TARBAR GIRMA
Hausa poem
Written by
Mujaheed Matashi
Appreciation to
Abubakar Abdullahi Alkas (King) for his contribution to this poem
Ƴar uwa barka da zuwa,
Yau masarauta za tai hawa,
Za ta yi murna ta yi yekuwa,
Domin tarbarki, babbar kawa.
Da ganinki ɗiya ce ma hali,
Na gari, kuma zakiyi tattali,
Da kamala, zurfin hankali,
Kunya, ma'ana mai tozali.
Wannan birni danginki ne,
Marubuta, dukka irinki ne,
Masu tsaftace harshe a bayyane
Ba sa ƙarya ko shaɓune.
Yanzu mu za mui tafiya da ke,
A ƙawa, ko ƙanwa ta mu, ke,
Ko yaya, ko ko mu ce da ke,
Babbar jigonmu da ba ya ke.
Ga nasiha gun ki ki ɗan tsaya,
In kina son shura duniya,
Ko'ina ki ka je marubuciya,
Za ki zauni da kowa lafiya.
Ki riƙe mu da zuciya ɗaya,
Ki tsare mana sirri guri ɗaya,
Taimaka nuna mu a duniya,
Mu ne Sarki da Sarauniya.
Masu waƙe ba zambo ciki,
Ga labaranmu daki-daki,
Fadakarwa ko murnar biki,
In ɗayanmu ya sami tabarruki.
Ki zamo mai bin duk ƙa'ida,
Kar ki wa kowa hassada,
Duk da ba kya yi na dai faɗa,
Don in daɗa kaurin tawwada.
Baje duk baiwarki a zahiri,
Kar ki tsoron wani ja'iri,
Mu nan kya ganmu cikin gari,
Kanki mui wa mutum dundu ɗari.
Ha in nemo birki a haka,
Ƴar goma na baki ki sa jaka,
Madadin membobin nan duka,
Allahu ya ƙaro ɗaukaka.
Tarbar girma na maza
Ɗan uwa barka da zuwa,
Yau masarauta za tai hawa,
Za ta yi murna ta yi yekuwa,
Domin tarbarka, dan uwa
Da ganinka mutum ne mai hankali
Na gari, kuma zakayi tattali,
Da kamala, zurfin ciki Kunya, ma'ana mai hankali
Wannan birni danginka ne,
Marubuta, dukka irinka ne,
Masu tsaftace harshe a bayyane
Ba sa ƙarya ko shaɓune.
Yanzu mu za muyi tafiya da kai
A boki ko dan,uwa zamu ce da kai
Ko yaya, ko ko mu ce da kai
Babbar jigonmu da ba ya kai
Ga nasiha gun ka ka ɗan tsaya,
In kana son shura duniya,
Ko'ina ka ka je marubuci a duniya
Za ka zauna da kowa lafiya.
Ka riƙe mu da zuciya ɗaya,
Ka tsare mana sirri guri ɗaya,
Taimaka nuna mu a duniya,
Mu ne Sarki da Sarauniya.
Masu waƙe ba zamba ciki,
Ga labaranmu daki-daki,
Fadakarwa ko murnar biki,
In ɗayanmu ya sami tabarruki.
Ka zamo mai bin duk ƙa'ida,
Kar ka wa kowa hassada,
Duk da ba ka yi na dai faɗa,
Don in daɗa kaurin tawwada.
Baje duk baiwarka a zahiri,
Kar ka tsoron wani ja'iri,
Mu nan kya ganmu cikin gari,
Kanka mui wa mutum dundu ɗari.
Ha in nemo birki a haka,
Ƴar goma na baka ka sa duka
Madadin membobin nan duka,
Allahu ya ƙaro ɗaukaka.
English
Welcome, to the King and Queen's noble domain,
Where pens and parchment weave a majestic chain.
Join our ranks, let your creativity reign.
In this hallowed chamber, your talent shall gain,
Guidance and support, through every strain.
Embrace our rules, let your craft sustain.
Avoid the pitfalls where ambiguity feigns,
Danger lurks where clarity wanes.
Write with purpose, let your words attain.
For here, unity binds us, a harmonious refrain,
Together we flourish, no room for disdain.
In this literary kingdom, let your voice maintain.
To the newcomer, we extend our warm domain,
In our fellowship, your efforts shall attain.
Welcome, dear writer, let your passion retain.
Here, amidst the quills and ink-stained plain,
You'll find companionship, a fertile terrain.
In your journey, let creativity reign.
With diligence and patience, you shall attain,
Mastery of craft, no effort in vain.
In our realm, your aspirations shall sustain.
But heed our counsel, where wisdom does explain,
Avoid the snares where uncertainty feigns.
For clarity's light, your writing must contain.
Within these walls, let camaraderie reign,
Let not envy or rivalry entertain.
In our sanctuary, let unity remain.
So welcome, dear writer, to our domain,
Where imagination and talent intertwine.
May your presence enrich our vibrant chain.
TARBAR GIRMA
Hausa poem
Written by
Mujaheed Matashi
Appreciation to
Abubakar Abdullahi Alkas (King) for his contribution to this poem
0 Comments