*HAUSA POEM*
*BY*
*I²Gusau*
*RAYUWAR MATASHI*
*King and Queen Writing Chamber*
https://www.kingarticlenovels.com.ng/
Gareka matashi kaida kake da damar inganta rayuwar ka
Amma ka koma Éan jagaliyar siyasa
Kazama Éan daba alal haĘiĘa
A cikin shekaru takwas mika mora a rayuwar ka
Kasamu ingantacciyar sana'a , domin itace rufin asirin ka
Kadaina neman ilimi duk da Ęaranci na shekarun ka
Ka canza Éabi'unka kafin ranar dana sani tazo maka
Komai yafaru dakai aida laifin ka
Domin kaika saida 'yancin ka da hannun ka
Naira dubu ko Éari biyar kana ganin zata inganta rayuwar ka
Tun kanada Ęima wata rana ka koma cikin sa'ar Ęannen ka
A kwana a tashi zaka haifi 'ya'ya har kakai ga jika
Kuma kullum burin ka Allah ya sanya masu albarka
Baka ajiye komai ba balantana kasha inuwa cikin gidan ka
Shin wane labari zaka baiwa 'ya'yan ka
Wanda ya shafi Ęuruciyar ka
Ka manta da su waye ahalin ka
Kafin azo ga 'yan unguwar ka
DaÉin daÉi harda malamin ka
Kai ake ba makami domin ka farmaki al'umma, kuma a ciki harda 'yan uwanka
0 Comments