*KOMAI YAYI FARKO ZAIYI KARSHE*
*Story and Written by : Fateemah (S) Ibraheem*
*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(Sarki da Sarauniya Writers)*
" *We Rule the World of Writing* "
*WhatsApp Group*
https://chat.whatsapp.com/EJyDTUGRuWoCSv2hvGEPB3
*Facebook Group*
https://facebook.com/groups/791305719158499/
BISMILLAHIRRAH MANIRRAHIM INA GODIYA GA ALLAH SUBHANAHU WATA ALA TSIRA DA AMINCI SU KARATABBATA GA FIYAYYAN HALITTA ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) DA ALAYANSA DA SAHABBANSA DAMA DA DUK WANDA YABI HANYA IRIN TASU DOMIN ITACE HANYA TA GARI
*Page 1*
A harkar rayuwa yau kaga fari ne gobe kaga baki domin ba kullum ake bacci a kan gado ba'! A rayuwata ban taɓa jina cikin farin cikiba sai ranar da mahaifina yabiya kudin kujerar zuwa aikin hajji, Kafin zuwan wannan rana da ALLAH yanufi dady da biyan kudin zuwa aikin hajji ƙawayena da muke wasa dasu waɗanda iyayensu sukaje makka sai tukiya da tun kaho sukemun, kowane lokacin kuma sunamun gori idan munyi faɗa saboda wai iyayen su sun zama (alhazai) Ana cikin haka wata rana dady yakiramu nida yayyena. Inada yayye maxa su biyu babban sunansa Aliyu muna kiransna da Alhaji, sai mai bi masa Sadiq, ni kuma babu abinda yake kara ɓatamun rai irin wannan gorin,wata rana ma idan gorin yayi yawa har kuka nake natafi gida nafadawa dady shikuma yabani hakuri akan komai lokacine. Nayi farin ciki sosai kasan cewar yabani kwarin gwiwa, to da UBANGIJI ya yarda yakuma bashi ikon biya, abun nema yasamu wai matar falke ta haifi jaki.wani abun kuma dayasa ni farin ciki dangane da tafiyarsa shine nasan idan yaje zai tahomun da jallabiya da kayan wasa da agogon hannu dan duk wadannan abubuwan suna bani sha'awa sosai agurin ya'yan alhazai wanda suka kawo musu daga makka bayan wannan nasan dazaran yadawo za'arika kiransa da (Alhaji Nuraddeen)tunda shima yaje makka ALLAH UBANGIJI maji rokon bawansa mai kuma biyan bukatun bayinsa, cikin hukuncin UBANGIJI kuwa duk abunda nasa rai dady na yataho mun dasu wannan shine dadi bisa dadi kenan. Ai daga nan nima nafara shiga cikin ya'yan manya, yayyena maza sune bro Ali, dayan kuma Sadiq muna ce masa yaya Sadiq sannan sai aunty farhan wacce daga ita sai aunty Ihsan, zaune muke da daddy a cikin falo, gyaran murya yayi kafin ya fara magana kamar haka: " Duk abunda nariga nafada yazama dole sai na aikatashi ko yayi muku dadi ko karyayi muku."
" Hmm haba dady ai kasan yanzu nafara canzawa.." Inji yayyena, Dady yace to " ai haka akeso ALLAH yayi muku albarka."
" Amin." suka fada atare, ƙara gyaran murya yayi sannan yaci gaba da cewa " farhan ke mace ce kuma kin mallaki hankalin ki kuma kinsan kanki dukda haryanxu baki gama fahimtar rayuwa ba amma nasan kindan fahimci wani abu ko kadan?" Ita kuma tace " hakane ddy." Dady yaci gaba da magana kamar haka: " kinsan aminatu kanwarki ce kuma ita kadai gareki yar' uwa mace duk abunda xatayi ba daidai ba kiyi kokari ki nuna mata dukda dai kina ƙoƙari",tace " hakane dady insha'allh zanyi iyakar kokari na"
"To ALLAH yabaki iko kuma yayi muku albarka."
" Amin" suka fada atare kowa yadanyi shiru na ya'n dakiku dady ne yace " Dama inaso nafada muku zankawo muku aunty wacce zata rika kula daku saboda zamanku a haka bai dace ba! Cikin murna sukace " eh wlh dady dama gidan ba dadi," amira tayi saurin cewa " hakane wlh aunty farhan kowa yaji dadin maganar."
" to bara ni zan tafi office." Inji daddy. Aunty farhan ce tace " am dady meza'a girka maka ne??" Yace " sakwara nake so da miya."
" ok to adawo lfy." dady yace " aliyu kai yanzu zaka fitane??" Mikewa yayi yace " yes dady," sadiq ne yace "farhan ina key din motarki ne bani naje school nawa yayi kura kuma bansa anwanke minba,"
" Ok amira dakko key yana saman mirrow"
*Page 2*
" ok." Inji Amira, da gudu tashiga tadakko tafito, " yaya sadiq gashi."
"ok thanks natafi sai nadawo."
" Bye adawo lfy yaya ayomun tsaraba."
" ok to saina dawo."bayan kowa yatafine yarage daga amira sai farhan, amira tace " wlh aunty farhan harna kagara yy ahmad yadawo asa bikinku."
" hmm amira meyasa kikace haka ko kingaji da ganina ne???"
" Laah a'a wlh sbd naga yayar khadija zatayi aure shiyasa kuma naga kusan sa'arki ce."
" wace khadija." cewa farhan.
" khadija kawata mana tagidan su farooq." tace " ohhh wai khadija??"
"ehm maryam din gidansu zatayi aure,"tace " ALLAH sarki waini yajikin maman su kuwa??"
"Hmm da sauki jiya ma munje ganinta" cewar amira, " to ALLAH ya bata lafiya," "amin." sunɗan jima suna fira saiga kiran yy ahmad murmushi amira tayu tace " kice ina gaishe dashi"
"ok zaiji bar natafi berdroom." Inji Farhan, " to sai kin dawo."
Tana zaune a falour tana kallo saiga bro Ali, amira " tace harka dawo yy??" Yace " eh angama girkine?? "Tace "yy yunwa kakeji ne??"
" Eh wlh sosai ma "
" hmm wlh ko daurawa ma ba'ayiba."
" what?? Tap to wlh bazan zauna yunwa ta kasheniba bara naje restaurant."
"To gaskiya yy mutafi dama wlh nagaji da zama nikadai." yace " to ina farhan din?"
"Tana daki yace to cemata zamu tafi kada taji shiru." cike da murna tanufi dakin aunty farhan " zamuje cin abinci nida bro Ali"
"Ok to adawo lfy ayomun tsaraba."
"ok to sai mundawo bye"
*Page 3*
Direct (AFNAN RESTAURANT) suka nufa bayan minti 2 da zamansu zuwa 3 saiga wata mace takawo musu list din abubuwan da ke akwai kowa yayi tic daidai abunda yake bukata.ba'ajimaba saigata dauke da su. Sunɗan jima suna fira saiga wata beutiful baby tazocin abinci itada kanwar ta azahirin gaskiya kyakkyawa ce dan duk namijin daya ganta sai yakyasa kai bama na mijiba har mace idan taganta saita raina kanta sbd kyanta dakuma surar da ALLAH yayi mata. Amira na ganinta tace " wow yaya kaga wata. Kyakkyawa gaskiya ta burgeni sosai bara nayi mata magana wlh tashiga raina." harara ya wurga mata yace " shiyasabanaso naje dake wani guri sbd sai kin bada mutum ga shege surutu sai kace Radio, nace miki banganta ba hala? a rayuwa babu abunda na tsana irin surutun ki sbd rabi duk shirmen banzane," ran amira ne ya baci ta ture plate din dake gabanta tana tafasa, cin snarks ɗin da batayi ba kenan, tana turo baki, " kuma ni kamayar dani gida" idanunta cike da kwalla, mamaki ya tsaya yi haba kafin kace kwabo tuni ta falla dagudu ta nufi wurin wannan yarinyar tana kiran " aunty aunty??" Yarinyar ita kuwa sunanta Khairat, juyowa tayi da ganin wake kiranta.amira ce takaraso tana shashsheka tace " sannu "cikin mamaki khairat ke kallonta tace" yawwa ykk? "
" Lfy lao" khairat ce tace " I am sorry fa bangane kiba" amira ce tayi murmushi wanda ya ba sunanta miemie. a bangaran bro Ali kuwa baki yasaki yana kallansu. Amirace tace " bara nayi wa yayana magana ku gaisa". " ok" tafada, ya tafi can duniyar tunani yaji amira na magana " yy kataso muje ku gaisa wlh batada matsala" "oya let's go mana " tanadan kashe masa ido jan hannunsa tayi harsuka isa gurinsu khairat.sallama yafarayicikin muryarsa mai rikata tunanin yan mata, kujera yaja bayan ya xauna ne yafara gabatar mata dakansa cikin kwanciyar hankali, miemie ce tace " amira xomudan xagaya kafin tunani ya fara xiyartar xuciyarta wanda itama batasan dalilinsa ba. shin itama tana sansa kenan? Tambayar datayi wa kanta kenan khairat maganarshi ce tadawo da ita duniyar tunani yace " pls karki biyemun kawai kifadi abunda ke ranki kina sona??" Sunkuyar dakai tayi tace "eh" kunyace ta kamata tarufe fuskarta da kyawawan hannayanta.murmushi yayi gamida jin dadi yace " ok ina godiya da lokacinda aka bani"
*Page 4*
murmushi tayi tace " nima haka." aliyu ne yace " bara mutafi gida munbaro farhan ita kadai"
"ok " tafada ahankali, " amma kinga na manta baki bani phone number dinki ba"
" eh nima namanta." Bayan sunyi exchenge din numbr ne su amira suka taho, " yaya mutafi koh inada islam fa." "eh dama tafiya xamuyi." yawwa aunty khairat ko zamu ajiyeku gida ne? " 'Aa wlh amira kubarshi kawai mungode" bata rai amiratayi tace " uhm" ganin ranta ya bacine yasata cewa " ok to muje" murmushi tayi taja hannun miemie suka nufi mota.baya suka shiga itakum khairat tashiga gaba.suna tafiya suna labari har suka isa g.r.a unguwarsu miemie kenan akofar gida ya sauke su sukayi ban kwana sukuma sukayo gida. Suna isa gida suka samu farhan ba lfy. " sunhanallh farhan lfy? " Cewar bro ali, aman da yataho matane yahana ta yin magana jikake shaaa sai kace fanfo amirace ta kidima tace munshiga ukku yy mutafi hospital kawai.hawaye ne cike da idanunta. " meyake damunki ne farhan cewar bro Ali. Ahankali tace " I don't know." ok canxo kaya mutafi asibiti, ok ahankali tanifi daki tasako kaya tafito tunda suka shiga mota take amai duk ya saka mata galabaita sosai direct emargency suka nufa.bayan an aunata ne akace tana dauke da typort ne.magunguna aka rubuta sann akasa mata drip tadan samu sauki hakan yasa drip din nakarewa aka sallamesu, bayan sunkoma ne sukasamu dady a flour yace "ina kukajene?? Gidan bakowa." Farhan ce ta kwanta kan tiles. " subhnlh farhan yadai." " dady batada lfy fa" cewar amira kamar xatayi kuka. " innalillh meyake damunta." "Typort" cewar amira "to ALLAH ya sawake ALLAH dai yasa ba ruwan fanfan can kika sha ba." " sutakesha mana." cewar Aliyu ko rann saida nayi mata magana tunda munada sona ammh wai tafisan na fanfo" " aikinga irinta sai kikiyaye"
" ok"tafada tace bara na tafi daki to bdmw kikula da kanki.murmushin yake tayi tanufi berdroom. Sundan jima suna fira saiga yy sadiq yashigo amirace tace (oyoyo)yaya harkadawo eh ndw masoyiya ykk? Lfy ammh ba lauba.xaro ido yayi yace lfy?? Aunty farhan ce b lfy topa meyake damunta?? Typort ok muje naduba ta.ahankali suka tura kofar "
*Page 5*
yace sannu ashe bakiji dadiba uhm daga masa kaitayi tace ammh dasauki to ALLAH y kara sauki to ga pizzarki koh murmusjin jindadi tayi tace ngd no bdmw idan ban yi mukuba suwa xanyiwa?? Eh hakane tashiyayi yace to saida safe sunbatar kumatun amira yayi yac( I HOPE YOU HARD A SWEET DREEMS) and you tafsa ahankali byee ban kwans sukayi.amirace tafito daga daki tasamu bro Ali a kwance kan kujera tace mekakeyi ne? Idansa nakan wayarsa yace chart ohh ALLAH dai yasa d aunty khairat ne? Tana murmushi, daga nan Amira ta nufi wurin Aunty Farhan, " Aunty Farhan baki ce kina gaida sabuwar antin Bro Ali ba," murmushi farhan tayi tace ke amira banasan karya wace aunty kuma?? Ninasan bro bashida wata budurwa"dariya amira tayi nan take takwashe komai ta fada mata tare da tambayarlafiyar jikinta,taji sauki.ohhh ALLAH yakara sauki cewar khady,ke na manta fa jiya uncle farooq yabada home work.pls tayani fiddawamira cikin fada.ohhh sorry kawata.amira ce t tashi tana dafe ciki tana washh khady ce ta lura da jinin da yabata mata rigarta.dafe kirji tayi kamar tayi magana kuma tafasa sbd tasan halin amira yanxu tasa mata kuka sbd tsabar an shagwabar da ita abun kukama baya mata wuya khady ce tace amira muje clinic koh?keni wlh ba inda xani hja kawai da mutum yaje karbar magani sai ace allura ni gaskiya baxan jeba idanunta acike d hawaye sbd ciwon kamar wasa ammh yafara fin karfinta.uncle farooq ne yashigo yasame su carko carko yace lfy?? Amirace tasa kuka dama kmar jira take tace uncle cikina ciwo yake garinya yafada atakai ce,ganinta batayi magana b yasashi cewa kuje clinic mana,lura d jininda ke jikin uniform dinta ne yasashi dogon tunani kenan wannn yarinyar ta fara priod ne yar karama d ita?? Hhhm tao lallai allh y sawake to banda ma shashanci tasan xaixo meyasa bata kintsa b? Tsikar jikinshi ce ketashi abmd ba abunda yatsana a rayuwarsa kamar ganin jini koda na dabba balle mutum.dawowa yayi daga tunanin yah haryanxu suna tsaye mtssww wai me kukeyi nanne?? Ke wuce kije clinic jebkum ki karbomn marker inajiranki yace wa khadija ok sir.tafada cikin yanayin rashin jin dadi axuciyar t tace lallai uncle baida tausayi me mekon m yace naraka ta sai yace ....jinya dsa mata tsawa ne yasa ta fita aguje tanufi principal office domin dakko marker.haryanxu amura bata isa clinic b tafiya take tanahutawa yayinda kowa yaketa kallanta maza d mata kowa da abunda yake ayyana wa gameda jinin masu dan hankali ne ke tysaya mata sbd basu san miye ba......
Za a ci gaba a ranar Laraba 4 September, 2023.......
*Faɗimatu Sani Ibrahim Kuki*
+234 904 020 8830
*KOMAI YAYI FARKO ZAIYI KARSHE*
*Story and Written by : Fateemah (S) Ibraheem*
*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(Sarki da Sarauniya Writers)*
" *We Rule the World of Writing* "
*Page 6*
khady ce ta hango Amira aikam tamanta da dakko marker tanufi gurinta amira, Zo muje kama mata hannu tayi suka shiga.uncle yusuf ne yace lfy?? Amirace tasa kuka wai bata da lfy? Ke dallah yiwa mutane shuru ke kullum idan aka tambayeki sai kiyiwa mutane kuka sai kace wata yargoye.mtss lura yayi da blood ɗin da ya ɓata mata uniform ne haan yasa yace on kikeyi?? Kallansa tayi cikin rashin fahimta.khady ce tace eh sir.tan sunkuyar dakai.zanan amira kukbta ne ya tsananta itadai tsoran uncle yusuf take sbd shine maiyiwa kowa allura idan hakan tataso.kin xuwa tayi tatsaya tana raba ido.ke ba magano ammh wayayimn? Nidai wlh nasan ba yar'iska bace ALLAH ma yana shedata.innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.mtwws uncle yusuf ne yace ke dallh kin ishi mutane uban waye yace cikine dake anan? Shiru tayi sbd batada amsa.dallh jeki toilet ki wanke.toilet din tamufa jiki b kwari.khadija yakira yabata pards d fant yace ta taimaka mata sbd yaga batasan komai b gameda wann.itakam tasani sbd tana xuwa karbar pard ok tafada tanufi toilet din kai tsaye ta shiga amira ce takara sa kuka khady ce yafara kwantar mata dhankali tace bakomai ammh idan taje gida tafadawa aunty farhan.ba gardama t amince direct class suka nufa daidai lokacin uncle farooq yafito daga class din xai wuce gida.ahankali yadago rararan idanunsa yace kuje nayi note ku kwafa sann nabada assingment.ahankali amira tace uncle pls nidai wlh baxan iya xamaba sbd uncke yusuf yabani wani famfas nasaka a fant dina kuma ni wlh baxan iya xamaba nidai dan ALLAH kabarni natafi gida tana fadar hakan tana kuka.shidai yayi mamaki sbd yarda yaga tana tafiya sai kace mai koyon tatata ammh bai damuba sbd acewar sa wann matsalar tace ♀kukanda takeyi ne yasashi jin tausayinta yace khady ta dakko mata school bag dinta xai sauketa agida mamaki khady tayi sbd tasan halin uncle farooq mata ma basu dameshi b sbd shigani yake yawuce d ajin yayi soyayya d wata yarinya a cikin school din
*Page 7*
Saboda yana ganin yaxubarwa kansa da mutumci sau dayawa yan ss3 suna xuwa domin nuna soyayyarsu amma ba fuska.hakan nema yasa kowa yashafa masa lfy .khady ce tashiga class ta dakko jkar tabata.uncle farooq ne yakarba sannan yabude wa amira kofar gaba.kowa mamaki yakeyi wata ss3 ce ta hango duk abunda yafaru aikam ranta sai tafasa yake tare da daukar alwashin indai ta bincika taganimo akwai wani abu tsakaninta dashi wlh Amira tashiga ukku a school dinnan. Tunda suka bar school amira ke sharbar kuka tun farooq bayajin komai akanta haryafara jin wani irin yanayi ajikin sa shikansa mamaki yake shin me hakan kenufi?? Ganin bashida amsa ne yasashi yin shiru.lura yayi da Amira tanata dafe ciki hakan yasashi cewa haryanxu jinin bai dainaba ne?? Eh tace idanunta alumshe kamar me barci.kura mata idanu yayi ahankali yana kallan kyakkyawar fuskarta dukda take mai kananan shekaru hakan baihana bayyanar kyawunda ALLAH yayi mata ba.ahankali yace masha ALLAH.bude ido tayi yace amma inane layi naku naga munshigo g.r.a. ehh kaga gidan can konanma xaka iya saukeni saina karasa ngd uncle ba musu ya sauketa ahankali take tafiya kamar batasan taka kasa.duk wanda yasan tafiyarta to yasan tabbas ta canxa kamar yadda shima yadade da lura da hakan,murmushi yayi fili yace allh sarki allh yakara sauki.kai tsaye falour ta shiga ananne ta tarar da aunty farhan tana karatun wani novel ganin Amira ce yasata ajiyewa tace lfy Amira? Daga ina naga lokaci baiyi ba kuma naga idanunki duk sun kumbura meya faru? hawayen da ke idantane suka xubo rungume aunty farhan tayi tana kuka hankalinta ne yakara tashi tace amira wai lfy?? Koso kike nima nayi kukan waya dakeki? Noo aunty farhan cikine dani fa subhanallh ciki kuma amira?? Kamarya waye yafada miki? Ninaga alama mtsww ke banasan hauka wana irin ciki ana xaune kalau yo wayayi miki cikin? Tamata hakane dan tagano wani abu nima wlh bansani b krma dai aikinsan ni ba yar'iska bace koh? Eh mn amira nasani ammh meyasa kikace haka? Ko hospital kikaje ne?? Aa. Aunty to fadaman.zaunar d ita tayi tanso taji abundake damun yar'uwar tata ahankali amira tafada mata komai tana kuka.hhhm murmushi farhan tayi tace ke bafa cikine dakeba bara nafada miki wata magana.gyara zama amira tayi sbd itadai hankalinta atashe yake tace inajinki aunty.
*Page 8*
to kafinnan taso muje kicire school uniform din koh? Daga mata kai tayi suka nifi berdroom cire kayan tayi sann tace aunty farhan wani famfas ne uncle yabani nasaka a fant dina fa nikuma wlh cireshi xan dukya hanani sakewa hhhhhm dariya farhan take tace badai famfas ba, pard dai ko? Eh kamar haka naji khady tace.hmm hankali farhan tafara magana .amira tunda nake ban taɓa yin magana mai mahimmanci dakeba kamar wannan saboda haka bansan wasa kijini sosai to tafada ahankali sbd takagara taji miye daliln wann jinin amira ke yarinya ce haryanzu ammh kisani yanzu girma yafara zuwa miki yakamata ki nutsu ki fahimci rayuwa kisan irin mutananda zaki rika mu'amala dasu kisan yadda zaki rika zama da mutane!ki kare mutuncin kanki sannan ki kare mana .kusan tarayyarda zaki rikayi da maza koda kuwa yan'uwanki ne kiguji shigewa maza domin hakan bashida amfani.kisani yanzu rayuwa ta canza amira maza ba abun yarda bane sbd zai nunamiki yana sanki kamar gaske ammh bake yakeso yanaso ya cutarda rayuwarki ma'ana ya lalata miki rayuwa.dasunga kin yarda dasu sai suyi amfani da wann damar su lalata miki rayuwa sann sugudu su barki.kisani idan harkika yarda kika zubarda mutuncinki a waje to wlh bazaki tabajin dadin zaman aure b ke bama lallai bane kisamu wanda zaizauna dake saida wani ikon ALLAH.dukda haka ba duka sukataru suka zama dayaba akwai masu kirki sosai wa'anda basu sa rayuwar duniya agaba ba sune masu tsoran ALLAH (SWA) saboda haka ki kwantar da hankalinki ki fahimci rayuwa kuma wannan period din dakikaga kinyi kowace mace dakika gani duniya tanayi kuma hakan yasamo asaline tundaga nana Hauwa'u matar Annabi Adam Alaihissalam) kuma duk wacce batayi ma to anaso asamo mata magani kuma idan anayi ba'ayin sallah kuma ba'ayin axumi ba'ataba alqur'ani mai girma sai idan akwai wani babban dalili.ammh kisani azumi idan harkikasha to zaki rama.kingane ?? Daga kai amira tayi tunda farhan tafara mata bayani kanta yake kasa kuma tabbas ta gamsu da abunda tafada mata don haka wannan ba abun damuwa bane murmushi amira tayi gami da jindadi harcikin zuciyarta
*Page 9*
ok bara naje nawatsa ruwa dan wlh jikin duk badadi.ok tafada.suna zaune a falour yy sadiq ya shigo yace amira lfy naganki agida?? Eh wlh bro ali zazzabi nake da ciwon cki ammh d sauki ohh to ALLAH yasawake amin.am farhan angama abinci kuwa?? Eh bro gashi ma a dining.yanaci suna labari saiga dady cewa yayi amira yana gank a gida?? Turo dan karamin bakinta tayi tace banida lfy.subhanallah meyasa meki? Xonan tabuda baki kenan zata fada masa sai takalli aunty farhan girgixa mata kai tayi hakan yasa tayi shuru. Amm zazzabi amnh dasuki ok to ALLAH yakaro sauki amin dady,fira suke cikin nishadi wanda kowa yaga hakan saiyayi sha'awar yayi rayuwa dasu kodan shima yasamu farin ciki.dady ga abinci mikewa yayi yace bara dai nafara yin wanka nayi magrib naji gatacan ana kira idan nadawo sai naci.ok adawo lfy suka fada atare kowa zuciyarsa cikeda san dan'uwansa.bayan sudawo daga masallacine amira tace dady akwai wasu text books daza'asiyamn gobe kau zaka kaini school koh?? Ok badamuwa amira ALLAH yakaimu.murmushi tayi tace amin dady,suna zaune suna lbr saiga yaya sadiq bayan yashigo ne yace amira kice harkin warware.rufe fuska tayi tace eh mn to ALLAH yakara sauki amin yy.dady ne yace bara yaje yadan huta bnkwana sukayi masa dafatan ALLAH yatashesu lafiya baki daya.aunty frhance tace nimadai bara nagudu gobe inada lucture 7:10 saida safenku ok byeee amira ce tace yy nim saida safe murmushi sukayi yace kema yau tunda wuri zaki kwanta?? Ehmn konazaun kuyimun tatsuniya hhhhhm dariya sukayi sukace aa kije ki kwanta sai da safe.amirace taje ta sumbaci kowane a kumatu tana musu byee.haryanxu murmushi suke gamida jin san kanwar tasu fiyeda kowa aduniya.amira ce tashiga berd room gani tati aunty frhan ta saka sleeping drees itama tabude trolly ta dakko tasa sannan ta canza pard sannan sukayi addu'ar bacci suka kwanta.Washe gari tunda dady yatashe su sallar Asuba ba wanda yakoma sbd yau kusan duk da safe xasu shiga school.amira ce tasaka school uniform dinta alokacin ne farhan tafito itama tace inasu yy sadiq ne kije kitaso su mu karya danni dawuri zan wuce ok ahankali ta fara konkosa kofar jin shirune yasa tashiga.
*Page 10*
yy sadiq tafara yayewa lullibin da yayi tace yaya yaya katashi ahankali yabude ido yana murmushi good mornig dear morning yy kazo mukarya zan wuce school ok yafada yanufi toilet.bangaran bro ali taje tafara huta masa iska akunne a razane yatashi ganin itace yasashi cewa ke koh bana hanaki ba? Eh ammh nasan idan kana barci kamar kamutu ammh idannayi haka ai tashi kake shiyyasa.ahankali yasauke ajiyar xuciya yace zankamaki.gwalo tayi masa tace kafito mukarya.da gudu tanufi falour tana dariya.ɓangaren dady tanufa tura kofar tayi ahankali tayi sallama amsawa yayi tace laaah dady katashi eh turare yake fesawa mai kamshin gaske. yan murmushi tace dady in kwana? Lfy lau ya jikin? Alhmdlh ddy kxo mukarya ok .atare suka fito kowa fuskarsa cikeda murmushi farhan suka samu zaune tana jiransu.daya bayan daya ta gaisheda su sannan suka fara karyawa .bayan sun gamane dady yace zaifita amirace tace dady kamanta yau kai xaka kaini school?? Ohh sorry na manta aikin gamako eh dady school bag dina kawai zan dakko.berdroom taje ta dakko farhan ce tashigo tace sai tafiya? Daga mata kai tayi tacewa to karbi kiyi amfani dashi idan kinje school pards ce tabata guda biyu murmushi tayi sann tafito tasamu dady yafita.ban kwana tayiwa su yy sadiq sann ta fita.direct school suka nufa har cikin makarantar dady yashiga sannan yasauke ta yanufi office din principal.uncle farooq ne ya fito tace good morning sir.morning how are you? Fine sir kanta akasa take magana sbd kunyar abunda yafaru jiya take.class tanufa .anan kuwa natarad da khady tazo yajiki tayima amira atakai ce taso ta tambyeta wani abu ammh sbd tasan halinta sai tayi shiru.suna zaune saiga dady, khady ce tace amira meya kawo dady?? ALLAH dai yasa bawani abu uncle farooq yayi mikiba saboda naga jiya yanata wani shishahige miki ni abunma mamaki ya bani wlh .amira ce tace qlh bakoma khady yaxo biyan school piess ne d kudin tex books ohhh khady tafada tana murmushi.uncle ishaq ne yashigo yace good morning class? Good morning sir. How are?fine sir.ok site down. Bayan kowa yazauna ne akfito da littattfai akafara note anayi ana bayani harkoqa yagane inda aka dosa.bayan yafitane aka aiko wata ss1 wai uncle farooq yace amira nuradden taxo.
Za a cigaba a ranar Juma'a 6 September 2023......
*Faɗimatu Sani Ibrahim Kuki*
+234 904 020 8830
*KOMAI YAYI FARKO ZAIYI KARSHE*
*Story and Written by : Fateemah (S) Ibraheem*
*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(Sarki da Sarauniya Writers)*
" *We Rule the World of Writing* "
BISMILLAHIRRAH MANIRRAHIM INA GODIYA GA ALLAH SUBHANAHU WATA ALA TSIRA DA AMINCI SU KARATABBATA GA FIYAYYAN HALITTA ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) DA ALAYANSA DA SAHABBANSA DAMA DA DUK WANDA YABI HANYA IRIN TASU DOMIN ITACE HANYA TA GARI
*Page 11*
Khady ce tazaro ido tace tooh amma gaskiya nifa amira bangane ba nagafa kamar wani abu acikin idon uncle jiya anya kuwa. hhhm murmushi amira tayi tace keni banasan shashanci to idan ma abunda kike tunanine laifine?? Ahhh khady tafada tana murmushi uhm gaskiya ne to ALLAH yasa albarka amin tafada atakai ce,direct office din uncle farooq tanufa tana shiga ta tsuguna tace gani uncle text book din ne yamika mata awata jaka mai kyau.karba tayi harzata fita yace ya jikin naki.gabanta ne yafadi saboda batayi zatan zai tambaya ba, dasauki tana fada tan in iy na, ficewa tayi cikeda jin kunya tana murmushi adai dai lokacin ne sukaci karo da husna zata shiga office din, harara ta galla mata tace ke meke tsakaninki da uncle farooq? Maganar ce tasata tsayawa sbd bata fahimci abunda take nufiba ke ko bakya jina? Aunty ni babu abunda ke tsakanina dashi, to mana kedallah malama jiran uban me kikazo yine? Shine yakirani, yakiraki? Eh texbook dina nakarbo, mtwss daga rana irin tayau idan nasake ganinki dashi saina miki mugun duka kinjini ko, daga mata kai tayi ta ture ta ta shiga thiga office din.amira sakin baki tayi tana mamaki to me take nufi?mtwss aikin banza dandai wlh anhani yiwa ss3rashin kunya da saina yimata .tana tafiya tana masifa ita kadai class tanufa ranta a bace khady ce tace lfy? Duk abunda yafaru ta kwashe tafada mata.dariya tayi sosai harta kunna amira mtsww kenifa banasan iskanci dariya ma kikeyi.aa yi hakuri abunne da mamaki kenifa dama tunba yanzuba na fahimci aunty husna tanasan uncle farooq sbd wata rana nataba ganinta tanayi masa magiya akan yasota shikuwa ko kulata baiyiba yawuce office kila tayi tunanin soyayya kuke shiyyasa.ammh to inhakane kema kifita harkarsa dama ni kinga ina shiga harkarsa ne jiyane fa kawai kuma shima dan akwai dalili.yauma kinga akwai dalili amma inba hakaba ni nataba ma zuwa inda yake??
*Page 12*
Girgiza kai tayi tana danne dariyarta.mtww ni wlh duktama batamun rai Alqur'ani mai girma taciro tafara karantawa a hankali sbd ta rabu da damuwar ta .cikin sa'a kuwa taji zuciyarta na sauka ahankali.saida ta tabbatar hankalinta yadawo jikinta sanna ntarufe suka fara bin darasin karatun. A bangaran alhaji nuradden kuwa tunda yatara yaransa akan maganar yanaso yayi aure tundaga lokacin yafara bincikawa cikin sa a kuwa yasamu hajiya aisha ya yaba da halayenta sosai sbd tunda yake baitaba jin ance tayi wani abuba a office.hajiya aisha matar wani dan kasuwa ne.wanda yayi suna a katsina sundade dayin aure ammh ALLAH bai basu haihuwa ba har allh yakarbi abinsa yanzu haka watanta ukku kenan agida hakan yasa alhaji nuradden cewa zai mata magana yaga ko za'a dace.yana zuwa office kuwa yasa meta zaune da takardu a gabanta .sannu da zuwa yallabai yawwa sannu.idan badamuwa inaso muyi magana ok badamuwa ranka yadade ok kibiyoni office to.office binsa tayi abaya harsuka isa batare da bata lokaciba yafara da cewa hjy aisha bazan boye mikiba inasanki niba karamin yaro bane dazan zauna ina miki boye boye saboda haka kema banaso kiboye min idan kinada wand kikeso kifada nabaki dama.murmushi tayi tace aa yallabai bawani wanda nayima alkhawarin aure kuma na amince badamuwa insha'allh .tabbas yaji dadi cikin ransa sundanyi fira daga bisani tanufi gurin zamanta ranta falda farin ciki.ahaka dai suketa soyayyarsu batare da bata lokaciba dady yasa kannan babansa sukeje neman aure.basu dawoba saida suka tabbatar ansa rana.ba'asa bikin ba sbd yace wata daya za'asa tunda su ba yara bane. Lokaci nata tafiya yau saura sati daya. Abangaran uncle farooq kuwa tunda yakoma gida yake tunanin amira shi kanshi abun mamaki yake bashi, kome hakan ke nufi tambayarda yayiwa kansa kenan nantake kuma zuciyarsa ta basa amsa da santa kake karma katsaya wahalar da kanka.duk wunin ranat haka ya wuni ba sukuni ko abinci yakasa ci saboda yanaso ya tabbbatar ma kansa gaskiya amma daya rufe ido ita yake gani hasalima daya rufe kyakkyawan murmushinta yake gani wunin ranar adaki yawuni kofitowa baiyiba.washe garim haka umma ce ta fahimci halinda dan nata yake.dakinsa tanufa tasame sa kwance saman bed, sallama take tayi amma shiru hakan yasa taahiga mamaki ne yakamata kura masa ido tayi tana nazarin sa haryanzu baisan tashigo ba.
*Page 13*
ahankali tazauna bakin gado tace farooq farooq a firgice yajuyo yace na'am ummah meyake damunka ne tundazu inata kwada sallama meyake damunka?? Noo ummah bakomai bata rai tayi tace kamarya bakomai yaushe ne kafara yimun karya?? Aa ummah zan fadamiki amma ni kaina bansan meyake damuna ba .kawai dai tunanin wata yarinya nake kuma ni nakasa gane me hakan kenufi.murmushi tayi tace lallai farooq kace dai soyayya kafara shine ka keboyemn koh? Murmushi yayi yadaura kansa saman cinyarta yana murmushi, aa ummah bafa haka bane.hhhm bafa haka bane dariya tayi yace to yane? Nidai kawai ummah ki tayani da addu'a.shikenan insha ALLAH, kar kadamu.shikenan ummah nagode da kulawarki akaina hmm kajika idan bandamu da damuwarka ba datawa zandamu?? Hakane ummah Love you so much and i promise to make you happy everytime.murmushi tayi tace ngd kaje kayi wanka kazo ka karya naga lokaci nakurewa ok yafada.Abangaran alhaji nurdden kuwa har ankai lefe yau yakama saura kwana 3 biki kowa kagani ransa cikda farin ciki su amira kuwa baki har kunne za'a kawi musu aunty amarya.Abangaran amarya kuwa itama anshiryata yadda ake shirya kowace amarya a al'adance kuma alhaji nuradden ya tura mata 1millon akan takara tayi kunshi .murmushi tayi doasai sannan tayi godiya doc fadila tafada mawa nanda nan kuwabsuka nufi kasuwa domin kara lodo wasu kayan itada friends dinta.Bayan biki da wata daya nebana zaune a falour ana karyawa sai aunty farhan tace aunty dan ALLAH kiyimun maganakarmu shntake lbari murmushitayi ta tashi suka shiga kitc da dady naga haryanxu bai fito b.ok tafada gamida tashi tanufi site dinta.ba'ajima ba saigasu sunfito bayan angaisa ne farhan tace dady dama munyi waya da ahmad ne yadawo kasar shine yace zaizo anjima.to badamuwa ALLAH yakaimu lfy amin dady.tashi yayi yace zai tafi office cewa yayi ke ba yanzu zaki shigo bane?? Aunty ce tace eh gaskiya dady zanyi komai a goda yau bazanje office b murmushi yayi yace shikenan saina dawo.atatr sukace adawo lfy.bayan kowa yazaunane aunty amarya tace yau meza'girka ne naga haryanzu ladi batazo ba kila wani abu tatsaya yi.
*Page 14*
amirace tace ayimana sakwara da miya.yaya sadiq ne yace eh wlh kichen suka nufa itada aunty farhan domin kama mata wani abun cikin kankanin lokaci kuwa suka kamala.bayan kowa yayi wankane sannan aka nufi dining.sunaci suna fira har aka gama.aunty ce tace kinga farhan taho muje muhadawa sirikinnan nawa abunda zaici heshi yayi yace masoyiyata kin ban domin yin wani girkin batare da bata lokaci ba suka kammala komai suka kai daining abinci ne kala kala sai kace mutum 10 zasuzo kowane da kalarsa.bayan wani lokaci ne ahmad yakira farhan yace yana bakin gate murmushi tayi sosai tace tana zuwa sboda takagara taga yadda hubbin nata yakoma saboda yanzu yayi kimanin shekara 2 a turai.dakin aunty tanufa tashaida mata ya iso.to kije kicanza kaya saiki shigo dashi ko? Eh dama batare da bata lokaciba ta kimtsa cikin wata doguwar riga mai kyau wacce tafito da tsantsan kyawunta, kiransa tayi ta waya tace yashigo batare da bata lokaciba kuwa yashigo fuskarsa dauke da fara'a sallama yayi sannan yashigo aunty farhan ce tasaki baki tana mamaki ganin yarda ahmad yakoma wani babban mutum ga kyau.shima mamaki yake yaga dukta canza masa murmurni tsaye murmushi tayi tace sorry dear naga kacan zamun ne sosai .zama yayi sukadan fara labari da nuna kewar kowa afili dining tamufa tace dear kazo kaci abinci ai kahuta ba musu kuwa yatashi yanufi dininig .yanaci yana santi yace anya kuwa ke kikayi gikin nan? Naji yayi dadi sosai hhhhhhm dariya tayi tace bara nasa maka waigi.bayan sungama ne yace waini ina auta naji banjiyo taba ko bata nanne? Hhm aa tana daki tare da aunty ok bakuwa kukayi? No namanta banfada makaba dady yayi aure wow masha' ALLAH, ALLAH yasa albarka.amin bara nayi musu magana kugaisa ok magana tayiwa su aunty batare da bata lokaci ba kuwa sukafito fuskar kowa dauke da murmushi.sunku yawa yayi yagaishe da aunty sann tayi masa ya hanya tatafi.amirace tazauna kusada shi suka gaisa tace aini yaya fushi nake dakai fushi kuma auta meya faru? Bakai bane tunsa katafi baka kara tambaya taba.hhhhjl dariya tabashi sosai yace waya fada miki ina tambayarki maybe dai ko itace bata fadamiki hmm shikenan inda kace haka ya hanya?? Alhmdlh auta y karatu lfy lau nakusa ma kammala secondry fa really?
*Page 15*
Amma gaskiya kinyi nisa yanzu aji nawa kike?? Ss2 wow masha' ALLAH, ALLAH ya taimaka amin tafada gamida tashi.ina zakije abu bake kama ma aunty shiyyasa ok ungo wann hannu yasa cikin aljihu yafito da bandidin yan 50 hamsin yabata ga wanna kinsiya alawa na manta banyo mikibtsara ba ba.aa nidai yy wlh nagode mezanyi da kudi?? Uhm aa ke ki kiyayeni aidai ba tambayata kikayi ba ninayi niyya saboda haka ALLAH saikin karba.bata rai yayi hakan yasa dole takarba tana godiya.fita tayi tanufi dakin aunty tana murmushi.aunty ce tace harkin dawo? Eh kinga yabani kudi wai nasiya alawa nace yabarshi amma yaki tana turo baki.too ikon ALLAH amma ai sunyi yawa nima nace masa ammh bai yarda ba.hmm shikenan kin gode ALLAH yasaka d alkhairi kuma yasa ayi damu amin aunty.yanzu dai rike kudinnan ki kirgamun naga nawa ne. Ba musu kuwa ta kirga kudi dubu 5 cip 5k hm to yanzu dai yadda za'ayi ki dauki 3k kibani 2k sbd wlh ba'abunda zanyi dasuaunty ce tace aa nim ba:abunda zanyi dasu bata rai tayi tace nidai dan'allh ki karba mana .amira aklh da gaske nakemiki kibar abunki kinga misali idan kinasan wani abu kamar fantd pards d bra kinga ai sai kisiya inda kinga irin wa'ann kayan kamata yayi ace ke kesiye basai kinfadawa dady b ko? Eh hakane aunty ammh dan alkh kidauka ganin tadage ne yasa ta ce to zandauka .murmushi tayi tave to ki ajiye agurinki idanbina bukarmta saina karba ok bdmw.abangaran ahmad kuwa cewa yayi amma farhan inasan magana dake.gabantane yafadi tace allh yasa lafiya? Murmushi yayi yace lfy mana dama inaso nafada miki abunda ke raina .ok inajinka.tunda nadawo ummi kemun magana akan nafito da matar aure idan kuma banida ita saita samo mun nikuma nace tabani lokaci.kinga yanxu kinkusa kammsla karatunki idan yaso sai asaka bikin da kingama adaura Amma yadda kikace.murmushi tayi tace shikenan ranka yadade yadda kace ai haka za'ayi .tabbas yaji dadi sosai yace kuma idan abbansa yadawo nigeria zaisa suxo suyi magana da dady .bankwana sukayi taraka sa bakin motarsa Wani dan madai daicin akwatine yabata wanda yaji kyakyali mai daukar ido karba tayi tana murmushi tace ngd sosai babe .nbdmw bara nawuce naga Magrib ta taho bankwana sukayi ta shigo falour cikeda farin ciki dakin aunty tanufa tamika mata akwatin tana murmushi.
Page 16
Aunty bude mana nan kiga miye aciki budewa tayi cikeda zumudin gani miye.wata sarkace ta gorld suka gani har kala biyu sunyi kyau sosai ba kadanba.daga kasan akwatin kuma wata tamfatsetsiyar waya ce mai daukar hankali.daga dayan bangaran kuma kayan ciye ciyane irinsu choculates etc.... Kiwa baki yasaki yana mamaki bakamar aunty.addu'a take sosai akan ALLAH ya tabbatar da alkhairi .amin amira tafada ciki farin ciki.farhn ce tace aunty idan dady yadawo kice yaxo jum yace idan abbansa yadawo zaizo suyi magana.murmushin aunty ne yakaru tace to madallh ALLAH yasa ayi damu amin tafada gamida barin dakin.kiransa tayi tana masa barka da sauka kuma tai masa godiya sosai shima godiyar yayi mata cikeda soyayya.dasan kasancewa da ita akowane lokaci.da misalin karfe 8:10 ne bro ali yadawo gida baibi takan kowa ba yawuce dakinsa mamaki ne yacika kowa sbd sunsan ba halinsa bane.anyi tunanin zai fito jin shirun yayi yawane yasa amira tashi tanufi dakin ganin yaya sadiq nabasa ruwa ne yasa amira rugawa tace yay lfy? Meya samesa ne?? Yace mun cikinsa ke ciwo kuma nabasa magani amma dai haryanxu bai denaba.hawayene cike a idanunsa hakan yasa amira kidimewa tafara kuka.innalillahi wa'innailaihirraji'un jin bro ali na sallallami yasa su kara kidimewa pls kukaini asibity mutuwa xanyi ganin abun natayin gaba ne gasi dafe mara yake jiyake kamar zata bare.aguje amira tashiga dakin aunty ke lfy? Suka fada agigice kuka ne take yace bro ali bashida lfy gashican zai mutu.innalh wa'inna ilaihirraji'un.farhan ce tariga aunty fita tanufi dakin ganinsa kwance kasa ne yana shashsheka yasa ta jijjiga shi yaya aunty ce tashigo tace kutashi mutafi hospital .fita sukayi su duka suka nufi mota farhan ce tashiga baya tarike bro ali shikuma sadiq yana driving.asibity suka nufa haryanzu amira kuka take tana cewa pls yaya dan ALLAH karka mutu kabarmu wlh muna sanka surutu take wanda ita kanta takasa gane me hakan kenufi.emargency aka karbesa sbd yanashan wahala .bayan ansamu anfara shawo kan matsalarne aka sa masa drip cikin ikon ALLAH yasamu sauki, dady ne aka kira akasanar dashi ba'afi minti 30 sai gashi shima akidime," ina aliyu??" Cewar daddy.
Za a cigaba a ranar Litinin 9 September 2023......
*Faɗimatu Sani Ibrahim Kuki*
+234 904 020 8830
*KOMAI YAYI FARKO ZAIYI KARSHE*
*Story and Written by : Fateemah (S) Ibraheem*
*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(Sarki da Sarauniya Writers)*
" *We Rule the World of Writing* "
*Page 17*
Aunty ce tace yana ciki yasamu barci ma. ok to ALLAH yakara sauki amin. Bayan wani lokaci ne saiga doctor.dady ne yace dctr zamu iya ganinsa?? Eh kushiga ai ya isa yagarka.amirace ta tura kofar ahankali taruga dagudu tana kuka ta rungume sa .amira yafada cikin kunnan ta meyasa kike kuka?kiyi shiru aina samu sauki yaya banaso ka mutu kabarni ME TOO IF I MISS YOU IS LIKE I MISSED EVERYTHING IN MY LIFE.MY LOVELY SIS I LOVE YOU.. Yasumbaci goshinta yana murmushi.dady ne yace aliyu y jikin? Alhmdlh dady to masha'ALLAH. Su aunty ne sukayi masa yakarfin jiki.doctor ne yashigo yace pls idan babu damuwa munaso kudan bamu guri.farhance taja amira suka nufi waje yayinda shima sadiq yafito.doctor ne yace more expicially maza suna samun ciwon cikine kona ce ciwon mara sakamakon desire kuna idan har ba'ayi gaggawa ba za'a iya rasa rayuwar mutum baki daya.saboda dayawa muna samun irin wanna matsalar sosai kuma muna bada shawara wadda idan akabi ta za'asamu waraka da izinin ALLAH.dyk wanda desire dinsa tayi yawa mukan ce yayi aure idan da hali saboda duniyar ta canza.ana samu masu irin wannan suna lalata yara kanana wanda kuma hakan babban matsalace dakuma wulakanta addini sbd addininmu ya haramta hakan.wannan shinee.dady ne yasauke ajiyar zuciya yace ba damuwa dctr mungoda nbdmw ga magunguna nan sai kusiya insha'ALLAH anjima za'asallame ku sbd naga jikin da sauki.aunty ce tace aliyu ammh dai yanzu bakajin komai koh? Sadda kansa kasa yayi yace aunty.su amura ne suka shigo sukace yy badai wata matsala ko? Murmushi yayi yace eh.fira suka danyi daga bisani doctor ya sallamesu suka nufi gida.dady ne yace kaje kadan watsa ruwa kahuta ok yafada sbd wani kunya ne ya lillibesa dakinsa yanufa yawatsa ruwa ya kwanta .aban garan aunty kuwa bayan kowa yasamu nutsuwa ne take shaidawm ma dady saurayin farhan yazo kuma yace zai aiko iyayensa.
*Page 18*
Dady ne yayi murmushi yace to madallh.aunty ce taje ta dakko kayanda yakawo tanuna ma dady yayi farin ciki sosai gamida sa albarka.amira ce tace bara naduba bro ali ok suka fada atare dakinsu ta nufa tasame sa kwnce saman katafaran gadansa murmushi tayi tace yaya baakayi barci ba? Daga mata Kai yayi alamun eh.hannunta yakama yana shafawa ahankali yace amira nagode da kulawarki akaina ina kaunarki sosai murmushi tayi tace yy idan ban kula dakai ba dawa zankula ?kaifa dan uwa nane.kadena mun godiya banaso ja mata hanci yayi yana murmushi.am yy nikam yau ka kira aunty khairat kuwa? Sai lokacin yatuna yace wlh kinga n manta bara nakirata.cikin sa'a kuwa Kira daya ta dauka tace ni gaskiya nayi fushi dakai shine ka manta dani koh? Shagwabe fuska yayi kamar tana ganinsa yace aa kiyi hakuri ina busy ne.amira ce tace bani ita mugaisa mika mata yayi suka gai tace aunty wlh bashida lafiy bamu dade d dawowa hispital b subhanallh tafada akidime garinya? Meyake damunsa? Ciwon ciki ammh yaji sauki ohhm ammah Shine bai fada munba? Yi hakuri wlh baya cikin hayyacinsa ne ok to ALLAH yakara sauki amin tafada tmatakai ce tace ina miemie? Kinganta can gurin umma sundanyi fira sann tabasa tanufi dakinsu.abangaran khairat kuwa cewa tayi ammh baby meya sa maka ciwon ciki? Murmushi yayu yace ke man hhhm dariya tayi tace aa ni ba ruwana .sundanyi fira sann sukayi ban kwana.abangaran amira kuwa bayan taje dakinw take shaidama farhan bikin maryam yayr khadija.sunjima suna labari har barci yayi awon gaba dasu,washe gari tunda wuri khady tazo gidansu amira dayake ba nisa wata jallabiya ce tasaka mai masifar kyau dady ne yadawo mata da ita daga london.itama khady wata riga tasaka tayi kyau sosai gaishe da aunty farhan tayi .bayan sun kara kimtsawa ne suka nufi dakin aunty suka gaisa dady ne yabasu kudi yace sukara suyi party sunyi murna sosai.amira ce tace bara nataso su yaya sadiq naga basu fito ba ok tafada tasamu guri tazauna .good morning dears.morning how are you! I'm fine ammh wanna cin kyan haka in zuwa tunda safe? Yay kamanta yaune fa bikin yayar khady ohh hakane nima ibrahim ya gayyaceni sai munshigo anjima ok.fitowa tayi suka nufi gidan sitting .bayan andaura aure ne .su kafito anan ne suka hadu da yaya sadiq.khady ce ta gaishe dashi cikin ladabi.
*Page 19*
yace ya hidima alhmdlh tafada tan murmushi to ALLAH yasa alkhari yakaimu naku dariya sukayi su duka.motocin daukar amarya ne sukazo basu ankara ba sukaga tacika.zara ido suka fara yi, Sadiq ne yace bara na kaiku.sunji dadi sosai ba kamar khady.tun suna hanya suketa labari.bayan ya sauke sune yace to idan kungama kuyimun magana sai n maidaku gida ni bara naje gurin ango,ban kwana sukayi yanufi gurin ango sukuma suka shiga gidan amarya.washe gari har wajan karfe 7:20 amira bata tashiba sbd gajiya aunty ce taje ta tasheta tace najiki shiru lfy? Mika tayi tace wlh aunty nagaji sosai ammh bar nashira.direct toilet ta nufa shaf shaf tashirya tafita falour ta karya tanufi dakinsu yy sadiq abakin kofa suka suka hadu yace muje nasauke ki.mamaki ne ya kamata tace to kawai sbd tasan halinsa yanzu yafasa.bayan sunfiti ne fita dady yace da aliyu idan kadawo zamuyi magana ok dady office yanufa shina.suna tafiya suna labarin khady waishi ta burgeshi sai wani yabanta yake amira ce tace yaya kodai kana enter ne dariya kawai yayi.cikinsa'a kuwa.
Amira ce tace bro ali ashe kanan? Eh wlh amira daga ina? Uncle farooq ne yace wai kasan tane? Murmushi uncle farooq yayi yace dalibata ce cikin mamaki tace yaya dama kasan sa ne? Eh mana abokina ne munyi karatu dashi a sudan.dan dai bakisan sa ba amm ai ina baki labarinsa.ohhh waidama shine kake fadamun? Eh mana murmushi tayi tace amm yy karfe nawa za'atafi dinner?uncle farooq ne yace ida n kunshira kiyimun magan asai mutafi tare,murmushi tayi tace thanks. Kirane yashigo wayar Bro ali.dagawa yayi yana murmushi adayan bangaran akace dear wai karfe nawa za'ayi diner ku muke jira ok bara nayima angunan magana muji inaga aisai 5:30 ammhbara zankira ki.ok kashe wayar yayi yace amira kicema farhan idan sun shirya sufito mu wuce tunda duk guri daya ne ok tafada tana murmushi.tanufi ciki .tana zuwa tasame ta tana waya d yy ahmad .aunty farhan yy yace idan kunshirya kufito sunyi waya d yy ahmad guri daya za'ayi.gashima muna waya bara mu shirya sai muyi magana.bayan sunshirya ne suka nufi kawataccen hold dinda aka maka .tabbas daga ganin yadda aka kawata gurin kasan ankashe kudi ba kadan ba.
*Page 20*
Aban garan amare kuwa sunsaka kaya iri daya.fararen riguna sunyi kyau sosai kowa kagani fuskar sa cikeda farin ciki💃🏼 .ankawata guri domin M.C natasa ka wakoki kala kala, uncle farooq ne yakira amira suka fita wajen hall din suka samu kujeru suka zauna.murmushi yayi yace amira ina tayaki murna kuma ALLAH yabasu zaman lfy,amin uncle nagode sosai n bdmw.wata jaka yabata yace ga gifts nan mh bayawa.a'a uncle nagode.meyasa? Za'ayimun fada ne murmushi yayi yace ba wanda zai miki fada indai kikace nina baki sbd dady yasanni sosai kuma kitam bayesa,sbd taji yace haka ne yasa tayi godiya ta karba.sundan yi fira haryake tsokanar ta akan abunda yafaru a school ranarda tafara priod.dagudu tabar gurin tana murmushi wai kunya taji.bayan taro yatshi ne khady tace waike miye tsakanin ki da uncle farooq? Hmm kije ki tambayesa mana,miye yabaki? Kai ke kam ki kware gurin sa ido.sai kiduba.murmushi tayi tace ai kobaki ceba baridai mukara gida,sadiq ne yafito yace kuzo muwuce gida.bayan sun isa gidane.suka watsa ruwa sukayi sallah.sannan suka bude jakar suka fara fito da wani kwali madai daici .Aunty ce tashi go tace ashe kundawo? Me kukeyi ne? Khady ce tace sirikin ki ne yakawo ma amira.duka takai mata a cinya tace khady bansan wulakan cinifa ba saurayi na bane,abokin bro ali ne fa.hhm aunty ce tace kudai kuka sani karbar kwalin tayi tabude waya ce mai kyau sosai tace kai gaskiya tayi kyau masha'ALLAH, khady ce takarba tace wow tayi kyau "wani amira ce tace ni nasan dady bazai bari narike waya ba😢 aunty ce tace a'a zai barki mana ai kinga yanzu kece kan layi.inda an kauda farhan hmm murmushi tayi tace kai aunty? Eh mn ai kebama sai kinyi wani karatu ba tunda ALLAH yakawo.khady ce tace wlh kuwa.harararta tayi.wani kwalin takuma fiddowa wani zobe ne na azurfa sai kyalli yake .daga jikin kwalin ne taga wata karamar paper .aunty ce tafita haka.yasa tabude paper ganin number tayi da sim card.a kasan pepar an rubuta idan kin koma gida ki kirani masoyiya.dafe kirji tayi tace dear kuma? Khady ce tace lfy? Oho keni dan ALLAH kin dameni .khady ce tace to wai yanzu kuma saboda uncle farooq din kike mun wulanci? Wh din barshi ahaka .dariya tayi tace kin nemeni wlh.firarsu sukayi cikin nishadi.
*Page 21*
Sim din tasaka a wayar takira sa.he'llo my dear? Ykk ya hidima? Alhmdlh uncle naga sako na... Bata karasa ba yace banasan godiyar kirike abarki.YOU ARE MY WIFE INSHA'ALLAH,saboda ina sanki ko kinyima wani alkawarin aure? Shiru tayi cikeda jin kunya yace ina miki magana kifadamn gaskiya pls karki cutar da zuciyata.unclle? Na'am barci nakeji saida safe.murmushi yayi yace shikenn HAVE A SWEET DREAMS MY FUTURE WIFE, OK GOOD NIGHT😴 takashe wayar zuciyar ta cikeda farin ciki.khady ce tace masoya? Amira ce tace gamufa.yy sadiq ne yashigo yace baku kwanta ba? Eh wlh amira tace bara nabaku guri nasan dai tadi kazo😜 harararta yayi yace eh din.fita tayi tanufi gurin aunty farhan,abangaran sadiq kuwa yanacan yana tsunkar fure💃🏼💃🏼 bayan yatafi ne amira tashigo tace angama soyewar? Eh mana kema ai yanzu kika gama .sundanyi fira sann sukayi barci😴 washe gari tunda safe haya niyar mutane ta tashesu gida kam yacika masha'ALLAH yan uwan momy ne sukazo su inna gaje da inna ladi yayyene agun momy,bayan sunyi wanka ne kowa ya shirya sunyi kyau bakadan ba wata riga ce amira tasa mai mugun kyau.haka itama khady komai nasu kala daya .gidan sitting suka nufa kai tsaye.Da misalin karfe 1:10pm aka daura aure.gida yacika yan'uwa da abokan arziki.amira ce tace waini khady duk yau banga bro aliba.ki kirasa mana tafada ata kaice,kiran wayarsa tayi farooq ne yadaga yace hello baby? Shiru tayi tana nazarin maganar tabbas tasan uncle farooq ne.am ols uncle ina bro ali ne? Haba gimbiya ta ai kin bari mugaisa ko? Murmushi tayi tace ina wuni? Lfy lau y hidima? Alhmdlh yy nki baya kusa.shine vaki kirani ko? A'a uncle bansamu time bane🤩 ok shikenan ki kulada kanki kada wani yayi mun wuf dake😞 murmushi tayi takashe wayar.A kwana a tashi ba wuya agurin allah soyayya takara kulluwa tsakanin farooq d amira haka ma khady da sadiq kowa yana samun kulawa sosai agurin kowa.Yau yakasan ce watan su farhan 5 agida jan mazajen su duk wanda yagan su yasan suna cikin farin ciki.amira ce tace dady pls yau zanje gidan aunty farhan da bro ali.ok kice nace sadiq ya kaiki amm karku dade,to dady nagode🙏 .uncle farooq takira tafada masa zataje gida bro ali hakan yasa yabar komai yaruga ta isa zuciyarsa cikeda farin ciki dama kwana biyu bai gantaba.
*Page 22*
Gidan farhan suka fara isa daga bisani suka nufi gidan aliyu.acan suka samu farooq mamaki ne yakama amira tace uncle daga ina? Khairat ce yace magana zakiyi aidama nasan saboda ke yazo gidannan .a'a aunty khairat nifa bansan ma ya zoba.ko uncle? Eh mana bayan sungaisa ne suka danyi fira farooq ne ya tura mata tex baby inaso muyi magana pls kisameni waje,farooq ne yafita bayan takaran tane tafita tagansa zaune bata rai yayi yace amira meyasa kike saka mayafi karami? Kinsan ina kishin ki sosai, banaso kidena .murmuahi tayi tace kayi hakuri insha'ALLAH zandena.fira suka danyi dannan tace bara mutafi dady yace karmu dade ok. A tare suka shiga ciki ban kwana sukayi suka fita.suna tafiya suna labari da yy sadiq harsuka isa gida,ba'ajima ba uncke farooq yasa iyayen sa sukaje neman auran amira kowa yayi farin ciki sosai bakamar dady.yarjeje niya sukayi akan idan anyi bikin zata cigaba da karatu.amince wa sukayi.bayan yan kwanaki ne akayi aike .ba'ajima ba akasa rana wata 1 tun ana saura sati daya ake rakashe wa anyi party kala kala.anan bangatan kuwa ba'acewa komai💃🏼💃🏼A kwana atashi yau biki saura kwana biyu.gida kam alhamdlh kowa yana cikin farin ciki. Washe gari aka daura auren( aminatu nuradden wato amira) da farooq abdullahi. Bayan anyi mata nasiha ne. ya'n daukar amarya sukazo tasha kuka sosai.kaibama itaba harda dady saida ya zubarda hawaye saboda farin ciki dakuma fatan allah yabada zuri'a tagari🚶♀️🏃 hakika amira tayi farin ciki sosai da ALLAH ya nuna mata ranar auren ta da farooq.anyi biki da sati biyune akayi na sadiq.rayuwa suke tajin dadi😜😜 .bayan shekara daya ne amira tasamu ciki.farooq ya kulada ita sosai har ALLAH yasuke ta lfy.kowa yay murna ta haifi yara biyu mace da namiji .macen ce aka sama sunan mahaifiyar amira wato husna.namijin kuma( nuraddeqn suna kiransa jenior) ,daga karshe dai nacika burina nazuwan mahaifina makka🕋 dakuma auran uncle farooq.
*ALHMDULILLAH*
WANNAN SHINE KARSHEN LITTAFIN KOMAI YAYI FARKO ZAIYI KARSHE🤩🤩
ina mika godiya ga gurin SHUGABAN KUNGIYAR KING AND QUEEN WRITING CHAMBER wato SARKI DA SARAUNIYA WATO ABDULKINGARTICLE🙏🙏 DA KUMA KINGBOY ISA🙏 DA MUJAHEED MATASHI🙏 BAZAN MANTA DAKAI BA WATO HUSSAINI KHALID SARDAUNA KAIMA INA GODIYA SOSAI 🙏❤💚💙 DA ISHAQ..... TURAWA BRAVE,DUKKAN KU INA KARA MIKA GODIYA SOSAI ALLAH YAKARA BASIRA
Faɗimatu Sani Ibrahim Kuki
+234 904 020 8830
0 Comments