💀💀💀
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
💀💀💀
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0⃣1⃣*
Karar kwankwasa kofane ke tashi,sa'annan wata siririyar murya ta soma biyo baya.
"Brother!! Brother!!,Katashi daga barcin nan,wallahi zamu makara school indan baka tashi daga wannan baccin naka ba,kuma kasani bana jure bulalar madam Fati"
Haka wannan Mai kwankwasa kofar keta nanatawa....
Baya murya tayi shiru kuwa sai karan *alarm* 🔔 ta soma tashi...so noisy.
" *Ohhh*!! wayyo ni,wai wacce iri makwabtane way'annan duk sunbi sun dami mutum awannan sanyi safiyar...."
......Karashe maganar yayi da tsaki
Cikin fushi ya d'ago daga kwanciyar da yake....sa'annan ya Yaye barkon dake kan kugunsa hade da yunkurawa ya wuce toilet,nan ya watsa ruwa sa'annan yayi brush....
Bai wani bata lokaci ba ya nufi hanyar fita,yayinda ya daura *tawal* a kugunsa,Cikin sanyin jiki da kwanciyar hankali yake taku har ya kaiga kofar yasa hannu ya bude ta,ganin kansa cikin uwar dakin ne yasakashi fisge wannan tawal dake kugunsa yayi jifa da ita cen gefe,But then yayi kara Aaaa!! hade da rugawa kan tawal din....da zuwansa gurin ya dauko cikin sauri ya maida a kugunsa.
"Azahirance banga komi ba"
"What the heck are you doing here,how did you get in *Muzaffar* ?".
Abinda ya fara fitowa daga bakin wannan santalelen saurayin kenan,mai kakkaurar gira da mulmulellen link ga kuma manyan idanu wacce take fara tas gashin kansa ko baki ne sid'ik
#Muzzaffar dai ya kasance Zaune yake a bakin katifa yayinda yake rike da *Coffee cup* a hannu....
"Oh actually I met your sister downstairs,ita ta sanar dani cewa kana ciki....."
Haka muzzafar ya basa ansa shiko yayi furucin" *Oh God* damn it"
"So mayya hana ka jirani a downstairs din?"
"Came on ai ba laifi danna shigo dakin ka na zauna Sabida ni friend nake,but I'm not sure banga komi ba"
Hakan ya mayar masa da martani yayinda ya karashe maganar nasa da dariya hade da kyakyatawa.
Dajiyo haka kuwa yasa hannu ya dauko filo,ya bugawa muzzaffar aka......
Haka dai muzzaffar yayi ta zuba yayin da wannan kyakyawan saurayi ke kokarin canza kaya,haka zalika kan Danny teble....yayin da yake karin kumallo,Mituna talatin ne ta dauke sa hakan ta sanadiyar saurin da yake,bayan ya kammala komi suka yunkura suka nufi hanyar fita,Bayyana sukayi a farfajiyar gidan inda ya kasance yayi shiga ta kananun kaya,sa'anan hannun sa rataye da wata yar jaka....taku suke ciki salon burgewa inda muzzaffar ke cewa.
"Kamata yayi ace ka godemin,bawai ka cikani da korafi ba, domin kuwa ni nayi su mufyda suka zauna a wajen if not da dukkannin su sai sunga halin da kake ciki"
"You fool"
Haka saurayin nan ya furta yayinda fuskarsa ke cike da annashuwa....
Fashewa sukayi da dariya dukkan ninsu biyu sa'annan suka cigaba da firar su har saida suka kai wajen wata gabjejiyar mota,shigewa ciki sukayi.....
Da shigarsu ko wata dake zaune cikin wannan motan a kujerar baya tace dasu......
"Atif and muzzaffar tuntuni ku muke jira"
Hakan ta furta cikin kasaita,d'ayarko tace.....dasu dukka.
"And also muna da bad news,har yanzu,shugaba bata janye fadarta na cewa zamuyi tafiyan nan tare da tawagar su Mu'azz ba,har yanzu tana kan bakarta"
Fadar haka take yayinda take jansu a motar.....
*wannan motar dai ta kasance dauke take da mutane biyar,wato *Atif,muzzaffar,Simon,Mufyda and Tina*
"Gaskiya hakan bayi bane,tasanfa Mu'azz basu shiri da Atif"
Haka muzzaffar ya furta inda,Tina tace dashi
"Nifa banga abin damuwa ba,yafa kamata ku sani wannan aikin da zamuje duration nashi 3days ne kawai"
Haka Tina ta furta inda mufyda tace da ita....
"Hold it,3days fa ba kawai bane ehhe"....
"Enough guys,cacan baki bazata cenza komi ba tunda mun riga munsan halayensu sai muyi taka tsantsan da su"......
Haka @Atif din ya furta inda @Tina tayi saurin cewa
"Nima hakan na gani"
Hakadai suka kasance har isar su ma'aikatar tasu,da shigarsu wannan gurin ko sai sukayi karo da shugawar tasu.....
"Oh my,wai Da ina kuka tsaya ne,shinko kunsan tun 7:00AM tawagar mu'azz ta hallara anan domin wannan tafiyar but you guys seems bakwa son ayi wannan tafiya".......
Haka sugabar ta furta inda inda Atif yayi saurin bata hakuri hade da yimata karyar cewa cinkusun ababen hawane ya rike su.
"Okay fine,amma ku sani next time bazan karbi complain naku ba"
Haka tayi musu rakiya har ta kaisu motar mufyda ko bata key motan ta tayi ta sanar da ita kanin ta zaizo ya dauka ita ko tace da ita ok kafin tayi musu sallama ta koma office...
Mituna talatin da tashin wannan motar dake dauke da tawagar mu'azz dana Atif amma tsakanin wa'yanan tagwayen kungiyoyi babu wanda yace da dan uwansa kala,they remain silent,amma daga bisani *Tina* tace dasu.
"oh My word,wai haka zamu kasance cikin wannan motan kamar wasu kurame,ya kamata mudance wani abu ai"..
"Hii Tina How are you,Happy now?"
Haka mu'azz ya furta yayin da ya karashe maganan da tsaki....
Daya daga cikin tawagar mu'azz Murtuke fuska tayi hade da cewa....
"Oh Ashe da tawagarku a cikin wannan motar,no wonder shiyasaka naji warin pigs yayi yawa a cikin mota"
bayan ta furta hakan kuwa sai sauran y'an tawagar tata suka fashe da dariya..
Tina murtuke fuska tayi,sa'annan tayi yunkurin cewa wani abu amma bayan tayi ido hudu da Atif saita maida wukar ta tayi shiru ta kyale su.
Tawagar mu'azz dai dauke take da members bakwai wato *mu'azz* din da kansa sai kuma *Nina* *Ahmad* *Forzy* *Samra* *Ali* and *Harun*
Haka dai suka soma fira tsakanin su,Atif ko da sauran yan uwan nasa karewa sukayi kamar wasu kurame....
*5 HOURS* sukayi suna wannan tafiya,wanda a wannan sa'in ko dukkan ninsu sun jikkata shiru sukayi babu mai cewa....komi
Kwatsam sai motar tasu ta tsaya....middle of nowhere🙄
Dogaren bishiyoyine a gurin billa adadin ta sanadiyar hakanne gurin tayi duhu,ciyayin gurin ko sunyi tsawo sosai sa'annan babu alamar wani a kusa..
Direbar dake jan motar ko sauka yayi ya bude gaban motar yadan duba sai yace dasu matsala muka samu....
Dajiyo haka dukkan nin su suka sauko sunamai hamma da mika....
"How long wannan gyaran zai dauka"?
Tambayar da Mu'azz yayi kenan inda Samra ta basa ansar cewa.
"Who knows,amma da dukkan alamu wannan babbar gyara ce"
"Gaskiya babbar gyara ce Mota kawai tana tafiya saita tsaya"
Haka Nina ta furta.....ahakan suka kasance yayinda suka ware kansu gefe guda...
Atif ko tsaye yake wajen direbar yana tayashi but still babu alamar motar zata tashi....
*30 minutes later......*
Zazzaune suke sun wani harhade rai nan sai mu'azz ya yunkura yace....
"Guys I got a idea,mai zai hana mu zaga cikin wannan guri kafin motarmu ta gyaru"?
"Wooo sounds cool"
Haka Forzy ta furta yayin da ta yunkura tsaye.....
"Bad idea,I'm super tired"
Haka Samra tace dasu but suka nace sai data amince tace dasu alright naji....
Haka suka gama a tsakanin su,sai mu'azz ya juya ya fuskanci Atif yace dashi....
"Atif maizai hana mu zaga kafin motar namu ta gyaru"
Dajiyo hakan ko Atif ya d'ago idanu hade da cewa...
"What? you gotta be kidding me,zagawa anan gurin gaskiya this is very bad idea we are in middle of nowhere"
Nanfa Samra ta sami baki ta soma cewa....
"Hakan na gani but tunda babu akin baki ballantana na fari da muke a nan sai nake ganin kamar ya fadi gaskiya"
Haka ta furta nanfa suka fara magana da junan su kamar cen basu taba batawa ba.
Daga karshe dai amince musu yayi yace dasu...
"Okay go and have fun,ni zan tsaya da direbar"
Amincewa sukayi suka shiga cikin motar suka dadauko jakunkunan su hade da bude bout suka dauko katuwar camera dan daukar hoto....
Tsusa kai sukayi cikin dogayen bishiyoyin nan inda Atif yabisu da kallo,tun yana iyya hango su har ya daina ganin su nan sai ya maida ganin sa direbar ko yace dashi.
"Dannan bisu kuje ku shakata,wannan aiki nane"
Murmushi yayi hade da cewa...
"It's alright,banason ka kasance cikin kadaici ne"
Fashewa yayi da dariya hade da kyakyatawa sa'annan yace dashi.
"Babu komi gacen wani mai babir na tahowa zai dan taimakamin kawai ka bisu kuje"
Hakan ya furta yayin da yayi masa nuni da hannu kan mai zuwa da babir din.
Sai Atif yace dashi..
"Alright shikenan"
Dauko jakarsa yayi babu bata lokaci yasa kai shima yabi bayan su.
Bangaren su mu'azz ko cewa yayi dasu duk hanyar da zasu bi su tabbatar sun karya rashi ko kuma ciyawa domin ajiye sheda incase ko motan nasu ya gyaru da wuri a turo Atif naiman su.
Haka ko suka kasance suna aikatawa amma kuma abinda basu sani ba shine duk ganyen da suka karyata daga zaran sun wuce ta dawowa take koma kamar ba'ataba tabata da hunnu bama ballantana karyata.🤔
*COMMENT COMMENT COMMENT*
Ku kasance masu comment idan har kunason cigaba comment naku kwarin gwiwarmu,saina jiku comment more typing always.
✍🏻...........Abdul10k Naku a kullum.
💀💀💀
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
💀💀💀
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0⃣2⃣*
Atif tafe yake cikin jerin dogayen bishiyoyin nan,yayinda yake waige waige alamar baigane inda suka nufaba kuma babu alamar takun kafafunsu ta ko'ina,nan saiya fara kokonto anya bashi bane yabi sababbiyar hanya......amma duk da haka bai koma bayaba duk da wasiwasin dayake haka yayi ta tsusa kai cikin dajin.
Al'amarin su mu'azz ko tafiye suke cikin nishadi yayinda suke dauke dauken pics(hoto) na duk abinda ya burgesu a wannan guri...
Haka sumadai sukayi ta tafiya mai nisa,yayinda suka kuma manta da abinda suka bari a baya wato mota da kuma dalilinsu na tsayuwa anan guri.
Cikin wannan tafiyar da suke dai,suka ci karo da wata hanya mai matukar burkewa yayinda aka kayatar da hanyan da furanni iri daban daban,sa'annan aka jera wasu kananun duwasu masu launin pink da blue. Abin donin ban sa'awa Kai hatta iskar dake kadawa a wannan gurin ta dabance haka suka shige wannan hanya suka fara taku kowannin su zuciyar sa cike fal da burin ganin inda wannan hanya zata kaisu.......
*[Hmm Masu iyya magana kance kaddara takan riga fata,dako sunsan bala'in da suke tunkara da kuwa sunyi gaggawar yiwa kansu fatar mutuwa domin tafi sauki.]*
Tafiye suke yayinda suka daga kawunan su sama suna ta kalle kalle kai kace dan kauye a *London*
"Wow gaskiya duniya na dauke da abubuwan mamaki iri daban daban....."
Haka Mufyda ta furta cikin muryar mamaki,inda samra tace da ita
"Gaskiya ni tausayawa Atif nake wallahi,gaskiya yayi mummunar choices,danko yayi missing na wannan nishadi"
Fashewa sukayi da dariya bayan ta furta hakan...
Wannan firar da suke sun kasance suna yintane yayinda suke wannan tafiya.
"Wow" Haka Samra ta furta yayinda ta hango wata kyakkyawar bishiya mai launin golden color,kai kace ko da ruwan gold din aka halince ta,danko itatuwan wannan bishiyar launin gold ne,furannin tako fararene gayayenta ko kore......cikin sauri ta karasa hade da ciro wayarta ta soma dauka da hoto..sauran abokan tafiyan natako cen ta barosu a baya danko, hango bishiyar da tayi ta ruga izuwa ga wannan bishiyar,haka dai tayi ta daukar hoton wannan bishiyar. Bayan ta dakata dayin haka sai taga jikin bishiyar na tsastsagewa abin mamakin data gani kuwa shine wannan tsagewar da bishiyar keyi wasu harrufan rubutune ke bayyan ajiki....
Itako ta Kame guri guda ko motsi bata iyayi,sa'annan ta wani zura idanu har saida taga karshen rubutun... Abinda aka rubuta jikin wannan bishiyar ko shine.
*This is a warning*
Karku kuskura kushiga wannan hanyar idan har kunason kanku da arziki.....
Sai kuma alamar kan korangwal☠️☠️☠️dake nuna had'arin gurin.
Bayan ta karanci hakar sai jini ta soma kwararowa ta jikin rubutun a hankali yadda hawaye ke zubowa a fuskar d'an adam.
"Samra........ Samra.... Samra!!"
Haka mu'azz ya furta har sau uku kafin ya dan duki kafadarta....
Firgicewa tayi hade da juyawa cikin sauri tayi ido hudu da mu'azz,tsaye bayanta
Cikin muryar tsoro ta soma jero sunayen abokan tafiyar nata kamar haka.
"Nina,Ahmad,mu'azz,simon,ali,Harun,mufyda,muzzaffar yah kamata mu gaggauta barin wannan gurin it's dangerous".
Haka ta furta inda dukkannin su suka kai ganinsu kanta mu'azz ko cike da mamaki ya wangale baki,sa'anan yace da ita.
"Samra what's wrong?,wai maiyake faruwa ne are you alright?"
"yeah Nasan idan na gaya muku da baki bazaku yadda ba,amma zaku iyya ganema kan ku"
Haka ta furta hade dayi musu nuni kan bishiyar dataga wannan rubutun.
Dukkannin suko suka kai idanunsu gurin inda take musu nunin wato jikin bishiyar amma sai suka tarar da jikin bishiyar normal babu abinda ke jikin bishiyar ta..
*[Reader kuma dai shedune danko tare muka ga wannan al'amari da samra amma nasan dole su karyatata kuma mu bamu data cewa🙄🙄]*
"Nasan idan naaaa"
Haka ta soma cewa but dataga jikin bishiyar sai tayi shiru....
Ta soma jujjuya idanu sa'annan ta sake da cewa...
"Wallahi a jikin wannan bishiyar naga rubutu wacce ke fadin cewa wannan haryar a kwai hadari muyi gaggawar komawa.....kuma..."
"Enough"
Haka mu'azz ya furta cikin kara hade da murtuke fuska,shiru yayi na 'yan wasu dakiku ka finnan ya fashe da dariya haka sukayi ta mata dariya suna cewa wallahi imagining ne kawai take haka tayi iyya kokarinta wajen ganin ta fahimtar dasu but inaaa suko sunyi nisa bazasuji kiraba......
Kara gaba sukayi haka samra itama ta bisu badan son ranta ba,inda da barinsu wannan guri,saiga hannun wani abu mai munin gani ya bayyana ta bayan wannan bishiyar,yayinda kuma ya shafi gurin nan da samra taga rubutun....
Hannun nasa ma kadai abin tsorone danko faratun wannan hannun sunkai tsayin karamar yatsa na bil'adam,sa'annan gashi ta lullube sassar hannun kuma bakin kirin fatarsa ma haka baki kirin.
Ahankali ya shafi daidai inda Harun yasa hannun lokacin da yakewa Samra dariya,daidai wannan gurin abin yasa hannu sa'annan bayan ya dan murza ya soma daga hannun a hankali yana kaiwa sama yayinda nake biye dashi domin son ganin fuskar wannan abar.
Kai hannu yayi kusa da hanci sa,sai yajaa wata kakkaurar nunfashi,hmm wannan abar ko baida kyaun gani,dukda rabin fuskar sa ake iyya gani amma ko gaskiya abin tsoro ne sosai.
Idanun sa jajir kamar garwashin uta,sa'annan yana kuma da dogayen hakwara ga kuma murkushesshen hanci,haka zalika ga murd'edd'en kohu a kansa dad'in da danwa kuma yanada fukafukai irin ta jemagu a gadon bayansa.......sa'annan kuma gashi ta lullube sassar jikinsa,bazama ka iyya banbance gashin da fatar jikinsa ba da dukkannin su bakake ne.
Bude baki yayi ya cire harshe ya lashi hannun nashi daya taba inda Harun yasa hannun sa.....
Harshen nasa ko ayanke take gida biyu kamar ta maciji.
Bayan yayi hakan ne sai yayi wani abu wanda da dukkannin bincike murmushi yake nufi da hakan amma ko da zakaga wannan murmushi nasa tofa ina mai sumewa zakayi a gurin.
Bagaren Atif ko tafiye yake cikin tsoro yayinda yake ambatar sunayen su. daya bayan daya....
"Wai inane wayen nan suka shige,sun wani wahal dani kawai wajen naiman su"
Haka Atif din ya fur ta cikin kasar zuci hade dayin tsaki bayan ya gama furta hakan...
Inda Atif yake nada matukar banbanci da inda su samra suke danko nasu ababen mamaki suke ta gani amma Atif ko hmm ba wani irin hakan a bangaren da yake.
"Samra ki kwantar da hankalin ki,karki saka tsoro a ranki danko imagining ne kike,kuma kinsa tunanine kesa hakan dan haka just relax"
Haka Nina ta furta inda Ahmed da forzy suka ce da ita....
"Sa'annan ai idan motar mu ta gyaru za'a turo Atif yazo ya fada mana,shiyasa muke saka sheda tuntuni,dan haka karki damu kanki muna tare dake"
Gyad'a kai tayi alamar shikenan,sai sukaji *simon* da muzzaffar na furta cewa...
"Wow kunga ikon Allah,irin gini ta mutanen daa,kai abin mamaki"
Cikin sauri sauran tawagar suka karasa wajensu simon inda suka hango wannan gini babu 'bata lokaci suka karasa wannan guri inda suka fara daukan hoto yayinda suke cike da mamaki dukda wannan guri abin tsorone amma su sai ta zame musu abin mamaki except samra ita data tsorata tuntuni.
nan suke tsaye bakin kofar,dukkanninsu babu wanda ke da niya ko sha'awar shiga wannan guri,dukkan ninsu burinsu shine su dau hoto kuma suna kan yin hankan.
Harun ko tsaye yake bayan su ya kurawa kofar wannan gini ido,yace "tofa kowace irin mulki akayi anan gurin oho,sa'annan ko maiyasa aka rufe kofar da bakin kaca ma oho"
Wannan kofa dai ta kasance anyita da bakin karfe,kofar nada fad'in gaske ga kumaa tsawo.....
Alamomin dake jikin wannan kofar ko duk kawunan kwarangwal ne da suffofin su akayiwa kofar ado.
Da kaga wannan kofar kasan ba'a banza aka tsara taba.
Harun sa hannu yayi ya rike wannan kubar da'aka kulle wannan kofar dashi,kawai fa sai kacan jikin kofar suka soma tsistsinkewa......
Haka suka tsistsinke gabaki daya nan da nan suka zube kasa hade kuma da koma tur'baya.
Aiko tuni dukkannin su sunji hakan sun kuma juyo sun kurama kofar ido suna jiran mai zai biyo bayan haka.
Kofar da kanta ta bude kanta nanfa dukkan ninsu cikinsu ta dau ruwa suka soma dudduba junan su....cikin mamaki.
Nan kawai sai sukaji wata iska mai karfin tsiya ta zugosu cikin wannan kofar,bayan ta kaisu cikin tayi watsi dasu sannan kofar taja kanta ta rufe.
Karfin Iskar nan sai data jijjiga kowani bishiyar dake fadin wannan daji hatta dabbobi sai dasuka zube kasa sa'annan suka sake tashiwa.
Atif shima haka wannan iskar ta bugashi da wata bishiya.....ya zube kasa dakiyar yake iyya d'ago hannayensa.
☠️☠️☠️☠️☠️☠️☠️☠️☠️☠️☠️☠️☠️☠️☠️☠️☠️☠️☠️☠️
*COMMENT COMMENT COMMENT*
Ku kasance masu comment idan har kunason cigaba comment naku kwarin gwiwarmu,saina jiku comment more typing always.
✍🏻...........Abdul10k Naku a kullum.
💀💀💀
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
💀💀💀
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0⃣3⃣*
Nan kawai sai sukaji wata iska mai karfin tsiya ta zugosu cikin wannan kofar,bayan ta kaisu cikin tayi watsi dasu sa'annan kofar taja kanta ta rufe.
Karfin Iskar nan ko sai data jijjiga kowani bishiyar dake fadin wannan daji hatta dabbobi sai dasuka zube kasa sa'annan suka sake mikewa tsaye.
Atif shima haka wannan iskar ta bugasa da wata bishiya.....ya zube kasa dakiyar yake iyya d'ago hannayensa,yana dubasu.
Dafa bishiyar dake gefen sa yayi da hunnun sa ta hagu a sa'in da yake mikewa,hakan ko ya mike cikin kasala,yayin da yake dafa goshi alamar yaji rauni a gurin.
Mikewar tasa keda wuya sai yaji wata kara mai kamada kukar Damisa a bayansa.
Hakan ko akayi danko juyawar da zaiyi sai yayi arba da wata halluta mai kama da Damisar amma kuma girman wannan halitta tama zarce na kosheshiyar doki.
Sa'annan kuma gashin jikin wannan abar bakine sid'ik,ga kuma many'an hakwara da kuma many'an idanu jajir.
Bayan yayi arba da hakanne ya tika gudu a dari,yayinda wannan abar ke biye dashi a baya,kamar kurar dayayi shekaru da dama ba tare da ci ba,yau kuma saiga abinci har gida.
*Toh Yakuke ganin abar zata kasance*
Haka fa sukayi ta zaga wannan guri duk ramin da Atif ya shiga ya boye sai wannan abar ta kwakuloshi,haka ya marnewa Atif a baya,amma kuma duk da girman tasa baisa ya iyya kamo atif ba.
Cikin wannan yanayin suka kasance har saida suka tsinci kansu gabar wannan gini inda sauran abokan tafiyan Atif suka shige ciki,wato kofar nan mai cike da abar al'ajabi.
Bayyana sukayi a gurin inda Atif garin gudu wani itaace ya shige tsakanin kafafun sa kawai saiyaga kansa a kwance kasa.
Cikin sauri ya d'ago,amma ko 70% na jikinsa still a kwancen danko gwafewa yayi a gwiwar hannayensa, ta baya ya dago kai.
ganin abar tayi kusa dashine yasashi yinkurin mikewa,amma sadly bai sami damar yin hakan ba,danko wannan halitta tasa kafafun gaba ta turashi da baya,Atif ko sake tsintar kansa yayi a kasa hakan yasakashi ya soma jan jiki yana kuma jan kansa da baya yana kokarin tserewa wannan abar duk dayasan hakan bamai yuwa bane,danko taku daya wannan dabba zatayi ta murkusheshi,amma hakan baisaka ya karaya ba.
Haka wannan abin ya tsaya kallon sa,saifa dayaga yayi nesa kadan kafinnan yayi wup ya dire kan kafafun Atif, nanko Atif yakwarma bagidajiyar ihu haka wannan abin ya daga hannun da niyar yamusar fuskan Atif amma kuwa bayan ya daga hannun yayi arba da wannan gini.
Kwarma bagidajiyar ihu yayi shima bayan yayi arba da wannan wuri,cikin abinda bai wuce dakika guda ba,ya tarwatse ya tashi sama kamar hayaki ya lulluka cikin gajimare,abin dariyar kuma shine Atif a tunaninsa wannan ihun daya yine ta tsorata wannan abar,shi baisannan meye wannan halitta ya hango ba.
Bakin hayakin nan yayi ta tafiya cikin sararin samaniya yana naiman hanyar tsiratar da ransa.
Bayan yayi tafiya mai nisa cikin gajimaren sai ya rikide ya dawo mutum mai suffar jemage,wato yanada fukafukai a gadon bayansa irin ta jemagu.
Atif cike yake da mamaki dan ko da fari ya dauka shi ya razana wannan abar amma bayan yayi arba da wannan wuri nanko yasan inda yake fa ba karamin guri bane.
Mikewa yayi ya kurama wannan gini ido,tsakanin sa kuma da wannan kofa bata wuci taku ashirin ba kacal,haka ya kakkabe kurar dake jikinsa sa'annan ya daga kai ya gamawa wannan gini kallo..
"Ina dalilin tsoratan wannan halitta?ina kuma dalilin rugawar sa aguje? Bani da ansar way'anan tambayoyin."
Haka Atif ya furta cikin siririyar murya.
Bangaren direba kuma tsaye yake gefe guda inda wannan daya tsayar akan babur yake kokari wajen ganin yasa motar tasu tayi tafia,amma kuma duk da kokarin daya yake motar taki motsawa,suna kan hakan ne sai suka jiyo wata kara mai kama da Direwar *New clear* a sararin samaniya.
Dajiyo hakan kuwa suka kai ganin su sama, gani sukayi wata bakar hayaki ta wuce ta samansu,su atunanin su jirgi ce amma basu san wannan itace shatin guwar wannan bakin halitta daya biyo bayan atif bane.
Al'amarin Atif ko karasawa yayi wajen wannan kofa inda ya karanci wata kalma dake jikin wannan kofa ba tare da ya tada da hannu ba.
Karance wannan kalma keda wuya wannan guri tadau duhu sararin samaniya ta gauraya da haduri baki wuluk.
Ko'ina a wannan guri ta dau duhu ta fitar hankali haka zalika ida motar tasu ta lallace,tsawa aka soma wadda ke direwa kan manyar bishiyoyi tana kuma konasu.
Haka kasa ta soma girgiza kai kace sama zata fado,Atif kasa tsayuwa yayi da kafafunsa ta sanadiyar wannan azabebbeyar hali daya kasance ciki haka yake ta mikewa yana kuma fadiwa kasa kai kace d'an dake koyon tafiya ne.
Haka wata jar iska mai kamada hayaki ta fitowa ta wata fuji dake jikin wannan kofa,haka Atif yanaji yana kuma gani wannan iskar ta mamaye sassar jikinsa sa'annan ta jawosa cikin wannan fuji dabai wuce fadin karamin yasaba.
Da karfin tsiya wannan iskar ta zugoshi ciki,dukda nisan gudun da wannan halitta daya biyo Atif yayi saida wannan kofar ta jawosa ciki shima.
Dukda karfin da yake nunawa yana jan Kansa da niyar kubuta amma inaaaa saida ta jawosa ciki.
Yin hakan keda wuya iskar ta dauke wannan bakin hadirin ta yaye,komai ya bubbude rana ya fito ya haskake gurin.
Abin mamaki a wannan gurin kuwa shine,duk bishiyar data karye sanadiyar wannan guguwar kokuma ta kama da wuta ta sanadiyar tsawar ko girgizan kasa toh daga zaran wannan hasken rana ta ratsa kanta sai komai nata ya dawo freshOne.
*Wannan dajinko da bala'i take,gaskiya na tausaya wa Atif wallahi*
Duhune ta ko'ina acikin wannan wuri dasu Atif suka kasance ciki,a yashe yake a cikin wannan guri sa'annan ya wani santare kaikace gawa ne shi.
Ta dalilin haka muke kyautata zaton a sume yake.😂
Dukkannin su dake wannan gurinko a wannan yanayi suka kasance har na wasu Awanni.
Samra ce ta soma bude idanu,duhun wannan gurinne ta soma mata sannu da zuwa danko bata maa iyya ganin Tafin hannun ta ballan tana inda kafafunta suke....ganin haka yasata kokonto kota makance ne.
Haka ta mike daga kwanciyar da take,nan ta soma cewa "da wani a nan gurin ne?"
Tsoratata muryar tata tayi danko gurin na ansawa.
Haka yasa ta soma dafedafe kamar makauniya,ta daina cewa komi.
Ji tayi ta shuri wani Abu da kafa cikin sauri ta risuna tasa hannu ta dauka,sai bayan ta dauko ne tukun ta tabbarar da jakar tace ba wani abun bane na daban.
Cikin sauri tasa hannun ta Ciro wayarta,sa'annan kuma tayi sauri wajen kunna haske.
Tarar da kanta tayi a tsakiyar kasusuwan mutane,wasu suna sanye da kayan yakin su irin ta mutanen daa wasun kuma kogunan kawunansu ne kawai ta saura.
Kwarma bagidajiyar ihu tayi bayan tayi arba da hakan,wannan ihun nata ko shine silar tashin Atif daga dogon suman da yayi.
Bude idanu yayi yaga gurin babu alamar haske ko kalilan.....
Nan da nan yasa hannu cikin aljihu da niyar ciro waya....
But bayan yakai hannu cikin aljihu ya tuno aiko wayar tasa ta fadi a lokacin da yake gudun wancen halitta.....
Tsaki yayi hade da furta *Ohhhh shet* hakan ya furta yayin da yake mikewa......
Mikewar tasako keda wuya,sai yaga wata farar haske na tunkaroshi cikin salon guduwa.
Kafin ya ankara ko ganin kansa yayi a kasa ta sanadiyar garo da wannan haske da yayi......
Jiyo muryar *Samra* yayi ta buga ihu,nan ne yasan mutumne ke rike da wannan haske a hannu.
Daga kai yayi,yayinda Samra ta dago hasken fitilar tata ta haske fuskar *Atif*
Sake karma bagidajiyar ihu tayi a karo na biyu,danko bata tsammaci zata gansa a wannan gurin ba Danko a mota suka kyaleshi.
*Al'amarin sauran tawagar tasuko sun kasance suna guri guda,sa'annan haska toci hade da kiran sunan samra......
Daga cen nesa kana ina hango hasken fitulun nasu,Basu jima suna naiman nata ba sai suka tarar da ita tare kuma da Atif,sun cika da mamaki matuka danko basu san taya ya shigo wannan matsifar da suka fad'a ciki ba
Duk da Haske da suka haska a wayoyin su hakan batayi sanadiyar daukewar duhu ba,wannan duhu bata gusa ko'ina ba,hakan suka kasnce cikin tsoro..
Suna kuma tambayar kansu shin *ina suke* suna cikin wannan yanayin ko sai wayar *Mufyda* ta dauke uta....
"Muna cikin wannan yanayin mai na kashe utan toooo"
Furucin Simon kenan nan mufyda ta budi baki tace dashi.
"Taya Zan kace haske bayan kunsan nafi kowa tsorata anan guri...."
Kafin ta karashe furta hakan sai duk wayoyinsu ta dauke uta daya bayan daya.......
Samra ce nata ya dauke karshe.........nanfa duk suka soma waige waige dukda basu ganin komi......
Wani kara suka soma ji kamar ta motsin mutum nan sai Harun yace dasu....
"Dan Allah kowa ya kama inda yake,ku daina motsinnan dan kuna tsorata mu....
Atif and Samra nasan kune"
"Taya zakace mune baya....."
Haka Samra ta soma furtawa amma sai taji Atif yayi shiiiiiiiiiiiit alamar tayi shiru.
Hakan ko sukayi dikkansu suka kasance suna jiran mai zai biyo bayan shirun da sukayi......
Soma jiyo wata sauti sukayi *DIM DIM DIM* kaikace sawun samudawane.......
*COMMENT COMMENT COMMENT*
Ku kasance masu comment idan har kunason cigaba comment naku kwarin gwiwarmu,saina jiku comment more typing always.
✍🏻...........Abdul10k Naku a kullum.
💀💀💀
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
💀💀💀
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebo.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0⃣4⃣*
Wani kara suka soma ji kamar ta motsin mutum nan sai Harun yace dasu....
"Dan Allah kowa ya kama inda yake,ku daina motsinnan dan kuna tsorata mu....
Atif and Samra nasan kune"
"Taya zakace mune bayan....."
Haka Samra ta soma furtawa amma sai taji Atif yayi shiiiiiiiiiiiit alamar tayi shiru.
Hakan ko sukayi suka kasance sunyi tsit suna jiran mai zata biyo bayan shirun da sukayi......
Soma jiyo wata sauti sukayi *DIM DIM DIM* kaikace sawun samudawane.......
⬇⬇
Wannan sautin bana komi bane illa wasu sanduna dake rarrataya a jikin bago bangaren ne,hagu da dama,suke kamawa da wuta.....domin bada haske.
Soma ci wayennan sanduna sukayi yayinda haskensu ta haskake farfajiyar gurin na y'an wasu dakiku kadan sa'annan suka sake kafewa,haka Suka sake tsintar kansu cikin wannan duhu a karo na biyu.
Sake jiyo wannan karar cen nesa na yowa ta gurin su inda suke iyya hango hasken ta daga cen nesan nanko suka yanke shawarar bin wannan haske da zarar ta karaso cewar mu'azz *wata kila hanya take son gwada musu.*
Haka ko suka laminci zancen suka kuma ankare suna jiran wannan haske ta karaso,kamar yadda suka tsara haka abin ya tafi ba sabani..... wannan haske na ratsowa inda suke suka bita a guje yayinda ta kasance tamkar fitulu dake haska musu hanya.....duk da cewar tana kunnuwa na bayanta na daukewa......
Haka suke guduwa yayinda duhun kebinsu a baya.....Basu kuma tsaya da gudunan ba har saida suka tsinci kansu a wani guri mai dan karen guhu ga kuma zafi har nunfashin mutum na yankewa ya kuma dawo....nanfa Mu'azz yayi danasanin shawarar daya bayar danko wutan nan ta dauke sa'annan basu da damar komawa inda suka fito,domin basuma gane inda suke ba....
Suna cikin wannan yanayi na kaka nakayi sai Samra ta soma cewa.....
"Zamu iyya kwana uku batare da munci ko munsha ba,mako guda batare da mun sami hutu ba amma bazamu iyya minti goma ba tare da shakar iska ba....dukkan mu mutuwa zamuyi"
Cikin muryar kuka ta furta hakan...
,Furta wannan kalma ta mutuwan da Samra tayi keda wuya sai gurin ta dau shecking [girgiza] kaikace tashin Duniya..
Ga bakin Duhu ga rashin Nunfashi ga kuma girgizar....sa'anan basu masan akanmeye suke tsaye ba.
Al'amarin Wannan halitta Mai Kama da jamage kuwa tsintar kansa yayi a wata kazamemmiyar guri......Gurin na d'oyi matuka gakuma kukan kananun kwari da suka cike gurin.
Nan da nan ya kime ganin kansa cikin duhune yasakashi bude tafin hannunsa nan sai wuta ta tashi cikin tafin hannun nasa.
Ganin hakan keda wiya yawani jujjuya tafin hanun nasa cikin salon burgewa nan wasu abubuwa suka soma fitowa tacikin tafin hannun nasa.... Suna kuma haske yayinda suka kasance cikin suffar malam bude littafi.....haka suka mamaye saman sa.
Nan da nan Guri tadau haske matuka,ganin haka yasashi komawa halittarsa ta ainihi wato wata kyakyawar y'a mai farar idanu ga kuma gashi har gadon baya...
Cikin farar kaya take wacce akayi mata ado dajan furan ni.....
Nan sai tayi kama da y'ar shekara 15...
*Cigaban labari*
Wannan guri da take kuwa takasance tamkar bolar matattune.....Danko gawarwakine birjik a gurin.....
(Hmm Harna tuno da wani sharerren littafi na marubuci king articles, *Gidan matattu* )
Gani kanta cikin wannan yanayi yasa ta saki fuska alamar takaici,jujuwa take tana ta ganin gawarwakin iri daban daban,na muggan halitu ne,na aljanu ciki harda na Bil'adama......
Mafiyaa yawa a gurin sune Bil'Adam saikuma
Jinnu,sannan wasu halittu na daban.
💀
Al'amarin su Atif kuwa sun kasance cikin wannan duhu hade da girgizan kasa sa'annan nunfashi na yankewa na wasu dakiku kafin suka soma ganin wata jar haske na fitowa ta kasa yayinda kasar ke tsage.
Wannan hasken ne tadan yaye musu duhu suka soma ganin idanun juna.
Haka sukayi ta gujema wannan tsagewar ta kasa har ta kai ga rabasu gida biyu,bayan takai ga rabasun ne wannan girgiza ta tsaya haske ta haskake koyina sa'annan kasar ta daina tsagewa,kamar daukewar ruwan sama cek haka ta tsaya.....Harun ko yace.....
"Kar kowa ya motsa,bamusan maike lullube akasan wannan guri da muke ba.....
Dan haka karmuyi saurin fadawa wata matsifar kuma"
Haka ya furta cikin salon shawara....inda yake tsaye kuwa sunkasance su Biyarne, dashi da Samra da kuma Atif sai kuma Nina da Simon...
Sauran mutane kuma suma suna guri guda mu'azz mufyda da sauran su.
Saidai kuma Forzy data kasance tsaye take ita kadai... danko kasa motsi tayi har wannan abu tayi mata zobe.....
Dukkan ninsu dakwai y'ar Rata a tsakani,wacce da wuya mutum ya iyya tsalle ya dira wajen dan uwansa....
"Gaskiya a tsorace nake"
Haka forzy ta furta inda Samra Da Atif sukayi sauri cewa da ita cikin hadin baki.
"Forzy take it easy we are coming for you"
Bayan taji hakan yasa ta soma zubar da hawaye,ganin hakan ya dugunzuma hankalin Samra da sauran mutanen guri.
Tsoransu karsu motsa wani abun ya faru dasu..
Amma duk da hakan suna mai nuna kula ga Forzy din haka suka kasance suna mai kwantar mata da hankali cen sai Ahmad yayi wup yace dasu.
"Wait shin wai How long are we going to stay like this...... kuna nufin zamu kare rayuwan mu anan gurin kenan,Ya kamata mu naimi mafita bawai mu tsaya muna jiran tamu tazo garemu ba?".
Bayan ya furta hakan ne mufydah tace dashi.....
"Ahmad mayya taushe maka kwakwalwane wai?,maiya saka baka ganewa ne?,we are in danger Bamusan meye muke tsaye a kaiba taya zamu naimi hanyar barin nan.....so kake mu kuma jefa kanmu cikin wata rikicin na daban?."
Haka mufyda ta basa ansar marne kuma da tambaya....nan suka soma sa'insa a tsakanin su har takai ga Ahmad ya fusata yace dole saiya motsa izuwa inda Forzy take tsaye.
Shugabar tawargar tasu wato *Mu'azz* shima yayi dashi karya motsa but ina Ahmad yaki sauraransa yasa kafa yayi tsalle izuwa gurinda Forzy ke tsaye....
Dirarsa gurin suka Rungume juna.....yayinda Forzy ke zubar kwalla tana kuma furta kalmar godiya ga Ahmad....
Kwatsam sai sukaga gurin nan ta soma sauka dasu,yana nitsewa dasu cikin kasa.
Haka zalika guraran nan da suka tsastsage suka soma sauka kasa....har suka nitse cen
Nanfa Ahmad yayi nadamar abinda ya aikata danko gani yayi sun daina hango kawunan sauran abokan tafiyan nasu....
Sannan hallau gurin bata daina sauka dasu kasa ba.
Ji yayi gurin ta tsaya cek.....yayinda suko tuni a rungume suke sun kuma rufe idanu suna jirar saukar su kasan gurin....
Basuyi zaton abin zai tsaya suna da Raiba amma gashi sai suka kasance suna mai nunfashi kamar sauran halittu.
Kasar su kuma wuta ne ke ambaliya.....cikin wannan wuta kuwa koda dungulellen Bakin karfe datakai girman zuma Rock ka jefa ciki tofa nan da nan zata narke....
Haka gurin tadau haske.... Al'amarin Mu'azz da sauran ko tsaye suke yayinda suka kasa ganin komi ta sanadiyar bakar hayakin dake kashe musu ido.....
Kin bude idanu sukayi har sai da suka jiyo muryar Tina da Simon na cewa....
"Gasu cen!!" Cikin kara hade da murna....
Yayin da suke kuma nuna Ahmad da Forzy.....da yatsa.
Ahmad da forzy dai sun kasance rungume suke da a tuna ninsu sun ruga da sun hallaka basu san wannan shine mafarin wahala ga mai taurinkai ba.
Da jiyo hakan kuwa suka saki jikin juna yayinda suka kai ganin su sama.....
Yan misti mitsi suke ganin su....danko akwai nisa tsakanin su.....
Inda badan hasken wutar nanba da saidai suce sun sheka.....
Tsintar kansu sukayi akan wata y'ar *Gada* wacce iyya ganin ka bazaka yiya kureta da kallo ba.....sanadiyar nisa da kuma wannan bakar hayaki data jaguda gurin.
Wannan Gada dai tayi kama da Gadar mayu dan kuwa babu madafa sa'annan wannan gada ba wata fadi bace da ita.
Idan ka leko kasan wannan gada.....ko tsoro kurun zatasa hanjin cikin ka kad'awa.....
Kasar gurin nan gaba daya ta nitse cikin wannan wuta illa gadodi ukun Nan ne suka rage....
Wato wacce take dauke da Atif da Samra sai kuma wacce take dauke da su mu'azz sannan na Forzy da Ahmad dake cen kasa.
*Al'amarin* wannan kyakkyawar y'a kuwa tafiya take cikin kasaita....
Bayan takaiga indasu Atif suka baro daga farko sai wannan haske data kunna da karfinta na tsafi ta soma daukewa daya bayan daya.
Haka ta zura idanu dan bata zaci haka ba......
Bayan duk sun kafe,sai ta sake busar iska ta kunna wacce kunnuwar wannan haske keda wiya suka sake dauke wa.
"Tirkashi.....wannan bala'i da mai tayi kama?"
Furucin ta kenan....nan ta soma tafia cikin duhun ba tare da tasan inda take sa jafafunta ba....
Wucewarta keda wuya sai wasu muggan halittu suka baiyana a gurin data tsaya.....
Yayinda suka bita da kallo hade da rugawa suka bi bayan ta.....
Bangaren Samra ko taku suke a kan wannan Gada yayin da sunayi nisa sosai......
Cen suka soma hango karshe gurin yayinda Samra taja gwauron nishi hade da cewa....
"Ga cen hanyar da zata 'bulle damu"
Haka ta furta yayin da take yimusu nuni da yatsa...
Kwatsam ba shiri saiga wasu halittu sun ciko wannan guri......
Ta haryar da suka shigone wayennan halittu ke shigowa....
Wayennan Halittu sun kasance suna kama kadangaru amma kuma girman su da suffar su na tsorone....
Danko sunkai girman jakuna ga kuma kwara awaje kai kace *Kada*
Haka suka lodu cikin wannan guri ganin haka yasa Tina ta buga dan karan ihu yayinda take nunawa sauran abokan nata ta bayansu.....
Yin hakanko yasa duk hankulan halittun ya dawo kansu......
Nanfa wayen nan halittu suka soma rige rige wajen hayewa kan wannan gada domin zuga ga Wayen nan mutane wato su Atif....
Yadda suke kokarin hayewa kan wannan gada ko kai kace sun shekara dubi ba tare da sun ci ba....
Kai kace kudan zuma haka suka taru suna nufar inda su Samra da sauran mutanen suke.....
Ganin haka yasa suka ruga a guje.......
*Hmmmm🙄 I pity does guys wallahi*
Hakafa suka kasance suna gudun ceton ransu.....
Wayen nan halittun kuwa sai faman hayewa kan wannan Gada....
Nan gadar ta soma tsagewa....yayinda kuma wayenan halittu still na kokarin hayewa....
Rushewa gadar ta soma ta sanadiyar nawi nasu.....
Cikin kankanin lokaci suka riske su yayinda daya yayi Wup da Harun....
Kucelcila shi wannan abin yake yayinda ya kamosa a jakar dake gadon bayansa ganin hakan yasashi cire kansa cikin jakar ya dire kasa....
Nan ya saki rugawa a dari....haka wayennan halittu suka taru kan jakar tasa bayan sun tabbatar ba nama bace suka yowa kansu but it too late already sunkai kofar nan da suke hangowa daga nesa.
Karasowar Harun suka ja kofar suka rufeta........
Hmm Masu iyya magana kance Rashin sani tafi dare duhu....
Kuma duk wanda yaki jin bari zaiji oho......
Da sunsan inda suka tsusa kansu da basuyi gaggawar kai kansu ba......
Zai fi musu idan jira sukayi wayen nan halittu su cinye su.
Amma ya suka iyya tunda kaddarar suce......
Bayan sunja kofar suka rufe na iyya ganin wani rubutu da akayi a saman kofar.
Wacce itace *Mashigar ajali*
Yayinda suka kasance cikin wannan daki kuwa tsaye suke jikin kofar sai famar haki suke nan sai suka soma ganin haske na kunnuwa cikin sauri suka waiga baya.....
Abar sukayi da wani abun dayasa suka wangale baki Tina ko ta....sumewa tayi lokaci guda.......
*Toh fa meye wannan abin?*
*THANKS FOR READING*
*COMMENT COMMENT COMMENT*
Ku kasance masu comment idan har kunason cigaba comment naku kwarin gwiwarmu,saina jiku comment more typing always.
✍🏻...........Abdul10k Naku a kullum.
💀💀💀
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
💀💀💀
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0⃣5⃣*
Rike *Ahmad* yake da Hannun forzy,yayinda suke sheka gudu na fitar hankali.
Bayansu kuma wayannan halittu masu kama da kadangarune ke biye dasu,wayannan Halittun kuwa sunyi matukar kusanci dasu, danko acikin idan da wani yayi missing step to fa sai wanin shi Bade shi ba,danko Loma daya zasuyi dashi.
Cikin wannan Yanayin suka kasance Nayen wasu dakiku,Har saida suka kaiga Mabilla kamar yadda su Harun suma suka sami tasu mabillar.
Kofa suka hango daga cen nesa babu Bata lokaci suka dad'a himma sai da suka tsinci kansu cikin wannan daki kafin suka taka biriki,ta sanadiyar sun kai bangon karshe na wannan daki.
Abin Da yayi matukar Dagula lissafin Forzy tare da Ahmad ko shine,a guje suka shigo wannan daki yayinda tsoro ta hanasu tsayawa surufe wannan kofa bayan sun shige cikin. amma kuma sai suka tsinci kansu a wani faffadar guri kuma babu abinda ya kasance a bayansu yayinda suka kai bangon wannan daki.
Cikin mamaki suka Dubi juna yayinda zuciyoyin su ke cike da tambayoyi amma babu wanda ya furta hakan ga d'an uwansa dan kuwa ko sunyi babu mai ansawa a cikinsu.
*Al'amarin* Wannan aljana kuwa tafe take cikin duhu,yayinda take wannan tafiyar ko sai tajiyo sautin takun kafan mutum ya wuce ta bayanta cikin sauri.. Sa'anan kuma a razane ta waige baya..
Amma meye kuwa kuke Tunanin zata tarar abayan nata?
meye kuwa zata gani daya wuce empty place sai kuma shiru da gurin yakeda ga kuma dan karen duhu......
Batare datace komi ba ta jujjuya idanu zuwa kowani lungu da sako amma still babu wanda ke wannan guri.....
Ajiyar zuci tayi sa'annan ta waiga da niyar tafiya,amma kuwa koda taku guda batayi ba, ta sake jiyo wannan sauti a karo na biyu,amma kuma wannan karan akwai dan banbanci,dankuwa hade da dariya cikin siririyar murya tajiyo....muryar kaman na karamin yaro ko kuma yarinya.
Cikin sauri ta sake waigawa ta karewa wannan guri kallo ba tare data ga komi ba,hakanne ya sake tunzura ta,ta juyawa ta kuma soma tafiya cikin sauri but sai tasake jiyo hakan wanda wannan karon harji tayi karamin yaro ya ta'ba mata kayan jikin ta.
"Da wani anan gurine?"
Abinda wannan yarinya ta furta kenan,jin babu ansan data samu ne yasa tajuya.... kwarma bagidajiyar ihu tayi dan kuwa ba karamar razana tayi ba.
Abinda ya tsoratar da itan ko shine juyawar da zatayi sai wutan dace wannan guri suka kunna kansu yayi da suka bada wani sautin a yayin kunnuwar mai razana mutum wani *buUuu* yadda kasan Tukunyar gas ce ta kama da uta.
*TIRKASHI WAI ALJANI DA TSORON DUHU*
Aiko bata sake 'bata lokaci anan gurin ba,cikin sauri ta kara gaba....
Cikin wannan siririyar hanya mai kama da cikin kogon dutse take wannan tafiya....
Cikin Abida bai wuci dakiku Goma ba ta tsinci kanta gaban wani Zabgegen kofa.....
Mai matukar tsayi ga kuma duk sassar jikin kofar ta mamaya da zanen ababen ban tsoro....ga kuma yana data baje jikin kofar,da kaga kofar kasan tayi shekaru da dama ba tare da an bude ta ba.
Al'amarin su Atif ko yayinda suka kasance cikin kofan nan da akayi rubutu a samanta wato Mashigar Ajali....
Bakomai Yasa Tina suman nan ba illa tayi arba da wasu muggan abubuwa wanda a zaton ta sunfi wanda suka fito daga ciki hadari....
*(KUMAFA HAKANE🤔)*.......
Ba komi bane wannan illa wasu sangararun mutane wanda aka nannadesu cikin farararen kelle,kamar wasu Ghost...
Girman dakin nan na mashigar ajali ta zarce misali sannan kuma tayi kama da ma'ajiya irin ta mutanen da.....
Wayen nan sangaranrun mutane dai sun kasance a jejjere suke layi layi kai kace taron *asambili* akayi musu,wayennan mutanen dai basa mosti sannan kuma dukkan su tsaye suke kem... Kamar Gumaka.
Iyyakar ganin ka baza iyya hango karshen layinnan nasu ba,hakan yasa suka matukar razana da farko but daga karshe cika sukayi da mamaki yayinda suka tambatar da mutanen basu mosti.
Dukkan tawagan ko sai suka shige layi guda suna mai tafiya ciki,yayinda suke cike da mamaki danko basu taba ganin irin wayennan halittun ba.....
Gasu da hannu da kuma kafafu kamar y'an'adam amma saidai kuma sunfi y'an adam girma da kuma tsawo....
A cikinsu kuma babu wanda ya zarce dan uwansa da koda misalin tsayin al'lura....kawunan su daya.
Dukda cewar basu ga fuskokin wayen nan halittu ba ta sanadiyar nadesun da akayi da kellen hakan bata sa sunji wani iri ba sakai sukayi cikin suna ta taku.
Yayinda suka kasance cikin tafiyan kuwa,bayan sun farfado da Tina daga sumar da tayi sai wayennan mutane suka koma binsu da kallo...
Ma'ana duk Layin da suka wuce na sangaranrun mutanen nan,sai kaga kawunan halittun nan na juyawa yana kuma binsu da kallo wanda wannan kollon abin tsorone matuka domin kuwa idanun su jajir kamar garwashi wuta...
Dukda kellen da suka kasance ciki hakan bata hana nuna hasken da idanun nasu keda shi ba..
Hasken ya matukar haske wannan farar kellen....🧟♂️
*bangaren Forzy Da Ahmad kuwa* cike da mamaki suke guri guda nan sai suka juyo ganin su zuwa wannan kofa da suka shigo ta ciki.....
Tarar da wayennan halittun sukayi yadda kasan Kudan zuma,amma kuma kaf cikinsu babu wanda ya iyya shigowa wannan daki....
Ganin Haka yasa Forzy tayi ajiyar zuci tace da *Ahmed*
"Meye ma'anar Haka?"
"It means that we are safe"
Haka *Ahmad* Din ya Bata ansa itako dajin haka ta naimi guri ta zauna kamar tana da tabbacin fadar *Ahmad* gaskiya ne.
"Ah Lafiya kuwa malama?"
Haka Ahmad din ya jefo mata tambaya inda ta ansa masa da....
"Ina kaga lafiya a nan gurin kuwa,Hmm Tunda mun kasa sanin inda muke bare mu iyya naimi hanyar fita"
"Karki sami Damuwa Y'ar uwa,ina tare dake duk tsanani duk wuya,ni mai kare ki ne dan haka ki kwantar da hankali daya bayan daya komi zai dawo daidai"
Bayan ya furta hakanne tayi gajeriyar murmushi hade kuma da cewa....
"Shin kana nufin Zamuyi ta zama a dakin nan kenan har sai tamu tazo garemu".....
Bata kammala fadin hakaba sai suka jiyo wata kara mai kamada rushewar tarkace......a bangare guda na wannan daki da shike dakin nada girma basuma kula da bangaren dakin ba har sai da suka jiyo wannan sauti.
Cikin mamaki suka juyo ganin su zuwa bangaren,haka kuma suka soma taku a Hankali suna mai riskar wuri.....
"Hello! Da wanine anan gurin?"
Haka Ahmad din yake furtawa yayinda suka kasance suna nufar inda suka juyo wannan kara kuma sa'annan wannan bangaren ba wani haske bane da ita sa'annan kuma ba duhun cen ciki bane.
Wannan guri dai dasuka kasance ciki tayi kama da ma'ajiya
Danko dogayen *kabot kabot* ne a gurin,cikin kowani kabot kuma cike fal da Kwalaban magunguna irin ta mutanen da ga kuma ganyayyaki da dama duk suma dan hada magunguna suka kasance a gurin.
Forzy rike take da hannu Ahmad kem yayinda suke tafiya cikin sanda danko still wannan kara bata tsayaba kamardai ana using na kayukan ciki.....
Yayinda suka soma jiyo karan na dadd'a karuwa kuwa sai Ahmad ya juya ya kalli fuskar Forzy a wannan lokacin kuwa labe suke jikin daya daga cikin wayennan manyan kabut kuma suna kyautata zaton bayan wannan kabot dai zasu gane ma idanun su ko meye wannan abinda ke kokarin tsoratar dasu.
Cikin tsoro da kuma Rashin tunani Ahmad ya dauko wani yar itacen daya gani a wuri ya rike a hannu alamar duka zai dashi......
Nan ko ya kalli cikin idanun Forzy sa'annan ya daga y'an yatsar sa....
Alamar dai daga ya dungule hannun nasa zasu shiga a guje....
Hakan kuma sukayi danko yana gungule hannu suka sa kai.....
Abika dasu Atif ko,tafiye suke cikin jerin wayennan mutane,Dukda cewar an lullube su da kelle hakan bata hana nuna hasken da idanun nasu keda shi ba..
Hasken ya matukar haske wannan farar kellen....🧟♂️
Kicabus sukayi da saurar tawagar,danko wayenda suka shigo kofar da fari sune Atif Harun Tina Samra mu'azz.....
Cikin tafiyar tasu ko sukayi karo da sauran abokan tafiyan nasu wato....
Muzzafar,Simon,mufyda,Nina da kuma Ali.....
Cike da mamaki suka Rurrungume juya......
Inda Ali ya soma cewa...
"Ina labarin Ahmad da kuma Forzy?"
Haka ya furta cikin salon tambaya indako babu wanda ya iyya basa ansa...
Nan sai Mu'zzaffar yace dasu.....
"Wait a minute karkuce daga cen karshen dakin kuka tashi?"
"Eh hakane" inji mu'azz Samra ko tace dashi
"Mayyasa kace Haka?"
"Ai kuwa Tun dazu muke ta zagawa cikin wayennan kuma mun gagara samin hanyar fita.....
A tunanina zagayen Zobe kawai muke"
Da jiyo haka ko Samra,Atif,Harun da kuma Tina suka dubi juna cike da mamaki.....
Suna kan wannan tattaunawar yayin da suka tsaya guri guda....
Nan sai Nina tajiyo kara a bayan ta ba tare da tace da abokan tafiyan nata komi ba ta taka izuwa wajen daya daga cikin wayennan sangararrun mutane....
Kura masa na mazurai tayi ko kiftawa batayi nanfa sai ta kula shi wanda take tsayen gabanshi yana da banbanci da saura.....
Dan kuwa sanye yake da wata sarka wacce idan ba babban subane toh yana da matsayi cikin su.....
Nanfa Nina ta d'ale kan kafar sa ta ciro wannan sarka.....
Ta rike tana mai kallo cike da mamaki....
Kai kasa ganewa tayi wannan sarka na lu'ulu'une ko kuma harda Gold ciki dan yadda wannan sarka ke sheki kasan tana da matukar daraja.
Maye ko zai biyo bayan hakan........Hmm
Wani siririyar kara mai fasa dokin kunne ne ya tsahi awannan gurin inda suka toshe kunnuwan su ta sanadiyar wannan kara.... har dauke warta kafin suka sauke hannu....
Abin mamaki kuwa anan guri shine wannan karan bata fitini Nina ba kokadan danko bata sanma anyi ba......itadai kokarinta ta boye wannan sarka dan kar abokan tafiyan nata su gani.....shine abinda ta kasance tanayi.
Sa sarkan cikin jaka keda wuya sai wayennan Mutane masu kama da gumaka suka fara furta wani kalma da kaf cikin Zugar su Atif babu wanda yasan meye suke fada.....Danko bazaka iyya banbanta Kalman da Chinanci ba.
Bagaren aljanan nan kuwa tura wannan kofa tayi sa'annan tayi wani surutan tsafi dan naiman tsari kawai sai tasa kai cikin dakin...
da shigarta guri yadau haske,nan ta iyya gano cewa dakin da take ma'adanar kundine da kuma taswirori da duk jansin Littattafai.
Takasance kamar y'ar kauye yayinda ta kasance cikin wannan guri....
Sai famar kalle kalle take ta daga kai sama.....
Takun da tayi bazaikai goma ba sai taji kofan taja kanta ta rufe....
Wajen kofan kuwa wani kalma ya bayyana a jiki wanda tayi kama da karfe da yaji wuta...domin bai wani jima sosai ba kalmar ta bace wacce kalmar itace..
*MATATTARAR AJALI*
Taku take Cikin salon mamaki inda bata damu da kofan nan daya rufe a kanta ba,kawai ta kai hankalinta wajen kallekallen abubuwan mamaki.
Nan fa sai tayi arba da wani kundi a tsakiyar wannan daki wacce ita kundin a iska take yawo yayinda akayi mata ado ta musamman da ganin sa kasan bata banza bace...
Hakan ko yasa wannan aljana ta nufi wajen zuciyarta cike fal da burin dauko kundin....
Bai wuci daku ashirin bane tsakanin ta da wannan kundi kawai sai taji ta taka wani guri ya sauka kasan nan da nan ta tabbatar da akwai tarko a gurin amma Kafin ta ankare sai taji parat kibiya ya shigeta ta kafad'a ya fice ta baya....
Zubewa tayi a kasa yayinda jini ya mamaye gurin......
Nan sai wutar dake wannan guri suka soma kafewa har saida gurin ya dawo baki wuluk....
*Gaskiya banda shedar ta mutu* 🤔
Haka bangaren forzy da Ahmad kuma buga ihu sukayi ahhhhhhhhh yayinda suke kai wannan farmakin but tarar da gurin sukayi babu kowa nan sai suka zubi idanun juna....Hade da murmusawa.
Amma kuma yin hakan keda wuya suka kwarma bagidajiyar kara danko damin jemagu ne suka fito awannan guri....alamar makwancin sune nan.
Yayinda Ahmad ya rufe idanun sa,dan gudun kar su shigemar ido kuwa sai yayi arba da wata y'ar karamar yarinya cikin idanun nasa tana mikamar hannu alamar yazo gare ta.
Bude idanu yayi cikin sauri inda ya tarar da Forzy na sheka dariya danko ta razana matuka amma kuma sai taga bats ne.....
Shiko sam hakan bata basa dariya ba domin burinsa shine yaga wannan yarinya azahiri....but bai iyya ganin hakan ba.
"Akwai hanyar da zamu iyyabi mu fice daga wannan gurin"
"What are you talking about?"
Haka forzy ta ansa masa yayinda take ganin babu wata mafita da suke dashi wacce ya wuce su cigaba da zama a wannan guri....
"A nan gurin naga wata yarinya tana mikamin hannu tana kuma cewa nazo muje.....
Amma kuma bata fadamin inda zata kaini ba"...
Haka ya furta inda forzy tace dashi
"Ahmad wai yaushe kaga hakan?"
"Yanzun Nan"
Ansar daya bata kenan ita kuma ta sake jefo masa da wata tambayar....
"A ina, kuma tayaya?"
"Cikin kwakwalwana,kuma hakan shine kadai hanya dazamubi mu sami mafita daga Nan guri"...
Haka ya bata ansa.....
Itako ta sake da cewa
"But we are safe here"
Bai kula taba kawai ya juya ya fuskanci inda yaga wannan yarinya....
Nanfa ya sake lumshe idanu....yin hakan keda wuya sai ya sake arba da wannan yarinya...tana kuma cewa...
"Come to me.....come to me"
Cikin siririyar murya,forzy kuwa babu abinda bata fadiba wajen ganin ta dawo da tunanin Ahmad baya but inaa kwatakwata baya jin hakan....
Wannan yarinyar ko na kokarin kaiwa jikin bango yayinda take taku da baya kuma ta mika masa hannu.... bayan takai jikin bangon sai ta tsaya yayinda shi Ahmad ya nufota....
Kaiwa gurinta yayi sa'annan suka hade tafukan hannu yayinda yarinyar ke tayimar musmushi y'ar karama da ita....kuma kyakkyawa.
"Nuna mana hanyar fita".
Haka Ahmad ya furta,Kawai sai yaji forzy ta tsinkamar mari......
Bude idanunsa yayi arba da hannayensa na lumewa cikin wannan bango.....zura idanu yayi...cike da mamaki hade kuma da firgita
Ashe kuwa jawosa cikin bango take,haka forzy ta kasance tana mai zubarda kwalla tana mai cewa karsu rabata da Ahmad but ina wannan bango sai dad'a zugoshi ciki take nan sai ya sake lumshe idanu da niyyar sake magana da wannan y'a but maimakon yayi arba da kyakkyawan fuskar nata sai yayi da mugan fuskoki masu matukar tsoratarwa kuma sunkai sama da Hamsin suna rike da hannayen nasa suna kokarin jawosa ciki.
Forzy na kokarin janyesa daga jikin wannan bango sai ga wannan yarinya ta bayyana a fili tace da forzy.....
*"KI KYALESHI KIBAR GURIN NAN"*
cikin murya marar dadin ji ta furta hakan......
Biris Forzy tayi da fad'ar tata itako ta sake maimaitawa har bakin ta uku....
Kafin ta 'bace sautin muryar tako ya ratsa gurin tana mai cewa.
"Karkice manyi miki kashedi ba"......
Haka forzy taji na gani Ahmad ya nitse cikin wannan gurin....itako sai gata jikin bangon dan kuwa sun kasance a rungume suke da juna....
Zaune jikin bangon take tana mai cewa.....
"Mayyasa kuka rabani da masoyina"
Haka tayi ta nanatawa..... But then sai taga anyi mata rubutu ajikin bako da jini...
*"Leave Now"*
"Bazan taba fita ba"
Furta hakan take yayinda ranta a bace amma bata san su mutanen boye ba'a musu galaje ....
Sake rubuta mata sukayi a karo na biyu......
"Leave now....."
Amma sai ta ki cewa komi kuma taki tashi tabar guri....
Shesshekar kuka kawai take tayi.
Nan sai taga an jawo hannun ta na hagu an soma zazzana rubutu jiki yayinda naman jikinta ke tsastsagewa.....jini kuma yana kwararowa kasa.
Itako sai famar ihu take amma ina zata iyya kwato hannun nata...
Bayan an gama zana rubutun ne ta iyya karance abinda aka rubuta wacce itace.....
*Mutuwa ce makomar Ki*
Ganin haka yasa ta zura idanu cikin sauri ta d'aga ganinta izuwa jikin bangon inda taga duk rubutun da akayi naacewa tabar gurin ya dawo *DIE* Cikin tsoro ta zura idanu nan sai taji kofon wannan daki taja kanta ta rufe......
Hasken dake ciki kuma ta dauke.........yayinda itan kuma ta buga ihu
*AHHHHHHHHHHHHHHHH*🤪🤪
*SORRY FOR LATE UPDATE*🙏🏼
*THANKS FOR READING*
*COMMENT COMMENT COMMENT*
Ku kasance masu comment idan har kunason cigaba comment naku kwarin gwiwarmu,saina jiku comment more typing always.
✍🏻...........Abdul10k Naku a kullum.
💀💀💀
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
💀💀💀
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0⃣6️⃣*
*"Leave Now"*
"Bazan taba fita ba"
Furta hakan take yayinda ranta a bace amma ita bata san mutanen boye ba'a yimusu galaje ....ba
Sake rubuta mata sukayi a karo na biyu......
"Leave now....."
Amma sai ta ki cewa komi kuma taki tashi tabar guri....
Shesshekar kuka kawai take tayi.
Nan sai taga an jawo hannun ta na hagu an soma zazzana rubutu jiki yayinda naman jikinta ke tsastsagewa.....jini kuma yana kwararowa kasa.
Itako sai famar ihu take amma ina zata iyya kwato hannun nata...
Bayan an gama zana rubutun ne ta iyya karance abinda aka rubuta wacce itace.....
*Mutuwa ce makomar Ki*
Ganin haka yasa ta zura idanu cikin sauri ta d'aga ganinta izuwa jikin bangon inda taga duk rubutun da akayi naacewa tabar gurin ya dawo *DIE* Cikin tsoro ta zura idanu nan sai taji kofon wannan daki taja kanta ta rufe......
Hasken dake ciki kuma ta dauke.........yayinda itan kuma ta buga ihu
*AHHHHHHHHHHHHHHHH*🤪🤪
_*6DAYS EARLIER*_
_*KWANAKI SHIDA DA SUKA GABATA*_
Tsakiyar farfajiyar Ma'aikata zugar Mu'azz ne ke tafe yayin da suke daukar feelings....Hade da batsewa da nuna issa,basuko tsaya ko Ina ba Sai ofishin shugabar wannan ma'aikatar....
Shigarsu ko suka tsaya cirkwa cikwar Kamar wasu masu tallar magani....
Ganin su cikin wanna yanayi yasa shugabar tace dasu....
"Da'alamun Kunga sunayen ku a Marne ko....?Tafiyar zatayi taking place Next week da fatan bazaku bamu matsala ba....
Domin Munyi tajin kofare korafe tuntuni daga gareku tsakanin ku da dayar kungiyar da muka hada ku wannan Tafiya."
Gajeriyar murmushi Mu'azz yayi hade da cewa....
"Ko kadan Baza'ayi hakan ba Inshallah....."
Ma'anar sako shine Baza'a Sami matsala daga garesu ba.
Babu Bata lokaci suka Sa kai suka fice daga ofishin izuwa ofishin su wacce take makotaka data su *Atif*
A daidai wannan lokacin ko Atif da sauran mabiyan sa suna wani project Mai matukar anfani....
Amma Bayan sun gane hakan sai suka naimi hanyar da zasu durkushe wannan harkallah tasu....haka ko sukayi nasarar lalata komi ta sanadiyar hanasu sakat da saukin presentation nasu...dariyan su Atif suka tayi a karshe yayinda suka gane aikin ta lalace Kuma shugaban gurin na musu surutu......Hade da barazanar Basu suspended.🙄
*CIGABAN LABARI*
Cikin Kasala Take bude idanu yayinda hasken Rana ta haskake idanun Nata....
Cikin sauri tasa hannu ta Kare idanun Nata daga wannan haske....but then Bayan Tayi hakan ne tukun ta gane inda take,domin kuwa ido biyu Tayi da blue sky yayi da tsintsaye ke ta shawagi a sararin samaniya ga Kuma iska Mai daddad'ar yanayi na kadawa.....
Ido biyu tare da koren ganyaye ta ko'ina, Gajeriyar murmushi tayi hade da Kuma yunkurawa ta mike tsaye,nan Sai ta duba kafafun ta da Kuma kayan dake Jikin ta.....
Sake murmushi tayi a karau na biyu Bayan taga komi na jikinta normal...nan tayi Yar Gajeriyar shewa hade da tsalle fuskarta na cike da annashuwa but then ta tuno dalilin suman Nata......nan da nan annashuwan dake fuskarta ta koma bacin Rai Danko hada fuska tayi.
*Idan Kuna biye da wannan labarin sau da kafa zakusan wa nake nufi*🙄😜
Ba kowa bace wannan illa aljanan nan Wanda ta tsinci kanta a *MATATTARAR AJALI* wato ma'ajiyar muhimman taswirori da Kuma kunduna.....bayan ta Sami Rauni a wannan gurin ta sanadiyar taka tarkon datayi Kuma ta Fadi kasa ta sume saita tsinci kanta anan Gurin,Mai abin al'ajabi.
Cike da mamaki take yayi data tuno abinda ya faru a baya,nan Sai ta Soma kokonto kodai mutuwane tayi....?
Sake bawa kanta ansa tayi cewa"ai idan mutuwace bazana iyya anfani da baiwar tawa ba...but I still feeling I'm normal"....
Sa'anan ta sake Yiwa kanta tambaya a karo na biyu .......Kodai mafarki nake ne??
Amma a wannan karo maimakon ta bawa kanta ansa Sai tayi anfani da faratunta wajen yamusar kafadar ta Sai taga jini na kwararowa....
Nan ta sake tsalle hade da shewa Tana fadin na *tsira* _I'm safe_ daga wannan had'ari Dana shige ciki....
Bayan ta gama fadin haka Sai ta wani tsunkuya kasa ta wani yiwa gadon Bayan ta doroo....
Nan Sai Fuka fukan ta suka bayyana cikin abinda bai wuce Yan daki ku ba.......
Nanfa ta tashi sama ta Soma shawagi a sararin samaniya...🙄😲Wai shin Ta tsirane??Hmm😏 *who knows*
Al'amari su Atif da Mu'azz da sauran tawagar tasu ko tsayen suke yayin da wayen nan sangaranrun mutane na anbata... Wani batu Cikin wata yare da Basu taba jiyowa ba....
Amma da dukkan alamu furucin mutuwa suke Danko bbu abinda ya fimusu Dadin fada a wannan Guri Data wuce ta mutuwa....
Samra cewa tayi "Maiyake Shirin faruwa da mune??"
Kowa dake wannan gurin yaji wannan tambaya Amma Kuma sun kasance Basu da ansar da zasu Bata.....
Nanfa Sai sukayi yunkurin Guduwa but kwatsam Sai suka ga daya da Cikin sangaranrun mutanen nan ya sauko daga kan layin da suke ya shige gaban su...
Nanko suka take biriki shiko Cikin zafin nama ya Soma karasowa gunsu.....
Da ganin haka suka juwa da nufin komawa baya,shiko Cikin abinda bai wuci dakika guda ba Sai gashi a tsakiyar tawagar tasu....
Da hannu Daya ya shako wuyar Harun yayi jifa Dashi gefe guda haka zalika Ali.... samra ko ya sharara mata Tafi....
Da Dukkannin tunani wannan abin baso jimusu ciwo yayi ba Dan Bayan ya gama jifan dasu Sai ya tsaya gaban Nina ya kura mata ido....Yana wanu gwauron Nishi....
*Nina* a rikice take Sai famar karkarwar tsiya take yayinda wannan halitta na tunkarar ta,Bayan ya karasa wajen ta ya dago hannu zai taba fuskar ta kawai Sai yaji anhausa da duka dukan nin tawagar haka sukayi kaca kaca dashi....
Amma Cikin dakiku dakan ya sake lillikewa ya Dawo normal....
Murmushi yayi sa'anan ya furta *Let Fight*
Haka Atif da sauran abokan tafiyan nasa ke tsaye...
Sai suka Soma juyo sauran sangaranrun mutanen na maimaita fadin Dan uwan nasu wato *let's fight*
Haka duk suka sassauka suka yukura kansu....inda *Nina* Tayi wani Dan karan Ihu,Wanda da yin wannan ihu Sai wata haske ta tashi a kansu yadda kasan spark na utar lantarki haka ta tashi a kansu....Domin kuwa tuntuni da ganin yadda sangaranrun mutanen nan na furta let's fight suka Marne Guri guda.
Wannan wutar daukewa tayi daidai da bacewar tawagar....
Inda sangaranrun mutanen nan da sukayi caa gurin Sai suka Tara Babu kowa,nan fa sukayi takaici hade da juyawa izuwa wajen wannan da Nina ta cire sarka a wuyan shi....
Yimasa zobe sukayi yayinda suka daddafe shi da hannu Wanda Kuma Bayi da damar dafashi zai dafa Wanda ke gabanshi haka sukayi inda suka taru Guri guda....
Yayinda shi Wanda aka cire sarkar a wuyan sa na kokarin tarwatsewa....
Haka suka Soma wasu surutai yayinda duk jikinsu ke bada haske....
Bayan yin hadan da sukayi nadan wasu dakiku sai suka dago fuskokin su sama hade da kwarma ihu da alamar sunajin radadin yin hakan.....
Bayan sunyi hakanne Sai Mayafan dake fuskokin su suka zuzzube kasa.....
Nanne Muninsu ta bayyana a sararin,Domin ko da makaranci zaiyi ido hudu da fuskar wannan halitta,toh da zai iyya Suma dan tsantsar Muni da Kuma firgita.........
*Bangaren wannan Aljana* kuwa Bayan Tayi ta shawagi a sararin samaniya Sai tayi niyar nitsewa Cikin gajimare.... _but guess what happened_
Ji tayi,tayi karo da rufin daki Wanda Kuma kaurinta Kamar ta dutse....ji kawai ta sauka kasa yadda kasan laida haka ta Fadi kasa.....
Nanfa ta daga idanun ta karewa wannan gurin kallo....yin hakan keda wuya sai wannan Guri ta Soma durkakewa Tana komawa ainihin yadda take da alamun wani salone ta sirihi ta fada ciki.....
Cikin abinda bai wuci dakika guda ba ta tsinci kanta a jerin wannan kabot kabot na taswirori....
Nan Sai tayi sukum ta kasa cewa komi, matukar tsora Tayi a zuci...har idanun ta ya cike da kwalla....saura kiris ya zubo but then Sai taji ihu mutum ba kowa ne ya Fara zuwa mata a kwakwalwa ba illa Atif......
Sai tayi wani magana a kasar zuciyar ta..... "Idan ni Aljana ina da kuka inaga Dan'adam Mai Rauni,yakama ta nayi iyyakan kokarina wajen kareshi domin na sakashi Cikin wannan matsifa"....
Wannan ihu data jiyo kuwa Bata kowa bace illa ta *Forzy* dake gudu Cikin high speed.....
Yayin da wata Bakar hayaki Mai duhu ke biye da ita abaya...
Wannan Bakar hayakiko ta kasance Koda karfene ta ratsa wannan karfe saita narke bare itatuwa ko Kuma Naman mutum....
Aljanan ko ganin ta Cikin wannan hali yasa taa bude fuka fukan ta tayi cep da ita suka tashi sama yayin da wannan hayakin ta mamaye ilahirin Gurin.... Wato Cikin Ma'ajiyar.
Forzy Lumshe idanu tayi yayinda wannan Aljana ta fire da ita Amma daga bisani ta bude idanun Cikin yanayin tsoro... Bayan Ta hada ido da Aljanan ko Sai ta kwarma bagidajiyar ihu hade da sumewa....
Yin Hakanne yasa Tayiwa Aljanan nawi ta kasa Rike ta dako Tana fama da Raunin dake kafadar ta....
Haka ta sadaukar suka fada Cikin wannan hayaki.....
Yayin fadowar suko Sai ta rungume Forzy hade da yimata Makari da Fukafukan nata....saukowa suke Cikin high speed hade da bagidajiyar ihu Mai Kada Hanjin Cikin Dan'adam.
Al'amarin Su Nina Ko baiyana sukayi wajen wata Gabjejiyar kofa yayin da sukayi arba da Wani Dan gini da akayi a gaban Kofan Mai kama da *standard table* saman sako shatin tafukan Hannu ne.....
Cikin mamaki suka gubi juna hade da karasawa wajen Kofan da niyar bude wa but Sai sukaga Tana da banbanci da wayenda suka baro abaya.....
Danko wayenda suka wuce a baya daga sun taba Jikin kofar saita bude kanta Amma wannan maimakon ta bude Sai ta tsaya kallon su.
Bayan sungane basuda karfin bude wannan kofa Sai suka juyo hade da gamawa gurin nan da suke kallo....suka duba lungu da sako ba tare da sun motsaba illa jujjuya idanu dasukayi tayi.
Hanyoyi sukayi abar dasu har uku wance suke Kama da Cikin kogo....
A Cikin kowace hanya dayako bala'in da suka baro a bayane ke zuwan musu ta ciki......
Hanyar farko Ruwan utane ke zuwa ta ciki yayin da take anbaliya.....
Ta biyun ko wayennan halittu masu Kama da kadangaru suke zuwa ta ciki....
Last one ko wannan Bakar hayaki Mai narkar da duwasu,itatuwa dadai sauransu ne...ke zuwa ta ciki.....
Ganin haka yasa suka buga ihu hade da rugawa izuwa Jikin kofar suna Mai bugawa hade da raukon kofar ta bude kanta.....
#Nina ko tsayen take Sai ta Soma jiyo wata siririyar murya nayi Mata Rad'a Cikin kunnuwan ta.....
Abinda take jiyowa ko shine.... *The Key* !! *Makullan* suna ina find it..... find the key.....
Haka take jiyowa Cikin kunnuwan nata,haka ta saki jiki ta karasa wajen wannan Abin Mai dauke da shatin hannun mutum a sama.....
Bayan ta haye Guri Sai tayi murmushi hade da cewa.... "Tafukan Hannu sune makullan Kofan nan I'm sure"
Nina batasan yayinda ta furta hakan Cikin karaba..... sauran abokan tafiyan nata dajiyo haka suka juyo izuwa gareta Atif yayi furucin "What do you mean??"
Maimakon ta basa ansa ko Sai ta Daura tafukan Hannu Nata kan wannan shatii.....nan da nan gurin ta nitse da tafukan hannayen Nata,iyya wuyan hannu....ne ta nitse.
Ganin haka yasa suka cika da mamaki Kamar suna da tabbaci hasashen Nina gaskia ce.....
Ji sukayi Kofan na kokarin bude kanta haka suka juya suka kura masa ido harta gama budewa....
Aikuwa kan Kace Kobo tuni sun shege ciki..... Juyawar dasukayi suna murna Sai suka tarar Nina Bata Cikin sahun nasu....
Cikin mamaki suka yiwa kawunan su tambaya ina Nina... Juyawar da zasuyi Sai sukayi arba da ita tsayen hallau wannan Abin dai na rike da hannun Nata...
Mu'azz yukurin Zuwa yayi Amma Bayan Atif yayi arba da wayennan muggan abubuwa dake kokarin karasowa garesu Kuma sunyi kusanci da ita nina sosai ta yadda Babu Wanda zaije gurin ya iyya ceko rayuwan ta su dawo tare... batare da muggan abubuwan sunyi kacala dasu ba.
Yasa Atif yaja Kofan da karfin tsiya ya rufeta..... wannan dalili yasa Atif yaja kofar ya rufe ba tare da Mu'azz ya fita domin ceto Nina ba.🙄
*TIRKASHI ANCE LAIFIN DADI KAREWA.*
*FANZ INA MAI MIKO SAKON GAISUWA GARE KU HADE DA BAKU HAKURI AKAN LATE UPDATE DANAYI NA WASU MONTHS INA FATAN MY FOLLOWERS KUNSAN DALILINA NA TSAYAWAN.....DAN HAKA BA SAINA SAKE DOGON BAYANI BA NA GODE DA SOYAYYAR KU FANS*
MUHADU A NEXT PAGE AMMA KU SANI COMMENT NAKE BUKATA MASU ZAFI DAN SAMUN KWARIN GWIWA😜
💀💀💀
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
💀💀💀
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0⃣7️⃣*
"Forzy!! Forzy!! Forzy!!"....
Cikin Sanyayyiyar murya takejiyo hakan,muryar maishi ko na Fita Cikin Rad'a alamar Mai Kiran wannan suna bai bukatar wani ko wata na daban ya jiyo hakan....Forzy ko cikin salon kasala ta bude idanun.....nata inda tayi Arba da abin daya matukar bata mamaki wanda wannan abun ko shine,hada Ido tayi da Ahmed a zaune gefen ta wanda shine Mai Kiran nan nata,Cikin farin ciki hade da murna ta yunkura hade da rungume sa.... zubar kwalla ta soma Tana mai cewa.
"Banyi Zaton Zan sake saa kwayan idona a naka ba *Ahmed* ,A tunani na Narasa Kane Har Abada.....Amma mayyasa ka zabi ka kyaleni a baya? Mai yasa kakijin shawarar Dana Baka??,Koda shike mubar wannan magana a gefe guda tunda gashi kaddara ta sake hadamu,Dan haka Ahmed Dan Allah karka sake barina Cikin kadaici.... domin kuwa Nayi kewarka sosai."
Hakan ta furta yayin da suke a rungumen da juna....Tana Kuma shesshekar kuka
*Guess what* Budar bakin Ahmed ko yace da ita.
"Yanzu atunanin ki tare muke ne Forzy??"
Tambayar Daya matukar razana Forzy Kenan hade da dagula tunanin ta,kasa sakar jinin nasa tayi danko still rungumen suke da juna...........
Zuciyar tako bugun uku uku ta Soma,Cikin yanayin tsoro ta saukar da idanun ta kan gadon Bayan Ahmed....
Cikashi tayi Cikin sauri hade dajan jikinta gefe guda Bayan tayi arba da gadon Bayan nasa Wanda jinine ke zubowa ta sanadiyar manya manyar Raunin dake gadon Bayan nasa,Wanda suka Kuma rube hakan yasa har Mayan tsutsotsi ke ta shagalin su aciki.
Forzy ko datasan Abinda zata tarar a fuskar nashi dako tayi hakuri su kasance a rungumen har *illa Masha Allah*
Bayan ta cikashin ne taja kanta da baya tayi Nesa dashi ba kadan ba,nanfa ta Sami damar duba hannayen nata......
Hmm Mai zaifaru kuwa??atunanin ku
Tsutsotsin ne suka mamaye hannayen nata biyu,yadda kasan Kudan Zuma haka suka mamaye ko'ina a hannun nata....
Forzy Ihu take tafitar hankali yayinda zazzafar kwalla take zubowa a fuskar,haka zalika ta kasance Tana kokarin sharesu daga Jikin nata Amma ta gagara hakan Domin Kuma kokari sune su shiga Cikin Naman Jikin ta.....
Dago idanun ta datayi kuwa Sai tayi arba da fuskar Ahmed din Wanda yin hakan yasa ta sake buga ihu hade da sumewa.....Hmm
Munnin Fuskar Ahmed tayi tsanani ta yadda ba mutum ba ko bakin aljanine zaiyi arba da Shi saiya razana.....
Ihu hade da yunkurawa tayi ta yadda saidata Mike tsaye kafin ta take biriki,Nishi tasoma nafitar hankali Kai Kace dutsen Uhud aka daura mata...a gadon baya.
Bayannan sai ta d'ago Hannayenta ta Dubai,shasshafawa tayi daga gwiwar Hannu zuwa wuyan sa kafin nan tayi ajiyar zuciya sa'anan tayi wata magana kasar zuci cewar ta shine.
"Allah Nogode da wannan bala'i ta kasance cikin mafarki ne.....Ba'a zahiran ce ba
Yah Allah ka kareni da kariyar ka,ka kuma gafartawa Ahmed idan nashi tariga ta riskeshi" ....
Bayan Tayi wannan addu'a Sai ta Duba hagun ta da muka dama.....iyya ganin ta duhu take iyya gani.... Nanfa Sai ta sake yin wata magana a kasar zuciyar ta akaro na biyu.
"Hmm Shin Yanzu zan kasance Cikin kadaici awannan Guri Mai matukar had'ari........."
Tana kan furta hakan kuwa Sai tajiyo muryar Atif juyawar dazatayi Sai taga gasu cen suna tafia Cikin wannan duhu....
Da faruwar haka bai wuci dakiku goma ba fitulun gurin suka kama kunno kanwunan su,Nanko Su Atif suka iyya ganin ta haka sukazo a guje suka rurrugume juna,Cikin Farin ciki da Kuma murna tayi ta hamdala...
Suko suka sakata a tsakiyar su,suna me cikata da tambayoyi akan yadda Tafiyar tasu ta Kaya sa'annan ina labarin Ahmed...
Babu bata lokaci ta kwashi labarin komi ta Basu hade da tabbatar musu da cewa Ahmed ya rigada ya mutu tuntuni.....
Budar makin Atif ko Sai yace da ita *"Kamar Yadda duk Nan muka mutu Kenan"* dajiyo wannan batu na Atif Sai Forzy tayi tsit na Yan dakiku kafin tace dashi....
"Atif kana Tsorata ni fa"
Dajiyo haka kuwa samra ta juyo kanta ta baya....ma'ana fuskar ta ta koma baya keyar takuma ta Dawo gaba Sai tace da ita...
"Kamar Haka??"
Haka Forzy ta sake shiga halin tsoro Wanda ya ninka wancen data Fita daga Cikin sau dari.....
*Al'amarin Su Mu'azz kuwa* yukurin Mu'azz yayi Domin zuwa ya ceto *Nina* Amma Bayan *Atif* ya tuno da wayennan muggan abubuwa dake kokarin karasowa gurisu Kuwa sai Yasa Hannu yaja Kofar da karfin tsiya ya rufeta.....
Mu'azz ko karasawa wajen nasa keda wuya ya shako kwalar Atif hade Kuma da cewa..
"Why do you do that?? You kill her"
Furta hakanne Yayi Cikin fushi yayinda ya shako kwalar Atif....
"Nayi Hakan ne Domin na ceto rayukan mu,You get it?"
Ansar da Atif din ya basa kenan....shiko Cikin sauri ya cika kwalar nashi hade da furucin *Oh shet*
"Shin kasan Mai ka aikata kuwa Yanzu?? Answer me
Haka ya sake mayarwa da Atif Samra ko tace dashi....
"Ai Ni kokadan Banga laifin da Atif yayi ba...
Domin Dukkannin mu Sabon rayuwa ya bamu Kuma Ina kyautata zaton koshi ya kasance a wannan yanayi zai so muyi hakan Domin mu tsira daga halakar da zamu shige ciki....
Kuma Bayan Nan Ina kyautata zaton Nina itama zatayi alfahari da haka Domin ita ta bamu damar tsira daga wannan hali."
Haka saura tawagar sukace Kwarai ckin hadin baki sa'annan Ali ya daura da cewa....
"Samra kinyi gaskiya Domin koni bazan so wannan taro tamu ta salwanta ta dalili na ba...."
Tina ko tace dasu
"Gaskiya I'm so scared.....Sai nakeji Kamar bazamu Fita daga Nan gurin ba...
Domin Tun d'azu sauka kasa muke tayi"
"What are you talking about??"
Haha samra ta jefo mata tambaya itako ta Bata ansar cewa...
"Shin Wai Baku ga hakan Ba,Tun dazo Sai sauka muke akan manyan matattakalu bacin munsan kofar daki Daya muka shiga Wanda girmar sa bai wuce misali ba Amma har Yanzu sai kwancecciyar hanya muke ta gani marar iyyaka"
Mufyda ko Shesshekar kuka ta Soma inda Simon ko yace da ita *meye hakan??*
Alamar ta bashi kunya itako Sai tayi musu Nuni hade da cewa...
"Gaskiyar ki Tina kudubi cen ku gani".....
Haka Dukkannin su suka juyo ganin su izuwa wannan Guri datake nuna musu....
Gani sukayi still sabuwar hanyace marar iyaka....
Da shike wannan daki da suka shige ciki ba wani duhun kirki bane gareta,shiyasa suka iyya ganin haka...
Hanyan Kuma ta kasance mamaye take da kasusuwan Mutane....
"Oh my!! we are all going to die down here!!"
Hala mufyda ce ta furta hakan Cikin muryar kuka yayinda *Muzzaffar* yace da su....
"Wait a minute guys shin gaskiya ne zancen Tina na cewa sauka kasan Gurin mukeyi....if yes Taya zamu kubuta daga wannan bala'i Kenan??".....
Harun Yace "Who knows.....Oiii gaskiya Tuntuni mukayi Kuskure Kuma I'm pretty sure bazamu iyya Gyara wannan Kuskuren ba"
"Hold it,what do you mean??"
Haka Atif ya furta nanfa suka fara cacan baki Kamar zasuyi fada..
Samra ko Kwarma bagidajiyar ihu tayi cewar ta shine *Ya issa* tsit sukayi Danko sunyi matukar razana Domin kuwa Guri ya anshi muryar nata....
"Yakamata mu dukufa Cikin Naiman Hanyar tsira daga wannan Gurin da muka kasance cikin bawai mu tsaya rigima a tsakanin mu ba"...
"I'm with you 💯%"
Cewa Ali Kenan Harun ko yace
"Maganar ki haka take, Dan ko masu iyya magana na cewa zama Guri daya Tsautsayi".....
"But am about to ce muku mu naimi Guri muya da zango Dan kuwa wallahi a gaje nake tilis...."
Cewar Mufyda inda Tina tayi sauri Bata ansa.....
"Ehye toh an Sami bakin magana harda cewa a huta....
Keda Kika cika Mana kunnuwa da Shesshekar kuka Amma Yanzu harda cewa muhuta Kamar Hutu ne ya kawomu Nan....."
"Hmm Kyale ta Tina....." Haka Samra ta furta yayinda take kallon Tina sa'annan ta juyo kan mufyda dake zaune tace da ita ..
"Kinga Yadda muke a tsayen Nan ko minti guda bazamu Kara a Nan gurin ba tunda kowa ya amince da aje a naimi mafita so idan Zaki iyya zama ki huta kibi Bayan mu anji toh wannan Kuma shawarar kine tarage Miki Amma mu a'a wallahi"....
Haka Suka Dauki zuga suka shige wannan hanya inda suka kyaleta a zaune but then ta mike Cikin sauri tace kujira ni....Haka tabi Bayan su...aguje
Bayan sun bar wannan Guri ko Lakanin wannan kofa ta baiyana wacce itace.....
*MAFARAR BALA'I*
Al'amarin Forzy kuwa Toshe kunnuwan ta tayi niyarta ya hanata jiyo dariyar da su Atif suke yimata Mai matukar Razanawa Amma hakan Bata hanatajin komi ba.....
Gangar Jikin Taki na kwance a Cinyar Aljanan Nan Yayinda Jikinta tayi matukar zafi ga Kuma birgima da takeyi....
Hakan ne ya tabbatar mini da cewa mummubar mafarki mai hadarin tsiya Forzy takeyi.....
Wacce ta gagara farkawa dukda cewa Aljanan Nan na iyya kokari ta tashe ta Amma hakan Babu abinta ta haifar....
Ganin haka yasa Aljanan tayi tunanin Mai zai hana tayi anfani da Karfin baiwar da take dashi wajen gano halinda Forzy tace ciki....
*Bad Idea*
Daura tafukan hannunta tayi a goshin Forzy hade da Lumshe idanu....Amma Bayan Haka Sai ta Soma kakkarwa kaikace sanyi takeji Tana Kuma kokarin bare hannunta a goshin Forzy but Ina saida jini ya Soma zubowa a hancinta daga bisani Taji iska Mai Karfin tsiya Yayi jifa da ita gefe guda....
Cikin Kasala ta d'ago Kai ta kalli inda Forzy ke kwance....
Nanfa Sai taga Forzy ta farka a fisace....yadda dai Ake farkawa idan akayi mummunar mafarki,Koda shike natan ba mafarki bane Danko Bayan ta farka Sai taga shatin Hannu Atif Daya matse Mata Hannu.. Amma Kuma abinda ya Bata mamaki shine Babu na wayennan tsutsa....
Nanfa Aljanan ta yunkura Cikin murna hade da ambatar sunan Forzy.....
Abinda ya matukar dagula tunanin Forzy Kenan har yasa ta Soma ja baya Tana *Karki cutar Dani,Taya kikasan Sunana??*
Aljanan ko Bayan taje gareta Sai tace.....
"Cutarwa kuma??"....
Shiru Forzy tayi ta Soma tunanin Ina taga fuskar wannan yarinya......
Aiko Bata tuno ba har sai da Aljanan ta taba ta duk da cewar tanawa Aljanan kashedi da kartayi hakan Amma sai datayi......
Nanfa Sai ta tuno yayinda wannan bakin hayaki yabiyo ta aguje,da Kuma lokacin da Tayi Ido hudu da Aljanan....a lokacin da suka fire sanan.
Nan Sai ta Soma cewa *kece wallahi kece.....kece wacce na gani!!* Tana ja da baya..... Daga karshe kuwa ta sume Dan ta razana.....da Kuma mamakin datayi.....
Kamar kiftawar idon sai Aljanan ta dire a gefen Forzy tace.....
"Oh Poor girl maiya kawoki wannan Gurin Mai wuyar sha'ani"....
Bata Gama Fadar Haka ba sai Taji sawun kafa na Guduwa a Bayan ta....
Nanfa sai ta tarwatse Kamar hayaki ta bayyana a gaban Mai guduwan....
Ganin haka yasa sake juyowa da niyar guduwa....but still ya sake shiga gaban sa.... Kamar walkiya
Bude tafin Hannu tayi Sai Wuta ya Soma ci a hannun nata.... sa'annan ta Soma cewa
"Who are you? and Why are you doing this to us"
Shiru kakeji babu ansa ganin Haka yasa ta karasa wajen maishi da niyar ganin fuskar sa amma kuwa sa Hannun da zatayi sai Taji ya Fadi kasa...
Saida ta tsunkuya kuwa ta fahimshi Suma maishi Yayi ta dalilin razana da maishi Yayi.....
Shin kokunsan Waye wannan ba kowa bane illa Nina....Wanda Tawagar ta suka kyaleta a baya.....
*_How possible_ ?? Gaskiya jikina bai dauka ba Amma muje zuwa*
Aljanan hadasu tayi Guri guda da Forzy inda ta zauna gefen su....
Nan Sai tayi magana kasar zuci cewar ta shine....
"Taya Mutum Daya na Koro izuwa wannan daki Amma Kuma sai hayayyafa suke??"
Idan muka leka bangaren su Atif kuwa zakuga Tafiya suke Cikin tsoro yayinda suke zaton a kowace lokaci mutuwa zata iyya riskar su....
Kuma Basu tsaya da hakanba har saida sukaji Samra tayi salati....
Nan Dukkannin su suka juyo hade da cewa.....
"What Again? Samra"
Cewa tayi Don't move.....Amma suka cikata da tambaya maiya sa....
Cewa tayi dasu....
"Muna saman Rijiya"
Atif ko shiru Yayi Danko tuni yaga hakan.....
Bakin wannan Rijiya ko Tayi Girman Roundabout guda na babbar jaha....
Wacce suka kasance suna tsakiyar saman wannan rujiyan......
Ask me how.....Rijiyar Rufe take da kankara ta yadda bazaka gane Rijiya bace saika hau tsakiya.....
Bayan kahau tsakiya ka kalli kasa to zakaga Rijiyane Mai matukar duhu a kasar Kuma duk wanda ya fada ciki Hmm *Bana Ce ba*
A tsastsaye suke suna ta kallon idanun juna kowa na tambaya meye nayi ne yanzu.....
Sabida motsin da sukayi akai tasa Gurin ta Soma tsagewa....
_*Kadan Daga Labarin wannan Rijiya Kuwa*_
Rijiyar ta kasance Gaba Dubu Wacce fadinta ta wuce misali.....Kasar tako manya manya macizaine masu Girman gaske ne a kasa.....
Kuma Duhun kasan wannan Rijiya takai makura ta yadda Koda Fitula ka fada ciki dashi bazakaga na gabanka ba...Balle ka fada Hannu Rabbana.
*CIGABAN LABARI*
Tsastsaye suke sun kasa tayi.....
Mufyda ko tuni ta kigicewa Tana ta rawar jiki.....Tana kuma waige waige ta hakan sai ta sake hango musu wani Bala'in na daban.....Meye wannan Kuma??
*Kunamu* Tagan su Zagaye dasu ta ko'ina ma'ana sunyi musu zobe....kuma ko wacce daya daga Cikin kunamun Girman sa takai Girman Akuya..... 🦂🦂
*Tirkashi Duniya nada Abin Al'ajabi* Kasan rijiya gaba Dubu macizai nee marasa iyyaka da Kuma girma,sama Kuma manyan kunamu Hmmm.....
HMM KUDAI KASANCE DANI RANAR WEDNESDAY DOMIN GANIN YA TAFIYAR TASU ZATA KAYA......
KUGA RASHIN COMMENTS TAJA MUKU HUTU KO DAN HAKA A KIYAYE IDAN ANA BUKATAR LITTAFIN YA CIGABA.
💀💀💀
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
💀💀💀
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0️⃣8️⃣*
Tsastsaye suke sun rasa tayi.....
Mufyda ko tuni ta kigice Tana ta rawar jiki.....hade kuma da waige waige ta hakan ne ta hango musu wani Bala'in na daban.....Meye wannan Kuma??
*Kunamu* Tagan su Zagaye dasu ta ko'ina ma'ana sunyi musu zobe....kuma ko wacce daya daga Cikin kunamun Girman ta takai Girman Akuya..... 🦂🦂
Cikin zafin Nama suka yiyo kansu Ganin Haka Yasa Duk suka Rikice, *Atif da Mu'azz* ko suka kalli idanun juna,kamar hadin baki sukayi tsalle suka dira da kafafun su Kan Wannan shunfudeddiyar kankarar da suke.. nan da nan suka tsunduma Cikin wannan makeken Rijiya......Ta sanadiyar tsastsagewa da wannan Kankara tayi,Ihu suke Ahhhh!! Yayinda suke fadawa cikin wannan Guri,A tunanin Atif da Mu'azz ko yin hakan zaisa Kunamun su koma inda suka fito but hakan Kara musu hazaka tayi Domin Kara sauri sukayi suna Kuma shiga Rijiyar yadda kasan taron kud'an Zuma.
▪️▪️▪️▪️▪️
"Gaskiya Nayi matukar mamaki, Domin banyi Zaton zanga hakan da idanuna ba.....Gaskiya Nayi mamaki sosai da sosai"
*Reply*
"Ah kina nufin bakya Jin tsoro na??,Nifa Gaskiya Jikina bai dauka ba"...
"Hmm Maizai saka naji Tsoron ki,Aiko Babu Abin tsoro a tattare dake Noor"
Haka Forzy ke jiyo Wannan Tattaunawa Nasu Nina Yayinda ta kasance kwance take gefe duga suko zaune Guri daya wato Nina da Noor....sun Kuma kasance sun Bawa Forzyn Baya.
Haka *Forzy* ta tashi Cikin Sand'a ta Dauki jakar ta ba tare da sun sani ba ta Ruga A Guje,Nina Da Aljanan Nan Kuwa Ko iyya juyo sawun Kafrnta Basu yiba har ta bar gurin..
Cikin Sauri hade da kuma Gudu Forzy ke Tafiya yadda kasan biyo ta akayi baya,Tana Wannan Sauri hade da Nishi Yayinda Take tunkarar Kofar wannan Daki data kasance a ciki Wanda a Halin Yanzu Bata wuci Taku Talatin Bane kacel tsakanin ta da Kofar....
Tuni Takai ga wannan kofa tasa hannu da Karfin tsiya ta bude....shiga ciki tayi sa'annan ta mayar da Kofar ta Rufe.
Al'amarin Nina da wannan Aljanar ko Fira Tayi Fira suka Soma Sako Forzy Ciki inda Nina Tace Da ita..... "Kawa tace ita,Kuma Ina......"
Bata karashe maganar nata ba ta sanadiyar ta juyo da niyar nuna inda Forzy ke kwance Amma Sai ta tarar da gurin Babu kowa...
Cikin mamaki ta Furta cewar "Ina Kuma Gangar Jikin Forzyn Ta shiga"...
Aljanan ko Tayi saurin cewa da ita "what are you talking about" Amma Bayan tayi Arba da shunfudar Forzy sai Ta cika da mamaki ta Kuma kasa cewa komi....
Nina kuwa ta ce da ita......
"Anan Take Kwance fa,Amma Ina ta shige"
"Kodai maiya dauke ta ba,Ina ko zataje Bayan Tuntuni anan take kwance Kuna ma a tsorace"
Cewar Aljanan Kenan wacce Nina keyi Mata lakani da *Noor*
"Badai Dauke taba... Da Kafanta ta bar gurin nan"
"Tayaya??" Tambayar da Noor din Tayima Nina Kenan inda nina'n ta tabbatar Mata da Haka yayinda ta nuna Satin kafafunta ma'ana inda tabi yayin guduwar.....
Cikin Mamaki Noor ta sake jefo Mata tambaya....."Amma Meye dalilin ta nayin Haka??"
"Allah ne kadai yasan Wannan,Kinga karmu Bata wani lokaci mubi bayanta watakila ko zamu tadda ita a hanya."
Haka suka kwashi summarsu suka Biyo Sahun..... Forzy,Idan mun leka Cikin Rijiyar Nan Mai gaba Dubu,Tare daku iyya Duhu zamu iyya gani Yayinda Ko zaka juyo sahun kafafun Kunamun nan na shiga yadda kasan Sahun dawakai.....
Dukda cewar Cikin nada matukar Duhu sosai ta yadda ko kaje da Fitular ka zata dauke hakan Bata hanasu shiga ciki ba....Duk tsawon lokacin nan da aka dauka Su Atif Basu kaiga kasar wannan Rijiya ba....Ihun kawai kake iyyajiyowa badai gani ba....
Amma Cikin Lokaci kalilan sukaji *tsit* Nayi iyya kokarin na Domin na jiyo karar Dirar su Amma hakan Bata yiwu ba....
An Dauki Dan Lokaci Cikin wannan yanayi Kafin Damin Butterfly *malam bude littafi* suka ratso saman Rijiyar suna ta shawagi cen sai suka Zurma Cikin rijiyar....
Wannan butterfly dai sunsha banban da sauran Butterfly sabida su tamkar fitula suke yayinda suka kifta wani Guri hasken su saita haskake ko'ina gurin,Ta sanadiyar sune na iyya gano Halin da Su Atif din ke ciki Danko sun mammakale Jikin wasu igiyoyi masu kama data bishiya....
Nan suke dukkan ninsu a mammakale suke sun rirrike,Da dukkan alamu hanya wayennan Damin Butterfly sukazo Domin su nuna musu Danko wani kogo sukayi ta shiga ciki Wanda yake kasar inda suke a makalen saidai ba Nan gizo take sakar ba..Bayan Ganin Hanyar Nan da sukayi Sai Kuma suka sake Arba da dubunnen macizai, nanfa suka sake rikivewa Danko saman 🦂🦂🦂🦂 kasan ko macizai........ saidai sa'ar da sukayi macizan na sheka bacci....
Haka Sukayi ta sauka Cikin Sauri,gudun kar Damin butterfly din su wuce su kyalesu agurin Haka Kuma akayi saida suka Gama sauka Dukkannin su illa Samra dake rataye a wannan igiya Taki saukowa Ihu suke Yi Mata datayi saurin ta saukowa but inaaa Taki yin haka,aikuwa Bata tashiyin ba har saida ta hada Ido da Scorpions dinnan dake zuwa,nan tayi Ihu hade da sake Igiyar......
Cepko hannunta Ali tare da Atif Sukayi suna kokarin jawota Cikin wannan hanya ko nace cikin wannan Yar kogon da wayennan butterfly ke shiga....nanfa garin jawota ta Dalewa Sai ta ballo katotuwar dutse ta sauka a Rijiyar....Dimm!! Haka Ta bada sauti.... Suko sukayi shiru.
Shiru gurin Yayi Nay'an wasu dakiku... Kawai Sai sukayi Arba Da wata katotuwar macijiya.....Wanda Girman ta,kaurin ta da Kuma tsayinta takai Bishiyar dafino....ta tashi Daga kasar Rijiyar ta Kuma Kura musu Ido Tana ta wani Huci.... Mufyda ko kasa rikewa tayi Ta buga Ihu....
Al'amarin Forzy Bayan ta shige kofar kuwa,tadda wannan daki tayi yadda kasan *Moscow* 🏔️🏔️ domin kuwa komai na wannan Daki A daskare yake....Tuni Ta Soma 'bari Tana Kuna jujjuya idanu.....
Tuni Kwakwalwar ta ya Soma Raya Mata *Forzy ki koma inda Kika fito Domin gara cen danan* ... Yayinda Kuma zuciyar ta ke Raya Mata *Karki kuskura kiyi hakan Domin Kuwa wancen Bakar Aljanar cinye ki zatayi*
Haka tayi ta Tafiya Cikin wannan hali Daga karshe sai Tace "Kai inaa I must go back"
Haka ta Dawo da baya Domin kuwa ta gwammace Gara ta koma ga wancen Aljanan data tsaya nan *sanyi* Mai karya garkuwar jiki ya kasheta.. kuma hakan tayi Domin ta koma wannan kofa data shigo ta ciki Dan ba wani Nina tayi da kofar ba...But *it's too late*
Wangale baki Forzy tayi ta sanadiyar taga dakin ya sauya Bayan ta bude kofar.... Komai dake Cikin dakin ta banbanta...
Dukda sauye sauyen da Forzy ta ganin hakan baisaka ta koma baya ba...Hala tasa kafa ta shige ciki.
Wannan dakin data shiga ko Tasha banban da sauran Danko Duk Inga ka Duba Jikin wannan daki zakaga hoton kanka yadda kasan *Mirror* "Madubi" Haka dakin yake.....
Bangaren Noor da Nina ko Cikin Sauri suka karasa kofar Nan da Forzy ta Shiga sai Nina Ta juyo fuska ta kalli Noor....
Batare da Noor din Tace wani Abu ba tasa Hannu ta bude kofar...nanfa na cike da mamaki matuka Danko Dakin Da suka tsinci kansu ciki Tasha banban da Wanda Forzy ta Shiga... Domin kuwa Forzy dusar Kankara ta gani cike da dakin yayinda su ko suka tarar da dakin wani iri....
Dakin nada abun ban tsoro matuka yadda kasan tafkin matattu,Kuma tayi Kama da *masarautar mayu* Domin kuwa komi na wannan Daki anyi sane da kasusuwan Mutane....
Kama Daga Kan kujeru zuwa Kan kabot kabot har fitulun gurin Duk da kasusuwan Mutane akayi.
Kan suce kobo....iskar Wannan daki ta zugosu ciki suka zube kasa....kofar taja kanta ta Rufe zanen Jikin kofar ko ta bada haske Wanda wannan hasken harufan rubutu ne suka bayyana wacce itace.... *FARFAJIYAR MUTUWA*
Haka suka mike suna waige waige hade da Tafiya Cikin Sand'a Dukkannin su biyu har zaka kasa gane wacece Aljanan a Cikin su Danko Duk a tsorace suke.
Karar Rushewar Tarkace suka jiyo Nan da Nan sai suka fiskanci wurin Cikin tsoro Noor Tace "waye??" Sake furta hakan tayi "waye? Wai waye anan gurin??" Amma Babu Wanda ya ansa Mata nanfa saita juya ta kalli idanun Nina.....
Nan Sai suka saki jiki suka Soma Tafiya Kamar Babu komi but then Sai Nina Taji an kamo Hannun ta....cewa tayi
"Haba Noor Yanzu tsoron naki harta Kai ki rike mini Hannu?,Domin karkiji Kamar ke Daya ce anan gun""
Haka tafurta yayinda suke Tafiya Cikin kwanciyar hankali... Noor ko Tace da ita
"Rike Hannu Kuma,Taya zanyi Haka baya ga hannayen nawa biyu kina kallo"
Haka tabata ansa hade da Daga hannayen nata Nina ganin Haka yasa ta kwarma Ihu hade da juyawa taga waya rike Mata Hannu....
Juyawar da zatayi kawai Sai ta tarar da *Ahmed* tsaye gefen ta.....
Cikin Mamaki hade da shewa ta kirawo sunan sa nanfa suka rungume juya.. ganin Haka Yasa Noor taje wajen su da sauri ta rabasu....
"What Got into You Noor? Abokina nefa Shi Kuma mun rabu dashi tun Lokacin da muka Shiga wannan Guri,Amma Mai yasa kike son hanani murna ko nace magana dashine"
Batare da Noor din Tace da ita komi ba ta sake riko Hannun Ahmed nanma Noor ta Raba Hannun,ta hanasu sakan da Ran Ahmed ya baci sai yace.....
"What the heck is going on with you??"
Cikin wata murya Mai matukar razana mutum...
Cikin Mamaki hade da razana Nina ta zuro idanu....
Idan Muka koma Bangaren su Atif kuwa zamu tarar dasu atsaye....yayinda sukayi Shiru Nay'an wasu dakiku... Kawai Sai sukayi Arba Da wata katotuwar macijiya.....Wanda Girman ta,kaurin ta da Kuma tsayinta takai Bishiyar dapino....Kura musu Ido wannan macijiya tayi Tana ta wani Huci.... Mufyda ko kasa rikewa tayi Ta buga Ihu....
Nanfa Suka Ruga a guje yayinda Macijiyar ta biyosu cikin wannan kogon da suka Shiga.... Haka zalika butterfly din Suma tsill suna ta Shiga.
Cikin gudun da suke kawai Sai sukaji sun taka wani Guri ya nutse dasu,ihu hade da shureshure suke tayi kafin sukai kasan wannan Guri.....
Zubewa sukayi a kasar wannan Guri.....yin hakan ko keda wuya suka mimmike tsaye suka Kuma Daga ganin su sama Domin sunga wannan Macijiyar.....
Katotuwar idonta suka gani ta laiko su...Danko wannan Guri da suka fada bazata isheta shigaba Haka tayi ta bugawa harta gaji ta koma...
Fitarta ko Scorpions🦂🦂🦂🦂 suka shige ciki......da dukkan alamu Gurin Suma zasuje Kuma inamai kyautata zaton idanko sukaje wannan Guri sai sun shige da zamin zatayi daidai dasu.....
Al'amarin su Atif ko tsintar kansu sukayi a tsakankanin zabga zabgan takubba wacce tayi Kama da irin ta samudawa.....
Cikin Mamaki suka bude baki suna kallon ikon Allah Domin kuwa Duk wayennan takubba sun kasance ta zinari ne...
Samra tsintar wasika tayi Cikin Mamaki hade kuma da Naiman sanin maike Cikin wannan wasika saita bude...
Rubutun Cikin wasikar da jini akayi ganin Haka Yasa ta zuro idanu...sanar dasu tayi inda suka naimi data karanta musu....nanko tayi gyarar murya ta Soma Kamar Haka.
*"Barkan Ku da shigowa kofar ajali, Yayinda kuka Riske wannan wasika kuka Kuma kasance Kuna karanta wannan sako,Toh Ku saurari zuciyoyin ku sa'annan kuyi aiki da kwakwalan ku..... Makullai ko nace Halin da zaku kasance ciki na jikin Takobin Da zaku bude wannan kofar dake gaban Ku.......dashi,Takubba shida Zakuyi anfani dasu wayenda suke dauke da Harufa Kamar Haka"*
*Ma*
*Uu*
*Ta*
*Uu*
*Wa*
*Aa*
Zura idanu Samra tayi Muzzaffar ko yace da ita "meye hakan ke nufi....??"
Mufyda Tace *"Mutuwa"*
..........................😲😲😲
💀💀💀
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
💀💀💀
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0️⃣9️⃣*
Wangale baki Forzy tayi ta sanadiyar taga dakin ya sauya Bayan ta bude kofar.... Komai dake Cikin dakin ta banbanta...
Dukda sauye sauyen da Forzy ta ganin hakan baisaka ta koma baya ba...Hala tasa kafa ta shige ciki.
Wannan dakin data shiga ko Tasha banban da sauran Danko Duk Inga ka Duba lungu da sako na wannan daki zakaga hoton kanka yadda kasan *Mirror* "Madubi" Haka dakin yake.....
Forzy Babu Bata Lokaci ta Soma taku Cikin sanyin jiki,Amma kuwa Abinda Bata sani ba shine Duk madubin da Ta wuce maimakon hoton ta na ciki ya Dauke a'a Sai hoton nata ya bita da kallo suna Mai dariya hade da nunata da yatsa.
Rashin Sani tafi Dare Duhu,Forzy da tasan Meye take barowa a baya data gaggauta komawa Domin ko wannan bala'i data tsinci kanta a ciki yafi waccen data baro abaya.
_CIGABAN LABARI_
*"Barkan Ku da shigowa kofar ajali, Yayinda kuka Riske wannan wasika kuka Kuma kasance Kuna karanta wannan sako,Toh Ku saurari zuciyoyin ku sa'annan kuyi aiki da kwakwalan ku..... Makullai ko nace Halin da zaku kasance ciki na jikin Takobin Da zaku bude wannan kofar dake gaban Ku.......dashi,Takubba shida Zakuyi anfani dasu wayenda suke dauke da Harufa Kamar Haka"*
*Ma*
*Uu*
*Ta*
*Uu*
*Wa*
*Aa*
Zura idanu Samra tayi Muzzaffar ko yace da ita "meye hakan ke nufi....??"
Mufyda Tace *"Mutuwa"*
*Mu'azz* alamar mamaki yayi hade da Furta "what" Cikin siririyar murya ba tare da na kusa dashi ma yaji hakan ba....
Ansar Wasikar yayi daga Hannun *samra* ya Soma dubawa inda *Atif* Shima yasa Ido suka karanta tare,Bayan sun kammala Haka ko Sai suka dubi idanun juna.
Suna Kan hakan kuwa Sai suka Soma juyo sawun Scorpions din..... yadda kasan girgizan kasa haka gurin ta Soma dauka Dan zunzurutun yawan su, Dukkannin su kuwa suka Daga kallon su izuwa saman wannan gini ma'ana inda sukabi yayin fadowa wannan Guri....
"What are we going to do??,I really don't want to died down here...."
Haka Mufyda ta furta Amma Babu Wanda ya kulata,Duk sunji hakan but they keep silent.
"Ya kamata Mu naimo Takubban" haka Harun ya furta,Cikin hadin baki kuwa Samra Simon Ali suka bashi Ansa "Mu naimo meye?" Hade da Kuma yin tsaki alamar hankali su Bata dauki shawaran nasa ba
"Have you lost it?"
Cewar Mufyda,inda Harun din ya Bata ansa irin ta yen Nigeria wato ansa tambaya da tambaya....
"What?" Itako Bayan Tajiyo tambayar tasa Tace dashi "Kwakwalwar ka,Kai Dama baka ga hakan a tattare da Kai ba....... Taya zakace mu naimo makullan Halakanmu da Kai mu,ai koba komi ya kamata ace mutuwar tamuce ta riskemu da ace mu muka risketa"
"Kwarai kuwa"Haka Tina da Simon suka Bata kwarin gwiwa...
Atif da Mu'azz suka dubi Tina da Simon Nan da Nan suka kame baki sukayi shiru.....
Al'amarin Nina Da Kuma Noor Cikin murya Mai matukar razanarwa sukaji Ahmed yace "What the heck is going on with you??" Cike da Mamaki hade da razana Nina ta zuro idanu ta Kuma kasa motsawa dankuwa Ahmed din na rike da Hannayen ta.
Jiyo Hakan da Noor tayi keda wuya Sai ta bude tafin hannun ta,ta shuri Ahmed da ita....
Cen Guri guda ya Fadi mikewar dazaiyi ko saiya Dawo ainahin halittarsa Mai matukar munu.....da Kuma bantsoro.
Yayi Kama da ababen tsoratarwa har kala uku na farko shine yayi Kama da dodo👹na biyu yayi Kama da horor🧟nna karshen ko shine fatalwa..
Ganin Haka Yasa Noor ta riko Hannun Nina suka Ruga a guje,Basu tsaya ko'ina ba har sai dakin Nan da Forzy ta kasance a ciki wannan daki Mai cike da dubban Madubi.
Take biriki Noor tayi bayan tayi Arba da wannan daki,fuskar tako cike da mamaki ta sanadiyar tayi Arba da wani abun Daya Bata mamaki ya Kuma tsoratata....
Cikin Sauri ta saki Hannu *Nina* hade da zura idanu...ta tsaya kallon fuskar Nina,juyawa Nina tayi ta kalli fuskar Noor.
"Nina who are you Really??"
Haka Noor ta furta Cikin mamaki....hade Kuma Naiman Sani.
Nina cewa tayi "what?" Hade da yunkurin riko Hannun Noor but tayi saurin ja da baya.....
Bakomi bane Dalilin Noor na taka birikin illa Arba da tayi da wayennan mirrors dake wannan daki.....
Abinda yasa ta saki Hannu Nina kuwa shine Cikin madubin da suke tsaye gaban sa kuwa Babu hoton ko mutum daya daga cikin su,hakan Kuma na faruwane da aljanu,ko Kuma fatalwa kadai.
Duk Wanda ya tsaya gaban mirror Dole yaga reflection nashi ciki Amma aljan ko hakan Bata faruwa dasu.
"Karki karaso kusa dani,wacece ke??"
Haka Noor ta sake fada,ganin yadda Noor ta matsa wajen ganin Sai ta binciko ko wacece ita...ya hassala Nina shiru tayi wup!!
Gashin kanta suka mike tsaye, ya Kuma kitsa kansa da kansa Nan da Nan ta koma ainahin halittarta..... Ba kowa bace wannan illa Yarinya Nan data nitsar da Ahmed Jikin bango...
Hada ido sukayi Sai hasken dake wannan dakin ta Dauke gurin tayi matukar duhu sosai....
"No no no no!!!"
Haka nake jiyo muryar Noor na furtawa Cikin murya Naiman tsari Haka Kuma na sake jiyo kofar ta ja kanta ta Rufe..
"Bazasu sake dawowa ba domin kuwa sun ziyarci lahira,sa'anan daya bayan daya sai Kun sheka izuwa barzahu".
Haka wannan Aljana ta furta inda nake kyautata zaton akan Ahmed da Nina take magana...
Bayan ta furta hakan da wasu dakiku na iyya jiyo muryar Noor ta buga ihu na fitar hankali.
Ihun Aljana Noor ce ta ratsa cikin wannan katafaren ginin inda karan ta ratsa ko'ina a fadin gurin ta Kuma kaiga riske *Forzy*, a firgice ta take biriki bayan ta duba ko'ina batare da taga komiba sai ta soma sauri danta hango wata hanya wacce take kyautata zaton Mai billewace.....
Bangaren Su Atif ko tsaye suke sun kasa tsaida magana daya kowa na fadar San ransa akan su tsaya ko su ƙara gaba,suna kan Haka ko sai sukayi arba da scopions🦂🦂dinnan masu girman gaske sun shige wannan guri inda Atif da sauran tawagar ke tsaye....
Aikuwa tuni cikinsu tadau ruwa a Karon da sukaga wayennan halittu na tinkarosu gashi Kuma babu mafaka Kuma Basu da ishesshen lokaci dazasu naimo wayennan takubba dasuka kasance sune makullen wannan kofan da suke tsaye gabanta.
Rashin wayennan abubuwa guda biyu wato hanyar tsira da Kuma ishesshen lokacin naimo makullan kofar ne yasa suka fara ja da baya...
Ai kuwa wayennan halittu Baku rage gudun da suke ba har Saida #Simon yasa kafarsa a wani guri data nitse da kafan tasa ta dama kafin Nan suka take biriki.....
Ganin haka yayi matukar bawa tawagar nasu mamaki Danko dukkannin scopions 🦂 din sunki motsawa....
Haka su Atif suma sukayi babu Wanda ya motsa sai Simon din da kafar tasa ta makale yake kokarin cirota....
Bayan shirun na Dan dakiku kuwa sai wata rezar wuta Mai kaifin tsiya ta tsaga katanga tsakanin su Atif din da wayennan halittu.
Yayin baiyanar wannan garkuwar rezar utar ko sai data sheke sama da scopions 🦂 dari da suka kasance suna setin inda ya bayyanar,Haka zalika tayi daidai da cirewar yatsan Simon biyu....
Buga ihu yayi na fitar hankali hade da dafe hannun nasa... Aiko jiyo Haka da sauran tawagar tasa sukayi hade da...Gani garkuwar rezar utan ta mamaye ilahirin gurin,yasa suka soma ammatar sunan Simon suna komawa a guje...
Aiko mantawa sukayi da scopions din zuwansu gurinsa keda wuya suka fara basa tallafi gaggawa #Mufyda ko tsayawa tayi kallon wannan rezar utan yayinda ta ciki zaka iyya hango abinda ke bayan wannan Rezar.
Juyawar ta tace Dasu "wannan garkuwar bazata wani Jima sosai ba,Ya kamata mu Kara gaba"
"Mai kike nufi #Mufy,Taya Kika San hakan?"
Fadar #Tina kenan inda #Samra tace Dasu..
"Ya kamata ku bar wannan maganar ku aje ta gefe guda...
Ku kawo abinda kuke dauke dashi mu samu mu tsayar da jinin dake zubo masa yafi surutun da kuke...."
#Simon kuwa sai ihu yake yayinda #Atif ke kokari tsayar da jinin dake zubo masa...
#Mu'azz da Kuma Harun kokarin Ciro kafarsa suke daga Ramin....
Wayennan Halittu na kallon duk abinda ke faruwa... Amma sunki motsawa Haka zalika sunki barin guri....
#Mufyda Hallau sa musu ido tayi sa'annan ta sake cewa...
"Tina tambayar da kikayi na cewa Taya nasan hakan shine ban sani ba Amma idan kuka dubi wayennan Halittu Kamar suna zaman jiran garkuwar ta balle su samemu...."
Jiyo Haka yasa #Samra ta d'ago idanu inda tayi arba da Nina tsaye cikin jerin kunamun...
Bayan sun hada Idanu kuwa ta juya ta koma... #Samra kuwa zura Idanu tayi hade da ambatar sunan ta.
#Atif #Mu'azz da sauran abokan tafiyar nasu suka jiyo ganin su izuwa kan #Samra...
Bayan sunyi Haka kuwa sai suka tarar da ita Tana kallon kunamun...
Haka suma suka d'aga ganin su izuwa bangaren da take dubawa... Suko Basu tarar da kowaba...Danko tuni ta bace cikin scorpions din..
Mikewa tayi hade da cewa "I saw her, wallahi I saw her Tana cikin hadari ya kamata mu taimaka mata".
Dukkannin su a tsaye suke inda Atif yadan dafe hannun Simon suka Mike tare...
Tsayawa kallon ta sukayi yayinda ta gigice Tana ta safa da marwa Kamar Mai naiman wani Abu...
Ganin Haka yasa Atif ya dafe ta inda ta tsaya cek juyawar ta ta soma cewa.....
"Y'ar Uwa Nina Tana cikin hadari"
"Nasani" Haka Atif din ya Bata ansa,Inda ta sake da cewa....
"Yah kamata muyi wani Abu akai Atif,mu ceto rayuwar ta"
Cikin muryar kuka take furta hakan...
Rungume juna sukayi inda ta soma shesshekar kuka Atif ko hada Idanu sukayi da mu'azz inda da faruwar Haka ya gyada kai....
Nan ya juya inda ya fuskaci katangar dake tsakanin su da wayennan Halittu...Amma sai ya tarar ba ko daya daga cikin kunamun ko sahun su babu....
"Abun mamaki Ina ne suka shige" haka ya furta inda dukkanin su,suka juya suka fuskanci gurin.....
"Oh no,This is a very bad sing" haka #mufyda ta furta inda da fadin hada sukaji wata Kara Mai kamada tashin nakiya a wannan guri da suke....tsaye
Guri tadau kura sai data dauki wasu dakiku kafin kurar ta yaye...
Cen suka hango gurin Nan data fashe kaikace fasata akayi da nakiya...Kuma a bangaren da suke ma'ana Ramin ta baro garkuwar a baya.
Tsit sukayi Babu Mai motsawa cen sai Atif yace da mu'azz...
"Find the key"
Gyada Kai yayi alamar ok inda Samra ta Soma cewa...
"Hakan bazai taba yuwa ba,bazamu sake barin Nina abaya ba..."
Haka tayi ta furtawa yayinda Atif da sauran mutanen ke kokarin shawo kanta Amma daga karshe ta kwace kanta daga hannun su ta ruga tana Mai dotsawa izuwa wannan Ramin daya fashe aikuwa sai daya saura taku talatin ta kaiga Ramin kawai sai taga wannan macijiya Mai girman bishiyar dafino ta billo ta wannan Rami....
Bayan tayi ido hudu da wannan macijiya ko tayi furucin "Oh no" cikin siririyar murya.
*_Mu Hadu a Episode 10_*
_@Abdul Alhaji Musa *Return*_
https://www.wattpad.com/1116988953?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Abdul10k&wp_originator=b2LZ7blrJjHg%2FvOfGZxWJ3AYIE8qslxtU9ClU2M%2FTT%2BSVKWX%2BlyffYS%2BvoISj0i81Vheq3cNh4IprLmP6xM79L36yrnAUAfinzWZ8S%2BGHI7tsPKxxPin1oz31xIOhKwE
💀💀💀
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
💀💀💀
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 1️⃣0️⃣*
*THE DEATH*
Ihun Aljana Noor ce ta ratsa cikin wannan katafaren ginin inda karan ta ratsa ko'ina a fadin gurin ta Kuma kaiga riske *Forzy*, a firgice ta take biriki bayan ta duba ko'ina batare da taga komiba sai ta soma sauri danta hango wata hanya wacce take kyautata zaton Mai billewace.....
Cikin sauri ta Soma tafiya tana kokarin kaiwa ga kofar,Amma Kuma sai ta Soma jiyo wata murya Mai kama da nata sak nayi mata dariya..abaya,Aikuwa cikin razana ta juyo inda ta tarar da bayan nata Babu alamar kowa,nanfa kirjinta ya soma bugun uku uku...ta Kuma soma magana a kasar zuciyar ta.
"Shin kodai kunnuwa na ba daidai suka jiyo bane....? Kamar naji anayimin dariya"
Aiko Bata kammala fadar haka ba taji tafin hannun mutane sunkai goma a kan kafadar ta....
*#Samrah*
"Hakan bazai taba yuwa ba,bazamu sake barin Nina abaya ba..."
Haka tayi ta furtawa yayinda Atif da sauran mutanen ke kokarin shawo kanta Amma daga karshe ta kwace kanta daga hannun su ta ruga tana Mai dotsawa izuwa wannan Ramin daya fashe aikuwa sai daya saura taku talatin ta kaiga Ramin kawai sai taga wannan macijiya Mai girman bishiyar dafino ta billo ta wannan Rami....
Bayan tayi ido hudu da wannan macijiya ko tayi furucin "Oh no" cikin siririyar murya.
Aikuwa macijiyar batayi Wasa da damar taba,dankuwa ta wani shure ta kaikace Shirin film....
Haka ta tashi sama kamar kwad'o Kuma Babu abunda ya tokare ta illa kofan ga dake bayansu domin kuwa sun bawa kofar baya....
Aiko Sumewa #Samrah tayi Atif, mu'azz da sauran mutanen suko zura idanu sukayi Dan mamaki...
Macijiyar ko ta Soma wani jujjuyawa cikin salo Mai matukar tsoratar tana ta bubbude wuya kamar wata jegariya nanfa ta kurama taron nasu ido....
Can tayi kansu sulululu ta yadda idan ta kaiga su wub daya zatayi musu ta hadesu Dan kuwa a tsaye suke guri guda sunki motsawa sai ihun tsiya da suke....
Kamar walkiya sai ga wani santalelen saurayi ya diro gaban wannan macijiyar, saurayi Mai cikar Kamala da Kuma kwar jini,ga faffadar kirji irin ta jaruman kwarai.
Bayyanarsa a wannan guri yayi daidai da budewar bakin macijiyar da niyar hade taron su Atif... Amma Allah bai Bata damar haka ba ta sanadiyar bayyanar wannan saurayi,kabbara yayi hade da dafe saman kan wannan macijiya aiko cikin kankanin lokaci ta koma baya da karfin tsiya Danko karfin kabbaran yafi karfin ta ba kusa ba.
Zuru zuru mu'azz,Atif da sauran mutanen gurin sukayi domin kuwa abin yayi matukar Basu mamaki,ko kibta ido basuyi...
Wannan saurayin ko tsaye yake yayin da wannan macijiyar ke kururuwa tana komawa baya.... Fadiwa kasa wannan macijiyar tayi cikin sauri da Kuma zafin nama ta Mike hade da yunkurin sake farmakar su...
Aiko wannan saurayin bai Bata damar yin haka ba Dan kuwa soma karanta *Suratul Jin* yayi bayan ya karanta Aya goma na wannan Sura sai wannan macijiyar ta Soma ihu cikin kankanin lokaci ta rikide ta dawo Suffan mutum... Atif da mabiyansa ko mamaki takai makura domin kuwa sun rasa ta cewa sai kallon ikon Allah.
"Meye naka ciki,idan na hallaka su?"
Haka tayi masa tambaya yayinda ta nunashi da hannu sa'annan ta kuma sake da cewa.
"Zaka iyya dakatar Dani daga hallakasu yanzu Amma Ina Mai tabbatar maka bazasu Kai labari ba,Domin matsifun dake tinkaro su ya wuce karfin tunani...Zanga iyya gudun ruwan ka Dan nasan bazaka iyya Basu kariya na har abada ba"
Aiko cikin kasaita saurayin yace da ita....
"Zaku iyya fin karfin Yan Adam Amma bazaku iyya da Allah ba...
Yafi karfin ku,Kuma shi zai bamu damar kare kanmu daga muggan halittu irin ku,masu hukunta mutane ba tare da sunyi laifi ba"
Kelkelewa tayi da dariya sa'annan tace dashi.....
"Mayyasa kake alfahari da karfin da ba taka bace...ita
Karfin da kake ikirari dashi kowa zai iyya mallakar ta... Sa'annan inaso in sanar maka Yau ka Kona ni Amma inaso kasani wannan kuskure da kayi sai dukkanin ku kunyi nadama haka, dukka saikun biya bashin da kuka dauka".
Aiko kafin saurayin ya sake bude baki tuni ta bace tamkar warkiya a tsakiyar dare..
Muryar ta suka soma jiyowa tana ikirarin sai sunyi nadamar konata da sukayi,cen sai tayi shiru hakan ya bawa saurayin damar juyawa ya kurama taron su Atif din Idanu.
*Forzy*
#Forzy #Forzyy cikin Rad'a take jiyo muryar maishi na Kiran sunan ta,juyawa tayi inda ta sake guba lungu da sako na dakin Bata ga kowa ba....
"Wai maike Shirin faruwa da nine?,gaba daya na kimauce.. Hm"
Haka ta furta sa'annan ta girgiza Kai alamar takaici Hadi da tsaki.. bayan tayi hakan ko ta juya da niyar cigaba da tafiyar Tata.
Ihu tayi bayan tayi arba da Tarun Y'an mata maru kama da ita sak saidai banbancin su shine fuskar wayennan y'an matan nada abin tsoro domin wata iriyar dariya suke Mai sa gashin jikin mutum ta Mike tsaye...
Aiko bayan #Forzy tayi ido hudu da wannan matsifar sai ta lumshe Idanu Hadi da hada tafin hannayen ta guri guda Dan zunzurutun tsoro ta Soma karanta *Suratull-Baqara* a cikin ranta....takeyi Dukda cewar tana sauyawa ayoyin gurare haka baisa ta daina karantawa ba haka tayi ta karantawa bakinta na raga haka zalika jikin ta na 'bari.
Dukda karatun da take Bata daina jiyo sautin muryoyin nasu ba...Bayanta ko sai ga wani hannu yazo cikin sauri ya dafe ta aiko yadda kasan Danko haka tajita a yashe gefe guda.
Bude Idanu Forzy tayi cikin sauri bayan taji karan fadiwan mutum Hadi da son sanin waya dafe tan.
Bude ido tayi ta tarar da gurin Babu kowa Babu y'an matan ko daya,cen ko guri guda ta tarar da wani a kwance maishi na kokarin tashi...Aiko yadda kasan barbela haka ta ruga izuwa ga wannan mutumin.
"Karki Tabanin karki Tabanin"
Haka ta furta cikin siririyar murya inda #Forzy ta dakata da niyarta na tallafa mata ta Mike..
Dago fuska tayi suka hada ido inda #Forzy tayi furucin "You?" Cikin mamaki Hadi da zura idanu...
"Yes me"
Haka ta Bata ansa aiko Babu abinda Forzy ta Soma tunowa illa bakar hayakin daya biyota a guje dazun da Kuma yarinyar Nan data taimaka mata Mai fuka fukai a gadon baya wacce ba kowa bace illa budurwar Nan dake zaune gaban ta.
Sake shiga yanayi ta Sumewa tayi sai yarinyar tayi ceb ta cebko ta Hadi da girgiza ta Amma ko bayan tayi haka ta buga ihu ta fitar hankali dan jikin Forzy na d'aye mata fatar jiki yadda Kanan kunar wuta har gurin na hayaki.....
Bude Idanu Forzy tayi yayinda yarinyar tayi saurin cika mata hannu ta bada rata a tsakanin ta da Forzy.
"Maike faruwa?" Tambayan da Forzy tayi kenan inda ta Bata ansa da cewa
"Kina matukar Kona ni Yar uwa, kinada tsari a tartare dake,Kuma Zaki cigaba da tarwatsani idan na tsaya tare dake"
Cikin mamaki hade da daurewar Kai ta wangale baki tana kallon *#Noor*
Bagaren su Atif da wannan jajirceccen saurayin ko.... kafin saurayin ya budi baki tuni ta bace tamkar warkiya a tsakiyar dare..
Muryarta ko ya ratsa cikin ginin tana mai ikirarin sai sunyi nadamar konata da sukayi,cen sai tayi shiru hakan ya bawa saurayin damar juyawa ya kurama taron su Atif din Idanu.
"Gaskiya muna Mai Godiya Dan uwa"
Haka mu'azz ya furta inda Atif shima yace dashi mun gode matuka Amma shiko hada Rai yayi ya kura musu ido...
Y'an matan dake guri tuni sukayi caa kan Samra dake kwance...
Zuwansu suka soma yimata fifita hade da yayyafa mata ruwa haka a hankali ta farka budewar idanun ta ko tayi Karo da mitar wannan saurayin yayinda yace cewa.
"Wai wace irin mutane ne ku?,Mai yasa kuke manta mahalacci a lokacin da kuka tsinci kanku cikin had'ari,Mai yasa kuka manta koyarwar da addinin mu tayi Mana game da naiman tsari a lokacin da muka shiga sabgar mutanen boye maiyasa bakwa naiman tsari daga uban giji sai ihun banza....da bazata kareku da komi ba"
Haka ya jera musu tambayoyi Babu kakkautawa,suko saukar da idanun su kasa sukayi bayan yayi shiru Sai Harun yace dashi
"Gaskiya munyi kuskure na rashin Mikawa mahaliccin mu damuwar mu,Amma insha Allah zamu gyara"
Hm yayi hade da juya baya da niyar tafiya Nan sai Atif yace dashi
"Gaskiya Dan Uwa munyi mantuwar da Bata da amfani... Mun sha'afa ne"
Aiko #samra cikin naiman sani tace da y'an matan dake kusa da ita
"Wai waye wannan? Ya sunan sa Kuma Mai yake a Nan gurin"
Juyawar sa yayi gajeriyar murmushi hade da cewa...
"Shin wai har mun saba da zaku iyya yimin irin wayen Nan tambayoyin?, Yar uwa ba keba dukkan ku anan gurin zuciyar ku cike fal da burin sanin koni waye"
Haka ya bata ansa sa'annan ya sake da cewa....
"Amma Matsifu Sama da dubu dari suna birne a kasan wannan guri.....
Tsayawar ku anan gurin Babu abinda zata tsinana muku illa ta karashe ku baki daya domin wannan garkuwa ta Rezar uta tana gab da dauke wa"
Aiko bayan ya furta haka Harun ya jefesa da tambaya kamar haka.
"Kana magana tamkar ka haddace wannan matsifeffen guri Taya kasan duk wannan malam?"
Gajeriyar murmushi yayi hade da cewa
"da zakubi ta nawa da Kun gaggauta naimo takubba Nan da suka kasance sune makullen kofar domin tsiratar da rayuwar ku,domin kowace dakika sake shiga hadari kuke ya kamata ku fahimci haka"
Shiru sukayi Babu Wanda yace dashi kala domin yama fara Basu tsoro domin tunaninsu ba bil'adam bane
Shiko dayaga alamun haka a tattare dasu sai ya Soma cewa...
"Al-Hussien sunana na kasance Dan bincikena tarini ne sa'annan iftila'i ne yasana shigo Nan gurin,ku yadda Dani ku naimo takubban".
"Maiyasa zamu yadda dashi??"
Fadar #Samra kenan inda Atif yace da Al-Hussien..
"Taya kashigo wannan guri, sa'annan tsowon wani lokaci ka dauka anan gurin"?
"Labari ne Mai tsawo Baku da lokacin sauraron haka"
Haka ya basa ansa shiko yasake da cewa..
"Kana nufin idan mun samu lokaci zaka sanar damu kenan?"
Dajin wannan tambaya ko ya kyalkyale da dariya....
"Don't tag me in,we are not us sabida bana cikin tawagar taku".
"Amma Aiko kaji abinda waccen aljanar tace,Dukda ta nuna bazaka iyya bamu tsaro ba ai ya kamata ka jarraba"
Abinda Simon ya fada kenan shiko ya girgiza ka sa'annan yace dashi.
"Aiko gaskiya ta fada,domin nida kaina bani nake kare kaina ba Allah ne ke kareni kamar yadda nake kyautata zaton zai kareku"
Aikuwa bayan ya furta hakan Samra ta Mike tsaye hadi da furta cewa...
"Hold on Guys,What did I miss??"
Dukkan ninsu ko suka juya idannun su izuwa kanta....cike da mamaki
#Mufydah gajeriyar murmushi tayi sa'annan tace da ita
"Alot"
Al'amarin Forzy da Kuma Noor ko zaune suke yayinda suke nesa da juna...Nan Forzy tace da ita..
"Taya kike tunanin kwakwalwata zata dauki abinda kike fadane,tayaya"
"Forzy nasan bazaki amince ba Amma gaskiyar kenan, waccen da Kika ganmu tare ba Nina bace"
Haka Noor ta furta inda Forzy tace da ita...
"Bama wannan ba Noor,Taya kike tunanin Zan yadda dake bayan ke da bakinki kikace kin koro daya daga cikin mu izuwa wannan guri Kuma nasan ba kowa bane wannan illa Atif.. toh nasani ko kece kike shirya komi ma'ana shirya nitsewar Ahmed da Kuma bacewar Nina da sauran tawagar mu hmm, wannan guri ba gurin yarda da mutun bane Noor cikin kalaman ki na dauki wannan darasin domin kin yadda da wata wacce tazo Miki a suffar Yar uwata daga karshe taso tarwatsa ki,Ina ganin ba kuskure bane nima idan naki amincewa dake".
Gajeriyar murmushi tayi sa'annan tace da ita....
"Bada mugun nufi nazo gareki ba Forzy, Amma kina da damarki nakin amincewa da batuna domin nayi kuskure Dana kasance Ina tsutarwa domin nasan idan da badan Ina tsutarwa ba da tsarin da kike tattare dashi bazata konani ba....
Amma inaso ki fahimci wani abu da da mugun nufi nake bazan iyya tinkaro inda kike ba Forzy ki amince Dani"
Shiru Forzy tayi tana ta nazari Noor ko ta kura mata Idanu....
*ATIF*
Tsaye suke gaban wannan gabjejiyar kofa inda sukasa takubban jikin kofar kamar yadda wasikar da suka karanta ta nuna....
Takubban dake da kalmomin mutuwa suka naimo suka Kuma makalata a jikin kofar a inda suke tunani mazaunin takubban ne....
Shiru kakeji Babu alamar budewar wannan kofa... Nan Tina tace dasu
"Anya kuwa daidaine mukayi hakan"
"Wata kila ba haka suke son muyi ba" fadar Samra inda Al-Hussien yace da ita "ya kamata mudan jingirta...
Aiko Samra tayi salati Hadi cewa....
Garkuwar na karyewa Kuma gashi kunamun sun sake bayana...
Al-Hussien ko ya juya ya duba Hadi da cewa...
"Dama rufe Mana Idanu tayi da karfin tsafi,kunamun sun kasance na gaskene ba Aljanu bane suka rikide....shiyasa suka kasance har yanzu suna gurin Ya kamata mu gaggauta barin nan"
"Tayaya Al-Hussien kanafa ganin abinda ke Shirin samun mu Amma ka gindaya Mana sharud'a idan munaso mu tafi tare da kai...kace Babu Mai taba ka Kuma Babu aikin da za'a saka kayi sannan komi saidai ka fada Mana da baki bawai ka tayamu yiba... Taya kake ganin haka zaiyi"
Samra ce ta furta hakan shigo ko shiru yayi Hadi da dauke idanunsa kasa...
#Tina da Mufydah ko suka hadakai guri guda cikin rad'a Tina tace da mufy..
"Ko meye dalilinsa nayin hakane oho"
Atif,mu'azz duk sunyi sanyi da sukajiyo wannan magana ta Samra....
*"Meye Al-Hussien ke Shirin boyewa gaskiya da lauje cikin nadi,"*
Haka Atif ya furta cikin kasar zuciyar sa.....
*2Hour Ago*
*Awanni biyu dasuka wuce*
"Tafukan Hannu sune makullan Kofan nan I'm sure"
Taimakon da Nina tayi abaya kenan ta sadaukar da rayuwarta wajen ganin ta tsiratar da abokan tafiyar ta abinda ya faru da itako bayan Atif yaja kofar ya rufe shine....
Gani tayi kowani lungu da sako wasu irin halittune ke bullowa ta ciki...Hadi da wayenda tayi musu sata wato sangaranrun mutanen Nan masu kama da gumaka....
Aiko Nan tasan nata yazo karshe...ajiyar zuci tayi dan Babu yadda ta iyya domin hannunta na makale hallau a wannan guri data saka....su
Jitayi hannuwata sun guntule nanfa ta buga ihu na fitar hankali jini ko ta soma kwararowa.... Izuwa kasan gurin,caa halittun Nan masu kama da kadangaru sukayo kanta sukayi gutsigutsi da namarta...Gaskiya tayi mutuwar wulakanci....
😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭
@*Abdul Alhaji Musa comment*
"Ahmed Da Nina Allah Ya jikanku da Rahama"
*_Mu Hadu a Episode 11_*
_@Abdul Alhaji Musa *Return*_
💀💀💀
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
💀💀💀
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 1️⃣1️⃣*
*THE CONFUSION*
#Tina da Mufydah ko suka hadakai guri guda cikin rad'a Tina tace da mufy..
"Ko meye dalilinsa nayin hakane oho"
Atif,mu'azz duk sunyi sanyi da sukajiyo wannan magana ta Samra....
*"Meye Al-Hussien ke Shirin boyewa gaskiya da lauje cikin nad'i,"*
Haka Atif ya furta cikin kasar zuciyar sa.....
Zuciyoyinsu Bugun uku uku take yayinda suka kasance a Ankare domin kuwa saura kiris wannan Garkuwa ta Rezar wuta ta kafe.
yadda suka kasance a ankaren hakama Scopions din suka kasance... Domin kuwa har sun soma matsowa wajen garkuwar.
Aiko daukewar wannan Garkuwa ta Rezar wuta tazo daidai da Tsinkewar wata siririyar murya Mai fasa dokin kunne...
Wannan Kara na bada sautin "Aaaaaaaaaaaaaaaaaaa!!" Cikin firgici da naiman kare kunnuwa su daga fashewar yasa suka toshe da hannayensu biyu..
Wannan Kara dai ya dauki lokaci kafin ya tsaya,bayan tsayawarta sai suka tsinci kansu cikin wani yanayi Mai wuyar sha'ani.
Kallon Abubuwa uku uku suke ta sanadiyar mugun jiri data kamasu dukka,ga kuma rashin jiyo sauti ta dalilin jini dake zubowa daga kunnuwan su...
Dukkan ninsu sun kasance cikin wannan yanayi illa Al-Hussien da ko daya daga cikin hakan bai samesa ba...
*ATIF*
Sai faramar Rintsa Idanu yake yanata Girgiza Kai da niyar ya samu waraka daga jirin dayake ji da Kuma rashin jiyo sauti.
Haka yayita fama Amma Babu alamar kaiga ci,hala bai daina wannan aba tasa ba daga karshe ya dago hannun sa ya daidaita setin kunnuwansa ya soma tafi dan yajiyo sautin Amma shiru kake ji....
*Noor*
Zaune take ta mansher da hannunta tamkar laita tana ta kunna wuta tana kashewa yayinda Forzy ke zaune gefe guda
"Noor! Zamafa bai same muba ya kamata mu Kara gaba ko Allah yasa mu dace...."
Fadar #Forzy kenan inda #Noor din ta Bata ansar cewa.
"Ni Kuma Ina ganin Nanne daidai gurin da ya dace mu yada zango,Ya kamata muhuta Domin Duk jiki na Rad'adi."
"Alright na amince Miki bawai Dan inaso ba dan ya zaman mini dole ne,Amma bayan Nan karki sake naiman agaji irin wannan"
Haka Forzy ta ce da ita...inda tayi Gajeriyar murmushi Hadi da cewa
"Cikin sauri haka kin amince da bukata ta kamar yadda Y'an Kungiya guda keyi, gaskiya kedin ta Daban ce"
Forzy ko tayi Gyaran Murya sa'annan tace da ita...
"Kina nufin Dangan taka kenan irin ta mutanen Team daya,Hm banason mu hada Dangan taka ta wannan sigar nafison mu zauna tare a matsayin Two sister Har izuwa karshen Rayuwan mu Dukda bansan goben mu ya zata kasance ba,ko mutuwa ko Kuma Rai Amma inason mu kasance sister Har ranar da daya daga cikin wayen Nan abubuwan Dana lissafa zata riske mu."
Haka tayi ta zazzaga bayani yayinda ta sauke idanun ta kasa...bayan ta karashe bayanin nata ko ta dago Idanu da niyar da kalli fuskar Noor ta Kuma cigaba da bayanin...Amma sai tayi kicabus da #Noor na sheka bacci hade da mishari..
"Noor!!.......Seriously?"
Haka ta furta bayan tayi arba da Noor din Hadi da dafa goshi bayan ta furta hakan ta dauki wata y'ar mitsitsiyar dutse ta jefi Noor din da ita.
Aiko cikin abinda bai wuci dakiku Goma ba itama ta fada duniyar bacci....Dukda surutan da take ita kadai.
"Atif,mu'azz,Simon,samra wai Bakwa jina ne ku kalleni anan gurin..."
Haka Al-Hussien ke furtawa yayinda yake ta d'aga musu hannu Aiko saidaga bisani suka Soma jiyo muryarsa yadda kasan ana Kara sauti na'ura haka suka soma jiyosa.
Bayan wasu Dakiku Jinsu ta dawo daidai....Nan da Nan sai Atif yace da Al-Hussien
"Maye yake faruwa?"
Al-Hussien nuni yayi musu da yatsa,suko cikin sauri suka juya ganinsu izuwa wurin da yake yimusu nuni....
Aikuwa bai wuci taku Ashirin bane tsakanin su da kunamun yayinda kuma suke karasowa cikin zafin nama....
Kansuce Kobo sai suka ji Kofar Nan dake bayansu taja kanta da karfin tsiya ta bude...
Wata irin zafine ya fito ta cikin wannan dakin,suko da suka kasance taku gomane kacel tsakanin su da kofar duk suka jike shakab Dan zunzurutun zafi ga muka wani hayaki dake bulbullowa ta ciki...Mai warin gaske.
Dakin ya kasance Babu haske ko kadan Danko bayan sunji kofar ta bude suka juyo ganinsu izuwa wurin haka zalika Scopions din suka take biriki...
Aiko cikin abinda bai Kaiga dakika guda ba suka Kara a guje da niyar shigewa Dakin....sabida basu da zabin da ya wuce shiga cikin dukda Basu san meye zasu tarar a gaba ba.
Aiko Saida sukayi gaf da shiga gurin sai Al-Hussien yace dasu.... *"Ku dakata"*
Tamkar daukewar Ruwan sama haka suka tsaya cek,Babu Mai motsawa,gurin sai yayi shiru domin sune Dama suke kokarin guduwa Dan tuntuni Scopions din sun tsaya guri guda.
Shuri kakeji ganin haka yasa Samra ta juya Hadi da yimusu alamar tambaya domin itace ja gabansu a guduwan....
Mu'azz cikin sauri yayi mata alamar *waya sani* nanfa ta juyo da niyar ta fuskanci kofar Aiko Bata sami damar yin haka ba,Ihun tayi Hadi da zura idanu ganin haka yasa mu'azz yayi sauri ya tureta suka zube kasa,haka ko duk sukayi cikin abinda bai wuci dakika guda ba duk suka kwakkwanta kasa ganin Al-Hussien shi bayi hakan ba yasa Atif Yaje a Guje da niyar yasa shi yayi hakan Aiko sai dayaje gab da tabashi sai ya gauce gefe guda nanfa Atif yasha kasa....
Dalilina Samra na yin wannan ihu ko shine Damin Jemagune🦇🦇 tayi arba dasu wayenda sukasha babban da ta duniya, domin girman su da Kuma yanayi su yayi Kama data horror films....
Sun Kai girman katon Zakara🐓 gasu da manya hakwara....da Kuma jajayen Idanuwa.
Bayan sun gama fitowa ko suka fara kaiwa Scopions dinnan Hari ta yadda idan sun kama daya sai sun kacelcela nama sa haka suma idan kunama ya saresu sai naman jikin su ya zagwanye su koma kwarangwal.
Haka suketa kakkashe junan su..Aiko Basu tsaya kallon wannan yaki nasufa shigewa cikin dakin sukayi bayan Al-Hussien ya tabbatar musu da cewa daga zaran sun daya daga cikin wayennan halittu sunyi Nasara kansu zasu koma ta dalilin haka yasa suka shige wannan kofa....
Aiko da shigarsu kofar taja kanta ta rufe.....Duhu kake iyya gani ta ko'ina
Kasancewar su a wannan guri tayi daidai da kasance a duniyar Mars ba tare da abin tallafawa mutum gurin Nunfashi ba,domin da shigarsu kofar suka sume.
Tsawon lokaci sukayi a sumen kafin suka dawo bacci....cenfa Atif Ya farka inda ya Mike tsaye hadi da yin hamma da Kuma mika,bayansa ko Samra ce ta Mike tsaye itama...
Cike da mamaki suke suna ta kallon yanayin Gurin domin kuwa basuyi zaton haka zasu yadda guri ba aikuwa Jin Tina Ta tsinke da ihu yasa suka Razana Hadi da juyawa gurin da suke tsammani zasu tadda ita...
Haka ko akayi tadda ita a gurin sukayi yayinda ta yunkura a fusace....Zura Idanu Samra da Atif sukayi bayan sun tadda abinda yasa Tina Ihun.
"Subbuhanallahi Aikuwa a Tsakiyar kaburbura muka kwana"
Haka Atif ya furta inda sauran matafiyan nasu suka Mike a gurguje domin kuwa tuntuni suna sauraran su kasala ce kurun ta hanasu mikewa...tsayen.
Aikuwa kamar yadda ya furta haka al'amarin ta kasance domin Kuma a tsakankanin Kaburbura suke tsaye...
"Oh My God, wannan wace irin Almara ce?"
Fadar #Muzzaffar inda #Ali yace
"Ban Tabba Halattar irin wannan gurin nayi 30minutes ba Amma sai gashi yau na kwanta nayi bacci a tsakankanin su, gaskiya ya kamata mu gaggauta barin wannan guri.
"Wayyo Ni, Gaskiya ya kamata mu gaggauta barin wannan guri."
Fadar Mufydah inda mu'azz yace da su....
"Guys Hold it,Ina Al-Hussien da Kuma Harun?."
Cikin mamaki Samra tare da Atif sukayi furucin...
"Al-Hussien?"
"Eh Ko kungansu a Nan gurin?"
Tambayan da ya jefesu dashi kenan a madadin ansa,suko maimakon suce a'a juyawa kawai sukayi suka soma naimansu Hadi da kiraye kirayen sunayensu cikin Kara....
Aikuwa barin su wannan guri keda wuya sai hannun mutum ya baiyana a cikin kasan tamkar yadda tsirrai ke fitowa.
Al'amarin Forzy ko farkawa tayi daga bacci inda taga kanta kwance jikin Noor takumayi follow da kafadar Noor... hakan ko bai Bata wani mamaki ba har sai datayi arba Da motar su fake bakin hanya,shewa tayi Hadi da tasar Noor daga bacci,Budar idanunta keda wuya tamike cikin sauri Hadi da Rungumar Forzy..
Bayan tayi hakanne ta tuno abinda ya faru da ita a lokacin da ta fire da niyar ta lulluka cikin gajimare....Aiko Tino haka keda wuya ta saki jikin Forzy Nan da Nan ko gurin ya sauya...
Sararin samaniya ya dawo jajir kamar jini,ganin haka yasa ta rude Hadi da cewa
"Forzy wannan bad sing ne, wannan gurin Chakwalwalin bakaken Aljanu be ya kamata mubar gurin Nan da sauri."
Riko hannun Forzy tayi Amma ko Forzy tayi kamar hakan bai dameta ba...
Hakan yasa tace da ita "Muje ko" fadar hakan yasa Forzy ta shureta da hannu... Ai kuwa cen guri guda ta fadi.
Noor a firgice ta d'aga Kai inda tayi ido hudu da jajayen Idanun Forzy....
Aiko Forzy ca tayi kanta inda ta Danko sawunta,yadda ake kakkabe daud'a a jikin katuwar barko haka Forzy tayiwa Noor tana ta bubbugata da kasa.
"Noor! Noor! Noor!!"
Haka Forzy ke furtawa yayinda ta kasance tayiwa Noor din filo da cinyarta tana Kuma jijjigata Hadi da cewa *Ki tashi*
Aiko hakan bai samu yuwa ga Noor ba Danko taso ta farka daga mafarkin da take Amma haka baiyu ba sabida hadarin da take fuskanta a mafarkin nata...
Idan muka koma cikin mafarkin nata ko zamu ga hallau tana a hannun Forzy wacce take gallaza mata bakar azabar...
A zahirance Kuma tana kwance ne a hannun Forzy gaske,gumi ko ya jikata shekaf sai famar shureshure take kamar Wanda ake Zara Ransa...
Forzy ta rasa maike damun Noor,dukda tasan Jensin su ba daya ba Amma sai take kokarin tallafa mata...
Kuma Bata Razana ba har sai dataga Noor na Aman jini,hakan kuma ta farune ta sanadiyar mugun naushi data Sha acikin ta,ta cikin wannan mafarki nata Mai wuyar sha'ani...yasata wannan Amai na jini.
Bude Idanu tayi inda tayi arba da Forzy dake kokarin dawo da ita a duniyar gaske Amma haka kwata kwata baiyu ba Danko tuni ta sake lumshe Idanu haka ta sake tsintar kanta a gaban waccen aljanar Mai kama da Forzy,Yun kurin Tayi danta Mike inda bakar aljanar ta take kanta da zabgegiyar kafarta haka yasa ta bude fukafukanta inda wannan wings nata ya bude Forzy dake kokarin tasarta daga mafarkin ta Fadi gefe guda...
Ganin tana kokarin tashi ta fire Kuma idan ta tashi saman zata iyya jin rauni yasa Forzy ta sake yunkurawa a guje ta haye kanta Hadi da riko goshinta da yatsa uku,Aiko duk Shure shuren ta a hannun Forzy takeyi domin kuwa riko goshin nata da Forzy tayi yayi matukar hanata sakat....
Haka zalika cikin mafarkin nata ma ta gagara mikewa su Kara da waccen aljanar....
Fashewa aljanar tayi da dariya Hadi da kyakyatawa sa'annan tace da ita...
"Ke bakiga hakan ba,Aiko Ajalin Duk aljanar data shige wannan guri na rataye ne a wuyar Y'an Adam,kamar Kuma yadda take Shirin faruwa yanzun a kanki Danko Zaki bakunci Lahira Hade Kuma da tallafawar Forzy wajen danne mini ke yanzu"
Aiko bayan ta furta haka ta bangare hannu saiga wata zabgegen takobi ya bayyana a tafin hannun ta Noor naji Kuma tana gani Amma ta gagara komi har ta taka a hankali tazo kusa da ita.....
Murmushi tayi Hadi da d'aga takobin sama da niyar sare mata Kai.
Idan muka Laika bangaren Guda na wannan katafaren guri kuwa zamu jiyo muryoyin Su Atif na Ihun Kiran #Al-Hussien da Kuma #Harun inda ko suke ta waige waige...
Aiko Al-Hussien da Harun na tsaye guri guda Jin wannan kiraye kirayen nasu yasa suka baiyana cikin sauri.
"What's Wrong Guys?,are You alright?"
Tambayan da Harun yayi kenan inda Samra tayi sauri basa ansa..
"Aww Har kana da bakin Tambayan haka,bayan ku biyun Kun d'aga Mana hankali Mai zai faru kenan idan kuka dawo kuka tarar bamu Nan."
Tarar bakinta mu'azz yayi da cewa...
"Samra ya kamata mu Basu damar fadar dalilin su na tafiya ai"
Itako tayi tsawa Hadi da cewa
"No!!, wannan bayi bane Taya zai yadda ya kebance da wannan din"
Haka ta furta Hadi da nuna Al-Hussien da yatsa
"Ya kike fadar haka Samra,what got into you didn't you see what he did to us?"
Fadar #muzaffar kenan inda Tina ta karashe maganar da cewa.
"He saved our lives,ya kamata Koda ta dakika guda kiji kin yadda dashi domin rashin yadda Babu abinda zata haifarwa illa gurkushewar al'amura."
"No She's right, I'm a stranger tana da damarta nakin yadda Dani ko rashin haka Amma kafin tayi hakan ya kamata ta naimi dalilai kwarara da zata tsaya akai"
Haka ya furta yayinda yake kallonta cikin ido,ganin haka yasa Harun yayi sauri shiga tsakanin su Danko daga irin wannan kallo sai fada Domin kuwa Kama sukayi masa da zakarun dake yunkurin fada.
"A lokacin da muka farka mun tadda kuna cikin giyar bacci Dan ko munyi kokarin tasar ku hakan bazata saka ku farka ba,shine dalilin mu na barinku a wannan guri sa'annan Zuwan mu Nan gurin kuwa Nine Wanda na bukaci haka Kuma badan wani abuba saidan mu naimo Mana mafita daga wannan had'ari da muka kasance ciki."
"Mafita? Kudin wai Haha Taya zakuyi hakan?"
Haka Samra ta furta inda Atif yayi mata tsawa...
"You had Enough,Ya kamata ki daina wannan shasahncin."
"But Atif" haka tasoma da niyar fadar wani Abu Amma mu'azz yayi saurin cewa.
"No but,kawai kiyi shiru we have had Enough of this kinji just stay silent."
Hmm haka tayi Hadi da juyawa ta karasa wajen Simon da Mufydah ta tsaya,Aiko ganin tabar gurin Al-Hussien da Harun suka dubi juna...Bayan Nan Harun yace dasu
"Guys Alhamdulillah bincike mu Bata Fadi kas banza ba Dan mun Sami taswirar wannan gini Kuma dashi zamu iyya fita daga wannan guri."
Cikin mamaki Samra ta zuro Idanu haka zalika Atif shima Amma duk sauran basuyi mamakin hakan ba.
"Taya haka zata faru, gaskiya wannan abin da Almara take"
Haka Samra ta furta a kasar zuciyar ta inda Atif shima ya furta cewa.
"Sai wuya takai wuya ake iyya bada satar ansa,Domi inda kaga ance daku kuyi open Examination a makaranta to ana da tabbacin Babu Mai samun ansa ne"
Shiru yayi na wasu Dakiku kafin yasake da cewa
"Wannan taswirar sabon hadarine a gare mu baki daya ya kamata nasan meye abinyi gashi Samra dake kokarin korafi akan tafiyar Harun tare da Al-Hussien tayi shiru sabida mun Mara musu Baya Amma ko Babu komi saina binciko maike kasar wannan taswira"
Haka yayi ta sumbato shi kadai inda sauran abokan tafiyar tasa sukayi can kan taswirar suna dubawa,aikuwa bayan sun kammala dubawa suka dau haramin tafiya Amma hallau tsaye Samra da Atif suke.
Saifa da suka ga kan abokan tafiyar tasu ta suka bace musu kafinnan suka juyo suka dubi juna.
Babu Wanda yace da Dan uwansa uffan haka suma suka biyo sahu,dakin nada matukar girma domin kuwa bazaka iyya kure dakin da kallo daya Tak ba.
*#Forzy*
"Taya Zan taimaka Miki na dawo dake duniyar gaske sister kibar duniyar ta mafarki,gaskiya kaina ya d'aure matuka Amma gaskiya ya kamata na taimaka"
Haka Forzy ta furta cikin siririyar murya idan Kuma muka Laika cikin mafarkin nata ko zamu tarar Aljanan Nan Mai kama da Forzy tana rike da takobin yayinda ta d'aga Tama kamar Mai faskaren itace,tana kokarin dire takobi a makoshin Noor.
Aiko takobin na kaiwa gab da kan Noor sai ta tarwatse ba tare da Takobin ya sare mata kai ba...
Nanfa ta dawo duniyar gaske inda ta tadda Forzy na zaune kanta,tashita ta rugumi Forzy Hadi da cewa
"Bacci matsifane a wannan guri Forzy, gaskiya Ina cikin had'ari kasance wata Anan,na gode Miki da Kika dawo Dani wannan duniyar"
Cikin shesshekar kuka take furta hakan inda Forzy tace da ita.
"Gaskiya #Allah da girma yake,baya marawa karya g**di koda tazo a hannu kafiri ko Kuma musulmi,haka zalika Yana goyon bayan gaskiya akowace hannun daya fito,Koda kuwa a hannun kafirine ko Kuma Mai addini,Noor da ayoyin #Uban-Giji Mai girma na naimo Miki masaluha dukda cewa tana konaki kema domin kin kasance daya daga cikin bakaken Aljanu,Amma abin mamakin Dana tarar game da yanayin da Kika shige kuwa shine kwata kwata wayennan ayoyi Basu konaki ba hassalima dai baki karfin farkawa tayi, gaskiya nayi mamaki."
Aiko sake Rungumar Forzy tayi inda tace da ita
"gaskiya nayi dace abokiyar tafiya."
"Hmm Kin jiki wai,Y'ar uwa ko abokiyar tafiya."
Fashewa sukayi da dariya inda suka Mike suka Kara gaba dadd'i da bode wata kofa suka shige ciki...
Aiko wannan kofa dasuka kasance cikinta ta kasance tamkar a doron kasa take domin imba rashin Ganin Rana da sukeyi ba da sai suce suna a cikin Dajine kawai...
"Wow Kinga abin mamaki"
"Eh Naga hakan Forzy".
Ruwane kwance a gurin ga Kuma bishiyoyi dake gurin saman ruwanko Fararen furanni ne koto ina..masu Jan hankali
"Kinga Fararen fure, gaskiya gurin gwanin ban sha'awa,ya kamata na Ciro guda."
Haka Forzy ta furta....Hadi da rugawa a guje ta nufi gurin.
Idan na dauke ku ko mukayi taku Dubu tare daku a wannan guri zamu riske Taron su Atif a bangare guda na wannan Rafi inda Samra ke cewa...
"Wannan itace Aikin Taswirar? meye wannan to?"
Haka ta furta yayinda take nuna ruwan da hannu ta...
Atif cewa yayi
"Fararen furanni irin wannan,Kuma duk sun mamaye saman ruwan hakan na nufin ruwan Babu zurfi."
"Karkuce ta cikin ruwan zamubi mu wuce"
Tambayan da Simon yayi kenan inda Tina tace Aiko kasar wayennan furanni na matukar sa mutumin kaikayi....
"Aiko Babu Daman tabasu domin kuwa daga zarar mun taba guda daga ciki tofa mun afka cikin chakwakiyar bala'i da Bamu San iyakarta ba"😳...
Fadar Al-Hussien kenan....
_*Readers kamar fa naji Forzy tace zata Ciro daya tofa Allah yayi Mana maikyau*_
*Cigaban labari*
Daga cen inda suka baro wato Kaburburan da suka farka a tsakankanin su,mutane dake cikin Kaburburan ne ke fitowa yadda Iiri ke tsaga kasa ya fito haka suma sukayi ta fitowa...
Kowani daya daga cikinsu idan ya fito sai yayi girgiza Nan sai namar jikinsa ya zagwanye ya zube kasa kwarangwal nasa ko sai ya ruga a guje. Haka sukayi ta fitowa suna nufan inda Su Atif suke.
😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳
*_Mu Hadu a Episode 12_*
_@Abdul Alhaji Musa *Return*_
_1st September 2021_
Sai hakuri nayi late update litin kwana daya😂🤣😁
💀💀💀
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
💀💀💀
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 1️⃣2️⃣*
🦇🦇🦇
"Aiko Babu Daman tabasu domin kuwa daga zarar mun taba guda daga ciki tofa mun afka cikin chakwakiyar bala'i da Bamu San iyakarta ba"😳...
Fadar Al-Hussien kenan....
Da juyo hakan ko Harun ya saukar da idanu alamar nazari,bayan Nan ya juya izuwa ga #Samra ya Mika Mata taswirar dake hannun sa.
"What?" Cikin salon Tambaya Samra ta furta hakan inda yace da ita..
"Ina son ki jagorance mu"
"What!!"
Cike da mamaki Tina ta furta hakan hade da zuwa idanu, sa'annan ta sake da cewa
"But why?"
"Wallahi Babu komi cikin Raina,kawai Naga jajircewar ta,Kuma inaga tafiyar tamu zata kayatar idan ita ke jagorantarmu."
"Hmm" hade da murtuke baki Samra tayi ganin yanayi da Samra ke ciki yasa Mufydah tayi sauri cewa.
"Guys shin kunsan ana binmu sallah na yini guda kuwa? Robonmu da sallah fa tun asuba'in jiya"
"Kuma hakane Fa ya kamata ku Sami guri da Kuma lokaci domin biyan sallolin da ake binku."
Haka #Simon ya furta shida ya kasance Kirista a cikin su.
Al-Hussien ko ya furta cewa
"Hm maiyasa kuke sakaci ne da yawa,Ashe bayan rashin tuno addu'o'i harda salloli ciki."
Aiko dukkan ninsu shiru sukayi inda Harun ya ce da Al-Hussien.
"Gaskiya mun sha'afa ne,domin wannan Guri na cike da Almara iri Daban daban,Amma duk laifina ne domin lokaci Dana farka daga sumar da mukayi na Tino cewa bamuyo sallah ba na yini guda,shiyasa nayi taimama na idar da sallar Amma lokacin da sauran abokan tafiyar na suka farka ban Tino musu da hakan ba,kuskure nane wannan."
"Tunda yanzu mun tuna hakan maizai Hana muyi ta yanzu."
Fadar Mufydah kenan inda Mu'azz yace dasu
"Uhm.. gaskiya Ya kamata Kam muyi yanzu,tunda yau shine karshen wahalar mu,kamar yadda Harun ya tabbatar Mana kunga kenan Babu bukatar mu buya sallah bayan mun fita daga Nan."
"Kwarai kuwa."
Hakan Tina ta mayar masa da martani, Harun shiru yayi Yana ta sauraron su...
Aiko saiga wata kudan zuman na kokarin shige masa Idanu cikin sauri ya soma korarsa da hannu Aiko Yana cikin haka ya hango taron korangwal dinnan na tunkaro su,Ganin haka yasa yayi furucin *Oh no*
"Ya dai?."
Tambayan da Ali yayi masa kenan shida ya fahimci yanayin Harun din ya sauya,ganin bai basa ansa ba ne yasa shi yunkurin juya Idanu izuwa inda Harun din ke fuskanta Amma sai Harun yayi saurin mayar masa da ganin sa hade da cewa...
"We have to leave this place... Now"
"What!,why?, sallar da muke kokarin Yi Kuma fa?"
Fadar Mufydah kenan inda mu'azz yayi saurin cewa...
"Ya kamata mu girmama fadan nasa domin bamu San dalilin sa na fadar hakan ba."
"Girmamawa sabida meye wai,munafa cikin had'ari Koda yaushe Mai zaka sanar da Uban Giji kenan idan iftila'i ta afka da Kai ka mutu?."
Tambayan da Tina tayi kenan Wanda yasa duk jikinsu tayi sanyi but Banda Harun da Kuma Al-Hussien,su sun kasance sun hada fuska domin basuji dadin hakan ba.
Samra Ganin kan abokan tafiyar tasu zata rabe gida biyu yasa tayi wub ta karbo taswirar dake hannu Harun ta bude,gani tayi taswirar na nuna Mata hanya a inda suke tsayen wacce ta cikin ruwan tabi ta wuce..
Bata ce dasu komi ba kawai tasa kafa ta shige ruwa,Aiko Babu Wanda ya sake fadar komi haka kowa yabi bayanta da dukkan alamu ta anshi tayin Harun..
*Al'amarin Forzy da Noor*
"Wow Kinga abin mamaki"
"Eh Naga hakan Forzy".
"Kinga Fararen fure, gaskiya gurin gwanin ban sha'awa,ya kamata na Ciro guda."
Haka Forzy ta furta....Hadi da rugawa a guje ta nufi gurin.
Zuwanta gurin keda wuya sai Noor ta kwala Mata Kira,Aiko cek ta tsaya inda ta juyo,fuskarta cike da annashuwa.
"Mai kike ci na baka na zuba,Aiko ta cikin furannin zamubi mu wuce Kinga kenan har Zaki koshi dasu Dan haka ki bar maganan cirewa kawai mu wuce."
Fadar Noor kenan inda Forzy tayi Gajeriyar murmushi Hadi da cewa.
"To ni banga kwale kwale ba Taya zamu bi cikin ruwan?."
"Fararen furanni na hayayyafa ne a gabar ruwa inda Babu zurfi sosai,to gashi sun mamaye kan wannan Ruwa haka na tabbatar Mana da cewa wannan ruwan Babu zurfi Dan haka muje,ta ciki zamubi mu wuce."
Aiko Babu Bata lokaci suka shige cikin wannan Ruwa wacce ta kasance daidai kugunsu suna tafiya cikin fira hade da Raha kamar tagwaye...
Kimanin Mintuna talatin both side din suka kasance suna tafiya Ruwan wato bangaren Su Atif da kuma tasu Noor, yayinda suka kasance sunyi matukar kusanci da juna Danko dabadan Hazon daya mamaye gurin bane da zasu hango juna.
Take biriki Samra tayi inda dukkannin abokan tafiyar nata suma suka tsaya..
"Impossible."
Zura idanu Tina tayi tun kafin taji dalilin Samra na furta hakan, Mufydah ko cikin sauri tace
"What's wrong?."
"Taswirar Bogi ce mukayi anfanin dashi,Kuma hakan na tabbatar min da cewa mun fada cikin iftila'i."
Ansar da Samra ta bayar kenan bayan taji tambayar da Mufydah tayi.
Aiko Atif cikin sauri ya anshi taswirar yasa Idanu inda Mu'azz shima yayi hakan...
Bayan mu'azz da Atif sunyi hakan ko suka dubi juna cikin mamaki shiko Atif yayi furucin cewa
"Taya taswirar ke nuna Nan itace hanyar fita?"
Haka ya furta a kasar zuciyar sa inda Mu'azz shima ya furta cewa..
"Shin Wacce bala'i ne yanzun muke kokarin Fadawa ciki?, gaskiya ya kamata mu gaggauta komawa baya."
Haka shima ya furta a kasar Ransa.
Daga inda Forzy da Noor ke tsaye suna iyya jiyo motsin mutum ta ruwan yayinda Forzy ta gano haka sai tayi saurin cewa..
"Da wasu anan gurin."
Fadar haka Forzy tayi inda Noor tayi sauri Bata ansar cewa.
"Haka ne,I can smell Humans watakila abokan tafiyar kine."
Aiko da jiyo haka sai tayi murmushi Hadi da yunkurin zuwa gurin Amma sai Noor ta riko hannunta sa'annan tace da ita.
"Gudun Fadawa matsifa,bai zama lailai sai munje gurin ba Zan iyya Gwada warware wannan kafin da Karfin Baiwata,na Gwada yaye wannan Hazo Dan mu hanko abinda ke nesa."
"But.." haka Forzy ta soma furtawa Amma dashike tasan abinda take niyar fada sai ta tari bakinta da cewa.
"Karkiyi kokarin dakatar Dani domin hakan shine mafita."
Shiru Forzy tayi wacce hakan ne ya bawa Noor karfin gwiwan amfani da baiwarta,Aiko hada tafin hannayen ta tayi inda ta soma surutan tsafi, Bayan ta karashe surutan nata ta raba tafin hannayen nata.
Aiko Nan da Nan sai wannan Hazo ta yaye gurin tadau haske,ganin gurin yayi haske yasa Forzy murmushi yayinda Noor ko d'igon jini ya fado daga hancin ta,ya Fadi Cikin ruwan.
Tana cikin yanayin na kasala da Kuma Jin jiri,kwatsam sai tayi arba da jinin dake kan ruwan na rubuta Mata wasu harrufa wacce sune...
"Idan Kika kasance kina anfani da baiwar da kike gadara da ita,toh wata Rana ba hancinki ne kadai zata zubar da jini ba har kwakwalwarki saita buga."
Dafa goshi tayi yayinda jirin ke kokarin daukan ranta Danko idanun ta sun kusan rufewa dan zazzafar jirin dake damunta.
Forzy ko ido hudu tayi da Tina inda tayi shewa Hadi da juyawa tana furta cewa.
"Wallahi sune,abokan ta.......
Aiko shiru tayi Bata karashe maganar nata ba Domin ta tarar da Babu kowa a tsaye inda Noor take dazun, ma'ana Bata sami Noor din ba.
"Noor! Noor! Noor!!!."
Haka Forzy ke furtawa yayinda take waige waige.
Tina ko kwarma ihu tayi yayin Kiran sunan Forzy Aiko karau daya sauran tawagar suka daga idanun su inda sukayi arba da Forzy,dukda cewa abin farin cikine haduwarta da sauran y'an uwan nata Amma sai ta kasance cikin takaicin rasa Noor datayi.
a zahirance Kuma Noor ta kasance tana tsaye gefenta yayinda take ta Kiran sunan ta harma tana cewa..
"Forzy gani Nan fa banje ko Ina ba" ,haka tayi ta furtawa Amma ganin Forzy ta wuce ta jikintane ya tabbatar Mata dacewa Forzy Bata iyya ganin ta.
Samra fuskar ta cike da annashuwa yayinda tayi tauzali da Forzy Domin kuwa Bayan kyewarta da suka tayi,sunji takaici da suka gagara tallafa Mata waccen karon Kuma hakan duk suka kasance a gurin,Harun ko ganin suna kokarin zuwa wajenta ne yasa shi cire daya daga cikin furannin dake gurin,ya murkushe ta Hadi da yasar da ita cikin ruwan.
Bayan ya gama wannan aika aikar ko ya daga kallonsa nanfa sai ya tarar da Al-Hussien na kallon sa..Basarwa yayi ya maida ganinsa gefe guda Hadi da gofe hannayensa
Aiko Cikin sauri su Atif sukaso su kaiga Forzy Domin kuwa guduwa bazatayo ba a cikin ruwa Amma sai suka gagara yin hakan Danko cire furen da Harun yayi shine sababin shigarsu cikin matsifar da basuyi zaton ba..
Aiko Cikin kankanin lokaci gurin ta sake hadewa Hazo ta mamaye ko'ina sa'annan saman gurin tayi baki Kai kace hadiri Danko har walkiya na faruwa a saman gurin...
Komi na gurin ya sauya cikin kankanin lokaci yayinda Samra da saura mutane suka tsaya domin kuwa sun daina ganin Forzy..
Juyawar da zatayi Dan sanar da sauran hakan ko sai ta tarar da Babu kowa aikuwa cikin sauri ta Soma furta cewa.
"Guys! Guys guys!!!"
Aiko abinda Bata sani ba shine dukkan ninsu a cikin wannan Hali suka kasance domin Babu wani daga cikinsu daya kasance tare yake da mutum kowa a gurin daya ya kasance.
Atif shima ya kasance sai kiraye kirayen sunayensu yake haka zalika mu'azz da sauran abokan tafiyar tasu....
Dukda cewar ba wani nitsa sukayi da junan suba Amma wanna hudu da kuwa tsawa Hadi da walkiyar ta hanasu ganin ko jiyo muryar y'an uwan su.
"Forzy Ina tare dake,gani Nan kusa dake Forzy."
Jiyo haka da Forzy tayi yasa bakin cikinta ya gushe Nan da Nan fuskar ya cike da annashuwa,wata y'ar murmushi ta saki Hadi da Soma tafiya da niyar takaiga Noor din.
Haka kowace bangaren suka Sami abokan tafiyar kamar yadda ya faru da Forzy haka ya faru dasu Kuma kowa na kokarin zuwa ga mutanen da suka tarar.
Atif ko Mu'azz ya ganin hakan ya Soma tafiya cikin sauri Dan ya kaiga iso sa, Samra ko Tina ta gani tare da muzzaffar...
Al'amarin Forzy ko sa hannu ta tayi cikin na Noor Nan sai wata ciyawa ya rike Mata kaya ta juya da niyar cirewa aikuwa ta cikin ruwan tayi arba da hoton Noor na kokarin fahimtar da ita cewa waccen din ba ita bace..
Ganin hoton Noor din ta cikin ruwanne yasa ranta yayi matukar tsinkewa domin kuwa da ganin fuskar wannan ta cikin ruwan tasan waccen data kasance a boyen itace Noor din asali toh Amma wacece wannan da ta riko hannun ta..Abinda take da burin sani kenan Aiko d'angowa tayi inda ta hada Ido da Noor din dake rike da hannun nata.
Hadewar idanunsu keda wuya taso su rungume juna Amma Forzy taki yin hakan sai wannan dake cikin suffar Noor ta rikede ta dawo mermaid🧜♀️🧜♀️ aikuwa rudewa Forzy tayi ta kwarma bagidajiyar ihu wacce kowannen su sai da ya jiyo wannan ihu na Forzy.
Kama daga kan Atif,samra,Simon mu'azz da sauran abokan tafiyar nata ko suka jiyo haka cikin kankanin lokaci mu'azz da ke tare da Atif shima ya rikide ya dawo mermaid🧜♀️🧜♀️ haka zalika Tina da muzzaffar wanda Samra ta hadu da suma suka rikide suka koma wannan suffar.
Aikuwa cikin mamaki dukkan ninsu suka zura idanu domin kuwa y'an matan kan ruwan sun kasance suna da manya hakwara...
Mufydah ko data kasance rungume take da daya daga cikin Wayennan halittu a tunaninta daya daga cikin abokan tafiyar na tane,ihun Forzy nakaiwa garesu ko sai wannan aba ta buga Mata hakwara a wuya Aiko tuni jini ya Soma kwararowa daga wuyarta..
Sai famar Shure Shure take ita Mufydah kamar wata karsanar da aka da'ba ma wuka a wuya,nanfa sai taji an duki mermaid din da karfin tsiya Nan ta cika Mata wuya ta fada cikin ruwan ta gudu...
Aiko ba kowa bane Wanda ya cece ta illa Harun.
Forzy ko juya bindi abar tayi ta bugeta dashi Inda ta Fadi kusa da Atif Amma sai suka kasa ganin juna...
Ganin abin na karasowa wajenta da karfin tsiyako yasa Noor ta shige gaba dukda tasan bazata iyya kareta daga hakan ba..
Dukkan ninsu fa dakyar sukasha a hannun wayennan halittu Amma bayan duk sun taru guri guda sai wayennan halittu suka kasa karasawa garesu..
Sa'annan Kuma sukaki kai mata Forzy farmaki dukda ta kasance tsaye take ita daya....
Shiru kakeji Babu mai motsi Dan zunzurutun tsoro da suke...
Bayan Shirun Nan ko sai suka Soma wata irin Kara Mai kamadata 🐝 kudan zuma.
"Car'uba."
Abinda ya fara fitowa daga bakin Tina kena inda Mufydah ta Soma cewa.
"I don't want to die"
Fadar hakan keda wuya sai Tina ta jiyo ta kalle ta da niyar tace da ita wani Abu but then kawai sai taji sulub an janye Tina ta saka kasar Ruwan.
Dukda katuwar rauni dake wuyarta tako bai Hana ta kwarma bagidajiyar ihu ba....
Aiko yin hakan keda wuya sai taron kudan zuma suka sauko akan Ali yadda kasan taron safa da marwa haka sukayi masa Babu abinda suka Bari a jikin sa,har firewa sukayi dashi suna ta kaimasa farmaki.
Aiko da zaka d'aga idanu ka kalli sararin samaniya tofa ko haske kadan bazaka gani ba Dan yawan wayennan zuma dake addabarsu.
bayan bala'in kud'an zuman Nanfa sai wayennan Fararen furanni suka Soma mikewa suna Kai Sara kamar macizai.
Aiko gurin ya dawo tambar filin yaki domin kowa na kare kansa al'amarin Tina ko Damin furanni ne suka nannade ta itama Babu abinda zaka iyya gani a sassar jikinta...🐉🧜♀️🐝haka ta kasance a kasan ruwan na iyya lokaci da suka dauka suka wannan fada.
Forzy ko takasance karfinta yasha Dan ko furanni sun nannade hannayen ta hagu da kuma Dama, sa'annan Kuma zuman sunayowa kanta ganin haka da Noor tayi yasa ta shige gabanta tayi kururuwa.
Aiko sai ta baiyana cikin haske Yadda kasan Bob na utar lantarki tana Mai shiki,abinda ta fada ko shine ki Kulla da kanki Y'ar uwa..
Nanfa sai hasken nata yafi kaifin ganin Forzy ta wannan dalilin ne yasa ta lumshe Idanu Noor ko tarwatsewa tayi yayinda hasken nata ya tsistsinke furannin Hadi da tarwatsa taron kudan zuman sa'annan Kuma duhun gurin ta yaye...
Cikin abinda bai wuci dakiku uku ba ruwan dake gurin ta tsotse guri yayi fili Aiko saiga Ali tare da Tina na kwance Rai a hannun Allah.
Tina tayi kore Shar kaikace green girl🧟hatta gashin kanta ya cenza Kama ganin haka yasa Samra ta soma zubar hawaye...
Ali shiko jikinsa ta dawo tamkar Rariya Dan yawan hujin dake jikinsa ga Kuma rasa ganin da yayi domin Kudan zuman sun rabasa da ganin sa...
Mufydah ko Nan take zaune ta rike wuyan nata da hannu biyu, muzzaffar ko ganin haka yasashi kama bakin rigarsa ya yage cikin sauri ya d'aurewa Mufydah wuyarta,domin Dakar da kwararowar jini.
"Wannan bala'i da meye tayi kama."
Fadar Samra inda Simon ya Mike hade da takawa izuwa inda Harun ke tsaye,bayan sun hada Idanu ko ya wanka masa tafi.
"Kai ka haddasa hakan,kasan komi Kai kake kokarin cutar damu."
Hakan Simon ke furtawa yayinda kwalla ke zubo masa a fuska.
Ganin haka yasa Mu'azz da Kuma Atif sukayi saurin shigewa tsakanin su,suna Kuma kokarin basa hakuri Aiko dajin kallamar hakuri yayin ihu yiyin fadar abarsa ya koyawa Harun din hankali.
Karar ya ratsa gurin har ya kaiga inda Forzy ke shesshekar kuka tana Kuma rike da Noor a hannu..
Bata iyya cewa komi ba Domin tana cikin yanayine na babbar Rashi..
Tofa *Wasa farin girki* Ni a tuna Nina komi yazo karshe Amma ko wannan shine soma tabi Danko bayan wasu Dakiku sai gurin tadau girgiza yayinda kasar ke tsagewa dad'in dad'awa Kuma saiga wayennan kwarangwal da suka baro a baya sunsa Kai...
Ganin haka yasa Samra Sallati Aiko jiyo haka da Mufydah tayi yasa ta Mike tsaye,arba tayi da taron korangwal dinnan Aiko batasan lokacin data soma kuka ba.
Amma kafin su karaso garesu sai wannan guri ta saura kasa dasu Nan take gurin yayi Rami Kai kace rijiya ce,yayin saukar su ko sai da suka ciyu Danko sunsha azabebbiyar wahala domin duwasu na Fado Musa aka.
Hakan wannan guri ta rabasu da Forzy domin Basu sake samun damar ganin taba.
Aiko nitsewar da gurin yayi dasu ba ko'ina ya kaisu ba illa inda suke da burin zuwa wato inda wannan taswirar keson kaisu..
Dukkan ninsu suna a gurin daya daga su har wayenda suka jikkatan wato Ali da Tina,Wanda mu'azz da Atif ne Basu kulawa.
Ganin gurin yasa suka Mike tsaye dashike da kwai rata tsakanin su sai it's,sai suka daga ganinsu sama suna kannon ikon Allah domin Basu taba ganin irin wannan abar ba.
Domin kuwa gadar da suka hango zakace *door of heaven* ne Danko wata doguwar gata me wacce Bata da madafa ga Kuma tsayi Danko da za'a daura wani a karshen gadan ta sama da zai kalli mutanen kasan gurin tamkar kiyashi,Dan zunzurutun tsayin wannan gada.
Gadar ta somane daga inda suke tsaye, matattakalu ne aka jera har izuwa karshen gurin,Kuma Babu abinda ya tokare ta atsakiya.
Aiko ganin hakan yasa Samra tasa Hannu ta Ciro taswirar inda taga taswirar na tabbatar Mata da Nanne gurin da suke naima,Nan sai tayi murmushi Hadi da Soma taku Aiko step biyu da tayi sai wata katuwar keji ta fado kan sauran tawagar nata ta kulle su a ciki.
Wanda wannan girman kejin da Kuma nawinta sai samudawa ne zasu iyya d'aga ta,da jiyo karar fadowar wannan abinko tajuya da niyar ganin mai ke faruwa Amma kawai sai ta jita a sume Dan ko naushi Tasha wacce ya sumar da ita,Karo daya.
Bayan ta Fadi kasan ko aka Ciro taswirar dake hannun ta.
_*TIRKASHI NA ZAUNE BAIGA GARI BA*_
*_Mu Hadu a Episode 13_*
_@Abdul Alhaji Musa *Return*_
💀💀💀
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
💀💀💀
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
*TRAILER EPISODE 13*
*_UPCOMING EPISODE OF KOFAR AJALI_*
"This is the only way out, and it's made for one person only... so Taya kuke tsammanin Zan tsaya kallo har na hallaka kaina."
Aiko bayan fadar hakan ya kyalkyalewa da dariya sa'annan ya cidaba da cewa.
"Wannan hanyace da aika yita Dan mutum daya Kuma wannan mutumin ba kowa bane illa ni."
🐉🦇🧟
🐉🦇🧟
🐉🦇🧟
"It's all your fault Atif."
Fadar Mu'azz
"Why are you blaming me?, bayan a idon kowa akayi haka."
Ansar da ya bayar kenan
Inda Samra ta furta cewa....
"Yeah laifin Kane Atif,idan da badan Kai ba da duk haka bazata faru ba,And now komi ya tabarbare."
"This is the final, sa'annan ita ake Kira da Hard way and the only way, wannan Guri tayi gaskiya duk Wanda ya shigeta ba lallai bane ya fita."
"Hakane sister Amma Ina ganin na Samo Mana mafita."
Cikin bacin Rai suke wannan tattaunawar............
*EPISODE 13 ZATA ZO MUKU RANAR JUMMA'A DA MISALIN KARFE TAKWAS NA DARE KUDAI KU KASANCE DA NI DOMIN WARWARE KILLIN.*
💀💀💀
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
💀💀💀
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/abdul.alhajimusa.94
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
* EPISODE 1️⃣3️⃣*
_FINAL EPISODE_
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
Cikin Kasala Samra ta soma bude Idanu,inda ta tarar da an daure Mata hannaye jikin Kejin da su Atif suka kasance a ciki,Aiko sai data duba ko'ina dake gurin kafin ta Ankare hannayen nata a daure.
Nanfa ta soma kokarin kunce hannayen nata daga jikin karfe but sai ta Soma jiyo tafi daga cen nesa shiru tayi tana sauraron abinda zai biyo Bayan wannan tafi,kalmar da mai wannan tafin keyi ne ya ratsa ilahirin guri wadda wannan kalma ko itace *well well well*
Cikin kasaita da nuna kwaraiwa wannan Mai tafin ke karasowa gare ta,Aiko sai daya baiyana gabanta be ta shige mamaki ba iyaka Hadi da wangale baki tana kallon sa.
"Harun?!!"
Abinda ya fara fitowa daga bakin Samra Kennan inda Harun din ya Bata ansar cewa
"Yeah it's me."
Kasa cewa komi Samra tayi tana ta iy'ina kamar dacen haka take magana,Aiko ganin Harun na rike da taswirar a hannu ne ya tabbatar Mata shine wanda ya buga mata naushi ta suma,Kuma shine Mai alhakin daure Mata hannaye.
"What are you doing Harun,Mai yasa kake yin hakan?."
Gajeriyar murmushi yayi Hadi da cewa..
"Sarauniyar Nuna kulawa ga wasu,yau Kuma bazaki duba halin da y'an uwan naki suke ciki ba kenan."
Haka ya furta cikin kasaita Hadi da yimata nuni da yatsa bayanta.
Zura idanu Samra tayi Hadi da waigawa cikin sauri,inda tayi arba da sauran abokan tafiyar nata na kokarin bawa Tina da Ali tallafi Hadi Kuma da Karin wani kwance gefe guda Yana Shure Shure..mutuwa
Samra na iyya kokarin ta wajen ganin fuskar wannan mai Shure shuren Amma Ina hakan baiyuba,tana kan hakan kuwa sai ta jiyo muryar Harun na cewa.
"Karki wahalar da kanki wajen naiman ganin fuskar wannan,Zan sanar dake ko waye wannan."
Jiyo hakan yasa Samra ta juyo cikin 'bacin Rai yayinda ta hade fuska idanuwanta jajir.
"Harun what got into You?."
Haka ta furta yayinda ta kasance cikin bacin Rai shiko ya sake cewa da ita.
"Ah Ah ya hakan? Kin fara nuna tausayi tun kafin na sanar miki cewa nine silar shigarsa wannan halin?."
Da jiyo hakan ta zuwa idanu,shi Kuma kyalkyale dariya hadi cewa.
"Kai ka haddasa hakan,kasan komi Kai kake kokarin cutar damu Harun,shin Zaki iyya Tino Wanda ya furta hakan bayan ya wanka min tafi idan Zaki iyya tunawa to shine wancen dake gabar mutuwa."
Sauke Idanu Samra tayi inda ta tuno lokacinda suka kasance cikin ruwan Nan dake kwance,hala lokacin da suke cacan baki...
Aiko bayan tayi hakan sai ta zura idanu Hadi ta furta cewar
"It must be him,Simon."
"This is the only way out Samra, and it's made for one person only... so Taya kuke tsammanin Zan tsaya kallo har na hallaka kaina."
Aiko bayan fadar hakan ya kyalkyalewa da dariya sa'annan ya cidaba da cewa.
"Wannan hanyace da aika yita Dan mutum daya Kuma wannan mutumin ba kowa bane illa ni."
_*Readers Bari Mu dawo baya da labarin*_
_Gwabzawar da akayi tsakanin Scopions da Jemagu_ ne Yasa Tawagar tasu ta tsira daga bala'i Scopions din but duk da hakan a guje suka shige kofarnan da suka bude ta da Takubba dake da Harafin Mutuwa a jiki.
Aiko da shigarsu kofar taja kanta ta rufe.....Duhu kake iyya gani ta ko'ina
Kasancewar su a wannan guri tayi daidai da kasance a duniyar Mars ba tare da abin tallafawa gurin Nunfashi ba,domin da shigarsu kofar suka sume,Tsawon lokaci sukayi a sumen kafin suka dawo bacci.
"Harun! Harun! Harun!."
Kusa da kunnuwarsa yake jiyo hakan,Aiko lullukawa cikin duniyar mafarki a yayinda kake jiyo sauti a kunnuwa ka abune Mai sauki..
Nanfa sai ya fada duniyar mafarki yayinda yayi mafarkin Mahaifiyarsa tilo,wannan mafarki dai tamkar tarihi ne domin abinda ya faru dashi ne yake sake gani.
Wannan mafarki ta soma da lokutan nishadi tsakanin sa da Mahaifiyarsa daga cen sai labrin ta dawo abin tausayi yayinda Mahaifiyarsa ke mummunar jinya Wanda Kuma shi kadai ne Mai kula da ita Aiko Yana ta ganin haka sai yaga wata katanga ta ginu tsakanin sa da Mahaifiyar tasa wacce take wanciyar jinya,Babu Mai dagata ya Bata abinci Babu Mai yimata komi gashi bazata iyya yiwa kanta komi ba.
A firgice ya farka idanuwan sa cike da kwalla, tarar da Al-Hussien a gefensa ne yasa shi Tino wannan kiraye kirayen sunan nasa da akeyi.
"Why don't you just wek me up? instead of calling my name's."
Bayan ya furta hakan ne yasa hannayen a fuska ya Kuma sauke Kai.
Al-Hussien Shiru nay'an wasu dakiku kafin Nan yayi wasu maganganu a kasar zuciyar sa Wanda yake cewa.
"Your mother will be alright,Amma farko let's help me with my plans."
Gajeriyar murmushi yayi bayan ya furta hakan a kasar Ransa Nan sai yabawa Harun ansar tambayan da yayi masa wato.
"Why don't you just wek me up? instead of calling my name's."
"Ina Mai baka hakuri,Kuma dalilina na tasarka ta wannan hanyar shine,we promise not to touch each other that's all."
Bayan Al-Hussien ya furta hakan ne yasa Harun dago Idanu izuwa kan da.
"Akwai abinda ya kamata ka sani Harun."
Dajiyo haka Harun ya murtuke fuska alamar rudewa... Al-Hussien ko ya sake da cewa
"Just follow me." Hadi da mikewa, Harun baida ta cewa kawai sai ya Mike ya bisa a baya dukda yasan Sauran tawagar tasa suna yanayi na nannauyar bacci.
*_Readers shin Taya Al-Hussien yasan da Mahaifiyar Harun? Naga a mafarki Harun din yaga Mahaifiyar tasa kuma bai sanar dashi ba, Amma Taya ya sani?_*
Tafiya sukayi wacce Bata da nisa sosai sai suka kaiga wata kogo Aiko sa Kai Al-Hussien yayi Hurun shima ya bisa a baya.
Tsintar kansu sukayi a ma'ajiyar littattafai wacce take da haske sosai ganin haka yasa Harun mamaki Hadi da wangale baki.
"Inane Nan guri?."
Tambayan da ta soma kubuta daga bakin Harun kenan inda da diyo haka Al-Hussien ya kame Kam Hadi da juya ganinsa izuwa kan Harun.
"Wannan Guri na dauke da d'inbun Tarihin,Wanda zasu anfane mu domin idan ka duba zakaga ababen anfani su ake adanawa a store to anan gurin Kuma ababen masu anfani su ake Tarawa a Ma'ajiya irin wannan,Dan hakan zamu iyya samun taswira ko Kuma tahirin gidan wance hakan zata matukar taimaka Mana Dan hakan ka duba wannan bangaren Ni Zan duba cen duk abinda kaga ba daidai ba karsanar dani."
"Okay."
haka Harun din ya furta Hadi da yunkurin juyawa Amma sai yayi arba da mirror *madubin* wacce ta ciki Hotonsa kadai yake iyya hangowa Babu ta Al-Hussien dukda Al-Hussien Yana gurin.
😳😳
Kasa motsawa daga gurin yayi yanata wasi wasi cewa.
"Anya wannan shine Al-Hussien da muka Sani Kuwa? Anya wannan ba tarko aka 'Danan na hayeba."
Yana kan fadar hakan sai wata kundi ta fado masa a gaba sa'annan ta bude kanta da kanta.
Wasu harrufa rubutu be suka baiyana inda ya karancesu cikin sauri,nanfa suka bace,Aiko jiyo muryar Al-Hussien ne yasa shi rawar d'ari...cewar Al-Hussien.
"Shin Ka Sami wani abinne?."
"A'a Babu komi."
Ansar daya bayar kenan inda Al-Hussien din ya cigaba da aikin gabansa shiko ya tsunkuya cikin sauri ya dauko kundin Hadi da lullube madubin da wani farin kelle daya tarar a gurin.
Juyawar sa sai yaji an yafe Kellen da karfin tsiya,Aiko zura idanu yayi cikin sanyin jiki ya jiyo inda ya tarar da wani rubutu a jikin madubin...
Zura Idanu yayi cikin tsoro ya kasa motsi sai Nishi yake Nan sai ya jiyo muryar Al-Hussien na cewa.
"I found something Harun."
Cikin sauri ya juya Hadi da karasawa wajen Al-Hussien din karasawar sa Al-Hussien din yace dashi
"Taswira na Samo wacce nake kyautata zaton zai kaimu ga kofar fita daga wannan matsifa."
Aiko jiyo hakan da yayi sai ya Soma waige waige Yana Kai idanun sa lungu da sako,abinda yayi matukar basa mamaki ko shine gani yayi taswirar an bajeta a kasa📜 ganin haka yasashi cikin zurfin tunani,Yana kokonto shin abinda ya tarar gaskiya ko kuwa.
Abinda ya tunoko shine rubutun da ya gani jikin madubin wacce itace.
"Maraba da Kasancewa cikin Dakin gaskiya,dakin zata bayyana kowace karyar da aka lullube da mayafan gaskiya."
Bayannan sai ya tuno da abinda kundin yace da shi sai yace da Al-Hussien din
"Ka cigaba da duba wannan gurin Ina dawowa"
Aiko cikin sauri ya koma ga madubin Hadi da zubewa gaban madubin ya Ciro kundin daya boye a jikin sa ya bude.
Taswirar, zaku tsinci taswirar da zata kaiku ga wata katafariyar gada saidai gadar ta mutum daya ce Tak daga zarar mutum sama da daya suka haye tuni zata zube...
Gajeriyar bayani daya Samu daga kudin kenan game da taswirar dake hannun Al-Hussien Nan sai ya gaskata maganan kudin haka ya sake amincewa da rubutun da kundin ta nuna Masa tunkan ya dauketa wato "idan kana son tabbatar da gaskiya sai ka yadda da kanka kafin ka gane gaskiya sa'annan,karka yadda da kowa idan ba kaiba....kowa ba abun yadda bane idan ya kasance cikin wannan gidi."
Komawa yayi wajen Al-Hussien yayinda Al-Hussien yake kokarin nuna mishi taswirar shiko Daban abinda yake shukawa domin sai daya Gwada taba gadon bayan Al-Hussien sai yaji sulub hannu sa tashige ciki Nan ya tabbatar Al-Hussien ba mutum bane.
*Cigaban labari*
Sauke Idanu Samra tayi inda ta tuno lokacinda suka kasance cikin ruwan Nan dake kwance,hala lokacin da suke cacan baki...
Aiko bayan tayi hakan sai ta zura idanu Hadi ta furta cewar
"It must be him,Simon."
"Yeah yeah shinefa."
Cikin bacin Rai Atif ya yunkura Hadi da furta cewa.
"Harun yaushe zaka bar wannan haukar taka, ka dakatar da abin Nan da ka jefawa simon"
Cikin tsawa ya furta hakan inda Mu'azz shima ya furta cewa
"Idan Yana tunanin ya Sami wani karfin zai ci Mana fuska da ita toh yayi tayi Allah na bayan Mai gaskiya."
Hahaha kyalkyalewa yayi da dariya Hadi da cewa
"Karkuyi tsammanin Ni na jefaku cikin wannan halin no,ku kuka jefa kanku domin Kun yadda da junan ku Kuma kun yadda da kowa, kowa kuka gani zaku yadda dashi kamar yadda kuka yadda da Al-Hussien Wanda ya kasance Yana son ganin bayanmu gaba daya."
Zura Idanu Al-Hussien yayi Hadi da cewa "what are trying to say?."
"Kamar baka San komi ba Bayan ka sanar Dani cewa wannan dakin mutane biyu me kacel zasu iyya barinta wance kake alakan tata Dani da kuma kai,Amma bakasan cewa na fika sanin gurin Nan ba."
Gajeriyar murmushi yayi Hadi da cewa
"Gaskiya kayi kuskure domin Ba'a amincewa Dani kamar yadda nima banayiwa kowa anan gurin kowa kallon gawa nake Yi Masa domin duk taron ku ko kunkai Dubu mutun daya ne zai koma gida Dan haka karku Damu idan na Kai gida Zan sanar da duniya cewa duk Kun sheka Babu Wanda zai sake tuna ku Dan haka na barku lafiya,idan Kuma akwai Mai sakon da yake son isarwa a duniya ya sanar dani idan Kuma Babu kunga tafiya ta."
Aiko Al-Hussien ganin duk plan nasa zasu bare idan ya cigaba da karyar shi mutum ne ya Kuma cigaba da tsayawan tare dasu a Kejin,yasa shi fita cikin Kejin yadda kasan hayaki ya tunkari Harun.
Dukda Harun ya basa baya hakan bai Hana ya gane cewar ya fita daga Kejin ba.
Kyalkyalewa yayi da dariya Hadi da cewa
"Now You show your true color Al-Hussien."
Aiko duk taron abokan tafiyar nasa suka shige mamaki Babu mai iyya cewa komi.
Samra da kanta kasa cewa komi tayi tana ta kallo Al-Hussien.
"If you go there alone you will kill me and kill your self please came down,zamu shawo kan Komi I promise Zan sanar daku dalilina nayin haka Amma karka yadda ka haye wannan gada Kai kadai I have my reason for doing that."
Haka yayita faman nanatawa Harun ko ya sauke Idanu kamar maganan ta shigeshi but daga karshe sai ya taka step biyu,dashike kasan gurin kamar interlock yake Nan da Nan suka nutse sai wuta ya kewaye Al-Hussien Yana ci Kai kace runfar Kara, wannan wuta ko tana iyya dakatar da kowace halitta yayin ketare ta bacin mutum Babu Mai ketarawa saman utan.
Ajiyar zuci Harun yayi Hadi da cewa
"I'm sorry but I had to do it,Dole Zan barku anan yayinda Zan haye na tsallaka izuwa duniya."
Aiko Al-Hussien Yana ta furunci karyayi hakan domin zai hallakasu Amma Sam yaki sauraron sa haka ya haye kan gadar yayi tafiyar sa.
Zubewa Al-Hussien yayi akan gwiwar sa yayinda kwalla take zubo masa a fuska..
"Wannan ce damata ta karshe na mallakar abinda na Dade Ina muradi wato gangan jikina Amma gashi cikin abinda bai wuci dakiku Goma zata bare..."
Sukum sukayi Babu Wanda yace dashi kala Nan sai ya yunkura Hadi da cewa
"ya kamata mu Kai Masa agaji domin zai rasa ransa,Kuma banason a mutu ta dalilina."
"Al-Hussien shin har akwai abinda zaka sake fada Mana mu amince da ne,You lie to us kawai Dan abinda kake burin ka samu sai Kuma gashi dukkan ninmu Muna adaure a guri guda gaskiya Allah Mai Jin kukan bayin sane domin Halinda kaso mu da ita sai gashi tare muke a ciki."
Al-Hussien Shiru yayi ya sauke Idanu Nan sai sukayi arba da gadan Nan na rusowa haka gadar ta zube Al-Hussien ko ya yunkura Hadi da cewa.
"This is the end of me."
"It's all your fault Atif."
Fadar Mu'azz
"Why are you blaming me?, bayan a idon kowa akayi haka Kuma har ya tafi Babu Wanda yayi kokarin dakatar dashi."
Ansar da ya bayar kenan
Inda Samra ta furta cewa....
"Yeah laifin Kane Atif,idan da badan Kai ba da duk haka bazata faru ba,And now komi ya tabarbare."
"Samra Mai kike fadane haka Taya na zama sanadin faruwan haka."
"This is the final, sa'annan ita ake Kira da Hard way and the only way, wannan Guri tayi gaskiya duk Wanda ya shigeta ba lallai bane ya fita."
"Hakane sister Amma Ina ganin akwai mafita domin kowace mashiga a kwai mafitar ta."
Tattaunawar karshe kenan tsakanin mu'azz Samra da Kuma Atif.
🥺🥺
Indan muka Laika bangaren Harun ko tsaye gaban wannan kofar da yake kyautata zaton shine hayar fita.
Aiko sa hannu yayi ya bude inda ya shige cikin Dakin Aiko Hamdala yayi Hadi da murmushi ba Komi yasashi hakan ba illa arba da yayi da hasken Rana Mai kokarin dauke ganin sa.
Murmushi yayi Hadi da takawa ya bada rata tsakanin sa da kofar Aiko juyawa yayi ya Ciro kundin Nan da ya saka a kugun sa yayi jifa da ita sa'annan yayi furucin cewa
"karshen wahalar ta zo."
Aiko fadin hakan daidai yake da kafewar hasken Nan da Nan koren gayayen da yayi arba dashi duk suka dauke kamar da cen a cikin TV yake kallo Komi ta sauya ta dawo abin tsoro Aiko Nan Harun yasan Yayi matukar kuskure na bijirewa da Kuma bin shawarar wannan kundin.
Domin kuwa ya fahimci Yar mitsitsiyar daki ya kasance a ciki wacce Bata da masuburbusar iska ko window,Babu Komi a dakin illa wata katuwar akwatin gawa kuma da dukkan alamu dakin zaiyi matukar duhu,domin Babu alamar fitulu a dakin,hasken dake haskake cikin Dakin ko ta cikin kofar yake shigowa.
Aiko Saida yayi arba da inuwar sa kafin ya tuno still kofar da ya shigo ta ciki yana bude Aiko cikin sauri ya yanke shawarar fita daga cikin Dakin aguje dukda yasan Koda ya fita Babu hanyar saukar sa d'aga saman inda yake.
Amma ya gwammaci yayi ta kallon haske yafi Masa daya kasance cikin Dakin nan shi kadai.
Nan ya ruga a guje da niyar fita but sai kofar taja kanta ta rufe,Nan sai wata Murya ta soma magana yayinda muryar ke fita uku uku Ya furta cewa.
*GAME OVER*
*_THE END_*
Karshen littafin Kofar aljali kenan littafi na daya,Mu hadu a littafi na biyu.... Ranar jumma'a Mai 15th October. Mai taken
*KOFAR AJALI*
_The Return_
```[Hard way and the only way]```
*_Ku kasance tare dani,Guys keep liking and commenting_*
+2349077974042
0 Comments