BOKO NE SILA







: *BOKO NE SILA*
            _(Fiction story)_



KING & QUEEN WRITING CHAMBER


HUSSAIN YUSUF


Page 1.

KANO
Dare ya tsala sosai ba ka jin sautin komai a garin, in ban da haushin karnuka da kukan gyare da yake amsa kuwwa! A ko'ina na garin. A wannan lokacin a gidan Malam Inuwa, babu wanda yake barci saboda tashin hankalin da suka tsinci kansu a ciki, sakamakon cikin da ya bayyana a jikin Fadila.

Mahaifiyar Fadila bakinta har kumfa yake yi saboda tsananin masifar da take ta zubawa ɗiyartata akan lallai sai ta gaya mata wanda yayi mata ciki ko kuma ta fice musu daga gida a cikin tsohon daren nan...
"Fadila ki yi sauri ki faɗa min wanda yayi miki ciki tun kafin tsinuwata ta tabbata a kanki, idan har kika bari na tsine miki Wallahi sai kin bar gidan nan har abada, na sallamawa duniya ke, ki koma can wajen kwarton naki ku cigaba da alfasharku..." 

Kuka sosai Fadila take yi kamar ranta zai fita, mahaifinta ne da yake tsaye can waje ɗaya ya jingina bayansa da bangon falon. Tunda suka fara hayaniyarsu yana tsaye kamar gunki, ya kasa furta komai, sai gumi da yake yanko masa yana gogewa...

Ganin matar tasa tana niyyar yiwa ƴarsu baki ne yasa yayi gyaran murya ya ce,
"Haba Hawwa'u hakan da kike yiwa yarinyar nan ba shine zai saka ta faɗa mana gaskiya ba, ki tsaya mu bi ta a hankali domin mu ji wanda yayi mata wannan cikin, idan ya so sai mu aura masa ita kowa ya huta ko ya kika gani?"
Harararsa ta yi kafin ta ja wani siririn tsaki, a fusace ta nufi kitchen ɗinsu. Da ido gaba ɗayansu suka bita, kafin mahaifinta ya juyo ya kalli sauran ƴan'uwan Fadila ya ce,
"Azima ku je ku kwanta da safe za mu yi magana" kamar jira suke da sauri suka nufi ɗakinsu, domin ba sa so mahaifiyar tasu ta zo ta iske su anan...
Da sauri Fadila ta tashi za ta bi bayan ƴan'uwanta "Fadila!" Mahaifinta ya kira ta da wata sassanyar murya, ita ma cikin sanyin murya ta amsa 

"Na'am Abba!" 

"Dawo nan ki zauna za mu yi magana"
cikin sanyin jiki ta dawo ta zauna ta jingina bayanta a jikin wata doguwar kujera, tare da sunkuyar da kanta ƙasa, wani zazzafan hawaye yana kwaranya akan kyakkyawar fuskarta.

A hankali mahaifin nata ya zo gabanta ya tsaya, cikin kakkausar murya ya kira sunanta "Fadila! Fadila!! Fadila!!! Sau nawa na kira sunanki?"
"Abba sau uku ne" 
"To kar ki kuskura na kara kiran sunanki, idan har kika sake na ƙara kiran sunanki ranki sai yayi mummunan ɓaci. Ina son ki dubi cikin idona ki faɗa min wanda yayi miki ciki, idan kuwa har kika ƙi faɗa mana Wallahi zan bi ra'ayin mahaifiyarki don ba za mu zauna da fasiƙa ba marar tsoron Allah.."

Wani kuka ne ya ƙwace wa Fadila a ranta ta yi nadama sosai, yau mahaifinta da mahaifiyarta waɗanda sun fi kowa sonta a cikin gidan, amma yau sune suke kiranta da fasiƙa marar tsoron Allah? "Ya Allah ka kawo min mafita Allah na tuba ka yafe min..." Abinda ta faɗi cikin zuciyarta kenan.

Aliyu ne ya fito daga cikin ɗakinsa yana murza ido, da alamu barcin bai ishe sa ba ya taso. Kallon Abba yayi da yake tsaye ganinsa yayi ya haɗe rai kamar an aiko masa da saƙon mutuwa mamaki ne ya rufe sa "To me ya faru haka cikin daren nan ban sani ba?".
Sosa kai yayi kafin ya ƙarasa inda mahaifin nasu yake tsaye cikin sanyin murya ya ce, 
"Abba lafiya kuwa na ganku anan cikin daren nan?"
"Ina fa lafiya Aliyu wannan yarinyar ta jawo mana abin kunyar da zai ta bibiyarmu har jikokinmu" ya faɗi yana nuna Fadila da yatsa...

Kallon inda Fadila take zaune yayi, kafin ya watsa mata wata muguwar harara ya ce,

"Ke Fadila me kika aikata ne haka?"

Sunkuyar da kai Fadila ta yi ta ƙi cewa komai. 
Fusata yayi ya zo kanta ya tsaya ya sake jefo mata tambayar
"Ba dake nake magana ba?"

"Ciki ne da ita, dama ai ba zata iya buɗa baki ta ce maka tana d'auke da cikin shege ba"
Umma ce ta faɗi yayin da take fitowa daga kitchen ɗin da ta shiga tun ɗazu, ko me ta yo a ciki oho!

"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un!" 

Shine abinda Aliyu ya faɗa yana dafe kansa da ya sara masa ciwo lokaci guda, cikin tsananin fushin da ya taso masa lokaci guda ya dubi Fadila ya ce,

"Uban waye yayi miki ciki?"

Ba zato ba tsammani sai ganin Umma suka yi ta nufo inda Fadila take zaune, kafin su yi yunkurin dakatar da ita tuni ta karaso wajen Fadilar.
Shaƙe mata wuya ta yi kamar za ta kashe ta, da kyar Fadila take iya numfashi idanunta gaba ɗaya sun fito waje, kakarin neman taimako take saboda riƙon da Umma ta yi mata ba na wasa bane..Da kyar Abba da Yaya Aliyu suka ɓanɓare Fadila daga hannun Umma, nan take kuwa ta hau tari na shaƙar da ta sha..

Wata muguwar harara Umma ta watsa mata kafin ta ce, 
"Wallahi Fadila idan har ba ki faɗa mana wanda yayi miki cikin nan ba, a cikin daren nan zan kashe ki kowa ya huta sai dai nima a kashe ni, sai a binne mu tare.."
Tana gama faɗin haka ta zaro wata sabuwar wuƙa daga ƙugunta ta nufi Fadilar, da sauri Abba da Yaya Aliyu suka nufo ta domin su dakatar da ita, kawo musu wuƙar Umma ta yi za ta yanke su da sauri suka ja da baya, tun kafin ta ƙarasa wajen Fadilar ta tashi ta kwasa a guje za ta nufi ɗakinsu..

Cikin zafin nama Umma ta yi nasarar damƙo gashin kanta, ta buga kanta a jikin bango nan take kuwa kan nata ya fashe jini ya fara zuba. Faɗuwa Fadila ta yi tana wani irin kuka mai tsuma zuciya tana ƙarasowa wajen da Fadila take a kwance, ba tare da shakkar komai ba ta ɗaga wuƙar sama da nufin caka mata a ciki...

Wani irin ihu Fadila ta saki tare da roƙon Umma akan ta ƙyale ta za ta faɗi gaskiya. 
"Don Allah Umma ki yi haƙuri ki ƙyale ni zan faɗo gaskiya don Allah Umma ki yi min rai"

Saurarawa Umma ta yi tana sakin wani irin huci mai cike da tsantsar bacin rai, da kyar Fadila ta iya miƙewa zaune tana rera wani kuka mai sauti mai cike da ban tausayi..
Daka mata tsawa Umma ta yi 
"Za ki faɗa min ko sai na idar da nufina akanki?"
Jikin Fadila yana kyarma ta buɗa baki da kyar muryarta har rawa take ta ce,

"Umma Abba ne yayi min cikin kuma ya gargaɗe ni akan kada na gayawa kowa komai rintsi da komai wuya ya zama sirri tsakanina da shi"

Gaba ɗayansu mutuwar tsaye suka yi saboda tsananin ruɗanin da suka shiga...
Abba ya fi kowa shiga cikin ruɗani, gani yake yi tamkar a mafarki wannan abun yake faruwa. Ji yayi ƙafafunsa sun kasa ɗaukarsa, tilas ya nemi waje ya zauna tare da dafe gefen ƙirjinsa da yake yi masa wani irin zafi, kamar ana hura masa wuta.

 Da kyar Aliyu ya dai-daita nutsuwarsa cikin tsananin fushi ya 
nufi inda Fadila durƙushe tana kuka, cikin ɗaga murya yake cewa
"Karya kike Fadila ba Abba ne yayi miki cika ba sharri ne kawai kika yi masa, Wallahi sai kin faɗa mana wanda yayi miki ciki amma ba Abba bane.." 

Yana ƙarasowa inda Fadila take durƙushe, cikin ɗacin zuciya ya ɗaga hannu da niyyar sharara mata mari, ji yayi an riƙe hannun nasa gam cikin tsananin fusata ya juyo domin ya ga wanda ya riƙe masa hannu..

#Comment 
#Vote
#Share.

Hussain Yusuf
: *BOKO NE SILA*
              _(Fiction story)_


KING & QUEEN WRITING CHAMBER


HUSSAIN YUSUF


Page 2.

Cikin fushi Aliyu ya juyo domin ya ga wanda ya dakatar da shi daga yunƙuri marin Fadila da yayi, Umma ya gani riƙe da hannun nasa sai faman aika masa da wata muguwar harara take da manyan idanunta..
   Da kyar ta buɗa baki cikin tsananin ɓacin rai ta ce, 
"Aliyu ya haka kuma? Abin ai sai yayi yawa ga mari ga tsinka jaka? Mahaifinka ya cuce ta ya ɗirka mata ciki a matsayinsa na Ubanta, kai kuma ka zo kana ƙoƙarin dukanta, bayan ba ta da laifi ko kaɗan a cikin wannan al'amarin tursasata kawai yayi!" 
Cike da mamaki Aliyu ya dubi Umma ya ce,
"Umma! Yanzu kina nufin kin yarda da maganar da Fadila ta faɗi?"

"Ai Fadila ba yarinya ba ce, ba za ta yiwa mahaifinku sharri ba, duk haukanta ta san abunda take yi, ni yanzu tsakanina da mahaifinku sai dai na ce, Allah ya isa! Ba zan taɓa yafe masa ba har abad...." 
Saurin tarar numfashinta Aliyu yayi hawaye duk ya wanke masa fuska ya dube ta ya ce,

"Haba Umma! Kada ɓacin rai ya sa hankalinki da tunaninki su tafi mana..."

Fashewa da kuka Umma ta yi tare da jero salallami kamar wacce aka yiwa mutuwa

"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un! Allahumma ajirni fi musibati! Yanzu Aliyu don ba ni ce na tsugunna na haife ka ba, ka ke kirana da marar hankali?"

Da sauri Aliyu ya ce, 
"A'a Umma ni ba haka nake nufi ba, gaskiya ce kawai na faɗi, ya za a yi ma Abba yayi wa Fadila ciki? Gaskiya Umma dole a binciki al`amarin nan, domin Abba ba shine yayi wa Fadila ciki ba.." 

"To, idan ba shi bane waye? Domin ita Fadila ba ta kula kowa a cikin samari ballantana ka ce saurayinta ne yayi mata don haka Wallahi sai na ƙwatowa ƴata haƙƙinta ko da zan rasa duk abinda na mallaka.." Ta k'arashe maganar tana sharar ƙwalla abin tausayi.

Shiru Aliyu yayi hawaye yana cigaba da wanke masa fuska, juyawa yayi ya kalli inda Abba yake zaune ya haɗa kai da gwiwa, yayi shiru. Nan take tausayin Abba ya mamaye masa zuciyarsa, a ransa yake jin Abba ba zai taɓa aikata alfasha da ƴar cikinsa ba. 

Ya daɗe yana kallon mahaifin nasu, kafin muryar Umma ta zaburar da shi..

"Inuwa na yi nadamar saninka a rayuwata! Na yi nadamar aurenka! Kalle ka ƙato da kai amma kana bibiyar ƴar cikinka Allah wadarai! Inuwa tur da hali irin naka tsohon najadu kawai mtssss!" 
Ta ja wani dogon tsaki tare da jan hannun Fadila suka nufi ɗakinta a tare...

Sai a wannan lokacin Abba ya ɗago da jajayen idanunsa kamar gauta, ya kalli Umma da take jan hannun Fadila, da hanzarinsa ya tashi ya bi bayansu yana kiran Umma...

"Hawwa'u! Hawwa'u! Don Allah ki tsaya ki saurare ni Wallahi ban aikata abinda kike zargina da shi ba.."
 Duk da Umma tana jin kiran da Abba yake yi mata, amma sam ta ƙi tsayawa ballantana ya saka ran za ta saurare shi, sai da ta je ƙofar ɗakin nata har ta riƙe handle ɗin ƙofar sannan ta tsaya, ta juyo ta kalli inda Abba yake tsaye, gumi duk ya wanke masa fuska. 
Wata muguwar harara ta watsa masa kafin ta ce,
"Inuwa ba ka da abunda za ka faɗa mini na yarda da kai! Domin daɗin bakinka ba zai taɓa yin tasiri a wajena ba. Dama ku maza ai haka kuke sai ku cuci mutum sannan ku zo ku yi masa daɗin baki, to Wallahi wannan karon daɗin bakinka ba zai taɓa yin tasiri a wajena ba. Ƴata ce ka riga ka cuce ta kuma Wallahi sai na bi mata haƙƙinta ko da zan rasa dukkan abinda na mallaka.." 
Tana faɗin haka ta shige cikin ɗakin tare da bugo kofar da ƙarfi..

Wani irin zazzafan hawaye ne ya zubo daga fuskar Abba, a hankali ya ce,
"Ya Allah ka fitar da ni daga cikin wannan bala'in da afko min!"

Juyawa yayi cikin sanyin jiki, zai tafi idanunsa ne suka sauka akan Aliyu da yake tsaye kamar gunki sai faman zubar da ƙwalla yake na tausayin mahaifinsu..
Wani murmushin dole Abba ya ƙaƙalo ya ce,
"Aliyu! Ka je ka kwanta da safe komai zai yi dai-dai in sha Allahu" 

Cikin sanyin murya Aliyu ya ce,
"To, Abba! Amma..."
"Dakata Aliyu ka wuce ka tafi ɗakinka sai fa safe.." "To, Abba!" Aliyu ya faɗi tare da juyawa ya nufi ɗakinsa zuciyarsa tana yi masa wani irin zafi, ji yake kamar ya je ya shaƙe Fadila ta faɗa masa gaskiyar wanda yayi mata ciki. Amma babu damar aiwatar da haka, duk da haka ya ƙudurce a ransa duk rintsi da tsanani sai ya fitar da mahaifinsu daga cikin wannan baƙin ƙazafin da ƴar cikinsa ta yi masa..

Bayan Aliyu ya shiga ɗakinsa, shi ma Abba tashi yayi ya nufi nasa d'akin. Jikinsa duk yayi sanyi, kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka Abba yake tafiya...
Yana shiga cikin d'akin ya zube akan faffaɗan gadonsa yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. Shi ma zuciyarsa ban da zafi da raɗaɗi babu abinda take yi masa. Nan take ya shiga karanto duk addu'ar da ta shigo bakinsa. A hankali ya ji zuciyarsa tana yin sanyi, kafin ya fara sauke ajiyar zuciya...

Tashi yayi ya shiga bathroom alwala yayi ya fito, sannan ya tayar da Sallah. Bayan ya idar addu'oi ya shiga yi akan Allah ya kuɓutar da shi daga wannan sharrin da ƴar cikinsa ta yi masa, a matsayinsa na mahaifinta..Ya daɗe yana addu'a kafin ya shafa ya zauna akan dardumar yana ta yin Istigfar domin gani yake yi wani babban laifi yayi wa Ubangiji shi yasa ya jarrabce shi da wannan mummunan ƙaddarar.... 
Shiru yayi yana tunani a cikin ransa
"Me na yiwa Fadila ta yi min wannan mummunan sharrin?
 Shin wanene yayi wa Fadila ciki? Menene matsayinsa a wurinta? Yanzu kenan Fadila ta zaɓi mutuncina ya zube akan mutuncin saurayinta ya zube?" 
Duk wannan tunanin da yake yi hawaye sai faman kwaranya yake akan fuskarsa, tunani kala-kala suka cika masa zuciya. 
Da haka barci mai nauyi ya ɗauke shi, ba tare da ya samu amsar tarin tambayoyin da suka cika masa zuciyarsa ba.
  
Haka a ɓangaren su Azima babu wanda ya iya runtsawa a cikinsu, domin sun ji duk abinda ya faru daga cikin ɗakinsu. Wani irin haushin Abba ne ya kama su, domin su dai a iya saninsu Fadila ba ta da saurayi ko a makaranta ballantana a gida, don haka babu wanda suke tunanin yayi wa Fadila ciki sai Abba, domin namiji ba shi da tabbas.

WASHE GARI

Misalin ƙarfe 7:30am na safe, a zaune Azima da Yasmin da kuma Najwa suke a falo sun yi jugum-jugum kamar waɗanda aka yi wa mutuwa. 
Abba ne ya fito daga cikin ɗakinsa sanye yake da shadda kalar maroon ta yi masa kyau sosai, ganin ƴaƴan nashi a zaune ne yasa ya kalle su da mamaki ɗauke akan fuskarsa ya dube su ya ce..

"Yasmin me kuke yi anan da safen nan, ba za ku je school ba ne...?"
Gaba ɗayansu shiru suka yi kamar ba magana Abba yake yi musu ba, ballantana ya saka ran za su gaida shi. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, ransa ya ɓaci sosai. Cikin fushi ya dubi Azima ya ce,
"Azima me ya same ku ne ina yi muku magana amma kun yi banza da ni?" 
Maimakon Azima ta ba shi amsar tambayar da yayi mata, sai ta yi shiru tare da kawar da kanta gefe. Cikin sanyin jiki Abba ya ƙaraso kusa da ƴaƴan nashi, ya zauna a kujerar da take facing ɗinsu ya haɗe rai tamkar bai taɓa dariya ba. Yana zama gaba ɗayansu suka tashi suka bar shi a wajen, ba tare da sun yi masa magana ba, da kallo ya bi su kafin ya sunkuyar kansa ƙasa...

Abinda ya faru jiya ne ya shiga dawowa masa, wani zazzafan hawaye ne ya zubo masa hannu ya sa ka ya share sannan ya ce,
"Fadila kin cuce ni! Amma ba zan yi miki baki ba, ban san dalilinki na yi min ƙazafin zina a matsayina na mahaifinki ba, ban san laifin da na yi miki ba Fadila ban san dalilinki na yi min ƙazafi ba, amma duk girman laifin da na yi miki ban cancanci wannan hukuncin daga gare ki ba" yana maganar hawaye yana ambaliya akan fuskarsa duk ya jiƙe masa fuskarsa...........

#Comment and share

_Ga masu son shiga group ɗin *BOKO CE SILA* ku yi magana ta cikin wannan numban 07069475482._
: *BOKO NE SILA*
           _(Fiction story)_



KING & QUEEN WRITING CHAMBER


HUSSAIN YUSUF


Page 3.

Da kyar Abba ya iya jan kafarsa ya nufi dining table, domin yayi breakfast ya fita da wuri. Kujera ya jawo ya zauna, yunwa yake ji sosai amma ya kasa zuba abincin. Abin duniya duk ya bi ya ishe shi, ya rasa me yake yi masa daɗi a duniya. 

Ya daɗe yana jiran wanda zai zo ya zuba masa abincin, amma shiru har yanzu babu wanda ya fito, ga shi ya kusa yin latti, bayan kamar minti goma sha biyar da ya ga babu wanda ya fito sai ya sa hannu ya jawo plate da plask ɗin abincin zai yi saving din kanshi. Yana buɗa plask din mamaki ya kama shi, babu komai a ciki sake jawo wani plask ɗin yayi nan ma bai ga komai a ciki ba. Ransa ne ya ɓaci sosai, miƙewa tsaye yayi cikin fushi ya nufi ɗakin Umma yana kiran
"Hauwa'u! Hauwa'u kina ina?"
Hannu yasa ya rinƙa dukan kyauren ɗakin cikin fushi.

Umma ce ta buɗe ɗakin ta fito tana murza ido, alamun daga barci ta taso.
Ta gefen ido ta kalli Abba sannan ta yi saurin kawar da idanunta ta nuna kamar ba ta ga mutum a ƙofar ba sannan ta ce,
"Wai waye yake damuna da sassafen nan ko tashi ban yi ba?" 
"Wai Hauwa'u me yake damunki ne? Yaushe kika zama haka? Yanzu saboda Allah Hauwa'u abunda kika yi min dai-dai ne? Ya za ki ajiye min kwanukan abinci bayan babu abincin a ciki?"
Fashewa da dariya Umma ta yi kafin ta dubi Abba ta ce,
"Malam ka manta abin kunƴar da ka jawo mana? Ai ni tun jiya na yanke duk wata alaƙa da take tsakanina da kai, daga yau babu wanda zai k'ara yi maka girki a cikin gidan nan sai dai ka girka da kanka idan ka matsu, don ba zan yi girki na bai wa kwarton cikin gida ba, wanda yake bibiyar ƴar cikinsa...." 
  "Ya ishe ki haka Hauwa'u! Me yasa ba ki da fahimta ne?Sannan ina gargaɗinki kada ki kuskura ki ƙara kirana da wannan mummunan kalmar..." 

Yana fadin haka ya juya ya tafi cikin fushi, ɗaukar jakar laptop ɗinsa yayi tare da fice wa daga cikin falon. A ƙofa ya tsaya yana jiyo sautin dariyar Umma tana cewa "Ai Inuwa kaɗan ka fara gani ba ka ga komai ba Wallahi, ni da kai mu zuba shege ka fasa, Wallahi sai na azabtar da kai a cikin gidan nan sannan na kai ƙararka kotu, domin a yanke maka hukunci dai-dai da abinda ka aikata..." 
Girgiza kai kawai Abba yayi sannan ya wuce ya tafi zuciyarsa duk babu daɗi.

***
"Hauwa'u tun sassafe ki ke ki kirana akan na yi sauri na zo akwai matsala menene ya faru ne yi sauri ki sanar da ni"
Hajiya Amina ce ta faɗi, ƙawar Umma ce wacce ba ta ɓoye mata duk wani sirrinta.
Ajiyar zuciya Umma ta sauke kafin ta ce,
"Hmm! Amina menene ma bai faru ba?" 
"Subhanallahi! Yi sauri ki sanar da ni don Allah domin mu san abin yi"

"Ai Hajiya maganar ce babu daɗin faɗinta, sai dai babu yanda na iya dole ne na sanar da ke" 
  
 "To, ina sauraronki"

"Hajiya Fadila ciki ne da ita" 

"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un Hauwa ciki fa kika ce?"
"Ƙwarai kuwa Hajiya ciki ne a jikinta watansa har uku ni ban sani ba"
"Tirƙashi! Yanzu ita Fadilan ta faɗa miki wanda yayi mata cikin?"

Hawaye ne ya zubo daga fuskar Umma ta ce, 
"Mahaifinta ne yayi mata"
"La'ilaha ilallah! Mahaifinta fa kika ce?"
"Ƙwarai kuwa Hajiya Wallahi shine yayi mata"
"Ita Fadilan ce ta gaya miki mahaifinta Malam Inuwa ne yayi mata cikin?"
"Hajiya bari na kira miki Fadilar sai ki ji komai a bakinta domin waƙa a bakin mai ita ai tafi daɗi"

"Yawwa kira min ita na ji"
Da ƙarfi Umma ta kwala kira "Fadila! Fadila" 
"Na'am Umma!"
"Zo nan!"

Cikin sanyin jiki ta fito daga d'akin, sanye take da doguwar riga, ga wani zurmemen hijabi da ta sanya a jikinta kamar wata mumina. Cike da ladabi ta zo ta zauna a ƙasa ta ce,
"Umma ga ni!" 
Sannan ta gaishe da Hajiya Amina, cikin sakin fuska ta amsa.

Cike da nutsuwa ta dubi Fadila ta ce,
"Fadila tambayarki zan yi amma don Allah kar ki yi min ƙarya kin ji, kar ki ji tsoron komai ki faɗa min iyakar gaskiyar abinda kika sani!"
Gyaɗa kai Fadila ta yi ta ce,

"To, Mama in sha Allahu zan faɗa miki iyakar gaskiyata"

Gyara zama ta yi sannan ta dubi Fadilar ta ce,
"Fadila da gaske ne mahaifinki shi yayi miki ciki?"
Gyaɗa kai Fadila ta yi ta ce,
"E Mama shi yayi min!"
Tafa hannu Hajiya Amina ta yi ta ce,
"Lahaula wala ƙuwwata illa billah! Wannan wanne irin zamani ne muka shigo? Uba ya rinƙa bibiyar ƴar cikinsa? Allah wadarai!"

Sake kallon Fadila ta yi ta ce,
"Yaushe ya fara bibiyarki har yayi miki ciki?"
Fashewa da kuka Fadila ta yi cikin kukan ta ce,
"Lokacin da Umma ta yi tafiya zuwa Kaduna ne, da yamma ina zaune a falo na yi wanka na yi kwalliyata, lokacin ni kaɗaice a gidan, duk su Anty Azima tare da su Yasmin sun fita shopping. Sai ga shi ya dawo daga office ya umarce ni akan na haɗa masa ruwan wanka...." Tana zuwa nan a zancenta kuka ya ƙwace mata, shiru su Umma suka yi suna kallonta har sai da ta yi mai isarta sannan ta dakata da kukan tana ajiyar zuciya..

Hajiya Amina ce ta yi gyaran murya ta ce,
"Fadila ke muke sauraro! Daga kai masa ruwan wanka sai kuma me ya faru?"
   "Ina cikin haɗa masa ruwan, kawai sai gani na yi ya shigo cikin bathroom ɗin, kafin na yi magana ya rufe ƙofar da makulli ta ciki. Sosai na firgita! Shine ya rinƙa kwantar min da hankali akan na ba shi haɗin kai babu abinda zai faru da ni, kuma yayi min alƙawarin kuɗaɗe masu yawa har da mota ma, sosai na nuna masa ba zan amince na yi tarayya da shi ba a matsayinsa na mahaifina, shine ya rinƙa yi min daɗin baki, har ya fara shafa min jikina, daga nan ban san yanda aka yi ba har na amince ya cika burinsa..."

"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un! Wannan wacce irin masifa ce Hauwa?" Hajiya Amina ta faɗi tana kallon Umma, jinjina kai Umma ta yi ta ce,
"Wallahi nima shine abinda ta sanar da ni."

Kallon Fadila Hajiya Amina ta yi ta ce, "Daga nan ya sake bibiyarki?"
"Jinjina kai Fadila ta yi ta ce,
"A'a sau ɗaya ne bai sake nemana ba, amma ya kirawo ni ɗakinsa yayi min gargaɗin kar na faɗawa kowa ya zama sirri tsakanina da shi"
Girgiza kai Hajiya Amina ta yi ta ce,
"Shikenan Fadila, amma ina son ki riƙe duk wannan abinda kika faɗa mana domin zai yi mana amfani anan gaba tashi ki je Allah yayi miki albarka"

Tashi Fadila ta yi ta koma cikin d'akinsu, tun jiya da dare take zaune cikin ɗakin ko falo ta kasa fitowa, sai yanzu da Umma ta kirata ta fito.
Bayan tafiyar Fadila Hajiya Amina ta juyo da hankalinta wajen Umma ta ce,
"Hauwa'u! Anya kuwa kina bai wa mutumin nan haƙƙinsa na aure da yake kanki?" 
Rau-rau Umma ta yi da ido, sannan ta ce,
"Wallahi Hajiya babu abinda na ragi Malam da shi, kawai ya bi son zuciyarsa da ruɗin shaiɗan ne"
"Ai kuwa zai ga ruɗin shaiɗan don ba za mu taɓa barinsa ya ci banza ba."

Kallon Hajiya Amina Umma ta yi kafin ta ce,
"Yanzu Hajiya menene abin yi?" Jinjina kai Hajiya Amina ta yi sannan ta cewa Umma "Kawo kunnenki ki ji...."
Babu gardama Umma ta kawo kunnenta, Hajiya Amina ta yi mata raɗa, tana gama faɗa mata Umma ta jinjina kai ta ce,

"Nagode sosai da wannan shawarar ƙawata! Allah ya bar mu tare in sha Allahu na yi miki alƙawarin zan yi amfani da wannan shawarar ta ki......"
   Murmushi Hajiya Amina ta yi ta ce, "Amma ki fara tuntuɓar Fadilar domin mu ji ta bakinta" 
"Karki damu Hajiya Fadila ba za ta bamu matsala ba, ai tana da hankali sosai kawai don an cuce ta ne...."


*Comment and share pls*

Duk mai son shiga _group yayi magana ta cikin wannan numban 07069475482._
: *BOKO CE SILA*
            _(Fiction story)_



KING & QUEEN WRITING CHAMBER


HUSSAIN YUSUF


Page 4.

Miƙewa tsaye Hajiya Amina ta yi ta ce,
"To Hauwa ni zan koma za mu ƙarasa maganar ta waya" "To shikenan ƙawata sai na kira ki" "To shikenan ni na wuce"
Bayan tafiyar Hajiya Amina, sai ga Aliyu ya fito daga ɗakinsa, durƙusawa yayi ya gai da Umma. Amsawa ta yi ba yabo ba fallasa, sannan ta kawar da kanta gefe.

Samun guri yayi ya zauna, cike da nutsuwa ya kalli Umma ya ce,
"Umma ina Fadila?"
Harararshi Umma ta yi ta ce,
"Uban me za ka yi mata?" "A'a Umma ba wani abu zan yi mata ba, wasu ƴan tambayoyi ne kawai zan yi mata akan maganar da ta faɗa jiya domin na fi son mu bi komai a hankali har gaskiya ta bayyana!" 
Kallonshi Umma ta yi ta ce,
"Wacce gaskiya kuma kake nufi Aliyu? Ai tun jiya da daddare gaskiya ta bayyana kanta!" Aliyu ya ce, "Yanzu Umma kin yarda da maganar Fadila? Ni a ganina ruɗewa ce ta saka ta faɗi haka amma..."
"Dakata Aliyu ba na son maganar banza anan wajen, Fadila dai ba yarinya ba ce ta mallaki hankalin kanta, don haka ba za ta taɓa yiwa mahaifinku ƙarya ba.." 
"Amma Umma yana da kyau ayi bincike kafin a yanke hukunci, domin aikin gaggawa ba ya haifar da ɗa mai ido.." Umma ta ce, "To, na ji amma yanzu ba zaka ga Fadila ba, don haka ka tashi ka tafi.." Ta faɗi tana nuna masa ƙofa, ajiyar zuciya Aliyu ya sauke ya ce, "Umma a tsaya dai a duba al'amarin nan" harararshi Umma ta yi ta ce, "Aliyu ka tashi ka tafi na ce tun kafin na ci mutuncinka anan wajen." Miƙewa tsaye Aliyu yayi ya ce, "To Umma haka zan tafi ban yi breakfast ba?" "Ai yau babu wanda zai yi muku girki a cikin gidan nan, ba iya yau ba ma har abada babu wacce za ta k'ara shiga kitchen ta dafa muku abinci a cikin gidan nan don haka ka  wuce ka tafi..." Girgiza kai Aliyu yayi sannan ya fice daga cikin falon, zuciyarsa cike da tunani kala-kala, "Yanzu kenan Umma ba ta yiwa Abba abincin breakfast ba? Lallai Umma ta ɗauki wannan abun da zafi, amma Wallahi sai na bai wa Fadila mamaki..." Da wannan zancen zucin ya shiga motarsa ya nufi ma'aikatar shari'ah domin Aliyu sabon lauya ne yana aiki a ma'aikatar shari'ah ta jahar Kano, bai daɗe da fara aiki ba, shi yasa yake tantama akan maganar da Fadila ta faɗi..

Bayan tafiyar Aliyu Umma ta tashi ta shiga ɗakinta Fadila ta gani a zaune gefen gado, ta yi tagumi hawaye yana zuba akan kyakkyawar fuskarta. Dafa kafaɗarta ta yi ta ce, "Fadila ki yi haƙuri dukkan tsanani yana tare da sauƙi, na yi miki alƙawarin ba zan taɓa bari wannan abun ya tafi a banza ba dole na tashi tsaye na ƙwatar miki haƙƙinki a matsayinki na ƴa mace, domin an zalunce ki, amma ki daina wannan kukan ba na son na ganki a cikin damuwa yi sauri ki share hawayenki.." A hankali Fadila ta sa hannunta ta goge hawayen ta dubi Umma ta ce, "Ni yanzu Umma damuwata ɗaya ce a wanne matsayi ɗan da na haifa zai rayu a cikin duniyar nan? Wacce amsa zan ba shi yayin da ya tambaye ni waye Ubansa ko kuma waye Kakansa?" Fashewa da kuka ta yi da kyar Umma ta rarrashe ta, tare da kwantar mata da hankali.. Har sai da ta yi shiru sannan Umma ta dube ta ta ce,

"Fadila sai kin so duk wannan abun zai faru!" Zaro ido Fadila ta yi ta ce, "Umma kamar yaya sai na so duk wannan abun zai faru?" Umma ta ce, "E! mana Fadila sai kin so za ki haifi ɗan ya rayu har yayi miki waɗannan tambayoyin da ba ki da amsarsu..." Shiru Fadila ta yi tana kallon Umma kana ita kuma ta cigaba da cewa..
"Ina son ki ba mu haɗin kai a zubar da cikin nan a sirrance ba tare da kowa ya sani ba, Hajiya Amina ita ce za ta yi mana hanyar da za samu likitan da zai zubar da cikin a sauƙaƙe kuma ta ce ya iya aikin sosai ba a samun matsala.." Cikin tashin hankali Fadila ta ce,
"Haba Umma! Ya za mu sake aikata wani laifin bayan wanda na aikata? Haba Umma idan aka zubar da cikin nan tamkar mun aikata kisan..." "Dakata Fadila ba dogon zance na tambaye ki ba, amincewarki kawai nake buƙata, idan kuma kin ga ba za ki iya ba sai ki je kiyi ta yawo ɗauke da cikin mahaifinki ke mutane za su yi ta zagi da tsinewa ƙarshe ki haɗiyi zuciya ki mutu da baƙin ciki..." Umma tana gama faɗin haka ta tashi ta fice daga ɗakin cikin tsananin fushi da ɓacin rai.

Fashewa da kuka Fadila ta yi ta ɗauki filo ta cillar da shi, ta hau dirza ƙafafunta akan gadon tamkar wata ƙaramar yarinya. Kuka take yi sosai a can ƙasan zuciyarta kuwa tsantsar nadamar abinda ta aikata take yi, cikin kukan take cewa "Me yake shirin faruwa da ni ne? Wannan wacce irin rayuwa ce na faɗa? Ya Allah ka kawo min mafita..." Sake rushewa da kuka ta yi tare da kwantawa akan gadon, zuciyarta cike da tunani kala-kala, da haka barci mai nauyi ya ɗauke ta ba tare da ta sani ba..

A ɓangaren Abba kuwa tun da ya je office ya kasa aiwatar da aikin komai, jikinsa duk babu daɗi ya rasa inda zai sanya zuciyarsa ya ji sanyi a duniyar nan. Har yanzu mamaki yake yi ta ya ƴar cikinsa za ta yi masa wannan mummunan ƙazafin? To laifin me ya aikata mata? Yanzu ta yaya zai wanke kansa daga cikin wannan ruɗanin?
Ire-iren tambayoyin da Abba ya rinƙa yi wa kansa kenan! Amma ko amsar tambaya ɗaya ba shi da ita, kuma ba shi da mai amsa masa....
     Bai san lokacin da wani zazzafan hawaye ya zubo masa ba, a hankali ya saka handkercif ya share hawayen, yana cikin tunani ya ji ana yi masa nocking ya ji ana yi masa, sai da ya daidaita nutsuwarsa sannan ya ce, "Yes come in!" Aliyu ne ya shigo office ɗin fuskarsa ɗauke da murmushi, tamkar babu wata damuwa a tattare da shi...
Shi ma Abba murmushin dole ya ƙaƙalo ya kalli Aliyu ya ce, "My son zauna mana!"

Jawo kujera Aliyu yayi ya zauna ya kalli Abba ya ce, "Abba ka tashi lafiya?" "Lafiya ƙalau my son wajen aikin za ka tafi?" "E! Wallahi Abba can zan tafi domin akwai wata shari'ah da za a fara ƙarfe goma, shine na biyo ta wajenka saboda abinda ya faru a gida jiya da daddare.." Numfashi Abba ya ja sannan ya ce, "Aliyu kai ɗana ne ka san ni ka san ko ni waye, tunda nake a rayuwata ban taɓa aikata zina ba, kuma me zai saka ni na aikata yanzu kuma da ƴar cikina?"

Aliyu ya ce, "Abba ko da duk duniyar nan za su yarda cewa kaine ka yiwa ƴarka Fadila ciki, Wallahi ni ba zan yarda ba. Domin na fi kowa sanin halinka amma Abba abin dubawar anan shine; me yasa Fadila ta yi maka sharri?" Cikin kuka Abba ya ce, "Aliyu Wallahi nima ban san dalilin Fadila ba, kuma ban san laifin da na aikata mata ba.." "To, Abba in sha Allahu komai zai zo da sauƙi ka kwantar da hankalinka ka daina saka damuwa a cikin ranka, kada hawan jininka ya motsa!" 
" My son in sha Allah zan yi ƙoƙari na ga na cire duk wata damuwa daga cikin raina, ka tashi tafi wajen aikinka kada ka yi latti.." Miƙewa tsaye Aliyu yayi ya ɗauko abincin da ya siyowa Abba a restuarant, miƙa masa abincin yayi ya ce, "Abba na san ba ka yi breakfast ba, kuma ba zaka iya zuwa restuarant ba, shi yasa na tsaya na siyo maka, amma don Allah Abba ko me Umma za ta faɗa maka kada ka biye mata domin yanzu ba a cikin hayyacinta take  ba kome za ta iya faɗa maka..."

Murmushi Abba yayi ya ce, "Haba my son na san duk abinda nake yi, ina ƙoƙarin danne duk wata damuwa da take cikin raina, in sha Allahu na yi maka alƙawarin ba zan kula Hauwa ba duk irin abinda za ta yi min zan yi haƙuri har Allah ya bayyana gaskiya..." Murmushi Aliyu yayi ya ce, "Yawwa Abba haka nake son ji, Allah ya bayyana mana gaskiya cikin ƙanƙanin lokaci" "Amin ya Allah! My son ka tashi ka tafi wajen aikinka kada ka makara na ga yanzu 9:30am ta yi.." Abba ne ya faɗi haka yana kallon agogon bangon da yake manne a cikin office ɗin nasa..
Ɗaukar jakarsa Aliyu yayi ya ce, "Abba ni zan wuce sai na dawo"
"To my son Allah ya tsare" da amin Aliyu ya amsa sannan ya fice daga cikin office ɗin da sauri, wata nutsuwa ce ta shige sa saboda ganin Abba da yayi cikin kwanciyar hankali tamkar babu abinda yake damunsa..Bayan fitar Aliyu Abba ya cigaba da aikinsa tamkar babu damuwa a tattare da shi.


A gida kuwa misalin ƙarfe biyar na yamma, Umma ce zaune a falo tare da ƴaƴanta gaba ɗayansu suna kallon news a tv. Gaba ɗayansu sun tattara nutsuwarsu ga labaran da suke kallo domin labaran fyaɗe ne wata ƴar jarida take karantowa inda take cewa 'An kama wani tsoho mai shekara 67 yayi wa yarinya ƴar shekara 15  fyaɗe' suna gama kallon labarin, Umma ta jinjina kai ta ce, "Gaba ɗayansu haka suke, ba sa duba girma da shekaru ko kuma abinda zai biyo baya bayan sun aikata, sai sun aikata su zo suna nadamar da ba ta da amfani mtssss!"' Ta ƙarashe maganar tare da jan wani dogon tsaki, kamar ƴarta aka yiwa fyaɗen.
"Assalamu alaikum!" Gaba ɗayansu suka kalli inda aka yi sallamar Salma ce ta shigo fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙaraso cikin falon. 


Har ƙasa ta durƙusa ta gaishe da Umma tare da sauran ƴan'uwanta. Ba yabo ba fallasa suka amsa mata kamar an yi musu dole. Jikin Salma ne yayi sanyi sosai, a ranta take tunanin lallai akwai abinda yake faruwa a cikin gidan nan.. Samun waje ta yi ta zauna ta yi shiru, tana son tambayar Umma amma tana jin tsoro saboda ganin Ummar fukarta a haɗe babu alamun fara'a ko kaɗan..

Shiru suna zaune kamar kurame babu cewa wani komai, sun zauna jugum kamar waɗanda aka yi wa mutuwa. Buɗe ƙofar falon aka yi, Abba ne ya shigo tare da Yaya Aliyu bakinsu ɗauke da sallama, da gudu Salma ta tashi ta nufi su Abba tana cewa "Oyoyo ga Abbana da Yayana!" wata uwar harara Umma ta watsa mata tare da jan wani dogon tsaki, sannan ta kalli Abba a wulaƙance kamar ta ga kashi. Ganin shi ta yi tamkar babu abinda yake damunsa, sai faman sakarwa Salma murmushi yake ita kuma tana ta zuba masa surutu kamar wata ƙaramar yarinya..

Ƙarasa shigowa falon su Abba suka yi tare da zaunawa akan kujerun falon inda su Umma suke zaune, Abba yana zama Umma ta watsawa ƴaƴanta wani irin kallo da sauri suka tashi gaba ɗayansu tare da shigewa ɗaki suka bar Abba da Umma da Aliyu da kuma Salma a zaune, cike da mamaki Aliyu ya buɗa baki ya ce, "Umma me ya samu su Azima daga zamanmu kuma sai su tashi?" Harararshi Umma ta yi ta kawar da kanta tamkar ba da ita yake magana ba, Salma ce ta buɗa baki ta ce, "Umma ko laifi muka yi musu ne?" 

Cikin fushi Umma ta buɗa baki ta ce, "Ai dole su tashi domin ba zan taɓa barin ƴaƴana su zauna guri ɗaya tare da kwarto ba!" Da sauri Aliyu da Salma suka kalle ta har haɗa baki suke yi wajen tambayarta "Kwarto kuma Umma?" Aliyu ya sake cewa "Waye kwarton a cikinmu?"

Wani ɗan murmushi Umma ta yi wanda kana ganinsa ka san bai kai har zuci ba, sannan ta ce, "A gidan nan akwai kwarton da ya wuce wanda yake zaune?" Ta faɗi tana nuna Abba da baki, cikin fushi Abba ya miƙe zai yi wa Umma magana, nan take muryarsa ta sarƙe ya hau kokawa numfashinsa dafe ƙirjinsa yayi da hannunsa ji yake kamar zuciyarsa za ta fashe saboda tsananin ɓacin rai, wani duhu ne ya gifta ta tsakanin idanunsa, nan take ya daina ganin komai kawai sai ji yayi ya tafi ƙasa luuuu zai faɗi, da sauri Aliyu da Salma suka nufi inda yake cikin tashin hankali suna kira Abbaaa! 

Cikin zafin nama Aliyu yayi sauri ya tare shi kafin ya kai ga ƙasa, yana kiran "Abba! Abba!! Abba!!!" Amma shiru kamar maye ya ci shirwa, babu alamun motsi a tare da shi, fashewa da kuka Salma ta yi ta ce, "Yaya Aliyu mu tafi asibiti......"

_Gaskiya ba kwa yin comment, kuma rashin comment zai iya sanyawa na mayar shi paid book idan kun fi son na daina posting sai an siya shike nan nima na fi son hakan..._

Comment and sshare

Hussain Yusuf
07069475482.
: *BOKO NE SILA*
           _(Fiction story)_



KING & QUEEN WRITING CHAMBER



HUSSAIN YUSUF


Page 5.

Kallonta Aliyu yayi ya ce, "Yi sauri ki kawo min ruwa mai sanyi!" 
Da gudu Salma ta ɗauko ruwa mai sanyi a fridge ta kawowa Aliyu da yake rungume da Abba. Karɓa yayi ya buɗe gorar ruwan ya yayyafawa Abba a fuska, a hankali ya buɗe idanunsa tare da sauke ajiyar zuciya. Kallonshi Aliyu yayi ya ce, "Sannu Abba!" Bai iya amsawa ba sai yunƙurin tashi zaune da yake yi, taimaka masa Aliyu yayi ya tashi zaune tare da jingina bayansa da kujera. 

Duk wannan abun da yake faruwa Umma tana zaune tana kallonsu faɗuwar da Abba yayi ko a jikinta fata take yi ma dama ya mutu kowa ya huta! Kallonta Aliyu yayi cikin tsananin ɓacin rai ya ce, "Umma! Wacce irin rayuwa ce wannan kike son shigo da ita cikin gidan nan? Yanzu ki dubi Abb...." Saurin dakatar da shi Umma ta yi ta ce, "Ya isheka haka Aliyu! Wato don ka ga ba ni ce wacce na haife ka ba shi yasa kake faɗa min magana son ranka ko? To ka cigaba daga kai har Ubannaka sai na yi maganinku!" Tana faɗin haka ta tashi ta shige d'aki da sauri cikin tsananin ɓacin rai.

Da ido Aliyu da Salma suka raka ta har ta shige ɗakinta ta rufo ƙofar da ƙarfi. Juyowa Salma ta yi ta ce, "Yaya Aliyu wai me yake faruwa a cikin gidan nan? Tunda na zo nake ganin sauyin al'amura da yawa.." Jinjina kai Aliyu yayi ya ce, "Zan sanar da ke yanzu bari na kai Abba asibiti domin a duba lafiyarsa.." "Yaya Aliyu nima zan bi ka mu tafi tare!" Wani irin kallo ya watsa mata kafin ya ce, "Babu inda za ki bi ni domin ba daɗewa za mu yi ba, kuma na san ba ki sanar da mijinki ba, don haka ki zauna ki jira mijinki kada ya zo ɗaukarki ya tarar ba kya nan!" Marairaice murya ta yi kamar za ta yi kuka ta ce, "Haba Yaya Aliyu don Allah ka bar ni mu tafi tare, yanzu bari na sanar da yaya Kabir ɗin, idan ya so sai ya biyo ta asibitin ya ɗauke ni." 

Girgiza kai Aliyu yayi ya ce, "Shikenan taho mu tafi!" Da kyar Aliyu ya miƙar da Abba tsaye da kansa ya dafe shi har bakin motarsa, saka shi gidan baya yayi ya ce Salma ta dafe shi zuwa asibitin. Shi kuma ya zagaya ya shiga ɓarin direba ya ja motar a guje ya bar gidan zuciyarsa cike da tunani da fargaba iri-iri.

Bayan su Aliyu sun tafi asibiti, Umma ce ta leƙo falon ta ga babu kowa a ciki. Da sauri ta fito ta ɗauki wayarta da take kan caji ta yi dialing ɗin numban Hajiya Amina... Ba ta daɗe tana ringing ba aka ɗaga...
"Hello Hajiya!" Daga can ɓangaren Hajiya Amina ta ce, "Hauwa'u kina lafiya?" "Lafiya ƙalau Wallahi Hajiya, dama akan maganar da muka yi da ke ne jiya!" 
"Yawwa Fadilan ta amince ne?" Ɓata rai Umma ta yi kamar Hajiya Amina tana ganinta ta ce,
"Ai Wallahi ki bar ni da ƴar iskar yarinya ta ƙi amincewa, wai ita a barta da cikinta!" Ita ma Hajiya Amina ɓata rai ta yi ta ce, "Haka ta zaɓa? Wallahi haka ta zaɓa ni gaba ɗaya ma na rasa ta yanda zan shawo kanta ta yarda, domin ba na son na matsa mata asirinmu ya tonu!" Numfasawa Hajiya Amina ta yi ta ce, "Shikenan! Ki bari gobe zan zo gidan naki sai mu tattauna!" "To shikenan sai kin zo!"
Daga nan ta katse kiran, tana ajiye wata nannauyar ajiyar zuciya, ta rasa ta yanda za ta ɓullowa wannan bahagon al'amarin, ko kuma kaddarar da ta afko musu lokaci guda. Ko kaɗan Umma ba ta damu da rashin ganin su Aliyu ba, domin gaba ɗayansu haushinsu take ji, ita yanzu duk wanda yake  tausayawa Abba to haushinsa take ji ba kaɗan ba.... 


Suna ƙarasawa asibitin da sauri aka karɓi Abba aka yi emergency da shi domin numfashinsa ne yake fita sama-sama. A reception aka tsayar da su Aliyu, samun kujera Salma ta yi ta zauna ta yi tagumi ta rasa inda za ta tsoma ranta domin tausayin Abbansu ya mamaye mata zuciyarta, ji take yi kamar ta dawo da ciwon jikinta...
   Ɗago da kanta ta yi ta kalli Aliyu ta ce, "Yaya Aliyu don Allah ka sanar da ni abinda yake faruwa a cikin gidan nan! Me yasa Umma ba ta biyo mu asibiti ba, kuma me yasa take yiwa Abba rashin mutunci a gabanmu ko nauyinmu ba ta ji?" Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke sannan ya dawo kusa da Salma ya zauna gumi duk ya wanke masa fuska, cikin nutsuwa ya kalli Salma ya ce, "Fadila ce duk ta haddasa wannan abun!" Da mamaki Salma ta kalle shi ta ce, "Yaya Fadila kuma ita ce ta haɗa Abba da Umma?" Gyaɗa kai Aliyu yayi ya ce, "Ƙwarai kuwa Fadila ce!" Gyara zama Salma ta yi ta kalli Aliyu ta ce, "Yaya don Allah ka faɗa min abinda Fadilar ta yi!" 

Kallonta Aliyu yayi kamar zai ce mata wani abun sai kuma yayi shiru tare da sunkuyar da kansa ƙasa, muryarsa can ƙasa ya ce, "Fadila ce ta yi cikin shege ta maƙalawa Abba ta ce shine yayi mata!" Kusan rikitowa daga kan kujerar Salma ta yi tana furta 'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un' ba ƙaramar jarumta ta yi ba wajen dai-daita nutsuwarta sannan ta dubi Aliyu ta ce, "Yaya ita Fadilan ce ta ce Abba ne yayi mata ciki?" Gyaɗa kai Aliyu yayi ya ce, "Ita ce mana, shi yasa Umma take yi masa duk abinda ta ga dama! take yi masa rashin mutunci son ranta ba tare da ta yi bincike ba ta tabbatar da maganar Fadilar!" 

Cikin zafin nama Salma ta miƙe tsaye ta nufi ƙofar fita daga reception ɗin, saurin dakatar da ita Aliyu yayi ya ce, "Ina kuma za ki tafi?" Juyowa ta yi ta kalle shi idanunta sun kaɗa sun yi ja ta ce, "Zuwa zan yi na samu Fadila Wallahi sai ta gaya min ɗan iskan da yayi mata ciki har ta zaɓi ta zubarwa da Abba mutunci a kansa!" Murmushi Aliyu yayi ya dube ta ya ce, "To yanzu idan kin je kina tunanin Fadila za ta ji tsoronki ta faɗa miki gaskiya? Ko kin je Umma ba za ta barki har ki yi mata wata tambaya ba, ni kaina tunda abin ya faru ba na samun ganin Fadilan! Dawo ki zauna mu bi komai a hankali..." 
Cikin sanyin jiki ta dawo ta zauna, jikinta har karkarwa yake yi saboda tsananin ɓacin rai, zancen zuci ta shiga yi "Me yasa Fadila ta yiwa Abba sharrin zina? Me Abba yayi wa Fadila? Wallahi ko za a bani Alƙur'ani sai na rantse da shi akan ba Abba ne yayi wa Fadila ciki ba kawai dai ta bi son zuciyarta ta yi masa sharri.." Tana zuwa nan a zancen zucinta wani kuka mai tsuma zuciya ya ƙwace mata! Da kyar Aliyu ya rarrashe ta shiru ta yi tana sauke ajiyar zuciya, gaba ɗaya tausayin Abba ya cika mata zuciya...

Likita ne ya fito daga cikin ɗakin da aka shigar da Abba, da sauri Aliyu da Salma suka tare shi. Aliyu yayi saurin cewa "Likita ya jikin nashi?" Kallon Aliyu Likita yayi ya girgiza kai sannan ya ce, "Biyo ni office!" Yana faɗin haka ya wuce da sauri ya nufi office ɗin nasa..
    Cikin sauri Aliyu ya bi bayansa, ai kuwa Salma ma ta bi bayansu da sauri. Juyowa Aliyu yayi ya ce, "Ki jira ni nan mu fito" bai tsaya jin abinda za ta ce ba ya wuce ya bar ta a tsaye..

Kira ne ya shigo wayarta da sauri ta ɗauko wayartata daga cikin jakar, Yaya KB shine sunan da yake yawo akan screen ɗin wayar. Sai da kiran ya kusa katsewa sannan ta yi picking tare da kara wayar a kunnenta.. 
Cikin sassanyar murya ta ce, "Hello! Yaya Kabir!" Daga can ɓangaren na ji an ce "My wife lafiya na zo gidanku ɗaukarki an ce min kin tafi" wani takaici ne ya zo ya tokare mata maƙoshi, nan take wani irin haushin Umma da Fadila ya ƙara kamata ta rinƙa jin kamar ta je can gidan ta shaƙe Fadila ta ci mutuncinta, da kyar ta daidaita nutsuwarta ta ce, "Wallahi ina asibiti ne!" Sai da ya razana sosai, cikin tashin hankali ya ce, "My wife asibiti fa kika ce?" 
"E! Muna asibiti" "To waye ba shi da lafiya?" hawaye ne ya zubo mata kafin ta ce, "Wallahi Abba ne bai ji daɗi ba, hawan jininsa ne ya tashi" "Okay! Yanzu kuna wanne asibiti ne?" Ta ba shi amsa "Muna asibitin Aminu Kano,amma da sauƙi jikin nasa" "Okay! Gani nan ƙarasowa dama ina kan titin." "Yawwa sai ka ƙaraso!" 
Suna gama wayar da mijin nata, ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, sannan ta kalli ƙofar office ɗin likiti ta zuba ido domin ta ga fitowar Yaya Aliyu..

Yayin da Aliyu ya samu Likita a office ɗinsa, bayan ya zauna ne Likita ya kalle shi cikin nutsuwa ya ce.....


*Comment and share*


_Ga mai buƙatar shiga group yayi min magana ta cikin wannan numban 07069475482._

Hussaiin
: *BOKO NE SILA*
          _(Fiction story)_



KING & QUEEN WRITING CHAMBER


HUSSAIN YUSUF


Page 6.

"Abokina menene sunanka?" Da sauri Aliyu ya ce, "Sunana Aliyu Inuwa!" Numfasawa Likita yayi ya ce, "Aliyu wanne irin ɓacin rai ne ya samu mahaifinku, wanda ya janyo jininsa ya hau sosai har ya kusa kai wa matakin da zai iya haifar masa da mutuwar rabin jiki? Ba don Allah ya sa kun kawo shi da wuri ba, komai zai iya faruwa.." Da sauri Aliyu ya ce, "Subhanallahi! Likita yanzu ya jikin nashi?" "Yanzu jikinshi Alhamdulillah! Allurar barci na yi masa, in sha Allahu da zarar ya farka komai zai dai-daita.."

Jikin Aliyu har rawa yake ya dubi Likita ya ce, "Likita yanzu zan iya ganin shi?" Kallon Aliyu Likita yayi ya ce, "Yes! Za ka iya ganin shi, amma ban da hayaniya domin barcin da yake shine samun sauƙi a gare shi.." "To Likita kamar minti nawa zai yi yana barcin?" Kallon agogon hannunsa likita yayi kafin ya kalli Aliyu ya ce, "Zai iya kai wa 35 to 40 minute yana barcin kafin ya farka!" Numfasawa Aliyu yayi kafin ya kalli likita ya ce, "Likita don Allah ka kai ni yanzu na gan shi, na matsu na gan shi ko raina zai yi sanyi.." Tashi tsaye Likita yayi ya ce, "Taho mu je!" 

Suna fitowa suka iske Salma tare da mijinta Kabir sun yi cirko-cirko, suna ganin su Aliyu sun fito suka nufe su da sauri suna tambayarsu...Kabir ne ya riƙe hannun Aliyu ya ce, "Yayanmu ina Abba ya jikin nasa?" Ɗan murmushi Aliyu yayi ya ce, "Jikin Abba da sauƙi yanzu ma wajen shi za mu je ku zo mu ƙarasa.." Gaba ɗayansu suka ɗunguma zuwa ɗakin da Abba yake kwance.
A kwance suka tarar da shi sai faman sharar bacci yake, kamar babu abinda yake damunsa, Aliyu ya kalli Abba sosai cikin zuciyarsa ya ce, "Haƙiƙa bacci rahama ne yana saukar da nutsuwa, na tabbata da ace Abba ba baccin nan yake yi ba, da yanzu yana zaune ɗauke da damuwa cikin ransa...." Muryar Salma ce ta katse shi daga tunanin da ya tafi ta ce, "Yaya Aliyu me likita ya gaya maka akan Abba?" Kallonta Aliyu yayi ya kawar da kai kamar ba zai ba ta amsa ba, ganin yanda Kabir ya zubo masa idone da alamu shi ma yana son ya ji amsar tambayar da matarsa Salma ta yi wa Aliyu, buɗe baki yayi tamkar wanda aka yiwa dole ya ce, "Jikinsa da sauƙi! Idan ya farka daga baccin nan muna sa ran zai warke in sha Allah ko Likita?" Ya faɗi yana zubowa Likita manyan idanunsa, gyaɗa kai Likita yayi ya ce, "Of course! Idan ya farka komai na jikinsa zai dai-daita dama rashin bacci ne da yawan saka damuwa a rai shi ya jawo masa wannan matsalar, amma in sha Allah komai ya zo da sauƙi.."

Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke kafin ya dubi Likita ya ce, "Likita mun gode" ya faɗi yana samun wajen zama, gyaɗa kai Likita yayi ya ce, "Yanzu zan je na duba wasu marasa lafiya idan ya farka ku yi gaggawar sanar da ni.." Gyaɗa kai Aliyu yayi ya ce, "To, Likita Allah yasa ya farka lafiya!" "In sha Allah lafiya zai farka" Likita ya faɗi tare da ficewa daga cikin ɗakin..

Bayan fitar likita Kabir ya dubi Aliyu ya ce, "Babban Yayanmu Allah ya tashi kafaɗun Abba!" "Amin" Aliyu ya amsa ba tare da ya ɗago ya kalli Kabir ɗin ba. Shiru ne ya ratsa ɗakin, can Aliyu ya numfasa ya ce, "Yakamata ku tashi ku tafi kada dare yayi muku" turo baki Salma ta yi ta ce, "A'a ni dai sai Abba ya farka zan tafi.." Kabir ma ya ce, "Babban Yaya! Ina ga yakamata mu tsaya mu jira farkawar Abba, saboda ko mun tafi fargabar halin da yake ciki ne zai dame mu.."
"Shikenan tunda haka ku kaga ya fiye muku!" Yana faɗin haka ya fice daga ɗakin ya bar su a ciki.

Reception ya je ya samu kujera ya zauna, wani irin haushin Umma da Fadila yana ƙara ruruwa a zuciyarsa. A ransa ya ƙudurce duk wuya duk rintsi, sai ya nemo wanda yayi wa Fadila ciki, sai ya nuna wa Umma kuskurenta na yarda da sharrin da Fadila ta yiwa Abba.. Yana cikin tunanin hawaye yana wanke masa fuska, tausayin halin da Abba yake ciki ya hana zuciyarsa sukuni.....


A can gida kuwa Umma ta yi ta zuba idanu ko za ta ga dawowar su Aliyu daga asibitin, amma har magriba ta yi ba ta ga dawowarsu ba. Zuwa falo ta yi ta zauna ta zuba tagumi, tunani da zullumin halin da Abba yake ciki ya hana zuciyarta sukuni. Lokaci guda tausayin Abba ya mamaye zuciyarta, jikinta yayi sanyi sosai, nan take wani ɓangare na zuciyarta ya shiga ba ta shawarar ta tashi ta bi su asibitin ta ga halin da Abba yake ciki ko za ta samu nutsuwa a zuciyarta. Yayin da wani ɓangaren yake ba ta shawarar ta yi zamanta kawai, ai kome ya faru da shi, shine ya janyowa kansa, domin da bai biyewa sharrin zuciyarsa ba da sharrin shaiɗan da tuni bai afka cikin wannan halin da yake ciki ba...
 

Cikin sanyin jiki ta tashi ta nufi ɗakin da Fadila take ciki. Tana shiga ta iske ta a zaune kan gado ta yi tagumi da hannu biyu, a hankali ta ƙaraso kusa da ita ta zauna, ba tare da ta kalli inda take ba ta kira sunanta da kakkausar murya...
"Fadila!" a hankali ta ɗago da fuskarta ta Kalli Umma sannan ta amsa cikin wata siririyar murya kamar wacce aka yiwa dole sai ta yi magana...
"Na'am Umma! Ta amsa tare da sunkuyar da kanta ƙasa...Cikin kakkausar murya Umma ta fara magana.
"Fadila ina son ki faɗa min gaskiya mahaifinki ne yayi miki wannan cikin? Domin zuciyata ta fara tantama akan haka...Domin da Malam ne yayi miki cikin nan ba zai fita hayyacinsa lokaci guda ba, tun daga ranar da kika ce shine yayi miki cikin ban ƙara ganin shi a cikin nutsuwa da walwala ba, kullum ya zauna ba shi da aikin da ya wuce tunani, saboda haka zuciyata ta fara gaya min cewa sharri ne kika yi wa mahaifinki ko?" Ta ƙarashe maganar tare da watsawa Fadila wani kallo mai ɗauke da tuhuma...

Fashewa da kuka Fadila ta yi cikin kuka ta ce, "Umma ba zan yi miki ƙarya ba, kuma ba zan yiwa Abba sharri ba, kin tilasta ni na faɗa miki amma me yasa kike tunanin ba gaskiya na faɗa miki ba? Umma kin sani tunda nake ban taɓa yi miki ƙarya ba!" Numfasawa Umma ta yi ta ce, "Fadila ba ƙaryata ki nayi ba, kuma ban ce ƙarya kika yi min ba, abinda yasa na yi miki tambayar nan shine; akwai matakin da nake son ɗauka, wanda shine zai kawo ƙarshen komai, shi ne dalilin da yasa na sake tambayarki, domin bana son mu ji kunƴa ne! Amma tunda kin tabbatar da shine yayi miki cikin shikenan komai ya kusan zuwa ƙarshe.."

Kallon Umma Fadila ta yi a ɗan razane ta ce, "Umma wanne irin mataki za ki ɗauka?"
Wani irin murmushi Umma ta yi ta ce, "Ke dai ki zuba ido za ki ga matakin da zan ɗauka nan kusa.." Tana gama  faɗin haka ta tashi za ta fita daga ɗakin, har ta je bakin ƙofa ta juyo ta kalli Fadila ta ce, "Kin yi Sallah kuwa?" Girgiza kai Fadila ta yi ta ce, "E! Tun ɗazu na yi!" "To ki fito ki ci abinci" Girgiza kai Fadila ta yi ta ce, "A'a Umma a kawo min nan, ba zan iya fita ba!" Wani kallon ba ki isa ba Umma ta watsa mata ta ce, "Fadila ba akanki aka fara cikin shege ba, tunda kika samu cikin nan kika ɗaura ƙawance da zaman ɗaki kamar wata mai yin takaba, to yau ba ki isa ba sai kin fito waje kin ci abinci tare da sauran ƴan'uwanki kamar yanda kuka saba. Idan kuma zaman ɗakin kika zaɓa shikenan sai ki yi ta zama da yunwa, babu wanda zai ƙara kawo miki abinci ɗakin nan!" Tana gama faɗin haka ta fice daga ɗakin da sauri.

A zaune Umma take tare da ƴaƴanta suna cin abincin dare akan dining table. Kowa sai faman cin abincinsa yake hankali kwance, in banda Azima da ta zubawa na ta abincin ido hawaye yana zuba akan fuskarta. Najwa ce ta ɗago da ta kalli Umma ta ce, "Umma zubowa Anty Fadila na kai mata tunda ba za ta fito ba!" Kallonta Umma ta yi ta ce, "A'a ki bar shi idan ba za ta fito ba, sai ta haƙura babu wanda zai kai mata abinc..." Ba ta ƙarasa faɗa ba ta hango Fadilan ta fito tana tafiya cikin sanyin jiki kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki.

A hankali ta zo ta ja kujera ta zauna, Umma ce ta miƙa mata abincinta jawo abincin gabanta ta yi tare da ɗaukar cokali ta saka a cikin abincin. Sai faman juya cokalin take a cikin abincin amma ta kasa kai wa bakinta, tsananin fargaba da tunani ya sa ta tsani abincin ko kaɗan ba ta marmarinsa ballanta har ta iya kai wa bakinta..

Kallonta Umma ta yi ta ce, "Ki ci abincin mana" sunkuyar da kai ta yi ta ce, "To, Umma!" Umma ta ce, "Fadila ki rinƙa cin abinci, rashin cin ba shine zai yaye miki damuwarki ba, kuma zama da yunwa ba shi da amfani musamman ga mai ɗauke da juna biyu yana da illa sosai.." 

Tashi Azima ta yi tare da ɗaukar mayafinta ta nufi hanyar fita daga falon, cike da mamaki Umma ta kalle ta ta ce, "Azima zo nan!" Kamar ba za ta juyo ba, domin wani irin haushin Umma take ji, cikin sanyin jiki ta juyo ta zo gaban Umma ta tsaya ta ce, "Ga ni Umma!" Wani irin kallo Umma ta watsa mata sannan ta ce, "Ina za ki je?" Kallon Umma Azima ta yi cikin ɗacin zuciya da takaici ta ce, "Zan je asibiti wajen Abba!"

Zaro idanu Umma ta yi ta ce, "Azima kin san me kike faɗa kuwa?" 
Hawaye ne ya zubo daga idanun Azima muryarta har rawa take ta ce, "Haba Umma! Wannan abun da kike kwata-kwata bai dace ba, tun yamma aka tafi da Abba asibiti amma ko a jikinki ba ki damu ba ballantana ki bi bayansu ki ji ya lafiyarsa, shine yanzu ni zan je na gano shi tunda ke ba za ki je ba..." Ba ta jira cewar Umma ba ta juya da sauri za ta fita daga falon.

Har ta je jikin ƙofar falon ta kama handle ɗin ƙyauren za ta buɗe, muryar Umma ta jiyo cikin tsananin fushi tana yi mata magana... 
"Azima idan kika buɗe ƙofar nan kika fita, Wallahi ba ni ba ke har abada ki je ki bi Uban naki tunda ya fi ni a wajenk..." Shiru ta yi sakamakon buɗe ƙofar da aka yi....

Abba ne ya shigo cikin falon, Aliyu yana biye da shi a baya yana ta jero masa sannu. A hankali yake tafiya cikin nutsuwa har ya zo inda wata kujera 2 seater take zama yayi tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya.
     Kallo ɗaya Umma ta yi masa ta ɗauke kanta tare da jan wani siririn tsaki can ƙasa yanda ba za a jiyo ta ba, da sauri Azima ta zo kusa da shi ta zauna a ƙasa dai-dai ƙafafunsa kanta a sunkuye ta ce, "Abba ya jikin naka?" Murmushi Abba yayi tare da dafa kanta ya ce, "Aziman Abba jiki yayi sauƙi Alhamdulillah yanzu!" "To, Abba Allah ya ƙara lafiya!" "Amin ya Allah Azimana!" Sake tambayarsa ta yi ta ce, "Abba me kake so na dafa maka?" Wani irin daɗi ne ya ziyarci zuciyar Abba, a ransa yake Allah wadai da hali irin na Umma, ashe ƴaƴanshi suna sonsa take ƙoƙarin raba shi da su? Allah yasa su Najwa ma su gane su daina gaba da shi a matsayinsa na mahaifinsu.

Kallonta Abba yayi ya sakar mata wani murmushi, ita ma murmushin ta sakar masa, nisawa Abba yayi ya ce, "Nagode da kulawarki Azima, amma yanzu bana jin yunwa saboda haka, ba zan wahalar da ke ba. Kawai ki haɗa min shayi mai zafi domin na ɗumama hanjin cikina..." Amsawa ta yi kanta a ƙasa "To Abba bari na je na haɗa maka" da sauri ta nufi kitchen da ido Abba ya rakata, duk cikin ƴaƴanshi yana ji da Azima da kuma Salma saboda suna nutsuwa da kamun kai sosai ba kamar ƴan'uwansu ba..
Juyawa yayi ya kalli inda su Umma suke, har yanzu suna zaune a dining sun yi shiru babu mai magana a cikinsu, sun zubowa Abba da Azima idanu, Umma sai faman jan tsaki take da ya zama kamar ɗabi'arta. Buɗa baki Abba yayi ya ce, "Najwa ba ku gan ni ba kun zubo min idanu babu wacce ta gaida ni daga cikinku sai Azima?" Ya ƙarasa maganar ransa a ɓace.. Buɗa baki Najwa ta yi za ta yi magana, da sauri Umma ta watsa mata wani irin kallo, aikuwa tuni ta gumtse bakinta, wani kallon Umma ta sake watsa musu da sauri suka tashi gaba ɗayansu suka nufi ɗakinsu, har da Fadila kanta a sunkuye ta kasa ɗagowa ta kalli inda Abba yake, sai maganarsa da take jiyowa a cikin kunnuwanta..

Kallon Umma Abba yayi ransa a ɓace ya ce, "Hauwa'u gaskiya na gaji da wannan salon da kika shigo min da shi cikin gida, ya ni da ƴaƴana kike ƙoƙarin raba ni da su?" Wani banzan kallo Umma ta watsowa Abba cike da gadara ta ce.......


*Ina baku haƙurin rashin jina kwana biyu, wllh na shiga busy da yawa ne ku yi haƙuri🙏🏻*


Comment and share pls

Duk mai son shiga group ɗin Boko ne Sila yayi magana anan 07069475482.
: *BOKO NE SILA*
           _(Fiction story)_



KING & QUEEN WRITING CHAMBER


HUSSAIN YUSUF


Page 7.

"Ba raba ka da ƴaƴanka nake son yi ba, ina hana su kusantar ka ne saboda ba na son abinda ya samu Fadila su ma ya same su!" Cikin fushi Aliyu ya ce, "Umma me kike nufi?" Harararsa Umma ta yi ta ce, "Ubanka nake nufi! Marar kunƴa kawai, to bari ka ji ni ba zan yi da kai ba domin ka yi min kaɗan, da Ubanka zan yi banza fitsararre kawai.." Buɗa baki Aliyu yayi zai yi magana, da sauri Abba ya dakatar da shi ya ce, "Ya isa haka Aliyu juya ka tafi ɗakinka!" Cike da ladabi Aliyu ya ce, "To Abba!" Sannan ya juya ya nufi ɗakin nasa zuciyarsa ɗauke da damuwa iri-iri.

Da harara Umma ta raka shi kafin ta ja wani dogon tsaki ta ce, "Ji be shi wai shi me Uba!" Gyaɗa kai Abba yayi zuciyarsa na yi masa zafi ya dubi Umma ya ce, "Hauwa'u yakamata zuwa yanzu ki manta komai, ki dawo mu cigaba da rayuwarmu kamar da, a gani na zai fi muhimmanci mu mayar da hankalinmu wajen binciken wanda yayi wa Fadila ciki, amma...." Da sauri ta katse shi tare da cewa "Amma me? Waye yayi mata cikin idan ba kai ba? Wato kana son ka liƙawa wanda babu ruwanshi a ciki ko? To Wallahi ba ka isa ba, ko ka ƙi ko ka so dole ka amshi cikin Fadila a matsayin naka.."

Shiru Abba yayi a ransa yana tunanin rashin tunani da rashin fahimta na Umma. Yakamata zuwa yanzu ta fahimci ba shine yayi wa Fadila ciki ba, amma ya bar wa Allah komai in sha Allah cikin ƙanƙanin lokaci gaskiya za ta bayyana kanta...Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Umma kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru. 
   Azima ce ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da tray Indomie ce da shayi mai zafi ta haɗowa Abba, saboda yanzu tausayi yake bata sosai, a ranta tana jinjinawa haƙurin Abba akan haƙuri da juriyar da yake da ita, ba kowa ne zai iya jure wulaƙancin da Umma take yi masa ba. Zuwa ta yi gaban Abba ta durƙusa tare da ajiye tray ɗin abincin, shayin ta ɗauko ta miƙa masa ta ce, "Abba ga shayin na haɗo maka!" Karɓa Abba yayi yana murmushi ya ce, "Nagode sosai Aziman Abba!" Murmushi ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa tana murmushi.

Harara Umma ta watsa mata kafin ta ce, "Ke Azima tashi ki tafi ɗaki wajen ƴan'uwanki!" Da sauri Azima ta kalli Umma, sannan ta sake sunkuyar da kanta ƙasa. Haushin Umma yana ƙara ruruwa a cikin zuciyarta. Ƙin tashi ta yi har sai da Umma ta sake maimaitawa, kallon Azima Abba yayi ya ce, "Aziman Abba tashi ki tafi ɗaki ki kwanta Allah yayi miki albarka!" A hankali ta furta "To, Abba sai da safe!" Tashi ta yi ta nufi ɗakin nasu, har ta je bakin ƙofa ta juyo ta ce, "Abba kafin ka kwanta ka daure ka sha magungunanka" murmushi Abba yayi ya ce, "Azima kenan! Ai tun a asibiti na sha maganina, sai gobe zan sake sha.." Azima ta ce, "To, Abba Allah ya tashe mu lafiya!" Ba ta jira amsawar Abba ba ta shige cikin ɗakin tare da rufo ƙofar. Cikin ƙululun baƙin ciki Umma ta ja wani dogon tsaki "Mtsssss! Aikin banza, Wallahi kar ka sake ka ƙara lalata min ɗiya ka ji na gaya maka" Tana faɗin haka ta tashi ta shige cikin ɗakinta da sauri. Da ido Abba ya bita kafin ya ce, "Hauwa'uAllah ya shirya Ki!" Yana faɗin haka ya ɗauki abincin da Azima ta kawo masa tare da ledar maganinsa, ya nufi ɗakinsa shi ma, amma zuciyarsa cike take da saƙe-saƙe da tunani iri-iri.

_Washe gari_

Misalin ƙarfe 7:30am na safe Abba ne ya fito daga bathroom, hannunsa riƙe da tawul yana tsane ruwan jikinsa, da alama wanka yayi. Nan take ya fara shirywa cikin sauri, yana cikin shirin Aliyu ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama. 
Juyowa Abba yayi ya kalli Aliyu sannan ya sakar masa wani murmushi, kafin ya amsa sallamar. Durƙusawa yayi har ƙasa ya gaishe da Abba kafin ya dube shi cike da mamaki ya ce, "Abba ba dai office za ka fita ba!" Murmushi Abba yayi ya ce, "Aliyu kenan, to idan na zauna a gidan me zan yi?" "Amma Abba na ga jiya aka sallame ka daga asibiti, ka bari idan ka gama warwarewa sosai sai ka koma office ɗin" 

Kallon Aliyu Abba yayi ya ce, "Aliyu kar ka damu na samu lafiya sosai..." Aliyu ya ce, "Amma Abba karka manta Likita ya ce ka rinƙa samun hutu sosai saboda hawan jininka.." Abba ya ce, "Aliyu ina da aiki sosai a office ɗin ya zama dole na fita shi yasa zan fita, amma ba zan daɗe ba zan dawo..." Aliyu ya ce, "To, Abba bari na je na shirya sai na zo na kai ka.." "Yawwa Aliyu sauri ka zo domin ba na son na yi latti!"

Juyawa Aliyu yayi zai fita daga ɗakin, sai ga Azima ta shigo hannunta ɗauke da food basket, tana sakin wani murmushi. Tana ƙarasa shigowa cikin ɗakin ta durƙusa har ƙasa ta gai da Abba, sannan ta juya ta gai da Aliyu. Cikin sakin fuska suka amsa mata gaisuwar...

Kallon Abba ta yi ta ce, "Abba breakfast na haɗo muku kai da Yaya Aliyu!" Murmushi Abba yayi ya ce, "Good my daughter amma na ji daɗi sosai me kika dafo mana?" Buɗe flask ɗin abincin ta yi ta ce, "Ka gani Abba Irish ne da ƙwai sai kuma jallof rice da farfesun kayan ciki!" Da sauri Aliyu ya dawo ya zo gaban Azima ya kalleta cike da murmushi a kan fuskarsa ya ce, "Na ji ƙamshin abincin nan ya cika mini hanci, my sister zubo min nawa na tafi da shi ɗakina.." Kallonshi Abba yayi ya ce, "Aliyu idan fa na gama breakfast ba zan jira ka ba, tafiyata zan yi"

Murmushi Aliyu yayi ya ce, "Sorry Abba! Wallahi ƙamshin abincin ne ya dame ni, idan ban ci ba akwai problem.." Hararar shi Abba yayi ya ce, "Ka ji da shi, ni dai ka je ka yi sauri ka shirya sannan ka zo ka karɓi abincin sai ka ci!"Juyawa Aliyu yayi ya tafi ɗakinsa, cikin sauri ya shirya sannan ya fito ya zo ɗakin Abba, zaunawa yayi Azima ta zubo masa nasa abincin, yana ci sai faman santi yake kamar ranar ya fara cin abinci..

Cikin ƙanƙanin lokaci ya kammala cin abincin, Abba kuwa kaɗan ya ci ya tashi sai faman zubawa Azima godiya yake. A zuciyarsa kuwa godewa Allah yake da ya ganar da ita gaskiya ba ta biyewa rashin fahimta na mahaifiyarta ba.

Gaba ɗayansu tare suka fito daga dakin, Abba sai faman sakin murmushi yake kamar babu abinda yake damunsa. Umma ce a zaune kan kujera 2seater ta harɗe tamkar wata basarakiya ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya....Da wani irin wulaƙantaccen kallo ta bi su Abba, karaf idanunta suka sauka akan Abba, da sauri ta kawar da kanta domin gani ta yi Abba yayi mata kwarjini a fuska...

Ko kallon inda take Abba bai yi ba, Aliyu ma ko kula da ita bai yi ba, ballantana ya gai da ita. Domin ko ya gaishe ta ba amsawa za ta yi ba, shi yasa shi ma yake share ta ya daina gaida ita.
   Umma tana kallon lokacin da Azima ta bi bayan Abba, hannunta riƙe da jakarsa wani baƙinciki ne ya zo ya toshe mata maƙoshi. Nan take a cikin ranta ta ce, "Tabbas sai na yi gaggawar ɗaukar mataki akan Azima, domin ba zan lamunci wannan shishshigin ba, mtssss!" Ta ƙarashe maganar tare da jan wani dogon tsaki...

Sai da su Abba suka shiga mota sannan Azima ta juyo ta nufo cikin falon, zuciyarta cike da farinciki marar misaltuwa. 
Tana ƙarasa shigowa cikin falon ta tarar da Umma a tsaye tana jiranta, cikin kakkausar murya da tsantsar ɓacin rai Umma ta dubi Azima ta ce, "Don Ubanki zo nan..." Zaro idanu Azima ta yi, ta ƙi zuwa inda Umma take, sai da ta sake maimaitawa "Ba kiranki nake ba ko ba za ki zo ba.....?"

Ayi haƙuri da wannan
 ba yawa ina busy ne sosai wllh🙏🏻



Comment and share


*mai son shiga group 07069475482.*
[7/24, 3:41 PM] HUSSAIN YUSUF: *BOKO NE SILA*
           _(Fiction story)_



Page 8.

Ko'ina na jikinta sai rawa yake, kamar wacce take jin sanyi. A hankali ta k'arasa wajen da Umma take zaune ta durk'usa bisa gwiwoyinta cikin sanyin murya ta ce, "Umma ga ni" wani kallo ta watsa mata, sannan ta fara yi mata faɗa cikin kakkausar murya..
  "Azima ni ban isa na hana ki abu ba, sai ki ce sai kin yi ko?" Da sauri Azima ta girgiza ta ce, "Ba haka ba ne Umma.." Wata tsawa Umma ta daka mata, wacce ta sa har sai da hantar cikinta ta kaɗa, cikin tsananin fushi ta nunata da yatsa ta ce, "Azima daga yau sai kar na ƙara ganinki, kin shiga ɗakin Abbanku, balle ki dafa abinci ki kai masa. Ko so kike abinda ya faru da Fadila ke ma ya faru da ke?" Da sauri Azima ta girgiza kanta ta ce, "A'a Umma! Amma ba Abba ba ne yayi wa Anty Fadila cik..." Da sauri Umma ta dakatar da ita, cike da masifa ta dube ta ta ce, "Azima yaushe kika raina ni haka? Wato yanzu wuyanki yayi kauri ina faɗa kina faɗa ko?" Hawaye ne ya zubo daga idanun Azima ta ce, "A'a Umma ba haka ba ne!" 
"To, idan ba haka ba ne, sai ki faɗa min yanda abin yake. Ke bari ma ki ji yanzun nan ina son ki zaɓi ɗaya tsakanin ni da Abbanku.." 

Fashewa da kuka Azima ta yi, ta daɗe tana kukan kafin ta rarrashi kanta. Ɗago da kanta ta yi ta dubi Umma cikin kuka ta ce, "Umma gaba ɗayanku mahaifana ne, ina sonku ina ƙaunarku..." Kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon kukan da ya ƙwace mata, da gudu ta tashi ta shige ɗakinsu tana rusa kuka kamar wacce aka yiwa dukan tsiya, da ido Umma ta bita kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Allah ya kyauta!"

Tana shiga d'akin ta ga Fadila a zaune gefen gado ta zuba tagumi, harararta ta yi sannan ta ja wani dogon tsaki ta ce, "Gaskiya Anty Fadila ba ki yiwa kanki adalci ba kuma mu ma ba ki yi mana ba" da sauri Fadila ta ɗago da kanta ta kalli Azima da ta yi mata tsaye a ka, tana jijjiga jiki alamun jira take Fadilar ta ce wani abu su kaure da faɗa.

Kawar da kanta gefe ta yi kamar ba ta ga Azima ba, sannan ta ce, "Me na yi na rashin adalci?" "Yanzu Fadila tambayata ma ki ke yi?" Harararta Fadila ta yi ta ce, "Ai dole na tambaya domin ni dai na san ban cuci kowa ba, akan me za ki rinka kirana marar adalci? Kuma gaskiya ba na son rashin kuny'a, domin Wallahi ubanki zan ci a cikin dakin nan!" Ta ƙarashe maganar tare da jan wani dogon tsaki...
    A hankali Azima ta zo kusa da Fadila ta zauna, sannan ta fuskance ta cike da nutsuwa cikin sanyin murya ta ce, "Anty Fadila! Don Allah ki yi haƙuri akan abinda na yi miki Wallahi zuciya ce ta ɗebe ni.." 

Ɗan murmushi Fadila ta yi sannan ta dafa kafaɗar Azima ta ce, "My angel karki damu, domin ni dama ban yi fushi da ke ba, but please karki ƙara yi min irin wannan abin kin ji!" Gyaɗa kai Azima ta yi ta ce, "In sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba.." Gyaɗa kai Fadila ta yi ta ce, "Shikenan my angel!" Sake kallon Fadila Azima ta yi kafin ta kira sunanta cikin wata siririyar murya.

"Anty Fadila!" Juyowa Fadila ta yi kalli Azima kafin ta ce, "My angel menene kuma?" Azima ta ce, "Don Allah tambaya zan yi miki, ki daure ki faɗa min gaskiya.." Shiru Fadila ta yi tana tunani, ta daɗe tana tunanin kafin ta ja numfashi ta dubi Azima ta ce, "My angel ki yi min ko wacce tambaya ce, ni kuma na yi miki alƙawari zan faɗa miki iyakar gaskiyata.." Gyara zama Azima ta yi ta kalli Fadila ta cike da nutsuwa ta ce....

"Anty Fadila! Don Allah ina son ki faɗa min gaskiyar al'amarin nan, shin da gaske Abba ne yayi miki ciki?" Kallonta Fadila ta yi wani zazzafan hawaye ya zubo mata akan fuskarta, nan take ta fashe da kuka mai tsuma zuciya....

Da kyar Azima ta rarrasheta ta yi shiru, cikin nutsuwa Azima ta dube ta ita ma idanunta duk sun kawo ruwa. Muryarta tana rawa ta ce, "Anty Fadila don Allah ki yi haƙuri idan tambayar da na yi miki ta taɓa miki zuciya! Wallahi da na san za ta sanya ki damuwa da ban yi miki ita ba, amma don Allah ki gafarce ni, na haƙura da tambayar kuma na yi miki alƙawarin ba zan sake yi miki makamanciyarta ba..." Tana faɗin haka ta sauko daga kan gadon ta nufi ƙofar toilet, da sauri Fadeela ta riƙe hannunta...

Tsayawa ta yi cak, ba tare da ta juyo ba ta ce, "Anty Fadeela ki cika min hannu mana, na ce miki na haƙura da jin amsar da na yi miki..!" Da sauri ta yi shiru sakamakon kukan da ya kusa ƙwace mata.. 
   Cikin kuka Fadila ta ce, "Haba my angel! Ki fahimce ni mana, kwata² ba tambayarki ce ta sanya ni kuka ba,  akwai abinda na tuna a cikin zuciyata, wanda babu wanda ya san mene sai Allan da ya halicce ni.. Don haka ki dawo na baki amsar tambayarki.." 

Cikin sanyin jiki Azima ta dawo ta zauna gefen gadon, sannan ta Kalli Fadila ta ce, "Ke nake sauraro" hannu Fadila ta saka ta share hawayen da ya kwanta akan fuskarta, cikin sanyin murya ta ce, 
    "My angel! Wannan cikin da yake jikina na ba na kowa ba ne, cikin Abba ne!" Da sauri Azima ta kalle ta sanann ta sunkuyar da kanta ƙasa ta yi shiru tana sauraron Fadila...

Ita kuwa Fadila cigaba ta yi da cewa "Babu wani ɗa namiji da ya taɓa riƙe min hannu da wata manufa idan ba muharramina ba.. Sannan babu wani ɗa namiji da ya taɓa keta min alfarmata idan ba Abba ba, shine namiji na farko kuma na ƙarshe da ya fara sani na a ɗiya mace shine.." Kuka sosai Azima take yi, a zuciyarta tana nadamar tambayar da ta yi wa ƴar'uwar tata, domin kunnuwanta ba za su jure jin irin wannan zantukan nan ba domin zuciyarta za ta iya bugawa lokaci guda....

Ji ta yi Fadila ta riƙe mata hannu, da sauri ta ɗago da kanta ta kalleta, ita ma sai faman kuka take kamar ranta zai fita... Cikin raunin murya ta ce, "My angel Wallahi ko Alƙur'ani aka bani zan dafa akan Abba ne yayi min cikin nan da yake jikin..." Ba ta ƙarashe maganar ba, kuka mai ƙarfi ya k'wace musu da sauri Azima ta shige cikin bathroom, ita kuma Fadila ta kwanta akan gado tana rusa kuka kamar wacce aka yi wa mutuwa...

Azima tana shiga cikin bathroom ɗin, ta dafe gefen zuciyarta da yake yi mata zafi, ji ta yi kamar ana rura mata wuta a can ƙasan zuciyarta... Kuka take yi kamar ranta zai fita, ta daɗe tana kukan kafin ta tashi ta yi wanka ta fito, cikin sauri ta shiga shiryawa domin ta kusa makara a makaranta, kuma yau suna da lecture mai muhimmancin gaske..
   Bayan ta gama shiryawa, ta juyo ta kalli Fadila ta ce, "Anty Fadila ni na tafi makaranta sai na dawo!" Ba ta jira amsawarta ba, ta sa kai ta fice daga ɗakin, domin ta matsu ta bar gidan ko zata samu sassauci a cikin zuciyarta, domin yanzu ji ta yi ta tsani gidan kamar kar ta dawo idan ta fita haka take ji...

Tana fitowa falo ta ga Umma a zaune ta yi tagumi. Ƙarasawa wajenta ta yi, ta ɗan rusuna ta ce, "Umma ni zan tafi makaranta!" Ko kallonta Umma ba ta yi ba, balle ta amsa. Ita kuwa Azima ba ta damu ba, juyawa kawai ta yi ta nufi ƙofar fita daga falon...
  Tana buɗewa ta ga wata matashiyar budurwa tana niyyar shigowa, kallon matashiyar budurwar ta yi suna haɗa ido ba ta san lokacin da ta sakarwa budurwar murmushi ba. Ita ma murmushin ta sakar mata, sannan ta buɗa baki ta ce, "Aziman Abba ina zuwa haka?" "Anty Mariya Wallahi school zan tafi" murmushi Mariya ta yi ta ce, "Ok! Fadeela tana ciki kuwa?" 

Sai da ƙirjin Azima ya buga da sauri, gabanta ya faɗi. Amma ko kaɗan ba ta bari Mariya ta gane halin da ta shiga ba, saurin dai-daita nutsuwarta ta yi ta ce, "E! Tana ciki" dubanta Mariya ta yi ta ce, "Lafiyarta ƙalau kuwa, kwana biyu ba ta leƙo school ba, shine na biyo na ji ko lafiya?" Ɗan murmushi Azima ta yi ta ce, "Ba ta jin daɗi ne amma ki shiga daga ciki na kusa makara.." Da sauri ta nufi parking space tana ƙwalawa direba kira da saurinsa ya zo, ya buɗe mata gidan baya shiga ta yi shima ya zagaya ya shiga a guje ya ja motar suka bar gidan..

Mariya kuwa ƙarasawa cikin falon ta yi, Umma ta iske a zaune tana breakfast. Umma tana ganinta ta saki murmushi tare da cewa "A'a wace nake gani haka?" Murmushi Mariya ta yi ta ce, "Umma Wallahi ni ce!" "To, sannunki da zuwa ga waje nan zauna." Ta faɗi tare da nuna mata wata kujera 2seater..
    Zama Mariya ta yi sannan ta shiga gaida Umma, kallonta Umma ta yi ta ce, "Mariya laifin me muka yi miki ki ka daina zuwa gidan nan? Idan ban manta ba rabon da na ganki a cikin gidan nan, tun wata biyu da suka wuce, lokacin da kika zo wajen Fadila da yamma.."

Sunkuyar da kai Mariya ta yi tana murmushi ta ce, "Umma kiyi haƙuri Wallahi karatu ne ya ɓoye ni, nima ina son zuwa Wallahi kullum sai Fadila ta yi min ƙorafi.." Umma ta ce, "To, ai shikenan ya su Hajiyar?" 
   "Suna nan ƙalau ta ce ma na gaida ke!"
Murmushi Umma ta yi ta ce, Ai kuwa ina amsawa Wallahi!" Kallon Umma Mariya ta yi kafin ta ce, "Umma ina Fadila na ga kwana biyu ba ta leƙa school ba, shine na zo na ji ko lafiyarta kalau........?"


*Comment & share*

Mai son shiga group 07069475482.
: *BOKO NE SILA*
           _(Fiction story)_



Sadaukarwa ga:
*T.Fresh Zahra*


Page 9.

Murmushin yaƙe ta yi, wanda kana ganinsa ka san bai kai cikin zuciyarta ba, sannan ta dubi Mariya ta ce, "Ayya! Ita Fadilan ba ta sanar da ke ba ta da lafiya ba?" Mariya ta ce, "Wallahi Umma ba ta sanar da ni ba!"Umma ta ce, "Aikuwa Fadila yau kwananta uku ba ta da lafiya!" 

Zaro ido Mariya ta yi ta ce, "Umma yanzu ya jikin nata?" Umma ta ce, "Yanzu da sauƙi Alhamdulillah! Tana cikin ɗaki, ki shiga daga ciki.." Da sauri Mariya ta tashi ta nufi ɗakin Fadila... Tana shiga ɗakin ta tarar da Fadila a kwance kan gadonsu, ta rufe idanunta wani zazzafan hawaye yana kwaranya daga cikin manyan idanunta...
    A hankali Mariya ta kira sunanta "Fadeela!" Kamar a mafarki ta ji muryar Mariya ta zo ta doki dodon kunnenta, sake jin kiran ta yi ya sake ziyartar kunnuwan nata...

A hankali ta buɗe idanunta, aikuwa ta yi tozali da Mariya tana sakar mata murmushi. Duk da halin damuwar da take ciki, haka bai hana mayarwa da Mariya murmushin ba, amma iyakarsa kan fuska ne bai kai har cikin zuciyarta ba..Domin damuwar da take ɗauke da ita a ƙasan zuciyarta ba zai bari wata walwala da farin ciki su samu gurbi a cikinta ba....
  Cikin sanyin murya ta kira sunan Mariya kamar ba ta son magana, "Mariya kece yau a gidanmu?" 
Zaunawa Mariya ta yi a gefen gadon har yanzu idanunta suna kan Fadeela, gani ta yi ta rame ta yi duhu.

Cike da tausayawa Mariya ta ce, "Fadila me yake damunki ne haka na ga duk kin fita hayyacinki?" Ɗan murmushi Fadeela ta yi ta ce, "Mariya ciwon ciki nake fama da shi amma yanzu da sauƙi Alhamdulillah!" "Kuma kun je asibiti an duba abinda yake saka ki ciwon cikin?" Mariya ta tambaya, girgiza kai Fadeela ta yi ta ce, "E mun je amma ba su faɗi abinda yake saka ni ciwon ba, sai magani suka ba ni suka ce na rinka sha kullum zan daina..Kuma Alhamdulillah yanzu da sauƙi.."

Kaɗa kai Mariya ta yi ta ce, "Shikenan Allah ya ƙaro sauƙi!" "Amin" Fadeela ta amsa tana murmushi. Miƙewa tsaye Mariya ta yi, sannan ta kalli Fadeela ta ce, "Ni zan tafi, dama na zo ne domin na duba lafiyarki, tunda na gama duba ki tafiya zan yi Ammi ta ce kada na daɗe.." Marairaice murya Fadeela ta yi ta ce, "Haba Mariri daga zuwanki kuma sai ki tafi?" "To, idan ban tafi yanzu ba, faɗa zan sha a wajen Ammi gara na yi sauri na koma da wuri.." "To, shikenan! Allah ya kiyaye hanya" Fadila ta faɗi tana niyyar saukowa daga kan gadon...

Da sauri Mariya ta dakatar da ita tare da cewa "Fadeela ina kuma za ki je?" Ɗan murmushi Fadeela ta yi ta ce, "Raka ki zan yi mana" "A'a Fadeela ki yi zamanki Wallahi, na hutar da ke. Ke da ba kya jin daɗi? Kiyi zamanki Wallahi.." Ƙarasa saukowa Fadeela ta yi cikin wasa ta ce, "Wallahi ko ba kya so sai na raka ki!" Murmushi Mariya ta yi ta ce, "To shikenan mu je, tunda kin matsa.."

A tare suka fito falo, tarar da Umma suka yi a zaune ita da Hajiya Amina suna hira. Umma tana ganin Mariya tare da Fadeela sun fito sai ta washe baki tare da cewa "Mariya har kin fito?" 
"E, Wallahi Umma na fito so nake na koma gida da wuri.." "To, shikenan mun gode Allah ya kiyaye hanƴa" "Amin" Mariya ta amsa tare da ficewa daga cikin falon ita da Fadeela sai hira suke yi cikin nishaɗi..

Bayan sun fita Hajiya Amina ta kalli Umma ta ce, "Hauwa! Waccan kuma wacece?" "Ƙawar Fadila ce, zuwa ta yi duba ta ta ga ba ta je makaranta kwana biyu ba." Jinjina kai Hajiya Amina ta yi kafin ta ce, "Tab Allah yasa ba ku faɗa mata abinda ya faru da Fadilar ba.." "ni dai haka na ce mata, Fadilar ba ta da lafiya. Amma ban san abinda ita Fadilar ta faɗa mata ba.." "To Allah yasa dai ba ta tonawa kanta asiri ba, kin san wannan zamanin wanda ka yarda da shi, shine zai fara watsa maka ƙasa a ido.." Umma ta jinjina kai ta ce, "Wallahi kuwa Hajiya, shi yasa nake so Fadila ta amince a yi aikin nan cikin sirri ba tare da kowa ya sani ba.." Hajiya Amina ta ce, "Ai don Ubanta dole ta amince, matuƙar tana son asirinku ya cigaba da rufuwa.."

Umma ta ce, "Wallahi Hajiya ina tunanin halin da zan shiga, yayin da mutane suka dan wannan abun kunƴar da Malam ya aikata da ƴar cikinshi.." "Ai ke dai bari abin ba a cewa komai! Wallahi lokacin da na ji wannan baƙon al'amarin kasa runtsawa na yi.." Umma ta ce, "To ya za'a yi abinda ya faru ya riga ya faru.."

Suna cikin hirarsu sai Fadila ta shigo cikin falon kanta a sunkuye, kallonta Umma ta yi ta ce, "Ke zo nan" juyowa ta yi ta zo gabansu ta tsugunna sannan ta ce, "Ga ni Umma" kallonta Hajiya Amina ta yi ta ce, "Fadila wai me yake damunki ne? Me yasa ba za ki amince a zubar da cikin nan da yake jikinki ba? Haba Fadila ya kike yin abu kamar ba wayayyiya ba..? Cikin sirri za a yi komai ba tare da kowa ya sani ba, ko so kike cikin ya girma ƙawayenki su samu abun cewa a kanki? Haba Fadila kiyi tunani mana, Wallahi daga ranar da cikin nan ya girma a jikinki daga ranar ke da farin ciki har abada, domin duk inda kika shiga a cikin garin nan, sai an yi zunɗenki. Ki daure ki amince ayi komai cikin sirri, kin ga sai ki koma makarantarki ma kamar babu abinda ya faru da ke.."

Duk waɗannan maganganun kan Fadila yana sunkuye, sai faman wasa take yi da yatsun hannunta... Shiru ta yi ba tare da ta cewa Hajiya Amina komai ba, ran Umma ne ya ɓaci, cikin fushi ta dakawa Fadila tsawa ta ce,
  "Ke muke sauraro.."

Ɗago da kanta ta yi, ta Kalli Umma sannan ta sake sunkuyar da kanta ƙasa ta ce, "Gaskiya Umma ba na son na sake aikata wani laifin akan wanda na aikata yanzu.. Kuma wannan abun da kuke cewa na aikata kun san haramun ne, amma kuna ƙoƙarin tilasta ni na amince...Kuma zan iya rasa raina garin cire cikin, me kike tunanin zai faru idan na je gaban Ubangijina da manyan laifuka har guda biyu Zina da kisan kai? Ni gaskiya Umma ban...."

"Ke Fadila ya isa haka!" Umma ta faɗi haka cikin tsananin fushi. Cigaba ta yi da cewa "Fadila ba wa'azi na kira ki kiyi mana ba, ko mu za ki gaya Allah? Da kin san Allahn kika je kika aikata wannan mummunan aikin.? To, Wallahi dole ki amince a zubar da cikin nan, don ba zan taɓa yarda ki kunƴata ni a idon duniya ba, ko kin ƙi ko kin so goben nan za mu je a zubar da shi, banza sakarya kawai. Ni tashi ki bani wuri.."

Da gudu Fadila ta tashi ta shige cikin ɗakinta, tana rusa kuka kamar wacce aka yi wa dukan tsiya.
Zaunawa ta yi akan gadonta tana tunani, yanzu idan ta amince a zubar da cikin nan, za ta iya rasa rayuwarta ta sanadiyyar haka, kuma ta je ta tarar da fushin Ubangiji yana jiranta. Don haka da ta amince a zubar da cikin nan, gara ta mutu kowa ya huta.
   Tana daɗe a zaune tana tunanin hanƴar da za ta bi ta kuɓutar da kanta da abun da yake cikinta daga sharrin su Umma, domin a yanayin da ta ga Umma za ta iya aikata ko mene..

Ta daɗe a zaune tana tunanin mafita, amma ba ta samu ba. Tashi ta yi ta hau zagaya cikin ɗakin nata, tana tunanin hanƴar da yakamata ta bi domin tseratar da rayuwar ɗan da yake cikinta....
    Ta tunani kafin wata dabara ta faɗo mata cikin ranta, jinjina kai ta yi a cikin ranta ta ce, "Tabbas haka zan yi, domin wannan hanƴar ce kaɗai mafita...." Daga nan ta hau gadonta ta kwanta, nan take barci mai nauyi ya ɗauke ta, domin da daddare tunani da fargaba ba su bar ta ta runtsa ba..."

Misalin ƙarfe 2:30am na dare, shiru kake ji a garin, ba ka jin sautin komai sai haushin karnuka. Ga wani irin duhu wanda ko tafin hannu ba a gani, a wannan lokacin idan ka dubi sararin samaniya ta yi baƙi ƙirin sakamakon wani irin hadari da haɗo, sai faman ƙugi yake alamun zai iya sako ruwa a kowanne lokaci...
    A wannan lokacin ne, na ga Fadila ta fito daga cikin ɗakinsu hannunta janye da trolley ɗin kayanta tana janta da ƙyar.. 
    Hawaye sai faman kwaranya yake akan fuskarta, tana fitowa daga ɗakin wani hawaye ya sake zubo mata, nan take kuka ya ƙwace mata da sauri ta saka hannunta ta rufe bakinta, gudun kar a jiyo ta. A hankali take jan trolley ɗin nata, har ta fito harabar gidan, duk irin hadarin nan da ya gangamo, lokacin har an fara yayyafi kaɗan, amma tsananin ɓacin rai bai saka Fadila ta ji tsoron dukan ruwan ba ballantana kuma tsananin duhun da ake yi. Duka waɗannan abubuwa biyun bai saka Fadila ta sare a zuciyarta ba, wato dare ta canja shawara ba wato tsananin duhu ga kuma hadari, kai tsaye ƙofar gate ta nufa, tana ƙarasawa wajen ta gan shi a rufe da makulli, tsayawa ta yi ta rasa inda za ta saka ranta, ta rasa abunda yakamata ta yi, domin ta matsu ta bar gidan a wannan lokacin kafin wani ya ganta ya daƙile mata burinta. Ta daɗe tana tunani, kafin ta zabura da sauri ta kunto wani spare key, a bakin zanenta. Wanda ta sato a ɗakin Umma, duk da tana kokwanton ba shine makullin gate ɗin ba, a haka ta nufi ƴar ƙaramar ƙofar gate ɗin ta gwada makullin, cikin sa'a kuwa tana murɗawa ta ga ya buɗe. Cike da murna da zumuɗi ta buɗe ƙyauren ƙaramar ƙofar gate ɗin, har ta saka kai za ta fita, sai ta juyo ta fuskanci gidan nasu fuskarta taf da hawaye ta shiga cewa.
"Umma ba da son raina zan tafi na barki ba, babu yanda zan yi ne. Ki yi haƙuri Umma ba zan iya jure zama a cikin gidan nan ba, zuciyata bugawa za ta yi, idan da rabon za mu sake saduwa za mu sadu nan gaba, Allah ya sada mu da alkhairi..." Tana faɗin haka ta buɗe ƙyauren tare da janyo trolley ɗin kayanta.........

_*Gaskiya comment yana yi min kaɗan, duk yawan mutanen group ɗin nan amma waɗanda suke comment basu da yawa, to gaskiya zan tankaɗe da rairaya a ciki, idan mutum ba ya son na cire sa to ya fito yayi comment tun kafin na cire shi....*_


Mai son shiga group
07069475482.
: *BOKO NE SILA*
           _(Fiction story)_


KING & QUEEN WRITING CHAMBER

HUSSAIN YUSUF


Dedicated by: 
Ummu Azan 


Page 10.

Cikin kukan ta shiga cewa, "Ki yi haƙuri Umma, nima ba da son raina zan tafi na barki ba. Ba zan iya amincewa buƙatarki ba, shi yasa zan yi nesa da ke har abada, idan da rabon za mu sake haɗuwa to Allah ya haɗa mu da alkhairi.." Tana faɗin haka ta juya za ta fita daga gidan, wata daureriyar fitila ta ga an hasko mata.

Da sauri ta dakata daga yunƙurin fita, ta ƙurawa hasken fitilar idanu gabanta yana dukan uku-uku. A hankali hasken fitilar yake kusanto inda take, har ya ƙaraso inda take. Umma ta gani cikin tsananin ɓacin rai, fuskarta har gatsine take saboda tsananin fushi..
    Tana zuwa ba ta jira cewar Fadila ba, ta ɗaga hannu ta sharara mata mari har sau biyu.

Saboda zafin marin durƙushewa Fadila ta yi ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Cikin fushi Umma ta k'wace trolley ɗin hannunta, sannan ta fincike ta da  ƙarfin gaske ta jata ta nufi cikin gidan da ita, sai faman rusa kuka Fadila take kamar ranta zai fita...

Suna shiga cikin ɗaki cikin fushi Umma ta dubi Fadila ta ce, "Fadila me kike shirin aikatawa ne haka? So kike ki shiga duniya ki lalata rayuwarki? Tunda abun nan ya faru ko bacci ba na iyawa, kullum tunanina shine; ta yaya zan k'wato miki ƴancinki, amma shine kike ƙokarin tozarta ni a idon duniya..?" Nunata ta yi da yatsa ta ce, "Wallahi Fadila duk ranar da kika saka ƙafa kika bar gidan nan da nufin guduwa, to Wallahi na sallamawa duniya ke, har abada karki ƙara tunanina a matsayinki na mahaifiyarki.." 

Zaunawa a bakin gadon Umma ta yi, zuciyarta tana suya. Ji take kamar ta je ta shaƙe Abba ta kashe shi har Lahira, domin shine wanda ya jawo duk wannan matsalar. Har ya saka ƴar cikinta tana ƙokarin shiga duniya, "Tabbas dole na ɗauki mataki gobe goben nan!" 

Juyowa ta yi ta kalli Fadila da take ta rusa kuka, kamar ranta zai fita. Cikin d'aga murya ta ce, "Fadila me yasa za ki gudu daga gidan nan? Ba kya tunanin halin da zan shiga yayin da muka wayi gari babu ke a cikin gidan nan? Fadeela ke ƴa mace ce, kuma an zalunce ki dole ne na ƙwato miki ƴancinki, ko da zan rasa duk abunda na mallaka, amma don Allah Fadeela kar ki sake yunƙurin guduwa daga cikin gidan nan na roƙe ki Fadeela..." Ta k'arashe maganar tare da sakin wani irin kuka mai ban tausayi..

Ita ma Fadila kukan ta sake rushewa da shi, cikin wani irin yanayi ta ce, "Umma a ragon tunanina, yin nesa da ke ne kaɗai abinda zai cire ni daga cikin ƙunci da baƙin cikin da nake ciki a yanzu.. Amma yanzun nan na fahimci yin haka ba mafita ba ne, sai dai ma ya ƙara jagula al'amarin, don Allah Umma ki yafe min bana son hawayenki yana zuba a kaina don Allah Umma kiyi shiru ki ce kin yafe mini.."
   "Fadila ni dama ba fushi na yi da ke ba...Na yi miki haka ne domin na nuna miki irin illar abinda kike ƙokarin aikatawa, Fadila yanzu idan kika shiga duniya rayuwarki lalacewa za ta yi, kuma har abada ba za ki sake samun farin cikin da kike ƙokarin guduwa saboda shi ba..Don haka yanzu ki kwantar da hankalinki in sha Allahu goben nan zan kawo ƙarshen komai, ki kwanta ki yi baccinki Fadila gobe ki zuba ido ki ga abinda zai faru..."

Kwantawa Fadila ta yi tare da lumshe manyan idanunta, nan take ta shiga tunanin me Umma za ta yi ta kawo ƙarshen wannan al'amarin? Ba ta da amsa kuma ba ta da mai amsa mata, a bisa dole ta haƙura ta zubawa sarautar Allah ido, daga nan ta sake lulawa wata duniyar tunanin, sai doshin asuba barci mai nauyi yayi awon gaba da ita ba ta sani ba...
   Umma kuwa kasa runtsawa ta yi, ji take yi a cikin ranta kamar ta janyo gobe, domin ta yi gaggawar aiwatar da abinda ta yi niyya. Ta ƙudurce a ranta ko me zai faru sai dai ya faru, amma sai ta bi kowacce irin hanƴa ce ta k'watowa ɗiyarta ƴancinta. "Ko me mutane za su faɗa, sai dai su faɗa, amma ba zan fasa aiwatar da abinda na ƙudurta a cikin raina ba.." Zancen Umma kenan da ta furta a fili, cikin tsananin fushi mai tattare da damuwa iri-iri...Ganin tunanin babu inda zai kai ta ne yasa ta tashi, ta shiga cikin bathroom. Alwala ta ɗauro ta tayar da sallah, ta daɗe tana addu'a tana kai wa Allah kukanta kafin ta shafa addu'ar. Tashi ta yi ta cire hijab ɗin sallar, sannan ita ma ta bi lafiyar gado, ta kwanta kusa da Fadila, ba ta daɗe da kwanciya ba ita ma bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita.


*_WASHE GARI_*

Da wani irin ciwon kai mai tsanani Abba ya tashi, dafe kan nasa yayi yana kiran sunayen Allah. A hankali ya ji ya ɗan sarara masa, da ƙyar ya iya yin sallah bayan ya idar da Sallar cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa ya rarrafa bakin gadonsa ya zauna ya dafe kan nasa da har yanzu yake sara masa kamar za faɗo, wayarsa ya janyo ya kira likitansa, bai haura 30 minute ba sai ga shi har ya ƙaraso.
    Yana zuwa ya shiga duba lafiyar Abba, allura yayi masa sannan ya bashi wasu magunguna ya sha. Nan take kuwa barci mai nauyi ya sake ɗauke shi sakamakon magungunan da ya sha akwai mai saka barci, sannan kuma likitan yayi masa alluran bacci..

Bai farka ba sai wajen ƙarfe 1:00pm na rana, da addu'a ɗauke a bakinsa ya farka, nan take ya ji ciwon kan ya tafi, ya ji ƙarfi sosai a jikinsa ba kamar yanda ya farka ɗazu ba. Da sauri ya shiga bathroom, wanka yayi ya fito, nan take ya sake jin ƙarfi ya sake shiga jikinsa kamar bai tashi da wata cuta ba.

Cikin sauri ya shiga shiryawa, cikin ƙanƙanin lokaci ya kammala shirin nasa. Key ɗin motarsa ya ɗauko, tare da jakar laptop ɗinsa. Yayin da ya fito falon babu kowa a ciki, kai tsaye harabar gidan ya fito. Da sauri ya nufi motarsa ya shiga ya bata key. Yana zuwa bakin gate ya fito ya buɗe da kansa, saboda babu mai gadinsu ya tafi gida ya duba mahaifiyarsa saboda ba ta da lafiya.
   Bayan ya fito daga cikin gidan, cikin hanzari ya fito daga motar tasa ya rufe gate ɗin, sannan ya nufi motarsa zai shiga..

Har ya shiga yana ƙoƙarin tafiya, ya hango wani mutum yana d'aga masa hannu alamun ya tsaya. Tsayawa Abba yayi har mutumin ya ƙaraso inda yake, kallon mutumin Abba yayi ya ce, "Bawan Allah lafiya kake tsayar da ni?" Ɗan murmushi mutumin yayi kafin ya miƙowa Abba hannu suka gaisa, sannan ya ce, "Ni ɗan aike ne, kuma wajenka aka aiko ni.." Da mamaki Abba ya kalle shi ya ce, "To ina sauraronka waye ya aiko ka wajena?" 

Zura hannu yayi a cikin aljihunsa ya ciro wata farar takarda ya miƙawa Abba, karɓar takardar Abba yayi tare da kallon mutumin ya ce, "Wannan takardar fa? Waye baka ka kawo min?" 
   "Ka buɗe ka gani mana!" Mutumin ya faɗawa Abba haka. Buɗe takardar Abba yayi da sauri ya furta "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Ai wannan saƙon Alƙali ne wai yana nemana.." Kallon Abba mutumin yayi ya ce, "E! Haka ne ka karanta dai-dai Alkali ne ya aiko ni na kawo maka, matarka Hauwa'u ta kai k'ararka akan tana zarginka da yiwa ƴar cikinka ciki! To ya ce lallai gobe ku je kotu gaba ɗayanku yana nemanku..." 

Nan take Abba wani irin yanayi, idanunsa suka kaɗa suka yi ja wur! Kamar gauta. Cikin karfin hali ya kalli mutumin ya ce, "Shikenan! In sha Allah zan zo" sallama mutumin yayi wa Abba sannan ya juya ya tafi abinsa..
Abba ya daɗe a tsaye jikin motarsa ya rasa me yake yi masa daɗi a duniya, "Me Hauwa'u take koƙarin aikatawa ne haka? Yanzu idan maganar nan ta je kotu a wanne irin matsayi mutane za su kalle ni?" Abba ya faɗi haka cikin wani irin yanayi.

Yana gama wannan tunanin ya juya da sauri ya koma cikin gidan, tun daga bakin gate yake kiran sunan Umma "Hauwa'u! Hauwa'u kina ina ne?" Tun Umma tana cikin ɗaki ta jiyo sautin muryarsa a cikin dodon kunnuwanta.. Don haka tun kafin ya ƙaraso cikin falon ta yi sauri ta fito daga cikin ɗakin, domin ta riga ta san akan abinda yake k'wala mata wannan kiran irin na mafarauta kuma ta shirya tsaf kome zai faru sai dai ya faru....
    Da ƙarfin gaske ya banko ƙofar falon kamar zai karyata, yana shigowa ya ga Umma a tsaye tana jiran ƙarasowarsa, kallonta yayi a masife ya ce, "Hauwa'u kin san illar abinda kika aikata kuwa? Ba kya tunanin abinda zai biyo baya yayin da aka je kotu?" 
    Wani irin kallo Umma ta watsa masa ta ce, "Ƴata nake nemawa ƴanci, duk abinda zai faru ya daɗe bai faru ba ehe!" Sassauta murya Abba yayi ya ce, "Hauwa'u don Allah ki je ki janye ƙarar da kika shigar, Wallahi idan muka je kotu ban san wacce irin fassara mutane za su yi min ba, alhalin ba nine na aikata laifin ba, kawai rashin fahimtarki ne ya janyo wannan abun, ba kya bin abu a sannu...."
    "Daɗin bakinka ba zai yi tasiri a zuciyata ba, ƙara ce na shigar kuma babu wanda ya isa ya saka ni na jany'e ehe..! Tana faɗin haka ta juya da sauri ta shige cikin d'akinta ta bar Abba a tsaye kamar gunki, da ido ya bita har ta shige cikin ɗakin...
  Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya nemi waje ya zauna. Nan take ya shiga tunanin rayuwarsu ta baya....

_*TUNA BAYA...*_

*Comment and share pls*

Mai son shiga group
07069475482.
: *BOKO NE SILA*
            _Fiction story_



KING & QUEEN WRITING CHAMBER


HUSSAIN YUSUF


Page 11.

_*TUNA BAYA*_

Umma ce a zaune cikin wani ƙayataccen falo, wanda ya sha kayan more rayuwa dai-dai rufin asiri. Kallo take a T.V tashar SUNNA T.V take kallo, wani Malami yana ta wa'azi akan yanda matan aure za su rinƙa jan hankulan mazajensu, su mallake su ba tare da bin Boka ko Malam ba. Murmushi Umma ta yi, saboda ita kaɗai ta san salon da ta yi amfani da shi ta mallake Abba, duk abinda ta ce yayi babu musu zai yi koda ransa ba ya so. Shi yasa a koda yaushe take alfahari da kanta, kuma ta ƙudurce a cikin ranta ƴaƴanta ma za ta koya musu wannan salon..
  Abba ne ya shigo falon bakinsa ɗauke da sallama, murmushi Umma ta yi, cikin wani irin salo ta ce, "Sannu da zuwa har ka dawo?" Ajiye jakar hannunsa yayi akan wani ɗan ƙaramin center table, sannan ya shiga ƙoƙarin cire babbar rigar da take jikinsa. Da sauri Umma ta taimaka masa ya cire babbar rigar, sannan ta ɗauki jakar tare da babbar rigar da kuma hularsa ta nufi cikin ɗaki da ita. Bayan ta kai ta dawo, zama ta yi ta kalli Abba ta ce, "Sannu! Ya aikin?" Numfashi Abba ya ja ya ce, "Aiki Alhamdulillah! Ya gida?" Ɗan murmushi Umma ta yi ta ce, "Gida yana nan k'alau kamar yanda ka bar shi.." Murmushi Abba yayi ya ce, "Ai ni na san indai kina gidan nan, to bani da matsala za ki kula min da Yarana da kuma kanki.." Sunkuyar da kai Umma ta yi tana murmushi kafin ta ce, "Bari na kawo maka abincinka na ga kamar kana jin yunwa ko?" Ba ta jira amsawarsa ba, ta tashi ta nufi kitchen...

Da kallo Abba ya rakata yana murmushi, a ransa yana ƙara godewa Allah da ya bashi mace ta gari mai kula da damuwarsa. Yana nan zaune yana jiran Umma ta fito daga kitchen, sai ga Salma da Fadila sun shigo falon bakinsu ɗauke da sallama. Kallo ɗaya za ka yi musu ka hango tsantsar farincikin da suke ciki, domin sai sakin murmushi suke yi bakinsu ya ƙi rufuwa...Suna ganin Abba a zaune cikin falon, cikin nutsuwa suka je gabansa suka zazzauna, suna sakin murmushi..Salma ce ta kalle shi ta ce, "Abba sannu da dawowa!" Fadila ma ta ce, "Abba sannu dai!" Murmushi yayi ya ce, "Yawwa my daughters sannunku da dawowa! Ya school ɗin?" A tare suka amsa "Alhamdulillah! Abba" Kallonsu ya sake yi ya ce, "Na ga kamar da magana a bakinku ko?" Kallonshi Fadila ta yi ta ce, "E! Abba akwai..." Sai kuma ta yi shiru tana wasa da yatsun hannunta..

Salma ce ta miƙo wasu takardu da ta ɗauko a cikin jakarta. Duba takardun Abba ya shiga yi, yana gama dubawa ya kalle su yayi murmushi ya ce, "Congratulation my daughters! Kowacce daga cikinku ta samu 9 credits gaskiya na jinjina muku...." Umma da ta fito daga kitchen hannunta riƙe da food basket tana sakin wani murmushi ta ce, "Da gaske ƴaƴan nawa sun cinƴe jarrabawar kammala secondary..?"

Murmushi Abba yayi ya ce, "Wallahi Hauwa kin gani duk sun cinƴe ta gaba ɗaya..." Karasowa Umma ta yi ta ajiye abincin gaban Abba, tana ƙoƙarin zuba masa da sauri Salma ta karɓe ta ta ce, "Umma kawo na zuba masa!" Murmushi Umma ta yi ta ce, "Salma kenan! Ba kya gajiya da aiki.."
"To, Umma idan ban yi miki ba wa zan yi wa?" 

Miƙewa Umma ta yi ta je kusa da Abba ta zauna, ta kalle shi sannan ta ce, "Ba ni nima na gani na saka wa ƴaƴan nawa albarka..." Karɓa Umma ta yi, ta hau dubawa tana murmushi da ta gama dubawa gaba ɗaya sai ta yi murmushi, ta kalle su ta ce, "Masha Allah! Ashe ƴaƴan nawa na daban ne..."

Abba ya kalli Umma ya ce, "Hauwa'u yanzun nan ina son, za mu yi magana" "To, Malam amma sai ka gama!" Umma ta ba shi amsa..
Bayan Salma ta gama zuba masa abincin, nan take ya fara ci...Yana cikin cin abinci sai ga Yasmin da Najwa sun dawo daga school a matuƙar gajiye, suna zuwa suka zube gaban Abba a tare suka faɗi "Wash! Mun gaji.."Dakatawa da cin abincin Abba yayi ya kalle su rai a ɓace ya ce, "Ku ba ku iya Sallama ba sai dai kawai ku shigo kamar waɗanda aka jefo daga sama?" Zazzare idanu suka hau yi, saboda suna tsananin tsoron fushin Abba.

"Ba da ku na ke magana ba?" Abba ya faɗi cikin tsawa tare da aika musu wata harara, da sauri Najwa ta tashi ta fita daga falon, Yasmin ma da sauri ta bi bayanta..A tare suka shigo cikin falon bakinsu ɗauke da sallama, "Assalamu alaikum!" "Amin wa'alaikumussalam!" Abba ya amsa tare da ba su umarnin zama.

Cikin sanyin jiki suka zauna tare da sunkuyar da kansu ƙasa, harararsu Abba yayi sannan ya kira sunan kowacce daga cikinsu ya ce, "Najwa!" "Na'am Abba!" "Yasmin!" Ita ma ta amsa "Na'am Abba!" 

Abba ya ce, "Kuna ji na  ko?" A tare suka gyaɗa kai, Yasmin ta ce, "E! Abba muna jin ka" Abba ya cigaba da cewa, "Wai menene yake damunku? Ina yawan zaunar da ku ina faɗa muku abinda yakamace ku a rayuwa amma kullum abun naku ƙara gaba yake, kullum girma kuke amma kullum kamar ƙara muku fitina ake, to daga yau duk wacce na sake gani tana irin wannan rashin nutsuwar, Wallahi sai ta gane shayi ruwa ne, kuna jina ko?" A tare suka gyaɗa kai "E! Abba mun ji in Allah ya yarda ba za mu ƙara ba.." Najwa ce ta faɗi haka muryarta tana rawa, domin tsoro take kada Abba ya kai musu duka...

Umma ce ta kalle su, ta yi murmushi sannan ta ce, "Ai sai ku tashi ku tafi ku canja umiform ɗin ko?" Cikin sanyin jiki suka bar wajen, Fadila da Salma sai kallonsu suke suna murmushi. Domin Najwa da Yasmin akwai rashin jin magana, ga rashin nutsuwa a tattare da su, idan ka gan su a nutse waje guda, to Abba yana gidan. Idan kuwa ya saka ƙafa ya bar gidan to daga sannan za su yi ta baragadarsu Umma kuwa sai dai ta zuba musu ido, domin ko ta yi musu magana ba dainawa za su yi ba...

Bayan sun tafi, sai Abba ya juyo wajen Fadila da Salma, ya ce, "Fadila ku tashi ku tafi ɗaki Allah yayi muku albarka" "Amin amin Abbanmu.." Sannan suka tashi suka nufi ɗaki zuciyarsu fal da farin ciki. Fadila ta fi Salma farinciki, domin tana da burika da yawa waɗanda sai ta shiga jami'a sannan za ta samu damar cika su, to ga shi damar ta kusa zuwa shi yasa take ta murna a cikin ranta kamar wacce aka yiwa wata gagarumar kyauta.

Bayan Abba ya gama cin abincin, sai ya juyo ya kalli Umma ya ce, "Alhamdulillah! Hauwa'u na gama, yanzu za mu iya yin maganar.." Umma ta ce, "To, Malam ina jin ka" ta faɗi haka tare da mayar da hankalinta wajen Abba.

"Alhamdulillah! Hauwa'u tunda Allah ya sa yaran nan sun kammala karatun nan lafiya, sai mu mayar da hankalinmu wajen yanda za mu aurar da su a wajen mazaje na gari, albashi idan mazajen nasu sun yarda sai su ƙarasa karatunsu a can ko ya kika gani..?" 
   Tunda Abba ya fara magana, Umma ta canja fuska daga murmushi ta koma ɓacin rai, cike da masifa ta dubi Abba ta ce, 
"Yanzu Malam nawa yaran nan suke, da kake yin maganar aure a kansu?" 
  Kallonta Abba yayi ya ce, "Haba Hauwa'u yanzu ki dubi Salma da Fadila amma ki ce min nawa suke? Ko wacce fa a cikinsu shekararta ashirin cif, amma ki rinƙa faɗin nawa suke? Gaskiya kar na ƙara jin maganar nan a bakinki.." Abba ya faɗi haka cikin tsananin ɓacin rai.
Cike da rashin tsoro Umma ta ce, " To, yanzu Malam idan ma auren za ka yi musu, kana da wanda za ka aura musu..?"


*Ku yi haƙuri da wannan aikin ba ya barina na yi typing da yawa..*

Comment and share


Mai son shiga group
07069475482
: *BOKO NE SILA*
           _(Fiction story)_



KING & QUEEN WRITING CHAMBER


HUSSAIN YUSUF

Page 12

"Idan ba ni da wanda zan aura musu, ai su ba zasu rasa wanda suke so ba.." 
   Abba ya bai wa Umma amsa, cikin matuƙar jin haushin maganarta.
    "Malam inda za ka ɗauki shawarata, ka bar yaran nan su kammala karatunsu, sai ka aurar da su hankali kwance.."

Cikin faɗa Abba ya ce, "Hauwa'u idan har kina son zaman lafiya, a tsakanina da ke to, ki bar yaran nan su yi aurensu. Domin shine babban gatan da za mu yi musu a matsayimu na iyayensu, amma ba karatu ba...."
   Tun kafin ya ƙarasa, Umma ta yi saurin katse shi, ta ce,
"Malam bari ka ji! Burin kowacce Uwa ce, ta ga ƴaƴanta sun auri hamshaƙin mai kuɗi ko ɗan siyasa, ko dai wani mai matsayi babba, idan mace ba ta yi karatu ba ta ya irin manyan mutanen nan za su neme su da aure? Don haka ni dai a bar min ƴata, sai ta kammala karatunta sannan ta yi aure.."

Cike da takaicin maganar Umma, Abba ya dube ta ya ce, 
"Hauwa na lura, kin ɗauki burin Duniya kin ɗora akan ƴaƴanki, don kin ga Allah ya basu sura mai kyau, to Wallahi ki bi Duniya a sannu, domin wanda ma bai zo na jiransa take..."
  "Tunda Allah ya bani ƴaƴa kyawawa, Wallahi ba zan taɓa barii su auri talaka ƙasƙantacce ba, a cikin ƴaƴana daga matar Gwamna sai matar Minister, gara ma ka ji tun wuri.."

Jinjina kai Abba yayi, cike da tsantsar mamakin Umma ya dube ta ya ce, "Na ji duk abinda kika faɗa, amma kin san Salma ba ke ce kika haife ta ba, kuma mahaifiyarta ta bar min wasiyyar na aurar da ita ga miji na gari, saboda haka zan aurar da Salma, idan ita Fadila ta gama karatun nata sai ta nemo mijin ta yi auren.."
    Yatsina fuska Umma ta yi, ta ce, "Amma Malam menene na yi min gori? Indai ƴaƴa mata ne ai nima na haifa ga su nan Tabarakallahu masha Allah!" 

"Gorin me na yi miki kuma?" Abba ya faɗa yana kallon Umma, 
   "Ai na ji ka ce ba ni ce na haifi Salma ba, amma wace ta riƙe ta har ta kawo wannan lokacin?"
    "To, na ji mu bar maganar!"
   Abba ya faɗi haka tare da tashi, ya fita daga cikin falon.

Yana fitowa waje ya ga Aliyu ya shigo cikin gidan fuskarsa ɗauke da murmushi, kallon shi Abba yayi shi ma ya sakar masa murmushin ya ce,  

    "Aliyu na ga kamar kana cikin farin ciki ko?" Maimakon ya bai wa Abba amsa, sai ya miƙa masa wata takarda.
   Karɓar takardar Abba yayi ya duba, sannan ya kalli Aliyu ya ce, 

"Ban gane abinda yake ciki ba!" Murmushi Aliyu ya sake yi kafin ya ce,
"Abba yanzu Alhamdulillah! Na samu aiki a babbar ma'aikatar Shari'ah ta Kano yanzu ni Lauya ne.." Wuf! Abba yayi ya rungume Aliyu yana cewa, 
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah nagode maka da ka cikawa Ɗana Aliyu burinsa Allah kai ne abin godiya.."
Sakinsa Abba yayi ya kalle shi ya ce, 
  "Aliyu yaushe ka samu wannan dama haka, har aka ɗauke ka aiki cikin gaggawa?" 
   Ɗan murmusawa Aliyu yayi ya ce,
   "Akwai wani abokina, ƙanen mahaifinsa babban Alƙali ne, shine yayi min hanya cikin ikon Allah na ga sunana ya fito a sababbin Lauyoyin da aka ɗiba a wannan shekarar.."

"Kai amma na ji daɗi sosai, zan je har gidan mahaifin abokin naka na yi masa godiya.." MMurmushi Aliyu yayi ya ce, "A'a Abba, ba sai ka je ba.." Wani kallo Abba ya watsa masa ya ce, "Me yasa za ka ce ba sai na je ba? Irin wannan abun alkhairin da suka samar mana amma ka ce ba zan je domin na yi musu godiya ba?" 
   "Ai ni na je na yi musu godiyar, kuma ba ka ga yanda ransu ya ɓaci ba, domin su ko kaɗan ba sa son irin wannan don sun yi maka abun alkhairi ka je godiya, sai dai kawai su ce ka godewa Allah domin shi ya basu ikon yi maka..."

Gyaɗa kai Abba yayi ya ce, "Shikenan Allah ya biya su abinda suka yi mana.." "Amin" Aliyu ya amsa sannan ya kalli Abba ya ce, "To, Abba bari na shiga daga ciki, na faɗawa Umma wannan albishir ɗin.." 
   "To Aliyu ni dama fita zan yi, idan na dawo ka zo ka same ni domin akwai maganar da za mu yi.." 
    "To, Abba sai ka dawo!" 

Daga haka ya wuce ya shiga cikin falon, shi kuma Abba ya shiga motarsa ya bar gidan...
   "Assalamu alaikum!" Ɗago da kanta ta yi ta kalle shi, sannan ta kawar da kai can ciki ta amsa masa sallamar...
  Zaunawa Aliyu yayi kusa da ita, ya ce, "Ummarmu sannu da hutawa!" 
"Yawwa Aliyu sannunka dai, har ka dawo daga neman aikin?" 
   Shafa kai yayi ya ce, "E! Wallahi Umma na dawo" 
"To, da fatan dai an dace?" Bai san lokacin da murmushi ya kuɓuce masa ba, cike da zumuɗi ya ce,
"Wallahi Umma cikin ikon Allah, yau dai na  zama Lauya" da sauri Umma ta kalle shi, cike da mamaki da tsantsar al'ajabi ta ce, "Kai Aliyu da gaske ka samu aikin?" 
"Wallahi Umma kin gani, har an yi confirming ɗina, ana gama yi min interview zan fara aiki in sha Allahu.."

"To, Allah ya taimaka!" Iya abinda Umma ta faɗa kenan, sannan ta tashi ta shige cikin ɗakinta, zuciyarta cike da takaici da baƙincikin aikin da Aliyu ya samu...
  Shikuwa Aliyu da ido ya bita, yana mamakin duk lokacin da wani abun alkhairi ya same shi, idan ya zo ya nunawa Umma, to nan take walwalar fuskarta take ɗaukewa. Tun bai ankara da haka ba, har ya zo ya gane, amma ya rasa me hakan yake nufi hassada ce ko bakin ciki? Ba shi da wannan amsar, sannan ba shi da mai bashi...

Cikin sanyin jiki ya tashi ya shiga cikin ɗakinsa, wani ɓangare na zuciyarsa cike da murnar cikar burinsa na rayuwa, wato zama Lauya, yayin da wani ɓangaren na zuciyar tasa yake ɗauke da damuwa bisa baƙin cikin da Umma take nuna masa, duk da ba Umma ce ta haife shi ba. Yana jin takaici idan ya zo mata da albishir ɗin abin alkhairin da ya same shi, sai ta rinƙa nuna baƙin ciki da ƙyashi, ba zai manta lokacin da ya sanar da ita scholarship ɗin da ya samu ba, a fili ta nuna masa bata farinciki da wannan damar da ya samu, tun daga lokacin ya gane ba ta ƙaunarsa ba ta son cigabansa ko kaɗan...

***
Tana shiga ɗakin ta zauna a gefen gado, zuciyarta tana cigaba da tafarfasa. Ji take tamkar garwashi ake rura mata a cikin zuciyarta, tsabar zafin da take yi mata. 
    Allah ya gani ko kaɗan ba ta k'aunar Aliyu, ba ta k'aunar mai k'aunarsa. Kullum ba ta da burin da ya wuce, ganin kasawar Aliyu, amma abin mamaki kullum daɗa cigaba yake samu daga ko ina. Ba ta taɓa tunanin Aliyu zai samu aikin Lauya cikin sauƙi haka ba, amma ga shi ya samu cikin sauƙi ba tare da shan wata wahala ba...

"Yanzu me yakamata na yi?" 
Ta tambayi kanta, a cikin zuciyarta. "Bari na kirawo Hajiya Amina!" 
  Da sauri ta d'auko wayarta da take ajiye  akan bedside drawer, nan take ta lalubo numban k'awartata...
  Bugu ɗaya biyu ta ɗauka..
"Hello ƙawata!" 
   "Hajiya kina ina yanzu?" 
  "Ina gida wani abun ne ya faru?" "A'a wata ƴar matsala ce nake son ki samo min mafita.."
   "Okay! Yanzu ina wani aiki ne, ki bari da Yamma zan zo gidan naki, sai mu tattauna..". 
   "To, shikenan sai kin zo"..
Daga nan ta katse kiran, tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya..

Bayan Abba ya dawo, ya ci abinci ya huta. Sai ya shiga ɗakinsa ya kirawo Aliyu, bayan ya zo Abba ya aika shi ya kirawo masa Fadila da Salma...
    Bayan sun zo gaba ɗayansu, har da Umma sun zazzauna, sai Abba ya dube su cikin nutsuwa yayi gyaran murya sannan ya ce.....


*Comment & Share*

Mai son shiga group
   07069475482.
: *BOKO NE SILA*
           _(Fiction story)_



KING & QUEEN WRITING CHAMBER



HUSSAIN YUSUF


Page 13.

"Alhamdulillah! Yanzu tunda Fadila da Salma sun kammala karatunsu, aure shi ya fi dacewa da s..." 
    Da sauri Umma ta dakatar da shi, cike da masifa ta ce,
  "Amma Malam ai tun ɗazu mun gama magana ni da kai, cewa Fadila ba yanzu za'a yi mata aure ba, sai ta kammala karatunta.."
     "Hauwa'u ke ce da ikon aurar da Fadila ko ni?" 
    "Amma dai nima ai ina da iko a kanta, saboda ni na raini ƴata. Don haka ba wanda ya isa ya nuna min ya fini iko a kanta ita Salmar da kake da iko a kanta sai ka aurar da ita, ba zan hana ka ba, amma Fadila sai ta kammala karatunta sannan za'a yi mata aure kuma in Allah ya yarda Fadila ba za ta auri talaka ba.."


Tana gama faɗin haka, ta ja hannun Fadila da sauri suka fice daga ɗakin. 
   Cikin tsananin ɓacin rai, Abba ya tashi zai bi bayanta, da sauri Aliyu ya riƙe hannunsa ya ce,
   "Haba Abba! Wannan ba girmanka bane, ka rabu da ita idan ka biye mata sai ku zama ɗaya.."
  Dawowa Abba yayi ya zauna, zuciyarsa tana yi masa zafi da raɗaɗi..
   "Abba ka yi haƙuri!"
 Salma ta faɗi haka cikin sanyin murya, kamar za ta fashe da kuka.
   Kallonta Abba yayi, nan take murmushi ya kuɓuce masa, cike da tsananin so da k'aunar ɗiyar tasa ya ce,
   "Salman Abba da fatan dai ke kin amince a yi miki auran?"
  "E! Abba na amince!"
Ɗaga hannu sama Abba yayi, ya ce,
    "Alhamdulillah! Allah nagode maka, da ka bani ikon cikawa mahaifiyarku aRabi'atu burinta, Allah kaine abin godiya.."
"Abba bangane abinda kake nufi ba!" Salma ta faɗi haka cike da zumuɗin jin abinda Abba zai faɗa mata..
    Kallonta Abba yayi sannan ya juya ya kalli Aliyu, ya ce, "Aliyu a gaban idanunka, yayin da mahaifiyarku za ta bar Duniya, ta bar min wasiyyar cewa idan ƴar k'aramar ƴarta Salma ta isa aure na aurar da ita ga miji nagari, shi yasa nake yiwa Allah godiya domin lokacin cika wannan Wasiyya da ta bar min yayi, Alhamdulillah Allah ya ji ƙanki Rabi'atu Allah ya gafarta miki..."
     Ya ƙarashe maganar ƙwalla tana zubo masa, kallon Salma Aliyu yayi ya ce,
     "Salma ki yiwa Abba biyayya, domin ya samu damar cikawa mahaifiyarmu burinta akanki, karki kalli Fadila ki ga kamar kema ba a yi miki adalci ba, kiyi aurenki domin shine rufin asirinki Duniyq da Lahira. Shi karatu ba wani abu bane  idan mijinki ya barki sai ki cigaba da karatunki a ɗakin mijinki cikin kwanciyar hankali.."
       "In sha Allahu! Yaya Aliyu zan yiwa Abbanmu biyayya, ga dukkan umarninsa.."

Daga nan Abba ya tambayi Salma "Kina da wanda kike so?"
     Girgiza kai ta yi ta ce, 
  "A'a Abba bani da shi"
"To, akwai wani yaro a companinmu mai suna Kabir na yarda da nutsuwarsa da tarbiyyarsa, idan ba za ki damu ba, sai na turo miki shi ku dai-dai ta."
   "To Abba, duk yanda kayi dai-dai ne"
Dafa kanta Abba yayi ya ce,
"Tabbas kin gado halin mahaifiyarku, domin tunda nake tare da ita kafin mai rabawa ta raba mu, ba ta taɓa yi min musu idan na gaya mata magana ba, kome na ce mata, sai dai ta ce min to, kuma kema ga shi kin biyo halinta. Allah yayi muku albarka..."
   A tare Salma da Aliyu suka ce, 
   "Amin ya Allah"..

Kallon Salma Abba yayi ya ce, 
   "Salman Abba, tashi ki je idan na sanar da Kabir ɗin, sai ya zo ku daidaita ko?"
Miƙewa tsaye Salma ta yi ta ce, 
  "To Abba sai an jima"
Daga nan ta fita daga ɗakin, zuciyarta cike da tunanin yanda za ta yi rayuwar aure tare da mutumin da ba ta taɓa gani ba a rayuwarta..
    Da wannan tunanin ta fito falo, ta tarar da Umma tare da su Fadila Najwa da kuma Azima, suna ta jira cikin nishaɗi. 
   Ita ma fuskarta cike da fara'a ta zo ta zauna kusa da su tana murmushi, harararta Umma ta yi cike da masifa ta ce,
   "Ke Uban waye ya baki ikon zaunawa anan?" 
Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi ta ce, 
"Yi haƙuri Umma, ganinku a zaune shi yasa nima na zauna.."
   "To, sauri ki tashi ki bai wa mutane wuri"
   Kallon Umma ta yi cike da mamakin maganarta, ta ƙi tashi daga wajen..
   Wata tsawa Umma ta daka mata..
"Ba za ki tashi ki bamu guri ba? Ko so kike na fasa wannan shegen k'aramin bakin, mai kama da na kurciya?"
   Da sauri Salma ta tashi ta shige cikin ɗakinsu, tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya....

*SU WAYE ABBA DA UMMA*

Alhaji Lawan haifaffen jahar Kano ne, a ƙaramar hukumar Gezawa.
   Ɗan kasuwa ne anan Gezawar, shinkafa yake saye mai yawa yana kai wa kasuwannin ƙauye yana sayarwa...
Matansa biyu ƴaƴansa bakwai, maza biyar mata biyu.
Matarsa ta farko sunanta Habiba, amma ana kiranta da Goggo. 
    Ƴaƴanta shida maza huɗu mata biyu Babban cikinsu sunansa Auwal, sai Isah Sunusi da kuma Saminu.
   Sai matan kuma akwai Na'ima da Surayya.
   Sai matarsa ta biyu mai suna Amina amma yaran gidan suna kiranta da Ammi. 
  Ɗanta ɗaya ne jal, mai suna Hisham amma ana kiransa da Inuwa. Kasancewar sunan mahaifinsa aka saka masa, shi yasa mahaifinsa ya rinƙa kiransa da Inuwa, a hankali kowa ya rinƙa kiransa da haka. Har sunansa na asali wato Hisham ya ɓata, sai Inuwa kowa da shi ya san shi..

Goggo masifaffiyar mata ce, ko kaɗan ba ta k'aunar Ammi ita da Ɗanta. Zaman haƙuri kawai take yi a cikin gidan.
   Ƴaƴanta ma gaba ɗayansu, sun ɗauko halayyarta ba su bar komai ba daga mazan har matan. 
   A rayuwarsu sun tsani su wayi gari, su ga Ammi ita da Inuwa a cikin gidansu, a wajen Alhaji Lawan kawai take samun sauƙi. Amma duk lokacin da yayi tafiya, to daga ranar Ammi ita da Inuwa sun shiga uku a cikin gidan, domin ko abinci suka dafa ba za su basu ba, koda mutuwa za su yi kuwa..
Duk halin da Ammi take shiga ko kaɗan ba ta bar Alhaji Lawan ya sani ba, wata rana yayin da ya dawo daga kasuwa. Bayan Sallar Isha'i ya shiga ɗakin Ammi, sai ya tarar da ita a zaune akan Sallaya tana kuka, ga kuma ɗan k'aramin Ɗanta Inuwa kwance akan cinƴarta yana bacci...
   Da sanyin jiki Alhaji Lawan ya k'arasa cikin d'akin, domin hankalinsa tashi yake idan ya ga Ammi a cikin damuwa..
   Zaunawa yayi a bakin gado, cikin nutsuwa ya kalle ta ya ce,
   "Amina menene yake damunki ne, na ga kina kuka?" 
   Firgigit ta yi, sannan ta sa hannu tai saurin share hawayenta, ta kalli Alhaji ta sakar masa wani murmushi kana ta ce,
     "Ba abinda yake damuna, kaina ne yake yi min ciwo.."
   Saukowa yayi daga kan gadon ya dawo kusa da ita, ya kalle ta ya gyaɗa kai kafin ya ja wani dogon numfashi ya ce.
  "Amina duk wanda ya kalle ki ya san akwai ɗumbin damuwa a tattare da ke, me yasa ba zaki sanar da ni damuwarki ba Amina? Ko babu komai zan yi iyakar ƙoƙarina wajen samo miki mafita akan abinda yake damunki, kuma kar ki manta ni mijinki ne kuma ni kaɗai kika sani a cikin garin nan, idan ba ki sanar da ni damuwarki ba, kina da wanda ya fini wanda  zaki sanarwa?"

Jikin Ammi ne yayi sanyi sosai, nan take ta sanar da Alhaji Lawan duk abinda su Goggo ita da ƴaƴanta suke yi mata yayin da ba ya gida. Haƙiƙa Alhaji Lawan ya ji haushi sosai, cikin fushi ya tashi zai je ɗakin Goggo domin ya ci mutuncinta ita da ƴaƴanta akan abinda suke yiwa Ammi.
  Da kyar Ammi ta lallashe shi ya haƙura, anan ya rinƙa kwantarwa da Ammi hankali tare da yi mata faɗa akan rashin sanar da shi da wuri, domin da tuni yayi wa tufkar hanci. 
   A daren Alhaji Lawan kwana yayi cike da baƙin cikin abinda Goggo take yiwa Ammi. Washe gari da Asuba ya tashi bayan yayi Sallah ya zo ya sanar da Ammi ya tafi kasuwar Gujungu, amma da wuri zai dawo. Allah ya kiyaye hanƴa ta yi masa, sannan ya fita ba tare da ya sanar da Goggo tafiyar tasa ba.
    Misalin ƙarfe biyu na rana, aka bugo musu waya aka sanar da su cewa Allah yayi wa Alhaji Lawan rasuwa sakamakon hatsarin mota da suka yi akan hany'arsu ta zuwa Gujungu..Iya tashin hankali iyalan Alhaji Lawan sun shiga, haka sauran maƙwabta tare da abokan arziƙi sun shiga ruɗani sosai saboda Alhaji Lawan mutum ne mai matuƙar kirki ga yawan kyauta domin ko kaɗan abin hannunsa ba ya tsone masa ido. Ammi ma ta shiga tashin hankali da rudani sosai, domin ba ta san irin rayuwar da za su fuskanta ba, ita da ɗanta dama a wajen Alhaji Lawan kadai take samun farin ciki da jin daɗi, to yanzu mai rabawa ta raba su ba ta san inda za ta sa kanta ba.

Bayan kwana bakwai da mutuwar Alhaji Lawan, bayan an taru an yi masa addu'a kowa ya watse, da daddare misalin ƙarfe 11:30pm na dare. 
  Ammi ce a kwance cikin d'akinta ita da tilon ɗanta Inuwa. Tunanin rayuwar da za su fuskanta a cikin gidan take yi, kuma ba ta san kowa a cikin garin ba balle ta tafi wajensa ta zauna. Tana nan kwance bacci ya ki ɗaukarta saboda tunani da fargabar da suka yiwa zuciyarta katutu, shi yasa bacci ya ƙi d'aukarta ko kad'an..
   Kwatsam ba zato ba tsammani ta ji ana buga kofar ɗakin nata da ƙarfin gaske kamar za a ɓalle k'ofar.

A firgice ta tashi tana faɗin "Waye?" Ba a yi mata magana ba, sai cigaba da dukan ƙofar da aka yi. Jikinta yana rawa ta tashi ta buɗe ƙofar. Cike da ɗumbin mamaki da fargaba take kallon wad'anda suke buga mata d'akin, Goggo ce ita da ƴaƴanta riƙe da makamai kala-kala. Babban cikinsu ne wanda ake kira Auwal ya dube ta ya daka mata tsawa ya ce,
"Kin tsaya kina kallonmu, ki fito waje.." Da sauri Ammi ta koma ta ɗauko ɗanta, sannan ta fito daga ɗakin da sauri, shiga cikin ɗakin suka yi gaba ɗayansu. Kayanta suka haɗo mata gaba dayansu, suka watso mata waje da sauri ta sunkuya ta fara harhaɗa kayan nata waje guda. Kallonta Goggo ta yi cike da masifa ta ce, 
  "Kina jina ko?" Da sauri Ammi ta gyaɗa kai ta ce, "E! Ina ji" 
"Ki yi saurin ɗaukar waɗan nan tsummokaran naki ki yi gaggawar barin gidan nan, idan kuwa har kika tsaya ɓata mana lokaci, yanzun nan zan saka ƴaƴana suka kashe ki keda wannan shegen ɗan naki..." 
  
Fashewa da kuka Ammi ta yi ta duƙusa har ƙasa ta ce,
"Don Allah Yaya ki taimaka min, idan na fita daga gidan nan Wallahi ban san inda zan je ba, a cikin daren nan.." Wani wawan mari Auwal ya ɗauke ta da shi, nan take ta rasa inda kanta yake taga Duniyar tana juyawa a cikin idanunta, jiri ya ɗebe ta za ta faɗi ƙasa, da sauri ta jingina jikin bango tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya nan take Ɗanta Inuwa ya fashe da kuka mai ƙarfi..
   Nuna ta da wuƙa Sunusi yayi ya ce, "Ki yi sauri ki ɗauki wannan shegen yaron naki, ku bar gidan nan tun kafin mu hallaka ku.." Ya faɗi haka tare da jefo mata ƴar jakar kayayyakinsu, da sauri ta ɗauki jakar ta rusa kuka, ta nufi hany'ar fita daga gidan. Ba su bar ta ta ɗauki komai a cikin gidan ba, illa kayanta su ma ba duka suka barta ta ɗauka ba. 
Yayin da ta fito daga gidan, sai ta ga garin yayi duhu sosai, d'aga kanta sama ta yi, nan take ta ga hadari ya haɗo sosai da alamu zai iya zubo ruwa a kowanne lokaci..
  Gabanta ne ya faɗi, ta ji zuciyarta tana luguden duka, ƙara rungume Ɗanta a ƙirjinta tana cigaba da rusa kuka, cikin sanyin jiki take tafiya tana tunanin inda za ta saka kanta, domin ba ta san kowa a cikin garin ba. Balle ta nufi wajensa, kai tsaye ta yanke shawarar barin garin gaba ɗaya, saboda haka ta nufi bakin titi ko Allah zai haɗa ta wanda zai taimaka mata, ga hadari kuma ya haɗo sai faman ƙugi yake..
  Ita da ba kanta take ji ba, ɗan ƙaramin Ɗanta take jimami, domin ba ta san inda za ta saka shi ba saboda kar ruwa ya dake shi. Tana tafiya cike da tunani, ba ta ankara ba ta zo dai-dai wasu karnuka, nan take kuwa suka taso kanta gaba ɗaya, ganin sun nufo inda take ne yasa ta firgita ta fita a guje, nan take kuwa karnukan suka rufa mata baya..Ta shafe kusan minti ashirin tana gudu karnukan suna binta, sannan ta iso bakin titi. Tana cikin gudun ba ta ankara ba, ta yi tuntuɓe da wani ƙaton dutse, nan take ta yanke jiki ta faɗi ƙasa sumammiya, ɗanta Inuwa da yake goye a bayanta ya tsandara wani uban ihu, daga nan shi ma yayi shiru alamun shi ma ya sume....

*Comment and share*


Mai son shiga group
07069475482.
: *BOKO NE SILA*
          _(Fiction story)_



KING & QUEEN WRITING CHAMBER


HUSSAIN YUSUF

Page 14.

Tana nan kwance kamar matacciya, numfashinta yana fita sama-sama. A bayanta kuma, ɗanta Inuwa ne yake ta faman kuka yana kiran "Ruwa" amma ko kaɗan ta kasa motsa jikinta balle ta taimaka masa, hawaye sai faman kwarany'a yake daga kan fuskarta. Bayan kamar minti talatin, lokacin har an fara ruwa amma bai yi ƙarfi sosai ba. K'ok'arin tashi Ammi ta shiga yi, amma ina? Ko hannunta ta kasa motsawa, balle har ta iya miƙewa zaune. Nan take wani kuka mai cin zuciya ya ƙwace mata, bakinta banda kiran sunan Allah babu abinda yake yi, domin ta hak'ik'ance a cikin ranta idan ba shi ba, babu mai iya fitar da ita daga cikin wannan mawuyacin halin. Tana nan kwance tana jiran tsammani, sai ga wata mota ta zo wucewa da gudun gaske, har motar ta gifta inda take sai ta yo baya a hankali, har ta zo dai-dai inda take kwance. Da sauri mamallakin motar ya fito ya nufo inda ya hangota a kwance, rai ga hannun Allah, cike da tausayawa gami da ɗumbin mamakin abinda ya kawo ta nan cikin tsohon daren nan, ya shiga ƙoƙarin kwance yaron da yake goye a bayanta. Yana gama kwance shi, ya kalle ta ya ce, "Baiwar Allah za ki iya tashi?" Ko motsawa ba ta yi ba, balle ta bashi amsar tambayar shi.

Da sauri ya juya ya kai yaron cikin motarsa, sannan ya zo ya ɗaga ta da taimakonsa ta taka da ƙafafunta har cikin motar tasa. Kwantar da ita yayi a gidan baya, sannan ya ɗauki ɗan nata ya ɗora shi akan cinƴarshi, nan take ya ja motar da gudun tsiya ya nufi cikin birnin Kano, domin ya kaita a yi saurin duba lafiyarta. Kallon yaron yayi nan take ya ji ƙaunar yaron gami da tausayinsa sun mamaye masa zuciya, gorar ruwa ya ɗauko ya kafa masa a baki, nan take kuwa ya rinƙa shan ruwan, kamar bai taɓa shan ruwa a rayuwarsa ba. Tafiyar minti arba'in ce ta kawo shi cikin birnin Kano, daga Gezawa inda ya ɗauko Ammi. Kai tsaye asibitin Malam Aminu Kano ya wuce da ita, yana zuwa kuwa likitoci suka amshe ta da gaggawa, suka shiga aikin ceto rayuwarta, domin tana cikin hatsari.

Bayan kamar minti ashirin da biyar, sai ga likitan ya fito ya kalli mutumin da ya kawo Ammi, ya ce, "Malam ina son ganinka a office" da sauri ya ce, "To, likita" bayan sun shiga office ɗin likitan ya kalle shi cikin nutsuwa ya ce, " "Malam wannan matar da ka kawo, matarka ce?" Shiru yayi yana nazari, yana tsoron ya ce ba matarsa ba ce, doka ta hau kanshi, a wani ɓangaren kuma yana tsoron ya ce matarsa ce yayi ƙarya abinda bai taɓa yi ba a rayuwarsa. Nan take ya yanke hukuncin faɗawa likitan gaskiya, kome ne ya faru da shi, akan gaskiyarsa yake. "Maganar gaskiya likita ba matata ba ce, na dawo daga jihar Jigawa a dai-dai wani a ƙauye a cikin Gezawa na ganta kwance gefen titi ɗanta sai faman kuka yake, ita kuma tana kwance ta kasa motsawa ga hadari ya gangamo zai iya zubar da ruwa a kowanne lokaci. Shi yasa tausayinta ya kama ni, na tsaya na taimaka mata na kawo ta nan asibiti. 
    
    Kallon Inuwa likita yayi da yake zaune akan cinƴar mutumin ya ce, "Wannan shine ɗan nata?" Ya gyaɗa kai ya ce, "E! shine" girgiza kai Likita ya shiga yi ya ce, "Wannan aikin da na yi maka, ba ƙaramin hatsari ne da shi ba. A ƙa'idar doka dole sai ka zo da ɗan sanda sannan zan amshe ku, amma ganinta da na yi ne cikin mawuyacin hali yasa na manta da wani batun ƴan sanda. Na taimaka muku cikin gaggawa, saboda haka idan ta farka daga allurar baccin da na yi mata, in sha Allahu za ta dawo normal kamar yanda take da, sai ka tambaye ta garinsu ka mayar da ita.." "To, Likita nagode! Nagode! Allah ya saka da alkhairi, Allah ya biya ka da gidan Aljanna.." Likiya ya amsa "Amin summa amin" kallon likita mutumin yayi ya ce, "Zuwa yaushe za ta farka daga baccin?" "Zuwa asuba in sha Allah" "To Likita Allah ya kai mu" amsawa yayi tare da ficewa daga cikin office ɗin, zai je duba wasu patience da aka kawo yanzu.

Cikin sanyin jiki mutumin shi ma ya fito, ya shiga ɗakin da Ammi take kwance, Inuwa rungume a hanunsa yana bacci. A kwance ya ganta tana bacci, nan take tausayinta ya ƙara mamaye zuciyarsa, a hankali ya duƙa ya kwantar da ɗanta Inuwa a gefenta, sannan ya samu wata kujera ya zauna. Agogon da yake liƙe a jikin bangon d'akin ya kalla, nan take ya ga 2:30am. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ɗauko wayarsa daga cikin aljihu...Wayar ya kara a kunnensa ya ce, "Kada ku ga ban dawo ba, zuwa safiya in sha Allah zan iso!" Sannan ya kashe wayar ya ajiye, nan take gyangyaɗi ya fara ɗaukarsa, bai ankare ba barci mai nauyi yayi awon gaba da shi, kiran sallar farko ne ya farkar da shi. Da sauri ya farka, ya tashi ya je gaban gadon da Ammi take kwance, a dai-dai wannan lokacin ne ita ma ta farka a razane tana kiran sunan ɗanta. 

Ganinshi ta yi a kwance a gefenta, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta shiga bin ɗakin da take ciki da kallo. "Sannu baiwar Allah!" Da sauri ta waigo inda ta jiyo muryar, ganinshi ta yi a tsaye a kanta yana murmushi. Nan take abinda ya faru a baya, ya fara dawo mata. Wani zazzafan hawaye ne ya fara kwarany'a akan fuskarta, anan ta fahimci wannan mutumin shine wanda ya ceceta har ya kawo ta asibiti. A hankali ta amsa masa sannun da yayi mata, muryarta can ƙasan maƙoshi ba ta fita sosai ta ce, "Yawwa nagode" daɗi ya ji sosai yayin da ya ji ta yi magana. "Bari na je na kirawo Likita ko?"

Da ido kawai ta bi shi har ya fita daga cikin d'akin, ba jimawa sai ga shi ya dawo tare da likita. Duba ta Likitan ya shiga yi, bayan ya gama sai ya dube shi ya ce, "Alhamdulillah! Yanzu na ga babu abinda yake damunta, saboda haka bari na rubuta muku wasu magunguna da za ka saya mata ta rinƙa sha, na ga akwai ulcer a jikinta.." "To Likita Allah ya saka da alkhairi!" Bayan ya gama rubuta masa magungunan, sai ya miƙa masa takardar sannan ya fice daga cikin ɗakin. Kallonta yayi ya ce, "Sunana Malam Musa! Ni haifaffen cikin jahar Kano ne, ina da almajirai da nake koyarwa a gidana, na je wajen wani Malamina a jahar Jigawa. Akan hany'ata ta dawowa motata ta samu matsala, sai na tsaya a wani gari mai suna Wangara aka gyara min motar, shi yasa na yi dare sosai, misalin ƙarfe ɗaya da rabi na zo wucewa sai hango ki a gefen titi a kwance kamar matacciya. Ga kuma yaro a bayanki yana kuka, sai tausayinku ya kama ni na zo ɗauko ku na kawo ku nan asibiti aka baki taimakon gaggawa... Daga nan yayi shiru yana kallon Umma, da kyar ta iya buɗa baki ta ce, "Allah ya saka maka da alkhairi bisa wannan taimako da ka yi mana.." Daga nan ta faɗa masa sunanta, tare da labarinta har dalilin da yasa ya tsince ta a bakin titi.

Ya tausaya mata matƙukar tausayawa, don har hawaye sai da ya zubar na tsananin tausayinta. Cike da alhini ya dube ta ya ce, "Ki yi haƙuri Amina! Ko me yayi zafi maganinsa Allah, kuma dukkan tsanani yana tare da sauƙi.." Gyad'a ta yi ta ce, "Nagode sosai da wannan taimakon naka Allah ya saka maka da alkhairi.." Fita yayi daga ɗakin ya nufi masallaci, domin har an kira assalatu. Ita ma da kyar ta iya tashi, ta shiga cikin toilet ɗin da yake cikin ɗakin ta gyara jikinta, sannan ta ɗauro alwala ta fito. Rasa dardumar da za ta shimfiɗa ta yi sallah ta yi, kallabin da yake kanta ta kunce, sannan ta shimfiɗa ta tayar da Sallah. Bayan ta idar ta daɗe tana addu'oi kafin ta shafa. Miƙewa tsaye ta yi ta zo gefen gadon ta zauna, kallon jikinta ta yi, sai ta ga duk kayan jikinta sun ɓaci sosai duk sun yi datti sakamakon faɗuwar da ta yi a cikin jar ƙasa gefen titi.

Nan take tunanin jakarta ya faɗo mata, dube-dube ta hau yi a cikin ɗakin. Hango ta tayi a ajiye a kusurwar ɗakin, wani farin ciki ne ya mamaye zuciyarta. Da sauri ta ɗauko jakar ta hau dubawa, gani ta yi babu abinda ya b'ata a ciki. Da hanzari ta hau canja kayan da yake jikinta, kafin wani lokaci har ta gama canjawa, ta zauna a gefen gadon ta faɗa kogin tunani. "Yanzu ina zan saka rayuwata? Idan aka sallame ni daga asibitin nan, ina zan je na samu sassauci a cikin wannan BAƘAR RAYUWAR da ta afko mini?" Tambayoyin da ta rinƙa yi wa kanta kenan a cikin zuciyarta. Hawaye sai faman kwarara yake akan fuskarta. Nocking ta ji ana yi a jikin ƙofar, cikin sanyin jiki ta tashi ta je ta buɗe. Malam Musa ta gani tare da wata dattijuwa mai cikar kamala, hannunsa riƙe da flask ɗin tea ga bread kuma a cikin wani ɗan k'aramin basket. Suna shigowa ɗakin, tsohuwar ta dube ta cike da tausayawa ta ce, "Sannu baiwar Allah!" Amsawa Ammi ta yi cikin sakin fuska..

Had'a mata shayin dattijuwar matar ta yi, da kyar ta iya shany'e shi. Magungunan da Malam Musa ya siyo, dattijuwar ta miƙa mata, sannan ta matsa mata har sai da ta shany'e shi tas. Nan take kuwa ta ji ɗan k'arfi a jikinta, dai-dai wannan lokacin ɗanta Inuwa ya farka daga bacci, da kanta ta kaishi bayi ta wanke masa jikinsa, sannan ta fito ta canja masa kaya. Likita ne ya shigo ɗakin, ya duba lafiyarta sosai. Sannan ya basu sallama suka tafi...

Tun daga lokacin Ammi ta dawo rayuwa a gidan Malam Musa, mahaifiyarsa tana kula da ita sosai tamkar ƴar cikinta. A gidan ta yi takabarta har ta gama, bayan ta yi idda ne Inna mahaifiyar Malam Musa ta bijiro mata da buƙatarta, akan tana so ta auri Malam Musa domin matarsa watanta shida rasuwa kuma har yanzu bai yi wani auren ba. Nan take tunanin tsohon mijinta Alhaji Lawan ya fad'o mata, ba ta san lokacin da hawaye mai zafi ya zubo mata ba, kallon Inna ta yi ta ce, "Inna! Na amince da buƙatarki, domin abinda kuka yi min yasa ba zan taɓa butulcewa buƙatarku ba, kowacce iri ce matuƙar ba saɓawa Allah ba ne." Murmushin jin daɗi Inna ta yi, ta buɗa baki cike da farin ciki ta ce, "Amina! Allah yayi miki albarka! Allah ya raya miki Inuwanki..Allah ya ɗora shi akan tafarki madaidaici."
   "Amin Inna! Amma ina neman wata alfarma a wajenku" da mamaki Inna ta kalle ta ta ce, "Amina! Ai kin wuce neman duk wata alfarma a wajenmu, domin kin yi min abunda ba zan taɓa mantawa da ke a rayuwa ba, don haka ki faɗi ko menene an yi miki.."
   "Inna don Allah ina son idan an ɗaura aurena da Malam Musa, ina son ya riƙe ni, ni da ɗana Inuwa tsakani da Allah, sannan kar ya nuna masa tsangwama ko kyara domin maraya ne..." Tana zuwa nan ta fashe da kuka mai cin rai, kallonta Inna ta yi ta ce, "Aminatu! Na yi miki alƙawari, Inuwa zai samu gata a wajen Musa, tamkar yanda zai samu a wajen mahaifinsa..." 
 Da sauri Ammi ta tashi ta shige cikin d'aki, ta fashe da kuka. Babban abinda ya fi ɗaga mata a hankali akan wannan auren da za ta yi shine; gani ta ke tamkar cin fuska ne ga tsohon mijinta wanda ya mutu Alhaji Lawan, inda ba Inna ce ta zo mata da batun auren nan ba, da ba zata taɓa yin wani auren a rayuwarta ba, domin gani take yi kamar ba za ta sake samun miji kamar Alhaji Lawan ba....
 
Tun da Ammi ta auri Malam Musa, ta samu jin daɗi da kwanciyar hankali, tamkar a wajen tsohon mijinta Alhaji Lawan. Nan take kuwa ta warware kamar ba ta tab'a shan wahala a rayuwa ba. Inuwa kuwa ya zama ɗan gata, duk wani gata da jin dad'i da ɗa yake buƙata a wajen Ubansa, to Inuwa ya same shi a wajen Malam Musa, haka ne ya ƙarawa Ammi ƙaunar Malam Musa a cikin ranta, domin yana ƙaunar tilon ɗanta Inuwa. A wajen Malam Musa Inuwa yake karatun allo tare da sauran almajiransa, shekararsa goma sha biyu ya sauke Alƙur'ani mai girma. Sannan Malam Musa ya saka shi a makarantar boko da kuma Islamiyya inda kuma yana karatun hadda a wajensa...

Bayan shekara ashirin, lokacin Inuwa yana da shekara talatin da ɗaya. Lokacin har ya kammala karatunsa ya samu aiki a wani babban company na y'an k'asar China saboda ƙwarewarsa da kuma jajircewarsa, ya samu muƙamin chief acconter na kamfanin. Da Malam Musa ya ga ya isa aure, da kansa ya haɗa shi da wata ƴar abokinsa mai suna Rabi'atu.. 
Yayin da Malam Musa ya kawo masa maganarta, bai yi masa musu ba domin dama can yana son yarinyar saboda kyawawan halayenta da ta gada a wajen mahaifiyarta da mahaifinta. 

Shekararsu biyu da yin aure sannan Allah ya bawa Rabi'atu ciki ta haifo santalelen jaririnta aka raɗa masa suna Aliyu. Bayan shekara biyu Allah ya sake bata wani cikin, ta haifo santaleliyar jaririyarta mai kama da ita sak, ranar suna aka raɗa mata suna Ummu-Salma, amma ana kiranta da Salma..
  Aliyu yana da shekara huɗu, ita kuma Salma tana da shekara biyu cif, lokacin ba a daɗe da yaye ta ba, Allah yayi wa mahaifiyarsu Rabi'atu rasuwa, sakamakon ciwon cikin da ya turnuƙe Rabi'atu cikin dare, da sauri aka ɗauke ta aka nufi asibiti da ita, tun kafin su ƙarasa rai yayi halinsa...Haƙiƙa Inuwa  yayi baƙin ciki sosai da mutuwar matarsa, domin gani yake ba zai taɓa samun madadinta ba. Ammi ita ta ɗauki Aliyu da Salma ta cigaba da kula da su, kafin mahaifinsu yayi aure. Bayan kwana arba'in Ammi da Inna suka matsawa Inuwa akan dole ya ƙara yin aure domin ya samu me riƙe masa ƴaƴansa...

Babu yanda Malam Musa ya iya, bisa dole ya je ya samo wata ƙaramar bazawara mai suna Hauwa'u. Bai aure ta ba, sai da ta yi masa alƙawarin za ta riƙe masa ƴaƴansa da gaskiya, sannan ya yarda ya aure ta. Yayin da ta shigo gidan, sai Aliyu da ƙanwarsa Salma suka dawo wajenta da zama, suka baro wajen Ammi. Tun da suka dawo wajenta, sai ta rinƙa nuna musu so da ƙauna a gaban mahaifinsu, amma idan baya nan kare ma ya fi su daraja a wajenta, haka za tai ta wahalar da su kamar bayi. Musamman Aliyu ba ta barinsa ko kaɗan ya huta, haka kawai za tai ta saka shi aikin da ya fi ƙarfinsa, kuma ta ja masa kunne akan kada ya faɗawa Abbansa, Salma kuma yarinya ce idan ta tambayi abinci haka za ta zaneta ta hanata kuka, abincin da za ta bata ɗan kaɗan kuma ta yi mata gargaɗin inda ta faɗawa Abbansu, sai ta yanke mata kunne....

A haka suka rinƙa rayuwa tana zaluntarsu, ba tare da mahaifinsu ya sani ba. 
  A haka dai har Allah ya bawa Hauwa'u ciki, murna a wajen Inuwa ba a cewa komai. A haka ya rinƙa kulawa da ita, har Allah ya sauke ta lafiya ta haifo masa santaleliyar jaririya mai kama da turawa, ranar suna yarinya ta ci sunan Fadila....Kasancewar Fadila mai saurin girma ce, kuma tana samun kulawa sosai a wajen mahaifiyarta. Sai ta rinƙa girma sosai, yayin da aka yaye ta kuwa tana da shekara biyu idan ka kalle ta sai ka ce shekararta huɗu, har ta kamo Salma a girma, idan ka kalle su sai ka ce Fadila ce gaba da Salma, saboda Salma duk ta lalace bata girma sosai...

Ranar wata Alhamis, Malam Musa tare da Ammi. Suka tafi garin Jigawa, bayan tafiyarsu da awa biyar, sai aka bugowa Inuwa waya cewa sun yi accident kuma babu wanda ya rayu a cikinsu...Iya ruɗani Inuwa ya shiga, haka ma almajiran Malam Musa sun shiga baƙin ciki da alhini na rasa babban Malaminsu...
  Bayan an yi addu'ar bakwai Inuwa shine ya dawo kula da makarantar Malam Musa, kuma yana iyakar ƙoƙarinsa wajen kwatanta yanda Malam ɗin yake. Daga nan ya samu laƙabin Malam Inuwa, kowa ya dawo kiransa da haka, idan ya je office ya taso a makarantar yake zaunawa yana biyawa ɗaliban da suke d'aukar karatu a wajensa...
     Bayan shekara biyar Allah ya sake bai wa Hauwa'u ciki ta haifo kyawawan ƴaƴanta su biyu, duka mata, da kanta ta zaɓi sunan da za a saka musu, "NAJWA DA AZIMA" tun daga sannan Malam Inuwa ya cigaba da kula da iyalinsa da kuma d'aliban mahaifinsa.

Cikin ikon Allah arziƙi ya rinƙa bunƙasa, domin har kasuwanci yake taɓawa. Kafin ka ce me? Har ya gina musu dank'areren gida a Nassarawa G.r.a. Shi kuma gidan mahaifinsa, ya gina k'atuwar makaranta, ya saka mata sunan marigayi Malam Musa. Shi yake ɗaukar duk wani nauyi na makarantar, har zuwa yanzu....
Wannan shine labarin Abba da Umma...

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Yayin da Kabir ya zo, shi da Salma sun fahimci junansu sosai. Kamar dama can sun saba, Fadila kuwa sai faman kushe shi take, ita kuwa Salma sai dai kawai ta kalle ta ta yi murmushi. 
   Wata rana da la'asar Salma ce tare da Kabir, suna hirarsu cikin nishaɗi. Cikin wata irin murya mai sanyin gaske Kabir ya ce, "Salma!" A hankali ta ɗago da dara-daran idanunta ta kalle shi, sannan ta yi saurin sunkuyar da kanta ƙasa, can ciki ta amsa a hankali..."Na'am Yaya Kabir!"

"Kin san yanda nake sonki a cikin zuciyata kuwa?" 
   "Ba ta sani ba, munafiki banza da wofi! Ka wani lallaɓo za ka lalata ƴar mutane ko? To yau dubunka ta cika munafikin Allah!" Da sauri Kabir da Salma suka miƙe tsaye, domin ganin wanda yake irin wannan maganar....


*~07069475482.~*
: *BOKO NE SILA*
        _(Fiction story)_



*KING & QUEEN WRITING CHAMBER*
  *(Sarki da Sarauniya writer's)*

 " *We rule the world of writing*"
https://www.facebook.com/profile.php?id=100063945240173

HUSSAIN YUSUF


Page 15.

Umma ce a tsaye fuskarta a murtuƙe kamar ta shanu. Sai muzuru take da manyan idanunta, sunkuyar da kai Kabir yayi cikin sanyin murya ya ce, "Umma ina yini?" Wani banzan kallo ta watsa masa kafin ta ce, "Yana gidan Ubanka!" Da sauri Kabir ya ɗago da kansa ya kalle ta, zuciyarsa tana tafarfasa kamar za ta ƙone...

Kallon Salma yayi ya ce, "Salma sai an jima za mu yi waya!" Yana faɗin haka, bai jira cewarta ya juya ya tafi. Zuciyarsa duk babu daɗi, tunda yake a rayuwarsa, ba a taɓa yi masa wulak'anci irin wannan ba. Yana fitowa ya ga Abba ya shigo gidan, har ƙasa ya durƙusa ya gaishe shi cikin sakin fuska. Kallonshi Abba yayi ya ce, "Kabir me yake damunka haka ne? Ko Salma ce ta yi maka wani abun?"

Duk yanda ya so b'oye damuwarsa, sai da Abba ya gane. Ɗan murmushin yaƙe yayi ya ce, "A'a Wallahi Abba, Salma ba ta yi min komai ba.."  "Na ga fuskarka d'auke da damuwa, me ya faru?" "Kaina ne ya ke yi min ciwo, shi yasa ka gan ni haka.." "Ayya! Allah ya sawwaƙe" "Amin ya Allah!" Har Abba zai wuce ya ga bakin Kabir yana motsi, alamun da akwai magana a bakinsa..

Juyowa Abba yayi ya kalle shi, ya daɗe yana kallonsa kamar wanda yake son gano wani abu game da shi. Sannan ya ja dogon numfashi, ya ce. "Kabir kamar da akwai magana a bakinka ko?" Ɗan sosai kai yayi ya ce, "Abba dama wata alfarma nake son nema a wajenka.." "Kabir ai yanzu mun riga mun zama ɗaya, faɗi kowacce alfarma ce na yi maka.."

"Dama Abba ina son ka gaggauta ɗaura min aure da Salma.." "Wannan ita ce alfarmar da kake nema?" "E! Abba ita alfarmar" "To ka kwantar da hankalinka, yaushe kake son a ɗaura auren yau ko gobe?" Da sauri Kabir ya kalli Abba, murmushi Abba yayi ya ce, "Kai nake sauraro.." Sunkuyar da kansa ƙasa yayi cike da kunƴa ya ce, "Da so samu ne dai, a ɗaura sati mai zuwan nan.." "To shikenan Kabir, nima na ji daɗin hakan Allah yayi maka albarka.." "Amin ya Allah! Nagode sosai Abba, Allah ya bar zumunci.."

"Amma Kabir me yasa ka damu a gaggauta ɗaura aurenka da Salma?" "Babu komai Abba, kawai na matsu na ganta a cikin gidana ne.." "To yayi kyau, idan ka je gida ka gaisar min da mahaifin naka..". "To Abba in sha Allah zai ji" daga nan suka yi sallama, Abba ya shiga gida shi kuma Kabir ya shiga motarsa ya bar gidan, zuciyarsa cike da farinciki marar misaltuwa..

Yayin da Abba ya shiga gida, bai ga kowa a cikin falon ba. Saboda haka kai tsaye ɗakinsa da yake sama ya wuce, bayan ya gama canja kayan jikinsa. Sai ya fito falon gidan ya zauna, Fadila ce ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da flate. Tana ganin Abba, ta zo ta durƙusa a gabansa ta ce, "Abba sannu da dawowa!"

"Yawwa Fadila! Ina Salma?" "Tana cikin ɗaki" ta bashi amsa a taƙaice. Abba ya ce, "Ki je ki kira min ita ku zo tare!" "To, Abba!" Ta tashi tare da shiga cikin ɗakin nasu da sauri. Ba daɗewa sai ga ta sun dawo tare da Salma. Bayan sun zauna, sai Abba ya kalli Fadila ya ce, "Fadila kema yakamata ki yiwa kanki karatun ta natsu,  ki fito da miji kema kiyi aurenki, domin ki kaucewa fitintinun zamanin nan, ki daina biyewa zancen mahaifiyarki, domin ba za su kaiki ko'ina ba, sai kogin nadama ni nasiha na yi miki, tashi ki je.." 

Da sauri ta tashi ta shige cikin ɗakinsu, jikinta duk yayi sanyi. Nan take ta fara tunanin ita ma ya kamata ta fito da miji ayi mata aure ta huta, amma da ta tuno burin da take da shi a boko, nan take ta watsar da batun aure daga cikin zuciyarta.

Kallon Salma Abba yayi ya ce, "Salma me kika yi wa Kabir?" Nan take ta fashe da kuka ta faɗawa Abba duk abinda ya faru. Ran Abba ya ɓaci sosai, kuma ya nunawa Umma kuskurenta, Fadila kuwa har dukanta yayi ranar dai haka suka kwana cikin tsananin ɓacin rai. Salma kuwa ba ta yarda ta haɗu da Umma ba, saboda abinda Abba yayi mata, za ta iya ramawa a kanta.

***
Bayan sati ɗaya aka d'aura auren Salma da Kabir, ranar Salma ta tsinci kanta a cikin farin ciki marar misaltuwa.

Ƙawayensu na makaranta, sun zo sai faman zuga Fadila suke akan kada ta yarda ko da wasa ayi mata aure yanzu. Domin tana haihuwa, wahalar raino da shayarwa za su tsofar da ita da wuri.

Bayan auren da sati guda, Abba da kansa ya nemowa Fadila gurbin karatu a B.U.K. Murna a wajen Fadila ba a cewa komai, domin burinta ya cika ta shiga jami'a, nan da nan kuwa girman kai ya shige ta, domin gani take ta yiwa kowa zarra. Musamman wanda ba ya yin jami'a.

Salma kuwa ta yi haƙuri ta zauna da mijinta lafiya, kome ta ce tana so da gaggawa zai samo mata. Ga wata irin soyayya da yake nuna mata, anan ta gane aure shine kwanciyar hankalin kowacce ɗiya mace.

Kuma shine zai ƙara fito mata da kimarta, da darajarta wacce Allah yayi mata. Bayan wata biyu Kabir ya je ya samo mata gurbin karatu a KUST WUDIL. Kullum shi yake kai ta, ya je ya ɗauko ta. Ko Abba bai sani ba, balle Umma da Fadila.

Fadila kuwa lokacin da ta fara zuwa makarantar, sosai ta mayar da hankalinta kan karatu. Jan ajinta da kyawunta, shine ya ja hankalin Malamai da ɗalibai kanta. Amma ko kaɗan ba ta kula su, ko fara'a ba ta fiye yi ba, idan ka ga fara'arta da dariyarta to a cikin ƙawayenta take. Ƴan class ɗinsu kuwa ko magana ba su cika yi mata ba, saboda kwarjinin da take yi musu...

Ko saurayi Fadila ba ta da shi, saboda kwarjininta da kuma kyawunta. Ko yaushe fuskarta a ɗaure, babu alamun fara'a shi yasa samari suke shakkar tunkararta maganar soyayya.
    
Kwatsam! Wata ranar laraba da cikin dare, ta tashi ta hau yin amai har ta galaɓaita sosai, lokaci guda ta fita daga hayyacinta. Jikinta ya mutu sosai, da kyar take iya ɗaga yatsanta. Nishinta ne ya tashi Azima da Najwa daga bacci.
  
Azima ce ta tafi da sauri ta shaidawa Umma, yayin da Najwa ta tsaya tana jerowa Fadila sannu! Da sauri Umma ta shigo cikin ɗakin, Fadila ta gani a kwance duk ta ɓata kayanta da amai.
   Bayi Umma ta shiga da ita ta tsaftace mata jikinta, bayan ta fito ta ɗauko mata wasu kayan ta canja domin waɗancan sun ɓaci da amai.

Kallon Fadila Umma ta yi, nan take gabanta ta faɗi. Cikin kiɗimewa Umma ta ce, "Fadila me zan gani haka? Ciki ne da ke?" "Ciki kuma Umma?" "Ciki mana!" "Ni gaskiya bani da ciki!" Fadila ta faɗi haka cikin tashin hankali.

Zuciya ce ta ɗebi Umma, nan take ta manta da wata rashin lafiyar da Fadila take yi. Ta hau jibgarta ba ji ba gani, tana dukanta tana cewa sai ta faɗa mata wanda yayi mata ciki amma ta ƙi faɗa, ƴan'uwanta Najwa da Azima sai faman kuka suke. Ihun Fadilar ne ya taso Abba da yake bacci, anan shi ma ya samu wannann baƙin labarin.

Nan take shi ma ya hau tambayar Fadila, amma ko kaɗan ta ƙi ta faɗi wanda yayi mata ciki. Daga ƙarshe da ta ga Umma tana niyyar hallakata, sai ta ce mahaifinta Malam Inuwa shine wanda yayi mata cikin ba kowa ba, kuma ta kafe akan haka. 

Umma kuma ba tare da wani bincike ba, ta rinƙa yiwa Abba rashin mutunci, daga ƙarshe ta kai ƙararsa kotu akan lallai sai an ƙwatowa ƴarta Fadila haƙƙinta a wajen mahaifinta Malam Inuwa.

*CIGABAN LABARI*
  
KOTU

Jama'a sun taru sosai, a cikin kotun. Shigowar Alƙali ake jira a  fara gabatar shari'a, jimm kaɗan Alk'ali ya shigo nan take kowa ya miƙe tsaye, bayan ya zauna sai kowa ya zauna. Ba tare da ɓata lokaci ba, aka fara gabatar da shari'a.
  
Magatakarda ne ya miƙe tsaye, ya fara karanto wata farar takarda da take riƙe a hannunsa.

"A yau ne sha biyar ga watan july, wannan kotu za ta fara sauraron ƙarar da Hauwa'u Rabi'u ta shigar da mijinta Malam Inuwa. Akan tana zarginsa da yiwa ƴarsu mai suna Fadila ciki.."

Ɗan rusunawa yayi ya miƙawa Alk'ali takardar, sannan ya koma ya zauna.

Rubuce-rubuce Alƙali ya fara yi, mutanen da suke cikin kotun, yayin da suka ji abinda Magatakarda ya karanto. Sai suka fara kallon-kallo a tsakaninsu, kafin su fara kallon Abba. Shi kuwa Abba sunkuyar da kansa ƙasa yayi, kwata-kwata ya kasa haɗa ido da mutane, saboda tsananin kunƴar da yake ji.

Ɗagowa Alk'ali yayi ya ce, "Kotu tana son ganin Malam Inuwa!"
  Dammmm! Abba ya ji gabansa ya faɗi da sauri, nan take mutane suka dawo da kallonsu kan Abba.

Shi kuwa Abba tashi yayi, ya nufo inda Alƙali ya nuna masa. Bayan ya tsaya Alƙali ya kalle shi ya ce........


*_Ayi min afuwa_*

Comment anda share.


Hussain YUSUF

07069475482.
: *BOKO NE SILA*
            _(Fiction story)_


*KING & QUEEN WRITING CHAMBER*
  *(Sarki da Sarauniya writer's)*

*"We rule the world of writing"*
https://www.facebook.com/profile.php?id=100063945240173


HUSSAIN YUSUF



Page 16.

"Za ka iya gabatarwa da kotu kanka?" 
  Kallon jama'ar kotun Abba yayi "Sunana Malam Inuwa, ni haifaffen jahar Kano ne sannan ni Malami ne, kuma ɗan kasuwa." 

Alƙali ya ce, "Kai ne wanda ya haifi Fadila?"
   "Ƙwarai kuwa Fadila ƴata ce, ni na haife ta."
  "Ka amince kai ne wanda yayi mata ciki?"

Da sauri Abba ya girgiza kai, "Ya mai Shari'a! Ni ba ni na yi wa ƴata Fadila ciki ba, kuma ban san wanda yayi mata ba.."
   Ya ƙarashe maganar hawaye yana zubo masa.

Ɗan rubuce-rubuce Alƙali yayi, sannan ya ɗago ya kalli jama'ar kotun ya ce, "Kotu tana neman Fadila Inuwa!"
   Cikin sanyin jiki ta fito ta tsaya, a inda aka nuna mata.

"Ya sunanki?" Alƙali ya tambaya, cikin rawar murya ta ce, "Sunana Fadila Inuwa!"
 "Da gaske Malam Inuwa shine mahaifinki?"

"E, shine mahaifina!" 
   Ɗan rubutu Alƙali yayi sannan ya ɗago ya kalle ta ya ce, 
    "Shin kin tabbatar shine wanda yayi miki ciki?" Gyaɗa kai Fadila ta yi hawaye yana kwarany'a akan fuskarta, ta ce.
  "E, cikin shi nake ɗauke da shi.." 

Ɗan rubutu Alƙali yayi, kana ya ɗago ya kalli Abba ya ce,
  "Malam Inuwa, ka ji abinda ƴarka ta faɗi. Cikinka take ɗauke da shi."

Da sauri Abba ya girgiza kai ya ce, "Ya mai Shari'a Wallahi ba ni na yiwa Fadila ciki ba, kuma ban san wanda yayi mata ba..."
   Abba ya faɗi haka, cikin tsananin baƙin ciki.
  Wai yau shine a tsaye gaban kotu, yana shari'a da ƴar cikinsa da kuma matarsa.

Wani ƙululun baƙin ciki ne ya turnuƙe shi, ya maƙoshinsa yayi masa ɗaci, da kyar ya ke iya haɗiyar yawu.
    Ɗan rubutu Alƙali yayi, sannan ya ɗago ya kalle su kafin ya fara magana.

"Kotu duk ta saurari jawabinku, yanda kowanne ya tsaya akan maganarsa. Saboda haka kotu tana son kowannenku ya samo Lauya, wanda zai tsaya masa kuma yayi bincike domin gaskiyar al'amarin ta fito.." 

"Saboda haka wannan kotu mai adalci, ta ɗage sauraron wannan shari'ar har zuwa sha ashirin da biyar ga wannan watan, amma kafin a dawo shari'ar kowa daga ciki ya tabbatar ya samu Lauya, idan kuma babu ku yi magana sai mu ba ku Lauyan gwamnati, kooootu!"

Tunda su Abba suka dawo gida, kwata-kwata ya kasa samun sukuni. Duba da yanda mutane suke kallonsa a matsayin Malami, amma ga shi ƴar cikinshi ta tozarta shi a idon duniya..

Tun a harabar kotun da suka fito, ya ga yanda mutane suke nuna shi da baki suna zunɗensa. Hakan ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba, daga zaman kotun ga shi duk inda ka bi a cikin unguwarsu zancensa ake yi, wasu zaginsa suke suna faɗin "A matsayinsa na Malam, suna tunanin ba shine ya aikata irin wannan abun ba.."

Yayin da wasu kuma suke ganin, ai zuciya ba ta da ƙashi. Kuma duk wani ɗan'adam ajizi ne, don haka ba abun mamaki ba ne, idan ya kasance Malam Inuwa ya aikata abinda ake zarginsa da shi.

Abba ya daɗe a cikin ɗakinsa, tunani da fargaba sun hana zuciyarsa sukuni. Wani irin haushin Fadila da Umma ne ya dabaibaye zuciyarsa. 
   A tunaninsa Umma za ta ba shi haɗin kai, domin su rufawa juna asiri.

Abba tun ba a je ko'ina ba, ga shi ta tozarta shi a idanun jama'a. 
   Zuciyarsa ya ji tana yi masa zafi, cikin tsananin fushi ya fita daga ɗakin nasa.

Kai tsaye ɗakin Umma ya nufa, yana zuwa ya iske ta a zaune gefen gado tana waya. 
   Tana ganin shi ya shigo, ta yi sauri ta ce, "Ina zuwa!" 
  Kashe wayar ta yi ta kalle shi, cike da rashin ɗa'a ta ce.

"Malam me ya kawo ka ɗakina?" Wani banzan kallo Abba ya watsa mata, kafin ya ce, 
   "Ni da gidana, ina da ikon na shiga ko'ina babu wanda ya isa ya hana ni.." 

Kawar da kai Umma ta yi, sannan ta yi shiru.
  Koda ganin haka sai Abba yayi gyaran murya ya ce, "Hauwa'u! Yanzu abunda kika aikata dai-dai ne?" 

Ya cigaba da cewa "Kin tozarta ni a idon Duniya, kin saka mutane suna zagina tare da shuna ni da baki, suna zunɗena. Mutanen da suke ganina da daraja, kin jawo kallona a matsayin mai daraja, yanzu menene amfanin wannan abun da kika yi?"

"Oho! Kai ka san da faruwar duk wannan abun, ka je ka aikata abunda ka aikata? Ai yana da kyau, kafin ka aikata laifi, ka fara duba abinda zai biyo bayansa. Saboda haka ni ban ga laifina, akan na kai ƙararka kotu ba. Domin duk tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa yake duka.."

"Haka kika ce ko?" Ko kallonshi, Umma ba ta yi ba balle ya saka ran za ta amsa masa. Ganin haka yasa ya fice daga ɗakin, da sauri cikin tsananin fushi. 

Yana fitowa ya ga Aliyu ya fito daga ɗakinshi, kallon Abba yayi ya ga yanda ya tamke fuska tamkar bai taɓa dariya ba..

Sunkuyar da kai Aliyu yayi, ya ce, "Abba daman wajenka zan je" 
    "To, Allah yasa lafiya!"
  "Lafiya ƙalau, dama magana nake son zan yi ni da kai.." 

"To, ina jinka!" 
  "A'a Abba mu shiga daga cikin ɗaki mana..." 
  Wucewa gaba Abba yayi zuwa cikin ɗakin, sannan Aliyu ya bi bayanshi.

Bayan sun zauna, Aliyu ya kalli Abba ya ce, "Abba dama akan kotu, nake so mu tattauna.." 
   "To, Aliyu ina sauraronka!"

"Yawwa Abba, dama ina son ka bani dama na tsaya maka a kotu. A matsayin Lauyan da Alƙali ya ce ku samo.." 
    Shiru Abba yayi na ɗan wani lokaci, kafin ya dubi Aliyu cikin nutsuwa ya ce.

"Aliyu ba ka tunanin mutane za su yi zargin, ka tsaya min ne don ka ɓoye gaskiyar laifin da ake zargin na aikata?" 
   "Abba! Koda mutane sun yi wannan tunanin, na tabbata kafin a ƙare zaman shari'ar gaskiya za ta yi halinta, ka ga daga nan maganar zargi ta ƙare.."

"Shikenan Aliyu! Allah ya bayyana gaskiya" 
   "Amin!" Aliyu ya amsa, sannan ya tashi ya fita daga cikin ɗakin.

Aliyu yana fita daga cikin ɗakin, Abba ya fara shirin office. Domin yana da tarin aiyuka masu yawa, waɗanda bai yi ba.
  Cikin sauri ya ke shiryawa, domin suna da meeting. Sannan ga ayyuka, shi yasa yake son ya je da wuri.

Domin ya fara rage ayyukan, kafin lokacin shiga meeting ɗin ya cika.
    Cikin ƙankanin lokaci ya kammala shiryawa, sannan ya fito daga ɗakinsa da sauri.
  A falo ya iske Azima da Najwa, sun shirya cikin school uniform za su tafi makaranta.

Murmushi Abba ya saki har sai da haƙoransa suka bayyana, yayin da ya ga Azima da Najwa, saboda sun burge shi sosai ganin kansu a haɗe babu tashin hankali a tare da su, da alama dai ba su san da labarin shari'ar da Umma take yi da shi ba. 
  Addu'a yake yi a cikin ransa, Allah ya raya masa su. Kuma Allah ya basu miji nagari, a ransa ya ƙudurce, ba zai yarda ɗayarsu ta yi karatun boko mai zurfi ba, da zarar sun kammala secondary school. Zai aurar da su, domin hankalinsa ya kwanta, don ba zai sake biyewa Umma ba ko ta ƙi ko ta so dole ne ya aurar da su Najwa da zarar sun kammala secondary school.

"Azima Najwa har kun shirya?" Da sauri suka juyo suka kalle shi, kafin su durƙusa har ƙasa a tare suka ce.
"Abba ina kwana?" 
   "Lafiya ƙalau! Ina fatan kuna lafiya?"
  "Lafiya ƙalau Abba!" 
  "Ma sha Allah! Ku zo sai na sauke ku ko?"

Cike da murna suka ce, "To Abba, mun gode.."
 "Ai babu inda za su bi ka, domin ba zan lamunci ka rinƙa ɗaukar min yara kana lalata min su ba.."
  Umma ce ta furtawa Abba wannan maganar, yayin da yake yunƙurin fita shi da su Najwa..

Juyowa yayi ya kalle ta, zuciyarsa na yi masa zafi da ƙuna, amma saboda gudun ɓacin rai, sai yayi shiru ya rabu da ita.
Hauwa'u Allah ya shirye ki!" Abinda ya iya faɗi kenan, sannan ya fice daga cikin falon.

Da sauri Azima da Najwa suka bi bayansa, suna jin kiran da Umma take yi musu. Amma suka yi kunnen uwar shegu da ita, kamar ba su take kira ba.
 Ta daɗe a tsaye cikin falon, ko za ta ga wacce za ta dawo wajenta, amma sai ta ji shiru. 

Leƙawa ta yi ta ga har ya ɗauke su a motarsa, sun fice daga gida.
  Ƙwafa ta yi ta ce, 
 "Indai ni ce za ku dawo ku same ni!" 
Ɗakinta ta koma, cikin matuƙar jin haushin Abba, da yanda ƴaƴanta suke nuna masa so, wanda ita ba haka ta so ba. Ta fi son ta ga suna nuna masa ƙiyayya, kamar yanda take nuna masa.

Tafiya suke a mota, amma babu mai magana a cikinsu. Abba tuƙi yake kawai, amma zuciyarsa cunkushe take da tunani kala-kala, bai san lokacin da hawaye ya fara kwaranya akan fuskarsa ba.

Hannu yasa a aljihu zai ɗauko handkercif, kawai sai jin saukar handkercif ɗin yayi akan fuskarsa ana share masa hawayen.
   A hankali ya kalli wanda yake share masa, Azima ce take share masa hawayen, yayin da ita ma suke zuba akan kyakkyawan dimple ɗinta.

Cikin raunin murya, kamar za ta fashe da kuka ta ce, "Abba ka yi haƙuri! Kome yayi tsanani yana tare da sauƙi. Kuma ka cigaba da haƙuri akan abinda Umma take yi maka, in sha Allahu Allah zai bayyana gaskiya, ka ji Abba..."

Ji yayi zuciyarsa ta fara yin sanyi, saboda ba ƙaramin kwantar masa da hankali kalamin Azima yayi ba. 
  Murmushi yayi ya dube ta ya ce, 
  "Aziman Abba! Nagode da wannan kalamin naki, Allah ya ba ku miji nagari, kuma Allah yayi muku albarka.."

Amsawa Azima ta yi har da Najwa da take gidan baya a zaune, dai-dai nan suka zo saitin makarantar su Azima, parking Abba yayi suka fito, sannan shi kuma ya ja motarsa yayi gaba.

Bai daɗe yana tafiya ba, ya ji motarsa tana slow. Tsayawa yayi ya fito ya duba, sai ya ga ashe tayar motar ce ta yi faci. Daga can tsallaken titi ya hango wani mai faci a gindin wata bishiyar darbejiya, mutane da yawa sun cika inuwar bishiyar. Domin rana ta fara yin zafi sosai, da ƙafafunsa ya taka ya nufi wajen mai facin, domin ya kirawo shi ya zo ya cire tayar ya ara masa wata, idan ya dawo sai ya bashi tasa ya ɗauki tashi idan ya gyara............


*Comment & share*

*~07069475482~*
: *BOKO NE SILA*
            _(Fiction story)_


*KING & QUEEN WRITING CHAMBER*
*(Sarki da Sarauniya writer's)*

*"We rule the world of writing*
https://www.facebook.com/profile.php?id=100063945240173

©️HUSSAIN YUSUF


Page 17.

Yayin da ya ƙarasa wajen mai facin, sai yayi sallama. 
   "Assalamu alaikum jama'a!" 
   Gaba ɗayansu suka amsa masa, suna zubo masa idanu, kamar masu kallon wata halitta daban.

"Don Allah ina mai facin nan?" 
  Wani mutum ne ya taso ya zo ya ce, 
 "Alhaji gani nan"
  Kallonshi Abba yayi ya ce, "Don Allah tayar motata ce, ta samu matsala kuma ina sauri..Shine nake son ka zo ka kunce ta, ka ɗaura min wata tayar na ƙarasa, kafin na dawo idan ka gyara tawa tayar sai na kawo maka taka,ka ba ni tawa.."

Murmushi mai facin yayi ya ce, "Alhaji in don wannan ne, kar ka damu, bari yanzu na zo na kwance ta..."

Ɗauko kayan kunce taya yayi, ya kalli Abba ya ce, 
  "Mu je ko?"
Juyawa Abba yayi da nufin tafiya, kawai sai jiyo matasan da suke zaune gindin bishiyar yayi suna cewa..

"Wancan shine Alhajin da yayi wa ƴar cikinsa ciki ko?" 
  Wani wanda ya fi kowa tsegumi ya ce, 
  "Shine mana, ba ka ga yana wani sunkuyar da kai ba? Kunƴar haɗa ido yake da jama'a..."

Wani ƙololon baƙin ciki ne ya zo ya tokare zuciyar Abba, bai san lokacin da hawaye mai zafi ya zubo masa ba. 
   Cikin sanyin jiki ya juya, ya bi bayan mai facin. Lokacin har ya fara kunce tayar motar.

Cikin ƙanƙanin lokaci ya kammala kuncewa, ya ɗaura masa wata tayar. 
 Godiya Abba yayi masa, sannan ya shiga motarsa ya ja ta da gudun gaske ya bar wajen. Zuciyarsa sai faman tafarfasa take, kamar za ta ƙone, saboda abunda ya ji matasan suna faɗi, hakan ba ƙaramin ɓaci ransa yayi ba.

Cikin ƙank'anin lokaci ya ƙaraso companyn nasu. Da sauri ya fito daga motar, domin tsayawar da yayi har ya makara, gani yayi har an shiga meeting ɗin shi kaɗai ake jira.
    Ba ɓata lokaci aka fara gabatar da meeting ɗin.

Chairman ɗin companyn ne ya fara magana, akan irin cigaban da Abba ya kawowa companyn. 
  "Saboda haka muka haɗa wannan taro, domin mu karrama shi tare da wasu jajurtattun ma'aikatanmu.."
   Murmushi Abba yayi tare da yiwa Allah godiya a cikin zuciyarsa. 

Manajan kamfanin ne ya fara magana cikin fushi.
  "Maganar gaskiya Inuwa bai cancanci wannnan promotion ba, domin duk matsayin da wannan kamfanin ya taka, mune sila ba Inuwa ba.."
    Marketing manaja ma ya miƙe cikin fushi ya ce..

"Ya za'a haɗa wannan taro na musamman, kawai don saboda mutumin da yake alfasha da ƴar cikinsa? Wallahi inda ace na san akan haka za'a tara mu Wallahi da ban zan zo ba.."

Yana faɗin haka ya tashi ya fice daga cikin meeting room ɗin. Da sauri Manaja ya bi bayansa, nan take sauran ma'aikatan ma suka yi koyi da su. Sai ya rage saura mutum huɗu kacal, Abba da Chairman na kamfanin, sai kuma wasu ma'aikatan guda biyu.

Runtse idanu Abba yayi, nan take wani zazzafan hawaye ya zubo masa. Zuciyarsa ta rinƙa bugawa da sauri, sunan Allah ya rinƙa ambata domin ya samu sassauci daga abinda yake ji.

Chairman ne ya kalle shi, cike da tausayawa, ya ce.
  "Inuwa ka yi haƙuri! Dukkan tsanani yana tare da sauƙi, kamar yanda dukkan duhu yake tare da haske. Ka cigaba da addu'a in sha Allahu Allah zai fitar da kai daga wannan mummunan zargin da jama'a suke jifanka da shi."

Shi dai Abba shiru yayi, bai iya cewa komai ba. Domin a halin da yake jinsa a ciki, ba zai iya magana ba. Domin bai san abunda zai ce ba.
   Chairman ne ya cigaba da cewa.

"Batun promotion kuma, babu gudu babu ja da baya. Kaine wanda ya cancanci wannan promotion, don haka ko suna so ko ba sa so, sai na baka. Na lura cutar hassada ce take damunsu, ka yi haƙuri komai mai wucewa ne.."
   Haka sauran ma'aikatan da suke wajen, suka rinƙa kwantarwa Abba hankali da kalamai masu taushi da sanyaya zuciya.

Nan take Abba ya ji zuciyarsa ta yi sanyi, godiya yayi wa Allah a zuciyarsa da shugaban kamfanin ya fahimce shi, har yake kwantar masa da hankali. 
   Da kyar ya iya buɗa baki ya ce.

"Nagode sosai da kulawarku a gare ni..Allah ya saka da alkhairi, su ma waɗanda ba su fahimce ni ba, Allah ya fahimtar da su gaskiya kuma ya ba mu ikon binta gaba ɗaya.."
   Gaba ɗayansu suka amsa da amin, sannan Chairman ɗin ya sallami kowa ya tafi.

Tunda Abba ya shiga office ya zauna, tunanin halin da yake ciki ya hana shi sukuni. Ji yayi ba zai iya aiwatar da aikin komai ba, ya daɗe a zaune yana tunani kafin ya tashi ya fita daga kamfanin. 
  Kai tsaye gida ya nufa, domin ya ɗan kwanta yayi bacci, ko zai samu sassauci a cikin zuciyarsa.

Umma ce a zaune gefen gado, ta zuba tagumi hannu tana ta tunani. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗauko wayarta, lalubo lambar Hajiya Amina ta yi.
   Calling ɗinta ta yi, sannan ta kara wayar a kunnenta..

Tun kafin ta yi magana, daga can b'angaren Hajiya Amina ta ce, "Ƙawata ina kan hany'ar zuwa gidanki, na kusa k'arasowa.." 
   Daga nan ta kashe wayar, ajiyar zuciya Umma ta sauke. Sannan ta shiga dakon jiran ƙawartata.

Cikin mintunan da ba su wuce talatin ba, Hajiya Amina ta ƙaraso. Da murna Umma ta tarbeta, bayan ta zauna ta kawo mata juice da ruwa mai sanyin gaske, kasancewar ana rana sosai a garin.
   Bayan ta sha ruwan nutsuwa ta zo mata, sai ta kalli Umma ta ce.

"Hauwa'u na ga kiranki, koda ba ki kira ni ba, ina nan da niyyar zuwa wajenki akan batun shari'ar da kike yi ke da mai gidanki Malam Inuwa.." 
   Ajiyar zuciya Umma ta sauke, sannan ta ce "Ke dai bari ƙawata! Wallahi zulumin kotun nan ya hana ni sukuni.."

Cike da mamaki Hajiya Amina ta kalli Umma ta ce, "Ke kuwa mene ya hana ki sukuni game da kotu, bincike ne fa za'a yi sannan a zartar da hukunci kan wanda ya faɗa.."

"Ni ba wannan ba ne ƙawata, Wallahi batun samun ƙwararren Lauya ne ya fi damuna, domin ban san inda zan samo jajurtaccen Lauya ba wanda zai tsaya ya ƙwato mana haƙƙinmu ni da y'ata ba..."

Murmushi Hajiya Amina ta yi, sannan ta ce.
  "Haba ƙawata! Tunda kina da ni menene kuma na fargabar samun ƙwararren Lauya? Ki kwantar da hankalinki, na samo mana Lauya amma mace ce ta ƙware sosai wajen iya magana, da kuma bincike. Saboda haka ki sha kuruminki, ranar da za'a sake zaman kotun za ki sha mamaki.." 

Dariya Umma ta yi, tare da miƙawa Hajiya Amina hannunta suka tafa, cike da tsantsar murna da farinciki.
   Kallon Umma Hajiya Amina ta yi ta ce, 
  "Shi gogan naki, ya samu nashi Lauyan?"
   "Oho masa! Da ya samu da kar ya samu, babu abinda ya shafe ni..." 

Sake tuntsurewa da dariya suka yi, suna tafawa. Hajiya Amina sai faman koɗa lauyar da ta samo wa Umma take, ita kuma Umma ji take kamar ana komawa kotu za'a yankewa Abba hukunci. 
   Haka ne yasa ta matsu ashirin da biyar ga wata yayi, domin ta ga yanda Abba zai yi da rayuwarsa. 

Suna nan zaune a falo, suna taɗinsu. Sai ga Abba ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, da kyar Hajiya Amina ta iya amsa masa sallamar Umma kuwa kawar da kai gefe ta yi, kamar ta ga ɗanyen kashi.
   Kwata-kwata ba su yi tsammanin shigowarsa a wannan lokacin ba, kuma ya shigo dai-dai lokacin da suke yin gulmarsa ko ya ji ko bai ji ba? Oho masa!.

Kallonsu Abba yayi kawai yayi murmushi sannan ya wuce ɗakinsa ya bar su nan a tsaye suna zazzare idanu, kamar wasu munafukai.
   Yana shigewa ɗaki, Hajiya Amina ta tashi tsaye, ta kalli Umma ta ce..

"Hauwa'u sai an jima tafiya zan yi, tunda mai gidan ya dawo.."
  "Haba ke kuwa ƙawata, muna cikin hirarmu mai daɗi za ki tafi ki bar mu? To ina ruwanki da dawowarsa, wani abun ya ce miki?" 
   "A'a ai gara na tafi tun kafin ya faɗa min, kin san Hausawa sun ce hany'ar lafiya a bita da shekara, don haka ni na tafi sai mun yi waya, ko kuma sai mun haɗu a kotu.

"To ƙawata bari na ɗan taka miki.." 
   A tare suka fita daga cikin falon, Umma sai faman zubawa Hajiya Amina zance take. Wanda ita ba ta fahimtar komai, domin ta matsu ta bar gidan saboda ganin Abba da ta yi, ta ga yayi mata kwarjini sosai. Shi yasa duk tsoronsa ya kamata, ba ta san me yasa duk lokacin da ta yi ido huɗu da Abba yake mata wani irin kwarjini ba....

*********
Ashirin da biyar ga wata, yau ne kotu za ta cigaba da saurarar ƙarar da Umma ta kai Abba. Saboda haka tunda sanyin safiya, ƴan jarida da ƴan gani da ido, suka hallara a kotu domin su ga yanda shari'ar su Abba za ta kasance.
   
  Domin zance duk ya karaɗe gari, wai wani malami kuma ma'aikaci ya yiwa ƴarsa ciki, yanzu haka uwarta shari'a take da shi shine zancen da mutane suke ta faman ce ku ce a kansa.

Wannan tsegumin ne yasa wasu suka zo kotun, domin su ga zahirin zancen da yake ta yawo a gari. A kafafen sada zumunta, da kuma bakunan mutane kowa da abinda yake faɗa akai, harda wanda bai faru ba ma faɗa ake yi.

Kowa ya gama hallara a kotun. Alƙali kawai aje jira ya shigo a fara gabatar da shari'ar.

Su Umma da Abba da su Aliyu duk sun shigo, Aliyu sany'e yake da uniform irin na Lauyoyi, zaune yake a tsakiyar wasu lauyoyin yana ta faman danna wayarsa kamar babu abinda ya dame shi

Bayan wasu ƴan mintuna sai ga Alƙali ya shigo, nan take kowa ya miƙe tsaye, bayan ya zauna sannan kowa ya zauna.

Magatakarda ne ya tashi ya fara karanto shari'ar, bayan ya gama ya miƙawa Alƙali takardar. Dubawa ya shiga yi, bayan ya gama sai ya ɗago kansa ya dube su ya ce.

"Lauyoyi za su iya gabatar da kansu..!"

Wata kyakkyawar budurwa na ga ta miƙe tsaye, sanye take da riga irin ta Lauyoyi, kanta kuma ta tattare gashinta a waje ɗaya, sannan ta ɗaura kallabin atamfar da take jikinta. Sannan ta ɗora hula irin ta lauyoyi akanta.

"Masha Allah!" Shine abinda na furta yayin da na ga wannan kyakkyawar baiwar Allah, a matsayin lauyar da Hajiya Amina take koɗawa.

Cikin siririyar muryarta ta buɗe baki ta ce,
  "Sunana Barrister Khadeeja Ishaq Auwal! Amma an fi kirana da Barr. Khady, ni ce wacce nake kare wanda yake ƙara.." 

Bayan ta zauna, sai Aliyu ya miƙe tsaye ya ce.
  "Sunana Bar.Aliyu Inuwa, ni ne wanda yake kare wanda ake ƙara.."
 Yana faɗin haka ya zauna.

Bayan Alkali ya gama rubuce-rubucensa, sai ya ɗago ya kalli lauyoyin ya ce.
  "Lauyan da zai fara Bismillah.."
  Tashi tsaye Barr.Khady ta yi, ta kalli Alƙali tana faɗin...

"Ina so kotu ta bani dama na yiwa Malam Inuwa mahaifin Fadila wasu tambayoyi.."
   Alƙali ya ce..
  "An ba ki dama! Kotu tana son ganin Malam Inuwa.." Alk'ali ya faɗa yana kallon jama'ar cikin kotun.

Cikin sanyin jiki Abba ya fito gaban kotun, cike da nutsuwa Barr. Khady ta dubi Abba ta ce...
  "Ko za ka iya faɗa min sunanka?"

"Sunana Malam Inuwa!"
   "Kaine mahaifin Fadila?"
"Ƙwarai da gaske nine mahaifin Fadila!"
  Barr.Khady ta ce..

"Me yasa tun farkon shari'ar nan ka ƙi amincewa kaine wanda yayi wa Fadila ciki, bayan ita Fadila ta yi mana bayanin yanda aka yi har ka yi nasarar yaudararta ta amince maka, ka biya buƙatarka...?"

A fusace Aliyu ya miƙe ya ce, 
  "Ya mai shari'a bai kamata lauya ya rinƙa takura wanda ake zargi ba, domin yana da ikon faɗin gaskiyar abinda ya sani, ba dole ba ne ya amince da abinda kowa ya amince ba nagode ya mai shari'a!......"
 
_*Ku yi haƙurin rashin jina kwana biyu, Wllh abubuwa ne suka yi min yawa. Amma in sha Allahu komai ya kusan dai-daita*_

Hussain Yusuf

07069475482
 *BOKO NE SILA*
           _(Fiction story)_


*KING & QUEEN WRITING CHAMBER*
   *(Sarki da Sarauniya writer's)*

*"We rule the world of writing"*
https://www.facebook.com/profile.php?id=100063945240173


HUSSAIN YUSUF

Page 18.

Kallon Barr. Khady Alƙali yayi ya ce, "Ki gyara kalamanki"                         Murmushi ta yi ta ce, 
  "Za'a kiyaye ya mai shari'a!" Sannan ta sake kallon Abba ta ce.
"Lokacin da ƴan'uwan Fadila suka tafi shopping, ita kuma matarka Hauwa'u ta tafi unguwa, ya rage sai Fadila ita kaɗai a cikin gidan, me ya dawo da kai gidan ba lokacin da ka saba dawowa ba?"

Wani gumi ne ya karyowa Abba, cikin sanyin murya ya ce.. "Gaskiyar magana ni ban san wannan lokacin da kike magana akai ba.."

Barr.Khady ta ce, "Ka tuna lokacin da matarka ta yi tafiya zuwa Kaduna, wajen wani kawunta?" Gyaɗa kai Abba yayi da sauri ya ce..."Ƙwarai da gaske na tuna lokacin!"

"To bayan tafiyarta me ya dawo da kai gida, bayan ba lokacin ka saba dawowa ba?" Shiru Abba yayi yana tunani, daga bisani ya ce.. "Ƙwarai na dawo gida a wannan lokacin, amma akwai abinda ya dawo da ni, na manta wasu takardun office ne, kuma ana buƙatarsu very urgent, shi yasa na dawo da kaina na ɗauka, ko tsayawa ban yi ba na fita..Sai da na ɗauko takardun ma na fito, sannan na ga Fadilar a falo tana kallo a TV."

Barr.Khady ta ce, "Amma ai ita Fadilar ta shaida mana cewa, ruwan wanka ka umarce ta da ta haɗa maka, yayin da take haɗa maka ruwan a cikin bathroom ɗin. Kawai sai ka faɗo ciki ka yaudareta da kalamanka har ka sa ta biye maka ka aikata alfasha da ita..."

Wani irin gumi ne mai zafi ya zubowa Abba, nan take hawaye ya wanke masa fuska. Cike da raunin murya ya dubi Barr.Khady ya ce, "Ban san lokacin da wannan abun ya faru ba, ina ɗaukar takarduna ficewa na yi ko minti biyar ban ƙara yi a cikin gidan ba.."

"Mai gadinka yana nan lokacin da ka dawo?" "Ƙwarai da gaske yana nan!" Barr.Khady ta ce, "Har lokacin da ka fito yana nan akan aikinsa?" Abba ya gyaɗa kai ya ce, "Ƙwarai da gaske yana nan a zaune kan kujera har na fito daga gidan!"

Juyawa Barr.Khady ta yi ta kalli Alƙali ta ce, "Ya mai shari'a ina son kotu ta bani dama, domin na yiwa mai gadi tambayoyi..." "Kotu ta baki dama!" 
 Kallonta kawai Aliyu yake yi, yana gyad'a kai, domin gaskiya al'amarin Fadila da Umma sun fara ba shi tsoro...

Bayan mai gadi ya fito ya tsaya a inda aka nuna masa, sai magatakarda ya tashi tsaye ya kalle shi ya ce, "Ya sunanka?" "Sunana Malam Sani" ya ce, "D'aga hannunka sama duk abinda na faɗa ka faɗa!" Da sauri ya ce "To"  tare da ɗaga hannun nasa amsa yana sauraron abinda magatakardan zai faɗa masa.

"Ni Malam Sani!" Nan take ya maimaita "Ni Malam Sani" "Na yi alƙawarin zan faɗi iyakar gaskiyata" "Na yi alƙawarin zan faɗi iyakar gaskiyata.." Magatakarda ya kalli Barr.Khady ya ce, "Bismillah!" Juyawa ta yi Barr.Khady ta fuskanci Malam Sani mai gadi ta ce..

"Malam ina son ka gabatarwa da kotu kanka" juyawa yayi ya kalli kotu ya ce, "Sunana Malam Sani, ina zaune a unguwar Hotoro nine mai gadin gidan Malam Inuwa.."
   "Malam Inuwa ya faɗa mama kana nan, lokacin da dawo gida ɗaukar takardu da yamma ko?" Gyaɗa kai yayi ya ce, "Ƙwarai da gaske ina nan, ni dama ba yawo nake yi sosai ba, idan kika ga bana nan to Hajiya ce ko Alhaji suka aike ni, ko kuma na zagaya..."

"Yawwa! Lokacin da ya dawo ɗaukar takardun minti nawa yayi kafin ya fito daga cikin gidan?" Tunani ya shiga, daga bisani ya ce, "Bai fi minti shida zuwa bakwai ba ya fito" shiru Barr.Khady ta yi daga bisani ta kalli Malam Sani mai gadi ta ce, " "Mun gode za ka iya komawa.."

"Ya mai shari'a iyakar tambayoyin da zan yi kenan!" kallon Barr.Aliyu Alƙali yayi ya ce, "Lauyan wanda ake ƙara ko kana da abin cewa?" Mik'ewa yayi ya ce, "Na'am ya mai shari'a!" Fitowa yayi ya tsaya ya kalli Alƙali ya ce, "Ya mai shari'a ina so kotu ta bani dama, domin na yiwa Fadila tambayoyi.."

"Kotu ta baka dama!" Fitowa gaban kotu Fadila ta yi ta tsaya. Cike da nutsuwa Barr.Aliyu ya kalle ta ya ce, "Fadila kin ce da  yamma ya dawo, ya ganki a cikin gidan har ya aikata alfasha da ke? Kuma yanzu mai gadin gidan ya shaidawa kotu cewa bai haura minti shida zuwa bakwai ba...?" 

Shiru Fadila ta yi ta kasa magana, daka mata tsawa Alƙali yayi ya ce, "Ke muke sauraro!" Fashewa da kuka ta yi cikin kukan ta shiga cewa, "Shine wanda yayi min ciki, kuma a lokacin da na faɗa ya zo min, shi ma mai gadi son ransa kawai ya faɗa..." Aliyu ya ce, "Yanzu kina nufin abinda mai gadi ya shaidawa kotu duk ba gaskiya ba ne?" 

Gyaɗa kai ta yi ta ce, "E haka ne ba gaskiya ba ne!" "Amma tunda kuke tare da mai gadi, kin taɓa jin ƙarya ta fito daga bakinsa?" A nan ma shiru ta yi, tana nazarin tambayar a cikin ƙwaƙwalwarta..
   Ganin ba ta da niyyar ba shi amsa ne yasa ya ce..

"Fadila yakamata ki daina wahalar da kotu,  ki fito ki faɗi gaskiyar wanda yayi miki ciki domin alamu sun nuna ba mahaifinki ba ne wanda yayi miki.." Kallonta yayi ya ce, "Za ki iya komawa!" Bayan ta koma Barr.Aliyu ya juya ya fuskanci Alƙali ya ce...

"Ya mai girma mai shari'a! Waɗannan tambayoyin kaɗai sun isa su nuna cewa Fadila ƙarya take ba mahaifinta ne yayi mata cikin ba, akwai wanda yayi mata kawai ba zata fito ta shaidawa kotu ba..Da wannan damar nake roƙon kotu da ta wanke Malam Inuwa daga zargin da jama'a suke yi masa, a matsayin wanda yake bibiyar ƴar cikinsa, nagode ya mai shari'a.." Daga nan ya koma ya zauna.

Kallon jama'ar kotun Alƙali yayi sannan ya kalli lauyoyi da waɗanda ake tuhuma ya ce, "Kotu ta ɗage wannan shari'a har zuwa goma sha biyu ga watan gobe, amma kafin a dawo lauyoyi su tabbatar sun gudanar da bincike kan yadda wannan al'amarin yake, su zo da gamsassun hujjoji da shaidu waɗanda za su fito da gaskiyar wannan al'amarin."

 Daga nan Alƙali ya sallami kowa, duk wanda ka gani albarkacin bakinsa yake faɗi kan wannan rikitaccen al'amari...
Wasu gani suke ba Abba bane yayi mata ciki, yayin da wasu kuma suke ganin shine ya aikata domin mugu ba shi da kama. Ƴan jarida kuwa kullum a bibiye suke da su, suna fitowa suka baibaye su da tambayoyi. Hawaye ne ya zubo daga idanun Abba, ya kasa magana, Aliyu ne ya zo ya ja hannunsa ssuka shiga cikin motarsa. Umma kuwa tsayawa ta yi tana yiwa Ƴan jarida tsarin yanda al'amarin yake.


*******
Tsaye Aliyu yake a cikin ɗakinsa, ya goya hannunsa a bayansa yana ta faman kai kawo a cikin ɗakin. Ya rasa ta inda zai fara bincikensa domin gano gaskiya, yana son ya sake yiwa Fadila tambaya a gida. Amma tsoron Umma ya hana shi ya tunkare ta, bayan haka kuma Fadilar ma ba za ta bashi haɗin kai ba..

Iska ya furzar daga bakinsa, a fili ya furta "Ta ina yakamata na fara?" Ɗaga kai sama yayi yana tunani, daga bisani ya ce, "Alhamdulillah! Ta makarantarsu yakamata na fara.." Nan take hankalinsa ya kwanta, bathroom ya shiga yayi wanka sannan ya ɗauro alwala. Ya daɗe yana salloli, tare da addu'a akan Allah ya bashi nasara akan wannan aikin da ya saka a gaba.

Bayan ya gama addu'oinsa, tashi yayi ya kwanta akan gadonsa yana karanto addu'ar kwanciya bacci. Bai daɗe ba bacci mai nauyi yayi awon gaba da shi, domin gajiya ce mai yawa a tare da shi.

Washe gari bayan ya tashi yayi sallah, da wuri ya shiga shiryawa domin aikine da shi ba kaɗan ba. Kuma ga shari'ar su Abba da ta sako shi a gaba, domin ya 'kudurce a ransa cewa dole ya nemo gaskiyar lamarin kafin a koma zaman kotu na gaba. Shi yasa ya jajurce sosai domin ya nemo gaskiyar lamarin cikin ƙanƙanin lokaci.

Yana shiryawa ya fito falo, ya tarar da Umma  ita da ƴaƴanta a zaune. Har ƙasa ya durƙusa ya gaishe ta, amsawa ta yi ba yabo ba fallasa, ko kaɗan bai damu ba, domin ya san kaɗan daga aikinta kenan. Har ya tashi zai fita, Azima da Najwa suka haɗa baki suka ce "Yaya Aliyu ina kwana?" Murmushin jin daɗi yayi ya ce, "Lafiya lau my sisters" yana faɗin haka ya fice daga cikin falon da sauri.
Harararsu Umma ta yi ta ce, "Banzaye waɗanda ba sa kishin uwarsu. Ku tashi ku bani waje.." Cikin sanyin jiki suka tashi, suka shige cikin ɗakinsu, sannan suka fara shiri tafiya school.

Yayin da Aliyu ya isa makarantar su Fadila, wato B.U.K. Sai ya rasa wanda zai tunkara da tambayoyinsa, kai tsaye kafteriya ya nufa. Yana zuwa ya hango wata budurwa a zaune ita kad'ai kan tebur tana cin abinci. Ba tare da shakkar komai ba ya k'arasa inda take. Sallama yayi mata, a can ƙasan maƙoshi ta amsa sallamar tana kawar da kai, murmushi Aliyu yayi ya ja kujerar da take fuskantarta ya zauna, sannan ya kalleta ya ce, "Sannu ƴan mata!"

Kawar da kai gefe ta yi ta ce, "Sannu dai! Amma me ya kawo ka nan za ka dame ni?" Murmushi yayi ya ce, "Ba wani abu ne ya kawo ni wajenki ba, tambaya ce kawai zan yi miki idan ba za ki damu ba.." Cike da mamaki ta kalle shi, sannan ta yi saurin cewa "Allah yasa na san abinda za ka tambaye ni!"

Koda jin haka, sai ya gyara zama cikin nutsuwa ya kalle ta ya ce, "Don Allah kin san Fadila Inuwa?" Da mamaki ta dube shi ta ce, "E na santa, amma waye kai da kake tambayarta?" Murmushi yayi ya ce, "Karki damu da sanin waye ni kawai ki bani amsar tambayar da zan yi miki."

"Amma ai yana da kyau na fara sanin waye kai, kafin na baka amsar tambayarka" "E, haka ne kina da gaskiya. Amma ki fara ba ni amsar tambayata sannan ni kuma na faɗa miki ko ni waye.."
  Cikin nutsuwa ta kalle shi, sannan ta ce..

"Ƙwarai na san Fadila Inuwa, amma ta fi wata biyu ba ta shigo school ba. Ƙawarta Mariya ta gaya mana bata da lafiya, yanayin karatu bai bar mu, mun je mun dubo ta ba...Amma kwanan nan nake jin wani zance, wai ciki ne da ita, kuma wai mahaifinta ne yayi mata, yanzu haka shari'a suke a kotu."

Gyad'a kai yayi ya ce, "Gaskiya ne maganarki, ana zargin mahaifinta da yi mata ciki. Amma alamu sun nuna ba shine wanda yayi cikin ba, kawai dai sharri ta yi masa.."
  Zaro ido budurwar ta yi ta ce, "Subhanallahi!" Ta faɗa tana dafe ƙirjinta.

Sai da ta dai-daita nutsuwarta, sannan ta ce, "Yanzu ita Fadilar ce ta yiwa mahaifinta wannan mummunan ƙazafin?" Gyad'a kai Aliyu yayi ya ce, "Ƙwarai da gaske, sunana Barrister Aliyu Inuwa, nine lauyan da yake kare mahaifin Fadila. Kuma ni ɗan'uwan Fadila ne, mahaifinmu ɗaya da ita. Yanzu haka na zo binciken wannan lamarin cikin makarantar nan, da fatan za ki bani haɗin kai, domin na gano gaskiyar al'amarin?"

Shiru ta yi na ɗan lokaci, kafin ta dubi Aliyu ta ce. "Zan baka haɗin kai ɗari bisa ɗari, kuma zan baka duk wani taimako, muddin ka buƙata daga wajena, amma wannan aikin ba zai yiwu ni kaɗai ba, dole sai da taimakon Mariya. Domin ita ma ƙawar Fadila ce a cikin makarantar nan.."

"Ok! Yanzu a ina zan ga Mariyar?" "Tana cikin makarantar nan, bari na kira ta a waya ta zo nan sai ka yi mata bayani.." Barr.Aliyu ya ce, "Da kin taimaka sosai kuwa.." 

Wayarta ta ɗauko daga cikin jakarta, nan take ta lalubo lambar Mariya. Bayan ta ɗauki wayar anan ta shaida mata cewa, ta zo kafteriya ta same su...Daga nan ta kashe wayar tata, ta kalli Barr.Aliyu ta ce, "Ba ka tambaye ni sunana ba?" Sosa kai Aliyu yayi ya saki wani ɗan murmushi ya ce.. 

"Na manta ne, yanzu sai ki faɗa min, tunda kin tuna min." Murmushi ta yi ta ce, "Nawa za ka biya na faɗa maka?" 
  "Wanne irin suna ne wannan?" Ta ce, "Sunana na daban ne ko a cikin mata, kuma suna ne mai tsadar gaske" murmushi yayi ya ce, "Ai kuwa zan so jin wannan ƙayataccen sunan!" 

"Ka biya yanzu sai na faɗa maka" "To na ji a faɗa min, idan na ji sunan ya burge ni sai na biya.." Wani ɗan fari ta yi da idanunta sannan ta ce, "Shikenan yanzun nan zan faɗa maka.."
  "To ina sauraronki!" 
Runtse fararen idanunta ta yi ta ce, "Sunana........"

_*©Hussain Yusuf*_

*~07069475482.~*
: *BOKO NE SILA*


*KING & QUEEN WRITING CHAMBER


HUSSAIN YUSUF

Page 19.

Sai kuma ta yi shiru, ta ƙi ƙarasawa. Cike da zaƙuwa Barr.Aliyu ya ce, "Ke na na ke sauraro" murmushi ta sake yi, ta ce, "Sunana NANA FATIMA BINTU" "Masha Allah! Suna mai daɗi.." Miƙo masa hannu ta yi ta ce, "To bani" chocolate ya ɗauko daga aljihunsa ya miƙa mata ya ce, "To ga shi na biya.."

Karɓa ta yi tare da cewa, "Wow! Kamar ka san ina matukar son choculaty.." Har ya  bud'a baki zai yi magana, sai ga Mariya ta iso wajen. Sallama ta yi musu, tare da neman kujera ta zauna. Kallon Aliyu ta yi ta ce, "Kamar kaine yayan Fadila yaya Aliyu ko?.." Gyaɗa kai yayi ya ce, "Ƙwarai ba kama ba ne nine nan.."

Ba tare da ɓata lokaci ba Fatima ta sanar da Mariya duk abinda ake ciki game da Fadila. Jinjina kai Mariya ta yi ta ce, "Tabbas biri yayi kama da mutum, lokacin da na je dubinta na ga kamar akwai abinda take ɓoyewa game da ita. Kwata² ba ta saki jiki da ni ba, har na baro gidan..." Shiru ta yi tana jinjina girman al'amarin a cikin ranta.

Kafin daga bisani ta ce, "Gaskiya Fadila ta tafka kuskuren da zai taɓa goguwa a cikin tarihin rayuwarta ba. Wannan abun da me yayi kama? Ta rasa wanda za ta yiwa ƙazafi sai mahaifinta?"
  Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke, kafin ya dube su gaba d'aya ya ce, "So nake ku taimaka mini, domin na wanke mahaifina daga zargin da ake yi masa. Yana cikin wani hali, kwata-kwata yanzu ba shi da nutsuwa. Ko da yaushe a cikin ɗimuwa da tashin hankali yake, duk inda ya wuce mutane sai faman shuna shi da baki suke suna zunɗensa akan laifin da ba shine ya aikata ba.."

"Tabbas za mu baka duk wani taimako da ka nema daga gare mu, matuƙar za mu iya..." Jinjina kai Aliyu yayi ya ce, "Yanzu za ku iya faɗa min saurayin Fadila a cikin makarantar nan?"
  Gaba ɗayansu shiru suka yi, daga can Mariya ta ja numfashi ta ce, "Gaskiya a iya tunanina babu wani saurayi da Fadila take kulawa a cikin makarantar nan.."

Fatima ta ce, "Gaskiya Fadila ba ta da saurayi a cikin school ɗin nan, suma mazan ko kusa da ita ba sa zuwa. Domin ba su ga fuskar  hakan a tare da ita ba, Fadila tana da matuƙar kwarjini a idanun mazan makarantar nan. Yanzu sai ta saka a kori ɗalibi idan ya fiye takura mata da yi mata shishshigi a al'amuranta..."

Da matuƙar mamaki Aliyu ya dube ta ya ce, "Ita Fadila ce mai saka wa a kori ɗalibi?" Gyaɗa kai suka yi a tare suka ce, "Ƙwarai da gaske ma kuwa!"
  Mamaki ne ya ƙara kama Aliyu ya dube su ya ce, "To ita Fadilar wace ita a cikin makarantar da har za ta saka a kori mutum?" 

Mariya ta ce, "Ba kowa ba ce amma wani Professor ne ya goya mata baya, ta taka kowa ta zauna lafiya..." Da mamaki Aliyu ya miƙe tsaye ya ce, "Professor fa kika ce?" Mariya ta ce, "Ƙwarai da gaske, shine ya ɗaure mata gindi ta yi duk abunda da ta ga dama a cikin makarantar nan, babu wanda ya isa ya hana ta, idan kuma mutum ya takura mata, yanzun nan za ta faɗa masa. Nan take a kori ɗalibi ko ɗan wanene, domin shine director ɗin makarantar.."

Cikin zaƙuwa Aliyu ya ce, "Ya sunan wannan Professor? Kuma menene alaƙarshi da Fadila da har yake yi mata irin wannan gata a cikin school ɗin nan?" Shiru suka yi gaba ɗayansu, daga bisani Fatima ta ce..

"Ina da amsar tambayarka ta farko, amma ta biyu sai dai mu je mu samu Deejah!" Numfashi Aliyu ya ja ya ce, "Ina sauraronki!" "Sunansa Professor Shareef Adam!" Da sauri Aliyu ya kalle ta ya ce, "Aikuwa na san wannan mutumin.." Mariya ta ce, "Dama sananne ne a ko'ina, domin malamin ƙasa da ƙasa ne..." Aliyu ya ce, "Ƙwarai da gaske, amma wacece Deejah? Yakamata mu gaggauta samunta, domin ina son sanin alaƙar Professor Shareef da Fadeela.."

Fatima ta ce, "Deejah wata ɗaliba ce a wannan makarantar, wacce ta san sirrin duk wani malami da yake cikin makarantar nan. Duk ɓoyayyen sirri na cikin makarantar nan Deeja ta san da shi, shi yasa muka ce a je wajenta wataƙila ta san alaƙar Fadeela da Prof.Shareef..."
   Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke, kafin ya tashi tsaye ya ce, "A ina za mu samu Deejar yanzu?" Mariya ta ce, "Wataƙila tana cikin labrary.." "Ok to mu je mu same ta.." Gaba ɗayansu suka fice daga kafteriyar suka nufi labrary wajen Deejah.

A zaune take akan kujera, littafi ne a hannunta tana karantawa. Idanunta manne da wani baƙin glass, babu alamun fara'a a fuskarta, tana da matsakaicin tsayi. Fara ce amma ba fari ƙal ba, farinta mai kyau ne.. Kyakkyawa ce amma idan ka kalle ta sau ɗaya ba za ka ga ainihin kyawun nata ba, sai ka daɗe kana kallonta.
 "Wajenki muka zo" Mariya ta faɗa tana kallonta, sai da ta gama yi musu kallon up and down, sannan ta buɗa ɗan ƙaramin bakinta ta ce, "Ina sauraronku me ya kawo ku?" 

Koda jin haka sai Aliyu yayi gyaran murya ya ce, "Ni ne nake nemanki" "Kai kuma? To me yasa kake nemana?" "Ki ba mu wajen zama mana, sai ki ji duk abinda yasa nake nemanki.." Nuna masa wata kujera da take facing ɗinta yi, zaunawa yayi Mariya da Fatima suma suka ɗauko kujeru suka zauna. 
  Sai da Aliyu ya dudduba kusa da su, ya ga babu kowa. Sannan ya dubi Deejah ya ce, "Tambaya ce zan yi miki, Allah yasa zan samu amsar tambayar tawa.." Deejah ta ce, "Ina sauraronka, Allah yasa na san amsar tambayar da za ka yi mini.."

Gyara zama Aliyu yayi ya ce, "Kin san Fadeela Inuwa?" Da mamaki Deejah ta kalle shi ta ce, "Ƙwarai ni na san Fadeela Inuwa, ta gaban goshin Prof.Shareef.." Da sauri Aliyu ya ce, "Kin san alaƙarta da Prof.Shareef?" Shiru ta yi kafin ta dubi Aliyu ta ce, "Ƙwarai da gaske na san alaƙar Fadila da Prof.Shareef, amma ba zan faɗa maka ba, sai ka faɗa min wanene kai? Kuma me yasa kake yi mini wannan tambayar?"

Nan take Barr.Aliyu ya sanar da Deejah duk abinda yake faruwa. Gyara zama Deejah ta yi ta kalli Aliyu cikin nutsuwa ta ce, "Gaskiya ƴar'uwarka ta tafka babban kuskure, saboda biyewa Prof.Shareef da ta yi..." Numfashi ta ja sannan ta cigaba da cewa, "Prof.Shareef hatsabibin mutum ne, ba shi imani ko kaɗan. Indai ya ƙyalla ido ya ga budurwa a cikin makarantar nan, to sai ya san yanda yayi ya rinjayeta ya rinƙa aikata alfasha da ita..Sannan idan yana kula yariny'a babu saurayin da yake kulata a cikin makarantar nan, idan kuwa saurayi ya ƙi jin magana yana kula macen da yake kulawa. Daga ranar ba za'a sake ganin saurayin ba, domin ya ɓatar da shi har abada ba'a san inda ya kaishi ba. Shi yasa samarin makarantar nan, ko kaɗan babu ruwansu da ƴan'matansa, sannan idan yana mu'amala da mace ƴar gata take zama a wajensa duk abinda take so yana bata kuɗi mota sutura babu abinda ba ya bata sannan duk wanda ya taka ta a makarantar nan, sai ya kawo ƙarshensa ko ɗan uban waye...Kuma duk wannan mummunar ɗabi'ar da yake yi, hukumar wannan makarantar bata sani ba, domin duk wata hany'a da ya san za'a gane shi duk ya bi ya toshe ta. Shi yasa har yanzu babu wanda ya san shi da wannan mummunar halayyar ta lalata da ɗalibai..."

"Yanzu kina nufin lalata yake yi da Fadila?" Deejah ta gyaɗa kai ta ce, "Ƙwarai da gaske ma kuwa, domin lokacin da ta shigo cikin makarantar nan ya ganta, tun daga lokacin yake bibiyarta har ya samu ya cika burinsa akanta..." Gaban Aliyu ya buga da sauri, domin ya san kama mutane irin su Prof.Shareef ba ƙaramin ganganci ba ne, domin yanzun nan sai rishe ya juye da mujiya..

Kallon Deejah yayi ya ce, "Yanzu kina nufin Prof.Shareef shine wanda yayi wa Fadila ciki?" "Ƙwarai da gaske shine wanda yayi mata ciki.." "To, me yasa ta ce Abba ne yayi mata..." Wani ɗan murmushi Dijah ta yi kafin ta ce, "Ba ka san wanene Prof.Shareef ba har yanzu, amma idan ka kai shi kotu za ka ji duk wannan bayanin daga wajensa ko wajen ƴar'uwarka Fadila..." Gyad'a kai Aliyu yayi kafin ya ce, "Yanzu ta yaya za mu kama Prof.Shareef? Kin san dai ba mu da wata hujja mai ƙarfi, wacce za mu tunkare shi da ita. Bayan haka kuma hatsabibin mutum ne, da zarar ya gano shirin da muke yi a kansa, sai ya kawo ƙarshenmu gaba ɗayanmu..."

Deejah ta ce, "Haka ne babu ɗan sandan da zai yi gangancin kama shi, ba tare da hujja ba. Koda hujjar ƴan sanda tsoron kama shi suke yi...Nima ina da babban burin da na ci akan Prof.Shareef wannan lokacin nake jira domin na ɗauki fansar abinda yayi min, saboda haka na ɗauki alƙawarin zan taimaka maka ɗari bisa ɗari domin mu kawo ƙarshensa a makarantar nan." Da sauri Aliyu ya kalle ta ya ce, "Me yayi miki har kike son ɗaukar fansa akansa?" Gyara zama ta yi kafin ta dube shi ta ce....

"Lokacin da Prof.Shareef ya nemi lalata da ni sai na ƙi amincewa, yayi fama da ni yayi naci akaina amma fur na ƙi amincewa. Koda ya ga haka kuma ya ƙyasa da ni sosai ya matsu ya ɗanɗani zumata, sai ya sa wasu matasa a makarantar nan suka sace ni a sirrance suka kaini wajensa bayan sun shak'a min wani abu mai fitar da mutum daga hayyacinsa. Yayin da aka kaini wajensa, lalatar ya sake nema domin na bashi haɗin kai ba abinda bai yi min alƙawari ba. Amma na ƙi amincewa, da yaga bani da niyyar bashi haɗin kai, nan take ya keta min alfarmata da mutuncina. Tun daga lokacin na sha alwashin sai na kawo ƙarshensa ko ta halin ƙaƙa, tun daga ranar nake bibiyarsa duk abinda yake aikatawa na sani, kullum tunanin hany'ar ɗaukar fansa nake akansa, amma na rasa ta inda zan fara. Lokacin da ka zo min da wannan maganar, sai na ga zan iya haɗa kai da kai, domin mu kawo ƙarshensa amma inda gizo yake saƙar shine ta ina za mu fara...?" 

Numfashi Aliyu ya ja kafin ya dubi Dijah ya ce, "Lallai Prof.Shareef ya cika hatsabibi, yanzu dai mu yi ƙoƙarin samun hujja mai ƙarfi wacce za ta gamsar da kotu kuma ta saka shi Prof.Shareef ɗin amsa laifinsa ko baya so..."
"Ta ina kenan za mu fara?" Deejah ta tambya. "Nima hany'ar da naje tunani kenan!"

Shiru suka yi gaba ɗayansu, domin ba su san hany'ar da za su ji ba domin samun hujjar da za su iya kama Prof.Shareef ba. Kallonsu Mariya da Fatima Aliyu yayi ya ce, "Ko kun san wata hany'ar?" Dariya suka yi gaba ɗayansu, da sauri Deeja ta dubi Aliyu ta ce, "Na gano wata sassauƙar hany'a wacce za mu iya samun hujjar da za mubiya tursasa shi ya je kotu ko kuma mu saka a kaishi..."
  "Wacce hany'a ce kenan?" Aliyu ya tambaya....

_*©Hussain Yusuf*_




*~07069465482.~*
: *BOKO NE SILA*
         _(Fiction story)_


*KING & QUEEN WRITING CHAMBER*
   *“(Sarki da Sarauniya writer's)”*


HUSSAIN YUSUF


Page 20.

Deejerh ta ce, "Hany'a d'aya ce zuwa biyu, idan muka bi su kuma muka samu nasara, to na tabbata Prof.Shareef da kansa zai iya miƙa kansa kotu. Ko kuma Y'an sanda su mik'a shi.." Gyara zama Aliyu yayi ya ce, "Ina sauraronki!" Deejerh ta cigaba da cewa, "Hany'a ta farko ita ce samun bidiyon baɗalarsu shi da Fadila, na tabbata idan har muka samu wannan bidiyo to komai ya zo k'arshe. Dole ya amsa laifinsa, kuma kotu dole ta yanke masa hukunci.." "Amma ta yaya za mu samu bidiyonsa shi da Fadila?" Murmushi Deejah ta yi ta ce, "Tambaya mai kyau.." Sannan ta cigaba da cewa, "Akwai wata budurwa mai suna Hadiza yanzu haka tana cikin makarantar nan, duk wata baɗala da Prof.Shareef yake yi tana yi masa bidiyo. Lokaci kawai take jira ta fara sakinsu a social media, domin ta ɗauki fansar abinda yayi mata. Na tabbata za'a samu bidiyonsa shi da Fadila a wajenta, kuma na san za ta ba mu haɗin kai ɗari bisa d'ari domin ta tsani Prof.Shareef kamar yanda ta tsani mutuwarta, kullum burinta shine: Ta yaya za ta kawo ƙarshensa? Amma idan har ta ji ƙudurinmu to za ta yarda ta bamu bidiyon ka ga mun samu hujja mai ƙarfi, wacce komai iya zancen Lauyansa bai isa ya ce wannan shaidar ƙarya ba ce, kuma na tabbata nan take Alƙali zai yanke masa hukunci.."

Jinjina kai Aliyu yayi ya ce, "Ƙwarai da gaske idan muka samu wannan bidiyon, shi kaɗai ya isa ya zama shaida a kotu" Deejah ta ce, "Haka ne amma ka san Hausawa sun ce, hannu da yawa maganin ƙazamar miya." Aliyu ya ce, "Me kike nufi kenan?" Gyara zama Deejah ta yi ta ce, "Abinda nake nufi anan shine; Prof.Shareef hatsabibin mutum ne, idan muka samo wannan shaida, to dole ne sai mun haɗa kai da wani babban ɗan sandan domin ya kamo shi, ya kawo shi kotu. To ka ga dole sai mun samu jami'in ɗan sanda, wanda babu ruwanshi da cin hanci da rashawa mun haɗa kai da shi ranar zaman kotu kawai ya ɗebi yaransa su kamo Prof.Shareef su kawo shi kotu ko baya so.."

Aliyu ya ce, "Kuma kin ga dole ne mu samu jajrutaccen ɗan sanda wanda ba zai ci amanarmu ba.." Deejah ta ce, "Ƙwarai da gaske ma kuwa, amma inda gizo yake saƙar shine; a ina za mu samo wannan ɗan sanda?" Shiru suka yi gaba ɗayansu, nan take suka faɗa kogin tunani. Daga bisani Deejah ta dubi Aliyu ta ce, "Na gano ɗan sanda da zai yi wannan aikin, ko ba'a biya shi ba na tabbata zai ji daɗin yanda zai wulaƙanta Prof.Shareef domin ya daɗe yana da buri akansa. Don ya d'auki fansa kan Prof.Shareef ya shiga aikin ɗan sanda, ka ga kuwa idan muka faɗa masa haka zai ji daɗi kuma zai riƙe mana amana har burinmu ya cika.." Aliyu ya ce, "Shi kuma me yayi masa?"

Deejerh ta ce, "Sunansa Inspector Auwal! Ta sanadiyyar Prof. Shareef mahaifinsa da mahaifiyarsa suka bar duniya..Lokacin da ya samu da ya nemi ƙanwarsa mai suna Asiya, sai ta ƙi amincewa. Yayi mata naci amma kwata² ta ƙi ba shi haɗin kai, haka yasa aka wasu samari suka kai masa ita, kamar yanda yasa aka yi min. Ba tare da ɓata lokaci ba, ya keta mata rigar mutunci. To sai aka yi a rashin sa'a ciki ya shiga, tsananin baƙin ciki da takaici yasa mahaifiyarta ta haɗiyi zuciya ta mutu. Baƙin cikin mutuwar mahaifiyarta yasa, shi ma mahafinta ya kamu da ciwon zuciya, bayan wasu y'an kwanaki shi ma ya bar duniyar. Tun daga ranar Inpector Auwal ya ƙuduri aniyar kawo ƙarshen Prof.Shareef. Amma ya kasa duk wata hany'a da ya bi, sai ya ga ba za ta yi masa ba, sai wani abokinsa ya bashi shawarar ya shiga aikin ɗan sanda wataƙila zai iya kawo ƙarshensa nan take kuwa ya bi shawarar abokinsa ya hau neman aikin ɗan sanda bai sha wahala sosai ba, ya samu aikin, har ya kai matsayin Inpector yanzu haka,ka ga kuwa ba zai ƙi karɓar tayinmu na kama Prof Shareef ba ko? Kuma na tabbata, ba zai ci amanarmu ba."

Aliyu ya ce, "Ƙwarai da gaske ma kuwa! Amma ta yaya za mu same su shi da Hadiza?" Deejah ta yi murmushi ta ce, "Ka bar komai a hannuna, zan ji da komai, idan na samo bidiyon zan turo maka ta whatsapp domin ya zamana kai ma kana da copy ɗinsa, sannan idan na samu Inspector Auwal. Zan haɗa ku sai ku yi magana akan irin shirin da za ku yi akan kama shi.."

Aliyu ya ce, "A gaskiya nagode miki sosai, domin ba don ke ba. Ban san yanda zan yi na nemo bakin zaren wannan shari'ar ba, amma sai ga shi ta sanadinki komai ya zo cikin sauƙi ba tare da shan wata wahala ba. Amma ki yi gaggawar nemo wannan bidiyon domin shine hujjarmu mai ƙarfi da zamu gabatar a kotu." Deejah ta ce, "Kar ka damu na yi maka alƙawarin yau ko gobe zan samo sai na turo maka."

Godiya sosai Aliyu yayi wa Deejerh, sannan suka yi exchanging ɗin number. Yayi mata sallama ya tafi, Mariya da Fatima suka yi masa rakiya, suna faɗin suma sun matsu a koma kotu domin su ga yanda idanun marasa gaskiya zai yi. Murmushi kawai Aliyu yayi, sannan ya karɓi numban kowacce daga cikinsu, domin su rinƙa zumunci sannan ya shiga motarsa ya bar makarantar zuciyarsa cike da tarin farinciki. Yana mamakin yanda komai ya zo masa da sauk'i a shari'ar nan, a wani b'angare na zuciyarsa yana ƙara godewa Allah da ya amshi addu'arshi cikin gaggawa domin ya san Allah ne kawai ya taimake shi, ya sauƙaƙa masa wahalar bincike.

Bayan ya isa gida, Umma ya tarar ita da ƙawarta Hajiya Amina suna tattaunawa akan zaman kotun da za'a yi sati mai zuwa. Murmushi Aliyu yayi, sannan ya ɗan rusuna ya gaishe su, kawar da kai Umma ta yi ta ƙi amsa gaisuwar. Sai Hajiya Amina ce ta amsa cikin sakin fuska tamkar babu wani abu a tsakaninsu. Wucewa ɗakinsa yayi, da ido Umma ta raka shi yana gama shiga ta ja wani dogon tsaki tare da cewa "Mtsss! Aikin banza, kai da mahaifin naka, za ku gane ba ku da wayo, idan aka koma kotu..."

Bayan Aliyu ya shiga ɗakinsa, wanka yayi ya canja kayan jikinsa. Sannan ya ɗauki key ɗin motarsa ya fito, Barr.Khady ya gani tare da su Umma sai faman tattaunawa suke akan shari'ar da ke gabansu.Suna ganinshi gaba ɗayansu suka yi shiru, suna masu zuba masa idanu, Barr.Khady ce ta yi ƙarfin halin ƙaƙalo murmushi ta dube shi ta ce, "Brr.Aliyu manya har an fito?" Cikin sakin fuska da fara'a ya amsa, har yana tambayarta ya aiki? Sannan ya saka kai ya fice daga falon, da saurin gaske.

Riƙe baki Hajiya Amina ta yi ta ce, "Ohh ni jikar Abu, anya kuwa yaron can bai taki wani abun ba? Na ga sai murmushi yake saki, kamar wata gonar auduga kamar babu abinda yake damunsa. Gaskiya ina tunanin ya taki wani abun, shi yasa yake irin wannan murmushin.." Ita ma Barr.Khady murmushin ta yi ta ce, "No ba wani abu da ya taka, kawai ƙarfin hali ne namu irin na Lauyoyi.." Jinjina kai Umma da Hajiya Amina suka yi, suna faɗin "Allah ya kyauta!"

Aliyu kuwa yana fitowa motarsa ya shiga, kai tsaye wani restaurant ya nufa. Abinci ya ci sannan ya fito, ya koma gida kayan jikinsa ya rage. Sannan ya miƙe akan faɗeɗen gadonsa nan take bacci mai nauyi ya ɗauke shi. Da la'asar ya farka wanka yayi sannan yayi sallah, bayan ya idar shiryawa yayi ya fita.
  
    Bayan kwana biyu Deejah ta turo masa bidiyon Fadila da Prof.Shareef yayin da suke aikata masha'arsu. Bidiyon ya kalla, sannan yayi murmushi domin fuskar Fadila da Prof.Shareef ga ta nan fayau kowa ya gani sai ya gane shi. Laptop ɗinsa ya ɗauko yayi copy ɗin bidiyon a cikin flash ya ajiye, sannan yayi wani murmushin samun nasara, waya ya ɗauko ya kira Deejah yayi mata godiya sosai...Ita ma murmushi ta yi ta ce, "Kada ya damu, ita ma ɗaukar fansar abin da yayi mata take yi, yanzu haka ta matsu lokacin zaman kotu yayi domin ta ga yanda Professor Shareef zai yi da rayuwarsa...

   Duk wannan abunda yake faruwa Prof.Shareef bai san abinda yake faruwa ba. Kullum abin nasa daɗa cigaba yake yi, yau idan yayi lalatarsa da wannan budurwar gobe da wata zai yi. Saɓon Allah a wajensa ba komai bane. Idan ka dube shi, za ka ga babu abinda ya dame shi, harkarsa yake yi hankali kwance alhalin bai san ƙarshensa ya kusa zuwa ba.

******
A kwana a tashi babu wuya a wajen Allah, yau ashirin da biyar ga wata. Saboda haka yau ne za'a yi zaman kotu na ƙarshe game da shari'ar su Abba. Tun sassafe mutane suke zuwa kotun, domin ganin yanda shari'ar za ta kasance. Bayan kowa ya hallara, shigowar Alƙali kawai ake jira, bayan wani ɗan lokaci sai ga shi ya shigo.Nan take aka magatakarda ya tashi, ya gabatar da shari'ar, sannan Alk'ali ya shiga gudanar da shari'ar...Kallon lauyoyi Alƙali yayi ya ce, "Lauyan da zai fara Bismillah!" Nan take Barr.Khady ta mik'e tsaye ta ce, "Ya mai girma mai shari'a ina so kotu ta bani dama na gabatar da shaiduna.." Ɗan rubutu Alk'ali yayi sannan ya ce, "Kotu ta baki dama..."

Kallon jama'ar kotun Brr.Khady ta yi ta ce, "Ina Azima da Najwa? Su fito gaban kotu" cikin sanyin jiki Azima ta fito, sannan Najwa ta biyo bayanta, bayan sun tsaya a inda aka nuna musu. Sai Barr.Khady ta dubi Azima ta ce, "Za ki iya yiwa kotu bayanin yanda kika iske mahaifinki tare da ƴar'uwarki Fadila a cikin wani irin yanayi..?" Fashewa da kuka Azima ta yi, cikin kukan ta shiga cewa, "Gaskiya mahaifina ba fasiƙi bane! Bai aikata komai da Fadila ba.." Da tsantsar mamaki Brr.Khady ta dubi Azima ta ce, "Ki daure ki tuna, ki daina jin tsoron komai babu abinda zai same ki.."Azima ta ce, "Ni ba iya abinda zan iya tunawa kenan, Abbanmu bai aikata komai da Fadila ba.." Barr.Khady ta ce, "Ki nutsu ki kalle ni, ki daina kallon jama'ar kotun ki daure ki yi mana bayani.." A fusace Barr.Aliyu ya mik'e ya ce, "Ya mai girma mai shari'a, yakamata lauya ya daina tilastawa mutum sai ya faɗi gaskiya bayan kuma gaskiyar ce yake fad'i.." Alk'ali ya ce, "Ki gyara kalamanki.." Ajiyar zuciya Barr.Khady ta sauke, sannan ta ce, "Za'a gyara ya mai shari'a!" Sannan ta kalli Najwa ta ce, "Ke fa za ki iya tunawa ki yiwa kotu bayani tunda ƴar'uwarki ta kasa bayanin?." Da sauri Najwa ta girgiza kai hawaye yana zuba a fuskarta ta ce, "Nima ban san komai ba, dama Umma ce ta ce mu zo mu bayar da shaida, amma ba mu san komai ba.." Barr.Khady ta ce, "Shikenan tunda kun kasa bayani, ku koma ku zauna.." Sannan ta juya ta kalli Alk'ali ta ce, "Na gama ya mai shari'a!"..

      Daga nan ita ma ta nemi waje ta zauna, tunda Azima da Najwa suka zauna Umma take harararsu. Sunkuyar da kai kawai suka yi, suka kasa haɗa ido da Umma kwata² saboda ƙin bin umarninta da suka yi. Daga nan Barr.Aliyu ya miƙe tsaye ya dubi jama'ar kotun, sannan ya dubi Alk'ali ya ce, "Ya mai girma mai shari'a! Ba Malam Inuwa ne yayi wa Fadila ciki ba, hasali ma bai san wanda yayi mata ba.." Koda jin wannan magana, gaba ɗaya hankalin jama'ar kotun ya dawo kansa, buɗa baki Alk'ali yayi ya ce, "Wanene yayi mata cikin, tunda ba mahaifinta bane?"

Barr.Aliyu ya ce, "Professor Shareef Adam! Shine wanda yayi mata cikin, sannan ya tursasata ta yiwa mahaifinta ƙazafi.." Da sauri Alk'ali ya cire farin glass ɗin da ke manne a idanunsa, cike da tsantsar mamaki ya dubi Brr.Aliyu ya ce, "Shareef Adam fa ka ce?" Brr.Aliyu ya gyaɗa kai ya ce, "Ƙwarai da gaske ya mai shari'a! Shine wanda yayi mata cikin, kuma ya tursasata ta hany'ar yi mata barazana, ta yiwa mahaifinta ƙazafi..." Wani gumi ne ya karyowa Alk'ali, hannu yasa ya share, kana ya dubi Brr.Aliyu ya ce, "Kana da gamsashshiyar sheda akan shine haƙiƙanin wanda yayi mata cikin?" Kafin Brr.Aliyu yayi magana Umma ta tashi, cikin fushi ta ce, "Ya mai girma mai shari'a! Kada ka yarda da zancensa, kawai dai ya je ya shiryo ƙarya da gaskiya don ya wanke mahaifins..." "Keeee!" Alk'ali ya daka mata tsawa ya ce, "Nan ba kasuwa bace, gidan adalci ne saboda haka dole mu tsaya mu saurare shi, idan kika ƙara yin magana anan, sai hukunci ya tabbata akanki.." Koda jin haka sai ta yi shiru, tana wani irin huci tamkar wata zakany'a, nan take ta ji a cikin ranta da tana da iko, da sai ta je ta shaƙe Aliyu shi da mahaifin nasa sun mutu gaba ɗaya saboda tsananin haushinsu da take ji.."

Kallon Aliyu Alk'ali yayi ya ce, "Brr.Aliyu! Za ka iya gabatar mana da shaida akan haka? Domin gamsu da abinda kake gaya mana?" Gyaɗa kai Aliyu yayi ya ce, "Ina da gamsashshiyar sheda akan haka, sheduna suna da yawa, amma zan so kotu ta bani dama na gabatar da shaidu guda biyu kacal daga cikinsu.." Alk'ali ya ce, "Kotu ta baka dama!" Kallon Inspector Auwal Brr.Aliyu yayi ya ce, "Inspector Bismillah!" Da sauri kuwa Inspector ya fice daga cikin kotun..........

_Ku yi haƙuri bisa rashin samun update kullum, Wllh ina cikin busy me yawa ne, shi yasa bana iya yin typing kullum sai na samu lokaci, ku yi haƙuri na san ba kwa jin daɗi amma dole ne ya saka.🙏🙏_


_*©Hussainyusuf*_
    *~07069475482.~*
: *BOKO NE SILA*
           _(Fiction story)_




*KING & QUEEN WRITING CHAMBER*
  (Sarki da Sarauniya writer's)


HUSSAIN YUSUF


🅿️age.......21.


Ba jimawa sai ga shi ya shigo da Prof.Shareef hannunsa ɗaure da ankwa. Gaba ɗaya hankalin jama'ar kotun ya dawo kansa, kowa da abinda yake saƙawa a cikin ransa game da wannan al'amari. Shi kuwa Prof.Shareef ya kasa had'a ido da mutane, domin yau ne karon farko da ya ji yana kuny'ar mutane a rayuwarsa. Nuna masa wani guri Brr.Aliyu yayi ya tsaya, nan take Inspector ya kunce masa ankwar da ke hannunsa, bayan ya tsaya sai Brr.Aliyu ya kalli Alk'ali ya ce, "Ya mai girma mai shari'a! Wannan shine shaidarmu na farko, domin da kansa ya amsa laifinsa kuma ya yarda cikin da ke jikin Fadila cikinsa ne..."

Alk'ali ya kalli Prof.Shareef ya jinjina kai kafin ya ce, "Shin Prof.Shareef ka yarda cikin da yake jikin Fadila cikinka ne, kaine ka yi mata?" Prof. Ya gyada kai ya ce, "Ƙwarai da gaske cikina ne, ni ne na yi mata ba mahaifinta ba ne.." Nan take kuwa kotun ta hargitse da kace nace, kowa ya rinka fad'in albarkacin bakinsa akan wannan al'amari.. Alk'ali yayi tsawa nan take surutun ya lafa, kallon Fadila Alk'ali yayi ya ce, "Da gaske Professor Shareef ne wanda yayi miki ciki?" Wani zazzafan hawaye ne ya zubo daga idanunta, a hankali ta gyad'a kai ta ce, "Shine yayi min!"

Barr.Aliyu ya ce, "Ya mai girma mai shari'a ina so kotu ta bani dama, na gabatar da shaidata ta biyu.." Alk'ali ya ce, "Kotu ta baka dama" nan take Brr.Aliyu ya ɗauko wani d'an ƙaramin flash daga cikin aljihunsa, Inspector ya miƙo masa laptop. Flash ɗin ya saka jikin laptop ɗin, sannan ya kunnawa Alk'ali bidiyon Fadila tare da Prof.Shareef. Da sauri Alƙali ya runtse idanunsa, ya kawar da kansa gefe yana fadin sunan Allah, ya cewa Brr.Aliyu yayi sauri ya ɗauke, nan take ya ɗauke laptop daga gaban Alk'ali sannan ya nunawa sauran lauyoyi tare da magatakarda, sannan ya nunawa Abba. Runtse idanu Abba yayi, a zuciyarsa yana kiran sunan Allah, wai yau ƴar cikinsa ce ake aikata alfasha da ita, har ana ɗaukarsu a bidiyo ana yaɗawa ko'ina. Bai san lokacin da hawaye ya wanke masa fuska ba, takaici da baƙin ciki suka mamaye zuciyarsa...

Bayan kowa ya gama gani, sai Barr.Aliyu ya kashe sannan ya kalli Alk'ali ya ce, "Ya mai girma mai shari'a! Wannan kaɗan ka gani daga irin mugayen hali na Prof.Shareef." Jinjina kai Alk'ali yayi ya kalli Fadila ya ce, "Fadila ya haka kuma? Me cuta daban mai shan magani kuma daban? Professor Shareef shine wanda yayi miki ciki, amma kika juyar da cikin ya koma kan mahaifinki, jama'a suna ta zaginsa akan laifin da ba shine ya aikata ba, anƴa kuwa Fadila kina so ki samu rahamar Ubangijin talikai?" Fashewa da kuka Fadila ta yi, da kyar ta rarrashin kanta ta yi shiru, sannan ta ce, "Ya mai shari'a! Wallahi ba yin kaina bane, tilasta ni yayi.." Alƙali ya ce, "Ki buɗa baki ki yiwa kotu bayani sosai yadda za mu fahimta..." Sake rushewa da kuka ta yi, har sai da Alƙali ya daka mata tsawa sannan ta yi shiru.

Tana sheshsheƙar kuka ta shiga cewa, "Tun lokacin da na shiga makarantar nan, ya hau bibiyata duk motsina akan idonsa nake yi, haka kawai sai yayi mana jarrabawa, yana sane zai bani carry over. Idan na je na kai masa ƙorafi, sai ya ce min sai ma bashi haɗin kai, ni kuwa sai na ƙi. Kullum a haka muke rayuwa da shi, har wata rana ya aiko kirana ofishinsa. Da kamar ba zan je ba, har dai na daure zuciyata na je. Ina zuwa kamar yanda na yi zato, buƙatarsa ya bijiro min da ita, nan take kuwa na ƙi amincewa. Tashi tsaye yayi da kansa ya rufo ƙofa, sannan ya juyo ya kalle ni ya ce, "Ko ki amince da buƙatata yanzun nan, ko kuma yanzu na yi miki fyaɗe na saka a ɗauke ki a kai can waje a cillar da ke ko kuma na kashe ki gaba ɗaya na jefar da gawarki bayan na yi miki fyaɗen.."
   Nan take tsoro da fargaba, suka ɗarsu a zuciyata. Ina da buri a rayuwa, shi yasa ko kad'an bana son a yi min zancen mutuwa. Saboda haka lokacin da na ji yayi min barazanar kisa, ban san lokacin da na amince da buƙatarsa ba, ya aikata alfasha da ni ba tare da son raina ba.

Bayan ya gama buƙatarsa ta biya, sai ya ɗauki kuɗi masu yawa ya bani. Ya ce, "Indai zan rinƙa amincewa da buƙatarsa kullum, zai rinƙa bani kuɗin da za su ishe ni rayuwar jin daɗi, kuma zai aure ni na zama matarsa.." Ni kuwa cike da tsananin murna, na ɗauki kuɗaɗen da ya bani na saka a jakata, sannan na yi masa godiya tare da yi masa alƙawarin gobe ma zan dawo indai zai sake bani irin kuɗaɗen nan da ya bani yanzu.. Nan take kuwa yayi min alƙawarin indai na dawo gobe zai linka mini yawansu, sannan yayi min alƙawarin babu wani saurayi da ya isa ya rinka kulani a cikin makarantar nan, ya ce duk saurayin da ya takura mini na faɗa masa zai yi maganinsa ko ɗan uban waye, sai ya kore shi daga makarantar nan. Sannan ya gargaɗe ni akan na riƙe masa sirri, kada na bari wani ya san abinda yake tsakanina da shi.

Yayin da na je gida da kuɗaden da Professor ya bani, sai na nunawa Umma. A tunanina za ta yi min faɗa, sai na ga tana ta murna da farin ciki anan na shaida mata cewa yayi min alƙawarin zai aure ni. Saboda tsananin murna har da rawa sai da Umma ta yi, ta rinka cewa "Dama ni na san ban haifi mai ƙashin tsiya ba, mai ƙashin arziƙi na haifa. Wallahi ki saki jikinki ki ci arziƙi ki more rayuwarki..." Wannan maganar ta Umma, ita ce ta fitar da duk wani tsoro da fargabar abinda muka aikata ni da Prof.Shareef. Tun daga ranar na zama tamkar matarsa, duk lokacin da ya so zai neme ni ya biya buk'atarsa ya bani kuɗaɗena.. Kullum idan na yi masa maganar alƙawarin aurenmu, sai ya ce min na yi hak'uri akwai lokaci, idan lokacin yayi da kansa zai nemi iyayena su yi maganar auren namu...

Ƙawayena musamman Mariya da Fatima sun yi ƙoƙarin fahimtar da ni cewa, yaudarata Prof.Shareef yake yi. Amma kwata² na kasa fahimtarsu, sai na ga kamar ma hassada ce suke yi min akan zan auri Professor. Haka yasa na raba k'afa da su na sake ƙawaye, na watsar da aminaina Fatima da Mariya, amma duk da haka Mariya tana kula ni ita ba ta watsar da ni ba, duk da irin wulaƙancin da take fuskanta daga wajena. Kuma kullum muka zauna nasiha take yi min akan na bi duniya a sannu, amma sai na yi kunnen uwar shegu da ita, Fatima kuwa tuni ta watsar da ni, ta shafe ni daga babin rayuwarta kwata². Ni kuwa bani da ƙawaye a cikin makarantar nan, sai ƴaƴan masu hannu da shuni, domin ina da kuɗi duk abinda suka yi na bajinta nima nan take zan yi da kuɗina, ko kuma na saka Professor yayi min.

Haka a kwana a tashi, muna tare da shi. Yana bani duk abinda nake buƙata, mota ce kawai ban siya ba saboda kada Abba ya fahimci halin da nake ciki. Umma kuwa kullum idan na kawo mata kuɗin da na samo a wajen Pro.Shareef, sai dai ka ga tana ta murna, bata taɓa tambayata dalilin da yasa yake bani kuɗi masu yawa haka ba. Sunkuyar da kai Umma ta yi, ta kasa haɗa ido da Abba, jinta take tamkar a cikin ruwa take zaune saboda tsananin kunƴar da ta rufe ta lokaci guda. A hankali ta d'ago da kanta, karaf idanunta suka sauka a cikin na Abba, suka yi ido huɗu. Da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa, a zuciyarta kuwa har ta fara nadamar biyewa ɗiyarta da ta yi har wannan abun ya faru. Fadila ta cigaba da cewa,
muna tare kullum yana waƙar zai aure ni, amma ko kaɗan ban ga niyyar haka a tare da shi ba. Kwatsam! Wata rana cikin dare, na tashi da matsanancin ciwon kai da tashin zuciya, ga wani irin zazzaɓi mai zafin gaske da ya gauraye jikina.

Lokaci guda na fita daga hayyacina, da kyar na iya tashi na ɗauko panadol na sha. Cikin ikon Allah, sai zazzaɓin ya ragu. Sai dai kasalar da rashin ƙarfin jiki, a haka na samu bacci mai nauyi ya ɗauke ni. Da gari ya waye, sai na sanar da Umma cewa bani da lafiya zan je asibiti a duba ni. Ba tare da wani dogon tunani ba, ta ce min "A dawo lafiya!" Yayin da na isa asibitin, na samu likita na sanar da shi abinda yake damuna. Tambayoyi yayi min, tare da gwada ni, gwajin farko ya tabbatar min ina ɗauke da juna biyu na wata uku...Iyakar tashin hankali na shige shi, ba kaɗan ba. Ban tsaya jin bayanin da likitan yake yi min ba, na ɗauki takardar gwajin na fice daga asibitin cikin tsananin tashin hankali.

Kai tsaye makaranta na nufa, ina zuwa na wuce ofishin Prof.Shareef. Gani na da yayi cikin yanayin da bai saba gani na ba, nan take hankalinsa ya tashi ya hau tambayata abinda yake damuna. Takardar gwajin na miƙa masa, ba tare da na ce da shi komai ba. Karɓa yayi ya duba, bisa ga mamakina maimakon na ga hankalinsa ya tashi kamar yadda nawa ya tashi, sai na ga ya saki murmushi. Cike da tsantsar mamaki na dube shi na ce, "Ya na ga kana murmushi, maimakon na ga kai ma hankalinka ya tashi?"
 
*Happy Eid al Adha!*
 _*May the great Allah prosper the work of your hands.*_
 *Enjoy  this joyous feast!*

_Comment and share_

*HUSSAIN YUSUF*
07069475482.
: *BOKO NE SILA*
           _(Fiction story)_



*KING & QUEEN WRITING CHAMBER*
   (Sarki da Sarauniya writer's)

*HAPPY EID MUBARAK☪️*
*Allah ya maimaita mana amin*


HUSSAIN YUSUF

🅿️age.......22.

Buɗa bakinsa keda wuya sai cewa yayi "Gaskiya Fadila kin bani dariya! Sai ki rinƙa yin abu kamar ba wayayyiya ba? Ki zo kawai mu je a zubar da cikin ba tare da kowa ya sani ba.." Zuwa wannan lokacin har ya fara bani haushi, cikin fushi na dube shi na ce, "Ba zan ƙara gangancin aikata wani laifin bayan wannan ba, kawai ka fito ka aure ni tun kafin cikin nan ya bayyana kowa ya gani.." Wata ƴar dariya yayi irin ta cikakkun ƴan duniya ya ce, "Ai ba zan taɓa aurenki ba Fadila, ba zan iya aurenki ba har abada, domin bana mu'amala da mace a waje, sannan kuma na aure ta na kai ta cikin gidana, wannan abun impossible.." Gani na yi duniyar tana juya min, na rasa inda zan saka kaina. Gani nake duk wannan abun a mafarki yake faruwa, ba'a zahiri ba. Addu'a na shiga yi akan Allah ya farkar da ni, daga wannan mummunan mafarkin da nake yi.

Da kyar na iya ɗaga hannuna, na nuna shi da yatsa muryata tana rawa na ce, "Professor! Me nake jin kana faɗi yanzu? Me kake nufi? Ba zaka aure ni ba?" Cike da gadara ya ce min "Ƙwarai da gaske Fadila ba zan aure ki ba, kuma ina so na gargaɗe ki akan wannan cikin da yake jikinki.." Da sauri na kalle shi, cike da tsantsar mamaki. A cikin zuciyata na ce "Gargaɗi kuma? To wanne irin gargaɗi yake nufi?" Daga nan ta dakata da labarin, ta fashe da wani irin kuka mai cin rai, da tsuma zuciyar duk wani mai sauraro. Ta daɗe tana kukan, sannan Alk'ali ya dube ta ya ce, "Fadila ke muke sauraro! Ya aka yi kuma kika ce mahaifinki ne yayi miki cikin alhalin ga wanda yayi miki? Me yasa kika zaɓi ki saka mahaifinki a cikin damuwa? Kuma wanne sharaɗi ya gindaya miki. Kotu tana sauraronki ki cigaba da bayani..." Daga nan ta cigaba da cewa...

Idanunshi ne suka firfito waje, lokaci guda ya canja daga siffarsa fara'ar da take fuskarsa gaba ɗaya ta ɗauke, tamkar ruwan sama. Idanunshi ne suka kaɗa suka yi jajur, juyawa yayi ya fara tafiya, ya nufi ƙofar fita daga ofishin. Yana zuwa daf da ƙofar, sai ya rufota ya saka key ya kulle. Sannan ya dawo inda nake tsaye ina kallonsa, domin ban san mai yake shirin aikatawa a kaina ba. Ɗan ƙaramin wardrobe ɗin office ya buɗe, ya ɗauko wata zundumemiyar kaifaffiyar wuƙa ya nufo inda nake tsaye. Cikin tsananin firgici da tashin hankali na fara ja da baya, a hankali ina ja da baya yana nufo ni da wuƙa tsirara a hannunsa. Addu'a na fara yi a cikin raina, akan Allah ya kuɓutar da ni daga sharrin wannan azzalumin bawan nasa. Kwata² bakina ya kasa furta kalmar komai, sai faman motsi nake yi da shi amma na kasa bashi haƙuri. 

A hankali yana biyo ni ina ja da baya, har na ji bangon da yake bayana yayi min waigi. Cike da tsananin tashin hankali da firgici, na buɗe bakina na ce, "Professor na don Allah ka yi haƙuri ka rabu da ni, karka kashe ni ka yi haƙuri don All..." Shiru na yi ina haɗiye wani yawu da ya tsaya min a maƙogwaron, sakamakon wuƙar da ya ɗora min a maƙoshina, motsi kaɗan zan yi wuk'ar ta yanke min wuyana. Idanu kawai na zuba masa, ina yi masa alama da hannu alamar yayi haƙuri ya rabu da ni. Sai da ya gama yi min barazana, sannan ya dube ni ya fara yi min magana da kakkausar murya ya ce, "FADILA wannan gargaɗi ne na yi miki, akan karki kuskura sunana ya fito a lokacin da ake tuhumarki wanda yayi miki ciki...Idan kuwa har kika sake kika ambaci sunana, Wallahi sai na kasheki, na kashe iyayenki da ƴan'uwanki, kuma sai na wahalar da ku sannan zan rinƙa yi muku kisan gilla, kisan wulaƙanci wanda ba'a taɓa yiwa wata halitta ba sannan na ɓatar da gawarwakinku gaba ɗaya yanda babu wani mahaluƙi da ya isa ya gano inda kuke, balle asirina ya tonu!..."

Cike da tsananin tsoro na dake zuciyata na dube shi na ce, "Barazanarka ba za ta taɓa yin tasiri a wajena b...." Da sauri ya daka min tsawa ya dube ni cikin fushi ya ce, "Fadila ko kad'an ba barazana nake yi miki ba, ina faɗa miki gaskiyar abunda zai faru da ke ne, idan har kika tona min asiri Wllh Fadila ba zan barki ba ke da ahalinku gaba ɗaya sai na hallakaku..." Hawaye ne ya zubo daga idanuna, na dube shi cikin raunin murya ina kuka na ce, "Idan ban sanar da iyayena gaskiyar wanda yayi min ciki ba, wa kake so na sanar da su..?" Wani ɗan murmushi yayi ya ce, "Duk wanda ya tambayeki waye yayi miki ciki? Ki ce mahaifinki ne Malam Inuwa yayi miki...!" Da sauri na dafe ƙirjina, da ya buga da ƙarfi, cikin tsananin tashin hankali na dube shi hawaye ya cika fuskata na ce, "Professor me kake nufi? Babu ruwan mahaifina a cikin wannan lamarin, saboda haka karka ƙara sako shi cikin wannan al'amarin.." Na faɗi haka cikin masifa, ina aika masa da harara.

Murmushi yayi ya dube ni ya ce, "Ko kin ƙi, ko kin so dole ki faɗawa mahaifiyarki da sauran jama'a cewa mahaifinki ne yayi miki ciki. Idan kuwa ba haka ba, kika yi min gardama kika ƙi faɗin sunansa, to hukuncin da zai biyo baya ba mai daɗi ba ne, domin shi zan fara kashewa, sannan na kashe mahaifiyarki sannan ƴan'uwanki. Ke kuma sai na gama ƙunsa miki baƙin ciki, sannan na kashe ki. Idan kuma kina shakkar abinda na faɗa, to ki ƙi bin umarnin da na baki..." Durƙushewa na yi a wajen na fashe da wani irin kuka, na hau roƙonsa akan ya janye wannan umarnin nasa a kaina, domin yayi tsauri da yawa. Maimakon na ga ya sassauta min, sai yayi murmushi ya dube ni ya ce, "Fadila kenan! Har yanzu ke yariny'a ce, kuma tunaninki ragagge ne, ba ki san dalilin da yasa na ce ki bayyana mahaifinki a matsayin wanda yayi miki ciki ba."

Shiru na yi ina kallonsa sannan ya cigaba da cewa, "Dalilin da yasa na ce ki ce mahaifinki ne yayi miki ciki shine: Idan kika faɗi wani ba shi ba, koda yayanki Aliyu kika yiwa wannan sharrin, to tabbas idan aka zurfafa bincike, da wuri zargi zai zo kaina. Amma idan kika ce mahaifinki ne yayi miki, to idanun jama'a zai rufe. Zarginsu ba zai taɓa kawowa kaina ba, koda kotu aka je kuwa..." Yana gama faɗa min haka, ya dube ya ce, "Kin ga kuwa dole ki bi umarnina, domin ba kece mace ta farko da na yiwa haka ba, kuma haƙuri suke su bi umarnin da na basu saboda haka daga yau, duk wani motsinki a kan idona yake, idan har kika yi kuskuren bijirewa umarnina, tabbas sai kin yi nadamar da ba ki taɓa yi ba a rayuwa sai kin gwammace kiɗa da karatu..." 

Yana gama faɗa min haka, ya je ya saka key ya buɗe ƙofar ya ce, "Zo ki fice min daga office, kuma daga yau karki ƙara shigo min office..." Cikin sanyin jiki nake tafiya, har na fito daga ofishin, tafiya nake tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Da haka har na fito daga office ɗin, ina ta rusa kuka tamkar wanda iyayensa suka mutu. Zuciyata da ƙwaƙwalwata babu abinda suke tunani irin umarnin da Prof.Shareef ya bani, tare da tunanin abinda zai biyo baya idan har na ƙi bin umarninsa...A bayana na ji ana kirana, da sauri na waiwaya sai na hango wata matashiyar budurwa tana nufo inda nake cikin nutsuwa. Tsayawa na yi har ta ƙaraso, inda nake tsaye.

Kallona ta yi ta ce, "Sannu baiwar Allah!" A hankali na amsa "Yawwa sannunki" sannan ta ƙara duba na ta ce, "Baiwar Allah! Na ga kamar kina cikin damuwa ko?" Kallonta na yi na kawar da kai ban ce mata komai ba, ba ta damu ba ta sake cewa da ni, "Don Allah idan ba za ki damu ba, mu je can domin akwai maganar da nake so mu yi..." Tana faɗin haka ta nufi wani waje da aka ajiye kujeru saboda hutawa. Koda ganin haka, ba tare da wani dogon tunani ba na nufi inda take.

Ina zuwa na zauna kusa da ita, kallona ta yi ta ce, "Fadila!" Cike da tsantsar mamakin jin kiran sunana da ta yi, na dube ta sannan na amsa "Na'am!" Cigaba ta yi da cewa, "Na ji duk abinda ya faru tsakaninki da Prof.Shareef..." Cike da tsantsar mamaki na dube ta na ce, "A ina kika ji?" Murmushi ta yi ta ce, "Duk abinda kuke tattaunawa, ina laɓe jikin ƙofar office ɗin ina sauraronku.." Jinjina kai na yi, sannan ita kuma ta cigaba da cewa, "Na kirawo ki nan ne, domin na baki shawara akan koda wasa kar ki yi yunƙurin bijirewa umarninsa. Domin akwai wata ƙawata da irin haka ya faru da ita, Wllh sai da ya hallakata ita da iyayenta gaba ɗaya, kuma irin umarnin da ya ba ki ya bata, ta yi zaton barazana ce kawai. Yayin da ta bijire kuwa ta faɗawa iyayenta gaskiyar wanda yayi mata ciki, nan take Babanta ya fusata ya tashi ya nufi wajen ƴan sanda domin ya shigar da report, yana cikin tafiya akan hany'a kan babur ɗinsa, wata babbar mota tirela ta zo ta yi gaba da shi ta bi ta kanshi, ko shurawa bai yi ba ya mutu. Mahaifiyarta kuwa ta tafi unguwa aka kashe ta aka cilla gawarta cikin kogi, jami'an tsaro suka gano ta. Ita kuma har gida aka je aka hallakata. Kuma har yanzu jami'an tsaro ba su gano wanda yayi kisan ba, sun ma daina bincike kan lamarin..."

Shiru ta yi sannan ta dubi Fadila ta ce, "Fadila shawarar da zan baki, a matsayina na mace ƴar'uwarki, kin san an ce ciwon ƴa mace na ƴa mace ne. To shawara da zan baki ita ce: idan har kina son ki rayu da iyayenki da ƴan'uwanki lafiya, to ki bi umarnin Prof. Shareef kawai, domin shine kaɗai mafitarki na barki lafiya!.." Tana faɗin haka ta tashi ta tafi, ta bar ni a zaune ina rusa kuka, lokaci guda na ji na tsani duniyar gaba ɗaya, "Wannan wacce irin ƙaddara ce?" Na tambayi kaina, ganin babu mai bani amsa ne yasa na tashi na tafi gida, zuciyata cunkushe da tunani da kala-kala, tare da fargabar abunda zai faru yayin da na bayyana mahaifina a matsayin wanda yayi min ciki...

Tun daga ranar na rinƙa ɓoye duk wata alama da za ta bayyanar da cikin da ke jikina. Wata rana da daddare, na tashi da tsananin zazzaɓi na rinƙa nishi da kakarin amai, duk yanda na so daurewa abin ya fi ƙarfina, ihun azabar da nake yi ne ya farkar da Azima daga baccin da take yi. Koda ganina cikin wannan mawuyacin halin, da gudu ta je ta sanar da su Umma. Dama Abba bai yi bacci ba, tare suka shigo ɗakin suna duba ni. Abba ne yasa Umma ta gyara min jikina, sannan ya ɗauke mu muka nufi asibiti mafi kusa da mu. Duba ni likita yayi sannan ya auna ni, ya cewa su Abba ina ɗauke da juna biyu ne, kuma na saka damuwa a raina shi yasa cikin yake wahalar da ni...

Iya tashin hankali Umma da Abba, sun shiga a ranar nan. Ba shiri kuwa suka ɗauko ni suka nufo gida da ni, ba su tsaya sauraren likita ba. Muna zuwa gida Umma ta hau tuhuma ra ita da Abba, Umma har ta rinƙa yi min barazanar kisa ko illatarwa. Abba kuwa nan take tausayina ya kama shi, ya hau tambayata cikin lallashi, ita kuwa Umma kitchen ta shiga ta ɗauko wuƙa ta ce, sai ta hallaka ni. Indai ban faɗi wanda yayi min ciki ba. Har na buɗe baki zan faɗa mata gaskiyar wanda yayi mini sai na tuno umarnin da Prof.Shareef ya bani, tare da abinda zai biyo baya idan na tona masa asiri. Nan take kuwa na buɗa baki na ce Abba ne wanda yayi min cikin. Nan take kuwa idanun Umma suka rufe nan ta yarda da maganata.

Da safe ma ta sake tuhumata, anan na shaida mata gaskiyar abinda ya faru tsakanina da Prof.Shareef, wanda yake bani kuɗi masu yawa ina kawo mata tana murna. Haƙiƙa iya tashin hankali Umma ta shiga, mun daɗe muna kuka ni da ita, kafin mu rarrashi kanmu mu yi shiru. Dubana Umma ta yi ta ce, "Fadila ina son ki tsaya, akan maganarki, karki kuskura ki canja ta duk rintsi da wuya duk inda za'a je ki tsaya akan maganarki, kar ki kuskura ki canja ko kaɗan. Dama ina da wani buri akan mahaifinku na ɗaukar fansa akan abinda yayi min. To zan yi amfani da wannan damar domin nima na rama kuma ɗanɗana masa raɗaɗin da ya daɗe yana ɗanɗana min a ƙasan zuciyata.." Da sauri kuwa na amince da buƙatarta, ba tare da wani dogon tunani ba. Tun daga ranar Umma ta shiga yiwa Abba rashin mutunci, ko kaɗan ba ta raga masa kullum sai ta danƙara masa baƙak'en maganganu akan cikin nan nawa...Kotu ma da ta kawo shi, ba don a ƙwata min haƙkina ta kawo shi ba. Ta kawo shine domin ta cusgunawa rayuwarsa...

Tana kaiwa nan a labarinta, ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Kallon Prof.Shareef Alk'ali yayi ya ce, "Prof.Shareef Adam! Duk abinda yariny'ar nan ta faɗa haka ne?" A hankali ya gyaɗa kai alamun haka ne. Alƙali ya daka masa tsawa ya ce, "Buɗa baki za ka yi ka yi mana bayani.." Da sauri ya ce, "E! Yallaɓai duk abinda ta faɗa haka ne, babu ƙarya a ciki!!" Alƙali ya ce, "Ka aikata duk waɗannan abubuwan kenan?" Ya ce, "Na'am Yallaɓai na aikata.." Rubutu Alƙali ya shiga yi...

Saboda tsananin ruɗan da ɓacin rai kasa zama Azima ta yi a cikin kotun. Da sauri ta faki idanun jama'a ta fice daga cikin kotun. Harabar kotun ta fito ta je gindin wata bishiya ta zauna ta zuba tagumi hannu biyu, tana tunanin yanda mahaifiyarsu take ƙoƙarin tarwatsa musu rayuwa. Tana nan zauna tana tunani hawaye yana zubowa daga idanunta, kawai ta ga wata danƙareriyar mota mai ƙirar _*prado land cruiser*_ ta danno cikin kotun. Kai tsaye parking space ta nufa, ko gama parking ɗin direban bai yi ba, ya ci burki tare da fitowa daga cikin motar da sauri. Back sit ya zagayo ya buɗe, nan take kuwa sai ga Hajiya Amina ta fito daga cikin motar tana taku cike da izza, ita a lallai uwar mata. Karaf idanunta suka sauka akan Azima da take zaune gindin bushiya tana kuka, cire glass ɗin da yake manne a idanunta ta yi, ta kalli Azima sosai a fili ta ce, "Waccan kamar Azima!" Cike da taku ɗai ɗai ta nufi inda Azimar take, tana isa ta kira sunanta da kakkausar murya ta ce, "Azima lafiya kike zaune anan ke kaɗai, ina Maman naku?" A hankali Azima ta ce, "Suna ciki ana gabatar da shari'ar su Fadila!" Murmushi ta yi ta ce, "Masha Allah! Fatan dai muna samun nasara?" Kawar da kai Azima ta yi, wani irin haushin Hajiya Amina yana ƙara kamata ta ce, "Sai dai kin shiga za ki ga kome yake faruwa!" Juyawa Hajiya Amina ta yi ta nufi cikin ainihin kotun. 

Ta shiga dai-dai lokacin da Deejerh take faɗin irin zaluncin da Prof.Shareef yayi mata. Tana shigowa ko kaɗan ba ta lura da Prof.Shareef ba, idanunta ne suka sauka akan Umma idanunta sun kaɗa sun yi ja wur kamar gauta. Cikin sanyin jiki ta ƙarasa kusa da inda Umma take zaune ta nemi waje ta zauna. Har zuwa wannan lokacin, ba ta lura da Prof.Shareef ba. Jiyo muryar Alƙali ta yi yana cewa "Kai kotu take sauraro ka yi mata bayani shin da gaske ne duk abinda Deejarh ta faɗi ka yi mata gaskiya ne?" Kansa a ƙasa yake, ko kaɗan ya ƙi ya ɗago ya haɗa ido da mutane, shi yasa bai lura da shigowar Hajiya Amina ba, daka masa tsawa Alƙali yayi ya ce, "Professor Shareef kai muke sauraro!"

Da sauri Hajiya Amina ta ɗago da kanta, ta kalli inda Prof.Shareef take tsaye, shi ma dai-dai lokacin ya ɗago da kansa. Karaf idanunsa suka sauka akan fuskar Hajiya Amina, ita ma nata idanun suka sarƙe cikin nasa, da sauri ta ce, "Abban Basma! Kai ne anan?" Shiru yayi ya kasa magana, sai ƙuro mata idanu da yayi. Da sauri Umma ta miƙe tsaye ta kalli Hajiya Amina ta ce, "Kin san shi ne?" Muryar Hajiya Amina tana rawa ta ce, "Mijina ne!" Zaro idanu Umma ta yi cike da tsantsar mamaki da al'ajabi ta ce, "Dama shine mijnki? Wannan fasiƙin ne mijinki?" Da sauri Hajiya Amina ta ce, "Hauwa'u me mijina yayi miki kike kiransa da fasiƙi? Ke don naki mijin ya lalace yana bibiyar ƴaƴan Cikinshi..?" Muryar Umma har rawa take cikin tsananin fushi ta dubi Hajiya Amina ta ce, "To shine fasiƙin da yayi wa Fadila ciki..."



Comment and share


*Hussain Yusuf✍️*
~07069475482~
: *BOKO NE SILA*
        _(Fiction story)_



KING & QUEEN WRITING CHAMBER


HUSSAIN YUSUF


🅿️age..........23.


Zaro idanu Hajiya Amina ta yi, ta dubi Umma ta ce, “Hauwa'u a bakin wanne mak’aryacin kika ji wannan magana?” Umma ta bud’a baki za ta yi magana, Alk’ali ya dakatar da ita ya ce, “Ya isa haka! Nan ba kasuwa ba ce, saboda haka ku nutsu ku san me kuke yi...” Shiru suka yi gaba d’ayansu, sai faman hararar juna suke kamar za su ci babu. Alk’ali ya cigaba da cewa “Akwai sauran mai wani ƙorafi akan Prof.Shareef?” Nan take Inspector Auwal ya mik’e tsaye ya ce, “Akwai ya mai girma mai shari'a!” “Kotu tana sauraronka!” Daga nan ya shigo zayyanawa Alk’ali irin cin zarafin da Prof.Shareef yayi wa k’anwarsa, har yayi sanadiyyar mutuwarta da iyayenta...

Daga nan ya zauna, Hadiza ta tashi ta fad’i irin cutarwar da yayi mata. Daga nan wasu ’yan mata guda huɗu suma suka tashi, suka faɗi duk irin cin mutuncin da yayi musu bayan ya yaudare su. Babban abin takaicin ma shine: Duka waɗanda ya cutar d’alibansa ne, na jami’ar Bayero Kano. Rubuce-rubuce Alk’ali ya shiga yi, sai da ya gama sannan ya d’ago ya kalli jama’ar kotun, sannan ya kalli lauyoyi ya ce, “Lauyan mai k’ara ko kina da abin cewa?” Girgiza kai Brr.Khady ta yi, ta ce, “Ba ni da abin cewa ya mai shari’a!” Gyad’a kai Alk’ali yayi sannan ya kalli Prof.Shareef ya bud’a baki zai yi magana, sai ga manyan malamai na makarantar  BAYERO UNIVERSITY KANO (BUK) sun shigo cikin kotun.

D’aya daga cikinsu ya ce, “Muna da magana ya mai girma mai shari'a!” Kallonsu Alk’ali yayi ya ce, “Kotu tana sauraronku!” Gyara tsayuwa babban cikinsu yayi ya kalli kotu ya ce, “Ya mai shari’a! Ina so kotu ta yiwa makarantarmu kyakkyawan zato. Wllh ko kad’an ba mu san abinda Professor Shareef yake aikatawa da d’alibanmu ba, mu muna yi masa kallon mutumin kirki ne, shi yasa ko kad’an ba mu tab’a tunanin zai aikata irin wannan aikin ba. Saboda haka muna so wannan kotu mai adalci, ta yi amfani da wannan dama ta wanke makarantarmu daga zargin da mutane suka fara yi mata. Sannan ta k’wato mana hakk’inmu a wajen Prof.Shareef na watsa mana sunan makaranta da yayi, mun gode ya mai shari’a!” 

D’an jim Alk’ali yayi kafin ya ce, “Kotu ta karb’i k’orafinku, kuma za ta kwatanta muku adalci iyakar k’ok’arinta..” Kallon jama'ar kotun Alk’ali yayi, sannan ya kalli lauyoyi ya shiga cewa, “Kotu ta saurari hujjoji da shaidu, kuma ta gamsu da su d’ari bisa d’ari..Don haka yanzu ba da dad’ewa ba za mu yanke hukunci, domin kowa ya girbi abinda ya shuka, kuma in sha Allahu za mu yiwa kowa adalci iyakar k’ok’arinmu..Amma kafin nan, ina so na yi amfani da wannan damar domin na yi jan hankali game da zina, saboda wad’anda suka d’auke ta ba a bakin komai ba..”

Shiru kotun ta yi, kowa ya kasa kunne domin ya ji jan kunnen da Alk’ali zai akan zina. Numfasawa Alk’ali yayi sannan ya dubi jama’ar kotun ya shiga cewa. “An tambayi Annabi (s.a.w) cewa wanne zunubi ne ya fi girma?” Sai Mazon Allah (S.A.W) Ya ce, “Shirka da Allah! Alhali shine ya halicce ka..” Sai aka ce “sai wanne?” Sai ya ce, “Sannan kashe d’anka, don kada ya ci tare da kai!” Sai aka ce “Sannan sai wanne?” Sai Manzon Allah (S.A.W) Ya ce, “Ka yi zina da matar mak’wabcinka..” Bukhari ne ya ruwato...
“Ku sani Allah mad’aukakin Sarki ya sany’a hukuncin wanda duk yayi zina kuma ya taɓa aure a jefe shi namiji ko mace. Idan kuwa bai taɓa aure ba, sai a yi masa bulala d’ari sannan a baƙuntar da shi a wani gari daban tsawon shekara guda. Anan duk wanda ya kalli hukuncin zina, zai ga Allah ya keb’ance shi da wasu abubuwa masu yawa saboda munin zina kad’an daga irin abinda hukuncin ya k’unsa shine: Kausasawa wajen uk’ubar mazinaci, ta hany’ar jefewa. Ko kuma bulala da bak’untarwar shekara guda. Hana jin tausayin mazinaci ko mazinaciya, yayin da ake yi musu uk’uba.
   Allah mad’aukakin sarki ya ce, “Mazinaciya da mazinaci, ku yiwa kowanne d’aya daga cikinsu bulala d’ari. Kada ku ji tausayinsu a cikin Addinin Allah, indai kun yi imani da Allah da ranar k’arshe (Annur:2) Allah yana nufin, idan za'a yi musu uk’uba (Haddi) a yi musu a gaban mutane, ba a yarda a yi musu a b’oye ba. Allah ya ce, “Wasu b’angare na muminai, su halarci wajen yi musu uk’uba (Haddi).“ (Annur:2).
Idan kuka dubi waɗannan abubuwan, suna nuna mana munin zina da rashin kyanta a Musulunci. Imamul Bukhari ya kawo a cikin ingantaccen littafinsa, daga Maimun Al-audiy ya ce, “A lokacin jahiliyya na taɓa ganin wani biri yayi zina da wata birany’a, sai sauran biran suka taru suka jefe su...” Mafi munin zina ita ce wacce mutum zai yi da mahaifiyarsa, sai da muharramarsa, sai wadda zai yi da matar mak’wabcinsa, Allah ya kare mu.”
    Babu shakka! Duk mai hankali ya san cewa zina tana tattare da illoli masu yawa, wad’anda suke shafar mazinacin ko mazinaciyar, ko su shafi al’umma gaba d’aya. Ɗaya daga cikin irin illolin zina na farko akwai: Zubar da mutunci da jawowa kai k’ask’anci; Duk matar da ta yi zina, to ta jawowa kanta da danginta da mijinta k’ask’anci! Ta kuma zubar musu da mutunci a idon duniya. Idan ta samu ciki ta haihu, sannan ta kashe D’an. To ta had’a laifi biyu, laifin zina da laifin kisan kai.  Idan kuma ta bar shi, to ta shigarwa danginta ko mijinta wanda ba ya cikinsu. Idan kuwa mai zinar namiji ne, to ya lalata mace, ya jawo mata lalacewa da tab’ewa, wanda hakan lalata duniya ne baki d’aya.
   Illa ta biyu da zina take haifarwa shine: Zina ta had’a sharri gaba d’aya, saboda a cikin zina akwai rashin tsoron Allah! rashin kunya; rashin tsantseni, rashin cika alk’awari, k’arya da butulci da sauransu...
Alk’ali ya cigaba da cewa, “Iyaye ku daina tilastawa ’ya’yanku lallai sai sun yi karatun boko, yayin da ’ya’yanku suka isa aure to ku yi gaggawar aurar da su, a tunanina wannan shine mafi alkhairi a gare su...” 

Daga nan Alk’ali yayi shiru, Prof.Shareef kuwa hawayen nadama ne ya hau zubo masa, domin ya riga ya san irin hukuncin da Alk’ali zai yanke masa, shikenan rayuwarshi ta zo k’arshe. Umma kuwa sai faman hararar Hajiya Amina take yi, sannan ta harari mijinta Prof.Shareef. A cikin zuciyarta kuwa, tsantsar nadama ce tare da dana sani. Har yanzu nadamar abinda ta yiwa Abba take, domin ko za'a ritsa ta da bindiga ba ta san dalilin da yasa ta tsani Abba ba. Ta rasa dalilin da yasa ta goyi da bayan d’iyarta, alhalin ta san k’arya ta gaya mata, tambayar kanta ta yi “Ko don gudun kar ya d’ora min alhakin cikin Fadila na yi masa haka? Ko kuma gudun kada Prof.Shareef ya hallaka shi ne ya sa na goyi bayan ’yarta?” Kasa bai wa kanta amsa ta yi, sai wani siririn hawaye da ya fito daga idanunta, ya sauka akan fuskarta. Ita a halin yanzu fargabarta d’aya ce, ta yaya za ta fuskanci Abba ta nemi yafiyarsa bayan an gama zaman kotu? Shine kad’ai abinda yake damunta a cikin zuciyarta.

Wani b’angare na zuciyarta kuwa, fargabar irin hukuncin da Alk’ali zai yankewa Fadila take. Kwata² zuciyarta ta kasa nutsuwa, domin a wani b’angaren na zuciyarta ta, tana fargabar irin matakin da Abba zai d’auka akanta. Domin duk ita ce, silar komai. Inda ace tun farko ta d’auki shawararsa, sun yiwa ’ya’yansu aure ba ta sany’awa ranta dogon buri ba, to da duk wannan abun bai faru ba. Amma ba yanda ta iya, ai bawa ba ya gujewa k’addararsa...
  Bayan Alk’ali ya gama rubuce-rubucensa, sai ya d’ago da kansa yayi gyaran murya nan take kotun ta sake yin tsit! Ta yi shiru kamar babu mai rai a ciki. Cikin nutsuwa da dattaku Alk’ali ya fara magana, “Alhamdulillah! Da farko wannan kotu ta jinjinawa Barrister Aliyu Inuwa, bisa namijin k’ok’arin da yayi ya bankad’o mana irin wannan laifi, ya sayar da rayuwarsa domin ya dakatar da mutane irin su Prof.Shareef daga aikata b’arna da fasadi a bayan k’asa, saboda haka wannan kotu ta jinjinawa Barrister Aliyu Inuwa! Allah yasa ya fi haka...” Gaba d’aya kotun suka amsa da “Amin” sannan suke yin shiru domin su ji irin hukuncin da Alk’ali zai yankewa Prof.Shareef..

Kallon Prof.Shareef Alk’ali yayi ya ce, “Shareef ka ji duk abinda ’yan matan nan suka fad’a akan ka da irin cin zarafin da ka yi musu, me za ka ce akai?” Da sany’in ya gyad’a kai ya ce, “Duk abinda suka fad’a haka ne, ba su yi k’arya ba...” Alk’ali ya ce, “Ka yiwa ’yan mata bakwai fyad’e, d’aya daga cikinsu ta mutu sanadin fyad’en da ka yi mata. Bak’in ciki yasa iyayenta ma sun mutu duk a sanadiyyarka ba wata ba ce face ’yar'uwa a wajen Inspector Auwal...” Da sauri Professor Shareef ya kalli Inspector Auwal, nan take ya tuno lokacin da ya zo yana neman maslaha a wajensa, akan ya daure ya auri k’anwar tasa, amma yasa aka yi masa dukan tsiya, kawai saboda tsabar zalunci...Murmushi Inspector Auwal yayi, a yayin da suka had’a ido da Professor Shareef. Ko kad’an bai fahimci ma’anar wannan murmushi na Inspector Auwal ba...

Alk’ali ya fara magana, “Professor Shareef Adam! Wad’an nan ’yan mata da ka ci musu zarafi ka keta musu haddi, ba bisa son ransu ba. Za ka biya kowacce daga cikinsu tarar naira miliyan biyu, saboda dama da kud’i kake yaudararsu, kana cutar da su...” Wani zazzafan hawaye ne ya zubo daga idanun Professor Shareef, wanda kana gani ka san hawayen nadama ne. 
  Alk’ali ya cigaba da cewa, “Shi kuma Inspector Auwal da ka yi sanadiyyar mutuwar k’anwarsa da iyayensa, za ka biya shi diyya! Domin kaine ka kashe ta da kanka, tunda da bak’in cikinka ta bar duniya, kamar yadda d’an uwanta ya shaida mana...” Alk’ali ya cigaba da cewa, “Za ka biya Fadila Inuwa, tarar naira miliyan biyar, domin ta raini cikin da yake jikinta har zuwa lokacin da za ta haihu ta raini d’an da ta haifa da kud’in da ka bata....”

Sunkuyar da kai Professor Shareef yayi, bai san lokacin da hawaye yake kai-kawo akan fuskarsa ba. Wai yau shine a gaban kotu, ana ta saka masa tara kamar wanda yayi wata gagarumar sata. A cikin ransa ya k’udurce matuk’ar ya kub’uta daga hannun hukuma, sai ya hallaka dangin Barrister Aliyu gaba d’aya ba zai bar d’aya da rai a cikinsu ba.....
   Muryar Alk’ali ce ta dawo da shi daga banzan tunanin da ya tafi, Alk’ali ya ce, “Wannan kotu mai adalci ta yankewa Professor Shareef hukuncin kisa, ta hany’ar jefewa..!” Daram!!! Prof.Shareef ya ji zuciyarsa ta buga da k’arfi, gani yake kamar a mafarki wannan abun yake faruwa bai tab’a tunanin hukuncin da za’a yanke masa, zai yi tsauri haka ba. A tunaninsa, prison za a tura shi, amma sai ya ga sab’anin haka, “To me yake shirin faruwa da ni?” Ya tambayi kansa, amma kwata² ya kasa bai wa kan nasa gamsasshiyar amsa....

Muryar Alk’ali ya jiyo ta doki dodon kunnensa inda yake cewa, “Wannan hukuncin da muka yankewa Professor Shareef, shine adalcin da za mu iya yi masa, kuma shine gatan da za mu iya yi masa ko a wajen Allah (S.A.W)...” Nan take kotun ta kauraye da kabbara “Allahu akbar!” Sannan Alk’ali ya cigaba da cewa, “Ba za’a zartar maka da wannan hukunci ba, har sai ka biya duk tarar da kotu ta saka maka, sai ka biya kowa sannan sannan a yi maka haddi, kamar yanda shari’a ta tanadar... Kuma idan an tashi daga kotu, za ka yiwa ’yan jarida bayani da bakinka cewa babu sanin Malam makarantar BUK ka ke aikata alfasha da d’aliban makarantar, a bisa bisa dole ba da son ransu ba.” Wani irin bak’in ciki ne ya turnuk’e Professor Shareef, wannan wanne irin tozarci ne Alk’ali yake son yi masa? A fusace Hajiya Amina ta tashi, ta nufi inda mijinta Professor Shareef yake tsaye, tana isa inda yake ta saka hannu biyu ta shak’o wuyan rigarsa cikin tsananin tashin hankali tana jijjiga shi da dukkan k’arfinta tana cewa “Allah ya isa tsakanina da kai! Ban tab’a tunanin da fasik’i mazinaci nake zaune ba, Shareef Allah ya isa tsakanina da kai ba zan tab’a yafe maka ba, ka cuce ni! Shareef ka cuce ni ni da ’ya’yana! Ba zan tab’a yafe maka ba...” Duk wad’an nan maganganun da take yi tana shak’e da wuyan rigarsa da hannu d’aya, d’aya hannun kuma tana kai masa duka ta ko’ina yana karewa. Da kyar wasu jami’an tsaro suka k’wace shi a hannunta, ita kuma wasu ’yan sanda mata suka yi waje da ita, amma kafin su jany’e ta sai da ta tofa masa yawu a fuska, har suka fita da ita bakinta bai daina tsinewa mijinta Professor Shareef ba, tare da faɗa masa bak’ak’en maganganu marasa dad’in ji...”

Bayan an fita da Hajiya Amina, sai komai ya dai-dai ta. Sannan Alk’ali ya juyo ya kalli inda Fadila take tsaye sannan ya d’auko wata takarda ya fara karanto hukuncin Fadila kamar haka: “Wannan kotu mai adalci ta yankewa Fadila Inuwa hukuncin bulala d’ari saboda zinar da ta aikata ba tare da aure ba tare da zaman gidan yari na tsawon shekara guda...Har ila yau wannan kotu ta sake yanke mata hukuncin bulala d’ari saboda k’azafi da ta yiwa mahaifinta...” Wani irin kuka ne ya k’wacewa Fadila ita da Umma, wani irin bak’in ciki da nadama ne suka mamaye zuciyarsu gaba d’aya... 
   Alk’ali ya kalli Fadila sannan ya cigaba da cewa, “Fadila ba za’a zartar miki da wannan hukunci ba, har sai bayan kin haihu sannan ki zo a yi miki naki hukuncin...” Sake fashewa da kuka Fadila ta yi, Umma ma kawai kukan take a ranta tana dana sanin kawo k’ara kotu da ta yi, ita a tunaninta za ta iya amfani da kud’i domin a hukunta Abba, alhalin ba shine ya aikata laifin ba. Amma sai ga shi rishe ya juye da mujiya, tun ba a je ko’ina ba, an yi abinda ake kira k’aik’ayi koma kan mashek’iya..
   Alk’ali ya cigaba da cewa, “Sannan wannan kotu ta wanke Malam Inuwa daga zargin da mutane suke yi masa, a matsayin mazinaci wanda yake bibiyar ’yar cikinsa, to daga yau kada wanda ya k’ara yi masa irin wannan kallon, Malam Inuwa mutumin kirki ne wanda kowa yake yabonsa saboda kyawawan halayensa. Kuma yana da hak’uri da juriya da kawaici. Duba da yanda yayi hak’uri da k’azafin da ’yar cikinsa ta yi masa, amma yayi hak’uri bai yi mata baki ba, kuma bai kore ta daga gidansa ba, har lokacin da Allah ya bayyana gaskiya kowa ya gani, yanzu an sallami kowa koooootuu!” Daga nan Alk’ali ya tashi tsaye ya fice, sannan kowa ya tashi aka fito daga cikin kotun, jama’a sai faman faɗin albarkacin bakinsu suke yi akan wannan al’amari.......

Comment and Share

_Hussain Yusuf_
07069475482.
: BOKO NE SILA
     

KING & WRITING CHAMBER


HUSSAIN YUSUF

🅿️age......24.

Nan take ’yan sanda suka saka wa Professor Shareef ankwa, suka tusa ƙeyarsa suka tafi da shi. Sai faman kuka yake yana faɗin su yi masa afuwa, zai yi magana da iyalinsa. Amma kwata² suka ƙi sauraronsa, wani ɗan sanda ya kalle shi ya ce, “Ka bari mu kai ka inda aka umarce mu, sai iyalin naka su zo su same ka, tunda ba yau za’a zartar maka da hukuncin ba...” 
 
Suna fitowa da shi, ya ga matarsa Hajiya Amina tana ta yiwa ƴan’jarida da ’yan kallo tsari, wani ƙululun baƙin ciki ne ya zo t
ya tokare masa zuciyarsa.. Bai san lokacin da ƙwalla ta taru a cikin idanunsa ba, wai yau shine matarsa wacce ya fi so, take tozartawa a idon duniya? Kallonsu kawai yayi ya kawar da kai, takaici da baƙin ciki duk sun mamaye zuciyarsa.

’Yan jarida suna hango an fito da shi, suka fara haska shi a camera. Wasu kuma suka fara yi masa tambayoyi, wani babban ɗan jarida ne ya kalle shi ya ce, “Prof.Shareef yanzu ne lokacin da za ka wanke jami’ar Bayero daga zargin da jama’a suka fara yi mata, akan Malamai suna yin lalata da ɗalibai, me za ka ce akai?”

Shiru yayi ya ƙi yin magana, har sai da wani ɗan sanda ya daka masa tsawa! Sannan ya buɗa baki yayi musu gamsashshen bayani game da lalatar da yake yi da ɗalibai, daga ƙarshe dai ya ce, babu sanin Malamai yake aikata irin wannan ɓarnar, ya k’ara da cewa da sun sani da tuni sun dakatar da shi.

Bayan ya gama yi musu bayani, sai ya nemi izini wajen ƴan sandan akan su daure su bashi dama yayi magana da matarsa Hajiya Amina. Wani d’an sanda ne ya je ya sanar da ita mijinta yana son magana da ita, wani kallo ta watsawa ɗan sandan ta ce, “Ka je ka sanar da shi, ba zan yi magana da shi ba, domin ba ni da lokacinsa..”

Nan take kuwa ɗan sandan ya je ya sanar da shi. Koda jin haka kuwa, take ƴan sandan suka saka shi a mota, suka tafi da shi prison domin su ajiye shi, kafin ranar zartar da hukuncin ta zo..” Sai bayan an tafi da shi, Hajiya Amina ta ga rashin dacewar abinda ta yi, yakamata ace ta tsaya ta saurare shi, ko ba komai shine mijinta uban ’ya’yanta..

Umma ce ta fito daga cikin kotun tana matsar hawaye, Fadila tana biye da ita a baya. Ita ma sai matsar k’walla take, a fusace Umma ta juyo ta kalli Fadila. Ba ta ce komai ba ta ɗaga hannu ta sharara mata mari har sau biyu a jere. Ta rinƙa wani irin huci, tamkar wata zakany’a.

Cikin tsananin fushi ta dubi Fadila ta ce, “Fadila kin cuce ni, kin cuce ni Fadila!” “Kin cuce ta dai, ke ce da kanki kika cuce ta Hauwa’u!” Abba ne ya faɗi hakan, yayin da ya ƙaraso wajen ya ji abinda Umma take faɗawa Fadila. Wani kallo Umma ta watsawa Abba, kafin ta dube shi cike da tsantsar ɓacin rai ta ce, “Haba Malam! Ta yaya zan cuci ƴar cikina da kaina?” Wani murmushin takaici Abba yayi, kafin ya dube ta ya ce, “Hauwa’u daɗina da ke saurin manta baya, yanzu har kin manta lokacin da na ce zan yiwa Fadila da Salma aure, amma kika dage akan ban isa na aurar miki da ƴa ba sai ta yi karatun boko mai zurfi, ta auri babban mutum. Yanzu wa karatun bokon ya amfana tsakanin ke da ita?” 

Shiru Umma ta yi, ta kasa furta komai, ganin haka yasa ta ja hannun Fadila za su bar wajen. Har sun fara tafiya Abba yana tsaye yana kallonsu, wani irin takaici da baƙin ciki duk sun mamaye zuciyarsa. Wani irin fushi ne ya taso masa, cikin hanzari ya d’aga murya ya ce, “Hauwa’u dakata anan!” Tsayawa su Umma suka yi, ba tare da sun waigo ba. Cikin sanyin jiki ya fara tafiya har ya isa inda suke a tsaye, yayin da ya ƙaraso inda suke sai ya tsaya ya fuskanci Umma sosai. Sannan ya buɗa baki ya fara magana cikin tsananin fushi. “Hauwa'u!” Ya kira sunan Umma da wata kakkausar murya, sai da Umma ta ɗan tsorata. Saboda ba ta taɓa jin Abba yayi mata magana da irin wannan murya ba.

Ita ma dakewa ta yi ta amsa kiran sunanta da yayi, “Na'am!” Ta amsa idanunta cikin na Abba. Dubanta yayi ya ce, “Hauwa'u! Ina so ki sani, kar ki sake ki doshi gidana, domin na daɗe da sakinki, tun kafin a fara zaman kotu. Abinda yasa ban sanar da ke ba, shine: Kada mutane su sake yi mini wata fassarar daban, shi yasa na rufe ban sanar da ke ba har zuwa lokacin da gaskiya za ta yi halinta, sannan zan sanar da ke. Saboda haka yanzu ke da Fadila, ban yarda ku koma min gida ba, ku san inda dare yayi muku, domin na daɗe da cire ku a cikin babin rayuwata.

Yana faɗin haka ya juya yayi tafiyarsa, ya bar su Umma a inda suke. Ko kad'an sun kasa motsawa, tamkar gumaka haka suke a tsaye. Idanun Umma suna kan Abba, har ya shiga motarsa ya fice daga cikin kotun. Sannan ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, ta dubi Fadila ta ce, “Fadila kin ji irin abinda kika jany'o mana ko?” Cike da tsantsar mamaki, Fadila ta dubi Umma ta ce, “Me kike nufi Umma? Na ga dai kome na yi kece kika saka ni, amma kuma yanzu kike ƙoƙarin juyar da laifin gaba ɗaya ya koma kaina? Gaskiya ba zai yiwu ba.” Cike da mamaki Umma take duban Fadila, wai yau ƴar cikinta ce wacce ta fi kowa so take mayar mata da martani haka? 

Saboda tsananin fushin da ya tasowa Umma, ba ta san lokacin da ta ɗaga hannu ta shararawa Fadila mari ba. Cike da tsantsar b'acin rai ta dube ta, ta ce  “Fadila yakamata ki san da wanda kike magana, ina matsayin mahaifiyarki amma kike gaya min irin wannan maganar?” Sunkuyar da kai Fadila ta yi, kwata² ta kasa haɗa ido da Umma. Da sauri Umma ta wuce ta nufi hany’ar fita daga kotun. Ai kuwa cikin hanzari Fadila ta rufa mata baya, tafiya Umma take yi cikin sauri, Fadila tana biye da ita, duk inda suka wuce sai dai ka ga ana nuna su da hannu. Ana zunɗensu wasu har zaginsu suke yi haka kawai, Umma sai dai ta kalle su kawai ta kawar da kanta. Saboda abin ya fi k'arfinta. 

   Tafiya suke har suka ƙaraso bakin titi. Tsayar da mai napep Umma ta yi, ta ce, “Darmanawa zai kai su” nan take kuwa suka shiga, ya tafi da su. Tafiya suke babu mai magana a cikinsu, ita Umma abinda take saƙawa a cikin ranta shine: Da wanne irin kalami za ta yi amfani, ta sanar da iyayenta abinda ya faru, ba tare da laifinta ya fito ba? Saƙa da warwara kawai take yi a cikin ranta, har suka shigo unguwar Darmanawa ba su sani ba, domin sun daɗe da faɗawa kogin tunani ita da Fadila, suna ta ninƙaya. Muryar mai adaidaitan ce ta dawo da su daga hayyacinsu, tambayar Umma yake “Hajiya mun k'araso Darmanawa, wajen ina za mu bi?” Nan take Umma ta nuna masa hanyar unguwarsu  a cikin Darmanawar.

Nan take kuwa kutsa napep ɗin hanyar ɗan lungun da Umma ta nuna masa. Tun daga nesa ta hango mahaifinta a ƙofar gida, a zaune akan wata ƙatuwar tabarma, ga mutane nan sun kewaye shi. Da alamu dai karatu yake biya musu, tunda kowa riƙe yake da ɗan littafi a hannunsa. Tun kafin su ƙarasa kusa da su, Umma ta dakatar da mai napep ɗin, fitowa suka yi ita da Fadila. Sannan ta biya shi kuɗinsa ya juya yayi tafiyarsa. Cikin sanyin jiki Umma ta fara tafiya, Fadila tana biye da ita a baya. Har suka ƙaraso ƙofar gidan nasu, inda mutanen suke zaune suna ɗaukar darasi a wajen mahaifin Umma. 

Cikin sanyin murya Umma ta ce, “Sannunku!” Sannan ta saka hannu za ta buɗe ƙyauren da ya rufe ƙofar gidan. “Ke dakata daga nan!” Ta ji muryar mahaifinta yana yi mata magana cikin kakkausar murya. Dakatawa Umma ta yi, ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana jiran ta ji abinda mahaifin nata zai faɗa. Tasowa yayi daga tsakiyar ɗaliban nashi, ya ƙaraso k'ofar gidan nasu inda su Umma suke tsaye. Yana ƙarasowa ya hau kallon Umma da Fadila tun daga sama har ƙasa, Fadila ce ta buɗa baki ta ce, “Baffa ina yini?” Wani banzan kallo ya watsa mata, kafin ya ce, “Ai da ban yini ba yanzu ba za ki ganni ba.” Koda jin haka nan take Fadila ta gumtse bakinta, domin ta san ba ƙaramin aikinsa ba ne ya kumbura mata fuska da mari yanzu.

Kallon Umma yayi kafin ya bud'a baki ya ce, “Sannu Hauwa'u!” Ƙasa ta yi da kanta ta ce, “Yawwa sannu Baba!” Cike da masifa ya fara magana, “Yanzu Hauwa'u abinda kika yi, kin yi dai-dai kenan? Irin tarbiyyar da na baki kenan? Hauwa'u kin ci mutuncina, ba iya mijinki kika tozarta a duniya ba Hauwa'u, har da ni a cikin waɗanda kika tozarta...” Sunkuyar da kai k'asa Umma ta yi, bakinta ya kasa furta komai. Kallon Fadila yayi ya ce, “Ke kuma uban me kika zo yi gidana?” Ita ma sunkuyar da kai ƙasa ta yi, gaba ɗayansu sun kasa haɗa ido da shi. Cikin fushi ya cigaba da cewa “Babu wanda ya isa ya shigar min gida daga cikinku, tunda duniya kuka zaɓa, ku tafi can ga ku nan, ga ta nan, wanda bai zo ba ma tana nan tana jiransa, don haka ku juya ku tafi, ba'a isa a haife min ɗan shege a gida ba.”

    Durƙushewa Umma ta yi akan gwiwoyinta, ta fashe da kuka. Cikin kukan ta dubi mahaifin nata ta ce, “Don Allah Baba ka rabu da ni, Wallahi idan na tafi daga nan ban san inda zan nufa ba, kai kaɗai nake da shi a duniyar nan.. Ka taimaka mana.” Wani wulaƙantaccen kallo ta watsa masa, kafin ya ce “Hauwa'u sai yanzu kika san ba ki da kowa sai ni? Lokacin da kike shuka tsiyarki, ai ba ki tuna da ni ba, ko don mutuncina ya tsira Hauwa'u ba za ki aikata abinda kika aikata ba. Ki juya ki tafi, kar ki sake ki ƙara minti uku a ƙofar gidan nan..” “A'a Malam ba za a yi haka ba, naka sai naka, idan ta tafi a tunaninka ina za ta je? Ko so ka ke ta shiga duniya ta sake kangarewa?” Mahaifiyar Umma ce ta faɗi haka, yayin da ta leƙo ƙofar gidan, ta ji abinda mijin nata yake faɗawa ƴar tata. Wani kallo ya watsawa matar tashi, kafin ya ce, “Salamatu waye ya ba ki izinin leƙowa?” Sunkuyar da kanta ta yi, sannan ta yi ladab cike da girmamawa ta ce, “Ka yi haƙuri Malam, na ji kana niyyar aikata ba dai-dai ba, shi yasa na lek'o” Jinjina kai yayi ya ce, “Shikenan koma cikin gida.” Ba tare da gardama ba ta juya ta koma, tana waigen Umma ita da Fadila da suke tsaye, tamkar gumaka.

Kallon Umma yayi ya ce, “Ke Hauwa'u ki san inda dare yayi miki, ku gaggawar bar min ƙofar gida, tun kafin ranku ya ɓaci..” Yana faɗin haka ya juya ya tafi, ya bar su a tsaye, sun rasa mafita ko kaɗan. Wani hawaye ne ya gangaro daga idanun Umma, kallon Fadila ta yi, ta ce. “Wuce mu tafi!” Cikin muryar kuka Fadila ta ce, “Ina za mu je?” Cikin b'acin rai Umma ta ce, “Na ce ki wuce mu tafi ko?” Cikin sanyin jiki Fadila ta wuce Umma ta bita a baya, suka nufi bakin titi. Zuciyar Umma cunkushe take da baƙin ciki, da tarin nadamar da bata da amfani. Tafiya suke sannu! Har suka ƙaraso bakin titi, mai napep suka tare suka hau Umma ta ce, “Unguwar Hausawa zai kai su” nan take kuwa ya ja napep ɗin suka wuce. Suna cikin tafiya Fadila ta kalli Umma ta ce, “Umma me za mu je yi a Hausawa?” Harararta Umma ta yi ta ce, “Gidan Kawuna za mu je” Fadila ta ce, “Umma kar mu je shi ma ya koro mu” “Idan ya koro mu ba sai mu shiga duniya ba?” Umma ta faɗi haka a zafafe. Shiru Fadila ta yi, ba ta sake yin magana ba, har suka ƙaraso unguwar Hausawa. 

   Sauka Umma ta yi ta biya mai napep ɗin, ta ce. “Za su ƙarasa a k'afa tunda babu nisa” Tafiya suke sannu a hankali har suka k'araso k'ofar gidan, tsayawa suka yi cirko-cirko, an rasa wanda zai fara shiga, domin suna tsoron kada yayi musu wulaƙanci kamar yadda Baffa yayi musu, duk da Umma tana kyautata masa zato. Umma ce ta yi jarumtar kutsawa cikin gidan, bakinta ɗauke da sallama.  Daga cikin d'aki wata dattijuwar mata ta amsa, “Wa'alaikumussalam! Wa nake ji haka kamar Hauwa'u?” Fitowa ta yi ta iske Umma da Fadila a tsaye, suna rarraba idanu. “Ashe dai Hauwar ce tare kike da Fadila? To sannunku da hany'a, lale marabanku!” Umma ta amsa “Yawwa Inna Ladi, ya kuke?” Inna Ladi ta amsa “Wallahi muna nan lafiya Hauwa'u kwana biyu shiru ake jin ku” Ta faɗi ta shiga cikin d'aki ta ɗauko tabarma, ta shimfid'a ta ce, “Ku zauna mana, kun tsaya a tsaye kamar wasu baƙi a gidan..” Zama su Umma suka yi, suna sauke ajiyar zuciya a tare. 

Ruwa Inna Ladi ta ɗebo ta kawo musu, ta ce. “Ga ruwa ku sha, na ga kun sha hany'a sosai ga rana...” Umma ce ta ɗauki ruwan ta kurɓi kaɗan, sannan ta ajiye Fadila ma ta ɗauka ta sha kaɗan, kallon Inna Ladi Umma ta yi ta ce, “Inna ina Kawu ya shiga ne tunda na shigo ban gan shi ba..” Inna Ladi ta ce, “Au Wallahi ya je bakin titi. Tun kafin ta rufe bakinta, sai ga shi ya shigo cikin gidan.. Dariya Inna Ladi ta yi ta ce, “Kin ga ɗan halak, muna zancensa sai kuma ga shi ya shigo.. Sannu da zuwa Malam!” Inna ta faɗa tana nufar inda yake tsaye yana ƙarewa su Umma kallo, maganar Inna ce ta dawo da shi hayyacinsa, daga kallon da yake yiwa su Umma. “Malam kawo kayan na ajiye” miƙa mata yayi sannan ya samu kujera ya zauna, yana sauke ajiyar zuciya. Umma ce ta buɗe baki cike da ladabi, ta ce “Kawu ina yini?” Wani irin kallo ya watsa mata, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa zuciyarta ta hau bugawa da sauri........

#Comment
#Share
#Vote

Hussain Yusuf🖋️
: *BOKO NE SILA*
      _(Fiction story)_


KING & QUEEN WRITING CHAMBER

HUSSAIN YUSUF

Page 25.

Buɗa baki yayi ya ce, "Hauwa'u yau ku ne a gidan namu?" Ajiyar zuciya Umma ta sauke, sannan ta saki wani murmushi ta ce, "E! Wallahi Kawu mu ne" gyaɗa kai yayi ya ce, "Ai mahaifin naki ya sanar da ni duk irin aika-aikar da kuka aikata ke da ƴar gwal ɗin taki..." Sunkuyar da kai Umma ta yi, shi kuma Kawu ya cigaba da cewa, "Haba Hauwa! Ina hankalinki da tunaninki suka tafi ne? Mijinki uban ƴaƴanki, kika biyewa wannan shashashar yarinyar kuka saka shi a cikin ruɗani da tashin hankali, kuka watsa masa suna aka rinƙa zaginsa a gari..? Ai koda ni aka yiwa haka Wallahi ba zan haƙura sai na ɗauki mataki, yanzu wa gari ya waya tsakanin ke da ƴar taki? Riba kuka samu ko asara? Gaskiya Hauwa halinki akwai gyara sosai, a ciki wannan abinda kika aikata, ba na jin mijinki zai iya yafe miki nan kusa, duk da mutumin kirki ne, bana jinsa idan na je na bashi haƙuri zai iya yafe miki ya mayar da ke ɗakin ki. Amma sai ya huce zan je na same shi. Ku gyara wancan ɗakin ku zauna, zan je na samu shi mahaifin naki, domin mu san yadda za mu ɓullowa al'amarin.." 

Hawaye ne ya zubo daga idanun Umma, ta ce, "Ku yi haƙuri Kawu na san ban kyauta ba, amma don Allah ka bai wa Baba haƙuri ya yafe min.." Ɗan jim Kawu yayi kafin ya ce, "Karki damu zan same shi, kuma in sha Allahu zai yafe miki..." Wani ɗan murmushin jin daɗi Umma ta yi, sannan ta yiwa Kawu godiya shi kuma ya sake fita daga gidan, domin an fara kiran Sallah. Daga nan Inna ta shiga yiwa Umma da Fadila nasiha mai ratsa jiki.. Sannan suka tashi suka yi alwala suma suka tayar da sallah.

***** 
Saboda tsananin fushi Hajiya Amina ba ta san lokacin da ta nufi gida a ƙasa ba. Ganin haka yasa direbanta ya bi bayanta da sauri, yana tarar da ita yayi sauri yayi parking a gefen titi. Cikin hanzari ya zo ya sha gabanta ya ce, "Hajiya ki zo ki shiga mota mana, tafiyar k'asa ba ta dace da ke ba.." Wani banzan kallo ta watsa masa, kafin ta cigaba da tafiyarta, hawaye yana ta faman kwarara akan fuskarta.  Bai damu ba ya sake shan gabanta ya ce, "Hajiya don Allah ki zo ki shiga motar nan, wall..." "Ka ga Idi je ka ɗauko motar.." Da sauri ya juya ya tafi inda yayi parking, da sauri ya shiga motar ya zo dai-dai inda Hajiya Amina take tsaye tana jiransa. Yana zuwa ya fito da sauri ya buɗe mata baya ta shiga, sannan ya zagaya ya shiga driving sit ya ja motar suka nufi gida. Ko gani Hajiya Amina ba ta yi, saboda tsananin baƙin cikin da yake ƙunshe a cikin zuciyarta. "Wai yau mai gidanta, Uban ƴaƴanta shi aka kama da laifin yiwa ƴan'mata har shida fyaɗe? Wasu ma ba'a san su ba. Yanzu kana hawa social media, ban da zancen abinda ya aikata babu abinda ake yi..." Ita kaɗai take zancenta a zuciyarta. Ba ta san lokacin da wani kuka mai cin zuciya ya ƙwace mata ba. 

Shi kuwa Idi direba sai faman ba ta haƙuri yake, tare da kwantar mata da hankali ta hany'ar yi mata nasiha mai ratsa jiki. A hankali ta ji abinda ya tokare mata zuciya, ya fara tafiya, ta ji zuciyarta ta yi sany'i sosai. Yayin da suka ƙaraso gidan, tun kafin ya gama parking Hajiya Amina ta fito da sauri ta shiga cikin gidan. Shiru ta ga gidan babu kowa, "To ina su Maryam ne?" Ta tambayi kanta, ganin babu mai bata amsa ne yasa ta hau stairs, domin a tunaninta suna can. Ai kuwa tun kafin ta ƙarasa ɗakin nasu da yake saman, ta rinƙa jiyo kakarin amai, tamkar mai yin aman yana son amayo hanjin cikinsa.  Da sauri ta ƙarasa hawa stairs ɗin, ai kuwa ta ga Maryam tana ta faman kwarara amai a cikin falon nasu, duk ta ɓata ko'ina babu kyawun gani. 

Da sauri Hajiya Amina ta ƙarasa wajenta tana dafe ta, "Maryam lafiyarki kuwa? Me ya same ki?" Shiru Maryam ta yi, domin zuwa wannan lokacin ta galaɓaita sosai. Cikin hanzari ta gyara mata jikinta, sannan ta taimaka mata, ta saukar da ita ƙasa tun daga cikin falon take ƙwalawa Idi direba kira, da hanzarinsa ya nufo falon, yana zuwa ya tarar da Hajiya Amina dafe da ƴarta Maryam, gaba ɗaya ta fita daga hayyacinta. Cikin tsananin fushi ta daka masa tsawa ta ce, "Dalla ka je ka kawo mana mota mu tafi asibiti ka tsaya kana kallonmu kamar wani maye.." Da sauri ya juya ya nufi parking space inda ya ajiye motar ɗazu da suka shigo. 

Yayin da suka isa Asibitin, da gaggawa likitoci suka karɓe ta aka shiga da ita emergency domin ba ta taimakon gaggawa. Bayan wasu ƴan lokuta, likita ya fito ya kalli Hajiya Amina ya ce, "Ki same ni a office!" Da sauri ta bi bayanshi suka shiga office a tare. Domin ta ƙosa ta ji halin da ɗiyartata take ciki, bayan sun zauna, likita ya kalle ta cikin nutsuwa ya ce, "Hajiya wannan abin ya bani mamaki sosai!" "Likita me ya faru?" Gyara zama likita yayi, ya fuskanci Hajiya Amina sosai har sannan ya ce, "Hajiya ga ku kamar wayayyu, amma me yasa ɗiyarki ba ta zuwa awo bayan ta san tana ɗauke da juna biyu har na wata uku?" A matuƙar firgici Hajiya Amina ta ce, "Likita ciki fa ka ce?" Ya gyaɗa kai ya ce, "Of course! Ciki ne a jikinta" Wata irin zufa ce ta zubo wa Hajiya Amina, duk da tana iya ƙoƙarinta wajen ɓoyewa likita abinda ya ke faruwa, amma sai da ya gane ta shiga cikin damuwa. Kallonta yayi ya ce, "Calm down Hajiya! Ba wata matsala ce sosai ba, yanzu ma za mu iya sallamarku ku koma gida. Amma pls ta rinƙa zuwa awu haka shi zai sany'a ta haifi ɗa mai cikakkiyar lafiya. Ita dai Hajiya Amina ba ta iya cewa komai ba, saboda tsananin ruɗanin da ta shiga. Zuciyarta sai faman bugawa take da ƙarfi. Takarda likita ya miƙa mata ya ce, "Magunguna ne a jiki, ku je pharmacy ku saya.." Karɓar takardar ta yi, sannan ta yi saurin ficewa daga office ɗin. Da ido Likita ya bita yana mamakin, dalilin da yasa ƴartata ba ta zuwa awo. Kuma kana ganinsu ka san ba rayuwar wahala suke yi ba, balle ace talauci ne ya hanata zuwa. 

Yayin da suka dawo gida, Hajiya Amina ta hau tuhumar ɗiyartata akan ta faɗa mata wanda yayi mata ciki. Sai faman rarrashinta take yi, kamar wata ƙaramar yariny'a amma sam ta ƙi faɗa mata. 

Ganin ta ƙi faɗa ne yasa ran Hajiya Amina ya ɓaci sosai, cikin fushi ta hau jibgar ƴartata ba ji ba gani.

Da ta ga tana niyyar yi mata illa, tuni ta ce, "Momy ki tsaya zan faɗa miki" saurarawa Hajiya Amina ta yi, tana mayar da numfashi. Ta tsaya tana sauraron ƴartata, kamar ba za ta yi magana ba, ta buɗa baki da kyar ta ce.

"Momy shine yayi min" "Shi wa?" Kamar ba za ta faɗi ba ta ce, "Yaya Abdul" "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!!" Shine abinda Hajiya Amina ta iya faɗi, kafin ta dubi ƴar tata ta ce.

"Maryam yanzu da gaske kike Abdul shine yayi miki ciki?" Gyaɗa kai ta yi cike da shagwab'a ta ce, "Momy wllh shine" "To ke banda shashashanci irin naki, me yasa kika amince masa, har wannan abun ya faru?"

"Nima ba'a son raina yake yi min ba, idan na nuna masa ba na so sai ya ce min ai aurena zai yi..." Dafe ƙirji Hajiya Amina ta yi, zuciyarta tana bugawa da ƙarfin gaske.

Ta yi nadamar barin Maryam ita da Abdul a gida, tana tafiya aiki. Yanzu ga abinda hakan ya jawo, mijinta yana can a tsare a yanke masa haddi. Yanzu ga ɗiyarta ɗauke da cikin shege.

Babban abin takaicin ma, shine; ɗan yayarta ne yayi mata cikin. Wayarta ta ɗauko, ta lalubo numban Abdul ɗin, domin ta kira shi ta ci masa mutunci.

Tun kafin ta danna kiran, sai ga shi ya kira. Da sauri ta yi picking sannan ta kara a kunnenta. Maimakon ta ji muryar Abdul kamar yadda ta yi zato.

Sai ta ji muryar wani ƙato yana cewa "Ina magana da mahaifiyar Abdul-malik?" Kamar ba za ta amsa ba, sai ta danne zuciyarta ta ce.

"E! Ita ce, ina mai wayar ne ka bashi za mu yi magana" daga can ɓangaren aka ce "A'a Hajiya ki yi sauri ki zo police station ta Shahuci. Domin mun kama ɗanki Abdul da laifin yiwa ƴan'mata biyu fyaɗe.." 

Jikin Hajiya Amina ne ya hau yin karkarwa tamkar wacce take jin sany'i. Ba ta san lokacin da jiri ya kwasheta ba, ta zube akan kujera ta fashe da wani irin kuka mai cike da tsantsar nadama da takaici.

********
"Sa'idu ka tashi ka bani guri, na faɗa maka bani ba Hauwa'u! Kada ta ƙara kirana da sunan mahaifinta.." "Haba Yaya! Idan rai ya ɓaci sai hankali ya gushe? Ka yi haƙuri ka yafewa Hauwa'u wllh suna cikin wani hali ita da ƴarta.."

"To ni ina ruwana? Duk halin da suka shiga su suka jany'owa kansu, domin duk tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa yake duka. Saboda haka ka tashi ka je ka sanar da ita, bani ba i..." 

Da sauri Kawu ya rufe masa baki ya ce, "Haba Yaya! Kada ka yiwa ɗiyarka baki mana!" "To idan na yi mata baki sai me? Ita ta jawo wa kanta, ka tashi ka je ka sanar da ita cewa duk abinda ya faru da ita Allah ya ƙara ya daɗa ƙarawa.." 

Hawaye ne ya zubo daga idanun Kawu, ya dubi yayan nasa ya ce, "Yaya ina Iliminka ya tafi ne? Ina kaifin tunanin da kake da shi? Ka yi amfani da su, ka tausashi zuciyarka ka yafewa ɗiyarka Hauwa'u, Yaya karka manta kullum sai mun yiwa Allah laifi, amma muna neman yafiyarsa nan take yake yafe mana, to kai ma Yaya don Allah ka daure ka zama mai haƙuri da yawan yafiya..."

Wani kallo ya watsa masa kafin ya ce, "Au Sa'idu ni za ka yiwa wa'azi? To bari ka ji tun kafin ka san kanka na san da waɗan nan abubuwan, don haka yanzun nan ka yi gaggawar fice min daga cikin ɗaki, tun ina ganinka da girma da arziƙi.."

Bisa dole Sa'idu ya tashi ya fita daga cikin ɗakin. Zuciyarsa duk babu daɗi, ya san Umma ba ta kyauta ba. Amma bai kamata don kowa ya guje ta mahaifinta ya guje ta ba.

A ƙofar ɗaki ya ci karo da mahaifiyar Umma, a tsaye. Duk ta gama sauraron abinda ya faru tsakanin mijinta da kuma ƙaninsa wato Kawu. Tana ganin shi ya fito ya nufi hany'ar waje. Da sauri ta bi bayanshi a zaure suka tsaya suna tattaunawa akan al'marin.

Fashewa da kuka mahaifiyar Umma ta yi, ta ce, "Ni dama na daɗe da sanin Malam ba ya ƙaunata ni da ƴaƴana a cikin gidan nan.." 

"A'a kar ki ce haka mana, in sha Allahu komai zai dai-daita, har yanzu fushi yake bai huce ba ne..." 

"Yanzu fisabilillahi sai yaushe zai huce? Tunda abun nan ya faru kake zuwa wajensa kake roƙonsa akan ya yafe mata, amma sam ya ƙi yafewa. Yakamata ace zuwa yanzu ya haƙura ya yafe mata, sannan ya kira mijin nata an sasanta su ta koma ɗakin mijinta wurin ƴaƴanta.."

Kawu ya ce, "Ki yi haƙuri komai zai dai-daita in sha Allah!" Daga nan Kawu yayi mata sallama, sannan ya saka kai ya fice daga cikin gidan.

A zaune Umma take tana yiwa Inna wanke-wanke. Koda ganin Kawu da sauri ta miƙe tana yi masa sannu da zuwa.

Amsawa yayi sannan ya zauna akan tabarmar da Inna ta shimfid'a masa. Umma ce ta taso cikin sany'in jiki ta zo gabansa ta durƙusa ta ce, "Kawu an dace?" 

Girgiza kai Kawu yayi ya ce.....

_Comment and share_

Hussain Yusuf✍️
07069475482.
: *BOKO NE SILA*
     _(Fiction story)



KING AND QUEEN WRITING CHAMBER


Page 26.

Girgiza kai Kawu yayi ya ce, "Hauwa'u ku yi haƙuri ku cigaba da addu'a domin har yanzu fushi yake yi da ku." Fashewa da kuma Umma ta yi, ta kalli Fadila ta ce, "Duk kece kika ja mana wannan bala'in, ga shi kin jawo mahaifina wanda ya fi kowa sona yau guduna yake yi gaskiya Fadila kin cuce ni.." Turo baki Fadila ta yi cike da rashin ɗa'a ta ce, "Mun cuci juna dai.." Cikin fushi Umma ta doke bakinta ta ce, "Fadila me yasa kin raina ni?" Kawu ya ce, "Hauwa'u duk abinda kika ga yariny'ar nan tana yi miki ke ce kika jawo, idan tana yin abu ba kya so a kwaɓe ta, kin mayarta ƴar gata ta gaban goshinki, to ga sakamakon gata nan kina gani, idan kika faɗa mata sai ta mayar miki.. Ke kuma Fadila yakamata ki daina, ki rinƙa girmama mahaifiyarki idan har kina son cigaba a rayuwa." Wani yaro ne ya shigo gidan ya ce, "Kawu ya zo ana kiranshi a ƙofar gida" tashi Kawu yayi ya fita a zuciyarsa yana jinjina rashin hali mai kyau irin na Umma.
   A ƙofar gida ya tarar da mahaifin Umma, fuskarsa a murtuƙe Kawu ya kalle shi ya ce, "Sannu Yaya! Kaine kake kirana?" "E! Nine nake kiranka ina Hauwa'u?" "Tana cikin gida a zaune" "Yi sauri ka kirawo min ita" da sauri Kawu ya shiga cikin gidan, zuciyarsa tana ta wasu-wasi akan wannan zuwan bazata na yayan nasa. Ba jimawa Kawu ya fito tare da Umma da Fadila suna biye da shi a baya, daga cikin zauren Umma ta tsaya ita da Fadila zuciyarta tana bugawa da sauri, wani kallo Baba ya watsa mata. Kafin ya ce, "Hauwa'u zuwa na yi na saka ki a gaba, ki je ki roƙi mijinki yayi haƙuri ya yafe miki, daga nan kuma ki kama gabanki ki san inda dare yayi miki" hawaye ne ya zubo daga idanun Umma, cikin muryar kuka ta durƙusa ƙasa ta ce, "Baba don Allah ka yi haƙuri ka yafe min, idan na tafi ban san inda za ni ba, ga Fadila da tsohon ciki.." Baba ya ce, "Wanne cikin kike magana? Cikin shegen zan bari a haife min a gida? To Wllh a yanzun nan ba sai an jima ba, za ku bar gidan nan, idan ta haihu sai ki dawo, amma karki kuskura ki dawo min gida tare da wannan sheɗaniyar yariny'ar." Ya faɗi haka yana shuna Fadila da baki. 

Kuka sosai Umma ta rinƙa yi, tana roƙon Baba akan ya daure ya ƙyale su. Kawu ma ba irin roƙon da bai yi masa ba, ƙarshe cewa yayi idan ya takura masa shi sai ya kore shi daga gidan domin ba nasa ba ne duka nashi ne.

 ★★★
Abba ne zaune a falo shi kaɗai ya haɗa kai da gwiwa. Har yanzu tunanin irin butulcin da Umma da Fadila suka yi masa yake, har yanzu ya kasa gane dalilinsu na yi masa wannan mummunan ƙazafin.

Azima da Najwa ne suka fito daga ɗaki, ganin Abba a wannan halin ne yasa suka ƙaraso wajensa. Cikin sanyin murya Azima ta buɗa baki ta ce, "Abba ka yi haƙuri da abinda Umma da Fadila suka yi maka, ka ragewa kanka wannan tunanin kada ka sa wa kanka wani ciwon."

Murmushin ƙarfin hali Abba yayi ya ce, "Azima ba wannan tunanin nake yi ba, ni yanzu babban abinda yake damuna shine menene dalilin da yasa Hauwa'u da Fadila suka yi mini wannan mummunan k'azafin? Wanda ba zai taɓa goguwa a cikin tarihin rayuwata ba." "In Sha Allah Abba komai zai zama tarihi, kuma mutane sun shaide ka, kuma kotu ta wanke ka daga zargi. Ka ga babu wanda zai ƙara yi maka wani kallo daban.."

Numfasawa Abba yayi ya ce, "Haka ne Azima, Allah yasa mu fi ƙarfin zuciyoy..."Shigowar Salma  ita da mijinta Kabir ne ya hana Abba ƙarasa maganar bakinsa. Washe baki Abba yayi yana cewa "Sannunku da zuwa!" Da gudu Azima da Najwa suka je suka rungume Salma suna cewa "Oyoyo Anty Salma!" Ita ma rungume su ta yi tana sakin wani ƙayatacce murmushi na jin daɗin ganin ƴan'uwan nata cikin farin ciki.

Durƙusawa Kabir yayi har ƙasa ya gaisar da Abba cike da girmamawa. Amsawa Abba yayi yana sakin wani murmushi, saboda ganin ɗiyarsa da yayi cikin farin ciki.  Salma ce ta taso ta zo kusa da Abba ta zauna, cike da ƙaunarsa ta ce.

"Abba fatan kana lafiya?" Murmushi yayi ya ce, "Lafiya ƙalau nake Salmana!" "Amma na ga ka rame da yawa?" "Ba na jin daɗin jikina ne shi yasa kika ga na rame.." Murmushi Kabir yayi ya ce.

"Abba dama mun zo mu sanar da kai cewa, Salma ta kammala karatunta na likitanci ɓangaren jiny'a. Yanzu haka na samo mata aiki a wani private hospital (Asibitin kuɗi) Ranar monday in sha Allah za ta fara aiki."
 
"Masha Allah! Na yi murna sosai Allah yasa ta fara a sa'a!" Cewar Abba, gaba ɗayansu suka amsa da "Amin!" Kafin Abba ya cigaba da cewa, "Yanzu da Fadila ta yarda an aurar da su tare da Salma ai da duk wannan abun bai faru ba. Yanzu ga shi na ta jawowa kanta zagi da tsinuwar mutane, ita ma Hauwa'u da ta biye mata ai ga shi nan suna girbar abinda suka shuka." 

Gyara zama Salma ta yi ta ce, "Abba menene ya faru da Fadila da kuma Umma?" Kallon mamaki Azima da Najwa suka rinƙa bin ta da shi. A cikin ransu suka ce "Yanzu duk wannan zancen da yake yawo a gari Anty Salma ba ta sani ba? Lallai abinda mamaki."

Kallon Salma Abba yayi cikin nutsuwa ya ce, "Salma yanzu duk wannan zancen da ya karaɗe gari lungu da saƙo ba ki sani ba?" "Wllh Abba ban sani ba, don Allah ku sanar da ni" Kallon Kabir Abba yayi ya ce, "Na san ka san komai, me yasa ba ka sanar da ita ba?"

Sunkuyar da kai Kabir yayi ya ce, " A yi min afuwa Abba, a lokacin tana matakin ƙarshe na karatunta, idan na sanar da ita haka zai iya zama nakasu ga karatun nata. Shi yasa ban sanar da ita ba, na kawo ta nan domin ka sanar da ita da kanka.."

Jinjina kai Abba yayi ya ce, "Sannunka Kabir!"Sannan ya mayar da kallonsa wajen Salma ya ce, "Ki yi haƙuri Salma bisa rashin sanin abinda yake faruwa ko kuma ya faru a cikin gidan nan.." 
"Ni komai ya wuce Abba, ban ga laifinka ba, laifin Yaya KB ne da ya ƙi sanar da ni" Abba ya ce, "To ai yanzu ya faɗi dalilinsa, don haka sai ki yi masa afuwa.." "To sanar da ni Abba na ƙagu na san abinda ya faru" ta faɗi cike da zaƙuwar jin wannan baƙin labarin.

Nan take Abba ya shiga faɗa mata duk abinda ya faru babu abinda ya ɓoye mata. Tun kafin ya kammala faɗa mata, fuskarta ta yi sharkaf da hawaye. Kallon Abba ta yi cikin raunin murya ta ce.

"Abba yanxu ina Fadila da Ummar?" Abba ya ce, "Ni yanzu ban san inda suke ba, tun a kotu na ba wa Hauwa'u takardarta. Na ce ta kama gabanta kar ta dawo min gida.." Hawaye Salma ta goge kafin ta dubi Abba ta ce, "Abba ban so ka saki Umma ba!"

Cike da mamaki Abba ya kalle ta ya ce, "Me yasa kika ce haka?" "Abba ko ba ka saki Umma ba, matuƙar ta dawo gidan nan to za ta fuskaci abinda ta aikata ba dai-dai bane. Da kanta za ta zo ta baka haƙur..."
"Dakata Salma!" Abba ya faɗa da ƙarfi cikin fushi ya cigaba da cewa "Irin cin mutuncin da Hauwa'u ta yi min inda ace wani ta yiwa Wllh sai ya ɗaure ta a prison lokaci mai tsawo. Amma da yake nine iya sakinta na yi, duk da haka kike cewa dama ban sake ta ba, to Uban me za ta dawo nan gidan ta yi? Ai ni da Hauwa'u har abada ba ni ba ita." 

Hawaye ne ya zubo daga idanun Salma ta dubi Abba cikin raunin murya ta ce, "Abba kome Umma ta yi maka, yakamata ka yafe mata. Ko babu komai ka dubi Azima da Najwa, ko ba su nuna maka rashin jin daɗin ganin mahaifiyarsu a kusa ba. Ai za su ji babu daɗi cikin zuciyarsu, na san Umma ba da Fadila ba su kyauta maka ba, kuma ba su yi maka adalci ba, amma don Allah Abba ka yi haƙuri ka dawo da ita ko don darajar Azima da Najwa ka yi haƙuri ta dawo don Abba ka ji..." Ta faɗa kamar za ta yi kuka.

Kabir ma ya ce, "Abba ka daina duban abinda ta yi maka, ka rinƙa duba darajar ƴaƴan da suke tsakaninku. Ka yi haƙuri ta dawo gidan, Abba Allah yana son masu yawan yafiya daga cikin bayinsa, kai ma ka yi ƙoƙari ka shiga sahunsu. Ka yi haƙuri komai na duniya ɗan haƙuri ne, ko zuwa yanzu na san Umma ta gane kuskurenta, kuma in sha Allah ta canja halayyarta gaba ɗaya daga ita har Fadilan." Kabir ya faɗa yana kallon Abba cike da girmamawa.

Numfashi Abba ya ja kafin ya dube su ya ce, "Haƙika na ji daɗin wannan shawara da kuka bani, kuma zan yi ƙoƙarin amfani da ita. Shike nan na yarda zan dawo da Hauwa'u da kuma Fadila cikin gidan nan, amma sai na ƙara aure. Dama zaman haƙuri nake yi da ita, to ni dama na yanke shawarar ƙara aure, tunda har kun bani haƙuri zan dawo da ita amma sai na ƙara aure."

Murmushi Salma ta yi ta ce, "Aure kuma Abba?" "Ƙwarai kuwa aure zan yi kwanan nan" "To Abba budurwa ko bazawara?" "Duk wacce Allah ya kawo min kuma na ga ta dace da ni, to in sha Allah ita zan aura budurwar ko bazawarar.." "To Abba Allah ya kawo ta gari" "Amin Salmana!" Abba ya faɗa cike da farin ciki da murmushi akan fuskarsa.

Nan suka cigaba da hira cikin nishaɗi. Azima da Najwa ma zuciyoyinsu cike suke da farin ciki, saboda jin Abba ya yafewa Ummarsu, kuma za ta dawo gare su nan ba da jimawa ba. A wani ɓangare na zuciyarsu kuma ji suke ba su da kamar Salma, yau suka ƙara tabbatarwa ba su da kamarta kaf cikin ƴan'uwansu idan ka cire ALIYU.

Sallama suka ji a can bakin gate, da sauri Abba ya tashi ya je ya dubo. Baba ne da Kawu tafe, Umma da Fadila suna biye da su a baya. Murmushi Abba ya saki saboda ganin surukansa, cikin fara'a ya ce, "Su Baba ne ke tafe? Ku shigo daga ciki." Ya faɗa yana nuna musu ƙofar falo.

Baba ne ya ce, "A'a Inuwa ba zama muka zo ba" da sauri Abba ya ce, "Duk da haka Baba ku daure ku shigo" Kawu ya dubi Baba ya ce, "Ka daure mu shiga!" Bai sake yi masa wata gardama ba, ya dubi Abba ya ce, "Wuce mu shiga.."  A tare suka karasa shiga falon gaba ɗayansu, ƙirjin Umma sai bugawa yake da ƙarfi, domin ganin Abba da ta yi ta ji gabanta ya faɗi, ta ga yayi mata kwarjini sosai har tsoronsa ya mamaye zuciyarta.......

Ayi haƙuri da rashin typing kullum uzuri ne pls

Hussain Yusuf 
07069475482

Post a Comment

0 Comments