RIBAR HAƘURI



👄👄👄👄👄👄👄
 RIBAR~HAQURI   
👄👄👄👄👄👄👄                             
                                                                    
                                                      
    
    
    
Story & writing 📝
       By: 👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
        [Samha Umar] 🥀

GODIYYA:
Godiya ta tabbata ga Allah (swa) daya bani damar kawo muku wannan littafi  tsira da aminci su qara tabbata bisa ga fiyyayen halitta annabiuhammadu {saw].

GARGAD'I
'"ban yarda wani/wata ya juyamin littafi ba batare da izini ba idan aka aikata hakan Allah ya'isa nah..!

DEDICATED:
   "I dedicated this novel to my family SHUFRAM FAMILY love you more than anything, 
     
       Page 1 I dedicated it , to my Happiness my daddy hon.justice Faruk Hassan bunza.!

PAGE 1

Bismillahi-Rahmanin-Rahim

"Motace qirar Corola l.c Red color Tay parking gaban wani tamgamemen gida mai kyau da tsari..

Bud'e murfin motar Akayi Wata budurwa kyakyawa ta fitoh fuskar ta da Alaman damuwa, shigewa cikin gidan tayi Bata tsaya ko ansa gaisuwar gateman ba ta wuce Fallon gidan.

    Tana shiga ba kowa A Fallon sallama ta shiga kwod'awa Asamu Alaikum" , Amma shuru .

Cen saiga Wata budurwa Tana saukowa daga upstairs Kalo d'aya naima fuskar tah na Gane Tana cikin tsantsar damuwa.

         Farar fuskarka duk tayi jajir Tana ida sawkowa wace ta shigo ta rikota jikinta zama sukayi bisa kujera mai zaman mutun biyu, wace ta shigo ce ta d'ago kan dayar Tana cewa Fateema meke damunki,? . Duk kin tasuwar mini hankali...

        "Tuni kuka ya kufcema Fateema cikin she-sheka take magana. Laila ina cikin tashin hankali marar misaltuwa.

       Fateema kimin bayani yanda zan fahimta.

"Laila docta ne shine Layla Wai Aure zaiyi.

     

              Aure Fateema 😳 kwota-kwota yaushe Akayi auren natu inaji jibi three weeks dazaice Aure zaiyi. 

"Bama Shiba Fateema yaje ya samu Didda  da maganar itakon tace wlh indae tanada Rae bani ba zama da kishiya, jin abinda tace yaje ya gayawa Daddy shiko yayi fad'a sosai harma Yana cewa duk Didda Bata bari ya auri sabeeterh ba, toh itama Abakin nata auren..

  

Fateema Sabeeterh fa.?
  
     Eh. 

Inalilahi to yanzu ya za'ayi.?

    " Layla ni bama wannan ba  shima docta din yazo ya sameni Yamin cin mutunci harma Yana cewa wlh duk Didda ta hanasa auren Sabeeterh toh sai nayi nadama.
           

          "Kuma layla zaima Iya fin Hakan ko yanzu ya nakeji, wlh inajin Da zamana wannan kaddararen gidan indama mutuwa Nayi..

 
 "Haba Fateema ki daena fadar haka komae ya faru kaddara ce ba yanda za'ai ki tsallake tah , kawai haquri ne naki Inshallah  watan-watarana zakiga RIBAR HAQURinki  Amma yanzu meye mafita..

 
   Hmm Laila na rasa menai ma way'n nan family suka tsaneni Saboda haka didda ta shiga matsaaloli da dama ta Dalilinah SBD haka lokaci yayi daya kamata na barta ta hutah.
    
    
    
"Dubanta Laila tayi tace toh Fateema me kike tunanin zakiyi.?

Laila Zan mutu.

 

  "Mutuwa..? Fateema kinada hankali kesan me kike fad'a?

         Eh, Laila amma ba mutuwar gaskeba I mean Zan tafi na barmusu dangi Kai koma duniya ne na shiga..

         

           Toh Fateema na fahimta Kuma Zan taemakeki Yanzu Saikiyi Tunani Gobe Zan dawo Saimu yanke Shawara keji ki kwontar da hankalinki!!

        

   "Toh Layla ngd sosai Allah ubangiji yabar zumunci ,

Amin Laila ta fad'a Tana Tashi Maya'finta ta gyara Tana ma Fatima sallama had'e da cewa "Fateema kada kisama kanki damuwa don Allah kinji , 

  

  Bakomai Laila ki gaedamin umma.

"Toh tace Tana fitah.

Bayan fitan Laila tagumi Fateema tayi tashiga duniyar Tunani.......

********************

 
 
 " Haba Didda Wai meyas kike son ki cutar da kanki Keji fa Abinda Daddy yace ,,,,

        

 "Didda dake zaune bisa bed side, tayi  tagumi, duban Husnah dake bisa sofa tayi  Tana cewa Husnah; Bintu (Fateema)fa Amanace a gareni Kuma nasan Sabeeterh ba Alkhairi bace, Wlh duk Salim (docta)  Ya auri sabeeterh indae nina Haifeshi to sai yayi nadama..
  

         

   Haba Didda kibar yiwa Yaya baki Akan Wata cen banz...... Bata Kai ga ida maganar taba ta dafe  bakinta Saka-makon Dukan da Didda tai Mata ,

    .

    "Cikin fad'a Didda ke cewa Wlh Husnah ki kiyayi Duniya je kiso wata'cen ga yr'uwarki ki , Daki so da kada kiso Bintu D'iyar K'aunwatah ce Uwa D'aya Uba d'aya kuma keda na Haifa Da ita duk d'aya kuke A gurina, 'ko ubanki bai Isa ya Rabani da'itaba balle ke,     "cikin tsawa ta'ida cewa fitar min daga d'aki Shashasha.
    
    
    

     
   Sum-sum Husnah ta miqe fita tayi daga d'akin Bedroom d'inta ta Wuce, Tana shiga ta dauko Wayarta dake bisa mirror..
              
  
           

     Contact ta shiga Number da'akayi saving da Jameey ta kamo Kira Tayi Amma har ya katse ba'a D'auka bah ,      
         

    
       

          tsaki tayi Tana aje Wayar Juyowa tayi Amma sai taji Ring Wayar Koda ta Duba Jameey ceh,  peaking tayi tana cewa , Ke kina ina Nakiraki baki d'aukaba.?
    

  "A cikin wayar Jameey tace Wlh Husnah bana kusa ne kafin in k'araso Kiran ya tsinke.

  
Okay dama So nake muyi magana Akan Bintu, Anna ya kamata mu had'u.

       

  "Ton shikenan Dama naji Anty Tace Anjima zata shigo gidan kuh, kinga sai muzo tare,

  
       "Toh shikenan sai kunzo Husnah ta fad'a Tana had'awa da cewa ki gaeda Antyn.
  
      

   Zataji Jameey ta fad'a ..

Yanke Kiran Husnah Tayi Tana zama bisa bed Tunani ta shiga yi, "domin dole ta samu mafita Akan Bintu............

        ***SHARE IT FOR ME****

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & writing📝
  
 By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
   [Samha Umar]🥀

" This page 2 I dedicated it to my lovely Momma HAJIYA YR'EGGE"

PAGE_ 2

Bismillahi_Rahmanin-Rahim

_____________Jamila kiyi sauri ki fitoh mu wuce kinji.

  Toh anty ganinan fitowa ta fad'a daga cikin d'akin!

Anty dake tsaye duk ta gaji "Fallo ta dawo ta zauna Tana duban Wayar dake hannunta , anty na fito taji Jamila ta furta a kusa da'itah

   'Dagowa tayi tana tashi, "toh muje ta fad'a Tana yin gaba."

 Suna fitowa sai parking space mota suka shiga Jamila ce ke driving Basu tsaya ko'ina ba sai gidan ALHAJI HASSAN SAUTA suna Isa babban gida ne wanda kallo d'aya zakai masa kasan namasu kud'ine, 

  "horn Sukayi gateman ya bud'e musu suka shiga cikin gidan a harabar Jamila Tay Parking , fitowa Sukayi suka nufi main Fallon gidan, shiga Sukayi fallon suna sallama ..

   "A maraba da Hajiya zulai Didda dake zaune bisa d"aya daga cikin kujerun ta fad'a , murmushin da baikai ciki ba anty zulai tayi tare da fad'in mun sameku lpy Didda?.

   

     Lpy qalau Didda tace Tana qarawa da "ki zauna Mana zulai."
    
    
    
    
    
    "A'a basai na zauna ba, Wurin Yaya nazo."
    

  "Ayya Didda Tace, tare da cewa Yana masjid . 
    
    
 

      Toh kawai anty ta fad'a Tana zama.
    

        "Tuni Jamila tayi bedroom d'in husnah Koh gaida Didda batayi ba" 

.'Ke tashi mai baccin Asara, Jamila ta furta Tana bubbuga husnah dake kwonce bisa bed Tana bacci..!

"Tashi husnah tayi tana yamutsa fuska haba jameey....! 'cikin sauri jameey Tace ke kullemin bakinki tashi muyi magana kega ba dad'ewa zamuyiba inji Jamila,,

      
  
   
        "Tashi husnah tayi, kusa gareta Jamila ta zauna tare da fad'in Inna jinki Husnah..!

 "Jamila Didda na tsananin son Bintu ko kad'an tafi sonta a kaina, gashi Yanzu tace Yaya bazai auri Sateey bah, "shine nakeso mui Mata abinda zaisa ta fita dangin mu.."

  

       "Husnah kinyi gaskiya domin koni na tsani yarinyar nan ' meya kamata muyi matah ..?

      

        "Inaga ya kamata mu Mata Abu d'aya daga cikin uku, na 1komu kasheta, na 2 komu laqamata Sata, na 3 komu haukatar da'itah..

    

  Ajiyar zuciya Jamila tayi tana cewa eh hakane ni kawae a kasheta shine burina, wlh duk sanda nai tozali da'ita ji nake kamar na shaqeta ta mutu...

   

 /"Duban jameey husna tayi tana cewa  Hakan yayi daede zamusa a kasheta toh Amma tayayah..
    
    

"Cikin sauri jameey Tace a kawae zamu tura a kasheta ki bari Zan bincika!"

    
Toh yayi kyau husnah tace, ″mutafi Fallo "tashi Sukayi suka nufi Fallo...″
    
    
    

★★★★★★★★★★★★★★★★

"Yaya dama akan maganar Salim ce "eh zulai Inna jinki.!

 

  "A Fallon daddy suke su biyu Anty zulai da Daddy. 

 
   "Yaya gaskiya abar Salim ya Auri sabeeterh Saboda kawai Yana auren yr kaunwar Didda sai Tace bazai auri Wata ba,.?  

       

      __Kuma wannan Auren na Salim da Bintu had'ashi Akayi Amma yayi HAQURI ya zauna da'itah Yanzu kuma sai abarshi ya Auri zab'insa..

   

    Eh zulai maganarki gaskiya ce Amma duk  Hadiza (Didda) Bata janye kudirin'ta ba na Hana yaron Nan Aure ba toh inanan akan bakatah,..
    
    
   

    
        "Toh Yaya Hakan yayi, dama maganar ce ta kawo ni bari na wuce sai Anjima.
    
  

 
              "Toh zulai sae Gobe ki gaeda ALHAJI ANAS (mijinta)"

"Yaya zaiji tana fitowa a fallo ta tarrada su Jamila Cewa tayi ta tashi su wuce , "ta dubi husna Tace 'ki cema Didda mun wuce!. 

 

 
     "Toh "suna fita itama husna ta tashi bayan ta biya ta gayama Didda anty ta wuce sannan ta tafi d'akintah.....

★★★★★★★★★★★★

"Wlh Khaerat saina auri docta Koda kuwa sama da kasa zata had'e, "ni sabeeterh Fateema matarsa ba matsala bace babu malami babu boka  a tsarina Amma duk Abinda na kwollafa rae sai burina ya ciki kisa a ranki saina Auri docta..!

   
     
      
 
   "Sateey ki bari wlh ki daina wannan halin naki. Way'n Nan abubuwan Basu Dace ba ki guji sharrin Duniya..!

 "Hmm khairat kenan, "Saboda Abu-uku nakeson dacta badon komai ba , na 1 kyawon sa Yana burgeni na 2 kudin su domin naji dad'in rayuwatah , na 3 d'aukan Fansa ..

       

   D'aukan Fansa..? khairat ta fad'a da mamaki..

      "Eh khairat d'aukan Fansa Akwoi wani kudiri a cikin zuciyatah "Akwoi wani sirri  shine nake son na d'auki Fansa a wannan famillyn na SAUTA , "Kuma kada ki tambayeni menene wannan abin.
    

    "Idan burina ya'cika Zan sanar dake , khairat Zan shiga famillyn Kuma Zan musu Babban Tab'o  Wanda bazasu tab'a mantawa dani'ba  ,.."
    
    
    
    Kuma tashi mu tafi...........
    
    
    

******SHARE IT FOR ME******

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & writing 📝
 By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
      [Samha Umar]🥀

*This page 3 I dedicated it to my Hajjaju HAJIYA AMINA  you are special to me...!*

PAGE_3

Bismillahi_Rahmanin-Rahim.

*Asalinsu*

"Malan Tukur Sauta babban malami ne Yana zaune ne A mafara "yanada mata d'aya juwaira da 'yr-ynsu uku , Hassan da Husaini sae Zulai..!

     

        "Malan Tukur amininsa d'aya wani bafulatani daya shigo gari, bukar , yryn malan Tukur sunyi karatu sosai. 

Lokacin ne da suka kammala secondary School malan Tukur ya Tara 'yr-ynsu Hassan da Husaini Yana tambayarsu..!

           "Yanzu tunda kun qare babbar makaranta menene ra'a yinku , "Hassan ne yace shikan yanaso yaci-gaba da karatu Abarsa yaje kano. Shiko Husaini yace baida ra'ayin Kara karatu wa, "Wanda yayi ya wadatar"

      *Toh maddalah malan Tukur ya fad'a dayin na'am da shawarar kowa a cikin'su "

"Inda yayi wa Inna wato mahaifiyarsu bayni, itama abin ya mata dad'i saide zuwan Hassan kano ne bai mataba "Amma Babu yanda zatayi"

        "Ana hakan akayi ma Hassan shirye-shirye ya kama hanya ya tafi cike da kewar gida"
    
    
    
    
    
    
    ★★★★★★★★★★★
    

__bukar Aminin malan Tukur yanada mata d'aya shatu sai 'yr-ynsu biyu matah "Hadiza da Amina
Sun taso cikin tarbiyya da sanin ya-kama ta"

"Sunyi primary 🏫 school da secondary"

★★★★★★★★★★

Hassan ya'isa kano da taemakon Allah yasamu sana"a a wani shago, inda-idan 
yaje makarantah ya dawo sai yaje shago,,,, 

 " A kwona a tashi Babu wuya a gurin Allah"

BAYAN-SHEKARA (4)

"Zaune suke tsakar gida suna murna A yau Hassan ya dawo.!

 Inda ya kammala makaranta result kawe Ake jira shine ya dawo gida"

      "Innalilahi_wa'inna-ilaihin-raji'um" 'inna ta fad'a.

      Meke faruwa..? Su mallan Tukur suka fad'a suna kallonta "

     "Alhaji kalli Inna ta fad'a tana nuna masa yamma da gidan su"

"Subhanalahi" malan Tukur ya fad'a Yana cewa gidan waye Ake gobara..?!

   Fita yayi daga gidan 'yr-ynsa ne suka mara masa baya "

Inda yake hangen mutane ya nufa Yana qarasowa ya zaro ido Yana furta menake Shirin gani.? Bukar gidansa.? Toh Yana ina Yana shiga gidan domin har an kase wutar, gani yayi gefe daya an lullub'e wani abu, gabansa na qara fad'uwa , ya karasa Yana bud'ewa ya furta innalillahi_wa'inna-ilaihin-raji'um....."

   "Ganin abin da bai yi zato ba, "gawar bukar da shatu ne aka lullub'e sai cen ya hango 'yryn su , hadiza da Amina zaune sai sharb'an kuka suke,.

  Tashi yayi ya isa inda suke , kuyi haquri ku tashi ku tafi gidana"

A gidan malam tukur akaima su bukar wanka  akai musu wanka aka wuce dasu gidan su na gaskiya.

   "A nan gidan malan tukur su hadiza suka ci gaba da zama inda yake yake kula dasu tamkar yryn sa!!!

   Cikin haka soyayya Mai karfi ta shiga tsakanin Hassan da hadiza Ina Hasan baiyi qasa a guiwaba ya sanar da malan tukur.. shima yayi na'am har ya tsaida ranar ..

      "Saura wata d'aya auren hassan da Hadiza result din Hassan ya fito yayi kyau sosai hakan yasa gwonnati d'aukansa aiki.

Yau da gobe sai Allah anyi auren Hassan da hadiza, inda suka wuce kano, kuma malan tukur yace suje da zulai ta Taya hadiza zama.....

  

    *BAYAM-SHEKARA 2*

Hadiza ta haihu ta samu d'a inda aka sa mishi suna Salim (sunan mahaifin malam tukur) anyu buki lpy aka watse , Hassan arzikinsa sai bunqasa yake, inda yake manager a wani babban kamfani na business ,  bai tsaya anan ba harda kwongila, yanzu kam yazama babban mai-kud'i.. inda ya Gina wani tamga-memen gidah , na ji da gani.."

  "Zulai kuwa ta samu miji shima d'an kasuwane a yayinda malan tukur sauta yaji lavari, saiya Kira hussaini ya tambayes ya fad'i wadda yakeso domin a had'a Dana zulai.

  Cewa yayi a basa kwona biyu .

   "Da tau malan tukur sauta ya ansa inda ya inda ya Kira Amina Yana tambayar ta Wanda take so.

   "Cikin Jin kunya ta amsa da akwoi, wanene ya tambayeta..? "A.s.p Kamal ta basa ansa, 'to mashaallah sai ki gaya masa ya turo a saka dai-dai Dana yr uwarki zulai .

  Da husaini yaji labari sai ransa ya b'ace domin yayi nauyin baki, haka ya yanke shawarar barin gari ,  ko zaiji sauqi cikin dare , yayi tafiyar sa,  

    "Koda safiya tayi an nemi husaini sama da qasa Amma ba'a gansa ba, har zuwa hantsi, inda akasa neman sa ko'ina ba'a gani ba, tun Ana sa rai har aka fidda rai.
    
    

Bayan watanni anyi aure ko wacce ta tare a gidan mijin tah,  "hadiza wacce Amina ke-kira Didda dama sauran mutane" ta sake haihuwa ta samu d'a Amma bizo da Rae ba"

   "Bayan shekara d'aya da Aure zulai wacce suke Kira (anty)  ta haihu ta samu d'iya inda aka samata suna zeenatu. Ba'a wuce shekaru biyu da watanni ba Amina ma ta haihu ta Samu d'iya aka samata Fateemah wato bintu. 

  Ba'afi 6month ba Didda ta haihu ta samu d'iya Ranar suna yr taci suna Asma'ul-husnah ana kiranta husna, bayan suna da sati Anty zulai ta haihu ta Samu d'iya aka sa mata Jamilah..

 
  Fatima da husnah da Jamila tare suka taso Amma suna da Jamila suna kano itako Fatima tana mafara.

   Bayan wasu shekaru Allah ya d'auki Ran ALHAJI TUKUR SAUTA.
  Mutuwar ta girgiza wanna ahalin bama su kad'ai ba hatta yn gari domin shi mutumen kirkine, 

 PLZ Comment and share✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing
  By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
    (Samha Umar)🥀
    

 This page 4 is special gift to My luvly elder Sister FATIMA FARUK BUNZA.

PAGE__4

Bismillah_Rahmanin-Rahim.

Sunyi kuka sosai sanadin mutuwar mahaifinsu, inda akai sadakan bakwoi, ALHAJI Hassan ya buqaci Inna ta dawo kano wurinsa , ada Bata amince ba Amma daga baya ta yarda.

    Bayan sun koma kano acen suka ci gaba da rayuwa inda Hassan ya biyawa Didda da Inna zuwa makka su sauke farali.
    
    
    
"Salim yaron su Wanda yake kama da Amina kaunwar Didda sak, da kyawonta da komai nata tamkar ita ce ta haifeshi,  primary school kawai yayi, mahaifinsa ya kaisa waje karatu ya cika burinsa na zama doctor.

★★★★★★★★★★

BAK'AR RANAH

Yau ta kasance ranar jumma'a zaune take Fallon gidanta Tawai take ma yrtah d'aya tillo duk da girmanta  , yishuru-yi shuru daddyn'ki ya kusa dawowa, bintunah "Kinga jibi zan kaiki gurin diddan'ki."

  Da gaske,? Yarinyar ta fad'a cikin muryarta ta yarintah, ..

To zan miki karyah.?

A'a ammi karya ke Aa ,

 Asalamu-Alaikum. Yayi sallama Yana shigowa gidan, ASP Kamal kenan mijin amina.

Wa'alaika-salam, Amina ta fad'a. Da gudu fatima ta rumgume daddynta , tana cewa ba wo wo, ,  d'aukan ta yayi Yana mata wasa harya  k'araso Fallon Yana sauke fatiman, Ansa gaisuwar da Amina ke Masa yayi, 

  Tashi tayi ta kawo masa abinci, bayan ya gama ci ya wuce masjid, yayi magrib sai bayan sallar isha'i ya dawo,  karfe 11 suna zaune su duka Fallon suna'cin Abinci, 

  Wlh "baban bintu yau haka kawai na tashi da fad'uwar gaba😥 .

Dubinta yayi Yana cewa wlh kedae ammin bintu, bakomai inshallah kawai kiyi addu'a,   Alhalin shid'in ma wani iri yajeji, 

  Tashi Amina tayi ta wuce bedroom inda ta d'auko takarda da biro to fara rubutu kamar hakah.!!!

    *Asalamu-Alaikum*
    
"Antynah yayatah diddatah, Ina fatan wannan wasiqar ta isa gareki"

Yayatah abar qaunata nasan duk duniya banda kowa sai ke"yr uwatah.

Awannan Rana bansan ya zata kasanceba, Ina mafarkin "innarmu da baban mu na fitomin idan na kwonta bacci, suna cewa inzo Amma a jiya na tamka kiransu"

  Amma ga Fatima bintu nan na baki amanarta wlh duk kika cucetah bazan tab'a yafe Miki ba.

Amana-Amana-Amana✍️

Allah ya had'a fuskokin nu da Alkhairi.

Linke takardan tayi tana zubar da hawaye,  tana fatan wannan wasiqar ta isa ga diddantah, 

Jin shigowar Fatima ya sata share hawayentah, Amitah meya sameki

Ba komi bintunah ta fad'a tana jawota jikintah, ni ba abinda ya sameni, to ammi bacci, 

To zomu kwonta yrtah , kwonciya sukayi bisa bed domin bazata tab'a yin bacci ba idan ba kwonciya tai da'ita ba, Bata San sanda bacci ya d'auke ta ba, ,,,,

Tashi yayi ya kashe kayan kallo Yana mamakin tafiyar Amina Bata dawo ba , 'Dakin ta ya shiga  ya tarar tayi bacci tare da bintu  qarasawa yayi bakin gadon Yana kallon fuskar matar shi .

Saida ya shafa fuskar Amina kafin ya wuce,  d'akin sa ya shiga domin kwonciya bacci😴.

Karfe uku na dare Agogon Nigeria ya nunah,  kamar daga sama ya fara jin karar harbi,  ya zabura daga bacci Yana furta Innalillahi wa'inna ilaihin raji'um.

Mutun biyu dake tsakiyar d'akin da yake suna sanye da bakaken Kaya, ko wannen su ya kulle fuskar sa,  da bak'in kyalle😷. Bakin gadon d'aya ya zo, tare da tunkud'e keyar sa zuwa fallo.

A tsakiyar Fallon suka yadashi kusa da Amina,

Wanda yake bisa kujera sai kyal-kyala dariya yake, 

ASP Kamal ne yace me kukeso don Allah wlh kome kuke so zan baku.

Alhaji Kamal bana buƙatar kuɗin ka , Rayuwarka ta fiyemin komai. SBD haka cikin minti ɗaya ku shirya baƙun tar lahira. Kaida matar ka, Burina zai cika na ganin bayan ka, ASO.

 ya 'ida maganar tare da harba bindiga daide saitin goshin Amina, faduwa tayi ƙasa tana Kiran sunan Allah,  Ya harbe ASP a gaggauce yace su wuce daga gidan.!

Jin ƙarar bindiga ya sata firgita daga baccin data ke,  tashi tayi tana Kiran Ami Ami taji shuru , shi ɗowa tayi daga Jan bed ta kama hanyar fallo tana Ami³ Abi³ ,...

"Tana isa fallo sai bisa Amina da har yanzu ranta bai Ida fita ba, Ami Ami 'kamo hannunta Amina tayi tana cewa.

Yrtah kiyi haƙuri da ƙaddarar da Allah ya Azo Miki ko wahala, ko ƙunci komai rintsi ki zauna da didda , baki da kowa sai itah kinji , 

Ami Ami me kika ce k , sai kuka Fatima keyi.

Kalumatul-Shahadah tayi tana runtse idoh Nan tace ga garin ku Nan,

Ami Ami take kirantahhhhhhhhh....

WASHE-GARI

Wayewar gari keda wuya aka cika gidan da mutane, domin makwob ta kowa ya ji Harbin.

"An samu wa 'yn da Suka d'auki waya suka Kira didda suka Gaya mata abin da ke faruwa, 

Tayi kuka sosae didda sai kuka take har suka iso Zamfara-Mafara  a gidan suka yi parking,
Har an musu wanna, domin mutanen-Mutanene jira kawai ake yn'uwa suzo..

Ko parking ba'a Ida ba didda ta fito  tana shiga gidan hannu bisa Kai, a tsakiyar Fallon taga Ansa musu likkafa ni, 

Ƙaruwa kukan ta yayi, isa tayi ta buɗe gawar Amina tana kallo , hannunta takai dai-dai inda Akayi Harbin tana furta Innalillahi wa'inna ilaihin raji'um,  wata Mata ce tace kiyi haquri hajia
Tana ɗagotah  Ahaka aka kaisu Gidan Gaskiya. .......

Akwona A Tashi..

Har anyi sadakar bakwoi tana gan-gama kayan d'akin domin jiki zata koma, "su daddy da anty zulai har sun zo sun kayi kwona uku suka koma".
To zali tayi da paper cikin drawer ɗauka tayi ta buɗe, Hawaye ke zuba a idon ta har ta kammalah karantawa..

Rumgume Fatima tayi dake bacci ..

A haka suka koma Kano da'ikon Allah didda ta ɗauki fatima tamkar Ameena tsokar jikin tah ,

"Tun Fatima na kukan tashin iyayenta harta Saba da didda , didda ta ɗauki son duniya ta ɗorawa Fatima , sauran mutanen gidan sun tsani Fatima hakan kawai, Donma suna Shankar didda da abin yafi haka.

    A haka didda ta roƙi Daddy da  asa fatima makaranta badon yaso ba ya Amin-ce 

 
A haka fatima ke haquri domin cikin asiri Ake muzguna-matah, har ta qare primary  school ta shiga secondary cikin haka Akayi auren yr Anty zulai babba wato anty zeenatu anyi biki anci an Sha, an watse lpy,

Yau da gobe sai Allah inda fatima ta kammalah secondary School ɗinta results na waec da ceco kawai ake jira wata ɗaya kenan suna jiran result tana so ta Zama doctor,.

Ya kammalah karatu da inda takardan sa ta Zama cikkaken babban Likita kawae yake jira.....

Plz comment and share✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & writing 📝
  By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
  {Samha Umar} 🥀

"This page 5 I dedicated to my elder sister AISHA FARUK BUNZA fatan Alkhairi antynah 🙏"

PAGE___5

Ayau Ne D.R SALIM HASSAN SAUTA ya dawo daga qasar waje karatu an masa tarba ta musamman inda ya zagaya ƴn uwa da abokan Arziƙi kowa yayi murna da ganin docta inda kowa ya gansa kamar ba'a Nigeria aka haife sabah.

   Yayi kyau kamar ɗan turawa.

Alhaji magana nake dakai.

    Eh, naji Hadiza auren Dole wa ɗanki to shikenan, in kika cuce shi kanki kikai mawa.
    
    
  Kamar ya Alhaji shifa yace na gayama Yana sonta.

 "I dole tun da kin tilastashi Amma keda ɗanki"

Na jiya didda ta faɗa tana fita daga d'akin husnah tasa ta Kira Mata docta.

Salim na maka Mata tun baka zo duniya ba.

What, didda kesan me kike nufi.?

  
  " Eh Mata Kuma ba kowa bace sai bintu ƴr kaunwar tah.."

Didda kesan me bakin ki ke furtawa.?

Kai yimin shuru, Kuma na cema Daddyn ku Kai kace kana sonta sannan indai nina haifeka kada kace Aa domin Ina tunanin Kaine kawai zaka riqemin ita Amana,

   
  Ina so bintu ta kasan ce Dani, "ban son ta auri wani sai Kai"

 Don Allah Salim kada ka cutar da bintunah ko kaɗan ngd ɗana Abin ƙauna tahhh.

Jiyayi duniya ta masa nauyi shin me didda ke nufi da ya auri ƴr kaunwar tah.?

★★★★★★★★

Daddy ne ya kira sa domin jin shin da gaske shiya zaɓi bintu a matsayin matah.

Wlh daddy bana sonta ko kaɗan ni saima ɗazu didda ke sanar Dani.

Cikin faɗa didda tace Salim ni zaka qarya ta a gaban mahaifin kah? To shikenan ta tashi tayi tafiyar tah, 

Shima zabura yayi ya bitah Bata tsaya ko'ina ba sai bedroom ɗinta.

   Didda don Allah kiyi haquri.

Aa Salim ni baka min komai ba, kasan Kai ɗan mahaifin kah ne je kayi yadda yace ta'ida kamar kuka zata yi.

              Na'amin ce didda indai hakan zai faranta Miki rae kinji, bana son ki shiga wani Hali ta dalilinah.

 

Shikenan jeka sanar da mahaifin kah, Allah yai maka Albarka.

Tashi yayi Yana tafiya kamar Wanda kwoi ya fashewa a ciki, ita ma tashi tayi Bata tsaya ko'ina ba sai part ɗin Inna wato mahaifiyar daddy, ta sanar da'ita Shirin su na haɗa auren Salim da fatima yayi.

Koda didda ta sanar da fatima Bata so ba Amma, Amma SBD biyayya ta Amin-ce...

 
Anyi aure bama wani biki Akayi ba, Fatima kan zaman haquri takae kowa ya takura tahhhhh.

★★★★★★★

Babban Likita ne a wani private hospital da Daddy ya buɗe masa Ana ji da wannan assibitin domin daga qasar waje kayan assibitin suke.

Sunan assibitin AL'UMMA PRIVATE HOSPITAL (APH) Wanda tai suna sosai a garin Kano.

Inda ya haɗu da sabeeterh kuwa, sun zo assibitin ne dubiya da maman tah tana dawowa, ta kasa zama ta kasa tsayi kulum, har tayi binci
Ken wanene? A kace Mata ɗan wannan hamshaƙin Mai kuɗi ne ALHAJI HASSAN SAUTA.

   Anan ta ƙuduri aniyar sai ta auri docta Ana haka  kulum saita je assibitin tun tana magana Yana korar tah, Yana Mata Wulakanci har da baya ya haqura, ya fara kulatah, harde maganar aure ta fito. Ake wannan ta'asar......

 

Wannan shine takaitaccen tarihim wannan ahalin...

Shin fatima zata gudu ace ta rasu?
Shin su husnah zasu aikata wani Abu ga fatima?
Shin didda zata bar Salim ya auri sabeeterh,?

To duk way'n Nan amso-shin suna gurin yr mutanen kebbi. Kudai ku dage da comment, share, da sharhi.

🥀Ta kuce ni✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & writing 📝
   By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
      (Samha Umar)🥀

This page 6 I dedicated to My sister yr'uwa rabin jiki NANA HADIZATU UMAR FARUK.

PAGE___6

Asalamu-Alaikum.

Wa'alaikk-salam Laila kece? Iso ciki.

Ƙara sowa bedroom ɗin Laila tayi bisa sofa ta zauna, kin tashi lpy Fatima ..?

   Lpy qalau Laila ya gida yasu umma.?

Alhamdullh.

Shawarar me kika yanke Laila.?

 Eh, nayi shawarar, Abin da ya kamatah yanzu dole zakiyi ma didda ƙaryan tafiya.

Tafiya kamar yah Laila?

          " Da farko Fatima Zaki cema didda zakiyi tafiya, wata ƙawar ki ce zatayi aure  in tace a Ina sai kice matah a jahar jigawa kuma don Allah ta barki kwona biyu kawai zakiyi, bayan ta amince nasan da driver zata haɗaki sai ku tafi kawai.

"Akwoi "wata ƴr uwar mu momy yayar umma a jigawa take mijinta ya rasu daga ita sai ƴr-ƴn tah 4 Ahmad, Salma, Hassana and hussaini."

Jiya na kirata na sanar da'ita komai hakan yasa ta Amin ce ki zauna gurin tah, inshallah sai kiyi shiri jibi al'hamis ki wuce domin nasan didda ba zata Hana ki bahhhhh...

      Ton naji Kuma nagode Laila kin taema keni Kuma na gode Allah ya saka Miki da Alkhairi, an jima zanje gurinta bayan sallar la'asar . Ngd Laila sosai.

Haba fatima meye Abin godiya bayan Kuma kin San ke babbar aminiya tah ce, ni tausayi ki Nike ji ba komai. 

Ni zan wuce gidah.

Toh Laila Ina gaida mutanen gidan gashi ko ruwa baki Sha.

Aa ba komai fatima Laila ta faɗa tana fitah ta wuce gidan su...

.ita Kam fatima bathroom ta shiga alwala tayi ta shimfiɗa salaya hijab tasa tayi Salam asir. 

    Tana kammalah wa ta shirya domin zuwa gidan didda, ta fito kenan ta Kira hajara yr aikintah,
    Hajara dama zan fita ne Kuma sai Isha zan dawo, so yasso idan kin gama aiki sai ki wuce gida kawai.
    
    Toh anty Allah yakai lpy.
    
    Amin.
    
Tana fita mota ta shiga  ta kama hanyar zuwa gidan ALHAJI HASSAN SAUTA.

Horn tayi gate man ya buɗe Mata ta shiga a parking space tayi parking, fitowa tayi , a hankali take tafiya ta'isa ƙofar main falo , Danna ƙara,-rawa tayi har so biyu, jin takon tafiyar har aka buɗe sofar, Mai aikin su didda ce har ƙasa ta duƙa ta gaida fatima, an sawa tayi tana mur-mushi .

Ƙara sawa tayi falon gidan cen ta hango didda zaune a kusa da'ita husnah ce.

Salamu-alaikum.

Wa'alaiki-salam didda ta faɗa tana ɗagowa , a maraba da daughter sannunki ya hanya, ta na rumgumo fatima jikintah, Bata tsaya komai ba  sai Jan hannun Fatima tayi zuwa sama.

Didda Ina Zaki? Husnah ta tambayeta cikin jin haushi.

Ina ruwan ki da inda zani, ko ajiye ni kinkayi eye.?, Bata ƙara cewa komai bah har suka haye sama, sai ɗakin didda tayi tana zaunar da fatima bisa bed.

Kina lafiya ƴrtah.?

Lpy ƙalau didda dama magana ce ta kawoni da Kuma neman watah alfarna.

Alfarma Kuma bintu?

Eh diddatah.

Toh inaji Allah yasa baifi ƙarfina bah.

Dama didda wata ƙawatah ce yr jigawa anan tayi karatu, kwonu kan baya babanta ya rasu sunan tah Salma, ban tae gaisuwa ba, yanzu kuma aurenta ya tashi, Kuma ban jiya da wuri-wuri ba shine nake son ki bari naje gobe al'hamis na dawo assabar , aurin auren jumma'a neh.

    Au dama kina da wata ƙawa bayan Laila? Har zaki'iya ɓoyema maman ki wani Abu bintu.?
    
    
Wlh didda ba haka bane don Allah kiyi haƙuri.

Toh na haqura Amma kin sanar da docta.

Aa

Saboda me?

Kin San Abin da ke faru kada yamin masifa.

To shikenan ni zan sanar dashi. Yau she Zaki ?

Ranar Al'hamis.

Amma kan yayi sauri.

To didda ya zanyi Amma idan kika ce kada naje, to bazanje bah..

Aa ƴrtah ki bari kawai kije mana Bari na sanar da salim.
Miƙomin wayatah gata cen a charge tashi tayi ta Ciro ta miƙo matah, karɓa tayi tare da kamo number docta tana shiga ya ɗaga Yana gaida tah , ansawa tayi tana cewa dama matarka ce ake auren ƙawartah a jigawa gashi gobe zata tafi...

Bata Ida ba yace Kai didda ta tafi Mana ya Ida Yana kashe Kiran, Yana jin haushin Kiran da didda ta masa, jiyayi Ana knocking ɗin office ɗin sa, come in , kawai yace, 

Buɗe ƙofar office ɗin Akayi  ta shigo tana tafiya kamar wacce Bata son tska ƙasa ,

Tun shigowar ta ya mata ya kauda Kai Yana jin haushin ganin tah, har ta Sarasota inda yake.

Good evening My honey heat,  sabeeterh ta faɗa a hankali.

Meya kawoki office ɗinah?

I'm sorry kwona biyu nayi missing Inka Kuma Kona Kira wayan ka baka peaking, shine na yanke shawarar zuwa na sameka, naji idan laifi na maka ka gafar ceni.

Ɗagowa yayi ya kalletah tare d furta bakimin komai ba, kawai na sanar dake mahaifiya tah Bata Aminta da auren mu ba, to ki kyaleni dole Saida ni zakiyi rayuwa?.

Eh, bazan iya rayuwa ba Saida kai... Bata idaba kawai ya fice daga office ɗin.

Wlh docta saina aure kah rubuta ka ajiye, itama fita tayi daga office ɗin tana jin baƙin cikin tafiyar da yayi ya bartah.

Ƴrtah kinji yanzu kije ki shirya gobe tunda safe zan aiko direban da zai kaiki, .

Toh diddah,

Tashi didda tayi ta buɗe bedside drawer, ta ɗauko rafar kuɗi ƴn dubu ta batah.

Wannan na minene didda?.

Ki ƙara kiyi guziri.............

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & writing 📝
  By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
       {Samha Umar}🥀

😍This page 7 I dedicated to my sister SARAT UMAR FARUK (husnah)😍

PAGE___7

Didda wlh da kin barshi inada.

Au bintu ada kinji nace bakida kuɗi? Dallah karɓah.

Ansa fatima tayi tana cewa didda ngd sosai, ni zan wuce.

   A'a ba yanzu ba ku bari kiyi sallar magriba kici abinci sai ki wuce, to kawai Fatima tace suka ci gaba da hira har akai kiran sallah.

Fatima ce ta fara yin sallar tana gamawa ta fito fallon didda ba kowa sai tv dake aiki zama tayi tana kallo.

Jin an kashe tv  ɗago kanta tayi domin ganin waye.

Husnah ce, ke Malama lpy Zaki kashe tv Ina kallo.?

Harara husnah ta watsa mata sannan tace  naga nan gidan mu ne, kuma tv idan naga dama na kashe damai hana ni na gani .?

Iya ɓacin rae ran fatima ya ɓace ta fara magana kamar haka , ke marar Mutun ci don tana ta gidan ku, eh ta gidan ku ce amma ba rasawa nayi bah.

Lah bintu ni Zaki zaga.?

 Ni bazan zage ki ba domin mahaifiyar ki tamkar uwa ta ce daddy ma uba ne a gareni.

toh wlh Fatima sai naga bayan ki don sai kin ƙare rayuwar ki a wulakan ceh..... Bata kulle bakin ta ba taji saukar zazzafan mari duka kunci biyu, ɗagowa husnah tayi domin ganin wani isasshen ne ya maretah.

 Idanun ta ne suka sauka cikin na didda, marina fa kikayi diddah ta'ida tana fashewa da kuka.

Eh, na mareki ko zaki rama ne? Marar Mutunci shasha-sha ..

Didda taja hannun Fatima zuwa dining domin yin dinner, bayan sun gama cin abincin ne Fatima ta wuce gidah.

★★★★★★★

Fatima kwona tayi tana shirya kayan tah a haka komai ya wakanah.

Safiya ta waye har tayi sallar asuba yaci gaba da shirya wa , ko abin ci batayi ba har tayi wanka.

Jin ana danna ƙara-rawa yasa Hajara da tazo aiki tun ɗazu zuwa duba waye, buɗewa tayi suka gaisa da Usman driver.

Yace don Allah ki cema Hajiya na'iso, to ta faɗa tana komawa ciki.

Hawa upstairs tayi sai room ɗin Fatima ƙon-ƙo sawa tayi.

Fatima wacce ke aikin shiryawa tace waye?

Hajara ce anty.

Shigo mana Fatima tace shigowa tayi har ƙasa ta duƙa ta ta gaida Fatima.

Ansawa Fatima tayi tana cewa har kin shigo Hajara.

Eh anty tun ɗazu dama dama Usman ne ya iso tun ɗazu yana jiran ki.

Okey kije kice masa gani nan fitowa amma fara fitarmin da kayanahhh...

     Fitowa tayi daga ɗakin ta jawo ƙofa domin tun ɗazu Hajara ta gama fitar mata da kaya, shiga ce ta Alfarma a jikin ta sai hijab da hand✋ bag ɗintah. Wayarta ta ɗauko a hand bag tayi Darling number Laila, Amma har ta tsinke ba'a ɗaga bah.

Mtwss tayi tsaki ƙofar falon ta fita har takai inda Usman yayi parking ɗin motar shi, duƙawa yayi ya gaida ta, amsawa tayi ya buɗe murfin motar ta shiga

Ɗago kanta tayi tun fitowar ta yake kallon tah ya dawo ne ɗaukan wani abu, ɗago kanta da tayi sukayi 4eyes da docta kallon juna suke kamar yau suka fara ganin juna, bata an kara ba saiji tayi motar har ta fita daga gidan.

A haka suka kama hanya sai taji wayarta na ringing kallon wayar tayi da har ta kusa yanke wa lailai ceh.

      Peaking tayi tana karawa a kunnen tah hello lailai kin tashi lpy.?

Lpy ƙalau Fatima kun taso.?

Eh mun taso lailai.

       Toh Allah ya tsare zan turo miki number momy sai tayi miki kotan Cen gidan ku.

   Toh lailai ngd sosai.

Ba godiya tsakanin mu Fatima Allah ya tsare hanya ya kai ku lafiya.

Amin Amin lailai Fatima ta faɗa tare da katse kiran.

Sauke wayar tayi daga kunnen tah, ajiyar zuciya tayi tana godiya ga Allah daya bata ƙawa kamar lailaih..........

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & writing 📝
  By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
      {Samha Umar}🥀

💅This page 8 dedicated to my kanwatah HAJARA FARUK BUNZA luv you sister 💅

*Masoya nah kuyi haƙuri na rashin jinah kwona biyu da bakuyi bah hakan ta faru ne da ɗan rashin lafiyar da nayi kuma ngd sosai da kaunah*

PAGE___8

Bismillah_Rahmani-Rahmin.

JIGAWA DUTSE

Sun'isa JIGAWA direba ya juyo ya kalletahh tare da chewa Hajiya sae inah•••?
  

  Chemasa tayi Ko itah ma bata sani ba saidai susamu Amusu kwatanche

       A bakin hanya direba yasamu wani ya musu kwatanche harsuka isoh, domin dama fateemerh takira mommy harsun gaesa taimata kwatanche 

   Fitowa tayi bayan sun iso tare da chewa direban yabari tashiga ta dawo.

 dan gidansu dan kyakkyawa, a pallo tayi sallama ɗagowa matar dake zaune bisa kujerar tayi tana kallon tah, har ƙasa Fatimah ta durƙusa ta gaida tah.

 amsa tayi tana mur-mushi Fatima Barka da zuwa harkun iso,  ƙara so mana xaunah. 

kitchen matar ta shiga ta kawo mata abin taɓawa .

uhm mommy xanje nacce da direban ya shigan mun da kayan.

 haka ne jekki fita tayi ta sanar da direban ya shigo da kaya kayan ya shigo dasu harya gama momy ce ta ce ya zauna yaci abinci sannan ya wuce amma yaqi a haka suka kyale shi yawuce.      

Abin Chi mommy ta kawowa Fatima sannan ta nuna mata daki tacce idan ragama taje Cen ta                           huta da Tom Fatima ta amsa mata fallo mommy tabar Mata ta wucce bedroom nata.

 Fatima ta kammala ta wucce ɗakin Da mommy ta nuna mata bayan tashiga bathroom tashiga ta watsa ruwa tare da sauri alwallah tapito tayi sallolin da ake bi ta 

   Mommy na dawo

   a harkin dawo Salamah?

 ehh wallahi kesan yau lecture d'aya garemu.

Madallah yanzu je kici abinci ki huta, sannan buƙuwar mu ta'iso.

Lah da gaske mommy.?

Zanmiki ƙarya? Tana cen ɗakin ki mah.

Aa , bazaki mini ƙarya bah, bari naje na gantah, fita tai daga ɗakin direct sai ɗakin tah ta wuce.

A hankali ta buɗe ƙofar ɗakin, da salama ta shiga Fatima wacce ke zaune a ƙasan cafet  tayi tagumi tana tunani.

Ansa salamar tayi tare da ɗago kanta.

Fatima brk da zuwa.

Barka dae Fatima tace.

Sunana Salma.

Ayya to sannu salma ykk?.

Lpy qalau Fatima wlh naji daɗin ganin ki kinga
Ni kaɗai ce mace sai hassanah.

Ayya haka ne Salma Nima naji daɗin haɗuwa dake.

Kinga yanzu na dawo daga school bari naje nayi wankah. Da tau kawai Fatima ta amsa.

Bayan salma ta fito daga wanka , shirya wa tayi cikin doguwar riga mai sharaf-Sharaf, taso muje fallo Fatima.

Tou Fatima ta faɗa tare da tashi a haka suka fito fallo, bayan Salma ta gama cin abinci domin Fatima cewa tayi ta ƙoshi zama sukayi suna fitah..

Salma yarinya kya-kyawa chocolate color bazata wuce sa'ar Fatima bah, suna cikin firar tasu hasnah da Hussaini suka shigo , dagudu suka faɗa jikin mommy dake fitowa daga ɗakin tah.

Kun dawo ƴn bintunah, to kuje Salma ta tuɓe muku kaya ta shirya ku.

Tasowa salma tayi bata tsaya komai ba ta kama hannun-su sai ɗakin tah, tuɓe su tayi tasa musu wasu kayan, fallo suka ta fito dasu, dining table ta kaisu abinci ta zuba musu.

Bayan sun kammala suka zauna fallo, salma ce tace Twins'ɗin mommy ga baƙuwa nan sunan tah anty Fatima.

Gaida ta suka yi , ta'ansa tana mur-mushi tare da tambayar su ya school.?

Ring wayarta dake hannunta ta fara, dubawa tayi taga ansa MY DIDDA peaking tayi cikin sanyin murya ta gaidatah.

     Amsa didda tayi tare da tambayar tah ya hanya.?

Hanya lpy ƙalau didda.

  Toh ƴrtah yanzu ki huta zuwa an jima zan kira ki.

Toh didda tah ngd.

Bkm bintunah ta kashe wayar.

Ajiyar zuciya Fatima ta sauke tana tunani'n halin da didda zata shiga idan aka ce mata ta rasu, amma Allah Ya sanya-ya mata zuciyar diddartah.

Ke Fatima tunanin me kikeyi? Salma ta tambayeta.?

Ba komai salma.
 
   Toh Fatima tashi mu shiga ciki muyi sallar magriba sai muyi dinner.

To fatima tace tare da tashi suka shiga bedroom bayan sunyi sallah sai suka fito domin cin abinci, koda suka fito suka tarra mommy na zaune tana fira ita da yaya Ahmad..

A yaya ka dawo amma yau kayi dare.

Eh wlh salma yau na tsaya yin aiki ne na marking takar dunku.

Okay Yaya sannu da aiki kaci abinci dae ko.?

Eh zauna mana kinyi tsaye.

'Fatima ce ta ce ina wuni, ansa yayi tare da duban mommy, mommy wannan ita ce Fatima.?

Eh, ita ce.

Ayya sannu Fatima .

Yawwa tace tare da zama kusa da salma, a haka suka ci gaba da zama ita Kam fatima daga uhm sai u-uhm sai kuma mur-mushi.

Shirin kwonciya sukayi sai Fatima ta tuna batayi ma laila adalci bah, fasa kwonciya tayi tare da jawo wayarta dake bisa bedside Dr  number Laila ta kamo ta kira.

Peaking Laila tayi tare da rangaɗa sallama.

Amsa Fatima tayi tare da cewa ƙawatah don Allah kiyi haƙ.....

Dakata laila ta faɗa  dama dai bakiyi niyya ba Fatima.

Wlh laila ba haka bane.

Ke wlh Fatima wasa nake ba komai fatan Dar kun isa lpy.

Harna tsoratah, hanya Alhamdullh.

To madallah yanzu ki kwonta ki huta gobe mayi magana, to Fatima tace tare da katse kiran.

Washe-Gari JUMMA'AT KAREEM tun safe su hassnah da Hussaini suka wuce makaranta, itama salma ta wuce domin suna da lecture 09:00 .

Zaune suke mommy na baiwa Fatima labari sai dariya take, a haka suka ji sallama.

A Hajiya haima sannu da zuwa ƙara so manah

Isowa tayi ta zauna tana wani harare-harare, Fatima ce ta gaidatah a daƙile ta amsa.

Mommy ce tace Fatima ta kawo mata ruwa.

Tashi tayi ta kawo mata tana aje wa ta wuce ɗaki.

Tana shiga waya ta ɗauka ta kira laila tana ɗauka tace laila meyasa baki kira ni ba.?

Wlh Fatima wani abu ne ya ɗauke min hankali.

Okey yanzu ina jinki.

Toh Fatima Kinga yanzu tunda ga yau kika cema didda za'a ɗaura aure gobe ki dawo, mommy za ki ba number tah.

Zan Kira mommy na mata bayani yanzu zuwa goben kiyi ƙoƙari kisa number didda a black list.

  Toh kawai Fatima tace ta yanke kiran, contact ta shiga number didda ta kamo tare da kira.

Peaking didda tayi tare da cewa ƴrtah kin tashi lpy? Ya kwonan baƙuntah.?

Lpy ƙalau diddatah ygd.?

Lpy gobe da saf-safe zan aiko driver ɗaukan ki.

A'a diddatah , basai kin aiko ba , zamu biyo matar Kano mu dawo don Allah kar ki damu kinji my diddatah.

Toh fatima tunda haka kika-ce ba komai sai goben. 

Toh Fatima tace tare da katse kiran.

★★★★★★★

Acen fallo kuwa ,

Lpy Hajiya halima na ganki da sassafe,.?

Lpy ba lau bah.

Toh me yake faruwa.?

Kinfi kowa sani ai, haba Hajiya halima da ace na sani ai hana tambaye ki bah.

Toh akan baƙuwar da kika kawo gidan nan ne.

Baƙuwa? Kadde kice min Fatima....

*Fans kuyi managing wannan Kuma ku tayani da addu'a inshaallah zuwa gobe zanyo muku typing da yawa*

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
   By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
      {Samha Umar}🥀

😍This page 9 I dedicated to my brother ABDULLAHI FARUK BUNZA yayanah mai halin kirki.😍

PAGE___9

Bismillah_Rahmanin-Rahim

Eh, ita Fatiman haba Hajiya karima yanzu saboda baki da hankali shine zaki kawo wadda baki sani ba cikin ƴrƴn ki? To nikam gaskiya Ni a matsayina na yayar marigayi (wato mijinta) ban lamun taba.

Dakata Hajiya halima mommy ta faɗa kar ki kawo min shirmen banza, ada baki nuna ke yayar marigayi bace sai yanzu,  to baki isa ba ki mulke ni bah koni ko ƴrƴr nahiyar.

Hakan kikace Hajiya Karima.?

Ba tare da shakkar komai ba mommy tace eh kiyi Abin da zakiyi.

   Cikin ɓacin rai Hajiya halima ta fita gidan ranta a matuƙar ɓacce.

Tashi mommy tayi tare da shiga ɗakin Salma, har yanzu Fatima nanan tayi tagumi sai tunani take.

Da fata mommy tayi tare da cewa Fatimah meya same ki?.

   "Mommy Ina tunanin yadda zan rabu da diddatah, Alh ina tunanin halin da zata shiga".

Ki wontar da hankalin ki, Kiyi haƙuri Fatima inshaallah wata rana zaki ga  RIBAR~HAQURIN da kika yi.

Toh mommy ngd SS.

  "Yanzu bani number diddah."

Toh fati ta faɗa tare da karɓan wayar mommy tasa Mata number diddah.

A haka mommy tayi saving.

Yau duk suku-ku Fatima ta wuni har ƴn makaranta suka dawo.

★*★*★*★*★
Yau ta kama ASSABAR bayan sun gama break fast , Fatima ce zaune a uwar-ɗaka kira ne ya shigo wayar tah, didda ce ɗauka tayi suka gaisa nan didda ke ce mata.

Bintu zuwa ƙarfe nawa zaku taso.?

Eh, didda sai zuwa an jima dai.

Toh bintu Allah ya maida ku lpy, ya tsare,.

Amin diddah sai mun iso Fatima na kashe wayar, tasa number diddah a black list Hawaye banin fuskanta.....

★*★*★*★

Laila ce ta kira  mommy tare da cewa karfe ɗaya su aiwatar da shirin su.

Toh mommy tace tare da katse kiran....

★*★*★*★

KARFE ƊAYA daidai a gogon Nigeria ya buga,
Didda ga wayar ki tun ɗazu ake kira husnah ta faɗa tana miƙa matah.

Karɓa didda tayi tare da yin peaking tana karawa a kunnen tah, Asalamu-Alaikum didda ta faɗa
A ɗaya bangaren taji ance, Wa'alaiki-salam don Allah Malama yanzu aka samu accident wurin fita dutse, kuma motar ma ta ƙone mun tsinci wayar ne a gurin da akayi hatsari, gashi babu Kari a wayar shine muka shiga Contact muka ɗauki number nah.......

Innalillahi wa'inna ilaihin raji'um kawai diddah ke faɗa , husnah ce dake tsaye take tana tambayar tah me yake faruwa.

Sai kawai taga ta faɗi da alamar bata motsi , da fata tayi tana kiran sunan ta cikin muryan kuka, didda ....daidai...did.

Daddy dake ɗaki ne ya fito kasan cewar yau weekend, fitowa yayi domin yaji kukan husnah.

Yana fitowa baiyi wata-wata ba ya ɗauko ruwa a frij ya yayyafa matah.

Ajiyar zuciya tayi tare da buɗe ida nuwan tah, husnah ce ta kama mata ta zaunar da'itah.

Daddy ne yace meya same kine haka..?

Alhaji wani mafarki nayi.

Mafarki kuma Hadiza.?

Eh, an Kirani a waya ne ake gayamin wai su bintu sun taso kuma sunyi hatsari, motar su ta ƙone gaba ɗaya, kuma na gode da Allah yasa ba gaskiya bane.

Ina wayar taki? Daddy ya tambaye tah, bata ce komai ba sai juye juyen da take, husnah ce tace daddy gata nan, tun lokacin dana kawo mata, an kira tana gama wayar ta faɗi.

Ansa daddy yayi number daya gani sama ya kira ɗauka akayi, ana cewa, Hajiya muna waya kin kashe, ku gafar cemu wlh har an tattara haɓin su an turbuɗe.

Innalillahi wa'inna ilaihin raji'um daddy ya faɗa husnah duk ta firgita.

Alhaji lpy didda ta faɗa tashin hankali ƙarara akan fuskanta.

Abinda kika ji ba ƙarya bane da gaske ne hadiza Fatima ta rasu har anyo tah.

Mutuwar zaune diddah tayi domin yanda taji zuciyar tah ta mata nauyi kamar dutse, faɗuwa tayi sune.

Husnah kuwa sai kuma take tana tunanin mugun nufinsu ga bintu.

Inna ce dake part ɗin ta ta fara juyi kukan husnah duk da cewa ba gani take sosai ba kuma ga matsalar kafa-fuwa , amma a haka ta taso har ta iso fallon.

A Hadiza me yake faruwa? Daddy ne ya Mata bayanin komai, mai aiki ce da husnah suka kama didda har suka Kaita cikin mota.

Daddy ne ke driving bai tsaya ko'ina ba sai A.P.H ba'a jira komai ba akayi emergency da didda har da Dr Salim a kamatah....

Fitowa yayi koda yaje office ɗin sa a cen ya iske daddy da husnah,  zama yayi tare da cewa husnah bamu wuri, ba musu ta fita.

Duban daddy yayi tare da cewa  Daddy meya Sami didda.?

Wlh Salim matar ka ce sukayi hatsarin mota kuma Allah ya Mata rasuwa, shine hankalin Hadiza ya tashi ta suma.

Innalillahi wa'inna ilaihin raji'um daddy shikenan didda ta kamu da ciwon zuciya.

Me kace Salim.?

Eh daddy .

To yanzu meye mafita?,  Daddy Dole sai ta samu hutu kuma aci gaba da bata kulawa ta musamman
   Kuma zan ɗora ta akan magani, yanzu an Kaita ɗakin hutu idan ta farka za'a iya jinyarta ta a gidah.

Toh daddy ya ce tare da fito zuwa dubo didda.

Husnah tana fita ta ciri wayar tah ta kira Jamila, tana ɗauka tace, jameey bintu ta rasu.....

Mee jameey ta faɗa tare da cewa amma dai na tayaki murnar husnah.

Murna kuma jameey.?

Eh mana husnah kinga kuɗin mu ma sun hutah.

Wlh jameey tun sadda naji hankali nah ya tashi, kuma jikina yayi sanyi, yanzu gamu ma a assibiti .

Assibiti.?

Eh, didda ba lpy.

Toh Allah ya sawwaka jameey ta faɗa tare da kashe kiran,  tana kashewa tayi Darling number sabeeterh.

Ring ɗaya ta ɗaga, hello Anty Sateey kin Tashi lpy.?

Lpy Jamila meya faru kike kiranah.?

Dama ashe bintu ta rasu.

Me, da gaske kike.?

Eh, wlh Anty, to kinci hoto, turomin account number ki.

Toh jameey ta faɗa tana katse kiran.....

★*★*★*★

Magana yaci gari anyi rasuwa gidan ALHAJI HASSAN SAUTA.  Kafin kace kwabo gida ya cika da mutane.

Didda sun dawo gida, zaune take ɗakunan tah ita da husnah, Laila ce ta shigo suna gaisawa, nan Laila ta wuni sai dare ta wuce gidah.

Ta kira Fatima ta ƙara bata haƙuri, salma ce ta shigo ɗakin tana ce da Fatima ta fito suje suci abinci.

      Fitowa sukayi su duka suka ci abinci .

Mommy ce ke magana da yaya Ahmad, 
Mommy gaskiya ya kamata tunda dama cen Fatima ta gama secondary mezai Hana a sama mata admission a inda nake lecturing  taci gaba bah.?

Toh Ahmad Amma kana ganin ba matsala.?

Eh mommy ba komai yafi ta zauna hakanan.

Shikenan zamuyi magana da'itah gobe in Allah yakai mu.

Toh mommy bari naje na kwanta sai da safe, fita yayi daga ɗakin, a fallo ya tarra dasu suna fira, salma ce tace yaya dama kana ciki, eh ina taya mommy fira.

Toh yaya kaga fa nima bacci nakeji, sai da safe ya faɗa yana wucewa.

Suma tashi sukayi tare da kashe kayan kallo.

A bedroom Fatima ta kasa bacci sai banda tunanin didda ba Abin da take sai kusan biyun dare bacci ya ɗauke ta...................

   🙏    Saimun haɗe a next page 😝

PLZ comment and share✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
   By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK      {Samha Umar}🥀

💔This page 10 dedicated to you MAMA AMARYA (Malama Ruqayyah) Ina sonki 💔

 

Bismillahi_Rahmanin-Rahim.

 _____acen gida kuma didda bata ci bata sha har gizo ma take ganin bintu na mata.
   (Ya Allah ka bamu ƙannen iyaye masu sonmu. Ina sonki mama Aminah ƴr ƙarama da halin manya👅)

Daƙyar ta samu bacci ya ɗauke tah,  waye War gari tun sa'adda didda tayi sallar asuba take zaune bisa daddumahhhh. 

Husnah ce ta shigo ɗakin da sallama, "didda don Allah kici abinci kiyi tawwakali ga Allah.

Husnah gani nake kamar ban riƙe amanar Amina bah.

    A'a wlh didda da ace za'a samu irin ki koda ɗari ne a duniya, to da duniya yayi kyau, don Allah didda kiyi haƙuri kici abinci.
    
    Daƙyar husnah ta lallaɓa didda taci abinci a safiyar.
    

★*★*★*★*★

Mommy ce tace salma ta kirawo mata Fatimah, kiran ta tayi, Mommy ce tace Fatimah kesan me yasa na kiraki..?

A'a Mommy dama sai kin faɗa.

Toh dama jiya nida ya'yan ku munyi shawara Muna so ki shiga makarantar gaba da secondary, shine muke neman amincewar kiii....

 Murmushi Fatimah tayi tana cewa kay gaskiya Mommy nayi farin-ciki da wannan taemako, thank you so much Mommy Allah ya biya..

A'a Fatimah ba komai, kuma Bama Ni zaki ma godiya ba yayan ki zakima.

Toh Mommy tashi tayi cikin farin-ciki ta shiga ɗakin salma.

Salma dake cikin shiri domin yau tana don ta fita, cikin farin-ciki Fatimah tace salma wai yau nice zan jona amma Mommy sun taimaka'n.

A'a Fatimah ai yiwa kaine , amma nayi farin-ciki marar misaltuwa, kuma wlh Fatimah yanzu kika fara ganin RIBAR~HAQURI yanzu muje kiyi ma yaya godiya........

Tashi sukayi suka nufo fallon anan suka tarrada  yaya Ahmad yana shirin fita.

Gaida sa sukayi sannan Fatimah ta fara masa godiya har da hawaye..

★*★*★*★*★

BAYAN TWO WEEKS

   Hadiza kinga yanzu kima nin sati biyu da rasuwar Bintu amma kin kasa kaƙura, Meta sa ba zaki baiwa Allah komai Bah, Ina Mai gaya miki wlh indai kika yi haƙuri to zakiga RIBAR~HAQURI .

Toh Alhaji zan ƙoƙartah.

Da yafi, sannan shekaran-jiya Salim yamin maganar auren sa da sabeeterh, shin kin amince yanzu..?

Alhaji Allah ya sanya Alkhairi.

Ameen Hajiya tah haka ne son ji daga gare ki, kinga yanzu bari inda tashi ina tafi , ina so naje wurin innah na dubotahh.

Ina gaida ta Alhaji, to zata ji.

★*★*★*★*★

Tafiya suke fitowar su daga lecture kenan.

  Fatimah tace hmm salma kinga yanzu duk na rage damuwa  , kinga kuma ina fahimtar karatu sosai.

Toh Fatimah Allah ya taimaka, yanzu muyi sauri mu duba idan yaya bai tafi gida ba sai ya wuce damu, suna cikin fitar Fatimah taji an kira sunan tah FATIMAH.

Juyowa tayi wacce ta kira ta ta ƙara so tare da faɗin tun fitowar ki nake kiran ki bakiji bahhhh.

 Eh wlh muna nan muna Suratu ne banji Bah.

Okay, dama na gama miki copying note Dana karɓa jiya ne.

 Wane kenan, Uses of English ta faɗa tana bata.

Amsa Fatimah tayi tana godiya haɗe da cewa amma ɗan tunamin sunan ki.

Meenal ta bata .

Ayya to kega mu wucewa zamu yi Fatimah ta faɗa tana murmushi. Sallama sukayi su Fatimah suka wuce office ɗin yaya Ahmad amma a kulle.

Salma ce ta dafe goshin ta tana cewa wasu yaya har ya tafi, Fatimah ce tace to ya zamu yi Banda mu fita ko zamu sami abin hawa.

A haka suka fito kamar daga sama Fatimah taji an kirata ko ba'a faɗa ba tasan waye Yaya Ahmad .

Juyowa tayi tana cewa yaya munyi fushi.

Fushi kuma toh kuyi haƙuri yanzu ku wuce mu tafi gida.

A haka suka shiga Mota basu tsaya ko'ina ba sai gida, suna fitowa a fallo suka tadda Mommy.

A ƴn makaranta har kun dawo.?

Eh Mommy.

Toh ku wuce ciki kuyi wanka sai ku fito kici abinci, to suka ce suka shiga ciki bayan sun fito fallo suka dawo suka ci abinci
   Suna kammala wa suka zauna nan suna kalli.

Fatimah ce tace salma bari na ɗauko mana handout muyi karatu kega gobe muna da text , to Fatimah ɗauko mana......

★*★*★*★*★
Wlh Ni nafi ƙarfin Hajiya karima taja dani wlh saina ɗauki mataki akan hakan, matar da tazo gidan Mommy shekaran jiya ke wannan maganar a ɗakin ta da ɗantah.

Ɗan dake gabanta babba ne domin a kallan zaikai shekara 40.

  Hajiya Ni banga laifin Mommy ba domin ba bisa kanmu wannan yarinyar zata zauna Bah to meye na damuwa, kuma tun rasuwar kawu bake kike kula dasu Bah...

Eh Hashim Amma dai duk da hakan inada iko akan ƴaƴan yayanah.

Kuma wlh indai Ni Hajiya halima ƴr hallak ce to sai Hajiya karima tayi nadamar ajiye wannan yarinyar a gidan tah.

Toh nidai ina mai gaya miki duk tsun tsun daya ja ruwa shi ruwa... Yana gama haɗar hakan ya fitahh.

★*★*★*★*★*★

Hadiza yanzu amsa ranar auren Salim Nan da one month anyi komai Lokaci kawai zamu jira.

 To Allah ya bada sa'a , Ameen , itakam didda tashi tayi ta fita daga ɗakin bata zame  ko'ina ba sai ɓangaren Inna tana shiga da sallama a bakin tahh...

Inna dake zaune ƙasan capet domin ita wai bata zama bisa kujerar.

Amsa sallamar didda tayi, gaida ta didda tayi cikin girmama wa , amsawa Inna tayi.

Inna ina so muyi magana in ba damuwa.?

Ba komai Hadiza ina jinki.

Wlh innah dauriya kawai nake, amma na kasa haƙura da auren da Salim zaiyi hankali na ya tashi matuƙa.

Haƙuri kawai zakiyi Hadiza.

Wlh inna duk salim ya auri sabeeterh indai nuna haifeshi to sai yayi nad... Dafe mata baki inna tayi.

Kull Hadiza kada ki kus kura kuwa ɗan ki baki kesan TSITSAN HORE YOFATA DANE ki masa addu'a kawai.

Toh innah Allah ya bamu mafi fi cin Alheri, Ameen inna tace, didda tashi tayi ta tafi...

★*★*★*★*★

Zaune suke a wani wurin shaƙatawa sabeeterh ce ta ɗago tana cewa khairat kega har yanzu bai ƙara so Bah.

   Ɗagowa khairat tayi tana cewa to ke meye naki tunda amsa muku rana, kamar kada ta rufe bakinta sai gashi ya faka motar sa.

Driver ne ya buɗe masa fitowa yayi cikin shiga ta kamala mai birgewa, iya kyawo yayi kyawo ya haɗu.

Cikin ƙasaita yake tafiya har ya ƙara so inda suke.

Murmushi ne ya bayyana a fuskar sabeeterh wlh harna fidda rai ga zuwan ka, Bismillah zaunah.

A'a ba sai na zauna ba ina sauri ina jinki, khairat ce ta gaida sa amsa yayi ita ko ta tashi tayi tafiyan tah.

Dama halan ka daina sona?, Naga Yanzu kwota-kwota ka daina nunamin soh meyasa.?

Ɗari idanun sa yayi ya kafe ta dasu kamar bazai yi magana ba, sai kuma yace .

  to ajiye aikina zanyi inzo na zauna dake kamar majnun.?

  A'a wlh ba haka nake nufi ba, kawai naga inba nina kiraka ba baka kiranah ka daina zuwa gidan mu meyasa my doctor.

 Okay, dama wannan ne to ina da aikin gaba na amma zan ƙo-ƙar ta koda duk bayan kwana biyu na kiraki. 

Two days fa .?

Ko yayi yawa ne...

A'a wlh , to Ni zan wuce nan yai mata sallama yay tafiyar sa abin sa.

★*★*★*★*★

THREE WEEKS LATER

Shirye shiryen biki ake yi domin yau saura 5days har ankai lefe na gani ga na faɗa anyi sadaki anyi komai.

Husnah da Jamila ne a fallo , jameey ce tace wlh kedai husnah naso ace wancan shegiyar nanan yaya zai anty Sateey da taga wulakan ci amma ko yanzu ba komai.

   Husnah dake riƙe da waya tana chart ta ɗago tana cewa.

Wlh nikam Jameey nayi nadamar abin da nayi a baya ma.

Keyi nadama fa husnah.?

Eh, Jameey ita ɗin ƴr uwa ta ce ta jina amma zuciya ta taƙi fahimta sheɗan ya ruɗeni kuma ina mai nadama, kuma wlh a halin yanzu koda ace bintu bata rasu ba a shirya nake dana nemi gafarar tah na bata haƙuri , domin muna nan zata ga RIBAR~HAQURI mu kuma mu taɓa a banza mun tashi 0 , Allah na tuba ASTGAFIRULLAH WA'A TUBU ILAIKA .

    "Ke husnah dakata baki isaba wlh da har zaki ce kinyi nadama.
    
Hmm Jameey kema Ina Mai baki shawarar ki tuba tun da saura lokaci,.

A haka suka ci gaba da sa'in sah..............

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
   By: 👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
    {Samha Umar}🥀
    
  
💝This page 11 dedicated to my sister UMMUL-KHULTUM FARUK BUNZA💝

PAGE___11

Bismillah_Rahmanin-Rahim.

_____suna cikin sa'in san ne sai anty zeenatu (ƴr anty zulai babba yayar Jamila) ta shigo da sallama, tana shigowa kowan nen su yayi shiru.

A me kuke haka ko faɗa kuke.?

      Husnah ce tace a'a wlh anty kesan Bama faɗa.
Toh me kuke.?

 Nan kan jameey ce tace fira, to Allah yasa ina diddah?, 

Tana ciki husnah ta bata amsa Sannan tace anty kawo Khalifa ( wato ɗan ta) kiwon chosa tayi tana miƙama husnah, amsa tayi tana cewa yanzu baza ki daina goyon sa ba kusan 3years garesa fah.

Toh ya zanyi yaron ne da son jiki ta ida maganar tana hayewa sama.

A hankali ta buɗe handle ɗin ƙofar didda da sallama a bakinta.

Didda dake zaune tana salati ta ɗago tare da amsa sallamar anty zeenatu.

Har ƙasa anty zulai ta duƙa tare da gaida didda, amsa didda tayi tana cewa tashi mana zeenatu, tashi tayi tana zama kusa da didda.

Ya mai gidanki.

Lpy ƙalau didda,.

Toh maddalah ina mai gidanah(Khalifa).?

 _"Ga shi cen fallo wurin mummyn sa Husnah."

Bari nasa a kawo miki abinci zeenatu, a'a didda a kwoshe nake, anan dai suka ɗan ci gaba da firahh.

  ******

A cen fallo kuwa zaune suke suna fira sai Khalifa dake rungume jikin husnah yana bacci (Ni Ko nace su jameey har an sauko)

★*★*★*★*★

A Fatimah salmah yau baku da lecture neh?.

  Eh, Mommy kega mu kusa fara Exam jibi next Monday.

Toh Allah ya bada sa'a ina twins ɗinah .?

Mommy Ina ga sun fita , salma ta bata amsa, to idan sun dawo ina neman su, to Mommy zamu gaya musu.

Salma ce tace Fatimah ina yaya Ahmad yau ban gansa ba duka, ya fita Fatimah ta bata amsa.

 Wai Fatimah me ma zamu fara.

Criminal law Fatimah ta bata amsa, 

Ringing wayar Fatimah ta fara tana dubawa taga sunan LAILA ne ɓarau ɓarau,  peaking tayi tare da karawa a kunnen tah.

Laila kin tashi lpy.?

Lpy Fatimah kp ya Mommy.?

Lpy ƙalau Laila ya diddatahhh.

Didda lpy lau take , kedai shekaran jiya nake jin lvrn wai ranar Saturday za'ayi auren ya docta .

Fatimah ce tayi sauri tace laila dawa, sabita.?

  Eh, Fatimah sabeeterh kawai addu'a zamu yi, kuma gobe zanje gidan diddah.

Toh laila ki dubamin lpyr ta da kyau.

★*★*★*★*★

Aure ya kam-kama yaune daren aure gidan ALHAJI HASSAN SAUTA ya cika da ƴn uwa da abokan arziki kowa sai hara Kar gaban sa yakeee.

Laila ce ta shigo fallon matan dake zaune har ƙasa ta ɗuƙa ta gaida su, amsawa sukayi cikin girma mawa.!

Aunty zulai ce ke saukowa daga upstairs gaida ta laila tayi amsa tayi tana cewa , "lpy qalau laila yagida ya ummanki.

Lpy anty ina didda.?

Tana cen part ɗin yaya, to laila tace ta dawo fallo ta zauna, bata fi minti 5 saiga didda ta shigo, laila ce ta tashi ta iskotahh.

Didda mun tashi lpy.?

A lpy ƙalau Laila ya hajiyar ku.?

Lpy ƙalau didda, Masha Allah isa ɗaki ki zauna, toh didda laila ta faɗa tana shigewa ɗakin.

Tana nan zaune sai ga Jamila ta shigo wai husnah take nema,  laila dake zaune bisa bed sai wasu mata da suka shigo yin Sallah, batanan laila ta gaya matah, bata ce komai ba ta fito nan tah haɗu da husnah.

★*★*★*★*★*★

Tun daga harabar gidan nake jin shewar su harna isa cikin gidan, mata ne zaune a fallo amma ba anan yayar take ba, ban tsaya ko'ina ba sai a bedroom ɗin sabeeterh.

   Ita da ƙawayen ta ne sai shir shirye suke Domin yau za'ayi kamu.

Khairat ce ta buɗe baki tace Sateey kuyi sauri time is going Kuma naga har yanzu gidan su docta ba wanda yazo.

Eh, haka ne sabita tace tare da cewa bari na kira my honey heat  naji lpy, tashi tayi daga kwoliyan da ake mata, wayar ta dake bisa bed kusa da ƙawar ta Abida .

  Abida miƙomin phone ɗinah, miƙa mata Abida tayi, Contact ta shiga number docta ta kamo tayi Darling , Saida ta kusa tsinke wa sannan ya ɗaga.

Brd da rana my honey heat.

Brk dae ya jama'a.?

Alhamdullh, dama naga har yanzu ba wanda yazo a cikin dangin kah yazo kamu Bah.

 Koh, ban sani ba bari na kira didda,.

To kaifa, kai kaɗai nake jira.?

Gaskiya bazan samu zuwaba.

Ba zaka zo Bah.?

Eh , kinga munyi oder na magun-gunna da kaya daga America Ina sa ran saukan su yau.

  Yanzu sun fi muhimmanci akai nah.?

Ba haka bane, bata ce komai ba ta kashe kiran,  tsaki kawai yayi tare da ci gaba da rubutun da yake a office, wayan sa ya ɗauko yayi Darling my didda Amma har ta katse ba'a ɗaga Bah.

★*★*★*★*★

Laila dake zaune taga wayan bisa mirror kira na biyu ya shigo ɗaukan wayan tayi taga amsa mu son, fita tayi sai fallon diddah.

Didda dake kitchen tana duba girkin da ake , a ƙofar fitowa tayi kiciɓis da laila.

   Didda ana kiran ki kega harma ya tsinke.

Ayya waye ke kira.?

Naga amsa my son, "to me Kuma salim ke nema,? jeki idan ya sake kira ki ɗauka, kafin laila tace wani abu tuni didda tayi gaba.

A haka ta koma bedroom, ko Kafin ta isa sabon kira ya shigo, ɗauka tayi ko Kafin tace komai aka ce.

   Didda Barka da rana, dama Sateey ce ta kirani tace har yanzu ba wanda yaje wurin kamu, shiru yayi domin jin abinda didda zata ce.

Cikin rawar murya laila ta fara magana "didda bata kusa amma zan gaya matah".

Mtwsss yaja tsaki tare da kashewa.

Didda ce ta shigo tare da cewa Mutanen dake zaune Hajiya sutura jeki ɗauko muku abin ci a fock.

Laila ce tace didda dama yaya docta ne yace wai har yanzu babu wanda yaje kamu.

Oh dama kega yanzu su Hajiya sutura suke da niyar suje, amma kuma zakije koh.?..

A'a didda aiki gareni gida kinga yanzu zan wuce.

Wucewa laila, eh didda umma na kiranah, to laila ina gida Hajiya, to laila tace tana ɗaukan jikanta da gyale ta ɗauka tare da wucewa.

Nan kuma mota biyu a cika zuwa gidan su sabeeterh kamu.

★*★*★*★*★*★

Fatimah ce ta kira laila domin jin lpyn diddan tah.

Lpy kau diddan ki kuma kega yaune kamu.

Ayya Allah ya bada sa'a.

Ameen laila ta faɗa.

Laila Ina son magana dake.

Ina jinki Fatimah.

Laila wlh Yaya Ahmad ne.

Yaya Ahmad yana sonki kohh.

 Eh, laila kusan hakan amma Ni ina dubin auren dake bisa kainah, wlh laila abu-buwa sun min yawa.

Toh shawarar me kika yanke.

Laila ke nake jira shawarar me kika bani.

Okey, ƙawa kawai kiyi accepting .

Ton laila nandai suka ɗan taɓa hira ta katse kiran, ɗakin Mommy ta nufa.

Mommy sannu da hutawa, 
Yawwa ƴrtah.
Mommy dama me za'a girka.?
Kawai ki girka mana tuwon semo da miyyar kuɓewa , to Mommy Fatimah ta faɗa tare da fita daga ɗakin.

Tana kitchen tana girki salma ta shigo tana kuka, fitowa Fatimah tayi tana cewa salma meyake faruwa.

Komai salma bata ce mata ba illa ina Mommy , tana ɗauki Fatimah ta bata amsa .

A tare suka shiga ɗakin jikin Mommy salma ta faɗa tana cewa Mommy twins ɗinki.
  Meya faru dasuh.?..

Hassanah ce ta faɗi amma yaya yayi asibiti  da itah.

Innalillahi wa'inna ilaihin raji'um wane assibitin.?

Genaral .

Bari nabi bayan sah.

Tashi salma tayi tana Kiran Mommy ta shirya.

BAYAN Mommy ta ɗauko hijabin tah  duban Mommy Fatimah tayi tare da cewa Mommy Allah ya sauwaƙa.

Amin Fatimah ki kula da gida sai mun dawo.

Toh Mommy tai musu rakiya, mota Mommy suka shiga sai assibitin , suna shiga basu sha wahala ba suka gano inda aka kwontar da hassanah.

Suna shiga ɗakin har amsa mata ruwa sai yayah Ahmad dake tsaye kusa garetah, a Mommy har kun iso...

 Eh, wlh ya jikin nata, jiki da sauƙi.
  Hussaini ne ya faɗa jikin Mommy Yana faɗin Mommy hasnatah.

Salma ce ta ju yoshi gabanta tare da cewa kayi haƙuri zata samu sauƙi.

Mommy ce ta dubi yaya Ahmad tare da tambayar me yake damuntah.?

Mommy wlh wai Asma ceh.

Asmah Innalillahi wa'inna ilaihin raji'um Wannan wace iriyar jarabawa ceh, toh Allah ya sawaƙe.

Ameen Mommy da sauƙi.  Anan sukayi sallar magriba bayan yaya Ahmad ya shigo Mommy tace ya tashi suje gida ta kan-kama Kayan ta domin anan zasu kwona.

Bayan su isa gida Mommy ce ya shigo fallon riƙe da hannun Hussaini.

Mommy sannu da zuwa ya mai jiki da salma .

Salma mu barota domin ta kula da hassanah har yanzu bata farfaɗo Bah.
  
Toh Mommy injin da sauqi jikinta, a da sauƙi.

Bayan Mommy ta kan-kama kayan da zasu buƙata ta ɗauko abinci suka koma assibitin, koda taje hassanah ta farka kuma drip ya ƙare.

Nandai yaya Ahmad da salma suka dawo gidah.

★*★*★*★*★*★

THE SATURDAY

Da misalin ƙarfe 11:00am duban mutane suka haɗu a babban masallacin dake GRA Ƴn siyasa likitochi ma'aikatan gwamnati dama manyan masu kuɗi suka shaida ɗaurin auren D.R SALIM HASSAN SAUTA da amarya SABITA IBRAHIM  bayan an gama wa jama'a Barka aka watse.

Zaune yake a ɓangaren sa shi da abokan sa, babban abokin sa mai suna ABDUL-HAKEEM  a jiya ya iso daga ƙasar waje ( koh auren docta da Fatimah baima da labari) 

Docta dama Ina son naje jigawa a wannan satin amso takarduna domin tacen zasu fito.

Murmushi docta yayi yana cewa ai na zata dai kace yau.. bai ida maganar ba kiran Sateey ya shigo wayar sa peaking yayi Yana karawa a kunnen sah.

  Cewa tayi Assalamu alaikum Amincin Allah da yardar sa su ƙara tabbata ga kya-kyawan mijinah.

Tare dake Amarya tah ,,,,,

Hmm kaga ƙarfe shidda ne za'a gabatar da dinner zaka zo kan dai.

Sosai ma dole kodon na faran ta miki.

Toh yayi sai mun haɗu.

06:00pm a wani babban hotel 🏨 da za'a gabatar da dinner an ƙawata wurin iya kyawo wurin ya haɗu da gani kasan nera tayi kuka kamar ta mutu.........

________Toh fans Ina Mai baku haƙuri kan rashin jina da bakwoyi akan lokaci zan gyara inshaallah.

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

  Story & writing 📝
  By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
      {Samha Umar}🥀

💞This page 12 dedicated to my sister SADIYYA FARUK BUNZA💞

PAGE___12

Bismillahi_Rahmanin-Rahimi.

   Hall ɗin cike yake da ƴn uwa da abokan arziki amarya da ango kaɗai ake jirah.

A harabar hotel ɗin motoci naji da gani suka faka kamar guda uku a hankali mutanen dake ciki suka fara fitowa.

Saida yakai mintuna5 da driver ya buɗe masa mota kafin ya fito.

Wow na furta lokacin da nayi tozali da kya-kyawar fuskar sa haɗa-ɗun tufafi ne a jikin sa sai sa takalma masu kyau ƴn ƙasar Turkiyya baƙaƙe, sai wani agogon diamond dake saƙale a tsintsiyar hannunsa.

Jin an kira sunan sa ya sasa juyowa wazai gani sabeeterh itama tayi kyau yadin langada ne tasa ɗinkin doguwar riga white and black, taci wani ɗaurin ɗan kwoli kudai abin sai wanda ya gani....

Dear mushiga ciki mana, nan suka shiga cikin hall ɗin tafi kowa ya ɗauka ganin shigowar amarya da ango.

   Anan m.c ya kira Shaikh Abdulkarim Ha'iri ya buɗe musu taro da addu'a, bayan haka aka ci gaba da shagali , mawaƙin da aka gayyata wato hamisu breaker domin nisha ɗan tarwa , fitowa yayi ya fara rera waƙa.

  Bayan amarya da ango sun nuna jin daɗin su sannan m.c ya buƙaci amarya da ango su fito su taka rawa.

Saida ya ɓata lokaci sannan ya fito , ya fara takawa kenan wayar sa ta fara Ring  Domin dama kiran da yake jira kenan.

Fita daga hall ɗin yayi yana fitowa yayi peaking, tare da karawa a kunnen sa.

Acen ɓangaren aka ce Hello mai sir kayan sun iso amma mun fito ta Niger ne mun kusa isowa nan da 20 minutes.

Ton Kabir yanzu nan nima mu haɗu a asibiti .

Toh sir tare da kashe kiran.

Baiyi wata-wata ba ya shiga mota ya sa mata wuta baifi 10 minutes ba ya'isa assibitin , da isar sa zuwa 5 to 6 minutes ba saiga wata mota Bus fara kya-kyawa .

Cikin karewa driver yayi parking a qatuwar harabar assibitin, fitowa mutun biyu sukayi daga motar gaisawa sukayi , yana gaba suna baya suka shiga assibitin
  suka hau upstairs  mutane na gaida shi, hannu kawai yake ɗaga musu  bai tsaya ko'ina ba sai office ɗinsa, Wanda saman ta  akayi rubutu da manyan harufa D.R SALIM .

  Yana isa p.a ta gaida sa ta buɗe masa kofa  shiga , Masha Allah sai wani irin kanshi da wata iriyar ni'ima ke tashi a office ɗin, a lallausar kujerar sa ya zauna, tare da musu nuni da hannu alamar su zauna.

Wani file ya ɗauko tare da sa hannu ya miƙo musu, amsa sukayi suna murmushi, telephone ya jayo yayi danne danne yana karawa a kunnen sa, tare da cewa come.

Buɗe ƙofar office ɗin akayi p.a ce ta shigo , nuni ya mata da da waƴn da ke zaune faɗi tayi okey.

Juyowa tayi ta kalli mutanen tana cewa let's go, ba musu suka bitahhhh.

Idonsa yakai kan agogon dake hannun sa 07:4pm zabura yayi tare da fita.

Motar sa ya shiga yana shiga kira na shigowa wayar sa domin dama a mota ya barta koda ya duba ABDUL HAKEEM ne.

★*★*★*★*★*★

ƁANGAREN AMARYA

Koda aka duba babu ango sama ko ƙasa hakan yasa hankalin sateey tashi number sa ta kira amma har 17 missed call baiyi peaking ba .

Abdul Hakeem ne ya kira zuwa yayi ya same ta tare da faɗin me yake faruwa.

Cikin murya kamar zata yi kuka ta sanar dashi halin da ake ciki, lallashin ta yayi sannan yace tayi a hankali kada jama'a su fahimta.

A haka har aka watse Allah yasa ba wanda ya fahimta sai khairat data sanar mah.

★*★*★*★*★

ANGO SALIM 

Yana ɗaga wayan Abdul Hakim yayi sauri yace haba docta me yasa zaka yi haka.?

Kai ya'isa docta ya faɗa.

Abdul Hakim ne yace oh, hakama zakace kako san halin da sateey ta shiga Please ka kirata Ni da su abu-sifiyan muna jiran ka a gida. 

Okey docta ya faɗa yana kashe kiran ganin missed call ɗin ta yasa yaji tausayin ta amma bai kira taba yaja motar sa.

Bai tsaya ko'ina ba sai a tamgamemen gidan su horn yayi gateman yayi sauri ya buɗe masa , yana shiga Sai parking lot yayi parking motar sa.

Ɓude motar yayi ya fito bai tsaya ko'ina ba sai ƙofar da zata sada shi da main Fallon Gidan saida ya danna ƙara-rawa sannan ya murɗa handle ɗin ya shiga.

Mutane kaɗan suka rage a fallon gaida su yayi ya haura sama sai sashen didda bedroom ɗin ta ya shi ga mutane ne zaune harda anty zulai da umman lailahhhh.

Gaidau yayi suka amsa ya dubi anty zulai yace, anty ina didda.?

Tana cen bathroom ta basa amsa.

Okey, yace yana fita sai ɓangaren sa yana shiga fallon duk abokan sa ne , nan suka fara mitan ya shanya su.

Haƙuri ya fara basu tare da shigewa bedroom, mutane biyu ne kawai bai tsaya jin me zasu faɗa ba , toilet ya shiga Domin ɗauro alwala , yana fitowa suna magana amma bai saura-resu bahhhh..

Prayer mat dake bisa Center drower ya ɗauko tare da shimfida wa ya fara gabatar da Sallah.

★*★*★*★*★

JIGAWA DUTSE

Zaune suke a fallon mommy ce sai Fatima da salma, sai hassanah dake kiwon ce bisa kafaɗar mommy, Fatima da salma duk karatu suke domin exam ta kusa.

Yayah Ahmad ne ya shigo ɗauke da sallama  amsa sukayi.

Mommy ina wuni.

Lpy ƙalau Ahmad ka samo magun-gunam.? (Domin an salla mosu daga assibitin.

Eh, mommy ya faɗa tare da miƙa mata ladar dake hannun sa, gaida sa sukayi ya amsa cikin girma-mawa...

★*★*★*★*★

Gidan sa dake ɗora yi sabon gini yayi ba wanncen gidan da Fatima ta zaunaba.

Haya niya ke tashi domin dare yayi a ƙallan 11 na dare tayi , ƴn kawo amarya sateey ne.

An kawo amarya anyi raha tsakanin abokan ango da na amarya, sannan kowa ya tafi aka bar ango da amarya..........

WACECE SABEETERH.?

Bari na baku takai taccen labarin sabitah,  ALHAJI MUGU shine sunan mahaifin tab  akan kwore watae wurin safarar miyagun kwayoyi daga Afrika ta yamma dama sauran ƙasashen duniya zuwa ƙasar mu.

Ya auri matar sa Sumayyah ƴr asalin jahar Katsina sunanan zaune a Katsina domin a wannan lokacin a jahar ya yada zango..

Anan ta samu juna biyu cikin ya dinga wahalar da ita yau da gobe sai Allah cikin ya shiga watan haihuwa, wata rana ne ta tashi da ciwon naƙuda tun safe har ta wuni,.

Saida Alhaji ya dawo ya tarar da ita a wannan halin baiyi wata wata ba ya ɗauke ta zuwa assibiti...

A labour room Akayi da'ita sai wajen ƙarfe 8 na dare ta haihu inda ta samu ƴr mace sak itah babu Abin da ya raba su.

Bayan kikitawa sun sanar da Alhaji MUGU  ta haihu ta samu ƴr har da sujjada yayi akan farin ciki wance ko sallah baya yi akan lokaci.

Shiga ɗakin yayi annurin dake fuskar sa ne ya ɗauke domin ganin mummunan halin da matarsa ke ciki.

Nus ce ta shigo da sauri ta koma suka kira likita, bayan zuwan likita ya fara aunata ganin numfashin ta na batun ɗauke wa yasa suka saka mata oxegen ............

PLZ comment and share✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing📝
  By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
    {Samha Umar}🥀
    

💖 This page 13 special gift to King of my heart, ƙauwatah my happiness ina sonki fiye da rayuwa tahhhhh💖💘💗

Da
PAGE____13

Bismillahi_Rahmanin-Rahim.

   Likitawa sun duƙufa kanta domin tuni sun kori Alhaji mugu ya fitahh.

Sai cen numfashin ta ya dawo, cikin murya mai wahala domin daga jinta kasan mutun saide abin da ya fito ga Ubangiji cewa tayi Please Dr ku kiramin Alhaji.

Ba musu suka kirasa bayan shigowar sa ta kama hannunsa tare da cewa , Alhaji ga jinji rata amana kuma ka yafemin ka nema min gafara ga sauran ƴn uwan mu, nan take ta cika da Kalumatul-Shahadah .

Nan Alhaji mugu yayta kuka inda aka ɗauki gawarta zuwa gida suna isa gida har ƴn uwa sun fara halarta domin tun a asibiti mugu ya sanar da ƴn uwa , nan aka sutur ta Sumayyah sai gidan gaskiya.

Akwona a tashi yau sati ɗaya ƴr taci suna Sabeeterh ana haka sai ɗaya daga cikin ƴn uwan marigayiya mai suna hannatu a Kano take zaune ta ɗauki Sabeeterh ta riƙa daƙyar da balai da masifa Alhaji mugu ya yarda.

Tun daga ranar hannatu da mijinta Ibrahim suka riƙe Sabeeterh babu wanda zai ce ba ƴr su nace.

Ana haka aka kama Alhaji mugu amma ga banza domin wannan ba shine na farko bah.

Har yau bai sake aure ba saide yana zuwa duba ƴrsa har gida ya gina a Kano inda yake sauka idan yazo duba ƴrsah shi da yaran sah.

  TO Wannan shi ne takaitaccen tarihin Sabeeterh.

★*★*★*★*★*★

Hajiya halima ce zaune a ƙayatat cen falon ta tana shan coffee wayarta ce ta fara ring ɗauka tayi tana cewa..

Mugu saikai ka buwayi hukuma da maƙiya .

Acen yayi dariya yana cewa Hajiya halima ya ake ciki ne, maganar Fatima ya kinkayi da matar yayanki,? Tunda kinga yanzu har anyi auren ƴrtah Sabeeterh shine nake so kiyi saurin kawar min da'ita.

 numfasa wa tayi tare da cewa Alhaji ina nan ina ƙoƙar tawa yauma nake son naje gidan ita Hajiya karima (mommy) domin ɗaya daga cikin ƴaƴanta ne Hassanah ba lpy.

To yayi ƴr çhaɓule sai naji daga gare ki ya kashe kiran.

★*★*★*★*★*★

A hankali ya buɗe ƙofar ɗakin shiga yayi tare da maido ta ya rufe.

har bakin bed yaisa a hankali ya yaye blanket data luluɓa dashi, rigar bacci ce a jikin ta sai kanta dako kallabi Babu gashin ta duk ya baje, hannunsa ya aza bisa nata yana jijjigata my sateey Sai cen ta ɗago kanta tana murza ido tayi kicin-kicin da fuska tana cewa wai don Allah ya kake so nayi da rayuwa tahhhhh.

Duban ta yayi tare da fara magana tun ɗazu baki gana da Ubangijin ki ba nayi taddaki amma har tara tayi .

Nace maka zanyi sallah .

         Toh tashi kije, muje na rakaki a hankali ya tashe ta  suka shiga bathroom.

.Akwona a tashi babu wuya a gurin Allah  yau sati biyu kenan da auren salim da Sabeeterh.

A kullum sabita saide hasiya mai aikin ta ke mata komai harda girki domin ba iyawa tayi ba, shi ko docta in akwoi Abin da ya tsana shine Abin cin ƴn aiki, saide kullum yaje gida ko restaurant ya ciyo abinci.

Kamar kullum zaune take bisa ɗaya daga cikin kujerun dake fallon ta tana chart , docta ne ya fito daga bedroom tashi tayi da sauri tasha gaban shi my honey dama inama magana ina son naje gidan mu amma ka kyaleni.

  Duban ta yayi tare da cewa haba my sateey anma dai kinsai bai kamata ba koh yau satin ki biyu a gidan nan.

cikin marai-recewa tace dan Allah dan Allah,.

Okey Bari idan nayi zuhur prayer sai nakaiki.

No problem my honey thank you so much.

Murmushi yayi yana cewa don't worry I'm your forever.

Wucewa yayi ita ko sabita dariya tayi tare da ayyana wa a ranta cewa haƙarta ta kusa cimma ruwa.

Zama tayi jin ana Sallama ya sata , shigowa wacce  tayi sallama tayi tare da cewa maraba da anty zul........

PLZ comment and share✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝

  By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
  {Samha Umar} 🥀

💔This 14 dedicated to my brother MUHAMMAD FARUK BUNZA💔

PAGE___14

  Maraba da zulaihatu yau keche a gidan namu.

Eh wlh, to zauna sabita ta faɗa.

Tana zama ta sara lalle lalle da wani merane baki.

Tabbas sabeeterh ta lura da hakan kuma taji haushi amma sai ta kyalle.

ina shi maigidan naki anty zulai ta faɗa ba tare da tunanin komai bahh.

 sabeeterh tace futawa yake yi zaki iya tafiya.

Juyawa anty zulai tayi tare da duban sabita tana cewa ohw nikike ma magana haka lallai ƴrnan.

Hararan ta sateey tayi tana cewa nayi tunda ga mahaifiya tah dole kimin na kyalle, to bari kiji Ni Ko mahaifiyar sa bata isa ta gayamin ba daidai ba balle ke gayyar soɗi gayyar tsiya.

 Tashi tsaye anty zulai tayi itama sateey tashi tayi, anty zulai ce tacce to baki isa ba domin 
koshi wanda ajiye ki bazai gayamin hakaba balle ke ko uwa......

Maganar ce ta maƙale sakamakon jin saukar mari 😯 a kuncin tah, sabeeterh ce ta cije lips cikin mafisa yace kada ki ƙara ambatar uwatah, domin ita ba shasha-sha bace irinki nonsense, mtwsss taja tsaki.

A ɗaku jin hayaniya yasa docta fitowa , jin takon sa yasa ta fasa wata razana biyar ƙara tare da kuka hakan yasa shi hanzar tawa ganin sateey kwonce a ƙasa dafe da ciki sai kuka take, ga kuma anty zulai dafe da kunci sake da baki kuma.

"A hankali ya tallafo sateey tare da cewa sateey Meya sameki,? Duban anty zulai yayi ganin sateey na nuna ta da yatsa bai firgita ba saida yaga tesle a hannun anty zulai."

Sateey what she do for you, please talk to me, say something duk a kiɗime yake waƴnnan magan ganu.

Cikin ranta tace , this is my opportunitie I have temporary time let me help my self and my daddy to use that first opportunity,  duk a cikin zuciyar ta take wannan zancen,. 
  

A fili kuwa cewa sateey tayi kaga honey  wai kawai don tazo na kawo mata ruwa sai tace in akwoi Abinci na kawo mata, sai nace a'a wlh yau hasiya bata zo ba , sai kawai ta fara masifa ina bata haƙuri banyi aune ba ta cika min tesle a ciki da duniya ta rinƙa juyi dani saida na jiyo kamshin mutuwa badom....sai kuma tayi shiru tana tsanan ta kukan tahhhhh

  Jawota jikin sa yayi yana duban anty wacce tayi zuru-zuru da idoh ( wlh nidai nace gwoi anty zulai dama ƙarshen alewa ƙasa.)

  Haba anty dama zuwa kika yi domin ki takura mata metayiki.?

Cewa anty zulai tayi wlh salim ba haka bane... Bata Ida faɗan me zata faɗa ba yaja hannun matarsa suka hau stairs, suna shiga ɗaki bisa gado ya zaunar da ita shima ya zauna.

     Duban ta yayi sannan yace kiyi haƙuri da abin da anty tayi miki.

Hannayen sa ta kama tare da cewa bakomai ya wuce ai.

Toh docta yace sannan yace je ki shirya kazo mu wuce ya ida tare da fita daga ɗakin, koda ya fito fallo ba anty zulai , a haka aiki shirya suka fito.

Shine ke driving suna isa ƙofar gidan su sateey dake ƙofar wambai parking yayi fitowa yayi shi ko yace ta shiga zaije ya dawo sai su wuce gidan su..

Tana shiga fallon gidan su mama dake tsaye da alama fita zata yi.

A ke sabeeterh sai yanzu kika samu damar tahowa tun ɗazu ina jiran ki amma shiru harma zan wuce.

Oh Mama yi haƙuri wlh wani abin murna na aikata.

Me kika aikata.?

Nan ta kwoshe labarin tsakanin ta da anty zulai ta gayama mamah, duban ta mama tayi tare da faɗin keyi daidai amma kesan meh.

Aa my mama sai kin faɗa.

Toh yanzu Kafin ku wuce gida ba sai kun biya cen gidan su shi mijin ki ba.

Eh mamah.

To idan kika je ki bawa iya yensa haƙuri akan abinda ita zulai tayi miki.

Toh Mama yanzu ina baban.?
Yana aiki .

Kega sai muje cen inda mahaifin ki ya sauka, to sateey tace suka fitahh.

Mama hannatu ke driving Basu tsaya ko'ina ba  sai ƙarshen layi kusa ga ƙofar wani babban gida tayi parking.

Fitowa sukayi a fallon gidan suka yada zango inda mama ta fito da wayar ta ta kira tace mun iso ta kashe.

Saukowa yake daga upstairs har ya iso inda suke zaune,  sateey ce race abbanah ina kwona.

Lpy ƴr ɗaya tamkar da dubu, duban mama hannatu yayi yana cewa bamu wuri zamu yi magana da ƴrtah.

Tashi tayi ta fitah.

Ƴrta dama ina so na sanar dake Fatima bata mutu ba tana nan raye.

Na shiga uku abbanah , Abba kenan burina bazai taɓa cika bah.?

Aa ƴrtah ki barta kawai Yanzu akwai wata Hajiya halima to gidan yayan ta Fatima take zaune, to Kinga ba'a rasa yanda za'ayi ba.

Kuma ina so ki kammala aikin ki cikin sauƙin.

Toh Abba yanzu zanyi yadda kace, bari naje gida kuma gwogon docta na mata sharri, nan ta kwoshe labarin komai ta gaya wa abban tah..

Dariya yayi yana cewa kinyi daide ƴrta, amma yanzu abinda nake so shine kije har gidan ta ki bata haƙuri.

Toh Abba bari mu wuce.

Waya ya ciro ya kira mama, mama wacce ke laɓe tana recording tayi saving , sannan ta ɗauki Kiran Abba , Zaki iya shigowa.

Shiga ciki tayi, to hannatu ngd da kulawar da kike bawa ƴartah.

Murmushi tayi tana cewa ba komai ai nona ƴrta ceh...

Tashi sukayi suka fita basu tsaya ko'ina ba sai a mota gidan mama suka koma domin kar docta yazo ya tarar bata nan.

Suna zaune fallo wayar sateey tayi ring tana ɗauka yace ki fito zamu wuce.

Mama ya'iso zamu wuce..

Toh baki manta komai ba de.
Eh, Mama na wuce.
Toh sai munyi waya.

Tana fitowa ta shiga mota yaja sai gidan ALHAJI HASSAN SAUTA parking yayi, ya dube ta kije ciki ina zuwa.

Buɗe murfin motar tayi ta fita bata tsaya ko'ina ba sai a ƙofar fallo, danna ƙara-rawa tayi, bayan ƴn seconds sai taji an buɗe, husnah ce ta buɗehh.

A anty kece.

Murmushi yaqe tayi sannan tace nice husnah, suka ƙara sa fallo.

Zama sateey tayi ta dubi husnah ina diddah.?

Didda suna falon Daddy ita da shi da anty zulai.

Bayan 5minuits sai ga diddah, tasowa sateey tayi har ƙasa ta duƙa cikin ladabi da biyayya ta gaida diddah.

Amsa didda tayi babu yabo babu fallasa.

Sateey tace didda dama ina son magana dake.

Toh inaji.

Dama akan wata magana ce jiyya........

PLZ comment and share

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
  By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
      {Samha Umar}🥀

This page 15 dedicated to my aunty HUSAINA UMAR FARUK (Ummu Hafsah)👌

PAGE___15

Bismillah_Rahmani-Rahim.

   __akan wata magana ce, ɗazu ne anty taje gidan mu, nan ta kwashe duk yanda ta gayawa docta ta faɗa ma didda.

 Juyowa didda tayi tare da faɗin, sabita ni bansoh ɗana ya aure kiba, yana zaune lpy da matarsa ya ja jabowa kansa auren ki, na haneshi yaƙi Alhaji da Zulai suka mara masa baya, babu yanda na'iya , har Allah ya ɗauki rayuwar ƴrtahh didda nakai sai kawai ga hawaye, hannu tasa ta share hawaye sannan taci gaba.

Toh ya aure ki amma Ni ban taɓa ɗaukan ki a matsayin surka ba, kuma su suje swo gani tana kaiwa nan ta tashi tayi tafiyar tab.

Iya haushi sateey taji haushi kawai danne wa tayi,.

Docta ne ya shigo didda yaje ya gaida bayan sateey ta gayawa masa ai sun gaisa.

Yana fitowa suka wuce part ɗin daddy Domin weekend ne yana nan , suna shiga suka gaida su domin shi da anty Zulai ne.

Sateey ce ta dubi anty Zulai saida ta harare ta ta yanda ba mai gani sannan ta ce don Allah anty kiyi haƙuri da abin da ya faru ɗazu, ƙala anty Zulai bata ce bah.

Daddy ne yace ba komai ku tashi, kuyi tafiyar ku tashi sukayi suka fito saida suka biya sukayi sallama da didda sannan suka wuce gidah.

daddy ne yace anty Zulai tayi haquri ya lallaɓa ta itama ta wuce gidah, domin ta sanar da shi komai.

★*★*★*★*★*★

*JIGAWA DUTSE*

Fitowa sukay baƙar riga ce abaya sai white hijab sunyi kyau Masha Allah kwo wannen su riƙe da handout, Fatima da salma kenan mommy tace a ƴaƴanah har zaku wuce.

Fatima ce tace eh wlh Mommy , kudai taya mu addu'a yau zamu fara exam.

Toh Allah ya baku Sa'a, tana cikin addu'ar yaya Ahmad ya shigo gaida sa sukayi.

Amsa yayi yana cewa a har kun shirya.

Mommy ce tace eh mana , kai kaɗai suke jira ka kaisu school 🏫.

aini mommy bazanje ba Amma bari na kaisu na dawo , ya faɗa yana wuce , mara masa baya sukayi bayan sunce Mommy sai mun dawo.

Suna fitowa suka shiga Mota ya jasu sai school, nan suka fito bayan sunyi sallama da shi.

Cikin makarantar suka nufa , suna cikin tpy ,sai ga meenal , gaisawa sukayi sannan suka jera, domin tuni sun zama ƙawaye ita da bintun'diddah.

Har aji suka je suka ci gaba da karatu kafin a shigo musu,.

Bayan sun fito daga exam Domin tayi zafi sosai, salma ce ta kira musu yaya Ahmad yazo ya ɗauke su.

★*★*★*★*★

AFTER ONE MONTH

Ikon Allah Fatimah sun ƙare exam, sai hutu, zaune a fallo Fatimah sai salma da Mommy and twins.

Salma dama anjima zan aike ki gidan Maman ku SARATU (ƙawar tah).

Toh Mommy zamu je da Fatimah.

A'a kije ke kaɗai ko hasnah ta rakaki.

Toh  kawai salma tace duk da bata ji daɗin hana Fatimah zuwa da Mommy tayi bah.

★*★*★*★*★

KANON DABO

Ta kasa zaune ta kasa tsaye sabeeterh kenan, wayar ta ta ɗauko tare da danna kiran khairat, .

Ɗagawa tayi tana cewa sateey lpy.?

 Ba lpy khairat kizo gida na yanzu akwai matsala.

Toh khairat tace ta kashe kiran.

Ba'a fi kamar 25 minutes ba sai ga khairat ta iso .

Lpy sateey khairat ta tambaye ta cikin tsoro.

Ina ko lpy ni da nazo ɗaukan fansa na ƙare da wahala , wai ciki ne dani , amma kesan me khairat kawai zubar dashi zanyi.

Baki da hankali sateey da zaki zubar da ciki You no it's harram.

Keh khairat ni dama nasan ke ustaziyya ce amma ki aje ustazan ci gefe domin Ni nayi nisa bana jin kira, idan har kika ga ban zubar da cikin ba wlh sai in gawata ce zata haife shi.

Da khairat taga tabbas sateey tayi nisa bata jin kira , tayi mata sallama sannu alaikum tayi tafiyar tah.

★*★*★*★*★*★

Shirya tayi tsaf cikin atamfa mai ruwan toka ɗinkin riga da skirt duk sun matse ta, skirt ɗin daga bakin gwuiwa har ƙasa an tsage shi , irin ɗinkin nan mai suna (akwora) ,  wani siri-rin mayafi white , dashi da babu duk ɗaya ta yafa a kafa ɗarta.

Fitowa tayi sai parking lot mota ta shiga direct sai DAWAKI HOSPITAL , tana zuwa sai office ɗin D.R HAMZA , gaida sa tayi ya amsa yana nuna mata gurin zama.

Bayan ta zauna ta fuskanci Dr Hamza fara jawa bi, Dr dama sunana Sabeeterh Ibrahim nazo nan ne domin ina son na zubar da ciki na.

Toh Hajiya indai wannan ne ba matsala bari na kira miki d.r fadila ya faɗa yana ɗaukan wayar da ya kira Dr fadila akan tazo.

Dr fadila ce ta shigo, Dr Hamza ne ya nuna mata sateey yana cewa Dr wannan sunan ta sabeeterh tazo ne tana so ta zubar da ciki.

Murmushi Dr fadila tayi tana cewa to muje, bin bayan ta sateey tayi sai office ɗin ta , suna shiga ta nuna mata gurin zama, bay an ta zauna , rubuce-rubuce Dr fadila tayi ta miƙo .a sateey takar da tasa hannu , sannan tace taje ta biya kuɗin.

Bayan sateey ta dawo zama ta sake yi a inda ta tashi, haɗa allura Dr fadila tayi, sannan tazo ta zauna kusa da sateey, fuskantar ta tayi ta fara jawabi kamar haka.

Ƴr uwa ina mai sanar dake komai ya faru da ɗan adam haka Allah ya tsara masa, kiyi haƙuri a sannu zaki ga RIBAR~HAQURI insha Allah , taya za'a yi ki kashe offspring da bai ma gama haɗuwa ba, kada ki manta ajiya ce Allah ya baki, to kenan bai isa dake ba, , sannan wani na biɗan haihuwa Allah bai basa ba.

Gani ni shekara ta 7 da aure amma Allah bai bani haihuwa ba, nayi kukan dare nayi na ranah taya Allah zai baki ki zubar haihuwa rahma ce kiyi tunani.

Sabeeterh ce ta dube ta tana cewa, malama idan zakiyi aikin ki kiyi idan ba haka ba inyi gaba.

A'a bata kai haka ba allura nan tai mata allura har da ta barci, sannan ta nuna mata wuri ta kwontah.

★*★*★*★*★*★

Tun ɗazu take fallo tana kwoɗa sallama, amma shuru.

Laila ce ta fito daga ɗakin ta, ganin didda yasa ta duƙawa har ƙasa tana gaida ta.

Ansa tayi tana cewa ina umman taku.

Tana ciki, bari na gaya mata, bayan ta kira wo umma suka sauko tare {dama umman laila suna zumunci sosai da didda}.

A Hajiya Hadiza wata sabon gani , sai yau kika samu zuwa gidan namu.

Murmushi didda tayi sannan tace ai kece baki da zumunci, dama laila ce kawai ke zuwa anma ko'ita tunda Allah yayi wa bintun'diddah rasuwa ta daina zuwa ta ida maganar annurin dake fuskanta na gushe wa.

Umma ce ta kawaad da zancen tana cewa wlh kwonan nan nake tunanin zuwa Jigawa domin ƴr wurin yayata ce ba lpy hasnah yarin ya ƙarama da ciwon axma.

Ayya umman laila Allah ya sa sawwaka.

Amin, nan suka ɗan taɓa fira didda tayi musu sallama tayi tafiyar tahh........

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️🙏

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
  By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
      {Samha Umar}🥀

💘This page 16 dedicated to  my brother YAYA ALIYU FARUK BUNZA 💘

PAGE____16

Bismillah_Rahmanin-Rahim

  Bayan kamar awa biyu sabeeterh ta farka, Dr fadila dake rubuce-rubuce a wani file ta ɗago kai ta dubi sabeeterh tana cewa , sannu sannan ba wata matsala zaki iya tafiya, ta bata wani file ta ƙara signing.

Bayan sabeeterh tayi signing ta dubi d.r fadila tana cewa d.r nikam banji wani alama ba na zubewar ciki.

Murmushi Dr fadila tayi tana cewa hakane ai ƴr sauƙi na miki da yake cikin baiyi ƙwori ba, kawai yabi jikin ki.

Toh kawai sateey tace bayan ta gama yadda da magan ganun Dr fadila, hand bag ɗin ta ta ɗauka, tana yima ta sallama ta wuce gida.

DON ALLAH FANS DAMA WANI WANDA YAGA SAƘONA, INA MAI NEMAN ALFARMA DA KU TAYANI ADDU'A , ALLAH YA CIKA MIN BURINA NA ZAMA D.R RUKAYYA UMAR FARUK. NGD.

Bayan sabeeterh ta dawo gida, a fallo ta zauna ta tarrad docta bai dawo ba duk da ba tambayar sa tayi ba da zata fita ba.

Tunanin maganar da Dr fadila  tagaya mata ta fara yi , tana jin nadama a ranta, amma kash ƙaddara ta riga fata abin da tace kawai ta shige bedroom....

★*★*★*★*★*★*★

JIGAWA DUTSE

zaune take bisa gado tana kallon wani abu a wayar ta, salma ce ta shigo wayar dake hannun ta ta anshe da ƙarfi.

Ɗagowa Fatimah tayi tana kallon Salma tana ƙarawa da cewa , Lpy Salma.?

duban screen ɗin wayar salma tayi tana cewa , haba Fatimah ke kenan kullum ki  ɗauko hoton didda kina kallo kina kuka, me yasa ba zakiyi tawakalli ga Allah kuyi haƙuri, hausawa suka ce MAI HAƘURI SHIKE DAFA DUTSE HAR YASHA ROMAN SA!

Hawayen da suka gangaro a idon ta, ta goge tana cewa , salma na rasa mahaifiya ta ammi ta , na rasa mahaifina abbanah , sai didda kaɗai gare Ni ta ɗauke ni ta jure baƙin ciki da ɓakin rai, ta fifi tani da ƴaƴan cikin ta ta bani kulawa , taya za'ayi na manta da ita, duk faɗin duniya'n nan banda Allah da Manzonsa sai didda, tayi min komai salma zan iya sadaukar da rayuwa ta .........

Ring wayar ta dake hannun salma ya hana ta ƙari shewa, salma ce ta miƙo mata tace gashi nan laila ce.

Amsa tayi bayan tayi peaking ta kara a kunnen ta.

Fatimah Meya sameki naji muryan ki wani iri.?

Ba komai laila mura ke ɗan damuna , ya abin sona didda tahhh.?

Dariya laila tayi tace wlh yau diddan'ki tazo gidan mu.

Da gaske ? Fatimah tace.

Eh, Fatimah anma bata  wani jima ba, ya mommy.?

Mommy lpy ƙalau gama salma a kusa dani.

Ayya bata waya laila ta faɗa, miƙa ma salma wayar Fatimah tayi.

Salma na amsa ta kara a kunnen ta, tana cewa bana son gaisuwar ma, tunda idan Bama Fatimah ba bakirana zaki yi ba har mu gaisa.

Dariya laila tayi tana cewa ƴr uwa ta ba haka bane, ya Mommy tah, ya jikin hasnah fatan ta samu sauƙi.?

Lpy ƙalau hasnah taji dama sosai, ya Mommy tah.?

Mommy lpy ƙalau Laila ta faɗa tana kashe kiran.

★*★*★*★*★*★
Sallama yaya Ahmad keyi a bakin bedroom ɗin Mommy. 

Ammsa tayi tana cewa shigo.

Shigowa yayi ya duƙa yana gaida tah.

Amsa tayi cikin far'a, duban sa tayi tana cewa Ahmad meke tafe dakai, da ganin ka akwai maganar dake tafe dakai.

Ɗan sosa ƙeya yayi yana duƙar da kansa ƙasa
A hankali ya fara magana, dama Mommy akan maganar Fatimah ce  , ɗan tsaya wa yayi ya dubu Mommy.

  Gaban sa ne ya daɗi ganin annurin dake fuskar Mommy ya ɓace sama ko ƙasa.

Ajiyar zuciya Mommy tayi , sannan tace haba Ahmad kana da hankali kuwa? Fatimah fa da auren wani akan ta, kama daina tunanin Hakan, kai nama Yi kuskuren .

Ɗaga muryan ta tayi tana kiran, hasnah Hussain, da gudu suka shigo suna rige-rige, Hussain  je kiramin yayun ka,.

Bayan kamar 2 minutes ya dawo yace Mommy ga sunan zuwa, toh kuje fallo kuyi wasa, to suka faɗa suna fita.

Assalamu alaikum.
Wa'alaikk-salam.
Mommy gamu salma ta faɗa.
Toh ku shigo ku zauna.

Ƙara sowa sukayi ciki, Fatimah ce takai duban ta inda ya Ahmad yake saida gaban ta ya faɗi.

Bayan sun zauna , Mommy tayi gyaran murya ta fara jawabi kamar haka.

Toh dama na kira ku ne domin na sanar daku nayi kus-kure, dana riƙe Fatimah na sata boko kuma da auren ta bada yardar mijin taba.

Saboda haka daga yau na yanke shawarar zata ajiye karatu, amma dai bazan mayar da ita gurin iya-yen ta ba sai randa ta buƙata da kantahh, tana kai nan tace shikenan kwo iya tafiya.

Fatimah na fita ta wuce ɗakin su.

Salma ce tace Fatimah kiyi haƙuri don Allah.

Murmushi'n ƙarfin hali Fatimah tayi tana cewa, ke salma wlh ba komai Hausawa suka ce duk Abin da babba ya hango  to yaro ko ya hau rimi bazai hange shi bah, saboda haka wlh ni ban damu ba ko kaɗan.

Nandai suka kwona kowa da abin ke cikin ransa.........……

Kuyi haƙuri da typing error da Kuma rashin typing mai yawa, zan gyara insha Allah ...

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

������
RIBAR~HAQURI
������

Story & Writing �
  By:�

�RUKAYYA UMAR FARUK
   {Samha Umar}�

�This page 17 dedicated to my brother YAYA UMAR FARUK BUNZA�
PAGE___17

PAGE____17

Bismillah_Rahmanin-Rahim.

AFTER  FIVE MONTHS

Rayuwa tayi tafiya , minti ya rikiɗe ya dawo awa bada sani ba awanni sun dawo kwona ki, kwonaki sun dawo satitika, sati ya shuɗe ya dawo watanni, ga watanni biyar.

Cikin ikon Allah ga sabeeterh ta wayi gari cikin wani hali, tun safe ciwon ciki mai tsanani ya hana ta sukuni sai jini ke zuba a jikin ta.

Docta ne ya ɗauke ta zuwa asibitin su , gwaje - gwaje aka fara mata cikin ikon Allah ga ciki na wata shida, amma sakamakon kwoyo yin hana ɗaukan ciki da tayi amfani dashi ɗan ya samu matsala, ( nikam nace Dr fadila baiwar Allah tamin daidai maganin irin su sateey kenan).

Iya ruɗewa docta ya ruɗe domin babu tabbas ɗan ya rayu, ya bata duk wani taimakon, inda da ace cikin yakai watanni bakwai ko takwas da anmata aiki an cire shi.

Ya mata komai domin ganin ɗan ya rayu, yana tunanin halin da zai shiga, idan ɗan dake cikin ta ya mutu.

   "Bayan ya sanar da didda akan tazo asibiti".

Bayan ta iso ya mata bayanin komai.

Ya samu ya daidaita matsalar sateey sannan ya Kaita ɗakin hutu, nan didda ta zauna kula da ita, babu wanda ya sani daga shi sai didda.

Ransa ya ɓaci da ƙoƙarin hallaka masa babu da sateey tayi, amma didda cewa tayi yanzu ma ya fara gani, kuma ya kuskura ya sanar da ko Daddy ne bata yafe bah.

       "Nan didda ta zauna wurin, bayan awanni biyar sabita ta farfaɗo nan docta ya shigo ya duddu bata yana mata wani kallo wanda Ni kaina na kasa fassara shi, najin daɗi ne ya kusa samun ƴr/ɗa ko kuma na jin haushi ne ohohhh.....

Ana yin sallar la'asar suka koma gida.

Bayan kwona uku sabeeterh na kwonce bisa gado riqe da wayar ta sai kira take ba'a ɗaga ba,  sai chen aka ɗaga Hakan yayi daidai da shigowar docta ɗakin da yake ta juyawa ƙofar baya bata iya ganin sa....!

Ana ɗauka tace, sateey kwona biyu wayar ki bata shiga.?

Eh , wlh sateey kwona biyu waya ta lallace sai jiya nasai sabo kuma bana kusa koda kike kirahh.

Okey, yana batun fita tunda yaji waya take saiji yayi tace.

Hmmm, khairat ashe cikin bai zuba ba, yaudara ta wancan likitar tayi kuma tace cikin ya fita..

Hmmm, ƙawata an rabaki ke ƙi gashi yanzu kina batun kashe kanki.

Wlh khairat tunda fansa nazo ɗauka bazan taɓa haƙur...... maganar ta ce ta maƙale jin motsin mutum yana tari.

Tana juyawa taga docta saida numfashin ta ya kusa ɗauke wa, rasa me zata yi tayi, shiko tarin kasa tsaya masa yayi.

Da sauri sateey fita fallo ruwa ta ɗebo masa ga Cup,  saida yasha sannan tarin ya lafa.

Duban ta yayi yace Nagode my wife ya faɗi hakan murmushi akan fuskar sa.

ganin haka yasa sateey cewa dama ka jima da shiga wa ne.?

Murmushi'n dai yayi yana cewa, a'a ai tarin ne ya kworo ni nazo ki ƴn min ruwa.

Oh, baka ji ina waya bah.?

Waya? A'a.

Hamdala tayi acikin zuciyar ta , shikan cewa yayi zai koma hospital sabo da akwai patient da zai duba, to tace tai masa rakiya har inda ya faka motar sa.........

★*★*★*★*★*★

JIGAWA DUTSE

Fatimah ce zaune bisa 2 ctr waya ce a hannun ta, duban salma tayi tana cewa, salma yau watanni biyar da rubutu exam ɗin mu , kuma har kun koma school an ci gaba da lecture second semester Amma results shiru, Ni ina so ko gani nayi.

Naji ana cewa an ci da yawa shiya sa aka jinkir ta result ɗin, amma kuma jiya da malam Ra'uf ya shigo lecture naji Ana tambayar sa yace bazai wuce 2 to 3 week's ba.
  

Hussaini ne ya shigo sai haki yake, yana cewa anty wlh muna wasa da hasnah da amba ƴr anty Maryam(makwoci yar su) shikenan ta faɗi.

Inalilahi Fatimah ta faɗa , suka kama hanya sai harabar gidan , kwonce take da alama ko numfashi barayi, nan salma ta kira Mommy , aka ɗauki hasnah sai asibitin da suke zuwa.

Suna isa akayi emergency da'ita, bayan two hrs sai ga likita ya fito, Mommy ce ke tambayar sa hasnah, .

Duban ta yayi yace muje office, suna shiga ta zauna, duban ta yayi yace.

Hajiya yarin yar sai Abin da ya fito... Ƙarar 
buɗe ƙofar da akayi  yasa likita bai ida ba, Ahmad ne likitan yace a ƙara so mana.

Yana ƙara sowa ciki yace Mommy ina hasnah dama salma ce ta kira Ni koda nazo suka ce min kuna ciki.

Komai Mommy kasa ce mai tayi illa duban sa da tayi ..

Likita ne yace ka zauna mana, zama yayi kujerar dake facing na Mommy.

Likita ne yace, Hajiya hasashen mu ya bamu, cewa lokacin da kina da cikin hasnah, kina yawan aiki bakya samun hutu, kina shiga iska shan abu mai sanyi , wanka da ruwan sanyi, cin abinci mai yaji, dama sauran su suna illa ta lpyr jinjiri to shine ya shafi hasnah har yasa mata ciwo....

 Mommy ce tace to shifa Hussain.?

Yace haka ne shi Hussain bai same shi ba saboda mata sunfi rauni , hakan yaja mata axma kuma da limonia , yanzu dai maganin da muka aza ta tana sha, sauran curun ya haɗe, za'ayi mata aiki.

A gaskiya bazan ɓoye miki ba , aikin ba'a nan za'ayi shi ba , I mean sai an fitar da ita land out, domin sun fimu ƙorarun kayan aiki.

Ajiyar zuciya Mommy tayi sannan tace kai taimaka min likita kada na rasa ƴrtah.

A gaskiya Hajiya na gama magana, nan likita ya fita ya barsu.

Bayan an fito daga hasnah daga emergency room , ɗakin hutu aka kaita anma nata farka bahhhhh.

Mommy ce zaune tayi tagumi tana tunanin mafita domin har yanzu bata ɗebe ran ƴrta zata rayu bah.

Cen taji Ana Mommy Mommy, da sauri ta ɗago ta dubi hasnah har yanzu bata buɗe idon ta ba  amma still tana kiran Mommy Mommy.

Hannun ta Mommy ta kama tana murmushi tana cewa twins ɗina ga Mommy ki tashi kinji.

Rungume ta Mommy tayi , hasnah na cewa Mommy , cikiah, kaina, .

Kiyi haƙuri zaki samu sauƙi, nan sai ga Fatimah sun shigo , domin sun ɗan je gida , Mommy tace Fatimah kira min likita.

Bayan likita ya shigo , cewa yayi a bata tea kaɗan tasha....

★*★*★*★*★*★

Tafe yake cikin mota hankalinsa a tashe, babu Abin da yake sa tunanin halin da ƙauwar sa ƙarama ke ciki, shin ta farfaɗo ko ya .

Ya kusa gan-gara wa yasha kwona yaga wani ɗan saurayi na ɗaga masa hannu alamar ya tsaya.

Parking yayi tare da fitowa daga motar, Meya sami motar taka.?

Murmushi saurayin yayi yana cewa, wlh ni baƙo ne kuma mota na ya lalace, gashi da alama bazan samu baka nike nan gurin ba, kuma babu abin hawa.

Murmushi Ahmad yayi , yace to muje mota na sai na kaika gurin baka nike.

Toh ya faɗa Yana shiga motah.

Anma bawan Allah ina ka fito na ganka cikin damuwa.

Duban sa Ahmad yayi yana cewa suna na AHMAD kaifa.

Murmushi saurayin yayi yana cewa Suna na ABDUL~HAKEEM ni ɗan jahar Kano ne , nazo nan ne Ansar wasu takaddu, waƴn da aka Turo mana daga ƙasar waje (H.I.D), watanni shida da suka wuce nazo na karɓa, kuma aka bamu saura abin dai sai a hankali wai su, suna son muyi aiki dasu achen.

Wow aboki na Allah ya bada Sa'a Ahmad yace yana ƙara wa da cewa ina zaune nan DUTSE nida Mommy ta, mahaifina ya rasu Daga ni sai ƙanne na, UMMU~SALMA sai twins 

Toh hasnah ce ba lpy kuma ance sai an fita da'ita waje.

Ajiyar zuciya Abdul-Hakeem yayi yana cewa Allah ya bata lpy.

Da Amin Ahmad ya amsa , yana cewa dare yayi ina zan kaika.

Hotel � nake so mafi kusa.

Toh amma in ba damuwa tun da Mommy na a asibiti zasu kwona, ka iya kwona a gidan mu.

Murmushi Abdul-Hakeem yayi tare da godiya.

Ahmad bai tsaya ko'ina ba sai gidan su yana horn  Mai gadi ya buɗe, parking yayi suka fito, sai fallo, ɗakin Ahmad suka nufa, toilet ya nuna masa yace ya shiga yayi wanka kafin nan ya kawo masa abin .............

Shin wane-ne Abdul-Hakeem.....?

PLZ comment and share�������

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story and writing 📝🖋️

     By:👇

🥀 RŪKAYYĀ ŪMAR FARUK
         {Samha Umar}🥀

This page 18 dedicated to my brother YAYA USMAN UMAR FARUK  🔸🔸🔸 much luv.

PAGE___18

A asibiti kuma Mommy ce ke bawa hasnah fruit tana ci har ta kwoshi, Mommy ciki na ke ciwo da gaba na zafi.

   "Murmushi'n ƙarfin hali Mommy tayi tana cewa zaki samu lpy ƴrtah da izinin Allah, lafewa tayi a jikin Mommy."

Bayan 2hrs Mommy tace Fatimah idan yayan ku yazo ku bishi ku wuce gida keji.

Toh Mommy.

,,,,,,,,,Bayan Abdul-Hakeem ya fito daga wanka abin cin da Ahmad ya kawo masa yaci, sannan yace saidai su tafi asibiti tare,,,,,,,,,

Sun fito suka shiga Mota, anan yah Ahmad ya ɗauki baka nike domin yasan da shike gyara masa mota, basu tsaya ko'ina ba sai inda suka bar motar Abdul-Hakeem ,.

Bayan sun aje baka nike Ahmad yace idan ya gama gyara yakai musu gida, suka ida wuce wa sai asibiti.

  "A harabar asibitin yah Ahmad yayi parking inda suka fito , Basu tsaya ko'ina ba sai ɗakin da aka kwontar da hasnah.

Suna shiga suka sami Mommy zaune bisa gado sai hasnah jikin ta, Hussaini kuwa a gefen ta, sai salma dake zaune bisa kujerar roba."

Assalamu alaikum.

Wa'alaikk-salam Mommy ta faɗa.

Ƙara sowa sukayi inda suka gaida Mommy suna tambayar ya mai jiki.

Da sauƙi Mommy ta Ansa.

Salma ce tace ina wunin ku yayah.

Lpy ya amsa yana cewa Mommy wannan sunan sa Abdul-Hakeem nan ya kwoshe komai ya gaya mata.

Allah ya bada Sa'a nema Mommy ta faɗa.

Duban Abdul-Hakeem yayi yana cewa wannan ita ce Mommy, sai wannan Ummul-salma  ƙaunwa ta , ga kuma twins ɗin Mommy kuma auta...

Toh Allah ya raya yasa  albarka.

Da ameen Mommy ta Ansa.

Fatima ce ta fito daga toilet tana cewa a yaya yanzu kazo.?

Eh, Fatimah ya nuna Abdul-Hakeem yana cewa wannan aboki nane, ina wuni Fatimah ta faɗa...

Amsa yayi yana kafe ta da ido, nan dai Mommy tace wlh ta gaji , Fatimah ta kwona tare da ita sai salma da Hussaini su koma gida.

Toh suka ce, suka miƙe suna Mata sai da safe.

Suna fita chak ya tsaya saka makon Ring ɗin da wayar sa keyi, duban Ahmad yayi yana cewa ina zuwa.

Chen ta baya yayi, bayan yayi peaking suka gaisa, cewa yayi wlh docta mota ta ce ta lallace sbd haka sai gobe zan dawo, dama ina don magana dakai amma sai gobe in na dawo,.

Okey docta yace yana kashe kiran.

Yana juyowa saiti da  window ɗakin da aka kwontar da hasnah , inda Fatimah ke tsaye saitin window tana murmushi, da alama magana take da Mommy.

Camera ya kamo a wayar sa inda ya ɗauke ta photo sannan ya maida wayar a aljihu, yana murmushi.(hmmm Abdul Hakeem kodai kodai....hmm nidai bance komai ba).

Koma wa yayi parking space inda ya bar su yaya Ahmad, ya iske har sun shiga Mota basu dai tada bah.

Shiga yayi yana cewa ku gafar ceni, na tsaida ku wani amini nane ya kira ni.

   "Ba komai Ahmad yace suka tada motar sai gidaah."

★*★*★*★*★*★*★

KANON DABO!

Didda ce ke saukowa daga upstairs riƙe da waya sai murmushi take tana cewa,  toh laila ina gama tanan ta iso.

"Sai anjima laila tace tana katse kiran."

A Hajiya Rukayya (umman laila) kece a gidan mu.

Eh, didda na same ku lpy.?

Lpy ƙalau ya gida, ai yanzu na gama waya da laila take gaya min gaki nan zuwa.!

eh , wlh yau tahiyaya nai miki.

Ayya didda ta faɗa tana zama bisa ɗaya daga kujerun gallon..

Imaru mai aiki ce ta kawo ma Umman laila abin taɓa wa a baki.

Didda ce tace Hajiya Rukayya dama zamu yi magana neh.

A to ina jinki diddan bintu.

Dogon numfashi didda ta sauke tana cewa wlh kedai maganar matar salim ce,  nan didda ta kwoshe komai ya gaya ma Umman laila.

  "Jajan ta mata umma tayi tana cewa wlh didda'n bintu ƴn matan yanzu ba kasafai ake samun na ƙoraiba , yita haƙuri Allah ya shirya, Allah ya sauke ta lpy, ya bada raya ye.

Ameen-Ameen didda tace tana ƙara wa da yanzu shike nan bintu kan Allah ya amshi abar sa,? Naso ace ita zata haifa min jikoki, ashe ba haka bane, ta ida maganar kamar zata yi kuka .

Hajiya Hadiza kiyi haƙuri komai daga Allah insha Allah komai yay tsana ni to sauƙin sa na tare da Allah, mai HAQURI yana dare da RIBA , ki fawala wa Allah komai.

"Ni bari nazo na wuce ta faɗa tana tashi daga zaunen da take'.

Didda ce ta tashi itama tana cewa to Rukayya nima na gode sosai da ziyara, Allah ya saka da Alkhairi.

Nan tai mata rakiya har ƙofar fita fallo ta wuce gidah.......

★*★*★*★*★*★

JIGAWA DUTSE

Koda suka koma gida har an mayar da motar Abdul-Hakeem gidah.

Nan suka shiga gida suka kwontahhh.

Bayan safiya ta waye nan Yah Ahmad suka fita da Abdul-Hakeem sai Ahmad ɗin ya raka sa a (H.I.D) ɗin  yayi abin da zai yi sannan suka wuce asibiti...

Koda suka shiga likita na cirema hasnah drip Wanda ya ƙare, Fatimah na zaune bisa carfect, Mommy kuma bata nan.

Bayan sunyi sallama Fatimah ta amsa , gaida ya'yan nasu tayi.

Amsa yayi yana tambayar likita jikin tah.

Cewa yayi yanzu duk lokacin da suka shirya swo iya tafiya da ita.

Toh Yah Ahmad ya faɗa likita na fita bisa kujerar roba ya nuna ma Abdul-Hakeem ya zauna, shiko yana zama gefen hasnah.

Fatimah ina Mommy.?

Mommy na toilet, ta basa amsa.

Okay, ya kwonan asibiti?.

Wlh lpy ƙalau ina su salma da Hussaini.?

Salma cewa nayi su zauna, ya hasnah da jiki.?

Wlh, yaya gata nan tun da assuba da ta tashi ta koma barci yanzu, taji sauƙi har taci abinci.

Okay Allah ya ƙara lpy.

Da Ameen Fatimah ta amsa..

Shiko Abdul-Hakeem yayi shuru , yana mamakin yanda take da surutu.

Kowa yayi shuru na wasu mintinan, sannan Mommy ta fito daga toilet, duban su tayi tana murmushi.

Nan suka gaida tah,
Amsa tayi tana tambayar su ya suka kwona, da lpy suka bata amsa.

Ya mai jiki Abdul-Hakeem ya tambaye tah.

Jiki da sauƙi....

Tashi suka yi inda Ahmad yace mom Abdul-Hakeem zai koma gida.

Ayya , Allah ya kaika lpy ya bada Sa'a.

Ameen Mommy NGD kworai , kuma Allah ya ba hasnah lpy.

Ameen Mommy tace tana wuce wa ta zauna, nan Fatimah tai masa Allah yakai lpy ya tsare hanya.

Ameen ya amsa yana wucewa, sai da suka koma gida sannan Abdul-Hakeem ya kama hanyar KANO.....

★*★*★*★*★*★

Bayan Abdul Hakeem ya isa Kano gidan su ya nufa, inda yai horn Mai gadi ya buɗe masa.

Buɗe motar yayi ya fito gidan ya haɗu sosai ba kaɗan ba.

"Yana shiga main fallo ɗauke da sallama a bakin sa,.

Mami (mahaifiyar sa) zaune a ƙayatatcen fallon gidan wanda sai ƙamshi ke tashi, sallama yayi, ta amsa ciki ciki.

Ƙara sowa yayi ciki har inda take, kusa gare ta, yana faɗin Wash maminahhh, barka da gida...

Lpy kawai tace masa kanta a sama .

Hannun ta ya kamo tare da cewa haba sweet Mamie baki ga rashin ganin ki duk na rame, ba kimin magana farin cikinahh.

Wlh Mamie banso kwona ba mota ta ce ta lallace Please forgive me my Mami.

Juyowa tayi ta fuskanci ce shi tare da cewa , haba ɗana, na haihu da yawa amma banda ɗa duniya sai kai.

"Taya zaka min haka,? Wlh jiya ban kwona ba kwona tunanin ka nayi"

Ada na yarda kaje U.k kayi karatu , yanzu kwota-kwota baka fi 9 months da dawo wa ba , tunda kace sai kaje u.k batun result ɗinku kace min ba kwona zaka yi ba kaje ka kwona,  sabi da kaga na damu dakai.

 Murmushi yayi tare da cewa haba mamin papa , kina iya fushi da ɗan papa? Da ɗan mami? Mota ta ce ta lallace, nan ya bata labarin komai.

Toh Allah ya bawa hasnah lpy, yanzu muje kaci abin ci.

A'a Mami bari nayo wanka,.

Im Mami zan so na nuna miki wani abu , gyara zama tayi tare da cewa inaji.

"Nan ya ciro wayar sa tare da kunna wa photon fatemerh ne ya bayyana, Mommy ga wacce nake so, kuma Insha Allah ita ce sirkar ku."

Karɓa Mamie tayi tare da cewa kai my son Amma ta haɗu , amma kamar na taɓa ganin wannan face, ɗan shuru tayi tana tunani, sannan tace nadai manta ko a ina ne....

"Haba Mommy wanna fa ƴr Jigawa ce , kuma ina ji baki taɓa zuwa Jigawa Ba, ƙila sai in zaku kai I SEE I LOVE 💘💘........

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
   By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
      {Samha Umar} 🥀

🌻This page 19 dedicated to my best sister BALKISU FARUK BUNZA 🌻

PAGE___19

____________hhh wlh kaga nama tunah inda na taɓa ganin face ɗin, matar abokin ka salin wlh sunyi kama sosai, saide ita ta rasu , takai ma kusan shekara a kushe wah"

"Ayya Mamie dama docta nada matar bayan Sabeeterh, anma bai taɓa gaya min bahhh.

Dama lokacin kana U.K koda akayi aure, kuma auren haɗi ne ƴr ƙaunwar mamar sa ko baban sa ni nama manta, ai bata fi wata ɗaya da rasuwa ba ka dawo.!

Ayya mamie Allah ya mata rahma, bari na shiga na watsa ruwa.

Okey sai ka fito.!

★*★*★*★*★*★

GIDAN ALHAJI MUSA (mijin anty Zulai)

Waya ce a hannun ta tana darling wata number kusan 2 missed call no peaking, a na ukun aka ɗauka.

Salama tayi aka amsa, ana cewa wai wace ƴr kan uban ce ke damu na da kira bayan ina fama da kainah..

   "Ni ce mana anty Jamila"

Oh, kice kema uwar ki ta koya miki takuran da ta'iya , yanzu an daina min sam'mako sai de ayi sam'makon kira na da waya, to wlh bazan ɗauka muku ba, ba uwar ba ƴr anbi an takurawa mutum , mtwsssssss tsaki tayi tare da kashe kiram.

Hmmm, ajiyar zuciya Jamila ta sauke tare da tashi domin fita fallo.

Koda ta fito ta tarrada anty zeenatu tazo gida suna magana da Anty Zulai, kuka ta sake..

Juyo wa suna kallon ta, anty zeenatu ce ke Jamila lafiyar ki , kike wannan kuka.?

Jikin anty zeenatu ta faɗa tana cewa anty kice ta yafe min don Allah, kada alhakin ta ya kama ni.

Ke, kiyi magana kin barmu a duhu cewar Anty zeenatu.

"Anty bintu"

Wacce bintu?.

"Anty bintu'n diddah."

Baki da hankali jameey ita wacce ta muku?, Ko cen cikin kabari zani na isko ta? Na roƙa miki ita, ai duniya ce wlh komai ka aika ta zata ga sakamako...

    Wlh anty sheɗan ne ya kiɗa mini gan-ga na taka rawa, anma wlh nayi nadama, nan jameey ta kwoshe komai da suka yi ma Fatima dama kudirin su ta gaya ma su.
    
Aiko sai saukar mari taji a kuncen , itakam uwar tasu anty Zulai ido ne kawai ta zuba musu, domin ko'ita tayi nadamar abin da ta aika tah.

Ai wlh Jamila da ki yarda da kada ki yarda duk tsinta ciyar mage bata mage, kuma bintu ta tafi ta barku da halin ku, taida maganar tana juyowa gefen Anty Zulai tare da cewa.

Yanzu anty kina kallon abin da ƴrki ke aikatawa , anma kama saboda sheɗan ya hure miki kunne ke kasa tsawa tar matah....

Kefa mahaifiyar mu ce shin idan baki mana faɗa ba kika nuna mana gaskiya taya zamu fahimta?.

  "Dogon numfashi Anty Zulai ta sauke tare da cewa Yayar su (haka take kiran ta domin ƴr fari ce) koni na ɗau zugan sheɗan anma nayi nadama, yanzu da ace zanga Bintu da riƙa gwoiwo wina a ƙasa na nemi gafarar ta , anma lokaci ya ƙure sai de na nemi gafarar Allah.

To Ni yanzu zanje har cen gidan Daddy domin ganin husnah ita ma nai mata faɗa anty zeenatu ta faɗa.

Jameey ce dake kuka ta ɗago tana cewa anty nima zanje don Allah.

Ba'in da zaki bini anty ta faɗa tana ɗaukan hand bag ɗin ta.

Anty Zulai ce tace Yayar su bari bari nazo sai muje mu duka .

Toh anty, nan suka ɗauko mayafan su , mota suka shiga jameey ke driving, ba wanda ya cewa ɗan uwan sa ƙalla har suka isa.

Gidan ALHAJI HASSAN SAUTA horn suka yi mai gadi ya buɗe musu sai parking space Wanda ke jere da motoci kala kala sun kai goma sha...

Parking tayi inda suka fito, sai da suka danna dorble , mai aiki ce imaru tazo ta buɗe musu, gaida su tayi.

A kaya tatccen fallon gidan wanda sai kamshin turaren wuta yake da air freshener ga sanyin air condition  ya bada wani irin atmosphere.

Zama sukayi inda ba kowa a fallon, imaru ce tace Hajiya ai da kun isa fallon diddah tana nan ciki.

Nan suka tashi sai ɓangaren diddah , nan ma bata fallo sai ƙarar tv ke tashi, bedroom ɗin ta suka shiga.

Nan take zaune gefen bed riƙe da hisnul-muslumin, tana karan tawa, sallama suka yi, inda ta ɗago kanta tana amsa wa.

    "  murmushi tayi tare da cewa a Hajiya Zulai kece mara ba ku zauna".
    
Bisa ƴaƴan kujerar data ƙara ƙawata bedroom ɗin anty zeenatu da jameey suka zauna, inda anty Zulai ta zauna bisa bed.

A lallai Hajiya Zulai yau naji daɗi domin ko ba komai , ko ba komai ke gargaɗo mun ƴrƴr nah.

Murmushi kawai anty Zulai tayi.

Anty zeenatu ce tace diddah mun same ku lpy?.

Lpy lau zeenatu ina mai gida nah (khalipha).

Yana cen gidan kakan-nin sa.

Jamila ce tace diddah husnah nanam.

Eh, tana cen ɗakin ta, to tace tare da tashi tana cewa ina zuwa ta fita.

Tana fitowa sai fallon husnah a nan ta iske ta zaune riƙe da waya , sallama tayi.

An sawa husnah tayi tana cewa mara ba , yaushe kinka shigo.

Sai da ta zauna , sannan tace yanzu tare nake da Anty dama anty zeenatu .

Ayya bari Naje mu gaisa.

Toh husnah mu gode Allah da har muka gane laifin mu da wuri, duk da cewa ita wacce muka aika tawa ta rasu, wlh na kira anty sateey kada ki ga yanda ta dinga zagi na sai kace na mata satah.

Dariya husnah tayi tare da cewa oh, ne, Asma'u wlh na huta dama ni na daina shiga harkan ta, yanzu tashi muje mu roƙi iyayen mu gafara.

Nan suka tashi a fallon diddah suka tarrada su, har ƙasa suka riƙa tare da cewa.

Yaku iyayen mu ku yafe mana don Allah tunda Allah yasa mun gane gaskiya , na ƙin ƴr uwar mu da muka yi, to mun tuba,

Husnah ce ta ɗora da kiyi haƙuri ke lurrar sani cewa , wlh duniya bayan ke da Daddy Babu wanda yakai min Fatima .

Hmmm, Alhamdullh, Allah abin Godiya nayi tawasalli da suna Yen ka.

Yau ni Hadiza Allah ya shirya min husnah da Jamila.

Nan anty Zulai ta ɗora da cewa , diddah wlh koni nayi kus-kure mun tashi gida ɗaya da mahaifiyar Fatima wato Fatima, anma na kasa ƙaunar ta, don Allah kiyi haƙuri.

Ba komai yanzu tsakanin mu da Fatima sai addu'a,.

Haka ne, anan suka zauna har sai da suka yi lunch sannan Daddy ya dawo aka dasa sabu war fira.

Saida akayi magrib , sukayi Sallah , inda suka ce zasu wuce , Daddy yace su bari suyi dinner .

Nan suka Amin ta suka yi dinner sannan suka wuce gidah...

★*★*★*★*★*★

Acen ɓangaren Abdul-hakemm kuwa , bayan ya watsa ruwa , ya cenza kaya ya fito, a dining area ya samu mamie, zama yayi tayi saving ɗin sa .

Bayan ya gama ci ya mata sallama haɗe da cewa yanzu zai dawo bayan 12 minutes.

Hello, docta , .

Na'am Abdul Hakeem.

Gani nan a ƙofar gidan ka.

Okay shigo mana.

Okay Abdul ya faɗa haɗe da kashe kiran

Da sallama ya shiga fallon wanda ke hargi tsere , ga ƴr aiki acen gefen kujera sai barci take.

Tsaki yayi sannan ya taka upstairs ya shiga fallon docta,  nan ya tadda docta wanda ke zaune riqe da remove yana chanza channel .

Juyo wa yayi yace zauna mana Abdul , zama Yayi yana cewa, wai docta kana aikin me gidan ka ya lallace haka, kaga yanda na tarrada fallon ka , wannan wane irin abu ne sai kace baka san muhimmancin tsafta ba, kai fa docta ne,.

Duban  Abdul-Hakeem yayi yana cewa ka gama , kaga kawai ka gaya min maganar dake tafe dakai.

Okey, Abdul-hakemm yace yana ɗora wa da dama lokacin da naje Jigawa , nan ya masa baya nin komai, haɗe da cewa to shine  nake ganin a kawo yarin yar asibitin ku ko za'a dace Domin mutanen kirki ne kuma ina tausaya wa yarinyar, ƙara ma ce ko 10 years batayi ba.

Dogon numfashi docta ya sauke yana cewa, Allah yana son mai taimako don haka ba komai zasu iya zuwa Allah yasa a dace.

Da Amin Abdul ya amsa yana cewa NGD aboki na .

Ba komai ai kai amini na ne.

"Abdul ne yace ai baka ɗauki hakan ba"

Kamar ya docta ya tambaye sa.

Eh, d.r salin ashe dama kana da wata matar bayan Sabeeterh .

Hmmm, Abdul meya kawo maganar wacce ta rasu , sannan kuma koda akayi aure na da bintu baka nan, kuma abin girshi ne.

Bakomai docta ai nona na samu mata a Jigawa.

Oh, shiya sa kake son na taimaka wa yarinyar.

"Ba haka bane bari ma kaga pics ɗin ta she's a beautiful"

Wayar sa ya jawo daga cikin aljihu Domin nunawa docta pics ɗin Fatima , yana juyowa yakai wayar daidai fuskar docta.............

Plz comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️

������
RIBAR~HAQURI
������

Story & Writing �
   By:�

� RUKAYYA UMAR FARUK
      

This page 20 I dedicated to my brother MUSA FARUK BUNZA , my best ƙane��.

 

PAGE____20

Bismillah_Rahmanin-Rahim.

Yana kai wayan dadai fuskar docta kira na shigo wa, aiko yana duba wa yaga mamie ce, ɗauka yayi yana cewa hello mamie.

Banji abin da aka ce a cikin wayar ba ya sake cewa gani nan tafe ya kashe wayar tare da maida wa aljihu.

To docta mamie ce wai maza na dawo gida.

Murmushi docta yayi tare da cewa muje na raka ka.!

Fitowa sukayi nan suka tadda sateey zaune bisa kujera tasa soyayyen kwoi gaba tana chi...

"Tana ganin sa tai wani uban tsaki haɗe da cewa wanne ɗan takura ne, kullum gidan ba'a barin masu gida su huta kai Allah ya raba mu da Mayun watah".

Docta ne yai mata mugun dubi tare da cewa don uban ki dawa kike? Badai Abdul-Hakeem ba?.

Ciki ciki tayi magana yanda ba mai jinta sai de bakin ta dake motsi.

Abdul-Hakeem ne yaja hannun docta yana cewa kai da Allah share ta indan nine, nan ya raka sa har get yay masa sallama ya tafi.

Ai koda ya dawo fallo babu sateey sama ko ƙasa kwofa yayi tare da kama hanyar bedroom ɗin sa.

★*★*★*★*★*★

Bayan Abdul Hakeem ya koma gida nan ya kira yah Ahmad, ya gaya masa yanda suka yi da docta tare da cewa su shirya gobe ma swo iya tahowa.

Godiya Yah Ahmad ya masa haɗe da katse kiran, ya fito fallo domin gaya wa Mommy wannan baza tar an salamo su ɗazu ne.!

Ita kaɗai ya iske fallon nan yai mata bayanin komai.

Albarka ta sama Abdul , tare da fatan Allah yasa a dace.

"Da ameen ya amsa yana ƙara wa da cewa, ton Mommy yanzu sai muyi shirye shiryen tafiya a gobe zamu je dani dake da ita hanayar..... 

Duban sa Mommy tayi tare da cewa to babu matsala yanzu sai naje gidan gwogon ku halima na gaya mata.

Mommy sai ke gaya mata? Ai bai kamata ta ace komai zamu yi sai mun gaya ma gwogon, tunda ita ma ba gaya mana nata zatayi ba...

Eh, haƙa ne Ahmad anma ita ƙaunwar mahaifin ku ce bai kama ta ba.

Bismillah Mommy kije ki gaya mata, yanzu ki shirya sai na kaiki cen gidan gwogon .

Okey, ashirye nake mayafi kawai , nan ta shiga kwolawa Fatima kira....

"Tana fitowa tace gani Mommy.

Jeki ɗauko min hijab ɗinah, to tace, nan taje ta ɗauko ta kawo ma Mommy.

Bayan Mommy ta saka hijab suka wuce, Ahmad ya jata sai gidan Hajiya Halima suna zuwa Mommy ta shiga gidan da sallama.

A tsakar gida ta iske ta tana hura.

Sallama tayi, amsa tayi tana ɗago wa.

Oh, kece karimah.

Eh, Halima ya kuke.?

Lpy, shiga ciki ina zuwa.

Okey, Mommy na shiga ciki Hajiya Halima ta ɗauko wayar ta dake bisa window, number Alhaji mugu ta kira.

   " Yana ɗauka saida tayi gyaran murya sannan tace , Alhaji Allah yaja da ranka, mugu kuma ɗa ga mugu, kuma uba ga mugu.

Murmushi Alhaji mugu yayi yana cewa, ina i jinki Halima mugun ya.

Dama Alhaji yanzu haka maganan da nake ma ga Hajiya karima nan a gida na...

What, da gaske kike…?

Ƙworai kuwa Alhaji.

Toh, yanzu zan aiko da wannan gubar da muka yi magana, zata ɗauki tsawon Sa'a guda kafin ta fara aiki, kega idan ta mutu sai laqawa Fatima.

Toh Alhaji yanzu ina jiran ka.

Okey"

Tana kashe wayar ta shiga fallo nan ta samu Mommy zaune.

Mommy ke sanar da ita cewa zasu kai hasnah asibitin Kano a A.P.H.

Lallai Hajiya karima to gaskiya ni kin ganni nan ko asi banda, imma don shine kika lallaɓo kika zo.

A'a nikam dama sallama nazo na miki.

Eh to ina zuwa, tashi tayi ta fita domin taji ana ƙwon-ƙwosa sallama, har garka ta fita inda ta amso saƙo, tana zuwa ta saka cikin zoɓo ga jub ....

Tana shiga fallo taba Mommy, Bata so tasha ba amma sanadiyyar naci Irin na Hajiya Halima tasha... 

Tana gama sha taima Hajiya Halima sallama.

"Inda tace komai ake ciki ta kirata."

Mommy na fita Hajiya Halima ta kira Alhaji mugu inda take shaida masa cewa tabbas tasha gubar.

Bayan kamar 10 to 15 minutes Mommy ta isa gida, tana zuwa ta tarrada Fatima kawai a fallo.

Sannu da zuwa tai mata, yawwa Mommy ta Ansa.

Inda Fatima ta kawo mata ruwa, tana sha ta shige ɗaki.

  " Bayan some minutes Yah Ahmad ne ya shigo gida , a Fatima ina Mommy, ina ce dai ta dawo".

Eh, yaya tana ciki.

Okay, a ɗakin Mommy ya shiga, koda ya shiga ya ganta kwance ƙasa bata numfashi ga kumfa da yake bulala ta bakin Mommy.

Mommy meya same ki? Innalillahi wa'inna ilaihin raji'um, Fatima da salma ne suka shigo , kama Mommy suka yi suka fita da ita waje.

Yaya Ahmad yaja mota sai asibiti, ana zuwa aka yi emergency da Mommy.

  "An ɗauki ƴn mintina duk suna nan tsa-tsaye sai cen likita ya fito.

Nan suka yi zuru, suna tambayar ya ake ciki."

A gaskiya saide kuyi haƙuri , domin Allah yayi ma Mommy rasuwa sakamakon gubar da tasha.

Ya Ahmad yace guba.?

Eh,.

Juyowa yayi ya dubi Fatima da salma, yana cewa me Mommy Tasha Bayan dawo warta da gidan Hajiya Halima.

Fatima ce da duk jikin ta ya mutu, ga wani uban tsoro da take ciki.

        
  Magana. ,take,  cikin, kiriniya 
dama.…uhm…ɗazu…uhm ,  tsawo ya daka mata, kiyimin magana mana.

Yayah ruwa tace na bata tasha ta ƙara she kukan da take maƙalewa na kufce mata.

Ruwa Fatima,? Innalillahi wa'inna ilaihin raji'um Fatima ke kashe mana uwa , wayasan me kika mata..…………

A zabure ta tashi daga bacci , sakamakon mum-munan mafarkin da tayi, tana Innalillahi wa'inna ilaihin raji'um.

Salma data shigo yanzu ta dube ta tare da cewa, Fatima lafiya.?

Salma mafarki nayi, Mommy nanan Kota  wuce gidan Hajiya.

Yanzu zata wuce , harma ta fito, Lafiya.?

Ina zuwa Fatima ta faɗa tare da miƙewa ta fice fallo, koda ta fito Mommy na tsaye tana jiran yaya Ahmad ya fito da car key.

"Mommy ina zaki Fatima ta faɗa."

Duban ta Mommy tayi tare da cewa Fatima har kin tashi daga bacci.?.

Eh, Mommy ina zaki.?

Gidan Hajiya Halima, mana .

Hannu wanta ta aza duka biyu tare da cewa, Mommy don Allah kada kije, don Allah ta faɗa tana fidda ƙwolla.

Yayah Ahmad ne daya fito yace , Fatima wlh koni banso zuwan ta gidan ba, amma ta ƙuƙe sai taje.

Murmushi Mommy tayi tare da cewa to shike nan, na fasa kai Ahmad jeka gaya mata...

Okey.....

★*★*★*★*★*★

KANO

Yaune daddy yayi magana da didda, akan cewa wani yazo Neman auren husnah, amma taje tayi mata magana inta amince to shike nan.

Da toh didda ta amsa, tana cewa ya sunan sa .?

Habib.

Okay, nan didda taje ɗakin husnah, a zaune ta same ta bisa kujera, sallama tayi.

"Amsa tayi tana cewa, didda kece aida ke kiraniiii.

Eh ba komai didda ta faɗa tana zama, dama husnah daddyn ku ne ya aiko ni.

Aike kuma didda.?

Ehh, dama wani ne yazo Neman auren ki, sunan sa Habib, kesan dashi kuma ke amince.?

Didda na sanshi, anma ni karatu nake..

Karatu husnah.?

Eh, didda.

To, bari na gaya ma daddyn ku ta faɗa tare da tashi ta fita.

Bayan ta gaya ma daddy baice komai ba..!

★*★*★*★*★*★

RANAR~LAHADI

Tunda safe suke shirye shiryen zuwa Kano, duk sun gama haɗa kayan su, inda sukayi sallama da kowa, har gate Fatima da Salma suka raka su, inda saida motar su ta tashi, sannan su Fatima suka dawo.....

"Suna cikin tafiya driver ke driving sai yaya Ahmad a ɓangaren mai zaman banza , Mommy da hasnah a baya."

Mommy ce ta jawo wayar ta tayi Darling number Hajiya Rukayya ( ƙaunwar ta mahaiyar laila) tana shiga ta ɗauka.

A Mommy'n salma kun taso , yanzu nake so na kira ki.

"Eh, harma mun taɓa tafiya."

Toh, Allah ya kawo ku lpy umma ta faɗa."

Da ameen Mommy ta Ansa tana kashe kiran.

★*★*★*★*★*★

Acen gida kuwa Fatima ce ke magana da salma tana cewa, taje ta ɗora girki domin ita bata jin daɗi...

Nifa Fatima bazan girkin gidan kowa ba.

Toh, shike nan cikin wa Fatima ta faɗa tana shige wa ɗaki...

"Bayan Fatima ta shige mtwsssssss tsaki salma tayi sannan ta shiga kitchen, tana cikin ɗora girki taji anyi sallama, fito wa tayi tana amsa sallama."

Lah, meenal kece yau a gidan mu.?

Murmushi meenal tayi tare da cewa, eh, nice nazo tunda ku bakwo da zumunci ina Fatima?..

Bahaka bane, tana ciki salma ta faɗa tare da nuna ɗakin da Fatima ta shiga.

Wucewa ɗakin meenal tayi tana cewa bari na dubo tah..

Tana shiga ɗakin ta tarrada Fatima zaune bisa bedside drower sai aikin danna waya take.

Jin an fixge wayar yasa ta ɗagowa da sauri, meenal ta gani..

Laaa, meenal kece,? Bismillah Zauna mana.

Xama meenal tayi tana faɗin nice Mana, don Allah ya kawo ni, tunda kee baki taɓa zuwa gidan mu bah.

   "Murmushi Fatima tayi tare da faɗin ba haka bane meenal, wlh bana samun fita ko yanzu ƙaunwar muce ba lpy kwonan mu biyu asibiti."

Ayya Fatima ya jikin ta,? Wlh banda labari dana dubo ta.

Bakomai meenal, ance sai an fitar da ita waje, yanzu sunyi Kano akwai wani asibiti A.P.H aikan sunyi chen..

Ayya Fatima Allah ya bata lpy , yasa a samu nasara.

Da ameen Fatima ta amsa tare da cewa bari na kawo miki ruwa..

A'a, Fatima ki barshi kawai yanzu ma zan wuce.

Toh, meenal dama biyowa kawai kika yi.

Hmmm, kawai meenal tace.

A fallon suka tarrada salma sallama meenal tayi musu, sannan ta wuce........

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
  By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
     

🧡This page 21 dedicated to my brother AL'AMEEN FARUK BUNZA 🧡

PAGE____21

Bismillah_Rahmanin-Rahim.

★*★*★*★*★*★

Alhamdullh, sun isa Kano lpy cikin ƙoshin lpy inda suka sauka gidan Hajiya Rukayya umman laila, a fallo suka iske ta nan aka gagai sa sannan aka kawo musu abin ci suka Chi....

Waya yaya Ahmad ya ɗauka ya kira Abdul-Hakeem inda yake shaida masa sun isa Kano lpy.

"Cewa yayi ya Turo masa address ɗin gidan ga shinan tafe, ."

Da to ya amsa masa, bayan ya kashe ya tura masa text message na address ɗin.!

★*★*★*★*★

Mommy ce zaune a bedroom ɗin Hajiya Rukayya su biyu ne kawai.

Laila ce ta shigo, inda ta gaida Mommy tai musu ya hanya, tana ƙarawa da tambayar ya Fatima da salma.

Duk suna lpy, sun ce ma suna gaida ki sosai Mommy ta faɗa tana murmushi da fuskar ta Dattaku.

Nan laila tace tana amsa wa ina hasanah.?

Tana cen ɗaya bedroom na hagu, umman laila ta faɗa tana murmushi.

Bari na dubo ta ta faɗa tana fita.

"Umman laila ta dubi mommy tace Mommy waini wani asibiti ne ma."

Na manta ban gaya miki ba ƴr uwa a A.P.H ne...

"Lahh, Mommy ai mai wannan asibitin shine mijin Fatima, kuma ɗan yayar Maman ta.

Kallon umma Mommy tayi tare da cewa Rukayya da gaske kike? Lallai akwai Magana, domin bazai taɓa yuwa ba Fatima tazo taya ni jinyar hasanah ba.

Duban ta Umma tayi, tare da cewa, wai ni to haka, zata ci gaba da zama, ita fa matar aure che, kada Allah ya kama mu.

   "Dogon numfashi Mommy ta sauke tare da cewa koni nayi wannan tunani'n amma....... Maganar ce ta katse sakamakon amsa salamar
Da tayi.

Yaya Ahmad ne ya shigo har ƙasa ya gaida su, sannan yace ga Abdul-Hakeem nan yazo duba jikin hasnah..

Nan suka tashi suka yo fallo.

Gaisawa sukayi ya dubi jikin hasnah, nan a gaban su ya kira D.r Salim , yana peaking yace dama baƙin Jigawa ne sun iso,.

  Acen ɓangaren docta yace to sai a kawo yarinya gobe, domin lokacin yana da isasshen time.

da to Abdul-Hakeem ya amsa yana kashe wayar, cema su Mommy yayi gobe su haɗu a asibiti da ƙarfe tara.

Nan ya basu address duk da cewa asibitin ba ɓoyaye bane , sallama yai musu ya tafi.

Yah Ahmad ne  da yayi masa rakiya, suna jingine a jikin mota, Ahmad ne yake Godiya.

  "Duban sa Abdul-Hakeem yayi yace ai yanzu mu abokai ne kuma mun zama ɗaya Allah dai ya bata lpy".

Ameen, Ameen, Ahmad ya amsa.

Nan Abdul ya dubi Ahmad yana cewa wai ni ina ƙaunwar ka, take?.

Wa salma.?

A'a ɗayar.

Kace min wife to be nagane ai jira nake komai ya lafa a sak....... Shuru ya Ahmad yayi jin yana batun sake layi.

Murmushin yaƙe Abdul-Hakeem yayi yana shiga mota zuciyarsa na zafi, inda ya ƙudur ta a ransa cewa wlh koda za'a sake yaƙin duniya saiya mallaki  Fatima a matsayin matar sa.

Cikin Gida Ahmad ya nufa yana tunani a ransa, shi kawai haquri zai yi da Fatima tunda, a na ɗaya ita matar aure ce, na biyu yaga Mommy ko ita bata so badon komai ba sai don ganin take Fatima fa har yanzu igiyoyi uku a bisa kanta.

  Jin yayi karo da mutum ya sashi ɗagowa laila ce tsaye wacce ta dafe kai.

Turo baki tayi tace, oh, yaya lpyr ka saura fa kaɗan ka maida Ni musaka ka rage min farashin sadaki.

"Murmushi yayi wanda ke ƙara masa kyau duk da shi ba fari bane amma yana da kyawo."

Haba ƙaunwar tawa ce zan mayar musaka, aida nima Dole na zama musaki..

Yaya shike nan Mommy tayi ɗaya biyu miskinai ..

Baka ciki.

Yaya me kake tunani haka.?

Ba komai ƙaunwa ta, rasa ta inda zai shararo ƙarya yayi , cewa yayi dama yunwa nake ji.

Ayya, yaya bari na kawo maka abin ci, bata bari yace komai ba tayi tafiyar ta...

Murmushi yayi yana bin bayan ta da kallo...

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
   By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
       {Samha Umar} 🥀

💃This page 22 dedicated to My daughte Nawwal love you so much baby girl 💃
N

PAGE_____ 22

Bismillah_Rahmanin-Rahim.

   _____tana shiga bayan ta haɗa masa Abin ci , Mommy ce tace ina zaki laila..

Mommy yaya ne zan kaima abin ci.

Oh, Ni karima yanzu fa ya gama cin abincib.

Itakam laila fita tayi bata ce komai ba, tunani tabbas tasan yana ɗakin da ya sauka, aiko cikin sas-sarfa ta isa da sallama ɗauke a bakin ta.

Yah Ahmad ne ya amsa , shiga tayi ta kaimai Abin Chi ...

Daban ta yayi yace ke wasa fa nake, ni bana jin yunwa.

Duban shi tayi kamar zata yi kuka, tace to shike nan, tare da sa hannu zata ɗauki tiren abin ci.

Jin an riƙe hannun ta yasa ta ɗagowa , murmushi yayi mata yace zanci ƙaunwatahhh indai zaki Chi.

Tom yaya bari naje zan taya Umma ɗaura girkin dare.

Haba ƙaunwata bazaki tsaya muyi fira ba.?

Kanta kawai ta jij-jiga tana ficewa daga ɗakin.....

★*★*★*★*★*★*★

Tun ƙarfe 08:00am  suka shirya inda baban su laila yace , Mommy taje ita da Ahmad ɗin da laila.

Nan suka karya sannan suka ɗauki hanyar AL'UMMA PRIVATE HOSPITAL APH , Basu sha wahala ba suka isa...

Ya Ahmad ne yace laila dole wannan asibitin tayi suna , abu kamar a ƙasar waje.

Murmushi Mommy tayi tana cewa asibitin ya haɗu, laila ce tace kaɗan ma kuka gani sai mun isa daga chiki , gaba ɗaya ma'aikatan Asibitin rabin su duk ƴan ƙasar waje ne .

Toh, Allah ya bada Sa'a Mommy tace hakan yayi daidai da parking ɗin da Ya Ahmad yayi.

Saida ya kira Abdul-Hakeem yake sanar dashi isowar su, shiko yace ga shinan tafe.

An ɗauki tsawon 5 minutes sannan ya iso, nan ya jagorance su cikin asibitin wacce ke kama da aljannar duniya, domin ko'ina ƙamshi ke tashi da sanyin A.c , baka ganin wilgawan kowa sai turawan likitoci sanye da fararen kaya ..

"Laila tacce to Mommy ke gani ko , eh, wlh laila asibitin yayi."

  Basu tsaya ko'ina ba sai a ofishin D.R SALIM p.a ce zaune bisa kujera bakin office ɗinsa domin sanar dashi abin da ke wakana.

Gaida Abdul-Hakeem tayi domin ta sanshi.

Cewa yayi feenah how are you.

Fine sir two days.

Normal, please tell Dr she hv a gst.

Okay, feenah ta faɗa tana shiga saida tayi knocking .

Tana shiga ta russuna tana cewa excuse sir.

Meye.?

Sir kana da baƙi.

Tell them I don't have time.

Sir, is your friend Abdul-Hakeem with some people.

Sai da yayi tunani sannan ya tuna su waye, sannan ya dube ta yace, okey, zasu iya shigowa.

Fita tayi inda su Mommy suka shigo.

Nan suka zauna, duban su yayi ɗaya bayan ɗaya sai kam laila.
Ina kwona yaya docta...

A laila kina lpy.

Lafiya ƙalau yayah..

Dama ke sansu? Ya faɗa yana nuna su Mommy...

Saida ta murmusa sannan tace , eh wannan yayar Umma ce Mommy ta faɗa tana nuna Mommy.

Mommy Ina kwana ya faɗa.

Lpy docta ya aiki ya gida.

Alhamdullh, laila ce tace wannan kuma yaya na ne ɗan Mommyn , ta faɗa tana nuna Ahmad, wannan kuma itace hasnah autar Mommy marar lafiya.

Ayya, ai na komai Allah yasa ayi a Sa'a, telephone yasa ya kira feenah , tana shigowa yace, jeki kiramin D.r Ali .

Okey, ba'a fi minti goma ba sai ga d.r Ali fari da ganin sa ɗan India ne.

D.r You calling me I hope is nothing.

Murmushi yayi yace, dnt mnd is nothing, I calling you about that girl, ya faɗa yana nuna Hasnah.

Okey sir I'm hearing you.

D.r Ali I need to go lap and tasted her well, plz tasted her with your self, I think you serious doctor , and bring me the result after testing.

Okay sir, juyawa yayi ya dubi hasnah yace baby let's go.

Docta ne yace hasnah je keji Sweet zai siyo Miki, ai kuwa da gudu ta bisa suka fita....

" Duban su docta yayi yace, yanzu za'a je a mata gwoji muga me result zai bayar.
Toh docta Allah ya taimaka..!

Ya Ahmad ne yace to docta yanzu bari muje mu biya kuɗin.

Murmushi docta yayi yace Mommy inshallah na ɗauki nauyin komai tun daga magani har aikin da za'a mata, ba komai ai gida ne.

Mommy ce wacce saida tayi hawaye tace , haba docta abin yayi yawa don Allah ka bari.

Hmmm, Mommy ba komai ko ai ko wani anwa balle ku, (haka kawai yaji yana ƙaunar Mommyn).

Ahmad ma godiya ya kama yi Abdul-Hakeem na taya su, jin ana knocking yasa sukayi shuru, Dr Ali ne ya shigo da murmushi, takardan dake hannun sa ya miƙama docta.

Amsa yayi yana warware wa saida ya gama karanta wa sannan ya juyo ya dubi, Mommy yace inshallah daga yau zata zauna asibiti na tsawon sati ɗaya za'a ɗaurata akan magani kafin sati biyu a mata aikin.

Zasu barta saide zasu iya zuwa duk bayan kwana biyu.

Toh docta Allah ya saka da Alkhairi anan Mommy tayi wa hasnah wayo da cewa allura za'a mata har suka samu suka tafi harda Abdul-Hakeem.

  "Fita docta yayi inda ya kira dr Rakiya matashiyar likita,ya bata maganin hasnah, yace ta kaita Room 808 ita ce zata kula da ita da maganin ta harna tsawon sati ɗaya , kullum za'a kawo kallar abin cin da zata Chi.

Toh, docta taja hannun hasnah suka wuce Room 808.

★*★*★*★*★*★*★*★

Bayan su Mommy sun isa gida cike da farin ciki, a fallo suka tarrada Umma nan sukai mata bayanin komai itama tayi farin ciki, inda tace anjima ita da Mommy zasu je gidan su didda su ƙara yin godiya.

Nan Ya Ahmad yace zai koma idan sati ya cika zai dawo, nan suka amince da hakan, laila har da ƙwollan tafiya'n yayan ta ( nidai nace ko dai…uhm.).

   Muje dai zuwa.

Bayan tafiyar Ya Ahmad da maraice Umma ta kira Abban laila ta sanar dashi zuwa gidan didda.

Sai sun dawo kawai yace, driver ke tuƙasu Mommy Umma Laila baya basu tsaya ko'ina ba sai gidan ALHAJI HASSAN SAUTA , suna parking suka fito, saida suka yi tafiya mai nisa, tsakanin inda sukayi parking da main fallo.

Danna doorbell suka yi imaru mai aiki ce ta buɗe musu ƙofa tana gaida su, amsa sukayi suka shiga didda ce a fallon.

A maraba da Hajiya Rukayya zama sukayi aka gaisa.

Didda ce da bakin ta yaƙi ruwa ( badai son jama'a ba like my mommy) ta dubi laila tana cewa shike nan laila bana ganin ki saida dalili, ko yanzu nasan Hajiya Rukayya ce tazo dake da bazan ganki ba, tunda wacce kike zuwa wurin ta bata nan ta ida zancen yanayin ta na chenzawa...

  " Wlh didda ba haka bane, makaranta muke zuwa, ina husnah dasu Jamila".

Husnah bata nan taje gidan su Jamila.

Ayya, Umma ce tace Didda'n bintu.

"Na'am."

Dama wannan yayata ce a Jigawa take Karima.

Didda ce ta dubi Mommy tana cewa ya hanya? Ya yara?.

Lpy ƙalau wlh,Umma ce ta ɗora da cewa kuma dama autar ita yayata hasnah da Husaini, hasnah ce ke fama da ciwo duk da ƙarancin shekarun ta, an kaita asibiti a cen Jigawa amma sunce sai an fita daita waje.

Toh sai wani bawan Allah yaje cen nandai Umma ta kwashe komai ta gaya didda harda ɗaukan nauyin da docta yayi.

Godiya sukai mata sosai, tana cewa ai babu komai, abin taɓa wa aka kawo musu, bayan sun ɗan taɓa didda tace su isa chiki.

A'a didda mu wucewa zamu yi Mommy ta faɗa tana tashi.

Toh tunda kunƙi, Allah ya bata lafiya saina shigo inshallah, har ƙofar fallo ta raka su, suna fitowa saiga husnah gaida su tayi tana wucewa, nan akayi sallama suka wuce..............

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
   By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
       {Samha Umar} 🥀

💣💣This page 23 dedicated to my best friend KAULATU UMAR FARUK💣💣💣

PAGE____23

Bismillah_Rahamanin-Rahim

★*★*★*★*★*★

D.R SALIM HOUSE

Wai ke sateey baki da hankali? taya zaki ce ki fita bayan kina fama da wannan lalurar dubeki fa ko kunya a ganki bakya yi duk jiki kumbure , docta ne ke magana da sabeeterh  wacce ke tsaye ta rataya gyale, ga jikin ta duk ya kumbura.

  "Haba Honey gidanmu fa zani ba wani gurin ba, sannan kuma jikina ko naka.

Docta ne ya ce wlh ban yarda ba, kada ki kuskura ki fita yaida zancen tare da ficewa....

Mtwssss tsaki taja kana tayo bakin window fallo, labulaye ta yaye inda take leƙonsa har ya shiga mota ya fita, tana ganin haka itama ta fito, mota ɗaya ta shiga domin dama ta ɗauko makulli ne zata fita.

Tana zuwa gate baba mai gadi ya taso , Hajiya mai gida yace kada ki fita.

Ashar ta ɗauko ta ran gaɗa masa gami da cewa tunda gidan uban kane da zaka hanani fita , sannu ubana Ibrahim wlh yi maza ka buɗe gate baka ganin halin da nake ciki, asibiti zani domin na kira wayar docta bata shiga.

Aikuwa da sauri ya buɗe mata gate ta fita bata tsaya tsaya ko'ina ba sai Ƙofar wambai gidan su horn tayi mai gadi ya buɗe tana parking daƙyar take tafiya har ta isa fallo nan ta tarrada mama hannatu.

Sabeeterh lafiyar ki kuwa? na ganki cikin wannan halin?. Jikin mama ta faɗa tana faɗin wash mamana wlh na gaji kawo min ruwa.

Duban ta mama tayi tana cewa bani amsa ta mana.

Haba mama wlh na gaji, wlh mama wannan cikin yana wahalar dani yanda bakya zato, mama don Allah ki kiramin Abba nah in yana gari ina son ganin sa ta faɗa tana fashewa da kuka.

Innalilahi, wa'inna ilaihin rajium, mama ta faɗa tana jawo waya, ta kira Abban sateey.

Yana ɗauka tace Alhaji kana gari.?

Acen ɓangaren bansan ma akace ba, mama dai tace to don Allah kazo gida na yanzu akwai matsala, ɗan daka tawa tayi sannan tace toh to shike nan tana kashe wayan.

Haba sabeeterh ki daina kuka don Allah, ruwa taje ta ɗebo mata daƙyar tasha..

Chen saiga sallamar Alhaji Mugu da gudu sabeeterh ta rungume mahaifin ta, tana ƙara kukan ta, mama ce tayi danne-danne a wayar ta (bari na baku satar amsa recording ta saka)
Tana ajewa tayi sama domin bawa ƴr da uba damar zantawa .

Zama Abban sateey yayi tare da ita yana share mata hawaye ƴr baba kiyi haƙuri , kiyi shuru kesan kece hasken rayuwa ta, ke nake gani naji sanyi idan na tuna rasuwar mamarki, mece damuwar ki?...

Abba na gaji docta ya daina sakin jiki dani, ga kuma wannan cikin,.

Ƴrta saurara na gaya miki wani abu, saida ta gyara zama ta dubi mahaifin ta...

   *Nima fans ku gyara zaman ku dakyau*

★FARKO★

    Sunana cikakke ALHAJI HUSSAINI TUKUR  SAUTA ni ƙanene abokin tagwoici ga mahaifin mijin ki ALHAJI HASSAN SAUTA , shine Hassan nine hussai uwarmu ɗaya uban mu ɗaya.
    
A zahiri sabeeterh tace what Abba kasan me kake faɗah.?

Kworai ƴrta, bayan naso Amina mahaifiyar Fatima amma aka mata miji bani ba shine na gudu nayi cikin Zamfara shine na fara dako ina samun ƴn chenji , amma ina da labarin gida domin wani abokina lukman ɗanchen ne.

Cikin haka na faɗa Katsina acen na haɗu da mahaifiyar ki tana sona sosai amma iyayen ta suka hana sai ta nace sannan aka bari na aure ta , har aka haife ki ta rasu, riƙon ki ya dawo hannun Hannatu ƙaunwar mamanki.

Na dawo cikin ZAMFARA naci gaba da zama , har tsawon shekaru biyar nan na samu labarin Amina ta haihu, har address ɗin ta aka bani.

Rannan faɗa ya haɗani da wani Yusuf na masa aiki yaƙi biyana, nan na shaƙe masa wuya annan take ya mutu.

Saida Abba ya numfasa haɗe da dubin sateey wacce ta tsare sa da ido, murmushi yayi kawai yaci gaba.

Nan aka kirawo ƴn sanda suka kamani suka kaini police station aka shiga kotu, an yimin sauƙi aka yanke min hukunci zuwa gidan yari na har abada.

A ɗaki ɗaya aka haɗani da wasu ƴn daba su uku Auwal, Sulaiman, Kabiru, nan muka yi shawarar gudawa , cikin ikon Allah muka gudu, mafara muka fara zuwa sai gidan A.S.P KAMAL .

Nuna kashe Amina da A.s.p Kamal iya-yen Fatima, daga nan muka rabu kowa ya kama gaban sa, Ni nayi ogun state anan na haɗu da wani mutum Alhaji Salihu mai safaran kwoyoyi daga ƙasashen waje.

Bayan ya ɗorani a harakar ya sake mini kuɗi sosai har komai nasa ya dawo hannu na, rana tsaka na kashesa inda na gudu da komai nasa na dawo Jigawa bayan na kulle bakunan mutane bayan ta hanyar basu kuɗi masu yawa....

  "Ina nan zaune Jigawa ina Safar miyagun kwayoyi kala-kala acen na haɗu da Hajiya Halima itama ƴr hannu ce, aka kamani nayi shekara biyar a gidan kaso duk da wannan ba shine na farko ba ina fitowa na koma Yobe state, ina kuma zuwa dubin ki har kika kawomin maganar aurenki da salim , muka yi wannan maganar dake ( nima dai bansan wacce magana sukayi ba).
  
      "Sabeeterh wannan shine taƙai tatchen      tarihina."

Lallai Abba kaga rayuwa sabeeterh ta faɗa tana kallon Abban ta.

Ƴrta ba wannan ba ina umartanki yanzu basai anjima ba ki koma gidanki, kuma ina so idan kuma mace dan kika koma ki kirani zan gaya miki wani abu komai ya kusa tahowa ƙarshe, inshallah....

To Abba na, sallama taima sa , ko sallama batayi da mama ba ta wuce gida.

Tuƙi take biya titi amma san hankalin ta baya gurin sai tunanin labarin da Abban ta ya bata, taji al'ajabi, a gaskiya Abban ta azzalumi ne ta faɗa tana fashewa da kuka.

Hakan yayi daidai da biyowar wata ƙatuwar tarikita ta banki motar sateey, wacce saida ta koma mul-mula bisa titi kafin ta tsaya guri ɗaya..

  Mutane ne suka taru gurin, daƙyar aka samu
Wasu suka buɗe motar, daƙyar kuma aka jawo sateey wacce bata numfashi kanta sai zubar da jini yake.

Jikarta aka ɗauka inda aka ciro waya, number farko ta khairan an kira kashe, maibi mata 
Khalisat Usman itako ba'a ɗaga ba, sai maibi mata MY HUSBAND aka kira.........

★*★*★*★*★*★*★

Cen baya, "bayan docta ya dawo ya shiga ko'ina baiga sateey ba ransa ne ya ɓaci domin yasan tabbas ta fita.

Fitowa yayi bakin gate inda baba mai gadi yake, baba ya'akayi yarinyar nan ta fita?.

Wlh yallaɓai takura ni yayi, harda zagina bayan da na'iya na buɗe mata ranka ya daɗe.

Bakomai baba ai zata dawo, wayar sa ce dake cikin aljihu ta fara ring, ɗaukowa yayi sunan MY WIFEY ya bayyana kamar bazai ɗaga ba sai Kuma yayi tsaki yana ɗagawa....

Cewa yayi me zaki gayamin kuma bayan ke fita ba tare da izini na ba.?

Acen ɓangaren aka ce baita bace mai wayar tayi accident.

What, innalilahi wa'inna ilaihin rajium, a Ina? Please turomin address ɗin , nan cikin waya yaimata baya ni,.

Mai gadi ne yake cewa, meye ranka ya daɗe, komai baice masa ba ya shige warsa mota.....

Gudu yake shararawa akan titi yana bugun kansa da hannu sai cije leɓe yakai, inda ya hango zan zazon mutane ya nufa, koda ya isa hannu biyu yasa ya cicciɓe ta sai a mota ko sauran mutanen dake tambayar yasan ta baiyi ba ya wuce yana tuƙa motar yana juyawa sit ɗin baya yana kallon ta, wacce sai jini ke fita ga kanta batama numfashi.

  Yana isa Asibitin ya kira manyan doctor's suka shiga emergency da'ita inda shiko waya ya ɗauko ya kira didda yana mata bayani ya kashe yana kashe wa ya kira Mama hannatu itama gaya mata yayi, sannan ya mara ma likitoci baya...

Kusan 2hrs numfashi'n ta ya dawo, fitowa yayi inda yaga didda da Mama hannatu ya nufa, tambayar sa suke ya ake ciki.

Didda sai an mata c.s numfashi'n ta ya dawo, sannan an mata ɗinki a goshi, amma abinda ke cikin ta baya motsi....

To ayi maza docta aje Mama ce ke wannan maganar, inda didda ko bakin magana, nan docta ya cike takardu aka wuce domin mata aiki..

Didda ce ta kira Daddy ta gaya masa komai, cewa yayi to Allah ya raba lpy bari ya kira anty zulai.

Toh, didda tace tana kashewa.......

Alhaji Mugu ne ya kira Mama domin yana barin gida ta kira sa ta gaya masa halin da sateey take ciki..

Shine yanzu ya kirata akan gashinan zuwa asibitin, daƙyar ta lallaɓasa ya haqura da tahowa asibiti.

Isowar anty zulai ne yayi daidai da fitowar docta daga theater room 2 didda ya miƙawa jinjirar dake naɗa cikin towel karɓa tayi.

Didda an mata theater an ciro ƴr mace, amma a gaskiya mahaifar ta tayi rauni watakila ba zata ƙara haihuwa ba....

Toh, salim Allah ya raya.

     Didda ameen Ameen, ƴr taci suna NANA AMEENATU.....

Bakin didda yaƙi rufuwa tace kay salim Allah ya maka Albarka Nagode da kasa sunan ƙanwata
Ɗaya tillo , ina ma Amina nada rai taga wannan abin farin ciki, ina ma ga bintu tayi murna yau ga mai sunan amminta taida hawaye na zubowa a idon ta.

Docta ne yasa hannu yana share mata hawayen, anty zulai ce ta karɓi ƴr tana Masha Allah ƴr kyakyawa sak mahaifin ta Allah ya raya...
Da ameen didda ta amsa.

Nan aka shiga gaya ƴn uwa da abokan arziki, inda sateey har yanzu bata farfaɗo ba, ƴn uwa sai zuwa duba ƴr sukai harda Daddy.

Har dare yayi sateey bata farka ba hankalin mutane ya tashi, nan aka kwona cikin jimami.

Bayan kwona uku har sateey ta farfaɗo washe garin ranar, tana jin ance sunan ɗiyar Amina ta kama mafisa wai ita sunan mahaifiyar ta za'a sama ƴr, saida docta ya taka mata burki sannan tayi shiru amma fa ta ciki na ciki.

Nan taji sauƙi aka sallame su direct gidan Alhaji Hassan sauta suka nufa da'ita, duk da Mama hannatu taso ta koma gidan ta amma sun hana.

Nan aka bata ɗaki a ƙasa, inda AMEENA ke samun kullawa duk da sateey ba sonta take ba , wai a cewar ta ƴr ta wahalar da'ita...

Su Mommy da Umma sunje asibiti sun Ameena.

★*★*★*★*★*★*★

A JIGAWA

Zaune suke a fallo suna cin abinci, Fatima ce ta ɗauko wayar ta dake ring Laila ce.

Peaking tayi tana cewa laila kina duniyar nan kwona biyu.?

Acen ɓangaren dariya laila tayi tana cewa wlh Fatima ba haka bane, kina lpy.?

Lpy laila, ya Mommy da Umma duk suna lpy.?

Lpy ƙalau.

Toh laila ya hasanah.

Hmmm , ai Fatima Mommy na cewa da suka je jiya hasnah na kama kuka wai saita ganki ki taho.

Hhh wayyo ƴr ƙaunwata idan kunje ina gaida ta.

Toh bintu kesan me.?

A'a laila sai kin faɗa.
Sabita ta haihu.
Lah, Meta samu.?
Ƴr macce shekaran jiya Lahadi..
Ayya, ina fatan suna cikin ƙoshin lafiya.
"Lpy Fatima ƴr taci suna NANA AMEENATU.
Da gaske kike laila.?
Wlh koh Fatima.
Kau kice yaya ya haifi Ammita.
Wlh kam Fatima.
Toh , Allah ya raya laila, idan Mommy na kusa kai mata waya.
"To"

Nan laila ta kaima Mommy waya nan suka gaisa suna maganar ya jikin hasnah, sallama suka yi bayan Fatima ta gaisa da Umma.......

PLZ comment and Share ✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
     By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
       {Samha Umar}🥀

*🍯This page 24 dedicated to my Friend AISHA BELLO UMAR (humairath) Ai ke tamkar ƴr uwata ta jini na ɗauke ki shatuuu🍯

PAGE_____24

Bismillah_Rahmanin-Rahim.

★*★*★*★*★*★

KANO

Su Mommy da Umma ne zaune a ɗakin da aka kwontar da Hasnah.

Mommy ce ta dubi Umma tana cewa Wlh Rukayya na gaji haka nan da zaman Fatima kesan da aure a kanta...

   "Yaya haka ne amma saide idan mun mayar da ita asa docta ya sake ta."

To Rukayya hakan yayi anma yanzu ina so tazo nan Kano, ta tayani jinyar hasanah, tunda kega ko motsi hasnah tayi saita kira sunan tah, taƙi yarda da kowa"

To yayya.

Yanzu sai ranar da Ahmad zai zo suzo tare, amma kada ta shigo asibitin bada niƙab.

    Yaya hakan ma yayi.

Rukayya bari ina tausaya Fatima Mommy ta faɗa fuskanta alamar tausayi...

Hasnah ce tace Mommy da gaske anty Fatima zata zo.?

Eh, amma wataƙilla a chenza shawara.

Duban Mommy hasnah tayi tace Mommy...... shigowar docta ne yasa bata faɗi abin da zata faɗa bah!.

gaida Mommy da Umma yayi, amsa sukayi suna tambayar ya mai-jego da ameenatu.

"Suna lpy."

Toh Allah shi raya sai mun ƙara shigowa, tashi sukayi su wuce har sun kai bakin ƙofa hasnah tace Mommy.

Juyowa Mommy tayi tana cewa Na'am ƴr Mommy.

   Fuskar tausayi tayi tace Mommy anty Fatima..... Tari ne ya sarƙeta shi yasa tayi shiru, docta ne ya fara dubata sannan yai mata allurar bacci.

Duban su Mommy yayi yana cewa suyi Haƙuri za'ai mata operation ranar Monday Insha Allah.

Salama sukai masa suna addu'ar Allah ya bada Sa'a yasa a dace, fita sukayi suka wuce war su gida................

★*★*★*★*★*★

Acen Ɓangaren Abdul-Hakeem kuwa kullum soyayyar Fatima ƙara ruruwa take a zuciyarsa, wanda takai kullum baida aiki sai kallon photon ta...

Inda mamie tace ya kwontar da hankalinsa kuma yasa a ransa Insha Allah har ya auri Fatimah an gama.

Haka kuwa ya ƙudur ta a ransa idan Ahmad ya dawo zai amshi number Fatima a gare sa...

★*★*★*★*★*★*★

Zanen sunan AMEENA an maida Two weeks domin sabeeterh ta ƙara samun sauƙin tunda aiki anka mata .

Yau Lahadi ana shirye-shiryen gobe za'ai ma Hasnah c.s docta Salim be zaune a ɗakin da ake jinyar hasanah.

Yayah.

Juyowa yayi ya dubi hasnah da fuskar tausayi, Hasnah me yake faruwa kinga ki daina saka kanki damuwa, Insha Allah zaki samu sauƙi....

Toh, yaya amma naso naga Anty Fatima.

Jin an kira sunan Fatima duk da baisan wacece ba amma sai da yaƙi sunan ya daki ƙirjin sa.

Hasnah kiyi haƙuri Insha Allah zanma Umma magana sai a kawo miki Antyn koh.

Eh, yayah.

Ton kwonta kiyi barcin ki my little , gyara mata kwonciya yayi saida tayi barci sannan ya wuce office ɗin sa...

★*★*★*★*★*★

JIGAWA DUTSE

Bayan Mommy ta kira yah Ahmad ta gaya masa batun zuwan Fatima Kano.

Baiso hakan ba domin ganin yake zata koma ma tsohon mijinta (inji shi ban san waya gaya masa docta tsohon mijin Fatima)!

  Nan dai ya kira Fatima da Salma.

Zaune suke a fallo Fatima da Salma Sai Hussaini dake barci sai yaya Ahmad.

Fatimahhhh.

Na'am yaya.

Dama Mommy ta kirani akan batun wai gobe za'a shiga theater da Hasnah, to shine gobe da zani muje tare dake domin ki kula da Hasnah.

Ta kawo min dalilan da yasa take son kije kamar haka, na ɗaya kinga Salma school take zuwa, na biyu ita Mommy tun Asali bata son zuwa hospital, Chen kuma ita ma Laila school take zuwa, kinga ba zai yiwu ba ta ɗora ma umma jinya ba, kuma a koda yaushe hasnah na kiran sunanki , idan kike je may be zata fi samun sauƙi Fatima.!!!!

Duban sa Fatimah tayi tace yaya nikam ba zani ba , nikam diddatah diddatah ta faɗa tana fashewa da matsanancin kuka haɗe da tashi ta wuce bedroom.

Duban Salma Yaya yayi yace ki tashi kije kikai Hussain ɗaki sannan ki lallashi ƴr uwar ki .

Bayan takai Hussaini ɗaki taje ta samu Fatima wacce ke faman zagga kuka.

Haba fatima wai shin ba zaki yarda da ƙaddara ba , kada ki manta da Allah shi ke tsara wa bawa kaddara sa , mai kyau ko akasin hakan, saboda Allah ya isa dake Fatima ya kamata kiyi hamdallah kisa hannu biyu haɗi da godiya ga Allah akan kaddara da ya ɗora miki.

Fatima wannan abin ya isa haka imma ke gaji da zama da mu Wlh ba matsala You Are free You have right fir your, for doing anything that you love.

Fatima idan kina son mijinki ki koma masa, Fatima ko keso Didda fiye da kowa da komai bane but you're parents is die, you Don't have anybody like Didda.
   
   Fatima Ina tausaya miki kuma ban taɓa miki fatan ki rabu da mijinki ba, ko don hallacin da mahaifiyar sa tai miki amma kuma ............

Salma dakata Fatima ta faɗa haɗe da cewa wa'ennen kalamai naki suna ƙona mini Rai, taya za'ayi na gujeku bayan kummin halacci.

  Sannan kuma ba wai ina gudun jinyar hasanah ba illa ina gudun na haɗu da wani dangin Sauta , amma Ni na amince, bata jira me salma zata ce ba ta tashi ta shiga toilet...

Saida ta wanke face ɗin ta sannan ta fito, bata ko dubi gefen Salma ba tayi waje, ba kowa a fallo nan ta fita waje a harabar gida cen ta baya tayi.

Hango sa tsaye tayi wurin icen ayaba🍌 ƙara sowa tayi gurin sa.

Yayahh.

Bai juyo ba kuma bai amsa ba , kuma tabbas tasan ya jita.

Yaya don Allah kayi haƙuri, ka yafe min, ni bada wata manufa nace ba zani ba amma don Allah kayi haƙuri zani...!

Juyowa yayi ya kalleta face to face yace Fatima ina gudun kije ki haɗu da tsohon mijinki , saboda ina tsananin ƙaunar ki Fatima ina kishin ki...

Hankalin ta ne ya ƙara tashi a zuciyar ta take cewa ina sonka yaya Ahmad amma kun kasa fahimta ina da igiyar aure bisa kaina.

A fili kuwa cewa tayi yaya Insha Allah kada ka damu ni Fatima bintu takace har abada dani dakai ba zamu yi rabewa ba.

Toh nasfil hayar yanzu idan an gama da batun hasnah sai ayi yanda za'ayi a raba auren ki da wancan sai na angwonce.

Cikin tsokana tace angon bazawara ko, ransa ne ya ɓace ita ko ta arche da guda, baiyi yunƙurin Binta ba saima cewa da yayi cikin ɗaga Murya gobe ki shirya da wuri domin za muyi tafiyar safe........

★*★*★*★*★*★*★

KANO'N DABO

GIDAN ALHAJI HASSAN

Shigowar sa kenan fallo , ba kowa a fallon illa kukan ameenatu da yai masa maraba, da sauri ya ƙara sa ɗakin da sabeeterh take.

Koda ya shiga ga sateey zaune bisa sofa riƙe da cup mai ɗauke da Black tea, Sai ɗaya hannun riƙe da waya tana chat, ga Amina bisa bed Sai tsula kuka take.

Da sauri ya ɗauko AMEENA wacce har Muryar ta ta shaƙe nufo sateey yayi bata yi aune ba yasa hannu ya fixge wayar haɗi da cewa.

Baki da hankali sabita? Taya kina jin yarinya baiwar Allah tana kuka amma keyi burus da ita, wannan wane irin hauka ne ko daƙiƙan ci?.

Sateey ce cikin masifa itama ta fara magana haba docta ina da iyaye kuma ni ƴrce ga wasu, yau sati na ɗaya da haihuwa kuma c.s aka mini , Amma docta taya za'ayi naita wahala da ƴr bayan baƙar azabar da nasha wurin haihuwar ta inda fa na mutu? Wlh inda ƴr mutuwa...

Keeeh dakata wlh ina miki gudun fushi na, wlh idan kika kaini bango zan miki abinda zaki gwonmoce mutuwar ki da rayuwar ki.!!!

    Kuka ta fashe dashi tana cewa dama ba sona kake ba taya za'ayi kaduba da docta haihuwar fari nayi amma tun safe banci komai ba sai yanzu na samu na haɗa shayi, hatta wanka Ni naima ƴr.....
    
Kai ina taƙaice maka yau kowa bai shigo ɗaki na ba domin duba lafiya ta kukan makirci ne ya kufce mata..

"Jawo ta tayi jikin sa yana jij-jiga bayan ta haɗe da cewa my sateey kiyi haƙuri bansan haka ake miki ba, amma zanyi maganin komai yau keji matata uwar ƴrƴrnah ummi Amina."

Ɗagowa sateey tayi tasa hannu biyu ta talkafo fuskar sa tana cewa mijina kaine komai nawa a kullum a koda yaushe inaima Allah godiya ɗaya bani kai a matsayin mijina.

Ada Ina tunanin rashin mama ne a kusa Dani yasaka Hakan.

Ba komai my sateey Insha Allah zan zamto garkuwar ki.

Murmusa sateey tayi haɗe da karɓa meenal ta bata nono.

Tashi yayi yai mata kiss a forehead ɗin ta yana fita, koda ya fito fallo ba kowa.

Upstairs ya hau sai fallon Didda, tun a fallo yake jiyo dariyar su a bedroom, maganar Jamila ce yaji tana ce ai husnah an ni wlh da badon meenal ba da Bama naje ɗakin anty sateey ba , amma wai saboda kawai naji kukan meenal naje wai mike haɗina da ƴrtah na fitan mata daga ɗaki....

Didda ce tayi magana tana cewa haba Jamila meya kaiki gurin ta? Koni naje kawai naima Amina wanka na fito tana ma mutane wani kallo.

Ni Ko kallo bata isheni ba kuma shi Salim da yake ɗaukarta wata aba sai yayi nadama (kekan Didda kibar a'a hakan mana sabeeterh team kundai ji koh.)

Fasa shiga yayi ɗakin ya juya ya koma zuciyarsa a zuciyarsa yana tunani'n shin wacece Sabeeterh? Ya kasa fa gane mata da tunanin nan ya koma gidan sa........"

PLZ comment and Share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
  By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
    {Samha Umar}🥀
    

 page 25 dedicated to you HUSAINA THALEED Ina ƙaunar ki🍉.

PAGE____25

Bismillah_Rahmanin-Rahim.

★*★*★*★*★*★

KANO 

Da yake tunda safe su Fatima suka kamo hanyar Kano haka sukayi saurin isowa,..

Anan gidan umma suka, a gaskiya Fatima tayi kewar garin suna isa suka rungume juna ita da laila.

A gaskiya laila nayi kewar ki matuƙa.

Nima ƙawata a koda yaushe ina tunanin ki.

Juyowa Fatima tayi ta gaida Mommy da Umma zazzauna wa akayi aka sake gaisawa.

★*★*★*★*★*★

Acen Ɓangaren kuwa tunda safe aka shiga operation da Hasnah, bayan su Mommy sunje sannan docta yace ko bayan an fito da ita su bari har gobe Thursday su dawo.....

Shi ko ya Ahmad suna'isowa ya kira Abdul-Hakeem inda yake sanar dashi sun iso Kano.

      Basu fi 30 minutes da isowa ba ga Abdul-Hakeem , a fallo suka gaisa dasu ,sannan ya fito ya wuce gida.

Tsayawa yayi yana tunani'n tabbas yau ko'ana yinta saiya gayawa Fatima yana sonta, dubara ce ta faɗo masa aiko nan da nan yace uhm..Fatih don Allah zoki karɓi saƙo.

Bai jira mai zata ce ba ya wuce, Fatima ce ta tashi taje sai Umma tace haba bintu zauna ki huta bari laila taje.

Ki bari taje kawai Mommy ta faɗa tana murmushi...

Nam Fatima ta wuce.

A bakin motar sa ta iske sa tsaye,.

Ayya Fatima magana zamu yi.

Juyowa tayi ta dube sa tana cewa ina ji yaya Hakeem.

Fatimahhhh sonki nake kuma da Aure, a gaskiya tun sa'adda na ganki naji zuciya ta ta kamu da wani matsananci sonki.

Idanu Fatima ta zaro tana cewa na shiga uku yaya sona fa.?

Eh, Fatima wlh ban taɓa jin ina son wata ƴr mace a duniyar nan ba bayan keeeh, hannun Fatima ya jawo ya ɗora saitin heat ɗin shi yana cewa Fatima my heart is beating saboda shaukin sonki.

Fixge hannun ta tayi tana duban yaya Abdul-Hakeem tana cewa yaya Abdul-Hakeem nifa matar aure.....kasa ƙara sawa tayi sakamakon kukan daya kufce mata.

Da gudu tayi cikin gida taci Sa'a na kowa a fallo ɗakin laila ta nufa, faɗawa jikin laila tayi wacce fitowar ta kenan daga wanka.

Jij-jiga ta laila ta fara yi tana cewa Fatima lafiyar ki kuwa?, Zama tayi bisa bed Tare da ɗago kan Fatima tana ƙara tambayar tah....

Laila ya Abdul-Hakeem ke sona ya zanyi ga yaya Ahmad na masa alƙawarin zan aure sa, Fatima ina cikin fushin ubangiji ga auren yaya docta dake kaina, kai ina tsaka mai wuya...!

Dafata laila tayi tana cewa fatin'didda kibar komai ga Allah yay miki zaɓi mafi alkhairi, Please stop crying go and ablution it's time for zuhur prayer.

Saida Fatima ta ɗago da kyau ta dubi laila, murmushi tayi haɗe da cewa , laila every day I'm happy do yo no why.?

Jij-jiga Kai kawai laila tayi.

But i have you, you are best friend, Laila you are my everything, Laila some people are hated me but you are loving me.

Laila you help my life the time that I'm in danger's, I don't know how I can thank to you.

Laila I love you I promise to do anything that make you happy, if it's my i will dedicated it to you and my Didda.

Hannu laila tasa ta rufe wa Fatima baki tana cewa Fatima ƙawa ta gari itace wacce a kowani halli ba zata guji ƙawarta ba, ba komai je kiyo alwala.

Itama laila tashi tayi domin yin salla itama...

Mommy datazo shigowa tun dawowan Fatima taga tana cikin wani halli shine ta biyo ta , jin magan ganun su ita da laila yasa ta fita fallo....!

Tana fitowa bata tsaya ko'ina ba sai baya cen inda aka ba yaya Ahmad ɗaki, tana shigowa tayi sallama, amsa wa yayi yana zaune bisa bed riƙe da wayar sa.

Ɗagowa yayi yace Mommy kece da kanki anan aida ke kirani.

Saida ta zauna gefen sa sannan tace ba komai badai nazo ba, magana nazo muyi.

Ɗagowa yayi ya dubi Mommy sannan yace Mommy na Ina jinki.

Toh, da farko Ahmad kada ka manta Fatima nada auren wani akan ta, taya zaka furta kalmar so gare ta bayan kasan haramun ne.

Kansa a ƙasa yace Mommy haka ne amma kiyi haƙuri.

Ba batun haquri Ahmad ina so ka fidda Fatima a ranka, ka ɗauke ta kamar yanda ka ɗauki salma kaji ɗan albarka....

Duban Mommy yayi yace Insha Allah Mommy na Miki alqawari.

       Allah maka albarka, sai wata alfarma kuma ko umarni duk yanda ka ɗauka.

Dafa hannun Mommy yayi yace Mommy duk abinda kika ce shi zan ɗauka koda kuwa zan rasa raina.

Toh, so nike ka auri laila ƴr Uwar ka, duk da bansan ko tanada wanda take so ba, amma nasan ba'a tsayar mata miji ba, ba dole bane ka tambaye ta kaji.

Saida yayi dariya yace an gama Maman ƴn biyu.

Saida ta dafa kansa sannan ta miƙe tace to na wuce ya'yan twins , saida yayi mata rakiya sannan ya koma ɗakin........

★*★*★*★*★*★

Cikin ƙunar rai rashin Ansar da Fatima ta bashi ya shiga Mota yana fita daga gidan..

Gudu yake tsulawa ya doshi unguwar zoom road bai tsaya a ko'ina ba sai a gate ɗin gidan su.

Yana ta horn maigadi yaqi buɗewa sai cen ya buɗe, aikuwa nan ya rufe sa da faɗa yana sauke haushin Fatima.....

Cikin gida ya shige, tun daga ƙofa yake kiran mamie mami cikin sauri ta fito tana kiran inalilahi lafiya Abdul me yake faruwa waya taɓa ka, a jere tayi wa'ennan tambayoyin.

Rasa me zai amsa mata yayi duban ta yayi yana cewa mamie Fatima Fatima ta kasa fahimtar irin son da nake mata..

Kansa ne ya fara juyawa bisa kushin ya zauna, mamie ce ta kira sunan sa, amma ya kasa amsa mata.

Wayar ta ta ɗauka ta kira Dr Mustapha (likitan su) inda yace gashi nan tafe.

Tana kashe wayar ta kama Abdul Sai bedroom ɗin ta kwontar dashi tayi, inda shika yake dafe da kansa dake mugun ciwo, yana jin zuciyarsa ta masa nauyi...

Mamie ce ta fara magana my son kayi haƙuri koma miye Insha Allah zaka ji sauƙi, na kira docta yana zuwa, sannan banson na kira Daddyn ka domin hankalin sa zai tashi tunda meeting sunka je Dubai kuma inaji sai jibi zai dawo....!!!!

Bai tamka ma Mamie bah.

Jin ana knocking ya sata fita tana buɗe wa Dr Mustapha ne, gaisawa sukayi sannan ta basa hanya ya shigo.

Itace ta masa jagora har bedroom ɗin ta , Abin awo ya ɗauka ya aunasa, allura biyu ya masa sannan ya dubi mamie yana cewa.

Hajiya ba wata matsala bace illa yasa damuwa a ranshi da ɓacin rai shine ya jawo masa ciwon kai amma na masa allura Insha Allah yana tashi zaiji ya warke, kuma gashi a siya wa'ennan magunguna ya miƙa mata takarda wacce ya rubuta sunayen magunguna.

    Toh dr ngd, drower ta buɗe kuɗi ta ɗauko wa'yanda sunkai 20k ta basa...
    
"Godiya yai mata ta rakasa, saida yace a kula da shan magani."

Toh dr Insha Allah...........

PLZ comment and Share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
   By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
      {Samha Umar}🥀

This page 26 dedicated to my friend RUMAISA luv you so much my Rumy 🤩🤩🤩

PAGE____26

Bismillah_Rahmanin-Rahim.

★*★*★*★*★*★
ALHAJI HASSAN SAUTA HOUSE

Didda ce zaune a main fallo Sai husnah dake zaune ita da Jamila, (tunda aka haihu jameey ta dawo gidan wai ita sai anyi suna).

Ɗagowa daga kallon wayar da suke sukayi suna ƙyal-ƙyalewa da dariya, didda ce ta dubesu tana cewa ku lafiyar ku.

Jamila ce tace kedai didda wani comedy ne muke kallo, Allah ya kyauta kawai didda tace.

   Husnah ce tace kesan me didda.?

A'a saikin faɗa.

Wlh kedai didda fita muke son yi sayayya kinga next week ne suna.

Toh ai sai kubari idan daddyn ku ya dawo ku gaya masa ko kuma idan ya'yan ku yazo.

Ton didda Jamila ta amsa.

Jin ana knocking yasa didda cewa husnah jeki duba waye, Jamila ce ta tashi ta wuce 'tana cewa didda ni zan buɗe...!

"Tana buɗe wa taga ashe Anty zulai ce rungume ta tayi tana cewa lah anty kece,? Toh sannu da zuwa."

  Toh ɗagani kada ki kada ni, sakin ta tayi suka ƙarasa fallow.

Husnah ce tace sannu da zuwa Anty.

Yawwa tace inda ta dubi didda tace ina wuni didda.

tana dariya tacce lafiya zulai ashe kina hanya.

Eh, wlh ta faɗa tana zama bisa kujera....

"Didda ce tace ke husnah jeki ɗauko mata Amo, saida husnah ta tashi sanna tace haba didda Amo fa inama kice Meenal.

   Naƙi zoki koyan ta faɗa tana bugota, da gudu ta wuce ɗakin sateey.

Ta shiga sallama ɗauke a bakin ta, ciki-ciki sabita ta amsa..

Shigowa husnah tayi ko duban inda sateey take batayi ba.

Amina dake bacci bisa ɗan bed ɗinsu na jarirai tasa hannu ta ɗauka, ta juyo haka ga sateey tsaye gaban ta..!

Bani ƴrtah.

Hararar ta husnah tayi tace nakeji bake kaɗai ce kike da iko da meenat ba ...

   Merane baki sateey tayi tare da miƙa hannu tana cewa i said give me my daughter.

Banke ta husnah tayi ta wuce ta ta fita daga ɗakin, kwofa sateey tayi tana cewa kun jagulo ƙaya dodo....

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
   By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
      {Samha Umar}🥀

*This page 27 dedicated to Maryam Umar 💖🍭*

PAGE_____27

Bismillah_Rahmanin-Rahim.

★*★*★*★*★*★*★
 THURSDAY

"Suna gama breakfast suka fara shirye-shirye'n zuwa hospital."
Fatima ce ta fito daga bedroom less me a jikin ta, ɗinkin riga da skirt, baƙine mai adon flowers red and pink, gyale ta yana sai kuma flat shoes ɗinta pink and hand bag pink.

A fallo tazo ta tsaya, Mommy ce zaune sanye da hijabi itama da shirin fita take.

Duban ta Fatimah tayi ta ce Mommy na shirya.!
Toh muje yayanki ma ya fita, su Rukayya sai zuwa anjima zasu zo, ke ɗauko niƙab.

 "Eh Mommy yana a hand bag ɗita."

Toh, muje.

Suna fitowa harabar gidan inda Umma tayo musu rakiya, saida suka shiga motar ya tayar..

Suna barin gidan ya yanki titi, Fatimah ce tayi ajiyar zuciya hand bag ɗin ta ta buɗe ta ɗauko niƙab ɗaurawa tayi akan fuskanta, tayi mata kyau sosai.!

 Ba wanda yacewa ɗan'uwan sa ƙalla, kai tsaye sai *AL'UMMA PRIVATE HOSPITAL*.

Yana parking gaban Fatimah ya wani irin bada dam da sauri zuciyar ta ke bugawa, suka fito suka tunkari cikin asibitin inda ta gyara yanin gyalen tah".

*FANS yakuke gani ? Shin kuwa ba ranar asirin Fatimah ne ba? Anya kuwa Fatimah na fitowa asibiti lafiya, kada ku manta didda nanan tafe .*

*Toh yah Abdul-Hakeem ya zaiyi da soyayyar Fatimah tunda shi yah Ahmad ya haƙura .*

*Kada ku manta sabeeterh ta barwa docta AMO, shin zata'iya kuwa.*

Toh duk wa'ennan amso-shin ku biyo Alƙalamin Ƴr mutan Kebbi  da sannu zaku san komai, .

________suna shiga cikin hospital a office ɗin Dr salim suka tsaya , Dr Ali ne daya biyo ta wurin, tsayawa yayi suka gaisa inda Yah Ahmad ke tambayar sa ko docta ya shigo.

  A'a Dr Ali yace yana ƙarawa da tun jiya ƙarfe tara daya shigo ya tarar hasnah ta farfaɗo kuma an dace, yanzu tana ɗakin hutu yace idan kun zo a kaiku..!

  Toh suka ce inda suka bi bayan sa, sai Aminiti Room 117 suka tsaya, a bakin ƙofa ya tsaya inda ya nuna musu sannan ya wuce.

"Shiga sukayi ciki ɗauke da sallama, ɗakin sanyin A.c ke tashi haɗe da ƙamshin air freshener"
Ga hasnah kwance bisa bed idanu wanta a buɗe , sai hannun ta sanye da robar ƙarin jini.
Gefen gado kuwa wata budurwa ce zaune bisa filastik chair , ita ce ta ɗago ta dubi su Mommy tabbas ta ganesu, murmushi tayi tare da cewa maraban ku Mommy, Kinga tun ɗazu take cewa ina su Mommy'n tah suke.

Mommy ce ta ƙarasa bakin gadon sannan tace aigamu mun iso , zama gefen ƙafa-funta tayi tana shafa fuskar hasnah wacce ta kafe ta da ido.
 Cewa Mommy tayi yanzu kam ga Mommy'n ki, kinji , Turo baki tana cewa to Mommy anty fatinah.

Oh, anty Bata zoba my daughter gadai ya'yan ki.

Kuka ta fara bil haƙƙi Rakiya ce tace Hasnah abin kuka baya miki wuya , ai tunda Kinga Mommy shikenan komai lafiya."

  Hmm kedai barta Mommy ta faɗa tana ɗago kanta, Fatima ta kira.
Aiko saiga Fatima wacce ta cire niƙab , hasnah na ganin ta ta washe baki.

Har inda take Fatima ta ƙarasa tana riƙo hannun ta haɗe da cewa muhasnah tah, yau ga antynki tazo...!

Anty ina anty Salma .
Tana lafiya tana miki sannu, tace ma na kiraki ku gaisa.

Toh ina Hussain ɗina.
Hussain lafiya har yanzu komai aka muku a class saiya miki copying note, assignment duk yana miki.

Nan Rakiya ta kawo ma Fatima kujera, tana fita daga ɗakin.
Hanyar office ɗin Dr salim ta nufa, tana isa ƙofar shima isowar sa kenan, sanye yake da kayan likitoci wa'enda sai kace donshi akayi su, ya dawo Black cover shops , Sai farin siririn glass na ido, kana iya hango sexy eyes ɗinshi, gashin sa na ka kwance lub-lub dashi ga sajen daya ƙara masa kyau.

Tafiya yake cikin ƙasaita kamar jinin sarauta , gefe kuma P.A ce riƙe da jakarsa wacce ke ɗauke da way'n su takardu da yake aiki dasu.

Yana ƙarasowa Rakiya ta ɗan russuna tana cewa Good morning sir.
Morning kawai yace yana ƙoƙarin shigewa office ɗin sa.
Ɗan sosa ƙeya tayi tana cewa sir ƴn'uwan hasnah sunzo, suna can tare da ita.
Bai juyoba yace, okey ke Bata maganin safe domin inshallah next Monday za'a sallame su.
Okay sir na Bata.
Toh zan shiga dubata zuwa anjima.
Okey, sir we have new patient her file is with me, I check her, she's pregnant, Amma ɗan nada matsala, na bata list ɗin magani taje pharmacy ta siyo.

Juyowa yayi yace mata, okey, give the file to  D.r Hashim.
Yana faɗar hakan ya shige office Wanda p.a ta buɗe masa.

Yana shiga ya cire White cover tp ɗin jikin sa ya ajiye.
Wa'ennan files da p.a ta shigo dasu ya ɗauko ya fara dubawa , yi yakai yana kallon Time .

Cen Sai ya ɗauki telephone ya fara kira,ana ɗauka cewa yayi , go and call D.r Shiva and rajhave for me, ya aje wayar.

   Ya ɗauko biro ya fara rubutu ga wata takarda, after some minutes aka fara knocking.
Yes come in.

Buɗe ƙofar akayi wasu likita wa su biyu maza suka shigo ba zasufi warin sa ba, da ganin su ba ƴn nan bane ...

Ƙarasowa ciki sukayi suna gaidasa, Good morning sir.
Morning have a sit ya faɗa yana nuna musu kujerun da yatsa,.

   Zama sukayi duban na right hand ɗin sa yayi, yace D.r Rajhave.
Yes sir.
Please list to me.
Okey sir.
Yesterday Dr homeos call me almust 06:00, we talk about new heat drugs.......

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
  By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
      {Samha Umar}🥀

This page 28 dedicated to Small Mom AMINA love you so much 📿📿💏

PAGE_____28

Bismillah_Rahmanin-Rahim.

______she tell me if I have time, she wan't see me in this month, we have new doctors meeting on 28 may.

That meeting is about heat sickness , and how we wan't control it,so idt wnt t g that meeting because that hsptl need m a lot, you rajhave and shiva I'm expecting one of you attend meeting.

  Dr rijhave ne ya dubi shiva suka kalli juna sannan suka maida kallon su ga docta ,
Shima duban su yayi yana cewa That's all you can go.

  Okay sir, tashi sukayi suka wuce kowa na saƙa wani abu a ransa.

Suna fita ya miƙe st ɗinsa ya ɗauka yasa yana fita, cen gefen hagun sa yabi ɗakuna jere ƙofar shiga an rubuta AMINITI (ROOM'S) PART 1,
Ɗakunan ya fara shiga, cen yakai room 117 dukda akwai ɗakunan da bai shiga ba.

"Da sallama ya shiga ɗakin da aka kwantar da hasnah, Mommy ce dake zaune ɗakin ta amsa."

Ƙarasowa yayi yana murmushi, gaida Mommy yayi yana tambayar ya mai jiki.
Da sauƙi Mommy ta bada amsa.

  Hasnah ce tace Yah likita.
Ɗagowa yayi tare da nufarta, nan ya jawo kujerar wurin ta, zama yayi ya jawo hannun ta yana cewa little hasnah ya jikin ki.?

Cewa tayi da sauƙi yaya ni zan bika.
Murmushi yayi yana cewa zuwa ina little.
Inda zaka ni na gaji zaman asibiti kaga Mommy Bata Sona Anty ma inaga ta daina sona tunda....

  "Ya'isa , ya'isa kiyi haquri ai wani satima za'a baki sallama kinji my little yanzu bari rakiya zata kawo miki Abin cin ki."
 Toh yaya.

Miƙewa yayi drip ɗin da'aka sa mata ya cire yana duban Mommy yana cewa Mommy yanzu za'a kawo mata abinci sai a duba idan da buƙatar wani abin.

Godiya Mommy tayiwa docta tana cewa AMINA.

Tana lafiya ya bata amsa yana wucewa, yana buɗe ƙofar itama ta iso kenan, kiciɓis sukayi suna kallon juna, cikin masifa yake cewa Are You a mad bakida hankali mtwsss yaja tsaki tare da jayeta gefe ya wuce yana kiran aikin banza, da gani matar aure ce tunda ga niƙabi a fuskanta amma ba kamun kai mtsww ya sake jan wani tsaki yana barin gurin....!

Tunda ya wuce taji wani irin haushi wannan abin tayama shi baiga abinda ya mataba zai kama ta da masifa, kenan docta bai canza halinsa ba..
Take taji kewar didda ya kamata tabbas da'ace da didda taci karo koda ace ancenza mata halitta zata ganeta, amma shi ko'a jikin sa mutuwar ta.
Tabbas idan har komai ya dawo dai-dai zata ce didda tasa ya sake ta ta auri mai sonta..

Itama tsaki tayi tana shiga ciki, a har kun dawo Mommy ta faɗa tana kallon Fatima.
 "Eh Mommy Yaya ya wuce cikin gari.

Hijabin'ta ta cire bayan ta cire niƙab, zama tayi a'inda docta ya tashi tana cewa Mommy sai yaushe zamu tafi gida wai..

Eh, to docta yace sai wani sati yanzu ma yafita.
Okey, Mommy ina zuwa, toilet ta shiga haushi ne ya kamata ganin har yanzu ƙamshin turaren docta da take ji bai bar hamchin ta ba.

   Saida tayi kusan 30 minutes sannan ta fito zama tayi kusa da hasnah bayan ta ɗauki wayar ta, Contact ta shiga sis-Salma ta kamo ring 1 aka ɗauka.

"Bayan sun gaisa, salma tace ya hasnah taji sauƙi".

Da, eh Fatima ta amsa.!

Fatima jiya meenal tazo kuna tafiya ta kawo mana invitation auren ta on 29 May.

Ƴr fuska Fatima tayi kamar salma na gaban ta tace ayya sister na wlh ban kyauta mataba 
Kinga shekaran jiya naga missed call nata amma ban kiraba amma yanzu zan kirata, ina Hussain.?

Yana Lafiya."

Ayya kinga ma yaya Nanan dawowa gobe ko jibi amma ga hasnah ku gaisa ta faɗa tana miƙama hasnah Waya.

Saida ta dundure baki sannan tace ai Anty salma Ni nayi fushi dake tunda baki nemeni, ni da Husaini ne kawai banyi faɗa ba...!

Saida salma tayi dariya sannan tace to haba my hasnah kiyi haquri kinji, ya jikin ki..?

Aini lafiya ta ƙalau jibi ma zamu dawo kuma nayi missing ɗin school..

Toh shike nan ai yanzu ba komai sai kun dawo..!

Toh Anty salma kice ma Husaini ina gaida sa.
Da to salma ta amsa tana yanke kiran...!

Amsa wayar Fatima tayi ta kamo number meenal, darling tayi har ta katse ba'a yi peaking ba, sake kira tayi nan ma saida ta kusa tsinkewa akayi peaking..

Salama fatima tayi, a ɗaya ɓangaren cewa akayi Wa'alaiki-salam wlh Amina bata kusa.

Jin muryam maman meenal yasa Fatima cewa lah mama ina wuni ya gida ya yara.?

Da lafiya maman meenal ta'amsa tana cewa don Allah wacece.?

Murmushi Fatima tayi tana cewa Mama Fatima ce.
Ayya Fatima yakike wlh ko ban gane kiba, don bamma duba suna ba, amma AMINA na gayamin keh, Allah dai bai nufa munga juna ba har yanzu.

  Wlh mama haka ne, amma don Allah kuyi haquri idan mun dawo zan shigo.

Toh Fatima ya mai-jiki .?
Lafiya Mama ina ƙannen mu.?
Kowa lafiya ki gaida Mommyn ku.
To mama kice ta kirani Fatima ta faɗa tana kashe wayar , duban Mommy tayi tana cewa Mommy Maman meenal na gaida ki.
"Toh ina amsawa" .

★*★*★*★*★*★*★

*GIDAN ALHAJI HASSAN SAUTA*

Handle ɗin ƙofar didda suka murɗa a tare suka shigo ciki.

Didda dake sanye da doguwar rigar roba ta manya sai hula data kulle dogon gashin ta, zaune bisa sofa take tana riƙe da waya, ɗagowa tayi tana cewa a ƴn biyu na.

Saida suka kalli juna sannan Jamila dake riqe da Meenal tace didda mun fasa tafiya asibiti.?

Duban ta didda tayi tace , jk Jamila badai son yawo ba, nikam cewa nayi mu bari har gobe, kinga antyn ku Nanan tafe kuma ga meenal yasso gobe asan yanda za'ayi Kada ku damu kinji ƴaƴan didda.

Toh suka ce, sannan suka fita...!

★*★*★*★*★★*★

Acen bangaren Sabeeterh kuwa, kwana kuka tayi safiya na wayewa ta kira khairat ta ce Don Allah tazo da sauri tana buƙatar ta.

Toh khairat tace, sannan tace sai zuwa sha-biyu zata shigo..!

Ai kuwa sha-biyu nayi ga khairat, ba kowa a fallon ɗakin sateey ta shiga, ganin sateey tayi sanye da riga da wando jeans kanta ba ko ɗan kwoli kamar wata inyamura tayi tagumi bata ma ji sallamar khairat ba.

  Saida khairat ta dafata, ɗagowa tayi ganin khairat yasa ta fashewa da kuka.
Zama khairat tayi tare da ɗora kan sateey a kafaɗar ta, tana cewa ki daina kuka kimin bayani ƙawata.

"Nan sateey ta kwashe komai ta gayama khairat.
Mtwsss, tsaki khairat tayi tana ture sateey daga jikin ta haɗe da cewa, lalle sateey bakida hankali Kuma komai ya faru ke kika ja, tunda ƙaramar ƙwaƙwalwa gareki, a kullum ina jan kunnen ki kiyi tawakkali ki rungumi auren ki amma ke ba haka ba.."

   Allah ya baki juna biyu amma ke kenan ki zubar da cikin a haka Allah ya nuna miki ikon sa aka haifi MEENAT, gashi ke tafka babban kuskure, kuma wlh ko nice docta da ko ganin MEENAT ba zaki ƙara yi ba shashasha ana nuna miki Gabas kina kallon yamma.

Kukan ta ne ya ƙaru ta dubi tana cewa khairat zuciya ta tafi ƙarfina shi yasa amma don Allah ki gaya min mafita.

Ko kallon ta khairat batayi ba tace shawara ɗaya shine ki nemi gafarar mijin ki, in yayarda ya baki ƴrki to idan kuma bai yarda ba saiki haqura.

Haqura fa khairat ?, Sabeeterh ta faɗa tana dafe zuciya.
Jin sallama yasa su amsawa Mama-hannatu ce .

Sallama tayi , a tare suka amsa.
Cewa tayi to ke lafiyar ki? Kuma ki kimtsa da baƙi muke ƴn tarbon Barka suna fallo kuyi ku fito.

Toh khairat tace mama ta fita cen fallo.

"Fallon didda cike yake dasu Anty zulai da sauran mata hayaniya ke tashi wurin."

Didda ce tace to zulai kuje kukai kayan ga ƴn'uwan Sabeeterh, suzo suna cen fallo, miƙewa sukayi suka fara jidan kaya.

Hajiya sutura ce ta juyo tana cewa didda wai nikam ina jariyar naje wurin maman ta sunce tana nan.

Oh, haka ne tana ciki ɗazu Jamila tazo da'ita , saida Hajiya sutura taje har ɗakin ta ɗauko Amo sannan suka wuce.

A Fallon suka samu mama hannatu bayan an gaggaisa suka nufi ɗakin sateey.
Nan aka aje kayan Barka su Anty kan suka tafi, a nan suka bar Aminat wurin Maman ta (domin ba wanda yasan Sateey ta yafe meenal.)..!

Bayan fitar su Anty zulai, nan su mama hannatu suka shiga buɗe kaya suna kallo .
Gaskiya sunyi kyau wa'ennan kayan kamar ƴr shugaban ƙasa .
Kai kuɗi da daɗi wata Inna Rashida ƙaunwar mama hannatu ke wannan maganar.

Mama hannatu ce tace haka ne kam, ai shiyasa ma da suka ce abar musu ƴr na yarda.
 
   Sabeeterh kam komai bata ce ba domin tun sadda Hajiya sutura (ƙawar didda) ta bata Amo da zasu fita, bata damuba tana nan riqe da ƴrtah.

Nan aka fidda na dangi sannan su Mama hannatu da sauran ƴn'uwa suka wuce.

Bayan tafiyar su, khairat ta miƙe tana cewa itama wucewa zata yi .
Toh khairat ki ɗauki wani abu mana cikin kayan.

A'a sateey NGD nidai sai jibi zan koma shigowa harda su abida da Habibah, da Hafsah.

  "Cikin marai-raicewa Sabeeterh tace din Allah ƙawata ki ɗauka , ganin khairat bata da niyyar ɗaukan wani abu yasa sabita aje meenal ta tashi...!"

Akwati ta buɗe turmin atamfa Holland ta ɗauko mai green da fari da salsa da turaren natural music ta bama khairat dakyar khairat ta amsa.

Sannan Sabeeterh ta buɗe wata hand bag ɗin ta kuɗi ta ɗauko wa'enda sun kai 200,000 ta miƙama khairat, tana cewa khairat wa'ennan kuɗin na sayayyar biki ne na baki wuƙa da nama, kije ayi duk abinda ya kamata,
Zanyo miki transfer 800,000 kega one million idan basu isa ba ki kirani , don Allah ki kirani ina so wannan bikin yayi suna a cikin wannan jahar.

Toh sateey zaki gani, nan sukayi sallama khairat ta tafi.

★*★*★*★*★*★
Cen ɓangaren didda saida su Hajiya sutura sukaci abinci sannan suka wuce gida, ya rage sai Anty zulai.

Suna zaune Fallon didda Anty ce tace gaskiya didda abinda kikayi kin birgeni .

Duban Anty zulai didda tayi tana cewa name kuma.?

Uwar sabita hannatu tace miki batun kayan gefen su sai suzo kika ce su barshi Bama buƙatar komai daga gare su.

Murmushi didda tayi tana cewa haba zulai, kosu dai faɗa kawai sukayi amma sun-san Bama buƙatar komai.

   "Husnah ce ta shigo tana cewa Anty, didda, inaji fa an barwa waccan MEENAT .
Anty zulai ce tace eh fa haka ne domin ɗazu da tayi kuka Hajiya sutura ta miƙama Sabeeterh ita.

Husnah ce tace lah, bari naje na karɓo ta.

Didda ce tace a'a husnah kesan bata da mutum ci, ki bari Ni naje yafi.

Haka ne keya kamata kije ta inji Anty zulai
Tashi didda tayi tana cewa ina zuwa.

  Tana fita sai ɗakin Sabeeterh, sallama tayi Sabeeterh kam bata ma san tana yi ba, domin hankalin ta naga MEENAT da take shayar wa tana mata wasa.

Ƙara wata sallama didda tayi, sai sannan Sabeeterh ta amsa tana ɗagowa, ganin didda saida gaban ta ya faɗi.

"Isowa didda tayi har wurin ta, tana cewa kawo ta inta gama.
Cikin marai-raicewa Sabeeterh tace didda don Allah kuyi haquri, wlh na tuba don Allah.

Tsaki didda tayi tana cewa ki bani ita, sateey na kuka ta ciro Amina taba didda.
Tabbas didda taji tausayi'n ta daurewa kawai tayi.

Tana fitowa ga Daddy , murmushi ya Mata Yana get Hadiza kishiyar taki ce kika ɗauko?................

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
 By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
      {Samha Umar}🥀

This page 29 dedicated to my friend A'ishah Muhammad 💜💜💜💜💜💜💜💜💜

PAGE_______29

Bismillah_Rahmanin-Rahim.

Eh, didda ta faɗa tana miƙama Daddy meenal, amsa yayi yana wucewa part ɗin sa tana biye dashi.

A fallo suka zauna didda ce tace Daddy yau ka dawo da wuri why.!

Murmushi yayi yana cewa yay ba'aiki da yawa, ya shirye shiryen biki Hadiza.?

Eh, Daddy ananan anayi yau an kai musu kayan Barka, kuma Hajiya hannatu mamar ita Sabeeterh tace batun kayan walima sai jibi, "Amma Daddy nace dasu kawai Bama buƙatar komai daga gare su.!

Kin kyauta Nana Khadijah adon mata ,
Knocking Akayi didda ce taje ta buɗe su husnah da Jamila ne.

    Didda ce tace oh ni Hadiza baku bari ya huta , Jamila ce tace wlh didda yau nake so in munyi sallar la'asar muje cen, amma bari mu koma.
    
A'a kuda daddynku hanya ta basu suka shiga, har ƙasa suka duqa suna gaida Daddy.

Amsa yayi yana cewa to nasan maganar ƴaƴan Daddy kuma yanzu zan baku ya faɗa yana sa hannu cikin Aljihu.

Husnah ce tace good Daddy, kulum didda Bata bari mu tambaye ka,.
Didda data zauna tace, lah yaran nan sharri zakumin .

Dariya sukayi su duka harda Daddy daya miƙa musu rafar ƴn dubu-dubu karɓa sukayi suna cewa
Mun gode daddyn mu baban Asma'u da Jamila kakan MEENAT kuma mai-gidan ta dariya sukayi su duka.

Anty zulai ce dake sallama Basu ji ba , cewa tayi oh Ni kun manta da ɗan gaban goshi Dr salim tunda ku kaɗai ya haifa.!

Ba haka bane Anty husnah ta faɗa tana kallon Anty zulai.

   Didda ce tace to ai yanzu an cire shi tunda yayi aure babu wani abu.
Zama Anty zulai tayi tana gaida Daddy , amsa yayi cikin farin-ciki yana cewa wai zulai duk wannan mai ƙaton kan ce ta saki yawon hanya.

"Daddy mukan ƴrmu bata da ƙaton kai Jamila ta faɗa, yayin da husnah ta ɗora da faɗin kedai wlh kishine kuma ba zamu bada ƴrmu ba."

Didda ce ke cewa maima zai yi da wannan baƙar ƴr taku, husnah ce tace haba didda ai baƙi ba laifi bane , kuma babu ma mai-ganin meenat yace mata baƙa tunda bata gaba ba.

Anty zulai ce tace if a child this resemble thr father most resemble the mother kuka san kota gefen uwarta..."

  Mudai babu wani nan Anty husnah ta faɗa tana amsa sallamar Yah dorta.

Yana shigowa gaida iyayen sa yayi 'sannan ƙannen sa suka gaida sa,
Amsa yayi yana zama kusa da Daddy , wash wlh didda na gaji yau da yawa.

       "Dafa kai didda tayi tana cewa oh ni Hajo kaga na manta ban kawowa Daddy ko ruwa ba duk kune yaran nan kuka hanani sakat ta faɗa tana nuna su husnah.

Jamila ce tace kedai didda bakiyi niyya ba ko kuma kishin Meenat ya hana ki.!

Murmushi kawai didda tayi tana miƙewa , kitchen ɗin ɓangaren ta nufa , ruwa da lemo da cups ta ɗauko bisa tray, bisa Centre table a aje,.

Bayan ta aje ta tsiyaya wa tayi a cup miƙama Daddy tayi , sannan tasa ma yaya docta shima , wucewa tayi domin kawo ma Daddy abinci.

Dakatar da'ita yayi yana cewa Hadiza nasan abinci ne ki barshi sai an jima.
Dawowa tayi ta zauna.

Yah docta ne da baiyi magana ba sai yanzu cewa yake Daddy magana zamu yi.

Toh ina jin ka my docta, 
Gaba ɗaya kowa shiru yayi, Jamila da husnah ne suka miƙe suna cewa Daddy mun tafi.

   Anty zulai ma tashi tayi tace gida zata koma, bayan Jamila tace yauma nan zata kwana .

Inda fallon ya rage daga Daddy didda sai Yaya, miƙewa didda tayi tana cewa bari nabar ɗa da uba su gaisa , a'a didda kiɗai zauna docta ya faɗa.

"Zama tayi, a hankali ya fara magana daddy dama akan wani meaning da muke da a U.k akan wani magani na ciwon zuciya da za'a fitar, domin mu rage yawaitar ciwon zuciya Bama tsofaffi ba harda yara masu ƙananan shekaru , to an sani cikin wa'enda zasu zauna meeting bayan d.r homeos ya gayamin
Amma ina ganin bazan samu zuwa ba domin asibitin yanzu muna yawan samun patients musamman na tiyata shiya sa nake so d.r rajhave ko shiva wanin su ya waƙilce ni."

To, salim naji ta bakin ka amma a matsayina na mahaifin ka ba umarni na baka ba ina so kaje wannan meeting ka ɗauki magana ta shawara na baka.!

Didda ce ta ɗora da faɗin gaskiya Daddy koni haka nike gani , yaje kawai don kayiwa kanka yafi waƙilta .

Toh didda da Daddy na amince.
Daddy ne yace to madallah yaushe ne.
Daddy 28 may.

Kace ya kusa Allah ya nuna mana da Amin suka amsa...

Jin an kira sallah yasa su tashi, amsar Amina dake hannun Daddy didda tayi wacce har tayi barci .

   Fitowa sukayi ita da Salim inda Daddy ya shiga ɗaki domin alwala.
A bakin corridor part ɗin didda suka tsaya cewa Didda tayi nifa Salim wlh ɗazu yarinyar nan ta bani tausayi.

Cikin siggar tambaya yace , wakenan .?

Sabeeterh ji nake mu bar mata ƴrta, bai kamata kana biye mata ba, kaifa namiji ne haƙuri ya kamata ka rinƙa yi, ba komai kayi fushi ba, ya kamata ace kana zama da'ita kuyi shawara sosai kaji.

Toh yaya salim yace haɗe da cewa Didda haka ne amma batun Meenat ki bari sai nan-gaba daidai tayi tayi hankali don Allah diddata.

   "to shikenan didda ta faɗa tana shigewa ciki, shike ya juyo kenan sai ga husnah da Jamila, sun ciyo wanka gaida sa sukayi, amsawa yayi yana cewa ina zaku.

Jamila ce tace yaya kasuwa zamu sayayyar biki, bai ɗago ya kallesu ba yace kunyi Sallah.

Eh, yaya munyi.
"To yace musu sannan ya ɗauko kuɗi masu yawa ya ƙara musu.

Amsa sukayi suna mai godiya.

Ko kallon su baiyi ba ya wuce nasa ɓangaren yana mai-jin haushin ya tsaya har an tadda sallah .
Suko mota suka shiga driver yaja su sai kantin kwore .

★*★*★*★*★*★*★

Cen bayan magriba domin su husnah har sun dawo.
Docta ne ya shigo main-fallo ba kowa a fallo, ɗakin sateey ya shiga ciki-ciki yayi salama , sabita dake zaune saman sofa sanye take da ƙatoton hijabi tayi tagumi, .

Bata ji sallamar docta ba har saida yazo inda take, a gefen ta ya zauna yana jin tausayi'n ta.
Hannun sa yasa ya ɗago kanta, sai sannan taji da mutun , tana ɗago kanta suka haɗa ido, "kuka ta fashe dashi tana faɗawa jikin sa .

Lallashin ta ya fara yi yana cewa , kiyi shuru kinji sateey, yanzu ki daina kuka.

Cikin sheshe-ƙar kuka tace don Allah my husband kayi haquri ka yafe min , wlh na tuba kayi haƙuri kaji kukan ta ne ya ƙaru.

Ɗago kanta yayi yana cewa daina kuka kinji, share hawayen ki sabita bana son ganin kina kuka ya faɗa yana ɗago kanta, babbar yatsar sa yasa yana share mata ƙwolla .

  Murya tamkar baya son magana yace kiyi haquri na yafe miki kinji.
Sannan ki shirya kayan da kike buƙata gobe da safe husnah da Jamila zasu tayaki kai kayan ki , zaki koma ɗaya part ɗin cen na gefen didda har ayi biki sai kici gaba da zama acen har ayi arba'in.

Duban sa tayi da rinanun idanuwan ta tana cewa to honey Amma Amin.....Bata kaiga idawa ba yasa hannu ya rufe mata baki yana cewa my sateey kibar maganar Amina, tabbas abu ɗaya zan miki ranar biki za'a barmiki ita amma ana watsewa da taro za'a karɓota kuma bana son wani surutu , karfa ki manta kece da bakin ki ba wani ya matseki ba kika ce kin yafetah.
Kada ki manta har zubar da ciki da kikayi ina sane, kawai dai na miki uzuri ne, amma sabita ina so ki sani fa Amina na amshi ƴrtah ...!

        Haka ya tashi ya fita ya barta, yana fita ya wuce part ɗin didda tana zaune ita da ƴaƴan ta bisa kujerun fallo , kallon tashar Arewa 24 suke ana mai-maicin Dadin Kowa (Sabon salo).

"Sallama yayi ya shigo saida ya zauna cen nesa da didda sannan ya gaida ta.
Amsa tayi inda inda su husnah suka gaida sa , bai amsa musu sai cewan da yayi gobe da safe ku taya sabita maida kayan ta cen part ɗin kusa da didda."

Okey yaya na right hand ko left,.?
Saida yakai kusan 1 minutes sannan yace left, miƙewa yayi yanama didda sallama.

Oh salim na manta ban tambaye ka ba .
Ina jinki didda.
Dama akan maganar hasnah ce ina fatan ta farfaɗo kuma an dace , ɗazu na kira RUKAYYA wayar ta kashe, kuma yau ban samu naje ba "gobe zanje Insha-Allah".

  Didda an dace taji sauƙi zuwa wani satima ina ganin, tunda safe ma ƴn'uwan ta sunje yana kaiwa nan ya ficeeehhh.

★*★*★*★*★*★

DARE MAFUTAR BAWA

Acen asibiti kuwa, Safa da marwa kawai take a ɗakin Mommy da Hasnah duk sunyi barci "cen Mommy ta tashi cikin maganar masu bacci tace Fatima lafiyar ki baki kwanta ba.?.

   "Mommy toilet na fito yanzu zan kwanta Fatima ta'ida maganar tana kwanci gurin hasnah.
Duk da Mommy Bata yarda ba amma a haka itama ta kwanta.

Oh ni Fatima wai miyake damuna a yau na kasa barci kaddai ace tunanin docta nake...... Da sauri wata zuciyar tace A'a Fatima kawai rashin sabon kwana a asibiti ne, dakyar bacci ɓarawo ya kamata....!

ASSUBA TA GARI

Tunda safe suna tashi bayan sunyi Sallah saiga Yaya Ahmad ya shigo, abinci ya kawo musu ! Mommy ina kwana .
Lafiya ƙalau.
Ya mai-jiki.
Alhamdullh kaga hassanah kam taji sauƙi .
Ton Mommy Umma tace tananan tafe zuwa da rana.

Toh Ahmad nima sai mu wuce yanzu domin ina so naje gida kaga tunda Rakiya nanan kuma ga Fatima sai kuma anjima na dawo.

Ahmad ne yace to Mommy yanzu ki shirya mu wuce, 'to aina shirya bari Fatima tazo tana bayi wanka zata yi ma hasnah.

Wanka Mommy.?
Eh, to zata ɗauraye mata wani sashi na jikin ta .

Sunanan tsaye saiga fatima ta fito riƙe da hannun hasnah .
A yaya ina kwana.?
Lafiya ykk, ya mai jiki.?
Kowa kowa lpy ta faɗa tana shimfiɗe hasnah bisa bed.

Mommy ce tace Fatima kega ma zamu wuce, amma zuwa Azhar zamu dawo.
Ton Mommy ina gaida laila.!
Okay.

Suna fita ba'a fi 10 minute ba Rakiya ta shigo abinci ta kawowa Hasnah,
Nan ta zauna suna fira da Fatima kamar sun'san juna.

★*★*★*★*★*★
A cen gidan su didda, nan su Jamila suka taya sabita komawa part ɗin cen .

Fallo'ne mai girma da Two bedroom sai kitchen, nan ta maida kayan ta a zuciyar ta tana cewa da zama gurin didda gwora nan .

Bayan su Jamila sun gama a ɗakin diɗda suka shiga, fitowar ta kenan daga bayi ,
Didda harke fito, kega sai yanzu muka gama Husnah ta faɗa tana duban didda.

Didda cewa tayi kuje ku shirya da anyi sallar azabar zamu wuce asibitin kuma muje da Amina domin bana son mu barta ga masu aiki.

Eh didda haka ne , bari muje mu shirya Meenat ma mu shirya ta suka faɗa suna wucewa..

★*★*★*★*★
Cen asibiti kuwa Fatima ta gama sallah Azhar ,  ɗankwalin ta ɗauka ta linke, kujera ta jawo ta zauna tana ɗauko abinci.

Zo muhasanat zona baki abinchi da magani.
Wlh Anty na ƙoshi hasnah ta faɗa tana kwaɓe fuskanta.

Saida Fatima tayi kamar tana yi sannan hasnah taci , shinkafa ce fara bako magi bale mai sai ganyen alanyahu da kabeji..!

Tana ci tana yamutsa fuskanta harde ta ɗanci ba sosai ba, nan Fatima ta ɗauko magani da ruwa ta bata tasha domin hasnah bata da rakin shan magani .

Jin sallama yasa Fatima ta'amsa, Mommy ce gaba sai laila da Umma.

gaida su Fatima tayi haka ma hasnah.
Amsa sukayi suna zama bisa kujerun roba wa'enda sukai guda biyar, sai gado biyu ɗaya na marar lafiya ɗaya na mai-jinya .

Zazzauna wa sukayi, sai ya'ya Ahmad daya shigo yanzu, shima zama yayi yana tsokanan hasnah, sunata fira akan rashin lafiyar hasnah da kuma warkewar da tayi cikin sauqi suna yaba ma Dr Salim.

★*★*★*★*★*★

Ɓangare Ɗaya.

Didda mun shirya ƴn matan nata biyu wato Jamila da husnah suka faɗa , wa'enda ke sanye da ke sanye da gizna ɗinkin doguwar riga mai stone, rigar Ash color sai gele da takalmi shigar su iri ɗaya ce .
Kuma sunyi kyau kamar ƴaƴan sarki.
Jamila ce rungume da Meenat.

  Didda dake bisa ɗaya daga cikin kujerun main gfallo itama taci wanka less mai kyau baƙi da adon goldstone ga sarƙar gold a wuyan ta.
Tasa ƙatoton mayafi da flant shop ɗin ta duka Golding ne tayi kyau sosai, ga farar fatar-ta sai kyalli take Bama zaka ce ta haifi ko warin husnah ba balle salim....

"Tashi tayi tana cewa muje tana gaba suna baya basu tsaya ko'ina ba sai parking space, wata mota suka nufa ɗaya daga cikin uban motocin dake gurin, mtar ƙirar Benz Black color sai sheƙi takeyi.

Didda ce tace Jamila kira sani driver,
Mommy ni zanyi driving husnah ta faɗa.

Toh didda tana shiga mota.....

Husnah ke driving  ɗaya bangaren Jamila ce hira suke har suka isa AL'UMMA PRIVATE HOSPITAL a harabar asibitin tayi parking.

Fitowa sukayi su duka, cikin asibiti suka dosa , husnah ce ta ɗauko wayar ta number Yaya docta ta kira.

  Yana ɗauka tace Yaya gamu hospital.
Cewa yayi to shikenan zan turo a shigo daku.

★*★*★*★*★*★

Cen kuma gidan su Abdul-Hakeem kuwa yaji sauqi sosai harma suna jayayya da mami waishi fita zai yi ai yaji dama.

"Daƙyar ta yarda ya fita, shima asibitin ya dosa"
Yana isa yayi office ɗin docta Salim baayi ƙoƙarin hana shi ba ya shiga ciki.

  Yana shiga ɗauke da sallama, amsawa docta yayi.
Bayan Abdul-Hakeem ya zauna.

Docta ne yake cewa, a Bawa kwana biyu ban ganka ba, ina fatan dai lafiya.

Murmushi Abdul-Hakeem yayi yana cewa "hmmm likita wlh kaide ina cikin matsala.

Zaro ido docta yayi yana cewa matsala fah.?

Eh, likita kasan zahra'tah sun zo Kano shekaran jiya.
"Eh, haka ne".
To, naje na sameta da cewa ina sonta amma sai kuka ta fashe dashi, docta ina fama da son Fatima har yana neman ya illatani , wlh docta ina tsakanin son fatima, idan ban aure ta ba zan'iya mutuwa.

Mtwsss, tsaki docta yayi yana cewa wai kai Abdul wane irin mutum ne kana wahalar da kanka a kan macce.

Hmmm, ba zaka gane ba docta.
Dariya docta yayi yana cewa wlh kaide kana bani dariya, wai ita wannan Fatimah'n tafi duk matan duniya kyawo ne.

"Ba zaka gane ba ya Abdul ya faɗa yana ɗauko phone ɗin sa , gallery ya shiga aiko ga photon Fatima ya bayyana, amsa docta amsa ka gani Wlh Fatima mace-ce ha mace ya ƙira ga kyawo.

Amsa docta yayi........

★*★*★*★*★
Cen kuma bayan bayan wanda Dr ya aiko yakai su didda ɗakin d aka kwantar da hasnah, gaida su yayi,

Jagora yai musu sai ɗakin da aka kwantar da hasnah, husnah ce ta murɗa handle ɗin kwofar kanta ta tura ta shiga su didda na bayan ta.

Sallama tayi gaba ɗaya amsawa sukayi, anyi rashin Sa'a karaf suka haɗa ido da Fatima.

   Cikin kiɗimewa da al'ajabi da tsoro husnah tace innalilahi wa'inna ilaihin raji'um Fatima.
Ai kuwa da sauri didda takai duban ta inda husnah ta kalla dafe ƙirji tayi tana zubewa sumamiya.

Ai kuwa da sauri sukayo kanta cikin ruɗewa Fatima na kuka diddatah don Allah ki tashi ,
Jamila dake rungume da Meenat bisa bed ta ajiye ta cikin sauri.

★*★*★*★*★*★
Cen ɓangaren kuma cikin wani irin yanayi da kuma mama ki haɗe da kishi kuma gauraye da wani ɗunbin al'ajabi yace What Abdul-Hakeem kana nufin kacemin wannan ce Fatima?, Wannan ai matata ce a,ina kasan ta wacce ta rasu.

Fisge wayar Abdul yayi yana cewa Kai da'allah malam wannan fa ba gawa bace ba, kuma ƴr jigawa ce.......jin an turo ƙofar da sauri yasa su dukan su juyowa .

Cikin kiɗimewa Jamila tace yaya---ya...fa...
Cikin tsawa yace kimin magana” .
Yaya wlh didda ce ta faɗi domin munga bintu a'inda muka je .

What, gaba suka fita daga office ɗin harda Abdul Hakeem..........

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
  By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
       {Samha Umar}🥀

This page 30 dedicated to my daughter Amina Abubakar 💅💅💅🧠.

PAGE_____30

Bismillah_Rahmanin-Rahim

        "Suna isa ɗakin hakan yayi daidai da farfaɗowar didda saka-makon ruwan da Umma ta yayafa matahh.!

Bata buɗe idanun ta ba take cewa Bintu.... Bintu...bintu......' hannayen Fatima ta riƙe tana cewa Mamatahhhh don Allah ki buɗe idon ki, kiyimin magana diddata.

Shikan gogan naku suman tsaye yayi kamar wani mutun-butume yana kallon ikon Allah da abin al'ajabi.

   A hankali didda ta buɗe idanun ta , tare da ware su bisa kya-kyawar fuskar Fatima wacce har tayi ja akan kukan da take....

Ƙoƙarin miƙewa take, Umma ce ta kamata ta tashi tana zaunar da'ita bisa bed.

Jawo Fatima didda tayi tana kafeta da'ido tace Bintu kece ko mafarki nake.?

Girgiza mata kai Fatima tayi tana cewa nice diddata ki yafeni Rabin raina,.
Rungume juna sukayi Fatima na kuka.

Kowa yayi jugun, shiko docta yana-nan tsaye.
Abdul-hakeem kuwa ya shiga tashin hankali, yana tunanin meye haɗin Fatima da Familyn Sauta .

"Didda ta ɗago Fatima tana share mata hawaye, husnah ce tazo ɗayan gefen Fatima tana cewa my sister."

Juyowa fatima tayi tana ma husnah murmushi rungume ta tayi.

Mommy ce tace to Fatima keji daɗi, yau gaki ga diddar'ki.

Murmushi Fatima tayi tana cewa Mommyyyyy.

Didda ce ta juya tana cema Umma Rukayya ina kuka samomin ƴrtah bayan ance ta rasu.

Mommy ce tace bari na gaya miki, da farko wata Rana laila ta kira ni tamin maganar Fatima akan zata dawo gida na nan Jigawa da zama, to shine........ masu karatu nan dai Mommy ta gayawa didda komai, ita ko laila tace wlh didda Bintu batayi hakan don cutar dake ba illa tayi haka ne kawai don taga farin cikin ki.

   Didda tace hmmm Fatima haryau dauriya kawai nake amma wlh mutuwar ki ta zama taɓo a zuciya ta .

"Cikin kuka Fatima tace don Allah diddata kiyi haquri ki yafemin banyi haka da gangan ba."

Hannun ta didda ta kama tana cewa ba komai ƴrtah, tashi didda tayi tana cewa yamai jiki.

Da sauqi suka amsa, hannun Fatima ta riqe tana cewa don Allah Mommy'n su ina so muje gidan mu, kuma harda ku.

Umma ce tace to bari Ni Na tsaya wurin hasnah.
A'a basai kin tsaya ba, rakiya nanan Fatima ta faɗa tana bin bayan didda.

Fita sukayi su duka, mota suka shiga inda Abdul-Hakeem ya ɗauki su Umma.
Docta ma mota ya shiga yabi bayan su domin yama rasa ta'ina zaibi kuma wane yanayi yake ji, farin-ciki ko baƙin ciki.

   Cen cikin mota didda da Fatima dake baya , meenal ce dake hannun Jamila ta fara kuka, didda ce tace ke Amo yaufa ranar farin-ciki amma kina samun mutane gaki dai baki da rigima.

Fatima ce tace, lah ƴrtah miƙomin ita'nan Jamila.
Ta gaba ta mika hannu ta amso Amina.

Rungume ta tayi a jikin ta, ai kuwa nan take tayi shiru, kafeta da ido Fatima tayi a zuciyar ta kuwa tana cewa, wannan yarinyar kamar mahaifinta.
Nan taji tana bala'in don meenal a hankali ta furta didda'tah maman tawa Bata da rigima, shine ke-ko Jamila kika fitomin da ƴrtah zuwa yawo.....!

Acen Jamila tace, to yanzu tunda kin dawo zaiki reni abarki gida muko muje yawon mu, sukayi dariya gaba ɗayan su.

  "A haka har suka isa gida, horn sukayi mai gadi ya buɗe, parking sukayi a parking lot."

Firfitowa sukayi , Fatima najin nishaɗi a ranta tana cewa, kowa bar gida-gida ya barshi.
Tana ɗago idon ta sai a kansa wanda ya jingina ga mota yana kallon ta.

Hararar sa tayi ta juya ganin kowa ya shige sai'ita , manna Amina tayi a kafaɗa tana kama hanya.

Mayafin ta yaja, juyowa tayi tasa hannun ta, tana ƙwoce gyalen ta.
Hannun sa yasa ya jawo ta baya , cikin jin haushi Fatima ke cewa ka sakeni da'allah malam.

"Baƙi ya faɗa a taƙaice, mima zanyi da taɓin wannan ƙazamin jiki naki? Wanda kika gama zubar da mutuncin ki waje , wama yasan inda kikaje? Kokuma me kika aikata a'inda kika je."
 
   Fisge hannun ta tayi hawaye na zuba daga idon tana kallon sa, ganin yana murmushi.

Allah ya'isa tsakanina dakai mugu azzalumi ta ida tana wucewa cikin sas-sarfa.

A fallo ta tarradasu zaz-zaune .
Didda dake waya tana cewa eh wlh Daddy kazo gida yanzu zakaga abin mama ki, cen tace toh tana kashe wayar.

Duban Fatima tayi tana murmushi tana cewa ƴrtah na barki koh, wlh ina zumuɗi na kira Daddy'n ku .

Ba komai Fatima ta faɗa tana aza kanta bisa kafaɗar didda bayan ta zauna.

"Didda ce ta sake kiran Anty zulai tana ɗauka tace idan da lokaci tazo yanzu."
 Saida tace lafiya dai didda.?
Lafiya lau wlh kada ki damu.
Toh.

Husnah ce tace didda bari na kira Anty zeenatu .
A'a kada ki kirata kesan tana da shigar-ciki shiyasa ma nace tayi zaman ta kawai, ta bari sai biki idan zata zo ....!

Uhmm Jamila jeki gayawa Inna , "to Jamila tace tana tashi ta nufi ɓangaren Inna wacce yanzu bata gani sosai shiyasa bata cika yawo ba, kuma jikin sai a hankali, ga ƴn aikin'tah ga komai nata har girkin ta daban aka samo mai-mata na gargajiya.

  Jamila na shiga fallon tana cewa ina kike tsohui mai ran ƙarfe, gawa keƙi rame, carraf a kunnen inna dake zaune bisa capect tana taunan goro.

Uban ki ne gawa yaƙi rame, shegiya mai idon mage , kuna-nan kuna zaman banza shekaru sun ja amma kunƙi Aure sai karatun nasara.

Murmushi Jamila tayi tana zama kusa da inna , tana cewa ke-ko Inna makauniya ga makan'ta gasa ido .

Sai'ido ya wuce na ubanki da harya ga uwarki ya nace,
Dafe baki Jamila tayi tana cewa nikam kefi ƙarfina, kega dama didda ce ta aikoni na sanar dake kizo zaki ga wani abu .

Kaini ki gayamin gaskiya domin idan wasa kike dani ki daina sa Hadiza domin ita ta kirki-ce .

Dariya Jamila tayi tana cewa inna kenan, ai daɗin abin didda kika yaba , amma wlh abin kamar armara Fatima ce ta dawo.

Cikin sauri inna batama san sanda ta mike ba tana cewa Fatimah "ke wannan ƴr ki daina don Allah .
Wlh inna muje ki gani .

Nan inna tabi bayan ta sai main fallo, isar-su yayi daidai da isowar Daddy, Inna ce tace ina kike ƴr albarka Hadiza gayamin kesan wa'ennan yaran girma buhu-buhu wayo kulle ga leda .

"Murmushi didda tayi tana cewa inna da gaske ne ba ƙarya ba Bintunah ta dawo.
Daddy shima tsaye yayi ya kafe Fatima da'ido."

Inna ce data zauna tana cewa zonan gurina zonan jikata Fatima zahra'u batular Bintu ɗiyar ma'aiki, fati-kana zabuwar mata fatiti mo Allah yiɗi soyata ko soye.

Gurinta Fatima taje tana zama gefen tah.

Husnah ce tace oh su inna ina aka'iya filatan'ci .
   "Hhhhh yarinya na muku wayo zama na da A'isha na'iya (mahaifiyar su didda da Amina kenan)  amma ku iyayen ku hillani amma baku iya ko warroy mi waruma ( taho in kasheki )...!

  Fatima ce tace to nidai innatah yakike, inna wlh nayi kewar ki.

Nima haka inna ta faɗa tana ɗorawa da ashe dama baki mutu ba Bintu.

Daddy ne yace ƴrtah Fatima zonan inda Daddy'n ki , nan tashi tayi inda Daddy taje ta zauna tana mai-jin kunyar sa ,
Hannun ta Daddy ya riƙo yana cewa don Allah ƴrtah kiyi haquri ki yafe mana kinji Kiyi haquri da komai wlh munyi kukan rashin ki Bintu amma muna ƙaunar ki ki yafe mana keji ƴrtah.

Ba komai Daddy Kai mahaifine a gare Ni kuma wlh ban taɓa riƙon ka da komai ba , Daddy ku yafemin tasar muku da hankali da nayi.

Ba komai ƴrtah.

Anty zulai ce ta shigo da sallama a bakin ta kusa da didda ta zauna tana cewa duk hankali na a tashe yake ina tunanin Lafiya...!

  Husnah ce tace kesan me Anty.
A'a don Allah kumin bayani yaran nan.

Didda ce tace zulai yau taɓon dake zuciya tah, ya warke ina cikin farin-ciki yau ga Fatima ta dawo.

Me kika ce didda Anty zulai ta faɗa tana ware idon ta ko'ina, ai kuwa carraf suka haɗa ido da Fatima dake murmushi, dafe baki tayi tana cewa inalilahi wa'inna ilaihin raji'um aljana ko fatalwa..

   Gaba daya dariya suka saka ƙara tsorata Anty zulai tayi tana tashi domin fita fallon.

"Didda ce ta riƙota tana cewa haba zulai wannan wane irin tsoro ne? Sai kace farar kura wannan fa ba aljana bace Fatima ce dai.

Hannun didda Anty zulai ta riqe tana cewa haba didda wanda ya mutu yana dawowa da zaki ce ba fatalwa bace , didda ce tace wlh zulai Fatima ce zauna kiji.

Zama Anty zulai tayi, inna ce tace kekan gado akwai tsoro wannan fa Bintun ce.

Hmmm ajiyar zuciya Anty zulai tayi tana cewa ya'ankayi Hakan ta kasance didda, kodai ƴr wasu kika samu aka sama fuskar Bintu.

  Murmushi didda tayi tana cewa wlh zulai ita ce dai Allah yaji tausayi na ya mayar'min da'ita.

Hmm ajiyar zuciya Anty zulai ta ƙara yi tana cewa zonan ƴrtah Bintu.
Cikin mamaki Fatima tazo inda take, rungume ta tayi a jikin ta.

Nan didda ko ta gaya musu komai kamar yadda Mommy ta gaya mata.
Nan Anty zulai da Daddy harma da inna sukayi ma su Mommy godiya.

"Shi kuma Abdul-Hakeem duk jikin sa Yayi sanyi, kuma har yanzu baiji son Fatima ya ragu a zuciyar sa ba" illa ma ƙaruwa da yayi....!!

Tashi su Mommy sukayi zasu wuce.

Toh Hajiya muna godiya na kullamana da ƴrmu da kukayi na kusan shekara 1 .

Ba komai didda ai muma Fatima ƴrce a gurin mu...
Daddy ne yace sai kinji daga garemu Insha-Allah.

Ba komai umma tace tana tashi, fitowa sukayi har harabar gida, Mommy ce tace Fatima ba zaki zo mu tafi ba ,
Itakam Fatima murmushi tayi tana noce kanta ƙasa.

Laila ce ta matso kusa gare ta, ta dafa ta tana cewa ƴr'uwa ta Fatima yau ina cikin farin-ciki ganin ki haka gaki ga dangin ki , Fatima kiyi abinda ya kamata.

Jijjiga kai Fatima tayi alamar to, gaba ɗaya mota suka shiga "Abdul-Hakeem ya kalle'ta saida suka haɗa ido tana jin tausayi'n sa.

   Suna ficewa daga gidan Fatimah ta kama hanyar komawa fallo,
Ke, dakata.
Tsayawa tayi amma bata juyo ba, ƙara sowa yayi ya tsaya gaban tah.

Malam lafiya ka tsare min hanya.

Ko duban ta baiyi ba yace meye haɗin ki da abokina Abdul-Hakeem.

Cikin gadara tace Saurayi na-ne.
Baisan sanda ya juyo ba yana cewa me saurayin ki? Kina hauka ne?  Da auren nawa.?

Kallon rainin hankali tai masa tana cewa wane aure mtwsss tsaki tayi tabi ta gefen sa tana wucewa.

Koda ta shiga fallon da sallama didda dake tsaye bata zauna ba tace Fatima zaki ci abinci.
Murmushi tayi tana cewa Didda na qoshi.

Ke ƙoshi fa.?

Daddy ne yace kinga Hadiza ki barta kawai, to shikenan didda ta faɗa tana zama.

Docta ne ya shigo da sallama a bakin sa "gefen didda ya zauna.
Tashi didda tayi tana cewa ƴrtah muje ciki, hannun ta Fatima ta kama suka wuce, itama Anty zulai bayan didda tabi.
.
Husnah da Jamila suma suka miqe , Daddy ma cewa yayi My son zan shiga ciki.
Okey, shima miƙewa yayi yana fita part ɗinsa ya nufa sai kuma ya juya na Sabeeterh.

  Koda ya Shiga bata fallo direct bedroom ɗin ta ya wuce "yana shiga ya faɗa bisa bed fillo ya jawo ya rungume.
Kusa gare sa Sateey taje tana cewa My Honey lafiyar ka, sai murmushi kake.

"Jawo ta yayi jikin sa yana kallon face ɗin ta haɗe da cewa my sateey kesan me.
Girgiza kai tayi alamar a'a."

Bintu ta dawo.

Zumbur ta miƙe tana cewa what kana ko da hankali wacce Bintu.
Tashi yayi ya zauna itama ya zaunar da'ita, ki kwantar da hankalin ki my sateey.

Cikin ɓacin rai tace taya zani kwantar da hankali ki.
   Nidai ka gaya min wacce Fatima.
Cikin mamaki hali irin na sateey yace Fatima matata.

Cikin azarma sateey ta tashi tare da kurma ihu ihu take babu ƙaƙƙautawa .

Shima cikin tsawa yace kimin shuru shashasha, fita yayi daga ɗakin Mtwsss yana jan tsaki.

Cikin wani hali sateey sai jifa take da kaya , wayar ta ta ɗauko number sateey tayi darling.
Ɗauka tayi.
Cikin kuka sateey ke magana don Allah khairat kizo ina cikin matsala, bata tsaya jin mai sateey zata ce ba ta kashe kiran.

Abban ta kira ba'a ɗaga ba, ta kira Mama itama gaya mata tayi tazo.

Ta kasa zaune ta kasa tsaye.
Shiko docta yana fita ya shiga mota ya wuce sai gidan sa.

★*★*★*★*★*★*★

Cen kuma didda ce sai rirrita Fatima take yi , tana cewa ta kwanta ta huta, Anty zulai ma haka daƙyar ta wuce gida.

  Husnah ce ta shigo da sallama ɗauke a bakin ta  , Fatima ce ta amsa tana duban tah.

Zama tayi tana cewa ƴr'uwa tah Fatima fito muje ga girki cen mun haɗa miki nida jameey .
Tashi Fatima tayi suka fita, itakam didda murmushi kawai tayi.

Suna fitowa a dining zauna Jameey ta zuba mata , ta fara ci sai santi take.
Suko farin-ciki ne fall ransu.
Yau ga Fatima ga ƴn uwan ta suna firar su...!!!

Sallama akayi aka shigo khairat ce.
Cikin mutunci suka gaisa.

Jamila ce ta nuna mata part ɗin da sateey ta koma, khairat na shiga ta fara jin sheshe-ƙar kukan sateey.

Bedroom din ta ƙara sa ko'ina a hargitse kamar ɗakin mahaukaciya tana zaune ƙasa dabbas.

Ɗagota khairat tayi tana cewa tashi mana sateey ki gayamin me yake faruwa.

Cikin kuka sateey ta gaya mata abinda docta ya gaya mata na game da dawowar Fatima.

Ajiyar zuciya khairat tayi tana cewa komai ya faru ke-kika ja sateey kullum bakya gina ramin alkhairi, ke kenan taki tayi kyau ta kowa ta ɓacce .
Toh bari kiji matar sa ta dawo idan zaki nemi yafiyar sa ku zauna lafiya, wlh sateey ke ɗauki duniya da zafi kina abu kamar sokuwa .

"Ɗagowa sateey tayi tana cewa khairat ke ƙawace ta gari, abar alfahari, amma wlh bazan iya zama da kishiya ba.

Tashi khairat tayi tana cewa kiyi haquri ki zauna da kowa lafiya mijinki surkarki kishiyar ki ƴn'uwan sa.

Share hawayen ta sateey tayi tana cewa to shikenan zan gwada qawata Nagode.
Sallama sukayi Khairat na fita, tunani sateey ta shiga yi.

★*★*★*★*★*★

Bayan su Fatima sun gama cin abinci, main fallo suka zauna suna ta hira , saiga mama hannatu ta shigo da sallama a bakin ta.

Bayan sun gaisa sai kallon Fatima take taga baƙuwar fuska .
Nanma Jamila ce takai ta part ɗin sabita.

Tana zuwa Sabeeterh ta gaya mata komai ‘cewa mama hannatu tayi ki kwantar da hankalin ki , in sun San wata basu san wata ba kwai ta kwantar da hankalin ta ayi biki bayan biki sai-su ɗauki mataki.

Sabita kodai itace na gani tare da su Jamila mama hannatu tai mata tambaya.
Ina ga itace Mama Sabeeterh ta bata amsa.

Ki kwantar da hankalin ki amma dai kan yarinyar akwai kyau.
Itakam Sabeeterh komai bata ce ba.........

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
 By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
      {Samha Umar}🥀

This page 31 dedicated to Inna mudda Allah ya jiƙanki da Rahmah A'ishah Allah yasa mutuwa hutuce a gareki.

PAGE_____31

Bismillah_Rahmanin-Rahim.

★*★*★*★*★*★

BAYAN SALLAH MAGRIBA

Fatima ce zaune ɗakin didda sai hira suke ita da didda dasu husnah da Jameey.

  Fatima ce sai tawai take ma ƴrtah Meenat, didda ce tace Bintu wannan soyayyar keda ƴrki.
Murmushi Fatima tayi tana cewa Didda Maman tawa Bata da rigima, amma a Kaita inda Maman ta mana.

   Fatima maman ta ai ta yafe mana ita, cikin mamaki Fatima tace Didda ta yafe fa.?

"Eh didda tace tana gaya mata komai, jinjina kai Fatima tayi tana mamakin hali irin na Sabeeterh.
Husnah ce tace Bintu aike samu ƴr kafin ki haifa mana wasu."

Murmushi kawai Fatima tayi, 
Anan ɗakin sukayi dinner, sannan su Jamila sukayi musu sallama.

Ɗakin ya rage daga daga didda sai Fatima.

Fatima dake zaune bisa bed rumgume da Meenat kamar ƴrtah, didda dake zaune bisa kujera tashi tayi haɗe da shigewa Bathroom.

Murɗa handle ɗin akayi haɗe da shigowa, ciki-ciki yayi salama, ko ɗagowa batayi ba amma ta amsa.

   Ƙara sowa yayi kusa gare ta ya zauna, gurgusa wa tayi tana hararar sa.
Hannun ta ya kamo, wani irin yarrr sukaji, tana ƙoƙarin fisge hannun ta amma ta kasa, a hankali tace don Allah ka sake ni.

"Zaro ido yayi yana cewa saki fa? Haba uwar-biyu magana zamu yi, "ɗagowa tayi ta kallesa tana cewa niko nace bana son magana dakai.

Haba uwar-biyu ki bari mana aiba magana mai tsawo bace.
Cikin zaƙuwa tace inaji.

Bintu uwar-biyu meye haɗin ki da abokina Abdul-Hakeem, Fatima abokina ne ke kuma matata.

  Cikin gadara tace Saurayi na-ne kuma wanda nake da burin aure Insha-Alla......bai bari ta ƙara sa ba ya kulle mata baki yana jin zafi a zuciyarsa.

Ɗagowa yayi sakamakon buɗe qofar toilet da'akayi didda ce , cikin ɗaure fuska tace Salim mekake anan .?

Sosa kai yayi yana tashi, murmushi yayi yana cewa uhmm.... didda nazo ne kawai naga uwar-biyu.

Uwar-biyu kuma a'ina? Didda tayi tambayar cikin neman amsa...
"Didda baki sam uwar-biyu ba.?
A'a nikam Salim wlh ban sani ba nidai nasan ban haifi ƴn biyu ba.

Okey, Bintu ce Uwar-biyu ya faɗa yana kallon Fatima.
Hararar sa didda tayi tana cewa Allah ya bata ƴn biyu ga mijin ta da zata aura nan gaba.

Fatima kam tashi tayi ta shige Bathroom, "haba didda Bintu nada wani mijin bayan ni.?

  Cikin faɗa didda tace Salim kaci Amana ta, Kai ɗana ne bazan ma baki ba amma ka sani Aure dakai da Bintu wlh sai a lahira badai duniya ba.

"Dam gaban sa ya faɗi , wani iri yaji baison Fatima amma baya jin zai'iya rayuwa ba tare da'ita ba."
Tsawa didda ta daka masa tana cewa Fatimah amana ce a gurina na aura maka ita domin ina gani ko bani zaka riqemin ita amanar tah, a haka ka wulaƙan ta tah ba komai kaje aiga rayuwar ka nan ( Sabeeterh) ta isheka rayuwa badai Bintu ba, zan sama mata miji na gari mai ƙaunar ta badai kai ba.

Sai yau docta yayi nadamar abubuwan daya aika ta, hannunsa ya haɗe guri ɗaya alamun ban haƙuri yana cewa Didda don Allah....

Hannun ta ɗaga masa tana cewa bana son jin komai daga gare ka fitar min daga ɗaki kuma kada ka sake shigo min ɗaki idan kuma don ƴrkah ce ɗaukar ta ka tafi.....!

  "Baice komai ba ya juya ya fita."

Bakin ƙofar toilet didda taje tana cewa ke-ko ki fito muna fuka (oh ni didda miye laifin tah)...!

Sum-sum Fatima ta fito daga toilet, Bata ma kalli didda ba ta wuce, salla tayi Isha da shafa'i da wutiri, tana gamawa didda tace anan zaki kwanta ko wurin su husnah.

  Bata ce komai ba illa noce kanta da tayi. "Oh ni Hadiza Bintu ba zaki cenza hali ba , to kwanta Anan.
To Fatima tace tana tashi, kwanciya tayi bisa bed, ita ko taci gaba da Sallah.

Wayar Fatima tayi ring Mtwsss taja tsaki, jawo wayar, Salma ce ɗauka tayi suka gaisa,...

Nan salma tace Laila ta kira ta, ta gaya mata Fatima ta dawo hannun iyayen ta tana tayata murna...

   Murmushi Fatima tayi tana cewa Salma haka ne yanzu ganin nan kwance bisa gadon didda tah.

"A Allah ya taimaka ya bada Sa'a ƴr uwa, "godiya Fatima tayi mata tana kashe wayar tai kwanciya tana murmushi.

Uwar-biyu ne ya faɗo mata arai a zuciyarta ta ce kome yake nufi da Uwar-biyu ohho nidai bani bace, wata zuciyar kuma tace idan idan dake yake ƴn biyu gareki.....!!!!
  "Kai gaskiya didda tayi qoqarin faɗan data yima ɗan ga nata , kuma duk a kaina to mezan yima didda na na biya ta da wannan abin da tamin naso da ƙauna , amma kuma ai ya'ya docta bazai sake ni ba kodai dama yana sona"cikin sauri wata zuciyar tace ina docta ba sonki yake ba , cikin kawadda zancen tace didda Salma ce ɗiyar Mommy tace a gaida ki.

  Ina amsawa didda tace, tana tashi shirin bacci tayi itama ta kwanta, bayan sunyi addu'a (niko nace ASSUBA ta gari)...

★*★*★*★*★*★*★

Tunda safe bayan sunyi Sallah suka koma bacci, itakam Fatima fitowa tayi sai kitchen.

Imaru mai aiki ce har qasa ta duƙa ta gaida Fatima haɗe da taya ta murnar dawowa domin jiya didda ta gaya ma kowa.

  Murmushi Fatima tayi tana duba kitchen ɗin , "Anty me kike buqata.?

Juyowa fatima tayi tana cewa ba komai kawai ki tafi nice zanyi girkin yau.

Dafe baki imaru tayi tana cewa rufamin asiri don Allah Anty.

Komai Fatima bata ce ba illa ɗauko arish da tayi miqama Imaru tayi tana cewa nidai kawai ki taimaka ki fere min kuma kada kice komai.

  Amsa imaru tayi ta fara ferewa wa , "gas Fatima ta kunna haɗe da ɗora ruwan zafi, saida sukayi zafi sosai sannan ta juye a flaks.

"Mai ta ɗora sannan ta fara soya arish Saida ta gama sannan ta soya kwai , 
Bayan ta gama duka ta jida izuwa dining table.

Upstairs ta hau sai ɗakin Husnah ba kowa fallonta, bedroom ta shiga ɗauke da sallama husnah dake ɗaure kanta da ribbon, tayi murmushi bayan ta amsa sallama tana cewa Barka da Safiya Bintu.

   "Haka itama Fatima ta mayar mata da martani ina kwana.
Jamila ce data fito daga wanka tace a Bintu harkin tashi.

Eh, Jameey ku fito mu karya, to suka ce husnah na cewa Didda ta hana ki kwana gurin mu ko.

Ita dai Fatima murmushi tayi kawai tana fita daga ɗakin koda taje didda na shirin fitowa daga ɗakin.

A Bintu daga ina.

Uhmm didda dama...naje .
Haba Bintu bakyamin ƙarya kada ki fara keji.

Cikin dariya Fatima tace naje kitchen nehhh.

"Me kikayi.?.

Na taya imaru aiki ne.

Didda kam bata ce komai ba, ta fita domin kiran Daddy main fallo break fast.

Itakam Fatima toilet ta shiga, bata fi 10 minutes ba ta fito koda ta fito ɗaure da towel mai ɗan girma.

Mai kawai ta shafa ta goga witlips, husnah ce ta shigo.

A Bintu ga kaya ki saka, "to Fatima tace tana karɓa, murmushi suka sakarwa junansu Husnah na fita.
  Riga ce da skirt na athampa super wax Ash and Yello color sabbi ƙal tayi kyau sosai kamar ka sace ka gudu.

A hankali take tafiya har ta isa fallon, dining table ta nufa kowa ya hallara wurin Daddy Didda ya docta husnah Jameey.

"tana isowa ta tsugunna ta gaida Daddy, ɗagowa da zata yi suka haɗa ido da docta, saida ta harare sa sannan tace Ina kwana yaya docta.

Lafiya ya amsa a takaice.

Wurin didda ta zauna, hararar ta didda tayi, cikin Shagwoɓa tace menene didda.?

 Yanzu Bintu daga dawowar ki jiya shine yau zaki shiga kitchen kinmin adalci.

Cikin damuwa Fatima tace Didda don Allah kiyi haquri kinji, naga bana jin baccine.
  "Ba komai Bintu ki daina daga yau"
Ɗaga kai Fatima tayi alamar tau.

Ba wanda ya ƙara cewa komai har suka gama, fallo suka zauna.
Daddy ne yace Fatima kada ki sake girki anan gidan kinji ban hana idan mijinki ne ya saki kiba..

  to Daddy na daina Insha-Allah sallama yayi ma didda zai wuce aiki, duban ya docta daya hakimce akan kujera yayi yana cewa Son ba zaka tafi aiki ba yau.?

Eh, Daddy zanje sai anjima amma.
Okay Daddy yace yana tafiya.

Imaru ce ta shigo da sallama rumgume da Meenat, tsugun nawa tayi tana cewa Fatimah Anty ga ƴrki ta tashi amma batayi kuka ba.

"Hannu Fatima tasa ta amsheta tana cewa Imaru taimaka min da madara.
To Anty imaru ta faɗa tana tashi, didda ce ta dubi yaya docta da tun ɗazu ya kafe Fatima da'ido.

   Cewa tayi kaiko tashi kaba mutane wuri, juyowa yayi yana cewa haba didda kiyi haquri yanzu zan tafi dama tambayar ku zanyi idan kuna buƙatar wani abu.

Cikin faɗa tace didda tace Bama buƙatar komai, Daddy'n ku yayi mana, duban husnah tayi tace keda Jamila ku wuce ciki don banga Amfanin zaman ku Anan ba komai basu ce ba, suka tashi suka wuce.

  "Juyowa tayi tace Salim Salim Salim so mawa na kira sunan ka. Cikin dashashiyar murya yace sau uku.

Toh ka fita harakar Bintu kuma ka sani Aure dakai da Bintu ya ƙare saidai ka nemo wata Fatima badai wannan ba , "kuma ina so kayi gaggawar sakin ta kaji ....!

 Cikin ruɗani da tashin hankali ya dawo wurin didda yace didda don Allah da Manzonsa kada ki raba ni da Uwar-biyu wlh ina sonta , don Allah kiyi haquri ya'ida kamar zai yi kuka...

  "Kai salim ka fita idona indai akan Bintu ne wlh idan kayi wasa saina tsine ma."
Tashi tsaye tayi tana cewa keee Bintu wuce muje, sum-sum suka wuce....

  Zama yayi wurin zuciyar sa na masa quna yana nadamar Abin da yayi a baya, yakai kusan minti 5 sannan ya miqe ya fita, motar da ya shiga yabar gidan.

★*★*★*★*★*★

Cen suna shiga Fatima tasa ma Didda kuka wai yanzu ta zama mafaɗaciya, nandai didda ta bata haquri, sukaci hirar su.

Haka dai Family suka yini cikin farin-ciki...

Fatima ta kira su Mommy sun gaisa da kowa rayuwa kenan.

  Da dare bayan sunyi dinner a fallon husnah suke zaune, husnah Jameey Bintu sai hira suke.

"Husnah ce tace gaskiya didda naga kwanukan ga ta ɗau fushi da yawa, kuma ga yaya tana fushi dashi.

Jamila tace hmmm husnah kenan ai wai ita didda idan bai saki Bintu zata masa baki.

Sallama akayi gaba ɗaya suka amsa imaru ce duqawa tayi ta gaida su , cewa tayi Anty Bintu Wani ne keson ganin ki.

Ni kuma Imaru Fatima ta faɗa tana nuna kanta.

"Eh Anty.
Yaya salim ne.?
A'a bashi bane.
Okey.
Itakam imaru tashi tayi tana fita.

Fatima ma tashi tayi, Husnah ce tace ke Bintu kiji tsoron Allah da auren wani a kanki.

Juyowa fatima tayi girgiza kai kawai tayi tana fita haɗe da mamakin sonkai irin nasu...

  Tana fitowa wurin didda taje, tana cewa Didda wai ana kira na. "To Bintu jeki duba."
Ba kowa a fallon haka tasa kai ta fita, tana fitowa harabar gidan ta duba bata ga kowa ba.

 Harta juya taga an hasko mata fitilar motar, cen ta nufa "buɗe motar akayi Abdul-Hakeem ne..

Assalamu alaikum.
Wa'alaika-salam Fatima ta amsa.

Murmushi yayi yana cewa Fatimah xahrah Fatima wlh ina sonki kuma auren ki zanyi tunda bakya son mijin ki, Fatima zan iya rasa raina a kanki.

"Duban sa tayi haɗe da cewa haba ya Abdul nifa matar aure ce kuma ina son mijina , bata saurari mezai ce ba ta wuce."
Yana kiranta ko juyowa batayi ba .

Tana shiga part ɗin didda ta shiga, tana shiga ta wuce ɗaki ba kowa, zama tayi bisa bed tana cewa na shiga uku Ni Fatima, wayar ta ta ɗauka ta kira laila.
.  Tana ɗauka bayan sun gaisa tace laila don Allah idan ba damuwa dobe kizo.

Lafiya dai ko.
Ehhh.
To saina zo.
Okey, fatima ta faɗa tana katse kiran.

Kwanciya tayi rumgume da Meenat amma ta kasa barci sai tunani takeeh.

★*★*★*★*★*★
Rayuwa kenan yau daren sunan Meenat..
 Tunda safe gidan ya fara cika da mutane ƴn aiki sai hidima ake tayi.

Fatima kam suna cen tare da su husnah a part ɗin husnah.

  Suna zaune suka ji sallama, "amsawa sukayi ya docta ne.
Gaida sa sukayi baima amsa musu ba ,miqe wa husnah da Jameey sukayi itama Fatima ta tashi..

Hannun ta ya riƙo yana mayar da ita inda ta tashi, shima zama yayi yana cewa haba uwar-biyu ina zaki nifa mijinki ne Fatima kiyi haquri kibar komai ya wuce.

"Nifa ka kyale ni yanzu inada wanda nake so kamanta cin mutuncin da kamin sai yau zaka san Ni matarka ce ...

Hannun wanta ya riqe yana cewa haba uwar-biyu ko Allah anawa laifi ya yafe balle Mutum , ki kasance mai yafiya kiyi haquri my Bintu uwar-biyu.

Taji daɗin maganar sa , tana ɗayowa suka haɗa ido sun kai some second's suna kallon juna, kauda kanta tayi tana cewa a zuciyar ta gaskiya duk macce data samu D.R SALIM Hassan Sauta ta gama dace, tunanin ta ne ya kau jin yace My Bintu me kike tunani.

Ɗagowa tayi tana cewa ba komai, kaga bari naje nabar Meenat ita ɗaya.
 "To mezai samata kinga Bintu ki kyale didda ko'ita fa naso take mu rabu ba kinji...

Jawo ta yayi jikin sa yana aza kansa bisa kafaɗar ta, sai sun-suna ƙamshin jikin ta yake, "ƙwoce jikin ta take sonyi amma ta kasa.

Ganin tana ƙoƙarin yimasa kachaɓu yasa ya kyale ta , tashi tayi cikin sauri tabar wurin.

Shiko yakai almost 5 minutes kansa na sara masa sannan ya tashi ya fita.

Fatima na isa part ɗin didda ga laila, gaisawa sukayi ganin akwai mutane ɗakin didda yasa Fatima jan hannun laila izuwa na kusa da didda.

Ba kowa ciki ko'ina a gyare, zama sukayi Fatima na tambayar mutanen gida.

Laila kesan me.?
Aa Fatima.
Dama didda ce tun dawowa ta, tasa yaya docta gaba akan saiya sakeni , kuma ko jiya Yah Abdul-Hakeem yazo gidan nan wai aurena yake so yayi kuma fa abokai ne.

Hmmm ajiyar zuciya laila tayi tana cewa Bintu da didda tace yaya docta ya sake ki mai yace.?

Duban ta Fatima tayi tana cewa laila cewa yayi bazai iya ba, yana sona, ko yanzu ma daga part ɗin husnah nake har cen ya iskoni yana bani haquri.

Fatima kina son sa Laila ta tambaye tah.?

Cikin mamakin wannan tambayar Fatima tace mee....e...lai....la so kuma? A'a nikam.

Murmushi laila tayi tace Fatima kina sonsa , yanayin ki ya nuna , kada ki manta so ba ruwansa da kyawo muni balle wani abu,.

"Nidai laila ba wani so.

 okey idan tayi tsami maji, yanzu shawara ta a gareki ita ce kada ki rabu da mijinki.

Laila Didda fa.?

Hmmm fatima kenan didda tafi kowa farin cikin kasancewar ki da ɗan ta, kawai de tana so ne ta raba auren domin gani take zaki cutu , amma nidai ki rungumi mijinki .

"Hmmm ajiyar zuciya kawai Fatima tayi tana cewa to laila Nagode kuma Insha-Allah zan gwada.
To , suka tashi suna fitowa sai fallon didda, mutane ne, gaisawa sukayi.

Wata daga cikin su ce tace kece Bintu.?
Eh, nice .
Ayya to Barka da dawowa nan suka shiga gaida ta tana amsa wa .

Miƙewa sukayi suka shiga ɗakin didda nanma mutane ne , gaida su sukayi nanma suka shiga yiwa Fatima Barka.

Didda dama laila tazo koma wa zata yi.

To Bintu bari nazo, "leda ta ɗauko ta bata da Naira dubu amma tayi suna godiya, rakota Fatima tayi bayan sun fito laila ta shiga mota, Fatima ta juyo.

Uwar-biyu..

Jin sunan saida taji sanyi a ranta. "Ƙara sowa yayi gaban tah, "hannun ta ya riqe yana cewa yanzu laila ce shine baki bari mun gaisa ba.

Uhmm,uhmm ai ban sani ba kananan.

Bintun ya za'ayi kisan inanan bayan hankalin ki baya guna .

Uhmm.

Fatihhhhhhh saida taji sunan wani iri "a hankali tace na'am.

Muje ki rakani.

Zaro ido tayi tana cewa A'a nikam didda nacen na jira na.
My Bintu ki bari muje kinji yanzu zamu dawo, "itakam Fatima cewa tayi A'a.

Hannu yasa a Aljihu ya xaro kuɗi bandir ɗaya miqamata yayi yana cewa gashi in kina buqatar wani abin "jiya nakai miki ɗinki fitar biki Insha-Allah anjima zan amso .

A'a kabar kuɗin nikam.

Nikam kidai amsa , bai amkara ba ta wuce da gudu, husnah ya kira a waya, tana zuwa, ya bata kuɗin yace ta kaima Fatima....

Tana zuwa ta bata , "shirya wa sukayi suka fito didda sukayi wa sallama Basu tsaya ko'ina ba sai wani babban shago SALON AND HENNA FASION,.

Suna shiga sukace lalle za'ayi musu da kitso , itakam Fatima cewa tayi salon take so..

Jameey ta dubi ma'aikatan wurin tana cewa wannan kam ai mata na musamman harda gyaran jiki domin amarya ce...

  Hararar ta Fatima tayi  aka ci gaba da musu Fatima harda gyaran jikin amma fa bada son ranta ba.

★*★*★*★*★*★*★

*Ɓangaren mutuniya Sabeeterh*

Tuni tabi umarnin mama hannatu ta watsar da komai, sai shirin biki ake. "Inda docta ya bata makudan kudade na biki..

Yauma ƙawayen ta ne cike sai lalle ake, domin wata mai lallece ke musu.

Inda docta yace didda ta bata Amina yau zuwa gobe don kawadda idanun mutane.

  Itakam Sabeeterh bata ma damu ba Meenat nanan hannun ƙawayen ta, sai yaba kyawon ta suke...

"Dama nonon ta baiyi ruwa ba shiyasa bai dameta ba kuma mama hannatu ta kawo mata magani ( nikuma nace shin anya kuwa sateey ta mance cewa sai Allah idan zata qara haihuwa ba).

Sun shirya wani dinner da za'ayi gobe suna idan anyi walima nan gida ... "Khairat ta gama shirya komai saidai a jira gobe suna.

★*★*★*★*★*★*★

Cen ɓangaren kuwa tuni amgawa su Fatima, wow fans kunga sosai ammata salon ko nasu husnah yayi kyau sosai, bayan an gama harda gyaran jikin kamar amarya da za'a kai gobe sai daddaɗan ƙamshi ke fita daga jikin ta....

Husnah ce ta kira yaya docta akan yazo ɗaukan su tunda da amaryar sa suke, to yace "ta tura masa address ɗin wurin.

Baafi 20 minutes ba yayi parking a wurin, yana zaune har suka fito...

Kallon ta yake cikin sha'awa da birgewa yaga ta qara kyau sosai..........

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
 By:👇

🥀RUKAYYA UMAR FARUK
  {Samha Umar}🥀

  🎈🎈🎈This page 32 dedicated to you FARIDAH SHEHU 🎈🎈🎈

PAGE_______32

Bismillah_Rahmanin-Rahim.

Suna isowa, gaida sa su husnah sukayi, "Fatima buɗe bayan motar tayi , Jamila ce ta harare ta, husnah kam ɗan jawo ta tayi tana buɗe mata gaban mota haɗe da  cewa Anty babba gashi na buɗe miki shiga.

Shiga tayi tana jin zuciyar ta wasai. 
Bayan kowanne su ya shiga .

Yana tada motar basu tsaya ko'ina ba sai gida, a parking lot yayi parking.

Bayan fitar husnah da Jameey, buɗe murfin motar Fatima tayi da niyar fita, “amma saita jita kulle, a hankali ta furta ka buɗe min na fitah.

    "Bintuuu ina tambayar ki miye haɗin ki da Bawa (Abdul-Hakeem).
Kamar zatayi kuka tace ba komai nidai ka buɗe min na fitah.”

Wayar ta ce tayi ring duba screen ɗin tayi saida gaban ta ya faɗi, jin docta zira hannu ya amshi wayar yasa ta ɗagowa.

Shiko ganin babu suna ga number, yasa shi peaking haɗi da sa handsfree..
  Acen aka fara magana kamar haka.

"Amincin Allah da yardar sa su ƙara tabbata ga Gimbiya sarauniyar mata Fatimah*Xahrah wlh Fatima na kasa samun natsuwa ta dalilin ki inanan ina tunanin ki a raina, "Fatima Abdul-Hakeem ne masoyinki kuma mijin ki........

Cikin ɓacin rai da ƙunar rai da wutar zuciya docta yayi jifa da wayar gaban mota, wanda yayi sanadiyar tsagewar glass ɗin gaban mota.

   Rinannin idanun sa wa'enda suka chenza color From white to red, watsama fatima yayi jikintah sai rawa yake yi.

Bintuuu..... bintuuu...da hakan komai bai ƙara cewa ba illa buɗe murfin motar da yayi ya fita.

Hawaye ne ke ƙwaranya a idanun Fatima itama buɗe murfin motar tayi tana fitowa, a hankali take tafiya harta isa ciki ta baya tabi.
   Tana shiga ɗayan ɗakin ba kowa, filo ta jawo ta'aza bisa capect ɗin daya ƙara ƙawata ɗakin, "kwanciya tayi tana kallon cili hawaye ne ke ƙwaranya a idanun ta wa'enda ta kasa tsayar dasu kuma bata san na miye ba.....!

Takai kusan minti 30 kafin bacci yayi nasarar kwasarta , cen cikin bacci taji ana kiran sunan ta .
  "Addu'ar tashi daga bacci tayi kafin kuma ta tashi, husnah ce tsaye cewa take Bintuuu didda ce tace na duba ki kuma kinga lokacin sallah yayi husnah na ida faɗar haka tayi tafiyar tahhh.

"Miqe wa Fatima tayi saida ta ɗora alwala ta fito tana kabarta sallah...."

★*★*★*★*★*★*★

DA DARE BAYAN SALLAH ISHAH

Shigowar Fatima kenan ɗakin Husnah.
A Bintu yanzu nake so na iakoki dama kaya ne from my Brother to my sister, zo kiga sunyi kyau sosai.

Ajiyar zuciya Fatima tayi bayan ta zauna tana jin ciwon kai, sunga kaya sunyi kyau itakam Fatima kalla bata ce ba saima tashi da tayi, bata tsaya ko'ina ba sai bedroom ɗin didda.

  “da sallama ɗauke a bakin ta ta shiga, amsa mata akayi”, Anty zeenatu ce tace Bintu tun ɗazu inata tunanin inda zan ganki, to ykk.?

Murmushi Fatima tayi bayan ta zauna tana cewa lafiya ta Anty zeenatu ina Khalifa.
Yana cen gida, nandai suka ɗan taɓa hira.

Tashi Anty zeenatu tayi tana cewa bari naje na dubo Meenat Bintu zo muje ki rakani , "Fatima bata so ba amma kuma ya zatayi  tashi tayi.
Fitowa sukayi Fatima ce tace Anty sai yanzu kika zo.

   Eh, Fatima amma nan zan kwana.
Ayya."

Suna shiga fallon sabita sallama ɗauke a bakinsu khairat ce ta amsa..
 Ƙara sowa Anty zeenatu tayi tana murmushi bayan ta zauna take cewa mun zo duba ƴrmu.

Khairat ce ta amshi Meenat dake hannun ɗaya daga cikin ƙawayen su tana miƙoma Anty zeenatu.
Bayan Anty zeenatu ta karɓa take cewa kai Masha Allah Meenat sai bacci take ba ruwanta, Bintu xoki karɓi ƴrki Anty zeenatu ta faɗa tana duban Fatima.

  "Toh Fatima ta faɗa haɗe da ƙara sowa domin karɓan Meenat, dakata....dakata... Sabita ta faɗa kull kada ki sake ki taɓa min ƴrda na haifa, domin kada ki cinye ta ."

Ɗaya daga cikin ƙawayen ta mai suna Aliya tace oh itace Bintu jakar lallai kam sateey yanzu kamar kee a rasa dawa za'a haɗaki kishi saida wannan mai suffar biri .

Duban Fatima Sabeeterh tayi tana cewa kee Aliya kishi da wannan matar tirse , baƙin jini ta tasa mai sonta shine aka liqawa docta wacce tayi gadon baƙin jini ga uwarrrrr....... Dafe kunci Sabeeterh tayi sakamakon marin daya sauka a fuskar ta , ɗagowa tayi domin ganin wani isasshen ne yayi ƙworin hannun marinta.

  idanun ta ne suka ga Fatima "cikin masifa Fatima ta fara magana wlh wlh iskancin ki da rashin mutunci su tsaya iya ni Fatima ‘tunda rashin isashiyar tarbiyya tasa kika zagi mahaifiya ta wacce ke kwance Cikin ƙasa, ƙara jan tsaki tayi tana fita ranta na ƙuna....!

"Mara mata baya  Anty zeenatu tayi bayan ta miƙa Meenat ga khairat, sai kiran sunan ta take Bintu...Bintu....

Ya fito kenan domin yana so ya ɗan fita , ganin Fatima cikin sauri take tafiya da'alama  akwai wani abin daya ɓata mata rai Uwar-biyu ina aita wucesa.

  Anty zeenatu ce ta ƙara so , cewa tayi a yaya docta kaine a nan.
Murmushi yayi yana cewa ehhh, zeenatu meya sami Bintu.?
Wlh ita da matarka ce nan dai ta gaya masa komai.

Fatima na shiga ta wuce, nan fallon husnah ta zauna, take tunanin mahaifiyar ta ya dawo mata sabo, tana jin baƙin ciki tabbas didda bata rageta da komai ba, amma tana kewar mahaifiyar ta.

   Jin an tallobo fuskanta yasata ɗagowa ba kowa bane face docta  haushin sa ne ya kamata a zuciyar ta take cewa ai duk abinda sateey ta mata shine yaja mata.

"Bintu uwar-biyu kiyi haquri da abinda matata tai miki kinji my uwar-biyu , haba Gimbiyar didda kiyi haquri kinji.
Uhmm.. kawai Fatima tace.

Zaman sa ya gyara tare da riqo hannayen ta yana cewa Fatimah shin zaki rabu dani kamar yanda didda take buqata.!?
Wlh Fatima yanzu na shirya zama dake kuma don Allah ki manta da abinda ya faru cen baya.

Hawaye ne taji yana zuba a fuskar ta bayan hannun ta tasa tana sharewa haɗe da cewa yaya nikam duk hukuncin da didda ta yanke shine daidai gareni ta'ida tana duban sa .
   "Rasa ma me zaice yayi domin shifa idan harta fahimci ya damu da sonta sosai to zata raina sa.

Toh kawai yace mata yana miƙewa fita yayi daga fallon.
Gyara zama Fatima tayi tana tunanin yanzu mijinta idan ta rasasa , kamar wai idan ta rabu dashi anya tayiwa didda adalci, ai yaci ace ta zauna da ɗan ta ko don ita , kuma ma idan tace idan tace bata son mijinta tayi ƙarya , idan kuma tace tana sonsa tayi ƙarya.

  Miqe wa tayi , da sallama ta shiga bedroom ɗin husnah, husnah ce kawai zaune saman prayermat ta gama sallah isha amsawa Fatima sallama tayi.

Zama bisa bed fatima tayi tana cewa husnah Please aromin wayar ki.
To husnah tace bayan ta ɗauko wayar bisa mirror ta miƙama Fatima.
  “fatima na amsa ta saka number salma da yake ta haddace ta , tana kira Salma na ɗauka gaisawa sukayi, salma na cewa a Fatima yana ganki da sabuwar number kodai mijin namu me ya cemza miki sim...

Uhmmm.. Salma aa na ƙaunwata ne husnah, ayya kawai salma tace.
"Fatima ce ta ɗora da faɗin wlh salma dama ina so ne ki turomin number meenal ta wannan layin ina so mu gaisa tun sanda na dawo nan bamuyi waya ba.

 Okey, Tom yanzu zan turomin , “to Fatima tace tare da katse kiran miqama husnah wayar tayi bayan ta miƙe ‘tana cewa Please husnah za'a turomin number ta inbox ki kulamin .
Toh husnah tace bayan ta amshi wayar ta....

★*★*★*★*★*★*★

Fatima na fita sai ɗakin didda, da sallama ɗauke a bakin ta ta shiga‘didda ce kawai a ɗakin amsa tayi tana cewa ƴrtah Kiyi haquri yau duk bamu samu mun zanta ba .
"Oh, ba komai didda."
   Bintuuu.....
Na'am didda Fatima ta amsa mata tana zama kusa gare ta .

  Zeenatu ke gayamin abinda Sabeeterh tai miki, kiyi haquri don Allah, ai duk laifin Salim me shine ya ɗaure mata gindi bata ganin kowa da gashi , to wlh sai Salim ya haɗu da ɓacin raina .

  "Fatima tace to didda shi yaya me yayi....!?

Riqe baki didda tayi tana cewa tohh me yayi kuma lallai ma Bintu ? to bari ki gani tashi didda tayi tana fita, bin bayan ta Fatima tayi sai part ɗin yaya docta....

   Suna shiga sallama ɗauke a bakin su , baya fallon zama didda tayi bayan ta harari Fatima tana cewa ba zaki zauna bahhh...
"Cikin lumana Fatima ta zauna, Salim... Salim.didda ke kwaɗa masa kira".

Fitowa yayi, “a didda Barka da dare.?
Uhum kawai didda tace, zama yayi kusa gare ta,
Tashi tsaye didda tayi tana yi masa mugun kallo Salim wlh na gaji da halin waccan matar taka,  marar tarbiyya Bintu ta fita tafi gaban tah kuma da taso da kada taso saida Fatima ta zama matarka kafin ita harwai tana kiran ta matar tirsa? "To alhamdullh ba tasa mijin aure tayi ba har a tirsasa maka auren tahh , Insha-Allah komai yazo ƙarshe domin ana gama sunan Amina zaka sawwaka ma ƴrtah ta auri mai sonta ta zama Matar so ba Matar ƙi ba.!

   Didda don Allah kiyi haquri zan yiwa sateey magana ita kuma Bintu kibar maganar saki kiyi haƙuri wlh ina santa itama haka, ya ƙara sa yana tsare Fatima da'ido.
Itakam noce kanta kawai tayi....

Didda ce ko Bintu naso ko bata so aure tsakanin ka da ita na yanke shi ko'a lahira ta'ida cikin tsawa haɗe da duban Fatima tana cewa wuce mu tafi kekooooooh.!

Tashi Fatima tayi ta mara mata baya, didda part ɗin Daddy ta wuce ita ko Fatima ɗaki tashi ga.
Hawaye ne ke zuba a idanun ta  itadai har yanzu ta rasa Sanin dalilin kukanta “murɗa akayi aka shigo.

Husnah ce , cikin sauri Fatima ta ɗago rinanin idanin ta tana duban husnah bayan ta share hawayen ta.
Ajiyar zuciya husnah tayi tare da zama tana dafa kafaɗar Fatima, "Bintu kiyi haquri da komai Insha-Allah komai mai wucewa ne, ki rungumi kaddara ki Allah bazai taɓa ɗorawa bawan sa abinda yafi ƙarfin sa , gashi an Turo number ta ƙarisa tana miqama Fatima wayar .

Karɓa Fatima tayi haɗe da cewa husnah NGD 🙏.
Itakam husnah tashi tayi, tayi tafiyar tah.

  Number fatima ta kwoshe haɗe da kira , tana shiga aka ɗaga " Assalamu alaiki.
Wa'alaiki-salam aka amsa mata.
Fatima ce ta ɗora da faɗin Meenal ykk Fatima ce.

Lah Fatima kece wlh inanan lafiya ƙalau fatan kenan haka wlh nayi kewar ki ɗazun ma na gama zancen ki da mama.

Ayya meenal nima nayi kewar ki, rannan dana kiraki Mama ce ta ɗauka take cewa bakya nan , "Eh, Fatima wlh ta gayamin bani da kati ne kuma layina baya vip , ya mai-jiki? Salma ta gayamin kin koma Kano yanzu inda Mommyn ki.

  Eh, Meenal hakane yanzu aurenki 25may Allah ya nuna mana kuma Insha-Allah zan shigo auren.
 Toh Fatima ai nima Kanon Allah ya kaɗoni, sannan Fatima kina da aure shine baki taɓa gayamin ba ....

Hmmm, kiyi haquri salma nidai kinga sai anjima ki gaida mama "to meenal tace Fatima na kashe wayar..."

Ajiyar zuciya tayi tare da miƙa Toilect ta shiga , ruwa ta watsa haɗe da ɗauro alwala nan ta kabarta sallah tana idawa ta kwanta......!!!!!

★*★*★*★*★*★*★
RANAr BIKi

Da misalin ƙarfe 9 ƙofar gidan Alhaji Hassan Sauta ya cika da manyan mutane ƴn siyasa ma'aikatan gwamnati dama likitoci aka zaba sunan NANA AMINATU SALIM HASSAN SAUTA.

 Cen cikin gida kuwa cike yake da ƴn uwa da abokan arziki sai hada-hada ake an shirya walima wacce za'ayi da ƙarfe 2 zuwa 4 domin akwai party da uwaye suka shirya ƙarfe 5...

  Su Fatima ne zaune fallon husnah da sauran ƙawayen su , sallama akayi daga bakin ƙofa ɗagowa sukayi bayan sun amsa.

Laila ce sai Salma dake bayan ta , riƙe baki Fatima tayi tana zaro ido haɗe da cewa mafarki nake kome Salma kece.?

Murmushi Salma tayi tana cewa nicedai nice Fatima.

To amma ai jiya da mukayi waya baki gayamin zaki zo bahhh.

Ahah ai jiya koda mukayi waya ina cikin Kano .
Ayya to ku zauna ya jikin hassanah tahhh..?

Taji sauƙi sosai sai neman ki take, nandai akaci gaba da hira......

Wayar husnah ce tayi Ring peaking tayi tana kadawa a kunnen ta , bayan kamar 1 minute tace okey Yaya haɗe da cire wayar daga kunnen tah...

Bintu zokiji ta faɗa tana shigewa ɗaki, "bin bayan ta Fatima tayi,
Zama husnah tayi tana cewa Bintu yaya yace yana kiran ki zaki gaisa da abokan sa. .

Hmmmmm, ajiyar zuciya kawai Fatima tayi.
  "Je kiyi wanka saina miki kwalliya ko'a hakan zaki husnah ta faɗa tana kallon Fatima.

Haka kawai taji tana so taje tayi wanka , ‘toilect ta shiga takai almost 20 minutes kafin ta fito ɗaure da towel, bisa kujerar mirror ta zauna  tana tsane jikin ta , haɗe da shafa Mai .

Husnah ce ta matso kusa gare ta cikin abinda bai gaza 10 minutes ba ta tsantsara ma Fatima kwoliya mai kyau, Fatima tayi kyau kamar wata amarya .

"Akwoti husnah ta jawo haɗe da cewa bari na zaɓo miki kaya, wani yadin material mai kyau da tsada green mai adon duwatsu ɗinkin yayi kyau sosai riga da skirt."

  Bayan Fatima tasa husnah ce ta fara ɗaura mata ɗan kwalli ,
 Turo ƙofar akayi laila ce da salma sai wata murja ( wai nikam nace dai fans ko kun ganamin mutuniya Jamila i miss her).

Laila ce tace kai Fatima kinga yanda kikayi kyau kamar wata amarya, nandai suka riƙa zuzuta kyawon Fatima har aka gama ɗaurin ɗan kwalli , sarƙa Golding mai kyau tasa sai takalma lemungreen sai ƙamshi ke tashi a jikin ta kamar ka sace ka gudu ......................

_Akullun ina ƙara godiya gareku masoya nah, ni taku ce ƴr mutan Kebbi-

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
 By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
     {Samha Umar}🥀

PAGE_______33

Bismillah_Rahmanin-Rahim

  Fitowa sukayi da sauran ƙawayen su, "suna fitowa sai ɓangaren docta, da sallama suka tura ƙofar fallon .

"Bayan sun shiga gaisawa sukayi, docta kam idanun sa akan Gimbiyar sa tauraruwa sa.

  Wani daga cikin abokan sa ne mai suna Sa'eed ke cewa to Uwar-gida Allah ya nuna mana munzo sunan ƴrki ko ɗanki , su husnah ne suka amsa da Amin itakam Fatima tananan rakuɓe jikin kujera ta kasa sakat. 
  "{Lalala kunga wani rashin kunya wai harda Abdul-Hakeem}"

Bayan sun gama fitowa sukayi domin ɗaukar hotuna , Habib ne kenan husnah magana amma sai sharesa take kamar bata san yanayi bah.!!

 Docta Kam kamar ya haɗiye Fatima don so , saida ya faki idanun mutane, hannu biyu yasa ya ɗauke ta chak , ai kuwa saiga idon Abdul-Hakeem" Inalilahi wa'inna ilaihin raji'um ya faɗa yana danne ƙafon zuciyar sa ......

  “yana shiga da'ita bisa bed ya kwantar da'ita shima gefen ta ya kwanta tare da ɗan ɗagowa saitin fuskanta.
"Bintuuu kinyi kyau" wannan kwoliya haka duk Ni kaɗai anya baso kike na zauce bahhh ya ƙarisa zancen tare dasa babbar yatsar sa yana shafa gefen kuncintahh...

  Motsi ta fara yi da baki alamun magana zatayi, hakan ya basa damar chafke bakin ta haɗe da sakar mata hotkiss sai ƙara jawo ta jikin sa yake .
Itakam duk tsikar jikin ta tashi ga wani fargaba daya mamaye zuciyar ta, 
   "Ƙoƙarin zuge mata zif ɗin riga yake, lallausan hannun ta tasa ta riƙe nasa amma ina yayi nisa baya jin kira ,.

Yayi nasarar zuge zif ɗin rigar Tata tare da ɗan zaneta daga jikin ta , ƙoƙarin kwonce mata brezia yake , riqe hannun sa Fatima tayi tana cewa yaya don Allah ka bari mutane nacen fallo suna jiran mu ta'ida maganar muryarta na rawa....!!!

    “baya so takura ta , hakan yasa ya raba jikin sa da nata, Toilect ya shige ya barta nan.”
    
Tashi tsaye Fatima tayi bayan ta gyara rigarta , saida tasa hannu ta ɗan shafe jikin ta kafin kuma a hankali ta buɗe ƙofar ta fito.

Koda ta fito ta iske su zazzaune su husnah an kawo musu abinci sai ci suke.
 “fatima ce ta dube su haɗe da cewa to ku wuce muje mayi shirin zuwa walima tana ida faɗar haka tayi tafiyar tah.

Suma tashi sukayi, Habib ne ke magana da husnah.
"Husnah wai meyasa hakan na turo Iyaye na kince baki tashi ba....

Hmmmmh, Ajiyar zuciya husnah tayi tana cewa to shikenan Amma ka bari saura wata shidda mu ƙare karatu nida jameey sai ka sake turowa ..
 Dariya yayi yana cewa haba My hussy ai koda na turo ba yanzu za'ayi auren ba sai kun ƙare karatu.!

Toh, husnah ta faɗa tana wucewa cikin sas-sarfa, su Fatima na shiga laila tace Fatima tare muke dasu Mommy.
 "Lahhh, da gaske laila muje na gaida su ta faɗa tana wucewa.

Koda sukaje fallon Didda Mommy da Umma sai sauran mutane, “Rumgume Mommy Fatima tayi bayan ta zauna kusa gare ta tana cewa My Mommy I miss you so much.”

Murmushi Mommy tayi tana cewa kina lafiya ƴrtah.?

Lafiya Mommy Ina hasnah da jiki ina kewar tah.

Hasnah taji sauqi sosai wlh tana gaida ki ,. 
  "Ina amsawa Mommy, sai sannan Fatima ta juyo tana gaida umma.”

Bata wani jima tana hira da Mommy ba ta miƙe domin tafiya , nan Mommy ke gaya mata sun ɗauko mata kayan ta dana cen Jigawa dana gidan Umma.
 "Toh Mommy NGD 🙏"

Kaya iri ɗaya suka saka husnah Jamila da Fatima, nan harabar gidan aka kafa Rumfuna tare da kujeru domin gudanar da Walima an ƙawata gurin yayi kyau sosai.
 Malama murjanatu ta gudanar da wa'azi.

Anyi rabon kaya sosai kamar ba gobe, "ƙatuwar jaka ce mai ɗauke da hoton Amina a ciki akwai Turmin atamfa , ƙaramin towel, memo, tare da majayi.
 Sai leda mai ɗauke da snaks peeza doughnut cin-cin haka dai aka gudanar da biki sai kuma zuwa party da za'a gudanar a wani katafaren hotel....

Su Fatima ne zazzaune suna shirya wa, nanma wani less darkred suka saka sunyi kyau sosai, "tuni an shigar mata da kayan ta , didda tace su ajiye mata a ɗakin dake kusa da nata ....!

 Laila ce ta shigo ɗauke da sallama a bakin tah .
Amsawa Fatima tayi tana murmushi, .
Uhmm Bintu mu zamu wuce.
 “tun yanzu laila ba zaku bari har ayi sallar magriba ba .
Murmushi laila tayi tana cewa wlh kega har yaya yazo ɗaukar mu .

Mayafi kawai Fatima ta yafa suka wuto, har sun fito harabar gida inda yaya Ahmad yayi parking matar sa , anan suka tadda su Mommy da Yaya Ahmad, docta ne tsaye suna gaisawa dasu Mommy....!!!!!!!

Fatima ce tace yanzu ku Mommy tun yanzu zaku wuce, murmushi kawai Mommy tayi.
  "Fatima ce ta ɗora da faɗin My salma sai yaushe zaki koma."
Eh, to Fatima sai an sallami hasnah sai mu koma tare , .

Toh shikenan nima zanyi ma Didda magana Insha-Allah zan shigo assibitin kafin a sallami hasnah, sannan kuma zanzo Jigawa auren Meenal.

  Toh Fatima sai kunzo, suka shish-shiga mota .

"Yaya yace Fatima zo kiji ya ida yana matsawa cen gefe ."
Ɗagowa Fatima tayi idanun ta sai cikin na docta dake mata mugun kallo .

Soke idanun ta tayi ƙasa, matsawa tayi Chen inda yaya Ahmad.

Magana ya fara yi , Fatima dama yanzu a gaskiya cen baya nayi kuskure dana sakama kaina zan aure ki , kuma ina neman yafiyar Allah, yanzu munyi magana da Mommy akan in maida akalar soyayya ta ga Laila.
  Laila ƙawarki ce nayi mata magana amma buɗar bakin ta cewa tayi, "wlh ita ko rasa mijin aure ba zata taɓa Aure na ba tunda harna taɓa furta kalmar so gareki, shine nake Ganin ya dace na miki magana sai kiyi mata magana ko zata amince....

  "Murmushi Fatima tayi tana cewa kada ka damu yaya Insha-Allah zan yi mata magana kuma zata amince."

Toh yaya Ahmad ya faɗa haɗi da godiya, wucewa yayi ya shiga motá yana tayar wa , Fatima na ɗaya musu hannu har suka wuce.

Hmmm, ajiyar zuciya Fatima tayi haɗe da juyowa, matsowa docta ya fara yi , inda take aikuwa ta arce da sauri tayi cikin gida.

Mutane duk sun fara wucewa wurin party , itama tare dasu husnah suka wuce.

Hall ɗin ya ƙawatu sosai inda har mutane sun cika, Sabeeterh da ƙawayen ta sunyi kyau sosai...!

"Cen gefe su Fatima suka zauna domin ita yanzu babu abinda ta tsana da yakai shan inuwa ɗaya da Sabeeterh.
Bayan an sake kiɗa Sabeeterh kam ta chashe da'ita da ƙawayen tahhh."

Bayan anci ansha , an raba kayan biki , an raba wa mutane kyaututtukan da za'a bayar , sai video ake tare da photo.

Sai Wuraren 7 aka watse , su Fatima duk jikin ta yayi laƙas , a haka suka dawo gida.

Sallar magriba kawai tayi ta ɓingire sai bacci.

  "Ita ce bata tashi ba sai gurin ƙarfe 11pm , tana tashi Toilect ta shiga tayi wanka ta ɗauro alwala salar isha'i tayi bata tsaya komai ba ta wuce ɗakin didda sallama ɗauke a bakin ta ..

Didda da yanzu ta fito daga bayi ta amsa salamar.

Zama Fatima tayi gefen gado tana cewa My didda magana zamu yi.

  to Didda tace haɗe da cewa yanzu bari ina zuwa, ta ɗauko hijabi tana zurawa ta fita, wayar didda dake jone a charge Fatima ta ɗauko haɗe da shiga Contact number da akayi saving da Hajiya Rukayya ta kamo haɗe dayin darling ...

Tana Shiga akayi peaking haɗe dayin sallama, amsa Fatima tayi tana cewa Umma Bintu ce kun koma gida lafiya.?

"Lafiya lau Bintu har assibiti saida muka biya."
Ayya Umma dama ina so magana da laila.
Toh Fatima bari akai Mata.

Tana kashe kiran ba'a fi 2 minute ba ga kira ya shigo, tana ɗauka laila tace Bintu.

Na'am laila Fatima ta'amsa haɗe da cewa laila magana zamu yi.
"Toh Bintu ina jinki."

Laila akan yaya Ahmad wlh kada kiyi duba dani imma danni kika ce bakya sonsa to ki cenza, kada kiyi duba da ya taɓa cewa yana sona ki duba zumunci ku.
Sannan Ni inada miji da aure na , kuma don Allah ki aure sa Wlh yaya yana da mutunci kinji.

Cikin waya laila tayi ajiyar zuciya kafin tace Bintu nifa naga bai kamata yace yana sonki ba kuma ya dawo yace yana sona ....!

Laila na gaya miki kada kiyi duba dani don Allah ki amince ki aure sah.

  'uhmm to shikenan Fatima daga haka laila ta katse kiran.

Ajiyar zuciya Fatima tayi kafin ta amsa salamar didda "bayan ta amsa ƙarasowa didda tayi tana zama gefen Fatima.

   Ajiyar zuciya Fatima tayi Kafin ta juyo tana kallon didda haɗe da cewa Didda maganar da zamu yi.

"Nisawa didda tayi tana cewa duk na gaji amma Bintu ina jinki "

Saida fatima ta ɗan yi shuru na wasu mintina, tana tunanin yanda didda zata ɗauki zancen tah, sai kuma a hankali tace didda don Allah kiyi haquri da abinda zance!!! “dama ina so ne ki gayamin wani abu game da Mahaifina.........

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

������
RIBAR~HAQURI
������

Story & Writing �
 By:�

� RUKAYYA UMAR FARUK
      {Samha Umar} �

PAGE_____34

Bismillah_Rahamanin-Rahim

      Bintu wanna save iriyar Tambaya ce kike min..?

Didda don Allah kada ranki ya ɓaci, kiyi haquri Fatima ta'ida hawaye na zuba a fuskar tah.
  "Gyara zama didda tayi kafin ta nisa tana jawo Fatima jikin ta haɗe da cewa kada ki damu didda ki bari yanzu zan gaya miki akan mahaifin ki share hawayen ki kinji Bintui..."

Tom didda hannu Fatima tasa tana share hawayen ta, qara lafewa jikin didda tayi.

   ```FARKO```

Lokacin da auren mahaifiyar ki Amina ya matso tazo nan gidan, muna zaune da'ita na dubeta haɗe da cewa Amina wai ina dangin A.s.p kamal.? Kuma su waye dangin sa.....!!!

Nisawa Amina tayi kafin ta dube Ni tana cewa Didda kamar yadda shi A.s.p yacewa su Malam da inna, shi ya tashi ya iske sa gurin Wani malami islamiyya, malamin ne ya sashi makaranta" shida matar sa ke ɗauke da ɗawainiyar sa , malam ya taɓa gaya masa iyayen sa ƴn naija ne sun kawo sa karatu gurin sa haɗe da maƙudan kuɗaɗe , kuma tun sannan iyayen sa basu ƙara dawowa ba, haka malamin sa ya gaya masa kuma su inna suka yarda bayan malam ya bincika shi malamin A.s.p.....!!

  To Bintu kinji yanda mukayi da mahaifiyar ki , ban taɓa zaton zakimin wannan tambayar ba, kuma Insha-Allah da izinin Allah zan nemo miki dangin Mahaifin ki..!!

Hawayen dake zuba a idanuntah ta share tana ɗagowa haɗe da cewa Didda kada ki samu damuwa, ke mini komai na rayuwa wlh kada ki ɗauki magana ta da wani abu, sannan didda don Allah ina so naje assibiti dubo hasnah.

   "Toh Bintu ba damuwa, Allah ya kaimu, kuma kada kada ki damu kinji sai driver ya kaiku keda ƴn uwan ki."

Toh Fatima tace haɗe da miƙewa tana cewa Didda saida safe.
  “to Bintu ba zaki kwana a nan ba.?
A'a didda Fatima na'ida faɗar hakan tayi tafiyar tah, kayan bacci kawai tasa kafin ta kwanta bacci,
  ASSUBA TA GARI matar docta

★*★*★*★*★*★*★

*WASHE GARI*

Fatima tunda tayi sallar asuba ta koma bacci itace bata tashi ba sai guraren ƙarfe 10.

Tana tashi Toilect ta shiga kusan minti 20 kafin ta fito ɗaure da towel, bisa dressing mirror ta tsaya mai kawai ta shafa sai fowder data goga ma fuskar ta da kwoli sai witlips..

Tana gamawa kaya tasa Athampa mai silver light blue riga da zani simple, tana gamawa ta ɗaura ɗan kwalli, sannan ta fesa bodyspayer.

Tana gamawa ta fito main fallo, tsaf-tsaf an gyara ko'ina sai ƙamshi ke tashi haɗe da sanyin a.c , husnah da Jamila zazzaune sai Anty zeenatu..

“a Bintu sai yanzu kika tashi? Kega wlh Didda ta hana a tayar dake, wai a barki ki huta.”

Murmushi Fatima tayi tana zama kusa da husnah dake maganar.

Didda Ce tace to ba zaki tashi ba , kije kiyi break fast , ‘to fatima ta faɗa tana tashi, dining table ta nufa zama tayi bayan ta zuba abinci a plate soyayyen kwai da yankaken bread � tana gamawa ta dawo nan fallon ta zauna.

 Duban Anty zeenatu tayi tana cewa Anty yaushe zaki koma ,.?
An jima kaɗan Bintu.

Didda ce tace to mana ku bari sai idan zaku assibiti ku biya ku ajiye ta gida , idan kun dawo kuma ku biya gidan goggo ku ajiye Jamila.

Zaro ido Jameey tayi tana cewa kai didda nikam wlh ba zan koma gida ba, nan zan zauna na..
Toh shikenan didda ta faɗa.

Husnah ce tace to didda bari mu tafi yanzu wlh bana son fita idan rana tayi .

duban su didda tayi tana cewa nikam ina ruwa na ku keda tafiya.!

Anty zeenatu ta miqe tana cewa to bari naje nayi sallama da inna sai nazo na haɗa koma tsainah.
Fatima ce tace ina zuwa Anty "toh".

A tare suka shiga fallon inna tsohuwa ɗauke da sallama, ai kuwa nan suka tadda ta zaune da'ita da wasu ƴn garin su da basu koma ba..

Bayan sun gaida ta suka zauna, Anty zeenatu ce tace to inna tsohuwa dama sallama nazo na miki zan koma gida..

  toh zeenatu Allah ya tsare hanya, kinga ga wa'enga nan duk ƴn uwa ne amma ba'a san juna ba inna ta faɗa tana nuna na zaunen.

Ɗaya daga cikin su mai suna baba haule ke cewa inna su waye..

Nuna Anty zeenatu inna tayi tana cewa wannan ai ƴr Xulaihahtu ce zeenatu ta fari, sai kuma wannan itako matar salim ce ɗan gurin Hassan.

Baba haule ce tace oh itace ta gurin Marigayiya Amina. Eh inna ta bata amsa, nan dai su Fatima suka taɓa fira kafin kuma fito.

Bayan Anty ta ganganma kayan ta suka fito, mota suka shiga sai rijiya-zaki , gidan Anty flat house mai kyau da tsari.

Suna yin parking tace ai wlh tace ai wlh su Fatima sai sun shiga ciki, ba yanda suka iya haka suka shiga, ko'ina tsaf-tsaf kamar tananan.
 “ƴr aikin'tah ce ta gaida su sannan ta kawo musu ruwa , ba wani komawa sukayi ba gidan Anty zeenatu suka fito sai assibiti.

Koda suka shiga ɗakunan da aka kwantar da hasnah , duk sunanan sunji daɗin zuwan su sosai, nan salma ke gayawa Fatima result ɗin su ya fito kuma da duba musu, basu da carry over ko guda..

Fatima tayi murna sosai amma ba halin ci gaba.

Laila ce ta samu ta fake da Fatima inda take gaya mata yanda sukayi da yaya Ahmad, laila ta gaya masa ta amince kuma ya tuntubi Mommy sunce a bari idan an sallami hasnah daga asibiti ayi maganar saka rana...

Toh Fatima tace haɗe da sanya alkhairi, sun jima a asibitin anayin sallar Azhar suka wuto sai gidan Anty Zulai.

Koda suka shiga gidan bata fallo har bedroom suka ƙarasa , ta'ida salla kenan.

"A, maraba da ƴrƴn didda daga ina haka.?"
Zama sukayi inda husnah ke cewa wlh kedai Anty daga gida muka sauke Anty zeenatu sai kuma asibiti daga cen sai nqn..!

Okey ton yanzu ku shiga kuyi sallah, ya jikin hasnah taji sauqi dai ko.?

Eh, taji sauƙi husnah ta bata amsa tana miƙewa Toilect ta shiga.
Fatima ya gabiyar biki Anty ta tambaye ta .
Wlh Alhamdullh Anty..!

Anan sukayi salla fallo suka dawo suka zauna, abinci Anty ta kawo musu , bayan sunchi nan aka dasa sabuwar fira, sune basu bar gidan Anty ba saida sukayi salla la'asar.

Koda suka koma gida Fatima kan fallon Didda ta wuce ɗauke da sallama a bakin ta.
Bayan didda ta amsa take cewa sun jima...

Murmushi kawai Fatima tayi, nan ta iske Meenat bacci hannun didda, karɓan ta tayi tana kwantar da'ita bisa gado haɗe da cewa kay didda abar mutun ya huta.

Nuna Amina didda tayi haɗe da cewa yanzu Bintu wannan itace mutum... ?

Eh, didda mutum ƴr mutuwa jikar rasuwa kama-kunnen gawa, tankaɗa haɓin ƙabari Fatima na'ida faɗar hakan tayi ficewa tahh...

★*★*★*★*★*★*★

_ƁANGAREN~SABEETERG_

Tayi ale-ale zaune bisa kujera tana shan sanyin A.c, waya ce riƙe a hannun ta ta kira harya katse ba'a ɗaga ba, mtwsss tsaki tayi kafin ta ƙara kira ai kuwa cikin Sa'a akayi peaking.

Sallama tayi tana cewa Abbanah.
"Murmushi yayi daga cikin wayar yana cewa shalele fatar anyi biki lafiya.” 

Cikin kwoɓe fuska sateey ke cewa uhm...uhm.. Abba lafiya dama na kiraka ne na gaya ma lokaci yayi daya kamata muyi maganar fansar ..

   “daga cikin wayar Abban sateey yace daughter na bincika komai, yanzu ana yawan fama da rashin lafiya to sunyi booking wasu magunguna da alurori , shine nake so muyi yanda za'ayi asa guba cikin maganin ma'ana a sauya su daga magani zuwa guba, idan sun kai amfani da su kinga za'a samu mace-mace a asibitin daga nan hukuma zata tuhumi asibiti kinga hakan zai yi sanadiyar da zai sa a kulle asibitin sannan kuma za'a kulle shi docta fursuna tunda dasa hannun sa aka shigo da ƙwayoyin kinga shalele ko'a nan mun musu illa..

Nisawa! Sabeeterh tayi kafin kuma a hankali tace Abba Ni inason mijina bana son a ɗaure shi..

Daga cen cikin wayar kuma abban sateey yace toh shikenan naji daughter sai'a ɗaure mahaifin sa ya miki..?

Eh, Daddy Sabeeterh ta basa amsa haɗe da cewa to shikenan Abba yaushe ne kayan zasu iso kuma ya za'a gudanar da abin..?

Eh, to yanda za'a gudanar shine akwai ɗaya daga cikin direbobin da muka haɗa hannu zan biya sa maƙudan kuɗaɗen sai idan sun kawo ta wurin boda zasu tsaya su kwana, to anan za'a sauya su i zuwa guba nanda kwana uku kayan zasu iso.

to Abba Allah ya taimaka ya baka amsa “da Ameen ya amsa, sateey na katse kiran...”

★*★*★*★*★*★*★
~ƁANGARE ƊAYA KUWA~

A main fallo didda ce zaune sai Fatima, salama Daddy yayi amsawa sukayi yana ƙarasowa .
N
Zama yayi didda ce tace Barka da dawowa i..
Barka dai Hadiza ya bata amsa, gaida sa Fatima tayi yana amsa daga nan itakam tayi tafiyar tah.

Duban didda Daddy yayi haɗe da cewa Hadiza magana zamu yi.
Murmushi didda tayi tana cewa Daddy inaji.

Nisawa Daddy Yayi kafin ya ɗora da faɗin Hadiza maganar Salim ce, Hadiza ya kamata ace ki manta da abinda ya faru baya, ki fuskanci gaba, ina mai haƙuri ki mayar ma da Yaron nan da matar sa..!!

Haba Daddy taya za'ayi na mayar ma Salim da Fatima halan hauka nike ne, to wlh Aure fa tsakanin Salim da Fatima hayatan-hayatan Didda ta'ida faɗar hakan cikin masifa...

“isowar docta kenan kusa da Daddy yazo ya zauna,” Daddy ne yace Hadiza kiyi haquri don Allah, docta ne ya ɗora da faɗin Didda wlh ina son Bintu itama haka...

  Gyara zama Didda tayi Kamar abin arziki yace to shikenan bari naji ta bakin tah, Bintu....Bintu... Cikin sauri Fatima ta ƙara so fallo haɗe da tsayuwa gurin tana cewa gani Didda..

Duban ta Didda tayi haɗe da cewa Didda kin amince zaki zauna da Salim , ratsatsau gaban Fatima ya faɗi sai zaro ido take, Didda ce ta daka mata tsawa tana cewa ki bani amsa nace....!!!

Uhmm...uhmm, Eh Fatima ta'ida tana sosa keya.

Shikan docta farin-ciki kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha , itako Fatima badon komai yasa tace hakan ba illa don Didda, yanzu shin yana yuwa gaban Didda tace bata son ɗan ta ..

  Didda ce ta ɗora da faɗin Fatima ki zaɓa koni ko Salim matukar da Auren Salim bisa kanki to ki cire ni a jerin iyayen ki , sannan kuma ko zama dani ko zama da Salim kuma idan har kika zaɓesa a kaina hakan na nuna cewa bani da wani muhimmanci a gareki Didda ta'ida faɗar hakan tana tsare Fatima da ido alamun neman amsa.

"Sun shiga tashin hankali da jin zancen Didda harda Daddy bama kamar docta..

Fatima hawaye na zuba a fuskar ta tace Didda kehh...keh kece farin-ciki ne kece komai nawa.

Docta cikin tashin hankali marar misaltuwa ya ɗago ya dubi Fatima domin bai zaci hakan daga gare ta ba , bai ƙara karaya ba saida yaji Didda na cewa Salim ina mai baka umarni yanzu basai anjima ba ka saki Bintu kafin ma na kawo maka takarda ka rubuta.....

Zufa ce ta shiga karyo masa dukda sanyin a.c , Didda akan masifa har fuskar ta tayi jah wlh Salim zan tsine maka albarka idan baka sawwaqewa Bintu bah.

"Ai kuwa cikin ɗar-ɗar ya fara magana Fatima na sak......

Dakata sukaji an faɗa daga bakin ƙofar fallon, gaba ɗaya suna duban ƙofar Didda kan cikin kiɗima tare da tashin hankali marar misaltuwa tace innalilahi wa'inna ilaihin raji'um Ami..........

```tabbas mai haquri yana tare da riba hausawa suka ce mahaƙurci mawa daci```

Shin wa kuke zaton Didda ta gani harta shiga wannan firgicin...?

PLZ comments and share ����������

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
  By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
     {Samha Umar} 🥀
    
    

PAGE______35

Bismillah_Rahamanin-Rahim

Gaba ɗaya cirko-cirko sukayi, cike da Al'ajabi, wa'enda suke bakin ƙofar ne suka ƙara so ciki, matar cike da kamala sai wa'enda suke tare da'ita.

Zama sukayi bisa kujera Didda sai zazzare ido take , matar nan data shigo tayi magana tana cewa Salim kada ka saki Fatima Bintuuu taka ce har abada tsan-tsar kama ce ta bayyana tsakanin docta da'ita..!

    Fatima tayi tsaye tana kallon matar mai cike da kamala a hankali ta furta Amm.... maganar tace ta maƙale , Didda ce tace tabbas Amina kece, " wannan wane irin tashin hankali ne.
    
"Murmushi Amina tayi tana cewa Didda nice dai ƴr uwarki ƙaunwar ki zauna mana kiji."

Zama Didda tayi a kiɗime , Daddy ma Zama yayi, kallon jariri yar dake hannun Amina Didda keyi tana cewa Amina wannan jariri fa...

Duban docta Amina tayi tana cewa My son jeka shigo da baƙi suna waje, 'cikin azama docta yace tau yana tashi ya fita.

  Duban Fatima Amina tayi tana cewa Bintuu na gane ki ba zaki zo inda Ammyn ki ba.?

Cen nesa da'ita Fatima ta zauna. 

Docta ne ya shigo da wasu mutane biyar ƙara sowa sukayi haɗe da zama.

Amina ce tace to nasan yanzu kuna so kuji daga gareni.

★*★*★*★*★*★*★*★

```GA YANDA ABIN YA KASANCE```

Lokacin da ƴn fashi suka shiga gidan, wani wanda shine ya shiga ɗakina domin fito dani .

Yazo bayan na tashi na furta inalilahi wa'inna ilahin rajium sai yace min yi shuru baiwar Allah magana zamu yi.

 Cikin firgici Amina ta girgiza mishi kai kawai, “zama yayi yana cewa tunda har kinga wannan mugun ya ƙudurta kashe ku to wlh babu mai hanashi saiya aikata hakan gareku.

Ina so ki natsu ki saurare Ni yanzu a cikin bindiga akwai wacce idan akai halin zai shigike Amma bullet ɗin ta baya lasa iya karshi fata , to na masa furfure i zuwa wannan bindiga  bazai gane ba har Insha-Allah.

Gobe da safe bayan mutane sun taru zan dawo idan idan aka fito da gawa-waki ku zuwa maqabarta , to daga nan idan hankali mutane basa kusa zan sauya ku idan hakan bai samu ba , to bayan an turbuɗe ku da wasu a wanni zan dawo........

Jin ana kiran me yake ɗakin mutane ya jima, "da haka Amina ta amince.

Duban su Didda tayi tare da sauke ajiyar zuciya tana ci gaba da cewa..!

Haka ko ta kasance, daga halbin bata san inda kanta yake ba sai farkawa nayi na gammu a asibiti, wannan mutumin na kula damu, daga nan aka sallame mu sai wani gida ya kimu...

Mun zauna gidan cike da kewar gida, ashe da ciki a jiki na watanmu shidda aka haifi juwairiyya takwarar inna.

    Daga nan A.s.p yace zaman bai dace ba ɗawainiya tayi ma mutumin nan yawa , a haka yayi shawara da wannan mutumin inda yace dole sai munbar garin, daga nan mukayi shawara garin da zamu , a.s.p yace naija ko Allah zai sa ya haɗu da iyayen sa.
    
A haka kuwa muka kama hanyar naija, isarmu naija saida na share shekara 7 a lokacin duk na sake haihuwa nanma mace Hafsah' cikin ikon Allah ga A.s.p ya gano dangin sa sunyi farin ciki sosai  inda mukaje gidan su .

Sun nuna min so sosai daga nan suke cewa su wlh basu su kai A.s.p makarantar ba yayan baban sa ne ba yanda basu yi ba Amma bai gaya musu komai akan a.s.p kamal ba sunyi nema har sun gani.

Gida mai nagarta da dottako , zama na gidan Allah ya bani haihuwar ɗa sunansa Tukur sunan Malam muna kiran sa Malam, haka rayuwa ta kasance kulum sai nayi kukan rashin ƴn uwa Amms ba yanda na'iya tahowa ba rawa bace....!!

   "Shekara 10 a wannan gidan, saiga wata mata mai suna hannatu , tazo bayan tace Ni take nema da muka gaisa take gayamin tana da labarin ku, "nayi murna sosai, kafin daga bisani ta fara gayamin ai Fatima ta auri docta har tafiya'n ta Jigawa ta gaya min da Auren Sabeeterh da yayi, da kuma sakin da Didda ke ƙoƙarin tirsasa Salim yaima bintuuu.

Daga nan Amina tayi shiru hawaye na ci gaba da zuba a idanun ta.

 “kowa jikin sa yayi sanyi saura ma hawaye ne ke zuba a idanun su, Hafsah ce ta matso kusa da Amina tana share mata hawaye haɗe da cewa Ammina ki daina kuka, itama juwairiyya matsowa tayi suka saka ta Tsakiya.”

Suna kama da Fatima sosai , Didda ce ta share hawayen ta tana cewa Amina ki daina kuka kinji.

Share hawayen ta tayi.

A.s.p ne yaci gaba da faɗin wannan itace juwairiyya ƙaunwar Fatima tayi aure harta haifi ƴr Xahrah wata shidda da suka wuce ya ida yana nuna ta gefen daman Amina .

Sai kuma wannan itace Hafsah, sai kuma na kusa gare sa mai sunan Malam , sai kuma wata mata ya nuna ta yana cewa wannan goggosu ce maimunatu , sai wannan ƙanena Labaran sai Isah ɗan ƙanen nawa labaran shine yake auren ita juwairiyya yanzu shekara ɗaya da wata huɗu, koda akayi auren shekarar juwairiyya 17 ta kammala secondary yanzu taci gaba , domin mahaifiyar mu ce ta buqaci hakan.....

Yana dasa aya gaba ɗaya nisawa! Sukayi tare da furta Alhamdullh daga nan kuma akaci gaba da sabuwar hira, shikam docta zuwan Amina ya masa rana domin ko ba komai ta hana Fatima.

  Didda Ce ta dubi Fatima tana cewa Bintuu ba zaki gaida mahaifiya ki ba.?

Turo baki Fatima tayi tana cewa nikam Didda banda wata uwa bayan ke, saide ƙaunwar uwa.

"Gaba ɗaya dariya suka saka Amina na cewa to dama nace miki ina buqatar ƴaƴan aro.? 
Kinga ƴrƴr na sun ishe Ni bana buƙatar ƙari.

Didda ce tace ai Bintu'n Didda ma bata buqata wata uwa.

Jin ana kiran sallah magriba a masallaci yasa Daddy miƙewa , to lokacin sallah yayi, tashi sukayi baba labaran , Docta Abban Fatima, Isa (mijin juwairiyya), sai Malam Daddy me ya jagorance sure zuwa masallacin..

Nan kuma Didda ce ta miqe tare da duban ƴr uwar ta, muje muyi salla muma.
Tashi sukayi Didda Amina Goggo sukayi ɗakin 
Didda.

"Itama Fatimah tashi tayi ta dubi ƙanen ta tana cewa ku muje , ɗakin ta ta shiga suma suka bita.

Zama tayi ta dubi Hafsah tana cewa ke muqomin ƴrta mai sunana...

Miqa mata ita Hafsah tayi tana cewa aikuwa Anty Fatima tana kama dake , duban ta Fatima tayi farin-ciki fal ranta wai yau ita ce da ƙanne,
Kai Alhamdullh ta godema Allah....!

Hafsah shiga kiyi alwala Fatima ta faɗa tana duban ƙauwata wacce tafi kama da'ita fiye da Juwairiyya, to Hafsah tace tana shigewa Toilect ɗin.

"Duban juwairiyya Fatima tayi tana fuskewa haɗe da cewa ke shekarar ki nawa"?.

18 da watanni juwairiyya ta bata amsa.

Kuma aka miki aure harda haihuwa hhhhhh Fatima ta'ida tana kyal-kyala dariya.
Fuskewa juwairiyya tayi domin har ga Allah taji zafin magan-ganun Fatima.

Turo ƙofar husnah ce! Tsaye tayi daga bakin ƙofar ta kali Fatima ta kali juwairiyya , inba don Fatima ta fita haske da kyau ba ba zaka banbance su ba domin suna kama sosai .

Ƙara sowa tayi tana zama gefen juwairiyya haɗe da riƙo hannun ta , tana cewa ƙaunwata juwairiyya ko Hafsah .

Murmushi juwairiyya tayi tana cewa juwairiyya dai Anty.

Yanzu Didda ke gayamin komai a gaskiya nayi farin-ciki.

   Duban Fatima juwairiyya tayi tana cewa Aunty fatima wanna fa.?
Ƴr mahaifiya ta ce ƙaunwata husnah.!
  "Ayya"

Hafsah ce ta fito daga bayi tana cewa Anty Fatima na ƙare, da tau Fatima ta amsa tana tashi, "miƙama Husnah Xahrah tayi tana cewa riƙe min takwora'ta.

Cikin farin-ciki husnah ta amsheta .

Fatima kam Toilect ta shiga, "Hafsah ce ta gaida husnah tana kabarta sallah......!!

★*★*★*★*★*★*★

~BAYAN SALLA ISHA'I~

Baƙi sunci Abinci, zazzaune suke a fallon inna tsohuwa ba abinda yake tashi sai sheshe-ƙar kukan ta tana cewa Alhamdullh ala kulli halin, yau ga Rinar~Haquri'n mu.

"Allah ka tabbatar da Alkhairi tsakanin mu, tayi murna sosai da ganin takwora'ta Juwairiyya da mai sunan mijinta Malam Tukur tayi ta ma su Amina godiya da sa musu albarka kamar ba gobe.'"

Nan sukaci gaba da hirar su, sune basu bar gurin ba sai dareeeeh...........

_Kai wlh na gaji kuyi haƙuri da wannan sai gobe kuma wlh zaku ga Ribar-Haquri_

PLZ comment and share ✍️ ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
 By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
      {Samha Umar} 🥀

PAGE_____36 

Bismillah_Rahmanin-Rahim

  ★*★*★*★*★*★*★

_BAYAN~KWANA BIYU_

Docta ne zaune gefen didda a Fallon ta, sai magiya yake mata akan don Allah ta basa matar sa bintu Amma taƙi.

Amina ce ta shigo Fallon dawowar ta kenan daga gurin inna.

"Zamq tayi gefen didda, docta ne ya dube ta Yana cewa ammytah don Allah kiyimq wannan yayar taki ta bani matata.”

Murmushi Amina tayi tana duban didda haɗe da have hannun ta guri ɗaya alamar ban haƙuri tana cewa didda kiyi haƙuri ki mayarma ɗana da matar sa....

Murmushi didda tayi tana cewa Dan kega na haqura da sakin,? To bintu Bata tashi komawa ba keji sai taga dama.

    Itakam Amina komai batace ba illa tashi da tayi tana duban docta haɗe da cewa, kaga tana mubar mata ƴrtah inta iya ta cinye ta tana ida faɗar hakan tayi tafiyar ta.
    
"Tana fitowa da hafsa ta fara cin karo , rumgume ta hafsa tayi tana cewa Ammyna ina kwana.”

Da lafiya Amina ta Bata amsa haɗe da cewa hafsa jeki gayawa juwairiyya ta basuwa ƴrku ki kaima goggon ku ɗaki zata mata wanka.

Toh kawai hafsa tace Tana wucewa.

Murmushi Amina tayi tana shigewa ɗakin didda.

★*★*★*★*★*★*★

Zaune yake Fallon sabeeterh, ita kuwa tana zaune ƙasa carfect.

Wayar sa ce tayi Ring dubawa yayi, aikuwa da sauri yayi peaking, bayan ya amsa sallamar da akayi yake cewa zuwa ƙarfe biyar zaku iso?.

Basan akace ba a ɗaya ɓangaren illa docta yace to yana kashe Kiran.

   Cikin marai-raicewa Sabeeterh tace don Allah likitana kayi haƙuri ka yafemin abinda na maka, ka maida min Amina don Allah...!

Wani irin tausayin ta ne ya mamaye shi, tashi yayi haɗe da cewa sai nayi tunani, Yana gama faɗar haka yayi tafiyar sa.

"Zamq Sabeeterh tayi tana tunanin shin Wai Anya kuwa tanama kanta adalci, waishin ma ina ta ɗauko wannan baƙin halin..”
Salamar khairat ce ta katse mata tunani da take.

Amsa tayi khairat na ƙarasowa, gaisawa sukayi tana zama.
Duban sateey khairat tayi tana cewa kiyi haƙuri sister na wlh ban samu na shigo ba , ya gajiyar biki.

Murmushi Sabeeterh tayi tana cewa Alhamdullh khairat ba komai wlh ai ke zan tambaya ya gajiyar.

Murmushi khairat tayi tare da cewa ya lafiya Amina.

Murmushi da yafi kuka ciwo sateey tayi tana cewa uhm khairat kenan wlh nayita ba docta haƙuri Amma dai yanzu yace na bari yayi shawara...wlh duk zuciya ta ta karaya yanda bakya zato nayi nadama.

"Dafa ta khairat tayi tana cewa sateey Allah yasa da gaske kike ba ƙarya ba, kuma har yau ina baki shawara yanzu kije ki baiwa matar sa haquri."

Murmushi sateey tayi tana cewa inshallah khairat ngd sosai kuma zanyi aiki da shawar warin ki, nandai suka taɓa hira kafin khairat ta tafi.

Ɗaki sateey ta shiga ta ɗauko hijabi ta saka haɗe da fitowa daga part ɗinta , tana fitowa part ɗin didda ta nufa ba kowa main fallo jin hayaniya Fallon didda yasata ƙarasawa da sallama ɗauke a bakin taa.

Gaba ɗaya suna zaune didda, Amin, Fatima, husna, Jamila, juwairiyya, hafsa da goggosu Fatima.

   Amsa mata sukayi kowa na binta da ido, banda Fatima da haushin ta ya rufe ta.

Ƙarasowa tayi Nan gefen didda ta durƙusa tana gaida ta, “ amsawa tayi tana cewa a kika fito da kanki ? Ai idan wani abu ne ke Kira koa waya.

Murmushi Sabeeterh tayi tana cewa ba komai didda, don Allah haƙuri nazo nq baki don Allah ki yafemin duk abinda nai miki.

Murmushi didda tayi tana cewa bakimin komai ba sabita dama ni banƙi ki ba , halin ki ne bana so , Amma ba komai.

   Ajiyar zuciya Sabeeterh tayi tana cewa wlh didda na daina.
"To, madallah didda ta faɗa haɗe da cewa kinga ƙaunwata nan Amina takworar ƴrki mahaifiyar bintu didda ta faɗa tana nuna Amina dake murmushi”.

Zaro ido sateey tayi tana cewa didda badai Amina mahaifiyar bintu ba.? Wacce ta rasu...

Murmushi didda tayi Wanda ke tattare da ma'anoni daban-daban tana cewa eh ita Allah yaƙi aniyar mai baƙar niyya.

   Murmushi Amina tayi tana duban sateey haɗe da cewa surkata an kinga ban samu na leƙo ki ba ya gajiyar biki? Allah ya raya mana takwora tah.

Da amim suka amsa, nan babu Wanda ya ƙara cewa all , Sabeeterh ce ta sauke nannauyar ajiyar zuciya Tana sosa ƙeya haɗe da cewa didda batun Aminar.......

“Twsssss Fatima taja wani tsaki haɗe da miƙewa tana ficewa daga Fallon” gaba ɗaya da kallon mamaki suka bita kafin didda ta nisa tana cewa to ba komai Sabita, batun ita Amina kuma kiyima shi mijin naki magana.!

        "Didda na mishi magana yace sai yayi shawara"

Toh, bari idan ya shigo zan masa magana ko kuma maman sa tayi masa magana.

Toh Nagode Sabita ta faɗa tana tashi haɗe da ficewa, didda ce ta dubi Amina tana cewa Amina zulai nanan tafe yau.

Murmushi kawai Amina tayi.

★*★*★*★*★*★*★*★

Sabeeterh na komawa part ɗin ta wayar ta ta jawo haɗe da yin darling number abban ta, tana shiga aka ɗaya , Abba nah Barka da yau.

Barka dai shale-le.

"Yawwa Abba wai shin kasan me yake faruwa.”
A'a shale-le sai kin faɗa.
Abba wlh kaide naga Amina gurin didda.
   Cikin gigita Abban ta yace kina da hankali shale-le ? Wace Amina badai wacce ta mutu ba.?
Wlh Abba ita na gani da ido na yanzu ma kuwa didda ke gayamin itace ƙaunwar ta Amina.

Cikin wayar Alhaji mugu ke cewa haba daughter maybe ba'ita ake nufi ba domin wannan kam inada tabbacin ta mutu.

Cikin sanyi Murya Sabeeterh tace to Abba ƙilan haka ne ba waccen Aminar ake nufi ba 'haka ya kashe kiran.

    Ajiyar zuciya Sabeeterh tayi tana tunanin kodai ƙilan Abba ta bai fahimci inda maganar ta, ta dosa ba , haka dai tai shigewa ɗaki..
    
    
★*★*★*★*★*★*★*★

"Salamar Anty Zulai kenan a main fallo ba kowa , a haka ta wuce Fallon didda sallama tayi haɗe da shigewa nanma ba kowa, bedroom ta wuce didda da Amina ta tarar zaune sallama tayi tana ƙarasawa.

Amsa sallama sukayi tana ƙarasowa haɗe da zama kusa da Amina.
Gaggaisawa sukayi , itama tayi farin ciki sosai dawowar Amina, inda didda ta kira mata su juwairiyya da Hafsah, sun gaisa sosai harda goggon su bintu....!

★*★*★*★*★*★*★

Fatima ce zaune bisa kujera Fallon su husna , wayar husnah ce tayi ring, dubawa tayi haɗe da miƙoma Fatima tana cewa ke ake kira.

Amsa Fatima tayi bayan tayi peaking tana karawa a kunnen ta  amsa sallama da'akayi tayi tana cewa Salma yakike.?
Acen Salma tace lafiya ƙalau Fatima Fatima gobe za'a sallame mu daga asibiti.

Murmushi Fatima tayi tana cewa to zaku biyo gidan mu , sannan Salma ga mamata ta dawo .

Kai Fatima da gaske? Amma nayi murna kuma inshallah gobe zamu shigo Mu duka.
Daga nan sukayi Sallama.

★*★*★*★*★*★*★*★

A Fallon didda, docta ne ya shigo, gaisawa sukayi docta na cewa Didda Daddy na neman ta fallon sa.
Da tau ta amsa ta amsa tana tashi nan tabar sa gurin Amina.

    Koda ta shiga fallon sa da sallama ɗauke a bakin ta , Nam ta zauna gurin sa.
    
Duban ta yayi yana cewa Hadiza jeki zo da ƴrki Asma'u, da tau didda ta amsa tana tashi "bayan minti biyu gata ta dawo husnah na biye da ita a baya.

"Bayan sun zauna" duban husnah Daddy yayi Yana cewa Asma'u.
Na'am Daddy husnah ta amsa wacce jikin ta sai ƙyarma yake .

A yau wannan yaron Habib ya sake turo iyayen sa neman auren ki a karo na biyu inda ya shaida min da Amincewar ki , kuma Ni banga dalilin da yasa ba zakiyi aure ba , karatu naku saura wata uku ku ƙare koh.?

Sunne kai ƙasa tayi tana cewa ehm Daddy.

Komai dai ba, baice ba Daddy, Didda ce tace Nima dai haka na gani Daddy, banga amfanin zaman ta ba .

      Sauke numfashi Daddy yayi yana cewa kuma saboda haka a matsayina na ubanki na zaɓa miki Habib a matsayin miji, na bashi ke kuma rana ita yau zasu dawo asa ranar auren ku idan kin kammala.

"Husnah kam ji tayi kamar tasa hannu a ka ta kurma ihu amma ba hali" Daddy ne yace zaki iya tafiya ai kuwa kamar jira take ta wuce fuuuuuu....

Koda ta koma fallo ta zauna, hawaye na zuba a idanun ta , Fatima da Jamila ne suka dube ta Jamila na cewa ke husnah lafiyar ki.?

Cikin zubar hawaye husnah tace ba dole nai kuka daddy ne fa zaimin Aure da Habib nanda wata uku.!

        Dariya ma ta basu, Fatima ce tace hmmm Gara ke za'a aura miki zaɓinki ki gaida wasu.
Jamila ce tace to lallai kam.

Daga haka basu ƙara cewa uffan ba.

★*★*★*★*★*★*★

A Fallon Daddy ci gaba sukayi da tattaunawa, kafin didda tayi masa sallama.

Tana fitowa ɗakin ta ta koma , nan ta iske su Amina da Aunty Zulai sai fira suke , zama tayi tana gaya musu abinda Daddy ke Kiran ta, Suma sunyi na'am da shawarar Daddy India Anty Zulai ke cewa wlh hakan yayi bari idan na koma gida nayi magana da baban su Jamilar a haɗe dana ƴr uwar ta domin Ni banga amfanin zaman su ba, nandai sukaci gaba da  tattaunawa kafin Anty Zulai ta koma gida bayan ta gaida inna.

Bayan Anty Zulai ta koma gida tayi magana da mijinta baban su Jamilar inda shima yayi na'am da shawarar ta na haɗa auren Jamila dana husnah yace zai yi shawara da Daddy.

★*★*★*★*★*★*★

```AL'UMMA PRIVATE HOSPITAL```

Docta ne zaune a office ɗinsa " Ƙwonƙwosa ƙofar akayi bayan ya bada izinin shigowa aka shigo, wanda ya shigo ne ya gaida sa haɗe da cewa ranka shi daɗe komai ya kammala domin har an shigo da kayan lb.

       To, docta yace haɗe da miƙewa yana cewa muke na dubo, to mutumin yace tare da wucewa.

Koda suka je babban gini ne mai ɗauke da hasken wutar lantarki shine A.P.H.L al'umma private hospital lab, an jera kwolayen magunguna inda ake kawai pharmacy na asibiti ya dudduba baiga wani abu ba haka suka fito ya dawo office inda mutumen ke gaya masa ankai saura pharmacy za'ayi amfani da shi....!!!

  ~DA DARE~

Bayan sun gama dinner zazzaune suke sai hira sukeyi, Amina ce tace Didda sati mai zuwa zamu koma naija.

Zaro ido didda tayi haɗe da cewa haba Amina nikam ai nace da anan zaki dawo muci gaba da zama domin gaskiya bana don kiyi nisa da Ni.

    "Murmushi kawai Amina tayi tare da kawadda zancen suka ci gaba da hira.”
    

★*★*★*★*★*★*★

KARFE 08:00am 

Yau docta a gidan sa ya kwana hakan yasa daya tafi sallar asuba bai dawo ba sai ƙarfe 08:00am , ai kuwa yana dawowa ya shige ɗaki bayi ya shiga yakai almost 30 minutes kafin ya fito.

Yana fitowa ringing ɗin da wayar sa keyi na katsewa, ai kuwa cikin sauri ɗauko wayar , Rasss gaban sa ya faɗi ganin almost 💯 missed call Wanda tun ƙarfe uku na dare ake kiran.
"Numbobin daban kuma duk a asibiti, nan kuwa wani kiran ya shigo."

Peaking yayi cikin sauri yana karawa a kunnen sa , amsa sallama yayi ana cewa ranka shi daɗe muke kiran wayar ka, wlh asibiti ba lafiya kazo da sauri muna cikin tashin hankali....

      Cikin sauri docta ya shirya ahaf-shaf yana fitowa.
Yana kawowa ƙofar fallon ya buɗe haka aka turo ƙofar, ɗan ja da baya yayi kaɗan domin bawa ko waye damar shigowa.

“Ƴn sanda ne su kusan biyar suka shigo , cikin zaro ido da zallar mamaki docta ya amsa sallamar su.”

Babban cikin su ne ya fito da I.D card ɗinsa tare da cewa sunana esp Jabir Umar munzo ne domin muyi aresting ɗinka.!

Cikin firgici docta yace aresting ɗina?.......

  _kuyi haquri da rashin jina kwana biyu, aski ya kusa zuwa gaban goshi_

PLZ comment and share ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
  By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
      {Samha Umar} 🥀

                     😍😍
😍😍

PAGE_____37

Bismillah_Rahamanin-Rahim.

______yalaɓai mun samu sanarwar asibitin ka ba lfy ana buƙatar ƴn sanda, kuma kunje mun tarrar mutane a cikin tashin hankali da wani hali sakamakon gurbatattun magunguna da kukayi amfani dasu gurɓataci ne SBD haka zamuyi aresting ɗinka i zuwa ofishin mu har sai kunga yanda hali yayi, sannan za'a tsaida aiki a wannan asibitin ma'ana za'a kulleta har sai mun gama binciken da zamuyi.

"Idanun docta sunyi jajir amma ba yanda ya'iya , maybe haka ƙaddara sa take".

Bayan su yabi sai'a mota, basu tsaya ko'ina ba sai office ɗin su an kaisa wani ɗaki zance ko me? An rufe.

Espct ɗin ne ya shigo tare da zama gefen docta yana dafa kafaɗar sa haɗe da cewa D.r idan har ka bamu haɗin kai to ina mai tabbatar mata cewa zamuyi bincike mu gano inda matsala take, yanzu ina so ka gayamin yanda akayi.....?

    Cikin danne ɓacin rai docta ya juyo yana cewa me kake so na faɗa maka? tunda ko asibitin kun hanani zuwa inga halin da patient ɗina suke ciki.!
    
Murmushi espct Jabir yayi yana cewa kayi haquri abokina kaji , inshallah komai zai zo da sauƙi, shin yaushe ne aka shigo da kayan domin ma'aikatan mu sun tabbatar mana da cewa kodai dama haka kuka shirya kuda ya kamata ku ceto rayukan al'umma a'a saide ku salwanta dasu.
A zafafe docta ya ɗago yana duban sa, komai espct Jabir bai ƙara cewa ba illa tashi da yayi ya fita.

★*★*★*★*★*★*★*★
Acen gida kuwa yanzu labarin ya cimma Daddy shima ya tsorata sosai, ai kuwa shima bai tsaya wata-wata ba ya kira lauyansa inda ya masa bayanin duk abinda ya faru, shiko yace su haɗu police station.

Da haka Daddy ya baro gida bai gayawa kowa ba.

*******A can police station Daddy ne zaune sai lauyansa da espct Jabir gaida sa yayi cikin girmamawa domin shi yasan Daddy, Daddy ne kawai bai sansa ba.

Magana espct Jabir ya fara Yana cewa ranka shida ɗe abinda ya kamata shine muyi solving matsalar anan tun bamu je kotu ba .
"Daddy yayi na'am da Maganar sa inda yake cewa to yanzu ya za'ayi?.

Eh,to a fara binciken drivoving da suka shigo da magunguna, shima brr yayi na'am da shawarar, "espct Jabir ne yasa aka shigo da docta wanda harya faɗa cikin ƴn awanni, bayan ya zauna ya gaida Daddy, amsawa Daddy yayi yana ƙara kwontar masa da hankali.

Daga nan espct ya dubi docta yana cewa, Yana cewa D.r shin zata iya haɗamu da drivoving, ƙalla baice ba! Ɗayowa yayi yana duban Daddy jijjiga masa kai kawai Daddy yayi, sannan ya maida kallon sa ga espct Jabir yana cewa ka bani wayar.
Miqa masa wayar yayi wacce ke cikin drower, bayan ya karɓa ya kamo number Mustapha driver, Yana ɗagawa docta ya amsa sallama da yayi , cewa docta yayi Mustapha waye ya tuƙo tp1 cikin wayar driver yace ranka shida ɗe nine, tp2 ranka shida ɗe buba, tp3 ranka shida ɗe sani ne, "okay to Kai kana ina docta ya faɗa yana tambayar sa.
Ina babbar tasha ya basa Amfa.

Okey, docta ya faɗa yana ɗorawa da faɗin kasan inda za'a samu buba da sani , "to nidai yau duk banga sani ba amma buba muna tare.

Okay kawai docta ya faɗa tare da katse kiran.

Murmushi espct Jabir yayi tare da fita daga ofishin sa , 'yana fita motar ƴn sanda ya haɗa haɗe da cewa suje babbar tasha, su iya takonsu yana so su kamo masa Mustapha da buba.....

You suka amsa masa, office ɗin sa ya dawo bayan ya zauna ya dubi docta yana cewa yaushe ne kayan suka taso, shikam docta ƙalla baice masa ba domin wani irin haushin sa da yake ji wai yau shine anan gurin?.............

★*★*★*★*★*★*★

Ɓangaren Oga Abdul Hakim

Tun dawowarsa bikin Amina hankalin sa ya kasa kwonciya , ya koma suku-ku itako mami hankalin ta yayi bala'in tashi to ya zata yi.

A yau ne kuma mahaifinsa Alhaji Awwal Ahmad ya dawo, shima hankalin sa ya tashi matuka gani halin da ɗa ɗaya tilo da Allah ya mallaka sa ke ciki.!

     Mami sai kuka take, zaune suke a ƙayatattcen fallon su ta dubi mijin nata tana cewa Alhaji bai kamata mubar yaronnan a cikin wannan halin ba ya kamata kusan abinyi.

HmmmmmAlhaji ya sauke numfashi haɗe da duban ta yana cewa Hajiya taya zamubi takan yaron nan ? Kada ki manta da yarinyar da auren ta kuma matar abokin sa ce.

Cikin ɗaga murya (Allah ya la'anci matar da take ɗagama mijin ta murya) tace haba Alhaji bafa zamu zuba ido ba muna ganin rayuwar ɗan mu a haka ba, nidai a nawa tunanin kamata yayi zuwa gobe ko jibi muje cen gidan su ita yarinyar muyi magana sai asan yanda za'ayi imma sakinta zaiyi ya saketa tunda shi dama ba sonta yake ba...!

Nisawa Alhaji yayi yana cewa hakane fa maganar ki uwargida bari zuwa goben sai muje cen ayi yanda za'ayi (ku jimin son zuciya jama'a)

 "Murmushi farin ciki Hajiya tayi tana cewa yanzu dai naji maganar gaskiya Alhaji, nandai sukaci gaba da tattaunawa zuwa gidan ALHAJI HASSAN SAUTA."

★*★*★*★*★*★*★

ALHAJI HASSAN SAUTA HOUSE.

A main fallo take kwance tana sharar bacci, ba kowa a fallon, jin an fara jijjiga ta ana kiran sunan ta Fatima.... Fatima yasa ta miƙewa daga baccin da take, ai kuwa ta ware idanun ta a fuskar Salma.

Zaune ta tashi tana kallon Mommy, Umma, laila Salma hasnah, cikin farin ciki tace lahhhhh 🤭Mommy dama kuna tafe ?, Hasnah ce ta rungume ta , ”itama Fatima Rungume ta tayi tana cewa mu-hasnah ko sati biyu baki cika ba har kin warke.

    Cikin Suratu hasnah tace ai Anty Fatima in baki lvr gaba ɗaya an sallame mu yau mutane suka ta faɗuwa harda ƴan sanda aka kawo........umma ce ta bugota tana cewa ke Sudan Uwar-Magana kiyima mutane shiru, haka kuwa hasnah taja bakin ta tayi shiru.
    
Fatima ta shiga zargin wani abu Amma ba yanda zata yi zazzaunawa sukayi tana cewa Umma ku bari na kirawo su didda da Ammynah da haka ta tashi , bata wuce 5 minute ba gata ta dawo zama tayi tana cewa ga sunan zuwa nan suka taɓa hira take basu taɓa hira take basu labarin Mahaifiyar ta da dawowar ta.!

Tabbas sun ƙara gaskata cewa mahaqurci mawadaci.

"Sallama akayi didda ce da Amina kamar su sak basai an faɗa ba kasan ƴn uwa ne , ƙarasowa sukayi kowanne su Murmushi a fuskar sa , zama sukayi aka ci gaba da gaisawa.”

Salma ce tace Kay wlh kowa yaga Ammy zai ce yayar yaya docta ce domin sunfi kama da juna fiye da didda, gaba ɗaya dariya sukayi didda na cewa ya mai-jiki ?.

Da umma ta bata amsa tana ɗagowa haɗe da cewa an sallame mu yau da safe mu ƙara yin godiya sosai, sannan idan daddyn su husnah ya dawo ku gaya masa gobe za'a saka ranar auren laila da ɗan uwanta Ahmad.

Kai masha-Allah Allah ya sanya alkhairi yasa ayi damu didda ta faɗa tana sakin murmushi, kowa ya sanya alkhairi.

"Didda ce ta kira goggon su Maimuna da kuma su juwairiyya da Hafsah da malam , domin su  Abban Fatima da baban su  labaran ƙanen Abba sai isa ɗan baba labaran mijin juwairiyya duk a G.Q aka sauke ke su ko malam anyi daidai daya shigo ne .
    Sunyi murna sosai su laila inda laila kamar ta haɗiye xara'u don so, sune basu bar gidan ba sai da akayi sallar la'asar bayan sun ci abinci sunsha abin shq.
    
Bayan sun tafi itama Fatima maganar hasnah ce ta dawo mata Sabuwa hakan yasa ta dubi didda tana cewa Didda wai yau duk yaya ya shigo gidan.?

A'a bintu ban ganshi ba  maybe aiki ne ya riƙe sa , kinga daddyn ku ma bai dawo ba har yanzu inaji ƙilan aiki ne ya riƙe sa domin na kira wayar sa ta shiga amma baiyi peaking ba.!

Allah ya sa lafiya kawai Fatima tace tana wucewa ciki.!

★*★*★*★*★*★*★
POLICE-STATION

Cikin ikon Allah kuwa ƴn sanda da espct Jabir ya tura sunyi nasarar kamo su Mustapha da buba , gurfanar dasu akayi gaban su Daddy.

"Espct Jabir ne ya dubi su Mustapha yana cewa Mustapha muna so tsakanin ka da Allah ka gaya mana abinda ya faru isowar ku, domin kaji abinda ya faru a asibiti ”.

    Cikin firgici da tashin hankali Mustapha yace na rantse da Allah ranka shi daɗe wlh bansan komai ba illa ma lokacin da muka kawo bd t amsa doka wato ba'a bi da Dr sai muka kwana amma wlh bansan komai ba bayan wannan,.....!!!!
    
Cikin sauri buba yace ranka shi daɗe nasan wani abu game da hakan, kuma wlh ni dama cen ina zargin sani.

Muna jinkq ka gaya mana.!

Sauke numfashi buba yayi kafin ya ɗora da faɗin, lokacin muna cikin tafiya bayan tsaya restaurant cin abinci naji yana waya da wani inda yake cewa kada ya damu komai yana tafiya daidai su zama cikin shiri, "sannan kuma bayan haka shine ya ƙuƙe mu tsaya mu kwana milali.

Da dare kuma na farka na gansaa idanun sa biyu baiyi bacci ba , dana tambaye sa menene yace yana tsammanin ne, nace nami? Baice min komai ba illa wayar sa da tayi ring, ya ɗauka yana cewa su ƙara so.
Nisawa yayi bayan ya gama faɗin abinda zai faɗa.

      Mutmushin gefen baki espct Jabir yayi yana cewa yanzu naji magana , yanzu ina kuke zaton zamu samu shi sanin.?

Cikin sauri Mustapha yace  eh, yalaɓai idan ban manta ba ɗazu ya kirani da safe yake cemin zaiyi tafiya ta wasu ƴn kwanaki,“dana tambaye sa ina zaije? Yacemin zai bai garin ƙasar ma duka zuwa Ghana, dana ƙara tambayar sa jirgi ƙarfe 4 zaibi a Aminu Kano da haka kukayi sallama.

"Cikin sauri espct Jabir ya dubi agogon dake tsintsiyar hannun sa saura minti 27 4 ta cika, cikin sauri espct Jabir ya dube su yana cewa a basa photon sani , ai kuwa buba ya miƙo masa wayar sa bayan ya kamo hoton sani.

Cikin sauri espct Jabir ya fita tare da motocin ƴn sanda sai Aminu Kano international airport, suna isa suka fara neman sa amma basu gansa ba, har an fara kiran facinjoji , espct na ɗaga ida nun sa ya kalli sani dake saɗaf-saɗaf baiyi wata-wata ba ya chafke sa sannan ya kira sauran ƴn uwansa suka shiga Mota.

   ”suna zuwa police-Satation akayi bayan kanta da sani , iya azaftuwa ya azaftu amma bai faɗi gaskiya ba, "espct Jabir ne yasa aka kawo office ɗinsa , inda su Daddy da da docta suke.

"Bayan an kawo sa duk ya galabai ta, duban sa espct Jabir yayi bayan ya zaro wuƙa ya saita inda hannun sani yake ya saita yana cewa shin zaka faɗi gaskiya ko saina ƙille maka hannu.?

Cikin galabai ta muryasa ko fita barayi yace zan faɗa ranka shi daɗe sani akayi................

*NOTICE*

_Bazan samu damar post number 38 ba SBD wani dalili har saina ƙare wato kenan zan tashi 39 SBD haka duk mai buƙatar page 38 yamin magana na turo masa_

WhatsApp : 08036280592

Message:08061128094

PLZ comment and Share✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
 By👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
       {Samha Umar} 🥀

*Godiya mai tarin yawa haɗe da fatan alkhairi aduk inda kuke masoya na ina muku fatan alkhairi a koda yaushe nayi typing ɗin nan saboda ku*

PAGE_____38

Bismillah_Rahamanin-Rahim

  ''''’'''okey muna jinka yanzu ka gaya mana waye yasa ka?.
Ai kuwa nan sani ya shiga zayyano musu akayi kamar haka "wani Alhaji ne ya sani inda yamin alƙawarin maƙudan kuɗaɗe masu yawa shine yasa lokacin da muka kwana a milalis sai suka zo suka chanza motacin gaba ɗaya yana kaiwa nan yayi shuru....!?

Meye sunan shi wanda yasa ka? Kuma a'ina yake espct Jabir ya tambaya cikin kufuluwa da maganganun sa.

Wlh ranka shi daɗe bansan inda yake ba , kawai muna magana a waya sai jiya daya turomin 5m ɗina cash,
“docta ne da sai yanzu yayi magana yana cewa, kai yanzu Sani kayiwa kanka adalci ? Sani taya zaka sa rayuwar al'umma a halaka, kako san hukuncin da Allah zai maka.

Cikin kuka sani ke cewa ranka shida ɗe docta don Allah kayi haquri wlh sharrin shaidan ne da kuma kwoɗayi mabuɗin wahala! Don Allah ku yafemin wlh na tuba .

' okay bamu number sa espct Jabir ya faɗa, shi dai docta ƙalla bai ƙara cewa ba, sani ne ya ƙara da cewa wlh ranka shi daɗe bansan inda yake ba.
Zaka iya fasalta min kaman ninsa

" Sani ya shiga duniyar tunani cen ya nisa yana cewa ranka shida ɗe na taɓa ganin sa , so ɗaya kuma zan'iya fasalta muku shi .”
Brr. Ne yayi saurin cewa abinda ya kamata a kira mai zane , saiya siffanta shi a zana mana shi.

Hakane espct Jabir ya faɗa haɗe da kiran ɗaya daga cikin ƴn sandan yake gaya masa yaje yazo masa da mai zane , haka ya fita ‘tashi sukayi su duka suka wuce masallaci.....

★*★*★*★*★*★*★

Sabeeterh ce yau duk ta damu bata ga docta ba , wayar ta , ta ɗauko da niyyar kiran sa, aikuwa kiran na shiga wayar hakan yayi daidai da dawowar mai kiran zane yana shigowa, kiran Sabeeterh na shiga ɗauka yayi haɗe da yin peaking anan sateey tace Assalamu alaikum.

     Honey lafiya yau duk bangankaba kodae aikine yanka yawa..........?    
Babban
       Ɗan sandan ne yake cewa  bashi bane yana cell  (domin baixata sunyi masallaci ba) innalillahi wa'inna illaihin raji'um shine kawae abinda ta iya faɗa kafin kuma ta ɗora da faɗin meye hadin docta dacell maganganun da tayi da dadin tane suka fara dawo mata kodai abinda kodai abinda ya ce mata shine ya faru Maganar dan sandane ya katse mata tunani  inda yake cewa wannan bani daki tambaya ba to yayi wane asibiti daga Nassarawa police station haka ya katse kiran taki tsoro sosai Sabeeterh number Daddy ta takamo tayita dealing switch off hijab ɗinta ta dauka

    ( Har nacce su sateey an musulunta) bayan tasaka hijab cikin sauri tafito harabar harabar gida yayi daidai da dawowar su husnah Domin yau sunada lecture tana karatu a bayani University business administration suke karantawa fitowa sukayi sai tsare Sabeeterh da ido suke domin ganinta airin wannan hali ƙarasowa inda suke tayi tana qoqarin shiga motar 
 da suka fito haɗe da cewa driver Wanda har ya fita dawo fita zamuyi.

Jamila ce tace Anty sateey lafiyar ki?
Hmmm, tayi ajiyar zuciya tana cewa wane lafiya police station zani.
   Lafiya? Me yake faruwa? Husnah ta jeho mata wa'ennan tambayoyin.

Ya'yan ku ne a cell daga haka daga haka ta juya ga driver tana cewa nasarawa police zamu daga haka yaja motar gateman ya buɗe musu gate suka fitah.......

  "Hawaye ne ke zuba a idanun husnah da gudu tayi cikin gida Jamila ce ta mara mata baya, " koda suka shiga ba kowa a fallon sai fallon didda, faɗawa jikin didda dake zaune bisa kujera husnah tayi tana ƙara fashewa da matsanancin kuka.

Ke, lafiyar ki? Nace lafiyar ki didda ke jero mata wa'ennan tambayoyin, Jamila ce tayi ƙarfin halin cewa Didda yaya ne a police-Satation sun kamasa.
   Innalillahi wa'inna illaihin raji'um su didda ke faɗa Amina ce tayi ƙarfin halin cewa Jamila ga wa kuka ji wannan maganar.?

Sai sannan husnah tace Ammy a gurin Sabeeterh yanzu haka tayi cen , Fatima da shigowar ta kenan taji wannan maganar ranta ne yayi matuƙar ɓaci jin wai docta ya rasa wazai gayawa sai waccan baƙar matar tasa hakan yasa dama ba wanda ya ganta tayi tafiyar ta ranta na mata mugun ƙuna .

Amina ce tace Didda to kira daddyn su ko Allah zai sa yayi peaking.!

To didda tace haɗe da ɗaukan wayar  dake kusa gareta tayi Darling number Daddy ai kuwa tayi Sa'a dawowarsa kenan daga masallaci, domin shi baima ga mised call ɗin ta na ɗazu ba hakan yasa, bai kirata ba kuma baiyi shawarar kiran ta ba domin baiga amfanin hakan ba illa tayar mata da hankali da zaiyi, ai kuwa yanzu kiran ta na shigowa tayi peaking haɗe dayin Salamah.

Acen kuwa didda daure wa kawai tayi ta amshi sallama haɗe da cewa Daddy naji ance ƙuna police station lafiya?.

Hadiza wlh ba wata matsala nace ki kwantar da hankalin ki inshallah komai zai zo ƙarshe, anjima kaɗan zamu dawo gida.
 Toh Allah ya tsare gaba a dawo gida lafiya daga nan ta kashe wayar ta ta juyo tana dubin su Amina da goggo Maimuna.

Amina ce tace Didda ki muna bayani , hmmm didda ta sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa Amina koni baimin bayani ba illa kawai yace min gasunan tafe.
  Toh Allah yasa muji alkhairi, da Amin suka amsa kowa yayi shuru yana tunanin abu a zuciyarsa.........

★*★*★*★*★*★*★*★

Husnah sai kuka take haka ma Jamila, Fatima kam shuru tayi ita ba tace komai ba, “turo ƙofar akayi juwairiyya na shigowa, turusss tayi tana cewa innalillahi wa'inna illaihin raji'um meya faru na ganku haka? Mutuwa akayi? Waye ya mutu? Ƙarasowa tayi ganin kowa yayi burus da'ita kusa da Fatima ta zauna tana cewa Anty Fatima kimin bayani meya faru kinii?.

Ɗagowa Fatima tayi ta watsa mata idanun ta waenda sukayi jah sbd ɓacin rae tana cewa ba komai Sarkin tambaya ina Hafsah?.

Hafsah tana cen gurin inna dasu malam da meenat da ƴrku ( xahra), " okey tashi kije Fatima ta faɗa tana hararar ta, Allah ya baki haquri daga haka tayi ficewar tahhhh.

★*★*★*★*★*★*★*★*★

*ƁANGAREN SABEETERH*

Sai tsawo take ma driver akan tayai sauri gashi kuma sai kiran wayar Abban ta take amma still switch up , haka taci gaba da kiran har suka ƙarasa police-Satation, fir sun hanata shiga sai masifa take dasu.

  Cen ciki kuwa suna dawowa da salla suka Zazzau na , ga mai zane cikin ƙworewa yaka zana siffofin Alhaji mugu wanda sani ke zayyano musu.

Daddy ne ya ƙurawa hoton ido , jin hayaniya a station yasa espct Jabir miƙewa domin ganin me yake faruwa.
Ganin sateey ɗaya daga cikin su ne ya masa bayani, cewa yayi su bari ta shiga.

"Haka ko ta shiga aikuwa bataji kunyar su Daddy ba ta faɗa jikin Dr salim ta rungume sa haɗe da fashewa da wani matsananci kuka.”

Ƙoƙarin rabata da jikin sa yake, ai kuwa yayi nasara duban ta yayi yana cewa miye haka Sabeeterh meya kawo ki nan?.

Cikin kuka take magana tana cewa , ai dole na damu idan ka shiga wani hali nidai kazo mu tafi gida...... maganar tace ta maƙale jin espct Jabir yana cewa ku duba ko akwai wanda ya taɓa ganin wannan fuskar.?

Aikuwa gaba ɗaya ɗagowa sukayi suna furta innalillahi wa'inna illaihin raji'um, docta ne ya dubi sani yana cewa kai sani baka da hankali daddyn ne mai laifi ya ida maganar yana nuna Daddy da hannu!.

Kallon Daddy sani yayi yana cewa, Eh, wlh kamar shine ma " sai sannan espct Jabir ya lura da photo fuskar Daddy.

Murmushi Daddy yayi wanda ke tattare da ma'anoni daban-daban yana cewa bani bane wannan shine ɗan uwa na Husaini daya ɓata .

Gaba ɗaya sukayi zuru-zuru, Sabeeterh ce ganin mahaifin ta ƙara ra nan take gaban ta ya faɗi ta furta innalillahi wa'inna illaihin raji'um cikin sauri ta fice daga office , mota ta shiga tana cewa driver ya wuce suje amma ba gida ba gidan Alhaji Ibrahim. 'suna isa driver yayi parking, Fallon ta ƙara so sallama ɗauke a bakin ta,
  "Mama da fitowar ta kenan daga kitchen murmushi tayi bayan amsa sallama sateey tana cewa maraba da Sabeeterh ƙara so mana.

Ƙarasowa Sabeeterh tayi tana zama.
Duban ta Mama tayi tana cewa Sabeeterh lafiya na ganki haka bako sanarwa.?

Nan Sabeeterh ta gayawa mama komai tun wayar da tayi da Abban ta har abinda ya faru da docta da Zuwan da tayi police-Satation da kuma photo daddyn ta da aka zana tana ƙare faɗar haka ta fashe da kuka tana cewa Mama Abba na yana cikin matsala ya zanyi? Na kira wayar sa switch up.

Jawota jikin ta Mama tayi tana lallashin ta haɗe da cewa ki kwantar da hankalin ki  inshallah ba abinda zai faru .

Nan Mama ta shawo kanta dakyar ta lallaɓata tayi shiru inda ta kawo mata White 🍚 rice da onion soup (shine Best food Nata) taci amma kaɗan da haka suka ci gaba da gwoda kiran layin Abba amma abu ɗaya ake faɗa switch up .

★*★*★*★*★*★*★

_Police-Station_

Espct Jabir ne ya fara magana yana cewa, yanzu munyi farin cikin shawo kan matsala, yanzu zamu sallami kowa saide zamu riqesa.
  Zamu watsa photo sa a offisho-shin wannan yankin dama ƙasa baki ɗaya, zamu baza neman sa idan munyi nasarar chafke sa sai a dawo a tattara bayanai izuwa kotu .

Da haka kowa ya watse.!

"Docta daya koma gida yaga soyayya ta ƴnuwa kamar su haɗiye sa”
Amma baiga matar sa ba gimbiyar sa Uwar-Biyu , part ɗinsa ya wuce yayi wanka, koda ya fito fallon an cika sa da chiye-chiye sai sannan Sabeeterh ta dawo itama zama tayi.

Nan Daddy ya fara basu labarin from A to Z sun jajanta hakan haɗe da addu'ar Allah ya bayyana Alhaji mugu domin bai gaya musu Husaini bane, da haka yai wucewar sa part ɗinsa.

★*★*★*★*★*★

Fatima ce zaune a ɗakin husnah tunanin take gaskiya ya kamata ya kamata taga yaya docta ko zata jajanta masa, turo ƙofar akayi Jamila ce, cewa tayi Bintu Ammy na kiran ki.

To tace ta tashi tana fitowa ta wuce part ɗin didda, didda ina Ammy?.
Tana ɗaki didda ta bata amsa, ƙara sawa tayi tana zama gefen Amina haɗe da cewa gani Ammy nah .

Bintu meyasa baki fito kika gaida mijin ki ba?.
  Ba komai Ammy.
Toh yi maza tashi kije har ɓangaren sa ki masa Barka ki jajanta masa, babu musu tace toh haɗe da tashi tana fito.

"Tana fitowa ɗakin ta, ta shiga haka ɗai ta samu kanta da sha'awar tayi wanka , haka kuwa akayi bayan ta fito daga wanka lotion masu daddaɗan kanshi dasa taushin fata ta shafa ma jikin ta.
 
Fowder ta murza a fuskar ta kaɗan sai witlips wanda keda kyali-Kyali pink , haka tasa wata riga doguwa wacce take sharaf-Sharaf duk ta kwanta mata a jiki tura-ruka masu ƙamshi da sanyaya zuciya ta shafa tare da ɗauko ƙaton hijab tana sakawa .

   Tana fitowa ta nufi part ɗinsa , Sallama ɗauke a bakin ta, ta tura ƙofar fallon, ba kowa sai wani ni'imtatcen ƙamshi da sanyi dake tashi .

"Ƙara sawa tayi bedroom ɗin sa, ta shiga sallama ɗauke a bakin ta, nanma ko'ina tsaf-tsaf sai kyalli yake ƙarasowa tayi tana zama bisa sofa.

Takai almost 5 minutes taji an turo ƙofar toilet ɗin, kallo ɗaya ta masa ta sunne kanta ƙasa .

Shima kallon ta yake cike da murmushi, ƙarasowa yayi yana zama gefen ta.
A hankali ta furta ina wuni yaya ashe abinda ya faru kenan? Toh Allah ya tsare gaba.

"Murmushi daga ƙara ƙawata fuskar sa yayi yana cewa lafiya ƙalau ngd sosai my beautiful wife Bintu Uwar-Biyu.

  tashi tayi amma ya ƙara jawota yana maida ta haɗe da cewa ba zaki cire hijabin ba ko bani akaima kwoliyar ba ya ida yana ƙoƙarin cire hijabin daga jikin ta.
 Barayi ƙoƙarin hanasa ba tunda dai harga Allah tana son kyauta-tawa mijin ta .

Jawota yayi jikin sa yana sinsinar ƙamshin jikin ta, ya shagalta da wasa da jikin ta , Saida tayi kamar tanayi kafin ya saketa, aikuwa ba tare da jinkiri ba ta fito.

Bakin ƙofar taci karo da Sabeeterh Bintu ta kira sunan ta, ƙalla Fatima batace ba illa ji da tayi kamar ta banke ta ta wuce..........

★*★*★*★*★*★*★

```BAYAN KWANA UKU```

Babu wani bayani daga gurin ƴn sanda, amma dai suna iya ƙoƙarin su bincike babu dare babu rana.

Docta ne zaune a fallon didda suna maganar tafiyar sa Outland nanda sati ɗaya da ƴn kwanaki , nan ya fara roƙo akan a bari yaje da Fatima.

Daddy kam cewa yayi ba maganar sa nace ba, a haka yaje gurin didda cewa tayi ba ruwan ta ba zata tilasta wa Fatima ba , bayan ya sami ita kuma Fatima cewa tayi aiga Sabeeterh nan, shikuwa cewa yayi ai Sabeeterh jego take .

Fatima tace ta amince amma a tambayi Didda, didda kuwa cewa tayi ai sun gama magana.

    "Amina ce tace bazai yuwu ba har sai Sabeeterh ta amince."

Ba yanda ya'iya yaje ya samu Sabeeterh da Maganar yana cewa inhar ta amince da yaje da Fatima shi kuma zai mayar mata da Ameena.

   Haka Sabeeterh ta amince domin ita rayuwar ma ta fita a ranta, da kanta taje ta samu su didda take gaya musu ta Amince docta yaje da Fatima....!

Kowa yayi mamaki da sauyawar Fatima.......

👄👄👄👄👄👄
RIBAR~HAQURI
👄👄👄👄👄👄

Story & Writing 📝
 By:👇

🥀 RUKAYYA UMAR FARUK
      {Samha Umar} 🥀

👄Alhamdullh I thank God for everything👄

PAGE____39 [Second to the last]

Bismillah_Rahamanin-Rahim

Haka kuwa aka mayar mata da ƴrtah meenat, didda bataso tafiyar docta da Fatima ba amma ba yanda ta iya.

Maganin gargajiya na gyaran jiki mai kyau ta shiga haɗawa ƴrtah cikin kwanaki ƙalilan Fatima ta wani chenza tayi fresh da'ita, ta wani ƙara haske fatarta ta wani irin laushi da tsantsi sai kyalli take, jikin ta sai wani ni'imtattacen ƙamahi ke tashi.

" Yanzu didda ta fito daga ɗakinta bayan ta gama haɗa mata wasu magunguna".

Kira ne ya shigo wayar husnah dake hannun ta, peaking tayi ganin Salma ce, Asalamu-Alaikum.
 Waalaiki sallama Salma ykk? Ya gida? Kwana biyu.

Da lafiya Salma ta amsa mata tana cewa Fatimah yau zamu koma Jigawa, sannan jiya amsa ranar auren laila da yayanah , nan da wata biyu sannan batun auren meenal kesan rana ita yau ne .

Dafe ƙirji Fatima tayi tana cewa innalillahi wa'inna illaihin raji'um na shige su , wlh Salma na manta shaf da maganar meenal domin ba waya a hannun na .
  Aɗaya ɓangaren Salma tace hakane Fatima kenan ba zaki samu damar zuwa ba .

"Wlh Salma wannan satin jibi larba zamuyi tafiya Outland ya zanyi kodai na fasa?"

A'a Fatima ba zai yiwu ba ki fasa ba kawai ki kirata kuyi magana, ki gaya mata ba zaki samu damar zuwa ba , ki bata haƙuri kinji? Saiki samu abinda kika tura mata..

    Toh shikenan Salma ngd daga haka ta katse kiran, tashi tayi ta saka ƙatoton hijabi har ƙasa domin didda tace ta daina fita hakanan .

Tana gamawa ta fito Sai Fallon didda zazzaune ta iskesu suna hira "zama tayi kusa da didda tare da aza kanta bisa kafaɗar didda tana cewa my didda magana zamu yi.
 Ina jinki my bintu ƴr albarka didda ta faɗa Murmushi ɗauke a fuskar ta.

"Wlh didda Auren meenal ne rana ita yau assabar Ni wlh duk na manta shine nace bari nayi miki magana ya za'ayi"?

Ajiyar zuciya didda ta sauke tana cewa my bintu nikam gaskiya ba inda zaki , kuma gama tafiyar da zaku yi a nizan je.......

Cikin sauri Fatima ta zabura mamaki marar misaltawa fuskar ta cike da Murmushi take kallon didda haɗe da cewa ' my didda da gaske zakije? Wow Amma nayi farin-ciki marar misaltawa ta rungume didda gam-gam farin-ciki na mamaye dukkan zuciyar ta.!

Da haka suka yini inda didda ta tabbatar wa Fatima akan zataje.

Fatima na komawa ɗaki ta kamo number meenal tayi darling Tana shiga meenal tayi peaking cikin sanyin murya tana cewa Asalamu-Alaikum.

Wasallama meenal.
Na'am Fatima ykk? Ygd?.

Lafiya Alhamdullh don Allah kiyi haƙuri meenal tunda akayi bikin nan banda lafiya.

"Murmushi meenal tayi a ɗaya ɓangaren tana cewa ba komai Fatima ya baby (meenal) ya jikin"?

Alhamdullh tana lafiya ƙalau magana zamu yi.
Ina jinki Fatima.
Don Allah meenal kiyi haƙuri kinji shaf na manta da maganar aurenki sai ɗazu meenal ke kirana ta gayamin, kuma naje na samu didda da maganar wlh meenal auren yayi daidai da bana ƙasar.

"Murmushi tayi a ɗaya ɓangaren tana cewa wlh ba komai Fatima Allah ya kai ku lafiya ku dawo lafiya.!
Ameen meenal ngd amma didda ta zata zo.
Lahhhhh da gaske Fatima, wlh da gaske nike "kay amma nayi farin-ciki domin dama nafi buƙatar zuwan ta akanki .

Ohh, haka ma zaki ce Fatima ta faɗa tana Murmushi.

Eh, mana aidama tafi mini kee tana kaiwa nan ta katse kiran.

Murmushi Fatima tayi ta kwanta abin ta.

★*★*★*★*★*★*★

Amsa auren husna 15 August ita kam Jamila sai tsiya take mata wai ta Habib ita kuwa sai kumbura take kamar an sama fulawa is kowa sai sanya albarka yake 

*BAYAN KWANA BIYU*

Kenan gobe zasu tafi duk wani shirye-shirye an kammala .

Daddy ne ke gayawa didda wai espt jabir ya kirasa yace suzo yanzu office ga wata mata tazo zata bada shaida.

Gaba ɗaya shirya wa sukayi suka tafi cen, bayan sun isa ga Aunty zulai Domin itama daddy ya kirata.

"Zaune suke office ɗin espt jabir Daddy, didda, Alhaji Musa , Aunty zulai, Brr, Amima,.

Espt Jabir ne yace yanzu za'a shigo da matar ko kulle bakinsa baiyi ba aka Turo ƙofar ga mama hannatu ta shigo ɗauke da sallama a bakin ta .

   Didda ce da Aunty zulai suka zabura suna cewa hannatu.
Murmushi kawai tayi tana zama, Amina ce tace hannatu kece? Ashe zan sake ganin ki .

Kowa ya zauna yana jiran ji daga Mama hannatu, Didda ce ta dubi Amina tana cewa Amina dama kesan hannatu?.

Nisawa tayi tana cewa didda itace taje har naija ta gayamin abinda ke faruwa a gida.

Murmushi baiwar Allah hannatu tayi tana cewa abinda zan gaya muku Ni sunana hannatu kamar yadda kuka sani , kuma mahaifiyar SABEETERH a gaskiya bani na haifi SABEETERH ba.

Ni haifaffiyar Katsina ce gidan mu muna da yawa amma mata mu biyu ne Sumayya sai Ni hannatu.

"Akwai wata rana da tafiya ta kamamu zuwa Zamfara sai mahaifiyar mu taje damu, a hanyar mu ta dawowa ƴn fashi suka tare mu muka yanki daji domin tsira da rayuwar mu..!

Muna gudu amma duk da haka bamu rabu da mahaifiyar mu ba , faɗuwa tayi sakamakon macijin daya sare ta a ƙafa lokacin zankai shekara 14 ita kuwa Samayya 16.

Nan muka rasa yanda zamu yi gashi duk abokan tafiyar mu sun gudu sun barmu .

Haka muka tallaba mahaifiyar mu cikin ikon Allah muka ci karo da wani bahillace kuma da ganin sa bahillacen garine.!

Ya taimaka ya kaimu gidan sa da baida wani nisa cikin garin mafara sai matar sa wacce mukaji ya kira da Shatu.

Nam suka sakawa mahaifiyar mu tayi bacci abinci suka kawo mana muka ci ' a gaskiya bamu taɓa ganin mutane masu kirki irin su ba .
 "Kwanan mu uku jikin mahaifiyar mu yayi sauƙi sosai anan muka ga ƴaƴan su HADIZA (didda) AMINA (ammy) duk da ba wani sanin juna muka yi ba da yake ba zama suke da yawa gidan ba suna gidan abokin baban su Malam Tukur wannan gidan ba gidan kowa bane illa gidan didda.

Satin mu ɗaya muka koma gida ƴn gidan mu sunyi farin-ciki satin mu ɗaya currr muka koma gida, ƴn gidan mu sunyi farin ciki rayuwa na tafiya _BAYAN WASU SHEKARU_ anyi auren Sumayya anan nida mahaifiyar mu muka yanke shawarar zuwa cen Zamfara domin gano su bukar da Shatu bamu kaɗai ba harda ƴn uwan mu baki ɗaya.

Koda muka je anan muka samu labarin gobara ta shinye su Gashi bamu san gidan Malam Tukur ba , haka muka dawo gida cike da kimanin tare da addu'a ga marigaya bayan dawowar mu gida aka saka aure na da wani Ibrahim ɗan Kano state.

Haka akayi auren ina ziyar tar gida akai - akai , to kafin iyayen mu su amince da auren yaya Sumayya da mijinta saida aka kai ruwa, rana domin basu sanshi ba basu san halin sa ba amma ba yanda suka iya daga ƙarshe suka amince" a ranar data haifi SABEETERH a ranar Allah ya ɗauki ranta munyi baƙin ciki sosai da sosai da haka riƙon sabeeterh ya dawo hannuna nida mijina domin har yau Allah bai bani haihuwa ba na riƙe sabeeterh riƙo na tsakani da Allah amma a haka mahaifin ta ya fara sauya mata ra'ayi, " lokacin da Salim ya fito neman Auren ta nan naji maganar ta ta farko ita da mahaifin ta na mugun tuggu da suke ƙulawa saura domin ganin bayan su " ban damu ba sai lokacin dana fara zuwa gidan ALHAJI HASSAN SAUTA da naga HAJIYA HADIZA na gane ta amma ita sam bata gane Ni ba , anan na fara tunani a raina kenan dama sune Alhaji mugu keson cutarwa amma babu mai bani amsa ta anan na ƙuddurta a raina tabbas bazan bari hakan ta faru ba .

Tun daga ranar na shiga bin takun su ina samun amsoshin tambaya ta a wani zama da yayi da Sabita bayan auren ta da Salim Nan zargina ya tabbatar min da wannan shine ALHAJI HUSSAINI SAUTA ƙane ga ALHAJI HASSAN SAUTA ina da labarin har tafiyar Fatima.

To nan cikin bincike naji yace ai shine ya kashe Amina da mijin ta A.s.p Kamal to naci gaba da bibiya harna A.s.p daga nan na samu lokaci mugu ya shigo garin abokin sa Auwal yazo gurin sa na biyo haka naji yana magana da Abokin sa suna maganar Amina daga yaɗn fita sai naji Amininsa na cewa Allah ya shirya ka Amina kam tananan raye da mijinta cikin ƙoshin lafiya.

Daga nan nayi shawarar tunkarar sa, haka kuwa akayi bayan na gaya masa komai a kaina da kuma burina na taimaka wa su Amina anan ya gayamin suna naija har address ya bani "wannan shine dalilin zuwa na naija na gano Amina tana kaiwa nan ta nisa tana cewa wannan shine sai kuma batu na biyu ina da ƙwaƙworar Shaidar Recording a waya na inda ya bayyana ma sabeeterh cikakken tarihin sa da kuma abinda ya aikata kuma Yanzu haka nasan inda yake , kawai ya gayamin ya cenza layi domin a ganin sa sabeeterh zata kirasa tai masa ƙorafin meyasa aka kama docta alhalin maganar a kama Alhaji Hassan sukayi kuma bai san cewa Allura ce ta tono galma yanzu haka yana naija state kuma bari na kirasa kuji.

Wayar ta ta jawo daga cikin hand bag ɗin ta, tayi darling number ALHAJI HUSAIN tana shiga ya ɗauka tasa hands free a hqjjaju ina shale-le fatan dai bata dami kanta ba?.

"Eh, Alhaji yanzu dai kana ina?.

Na gayamiki ina naija state.

Eh fa haka ne Na manta sai an jima ta kashe wayar , kowa jikin sa ya mutu da wannan al'amarin , zuciyoyin su basu ƙara karaya ba saida suka ji wannan Recording kowa ya shiga jimami inda Espt Jabir tace tace masa yana ina gobe zatazo sai suke ita da ƴn sanda da shi a kamo sa.

Ta Amince da hakan nan kowa ya koma gida , ba wanda ya gayawa inna komai.

★*★*★*★*★*★*★

Gobe da ƙarfe 9 jirgin su Fatima ya lula daga ƙasar Nigeria zuwa U.k , bayan tafiyarsu u.k soyayya mai cike da tsafta suke gudanar wa a tsakanin su inda docta yake ji kamar ya haɗiye ta don so itama yanzu ta cire kunya ta kama mijin ta sai tattalin sa take tana nuna masa soyayya marar algus.

Hakan bai hanasa gudanar da aikin sa ba  saide yana bata lokaci sa domin imma ba dole ba baya son abinda zai sa suyi nesa da juna saidai muce Allah ya bada zaman lafiya......

★*★*★*★*★*★*★

```NIGERIA```

An shirya zuwa naija, kuma anyi nasara kamo Alhaji Mugu haɗe da haɗin gwiwa Mama hannatu 💯 an bata lambar yabo domin tayi namijin ƙoƙari mijin ta bai hana mata ba .

Sabeeterh bata da labarin abinda ke faruwa, Alhaji Hassan da yaga ɗan uwan sa saida yayi kukan baƙin ciki.

Yaje ya samu inna ya mata bayanin yanda komai ya faru amma bai gaya masa wasu abu-buwa ba domin yasan wani abin sai zuciyar ta , ta buga " cikin lallashi ya gaya mata ai kuwa ta fahimta.

Ya ɗauke ta ya Kaita inda Alhaji Husaini.

Mugu yayi kukan baƙin ciki yayi nadamar rayuwar sa inda yace don Allah yana son ganin kowa da kowa zai nemi gafarar su domin yasan tasa ta ƙare .

"Haka kuwa akayi, bayan zuwan sabeeterh anan inna ta fahimci cewa (sabeeterh jikarka ce ƴr Husaini ta) ya nemi yafiyar kowa harda su Amina.....

★*★*★*★*★*★

~BAYAN KWANA BIYU~

Yanzu an shigar da case ɗin kotu.

Tashin farko Alkali ya yanke masa hukumcin kisa ta hanyar rataya domin basai anyi wani dogon Zama ba , " kowa ya gamsu da hujjojin da aka bayar a kotu.

Haka kuwa suka tashi bayan kowa ya watse ya nemi ganin ƴn uwan sa ya gaya musu duniyoyin sa na Haram a miƙa su hannun kotu na halar ya mallaka wa tillon ƴrsa sabeeterh.

Yaga jikar sa Amina inda yake don Allah a nema masa gafarar FATIMA da D.R SALIM ya ida yana Murmushi inda kowa ka gani indai yana da ɗigon imani kuka yake yi gashi sai nanda WATA DAYA za'a kashe shi domin basa damar tuna izuwa ga mahaliccin sa wannan shine sassaucin da kotu ta masa..

★*★*★*★*★*★

Suna fitowa daga kotu inda daga cen aka ƙarawa Espt Jabir matsayi mai girma domin yayi ƙoƙari tunda kotu na neman Alhaji Mugu amma kuma an kasa samun cikakken bayani sai yanzu.

"An sauya masa gurin aiki i zuwa babbar police-Satation dake Abuja."

   Suna fitowa ya dubi Alhaji Musa (mijin anty zulai) yace Abba batun maganar mu.

Nuna daddy Alhaji Musa yayi yana cewa gashin ai dashi zaka yi magana bani ba.
 "Juyowa daddy yayi Yana cewa meye akeson magana sani?.
Dama daddy ina so q bani Auren Jamila tun ba a shigo min da wannan case ɗin ba na masa magana yace kaine mai bayar da Jamila.

Murmushi Daddy yayi yana cewa a gaskiya na yaba da hankalin ka kuma na baka Jamila halal malak ko gobe idan ka shirya ka Turo.

    Yayi godiya sosai nan kuwa suka koma gida.
    
"Gobe da maraice ga Espt Jabir yazo da iyayen sa , Daddy yayi mamaki domin bai zafi hakan ba , haka kuwa aka saka dai-dai da auren husna bayan sun kawo kaya naji da gani (I see I love)  na gani ina so ake cewa.

Da Jamila taji labari batayi wani magana ba domin tasan shi itama tana son abinta Yana birgeta.

Kuma bataso husnah ta tafi ta barta........

*Amm nace kuyi haƙuri da rashin jina da kukayi wlh kwanan nan ina cikin exam ne nama daina post ta facebook iya ka ta WhatsApp koshi wlh dakyar*

Post a Comment

0 Comments