🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CHE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*Etc*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 1&2*
Karo na biyu ke nan tana lek'o sauron gidan har yanzu Malam na nan, "mtwsss" ta ja tsaki tana komawa daga cikin gidan.
Sid'uf_sid'uf ta shige d'aki kamar wata tsohuwar b'arauniya.... Kililin taji wayar dake rik'e a hannunta tayi ring sai da ta zauna saman gado kafin ta yi peaking, "Hello Sauban wlh ka jini shuru har yanzu Malam na soro ba yanda za'a yi na fito."
D'an jin tayi kafin ta tace "okey" tana sauke wayar daga kunnenta! 'Hmmmm!' Ta sauke dogon numfashi.
Yarinya ce da ba zata haura shekaru sha takwas ba kyakkyawa mai kyawon fasali.
Mik'ewa tayi da zimmar sake lek'awa ko Malam na nan amma sai dai wannan karon tana fitowa tayi kicib'is da Maman Fati, d'an kauce fuska tayi tana basarwa had'e da kok'arin wucewa.
"Keh, Fadima!
Dimm gabanta ya bada sauki kafin ta juyo tana k'ak'alo murmushin dole! "Na'am Mama."
"Ina kike ko karin zuwa har kike b'oyewa kada na sani" Mama tayi tambayar tana kafe Fadima da idanu.... "Uhmmmm amm...Dama Mama nan kawai zani yanzu zan dawo.. Tana dasa aya ta fece bata ma jira abinda Mama zata ce ba.
Wannan karon Malam baya nan a hankali take taka k'asa har ta samu fitowa daga gidansu' "hmm!" Ta shak'i iska tana jin farinciki.
tafiya ta shiga yi har ta samu damar tsallakawa gangare kusa ga bakin titi.
Wata mota ce anyi parking bak'a mai tinted sai ta juya ta kalli bayanta ba kowa kafin ta shige gurin zaman banza.
"Baby sai yanzu?" wannan saurayin dake cikin motar ya fad'a yana rik'o hannunta, fisge hannun tayi tana hararsa "Sauban ka dai san bana son irin haka?" "Sorry" ya fad'a yana ta yarda motar, "yanzu baby haka zamu k'arasa night club d'in" ya fad'a yana kallonta Sama da k'asa, ita ma jikinta ta shiga kallo domin bataga abin kushewa ga shigarta ba, Riga ce gow ta material kuma bai ma tsofe ba sai gyalenta brow kalar material d'in "miye illar shigata?" Tayi tambayar tana kafesa da idanunta" "babu" ya fad'a domin ya san k'aramin aikinta ne tace ta fasa fitar sai ya sauketa...
*Youth Enjoy life*
_night club_
Shi ne sunan club d'in da Sauban ya faka motarsa, a tare suka fito baka jin komai sai tashin kid'a har tsuma jikin Sauban keyi.
Koda suka k'arasa ciki yan'mata da samari ne ke chasewa sai rumgume rumgumen juna suke wasu kuma sai d'irkar kayan maye suke *duk wa'ennan abubuwan babu ko d'aya daya kawo Fatima nan wurin*.
"Baby mu k'arasa mana ko yau ma d'an halin zakiyi?" Jijjiga masa kai tayi tana cewa "Yau bana jin shiga 'Yan iska sun yi yawa kawai ka shiga idan kun gama ka sameni anan" ta fad'a tana gyara zamanta bisa kujerar robar dake kusa da k'ofar shiga.
Dubanta yayi da alamun b'acin rai kafin yayi kwofa yana shigewa ciki, da kallo ta bisa ko a jikinta wayarta ta jawo Tecno k'irar pop 3 WhatsApp ta shiga bata zarce ko ina ba Sai *SAMHA PALACE* Shiga tayi aka ci gaba da hira da ita domin ita kaf marubuta Samha ce ke birgeta tana son littatafanta irin yanda ta iya bada labari musamman littafinta SAD'AKA..
"AssalamuAlaikum!" Aka yi sallama bai sa ta d'ago ba domin ta shagalta da karatun *TAKABA* Da sauri ta d'ago jin an fisge wayar dake hannunta cikin masifa sai dai fuskar da taci karo da ita tayi bala'in yi mata kworjini harararsa tayi tana "bani wayata" had'e da mik'a hannu.
Murmushi Yayi har dimple d'insa na lotsawa matashin saurayi ne wanda ak'allan zai yi shekara 27 sanye yake cikin wasu k'ananan kaya masu bala'in kyau.
"Ke kuwa wannan baiwar Allah miye had'aki da night club? gaki mai fuskar salihai" Ya fad'a yana mik'a mata wayarta, karɓa tayi kafin ta kama hanyar ficewa daga club d'in sai sauri take bakin titi ta tsaya ko zata samu abin hawa "haba baiwar Allah pls ki tsaya ki saurareni," wayarta ta shiga contact number Sauban tayi darling " hello Sauban ka fito mu tafi!," shi kuwa Sauban baya ma jin abinda take fad'a ya shiga wata duniya ga sautin kida dake tashi! "Wai baka jina? Mtwss taja tsaki jin bai ma amsa ko d'aya daga cikin tambayoyinta ba, shi kuwa sai binta yake yana "haba baiwar Allah don Allah ki tsaya muyi magana"
Sai da ta kawo dai-dai bakin titi sannan ta tari abin hawa, kwotance ta yi masa cikin minti talatin ta iso bakin titin gangarawa zuwa gidansu. "Anan ta tsayar da mai abin hawa, bude jikarta tayi amma ko naira biyar batada, "mtwsssss" taja dogon tsaki kafin ta dago tana cewa "nawa ne kud'in ka?" 200 ya bata amma cikin k'aguwa data sallame shi. Narai narai tayi da idanu kafin ta juya tana duban inda wannan saurayin ya faka motarsa can gefe da inda suke wanda ya biyo bayanta "wani murmushi tayi mai dauke da ma'anoni kala-kala kafin ta dubi mai abin hawa tana cewa "bawan Allah je gurin mai motar can kace nace ya baka kudin ka" ta fada tana nuna motar can ta wannan saurayin ya biyota.
Ai ko kafin mai abin hawa ya dago tuni ta arce harta tsallaka titi.
A hankali ta lek'a k'ofar gidansu hmm! Ta sauke numfashi tana jin farin ciki ganin babu kowa sai yan kwororin Almajirai" shigewa gida tayi turus tayi tsakar gidan tana zaro ido ganin Allah gafarta malam zaune bisa tabarmar roba rik'e da wani littafi yana karantawa.
Kallon-kallon suke yiwa juna, wani azababben miyau ta hadiye jin makwoshin ta ya bushe.
"Fadima ki karaso mana" Inna Mairo wacce ta kasance kishiyar Mamanta ta fad'a tana duban Fatimar, Uhumm..hhh...tayi murmushin yak'e tana cewa "to Inna" ta fara tafiya domin k'ara sawa.... "Ke ki dakata nan."
Ba fatima kad'ai ba hatta Su inna d'agowa su ka yi suna kallon Malam cike da mamaki, domin su a ganin su wannan ba shine karo na farko da Fatima ke fitar dare ba! "in ma sabawa ne yaci ace sun saba da wannan jarababbiyar yarinyar da Allah ya d'ora musu kaddarar zama da ita, yr d'aya ta zame musu babban masifa (yar Malam tak'i halin Malam😉).
"Karki kuskura ki k'araso da k'afarki cikin gidana! Ki fita ki koma wurin karuwancin da kika fito",,,, ... Subhanallah Malam ka san me kake fad'a" inna Mairo ta fad'a tana duban Malam cikin firgita.. "Mairi kada ki sake tsoma bakin ki ba huruminki ba ne."
"Na gaji da zama da wannan yarinyar ana zagina a gari, da mutumcina tana kokarin zubar min dashi a idanun mutane, yar d'aya ta zamto barazana a garemu? Mutane ana cewa na lalata yartah bazata tsaida k'afa tayi karatun zaure ba, sai yawon karuwanci? To wlh zan dauki mummunan mataki."
Maman Fati kuwa wani irin kukan bak'in ciki ne ya turnik'e zuciyarta, ganin ba zata iya jure jin zantukam malam ba ya sakata shigewa d'aki abinta.
"Malam kayi ma girman Allah kayi hak'uri da Fadima, ita d'in kaddarar mu ce babu yanda zamuy! Don girman Allah ka sassauta zuciyar ka, su yryr rahma ne kuma amana ce Allah ya bamu, yanzu idan ka koreta baka san Inda zata ba, gara dai a lallab'a da wa'ennan kalaman inna mairi ta baiwa malam haquri, ficewa ma yayi daga gidan.
Fatima koga fishin kanta, d'akin Maman fati ta shiga da Assalam ko d'agowa maman fati ba tayi ba daga zaunen da take balle har tasa ran zata amsa mata.
"Mama sorry bud'e min zif fatima ta fad'a tana juyo da bayanta ga Mama, ganin mama tayi biris da'ita tab'e baki tayi ko'a jikin ta..inna Mairi zoki bud'emin Zif din rigata.
Da sallama Inna Mairi ta shigo saida ta budema Fatima zif kafin ta fito, cire kaya tayi tana daura zane "mama bari naje nayi wanka kinga akwai zafi.. Shuru Mama bata amsa mata ba.
Wai don Allah mama me nayi da zakiyi fishi dani?
Wlh Fadima kin samin bak'in ciki a zuciyata, kuma sai Allah ya baki yryn da zasuyi miki fiye da abinda kikamin.
"duban mama take sokwor-kwotai, Mama ni gaskiya bazan iya ba kawai saboda ina d'iyar Allah ramma saina tauye rayuwata ga ustaziyya? Gaskiya ni rayuwar ynci nake so nayi bawai rayuwar tauye hak'k'i ba...kililin wayarta tayi k'ara jawota tayi ganin sunan dake yawo saman screen d'in wayar ya sakata sakin murmushi tana ficewa daga d'akin.
"peaking tayi tana karawa a kunnen ta, Hello my Sadam ya kake? Fatima ta fad'a tana sakin murmushi"
Lafiya lovy dama kiranki nayi yau akwai chasu karfe 12 dare zamu gama karfe 3 Big girl ce na'isa ta had'a muna na murnan dawowarta daga karatu a Malaysia, to kinga kema ba za'a barki a baya ba.
"Hmmm! Fatima ta sauke numfashi kafin ta shiga duniyar tunanin yanda zata fita daga gidan"Hello lovy kina jina? Uhmm Eh ina ji"
Okey ki shirya yanzu 11:30pm ganinan zuwa kiyi maza ki shirya saimu wuce tare.
Okey, my sai ka biyo daga haka ta yanke kiran.
"Ya zama tabbas yau koda bala'i koda masifa saina halarci wannan chasun" babu wanda zai takura rayuwata, haka kawai a hanani sakat da kuriciyaahhh..
*Don't forget with share fisabililah albarcin manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*☺
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CHE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*Etc*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 3&4*
Bokiti ta d'auka kafin ta shiga toilect shaf-shaf ta gama wanka, akan sauri koda ta fito jikin ta da kumfa.
D'aki ta shiga sai dai har yanzu mama nanan a inda ta barka, tab'e baki tayi kafin ta fara wak'a abin ta "Waya kamata naso? uwa wazan nunawa kauna? Sai Mummy na a cikin mata wazan ba fansan raina Sai Mummy na a tunani na kam ba tamkar Ummana, sai Mummy na daga Allah farkon zuciyata sai Mummy na....." Haka Fatima taci gaba da wak'ar tana Shiryawa, d'agowa tayi tana duban Mama dai dai ta jawo gyalen ta, ido biyu sukayi da Mama.
"Yanzu ko Fadima ina zaki wai anya kuwa kina so kiga dai dai?" Hmmm! Fatima ta sauke numfashi had'i da zama gefen Mama, "Mama kiyi ma Allah kibar ya ana ta kada bakin ki ya bini! Kega Mama naga dai fitar nan da nikai ba karuwan ci nake zuwa ba? Kawai ina shawo iska ne, Mama kiyi hak'uri.
"Fadima yau ko sallar magriba kinyi Balle isha'i? Kuma fita zaki koma yi shin bakya tsoron bakin malam?".
Mik'ewa Fatima tayi tana k'ok'arin ficewa daga d'akin sannan tace "Mama idan naje cen zanyi Sallar ai walima ce ma zani yanzu", "Fadima Walimar gidan ku? Shi cha-chan da zakije shine walima?". Ba tare da Fatima ta bata amsa ba tayi ficewarta daga dakin.
Duban kanta tayi Riga da skirt ne na wata atamfa masu masifar kyawo, "kai kodai na chenja gyale? Tayi ma kanta tambayar.
"Fadima ina zaki?". Inna mairi data fito daga d'aki yanzu tayi ma Fatima tambayar tana duban ta, Inna zanje Walima ne.
"Walima kuma Fad'ima? Walima a wannan lokacin, wace iriyar walima ce wannan?".
"Dama Inna walimar auren k'awarmu ce", d'an Jim Inna tayi kafin tace "au na tuna wanda Hauwa'u wacce tazo gidan nan shekaran jiya harta kawo miki katin aure"?
"Kay shiya sa nake bala'in sonki Inna ashe dai kin gane? Wlh kuwa ita ce".
"To Amma ke Fad'ima Walima a wannan lokacin? Ke dubi lokaci kuwa? 12 tayi fa",
"To Inna ya za'ayi haka za'a lallab'a" Fatima ta fad'a cikin marai-recewa.
"To Fatima amma dai ni Malam nake tsoro kar kuma wata masifar ta taso!"
"Ni Inna ya zanyi? Kawai don Allah ki rufamin asiri yanzu zan dawo minti 30", itakam Inna tama kasa cewa uffan da kallo take bin Fatima har ta fice daga gidan.
Babu alamun damuwa a fuskar ta sai zallar dariya da take fuskar ta, Kyakyawar fuskar ta wacce bata cika da kwaliya ba Fauda kawai ta shafa sai witlips a saman leb'e,,, Tafiya take tana kwar-kwarsa dube dube ta shiga yi sai cen ta hangi motar Sadam, k'arasawa tayi tunda ya hange ta yake sakin murmushi fitowa yayi yana bud'e mata gurin zama ta shiga ya rufe sannan ya koma gurin zaman driver.
"Lovy kin tsayar dani", ya fad'a yana sakin murmushi, itama murmushi ta sakar masa tana cewa "Kayi hak'uri My kasan gidan sai a hankali".
"Hakane Lovy".
Minti 27 ya kai su wani kata-faren Club wanda had'uwar sa bama zata misaltu ba! Hatta k'ofar shiga Club d"in wata jar duniya ce.
*BIGGEST CLUB*
Koda Sadam yayi parking wani farin-ciki ne ya ziyar ci zuciyar Fatima yau zata shiga babban Club, "Wow!" ta fad'a tana sakin k'arar Jin dad'i.
Saida ya fito ya bud'e mata kafin ta fito, "Lovy kin ganki? kinga yanda kikayi Fresh sai yanzu na k'ara ganin ki wlh kin k'ara kyau sosai ko dan munyi kwana biyu bamu had'u ba?".
Hmml! Fatima ta sauke numfashi tana cewa "nidai mu k'arasa ciki, wlh na zak'u ban ganni cikin Club d'in ba".
"Okey muje", haka suka jera kamar wasu shaha-rarrin masoya.
Cikin club an matuk'ar tsarashi yanda baki bama zai furta ba, wani sanyayyen kid'a ne ke tashi.
Yryn manyan mutanene suke shek'e ayar su son ransu, daga K'asar waje akayo odar kayan maye duk Na'isa ce ta shirya wacce ta kasance yr ce ga Tsofon minister man fetur...
Bisa kujerunbdake jeren gurin suka zauna, Lovy me kike buk'ata?
Jijjiga kai Fatima tayi tana cewa A'a bana buk'atar komai.
Sake baki tayi tana duban yanda suke chasu sai rawa wasu keyi abin yayi bala'in birge ta.
My muje muyi rawa Amma fa kar kace zaka kai ga jikina ta fad'a cike da garga d'i.
Hmm! Wai ke Lovy mi yasa ko d'an romance d'innan bakya bari ayi dake? Jikinnan fa ko an tab'e shi ba ragewa zaiyi ba, ko irin wannan rayuwar ta zamani bakya yi, wai shin bakya ganin yanda ake rayuwa duk Clubs d'in da muke zuwa.
Sadam ni a haka nike son rayuwa ta, kuma a haka zanci gaba da gudanar da tawa Rayuwar! Okey a tare sukayi rawa amma ko hannunta bata bari ya rik'a ba, duban Agogo tayi 02:30am Kai My sadam ashe lokaci yayi nifa kazo ka maida ni gida, na gaji ta fad'a cikin marai-rere wa da kuma alamun gajiya.
Cikin maye Sadam ke cewa Haba lovy ni kinga dare yayi ki bari mu kwona, gobe tun da safe zan maida ki.
D'anja da baya tayi tana toshe hanci jinbyanda ta shak'i iskar warin Giya da sauran kayan maye had'e da cewa Haba Sadam taya zani kwona a wani gurin k'arfe uku ta kusa fa? Nidai wlh gida zani kuma muje ka maidani.
Ganin yanda ta Nace yasa shi cewa to muje cikin tangad'i yake tafiya tabi bayan sa har suka fito harabar gidan, baima samu bud'e mata mota ba.
Koda ta shiga tada motar yayi, yana fitowa ya yanki titi wani irin sharara gudu yake yi saman titi.
Sadam kabi a hankali damu don Allah, ko sauraran ta bayayi domin dishi dishi ma yake gani saboda yanda giyar ta bugesa.
Sadam don Alla.....Maganar ta ce ta mak'ale ganin yanda sitarin motar ya kufce daga hannun Sadam
Take motar ta yanki daji....wayyo Allah naga bone na bani na Lalace...Wayyo don Allah sadam..Kif bakinta ya kulle banda taslima babu abinda take jin yana fitowa daga zuciyata.
Wata k'atuwar itaciyar murna ce gudar babba take motar tayi kanta Gadan-gadan.....
*Don't forget with share fisabililah albarcin manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*☺
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CHE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*Etc*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 5&6*
*ALLAH UBANGIJI YA SAKA MUKU DA MAFIFI CIN ALKAIRI, A GASKIYA BANYI TUNANIN ZAKU KARB'I WANNAN LITTAFIN HAKA BA, NA GODE DA SOYAYYA WANNAN SHAFIN NAKU NE MY FAN'S* 🌹
📖Wani wawan birki Sadam yaja girif motar ta samu ta gwori dutsi wanda yai sanadiyar motar ta tsaya.
Ko secon guda Fatima bata k'ara ba ta bud'e murfin motar tana fitowa kamar zata b'alla shi.
Duk ta rikice da hannu ta rik'o gyalenta tana jin ta shak'i iskar waje ta sauke numfashi tanq cewa Alhamdullh! Allah na gode maka daka tseratar da rayuwa ta, da yanzu na mutu? Shikenan bazan k'ara ganin Maman Fati ba? Innalilahi wa'inna ilaihin raji'um.
Lovy don Allah kiyi hak'uri Sadam wanda ya fito daga mota ya fad'a yanzu ya fad'a yana had'e hannun sa guri d'aya, tuni ganin mutuwa kusa kusa ya saka Giyar sakin sa.
Hararar sa Fatima tayi kafin ta nuna kanta tana cewa Wah? Ni? Ai wlh ni da kai sai lahira ka tashi salwantar da rayuwata sannan kuma mu sake bin inuwa d'aya? Bama kai ba babu ni babu fitar dare daga yau...Tana ida fad'ar hakan ta kama hanya, shi kuwa Sadam da kallo ya bita yama kasa cewa komai, ganin har ta gota shi yasa shi d'aga murya yana cewa 'Lovy bakya tsoron bin hanya? Ina zaki samu abin hawa? kada ki had'u da miyagu ko yn patrol.
Tana jiyo savamma tayi banza dashi domin ta gwommace gwora yn patrol su kamata da tayi gan-gan cin sake shiga Motar Sadam... Ga duhu sai d'an hasken farin wata kad'an.
Wash Allahna! Ta fad'a jin k'afarta ta tokare da wani icce inda yayi mata mugun sarb'e, wata iriyar azaba ta ziyarce ta dakyar cikin jarumta ta danne kukanta.
Wayyo Allah na, ni Fadima naga Rayuwa iri iri, cikin d'in gishi ta shiga taka k'afar da kyar da sud'in goshi ta samu isowa bakin titi, babu alamun mota ko d'aya, haka ta kama bin kyage kyagen titi tana tafiya ita d'aya.
Ta wahala ta azabtu, cikin tsananin ciwon da k'afar ke mata bata san sa'adda takai zaune ba tana sakin wani marayan Kuka.
Wata mota ce ta gifto da gudu saida da watsa mata iska, da baya motar ta dawo dai dai saitin ta fitilar motar aka dallo mata cikin hasala tasa tafukan hannun tana kare fuskar ta.
Fitowa yayi daga motar domin ya gane ta tun lokacin daya biyo (ba kowa bane face wannan saurayin daya fisge wayar ta a club d'in da suka je ita da Sauban).
Gurin ta ya Nufa kafin yace Barka.
Jin maganar sa wacce zata iya cewa ta tuna, d'agowa tayi tana duban sa duk da ba sosai take ganin sa ba, Ke kuwa lafiya na ganki a wannan halin kuma a wannan lokacin?
D'am jim tayi tabbas a wannan halin tana buk'atar taima kon wannan bawan Allahn.
Hararar sa tayi tana cewa Malam ba ruwan ka da inda na fito domin ba shafar ka rayuwata tayi ba kaji?
Okey shikenan Ya fad'a yana k'ok'arin mik'ewa, bata san lokacin data mik'e ba, Daka ta! Malam nidai idan zaka taima ka min saboda Allah to.
Juyowa yayi yana cewa Ni ba Malam suna na ba, Sunana Isma'il.
To naji nidai ka taimaka don Allah ka k'arasa dani gidan mu, d'an tab'e baki yayi yana Cewa muje ya fad'a yana shigewa mota.
Cikin azama ta shiga motar kafin ta sauke numfashi.
Jan motar yayi dama babu nisa da gidan su, kamar kurame babu wanda yace da d'an uwan sa k'ala itakam azaba ce ke cinta... Bai tambaye ta ba sai kusa da gidan su yayi parking, d'agowa tayi tana duban sa kafin tace Ya akayi kasan gidan mu?.
Au har kin manta d'azu da kika tura min mai abin hawa na basa kud'i?
Kunya ce ta lullub'e ta cikin tabarmar kunya tace ngd bata saurari me zaice ba tayi fivewar ta
Ki tsaya dan Allah, amma ko sauraren sa batayi ba ita dai badai burinta ya cika ba gata a gida Alhamdullh.
Yanzu kam ko tsayawa lek'e batayi ba tayi shigewar ta gida.
Ko'ina tsit babu motsin ko tsuntsu d'akin su ta shige tana ta sakin ajiyar zuciya, akwoi hasken kwon fitila Mama ce Bisa tabarma tana sallah.
Jifa da gyalen ta tayi, ko tufafi bata cire ba ta fad'a bisa gado duk da ciwon da k'afar keyi mata ammq hakan bai hana cikin k'ank'anin lokaci bacci yayi awon gaba da'ita ba ba ko tunanin Sallah.
Mama ce da takaici ya cikata ai kuwa tana Sallame Sallah ta mik'e waje ta fita k'ark'ashin iccen goro inda suka girke tukunyar laka wacce ruwan cikin ta keda bala'in sanyi, saida Mama ta ciko cup kafin ta dawo d'aki.
Duban Fatima tayi had'e dayin kwofa, tsakiyar fuskarta ta Fara zuba mata ruwan daga Saman kai har k'afafu..
WayyovAllah na Fatima ta saki wata gigitatciyar k'ara saida Mama ta jima da duban kun cinta kafin ta yarfa mata mari tana cewa wlh ko kiyimin shuru ko kuma na k'ara miki.
Mukwui tayi ta saka duka hanuAn ta tana dafe baki saboda kukan.
Tashi kiyo alwallah kiyi Sallah ko Allah zaiji tausayin ki ya sauya miki d'abi'u marar mutumci Shashasha, Ke dawo da yawon ki kin bid'i shimfid'a kin kwonta babu Azhar babu la'asar babu magriba babu isha'i babu Shafa'i da wutri balle ma har ayi maganar nafila.
Wlh Mama nayi azhar nayi la'asa...make bakin ta Mama tayi tana cewa Yimin shuru da rub'ab'en bakin ki Anda baya Salati, ba zaki tashi kiyi abinda nace ba.
Babu yanda ta iya ga sanyin ruwan da Mama ta zuba mata ga zafin mari, ga Kuma inda taji ciwo bone Saffo-saffo.. A hankali ta shiga taka k'afar harta fita Mama na binta da kallon tsana......
*_wash yau ina fama da ciwon kai, babu Typing mai tsawo kuyi maleji har gobe_*
*Don't forget with share fisabililah albarcin manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*☺
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*Etc*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 7&8*
Da kyar tayo Alwallah koda ta shigo da harara Mama tayi tana cewa to da w'ennan kayan masu warin giya zakiyi Sallah? D'an juyawa Fatima tayi tana duban Mama kafin ta d'an sin-sina jikinta tana cewa Wlh Mama babu warin giya a jikina Mama ban sha giya.
Fatima kina tunanin ni zan iya shaidar ki Inah, ki duba kalamen da Mahaifin ki Yayi amma baki daddara wai kina d'iyar Limami jikanyar malumma amma hae ki iya kona ba gidan ku ba?
Yo miye marabar ki da wanda yake kwana a waje? Kedai kiyi sallah kafin gobe muji hukuncin da malam zai yanke miki idan gidan zaki bari to domin Wlh kiji rantsuwar musulmai indai har ni zan baiwa Malam hak'uri akan ki to na gommace ki Mutu...
Mutuwa Fatima ta fad'a cikin tashin hankali tana zawo idanu...cikin tsoro ta tuno hatsarin daya tashi faruwa da su, Wayyo Mama yanzu idan na mutu wa kike da?..
Ai ko bani da Kowa wlh Fad'ima bana k'aunar zama dake Domin ke kasan ce Ciwon Idanu a gare mu.
Hmmm! Mama Mama Ina sonku. Tab'e baki Mama tayi kafin taci gaba da Nafil filin ta, Itama Fatima da d'in gishin k'afar tayi Sallah magriba tayi isha da Shaf'i da wutri tana gama sallamewa ko add'u batayi ba ta b'ingire sai Bacci.
*WAYE WAR SAFIYA*
koda Mama ta tada ta yin sallah asuba tana gamawa ta Koma bacci, koda Malam ya tambayi Inna Mairi shin Jiya Fad'ima tayi d'an halin? Cewa tayi A'a ai fad'an sa ya shigeta.. To Allah ya shirya kawai za'ace.
*10:39am*
A hankali ta bud'e idanun ta tana k'ok'arin mik'ewa ai kuwa da sauri ta koma jin ba zata iya taka k'afaeta ba, jawo k'afar tayi tana dubawa Faritan ta duk sun kumbura wurin duk ya kwoye abin tausayi.
Wasu irin hawaye ne suka zubo daga idanun ta na azabar da k'afar keyi mata! Wayyo Allah na Mama Malam Inna kuzo kada na mutu Wayyo Allah ni Fatima k'afata ai kuwa da sauri Inna mairi da Mama suka shigo tattare, Mama ce tayi saurin rik'o k'afar tana dubawa.
Innalilahi Wa'inna Ilaihin Raji'um Subhanallah Fad'ima meya sami k'afar ki haka Mama tayi tambayar A kid'ime, Inna mairi ce tace kiyi mana bayani Fad'ima Bari a kira Malam Inna mairi ta k'arasa Fad'a tana ficewa daga d'akin.
Banda Kuka babu Abinda Fad'ima keyi ita kuwa Mama sai aikin Sannu take, a tare Inna mairi da Malam suka shigo k'ara-sowa bakin gadon Malam yayi kafin yace Miya sami k'afar tata? Cikin Tausaya wa Mama tace Wlh muma bamu sani ba mun tambaya ta kasa ce muna k'ala.
Rik'o k'afar Malam yayi da hannu d'aya kafin ya saka d'aya hannun yana matsa Inda ya k'abe da Sauri Fad'ima ta saki k'ara tana cewa Wayyo Anah na! Na mutu na lalace ture hannun Malam tayi daga k'afar.
Cikin jin haushi Malam Ya daka mata Tsawa Ke kiyima mutane shuru, ai dama Wanda baiji bari ba yaji jowo bide-bide Same-same, mukui Fatima ta danne kukan ta dole sai Hawayen dake ta Bulala kamar an bud'e fan-fo.
Inna ce tace Malam a kaita assibiti kada abin ya zama matsala, bai bata amsa ba Illah maida duban sa da yayi ga Fatima yana cewa Menene ya Samu k'afar ki?
Malam nima ban sani ba kawai na tashi ne yanzu naji k'afar na ciwo ta fad'a tana matsar idanu.
To Yanzu saka Hijabi aje assibiti.
*(tsakanin yryr da iyaye sai Allah, Allah ka sakama iyayen mu da mafificin Alkairi)*
Koda sukaje Assibiti Saida aka wqnke k'afar aka cire karan daya sarkafe ciki, magani aka basu bayan an mata allura suka dawo ita da Inna mairi datai mata rakiya, koda suka dawo K'ark'ashin itaciya Maman Fati tayi mata Shimfid'a ta kwonta, abin ci Mama ta kawo mata mai rai da Lafiya.
Nan Fatima tayini Sallah kawai ke tada-ta sai lallashin ta akeyi bani-bani malam ya shigo ita kuwa Mama tana nan zaune tanayi mata Fifita Inna mairi kuwa sai faman yi mata Sannu takeyi nan da nan labari yabi unguwa wasu nq cewa k'arshen yawo kenan kowa dai na tofa albarka cin bakin sa, batama waiwayi wayarta ba..
Assalamu-Alaikum! Akayi Sallama daga bakin k'ofar shigowa gidan a tare Mama da Inna suka amsa, wata matashiya ce Rumah kenan yr anguwar wacce mutane zasu iya cewa ita kad'ai ce k'awar Fatima.
Koda ta shigo saida ta gaida su Mama kafin ta k'arasa gefen Fatima tana zama kusa gareta gefen tabarma.
Ashsha Fad'ima sannu da jiki Wlh sai yanzu nake samun labarin gurin harira.
Narke fuska Fatima tayi kafin tace naji sauk'i ai Rumah kwona biyu?
Qalau Hmm wai ni kuwa Fad'ima ya akayi kikaji Ciwo? Kedai bari Rumah Fad'ima ta fad'a tana d'agowa ido biyu sukayi da Mama, cikin basarwa tace Mama don Allah kawo min ruwa da harara Mama ta bita kafin ta mik'e, Fad'ima na ganin Mama ta tashi ta shiga baiwa Rumah labari from A to Z.
Kam bala'i lallai Fad'ima ke kuru yanzu gobe ki koma, Hmm! Kedai bari Ruma ni da Fitar dare sai lahira, to yanzu Kam ba zaki je bikin Hauwa'u ba?
Wah ni? nikam wlh sai naje bikin hauwa Gobe, Haba Fad'ima da wannan k'afar Eh nifa sai naje hhhhh Rumah ta kyal-kyale da dariya..
Haka ta jima suna hira kafin ta tafi da zummar gobe zata biyoma Fad'ima zuwa bikin hauwa'u...
*ASALIN SU*
*Don't forget with share fisabililah albarcin manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*☺
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*Etc*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 9&10*
*ASALIN SU*
Malam Shehu babban Shehi ne zaune yake cikin jihar kano a unguwar Rijiyar zaki babban Malami ne asalin su yn k'auye ne zama ya maido su kano, Malam Shehu shi kad'ai iyayen sa suka haifa har Allah ya d'auki ransa.
Ya auri matar sa Aisha wacce ta kasance Yr Malamin daya koyar dasu karatun allo auren su da shekaru biyu ta samu ciki, Da wahala da komai Aisha ta haihu ta samu d'iya macce Ranar suna yr taci sunan mahaifiyar sa Fad'ima, Fad'ima nada shekaru biyu Mama ta sake samun ciki wannan karon abin da ta haifa baizo da rai ba, haka dai haihuwar daga ta haifi d'a bai zo da rai ba sai ciki ya zube.
Fatima nada Shekaru 8 Malam ya auri Mairi wacce ta kasance bazawara ce acen kauyen su ya aurota itama dai har yanzu Auren su shekara 10 amma bata taba ko b'arin ciki ba.
Inna mairi da Maman fati zaman mutumci sukeyi tamkar yn uwa na jini babu wanda ya tab'a jin kansu ko da Malam kuwa, sun nunawa Fatima so dai dai k'a'ida tun tana da Shekaru 12 ta sauke Al'kur’ani sai dai babu jin magana ko kad'an yau itace tsokani wannan tsoka wancen an sakata makaran tar boko da Primary har Secondry wacce ta kammala Watanni biyu, kulum cikin yawon gidaje takeyi duk inda taji ance akwai Fati to ko k'afarta zata k'alle sai taje.
Tunbtana Ss1 ta fara tara Samari babu dukan da batasha ba, Fad'a amma duk tayi kunnen sheggu, Amma fa masifar son iyayen ta take a unguwa kowa ya shedeta d wannan halin wasu na ganin laifin iyayen ta wasu kuma basu gani (Mai kunnen k'ashi😂) Har ta fara fita zuwa Club sai dai fa ko hannun ta bata bari Saurayi ya rik'e, Idan nace zan lissafa muku adadin Samarin Fatima to sai an gaji...
*WANNAN KENAN LABARIN FAD'IMA*
_Back to story_
Kafin bayan magriba Fatima ta d'anji sauk'i Domin ba kad'an ba ta samu kulawa.
Har dare yayi yau Fatima kota kan wayarta bata bi ba, Sai yanzu taji wayar na ringin wanda Wannan shine karo na ba adadi,, tsaki tayi kafin ta jawo wayar daga k'ar-k'ashin Fillon da take kwonce Sadam ne mtws ta k'ara jan tsaki "ke da waye"? Mama data shigo d'akin yanzu tayima Fatima tambayar.
Mama ba kowa Fatima ta Fad'a tana duban Missed calls gasu nan babu iyaka Harda na Sauban, d'an jim tayi kafin tace Hankali na ya gushe ne wlh har na sha'afa Da banyi blocking number Sadam ba...
*Wayewar Safiya*
Zaune suke tsakar gida Mama da Inna Mairi sai kuma "Inno wace ta zo dubin Fatima Inno dai k'auwar Mama ce"..
Fira suke nan tsakanin su kuma duk abinda ya shafi Fatima ne, Sai addu'ar Allah yasa ta d'aure tunda Jiya duk bata fita ba.
Fatima ce ta Fito daga d'aki nan ta zauna Gefen Inna mairi cikin su babu wanda ta d'aga kai ta kalla balle ta gaida su, Inno ce ta dubeta cikin tausaya wa kafin tace Sannu Fad'ima ya jikin? Ai kinyi arziki abin bai kai-ki mugun wuri ba. K'ala batace da Inno ba Mama ce tace ke Fad'ima ba magana ake miki ba? Sai a lokacin ta d'ago tana cewa Yi hak'uri banji ba! Sannan ta maida duban ta ga Inno tana cewa Inno naji sauk'i ina wuni.
Lafiya Inno ta amsa, Fatima ce ta dubi Mama tana cewa Mama yanzuake son na shirya kada Rumah tazo ta tarar ba shirya ba!. Kallon ta Mama tayi kafin tace ki shirya Fatima? Zuwa ina?
Mama auren Hauwa'u ta fad'a tana mik'ewa tsaye, Inno ce tace Fad'ima da wannan k'afar zaki fita yawo? Mama ce ta karb'e zan cen da cewa Nima abda na gani kenan ai dama mai hali baya fasa halin sa Yawo sai kace wacce taci k'afar kare mutum kwota-kwota babu kamun kai Mtwsss kaico da wata Rayuwa wlh.
Inna mairi ce tace Haba Fad'ima ki bari ki k'ara koda kwona biyu, Haba Inna yanzu bikin hauwa'u za'ace kar naje? To idan banje bikin hauwa'u ba bikin waye zanje? Fad'ima ta k'arasa fad'a kamar zatayi kuka.
Ganin abin nata reni ne ya saka Mama cewa to Wallahi summa tallahi Fad'ima yau kam babu inda zaki yr neman Jarrababbiya.
Cikin b'acin rai Fatima ta shige d'aki tunda ta shiga bata k'ara fitowa ba har akayi la'asar saida ta jiyo sallamar Rumarh sai dai taji Mama ta tarbe ta kuma bata san mita gaya mata ba hatta sallah dkyar tayi, a cikin haka da bala'i da masifa Fad'ima tayi kwona uku ko k'ofar gida bata taka ba...
*LARBA*
Yau kam ta k'udiri anniyar sai ta fita wlh kota yaya, Kowa bata bari ya gane nufin ta ba.
Tana gama Sallar la'asar ta shirya, gashi yau tayi arziki Mama bata nan tana gidan su sai Isha'i zata dawo.
yanzu ke Fad'ima fita zakiyi?, hmm...hml Inna kenan yau fa Kwona kusan 4 banje ko'ina ba da d'azu kuma Mama nanan bata bari na fita wlh Inna yanzu zan dawo keji na rantse gidan Hauwa'u zani.
Gidan Hauwa'u fa? Yanzu? To Inna da yaushe zani nidai yanzu zan dawo daga haka fice, bakin titi ta nufa takai minti 5 tana Jiran abin hawa, kamar daga sama taga mota ta tsaya gabanta akwai d'an haske gurin Zuge glass d'in motar akayi o wrurnoyi hore makko..Ba kowa bane sai Wannan saurayin Isma'il.
Yauma Allah ya sake had'a mu ya fad'a cikin murlushi, d'an tab'e baki tayi batace komai ba, ina zuwa yau kuma?
Wani guri.
Wani guri? Muje to na sauke ki, A'a ka barshi kawai.
A'a fa kedai kizo muje hmmm ta sauke numfashi kafin ta zagayo tana shiga..
Saida ya tada motar kafin ya dubeta yana cewa wacce unguwa zamu, Wayarta ta duba adireshin da Hauwa'u ta turo mata ka ranto masa tayi dubanta yayi yana wani irin murmushi wanda na kasa gane manufar sa....
*Don't forget with share fisabililah albarcin manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*☺
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*Etc*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 11&12*
_Khadija S Kaita this page is for you kiyi yanda ki kaga dama dashi_😘 *Ina jin dadin sharhin ni sosai ba kad'an ba*
A hankali yake tuk'i Sai anguwar Tudun wada, wanda nane unguwar da Hauwa'u tayi aure! Duban sa Fatima tayi kafin tace Am mu nemi wani ayi mana kwotancen gidan kaga sai tafiya muke, kuma mun shigo unguwar kar aje mu wuce gida bamu sani ba.
Karki damu aini wannan unguwar ba bak'uwa ta ce ba, babu inda ban sani cikin ta ba, tunda kega anan Yayana yake zaune da matar sa.
Duban sa Fatima tayi tana cewa Ayya lallai kuwa kai d'an unguwa ne, to lallai kam ya bata amsa a tak'aice, yn minto ci kad'an ya sake duban ta kafinbyace komu biya ki gaida matar yayan nawa?.
A'a nikam Fad'ima ta fad'a cikin halin ko in kula ci gaba sukayi da tafiya saida suka kawo dai dai gurin wasu matasa d'an tsayar da motar yayi kafin ya zuge glass yana tambayar su gidan amma sunce sukan basu sani ba...har kusan mutum 4 suna tambaya amma kowa cewa yake bai sani ba.
Am Fatima kega gashi lokaci na tafiya kuma har yanzu bamu samu wanda zai nuna mana gidan ba, mizai hana ki d'auki shawarar da zan baki.
A mamakin ce ta dube sa kafin tace Shawara kuma wacce iri? Hmm! Isma'il ya sauke numfashi kafin yace muje gidan yayan nawa kinga sha'ani na mata Ita Anty matar Yaya ba zata rasa sanin gidan ba, amma fa shawara ce na bayar.
Duniyar tunani Fatima ta shiga domin gaskiya sunfi one hour suna zagayen unguwa, Shi kuwa Isma'il ya wanu basar tamkar babu abinda ya shafe shi sai tsintar muryan Fatima yayi tana cewa to Yayi muje cen d'in wani irin farin-ciki ne ya lullub'esa wanda bai bari ya bayyana ba kada ta zargi wani abu da gudu ya fisgi motar saida Fatima ta firgita tana cewa don Allah kabi a hankali damu.
babu wani nisa yayi parking motar sa a wani d'an matsa-kaicin gida fitowa yayi kafin ya bud'e mata itama.
Mu k'arasa ga gidanan, cikin d'ari-d'ari ta shiga tafita zuciyarta sai sak'e sak'e take mata, tura kofar gate d'in gidan tayi kafin ta shiga tsaye tayi saida ya k'arasa wannan karon kan shine ya shiga gaba tabi bayan sa. Wata K'ofa ya shiga d'an matsakai cin Fallo ne "ki zauna bari na kira matar Yayan" Okey Fatima ta fad'a tana zama bisa kujera.
Tunda ya shiga d'akin yakai 5 kafin taga ya fito.
Am, wai Antyn tace ki k'arasa ciki tana zuwa.. "Ita Antyn"? Fatima tayi tambayar a mama kince, Eh wai ko bata jin dad'i amma no pro. Ki shiga kawai.
Hmmm! Fatima ta sauke numfashi kafin ta mik'e domin ita harga ranta bata kawo komai ba, d'akin da taga ya fito ta shiga, shigar ta keda wuya taga d'akin Wayam babu kowa wata yr katifa ce kawai da fillows Dube dube ta shigayi sai dai fa tabbas wannan d'akin baiyi kama da wanda ake zaune a cikin sa ba, motsin da taji a bayan ta ne yayi sanadiyyar juyowar ta da k'arfi, d'an ja da baya tayi ganin Isma'il.
Magana ta fara yi cikin zargi, Kai kuwa da alamu kayi kus-kure domin wannan d'akin baiyi alama da ana rayuwa a cikin sa ba, ina matar yayan naka?.
"Hmmm! Fatima a gaskiya babu wata matar Yayana sannan kuma na kawoki wannan gidan ne Saboda buk'atar kai na, wlh Fatima tun ranar dana Fara ganin ki na kamu da tsananin Sha'awar ki, wlh Fatima ina son kasan cewa tare dake, Fatima a wannan ranar ban iya bacci ba saida nasan komai a kan ki, Fatima ki yarda dani wlh nayi Alk'awarin zan baki duk abinda kike so"..
"Innalilahi Wa'inna Ilaihim Raji'um, Isma'il dama da wata manufa kake neman shigowa rayuwata? Ya subhanallah ni fatima naga rayuwa wayyo ni kaina, Don Allah kayi hak'uri ka rufamin asiri..Isma'il kada ka tozarta ni da mutumci na.
"Mutumci..?Hhhhh😅 lallai Fatima dama ke kina tunanin kina da sauran mutumci? Ai wlh bari kiji ba 'yn unguwa ba yau kowa yasan ke kam ba kida mutumci, bayan kin gama zubar da mutumcin ki a duniyaa! Nidai ki Ki amince yanzu zanyi na gama kowa ya kama gaban sa"..
Zaro ido Fatima tayi Wasu irin zafafan hawaye na kworanya daga idanun ta, "Wayyo ni Allah na wlh Isma'il ni ba yr iska baci, ban tab'a aikata Zina ba!".
"Haba Fatima wannan ai k'anzon kurege, wazai yarda da zantukan ki? Yanzu ki bari muyi ko romance ne".(Hmmm! Yau kam Fatima takai k'arshen yawon dare).
Ta shiga tashin hankali marar misal tuwa banda sunan Allah kawai take kira domin tasan babu wanda zai fiddata daga hannun Isma'il sai shi. Wani tunani ne babu zato balle tsammani ya fad'o mata, d'an murmushi tayi kafin tace to Yayi Yaya Isma'il na Amince.......
*Don't forget with share fisabililah albarcin manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*☺
*Don't forget with share fisabililah albarcin manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*☺
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*Etc*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 15&16*
............"Wallahi kuwa matata ce, ai idan abin ya bigeta sai ma an d'aure ta, ni nama gode muku saboda idan ba donku ba da yanzu bamu san inda ta nufa ba".
Abdul ne yace to ai anyi arziki, kafin ya juya izuwa Yusif yana d'an danne dariyar sa ciki-ciki...to mr Man saika wuce mu tafi.
Hararar sa Yusif yayi kafin ya kama hanyar komawa cikin mota.
"Wannan maganar ce ta far-fad'o da Fatima jkn zancen Isma'il na godiyar da yake yi musu, “Nagode bayin Allah wallahi kun taima ki matata.....Zumbur Fatima ta mik'e tana cewa "Wayyo Allah na jama'a kuzo ku taima ke ni" gaba d'aya daga Abdul har Yusif juyowa sukayi suna kallon ikon Allah.
Da gudu Fatima tayi gurin su tana cewa "Don Allah kar ku barshi ya tafi dani! Na rantse da Allah sato ni yayi ta k'arasa fad'a tana sakin kuna".
"Kunga abin da nake gaya muku? Aljannun ta ne wallahi haka sukeyi, kudai ku tafi na gode Isma'il ya k'arasa fad'a yana matsawa kusa ga Fatima".
Da sauri ta koma bayan su tana cewa "Don Allah kar ku bari ya tafi dani wlh sato ni yayi wiwiwi...Fatima ke kuka bakin k'arfin ta.
Abdul ne yace "to kai tace ba mijinta bane sato ta kayi?"?..
Wlh Yallab'ai na gaya muku Aljannu gareta, yanzu haka ba ita ce ke magana ba Aljannun ta ne.
Sauke numfashi Yusif yayi kafin yace, "gaskiya batayi kama da mai Aljannu ba! Saboda idan Aljannu ne taya zata tsaya nan tana ba'asi bayan kace mana gudu take yi"?
D'an sosa kai Isma'il keyi ya rasa ta cewa, Abdul ne yace "Am Yusuf why not muje ya kaimu gidan sa? Kaga yanda duniyar ta koma! "Idan ya kaimu muka tabbatar da matar sa ce kaga shike nan".... Ai ko kafin ya kulle bakin sa tuni Isma'il ya shige motar sa yana janta da mugun gudu.
Da kallon mamaki suka bisa, Yusif na cewa Abdul ka gani ko? Yanzu saboda Allah idan da ace mun tafi munbar wannan yarinyar da sai yaya?.
Hmmm! Kai dai bari Yusif yanzu kawai muje mu kaita assibiti ya ida fad'a yana maida duban sa izuwa Fatima had'e da cewa Sannu baiwar Allah! Tama kasa amsawa.
ganin halin da take ciki ya saka Abdul shigewa mota shidai Yusif kallon ta kawai yake yama kasa cewa k'ala, bayan mota ya bud'e mata ta shiga kafin ya koma mazau nin driver, yana shiga yaja mota da mugun gudu babu wanda yace da d'an uwan sa k'ala har suka isa assibiti wacce babu wani dogon nisa.
Koda yayi parking a Assibiti fitowa sukayi kafin su k'arasa ciki.
Saida aka cire mata kwolaben da suka sos-soke ta aka d'inke aka saka filasta, Gado likita ya bata domin saida aka saka mata k'arin ruwa!
Kwonce take bisa gadon majin-yata Idanun ta a bud'e suke amma Zuciyar ta na gida abu-buwa kawai take tunani kala-kala....Abdul ne ya dubi Yusif yana cewa yanzu ni zan tafi gida "Idan na dawo sai ta gaya muna gidan su, nasan zuwa lokacin ta k'ara far-fad'owa.
To kawai Yusif yace kafin Abdul ya fice...
Tunani Fatima ta shiga yi "yanzu idan na gaya musu gidan mu suka bincika aka gaya lusu halayyata kenan suma irin kallon da Isma'il kemin zasuyi min? Yanzu idan suka gayawa iyaye na ina assibiti haka zasu kama zargina tunda nasan ce musu zaiyi ga wani gardi suka kwoto ni?.....haka ta kama tunani kala-kala, Sallar magriba ce ta saka Yusif ficewa daga d'akin duk da magana kota yr-biyar bata had'asu ba!.
*09:23pm*
A tare Yusif da Abdul suka shigo d'akin d'auke da Sallama, ciki-ciki ta amsa.
Abdul ne ya ajiye ledojin dake hannun sa yana cewa Sannu da jiki?
Yauwa kawai Fatima tace tana duk'ar da kanta k'asa.
Yusif ne yace "to sai ta gaya mana gidan su saboda nasan duk yanda akayi hankalin su ba a kwonce yake ba" Abdul ne ya karb'e zancen da cewa takwon na mu bari taci abinci ko?
Ni na k'woshi bana jin yunwa, suka tsinci muryar Fatima duk da kallo suka bita kafin Yusif yace "Ke k'woshi fa? Eh....haka sunyi sunyi amma Fatima tace ba zata sha ko ruwa ba!.
To ki gaya muna Adress d'in gidan ku Yusif ya fad'a yana gyara zaman sa bisa kujera.
Kuka Fatima ta fashe dashi babu k'akk'au-tawa Abdul ne yace Lafiya na kuka daga tambaya?
Dole kuga nayi kuka saboda rayuwa ta cike take da k'alu-bale iri-iri kala-kala masifu wa'enda ba zasu misaltu ba.
Duk kallon sa sukeyi tausa-yinta na k'ara ratsa-su duk sun matsu suji labarin ta.
"da farko ni yr Abuja ce Allah ya yiwa iyaye na rasuwa tun inada shekara 10 sanadiyar hatsarin mota" "Rik'o na ya koma hannun Shi Yayan Baba na nan Abuja, tunda na shiga gidan kullum cikin masifa nike sun maida ni yr aiki wankin su, shara, wanke-wanke, girki komai nice sun hanani zuwa makaran ta, sun maida ni jaka😭😭😭😭 "kullum cikin tallah nike, shine naga masifar tayi yawa daga nan na yanke shawarar gudowa har Allah ya bani ikon shigowa nan Kano "shine na had'u da wannan mutumen da kuka k'woce ni a hannun sa.....Hmmmm... Yace zai taima ke nii daga nan ya kaini wani gida yana son yayi lalata dani!😢😢 daga nan na gudo ta window toilet har glass ya far-fashe min jiki ta Fad'i hakan tana nun-nuna jikin ta......
Cikin tausaya ko wannen su saida ya zubar mata da hawayen tausayi😢 domin labarin Fatima abin tausayi ne😭😭😭😭😭😰😥
*Wayyo Allah na* 😂😂😂 *Team Fatima yr Habuja*💃💃💃💃💃💃💃
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*Etc*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 17&18*
...............baiwar Allah sannu, kuma a gaskiya labarin ki abin tausayi ne Abdul ya fad'a yana duban Fatima.
Yusif kuwa yama kasa cewa komai illa kallon ta da yeke yi, kallon tausayi.
Abdul ne ya matsa mata da taci abin ci amma fa-fur tak'i kallon abin ci, ita wallahi "kaco-kan hankalin ta na gida!" yanzu tasan ta saka Inna mairi a wani hali “Kaico da wata Rayuwa”.
Yusif ne ya dubi Abdul yana masa alama da idanu da su fita, Fita sukayi nan bakin d'akin "shawara suke akan yanda zasu taima ke ta",
D'an jim Abdul yayi kafin ya dubi yusuf yana cewa "Yusif mezai hana mu kaita gidan Yaya Bashir ta kwona tunda kaga key d'in gidan a hannuna yake, yanzu idan muka kaita cen ta kwona gobe da safe a kaita ko gidan mu ko gidan ku", "yanzu dare yayi bazai yu mu kaita gidajen mu ba".
_("Yaya Bashir yayan Abdul ne anan gidan sa yake sedai baya gari shi da iyalin sa da yake banan yake aiki ba")_
To Abdul shikenan sai mu kaita cen d'in tunda likita yace muje mu karb'i takardar Sallama, yanzu kai sai kaje ka karb'o ni bari naje nace ta fito.
Okey, Abdul ya fad'a yana wucewa shi kuwa Yusif komawa yayi d'akin zama yayi bisa kujera yana jiran Abdul ya dawo.
Turo k'ofar d'akin akayi ana shigowa had'e da Sallama Fatima bata amsa sallamar ba illa yusif ne kawai ya amsa.
Wata nus ce sanye take cikin fararen kayan ma'aikatan jinya, "Excuse sir dama doctor ne yace nazo na k'ara dubata"!
"Okey no pro.
K'arasa nus d'in tayi kusa da Fatima Abin awo tasa tana k'ara duba lafiyar ta, saida ta k'arayi mata allura tayi haka ta tafi Fatima ta d'ago da kanta sosai d'an ja da bata tayi tana cewa “FAD'IMA”.
Da sauri Fatima ta noce kanta k'asa tayi kamar ma bataji abinda nus ke fad'a ba.
Yusif ne ya d'ago yana duban Fatima had'e da cewa ba dake ake ba?
Wah!..ni? A'a kam wlh bada ni take ba.
Nus d'in ce ta sake duban Fatima tana cewa "Shin ba Fatimar Malam bace? Gidan su Maman Fati"?.
A'a ba'ita bace, baiwar Allah gaskiya ni ban san ki ba! Wata-k'ila kama ce kawai kika ga muna yi amma ni bama a garin-nan nake ba.
Cike da Al'ajabi Nus tace "Amma kuna kama sosai...kunyi bala'in kama haka doctor ke fad'a tana juyowa tana kallon Fatima har ta fice daga d'akin..
Duban ta Yusif yayi sai dai bai kawo komai a ransa ba, ita kuwa Fatima sai ajiyar zuciya take yi tayi bala'in arziki da Karima bata gano ta ba.
_Bayan Minti Biyar_
Abdul ne ya shigo d'akin takar dar dake hannun sa ya mik'a-ma Yusif yana cewa ga takar dar sallamar sai ku tashi mu tafi.
Jikin Fatima yayi sauk'i sosai sai d'an abinda ba'a rasa ba, gaba suka sakata sai harabar assibitin Mota suka shiga Yusif najan motar sai Unguwar su Yaya Bashir.
A wani k'aton gida sukayi parking Koda suka shiga gidan baida wani datti sai d'an abinda ba'a rasa ba wani d'aki suka nunawa Fatima su kuwa Yusif anan Fallo suka zauna.
"Yusif Fatima ta bani tausayi matuk'a" inama da hali da na Aure ta.
Aure kuma? Yusif ya fad'a a matuk'ar hasale, Eh Yusif auren Fatima ko kana da matsala da hakan? Sosai Abdul nine da matsala da hakan Abdul ina jin tausayin Fatima matuk'a Abdul Fata *TSARINA CE* Fatima burina ce ina son na Aureta.
Mik'ewa Abdul yayi yana nuna Yusif had'e da cewa wlh Yusif baka isa ba de saita barmin Fatima domin ita d'in _TSARINA CE_ Son ta nake.
Kar muyi haka dakai Yusif kada mace ta shiga tsakanin mu ka hak'ura kawai ka barmin ita.
Cikin jin haushin Yusif Abdul yace, naji amma wlh ka gaggauta barin gidan nan da'ita yana ida fad'ar haka ya fice cikin tsananin b'acin rai hatta mota bai d'auka ba domin motar Yusif ce da k'afa ya fita sai da yakai bakin titi sannan ya salu abin hawa cikin minti 30 ya'isa tsararren gidan su wanda yayi matuk'ar had'uwa.
Yana shiga Main fallo na gidan da Momyn su yaci karo tsaye take sai safa da marwa take, tana shigo ta juyo tana wanke sa da mari.
Abdil baka da hankalu a'ina ka saka wayar ka babu kiran diyar da bamuyi maka ba, Mommy ta fad'a a matuk'ar firgice, shima Abdul d'in kallon ta yayi cikin tashin hankali da rikicewa "y lafiya? Me yake faruwa"? Babu abinda ya fad'o masa a rai tamkar Daddyn sa " Mommy ina Daddy?" ya fad'a yana zaro wayar sa koda ya duba wayar na silect ga missed call bila dadin, Mommy ta kasa ce masa komai domin hankalin ta bata ma san inda yake ba.
Ta bud'e baki da niyyar magana sukaji maganar doctor wanda ya fito daga d'akin da Daddy yake kwonce cikin halin ciwo, "Hajiya gaskiya ciwon Alhaji ya wuce sanina, zuciyar sa ta daina aiki kwota-kwota tayi kumburin da nan da a wani d'an lokaci zata iya Fashewa"... A firgice Abdul yayi d'akin mahaifin sa Alhaji Aliyu yana kwonce bisa gado gaba d'aya jikin sa wayoyi ne ga oxygen da aka saka masa, k'ara sawa yayi gaban gado yana kallon mahaifin sa wanda ke kwonce tamkar gawa, Mommy ce da Doctor sika biyo bayan sa.
Juyowa Alhaji yayi ga Doctor yana cewa "Doctor ya za'ayi? Don Allah ka taima ke ni bana son rasa mahaifina" Abdul ya k'arasa fad'a yana goge guntayen hawayen sa..
Eh, to a gaskiya sedai a fita dashi Egypt domin dune suke da kworarrun likitoci......
*Don't forget with share fisabililah albarcin manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*☺
```It's your 7......sauke numfashi Abdul yayi yana duban Doctor had'e da cewa, Doctor don Allah ayi duk yanda za'ayi a fitar da Daddy wake kafin wayewar safiya.
Hmmm! Doctor ya sauke numfashi yana cewa to akwai yanda za'ayi kawai mu nemi ticked ta Online, a wannan daren suka yi cuwa-cuwa sedai dirgin ba'a Kano zai tashi ba a lagos ne, inda zasu shiga jirgi i zuwa lagos d'in dashi Abdul d'in da Mommy da Doctor d'in wanda ya kasan ce Family Doctor d'in. "su kuwa Mommy wato Hajiya Maryam da Daddy Alhaji Muhammad, "Bashir ne d'ansu na farin sai Abdul sune kawai 'yryn su".
Cikin wannan daren suka wuce Airport sun kira shi Yaya Bashir yace su had'u a lagos d'in.
Saida aka tan-tance su,nan gurin tan-tancewar Abdul ya zaro wayar sa kenan ta fad'i take tayi ratsa-ratsa...."Subhanalah Abdul kanq aikin me? Mommy ta fad'a cikin jimami.
Wallah Mommy hankali na ne baya gurina ya fad'a yana d'aukar wayar, an gama tan-tancewar sun fito Abdul ya mik'ama Driver wayar had'e da cewa, Idi don Allah ka wuce da wayar akwai abu-buwa na masu muhimman ci, plss a gyaramin ita kafin mu dawo.
Mommy ce ta dubesa tana cewa haba Abdul idan ka bada wayar layukan ka fa? "Dame za'a kira Bashir"?
Mommy baga wayar ki ba akira Yayan da'ita, sannan ni idan mun isa zan siye layi da waya.
"Okey"
Da haka suka jira jirgin k'arfe 12:32am jirgin ya tashi izuwa Lagos.
_Allah ya sauke ku lafiya Abdul na Fati_
*B'ANGAREN YUSIF*
Abdul na fita daga Fallon saman kujera Yusif ya zauna yana fitar da wani huci, zuciyar sa na tafar-fasa "Kai bai dace ace wani abu ya had'ani da Abdul ba kuma wai mace"? Kay... !ya subhanallah ya fad'a yana dafe kansa cikin jin haushi kan sa, mik'ewa yayi da zummar shima yabar gidan har yakai k'ofar fita daga fallon sai kuma ya tuna ya zaiyi da wacce take gidan? Bazai yuwu ya tafi ya barta ita kad'ai ba!.
Komawa yayi bisa kujera ya zauna wayar sa ya jawo wata number ya kamo kafin ya fara rubuta text message yana gamawa ya kashe wayar.
_*GIDAN SU FADIMA_*
Bayan Isha'i itakam Inna mairi duk hankalin ta a tashe yake yanzu idan Maman Fati ta dawo me zata ce masa? Me zata ce da Malam? Kai Fatima ta saka ta a matsala...cikin zullumi tayi sallar magriba har ta kammala, hatta abinci ta kasa ci.
Tananan zaune filin gida inda ta kammala sallah bisa dar-duma.
AssalamuAlaikum Malam yayi sallama yana shigowa gidan.
Amin wa'alaika Salam, Malam barka da shigowa Inna mairi ta fad'a tana mik'ewa shimfid'ar Malam ta kawo masa kafin ta kawo masa abinci.
Ruwa kawai yasha kafin yace mata "Aisha bata dawo ba"? Cikin sauri Inna mairi tace Bata dawo ba tana Alla...allah kada Malam ya tambaya-yawa Fatima ita kam data shige su ai kuwa kamar tasan abin da yake ran malam sai tsintar muryan sa tayi yana cewa "to banji motsin Fad'ima ba, ko tana ciki"? Cikin in..ina da jin bak'in cikin maganar Inna Mairi tace Eh...ehhhh Malam tana ciki.
To, Malam ya fad'a yana k'wola kiran Fad'ima Fad'ima shuru Inna Mairi ce tace "Malam inaji fa ko ta kewaya".
Shidai Malam komai bai ce ba Saida ya gama cin abin ci sa.
Assalamu-Alaikum sannun ku da gida, kun ganni sai yanzu Maman Fati ta shigo gida da wannan maganar, gaba d'aya amsa sallamar tata sukayi, Inna mairi na cewa wallahi kuwa sai yanzu kin dawo lafiya? Ya cen gida?.
Wallahi Alhamdullh Maman Fati ta fad'a tana russunawa had'e da gaida Malam tana gaya masa iyayen ta na gaida sa.
D'aki Mama ta shiga minti biyar ta fito duban su tayi tana cewa "Wai ina Fadima"? Inna mairi ce tace Fadima ta kewaya, Malam kuwa duban Innar yayi yana cewa Makewayi kusan mintu 20?
Hmmm....uhmm Malam k'aryar ta ta k'are "maganar gaskiya maganar Allah Fadima bata gidan nan! "Kuma wallahi sai da nace kar ta fita karta fita Inna Mairi ta fad'a tana goge hawayen ta.
Innalilahi wa'inna ilaihin raji'um Mama ta fad'a tana dafe kanta cikin jin bak'in ciki, shidai Malam k'ala baice ba illa d'aki daya shige...
Itama Mama d'aki ta shige Inna mairi kawai aka bari a tsakar gida cikin jimami da tashin hankali..
*Don't forget with share fisabililah albarcin manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*☺
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*Etc*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 21&22*
*FATIMA*
..........Ko zama ta kasa abubuwa kawai ke bijirowa a zuciyar ta, ta k'udurta a ranta wallahi sai ta samu yanda tayi tabar gidan domin komawa gidan iyayen ta.
Taji lokacin da su Yusif na haya-niya sedai bata san ko akan liye ba domin hankalin ta baya kan su, d'an dafe kanta tayi da taji ya sara mata kafin ta sake lek'a kanta cikin Fallon bata hangi kowa ba bata hangi komai ba! Hmmm..! Alhamdullh Allqn na rok'e ka "ka fitar dani daga gidan.
Cikin taku a hankali ta sauko fallon gashi bata da takalmi amma ko'a jikin ta burin ta kawai ta ganta gida maybe ma takalmin tun inda Ism'il ya biyota suka fad'i.
Hanyar da tasan an biyo d'azun duk nan tabi, har ta samu fitowa daga cikin gidan, titi ta kama domin a wannan lokacin zan iya kwotan-ta lokaci da k'arfe 11:00pm haka fatima ke tafiya ko'ina tsit baka jin motsin komai gashi unguwar ba sanin ta tayi ba.
Haka take tafiya bata had'u da ko tsun-tsu ba har ta samu isowa bakin titi nan ma babu alamar mota zata wuce. Cikin gaji yawa ga ciwukan dake jikin ta har tayi nisa kafin ta hangi wani d'an adai-daita sahu shi ta tsayar babu wata_wata sunan unguwar su ta gaya masa.
Kusan mintu 32 kafin ya shiga cikin unguwar kwotan cen gida tayi masa sai k'ofar gida yana ajiyeta ta futo, duban sa tayi cikin langab'ar da kai tace don Allah bari na karb'o maka kud'in ka cikin gida tana k'arasa fad'a ta shige gida.
AssalamuAlaikum warahmatullahi ta'ala wa barakathu... Fatima tayi sallama tana tura kanta cikin gida.
Ba kowa sai Inna-Mairi wacce har yanzu tana nan zaune gurin nan ai kuwa jin sallamar Fatima ya sakata d'agowa da sauri kafin tayi kiran sunan ta "FA‘DIMA...!! Malam Yaya Shatu kuzo.....kuzi ga Fad'ima" ai kuwa bata gama rufe bakin ta ba a tattare Malam da Maman Fati suka fito kamar wa'en da aka kworo.
Sokwor-kwotai sukayi suna kallon Fatima kallon daya k'unshi abu-buwa marassa iyaka!
Duk'ar da kai Fatima tayi tana goge hawayen dake zuba daga idanun ta, tayi nadamar duk abubuwan da ta aikata, Mama ce tayi saurin k'arasawa inda Fatima take d'ago kan Fatima tayi kafin ta saka hannun ta tana sharara mata zazzafan mari wanda ta rink'a jera mata cikin hasala da takaici had'i da jin haushin ta.
Fadima na tsaneki Fad'ima bana sonki, Fad'ima bana k'aunar sake ganin ki tsakani na dake Allah ya'...
.Inna-Mairi ce tayi saurin rik'o Mama tana danne bakin ta...haba Yaya bai dace ba ki daina banda kawai muyi fatan Allah shirya, Malam ne ya k'ara so gurin yana duban Fatima had'e da rik'o hannun ta d'an baya yaja da'ita yana cewa Fad'ima meya same ki? Ya k'ara mata duban tausayi ganin dik jikin ta raunuka ga bandeji ga kanta da sauran gurare.
Wani irin kuka ne ya kufce mata bata ji ciwon marin da Mama tayi mata ba ko kad'an ita kawai Mama tayi hak'uri.
Fad'ima meya same ki?
Duban Malam tayi tana k'ara matse hawayen ta kafin tace "dama Malam gidan Hauwa'u zani dana samu abin hawa muna cikin tafiya garab mukayi kaura da wata mota.....uhml....wayyo Allah sai farkawa nayi na ganni kwonce a gadon assibiti duk jikina ciwo Fatima ta'ida fad'a tana nuna ciwukan jikinta.
Cike da tausaya wa Malam kamar ya zubar mata da k'wolla.
Ashsha Fad'ima sannu (Malam a ganin sa Mama tayi fushi da'ita shi kuwa idan suka taru suka d'auki zafi ya zatayi?).
Mairi je da Fad'ima ta huta Malam ya fad'a yana duban Inna-Mairi baiwar Allah jikin ta na mazari ta k'araso hannun Fatima taja sai d'akin ta.... Jin Sallamar da ake kwod'awa ya saka Malam ficewa daga gidan d'an sahu ne bayani yai ma Malam nan take ya cire kud'in sa ya basa..
Mama kuwa kwofa tayi tana shigewa d'akin ta cikin jin tsananin haushin fatima.
*_EGYPT_*
_Hospital_
Sai wayewar safiya suka samu isa Egypt directly assibiti suka wuce dama Doctor yayi magana dasu cen, suna zuwa aka tarbe su tiyatar gaggawa aka shiga da Daddy inda za'ayi masa aikin zuciya.
Abdul ya siye waya da layi koda ya fara amfani dashi wani abokin aikin sa ya kira ya turo masa numbobin mutane amma banda ta Yusif saboda tsananin haushin sa da yake ji, sai a lokacin ya samu sanarwa a gurin aikin sa sunyi masa uzuri sosai da sukayi addu'ar samun lafiya ga Mahaifin sa
Zaune suke suna jiran likitoci su fito Abdul, Mommy da Yaya bashir Mommy duk tabi ta d'auki duwa ta d'aura wa ranta ji take talkar su raba ciwon ko wannen su ya d'an-d'ana.
Mommy Yaya Bashir ya k'ara kiran sunan ta a karo na biyu wanda sai a sannan taji shi, Mommy refuse deduction anxiaties in your soul, InshaAllah Daddy zai samu sauki.
Hmmm...! Haba Bashir ai dole na sh...maganar ta ce ta mak'ale k'arasowan doctor zama yayi yana duban su kafin yayi magana yana cewa "Hajiya a yanda bayanai suka fito daga bakin likitoci Alhaji ya auna arziki, ya tsallake rijiya da baya!, "wato ciwon duk ya gama k'are rayuwar sa numfashi ne kawai ya rage masa".
Abdul ne yace "amma naga bayanan da wa'ennan Doctors suka bamu ya ban-ban ta dana saura, ko wacce assibiti abin da take gaya mana daban.! Duk ta silar hakan muka koma neman laganin gar-gajiya, a da ko numfashin da tsaiko yake fita sai da aka had'a da ayoyin ubangiji sannan abin yayi sauk'i.
*_B'ANGAREN YUSIF_*
.......*ASUBAR FARI*
Bai san lokacin da bacci ya d'auke sa ba nan fallon sai ring d'in wayar sa ne ya tayar dashi lokacin ana ta kirayen farko.
Duban Fuskar wayar yayi domin ganin wake kira *MY HAPPINESS*
cikin sauri yayi peaking yana karawa a kunnen sa, Assalamu-Alaiki Hajjah barka.
Amin wa'alaiki salam Yusif lafiya kuwa baka kwona a gida ba? Aka basa amsa daga cikin wayar, d'an jim Yusif yayi yana tunani ko kad'an baya son yayi ma Hajjah k'arya tsintar muryan sa tayi yana cewa Hajjah yanzu zan dawo kuma zan miki bayani abinda ya hanani dawowa gida.
To, Yusif sai ka dawo daga haka ta katse kiran.
D'an Jim Yusif yayi yana tunanin abubuwan da suka wanzu a daren jiya tsaka nin sa da Aminin sa, mik'ewa yayi da zummar yaje ya duba Fatima kafin ya wuce gida gurin Hajjah ya saka ma rqnsa zqije har gida ya baiwa Abdul hak'uri.
Koda ya shiga d'aki Wayam babu Fatima babu alamar ta.
Cikin firgici ya shiga toilet kai lungu da sak'o na gidan saida Yusif ya lek'a amma babu Fatima babu mafarin ta, firstly abinda zuciyar sa ta nasa masa Abdul.
Kayy...Abdul baka kyauta min ba Yusif ya fad'a yana dafe kansa da duka hannu biyu, taya zaka sace Fatima ka gudu da ita alhalin kasan *TSARINA CE* ina matuk'ar k'aunar Fatima ina sonta cikin takaici ya fice daga gidan yako tarar da motar sa shiga yayi yana figan ta da mugun gudu, ikon Allah ne kawai ya kawo sa gida koda ya shiga gidan bai bi ta kan kowa ba sha-shen daya kasance mallakin sa cen ya nufa da kyar ya samu yayi wanka had'i da alwala kafin ya wuce masjid, koda ya dawo bai koma cikin gida ba mota ya shiga yana ja ya nufi unguwar su Abdul..
Gateman ne ya tarbesa cikin matuk'ar sani suka gaisa cikin mutimci.
Am yallab'ai halan kazo d'aukar wani abin ne? Gateman ya tambayi Yusif yana d'an dud-duk'ar da kai alamun girmama-wa, cike da mamaki Yusif ya dube sa yana cewa "dama gurin Abdul nazo".
Au yallab'ai k'ila ba'a samu gaya maka ba da yake saurin da suke, ai su Alhaji kam tun jiya suka bar wannan Jihar zasuje cen Ikeja su had'u da Alhajin cen daga nan su d'un-guma zuwa k'asashen masu jajjayen kunne Gateman ya ida fad'a yana share hawayen sa cikin jimami.
Yusif bai k'ara cewa komai ba illa komawa da yayi cikin mota sai faman kiran Abdul yake amma a kashe..
"Kenan Abdul ya d'auke Fatima kwota-kwota daga wannan k'asar? Kenan bayan bacci yayi awon gaba da ni dawowa yayi cikin gidan?... " haka Yusif ya ka tambayar kansa da kansa yana jin tsanar Abdul na tasiri a zuciyar sa.....
*Don't forget with share fisabililah albarcin manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*Etc*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 23&24*
..........Cikin haka Yusif ya koma gida yana shiga b'angaren Hajja ya wuce seda ya dai-dai ta nutsuwar sa kafin ya shiga fallo da sallama d'auke a bakin sa.
Ba kowa a fallon ko'ina tsaf-tsaf gwonin birgewa ga wani dadda d'an k'amshi wanda ya game da sanyin A.c yayi kamar ya koma har ya juya yaji an kira sunan sa Yusif.
Juyowa yayi kafin ya duk'ar da kansa yana cewa Hajja barka da safiya, wannan matar mai far'a da kamala murmushi tayi tana cewa lafiya Alhamdullh ka zauna ta fad'a tana nuna masa d'aya daga cikin kujerun da suka k'ara k'awata fallon, ba tare da gardama ba ya zauna....
*Waye Yusif?*
"Alhaji Ahmad wanba haifaffen garin Adamawa ne fullanin asali gaba da baya, su biyu ne iyayen su suka haifa daga shi Ahmad shine babba sai Ibrahim, sunyi karatu boko dana Allo".
Karatu ne yayi silar dawowar Ahmad kano a bayero university inda ya karanci business administration anan Jami'ar ya had'u da Hajara ba department d'insu d'aya ba ita aikin jarida take karanta, zazzafar soyayya ce ta b'ullu tsakanin su ba'a samu matsala ta ko wanne fanni ba da yake ita Hajara ita kad'ai iyayen ta suka haifa kuma duk 'yn asalin kano ne mahaifin ta tsohon soja ne shima Ahmad iyayen sa sunyi na'am seda ko wannen su ya kammala karatun sa kafin aka sha biki na gani na fad'a.
"Iyeyen Ahmad sun basa dukiya mai yawa inda ya dawo kano da sana'a ya samu aiki a wani kamfani amma yak'i yin aiki da su, "shi da wani abokin sa mai suna Mustafa suka yi had'in gwuiwa suka gina kamfanin kansu da kansu wanda suke saro kaya daga k'ashashen k'etare suna shigowa dasu gida nigeria dafa haka cikin k'udurar ubangiji hanyoyin arziki sai bud'e musu suke".
"zaman Ahmad da Hajara abin gwonin birgewa tsan-tsar soyayya ce suke nunawa juna cike da tsafta, "gidan da suke zaune mahaifinta ne ya mallaka musu shi" daga nan Ahmad wanda ya koma Alhaji Ahmad a lokacin yayi shawara dawo da k'anen sa Ibrahim inda ya d'ora sa a harkar kasuwan ci.
Shima Mustafa yayi aure amma shi ba yr garin ba ce ye Gombe shekara mai suna Halima sun k'ula zumunci da Hajara ba na wasa ba, har Halima ta haihu Allah bai baiwa Hajara ko ciki ba, Halima ta haihu ta samu d'a namiji inda aka saka masa suna Bashir sai da yayi shekara Biyar kafin Hajiya Halima wato Mommy ta sake samun ciki, cikin Tsananin mamaki sai ga Hajara wato Hajjah da ciki kusan zan iya cewa xikin sati d'aya suka haihu ko wacce su yr mace ba'ayi biki ba yr Mommy ta koma, Anyi biki lafiya d'iyar Hajjah taci suna Maryam sai lokacin Ibrahim k'aneb Alhaji Ahmad yayi aure bayan ua zaunu cikin kasuwan ci a cen Yola ya koma domin iyayen da basa tare da kowa sedai yana shigowa kano akai-akai.
Maryam nada shekaru uku kusan lokaci d'aya su Hajjah suka koma samun ciki sedai dukkanin su a lokaci d'aya suka haihu kuma duk d'iya maza ansha Shagalin biki sosai ba kad'an ba Inda aka sama d'an Mommy Abdul-Alimu ita kuwa Hajjah aka sakama d'an ta Yusif daga lokacin babu wacce Allah ya sake baiwa ciki.
Duk da gidajen su ba guri d'aya suke ba amma babu nisa haka suke rayuwa cikin kulawa da soyayyar juna Bayan sun girma aka aurawa Bashir Maryam cikin farin-ciki da k'aunar juna har aiki ya maida sa Lagos.
Yusif da Abdul makaran ta d'aya sukayi daga primary har secondry har abada suna tare babu wanda ya tab'a jin kansu dedai da minti d'aya, anan gida Nigeria suka had'a degree su na farko inda ana biyun suka tsallake izuwa K'asar U.K ko wannen su abin da yake karan ta daban shi Yusif yana karantan Aikin likitan ci ta fannin brain shi kuwa Abdul yana karantar Aikin Jami'in sirri, yanzu shekarun su Biyu da kammala karatu Abdul ya fara aiki tun tuni, shi kuwa Yusif yak'i fara aiki har yanzu wai bai shirya ba haka rayuwa ta kasance.
Alhaji Mustafa wato Daddy dama cen yanada ciwon heart mai bala'in tsanani idan ya tashi kwonan sa ne kawai gaba har de yanzu abin yayi nisa an zauna assibiti har aka dawo da jinyar gida..
_*Wannan shine tak'aitatcen labarin wa'ennan abokai guda biyu wato Yusif da Abdul-Alimu*_
*Back to story*
Yusif ka zauna mana Hajjah ta sake mai-maitawa tana k'ara nuna ma Yusif bisa kujera Hmmm...! Yusif ya sauke numfashi yana zama bisa kujerar da Hajjah ta nuna masa, itama Hajjah kujerar dake facing d'in sa ta zauna kafin tace Inaji Yusif gayamin meya hanaka kwona gida?
Gyara zaman sa Yayi kafin yace Hajjah dare ne yayi wlh ban san sanda bacci ya d'aukeni ba gurin Abdul.
Abdul..Abdul? Hajjah ta sake mai-maitawa kafin tace shi Abdul d'in da jiya basu kwona a wannan jihar ba?? Yusif baka saba yimin k'arya ba saboda haka kada ka fara.
"To kenan Hajjah sun samu labarin tafiyar su Daddy"? Yusif yayi tambayar a cikin ransa kafin ya dubi Hajjah cikin sanyin murya yace " Hajjah dama jiya ni da Abdul munje gidan su Yaya Bashir muka samu misunderstanding daga nan yayi fushi ya tafi shine nima ban samu dawowa ba har bacci yayi awon gaba da ni.
Hmmm...! Dama nasan a rina yanzu fisabililahi Yusif shi Abdul d'in zakuyi fad'a? Yanzu har akwai abin da ya'isa ya shiga tsakanin ku? Har ciwon Alhaji ya tashi a tafi dashi assibiti a fitar da shi daga wannan k'asar baka da labari? Lallai baku da hankali hmm.!
Hajjah don Allah kiyi hak'uri, "Ina Alhaji"?.
Sauke numfashi Hajjah tayi kafin tace "ai Alhaji bai jima da fita ba shima zaibi bayan su Abdul ne, kaima saika k'ok'arta ziwa gobe muje".
Okey, kawai Yusif yace had'e da mik'ewa yana ficewa daga fallon.
*B'ANGAREN FATIMA*
A cen d'akin Inna-Mairi ko bacci da kyar ta iya yinsa, koda aafiya ta waye kasa fitowa waje tayi hatta Sallah ta kasa saboda yanda ta samu raunuka.
Saida aka sake kaita assibiti kafin suka dawo, tananan zugum ga yunwar dake addabar ta amma ta kasa cin abinci! Har da Malam yayi mata magana amma tace bataci, anyi anyi gashi ita d'in ma yunwa take ji sosai.
Don Allah Yaya Shatu ki saka bakin ki ko Fad'ima zataci abinci, gashi likita yace a tabbatar taci abinci kafin a bata magani, harda Malam yayi-yayi tak'i ci shine don Allah kiyu magana ko ke zata aminta da zancen ki taci.
Hmmm..! D'an duban Inna-Mairi Mama tayi kafin tace Kesan Allah? Wallahi Mairi in don ta tawa ce kada Allah yasa taci abinci, kan wa? Kanta din babu wanda lafiyar ta da rashin lafiyar ya shafa, tunda mu in lafiyar ce da'ita ba shafar mu tayi ba.
Haba Yaya a daina duk wani tone-tone nidai saboda Allah na rok'eki muje a lallab'a Fad'ima ta samu taci abinci kinji Yaya.
Akwai tsagoron ganin girma a tsakanin su, Mama bata son wani ja-in-ja na shiga tsakanin su da Inna-Mairi hakan ya sakata mik'ewa.
A tare suka shiga d'akin Inna-Mairi, Fatima tana nan zaune a gefen gado tayi tagumi cikin yanayin tausayawa, harar ta Mama tayi cikin jin haushi tana d'auke fuskar ta daga kallon ta..
*Don't forget with share fisabililah albarcin manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*Etc*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 25&26*
......Inna-Mairi ce ta d'auko abincin tana ajiyewa kusa da Fatima, "Mama ce ta matso gaban Fatima ji take kamar ta k'ara mata wani haushin ko zataji sauk'i ita a zuciyarta".
Ke, Fad'ima ki d'auki abincin nan kici kuma dole ne domin ba zaki mutum muna muse ba.. Gaba d'aya daga Inna-Mairi har Fatima d'agowa sukayi suna duban Mama duba na mamaki ita kuwa Mama sai faman hararan Fad'ima take.
Salun-alun Fatima ta jawo abincin tana fara ci kwofa Mama tayi tate da ficewa daga d'akin.
"Don Allah Fad'ima kiyi hak'uri, kesan iyaye ahankali ake binsu" Inna-Mairi ta fad'a cikin lallami kafin ta zauna gefen ta.
Hmmmm..! Kada ki damu Inna ba komai Fatima ta fad'a tana share guntayen hawayen ta, cusa abincin taci gaba dayi duk da ba wani jin dad'insa takeji ba.
Saida ta kammala cin abinci kafin tasha magani..
Haka Fatima taci gaba da jinya duk da kwona biyu Mama ta d'an rage tamke mata fuska.
*EGYPT*
*B'AMGAREN ABDUL*
"Sai kusan la'asar kafin aka fito da Daddy daga theater room" an samu nasarar aikin "dai-dai lokacin da aka fito dashi dai-dai sanda Alhaji Ahmad (babban Yusif) ya k'araso".
"D’akin hutu aka shigar da Daddy, likitoci sunce kada a dame sa da hayaniya "shiyassa Mommy kawai aka bari! Gaba d'ayan su masauki suka nufa.
*BAYAN SATI BIYU*
_B'ANGAREN YUSIF_
duk cikin wa'ennan kwonakin ya kasa sukuni "kullum cikin tunanin Fad'ima yake"
"da'ita yake kwona da'ita yake tashi", "Hajjah tayi-tayi suje Egypt dubo jikin Daddy sai-dai yace mata baida lokaci ko kuma yace baida lafiya, har ta gaji bayan Alhaji yayi sati d'aya ya dawo sukaje tare yanzu haka suna cen Yusif d'inne kawai a gida".
"Karo na biyu yanajin Ring d'in wayar amma ya kasa d'auka har ya gaji ya tsinke", sake kira akayi Mtwss yayi tsaki ciki ciki kafin ya mik'a hannu yana jawo wayar dake bisa bedside drower da sauri ta tashi zaune ganin mai kiran *MY HAPPINESS*.
Cikin sauri yayi peaking yana karawa a kunnen sa "Assalamu-Alaikum" "Hajjah barka da rana, Ina wuni".
Lafiya k'alau Yusif "ya zaman kad'aici"?
Hmmm... "ina kewar ku Hajjah".
"Ya jikin Daddy"?
Yaushe zaku dawo?.
"Jikin Alhaji yayi sauk'i fiye ma da yanda muke tsammani domin kwonan-nan za'a sallame su" mu kuwa gode in Allah ya yarda zamu dawo.
To yayi Hajjah dama ina so na miki wata tambaya please.
Okey, ina jinka.
"Hajjah dama tambayar itace “shin tun lokacin da kukaje ke lura da Abdul”?.
Cikin mamaki daga cikin wayar Hajja tace Lura kuma Yusif? Kamar me fa? “am Hajjah kamar dai shin yana yawan fita ko kuma dai kunajin yana waya? Sannan a'ina yake kwona? Ko kun tab'a jin yana wasu zantuka haka.!
Zaro ido Hajjah tayi kamar yana ganin ta kafin tace “kai Yusif”! Wallahi kaji tsoron Allah ai ba saka masa ido ya kawo mu ba, sai kace wanda kake zargi wa'ennan tambayoyin haka?, Nidai kawai kayi niyya tunda nasan yanzu kaji sauk'i ka samu kazo "kaga fa harda Yayarku nan muke tare da'ita".
To, Hajjah sai anjima ki gaida Alhaji da Mommy da Anty Maryam ina yiwa Daddy ya jiki.... Yana kaiwa yana yayi saurin katse kiran yana sauke ajiyar zuciya domin yasa yanzu Hajjah zata kama yi masa wasu tambayoyi tsakanin sa da Abdul.
*FATIMA*
...cire hijabin dake jikinta tayi tana sarkafe shi ga igiya kafin tace "Wash Allahna" Mama na gaji ta k'arasa fad'a tana duban mama dake zaune bisa tabarma tana k'womdar magi".
D'agowa Mama tayi had'e da dubanta kafin tace "Ya jikin Tsohuwar"? A d'an shagwob'e Fayima ke cewa Mama bama zaki bari na huta ba? Kin cikani da tambayar jikin Tsohuwa...Tsohuwa dai Tsohuwa ni na rasa sanin wane irin so kike yima wannan kingin gawa?.
Uwarki nace! Rufamin baki zoki kasheta idan ke ke da ranta, marar mutumci sokuwa yanda kike son taki uwar nima haka nike son tawa.
D'an tab'e baki Fatima tayi tana cewa "yanzu Mama daga magana"? Ni ai tawa uwar ba tsohon babur bace daya gama rauyuwa Fatima na kaiwa nan ta shige d'aki da sauri, kwofa Mama tayi tana cewa zaki fito ki sameni, kada Allah yasa ki gayamin ai zanje da kaina na dubo ta.
Inna-Mairi ce ta fito daga d'akinta "duban Mama tayi tana cewa Yaya keda wa? Kaddai har Fad'ima ta dawo"?
"Nida ita ne Mairi, ta dawo mana" “ai tinda gidan mu ne Fad'ima sai kace cikin wuta take idan taje" kiji fa yanzu kwota-kwota bata fi awa d'aya da mintina ba amma gata ta dawo".
"Haba Yaya ai Fad'imar da kika sani da ba'ita bace", "yanzu ta sauya kiji fa kwota-kwota Fad'ima bata k'aunar zuwa ko da k'ofar gida" “ai sedai muce Alhamdullh Fad'ima kam”.
Hmmm... To Mairi Allah yasa ta nare.
“Amin Yaya”
*B'ANGAREN ABDUL*
"Shikam ya damu ganin ganin Yusif ya saka sa a kwondon mantuwa" “yayi shuru ne kawai, amma zuciyar sa fal mamakin Yusif "wai akan mace"? Ganin har Alhaji yazo Har ya koma ya dawo tare da Hajjah amma babu alamar Yusif, "shikam yaga ishara domin koda ance masa Yusif zai iya rabuwa dashi bazai yarda ba".
Zaune yake bisa sallaya a inda ya kammala Sallah nan cikin masaukin su, jinginawa yayi gefen bed kafin yaci gaba da addu'o'i na rok'awa Daddy lafiya da dai sauran su, “Ya ubangiji Allah na rok'eka ka kore shed'an tsakanina da aboki na”.... Yana shafa addu'ar wani tunani ne ya fad'o masa wayar sa dake gefen sa ya d'auko contact ya shiga yana darling number Yusif amma har ta kammala ring ba'a d'auka ba kira uku sai a na hud'u akayi peaking.
Ko sallama Abdul bai tsaya yi ba “Yusif ho? Sannu...wallahi kaban mugun mamaki saboda ban tab'a tsammanin akwai abinda zai shiga tsakanin mu ba”? "Wai kuma mace wacce daga ni har kai babu wanda yasan ta", "amma babu komai rayuwa ce".
Wait Abdul nifa ka kyaleni amma ai kasan komai ya faru laifin ka ne “taya zakamin zagon k'asa"? Kasan yarinyar nan sonta nake amma har ka'iya sace ta ka tafi wani gun da'ita wallahi kaban mugun mamaki".
Zaro ido Yusif yayi acen b'angaren kafin ya iya futa " me kake nufi Yusif? Ko so kake kace min zargina kake da sace Fatima"? Amma kayi kuskure domin ni ba haka nike ba “wallahi Yusif koda ace macen da mukayi shekaru muna soyayya ranar da za'a d'aura muna aure kace kana sonta to zan iya bar maka, kuma ko'a waccen ranar sharrin zuciya na biye, shine ina mai baka hak'uri d'an uwana Abdul ya k'arashe cikin sanyin murya..
"Don Allh nima Abdul ka gafarceni wallahi nima son zuciya na biyewa har muka b'ata dakai amma inshaAllh komai zai koma dedai", sannan koda safiya ta waye na nemi Fatima sama da k'asa na rasa saboda haka nima na hak'ura kaji abokina".
"Yusif A'a tunda kana sonta ni Abdul nayi maka Alk'awari" “a duk ranar da muka dawo saina nemo maka ita”..
*Don't forget with share fisabililah don manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*Etc*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 27&28*
_Bayan kwona 2_
___________An sallamo su Abdul daga Assibiti sai a kashe gari suka dawo gida.!
“Cewa kawai sukayi Yusif yayi zaman sa kawai basai yaje k'asar ba, shine ya d'auko su daga Airport direct gidan Alhaji Almustafa suka nufa Daddy yaji sauk'i fiye da misali sai d'an abinda ba'a rasa ba.!
"Zaune suke a harabar gidan su Yusif d'an tattaunawa sukeyi akan abubuwa masu yawa".
_*FATIMA*_
_Bismillahi-Arrahman-Arrahim_
_Alhamdullilahi lazih khalak'al'samawatiy wal ardah waja'alal zulumatin wal nuwrra summah lazinah kafaru bi rabbihim ya'adiluna_
"Hmmmmm..! Fad'ima ana dai nan ana karatun?, ubangiji ya k'ara shiryawa" shigowar Maman Fati kenan tana fad'ar wa'ennan zantuttukan ganin Fatima zaune tana karatun Alk'ur'ani mai girma.
Zama Mama tayi tana kafe Fatima da kallo "saida ta kammala shafin farko na suratul An'am tana kai aya ta rufe k'ur'anin had'i da ajiye shi gefe.
"Mama sannu".
“Yawwa Fad'imatun Mama”Fatiti bintu rasullulah Fad'imatu zahra'u batulah Fati kana zabuwar mata, Fati fatar kud'i kud'in kashi ba kud'in ajiya ba.... Sai kwosar dariya Fatima keyi najin kirarin da Mama keyi mata.
Mama duk ni kad'ai?
"Eh Fad'iman Malam ai kema fi hakan, yanzu ki shirya zan aikeki nan bayan layi gidan Inno"... Kay Mama nifa kin san bana son zuwa gidan su Inno? Amma shikenan tunda kece bari kawai naje. Yawwa Fad'ima yi sauri ki shirya.....
*04:32*
"Rana ta fara sauka, tafiya take taga ta koma gida duk da babu wani nisa tsakanin unguwar su da ta su Inno, Sai faman zuba sauri take ga tafiyar k'asa ga rana"....
Slow yake tuk'i ya durfafi wata kwona, Wayar sa ce tayi ring saide shi baya son d'aukar waya arhalin yana drivin, tunani yake a zuciyar sa ““ko ina ne gidan malamin”? Yana d'ago da idanun sa saikin glass “What.... Ya fad'a yana jan birki da k'arfi domin yayi matuk'ar firgita da abinda ya gani, FATIMA ya kira sunan cikin Al'ajabi kamar k'eftawar ido ya nemeta ya rasa, Shifa tabbas yaga Fatima amma yanzu bai ganta ba.... Da sauri ya jawo wayar sa missed calls ya gani kuma duk na Yusif darling d'in number yayi harta katse ba ayi peaking ba, sake kira yayi nan kuwa saida ta kusa katsewa akayi peaking.
“Hello, Yusif kana ina?” " wallahi yanzu naga Fatima ko kamin na ankara na nemeta na rasa"..
What shine baka kirani ba? A ina? Pls turomin adress d'in gurin yanzu ganinan tafe.
Okey, Abdul ya katse wayar cikin mintina ya turawa Yusif adress ba'a d'auki wani lokaci mai tsayi ba ga Yusif.....
Abdul A'ina ka ganta? Yusif ya fad'a yana rik'o hannun Abdul.
Nuni yayi masa, amma babu alamun giftawar ko tsuntsu “saida suka shiga zagaye unguwar amma babu Fatima sama ko k'asa, sunyi yawon nema har akayi magriba, nan massalacin unguwar suka tsaya sukayi sallah.!
“Yusif yanzu saika rakani gurin Mallamin da zani, za'a karb'owa Daddy rubutu”.
Hmmmm....! Yusif ya sauke numfashi yana cewa “A gaskiya Abdul bazan iya ba” ni gida zani wallahi duk jikina ya mutu, banajin zan iya doguwar magana kawai sai gobe zan shigo.
Okey,,,, haka sukayi sallama Yusif na komawa gida.
*FATIMA*
Da sallama ta k'arasa gida Mama da Inna duk suna tsakar gida amsawa sukayi Mama na cewa Fatima har kin dawo?.
Ehh Inna Fatima ta fad'a tana zama gefen tabarmar da Inna ke zaune.
“Mama na dawo Inno na gaida ki, sannan tace a gaya miki kiyi k'ok'ari zuwa gobe ki dibo Innarku ko bata da lafiya”? Tadai ce kije.
Na shige su, Allah na gode ma, kaddai ace ciwon tsohuwa ya tashi? Tab'e baki Fatima tayi tana cewa “to nidai Mama tace kidai yi k'ok'ari ki dubota.
Inna ce ta dubi Mama tana cewa "Allah yasa da sauk'i Yaya, idan Malam ya shigo sai muje dubota..
*YUSIF*
Yana k'arasawa gidan gateman ya bud'e masa gate a harabar gidan yayi parking yana fitowa sai main fallo, ba kowa a ciki Upstairs ya haye sai room d'in Hajjah, knocking izinin shiga ta basa tura k'ofar yayi yana shiga cikin d'akin.
Hajjah barka?
Barka dai Yusif ya ayyuka?
Alhamdullh. Ina Alhajin?
Yana gidan Daddy.
Okey, mik'ewa yayi da zimmar komawa ““Yusif ka zauna zamuyi magana.
Okey Hajja ina jinki.
"Yusif ya kamata ace ka fara aiki yanzu, Yusif ga Abdul nan yana aiki kaima yaci ace ka fara aiki yanzu, kuma ga maganar aurenka da Balkisu, kasan magabar nanan ta kwonta ne kawai? Wallahi Yusif ka maida hankali in mune yau gobe bamu bane, ka tsaya da k'afafun ka.
Hajjah i will adjust, barely you defers me.
“Yusif har tsawon wane lokaci?”
Hm..., kedai Hajjah.
Okey, Allah ya taimaka.
Amin Yusif ya amsa yana ficewa daga d'akin...
*Don't forget with share fisabililah don manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*E.t.c*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 29&30*
............. Bayan Magriba Malam ya shigo gida, su Mama sun masa maganar zuwa dubo tsohuwa ya yarje musu da suje.
"koda su Mama sukaje baiwar Allah tsohuwa jikinta tayi tsanani sosai ko magana batayi sai kallon mutane, Mama ta tarar da yayunta wa'enda ba garin suke ba, Duk sunyi zugum ance a kaita assibiti tace ko alama itakam, anyi anyi tak'i yarda a kaita assibiti, sai wuraren 10 na dare sannan wani yayan Mama yace su ta tashi su koma gida duk abinda ya faru zai kirata a waya.
Haka suka dawo gida ba tare da Mama taso hakan a ranta ba.
Kwonan zullumi shine za'a kira da wannan daren ga Mama hatta bacci ta kasa, seda Malam yace aida ta kwona da yafi kwonan zullumin da zatayi.
Ta kasa Bacci tana ganin dare yayi mata wani irin tsawo sai guraren 2 na dare bacci yayi nasarar saceta...
“Taron jama'a ne bila adadin cikin gida waje, maza mata matasa sai faman koke-koke suke hatta k'ananam yara sai faman rusar kuka suke Mamace ta iso de-dai k'ofar gidan nasu, hankalinta a matuk'ar tashe sai faman bin mutane take tana "lafiya? Kukuku ku gayamin me kukewa kuka" duk wa'ennan zantukan babu wanda ya tamka mata, cikin gida ta k'arasa Nan duk jama'a ne Suma magana ta fara musu tana cewa “me kuke ma kuka? Kuuyi shuru ku gayamin in tayaku” saidai shuru wani taron jam'a ta gani daga gefen d'akin tsohuwa cen ta nufa abinda ta gani ne yayi silar tashin hankalin da yayi sanadiyyar farkawarta daga baccci kalmar shahada bata gushe daga bakinta.
Sharce zufar data karyo mata tayi tana duban yanda jikinta ke kakkarwa zuciyarta na bugawa da k'arfi dubanta ta mayar dai-dai tamgamemen agogon dake d'akin k'arfe 05:13am dafe goshinta tayi da hannunta.
A ranta kuwa sai nanata "Innalilahi wa'inna ilaihin raji'um" take, motsinta ne yayi silar farkar da Fatima a firgice Fatima ta dubi mama tana ce "Subhanallah Mama! Lafiya? Mama meya sameki?".
Hmmm..! Saida Mama ta sauke zazzafar numfashi kafin ta d'ago tana duban Fatima had'e da cewa " Fatima mafarki nayi naje gida anata koke-koke kowa na tambaya sai yayi banza dani daga nan na wuce ciki nan na tarrae su Yaya k'ofar d'akin Inna kesan mena gani?
Girgiza kai Fatima tayi alamar A'a.
Fad'ima D'anyen nama naga sunata rabo yayi jajawur, a firgice Fatima ta dafa k'irji tana cewa subhanallah Mamma kaddai Tsohuwa ta rasu.?
Dafe kai Mama ta koma yi tana nanata Innalilahi wa'inna ilaihin raji'um. Innalilahi wa'inna ilaihin raji'um, Subhanallah! Hasbunallahu wani'imar waki, la'ila fa'illah anta'subhanaka inni kumtu minar zaliminah.... Addu'o'i sun kasa barin zuciyar Ma harta samu nutsuwa jin ana kiraye kirayen Sallah ya sakata mik'ewa Alwala ta d'auro tana shigowa duban Fatima tayi tana cewa kema saiki d'auro alwala zama tayi tana jan charbi har akayi tada sallah tabi jam'i....
Bayan sallar Asuba rana ta b'ullo, Mama tana jiran Mallam ya shigo gashi ko break fast ta kasa Duk jikinta a mace, tananan zaune akan k'wofa bisa kujera yr tsugunno.
AssalamuAlaikum Malam yayi sallama yana shigowa cikin wani yanayi, Mama ce ta amsa sallamar tana d'agowa.
Duban Maman yayi yana cewa "Aisha ki shirya kuje gida ance jikin tsohuwa ya tashi", A firgice Mama ta d'ago tana danne zuciyarta dake barazanar tarwatsewa "Malam kawai ka gayamin gaskiya nasan Inna ta rasu" ta fad'a tana goge hawayen dake k'ok'arin zubo mata, Inna mairi ce ta fito daga d'akin tana yiwa Malam barka da shigowa amsawa yayi yana dubanta had'e da cewa “Mairi ku shirya da Aisha kuje chen gidan su" itama cikin tsinkewar zuciya ta maida kallonta ga Mama tana cewa "Yaya, Yaya lafiya? Yaya meya faru"? "Mairi nima ban sani ba Kawai Malam yace in shirya zamuje gida".
"To Yaya ubangiji yasa mu riski alkhairi tashi ki shirya"
Haka Mama ta tashi cikin mutuwar jiki dakyar ta shirya ko wanka ta kasa tare suka fito da Inna Mairi Fatima kam nadai duban ikon Allah, Malam ne yace su tafi zai biyo bayan su, da sassarfa suke tafiya babu wani nisa tsakanin gidajen su..
"Innalilahi wa'inna ilaihin raji'um" Mama ta fad'a ganin jama'ar dake k'ofar gidan, da Inno sukaci karo wacce k'ok'arin fita ta saka kyalle ta rufe fuskarta.
"Inno, Inno lafiya"? Mama ta tambayeta tana jawota k'ok'arin rik'e kukanta Inno keyi amma ina cikin kuka ta fara magana "Yaya Shatu Inna ta rasu" Innalilahi wa'inna ilaihin raji'um kawai suke nanatawa haka suka k'arasa ciki ga gawar tsohuwa nan har an mata wanka an suturtata Sallah kawai ya rage a kaita hidan gaskiya (Ubangiji yasa mu cika da imani) Saida Malam ya k'araso anka yiwa Inna tsohuwa Sallah aka kaita gidan gaskiya dama mahaifin su ya jima da rasuwa(Allah ya gafarta Inna tsohuwa).
*FATIMA*
Duk kewar gida ta dameta ko'ina shuru tayi dannar waya har ta gaji tananan zaune akayi sallama fitowa tayi daga d'akin cikin tsananin mamaki ta rumgume Jidda tana cewa "Jidda yau kece a gidanmu"?
Murmushi wacce aka kira da Jidda tayi tana cewa "wallahi kuwa nice Fatima ya gida? "
Lafiya k'alau Fatima ta fad'a tana janta i zuwa uwar d'aka.
"Jidda na rasa contact d'inki gashi ban samu zuwa gidan Umma ba, na tambayi Salma Sa'id tace cemin ai bakya gari kina abuja kina shagalinki, nama ji ance kin jona university"? Fatima ta k'arasa fad'a cikin siggar tambaya.
Hmmm...! Jidda ta sauke numfashi tana cewa "Eh Fatima na jona university shekaranjiya nazo gida auren Anty Ummu ya maidoni, shine nace bari yau nazo gidan ku".
"Ayya Jidda nako gode gashi ke tarar dani ni kad'ai a gida, Maman basana tana gida daga ita har Inna mairi", "to Ubangiji ya maidasu lafiya, kinga wallahi kada kice ban gayamiki auren Antyn ba dama na kawo miki katin dinner don Allah kiyi k'ok'ari kije kesan dai Anty Ummu"
D'an jim Fatima tayi kafin ta dubi Jidda tana cewa "Jidda yaushe"?
"Yau da k'arfe 09:00pm"
A nata b'angaren gaskiya ba zata ita aikata hakan ga Jidda ba saidai tana tunanin yanda zata kasance dafata d'in da Jidda tayi yayi silar d'agowarta a firgice "Na'am Jidda zanje Fatima ta fad'a tana karb'an katin mik'ewa Jidda tayi da niyyar tafiya sai kuma ta tsaya tana juyowa ga Fatima "Teemerh kada ki manta da wani abu"
"Me"?
Da baya dawo tana saita bakinta dai-dai kunnen Fatima had'e da mata rad'a wacce ni ban samu jiyo ko menene ba.
"kai Jidda" Fatima ta fad'a tana kaucewa da sauri Jidda ta fice tana yiwa Fatima bye"
Zugum Fatima tayi tana tunani ta nanata kalmar da nidda ta gayamata ba adadi wai naje da saurayi? Kai inahhhhh....
*YUSIF*
".... Yusif.. Yusif" Abdul ya k'ara kiran sunan sa a karo na ba iyaka wanda yayi silar d'agowar sa a firgicd yana duban Abdul.
Dafasa yayi yana cewa "Friend lafiya meya sameka? Kodai duk tunanin Fatima ne"?
D'agowa Yusif yayi yana kallon sa had'e da cewa "Aboki Abdul abubuwa ne sukayi yawa, Hajjah ce ta matsamin akan na fara aiki and then kuma ga maganar wai auren Bilkisu da zaniyi, kuma wallahi Abdul bana sonta".
"Haba Abokina ka sanyaya ranka please kaji? Sannan inshaAllah cikin sauk'i komai zaizo k'arshe kaji"?
"naji Abdul amma ta yaya komai zaizo k'arshe"?
"idan lokaci yayi zaka gani, yanzu dai abinda nake so dakai dama kasan auren Ahmad kuma duk event d'in babu wanda muka halarta shine yau za'a gudanar da dinner don Allah ka k'ok'arta yau dai muje dinner".
D'agowa Yusif ya da niyyar yace wani abu Abdul yayi saurin dakatar dashi ta hanyar cewa "Don Allah kada kace A'a".
Sauke numfashi kawai Yusif yayi ba tare daya sake cewa uffan ba.
*FATIMA*
Saida ta k'ara gyara gidan tsaf kamin ta nemi guri ta kwonta barci ne yaso kwosarta saida tayi yak'i dashi dak'yar, sallah la'asar ta gabatar, nan inda ta kammala Sallah ta zauna wayarta ta jawo tana tunanin to da wane saurayi ma zata dinner? Wani abu ne ya fad'o mata a rai murmushi tayi tana shiga Inbox d'in wayarta wata number ta kamo tana dubawa a cikin rai ta shiga karanta sak'onni sai murmushi take wanda ni bansan ma'anarsa b.
Darling number tayi har tayi ring d'aya tayi saurin kashewa a firgice zuciyarta na beating da sauri sauri, ai kuwa ko second's 2 ba'ayi ba kira ya shigo ta kasa d'auka har kiran ya katse, saida aka jera kusan kira 5 kafin tayi peaking a na biyar d'in.
"AssalamuAlaikum" tayi sallahma.
Hmmmm...! Hashim ya sauke numfashi yana cewa "yau wace ranah? A gaskiya wannan ranar ta kasance d'aya daga cikin ranaku masu matuk'ar muhimmanci a rayuwata, Fatima sarauniyar dake mulkin zuciyata, Fatima wallahi na rasa farinciki sanadiyyar shariya daga gareki, Fatima wallahi sonki nake kuma inaso ki aminta dani bazan tab'a cutar dake ba".
Sauke numfashi Fatima tayi tana cewa "naji dama kiranka nayi kazo zata rakani dinner wata Antyn mu".
"Okey, an gama Gimbiya gani nan zuwaa".
"A'a ba yanzu ba sai k'arfe 09:00pm"
"Okey Allah ya kaimu" daga haka suka yanke kiran sauke numfashi kawai Fatima tayi tana dubn fusjar wayar mintina masu yawa tana a zaune har saida taji sallamar Inna Mairi......
*Don't forget with share fisabililah don manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*E.t.c*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 31&32*
............Amsa sallamar Fatima tayi taba fitowa daga d'akin "A maraba da Inna har kun dawo?" cikin yanayi marar dad'i Inna mairi tace "Yawwa Fatima nadai dawo Yaya nacen, Fatima Allah yayiwa Inna rasuwa" Inna Mairi ta k'arasa fad'a tana fashewa da sabon kukan dake cinta.
"Innalillahi wa'inna ilaihin raji'um, Subhanallah Subhanallah, Inna yanzu wannan tsohuwar ta rasu? Ashe Hajo lokaci yayi? To Ubangiji ya kyautata makwoncin ta" da "Ameen" mama ta amsa tana cewa "Fad'ima koda mukace har an suturtata, munyi kuka har mun gaji, Inna Hajo ba Yaya ce kawai 'yrta ba harmu ta had'e, munyi rashi ubangiji ya jaddada rahmar sa gareta" Inna Mairi ta fad'a tana share hawayenta kafin ta d'ora da fad'in "yanzu su Yaya duk suna ce en kega ba zaiyuwu mu zauna mu duka ba shine ni na dawo, ita yayan sai anyi sadakan uku zata dawo".
Fatima ta shiga wani hali na rashin kakarta dukda bata yawan zuwa gurinta amma duk lokacin da taje sai sun kwoshi dramer, zuciyarta ta sosu saida ta zubar da hawayen tausayi d'aki ta koma tana zama saida ta ida kukanta mai isarta kafin ta share fuskarta jin an fara kiraye-kirayen sallar magriba a wasu massalatai.
Sallar magrib ta gabatar koda ta kammala ta d'an waske, jinginawa tayi da bed abubuwa da yawa na faruwa daga cikin zuciyarta mutuwar tsohuwa ta shigi Fatima yanda bakwo zato, tunani take akan dinner da zataje shin ko kada taje? Sai dai wata zuciyar na nuna mata bata kyautawa Jidda ba! Tunanin ta ne ya katse jin wayarta na ring mik'a hannu tayi tana d'aukota peaking tayi batare data duba mai kiran ba koda ta kara wayar a kunnenta bata furta komai ba.
"Amincin Allah tare da yardar sa su tabbata ga fuskar dake wanzar da farinciki gatuk idanun da sukayi tozali da'ita, yake mai kyakyawar fuska, sarauniyar mata" d'an d'ago wayar Fatima tayi daga kunnuwanta tare da duba sunan mai kiran *HASHIM* hmmm ta sauke ajiyar zuciya tare da mayar da wayar a kunne, dak'yar ta tattaro amsar da zata basa "tare dakai".
Murmushi Hashim yayi wanda har tana iya juyo sautin sa had'e da cewa " Gani a k'ofar gida ina jiran gimbiyata idan ta shirya sai ta fito ina jiranta", d'an jim Fatima tayi kafin ta iya cewa "Okey, yanzu zan fito, kad'an jira kad'an".
"an gama tauraruwar mata Zahrata" itakam Fatima ba tare data k'ara furta komai ba ta sauke wayar daga kunnenta tana ajiyeta saman bed, sauke numfashi tayi cikin mutuwar jiki had'e da mik'ewa, koda ta fito tsakar gidan ba kowa dama daga ita ne sai Inna Mairi, wanka tayi wanda bai d'auketa dogon lokaci ba koda ta fito alwala tayi domin ganin an fara kirayen sallar isha d'an jinkirtawa tayi saida tayi sallar ta kammala..
Shiri ta shiga yi duk da simple makeup tayi, aikuwa tayi matuk'ar kyawo, less ta saka blue mai ratsin skayblue yayi matuk'ar karb'anta d'inkin riga da skirth sun fitar da shape d'inta, takalmi ta saka masu tsini had'e da gyalenta skayblue handbag d'inta duk kalar kayanta saida ta fesa turare ko'ina kamshi na tashi.
Kay Fan's kuzo kuga Fatima kamar wata amarya tayi masifar kyawo, fitowa tayi da niyyar tafiya har takai k'ofar gida saidai ganin idan ta fita ba tare data sanar da Inna Mairi ba tamkar ta sakata a rud'u ne! Hanyar d'akin Inna Mairi ta nufa sallama d'auke a bakinta ta shiga, amsawa Inna Mairi tayi wacce ke zaune inda ta kammala sallah tayi zugum, d'agowa tayi had'e da tsurawa Fatima ido tayi "Inna ina wuni? Ya gajiya?" "Allahmdullh Fad'ima yana ganki da shirin fita? Badai wani gun zaki ba"? Inna ta rink'a jerowa Fatima wa'ennan tambayoyin.
"Hmmm... Uhmmm... Inna kenan, wallahi dana d'azune Jidda khalil ta kawomin katin dinner auren antyn su, to shine nakeso yanzu naje zan dawo zuwa 10:00pm". Zaro ido Inna Mairi tayi tana cewa "Kehh, Fad'ima don Allah ki rufamin asiri! Wallahi matsala kawai zakija mana daga ni har kehh.
Murmushi Fatima tayi tana cewa " Kay Inna yanzu zan dawo" tana kaiwa nan ta ficewarta "Fadima Fadima" Inna ta shiga kiran sunanta amma a banza.
Koda Fatima ta fito sai wani karai-raya take kamar Agwogwo, hangen motar sa tayi cen gangaren titi k'arasawa tayi had'e dayin sallam, Hashim Sa'id kenan matashi mai shekara 33 d'an asalin kaduna ne yana da mata daya harda yara biyi saidai a bayan fage shi manemin mata ne d'an isa na k'arshe ya baro matar sa ya dawo nan sai yaga dama yake zuwa wurinta, *Fatima* ya had'u da ita ne gurin wani party daga nan ya biyota da sunan yana sonta, wani lokaci tana d'an kulasa amma dai har yanzu bata tsayar masa ba!.
"AssalamuAlaikah"! Fatima tayi sallama cikin zazak'iyar muryar ta mai sanyaya zuciyar mai sauraro.
Hashim Murmushin sa ya k'ara fad'ad'awa had'e da amsa mata sallamar " Amin wa'alaikissalam" kafin ya d'ora da fad'in "barka da fitowa zahra'uta tauraruwar tausari" murmushi kawai Fatima tayi tana cewa "ina yini Yaya Hashim? " sai da ya gama kallonta tsaf kafin ya bata amsa da cewa "lafiya Gimbiya ya gidan dasu Umma? " "kowa lafiya" Fatima ta basa amsa cike da gajiyawa "MashaAllah Gimbiyar mata," ya fad'a yana saka hannun sa cikin aljihu kud'i ya zaro saida ya k'irga naira dubu hansim yana mik'a mata d'ago da idanuwanta tayi tana kallon sa cikin siggar tambaya "Ki karb'a" ta tsinkayi muryar sa kafin ta mayar masa da amsa "Kud'in meye? " kafeta yayi da idanu wanda ya sakata duk'ar da kanta k'asa "Don Allah Fatima ki karb'a, don sonki da ma'aiki (s.a.w). " idan na karb'a mezanyi dasu ni kawai mu tafi".
"Fatima" ya koma kiran sunanta! "Ki taimka wallahi baki tab'a karb'an abu daga gareni ba, don Allah ki karb'i wannan, don darajar iyayenki, wallahi idan ba zaki karb'a ba saidai mu dawwama anan", (Hmmm, tunda ance dakai Fatima tasan darajar iyayenta😄), d'an jujjuya idanu Fatima tayi kafin ta saka hannu biyu zuciyarta ta rabu biyu tana karb'a, amma a ranta ta saka su dawo kawai zata mayar masa da kud'insa.
" an gode Yaya Hashim ubangiji ya saka da alkhairi, Allah ya biya da ameen ya amsa cikin farinciki.
"Ina zuwa" Fatima ta fad'a tana kama hanya, shagon Iliya ta nufa fuskarta d'auke da murmushi "Malam Iliya barka da dare" murmushi Iliya mai shago yayi yana cewa "a Hajjaju Mama Fad'ima kece nake gani? " murmushi ta mayar masa tana cewa Eh Iliya nice dama wannan na kawo ka ajiyemin zuwa aniima Fatima ta fad'a tana mik'a masa kud'in da Hashim ya bata, hannu bibbiyuIliya ya saka yana karb'a had'e da cewa "to.. To Hajjaju sai kin dawo, Allah ya tsare hanya" da Amin Fatima ta amsa tana wucewa koda ta koma a mota ta tarar da Hashim itama shiga tayi yana tada mota tana karanto masa adress hall d'in da za'ayi dinner.
****
Mintina k'alilan su Fatima suka isa hotel d'in da za'ayi bikin, tare suka shiga ciki dakyar ta samu ganin Jidda ta karramasu kuma taji dad'in zuwanta harma sun haisa da Anty Ummu (amarya) suna zaune wayarta ce tayi ring peaking tayi tare da karawa a kunnenta sedai ba'aji hayaniya tayi yawa mik'ewa tayi da niyyar fita inda babu hayaniya "Yaya Hashim ina zuwa" murmushi kawai yayi tana wucewa harabarhotel d'in duk motoci na? Daga gefe ta koma tana peaking Hauwa'u ce gaisawa sukayi tanayi mata k'orafin bataje gidanta ba hak'uri ta bata tare da mata alk'awarin kwonan nan zataje.
Sallama sukayi tana sauke ajiyar zuciya, d'agowa tayi gabanta ne ya bada wani irin bugu wanda ya kusa sanadiyyar tarwatsewar zuciyarta "Ya Yusif" ta fad'a a firgice Yusif da Abdul wa'enda suka tsuramata ido cike da mamaki da kuma Al'ajabi.
Alhamdullh Yusif ya fad'a cikin tsananin farinciki, kafin su k'arasa kusa gareta "Innalilahi wa'inna ilaohin raji'um wata masifa" Fatima ta fad'a hawaye na zubowa daga idanunta Abdul ne yayi karfin halin maga shikuwa Yusif ji yake kamar ya rumgumeta "Fatima ashe zamu sake ganawa? Fatima meya sameki, Fatima meyasa zaki fito daga gidannan? "
K'ok'arin b'oye wayarta tayi cikin skirth d'inta had'e da d'agowa tana share hawayenta, "don Allah Yaya Yusif ku taimakeni su yafemin wallahi bafa son raina bane, k'ara rikicewa tayi hangen Hashim ya fito yana dubanta, " kinga wancen? Ta fad'a tana nuna Hashim ga baki d'ago juyawa dukayi suna kallon Hashim kafin su juyo i zuwa gareta Abdul na cewa "Eh wayeshi" ? "Shine wanda ya sace ni, nayi k'ok'arin tafoya daga gidan da kuka kaini saboda ina tsoron kada kumin abinda wannan Saurayin yayi niyyar yimin, shine wannan ya sace ni dama d'an yankar kaine yana kaini gidan sa saina rok'esa da niyyar kada ya yankani shine ya d'aukeni a 'yr aiki kullum cikin wahalar dani yake da sakani yawo duk inda zaina tare dani, baya yarda nayi nesa dashi, ko yanzu ya d'aukoni nan ne gutin wani biki shine nace masa zanje na kewaya daga nan na fito 😂yanzu har kuka ganni gashi yanzu na samu ganin ku kuma ya fito nema na Fatima ta fad'a cikin kuka duk sun rud'e da tsananim tausayimta...
*(Hhhh😂😂😂😂 lallai Fatima kin iya kalya😅, wayyo Hashim ka bani tausayi😢 amma wannan shine dai-dai dakai😜)*
*ina mai baku hak'uri na zaman jirana masoyan asali, banda lafiya😭 ina buk'atar addu'arku🙏, ya Allah don darajar ma'aiki (s.a.w) Allah don k'arfin mulkin ka da hasken salatin annabi muhammad (s.a.w) ka baiwa baiwarka Rukayya lafiya*
_Sannan don Allah ku tayani da addu'a ubangiji ya bani nasarar cin jarabawar da zani fara jibi litanin, Allah ka bani nasara samun marking da ake buk'ata wannan shine karo na uku da zan rubuta, u abangiji yasa k'arshen wahalar kenan_
```Nagode Nagode Nagode```🙏
🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴
*Don't forget with share fisabililah don manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*E.t.c*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 33&34*
........ "Ayya sannu Fatima" Abdul ya fad'a cikin tausayawa kafin ya maida kallon sa i zuwa Fatima wacce sai share hawayen makirci take fuskar ta abin tausayi.
"Abdul a gaskiya ya kamata a kama wancen mutumen, saboda kaga bamu san iya adadin al'ummar da ya illata ba tsafi fa ba wasa ba", duban Yusif Abdul yayi bayan ya dasa aya daga maganar sa kafin yace "gaskiyar maganar ka ce yanzu d'auki Fatima ku wuce, ni zan kula da komai sai nayi aresting d'insa, yanzu ku wuce cen gidan Yaya Bashir zanzo na sameka musan yanda za'ayi".
" Okey" kawai Yusif yace tare da wucewa sai da akayi mintina da barin su gurin kafin ya d'auki wayarsa yana kiranwata number, bayan ya gama magana Hashim daya lura har yanzu yana nan yana kai-kawo sai faman neman Fatima yake nufarsa Abdul yayi gadan-gadan lura da haka ya sanya Hashim tsayuwa kallon Abdul kawai Hashim keyi.
Sallama Abdul yayi masa, wanda ya amsa yaba masa kallo mai d'auke da tambayoyi, "naga kamar akwai abinda kake nema? " Hashim ya tsinci muryar Abdul a lokacin da baiyi tsammani ba, d'an kallon sa Hashim yayi ta k'asan ido kafin yace "babu abinda nike nema, me ka gani? "
"Babu" Abdul ya fad'a, jin tafiyar motar ya sanya shi juyowa, daga cen motar tayi parking kafin yaji ring d'in wayar sa banji abinda ya fad'a ba har ya kammala wayar.
"Am kace babu abinda kake nema? " Abdul ya k'ara tambayar Hashim wanda ya cika da mamakin abubuwan da Abdul ke masa a harzuk'e yace "Malam ka tafi zuwa sha'anin gabanta meye ruwanka dani? Eyye?" Hashim na k'arasa fad'ar hakan ya kama hanyar barin gurin saurin jawosa Abdul yayi kafin yayi wata magana sauran yaran su sun k'araso sarama Abdul sukayi shikuwa I. D card d'insa ta zama cikaken ma'aikacin C.I.D ya fito da ita had'e da cewa "Shrugging we are arresting you regarding forging" zaro ido Hashim yayi cikin makarkata yana cewa "me...mm lai..fin nayi..muku? Ko sauraren sa basiyi ba aka tasa k'eyarsa gaba sai cikin mota, daga nan sai babban ofishin su dake nan cikin jahar Kano.
******
_*YUSIF&FATIMA*_
Koda ya d'auketa a mota babu wanda yace da d'an uwan sa k'ala har duka k'arasa gidan Yaya Bashir, koda suka isa har bedroom ya rakata kafin ya dawo fallo ya zauna yana tsammanin kiran Abdul.
Bayan wasu mintuna har kusan awa d'aya ga kiran Abdul peaking Yusif yayi yana karawa a kunnen sa " Hello Yusif an kamasa yanzu haka yana hannun hukuma, ko da abinda zan biyo dashi, don yanzu haka ganinan hanyar gida".
"Ba komai Abdul kawai ka biyowa Fatiman da Abinci maybe ko abincin baya bata Yuaif ya fad'a cikin tausayawa wa".
" Okey" daga haka ya yanke kiran jingina yayi yanata sake-sake a zuciyar sa na abubuwa masu yawa.
_After 2 hours_
Yanaban zaune a gurin ya jiyo sallamar Abdul amsawa yayi Abdul na k'arasowa hannun sa d'aya rik'e da leda mai tambarin Al'azzum Restaurant bisa center Drower ya d'ora ledar tare da dawo nan kusa da Yusif yana zama, duban sa yayi yana cewa "Yusif ina Fatiman take? " "tana cikin" kawai Yusif ya basa amsa k'ara maida hankali garesa Abdul yayi yana cewa "ka kaima Fatima abincin sai ka dawo muyi magana".
Kallon sakanni yayima Abdul kafin ya mik'e wayarsa ce tayi ring bai duba ko waye mai kiran ba, ledar da Abdul ya shigo da'ita ya d'auka yana nufan d'akin da Fatima ke ciki, saida yayi knocking kusan sau 3 kafin yayi maganar ta cikin sanyin muryanta " Shigo" tura k'ofar bedroom d'in yayi yana shiga, Fatima na zaune gefen gado tayi tagumi fuskarta duk damuwa k'arara gefenta ya ajiye ledar ya bud'e baki da niyyar magana wayar sa ta sake ring "MY HAPPINESS" Shine sunan daya bayyana akan screen d'in wayar "Hajja" ya furta ahankali cikin sanyin murya "Na'am Yusufa kana ina? Dama na kiraka ne na sanar dakai idan zata dawo gida ka biyo gidan Mommyn ku ka d'auko ni, driver ya kaini dubo jikin Daddy domin ko da daren nan saida ya tashi"!
" to Hajjah yanzu ma zan dawo", “Okey sai ka zo”
Sauke numfashi Yusif yayi bayan ya kammala wayar da Hajja maida duban sa yayi ga Fatima wacce har yanzu idanunta a noce suke, "Sannu Fatima! Kici Abinci Kiyi Sallah sai ki huta, InshaAllah gobe zamuyi magana don Allah ki saki jikin ki, ki d'auka nan tamkar gidan ku ne, InshaAllah babu wani abu da zai sake faruwa dake".
Share Hawaye Fatima tayi kafin ta d'ago da idanun ta sedai ta kasa d'aga ido ta kallesa wani bala'in nauyin sa takeji fiye da misali, a hanki ta furta " Nagode Yaya Yusif ubangiji ya saka da alkhairi tana" yaji dad'in addu'ar ta matuk'a da Ameen ya amsa yana ficewa da Abdul yaci karo a fallon yana zaune a inda ya barsa, shima a gefensa ya zauna yana dubansa had'e da cewa "Abdul Aboki ina jinka wace shawara zaka bayar, domin kasan ba zaiyu mu ajiyeta a wannan gidan ba tare da munyi wata matsaya ba! " duban Yusif Abdul yayi bayan ya dasa ayar yana cewa "Naji Yuaif, ni a ganina kawai ka auri Fatima" cikin firgici Yusif ya d'ago uana cewa "kako san abinda kake fad'a Abdul? Na auri Fatima fa? "
" Eh, Yusif ka auri Fatima inaji wannan shine taimako na farko da zakayi mata, sannan dum abinda zai faru ya fatu. "
"Abdul taya zan auri Fatima ba tare da iyaye na sun sani ba? Kaifa kasan su Hajja na nan da batun auren da za'a had'ani da Balkisu, gaskiya Abdul wannan shawarar batayi ba", dafa Yusif Abdul yayi yana cewa " ka tsaya ka fahimce ni aboki, idan ka auri Fatima duk abubuwan da zasu biyo baya masu sauk'i kawai idan ka Amince ni nasan wanda zai d'aura auren, badai kana son Fatimar ba"?
"Abdul kada a samu matsala"? " InshaAllah babu abinda zai faru, bari yanzu zan kira Sadiya tazo ta tayata zama tunda kaga gida zamu wuce”.
"Okey" haka kuwa akayi koda su Yusif suka fito saida suka biya office d'in su Abdul su d'auko Sadiya suka kawota gidan nan inda sukayi mata bayanin komai, gida Yusif ya sauke Abdul kafin ya d'auki Hajja suka koma gida.
*Sadiya*
Abokiyar aikin su Abdul ce a makaranta d'aya sukayi karatu har suka samu aiki 'yr river state ce, ita d'aya ta kama gida tana haya tunda nan aiki ya kawota kafin ta samu ayi mata tranfer ta koma jiharsu.
******
Koda suka sauke Sadiya ta shiga gidan, sallama tayi saida ta dudduba dukkan bedrooms d'in kafin ta gano wanda Fatima take ciki, da sallama ya shiga d'agowa Fatima tayi had'e da amsa sallamarta.
.
Ajiye jikar kayanta tayi bisa sofa kafin ta zauna gefen Fatima wacce ta gaidata da "Ina Wuni".?
" Lafiya k'alau Qauwata, ya gajiya"?
Dan yatsine Fuska Fatima tayi kafin ta amsa mata da "Lafiya" tamkar wacce ke koyon magana.
Haka Sadiya tai ta jan Fatima da magana amma tak'i amsa mata sai idan ta mata dad'i, har de ta d'an sake da'ita......
*******
*GIDAN SU FATIMA*
Sai bayan isha'i Malam ya dawo Inna Mairi kam ahankalin ta duk a tashe, gaida Malam tayi tare dayi masa ya gajiya.
Cen bayan wani lakaci ya dubeta yana cewa "wai Mairi ina yarinyar nan? Kaddai abinda nake tunani ya faru? "
A firgice Mama ta d'ago tana cewa "Malam don Allah ka yafemin wallahi Fad'ima bata jin maganata nayi k'ok'arin hanata amma ga banza"..... Inna ta k'arasa fad'a tana fashewa da matsanancin Kuka anda bil hakk'i k'una zuciyarta keyi....
Shidai Malam k'ala baice ba haka suka zauna zugum har Inna ta gaji tayi shuru sai sheshshekar kukanta tun suna tsammanin ganin Fatima har dare yayi babu ita babu labarinta hankalin su ya tashi shidai Malam kawai yana dannewa ne amna shi kad'ai yasan halin da yake ciki....
Basuyi yunk'urin nemanta ba duk da Inna taso amma Malam ya dakatar da ita ta hanyar cewa " duk inda taje zata dawo" bacci b'arawo baiyi nasarar satar su ba har garin Allah ya waye.
Ta ina ma zasu fara nemanta? Duk inda Inna Mairi ke tunanin ganin Fatima taje amma babu ita babu labarin ta, ta kasa gayawa Mama har cen gidan gaisuwar taje wai ko za'a iske Fatima cen amma babu ita sedai bata gayawa kowa ba haka ta dawo jiki duk a sabule Malam kuwa bai wani jimq ba shima gidan makoki ya dawo da k'yar bayan axhar ya samu zama da almajirai a k'ofar gida.
*FATIMA*
Haka suk kwona da Sadiya koda gari ya waye sadoya ce ta fita nemo musu abincin, wanda Fatima duk hankalinta a tashe tana tunanin yanda za'ayi tabar gidan, kwona a wani gurin lalle ta shiga masifa tayi nadama marar iyaka. .
*YUSIF*
Basu samu damar had'uwa da Abdul ba sai bayan azhar, sun k'ara daddale magana Abdul ne ke zansu sai unguwar Rijiyar zaki direct k'ofar gidan Malam Shehu sukayi parking koda suka fito yana zaune tsakiyar almajiran sa, har k'asa suka durk'usa had'e da gaida sa cikin sakin fuska ya amsa musu, Abdul ne yayi masa bayanin akan suna son su keb'e akwoi maganar data kawo su.
Sai da Malam ya aiki almajiri cikin gida ya karb'o musu tabarma aka shimfid'a a soron gidan kafin suka koma cen, sai da suka k'ara gaisawa sosai kafin Abdul ya dubi Malam yana cewa "Alaramma magana ce ta kawomu mai muhimmanci, wannan da kake gani aboki naa ne" Abdul ya fad'a yananuna Yuaif kafin ya d'ora da fad'in "dama Malam wata yarinya ce da aka rik'a gidan su yarinyar marainiya ce tsintar ta akayi shine yanzu take son sa shima yana sonta, 'yn uwan sa dai basu amince daya aureta ba saboda suna ganin bata da dangi, shi kuwa yaron yana sonta shine mukazo idan da yuwar ka d'aura musu aure da kanka"! Abdul ya dasa aya yana sauke numfashi.
Shikam Yusif sai kallon Abdul yake yana mamakin wannan k'aryar tasa yanda ya iya shiryata.
Sauke numfashi Malam yayi yana jinjinaa wannan al'amarin kafin ya dubi Abdul yana cewa " to shi yaron iyayen sa sun amince? "
"Eh Malam da yardar mahaifin sa".
" to mashaAllah aikin jihadi kenan!! To yanzu abinda nake so daku kuje kuzo kin da mahaifin sa idan yaso ana kammala sallar la'asar sai nayi sanarwa a masalaci a d'aura aure...
Godiya sukayiwa Malam kafin su fito, "Abdul meyasa zakayi masa k'arya? Yanzu gashi yace azo da mahaifina" Yusif ya ida fad'a cikin jin haushin Abdul yana d'otawa da jan tsaki, murmushi Abdul yayi kafin ya dubesa yana cewa "kai Aboki ban baka shawara ba saida na kammala shirya komai, haka Abdul yaja motar
Sai Goron dutse a wani natsakaicin gida Abdul ya faka, wayar sa ya jawo kafin ya kira wata number " Eh mun k'araso" yana fad'ar haka ya kashe wayar ba'a d'auki mintina ba ga wani d'an dottijo ya fito d'aya biye bayan sa, tsoffine sedai cikin shiga ta kamala kowannen su cikin manyan kaya, Abdul ne ya fito tare da bud'e musu sit d'in baya bayan sun gaisa, shiga sukayi tare da gaida Yusif shima amsawa yayi kansa duk ya kulle...
Jan motar Abdul yayi sai gidan Malam shehu wanda har an fara kiraye-kirayen sallar la'asar, nuna masa wa'ennan dottijan Abdul yayi had'e da cewa d'ayan mahaifin Yusif Alhaji Idris d'ayan kuma Alhaji Lawal yayan mahaifiyarsa, Malam ya tarbesu tamkar bak'insa bayan angama gaisawa gaba d'aya suka wuce massalaci ana idar da Sallah Malam yayi snarwa ba b'ata lokaci dama sunzo da alawa da goro mintina k'alilan aka d'aura aure *FATIMA DA YUSIF* akan sadaki 80,000.............
_wash Allah na, yau nasha typing nasan zan faranta ran masu dakon jirana_ *kuyi hak'uri da jinkiri wallahi mun fara jarabawa ne, ina buqatar addu'arku.._
*Don't forget with share fisabililah don manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*E.t.c*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 35&36*
..............tafiya suke cikin mota bayan su mayar da dottijan gidan su, yayi zugum ganin dai tabbas Abdul baida niyyar cemasa komai ya sakasa d'agowa yana duban Abdul d'in wanda ke driving hankalin sa kwonce.
"Abdul! Abdul dallah Malam ka tsaya muyi magana" salun alun Abdul ya gangara had'e dayin parking gefen titi kafin ya d'agowa yana tsurawa Yusif idanu.
"Ina jinka Aboki Yusif kace na tsaya kuma na tsaya yi magana", " Hmmmm..! Abdul kadai ga duk wa'ennan abubuwan kaine ka shiryasu ko? To ka nemi mafita yanzu me zamuyi, ya zanyi da auren Fatima alhalin iyayena basu sani ba?" Yusif ya k'are bayanin sa idanun sa kaf akan Abdul yana jiran yfuskaji me zaice.
"Oh ni Abdul, wai kai Yusif meyasa ka cika azalb'ab'i, kadai sam yanda na shirta abin InshaAllah komai zai tafi dai-dai, kai dai kanada gajen hak'uri", "dole ne kaga haka Abdul ni ina tsoron yanda zan fuskanci Iyaye na da maganar, bana son ransu ya b'ace ta dalilina.
"Yusif na gaya maka kada ka damu InshaAllah komai zaizo cikin sauk'i kada ka tayar da hankalin ka" Abdul ya'ida fad'a yana tayar da motar had'e da juyowa yana duban Yusif kafin yace "Ango kasha k'amshi gida muka nufa, ko kuma gurin Amaryar tamu zamuje?" Abdul ya k'arasa fad'a cikin zolaya yana sakin dariyar sa ciki-ciki kwofa Abdul yayi ba tare da yace komai ba shi abubuwa sun sha masa kai, "Shin dame zai kira wannan auren? Auren so ko Auren k'i? Shi yasan yana son Fatima amma ita fa? Zata yarda ta zauna dashi? Abubuwa dai duk sunyi masa yawa a brain!
Direct Gidan Yaya Bashir suka nufa koda Abdul yayi parking Yusif yakai kusan minti 5 kafin ya iya fitowa koda suka k'arasa Fallon Sadiya suka tarar zaune tana duban television, gaisawa sukayi kafin kowannen su ya samu guri ya zauna " Sadiya kin ganmu sai yanzu? Wallahi abubuwa ne sukayi mana yawa, ya gajiya ya mutuniya" murmushi Sadiya tayi cikin far'ata kafin ta dubesu tace "bakomai wallahi Fatima nanan cikin k'oshin lafiya, sedai tak'i ta saki jiki dani.
“hhh ai da sannu zata saba, yaukam mun saki zaman gida baki fita aiki ba“ Sauke numfashi Sadiya tayi kafin tace ai babu komai "d'azu na fita nayo sign ba komao wallahi", to Halima mungode Yusif ya fad'a kacokan hankalin sa naga k'ofar d'akin da Fatima ke ciki kamar yayi tsuntsuwa ya ganta.
“eh, to tunda kunzo yanzu bari naje cen gida akwai abinda zanyi zuwa anjima zan dawo“
" Okey suka amsa mata dashi Abdul na cewa muje na saukeki gida" “Okey sir” haka suka fice daga fallon....
*FATIMA*
Fatima tunda Sadiya tayo musu order abinci, kad'an taci dama ita ba gwonar cin abinci bace, tana nan zaune guri d'aya sallah ce kawai ke tadata, tun Sadiya nad'an shigowa tana tayata da fira har bacci da bata san dashi ba yayi awon gaba da'ita.
Ahankali ta tashi abdu'ar tashi daga bacci d'auke a bakinta, mik'a tayi kafin ta mik'e, wayarta ta fara lalaba wacce sai lokacin ta fad'o mata a rai, dube-dube ta shiga yi sedai ko'ina ta dubq amma babu waya tunani ta shiga yi wanda har ga Allah bata da tabbacin ko ta shigo da wayar cikin gidan...
Fallo ta sauko ko anan ta ajiyeta, turus tayi ganin Yusif, idanun su ne suka sarkafe cikin na juna, k'ok'arin duk'ar da kanta tayi kafin ta bud'e baki cikin sanyin murya tana cewa "Ina wuni Yaya Yusif"
Kallon ta yake yana jin sonta na k'ara zagaye ko wanne sassa na jikine “Lafiya Fateema, ya bak'inci?" “Alhamdullh” abinda ta fito nema ma ta kasa dubawa, illa tsayen da tayi ta rasa duniya ina zata ta kasa komawa d'aki.
Ganin tayi tsaye zugum ya saka Yusif sakin murmushi wanda ya k'ara masa kyawo kafin ya dubeta yana cewa "Ki k'arado ki zauna kada k'afafuwanki kiyi sanyi" "To" ta fad'a tana k'arasowa nesa dashi ta zauna bisa kujera mai zaman mutum d'aya had'e da sunne kanta k'asa.
"Fatima" ya kira sunanta cikin wata murya wacce ta sakata jin wani iri, bata iya amsawa ba harya mai-maita kiran sunanta "Na'am",
'Yn tambayoyi yayi mata yana janta da surutu wanda daga " Uhm sai uhm'uhm kawai take basa amsa duk ta tsargu da kallon da yake mata, shikuwa a nasa b'angaren tunani yake yana jin zuciyarsa fes "wai yanzu wannan Matarsa ce? "
Hakadai suka kasance har Abdul ya dawo da Sadiya sun ciyo abinci, sai magriba sannan su Yusif suka tafi gida....
*GIDAN SU FATIMA*
sunyi cigiya har cikin gari amma babu Fatima babu labarinta, labarin b'atan su Fatima yabi ko'ina, wasu na cikin bak'in ciki wasu kuma na Allah gwoi, sai bayan magriba ga Iliya mai shago na kuka nan ya zayyanewa Malam komai da ake ciki na fitar da Fatima tayi da kud'in data bashi ajiya "Malam bbillahil'azim na ganta da shirin fita dubu Hamsin ta bani ajiya, dama ina binta dubu uku tun kwonukan baya, don Allah Malam kayi hak'uri wallhy babu laifina kuma ban san inda Fatima tayi ba".
Haka Malam ya danne zuciyarsa ya karb'i kud'in sannan ya cire dubu uku daban ba cikin hamsin d'in ba ya baiwa Iliya mai shago, cikin jimami har kwona uku suka shud'e babu Fatima babu labarinta lokacin kam dole aka sanar da Mama tashin hankali ya dawo sabo kowa ya shiga matuk'ar tashin hankali har gidan radio sunkai a musu cigiya amma babu Fatima babu labarinta, cikin sati d'aya hankalin Mama ya tashi duk ta rame ta shiga matsananciyar damuwa ina kuma ga Inna Mairi wacce take ganin komai ya faru ita ta jawo sakacinta ne sai Mamace ke dafanta da sanyayan kalamai.
*B'ANGAREN FATIMA*
haka rayuwa taci gaba da kasancewa kullum nan su Yusif ke rabin yini Sadiya ta tayata bacci, a duk lokacin data shirya guduwa sai ta rasa hanyar fita duk damuwa tayi mata yawa.
Yusif kuwa shima yanzu shurun bazai yuwu ba shi yau ya yanke shawarar tunkarar Hajja da maganar koda Abdul bai amince, ba...
Zaune yake fallon gidan Yaya Bashir sai kiran number Abdul yake amma bata shiga ga Sadiya ma bata nan, so yake yaje gida kuma ba zai yuwu ya tafi yabar Fatima ita d'aya ba, ganin babu mafita ya saka shi mik'ewa ya nufi bedroom d'in da take ciki domin sanar da'ita ya tafi ya dawo ta kula.
Da sallama d'auke a bakin sa ya tura handle k'ofar, turus yayi tsintar kansa cikin wani yanayi wanda yayi silar saukar masa da kasala, ya tsureta da idanu Fitowarta kenan daga Bathroom towel ne wanda da kad'an ya wuce cinyarta, batayi tsammanin ganin sa ba wata kunya ce ta lullub'eta ji take kamar k'asa ta tsage ta shige, a zuciyarta kuya sai tir take da wannan d'abi'ar ta lura kwona biyu bawan Allahn nan idan zai shigo d'akin nan baya neman izini yasan a wane hali zai tarar da'ita?
K'ok'arin dai-daita nutsuwar sa yake amma ina kwonyarsa sai azal-zalarsa take, duk tsikar jikin sa ta tashi wani irin feeling ke taso masa, lokaci d'aya hankalin sa ya gushe ya mance dawa yake tare, a'ina yake shidai abu d'aya ya iya tunawa da aure a tsakanin su, Fatima inama Allah bai haramta kisan kai ba da tabbas ta kashe kanta a wannan rana, ranar da take jinta bak'ar rana a rayuwarta, ranar data kasance ranar rabuwanta da mutumcinta, ta furta baka da zuci tayi nadama babu iyaka tayi kuka kamar Allah ya aikota...
*_a yanda kuka tsinci labarin duk a hakan na tsarasa_*
*Don't forget with share fisabililah don manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*E.t.c*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_*(😂😂hhhhh jiya naci karo da sak'una mabanbanta, ina matuk'ar godiya a gareku masoya na🙏 tabbas ana tare muddin rai)*_
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 37&38*
..... Bayan komai ya lafa Fatima tayi kuka har ta godewa Allah, wata iriyar nutsuwa yakeji da annashuwa, farin-ciki duk ya baibaye zuciyarsa sai ciwon da kansa keyi, duk magiyar da yake yana baiwa Fatima hak'uri tak'i d'agowa ta kallesa domin a wannan lokaci ji take duk duniya babu wanda ta tsana kamar Yusif batada wani mak'iyi a doron k'asa bayan shi kalaman da suke fita daga bakinta sune "Dama zuciyar kafirai gareku? Dama kawoni nan kukayi bada niyyar taimako ba sai don ku tozarta ni, kun kaeoni nan ne don ku zalumceni ku kassara rayuwata ku wulak'anta ni, ka cuceni ka zalumce ni, wallahi tallahi tsakanina dakai Allah ya'isa.. Haka Fatima ke sakin zantukan cikin k'una rai da bak'in ciki.. Ya lallasheta har ya gaji sai d'aukarta yayi zuwa bathroom, bata dawo hankalinta ba sai da taji rad'ad'in daya ziyarci ruhi da gangar jikinta wata k'ara ta sake tana k'ok'arin fusgar jikinta daga nashi wasu zafafan hawaye na ambaliya daga cikin k'wormin idonta, k'ara rik'eta yayi yana cewa " Am Sorry My Trustee gazing not handing Willful Spectral Perpetrator, don ki Allah ki yafemin Bintoto.
"Don Allah ka rabu dani, kasa na k'ara fahimtar duk mazan duniya halin su d'aya,wannan ya zamto izna ga 'yn baya, ka cuceni kaci amanata, tsakanin..... Bata k'arasa fad'ar abinda tayi niyya ba sakamakon rufe mata baki da yayi da lallausan tafin hannunsa "My Trustee don Allah forgive me, ki daina ya'anata, kada bakinki ya bini, nasan na cucuki amma don Allah ki yafemin kinji Bintu" fisge kanta tayi tana nunasa da yatsa cikin fushi had'e da kuma gushewar hankali na wucin gadi a zafafe ta mik'e dukda halin da take ciki "wallahi Yusif idan baka fita daga nan gurin ba, saina illata ka" murmushi Yusif yayi yana mata kallon tausayi domin shi har ga ransa baiji haushinta ba illa zallar soyayyarta dake d'awainiya da gangar jikinsa, yasan ya tabbata gurin babu abin da zata iya yi masa domin ko'ita ba k'arfi ne da ita ba, amma salun-alun ya fice daga Bathroom d'in..
Koda ya fito wayarsa ya samu tana ta faman ring wanda yama manta da'ita ko kafin ya k'arasa har ta katse koda ya duba almost 3 missed calls duk daga b'angaren Abdul, kiran ne ya sake shigowa peaking yayi had'e da karawa a kunnen sa..
"Yusif inata neman ka na kira bakayi peaking ba, dama na dawo ne ban ganta gidan ba".
Cikin sanyin murya yace " Abdul ina ciki ina zuwa" yana kai nan ya sauke watar had'e da jefata saman bed, jinginawa yayi ga Building yana dafe kansa sakamakon jirin da yake niyyar d'ibarsa, ya d'auki wasu mintuna kafin ya samu natsuwar kansa fallo ya nufa tunda ya fito Abdul ke kallon sa bako kyaftawa.
Gefen Abdul Yusif ya zauna yana lumshe Glare eyes d'insa, "Aboki ya naga yanayinka duk ya chenza? Kodai wani Abu na damunka wabda har ni zaka iya b'oye min? ".
Ya d'auki mintina kafin ya d'ago yana duban Abdul d'in kafin ya motsa bakinsa yana cewa “Abdul babu b'oye-b'oye tsakanin mu, wallahi yau kaddara ce ta gifta, Abdul na kusanci Fatima"! "Me?? Abdul ya fad'a yana d'agowa a firgice kafin ya dubi Yusif yana k'yalk'yacewa da dariya kafin cikin tsokana wacce take daga jininsa ya fara magana " a lallai oga Yusif ka cemin yau an shiga daga ciki? Hhhh😂 babban gib'i, kai kuwa miye a ciki ba Matarka bace? "
"Haba Abdul baka fahimta ba, Fatima ta kasa fahimtata tana min kallon azzalumi" Yusif ya k'arasa fad'a kamar ya zubda hawaye, "haba Aboki ai zata gane kasan farkon shiga ga yanda abin yazo mata a bai-bai hhhhh"
"Gaskiya Abdul ni na gaji yau zan fallasa komai, yau zan gayawa Hajjah duk halin da nake ciki saboda bazai yuwu muna tarayya a bai-bai ba, yanzu a ayyana a ranka Fatima ta samu ciki taya zan fuskanci su Hajja har su amince😒?
" oh oh Abban Boy Allah nuna mana, ni gaskiya ka bani 2days zan fiddo mana da wata mafita"..
*FATIMA😜*
ta d'auki mintinoni kafin ta fito daga Bathroom har lokacin hawaye ke ambaliya a saman fuskarta tamkar an bud'e fanfo, a hankali take tafiya wanda take jinta har cikin k'ashi da b'argo, gefen bed ta zauna tana dafe kuncinta cikin azabtuwar ruhi...
*(😂nidai abinda zance masu hali irin na Fatima wannan ya zamto izna a gareku, kada kuyi duba da wannan k'agaggen labarine A'a wallahi hakan takan faruwa Majority cikin Societal, marubuta 'yn baiwa ne duk lalacewar novel wallahi idan ka karanta sai wani abu ya shigeta, ko wanne littafi zaka tarar da b'angaren da marubuciya ta tab'o wanda zaka sami abin na faruwa cikin Al'umma😔, Rubutu baiwa ce da wa'enda suke zagin marubuta da kuma marubutan da suke zagin junan su duk halin su d'aya,)*
_don Allah 'yn uwa mu kiyaye mu rink'a bin umarnin iyayen saboda suna hango muna abinda mu bama hangowa kanmu_
*Kada mu zab'i rayuwa a kanmu wacce mu karan kanmu munsan ba dai-dai bane amma muna aikatawa, saboda kawai mu morewa rayuwar duniya wacce take k'alilan*
*Ya ubangiji ina mai rok'onka ka d'aukaka muryar marubuta a fad'in duniya*
*Ya ubangiji ka tsarkake Alk'alunman mu daga aikata abinda kai kayi hani dashi*
*ya Ubangiji ka shiga lamurran mu, ka gafarta mana da laifin da muka aikata a sane da kuma wanda muka aikata bada sanin mu ba*
*na fad'a na k'ara RUBUTU BAIWA CE, MARUBUTA 'YN BAIWA NE😇😎📚*
*Wann littafin kacokan sadaukarwa ne ga mai hali irin na Fatima, ubangiji ya shirya😏)*
~~Samha~
*Don't forget with share fisabililah don manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*E.t.c*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 39&40*
..........Ta d'auki mintuna, kafin taji sanyi ya fara ratsata, bed d'in babu Bedsheet babu duvet, Mik'ewa tayi tare da nufar kayanta hadda wa'enda Sadiya ta kawo mata tun shekaranjiya, doguwar riga ta d'auko wacce batada nauyi sakawa tayi kafin ta saka hijab a daddafe ta gabatar da sallar la'asar kafin ta konta tana nannad'ewa cikin hijab d'in take jikinta ya d'auki zafi, abubuwa ne suka shiga bijiro mata a zuciya tana jin tsanar Yusif fiye da misali, tabbas tasan haqqin iyayenta ne ke bibiyarta, bata san lokacin da wahalallen barci yayi awon gaba da'ita ba...
*YUSIF*
Koda Sadiya ta dawo nan ta tarar da ita kafin ko wannen su ya wuce gida, kowa da abinda zuciyarsa ke sak'a masa, koda Yusif ya koma gida duk wani iri saida Hajja tayi ta tambayar sa lafiya amma duk amsar d'aya ce "Bakomai"....
***
Koda Sadiya ta shiga d'akin tayi mamakin ganin Fatima na bacci, sedai batayi k'ok'arin tadata ba Bathroom ta shige nan ta tarar da Bedsheet gashi wanke amma duk ruwa ne da Alama babu gurin shanya ta cika da mamaki, amma kawai tayi abinda ya kaita ta fito saida ta kammala Sallar itama kafin ta d'auko bedsheet d'in cen baya ta shanyo, sai kusan magriba Fatima ta tashi dak'yar ta'iya mik'ewa duk jikinta yayi tsami, ga wata azababbiyar yunwar dake addabarta, saida ta k'ara shiga ruwan d'umi kafin ta fito nan ta tarar da Sadiya cin karo sukayi Fatima tana sunne kai domin gani take Sadiya ta gama fahimtar duk wani abu daya shiga tsakaninta da Yusif, " Fatima lafiya meya sameki? " Sadiya ta zayyano mata wa'ennan tambayoyin cikin tausayawa domin ganin yanayinta kamar batada lafiya.
"Wash Anty Sadiya banda lafiya wallahi" Fatima ta fad'a tana k'ok'arin zama bisa gado k'arasowa gurinta Sadiya tayi tana cewa "Ayya sannu Fatima".........
"Wayyo Allah na sannu sis Allahu ya baki lafiya", Sadiya ta fad'a tana dawowa kusa gareta had'e da zama dafata tayi tana shafa wuyanta ji tayi zafi rad'au kamar garwashi cikin tausayawa ta sake duban Fatima had'e da cewa "sannuh Fatima, bari na kira Yallab'ai na gayamasa" ji Fatima tayi kamar ta dakatar dashi sedai rad'ad'in da takeji yafi a misalta.
Dialing number Abdul tayi tana fara ring yayi peaking "AssalamuAlaikum, barka oga" d'an numfasawa Abdul yayi yana amsa sallamarta had'e da d'orawa da fad'in "Barka Sadiya, ya gajiya??".
" Alhamdullh! Oga dama Fatima ce gatanan ba lafiya, ina tunanin fever ce" daga cen b'angaren Abdul saida yayu jim yma ransa yana tunani dama yasan ai dole zatai rashin lafiya "Okey Sadiya bari nazo mu kaita assibiti, sai ku zama cikin shiri".
" okey" Sadiya ta fad'a tana sauke wayar, duban Fatima tayi had'e da cewa "Ayya Sannu Fatima, sai mu shirya yace zai zo mu tafi assibiti".
"Assibiti Anty? Gaskiya A'a nikam kawai fa kaina ke ciwo ni ko farastamol na samu sai nasha, InshaAllah kan zai dena" Fatima ta k'arasa tana murmushin yak'e.
"To Fatima bari na kira sai a bar batun zuwa assibitin" Sadiya ta k'arasa fad'a tana mik'ewa "Eh, Anty da yafi" har takai bakin k'ofa sai kuma ta juyo duban Fatima tayi tana cewa "Am Fatima bakijin dad'i naga har ke wanke sheet kuma baiyi wani datti ba", " OMG😧 dafe kai Fatima tayi a ranta tana cewa wannan Sadiyyar ta cika matsala" kafin ta fara tunani sai cen ta d'ago tana duban Sadiyya had'e da cewa "dama bana aikin komai ne naga yayi k'ura shine na wanke" Fatima ta k'arasa fad'a tana sakin murmushin dole a ranta kuwa sai tsinewa Yusif take da Allah ya isa sunfi dubu....
Koda Sadiya ta fito daga Bedroom tana shigowa fallo ta kira Abdul inda take sanar dashi ai Fatiman tace magani kawai zatasha ba wani ciwone da sai anje assibiti ba..
Abdul kuwa yana kammala waya da Sadiya dama niyyarsa basai ya kira Yusif yaje kawai ya kaisu assibiti a dubata amma jin sun cenja shawara ya saka yana gama waya da Sadiya yayi dialing number Yusif har ta gama ring baiyi peaking ba sake kira yayi sai cen ya d'auka.
"Hello, Yusif yakake???".
" Lafiya" Yusif ya fad'a a tak'aice wanda shima bajin dad'in jikinsa yake ba.
"Dama Fatima ce batada lafiy.... Ai ko kafin ya k'arasa Yusif yayi wata k'ara a firgice yana cewa " What Abdul Fatiman tawa?" "Eh, ita shine da assibiti zamuje yanzu kuwa an fasa tace magani kawai take buk'ata shine nace bari na gaya maka tunda kaine musababbin ciwon sai ka nemi magani".
"Yanzu kuwa Abdul! Shikenan nagode sai mun had'u cen"...
" Cen ina? A'a kawai ka siye magani ka kai musu, ni ba mai zaman kashe wando bane irinka, yanzu haka munanan cikin binciken wani case, kawai idan kaje ka gaida mai jiki".
"Okey" Yusif ya fad'a yana sauke wayar daga kunnen sa, baiji dad'i ba da Fatimar sa batada lafiya da sauri ya mik'e bai d'auki wani dogon lokaci ba gurin shiri yana kammalawa ya fito a harabar gida ya tarar da Alhaji zaune bisa kujerun da aka k'awata cikin rumfa.
"Alhaji barka, an wuni lafita".
Murmushi Alhaji yayi cike da dottako kafin ya shafo kan Yusif wanda ke tsugunne shafa kansa yayi yana cewa " Allah yai maka albarka my one and only son",
"Thank you Sophisticated Father" murmushi Alhaji yayi yana cewa "Yanzu sai ina??" d'an sosa kai yayi had'e da mik'ewa duban Alhaji yayi yana cewa "Alhaji yanzu zan dawo, nan kawai zani", " Okey a dawo lafiya, Allah yayi Albarka" da "Amin" Yusif ya amsa yana wucewa Mota ya shiga gateman na bud'e masa gate koda ya fito bai tsaya ko'ina ba sai pharmacy magani ya siyamata kafin ya wuce yayi siyyayya mai yawa ta Abubuwa koda ya k'arasa gidan da sallama ya shiga falon Sadiya kawai ya tarar zaune gaisawa sukayi yana ajiye d'ayan ledar tambayarta yayi ya mai jiki? "Da sauk'i, tana ciki" Sadiya ta k'arasa fad'a tana nun masa d'akin da Fatima ke ciki ai kuwa baiyi wata-wata ba ya tura kai ga k'ofar knocking yayi amma shuru yanzu kam baiyi gigin shiga ba, sake knocking yayi shuru har kusan karo na 6 amma shuru, ganin haka yasakashi tura k'ofar yana shiga dube-dube ya shigayi sai cen ya hangota kwonce bisa bed duk ta takure kanta! Cike da tausayawa ya k'arasa kusa gareta nan gefenta ya zauna idanun sa kafe a fuskarta "Fatima" ya kira sunan ahankali yana shafa kuncin ta wanda yake sakashi shiga cikin shauk'i da begen k'aunarta.
Fatima dama ba mai nauyin bacci bace jin kamar hannun Mutum na yawo cikin sassa na jikin ya sakata bud'ewa idanunta wa'enda basu sauka cikin ko'ina ba sai na Yusif da sauri ta tashi zaune tana tasalima "Innalilahi wa'inna ilaihin raj'um, na shigesu ni Fatima wannan wace iriyar jarabawar rayuwa ce? Wai don Allah so kake sai ka tabbatar da an zare raina da gangar jikina? Wallahi kun cuceni kun zalumceni daga kai har abokin ka, hak'k'ina dana iyayena saiya biku na shace musu da kukayi Shidai Yusif kallonta kai yake tana surfa masifa saida Fatima tayi mai isarta taga dai da alama wannan bawan Allahn ba tanka mata zaiyi ba kukane ya kunce mata na tausayi kanta da kanta, cike da tausayawa ya rumgumota jikinsa ya d'auki mintuna yana rarrashinta kafin ta tsahirta.
D'agota yayi daga jikinsa tare da fito abinci ya d'auko mata da fruit koda ya kawo mata saida suka kai uwa rana kafin taci kuma akazo bstun magani tace ita fa ba zata sha ba sai da taga alamar d'ure zai mata kafin tasha girma da arziki saida akayi sallar magriba kafin Yusif ya fito saida ya biya ta massalaci yayi Sallah kafin ya koma gida.
A fallon Aljahi ya sauka har Hajjah saida suka kammala Dinner kafin Alhaji ya dubesa yana jero masa zantuka masu yawa " YUSIF na kiraka ne akan Abubuwa guda biyu, na farko batun auren ka da Balkisu wanda jibin nan ni da d'an uwa na muke k'ok'arin saka rana wanda bazai d'auki dogon lokaci ba, na biyu maganar Aiki a gaskiya ba zaiyuwu mu zuba ido ba ace ka kammala karatu amma kak'i tsaida k'afa ka kama aiki saboda haka dama acen baya mun fara ginin assibiti ni da Aboki Daddy to a yanzu ni zan k'ara saika koma cen da aiki Ina fatan ka fahimci zantuka na""!!
Duk wa'ennan bayanai na Abban sa ya kasa sanin wani matsayi bai basu a zuciyarsa, aiki koshi karan-kansa yana so ya fara aiki sedaj batun aure tirk'ashi wata ga wata tabbas baya jin ko matan duniya duka za'a aura masa zai basu matsayi koda k'worar zarra illar da Fatima taiwa zuciyarsa wacce bazai tab'a warkewa ya riga ya kamu da sonta son da bazai iya kwotantuwa ba yana sonta tamkar bugun numfashi Fatima itace *RAYUWARSA.*
ya kasa cewa uffan saida ya tsinci muryar Hajja tana cewa "Kai muke jira Babba" dak'yar ya iya furta “Alhaji duk abinda kuka yanke" yana gama fad'ar hakan yabar fallon zaune yayi bisa sofa bayan ya shiga Bedroom tunani ya shigayi tabbas bazai zama lusarin namiji ba ace komai sai Abdul tabbas yanzu zai sanar da Hajjah komai ma ta fanjama fanjam.....
*WASHE GARI*
koda ya tashi bai samu natsuwa ba sai gurin k'arfe 10 bayan sun kammala break fast Alhaji ya tafi samun Hajjah yayi zaune bisa d'aya daga cikin kujerun fallon ta "Hajjah barka da hutawa" "Barka dai Yusif d'ina yakak? "
"K'alau Hajjah magana nikeso muyi idan ba zaki damu ba, kuma don Allah ki yafemin sannan toshe kunnuwanki daga abinda zan gayamiki ki taushe zuciyar.. " dakatar dashi Hajjah tayi domin iri take ciki takeji a zuciyarta "Yusif ka sanar dani menene?? "
"Hmmm..! Saida Yusif ya sauke numfashi kafin ya fara gayawa Hajjah komai da komai abubuwan daya gaya mata sune " da farko sun kub'utar da Fatima daga hannun isma'il daga nan suka kaita gidan Yaya Bashir har b'acewar da tayi suka nemeta har ganota da sukayi gurin dinner inda Hashim ya saceta har maidota gidan Yaya Bashir da kuma aurenta da yayi...
Yana dasa aya Hajja ta d'ago a hargitse cikin fusata sai saukar mari yaji akan tattausan kuncin sa, "Yusif kana hauka ne? Baka da hankali? Taya zaka had'a matsayinka da tsintacciya wacce ba'asan asalinta ba? Harma kai zaka auri tsintaciyar mage? wallahy Yusif ban lamunta ba ban, Sabida haka kayi gaggawar rabuwa da'ita tunbkafin ranka ya b'ace ka fice min da gani, yanzu kaje mota ka jira ni zaka kaini cen inda take idan kai ta tsahirceka to ni nafi k'arfinta, bakasan mutum baka san inda ya fito ba ka kaiwa Bashir gidan sa? Lalle Yusif to maza-maza ganinan fitowa ka kaini" cikin tashin hankali wanda ake cewa ba'a samaka rana a rikice Yusif ya d'ago da niyyar magana amma Hajjah ta dakatar da ita ta hanyar d'aga masa hannu tana cewa "bana son jin komai, umarni na baka", haka yana ji yana gani Hajjah ta shige d'akin ta shima jiki a sabule ya mik'e had'e da ficewa harabar gidan..
Haka Yusif yayi zugun cikin tsananin damuwa sai ga Hajjah haka ta shiga mota yaja sai gidan Yaya Bashir.!
*(Wannan kenan!!! 😏)*
*FATIMA*
Koda Yusif ya fito haka tadai yita ciccin magani bani-bani taja tsaki ita dai Sadiyq na hankalce da'ita amma k'ala batace ba tadai ga magani bisa centre drawer, sai bayan magriba ta kawo mata abinci taci da taga batada alamun shan magani ta matsa mata, haka suka kwona da safe sadiya ta wuce gurin aiki bayan ta kawoma Fatima abinci, haka Fatima tananan kwonce jikinta duk a mace duk-da taji sauk'in jikinta sai d'an abinda ba'a rasa ba!
Ji tayi duk zama ya isheta ga kewar gida da nadamar abubuwan data aikata a baya, ga turirin wutar dake addabar zuciyarta na abinda Yusif yai mata, tsaki taja tana mik'ewa Fallo ta fito nanma kwonciya tayi bisa 3c gq kayan kallo amma batajin son komai ga ranta ga rashin wayarta wacce har i yau batasan takaman-men inda take ba!
Tananan kwonce har bacci ya fara fisgarta taji Sallamar cikin karaji ai kuwa da sauri ta d'ago tana k'ok'arin mik'ewa Yusif wanda ke biye Hajjah dw sauri yayo gurinta yana k'ok'arin taimaka mata ta tashi zaune "Sannuh" yai mata amma ta d'aga hannu alamar zata iyatashi zaune da kanta, haka ta mik'e zaune tana duban Hajja "Ina Kwona" ta gaidata ganin fuskar matar cike da kamala b'angaren Hajjah kuwa duk kwondon masifar da tazo dashi wanda ba halinta ba ganin Fatima ya sakata jin tausayinta farat d'aya domin taga hankalin yarinyar kuma batayi mata kama da mutuniyar banza ba, "Lafiya" Hajjah ya amsa a dak'ile kafin ta dubi Fatima tana cewa "je ki d'auko hijabinki mu tafi" da mamaki Fatima ta dubeta sai dai kworjinin matar ya hanata yi mata gardama zuciyarta na dukan goma-goma ta mik'e d'akin ta shiga ta sako hijabi ido biyu sukayi da Yusif cikin takaici ta banka masa harara tana d'auke idonta, sai addu'a take a ranta Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu.
Haka Hajjah ta tisata gaba har cikin mota duk baya suka shiga Yusif na jan motar.....
*Don't forget with share fisabililah don manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*E.t.c*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 41&42*
*GIDAN SU FATIMA*
.......Rayuwa kenan su Mama sunyi kuka har sun sakawa zuciyar su tawakali, dukda da sakacin Inna Mairi amma babu wanda ya furta magana marar dad'i a gareta daga Malam Mama har sauran dangi wa'enda yanzu labarin b'atar Fatima ya bi ko'ina! 'Yn uwa sin taya su Malam jaje anyi addu'a anyi saukar k'ur'ani ba adadi amma shuru Fatima kan sai ikon rabbi, har an cire ran ganinta sai dai mutum baya cire rai da rahmar ubangij.
Mama har kwonciya rashin lafiya tayi wanda har yanzu yau lafiya gobe ciwo ga tunanin mutuwar Mahaifiyarta ga kuma rashin Fatima, dukda haka bata tab'a sakawa ranta Fatima wurin yawon banza taje ba itadai ta d'auka Fatima ta fita anyi garkuwa da'ita tunda yanzu tsantsar ta'addanci kawai ake aikatawa, bata tab'a zargin 'yrta ba, tana rok'on ubangiji daya tsareta ya kareta da kariyarsa ya bayyanata indai har tana raye.....
"Yaya... Yaya" jin shuru bata amsa ba ya saka Inna Mairi tura kai cikin d'akin koda ta shiga Maman Fati na zaune gefen gadonta tayi tagumi hawaye bak'in ciki na zubowa daga kwormin idonta, "Subhanalla!" Inna mairi tayi tasalima tana d'ora kwonon abincin data shigo dashi bisa mirrow had'e da dawowa gefen Mama tana zama dafa kafad'ar Maman tayi tana kiran sunanta "Yaya..! Yaya fa" sai lokacin Maman Fati ta d'ago tana duban Mama had'e da cewa "Yaya don Allah ki gafarceni wallhy duk laifina ne, gashi yanzu na sakaki a matsala, Yaya don Allah ki yafemin" Inna Mairi ta k'arasa fad'a tana fashewa da Kukan nadama jawota jiki Mama tayi tana cewa "Haba *Mairi ta Malam* (haka Mama ke kiranta idan tana son tsokanarta) Mairi ni banga laifinki ba haka Allah ya nufa don sonki da Ma'aiki kada ki k'ara cewa laifinki ne, Mairi ta ki daina kuka koni ina kuka ne na bak'in ciki idan ma Garkuwa akayi da Fad'ima ai ya dace mu samu labari idan kuma mutuwa tayi gara muga ko gawarta ce kinga zamu cire tsammani.
"Yaya ki daina InshaAllah Fatima bata mutu ba kuma Allah zai bayyanata, Allah bai bamu 'yr'yr ba sai ita kuma InshaAllah Yaya zamuga 'yr'yn Fatima, Fad'ima zata haifa mana jikoki...... Inna Mairi ta k'arasa fad'a tana sakin kukan b'acin rai.
Haka Mama ke faman rarrashinta kafin su dawo rarrashin juna....
_*FATIMA😇*_
Yusif bai tsaya ko'ina ba sai gida horn yayi gateman ya bud'e tare da tura kan motar sa cikin gidan, itakam Fatima tayi matuk'ar mamakin ganin tangamemen gidan da suka shigo cikin tsoro a zuciyarta take cewa " Na shifa uku ni Fad'ima bakina zai bini idan k'arya nayiwa Hashim na cewa shi d'an yankar kai ne to yanzu gashi nan an kawoni gidan 'yn yankar kai", "Wayyo ni Fadima nasan hakk'in su Malam ne ke bibiyata...... Birkin d'in da Yusif yaja da k'aryi shi yayi silar dawowarta daga duniyar tunani " tsintar muryar Hajjah tayi tana cewa "Kai.. So kake ka karai-raya mu? Don an b'ata maka rai me zakayi? Aikin banza" Hajjah na faman fad'a ta juyo ga Fatima wacce ta tsira mata ido tsaki taja tana cewa "Ki fito muje" daga haka ta bud'e k'ofar ta fito itama Fatima cikin bugawar zuciya haka ta fito Hajjah na gaba Fatima na baya sai a k'ofar shiga main fallow suka tsaya k'wonk'wosa k'ararawa Hajjah tayi ba'a d'auki time ba aka bud'e Hadiza 'yr aiki ce har k'asa ta duk'a tana gaida Hajjah kafin ta bata hanya su wuce, Tangamemen fallo ne wanda ke d'auke da kujeru Royal set3 duk wani abu na alatu da k'awata guri to an k'awata wannan fallo idan nace zan zayyano muku to har mu gama wannan page bazan k'are ba.
Fatima ita bata ma lura da irin daular da ta shigo ba abu d'aya dai hankalinta yana ga k'arshenta ne yazo za'a fille kanta asha jininta ba tare data nemi gafarar su Inna ba! "Hadiza wannan bak'uwa ce kuma inaso ki d'auka tamkar aikin ku d'aya, ki kaita b'angaren ku acen zata zauna saiki samu aikin da zaki bata" a firgice Yusif ya d'ago yana duban Hajjah "Hajjah me kike cewa.... "saurin dakatar dashi tayi tana d'aga masa hannu had'e da daka masa tsawa, itadai Fatima duk tama rasa dame zata misalta rayuwarta k'ara duk'ar dakai Hadiza tayi tana cewa "an gama Hajiya" d'agowa tayi tana duban Fatima had'e da cewa "muje" haka Hadiza ta shiga Fatima na binta a baya sai b'angaren 'yn aiki koda suka je 'yn aikine su 6 ko wanne da aikin sa Salame, Hadiza, Rakiya, Saude, Habi, Ladingo duk sun girme Fatima Rakiya ce kawai yarinya, gurin dukda babu wata k'azantar amma babu dad'in zama kam ga mutum mai hali kamar Fatima tayi amai gefen hijabinta ta saka tana toshe hancin ta dubanta Hadiza tayi tana cewa "Iyye lalle 'yr nan kin samu guri yanzu mu kike toshewa hanci kamar kega kashi?? Ai kesan komai lalacewar assibiti tafi kasuwa sauke hannunki" Hadiza ta k'arasa fad'a tana fisge hannun Fatima data toshe hanci Salame ce ta dubi Hadiza tana cewa "keko Hadiza wannan wacece??" tayi tambayar tana nuna Fatima.
"Hmmm..! Wallhy Salame sabuwar mai aikice Hajiya ta samo, kinga zata rik'a rage muna ayyuka", " Ah lallai kam kinga sai ta rik'a tayamu aikin kitchen ko" Salame ta k'arashe maganarta tana washe hak'ora itadai Hadiza komai batace ba illa hararar Fatima da tayi tana cewa "kinyi mana tsaye cirko....
....."Hajjah don Allah wai me nayi miki? Hajjah wallahi Fatima bata da wani aibu kuma sonta nake har zuciyata...." Kaga Malam dakata! Ka sani ni ba shasha-sha bace ai taimakonta nayi da har na d'auketa 'yr aikin gidana kasan me nake so dakai? Yanzu kaje ka saketa imma har da gaske kake an d'aura muku aure shikenan sai tayi zaman 'yr aiki kaga magama maraba ko?".
"Hajjaju haba Ummoul don Allah nasan zuciyar imani gareki Ummi muba.... Dakatawa yayi ganin Hakkah ta shige d'aki tana cewa " Kanka ake ji" cikin jin tsananin azabar ruhi da tunanin wannan kuma wacce iriyar kaddarace? Wannnan wane irin iftilahi ne? Yaushe halayen Hajjah suka cenza? Shin meke shirin Faruwa.... Har ya share dogon lokaci yana wa'ennan tunanukkan.
Da k'yar ya samu ya koma B'angaren sa gabaki d'aya ji yake rayuwar sa na juyawa juyin masa, dafe kansa yayi yana tunanin mafita sedai mafita d'aya ce ALHAJI! Alhaji shi kad'ai ne zai iya takawa Hajjah birki saboda haka Alhaji ne kawai ze gayawa da wannan tunanin har lokaci ya tafi bai sani ba saiji yayi ana kiran Sallar azhr daga azhur ar la'sr da magrib duk a d'aki yayi su...
*FATIMA*
Cikin su babu wanda yace da ita k'ala hirarrakin su suke suna kwosar dariya, Sai gurin 12:00pm Hadiza tace to sai a kama aiki shabiyu tayi duk mik'ewa sukayi suka fice aka bar Fatima ita d'aya, had'e kai tayi da guiwa tana kuka wanda duk wanda ya ganta a wannan halin saita basa tausayi....
A wannan karon babu wanda yace mata uffan saima abincin da aka baiwa Ladingo ta kawo mata wanda bai wuce loma 6 ba, haka yunwa ta addabeta dole taci, Da maraici suka gargad'ota kitchen da'ita da Salame, Habi, Ladingo haka suka shiga kitchen duk wani aikin wahala ita aka tulawa babu yanda zatayi haka suka kammala girki wanda ya d'aukesu awa 3 sai magriba suka kammala nan aka en mata d'an tsakure duk jikinta a wahalce ta koma shiga d'aki....
*YUSIF*
Yananan yana dakon juran shigowar Wlhaji sai 09:00pm ya fito yana shiga Fallo Hajja ce kawai zaune ta tsurawa tv ido tana kallon labarai, zama yayi gefenta kallon sa tayi cike da tausayawa tana cewa "yau duk baka fito ba, bakaci abinci ba tun breakfast Lafiya kuwa Yusif??" murmushin da yafi kuka ciwo Yayi yana duban Hajjah kafin a ransa yace "Allah mai iko, Hajjah kamar batasan komai ba!" (oh Yusif imma Hajja ce tama manta😄).
"Hajjah maganar Fatima... " saurin katsesa tayi tana cewa "au wai har ka saketan" a firgice ya d'ago yana duban Hajjah had'e da cewa "don Allah Hajjah kiyi hak'uri, ni ban damu da asalin Fatima ba kawai ina sonta kuma Fatima *TSARINA CE* Hajjah don Allah kada ki rabani da ita" duk maviyar da yake Hajjah tayi kamar bataji har ya gaji don kansa yayi shuru.
Sallsmar Alhaji ce ta dawo dashi daga duniyar tunani, d'agowa sukayi su duka "Alhaji sai yanzu ka dawo??".
" A'a Son gurin aiki dai na shekara nadai dawo da masjid, kuma yau duk ban ganka ba na tambayi Mamanku tace baka gidan", Alhaji ya k'arasa Fad'a yana zama gefen Yusif d'in.
A marairaice ya d'ago yana duban Alhaji cikin fuskar tausayi shafa kansa yayi yana cewa "Lafiya kuma Yusufa, menene? ".
"Alhaji abubuwa masu yawa don Allah nidai ka yafemin kaji? Alhaji na aikata maka laifuka masu yawa.. " saurin dakatar dashi Alhaji yayi yana cewa "miye haka Yusif? Don Allah ka daina me kayi mini, nidai nasan baka aikatamin ko wanne laifiba!.".
" Hmmm.. Ai dole yace haka Alhaji, to aure yayi" Hajjah tayi maganar wacce Alhaji yajita a matuk'ar mamaki...
"Me? Aure Yusif aure?".
" Alhaji aure yayi kuma yanzu hakan matar tananan cikin wannan gidan".
"Innalillahi wa'inna ilaihin raji'um, Yusif da gaske aure kayi?" Alhaji ya tambayi Yusif yana kallon sa don tabbatarwa.
"Alhaji ka yafemin da gaske Aure nayi, kuma wallahi sonta nake, Abba sonta nake Abba *TSARINA CE*...
Hajjah ce ta daka masa tsawa tana cewa " yima mutane shuru" shidai Alhaji daga nan mik'ewa yayu ya haye upstairs ya shige d'aki, duban Yusif Hajiya tayi tana cewa "sai ka k'ara kaimi har ka kashesa" haka itama ta wuce koda ta samu Alhaji itace ta gaya masa komai abinda Yusif ya sanarmata da kuma d'auko Fatiman da tayi da hukuncin data yanke shidai komai baice mata ba domin jin abin yake kamar Almara.
```BAYAN KWONA BIYU```
Rayuwar Fatima gidansu Yusif tamkar Rayuwar kurkuku, Rayuwa ta mata juyin waina a dadd'aureta da igiyoyi an sarkafo ana shillo tamkar lilo, jinta take cikin k'unci da azabar rahi bata tab'a tunanin rayuwa zata maidata haka ba, kullum tunaninta yaushe zata nemi gafarar iyayenta? Domin gafarar ubangiji kam kulun cikin nema take ba dare ba rana, gashi daga kitchen sai d'aki kullum cikin tsangomarta suke ba sassauci, sun maidata ma wani d'aki babu komai ciki...
YUSIF
B'angaren Yusif shima dai tun da sukayi magana da Alhaji baice masa komai ba, daya d'auko masa zantukan Fatima Alhaji ke dakatar dashi daga k'arshe shida suka Abdul suka samesa wanda dak'yar ya amincr ya rakasa don gani yake duk laifin Yusif.
Duban su Alhaji yayi kafin yace "To ku da kuka kwoso k'afa kukazo me kukeso nai muku? ", Abdul ne ya gyara zama yana dubansa had'e da cewa "Alhaji don Allah kayi hak'uri ka saka baki Hajjah ta yafewa Yusif wallahi duk munada laifi kuma yana son Fatima".
"Naji amma taya zaku aikata hakan ba tareda sanin iyayenku ba? Ehye ai hakan bai dace ba kunyi babban kuskure saboda kunga ni banma da tabbacin k'arya kuke ko gaskiya".
"Wallahi Alhaji da gaske an d'aura auren barima muje dakai har gurin limamin daya d'aura auren".
" to naji Amma bari na kira Hajja muni me zatacs".
Waya Alhaji ya saka ya kira Hajjah babu jimawa gara kallo d'aya tayi musu tana d'auke kai had'e da tamke fuska duk gaidata sukayi amma kamae bataji ba, zama tayi gefen Alhaji tana cewa "gani Alhaji".
Sauke numfashi Alhaji yayi yana cewa " shin menene hukuncin da kika yanke??" saida tayi jin tana jin tausayin Yusif da kuma na Fatim kafin ta iya cewa "Alhaji ya saketa in yasso sak taci gaba da zama matsayin 'yr aikin gidannan!" a firgice duk suka d'ago Alhaji ne yace "kiyi hak'uri ki sassauta, Maikud'i, Talaka, baki, fari, dogo, guntu, gajere, mummuna, kyakyawa duk Ubangiji ya haliccemu kuma aduk yanda mukafa kanmu shine yaso ya ganmu haka, Hajjah hukuncin baiyi ba Fatima a yanda naji labarinta marainiya ce abar a tausayawa, minga kuwa bai dace ta zamto abar k'yama a garemu ba kawai ki barau su zauna tare ki'la hakan shine yafi zama alheri".
" hmm! Naji kuma na amince sedai da sharad'i".
Duk sunji dadin amincewarta sedai sharad'in menene.....
*WANE SHARAD'INE KUKE TUNANIN HAJJAH TA GINDAYA?*
*Don't forget with share fisabililah don manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*E.t.c*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 43&44*
..........."Yusif d'a na kowa ne, saboda haka sharad'in shine, kaje ka nemo shi k'anen Mahaifin Fatima, ka rok'esa idan ya baka aurenta shikenan, wannan shine sharadin nawa!" da kallo suka bita kafin ta mik'e tayi wucewarta, maida akalar kallon su sukayi ga Daddy "Daddy don Allah.... Saurin dakatar dashi Daddy yayi ta hanyar cewa "dakata Yusif, kawai kayi abinda tace" shima Daddy barin fallon yayi "innalilahi wa'inna ilaihin raji'um" d'an hararar sa Abdul yayi yana cewa "wane Innalilahi ai komai ma ya faru kaine ka jawo, ni ba haka na tsara ba, kwota-kwota duk ka b'ata muna shiri".....
*AFTER ONE MONTH*
_*GIDAN SU FATIMA*_
Allahu akbar kwota-kwota Rayuwa ta sauya musu, akoda yaushe idan ka shiga gidan kamar gidan mutuwa, tabbas komai ya faru da bawa to haka Ubangiji ya kudurta masa kuma wannan abin shine dai-dai, sun daina kuka yanzu saidai kukan zuci, abubuwa sunyiwa Mama yawa wanda zuciyarta ta kasa d'auka har yayi silar kwonciyarta asibiti cikin wani hali wato rai da rayuwa.
Tana tunanin 'yarta mafi soyuwa a zuk'atansu wacce itace d'aya tilo da Sarkin dake rayawa ya mallaka musu, amma yanzu ta yimusu nisa, nisan da saidai su hadu a darrusalam, ta cire rayuwar Fatima a ranta domin tasan har abada idan dai Fatima na numfashi to ba zata taba barin su ba, ba zata tafi ta barsu ba, amma ina Fatima ta tafi, abubuwa sun mamaye zuciyarta cikin jimamin mutuwar uwa kuma ga wannan......
Yanzu dai Mama na asibiti rai ko rayuwa.
*Ya ubangiji ka saka muna tausayi da jink'an iyayen mu a zukatan mu, ya Allah kasa mu kyautatawa iyayen mu har lokacin da zaka rabamu, Ya ubangiji ka dawwamar da Farin-ciki a zuciyar iyayen mu, Ya ubangiji ka baiwa iyayen lafiya mai amfani, ya sarkin da babu na biyun sa ka k'ara mana jinkiri da iyayen mu, Allah alfarmar sayyidulwarrah kasa mu mutu cikin salihai bayin Allah duk musilman duniya wa'enda sukabi hanya madai-daiciya, su kuwa wa'enda suka kauce Ubangiji ka ganar dasu gaskiya.
****
Zaune take gefen katifar d'akin nasu na 'yn aiki, tayi tagumi, tayi nisa cikin duniyar tunani sai hawaye ke kworanya daga idanunta, zuciyarta a chunkushe.. Firgigit ta dawo daga duniyar tunani jin kiran da Rakiya ke k'wola mata, hankali a tashe ta mik'e ko kafin ta fito har Rakiya ta shigo dakin "ke don luguden iskanci har ina kiran ki ba zaki fito ba? Don ubanki wa kike so yai miki aiki? To kije kuci gaba da aiki keda Ladingo da Habi idan ba haka ba naci mutuncinki"... Ita dai idanu kawai ta tsura mata tana kallonta har ta gama Masifarta ta fice, share hawaye tayi kafin tace " Ya Allah ka fitar dani daga wannan rayuwar bauta" fitowa tayi tana tafiya tamkar wacce kwoi ya fashewa a ciki, yau watan ta daya da wani abu amma bata tab'a haduwa da wani mahaluki ba bayan su Hadiza, Salame, Ladingo, Rakiya, Saude, Habi, su kad'ai ne take Rayuwa dasu rayuwar bak'in ciki da nadama, tayi nadama har babu iyaka...
Girki suka shigayi duk a daddafe take gudanar da ayyukan saboda yanayin jikin da takejin babu dad'i, Salame ce ta harareta tana cewa "kewai Fatima wane irin iskanci ne? Kina aiki kamar bakya son yi? Ai wallahi ko mutuwa zakiyi sai kinyi wannan aikin", cikin karfin halin dole Fatima ke cewa "wallahi Inna Salame banida lafita..." saurin dakatar da ita Salame tayi tana cewa "ke dakata na rantse da Allah kada ki koma kirana da Inna saboda ni baahaifiyarki bace, ni banda 'yar 'yr iska, sannan wallahi komi talauci na bazan kawo 'yarta kamar ki aikatau ba! Saboda haka kada ki koma kirana Inna aikine ya kawoni kema shi ya kawoki saboda haka kowa tashi ta fisheshi". Fatima tayi kunnen uwar sheggu da ita kamar da iska take magana, albasa kawai take yanka ko wannan ya isheta abinda tafi tsaka kenan mugun hawan mata kai albasa keyi....
*_YUSIF_*
.... " Abdul Hajjah Thru Hinderer me Beholds Fatima, Necessitated Belonging Enlist Irreversibly, ina ganin babu wani azzalumi daya kaini, na cuci Fatima ba zalumceta, Abdul ina nasan zan samo danginta? ta hanani ganinra balle tamin bayani, wallahi Hajjah na sane tamin haka, amma wallahi ko duniya zata taru bisa kaina ni da Fatima sai mutuwa".
"Yusif wannan duk ba mafita bace, kawai kaci gaba da lallab'a Hajjaju har lokacin da zata sauko" d'an jim Yusif yayi kafin yace "Abdul zan kira Maryamu idan da lokaci tazo, idan tazo sai nayi mata bayanin duk abinda ake ciki, inada yak'inin InshaAllah Hajjah zata saurareta kuma zataji maganarta." "to Yusif Allah yasa"...
*Juma'at*
_07:00pm_
Ring d'aya tayi picking tun kafin yayi magana tace " kai kai wai Yusif ne kuwa kodai mafalki nake? Yaushe rabo?" dan sauke ajiyar zuciya yayi yana cewa "baki bari mu gaisa?" "nama manta k'anina wallahi gani nake kamar almara wai kaine da kirana hmmm! Lallai".
" Antyyyyy" ya kira sunanta kafin ya d'ora da fad'in "Anty Maryamu ya bayan rabuwa? Ya gidan?".
" Lafiya k'alau Alhamdull fatan komai lafiya??" saida yayi jim kafin yace "Anty da dama dai, wallahi akwai matsala b'angarena...." katsesa tayi da fad'in "subhanalla na shigesu ni Maryam meyake faruwa?, lafiya? Don Allah ka sanar dani"! Ganin yanda tayi bala'in rikicewa ya saka Yusif sakin dariyar da baiyi niyya ba "please ki kwontar da halinki" wata doguwar ajiyar zuciya Maryam ta sauke kafin tace "Alhamdullahi, ai da dama to sai ka gayamin miye??" gyara zama Yusif yayi kafin ya zayyanewa Anty Maryam komai da komai sai dan abinda ba'a rasa ba, dorawa yayi da fad'in "Anty don Allah kizo kiyiwa Hajjah magana ko ke zataji maganarki, sannan kuwa wannan ya zama sirri a tsakanin mu biyu, kada zuwanki gida ya fito da wannan maganar kinji Morality sister ('yar uwa mai halin kirki)", cikin al'ajabi had'e da d'unbin tausayi Maryar ke cewa " kada ka damu k'anina, InshaAllah k'arshen wannan watan zanzo, kuwa na maka alk'awarin wannan har abada ya zamto tsakanin mu biyu, zan lallab'a Hajjah kuma insha Allah zata fahimta". Cikin farin ciki Yusif ya shiga zuba mata godiyar tsananin farin ciki "Anty nagode allah ya baki arzikin duniya da lahira, ubangiji ya tsare gabanki da bayanmi", dariya kawai Anty Marya tayi tana cewa " you are the one and only my Beloved brother wa zanso tamkar kai??" cikin k'ara son yayar tasa yace "babu Anty Allah yabar zumunci" da Amim ta ansa kafin suyi sallama.
Zugum yayi yana tunanin Fatima wabda dai-dai da second d'aya bai tab'a barin zuciyar sa ba, yana kewarta fiye da misali, yana tausayinta tamkar duk wata wahalar duniya ya dauke mata, itace ciwon idanunsa.
Sai sak'e-sak'en abuwa masu yawa yake a zuciyar sa, wata zuciyar sa ce ta ayyana masa a rai 'Idan fa bata sonka?' da k'arfi yace inahhhh Fatima ba zata min haka ba.......
*Don't forget with share fisabililah don manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*E.t.c*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 45&46*
```FATIMA```
..........A daddafe ta kammala sallar la'asar, addu'a taci gaba dayi tana rok'on ubangiji akan ya kub'utar da ita, yaunwar dake addabarta ce ta sakata mik'ewa.
Koda ta fito tun kafin ta shiga kitchen ta fara jiyo dariyar su Salame sai hiraraki suke, ai kuwa kamar d'aukewar ruwan sama wanzuwarta a gurin saima hararar da suka shiga zabga mata lokaci guda duk taji ta tsargu, Habi ce tace "ke don ubanki sai kizo kiyiwa mutane tsaye? Bak'ar munafuka to wallahi idan ma maita kika fara sai dai kici kanki mu munfi k'arfin ki" wani iri takeji ita duk basa gabanta ji take kamar ta mutu akan tsanani yunwa tamkar ana yankan 'yar'yan cikin ta cikin sanyin murya ta fara magana "Inna Habi don Allah ki taimaka min wallahi yunwa nakeji kamar zata kasheni" duk kallon sa sukayi kafin su k'yalk'yace da dariya Habi na cewa "lallai Fatima kinga walle na, to ai dama naga alamun kin fara maita saidai kici kanki, idan zaki zo aci gaba da girki kizo idan ba haka ba ke da Hadiza" Salame ce tace ke ko Habi bari a karkaro mata ko k'anzo", "ke Salame ina mukaga k'anzo? Har wane girki muke da zamu fitar da k'anzo tab lallai" dubanta Salame tayi tana k'ok'arin danne dariyarta domin ita tana da sauran imani, duban Fatima tayi had'e da cewa "ayya Fatima kiyi hak'uri, idan an kammala girkin dare za'a kawo miki, jeki ki futa", cikin azabtuwa harma ko tsayuwa na gagararta ta dubi Salame cikin fuskar tausayi tana cewa " don Allah ki taimaka min ko kingin masu gadi ne, wallahi zan mutu idan banci abinci ba d'iyan hanji na sun k'ulle" tankawa yabawa k'yalewa babban wulak'anci haka sukayi biris da Fatima.
Ganin duk sunyi banza da ita ya saka ta ficewa daga kitchen d'aki ta koma tayi kwonciyarta sai dai ta kasa sukuni, mtws taja tsaki tana mik'ewa domin zuwa nemo abinci kota halin Yaya.
Rana ta farko da tayi tunanin shiga main fallon gidan tun ranar data shigo gidan, da zummar samun damar ficewa daga gidan.
Tun da ta durfafo fallon take jin alamun magan-maganun mutane dole ta sakata komawa, haka Fatima ta wuni sai bayan kammala dinner aka kawo mata d'an abincin wanda bai wuce loma 5 ko 6 ba.
*MAMAN FATI*
Saida suka share sati biyu cif cif kafin a sallamosu daga assibitu, bayan sun dawo gida ta d'an warware domin tana magana amma ba sosai gashi doctor yace tana gab da kamuwa da ciwon zuciya.
Ganin ta kasa fitar da abin a ranta duk da yanda sukazo mantar da ita amma ina abin yaci tura har Inna Mairi wacce itama tunanin duniya duk ya isheta, sai da Inno tace 'yarta Suwaiba tazo ta tayata zama tana d'ebe mata kewa.
```YUSIF```
B'angaren Yusif ya kwontar da hankalin sa k'orai jiran zuwan Anty Maryam kawai yake, sai dai tunanin Fatima kawai dake addabar sa kawai babu yanda ya iya, kwota-kwota maganar Fatima bata sake had'asa da Hajjah ba ko Alhaji, kullum dai suna k'ara tattaunawa tsakanin sa da Abdul wanda cikin wannan lokacin Alhaji yaci gaba da ginin assibitin da yakeyi shida Daddyn su Abdul.
A lokacin jikin Daddy yayi sauk'i sosai yana magana kuma yana cin abinci sai dai harma fita sai dai cikin gida kawai baya fita waje kullum sai Alhaji yaje gidan aminin nasa.....
_Fatima_
*12:11pm*
Cikin nannauyan baccin daya d'auketa ta zabura sakamakon kukan da cikin keyi cikin jin yunwa, mik'ewa tayi tana taslima kafin ta d'ora hannu a ka tana cewa "wayyo Allah na shiga uku ni Fatima, wannan yunwar dake addabar cikina ina zaki da'ita" ta k'arasa cikin tambaya alhalin babu mai amsa mata, mik'ewa tayi ganin d'akin dulun-dulun lalabawa tayi gefen ta Rakiya ce sauke numfashi tayi kafin ta dafa katifar tana mik'ewa batasan lokacin data koma ba jin k'afafuwanta sun gaza d'aukarta, takai minti biyar kafin ta sake k'ok'arin mik'ewa, cikin lalabe har ta samu ta fito daga d'aki ko'ina dif ba hasken lankarki koda ta shiga kitchen tsoro ne ya kamata ganin yama fi ko'ina duhu, haske ta hanga ta main falo wanda hasken ke kutsowa a window store daga kitchen, tunani tayi kodai ubangiji ne ya kawo mata mafitar fita daga gidan? Ai kuwa daram tunanin ya zaunu a zuciyarta.
First time shigowarta fallon gidan tun lokacin data takok'afarta cikin gidan, kalon falon ta shigayi ko'ina tsaf-tsaf gwonin birgewa, falon nada girma sosai, k'ofar fita daga fallon ta nufa sai dai ta kasa bud'ewa duk iya yinta dfe goshinta tayi ganin alamun an rufe k'ofar da key! hawaye ne suka shiga kworanya daga idanunta na tsananin damuwa batasan lokacin data durk'ushe gurin ba tana sakin kuka mai ciwo.......
*My Bloodstream* kamar daga sama wanda taji maganar gab da ita, gefen hijab d'inta ta saka tana goge hawayen ta kafin ta fara d'agowa ahankali tun daga doguwar k'afarsa fara tas mai d'auke da kyawawan 'yn yatsu, tun kafin tayi tozali da fuskarta gabanta ya fara faduwa zuciyarta na bugawa da k'arfi a firgice ta mik'e tozali da tayi da fuska mafi muni a gareta, fuskar mutumen data tsana fiye da mutuwarta wanda yayi sanadiyyar rugujewar farin cikin ta, kallo d'aya tai masa tana jaye fuskarta gefe had'e da k'ok'arin barin gurin.... Chak ta tsaya sakamakon hannunta daya rik'o ba tare da ta juyo ba tayi k'ok'arin danne kukan ta tana cewa "Don Allah, indai har annabi ya isa da kai ka sakemin hannu, Yusif na tsani kallon fuskarka wallahi itace abu mafi muni dana tsana, bana k'aunar ganin ka, ka cuceni, ka zalumceni, ka yaudareni, ka sakani a mafi k'ask'antar rayuw... Katsewa maganarta tayi jin ya wani birkitoto kafin ya d'ora hannyen sa bisa kafad'unta jijjigata ya shiga yi yana cewa "Fati... Fati... Fatima ki natsu, Fatima ban had'u dake ba da niyyar cutar ki, Fatima wallahi ni taimakon ki nake da niyya, Fatima wallahi sonki nake fiye da rayuwata, kece bugun numfashi na, kec... Da k'arfi ta saka hannu bibbiyu tana turesa gefe kafin taja baya cikin d'an d'aga murya ta shiga fad'in "bana sonka ka cuceni kaci amanata, ka rabani da mutuncina ka kawoni gidan bauta an kassaramin rayuwa..! Ganin ya nufota ya sakata arcewa tana komawa d'aki mantawa ma tayi dq yunwar cikin ta, zama tayi tana had'e kai da gwuiwa ta shiga rubza kuka wanda sautin sa baya fita sosai....
****
Hajjah wacce duk wannan abin ya faru akan idonta, hangen wutar falon a kunne ya fito da ita dama Yusif aka bari da niyyar ya kashe wutar da sauran electric.
Wucewar Fatima da kalaman data yab'a masa suka haddasa masa raunin zuciya, bin bayanta yayi sedai tsintar muryar Hajjah yayi tana cewa dakata! Kafin ta k'arasa saukowa daga step d'in "Yusif dama bakayi bacci ba??" Hajjah tayi tambayar cikin basarwa tana nuna alamar saukowarta kenan, sannan bata gane yanayin da yake ciki ba, ganin wannan abin ya saka Yusif k'ok'arin dai-daita nutsuwar sa kafin yace "Hajja yanzu zan wuce" kai kawai ta jijjiga masa alamun to kafin tana kallon sa ya cenza akalar tafiyar sa zuwa b'angaren sa, saida ya b'acewa ganinta kafin ta kashe ko'ina......
_*Fatima*_
Yanda taga rana haka taga dare bata runtsa ba tana nan dai inta tab'a kuka tad'an sassauta sai kuma cen taci gaba, daga k'arshen da kwonce aka koma kukan ganin kamar zata iya tada Rakiya yanzu ta balbaleta da masifa ya sakata sa gefen hijab tana toshe bakinta kada kukan ya fito😭 _(sannu Fatima😜)_ saida taji kiran fari a kunnuwanta batasan sanda ta mik'e ba, takai minti 2 rana kallon d'akin wanda take fatar ubangiji yasa wannan fitar da zatayi ta kasance ta k'arshe, duk da ko'ina d'if babu haske amma haka tabi d'akinda kallo tsawon minti 2 kafin ta fito kitchen ta shiga window dake saiti da gate d'in gidan ta yaye labule tana lek'awa saidai ko haske babu in bana lantarki ba, tananan gurin har akayi kiran sallah tana tsaye gurin ta tsura gate d'in gidan ido kamar mai kallkn wata darehud'ua sha hud'u, har dai-dai lokacin da mai gadi ya fito alwala yayi kafin ya wuce taso sauran ma'aikatan gidan, kamar, driver, masu baiwa flowers ruwa, masu wankin abubuwa kamar mota da dai sauran su, duk alwala sukayi suna batun wucewa k'aton maslacin wanda yake manne da gidan, Alhaji ne ya fito cikin kamala sanye da jallabiya fara a tare suka fito shiga Yusif rana ta farko da taga Mai gidan a hankali ta furta "Albasa batayi halin ruwa ba" (oh ni 'yar nan wai dama Fatima tasan halin Daddy ne da zatace haka? Ba ruwa na ita da fan's d'in Yusif😂).
Duk'ar da kanta tai domin ta tsani ganin Yusif kusan minti 2 kafin ta d'ago babu kowa duk sun fice zuwa masalaci, sauke numfashi tayi tana alla allah domin tasan yanzu su Hadiza zasu fito, ficewa tayi daga kitchen d'in koda ta kawo k'ofar falo ta mud'a kenan taji an turo k'ofar saurin komawa baya tayi tana lab'ewa bayan ganbun har Hajjah ta shigo amma bataira da ita ba d'akunan masu aiki ta nufa sai zantuka take "nasan basu tashi daga bacci ba, bari nayi sauri kada mutun ya makara gurin sallah", tana wucewa Fatima ta fito cikin sassarfa ta shige falo bud'ewa tayi wani irin farin ciki ne ya shigeta bayyanarta harabar gidan wata daya da kwonaki gata tasha iskar ubangiji bata bata lokaci ba ta isa bakin gate kiciniyar bud'e k'ofar tashiga yi amma ta kasa, sai tura ganbum take dak'yar ta samu bud'e k'ofar tana fitowa ta yanki titi gudu take bil hakk'i iya k'arfinta, titine ya yanka babu iyaka unguwar tsit babu alamun ko tsun-tsu gidaje k'erarri amma ita Fatima batama lura da komai ba sharara gudu kawai take iya k'arfinta.....
Takai kusan minti 10 tana gudu saida ta fito daga layin kafin ta fad'i k'asa tana maida numfashin wahala cikin ta ya wani k'ulle ko iya tashi batayi, dak'yar ta mik'e zaune gefen titin hannu ta shiga d'agawa alamun taimako amma shuru babu alamun mota, takai kusan minti 10 gurin kafin ta iya mik'ewa gefen cikinta ta dafe a haka ta shiga tafiya a daddafe tana sauke ajiyar zuciya a jejjere.
Haka su Fatima taci gaba da tafiya gefen titi duk jikinta yayi gala-gala gashi har rana ta fara ketowa, motar data hango ce ta shiga d'agawa hannu tana dudduk'ewa domin k'arfinta ya k'are, tsayawa motar tayi kafin wacce ke cikin motar ta fito.
Wata mata ce wacce a k'allan zatayi shekaru 36! cikin tashin hankali ta dubi Fatima kafin tayi taslima tana k'arasawa gurin Fatima rik'ota tayi tana d'ago da kanta kafin tace "baiwar Allah lafiya? Meya sameki??" cikin aron jarumta Fatima ta fara tattato zancen tana cewa "don Allah ki kaini gidan mu, satoni akayi na gudo" cikin tausayawa matar tace "subhanallah" kafin matar ta d'ora da fad'in "inane gidan ku" "nidai mu tafi kinji" kama Fatima matar tayi ta sakata a mota dishi-dishi Fatima ke gani haka ta shiga yiwa matar kwotance sai k'ofar gidan su "nan ne" Fatima ta baiwa matar amsa kafin tace "Okey" tana parking motar bakin gidan Fatima batama jira matar ba ta b'alle murfin motar da gudu tayi cikin gida ba tare data lura da abinda yqke gabanta ba.
Fitowar Mama kenan daga kitchen zuciyarta ce tayi kusan tarwatsewa tozali da tayi da halitar data kasance rabin jikin ta, numfashinta ne ya d'auke na wucin gadi, saurin k'arasowa tayi gaban Fatima wacce keta maida numfashi Fad'ima, Fad'ima suuuu sai ganin Fatima tayi ta fad'i k'asa sumammiya "Innalilahi wa'inna ilaihin raji'um, jama'a ku taimakeni, innalilahi.." a firgice Inna Mairi ta fito wanda yayi dai-dai da shigowar wannan matar cikin gidan, ga baki d'aya kan Fatima sukayi Inna Mairi cikin matuk'ar mamaki itace tayi k'arfi halin d'ebo ruwa aka yayyafawa Fatima amma shuru, wannan matar ce wacce kosu Inna Mairi basuyi tunanin tambayar wacece ba kama Fatima sukayi ita da Inna Mairi Mama da ko mayafi batada tabi bayan su.
A mota suka saka Fatima Inna Mairi na cewa "Yaya ki koma ki sako mayafi" girgiza kai Mama tayi tana cewa "A'a Mairi bazan iya komawa nabar Fad'ima ba " Inna Mairin ce dole ta koma ta d'auko mata mayafi haka Matar nan taja mota sai assibiti mafi kusa, emergency aka shige da Fatima duk sunyi cirko cirko.
Inna Mairi ce tayi k'arfin halin cewa "Yaya gashi su Malam basuda labari" cikin danne kukan da yake k'ok'arin kufce mata tace "Mairi ya zamuyi? Ko waya bamu fito da ita ba" duk basu lura da fitowar da doctor yayi ba sai Matar nan ce gurinsa ta k'arasa tana cewa "Doctor how Huh Patient?, i hope Their Agitate" sauke numfashi doctor yayi yana cewa muje office nai muku bayani sai lokacin su Mama suka haka suka biyosa sai office d'insa duk zama sukayi banda Mama da tayi tsaye tana cewa "don Allah ka taimakemu, wallahi daga ni har Malam da Mairi ita d'aya muka mallaka" Mama ta k'arasa fad'a cikin fuskar tausayi, murmushi Doctor yayi yana cewa "ba komai ki zauna" girgiza kai kawai Mama tayi do tor ne ya d'aura da fad'in....
Da farko tayi matuk'ar saka damuwa a zuciyarta, sannan bata samun ishashiyar kulawa musamman saboda lalurar ta, damuwa tai tama yawa har ta haifar mata da hawan jini wanda ba wani abin damuwa bane domin yawanci masu fama da lalura irin tata suna samun wannan matsalar na wucin gadi, sedai tana buk'atar kulawa saboda abin kada ya shafi abin dake cikin cikin ta......
_*(😂😂😂😂 Fan's d'in Fatima a shiryawa shagli🎉🎉🎊🎊)*_
"Likita ci me?" k'ara duban Mama Doctor yayi ganin yanda ta firgice yana cewa "eh ciki, ciki mana ko bakusan dashi ba" "Innalilahi wa'inna ilaihin raji'um shine abinda suke mai-maitawa daga Mama har Inna Mairi, Mama ce takai zaune k'asan Carpet tana cewa " wannan wace iriyar masifa ce Fatima cikin shege? Wayyo Allah na dama Fatima ta mutu da yafimin da wannan masifar dake tunkarar mu, Fatima halinki ne ke bibiyar harmu iyayenki Fatima.......
*Don't forget with share fisabililah don manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*E.t.c*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 47&48*
_Second to the last_
..... Wannan matar ce tayi k'ok'arin tsayar da Mama daga zantukan da takeyi wanda duk ta fita hayyacinta batama san me take fad'a ba "haba Mama don Allah kidaina, abi lamarin a sannu" "baiwar Allah Fatima bata kyauta mana ba" Inna Mairi ce ta tayar da Mama, duk abinda ake buk'ata wannan Matar ce ta biya komai, basu zarce ko'ina ba sai d'akin hutun da aka kwontar da Fatima.
Tana kwonce fuskarta tayi farau, sai bacci take sha wanda da ganin sa kaga baccin gajiya an d'aura mata a hannu, Inna Mairi ce tayi saurin k'arasawa a gareta tana shafa goshinta had'e da cewa "Sannu Fad'ima, ubangiji ya baki lafiya" Inna Mairi ta ida fad'ar haka tana duban cikin Fatima wanda yake a shafe gani take kamar almara wai Fatima da ciki.
Matar ce ta dubesu tana cewa "Mama ni zan wuce, Insha Allah anjima zan dawo idan na samu lokaci, ayi hak'uri komi zai zo da sauk'i" ita dai Mama batace komai ba sai Inna Mairi ce ke cewa "Mungode baiwar Allah ubangiji ya saka da alkairi" "Amin" haka matar ta wucewarta wacce ko sunanta babu wanda ya tambaya domin hankalin su baima kawo nan ba.
*GIDAN SU YUSIF*
bayan duk sunyi Sallah sannan aka fara aikace-aikacen gida Salame ce wacce ke fere doya ta dubi Habi wacce ke suya kwai "a to kanta, kesan yanzu yarinyar wani isakanci takeji dashi, gashi Hadiza tace wai Hajiya tace a daina sakata aiki" Habi ta k'arasa fad'a tana tab'e baki "hmn, lallai namu ido ne".
Babu wanda ya k'ara cewa komai har suka kammala girki, Habi ce ta mik'ama Rakiya break fast faranti tana cewa " kaima waccen abinci" karb'a Rakiya tayi tana ficewa d'aki ta shiga sai dai wayam babu Fatima babu alamarta, kuma fa tare suka kwota, ajiye abincin tayi tana fitowa kewayen su ta zagaya kwon-kwosawa tayi tana cewa "Fatima Fatima.. Kina ciki??" jin shuru ya saka tura k'ofar kewayen ganin tayi babu kowa juyowa tayi da Ladingo taci karo a firgice ta rik'o Ladingo tana cewa "waalahi Ladingo Fatima na kawowa abinci amma na duba ko'ina ban ganta ba". "Innalilahi wa'inna ilaihim raji'um" Ladingo tayi taslima tana komawa Kewayen domin ta ganewa idonta! Ai kuwa hakane kamar yanda Rakiya ta fad'a a firgice ta rik'o hannun Rakiya sai d'ayan d'aki cikin tashin hankali, su Hadiza ce da Salame zaune suna karyawa "Hadiza Salame wallahi Fatima bata nan, ko'ina mun duba" soyayyar doya da kwai data d'auko da niyyar afkawa bakinta ta sub'uce mata "subhanallah ni Hadiza na bani, Ladingo da gaske kun duba ko ina??" "Eh, wallahi ko'ina na duba amma batanan" a firgice Hadiza ta mik'e Salame na mara mata baya haka sukaci gaba da dubawa amma babu ita babu alamarta, Hadiza duk jikinta ya mutu zuciyarta sai dukan tara tara take tunaninta taya zata fuskanci Hajiya da maganar cewa an nemi Fatima amma an rasa? "Hadiza bazai yu ayi shuru ba, wallahi gara a sanar da Hajiya kada aje bamu sanar mata da wuri ba abin ya zama mana masifa" "Wallahi Salame ina jin tsoro sanar da Hajiya, wallahi tallahi ko jiya saida tamin gargad'in akan a lura da Fatima sosai" gaba d'aya sun matsa akan Hadiza ta sanar da Hajiya gashi dama Hadiza itace shugabar su....
*YUSIF*
koda suka dawo daga masjid shi da Alhaji b'angarensa ya zarce tunanin Fatima ya hanasa sak'at, wayarsa ya jawo da niyyar kiran Anty Maryam yaji shin yaushe zata shigo sedai wayar a kashe take yayi ta trying amma swich up, mik'ewa yayi da zummar zuwa gaida da Hajjah.
Koda ya shiga falon tana zaune bisa kujera mai zaman mutum biyu rik'e da casbi tana azkar k'asa ya zauna gefen k'afafuwanta yana cewa "Hajjah barka da safiya" "yauwa an tashi lafiya" "lafiya Alhamdulilahi" shuru ne ya biyo bayan gaisawar da sukayi kafin ya dubi Hajjah wacce ta kishingid'a ta lumshe idanun ta, abubuwa da yawa ya shiga kissimawa a ransa kafin a hankali ya kira sunan sa har sau biyu kuma a jejjere "Hajjah Hajjah" d'agowa tayi tana kafesa da ido fuska a tamke hakan ya sakashi sauke idanun sa k'asa! tsintar muryarta yayi tana cewa "lafiya? Menene? Nifa bana son damuwa" sauke numfashi yayi kafin yace "Hajjah kiyi hak'uri" ta bud'e baki niyyar magana ta fasa ta hanyar amsa sallamar Alhaji "Alhaji barka da safiya" amsama Yusif Alhaji yayi yana zama bisa kujerar dake kallon su Hajjah.
"Yusif ya akayi?" "Alhaji maganar Fatima ce don Allah ka bawa Hajjah hak'uri a duba lamarin nan" duban sa sukayi daga Alhajin har Hajjah kafin yace "Yusif ai mun gama da wannan maganar tunda anyi matsawa." "Alhaj...." Hajjah ce ta katsesa ta hanyar daka masa tsawa tana cewa "kai kiwa mutane shuru, wallahi, zanyi mugun sab'a mata, saboda naga alamun yarinyar nan so kake ka zamto zautatce a kanta" haka Hajjah tayita fad'a saida ta gaji don kanta shidai komai baice ba yayi shuru yana sauraren ta a ransa yana "Hajjah baki san yanda nake matuk'ar k'aunar Fatima ba, Allah dai ya kawo Anty Maryama" Alhaji ne ya dubi Hajjah yana cewa "its okey, ya isa" kafin ya d'ora da fad'in "Hajjah kiyi hak'uri abar duk wani abu ya wuce kawai ya aureta kuma yana sonta, saboda haka kibar komai ya wuce naga wa'enda suka sheda auren don haka kawai mubar komai a bashi matar sa tunda yana sonta" "Alhaji...." dakatar da Hajjah yayi ta hanyar d'aga mata hannu kafin ya juya ga Yusif yana cewa "Son jeka, anjima kazo akwai maganar da zamuyi" "to Alhaji nagode sosai, ubangiji ya saka da alkhairi" "Amin" tashi Yusif yayi da niyyar komawa part d'insa shigowar Hadiza ne ya dakatar dashi a firgice sai haki take hankalinta a matuk'ar tashe gaban Hajjah ta durk'usa tana sauke numfashi.
D'agowa Hajjah tayi tana cewa "lafiya Hadiza me yake faruwa??" "Hmmh wallahi Hajiya Fatima ce mun nemeta ko ina na cikin gidan nan amma babu ita babu labatinta, kuma Rakiya ta sheda min tare suka kwonta, sai dai koda safiya ta waye babu ita babu labarinta".
" me kike cewa Hadiza? Ta b'ata fa? Innalilahi wa'inna ilaihin raji'um subhanallah, subhanallah, subhanallah," Yusif ne a firgice yayo gurin Hajjah yana cewa "Hajjah wace Fatimar?" "Yusif Fatimar ka Fatima dai Fatima" ji yayi gaba d'aya duniyar ta juya masa baya, zuciyarsa ke zagwor-gwod'a kamar zata faso k'irjinsa ta fito "Hajjah Fatima ta tafi ta barni a karo na biyu, ta tafi da ni cikin ranta tana tunanin naci zalinta Innalilahi wa'inna ilaihin raj'um" basu ankara ba sai sukayi abu ya fad'i k'asa tim a sume! A firgice da Hajjah har Alhaji suka k'ara garesa a matuk'ar firgice Hajjah sai hawaye ke zarya a kuncinta cikin muryar kuka take cewa "don Allah Yusif kada ka mutu ka barmu, nayi nadama ka tashi wallahi zan nemo maka Fatima koda kuwa zan rasa rayuwata, ina sonka kai kad'ai Allah ya bamu d'a kada ka mutu alhalin banga 'yar'yan ka ba" Hajjah tayi matuk'ar shiga tashin hankali, Alhaji ne tayi k'arfin halin d'ebo ruwa yana watsa masa amma shuru.
A gajiye tayi sallama tana shigowa cikin falo, ganin yanda ta tarar da mutanen gidan ya sakata sakin hand bag d'inta tana tasalima "Innalilahi wa'inna ilaihin raji'um" cikin tashin hankali ta k'araso gurin su "Alhaji Hajjah lafiya? Meya samu Yusufa? Ya Allah kada ka nufeni da ganin wannan ranar dama abinda yake gayamin kenan? Nayi sauri nazo" ta k'arasa fad'a tana sakin kuka mai tsanani Alhaji ne yayi k'arfin halin cewa "Maryam" "Na'am Alhaji Yusif ya tafi ya barni ko? Wayyo Allah na na shiga uku na, oh ni Maryam dama ya fad'amin" Anty Maryam ta k'arasa fad'a tana sakin kuka cikin alhini kan kace me hatta 'yan aiki kuka suke, dak'yar sukati k'arfin halin d'aukar zuwa mota sai assibiti Anty Maryam sai kuka take tana rumge dashi jikinta har suka shiga cikin assibiti emergency aka shige dashi domin ceto rayuwarsa daga Hajjah har Alhaji sunyi curko curko sai Anty Maryam wacce keta zarya kai komo, kusan mintuna 40 amma shuru har su Daddy suka k'araso suma sun shiga matuk'ar tashin hankali.
"Hajja Hajjah ku dubi girman ma'aiki (s✅a✅w✅) ki gayamin me aka yiwa Yusif, shkn me yake faruwa kuka b'oyemin??" share hawaye Hajiya tayi kafin ta shiga labartawa Anty Maryam duk abinda ya faru from A to Z".
*FATIMA*
Sai kusan awanni Uku zuwa hud'u sannan ta farka, jin motsin hannunta ta ne wanda yake cikin na Inna Mairi ya ankarar da ita, share hawayenta tayi tana cewa "Alhamdulilahi ala kulli halin, Fad'ima kai Alhamdulilahi" murza ido Fatima tayi kafin ta shiga tunani nan take abubuwa suka shiga dawo mata cikin k'wok'wolwa juyowa tayi gefen Mama mik'ewa tayi da sauri Inna Mairi mayar da ita tana ficewa domin kiran likita "Mama Mama... Mama" Fatima sai kiran sunan Mama take cikin kuka! koda likita ya shigo dubata yayi kafin yace bari ya kira nus a d'ora mata wasu ruwan domin ya cire wa'enda aka saka mata domin sun k'are.
Cikin k'arfin hali Fatima ta tashi zaune duban Mama tayi tana cewa "Mama don Al.." bata k'arasa ba sakamakon hannu da Mama ta d'aga mata.
Mik'ewa tsaye Mama tayi kafin tace "ku tashi mu tafi" "Yaya ai ba'a sallamemu ba" hanyar fita daga d'akin Mama tayi hakan ya saka Fatima bin bayanta babu ko takalmi ganin da gaske tafiyar zasuyi ya saka Inna Mairi bin bayan su tana cewa "ku jirani" itace ta rik'o Fatima har suka fito a harabar assibitin suka samu abin hawa sai gida.
Mama dai bata dubesu ba iatace gaba da shiga gidan da sallama turus tayi cin kato da Malam "daga ina kuke ku duka" dakatawa yayi ganin Inna ta shigo rik'e da Fatima tuna Fatima yayi da hannu yana makarkata "Fa... Fadima kece" "Malam itace ta dawo daga yawon tamb'ele, Malam Fatima ta cucemu, Malam Fatima cikin sheg.. Ta.. Yo.." Mama ta fad'i kalmar a rarrabe tana sakin kuka had'e da shigewa d'aki.
Jin maganar Fatima tayi kamar saukar aradu duban Inna tayi cikin kuka tana cewa "Inna da gaske ciki ke gareni??" jinjina mata kai kawai Inna tayi alamar Eh, durk'ushewa Fatima tayi tana sakin kuka cikin k'unar zuciya ficewa Malam yayi sai Inna ce ke lallashin ta...
*09:00pm*
Bayan Malam ya gama musu nasiha mai ratsa jiki da tunatarwa akan yarda da kaddara mai kyau ko akasin hakan, jikin Mama yayi sanyi sunayen Allah kawai take nanatawa cikin ranta labari Fatima ta shiga basu cikin kukan bak'in ciki har ta kawo k'arshe, Nasiha Malam ya k'ara yi musu sosai mai ratsa jiki kafin ya sallamesu.
Zama Fatima tayi tana tagumi gefen gadon Mama, shigowa d'akin Mama tayi cikin alhini ta dubi Fatima kafin ta zauna gefenta cikin jimami tana cewa "Fadima kiyi hakuri" daga shi komai bai sake shiga tsakanin su ba daga haka har kwona biyu Fatima ta d'an sake sai dai ta zama wata saliha ta k'arshe duk labarin dawowarta yabi unhuwa kowa sai cewa yake Fatima taje karuwanci ta dawo da cikin shege, wasu gulma ke kawosu.
Mama da Malam da Inna kullum cikin lallashin Fatima suke ko k'ofar gida bata tab'a gigin takawa ba.
*YUSIF*
"Hajja ba'a kyautawa Yusif ba gaskiya" Anty Maryam ta fad'a cikin bak'in ciki.
Sai kusan k'arfe 2 aka fito dashi daga emergency, direct d'akin hutu aka wuce dashi , duk sunyi tsaye bisa kansa sai kusa biyar ya falka sunan Fatima kawai yake kira, tun abin baya damun su har kusan kwona d'aya kulum baida aiki sai kiran sunan Fatima dak'yar aka lallab'a ya kwontar da hankalinsa daga Hajjah har Anty Maryam an rasa wa yafi shiga damuwa satin su d'aya aka sallamesu..
Kullum cikin nasiha suke saidai kullum abu shuru, Anty Maryam ta shiga damuwa itace kawai mai rarrashin sa yaci abinci, Rayuwa duk ta sauya musu Abdul kuwa kwona ne kawai baya yi cikin gidan..
Anyi neman Fatima duniya har an gaji...
*AFTER ONE MONTH*
Fatima ta fara sakewa cikin gida sai dai kullum kwona takai tana kuka yauma hakan ta kasance.
Zaune take bisa capet d'in data kammala sallar asir tsurawa abinci dake gabanta ido tayi kafin ta saka hannu tana goge hawayen dake kworanya daga idanunta hannunta ta d'ora bisa cikin wanda yake shafehar mamaki take wai ciki gareta cikin kuka ta fara magana "kiyi hakuri ko kayi hak'uri hallitar Allah, komai ni naja laifina ne nice na cuce ka/ki yanzu a haka za ki/ka tashi shege? Wayyo ni rayuwata na citar da kaina Allah kada ka kamani da laifin daya zamto kaddarata bada son raina ba, yanzu ya zanyi da wannan cikin?? Idan yasan mena aikata fa" Fatima ta k'arasa fad'a tana sakin wani kuka mai cin rai tana jin kamar ta mutu ta huta ga tausayin 'yarta ko d'anta da takeji Mama ce ta shigo d'akin d'auke da Sallama tausayin 'yarta ne ya shigeta lallashinta ta shiga yi "Mama na citar da kaina na zalumci rayuwata ku yafeni"" Fatima kaddarar ki ce kiyi hak'uri"! Haka Mama ta shiga rarrashinta dak'yar tayi shuru" fitowa sukayi waje inda Malam ke kiransu cikin b'acin rai wanda basu tab'a ganinsa ciki ba "Fatima je ki sako hijabi kizo ki kaimu gidan su yaron" wani iri Fatima taji maganar cikin tashin hankali tace "Malam.." dakatar da ita yayi ta hanyar d'aga mata hannu yana ficewa daga gidan babu yanda ta iya haka ta sako hijabin a waje ta samu Malam shiga wani abokin sa Baba Alhaji da k'anin sa, gaidasu tayi tana jin matsananciyar kunya ganin takai duk dattin duniya ya k'are bisa ranta ta tsani rayuwarta haka suka shiga motar Baba Alhaji tana musu kwotance kanta a k'asa har suka k'arasa unguwar direct sai k'ofar gidan su Yusif, maigadi suka ce ya sanar suna sallama da mai gidan...........
*Don Allah kumin addu'a da bakunan mu masu albarka wallahk banda lafiya, yau ciwo gobe lafiya shiyasa kume jina suru shuru😭😭😭😭😭😭*
*Don't forget with share fisabililah don manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
🍀🍀🍀🍀🍀
*TSARINA CE*
🍀🍀🍀
```Labari da rubutawa```
*RUKAYYA UMAR FARUK*
_(Samha Umar)_
~Writer of~
*RIBAR~HAQURI*
*TAKABA*
*SA D'AKA*
*E.t.c*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
a5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
_Bismilahi_Arrahman-Arahim_
*Episode 49&50*
*🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚* doyorgal
...... Shiga ciki mai-gadi yayi cike da mamaki Alhaji ke tambayarsa "Nuhu kasan su ne" "Allah ya taimaki mai gida gaskiya ban gane su ba, da Allah bak'i ne" "to je ka shigo dasu fallon bak'i" ficewa mai-gadi yayi inda ya sanar dasu jagora yayi musu sai falon saukar bak'i na gidan.
"Alhaji Allah masanin wa'enni irin bak'i, ubangiji dai yasa lafiya" "Ameen Maryam je ku shirya idan na dawo sai mu wuce assibiti kega jikin Yusif d'in sai a hankali" Alhaji ya k'arasa fad'a cikin alhini "Allah ya basa lafiya" kawai Anty Maryam tace domin yafi kowa shiga damuwa da halin da k'anenta yake.
Da sallama Alhaji ya shiga falon bak'i, turus yayi ganinsu domin kaf ko a mafalki bai tab'a ganin d'aya daga cikin fuskokin su ba, hannu yq basu suka gaisa kafin ya zauna cikin d'arin murya Fatima ta gaidasa amsawa yayi kafin ya maida dubansa gasu Malam yana cewa "bayin Allah sai dai ban ganeku ba" kawu d'an uwan Malam wanda yake tamkar k'ane a garesa gyaran murya yayi kafin ya fara magana "Alhaji wanna yarinyar da kake gani" kawu ya fad'a yana nuna Fatima kafin ya d'ora da fad'in "'yarmu ce.... " haka da kawu ya shiga bawa Alhaji labari from A to Z kamar yanda Fatima ta sanar da Malam shi kuwa ya sanar musu..
Jinjina kai Alhaji yayi a ransa yana godiya da ga Allah daya bayyanar da Fatima cikin sauk'i kafin yace "to Alhamdulilahi sai dai wani hanzari ba gudu ba, gaskiya yanda kuka fad'a hakane amma ni yanda yaron gurina ya fad'a min cewa yayi yarinyar marainiya ce har yayi niyyar taimakonta ta hanyar aurenta".
Cikin firgici duk suka had'a baki gurin cewa " Aure, Fatima" kafin su maida kallonsu ga Fatima girgiza kai tayi tana cewa "na rantse da Allah Malam ba haka bane, wallahi ni ban auri kowa ba" ta k'arasa fad'a tana sakin kuka Baba Alhaji ne cikin masifa yace "Wallahi baku isa ba, ai dai yarinya da hankalinta wane irin aure? Kawai d'anku ya cuceta ya mata ciki don haka wallahi tallahi sai mun kai maganar kotu an mana hukunci, yasso idan ta haifi shegen d'anku ta maido muku" "Malam kada ka koma kiran d'an mu da shege kaji na gaya maka idan bakuyi k'arar mu ba ni zanyi k'arar ku" duk d'agowa sukayi suna kallon Anty Maryam wacce basu ankara da shigowarta ba fashewa tayi da kuka tana cewa "Alhaji don Allah kazo kuyi ban kwona da Yusif domin nasan mutuwa zaiyi" ta fad'a tana sakin kuka kafin ta fice daga falon, Alhaji yayi matuk'ar firgit har yabi hanya kafin ya juyo yana duban su Malam da hannu ya nunasu kafin yace "rayukan ku fansar rayukan jikana" daga haka fuuuu ya wuce duk sororo su Malam sukayi sai Baba Alhaji ne yace ku wuce muje wallahi sai munyi k'ararsu daga haka suka fice Fatima sai kuka suke, fitowa Alhaji yayi "Mudasir Mudasir" ya shiga k'wolawa Mudasir driver kira fitowa yayi cikin sauri yana durk'usawa ga "gani ranka shi dad'e" "idan bak'in da suka shigo suka fito ka bimin bayan su ka ganomin gidan su" “to Alhaji an gama" ciki alhaji ya shiga d Hajiya yaci karo cikin kuka ta nufesa tana cewa “Alhaji don Allah kazo a ceci rayuwar Yusif wallahi gani nake kamar na zalumcesa" wuceta Alhaji yayi nufarsa tayi tana kiransa sunansa amma yayi banza da ita kamar baiji ba, b'angaren Yusif suka nufa Abdul zaune gefensa sai Anty Maryam wacce duk ta susuce ganin shigowar Alhaji ya saka Yusif nufarsa yana k'ok'arjn rik'o hannunsa fisgewa yayi tare da yarfa masa mari ta kowanni kunce cikin tashin hankali ko wannen su yake kallon ikon Allah Hajjah ce ta rik'o Yusif zuwa cikin tana cewa "Alhaji narin sa fa kayi??" "Eh, na maresa ko zaki rama masa? Da ashe bakada mutunci ban sani ba? Da girma na a gari zaka nemi ka tozaeta ni? Har ku sako yarinya kai mata ciki sannan kazo kana kame kame, iyayenta sun zo kuma wallahi duk matakin da zasu d'oka babu ruwa na.Alhaji na ida fad'ar haka yayi tafiyarsa fuuu duk sun shiga tashin hankali marar misaltuwa Abdul ne ya d'auki wayarsa number Daddy ya kira yana d'auka yace "don Allah Daddy kazo nan gidan Alhaji wallahi akwai matsala" daga haka ya kashe kiran Anty Maryam ce ta matsa kusa ga Yusif hawayen da taga ya zubo da idanun sa ne ya saka ta sake shiga rud'u "kayi hak'uri k'ane na, komai zai zo da sauk'i InshaAllah muna bayanka" Hajjah ce ta zaunar dashi itama tana zama gefensa "d'ana kayi hak'uri, insha Allah komai zai zo da sauk'i haka sukaci gaba da rarrashin Yusif.......
*FATIMA*
Koda suka dawo gida rarrashin ta su Inna sukaci gaba dayi, Malam ne ganin tabbas Baba Alhaji k'ara zai shigar ya saka shi basa hak'uri ta hanyar cewa subi komai a sannu.
*Yusif*
A gaggauce Daddy ya iso har falon sama ya samu Alhaji komai ya labarta masa kafin ya shiga basa hak'uri yana tausar zuciyarsa akan abi komai a sannu.
*****
A cen kuwa Anty Maryama ce ta shiga basu labarin zuwan iyayen Fatima duk da ba komai ta sani ba, dak'yar suka lallab'a Yusif.
Daddy ne ya shawarci Alhaji akan cewa tunda har ya saka driver bibiyar gidan su to su suje cen a sulhunta komai.
Haka akayi bayan magriba da Daddy da Alhaji da wa'ennan dottijan da suka wak'ilci auren suka rank'aya sai gidan su Fatima, koda suka isa Malam na zaune zaure ana karatun dare iso akayi musu kafin su k'arasa zama sukayi aka gaisa, duk da Malam ya d'ago Alhaji amma bai nuna komai ba jawabin farko hak'uri Daddy ya fara basu kafin d'ora da bada labarin abinda suka sani na tabbacin auren Yusif dake kan Fatima ta hanyar nuna waliyan auren zuru zuru sukayi kafin d'aya daga cikin su yace "to ai Malam kaine wanda ka d'aura auren" duk kallon mai maganar suke kafin Malam ya nuna kansa yana cewa "ni kuma?" "eh tabbas kaine" kafin mutumin ya gayawa Malam yanda akayi, sai a lokaci ya lura kafin ya jinjina kai alamun tabbas hakane anyi haka.
Malam ya amince kuma ya hak'ura, ya d'auki hakan a matsayin kaddarar su daga su iyayen har Fatima, batun aure kuma ace abari idan yarinyar ta amince zata zauna dashi shikenan.
Da haka kowa ya watse cikin gida Malam ya nufa inda ya gayawa su Mama komai sai dai babu wanda yayiwa Fatima maganar data shafi cikinta.
*****
Koda su Daddy suka koma haka suma suka sanar da yanda sukayi da mahaifin Fatima.
"Yusif kayi hak'uri kaga yanda Allah yake komai tunda su iyayenta basu da matsala, kuma insha Allah Fatima ba zatace bata sonka, dama akwai wata 'yar mace da zata dubi kyakyawan k'anena tace bata so??" Anty ta fad'a cikin raha Yusif kuwa tunani kawai yake yanda Fatima ta shirya musu k'arya "dama duk abinda ta fad'a min k'arya ne?" yayi tambayar cikin ransa babu mai bashi amsa, kafin ya dubi Anty Maryam yana cewa "Anty idan fa tace ba zata zauna dani ba??" murmushi Anty Maryam tayi cikin kwontar masa da hankali tace "insha Allah bro. hakan ba zata kasance ba, zaka rayu da Fatima Rayuwa ta har abada mutuwa ce kawai zata raba ku zata haifa maka 'yar'yar kyawawa tamkar kai" ya bud'e baki da niyyar magana aka turo door ana shigowa Hajjah ce murmushi d'auke a fuskarta zama tayi gefen Yusif suna sakashi a tsakiya kafin ta dubi Anty Maryam tana cewa "to ke kuwa 'yar azarb'ab'i sai ki koma ki kula da naki d'akin kafin ita Fatima ta dawo nata" sauke numfashi Anty Maryam tayi tana cewa "wallahi Hajjah ni nama mance da wani aure bale d'akin miji ko 'yar'yar tun da na tarar da D'an uwa na cikin wani hali, kamar na fishi shiga tashin hankali". Anty ta k'arasa fad'a cikin alhini Yusif ne yace " Anty da mukayi magana baki zo ba sai a k'urarren lokaci" "hmm..! Kai dai bari koda jirginmu ya sauka sai kusan magriba daga nan na zarce gidan Daddy acen na kwona safiya ta waye nayo sammako yaran kuwa duk cen na barosu gidan Daddy dama banzo ba saida akayi musu hutu, mu kad'ai ne Yaya Bash yana Lagos d'in, kaji yanda akayi da safe nazo" nan ta d'ore da basu labarin had'uwar da tayi da Fatima har ta maidata gida. Hajjah ce tace "to sai kiyi harramar komawa" murmushi Anty tayi tana cewa "Hajjah bazan koma ba har sai Amaryar mu ta tare🙊😂, yanzu ma shiri nake zan raka bro biko" ta k'arasa fad'a cikin raha Hajjah ce tace to muma zamuje biko mu bada hak'uri nida Momy ku taku tafiyar ku bari har gobe", "to" haka Hajjah ta fice ta barsu cikin d'akin sukaci gaba da tattaunawa.
*FATIMA*
Bayan la'asar sai gasu Hajjah cikin mutumci su Inna Mairi suka tarbesu bayan an gaisa suka k'ara bada hak'uri Momy ce tace "ina Fatiman take tazo mu gaisa?" Inna Mairi ce tayi murmushi kafin ta mik'e tana cewa "bari na dubota" haka ta shiga d'aki Fatima na kwonce bisa gado tamkar mai bacci amma idonta biyu, k'arasawa Inna Mairi tayi gabanta tana cewa "Fatima kizo ku gaisa da bak'i" bata d'ago ba muryarta na kakkarwa take magana "ni Inna salon kawai su ganni suce ga wacce tayi cikin shege" zaro ido Inna Mairi tayi tayi tana cewa "don Allah ki rufa mana asiri kada bak'in suji, haba Fad'ima taya zaki kira d'an cikin ki da shege??" gunguni tayi tana "nidai wallahi babu inda zani gurin azzaluman mutane." salun alun Inna Mairi ta fice koda suka tambayeta ce musu tayi Fatima na bacci haka sukayi rabin yini sai kusan magriba suka tafi bayan bajesu da abubuwa alkhairi kala-kala.
Koda Malam ya dawo su Inna suka sanar masa Madallah kawai yace.
*WASHE GARI*
_11:30:09_
Gasu Anty Maryam gidan da sallama ta shigo gidan "a maraba" Inna Mairi ta fad'a duban Anty Maryam itama Anty Maryam sai murmushi take, tabarma Mama ta shinfid'a mata haka ta zauna kafin ta kawo mata ruwa gaisawa tayi da Mama wacce fitowarta daga d'aki kenan bayan Inna Mairi ta sanar da ita.
"Baiwar Allah sannu, mun gode sai yanzu kika samu damar dawowa? Nasan keje assibiti baki tarar damu ba" sai lokacin Anty Maryamu ta lura da inda Matar ta dosa murmushi tayi tana cewa "eh to dama nima munzo ne mu k'ara bada hak'uri, ai nice yayar shi wanda Fatima take aure" nan Anty Maryam ta basu labarin komai sunyi mamaki koda ikon Allah yafi gaban mamaki haka dai suka kasance.
Inna Mairi ce ta dubi Anty Maryam tana cewa "to shi surkin namu bazai shigo ba mu gaisa??" Da murmushi Anty Maryam ta mayar mata tana cewa "to" mik'ewa tayi da niyyar tashi "A ..a ..a ki bari ga Fad'ima bari kawai tace ya shigo" Mama ta k'arasa fad'a tana kiran "Fad'ima Fad'ima" jin shuru yayi yawa ya sakata mik'ewa had'e da nufar d'akin "ke Fad'ima wai yaushe kika zama kurma? Ana kiran ki kamar wata marar ji" tama ta fad'a tana kaimata duk a firgice Fad'ima ta mik'e zaune tana sakin 'yar k'ara a hankali gefen cikin ta ta dafe kafin ta fara matsa hawaye tana cewa "wallahi Mama ba ruwana komai ya same sa kece" zaro ido Mama tayi tana cewa "shi me??" Da hannu Fatima ta nuna mata cikin dake jikinta tana cewa "shi" filo Mama ta jawoda niyyar bugun Fatima ai kuwa batasan lokacin data diro daga sama gadon ba a tsiyace ta fito waje ganin kallon dasu Inna Mairi ke mata ya sakata duk'ar da kai tana cewa "sannun ku" Anty Maryam ce tace "yauwa k'aunwata ya k'arfin jiki" "lafiya" duban Mama tayi jin maganar da take cewa "Fatima je ki shigo da bak'o" ta bud'e baki da niyyar magana da hannu Mama tayi mata alamar tayi shuru tana nuna mata hanyar k'ofa cikin d'an gunghni ta gyara hijabinta takalmin Inna Mairi ta saka tana fitowa.
Ido biyu sukayi da Yusif yana tsaye jikin motar rik'e da key mota yana karkad'awa.
Dube dube tashiga yi kamar ba taga wata halitta ba, "Tanimu" ta k'wolama almajirin dake duk'e yana wankin alo kira gurinta yayo, d'an d'aga murya tayi tana cewa "kako ga bak'uwar fuska nan gurin??" "Eh" Tanimu ya fad'a tana nunawa Fatima Yusif da hannu harararsa tayi tana cewa "tafi" daga haka ta juya da niyyar komawa cikin gida tana tafiya sannu sannu jin an fisgota ya sakata sakin k'ara da sauri ya rufe mata baki yana birkito da ita tana facing d'insa hannuwan sa tasa tana jaye hannunsa daga bakinta hararsa tayi tana cewa "meye kuma had'in kaska da kifi? Meya kawoka gida na? Mugu kawai" "i come to see my unborn baby" ya fad'a yana shafo cikinta saurin janyewa tayi duk da bai sake hannunta ba "nidai wallahi ka rabu dani mayaudari kawai" "Fatima mijinki?" Tofar da yawu tayi tana cewa "Allah ya tsare kazan mijina, ni nace ka aure ni? Ko kuma ina sonka?" Fatima ta fad'a cikin borin kunya tana tuno k'aryayakin data shishirya musu shida Abdul.
"Taya baki sona kuma ga cikina jikin ki? Ai kinga so kam" hararsa tayi cikin takaicin daga shi har cikin hawaye na taruwa a idanunta "wallahi bansin cikin nan kuma bazan haifeshi ba komai zai faru kuwa" cikin sanyin murya yace "don Allah Fatima kiyi hak'uri kada ki b'arar min da jinina kinji Sweet teemah Matar D.r Yusif mummyn unborn kiyi hak'uri ni sonki nake kuma ina son d'an da zaki haifamin" "naji amma idan na haifeshi zata sakeni na auri wanda nake so??" Zaro ido yayi kafin yayi jim yana cewa "Eh" "Alk'awari" "kaya ne" murmushi tayi tana cewa to muje ka shiga ciki ku gaisa dasu Mama shima murmushi yayi yana "to" bai saki hannun Fatima ba haka suka shiga ciki ganin kallon dasu Inna ke musu ya saka ta ankara fisge hannunta tayi tana fad'awa d'aki.
Bayan ya gaidasu kafin su dawo shi da Anty Maryam yaso ganin Fatima amma haka ya hak'ura suka dawo.
Alhaji yaje har garin su yayiwa Mahaifiyarsu bayani, Rayuwa kenan abubuwa da dama sun faru tsawon lokaci har cikin Fatima ya shiga watan haihuwa kullum Yusif cikin zaryar zuwa gidan su yake babu ruwanta tunda yayi alk'awarin sakinta, Alhaji da Daddy dun kammala ginin assibitin su tuni an fara aiki inda Yusif ke jagoranta Anty Maryam ta koma yanzu kam sai Fatima ta haihuwa saidai sometimes idan Yusif yazo yana bata su gaisa da Fatima ta waya, Hajjah da Mommy ma kullum suna bisa hanya.
Fatima ta haihunta lafiya ta samu 'yarta mace kyakyawa sak mahaifinta zo kaga farin-ciki ga wa'ennan dangi kamar a had'iyeta kowa sai santi yake Anty Maryam a ranar ta dira kano, sai bayan magrib Yusif yazo gidan shi da Abdul bayan sun dubi 'yar suka fito sallama sukayi da 'yan barkan dake waje, "kai tsaya" dakatawa yayi daga bud'e motar da yayi kallon Fatima yayi cike da mamaki ganin ta, k'arasowa tayi gabansa sai sauke numfashi take "lafiya na kallo na" girgiza mata kai kawai yayi juyar da idanu tayi saida ta duba ko ina babu kowa sai Abdul hsrararsa tayi tana cewa "ka bamu guri" "an gama uwar gida ran gida" ya k'ara cikin tsokana yana d'an barin gurin tab'e baki tayi kafin ta maida duban ta ga Yusif tana cewa "maganar mu kyan alk'awari cikawa" "wace magana??" "Cewan da kayi zata sake ni idan na haifi cikin ka" kallon bakida hankali yai mata kafin yace "okey yanzu meya faru" "ka cikamin alk'awari" "idan na sakeki wazai rik'e mana 'yar mu" dan jim tayi alamun tana tunani kafin tace "zan rik'e mana idan na samu wanda nakeso zan auta sai na tafi da ita" "idan yace bazai bari kije da ita gidan sa ba??" "Zan bar Mama ta rik'emin ita sai kullum na rik'a zuww ganinta" kallonta yake yana ganin zallar wautar ta murmushi yayi yana cewa "to na amince amma zan karb'e 'yarta na kaima Hajja idan na samu matar da take sona sai na bata ita shikenan" kallonsa tayi tana cewa "wallahi ni babu jahilar matar ka da zata rik'emun 'yar" "lalle Fatima bkida hankali taya zaki rik'emun 'yar alhalin bakya sona?? Kuka ta fashe dashi tana shigewa gida mamaki ne ya kama mutane da yawa ganin Fatima na kuka gashi ba asan ina ta fitoba anyi tambayar duniya amma babu wanda taba amsa Mama ce ta d'ora mata jaririyar wacce keta faman kuka tana barin d'akin, rumgumarta Fatima tayi tana kallon fuskarta " yi shuru please nasan wancen ne kema ya b'ata miki rai, babu shakka keji abinda muke fad'a, kiyi hak'uri indai ina da rai babu mai rabani dake" haka Fatima ma ta shiga kuka Inna Mairi ce ta shigo gefen Fatima ta zauna tana karb'an jaririyar ruwan data shigo dasu ta bata kafin ta lallab'ata har bacci ya d'auketa kwontar da ita tayi tana duban Fatima had'e da ceaa "lafiya ke kuwa, an girma ba'asan an girma ba" Inna taba labarin tun alk'awarin da sukayi da Yusif har zuwa yanzu, lallab'ata Mama tayi kafin tace "to ke meyasa ba zaki zauna dashi ba" "Inna ban san sa da ya aure ni ba" lallab'ata Inna ta shiga yi tana ce mata odan bata zauna dashi ba to zai amsge 'yar sa....
Sun kawo uban kayan barka kamar wanda zai bud'e kanti, ranar suna 'yar taci sunan Hajja wato Hajara ana mata inkiya da Ammie.
*Bayan wani lokaci*
An lallab'a Fatima ta koma d'akinta kafin ya shawo kanta dak'yar ta yarda ya yadda makaman yak'inta, rayuwa suke gudanarwa cikin soyayya da k'aunar juna kamar wasu masoya asali suna kula da Ammie yanda ya kamata Abdul ma yayi aure ya tare da Matarsa Khadija, Fatima ta koma karatu inda take karantar political science a ATTANZEEL...
*AFTER 7 YEARS*
_lady birds nurs/primary school_
A hankali tayi parking motar ta bakin gate d'in makarantar duban yara biyu dake zaune gidan gaba tayi tana cewa "my Preteen ku jira ni kad'an zanje kiran Ammie" ta k'arasa fad'a tana shafa kan ko wanne daga cikn su kafin ta dubi cikin dake jikin wanda a k'allan zaiyi wata biyar murmushi tayi tana cewa "you too my unborn i love you" bud'e murfin motar tayi had'e da ficewa cikin yanga take tafi da ganinta kunga wayayiyar mace cikakkiyar 'yar boko, k'wonk'wosa gate d'in makarantar tayi bud'ewa akayi har k'asa mai gadi ya duk'a yana gaidata amsa tayi tana cewa "don Allah Baba nazo d'aukan Ammie ne" dubanta yayi yana cewa "ai Hajiya babu wanda ya rage daga cikin student kusan minti 40 da tashi "what! Innalilahi wa'inna ilaihim raji'um" mota ta koma tana zaro wayarta number Yusif ta shiga dialing amma no picking haka ta tada motar cikin gudu har ta iske tamgamen gidan su wanda tsayawa misaltashi zai d'aukemu dogon lokaci horn tayi gate man ya bud'e tana shiga cikin gidan tana gama parkin ta fito zagawa tayi tana bud'ewa yaranta 'yan shekaru Hud'u Amir wanda yaci sunan Alhaji da kuma Ammar wanda yaci sunan Daddy ko jiran su batayi ba suna Momy Momy haka ta wuce ta barsu koda ta shiga falo yana zaune bisa kujera mai zaman mutum d'aya computer a gabansa ya duk'ufa yana aiki jin k'arar tafiyarta ya saka shi d'agowa gefe ya ture computer yana ware mata hannu birki taja tana hararsa ganin hakan ya saka shi mik'ewa mufarta yayi yana cewa "Momyn twinc lafiya waya tab'omin ke??" "Ammie ce" ta basa amsa tana turo baki "Ammie yanzu itace ke shirin sakaki kuka?" "Wallahi na gaji da halin yarinyar kullum rashin ji, tun tana haka tasan yawo be ace ta girma? Ko yanzu bata scholl naje d'aukanta nasan yauma ta dawo da k'afa kanar yanda ta saba" Fatima ta k'arasa fad'a tana k'ok'arin danne hawayen dake zubo mata "UMMY" ta fad'a tana rumgumota fisgewa Fatima tayi tana k'ok'arin kai mata duka Yusif ne ya rik'e hannun yana mata gargad'i da ido kafin ya dubi Ammie yana cewa "Ammie jeki ki cire Uniform ga Mummyn zuwa" kwob'e fuska tayi tana wucewa hannu Fatima ya k'ara rik'ewa cikin nashi yana cewa "mai sunan Hajjah zaki daka??" turo baki tayi tana cewa "ai bata jin magana" "halinki ne ta d'auko ai, babu abinda ta baro kema sai kiji yana su Mama sukaji ina my twinc?" Bata basa amsa ba illa dukan wasan data kai masa a k'irji bakinsa yakai dai-dai kunnenta yana mata rad'a zaro ido tayi kafin ta k'yalk'yacewa da dariya.......
ALHAMDULILAHI Alhamdulilahi Alhamdulilahi dukkan godiya su tabbata ga allah (s.w.a) tsira da amincin Allah suk j'ara tabbata ga fiyayyen halitra, duka-duka anan na kawo k'arshen wannan littafin mai dogon zango ina godiya akan hak'urin da kukayi na jira har yau da Allah ya nufa na kammala! Allah ya bamu ikon amfani da darsi da littafin ke d'auke dashi, abinda bana k'worai ba kuma muyi watsi dashi.
Taku har Abada Samha nace dai sai mun had'u a litattafaina na da zasu zo muku nan gaba, nagode sosai da sosai masoya na kusa dana nesa da wa'enda na sani da wa'enda ban sani ba😊😇👌💃
*💖ONE LOVE💘🌹*
*♡TALLAH.. TALLAH♡*
*✿❀The Purest pen Belonging Impose With ASMEY KHALIL & FIYANA✿❀*
*🔈🔈ZAZZAK'IYAR BUSAR ALGAITA 🎷 tana sanyaya zuciya da wanzar da ni'ima a garkuwar jiki🤗! Haka ma Alk'alami🖊 ya kasance tamkar algaita👌🥳 wacce ake busata a duk sa'anda ake so😏 domin rubutu cikin aminci da tsaftatacen harshe👌, ilmantarwa🤗, fad'akarwa😎, nishad'antarwa🙌🙌*
❀✿♡☆♡✿❀
*ASMEY KHALIL & FIYANA zafafan littatafai ne da zasu zo muku a 1st jan. 2023, wa'ennan littatafai zasu zo muku da salo mai k'ayatarwa salo na daban tsantar soyyaya marar algus💏 mai sanyaya k'ashi har da b'argo💘💖 RUQAYYA OMAR FAROUK👉 wacce kukafi sani da ✿Samha✿🙏 itace dai marubuciyar ku mai son farin cikin ku😻🌹🎉!.*
```ASMEY KHALIL & FIYANA```
_zasuzo muku cikin farashi mai sauk'i👌 guda 1 akan 300✅ idan kuma duka biyu kuke buk'ata zaku samesu akan 500✅ kacal👌_
*Hhhhhh😂😂😂 wasu kaya sai amali kada ku bari a baku labari, kuma ku garzayo ku kwoshi garab'asa domin ina da tabbacin ba zakuyi dana sanin sayen littatafaina ba💪💃💃💃💃, ko wanne da nasa salo, salo mai narkar da zuciya😊 kudai kada na cika ku da surutu🎊🎉! Kada ku manta duk 1 akan 🔥300🔥 idan kuwa duka biyu kuke da buk'ata 🔥500🔥 sai naji ku😇*
````taku Samha Star☀✨🌠💫 tauraruwar marubuta✨ masoyan asali kada ku bari ayi baku⚡✅```
*namu ba irin nasu bane💪*
*Don't forget with share fisabililah don manzon Allah* *_idan kin karanta Aunty ki taimaka kiyimin share_*
```It's your Samha the Queen of writer's```👸
0 Comments