*HAUSA POEM*
*BY*
*I²Gusau*
*SAƘO GAREKI 'YAR UWATA*
*King and Queen Writing Chamber*
https://www.kingarticlenovels.com.ng/
Zan baki shawara cikin a zanci
Inada tabbacin kinada mutunci
Ɓangaren bauta kinada naci
Gashi kinyi gadon karamci
Nasan kina fatan samun rayuwa mai inganci
Miyasa kike son jefa rayuwar ki cikin kaɗaici
Idan barci kikeyi yakamata ki farka
Kada ki koma kamar iccen dabinon da anka shuka
Ki fahimci masoyin gaskiya da mai halin cinnaka
Idan da gaske yake sonki tunda wuri yakamata ya aika
Ma'ana ya aiko gidan ku domin a sanya maku albarka
Inkin samu mai rufin asiri kibashi zuciya domin ya mallaka
Kada kice sai mai abun duniya zaki ɗauka
Domin wata rana zaki jefa rayuwar ki cikin shakka
'Yar uwa wannan dama ce gareki
Idan kin kayi wasa da lokaci shima wata rana zaya barki
Gidan mji shine rufin asiri a gurinki
0 Comments