[1/26, 5:18 PM] Miss Green: *_✨INDA BA ƘASA...!!!_✨*
_(Littafi na 1📃)_
NA
*_®️UMMU MAHER(MISS GREEN)🍀_*
*_AREWA BOOK👉🏻_*
INDA BA ƘASA!!!:: https://arewabooks.com/book?id=63ce1eb0ec00e12124ce9eb0
---------------------------
*_WATTPAD👉🏻_*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
---------------------------
*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_* ---------------------------
*((بسم الله الرحمان الرحيم*))
ƊAN ƊANO DAGA GAWURTATTU UKU🤟😋😋😋
*Page⬜1*
--------------wasu yara ne na hango a wani ƙaton falo, kana ganinsu kasan ƴan ƙauye ne, sai kallon falon suke suna yaba kyau da kuma tsaruwarsa, ɗaya daga cikinsu ta ce"Gaskiya matar gidan nan tana jin daɗi, ki duba kiga gidanta tamkar shi yayi kansa?gida kamar aljannar duniya?."
Hajiya Adama ce ta ce"kai dalla malamai kuyi wa mutane shiru, gidan aiki na kawo ku ko gidan surutu?ina ruwanki da matan gidan suna jin daɗi ko kuwa basa ji?kinga Ummita ki kiyaye ni?kada inji kada na gani?ni dai kiyi aikinki tuƙuru,kuma duk kuɗin da za'a baki kada ki yarda ki kashe su,ki ajjesu har nazo na amsa ehe". . . . .
Shiru tayi lokacin da matar gidan ta fito,tayi mugun kyau cikin tsadaddan les ɗinta, wanda kana ganinsa ba sai an faɗa maka ba kasan kuɗinsa bazai faɗu ba.
Ummita ta dinga kallon matar kamar zata sace ta, mata kyakkyawa da ita kamar ita tayi kanta, gashi Allah ya bata duniyar wato kuɗi.
Tun kafin ta zauna Hajiya Adama tayi sauri ta tsugunna tana gaida matar.
Matar ba ta da girman kai,ta amsa cikin sakin fuska,tana magana amman Ummita na kallon bakinta don haƙoranta kusan uku duk haƙoran makka ne.
Ummita tayi tagumi tana kallon matar,ji take dama ita ce Allah yayi mata wannan baiwar,sai take ganin kamar ta tashi ta zauna akan kujera tace itama matar gidan ce, amman tasan ko hauka tayi hakan bazai taɓa yiwuwa ba.
Tana cikin tunanin Hajiya Adama ta taɓa ta, da sauri ta dawo cikin hayyacinta ta sunkuyar da kanta, don gani take kamar matar ma ta ganta.
Hajiya Adama tayi murmushi sannan ta ce"Hajiya waɗannan sune yaran dana kawo miki suyi aikin."
Ta nuna Ummita sannan ta ce"wannan sunanta Ummita, Asalinsu Shuwa arab ne to sun shigo garin nan basu da kowa, kuma basu da komai to shine mahaifiyarta ta ce don Allah in nemo mata gidan aiki don ta fara yi,suna rufawa kansu asiri, waccen kuma sunanta Khairat yayar Ummita ce uwa ɗaya uba ɗaya."
Murmushi kyakkyawar matar tayi sannan ta ce"Allah sarki sannunku ko?".
Ta cewa su Ummmita.
Ita kuwa Ummita tunda ta fara kallon wannan matar har yanzu bata daina ba, tana ta tunaninta cen mara tushe da kuma yarinta.
Suna cikin wannan halin ne,wata kyakkyawar yarinya ta shigo,amman bata kaisu Ummita ba, don bata fi shekara 16 ba Ummita kuma za ta kai sha tara ma, yayar ta kuwa zata kai ashirin da biyu ko fin haka ma.
Ummita tabi yarinyar da kallo, yadda kasan ƴar larabawa duk kyaunsu da mutane suke gani na shuwa har maza suke wawaso ashe aƙwai waɗanda suka dame su.?????
Da gudu yarinyar ta taho ta rungume wannan kyakkyawar matar, kuma kana gani ba sai an gaya maka ba kasan ƴarta ce,saboda yadda suke kama sosai kamar an tsaga kara sai dai yarinyar yarinta kawai ta fita.
Kyakkyawar yarinyar ta kallesu sannan ta ce"mom waɗannan su waye?".
Ta faɗi maganar cikin shagwaɓa, tamkar ƴar jaririya Matar ta ruƙo hannunta ta ƙwantar da kan yarinyar akan cinyarta kamar ƴar jaririya.
Ummita kuwa ta tsura musu idanu,tana mamakin shagwaɓa irin ta wannan yarinyar, ƙatuwa da ita aka ƙwantar akan cinya?lallai wani abin sai kuɗi, don ita dai ko tayi hauka bata i'sa ta ƙwanta akan cinyar mahaifiyarta ba, don safiya na yi kowa zai kama gabansa ya tafi nema, sai dare suke dawowa daga bara daman su biyu mahaifiyarsu ta haifa.
Matar ta shafa kan ƴar ta gwanin sha'awa, ta fara magana cikin kulawa"Baby wannan sunanta Ummita, waccen kuma Khairat zasu iya zama ƙwayenki don ba ƴan aiki bane, kin san shi mutum yana da daraja fiye da komai, kawai dai zasu dinga taya mu wasu ƴan aika ce aika ce ne, tunda kinga daga ni sai ke agidan."
Baby ta ɗago tana kallonsu Ummita ta ce.
"hi"!
my name is Zahra Muhammad Aliyu."
ta faɗi hakan da murmushi akan fuskarta.
Hajiya Adama taji daɗi sosai, don daman an bata labarin matar da kuma ƴarda take riƙo wato Baby, ƴar yayarta da ta rasu.
Nasan zakuyi mamaki idan nace Baby ba ƴar wannan matar bace,Baby mahaifiyarta ta rasu sanadiyyar Haihuwarta, Halima kuma ƙanwar mahaifiyar Baby ce, bayan ta rasu sai Baban Baby ya auri Halima, tun Baby na ƙarama Halima ke riƙe da ita,har kawo i yanzu da take da kusan shekara 16.
Halima ta kawo kuɗi masu yawa ta bawa Hajiya Adama, Hajiya Adama ta amsa tana ta godiya, har zuciyarta matar tayi mugun ƙwanta mata, don ba kasafai aka fiya samun masu kuɗi da zuciya me kyau har haka ba, wasu masu kuɗin sun ɗauki talaka a matsayin abu mummuna, ko kuma abin ƙi Alhali awajen Allah duk ɗaya muke, kuma matuƙar Allah ya baka dukiya to ba fa kai kaɗai ya bawa ba, don ka taimaki al'ummarsa ya baka, ba kai kaɗai da matarka da ƴaƴanka ba, wani ma ko mahaifansa baya taimakawa, Allah kasa mu cika da imani Amin.
Baby ta taso da sauri ta kama hannun Ummita da Khairat ta ce"our welcome my sister's,kunga wannan Momy na ce,ina sonta sosai whith all my heart,kunga wancen na hoton ?Dady na ne ina sonshi sosai ba kaɗan ba."
su Ummita suka kalli hoton, wani mugun bugawa gaban Ummita yayi, don har sai da ta tashi tsaye tana kallon hoton, kyakkyawa ne bana Ƙarya ba, don idan har ba faƊa maka akayi ba, tsaf zakace ba mahaifin Baby bane, saboda a fuska ma zaka iya cewa baifi shekara ashirin da Ɗoriya ba, yana sanye cikin kayan sojoji amman ba Ƙananan sojoji ba, irin manyan riƘaƘƘu waƊanda suka amsa sunansu sojoji ba muna soja ba.
Khairat ma kallon hoton take, sannan ta kalli Baby ta ce"Allah sarki Allah ya barku tare Baby, amman kuna kama sosai wallahi".
Tuni Ummita ta mace a kallon wannan hoton, Halima kuwa tuni ta tashi ta shige Ɗakinta, don yau me gidanta zai dawo gashi bata shirya masa komai ba.
Sai da Khairat ta taɓa Ummita sannan ta dawo hayyacinta, Baby ta sakasu agaba ta kaisu Ɗakin kusa dana ta, suma Ɗakinsu kamar na baby ne sai dai wasu abubuwan da suka banbanta.
Ummita ta dinga kallon Ɗakin, tsabar murna harda hawaye, don gani take ko a mafarki bata taɓa hasashen zata zauna a Ɗaki ke kyau irin wannan ba, dukiya har dukiya, kuƊi har kuƊi, don ba Ƙaramar dukiya aka zuba aƊakin ba, kai shi kansa gidan ma kana ganinsa kasan gidane wanda ya amsa sunansa gida.
Ummita tana hawaye taji an dafa kafaɗarta,yayarta ce Khairat ta ce"Ummita kinga ikon Allah ko?gaskiya mutanan nan basu da girman kai, gasu basa banbanta kansu damu, ki duba fa kiga kayan jikinmu?kanar tsumma amman a haka Yarinyar nan ta riƘe hannunmu har tana bamu labari, gaskiya wannan matar ta koyawa Ƴarta tarbiyya me kyau, kuma ta koya mata son talakawa, gaskiya Ummita mu riƙe su da amana."
Ummita ta ce"ni mamaki ma suke bani, ni fa ko nice a matsayinsu wallahi bazanyi haka ba, tsakanina da talaka daga nesa ne amman ba akusa ba, gaskiya sun bani mamaki wallahi kamar ba masu kuƊi ba."
Khairat ta tsirawa Ƙanwarta ido, tana mamakin hali na son zuciya irin nata, ta ce"Ummita duk wanda kika ga yana wulaƘanta mutane to tabbas fa bai gaji arziƘi ba, duk wanda ya gaji arziƘi sama da Ƙasa wallahi baya wannan wulaƘancin da ke kike Ɗorawa kanki, don haka ina me jan hankalinki daki cire buri arayuwarki, ki zamo me biyayya gana samanki, kamar dai ita wannan matar mu zama masu yi mata biyayya kuma mu zauna da i'ta a kowani hali take."
Ummita bata ma san tana yi ba, ta Ƙwanta ta baya akan Ƙaton gadonsu sannan ta ce"kai sabuwar duniya kenan, ya Allah mun gode maka da wannan ni'imar, gaskiya daga yau nima na fara jin kai na asama,don kaf unguwar babu me gida irin wannan har masu ji da kuƊin ma".
Khairat bata kulata ba, don sam ummita bata sauraran wa'azi ballantana ma har tayi aiki dashi.
-----*****-----
*ƘAUYEN ME SAMARI*
. . .gudu take sosai kamar zata tashi sama sai haki take, wani ƙaton mutum ne ke binta gashi ƙato dashi, yana da ƙiba sosai don gudun ma da ƙer yake gudun abin tausayi, Indo ƴar caskale ta juyo tana mishi gwalo, tana gudun tana ce wa.
"a'i daman na faɗa maka aradun Allah baka isa ka kamani ba, ƙato da kai kamar buhun lalle".ta faɗi hakan tana mishi dariyar mugunta.
Shi kuwa sai nausa mata zagi yake, yana fatan Allah yasa ya kamata sai ya kusa karyata, don yarinyar sam ba tada mutunci tasha zuwar masa gona tana lalata masa kayan marmarinsa, sai kace ɓera gashi sam ba tada tsoro, idan ka kamata kayi mata gargaɗi to fa kamar ka zugata ne, don gobe ma sai tayi tsayawa yayi yana hakki, yana nuna ta da yatsansa ya ce."he giya me gudu kamar na barewa,in sha Allah sai kinyi nadamar zaluntar mutane arayuwarki".
Kash!mutane don Allah mu dinga faɗin alkhairi, saboda baki arayuwa ba ƙaramin abu bane.
Indo Ƴar caskale kuwa kai tsaye gidan kakarta ta wuce, ta zauna tana haki a tsakar gidan,Inna tana fitowa daga mazagaya ta ce"oh Indo yau kuma wa kika tsokani"?.
Chono baki tayi gaba ta kyal kyale da dariya sannan ta ce"wallahi Musa me gonar mangoro na tsokano,hege muka dinga gudu dashi Aradu daya gaji tsayawa yayi yana haki, wai har yana ce wa sai ya kamani ya dake ni, ni kuma nace dake ni in gani?hi ne fa muka dinga ƴar tsere dashi har ya gaji".
Kaka ta ce"Kin kyauta Indo ,daman rowar tsiya ce dashi gashi ba shida mutunci ko kaɗan, bai san taimako ba a'i gwara da kika yi mai ɓarnar ko Allah yasa ya gane Ya fara taimako".
Kaka na maganarta ni kuma ina fito da Mangwaro da kashu dana ɗakkowa Musa, Na dinga shan abina hankali ƙwance Na miƙowa Inna wai tasha?ta ce"a'a Indo sha abinki ki more ni cikina yanzu sai a hankali."
Dariya Indo tayi har tana riƙe ciki sannan ta ce"hhhh wo Kaka jiya ma ina jinki da daddare kina ta sakin ɗan wake".
Kaka ta biyo ni zata ranƙwashe ni, nayi mata gwalo na ce"to na tafi gida sai ki ga wanda zaki daka".
Na taho ina shan mangwaro na, ina waƘata abina ko ajikina don yanzu idan tsokana tazo yinta zanyi, in kuma tsere abina dai dai ka gama wahalarka ka koma, Allah ya taimakeni ina da tsokana kuma ina da Ƙarfi, don Ƙawaye na da dama ni ke tare mudu faɗa musamman ma Bintu don Ƙawata ce aminiya, sai dai ita sam ba tada faɗa ko kaƊan, tana da matuƘar sanyi da kuma haƘuri, saɓanin ni da bana zama lafiya kullum cikin Tsokanar mutane nake.
Saboda tsabar faɗana aka sakamin suna'Indo Ƴar caskale,tun daga tashar garinmu indai har ka Ƙwatanta sunana to za'a kawoka har gidanmu.
Indo kyakkyawace sosai, don gata daman Ƴar fillo uwa da uba, duk fulanine tana da kyau na ban birgewa, Indo dai irin Ƴan duma duman mata ne,ba tada wani tsayi sai dai tana da Ɗan jiki amman ba cen ba, fara ce amman ba fara cen ba, tana da dogon hanci da kuma Ɗan Ƙaramin baki, fuskarta a zagaye take da kyakkyawan saje wanda yayi matuƙar Ƙawata fuskarta.
ansha faɗa akan aƘauyen me samari, sai dai fa Indo ko ajikinta don daman haka Indo take tafi son taga ana ta tashin hankali, don har faƊa take indai taga Ƙwana biyu ba'ayi faƊa ba sai kaji tana cewa'kai gaskiya ya kamata aƊan samu hayaniya a garin nan,haba gari sai kace na malamai'.
Sosai Bintu ke tsoron halin Indo,ita dai kawai don Allah ya haƊa jininta ne da Indo da tuni ta daɗe da daina Ƙawance da ita.sai a kullum addu'ah take wa aminiyarta akan Allah ya shiryeta, don tun yanzu Indo ta fara haka, ina ga gaba kuma?don a yanzu tana ma shekarunta basu wuce 14 Ba amman ta iya haƊa gwarama . . . . .✍🏾
Miss green ce🤏🏼
To ya kukaji salon?????wannan salon na dabanne,don Allah duk wanda ya karanta ya tayani share Domin su ma susha dariyar,Indo ƳAR CASKALE😄😄.
[1/27, 12:23 PM] Miss Green: *_✨INDA BA ƘASA...!!!_✨*
_(Littafi na 1📃)_
NA
*_®️UMMU MAHER(MISS GREEN)🍀_*
*_AREWA BOOK👉🏻_*
INDA BA ƘASA!!!:: https://arewabooks.com/book?id=63ce1eb0ec00e12124ce9eb0
---------------------------
*_WATTPAD👉🏻_*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
---------------------------
*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_* ---------------------------
*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIE DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
Page🟩2
------Baby ta leƙo ɗakinsu Ummita ta ce"hey guys ku fito Momcy na kiranku??kun san yau Dady na zai dawo kunga sai ku taya mu sauran aikin ko".?
Ummita ta ɗan ɓata rai kaɗan, don i'ta arayuwarta ta tsani aiki wannan aikin ma don babu yadda za tayi ne da babu abinda zaisa tayi.Ta turo baki gaba suka fito tare falon Khairat kuwa ko kallonta bata yi ba, don mugun haushinta take ji saboda mugun burin da take dashi arayuwarta, kana ɗan talaka?amman ka dinga ɗorawa kanka rayuwar da ba taka ba?.
Suna i'sowa falon Kyakkyawar matar na zaune tana waya, hankalinta ƙwance Ummita ta kalli ƙafarta yadda aka rangaɗa mata lalle me matuƙar kyau, daman gata fara sol kamar balarabiya sai lallen yayi kamar don ita aka yishi.
Tuni Ummita taji wani irin mugun mashin baƙin ciki ya tsarga mata, sai taji dama ita ce Wannan matar Yadda take rayuwarta ita kaɗai agidanta, ka mijinta kyakkyawan ƙarshe, wanda take ji dama ace mijinta ne, to da daga ranar ta hanashi fita saboda sa idon ƴan mata.
Bayan Halima ta gama wayar ne ta ce"Ummita Khairat ku tashi mu shiga kitchen, dafatan dai kun iya girki ko"???.
Ɗaga kai sukayi dukansu, Ummita kuwa sai kallonta take har sai da Khairat ta ɗam dungure ta sannan ta juyo suka shiga kitchen ɗin, sosai Take kallon kitchen ɗin tana yaba irin mugun kyaun da ya yi, kitchen ne me mugun girma gashi an tsarashi sosai, komai na kitchen ɗin ja ne da fari harda wata ƙatuwar Tv a kitchen ɗin, Ummita fa ta samu abin kallo don har Halima ta fito musu da kayan aikin bata san ma an fito dasu ba, ita dai hankalinta yana kan kayan kitchen ɗin wani abin ma idan ta ganshi tsoro yake bata.
Khairat ta ɗan taɓata kaɗan sannan ta dawo hayyacinta, Halima ta fara koya musu komai yadda ya zasuyi amfani da kayan kitchen ɗin, nan da nan suka fara aikinsu cikin ƙwarewa, Ummita ta ƙware a girki sosai, don aƙwai wata me siyarda abinci da tayi aiki awajenta to ananne ta zama star awajen girki.
Halima tayi mamaki sosai, don wani abin ma itace ke koya mata yadda za tayi, don haka sai ta saki jikinta ta barsu suka cigaba da gabatar da komai yadda ya kamata.
Halima ta wuce kai tsaye ɗakinta ta shirya cikin wasu haɗaɗɗan leshi wanda ya amsa sunansa, tayi kyau sosai sai walƙiya take gwanin sha'awa, kai ka ce yau take sallah Ummita ta saki baki da hanci tana kallon Halima, alokacin da take shigowa cikin madafar,ta nuna musu yadda zasu jera kayan abincin,shi kanshi dining ɗin abin kallo ne, ƙato ne sosai zai iya cin kujeru sha huɗu,an ƙawatashi sosai bayan sun gama aikinne Halima ta basu kaya tace su sanya,Kaya ne masu kyau sosai kana ganinsu kuma kasan masu tsada ne sosai.
Ummita ta ajje kayan ta shiga banɗaki wanka, sosai take kallon banɗakin yadda akayi matuƙar ƙayatashi,komai na banɗakin kalar sararin samaniya ne, Ummita kam bata iya amfani da komai ba, don haka ta fito kai tsaye,Khairat ta kalleta ta ce"lafiya dai Ummita?ke fa nake jira inyi wanka?".
Ummita ta ɓata rai sosai sannan ta cuno ɗan ƙaramin bakinta ta ce"Anty Khairat Allah na rasa yadda zanyi anfani da komai na banɗakin nan".?
Khairat ta ce"to ba sai mu tambayi Baby ba?a'i ina ganin zai fi sauƙi ko"?.
Ummita ta ɓata rai sannan ta ce"Hmm Gaskiya Khairat kina son jaza mana raini wallahi,yanzu idan banda haka a'i ba sai mun tambaye ta ba?muje kawai muyi ta gwadawa har mu samu mu iya komai".?
Khairat ta kalli ƙanwarta sosai sannan ta ce"kash!gaskiya Ummita girman kanki yana bani mamaki?idan banda haka wai har kike faɗar zan jaza mana raini wajen Baby?ke idan kina da nutsuwa da hankali,a'i mu awajensu musakai ne mu?amman basu ɗauke mu haka ba?don me mu baza mu yi musu biyayya ba?yanzu idan muka shiga banɗakin muka ɓata wani abin fa?ke kina ganin zamu iya gyarawa?kuma sai muje muce musu me"?.
Ummita ta taɓe baki sannan ta ce"To sai dai ke kije ki tambaya amman ni dai bazanje ba?wannan ma a'i salon jazawa kai raini ne."
Ita dai Khairat bata kulata ba ta wuce wajen Baby,A falo ta same ta tana waya,sai da ta ɗan tsaya ta kamalla sanna ta juyo da murmushi ta ce"Anty Khairat ya naga bakiyi wankan ba"?.
Khairat ta ɗan murmusa sannan ta ce"daman wallahi banɗakin ne muka kasa amfani dashi,to shine nace bari mu tambayi Baby".
Baby ta ce"to muje Anty Khairat,don yanzu saura minti sha biyar jirginsu Dady ya sauka,kuma kunga tare zamuje daku don taro Dady na".
Khairat dai bata ce komai ba,don ita sam ba tada magana,idan kaji tayi magana to sai dai abu ne me muhimmaci,ita a ganinta a'i bai kamata a tafi dasu taro wannan hamshaƙin kyakkyawan ba,gashi kuma su da suke masu aiki?a'i gwara a barsu agida su ƙarasa wasu ayyukan,kuma sai take gani kamar dai matar gidan tasa an kawo sune don su ɗauke musu kewa,don masu aiki maza da mata sunfi Goma agidan,duk kuma suna sanye ne da uniform ɗinsu gwanin sha'awa.
Ummita na ganin shigowarsu ta miƙe ta tashi,tana ɗan sosa ƙeya don ita aganinta a'i abin kunya ne wannan.
Baby kuwa kai tsaye ta shige banɗakin,ta koya wa Khairat komai ita kuwa ƴar girman kan tana ɗaki ta kasa zuwa taga komai.
Baby ta fito abinta,tana tsokanar Ummita ta fita waje,Ummita na ganin ta fita ta matso kusa da Khairat ta ce"ni wallahi Kunyar Babyn nan nake ji wallahi,musamman ma yanzu da kika sa ta gane mu ƴan ƙauye ne".Khairat dai bata ce mata komai ba ta fara cire kayanta tana ɗaura wani tawul alamar zata shiga wanka.
Ganin hakan yasa Ummita ta wuce banɗakin da gudu tana cewa"tunda an kunna fanfon a'i ba komai,bari inyi wanka na wankan da ban taɓayi ba,don taro kyakkyawa Baban Baby".
Ita dai Khairat kasa magana tayi,saboda yadda take nuna abu afili babu wani ɓoye ɓoye,Baban Baby shi kuwa wata irin macece bai taɓa gani ba?tunda yanzu ma wataƙil daga garin turawa xai dawo?."
Wani irin mugun ihu Ummita tayi,da gudu ta fito tana ihu tana cewa"wayyo Allah na fuskata,na ƙone Wallahi fuskata ta ƙone don Allah Khairat ki duba min"?.
Abinka da ɗan uwa da sauri Khairat ta fara duba mata fuskar,da yake Ummita fara ce sai ga wajen har ya ɗashe yayi jawur..sai kuma lokacinne Khairat ta tuno Baby ta ce mata fanfan na ruwan zafi ne,ga bokiti nan idan tana son ta haɗa ga fanfan sanyi nan gana Zafi,idan kuma da shower zasuyi gashinan,duk ta koyawa Khairat komai ita kuma ƴar girman kai bata tsaya ta koyi komai ba,ita dai abinda ta sani girman kai da kuma Buri.
Sosai Ummita ke kuka,Khairat tayi rarrashin har ta gaji sannan ta miƙe ta ce"Kizo muje in nuna miki yadda ake amfani da komai,don naga ke har yanzu baki san komai ba amman kuma girman kai ya hanaki ki koya".
Babu yadda Ummita za tayi,dolenta ta shige gaba suka shiga banɗakin don itama tana son koya,ko don gaba tunda sunzo gidan ne bada niyyar yini ba.
Khairat ta nuna mata komai sannan ta fito daga banɗakin,Sosai Ummita tayi wanka kamar zata canja fatar jikinta,tana yi tana santin ruwan da kuma sabulun,saboda ruwan wani irin mugun daɗin wanka ne dashi,ga sabulun da mugun ƙamshi gami da kumfa kamar kamfanin sabulu.
Ta ɗauki mintina da dama tana wannan wankan,har Khairat ta gaji taje bakin banɗakin tana bugawa,amman Ummita ko ajikinta sai da ta gama tsaf sannan ta fito,alokacin har Baby ta iso kuma lokacin bai fi mintina ya sauka ba.
Baby ta ce"kash!har yanzu baku gama ba?Momy na ta jiranku?to bari mu tafi saboda wallahi sun kusa sauka,gwara muje kuyi haƙuri yanzu zamu dawo".
Ummita ta kasa magana saboda tsabar baƙin ciki,ji take kamar ta kamo Baby ra daka taso ace yau ɗaya sunje filin jirgi amman Baby ta hana faruwar hakan,a cewarta wannan a'i baƙin ciki ne don kada aga Babanta.
Ita kuwa Baby taba fitowa ta samu Halima har ta shiga danƙareriyar motarta tana jiransu,Securities suna tsai tsai suna jiran su shiga su rufe.
Baby na shiga kuwa suka rufe,Halima ta ce"Baby lafiya kika taho ke kaɗai?ko basu shirya bane"?.
Baby ta ce"eh Momy basu shirya ba,kuma kinga Dadyna ya kusa sauka."
Halima ta ce"haka ne gaskiya don yanzun ma sai dai muyi sauri".
Halima na bada uder ɗin su tafi,motocin suka biyo bayansu wasu agabansu wasu a bayansu haka suka tafi Filin jirgin Baby sai murna take ita dai za taga Dadynta.
Halima kuwa duk bayan mintina sai tayi murmushi,yau wata biyu kenan rabonta da ta saka gwarzon mijinta a idonta,tana masifar son mijinta da kuma ƙaunarsa,bata son duk wani abunda zai shiga tsakaninta da mijinta,tana addu'ar Allah ubangiji ya barta da mijinta har abada.
********
. . .kai tsaye Indo gidansu ta wuce,tana shigowa gidan ta iske Innarta na tankaɗe,Indo ta zumbuɗo baki gaba sanan ta ce"gettere ! Yauma tuwon zakiyi Inna?gaskiya ni bazanci ba".?
Ko kallonta Innar bata yi ba,ta cigaba da tankaɗenta,Yayar Indo Aminatu nata wanke wanke,ta ce"don Allah Indo zo ki ƙarasamin zanje Makarantar Allo in bada hadda"?.
Indo ta ce"oh ni sai akace miki gantali nake ko?to zauna ki ƙarasa kayanki,kije kuma kisha bulalar malam Modibbo".
Aminatu tayi rau rau da idanuwa sannan ta ce"Inna kice mata ta tayani Allah za'a dake ni,ita kuma kinga ba zuwa take ba yanzu".
Inna ta kalli Indo sannan ta ce"ke yanzu Indo sai ance miki ki taya yayarki aiki?ke kullum babu abinda kika iya sai shegen yawo?babu arabi babu boko"?.
Indo ta zumɓuro baki sannan ta ce"Allah don Inna ta saka bakine da babu abinda zanyi,tunda ke kin iya haɗa mutum da iyayensa."
murmushi Amina tayi kawai ba tare da tace komai ba,don Idan Indo na da kunya baza ta ce mata wai tana haɗa ta da iyayenta ba,don mahaifinsu yana masifar son Indo akaf cikin ƴaƴansa,yana son Indo sosai son da shi kansa baya yiwa kansa,bai ƙi yarasa komai ba indai zai buɗe idanuwansa ya gansa gashi ga Indo.
Aminatu ta wuce kawai ta sanya hijabinta,sannan ta ɗauki allonta ta wuce abinta,Indo kuwa sai harararta take ita kuwa Inna sai kallonta take sannan ta ce"idan kin gama hararar ƴar uwar taki sai ki wuce kiyi wanke wanken".
Indo ta zauna ta ƙarasa wanke wanken,tana roƙar ubangiji Allah yasa wani ya shiga gonarta yaji jiki,ai kuwa akayi sa'a sai ga Matar Babanta ta fito daga ɗaki,wacce ake cewa Inna Harira ta ce"Indo yau kuma ke ce da wanke wanke?duk rashin kunyarki?duk yadda akayi wani rashin mutuncin kike so ki ƙulla".
Indo bata kulata ba ta cigaba da wanke wankenta,Innar Indo kuwa Murna take Indonta ta fara hankali,tunda gashi an kulata don ayi rigima kuma taƙi kulawa.
Daman matan Mahaifin Indo Huɗu ne,Kuma mahaifiyarta ce uwar gida ammanfa mahaifin Indo mutun ne me auri sake,ya auri mata yafi sai a irga,wasunsu akan Indo ake sakinsu wasu kuma wani dalilinne,su Indo suna da yawa a ƙalla zasu kai Su ashirin da biyar wasu yaran suna gidan wasu kuma suna wajen iyayensu,Indo ƴar gata ce sosai awajen mahaifinta,ko da mahaifiyarta ne kuwa zai iya yin kacaca don yana masifar sonta kamar ruhi.
Indo ta kammala wanke wankenta ta kai ɗaki ta ajje,Allah ya taimaketa Inna ta gama Tuwonta da wuri.
Inna Harira ta kalli Mahaifiyar Indo a wani wulaƙance sannan ta ce"yauwa Idan kin sauke zan ɗora ruwan zafi".Innar Indo ta ce"la babu komai zo ki ɗora Harira".
Inna Harira ta ce"saka Indo ta ɗoramin saboda kaina ke ciwo".Innar Indo tasan babu wani ciwon kai amman saboda kada dai ta bada ita awajen Indo ta ce"Indo zo ki ɗorawa Innarki ruwan zafi".
Nan ma Indo bata ce komai ba ta wuce abinta wuce ta ɗora mata ruwan zafin,Tazo zata shiga ɗakinsu kenan Inna Harira ta watso mata ruwa,sai tayi sauri ta ce"yi haƙuri fa ban sani ba".
Tana faɗar hakan ta tintsire da dariya sannan ta wuce ɗakinta,Innar Indo tana jinta tasan babu wani tana sane tayi hakan,Indo ta shigo ɗakin ko ajikinta ta cire kayanta,agaban Innarta babu ruwanta don ita kullum ganin kanta take ƙaramar yarinya.
Innar ta ce"Indo wai ke haryanzu baki girma bane?a yanzu fa kina da kusan shekara sha huɗu amman baza ki daina wannan haukar taki ba"?.ki kiyaye ni akan kina cire kaya agabana."
Indo ta turo baki sannan ta ce"ba Inna Harira ce take son ta kaini ƙarshe ba?Allah ina tsoron muguntar da zan mata,don wallahi har ta mutu baza ta manta dani ba ehe".
Indo ta faɗi hakan tana cire wasu kaya riga da wando kamar na pakistan,cikin kayan da Baffanta ke siyo mata.tana saka kayan tana murguɗa baki tare da mita.
Innar Indo ta girgiza kanta don tasan Indo baza ta daina abinda take ba,sai kuwa taji Indo ta kyalkyale da dariya sannan ta ce"hhhhhh ho ni Indo magani Hegi da Hegiya maganin ƴar banza da ɗan banza,a taɓoni a taɓo masifa ka barni ka zauna baki alekum".
Innar ta kalleta sosai,ita wani lokacin ma idan Indo tayi wani abun gani take kamar ba ita kaɗai ce tayi ba saboda yadda ta iya zaro maganganu.. . . . .✍🏾
*Ku nuna mana soyayya wajen share,tare da comments wannan ita kaɗai ce hanyar da zamusan kuna ƙaunarmu🙏🏼Allah kabarmu da masoyanmu na asali Amin.*
*Noticed!Noticed🗣️🗣️!!*👇🏻👇🏻
Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent,sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki,kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻
07068606171
08104335144
08179523215
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
*MISS GREEN CE👉🏾👉🏻*
[1/28, 10:35 AM] Miss Green: *_✨INDA BA ƘASA...!!!_✨*
_(Littafi na 1📃)_
NA
*_®️UMMU MAHER(MISS GREEN)🍀_*
*_AREWA BOOK👉🏻_*
INDA BA ƘASA!!!:: https://arewabooks.com/book?id=63ce1eb0ec00e12124ce9eb0
---------------------------
*_WATTPAD👉🏻_*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
---------------------------
*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_* ---------------------------
*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIE DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
Page🟫3
*AMINU KANO INTERNATIONAL AIPORT*
------A hankali ya fara sakkowa daga matattakalar Jirgin, yana tafiya cikin nutsuwa kana ganinshi kasan cewa mutunne me ilimi da sanin ya kamata, don nagarta ce fal a fuskarsa da kuma kamala, sanye yake cikin manyan kaya kamar kowanni lokaci, don shi mutunne me son manyan kaya,da wuya kaga ya saka ƙananan kaya.
Shadda ce ajikinsa kalar sararin samaniya, ɗin kin taxarce a mutunce, ya sanya hularsa kalar sararin samaniya, takalminsa baƙi agogon hannunsa ma baƙi ne sai walƙiya yake.
General Muhammad Aliyu Maska,shine asalin sunanshi Maska kuma shine asalin garin mahaifiyarsa dana mahaifinsa, don mahaifansa duk ƴan gari ɗaya ne dangi ma ɗaya.
Kyakkyawane shi ta ko'ina, idan kayi mai kallon farko wajibine ka ƙara kallonsa, yana da kyau na ban burgewa da nunawa sa'a, yana da ƙwarjini sosai a idon mutane saboda komansa a nutse yake yinsa, sannan Miskili ne shi sosai don ba kowa ke ganin haƙoransa ba, sai wanda Allah yayi zai gani,sai dai duk miskilancinsa agidansa ba haka take ba, don idan ka ganshi da iyalinsa abin sai ya baka sha'awa,don ko bature bai isa ya kama ƙafarsa ba.
Da gudu Baby ta taho tana zuwa ta rungune mahaifinta sosai,shima rungume ƴar tasa yayi sannan ya ce.
"Baby kinyi girma fa yanzu Masha Allah,b azan iya ɗaukar ki ba?don haka a daina rungumeni ni dai tunda yanzu kin girma".
Doka ƙafarta ta hau yi kamar ƴar jaririya,ya lakuci hancinta sannan ya ce"yimin murmushi mana My mom".?
Ya faɗi hakan yana kama kunnensa,Sosai Baby take dariya sannan ta ce"Dady ka siyomin teddy ɗin"??.
Sosai ya fashe da dariya sannan ya ce"yeh!na bada oder ɗinta za'a kawo miki Teddy me girma kamar ke my Daughter".
Halima na gefe tana kallonsu cikin sha'awarsu don tana masifar jin daɗin ganin Baby da mahaifinta a haka,wani tsohon son yayarta ya tasar mata,ta rufe fuskarta kaɗan tana hawaye na tunowa da yayarta marigayiya wato mahaifiyar Baby,har yanzu gani take kamar taci amanar yayarta na aure mata mijinta,sai dai babu yadda za tayi don haka rabbi ya tsara.
Kuma ayanzu baza ta iya rabuwa da mijinta abin sonta ba,tana masifar son MD son da baza ta taɓa iya daina yi masa ba,sonshi acikin jininta yake.
General Muhammad Aliyu ayanzu haka yana neman takarar kujerar gomna,wanda a halin yanzu har an kusa zaɓe,Filin jirgin cike yake da masoya da magoya bayansa,har bai san yawansu ba mutane suna son MD sosai,don ba da kanshi ma ya nemi kujerar ba,mutane ne suka nemar masa saboda da cewarsa,don mutunne me son mutane,maƙwaftansa kuwa ba ƙaramin taimakonsu yake ba,kyaun gidansa da tsaruwarsa kamata yayi ace yana G.R.A unguwar masu kuɗi,amman yana cikin mutane abinsa,don ya taso cikin mutane,don ayanzu haka su goma sha huɗu ne awajen mahaifiyarsu,sannan kishiyarta ba sa guda 8.
Don haka shiyasa ya taso da son mutane sosai,Gashi da taimakon marayu da waɗanda basu da ƙarfi,bai ƙi ya zauna haka ba indai har zai taimaki marayu,duk bayan ƙarshen kowani wata yana zuwa gidan marayu don ziyartarsu,tare da kai musu taimakon abinda ba suda shi,baya ɗora kowa akan taimakon mutane,shi da kansa yake zuwa ya kai babu ruwanshi da girman kai,shiyasa iyalinsa ma suka taso cikin wannan rayuwar,bai nuna musu su daban suke ba,ya nuna musu duk ɗaya suke da Talakawa,hatta ƴarsa Baby makarantar Gomnati tayi,don shi bai yarda makarantar gomnati ba'a samun ilimi me nagarta ba,abinda ya lura dashi makamai ne babu na gari kuma indai aka samu malamai nagari to tabbas za'a samu ilimi na gari.
Sunan Mataimakinsa Dr Aliyu Umar Mashi,shima mutunne nagari don babu ruwanshi da abin duniya da kuma abinda ke cikinta,don abinda ya ɗauka shine duniya ba abar zama ba ce,yau gare ka gobe ga waninka in yau kai ne gobe ba kai bane.
Bayan sunyi musabaha da mataimakinsa suka gaisa da magoya bayansa,sannan ya nufo Inda Halima take,ya rungumo abarsa ya rungume agaban mutane babu ruwansa,don kowa yasan matarsa ce kuma shi fa bai ɗauki runguma awani abuba,don runguma ba turawa ne suka fara yinta ba,larabawa musulmai sune suka shigo da ita da kuma(sumba)wato kiss,ashi ko agaban waye yin abinsa yake ga matarsa don bai ɗauki abin a matsayin wani abuba.
Mota ɗaya suke da matarsa da kuma ƴarsa Baby,Mataimakinsa kuma da sauran mutanensu,sai kuma securities ɗinsu waɗanda suka rakosu.
Kai tsaye gidan mahaifansa ya fara zuwa,Halima tayi shiru tana tunanin haɗuwarta da Hajiyar Maska,surukarta ba tada ta ido ko kaɗan,maƙasudin daya sa mijinta ke yawaita tafiye tafiye kenan,saboda mahaifiyarsa mutunce me matuƙar faɗa da kuma rashin sanin darajar mutane,takan rufe idonta ta yiwa mutun ta tas,shiyasa sam Halima bata son zuwa wajenta,indai ba da mijinta ba shima kuma don babu yadda za tayi ne dashi,don indai yayi tafiya kafin yaje gida sai ya fara zuwa yaga lafiyar iyayensa.
Gidane ƙato me kyau da tsaruwa,gidane wanda ya amsa sunansa gida gashi ƙato sosai,yana da part kusan guda Baƙwai agidan,Ɗaya na mahaifinsa,ɗaya kuma na mahaifiyarsa,ɗaya na kishiyar Hajiyarsa,ɗaya kuma na kakar MD wacce aka fi sani da Hajiya Kaka.sauran part ukun kuma na ƙannensa ne,na mata guda ɗaya na maza kuma guda biyu don maza sunfi yawa agidansu,a haihuwa shine na biyu agidansu.
Gate biyu ne agidan,wanda yake cike da sojoji waɗanda suke a tsaye sun saita bindigunsu kamar zasuyi harbi,ba abin mamaki bane don an samu sojoji agidan ba,don bayan MD ƙannensa goma maza duk sojoji ne kowanne kuma da muƙaminsa,aƙwai major general,aƙwai captain,aƙwai Admiral,aƙwai general da sauransu.
Shiyasa tun daga gate ɗin farko zaka san lallai gidan Sojoji kazo saboda tsaron da gidan yake dashi da kuma yawan sojojin gidan.
A hankali Halima ta fito,duk jikinta a matuƙar sanyaye tana tunanin irin haɗuwar da zatayi da Hajiyar MD,tuni taji zuciyarta babu daɗi,bawai bata son mahaifiyar mijinta bane?a'a abu ɗaya ne yasa take nesa da ita,na komai bane illa gorin rashin haihuwa,wanda ta sanya ta agaba ta hana ta shan ruwa,gorin haihuwa abune me ciwo,wanda ba kowacce macece tasan hakan ba,sai wadda take cikin wannan matsalar,ita kaɗai ce zata iya fahimtar abinda take ji.
Shi kuwa MD tuni ya wuce sashen mahaifinsa,don yaga ƙofar a buɗe ita kuwa Halima kasa shiga cikin gidan tayi,don bata san kalar masifar daza ta haɗu da'ita yau ba,tayi ta gumi a jikin motar har Baby tayi gaba kuma sai ta dawo baya ta ce"a'ah Momy lafiya naga kin tsaya"?.
Halima bata amsa mata ba,don tasan Baby aƙwai kaifin basira,tsaf zata iya gano abinda ya hanata shiga.
Baby ta ce"Momy nasan abinda ya hanaki shiga?Hajiya ce ko?don Allah momy ki cire tunanin Hajiya aranki,bana son kina ɗorawa kanki tunani akan Hajiya,Hajiya fa bata da wuta ba tada aljanna,duk faɗanta sai dai tayi ta gama,kuma don Allah kada kiyi kukan nan da kikewa Hajiya,shiyasa takw miki yadda take mikin,amman idan kika nuna abin bai miki zafi ba sai kiga an zauna lafiya,tunda dukkanku dai babu yadda zakuyi da juna,ita mahaifiyar mijinki ke kuma matarsa,kowaccenku zata iya kaishi wuta,don haka don Allah Momy kada ki nunawa Hajiya wani abu."?
*INDO ƳAR CASKALE*😂
--------Indo na ganin Inna Harira ta shiga wanka,ta sheƙe da dariya sannan ta ce"hhh yau za'ayi allan dungure agidan nan,yau za'aci uwar sabada Inna Harira yau zaki gane kurenki,sai na nuna kiki ni ba kanwar lasa bace,ba'a taɓani abanza sai na rama zansan na haifu".
Shigewa ɗakin Innarta tayi,alokacin tana Sallah Indo tayi dariya ciki-ciki wato ta samu yadda take so kenan,ta buɗe wata samira ta ɗakko wani abu,ta ɓoyeshi a hannunta ta fita a hankali,Dai dai lokacin Amina ta dawo daga makaranta,Indo na ganinta ta harare ta wuce,ashe bata sani ba ledar ta ɗan leƙo ana ganin komai.
Amina ta ce"Indo ke kuma me zakiyi da Yaji me uban yawa"?.
Indo ta ce"gettere zanci wanda Inna tayi,kinsan cinsa dole sai da yaji gwara in ɗan saka yafi daɗin ci".
Amina ta kalle ta ba tare da tace mata komai ba,sai dai sam bata yarda da Indon ba,don tasan halin ƙanwarta ba tada yafiya ko kaɗan.
A hankali Indo ta ɗan zira hannunta,sai taji ta taɓa bokitin,kuma da alama Inna Harira ta juya bayanta ne,ta buɗe ledar yajin ta juye sa duka aciki.
A hankali ta koma ɗakinsu,ta sheƙe da wata dariya ta ce"wooo ni Indo,yau za'a ga rawar asosa agidan nan,daman na daɗe banga rawar banga ba,yau Allah yasa zan ganta agidan nan."
Inna ta kalleta sannan ta ce"Indo me kika aikata?ke fa bakyason zaman lafiya a rayuwarki?kinsan Allah jikinkine zai gaya miki,saboda bazaki kashe ni ba,tunda ba ke kaɗai na haifa ba kinji".
Indo kuwa kamar mutuniyar arziƙi ta wuce,ta buɗe samirar tuwo tana turo baki sai dai babu yadda za tayi dole taci don Baffanta baya nan.
Don tasan da Baffanta yana nan babu abinda zaisa taci tuwo,da cen bakin kasuwa zai kaita taci abinda take so ta ture.
Tana cikin cin tuwon ta fara jiyo ihu a banɗaki,Ta kasa kunne sai taji Inna Harira tana cewa.
"Wayyo Allah na!wayyo Allah na!!!jama'a a kawo ɗauki zan mutu,yaji zai kashe ni wayyo Allah na".
Sosai take ihu,matan gidan da yaransu duka suka fito don ganin abinda ke faruwa,Indo kuwa ko ajikinta ƙara gyara zamanta ma tayi,ta cigaba da cin tuwonta tana ƙara haɓɓaka muguntarta akan duk wanda yayi gigin shiga sabgarta.
Da ƙer Inna Harira ta samu ta sanya zaninta sannan ta fito,ta cigaba da ihu idanuwanta a rufe tana neman taimako,amman babu wanda ya iya zuwa wajenta,don duk daman haushinta sukeji,saboda yadda take da shisshigi ga kuma muguwar muguntarta.
Ƴaƴanta ne ma sukazo suna kuka suna tambayarta abinda ke faruwa,Da sauri Innar Indo ta ƙaraso tana cewa"subhanalillah sannu Harira?me ya faru?a ina kika samo yaji"?.
Inna Harira ta taƙarƙare ta zunduma wani irin ihu tana cewa"wayyo Allahna mutane ku kawo min ɗauki,fatata zata yage wayyo yaji zai kashe ni".
Mutuniyarku Indo gwalo tayi sannan ta wuce abinta ta sauke ruwan zafinta,sannan ta shiga wankanta bayan ta wanke banɗakin,Harira kuwa da ƙer aka ta aka shiga da ita ɗaki,ta sandare ta koma kamar me aljanu sai surutai take tana ihu,Indo kuwa cewa take"gobe ma kya sake muguwa kawai me mugun nufi,aini duk muguntarki a tafin hannuna kike,tayi wata shewa ta ce"woo ni Indo uwar mugu da muguwa,Wooo sai ni Indo ƴar gidan Baffa sango Woo ni Indo".
Ita kaɗai take abinta tana shafa mai,Amina ta kalleta sannan ta ce"amman gaskiya Indo bakya kyautawa wallahi,ai kome Inna Harira tayi miki bai kamata kiyi mata haka ba,ke sai kace me zuciyar fir'auna ace mutum yana musulmi amman baya yafiya?gaskiya Indo ki canja ɗabi'a wallahi,wannan ba ɗabi'ace ne kyau ba,kema fa kina yiwa Allah laifi kuma ya yafe miki".
Tunda Ta fara maganar Indo ta tsaya tana kallonta,kai kace wata ta Allah sai kuwa ta ce"ni dai wallahi Yaya Amina da masallaci ma kika koma kika fara wa'azi da ba ƙaramar jama'a zaki tara ba,don haka tun wuri ma gwara a fara kiranki da ya sayyada".
Tana faɗar hakan ta kyakyale da dariya,tana janyo gazal ɗinta tun daga gefen ido har kunne,sannan tazo tayi ɗiso ɗiso irin nasu na ƴan ƙauye,ta tashi ta sanya kayanta irin na fulani,har da sarƙar ƙafa tayi wani irin mugun kyau,duk da yanayin ƙwalliyarta.
Taraba gashin gida biyu irin yadda akewa yara,yayi mata bala'in kyau tamkar sarauniya sannan ta kitse abinta da kanta,duk Amina na kallonta amman bata isa tayi magana ba,yanzu sai cibi ya zama ƙari shiyasa taja bakinta tayi shiru,don ita kanta ma Indo ba kyaleta tayi ba.
har Indo ta fita sai kuma ta dawo da baya,ta ɗan leƙo ɗakin Inna Harira,ta hango Innarta tana haɗa manshafawa da farar hoda tana shafawa Inna Harira,don daman shine maganin Wannan raɗaɗin,musamman na yaji don haka sai shafa mata take ta yi,wasu wajajen kuma tana bata tana shafawa da kanta.
Sam Indo bata ji daɗin hakan ba,taso acean barta ta ɗanɗana kuɗarta,ba da wuri haka ba amman hakanma ko yaya ta ɗan gane karon fa da wuya,kuma ta gane shayi ba ruwa bane gobe ma ta ƙara shiga harkarta.
Tuni Innarta ta ganta don haka ta ce"Indo lafiya kike leƙowa"?.
Ganin anganta yasa ta shigo,tayi kalar tausayi sannan ta ce"ayya sannu Inna Hari Allah ya baki lafiya?Inna akira mata Malam na soro yayi mata ruƙiyya".?
Inna ta wurgamin wani kallo sannan ta ce"liman zaki kira kinji?mara kunya kawai ni dai ina faɗa miki Indo kibi duniya a sannu wallahi,idan ba haka ba wataran sai kinyi nadama me yawan gaske".
Indo ta sosai ƙeya sannan ta ce"ni dai na tafi dandali don nasan yanzu su Surbajo na nan suna jira na".
Tana faɗar hakan ta fita da sauri,don tasan ba tada gaskiya ta tsaya a soro ta dinga dariya kamar wata mahaukaciya.
Inna Harira Tayi shiru tuno da wani abu yasa ta tashi da sauri tana ce wa.
"Wallahi tallahi bazan yarda ba,aradun Allah bazan yarda ba sai an ƙwatomin Hakkina Hegiya Indo ina kike ......✍🏾😂😂
Ni kuwa Ummy maher nace ki bita dandali tana cen,Indai Indo Ƴar Caskale ce dai dai take da ke😩😂😂😂
*Ku nuna mana soyayya wajen share,tare da comments wannan ita kaɗai ce hanyar da zamusan kuna ƙaunarmu🙏🏼Allah kabarmu da masoyanmu na asali Amin.*
*Noticed!Noticed🗣️🗣️!!*👇🏻👇🏻
Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻
07068606171
08104335144
08179523215
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
*MISS GREEN CE👉🏾👉🏻*
[1/29, 10:43 AM] Miss Green: *_✨INDA BA ƘASA...!!!_✨*
_(Littafi na 1📃)_
NA
*_®️UMMU MAHER(MISS GREEN)🍀_*
*_AREWA BOOK👉🏻_*
INDA BA ƘASA!!!:: https://arewabooks.com/book?id=63ce1eb0ec00e12124ce9eb0
---------------------------
*_WATTPAD👉🏻_*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
---------------------------
*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_* ---------------------------
*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIE DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
Page🟪4
---------Babu yadda za tayi haka tabi Baby suka shiga sashen Hajiya gabanta sai faɗuwa yake,suna shigowa ɓangaren Allah ya taimakesu Hajiya bata falon,Sosai hakan ya faranta ran Halima ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da suke a danƙareren falon Hajiya.
Ta cewa Baby"bana son in shiga ɗakin Hajiya don ina tunanin ko ba ita kaɗai bace,in kin shiga Baby sai kice tare muke don wataƙil ko Baba yana nan don naga sashensa abuɗe".
Baby ta ce"to Momy bari in shiga sai in gaya mata,amman ni wallahi da nayi zamana anan,don bana son masifar wannan jarababbiyar tsohuwar".Baby ta faɗi hakan tana chono baki gaba don ta tsani duk wanda baya son mahaifiyarta,don ita fa haryanzu gani take Halima ce mahaifiyarta,don bata taɓa nuna mata wani abu da zaisa ta san ita ba mahaifiyarta bace,kuma ko gorin da akewa Halimar ma cewa take'wai su Momy basu san sanda kika haifeni bane?ko don sunga har yanzu baki sake haihuwa bane'?.
Sosai maganar ke dukan zuciyar Halima,sai dai babu yadda za tayi don tasan ba itace ta haifi Baby ba,amman har aranta tana jin kamar itace ta tsugunna ta haifi Baby,tunda yayarta ce ta haife ta.
Baby na shiga ta iske Hajiyar Maska na waya,tana ganinta ta kashe wayar tana cewa"sai da Safe Hajiya Talatu".
Baby ta ce"Hajiya Ina wuni".?
Hajiyar ta kalleta sannan ta ce"lafiya klau Taƙwarata,ya gidan?yau uwar baƙin halin ta barki kizo inda muke?saboda kada mu cinye ki?amman a'i kina zuwa gidan Hajiya Xulaiha ko?tunda ita wannan kakarki ce ta wajen uwa ko"?.
Baby ta zumɓuro baki gaba tamkar zatayi kuka ta kalli Hajiya da Lulu Eyes ɗinta ta ce"Hajiya ni fa Momy bata hanani zuwa nan gidan,nima makaranta ce ke hanani zuwa wajenku".
Hajiya ta ce"ni zaki faɗawa makaranta?babu weekend ne?ke dai kawai kice uwar riƙonki ta koya miki baƙin hali?to a'i kuwa idan kika ce halin wannan zakiyi zakisha wahala sosai".
I'ta dai Baby bata ƙara magana ba,don Allah Allah take ta fita daga ɗakin,sam bata san taji wani ko wata yana zagar mata mahaifiya,kuma ta tsani kalmar nan da mutane ke faɗa mata a kullum wai Mimynta ba mahaifiyarta ba ce.
Tana cikin wannan halinne taji Hajiya na cewa"kinzo kin tsaya min aka kamar wata sandar ba'are,ke idan an faɗi laifin uwar riƙonki sai ki hau cika kina batsewa kamar zakiyi duka ko?".
Baby ta fara magana a ƙage ta ce"Hajiya don Allah abar wannan maganar,ni da Momyna ce ita tana falo,kuma mun rako Dadyna yau ya dawo daga tafiyar da yayi".
Hajiyar Maska ta fara magana cikin faɗa.
"Oh aiko ki tayi kizo ki jawo ni ki kai ni?bata san ɗakina ba?ko kuwa yau ma ranin tazo ta gwadamin?to wallahi Halima ta kiyaye ni,idan ba haka ba zata san tayi da ƴar garin Maska".
Baby kuwa tsabar fushi kasa tsayawa tayi,ta fice fuuu cikin fushi sai taji sam bata san ganin matar,saboda yadda ta tsani mahaifiyarta dama ta hana kowa zaman lafiya,Alhali ita ta zauna lafiya da mijinta,don Hajiya kaka ba mutum ce me tsaurarawa ba,duk da dai tana da faɗa amman faɗanta sai an taɓa ta sannan takeyi ba haka kawai irinna Hajiyar Maska ba.
Baby na fita Hajiyar Maska ta ce"Ni wallahi al'amarin Baby yana bani mamaki?Yarinya kamar wacce aka yiwa asiri?kullum ana gaya miki ga hanyar da zakibi don ki cusgunawa wannan mayyar data liƙewa ubanki,ammanke kullum kare ta kike?to ni nasan abinda zanyi don yau ɗinna ba sai gobe ba,zan nunawa Halima cewar ita bata isa ta dinga haɗani da ɗana ba."
Itw kaɗai dai take ta faɗanta.
MD yana shigowa ya ce"a'ah Ya kuma kika zauna anan Halima"?.
A hankali ta ɗago don kanta ne yake sara mata,haka take ita bata iya saka abu aranta ba,yanzun nan sai kaga ta rame ta zama abar tausayi.
"Hajiyar na ciki ne shiyasa ban shiga ba,ba jira ta fito amman Baby ma tace ita kaɗai ce,yanzu ma shiga zanyi mu gaisa".
Bai ce mata ƙala ba ya wuce abinsa,don shi ba mutunne me magana ba,shiyasa wasu suke ganin kamar yana da girman kai,kuma shi haka Allah yayi sa aƙwaishi da miskilanci,wannan kuma halin mahaifinsa ne,don shima ba ruwansa ba komai ya kewa magana ba,sai dai yana da zuciya sosai,don ko su Hajiyar Maska suna shayinsa sosai.
Yana shiga Hajiya tayi masa banza kamar bata san Allah yayi ruwansa ba,yana ganin hakan yasan lallai aƙwai abinda ya faru,sai dai bai kawo komai ba ya tsugunna har ƙasa,sannan ya fara gaida mahaifiyar tashi cikin girmamawa.
Hajiyar Maska ta kalleshi sannan ta ce"yanzu Muhammad har nayi lalavewar da za'a rainani haka?matar ka ta zauna min a falo sannan ta ce wai inzo mu gaisa?tasan kuwa ni wacece awajen ta?Muhammad kana neman aljanna kuwa?kana son ka gama da duniya lafiya kuwa?".
Da sauri ya kalli Hajiyar tasa sannan ya ce"Hajiya wallahi ban san abinda ke faruwa ba?na tambayeta yanzu tace abinda yasa bata shigo ba ta ɗauka ba ke kaɗai bace,shiyasa bata shigo ba amman kiyi haƙuri Hajiya".
Da sauri Hajiyar Maska ta ce"inyi haƙuri Muhammad?saboda an cuce ni?sai ka zuba ido yanzu matarka tana wulaƙantani?ta inda Salis ya fika kenan?matansa guda biyun nan bai yarda kowaccensu ta nemi rai nani ba,amman kai sai ka tsaya mace na juya ka kamar sitiyarin mota".
Kasa magana yayi,amman kana ganinsa kasan ransa a matuƙar ɓace yake amman ya daure ya sunkuyar da kansa.
MD mutunne me mugun haƙuri,sai dai yana da zuciya sosai saboda haka bai fiya son zaman garin ba,saboda Tashin hankalin daya ke ciki,tsakanin matarsa da mahaifiyarsa,yasha zama yayi tunani akan abinda yake haɗa mahaifiyarsa da matarsa amman bai taɓa gano komai ba,kawai dai abinda ya gane abune guda ɗaya shine matuƙar Halima zata zo inda Hajiya take,to dole sai an samu matsala idan kuma bata zo ba shima matsalar ne,tunda matan ƴan uwansa duk suna zuwa gidan,bai kamata ace matarsa ce kawai bata zuwa ba,saboda wani dalilin ɓatawarta da Mahaifiyarsa,shi kuma ya rasa yadda zaiyi a samu maslaha.
A hankali ya tashi tsaye duk karsashin daya zo dashi sai yaji yanzu duk babu shi saboda ɓacin rai,haka ya fito zuciyarsa na masa wani irin zafi.
Ko daya ke yanzu dai idan akayi duba na tsanaki,za'a ga tabbas Halima ce da laifi saboda a'i ita ya kamata taje har inda Hajiya take,ba Hajiyar ce zata zo inda take ba.
Halima na ganin fuskarsa tasan lallai Hajiya ta haɗa ta da mijinta,sai dai koma menene ta shirya ƙarɓarsa tunda yau tazo inda Hajiya take,kuma tasan dole sai wani abin ya faru.
"Halima me yasa bakya son zaman lafiya ne?me yasa kullum kike son haɗani da Hajiyata ne?ne yasa bakya son in zauna lafiya da mahaifiyata?kina son in shiga aljanna kuwa?Halima bana son inyi miki abinda zakizo kina dana sani ne,shiyasa nake kyale ki kullum ina ɗorawa mahaifiyata laifi,akan wannan matsalar da muke ciki,amman ke bakya ganin duk wani ƙoƙarina?zan amshi raganar duka al'umma yanzu,kina son in shiga tashin hankalin da zan kasa biyawa mutane buƙatarsu,waɗanda suka ɗauramin nauyi?Halima ina son ki shiga har ɗakin Hajiya yanzu ki bata haƙuri,haƙiƙa abinda kika yimin yau ya ɓata min rai sosai."
Halima kuwa tunda ya fara magana ta sunkuyar da kanta,ta kasa ɗagowa ma ta haɗa idanu dashi duk da daman idan Mijinta na mata magana ko haɗa idanu bata yi dashi,don dai ta bashi girmansa na mijinta tare dayi masa biyayya.
Wasu hawaye ne masu zafi suka fara zubo mata,ita da Mijinta zata iya irga sau nawa suka taɓa yin faɗa,tasan mijinta ba shida matsala zasu iya shekara ba tare da wani abu ya shiga tsakaninsu ba,kullum cikin zaman lafiya suke gwanin sha'awa.
Hajiya na tsaye duk tana kallon diramar dake faruwa,duk da haka bata ji daɗin yadda Muhammad ya yiwa Halima ba,taso ace yaci mata mutunci sosai idan ma har da dama ya haɗa mata da takaddar saki,don ita ayanzu babu abinda take farin cikin gani irin taga an saki Halima,amman shiru duk abinda take haɗa mata bata ji sakamako ba.
Hajiya ta ce"Muhammad a'i ni har yanzu baka burgeni ba,saboda daman irin wannan faɗan da kake mata kamar wani lusari shiyasa take rai na ka,amman babu komai ni nasan matakin da zan ɗauka.
Wata irin tsawa ya yiwa Halima yana cewa"Halima!ba cewa nayi kije ki bawa Hajiya haƙuri ba?me yasa kike son ɗoramin magana ne?me yasa bakya son zaman lafiya ne"?.
Halima ta tashi a hankali,jikinta har kakkarwa yake saboda tsawar da MD yayi mata,ta je har gaban Hajiya ta tsugunna sannan ta ce.
"Hajiya don Allah kiyi haƙuri,in sha Allah bazan sake miki makamancin haka ba,ki yafe min don Allah"?.
Hajiyar Maska ta kalle ta sannan ta ce"sai anyi magana ki dinga sunkuyar da kai,daman irinku haka kuke Ni dai Allah ya haɗa ɗana da masifa ta aurenki,aure kusan shekara goma sha amman babu ɓatan wata har yau."
*****---*****
. . .Inna Harira ta miƙe tana masifa tana ce wa"Wallahi bazan yarda ba,wannan shaiɗaniyar yarinyar ce ta sanya min yaji acikin ruwa,wallahi bazan yarda ba hegiyar yarinya mara kunya,wacce bata aan mutuncin mutane ba Allah ya isana wallahi".
Ta faɗi hakan tana kuka kamar ƴar ƙaramar yarinya.
Ita kanta Innar Indo ta gane ƴar tata ce tayi,amman tasan ta inda zata biyowa Indon,don daman mahaifinta ke ɗaure mata gaba don ta raina kowa.
Inna Harira dai ranar masifa ta dinga yi,matan gidan kuwa ko kallon arziƙi bata ishe su ba don daman tuni sun daɗe da yin faɗa da ita,don bayan Innar Indo itace me fawa agidan,don su ƴan kallo ne agidan,don ko Innar Indo darajar ƴarta take ciki ne gidan yake ɗaga mata ƙafa,amman Inna Harira ita ce me gidan sai yadda ta dama haka ake sha,sai dai fa Indo ƙadangaren kan tulu ce,bata fito ba sai da ta shirya don babu inda bata je ba,akan a haɗa Indo da mahaifinta amman sai suce mata su baza su iya ba,don sun gano wani babban al'amari a tsakanin Baban Indo da ƴar tasa.. . . .✍🏾
*Ku nuna mana soyayya wajen share,tare da comments wannan ita kaɗai ce hanyar da zamusan kuna ƙaunarmu🙏🏼Allah kabarmu da masoyanmu na asali Amin.*
*Noticed!Noticed🗣️🗣️!!*👇🏻👇🏻
Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent,sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki,kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻
07068606171
08104335144
08179523215
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
*MISS GREEN CE👉🏾👉🏻*
[1/30, 1:10 PM] Miss Green: *_✨INDA BA ƘASA...!!!_✨*
_(Littafi na 1📃)_
NA
*_®️UMMU MAHER(MISS GREEN)🍀_*
*_AREWA BOOK👉🏻_*
INDA BA ƘASA!!!:: https://arewabooks.com/book?id=63ce1eb0ec00e12124ce9eb0
---------------------------
*_WATTPAD👉🏻_*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
---------------------------
*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_* ---------------------------
*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIE DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
Page🟧5
----------Da sauri Halima ta kalli Hajiyar Maska,saboda babu abinda taƙi jini a duniyarta irin ayi mata gorin haihuwa,ita a ganinta Haihuwar nan ba don Allah ya tsaneka bane baya ba ka ba,kawai dai Allah ya jarabceka ne don yaga yadda zakayi,tunda Allah bai bawa Uwar mumunai ba,to waye ba zai jarabta ba?ko so take tayi hauka tunda bata haihu ba?ita a ganinta tunda tana da Baby wani kukan Haihuwa za tayi?a ganinta bai kyautu tayi wani kuka ba,tunda har tana da Baby yarinya me nutsuwa,yarinyar da har yanzu bata yarda ba ita ce mahaifiyarta ba,tasha kama Baby tana kuka idan ta tambayeta dalilin kukan sai ta ce,Wallahi Momy ni bana son ana cewa ba ke ce kika haifeni ba,idan ma ba ke ce kika haifeni ɗin ba a'i kin haifi,tunda tun ina jaririya ke kika kula dani har girma na,to kuwa idan na butulce miki a'i kai na na butulce wa.
Tana cikin wannan tunanin taji MD na cewa"Hajiya zamu tafi,sai Allah ya kaimu gobe zan leƙo In sha Allah".
Hajiyar Maska ta ce"Allah ya kaimu ta wuce abinta zuwa sashen Mijinta,don Allah ya sani ko fuskar Halima bata son gani,saboda ta tsani yarinyar duk ta mallake mata ɗa,komai Halima!Halima kafin ya kira sunanta sau ɗaya,ya kira sunan matarsa shiyasa abin yake dagula tunaninta baki ɗaya.
A kaf cikin ƴaƴanta tafi son Muhammad,kawai dai tana cewa tafi son autanta saboda kada Halima taji daɗi ta miƙe ƙafafunta,shiyasa take nunawa agabanta ta tsani Halima.
Baby kuwa ko sallama bata yiwa Hajiya ba,saboda sam yanzu ta tsani matar sai dai babu yadda za tayi da ita tunda dai kakarta ce,sai dai addu'ar da take a kullum shine Allah ya dawo da hankalin Hajiya kan Mominta,ta dinga sonta kamar sauran surukanta.
Baby ta kalli Abbanta sannan ta ce.
"Dady".
A hankali ya kalle ta Amman bai ce mata komai ba,da yake mutunne me saurin sauka ko da ma ace yayi fushi,ta cigaba"Dady bamu shiga part ɗin Hajiya ƙarama ba,kuma bamu shiga part ɗin Hajjiya kaka ba."
A hankali ya ce"muje tare nima ban shiga ba."
Halima dai na jinsu amman bata tanka musu ba,saboda yadda kanta ke matuƙar sara mata,bata son tashin hankali ko kaɗan a duniyarta,bata son duk wani abinda xai shigar mata rayuwa ya hanata rawar gaban hantsi,sam bata son zuwa gidan Hajiya saboda tashin hankalin dake gidan,tun tana amarya har yanzu,da sahu ya fara daɗewa amman Hajiya na nan akan turbarta ta tsanar Halima,ita ta rasa dalilin wannan tsana,ko da ake bata labarin surukai ita dai bata taɓa ganin irin tata ba,Hajiya ko atamfa taga Halima ta saka to tabbas,sai ta saka ɗanta ya siyo mata,a faɗarta wai Halima na tatsewa ɗanta tattalin arziƙi,kullum cikin hidimta mata yake da ƴan uwanta.
Kuma Allah ya sani Halima bata taɓa roƙar wani abu a wajen MD ba,shi dai da kansa yake dubawa yaga ya cancanta daya bawa ƴan uwanta wani abu,duk da suma fa ba baya bane wajen kuɗi,don daman cen karayar arziƙi ce ta samu mahaifinta,amman babu wanda bai san kuɗin da mahaifinsu yake dashi ba,ko kama ƙafarsu gidansu Muhammad basuyi ba,tunda su gidansu Muhammad duk ma'aikatan gwamnati ne,ita kuwa mahaifinta babban ɗan kasuwa ne kuma ɗan siyasa,babu wanda bai sanshi ba mahaifinta bai taɓa roƙar wani abu gun mijinta ba,ko kuma ya sata ta roƙar masa ba amman duk da haka Hajiyar Maska bata ƙyale ta tasha ruwa ba,kullum cikin masifa da hantara da zagi,ko kishiyarta bata yiwa haka ballantana ita da take matar ɗanta,abin yana damunta sosai gashi Halima tana da zurfin ciki,don duk wannan abinda ke faruwa iyayenta basu taɓa sani ba,saboda macece me zurfin ciki sosai,don ko mahaifiyar Baby ba halinsu ɗaya ba,don ita tana da zafi sosai don itama sunsha yi da Hajiyar,sai dai da taga mahaifiyar Babyn ba baya bace wajen masifa itama,sai ta haƙura sai data bari zamanin Halima yazo sannan ta ɗora,bayan ta gane matsanancin haƙurin da Halimar ke dashi.
Kuma daman idan aka ga kana da haƙuri to ko wani kashi sai a ɗebo azuba a kanka,sai dai fa haƙuri shi kansa baiwa ne ba kowani ɗan adam ke dashi ba,sai wanda Allah ya bawa haƙuri rahama ne.
Sashen Hajiya Ƙarama suka fara shiga,babu kowa a falon sai Karimatu da Rabiah sune ƴammatan Hajiya Ƙarama,kishiyar Hajiyar Maska yaran suka taso da gudu suka rungume Halima.
Halima ta saki murmushi wanda ya ɓace a fuskarta tun bayan shigowarsu gidan Hajiya,sai yanzu tayi murmushi ta shafa gefen fuskar Rabiah ta ce"kai lallai Autar Hajiya wannan man ya karɓeki,nima a faɗamin sunanshi in siya".?
Da sauri kuwa Karimatu ta ce"yauwa Anty yi mata faɗa dai,mutun yana ɗan baƙi yace wai shi sai yayi fari?a ina aka taɓa yin haka?mu dai tunda farare ne ayi haƙuri a zauna haka,kada a canja halittar Allah."
Sai kuwa Baby ta ce"a'i kuwa dai Little momy man yayi miki kyau,Allah yasa Yaya Abbas ya gani"?.
Sam su Rabiah basu kula da Babban yayan nasu ba,dai da sukaji ya wuce ɗakin Hajiya sannan dukansu suka kama bakunansu,tare da zaro idanu suna magana da hannu sa idanuwa,wai yaushe yazo?ko tare suke ne"?.
Halima tayi murmushi sannan ta ce"tare muke mana a'i yana jinku,kinga ke Autar Hajiyar ta kanki za'a fara"?.
Ta nuna Rabiah wacce ta fito da idanuwa waje,ƙwalla ta cika idanuwanta don aƙwaita da saurin kuka,ga tsoro kamar farar kura sai kuwa ta ce"Don Allah Anty Halima ki bashi haƙuri,don wallahi daman haushina yake ji,tun wata biyu da suka wuce daya ganni da Aliyu a Wani Shopping,kuma kinsan baya son Aliyu saboda halayensa,ni kuma wallahi Antu shi nake so whith all my heart(da dukkanin zuciyata)."
Halima ta kalle ta da tausayin Rabiah aranta,don a sha'anin gidan sam basa son bawa bare ƴaƴansu,sun fi yin auren zumunci,don gidansu Aliyu duk da iliminsu har yanzu ƴan gargajiya ne,kamar suna garinsu Maska don itama abinda yasa Hajiya ta ƙara tsanarta kenan saboda ita ba ƴar uwarsu ba ce,bare ce ita shiyasa suka tsane ta,don bayan Hajiya har ƴan uwan Hajiyan ba sonta suke ba,don tasha zuwa biki a danginsu a wulaƙantata,inda dai take samun sauƙi awajen ƴan uwan mahaifin Aliyu,don su dai sun san darajar ɗan adam sosai,sai kuma wajen Hajiya Ƙarama kishiyar Hajiyar Maska,itama macece me son mutane,kuma babu ruwanta macece me sauƙin hali da kuma haƙuri,don idan banda haka bata isa ta zauna da Hajiyar Maska ba,don mai zama da Hajiyar Maska sai ya shirya,don Hajiyar Maska aƙwai faɗa tare da son ƙuntatawa mutum.
-----*****-----
. . . .Indo na fita kai tsaye dandali ta wuce,tana tafe tana wani yauƙi da ƙwarƙwasa,don Allah ya zubawa Indo iya tafi salo salo,gashi Allah yayi mata halitta me kyau da tsari,don irim matan nan ce ƴan duma duma,don ma ta saka fitina aranta don sai tafi haka girma.
Tana zuwa taga kowa yayi tagumi a Dandalin,ta kallesu kallon ƙasa da sama ɗinnan sannan ta ce"kai Lafiyarku kuwa?kamar an ce muku me gari ya mutu?alhali yanzu naga me Gari ya babbake ƙatuwar Rigarsa yana zaune ƙofar gidansu Hanne,ƴar zamanin taƙi fitowa sai ta gama ƴan ƙwanasa sannan ta fito?kai Allah na gode maka daka kawo me cin gidansu Megari".
Dariya ce ta kufcewa kowannensu,don daman zamanda sukayi na rashin Indo ne,suna masifar son Indo duk da faɗanta amman indai kana kusa da ita ka dai na shiga ƙunci.
Sosai samarin da ƴammata suke ihu tare dayi mata kirari suna ce wa.
"She Indo Me maganin ƴar banza da ɗan banza,ƙadaran kan dutse baki fito she da kika shirya."
Wani irin juyi tayi sannan ta fara kallonsu a nutse,ta ƙurawa wani waje ido sannan ta ce"wai Inna Surbajo ne?yau bata zo bane?me ya hanata zuwa?ince dai wannan kawun nata ɗan gajere me wandon saƙa,shine ya hanata zuwa ko?to Alƙur'an indai shine She nayi maganinshi,me ƙaton ciki kamar tulu yau he na sakashi yayi rawar banjo".
Ƙwashewa sukayi da dariya,suka cigaba dayi mata kirari,sannan ta zaɓo ƴan mata biyu acikin ƴan dandalin,Harda aminiyarta Bintu da yake tsoro ne da ita sai zare idanu take tana ce wa.
"Allah ni dai Indo ki barta?tunda dai bata zo ba,a'i shikkenan ko?mu ba iyayenta bane ballantana mu ɗakko ta tazo nan,don Allah Indo ki barta tunda Kawunta ne ya hanata."
Indo ta juyo a hankali,ta juya mata kyawawan idanuwanta,masu kama da madarar Luna ta ce"ke Mage koma don Allah,sai shegen tsoro kamar wacce ta daɗe acikin daji,koma kada ki ɓata mana shiri ƴar ruwa kawai".
Da sauri Bintu ta koma,don tsaf tasan halin mutuniyarta,yanzu sai a biyo su ta tsere su ta barsu suci na jaki,ita kuwa Indo shegen gudu gare ta kamar barewa,shiyasa sam bata son Indo taja ta ayi wata ta'asar.
Tun daga ne sa ta hango Kawun Surbajo,ta sheƙe da wata munafukar dariya,don ta shirya tsiyar da za tayi masa,don Kawun Surbajo tuni ta daɗe da gane Inda ya dosa,don haka yau ba sai gobe ba za tayi maganinsa.
Suna zuwa Indo ta wuce gaba,ta ɗan ɓoye fuskarta ta tura Hanne sannan ta juya bayanta.
Hanne ta shiga gidansu Surbajo,ita kuma Indo tana ganin haka taga wani yaro yazo wucewa ta ce"kai yaro don Allah je ka cikin waɗancen masu zaman banzan kace wai,Baffan Surbajo yazo"?.
Yaro ya tafi da sauri,yana zuwa ya faɗi abinda Indo ta faɗa masa,sannan ya tafi Shi kuwa Kawun Surbajo jin ance mace ke kiransa,a'i tuni ya jishi a kogin murna,sai washe jajayen haƙoransa yake,daman Malum Malun ce ajikinsa,gashi ɗan gajere kamar wada ɗan kuyat dashi,ya sanya zororuwar hularsa kamar zashi fadar sarki.
Indo kuwa ce wa take,He ge gajere sai sauri yake zaizo wajen Budurwa,baka san ƙwahe ka zamuyi ba.
Indo na ganin ya taho ta wuce da sauri zuwa Dandali,Ita kuma Hanne ta shiga ta fito da Surbajo suka gudu,daman sun san indai yana ƙofar gidan ba yarda zaiyi Surbajo ta wuce ba,shiyasa su Indo suka haɗa wannan dabarar. . . .✍🏾
*Ku nuna mana soyayya wajen share,tare da comments wannan ita kaɗai ce hanyar da zamusan kuna ƙaunarmu🙏🏼Allah kabarmu da masoyanmu na asali Amin.*
*Noticed!Noticed🗣️🗣️!!*👇🏻👇🏻
Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent,sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki,kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻
07068606171
08104335144
08179523215
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
*MISS GREEN CE👉🏾👉🏻*
[2/1, 1:28 PM] Miss Green: *_✨INDA BA ƘASA...!!!_✨*
_(Littafi na 1📃)_
NA
*_®️UMMU MAHER(MISS GREEN)🍀_*
*_AREWA BOOK👉🏻_*
INDA BA ƘASA!!!:: https://arewabooks.com/book?id=63ce1eb0ec00e12124ce9eb0
---------------------------
*_WATTPAD👉🏻_*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
---------------------------
*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_* ---------------------------
*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIE DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
Page🟩7
------------Ummita ta sau baki da hanci tana kallon MD,ta kasa ɗauke idonta a kansa,har Khairat ta fito ta samu ƙanwata acikin wannan halin,da sauri ta riƙe hannunta suka shiga ɗakinsu,don gudun kada kowa ya ganta,don tasan hakan da ƙanwarta tayi zai fassara komai.
Khairat ta ɓata rai sannan ta ce"Ummita wai meye hakanne?kin san kuwa abinda kike a'ikatawa?kina son su koremu daga wannan gidan?gaskiya Ummita ki canja halinki,don wannan sam ba haline me kyau ba,mace da mijinta ki nemi yi mata ƙwace har kina kallon mijinta haka?yanzu da ta shigo ta ganki fa?me kike son a ɗaukemu?".
Ummita ta fisge hannunta sannan ta fara magana cikin faɗa"kinga Khairat ki fita daga sabgata?ita zuciya ba'a canja ta,tun lokacin da naga wannan bawan Allahn sonsa da ƙaunarsa ya ɗarsu azuciyata,tun lokacin da na ganshi a hoto naji ina masifar sonshi,don haka Khairat ki sakamin ido kawai,amman fa zuciyata ba zata daina son bawan Allahn nan ba."
Tana faɗar hakan tayi hanyar fita daga ɗakin.
Da sauri Khairat ta dawo da ita tana ce wa"wallahi tallahi baza ki fita ba,kina son ki koma ki cigaba da kallonsa kamar mayya?haba Ummita a'i ana barin halas don kunya ko?".
Ummita ta buga mata wata muguwar harara za tayi magana aka turo ƙofar.
Baby ta kallesu ganin kowaccensu ta harzuƙo kamar za suyi faɗa,Baby ta ƙel ƙele da dariya sannan ta ce"ikon Allah sister's faɗa za kuyi ne?haba don Allah cool down mana,kada kuyu faɗa ku fa ƴan uwa ne?don Allah kada kuyi kunji?Momy ta ce ku fito ku gaisa da Dadyna".
A'i Ummita na jin anyi maganar Dady da sauri ta fice,ba tare da ta jira abinda Babyn zata faɗa ba,Khairat ta bita dana mujiya kawai tana mamakin ƙanwarta,daga zuwa gidan mutane kawai sai kiga mijinta kice kina sonta?ita abin ma mamaki yake bata,sai dai tasan duk abinda Ummita tayi niyya babu wanda ya isa ya dakatar da ita,daman ita haka take tun tana ƙarama,kuma laifin mahaifiyarsu ne don ita ce ta shagwaɓa ta.
Ummita na fitowa ta kusa sandarewa a wajen,biyo bayan abinda idanuwanta suka gane mata,Halima ce zaune akan cinyar mijinta tana feeding ɗinsa gwanin sha'awa,shima yana ɗakkowa yana bata sai abin ya bata mamaki,taji wani irin mugun mashi ya dako zuciyarta,sai take jin kamar taje ta shaƙe Halimar ta mutu,sai dai ta kasa control ɗin kanta kai tsaye tayi wajen,ranta a matuƙar ɓace ga wani irin mugun kishin MD daya cika mata zuciyarta.
Dai dai lokacin su Khairat suka fito Khairat ta ce.
"Ummita!".
ta ɗan faɗi hakan da ƙarfi Sai ta fara yi mata magana da yarensu na shuwa,Ummita ta tsaya cak amman idanuwanta cike suke da ƙwalla,tana ji kamar ta ɗaga hannu tayi ta zunduma ihu.
Khairat ta tsugunna ta fara gaida MD,ya amsa ammanfa ko kallon inda take baiyi ba,ba don girman kai ba a'ah sai don matane bai kamata ya kallesu kallo me yawa ba,don MD aƙwaishi da kiyaye gani da kuma ji,don duk zamanda yake a ƙasashen turawa bai taɓa ko da budurwa ba,ballantana kuma ya nemi matan banza ba,ƴan matan dai sunsha kawo kansu har inda yake,amman ko kallo basu ishe sa ba abinda kullum yake cewa shine,baya shiga gonar da duk ba tashi ba,har sai muharramarsa matarsa.
Itama kuma Halima ta yarda da mijin nata ɗari bisa ɗari,babu ruwanta da zarginsa ko damuwa idan baya nan,ko tayi tunanin yana cen da wata bata tama yin hakan ba don ta yarda da mijinta sosai.
Ummita ma ta gaishesa,sai dai tana gaishe sa ɗin ta wuce da sauri,sai dai da yake duk suma mutanen wajen hankulansu basa wajen basu lura da yanayin nata ba,Sai dai Khairat na lura da yanayin ƙanwarta Ummita,da sauri itama ta bita ɗakin don ganin halin da ƴar uwarta ke ciki.
Tana zuwa ta isketa a ƙwance a bakin gadonsu,ta haɗa kanta da guiwa ta shiga rera kukanta da ɗan ƙarfi,jin zuciyarta take kamar zata fashe,tun kallon farko da ta yiwa bawan Allahn taji soyayyarsa na nuƙurƙusar zuciyarta,tabbas son Mahaifin Baby ya kama zuciyarta sosai.
Khairat ta sanya hannunta ta ɗago kan Ummita a hankali,ta ɗora akan cinyarta sannan ta shiga yi mata nasiha akan rayuwa,tare da haƙuri akan ta cire mahaifin Baby aranta,saboda wanda take don shima bai san tana yi ba.
Da sauri Ummita ta miƙe tsaye ta nuna Khairat da hannunta ta ce"Na fahimce ki Khairat,wato in daina sonshi ke ki soshi ko?to bari ki ba zan dai na sonshi ba,sai dai duk abinda za kiyi kiyi,don haka wallahi tun wuri ki fita daga harka ta,tunda bazaki goyamin baya ba,goyon bayan wata kike a madadin ƙanwarki."
Khairat tayi tagumi tana kallon ƙanwarta Ummita,sai take ganin Ummita nan gaba fin ƙarfin kowa za tayi,don tun yanzu gashi ta fara nuna hakan.
Khairat ta tashi a hankali sannan ta kalli ƙanwarta ta ce"babu komai Ummita,tunda haka kika ɗauka cewar nima ina sonshi ne,to ki cigaba da ɗaukar hakan amman ko yarda ko kada ki yarda gaskiya ce sai na faɗa miki,kuma ina fatan Allah ubangiji ya shiryar dake shirin addinin musulunci.tunda ke har yanzu baki san annabi ya faku ba."
Ummita ta wuce da sauri banɗaki ta bar Khairat awajen,Khairat ta zauna tayi tagumi sosai ta tsunduma a kogin tunanin halin da zasu tsinci kansu a wannan,da kuma yadda matar gidan zata kallesu,don ba iya Ummita zata kalla da laifi ba,har ita saboda tare suke kuma yayar Ummita ce.
Halima kuwa tana cen wajen mijinta,bata san ma abinda ke faruwa ba da yake MD mutunne mara ruƙo don haka tuni ta rarrashi abinta,suka cigaba da soyewarsu don MD ko bature haka ya barshi ya ƙyale.
Ashe Ummita na da aiki babba,don indai tana gidansu Halima to sai zuciyarta ta kusa fashewa,don ko agaban Baby ne basa kunyar yin soyayyarsu,don Baby ma bata ɗauki wannan abin a matsayin wani abu ba,tunda dai mata da miji ne don ita an nuna mata cewar matuƙar mijinta ne duk abinda zasuyi lada zasu samu,matuƙar bai take hukuncin Allah ba,kuma an nuna mata haramcin yin hakan ga wanda ba muharraminka ba.
-----*****-----
. . . . .Indo kuwa sam hakan baya damunta,don ita daman ta tsani wani namiji yace yana sonta,to tabbas sai taji tamkar an gingima mata wani dutse aranta,ta rasa dalilin hakan sai dai tasan komai lokaci ne wataƙil nan gaba idan ta samu wanda take so ta dai na jin hakan.
Bayan an tashi daga gaɗar dare,Suna tafiya suna hira ita da Bintu don hanyar gidansu ɗaya ne.
Har sunyi hanyar gida sai kuwa Indo ta chono baki gaba ta ce"Bintu don Allah ki rakani wani waje mana"?.
Bintu ta zaro ido sannan ta ce"haba Indo yanzu fa dare yayi?kuma kinsan faɗa za'ayi min don Allah mu tafi gida Indo,ni dai bana son ki tsokano wani da daddaren nan gwara mu tafi gida"?.
Indo ta juya idonta ta kalli wani layi sannan ta ce"Bintu zaki rakani ko baza ki rakani ba"?.
Bintu tayi shiru bata ce komai ba,Indo ta ce"to aradun Allah idan baki rakani ba sai ki gane kurenki Allah,don duk ranar da aka biyoki na daina tsarw miki faɗa".
Bintu ta ce"Indo muje don ni nasan halinki ba iya tsaremin faɗa zaki dai na ba,nasan sai kin ɓaromin wata wutar muje Indo".
Indo ta sheƙe da dariya sannan ta ce"muguwa Bintu wato baki son in miki tallan silili ko?".
Bintu dai bata ce komai ba,don ita yanzu Indo ma tsoro take bata,don idan tayi wani abun kamar ba ita kaɗai tayi ba.
Suna zuwa ƙofar wani gida Binti taja ta tsaya sannan ta ce.
"Ayya Indo yanzu don Allah bazaki kyale Sunusi ba?ni daman nasan gidan nan zamu zo?abinda yayi miki fa ya kai sati?haba don Allah ke kuwa Indo ki kyaleshi mana?ki dinga yafiya don Allah Indo"?.
Indo tayi mata wani kallo sannan ta ce"to uwar wa'azi,ki kyaleni don wallahi sai na rama abinda yayi min,har sauran duk sai sun gane kurensu don wallahi tallahi bazan barsu ba,tsabar mugunta ban shiga harkarsu a gari ba,sai su saka ayimin wannan ɗan banzan dukan?don sun san Baffana baya nan?Alƙur'an sai na rama da kai na shima me garin zai gane kurensa".
Bintu dai bata ce komai ba,suka shiga gidan Suna shiga suga dinga sallama amman ba'a amsa musu ba,Indo ta ƙare gwale bakinta tayi sallamar da ƙarfi.
Sailuba ta tashi a firgice,ɗanta dake gefenta yana shan mama ta cireshi ta tashi ta fito daga ita sai ɗaurin ƙirji.
Ganin ƴammata a tsaye yasa ta ce"lafiya dai ƴan mata?".
Indo tayi murmushi sannan ta ce"haba baiwar Allah a'i kya bamu waje mu gaisa ko?don mudai ba cutar dake mukazo yi ba".
Ta faɗi hakan tana yiwa Sailuba gwalo.
Sailuba ta ce"kuyi haƙuri ga tabarma nan ku zauna."
Indo ta ɓoye fuskarta tana mata gwalo,sannan ta ƙara gaishe da Sailuba kamar abin arziƙi ta fara ce wa.
"Don Allah kece Sailuba matar Sunusi?".
Sailuba ta gwalo ido waje ta ce"eh ni ce?lafiya dai ko,Allah yasa ba wani abinne ya samu Sunusi na ba?don wallahi ba nida kowa kaf duniyar nan,sai Sunusu don iyaye na sun mutu."
Indo ta langaɓe kai kamar mutuniyar kirki sannan ta ce.
"A'i gwara ma mutuwar Sailuba,da abinda Sunusi yake shirin ɗakko miki" . . . . .✍🏾
*Ku nuna mana soyayya wajen share,tare da comments wannan ita kaɗai ce hanyar da zamusan kuna ƙaunarmu🙏🏼Allah kabarmu da masoyanmu na asali Amin.*
*Noticed!Noticed🗣️🗣️!!*👇🏻👇🏻
Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent,sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki,kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻
07068606171
08104335144
08179523215
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
*MISS GREEN CE👉🏾👉🏻*
[2/2, 2:41 PM] Miss Green: *_✨INDA BA ƘASA...!!!_✨*
_(Littafi na 1📃)_
NA
*_®️UMMU MAHER(MISS GREEN)🍀_*
*_AREWA BOOK👉🏻_*
INDA BA ƘASA!!!:: https://arewabooks.com/book?id=63ce1eb0ec00e12124ce9eb0
---------------------------
*_WATTPAD👉🏻_*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
---------------------------
*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_* ---------------------------
*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIE DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
Page⬜8
---------Da sassafe Halima ta tashi,ta shiga kitchen da kanta ta girka musu abincin karyawa,ƙamshi ya fara tashi kai kace gidan amare ne.
Ummita tana ganinta duk abinda take yi,ta cije leɓenta sosai ganin Har Halima ta sauke ferfesun kaza,wanda yake ta tashin ƙamshi gwanin sha'awa yasha kayan ƙamshi.
Halima ta sauke ta zuba komai acikin foodflask me kyau,wacce ba sai an gaya maka ba kasan ta masu kuɗi ce sosai,ta gama jera abincinta akan dining,sannan ta wuce ɗakinta don shiryawa don yau ma MD ya shaida mata da wuri zai fita,saboda ƴan jam'iyayya na nan suna jiransa ta shiga ɗakinsa don tayar dashi.
Ummita na ganin ta shiga ɗakin,tayi wuf ta fito ta shiga kitchen ta duba sosai ta samu gishiri,tayi wata irin muguwar dariya sannan ta ɗakkoshi ta cika chokali har guda biyu ta zuba a farfesun,ta ɗan juya kaɗan yadda babu wanda zai fahimci abinda aka saka.
Da sauri ta koma ɗakinsu,ta iske Khairat tana azkhar,jikinta Ummita yayi sanyi sosai ta sunkuyar da kanta ta wuce.
Khairat ta bita da kallon takaici,don tasan duk yadda akayi wani abin take son a'ikatawa,don tasan halin ƙanwarta aƙwaita da mugun hali.
Halima ta matse sosai acikin ƙananan kaya,tayi kyau sosai daman gata irin siraran mutane ne,irin ƙirar turawa silindium amman Halima nada shape ɗinta dai dai gwargwado.
MD ma yayi kyau cikin manyan kayansa,shadda fara sol sai walƙiya take,yadda kasan wata acikin zarah,Halima sai kallonsa take saboda yadda yayi mata mugun kyau.
Ya riƙo hannunta sannan ya hure mata idonta ya ce"habibty kallon yayi yawa haka?".
Murmushi kawai Halima tayi ta wuce ba tare da ta ce komai ba,suka zauna kan dining Halima ta buɗe komai,ƙamshi ya bugi hancin MD ya lumshe idonsa sannan ya ce"i'm really miss this delicious food Halima".ya faɗi hakan yana janyota zuwa kusa dashi.
A hankali ya fara kurɓar ruwan shayin,sannan ya fara cin farfesun cikin nutsuwa,sai dai yana kaiwa bakinsa yaji wani irin mugun gishiri me firgita harshe.
Da sauri ya furzar sannan ya goge bakinsa da tissue ya kalli Halima wacce itama shi take kalla saboda yadda taga hankalinsa a tashe,uwa uba ma bata san abinda yasa ya furzar da abincin ba.
Baban Baby lafiya kuwa ka zubar da abincin?ko baiyi daɗi bane?".ta faɗi hakan hankalinta a tashe.
Ganin hankalinta ya tashi ne yasa ya ce"next idan zaki zuba gishiri ko magi adanga kula,don gishirin yayi yawa Halima kamar zai cire harshe".
Da sauri Halima ta ce"gishiri kuma Baban Baby?wallahi ni ban ma zuba gishiri ba,magi ne kawai ma sanya?".
Ta faɗi hakan da tsoro fal akan fuskarta,don dai tasan ita bata zuba gishirin ba.
A hankali ya shafi kumatunta sannan ya ce"muje ki rakani Halima don mutanen nan sun dameni,don tun ɗazu suke ta bugomin waya".
Halima ta tashi ta wuce ɗakinta,ta ɗakko jalbab ɗinta ƙato har ƙasa sannan ta rakoshi har waje,sai da securities ɗinsa suka shir shiga motocinsu sannan ta dawo.
Jikinta har yanzu a matuƙar sanyaya yake,gani take tamkar cin fuska MD ke son yi mata,to idan banda cin fuska yaushe ma da ta saka gishirin ita kanta a girkin?saboda ja mata kunne da likitoci sukayi akan ta daina cin gishiri sam,saboda hawan jinin daya sako ta a gaba,sannam sunce matuƙar tana son ta samu ciki to ta ƙauracewa cin gishiri,don yawan cin gishiri yana kawo ruwan mahaifa,daga nan kuma sai kaga cikin yaƙi samuwa.
Ta tashi a hankali ta buɗe foodflask ɗin ta fara shan farfesun,da sauri ta furzar saboda mugun gishirin daya ziyar ce ta,ta goge da tissue tana kallon farfesun cikin mugun tsoro,don ita dai tasan bata zuba gishiri cikin abincinta ba.
Hankalinta ya tashi sosai,ta leƙa kitchen ɗin ta ɗakko gishirin tana dubawa,yana nan a yadda ta ajjesa,mamaki ya kamata sosai to ko dai ta zuba ta manta ne?.
Kasa tuna hakan tayi ta fito ta zauna shiru kan rantsatsun kujerun falon,tana cikin wannan halinne Baby ta fito daga ɗakinta,da kayan bacci ajikinta cikin shagwaɓa ta taho ta ɗora kanta akan cinyar Halima.
Baby ta ce"mom good morning"?.
Halima ta shafa kanta sannan ta ce"ɗazu kin shiga kitchen ne?".
Baby ta lumshe idonta sannan ta ce"No mom".
Halima ta faɗawa Baby duk abinda ya faru,Baby ta ce"Mom kuma su Ummita basu tashi ba"?.
Sai lokacin Halima ta tuno dasu.
Sannan ta ce"gaskiya ko da ace sun tashi bana tunanin zasuyi haka gaskiya,sai dai ina ganin ni ce na sanya gishirin na manta."
Baby ta ɗaga kai kawai,sannan ta shiga ɗakinsu Ummita dukkansu yanzu bacci suke,don Khairat tana gama Azkhar ɗin ta samu kanta a wani irin bacci,sai kuwa ta hau barci duk da tana tunanin tashi ta girka wani abin,amman kuma tana tunanin yin hakam tunda matar gidan bata bada dokar a dafa komai ba.
Baby taga suna barci don haka ta fito daga ɗakin.
Duk abinda ake Baby na jinsu,don har kitchen ɗin da Halima ta shiga ta ganta,sai dai da taji motsin tafiya sai ta koma da sauri,yanzu ma da taga Baby ne yasa ta koma da gudu ta fara barcin ƙarya,zuciyarta fes saboda ganin abinda ya faru,tsakanin Baban Baby da Halima.
Ta tashi ta rufe ƙofar sannan ta hau tsallen murna,tuni ta fara hango kanta acikin wannan tafkeken gidan a matsayin matar aure,matar ma kuma matar Baban Baby kyakkyawan soja,ne cikar haiba da ƙwarjini.
-----*****-----
. . . .Sailuba ta kalli Indo tana zaro fici ficin idanuwanta sannan ta ce"Na higa uku na ni Sailuba?me Sunusi yake shirin ɗakkomin daya fi mutuwa"?.
Indo ta ɗan juya tayi dariyarta son ranta sannan ta juyo..ta haɗe fuska tayi kamar za tayi kuka,ta kalli Bintu ta karkatar da baki gefe sannan ta ce"Bintu in faɗa?ni na kasa faɗa Bintu ke ki faɗa mata"?.
Bintu ta zaro ido waje,Indo na son jaza mata masifa don dai tasan ita bata san wani abin kunyar da Sunusi yayi ba?ita dai tasan tunda ya taɓa Indo baza ta barshi haka banza ba,sai ta horar dashi kafin daga bisani a gane manufarta.
Bintu ta kalli Indo da mamakinta sannan ta ce"ni Indo ban. . . ."
Da sauri Indo ta katse ta da ce wa"to na gane Bintu,kema bakyason faɗar wannan maganar,amman ni dole in faɗawa matarsa don kada abu yayi nisa."
Sailuba ta waro idanuwa tana kallon Su Indo.
Indo kuwa ta gyara zamanta sannan ta ce"daman ɗazu ne da muka taho muka ga Sunusi awajen Lami,suna taɗinsu Kuma ba wannan ce rana ta farko da muka ganshi ba,mun daɗe muna ganinsa kullum idan muka dawo daga Dandali,shine muka yanke shawarar zuwa mu gaya miki,don wallahi Lami iccen kabari ake ce mata,indai har ta shigo gidanka to fa sai ta lalata komai,sai ta sakaki kinyi yawo tsirara Allah idan baki tashi tsaye ba,kika bari aka auro miki ita to alƙur'an kin kaɗe har ganyenki".
Da sauri Sailuba ta tashi tsaye tana ƙunduma ashar kamar bamagujiya.
Indo ta miƙe tsaye tana cewa"to mu dai bari mu tafi,kada yazo ya same mu yace mun kawo miki gulma".
Indo ta faɗi hakan tana wa Sailuba gwalo,irin gwalon nan na sokuwa ce ke.
Sailuba ta ce"na gode muku sosai ƴammata,Allah yabar zumunci yau sai ƙauyen nan ya tashi baki ɗaya,don wallahi idan har na bari aka auromin Lami hegiya nake."
Su Indo suka fara shirin fita,sai kuma ta dawo da baya ta ce"am idan yazo ki faɗa masa Indo da Bintu ne suka gaya miki,don kada yace zai musa miki don nasan yanzu bazai yarda ba,gaddama zaiyi miki don yasan baida gaskiya.
Suna fito Indo ta tintsire da dariya sannan ta ce"a'i wallahi Sunusi zai san ni ya taɓo,da zai kama ni ya hau duka kamar ya samu jaka,a'i yanzu kinga haɗa masa abinda zai zo yana da nasanin yimin wannan dukan".
Bintu ta ce"ni dai ban yafe ba Indo,don me zaki dinga sanya ni acikin masifa?ke aka daka ko ni?da zaki dinga sakani cikin masifa?Allah ni dai Indo na kusa raba hanya dake don ni dai wallahi indai har baki canja hali ba,Allah zan yi hannun riga dake duk kuwa da son ƙawancen da muke.
Indo ta ce"to sai me Bintu?ga hanya nan a'i?ke da kanki ke son ƙawance dani don daman ke ce kika laƙemin kamar mayya,amman mi kinsan ko ajikina,tunda idan ma nayo tsokanar inada ƙarfin ƙwatar kai na."
Bintu tayi hanyar gidansu,don dare har ya fara yi don goma ma ta wuce. . . . . .✍🏾
*Ku nuna mana soyayya wajen share,tare da comments wannan ita kaɗai ce hanyar da zamusan kuna ƙaunarmu🙏🏼Allah kabarmu da masoyanmu na asali Amin.*
*Noticed!Noticed🗣️🗣️!!*👇🏻👇🏻
Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent,sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki,kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻
07068606171
08104335144
08179523215
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._
*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
*MISS GREEN👉🏾👉🏻*
[2/3, 7:25 PM] Miss Green: *_✨INDA BA ƘASA...!!!_✨*
_(Littafi na 1📃)_
NA
*_®️UMMU MAHER(MISS GREEN)🍀_*
*_AREWA BOOK👉🏻_*
INDA BA ƘASA!!!:: https://arewabooks.com/book?id=63ce1eb0ec00e12124ce9eb0
---------------------------
*_WATTPAD👉🏻_*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
---------------------------
*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_* ---------------------------
*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIE DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
Page🟨9
---------Ummita bata bar Halima ba,ta shiga shirya mata munafunce munafunce,duk don dai ta haɗata faɗa da mijinta,sai dai fa duk abinda tayi sai taga cikin lokaci ƙanƙani an manta komai,sosai abin ya baƙanta ranta har ta shiga wani hali,ta shiga yin zazzaɓi sosai a lokacin kuma MD yayi tafiya,daga Su sai halinsu Suka kai Ummita asibiti,sai dai tashi ɗaya likitan ya gano Ummita na da hawan jini.
Sosai Halima ta tsorata,ƴar wannan yarinyar da hawan jini?Bayan sun dawo gida Halima ta shigo har ɗakinsu Ummita,ta same ta a bakin gadonsu ta zabga uban tagumi.
Sosai tausayin yarinyar ya dirar mata,ta ƙarasa da karsashinta ta ɗaho fuskar Ummita sosai tana kallon nata face ɗin ta ce"Ummita don Allah ki faɗamin abinda ke damunki?bana son wannan abinda kike?tun da kuka zo gidan nan nake kula dake,bakya walwala ba kamar ƴar uwarki ba,ko bakya son nan gidan ne?ko kuwa wani abin ake miki wanda yake baƙanta ranki?".
Ummita taji Halima kamar ta soka mata wani irin mashi,taji tamkar ta shaƙe ta kallon fuskar Haliman da take,amman sai ta goge hawayenta ta ce"ba komai Anty kawai dai gani nake kamar kina cikin damuwa ne,saboda yawan tafiye tafiye da mijinki yake yi,dubi fa wannan zuwan da yayi bai fi sati biyu ba,amman har ya koma ya barki ke kaɗai?gaskiya maza ba suda tausayi".
Ummita ta faɗi hakan tana hararar Halima ta gefe,bata san ma me yasa yanzu take ganin Halimar muguwa ba,don gani take kamar tana yiwa mijinta asiri,saboda yadda ko da ta haɗasu faɗa sai taga kuma sun shirya.
Halima taji son yarinyar ya ƙaru acikin zuciyarta ta ce"Ummita dole zan damu mana,amman tafiyarsa itace mafi alkhairi agare ni dama shi kansa ɗin,saboda matsalar da muke ciki ni dashi".
Ummita ta zaro ido waje ta ce"wata matsala kuma Anty"?.
Don tana son jin matsalar da take haɗa Halima da romio ɗin mijinta MD,don a ganinsu babu abinda zai haɗasu kuma duba da yadda suke ƙaunar junansu,gwanin ban sha'awa don yadda suke soyayyar yana ƙona mata rai sosai,so take taga duk wannan son ya tafi sai kuma ƙiyayya don wani buri nata da take son cikawa.
Halima ta share ƙwallar da ta taru a idonta ta ce"Ummita mahaifiyarsa baza ta taɓa bari mu zauna Lafiya ba,kullum naje da problem ɗin da zata zo min dashi,Musamman idan taga yana gari amman yanzu kinga idan yayi tafiyarsa shikkenan."
Ummita na jinta,ta ɗan matso hawayen munafurci ta ce"Allah sarki Anty,gaskiya cikib matsala babba sai dai Allah ya fitar dake."
Halima ta ce"amin Ummita,yanzu dai tashi muje fali muyi hira tunda dai kin samu lafiya,kuma yau dai naji damuwarki".
Ummita ta ce"to Anty".
Amman fa ba don taso hakan ba,Halima ta wuce gaba itama ta biyo ta a baya,tana jin kamar ta tsire Halimar kowa ya huta.
Hira ake sosai,ammanfa ita hankalinta yaba kan wani ƙaton hoton MD wanda yayi kyau matuƙa gaya.
Khairat ta fuskanci abinda take kallo,ta juya ta kalli Halima da Baby taga hankalinsu baya wajensu,sai kuwa ta taso da sauri ta rufe idon Ummita,ta raɗa mata wani abu acikin kunnenta sannan ta buɗe mata idon.
Ummita ta galla mata harara,sannan ta tashi ta shige ɗakinsu don ita shi kansa gidan ma ta tsaneshi don bata samu abinda take so ba har yanzu.
Khairat na ganin hakan tabi ƴar uwarta ɗaki,tare da rufo ƙofar don kada ma su Halima su biyo su,duk tasan ba lallai suyi hakan ba don Halima bata fiya shiga ɗakinsu ba.
Baby ce daman me yawan shiga,don Baby aƙwaita da son hira sosai.
Ta harɗe hannayenta a ƙirji,tana tsaye bakin ƙofar ɗakin bayan ta rufe,tana hango ƙanwarta tayi ruf da ciki alamar tana tunanin nata da ta saba.
Ta ƙarasa har inda take sannan ta ce"Ummita wai meye ribar wannan halinda kika saka kanki ne?me yasa kike son janyo mana masifa haka?kina tunanin idan kika cigaba da hakan mutanen gidan baza su gano halin da kike ciki ba?ko kuma an gaya miki ba suda ƙwaƙwalwar da zasu gano hakan?gaskiya Ummita wannan ƙazamar rayuwar da kika jefa kanki tayi miki tsauri da yawa,ki sassautawa kanki ki cire mutumin nan aranki,tunda shi bai ma san kina yi ba abinda ya sani kawai shine matarsa da ƴarsa,kuma kinga alkhairan matar nan awajenmu bai kamata muci amanarta ba,mu zamo masu cika alƙawari ba masu Butulci ba". . . . . . . . . . . .
Tun kafin ta ƙarasa Ummita ta daka mata wata irin tsawa,wacce tasa Khairat gimtse maganar ba tare da tayi niyya ba.
Don ita a halin yanzu ma ta fara tsoron Ummita,tamkar dai Ummita ɗince yaya ita kuma ƙanwa,don daman can ba'a nunawa Ummita yiwa yayarta biyayya ba,saboda ita ƴar so ce shiyasa ba'a koya mata hakan ba.
"Khairat na gaya miki ki fita harkata ko?don me ba zanso shi ba?saboda matarsa?to bari kiji indai har kika ga ban auri Baban Baby ba to mutuwa nayi,don Wallahi kinji na rantse ko ta wata hanya sai na aure shi.
Khairat ta ce"Ummita kin san abinda kike faɗa kuwa?kina son ki jefa kanki cikin masifa ko?wannan wani irin so ne haka?don ni dai a tarihi ban taɓa jinsa ba."
Ummita ta juya abinta ta cigaba da aikin tunaninta,ta bar Khairat anan tsaye tana tunanin halin da Ummita ke ciki.
Suna hirar Halima ta neme su ta rasa,Baby ta ce"Momy aƙwai abinda kike nema ne?".ta faɗi hakan tana kallon Halima wacce ke ta kallon gefansu,don dai tasan anan ta bar su Ummita yanzu kuma taga ba ta gansu ba.
-----*****-----
. . . .Suna cikin hirar suka ga Sailuba ta fito daga cikin gidan cikin mugun fushi,daga ita sai ɗaurin ƙirji sai kuma zanin da ta goya ɗan ta,wanda yake barcinsa hankalinsa ƙwance.
Indo ta tintsire da dariya ta ce"haka nake so Sailuba,so nake taje ta tarwatsa wannan nishaɗin,ta haukace masa yadda zai kasa gane komai,ta yadda zan sanya musu rigima me ƙarfi a tsakaninsu,sai yazo ya dafa ƙafa ta ya ce don Allah Indo ki yafe min,don kinsan tunda ya taɓoni sai yasan ya taɓoni don wallahi bazan yarda yaci bulus ba.
Bintu ta ce"Hmm ke kam Indo kin fi ƙarfina wallahi,ni ban ma san abinda yasa na tafi gida na dawo wajenki ba?".
Indo ta kyalkyale da dariya sannan ta ce"hegiya Bintu wato kin gano amfani ko?daman idan kaga kare na shinshina takalmi to yasan abinda ya hango,da bani da amfani da tuni kin fita a harkata."
Bintu taja hannun Indo wai au tafi gida,Indo ta fizge hannunta ta ce"ke Bintu kyale ni a'i dole sai naje naga yadda abin zai kaya,ko so kike in tafi gida banga yadda zasu kaya ba"?.
Ta fisge hannunta tayi gaba abinta,Bintu ta kalli ƙawarta kallon tausayi don ita yanzu Indo tausayi ma take bata,ayi mutum bai da aiki sai tsokanar mutane da son tashin hankali?ita Indo wacce irin mutum ce?babu yadda zatayi da halin Indo,kuma baza ta iya rabuwa da Indon ba don son Indo azuciyarta yake,sai dai kullum addu'arta Allah ya shirye ta.
Sailuba na zuwa ƙofar gidansu Lami ta hango mijinta Sunusi,sai tsara Lami yake ya kafo hularsa a gaba yana mata daɗin baki.
Sailuba ta wuce ta tsaya a tsakiyarsu tana kuka ta ce"wallahi She Allah ya kamaka mugu azzalumi kawai,macuci maci amana yau Allah ya toni asirinka."ta faɗi hakan tana kuka sosai,jin tana kuka sai ɗan tama ya fara kukan sosai.
Sunusi yayi tsuru,kamar kazar da ƙwai ya fashewa aciki,ya buɗe bakinsa xaiyi magana Sailuba ta ce"yimin shiru Sunusi,babu abinda zaka ce min ashe daman wajen wannan ƴar iskar karuwan kake zuwa?wajen wannan shaiɗaniyar ka tare?so kake ka ɗebomin masifa da ƙazanta ka kawo min gida?Allah ya wadaran Halinka Sunusi".
Sunusi ya kasa magana,saboda iya kunya yau dai ya jita kuma yasan halin Sailuba da mugun taurin kan tsiya,ba tafiya za tayi ba tunda taja ta tsaya ɗinnan.
Lami ta kalli Sailuba kallon sama da ƙasa ta ce"kan uba ni kike antayawa zagi haka?to wallahi baki isa kisha ruwa ba yau,sai na cire miki haƙoranki kaf kin kasa tauna ko da abinci ne,tunda ke agidanku ba'a koya miki tauna magana ba".
Ta kawowa Sailuba wani mugun naushi,don Lami irin manyan matan nanne masu ƙiba ta ko'ina.
Da sauri Sunusi ya kai hannunsa don ya tare dukan da Lami ta kaiwa Matarsa Sailuba,ji kake ƙum-ƙum an buge Sunusi a bakinsa.
Indo ta sau dariya a inda take har tana riƙe ciki tana ce wa"Hegi Sunusi yau sai anyi maka ruwan zafi". . . . . . . . .✍🏾
*Ku nuna mana soyayya wajen share,tare da comments wannan ita kaɗai ce hanyar da zamusan kuna ƙaunarmu🙏🏼Allah kabarmu da masoyanmu na asali Amin.*
*Noticed!Noticed🗣️🗣️!!*👇🏻👇🏻
Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent,sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki,kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻
07068606171
08104335144
08179523215
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
*MISS GREEN CE👉🏾👉🏻*
0 Comments