*⚖️AYI MIN ADALCI⚖️*
*Story and writing*
Hussein Yusuf
*King and Queen Writing Chamber*
https://chat.whatsapp.com/JYf24KycEteGEsafaDOMJU
_Bismillahir rahamanir rahim_
*Page 1&2*
__"You're under arrest" ita ce kalmar da ta fito daga bakin wani ɗan'sanda, yayin da yake nunawa wani kyakkyawan matashi ankwa. Tsaye matashin saurayin yayi da mamaki a fuskarsa ya kalli ɗan'sandan ya ce "Yallaɓai me na yi kuma zaku zo ku kama ni?"
"Ok! Kai ba ka san ma laifin da ka aikata ba ko?" mamaki ne ya ƙara rufe matashin ya dubi ɗan'sandan ya ce "Wallahi yallaɓai ban san me na aikata ba, ya kamata ka saurare ni....."
Kallon wajen ƙofa ɗan'sandan yayi da ƙarfi ya ƙwala kira "Sajan ku shigo ku kama shi" nan take kuwa wasu ƴan'sandan wajen su biyar suka shigo cikin gidan, da ƙarfin tsiya suka tusa ƙeyar matashin suka tafi da shi.
Sai faman tambayarsu yake yi akan me za su kama shi, bayan bai san laifin da ya aikata ba. Kallon wani ɗan'sanda yayi wanda yake tsaye a waje ɗaya ya ce "Don Allah yallaɓai ku daure ku faɗa min laifin da na yi muku."
Haɗe fuska ɗan'sandan yayi, ya dubi matashin kafin ya daka masa tsawa "Ko ba kaine FAISAL ba?" Da sauri kuwa ya ce "Ni ne yallaɓai" b'ata rai ɗan'sandan ya sake yi kafin ya dubi Faisal ya ce "Muna zarginka da kashe uban gidanka Alhaji Hashim mai Dala."
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abin da ya fara fitowa daga bakin Faisal, duban ɗan'sandan yayi ya ce "Wallahi yallaɓai ni ban san ma ya mutu ba sai yanzu da na ji daga bakink....."
"Rufe mini baki, munafukin banza da wofi." Ɗan'sandan ya faɗa a fusace yana kallon Faisal da har ya fara zubar da hawaye a kan kyakkyawar fuskarsa idanunsa sun kaɗa sun yi ja wur kamar gauta.
"To idan ba kaine ka kashe Alhaji Hashim ba wanene? Domin matarsa ta shaida mana kai ne mutum na ƙarshe da yayi magana da shi." Kuka Faisal ya fashe da shi "Allah sarki Alhaji mutumin kirki Allah ya ji ƙanka yayi maka rahama ya gafarta maka zunubanka."
Shine abin da Faisal ya rinƙa faɗa. Wanda hakan ba ƙaramin fusata ƴan'sandan yayi ba, wani kurtun ɗan'sanda ne ya dube shi ya kifa masa wani irin mari, saboda ƙarfin marin har taurarin wuya sai da Faisal ya gani a cikin idanunsa.
Danshi Faisal ya ji a bakinsa, da sauri ya kai hannunsa bakin nasa aikuwa sai ya shafo jini, kuka ya saka yana ce wa "Wallahi ba ni ne na kashe Alhaji ba sharri ne aka yi min."
Babu wanda ya saurare shi a cikinsu, sai ma kama shi da suka yi suka ɗaga shi sama suka wurga shi cikin motar tasu. Kamar yadda ake wurga jaki a cikin mota idan za'a kai su kudancin Najeriya a siyar. Faisal kuwa ji yayi kamar ƙashin bayansa zai karye, saboda buguwar da yayi.
Nan take kuwa suka tayar da motar suka nufi division ɗinsu da shi. Nan take kuwa mutanen da abun ya faru a gaban idonsu, suka hau yin kace-nace akan zancen. Wasu gani suke yi Faisal ne ya kashe uban gidansa, yayin da wasu kuma suke ganin Faisal ba zai taɓa iya aikata kisan kai ba. Sai dai masu iya magana sun ce "MUGU BA SHI DA KAMA."
_ _ _ _ *********_ _ _ _
A zaune take tana akan kujera ƴar tsugunne tana tankaɗe garin da zata yi musu tuwo da rana. A guje wani matashin saurayi ya shigo cikin gidan, yana zuwa ya zube a gaban dattijuwar matar yana mayar da numfashin gudun da ya sha.
Dakatawa ta yi da tankaɗen garin ta kalle shi kafin ta ce "Habibu lafiya kuwa na ganka a irin wannan yanayin?" Sai da ya ajiye ajiyar zuciya sannan ya dubi matar ya ce "Goggo yanzun nan ƴan'sanda suka tafi da Faisal wai ana zargin shi da kashe uban gidansa Alhaji Hashim."
Tafa hannuwa Goggo ta shiga yi tana salallami "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Kai yanzu Habibu a bakin wanne maƙaryacin ka jiyo wannan maganar?"
Ka da baki matashin yayi ya ce "Goggo a gabana fa suka tafi da shi, motarsu tana tafiya ni kuma ina ƙarasowa wajen. Shine jama'ar wajen suka shaida mini abin da yake faruwa."
Da sauri Goggo ta miƙe tsaye ta shiga cikin ɗakinta, ba jimawa ta fito da hijabi a hannunta. Duban Habibu ta yi ta ce "Yi sauri ka zo mu tafi can police station ɗin mu ji abin da yake faruwa a wajen Faisal ɗin."
Ganin yadda Goggo duk ta bi ta gigice ne ya saka Habibu tashi da sauri ya wuce gaba Goggo kuwa da sauri ta bi shi a baya. Suna fitowa daga gidan, Goggo ta shiga gidan wata maƙofciyarsu mai suna Ladi ta ce "Idan Anwar ya dawo daga makaranta ya shigo nan gidan kafin su dawo."
Bata tsaya jin abin da Ladin take faɗa ba, ta juya da sauri ta fice daga gidan. Tana fitowa ta tarar da Habibu yana jiranta, bakin titi suka nufa. Suna zuwa kuwa suka tare wani keke napep suka hau, suka nufi can police station ɗin.
********* *********
Dukan shi suke yi kamar Allah ya aiko su, kusan kowacce gaɓa ta jikinsa sai da suka dake ta da wani ɗan ƙaramin sanda mai ƙwarin gaske. Amma duk dukan nan da Faisal yake sha a wajen ƴan'sandan nan, kalma ɗaya ce take fitowa daga bakinsa ba ni bane.....
Gaba ɗaya jikinsa duk ya ɓaci da jini babu kyawun gani. Sai numfashi yake fitarwa sama-sama, yana wani irin nishi kamar ransa zai rabu da gangar jikinsa. Amma saboda rashin imani irin na ƴan'sandan nan sun ƙi su rabu da shi, a lallai a dole sai ya amsa laifinsa, shi kuma ya dage akan ba zai taɓa amsa laifin da ba shine ya aikata ba.
Ganin ya galaɓaita sosai ne yasa suka rabu da shi. Wani kallo ɗaya daga cikinsu ya watsa masa ya ce "Kai wai dole mai taurin kai ko? To ka sani Wallahi idan muka dawo ba ka bamu amsa ba, sai mun yi maka horon da ya fi wannan wahala, sakarai kawai banza!" Suna gama faɗin haka suka fice suka bar shi a cikin wani irin yanayi.
^^^^^^^^^^^^^
Hajiya Bilkisu ce a zaune a ofishin D.P.O fuskarta a murtuƙe kamar fuskar shanu. Kallo ɗaya za ka yi mata ka gano tsantsar ɓacin rai a tattare da ita, kallon D.P.O ta yi ta ce "Gaskiya ni na gaji me yasa kuke ce wa wai lallai sai ya amsa laifinsa? Bayan akan idanuna ya caka wa mijina wuƙa nima yayi yinƙurin kashe ni Allah yasa da sauran kwana na a gaba, da tuni nima an binne ni."
"Kiyi haƙuri Hajiya yana amsa laifinsa sai mu rubuta muku R.F.I mu tura shi kotu a yanke masa hukunci a can." Dakata D.P.O Hajiya Bilkisu ta faɗa ranta a ɓace ta kalli D.P.O ta fara magana "Gaskiya D.P.O idan har ba za ku iya ƙwatar min haƙƙina ba zan je gaba inda za'a ƙwatar min. Komai sai ku ce wai sai ya amsa laifinsa bayan dumu-dumu na kama shi da wuƙa a hannu yayin da ya gama kashe shi, nima yayo kaina Allah yasa da sauran kwana na a gaba."
"Hajiya kiyi haƙuri insha Allahu za mu yi miki yadda kike so." Shiru yayi sannan ya cigaba da ce wa "Amma Hajiya na ji kin ce kin ritsa shi da wuƙa a hannu lokacin da ya kashe Alhaji, Amma me yasa da muka je ba mu ga wuƙar ba?"
Gyara zama Hajiya Bilkisu ta yi ta ce "Wataƙila ku ne ba ku kula ba, amma tabbas wuƙar tana ajiye a falonsa. Ni tun da aka fito da shi ma aka kai shi asibiti na kulle falon ban ƙara shiga ba." Da sauri D.P.O ya ce "Yanzu Hajiya kin tabbatar idan muka je zamu samu wuƙar a can?"
"Of course yallaɓai. Na tabbata idan kun je zaku ga wuƙar indai ba'a ɗauke ta ba."
"Ok kina nufin akwai wanda zai iya zuwa ya ɗauke ta kafin mu je?" D.P.O ya tambaya yana kallon Hajiya Bilkisu.
Yatsina fuska ta yi sannan ta ce "Ni gaskiya babu wanda na ke zargin zai ɗauke ta amma ka san shi Faisal ɗin wataƙila yana da wasu yaran a can waje ɗaya, ba mamaki su iya ɗauke ta kafin ku je"
Da sauri D.P.O ya ce "Calm down Hajiya. Insha Allahu za mu gan ta ma."
Wayarsa ya ɗauko ya kira wani ɗan'sanda ya ce "Ya zo yanzu ya same shi a office yanzu." Ba' a ɗauki wasu minutes masu yawa ba sai ga wani ɗan'sanda ya shigo. Ɗaga ƙafa yayi ya sarawa D.P.O ya ce "Ga ni yallaɓai."
Kallon shi D.P.O yayi ya ce "Inspector yanzun nan zaka bi HAJIYA gidanta, domin ta nuna maka ɗakin da aka kashe Alhaji ka duba sosai ta ce wuƙar da aka aikata kisan tana cikin falon don haka yanzun nan sai ka bita. Amma fa ka tabbatar ka duba sosai, domin indai aka ga wuƙar to komai zai zo mana da sauƙi" sake sarawa ɗan'sandan yayi ya ce "Ok sir."
Kallon Hajiya Bilkisu D.P.O yayi ya ce "Hajiya zaku iya tafiya."
Miƙewa tsaye ta yi ta kalli D.P.O ta ce "Shikenan yallaɓai bari na je mu duba"
"Ok Hajiya Allah yasa mu dace."
Har ta juya za ta tafi sai kuma ta dakata ta kalli D.P.O ta ce "Amma yallaɓai yaushe zaku ba ni mijina domin ayi masa jana'iza kamar yadda ake yi wa kowanne mamaci.?"
Shafa kai D.P.O yayi ya ce "Yanzu Hajiya muna sauraron abin da likita zai faɗa mana ne, da zarar sun gama binciken su akan gawar insha Allah zuwa gobe zamu ba ku shi domin ayi masa sutura."
"Shikenan to yallaɓai bari mu je" buɗe kyauren office ɗin ta yi ta fice nan take kuwa Inspector ya bi bayanta domin ya je gidanta ya ɗauko wuƙar da aka kashe Alhaji da ita.
*:::::::::::::::::*
A firgice Goggo ta shigo cikin station ɗin fuskarta taf da hawaye. Kallo ɗaya zaka yi mata ka hango tsantsar ɓacin rai da damuwa a fuskarta. Wani ɗan'sanda ne da yake kan kanta, ya kalleta ya ce "Iya lafiya kika shigo mana a haka?"
Ka da baki Goggo ta yi ta ce "Ina lafiya yallaɓai kun kama min ɗana kun kulle, wallahi yallaɓai Faisal ba shine ya kashe Alhaji Hashimu ba sharri ne aka yi masa."
"Dakata tsohuwa kar ki yi mana zancen banza anan wajen, dumu-dumu a kama mutum kuma ki zo kina ce wa "Wai ba shine ya kashe shi ba? To idan ba shi bane sai ki fada min wanene."
"Tabbas gaskiya Goggo ta faɗa muku ba Faisal bane ya aikata wannan kisan kan ba. Saboda mu nan shaida ne FAISAL mutumin kirki ne, kuma mai tsoron Allah a duk inda ya tsinci kansa."
Hararar shi ɗan'sandan yayi ya ce "Kai kuma wanene da zaka zo kana yi mana zancen banza anan?"
"Ni sunana Habibu kuma tare nake da Goggo, mun zo ne domin mu yi magana da Faisal."
Wani murmushi ɗan'sandan yayi ya ce "Ko kun manta laifin da ya aikata ne? To babu wanda ya isa ya gan shi, don haka ku juya ku fice daga nan kafin ranku ya ɓaci."
Wata zazzaƙar murya ce ta zo ta daki dodon kunnuwansu "Wacce doka ce ta hana a bar mutum ya ga ɗan'uwansa akan ana zargin shi da wani laifi?"
Gaba ɗayansu suka waiwaya bayansu domin su ga mai yin wannan maganar ɗan'sandan nan ne ya fusata ya dubi kyakkyawar budurwar cikin ɗaga murya ya ce "Ke kuma wacece da zaki zo kina wata magana?"
Zura hannu ta yi a cikin jakarta ta ɗauko wani I.D card ta ajiye akan kantar sannan ta ce "Sunana BARRISTER SHAHEEDAH (Littafin AYUSH ABDULLAH)............"
✍️
_*To be continue......*_
_More comment more typing_
Ina son na ga ruwan comment domin shine ƙarfin gwiwar kowanne marubuci, don haka ku nuna min yadda littafin ya karɓu a wajenku ta hanyar comment nagode.
_*HUSSAIN*_
07069475482
*King and Queen Writing Chamber*
*⚖️ AYI MIN ADALCI⚖️*
*Story and writing*
Hussein Yusuf
*King and Queen Writing Chamber*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*Page 3&4*
Kallonta ɗan'sandan yayi ya ce "Sorry Madam ban san ke ba ce shi yasa...."
"Dakata Malam wallahi kai dai ba ka san aikinka ba, wulaƙanci da rashin mutunci ba shine zai saka ka cigaba a aiki ba. Wannan shawara ce na baka saboda gaba..."
Kallon su Goggo ta yi ta ce "Kuyi haƙuri Goggo insha Allahu yanzun nan za ku gan shi kuma ina mai tabbatar muku da cewa zai fita daga wannan sharrin da aka yi masa."
Da sauri Goggo ta ce "Allah yasa yarinya mun gode sosai."
Sake kallon ɗan'sandan Barrister Shaheedah ta yi ta ce "D.P.O yana ciki?"
Da sauri ya ɗaga mata kai kamar ƙadangare, duk kunya ta bi ta kama shi kamar ya nutse a wajen haka yake ji.
Sake tambayarsa ta yi nan ma da sauri ya ce "E, Madam yana ciki."
Murmushi Shaheedah ta yi sannan ta dubi su Goggo da Habibu ta ce "Su biyo ta a baya" da sauri kuwa suka bi bayanta.
Suna isa ƙofar office ɗin Barrister Shaheedah ta kama handle ɗin ƙofar za ta buɗe kafin ta murɗa ƙofar ta ga an buɗe. Hajiya Bilkisu ce ta fito, kallon-kallo aka shiga yi tsakaninta da Barrister Shaheedah.
"Mtssssss!" Hajiya Bilkisu ta ja wani dogon tsaki sannan ta dubi *Barrister Shaheedah* ta ce "Ke nan yarinya da ke zaki ɗebo wasu shegun ƙafafunki, ki taho wai ke lauya za ki kare wani banza ko?" To bari ki ji "Wallahi summa tallahi ko ke ce shugabar lauyoyin duniyar nan ba ki isa ki fitar da Faisal daga tarkona ba. Sannan ina ƙara tabbatar miki a gaban idonki za'a yankewa Faisal hukunci dai-dai da abin da ya aikata."
Sannan ta mayar da kallonta wajen Goggo ta ce "Ke kuma tsofai-tsofai da ke zaki wani taho ganin wani banza wanda a banza ku ka gan shi, wai ku masu tausayi ku ka dauke shi a matsayin ɗa ko? To bari in tabbatar miki wallahi TSINTACCIYAR MAGE BATA MAGE tun wuri ina baki shawara da ki rabu da Faisal, ɗansa ma da yake hannunki ki je can wani wajen ki jefar da shi kafin wani ya sam....."
"Ke dalla rufe mana baki shashasha kawai" da sauri Barrister Shaheedah ta ce "Me yasa ka tanka mata? Ai da ka bari ta ƙarasa faɗin abin da yake bakinta. Ka san idan kare yana haushi duk wanda ya kula shi akansa yake hucewa don haka ni ban ga abin tsayawa ina cacar baki da wannan abun ba mtssssss!" Ta ja wani tsaki tare da tsartar da miyau da sauri ta buɗe ƙyauren ƙofar ta shiga da sauri kuwa Goggo ta bi bayanta sai da Habibu ya watsa mata wani banzan kallo sannan shi ma yayi shigewarsa ciki.
A tsaye suka shiga suka bar Hajiya Bilkisu tana ta faman cizon leɓenta. Tun da take a duniyar nan babu wani mahaluƙi da ya taɓa yi mata kwatankwacin wannan wulakancin da Barrister Shaheedah ta yi mata.
"Gaskiya ya zamar mini dole na dakatar da wannan yarinyar da shiga abin da babu ruwanta. Idan har na yi sake wallahi wannan ƙaramar za ta watsa mini shiri na, kuma ta tona min asiri a idon duniya."
"Don haka ya zamo min dole na fara sanin wacece ita waccan yarinyar kafin na san abin da zan aiwatar akan ta."
Tana gama wannan tunanin ta saki wani shu'umin murmushi sannan ta yi gaba.
A jikin motarta ta tarar da Inspector yana jiranta. Murmushi ta yi ta ce "Ka yi haƙuri Inspector na bar ka a tsaye ko?"
Shi ma murmushin yayi ya ce "Babu komai Hajiya tun da kin ƙaraso kawai mu tafi."
Da sauri direbanta ya zo ya buɗe mata gidan baya ta shiga, yayin da shi kuma Inspector ya shiga gaban motar kusa da direba kujerar me zaman banza ya zauna.
Da gudu direban ya ja motar suka bar harabar Police station ɗin.
********* **********
Yayin da Barrister Shaheedah ta shiga ofishin D.P.O tare da su Goggo da Habibu. Kallonsu D.P.O yayi kawai ya kawar da kansa, ya cigaba da abin da yake yi.
Ko kaɗan Barrister Shaheedah ba ta damu ba, sallama ta yi masa ɗagowa yayi daga duba files ɗin da yake yi ya amsa mata sallamar sannan ta tsaya yana sauraron ya ji abin da yake tafe da su.
I.D card Barrister Shaheedah ta ɗauko ta nunawa D.P.O sannan ta ce "Sunana Barrister Shaheedah ni ce lauyar Faisal wanda kuke tuhuma da laifin kisan kai."
Murmushi D.P.O din yayi kafin ya ce "Ok na gani, ku zauna mana" gaba ɗayansu suka samu waje suka zauna.
Bayan sun zauna gaba ɗayansu sai D.P.O ya kalli Barrister Shaheedah ya ce "Na ji kin gabatar min da kanki sai dai ban ji kin ce komai akan waɗannan da kike tare da su ba."
Murmushi Barrister Shaheedah ta saki ta ce "Sorry sir wallahi na sha'afa ne" sannan ta nuna Goggo ta ce "Wannan ita ce wacce take riƙe da Faisal, domin ba ita ce ta haife shi ba. Mamaki ne ya kama Goggo nan take ta hau tambayar kanta "Wai wannan yarinyar a ina ta san mu har ta san Faisal ba ɗana ba ne? Kuma shi Faisal ɗin bai taɓa yi min zancenta ba, amma dai ko wace ita da sannu zan sani insha Allahu" tunaninta ne ya yanke yayin da ta ji Barrister Shaheedah ta na gabatar da Habibu.
"Wannan kuma" ta nuna Habibu "Ɗan wannan dattijuwar matar ne, tare suke da Faisal abokai ne sosai. Sun zo ganin Faisal ne da yake wajenku."
Mamaki ne ya ƙara kama su Goggo suna mamakin inda Barrister Shaheedah ta san su haka alhalin su ba su taɓa ganin ta ba ma ballantana su shaida ta.
D.P.O ne yayi gyaran murya ya ce "Ok na fahimta, yanzu dai a iya yau zan iya ba su minti goma sha biyar su gan shi. Ke kuma zan iya baki 30 minute."
Da sauri Barrister Shaheedah ta ce "Mun gode yallaɓai."
Cigaba D.P.O yayi da cewa "Amma fa ki faɗa musu daga yau baza su sake ganin shi ba sai abin da hali yayi, sai dai ke tun da lauya ce always zaki iya ganinsa domin ki yi aikinki yadda ya kamata."
Fashewa da kuka Goggo ta yi cikin muryar kukan ta dubi D.P.O ta ce "Yallaɓai me yasa ba za ku sake barinmu mu gan shi ba?"
Cikin kwantar da murya D.P.O ya ce "Saboda yanzu nan ba da daɗewa ba case ɗinsa zai bar hannunmu, za mu miƙa shi kotu idan muka tabbatar da laifinsa da fatan kin gane?"
Ɗaga kai kawai Goggo ta yi ba don ta gamsu da bayanin D.P.O ba.
Ɗaga murya D.P.O yayi ya kira wani ɗan'sanda, da hanzarinsa kuwa ya shigo ya sara sannan ya ce "Ga ni na ji kana kirana."
Je ka da waɗannan mutanen za su yi magana da wannan criminal ɗin na cikin cell, sake sarawa yayi ya ce "Ok sir an gama." Kallon su Goggo yayi ya ce "Ku tashi mu tafi."
Bayan shi suka bi har suka je wani waje mai bala'in duhu amma daga waje akwai ɗan hasken rana da ya ratso ciki ta wata ƴar ƙaramar ƙofa. Amma cikin ɗakin da Faisal yake, ko tafin hannu ba a gani saboda tsananin duhu.
Kallon su Goggo ɗan'sandan yayi ya ce "Ku zauna anan" ya nuna musu wani benci mai kyau a ajiye ba tare da gardamar komai ba kuwa suka zauna. Suna kallo ya ɗauko wayarsa daga cikin aljihu ya kunna fitila sannan ya haska ya shiga cikin ɗakin.
A kwance ya ke, ya yi ruf da ciki ya rufe idanunsa, hawaye ne yake ta faman yawo akan kyakkyawar fuskarsa. Motsin mutum ya ji da alamun shigowa ɗakin aka yi, haske ya hango da alamun hasken fitila ne a hankali ya ga hasken yana nufo inda yake da sauri ya tashi zaune yana ihu! yana cewa "Don Allah ku yi haƙuri ku yi mini rai wallahi ba ni ne na aikata kisan ba sharri aka yi min."
Tsayawa ɗan'sandan yayi tare da haske shi da tocilan ɗin wayarsa. Cikin ɗaga murya ya ce "Kai rufe mana baki" shiru Faisal yayi yana sauraron abin da ɗan'sandan zai yi masa.
Sake haske shi ɗan'sandan yayi ya ce "Taso ka biyo ni a baya" yana faɗa masa haka ya juya ya nufi ƙofar fita. Da sauri kuwa Faisal ya tashi ya bi bayansa, da kyar yake iya ɗaga ƙafarsa da ta yi masa wani irin nauyi ji yake kamar ya faɗi amma a haka yake daurewa yana bin bayan ɗan'sandan.
A haka har ɗan'sandan ya fito daga cikin ɗakin, tsayawa yayi a ƙofa yana jiran Faisal ɗin ya ƙaraso.
Su Goggo kuwa duk sun zubawa ƙofar idanu, domin su ga FAISAL ɗin ya fito, a hankali suka ga ya fito yana taka ƙafarsa da ƙyar.
Da gudu Goggo ta je ta rungume shi tana kuka shi ma kukan ya saki, Habibu kuwa shi ma tsaye yayi yana kallonsu yana share ƙwallar da take taruwar masa a cikin idonsa.
"Kaiii! Minti goma sha biyar ne kwata-kwata da ku don haka ku yi sauri ku gama abin da ya kawo ku..."
Da sauri Goggo ta saki Faisal tana kallonsa yadda duk ya bi ya rame cikin ƙanƙanin lokaci, tausayinsa ne ya cika mata zuciya, kuka ta cigaba da yi Habibu kuwa kasa rarrashinta yayi saboda ya san kukan ne kadai zai iya rage mata raɗaɗin da zuciyarta take yi mata.
Ganin kukan ya ƙi ƙarewa ne Habibu ya dubi Faisal ya ce, "Faisal garin ya haka ya faru? Kawai muka ga ƴan'sanda sun ɗauke ka akan wai kai ne ka kashe Alhaji Hashim, ya gaskiyar maganar take?"
Fashewa da kuka Faisal yayi ya ce, "Habibu tun da nake a rayuwata zuciyata ba ta taɓa saƙa min wani mugun abu game da wani mutum ba. Ballantana har ta kai ga zuga ni akan na aikata kisan kai, Wallahi ban san wanda ya kashe Alhaji ba kawai sai na ga ƴan'sanda sun zo sun kama ni wai ana zargina da kashe Alhaji."
Shiru yayi yana ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa, "Wallahi Goggo ko da ni makashi ne Alhaji ba ya cikin waɗanda zan kashe, domin na tsani maci amana da mayauari a rayuwata, amma yau sai ga shi lokaci ɗaya rayuwa ta canja min ni ake kallo a matsayin maci amana mayaudari, ya zan yi Goggo da Habibu ku taimaka min don Allah mutane su daina kallona a haka." Yana kai wa nan a zancensa sai ya sake rushewa da wani sabon kukan, Goggo ma kuwa ita ma sai ta sake rushewa da kuka, Habibu ma duk dauriyar da yake yi sai da suka karyar mai da zuciya nan take shi ma ya fara kukan.
"Ka yi haƙuri Faisal dukkan tsanani yana tare da sauƙi, kamar yadda dukkan duhu yake tare da haske. Ka sani Allah ne ya tsara maka haka a cikin littafin kundin ƙaddararka idan ka yi haƙuri ka fawwalawa Allah komai Insha Allahu da sannu komai zai warware."
Habibu ne yake fada yayin da yake share ƙwallar da take ta faman zubo masa.
"Nagode Habibu, insha Allahu zan zamo mai yin haƙuri a duk halin da na tsinci kain....." Bai ƙarasa faɗa ba kuka ya ci ƙarfinsa shiru suka yi gaba ɗaya suna sauraron sautin kukansa Goggo kuwa zuwa wannan lokacin zuciyarta ta bushe kukan ma ya ƙi zuwa ballantana ta yi ta ji sauƙi a cikin ranta.
Sai da Faisal yayi kuka sosai sannan yayi shiru yana ajiyar zuciya. Duban shi Goggo ta yi ta ce, "Faisal kalmar dai da Habibu ya faɗa maka ni ma ita zan ƙara jaddada maka. Ka kasance mai haƙuri kuma ina son ka saka a cikin ranka cewa babu wanda ya isa yayi maka abun da Allah bai tsara maka a cikin littafin rayuwarka ba. Ka saka a ranka cewa duk abin da ya same ka dama can ya kasance zai same ka, haka kuma duk abin da ba ka samu ba dama can ba rabonka bane. Sannan ko da duk mutanen duniyar nan za su taru akan su cutar da kai ba za su taɓa samun nasara akan ka ba, matuƙar Allah bai tsara za su cutar da kai ba, haka kuma ko da dukkan mutanen duniyar nan za su haɗu akan su cire ka daga wannan ƙaddarar da ta afko maka matuƙar Allah bai tsara maka haka a cikin kundin ƙaddarar ka ba, ba su isa su fitar da kai ba."
"Wannan faɗin Annabinmu Muhammad (S.A.W) ne, don haka Faisal ka rinƙa yawan addu'a kana neman yawan ambaton Allah kar ka manta da wannan Faisal insha Allahu zaka fita daga wannan wahal....."
Tana kai wa nan kuka ya ƙwace mata ɗan'sandan da yake kula da su ne yayi gyaran murya ya ce, "Lokacinku ya cika don haka ku tashi mu tafi" kallonshi Goggo ta yi ta ce, "Don Allah ka yi mana haƙuri ka ji."
Tausayin Goggo ne ya kama shi jikinsa yayi sanyi cikin sanyin murya ya dubi Goggo ya ce, "Iya ki yi haƙuri lokacin da D.P.O ya ɗeba muku kenan, nima umarni aka ba ni idan lokacin ya cika na sallame ku."
"Shike nan yallaɓai mun gode Allah ya saka da alkhairi da kuka bar mu, muka gan shi ma."
Tashi suka yi za su tafi sai a wannan lokacin Faisal ya ji wani kuka ya zo masa, babu shiri kuwa ya shiga yin abinsa. Cikin muryar kuka ya dubi Goggo ya ce "Don Allah Goggo ki kula min da Ammar, ki ba shi kulawa sosai. Sannan duk lokacin da ya tambaye ki inda na tafi ki ce masa na kusa dawowa."
Yana gama faɗin haka ɗan'sandan bai bar shi ya ji amsar da Goggo za ta ba shi ba, ya ja shi ya mayar da shi cikin ɗakin duhun nan da yake shi kaɗai a ciki.
Fashewa da kuka Goggo ta yi wata sabuwar soyayya da tausayin Faisal ne yake ƙara yin yabanya a cikin zuciyarta.....
Bayan ɗan'sandan ya rufe Faisal sai ya juyo ya nufi hanyar fita, tare da yi wa su Goggo alama su biyo shi. Bin shi suka yi a baya har suka isa ofishin D.P.O.
Sarawa ɗan'sandan yayi ya ce, "Sir sun gama tattaunawa" kallon su Goggo D.P.O yayi ya ce, "Ok za ku iya tafiya."
"To yallaɓai mun gode" Goggo ta faɗa tana ɗan rusunawa D.P.O kallonta ya sake yi ya ce, "Babu matsala ku je kawai."
Kallon Barrister Shaheedah Goggo ta yi ta ce, "Ranki ya daɗe ko mu jira ki ne?"
Murmushi Barrister Shaheedah ta yi ta ce, "No Goggo ku yi tafiyarku kawai don ni daga nan ma ba gida zan nufa ba, akwai wata mata da ta kira ni na je na bata shawara wai akan mijinta zai ƙara aure. So don haka kawai ku yi tafiyarku."
Godiya suka ƙara yi mata sannan suka juya suka tafi.
Bayan fitar su Goggo D.P.O ya kalli Barrister Shaheedah ya ce, "Barrister za ki iya zuwa wancan ofishin ki jira sai a kawo miki shi Faisal ɗin amma fa ki sani mintuna 30 kaɗai ki ke da shi."
Godiya Barrister Shaheedah ta yi wa D.P.O sannan ta miƙe ta nufi cikin office ɗin da D.P.O ya nuna mata domin ta jira a kawo mata Faisal ta fara aikinta................
_To be continue....._
Typing da wahala ku dai ku rinka yi min comment domin shine karfin gwiwata...
_*HUSSAIN*_
07069475482
*King and Queen Writing Chamber*
*⚖️AYI MIN ADALCI⚖️*
*Story and writing*
Hussein Yusuf
*King and Queen Writing Chamber*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*Page 5&6*
_A zaune Barrister Shaheedah take a cikin office ɗin, sai faman danna wayarta take yi, da alamu saƙonni take gani, saboda sai faman murmushi take yi.
Ba ta jima a zaune ba wani police ya shigo da Faisal, nuna masa kujerar da take facing ɗinta ta yi da wani tebur a tsakiyarsu ta ce, "Ya zauna" Babu musu kuwa Faisal ya zauna yana kallonta.
Kallon Police ɗin da ya kawo shi ta yi ta ce, "Yallaɓai don Allah ɗan ba mu wuri zamu yi magana." Babu musu kuwa ya fita ya tsaya a waje kafin ta gama ya mayar da Faisal ɗin inda ya ɗauko shi.
Faisal kuwa sai faman kallon fuskar Shaheedah ya ke, ƙoƙarin tuno inda ya taɓa ganin wannan kyakkyawar fuskar ya ke amma ƙwaƙwalwarsa ta ƙi ta ba shi haɗin kai.
Da Barrister Shaheedah ta ga sai faman kallonta yake sai ta saki wani murmushi ta ce, "Kar ka damu Faisal zuwa na yi domin na wanke ka daga wannan zargin da ake yi maka amma fa sai ka ba ni haɗin kai sannan zan san ta inda zan fara."
Murtuƙe fuska yayi kamar an aiko masa da saƙon mutuwa, kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya buɗi bakinsa da kyar ya ce, "Kin ga da kin yi haƙuri kin yi tafiyarki kin rabu da ni, domin wahalar da kanki zaki yi a banza, Hajiya Bilkisu ba za ta taɓa barin ki ki fitar da ni ba."
Miƙewa tsaye Barrister Shaheedah ta yi ta yi taku kamar uku sannan ta tsaya ba ta juyo ba ta fara magana "Faisal ina son ka sani Hajiya Bilkisu ba ta isa ta hana ni taimakonka ba, muddin ina numfashi a doron ƙasa."
"Domin na daɗe ina neman hanyar da zan saka maka abin da ka yi min shekara biyu da ta wuce amma na rasa sai yanzu ne nake da cikakkiyar dama ta taimaka maka, don haka ban ga wani mahaluƙi da zai iya dakatar da ni ba."
Da mamaki Faisal ya ke kallonta kafin ya ce, "Dama kin san ni ne? Kuma wanne taimako na taɓa yi miki a rayuwa da har ki ka kasa mantawa? Alhalin ni ban taɓa ganin ki ba."
Jin haka yasa Barrister Shaheedah ta dawo ta zauna ta ƙurawa Faisal manyan idanunta, shi ma ƙura mata idanunsa yayi ya kasa ɗauke idanunsa daga kanta. Kamar yadda ita ma ta ƙi ɗauke na ta.
Ajiyar zuciya ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa tana murmushi, a ɗaya ɓangaren zuciyarta kuwa mamaki ne fal a cikin ranta "Yanzu duk dakon sonsa da take yi har tsawon shekara biyu, amma shi sam ya manta da ita ma a babin rayuwarsa?"
Barrister Shaheedah ce take yin wannan tunanin a cikin ranta, ɗago da kanta ta yi ta sake zubawa Faisal idanunta.
Ta ce, "Yanzu Faisal ka manta shekara biyu da suka wuce, kana tafiya a gefen hanya, ka jiyo ihun wata yarinya a cikin wani kango wasu samari suna ƙokarin yi mata fyaɗe? Ka zo ka yi amfani da ƙarfin da Allah ya baka ka ceceta?"
Nan take kuwa ƙwaƙwalwar Faisal, ta hau yi masa remembering ɗin abin da ya faru lokacin. Ba zai taɓa mantawa ba, wata rana yana sana'arsa ta sayar da rake lungu-lungu da saƙo-saƙo yake shiga domin samun ciniki.
Wata rana wajen doshin la'asar ya biyo ta wata unguwa, kowanne layi idan ka bi a unguwar shiru babu mutane. Sai faman kira yake a sai rake, wani lungu ya biyo, tun daga bakin lungun yake jiyo ihu kamar na mace. Shiru yayi ya tsaya yana sauraro ko zai sake jin muryar "Don Allah ku yi haƙuri kar ku keta min haddina, ku taimake ni don Allah." Ita ce muryar da ta zo ta doki dodon kunnensa, nan take kuwa ya tura wheel barrow ɗin raken na shi cikin wani lungu, kai tsaye ya nufi inda yake jiyo muryar yarinyar tana roƙon ƴan daban akan su ƙyaleta.
Cikin sanɗa ya rinƙa tafiya yana nufar lungun, wani karyayyen katako ya ci karo da shi. Murmushin farin ciki yayi, a hankali ya sunkuya ya ɗauke shi, cike da ƙwarin gwiwa ya nufi cikin kangon.
"Ba ke ba wai lauya me kare haƙƙin talakawa? To daga yau sai mu sake ganin wanda za ki kare, ai indai muna raye ba ki isa ki yi sanadiyyar ɗaure mai gidanmu ba, Alhaji Lauwali. Saboda haka yanzun nan za mu keta miki haddi, sa'annan mu kashe ki, mu jefar da gawar ki a can gefen titi, idan ya so sai ki je can lahirar ki yi lauyancin." Irin wannan zancen Faisal ya rinka ji, nan take kuwa ransa ta ɓaci. Shawara yake yi da zuciyarsa akan ya shiga ko ya juya yayi tafiyarsa.? Ya daɗe a tsaye a wajen zuciyarsa ta kasa yanke masa hukuncin da ya dace.
"Ka shiga wataƙila Allah ne ya biyo da kai ta nan domin ka yi ceton rai." Har ya yunƙura zai shiga cikin kangon, sai wani ɓangaren na zuciyarsa ya gargaɗe shi "Kul ! kada ka kuskura ka kutsa kanka ciki, ba ka san su ba kuma ba ka san adadin yawansu ba. Wataƙila sun fi ƙarfinka ajaline ko kuma tsautsayi yake kiranka, don haka kawai ka yi tafiyarka hankalinka kwance."
Har ya juya zai tafi, sai ya ji muryar shugaban ƴan daban yana cewa "JAGWA ki riƙe min ita, ni ne zan fara" ji yayi yarinyar da za su yiwa fyaɗen ta ƙwalla wata ƙara mai ƙarfin gaske. Ai bai tsaya shawara da zuciyarsa ba ya kutsa kansa ciki, kamar Aljani haka ya faɗo musu ba su ankara ba.
Kafin su yi wani yunƙuri ya ɗaga katakon da ya shigo da shi, ya saukewa shugaban ƴan daban a tsakiyar kansa. Nan take kuwa ya faɗi ƙasa wanwar yana fitar da numfashi sama-sama, sauran ƴan daban ko da suka ga haka sai duk suka tarwatse kowa ya ari ƙafar kare. Domin ba ƙaramin kwarjini Faisal yayi musu ba, kallon budurwar Faisal yayi ya ce, "Yi sauri ki biyo ni mu gudu daga nan domin za su iya dawowa a kowanne lokaci."
Da sauri kuwa ta tashi ta bi bayansa, hannunta riƙe da mayafinta jikinta ban da kyarma babu abin da yake yi. Kama hannunta yayi suka nufi bakin titi, suna zuwa kuwa suka samu mai napep ya ɗauke su, ya tafi da su.
Ban da hamdala babu abin da budurwar take saukewa, lokaci-lokaci tana satar kallon fuskar Faisal. Muryar me a dai-daita sahun suka ji yana tambayar ina zai kai su, kafin Faisal yayi magana budurwar ta riga shi "Sabon gari za ka kai mu."
Kallonta Faisal yayi ya ce, "To ni ba can na nufa ba" murmushi kawai ta yi sa'annan ta ce, "Na sani ba can ka zaka je ba, kuma ba anan unguwarku take ba, ina son mu ɗan tattauna ne na san ko kai wane, da yadda aka yi ka san har inda aka sato ni ka zo ka cece ni."
Murmushin gefen baki Faisal yayi, kafin ya ce, "Sanin ko ni wane ne bai dame ki ba, kuma dalilin da yasa na zo na ceci rayuwarki, tallan rakena nake yi hanya ta biyo da ni ta wajen kangon da suka kai ki, sai zuciyata ta raya mini cewar na zo na taimaki rayuwarki."
Yana gama faɗin haka ya dakatar da mai napep ɗin, babu musu kuwa ya tsaya. Yunƙurawa Faisal yayi zai fita daga ciki, da sauri ta riƙe rigar shi ta ce, "Don Allah ka taimaka ka sanar da ni, sunanka."
Ɗan ɓata rai Faisal yayi ya ce, "Sunana Faisal" da sauri kuwa ta maimaita sunan a cikin zuciyarta "FAISAL" ba ta san har ya fito fili ba, kallonta yayi ya ce, "Ko da wani abun ne?" ganin yanda ya haɗa rai ne yasa ta ce, "A'a ba komai, amma nima ba ri na faɗa maka sunana."
Ɗan dakatawa yayi da daga fitar da yake niyyar yi, "Sunana BARRISTER SHAHEEDAH ni lauya ce, a babbar kotun Kaduna" tana gama faɗin haka kawai ya ce, "Na ji to" bai tsaya jin wani abun ba ya fice daga cikin napep ɗin yayi tafiyarsa.
Kallonshi kawai Barrister Shaheedah ta ke yi, har ya ɓacewa ganinta. Sa'annan ta umarci mai napep ɗin ya ja su tafi.
Faisal yana zuwa nan a tunaninsa, sai ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. Duban Barrister Shaheedah yayi ya ce, "Na tuno inda na san ki, amma ni ban taimake ki don ki taimaka min ba." Murmushi Barrister Shaheedah ta yi, ta ce, "Na sani, kuma ba don taimakon da ka yi mini ba ne yasa zan taimake ka. Saboda aikina ne taimako, ƙwatowa marasa ƙarfi ƴancinsu shine babban aikina."
"Saboda haka ina son ka saka a cikin ranka, ba don ka taimake ni ba zan taimaka ma ka. Kawai zan taimaka maka ne a matsayinka na wanda yake buƙatar taimakon, da fatan ka fahimce ni."
Jinjina kai Faisal yayi alamun gamsuwa da abin da ta faɗa masa. Gyaran murya yayi ya ce, "Amma a ina ki ka gano inda nake har ki ka zo domin ki taimaka min, kuma a ina ki ka samu labarin ina nan wajen?"
Ɗan murmushi Barrister Shaheedah ta yi, kafin ta ce, "FAISAL tun lokacin da ka rabu da ni a cikin adaidaita sahun nan, nake bibiyarka, na samu labari sosai akan ka hatta alaƙarka da su Goggo na sani."
"Kai har dalilinka na baro Kano ka dawo Kaduna na sani. Sannan batun yadda aka yi na san ƴan sanda sun kama ka, labari ne da ya watsu ko ina ban da labarin abin da ya faru da kai, babu abin da ake watsawa, a garin Kaduna da kewayenta. Haka idan ka hau social media, labarin ne yake ta yawo akan wani matashi ya kashe uban gidansa don ya mallake dukiyarsa."
"Haka ne yasa na tashi tsaye domin na wanke ka daga zargin da mutane suke yi maka, yanzu ka ji dalilin da yasa na san komai a kanka? Sai dai har yanzu akwai wani abu guda ɗaya da nake ƙoƙarin sani akan ka, wannan abun kuwa shine: Alaƙarka da Hajiya Bilkisu, domin na samu labarin cewar akwai alaƙa me ƙarfi a tsakaninku. Sai dai babu wanda ya san wannan sirrin daga Allah sai kuma ku biyu kaɗai."
Tana kai wa nan a zancenta sai ta yi shiru tana kallon Faisal da yake ta faman goge ƙwallar da take zubo masa, kallon Barrister Shaheedah yayi ya ce, "Ki yi haƙuri yanzu ba zaki iya samun wani gamsashen bayani daga waje na ba, ki je bayan kwana biyu ki dawo zan sanar da ke iyakar abin da na sani."
Girgiza kai Barrister Shaheedah ta yi ta ce, "Babu damuwa insha Allah bayan kwana biyun zan dawo domin ka sanar da ni, sai na san ta hanyar da ya kamata na taimaka maka."
Tana gama faɗin haka ta kira ɗan sandan da ya kawo Faisal, ta umarce shi ya mayar da shi, nan take kuwa ya saka Faisal ɗin a gaba ya mayar da shi cikin ɗakin duhun nan kamar kabari. Ya kulle shi yayi tafiyarsa.
Barrister Shaheedah kuwa kasa ɗaga ƙafafunta ta yi, saboda wani irin nauyi da suka yi mata. Ji take kamar kar ta tafi ta bar Faisal a cikin wannan halin, wani sabon tausayinsa da kuma ƙaunarsa ce take ratsa duk wani sassa na cikin zuciyarta. Fita ta yi daga cikin office da suka tattauna tana sharar hawaye, a cikin ranta kuwa ta ƙudurce duk tsanani duk wahala sai ta fitar da Faisal daga cikin wannan halin da yake ciki.
_HAJIYA BILKISU_
Lokacin da su Hajiya Bilkisu suka isa gidanta, tare da Inspector domin ya ɗauko wukar da Faisal ya kashe Alhaji Hashim mai dala.
Wani ƙayataccen falo ta umarci Inspector da ya biyota, nan take kuwa ya bi bayanta, yayin da suka shiga cikin falon, mamaki ne ya cika ran Inspector ganin jini da yayi ko'ina face-face. Da alamu an sha artabu da Alhaji kafin a kashe shi, a cikin ransa kuwa ya furta kai "Gaskiya yaron nan ba shi da imani". Tsinkayo muryar Hajiya Bilkisu yayi tana cewa "Yallab'ai sai ku fara aikinka" nan take kuwa ya fara binciken falon, duba ko'ina yake amma bisa ga mamakinsu ba' a ga wuƙar ba sama da ƙasa.
Sai da ya ɗauki dogon lokaci yana binciken, amma bai ga wuƙar ba. Hajiya Bilkisu ce ta ce, to aje a duba ɗakin da Faisal yake mana ko ya ɓoye ta, babu musu kuwa Inspector ya ɗauki shawararta, amma sai da ya fara tambayar Hajiya Bilkisu "Hajiya Faisal ɗin anan gidan yake kwana ne?" Girgiza kai ta yi ta ce, "No ba anan yake kwana ba, zuwa yake yi idan ya gama aikin da yake can gidansu yake tafiya ya kwana. Amma akwai wani ɗaki da yake yin barcin rana, ba mamaki ko can ya je ya ɓoyeta."
"Ok Hajiya nuna mana ɗakin mu duba" wucewa gaba Hajiya Bilkisu ta yi Inspector ya bi ta a baya har ɗakin Faisal....
Suna buɗe ɗakin kuwa, sai ga wuƙar a tsakar ɗakin a ajiye jinin jikinta har ya fara bushewa...........
Comment and share
*HUSSEIN*
07069475482
*King and Queen Writing Chamber*
*⚖️AYI MIN ADALCI⚖️*
Writing by:
Hussein Yusuf
*King and Queen Writing Chamber*
*Bismillahir rahamanir rahim*
*Page 7&8*
Kallon wuƙar Inspector yayi, kafin ya ɗauko handkercif a cikin aljihunsa, sunkuyawa yayi ya ɗauki wukar sai faman jujjuyata ya ke yi a hannunsa. Kallon shi Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Inspector amma dai da zarar kun gama bincikenku akan wuƙar nan, za ku miƙa shi kotu ko?”
“E, Hajiya idan har muka ga zanen hannunsa a jiki, ba buƙatar sai ya amsa laifinsa, kawai kotu za mu tura shi domin a yi masa hukunci.”
Murmushi Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “In sha Allahu yallaɓai za ku tabbatar da Faisal ne ya aikata kisan nan, da zarar kun auna wannan wukar. Domin ni ganau ce ba jiyau ba, amma kun wani dage akan sai ya amsa laifinsa.”
Murmushi Inspector yayi ya ce, “Ai Hajiya ƙa'idar aikinmu kenan sai mun tabbatar da laifi, sannan mu miƙawa alƙali ya yanke hukunci.”
Girgiza kai Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Shi kenan ai tunda haka ka ce, amma wallahi barin Faisal a raye wani baƙin ciki ne ya ke ƙara ruruwa a cikin zuciyata.”
“Ki yi haƙuri Hajiya shi case irin wannan sai an faɗaɗa bincike sannan ake samo bakin zaren, kuma laifinki ne tun wuri da ki ka kirawo mu, mu kama Faisal, ai ba ki yi mana zancen wuƙar nan ba, da ace kin faɗa mana tun wuri, da tuni an yi komai an gama.”
“Ka yi haƙuri Inspector wallahi mutuwar ce ta ruɗani sosai, shi yasa ma na manta da zancen wata wuƙa amma yanzu tun da ga shi kun ga ta, sai mu godewa Allah kawai.”
Murmushi Inspector yayi ya ce, “Shi kenan Hajiya ni bari na koma bakin aiki”.
“Shikenan yallaɓai bari na saka direba ya mayar da kai” murmushi kawai Inspector yayi ya ce, “Nagode Hajiya” kiran direba Hajiya Bilkisu ta yi da ya zo ta ce ya mayar da Inspector division ɗinsu.
Nan take kuwa ya ɗauke shi ya fice da shi daga gidan.
★★★
Bayan Hajiya Bilkisu ta rabu da Inspector, kai tsaye cikin falonta ta shiga. Yayin da ta shiga cikin falon, zaunawa ta yi a ɗaya daga cikin ƙayatattun kujerun falon, nan take ta shiga cikin tunanin yadda za ta yi babban companin Alhaji ya zama mallakinta.
Bayan ta gama duk tunaninta, sai ta tashi ta haura sama, cikin ɗakinta ta shiga. Tana shiga ta ajiye jakarta akan wani shimfiɗaɗɗen gado, zama ta yi gefen gadon tare da ɗauko wayarta ta.
Lambar wata ƙawarta mai suna Bara'atu ta yi dialing. Ringing ɗaya biyu ta ɗauka, kafin Hajiya Bilkisu ta yi magana daga can ɓangaren Bara'atu ta ce, “Hello! ƙawata ya kike?”
Murmushi Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Ina lafiya! yanzu kina ina? Daga can ɓangaren Bara'atu ta ce, “Ina gida wani abun ne?”
Ƴar dariya Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Wallahi akan zancen wancan matsiyacin ne Faisal”
Ita ma Bara'atu murmushi ta yi ta ce, “Wani abun ne ya sake faruwa? Ko ba ki yi plan ɗin da muka shirya ba ne?”
Gyara zama Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Na yi mana sai mun rufe wata ƙofar wata kuma ta sake buɗewa”.
“To, menene kuma ya sake faruwa?”
“Ke dai yanzu idan babu abin da ki ke yi, ki yi sauri ki zo domin mu san abin yi.”
“Ok! ƙawata ki jira ni gani nan zuwa yanzun nan in sha Allahu.”
“To, sai kin ƙaraso.” Sannan ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya domin abubuwa da dama sun cushe mata kwaƙwalwa ko barcin kirki ba ta iyawa.
Kwantawa ta yi akan gadon, nan take kuwa wani barci mai nauyin gaske yayi awon gaba da ita.
**********
A ɓangaren Barrister Shaheedah kuwa, gaba ɗaya ta rasa ta inda ya kamata ta fara taimakawa Faisal. Domin ta daɗe ba ta haɗu da case mai sarƙaƙiyar wannan ba.
Sai dai da ta tuno kalaman Hajiya Bilkisu yayin da suka haɗu a police station, sai ta fi mayar da zarginta akanta. Duba da yadda ta rink'a kiran Faisal da banza, kuma ta nuna mata ba ta isa ta iya fitar da Faisal ba, daga zargin da ake yi masa.
Murmushi Barrister Shaheedah ta yi, sannan a fili ta furta na san ta inda zan fara. Tashi ta yi ta fito daga cikin office ɗin nata, bakin titi ta nufa, keke napep ta tare ta ce, gidan zai kai ta.
Nan take kuwa ya ɗauke ta ya nufi unguwarsu da ita. A cikin wata unguwa cikin Sabon gari local government ya ajiye ta. Dai-dai wani ɗan madaidaicin gida, mai kyan tsari da fasali.
Bayan ta sallami mai napep ɗin, kai tsaye cikin gidan ta nufa. Tun daga soro ta ke jin muryar mahaifinta, da alamu Ummarta ya ke yi wa masifar nan tashi da ba ta ƙarewa.
Tsayawa ta yi daga soron duk faɗan da ya ke yi tana jin sa. Amma sam ta kasa shiga, saboda ta riga ta san tana shiga kanta zai juyo da faɗan. Ganin wankin hula yana niyyar kai ta dare ne, kawai sai ta kutsa cikin gidan bakinta ɗauke da sallama.
Umma ce ta kalleta ta ce, “A'a Shaheedah har an dawo kenan?” murmushi Shaheedah ta yi ta ce, “E, Umma na dawo” kallon Babanta tayi da ya ke tsaye ya haɗe rai sai faman zabga mata wata irin harara ya ke yi.
Cikin sanyin murya ta ce, “Baba sannu da hutawa” ai kuwa kamar jira ya ke daman ta yi magana. “Rufe min baki shsha-sha-shar banza da wofi, wallahi Shaheedah ki fita daga idona na rufe, ko kuma na saɓa miki wallahi.”
“Baba ka yi haƙuri don Allah” tana faɗin haka ta tashi da sauri ta shige cikin ɗakinta.
Kallonshi Umman Shaheedah ta yi ta ce, “Abban Shaheedah, bai kamata ka rinƙa yi wa ƴar cikinka haka ba, sai ka ce ba kaine ka haifeta ba? Gaskiya abin nan yayi yawa, gara ka rinƙa tsayawa iya kaina. Amma ka daina takurawa yarinya haka kawai, da me za mu ji don Allah?”
“Yarinyar nan kullum iyakar kokari tana yi a gidan nan, kai kuma ban da zaman majalisa babu abin da ka ke yi, sai ka zo ba a gama abinci ba ka ishi mutane da masifa. Bayan ba kai ne ka ke kawo wa a dafa ba, yarinyar nan ita ce take yin komai amma ka kasa gane wa kullum cikin ƙuntata mata ka ke yi, ni wallahi na rasa wannan wacce irin rayuwa ce.”
Duk maganar da Umman Shaheedah ta ke yi, yana tsaye yana jin ta ko uffan bai ce mata ba. Har sai da ta gaji don kanta ta yi shiru, ta cigaba da abin da ta ke yi.
Jin ta yi shiru ne ya sa ya kalleta ya ce, “Sannu uwata, ai shiru na yi ina sauraronki har ki gama. Tun da kin zama uwata.” Ita dai kawai cigaba ta yi da dafa abincinta, ko ɗagowa ta ƙi yi ballantana ya ce, tana sauraronsa.
Ganin ta ƙi kula shi ne ya sa ya tashi a fusace, ya dubi Umman Shaheedah ya ce, “Yanzu ke Salamatu in ban da rainin wayo irin na ki, kina ji ina yi miki magana amma kin yi wani banza da ni? Tabbas haka ne, wato in yi ihuna na gama ba zaki kula ni ba, ni ga kare ko?”
Da sauri ta ɗago da kanta ta kalle shi ta ce, “A'a Malam ni ban haɗa ka da kare ba, kawai dai na ce, abin da kake yi ba ka kyautawa.......” Tana faɗin haka ta tashi ta shige cikin ɗaki shi kuma sai faman masifarsa ya ke, da ya ga dai babu mai tanka masa, nan take ya saka takalmansa ya fice daga gidan yana ta faman huci kamar wanda ya sha gudu.
A kwance ta ke akan ɗan madaidaicin gadonta, kallon rufin ɗakin ta ke yi. Kana kallonta ka san ba rufin ta ke kalla ba, idanun ne a wajen rufin, amma zuciyar tana can wani wajen dabam.
Umma ce ta shigo cikin ɗakin, kallon inda ta ke kwance ta yi ta ce, “Shaheedah tashi ki ci abincinki na san yau kin gaji sosai” shiru Umma ta ji, haka yasa ta sake maimaita abin da ta faɗa. Amma bisa ga mamakinta sai ta sake jin shiru.
Mamaki ne ya rufe Umma zuwa ta yi dai-dai inda fuskarta ta ke, a hankali ta ce, “Shaheedah tunanin me ki ke yi haka ne? Tun ɗazu na shigo ina yi miki magana amma kin yi shiru kin ƙyale ni.” firgigit Shaheedah ta dawo cikin hayyacinta, kallon Umma ta yi da ta ƙura mata idanu ko ƙiftawa ba ta yi.
Kame-kame ta fara yi, “Hmm Umma yaushe ki ka shigo?”
“Au! ikon Allah yanzu Shaheedah duk maganar nan da na ke yi miki ko kaɗan ma ba ki ji ni ba? Ni kaɗai na ke ta ihuna?”
Sosa kai Shaheedah ta yi ta ce, “Wallahi Umma ba na jin daɗi ne shi ya sa”
“Ayya! menene ya ke damunki?”
“Kaina ne ya ke yi min ciwo tun ɗazu?”
“To, sannu kin sha magani kuwa?”
“E, Umma ɗazu da na shigo ɗaki na sha”
“To, Allah ya sawwaƙe dama abinci na kawo miki na ga kin dawo daga wajen aiki a wahale.”
_
Murmushi Barrister Shaheedah ta yi ta ce, “Yawwa Ummana kamar kuwa kin san na kwaso yunwa da gajiya ba kaɗan ba Wallahi.”
“Aikuwa dai, sai ki tashi yanzu ki yi wanka sannan abincin ya huce sai ki ci” cike da zolaya Barrister Shaheedah ta kalli Umma ta ce, “Me kika dafa mana yau Umma?”
“Abin da kika fi so shi na dafa, kuma saboda ke kaɗai na dafa”
“Allah Ummana da gaske shinkafa da wake ki ka dafa?”
“Ƙwarai kuwa tashi ki buɗe ki gani” da sauri Barrister Shaheedah ta sauko daga kan gadon, ta zo ta buɗe plask ɗin abincin.
Aikuwa ta yi tozali da shinkafa da wake, ta sha man gyaɗa da kayan ganye, sai faman zuba ƙamshi ta ke yi. Wuf ta yi ta rungume Umma tana cewa “Gaskiya Ummana kina sona da yawa”.
“Shaheedah idan na ban so ki a duniyar nan ba, wa zan so? Ke kaɗai ce na ke kalla raina yayi sanyi. Kuma ke kaɗai na ke alfahari da ke a duniyar nan, tun da ba ni da kowa sai ke Shaheedah ke kaɗai ce ki ke son gani na a cikin farin ciki da walwala ko yaushe. Saboda haka idan ban faranta miki rai ba, wa zan farantawa?”
Ɗan tsuke ƙaramin bakinta ta yi, ta ce, “Don Allah Umma ki yi haƙuri ki daina irin wannan zancen ba na so wallahi”.
“Dole ne na faɗa Shaheedah domin kin cika ƴa ta gari abar alfahari a wajen iyayenta, kullum tunaninki da kokarinki akaina ne, da mahaifinki, duk da shi kullum ba ya ganin abun da ki ke yi.”
Hawaye ne ya zubo daga idon Umma da sauri ta share, don ka da Shaheedah ta gani. Cikin sanyin murya ta ce, “Shaheedah don Allah ina roƙonki akan ki ƙara haƙuri akan wanda ki ke yi yanzu, in sha Allahu nan gaba zai gane abin da ya ke yi ba dai-dai ba ne.”
Murmushi Barrister Shaheedah ta yi, ta ce, “Don Allah Umma ki daina ɗaga hankalinki akan Baba, kullum ina yi masa addu'a in sha Allahu zai daina duk abin da ya ke yi yanzu”.
Buɗa baki Umma ta yi da niyyar yin magana da sauri Barrister Shaheedah ta katseta ta hanyar cewa “Kai Umma wannan abincin na ki zai yi daɗi, wallahi Umma sai na ci abincin nan zan yi wankan saboda gaskiya na kwaɗaitu da shi sosai.......”
'Yar dariya Umma ta yi, ta ce, “Ai shikenan sai ki zauna ki yi ta ci” nan take kuwa ta ɗauko cokali ta fara cin abincin, tana ci suna hira da Umma.
Kallon Umma Barrister Shaheedah ta yi ta ce, “Umma kin ji labarin wani matashi da ƴan sanda suka kama, wai ya kashe uban gidansa?”
“E, ƙwarai kuwa jiya na ji a rediyo, wai an kama shi amma ba'a tabbatar shi ya aikata laifin ba, wai hukumar ƴan sanda suna bincike akansa.”
“To, Umma wannan matashin, shine wanda ya taɓa cetona daga hannun wasu ƴan daba da suka sace ni, za su kashe ni, shekara biyu da suka wuce idan za ki iya tunawa”
“Haba Shaheedah yaushe zan manta wannan shekarar, ai ba don Allah ya kawo wannan matashin ya ceceki ba, da tuni sun raba ni da ke”.
Ajiye cokalin da ta ke cin abincin ta yi ta ce, “To, Umma wannan matashin shine wanda ya ceceni, kuma wallahi Umma ba na zaton shi ya aikata kisan nan. Kawai dai an yi masa sharri ne, don an ganshi ba shi da kowa.”
“To, yanzu ke Shaheedah ta yaya ki ka tabbatar ba shine ya aikata kisan ba?”
“Ai Umma idan ki ka kalli Faisal, za ki gan shi da nutsuwa, kuma ga shi da cikakkiyar kamala. Kwata-kwata Faisal bai yi kalar wanda zai iya aikata kisan kai ba, wallahi Umma ba ki ga dukan da ya sha a wajen ƴan sanda ba, amma wallahi ya ƙi amsa laifinsa.”
“Ni shi yasa ma na ke zargin ba shine wanda ya aikata kisan ba, wataƙila sawun ɓarawo ya taka.”
“Haka ne Shaheedah, nima a yadda na ji kin faɗa min shi, na ji ina shakkar ba shine ya aikata kisan ba, sharri ne kawai aka yi masa. Amma ba za mu tabbatar da haka ba har sai mun ga abin da bincike ya nuna, idan nagari ne za mu gani haka idan ma mugu ne duk bincike zai nuna domin masu iya magana sun ce ba a yabon ɗan kuturu sai girma da yatsunsa. Saboda haka Shaheedah ina yi miki fatan alkhairi da nasara akan aikin da ki ka sanya a gabanki, sannan ba zan gaji da tunatar da ke ba, muddin ki ka gano mutum ba shi da gaskiya, kar ki kuskura ki sanya hannu a wajen ba shi kariya. Amma in dai kin gane mutum yana da gaskiya, kuma ana son tauye masa haƙƙinsa, to ki yi iyakar kokarinki wajen taimaka masa............
Comment and share
_*HUSSEIN YUSUF✍️*_
. *07069475482*
*King and Queen Writing Chamber*
*⚖️AYI MIN ADALCI⚖️*
Writing by:
Hussein Yusuf
*King and Queen Writing Chamber*
Bismillahir rahamanir rahim
*Page 9&10*
_
“Shike nan Umma in sha Allahu zan yi iyakar kokarina wajen ganin na taimakawa mai gaskiya a duk inda ya ke. Kuma komai ƙaskancinsa.”
Ɗan murmushin jin daɗi Umma ta yi, ta ce, “Yawwa Shaheedah haka na ke son ji daga bakinki, Allah yayi miki albarka. Ya ba ki nasara a duk abin da ki ka sanya a gabanki. Ya baki miji nagari wanda zai rinka jin tausayinki, da kuma taimaka miki a rayuwa.”
“Amin Ummata ke ma Allah ya sa Baba ya daina wannan abin da ya ke yi miki” murmushi Umma kawai ta yi ta ce, “Allah ya sa dai Shaheedah nima kullum fatana kenan, kuma ina sa ran in sha Allahu nan gaba zai daina.”
Da haka dai suka yi ta yin hira, har aka yi kiran sallar la'asar. Tashi Shaheedah ta yi ta shige cikin bathroom ɗinta, na cikin ɗakinta. Ita kuma Umma fita ta yi ta ɗauki buta ta shiga cikin bayin tsakar gidan nasu.
*******
A ɓangaren Goggo kuwa tun daga ranar da ta je ta gano Faisal, a hannun ƴan sandan nan. Kwata-kwata ta hankalinta ya gaza yin kwanciya, kullum tunaninta da kuma fatanta shine ta sanya Faisal a cikin idanuwanta.
Kullum ba ta da burin da ya wuce ta ga an sako Faisal ya dawo gida, haka ne ya sa ta daina yin barci. Kullum sai ta tashi cikin dare tai ta faman jera salloli da addu'o'i akan Allah ya fitar da Faisal daga cikin wannan bala'in da ya afka. Yau ma kamar kullum, Goggo ce a zaune bisa darduma, bayan ta idar da sallar Asubah, sai faman lazimi ta ke yi.
Amma idan ka dubi fuskarta, hawaye ne ya ke ta faman kwarara, amma duk da haka ba ta fasa jan carbin da ya ke hannunta ba.
Habibu ne ya shigo cikin ɗakin, bakinsa ɗauke da sallama “Assalamu alaikum” ba ta amsa sallamar sai ɗaga masa hannu kawai da ta yi. Ganin haka ya sa ya samu waje ya zauna yana jiranta ta gama lazimin da ta ke yi.
Bayan ta ɗauki dogon lokaci tana yi, sannan ta yi addu'a ta shafa, kallon Habibu ta yi ta ce, “Habibu ya aka yi ne na ganka da sassafen nan?” Saukowa yayi daga kan ƴar kujerar da ya ke, har ƙasa ya durƙusa ya ce, “Goggo ina kwana?” amsawa ta yi da “Lafiya ƙalau Habibu ya kake? Wallahi lafiya ƙalau Goggo”.
Gyara zama yayi ya ce, “Goggo lafiya kuwa na ga hawaye akan fuskarki?”
“To, Habibu menene ma ba zaka gani ba, ai idan ba Faisal na gani ya dawo gidan nan ba. To, hankalina ba zai taɓa kwanciya ba.”
“Goggo don Allah ki daina saka wa kanki damuwa, kar ki je ki jawo wa kanki wani ciwon kuma. In sha Allahu Faisal zai fito, kuma zai cigaba da rayuwa cikin ƴanci da kwanciyar hankali.” Fashewa da kuka Goggo ta yi cikin muryar kukan ta ke cewa “Habibu kullum idan na yi maka maganar Faisal, sai dai ka ce min zai fito. To wai sai yaushe ne zai fito? Ga shi zuwanmu har uku amma saboda zalunci an hana mu mu ganshi ma.”
“Goggo haƙurin dai zan cigaba da ba ki, in sha Allahu komai zai zama tarihi. Faisal zai fito, Goggo don Allah ki rage wa kanki tunani kada wani ciwon ya zo ya kama ki.
“Habibu idan na ce maka ba na kokarin cire komai a raina, to na yi maka ƙarya. Kullum babban abin da ya fi ɗaga min hankali shine; idan na dubi yaron nan da Faisal bari. Sai na ji zuciyata kamar za ta buga, kullum yaron nan Anwar idan ya taso daga makaranta, sai ya tambaye ni yaushe zan kai shi wajen Abbansa. Sai dai kullum na yi kokarin kawar da zancen ta hanyar ba shi wata kyautar da za ta mantar da shi tambayar da yayi min. To, amma babban abin da na fi tsoro shine; kada nan haba yaron nan ya zo ya saka ni na fara yi masa ƙarya. Domin ni kaina ban san ranar dawowar mahaifinsa ba.”
Dafe kai Habibu yayi ya ce, “In sha Allahu Goggo komai zai zo da sauƙi, kuma shi Anwar ki cigaba da kwantar masa da hankali, har ya mu samu Faisal ya fito.”
“To, shikenan Habibu Allah yasa mu dace” da amin ya amsa sannan ya ce, “Dama Goggo na zo ne, domin na sanar da ke cewa jiya wata lauya mai suna SHAHEEDAH ta zo ta same ni, ta shaida min cewa idan an shiga kotu ita za ta tsaya mana, sai ta tabbatar da an yi mana adalci.”
“Amma dai Habibu ka fi kowa sanin ba mu da kuɗin da za mu ɗauki lauya ko?”
“Haka ne Goggo! Amma ita wannan lauyar taimaka mana za ta yi. Domin tausayin Faisal ta ke.”
Murmushi Goggo ta yi ta ce, “Allah sarki! A ina ta san Faisal ɗin?”
“Ai Goggo ba kowa ba ce, wannan lauyar ce da muka haɗu da ita a police station. Wacce ta taimaka mana muka ga Faisal, idan za ki iya tunawa.”
“Ƙwarai kuwa na tuna ta, dama sunanta Shaheedah?”
“E, ni dai haka ta sanar da ni jiya da ta zo ta same ni.”
“Allah sarki baiwar Allah! A ina ta same ka?”
“Da la'asar ne ina zaune a shago ta zo ta sanar da ni.”
“To, ni dai yanzu babu abin da zan ce sai dai Allah ya bayar da sa'a da nasara. Kuma Allah ya fitar da Faisal daga cikin wannan bala'in.”
Da amin Habibu ya amsa sannan ya tashi ya fice daga cikin ɗakin, ita ma Goggo tashi ta yi domin ta haɗa musu abin karin kumallo.
****************
Hajiya Bilkisu kuwa, tun da ta gama waya da ƙawarta Bara'atu, wani barci ne mai nauyi ya kwashe ta. Ba ta jima da fara barcin ba, ta yi wani irin mummunan mafarki, wanda ba ƙaramin tsorata yayi ba.
Mafarki ta yi ta gan ta a wani irin daji, mai tsanani duhuwa, da sarƙaƙiya. Sai faman ihu da kururuwa ta ke yi, amma shiru ko kukan tsuntsaye babu dajin, ballantana ta saka ran za ta samu mai taimaka mata.
Ganin ta gama ihun nata ba ta ji ko da kukan gyare ba, kuma ga duhun magariba, ya fara sako kai. Wani kogon dutse ta hango, kuma daga inda ta ke, tana iya hango wuta a cikin kogon. Ba ta tsaya wani tantama ba, kawai ta nufi cikin kogon. Domin zuwa wannan lokacin, zuciyarta ta gama bushewa ba ta tsoron wani abu, fata ta ke yi ma a cikin ranta akan Allah ya sa ko menene a cikin kogon ya kashe ta, ko za ta huta da baƙincikin da ta tsinci kanta a ciki.
Yayin da ta kusanto kogon dutsen, sai ta hango wani mutum da farin tufafi, ya naɗe fuskarsa da farin rawani ba za ka taɓa iya ganin fuskarsa ba komai kurillarka kuwa.
A tsugunne ya ke gaban wutar da ta ke faman ci, kamar ana zuba mata fetur.
Ba tare da shakkar komai ba, ta tunkari inda mutumin ya ke a tsungunne. Tana zuwa daf da shi, kawai sai gani ta yi ya zaro wata sharɓeɓiyar wuƙar, daga cikin gidanta. Ba tare da wani ɓata lokaci ba, ya tunkaro ta da wuƙar da nufin ya hallakata.
Aikuwa tana ganin haka ba ta san lokacin da ta fita daga cikin kogon ba a guje. Aikuwa shi ma take ya bi ta a baya.
Gudu ta ke yi iyakar ƙarfinta, amma duk lokacin da ta waigo bayanta, sai ta ga mutumin a kusa da ita. Sun share fiye da awa guda suna gudu, duk Hajiya Bilkisu ta gaji, amma shi mutumin shi ko alamun gajiya babu a tare da shi, tamkar ma a lokacin ya fara gudun.
Suna cikin gudun ba ta ankara ba, sai kawai gani ta yi sun faɗo wata hanya mai yawan ramuka, kuma ga wasu irin duwatsu masu tsananin kaifi da tsini kamar reza. Ai kuwa ta ke Hajiya Bilkisu ta fara yankewa a kafafunta, kasancewar babu takalmi a ƙafartata. Jini sosai ya ke ta faman zuba daga jikin kafarta, nan take kuwa idanunta suka fara gani dishi-dishi. Nan take ta fara yin sassarfa a gudun nata, kwatsam! babu zato babu tsammani, sai kawai ji ta yi ta caki wani rami da ya ke tsakiyar hanyar. Nan take kuwa wani irin duhu ya gifta ta tsakanin idanuwanta, aikuwa ba ta ankara ba sai jin ta tayi a ƙasa ta faɗi.
Dai-dai wannan lokacin mutumin da ya ke binta ya ƙaraso wajen, yana zuwa kuwa ya sa hannu ya yaye rawanin da ya rufe masa fuska. Nan take kuwa fuskar marigayin mijinta Alhaji Hashim ta bayyana, ba ƙaramin razana Hajiya Bilkisu ta yi ba, buɗe baki ta yi tana nuna shi da hannu cikin harɗewar harshe ta ce, “Kaiiii kaiii kaiine?” Bai yi mata magana sai zaro wukarshi yayi ya nufo inda ta ke, yana zuwa bai tsaya wani jinkiri ba, ya ɗaga wuƙar sama ya saita dai-dai ƙahon zuciyarta.
Nan take kuwa ta rufe idanunta, ta takure jikinta waje guda, mutuwarta kawai ta ke jira, jin shiru ta yi, har yanzu bai caka mata wuƙar ba. A hankali ta buɗe idanunta, ai kuwa sai ta razana, sakamakon ganin Faisal da ta yi ya riƙe wuƙar da marigayin mijin nata ya ke kokarin caka mata.
Babu wanda yayi mata magana daga cikinsu, kawai ganin Faisal ta yi ya ja hannun Alhaji Hashim sun yi tafiyarsu sun bar ta a wajen, ai kuwa suna tafiya wata damisa ta fito daga cikin wani kogon bishiya.
A razane ta miƙe ta bi bayansu su Faisal da gudu, ji ta yi ƙafafunta sun yi mata wani irin nauyi. Nan take kuwa ta faɗi k'asa, dai-dai inda ta hango su Faisal sun ɓacewa ganinta, tana juyawa bayanta ta ci karo da damisar nan tana lasar baki, tana nufo inda ta ke, tashi ta yi da niyyar guduwa kawai sai ganin damisar ta yi, ta ja da baya ta yi wani irin tsalle, aikuwa sai ga ta ta bayyana a gabanta.
Nufo ta take yi, ita kuma tana ja baya, tana kara nufota tana ƙara ja da baya. ba ta ankara ba, sai ganin damisar ta yi ta daka tsalle ta nufo kanta.......Firgigit ta farka daga barcin da ta ke, tana tsandara wani uban ihu. Bara'atu da ta ke zaune, kusa da ita a gefen bed ɗin, ita ma ba ƙaramin razana ta yi ba, sakamakon jin ihun da Hajiya Bilkisu ta saki.
A razane ta kalle ta ta ce, “Bilkisu lafiya kuwa wannan ihun naki?” sai a wannan lokacin, ta san da mutum a ɗakin. Wata irin zufa ce, ta rinka karyo mata, tana gogewa wata tana ƙara tsatstsafowa. Kallonta kawai Bara'atu ta ke yi ta kasa gane wannan wanne irin abu ne mutum ya farka daga barci a razane haka.
Dafa kafaɗarta ta yi, ta ce, “Bilkisu menene ya razana ki a cikin barcin da har na ga kin fita hayyacinki?”
Fashewa da kuka Hajiya Bilkisu ta yi, ta ce, “Na shi uku ƙawata!” Ni kuma na ce “Kaico!” maimakon ta kira sunan Allah kawai ta kama kiran ta shiga uku.
Sake tambayarta ta yi, ta ce, “Don Allah ni ki yi min bayani yanda zan fahimta, menene ya razana ki a cikin barcin?” Share gumi Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Ƙawata wani irin mummunan mafarki na yi, tun da na,ke a rayuwata ban taɓa yin kwatankwacin irin mafarkin nan ba, domin ba ƙaramin razana ni yayi ba.”
Maimakon ta ba ta shawarar yadda ake yi, idan an yi mummunan mafarki, sai ji na yi ta ce, “Ƙawata dama haka abun ya ke, indai mijinka ya mutu dole ka rinka yin mafarkinsa, a hankali za ki ga kin daina mafarkin nasa.”
“Ƙawata ba za ki fahimta ba ne, ni mafarkin da na yi ba irin wanda ki ke nufi ba ne.” Murmushi Bara'atu ta yi, ta ce, “To, faɗa min na ji wanne iri ne”
“Ƙawata kenan ai ba zan taɓa iya faɗa miki mafarkin nan ba, tun da na san ba ki ya fassarar mafarki ba.”
“To, shike nan tun da ba za ki faɗa min ba, idan ta yi wari ai za mu ji.”
Gyara zama Hajiya Bilkisu ta yi cikin nutsuwa ta kalli Bara'atu ta ce, “Ƙawata don Allah kin san mai fassarar mafarki, ki raka ni ya fassara min mafarkin nan, domin wallahi ba karamin tsorata ni yayi ba kuma ya saka zuciyata a cikin shakku”.
“Gaskiya ƙawata ban san wani mai fassarar mafarki nan kusa ba, amma dai na san wani boka a can wani ƙauye mai suna A MUTU hatsabibin boka ne, na tabbata idan har na raka ki wajensa zai fassara miki mafarkinki dai-dai.”
“To, shike nan ƙawata, yanzu tun da na ga yamma ta yi, gobe da safe ki zo sai mu je wajen bokan, wallahi na ƙagara na san menene ya ke faruwa da ni”. “Goben sai ki shirya mu je da wuri don wurin akwai ɗan nisa da yawa ba laifi.”
Godiya sosai Hajiya Bilkisu ta yi wa ƙawarta Bara'atu, sannan ta mike tsaye za ta shiga cikin toilet, da mamaki Bara'atu ta kalleta ta ce, “A'a ƙawata ni fa har yanzu ba ki faɗa min dalilin da ya sa ki ka kira ni ba.” dafe kai Hajiya Bilkisu ta yi, ta ce, “Akwai dalilin da yasa na kira ki, amma ki bari mu kawar da wannan matsalar sannan sai mu tunkari ɗayar.”
“Shi kenan to ƙawata bari yanzu ni na koma dama akwai abin da nake yi, na bari na taho.”Daga nan suka yi sallama akan sai gobe ta zo ta raka ta wajen boka A mutu domin ya fassara mata mafarkin da ta yi.
××××××××××××
A ɓangaren Faisal kuwa, ba ƙaramin wahala ya ke sha a wajen ƴan sandan nan ba, kullum horon yau da na gobe daban. Duk ya rame yayi baƙi, amma duk da tsananin wahalar da ya ke sha, ya ƙi amsa laifinsa.
Wata ran da suka ba shi horon akan ya amsa laifinsa ya ƙi, kawai sai suka ɗauke shi, suka kai shi wani ɗaki suka saka igiya suka ɗaure ƙafafunsa, suka ratayo ƙafafunsa a sama kansa yana ƙasa, duk da haka ba su bar shi ba sai faman dukansa suke yi.
Sai dai yayi ta faman ihu, da suka ga ba shi da niyyar amsa laifinsa, dole suka kwance shi. Suka mayar da shi cikin cell.
Yau ma kamar kullum, a zaune ya ke yayi tagumi hawaye ya ke ta faman kwarara a kan kyakkyawar fuskarsa..........
mu haɗu a kashi na gaba
Comment and share
*Hussain Yusuf✍️*
07069475482.
*King and Queen Writing Chamber*
*⚖️AYI MIN ADALCI⚖️*
NA
HUSSAINI YUSUF
*King and Queen Writing Chamber*
*Ina roƙon afuwarku na rashin jina da kuka yi kwana biyu hakan ya faru ne saboda uzuri na gaggawa da ya zo min. Amma in sha Allahu daga yau zamu cigaba da posting har mu gama.*
*PAGE 11/12*
A hankali yasa hannunsa ya goge hawayen, amma yana ɗauke hannun nasa daga fuskar tasa, sai ka ga wasu hawayen sun sake surarowa.
Wasu ƴan sanda ya hango sun nufo ɗakin da ya ke, nan take kuwa ya tsure, ƙirjinsa ya rinƙa dukan uku-uku. Fatanshi Allah yasa ba dukanshi suka zo su ƙara yi ba.
Yayin da ya ga sun kusanto ɗakin da ya ke, sai yayi sauri ya miƙe tsaye. Yana rarraba idanu, kamar wani mai shirin yin gudu, suna zuwa ƙofar cell ɗin da yake ciki. Sai ya ga ɗaya daga cininsu ya saka key ya buɗe shi, sai da ya ƙare masa kallo tun daga sama har ƙasa, sannan ya ce, “Biyo ni a baya” yana faɗin haka ya juya ya tafi.
Ɗaya ɗan sandan ne ya kalli Faisal kafin ya daka masa tsawa “Za ka je mu tafi ko sai na buge ka anan wajen?” yana jin haka kuwa ya bi bayan ɗan sandan, shi ma ɗaya ɗan sandan ya bi bayanshi.
Ba su yi wata doguwar tafiya ba, sai ga su a offishin D.P.O, yayin da suka shiga ciki. D.P.O ya umarci Faisal ya zauna a ƙasa, babu gardama ya nemi waje ya zauna, akan carfet ɗin cikin ofishin.
Bayan ya zauna sai D.P.O ya kalli ƴan sandan da suka kawo Faisal ɗin ya ce, “Kofur za ku iya tafiya” a tare suka ɗaga ƙafa suka sara masa tare da cewa “Okay Sir” sannan suka juya suka fita daga cikin ofishin.
Bayan sun fita D.P.O ya mayar da hankalinsa kan Faisal, da ya ke tsungunne a gabansa cikin wata kakkausar murya ya ce, “FAISAL!!! ka yi sani cewa duk wata azaba da ake bai wa mai laifi akan ya amsa laifinsa, an yi maka amma shiru ka ƙi amsa laifinka. To, maganar gaskiya. Yanzu mu a wajenmu abin ya fi ƙarfinmu, saboda haka ranar litinin mai zuwa za mu tattara ka mu tura ka kotu, wataƙila a can za ka iya amsa laifinka. Don yanzu ma haka da nake yi maka wannan zancen, na sanar da lauyarka ranar monday za ku fara zaman kotu.”
Sunkuyar da kai Faisal yayi zuciyarsa tana wani irin luguden duka, babban abin da ya fi ɗaga masa hankali shine; zaman kotu da aka ce za'a yi.Domin shi a rayuwarsa bai taɓa zuwa kotu ba, bai san abin da zai faɗa ba domin ya fitar da kanshi daga zargin da ake yi masa.
Don haka sai ka jira ranar monday, domin ku fara zaman kotu, amma dalilin da yasa aka kawo ka nan shine; lauyarka Barrister Shaheedah ce, za ta zo domin za ta yi maka wasu ƴan tambayoyi don haka sai ka jira ta ta ƙaraso.
Gyaɗa kai kawai yayi ba tare da yayi magana ba, ba'a fi minti ashirin ba sai ga ta ta shigo tana shigowa ta ga Faisal a zaune akan carfet, murmushin farin ciki ta saki sannan ta yiwa D.P.O sallama gaishe shi ta yi. Sannan ta samu kujera ta zauna, “D.P.O ranar monday kace zamu fara zaman kotu ko?”
“E, Barrister ranar monday za ku fara zama don haka sai ki dage wajen bincike. Domin alamu sun nuna bai Faisal ne ya aikata kisan nan ba, amma sanin wanda ya aikata sai Allah bincike ne kaɗai zai iya fitar da Faisal.”
“In sha Allahu yallaɓai zan yi iyakar koƙarina wajen ganin na binciko duk wanda ya ke da hannu wajen aikata kisan nan. Kuma sai mun gurfanar da shi a gaban kotu koma waye shi.” Rashin tsoron Barrister Shaheedah yana burge D.P.O ba kaɗan ba, murmushi kawai yayi ya ce, “Allah ya bayar da sa'a da nasara.” Da amin ta amsa sannan ta ce, “Don Allah yallaɓai idan ba zaka damu ba, ina son keɓewa da Faisal domin akwai tambayoyin da nake son yi masa.”
“Babu damuwa Barrister bari na saka akai miki shi wancan office ɗin”.
“Okay to shikenan nagode” shi dai Faisal tun da Barrister Shaheedah ta shigo yake kallonta, kuma ya ji duk abin da ta faɗa sai dai ta yaya za ta iya binciko yanda aka kashe Alhaji domin ya san Hajiya Bilkisu hatsabibiyar mata ce baza ta taɓa barin kowa ya san sirrinta ba, haka kuma duk yaranta ko ba'a fada masa ba ya san ta yi musu gargaɗin faɗin wani abu akanta. Don haka da kamar wuya gurguwa da auren nesa Barrister Shaheedah ta iya fitar da shi daga cikin wannan bala'in.
Tunaninsa ne ya katse inda wani ɗan sanda ya zo yana yi masa magana akan ya tashi ya kaishi wajen Barrister Shaheedah. A hankali ya mike tsaye, ya wuce gaba ɗan sandan ya bishi a baya har zuwa cikin office ɗin da Barrister Shaheedah take ciki.
Nuna masa wajen zama ta yi, bayan ya zauna a nutse ta kalle shi ta ce, “Faisal saura kwana uku kacal a fara zaman kotu, ka sani idan har ba mu gabatarwa da kotu ƙwaƙƙwaran shaida akan zargin da ake yi maka ba, zaka iya fuskantar hukunci mai tsanani. Saboda haka don Allah ina son ka bani haɗin kai, idan na yi maka tambaya don Allah ka sanar da ni iyakar abin da ka sani.”
Ɗan gyara zama Faisal yayi ya ce, “In sha Allahu zan sanar dake iyakar gaskiyar abin da na sani.” “Yawwa Faisal, dama haka nake son ji daga bakinka”.Gyara zama ta yi sannan ta kalli Faisal cikin nutsuwa ta ce, “Faisal menene matsayinka a gidan marigayi Alhaji Hashim?”
“Ni yaron gidansa ne, aikina kullum shine; wanke masa motoci da kuma kayansa. Amma wani lokacin yana aikena kasuwa na yo masa cefanen gidansa.”
Sake jefo masa wata tambayar ta yi “Tsawon wanne lokaci ka ɗauka kana aiki a gidan?”
“A gaskiya ban wani daɗe da fara aiki a gidan ba, kwata-kwata satina biyu da fara aiki a gidan?” “Good! Ku nawa ne kuke aiki a gidan?”
“Mu uku ne, akwai Idi mai gadi, sannan akwai Lawan direba, wanda shi yake jan Alhaji a mota ya kai shi duk inda za shi.”
“A cikinsu ka taɓa samun saɓani da wani?”
Girgiza kai Faisal yayi tare da cewa “Gaskiya ni dai a iya sani na ban taɓa samun saɓani da wani a cikin gidan nan ba, sai dai kin san ɗan adam ajizi ne, yana tara bai cika goma ba, wataƙila a rashin sani na yi wa wani daga cikinsu laifi, kin san zaman tare?”
“Haka ne! To, menene alaƙarka da Hajiya Bilkisu?“ Sai da Faisal ya razana sosai da jin wannan tambayar, nan take idanunsa suka kaɗa suka canja launi, tsigar jikinsa ta tashi. Duk wani gashi da ya ke jikinsa ya miƙe. Sai da Barrister Shaheedah ta firgita da ganin halin da ya shiga lokaci guda.
Cikin sanyin murya ta ce, “Kayi haƙuri idan tambayar ta sosa maka rai” murmushin ƙarfin hali ya ƙaƙalo ya ce, “No, karki damu babu komai wallahi”.
Cigaba yayi da cewa “Gaskiya akwai alaƙa mai ƙarfin gaske a tsakanina da Hajiya Bilkisu wani sirrine tsakanina da ita, ba ta son kowa ya san wannan sirrin, haka ne yasa da ta ganni na zama yaron gidanta, sai ta yi tunanin na zo ne domin na tona mata asiri a wajen mijinta. Yayin da ta ga mijinta yana ji da ni, kuma zuwa na gidanta, sai ta daina samun duk wata kulawa daga gare shi. Ita duk a zatonta na tona mata asiri ne, shi yasa ta kashe Alhaji ni kuma ta ɗora min laifin kisan.”
Numfasawa Barrister Shaheedah ta yi, sannan ta ce, “Wannan wanne sirrine tsakaninka da ita wanda har ta aikata kisan kai saboda shi?”
“Maganar gaskiya ba yanzu na ke son sanar da kowa wannnan sirrin ba, saboda idan na faɗa mutane ba za su taɓa yarda ba. Amma idan lokacin da yakamata kowa ya sani to kowa zai sani.....Ɗaga kai sama Barrister Shaheedah ta yi tana tunani, bayan ta gama tunaninta kawai sai ta yi murmushi ta ce, “Okay! shikenan tun da ba zaka sanar da ni sirrin ba, nima ba na buƙatar sani. Amma na san hanyar da zan bi domin Hajiya Bilkisu da kanta za ta amsa laifinta, kuma ina mai tabbatar maka indai ta halarci zaman kotu ita ce za'a yankewa hukunci amma ba kai ba, kuma a kotun zamu tona mata asiri kowa ya san halinta, da kanta za ta tonawa kanta asiri ka rubuta ka ajiye wannan zaka ce na faɗa maka.”
Murmushi Faisal yayi saboda daɗin da yaji ashe har yanzu yana da sauran masoya a duniya, kallon Barrister Shaheedah yayi ya ce, “Nagode sosai Barrister ni kuma na yi miki alƙawarin indai har ki ka fitar da ni, daga cikin wannnan ƙangin zan baki labarin rayuwata tun daga farko har ƙarshe, saboda na san kin matsu ki ji labarina.”
“Ƙwarai kuwa Faisal kamar ka san abin da yake cikin zuciyata, in sha Allahu ranar zaman kotu za ka sha mamaki sosai.”
“To, nagode Barrister Allah ya kai mu zaman kotun domin mu ga yadda za'a yi.”
Miƙewa tsaye Barrister Shaheedah ta yi, ta ce, “Ni zan tafi sai ranar monday mu haɗu a kotu”.
“To, shikenan Allah ya kai mu nagode sosai Barrister Allah ya biya ki abin da kika yi mini”.
Murmushi kawai Barrister Shaheedah ta yi, sannan ta fita daga office ɗin. Ɗan sandan da ya kawo shi ne ya zo ya saka ahi a gaba domin ya mayar da shi cikin cell ɗin da yake.
----------------------------------
Al'amarin Hajiya Bilkisu kuwa, ƙarfe 7:00am ƙawarta Bara'atu ta iso gidanta. Tana zuwa ta tarar Har Hajiya Bilkisun ta gama shiryawa, nan da nan kuwa suka fito, daga cikin falon.
Wata mota na gani sun nufa, Hajiya Bilkisu ce ta shiga mazaunin direba, sannan Bara'atu ta zauna a gefenta. Da gudu direban Hajiya Bilkisu ya zo wajen motar, ɗan rage tsayi yayi ya ce, “Hajiya ko nayi wani laifin ne na ga zaki yi tuƙi da kanki?”
Ɗan murmushi Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Lawan ba kayi laifin komai ba, yau da kaina nake son yin driving neshi yasa, kuma inda za mu je ba shi da alaƙa da kai.”
“To, shikenan Hajiya Allah ya dawo da ku lafiya” da amin ta amsa sannan ta zuge glass ɗin motar ta ja ta a guje ta nufi ƙofar gate.
Da gudu mai gadi ya wangale gate ɗin, a guje ta ja motar ta fice daga gidan. Tana hawa titi kai tsaye hanyar fita daga cikin gari ta yi, sun haura minti ashirin suna tafiya amma babu mai cewa hmm a cikinsu.
Ganin shirun yayi yawa ne Hajiya Bilkisu ta dubi Bara'atu ta ce, “Ƙawata kin barni sai faman tsuga gudu na keyi a kwalta, amma ba ki nuna min inda ya kamata mu bi ba, kin san ni dai ban san wajen ba ko?” Ƙurawa hanya Bara'atu ta yi, sannan ta ce, “Tafiyar fa da ɗan nisa sosai ke dai kawai ki cigaba da tuƙi da zarar mun iso inda yakamata mu bi ai zan nuna miki.”
Gyaɗa kawai Hajiya Bilkisu ta yi, sannan ta cigaba da tuƙinta, sai da suka share awa biyu suna tafiya, tun suna hira, har suka dawo suka yi shiru saboda ganin sun shigo wani irin daji mai ban tsoro. Wasu dogayen bishiyoyi ne, masu tsayin gaske, ga kuma suƙiƙiyar da take cikin dajin.
Wata hanya ce ta ratsa ta cikin bishiyoyin, idan ba ka ƙura idonka ba ba zaka taɓa tunanin da hanya a wajen ba. Suna zuwa dai-dai hanyar, Bara'atu ta ce, “Ta bi hanyar ita ce za ta kaisu cikin kauyen da boka A MUTU ya ke .”
Zaro ido Hajiya Bilkisu ta yi a tsorace ta ce, “Ƙawata kin san abin da kike faɗa kuwa? Wannan hanyar za mu bi sai ka ce wadanda suka gaji da rayuwa suke neman mutuwa da kansu?”
Ɗaure fuska Bilkisu ta yi ta ce, “Ni fa gaskiya bana son gardama, yaushe zan kai ki inda za ki hallaka. Idan har muka bi hanyar nan za ta sada mu da garin su boka A MUTU. Idan kuma ba zaki iya ba, kawai ki juya mu koma.” Da sauri Hajiya Bilkisu ta ce, “A'a ai ba zancen komawa, kin san kuwa yanda na matsu na ji fassarar mafarkina?”
“To, da kin matsu kuma kike jin tsoro? Kawai ki ja mu tafi domin mu yi sauri mu koma da wuri.”
Babu gardama Hajiya Bilkisu ta ja motar suka nufi hanyar, tafiya suke yi amma ko alamun gari Hajiya Bikisu ba ta gani ba, kasa haƙuri ta yi ta kalli Bara'atu ta ce, “Ƙawata ni fa har yanzu bana gano alamun gari a kusa” harararta Bara'atu ta yi ta ce, Ni fa matsalata da ke rashin haƙuri, ki cigaba da tuƙa motar mana ai mun kusa isa.”
Sai da suka share minti talatin 30min suna tafiya, sannan suka iso bus stop, ma'ana hanyar ta ƙare. Amma ko alamun gari ba sa hangowa, kallon Bara'atu Hajiya Bilkisu tayi buɗa baki ta yi da niyyar yi mata magana da sauri Bara'atu ta ce, “Sai ki kashe motar anan mu ƙarasa a ƙafa domin mota ba ta shiga garin.”
Ba tare da gardamar komai ba, Hajiya Bilkisu ta kashe motar sannan ta fito. Sai da ta tabbatar ta kulle ko'ina sannan ta cewa Bara'atu “Mu tafi” wucewa gaba Bara'tu ta yi Hajiya Bilkisu ta bita a baya, wata siririyar hanya suka hau suka fara tafiya.
Tinkis-tinkis haka suka yi ta tafiya, sai da suka share minti 40 suna tafiya sannan suka ƙaraso wani ɗan ƙaramin ƙauye.
A bakin garin suka ga wata rijiya kusan duk mutanen ƙauyen, sun zagaye rijiyar suna ɗiban ruwa. Sai faman kokawa suke yi mata da maza, can ɗan nesa da rijiyar kaɗan wata ƙatuwar bishiyar mangwaro ce. Mata da yawa a gindin bishiyar sai faman daka suke yi a turmi wasu kuma sai faman casar hatsi suke.
Mamaki ne ya kama Hajiya Bilkisu sosai yanda ta ga mutane da yawa a cikin ƙauyen, ba ta taɓa yin zaton akwai gari a cikin surƙuƙin nan ba, kuma har da mutane da yawa a cikin garin suna rayuwa.
Sai faman kalle-kalle take yi, har suka ƙaraso gindin bishiyar mangwaron nan, inda matan nan suke ta faman aikace-aikacensu.
Sallama suka yi musu, cike da kulawa matan suka amsa, Bara'atu ce ta tambaye su inda ruwa su sam musu a tafiye suke. Wata dattijuwar mata ce, ta ɗebo musu ruwan a cikin wata randa mai sanyin gaske, a cikin wani ɗan ƙoƙo ta kawo musu ruwan, Bara'atu ce, ta karɓa sai da ta musa shanye rabi saboda daɗin ruwan kamar an saka masa sukari. Miƙawa Hajiya Bilkisu ta yi, ita ta kafa kai, sai da ta kusa shanyewa sannan ta miƙawa matar ƙoƙonta.
Godiya sosai suka yiwa matar, sannan Bara'atu ta ce, “Don Allah baiwar Allah ta ina zamu bi, mu je gidan boka A MUTU?” murmushi matar ta yi ta ce, “Ayya! ai yayana ne shi, ku taso sai na raka ku da kaina” ba tare da gardamar komai ba, suka tashi matar ta wuce gaba su kuma suka bi ta a baya.
Duk inda suka ratsa a cikin ƙauyen kallonsu ake yi.............✍️
Comment and Share
*HUSSAIN YUSUF*
07069475482.
*King and Queen Writing Chamber*
*⚖️AYI MIN ADALCI⚖️*
NA
HUSSAIN YUSUF
*King and Queen Writing Chamber*
*PAGE 13&14*
Ba su yi wata tafiya mai tsayi ba, sai ga su sun ƙaraso ƙofar gidan boka A mutu. Tsayawa matar ta yi, ta dubi su Hajiya Bilkisu ta ce, “Ga ƙofar gidan mun ƙaraso, sai ku shiga amma ni ba zan shiga ba, daga nan zan juya”. “To, baiwar Allah mun gode sosai, ba don kin taimaka mana ba, da sai mun sha wahala sosai” Bara'atu ce ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushin farinciki. Hajiya Bilkisu kuwa ɗauko kuɗi ta yi a cikin jakarta, ta miƙawa matar ta ce, “Ungo Iya karɓi sai a sayi goro.” Da murnarta kuwa ta karɓi kuɗin, tana ta zuba musu godiya kamar Aljanna suka bata. Bayan tafiyar matar, sai Bara'atu ta kalli Hajiya Bilkisu ta ce, “Ƙawata ai sai mu shiga ko?” Ɗan washe baki Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “To, ƙawata ai sai mu shiga, domin na matsu mu gama abin da ya kawo mu, mu koma. Juya wa Bara'atu ta yi, tare da shigewa cikin gidan, da sauri Hajiya Bilkisu ta bi bayanta. Suna shiga cikin gidan, wanda aka kewaye shi da dangan kara. Kalle-kalle suke saboda ba su taɓa tsintar kansu a irin wannan gidan ba, a hankali suka nufi cikin bukkar da suka gani a tsakar gidan.Kamar daga sama suka ji an daka musu wata irin razananniyar tsawa “Ku dakata anan......”Babu shiri kuwa suka dakata, suna kallon juna. Hajiya Bilkisu kamar ka ce “Ƙyatt.....” ta fita a guje saboda tsananin tsoratar da ta yi, ita kuwa Bara'atu jikinta sai faman rawa yake yi, kamar mazari. Sake jin muryar bokan suka yi yana cewa “Ku shigo da bayaaaaa......” Nan take kuwa suka nufi cikin bukkar da tafiyar baya, Hajiya Bilkisu har kusan faɗuwa ta yi, amma a haka ta daure har suka shiga cikin bukkar.
Yayin da suka gama shiga cikin bukkar, sai suka sake jin muryar bokan yana ce musu “Ku juyo ku zauna” a hankali suka juyo, ai kuwa sai suka yi arba da wani ɗan tsoho mai ƙyamurmurin jiki. Gemunsa fari fat ne, babu riga a jikinshi, fatar jikinsa kaɗai zaka kalla ka san ya daɗe a Duniya, saboda duk ta tauye ta yamushe. Nuna musu wata tabarmar kaba yayi ya ce, su zauna. Bayan sun zauna ne, sai ya kama sambatunsa irin nasu na bokaye, sai da ya daɗe yana yi. Sannan yayi shiru ya dubi su Hajiya Bilkisu ya ce, “Me yake tafe da ku?” Kasa magana Hajiya Bilkisu ta yi, sai Bara'atu ce ta buɗa baki ta ce, “Daman mu zo ne akan........” Bata ƙarasa faɗin abin da yake bakinta ba, ya daka mata tsawa da ƙarfi ya ce, “Dakataaaaa...” nan take kuwa Hajiya Bilkisu ta gumtse bakinta, dubansu yayi ya ce, “Aljani ɗan tsito ya sanar da mu zuwanku.” Nuna Hajiya Bilkisu yayi da wani ɗan ƙaramin sanda na hannunsa ya ce, “Kin zo ne akan a fassara miki mafarkin da kika yi, ko ba haka ba ne ?” Cike da mamaki Hajiya Bilkisu ta gyada kai ta ce, “Ƙwarai boka haka ne” fashewa da dariya boka A mutu yayi sai da yayi mai isar shi, sannan yayi shiru don kansa. Dubanta yayi ya ce, “Kin zo inda za mu fassara miki mafarkinki dai-dai, sannan mu baki kariya daga abin da yake tunkaro ki.” Cike da razana Hajiya Bilkisu ta ce, “Boka menene kuma ya ke tunkaro ni?” Da wata irin kakkausar murya ya fara magana “Wani al'amari ne, ko kuma na ce wata masifa mai girman gaske ce take tunkaro rayuwarki, shi yasa mu ka saka Aljani ɗan tsito ya je ya sanar da ke a cikin baccinki. Saboda mun san dole ne ki zo gare mu domin samun mafita.” Idanun Hajiya Bilkisu ne suka yi rau-rau hankali a tashe ta dubi boka ta ce, “Boka don Allah.....” wata tsawa ya daka mata “Keeeeee......Ba' a kira mana Allah anan wajen, domin da kin san da Allahn ba za ki zo gare mu ba domin mu share miki hawayenki.” Da sauri Bara'atu ta ce, “Boka ayi haƙuri ba ta taɓa zuwa ba ne shi yasa ka ga haka.” girgiza kai yayi ya ce, “Ki faɗa mata ta kiyaye” mayar da hankalinsa kan Hajiya Bilkisu yayi ya ce, “Babbar masifar da take tunkaro ki, ba komai ba ce illa wannan matashin da kika yi wa sharrin kisa kina ganin kamar ba shi da kowa, to ko da an yanke masa hukunci, wata rana sai ya fito kuma sai kin je gabansa kin durƙusa har ƙasa kina neman yafiyarsa, amma ba lallai ya yafe miki. Sannan sai kin faɗa wulaƙantacciyar rayuwa, wacce sai ta kai ki ga yin bara sannan ki samu abin saka wa a cikinki.” A razane Hajiya Bilkisu ta miƙe tsaye, wani gumi yana keto mata, Bara'atu ce ta kama hannunta ta jawo ta akan ta zauna. A diririce ta zauna, tana wani irin haki tamkar wacce ta sha gudu ta gaji. Bara'atu ce ta yi ƙarfin halin cewa “Boka yanzu menene mafita?” Tuntsirewa da dariya boka A mutu yayi sai da yayi mai isarsa sannan ya tsuke bakinsa ya turɓune fuska tamkar ba shine ya gama dariya ba, dubansu yayi ya ce, “Idan har kin bani wuƙa da nama ina da abin da zanyi akan lamarin amma fa aikin yana da matuƙar wahalar gaske.” Da sauri Hajiya Bilkisu ta ce, “Boka na baka wuƙa da nama ka yi duk abin da ka ga ya dace” Sai da yayi wa kansa kirari sosai sannan ya dubeta ya ce, “Duk wannan abin da na lissafa za su same ki, zan iiya juyar da su, su koma kan Faisal amma fa sai ki saki hannu domin aikin yana da matuƙar wahalar gaske.” Cike da zumuɗi Hajiya Bilkisu ta ce, “Boka ni kuɗi ba matsalata ba ce, indai aiki zai yiwu zan iya bayar da ko nawa ne” sake bushewa da dariya boka yayi sannan ya ce, “Yanzu za ki ajiye dubu ɗari biyar, idan aiki ya kammala zaki cika sauran dubu ɗari biyar ɗin.” Alama Hajiya Bilkisu ta yiwa Bara'atu, nan take kuwa ta ciro kuɗin daga cikin jakarta bandir ɗin dubu-dubu har guda biyar, sannan ta ajiye su a gaban bokan. Murmushi yayi ya ce, “Ki xuba ido ki ga yanda Faisal zai wulaƙanta a idon duniya, kuma ina mai tabbatar miki cewa sai Alƙali ya yanke masa ɗaurin rai da rai a gidan maxa, kuma baƙin ciki.ne zai kashe shi a gidan maxan, idan har aiki ya kammalu za ki ciko sauran kuɗin, don haka daga lokacin da aikin ya kammala, za mu turo Aljani ɗan tsito ya zo ya karɓi cikon kuɗin.” Zaro idanun Hajiya Bilkisu da Bara'atu suka yi, Hajiya Bilkisu ce ta kada baki ta ce, “Boka ta yaya Aljani zai zo wajena karɓar kuɗi?” Cikin tsawa ya ce, “Kee! Ba ki san Aljani ɗan tsito ba? Idan ranar irin ta yau ta kewayo, ki ɗauko da daddare ki ajiye su inda ba wanda yake zuwa a cikin gidanki Aljani ɗan tsito zai zo ya ɗauka” a tare suka ce “To, boka mun gode” Bara'atu ce ta ce, “Zamu iiya tafiya kuwa?” Da sauri bokan ya ce, “Ku tashi ku tafi ɗan tsito ya sallame ku” a tare suka miƙe tsaye, za su tafi. Daka musu tsawa Boka A mutu ya.sake yi ya ce, “Da baya za ku fitaaaa.......” Ai kuwa da bayan suka fita, sannan suka bi hanyar da ta kawo su, gidan bokan. Ai kuwa sai suka rinƙa sauri, cikin ƙanƙanin lokaci sai ga su sun ƙaraso har wajen motarsu, mamakin saurin ne ya ishe su. Kamar daga sama suka ji ana cewa “Ku yiwa Aljani ɗan tsito godiya domin shine ya rage muku hanya” nan da nan kuwa suka hau yin waige-waige kuma basu ga kowa ba, sake jin muryar bokan suka yi yana cewa “Ku yi masa godiya mana sauri yake domin zai je ya fara aikin da kuka ba shi” duk da ba wanda suka gani, amma sai suka haɗa hannayensu wuri guda alamun godiya, suna yin haka kuwa suka shige cikin motar . Wannan karon Bara'atu ce mai.jan motar ita kuma Hajiya Bilkisu tana front seat a zaune.
****************
Barrister Shaheedah kuwa, tana baro police station. Kai tsaye gidan Hajiya Bilkisu ta nufa, don akwai tambayoyin da take son yiwa abokan aikin Faisal na cikin gidan, ba ta son ma Hajiya Bilkisu ta san da zuwanta.
A cikin napep take, lokaci zuwa lokaci sai ta saki wani murmushi, sannan ta yi ƙwafa. A ckin zuciyarta kuwa cewa take “Hajiya Bilkisu yau za ki san kin taɓo Barrister Shaheedah, sai kin san kin ɗebo ruwan dafa kanki da hannunki.” Muryar mai napep ɗin ce ta katse ta daga tunanin da take yi, “Hajiya mun ƙaraso”.
A hankali ta ɗauki jakarta ta fito daga cikin napep ɗin, kallonshi ta yi ta ce, “Don Allah idan bazaka damu ba, ka jira ni anan, idan na gama sai ka mayar da ni na sallame ka.” Ɗan shafa kai yayi ya ce, “Ba komai Hajiya amma fa sai kin yi sauri fa” murmushi kawai ta yi ta ce, “In sha Allahu ba daɗewa zan yi ba.” Tana faɗin haka ta juya ta nufi ƙofar gidan, yayin da ta kusa ƙarasawa tsayawa kawai ta yi tana ƙarewa gidan kallo. Saboda tsananin haɗuwarsa, da kallo gidan nan an kashe naira wajen gina shi.
Murmushi ta yi a fili ta furta “Hajiya Bilkisu kin kusa fita daga cikin wannan rayuwar ki koma ta ƙasƙanci da wahala, kuma sai kin yi nadamar zuwanki duniya, za ki san Barrister Shaheedah ba kanwar lasa ba ce......” Tana faɗin haka sai ta nufi ƙofar danƙareren gate ɗin, cikin takunta na ƙasaita wanda ya ke matuƙar yi mata kyau kuma yake saka mata kwarjini a idanun maƙiyanta.
Yayin da ta ƙaraso ƙofar gate ɗin, zuwa ta yi dai-dai ƙaramar ƙofar, hannunta ta saka ta ƙwanƙwasa. Sannan ta tsaya ko za'a buɗe, amma sai ta ji shiru, sake ƙwanƙwasawa ta yi sai a sannan ta ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Ganin haka yasa ta koma gefe, ta ƙurawa ƙofar idanu tana sakin wani murmushi wanda yake ƙarawa fuskarta haske da kwarjini, ga kuma wani sirrintaccen kyau da Allah ya horewa Barrister Shaheedah. A hankali ta ga wani baƙauyen buzu ta gani ya buɗe ƙofar yana hangen waje, karaf!! Idanunsa suka sauka akan Barrister Shaheedah, cikin muryarsu irin ta buzaye ya ce, “Kaii baƙo Hajiya bash shi nan yayi tahiya” turɓune fuska Barrister Shaheedah ta yi kafin ta ce, “Ina ta tafi?” Ba ta amsa yayi “Wallahi mu ba mu shani ba kawai dai ya she mana yayi tafiya”.
Gyara tsayuwarta Barrister Shaheedah tayi ta ce, “Daman ba wajen Hajiya na zo ba, wajenku na zo......” Zai yi magana ta katse shi ta hanyar ɗaga masa hannu, shiru yayi kuwa yana zare idanu. Cikin ɗaga murya ta ce da shi, “Za ka buɗe min na shiga ko kuma a tsaye za ka cigaba da barina?” Da sauri kuwa ya buɗe mata, kasa haƙuri yayi ya kalleta ya ce, “Amma Hajiya lahiya kike nema na?” Cikin ɗaga murya Barrister Shaheedah ta ce, “Saurin me kake yi ne? Ai idan ka yi haƙuri zaka ji duk abin da ya kawo ni wajenka” tana gama faɗin haka, sai ta ja kujerar da ta gani guda biyu a ajiye, bayan ta zauna a guda ɗaya sai ta umarce shi, shima ya zauna a guda ɗayar ya fuskanceta.
Babu musu kuwa ya zauna, jikinsa har rawa yake yi, saboda Barrister Shaheedah ba ƙaramin kwarjini ta yi masa ba. Cikin wata kakkausar murya ta fara magana “Ni nan da ka ganni, lauya ce. Na zo ne domin na yi maka wasu ƴan tambayoyi, idan har ka sake ka yi min ƙarya zan gane, kuma sai na ɗaure ka domin ni ba'a yi min ƙarya a zauna lafiya, da fatan ka fahimce ni?” Da sauri ya gyaɗa kai, cikin muryarsu irin ta buzayen ƙasar Nijar ya ce, “In sha Allahu Hajiya ba zan yi maka ƙarya ba” jinjina kai Barrister Shaheedah ta yi ta ce, “Da ka taimaki kanka kuwa”.
Fara tambayarsa ta yi da “Ka san Faisal?” cikin rawar murya ya ce, “E, Hajiya na san ta mun yi aiki tare anan gidan” sai a sannan Barrister Shaheedah ta saki wani murmushi wanda ni kaina ban san ma'anarsa ba, sake jefo masa wata tambayar ta yi “Menene aikinsa a cikin wannan gidan?”
“Shine ya ke wankewa marigayi Alhaji motarsa da kayansa, kuma Alhaji yana ji da shi.....”
“Me yasa yake ji da shi duk cikinku?”
“Saboda Faisal ya fi mu.hankali da nutsuwa da kuma kaifin hankali da tunani”.
“To, me yasa Hajiya Bilkisu ta ce, shi ya kashe Alhaji?” Shiru yayi yana zazzare idanu, domin Hajiya Bilkisu ta yi musu warning (gargaɗi) akan kada su sake su ce ba Faisal ne ya kashe Alhaji ba, tace musu indai suka tona mata asiri sai tasa an kashe su su da iyalansu, haka ne yasa gaba ɗaya buzun mai gadin ya diririce da ya ji tambayar da Barrister Shaheedah ta jefo masa.
Sake maimaita masa tambayar ta yi, “Na ce maka menene yasa Hajiya Bilkisu ta ce Faisal ne ya kashe Alhaji, da gaske shine ya kashe shi ɗin? Idan har ka faɗa min ƙarya wallahi ka ji na rantse ko? Sai ka fuskanci hukunci mai tsananin gaske, domin mu lauyoyi indai an yi mana ƙarya muna ganewa.” Fashewa da kuka buzun yayi, mamaki ne ya kama Barrister Shaheedah, nan take kuwa ranta ya ɓaci ta daka masa tsawa “Za ka ba ki amsar tambaya ta ko kuma sai na tafi da kai, idan ya so a can sai ka bayar da amsa, bayan na saka an yi maka dukan tsiya?” Shiru yayi yana ajiyar zuciya a nutse Barrister Shaheedah ta dube shi ta ce, “Me yasa daga tambayarka zaka kama yin kuka kamar wani ƙaramin yaro” cikin rawar murya ya ce, “Hajiya ce ta ce mana idan har aka zo bincike nan gidan, muka saka ta a ciki sai ta saka an kashe mana iyalanmu, kuma muna son iyalanmu domin su muke baro ƙasarmu mu taho nan neman kuɗi.” Sai a wannan lokacin, Barrister Shaheedah ta yi murmushi ta ce, “Ƙarya take yi muku, ba abin da za ta iya yi wa iyalanku. Ko ta san inda iyalan naku suke ne?” Da sauri ya girgiza kai ya ce, “A'a ba ta sani ba amma cewa ta yi za ta saka a nemo mata inda suke” jinjina kai Barrister Shaheedah ta yi ta ce, “To, ƙarya take yi muku, don ku ji.tsoro ku ƙi faɗin gaskiya in dai har ka faɗa min gaskiya zan rabu da kai amma idan ka faɗa min ƙarya zaka gane kurenka, kuma na yi maka alƙawarin ba zan taɓa faɗawa Hajiya Bilkisu abin da ka faɗin min ba.” Murmushi buzun yayi ya ce, “Ka yi alƙawari ba zaka faɗawa Hajiya abin da muka faɗa maka ba?” Gyaɗa kai Barrister Shaheedah ta yi ta ce, “Nayi alƙawari babu wanda zan faɗawa” ƙasa yayi da muryarsa ya fara yi mata bayani, ita kuma nan take ta kunna recording ta fara naɗar muryarsa a wayarta.................
To be continue......
*Hussain Yusuf*
my new whatsapp number 08109373275
*King and Queen Writing Chamber*
*⚖️AYI MIN ADALCI⚖️*
NA
HUSSAIN YUSUF
*Page 15&16*
*King and Queen Writing Chamber*
Nutsuwa Barrister Shaheedah ta yi, ta ƙurawa Idi mai gadi idanu, shi kuma sai faman zuba mata surutu ya ke yi. “Ai tun farkon zuwan Faisal cikin gidan nan, na lura akwai wani ɓoyayyen sirri a tsakaninsa da Hajiya Bilkisu, domin a ranar da marigayi Alhaji ya kawo Faisal gidan nan, hankalin Hajiya ne ya tashi sosai. Ta cewa Alhaji ya sallami Faisal daga gidan nan, domin ita ba ta gamsu da shi ba, amma sai Alhaji ya ba ta amsa da ba ki san waye Faisal ba, sai kin zauna da shi sannan za ki fahimci halinsa, na karamci da haƙuri, uwa uba kuma ga kawaici da kamun kai, sai kuma gaskiyarsa da riƙon amanarsa suka yi masa ado.”
“Duk da haka Hajiya Bilkisu ba ta yarda ba, ta dage akan dole sai Faisal ya bar gidan nan, ko kuma ita bar shi. Ƙiri-ƙiri Alhaji ya nuna mata, sai dai ta bar gidan amma Faisal kam ba zai bar gidan nan ba. A bisa dole Hajiya Bilkisu ta yarda Faisal ya zauna a cikin gidan nan, ba don ranta ya so ba.”
Shiru yayi yana tunani kome ya tuna kuma, sai ga hawaye sharrr! ya biyo fuskarsa. Da mamaki Barrister Shaheedah ta dube shi ta ce, “Subhanallahi!! menene kuma ya faru na ga hawaye akan fuskarka?” Goge hawayen yayi da hannunsa, sannan ya dubi Barrister Shaheedah ya ce, “A ranar da Faisal ya cika kwana goma sha biyu a cikin gidan nan ne, ranar saura kwana biyu a kashe Alhaji...... Da misalin ƙarfe 9:30pm na dare, ni da Faisal muna zaune anan ƙofar gate, akan wancan bencin da kike gani, lokacin ma Faisal Alhaji yake jira ya dawo domin akwai saƙon da zai ba shi. Shi yasa bai tafi gida da wuri ba, domin babu yadda ba mu yi da Faisal ba akan ya dawo nan gidan da kwana amma sam ya ƙi yarda ya dawo. Domin Faisal indai kana zaune da shi zaka ƙaru da ilimi sosai, shi yasa ko kaɗan ni da Lawan direba ba ma son rabuwa da shi......”
“Muna zaune muna ta taɗi mai daɗi ni da shi, sai labarai yake ba ni masu hikima da tsantsar ilimi a ciki. Kwatsam!!! Baby zato ba tsammani, sai muka ga Hajiya Bilkisu akanmu a tsaye, babu wanda ya san da zuwanta sai ganinta kawai muka yi akan mu tana ta faman zabgawa Faisal wata muguwar harara. Duban Faisal ta yi, cikin ɗaga murya da tsawa-tsawa ta ce da shi taso ka biyoni domin ina son ganinka yanzun nan....”
“Babu musu kuwa Faisal ya tashi ya bita a baya, zuwa gefe ta yi can nesa da inda muke ta tsaya, shi ma kuwa Faisal a nutse ya je kusa da ita ya tsaya yana mai fuskantarta. Ni kuwa zuwa wannan lokacin, har na fara jin haushin Hajiya, domin ƙiyayyar da take nunawa Faisal ta yi yawa. Ganin zan iya jin abin da za su faɗa ne, yasa ta ja Faisal har cikin falonta, ni kuma ganin haka yasa na tashi cikin sanɗa na bi bayansu, domin na ji abin da za su tattauna.”
Cikin tafiyar sanɗa na je jikin ƙofar falon na tsaya, ban ankara ba na fara jiyo muryar Hajiya Bilkisu tana yi wa Faisal faɗa cikin ɗaga murya da alamu dai umarni take ba shi. “Wallahi Faisal tun wuri ka bar gidan nan, tun kafin na jefa ka a masifar da sai ka gwammace kiɗa da karatu, tun wuri ka fita daga idona na rufe, saboda tsabar rashin mutunci da rashin zuciya, har cikin gidan aurena zaka biyo ni ka tona min asiri? To, ina ba ka shawara gobe-goben nan ka bar gidan nan, tun kafin ka tona min asiri. Idan kuwa har ka ƙi barin gidan nan gobe, to ka sani sai na jefa ka a masifar da za ta yi ajalinka......” Ko da na ji haka ba ƙaramin faɗuwa gabana yayi ba, zuciyata ta rinƙa bugawa da sauri. Saboda jin abin da Hajiya Bilkisu take faɗawa Faisal wai zata yi ajalinsa.
Jiyo muryar Faisal na yi yana cewa “Ni ban zo gidan nan don na tona miki asiri ba, domin Allah ne ya rufa miki, amma fa ki sani rana dubu ta ɓarawo ce, rana ɗaya tak ta me kaya. Ko da ni ban tona miki asiri ba, ki sani Allah yana sane da ke, kuma ya barki ne domin kiyi son ranki wata rana dole sai sirrin nan da kike tsoron tonuwarsa ya tonu, kuma daga ranar da ya tonu kin san hukuncinki. Kuma in sha Allahu sai kin yi nadama, domin aure kan aure babban saɓon Ubangiji ne, ke kuma ga shi kin zo kin yi, ni shawarar da zan ba ki ita ce.......Dakata Faisal, Hajiya Bilkisu ta katse shi daga zancen da yake yi, jiyo muryarta na yi har rawa take yi, tana cewa “A taƙaice dai Faisal ba zaka bar gidan nan ba ko?” jiyo muryar Faisal ɗin na yi yana cewa “Of course Hajiya ba inda zan je, domin Alhaji shi ya kawo ni gidan nan, shi ya nemi da na zo na rinƙa yi masa aiki yana biyana. Saboda tsananin kyautata min da yake yi ba zan taɓa butulce wa umarninsa ba, idan ba ki da abin cewa ni kin ga fita ta....”
Ko da na jiyo Faisal yana ƙoƙarin fitowa daga cikin falon, da gudu na koma wajen zamana wato ƙofar gate na yi zamana kamar ba nine na tashi ba. Hango Faisal na yi, ya taho ransa a ɓace. Ko da ya zo inda nake zaune, sai ya ga ina ta faman kallonsa, murmushi yayi min wanda ni na san iyakarsa fuska bai cikin zuciyarsa ba. Nima murmushin na yi masa na ce da shi “Faisal ka yi haƙuri da halin Hajiya sai haƙuri, Alhaji ma haƙuri yake yi da ita” dafa kaɗata yayi ya ce da ni, “Idris domin haka yake kirana, tun farkon zuwana gidan nan, inda ba ni da haƙuri da tuni na tafi na bar shi amma ka sani Hajiya Bilkisu ba ta isa ta na bar gidan nan ba, har sai in Alhaji ne ya ce na bar shi da kansa.”
Nima murmushi na yi na ce “Ai Alhaji yanda yake ji da kai a gidan nan, ba zai so ka bar shi......” jiyo horn ɗin motar Alhaji ne ya sa na kasa ƙarasa zancen da yake bakina.
Da ɗan guduna na tashi na je, na buɗewa Alhaji murfin gate ɗin. Nan take kuwa ya shigo da motarsa kai tsaye wajen ajiye motocin gidan ya nufa, bayan ya ajiyeta sai ya fito ya nufo inda muke ni da Faisal a tsaye muna ɗaga masa hannu.
Yayin da ya iso inda muke, maimakon ya amsa gaisuwar da muke yi masa ni da Faisal, sai ya miƙo mana hannu muka yi musabaha. Bayan mun gama gaisawa da Alhaji Hashim, sai ya dube ni ya ce, “Idi mai gadi sannu da ƙoƙari” nima amsawa na yi da “Yawwa Alhaji ai kune za mu yiwa sannu, domin mu koda yaushe a zaune muke, ku kuma kullum sai kun fita aiki..” Ɗan murmushi kawai Alhaji Hashim yayi, sannan ya dubi Faisal ya ce, “Faisal ka yi haƙurin rashin dawowata da wuri wallahi meeting muka shiga shi yasa, ga shi na tsare ka, karsu Goggo su ji shiru su biyo baya....”
Ɗan murmushi Faisal yayi ya shafa kansa sannan ya ce, “Wallahi ba komai Alhaji, ai nasan akwai abin da ya tsare ka shi yasa ma na yi ta jira. Saboda na san ba ka da saɓa alƙawari.” Dafa kanshi Alhaji yayi ya ce, “To, Faisal mu je cikin falo mu yi magana ko?” Daga nan suka nufi cikin falon, amma ban san abin da suka tattauna ba, ranar dai Faisal bai bar gidan nan ba, sai wajen ƙarfe 10:00pm na dare.
Washe gari ma haka Faisal yayi jiran Alhaji har ya dawo, ni kaina ban san akan abin da suke tattaunawa ba. Ranar a falon da Alhaji yake saukar baƙinsa, suka shiga, ganin haka yasa Hajiya Bilkisu ta gigice domin duk a tunaninta Faisal tona mata asiri yake yi a wajen Alhaji. Dalilin da yasa na ce haka shine; wasu mutane ne suka kawo wasu atamfofi, wai na Alhaji ne, sai na karɓa zan kai cikin gidan, a ƙofar falon na ji Hajiya tana waya tsayawa na yi tsam domin na ji wayar da take yi “Ƙawata kinga wannan matsiyacin, yana can yana tona min asiri a wajen Alhaji ko?” Ban ji abin da waccan take faɗa ba, sai kawai ji nayi Hajiya ta ce, “To, shike nan ƙawata da shawarar nan taki zan yi amfani, ki bari sai dare ya raba sannan ki turo su, amma fa ki tabbatar ba'a samu matsala ba.....” Daga nan ban ƙara jin komai ba, sakamakon ƙasa da ta yi da muryarta.
Ina shiga sai na miƙa mata kayan. Na ce wasu ne suka kawo wai na Alhaji ne, karɓa ta yi tana bina da wani irin kallo, nan take kuwa na sha jinin jikina, cikin sanyin jiki na juya zan fita daga falon. Kamar daga sama na ji an daka min tsawa “Kai Idi” da sauri kuwa na jiyo, ina kallonta, sake daka min tsawa ta yi “Ba zaka zo bane?” Zuwa na yi na durƙusa a gabanta, jikina sai rawa yake yi, saboda ba ƙaramin kwarjini Hajiya ta yi min a wannan lokacin ba.
Jiyo muryarta na yi tana cewa “Me ka ji ina faɗa a cikin waya?” Gabana ne ya bayar da sautin rasss!! zuciyata ta rinƙa bugawa da saurin gaske. Cikin harɗewar harshe na rinka magana “Wall....Wallahi Hajiyya babu abin da na ji..Ni ban san ma kina waya ba, kawai shigowa na yi.” Ta daɗe tana kallon cikin idanuna kamar mai son gano wani abun sannan ta ce, “Idan ma ka ji, to, bakinka ƙanen kafarka, karka kuskura na ji maganar nan a bakin wani, idan kuwa har ka sake na jita a bakin wani hmmm!!!” Sai ta yi ƙwafa, daga nan ta ce, '“Na tashi na fice mata daga cikin falo.”
Da sauri kuwa na tashi zan fita har tuntuɓe nake yi, saboda tsabar ruɗewar da na yi. Kama handle ɗin ƙofr na yi zan fita, jiyo muryarta na yi tana kiran sunana da wata kakkausar murya “Idi dakata” tsayawa na yi jikin ƙofar kamar gunki, sai zare idanu na ke yi, ina nadamar shigowata cikin a irin wannan yanayin. “Idan har ka kuskura na ji maganar nan, a bakin wani wallahi kai kuka da kanka!! Domin sai na saka an kashe min kai kisan ma na wulaƙaci” tana faɗin haka ta daka min tsawa ta ce, “Get out” da sauri kuwa na fice daga falon jikina yana wani irin rawa. In taƙaice miki labari dai, a daren kasa bacci na yi saboda tsananin fargaba da tsoron da na shiga. Domin Hajiya Bilkisu za ta iya aikata komai don ba imani ne da ita ba, ko kaɗan.
Ina zaune gaba ɗaya na fita hayyacina, misalin ƙarfe 11:30pm na dare, sai ga Faisal ya fito daga falon Alhaji. Da alamu dai sun gama tattaunawa, murmushi yayi min sannan yayi min sai da safe ya tafi. In taƙaice miki labari dai Hajiya da cikin dare da misalin ƙarfe 2:30pm na dare, wasu ƙarti suka shigo gidan nan hannayensu ɗauke da makamai, ban san wanda ya buɗe musu gidan ba, domin turowa kawai suka yi suka shigo. Ina ganinsu kafin na yi wani yunƙuri, wani garjejen ƙato a cikinsu yayi duka ɗaya a tsakiyar kaina da kokara (Sanda) daga nan ban sake jin inda kaina yake ba, kawai sai da safiya na farka na tsinci kaina a gadon asibiti, an ɗaure min goshina da bandeji.
Anan na ga Lawan direba yana yi mini sannu, domin shi lokacin da aka aikata kisan ranar bai kwana a gidan ba, Alhaji ya aike shi can wani ƙauye domin ya kaiwa wani kawunsa kayan abinci domin azumi ya kusa zuwa.
A bakin Lawan nake jin labarin wai Faisal ya ɗebo ƴan fashi, sun je sun kashe Alhaji har lahira sun ɗebi kuɗi masu yawan gaske. Nan take kuwa na gigice, da sauri na sauko daga kan gadon, da ƙarfi nake cewa “Wallahi ba Faisal ne ya kashe Alhaji ba” da sauri Lawan mai gadi yasa hannunsa ya toshe min bakina, yana cewa “Idi ka yi shiru da bakinka, idan har ba ka son kai ma a kashe ka” koda jin abin da ya faɗa min sai nan take gargaɗin da Hajiya Bilkisu ta yi min ya faɗo min cikin raina. Nan take kuwa na yi shiru da bakina, muna ji muna gani ƴan sanda suka je suka tafi da Faisal, alhalin ba shine ya aikata kisan nan ba, ni dai na fi mayar da zargina akan Hajiya tunda har gargaɗi ta yi mana ni da Lawan bayan wanda ta yi min da farko, a wannan karon haka ta ce, “Sai ta saka an kashe mana iyalanmu da mu kanmu, idan har muka faɗi wani abin akanta, shi yasa muka yi shiru da bakinmu, amma maganar gaskiya ba Faisal ne ya aikata kisan nan ba, sharri ne kawai aka yi masa.
Idi mai gadi yana zuwa nan a zancensa, sai ya fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Domin gani yayi a lokacin komai ya dawo masa sabo, gani yake shi yayi sanadiyyar shigar Faisal cikin wannan halin, rarrashin shi Barrister Shaheedah ta shiga yi, da kyar ta samu yayi shiru. “Ka yi haƙuri Idi komai ya kusan zuwa ƙarshe, da yardar Ubangijin talikai”.
Ɗaga hannayensa sama yayi ya ce, “Ya Allah ka fitar da bawanka daga tsanani, domin Faisal bai ji ba, bai gani ba, yau ga shi a cikin halin ƙaƙa nika yi” murmushi Barrister Shaheedah ta yi ta ce, “Ashe haka ka iya Hausa?” Sai a sannan ya saki ransa, ya saki wani murmushi ya ce, “Da farko don ki rabu da ni, na nuna miki ban iya Hausa sosai ba, amma da fahimci ta wannan hanyar ce kaɗai zan iya taimakawa bawan Allah Faisal, sai na saki raina, kuma na faɗa miki iyakar gaskiyar da na sani.”
Miƙewa tsaye Barrister Shaheedah ta yi, duban Idi mai gadi ta yi kafin ta ce, “Malam Idi na gode maka sosai, bisa bani haɗin kanka da kayi” murmushi yayi ya ce, “Hajiya ai nima sai na yi miki godiya, domin kin taimaka mini wajen warkar min da ciwon da yake damuna a cikin zuciyata".
Ɗaukar jakarta ta yi sannan ta kalli Idi mai gadi ta ce..............
Kuyi haƙuri da wannan ina alfahari da ku my fan's na AYI MIN ADALCI.
Idan har kuna son ku rinƙa samun update kullum, sai kun dage da yawan comment domin maganar gaskiya ina raina yawan masu yi min comment.
Hussain Yusuf
08109373275.
*King and Queen Writing Chamber*
.*⚖️AYI MIN ADALCI⚖️*
NA
HUSSAIN YUSUF
*King and Queen Writing Chamber*
*Page 17&18*
Ɗaukar jakarta ta yi, sannan ta kalli Idi mai gadi ta ce, “Malam Idi ko ka san sirrin da yake tsakanin Hajiya Bilkisu da Faisal?” Girgiza kai yayi ya ce, “Wallahi Hajiya nima abin da nake ta son na sani kenan, domin na lura akan wannan sirrin ne, Hajiya Bilkisu ta kashe mai gidanmu Alhaji Hashim....” Jinjina kai Barrister Shaheedah ta yi ta ce, “Shikenan babu damuwa, amma ina buƙatar abu guda a wajenka.”
Da mamaki ya kalleta ya ce, “Wacce buƙata ce wannan Hajiya?” Ɗan murmushi ta yi sannan ta ce, “Ina son ka yi min alƙawarin, idan ranar zaman kotu yayi, ina son ka fito gaban kotu ka yi musu wanann bayanin da ka yi min” shiru yayi yana tunani daga can ya nisa ya ce, “Hajiya kar ki damu na yi miki alƙawarin, indai an kira ni gaban kotu zan fito na bayar da shaidar iya abin da na sani, indai Faisal zai fita daga wahalar da ya faɗa.” Wani daɗi ne ya ziyarci zuciyar Barrister Shaheedah duban Idi mai gadi ta yi sannan ta ce, “Yawwa ina son ka riƙe wannan maganar da muka yi ni da kai, ta zama sirri. Kar ka bari kowa ya sani, idan Hajiya Bilkisu ta dawo ka sanar da ita na zo....”
A firgice Idi mai gadi ya dubi Barrister Shaheedah ya ce, “Me yasa kika ce na faɗa mata?”
“Gobe idan Allah ya kaimu zan dawo gidan nan, kuma wajenta zan dawo. Amma idan ka faɗa mata cewa na zo, ka nuna mata ba abun da na tambaye ka, ita na zo yi wa tambayoyi kuma ban sameta ba, amma gobe zan dawo.”
Ajiyar zuciya Idi mai gadi ya sauke ya ce, “Shike nan Hajiya in sha Allahu zan sanar da ita, amma fa ina jin tsoron kar ta zarge ni ko na tona mata asiri” murmushi Barrister Shaheedah ta yi ta ce, “Kar ka damu ba abun da zata fahimta, har mu gama bincikenmu, domin zaka sha mamaki a ranar zaman kotu, domin Hajiya Bilkisu a ranar za ta girbi abin da ta shuka, kuma a ranar za ta san ni Barrister Shaheedah ba kanwar lasa ba ce.” Ɗan murmushin yaƙe Idi mai gadi yayi ya ce, “Ni kuwa zan so na ga wannan ranar domin Hajiya Bilkisu, za ta ƙasƙanta a gabana, Allah yasa a yanke mata hukuncin kisa.” murmushi kawai Barrister Shaheedah ta yi, sannan ta ciro kuɗi a cikin jakarta ta miƙawa Idi mai gadi. Karɓa yayi yana cewa “Hajiya wannan kuma na menene?” Ƴar dariya Barrister Shaheedah ta yi, ta ce, “Wannan kyauta na baka, saboda na ji daɗin haɗin kan da ka bani”.
Karɓa yayi yana ta faman zuba mata godiya, kamar wacce ta bashi kyautar kujerar Makkah. Saboda daɗin da ya ji har cewa yake “Rabon da ayi min kyautar kuɗi a cikin gidan nan, tun marigayi Alhaji yana da rai, amma bayan mutuwarsa babu wanda ya ƙara ɗaukar naira ɗari ya bani. Wata ran ma sai albashina sai wata ya kusan ƙarewa aka ba ni, idan kuma na yi magana a ce min idan ba zan iya ba na tafi....”
“Da izinin Allah komai ya kusan zuwa ƙarshe” Barrister Shaheedah ta faɗa tana yiwa Idi mai gadi kallon tausayawa, daga bisani kuma ta ce, “Malam Idi ni zan tafi sai goben idan na dawo”.
“To, Hajiya Allah ya kiyaye hanya, Allah ya bayar da sa'a da nasara a duk abin da aka saka a gaba.”
Da amin Barrister Shaheedah ta amsa sannan ta fice daga cikin gidan, zuciyarta fes aikinta yana tafiya dai-dai yadda take so. A ƙofa ta tarar da me keke napep ɗin yana jiranta, tana zuwa kuwa ta shiga, shi kuma ya ja suka tafi.
**************
Su Hajiya Bilkisu da ƙawarta Bara'atu, suna tafiya a mota, sai faman hirarsu suke yi, cikin nishaɗi da farin ciki. Hajiya Bilkisu ce ta kalli Bara'atu ta ce, “Kin ga ƙawata Faisal sai ya gane kurensa, sai ya san ni ba kanwar lasa ba ce, sai ya gane ruwa ba sa'an kwando bane, a ranar da za'a yi zaman kotu, a ranar zai banbamce tsakanin aya da tsakuwa.” Tana faɗin haka, suka bushe da dariya, har da tafawa.
Cikin dariya Bara'atu ta ce, “Kai ƙawata ba ki da dama wallahi” a haka dai suka yi ta hirarsu, cikin walwala da annashuwa. har suka fito bakin titi, suna hawa kwalta kuwa suka miƙi titi, cikin matsanancin gudu. Suna cikin tafiya suna hirarsu, yawancin hirar akan Faisal ne, suna ta tattaunawa akan irin rayuwar da zai yi a prison, sai su bushe da dariya, da haka har suka yi nisa a tafiyarsu. Dafe ƙirji Hajiya Bilkisu ta yi cikin tashin hankali ta ce, “Na shiga uku!!” Da sauri Bara'atu ta kalleta ta ce, “Ƙawata me ya faru kuma?” cike da tsananin tashin hankali, Hajiya Bilkisu ta ce, “Wallahi mun yi babbar mantuwa.....”Da mamaki Bara'atu ta dube ta ta ce, “Mantuwa kuma? To, me muka manto?”. “Wallahi kwata-kwata na manta, ban faɗawa boka yayi mana aiki akan wannan shegiyar lauyar ba.”Dafe ƙirji Bara'atu ta yi, ta ce, “Gaskiya mun yi babbar mantuwa, kuma ga shi bana son komawa garin nan, don yanzu ma ba kiji yadda na gaji ba. Amma ina da shawara.” Da sauri Hajiya Bilkisu ta ce, “Wacce shawarar ce da ke?” Ɗan rage gudun motar Bara'atu ta yi, sannan ta dubi Hajiya Bilkisu ta ce, “Kin tuno da Lubabatu?” Sai da Hajiya Bilkisu ta ɗan yi jim sannan ta ce, “E, na tuno ta. Murmushi Bara'atu ta yi, sannan ta ce, “Yawwa! Kin san dai yadda ta ƙware a wajen munafurci, da kuma haɗa faɗa ko?”
Jinjina kai Hajiya Bilkisu ta yi, ta ce, “Ƙwarai kuwa ni zan faɗa miki wannan domin ta yi min na gani, kuma har abada bana son sake haɗa wata mu'amala da wanann munafukar matar.”
“Yanzu kuwa kike buƙatar Lubabatu a cikin rayuwarki..” Da mamaki Hajiya Bilkisu ta dubi Bara'atu ta ce, “Kamar yaya? kiyi min bayani sosai yadda zan fahimta”, mayar da hankalinta kan tuƙin da take yi, ta yi sannan ta ce, “Kin san wannan hatsabibiyar lauyar na santa, domin lokacin da Garzali ɗan wajena yayi wa wata budurwa fyaɗe, ita ce ta shiga ta fita sai da ta ga alƙali ya yanke masa hukunci, kuma ba irin kurɗa-kurɗar da ban yi ba, na je wajen bokaye sosai akan su yi min maganinta, amma sun kasa. Shi yasa na rabu da ita, sau uku ina sakawa a kashe min ita, amma ba su taɓa samun nasara akanta ba, har sai da Garzali ya je prison kuma duk ita ce sanadi. Shine nake ganin, idan ma mun haɗa ta da bokaye sai dai su ci kuɗinmu, domin ba za su iya yi mata komai ba. Shiru ta yi tana jan numfashi sannan ta cigaba da cewa.......
“Shine nake ganin idan ba za mu iya hanata ta hanyar asiri ba, to, mu biyo mata ta hanyar makirci. Idan har muka kira Lubabatu, muka yi mata bayanin komai, tabbas za ta san abin da za ta yi domin ta kawo mana ƙarshen wanann tantiriyar yarinyar.” Numfasawa Hajiya Bilkisu ta yi, sanann ta ce, “Shikenan ƙawata idan mun koma gida, sai ki kira Lubabatun kiyi mata bayanin komai, ki faɗa mata ko nawa ne za mu iya ba ta indai har ta dakatar da lauyar nan daga shiga sabgoginmu......”Daga nan babu wanda ya ƙara cewa komai a cikinsu, har suka iso cikin gari, kai tsaye gidanta ta nufa da yake cikin unguwar Sarki Kaduna. Ba su yi wata doguwar tafiya ba, sai ga su sun iso ƙofar danƙareren gidanta, horn ta yi, nan da nan Idi mai gadi ya wangale mata gate, nan take kuwa ta cusa hancin motar cikin gidan. Sai faman sannu da zuwa yake ta faman jero musu, amma duk cikinsu babu wanda ya ɗaga kai ya kalleshi, ganin suna niyyar shigewa cikin falon gidan, kuma ya tuna bayan mutuwar Alhaji, Hajiya Bilkisu ta yi musu iyaka da shiga cikin falonta. Da gudu ya je ya sha gabansu, wani mugun kallo Hajiya Bilkisu ta watsa masa ta ce, “Kai Idi lafiya muna tafiya zaka zo ka sha gabanmu?” Ɗan sosa kai yayi ya ce, “Lafiya ƙalau Hajiya saƙo aka faɗa mini na sanar da ke..” “Mtssssss!!!!” Sai da ta ja wani dogon tsaki sannan ta ce, “Waye ya baka saƙon?” Wata ƴar dariya yayi ya ce, “Ta faɗa mini sunanta wai BARRISTER SHAHEEDAH ” duffff!!! haka kirjin Hajiya Bilkisu ya buga, cikinta ya bayr da sautin ƙulululu, saboda tsabar firgitar da ta yi. A kiɗime Hajiya Bilkisu ta dubi Idi mai gadi ta ce, “Wanne saƙon ta baka ka bani?”
“Haka ta ce min na faɗa miki ta zo bata same ki ba, amma gobe za ta dawo....”murya a sama Hajiya Bilkisu ta ce, “Ta dawo ta yi min uban me a gida, Wallahi! Wallahi!! ta dawo min cikin gidan nan sai na saka an yi mata ɗan uban duka. Ni zata rainawa hankali, kenan ma ni take zargi da aikata kisan ko me?” Ita dai Bara'atu ta yi tsaye, ta rasa bakin magana domin mamakin Barrister Shaheedah take yi, to akan me zata zo neman Hajiya Bilkisu ko kuma ta gano ita ce ta aikata kisan?Kallon Idi mai gadi Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Da ta zo ta yi maka tambayoyi? Da sauri kuwa ya ce, “A'a Hajiya ni babu tambayoyin da ta yi min, kawai ke ta tamabaya kuma na ce mata ki fita.”
Kallon Idi mai gadi ta yi ta ce, “Je ka koma wajen aikinka, Allah ya kai mu goben ta zo ina jiranta” da gudu kuwa Idi mai gadi ya koma ƙofar gate, wani daɗi yake ji yanda ya ga Hajiya Bilkisu ta firgita daga faɗin sunan Barrister Shaheedah. Addu'a yake yi a cikin ransa, akan Allah ya baiwa Barrister Shaheedah sa'a da nasara akan mutanen nan.
Hajiya Bilkisu kuwa yayin da ta shiga cikin falon, zubewa ta yi akan wata kujera 2seater. Sai faman ajiyar zuciya take saukewa, a can ƙasan zuciyarta kuwa wani haushin Barrister Shaheedah ne a cushe a ciki, a yanda take jin haushinta yanzu zata iya aikata mata komai, yayin da ta zauna shiru ta yi tunani kala-kala ya cika mata zuciya. Dafa kafaɗarta ta ji an yi, ko ba'a faɗa mata ba, ta san ƙawarta ce Bara'atu. “Ƙawata ki kwantar da hankalinki, in sha Allahu na yi miki alƙawarin duk rintsi duk wuya, wannan lauyar ba zata yi nasara akan mu ba.” Miƙewa tsaye Hajiya Bilkisu ta yi, juyawa Bara'atu baya ta yi, sannan ta ce, “Wallahi ƙarya take, bata isa ba. Ni Hajiya Bilkisu za ta yiwa haka? To wallahi sai na nuna mata cewa duk lalacewar kura tafi ƙarfin kare ya kawo mata wargi....Sai na nuna mata ni ɗin ba kanwar lasa bace.”Kama hannunta Bara'atu ta yi ta zaunar da ita a gefen gado, har sai da ta samu nutsuwa. Sannan Bara'atu ta dubeta a nutse ta ce, “Haba ƙawata, me yayi zafi haka? da har kike ƙoƙarin ficewa daga hayyacinki, abin kunya ne ace wata ƴar yarinya wacce ba ta kai kwatar shekarunki ba duk ta bi ta ɗaga miki hankali har haka.”
Miƙewa tsaye Hajiya Bilkisu ta yi, ta dubi Bara'atu ta ce, “Babban abin da yafi ɗaga min hankali shine; yadda kika bani labarinta, wallahi tsoro take bani, tsorona ma ɗaya kada Faisal ya sanar da ita wannan sirrin da yake tsakanina da shi, domin duk ranar da duniya ta san wannan sirrin to Wallhi na gama tagayyara a duniyar nan, kuma Hausawa sun ce ɗan hakin da ka raina.....Shine yake tsone maka ido...”
“Haka ne ƙawata! Amma ina son ki sani cewa duk sammakonka wani a tafe ya kwana. Kuma abin da babba ya hango, yaro ko ya hau kan tsauni ba zai iya hango shi ba, ina son ni da ke mu haɗa kai mu nunawa yarinyar nan daɗewa a duniya ma wani abu ne daban.”Bara'atu ta faɗa tana faman huci, kamar wata zakanya. Domin zuwa wannan lokacin, ta fara jin haushin Barrister Shaheedah, kuma ta sha alwashin wannan karon ba ta isa ta yi nasara akansu ba, indai tana numfashi a doron ƙasa.
Dubanta Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Don Allah kiyi ƙoƙari kiyi magana da Lubabatun a cikin daren nan, domin nafi son ayi komai da wuri, tun kafin lokaci ya ƙure mana” ajiyar zuciya Bara'atu ta sauke ta ce, “in sha Allahu zan yi magana da ita, wayanta ba ta shiga, shi yasa ma ban kirata ba, amma yanzu idan na fita ta gidansu zan biya mu tattauna akan lamarin. Ina mai tabbatar miki Lubabatu da wuri za ta samo mana mafita.” Tana faɗin haka ta ɗauki jakarta sanann ta kalli Hajiya Bilkisu ta ce, “Ƙawata ni zan tafi, duk yanda muka yi da Lubabatun zan sanar da ke ta waya.”
Miƙewa tsaye Hajiya Bilkisu tayi hade da cewa “To, ƙawata nagode sosai Allah ya bar zumunci, mu je na raka ki, a tare suka fice daga cikin falon......
***************************
Goggo ce a zaune, tana wanke kwanukansu na abinci. Kome ta tuna kuma, sai kawai ta bar yin wanke-wanken ta zuba tagumi. Hawaye ne ya rinƙa biyo kan fuskarta, hannu tasa ta goge, amma sai ga wani ya sake fitowa. A fili ta furta “Ya Allah ka kuɓutar da Faisal daga sharrin azzaluman bayinka.”
Habibu ne ya shigo cikin gidan, hannunsa riƙe da Anwar yana tsotsan alewar lollipop, yana ganin Goggo ya tafi da gudu ya ɗare cinyarta alewar ya miƙa mata ya ce, “Goggo kin ga Abba ƙarami ya siyo min alawa, karɓi ki sha” sanin halinsa yasa Goggo ta karɓi alawar ta ɗan tsotsa, sannan ta ba shi ta ce, “Ungo alewarka ɗan Goggo” karɓa yayi ya tashi daga kan cinyarta da gudu ya shige cikin ɗakin Goggo, wai zai ɗebo kayan wasansa. A tare Habibu da Goggo suka bi shi da kallo, har ya shige cikin ɗakin, Goggo ta daɗe tana kallonshi, sanann ta juyo ta kalli Habibu ta ce, “Allah sarki yaro! Ka ga har ya manta da babansa ya daina tambayarsa” murmushi Habibu yayi ya ce, “Ai Goggo haka lamarin yara yake, suna da mantuwa, amma yanzu da zai ga mahaifin nasa tuni zai tuno shi gyaɗa kai Goggo ta yi, cike da tausayawa Goggo ta ce, “Hakane kam wallahi......” Wata kujera ƴar tsugunne Habibu ya jawo ya zauna, sannan ya fuskanci Goggo ya ce.......“Goggo an kusa a fara zaman kotun nan fa dana faɗa miki” ajiye wanke-wanken Goggo ta yi ta dubi Habibu ta ce, “Yaushe ka ji ance za'a yi zaman kotun?”
“Ai Goggo ina tunanin saura kwana uku” jinjina kai Goggo ta yi ta ce, “Shike nan to, Allah yasa mu ji alkhairi?” Da amin Habibu ya amsa, sannan yake kokarin tashi, dakatar da shi Goggo ta yi ta ce, “Dakata Habibu akwai abun da nake son tambayarka” babu musu kuwa ya koma ya zauna, yana mai fuskantar Goggo ya ji abin da za ta ce.......
. “Wai ni kam Habibu ya kuka yi da lauyar nan da ta ce zata taimakawa Faisal?” Ɗan murmushi Habibu yayi ya shafa kansa ya ce...................
Hussain Yusuf
08109373275
*King and Queen Writing Chamber*
*⚖️AYI MIN ADALCI⚖️*
NA
HUSSAIN YUSUF
*King and Queen Writing Chamber*
*Page 19&20*
Ɗan murmushi Habibu yayi, ya shafa kansa ya ce, “Ai Goggo jiya mun yi magana da ita, a waya ta sanar da ni cewa aikinta yana tafiya dai-dai yadda take so, kuma ta fara samun nasara a bincikenta”murmushi Goggo ta yi, ta ce, “Alhamdulillahi! Allah ya taimaka, Allah yasa gaskiya ta bayyana a ranar zaman kotun nan.”
“Amin Goggo ai ina mai yi miki albishir ɗin Faisal ya kusa fitowa”.
“To, Habibu Allah ya nuna min wannan ranar.” Murmushi Habibu yayi ya ce, “In sha Allahu Goggo za ki ga Faisal ɗinki ya fito cikin kwanciyar hankali.”Gyara zama Goggo tayi ta ce, “Ai kullum cikin addu'a nake ba dare ba rana, duk don saboda Faisal ya fito, kuma na tabbata Allah ne ya fara amsar roƙona” ƴar dariya Habibu yayi ya ce, “Gaskiya ne Goggo Allah ya sa Faisal ya fito a cikin ƴan kwanakin nan.” da amin Goggo ta amsa, sannan ta ɗauki buta ta shiga cikin banɗaki.
****** ********
A zaune take tana ta faman danna waya, gaba ɗaya hankalinta ya koma kan wayar da alama abin da take yi da wayar yana da matuƙar muhimmanci a gare ta. Daga can soron gidan ta ji sallama, ajiye wayar ta yi, ta tashi ta nufi soron domin ta ga me yin sallamar. Tana zuwa turus ta yi, fuskarta ɗauke da mamaki ta dubi mai sallamar ta ce, “Bara'atu! Dama kece mai yin sallama? me yasa kika ƙi shigowa?” Dariya Bara'atu ta saka sanann ta ce, “Lubabatu Wallahi sauri nake yi shi yasa ba zan shiga ba.”
“Haba Bara'atu karki yi min haka, ki daure ki shigo ko ruwa ki ɗan sha ai zan ji daɗi” ganin yadda ta damu yasa Bara'atu ta ce, “Shikenan Luba tun da kin matsa sai na shiga, mu je na shiga amma ba daɗewa zan yi ba.”
“E, na ji to, ai dai kin shiga” a tare suka ƙarasa shiga cikin gidan, Lubabatu da kanta ta ɗaukowa Bara'atu kujera ƴar tsugunne, zaunawa Bara'atu ta yi. Sannan Lubabatu ta je ta ɗauko mata ruwa a fridge ta ajiye mata a gabanta. Ita ma wata kujerar ta ɗauko ta zauna, sannan ta fuskanci Bara'atu ta ce, “Bara'atu me yake tafe da ke? Don da ganinki na san wannan zuwan naki ba'a banza ba” Gyara zama Bara'atu ta yi ta ce, “Gaskiya ne hasashenki ya tafi dai-dai, wata buƙata ce ta kawo ni wajenki, kuma buƙatar ba tawa ba ce, ta mutuniyar ce. Ta ce, na faɗa miki idan har kika yi mata yadda take so, to za ta dawo da ke aminiyarta kuma ta yafe miki laifin da kika yi mata a baya, bayan maƙudan kudaɗen da zaki samu daga wajenta.” Murmushin jin daɗi Lubabatu ta yi, cike da zumuɗi ta ce, “Bara'atu wannan wacce irin buƙata ce mai girma da Hajiya take nema a wajena?”
“Kawo kunnenki ki ji” nan take kuwa Lubabatu ta miƙa wa Bara'atu kunnenta ta faɗa mata komai. Dariya Lubabatu ta saka irin ta ƴan duniyar nan, dariyar ta cigaba da yi kamar ba za ta daina ba, har sai da ran Bara'atu ya ɓaci, cikin fushi ta ce, “Don Allah mafita muke nema a wajenki amma sai faman wata shegiyar dariya kike yi” murmushi Lubabatu ta yi ta ce, “Ai wannan aikin shan ruwa ma ya fishi wahala, ai wannan lauyar da kike faɗa min na santa na san gidansu, ke ƙarewa ma na san har iyayenta kuma na san halin kowanne a cikinsu. Saboda haka ki sanar da Hajiya ta kwantar da hankalinta tamkar tsumma a cikin randa, ranar zaman kotu za ta sha kallo kuma za ta sha mamaki sosai, domin wannan lauyar idan ba da makirci aka biyo mata ba da wuya a iya dakatar da ita daga abin da ta yi niyya.” Cikin jin daɗi Bara'atu ta ce, “To, Lubabatu! Ni zan koma don akan hanya nake, idan kin gama shirin naki ko kuma kina buƙatar wani abun yanzu zan baki lamban Hajiya sai ku yi magana ta waya.”
“To, shikenan ƙawata in sha Allahu wannan karon lauyar nan, za ta san ta haɗu da makircin Lubabatu” tafawa suka yi ita da Bara'atu har da shewa, sannan Bara'atu ta miƙe tsaye ta ce, “Luba kawo wayar taki na saka miki lambar Hajiyar” mike tsaye Luba ta yi, sannan ta shiga cikin ɗakinta sai gata ta fito da wayarta a hannu. Miƙawa Bara'atu ta yi, ita kuma ta saka mata lambar Hajiya Bilkisu, sannan ta yi mata sallama ta tafi...........
===============
Barrister Shaheedah kuwa, yayin da ta baro gidan Hajiya Bilkisu, kai tsaye gidansu ta nufa domin ta gaji sosai. Kuma ga yamma tayi, tana buƙatar hutu, domin ta samu ta tattara hujjojinta waje guda, yadda za ta ji daɗin bai wa Hajiya Bilkisu kunya a kotu.
Lokaci zuwa lokaci, sai Barrister Shaheedah ta saki wani murmushi. Wanda ni kaina ban san ma'anarsa ba, da haka dai har ta ƙaraso ƙofar gidansu. A zaune ta tarar da mahaifinta shi da wasu mutane, da alama dai abokansa ne. Har ƙasa ta durƙusa ta gaishe su, cike da fara'a da yabon kyawawan halayenta suka amsa mata gaisuwar. Saɓanin mahaifinta da ya rinƙa wurga mata harara, sau ɗaya ta kalle shi ta sunkuyar da kanta ƙasa. Sannan ta tashi jikinta a sanyaye ta shiga cikin gidan.
Bayan ta shiga ne, wani dattijo daga cikin abokan mahaifin nata ya kalli mahaifin Barrister Shaheedah ya ce, “Malam Hamza wai sai yaushe zaka aurar da Shaheedah ne? Na ga yarinyar ta girma kuma naga tana da hankali sosai, domin da wuya a samu kamarta a cikin unguwar nan” ɓata rai yayi ya ce, “Malam Tanimu nima kaina ba tun yanzu nake son aurar da wannan yarinyar ba amma mahaifiyarta ce ta dage akan wai sai ta zama lauya, kuma yanzu ta zama lauyar na sake yin magana ta sake cewa wai mu rabu da ita ta zaɓi wanda take so da kanta, shi yasa ma ni duk na watsar da ita, idan aikin ne taga ya fiye mata sai ta je tayi ta yi......”Jinjina kai Malam Tanimu yayi ya ce, “Allah ya kyauta! Amma dai yakamata ace yanzu Shaheedah tana da miji......” Shiru yayi na rabin lokaci, sanann ya cigaba da cewa “Don Allah Malam Hamza idan ka tashi aurar da Shaheedah ina yiwa ɗan wajena Mukhtar kamu”. Murmushi mahaifin Shaheedah yayi ya ce, “Haba Malam Hamza bai kamata muyi ta maimaita zance ɗaya ba, ina yanzu na gama fada maka cewa mahaifiyarta ta ce, baza'a yiwa ƴarta auren dole ba...Sai ta samu wanda take so da kanta sannan mu kuma mu aura mata shi, ni dama bani da burin yiwa ɗiyata auren dole, koda mahaifiyarta bata hana ba.” Ƙwafa Malam Tanimu yayi ya ce, “Shikenan Malam Hamza nagode ni bari na tashi zan shiga gida” bai tsaya jin abinda mahaifin Shaheedah zai faɗa ba yayi tafiyarsa ya bar shi tsaye yana ta faman kiransa amma ko ya waigo mutane kenan................Yayin da Barrister Shaheedah ta shiga cikin gidan, mahaifiyarta ta tarar tana ta faman ƙoƙarin haɗa musu abincin dare, murmushi ta yi sannan ta ce, “Assalamu alaikum” da sauri Umma ta ɗago da kanta daga aikin da take yi tana ganin Barrister Shaheedah sai ta saki wani murmushi ta ce, “Wa'alaikummussalam ɗiyata har kin dawo ne?” ajiye jakarta ta yi ta ce, “Wallahi Umma na dawo” zama ta yi akan wata ƴar kujera tare da cewa “Washhh!! Umma wallahi yau na gaji sosai a wajen aiki” cike da tausayawa ta ce, “Ayya!! sannu! Ai ba zama zaki yi ba, tashi zakiyi ki je kiyi wanka sannan ki zo ga abincinki na saka miki a cikin flask sai ki ci abinki da ɗuminsa, sannan ki kwanta ki huta sai kuma gobe idan Allah ya kaimu” murmushi ta yi ta ce, “To, Umma bari na tashi na yi wankan, amma fa barci bai kama ni ba...” Da mamaki Umma ta kalle ta ta ce, “Subhanallahi! Me yasa baza ki yi barcin ba? Kuma ga shi kin ce gaji sosai?” Murmushi ta yi ta ce, “Ai Umma yanzu na fara samun nasara akan case ɗin matashin nan da na baki labari, shi yasa ba zan yi barci ba har sai na gama tattara rahoton waje guda, yadda zan ji daɗin bayar da shaida a kotu.” Ɗan murmushi Umma ta yi ta ce, “Kai amma gaskiya na ji daɗi sosai, kuma abin alfahari ne ace ta sanadinki wannan matashin zai fita daga cikin bala'in nan da wasu suka jefa shi.”
“Ai Umma a ranar zaman kotu duk sai sun raina kansu, jira nake ranar kawai ta yi, domin na tabbatar musu ni ɗin ba abar wasa ba ce....”Dariya Umma ta yi ta ce, “Gaskiya ne ƴata ta kaina, amma fa gaskiya ki rinƙa kula sosai domin ba na son wasu su cutar min da ke ko kaɗan...”
“In sha Allah Umma babu abin da zai same ni har a kammala wannan case ɗin, zan kula da kaina sosai”.
“Har kinsa ka naji daɗi wallahi, Allah ya bayar da sa'a da nasara Allah kuma ya ƙara kare ki daga sharrin mutane da aljanu.” Da amin Barrister Shaheedah ta amsa sannan ta mike tsaye ta dubi Umma ta ce, “Umma ni zan shiga ciki na yi wankan”
“To ƴar Umma sai kin fito” har ta shiga cikin ɗakin Umma ba ta daina kallonta ba tana sakin wani murmushi, daga nan ta juya ta cigaba da aikin da yake gabanta.
*******
Hajiya Bilkisu kuwa bayan tafiyar ƙawarta Bilkisu, ita ma tashi ta yi ta shiga cikin bathroom ta yi wanka, sannan ta fito. Har zuwa wannan lokacin, tunanin Barrister Shaheedah ne fal a cikin zuciyarta, ta rasa ta inda yakamata ta ɓullowa yarinyar, domin ta riga ta san ta da binciken ƙwaƙwaf, duk da Bara'atu ta faɗa mata cewa Lubabatu zata iya yi musu maganinta, amma sam zuciyarta ta ƙi aminta da hakan. Domin haka kawai, idan ta tuno da ita, sai ta ji gabanta yana tsananta faɗuwa, lokaci daya tsoron Barrister Shaheedah ya mamaye zuciyar Hajiya Bilkisu, wanda ko barci ta kwanta sai ta yi mafarkinta, idan kuma ta zauna ban da aikin tunaninta babu abin da yake addabar zuciyarta.
Waya ta ɗauka ta lalubo numban D.P.O bugu ɗaya ya ɗauka, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta yi masa sallama “Assalamu alaikum yallaɓai” daga can ɓangaren D.P.O ya amsa “Wa'alaikissalam! Hajiya an yini lafiya?” Murmushi ta yi kamar yana ganinta ta ce, “D.P.O. ya batun case ɗin nan na Faisal, ni fa gaskiya na gaji har yanzu wanda ya kashe min mijina a ce yana shaƙar numfashi?”
“Hajiya kiyi haƙuri ai ranar Monday mai zuwa zamu mika shi kotu” wani daɗi ne ya ziyarci zuciyar Hajiya Bilkisu sannan ta ce, “To, D.P.O da fatan dai hukunci kawai za'a yanke masa?” Ɗan jim D.P.O.yayi ya ce, “E, to gaskiya Hajiya ba mu samu wata kwaƙƙwarar shaida ba akan zargin da ake yi wa Faisal. Haka kawai dai za mu tura shi kotun, domin mu gaskiya mun gama duk binciken da zamu yi, idan ya so a kotun sai ya samu lauya kema ki samu kinga idan aka zurfafa bincike sai a gano gaskiyar lamari, duk da yake dai shi Faisal ɗin yana da lauya ke yakamata kiyi magana da lauyanki, domin shi ma yayi nasa kokarin.”
Numfashi Hajiya Bilkisu ta ajiye sannan ta ce, “D.P.O amma ba ku bincika wukar nan da na baku ba ko?” shiru D.P.O yayi na ɗan lokaci sannan ya ce, “Wallahi Hajiya ni na manta ma da batun wannan wuƙar sai yanzu da kika bani, amma ba komai ai na bayar da ita a bincika in sha Allahu yanzun nan zan yi magana da wanda yake bincika wuƙar kin ga da zarar mun gano zanen hannun Faisal a jikinta, to kawai idan an kaishi kotu yanke masa hukunci za'a yi....” Murmushin jin daɗi Hajiya Bilkisu ta yi sannan ta ce, “Shike nan D.P.O in sha Allahu gobe zan zo nan station din naku akwai maganar da nake son mu tattauna da kai.”
“To, Hajiya Allah ya kawo ki ina jiranki” daga nan suka yi sallama ta kashe wayar nan take ta fara jin hankalinta ya kwanta, saboda ta san indai an bincika wukar yanda yakamata tabbas za'a ga zanen hannun Faisal a jiki.
Tana ajiye wayar sai ga kiran Bara'atu ya shigo da sauri ta yi picking. Daga can ɓangaren Bara'atu ta ce, “Ƙawata albishirinki!!” da sauri Hajiya Bilkisu ta ce, “Goro ƙawata!!”
“To, ki buɗe kunnuwanki da kyau ki saurare ni”
“Ina jin ki ƙawata”
“To, Lubabatu ta faɗa min duk irin shirin da zata yiwa Barrister Shaheedah, kuma ina mai tabbatar miki wannan shirin zai matuƙar tasiri sosai” da sauri ta ce, “Kai haba ƙawata da gaske kike yi kuwa?” Ɗan ɓata rai Bara'atu ta yi kamar Hajiya Bilkisu tana ganinta ta ce, “Na taɓa yi miki ƙarya ne ƙawata?” Girgiza kai Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “A'a ai nima da wasa nake yi miki..Kiyi haƙuri” daga can bangaren Bara'atu murmushi ta yi ta ce, “Amma tana buƙatar kuɗi masu ɗan kauri, wanda da su zata yi amfani wajen gudanar da plan ɗin nata”
“To, shikenan k'awata ki turon account dinki sai na saka miki kuɗin, idan ya so sai ki bata”
“To, shikenan bari na turo miki” daga nan suka yi sallama Hajiya Bilkisu ta kashe wayar tana sakin wani murmushin farin ciki domin haƙanta ya fara cimma ruwa.............
*Washe gari*
Cikin sauri Hajiya Bilkisu take shiryawa, domin da wuri take son ta je ta samu D.P.O domin akwai magana mai muhimmancin gaske da take son ta yi da shi. Ƙarfe 9:30am dai-dai ta hau motarta ta fice daga cikin gidan, ba ta ɗauki wani dogon lokaci ba, sai ga ta ta isa police station ɗin. Tana zuwa ta yi parking ta fito, sannan ta shiga ciki, ƴan sandan kan kanta ta gani tambayarsu ta yi ko D.P.O. yana ciki? Da sauri kuwa suka ce “E, yana ciki Hajiya” kai tsaye ra nufi ciki ofishin nasa. Tana shiga ta ganshi yana ta faman duba wasu files, mikewa tsaye yayi, ya ce, “Hajiya har kin ƙaraso kenan?”
“E, Wallahi D.P.O ka san yanzu da zafi-zafi ake dukan ƙarfe.....” Gyaɗa kai D.P.O yayi ya ce, “Gaskiya ne Hajiya ga kujera nan ki zauna, jawo kujerar ta yi ta zauna sannan ta gyara zama cikin nutsuwa ta fuskanci D.P.O..............
*Kowa ya tanadi kuɗinsa domin BOOK 1. Ya kusa ƙarewa dama iya book 1 ne free amma book 2 sai an siya.*
Comment and share
Hussain Yusuf
My whatsapp number 08109373275.
*King and Queen Writing Chamber*
*⚖️AYI MIN ADALCI⚖️*
NA
HUSSAIN YUSUF
*King and Queen Writing Chamber*
*Page 21&22*
Cikin nutsuwa ta fuskanci D.P.O ta ce, “Yallaɓai kun gama bincika wukar kuwa?” Murmushi yayi ya ce, “Ai Hajiya a jiyan na sa aka kammala bincikata, kuma cikin ikon Allah mun ga zanen hannun Faisal a jiki” girgiza kai Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Yawwa D.P.O haka nake son ji, amma akwai abin da nake son ka yi min idan har zaka iya”
“Ai Hajiya ki faɗi ko menene in dai a ɓangaren aikina ne, to zan baki gudummawa ɗari bisa ɗari”murmushin jin daɗi ta yi ta ce, “D.P.O ina son a ranar zaman kotu, idan zaku gabatar da laifin Faisal a wajen alƙali to, ku ƙara da cewa ba Alhaji kaɗai yayi niyyar kashewa ba, ku ce har da ni, da bai samu nasara akaina ba, sai yayi raping (Fyaɗe) ɗina ya tafi ya barni a haka, kuma ina son ku ɗora masa laifin fashi da makami, yanda alkali zai fusata ya yanke masa hukunci mai tsaurin gaske.
Shiru D.P.O yayi yana nazari daga can ya nisa ya ce, “Amma Hajiya ta yaya zamu ɗorawa mutum laifin da bai aikata ba? Ki sani fa kisan kanma ni ban yarda Faisal ne ya aikata shi ba kawai dai sharrine nake tunani” a fusace Hajiya Bilkisu ta mike tsaye ta ce, “Dakata D.P.O ba'a kyauta fa zaka yi min wannan aikin ba, biyanka zan yi har naira miliyan biyar idan har ka yi min yadda nake so.”
Jin kuɗin da ta faɗa ne, nan take kuwa D.P.O ya ji a ransa indai zai samu wadannan kuɗaɗen to zai iya aikata ko menene, kallon Hajiya Bilkisu yayi ya ce, “I'am sorry Hajiya, calm down! Na ji zan yi duk yadda kike so, amma fa bana son karya alƙawari ki hana ni kudin da kika yi min alkawari” murmushi ta yi ta ce, “D.P.O ai indai ni ce baka da damuwa ko kaɗan, indai har ka yi min yadda nake so, to, zan ƙara maka kuɗin akan yadda na yi maka alƙawari, zan baka naira 7million naira, indai har kayi min yadda nake so.” Murmushi D.P.O yayi ya ce, “An gama Hajiya in dai wannan ne baki da damuwa, an riga an gama”
“Yawwa yallaɓai yanzu bari na baka rabin kudin idan har na ga aiki ya tabbata zan cika maka sauran kudinka” mikewa tsaye ta yi ta ce, “Zaka iya biyoni mota ka karɓi kuɗin ko kuma ka haɗa ni da wani police ɗin ya karɓo maka”
“Okay Hajiya mu je tare sai na karɓo da kaina, saboda wannan sirri ne tsakanina da ke”
“To, shike nan yallaɓai nagode sosai” mikewa tsaye ta yi, sannan ta ɗauki jakarta ta fita daga cikin ofishin, tana fita D.P.O ya sheƙe da dariya har da dukan benci, a zuciyarsa kuwa har ya fara fasalta abin da zai yi da miliyan bakwai ɗin nan, da Hajiya Bilkisu zata ba shi.
Bata daɗe da fita ba, D.P.O ya tashi ya bi bayanta, a jikin motarta ya ganta a tsaye, tana jiransa. Yana zuwa kuwa ba tare da ɓata lokaci ba, ta buɗe bayan motarta ta ɗauko masa naira 7 million a wata ƴar jaka, cike da murna da zumuɗi ya karɓi jakar da sauri ya buɗe bayan motarsa ya saka su sannan ya kulle ko'ina na motar.
Kallon Hajiya Bilkisu yayi ya ce, “Hajiya ba ki da damuwa kamar an yi komai an gama ne, in sha Allahu za'a aikata yadda kike so, ko fiye da haka ma kike so a yi masa a shirye nake” murmushin samun nasara Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “A'a haka ma ya isa indai ka yi masa haka to ni ka gama min komai”
“Ai Hajiya kawai ki saurari ranar zaman kotu, hukunci kawai za'a yanke masa...” Ƴar dariya ta yi sannan ta ce, “Yawwa yallaɓai ni bari na koma gida, akwai abin da zan yi yanzun nan”...Tana fadin haka ta shige cikin motarta, shi kuma D.P.O komawa yayi cikin ofishinsa, zuciyarsa cike da murnar samun kuɗaden da yayi a lokaci guda......
***********
Sauri kawai take yi ta shirya, domin yau za ta je ta ritsa Hajiya Bilkisu, ta sha alwashin Hajiya Bilkisu da kanta za ta tonawa kanta asiri, kuma da bakinta za ta faɗi duk abin da ta aikata.....Tana cikin shafa hoda, sai ga Umma ta shigo cikin ɗakin, kallon Barrister Shaheedah ta yi, da mamaki ɗauke da a fuskarta ta ce, “A'a Shaheedah ina kuma zaki je da sassafen nan?” Murmushi ta yi ta ce, “Umma zan je gidan Hajiya Bilkisu ne matar uban gidan Faisal, domin akwai tambayoyin da nake son na yi mata”
“Shi yasa kike ta wannan shirin haka da sassafen nan?”
“E, Umma so nake na je na same ta da wuri domin akwai ta da shegen yawo, kamar karya” ɓata rai Umma ta yi a fusace ta dubi Shaheedah ta ce, “To, babu inda zaki je, tsabar zumuɗi ko karyawa baki tsaya kin yi ba, zaki kwashi ƙafafu ki fita? To, babu inda zaki je har sai kin tsaya kin karya” cikin muryar shagwaɓa ta dubi mahaifiyartata ta ce, “Kai Umma ni fa yau bana jin yunwa, kuma idan naje wajen aiki ai zan karya”
“To, ni ban yarda ba, haka kawai, ki je ulcer ta kama ki a banza? To, idan har kina son ki tafi ki barni a cikin farinciki ki tsaya kawai ki karya”...Babu yadda ta iya bisa dole ta haƙura, ta zauna ta ci abincin breakfast ɗin. Amma sama-sama ta rinƙa cin abincin, saboda da duk hankalinta ya riga ya kaɗa can wani wajen dabam, domin babban burinta a yau shine; ta je ta firgita Hajiya Bilkisu ko ranta zai yi sanyi.
Umma ce ta saka ta a gaba har sai da ta cinƴe abincin tas, sannan ta barta ta tashi. Cikin sauri kuwa ta ɗauki jakarta ta fice daga cikin gidan. Tana fitowa waje ta ga mahaifinta shi da wata mata, wacce bata san kowa ce ba. A tsugunne matar take a gaban mahaifin nata sai faman zuba masa zance matar take yi, cikin sanyin jiki ta je gaban mahaifin nata ta tsugunna, gaishe shi ta yi cike da ladabi da biyayya iri ta ɗa a wajen ubansa. Amma da ya amsa mata kamar yadda ta gaishe shi, sai ya turɓune fuska kamar an aiko masa da saƙon mutuwa, sama-sama ya amsa gaisuwar, gaishe da matar ta yi, ita kuwa cike da fara'arta ta amsa da kulawa, sai faman yabon aikin Barrister Shaheedahn take yi, kamar dama ta santa..
Kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, haka ta bar wajen, zuciyarta na ji zafin abin da mahaifinta yayi mata a gaban mutane addu'a ta yi masa a fili ta furta “Ya Allah ka ganar da mahaifina ya daina irin wannan halin”.Tana ƙarasowa bakin titi, keke napep ta tare, shiga ta yi sannan ta faɗa masa unguwar da zai kaita......Nan take kuwa ya ɗauke ta suka tafi, ba su daɗe suna tafiya ba, sai ga su sun ƙaraso ƙofar gidan Hajiya Bilkisu. Fitowa ta yi ta sallami me napep ɗin, ya juya ya tafi, ita kuma kai tsaye ta nufi gidan. Tana zuwa gaban ringijejen gate ɗin, tsayawa ta yi sai da ta ƙarewa gidan kallo tsaf, a fili kuwa ta ce, “Tabbas dole Hajiya Bilkisu ta manta da Allah, irin wannan gidan ƙeruwarsa da kuma girmansa ya isa kaɗai ya shagaltar da kai daga tunawa da Allah, addu'a ta yi a fili ya Allah ka bamu arziƙi dai-dai buƙata amma ba irin wannan ba da zai hallakar da mu ya kai mu jahannama ba mu ji ba bamu gani ba......”
Nocking ta fara yi, Idi mai gadi ne ya leƙo ta wata ƴar karamar ƙofa, yana ganin Barrister Shaheedah ce, sai ya saki wani ɗan murmushi nan take kuwa ya buɗe mata ƙofa shiga ta yi, tana ƙara kallon gidan, domin wancan lokacin da ta zo ba ta ƙarewa gidan kallo kamar yau ba, domin ganinshi ta yi wani ƙaton gida, kuma kallo ɗaya zaka yi masa ka tabbatar da an kashe naira wajen gina wannan ƙayataccen gidan. Idi mai gadi ne ya kalleta ya ce, “Hajiya barka da zuwa” murmushi ta yi ta ce, “Yawwa barka dai Malam Idi yakake ya aiki?”
“Alhamdulillahi! Hajiya aiki kuma ai sai ku”murmushi kawai ta yi ta ce, “Hajiyar taka kuwa tana nan?”Girgiza kai yayi ya ce, “A'a Hajiya bata nan, amma baza ta dade ba yanzun nan zaki ganta ta shigo” cike da mamaki Barrister Shaheedah ta kalle shi ta ce, “Ina kuma ta tafi da sassafen nan?”
“Wallahi ban san inda ta tafi ba, amma ki ɗan jira yanzun nan za ki ganta ta shigo, don ta daɗe da fita.”
“Okay to, bari na jirata ta dawo” da hanzarinsa ya je ya ɗauko mata kujera ya ajiye mata a kusa da fulawowin gidan ya ce, ta zauna. Zuwa ta yi ta zauna, tana duba wani ɗan littafi da yake hannunta.
After 20 minute da zamanta, sai ga Hajiya Bilkisu tana horn a ƙofa, jiki na karkarwa Idi mai gadi ya je ya buɗe mata gate ɗin, a guje kuwa ta danno hancin motar cikin gidan, kai tsaye parking space ta nufa. Tana zuwa ta ajiye motar ta fito, da gudu Idi mai gadi ya je wajenta ya ɗan yi ƙasa da kansa ya ce, “Hajiya kin yi baƙuwa” kallonshi ta yi ta ce, “Wacce baƙuwa ce ba ka faɗa mata bana nan ba ne?” ɗan ƙara sunkuyawa yayi ya ce, “Ranki ya daɗe wannan lauyar ce ta dawo, wai ta zo bincike ne akan kisan Alhaji da aka yi” ba ƙaramin razana Hajiya Bilkisu ta yi ba, amma saboda kada Idi mai gadi ya fahimci wani abu, sai ta ɓoye duk wani tsoro da yake cikin ranta. Cike da ƙarfin gwiwa ta ce, “Je ka shigo da ita ina falo ina jiranta”. A guje kuwa ya juya, ya nufi wajen da Barrister Shaheedah take zaune, zuwa yayi ɗan ƙas da muryarsa ya ce, “Hajiya ta ce, ki ƙaraso tana jiranki”.
Murmushi ta yi ta ce, “Okay bari na je” tashi ta yi ta ɗauki jakarta, sannan ta nufi ƙayataccen falon Hajiya Bilkisu, sai faman sakin murmushi take yi kamar gonar auduga.
Tana zuwa jikin ƙofar a hankali, tasa hannunta ta kama handle din ƙofar, a hankali ta murɗa sai ga kofar ta buɗe. Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga cikin falon, “Assalamu alaikum” lokacin Hajiya Bilkisu tana duba wayarta ne, kwata-kwata bata ji shigowar Barrister Shaheedah ba, sai sallamarta ta ji, cikin fushi ta mike tsaye ta nuna Barrister Shaheedah da yatsa ta ce, “Uban me ya kawo ki cikin gidana?” Barrister Shaheedah ba ta kula ta ba, sai wani taku na ƙasaita take, tana zagaye Hajiya Bilkisu, ita kuwa sai faman binta take da ido, sai da ta gama zagayeta tas, sannan ta je ta samu wata royal chair ta yi zamanta. Har da harɗe ƙafafuwa ta yi wani zama na ƙasaita. Ita dai Hajiya Bilkisu sai ta zama tamkar gunki, mamaki ne ya hana ta magana, to, ita wannan yarinyar me ta taka ne da har za ta zo gidanta ta rinka yi mata wannan shishshigin? Ba ta gama tsinkewa da al'amarin Barrister Shaheedah ba, sai da ta ganta ta tashi cikin takunta na ƙasaita, ta je fridge ta ɗauko juice, sannan ta dauko wasu kofuna guda biyu da suke ajiye akan fridge ɗin, dawowa ta yi ta ajiye juice ɗin akan wani dan ƙaramin center table, sannan ta tsiyaya shi a cikin kofunan. Ɗaukar ɗaya ta yi ta kurɓa, sannan ta kalli Hajiya Bilkisu da take tsaye kamar gunki ta ce, “Hajiya ga lemo nan mai sanyi ki ɗauka ki sha ko zuciyarki za ta yi dan sanyi, daga zafin da ta ɗauka a kaina” tana faɗin haka ta sake tsiyaya lemon ta sake kurɓa. A fusace Hajiya Bilkisu ta nuna ta da yatsa ta ce, “Kece baƙuwar shan lemo munafukar banza, gidan ubanki ne da zaki zo kina nuna min wannan taƙamar? Maza ki tashi ki fitar min daga gida tun kafin na saka a fitar min da ke?”
Ita dai Barrister Shaheedah kawai lemonta take kurɓa, ko ta ɗaga kai ta kalleta. Ita kuwa Hajiya Bilkisu, sai faman cika take tana batsewa saura ƙiris ta fashe. Sau ɗaya Barrister Shaheedah ta kalleta sannan ta sunkuyar da kanta tana sakin wani murmushi. Bayan ta sha lemon wanda zai isheta, sake tashi ta yi ta je ta sake buɗe fridge ɗin ta ɗauko apple a ciki, sannan ta dawo ta zauna ta fara ci hankalinta a kwance.
Cikin murya irin ta wanda yake santi, Barrister Shaheedah ta ce, “Kiyi hakuri Hajiya wallahi ina matukar son apple kuma na ga idan na tambaye ki baza ki bani ba, shi yasa na ɗauko da kaina. Zuwa wannan lokacin, Hajiya Bilkisu ta cika tayi fam! Amma tana tsoron taɓa lafiyar Barrister Shaheedah domin ta san da biyu take yin wannan abin, tabbas ruwa ba ya tsami banza, dole akwai abin da ta taka shi yasa take yi mata irin wannan isar. Cikin fushi Hajiya Bilkisu, ta dubi Barrister Shaheedah ta ce, “Wai ke don Allah menene ya kawo ki gidana da har kika samu damar yi mini wannan cin mutuncin?” Dariya Barrister Shaheedah ta saka sannan ta ce, “Ni Hajiya ba cin mutunci ne ya kawo ni gidanki ba, akwai abin da ya kawo ni.....” Kallonta Barrister Shaheedah ta sake yi ta ga yadda ta wani cika ta yi fam, murmushin mugunta ta saki, sannan ta fara tunanin yadda za ta ƙara fusata Hajiya Bilkisu, kamar wacce aka tsikara ta tashi zumbur ta nufi kitchen ɗin Hajiya Bilkisu, bata jima a ciki ba, sai ga ta ta fito da abinci akan plate har da nama, ai kuwa Hajiya Bilkisu ta fusata ba ta san lokacin da yi kukan kura ta shaƙo wuyan Barrister Shaheedah ta makure ta a jikin gini, tana wani irin huci tamkar wata zakanya.............
_Book 1 fa ya kusa ƙarewa duk mai son ƙarashen labarin sai dai ya biya #300 na saka shi a group ɗin da zai rinka samun update ko kuma ya shiga account ɗina na *Arewa books* ya karanta, amma fa ina tuna muku BOOK 1 ya kusa karewa ku zama cikin shirin biyan kuɗi._
Comment and share
Hussain Yusuf
08109373275
*King and Queen Writing Chamber*
*⚖️AYI MIN ADALCI⚖️*
NA
HUSSAIN YUSUF
*King and Queen Writing Chamber*
*Page 23/24*
Sosai Hajiya Bilkisu ta shaƙe Barrister Shaheedah, idanunta ne suka firfito waje, tana son ta yi ihu amma babu hali. Ko ta yi ma babu wanda zai ji ta, saboda muryarta ma ba zata fita ba, ballantana wani ya ji. Cikin fushi Hajiya Bilkisu take magana “Wallahi sai kin faɗa min abin da kika taka, da har kike min irin wannan cin mutuncin.” Ita dai Barrister Shaheedah ba ta sauraron abin da Hajiya Bilkisu take faɗi, kawai kokarin ƙwatar kanta take. Gaba ɗaya jikinta ya jiƙe da gumi sharkaf, cikin dauriya da jarumta ta hankaɗar da Hajiya Bilkisu, ai kuwa sai gata ta faɗi warwas! a ƙasa, sai faman haki take yi, hannu tasa ta dafe ƙirjinta da yake yi mata wani iri zafi, tamkar garwashi ne yake ruruwa a cikin zuciyarta saboda raɗaɗi da zafin da ta ji tana yi mata.
Cikin kakkausar murya ta ce, “Wallahi idan kika ga kin bar gidan nan, to kin faɗa min abin da ya kawo ki har cikin gidana, na san ba'a banza kike yi min duk wannan abin ba” murmushin ƙarfin hali Barrister Shaheedah ta yi, ta ce, “Ni kuwa nake da dalilina na zuwa gidanki”
“Maza ki faɗa min kafin nasa ayi min ƙasa-ƙasa da ke a cikin gidan nan”
“Maganar ba ta tsaye ba ce yakamata mu zauna, domin sai mun fi fahimtar junanmu”.
Ba tare da wata gardama ba Hajiya Bilkisu ta nemi kujera ta zauna, ita ma Barrister Shaheedah ta samu wata kujerar da take facing din Hajiya Bilkisu ta zauna.
Bayan sun zauna gaba ɗayansu, shiru ne ya wanzu a tsakaninsu, sun kai wajen minti biyar babu wanda ya furta ƙala..........
Ganin shirun yayi yawa ne, yasa Hajiya Bilkisu ta ce, “Ke nake sauraro” gyara zama Barrister Shaheedah ta yi ta kalli Hajiya Bilkisu cikin nutsuwa ta fara yi mata magana.....
“Ba tambayoyi ne suka kawo ni gidan ki ba, kuma ba na zo ne domin na san wani game da kisan da kika aikata ba...” Zazzaro ido Hajiya Bilkisu ta yi, nan take ta fara fita daga hayyacinta sakamakon abin da ta ji Barrister Shaheedah tana faɗa mata.
Gumi ne ya fara tsatstsafi mata, a ɗimauce ta dubi Barrister Shaheedah ta ce, “Waye ya faɗa miki cewa na aikata kisa?” Ɗan murmushi Barrister Shaheedah ta yi sannan ta ce, “Ai ba sai an faɗa min ke kika aikata kisan ba, alamu duk sun nuna kece da sa hannunki a aikata kisan Alhaj.......”
“Ke ya isa haka.....” Hajiya Bilkisu ta faɗa tana mai ɗagawa Barrister Shaheedah hannu, ba shiri kuwa ta yi shiru a zancen nata, tana kallon Hajiya Bilkisu.
“Idan ni kike zargi da kisan kai, kina da hujja ne?”
“Ƙwarai kuwa ni nake da ƙwaƙƙwarar hujja da shaidun, da za su nuna ke ce kika aikata kisan nan......Domin Faisal ya sanar da ni komai a game da ke, hatta sirrin da yake tsakaninku wanda saboda shi kika aikata kisan kai, to duk ya sanar da ni komai, saboda haka sai ki jira ranar monday domin ki karɓi hukuncinki a wajen alƙali.”
Hannu tasa ta share gumin da ya karyo mata, amma tana sharewa sai ga wani gumin ya sake karyo mata. Cikin harɗewar harshe ta dubi Barrister Shaheedah muryarta tana rawa ta ce, “Don Allah ki rufa min asiri” murmushi Barrister Shaheedah ta yi ta ce, “Ta yaya zan rufa miki asiri? Alhalin kece wacce ta kashe mijinta da hannunta, sannan kika nemi saka bawan Allah wanda bai ji ba bai gani ba a cikin masifa, da haka ki ke tunanin zan rufa miki asiri....? Tun wuri ma ki cire wannan tunanin daga cikin ranki, domin buƙatarki ba zata taɓa karɓuwa a wajena ba.”
Tana gama faɗin haka ta ɗauki jakarta, za ta fice daga cikin falon, da sauri Hajiya Bilkisu ta sha gabanta ta haɗa hannuwanta wuri guda ta ce, “Don Allah Barrister na roƙe ki, ki zo mu zauna mu yi magana ta fahimta ni da ke” waigowa Barrister Shaheedah ta yi ta kalli Hajiya Bilkisu, kawar da kanta ta yi, ta kama handle ɗin ƙofar tana niyyar fucewa gaba ɗaya. Da sauri Hajiya Bilkisu ta riko jakarta, tana ta faman haɗa ta da Allah akan ta tsaya.
“Don Allah ki daure ki tsaya mu yi magana mana” a fusace Barrister Shaheedah ta kalli Hajiya Bilkisu ta ce, “Ke nan kin san Allah? Wallahi ba ki san Allah ba, inda kin san Allah ba zaki aikata abin da kika aikata ba.”
Cikin kiɗimewa Hajiya Bilkisu ta ce, “Ni dai na ji! Don Allah ki dawo mu yi magana” dan jim Barrister Shaheedah ta yi, kome ta tuna? Kawai na ga ta juyo ta kalli Hajiya Bilkisu ta ce, “Okay mu je mu zauna, sai mu yi maganar”.
Da sauri Hajiya Bilkisu ta juya ta zauna a kujerar da ta zauna ɗazu, ita ma Barrister Shaheedah ta zo ta zauna ta kalli Hajiya Bilkisu cikin nutsuwa ta ce, “Ke nake sauraro kuma kin yi shiru” sosa kai Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Don Allah so na ke ki rufa min asiri, ki faɗi ko nawa ne zan iya baki wallahi, indai kin rufe sirrina” ɗan jim Barrister Shaheedah ta yi sannan ta ce, “Idan na rufa miki asiri muyi yaya da Faisal kenan?”
“Ai ke lauya ce, kin san hanyoyin da zaki bi domin ki tseratar da shi, ni kuma ki zare ni daga cikin case ɗin” cikin hikima irin ta lauyoyi Barrister Shaheedah ta ce, “To, na ji duk abin da kika faɗa, amma nawa za ki biya ni?”
“Zan baki naira miliyan biyar” a fusace Barrister Shaheedah ta miƙe tsaye ta dubi Hajiya Bilkisu ta ce, “Miliyan biyar fa kika ce? Na ga alamun so kike na bankaɗa sirrinki duniya ta gani” da sauri Hajiya Bilkisu ta ce, “A'a wallahi ba haka bane! Zan baki naira miliyan goma”
Ɓata rai Barrister Shaheedah ta yi cikin ɓacin rai ta fara magana “A gaskiya Hajiya ni ba zan iya yin wannan aikin a naira miliyan goma ba, kisan kai fa kika aikata? Amma kike tunanin zan rufa miki asiri a naira miliyan goma kacal! To yanzu ki ɗauka diyya za ki biya, a tunaninki za'a karɓi miliyan goma ne a matsayin diyya?” Da sauri Hajiya Bilkisu ta ce, “To, na ji shikenan, zan baki naira miliyan hamsin” sai a sannan Barrister Shaheedah ta yi murmushi ta ce, “To, na ji haka yayi don haka yanzu ba ki da wata fargaba, kiyi zamanki a gidanki, zaki ji an yankewa Faisal hukunci. Domin indai na fitar da shi daga cikin wannan case ɗin, ba'a yanke masa hukunci ba, to indai ya fito sai ya tona miki asirin da kike gudu, kin ga kenan yafi a yanke masa hukuncin kawai. Idan ma rataye shi za'a yi a rataye, kin ga baki da sauran wata fargaba kenan.....”
Girgiza kai Hajiya Bilkisu ta yi alamun gamsuwa da abin da Barrister Shaheedah ta faɗa, nan take kuwa murna da farinciki suka mamaye zuciyar Hajiya Bilkisu “Gaskiya babu wanda ya kaini sa'a a rayuwa, yanzu lauyar ma da nake tunanin za ta zame min ƙarfen ƙafa. Yanzu ga ta a hannuna, sai yadda na yi da......”Muryar Barrister Shaheedah ce ta katseta da cewa “Sai maganar biyan kuɗi ya za'a yi kenan?”
Ƴar dariya Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Ai ta wannan ɓangaren baki da damuwa, yanzu zan baki rabin kuɗin, idan kin kammala sai na cika miki sauran” da sauri Barrister Shaheedah ta ɗaga mata hannu tare da cewa “A'a na yiwa mutane da yawa aiki amma ban taɓa karɓar kuɗinsu ba, har sai na kammala musu aikinsu, saboda haka idan aiki ya kammala zaki biyani kuɗina cass!! idan kuwa kika rage min ko naira ɗaya a ciki, sai na tona miki asiri Wallahi kin ji dai na rantse...? To, ba zan yi kaffara ba.”
Girgiza kai Hajiya Bilkisu ta yi alamun gamsuwa, cewa ta yi “A gaskiya nagode sosai Barrister, kiyi haƙuri da abin da na yi miki da farko. Ban fahimce ki bane shi yasa” murmushi Barrister Shaheedah ta yi ta ce, “Laaa!! Babu komai wallahi, ai don ki ɗauki abin da muhimmancin gaske shi yasa na faɗa miki haka......Amma komai ya wuce a wajena, Faisal ba shi da komai don haka kin san ni bana aikin banza, dama don naji komai shi yasa na je a matsayin wacce za ta kare Faisal a zahiri, amma a baɗini ba shi zan taimakawa ba”.....
Jinjina kai Hajiya Bilkisu tayi, al'amarin Barrister Shaheedah yana matuƙar bata tsoro. Miƙewa tsaye Barrister Shaheedah ta yi sannan ta kalli Hajiya Bilkisu ta ce, “Hajiya na ji duk bayananki, kuma na yi miki alƙawarin zan rufa miki asiri, amma sai kin sanar da ni yadda aka yi kika kashe mijinki Alhaji Hashim” ba tare da tunanin komai ba, Hajiya Bilkisu ta sanar da Barrister Shaheedah duk yadda ta yi wajen kashe Alhaji, har yanda ta yi wajen ɗauko hayar ƴan fashi ta biya su suka kashe mata Alhaji. Tana gama faɗa mata, sai ta saki wani murmushi mai ma'anoni da yawa, wanda ita kaɗai ta san ma'anar yinsa.
Ɗaukar jakarta Barrister Shaheedah ta yi, sannan ta yiwa Hajiya Bilkisu sallama, sannan ta tafi..........
_*WASHE GARI MONDAY*_
7:30am na safe, Barrister Shaheedah ce a zaune tana shan coffee, ga kuma laptop a gabanta. Sai faman danne-danne take yi tana murmushi, ji na yi ta kunna muryar Hajiya Bilkisu yayin da take faɗa mata yanda ta kashe Alhaji Hashim. Tana gama saurara a wayarta, sai kuma ta kunna muryar Idi mai gadi, yayin da yake tonawa Hajiya Bilkisu asiri. A haƙiƙanin gaskiya Faisal bai sanar da Barrister Shaheedah komai ba, a tsakaninsa da Hajiya Bilkisu, ta yi wannan dabarar ne domin Hajiya Bilkisu ta faɗa mata yanda ta kashe Alhaji Hashim da bakinta, kuma aikinta ya tafi dai-dai yanda take so....Yanzu tana da hujjojin da shaidun da zata gabatar a gaban kotu, wanda za su iya sa wa a yanke wa Hajiya Bilkisu hukunci, saɓanin Faisal da kowa yake kallo a matsayin ɗan fashi da makami, murmushi kawai Barrister Shaheedah take saki lokaci-lokaci sai ta ɗauki coffe ɗinta ta kurɓa, a fili ta furta “Hajiya Bilkisu yau kashinki ya bushe, Faisal yau gaskiya za ta yi halinta. A yau mutanen da suke yi maka kallon maci amana za su dawo yi maka kallon managarcin mutum mai riƙon amana, da kuma kare mutuncin shi a duk inda yake...”
Muryar Mahaifinta ta jiyo a ƙofar ɗakinta yana ƙwala mata kira cikin masifa “Shaheedah! Shaheedah!! Wai saboda rainin hankali kina ji ina kiranki amma kin yi shiru kin rabu da ni?” Da sauri ta ɗauko hijabinta ta saka, sannan ta fito ƙofar ɗakin, ta zo har inda yake tsaye ta durƙusa har ƙasa, cikin sanyin murya ta ce, “Baba gani...”
Masifa ya fara zuba mata kamar ba ƴar cikin shi ba, “Yanzu ke Shaheedah kina ji ina kiranki, sai kin ga dama ki fito ko? To, yayi kyau..” Buɗa baki ta yi za ta yi magana, ɗaga mata hannu yayi aikuwa sai ta gumtse bakinta gum...
Cigaba yayi da yi mata masifa “Yanzu ke Shaheedah lalacewar taki har ta kai ki rinƙa zuwa kina kare ɗan fashi da makami? Da sauri ta ɗago kanta da yake sunkuye ta ce, “Baba ɗan fashi da makami fa kace?”
“E, mana ko bakya kare su ne? Wannan yaron da ya aikata kisan kai, waye shi da kika je kotu kare shi? Na ji labarin yau za'a yanke masa hukunci, kuma wai saboda lalacewa wai ke ce wacce za ta kare shi a kotu, Wallahi Shaheedah ba irin tarbiyyar da na baki kenan ba. Inda na san haka zaki rinƙa aikinki, Wallahi tun wuri ba zan barki kiyi aikin ba kwata-kwata.
Ita dai Barrister Shaheedah baiwar Allah shiru ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa, hawaye yana ta faman zuba daga cikin idanunta, addu'a take yi a cikin ranta kada mahaifinta ya hana ta zuwa kotu, ta san indai ba ta je ba, to, Faisal za'a yanke wa hukunci, bai ji ba bai gani ba. Jiyo muryar mahaifinta ta yi a cikin dodon kunnenta yana cewa “Ina so ki buɗe kunnuwanki da kyau ki saurare ni, idan har nine mahaifinki kuma na isa da ke to karki sake na ganki a kotu, a yau ɗin nan. Idan kuwa har kika tsallake maganata kika je domin kare wani banza! To, zan sallamawa duniya ke, har abada mun farraƙe ni da ke, karki sake kallona a matsayin mahaifinki.” Zuciyar Barrister Shaheedah ce ta shiga luguden duka, wani abu ya zo ya tokare mata maƙoshi ta kasa haɗiyar yawu. Ji ta yi ya cigaba da cewa “Ban yarda ki taimakawa wannan yaron ba, ta kowacce fuska, ke ko shaidun da kika tattara ban yarda ki bai wa wani ya je kotun ya gabatar da su ba. Idan kuwa har kika yi haka to har abada ba zan taɓa yafe miki ba, a matsayina na mahaifinki, kuma kin nuna min iyakat....Da sauri mahaifiyar Barrister Shaheedah ta fito daga ɗaki, hannu tasa ta rufe masa baki, tana wani irin huci, cikin raunin murya ta dube shi ta ce, “Malam ta ji za ta yi duk abin da ka saka ta ba sai ka yi mata baki ba” da mamaki Barrister Shaheedah ta kalli mahaifiyarta, tana niyyar buɗa baki ta yi magana amma ba hali, saboda bakin yayi mata nauyi, kallonta mahaifiyarta ta yi cikin tausayawa ta ce, “Shaheedah ki yiwa mahaifinki biyayya......”
Comment and share
Ina tuna muku BOOK 1 ya kusa ƙarewa kowa yayi niyyar mallakar na shi.
Hussain Yusuf
My whatsapp number
08109373275
*King and Queen Writing Chamber*
*⚖️AYI MIN ADALCI⚖️*
NA
HUSSAIN YUSUF
*King and Queen Writing Chamber*
_Wannan shine ƙarshen littafi na ɗaya duk mai son karanta littafi na biyu sai ya biya #300._
*Page 25/26*
Cike da raunin murya ta ce, “Umma kin san me kike faɗa kuwa?”
“Na sani Shaheedah Allah ya ga zuciyarki, amma ko kaɗan bana son naga abin da zai silar lalata miki rayuwa, mahaifinki ya fi komai muhimmanci a rayuwarki, idan har ki ka je kotun ba tare da umarninsa ba, wallahi zai iya tsine miki babu abin da ya shafe shi...”
“Yawwa gara da kika faɗa mata tun wuri, don ni bana magana biyu Wallahi idan har na ji labarin kin je wannan kotun sai na tsine miki albarka kuma sai kin bar min gidana har abada, ki je can ki bi ɗan fashi da makami..” Cikin rawar murya mahaifiyarta ta ce, “In sha Allahu Malam ba zata je ba, ballantana ka tsine mata”.
Nuna ta da yatsa yayi ya ce, “Kin ji dai abin da nace kuma babu wanda ya isa ya sauya min ra'ayina.” Yana faɗin haka yasa takalmansa ya fita waje abinsa.
Fashewa da kuka Barrister Shaheedah ta yi, cikin kukan take magana “Umma wai me yasa Baba ba ya sona? Me na yi masa ne tun ina yarinya ya tsane ni, ban taɓa samun soyayyar da kowacce ɗiya take samu a wajen mahaifinta ba” riƙe hannun mahaifiyarta ta ta yi ta ce, “Umma don Allah ki faɗa min anya Baba ne ya haife n......”Bata gama faɗar abinda yake bakinta ba, Ummarta tayi sauri ta rufe mata baki, ita ma kukan ta saka ta ce, “A'a Shaheedah idan rai ya ɓaci kuma hankali sai ya gushe? To, ina son ki sani duk duniya ba ki da wani uban da ya wuce mahaifinki, shine ya haife ki don haka kar na ƙara jin bakinki ya furta irin wannan mummunar kalmar, so kike maƙiyanki su samu dama akanki wajen ɓata miki suna?”
Girgiza kai ta yi ta ce, “A'a Umma”
“To, kar na ƙara jin wannan maganar a bakinki kin ji ko? Kuma ina son ki saka a ranki, komai rintsi da tsanani ko babu ke babu wanda ya isa yayi wa Faisal komai, sannan ki dage da addu'a biAllah ya kuɓutar da Faisal daga sharrin maƙiya.”
Gyaɗa kai ta yi ta ce, “To, Umma! Yanzu kenan ina ji ina gani za'a yankewa Faisal hukuncin da ba shine ya aikata laifinba? Kuma gani da cikakkiyar damar da zan iya taimaka masa amma Baba ya zo ya hana ni? Umma don Allah ki faɗa min dalilin Baba na hana ni zuwa kotu yau”
“Shaheedah nima ban san dalilin mahaifinki da ya hanaki zuwa kotu ba, amma gaskiya nafi zaton azzaluman da kike ƙoƙarin tonawa asiri sune suka haɗaki da shi.” Sake fashewa da kuka ta yi cikin muryar kukan ta ce, “Yanzu kenan Umma ina ji ina gani za'a zalunci salihin bawan Allah kuma ina da damar da zan taimake shi amma Baba yayi min iyaka?”
Gyaɗa kai Umma ta yi ta ce, “Tirƙashi! Wannan shi ake kira rijiya ta bayar da ruwa kuma guga ya hana. Amma ina son ki saka a cikin ranki komai rintsi da tsanani Faisal zai fita daga cikin wannan bala'in da Allah ya saukar masa, ki saka a ranki Allah ne ya saukar masa kuma shi zai yaye masa kin ji ko? Kuma don Allah ina son ki cire komai daga cikin ranki, kada wani ciwon ya zo ya kamaki, kin san sai nafi kowa shiga damuwa ko? Cikin kuka ta ce, “In sha Allahu Umma zan cire komai daga cikin raina, amma ya zan yi da alƙawarin da na ɗaukarwa Faisal duk rintsi da tsanani zan fitar da shi?”
Hawaye ne ya zubo daga cikin idanun Umma muryarta na rawa ta ce, “Shaheedah Allah ya ga zuciyarki da niyyarki, in sha Allahu ina mai tabbatar miki Faisal ba zai taɓa zarginki da yaudara da karya alƙawari ba....”
Riƙe hannun Ummanta ta tayi hawaye na cigaba da kwaranyowa daga idanunta kallon mahaifiyarta ta take sosai, kamar mai nazarin wani abu. Dakatawa ta yi daga kukan da take yi ƙoƙarin saita kanta ta yi cikin sanyin murya ta fara magana “Umma don Allah zan tambaye ki, kiyi min alƙawarin bani amsar tambayata matuƙar bata ɓata miki rai ba.”
“Shaheedah kiyi duk tambayarki, ina jin ki indai na san abin da kika tambaye ni, to na yi miki zan baki amsar da za ta gamsar da ke.”
“Umma don Allah ina son ki faɗa min asalinmu, daga ina muka fito? Ina ne asalin garinmu? Kuma don Allah ki sanar da ni dalilin da yasa mahaifina ya tsane mu ni da ke, bayan kin taɓa faɗa min cewa auren zumunci aka yi muku ke da shi, kuma kuna matuƙar son junanku to, me yasa ya canja miki yake wahalar da ke yake nuna miki ƙiyayya wacce har ni da kika haifa sai da ƙiyayyar ta shafe ni?”
Shiru mahaifiyar Shaheedah ta yi, hawaye ne ya zubo mata kallon Barrister Shaheedah tayi tana son motsa bakinta ta yi magana amma sai bakin yayi mata nauyi, ganin haka yasa Barrister Shaheedah tasa hannunta ta goge mata hawayen da ya zubo mata, sannan ta ce, “Umma kiyi haƙuri idan tambayar tawa ta sosa miki rai, tun da na ga ba kya son sanar da ni nima na haƙura da son na sani ɗin.....” Tana faɗin haka ta miƙe za ta shiga cikin ɗaki, har ta je ƙofa ta jiyo muryar mahaifiyarta ta kira ta da kakkausar murya “SHAHEEDAH! Zo nan ki zauna” kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki haka ta dawo ta zauna, jikinta ban da rawa babu abin da yake yi.
Bayan ta zauna kusa da mahaifiyarta ta, sosai take jin nadamar tambayar da ta yiwa mahaifiyarta, domin duk lokacin da ta yi mata irin wannan tambayar to wuni take yi a cikin ƙunci da ɓacin rai, to yau ma su ta hango akan fuskar Ummanta ta, shi yasa take matuƙar nadamar tambayar da tayi mata, domin ko kaɗan ba ta son ganin ɓacin rai ya bayyana akan fuskar Ummanta, saboda duk duniya bata da kamarta.
Cikin nutsuwa mahaifiyarta ta kalleta ta ce, “Shaheedah dawo nan gabana ki zauna” tashi tayi ta dawo gaban Umma ta zauna sannan ta kura mata ido, shiru Umma ta yi tana kallon Barrister Shaheedah sannan ta ja numfashi ta ce, “Shaheedah tambayar da kika yi min duk ina da amsarta, amma labari ne mai tsawon gaske, ina son yanzu ki je ki huta na yi miki alƙawarin da daddare zan baki labarinmu da ƙasar da muka baro muka dawo nan Najeriya da zama. Amma yanzu tun da naga ba'a nutse kike ba, ki bari sai dare sannan kin samu nutsuwa sosai yadda labarin zai fi shiga kunnenki kin ji” Murmushin yaƙe ta yi ta ce, “To, Umma Allah ya kai mu daren! Amma don Allah Umma ki taimaka min ki rarrashi Baba ya bar ni na je kotun nan, Wallahi idan ban je ba Faisal zai iya faɗawa wani hali, domin hukumar ƴan sanda sun tattara shaidunsu waɗanda Hajiya Bilkisu ta basu, na tabbatar idan suka gabatarwa da Alƙali shaidun babu abin da zai sa ya ƙi yankewa Faisal hukuncin kisa ko kuma ɗaurin rai da rai a gidan yari. Ni kuma ba zan so Faisal ya shiga cikin ƙunci da baƙin ciki ba, alhalin ina da damar da zan iya kare shi.”
Jinjina kai Umma ta yi ta ce, “To, Shaheedah zan ƙoƙarta na gani Allah yasa mu dace” da amin Barrister Shaheedah ta amsa, sannan ta shiga cikin ɗakinta.
A gefen ɗan ƙaramin gadonta ta zauna, tagumi ta zuba hawaye yana ta zubowa akan kyakkyawar fuskarta. Tunanin halin da Faisal zai faɗa take idan ba ta halarci zaman kotun na yau ba, ji ta yi duk duniyar ta yi mata ƙunci, ji take a cikin zuciyarta indai ba ta taimakawa Faisal a wannan lokacin ba, to tamkar aikin lauyan da take yi ya tashi a banza, tunani ne kala-kala ya cika mata rai, waya ta ɗauko za ta kira wani lauya abokin aikinta domin ya taimaka mata.. Da sauri ta ajiye wayar sakamakon jiyo sallamar mahaifinta, yana yin sallamar bai tsaya ko'ina ba, sai ɗakin Barrister Shaheedah yana shigowa ya ganta riƙe da waya a zaune gefen gado. Hannu ya miƙo mata cikin tsawa ya ce, “Ba ni wayar nan” hannunta na karkarwa ta miƙa masa wayar, kallonta yayi ya ce, “Sai na ga ta yanda zaki taimaka masa, marar jin magana kawai, kuma ina son ki saka kunnuwanki da kyau ki saurare ni a yau ban yarda ki fita ko nan da ƙofar gida ba, kuma ban yarda kowa ya zo wajenki ba, idan kuwa har kika tsallake umarnina hmmm!” Yayi ƙwafa sannan ya ce, “Kin san abin da zai faru da ke, ki ƙyale wancan ɗan fashin a yanke masa duk hukunci da ya dace da shi, amma karki kuskura na ji kin saka baki ta kowacce hanya a cikin shari'arsu”, cillo mata wayarta yayi ya ce, “Ga wayarki nan idan kina son ki nuna min ban isa da ke ba to kiyi abin da na hana ki.” Yana faɗin haka ya juya da sauri ya fice daga ɗakin, nan take zuciyar Barrister Shaheedah ta karaya, gani ta yi duniyar tana juyawa a cikin idanunta, miƙewa tsaye ta yi da nufin ta fito daga cikin ɗakin, kawai sai ganin duhu ta yi ya mamaye idanunta ta daina ganin komai, ba ta san lokacin da ta tafi ƙasa ba luuuu za ta faɗi. Dai-dai wannan lokacin Umma ta sako kai cikin ɗakin, da sauri kuwa ta je ta tare ta tana kiran sunanta “Shaheedah! Shaheedah!!!” amma shiru kake ji, da sauri Umma ta fita daga ɗakin ta ɗebo ruwa mai sanyi ta watsa mata a fuska, nan take ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, tana kallon mahaifiyarta ta, ganin Faisal ta yi yana nufo ɗakin da take hannayensa, sanye da ankwa ga ƴan sanda nan biye da shi a bayansa. A firgice ta nuna ƙofar da yatsanta, a hankali ta furta “Umma Faisal” tana faɗin haka ta sake rufe idanunta, jikinta ya daina motsi, alamun ta suma. Da sauri Umma ta kalli ƙofar amma ba ta ga kowa ba, kiran sunan Barrister Shaheedah ta shiga yi, shiru ta ji, jijjigata ta shiga yi tana kiran sunanta amma shiru kake ji tamkar maye ya ci shirwa, nan take ta ruɗe ta fara kiran sunan Allah. Ganin da gaske ba ta, motsi yasa Umma ta fita daga ɗakin da sauri, dama da hijibi a jikinta, mahaifin Barrister Shaheedah ta nema amma baya ƙofar gidan, wani maƙwabcinsu ta gani da ya ke sana'ar tuƙa keke napep ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta ƙarasa wajensa ta yi masa bayani, da sauri kuwa ya tashi ya shiga gida domin ya ɗauko makullin napep ɗin, Umma kuwa da sauri ta koma cikin gidan jikinta sai faman ɓari yake.
Da kyar mai napep ɗin ya taimaka mata, suka saka Barrister Shaheedah a ciki Umma ta dafe ta sannan shi kuma ya ja napep ɗin suka nufi asibiti.
*HIGH COURT OF JUSTICE KADUNA*
Duk inda ka duba a harabar kotun mutane ne ko'ina birjik, kuma idan ka duba duk kusan sun zo ne domin su ga irin hukuncin da Alƙali zai yankewa Faisal. Saboda tun jiya aka sanar a kafafen yaɗa zumunta, yau ne za'a yankewa Faisal hukunci, a bisa laifin kisan kai da ya aikata. Tun wuri ƴan jarida da ƴan shaidar gani da ido suka halarci kotun, domin sun matsu su ga Faisal domin akwai tambayoyin da suke son yi masa. Misalin 9:30 dai-dai motar ƴan sanda ta shigo harabar kotun sai faman jiniya suke yi kamar waɗanda suka yi nasarar kamo wani hamshaƙin ɗanta'adda. A hankali motar ta je inda ake yin parking, tana tsayawa ƴan sandan suka hau dirowa daga motar, hango Faisal na yi hannayensa sanye a cikin ankwa. Ƴan sanda wajen su biyar biye da shi, sun zagaye shi da bindigogi. Kamar wanda yayi attempting guduwa, ƴan sanda ne wajen su shida kewaye da shi, biyu a bayansa biyu a gabansa, yayin da wasu ƴan sandan kuma suke gefensa hagu da dama. Ƴan jarida suna ganin shi suka yo kan shi, kowa da irin tambayar da yake watso masa, Allah Sarki! Bawan Allah Faisal ya sunkuyar da kansa ƙasa hawaye yana zuba akan kyakkyawar fuskarsa da ta koɗe saboda wahala. Tun da yake a rayuwarshi bai taɓa tunanin zai tsinci kansa a cikin irin wannan halin ba, amma yau ga shi duniya tana kallonsa a matsayin ɗan ta'adda kuma makashi, duniya kenan juyi-juyi wata rana a ji daɗi wata rana kuma wahala za a sha, wataran kuma idan aka sha wahala idan aka yi haƙuri daga baya sai aji daɗi....
Duk yadda ƴan jarida suka so su yi magana da Faisal, ba su samu dama ba. Saboda haka wasu daga cikinsu suka rinƙa ɗaukar hotunansa a camera, suna faɗin albarkacin bakinsu akansa. Ana shiga da shi cikin ainihin kotun, sai ga su Goggo da Habibu sun shigo cikin harabar kotun a matuƙar firgice. A tare da su akwai ɗan Faisal wanda suke kira da Anwar, gaba ɗaya hankalin Goggo ya tashi saboda ganin mutane masu yawa a cikin kotun, so take kawai ta ga Faisal ɗin, amma duk iyakar hangenta ba ta ganshi ba.
Hannunta Habibu ya kama suka ƙarasa cikin kotun, da kyar suka samu wajen zama saboda cunkoson jama'a. Hango Faisal Goggo ta yi a tsaye a wajen da aka tanadar don tsayar da mai laifi idan zai amsa tambayoyi. Miƙewa tsaye ta yi za ta nufi wajensa, da sauri Habibu ya riƙe hannunta ya ce, “Don Allah Goggo kiyi haƙuri, in sha Allahu za ki gana da Faisal idan an gama shari'a.” Da kyar Habibu ya samu Goggo ta haƙura da zuwa wajen Faisal ɗin.
A can waje ɗaya na hango Hajiya Bilkisu ita da Bara'atu har da Lubabatu, sai faman sakin murmushi suke yi, wanda kana kallonsu ka san murmushin mugunta ne. A ɓangaren Faisal kuwa sai faman raba idanu yake ko zai hango Barrister Shaheedah, amma ko kaɗan bai ga alamunta ba. Mamaki yake abinda ya hanata zuwa, amma da ya hangi su Hajiya Bilkisu sai yake ganin kamar da sa hannunsu a rashin zuwan nata. Habibu ma sai faman hangen ɓangaren lauyoyi yake ko zai ga Barrister Shaheedah amma ko kaɗan bai hangota a cikinsu ba. Wayarta ya shiga kira, swtich off!!! Kawai yake ji, jinjina kai yayi a zuciyarsa ya ce, “Tabbas ba lafiya ba”.
Alƙali ne ya shigo cikin kotun, nan take jama'ar cikin kotun kowa ya mike tsaye. Sai da Alƙali ya zauna sannan kowa ya zauna. Ba tare da ɓata lokaci ba, Alkali ya shiga aikinshi. Bayan an gabatar da wata shari'ar sai aka juyo kan su Faisal, wani ne ya tashi tsaye ya fara karanto wata takarda “A yau Litinin 12 ga watan October 2023 wanda yayi dai-dai da 15 ga watan Rajab. Hukumar ƴan sandar jahar Kaduna sun gurfanar da wannan matashi _(Ya nuna Faisal)_ a gaban kotu, domin a yanke masa hukunci bisa laifin kama shi da aka yi da kisan kai da kuma fashi da makami sannan ga attempting ɗin fyaɗe da yayi wa matar mamacin” yana gama karantawa ya miƙawa Alƙali takardar sannan ya zauna. Nan take kotun ta hargitse da hayaniya, kowa yana faɗin albarkacin bakinsa akan Faisal. Shi kuwa Faisal hankalinsa ne ya tashi, saboda jin an zayyano laifukan da ya aikata, alhalin shi bai san ma ya aikata ba.
Ganin hayaniyar ta yi yawa ne yasa Alƙali ya hau dukan tebur ɗin da yake da wata ƴar guduma yana cewa “Oda! Oda!! Oda!!!” Nan take kotun ta yi tsit ba ka jin sautin komai face na numfashin jama'ar da suke cikin kotun. Gyaran murya Alƙali yayi sannan ya fara magana “Bisa tarin hujjoji da shaidun da hukumar ƴan sanda suka gabatar mana, wannan kotu mai adalci ta yankewa wannan matashi mai suna FAISAL MUHAMMAD hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari tare da horo mai tsanani.....” yana gama faɗin haka ya buga ƴar gudumarsa ya ce, “Kooootu!!!” Sannan ya tashi ya fita. Yana fita kuwa Faisal ya fashe da kuka mai tsuma zuciya, Goggo kuwa daskarewa ta yi a wajen da take zaune, saboda jin hukuncin da Alƙali ya zartar akan Faisal bawan Allah. Da kyar Habibu ya iya tashi daga inda yake ya riƙe hannun Anwar ya zo gaban Faisal fuskarsa hawaye yana zuba duban Faisal yayi ya ce, “Kayi haƙuri Faisal kalar taka ƙaddarar kenan, ka yi haƙuri komai yayi zafi....Maganinsa Allah, ka rungumi wannan ƙaddarar da ta tunkaro ka in sha Allahu wata rana sai labari. Da yardar Allah sai ka fito ka cigaba da rayuwarka cikin ƴanci kamar kowa”.
“In sha Allahu kowaye yake da hannu wajen saka ka a cikin wannan halin sai ya fuskanci bakinciki da ƙuncin rayuwa fiye da kake fuskanta a yanzu.” Goggo ta faɗa fuskarta hawaye yana zuba na tausayin halin da Faisal ya shiga. Shi dai Faisal yayi shiru! kawai hango sabuwar rayuwar da zai fuskanta a gidan yari yake, kuma rayuwa ta har abada kawai sai ya ji hawaye ya zubo masa daga akan fuskarsa. “Abba nima zan bika mu tafi....” Muryar Anwar ce ta daki dodon kunnensa. Ƙaƙalo murmushin dole yayi ya sunkuya ya kama hannuwan yaron ya ce, “ANWAR karka damu ka.ji ko? Ba zan daɗe ba zan dawo in sha Allahu ka kwantar da hankalinka zan dawo ka ji” shi dai yaron kawai girgiza kai yake don da alamu babu abin da yake fahimta a zancen da mahaifinsa yake yi masa.
Wani ɗan sanda ne da ya gaji da jiransu ya ce, “Kai hirar ta isa haka” nan take ya bugawa Faisal ankwa ya ce, “Wuce mu tafi” ba tare da gardamar komai ba Faisal ya wuce gaba suka ƴan sandan suka bi shi a baya. Ana fitowa da shi ƴan jarida suka yanyame shi da tambayoyi amma ko uhmm! Bai ce musu ba, Ana zuwa za'a saka shi a cikin motar da za'a kai shi can kurkukun kawai sai ganin Hajiya Bilkisu yayi kamar an cillo ta kallosa ta yi ta ce, “Faisal yau ka yarda da abin da na faɗa maka? Kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha, don haka mu je zuwa wai mahaukaci ya hau kura.” Tana faɗin haka ta wuce ta bar shi a tsaye yana kallonta ya rasa dalilin da yasa ya kasa mayar mata da martani. Ba zato ba tsammani kawai ya ji an hankaɗa shi cikin motar har ciwo sai da ya ji amma babu wanda ya saurare shi daga cikinsu. A cikin motar ya ga waɗanda aka yankewa hukunci za'a kai su gidan yari, tare aka haɗa su aka rufe sannan aka ja motar suka nufi prison da su Allah ya fitar da kai Faisal In sha Allahu zaka dawo ka cigaba rayuwa kamar kowanne ɗa.
Su Goggo suna ji suna gani aka tafi da Faisal prison, share hawaye kawai Goggo ta yi sannan ta ce, “Habibu taho mu tafi” kallon Goggo Habibu yayi ya ce, “Goggo har yanzu mamaki nake yi na rashin zuwan Barrister Shaheedah wajen shari'ar nan, amma ba komai idan mun koma gida zan je har gidansu na same ta na ji dalilinta na rashin zuwa, bayan ta yi mana alƙawarin za ta kare Faisal.” Ita dai Goggo shiru ta yi domin a yanzu ba abin da zata iya fada saboda abin ya fara ba ta tsoro, ba ta taɓa tunanin Faisal zai shiga cikin irin wannan rayuwar ba.......
ALHAMDULILLAH!!!!
A yau na kawo ƙarshen littafi na ɗaya sai mun haɗu da ku a cikin littafi na biyu.
Shin Faisal zai fita daga cikin kurkukun da aka kai shi?
Wanne sirri ne a tsakanin Faisal da Hajiya Bilkisu?
Yaya Barrister Shaheedah za ta yi idan ta samu labarin an yanke wa Faisal hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari?
Yaya ƙarshen Hajiya Bilkisu zai zama?
_Domin samun amsar waɗan'nan tambayoyin naku mu haɗu da ku a *AYI MIN ADALCI BOOK 2*_
Duk mai son karanta littafi na biyu yayi magana ta cikin wannan lambar 08109373275.
Babu tsada naira #300 ne kacal ku yi saurin mallakar naku
*HUSSAIN YUSUF✍️*
08109373275.
*King and Queen Writing Chamber*
*AYI MIN ADALCI*
*King and Queen writing chamber*
🔚🔚🔚🔚
BONUS! BONUS!! BONUS!!!
BAYAN WATA SHIDA
Abubuwa da dama sun faru ciki har da zamowar mahaifin Barrister Shaheedah sarki, sannan an ɗaura auren Faisal da Barrister Shaheedah. An sha shagali sosai, har sarauta aka yiwa Faisal Sardaunan samarin Muri, arziƙin ya auri ƴar sarki shi yasa aka yi masa sarauta.
Faisal kuwa naira ta zauna masa sosai, idan ka kalle shi ba zaka taɓa cewa shine Faisal ɗin da ka sani a baya ba. Yayi jajur da shi kamar balarabe, ga wani kyau da yake ƙara yi kullum.
A wata unguwar hamshaƙan masu kuɗi waɗanda ake ji da su a Kaduna ya sayi ƙaton gida. Inda suka zauna shi da amaryarsa Barrister Shaheedah ko kuma na ce Gimbiya Shaheedah tunda yanzu ta zama ƴar sarki. A nan kusa da unguwar da suke ya sayawa su Goggo wani danƙareren gida ya zuba musu duk wani kayan more rayuwa, da ƴan aiki da za su rinƙa yin komai...Sannan ya bai wa Habibu aiki a babban kamfaninsa na man fetur, dama yayi karatu aikin ne dai Allah bai kawo ba.
Haka a ɓangaren su Oumar da Auwal su ma Faisal bai manta da su ba, ya samar musu aikin yi a manyan ma'aikatun Gwamnati. Kasancewar Faisal ya san manyan mutane ta hannunsu ya bi ya samowa Oumar aiki a NNPC shi kuma Auwal a CBN, Mudassir kuwa tun daga ranar ya zama abokin su Faisal sosai suka zama kamar da can sun san juna lafiya k'alau suke zaune babu wanda yake ƙyashi wani.
Su Goggo an samu duniya, ta je Umra ta je Hajji. Ga muhalli mai kyau sutura mai kyau ga lafiyayyen abinci, ko aiki Goggo ta yunƙura za ta yi da sauri ƴan aikinta suke dakatar da ita...Wani lokacin idan Goggo ta zauna tana tunanin rayuwar da suka yi a baya sai ta fashe da kuka ita kaɗai, tunda take a rayuwa ba ta taɓa zaton za ta tsinci kanta a irin wannan daular ba, lallai yanzu ta yarda da karin maganar nan dare ɗaya Allah ya kan yi bature. Hutu da jin daɗi sun zauna a jikin Goggo idan ka kalleta ba za ka taɓa zaton tsohuwa ba ce sai an faɗa maka...
Haka a ɓangaren Faisal shi da amaryarsa Gimbiya Shaheedah, soyayya suke zubawa junansu kamar ba gobe. Gimbiya Shaheedah ba ta san tana son Faisal ba har sai da ta aure shi, sannan ta tabbatarwa zuciyarta babu wanda take matuƙar so da kauna kamar shi...Akwai fahimtar juna sosai a tsakaninsu, lafiya kalau suke zaune sai zubawa juna soyayya suke idan ka kalle su dole su burge ka yanda suke matuƙar kulawa da junansu. Duk bayan sati biyu sai Faisal ya ɗauki amaryarsa Shaheedah sun je sun gaida mai Martaba wato mahaifin Barrister Shaheedah. Ƙasashen waje kuwa duk bayan wata biyu sai sun je yawon shakatawa sai sun daɗe a can suna shan love ɗinsu kafin su dawo.....
Haka kawai Barrister Shaheedah ta ji tana sha'awar yin kasuwanci. Ba ta yi wani jinkiri ba ta sanar da mijinta wato Faisal, ba tare da shakkar komai ba kuwa ya ba ta 50million ya ce ta fara da wannan.Idan ya ga kasuwancin ya karɓe ta sai ya kara mata wasu kudaɗen. Nan take Barrister Shaheedah ta shiga safarar gold and diamond, daga ƙasar Dubai tana kawowa nan Nigeria ta sayar. Ba iya nan ta tsaya ba har da su rigunan abaya take sayowa ta zo tana sayarwa a nan gida Najeriya. Sosai kasuwancin nata ya karɓu nan da nan kuwa kuɗi suka fara zauna mata, ganin haka yasa Faisal ya ƙara mata wasu 50million din ya ce ta ƙara jari.. Cikin ƙanƙanin lokaci Barrister Shaheedah ta zama matashiyar attajira, domin ta iya kasuwancin sosai...Dama tuni ta daɗe da ajiye aikinta na Lauya..
A cikin masarautar Muri kuwa Umma ta zama matar Sarki, komai sai dai ayi mata. Ba ta da kishiya ko ɗaya, shi kansa Sarki Hamza da kansa ya ce, ba zai yiwa Umma kishiya ba saboda ta yi masa halaccin da ba zai taɓa mantawa da shi ba. Duk da jama'a suna damunsa sosai akan ya ƙara aure bai kamata ba yana babban Sarki ya zauna da mace ɗaya ba. Shi kuwa yana ji sai ya share kawai domin gani yake idan ya ƙara aure tamkar ya ruguza duk wani farin ciki da yake tsakaninsa da iyalinsa ne, shi yasa ko kaɗan ba ya sha'awar ƙarin auren. Umma tana da kirki sosai, kowa a cikin gidan sarautar idan ya buɗe baki sai dai ka ji ya yabe ta.
Wani danƙareren gida ta ba wa mahaifinta Aminu da kakanninta Malam Tijjani da Inna Mairo. Anan suka yi zamansu lafiya cikin kwanciyar hankali sun manta ma da sun yi zaman Nijar sai dai idan sun tuno su yi ta labarin abun..
*INA LABARIN HAJIYA BILKISU?*
Barrister Shaheedah ce a zaune ita da Faisal a kayataccen falonsu wanda ya gaji da haɗuwa sai shagwaɓa take zuba masa "Baby ka tashi don Allah mu tafi" kallonta yayi ya saki wani murmushi kafin ya ce,
"Yanzu shopping ɗin lallai sai da ni za ki je?"
"To, ai idan babu kai ba zan ji daɗin tafiyar ba" murmushi kawai yayi tare da miƙewa tsaye ya ce, "Alright tashi mu tafi."
Da sauri kuwa ta miƙe tare da riƙe hannunsa ta ce, "Baby mu tafi"
Hannayensu sarƙe a cikin na juna suka fito compound ɗin gidan, kai tsaye inda ake ajiyar motoci suka nufa...
Da gudu wani dattijo ya zo gabansu ya ɗan rusuna kafin ya ce, "Alhaji fita za mu yi ne?" Gyaɗa kai Faisal yayi ya ce,
"E! Fita za mu yi amma da kaina zan yi driving na hutar da kai"
"To, Alhaji Allah ya kiyaye hanya" yana faɗin haka ya juya ya bar wajen da sauri..
Wata mota mai ƙirar benz suka shiga, suna ƙoƙarin fita daga gidan suka hango Goggo ta shigo hannunta riƙe da Anwar. Dakatawa Faisal yayi tare da fitowa daga cikin motar, da saurinsa ya nufo su Goggo sai faman sakin murmushi yake, Anwar kuwa da ya hango Abbansa ya nufo inda suke shi ma da gudu ya nufe shi. Suna haɗuwa Faisal ya ɗaga Anwar sama tare da rungume shi tsam a ƙirjinsa, ƙaunar yaron yana jin yanda take mamaye masa duk wani lungu da yake cikin zuciyarsa.
Kallon Goggo yayi kafin ya saki murmushi ya ce, "Goggonmu mu shiga daga ciki ko?"
"A'a ba zama na zo yi ba, na ga alamun ma fita za ku yi." Gyaɗa kai Faisal yayi ya ce,
"E fita za mu yi yanzun nan Wallahi sai ga shi kun shigo"
Ya ƙarashe maganar yana sakin wani murmshi.
"Dama ɗanka ne ya taso ni lallai sai na kawo shi wajenka, to ga shi nan na kawo ka ga sai ku fita tare ko?"
Murmushi mai sauti Faisal yayi kafin ya ce,
"Anwar me yasa ka taso Goggo da ranar nan?" Shiru Anwar yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa.....
Barrister Shaheedah ce ta gaishe da Goggo da sauri kuwa Goggo ta juya ta fice daga gidan, tare da Anwar su Faisal suka koma motar tasu suka fita daga gidan.
Bayan sun gama siyayyarsu sun fito inda suka ajiye motarsu, suna ƙoƙarin shiga motar "Faisal!" Gaba ɗayansu suka waiwaya inda suka jiyo amon muryar wacce ba za su taɓa mancewa da ita a rayuwarsu ba.
Ganinta suka yi cikin wani mawuyacin hali, sai tafiya take da kyar tana jan jiki kamar wata macijiya....
Kallo d'aya Faisal yayi mata ya kawar da kai tare da jan wani dogon tsaki.
"Mtssss! Taho mu tafi" ya faɗi tare da jan hannun Barrister Shaheedah, ƙin tafiya Barrister Shaheedah ta yi ta ce, "Faisal Hajiya Bilkisu ce fa ba ka ga a halin da take ciki ba tana buƙatar taimako pls mu taimaka mata..."
"Allah ya kiyaye na taimakawa wannan matar Wallahi da na taimaka mata gara a ce zubar da kuɗin na yi... Ke yanzu har kina da bakin zuwa ki ce na taimaka miki?"
Hawaye ne ya zubo daga idanun Hajiya Bilkisu ta durƙusa har ƙasa tana roƙon Faisal,
"Don Allah Faisal ka taimaki rayuwata ka daure ka biya min kuɗin magani Wallahi idan ba ka biya min ba mutuwa zan yi...."
"Ai Bilkisu mutuwar ita tafi dacewa da ke, gara ki mutu ki je can ki tarar da abinda kika aikata..."
Fashewa da kuka Hajiya Bilkisu ta yi, ta tsugunna har ƙasa tana roƙon Faisal akan ya taimaka amma Faisal yayi kunnen uwar shegu da ita ya ƙi kulata ballantana ya saurareta. Barrister Shaheedah kuwa ranta ne ya soma ɓaci ganin yadda Faisal ya ke wulakanta Hajiya Bilkisu....
Kallon Anwar Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, "Ɗana Anwar taho gare ni, ni ce Ummanka ka ji ko?"
Maƙe kafaɗa Anwar yayi ya ce, "A'a ni ba ke ce Ummata ba, ni kin ga Ummata" ya faɗi yana nuna Barrister Shaheedah..
Fashewa da kuka Hajya Bilkisu ta yi cike da gadara Faisal ya ce, "Alhamdulillah! Ko iya wannan abunda ya faru a nan wajen yanzu, ya isa ya zamo miki darasi Bilkisu, ga shi dai ɗanki na cikinki gudunki yake duk me ya janyo wannan son duniya da amsa kuwwar shaiɗan..Don haka ni yanzu ba ni da lokacinki ki kama gabanki ki san inda dare yayi miki ina gargaɗinki karki kuskura ki ƙara zuwa inda nake idan kuwa kika ƙi ji Wallahi sai na ba ki mamaki, sannan ina son ki jira sakamakon da zai biyo bayan abinda kika aikata ba ki ga komai ba Wallahi wasa farin girki...." Yana fadin haka ya juya da sauri ya shige cikin motarsa, cikin sanyin jiki Barrister Shaheedah ta ɗauko kuɗi a cikin jakarta tana niyyar miƙawa Bilkisu...
"Idan kika ba ta ko naira biyar ce Wallahi ban yafe miki ba" Faisal ne ya fadi daga cikin motar yayin da ya ga Barrister Shaheedah tana shiri miƙawa Hajiya Bilkisu kuɗi...
Cike da tsananin ɓacin rai Barrister Shaheedah ta zo ta shiga cikin motar zuciyarta duk babu daɗi, kallon Hajiya Bilkisu take a tsaye cikin rana jikinta ban da wari babu abinda yake yi. Tun tana kallonta har suka ɓacewa ganinta gaba daya, durƙushewa Hajiya Bilkisu ta yi a wajen ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya gami da tsantsar nadamar abinda ta aikata...
A cikin ranta take tunanin yanzu da tuni ita ce a cikin waccan motar, da tuni ita ce cikin kwanciyar hankali da jin daɗi...
"Gaskiya na cuci kaina ni Bilkisu ban san ya zan yi ba Allah na tuba ka yafe mini" ta faɗi tana rushewa da wani sabon kukan, mutane kuwa zagayeta suka yi wasu tausayi ta ba su duk da basu san abinda ta aikata ba, yayin da wasu kuma suke ta faman faɗin Allah ya ƙara dama ita duniya ai haka take idan ka bita a sannu ma da ya ka ƙare balle ka bita da gaggawa....
Ko da su Faisal suka koma gida, kwata-kwata ya kasa samun nutsuwa a cikin ransa. Wani irin ɗaci zuciyarsa ta rinƙa yi masa, sakamakon ganin Hajiya Bilkisu ji yayi a ransa inda yana da ikon kasheta da tuni ya kashe ta saboda tsanar da yayi mata....
Yana zaune a falo shi kaɗai yana ta faman tunani, Barrister Shaheedah ce ta kawo masa juice mai sanyi tana lallashinshi da kyar ya ɗan kurɓi juice ɗin sai ya ji zuciyarsa ta ɗan yi sanyi kaɗan, nan take ya shiga ambaton Allah.
A hankali ya ji zuciyarsa ta sanyi sosai, shiru yayi yana ta tunani...
Nocking ɗin da ake yi ne a ƙofar falon nasu ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya tafi, a hankali Barrister Shaheedah ta je jikin ƙofar ta leƙa ta jikin ƴar ƙofar nan da take jikin ƙyauren, hankalinta ne ya tashi sakamakon ganin Hajiya Bilkisu jikinta yana ta faman rawa.
Cikin sanyin jiki ta saka hannu ta buɗe ƙyauren.
Faisal da ya ƙurawa ƙofar idanu domin ya ga wanda zai shigo,
Ana gama buɗe ƙyauren ya miƙe tsaye a fusace ya ce,
"Uban waye ya kawo ki gidana? Ki yi saurin fice min daga gida tun kafin ranki ya ɓaci"
Barrister Shaheedah ce ta tako ta zo har inda yake ta kama hannayensa ta riƙe
"Please Habiby ka yi haƙuri don Allah ka saurareta please my horny"
Ɗan rusunawa Faisal yayi ya dubi Bilkisu a wulaƙance ya ce, "Ina sauraronki"
Wani yawun baƙin ciki Hajiya Bilkisu ta hadiye,
yanzu wai ita ce sai wata ta saka baki sannan mijinta zai saurareta? "Gaskiya ni BILKISU na cuci kaina" durƙusawa ta yi a gaban Faisal ta dafa kafafunsa cikin raunin murya irin mai cike da tsantsar nadama ta ce,
"Don Allah Faisal ka yafe min laifin da na yi maka, ka yafe min don Allah ko zan samu sassauci a cikin halin da nake ciki. Na san duk alhakinka ne yake bibiyata, idan ba ka yafe min ba Wallahi ban san yanda zan yi ba..."
Zaunawa Faisal yayi akan kujera ya dafe kansa, yayi shiru...
Ganin haka yasa Barrister Shaheedah ta zo kusa da shi ta zauna tare da dafa kafaɗarsa ta ce, "Haba my Habiby ka yafe mata mana, ka san Allah yana son masu afuwa daga cikin bayinsa" wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya dubi Bilkisu ya ce,
"Tunda matata ta saka baki na ji na yafe miki duniya da lahira, amma batun igiyar auren da take tsakanina da ke babu ita na tsinke ta gaba ɗaya ukun kar ki ƙara yin tunanin sake zama inuwa ɗaya da ni..."
Ɗora hannu a kai Bilkisu ta yi, kafin ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya gami da tsantsar nadama..
"Ke Bilkisu ya ishe ki haka, kiyi saurin fitar min daga gida yanzun nan tunda na yafe miki, kuma na daƙile igiyar auren da yake tsakanina da ke..." Faisal ne ya faɗi yana nuna Bilkisu da hannu cikin tsananin ɓacin rai.
Durƙushewa Hajiya Bilkisu ta yi a wurin, ta dubi Faisal cikin muryar ban tausayi ta ce,
"Faisal na sani ka daƙile duk wata alaƙa tsakanina da kai, na san na ɓata maka kuma na cancanci duk wani hukunci daga gare ka amma don Allah ina neman wata alfarma a gare ka.."
A wulaƙace Faisal ya dube ta ya ce, "Ina jin ki Allah yasa zan iya"
"Don Allah ka daure ka siya min magani Wallahi idan ban samu maganin ba nan da kwana uku mutuwa zan yi" ta faɗi hade da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi...
A wulaƙance Faisal ya dube ta ya ce, "Bilkisu kenan! Ina tarin dukiyar da kika samu a wajen marigayi Alhaji Hashim? Kar dai ki ce min yanzu duk babu ita?"
Girgiza kai Bilkisu ta yi ta ce,
"Tun lokacin da aka raba gado aka bani nawa, sai na haɗu da wani mutum mai suna Alhaji Kamilu, shine ya ce min na kawo kuɗin nawa shi ma ya kawo na sa mu fara business a Dubai..Na yarda da shi sosai, na ɗauki gaba ɗayan dukiyata har da kadarorina muka haɗa ni da shi muka tafi Dubai domin mu fara kasuwanci tare..
Yayin da muka je can, ni ban san komai ba kuma ban san kowa ba ban da shi, sai ya rinƙa amfani da wannan damar yana cutar da ni. Kullum idan zai fita waje sai ya kulle ni a gida, sai bayan magriba yake dawowa idan na yi masa maganar kasuwancin namu sai yi min masifa yana cewa ba ni da haƙuri ko kuma ya ce ina zarginshi zai cinƴe min kuɗi...A ƙarshe da ya gaji da takurawar da nake yi masa, sai ya fara nuna min ainihin kalarsa. Sai ya shiga nemana tun ba na amincewa ina guduwa har ta kai yana zuwa har ɗakin da nake ko ba na so sai yayi min ta ƙarfi da yaji, sosai ya mayar da ni matarsa duk lokacin da ya so amfani da ni zai zo ya biya buƙatarsa ba tare da tunanin halin da zan kasance a ciki ba...
Tun ina damuwa har na zo na daina na rinƙa ba shi hadin kai yana yin yadda ya ga dama da ni...
Kwatsam! Wata rana ya ce min na shirya zai tura ni can Germany tare da wani abokinsa na fara saro mana kaya domin mu fara kasuwancin namu, da murnata kuwa na shirya ya haɗa ni da abokin nasa wai shi Joseph ƙarfe 11 na safe muka shirya muka hau jirgi, ashe ban sani ba duk shirinsa ne a jirgin Najeriya ya sako ni ba a cikin jirgin Germany ba, ashe yaudarata yayi shi da abokinsa tunda muka sauka a aiport ɗin Malam Aminu Kano ban kara ganin Joseph ba, kuma nan take na fahimci Najeriya aka dawo da ni..Nan take kuwa na shiga cikin rudani domin gaba ɗaya dukiyata tana hannun Alhaji Kamilu, da kyar na samu wani mai taxi ya kai ni unguwa uku na ba shi ƴan sauran canjin da suka rage mini, sauran kuma na kama gida haya anan unguwar..Kullum tunanina shine ya zan yi na koma Dubai domin na haɗu da Alhaji Kamilu haka ne yasa shiga neman kuɗi a lallai sai na tara kuɗin komawa Dubai ɗin na karɓo kuɗina a wajen Alhaji Kamilu. Sana'a na ke yi da kyar wani Alhaji ya ara min bashin dubu ɗari biyar na kama shago na fara sana'ar sayar da abinci kala-kala, sosai kasuwar tawa ta karɓu nan take kuwa na fara tara kuɗin komawa Dubai wajen Alhaji Kamilu...
Kwatsam wata rana na tashi da wani matsanancin ciwon kai, da zazzaɓi mai zafin gaske, da kyar da siɗin goshi na kai kaina asibiti. Anan likita yake shaida min ina ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato (H.I.V AIDS) kuma ta fara yin ƙarfi a jikina. Hankalina ya tashi sosai, karo na farko da naji nadama ta shige ni akan abinda na aikata a rayuwata..
Sosai likitan ya kwantar min da hankali tare da ɗora ni akan magani, duk ƴan kudaɗen da na tara domin na koma Dubai sai da suka k'are gaba ɗaya a wajen sayan magani, na dawo kan jarin da nake juyawa su ma ba su daɗe ba suka kaf na dawo abincin da zan ci ma yana bani wahala. Ga Alhajin da ya ara min kuɗin nake juyawa ya saka ni a gaba a lallai sai na biya shi kuɗinsa, ga gidan da nake haya su ma sun saka ni a gaba ban biya kuɗin haya ba. Ga maganina ya kare gaba ɗaya kuma babu kuɗin sayan wani, haka ne yasa na tashi na dawo nan Kaduna na miƙa ƙoƙon barata a wani masallaci ana nema min taimako, da kyar wata mata ta taimaka min da wani dan ƙaramin d'aki a gidanta nake kwana, idan ka kalli ɗakin ba zaka taɓa cewa mutum zai iya kwanciya a cikinsa ba. Ranar da na ganku na zo wucewa ne na hango Shaheedah ta shiga mota shi yasa na ƙaraso wajenku domin na nemi yafiyarku ko zan samu sassauci daga rayuwar da nake fuskanta mai cike da ƙunci da baƙin ciki fiye da wanda na jefa ka a ciki...."
Tana kai wa nan a zancenta sai ta sake fashewa da kuka mai har da sheshsheƙa, Barrister Shaheedah ma hawaye sai faman kwaranya yake a kan fuskarta kamar da ita abin ya faru,
A hankali Faisal ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya dubi Hajiya Bilkisu ya ce,
"Haƙiƙa Bilkisu kin ga karshen maci amana tun anan duniya ko? To ina ga an je can Lahira? Ki godewa Allah ma da kika same mu har kika nemi yafiyarmu amma ya zaki yi da alhakin marigayi Alhaji Hashim?"
Sake fashewa da kuka Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, "Wallahi ban sani ba na yi nadamar abunda na aikata a rayuwata don Allah Faisal ka taimaka min"
A nutse Faisal ya dubeta ya ce, "Na ji zan saya miki magani in sha Allah ba zaki sake yin rashinsa ba, zan hada ki da wani Likitana da zai rinƙa duba ki kullum, sannan zan baki gida ki zauna iya tsawon rayuwarki ba zaki rasa ci da sha ba..." Durƙusawa Hajiya Bilkisu ta yi tana ta faman zubawa Faisal godiya domin jita yi kamar kyautar Aljanna ya bata..
Numfasawa Faisal yayi ya ce,
"A dalilin kaza ƙadangare ke shan ruwan kasko saboda haka ina son ki sani duk wannan abinda na yi miki saboda kin ci darajar ɗan da yake tsakaninmu wanda kika gudu kika bar shi a lokacin da yafi kowa buƙatark..."
Shiru yayi sakamakon buga ƙofar da ake yi da karfi kamar za'a karyata,
Ba tare da tambayar ko waye ba Faisal ya buɗe ƙofar, ƴan sanda ne wajen su goma a tsaitsaye. Cike mamaki Faisal ya dubi ogansu ya ce,
"Yallaɓai lafiya kuwa?"
Murmushi dan sandan yayi ya ce,
"Kayi haƙuri Faisal mun zo tafiya da Hajiya Bilkisu ne"
Shiru Faisal yayi na dan wani lokaci kafin ya dubi ɗan sandan ya ce,
"Yallaɓai indai don ni za ku kama Bilkisu na riga na yafe mata ku yi haƙuri ku koma"
"Faisal kenan! Idan kai ka yafe mata su ƴan'uwan marigayi Alhaji Hashim sun yafe mata? Kuma hukumar ƴan sanda ma ai ba su yafe mata ba"
"Amma yallaɓai...."
"Ka ga dakata Faisal duk abinda za ka faɗi ka bari aje can station ɗin muma ƴan aike ne"
Ganin haka yasa Faisal ya buɗe musu ƙofar ya ce, su shigo, nan take kuwa suka shiga suka kama Hajiya Bilkisu tare da saka mata ankwa a hannu suka tusa ƙeyarta tana kuka tana komai amma ko tausayinta babu a tare da su kawai ingiza ta suke yi kamar za su cinƴeta ɗanye.....
Gaba ɗaya Faisal sai ya ji jikinsa ya mutu ya rasa mai yake yi masa daɗi, domin har yanzu akwai sauran rububin son Hajiya Bilkisu a cikin ransa duk da tsantsar butulcin da ta yi masa a rayuwa...
BAYAN KWANA UKU
Faisal ne da Barrister Shaheedah a zaune a falonsu suna kallon tv, BBC HAUSA ne suke labarai gaba ɗaya hankalinsu yana kan tv din. Ji suka yi ɗan jaridar yana cewa
"Kotu ta yankewa matar marigayi Alhaji Hashim mai dala hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa zarginta da kashe shi har lah..." Bai kai ga ƙarshen labarin ba Faisal ya kashe tv ɗin yana dafe kansa da ya sara masa ciwo lokaci guda, Barrister Shaheedah kuwa fashewa da kuka ta yi ta tashi ta shige cikin dakinta.Gaba ɗaya yinin ranar su Faisal ba su yi shi a cikin walwala ba, har su Goggo sai da suka jinjina abin tausayin Bilkisu gaba daya ya kama su, ba ta da kowa a Najeriya da ya wuce su Faisal shi yasa suka shiga tsananin damuwa bisa hukuncin da aka zartar mata, haƙiƙa Faisal da yana da halin da zai ceci Hajiya Bilkisu da tuni ya ceceta sai dai babu hali idanu ne kawai nasa....
BAYAN WATA ƊAYA
Barrister Shaheedah ce ta tashi jikinta duk babu daɗi, ga kasala da tashin zuciya da suke damunta. Ganin haka yasa Faisal ya kirawo likitansa domin ya duba ta, gwajin farko ya tabbatarwa da Faisal tana ɗauke da ciki wata biyu...
Sosai Faisal yayi murna tare da yiwa Allah godiya, zai samu zuri'a tare da matar da ya fi so a cikin mata, Anwar ma da aka faɗa masa an kusa haifa masa sabon baby kullum murna yake tare da ɗokin yaushe Ummarsa za ta haifo masa babyn sai dai ta kwantar da hankali amma duk da haka kullum sai ya tambaya.
Sosai Faisal yake tarairayar Barrister Shaheedah tare da bata kulawa ta musamman, har cikin nata ya cika wata tara...
Ranar Juma'a da safe nak'uda ta taso mata, nan da nan kuwa Faisal ya ɗauke ta sai asibiti, ba ta daɗe tana naƙudar ba Allah ya sauke ta lafiya ta haifo kyawawan ƴaƴanta su biyu...
Identical twins kamar su ɗaya sak kamar an tsaga kara, mace da namiji ne.
Murna a wajen Faisal da sauran ƴan uwa da abokan arziƙi ba a cewa komai, da ranar suna ta kewayo aka raɗawa yaran suna...
Namijin aka saka masa sunan mahaifin Faisal wato Muhammad Sani amma ana kiransa da Halim ita kuma macen aka raɗa mata sunan Umma mahaifiyar Barrister Shaheedah SALMA amma ana kiranta ana kiranta Ummi...Mai martaba ma sosai ya ji daɗin samun jikokin da yayi ya rinƙa murna tare da yiwa iyayensu kyaututtuka na musamman.......
Haka rayuwar wannan ahali ta cigaba da gudana cikin tsafta da kwanciyar hankali, Faisal ya zama Daddy Barrister Shaheedah ta zama Umma......
*Tammat bihamdillah*
Alhamdulillah anan na kawo karshen wannan littafin nawa mai suna AYI MIN ADALCI BOOK 2 abinda muka karanta dai-dai Allah ya bamu ladan abinda muka yi kuskure Allah ya yafe mana gaba ɗaya.......
Duk mai bukatar complt BOOK 2 kai tsaye yayi magana ta cikin wannan number 07069475482 ɗari uku ne #300 babu tsada sai na ji daga gare ku.....
*HUSSAIN YUSUF*
2347069475482
0 Comments