ya faɗa da alamun ranshi ya so ya fara b'aci

"Eh mana, ko kana da matsala da hakan ne?"

"Matsala ma kuwa, wannan fa maganar aikinka akeyi ba wai zancen soyayya ba"

"To me kake nufi?"

"Ni kwata-kwata ban yarda da wannan kwangilar ta MK ba, kar ka amince, dan banson abunda za ka dawo kana dana sani"

Murmushi AAJ yayi, ya ce "ba maganar dana sani, na tabbata da akwai matsala, Hanan ba za ta so in amince ba, yanzu ma na jinkirta ne dan ina so sai nayi magana da ita"

Tsakin takaicin wannan magana ta AAJ Sajjad yayi, sannan ya ce "ta ya Hanan zata iya gane abunda ke cikin ranshi!?"

"Calm down Man, na ga ranka ya b'aci, na san ba ka yarda da MK ba, nima haka, amma in sha Allah ba abunda zai iya yi"

"Matsala ta da kai na ci, duk abunda zan gaya maka na san ba ganewa za kayi ba tunda har ka yarda da Hanan, amma ba komai, Allah ya tabbatar mana da alkhairi"

"Ameen...haka ya kamata ka ce kawai My Man, just relax"

Ajiyar zuciya Sajjad yayi, sannan ya mishi sallama kan cewa yana da aikin da zaiyi a office, sai ya fita ya barshi shi ma ya ci gaba da na shi aikin

********************

Hanan na komawa gida bayan la'asar, tayi wanka tayi sallah ta ci abinci, sannan ta ce ma Ummi zata tafi wurin Yuhanees

A tsakar gida ta taradda Yuhanees da Umma zaune suna gyara alayyahu, sai da suka gaisa da Umma sannan suka shiga palour da Yuhanees

Tsab ta karanto mata mafarkinta na jiya, ta ƙara da cewa "Rabin Rai mafarkin nan ya tsaya mun a rai wallahi, jikina na bani kamar da gaske ne rabuwa za muyi, kuma wallahi ina tsoron wannan ranar"

Yuhanees ta ce "kai Hayatee, ni wallahi har kin sa na ɗauka wani babban abu ne, mafarki ne fa"

"Hmm, Rabin Rai kenan, amma kin san wani lokacin mafarki na zama gaskiya ko?"

"Wani kika ce Hayatee, in sha Allah wannan ba komai ba ne, kawai dai dan kinsa maganar Amminshi ne a ranki ya sa kika fara wannan tunanin, amma ai kin ga da ba kiyi wannan mafarkin ba"

Shiru ta dan yi, sannan ta ce "kuma fa maganarki akwai kamshin gaskiya, tunda ance mutum na yawan mafarki ne akan abunda ya sa ma ranshi, sai dai gaskiya hankali na bai kwanta ba"

"Dallah kar ki ba ni kunya mana, in sha Allah ke da AAJ har abada"

"Allah yasa hakan Rabin Rai"

"Ameen, yanzu dai tashi mu koma wurin Umma"

Suka tashi suka fito cikin gidan, sai suka ga Yayan Yuhanees, Mashkur su na magana da Umma, Yuhanees ta ce "Ya Mash yaushe ka shigo?"

"Anty Yuha da Anty Hany, magulmatan Umma, ku na ɗaki kuna gulmar ina za ku san lokacin da na shigo?" 

Hanan ta ce "ba wani gulma, mun gaya maka ka daina ce mana magulmata, za muyi maganinka fa!"

Ɗan buɗe baki yayi, ya ce "yi haƙuri Anty Hany, na manta yanzu ke matar AAJ ce ko?"

Turo baki tayi ta ce "Umma kice ya kyale ni"

Umma ta ce "tsakaninku ne, ba ruwana"

Dariya yayi ya ce "nima sake fita zanyi ba sai kin b'ata rai ba Hajjaju, bye"

Ya fita yana dariya, su ma dariyar suka yi sannan suka zauna suka ci gaba da yanka alayyahun

********************

Bayan magrib sai ga Arshad ya zo, cikin zaure suka zauna suka yi hirarsu, fiye da minti talatin, sannan Arshad ya ce "Hanan!"

Kallonshi tayi dan ta daɗe bata ji sunanta a bakinshi ba, ta ce "na'am"

"Meye gaskiyar maganar contract ɗin nan na MK?"

A shagwab'e ta ce "ban sani ba, ni da kayi ma wulaƙanci ɗazu dan kawai munzo wurinka, ko dan nayi shiru?"

Dariya yayi ya ce "haba gimbiyar Arshad, kiyi haƙuri, nima banyi dan in b'ata miki ba, nayi ne kawai saboda MK"

"Amma shi ne ka kore mu hadda cewa baka ganni ba"

"Naji dai, kiyi haƙuri duk saboda shi ne Allah, kinji"

Sai tayi ajiyar zuciya ta ce "to naji"

"Yawwa matas, to gaya mun"

"Nima ban sani ba, amma Zayyad ɗin abokinshi ne, suna kasuwanci tare"

"To meyasa wannan ba za suyi shi tare ba sai dani? Ba kya ganin kamar akwai matsala?"

"Da shi ya so suyi, sai dai yanada contracts biyu da ya karb'a shiyasa ya ce zai kawo maka shi ko dan ka sake yarda da tuban da yayi, ku shirya"

"Mu shirya? Ai ba shiri tsakanina da shi"

"Amma contract ɗin fa? MK yana so ka yafe mishi fa"

"Ta ya kika gane?"

"Yayi sanyi sosai, kamar ba shi ba, na tabbata ba wani mugun abu a ranshi"

"A taƙaice dai kina so in karb'a"

"Eh, ka yarda dani ba komai"

Shiru yayi bai ce mata komai ba, ta ce "ka yarda mana My Charming Prince, nothing will happen (ba abunda zai faru)"

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce " shikenan, naji, ki gaya mishi ina son ganin Zayyad ɗin gobe"

"Yawwa, to mun gode"

"Ba komai......yanzu dai kam bari in wuce ko! Dare yayi"

"To shikenan Sweetie na, Allah ya kai ka lafiya"

"Ameen"

Suka tashi, ta mishi rakiya har bakin mota, ya haɗa ta da tsarabarsu tayi godiya sannan ya wuce, ita kuma ta shiga gida...............






KUYI HAƘURI DA WANNAN HAKA NAN DAN ALLAH🙏


🥰UMMEETA🥰......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA



        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 21* 

Yana zuwa gida bai tsaya ko ina ba sai main palour, Inna Asabe ce kawai a palourn tana gyarawa

Ko kallonta bai yi ba, sai ihun kiran Yasmin da yake yi

"Yasmin!....Yasmin!.....Yasmin!!!"

Inna Asabe tayi tsaye tana kallonshi, kamar za tayi magana, sai ta ga su Yasmin ɗin ma suna saukowa

Yasmin ce a gaba, Yasna na bayanta, sai sauri take yi, tana ƙarasowa kusa da shi ta tsaya

"Big Bross ga...." ba ta kai ƙarshe ba, ya ɗauke ta da mari, hakan yayi dai-dai da saukowar Ammi dan ta ji shigowarshi

Sake marinta yayi, sai dai wannan karon bai samu fuskarta ba, dan ta rufe fuskar da hannunta, sai ya same ta a hannu, Ammi ta zo da sauri ta ja ta zuwa bayanta

Yasna ce ta riƙe ta, dan ta tausaya mata saboda ta maru musamman marin farko, haka ma Inna Asabe ta tausaya mata, ba ta dai ce komai ba

Ammi ta ce "Arshad kanka ɗaya kuwa? Marinta fa kayi, Yasmin ka mara!"

Shi ma cikin fushi ya ce "na sani Ammi, ta ma gode ma Allah ita ce, wallahi da sai na kusan karya ta a gidan nan, amma yanzu ma ki jira dawowa na, wallahi idan naji abunda bai mun dai-dai ba, sai na ba ki mamaki" ya ƙarasa zancen yana nuna Yasmin dake ta faman rusa kuka a kafaɗar Yasna, ita kuma sai shafa mata baya take tayi kamar wata jaririya

Ammi da tayi wani sororo tana kallonshi, ta ce "Arshad?"

Ko kallonta bai yi ba, ya juya ya bar palourn, haka tayi ta kiranshi, amma har ya fita ko juyowa bai yi ba

"Arshad! Arshad!.......tabɗijam"

Juyawa tayi ta ja Yasmin suka koma kan kujera suka zauna, ta kalli wurin da ya mare ta, ga shatin hannunshi nan ya kwanta, fuskar nan tayi ja

"Yi shiru ya isa haka, kyale shi, dani yake zancen ai"

Kallon Yasna tayi za tayi mata magana, ta ga hawaye shane-shane a fuskarta, sakin baki tayi ta ce "hadda ke ya mara?"

Girgiza kai tayi tana share hawayen, Inna Asabe ta ce "bai mata komai ba Hajiya, kawai dai kin san abunka da jini ɗaya"

Ammi ta ce "hmm, to ya isa kema, je ki ɗauko mata ruwa ta sha"

Yasna ta wuce ta ɗauko ruwan ta bata, sai da ta sha sannan Ammi ta ce ta ja ta su koma ɗakinsu, ta ɗan kwanta kafin a kira sallar Magrib

Yasna ta ce "amma Ammi ba kyau baccin bayan la'asar fa"

"Ba bacci nace tayi ba ai, uwar iyayi, kuje ta ɗan kwanta ne"

Ba ta ce komai ba, ta kama ta suka wuce ɗakinsu

Bakin gadonsu suka zauna, Yasmin sai share hawaye take tayi, Yasna ta kalle ta ta ce "kin gani ko twinny, sai da nace miki kar ki tafi amma kika ƙi, yanzu ai ga abunda kika ja wa kanki"

Yasmin ta ce "dalla malama ki kyale ni, ina ruwanki da ni, munafuka kawai, kuma wallahi ba zai tab'a aurenta ba"

Sakin baki Yasna tayi tana kallonta, wato ma har yanzu ba za ta canza ba

"Yasmin ni ce munafuka? To shikenan kar ki daina, kuma ki daina rantsuwa akan abunda ba ki da tabbas"

"Akan menene ban da tabbas ɗin! Auren Hanan? To na maimaita wallahi ba zai aure ta ba"

Yasna ta miƙe tsaye ta ce "Ashe kuwa ki shirya ma azumin kaffara"

Ba ta tsaya jin komai daga gare ta ba kawai ta fita daga ɗakin, ita ma Yasmin rakata tayi da harara, sannan tayi tsaki ta kwanta

********************

 Arshad kuwa tun bayan da ya fita daga palourn, ya wuce part ɗinshi

Zama yayi kan kujera, ya sa hannu biyu ya riƙe kanshi ya rufe ido, sai faman furzar da iska yake yi lokaci zuwa lokaci

Sallamar Sajjad ce ta sa shi ɗagowa, suna haɗa ido ya sake komawa yanda yake

Sajjada ya zo kusa da shi ya zauna yana kallonshi, sannan ya ce "Super lafiya?" ya tambaye shi cikin damuwa

Sai da yayi kusan minti uku sannan ya ce "Ina zuwa Man" ya tashi kawai ya shiga bedroom ɗin shi, Sajjad kuwa sai roƙon Allah ya ke yasa lafiya

Wanka yayi, sannan yayi alwala, ya fito ya shirya cikin wani yadi milk colour, yayi masifar yi mishi kyau, ya feshe jiki da turare sannan ya ɗauko wasu takalmanshi baƙaƙe ya sa suka yi kyau ma farar ƙafarshi, ya shace gashin kanshi sannan ya ɗauko sallaya ya fito palour wurin Sajjad

Kallonshi Sajjad yayi, sannan ya ce "yau laraba, kuma yanzu karfe biyar, bare ince ko masallaci zaka tafi, ina zuwa haka?"

Murmushin da bai kai cikinshi ba yayi mishi, sai ya cire takalminshi can wurin ƙofa sannan ya dawo ya shimfiɗa sallaya ya fara sallah, sai da ya gama yayi addu'a sannan ya gyara zama ya fara zayyana ma Sajjad duk abun da ya faru

Shiru ya ɗan yi na wani lokaci sannan ya ce "amma Yasmin ta ba ni mamaki wallahi"

Arshad ya ce "banyi mamaki ba ni, dan na san wacece Yasmin"

"Hmm, amma kai ma baka kyauta ba da ka dake ta"

Wani wawan kallo yayi mishi, yayi tsaki ya ce "ni ba wannan ne ya dame ni ba, yanda ma zan tunkari gidansu Hanan nake ji"

"Ka kwantar da hankalinka, insha Allah ba wani abun da zai faru"

"I hope so"

"Yanzu ka bari idan muka yi sallah, sai mu tafi"

"To shikenan"

**********************

"Mummy wallahi na ji daɗin wannan plan ɗin na ki, kin ga yanzu, dole ne ma ta rabu da shi" cewar Farha

Hajiya Karime ta ce "yaro dai yaro ne, ba ki fahimci abunda na fahimta ba kenan"

Farha ta ce "Mummy me kika fahimta?"

"Yarinyar nan Hanan, ban ga alamar tsoro a tattare da ita ba, bare kuma wai har tayi tunanin rabuwa da shi, sannan kuma kin ga wannan ɗayar, ban san sunanta, ita kanta za ta iya hana Hanan rabuwa shi"

Murmushi Farha tayi, ta ce "kai Mummy, ai ni na fi so in ga sauyi a fuskar mahaifiyarta, dan ita ce take da ikon hana ta da kuma sa ta, to kin ga kuwa duk yanda take son shi, in dai mahaifiyarta ta raba su dole ne ta kyale shi, ke ba ki ga yanda ran mahaifiyarta ya b'aci ba?"

Ɗan ƙaramin nazari Hajiya Karime tayi, ta ce "tabbas, maganarki akan hanya take, amma duk da haka ba za muyi sake ba, dole ne in ƙulla wani abu"

"Me kenan Mummy?"

"Zan gaya miki nan gaba"

"To shikenan, bari inje inyi wanka"

"Yawwa ƴar Mummy, ina tunanin ma friday Daddynki zai dawo"

Wani tsalle tayi ta ce "wow, wallahi i really missed him alot"

Murmushi tayi, ta ce "to je kiyi wanka kafin a kira sallah"

Wucewa tayi ɗakinta tana ta fara'a

********************

A ƙofar gidansu Hanan, Arshad yayi parking, suka fito suka tsaya jikin motar.Wayar Hanan ɗin ya kira har ta tsinke ba ta ɗauka ba, ya sake kira na biyu, sai Siyama ta ɗauka

"Hello Ya Arshad"

"Na'am Siyama, ina Hanan"

"Ba ta nan, ta je ta raka Anty Yuhaness"

"To zo kiji, ina ƙofar gida"

"To, gani nan zuwa"

Sai suka kashe wayar, ba ta fi minti biyu ba, sai ga ta ta fito

Sai da suka gaisa da Sajjad sannan ta mayar da hankalinta kan Arshad

"Siyama, ɗazu wasu sun zo gidan nan?"

Shiru ta ɗanyi, sannan ta ce "eh"

"Su nawa?"

"Su biyu, ɗayar kusan shekarunsu ɗaya da Sister, ɗayar kuma dattijuwa ce"

"Kika ce su biyu?"

"Eh su biyu ne"

Hamdala yayi cikin ranshi, dan hakan ya nuna mishi cewar ba su san tare da Yasmin suka zo ba, sannan ya ce "me suka yi da suka zo?"

Ai kuwa yayi sara akan gab'a, dan ya tambayi radio, labari ta ba shi tun daga farkon shigarsu gidan har fitarsu, duk abunda suka faɗa ba wanda ta manta, hatta gwallo da bokitin da Farha tayi sai da ta gaya mishi

Shiru suka yi daga shi har Sajjad ɗin, sannan suka kalli juna, Sajjad ya mayar da kallonshi kan Siyama ya ce "Siyama, ki shiga ki ce ma Ummi dan Allah muna son ganinta"

Arshad yayi saurin kallonshi ya ce "Man!?, taya kake tunanin zan iya fuskantar Ummi?"

Siyama ta ce "may be za ta saurare ka Ya Arshad, amma tun ɗazu su Sister ke son yin magana da ita amma ta ƙi ba su fuska, yanzu ma kafin Anty Yuhaness ta wuce sai da suka shiga dan su mata magana amma ta ce idan maganar ce su kyale ta kawai"

Arshad ya dafe kai ya ce "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un, Man ka ga abunda nake tsoro ko?"

Sajjad ya ce "haba Super, to idan ba ka fuskance ta ba ka ba ta haƙuri, me za kayi?"

Siyama ta ce "haka ne Ya Arshad, in sha Allah za ta saurare ka"

Sha fa fuskarshi yayi, ya ce "to shikenan, shiga ki mata magana"

Komawa tayi cikin gida, Ummi na ɗaki ta isko ta, ta gaya mata Ya Arshad na son magana 

Ta ce "ɗauko tabarma bayan ƙofa, ki shimfiɗa tsakiyar gida, sai ki ce ya shigo"

"Su biyu ne, da abokinshi"

"Su shigo mana"

"To"

Ɗaukar tabarmar tayi ta shimfiɗa kamar yanda Ummi ta ce, sannan ta fita ta gaya musu su shigo, sannan suka biyo bayan Siyama har cikin gidan, suka zauna kan tabarmar

Ummi ce ta fito sanye da hijab ɗinta, ta jawo kujerar dake gefen ɗakin ta zauna, sannan suka risina suka gaishe ta, cikin sakin fuska ta amsa musu tana tambayarsu ya aiki

Shiru suka yi na kusan ƴan mintuna, sannan Arshad ya fara magana kan shi a ƙasa

"Ummi dan Allah kiyi haƙuri abun da ya faru ɗazu, wallahi ban san da zuwansu ba sai daga baya Yasna ta gaya mun, amma in sha Allah na miki alƙawari zan ɗauki mataki amma dan Allah Ummi kiyi......"

Ummi ta katse shi "Arshad!"

Shiru yayi amma ya kasa ɗaga ido ya kalle ta, ta sake kiranshi

"Arshad!"

Da ƙyar ya iya ɗagawa ya kalle ta ya ce "na'am"

"Ka na son Hanan?"

Jin tambayar yayi wani iri, ya kasa cewa komai, sai da ta sake tambayarshi

Sannan ya ce "Ummi ina son Hanan, kuma tsakani da Allah nake son ta" hakan yayi dai-dai da shigowar Hanan

Tana ganinsu sai da gabanta ya faɗi, wucewa tayi bakin ƙofar kitchen kan turmi ta zauna

Ummi ta ce "ka tabbata?"

"Eh Ummi, ina sonta wallahi, dan Allah kiyi haƙuri"

"Waɗannan ɗin su waye?"

"Yarinyar tana so na ne amma ni bana sonta, to shi ne ta biyo ta wannan hanyar dan kawai Hanan ta rabu da ni"

Ummi tayi ajiyar zuciya, ta ce "Allah ya kyauta, dama ba ta ɗaga mun hankali ba, tunda ba kai ka aiko ta ba sannan kuma ba mahaifiyarka ba ce, ina so ne dama in sake tabbatar da irin son da kake mata....ba damuwa Arshad, Allah ya mana mai kyau"

Ɗagowa yayi da sauri ya kalle ta, ya ce "Ummi kin haƙura?"

Murmushi tayi ta ce "Arshad ai ban yi fushi ba dama, haƙurin me kake bani? Ba ka yi mun komai ba"

Wani irin farinciki ne ya baibaye zuciyoyinsu, Arshad da Hanan, dan dukansu tsoro ɗaya ne a ransu kar Ummi ta raba su

Sajjad da bai ce komai ba tun bayan da suka gaisa, sai yanzu ya ce "mun gode sosai Ummi"

Nan ma murmushin tayi, ta ce "ba komai, ya sunanka kai"

Ya ce "Sajjad"

"Masha Allah, suna mai daɗi"

Arshad ya wani kalli Sajjad dake murmushi, sannan ya kalli Ummi ya ce "to Ummi ni kuma fa?"

Dariya tayi ta ce "kai ma haka ai Arshad"

Sannan suka yi dariya, nan dai Ummi ta koma ɗakinta wurin Siyama, ya rage da ga su Arshad sai Hanan

Tashi yayi ya koma kusa da ita ya tsugunna ya kallon fuskarta, duk da ya kasance dare ne, amma bai sa gidan yayi duhu ba kasancewar akwai wuta

Ƙoƙari yayi ya fara tattaro zance, sannan ya ce "i'm really sorry for what happen"

Kallonshi kawai take yi da kyawawan idanunta masu ɗaukar hankali

Rufe ido yayi yana girgiza kai, haɗi da yin wani killer smile, sannan ya sake buɗe ido ya kalle ta, ya ce "dan Allah ki daina mun irin wannan kallon, wani iri nake ji, kiyi haƙuri dan Allah"

Ita ma murmushin tayi, ta ce "haƙuri akan me?"

"Abunda su Farha suka yi"

"Farha daban Arshad daban, Farha ce tayi laifi, meyasa Arshad ke ba da haƙuri?"

"Saboda shi ya san darajar abunda aka tab'a mishi"

Murmushi ta sake yi, ta ce "meyasa ba ka gayawa Ummi cewar Ammi ba ta so na ba?"

Kallon ƙofar ɗakin Ummi yayi, sannan ya ce "dan Allah kar ki gayawa Ummi wannan maganar please"

"Amma meyasa?"

"Daga maganar da tayi ɗazu, na fahimci idan har mahaifiya ta ba ta sonki to lallai raba mu za tayi, kuma Hanan banajin zan rayu ba tare da ke ba"

"Amma ka san dole ne wata rana sai ta sani!"

"Na sani, amma ina fatan kafin wannan lokacin Ammi ta gyara halinta"

"Kenan za mu ɗauki shekaru a hakan?"

"A'a"

"Amma yanayin maganarka haka ya nuna"

"Ba haka nake nufi ba Hanan, ina so zan tafi wurin kakarmu, anan ne na san in sha Allah komai zai yi dai-dai"

"To ina fatan haka"

"Yawwa your highness haka nake son ji.......har yanzu MK bai ce miki komai ba?"

"Eh ba abun da yace mun, but i know he's up to something"

"Nima ina jin hakan, amma kar ki ji tsoro, Allah ya na tare da ke, ba abunda MK zai iya yi miki"

"Shikena , Allah ya sa"

"Ameen, kinga bari mu wuce kar Ummi ta ce bani da kunya"

Dariya ne ya sub'uce mata, ta ce "na yaushe kuma?"

Shi ma dariyar yayi, sannan ya juya da niyar yi m Sajjad magana, amma ya ga tabarma wayam ba kowa akai

"To shi kuma wannan ina ya tafi?"

Dariya ta kuma yi, ta ce "kana nufin kace ba ka ga lokacin da ya fita ba?"

Girgiza kai yayi, ta ce "ai kuwa ya daɗe da fita"

Murmushi yayi ya ce "ai ba laifi na bane, ke ɗin ce idan ina kallonki bana ganin kowa"

"Hadda Ummi dake bayanka?"

Da sauriya juya amma bai ga kowa ba, ya juyo yana kallonta sai faman dariya take tayi, ba ƙaramin kyau ta mishi ba

Sai da ta gama dariyarta sannan ta tashi ta raka shi har wurin mota, Sajjad ya fito, ta ce "malam tafiya ba sallama?"

Dariya yayi ya ce "kin san ni tsoron masoya nake ji musamman wannan, dan ba ko da yaushe yake gane kan shi ba"

Dariya tayi ta ce "ai kuwa"

Arshad ya haɗe rai ya ce "to idan kun gama sai ki koma gida kai kuma ka shiga mu tafi"

Dariyar suka sake yi, sannan ta ce "to yallabai, Allah ya kiyaye"

Yayi murmushi ya ce "ameen madam, sai na kira ki"

"Bye" 

Sannan ya shiga motar suka wuce, sai da suka bar layin sannan ta koma cikin gida..........









🥰UMMEETA🥰......📝



♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 22* 

Yau tsawon kwana biyar kenan da faruwar wannan abu, ba abunda ya sauya a soyayyar Arshad da Hanan sai ma abunda ya ƙaru, dan yanzu ma idan ya zo wurin Hanan ɗin, yakan shiga har cikin gidan su zauna suyi hira da Ummi da Siyama, sun ɗauke shi tamkar ɗan gidansu

Farha kuwa tunda ta samu labarin yanda Arshad yayi ma Yasmin take shakkar haɗuwarsu, dan tana da tabbacin tunda har ya iya marin Yasmin to ita zane ta ma zai yi, duk yanda Hajiya Karime ta so su tafi gidan, amma ta ƙi yarda

Sai dai sun tafi wurin wani malamin daban, akan ya raba Arshad da Hanan, kuma ya tabbatar musu da hakan zai yiwu, sai dai yana buƙatar kuɗi da kuma lokaci, inda suka ba shi naira dubu ɗari da ashirin, su na jiran tsammani

Ammi kuma ta kira Abba akan maganar Arshad ɗin da Farha

"Abban Nabeel na ji kayi shiru akan maganar auren nan na Arshad, lafiya dai?"

"Haka ne, amma kin san komai yana buƙatar bincike, musamman sha'ani na aure, so zanyi bincike akan ita yarinyar"

"Amma wane bincike za kayi Abban Nabeel!? Ina ce yarinyar nan na gaya maka ƴar aminiya ta ce, sannan kuma ka san mahaifinta, Alhaji Mas'ud, to me kuma ya rage?"

"Tabbas mun san iyayenta, amma ba mu san ainihin halayenta ba, kuma kin ga ita zai aura ba iyayenta ba"

"Amma ai......"

"Kiyi haƙuri ayi binciken dan Allah, in Allah ya rubuta matarshi to sai ya aure ta" ya katse ta

Ba dan ta so ba ta ce "to shikenan, nagode"

Daga hakan su kayi sallama, sai zulumi ta ke yi, anya kuwa ba wani abu bane a ranshi
Shi kuma ba wani bincike da ya fara akanta, kawai dai yana so ne sai Arshad ɗin ya zo sun yi magana sannan ya san abun yi

********************

Yau Hanan na zaune a reception, su na hira ita da Zulaihat, sai ga wani Shehu ya zo wurinsu

"Hajiya Hanan da Zulaihat, sannunku da hutawa"

Murmushi tayi ta ce "Hajiya Zulaihat ɗin dai, ni kuma Hanan"

Ya ce "meyasa to ba za'a kira ki da Hajiya ba?"

"Saboda banyi kama da su ba"

Zulaihat ta ce "ai ko kin yi kama da su, ki na matar AAJ"

Bugun wasa Hanan ta kai mata, sannan ta ce "ba AAJ ba, ƴar rainin hankali"

Dariya Shehu yayi, ya ce "ni dai duk ba wannan ba ma, kun ga kun mantar da ni, Hanan MK na kiranki"

Ras, ta ji gabanta ya faɗi, Zulaihat ma kanta sai da ta zaro ido

Hanan ta ce "lafiya yake nema na?"

"To ta ya zan sani? Ki je ki gani"

Zulaihat ta ce "ki je kawai Hanan, in sha Allah ba komai"

Sai da ta ɗan ɗauki lokaci tana tunani sannan ta wuce

Ta kusan minti biyar a bakin ƙofar office ɗin shi sannan tayi knocking ya ce ta shigo

Bata yarda suka haɗa ido ba har ta kai kusa da table ɗin shi ta tsaya

"Ki zauna mana" ya faɗa cikin murya mai sanyi

Tayi matuƙar mamakin jin yanda ya mata magana, hakan ya sa ta kalle shi, sai ta ga yana mata murmushi, sakin baki tayi tana kallonshi

Ya ce "ya dai Hanan? Feel free and get seated (ki saki jikinki, ki zauna)"

Haka ta ja kujera ta zauna, sai da ya gama abunda yake yi cikin system ɗin gabanshi sannan ya mayar da hankali kanta

"Hanan"
Ya kira sunanta, ba ta amsa ba sai dai ɗaga kai da tayi ta kalle shi

"Na san kina jin haushi na akan abunda na miki sannan kuma kina jin tsoro kar inyi miki wani abu, ko ba haka ba?"

A hankali ta ɗaga mishi kai, ya sake yin murmushi ya ce "to ki kwantar da hankalinki, na kira ki nan ne saboda in ba ki haƙuri akan abunda ya faru, kullum ina so in ba ki haƙuri amma ban san ya za ki ɗauki maganar ba, ban sani ba Hanan za ki yafe mun ko kuma a'a"

Kallon mamaki kawai take mishi, dan ba ƙaramin mamaki ya ba ta ba

Da ƙyar ta ce "ba komai yallab'ai, komai ya wuce"

"Da gaske kike yi?"

"Eh, komai ya wuce"

"Nagode Hanan, saura kuma wata alfarma ɗaya"

"Ta me?" ta faɗa tana kallonshi

"Ina so ki saki jikinki da ni, duk wata matsalar da ta shafe ki ina so ki sanar da ni, idan  ina da halin taimaka miki zan taimaka miki, na san za kiyi tunanin banda abun taimaka miki da shi saboda kina tare da AAJ, amma karki manta kowane mutum da irin baiwar da Allah ya mishi, na koyi wannan zancen ne a wurinki, dan Allah kar ki ce a'a"

"Kamar ya yallabai?"

"Na san kin gane me nake nufi Hanan, amma zan ƙara miki haske, ina so ne in zama tamkar ɗan uwanki, na fahimci duk wanda yqyi mu'amala dake zai ci riba, ina so in canza halaye na su koma tamkar na ki halayen, na sanin darajar ɗan adam, ki amince mun, za ki samu lada Hanan, sannan ina so ki taya ni ba AAJ haƙuri kafin nima in samu damar ba shi haƙurin da kaina"

Shiru tayi na ƴan mintuna, sannan ta girgiza kai ta ce "ba komai, Allah ya ƙqra ganar da mu baki ɗaya, kuma in sha Allah zan mishi magana"

"Nagode sosai Hanan" ya faɗa yana ta mata murmushi

"Zan iya tafiya?"

"Eh Hanan, tafi kawai"

Tashi tayi jiki a sanyaye ta fita, bin ta yayi da ido har ta fita, sannan ya jingina da kujerarshi yana jujjuyawa, ya saki wani irin dariya, ya ce

"I pity you Hanan(na tausaya miki Hanan), a tunaninki MK na bada haƙuri ko? You're wrong, i will definately make you cry(kinyi kuskure, tabbas sai na sa ki kuka)" ya ci gaba da murmushi

*******************

Bayan sallar magrib Arshad ya zo wurin Hanan sai dai yau ko gidan bai shiga ba, su na cikin mota

Sun daɗe su na hira sannan Hanan ta gaya mishi cewa MK ya bata haƙuri ɗazu sannan kuma ta gaya mishi ya ce ta ba shi haƙuri shi ma, sai dai bata gaya mishi ɗayan maganar ba na cewa ta saki jikinta da shi kamar yanda Yuhanees ta ba ta shawara

"Yanzu ke kin yarda da haƙurin da ya ba ki?"

"Eh to, alamun shi sun nuna mun kamar da gaske yake yi"

"To shikenan, Allah ya sa" ya amsa mata da hakan ne kawai dan ya ga kamar ta yarda da tuban MK, amma shi ya san ba banza ba, baya son dai yasa mata shakku ne

"Ameen"

"Yawwa kin san me?"

"Sai ka faɗa"

"Ina so zanyi tafiya ne gobe, zanyi kwana biyu"

'Bata rai tayi ta ce "tafiya fa kace"

"Eh, amma ai kwana biyu nace miki zanyi, ba daɗewa zanyi ba"

"Ko ma dai yini ɗaya ne, ai za ka tafi ko!"

Murmushi yayi ganin yanda take yi kamar za tayi kuka, ya ce "to ke in banda abun ki, ai idan na tafi ba wai shikenan ba za ki sake ji na ba, za muyi waya mana kamar yanda muka saba"

Shiru tayi kawai tana wani yamutsa fuska, kallonta yake yana murmushi sai wani sonta dake ƙara shiga ranshi

"Shikenan baby doll, idan ba kya so in tafi ai sai in kira Abba in ce mishi na fasa zuwa"

Da sauri ta kalle shi ta ce "a'a, akan me?"

"Na ga ai ba kya so ne"

"Amma ai kiran Abbanka ya fi nawa"

"Abbana kuma? Ban da ke kenan?"

"Ba fa haka nake nufi ba" ta faɗa a shagwab'e

Dariya kawai yayi, sai ya duba agogon hannunshi, ya ce "kin ga dare yayi, ki shiga gida kawai, ni zan wuce"

"To, Allah ya kiyaye ya kai ka lafiya"

"Ameen Hearty, ki gaida Ummi da radio" ya ƙarasa yana dariya

Ita ma dariya tayi ta ce "ba ruwana ni dai"

Sannan ya ɗauko wasu ledodi a backseat ya bata, ya nuna mata ledar ta da na Ummi da na Siyama da na Yuhanees

Sakin baki tayi ta ce "amma ai sunyi yawa dear"

"Idan kin fita ki zubar da su"

"Allah ya baka haƙuri, mun gode Allah ya saka da alkhairi ya ƙara arziki"

"Ameen, sai da safe"

"Allah ya bamu alkhairi, i will miss u so much(zan yi kewarka sosai)"

"I will miss u too(zan yi kewarki nima)"

Sannan tayi murmushi ta fita daga motar, sai da ta shiga gida sannan ya ja motar ya wuce

********************
Washe gari da safe ya gama duk wani shirin da zaiyi na tafiya, wata ƴar ƙaramar jaka mai kyau navy blue, ya sa kayanshi a ciki, sannan ya fito palour, in da Yasna take zaune, kasancewar yau ɗin asabar ba makaranta sai islamiya 12pm

Tashi tayi ta karb'i jakar sannan suka wuce main palour, Ammi na zaune a kan cushion Yasmin ma haka, ya zo kusa da Ammi ya zauna sannan suka gaisa, Yasmin ma ta gaida shi, ya amsa mata da "lafiya", haka yake amsa gaisuwarta tun lokacin da su ka samu matsala, abun yana matuƙar damunta, duk yanda take da Arshad tana son shi sosai dan ko mutum bai da hankali in ya ga irin yanda yake kyautata musu yake tarairayarsu dole ne ya burge ka bare kuma su da yake yi ma

Ammi ta ce "wai har ka fito tafiyar kenan?"

"Eh Ammi, ina so in isa da wuri ne shiyasa"

"Ni wannan tafiyar ta ka ma da rana ɗaya na rasa dalilin yin ta wallahi"

"Ammi na gaya miki ina son ganin Hajjo da Anty Fati shiyasa, kuma kin ga kwana biyu kawai zanyi"

"To company kuma wa ka bar ma?"

"Sajjad mana, ko kin manta da shi? Sannan yau saturday, monday zan dawo"

"Hmm to shikenan, Allah ya kiyaye hanya, ka gaishe su.......Yasmin je ki ɗauko saƙon da nace zai kaiwa Antynku"

Yasmin ta tashi ta wuce ɗakin Ammi. Shi kuma ya fita Yasna ta bi bayanshi.A parking area Yasmin ta taradda su, Yasna na ta gaya mishi abunda zai dawo mata da shi

Ta buɗe backseat ta sa saƙon, sannan ta dawo gabanshi, ta ce "Big Bross na san har yau kana fushi da ni, dan Allah kayi haƙuri, bana so ka tafi da haushi na Bross, i'm really sorry" sai hawaye kawai suka biyo kumatunta

Fitowa yayi daga cikin motar, ya riƙe mata hannu, sannan ya sa ɗayan hannunshi ya share mata hawayen, ya ɗaga fuskarta yana kallon cikin idanunta, ya ce "stop crying sweetie(ki daina kuka sweetie), na haƙura ai, kuma bazan iya yin fushi da ƙanwata ba, kawai dai ban ji daɗin abunda kika yi ba"

"Ba zan sake ba bross"

"Shikenan ya wuce, ki kula da kanki kinji"

Murmushi tayi ta ɗaga kai, Yasna dake gefe ta ce "ni kuma fa Sweet Bro?"

Murmushi yayi, ya jawo su ya rungume su tare, kusan munti biyu sannan ya sake su suka yi sallama ya shiga mota ya wuce

Yasna na murmushi, ta ce "ko ke fa twinny, amma ke ki ce ba ki son abunda Sweet Bro yake so!"

"To yanzu ma wa ya gaya miki ina sonta ne? Kawai ina jin wani iri ne yanda bross yake fushi dani amma ba wai dan na haƙura ya auri wata Hanan ba"

"Kina nufin tuban muzuru ki kayi kenan?"

"Na gaskiya ne nayi, amma ai ba cewa nayi ina sonta ba ko?"

"Hmm you won't change twinny(ba za ki canza ba twinny) Allah ya shirye ki" bata sake kallonta ba ta wuce cikin gida

Yasmin ta ce "ameen in da gaske kike yi" ta fita daga wannan second gate ɗin, ta wuce wurin swimming pool ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun da ke wurin


Ammi kuwa bayan fitarsu, ta ɗauki wayarta ta kira Hajiya karime

"Hajiya kin ga kuwa tafiyar nan ta Arshad da gaske yake yi"cewar Ammi bayan sun gaisa

"Ya tafi ne?"

"Bai daɗe ma da ya fita ba"

"To Hajiya meye wai abun ta da hankalin? Ya ce Hajjo yake so ya gani sai Antynshi, kin ji bai ma yi maganar Abbansu ba"

Ammi ta ce "ba za ki gane ba ne Karime, yaron nan da kike gani wayon tsiya ne da shi, na tabbata ko da ba Abban Nabeel ya je gani ba, to tabbas maganar Hanan ce za ta kai shi Adamawa, amma in ba shi ba, wata nawa ya rage ayi hutun makaranta sai mu tafi gaba ɗaya?"

"Haka ne kuma da maganarki, amma dai kar ki ce komai yanzu, mu bar komai wurin Malam, kin san na gaya miki ya ce zai iya raba su, kuma na yarda da shi"

"Haka kike gani?"

"In sha Allah komai zai tafi yanda kike so"

"To ba damuwa, nagode"

"Ai an zama ɗaya, ba komai"

"To ki gaida Farha, sai anjima"

"Za ta ji"
Suka yi sallama kowa ya kashe wayar

Farha dake gefe tana sauraren Mummynta, ta ce "Mummy ya tafi ne?"

"Eh, ya tafi"

"Mummy ko za mu koma wurin Malam ne wai, mu ji ya ake ciki?"

"Kar ki samu damuwa, nasan zai iya raba su"

"Amma ni ina shakku akan wannan aikin Mummy, saboda ance yi wa Arshad aiki ba abu bane mai yiwuwa"

"To ai ya ce ba ainihin Arshad ɗin zai yi ma ba, zai yi ma wanda yasan zai iya hana aurensu ne kuma ya hanu ko yana so ko baya so"

"To Allah ya sa"

"Ameen daughter, ai ki kwantar da hankalinki, ba dai aikin da zai karkata gare ki bane ba zai yiwu ba? To idan akayi wanda zai aure ki ko da baya son ki ne ai dole za ki samu chance ɗin wawuro mana kuɗinshi hankali kwance, tunda kin zama matarshi"

Farha tayi dariya ta ce "wa ya ga Farha a matar AAJ, tab, za'a shuka tsiya Allah" su ka sake yin dariya

Hajiya Karime ta ce "idan ana sallah ai ba'a magana daughter, Allah dai ya nuna mana wannan ranar"

"Ameen Mummy"

Suka ci gaba da hirarsu................







🥰UMMEETA🥰......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 23* 

Kusan ƙarfe 4:20pm ya isa gidan Hajjo, bakinta kuwa har kunne, tana ta jin daɗin ganinshi

Tarba ta musamman aka mishi, dan ta sa an dafa mishi tuwon shinkafa da miyar zogale wanda ya ji nama da ƙashi, sannan aka mishi farfesun cow tail da pepper chicken, sannan an haɗa mishi haɗaɗɗen kunun aya, ga fura da aka sa ma kindirmo wanda bai da surki da komai, ya sha sanyi dai-dai sha. Daga gidan Anty Fati kuwa, Nabeela ce ta aiko mishi da favorite food ɗin shi, fried spaghetti da banana smoothie.

A tsakiyar palourn Hajjo aka baza mishi komai sai wanda ya zab'a

Ɗakinshi da ya saba sauka ya fara shiga, yayi wanka ya sa ƙananan kaya, farin wando da riga army green, yayi sallar la'asar sannan ya dawo nan palour wurin Hajjo ya zauna a ƙasa kusa da ita ya naɗe ƙafa

"Sannu, ka kwaso gajiya kam" cewar Hajjo tana kallonshi

"Bari kawai matas, har jiki na ke ciwo" ya faɗa yana wani b'ata fuska

"To wani ya sa ka biyo mota? Ina ce jirgi kuka saba biyowa"

"Ai ka ji irinta kuma, ke maimakon ki tausaya mini shi ne kike cewa haka!...anya matar nan kina so in ɗaga miki ƙafa ki shiga Aljanna kuwa?" ya faɗa cikin sigar wasa irin wanda suka saba

Harararshi tayi, ta ce "dan gidanku idan kai ke bada aljannar ka hana ni"

Dariya yayi, ya ce "ba zan hana ki ba, amma ke ce ta ƙarshen shiga"

Larai da ta shigowarta ɗakin kenan, dariya ya sub'uce mata, Hajjo ta aika mata da zagi ta ce "Ladingo kika yi wa dariya"

Larai da kama bakinta tana ƙara ƙumshe dariyar, Arshad yayi dariya, ya ce "abun har da zagi?"

Bata ce mishi komai ba dai sai harara da take aika mishi, yayi murmushi ya kalli Larai ya ce "kyale wannan tsohuwar kinji"

Ita ma murmushin tayi, ta ce "to yallab'ai.......Me za'a zuba maka?, ina so zan wuce gida ne, na gama aiki na na yanzu"

"Je ki kawai, matata zata zuba mun"

Murmushi tayi, ta ce "to yallab'ai, a huta gajiya....Hajjo na tafi, sai na dawo" bata jira amsawarta ba ta wuce dan ta san ba lallai ta amsa mata ɗin ba, haka kuwa aka yi, har ta fita bata ce mata komai ba

Arshad ya ce "Hajjo ki zuba mun mana"

"Wa? Ni!!, ai wanda ya ce ka bari Larai ta wuce, shi zai zuba maka abincin"

"Ba za ki zuba ba kenan"

"Eh" ta faɗa tana ƙara gyara pilon da ta kishingiɗa da shi

"To Allah ya shirya mun ke"

Turo ƙofar palourn da akayi ne ya sa ba ta samun damar cewa komai ba, Adnan ne da gudunshi, sai kan jikin Arshad, sai dariya yake ta yi

Arshad ma dariyar yake yi, ya ce "my brave bro(jarumin ƙanina)"

Adnan ya ce "Ya Arshad yaushe ka zo?"

"Yanzu na zo"

Meerah ma da gudu ta ƙaraso, ta zauna gefenshi ta rungume shi "sannu da zuwa Ya Arshad"

Peck ya mata a goshi ya ce "tnx dear"

Sai yanzu ma ya lura da Nabeela da Jafar da suka zauna kan kujera, cikin fara'a Nabeela ta gaida shi tana tambayarsu Ammi

Sannan Jafar ya cire bluetooth ɗin da ke kunnenshi ya ce

"You're welcome Bross(sannu da zuwa Bross)" 

"Na same ku lafiya?"

"Lafiya ƙalau"

Kallonshi Arshad ke yi ganin yanda ya sake toshe kunne ya ci gaba da danna wayarshi, Ya ce ma Nabeela "wai shi wannan har yanzu bai daina wannan banzar ɗabi'ar ba?"

Nabeela ta kalli Jafar da hankalinshi ba ya ma kansu, ta ɗaga kai ta ce "haka yake kullum"

"To Allah ya kyauta....sauko ki zuba mun abinci"

"Wai har yanzu ba ka ci abinci ba?"

"To ba ta bani ba" ya faɗa yana kallon Hajjo da ta wani rufe ido kamar mai bacci, yana dariya

Dariya ita ma tayi, dan ta san tana jin su, tayi shiru ne kawai dan yanda suka mayar da hankalinsu wurin Arshad suka kyale ta

Fried spaghettin ta zuba mishi kamar yanda yace, anjima sai ya ci tuwon, sai fura da ta zuba mishi, sannan ya sa ta zuba musu abunda suke son ci, Jafar kunun aya kawai ya sha, su kuma suka ci gaba da bidirinsu

Meerah da Nabeela suka kwashe kayan bayan sun gama cin abincin, sannan suka dawo suka zauna, ya ba su tsarabar da ya zo musu da shi

Sai da aka fara kiran sallar magrib, sannan kowa ya wuce wurin sallah, su na dawowa Jafar ya wuce, Arshad kuma ya kwashe su cikin motarshi suka wuce gidan Anty Fati, duk yanda ya so Hajjo ta biyo su, ƙi tayi ta ce sai ya dawo dai


A palour suka tarar da Anty Fati, zaune tana kallo

"Aaaa, maraba da mutanen Kaduna"

Yana murmushi ya zauna kusa da ita, ya ce "Anty ina wuni"

"Lafiya ƙalau ɗan Anty, ka zo lafiya?"

"Lafiya ƙalau....Anty ina Babban Yaya?"

Muryar Nabeel suka ji daga bakin ƙofar palour yana shigowa "ka ga Mr.AAJ, sardaunan samarin arewa"

Miƙewa Arshad yayi, suka yi musabaha sannan suka rungume juna suna dariya

"Wannan kirarin duk ni kaɗai Babban Yaya?"

"Ai ka wuce hakan ma"

"To na gode"

Suka zauna kan two seater, Nabeel ya ce"saukar yaushe? Ni ɗazu Umma ke gaya mun wai kana hanya"

"Wallahi kuwa, da yamman nan na iso"

"To ya su Ammi, ina su Yasmin?"

"Lafiya ƙalau, su na gaishe ku"

"Muna amsawa"

Nan dai suka yi ta hira har sai da suka yi sallar isha'i suka dawo, sannan Arshad ya duba lokaci, ƙarfe tara, ya ce "Anty wai sai yaushe Abba zai dawo ne?"

"Yau su na da meeting ƙarfe takwas da rabi, ina tunanin ba su gama ba"

"Tab,ba dawowan yanzu ba ne kenan, kuma Hajjo na san tana jira na, sai dai mu haɗu gobe"

"Lallai dai kam, gobe ma da rana in sha Allah za ka iya samunshi"

"To Allah ya kaimu"

Sallama suka yi dukansu, sannan ya wuce

Lokacin da ya dawo Hajjo kam ta ma yi bacci, sai kawai ya wuce fridge ɗauko kunun aya ya wuce ɗakinshi, dan ji yayi ba zai iya cin abinci ba, ba abunda yake buƙata yanzu sama da ya ji muryar Hanan cikin kunnenshi, dan tun da ya iso ba su sake yin magana ba

Wanka ya fara yi, yayi alwala sannan ya sa kayan bacci, ya zauna ya kira ta, kusan minti arba'in suka yi suna waya, sannan suka kwanta

*******************

Tun da safe, Hajiya Karime da Farha suka shirya suka nufi gidan malam domin jin inda aka kwana

"Tabbas yaron nan yayi tafiya ne dan ya samu gyara yanda zai auri Hanan"

Farha ta ce "dama na faɗa, to yanzu Malam ya za'a yi kenan?"

"Ai ni nace ku kwantar da hankalinku, ban tab'a yin aiki ba tare da na samu nasarar wannan aikin ba, nayi muku alƙawari sai na raba shi da ita, ba zai tab'a auren ta ba"

Hajiya Karime ta ce "na yarda da aikinka Malam, mun ba ka wuƙa da nama, kar ka bamu kunya"

"Ba ki da matsala Hajiya"

"Yawwa" ta buɗe jakarta ta ciro kuɗi ta ba shi sannan suka fita daga gidan

********************

"Hanan ina so ne za ki raka ni company ɗin AAJ" cewar MK dake waya da Hanan

"Ayya, ai baya nan, yayi tafiya" inji Hanan

"Tafiya kuma? Lafiya?"

"Lafiya ƙalau"

"To ba damuwa, idan ya dawo sai mu haɗu ɗin"

"To shikenan"

"Yawwa, gobe kiyi ƙoƙarin fitowa da wuri, akwai aikin da zan sa ki"

"In sha Allah zan fito da wuri"

"Aha, sai anjima"

Kashe wayar suka yi, Hanan ta ce "yau kuma aikin ta kaina ya biyo kenan!"

Yuhanees dake gefenta, ta ce "ba wani ta kanki ya biyo, dan kawai ku ƙara shiryawa ne"

"Hmm, da alama kam, dan bai ta'a sa ni wani aikin ba bayan wanda nake yi"

"Ke dai ki kula, Allah ya kyauta"

"To ameen......kiyi sauri ni dai ki gama wannan kwalliyan na ki, mu je mu dawo da wuri"

"Ni wallahi dan kin takura mun ne, amma Allah ya gani ban so zuwa wurin bikin nan ba"

"Na dai ji, ai ba'a biye ma halin mutum"

"To malama, ni dai tashi mu tafi" ta miƙe ta ɗauki mayafinta suka fito

********************

Abba ne zaune a palournshi, Arshad kuma na zaune ƙasa, kusa da ƙafarshi

Abba ya ce "ya gajiya Arshad?"

"Alhamdulillahi, ya aiki?"

"Alhamdulillahi, jiya Antynka ta ce ka jima kana jira na, muna can muna meeting ne"

"Haka ta gaya mun ai"

Murmushi Abba yayi, ya ɗan nisa, sannan ya ce "yawwa, ina jinka, gaya mun ya maganar da muka fara da kai?"

"To Abba, dama kamar yanda na gaya maka, akwai wacce nake so Hanan, to sai kuma ita wannan Farha ɗin, Ammi ke so in aure ta, sai dai wallahi Abba bana sonta ko kaɗan"

"Arshad ban tari hanzarinka ba, amma abunda nake son ji shi ne, dalilin da ya sa baka sonta"

Shiru Arshad ya ɗan yi, sannan ya ce "Abba, ka ga dai ba ta da kamun kai, bata da natsuwa, ga rashin tarbiyya.....ni dai kawai Abba ba ta mun ba"

Sauke ajiyar zuciya Abba yayi, ya ce "Arshad, wane irin rashin natsuwa take da shi? Tana bin maza ne? Ko kuma ya ya?"

"Abba gaskiya bana ce ba, dan banda tabbas, amma dai wallahi...."

"Dakata da rantsuwar haka, Arshad! Zanyi bincike akanta sosai, idan har ban samu wata matsala a wurinta ba, to sai dai kayi haƙuri ka bi abunda mahaifiyarka ta ke so"

Ɗagowa yayi da sauri ya kalle shi, ya ce "Abba kana nufin in aure ta?"

"Eh Arshad"

"To Hanan kuma fa? Kuma na gaya maka bana son Farha..."

"Arshad, ka kwantar da hankalinka ka ji bayani na, idan Farha ba ta da wata matsala, to za ka aure ta dan ka farantawa mahaifiyarka, kar ka manta idan ka sa mahaifiyarka farinciki, to zaka samu lada, sannan kuma zata iya yiwuwa idan ka bi umarninta, ya zame maka alkhairi nan gaba, dan sannu a hankali Allah zai iya sa maka sonta. Sai kuma maganar ita Hanan ɗin, ƴar asalin ina ce? Su waye iyayenta?"

Fuskar nan ba annuri, ya ce "nima ban sani ba, amma dai na san ba ƴan asalin Kaduna ba ne, kuma mahaifinta ya rasu"

"To ba damuwa, ita ma zanyi binciken, idan bata da wata matsala, sai ita Amminku ɗin tayi haƙuri ka haɗa su su biyu"

"Amma Abba ni mijin mace ɗaya ne, bani da ra'ayin mata biyu"

"Allah kuma ya halatta maka auren har huɗu, kuma ina da tabbacin in dai ka aure su, za ka iya kwatanta adalci ai"

"Abba ni......"

Ɗaga mishi hannun da Abba yayi ne ya sa shi yin shiru

"Iya adalcin da zan iya yi kenan a wannan maganar, dan ina maka kallon da nake ma Nabeel ne, fatana Allah ya maka zab'in da ya fi alkhairi"

Shiru yayi bai ce komai ba rai a b'ace, sai kuma ya tashi ya fita ba tare da ya mishi magana ba, shi ma Abba rakashi yayi da ido har ya fita, sai ya girgiza kai kawai ya ce "Allah ya kyauta"



Tunda Arshad ya fita, bai tsaya ko ina ba sai gidan Hajjo, dan ko Anty Fati bai tsaya yi ma sallama ba

Tura ƙofar palourn yayi ba tare da yin sallama ba, ya je kusa da Nabeel ya zauna, kasancewar su na palourn tare da Hajjo da Ja'afar

Hajjo ta ce "iskancin ya tashi ko? Ka shigo mana gida kamar gidan arna!"

Ko kallonta bai yi ba, kanshi na ƙasa, shi kaɗai yasan irin tunanin da yake yi

Nabeel ya kalle shi da kyau, ya dafa kafaɗarshi ya ce "me ya faru ne AAJ?"

Girgiza kai yayi ya sauke ajiyar zuciya, Nabeel ya ce "ka gaya mun mana, ya ku kayi da Abba?"

Ɗagowa yayi, a sanyaye ya ce "Ammi has ruin everything Big Bro(Ammi ta lalata komai BabbanYaya)"

"Meyasa ka ce haka?"

Duk yanda suka yi da Abba ba abunda bai gaya mishi ba, ya ƙara da cewa "ta ya kake tunanin zan iya auren mata biyu dan Allah?"

Hajjo tayi karaf ta karb'e zance da "to meye dan ka auri mata biyu? Baka isa auren ba ne ko me? Har kake wani b'ata rai haka"

Tsaki Arshad yayi dan bai ma da lokacinta, Nabeel ya ce "haba Hajjo, Arshad ɗin guda nawa ne da har za'a ce ya auri mata biyu? Da ma ace yana son su ne dukansu ɗin"

Arshad ya ce "ba ma zai yiwu in so mata biyu lokaci ɗaya ba, kuma da sunan aure, sai dai ɗaya ta haƙura, infact ma ni ba zan iya haɗa Hanan da wata ba wallahi"

Hajjo ta ce "toooo!!! Sannu Majnoon uban soyayya"

Murmushi Nabeel yayi, ya ce mishi "take it easy dear"

Ja'afar da ke saurarensu tun ɗazu ya ce "look Ya Arshad, i have an idea(ka ga Ya Arshad, ina da shawara)"

Kallonshi Arshad yayi da alamar ina jinka

"Ka ce baka san asalinsu ba ko? To kayi ƙoƙari kayi binciken asalinsu da kanka, idan har aka samu yanda ake so, kar ka damu da matsalar Farha, i know how to deal with, there's no way you can marry her, because i so much hate that lady, infact i don't trust her and her parents(na san ya da zanyi maganinta, ba yanda za'ayi ka aure ta, saboda na tsani yarinyar nan, kai ban ma yarda da ita ba ita da iyayenta)" ya ƙarasa zancen da turanci saboda baya son surutun Hajjo

Arshad ya ce "what will you do then?(me za kayi to?)"

"Just trust me, i will never let that marriage happen between you and that foolish girl ( ka yarda da ni, ba zan tab'a barin wannan auren tsakaninka da waccen wawuyar yarinyar ya faru ba)"

Hajjo dake ta harararsu ta ce "to munafukai, shi ne kuma koma yaren nasara ko? To ko me zaku ce dai duk yanda muka yanke hakan za'ayi, dan ba ku kuka haifi kanku ba"

Arshad ya ce "kanki ake ji dai, ni na shiga inyi wanka, dan ƙanina ya sa na ɗan samu natsuwa, dan na yarda da irin ƙwaƙwalwarshi"

"Kan Ruƙayya dai ake ji, ɗan rainin wayo mara kunya kawai"

"Gobe dai zan bar miki gidan ai sai kiyi ta masifar ke kaɗai" ya tashi kawai ya wuce ɗakinshi

Shi ma Nabeel tashi yayi, haka ma Jafar, suka yi mata sallama akan zasu wuce

"Dama ba wanda na gayyata" abunda kawai ta amsa musu da shikenan, a su kula ta ba dai suka fita..........










Manage this pls❤️



🥰UMMEETA🥰......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 24* 

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" abunda Hanan ta faɗa kenan a razane bayan farkawar da tayi daga bacci a firgice

Bin ɗakinta tayi da kallo, ta ga tabbas ita kaɗai ce a ciki kamar yanda ta saba kwana ita kaɗai

Sannan ta ɗan sauke ajiyar zuciya, tayi shiru tana sake tuna abunda ta ji da wata irin murya da ta kasa gane mace ce ko namiji

'Hanan!!! Tabbas soyayyarku ke da Arshad abun burgewa ce, duba da yanda kuke son juna tsakani da Allah, amma ina miki albishir da cewa ke ɗin ba za ki tab'a zama matarshi ba, dan haka ki cire shi a ranki tun wuri, sannan kuma ina so ki sani, wani al'amari zai iya kasancewa akanki ko akan Arshad kuma mummuna, ina nufin ɗaya daga cikinku zai ji rayuwa ta daina mai daɗi, har ma ya gwammaci mutuwarsa, sai dai bansan taya hakan zai faru ba, amma dai ku shirya.....Hahahaha" haka aka ƙarasa zancen da dariyar mugunta, mai firgitarwa

Wayarta ta ɗauka, zuciyarta na dukan uku-uku, ta shiga neman numbern da tayi saving da HEARTBEAT, ta daɗe tana ringing sannan ya ɗauka

"Hello" ya faɗa cikin muryar bacci

Ajiyar zuciya ta sauke da taji muryarshi, "hello" ita ma ta sake maimaitawa

"Lafiya dai Jasmine? Kin ga time ɗin da kika kira kuwa?" ya faɗa yana hamma yana ƙara murza idanunshi dake ta rufewa saboda bacci

Sai a lokacin ta tuna ma dare ne, wayarta ta duba, karfe 2:39am na dare, sai ta ɗan rufe baki "kayi haƙuri dan Allah, wallahi na manta ne"

Tashi yayi ya zauna, ya ce "ba mantawa kika yi Angel, a ruɗe kike ne lokacin da kika kira ni, ko ba haka ba?"

"Ya aka yi ka sani?"

"Na san lafiya ba zata sa ki kira ni cikin wannan daren ba, dole akwai matsala, kuma wannan matsalar ce tayi forcing ɗin zuciyarki ta kira ni ba tare da kin duba agogo ba, dan haka ki gaya mun menene, jikin Ummi ne?"

"Hmm, a'a"

"To mafarki kika yi?"

A hankali ta ce "eh"

Murmushi yayi ya ce "kin yi mafarkin na mutu ne ko kuma zan mutu gobe a hanya?"

Ji tayi gabanta ya faɗi, ta ce "meye haka kuma dan Allah?"

Dariya ta ba shi saboda yanayin yanda tayi maganar kamar zata yi kuka

"To i'm sorry (kiyi haƙuri)" ya faɗa yana dariya

Ƙaramin tsaki tayi, ta ce "sai da safe"

"Don't hang up please (kar ki katse dan Allah), na ce kiyi haƙuri wasa nake yi"

"Wasa da mutuwa?" ta faɗa tana b'ata rai

"To bazan sake ba your highness, kinji"

Shiru tayi ba ta ce mishi komai ba, ya sake ce wa "dan Allah kinji"

"Shikenan, naji"

"Yawwa, to gaya mun menene"

"Kawai mafarki nayi, amma ka bari sai ka dawo sannan zan gaya maka"

"Meyasa ba za ki gaya mun ba yanzu"

"Ka dai bari sai ka dawo, yanzu ka kwanta, dama muryarka nake son ji shiyasa na kira"

"To shikenan, lafiya ƙalau nake, kuma zan dawo lafiya in sha Allah, kinji ko!"

"Allah ya dawo da kai lafiya to"

"Ameen Hearty, matar AAJ" ya faɗa cikin daddaɗar murya

Ta ji daɗin abunda ya faɗa, sai dai ta tuna da mafarkinta, a ranta ta ce 'ina fatan hakan Chubby', a zahiri kuma ta ce 

"Sai da safe dear"

"Bye" sai suka kashe wayar tare

Ta daɗe a zaune, sannan dai tayi addu'a ta kwanta, shi kuma sai da yayi nafila sannan ya sake kwantawa

********************

Da safe bayan su Yasmin sun gama shirin makaranta sun yi break-fast, Ammi ma ta shirya cikin swiss less ɗinta mai kyau, ta sa gyale 3 in 1, sai suka fito tare

Da gudu driver ya zo, ya durƙusa ya gaida Ammi, ya tashi zai buɗe mata mota, sai ta ce

"Bani mukullin kawai, zan kai su da kai na dan akwai wurin da nake son zuwa"

"To Hajiya, Allah ya kiyaye" ya faɗa cikin girmamawa yana bata mukullin

Buɗe motar suka yi suka shiga, sannan ta ja su suka wuce. A bakin gate ɗin makarantar ta ajiye su, sannan ta wuce, bata tsaya ko ina ba sai ƙofar gidan Hajiya Karime, aka buɗe mata gate ta shiga

A palour ta taradda Hajiyar, ta zauna suka gaisa

Ammi ta ce "ina Farha? Ko bata tashi daga baccin ba?"

Hajiya Karime ta ce "ta tashi har ma ta fita ai"

"Ok....Hajiya kin ga na miki zuwan safe ko?"

"Nima dai shi ne nake ta mamaki ai, Allah ya sa lafiya"

"Lafiya ba amma lau ba, dan wallahi Hajiya na kasa natsuwa akan yaron nan, kin san yau zai dawo, to ban san da wane irin zance zai dawo ba, ina fargaba kar su amince mishi da auren Hanan fa"

Ajiyar zuciya Hajiya Karime tayi haɗi da yin murmushi, ta ce "yanzu kina nufin ɗan wannan abun ne ya taso ki da safe haka?....Hmm to yanzu ya kike so ayi?"

Gyara zama tayi, ta ce "yawwa, ina maganar Malamin da kika ce ya tabbatar miki zai iya raba mana su! To ya ake ciki?"

"Shekaran jiya mun tafi, kuma ya ce aiki na tafiya yanda ya kamata"

"To alhamdulillahi, amma dai ina so ki tashi yanzu mu tafi sai mu ji"

Dariya tayi ta ce "kin dai tsorata da maganar zuwa  Adamawan nan da yayi"

"Bari kawai, ni na san ba zuwan Allah da Annabi ba ne, kin san yanda na ƙi jinin talaka wallahi, ke ni da ya aure ta gwara ya sake shekaru biyar ba aure"

"Har biyar! Kar fa ayi abun kunya" Hajiya Karime ta faɗa tana ƴar dariya

"Yo da ya ɗauko mun tsiya kuma fa?"

"Allah dai ya kyauta, amma ba zai aure ta ba kuma ba zai ƙara ko da shekara ɗaya ba tare da ya auri Farha ba"

"Allah ya sa" cewar Ammi

"Ameen, amma yanzu kin ga 8:32am, mu bari zuwa 10 sai mu tafi"

"To ba damuwa"

Sai suka ƙara zama suka ci gaba da tattaunawa

********************

Duk wani shirin tafiya Arshad ya gama shi, ya je gidan Anty Fati su yi sallama da ita da sauran ƙannenshi kafin su wuce makaranta, dan fitar safe yayi dan ya same su gida

Ya gama sallama da su sai ya wuce palourn Abba, kamar yanda Anty Fati ta gaya mishi cewa yana son ganinshi, kasancewar sun gaisa, sai kawai Abba ya fara maganarshi dan kar ya tsayar da shi

"Arshad, na san abunda na gaya maka jiya bai maka daɗi ba kasantuwar saboda wannan maganar ce ya sa ka zo garin nan, ko ba haka ba?"

Ɗaga mishi kai Arshad yayi, sai ya ci gaba da cewa "to ina so ka sa ma zuciyarka tawakkali da haƙuri, na san kana da su, amma akan wannan yarinyar sai naga kana nema ka cire su a ranka, to ka sani, duk jajircewar da za kayi, matuƙar ba matarka ba ce, ba za ka tab'a samunta ba, idan kuma matarka ce, ko ana muzuru ana shaho sai ka aure ta, kuma ni kai na zan so ace ka auri yarinyar da kake so ɗin"

Kallonshi Arshad yayi ya ce "to Abba idan haka ne, ka taimaka mun dan Allah kar ka bari in rasa Hanan, wallahi Abba ina sonta, bana jin zan amfana a duniyar nan idan har ba same ta ba"

Shiru Abba yayi saboda yayi mamakin yanda Arshad ya iya kallonshi ya ce wai yana son wata, duk da ba shi bane mahaifinshi, amma ya san Arshad na da kunya, kuma bai yi tunanin zai iya gaya mishi haka ba, sai ya ce "Arshad kayi haƙuri, ka riƙa yin addu'a ba abunda zai same ka ko da ace ka rasata, amma ba na fatan haka, ka je kawai in sha Allah nan da sati ɗaya zan aiko wani tare da Jafar dan ayi bincike ƙwaƙwara akansu"

"To Abba, nagode sosai, Allah ya ƙara lafiya"

"Ameen, Allah ya kai ka lafiya"

"Ameen, na bar ka lafiya"

Sai ya tashi ya fita ya bar Abba zaune yana tunani

A bakin motarshi ya taradda Jafar, dan shi kaɗai ne bai fita ba sai anjima

Jafar ya ce "ya dai Ya Arshad?"

"Hmm, maganar ɗaya ce dai, wai za'ayi bincike, amma ka san wai hadda kai cikin masu binciken"

Gyara tsayuwarsa Jafar yayi ya ce "da gaske Ya Arshad?"

"Eh, amma meye abun jin daɗi haka?"

"Ai dole ne mu ji daɗi dan har da kai, ba dai da ni za'a yi bincike ba! To ka sa ma ranka ba za ka tab'a auren Farha ba, dan wallahi binciken ƙwaƙwaf zan mata"

Murmushi Arshad yayi ya ce "Jafar idan baka son mutum ya shiga uku wallahi, mutum ya ji tsoron Allah ya ji tsoron miskilin mutum"

Wani murmushin gefen baki Jafar yayi, wanda duk wanda ya gani ya san na mugunta ne, ya ce "Allah dai ya kai ka lafiya Ya Arshad, sai mu zo"

"To shikenan, Ameen", suka rungume juna sannan Arshad ya shiga mota shi kuma Jafar ya wuce part ɗin su

Sai da ya ƙara komawa gidan Hajjo ya ɗauki kayanshi, suka sake yin sallama bayan sun yi halinsu kamar yanda suka saba, sannan ta rako shi har bakin mota, tana jin ba daɗi, har da ɗan hawayenta

Dariya ma ta ba shi, ya ce "Haba matas, kar ki damu, zan sake dawowa ai nan ba da daɗewa ba, sai dai ni da kishiyarki za mu zo dan ta gaishe ki"

Tana share hawayen ta ce "ai ba zan bari ma sai ka zo ba, ni da kaina zan zo ganin wannan kishiyar ta wa"

Mutmushi yayi, ya ce "to Allah ya kawo mana ke ƙalau"

"Ameen, A sauka lafiya"

Ya shiga mota ya wuce sannan ta koma cikin gida

********************

Zaune yake kan kujerarshi ta aiki yana ta aiki cikin laptop ɗin shi, lokacin da Gboy ya shigo tare da wani mutum

Tashi yayi suka yi musabaha da mutumin sannan ya ba shi damar zama, suka zauna tare, Gboy ma ya ja ɗayar kujeran ya zauna

"Alhaji Zayyad manya ƙasa" cewar MK yana dariya

Shi ma Zayyad ɗin dariya yayi, ya ce "idan ba ku nan kenan MK"

Dariya yayi ya ce "haka dai ka faɗa"

"Haka ne ma"

"To shikenan, yanzu dai taimakonka nake nema shiyasa na buƙaci ganinka"

"Ai ka fi ƙarfin ka nemi taimako, ka gaya mun kawai me kake so"

"Zayyad, harka ce ta samu, waɗannan kayayyakin ne nake so za'a shigo mun da su"

"Kai kuma?" Zayyad ya faɗa da mamaki

"Ƙwarai kuwa, sai dai ba da sunan company ɗinnan ba"

"To da wane company kenan?"

"Zan gaya maka dan cikin sirri nake so ayi, kamar yanda muka tab'a yi a Katsina"

Murmushin mugunta Zayyad yayi, ya ce "kenan dai akwai wanda ya shiga gonarka"

"Ƙwarai kuwa, kuma fita zai mishi wuya ba"

Dariya Zayyad yayi ya ce "wallahi kai dai mugu ne, waye wannan ɗin"

"Abokin mugu ma mugu ne, dan haka ni da kai muna tare"

"Amma ai kai ne babba, yanzu dai duk ba wannan ba, wanene wannan da fitina ke shirin ƙwanƙwasa mishi ƙofa?"

MK ya buɗe baki zai yi magana, sai dai bai samu furta zancenshi ba, aka ƙwanƙwasa ƙofar office ɗin, kallon ƙofar suka yi a tare, sannan MK ya ce "come in (shigo)"

Hanan ce ta turo ƙofar ta shigo, sai da ta kai tsakiyar office ɗin sannan ta tsaya, ta gaida su, suka amsa mata, MK ya ce ta ƙaraso.Kusa da table ɗinshi ta tsaya daga gefe

Kanta a ƙasa, ta ce "Yallab'ai gani, ina fatan ban makara ba"

Agogo ya duba, sannan ya ce "a'a Hanan, kin zo a lokacin da ya dace, nagode da cika alƙawari"

Murmushi kawai tayi, sai ya ci gaba da cewa "Hanan dama aikin da nace miki zan sa ki, ba wani babban aiki bane, kin ga wannan" ya faɗa yana nuna Zayyad, wanda tun lokacin da ta shigo har yanzu idanunshi na kanta, har ta gaji da wannan mayen kallon

Ba tare da ta kalle shi ba, ta ce "eh na ganshi"

"Sunanshi Zayyad Abdallah, ƙwararre ne wurin iya shigo da kayayyaki masu ƙarko da inganci daga ko wace ƙasa, ya kawo mun wani contract ne (kwangila) dan inyi signing, sai dai na akwai waɗanda aka kawo mun kusan guda uku, idan na haɗa da na shi za su mun yawa, to shi ne yake so yayi da wani babban company, kuma na san ba wani babban company a garin nan sama da na AAJ"

Kallonshi take cikin rashin fahimtar inda zancen na shi ya dosa, ta ce "sai dai yallab'ai ban san me kake so ni inyi ba, ai irin wannan ba aiki na bane"

"Tabbas ba aikinki bane, amma anan ya zama aikinki, kin san na san AAJ na cike da haushi na, duk da kince kin ba shi haƙuri, amma ina shakkar tunkararsa, sai nake ganin kamar ba zai yarda da ni ba......abunda dai nake so ki mun shi ne, ina so kiyi mana jagora izuwa wurin AAJ dan in ƙara ba shi haƙuri sannan kuma in gabatar mishi da contract ɗin"

Shiru tayi tana nazari, sannan ta ce "amma taya ni zan maka jagora, bayan ni ba secretary ɗinka bace?"

"Za ki wakilce ta"

"To amma....."

"Dan Allah Hanan, kar ki manta kince za ki ɗauke ni tamkar ɗan uwanki, kenan ba za ki iya taimaka ma ɗan uwanki ba?"

"A'a ba haka nake nufi ba......shikenan dai, zan raka ka, amma a matsayin ma'aikata zamu tafi ba wai a matsayin wacce ke da alaƙa da AAJ ba"

"Ba damuwa, godiya nake, gobe sai mu tafi ko?"

"Allah ya kaimu"

"Ameen, za ki iya tafiya"

Haka ta ja jiki, ba ƙwari ta fita, dan tunani ne ke zuwa kanta kala-kala

Tana fita MK yayi murmushi, ya ce ma Zayyad "kana tambaya akan wanda fitina ke tunkara ko?"

Zayyad ya ɗaga kai, MK ya ce "to AAJ ne da wannan yarinyar, sai dai kowa da irin na shi fitinar"

Zayyad ya ce "AAJ dai!?"

"Ƙwarai kuwa"

"Kana nufin waccen asarar da ya saka shekarar da ta wuce shi ne har yanzu baka ɗauki mataki ba?"

"Eh, amma yanzu hukuncin biyu ne, dana asarar da ya sa ni da kuma na tozarta ni da yayi gaban ma'aikata na"

"Lallai ashe ya ɗebo ruwan dafa kansa......amma ni fa wannan yarinyar kar ka mata komai, ka bar mun ita mana"

"Ta maka kenan?"

"Sosai ma kuwa, ai irinsu ake kira hot ladies"

Dariya MK yayi, ya ce "ai shikenan, kayi yanda kake son yi da ita, dama budurwarshi ce, kuma ya ce wai she's his own happiness (ita ce farincikinshi) ina so ka lalata mishi wannan farincikin"

"Ba ka da matsala MK, ka san ni, ba ni da dama ai" ya ƙarasa yana wani murmushi

"That's good (yayi kyau)......Gboy, ka raka Zayyad, daga nan sai ka ƙarasa mishi bayanin da ya rage"

Gboy dake zaune tun ɗazu bai ce komai ba sai faman gyara wasu takardu yake yi, ya ce "to Yallab'ai"

Suka tashi shi da Zayyad suka fita.MK yayi murmushi yana girgiza sannan ya ci gaba da aikinshi

********************

Ammi da Hajiya Karime ne zaune a gaban Malam yana ta jan carbi yana zane da ƙasar dake cikin tray

Sannan ya kalle su ya ce "Hajiya, wannan aikin an gama shi, domin tabbas naga ranar rabuwar Arshad da Hanan"

Fara'a fal a fuskokinsu, Ammi ta ce "alhamdulillahi, ɗa na zai rabu da tsiya, sai dai a bi wani bokan"

Hajiya Karime ta ce "ƙwarai kuwa Hajiya"

Malam ya ce "sai dai kuma, na fahimci ɗanku yana da tarin maƙiya, ma su son ganin bayanshi"

Hajiya Karime ta ce "ai dama duk inda mai arziki yake yana da maƙiya, daga cikin maƙiyansa ma ai hadda wannan matsiyaciyar Hanan ɗin"

Ammi ta ce "tabbas, kuma in Allah ya yarda ya fi ƙarfinsu wallahi"

Malam ya ce "to shikenan, za ku iya tafiya ai, ina da baƙi waje" ya faɗa dan ya fahimci duk yanda zai musu bayani ba fahimtarshi za suyi ba

Ammi ta ciro bandir ɗaya na ƴan dubu-dubu guda ɗaya ta ba shi sannan suka fita su na ta murnar samun wannan labari

********************
Sai da yamma sannan Arshad ya iso gida, yana ajiye motar ya wuce part ɗinshi, wanka yayi, yayi sallah, sannan ya dawo main palour

Yana shiga, Yasmin da Yasna suka zo da gudu suka rungume shi su na ta jin daɗi

Ammi dake zaune ta ce "to kuyi sauri ku yadda shi, mutum ya dawo da gajiya ku wani riƙe shi haka"

Yasmin ta ce "ai Big Bross ɗina jarumi ne, ba zai faɗi ba, ko?" ta ƙarasa tana kallon Arshad

Murmushi yake tayi, ya ce "sosai ma kuwa, ba kiyi ƙarya ba ta Big Bross"

Suka yi dariya, Ammi ta ce "au haka ma ka ce"

Yasna ta ce "ai gaskiya ne Ammi"

"To ai shikenan, sai ku bar shi ya ci abinci"

Suka yi dariya, sannan suka wuce dinning area dan haɗa mishi abinci, shi kuma ya ƙaraso wurin Ammi suka gaisa tana tambayar su Hajjo

Yasna ta zo ta ce "Sweet Bro mu tafi ga abincin can"

"Yasna ba yanzu ba, sai anjima"

Ammi ta ce "haba! Tun ɗazu fa nake bibiyarsu su ci abinci suka ce sai ka dawo ku ci tare"

"Oh! To kuyi haƙuri, mu tafi"

Ya ja su suka je suka ci abincin, yana basu labarin su Nabeela da Hajjo

Yasmin ta ce "wallahi nayi kewarsu"

Arshad ya ce "ai zuwa next week in sha Allah Jafar na nan zuwa"

Yasna ta zaro ido, ta ce "me!!??"

Dariya Arshad yayi sosai, dan ya san Yasna ba ta son abunda zai haɗa ta inuwa ɗaya da Jafar, saboda tsoronshi take ji, ya ce "eh, kuma sati biyu ma zaiyi"

Kamar za tayi kuka, ta ce "shikenan watan kuka na ya tsaya"

Arshad ya ce "ai dan ba kya jin magana ne yasa ba kwa shiri, amma kin ga ai Yasmin ba ruwanshi da ita"

"Ina jin magana fa, kawai dai baya so na ne"

"Wa ya gaya miki! Yana sonki sosai Sweetie"

Turo baki tayi kawai alamar dai ba ta yarda ba, Ammi da zuwanta kenan taji ana maganar Jafar, sai ta zauna, ta ce

"Zuwa zai yi ne?"

"Eh Ammi, amma sai next week" cewar Arshad

"Lallai, ashe muna da babban baƙo a gidan nan, ni ya zo ma ya mun maganin wannan fitinanniyar kafin ya koma"

Yasmin da Arshad suka sa dariya, Yasna kuwa ta shagwab'e ta ce "Ammi har da ke? Autarki ce fa"

"Ayya yi haƙuri, na ɗauka ai Yasmin ce, yi haƙuri autar Ammi"

Sai ta jawo ta ta rungume kasancewar su na kusa, sai murmushi take tayi, Arshad kuwa in banda aikin kallon Ammi ba abunda yake yi, ya gaza haƙuri, sai da ya ce 

"Ammi tun da na dawo na fahimci kamar kina farinciki sosai, na kwana biyu ban ga fara'arki haka ba"

Yasna ta ɗaga daga jikin Ammi, ta ce "wallahi nima yau mamakin Ammi nake tayi, Ammi ki gaya mana menene?"

Ƙara faɗaɗa murmushinta tayi ta ce "ina farinciki ne saboda wani fitina dake tunkaro gidan nan, na kau da shi"

Yasmin ta ce "fitina kuma?"

Ɗaga mata kai tayi, Arshad ya ce "wace irin fitina kuma Ammi?"

"Kar ku ɗaga hankalinku, zan gaya muku amma ba yanzu ba, sai na tabbatar da mun rabu da fitinar"

"To shikenan, Allah ya tsare mu daga wannan fitinar da sauran fitintinu na duniya da lahira" cewar Arshad

Suka haɗa baki wurin amsa mishi da "ameen"

Ammi kuwa a ranta cewa tayi 'na ji daɗin wannan addu'ar da kayi da kanka, kuma in sha Allah wannan fitinar Hanan, sai ta rabu da kai kwanan nan'...........









MUJE ZUWA DAI, AI YANZU AKA FARA🤩




🥰UMMEETA🥰......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 25* 

Bayan sallar magrib, Arshad ya tafi gidansu Sajjad, a harabar gidan suka haɗu, Sajjad ɗin na ƙoƙarin shiga mota, sai ya rufe motar ya fasa shiga har Arshad ya gama parking ya fito

Rungume juna suka yi cikin murna sai ka ce waɗanda suka yi wata ba su haɗu ba, Sajjad ya ce
"Shi ne ka zo ba ka jira ni ba, dan fitowar nan da nayi wurinka za ni"

Arshad yayi murmushi ya ce "yau fa Monday, na san ka gaji da aikin company shiyasa kawai na ce zanzo"

"To mu shiga daga ciki" ya faɗa yana murmushi

Palourn gidan suka shiga, Hajiya(mahaifiyar Sajjad) tana shirya abinci kan dinning, ganinsu da tayi ne ya sa ta sauko tsakiyar parlourn da fara'arta

Ta ce "mutanen Adamawa, an dawo lafiya?"

Sai da suka ƙaraso cikin parlourn suka zauna, sannan Arshad ya ce "lafiya ƙalau Hajiya, ya gida"

"Lafiya ƙalau" ta amsa bayan ta zauna

Ya ce "ina Inti da Mujaheed?"

"Su na gidan Zainab, mijinta yayi tafiya, shi ne suke taya ta kwana"

"Allah sarki"

Daga nan suka yi ta hira su uku, har aka yi isha'i, Alhaji (mahaifinshi) ya dawo, sai suka wuce masallaci, su na dawowa suka wuce part ɗin Sajjad su ka ci gaba da hirarsu

Sajjad ya ce "yawwa Super, na ma manta ban gaya maka ba, ɗazu Mr Joseph ya zo tare da manager ɗinsu, sai dai na gaya musu su dawo gobe"

"Eh Directornsu ya kira ni ina hanya, mun yi magana, ya turo mun da waɗancan kuɗin, yanzu kayan da suke so ɗin ne za'a basu idan sun zo goben"

"Da yawa suke so fa"

"Kayan 5billions ne ya ce"

"Amma kana ganin ba matsala idan aka basu? Ka san fa yanda muka yi da su a waɗannan fa!"

"Zamu yi yarjejeniya da su gobe ɗin"

"To a damuwa, Allah ya kaimu lafiya"

"Ameen, bari in wuce, ka ga har ƙarfe goma ta wuce"

"To shikenan, nagode sai mun haɗu goben"

"Yawwa"

Har bakin motarshi ya raka shi sannan ya koma cikin gida

Sai kusan goma da rabi sannan Arshad ya isa gida, part ɗinshi ya wuce dan ya san sunyi bacci, shi ma yana shiga wanka yayi, yayi alwala yayi shafa'i da wutri sannan ya kwanta ya tura ma Hanan  night message mai daɗi dan yana tunanin tayi bacci ita ma, yana gama turawa ya kwanta.

********************
Washe gari da safe Arshad na office ɗin shi tare da Khairat, tana mishi bayanin abubuwan da akayi da ba ya nan, Sajjad ya shigo tare da su Mr Joseph su uku kasancewar ƙofar a buɗe take, umurtarsu yayi da su zauna ka cushions ɗin, sannan ya sallami Khairat shi kuma ya zo wurinsu ya zauna

Sai da suka gaisa sannan suka fara gabatar da abunda ya kawo su, sunyi yarjejeniya akan nan da wata huɗu za su biya shi kuɗin, suka yi signing sannan ya umurci Sajjad da yasa a ba su kayan

Bai jira su ba ya tashi ya koma kan kujerarshi ta aiki, su ma suka tashi suka fita, a bakin ƙofar office ɗin suka haɗu da su MK za su shiga, Mr Joseph yayi ma MK murmushi, shi ma MK murmushin ya mishi a fakaice kamar yanda ya mishi

MK, Zayyad, Gboy da Hanan suka ƙarasa cikin office ɗin yayin da su Sajjad suka fita bayan ya gama kallon MK cikin mamaki

AAJ bin su yake da ido, fuska a turnuƙe kamar bai tab'a jin kalmar fara'a ba a rayuwarshi, har suka ƙaraso bakin table ɗinshi

Gboy da Hanan suka tsaya daga bayan kujerun da ke wurin, Zayyad da MK kuma suka ja kujerun da niyar zama

A tsawace AAJ ya ce "are you insane?(ba ku da hankali ne?)" yana bin su da mugun kallo, su kuma suka yi tsaye su na kallonshi

MK ya ce "what happen?(meya faru?), kayi haƙuri wurinka muka zo kuma da alkhairi"

Ƙara haɗe rai yayi, ya ce "da ku ka zo wurina sai kuma akace kar ku nemi izinina kafin ku shigo? Har kuke ƙoƙarin zama?"

Zayyad ya ce "amma ai munyi magana da secretary ɗinka"

"Ita ce AAJ ɗin ko kuma ni?"

Kallon-kallo MK da Zayyad suka shiga yi, Gboy ya ce "kai ne yallab'ai, amma kayi haƙuri tunda mun shigo"

Wani kallo ya aika ma Gboy ya ce "ba da kai nake magana ba, da ubangidanka nake yi"

MK ya ce "to kayi haƙuri, ko dan albarkacin Hanan, wani aikine ya kawo mu"

Ko kallon gefen Hanan baiyi ba, ya ce "aiki ka zo yi nan ko nuna mun mace? To ban ganta ba, ku koma ku nemi izini sannan ku shigo"

Wannan karon hadda Hanan sai da ta kalle shi cikin mamaki, dan ji take yi  bata tab'a jin tana tsoronshi ba sai yau, dan kamar ba Arshad ɗinta da ta sani ba

MK ya ce "amma ai......."

A tsawace ya katse shi da "ai me?? Dallah Malam ku fita idan na baku izini sai ku shigo, ko kuma ku koma inda kuka fito"

MK zai yi magana, Zayyad ya dafa shi yana girgiza kai, sai suka fita, MK sai huci yake

Gboy yayi ma Khairat magana, sannan ta shiga office ɗin AAJ ta barsu a nan

Zayyad ya raɗa ma MK cewar "ka kwantar da hankalinka mutumina, wannan fushin ba naka bane, ka barshi ya shigo hannu kawai, zai yi bayani, kyale shi yayi iskanci da ya ga dama yanzu, lokacinshi ne, muma namu na zuwa" daga jin haka sai kawai MK yayi murmushi, ya ji ya manta da wulakancin AAJ

Khairat ce ta fito sannan ta ba su izinin shiga, sai da suka sake neman izininshi sannan suka zauna suka gaisa

Haƙuri MK ya fara ba shi akan abunda ya faru kwanan baya, sannan ya gabatar mishi da Zayyad da kuma ƙudirinsa

Shiru AAJ yayi, ya ce "i can't accept this contract (ba zan iya yarda da wannan kwangilar ba)"

Zayyad ya ce "meyasa?"

"Sabida ban tab'a harƙalla da kai ba"

"Amma ya kamata ka yarda dani, nima ina so na shiga jerin waɗanda suke harka da kai, kana burge ni yanda kake tafiyar da kasuwancinka"

"Duk da haka dai, zanyi tunani"

MK ne ya kalli Hanan da alamar ta sa baki

Cikin fargaba ta ce "dan Allah ka yarda yallab'ai, muna son yin harka da company ɗin nan shiyasa takanas muka zo ba muyi aike ba, dan Allah"

Kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke ido, ya ce "ban amince ba, nace zanyi tunani akai"

Ta ce "tunanin m......"

Katse ta yayi da "ban son takura, nace  zan duba, dan haka you can leave pls(zaku iya tafiya dan Allah) akwai aiki a gabana" ya faɗa rai a b'ace, sai dai a zuciyarshi yana jin ba daɗi saboda yanayin da yake mata magana

MK ya ce "shikenan, mun ba ka lokacin, mun gode"

Sai suka tashi suka wuce, Hanan jiki a sanyaye dan tana ji kamar ta ba shi haushi, shi ma binta yake da ido har suka fita, sannan ya nisa ya ci gaba da aikinshi


Kusan minti talatin da wucewarsu MK sannan Sajjad ya shigo ya zauna

Ya ce "Man me MK ya zo yi nan kuma na ganshi tare da Hanan, ko wani abu ne"

Sai da ya jingina bayanshi jiki kujerarshi sannan ya ce "ba wani abu bane, wai abokinshi ya kawo mun yana so muyi aiki tare"

"Sai ka ce me? Ka amince?"

Murmushi yayi, ya ce "ban amince ba, sai dai ina tunanin amincewa saboda Hanan"

"Ban gane saboda Hanan ba!" Sajjad ya faɗa da alamun ranshi ya so ya fara b'aci

"Eh mana, ko kana da matsala da hakan ne?"

"Matsala ma kuwa, wannan fa maganar aikinka akeyi ba wai zancen soyayya ba"

"To me kake nufi?"

"Ni kwata-kwata ban yarda da wannan kwangilar ta MK ba, kar ka amince, dan banson abunda za ka dawo kana dana sani"

Murmushi AAJ yayi, ya ce "ba maganar dana sani, na tabbata da akwai matsala, Hanan ba za ta so in amince ba, yanzu ma na jinkirta ne dan ina so sai nayi magana da ita"

Tsakin takaicin wannan magana ta AAJ Sajjad yayi, sannan ya ce "ta ya Hanan zata iya gane abunda ke cikin ranshi!?"

"Calm down Man, na ga ranka ya b'aci, na san ba ka yarda da MK ba, nima haka, amma in sha Allah ba abunda zai iya yi"

"Matsala ta da kai na ci, duk abunda zan gaya maka na san ba ganewa za kayi ba tunda har ka yarda da Hanan, amma ba komai, Allah ya tabbatar mana da alkhairi"

"Ameen...haka ya kamata ka ce kawai My Man, just relax"

Ajiyar zuciya Sajjad yayi, sannan ya mishi sallama kan cewa yana da aikin da zaiyi a office, sai ya fita ya barshi shi ma ya ci gaba da na shi aikin

********************

Hanan na komawa gida bayan la'asar, tayi wanka tayi sallah ta ci abinci, sannan ta ce ma Ummi zata tafi wurin Yuhanees

A tsakar gida ta taradda Yuhanees da Umma zaune suna gyara alayyahu, sai da suka gaisa da Umma sannan suka shiga palour da Yuhanees

Tsab ta karanto mata mafarkinta na jiya, ta ƙara da cewa "Rabin Rai mafarkin nan ya tsaya mun a rai wallahi, jikina na bani kamar da gaske ne rabuwa za muyi, kuma wallahi ina tsoron wannan ranar"

Yuhanees ta ce "kai Hayatee, ni wallahi har kin sa na ɗauka wani babban abu ne, mafarki ne fa"

"Hmm, Rabin Rai kenan, amma kin san wani lokacin mafarki na zama gaskiya ko?"

"Wani kika ce Hayatee, in sha Allah wannan ba komai ba ne, kawai dai dan kinsa maganar Amminshi ne a ranki ya sa kika fara wannan tunanin, amma ai kin ga da ba kiyi wannan mafarkin ba"

Shiru ta dan yi, sannan ta ce "kuma fa maganarki akwai kamshin gaskiya, tunda ance mutum na yawan mafarki ne akan abunda ya sa ma ranshi, sai dai gaskiya hankali na bai kwanta ba"

"Dallah kar ki ba ni kunya mana, in sha Allah ke da AAJ har abada"

"Allah yasa hakan Rabin Rai"

"Ameen, yanzu dai tashi mu koma wurin Umma"

Suka tashi suka fito cikin gidan, sai suka ga Yayan Yuhanees, Mashkur su na magana da Umma, Yuhanees ta ce "Ya Mash yaushe ka shigo?"

"Anty Yuha da Anty Hany, magulmatan Umma, ku na ɗaki kuna gulmar ina za ku san lokacin da na shigo?" 

Hanan ta ce "ba wani gulma, mun gaya maka ka daina ce mana magulmata, za muyi maganinka fa!"

Ɗan buɗe baki yayi, ya ce "yi haƙuri Anty Hany, na manta yanzu ke matar AAJ ce ko?"

Turo baki tayi ta ce "Umma kice ya kyale ni"

Umma ta ce "tsakaninku ne, ba ruwana"

Dariya yayi ya ce "nima sake fita zanyi ba sai kin b'ata rai ba Hajjaju, bye"

Ya fita yana dariya, su ma dariyar suka yi sannan suka zauna suka ci gaba da yanka alayyahun

********************

Bayan magrib sai ga Arshad ya zo, cikin zaure suka zauna suka yi hirarsu, fiye da minti talatin, sannan Arshad ya ce "Hanan!"

Kallonshi tayi dan ta daɗe bata ji sunanta a bakinshi ba, ta ce "na'am"

"Meye gaskiyar maganar contract ɗin nan na MK?"

A shagwab'e ta ce "ban sani ba, ni da kayi ma wulaƙanci ɗazu dan kawai munzo wurinka, ko dan nayi shiru?"

Dariya yayi ya ce "haba gimbiyar Arshad, kiyi haƙuri, nima banyi dan in b'ata miki ba, nayi ne kawai saboda MK"

"Amma shi ne ka kore mu hadda cewa baka ganni ba"

"Naji dai, kiyi haƙuri duk saboda shi ne Allah, kinji"

Sai tayi ajiyar zuciya ta ce "to naji"

"Yawwa matas, to gaya mun"

"Nima ban sani ba, amma Zayyad ɗin abokinshi ne, suna kasuwanci tare"

"To meyasa wannan ba za suyi shi tare ba sai dani? Ba kya ganin kamar akwai matsala?"

"Da shi ya so suyi, sai dai yanada contracts biyu da ya karb'a shiyasa ya ce zai kawo maka shi ko dan ka sake yarda da tuban da yayi, ku shirya"

"Mu shirya? Ai ba shiri tsakanina da shi"

"Amma contract ɗin fa? MK yana so ka yafe mishi fa"

"Ta ya kika gane?"

"Yayi sanyi sosai, kamar ba shi ba, na tabbata ba wani mugun abu a ranshi"

"A taƙaice dai kina so in karb'a"

"Eh, ka yarda dani ba komai"

Shiru yayi bai ce mata komai ba, ta ce "ka yarda mana My Charming Prince, nothing will happen (ba abunda zai faru)"

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce " shikenan, naji, ki gaya mishi ina son ganin Zayyad ɗin gobe"

"Yawwa, to mun gode"

"Ba komai......yanzu dai kam bari in wuce ko! Dare yayi"

"To shikenan Sweetie na, Allah ya kai ka lafiya"

"Ameen"

Suka tashi, ta mishi rakiya har bakin mota, ya haɗa ta da tsarabarsu tayi godiya sannan ya wuce, ita kuma ta shiga gida...............






KUYI HAƘURI DA WANNAN HAKA NAN DAN ALLAH🙏


🥰UMMEETA🥰......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA




        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 26* 

Kamar yanda Arshad ya ce Hanan ta gaya ma MK yana son ganin Zayyad, haka kuwa akayi, dan ya zo ya sameshi da safe, suka tattauna akan contract ɗin sannan ya sa hannu, Zayyad sai faman godiya yake yi kamar da gaske

Duk maganar da suka yi, Sajjad na zaune yana kallonsu,  lokacin da AAJ ya sa hannu a takardar sai da ya ji gabanshi ya faɗi, gaba ɗaya hankalinshi ya kasa kwanciya da wannan abu da Arshad yayi

Bayan Zayyad ya fita, Arshad ya kalli Sajjad da ya ɗaure fuska, ya ce "wai menene kake ta wani cin magani ne haka? Tun da ka shigo office ɗin nan na ga ranka a b'ace, ko dai dan kunyi faɗa da baby love ɗinka ne?" ya ƙarasa maganar da zolaya

A tsawace cikin b'acin rai, Sajjad ya ce "just stop pretending as if you don't know what's going on, i'm very sure you know what's in my mind (ka daina wayancewa kamar ba ka san abunda ke faruwa ba, na tabbata ka san abunda ke raina), me ka aikata ne haka? Maganar da nayi maka jiya a banza nayi ta kenan?"

Yayi mamakin yanda Sajjad ya mishi tsawa, dan tun da suke bai tab'a yi mishi magana irin haka ba, duk kuwa yanda ya b'ata mishi, hakan ya tabbatar mishi da bai ji daɗin yarda da wannan contract ɗin da yayi ba

Ya ce "ba'a banza kayi ba My Man, amma ai na gaya maka zanyi magana da Hanan inji gaskiyar wan......"

Katse shi yayi da "wai ka ji gaskiyar me Arshad?! Ta ya kake tunanin wai za ta san abunda ke ranshi? Sakarai ne shi aka gaya maka da har zai bari ta gano manufarshi?"

"Amma ai zata iya fahimta daga yanayinshi, na tabbata yanda Hanan ke sona, ba zata yarda ta haɗa baki da waɗanda za su cutar da ni ba, hasali ma tana da ra'ayi a hakan kuma zan iya yi mata komai a duniyar nan"

Wannan maganar ta ƙara harzuƙa Sajjad, ya ce "amma ban tab'a sanin baka da hankali ba sai yau, wallahi na san kai ma a ranka ba ka so yin hakan ba, saboda kawai Hanan ta sa ka ne, kana so mace ta fara juya ka kenan tun yanzu? Ka zama bawan mace?"

A nan take Arshad ya ji shi ma ranshi a b'aci, ya ce "dan kawai nayi abunda nake ganin dai-dai ne shi ne kake mun kallon mahaukaci? Me ya ba ka tabbacin ban so yin hakan ba?"

"Dole in maka kallon mahaukaci Arshad, a sanin da na maka, in har ba ka tab'a harka da mutum ba ya zo maka ba ka accepting, amma shi ne wannan ma da kasan akwai wani abu a tsakaninku, shi ne har ka yarda ka haɗa hannu da shi, ina......"

A tsawace Arshad ya katse shi da "wai Sajjad ina ruwanka! Company na ne, dukiya ta ce,  kuma ra'ayi na ne, so duk abunda zanyi ka zuba mun ido kawai idan za ka iya, idan ba za ka iya ba ka san mafita ai, na gaya maka kuma zan sake maimaita maka, akan Hanan i can do anything it takes (zan iya yin komai)"

Sajjad yayi matuƙar mamaki da jin haka, sai ya tashi tsaye, ya ce "haka kace?"

"Eh haka nace"

"Shikenan, fine! Allah ya bada sa'a"

Sai kawai ya fita a fusace, shi ma Arshad ɗin ko ameen bai ce ba banda wani cika da yake yana batsewa

Fitar Sajjad bai tsaya ko ina ba sai parking space, ko office ɗinshi bai koma ba, ya ja motarshi ya fita

********************

MK da Zayyad ne a guest house ɗin MK su na zaune sai faman sheƙa dariyar mugunta suke tayi

Zayyad ya ce "yanda fa naji mutumin nan yanada taurin kai, banyi tsammanin zai yi saurin sa mana hannu ba"

MK ya ce "ai shiyasa na bi ta hannun Hanan, dan yayi kuskure da ya faɗi cewar farincikinshi ce a gaba na, dan na tabbata zai ji maganarta, yanzu ga shi mun samu signature(sa hannu) ɗinshi cikin sauƙi"

Zayyad ya ce "shiyasa nake yinka mutumina, duk wata hanya da zata ba ka damar cimma burinka, ba ka sakaci da shi"

Ƴar dariya yayi, ya ce "ai lusari ke ganin hanya mafi sauƙi, amma ya kauce mata ya bi mai wahalar b'ullewa, Hanan ba ƙaramin taimaka mana za tayi ba"

"Ai yanzu ma a hakan ta taimaka mana, dan signature ɗin shi kawai muke buƙata, yanzu gobe zan ba Blessing sai tayi signing ɗin a wancan papers"

"Blessings kuma? Ina ka samo wannan? Ba Faruk ke yi ba?"

"Yana ƙasar Thailand yin wani aikin, shi ne ya samo mun wannan ɗin, abun mamakin ma ta fi shi iya satar signature ɗin mutum, dan idan tayi, duk sa idonka ba zaka gane banbancinsu ba"

"Ka tabbata?"

"Haba dai, Zayyad ne fa"

Murmushi MK yayi ya ce "haka ne kuma fa, ba ka wasa da aikinka"

Ƙwanƙwasa ƙofar aka yi, sannan aka buɗe ba tare da jiran izini ba, Farha ce cikin shigar jeans da t-shirt, sai ta ɗora after-dress tayu rolling kanta da ɗankwalin

"Alhaji Zayyad manya, ba'a ganinka sai in MK ne ya neme ka" ta faɗa bayan ta zauna kusa da MK

Murmushi yayi ya ce "ai kune manya, ganinku sai da ticket"

"Ba wani nan"

Dariya yayi, ya ce "kinga dai wannan zuwan kai na ne ai"

"Wallahi ban yarda ba, na sanka sarai, MK ne ya neme ka, kuma shi ma ba ya nemanka sai zaku ƙulla tsiyarku"

Wannan karon hadda MK sai da yayi dariya, ya ce "yanzu shaidar da kika mana kenan?"

Ɗora ƙafa ɗaya tayi kan ɗaya, ta ce "ka san hausawa sun ce sanin hali ya fi sanin kama, ko za ka ce ba wani mugun abun kuke ƙullawa ba?"

Zayyad ya ce "ai kin ce kin sani, meye kuma abun tambaya? Ke dai kawai ayi shagali"

"Shagali kuma? Ai ni shagali na ba yanzu ba, sai ranar da na tabbata abunda nake so ya zama na wa, ya rabu da waccan fitsararriyar, sannan hankalina zai kwanta"

MK ya ce "wai kina so ki ce har yanzu maganarki da wannan da kike so ɗin baku daidaita ba?"

"Hmm ina fa! Amma ana kan hanyar daidaitawa"

MK ya ce "wai waye wannan da ya same ki da yawa ne? Kin ƙi gaya mun, ban tab'a ganin kin tada hankalinki akan namiji ba sai wannan, waye dan Allah?"

Ƙayataccen murmushi tayi, ta ce "tunda ka takura zan gaya maka, ba kowa bane fa ce Arshad, AAJ"

Da sauri ya kalle ta ya ce "AAJ dai wanda na sani"

"Ƙwarai kuwa"

Zayyad ya ce "to ai shi ne......."

MK yayi saurin yi mishi alama da ido akan cewa yayi shiru, Zayyad kuwa tsab ya gane, sai kawai ya ce "shi ne wanda na zo garin nan saboda shi, kin san ƙwararre ne ta fanni kasuwanci, shi ne nake son haɗa hannu da shi"

Farha na jin daɗi tana buɗe haƙora, ta ce, "ai ta ko wane fanni ƙwararre ne, shiyasa nake matuƙar sonshi......ka ga yanzu ma wurin Samy zan tafi, daga nan sai in wuce gidansu, dan haka sai anjima"

Ta miƙe tsaya za ta wuce, Zayyad ya ce "amma za ki dawo muyi sallama ko, gobe zan koma"

"Ai ba wurina ka zo ba"

"Haba Hajjaju"

A yatsine ta ce "idan na dawo da wuri za ka ganni, idan ban zo ba kuma, Allah ya kiyaye"

"Ameen, in ma ba ki dawo ba, idan na sake dawowa ke zan fara nema"

"Idan kun sake tuno sabon mugunta ne zaka dawo?"

Dariya yayi, ya ce "a'a, nan da two weeks zan dawo"

"Umm, a dawo lafiya, na wuce" ta kalli MK ta ce "bye"

Daga nan ta fita, MK ya gyara zama ya ce "Zayyad kar kayi kuskuren gaya ma Farha wannan abu, dan wallahi yanda take sonshi ba za ta bari mu aiwatar da nufinmu ba"

"To shikenan ba damuwa"

"Yawwa, Allah ya sa muyi a sa'a"

"Ameen, maganar Hanan kuma, idan na dawo zan gama da matsalarta"

Dariyar ƙeta MK yayi ya ce "a dawo lafiya mutumina"

Suka sheƙe da dariya

********************

Sai bayan fitar Sajjad daga office ɗinshi, bayan ya gama huci, sannan ya tuna maganarshi ta ƙarshe da ya gaya ma Sajjad ɗin, nan ya fara jin haushin kanshi, dan ya san Sajjad bai kamaci hakan daga gare shi ba, aiki yake son yi amma gaba ɗaya ma ya rasa ta inda zai fara, sai tsaki yake ta jerawa

Ɗaukar wayarshi yayi ya kira Sajjad, kusan kira biyar amma ko ɗaya bai ɗauka ba, hakan ya sa ya tashi ya nufi office ɗin shi, sai aka gaya mishi ai Sajjad ya fi awa ɗaya da ya fita, a ranshi ya ce 'na san za'ayi haka ai'

Sai ya dawo office ɗinshi, ya daure ya ci gaba da aikinshi, har zuwa ƙarfe uku, sannan ya bar company ɗin, kai tsaye gidansu Sajjad ya nufa

Ya shiga suka gaisa da Hajiya, sai tunanin yake ta ya zai tambaye ta in Sajjad ya dawo gida

Jin maganar Hajiya kawai yayi a kunnenshi, tana ce wa "ina mutumin na ka? Ko yau ma guduwa kayi kenan, na san halinka" ta ƙarasa tana ƴar dariya

Yana jin haka, ya tabbata Sajjad bai dawo gida ba, sai kawai yayi murmushi ya ce "a'a Hajiya ba guduwa nayi ba, akwai wurin da naje ne, sai hanya ta biyo da ni ta nan, shi ne na zo gaida Hajiya ta" shi ma ya faɗa yana ƙoƙarin b'oye abunda ke ranshi

"Ka kyauta kuwa, bari in kawo maka abinci to"

"A'a na gode Hajiya, ina ɗan sauri ne, zan wuce"

"Ba za ka ci ba kenan"

Murmushi yayi, ya ce "ba haka bane, sauri nake yi ne"

"To ai shikenan, ka huta"

Ya sake yin murmushi, ya miƙe ya ce "sai anjima Hajiya"

"To ka gaida Amminku"

"To za ta ji"

Sai ya fita, ya daɗe zaune cikin motarshi, sannan ya ja motar ya wuce gida yana ta ƙara jin haushin kanshi

Part ɗinshi ya wuce, ya zauna parlour ya sake kiran wayar Sajjad sau uku, ko ɗaya bai ɗauka ba, sai ya ajiye wayar kan cushion ya rufe ido, tunani yake yi akan abu nda Sajjad ya gaya mishi, kuma shi ma ya san bai kamata yayi saurin sa ma Zayyad hannu ba, amma ya zai yi? Hanan ta nuna tana so, kuma akan Hanan ya yarda yayi komai indai zai faranta mata rai, shi kanshi ya kasa gane irin son da yake mata, abunda kawai ya sani, ita ɗin jinta yake tamkar rayuwarshi, ko wace rana sonta ƙara shigarshi yake yi

Yana cikin wannan tunanin ne Yasna ta shigo, sai da ta zauna kusa da shi sannan ya ganta, ta ce "Sweet Bro ashe ka dawo?"

"Eh, ban daɗe da shigowa ba"

"Ban ma ji ba kuwa"

"To me ya kawo ki nan bayan kin ce ba ki san na dawo ba"

Sai da ta ɗan b'ata rai tayi tsaki, sannan ta ce "waccan yarinyar ce ta zo, shi ne na basu wuri kar haushi ya cika ni, Farha"

"Yaushe ta zo?"

"Ba ta fi 30mins ba"

Ba tare da yace komai ba, ya tashi ya shiga bedroom dan yayi wanka, ita kuma ta kunna TV ta fara kallo


Sai kusan magrib Farha ta wuce, duk yanda kuwa ta so ta ga Arshad ba ta samu ganinshi ba, dan bai shiga main parlour ba, ita kuma tana tsoron zuwa part ɗinshi yanzu, haka ta haƙura ta wuce

Bayan sallar isha'i, ya shiga main parlour, suna cin abinci, Arshad ya ce ma Ammi

"Ammi, Jafar ya ce jibi zai zo idan Allah ya kaimu"

"To, Allah ya kawo shi lafiya"

"Ameen"

Yasna ta ce "wai shi kaɗai zai zo?"

"Eh"

"Allah ya kawo shi lafiya, ni kuma in fara kama kai na kenan"

Dariya suka yi, Ammi ta ce "ke dai kika sani"

Nan suka ci gaba da cin abincinsu har suka gama, kowa ya wuce ɗakinshi

Bayan ya gama shirin baccinshi kamar yanda ya saba, sai ya kira Hanan, wacce yau gaba ɗaya ba suyi waya ba

"Sai yanzu ka tuna da ni ko?" cewar Hanan

Murmushi yayi, ya ce "ai ban manta da ke ba, aiki ne ya mun yawa"

"Aikin ya fini kenan"

"Haba, ai ba wani abu da ya fi mun ke"

"Ka ji shi, kamar da gaske"

"Au, ba ki yarda ba kenan"

"Umm"

"To gobe tun la'asar zan zo har sai nayi magrib sannan zan wuce, dan in goge wannan laifin"

"Bana so" ta faɗa a shagwab'e

Yayi murmushi ya ce "to idan ke ba kya so, ai Ummi na da Siyama su na so"

"To shikenan, sai da safe"

Ba ta jira komai ba, ta kashe wayar, shi kuma sai dariya yake tayi, sai ya tura mata haɗaɗɗen love message, sannan ya kwanta
Tayi matuƙar jin daɗin message ɗin, sai dai bata yi mishi reply ba, ita ma ta kwanta

********************

Ƙarfe tara, Arshad na office, Khairat ta shigo ta sake sanar da shi Sajjad bai shigo ba, wanda karo na huɗu kenan da ya aike ta akan ta duba idan ya zo, amma shiru har yanzu

Ya ɗauki waya dan sake kiranshi, sai kiran Nabeel ya shigo wayarshi, ɗauka yayi suka gaisa, sannan Nabeel ya ce

"Arshad me ya haɗa ka da Sajjad?"

Cikin mamaki ya ce "me ya ce mak ya haɗa mu?"

"Tambayarka nayi fa, shi ne kake mun wata tambayar?"

"Oh, yi haƙuri, kawai ɗan misunderstanding ne wanda ba za'a rasa ba"

"Meye matsayin Sajjad a wurinka?"

"Kamar ya" cewar Arshad cikin rashin fahimtar zancen na sa

"Yanda ka ɗauke shi nake son sani"

"Haba babban yaya, ai ka fi kowa sanin yanda Sajjad yake a wurina, ya fi ƙarfin in kira shi da aboki ko kuma amini, sai dai ɗan uwa, kuma na jini, haka nake jinshi a raina"

"To idan haka ne, meyasa za ka yanke hukunci ba tare da ka ji shawararshi ba?"

Sai yanzu ya gane ashe bai gaya mishi abunda ya faɗa mishi ba ma, sai ya ce "akasi aka samu, amma hakan ba zai sake faruwa ba"

"Allah ya sa, dan ya gaya mun bai ji daɗin haka ba ko kaɗan"

"Bazan sake ba ai, ina ta kiranshi ma dan in ba shi haƙuri, amma ya ƙi ɗagawa"

"Zan sa ya kira ka to"

"Yawwa big bross, thank you"

"Shikenan, take care"

Kashe wayar suka yi, bayan kamar minti biyar da gama wayarsu, sai ga kiran Sajjad ya shigo, ɗauka yayi, ya ce

"Haba My Man, wannan wane irin punishment (hukunci) ne?"

Ɗan ƙaramin numfashi ya ja, sannan ya ce "ai ba ni da amfani ne, shiyasa na yanke shawarar barinka da wacce ta fi ni muhimmanci a wurinka"

"Wa ya gaya maka ta fi ka, kawai dai kowa da matsayinshi ne.......ba wannan ba dai yanzu, kayi haƙuri"

"Ai dole inyi haƙuri tunda aikin gama ya gama, Allah dai ya mana mai kyau"

"Ameen Man, to yaushe za ka shigo company?"

"Sai na gama hutu"

"Haba dan Allah, ba ka haƙura ba kenan ko?"

"Na haƙura mana"

"To dan Allah ka zo"

"Shikenan, naji, sai na zo"

"Yawwa, Allah ya kiyaye mun kai"

Dariya yayi, ya ce "ameen"

Shi ma AAJ dariyar yayi, sannan suka kashe wayar, sai a lokacin ya samu ƙarfin ci gaba da aikinshi

********************

Zayyad ne a office ɗinshi, tare da Blessing, ya na nuna mata wata takarda da akayi ma rubutu ku san shafi ɗaya, sai ƙasa da aka bar wurin da mutum biyu za su sa hannu, sannan da ɗayar takardar da AAJ ya sa hannu akai, ya bata, sannan ya mata bayanin yanda yake so ayi, tare da ja mata kunne akan kar a samu wani banbanci a signing ɗin

Tsab ta gama fahimtar abunda yake buƙata, dan ba wannan bane karo na farko da ta fara mishi irin wannan aiki, ta ce "just trust me sir, i will sign exactly as this, without any differences (ka yarda da ni kawai yallab'ai, zan sa hannu kamar yanda wannan yake, ba tare da wani banbanci ba)"

"I trust you Blessing, all the best (na yarda da ke Blessing, fatan alkhairi)"

"Thank you sir (na gode yallab'ai)"

Tashi tayi ta fita, shi kuma ya jingina jikin kujerarshi ya rufe ido, ba abunda yake gani sai kyakkyawar fuskar Hanan, ji yake kamar ya ɗauko ta yanzu, amma ba halin yin hakan, sai dai yayi ma kanshi alƙawarin yana gama wannan aikin na MK, to Hanan ce akan gaba

********************

"Jafar" Abba ya kira Jafar da ke zaune a gabanshi

"Na'am Abba"

"Ka san na san halinka ko! Ina so ka sani, na zab'e ka ne cikin masu yi mun wannan binciken ne saboda ina so a samu ɗan gida a wannan lamarin binciken ba dan komai ba, Nabeel na so ace ya mun wannan aikin, amma yanayin aikinshi na duba shiyasa na sa ka, kar ka duba abunda ɗan uwanka ya fi so, kayi tsakani da Allah"

"In sha Allah Abba, ba zanbbi ra'ayi na ko na Ya Arshad ba, binciken gaskiya zan maka"

"Allah ya sa, dan kai wuyar sha'ani ne da kai, yanzu za'a ganka a mutum anjima kuma sai a hankali"

Murmushi Jafar yayi, ya ce "Abba ka yarda da ni kawai"

"Shikenan, tashi kaje, Allah yayi albarka, ya mana zab'i mafi alkhairi"

"Ameen"

A parlour ya haɗu da Ya Nabeel yana koƙarin shiga ɗakin Ummansu, sai ya mishi alama da hannu, cewar ya zo

Sai da suka gaisa da ita sannan Nabeel ya ce "Umma, kin ga yaron nan na ki ko, wallahi sai kin ja mishi kunne akan aikin da Abba ya sa shi, dan wallahi Allah kaɗai ya san muguntar da yake shirin yi"

Anty Fati ta ce "ban son sharri, ya akayi ka san mugunta zai yi?"

"Wallahi mugunta zai yi, dan akwai wacce yake jin haushi cikinsu"

Kallon Jafar tayi, da ya wani sunkuyar da kai kamar wani maraya, ta ce "Shalele gaya mun gaskiya, wai akwai wacce ba ka so?"

Ɗaga kai yayi ya kalle ta, sai kuma ya kasa cewa komai, ta ce "ƙaryar ta ƙi fitowa ko? To gaya mun gaskiya kawai"

Murmushi yayi ya ce "eh Umma, amma wallahi ba mugunta zanyi ba fa"

Nabeel ya ce "me ka gayawa Arshad ranan a gidan Hajjo?"

Anty Fati ta ce "bari sunkuyar da kai, gaya mun me kace mishi?"

"Cewa fa kawai nayi binciken ƙwaƙwaf zanyi"

Nabeel ya ce "ka kalli cikin ido na ka gaya mun shi kaɗai ka faɗa"

Ya ce "kai Ya Nabeel, tone-tone ba kyau wallahi, abar maganar haka, ka yarda da ni, ba zanyi mugunta ba, tsakani da Allah zanyi komai"

Umma ta ce "promise? (Kayi alƙawari?)"

"Eh Umma"

Nabeel ya ce "hmm Allah ya sa"

Jafar ya ce "ameen"

Nan Nabeel ya fita ya ba su wuri, ta ci gaba da ja mishi kunne, dan ita ma ta san halin ɗan na ta, ko yace ba zai yi ba, bai zama lallai ya ƙi yi ba in dai har yana son yi, Jafar kam sai dai du'a'i, dan halinshi daban ne da na sauran ƴan uwanshi, shiyasa tun daga kan Nabeela, Yasmin, Yasna, Meerah, da Adnan duk shakkarsa suke yi, sai dai wani lokacin yakan sakar ma Yasmin fuska suyi hira kamar na mintuna ashirin, shi ma tana takatsantsan da abunda za ta faɗa kar ta mishi ba dai-dai ba, ta sha mazga

********************

Kusan la'asar Arshad ya dawo gida, yayi wanka yayi alwala, sannan shirya ya fita, a masallacin dake jikin gidansu ya tsaya yayi sallah sannan ya wuce

Bai tsaya ko ina ba sai gidansu Hanan, kamar yanda ya mata alƙawari, kiran wayarta yayi, sai dai Siyama ce ta ɗauka

"Hello Ya Arshad ina wuni?"

"Lafiya ƙalau kanwata, ina yayarki?"

"Ummi ce ta aike ta maƙwabta"

"Ummi na nan?"

"Eh"

"Ki gaya mata na zo gaishe ta"

"To shikenan"

Ko minti biyar ba suyi da kashe wayar ba, sai ga Siyama ta zo ta ce wai ya shiga

Tare suka shiga, Ummi na zaune kan kujera daga gefen ɗakinta, sai ya zauna kan tabarmar da ke shimfiɗe a tsakiyar gidan, suka shiga gaisawa da Ummi cikin fara'a kamar yanda suka saba

Su na cikin haka ne Hanan ta shigo, kallo ɗaya ta mishi ta wuce ɗaki, sannan ta fito, ta wuce wurin murhu dan ta hura wuta

Ummi ta ce "Hanan yau bakinki ciwo yake yi ne da baki iya gaisuwa ba?"

Ko kallonshi ba tayi ba, ta ce "Ummi ai ba wurina ya zo ba"

"Kin ci gidanku"

Murmushi Arshad yayi, ya ce "ƙyale ta Ummi, ai wurinki na zo ke da ƙanwata"

"Ka kyauta ɗan Ummi, yau shegen halin ne ya motsa"

Dariya yayi, sannan ya kalli Siyama da ke fitowa daga ɗakin Ummi hannunta riƙe da plate da ruwa akai, ya ce "yawwa ƙanwata, zo nan muyi labari"

Zuwa tayi ta zauna kan tabarmar da murmushi a fuskarta, ta ajiye ruwan sannan ta ce "to Yayana, labarin me za muyi?"

Shi kan shi bai san labarin me za suyi ba, sai kawai ya ce "ki bani tarihinki"

Dariya tayi, ta ce "tarihina kuma? To idan na baka tarihin na wa kai ma za ka bani na ka?"

"Eh mana"

"To shikenan" gyara zama tayi, ta ce "sunana Siyama Abdul-Aziz, ƴar asalin jahar Borno, Maiduguri, yarenmu Margi, sai dai na girma a nan jahar Kaduna, mahaifina ya rasu ina ƴar ƙarama, ina da shekara biyu, ya barmu da ƴan uwanshi kawai, suna maiduguri su, ina zaune tare da Ummina Halima, sai Yayata Hanan, sai ɗayar Yayata Yuhanees, sai dai ita ba gida ɗaya muke ba"
Daga nan sai tayi shiru tana kallonshi

Ya ce "ya kika yi shiru?"

Ta ce "tarihin na wa ya ƙare"

"Nan dai kika sani"

Dariya tayi, Ummi ma da ke kallonsu sai da tayi murmushi, Siyama ta ce "to saura kai"

"Ni??? Ai wayo na miki"

Kamar za tayi kuka, ta ce "wallahi bazan yarda ba"

Yayi dariya ya ce "to shikenan.......kin ga sunana Arshad Ahmad Jalal, amma anfi sani na da AAJ.."

Katse shi tayi da "sai yau na san ma'anar A da J ɗin nan na ƙarshe"

Ya ce "kaii, amma kinyi abun kunya"

 Hanan sai da tayi dariya, dan ita Ummi wani nazarin na daban take yi, Siyama kuwa kwab'e fuska tayi

Sai yayi murmushi ya ce "yi haƙuri ƙanwata, kina ji na!"

Ɗaga mishi kai tayi, sai ya ci gaba "ni ɗan asalin jahar Adamawa ne, kuma bafulatani, Mahaifina ya rasu ina da 11years, ya bar mahaifiyarsa Hajjonmu kenan dan mahaifinshi ya rasu shi ma, sai ƙanwarsa Anty Fati, ina zaune tare da ƙannena Yasmin da Yasna, sai kuma Ammina, Ruƙayya"

Nan Ummi ta ji gabanta ya faɗi, dan tunda ya fara tarinhinshi take roƙon Allah ya sa ba abunda ta daɗe da zargi bane zai tabbata, a ranta ta ce 'Ruƙayya? Ahmad? Baffa Jalal? Kuma ga Fatima! Kar dai tunani na gaskiya ne!? Ai kuwa in haka ne akwai matsala'

Muryar Siyama ce ta dawo da ita "to Ya Arshad ka ga kai ka san Ummina, amma ni bansan Amminka ba"

"Zan kai ki ki ganta"

"To ka fara nuna mun hotonta"

"Shikenan" ɗaukar wayarshi yayi, ya shiga neman hoton Ammi, sannan ya ba ta

"Masha Allah, ashe tushen kyanka daga nan ne"

Murmushi yayi, ya ce "a'a daga Abbi na dai, dan ba ki sanshi ba ne"

"Gaskiya daga Amminka ne....Ummi kalla ki gani dan Allah ba da Amminshi yake kama ba?" ta faɗa yayinda take tunkarar Ummin da hoton Ammi a wayar Arshad

Kallo ɗaya ta ma hoto ta rufe ido, ta ce "lahaula wala ƙuwata illa billah"

Duka su ukun kallon Ummi suke da mamaki, Siyama na dariya ta ce "Ummi duk kyanta ne ya ruɗaki haka? To ai ba ta fi ki kyau ba"

Ko ta kan Siyama ba ta koma ba, ta ce ma Arshad "Ruƙayya ce mahaifiyarka?" ta faɗa cikin wani yanayin da ke da wuyar fassara

Arshad sai da ya ji fargaar ba ta amsa, amma ya daure ya ce "eh, Ummi lafiya?"

Hanan ma mayar da hankalinta tayi kacokam kan Ummi, dan ji take gabanta na faɗuwa duk da cewar ba ta san dalilin da yasa Ummi tayi hakan ba

Cikin b'acin rai, Ummi ta ce "har abada ba zai tab'a yiwuwa ba"

Hanan ta ce "me kenan Ummi?"

Ummi ta kalli Arshad ta ce "Arshad zan neme ka"

Ɗan girgiza kai yayi, alamar rashin fahimta, ya ce "kamar ya Ummi?"

"Na ce zan neme ka da kaina idan da buƙatar hakan"

Hanan cikin rawar murya, ta ce "amm..amma Ummi me..meyasa kika ce haka?"

Arshad ya ce "to tsare ta za kiyi? Ummi ina jiran kiranki" ya ƙarasa yana murmushi, ba wai dan bai ji tsoron maganar Ummi ba, sai dai dan ya b'oye damuwarshi, dan ya fahimici Hanan ta tsorata ita ma, amma a ranshi ya tabbata ba a banza Ummi tayi wannan maganar ba, dole akwai wani abu

Ƙarb'ar wayarshi yayi daga hannu Siyama sannan ya fita, da gudu Hanan ta taradda shi yana ƙoƙarin shiga mota, ta ce "bai kamata ka wuce ba fa, akwai alamar tambaya a zancen Ummi, Allah"

Ajiyar zuciya yayi, ya ce "kin tab'a ganinta a haka? Ko ta tab'a magana makamancin haka?"

"A'a"

"Then, takurawa akan sai munji ko menene yanzu bai da amfani, mu bata lokaci ko da kwana biyu, za ta gaya mana ko menene"

"Haka kake ganin shi ne mafita?"

Murmushin da bai kai zuciyarshi ba yayi, ya ce "eh...na ga kin tsorata"

"Hmm ai dole ne, wani abu zuciya ta ke gaya mun"

A ranshi ya ce 'Allah ya sa ba irin abunda ta wa zuciyar ke ƙoƙarin gaya mun ba ne' a zahiri kuma ya ce "ba abunda zai faru sai alkhairi kinji, ki shiga gida kawai"

Jiki a sanyaye ta ɗaga mishi kai sannan ta shiga gida, shi kuma ya tada motar ya wuce

Tana shiga gida, ta ga yanayin Ummi ya fi na ɗazu, dan kana ganinta za ka ga b'acin rai fal a fuskarta

Cikin wannan b'acin ran, ta ce "Hanan"

"Na'am Ummi" ta amsa a tsorace

"Ni ce mahaifiyarki?"

"Eh Ummi"

"Da kyau, to ina so ki sani, daga yau babu ke babu Arshad, har abada"

Hanan jin wannan maganar tayi tamkar saukar aradu, dan har cikin kanta ta ji ya amsa, kai hatta Siyama sai da gabanta yayi mummunan faɗuwa da jin wannan kalmar ta Ummi.........







TIRƘASHI, ASHE WATAN MUTUWAN ARSHAD YA TSAYA TUNDA YA CE IDAN YA RASA HANAN MUTUWA ZAIYI😂😂💃💃

NAYI NAN🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️😁😁






WAITING FOR UR COMMENTS🤍





🥰UMMEETA🥰......📝

07069344041

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 27* 

Yuhaness da ke tsaye bayansu ba tare ma da sun san ta shigo ba, cikin tsananin mamaki ta ce "Ummi meyasa kika ce haka? Lafiya kuwa?"

Juyawa Siyama tayi tana kallonta, Ummi ma ɗaga kai kawai tayi ta kalle ta sannan tayi ma Hanan wani kallo mai kama da harara sai ta shige ɗakinta

Hanan gaba ɗaya tayi mutuwar tsaye, tunani take yi anya kunnuwanta sun ji abunda Ummi ta faɗa da kyau kuwa? Ko dai Mafarki take yi ne?

"Idan kuwa mafarki ne ya kamata in farka daga wannan mummunan mafarkin dake shirin tarwatsa mun zuciya" abunda ta faɗa kenan a zahiri wanda ita kanta bata san maganar ta fita ba

Sanadiyar riƙon da Yuhanees ta mata ne ya sa ta dawo hayyacinta

"Zuciyarki ba zata tarwatse ba Hayatee"

Ɗaga ido Hanan tayi ta kalle ta, hawayen da suka cika idanunta tun ɗazu sai a lokacin suka samu damar gangarowa kan kyakkyawan fuskarta, Yuhaness ta riƙe ta suka wuce ɗakinta, Siyama kuma ta koma kan tabarmar ta zauna tana mamakin Umminta

A bakin gado suka zauna, Yuhanees ta shiga share mata hawaye tana lallashinta, ta ce

"Kiyi shiru haka nan Hayatee dan Allah"

Cikin sheshsheƙar kuka Hanan ta ce "haba rabin rai, ya za ki ce inyi shiru? Ba ki ji abunda Ummi ta faɗa ba ne? Cewa fa tayi ba ni ba Arshad"

"Na ji Hayatee, amma ai ba wai hakan na nufin komai ya zo ƙarshe tsakaninku ba"

"Meyasa kike tunanin za ki iya kwantar mun da hankali ta wannan sigar? Sanin kanki ne Ummi ko da wasa bata tab'a nuna b'acin ranta akan Arshad ba, bare kuma tayi mishi faɗa, amma yau cikin tsananin fushi da b'acin rai tace wai in rabu da shi, ba za kiyi tunani akai ba?"

Ɗan gajeren ajiyar zuciya Yuhanees tayi sannan ta ce "tabbas ban tab'a ganin Ummi a haka ba, amma karki damu, in sha Allah zan same ta in mata magana koma menene dalilinta zan ji sannan kuma za mu san yanda za muyi maganin abun kinji, kiyi haƙuri" ta jawo ta jikinta tana shafa bayanta tana ƙara bata haƙuri


********************

A b'angaren Arshad kuwa, tuƙi yake yana tunanin meyasa Ummi ranta ya b'aci bayan ganin hoton mahaifiyarshi, hakan na nufin ta santa ne ko me, ko kuwa Ummi ta hango mummunan halin Ammi ne daga kallon fuskarta?
'Haba dai Arshad, ta ya mutum zai iya saurin gane halin wani daga yi mishi kallo ɗaya kuma a hoto?' zuciyarshi ke gaya mishi hakan

A zahiri kuma cewa yake "kuma haka ne fa, to ta santa kenan? Amma a ina?"

Wannan tunanin ne fal a ranshi har ya isa gida, wanka kawai ya samu yayi sannan ya wuce masallaci dan gabatar da sallar magrib

Yana dawowa ya wuce gefen swimming pool wanda ya sha manyan glubs masu hasken gaske farare da blue, zama yayi kan ɗaya daga cikin kujerun da ke wurin, ya zaro wayarshi daga aljihu ya shiga neman numbern da yayi saving da My Twin, bugu biyu ya ɗauka

"Hello My Man"

"Super ya aka yi? Sai yanzu ta sallame ka?" Sajjad ya faɗa cikin zolaya

Dan guntun murmushi yayi, ya ce "Ina neman shawararka Sajjad"

"To lafiya?"

Zayyana mishi abunda ya faru yayi, sannan ya ce "Man, yanayin da Ummi tayi maganar ta ɗan tsorata ni"

"Eh to abun akwai mamaki, saboda na lura Ummi macece me fara'a da sanin darajar ɗan adam, amma kai a naka tunanin, me kake ganin zai iya zama dalilin da yasa Ummi ta ce sai ta neme ka?"

"Sajjad ina tunanin kamar ta santa ne"

"Amma kana ganin kuwa Ummi ta san Ammi? Ba na jin hakan gaskiya"

"Ka fa san halin Ammi na ƙyama da wulaƙanta talaka, ba ka tunanin ko wani wuri suka haɗu ta mata irin wulaƙancin da ta saba?"

"Kuma fa maganarka akan hanya take, to yanzu me ya kamata muyi dan magance wannan matsalar kafin ta girma?"

"Mafita ɗaya nake tunani, Hanan zata yi ƙoƙarin jin dalilin Ummi na wannan b'acin ran, idan abunda muke tunani ne, dole Hajjo da Abba su zo garin nan dan su sa Ammi gaba ta je ta ba Ummi haƙuri"

Wata irin dariya Sajjad ya fara saboda wannan tsarin na mutuminshi ya bashi dariya sosai, ɗan b'ata rai Arshad yayi, ya ce "ban son rainin hankali ka sani ko! Meye abun dariya?"

Sajjad na ƴar dariya, ya ce "Haba! Haba Super, yanzu akan ɗan wannan abun kake tunanin ɗauko tsohuwar mutane da Abba dan kawai a ba Ummi haƙuri?"
Sai ya ɗan daidaita kanshi daga dariyar da yake yi sannan ya ci gaba da cewa "kaga Arshad, idan ma har wannan zargin na ka gaskiya ne, to mu da kanmu za mu iya magance matsalar, mu bar Abba ya ji da binciken ma da ka sa shi"

"Hmm, Man kenan, sai ka ce dai baka san Ammi ba? Kana tsammanin ni ko kai akwai wanda ya isa ya sa Ammi ta je ta ba wa Ummi haƙuri?"

"I know it's impossible (na sani ba zai yiwu ba), ba yanda kake tsammani za muyi  ba, ka fara dai tabbatar da menene dalilin, sannan sai ka ji yanda za'a yi"

Gwauron numfashi Arshad ya ja, sannan ya ce "shikenan to, ka gaida mun Hajiya da su Intisar"

"Za su ji in sha Allah, sai da safe"

"Aha, tnx"

Sai da suka kashe wayar, sannan ya ɗan zauna, sai kuma ya tashi ya wuce masallaci domin yin sallar isha'i, kafin ya shiga gida wurinsu Ammi

********************
Washe gari Jafar ya gama shirin tafiya Kaduna, yayi sallama da ƴan uwanshi da iyayenshi, Abba ya ƙara ja mishi kunne, ya sanar da shi kuma in ya isa zai haɗa shi da wanda za suyi binciken tare, Umma ma ta haɗa mishi tsarabar da zai kai ma ƴan biyunta

Daga nan ya wuce gidan Hajjo dan suyi sallama, ita ma ta haɗa shi da nata tsarabar, sannan ta ja mishi kunne akan abunda aka tura shi yi, sai da suka yi faɗan da suka saba kamar dai kullum

"Dan Allah Hajjo ki kyale ni haka nan in wuce, kina ta wani b'ata mun lokaci, wai in ji tsoron Allah, to da tsoronki nake ji ne" Jafar ya faɗa yana miƙewa tsaye, dan ya fara jin haushin maganganun Hajjo, kalma ɗaya take ta maimaita mishi, ya ji tsoron Allah

Ita ma b'ata rai tayi, ta ce "sai na gaya maka gaskiya dan kai ba son gaskiyar kake yi ba"

"Ai ba dole ne sai na so gaskiya ba" yana faɗar haka ya sa kai zai fita daga parlourn, ta tashi ta bi bayanshi tana tafiya kamar tana tsoron ƙasa

Ta ce "ai ko ba ka son gaskiyar, sai ka tsaya in maka addu'a ko!"

Sai bakin motarshi ya tsaya, ya ce "idan ban tsaya ba ki ce in mutu a hanya dama ba so na kike yi ba"

"Ko mutuwa kayi ai lokacinka ne yayi, mutumin kawai"

Rufe ƙofar motar yayi, ya ɗan matsa kusa da ita ya ce "yanzu Hajjo da ma so kike yi in mutu?!"

Ɗan guntun murmushi tayi, ta ce "eh, amma sai bayan kayi aure ka tara ƴaƴa da jikoki sannan sai ka mutu"

Shi ma murmushin yayi, ya ce "ina sanki kakus, na wuce" ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe mota

"Allah ya kiyaye, kuma kar ka manta da abunda na gaya maka kuma, ka ji tsoron Allah"

"Ai kinji matsalarki kuma" bai tsaya jin komai ba, ya shige motar ya bar gidan

Bin motar tayi da kallo har ya fita gate ɗin, ta girgiza kai ta ce "hmm, Jafaru kenan" sai ta koma cikin gida

********************

MK ne kwance kan kujerar parlournsu, yana waya da Zayyad

"Ya ake ciki ne?"

Zayyad daga ɗayan b'angaren ya ce "aiki ya kusa kammala, ka duba e-mail ɗinka na turo maka da saƙon takardun, gobe kuma zan aika da takardun dan sauran aikin ya kammala"

"That's good(yayi kyau) aikinka yana tafiya yanda ya dace"

Murmushi Zayyad yayi, ya ce "ina so in kammala nawa aikin ne cikin satin nan, in ya so sai mu jira sakamako kawai"

Dariya MK yayi, ya ce "na ƙagu wannan sakamakon ya fito, dan zai bada citta"

"Tabbas kuwa ba kayi ƙarya ba"

"To amma da kace sati biyu zaka ɗauka saboda sai ka kammala wani aiki, meyasa yanzu ya dawo sati ɗaya? Ko ka fasa wancan aikin ne?"

"Ba zaka gane ba, wancan aikin na ba wani daban, dan aikin dake gabana yanzu kuma ya fi kowane irin aiki, shiyasa nake so in kammala da wuri in dawo"

"Wane aiki ne kuma wannan ka samu?"

"Hanan mana, guy yarinyar nan ta haɗu ta ko ina, kullum cikin tunaninta nake, kai in ƙarƙare maka ma, jiya har mafarkinta nayi"

Ba ƙaramin dariya Zayyad ya ba MK ba, ya ce "lallai Hanan ta gama da kai, mafarki fa kace!" ya ƙarasa yana dariyar

"Hmm, idan ana sallah ba'a magana ka sani, sai ka ji ni dai"

"To shikenan na Hanan, sai anjima" ya faɗa cikin zolaya

"Na ɗauki sunan ai, bye" suna dariya suka katse wayar tare

Mahaifiyar MK dake zaune gefenshi, ta ce "Marwan da wa kake waya ne haka wai?"

Tashi yayi ya zauna, ya ce "Zayyad ne"

"Ba na ce ka rabu da wannan Zayyad ɗin ba?"

"Umma wai meyasa ba kya ƙaunar Zayyad ne?"

"Saboda kwata-kwata hankali na bai kwanta da shi ba duk cikin abokananka da na sani"

"To naji"

Kallonshi kawai tayi, sai kuma ta ce "yau ba za ka fita ba?"

"Sai anjima kaɗan, ina so in huta ne"

"Shikenan, ni ma fita zanyi yanzu, sai na dawo"

"To Allah ya kiyaye"

Ta tashi ta fita tana cewa "ameen"

Tana fita, ya sake kwantawa ya ce "am sorry mother, amma ba zan iya rabuwa da Zayyad ba, dan shi ke taimaka mun wurin maganin duk wani tantirin da ya shiga gonata, sai dai as i promise (kamar yanda nayi alƙawari) idan ba irin haka ya taso ba, ba zan neme shi ba"

Ya ɗauki wayarshi ya shiga daddannawa, sannan yayi tsaki ya tashi da sauri, kamar wanda ya tuna wani abu, sai ya haura saman stairs, ya shiga ɗakinshi, cikin mintuna 20 yayi wanka ya shirya, sannan ya fita daga gidan

********************

"Ummi, ke mahaifiyarmu ce, kuma ni shaida ce akan yanda kike ƙoƙari wurin ganin ƴaƴanki sun samu farinciki a rayuwa, duk da cewar Allah be yi ki mai arziki ba, amma kina amfani da wadatar zuciyarki domin sauke nauyin da ke kanki, Ummi kin san Hanan na son Arshad sosai, amma kika ce ta rabu da shi, tabbas kina da hujja akan hakan, dan Allah ki gaya mun meyasa?"

Tun da Yuhanees tayi magana akan Hanan da Arshad, Ummi ta ɗauke idanunta daga kanta, ta ci gaba da ninke kayanta

Yuhanees ta sake matsowa kusa da ita, ta ce "Ummi dan Allah ki gaya mun dalilinki na raba Hanan da Arshad, dan Allah"

Nan ma dai Ummi bata kalle ta ba, sai ma tashi da tayi ta nufi wurin da akwatinta yake dan ta sa kayan ciki

"Ummi dan Allah ki mun magana, me Arshad ya mik....."

"Yahanazu!!!" Ummi ta katse ta ta hanyar yi mata tsawa

Yuhanees ta tsorata da jin yanda Ummi ta mata tsawa kuma ta kira ainihin sunanta, bata tab'a jin Ummi ta kira ta da haka ba

"Idan kina so mu ci gaba da zaman lafiya ni da ke, kina so in ci gaba da ganinki a matsayin ƴata, to kar ki sake mun magana akan abunda ya danganci Arshad ko wani na shi, hukunci ne na yanke shi, ba shi ba ƴa ta Hanan har abada"

Gaba ɗaya Yuhanees kanta ya gama ƙullewa, ta rasa ma me zata ce ma Ummi, wani kallo Ummi ta mata, ta ce "ki fita ki bani wuri kafin ranki ya b'aci"

Kallon Ummi take yi baki buɗe cikin tsananin mamaki, "ba za ki fita na kenan!"

"Allah ya baki haƙuri Ummi" shi kaɗai Yuhanees ta iya faɗa sannan ta fita

A ɗaki ta taradda Hanan ta sha tagumi, sai hawaye ke bin fuskarta, tana ganinta tayi saurin share hawayen, ta miƙe da sauri ta riƙe ta

"Rabin rai me ta gaya miki?"

Girgiza kai Yuhanees ke yi, ta kasa cewa komai dan ita kanta yanzu al'amarin nan na Ummi ya fara ba ta tsoro, jiya ta ɗauki abun wasa, amma yau ta tabbatar da Ummi har cikin ranta bata son zancen Arshad

"Rabin rai dan Allah ki ce wani abu, idan laifi ya mata wallahi na san a shirye yake da ya bata haƙuri"

Janta Yuhanees tayi suka zauna kan wani cushion 2seater dake ɗakin, sannan tayi koƙarin share mata hawayen da ke zubowa

Ta ce "kiyi haƙuri Hanan, amma maganar gaskiya Ummi bata ma son magana akan Arshad"

"Amma meyasa dan Allah?" ta faɗa cikin damuwa

"Ban sani ba Hayatee, amma ko menene ba ɗan ƙarami bane, dan ban tab'a ganin Ummi ta nuna tsantsar b'acin ranta ba akan wani haka ba"

Dafa goshi Hanan tayi, ta ce "inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un, Ummi menene dalilinki na son raba ni da Arshad, bayan ke kika bani ƙarfin gwiwar fara son shi? Da kin raba ni da shi tun soyayyar da nake mishi bata kai haka ba Ummi" ta saki kukan da take ta riƙewa tun ɗazu

Yuhanees ta matuƙar tausayawa Hanan, dan ta san ƙawarta na son Arshad ba kaɗan ba, to yanzu taya ma zata gaya ma Arshad wannan abu? Tunanin da ke ran Yuhanees kenan

********************

Kusan lokaci ɗaya Arshad da Jafar suka yi parking a parking area, kasancewar yau Arshad be tashi daga aikin ba sai bayan la'asar

"Sannu da zuwa Jafar" Arshad ya faɗa bayan kowanensu ya rufe motarshi

Murmushi Jagar ke yi, ya ce "yawwa ya Arshad, yanzu ka dawo kenan?"

"Eh, mu shiga ciki"

Sai da Jafar ya buɗe booth ya ɗauko jakarshi, sannan suka shiga ciki

Da gudu Yasna ta zo cikin murna, ganin Arshad da Jafar, sai dai tana isa kusa da su, tayi tsaye tare da sunkuyar da kai ƙasa

Arshad ya ce "ya kika tsaya?"

Ɗaga ido tayi a hankali ta kalli Jafar kamar wata maƙaryaciya, nan Arshad ya gane me take nufi, sai yayi murmushi kawai, Jafar kuwa tsaki yayi, ya ce "kya ji da shi dai"

Ya bi ta gefenta ya wuce, sai ta rungume Yayanta tana wani kwab'e fuska, Yasmin kuwa ta karb'i jakar Jafar ɗin bayan sun gaisa

"Lale marhaban, ga mutanen Adamawa" cewar Ammi tana kallon Jafar da fara'arta

Zuwa yayi kusa da ita ya zauna, ya ce "Ammi ina wuni"

"Lafiya ƙalau, ya hanya?"

"Alhamdulillahi"

"Masha Allah, Yasmin kira Asabe ta jera abincin Jafar da Arshad, ga su nan sun ƙaraso" ta faɗa tana kallon Yasmin

Arshad ya ce "Yasmin a kawo na Jafar kawai"

Ammi ta ce "kai fa?"

"Ba yanzu ba Ammi"  sai kawai ya sa kai ya bar parlourn

Jafar ya ce "Ammi kamar akwai abunda ke damun Ya Arshad, ba haka na saba ganinshi ba fa"

"Nima haka nake zargi tun safe, yanzu dai ka ci abinci sannan "

Nan ya tashi suka nufi dinning area tare da Yasmin, Yasna kuma ta ɗauki akwatinshi zuwa part ɗin Arshad

Zaune Yasna ta same shi, sai faman kiran waya yake tayi, tsaki yayi ya ajiye wayar gefe, Yasna ta zauna ta ce "lafiya kuwa Sweet Bro?"

Cikin damuwa ya ce "yau gaba ɗaya Hanan ta ƙi daga kira na"

"Kunyi faɗa ne?"

"Wane irin faɗa kuma Sweetie?"

"To Allah ya sa lafiya, amma ka je gidansu mana to"

Shiru yayi dan ya tuna yanda ya bar Ummi jiya, da kuma cewa da tayi ya wuce zata neme shi, yana tsoron komawa kar ya mata laifi

"Sweet Bro!" ta sake kiranshi

"Tashi ki tafi kawai Sweetie, na gaji da yawa, ba sai na tafi ba, na san idan ta gani zata kira"

"To shikenan, bari in tafi in ji da wancan Yaya masifau, kafin ya ce ban iya gaisuwa ba kuma"

Ɗan murmushi yayi, ya ce "to yi sauri, nima zan zo"

"To" 

Sai da ta shigar da akwatin ɗayan ɗakin dake gefen ɗakinshi, sannan ta bar parlourn zuwa main parlour

Jingina yayi jikin kujerar, ya dafe kanshi, dan zuwa yanzu kam zuciyarshi ta gama tabbatar mishi da cewa akwai wata matsala, musamman idan ya tuna yanda ya bar Ummi, sannan be tab'a yi ma Hanan koda kira biyu ba ba tare da ta ɗauka ba, idan kuwa bata kusa, tana gani zata kira, amma daga safe zuwa yanzu ya mata kira ya kai ashirin da wani abu, abunda ma yafi ɗaga mishi hankali shi ne, idan ya tuna da Hanan sai ya ji gabanshi ya faɗi, ya rasa gane me hakan ke nufi, fatanshi Allah yasa lafiya take............






🥰UMMEETA🥰......📝


♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 28* 

Jafar ya ɗauki kusan fiye da mintuna talatin wurin Ammi, duk da cewar ba wata hira suke yi ba, sai dai yayi ma Yasna faɗa ya fi sau biyar, duk kuwa irin natsuwar da tayi dan kar tayi abun magana, amma bata tsira ba dan ba ta iya zaman minti goma ba tare da tayi ƙiriniya ba sai dai idan Farha ce a gidan ko kuma Hajiya Karime, shi ne kawai zata koma ɗaki ita kaɗai ta zauna

Gaba ɗaya jinta take a takure amma ya ƙi barin parlourn, sai kawai ta ce

"Laaaa, Ya Jafar na manta, Sweet Bro ya ce idan ka gama cin abincin ka same shi part ɗinshi"

Wani wawan kallo ya aika mata, ya ce

"Har yanzu ke ba za ki daina wannan sakarcin ba ko! Sai a aike ki ki wani ce wai kin manta"

Ɗan turo baki tayi, ta ce "Ya Jafar mantawa fa nayi, ai ba da gangan ba ne"

Fuska a murtuƙe ya ce "zan fasa miki baki wallahi, kin san halina"

Kallonshi take ta ƙasan ido dan taga ta inda zai taso ta ƙara ma ƙafar ta mai, sai ta ga ya tashi ba tare ma da ya sake kallon gefenta ba ya fita

Kwantawa tayi tana cewa "wai, na gode Allah na sallame shi, in ɗan huta kafin ya sake dawowa"

Yasmin ta ce "kin sallame shi? Lallai ma yarinyar nan, ba za ki daina ba dai kenan"

"Meye to, sallamarshi nayi ai, Sweet Bro bai ce in kira shi ba"

Ammi ta ce "kin san idan yana jibgarki ko a jikina ko!"

"Ai Yayana ba zai bari ba" ta faɗa tana wani turo baki, ita mai Yaya

Yasmin ta ce "jikinki ne ke ƙaiƙayi yarinya"

Ko kallonta ba tayi ba ta tashi ta canza channel ɗin da ya sa na ƙwallo, zuwa Star Life


A b'angaren Jafar kuwa, lokacin da ya shiga part ɗin Arshad, a zaune ya same shi cikin parlour kan one seater, ya ɗora ƙafafunshi gaba ɗaya kan center table, ido a rufe

Bai tsaya wurinshi ba ya wuce ɗakin da Yasna ta kai mishi akwatinshi, dan nan yake sauka idan ya zo dama, yayi wanka ya sauya kaya sannan ya fito, yanda ya bar Arshad haka nan ya zo ya same shi, sai da ya ɗauko drink a fridge sannan ya zo ya tashe shi

A tunaninshi bacci yake yi, amma sai ya ga yana ɗora hannunshi a ƙafarshi ya buɗe ido

Hannu biyu ya sa ya shafa fuskarshi, sannan ya gyara zama haɗi da sauke ajiyar zuciya, ya ce "Ya dai Jafar, har ka shigo?"

Cikin mamaki Jafar ya zauna, ya ce "har na shigo fa ka ce! Tun ɗazu nake zaman jiranka wurin Ammi, ka ce za ka dawo, amma har na gama cin abinci, shiru"

Ɗan guntun tsaki AAJ yayi, sannan ya ɗauki wayarshi da ke kan table ɗin, ƙarfe biyar da mintuna arba'in da biyu, sai ya sake kiran numbern Hanan, har ta tsinke ba'a ɗauka ba

Fuskarshi cike da damuwa, Jafar na kallonshi, ya ce "Ya Arshad dan Allah wai me ke damunka ne?"

Kamar ba zai yi magama ba, sai kuma ya ce "Jafar ina cikin damuwa, na kasa gane meke shirin faruwa, gaba ɗaya zuciya ta abubuwa take kawo mun wanda ba zan iya ɗauka ba"

"Wace irin damuwa Ya Arshad?"

Tas ya kwashe duk abunda ya faru jiya bayan zuwanshi gidansu Hanan ya gaya mishi, sannan ya sanarda shi yau tun safe yake kiranta amma bata ɗauka ba

Jafar ya ce "amma sai nake ganin kamar ba matsala ba ce hakan da mahaifiyarta tayi, idan ma da matsala to rashin ɗaukar waya ne"

"Jafar ba za ka gane ba, lokacin da Ummi ta mun wannan maganar ranta a b'ace yake sosai, kuma ni ban tab'a ganin fushin Ummi ba"

Shiru Jafar yayi, can kuma ya ce "je kayi wanka dai first Ya Arshad, daga baya mu san abunyi"

Ɗan murmushi AAJ yayi, ya ce "wai yau ni ake ce ma in je inyi wanka, lallai akwai matsala kuwa"

Dariya Jafar ke yi, ya ce "to Antynmu ce ta gama da kai"

"Ai kuwa ta gama da ni.........bari in fito"

"Aha"

********************

"Hayatee na rantse idan kika ce kukan nan za kiyi ta yi, za ki daina ganina, na gaya miki komai a hankali za mu bi shi, amma tun ɗazu ko saurara ta ba kya yi!" Cewar Yuhanees a hasale

Hanan na yaƙin dakatar da kukanta, ta ce "kiyi haƙuri rabin rai na daina, Ummi ta raba ni da Arshad ke kuma kina maganar rabuwa da ni, ya kike so inyi to, ke kaɗai ce kika damu da ni rabin rai, Ummi ko kallona ma ba tayi dan kawai kar na mata magana akan Arshad"

Yuhanees ta ji kuma tausayinta, sai ta ce "shikenan ya isa haka nan, in sha Allah zanyi ma Umma magana, ta zo da kanta, may be Ummi ta gaya mata dalili, kinji"

Ɗaga kai tayi tana sharar hawaye, Siyama ta shigo hannunta riƙe da wayar Hanan

"Sister ga wayarki, yanzu na shiga ɗakin Ummi na ji tana ƙara, kin sha missed calls"

Yuhanees ta karb'i wayar, tana kallon missed calls ɗin ta buɗe ido, "37 missed calls! How comes!"

Hanan na jin haka, ta karb'i wayar da sauri, dan zuciyarta ta bata cewa Arshad ne, kwata-kwata ba tayi tsammanin yau zai kirata ba, shiyasa ko wayar ba ta nemi inda take ba. Ai kuwa tana dubawa, ta ga 2missed calls na MK, 2missed calls na Zulaihat 1missed call na wata ƙawarta, sai dai ba su ne suka dame ta ba, irin 32missed calls ɗin Arshad da ta gani, da sauri ta shiga kiranshi

Fitowarshi daga wanka kenan ya gama shiri yana zaune bakin gado, Jafar ya kawo mishi wayar, yana faɗin "ga Antynmu ta ga daman kira"

Da sauri ya miƙe ya karb'i wayar, "da gaske?"

Yana ganin ita ɗin ce bai tsaya b'ata lokaci ba ya ɗauka, lokaci ɗaya kuma ya zauna yana cewa "Hanan yau kin wahalar da ni, lafiya kika ƙi ɗaukan kira na?"

Shiru tayi tana ƙoƙarin share hawayen da ke ta gangarowa kan fuskarta

Jin tayi shiru yasa ya sake kiran sunanta "Hanan!"

"Na'am" ta amsa a hankali, ba ta ma yi tsammanin ya ji ta ba

Rasa natsuwarshi yayi, dan tabbas daga yanda ta amsa mishi ya san akwai wani abu, "Hanan lafiya kuwa? Me ke damunki?"

"Ummi ce......" daga faɗin haka ta kasa ƙarawa da komai dan kukan ya fi ƙarfinta

"Hanan ki natsu mana ki mun magana, bata da lafiya ne ko me?" 

Girgiza kai ta riƙa yi sai ka ce yana ganinta, Yuhanees ta karb'i wayar daga hannunta

"Hello AAJ"

"Na'am....Yuhanees ko!?" ya faɗa, hankalinshi a tashe, dan yau ne karon farko da ya fara jin Hanan na irin wannan kukan

"Eh ni ce"

"Me ke damun Ummi ne?"

"A'a lafiya ƙalau take..."

"Amma shi ne Hanan ke kuka? Ki gaya mun gaskiya dan Allah" ya katse ta, dan ya ƙagu ya ji menene

"Ka ga AAJ, calm yourself down pls, ba wani babban abu bane fa"

"Kamar ya ba babban abu bane! Take kuka?"

Ɗan rufe ido tayi ta dafa kai, dan ta fahimci wannan ba ma tsayawa zai yi ta mishi ƙwaƙƙwaran bayani ba, a ranta ta ce 'anya ma kuwa AAJ zai iya kwantar ma Hanan hankali idan ya ji abunda ke faruwa kamar yanda nake tunani? Na ga alamar tun yanzu yana cikin damuwa.....' 

Zancensa ne ya katse ta "kinyi shiru, ko in zo ne"

Da sauri ta ce "a'a ba sai ka zo ba" dan ta san Ummi ba za ta so zuwan wanda ko maganar da ta shafe shi ma ba ta son ji ba

Ta ƙara da cewa "gobe zan zo in same ka company in sha Allah, za ka ji ko menene"

Cikin yanayi na damuwa ya ce "amma kukan da take yi fa?"

"Wannan ma ka manta da shi, duk zan gaya maka gobe"

"To amma....."

"Dan Allah ka kwantar da hankalinka, ina nan tare da ita, ba komai trust me"

Ba wai dan ya yarda da ba komai ɗin ba, ya kawai ce mata "shikenan"

"Yawwa sai anjima" ba ta tsaya ta ji ko yanada wata maganar ba, ta kashe, kallon Hanan tayi da ke ta sharar hawaye, ta taya ta share hawayen ta ce "yi haƙuri hayatee kinji"

"Rabin rai ina tunanin yanda Arshad zai ji maganar nan, ya sha gaya mun ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, lokuta ba adadi, cewa ba zai iya jure rashina ba, Rabin rai idan jin wannan hukunci na Ummi ya jefa shi wani hali kuma fa? Wallahi ba zan yafe wa kai na ba idan wani abu ya same shi ta dalili na"

"Haba Hayatee, yanzu dan ya faɗi haka shikenan aka ce miki wani abu zai same shi? To idan dama can Allah bai ƙaddara ke matarshi ba ce shiyasa Ummi ta zama sanadiyyar raba ku fa, dole ne ya ɗauki ƙaddara ai"

"Da gaske fa yake yi Yuhanees, duk lokacin da zai faɗi hakan, ba wasa a fuskarshi yake magana"

"Hanan wannan duk soyayyar da yake miki ne ya sa ya ce haka, amma ba dan wani abu zai same shi ba, duk wasu masoyan gaskiya haka suke ji a ransu cewa za su iya mutuwa idan ba ɗaya, amma ba abunda zai same su ko da a ce sun rabu, shi ma AAJ haka ne, nothing will happen to him (ba abunda zai same shi)"

Tayi shiru tana tunanin ta yadda zai ɗauki wannan maganar, da irin kallon da zai musu ita da Ummi, yaudararshi su kayi ko kuma cutarshi su kayi? Wane irin tunani zai yi akan hakan? Tunanin dake yawo a ƙwaƙwalwarta kenan


Arshad kuwa tunda Yuhanees ta kashe wayar, yake jin bugun zuciyarshi na ƙaruwa, "me ke shirin faruwa ne wai?" tambayar da ta fito bakinshi kenan

Jafar ya ce "ko ma menene ina fatan alkhairi ne Ya Arshad....na ga gaba ɗaya ka sake canzawa, menene?"

Kamar wani me tsoron magana, ya ce "ban sani ba Jafar, sai gobe zan sani, sai dai ko menene jikina ya bani ba alkhairi bane"

"Ka daina munanan ma kanka zato mana Ya Arshad...yanzu ka tashi mu tafi masallaci, an fara kiran sallah, daga nan sai ka roƙi Allah ya sa ka ji alkhairi, nima zan taya ka, amma damuwan nan ba na ka bane Yaya, sai ka ce dai ba AAJ ɗin da na sani ba?! You've totally change today ( yau gaba ɗaya ka canza)"

Ya kusa mintuna uku a zaune, sannan ya je yayi alwala ya fito, Jafar ma yayi, sannan suka wuce masallaci tare

********************
Washe gari da safe, Arshad da Jafar suka tarar da su Ammi a dinning area domin yin break fast, a gaggauce suka gama saboda Arshad ji yake kamar yayi tsalle ya ganshi a company

Suna gamawa suk fito tare zuwa parking area, Jafar ya nufi wurin motarshi, Arshad ya ce "ka zo mu tafi da wannan mana, meye amfanin raba mota tunda wuri ɗaya za mu je"

"Ya Arshad zan biya wurin abokin Abba ne, jiya da muka yi waya da shi da daddare, ya ce mun da safe in zo, ka je kawai zan same ka"

"Shikenan to, sai ka zo"

"Yawwa safe journey"

Daga nan kowa ya ja motarshi ya bar gidan


A office Arshad sai duban hanya yake tayi ta inda zai ga Yuhanees, gaba ɗaya ya gagara natsuwa yayi aiki

Ganin Sajjad da yayi ne ya sa shi buɗe ƙofar

"Ya dai Super, yau ka shigo da wuri, akwai wani sabon deal ne?" Sajjad ya faɗa yana ƙoƙarin zama

"Wane deal, kai dai zauna, gulma ce ta kawo ka"

Dariya Sajjad yayi, ya ce "naji dai.....wai ina Jafar? Na ɗauka tare za ku zo"

"Ya tafi wurin abokin Abba ne, amma zai zo"

"Ok, to sai ya zo"

Daga haka ba su sake magana ba, sai Sajjad da ke haɗa wasu takardu, Arshad kam sauraren zuciyarshi kawai yake tayi

Suna cikin wannan yanayin ne ya hango Yuhanees wurin Khairat, shi da kanshi ya kira Khairat ta wayar telephone ya sanar da ita Yuhanees ta shigo, ko kafin ta ƙaraso ya danna mabuɗin ƙofar, shigowa kawai tayi

Sai da suka gaisa, sannan Sajjad ya ce "kamar ƙawar Hanan ko!"

"Eh ni ce" cewar Yuhanees bayan ta zauna a kujerar da ke fuskantarshi

"To ina Hanan ɗin?"

"Ai ba ta ma san zanzo nan ba"

"To lafiya?"

Arshad ya ce "Ya salam! Dan Allah kayi haƙuri da tambayoyin nan haka.....Yuhanees ina jinki"

Ɗan murmushi tayi ta ce "umm AAJ, wato matsalar da ke nan shi ne, a yanda Hanan ta mun bayanin yanda Ummi ta yi bayan ganin hoton Amminka, hakan ya sa nake zargin akwai wani abun da ya faru tsakaninsu, wanda ya sa duk haƙurin da Ummi take da shi sai da ya zama silar b'acin ranta, maganar gaskiya jiya da kaina na je domin jin dalilin da yasa Ummi ta b'ata rai bayan ganin hoton Amminka, sai ta nuna mun gaba ɗaya bata son maganar......"

Jan numfashi yayi, a hankali yana furta "inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un, dama sai da nayi wannan tunanin, dole akwai abunda ke tsakaninsu"

Shiru yayi, sai kuma a sanyaye ya ce "to idan Ummi tayi tunanin hanani Hanan kuma fa ta sanadiyyar halin Ammina.....astaghfirullah, ba na fatan hakan ma" ya ƙarasa yana girgiza kai ido a rufe

Yuhanees kuwa da ke kallonshi, cike da tausayi a ranta ta ce "sai dai kar a sake, amma tun a ranar Ummi ta yanke alaƙar dake tsakaninka da ƴarta, i'm sorry AAJ, amma ba zan iya kallon cikin idanunka in gaya maka Ummi ta raba ku ba, ko dan halaccin da kayi mana a baya..' maganar Arshad ɗin ce ta dawo da ita daga zancen zucin da take yi

"Yuhanees yanzu me kike tunanin ya dace? Ba kya ganin idan na tafi da kaina may be Ummi za ta iya gaya mun ko ma menene?"

Sajjad ya ce "anya kuwa? Kana ji fa tace Ummi ba ta son maganar, zuwanka kuwa ba zai ƙara b'ata mata rai ba?"

"Man idan ban je ba, Ummi za tayi tunanin halinmu ɗaya da Ammina na wulaƙanta ɗan adam, it's better idan na bata haƙuri"

Yuhanees ta ce "amma da ka saurare shi, domin maganarsa a kan hanya take, ni a ganina, mahaifiyarka ya kamata ka tambaya abunda ke tsakaninta da Ummi"

Arshad ya ce "amma taya zan tambaye ta, bayan ba ta ma san Ummi ba?"

Yuhanees ta ce "na tabbata ta santa, idan kayi mata ƙwaƙƙwaran bayani zata gane"

"Amma..."

Sajjad ya katse shi da "na san kana tunanin abun da kamar wuya, amma nima a nawa ganin, Ammi ya kamata mu ji ta bakinta, tunda har ran Ummi ya b'aci haka, da wuya ta saurare ka"

Ajiyar zuciya yayi yana shafa fuskarshi da ya ji ta fara zafi, sannan ya ce "shikenan Yuhanees, nagode. In sha Allah zan bincika, ko ma menene san sanar miki....amma dan Allah ki kula da Hanan, na ba ki amanarta, dan Allah"

"Na ɗauka, in sha Allah zan kula da ita, komai zai daidaita, ka kwantar da hankalinka"

Lumshe ido yayi, yayi mata murmushin ƙarfin hali, dan bai kai zuciyarshi ba, ya ce "nagode"

Miƙewa tayi tsaye, ta ce "ni zan tafi.....amma dan Allah ina son magana da kai" ta faɗa gana kallon Sajjad

"Ni!!!"

"Eh, ko sai an sa hannu sannan ake magana da kai?"

Murmushi yayi, ya ce "to may be"

Sannan ya tashi ya bi ta bayan ta sake yi ma Arshad sallama, ko ta kansu bai bi ba, dan abunda ke ranshi kawai ya ishe shi

Sai da suka kai harabar kampanin, sannan suka samu ƙarƙashin wata bishiya suka tsaya

"Sajjad!" Yuhanees ta kira sunanshi

"Ina ji ki Yuhanees"

"Zancen gaskiya, maganar da ta kawo ni, ba ita na faɗa ba"

"Kamar ya?"

"Abunda na zo in gaya ma Arshad, ba shi na faɗa ba, saboda ban san ta inda zan fara kallon fuskarshi ba in ce mishi wai Ummi ta raba tsakaninsu da Hanan"

Wani zaro ido Sajjad yayi, ya ce "kamar ban fahimce ki ba, ki mun bayani yanda san gane"

Gyara tsayuwarta tayi, ta ja numfashi, sannan ta ce " Sajjad, tun a ranar Ummi ta yanke alaƙar Hanan da Arshad, dan kuwa ta ce ba Hanan ba Arshad, jiya na shiga domin jin dalilinta na rabasu, amma sai ta nuna mun b'acin ran da ban tab'a ganinta da shi ba, kuma ta ce mun idan ina so in ci gaba da rayuwa da ita cikin farinciki, kuma ta ci gaba da ɗauka ta a matsayin ƴarta, to ko da wasa kar na sake yi mata magana akan Arshad ko danginshi, ko kuma abunda ma ya shafe shi, hakan ya tabbatar mun da akwai wani babban abu tsakanin Ummi da Ammi, ba wai wulaƙanci ba kamar yanda AAJ ke tsammani, tabbas akwai wani b'oyayyen al'amari a ganina"

Sajjad jin maganar yake kamar almara, da bai tab'a zaton haka daga Ummi ba, sai dai ya yarda Yuhanees na da gaskiya, akwai wani abu wanda basu sani ba

Ganin ya tsunduma cikin tunani ya sa Yuhaneea ta ce "ni ma nayi matuƙar mamaki ranar da naji haka, kamar dai yanda ka ji, amma na gaya maka ne ba wai dan ka tsaya tunani ba, sai dai dan ka san ta hanyar da ya kamata ka gaya ma Arshad wannan magana, ni dai wallahi ba zan iya ba"

"Yuhanees akwai matsala, dan ni ma ban san ta inda zan fara ba, amma dai zan san abun yi"

"Shikenan, bari in wuce, dan zan shiga makaranta"

"Ok, ba damuwa, Allah ya taimaka"

"Ameen, sai anjima" sannan ta fita ta bar kampanin

Sajjad kuwa ya daɗe wurin a tsaye yana nazarin maganar nan, kafin daga bisani ya koma ciki, sai dai office ɗinshi ya wuce

********************

Jafar na zaune cikin wani parlour mai girma, parlourn ya haɗu ba laifi, sai kayan drinks da snacks dake gabanshi kan center table, wayarshi kawai yake dannawa

Wani babban mutum ya sauko daga saman stairs, yana hango Jafar ya fara murmushi, shi ma Jafar ɗin miƙewa yayi tsaye har ya iso wurinshi, sannan ya ɗan risina ya gaishe shi bayan mutumin ya zauna

"Malam Jafar, zauna mana"

Komawa yayi ya zauna, sannan ya ce "na same ka lafiya?"

"Lafiya ƙalau, Jafar an girma, an zama babban mutum"

Ɗan murmushi yayi kai a ƙasa, sannan mutumin ya ce "Alhaji Yusuf ya sanar da ni komai akan zuwanka, ina fatan zaka iya"

"Eh Abba zan iya"

"To madallah, ina fatar kasan yarinyar ko, dan ni dai a saninta nayi ba"

"Eh na san ta"

"Yawwa, to akwai yaron da zan haɗa ka da shi sai kuyi tare, yanzu zan ba ka numbernshi sai kuyi magana"

"To Abba"

Wata ce ta shigo da sallama, ta sunkuya, "Daddy barka da hutawa"

Shiru yayi yana duba wayarshi, sai da ya ga numbern da yake nema, sai ya miƙa ma Jafar wayar, sannan ya ce "Samira kin dawo"

Shiru, Samira ba ta ji, dan hankalinta ya karkata wurin kallon Jafar, shi kuma bai ma san tana yi ba, dan tun da ta shigo ko kallonta bai yi ba

Alhaji Sa'ad ya ɗan murmusa, ya ce "Samira!!"

"Na'am Daddy" ta faɗa a razane

"To tashi ki shiga ciki"

"Dadday baƙo kayi?"

"Eh, Jafar kenan, ɗan Alhaji Yusuf na adamawa"

"Ayya, sannu Jafar"

Ko ɗaga ido bai yi ya kalle ta ba, ya ce "sannu"

Alhaji Sa'ad ya ce "ya sunan yaran ma?"

"Farha da Hanan" ya faɗa yana miƙa mishi wayar bayan ya ɗauki numbern

"To shikenan, sai na ji ku"

"Yawwa Abba, sai anjima"

Sai da ya fita sannan Samira ta ɗauke idanunta daga gare shi, ta ce "Daddy na ji kunce Farha da Hanan, wani abu suka yi ne? Kuma shi ma Jafar ɗin ɗan sanda ne?"

Murmushi yayi, ya ce "a'a Samira, ba ɗan sanda ba ne, shi ɗan kasuwa ne, tare da babanshi yake aiki, amma yana karatun likitanci....Farha da Hanan kuma, wasu ne da ake so ayi bincike akansu, waɗanda Yayanshi zai aura ne"

Ba ta bari mamakin fuskarta ya bayyana ba, ta ce "Ayya, to Allah ya taimaka"

"Ameen"

Tashi tayi ta shiga ɗakinta, mayafinta ta ajiye, sannan ta kira Farha

"Samy lafiya? Na ga yanzu muka rabu" cewar Farha

"Lafiya ƙalau, kawai wata gulmar ce na samo"
 
Dariya Farha tayi, ta ce "to ki bari in isa gida sai in kira ki"

"A'a, da zafinshi nake son gaya miki"

"To ina jinki"

"Yanzu da na shigo gida, na taradda ƙanin AAJ tare da Daddy suna magana akanku ke da Hanan"

"Ban gane ba, AAJ fa ba shi da ƙani"

"Yana da shi, daga adamawa ya zo, Daddy ya gaya mun wai za'a yi bincike ne akan halayyarku ke da Hanan, saboda Arshad zai aure ku, amma Daddy bai san na sanki ba"

"Toooo!!! Bincike kuma shi ne ban sani ba?"

"To in ban da abunki, ai ba za'a gaya miki ba"

"Amma ko Mummy ba ta sani ba, dan tabbas da ta gaya mun, kuma wai ni da Hanan, wallahi ba zan yi zaman kishi da wannan ƙazamar ba, dole ni kaɗai zai aura"

"Haka ne"

"To ni tashin hankalin ma, kar a je a binciko abunda bai da ce ba"

"Wannan ba abun damuwa bane, naji wai da Jafar ɗin da wani ne za suyi binciken, to na tabbata ko waye cikin mutanen Daddy ne, ni zan ji da komai"

"Na san me za ki iya Samy, amma shi Jafar ɗin kina ganin zai yi yanda kike so ne? Ɗan uwanshi ne fa"

"Kar ki damu, ni gayen ma ya mun wallahi, sai dai da alama yana da jin kai, sai dai i can manage to deal with him"

Dariya tayi, ta ce "na san za ki iya, sai dai idan ba ki kyasa ba, Allah ya bamu sa'a ƙawas"

"Ameen, bye yunwa nake ji" suka katse wayar suna dariya.........








🥰UMMEETA🥰......📝



♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 29* 

Zayyad ne ke waya da MK yana sanar da shi sun kammala komai

"Komai ya kammala MK, abunda ya rage kawai mu jira isowar kayan, dan na gama magana da su"

"Kai amma wallahi na ji daɗi sosai, burina ya kusa cika, Alhamdulillahi" MK ya faɗa cikin farinciki yana jujjuyawa kan kujerarsa

"Amma fa za su ɗauki kusan wata ɗaya zuwa biyu kafin kayan su ƙaraso"

"Haba! Ni da nayi jiran shekara ɗaya da watanni, ai dan wata biyu ba komai ba ne in dai zan samu yanda nake so"

"Za ka samu mana, ai ka san yanda suke, ba wasa"

"Yayi kyau, to yanzu yaushe za ka dawo?"

"Nan da kwana uku in sha Allah, ina fatar dai kana kula da mutumiyar"

Tsaki ya ɗan yi, ya ce "kwana biyu ban ganta ba ma, kuma na kira wayarta ba ta ɗauka ba, haka ma ƙawarta na sa ta kira ta, still ba ta picking"

"Me kake nufi kenan? Dan Allah ka aika a duba mun ita, please"

"A'a Malam, akan me zan wani duba ta? Kai ke buƙatarta ba ni ba fa"

"Amma ai idan ka duba ta, amfaninmu ne gaba ɗaya"

"Amfaninka dai, ta ya yake amfani na?!"

"Kar ka manta fa, kana so ta yarda da kai, kana so ta yarda ka canza, to ta ya hakan zai faru idan dai ba kana nuna kulawarka akanta ba?"

"Ni ai na gama da wannan matsalar, dan ta taimaka mun ne fa yasa nayi hakan, kuma an wuce wurin"

"Wai meyasa wani lokacin ba ka lissafi ne? Yanzu fa idan ka koma halinka na da, za'a yi saurin zarginka idan wannan abun ya tabbata, amma idan kana kula da ita ba zata kawo ka cikin suspects ba"

Shiru MK yayi yana nazarin maganar, sai kuma ya ce "haka ne kuma, to zan duba......amma dai na san wannan bayanin duk dai kanka ne kayi ma"

Dariya Zayyad yayi, ya ce "whatever dai, tunda ka yarda za ka duba mun Hanani ta"

Shi ma MK dariyar yayi, ya ce "uban soyayya, sai dai ba na tsakani da Allah ba"

"Kai ban son tone-tone, ina da abun yi, sai anjima" ya faɗa yana ƴar dariya, sannan suka kashe waya

********************
Yuhanees na cikin gida tana wanke-wanke, Umma kuma na kan kujera gefenta tana gyara mata kayan miya, sai Yuhanees ta ce

"Umma"

"Na'am"

"Dan Allah wani taimako nake so"

"Kuɗi ko!"

Dariya Yuhanees tayi, ta ce "kai Umma, shikenan idan na ce taimako na kuɗi ne?"

"Eh mana, halinki na sani"

"To Umma ba wannan ba ne, akan maganar su Hanan ne da Arshad da na gaya miki"

"To, ya ake ciki kuma yanzu?"

"Kin san na gaya miki yanda muka yi da Ummi da na je tambayarta ko!"

"Eh" cewar Umma ta na ƙara mayar da hankalinta wurin Yuhanees

"Yawwa, to shi ne nake so ki je da kanki dan Allah kuyi magana, may be ke zata iya gaya miki"

"Anya kuwa Yuhanees!?, ni fa a yanda nake gani, kamar wani abu ne wanda kwata-kwata ba ta son tunawa da shi, shiyasa ma ta dakatar da ke tun wuri akan maganar, kina ganin nima idan na koma ba zata ga an takura mata ba"

"Amma Umma so kike a kyale abun haka ba tare da ɗaukar mataki ba? Wallahi Umma Hanan ta canza gaba ɗaya, ta zama abun tausayi, ko dan ita ki tafi ki rarrashi Ummi dan Allah"

Shiru tayi tana tunani, Yuhanees ta sake cewa "dan Allah mana Ummana, kar ki ce a'a"

Ajiyar zuciya tayi, ta ce "to shikenan ba damuwa, anjima idan rana tayi sanyi, zan tafi"

"Yawwa Ummana, na gode sosai"

"To yi sauri ki gama wanke-waken, ga kayan miyan nan na gyara, ki zo ki ɗora abinci, kin san Yayanki yanzu idan ya dawo ba ji ba gani"

Dariya tayi ta ce "wallahi kuwa, kamar ya fi kowa jin yunwa"

"Namiji ne to, kin san akwai su da cin tsiya"

Ita dai Yuhanees dariya kawai take yi, ta juya ta ci gaba da wanke-wankenta

********************

 "Sister dan Allah ki ci abinci dan Allah, wallahi zama da yunwa ba zaiyi miki maganin komai ba" cewar Siyama dake zaune gaban Hanan a tsakar gida, ta sa ta gaba da abinci

"Seema ba zan ci ba, na gaya miki ba na jin yunwa"

"Kamar ya za ki ce ba kya jin yunwa? Jiya ba ki ci abinci da daddare ba, yau da safe ma ba kiyi breakfast ba, sannan yanzu abincin rana ma ki ce ba za ki ci ba?"

Share hawaye tayi, ta ce "ba za ki gane yanda nake ji bane Seema shiyasa kika takura akan sai na ci abinci"

Ita ma Siyama na ƙoƙarin mayar da hawayen da suka taru cikin idonta, ta ce "na san yanda kike ji Sister, amma hakan ba shi zai sa in bari wani abu ya same ki ba, dan Allah ki ci ko kaɗan ne"

Su na haka ne, Ummi ta shigo gidan, da sauri Siyama ta isa wurin Ummi ta ce "Ummi dan Allah kiyi mata magana ta ci abinci ko kaɗan ne"

Wani kallo Ummi tayi ma Hanan, ta ce "ke!"

Ɗaga ido Hanan tayi ta kalle ta, sai ta sauke, Ummi ta ce ma Siyama "to ke meye na ki dan ba ta ci abinci ba? Cikinki ne ko na ta?"

"Amma Ummi....."

"Ke ki rufe mun baki, in dai akan Arshad ne ta ƙi cin abinci, to wallahi ba zan tab'a lallab'arta akan ta ci ba, ta tabbata a hakan, ke ma idan kika sake mun magana makamanciyar wannan, wallahi sai na sab'a miki" tayi tsaki ta wuce ɗaki

Hanan kuwa kuka ta saki mai cin rai, ta yanda ta ji Umminta ce yau ba ta damu da ita ba, tunani take wannan wace irin ƙiyayya ce tsakanin Ummi da su Arshad da har akan hakan gaba ɗaya ta canza kamar ba ita ba......Da wannan tunanin ta tashi ta shiga ɗaki ta kwanta har bacci yayi awon gaba da ita, dan jiya ma bata samu bacci ba


Siyama kuma gaba ɗaya tausayin Yayarta take ji, hakan yasa ta ɗauki wayar Hanan da ke wurin, ta shiga kiran Arshad

Yana zaune balcony ɗin part ɗinshi, yana aiki cikin laptop, sai dai rabin hankalinshi ba nan yake ba, ji yayi wayarshi na ringing, sai ya ajiye laptop ɗin ya ɗauki wayar, yana ganin numbern Hanan ya ɗauka, sai dai ya ji muryar Siyama maimakon ta Hanan

"Siyama lafiya na ji muryarki ta sauya?"

"Ya Arshad kai kaɗai ne za ka iya yi ma Sister magana yanzu ta ɗauka"

"Me tayi?"

"Ya Arshad tun ranar da Ummi ta ce ta raba ku take cikin damuwa, kullum ba ta da aiki sai na kuka, yanzu ma abinci tun jiya da rana rabonta da shi, nayi mata magana amma ta ƙi saurarata"

Duk abunda Siyama ke cewa, ba abunda ya shiga kunnen Arshad illa 'tun ranar da Ummi ta raba ku', tun da ya ji hakan, zuciyarshi ta wani buga har cikin kanshi

Da ƙyar ya iya cewa "me kika ce Siyama? Me Ummi ta yi?"

"Ya Arshad tun ranar da ka zo last ɗin nan, bayan tafiyarka, Ummi ta ce ma Sister ba ta ba kai, infact dai tun wannan ranar, gidan nan ba daɗi dan Ummi ta canza ga baki ɗaya, Sister kuma kullum cikin kuka take"

"Siyama ban son wasa irin wannan....." ya faɗa yana ƙoƙarin cire wannan maganar a ranshi, dan so yake ya tabbatar ma kanshi maganar Siyama ƙarya ce 

"Ya Arshad wallahi ba wasa nake yi ba"

A ranshi yake maimaita 'La haula wala quwata illa billah' sau uku 'me Siyama ke cewa ne haka? Ya Allah ka sa ba haka bane, ita ce bata fahimci Ummi ba'

A zahiri ya ce "Siyama, ina zuwa" sannan ya kashe wayar, ya dafe kanshi da ya ji yqna barazanar fara ciwo yayi

Sajjad da zuwanshi kenan, ya ga Arshad a zaune ya matse kai, sai ya ja ɗayan kujera ya zauna yana tab'a shi, ya ce

"Super!"

Buɗe ido yayi ya sauke su kan Sajjad, sai ya ce "yawwa Man, zo muje" jan shi yayi zuwa parking area wurin motar Sajjad ɗin

Sajjad na ganin haka ya ce "lafiya dai?"

"Gidansu Hanan za ka raka ni"

"Gidansu Hanan? Ka yi me?"

"Shiga dai muje"

 Ba tare da ya ce komai ba ya buɗe motar ya shiga cike da fargabar anya kuwa Arshad be ji hukuncin Ummi ba kuwa?

Shi ma Arshad ya buɗe motar ya shiga, sannan Sajjad ya ja suka bar gidan

********************
Ummi na zaune tsakar gida ita kaɗai, kasancewar ta aiki Siyama, Hanan kuma na ɗaki, sai ta ji sallamar Umma

Da fara'arta ta miƙe ta ce "maraba da Umman Yuha, bismillah ƙaraso ciki mana" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin shiga ɗaki

Umma na murmushi ta bi bayanta suka shiga tare, zaunawa suka yi suka fara gaisawa

Ummi ta ce "ke ce tafe"

"Wallahi kuwa, ya gidan"

"Lafiya ƙalau, ya ƙoƙari?"

"To alhamdulillahi" cewar Umma

"To madallah, bari in samo miki ruwa" tana ƙoƙari miƙewa Umma ta dakatar da ita

"A'a bar ruwan nan, zauna dai magana ce ta kawo ni"

Komawa Ummi tayi ta zauna, ta ce "to wace irin magana kuma?"

"Ummin Siyama, Yuhanees ta mun bayani akan abunda ke faruwa, sannan kuma ta gaya mun kina fushi sosai, shiyasa na zo dan in taya su bada haƙuri, dan Allah ko ma menene kiyi haƙuri tunda ya wuce, ke shaida ce akan yaran nan su na son junansu, to dan Allah ki bar su tare kar ki raba su"

Ummi na jin haka, nan take yanayin ta ya canza, ko kallon Umma ba tayi, Umma na lura da hakan, ta dawo kusa da ita ta zauna, ta ce "ba takura miki zanyi ba akan sai kin haƙura, amma dan Allah kar ki zama uwar da za ta zama silar rugujewar farincikin ƴarta"

"Ba farinciki ba, wallahi zan fi murna idan na ga gawar Hanan a gabana, akan ta haɗa alaƙa da wancan dangin"

"A'uzubillahi mina shaiɗanir rajim! Kin san me kike faɗa kuwa? Mutuwa fa kika ce!"

Ummi ta ce "ni kuwa na san me nake faɗa, wallahi na gwammaci ganin rugujewar rayuwarta akan in yarda ta haɗa alaƙa da dangin macuta, maha'inta, mugaye masu kashe rai ba tare da laifin komai ba, azzalumai" ta kai zancen hawaye na zuba daga fuskarta

Nan bakin Umma ya mutu, sai kallonta take yi cike da mamaki, tana da tambayoyin da take son yi wa Ummi, amma a yanayin nan ba zata iya tambayarta ba, share mata hawayen tayi

Ta ce "kiyi haƙuri Ummim Siyama na zamana silar hawayenki, tabbas ba ƙaramin abu bane ya sa ki yanke wannan hukuncin, Allah ya baki haƙuri ya sa mu dace"

"Ba komai, kuma na gode sosai da kulawarku, Allah ya ƙara danƙon zumunci, na san kun damune da farincikin ƴata, haka nima ina son ganin Hanan cikin farinciki, amma a wannan kam sai dai haƙuri dan ba zan lamunta ba"

Sauke numfashi Umma tayi, ta ce "haka ne, amma....."

Sallamar da suka ji ne ya katse mata magana, Ummi ta ce "bari in ga ko waye"

Hijab ɗinta ta ɗauka daga kan ƙofa ta sa, sannan ta fito, Arshad da Sajjad ta gani a tsaye, sai Hanan daga gefe, gaba ɗaya ta canza, sai kallon-kallo suke ita da Arshad, ya na ƙoƙarin tantance gaskiyar maganar daga fuskarta

Da ɗaurarriyar fuska, Ummi ta ce "lafiya?"

Sai a lokacin suka ganta, risinawa suka yi suka gaishe ta, amma bata amsa ba, tun anan jikin Arshad ya fara sanyi

Umma na jin muryarsu, ita ma ta fito, gaishe ta su kayi ta amsa musu tana kallon yanda Ummi ta wani ɗaure fuska

Arshad ya ce "Ummi na ga gaba ɗaya kin sauya, lafiya kuwa?"

Wani mugun harara ta zabga mishi, ta ce "Arshad me ya kawo ka gidan nan?"

"Ummi wurinki na zo, dan Allah ki gaya mun meke faruwa, me ya kawo wannan sauyin naki?, Ummi ba haka kike yi ma Arshad ɗinki ba"

"Tabbas da kai ɗana ne, amma banda yanzu da na yanke duk wata alaƙa da kai"

Mummunan faɗuwar gaba ya ji, kenan Siyama da gaske ta keyi, da ƙyar ya ce "Ummi ban gane ba"

Ɗan tab'e baki tayi, ta ce "za ka gane, amma ba ni zan maka bayani ba, ka koma gida ka tambayi mahaifiyarka, ita za ta gaya maka komai, abunda kawai za ka ji daga gare ni shi ne, ba kai ba Hanan har abada"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" abunda yake maimaitawa kenan idanunshi a rufe, har kan shi na sara mishi sosai

Sajjad dake kusa da shi ya riƙe shi, cikin damuwa ya ce "Ummi dan girman Allah kar ki ce haka, ko menene ki bari a sasanta, dan Allah kar......"

Katse shi tayi ta hanyar ɗaga mishi hannu, ta ce "dakata Sajjad, ka daina haɗa ni da Allah akan abunda ba zai yiwu ba, maganar sasanci ma ka daina yin ta, ku fita ku bar mun gida kafin ranku yayi mummunan b'aci"

Arshad ya ma kasa cewa komai, sai saurarar zuciyarshi yake yi dake buguwa a hankali, kan shi na ciwo, a hankali ya ɗaga ido ya kalli Hanan da hawaye ya gama jiƙa mata fuska, ko motsi ba tayi banda kukan da take yi

Juyawa yayi da niyar barin gidan, dan ba zai iya kallon hawayen Hanan haka ba, is better ma ya je yayi maganin wannan abun, tana ganin ya juya ta bi shi da gudunta, ta tsaya gabanshi, cikin kuka take cewa

"Arshad dan Allah kar ka tafi dan Allah ka tsaya ka ba Ummi haƙuri"

Matse ido yayi, ya buɗe, ya ce "Hanan ba tafiya zanyi ba, ai zan dawo kinji"

"Dan Allah da gaske za ka dawo?"

Kafin yayi magana, Ummi ta ce "wane gidan za ka dawo? Wannan gida na ne, kar ka kuskura in sake ganin ƙafarka a nan, idan ba haka ba wallahi Arshad sai kayi nadama"

Umma ta ce "haba Ummin Siyama, da kanki kike haka?"

Kallonta kawai tayi, ta kuma mayar da kallonta gun Arshad da ya riƙe hannun Sajjad da niyar su wuce, Hanan ta sake ɗaga ƙafa da niyar bin shi, a tsawace Ummi ta ce

"Wallahi idan kika ƙara taku ɗaya wurin nan sai dai ki zab'i ko ni ko shi"

Ba Hanan da ta gaya ma haka ba, hatta Arshad sai da gabanshi ya faɗi, da sauri ya ce "Hanan ki koma dan Allah, komai zai wuce kinji, dan Allah......Ummi kiyi haƙuri" yana faɗin haka ya sa kai ya bar gidan, dan zuwa yanzu ji yake ma ba zai iya tsayuwa ba

Sajjad ma fita yayi, Hanan sai durƙushewa tayi nan ta sa sabon kuka, Ummi ko kallonta ba tayi ba ta shige ɗaki, Umma ce ta zo ta ɗaga ta zuwa ɗakinta tana ta rarrashinta


Arshad kuwa a mota ya kwantar da seat ɗin ya kwanta ya dafe kai, gaba ɗaya tunaninshi ya tsaya cak, bai ma san ainihin yanda yake ji ba yanzu, ya matsu ya ganshi a gida dan ya tambayi Ammi meke faruwa

A parking area Sajjad yayi parking, yana ƙoƙarin buɗe ƙofa, Arshad ya riƙe mishi hannu, a hankali ya ce "ka tafi wurin da ake kiranka kawai"

"Wa ke kira na Arshad?"

Ɗan guntun murmushi yayi, ya ce "Sajjad, na ji lokacin da kayi waya da Abba, yana nemanka, dan haka ka tafi kawai, ko ma ya muka yi da Ammi zan gaya maka"

Shi ma murmushin yayi, ya ce "to shikenan, Allah ya shiga wannan lamarin"

"Ameen" ya buɗe ƙofar ya fita, Sajjad kuma ya wuce


Arshad na shiga main parlour, ya taradda Hajiya karime da Farha duk suna nan, sai Ammi, Yasmin da Yasna

Ko kallonsu bai yi ba, ya durƙusa kusa da Ammi ya ce "i need to talk to you Ammi (ina son magana da ke Ammi)"

"Ba ka iya gaisuwa ban ne yau?"

"Ammi dan Allah magana za muyi"

Kallonshi tayi, fuskar nan a tamke, ta ce "wai yaushe ka fara ina magana da kai kana wani cin magani?"

Hajiya Karime ta ce "ki saurare shi mana Hajiya, kika san me ke damunshi?"

"Kyale shi Hajiya, yau iskancin ne ya motsa"

Farha ta ce "haba Ammi, ki saurare shi dai, kin sa......."

Mummunan tsawan Arshad ya katse ta "idan ina magana da Ammi na kar ki sake tsoma mun bakinki, ina ruwanki idan ma ata saurare ni ba"

Farha ta ce "to ina laifi dan kawai na sa baki a lamarin mijina!"

"Zan tsinka miki mari idan na sake jin wannan sunan wallahi"

Ammi ta ce "ko kuma ni in tsinka maka mari ba, tunda baka da mutunci, a gabana kake cewa haka?"

A fusace ya ce "to shikenan" ya tashi ya bar parlourn hadda buga musu ƙofa

Ammi ta ce "ɗan rainin wayo mara kunya"

Hajiya Karime ta ce "ki daina haka mana Hajiya"

"Ki bar ni dashi kawai"

Yasna ta tashi da sauri ta bi shi, ta tsani ta ga Yayanta cikin damuwa, harara kawai Ammi ta bi ta da shi


A parlour ta ganshi tsaye dafe da kai, tab'a shi tayi, ta ce "Sweet Bro menene"

Ƙwace hannunshi yayi da ƙarfi, ya ce "fita ki ba ni wuri"

Ɗan buɗe ido tayi, ta ce "Ya Arshad in fita fa kace! Dan Allah menene?"

A tsawace ya ce "wai ina ruwanki da ni ne? Ki fita kafin in karya ki anan"

Rungume shi tayi da ƙarfi, ta ce "Ya Arshad sai dai ka karya ni, amma bazan kyale ka ba, kana cikin damuwa laifi ne dan na tambaye ka?"

Hawaye suka fara zubo mata, ta ce "Ya Arshad kai ba Yayana ne kawai ba, you are my everything, kai Abbana ne, kai Yayana ne, kai abokina ne kai farinciki na ne Ya Arshad, ba zan iya jure ganinka a haka ba bayan kai kullum burinka bai wuce ka ga farincikina ba"

Nan ya ji tausayinta, shika ya san b'acin rai ne ya sa ya ce ta fita ba wai dan ya so ba, a hankali ya ɗora hannunshi a bayanta, ya rungume ta, ya ce "kiyi haƙuri Sweetie, i'm sorry"

Ya ɗaga ta ya share mata hawayen, ya ce "ya isa haka nan, forgive ur bro pls (ki yafe wa Yayanki dan Allah)"

Sake rungume shi tayi, tana girgiza kai, sannan yaja ta suka zauna, ya ce "bari inyi wanka, kafin a kira sallah kinji"

"Me ke damunka to"

"Zan gaya miki idan na dawo masallaci"

"Shikenan"

Nan ta zauna har yayi wanka, suka fito tare, ya wuce masallaci ita kuma ta koma main parlour ta wuce ɗakinsu ba tare ma da ta kalli gefensu ba..............









🥰UMMEETA🥰......📝



♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata sai a mun uzuri dan akasi aka samu👏👏👏


 *Page 30* 

Masallaci Arshad ya haɗu da Jafar, suka yi sallar magrib, suka jira aka yi isha'i suka yi, sannan suka shigo gida

Main parlour Jafar ya nufa, sai ya ga Arshad ya bi hanyar part ɗinshi, ya ce "Ya Arshad me za kayi can kuma?"

"Ka je kawai, ina zuwa"

"To sai ka zo"
 Sannan ko wanensu ya wuce

Jafar na shiga parlourn ya ga su Hajiya Karime da Farha, gaida Ammi yayi sannan ya gaida Hajiya Karime

Farha kuwa bim sho tayi da ido a ranta tana cewa da alama shi ne Jafar ɗin da Samira ke magana, ko kallon gefenta bai yi ba, ya haura dinning area ya zauna, Inna Asabe ta zo tayi serving ɗinshi

Hajiya Karime ta ce "Hajiya wannan kuma fa? Ban san shi ba"

"Kin san shi mana, sai dai ba lallai ki yi saurin gane shi ba, Jafar ne ƙanin Nabeel"

"Oh Allah sarki, tabbas kuwa ba zan gane shi ba"

Murmushi Ammi tayi ta ce "kin san miskilin yaro ne, ba son shiga jama'a yake yi ba, shiyasa ko sun zo nan ba kya yawan ganinshi sai dai ƴan uwanshi"

"Wallahi kuwa, sauran sun fi shi sakin jiki da mutane"

"Ai haka ta shi rayuwar take shi kuma.....Farha lafiya ba ku gaisa ba?" ta tambayi Farha da ke ta faman latsa waya

Murmushi tayi ta ce "Ammi ai ina jira ne ku gama magana sai in ji ko waye"

"To ɗan uwan Arshad ne, na san ya girme ki a shekaru, amma ta wani fannin za ki iya kiranshi da ƙaninki"

Dariya Farha tayi ta ce "na zama Antyn manya kenan...to bari in je mu gaisa"

Ita ma Ammi dariyar tayi, haka ma Hajiya Karime, sannan ta tashi ta tafi wurinshi, ita kuma Hajiya Karime ta shi gaba da dukan cikin Ammi dan ta ji gaskiyar abunda Jafar ya zo yi kamar yanda Farha ta gaya mata, dama abunda ya kawo su kenan

Ƙarasawarta ke da wuya, ta ja kujerar da ke fuskantarshi ta zauna tana wani salo, sai dai ko ɗaga kai bai yi ba daga abunda yake yi, yana cin abinci ne yana kallo a wayarshi

Kusan minti biyar tayi a zaune ba um ba um um, sannan ta sauke numfashi ta ce "tunda har ƙanina ba zai iya gaida ni ba, ni zan iya ce mishi sannu da hutawa"

Yana jin ta, amma ya ƙyale ta, ƙare mishi kallo tayi da kyau, a ranta ta ce 'lallai wannan yana ji da kanshi, sai dai maganinka zanyi in har ka tono abunda zai raba ni da Arshad" tayi wani guntun murmushin da ita kaɗai ta san ma'anarsa, ta jujjuya idanunta, sannan ta ce "Malam Jafar"

A shaƙiyance ya ɗaga ido ya kalle ta, sannan ya mayar da idanunshi cikin wayar, ya ture plate ɗin gefe 

"Sannunka da zuwa"

Ba tare da ya ɗaga ba ya ce "sannu"

Murmushi ta sake yi tana ɗaga kai a hankali, sannan ta ce "na zo ina ta magana ka ƙyale ni"

A hankali ya ajiye wayar, ya jingina jikin kujerar, a gadarance ya ce "bana sa kaina cikin abunda ba'a saka ni ba shiyasa"

"Amma ai da kai nake"

"Ban ga alamar hakan ba"

"Ko meyasa? Bayan ka san kai kaɗai ne a wurin?"

"Bana da tabbas saboda akwai na b'oye, kuma kalmar da kika faɗa bata nuna alamar da ni kike ba"

"Wace kalma?"

Ɗan rufe ido yayi alamar ta ishe shi, ya ce "tuna da kanki"

"Wai ƙanina da nace? (Tayi murmushi) to ai dalili ne dani shiyasa na faɗa...oh sorry, ban maka introducing kaina ba, sunana Farha Mas'ud, ni ce wacce Arshad yake so kuma zai aure, kaga ai dole in kira ka da ƙanina"

"Ai da ba kiyi wahalar gaya mun sunanki ba dan na sanki sai dai ba lallai ke kin sanni ba, sannan da ba kiyi mun ƙaryar ke Ya Arshad ke so ba, sabida na san ke ce ke sanshi ba shi ke sanki ba"

"Hmm abunda ya gaya maka kenan?"

"A goshinki aka rubuta" ya faɗa yana mata wani mugun kallo, ya miƙe ya ɗauki wayarshi ya bar parlourn gaba ɗaya

Har sai da ya fita sannan ta daina kallonshi, ta ce "tabɗijam" sannan ta sauka parlourn wurinsu Ammi

"Mummy mu tafi haka nan"

Hajiya Karime ta ce "yanzu kin tashi kenan, ai tun ɗazu na ce mu tafi kika ce a'a"

"Mummy Arshad na so gani in ba shi haƙuri ai shiyasa amma bai dawo ba"

Ammi ta ce "ai ba zai dawo ba yanzu a yanda ya fita kam"

Hajiya Karime ta ce "dan Allah dai Hajiya idan ya dawo kiyi ƙoƙarin saurararsa"

"Ai na amsa miki da to tun ɗazu"

"To shikenan, mu bari mu tafi, sai da safe ko"

"To nagode sosai, Allah ya kai ku gida lafiya"

"Ameen" daga nan suka fita Ammi kuma ta wuce part ɗin Arshad



Arshad na kwance, Jafar kuma na ɗayan kujera a zaune

"Ya Arshad wai me ke damunka ne dan Allah"

"Jafar ina cikin damuwa"

"Ta me?"

"Ana ƙoƙarin raba ni da Hanan"

"Hanan? Wa ke son raba ku kuma?"

"Wacce ban tab'a tsammani ba, mahaifiyarta"

"Ta ya? Kace mahaifiyarta kuma ta yarda da alaƙarku"

Ɗari bisa ɗari ma kuwa, amma kwatsam ta sauya, irin sauyin da ya masifar ɗaure mun kai, kuma ta mun bayani ta ce sai dau in zo wurin Ammi"

"Hakan na nufin Ammi ce musabbabin hana ka Hanan ɗin?"

"To idan ba ita ba ce waye?"

Kafin Jafar yayi wata maganar, Ammi ta turo ƙofar ta shigo, Arshad ya tashi ya zauna, ta ƙaraso ta zauna kan kujerar da yake

"Sannu Ammi" cewar Arshad

Sai da ta kalle shi da kyau, ta ce "kai ma sannu......ɗazu me kake son gaya mun"

Kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Ammi akan maganar Hanan ne"

"Hanan, wacece kuma Hanan?"

Kallonta kawai yayi dan ya san ta san wacece Hanan, sai dai kuma ya ce "wacce zan aura"

"Wacce zaka aura ai kamar sunanta Farha, ce mun za kayi Hanan mayyar da ta asirce ka, to ni meye haɗi na da ita da har za ka mun magana akanta?"

"Ba akanta zan miki magana ba, aka mahaifiyarta ne, Ammi dan Allah meke tsakaninki da ita, me kika mata da har take ƙoƙarin raba ni da Hanan?"

Wani dogon tsaki ta ja, ta ce "wallahi Arshad ka raina ni ba kaɗan ba, ita mahaifiyarta ɗin ce ta gaya maka na santa ko na tab'a ganinta? Ni na ma Allah da ta ƙara rage mun aiki akanka da ta raba ku ɗin, tayi aikin hankali da ta gane kai da ƴarta baku dace ba....."

Cikin b'acin rai ya ce "Ammi stop it please, kina pretending kamar ba ki san abunda nake magana akai ba, a yanda Ummi ta mun maganarki ya tabbatar mun da cewa kin santa"

"Ba shakka Arshad wuyanka yayi kauri, ni ke pretending kenan!"

Sauke numfashi yayi ya rufe ido, sannan ya ce "i'm sorry Ammi, amma dan Alkah kiyi tunani, na santa dan a yanda tayi tabbas kun san juna, kiyi haƙuri taimaka mun in samu Hanan, zan raka ki har gidan da safe dan Allah kiyi magana da Ummi, na san idan kika je da kanki za ta sauko"

"Kana da hankali kuwa? Ni zan je gidan matsiyata domin in bada haƙuri a baka auren ƴarsu? Ni ina nan da wacve nake so ka aura ka ƙi, amma shi ne zan je wani wuri roƙa maka auren wata? To bari in gaya maka, ko da ace Hanan sa'ar aurenka ce, muddin mahaifiyarta ta raba ku to ba inda zanje domin bada haƙuri bare kuma ba sa'arka ba ce"

"Ammi in dai kika taimaka mun na samu Hanan, to na yarda zan haɗa har da Farha in aura, dan Allah Ammi ki taimake ni"

Wani murmushi tayi ta ce "Arshad ka daina roƙona, dan ba inda zan je na gaya maka, ka cire ta a ranka gaba ɗaya, kayi shirin auren Farha kuma"
 Ta tashi da nufi barin parlourn, ya ce "Ammi ko da rashin Hanan zai iya zama sanadin mutuwa ta, ba za ki je ba?"

Juyowa tayi ta kalle shi, ta ce "Arshad giyar soyayya ce ke caza maka kai shiyasa kake tunanin zaka mutu, amma mace ba zata zama sanadiyyar mutuwarka ba, ina fatar ka fahimta....Jafar zo ka kulle muku part ɗin, sai da safe" daga ta bar part ɗin, Jafar ya bi ta domin rufe ƙofar

Hannu biyu yasa yana ya mutsa gashin kanshi da ƙarfi yana huci, Jafar ya miƙa mishi cup ɗin ruwan sanyi, da ƙarfi ya jefar da cup ɗin ya fashe, Jafar ya riƙe mishi hannu, ya ce "Please control yourself Ya Arshad, komai zai wuce"

Da ƙarfi ya fizge hannunshi, idanunshi sunyi ja sosai, jijiyoyin kanshi sun tashi, a tsawace ya ce "Control! Control! Control! How?! Ta ya kake tunanin zan iya natsuwa bayan kana ganin ina dab da rasa Hanan, Ammi ma da na sa ran idan nayi magana da ita komai zai daidaita, amma sai naga ashe ƙara tsananta ma zai yi, ita daɗi ta ji, ba zancen ma ta taimaka mun, yanzu me zan iya yi? Me zanyi?" ya ƙarasa kamar me shirin yin kuka

Gaba ɗaya tausayinshi ya kama Jafar, ya ce "kayi haƙuri Ya Arshad, na maka alƙawari da kaina zan je inyi mata magana"

"Haka kake gani kamar za ta saurare ka ne?"

"Zanyi ƙoƙari dai"

"Hmm" abunda ya faɗa kenan kawai, ya kwashe wayarshi ya wuce bedroom

********************
Su Hajiya Karime kuwa suna kaiwa gida, suka zauna a parlour

Hajiya Karime ta ce "daughter ina tunanin Samira ba ta gane abunda ake magana akai bane dai"

"Mummy har gidansu Jafar yake, kuma a gabanta aka yi, na tabbata Samira ba ƙarya take yi ba"

"Idan kuwa haka ne, to Hajiya Ruƙayya ba ta da masaniya, dan ba yanda banyi ba dan inji tayi magana akai amma shiru"

"Nima ina kyautata zaton haka, abunda ya kai shi adamawan kenan"

"Ƙwarai kuwa"

"Amma ba komai Mummy, ni da Samira zamu yi na mu ƙoƙarin"

"Na san za ku iya ai, Allah ya taimake ku"

"Ameen, zan shiga in kwanta Mummy, na gaji"

"Sai da safe, nima zan shiga ciki ne"
Ko wanensu ya wuce ɗakinshi

********************
        *WASHE GARI* 

Siyama ta gama sharar gidan, ta wanke hannunta ta wuce ɗakin Ummi ta zauna, Ummi na kan sallaya tana karatu, ta rufe Qur'anin ta mayar da hanialinta kan Siyama, ta ce

"Lafiya kika dawo kika zauna? Makarantar kuma fa?"

Yamutsa fuska kawai take yi tana murza idanu, Ummi ta sake cewa "ko kema kin shigq yajin aikin ne kamar yanda ita waccan ta shiga ya jin aiki, ta daina fita?"

"A'a Ummi, jikina ne ba daɗi shiyasa"

"Tun yaushe?"

"Da safen nan"

"Hmm, Allah ya sauwake" abunda kawai ta faɗa kenan dan ta san ƙarya take yi, saboda Siyama ko kanta kawai ke ciwo zama take tayi ta kuka saboda tsabar lalaci

Hanan da ta rame ta zama abun tausayi, yunwa ta addabe ta, ta fito ta ɗibi ruwan zafi cikin tukunya, ta je ta haɗa lipton ta sha, bayan ta gama ta wanke cup ɗin ta mayar kitchen ta koma ɗakinta da shi ya zame mata wurin zama yanzu

Wayarta ta ɗauka wacce rabonta da ita kwana biyu kenan, messages masu yawa ta gani da missed calls, fiki harda na Yuhanees, MK, Zulaihat da Arshad wanda duk na shi sun fi yawa a ciki

Messages ɗin shi ta shiga karantawa ɗaya bayan ɗaya, wanda duk haƙuri ne yake ba ta da kuma kwantar mata da hankali tare da tabbatar mata da cewa ba abunda zai raba su, karantawa take tana hawaye har Yuhanees ta shigo ba ta ma sani ba

Ƙwace wayar tayi, ta zauna, sannan ta ce "haba Hayatee, wai wannan kukan kina ganin shi ne ya dace da ke? Kalli kanki ki ga yanda kika wani lalace dan Allah!"

Share hawaye Hanan tayi, ta ce "kiyi haƙuri rabin rai, amma ba zan iya dainawa ba"

"Na san yanda kike ji, amma dole ki tausayawa kanki kiyi haƙuri"

"Mahaifiya ta ma ta kasa tausaya mun rabin rai, ta ya kike tunanin ni zan iya tausayawa kai na?"

"Hana duk abunda Ummi tayi ko in ce take yi yanzu, tabbas tana da ƙwaƙƙaran dalili, saboda Umma ta gaya mun yan da suka yi, hakan ya sa na rage ganin laifin Ummi, sabida duk uwar da zata dage akan irin haka, to dalilinta abun dubawa ne"

Gyara zama Hanan tayi ta ce "ya suka yi da ita? Me ta gaya mata? Menene dalilinta?"

Ɗan murmushi tayi saboda yanda ta jero mata tambayoyi, ta ce "ba zan iya gaya miki ba gaskiya, sai dai akwai shawara ɗaya da zan ba ki"

"Wace irin shawara?"

"Ina so ki samu ki kira wasu daga cikin  ƴan uwan Ummi dan ki ji me ya haɗa ta da zuri'ar Ahmad Jalal?"

Da alamun mamaki a fuskarta, ta ce "kamar ya, ban gane ba"

"Hayatee, a yanda Umma ta mun bayani, na fahimci duk abunda ke tsakanin mahaifiyar Arshad da Ummi, ba abu bane na yanzu, akwai wani abu a ƙasa"

"To ki mun bayani mana"

"A'a, ki dai yi yanda na gaya miki"

"Mutum ɗaya zan iya ma wannan tambayar, shi ma kawun Ummi ne"

"To ki yi ƙoƙarin kiranshi kuwa"

"Shikenan, zan kira shi, amma ana wuyar samun shi, saboda wurin da yake bai cika network ba"

"Ki dai ƙoƙari, yanzu ni zan je makaranta, kin san muna shirye-shiryen ƙarb'ar final result"

"To Allah ya taimaka rabin rai, sai kin dawo"

"Ameen, sai anjima"

Ta fita ta bar ta nan tana nazari kala-kala

********************

"Umar ina fatan ka fahimci abunda na gaya maka ko?" cewar Alhaji Sadeeq  dake zaune a parlourn shi tare da wannan saurayin Umar

"Eh yallabai na fahimce ka, kuma insha Allah zanyi ƙoƙari in yi maka tsakani da Allah kamar yanda ya dace"

"Na san za ka iya Umar saboda na yarda da kai.....kayi magana da shi Jafar ɗin ko?"

"Eh ya kira ni, sannan yau ma munyi magana za mu haɗu"

"To madallah, Allah ya taimaka"

"Ameen yallabai, nagode.....ni zan tafi"

"To a sauka lafiya"

Umar ya tashi ya bar parlourn, a compound ɗin gidan ya isko Samira jikin motarshi

"Hajiya zan wuce" ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe motar"

Matsawa tayi kusa da shi tama wanu rangwaɗa ta ce "ba sunana Hajiya ba Malam, sunana Samira"

"To Samira, nima sunana Umar ba Malam ba"

Murmushi tayi ta ce "Umar Faruk, nice name!......Umar na san me Abbana yake so ka mishi, amma ina neman taimakonka nima"

"Ikon Allah, taimakon me kuma?"

"Yawwa ɗan gari, waɗanda za kuyi bincike akansu, Farha da Hanan, Farha ƙawata ce"

"Ina jinki sai akayi ya?"

"Ina so a binciken da zaka yi, ka sanar da mahaifina cewar Farha mutumiyar kirki ce, ka gaya mishi magana mai daɗi akanta, sannan ka b'ata waccan Hanan ɗin"

Gyara tsayuwa yayi, ya ce "to ke kuwa meye dalilinki na wannan aikin?"

"Ba abunda ya shafe ka bane, kawai kayi mun yanda na ce, biyanka zanyi"

Murmushi yayi, ya ce "nawa kike da shi da har za ki iya biya na?"

"Zan biya ka naira miliyan biyu"

"Miliyan biyu? Kwana nawa za su mun?"

"To zan baka miliyan biyar"

"Biyar?"

"Ka raina?"

"Da alama"

"Zan baka goma to, biyar kafin aiki, biliyar bayan ka kammala"

"Hmm, na fahimci kanki ba ya kawo wuta, to bari in hutar dake, wannan aikin ba na masu tsoron Allah bane, kuma ni ina tsoron haɗuwa da shi, dan haka ba zanyi ba, kuma ki bani hanya ko in bi ta kanki" yana faɗar haka ya buɗe motar ya shiga

Ya mtsa mishi tayi ya ja motar ya bar gidan, ta ce "yau ni naga mai ƙashin tsiya, ban san wurin da Abba ya samo wannan ba wallahi, shiyasa na so da cikin su Kamal ne, cikin kwanciyar hankali za su mun komai......amma kai ma ba kyale ka zanyi ba, dole sai ka mun yanda nake so" ta juya ta koma ciki

********************
Ummi da Siyama na aiki cikin gida, Zulaihat ta shigo da sallamarta, ta shiga gaida Ummi

"Ummi ina wuni"

"Lafiya ƙalau Zulaihat, ya aikin"

"Alhamdulillahi"

"Ina wuni Anty Zulaihat" cewar Siyama

"Lafiya ƙalau Siyama, yau ba ki je makaranta ba?"

"Eh"

"To.....ina Hanan"

"Tana nan ciki"

Ta sa kai ta shiga, ta same ta zaune ta rabka uban tagumi

"Hanan!"

A tsorace ta kalle ta dan ba ta ma san da shigowarta ba

"Zulaihat"

"Na'am, Hanan ba ki da lafiya ne? Kin gan ki kuwa?" ta faɗa tana koƙarin zama kusa da ita

Murmushi tayi ta ce "ban jin daɗi ne"

"Allah sarki Allah ya ba ki lafiya.....mun ji shiru kwana biyu kuma ga shi ba kya ɗaga wayar kowa"

"Wayar ce tana silent ne kuma ba ta kusa da ni shiyasa"

"Ayya, to ki tashi mu je idan za ki iya, tare da MK muka zo" 

Da mamaki ta ce "MK? Gidan nan?"

"Ƙwarai kuwa"

"To muje"

Ta sa hijab suka fita, wurin Ummi ta fara tsayawa ta gaya mata MK na waje za ta je su gaisa, sannan ta fita

Yana zaune cikin mota, ya bar ƙofa a buɗe, ta isa kusa dashi, ta ce "ina wuni yallabai"

Kallon tsaf ya mata, ta wani ƙara haske kyaunta ya fito b'aro-b'aro, sai dai ta rame, kuma alamun damuwa sun bayyana a fuskarta, ya ce "Hanan! Lafiya kike kuwa"

Murmushi tayi ta ce "da sauƙi dai"

"Allah sarki, Allah ya sa kaffara ce"

"Ameen nagode"

"Ba komai, na ga kwana biyu ban ganki ba ne shiyasa na zo in ga ko lafiya"

"Nagode sosai, amma shi ne sai ka zo da kanka baka aiko ba?"

"Ai ke ta musamman ce shiyasa na zo da kaina"

Ta sake wani murmushin, ta ce "to nagode"

"Sai faman godiya kike tayi....ga wannan to"

Kallonshi take da mamaki ganin ya miko mata kudi, abunda ko a mafarki bata tab'a ganin yayi ba, wai sadaka, ta ce "a'a yallabai, ka bar shi kawai"

Kallon kuɗin yayi, ya ce "na san kin fi ƙarfinsu, sabida duk wanda yake tare da AAJ ya fi ƙarfin million hamsin ma bare kuma dubu hamsin, amma dai kiyi haƙuri ki karb'a"

Girgiza kai tayi, ta ce "ba haka bane ai"

"To ki karb'a"

Amsa tayi tana godiya, sannan suka yi sallama ta koma ciki. A zaure ta haɗu da Zulaihat za ta fito, ta ce "ba dai wucewa za kiyi ba"

"Bari kedai in tafi, first in history yau ni ce a motar MK, ai kinga kuwa dole in kama kai na, sai dai munyi waya, Allah ya ƙara miki lafiya" bata jira amsar Hanan ba ta fita, ita ma Hanan ɗin murmushi tayi ta shiga cikin gida

Ummi ta miƙa ma kuɗin, da fari bata so karb'a ba, sai daga baya kuma ta karb'a ta ce "an gode, anjima Yuhanees ta ce zata shiga kasuwa, sai ta mana siyayyan kayan da ake buƙata na gida"

"Allah ya kaimu" daga haka nan ta koma ɗaki

********************
Jafar da Umar na zaune kan kujeru da drinks a gabansu kan table, cikin wani park

Umar ya ce "ka ji yanda muka yi da ita"

Ajiyar Zuciya Jafar yayi, ya ce "ban yi mamaki ba, na san zata iya hakan, sai dai na so ace ka amince"

"In amince kuma? Ta ya kake tunanin zan iya wannan abun, ko dai kai ma ka fi son Farha ɗin ne?"

"Ko ɗaya, amince mata ɗin zai taimaka mana"

"Kayi mun bayani yanda zan fahimce ka"

Murmushi Jafar yayi, ya ɗauki wayarshi ya shiga camera, sai da yayi zooming sannan ya ɗauki hoton, ya mayar da wayar ya ajiye, ya gyara zama ya mayar da kallonshi kan Umar da ke kallonshi shi ma, ya zayyana mishi yanda yake nufi da kuma irin amfanin da yardan zai yi musu

Dariya Umar yayi, ya ce "lallai gayen nan na sara maka, na yarda ka fini zafi ma ashe"

Murmushi Jafar yayi, yace "tafiyar mu ɗaya da kai dai, shiyasa na ji kayi saurin kwanta mun...to yanzu taya za ka koma ka ce mata ka amince bayan yanda ku ka yi"

"Kar ka samu damuwa, irin su ba wuyar sha'ani ne da su ba, musamman da yake su suke buƙata"

"To shikenan yayi kyau"

"Zan bar ka nan, akwai wani aikin a gabana"

"Ba damuwa, a sauka lafiya, sai na ji ka"

"Aha"

Umar na barin wurin, sai ga Farha, ta isowa ta ja kujera ta zauna, ta ce "Malam Jafar, barka da hutawa"

Kallonta kawai yake yi ba abunda ya ce mata, ta ce "hmm, na so a gidan sarauta kake, na san da kayi mulki ba kaɗan ba"

"Kuma da na sa an ɗaure mutane ba kaɗan ba, ciki har da masu shigar banza"

Kallon kayan jikinta tayi, riga ce da skirt na shadda kalar sea green, ɗinkin ya matse tamau gaba ɗaya shape ɗin jikinta a bayyane yake, sannan ko mayafin nan na fashion babu a jikinta, sai tayi murmushi ta ce "wayewar kenan ai" 

"Wayewa? Allah ya tsari Ya Arshad da auren wayayya kuwa, gwara ya auro bagidajiya mun san yanda zamu zauna da ita"

"Ai kuwa da ka tafka kuskure idan ka yarda ya auri bagidajiya"

"Wannan kuskuren kuwa shi zan aikata"

Murmushin gefen baki tayi, ta naɗe hannayenta a ƙirji, ta ce "na fahimci kamar kana cikin ƴan adawata, kamar ba ka son aure na da AAJ"

"Ba aurenki da aAJ ne kawai bana so ba, alaƙarki da gidanmu ne ma bana so"

"Sai dai kuma ka makara, dan aikin gama ya gama, ni zai aura"

"Me ya baki ƙarfin gwiwar faɗar haka?"

"Ammi"

"Ita ce zata aurar da shi?"

"Mahaifiyarshi ce dai, kuma ka san ta fi ƙarfin wasa"

"Idan kuma na ce zan iya hana faruwar hakan fa?"

"Ga fili ga mai doki idan za ka iya, amma ina so ka fara shirin kirana da Anty ko matar yaya"

Murmushi yayi shi ma ya ce "ki fara nema ma kanki mijin aure daga yau"

"Wai kana ji zaka iya ne?"

"Kina tantama ne?"

"Mu zuba mu gani"

"Za ki gani kuwa" ya tashi ya ɗauke wayarshi ya bar wurin

Ta sauke numfashi ta ce "lallai wannan yana wasa, bai san Farha ba, amma zanyi maganinka" ita ma ta miƙe ta bar wurin............



🥰UMMEETA🥰......📝



♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

           ZUCIYA ƊAYA

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata, a mun uzuri akasi aka samu👏👏👏

 *PAGE 41* 

Ku san mintuna uku su Ammi na rungume da juna, sai hawaye da yake bin fuskokinsu gaba ɗaya, a hankali suka saki juna 

Ammi ta riƙe hannayen Ummi gam, tana kuka ta ce "Halima ashe kina nan, ashe ina da rabon sake ganinki?  Halima na neme ki kamar zanyi hauka... Ina kika shiga?"

Ita ma Ummi kukan take yi, ta ce "Ina nan Ruƙayya, ina nan garin, Ruƙayya nayi kewarki sosai, ki yafe mun na guje ki a lokacin da ya kamata in tsaya tare da ke, amma na guje ki, na kuma bi ku da mummunan zato" ta sake sakin wani kukan

Ammi na ƙoƙarin share hawayenta, ta ce "Meye abun bada haƙurin kuma Halima, ni ba kiyi mun komai ba, idan ma kinyi, to ganinki ɗin nan da nayi ya yaye mun duk wani ɓacin rai dake tare da ni"

Sake rungume juna suka yi, kafin Ummi ta ce "ina Arshad?"

Arshad da ke can baya, ya mutu wurin kallon Hanan, jin maganar su Ammi ne ya dawo da shi tunaninshi dan bai ma lura da su ba, cikin mamaki yake kallonsu, yanda suke magana su na kuka, to ko menene dalili?  Sai ji yayi Ummi na tambayar ina yake? 

Juyawan da zata yi, sai ta hango shi a tsaye, ta ce "zo nan mana ɗana"

Ɗaga ƙafa yayi kaman bai son tafiya, har ya kai gabanta ya tsaya, hannunshi ta riƙe tana kallon bandage ɗin da ke zagaye da hannun, sannan ta sa hannu ta shafa fuskarsa a hankali, dan tabbas fuskarsa kaɗai ta tabbatar mata da ya ji jiki

Cikin tausayi ta ce "sannu Arshad, dan Allah ka yafe mun, na san ni ce nayi silar shigarka cikin wannan yanayin, nayi ƙoƙarin raba ka da Hanan, dan Allah kayi haƙuri ka ji"

Da sauri ya ce "haba Ummi, dan Allah ki daina ba ni haƙuri, ni fa ɗanki ne, taya zan iya jure mahaifiyata tana ba ni haƙuri kuma? Ƙaddara ta ce a hakan, kuma na ɗauka"

"A'a Arshad, ƙaddararka ba ta zo yanda za ta raba ka da Hanan ba, ai Hanan matarka ce in sha Allah, ba wanda zai shiga tsakaninku"

Kallonta yayi ya ce "Ummi kina nufin kin yarda kin ba ni Hanan?"

Ta share hawayenta ta ce "ai Hanan ta ka ce"

Wani irin farinciki ne ya ziyarce shi, yayi godiya ga Allah da ya nuna mishi wannan lokacin

Ammi ta kalli Hanan, da sai yanzu ma ta ganta, ta ce ma Ummi "dama kin san Hanan ne?"

Hajjo tayi murmushin farin ciki, ta ce "ai Hanan ƴar Halima ce, ko kuma in ce ƴarki ce"

Gaba ɗaya ma Ammi ta rasa abun faɗa, baki a buɗe take kallon Hanan, sannan ta kalli Ummi, ta ce "tabbas, akwai kama a tsakaninku, shiyasa kenan kallo ɗaya na mata, na ji sonta ya shige ni, ashe ƴa ta ce.... Hanan zo nan" ta faɗa tana buɗe hannayenta

Da sauri ta faɗa jikinta tana kuka, Ammi ta ce "ya isa kinji, rashin sani ya fi dare duhu, na so in nisanta ki da kai na Hanan, cikin ikon Allah ban samu nasarar yin haka ba, saboda Allah ne ya haɗa alaƙar mu tun farko, warware shi zai yi wuya kuwa"

Gaba ɗayansu sai murna suke yi, tun daga kan Hajjo, Ammi, Ummi, Umma, Hajiyar Sajjad, Arshad, Jafar, Hanan, Siyama da Yasna. A wani ɓangaren kuwa, Yasmin baƙin ciki ne ke cinta, wai yau ƴan gidansu ƙalau suke kuwa? Musamman ma Amminta, barin ma ita Farha da take ji kamar ta haɗiye ranta ta mutu, 'Ammi na nufin ta manta alƙawarin da ta mata ne akan cewa ita zata auri Arshad ko me?  Wai ma wannan Ammin da ta sani ce ko dai wata ce?' gaba ɗaya kanta a ɗaure ya ke, ta kasa fahimtar me mutanen  nan ke nufi? 

Kallon gefenta tayi, dan ta ji me Mummynta za ta ce, amma ga mamakinta ba kowa a wurin, dubawa tayi da kyau, amma ba ta ganta ba, cikin ɓacin rai ta bar wurin tana ji kamar zata yi ihu

Dr. Yusuf ne ya ƙaraso wurinsu, ya gan su tsaye cirko-cirko, ya kalli Arshad, ya ce "lafiya dai ko?" dan a tunaninshi wani abun ne kuma ya same shi 

Murmushi yayi ya ce "lafiya ƙalau Dr"

Shi ma murmushin ya mayar masa, ya ce "to zo mu shiga daga ciki, zan duba ka, sannan a sallame ka"

Cikin farinciki Hajjo ta ce "kai alhamdulillahi, wallahi dama can ni ba son zamaj asibitin nan nake yi ba"

Yasna ta ce "ke dai ki ce kina tsoron kar a miki allura"

Hajjo ta ce "wallahi zan ɓata miki rai fa, ja'ira kawai"

Dariya suka yi gaba ɗaya, Dr. Yusu da Arshad suka shiga ɗakin suka bar su a wurin

Ammi ta ce "Jafar ka kira su Sajjad ka ce mu haɗu a gida kawai"

"To" ya amsa mata

*******************

Sajjad da Nabeel sun kusan minti biyar a tsaye jikin mota, ba wanda ya iya cewa komai

Ajiyar zuciya Nabeel ya sauke ya ce "Sajjad me ye abunyi wai, abun nan ya ɗaure mun kai sosai wallahi"

"Nima nan kai na a ɗaure ya ke Ya Nabeel, amma mafita ɗaya ce, dile be mu koma mu gaya ma Arshad, dan muji ta ya aka yi ya saka hannu a waɗannan takardu haka? "
"Hmm, haka ne, ban san ya Arshad zai ɗauki maganar nan ba"

"Kuma dole sai ya sani kam... " wayarshi da tayi ƙara de ta katse shi

Ganin Jafar ne mai kiran, ya sa ahi ɗauka, "Hello Jafar, ya akayi? "

"Ammi ce ta ce wai kar ku  dawo asibitin, mu haɗu a gida kawai, an sallame shi"

"To alhamdulillahi, gamu nan zuwa in sha Allah"

"Aha"

Suka kashe wayar, sannan ya gaya ma Ya Nabeel, ba su tsaya ɓata lokaci ba, suka shiga motocinsu suka bar wurin 

*********************

Farha kuwa bayan fitowarta, ta tarar da mahaifiyarta na ta safa da marwa a bakin motarsu, kallo ɗaya zaka mata ka san hankalinta a tashe ya ke

Cikin ɓacin rai Farha ta ƙaraso wurinta ta ce "Mummy kin bani kunya wallahi, a gabanki kina ji waccan matar tana cewa AAJ ba shi da matar da ta wuce Hanan, na ɗauka za kiyi wani abun ne, amma sai kika wani dawo nan kina ta kai wa da kawo wa! "

"Farha ba za ki gane ba ne, masifar da kike hangowa sam ba ta kai rabin wanda ni na gani ba... Ke tashin hankalinki za ki rasa Arshad, ni kuma idan har ban ɗauki mataki akan lokaci ba, rayuwa ta ce zan rasa gaba ɗaya"

Cikin rashin fahimta, Farha ta ce "ban gane ba"

"Ba za ki gane ba ai... Kira mun Daddynki, dan ni ko gani ba nayi da kyau" ta faɗa tana miƙa mata wayarta

Karɓa tayi ta kira shi, bugu biyu ya ɗauka, sann ta Miƙa mata

"Hajiya muna meeting ne, zan kira ki" abunda kawai ya faɗa kenan, yana ƙoƙarin kashewa tayi saurin dakatar da shi

"Tsaya Alhaji, matsalar da ke gabanmu yanzu ta fi ƙargin meeting ɗinka"

"Kamar ya? "

"Matar Abdul tana raye ashe, kuma yau ɗin nan suka haɗu da Ruƙayya, yanzu haka ma su na tare"

Da sauri ya miƙe a firgice, yana faɗin "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un....... Da gaske kike? "

Ita ma a ruɗe ta ce "na taɓa maka irin wannan wasan? "

Wani irin zufa ne ya fara karyo mishi, ko sallama bai yi da mutanenshi ba ya bar wurin, kiranshi suke amma bai ma san su na yi ba

"Karime mu haɗa gidan Malam" bai jira jin ta bakinta ba ya kashe wayar, da sauri ya buɗe motarshi ya shiga yana faman tattara babbar riga, ko jiran driver bai tsaya yi ba

*********************

Dr. Yusuf ya gama duba Arshad, ya rubuta mishi takardar sallama, sannan suka fito ya wuce

Tun kafin su fito, su Yasna da Siyama da Yasmin suka kwashe kayansu suka kai mota, hakan ya sa yana fitowa suka fito harabar asibitin wurin motocinsu

Ammi, Ummi, Hajjo da Hajiyar Sajjad, mota ɗaya suka shiga, Ammi ce a driver seat

Sai motar da Jafar ya zo da ita, Hanan ta shige can baya, Yasna na ƙoƙarin shiga, Arshad ya jawo ta ya ce "kina da kunya kuwa za ki shiga tsakanin mata da miji?"

"Iyeeee, yanzu Sweet Bro ni da kai waye mara kunya? Ba mu ba ka ita ba fa"

"Waye ba ku ba ni ba?"

"Anty na mana"

"Kawai ki ce in koma in da na fito"

Siyama ta ce "Ya Arshad daga ina ka fito? "

"Gadon asibiti mana, kuma this time around ba zan tashi ba"

Siyama ta ce "tabɗi, ai dole ma a baka ko rai ba ya so"

Yayi dariya ya ce "haka ne ƴar gidan Yayanta... Amma dai zo ki shiga na haƙura saboda girmama addini"

Dariya tayi ta ce "da dai ya fi"

Sannan ta shiga, Yasmin da Siyama kuma suka zauna a tsakiya, Arshad kuwa ya shiga gaba

Duk abunda suke yi, Hanan kallonsu kawai take yi tana murmushi, har suka gama shiriritarsu, Jafar kuwa ji yayi kamar ya barsu a wurin dan sun ɓata mishi lokaci

Saƙo ne ya shigo wayar Hanan, Yasna ta miƙa mata kasancewar wayar na hannunta tan kallon hotuna

Kamar ba za ta buɗe ba, amma ganin number ce ya sa ta buɗe ta karanta kamar haka:
'Gaisuwa ga tauraruwar mata, ban ga laifinki ba dan kin nuna soyayyarki akan wanda yake sanki, amma ki sani very soon za ki rasa shi, kuma na an ba za ki so hakan ba, dan haka na ba ki damar nema na a duk lokacin da kika buƙaci ki ceci masoyin na ki, idan ba haka ba kuwa, kina ji kina gani zai tafi magarƙama'

Gabanta ne yayi mummunan faɗuwa, "to waye wannan? Me yake nufi? " tambayoyin da tayi ma kanta kenan

Yasna ta ce "lafiya Anty Hanan? Na ga kamar a tsorace kike"

Ko kallonta ba ta iya yi ba, sai cewa kawai ta yi, "hmm... Umm.. I'm.. I'm ok"

Arshad kuwa tunani yake yi mai ya ɗaga mata hankali haka? Dan tun ɗazu yake kallonta ta mirror, dan yana shiga motar yayi ƙoƙarin saita mirrorn zuwa fuskarta

Ɗaga ido Hanan tayi, sai suka haɗa ido kuwa ta madubin, take ta ji gabanta ya sake faɗuwa, a hankali ta ke karanto addu'o'i ba tare da ta ɗauke idanunta daga kanshi, shi ma ita ɗin yake kallo............ 




🥰 UMMEETA🥰.....📝📝📝

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA* 

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata, a mun uzuri akasi aka samu👏👏👏

 *PAGE 42* 

Farha na driving tana faman yi wa Mummynta masifa "Mummy na ce ki gaya mun meyasa kina jin abunda Ammi ta ce amma kika yi shiru, kin fi kowa sanin ina son Arshad, ina son aurenshi, amma ga shi za'a raba ni da shi kinyi kamar ba kya wurin, yaushe kika daina ɗaukar farinciki na da muhimmanci? Yaushe kika fara jin tsoron Ammi? Ni wallahi idan..... "

A tsawace Hajiya Karime ta katse ta "Kai Farha! Haba! Ki barni inji da abunea yake damuna mana dan Allah, ke kin fi kowa sanin na fi ki son ki auri Arshad, amma tunda har kika ga nayi shiru, ke ma kin san ba ƙaramin abu ba ne"

"To amma Mummy dama akwai abunda ya fi ƴarki girma ne a wurinki? Ni na san da Daddy na ne ba zai yi shiru ba" ta faɗa ita ma cikin fushi 

"To dan ubanki sai ki gaya wa Daddyn na ki ya zo yayi abunda ni na gagara yi, shashashar banza da ba ta gane bayani! "

Farha na jin Mummyn ta ta danƙara mata zagi ta tabbatar yau rana ta ɓaci, lallai akwai abunda ke damunta sosai, hakan ya sa tayi shiru, sai sharar hawaye da take yi lokaci zuwa lokaci, har suka iso ƙofar gidan Malam, anan suka tarar da Alhaji Mas'ud jikin motarshi

"Hajiya sai yanzu zaku ƙaraso kamar abun bai dame ki ba?!" ya faɗa rai a ɓace

Ita ma Hajiya Karime cewa tayi "yanzu dai ba mun zo ba? Mu shiga dan Allah"

Har ya sa kai zai shiga, Farha ta kira shi da muryarta ta kuka "Daddy"

Ya tsaya ya kalle ta "ya aka yi"

"Daddy ina gab da rasa Arshad, amma hankalin Mummy ba ya kai na"

"Kin ga ƴar gidan Daddy, bari mu haa kashe wutar gabanmu, san dawo ta kanki" bai tsaya jin komai ba ya wuce cikin gidan, Hajiya Karime ta bi shi

Farha tsaye tayi tana cizon yatsa, hawaye na ba gangarowa ian fuskarta, sai kuma ta yi tsaki ta share hawayen sannan ta shiga ita ma

Zuwa tayi kusa da Mummyn ta ta zauna, dan ta ji me ke faruwa

"Malam akwai babbar matsala, dan yanzu na gane ko wace ce ka gaya mun Hajiya Ruƙayya ta haɗu da ita, Hanan ce ƴar gidan Halima.... To yanzu babbar matsalar ita ce yau ɗin nan Ruƙayya da Halima suka haɗu" cewar Hajiya Karime hankali a tashe

Tana bayani ne Malam yana wasa da ƙasar da ke gabanshi, numfasawa yayi ya ce "Hajiya tun kan ku zo nan na ga wannan matsalar, kuma asirinki yana gab da tonuwa idan ba'a yi wani abun ba"

Cikin ɓacin rai Alhaji Mas'ud ya ce "ta ya zaka gaya mana wannan maganar Malam! Meye amfaninka to idan har zaka iya bari asirin da muka shafe shekaru muna rufewa ya tonu! "

Malam ya ce "kayi haƙuri Alhaji, amma gaskiya ce na gaya maka"

"To ka riƙe gaskiyarka, ka gaya mun ko nawa ne ake buƙata zan baka dan kayi ƙoƙarin rufa kana asiri ko ta wane hali ne, kai in ta kama sai ka kashe su gaba ɗaya, ni ba damuwa ta ba ne matuƙar za ku saku kwanciyar hankali"

Ɗan guntun nazari Malam yayi ya ce "to shikenan, zan duba in ga abun da zai iya yiwuwa"

"Ba wai zaka duba ba, dole ne ma ka duba"

Hajiya Karime ta ce "Alhaji calm down, ka bari ya duba mana a hankali, na yarda da shi....... Yanzu Malam zuwa yaushe za mu ji ka? Dan maganar gaskiya hankalinmu a tashe ya ke"

Malam ya ce "na sani, ku bani nan da kwanaki biyu zuwa uku "

"To Allah ya kaimi, mun gode"

"Ba damuwa"

Tashi suka yi dukansu su uku suka fita waje kowa da irin zulumin da ke ranshi, Farha kuwa tambayoyi ne fal a ranta

Bayan fitarsu, Malam ya sauke numfashi ya ce "bakn alƙalami ya bushe, sai dai haƙuri"

**********************

Su Jafar kuwa lokaci ɗaya suka shiga gida tare da su Ammi, A parking area suka jera motocin sannan suka fito, su Yasmin ne suka fara kwashe kayan zuwa ciki, kafin masu aikin suka fito suka shiga da sauran suna yi ma Arshad ya jiki

Nan kowa ya kama hanyar shiga cikin gidan, Hanan na ƙoƙarin wucewa ita ma, Arshad ya tsaya gabanta, dole ta tsaya tana kallonshi, bai ce mata komai ba har sai da ya ga su Ammi sun fara shiga cikin parlourn, sannan ya kalle ta ya ce "zo nan"

Komawa yayi jikin mota, ta bi shi ta dawo gabanshi ta tsaya, kallonta yake da kyau, ya ce "me ya ɗaga miki hankali ɗazu? "

"Kamar ya?  Yaushe kenan"

Murmushi yayi ya ce "har yanzu kina tantama kenan na urin son da nake miki, Hanan soyayyar da na ke miki ta sa zuciya ta da ta ki suka ƙulla kyakkyawar alaƙa, ta yanda ko bana tare da ke, na kan fahimci halin da kike ciki, bare kuma ga ni ga ki, idanunki sun gama gaya mun abunda ke damunki, dan har yanzu a tsorace ki ke, so feel free and tell me the truth (dan haka ki saki jikinki ki gaya mun gaskiya)"

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Ba komai, wani abu ne nake tunani"

"Abunda kike tunanin nake son sani ai"

"Wani saƙo n...... "

Ƙarar wayarshi ce ta ƙatse ta, dubawa yayi, ya ga Khairat ce, sai ya ɗauka

"Hello Khairat"

"Na'am Sir, ya ƙarfin jiki? "

Alhamdulillahi, gani a gida ma... Lafiya? "

"Masha Allah.... Nayi ta kiran wayan MD amma bai ɗaga ba shiyasa na ce bari in kira ka"

"Menene? "

"Yallaɓai akwai matsala ne, jami'ai sun rufe kampani, wai sai an gama bincike, yanzu haka sun fitar da kowa daga ciki, anya kuwa lafiya yallaɓai? "

"Sun rufe? Kampanin nawa aka rufe? "

"Eh, yanzu ma gamu nan a waje"

"Tirƙashi" ya faɗa rai a ɓace, sai kawai ya kashe wayar

Motocinsu Sajjad da Ya Nabeel ne suka tsaya a wurin, Sajjad ya fara fitowa kafin Ya Nabeel

"Sajjad shiyasa na ce maka zan tafi wurin nan da kai na amma ka sa aka hana ni, yanzu ga shi nan ai sun rufe kampanin, kuma wallahi abunda ba zai taɓa yiwuwa ba kenan" cikin ɓacin rai Arshad ke magana

Sajjad ya kalli Ya Nabeel, a ranshi ya ce "dama nasan dole sai an rufe, Ya salam"

Ya Nabeel ya ce "kai ka natsu mana, ko ka tafi aikin banza ne, tunda har kayi gangancin sa hannu"

"Sa hannu a ina? "

"A ina ma kake tambaya? "

Sajjad ya ce "Ya Nabeel dan Allah kayi haƙuri mana kai ma,  na gaya maka ni har yanzu na kasa yarda Arshad na sane yayi signing ɗin nan"

A tsawace Arshad ya ce "wai wane signing!  Ni fa ban ga amfanin zuwanka ba Sajjad, shiyasa na so zuwa da kaina dan na san yanda zanyi handling komai amma kuka nace akan ba zan tafi ba, ai yanzu ga abunda ya faru, kuma wallahi duk wanda ya rufe kampanin nan, da kanshi zai buɗe shi"

Sajjad ya ce "Arshad ka tsaya ka ji mana, ko kai ka tafi ba abunda zaka iya yi saboda komai ya lalace, wannan signing ɗin shi ya ɓata komai"

Jafar ne ya zo ya same su a wurin, dan suna jin hayaniya, shiyasa ya fito ya ga ko menene, sai ga su Ammi su ma sun fito, Hanan na tsaye gefe tana kallon ikon Allah, dan ba ta taɓa ganin Arshad yayi fushi ba

Arshad ya ce "kuna ta maganar signing, wane irin signing? "

Ya Nabeel ya ce "abunda zaka tambaya kenan, amma kana ta mana faɗa kaman ka ajiye wani a cikinmu... Wa ya maka signing takardar da aka aika dan a kawo maka drugs, wa ya biya kuma?"

"Ni?! " yayi maganar cikin mamaki, Kallon Sajjad yayi ya ce "kai ba ka san Signature ɗi na ba ne?"

"Na sani mana Arshad, kuma na ka ne"

Da ƙarfi ya bugi motar da ke kusa da shi, sai da Hanan ta firgita dan jikin motar ta ke, ya ce "impossible, wannan rainin hankalin da suka muku ni ba za su mun shi ba, i'm telling you"

Ƙarar shigowar motoci suka ji, ciki kuwa har da ta ƴan sanda, gaba ɗaya hankalin su Ammi ya tashi, sai rabon ido suke yi su na jiran isowarsu

A harabar gidan suka tsaya, motoci ne guda biyu ƙirar EOD da 406,sai ta ƴan sanda guda ɗaya, wani mutum ne kimanin shekaru 32 ya fito daga motar, yana saye da suits baƙaƙe, da madubi baƙi, a hankali ya fara takowa zuwa gabansu, sauran suna biye da shi a baya

Kallonsu yayi da kyau, sannan yayi musu sallama, Sajjad ne ya iya amsa mishi, sannan ya ce "wanene Arshad Ahmad Jalal? "

Umma tayi ƙarfin halin ce wa "lafiya dai ko?"

Murmushi yayi ya ce "zan iya ce miki eh, amma ba ƙalau ba, mun zo da Arrest Warrant ne, zamu kama shi"

Yasna ta ce "ku kama shi? Sai ka ce wani kifi?"

Hajiyar Sajjad ce ta jawo ta kusa da ita, ta girgiza mata kai alaman tayi shiru

Hajjo da ta gama tsorata, ta ce "ɗan nan me kake cewa wai? Jikan na wa za ka kama? Laifin me ya aikata maka?"

"Hajiya nima aiko ni aka yi, amma idan muka tafi can, zai san me ya aikata... Waye Arshad Ahmad Jalal? "

Arshad da ke tsaye naɗe da hannu a ƙirji tun isowarsu, yana musu wani kallon rainin hankali, cikin gadara ya ce "Arshad Ahmad Jalal, AAJ, mai kampanin AAJ IMPORT AND EXPORT CO. LIMITED kake nema, i'm right here"

A hankali mutumin ya cire madubinshi yana kallon Arshad, ya ce "AAJ... Na daɗr da sanin labarinka kafin na sanka, ban yi tsammanin za ka aikata haka ba... Amma dai anyway, you're under arrest, ka zo mu tafi" ya kai hannunshi kan na Arshad zai riƙe shi, da ƙarfi ya buge mishi hannu

Ya ce "don't you dare touch me (kar ka kuskura ka taɓa ni) "

Da mamaki yake kallonshi, ya ce "kar na taɓa ka?"

Jafar ya ce "haka ka ji, kuma haka yake nufi, amma in kana tunanin you have the guts to touch him, then go ahead" yana maganar ne yana mishi wani kallo

Ɗaya daga cikin mutanen da suka zo tare ya ce "ai kuwa dole ya bi mu, ko da lalama ko da tashin hankali"

Jafar ya ce "ai ba so nake ayi da lalama ba, idan ka isa ka zo ka taɓa shi"

Ai kuwa a fusace ya yo kan Arshad da nufin janshi, sai dai kafin ya kai hannunshi, Jafar ya ɗauke shi da mari, su Ammi gaba ɗaya sai da suka rufe baki, Ammi ta ce "Jafar!!! " ko kallonta bai yi ba

Sauran jami'an ne suka yo kansu, sai dai ogan na su yayi saurin ɗaga musu hannu, ko wanensu ya tsaya

Ya kalli Arshad ya ce "Malam AAJ, suna na inspector Ameer, mun zo kama ka amma ka mana taurin kai, har da dukan jami'in mu, me kake gadara da shi? Kana tunanin ba za mu iya tafiya da kai ba ne? Ina bin ka a hankali ne saboda na samu labarin daga asibiti kake sannan kuma ina tuna halinka na kirki ne, ba dan haka ba, da yanzu kana station"

Murmushi AAJ yayi ya ce "ni kuwa ka san me yasa na ɗaga maka ƙafa? Saboda kai aiko ka aka yi, baka san me ya faru ba, da ace waɗanda suka aiko ka ne suka zo da kansu, ina tabbatar maka sai dai a fitar da su da ambulance... Dan haka ka tattara mutanenka ka bar gidan nan"

Kafin yayi magana Ya Nabeel ya ce "yo haƙuri dan Allah, amma zo muyi magana", ya ja shi zuwa gefe

Maganar kusan minti biyar su kayi, sannan Inspector Ameer ya juya ya ce "Guys, ku zo mu tafi"

Ba gardama suka juya suka bi shi bayan sun gama yi wa Arshad da Jafar wani mugun kallo, suka shiga mota suka bar gidan

Ammi cikin tashin hankali  ta ce "Nabeel lafiya?"

"Ammi ku kwantar da hankalinku, everything will be ok, just get inside"

Hajjo ta ce "Uwa ka kai da turancin, ka mun magana da yaren da zan fahimta.... Me yayi? "

"Hajjo, ba abunda yayi, ku shiga ciki zan miki bayani"

"To shikenan"

Gaba ɗayansu jiki ba ƙwari suka wuce, aka bar Ya Nabeel, Sajjad, Arshad, Jafar da Hanan dake can gefe a rakuɓe, tunanin saƙon ɗazu take tayi

Ya Nabeel ya ce "Hanan zo ki shiga kinji"

Kallon Arshad tayi ta ce "What's wrong?"

A hankali ya girgiza mata kai, yana rufe ido

"Dan Allah, ka gaya mun" ta faɗa a hankali idanunta na cikowa da hawaye

Kallonta yayi, ya ce "dan Allah kar ki bari hawayen nan su fito, i can't bear to see your tears(ba zan iya jure ganin hawayenki ba) , zan gaya miki"

Wayar Nabeel ce tayi ƙara, ya ɗauka, "na'am Abba" abunda ya fara faɗa kenan

Sai kuma ya ce "eh ga shi nan" sai ya miƙa wa Arshad wayar ya ce "Abba ne"

Sallama ya mishi, sannan Abba ya ce "ɗazu Nabeel ya kira ni ya gaya mun abunda ke faruwa, gobe muke shirin zuwa, amma bayan ya gaya mun, sai na je nayi mana booking flight, in sha Allah nan da wasu awowi zamu zi, amma kafin nan, ina so ka yi duk abunda Nabeel ya umarce ka da shi, ban son taurin kai"

Ajiyar zuciya Arshad yayi ya ce "shikenan Abba, in sha Allah zanyi "

"Yawwa, sai na zo"

Ya miƙama Ya Nabeel wayar, sai da suka sake yin magana sannan ya kashe

Ya Nabeel ya kalli Hanan, ya ce "ki shiga ciki, idan muka dawo zan gaya miki komai, kai kuma Arshad ka zo mu je station, dan nayi ma Inspector Ameer alƙawarin zan kawo ka"

Hanan ba ta ce komai ba, jiki a sanyaye ta wuce, Arshad ma shiga motar yayi dan ya a amsa ma Abba zai yi abunda Nabeel ya ce yayi, mota ɗaya suka shiga, Jafar ke jansu

**********************

Su Hajiya Karime na cikin parlourn su, kowq da tunanin da yake yi, Farha ce ta sauko daga sama, ta zo kusa da Daddynta ta zauna 

Ta ce "Daddy i have a lot of questions to ask(ina da tambayoyi da yawa da zanyi) "

"Ina jinki"

"Daddy ban taɓa ganinka cikin tashin hankali irin na yau ba, lafiya? Wane asiri ne kuka daɗe kuna rufewa da yaje shirin tonuwa? Shin dama kunsan su Hanan ne tun kafin yanzu?"

Shiru yayi yana nazari, ya ce "daughter, tabbas mun daɗe da saninsu Hanan, sai dai yanzu ne muka gane su"

"To amma meyasa hankalinku ya tashi haka?"

"Sabida ganinsu ba alkhairi ba ne a wurinmu, asurun da kika ji muke magana, matuƙar ya tonu, to tabbas zaki rasa mu a kusa da ke"

"Ban gane ba Daddy, ka mun cikakken bayani mana"

Alhaji Mas'ud ya nisa, ya ce "Shikenan zan miki bayani, dan nasan dole ne yanzu kam sai kin san komai, wataƙila ma zaki iya taimaka mana"

*********************
A asibiti kuwa Dr Yusuf ne kan mutumin da Arshad ya biyawa kuɗin aiki, har an fito da shi, sai dai bai farka ba tukuna

Babban ɗan shi ne ya shigo da sauri, kallon Fa'iza yayi ya ce "Fa'iza ya iikin Baba?"

Murmushi tayi ta ce "lafiya ƙalau da sauƙi Yaya, har ma an mishi aikin kuwa"

Da mamaki ya ce "anyi aikin? Ina kuka samu kuɗi? Ko Tahir ne ya biya? "

Ta ce "a'a ba shi ba ne, wani mutum ne"

Dr Yusuf ya juyo bayan ya gama duba shi, gaisawa suka yi da shi, sannan ya ce "Dr wai anyi aikin? "

"Eh anyi Gboy, AAJ ne ya biya muku, sannan ya biya har kuɗaɗen maganin da za'a buƙata, sannan ya biya muku kuɗin wannan ɗakin shiyasa ma ka ga an ɗauko shi daga wancan ward ɗin zuwa nan aminity"

"Dr wa ka ce ya biya? "

"AAJ"

"AAJ? " ya maimaita a hankali cikin tsananin mamaki

Dr Yusuf ya ce "yanzu dai ga shi nan, idan ya farka sai ku kira Dr Hassan, dan shi ke kula da shi, yanzu ma shigowa nayi dan baya kusa ne, Allah ya ba shi lafiya" daga haka ya fita

Fa'iza ta zo kusa da shi tana kallon yanda yake rabon ido, ta ce "Yaya menene? Ka san AAJ ne? Zaka san shi ma ai, wallahi mutumin kirki ne shi, har shagon bakin asibiti muka tafi da shi ya siya mun kayan daɗi, ka gansu a can, kuma ya ce mun kyakkyawa, gaskiya na ji daɗi Yaya, AAJ ba kamar ogan nan naka ba ne MK, na tsane shi"

Kallonta kawai yake yi, amma shi kaɗai ya san irin abunda ke yawo a ranshi

************************

Ko da Hanan ta shiga ciki, bata ƙarasa cikin mutane ba, daga bakin ƙofa ta samu wuri ta zauna, kira ne ya shigo wayarta, lambar da aka turo mata saƙo ne ɗazu, hakan ya sa sai da ta fita kafin ta ɗaga

Shiru tayi ba ta ce komai ba, sai ta ji ance "Hanan ya dai? Ina saurayin naki?  Oh sorry, na manta fa yana ofishin ƴan sanda ko? "

Tsav ta gane muryar, a hankali ta ce "Zayyad?! "

Dariya yayi ya ce "ƙwarai kuwa, ni ne.... Hanan idan baki manta ba, na gaya miki ki daina ɓata lokacinki akan macuci, amma ba ki saurare ni ba, to yanzu ga shi can a hannun jami'ai saboda safarar miyagun ƙwayoyin da yake yi, da kuma ƴan mata, ko wa ya san ranar fitowarshi, oho! "

Cikin fushi ta ce "ka rufe mun baki, kar in sake jin ka jefi Arshad da waɗannan munanan kalaman naka, idan ba haka ba duk abunda ya biyo baya kai ka ja wa kanka"

Dariya yayi ya ce "Relax dear! Ni fa ban kira ki dan in ɓata miki rai ba ne, kawai dai ina ƙara tuna miki, idan kina buƙatar taimakon Zayyad, ƙofa a buɗa take ƴam mata.... And i still love you beauty"

Ranta ya ƙara ɓaci, ta ce "and i hate you, kuma Allah ya tsare ni neman taimako a wurinka, Allah ya san da shi, kuma shi zai taimake shi, ba shashasha irinka ba" tayi tsaki, lokaci ɗaya kuma ta kashe wayar tana huci

Wani kiran ne ya sake shigowa wayarta, ba tare da ta duba ba, ta ɗaga, a fusace ta ce "kar ka sake kira na, i have nothing to do with you"

"Hayatee, ke da waye?" ta ji muryar Yuhanees

A hankali ta fara sauke numfashi tana ƙoƙarin controlling ɗin kanta, ta ce "Rabin rai! "

"Na'am, kuna ina ne?  Tun ɗazu nake ta zuwa gida ba kwa nan, yanzu na shigo gidan Maman Nana ta ce tun ɗazu kuka fita"

"Nayi ta kiran wayarki amma switch off, na Umma kuwa dama wayar ta faɗa ruwa"

"Hmm bari kawai, yau na wahala, ina can wurin interview, ban fita da wayar ba, na ara wa Ya Mashkur ne, may be ya cire sim card ɗin.... Yanzu dai kina ina? "

"Rabin rai muna gidan su Arshad ne"

A razane ta ce "me? Gidan su Arshad?  Lafiya? "

"Magana ce mai tsawo Rabin rai, shiyasa nake ta nemanki, yanzu ma akwai abunda ke damuna shiyasa kika ji na fara faɗa, i need your assistance(ina buƙatar taimakonki), ke kaɗai zaki bani shawarar da zata gamsar da ni"

"To ki mun bayani mana Hayatee, kin ɗaga mun hankali"

"Ba maganar waya ba ce, gani nan zuwa zan same ki"

"To shikenan sai kin zo, mu haɗu a gida"

"Ok" suka kashe wayar a tare

Miƙewa Hanan tayi, ta duba parlourn ta hango su a zaune, suna magana jefi-jefi, dan suna cikin damuwa, sai da ta tabbatar ba su ganinta, sannan ta bar wurin, ta nufi hanyar fita gidan........... 




🥰 UMMEETA🥰.....📝📝📝

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA* 

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata, a mun uzuri akasi aka samu👏👏👏

 *PAGE 43* 

Zaune suke a office ɗin DPO, Kowa fuska a ɗaure musamman Arshad da yake jin haushin mutanen wurin gaba ɗaya

DPO ya ce "AAJ, ana maka magana tun ɗazu amma kayi banza da mutane, what do you mean (me kake nufi?)"

Ajiyar zuciya kawai ya iya yi ba tare da ya ce komai ba, Ya Nabeel ya kalle shi ya ce "Arshad say something (Arshad ka ce wani abu) "

"Me kake so in ce? " Arshad yayi maganar ba tare da ya kalli Ya Nabeel ba

DPO ya ce "magana nake maka, akan kayan da aka kama naka"

Cikin ɓacin rai ya ce "wai kamar ya kaya na? Na gaya muku bani da alaƙa da wannan gaba ɗaya, ku daina cewa kaya na"

DPO ya ce "lower your voice (kayi ƙasa da muryarka), kar ka raina mana hankali akan ba naka bane bayan duk wani evidence ga shi a hannunmu"

"Evidence? "

Miƙa mishi takardu DPOn yayi, ya ce "wannan idan ba evidence ba ne menene? Sa hannu na ne? "

Kallon takardun Arshad yayi da kyau aƙalla ya kai mintuna 2 yana kallonsu, kafin yayi wani murmushi na rainin hankali ya ce "sai dai a raina muku hankali, ba dai ni ba... DPO, wannan ba signature na ba ne"

"Ba naka ba ne? Hmm, AAJ ina so ka fahimci wani abu, muna yi maka sassauci da ɗaga ƙafa ne saboda umarnin CP, da yanzu ka daɗe a cell, amma hakan kar ya sa ka raina mana hankali"

"To meye abun rainin hankalin, signature ne na ce ba nawa ba ne, Amma idan baka yarda ba, fine! "

Sajjad ya ce "kamar ya Arshad?"

"Kai baka san signing ɗina ba ne? "

"Amma ai Arshad wannan naka ne, ka duba da kyau, wannan ba shi ya kamata mu tsaya ja akai ba, yanda hakan ya faru zamu sani"

"Sajjad kar ka ƙara ɓata mun rai dan Allah, na yarda duk wanda ya kalli signing ɗina da qnnan, zai ce duka nawa ne, amma ni da ke yi na san ba nawa bane, zan yi jinjina ma duk wanda yayi signing ɗin nan, sai dai yayi missing wani abu"

DPO ya ce "ka yi bayani yanda zan fahimta, yanzu ga wata takarda mai ɗauke da signing ɗinka wanda muka samu daga ma'aikacinka, sannan ga wannan da hukumar NDLEA ta ba mu, differentiate them(ka banbanta su) "

Gyara zama Arshad yayi, kafin ya ce "ba sai na kalla ba, amma kai ka sake dubawa da kyau zaka ga abunda zan gaya maka.... Signing ɗin irin nawa ne, amma ka duba cikin nawa, zaka ga akwai AAJ dake rubuce cikin wannan jagwalgwalon, saɓanin wannan da babu"

Sosai DPO ke kallon takardun duka biyu, ya ɗauki lokaci yana kallo amma bai gani ba, hakan ya sa AAJ ya nuna mishi da kan shi kafin ya gani kuma ya tabbatar

DPO ya ce "tabbas suna da banbanci, kenan haka na nufin ba kayanka ba ne? To amma ya aka yi wannan kitimurmurar ta faru?"

Sajjad ya ce "kamar yanda na gaya maka tun farko, shirin maƙiya ne"

DPO ya ce "zan iya yarda da hakan, sai dai ba wai mun daina zarginka ba ne AAJ, dole za muyi bincike mai ƙarfi akan hakan"

Ya Nabeel ya ce "haka muke so ai, kuyi binciken, amma zamu wuce gida ne tare da shi ko? "

"Ai hakan ba zai yiwu ba, a nan zai zauna har sai mun gama binciken da ya kamata"

Kallon baka isa ba, Arshad ke ma DPO, ba tare da ya ce komai ba

Wani ɗan sanda ne ya shigo, tare da sara ma DPO

"Easy.. Ya aka yi? " cewar DPO

"Sir, wani ne ya zo, ya ce ya buƙatar ganinka"

"Ka gaya mishi ya jira ni kaɗan, ina da baƙi"

"Na gaya mishi hakan amma ya ce yana da alaƙa da wannan case ɗin da kuke yi"

"To ce ya shigo"

Ɗan sandan ya juya ya fita, bayan kamar mintuna uku, sai mutumin ya shigo, gaba ɗayansu idanunsu na kanshi da ganin ko waye

Kallonshi Arshad yayi da kyau, ya ce "kai kuma? Meye haɗinka da wannan case ɗin? "

DPO ya ce "ka san shi ne?"

"A'a, a kampanin MK yake aiki dai"

"Lafiya bawan Allah? " DPO ya tambaye shi

"Lafiya ƙalau yallaɓai, na zo ne dan in faɗi gaskiyar abunda na sani akan wannan abun"

"Kamar ya?  Ka mun bayani"

"Yallaɓai sunana Garba Musa wanda aka fi sani da Gboy, ni ma'aikaci ne a kampanin MK Investment, sam AAJ ba ya da masaniya akan drugs ɗin nan da kuma matan nan, wannan abun shiri ne dan akwai a rusa AAJ da kampaninsa, sai dai an manta cewar duk wanda ke da sa Allah a gaba a duk al'amuransa, to ƙaryar mahassada su ga bayansa"

"To wa ya haɗa wannan shirin?  Kuma ya akayi ka sani? "

"Yallaɓai na sani ne saboda a gaba na aka shirya komai, sannan ba kowa ya haɗa wannan abun ba sai MK da abokinsa Zayyad"

A hankali Arshad ya ɗaga kai ya ce "MK? "

"Eh AAJ, ba zan iya yafewa kai na ba idan har na bari burin MK ya cika akanka, ka kun abunda MK nmma da nake tare da shi bai yi mun ba, mahaifina na raye ne saboda taimakon da kayi mana na biyan kuɗin aikin shi ɗazu"

"Ban gane ba? " cewar Arshad

"Ƙanwata Fa'iza, da Dr Yusuf, su suka gaya mun kai ka biya mishi kuɗin aiki"

DPO ya ce "gaya mana ya aka yi suka yi wannan shirin, sannan ta ya suka samu wanann signing ɗin da reciept ɗin nan? "

Nan Gboy ya fara ba su labarin abubuwan da suka faru wurin haɗa wannan shirin, ba abunda ya rage ba abunda kuma ya ƙara

Gaba ɗayansu mamaki ne fal a ransu, banda AAJ da bai yi mamakin abunda MK yayi ba, dan ya san halin MK tun ba yanzu ba, ya ji labarin shi da daɗewa

DPO ya ce ma wani ɗan sanda da ke tsaye gefenshi, "copral, ka kira Inspector Ameer, ka gaya mishi na ce ya ajiye wanann aikin, ya haɗa team a je a kawo kun MK yanzu"

"Ok Sir" sannan ya fita 

DPO ya ce musu "kai Gboy zaka zauna anan har sai an kawo shi... Haka kuma ku jira zuwanshi"

Ba wanda ya ce komai a cikinsu, sai nazarin abunda Gboy ya faɗa suke tayi

*******************
Gauron numfashi Yuhanees ta sauke bayan ta gama jin abun da Hanan ta gaya mata, ta ce "shiyasa ake cewa yana da Kayu mutum yayi bincike kafin ya yanke hukunci, yanzu ga shi Ummi ta ɗauki laifin duniya ta ɗorawa su Arshad"

"Hmm bari kawai Rabin rai, abun ya razana ni"

"Yanzu dai ba wannan ba Hayatee.... Wannan matsalar ta AAJ, me kike tunani akai? "

"Me nake tunani kuwa Rabin rai ban da kawai in ta yo mishi addu'a"

"Haka ne addu'a makamin mumini, amma kuma ga ki da hanyar da zaki kuɓutar da shi kina gani za ki barta! "

"Rabin rai ta ya zan kuɓutar da shi bayan ban ma san taƙamaiman abunfa ke faruwa ba"

"Za ki sani idan har kika so ki sani"

"Kamar ya, bayan na gaya miki bai gaya mun komai ba"

"Ai ba shi zai gaya miki ba, Zayyad zai gaya miki"

"Meyasa kike tunanin Zayyad zai san abunda ke faruwa? Zayyad fa ba abokinshi ba ne"

"Tabbas na sani Hayatee, amma ni na tabbata Zayyad ya san abunda ke faruwa kuma da sa hannunshi"

Girgiza kai Hanan tayi, ta ce "Meyasa kika ce haka? "

"Kai! Lokuta da yawa ina gaya miki ba kya amfani da number six ɗin ki, and it's true wallahi..... Hayatee idan har Zayyad ba ya da masaniya ko sa hannu a kama Arshad, meyasa tun farko zai fara turo miki message akan idan kuna buƙatar taimakonsa ki gaya masa? Sannan kin gaya mun a cikin gida ƴan sandan suka same shi, which means ba wani wanda ya san da haka, amma kuma ya kira ki yana sake jaddada miki he's free idan kin tashi, ya aka yi ya san ƴan sandan su zo?  Hayatee., in har da gaske kina son Arshad kuma ba kya son ganinshi cikin matsala, to kima da hanyar da za ki kuɓutar da shi, amma idan kin so"

Shiru Hanan tayi ta na nazari, ta sauke numfashi ta ce "Rabin rai to ya zanyi? "

"Yawwa.. Abu na farko shi ne, za ki san meyasa aka kama shi, sannan sai ki gano shin Zayuad na da sa hannu?  Sannan kuma meyasa ya aikata hakan?  Menene manufarsa?  Za ki samu amsoshin tambayoyin nan ne kawai idan kika je wurin Zayyad"

"Amma ta ya  zan tafi wurin shi, ina tsoro"

"I'm right here by your side, tare za mu tafi, sai dai zan tsaya daga waje da ƴan sanda, if anything goes wrong, just flash me, ba abunda zai faru sai alkhairi"

Girgiza kai tayi da alamar gamsuwa, ta ce "shikenan Rabin rai, bari in kira shi"

Ta ɗauki wayarta, ta kira numbern Zayyad, bugu ɗaya ya ɗauka kamar yana jira

"I knew it dear, na san za ki kira ni ai"

Girgiza kai tayi tana sauke numfashi kafin ta ce "a ina zan same ka? "

"Haba, ai ni ya kamata in zo ko, sai mu tafi"

"Ka gaya mun kawai kana ina? "

Dariya yayi,  ya ce "shikenan kyakkyawa, zan turo miki da address ɗin"

Ba ta tsaya jin komai ba ta kashe, ba'a fi mintuna uku ba, sai ga saƙon address ɗin ya turo mata, tashi suka yi ita da Hanan, suka yi ma Umma sallama, ta musu fatan alkhairi, sannan suka fita

Dai-dai gidan da Zayyad ya gaya musu suka tsaya, sai da suka ƙarewa gidan kallo tsab, kafin Yuhanees ta ce "kar ki ji komai Hayatee, ki shiga ina nan, yanzu zan kira ƴan sanda dan su zo su same mu"

Ɗaga mata kai tayi tare da yin guntun murmushi, sannan ta tura ƙofar gate ɗin ta shiga

Gida ne ɗan madaidaici, amma kuma tsarinsa mai kyau ne, tsayawa tayi tana nazarin ta ina za ta bi, sai ga Zayyad ya fito da fara'arsa

"You're highly welcome"

Kallonshi kawai take yi, ta gagara cewa komai

"Zo mu shiga"

"A'a, daga nan ma ya isa"

"Haba ke kuwa? Tsoron me kike ji? Ba fa ni kaɗai ba ne a gidan to, saki jikinki... Mu shiga ciki zan fi fahimtarki yanda ya kamata"

A hankali ta sauke numfashi, sannan ta fara ɗaga ƙafavkamar mara lafiya, tana bin shi, har suka shiga cikin parlourn 

Nuna mata kujera yayi, ya ce "zauna, ina zuwa" sannan ya wuce ciki

A tsorace ta zauna tana bin parlourn da kallo, tsawon mintuna biyar, sai ga shi ya dawo da drinks a hannu, ya ajiye mata a gabanta, sannan ya zauna yana fuskantarta, ya ce "to, Malama Hanan, ga ni. Me kike so? "

Gaba ɗaya jikinta rawa yake yi, sai dai ba lallai mutum yayi saurin ganewa ba, amma fuskarta ta bayyana tsoron da ke zuciyarta

Murmushi yayi ya ce "har yanzu kin ka sa sakin jikinki, to ki sha drink, za ki samu relief"

Da ƙyar ta buɗe baki ta ce "ba wannan ya kawo ni ba, ina so ne in san, meyasa ka sa aka kama Arshad? "

"Hmm, dalili za ki nema, ko taimako? "

"Dalili nake so in sani, ba taimakonka nake nema ba"

Ƴar dariya yayi ya ce "to idan kika san dalilin, me zai amfana miki? Ina ce saurayinki kike so ki taimaka ko? "

"Ƙwarai kuwa, shiyasa nake so in san dalilin da ya sa aka kama shi dan zarginka nake yi, kuma idan har ya tabbata cewa da sa hannunka, zan sa ka yi nadama"

Dariya yake yi sosai, sai dai kafin ya samu cewa wani abu, ta jiyo muryar MK dake fitowa daga ɗaki yana faɗin "Hanan ki fara samun courage ɗin da kika natsu a nan wurin kafin kiyi maganar hukunta wani"

Da sauri ta miƙe tsaye, ta ce "MK? "

Zayyad da MK suka kalli juna suna dariya, sannan MK ya haɗe rai ya ce "Hanan karki wahalar da kanki wurin bincike, ni ne nan da kai na nayi sanadiyar kama saurayinki, Hanan wani abu da baki sani ba shi ne, ba'ayi wa MK bai rama ba, Saurayinki ya sa nayi asarar kuɗaɗe kusan shekara ɗaya da rabi kenan, sanadiyar wani contract da ya sa nayi loosing, tun a wannan lokacin na sa ma raina sai na sa shi ma yayi asarar dukiya mai yawa, ko kuma ma ya rasa ta gaba ɗaya, shiyasa na haɗa mishi wani makirci wanda yanzu haka yana hannun ƴan sanda saboda drugs ɗin da ake zarginshi da safararsu tare da ƴan mata"

Zaro ido tayi kamar zata yi kuka,  ta ce "MK me kayi kenan?"

Murmushi yayi ya ce "ai banyi komai ba ma.... kin san kuma ya ɗaga hannunshi ya mare ni saboda ke a gaban ma'aikata na, shi ma wannan na shi hukuncin daban, sai dai Zayyad ne zai rama mun wannan, kuma akanki zai rama"

A tsorace ta ke kallonsu gaba ɗaya, ido a waje, da ƙyar ta iya haɗiyar yawu, ta ce "MK kai mugu ne, kuma ba zaka samu nasara ba"

Dariya ya sake yi ya ce "na sani, ni mugu ne ba sai kin gaya mun ba"

Ckin rawar jiki take ƙoƙarin cire securityn wayarta, sai ji tayi an fizge wayar da ƙarfi, ɗaga idanunta tayi waɗanda suka cika tab da hawaye tana kallon Zayyad, ta ce "ka bani waya na"

"Wayarki ba za ta amfane ki da komai ba, ƙawarki za ki kira ko dan su shigo ita da ƴan sandan da ta kira? To zamu kira miki su amma bayan mun bar gidan nan" cewar Zayyad

MK ya ce "kinyi wautar barin ƴan sanda su ƙaraso ƙofar gidan nan, tun shigowarki na ga ƙawarki, daga baya kuma ƴan sandan suka zo, sai dai abunda ba ku sani ba shi ne, akwai wata ƙofa ta baya, dan haka ki wuce mu tafi"

Kuka take yi sosai, ta ce "ba in da zan tafi"

Zayyad ya nuna ta da bindiga ya ce "za ki wuce ko sai na fasa kanki? "

Da sauri ta bi hanyar da suka nuna mata, har suka fito ta ƙofar baya, suka shiga motarsu da ke wurin suka wuce


Daga ɓangaren su Yuhanees kuwa, sai safa da marwa take yi tana ta duba wayarta, amma har yanzu ba ta ga kiran Hanan ba, wani ɗan sanda ne ya ce mata "Anya kuwa lafiya? "

Cikin damuwa ta ce "nima abunda nake tunani kenan, amma bari ni in kira ta"

Ta shiga kiran Hanan, sai kuwa aka ɗaga, da sauri ta ce "Hanan ina fatan lafiya, ba wata matsala ko? "

Zayyad ya ce "ƙwarai kuwa, ba wata matsala, idan kun gama gadin gidan za ku iya tafiya, na fa gode sosai da kika kawo mun ita, dan na tabbata da shawararki tayi amfani" daga haka ya kashe wayar yana dariya

Gaba ɗaya Yuhanees jikinta ya mutu, ta ma rasa ihu zata yi ko kuka

"Lafiya dai? " ɗan sandan ya tambaye ta

A hankali ta ce "sun bar gidan nan, na tabbata akwai hanya ta baya" ta ƙarasa hawaye na bin fuskarta 

Da gudu suka shiga cikin gidan suka bar ta wurin a tsaye, sai da suka bincike gidan tsab, ba su nan, su ka ga ta hanyar da suka bi suka fita, sannan suka dawo wurin Yuhanees

"Zo mu tafi station"

Cikin kuka ta ce "shikenan sun tafi da ita? Ni na kawo ta wurin da za'a cutar da ita da kaina, meyasa na yi haka?  Ta yarda dani fiye da kowa, tana ɗaukar duk shawarar da na ba ta ba tare da tayi gardama ba, for the first time i put her life in risk"

"Ya isa haka, kiyi haƙuri, mu je station, i promise you zamu samo ta safe and sound" cewar babban su

Da ƙyar suka lallaɓa ta, ta tashi suka tafi sai kuka take tayi tare da nadamar rashin bin ta cikin gidan da tayi

**********************

Farha ce ke kuka bayan ta gama sauraren abunda Daddynta ya gaya mata, aƙalla ta kai mintuna goma tana kuka, ba wanda ya hana ta cikinsu

Ajiyar zuciya tayi, ta share hawayenta, cikin ƙarfin hali, tana ƙoƙari mayar da hawayenta, ta ce "welldone Dad, ke ma Mummy, aikinki yayi kyau... Ban taɓa tsammanin iyaye na haka suke ba, ashe kun ma wuce sani na, na ɗauka abun na ku kaɗan ne irin wannan da na sani, ashe kun shahara" kukan da take dannewa ne ya fito

Alhaji Mas'ud ya ce "haba daughter, me ya na rin wannan kukan kuma? "

"Tambaya ta ma kake yi? Iyaye su kasance terrorist haka amma kana tanbayan kukan me nake yi? Dan ni ban raba halinku da na terrors ba, duk iskanci na da rashin ji na, ban taɓa mafarkin yin abunda ku ka yi ba"

Hajiya Karime ta ce "Farha yanzu ba lokacin wannan maganar ba ne, ki bari mu fara samun solution, daga bay sai muyi wannan maganar"

"Solution? Solution fa kika ce Mummy? Kina tunanin za ku samu wani solution ne? Mummy daga jin abunda ku ka aikata, na ji na tsani kai na, na tsani kasancewa ra ƴa a wurinku, na tsani duk wani hali na wa, na tsani supporting ɗinku da nake yi a rayuwa, na tsani komai Mummy " ta ƙarasa tana kuka mai taɓa zuciya

Tun daga Alhaji Mas'ud jar Hajiya Karime, hankalinsu a tashe ya ke, dan ba su taɓa ganin Farha haka ba sai yau, Alhaji Mas'ud ya ce "dan Allah daughter kiyi shiru, kiyi haƙuri, just help us to find a way out (ki taimaka mana mu samu mafita)"

"Way out! Hmm, zan taimaka muku, ta hanyar da ta dace"

Hajiya Karime ta ce "yawwa ai na san ƴa ta ba zata ki taimaka mana ba"

Tana share hawaye, ta ce "haka ne, zan taimaka muku "

Sai kawai ta juya da sauri ta fita, bin ta suka yi suna kiranta, tare da tambayar ina za ta je, amma ko waiwayowa ba tayi ba, ta shige motarta, ta bar gidan a sittin, tsayawa suka yi su na tambayar kansu ina zata tafi to? 

Ita kuwa tun da ta ja motar ta bar gidan, ta ɗauki hanyar gidan su Arshad...........




🥰 UMMEETA🥰.....📝📝📝

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA* 

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata, a mun uzuri akasi aka samu👏👏👏

 *PAGE 44* 

Tunda MK ya fara jan motar bai tsaya ko ina ba sai bayan gari, dai-dai wani gida ya tsayar da mota, sannan ya fito ya buɗe gate ya shigar da motar ciki

Waige-waige Hanan ke yi tana kallon gidan, da dukkan alamu gidan ya daɗe a rufe saboda duk ganye ne fal a harabar gidan na itacen da ke wurin

Fita suka yi, Zayyad ya zagaya ya baɗe mata ƙofa ya ce "fito"

Kallonshi tayi ta ce "ina ne nan? "

"Idan kika fito zaki gani"cewar MK, sannan ya ƙarasa ciki bai tsaya jiransu ba

A hankali ta fara fito da ƙafarta, sannan ta fito, sai da ta fara tafiya kafin Zayyad ya bi bayanta har cikin parlourn, suka tarar da MK na faman kakkaɓe ƙura

Zayyad ya ce "Zauna nan"

"Ban gane in zauna ba, wai me kuke nufi da ni ne, ku mayar da ni wurin da ku ka ɗauko ni"

MK ya tsaya daga kakkaɓe ƙurar da yake yi, ya kalle ta ya ce "a mayar da ke? Lallai yau na tabbatar ba kya da hankali, ai ke da sake komawa kuma har abada"

Zaro ido tayi ta ce "har abada? "

"Eh, saboda komawarki barazana ce a wuri na, dan kowa zai san da sa hannu na a sace ki, Zayyad kuwa dama ba mazaunin ƙasar nan ba n, komawa zai yi idan ya gama, a nan za ki mutu"

Zayyad ya ce "a'a MK, ai bana so ta mutu, ina sonta fa, da ita zan wuce dai, ka ga zata rage mun kewa ai" ya ƙarasa maganar yana dariya

MK ya ce "as u wish ai, idan haka ne, yau zan fara ƙoƙarin haɗa mata visa, gobe sai ku wuce, shikenan burin MK ya cika" shi ma yayi dariya

Kallonsu kawai take yi, hawaye na bin fuskarta, ta ce "na ji ƙudirinku a kai na, amma dan Allah MK na roƙe ka, ka kuɓutar da Arshad daga zargin nan da ake mishi, kai ka san garin nan ana mutunta shi, idan wannan sharrin ya fito fili kowa zai tsane shi ne, dan Allah" ta ƙarasa tana kuka

Zayyad ya ce "sorry ƴam mata, amma wannan ba zai yiwu ba"

MK ya ce "after all this long process za ki ce wai in kuɓutar da shi, ki ma cire wannan haukar a ranki, ke kina nufin ma kinfi damuwa da wani fiye da kanki?"

Za tayi magana, wayar MK ta fara ƙara, alamar kiranshi ake yi, dubawa yayi ya ga me kiran kafin ya ɗaga

"Ya aka yi? " abunda ya fara faɗa kenan

Daga ɗayan ɓangaren aka ce "Yallaɓai ƴan sanda sun zo nemanka"

"Ƴan sanda kuma? "

"Eh yallaɓai, sun zo nan kampani ba su same ka ba, sai suka ɗauki Idris wai ya nuna musu gidan ku, can ma ba su same ka ba, har guest house ɗinka sai da suka tafi"

"Ina Idris ɗin? "

"Ga shi nan ya dawo"

Shiru ya ɗan yi, kafin ya ce "Gboy ya shigo? "

"A'a"

"Idan ya shigo ka ce ya kira ni"

"To yallaɓai"

Daga haka ya kashe wayar, ya gay ma Zayyad abunda ke faruwa

Zayyad ya ce "lafiya kuma ƴan sanda ke nemanka?"

"Nima abunda  nake tunani kenan, meyasa suke nema na? "

Dariya Hanan tayi, ta ce "kana mamaki ne! Wanda ma bai ji ba bai gani ba ka sa ƴan sanda suka kama shi, bare kai tantiri dan ana nemanka har abun mamaki ne? Ai wallahi Allah ha zai baka nasara ba, dan Allah ba azzalumin bawansa ba ne, kuma yana tare da me gaskiya, Shashasha kawai"

Haushi maganar ta ta ba MK, bai san lokacin da ya ɗauke ta da mari ba sai da ta faɗi kan kujera, Zayyad ya ce "Haba MK meye haka, i can't take it, kar ka sake marinta"

"Zan ci gaba da marinta kuwa matuƙar ta sake mun magana makamanciyar wannan"

Tana kuka take faɗin "ba zan daina ba sai dai ka kashe ni, amma wallahi burinka ba zai taɓa cika ba"

"Za ki gani kuwa, bari in je in dawo" MK na faɗin haka ya bar gidan da sauri

Zayyad ya kalle ta, ya ga yanda take kuka, sai kawai ya rufe ƙofar parlourn da mukulli, ya wuce ɗayan ɗakin ya bar ta a wurin

*******************

"Sir, ba mu samu MK ba, duk wurin da muke tunanin ganinshi, ba ya wurin" cewar Inspector Ameer

DPO ya ce "to ina ya tafi? Ko ya samu labari ne? "

Gboy ya ce "ba zai sani ba, dan ba zai yi tsammanin asirinshi zai tonu ba, na fi zaton yana tare da Zayyad ne"

Insp. Ameer ya ce "amma a tunaninka ina za su tafi? "

"Wuri ɗaya nake da tabbacin za'a same shi, guest ɗinshi, kuma kun ce ba ya nan"

Shiru DPO yayi, ya dafe kai, Ya Nabeel ya ce "amma Gboy why not ka kira shi ka ji ko yana ina? "

Sajjad ya ce "eh ka kira shi"

Ɗaukar waya yayi, ya kira MK, kira biyu bai ɗaga ba, ya ce "yallaɓai bai ɗaga ba"

"Hmm, we must to find him" cewar DPO

Arshad da Jafar kallonsu kawai suke yi, dama dai shi Jafar tun a mota Ya Nabeel ya ja mishi kunne akan kar ya ce komai, dan ya san idan yayi magana zai faɗi duk abunda ya zo bakinshi ne, shi kuwa Arshad tunanin yanda zai yi da MK ne a ranshi

Turo ƙofar office ɗin aka yi, gaba ɗayansu suka juya dan ganin ko waye, Yuhanees ce da ɗan sandan da suke tare

Ganin yqnda take kuka ya sa Arshad miƙewa ya ce "Yuhaness lafiya? "

Ɗan sandan ya ce "sorey for the interruption Sir, there's a new case na kidnapping"

DPO ya ce "kidnap?  Wa aka sace?"

"Ƴar uwar wannan baiwar Allah"

Arshad ya ji gabanshi ya faɗi, ya ce "Yuhanees stop crying and tell me, menene"

Da ƙyar ta iya haɗiye kukanta, kai a ƙasa ta ce "Zayyad ne ya ɗauke Hanan"

"What!!! Ya ɗauke ta ya kai ta ina?" ya faɗa a razane cikin zafin rai

Kuka take yi ba ta ma iya ɗaga kai ta kalle shi ba, ganin yanda ya wani rikice ya sa Sajjad riƙe shi ya ce "calm down Super.....  Yuhanees ya aka yi ya ɗauke ta? "

Cikin kuka take gaya musu yanda aka yi, ba abunda ta ɓoye musu, DPO ya ce "amma kunyi wautar barinta ta shiga ita kaɗai, ya kamata da shiga kawai za kuyi sai ku zo da shi, idan yana da gaskiya a nan zai wanke kansa, yanzu meye amfanin haka? "

"Nima da na san haka zai faru ba zan taɓa bari ta shiga ba, ni dai dan Allah ku nemo ta dan Allah" ta ƙarasa tana kuka

Insp. Ameer ya ce "ya isa kiyi haƙuri, zamu nemo ta in sha Allah"

Wani wawan kallo Arshad ya mishi, gaba ɗaya ranshi ya gama ɓaci, zuciyarshi har bugawa take yi, ya ce "zaku nemo ta! "

DPO ya ce "relax Arshad, tunda har muka samu wannan labarin, i promise you za mu nemo ta"

"Relax? I should relax! Kana so yanda na zauna nan nayi shiru when you're accussing me, hqkq ka ke yanzu ma in zauna inyi relaxing zaku nemo ta ko! impossible Sir"

"Ni na ce maka zamu samo ta ko, ka zauna, ka san you're under custody"

"Yallaɓai, i cam't seat here while Hanan is there with that stupid guy"

Yana ƙoƙarin fita, wayar Gboy tayi ƙara, ya ce "MK ne"

Hakan ya sa Arshad ya tsaya, yqna kalon Gboy, sannan ya ɗaga ya sa handsfree, "hello MK"

"Gboy kana ina wai?  Yanzu na ga missed calls ɗinka, ka kira ina driving ne, dama ina so in kira ka yanzu"

Gboy ya ce "nima na je kampani baka nan shi ne na kira ka inji ko kana ina?"

"Mun fita ne tare da Zayyad, akwai labari ai... Amma kana kampani ne yanzu? "

"Eh, ina nan"

"Yanzu na shigo asibiti zan duba jikin mahaifinka in ga yanayinshi dan in san me zan iya taimaka maka da shi, ashe ma ka fita"

"Asibiti? Eh na fita, amma gani nan dawowa ai ka jira ni, ka je aminity room no.11, Tahir da Fa'iza suna nan"

"Ka san fa ba son zaman asibiti nake yi ba, dan ina son magana da kai ne ma yasa zan tsaya, akwai abunda zan sa ka, kayi sauri"

"Kar ka damu, gani nan zuwa"

Daga haka ya kashe wayar, ya kalli DPO ya ce "yana asibiti"

"Insp. Ameer kuyi sauri ku tafi, ku zo mana da shi, zamu samu ma information akan wurin da ita Hanan ɗin ta ke"

"Yes Sir" cewar insp. Ameer, kafin suka fita shi da Gboy

Suna fita Arshad ya bi su, duk irin kiran da DPO da Ya Nabeel ke mishi, bai sa ya tsaya ba, su ma suka tashi suka bi bayanshi

Su na kai wa harabar station ɗin, suka ci karo da Abba, wanda tun kafin su sauka Ammi ta tura musu driver, sai da aka fara kai su Nabeela gida, sannan ya ce ya kawo shi station

"Lafiya dai? Ina kuma za ku tafi haka? " cewar Abba yana kallonsu

Ya Nabeel ya ce "thank God you are here, zai ji maganarka.... Zai je ne yayi akin da ƴan sanda za su yi"

"Kamar ya?"

Cikin ɓacin rai Arshad ya ce "Abba Hanan fa aka ɗauke shi ne za'a ce ni ba zan tafi ba! "

"Hanan kuma?... Ka ga Arshad, zo mu koma ciki, na san za su samo ta, kayi haƙuri"

"In koma fa ka ce Abba"

"Ko ban isa in ce ka koma ba?"

Ji yayi kamar ya haɗiye ranshi, wani irin baƙin ciki ne ya turnuƙe shi, zuciyarshi sai bugawa take yi, da ƙarfi ya shuri tayar mota, ya ce "darn it.." a hankali yake ja baya, har ya kai dai-dai varenda ya zauna, yana huci

Abba ya ce "Arshad in har na isa da kai, to ban yarda ka bar wurin nan ba..... DPO mu shiga daga ciki inji" suka shiga ciki suka bar Arshad da ke ji kamar yayi kuka, amma sam wannan ba lokacin da zai zubar da hawaye ba ne, dan Zayyad bai kai wannan matsayin ba, sai Jafar shi ma dake gefe haushi ya gama cika shi, Yuhanees ma na gefe ɗaya, kuka kawai take yi,  Sajjad ne kawai yayi ƙoƙarin rarrashinta, sannan ya dawo wurin Arshad yana kwantar mishi da hankali, sai dai a banza yake yi dan ba ma jinshi yake yi ba

A ɓangaren MK kuwa, da tambaya ya ƙarasa room no. 11 kamar yanda Gboy ya gaya masa, yana shiga ɗakin kuwa ya tarar da su Fa'iza da Tahir, sai Babansu da ke cikin ayaba

Gaida shi su Tahir da Fa'iza suka yi, kafin ya ja kujera ya zauna, yana gaida Baba tare da tambayarshi ya jikinshi

Baba ya ce "yallaɓai na gode fa sosai da taimakon da ka mana, na san ra baka taimaka mana ba sai dai in mutu a nan dan yaran nan na san ba su da wurin da za su samo waɗannan kuɗin"

Kafin MK ya samu bakin magana, Fa'iza ta ce "Baba ba fa shi ba ne ya biya maka kuɗin, AAJ nace maka ba MK ba, ai wannan ma ba ya da tausayi, ɗazu na ji Ya Garba na gaya ma Ya Tahir wai maigidan nan na shi mugu ne kuma zai kai ƙararshi wurin ƴan sanda... To ya aka yi ba su kama ka ba kai kam" ta ƙarasa zancen na ta da tambayar MK

Tun da ta fara bayani MK ya ji kanshi ya ɗaure, me yarinyar nan ke nufi ne wai? Shi kuwa Tahir sai zungurin ta yake yi tayi shiru, amma ina! Ta riga da ta fara bada bayani ba ji ba gani

Murmushin ƙarfin hali Tahir ya ƙirƙira, ya ce "wallahi ke kam Fa'iza akwai son bada labari, ga sui ba kya tsayawa ki fahimci abunda aka ce"

"Ba wani nan, wallahi haka na ji ya faɗa, kuma ma ni shaida ce, dan wannan ya daɗe da ya san ni amma ko sweet ɗin naira biyar bai taɓa siya mun ba, amma wancan kuwa leda biyu ya ciko mun da kayan daɗi hadda abunda ban taɓa gani ba"

Ba MK ba, shi kanshi Baba sai da ya ji kunya, ya ce "Fa'iza kama mun bakinki, wa ya tanbaye ki? Da aikinshi zai ji ko da siyayyan kayan daɗi?"

Sai yanzu MK ya samu damar tattaro kanshi, yayi murmushin yaƙe, ya ce "hmm Fa'iza kenan, to kiyi haƙuri ba ki fahimce ni da kyau ba ne, amma zan wanke laifi na in sha Allah, bari in je in dawo yanzu za ki ga abunda zan kawo miki"

Baba ya ce "dan Allah ƙyale ta Yallaɓai, a haka ma ai mun gode"

Ya sake yin murmushi ya ce "a'a Baba, ina zuwa dai" bai tsaya jin komai ba ya fita daga ɗakin

Tsayawa yayi bakin ƙofar ya ce "ni Gboy zai munafunta kenan! Wato shiyasa yake ra tambaya na wurin da nake?... Lallai zan yi maganinshi, amma ban  kamata in ɓata lokaci anan ba"

Sai ya juya da sauri ta har wurin, ya kai ƙarshen corridorn wurin, ya hangi Gboy da insp. Ameer, duk da cewar coat ce a jikinshi hakan bai hana shi gane ɗan sanda ba ne, sai kuma ya ga wasu ƴan sanda biyu daga bayansu, dubawa yayi ya ga babu wara hanya da zai bi dan ya kuɓuce musu dole sai sun haɗu, ya sake leƙawa ya ga sun kusa ƙarasowa, da sauri ya juya ya tura ƙofar wani ɗaki da ke wurin, yayi sa'a a buɗe yake, na'u'rorin aiki ne kawai a cikin ɗakin, ta jikin ƙofa ya ga lokacin da suka wuce, da sauri ya buɗe ƙofar ya fito ya nufi wurin da yayi parking motarsa

Yana kusanto wurin ya tsaya, ya ce "oh my God" ya dafe kai, ya juya dan ya ga ko zai ga su Gboy, sai bai gansu ba, ya sake kallon motar ƴan sandan dake kusa da motar shi, "yanzu ya zanyi da waɗannan kuma?.... Yawwa, na gode Allah" ya sa hannu ya ciro face-mask ɗin da ke aljihunshi ya saka, sannan ya wuce kai a ƙasa ko kallon gefensu bai yi ba, ya buɗe motar ya shiga, sannan ya ja ta da sauri ya bar asibitin 

Su Gboy kuwa bayan shigarsu ɗakin, Insp. Ameer ya gaida Baba, sannan Gboy ya ce "Tahir MK bai shigo nan ba? Na ga motarshi a waje"

"Ya shigo, sai dai yanzu ya fita, amma ya ce zai dawo"

Da mamaki Gboy ya ce "zai dawo? Anya kuwa?"

Insp. Ameer ya ce "kana ganin ya fahimci akwai matsala ne? "

"Haka nake sa rai"

Tahir ya ce "haka ne ma, ya fahimci komai" ya gaya musu yanda suka yi da Fa'iza

Gboy ya ce "ai shikenan kuma, ba zai dawo ba..... Shegen kanta kaman kwano, ba dai ina hana ki surutun nan ba, ba kya ji ko! " ya ƙarasa yana ma Fa'iza faɗa

Insp. Ameer yayi murmushi ya ce "kyale ta Gboy, ai haka yaro yake da shegen surutu, in sha Allah zamu kama shi, munyi loosing wannan chance ɗin, amma we'll catch up next time"

Baba ya ce "wai menene? "

Gboy ya ce "Baba, Tahir zai maka bayani, kayi haƙuri, muna sauri ne" daga haka suka bar ɗakin suka bari Tahir na mishi bayani 

*********************

A harabar gidan su AAJ, Farha tayi parking motarta, sannan ta shiga ciki

Kallonsu take ɗaya baya ɗaya, dan yau sai ta ga gidan ya cika sosai, ga Hajjo, Ammi, Hajiyar Sajjad, Ummi, Umma, Yasmin, Yasna, Siyama, Nabeela, Meerah da Adnan, sannan sunyi jugum-jugum banda Adnan da ke ta jan Meerah faɗa, sai dai ta mishi magana ba wai ta bi shi ba kamar yanda suka saba

Gaba ɗayansu kallonta suke yi, barin ma Ammi da ba ta taɓa ganin Farha haka ba, kullum cikin fara'a take, sai kuma idan ƴar shagwaɓar ta ta motsa idan tana fushi da Mummynta

Duk da cewar tun lokacin da Ammi ta fara ganin Hanan, ta ji ta rage wannan zafin son da take yi ma Farha, amma hakan bai hana ta nuna kulawarta akan ta ba

"Zo nan Farha, meke damunki na ga kin wani kumbura haka, kuka kika yi?"

Wani kukan ne ya sake kuɓuce mata, da sauri Ammi ta tashi ta jawo ta jikinta, suka zauna tana rarrashin ta, "yi shiru mana haka nan Farha, ki gaya mun menene?  Me ya faru? Ina Mummynki? "

Hajiyar Sajjad ta ce "kin ga Farha, kiyi shiru ki amsa mana, ana tambayarki"

Kuka take, ta ce "Ammi dan Allah ki yafe mun, na roƙe ki, idan har ba ki yafe mun ba, ban san makoma ta ba"

Da mamaki suke kallonta, musamman Ammi da ta kasa gane dalilin hakan, "Farha me kika mun da kike neman gafara haka? "

"Ammi komai ma na miki ni da iyaye na, ban san ta ya zan iya kallonki ba"

Tsaki Yasna tayi, ta ce "dallah can Malama stop shedding that crocodile tears of yours, ki bari muji da abunda yake damunmu, don't create a scene here, kina wani a yafe miki, ai kin san wyrin da zaki nemi gafara idan har da gaske kike yi, kin ga alamar rashin sa'a a tattare da ke dole ai za ki canza salo"

Farha ba ta ko ɗaga kai ta kalle ta ba, dan yau ta shirya ma ɗaukar duk wani abunda za'a faɗa mata, Umma ta harari Yasna ta ce "kar in sake jin bakinki"

Shigowar Yuhanees da wani ɗan sandan ne ya katse Ammi daga maganar da za ta yi, suna kallonsu, Hajjo ta ce "yau mun shiga uku da ranar kuka, ke kuma lafiya? "

Ummi ta ce "Yahanazu lafiya? "

Kuka take tana girgiza kai, ta kasa cewa komai, da gudu ta faɗa jikin Ummi tana kuka, Hajjo ta ce "iko sai Allah, to kai Malam ɗan sanda me ku ka mata?"

"Hajiya, ƙawarta Hanan aka sace ne shiyasa"

Gaba ɗaya suka haɗa baki wurin cewa "meye?? "

Siyama ta ce "Anty na? "

Ya ce "ku kwantar da hankalinku, im sha Allah za'a samo ta, saboda wanda ake zargin an san shi, kun ga aikin nemo shi kawai zamu yi, kuma ana kan yi"

Ammi ta ce "wa ake zargi? Wa ya ɗauke ta? Yaushe ma ta bar gidan nan?"

Yuhanees ta ce "Zayyad ne, kuma an neme shi an rasa"

Farha ta miƙe ta ce "Zayyad!? "

Ɗan sandan ya ce "eh, abokin MK ne"

Share hawayen fuskarta tayi, ta ce "ka ce ba'a same shi ba?"

"Eh amma ana ta neman shi ɗin dai"

"Idan ba damuwa, zan taimaka muku wurin nemo shi"

"Ke kuma? Kin san shi ne? "

"Kayi wannan tambayar daga baya, amma yanzu mu fara nemo Hanan"

"Hmm, to shikenan, muje sai in haɗa ki da DPO"

Da sauri ta bi bayanshi suka fita, Umma ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wannan masifa da me tayi kama! Allahumma yassir wala ta'asir"

Ummi dai ta zama speechless, ta kasa cewa komai, sai shafa bayan Yuhanees take a hankali

***********************

Hanan ta gama kukanta, ta tashi ta nufi ƙofar parlourn, jijjiga shi take iya ƙarfinta, amma ko alamar buɗewa bai yi ba, Zayyad da fitowarsa kenan, ya ce "ƴam mata da ma kin dai na wahalar mun da kanki, da ba buɗewa zai yi ba"

A tsawace ta ce "wai kai wane irin mutum ne?  Ka zo ka buɗe ƙofar nan in fita, ina da abubuwan dake gaba na, zama na a nan ba zai taɓa canza mun zuciya ba, is better ma idan ka ƙyale ni"

Dariya yayi ya ce "kina da abubuwan yi? Saurayinki kike so ki gani? Allah sarki tantabara uwar soyayya, to ai matsalar yana cell da na kira miki shi, but lemme try" ya faɗa yana wani murmushi, ita kuwa hawaye ne suka fara bin fuskarta, dan ta tsani ta ji an ce wai yana cell ko kuma ita tayi tunanin hakan, ji take gaba ɗaya jikinta yayi sanyi

Kiran layin AAJ ya shiga yi, bai yi tsammanin ma zai ji ta a kunne ba, sai ga shi an ɗaga kiran ma

Mamaki yayi da jin muryar AAJ ya ce "hello" dan yau ko sallamar ma ba'a samu

"Hi dude, ya aka yi ka ɗaga wayar?  Ko ba'a sa ka a cell ɗin ba tukunna? Oh na manta, za ka iya shiga gefen VIP ko? "

Arshad da ya kasa zama ya kasa tsayuwa, cikin tsananin ɓacin rai ya ce "Zayyad kayi kuskuren crossing limits, wannan abunda ku ka ɗauko, da kun sani da a kai na ku ka tsaya, amma taɓa Hanan is a great risk"

Dariya yayi, ya ce "to ai Hanan ɗin ce sai dai a ce masha Allah, amma fa kar ka damu i'm taking good care of her"

Jin maganar yayi kamar an huda mishi zuciya, ya ce "Zayyad ka ji tsoron haɗuwarmu"

"Meye abun tsoron"

"Ta yiwu yanzu ba za ka sani ba, amma idan muka haɗu, definately zaka sani"

"To kayi fatan haɗuwarmu tukunna, kafin kayi nazarin abunda za ka iya mun"

"Kana tantama kenan"

"Ƙwarai kuwa, dan ban ga abunda za ka iya yi ba"

Wani murmushi yayi mai ma'ana daban-daban, ya ce "bari in gaya maka wani abu, a common man is like a sleeping lion, don't wake him up, or else you will be turn apart... Za ka fahimta very soon"
Bai tsaya jin komai ba ya kashe wayar, tare da yin jifa da ita cikin ɓacin rai, jijiyoyin kanshi sai harbawa suke yi................





🥰 UMMEETA🥰.....📝📝📝

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA* 

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata, a mun uzuri akasi aka samu👏👏👏

 *PAGE 45* 

Shiru Arshad yayi yana ƙoƙarin relaxing kanshi dan yana jin harbawar da zuciyarshi ke yi yana sauyawa zuwa wani yanayi na daban, Jafar da Sajjad su na tambayarshi ko lafiya, amma shiru bai ce musu komai ba, hakan ya sa su ma suka zuba mishi ido kawai su na kallonshi sai sauke ajiyar zuciya yake yi akai-akai yana rufe ido

A cikin office ɗin DPO kuwa, Abba na magana da shi akan case ɗin drugs ɗin

"Yallaɓai kamar yanda na gaya maka tun farko, ni ban yi tsammanin Arshad zai yi haka ba, sai dai ban nuna mishi ba saboda abu ne wanda muka gani a zahiri, sai ga shi kuma shi wannan yaron ya zo mana da maganar MK"

Abba ya ce "haka ne, to yanzu ya ake ciki kenan? "

"MK muke so ya zo tukunna sannan sai mu tabbatar da gaskiyar maganar, in ya so sai mu tura su kotu"

Jinjina kai Abba yayi, ya ce "shikenan Dpo, na gode sosai"

"A'a a ba komai, dole ne saboda aikin mu ne kare haƙƙin ko wane ɗan ƙasa"

Murmushi Abba yayi ya ce "ƙwarai kuwa, nayi waya da CP kafin in ƙaraso nan, ya ce akwai uzurin da ya riƙe shi a headquater, amma zai zo"

"Haka ya gaya mun nima"

Ya Nabeel ya ce "bari in duba mutumin"

Abba ya ce "yawwa, mu je, nima ina so in gan shi"

Suka fito waje dan ganin yanayin Arshad ɗin kuma, sai dai yana nan a yanda yake, ya kasa daina sauke ajiyar zuciya 

Abba ya kalli Sajjad ya ce "har yanzu bai tashin ba? "

"Ya tashi Abba, kiranshi aka yi a waya, na kasa gane ko waye amma ina kyautata zaton Zayyad ne"

Ya kalli Arshad da kyau ya ce "Zayyad ne ya kira ka? "

Ɗaga mishi kai kawai yayi, Abba ya ce "in gani, ina wayar? "

Jafar ya ce "ga wayar nan ya jefar da ita, screen ɗin ma ya mutu"

Ya Nabeel ya karɓa ya duba da kyau, ya ce "oh God, screen ɗin ya fashe gaba ɗaya"

"Na so kuwa a ɗauki numbern Zayyad ɗin saboda ayi tracking ɗinshi" cewar Abba

Jafar ya ce "to yanzu ya za'ayi kenan? "

"To nima ban sani ba kam ko akwai yanda za'a yi ɗin" cewar Abba

Lokaci ɗaya motocin su Insp. Ameer da na su Farha suka tsaya, kallon juna Farha da Gboy ke yi, kowa na mamakin me ya kawo wani, ba dai wanda ya ce komai suka ƙarasa kusa da su Abba, sai da suka gaisa kafin suka shiga ciki wurin DPO, wannan karon hadda Arshad ya shiga 

Dpo ya kalli insp. Ameer ya ce "ya na ga ku kaɗai kuka dawo, shi kuma fa? "

"Yallaɓai ba mu samu kama shi saboda ya gane wurinshi zamu je, sai ya riga mu wucewa"

Dukan table Dpo yayi, ya ce "oh God... Yanzu ta ya zamu kama shi kenan? "

Farha ta ce "Sir, ba wai zan yi interferring a aikinku ba, amma ni zan iya kai ku har wurin da MK da Zayyad suke"

Da mamaki suke kallonta, ya ce "ta ya aka yi kika san wurin da suke? Ko da sa hannunki a abunda suka yi? "

"Ko ɗaya, ban ma san sun aikata ba, amma ni na san in har ba'a samu MK a company ba, ba'a same shi a gida ba sannan kuma ba ya guest house, to wuri ɗaya zaku same shi in har yana garin nan "

Insp. Ameee ya ce "ina kenan? "

"Kar mu ɓata lokaci anan wurin wannan surutun, ku zo muje kawai zan kai ku"

Dpo ya bada umarnin su bi ta kawai su tafi, gaba ɗayansu suka fito banda Abba da Dpo, su na fitowa Arshad ya ce Farha ta shiga mota, ba yanda Jafar bai yi da shi ba akan ya bari yayi driving saboda hannunshi amma ya ƙi kula shi, hakan ya sa Jafar ɗin ya haƙura ya shiga passenger seat ya zauna, Farha na baya, Ya Nabeel kuma shi da Insp. Ameer da Sajjad a motarshi, sai wata motar ta ƴan sanda guda ɗaya, haka suka bar station ɗin Farha na nuna musu hanya

A ɓangaren MK kuwa, yana komawa gidan, ya tarar da Hanan a kan carpet kuka ya ƙi ƙarewa, Zayyad kuwa ko a jikinshi sai faman danna wayarshi yake ta yi, Hanan na ganin shigowarshi ta kyale shi, shi kuma Zayyad ya tashi ya ce "ya dai!  Har ka dawo?"

"Dawowar dole ce, wai ni Gboy zai munafunta" cewar MK

"Me yayi maka? "

"Ya haɗa baki da ƴan sanda mana a kama ni, kuma na san kai suke nema, shiyasa na gam haɗa muku komai, yanzu ka tashi in kai ku airport, na riga da nayi magana a haɗa muku komai da komai"

Zayyad ya ce "amma kuwa Gboy bai kyauta ba"

"Ba kyauta wa kanshi ba dai, ya san halina sarai.... Amma yanzu ba wannan ba, ka tashi ban son ɓata lokaci anan"

"Kwantar da hankalinka mana, ai babu wanda ya san gidan nan ko? "

"Babu, Farha kawai ta sani, amma dai hankalina zai fi kwanciya ne idan ku ka bar garin nan"

"To shikenan, ina zuwa" daga haka Zayyad ya shiga ɗayan ɗakin

MK ya kalle ta ya ce "ke kuma so kike sai na ɗaga ki ko me? "

Harara kawai ta iya watsa mishi, ya ce "wallahi zan ɓalla ki, ki tashi na ce"

"Idan na tashi uban me zan maka, ni fa ba inda zan tafi"

"Ke!!  Ni kike gaya wa magana? "

"To ajiye ni kayi da ba zan gaya maka magana ba?  Ni fa ba tsoronka nae ji ba, dama can da ka ga ina kyale ka dan kawai ina ƙarƙashinka ne, amma ba wai dan bazan iya gaya maka magana ba"

Cikin fushi yayo kanta, bai tsaya ɓata lokaci ba ya ɗauke ta mari, yana sauke hannu ta rama, rufe ido yayi ya buɗe kafin ya ce "ni kika mara? "

Bai jira ta amsa mishi ba ya sake marinta sai da ta kai ƙasa, ya sa ƙafa ya shure ta sai ihu take, jin ihunta ya sa Zayyad fitowa da sauri, hakan yayi dai-dai da shigowar Arshad, aian idonshi ya shure ta, zuciyar Arshad har tafasa take yi, da gudu ya ƙaraso wurin MK, Zafafan mari biyu ya mishi, kafin ya jawo kwalar rigarshi da ƙarfi ya buga kanshi da center table, Zayyad ya zo da sauri ya riƙe Arshad, ya sa hannu ya ture shi, Jafar ya ja Zayyad ya fara dukanshi kasancewar shi ya shigo bayan Arshad ɗin, Farha kuwa ta jawo Hanan jikinta tana rarrashinta suka koma gefe

Sai wannan lokacin su Ya Nabeel da Sajjad da ƴan sandan suka shigo, dan su Arshad sun riga su shiga gidan, sakin baki Ya Nabeel yayi ganin yanda ƙannenshi ke dukan su MK da Zayyad, Har sun ba shi tausayi musamman MK da kanshi ke zubar da jini, da sauri ƴan sanda suka zo suka riƙe su, wasu kuma suka kama su MK

Insp. Ameer ya ce "meye kuka yi haka? Ɗaukar doka fa kuka yi da hannunku, yanzu idan ku ka kashe su kuma fa? "

Cikin tsananin ɓacin rai Arshad ya ce "to sai me? Ni wallahi wannan in ma zaku bar ni sai na kashe shi anan gidan" ya faɗa yana nuna MK da ke wani wahalallen nishi

Insp Ameer ya ce "meyasa zaka kashe shi? Ko fa kotu aka kai shi ba hukuncin kisa za'a yanke masa ba saboda sharri ya maka ba kisan kai ba"

Wani banzan kallo ya mishi ya ce "sharri!  Wai kai kana tsammanin saboda abunda ya mun ne ya sa na mishi haka?... Kalli fuskarta ka gani" ya nuna mishi Hanan da ke ta rusa kuka jikin Farha, "dukanta fa yayi, zai fi mishi sauƙi ya kwanta kan titi akan ya dake ta"

Kallonta Insp Ameer yayi sai kawai ya jinjina kai, ya kalli sauran ƴan sandan ya ce "ku wuce da su" suka ja su zuwa waje kafin ya bi bayansu

Ya Nabeel ya zo kusa da Arshad, ya riƙe hannunshi da ke jini saboda ya fama ciwon na shi, ya ce "sai ka wuce mu tafi ko chemist ne a ɗaure maka kafin mu je station ɗin"

Sajjad kuwa ya matsa kusa da su Hanan, ya kalle ta ya ce "ba abunda suka miki? "

Ɗaga mishi ki kawai tayi tana share hawaye, Arshad ya cire hannunshi cikin na Ya Nabeel ya matsa kusa da ita yana kallonta kanta a ƙasa, hannun shi kawai take kallo
Ya ce "me suka yi miki?"

A hankali ta girgiza kai ta ce "ba komai"

"Kuma kike kuka?"

Kallonshi tayi da idanunta da suka sauya kala, ta ce "da gaske ba komai"

"To me kuma yake sa ki kuka bayan ga ni a gabanki"

Hannunshi ta nuna mishi wasu hawayen na bin fuskarta

Jafar yayi wata ƴar dariya ya ce "iyeee, lallai soyayya na aiki wurin nan,  mai ciwo daban, mai kuka daban"

Ya Nabeel ya ce "baka ma ga ni mayar mara aikin yi ba, ina mishi magana amma ya wuce ni"

Sajjad yayi murmushi ya ce "Ya Nabeel Hanan ce fa"

Shi ma murmushin yayi ya ce "soyayyar ta gyara maka hannun ai, ni kun ga tafiya ta"

Jafar ya ce "nima ba zaka bar ni a nan ba, kai na ma har ciwo yake yi wallahi"

Hararar shi yayi, ya ce "abunda ya fi kanka ma sai yayi ciwo tunda ba zaku iya controlling fushinku ba" yana gama faɗar haka yayi waje, Jafar ma ya bi shi

Sajjad ya kalli Arshad ya ce "Super kar muyi wasting time a nan, zo muje ko saboda hannunka" shi ma ya juya ya fita

Farha ta share ɗan guntun hawayenta ita ma, ta juya za ta fita, Arshad ya kira sunanta, ta juyo tana kallonshi, a hankali ya ce mata "i'm sorry, and..... Thank you"

Murmushin ƙarfin hali tayi, ta ce "sorry for what? And why are you thanking me?"

"I have to do so, shiyasa nayi, i'm sorry saboda abubuwan da na miki a baya wanda bai kamata a ce nay miki ba, na manta da duk wani ɗan adam yana da na shi amfanin, nayi miki wulaƙanci sosai, sannan kuma na nuna miki ƙiyayya ta zahiri, kuma hakan bai dace ba, kiyi haƙuri.... Sannan na gide miki ne saboda ta dalilinki ne muka gano wurin da Hanan take"

Murmushin ƙarfin hali tayi, ta kalli Hanan ta ce "ai Hanan ƙawata ce, kuma ina fata za ta ɗauke ni tamkar ƴar uwarta, ka ga kenan dole zan yi iya ƙoƙari na dan ganin an samo ta...... Sannan maganar haƙuri kuma, ni ya kamata in baka haƙuri, da a ce ina da kunya ma ko kallomka bai kamata in iya yi ba, anma da yake hali na bai da kyau sai ga shi har magana nake maka, dan Allah ka yafe mun" ta ƙarasa tana share hawaye

Ya ce "meye abun kuka kuma Farha? Kiyi shiru"

Wani daɗi taji saboda yau ta ji ya kira ta da sunanta kuma cikin sanyin murya, sai dai hawayenta ba su tsaya ba, ta ce "dole ne inyi kuka ha wai dan ina so ba, amma un na tuna abunda nake so in gaya maka sai inji gaba ɗaya na tsani kai na, na tsani iyaye na, Arshad ka san irin gatan da iyaye na suka nuna mun, amma yanzu ji nake duniyan nan na fi tsanarsu fiye da kowa, ji nake ina ma a ce a wani daji aka haife ni wurin da har in gama rayuwa ta bazan san wani daɗi na duniya ba akan dai a ce su ne iyaye na, amma ta wa ƙaddarar ce a haka" ta sake sakin wani kuka, abun tausayi

Hanan ta sa hannu ta share mata hawaye dan tun da ta fara maganar ta ji ta bata tausayi, ta ce "kiyi haƙuri Farha, amma bai kamata ki na magana irin haka ba, ko ma me suka miki hakan bai dace ba, iyayenki ne fa, komai lalacewarsu kar ki manta su ne suka kawo ki duniyan nan kuma suka nuna miki gata"

Jinjina kai Farha tayi tana share hawayen ta ce "na yarda da abunda kika faɗa, amma in kika ji abunda suka yi Hanan ke ma za ki tsane su, har ni ma sai kin tsane ni"

"Ba zan tsane ki ba Farha, su ma haka"

"Hmm, haka dai kike gani.... Zo mu tafi kawai" ta ja Hanan suka bar parlourn, shi kuwa Arshad mamaki ne ya cika shi, meyasa Farha take wannan maganar, bai taɓa ganinta tana kuka irin haka ba sai yau, kusan minti biyu yayi a tsaye kafin shi ma ya fita

A harabar gidan ya tarar da su cikin mota, Farha da Hanan na back seat, sai ya buɗe gaba ya zauna, ya kalli Sajjad ya ce "su Ya Nabeel fa? "

"An gaya maka zai tsaya jiranka ne? Sun wuce da Jafar"

"Idan ka ga chemist a hanya mu tsaya su ɗaure mun hannun nan dan Allah, zafi yake mun wallahi"

Dariya Sajjad yayi ya ce "yanzu ka tuna kenan" sannan ya tada motar suka wuce 

Su kuwa su Ya Nabeel da Jafar, da suna hanyar zuwa station ɗin bayan sun baro gidan, Jafar ya ɗauko takardun ABMAD ɗin da ya ɗauko daga gidan su Farha tare da hoton a wurin da ya ajiye su, kasancewar motar da ya ajiye su ne, ya miƙawa Ya Nabeel

Duba su Ya Nabeel yayi, ya ce "menene wannan kuma, me zanyi da su?"

"Ina ta so ai muyi magana da kai ai, amma ba mu zauna ba... Wannan takardun gidan su Farha na ɗauko su, a fahimtar da nayi, kamar contract ne suke so su haɗa da store ɗin.... "

"Contract? Akan me to?  Ba Abba ya ce kar a haɗa contract da wannan store ɗin ba? " Ya Nabeel ya katse shi 

"Nima abunda ya bani mamakin kenan ai, shiyasa na ɗauko shi"

"Ka kyauta ai, shi kuma wannan hoton fa? "

"Ka duba da kyau Ya Nabeel, wa ka gane a cikinsu? "

Ya ɗan ɗauki lokaci yana kallon hoton, sannan ya ce "na gane wannan, Alhaji Mus'ab.... Sai kuma wannan, kaman yana cikin mutanen da suka kawo gawar Abbi ko? "

"Ka gane kenan, shi ne... A tunanin ka me yake yi tare da Alhaji Mus'ab? "

Ya Nabeel ya ɗan yi shiru, kafin ya ce "akwai alamar tambaya kam tabbas, amma bari zamu yi wannan maganar, bari mu koma gida, binciken da Hajjo ta hana Abba yi, dole shi zamu yi"

"Nima dai ina ganin akwai lauje cikin naɗi"

"Sosai kuwa" cewar Ya Nabeel 

A lokacin suka shigo cikin station ɗin, hakan ya sa suka bar magar, Ya Nabeel ya mayar da su wurin da ya ga Jafar ya jawo su, sannan suka fito


A ɓangaren su Hajiya Karime kuwa, bayan Farha ta fita, Suka koma cikin parlourn, Hajiya Karime ta ce "wai Alhaji ina yarinyar nan ta tafi ne? "

"To taya zan sani? Amma ki kwantar da hankalinki, na san duk in da ta tafi zata dawo ai"

"Alhaji ba wai dawowar ba, a ya zata dawon? Ka ga fa yanda ta fita"

"Lafiya ƙalau ƴata zata dawo... Yanzu ba wannan ba, zan je in ga Alhaji Isah, in gaya mishi halin da muke ciki"

"To shikenan, sai ka dawo"

"Yawwa" ya faɗa sannan ya nufi hanyar fita yana gyara babbar riga

Tsawin mintuna ashirin tayi a zaune tana nazari kala-kala, kafin ta yanke shawarar zuwa gidan su Arshad dan ta ga meke faruwa saboda ta san ta inda za su fara, ta ɗauki mayafinta ta bar gidan


A gidansu Arshad kuwa, yaran gaba ɗaya su na ɗakinsu Yasmin, Siyama sai kuka take yi, Yasna sai rarrashinta take yi, "kiyi shiru mana Siyama, na san ba abunda zai same ta, in Allah ya yarda zata dawo lafiya"

Yasmin dai kallonsu kawai take yi, sai tsaki take ta faman yi Nabeela ta ce "wai ke kin dame mu da tsaki sai ka fe wata tsaka, addu'a za kiyi musu gaba ɗaya ba wai tsaki ba "

Yasna ta ce "ba sai abun ya dame ta ba ne zata yi addu'a!"

"Ban gane sai ya dame ta ba, ke fa ƴar rainin hankali ce wallahi"

"Ga ƴar rainin hankalin nan dai kusa dake ai, ni wallahi Yasmin ta ba ni mamaki sosai, ban taɓa tsammanin zata iya juyawa Sweet Bro baya ba akan abunda yake so, to ko dai Ammi ta dawo hanya, saura ke kiyi ma kanki faɗa" tana gama faɗar hakan, ta miƙe daga kan gadon, ta ja hannun Siyama suka bar ɗakin

Nabeela ta ce "Yasmin, wai ke har yanzu kenan ba kya son Hanan?"

Numfashi Yasmin ta sauke ta ce "ba haka bane Nabeela, ni yanzu ban ma san me nake ji ba akan ta.... Wai ke ba ki san wani abu da ke tsakanin Ammi da mahaifiyarta ba? "

"Ke ba ki sani ba ma bare kuma ni? "

"Ko su Hajjo ba ki taɓa jin sunyi magana akansu ba? Ni abun nan yana ɗaure mun kai, yanda na ga Ammi ta ji daɗin ganinta"

"Hmm, ko ma dai menene, yanzu mu jira komai ya lafa, sai mu tambaye ta"

Ɗaga kai Yasmin tayi ta ce "shikenan"

"Sannan ƙiyayyar da kike yi wa Hanan ki daina, ko saboda Ya Arshad, ya kamata duk wani abu da yake so ku nuna mishi kun fi shi son abun nan komai muninshi matuƙar ba saɓon Allah ba ne, Yasna ta fi ki wannan tunanin shiyasa kika ga komai da ya shafe shi Yasna ta fi ki saninshi, amma hakan bai sa ya banbanta son da yakw miki da na ta ba, Ya Arshad bai taɓa bari ku ka yi kukan rashin Abbi ba, duk da ba wani saninshi muka yi ba, amma i mahaifi na da daɗi shiyasa har ya maye muku gurbinshi, tunda muka yi wayo na fahimci Ya Arshad duk maganarsa ku ne, haka ma damuwarsa, ina zaka Twins, ina ka fito Twins, me ka siyo, na Twins ne, me zaka yi, su Twins zan yi ma abu kaza... Maganar shi fa kenan, amma ke ko kunya babu ya zo da mata ya ce yana so akma ki nuna ke bata miki ba, kuma ni a yanda Yasna ta ba ni labarinta ban ga wani aibu da take da shi ba, ya kamata kiyi ma kanki faɗa Yasmin you're no more a child, You're matured, 18years ba 8 years ba ne, amma shawara na baki idan za ki iya ɗauka, dan ke wani lokacin kina da wuyar sha'ani, kusan halinku ɗaya da Ya Jafar, so left to you, ko ki ɗauka ko ki barshi, Nabeela dai na ta shawara ne kawai"
Ita ma ta tashi ta bar ɗakin

Shiru Yasmin tayi tana nazarin maganganun Nabeela, tabbas duk maganar da Nabeela ta gaya mata ba ƙarya a ciki, ita ma yanzu ta gane lallai ba ta kyauta ba abunda tayi, hakan ya aa ma har ta fara jin kunyar Arshad ɗin, hawaye ne ke bin fuskarta, a hankali ta ce "i'm sorry My Brother, i'm so sorry" sai kawai ta juya ta kwanta tana share hawaye


Daga ɓangaren su Arshad kuwa, bayan sun isa station, suka tarar da CP a office ɗin, sai dai cikin manyan kaya yake ba uniform ba, sai Umar

Lokacin da suka ƙaraso, har an gama yi ma su MK tambayoyi, kuma yayi confessing laifinshi dan duk wasu hujjoji Gboy ya kawo musu shi, kasancewar sai da ya je kampanin MK ya ɗauko musu duk wani abu da yasan zai iya zama evidence, ya ba su

CP ya ce "to yanzu meye amfanin hakan Marwan? Kana samun profit a kasuwancinka, to meye sai ka ga bayanshi, bayan shi bai damu da kai ba, haka ita ma wannan baiwar Allah da kuka ɗauke kai da wanann abokin na ka, me tayi muku?"

MK ya ce "bai damu da ni ba? Ka san kuwa irin asarar da ya sa nayi yanzu kusan shekara ɗaya kenan da watanni, nayi asarar millions of Naira sabida shi, shiyasa ni kuma ba zan iya haƙura ba dan dama ban san haƙuri ba, nake so sai na sa shi yayi asara fiye da yanda nayi, ita kuma wannan na fahimci irin son da yake mata, shiyasa na so har ita sai na raba shi da ita"

"Hmm, ba ka san haƙuri ba ko?! To yayi kyau, ita ma kotu ba haƙuri ta sani ba, zaka musu wannan bayanin a can ai.... DPO, i'm done with this, kuyi abunda ya kamata, ku tattara komai ku miƙa su kotu, that's all" cewar CP, kafin ya miƙe ya fita Abba ya bi bayanshi, sannan sauran suka fita

Ƴan sandan suka kama su MK za su shigar da su cell, ya tsaya gaban Arshad ya ce "kana tunanin wai ka tsira saboda za'a kai ni kotu? To ka jira fitowa ta, zan rama abunda ka mun ne, saboda Marwan Kabir, MK, ba ya mantuwa"

Arshad ya gyara tsayuwarsa a gaban MK, ya sa hannu a aljihu ya ce "zan fi kowa farin ciki da fitowarka Marwan Kabir, saboda zan samu damar cire maka hannu da ƙafa, in gaya maka banbancin Hanan da sauran matan da ka sani, kuma zan jira dawowarka, saboda Arshad Ahmad Jalal, AAJ, ba ya tsoro, kuma ba ya ja da baya, musamman akan Hanan" sai kawai ya matsa mishi, ƴan sanda suka wuce da shi, ya raka shi da wani mugun kallo


CP da Abba kuwa su na daga can gefe jikin motar CP, Abba ya ce "na gode CP"

Murmushi yayi, ya ce "godiya kuma da me?.... Yawwa, maganar yaran nan da muka yi"

"Ina so kuwa nima inji, ya ake ciki? "

"To anyi binciken kamar yanda na gaya maka, Jafar da Umar suka yi, kuma sun tabbatar mun da cewar Hanan ta fi Farha kamun kai da tarbiyya, da dai komai da ake buƙata a wurin mace, har kuma nima na gamsu da hakan, saboda Umar ya kunna mun recording ɗin da yayi, wanda ita Farha da ƙawarta suke magana akan za su ba shi kuɗi dan ya bada report ɗin ƙarya akan Hanan, anan na gane ita wannan ƙawarta ɗin, ƴata ce, Samira, kuma na tambaye ta, ta tabbatar mun da gaskiyar maganar"

"Ikon Allah, da alama dai yaron nan Hanan ɗin nan ita ce matarshi"

"Eh to, Allah dai ya sa ita ce alkhairi a wurinshi...... Amma ka san me ya bani mamaki kuma, Farha ita ta taimaka har aka gano Hanan"

"Nima dai da na samu labarin ita ce Farha, nayi mamakin haka, amma dai ko menene dalilinta ɗin zan ji"

"To shikenan Alhaji Yusuf, Allah ya sa mu ji alkhairi"

"Ameen ameen"

"To ni bari in tafi, ina da wani uzurin... Na bar ka lafiya" suka yi musabaha, CP ya shiga motarshi, ɗan sandan da ke ciki ya ja shi suka wuce

Sannan Abba ya koma wurinsu Ya Nabeel, ya ce "to ku mu tafi gida ko"

Suka amsa mishi da "to", sannan suka shiga motocin su ka wuce bayan Jafar yayi sallama da Umar

A babban parlourn suka samu su Hajjo, da gudu Yuhanees ta zo ta rungume Hanan tana kuka, share mata hawayen Hanan tayi ta ce "meye haka wai Rabin rai, ki daina bana so"

"Kiyi haƙuri Hayatee, duk ni na kai ki wurin da za'a cutar da ke"

"Waya gaya miki an cutar da ni? Ba abunda suka mun Rabin rai"

Yuhanees ta kalle ta da kyau, sannan ta sake rungume ta, sai gasu Yasna sun shigo ɗakin da gudu suka faɗa kanta ita da Siyama, Arshad kallonsu yake yi kafin ya ce "yau ni na ga ikon Allah, to ni kuma fa, ba ku ganni ba ne? "

Dariya suka yi, Ummi ta ce "so nan ka ji, kyale su, kai da kake da uwa ma"

Murmushi yayi ya ƙarasa kusa da Ummi ya zauna, Hajiyar Sajjad ta kalli Hanan da ta wani kwaɓe fuska, ta ce "da dai Arshad me ɗana, amma ynx na yafe shi, mata sun fi guarantee, zo kinji Hanan" ta ƙarasa wurinta tana jin daɗi, Ammi dai sai murna take yi

Nan suka zauna Abba yayi musu bayanin komai da ya faru a station ɗin banda maganar sa suka yi da Cp akan Farha kasancewar tana zaune, ba zai iya yin maganar ba, Yasmin da ke ɗaki ta gama kukanta ta sauko, kusa da Umma ta zauna

Farha ta gyara zamanta ta ce "ku gafarce ni dan Allah, akwai abunda nake so in gaya muku, na san ba zai muku daɗi ba, amma ina roƙonku da ku yafe mun" ta ƙarasa maganar tana kuka

Ammi ta jawo ta jikinta ta ce "ya isa mana Farha, gaya mun menene? "

Sai da ta gama share hawayenta, ta natsu kafin ta ce "Ammi ba kowa ba ne ya raba ku da su Ummi ba sai Alhaji Mus'ab da Hajiya Karime, iyaye na"

Da mamaki suke kallonta gaba ɗayansu, Ammi ta ce "ban gane ba, kamar ya? "..........



🥰 UMMEETA🥰.....📝📝📝

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA* 

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata, a mun uzuri akasi aka samu👏👏👏

 *PAGE 46* 

Farha ta fara bayani kamar haka "Ammi, ɗazu Daddy ya bani wannan labarin, ya matuƙar bani mamaki, ban yi tsammanin haka yake ba.... Ammi kamar yanda ku ka shaida mahaifinsu Arshad da mahaifinsu Hanan aminan juna ne komai tare suke yin shi, haka ma kasuwancinsu, daga baya suka yanke shawarar dawowa nan Kaduna, ba kowa ya ba su wannan shawarar ba sai mahaifina saboda ya ce idan suka shigo nan Kaduna yin kasuwancin na su, su na haɗuwa, anan ya fahimci sun fi shi experience na kasuwanci, yayi ƙoƙari awannan lokacin ya shiga cikinsu saboda duk profit ɗin da za su samu ya kasance ya kwashe kaso mafi yawa a ciki, amma ya ce mahaifinsu Hanan, wato Abdul bai da saurin yarda da mutane, sannan yana matuƙar kula da abunda ya shafe shi ko kuma aminin na shi, hakan ya sa yayi saurin fahimtar manufar Alhaji Mas'ud, saɓanin shi Ahmad da yake matuƙar yarda duk wanda yake tare da shi... Abdul yayi ƙoƙarin janye su daga Alhaji Mas'ud, amma shi kuma Alhaji Mas'ud ya sa ma ranshi dole sai yayi kuɗi ko ta wane hali ne kuma yayi suna a fannin kasuwanci, sannan waɗanan mutanen su za su taimaka mishi, sai dai kuma in har Abdul na nan ha zai taɓa samun yanda yake so ba, hakan ya sa yayi shawara da wani abokinshi Alhaji Isah akan cewar za su kashe Abdul tunda shi ne ke hana ruwa gudu, Ahmad bai da wata matsala, sai dai Abdul ya ji lokacin da suke wannan maganar, ya gaya musu zai je ya bada report wurin ƴan sanda amma suka tayi mishi magiya akan yayi haƙuri sharrin shaiɗan ne, suka mishi alƙawarin ba za su sake ma zuwa wurinsu ba, duk irin tsaurin kai na Abdul yana da tausayi, sai ya ji tausayinsu ya ce ya fasa kai su ƙara amma duk abunda ya same shi ko abokinshi to su kuka da kansu, suka amince da hakan, daga wannan lokacin ba su sake ganin Alhaji Mas'ud ba.... Bayan wata ɗaya da faruwar hakan, tafiya ta kama Abdul zuwa garinsu, sai ga Ahmad ya zo Kaduna dan ya nema musu gidajen da za su zauna, shi da kanshi ya nemi Alhaji Mas'ud dan ya taya shi nema musu gidan saboda Abdul bai gaya mishi abunda ya faru tsakaninsu ba, a lokacin ya tambaye shi ina Abdul sai ya gaya mishi ai ya tafi garinsu, Maiduguri, saboda ya kusa yin aure zai je ya ɗan yi shirye-shirye kafin lokacin biki
Alhaji Mas'ud ya ce 'to meyasa ba ku tafi tare ba, na ga komai tare kuke yi'
 Ahmad ya ce mishi 'nima na so ace ya bari mun tafi tare amma ya ce a'a ba daɗewa zai yi ba'
Cikin firar ta su yake tambayarshi a wace unguwa su ke saboda shi ma'abucin zuwa garin ne, alhalin kuwa ƙarya yake yi, Ahmad kuwa ya mishi kwatance tsab, kuma ya gaya mishi in har ya je wurin ya tambayi gidansu Abdul-Aziz, har gidan za'a kai shi, Alhaji Mas'ud ya matuƙar jin daɗin wannan bayanin, ya taimaka mishi wurin samun gidajen kafin Ahmad ya koma Adamawa... Kwanaki biyu da tafiyar Ahmad, Alhaji Mas'ud da Alhaji Isah tare da wasu mutanen suka shirya zuwa garin Maiduguri, a unguwarsu Abdul suka nemi wani gidan haya suka sauka, sai da suka yi kwana biyu suna lura da shiga da ficen Abdul, suka karanci yanda tsarin gidan na su yake kasancewar ba wani babba bane, ɗan madaidaici ne dai-dai su, daga shi sai kawunshi da matarshi sai ɗansu guda ɗaya ɗan shekara sha biyu, sai kuma Haleema(Ummi).... Wata rana da daddare suka ɓoye fuskokinsu suka shiga gidan da makaminsu a hannu sai kace ɓarayi, Kawun Abdul ya tsorata sosai da ganinsu, yayi ta ba su haƙuri yana musu magiya akan su kyale su saboda basu da wani abunda za su ba su, ɗaya daga cikinsu yayi magana ya ce 'to kai wa ya gaya maka wani abu muka zo nema a wurinku?'
'To ku gaya mun me kuke so? ' Kawunshi ya tambaye su, Alhaji Mus'ab ya zo har gaban Abdul da ke ta kallonsu kawai dan shi yana ji a jikinshi kamar ya san su, Alhaji Mus'ab ya buɗe fuskarsa ya kalli Abdul ya ce 'kana mamakin gani na a nan ne? To amininka ne ya bani kwatancen gidan nan, Abdul ka mun wata barazana a baya kana tsammanin ka tsorata ni ne ko, to ɗaga maka ƙafa nayi zuwa lokacin da zan samu cikakkiyar damar da zan halaka, kuma yanzu lokaci yayi, zan kashe ka, sannan kuma in kashe waɗannan mutanen, sai kuma in koma can wurin aminin naka bayan na gama samun abunda nake buƙata wurinshi shi ma sai in aika shi barzahu, sabisa in har na bar shi, zai iya hana sunana ya kansance na farko a manyan ƴan kasuwa'

Abdul ya ce 'kisa? Ni kake tunanin zaka iya kashewa sabida kawai ka zo da waɗannan abubuwan?'
Kawun Abdul ya ce 'Abdul-Aziz ban son taurin kai, mutumin nan da gaske fa zai yi abunda ya ce... Bawan Allah kayi haƙuri dan Allah kar ka kashe mu, kap zuri'armu mu kenan dan Allah kayi haƙuri'
Alhaji Mus'ab yayi dariya ya ce 'to shikenan Baba ba xan kashe ku ba amma da sharaɗi, daga yau ba Abdul ba Ahmad, ba Abdul ba garin Adamawa ko Kaduna, ko a waya kar suyi magana, sannan kuma ku tattara komatsanku ku bar unguwar nan kar kuma kowa ya samu labarin wurin da kuka koma,  in har hakan ya faru to za ku tsira, in kuma na gano ba su rabu ba, to wallahi sai na fara kashe Ahmad da ke can kafin in dawo kanka'
Sai da Kawu ya ce ya amince da wannan sharaɗin karin suka bar gidan, washe gari kuwa da sassafe Kawu ya takurawa Abdul akan ya nema musu wani gidan, ba irin ɓacin ran daAbdul bai nuna mishi ba amma ya ce dole sai yayi yanda yace ɗin, haka ya je ya samo musu wani gidan, cikin ƴan kwanaki suka tattara suka bar unguwar ba tare da kowa ya san inda suka koma ba, sai da Alhaji Mas'ud ya tabbatar da sun bar gidan sannan suka dawo garin Kaduna, zuwa wannan lokacin kuwa Ahmad sun tare a sabon gidansu na Kaduna, abu na farko da Alhaji Mus'ab ya fara yi bayan komawarsa shi ne sace wayar Ahmad, ya karya sim card ɗin saboa ma kar Abdul ya kira shi, kuma lokacin da suka shiga gidansu Abdul ɗin sun ɗauke ta shi wayar shi ma, Ahmad ya hardace numbern Abdul, bayan ya siyo sabon sim ko ya kira sai ya ji wayar a kashe kasancewar shi ma Abdul bai yi welcome back ba kamar dai Ahmad, duk lokacin da ya ɗauko ma Alhaji Mus'ab zancen Abdul sai ya nuna ai ya damu sosai da rashin samun labarinshi.... Abdul kuwa gaba ɗaya ya kasa samun sukuni, kullum cikin ɓacin rai yake, duk lokacin da ya kira wayar Ahmad kuma ba samunshi yake yi ba, ga shi kuma Kawunshi ya mishi rantsuwa akan kar ya bar garin Maiduguri saboda yana tsoron abunda zai same shi, gaba ɗaya Abdul ya rasa abunda ke mishi daɗi,  suna a haka har aka yi aurensu da Haleema wacce ita kanta wannan abun yana damunta sosai, a kwana a tashi suka haifi ƴarsu ta farko, wato Hanan, amma kullum al'amarin Abdul gaba yake yi akan wannan abun, ya zama kamar ba shi ba, kuma yana yawan mafarkin Ahmad, gaba ɗaya hankalinshi ya ƙi kwanciya har Hanan ta kai shekara hudu da haihuwa, hakan ya sa yayi ta roƙon Kawunshi akan ya ba shi damar zuwa wurin abokinshi, yayi mishi alƙawarin ba zai bari wani abu ya same shi ba, ganin yanda yake ta roƙonshi yasa ya ba shi izinin tafiya ba dan ranshi ya so ba, a ranar Abdul da Haleema suka haɗa kayansu, washe gari suka nufi garin Adamawa, a wuri abokanan kasuwancinsu ya samu labarin ai Ahmad ya koma Kaduna kuma yayi tunanin haka, sam bai tsaya wurinsu Inna ba saboda a tunaninshi hadda ita dan haka aka gaya mishi, kwanansu ɗaya a nan suka wuce garin Kaduna ya kama haya a wata unguwa dake bayan gari, sai da ya shafe shekara ɗaya da rabi, kafin ya samu labarin Ahmad, dan a wannan lokacin ba wani suna yayi ba, ko a kasuwa ba kowa ya san shi da sunanshi Ahmad ba sai da Abmad, sai dai a ranar da Abdul ya samu labarin Ahmad, a ranar ne Ahmad ɗin ya bar ƙasar shi da iyalanshi lokacin Arshad yana da shekaru tara a duniya, Hajiya Ruƙayya kuma tana da cikin twins, Hanan kuma tana da shekara huɗu da watanni kuma Haleema tana da cikin Siyama,... Abdul ya ji ba daɗi da ya saku labarin tafiyar, sai dai ya gode ma Allah tunda har ya gane wurin da yake ɗin, kullum Abdil cikin jiran dawowar Ahmad ya ke amma shiru ba amo ba labari har Haleema ta haifo ƴarta Siyama, sai dai haihuwar ta zo mata da matsala, dole ya shirya suka koma gida Maiduguri a can tayi jinya tsawon watanni kafin suka sake dawowa Kaduna, ya koma wurin da yake samun labarin Ahmad, aka gaya mishi ai sun dawo, amma suna Adamawa saboda a can ƙasar da suka tafi matarshi ta haifi ƴan biyu, shiyasa ba su tsaya nan ba, a taƙaice dai Abdul da Ahmad ba su saku haɗuwa ba sai bayan shekara ɗaya zuwa biyu ma, saboda Ahmad ba zama yake yi ba.... A kasuwa suka haɗu, Abdul ya same shi a shagonshi na ABMAD, Ahmad yayi murna sosai kamar ba gobe, cikin farin ciki ya ɗauki waya zai kira Hajiya Ruƙayya, amma Abdul ya hana shi, ya mishi bayanin komai da ya faru da kuma dalilin rashin jinshi da yayi tsawon shekarun nan, sosai Ahmad yayi mamaki, sannan kuma ya fahimci abu uwan da suka faru cikim waɗannan shekarun dan kullum kasuwancin na shi ja baya yake yi shi kuma Alhaji Mus'ab sai gana yake yi, yana yawan fita ƙasashen waje amma gaba ɗaya kayan Alhaji Mus'ab ne yake kawowa... Abdul ya ce mishi kar yayi saurin bayyana ma kowa sun haɗu, za su yi ta haɗuwa a ɓoye har zuwa lokacin da za su fallasa Alhaji Mus'ab, haka kuwa aka yi har aka yi wata biyu, ana gobe twins za su cika shekara biyu, suka gama haɗa plan na yanda za su kawo ƙarshen muguntar Alhaji Mus'ab, suka tsara a gobe za su gama da matsalarshi sannan kowa ya san sun sake haɗuwa, sai dai abunda ba su sani ba shi ne ba abunda Alhaji Mus'ab bai gane ba a abunda suke shiryawa... Gobe nayi aka haɗa bikin birthday ɗinsu twins, Ahmad ya gaya musu su fara bikin zai je ya dawo zai yi suprising ɗinsu, haka ma Abdul yayi sallama da Haleema ya kuma gaya mata ta shirya tsab ita da yaranta, zai turo mata wani address in ta ga ya kira ta to su zo wurin zai kai su wani gida, ta amsa mishi kawai da to.... Wurin da suka tsara haɗuwar suka haɗu sannan Ahmad ya kira Alhaji Mus'ab ya ce ya zo ta same shi akwai wani harƙalla, already a cikin shirinshi yake, ba ɓata lokaci ya isa wurin tare da mutanenshi su biyu amma suka tsaya daga waje... A fuska Alhaji Mus'ab ya nuna musu tsoro da mamakin ganinsu tare har sua fara tunanin sunyi nasara, suka gaya mishi za su kira ƴan sanda dan a kama shi, amma ya fara musu dariya abunda ya ɗaure musu kai kenan, ya ce 'a tunaninku zan ji tsoro ne? To ku ne sakarkaru dan na daɗe da sanin Abdul ya shigo garin nan, dama na gaya maka in har ka sake ka zo wurinshi sai na kashe ku ko, za ku ga yanda zan yi da ku'... Ya kira abokan ma shi suka shigo, ɗayan na riƙe da bindiga, ganin haka ya sa Abdul ƙoƙarin kiran ƴan sanda, sai dai garin sauri ya danna numbern Haleema a maimakon na ɗan sandan,  ɗaya daga cikinsu ya ƙwace wayar har ta fara ringing ya kashe ya jefar da wayar sannan ya kama hannunshi ya riƙe, suka fara dambe tsakaninsu kafin shi ma Ahmad ya fara ƙoƙarin dambe da su, sun kai mintuna biyar a hakan, Ahmad ya lura da bindigar da suka jefar, da sauri ya ɗauke ta ya saita ta jikin Alhaji Mus'ab, cak suka tsaya, ya ce 'in har ku ka motsa daga nan sai na kashe ku'.. Ba wanda ya motsa, Ahmad kua ya rasa ma yanda zai yi da bindigar dan ba zai iya kashe kiwa ba, barazana ce kawai, aljihunshi ya fara taɓawa ko zai ji wayarshi amma babu, Abdul kuwa bai ma ga wurin da wayarshi ta faɗa ba, su na a haka suka jiyo takun mutum na tunkaro wurin an incomplete building ne, alama Alhaji Mus'ab yayi ma wanda ke kusa da Ahmad, da sauri yayi kanshi yana ƙoƙarin karɓar bindigar amma bai samu nasara ba, sai kawai ya kai hannunshi wurin kunamar bindigar ya danna, sai ƙarar fitar alburushi suka ji, da sauri mutumin ya ja baya, hakan yayi dai-dai da shigowar Haleema, suman tsaye tayi ganin Abdul ɗinta kwance ya dafe cikinshi dake fitar da jini yana shure-shuren mutuwa har idanunshi suka rufe a hankali, sai a lokacin ta dawo hayyacinta, kallon Ahmad take yi dake riƙe da bindiga shi ma dai kusan mutuwar tsaye yayi, Alhaji Mus'ab cikin ruɗu ya ce 'haba Alhaji Ahmad, meyasa zaka kashe shi, sai da na gaya maka kar ka kashe shi saboda laifin da wataƙila ma bai aikata ba amma yanzu ji abunda ka mishi, hakan bai dace ba wallahi'... Sakin baki Ahmad yayi yana kallon Alhaji Mus'ab, Haleema kuwa gaba ɗaya kalaman bakinta ta nema ta rasa, hawaye kawai ke zuba wani na korar wani, sa ƙyar ta iya sauke wani ajiyar zuciya wanda ya fito da sautin kukanta, da sauri ta juya ta har wurin tana kuka, jefar da bindigar yayi zai bi bayanta yana kiran sunanta, sai dai kafin ya kai ƙofar, Alhaji Isah ya buga mishi wani sanda a kai da ƙarfi, yana juyowa ya ƙara mishi wani, ya faɗi ƙasa, Alhaji Mus'ab yayi ta buga mishi sandar har sai da kanshi ya fashe jini ke ta zuba, ya taɓa shi ya ji alamar baya numfashi, sai ya gaya ma mutanenshi su ɗauki Ahmad su kai shi gida su ce a hanya kawai suka ganshi, shi kuma Abdul ɗin su bar shi a nan kawai.... Duk wannan abun kuma da Alhaji Mus'ab yayi, shawarar matarshi ce Hajiya Karime yake bi, wacce ta ke bin bokaye, dan ma su ne suke gaya mata yanda za suyi dan mijinta yayi dukiya, shi yayi musu wani asiri ta yanda zuciyar Haleema zata rufe da tsanar Ahmad da danginshi in ba haka ba kuwa watarana zata iya yin nazarin da zai sa ta fara zargin Ahmad ba zai iya kashe Abdul ba amma ya sharɗanta musu cewa in har wasu daga cikinsu suka haɗu to tabbas duk wani ƙullinsu zai warware ne, ga shi kuma tana nan maƙale da Hajiya Ruƙayya har ma ta mallake ta duk abunda ta ce tayi shi take ƙoƙarin yi, burinta bai wuce ta ga Arshad ya girma ba ta haɗa auren shi da ni (Farha), a lokacin da na fara wayo tayi ta ƙoƙarin ganin na fara son Arshad amma ni baya ma gaba na dan ni dukiyarshi ba damuna tayi ba, ashe kai ni tayi wurin malamin nata dan ya juyar da tunani na, ido na ya rufe akan son Arshad da dukiyarsa kuma ta samu cin galaba, a tsarin da tayi in har na auri Arshad zamu sa shi ya mayar da gaba ɗaya takardun dukiyarshi da kadarorinshi da komai zuwa suna na, sannan mu mayar da su tamkar bayinmu, sai abunda muke so za suyi, amma Allah ba azzalumin bawansa ba ne, kuma ba ya bari zalunci bayinsa musamman waɗanra suka dogara da shi.......  mahaifiya ta ce ta kai ni wurin boka dan kawai son abun duniya.. Wanann wace irin rayuwa ce? Ina nadamar kasancewa ta ƴa ga waɗannan mutanen wallahi.... Ban san da wane irin ido zan kalle ku ba, amma dan girman Allah ku yafe mun, ba da san raina bane, kuyi haƙuri kuyi haƙuri..... " Farha na kai wa ƙarshen wannan labarin ta saki kuka mai taɓa zuciya, dama can tana labarin ne tana kuka sai dai yanzu kukan ya fi taɓa zuciyar duk wani mai saurarenta

Parlourn shiru kamar ba kowa a ciki, gaba ɗayansu hawaye suke yi banda Abba wanda shiga taushe zuciyar shi yayi dan kar abun yayi yawa, waji dogon ajiyar zuciya Abba ya sauke amma ya kasa cewa komai

Farha ta riƙe hannun Ammi tana kuka ta ce "Ammi dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mun na tuba" ta sake ta ganin ko kallonta ta kasa yi sai kuka, ta ƙarasa wurin Ummi, "Ummi ki yafe mun dan Allah Ummi kinji" ta sake kallon Hajjo dake kusa da Ummi tana ta neman afuwarta, ta durƙusa gaban Arshad ta ce "Arshad pls say something, forgive me pls, banyi komai intentionally ba, sharrin shaiɗan ne da kima muguwar uwa da nake tare da ita, it's not my fault Arshad, pls talk to them, say something"

Durƙushewa tayi tana kuka sosai iya ƙarfinta, Hanan ta rarrafa kusa da ita, ta taɓa ta, a hankali ta ɗago, tana ganin Hanan,  ta ce "Hanan dan Allah ki gaya musu ba da san raina nayi duk abubuwan da nayi a baya ba, kuma wallahi da ace ina sane da wannan abun a baya, ba zan taɓa bari su kai wannan lokacin ba, Hanan iyaye na ne amma ji  nake duk duniyar nan na fi tsanarsu fiye da kowa a rayuwa ta, na tsane su..... " 

Hanan ta katse ta ta hanya rufe mata baki, sannan ta ja ta jikinta ta rungume ta suna ta kuka, tsawon mintuna uku, Kafin Ammi ta tashi ta ƙarasa kusa da su ta ɗago Farha, ta share mata hawaye ta ce "it's okay" sai ta kwantar da ita a kafaɗarta, ita ma tana share nata hawayen a hankali 

Turo ƙofar parlourn aka yi, gaba ɗaya suka juya dan ganin ko waye, Hajiya Karime ce, da sauri suka miƙe tsaye suna kallonta, ganin irin kallon da suke mata ya sa ta fara jin wani ɗar-ɗar a ranta amma sai ta dake ta ƙarasa cikin parlourn, ta tsaya kusa da su Ammi ta kai hannunta za ta taɓa Farha, amma sai ta matsa

Ta ce "daughter menene? Lafiya? Ashe kina nan, i'm so worried"

Ko kallonta Farha ba tayi ba, sai ma Ammi da ta dage iya ƙarfinta ta ɗauke Hajiya Karime da mari sai da jakar hannunta ta faɗi ƙasa, Ummi ma ta sake zabga mata wani marin, ido q buɗe Hajiya Karime ke kallonsu ta ce "ni kuka mara? Me nayi muku? "

Hajjo ta ce "ba abunda kika mana, kawai marin daɗi ne suka miki.... Shashashar banza muguwa azzaluma, ke kam wallahi kin yi asarar rayuwarki, kuma ki jira ƙarshenki"

Daga nan Hajiya Karime ta gama kiɗimewa, tabbas Farha ta tona musu asiri yau, kuka ta fara ta ce "Farha haka kika mana? Mu fa iyayenki ne, amma kika zaɓi ki tona mana asiri a idon duniya ko? Farha me na rage ki da shi da har ki.... "

Farha ta katse ta da "tarbiyya, kin rage ni da tarbiyya Mummy, sannan kin cutar da ruyawa ta, Mummy zan fi kowa farin ciki in ga an hukunta ku" kuka take tana maganar 

"Ni Farha?" 

Abba ya ce "shiyasa ake cewa duk wanda zai gina ramin mugunta, ya gina shi gajere, sannan makashinka yana nan tare da kai, wani irin yarda ne Hajiya Ruƙayya bata ba ki ba, ba ta da aminiyar da ta wuce ki, ashe ke ba mutumiyar arziki ba ce, duba ki ga yanda kika ruguza rayuwar ƴarki da kanki, har ta kai ƴar da kika haifa ta furta miki kalmar tsana.... Hmm Allah ya kyauta"

Hajiya Karime na kuka ta ce "dan Allah ku yi haƙuri ku yafe mun, sharrin shaiɗan ne.... "

Ya Nabeel ya ce "shaiɗan? Dama akwai shaiɗanun da suka wuce ku ne?"

Hanan ta ja hannun Farha suka wuce sama, dan ta san dole duk yanda take jin haushin iyayenta, deep down tana son su ba kuma zata ji daɗin ganin wannan abun ba, dan komai lalacewar iyayenka, iyayenka ɗin ne 

Sai a lokacin Arshad ya saku bakin magana, dan in ya so yin magana daga ya kalli Farha zai ya ji ba zai ita ba, dan ba lallai ya iya furta kalma mai daɗi ba, ya ce "ita ai ta fi ƙarfin shaiɗan ɗin, mu ba wani abunda za muyi miki, dan wallahi in nace inyi miki wani abun to kashe ki kawai zan yi... Amma na kira ƴan sanda, ki jira zuwansu"

Yana rufe baki kuwa sai suka ji knocking, sai ga ƴan sanda su biyu da Insp. Ameer sun shigo, Arshad ya musu bayani a taƙaice sannan ya ce su tafi da ita, kuma su biya wurin Alhaji Mus'ab shi ma su kama shi, Hajiya Karime na kuka suka tafi da ita

Sai da su Abba da su Arshad suka yi wanka kafin suka je station ɗin, ba ɓata lokaci aka shirya komai aka tura su kotu su ma dan a yanke musu hukuncin da yayi dai-dai da laifin da suka akaita, su Arshad kuma sun yi murna sosai da faruwar haka, ko ba komai dai yau an samar wa iyayensu adalci, Ummi ta so su koma gidan su amma Abba ya ce ai ba su da gidan da ya fi wannan, haka ma Ammi da Hajjo suka nuna mata ba zasu so ta koma gidan haya ba, dole suka zauna gidan, sai dare sannan su Yuhanees da su Sajjad suka wuce

Bayan kwana biyu, hankalinsu ya kwanta gaba ɗaya daga wannan stress ɗin da suke fama da shi, cikin kwanaki biyun nan kuwa soyayya da kulawa ne tsakanin waɗannan ahalin guda biyu, Farha kuwa ta kasa sakin jikinta a gidan dan ita ma Ammi ta ce a wurinsu zata zauna, Hanan na ƙoƙarin janta a jikinta saboda kawai ta ga a rage damuwar da take ciki 

Abba ya buƙaci ayi auren su Arshad da Nabeel a wannan hutun da suka samu kar a wani ɓata lokaci, Ummi ta kira kawunsu da ke Maiduguri ta gaya mishi komai, ya ji daɗi sosai kuma ya tabbatar mata da zai shirya komai, in su Abba sun shirya kawai su zo, haka ma anyi iyayen Bilkisu maganar za su zo tambaya, Abba da wasu abokanansa suka tafi maiduguri tambayo auren Hanan, ƙanin Abba kuma da wasu abokanansa su ma suka je tambayar auren Bilkisu, kuma an ba su, aka sa ranar auren nan da wata ɗaya, ba su bar wurin ba sai da suka bayar da sadaki naira dubu ɗari ko wacensu kafin suka dawo

Su Hajiya Ammi kuwa ta  dage sai haɗa kayan lefe take tayi, a cewar ta ƴarta ta musamman ce dan haka dole zata tanbatar a sa maka komai a lefenta, haka tayi ta ordering kaya ƙasashe daban-daban, da na Hanan da na Bilkisu, Ummi da Umma dai ƴan kallo suka zama, har ta gama haɗa su, ko wacensu set uku ta haɗa mata, faɗin yawan kuɗin da ta kashe ma ɓata lokaci ne, Abba ya haɗa musu da mukullin mota ƙirar Matrix, duk wanda ya zo ganin kaya sai san barka, masha Allah, daga nan Abba ya koma Adamawa zuwa lokacin bikin, Nabeel ma ya koma ya sanar da abokanshi da kuma wurin aikinsu, aka ba shi hutu, sannan ya dawo Kaduna,  ana saura kwana goma ayi bikin gaba ɗayansu suka wuce Adamawa


Hanan da Yasna da Nabeela ne a ɗakinsu suna ta fira, Hanan ta kalli Yasna ta ce "yawwa Yasna ni kuwa akwai maganar da nake so in gaya miki"

"Ina jinki Antyna"

"Akwai ranar da muna asibiti kika gaya wa Ammi magana son ranki sai kace ba mahaifiyarki ba, har yau maganar tana raina, ban ji daɗin hakan ba ko kaɗan Yasna"

Yasna ta ce "nima Anty Hanan maganar ta na gaya mata ban ji daɗinta ba daga baya, rai na ne ya ɓaci a lokacin shiyasa amma ba zan sake ba ai"

"Na ji, amma kuma hakan bai wadatar da ni ba dan kince ba za ki sake ba, ina so ki je ki bata haƙuri kuma ki ce ta yafe miki"

Yasna ta ɗan yi shiru kafin ta ce "shi kenan Anty Hanan, zan bata haƙuri yau ɗin nan"

"Yawwa ƴar albarka, ko ke fa"

Nabeela ta ce "ni kuma fa? "

"Ke ma ai ƴar albarka ce ƙanwata"

Sannan suka rungume ta suna dariya kafin suka tashi suka bar ɗakin, sai ga Yasmin ta shigo

"Yasmin ƙaraso mana, me kike nema? "Hanan ta tambaye ta

"Wurinki na zo Anty"

"Ina jinki to"

"Dan Allah Anty ki yi haƙuri abunda na miki a bay... "

"Haba Yasmin, me kika mun to? Kin ga ni kar ki sake mun irin wannan maganar, ba abunda kika mun kinji ko"

Murmushin farin ciki tayi, ta rungume ta ta ce "nagode Antynmu, Allah ya bar ki da Big bross har abada"

Murmushi tayi ita ma ta ce "thank u sisto"

"Bari in je in dawo sai muyi labari, Big bross na kira na"

"To ina jiranki"

Yasmin ta fita sai murna take yi, kai tsaye ɗakin Arshad ta wuce, Ya Nabeel ta gani, da Yasna, Siyama da Nabeela, sai ta ƙarasa ciki ta zauna ta ce "big bross gani"

"Yawwa... Kun san me, sai yanzu na sake tabbatar da na girma sosai fa, wai ni ke da waɗannan sisters ɗin" ya faɗa yana murmushi 

Ya Nabeel yayi tsaki ya ce "Allah ya shirye ka, sai kayi sauri kayi aure to kafin su riga ka kuma"

"Haba dai, impossible ai, ni da aure na yau ko gobe ne fa"

Nabeela ta ce "yau ko gobe kuma Ya Arshad? Ba mu shirya ba fa"

Ya Nabeel ya ce "to uwar biki, yi sauri ki shirya"

Dariya suka yi, Yasmin ta ce "yana nufin an kusa yi ne"

"Oh, na gane to"

Ya Nabeel ya ce "malam ka gaya musu abunda zaka gaya musu ni dai, ina da magana da kai"

"To babban yaya, na ji, ka san Allah ya azurta ni ne da ƙanne kyawawa dole kowa sai ya biyo ta wuri na..... Um, kuna ji, samari suka same ni ɗaya bayan ɗaya suka gaya mun abunda ke ransu akan ku,  cewar su na sonku, sai dai na gaya musu ko da kun amince, sai kun gama makaranta sannan zan aurar da ku, kuma sun amince, yanzu saura amincewarku, na ba su numbobinku, zasu kira ku, Yasmin Dr Yusuf zai kira ki, in kina sonshi shikenan, in kuma ba kya sonshi ba matsala dama na gaya musu ba wanda zan ma dole, Nabeela, Umar abokin Jafar zai kira ki kema, ke kuma Siyama Jafar zai neme ki, sai ke fitinatu, Yasna Sajjad, mutuminki ne dama"

Gaba ɗaya su ba wanda ya ce komai, Ya Nabeel ya ce "um, wai zaka aurar da su, shirme kawai.... To ku sai ku tashi ku tafi"

Suka miƙe suka fita ba tare da sun ce mishi komai ba, Ya Nabeel ya ce " Sajjad na parlour yana jira mu je mu ƙarasa shirya abunda ya rage"

"To shikenan " yana gama faɗar haka, suka tashi suka fita

A ɓangaren matan kuwa, ƙirjin biki kenan, shirye-shirye suke tayi kaman ba gobe, duk wani events da za suyi sun shirya mishi, tun daga kan bridal shower, fulani's day, wushe-wushe da arabian night sun fitar da kayan da za su saka na ko wane event, Farha, Yuhanees, Yasmin Nabeela, Siyama da Yasna, haka ma iyayensu sun shirya ma bikin, Ammi kuwa duk wani gyara da amarya ke buƙata ba wanda ba tayi ma Hanan ba, daga garuruwa daban-daban ta sa aka turo mata da kayayyaki tayi ta ba Hanan, kuma a kwanakin nan goma da suka rage ta hana ta haɗuwa da Arshad, saboda so take ranar da zai ganta ya sha mamaki, tayi ɓulɓul da ita, sai sheƙi take yi, tayi wani masifar kyau, masha Allah, yanzu kam lokaci kawai suke jira ..............




🥰 UMMEETA🥰.....📝📝📝

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA* 

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA*

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

         _A Hot Love Story_
            🥰🥰🥰

         Created And Written
                 _BY_ 
       🥰UMMEETA🥰.

*🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~

   Wannan littafin ƙirƙirarshi nayi,idan yayi dai-dai da rayuwar wani ko wata, a mun uzuri akasi aka samu👏👏👏

 *PAGE 47* 

 *THE END* 

A kwana a tashi, yau za'a fara event ta ko wane ɓangare, ɓangaren su Hanan da Bilkisu, tare za'a yi komai a hall ɗaya, an fara da bridal shower, amaren sun saka wani material gown peach colour da ɗan kwali milk, su Farha da Yuhanees da sauran ƙawayensu su ma gown ɗin ne amma milk colour da ɗan kwalinsu peach, hall ɗin ma ya sha decoration sosai peach and milk

Tun ƙarfe biyu suke abu ɗaya sai kusan magrib suka koma gida, abun ba'a cewa komai, da daddare Yasmin ta tura ma Arshad hotunan da suka yi kasancewar sun tafi Kaduna shi da Sajjad da Jafar, ya fi minti goma yana kallon kyakkyawar amaryarshi dan ta sha kyau 

Ƙarfe goma ya kira ta, lokacin suna ɗaki da su Farha da Yuhanees, sai ta koma gefe ta ɗauki wayar suna ta fira har kusan karfe goma sha ɗaya kafin suka kashe, ta shiga tayi wanka sannan ta kwanta 

Washe gari ma suka tashi suka fara shirye-shiryen fulani's day, shigar fulani suka yi gaba ɗayan su gwanin burgewa, wannan ma kusan wuni suka yi suna bikin kafin suka gama, sannan yau ma da daddare Yasmin ta sake tura mishi hotunan da suka yi

Haka suka yi ta shagalin biki ba kama hannun yaro, sai da za'a yi arabian night su Arshad suka dawo, da su akayi wannan bikin, mata suka saka jallabiya baƙi suka yi rolling, mazan kuma jallabiya n da suka yi order daga saudiyya suka saka, jallabiyan fari ne an mishi wasu desugn daga sama da baƙin zare, sai suka sa rawani a kansu suka ɗora makawiya, shigar ta fito da su sak kamar larabawa, ba mazan ba, ba matan ba ko wanensu kamar ka sace shi ka gudu

Ranar da za'ayi wushe-wushe kuwa, Maiduguri suka koma, flight suka bi, kwanan su biyu a can suna biki kafin sauran mutanen suka dawo Adamawa aka bar Hanan, Farha, Yuhanees, Yasmin da Nabeela, sai ranar da aka ɗaura aure sannan za su dawo tare da amarya

Yau ranar Jumma'a 23/3/2018,da misalin ƙarfe biyu na rana, a garim Maiduguri aka ɗaura auren ARSHAD AHMAD JALAL da HANAN ABDUL-AZIZ, dai-dai wannan lokacin kuma, a garin Adamawa aka ɗaura auren NABEEL YUSUF ALIYU da BILKISU MUKHTAR TURAKI, ɗaruruwan mutane ne suka shaida waɗannan ɗaurin auren, musamman wanda aka yi a Maiduguri  kasancewar har da abokanan kasuwancin Arshad daga garuruwa da ƙasashe daban-daban 

Da yamma mutanen Maiduguri suka biyo jirgi zuwa Adamawa, da daddare bayan sallar isha'i aka yi gagarumar walima zuwa ƙarfe tara sannan suka koma gida

Tara da rabi kuwa aka je ɗauko amarya Bilkisu zuwa gidan mijinta, aka yi musu fatan alkhairi kafin kowa ya wuce gida

Washe gari da safe suka shirya zuwa Kaduna, da yamma aka yi haɗaɗɗiyar liyafar da abokanan Arshad suka haɗa mishi sai bayan magrib suka gama, ba laifi su ma abokanan shi sun zuba naira, sannan ko wanensu ya bi su da gift, abu sai son barka

Da misalin ƙarfe tara, aka kai amarya Hanan katafaren gidan mijinta, ba ƙananan kuɗi Arshad ya zuba a gidan nan ba, sun sha royal funitures na gani na faɗa, duk wanda ya shiga sai ya fita yana yabon kyaun da gidan yayi, sai kusan ƙarfe goma sannan suka wuce suka bar amarya da angonta

Lulluɓe take cikin mayafinta, ya hau gadon ya zauna, zuciyarshi fal da murna, ya ce "amarya" ko ɗaga kai bata yi ta kalle shi ba, ya sake kiranta "amarya da ke nake magana fa"

Ganin yanzu ma ba ta da niyan ɗagowa ta sa shi ɗaga mayafinta, kuka ya ga tana yi, abunda ya ba shi mamaki kenan, ya fe "ke lafiya? Menene? "

Girgiza mishi kai tayi alamar ba komai, ya ce "ban yarda ba, ba kya so na ne? "

Da sauri ta sake girgiza kanta, ya ce "gidan bai miki bane?" nan ma dai girgiza kai tayi tana share hawaye, ya ce "to menene? Ki daina kukan nan pls, i hate it "

Cikin salon shagwaɓa, ta ce "Ummi na"

Ba ƙaramin dariya ta ba shi ba yanayin yanda tayi maganar, ya ce "wurinta kike son zuwa? "

Ta ɗaga mishi kai, yayi murmushi ya ce "to ke da kika yi shekara da shekaru kina kallonta shi ne yau zaki yi kuka dan kin zo wuri na?"

"To wa ya gaya maka ana gajiya da mahaifiya" ta faɗa tana turo baki

"Rufa mun asiri ba abunda nake bufi ba kenan Hajiya, to wai ni ba ki ga kin raba ni da Ammi na ba ne? Amma ai banyi kuka ba"

"Kai fa kullum zaka iya zuwa ka ganta, amma ji kuma fa?"

"Ke ma kusan kullum zaki iya zuwa ki ganta ai, ba nisa fa daga nan, sai ki je ki gan su.... Kuma ma kukan me kike yi, ynx ni ne Umminki ni je Siyama ni ne kowa naki Hanan, zan kasance tare da ke har abadazan kula da ke fiye da yanda zan kula da kai na,  i will always support you Mrs AAJ"
A hankali ya cigaba da gaya mata kalamai masu daɗi, sai da ya tabbatar ta daina kuka tayi dariya sannan ya sa taje tayi alwala sika yi sallah suka gode ma Allah sannan suka yi ma kansu addu'ar zaman lafiya mai ɗorewa, kafin ya dafa kanta ya mata addu'o'i sosai, sannan suka kwanta....

Sau kusan ƙarfe goma na safe aka aiko musu da abinci daga gida, lokacin ma har sun daɗe da yin braekfast, suka aje sai sha biyu sannan suka ci, da rana sai ga su Yasna sun zo gidan, a nan suka wuni sai dare suka koma gida, haka suka jera kwana uku kullum sai sunzo gidan, kafin a rana ta huɗu suka fara shirin komawa Adamawa saboda jibi za su koma makaranta, ranar da za su wuce sai da su Yasmin suka yi kukan rabuwa da Nabeela saboda a kwanakin da suka yi komai tare suke yi sao suke jin ba daɗi amma dole suka haƙura ko saboda makaranta, Siyama kuma Arshad ya dawo da ita makarantar su Yasmin suka ci gaba da zuwa tare tunda gaba ɗayansu SS3 suke yanzu

Rayuwar auren AAJ da Mrs AAJ abun burgewa ne, so, ƙauna, kulawa sa tausayi shi ne a tsakaninsu tsawon sati biyu, kullum soyayyarsu ƙaruwa take yi

Tun lokacin da su Farha da Yuhanees suka bar gidan bayan kai amarya da kwana uku, ba su koma gidan ba sai yau, suka yi sa'a kuwa Arshad ya fita, suka zauna a parlourn ta sai fira suke tayi, dan yanzu Farha ta gama sakin jiki da su, bata da wasu ƙawaye idan ba su ba, su ma ba su nuna mata banbanci a tsakaninsu

Yuhanees ta ce "Hmm wai kun san me?"

"sai kin faɗa" cewar Hanan 

"Ogan wurin aikinmu ne ya zo mun da zancen soyayya tun bayan bikinku, amma ni har yanzu na kasa ce mishi komai"

Farha ta ce "to meyasa? "

"Kawai dai"

Hanan ta ce "in dai kina sonshi Rabin rai meye kuma abun jan class kawai ki amince mu sha biki"

Dariya tayi ta ce "to naji Matar AAJ, amma fa sai an ja class ɗin nan"

Suka yi dariya baki ɗaya, Hanan ta ce "to kar dai ya tsinke.... Farha ke fa?  Ni fa na gaji da ganinku a haka"

Farha ta ce "iyeee, me Arshad ɗin ke baki ne da har cikin sati biyu kika san daɗin aure haka? "

" ke dai kawai ayi sha'ani... Gaya mun waye? "

Dariya tayi kafin ta ce "nikam na daɗe ina shan love da sweety na, Insp. Ameer"

Yuhanees ta ce "yayi kyau matar inspector"

Dariya suka sake yi, Hanan ta ce "to Allah ya tabbatar da alkhairi "

Suka amsa da ameen kafin suka ci gaba da hurarsu, sai bayan magrib sannan suka wuce gida

Haka rayuwar ke ta tafiya gwanin sha'awa, soyayyar Yuhanees da Oganta Samir yayi ƙarfi har an kai maganar aurensu nan da wata biyu, haka ma Farha da Ameer, sai dai nata auren nan da wata ɗaya ne

A kwana a tashi ha wuya a wurin ubangiji, sati ɗaya aka buge ana suan bikin Farha da Ameer, bayan wata ɗaya aka yi na Yuhanees da Samir, sai dai a wannan bikin Hanan ba tayi yanda ta so ba kasancewar laulayim da take tama da shi, duk wanda ya kalle ta sai ya tausaya mata, da ƙyar dai aka gama bikin ta dawo jinyar kanta, Arshad ji yake kaman ciwon a jikinshi yaje, dan gaba ɗaya ya yafe zuwa company sai in har ana buƙatarshi dole sannan yake zuwa, bai daɗewa kuma sai ya dawo

Haka suka ci gaba da rainon cikin jar ya kai wata tara, Hanan ta haifo ƴarta kyakkyawa kaman iyayen nata son kowa ƙin wanda ya rasa, murna kuwa a wurin su ba ya misaltuwa, tin daga ranar da aka haifi jaririyar ake ɓannar kuɗi sai kace ba sa so, abun ma ya sama kamar da gasa a ciki, har zuwa ranar da aka yi suna, aka sa ma yarinya sunan Ammi kamar yanda Hanan buƙata, sai dai suna kiranta da IBTISAM, ranar da Ibti ta cika sati uku, da haihuwa, Bilkisu ta suntulo ɗanta kyakkyawa, aka sa mishi Muhammad Ashraf, shi ma an kashe naira sosai

 *Bayan shekara ɗaya*

Biki ne ake ta sha a wannan gidan kamar ba gobe, sai hidima ake tayi, ana kai wa ana kawo wa, aure ne na gani na faɗa, auren mutum huɗu, Yasmin da Yusuf, Nabeela da Umar, Siyama da Jafar sai kuma Yasna da Sajjad

Ba abunda zai burge ka irin tanda Arshad da Hanan suka fi kowa jigatuwa a wurin bikin nan, saboda sun kasance ƙirjin biki, ko ina da ruwansu musamman Arshad , shiyasa ba su da natsuwa, Ibtisam ma wurin Hajjo aka kai ta da take fama da ciwon ƙafa, ta ce ba abunda zai sa ta wahalar da kanta, a kyale ta ta zauna wuri ɗaya kawai ta huta 

An sha bikinsu cikin annashuwa da kwanciyar hankali, a lokacin kuwa Farha da Yuhanees suna fama da ciki 

An kai Siyama  garin Adamawa, kasancewar a nan Jafar yake aikin shi a wani private hospital, Yasmin kuwa Abuja dan Dr Yusuf ya koma can shi da iyayenshi, Yasna da Nabeela kuwa suna nan Kaduna, sai dai muyu musu fatan zaman lafiya na har abada

 *Bayan shekaru uku*

Abubuwa daban daban sun faru masu daɗi da mara daɗi, dan Allah ya ma Hajjo cikawa, sannan kap ɗinsu na wanda baida ɗa ko ƴa a hannu, hankali  ya ƙara shigarsu, sai dai Yasna d wani lokacin yarintarta tan motsa mata, wataƙila kuma dan ita kaɗai ce ke tare da Amminta da Yayanta, oho! 

Arshad kuwa ya gina ma Hanan katafaren mall mai suna MRS AAJ SHOPPING MALL, sannan ya sake bunƙasa store ɗin ABMAD, haka kuma ya sake buɗe wani branch na AAJ IMPORT AND EXPORT CO. LIMITED, arziki sai shigo su yake ta kowa ne ɓangare, haka ma Ibtisam ta fara zuwa makaranta, rayuwar ko wane ɓangare sai dai a ce Masha Allah, Allah ya ƙara musu so da ƙaunar junansu Allah ya ƙara arziki........






ALHAMDULILLAHI, ANAN NA KAWO KARSHEN LITTAFINA NA ZUCIYA ƊAYA, INA ROKON ALLAH YA YAFE MANA A DUK WURIN DA NA YI KUSKURE, NI DA NA RUBUTA DA KUMA WAƊANDA SUKA KARANTA, DUK WANDA KUMA NA ƁATA MA RAI, INA NEMAN AFUWARSA, BANYI DAN CIN ZARAFIN KOWA BA, INA FATAN KUN ILIMANTU KUMA KUN NISHADANTU DA ABUNDA KUKA KARANTA

ALLAH YA BAMU IKON BAUTA MISHI A CIKIN WANNAN WATAN NA RAMADAN DA ZAMU SHIGA, ALLAH YA KARBI IBADUNMU BAKI ƊAYA, INA MUKU FATAN ALKHAIRI 🥰😘

MU HAƊU DA KU BAYAN SALLAH IDAN ALLAH YA KAIMU A CIKIN SABON LITTAFINA, MAI SABON SALO, WATO *ƳAR SENATOR*💫🤍

TAKU HAR KULLUM
    *UMMEETA* 🥰🥰🥰





🥰 UMMEETA🥰.....📝📝📝

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

        *ZUCIYA ƊAYA* 

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

Post a Comment

0 Comments