🌟🌟CHANJIN BA ZATA🌟🌟
By
MARYAM IBRAHIM LITEE MALUMFASHI
Babi na ɗaya
Da sunan Allah me rahma me jin kai
Kwashe tuwo nake a cikin kicin idona duk ya yi ja saboda hayaƙi dan gidan yawa ne, kowa ya hura murhun sa, amma duk da haka hankalina na can wurin sauraron hirar da Baba Ladi da Baba Gambo suke yi, waɗanda ke ƙarƙashin baranda daga yamma.
Yayin da Mahaifiyata Fatima wacce muke kira Innarmu mu ƴaƴanta, take daga na ta kofar ɗakin, itama a ƙarƙashin baranda amma ita a ɓangaren gabas take, kenan suna kallon juna, wanda na tabbatar itama tana sauraren su suna tattaunawa ne kan bikin wata yarinya a makwabtanmu na irin mahaukatan saitin da aka dan ƙara mata da kayan kicin ɗin da aka yi mata sai da aka maido ma uwar da saura.
Gara kuwa da aka soma loda ta sai da aka cika store har ma ya yi kaɗan. Baba Ladi kenan take faɗawa Baba Gambo, Baba Gambo tayi tsaki cikin nuna damuwa.
"Ai wallahi kallo ya bar ni, duk wannan mayataccen tarin ne da ya sani gaba shi ya hanani zuwa dankin nan, amma in Allah ya yarda da ni za'a ranar bikin in je in kashe kwarkwatar ido".
Tsam Innar mu tayi ta shige ɗaki, nima na kammala kwashe tuwon cikin wata babbar cooler na kai ɗaki na komo na ɗauke tukunyar miyar na aje a kofar ɗakin mu.
A ɗaki na samu Innar mu tana zaune kan ƙaramin gadonta na katako
ta dora kanta jikin gadonta, ganin har na zauna bata ɗago ba ballantana tayi min sannu da sanya albarkar da ta saba a duk sanda aka yi mata abinda ya faranta mata, na san abinda ke damunta dan haka sai na ƙara matsawa kusa da ita Innar mu " na kira sunanta firgigit ta yi alamar tayi nisa cikin tunani.
"Me ya same ki? " Na tambaye ta shiru tayi na cigaba.
Innar mu kwanan nan, kin tsangwami kan ki, tun randa su Baba Ramu suke hirar auren Jamilar Alh Babajo har suke cewa wasu sai dai aukin tara yaya mata amma ba a da zuciyar da za a huce takaicin kai masu kayan ɗaki, tun daga nan kika rasa walwalarki.
Na sani auren Anty Ummu kike tunani, wanda ko shi mijin naga ai yasan halin da muke ciki, har kuma ɗakin nan ya zo ya ce kar ki damu kanki, abinda Allah ya hore shi za'a kai mata, kuma arzikin bawa ai yana goshin sa Malamin mu ma ce mana yayi duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa sai ki ga abinda ba'a zata ba, kofofin Allah ai yawa gare su".
Zuba min ido tayi ganin yarinya ƴar shekara sha biyar ce da wannan zurfin tunanin, duba na tayi sosai sannan ta ce duk na sani Shuhaina abinda ke damuna duka yau saura kwana ashirin da hudu bikin nan ga gonar mahaifinku wacce kuka ci gado na ce a sata a kasuwa amma dillalan sun ƙi mata sayen daraja, kuɗin su ɗan yi auki, dan nufina a raba kuɗin biyu ayi mata hidima da rabi rabin sai a adana maki a banki tunda ke ma idan muna da rai kwana nawa ne? " Jin ban amsa ba yasa ta gane kunya nake ji ta cigaba "Wannan yarinyar jiya da ta zo har kuka tayi dan mijin nata shi ma sai jiya aka sako shi na yarinyar da ya bige a hanyar kafancan dubu goma ta kawo tana kuka wai yaci ace ita ce komai a bikin kannenta amma ji abinda ta kawo da kyar na taushe ta na nuna mata komai nufi ne na Allah, ga matsalar mutanen gidan nan abu bai samunka a tausaya maka sai dai ayi tayi da kai ".
Na ce "Ki yi hakuri Innarmu wannan kuma sha'anin yawa ne".
Yusuf wanda ya dade tsaye a bakin kofa yana sauraronsu ya ƙaraso ya zauna yana cewa ; "Haba Innar mu a yanda na sanki da juriya da tawakkali me zai sa ki tada hankalinki kina raunana zuciyar ki abu ya kama damun ki ban jin dadin ganin ki a yan kwanakin nan kina cikin kunci,
nima zubi nake ba'a bani kwasata ba nayi niyyar sai dai in je in ce ma yayar mu ta fito mu je mu sawo ma Ummu kaya, a yan kwanakin nan duk aikin karfin da na samu hadawa nake da shi kafin in je wurin aikin walda ta har taɓa ka lashe nake karɓa na mashin ".
Ya sa hannu a aljihu ya fiddo Kuɗi ya ba Innar mu.
"Wannan na ƴan ayyukan da nake yi ne, suna zubin idan aka bani sai mu san abin yi ina son ganin walwalarki Innar mu ki aurar da Ummunki ki kai mata komai kamar sauran yaya".
Dan murmushi ta yi.
Allah ya yi maku albarka dukkanku".
Yusuf ya ce "Yawwa Innar mu".
Ta ce "Ga uwata itama shiru ko duriyar ta an rabu da ji ".
Ya ce; "Kai na mance Innar mu in faɗa maki jiya da daddare ta kira ni har ta nemi in kawo maki wayar na ce mata dare ya yi nisa har nake faɗa mata bikin Ummu ta ce mijinta ya kammala karatun shi dama ita yake jira ta karasa nata, sannan tana ganin kafin ma bikin za su dawo'.
Wani tsalle nayi na jin dadi wanda har sai da Yusuf ya dube ni.
"Ke fa Malama lafiya? Meye haka? Na ce "Yaya Yusuf murna ce fa rabon da in ga Anty Amina tun Ina shekara goma koma zan gane ta?.
Ya harare ni kar ma ki gane ta tunda sanda ta tafi ke ɗin jaririya ce."
Dariya nayi.
Innar mu kuwa ba ka cewa ta ji dadin labarin da aka bata, na san ta hadiye murnar ta ne a cikin ta, dan ita ɗin me bar ma Allah komai ce.
Yusuf ya dube ni.
Me kika dafa mana ne? "
Bai ko sauke numfashi ba
na ce; "tuwon shinkafa miyar kubewa danya" bata fuska ya yi "Yanzu da ranar nan?
Na ce "To komai na mu ya kare ita kenan shinkafar ta rage kuɗin cefanen da ka bayar kuma na sawo kubewa ɗanya da kayan miya".
Ciro kuɗi ya yi a cikin aljihun shi
"Amshi ki sawo taliya ki dafa mana da yamma, akwai wani aikin ginin da muka yi ranar lahadi mutumin bai biya ni ba idan ya bani sai in sawo kayan abincin.
Ba mu ankara ba sai dai muka ga Innar mu tana share hawaye.
Mun san bai wuce mahaifinmu ta tuna ba, sai muka yi tsit! Sai da ta natsa.
Yusuf ya ce "Ina Ummun ne? "
Na ce Tana gidan Hajiya, aikowa tayi kiranta".
Ya ce "Zubo min tuwon nan in ci in kama kaina".
Sai da na zuba masa sannan na dawo na zauna.
Matar Baba Auwalu tayi sallama ta shigo Baba Auwalun abokan wasa suke da babana,
Ta zauna dai dai Yusuf na cewa
"Gaskiya randa kika yi aure kika tafi za mu yi kewar girkin nan naki me dadi
ga shi tafiyar ki tana nufin innar mu ce za ta ci gaba da girki
wanda ni bana son tana wahala. "
Matar Baba Auwalu Gwoggo saratu ta ce
To kai kuma sanda za ta tafi ai surukarmu tana shirin isowa ko? "
Sosa kanshi ya yi
Ai ni Gwoggo ko zan yi aure sai na aurar da salma"
Baki ta rike
"Salmar me shekara goma za ka tsaya jira?
Ya ce "To idan ban kauda ta ba, abin ne na talaka sai a hankali. "
Ta yi murmushi
To Yusuf ubangiji ya rufa asiri, ya cigaba da ba ka wuyan daukar nauyin mahaifiyar ka da yan uwanka ya ba ka mata ta gari wacce za ta rika kara maka kwarin gwiwa ta soka kai da yan'uwanka".
Sosa keyar shi yake har ya fice
Innar mu ma duk da dadin da addu'ar tayi mata a fuskarta ba ta ce komai ba.
.......................................
Da safe misalin karfe bakwai da rabi, kari muke da kokon dana dama mana, kasantuwar yau din lahadi ne babu makarantar Boko duk da dai Exam) muke an kusa hutu da yake je ka ka dawo nake yi a (Government Day senior secondary school malumfashi) Ina aji hudu ss 1 bamu da islamiya yaron me makarantar ya rasu
Daga kofar dakinmu aka yi sallama.
Baba sani ne kanen mahaifinmu shi ma cikin gidan yake zaune.
Ya shigo bayan an amsa masa sallamar.
Kan kafet din dake malale a dakin ya yi nufin zama kasantuwar ba kujera, amma tuni na dauko masa pillow a uwar daka ya ce .
"A'a malama shuhaina ba'aje makarantar bane? "
Na ce "Eh"
Na ba shi labarin abinda ya hanani
muka gaishe shi, suka gaisa da Innar mu,
Ya dubi Innar mu
"Zuwa na yi in ji na ki shirye shiryen game da bikin nan dan abin na ta matsowa. "
Ta ce "Dama maganar gonar nan ce da na gaya maka kuma har yanzun dai ba'a samu masu sayenta ba da daraja"
Dafe kansa ya yi ya yi shiru na dan wani lokaci
Kafin ya dago
Allah ya rufa mana asiri ya raba mu da babu ".
Ta ce "Amin Ta gyara zama
Ba na so a sai da gonar nan amma tun da nake ta bige bigen in ga nawa zan samu in hada da sadakinta Wallahi da kyar na kulla dubu ashirin"
ya fiddo su ya mika mata
ta sa hannu ta amsa tare da godiya me yawa
Wasu ya kuma fiddowa wannan sadakinta ne da na jin magana da suka kawo na so barin su wajena ko zan samu in kulla in yi mata saitin kamar kowace ya amma abin ya faskara su kuma sauran yan'uwana Ina yi masu magana to Auwalu ne dai ya bani dubu biyar
Ya miko ta ita ma
ya karasa maganar tare da damuwa me yawa akan fuskar shi.
Ta ce Babu komai Baban yara ai kana iya kokarinka Ina laifin wanda ya tsaya maka akan al'amarinka? Koma bai baka komai ba, adduata agareka ita ce Ubangiji ya saka maka da mafificin alheri ya ba ka ladan zumunci ya raya zuriarka yasa masu albarka.
Wannan yarinyar ma ta kawo dubu goma shekaranjiya.
Ya ce Wai Azima?
Ta daga kai
Ya ce Allah ya saka mata da alheri
Ta ci gaba Inna ma ta aiko in je jiya buhun shinkafa biyu da buhun gero da na masara ta nuna min da fridge ta ce in ji dan ta ita kuma ta bani dubu talatin ".
Ya yi murmushi 'Ma sha Allahu, in sha Allah asiri zai rufu
Itama murmushin ta taya shi
Yusuf ma adashi yake yi shi yake jira a ba shi sai su tafi da yayar ta su su sawo kayan dakin, to ba ka aje komai ba duk dan abinda ka samu ciki ke cinyewa"
Dan murmushi ya kara yi ya yi addua ya fita.
Na umarci kanwata salma da ta kwashe kayan da muka yi kalaci ta je ta wanke, ni kuma na kama gyara dakin
Cikin lokaci kankani na gyare shi
dama ba wani tarkace mai yawa a cikin shi.
Falonmu kafet ne dan ubansu, me tsada wanda Hajiya kanwar kakarmu wadda,
ta haifi innammu ta bata da yake ya hadu da masu tsafta kullun cikin tsaftace shi muke
Sai keken dinki da innammu ke yi shi din ma hajiyar ce ta saya mata
Sai labulayyar mu masu kyau su ma hjy ce ta bamu.
Uwardaka gado ne me rumfa sai fameka karami.
Na kunna turaren tsinke.
Zuwa lokacin Yusuf ya dade da fita wurin aikin shi na walda
Anty ummu ko in ce Amarya kwance take kan karamin gadonmu tayi shiru kome take tunani oho
Ita innammu azkar take wanda in dai zaka same ta ita kadai to baka rabata da hakan,
Ni ma wanka nayi na kwashi kayan wankin innar mu na fita tsakar gida in da mutanen gidan ke ta harkokinsu na yau da kullun.
Wani abin tashin hankalin, shi ne har bikin ya rage saura kwana goma ba'a ba Yusuf adashin sa ba
wanda duk da taurin ransa fidda kwalla ya rika yi gaban innar mu
ga shi duk tarin yawan mutanen gidan mu dubu goma suka hado ma innammu.
Wai gudummawar su kenan
Dakin kishiyar innar mu kuma waanda muke uba daya da su Dubu goma mahaifiyar su ta bada ta ce ga na su
Wanda a dakin na su ma mutum daya ma za ta iya gama komai
Zuwa lokacin matan gidan suna ta ma innammu tunin yanzu fa ana saura sati guda ake zuwa danki
A son innar mu aje da kudin da ke hannu a sawo abinda ya samu
A cewar ta sandar da ke hannunka ai da ita kake kai jifa
ba ka da gashin wance ba ka cewa sai ka yi kitson wance
Amma Yusuf ya kafe
Sai ana saura kwana takwas innar mu ta nuna matukar bacin ranta
Sannan ya hakura da niyyar washegari asabar yayammu za ta zo sai su tafi su sawo abinda ya samu.
Wayewar garin asabar ko ni ban je makaranta ba Ina jiran ganin tafiyar su.
Yusuf tuni ya shirya yayar mu kawai yake jira takwas da rabi tayi sallama na ce
kai yayammu kin yi sauri, "
Ta ce bayan ma sai da na shirya yara na tura su islamiya na ce idan an tashi su nufi wajen gwoggo (surukarta)
Ballo dan da ke bayanta nayi
Yusuf ya bata rai
yanzu zama za ki yi ni in don ta ni ai da yanzu Ina birni"
Kallon shi tayi dai dai tana zama
Ai duk Saurinka dai ka bari in gaida uwata ko?.
Ta shiga gaishe ta tana amsawa cikin nutsuwa
Nima na gaishe ta Yusuf ma ya gaisheta
Ta tanbayi salma da ummu
Innammu ce ta bata amsa salma na gidan inna can ta kwana ummu ta fita yanzu kasuwa ta nufa wai zata sawo kayan dinki
Ta idasa maganar tana mikewa
Bari ka gani in yi kokarin ida ma mutane dinkunansu ".
Yayar mu ta ce Allah kuwa innar mu kafin a fara biki".
Hayaniyar da muka ji tsakar gidan ya dauka ne yasa mu saurarawa
Bamu fahimci meke faruwa ba Yusuf ya tashi ya leka da sauri ya juyo
"Wallahi innar mu ga Amina nan".
A guje yayammu Azima ta fice
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: 🌟🌟CHANJIN BA ZATA🌟🌟
By
MARYAM IBRAHIM Litee
Babi na biyu
Ni ma na bita tana mamutse da ita suka shiga ɗakin, murna yaya Azima take sosai, ita kuma ta faɗa kan Innarmu ta na kuka.
Mutanen gidan ma kan ka ce me sun cika ɗakin sai da aka natsa kowa ya kama gaban sa sai mu kaɗai.
Labari take ta bata na bayan bata, zuwa can sai ta zura min ido, "Wai Shuhainar Inna ce ta zama haka? "
Jawo ni ta yi, "Ba ki gane ni ba ko?
Na ce "Da dai a hanya na hadu da ke zan rinƙa tunanin ina na san ki, dan ko hotunanki da ke akwai ba haka haka kike ba".
Ƴar dariya ta yi.
Ni kuma mamakin irin kyan da ta ƙara nake, duk da dai dama mutane suna cewa ba me kyanta a ɗakin mu, gata doguwa ce ita, kuma bata da jiki amma tsananin jin dadi yasa fatarta ta murje ta yi lukwi-lukwi kyan fuskarta kuwa ya isa.
A ɗakin da Yusuf kaɗai na ga take kama, dan dai shi ba fari ba ne
Ita kuwa kalar jikinta wani yallow yallow ta koma dan tsananin kyan da tayi, ɗakinmu kuwa tunda ta shigo tamkar kana a cikin birnin paris tushen turaren saboda tsabar kamshin da yake, wani danƙararren less ne jikinta wanda kallo ɗaya kai masa ya wadatar da kai gane ba na me ƙaramin karfi ba ne.
Yaya Azima ta dubi Yusuf amma dai ɗan Ƙanina tafiyar nan ba yau ba ko? "
Ya murmusa.
Ga fa sister ta iso wane tafiya sai dai kuma lokaci yana kurewa ".
Amina ta nemi jin inda za su aka faɗa mata ta ce; jiya bayan mun isa Kaduna na tsaya na saya mata kayan daki ".
Yusuf ya ce Kaduna kuka sauka?
Ta girgiza kai .
Abuja muka sauka.
Mun samu mahaifin shi ya gyara ma shi ɗaya daga cikin gidajen shi, kwanan mu biyu, jiya muka isa Kaduna
ya ga wani dan uwan shi, ni kuma sai nayi sayayyar anjima kaɗan kayan za su iso, har da kayan kitchen da na saya mata a Dubai dan sai da muka biya ta can har da su kafet su zannuwan gado da labulayya duk an yi sayayyar su.
Yaya Azima ta ɗaga hannu sama
Allah kai ne Almusawwiru Mun gode maka bisa ga wannan rufin asiri da kayi mana Allah ka kara rufa mana.
@@@@@@@@@@
Innar mu kuwa sai dai
muka ga ta fadi tayi
sujjada
kafin ta dago
tayi ta sa mana albarka
Ta dubi Anty Amina
"An tsinke da labari ba'a tanbaye ki mijin na ki ba.
Gyara zama tayi
"Tare muke sai dai ya ce ba zai shigo yanzu ba
wai yanda nake dokin nan suma mutanen gidan suna dokin ganina
sai dai idan sun dawo gidan abokin shi da muka zo tare
Abokin nasa dan katsina ne
sunan shi Abdullahi ".
Innar mu ta ce na gane shi
Dai dai nan amarya ummu ta shigo da gudu sai wurga ido take in da za ta ga Aminan
A guje ta fada mata
Innar mu ta rike haba
Ke kam yau sai jikin ki ya yi ciwo
Muka yi dariya
Amina ta ce
Yayan mu Ina yaran ki? "
na san kin tara su da yawa wai Yusuf ya ce min uku ne.
Ummu ta yi karaf ta ce
Haka ne, khadija ce babba mai sunan mahaifiyar shi sai yakub sai na bayanta khalid ".
Ta karbe shi a hannuna tana ma shi wasa
Anjima salma ta dauko min su in gani su amma na sha sun kai hudu
Azima ta ce Haba dai sai ka ce duk shekara ake haihuwar duka auren shekaru shida ke ba ga shi ko daya ba ki haiho mana kin taho mana da shi ba
Murmushi tayi
Karatu na ke amma na yi ta bari
Ummu ta ce
Amma ba yanzu za ku koma ba ko? "
"Mun dawo kenan ai mun sha turai
Ta kamo hannuna
Me za ki dafa mana da rana na san innar mu in dai tana da budurwa to ta kan horar da ita aikin gida".
Na dubi Yusuf
Ga mai gidan nan bai riga ya bada kudaden cefanen ba. "
Tana dan murmushi ta dube shi
Ran maigida ya dade me za'a yi mana ne"?
Yana yar dariya ya ce
Ai bakin ne sun fi karfin aljihuna, "
Yanda ya yi maganar shi ya ba kowa dariya
Jakarta ta hannu ta jawo
Bandir ne na yan dari biyu wanda ban yi tunanin an zari wasu masu yawa ba ta mika ma shi
"Ayo mana cefane"
Ya karba yana Yawwa ko ke fa
Na mika hannu
"To bani tunda dama kowa ya san ni kake ba in lissafa sai in sawo
Tsaye ya mike
A'a wannan ya fi karfin ki da kaina zan sawo
Yayammu ta murmusa
Yusuf ho in dai kudi ne".
Bai saurari komai ba ya fice.
Anty Amina ta ci gaba da tanbayar abinda za'a bukata na fannin bikin
yayar mu na gaya mata
Sha daya Yusuf har ya kawo, mun dora ni da ummu, dan har zabi ya sawo, muka shirya ma baki lafiyayyar miya.
Zuwa sha biyu kayan amarya suka iso,
dama tun kan isowarsu, an gaya ma mutanen gidan su shirya
A ( Area) za su zauna mijin ma'aikaci ne
kaf mutanen gidan sun tafi .
Yayan mu ma ta tafi, sai yara.
Mun gama girki, muka dauko kulolin ummu da take tarawa, muka Zazzuba abincin mijin Anty Amina da abokin shi.
Muna sallar azahar, muka ji sallamarsu. Amina ce a falon dan ta idar. Innar mu ta fara fita, suka gaisa, tayi waje, kamar jira yake ta fita, sai cewa yayi"
"ke kuma fa lafiya kike kwance kasa?? Tace " sanyin kasan dadi yake min."
Yace" tohm ban yarda ba tashi"
ta ta shi, ta shirya masu abincin a gaban su, abokin shi na mata tsiya, wai har yanzu gajiyar ce bata wartsake ba.
Suna fira
ummu ta fara fita
ta gaishe su,
tayi waje.
Ni ma ban tsaya cire hijabin ba, na fito na gaishe su
na fita,
Ina mamakin kyau na irin mijin Anty Amina
Dogo ne fari, dirarren namiji mai cikar halitta,ga sajen shi wani irin dogon hanci gare shi da wasu kyawawan idanuwa masu jan hankali, farin yadi yasa bashi da nauyi sosai da farar hular da su kai matukar tona asirin kyansa.
Da na fito na ce ma innar mu bari in je in ce ma kawata ( hafsat) ta kusa da gidan mu, ba zan samu zuwa makaranta da yamma ba. Inna Ta ce" anya shuhaina ba fa kije da safe ba, yanzun ma ki ce ba za ki ba?? Nace" kin san dai innar mu bana fashi. Allah ban gaji da ganin aunty Amina ba. Na fice. Da yamma bayan yaya Azima ta dawo. Amina ta umarce ni in ta jawo jakunkunan da ta zo dasu, nayi kamar yanda Ta ce.
Jakar farko amsa sunan innar mu,
dan haka ita ta aje mawa,
sai ta
ba Azima tata daya, ta yaranta daya.
Sai ummu wadda Yusuf
ya ce
"kawai kin kama sawo ma wannan yarinyar kaya,
ba ki ga akwatunan da aka dankaro mata bane?
Tace"na sa daban, nawa daban. Matsayin shi daban, na wa daban."
ummu ta fara masa gwalo
ya ce Allah zan make ki"
Innar mu ta ce
"Ka rufa min asiri, ke kuma ki bari.
"Ta ce "To."
shima Jaka guda aka ba shi
wadda ya ja ta zai waje da ita.
Azima ta rike
Ta ce "
Allah yadda kaga na kowa
sai an ga naka
Dolen sa ya bude,
yadiddika ne
na maza masu matukar kyau
da tsada,
sai shaddodi da takalma
da agoguna har da su turare,
Salma ma Jakarta daban ,
aka ba innar mu,
jakar innar mu atomfofi ne masu asalin tsada
hada mai (golding) da kuma lesussuka
da hijabai
da takalma flat,
haka na Azima.
Na ummu kayan barci ne dasu turaren wuta
. Nawa riguna ne dogaye da kuma riga da sket da takalma da hijabai (jilbab)
Ta dube ni.
" Yusuf yace min" Ba ki sa gyale."
Na gyada kai,
Yusuf ya ce"
Ai kin daba a kas!
Wannan da ki ke gani.
ya nunani da hannu,
"da ni kika ba su
da sunyi min rana,
dan kalarsu zan nema.
Amma kin ga wannan
yadda kika ganta haka
da hijabin nan,
to kullum a haka take. "
Azima Ta ce
"Allah dai wadaran babban kwabo
Yusuf dai sai ya ja jakar shi ya yi waje
, ta cire sarka da dan-kunnen dake jikin ta. Ta mika ma Yayan mu,
dan tun zuwan ta Yayan mu ta yaba kyansu.
Saura jakunkuna uku
, ta tura ma innar mu,
"ga shi nan
abinda ya kama mutanen gidan nan,
zuwa abokan arzikinki ki ba kowa
na hajiya ma suna nan ciki."
Nan muka yi ta godiya
Innar mu wadda tunda
aka fara bude kayan take kame da baki,
Ta ce
" Hala dai tun randa ku ka sauka garin,
kika fara sayen wadannan uban kaya?
Tayi 'yar dariya
"Haba dai, na jima tukuna."
"Ummu ta ce "uhm!
Anty Amina ta ta dube ta
Yi maganar ki.
"Ta ce na ga kin ba Yayan mu
takalma da agogo da turare,
kince na baban su khaleed ne,
shi ne .....
Sai kuma ta kara shiru
Ta ce
"Da kin je direct! Yusuf ya harare ta
"Mara kunya,
ita nufin ta ba'a ba nata mijin ba."
ai kuwa a guje ta bar dakin..
Da daddare sallar isha'i kawai nayi, Na hau gado.
Aunty Amina Ta
ce" ba dai barci za kiyi ba??
Na ce "Hutawa zanyi, idan kuma barcin ya zo tom duk daya."
Ta ce
"ke baki da saurayi ne?
Ummu da ke ta kwalliyar tafiya wajen angon ta , ta tabe baki
"Wannan, ai ta dai yi aikin gida,
amma duk wanda ya zo , ya ma gaji ya kama kansa,
bata sauraron kowa.
innar mu tana ganin ta fara kuka, idan aka aiko kiran ta,
za ta ce a rabu da ita akwai sauran time.
"Amina tayi 'yar dariya,
ita kuma ta fice.
Innar mu tana tsakar gida in da mutanen gidan ke shan iska.
Aminar ma ta fita tsakar gida,
shigowar ta naji tana magana.
"Inah ka bar Abdullahin??
Ya ce" zan zo wajen matata kuma sai na dakko shi."
dai-dai yana zama wata carpet data shimfida masa,
ta ce
"Amma dai gari ya gari ka dauko shi?
Ya ce
"kin manta jihar shi ce nan, yanzu haka ya isa katsina."
Ta ce
"ka hana in maka girki, to me kaci?
Ledar dake hannun sa ya miqa mata.
cire ma su mama leda guda, ki aje mana guda.
"Suna ci tana jan shi da fira, wanda dama magana bata dame shi ba,
ban san lokacin da suka tashi ba
na dai farka naga innar mu da amina suna ta fira, ba alamar barci,
Aunty ummu ce kusa da ni,
itama barcin take,
da asuba tunda nayi sallah na kwanta,
Ina karanta addu'oi'n da ke cikin (hisnul Muslim).
Sai da 7:00 tayi,
na dora koko.
Yusuf ya kawo kosai ( Enough) har da bread.
Innar mu ce ta dubi Amina data shigo lokacin tayo brush,
ta ce"zaki iya shan kokon kuwa?
dan murmushi tayi "ka ji innar mu,
ke ki ka sha, 'yan uwana suka sha, sai ni ce ba zan iya ba.
Shuhaina zubo min."
na ce To, sallamar da aka yi a bakin kofa ne
, ya samu saurarawa.
Na san ba ni kadai na shiga mamaki ba,
kuma ba sallamar na ke mamaki ba, me muryar.
Watau baba ya'u
Kanin mahaifin mu shi ke bi masa,
dan sanin da nayi masa
baya hulda da mahaifiyar mu,
tun auren su Azima
daya kawo wani tsohon mai kudi,
ta ce bata san shi, Sai ya ce innar mu ke zuga ta
, tun daga nan bai kuma sake bi takan mu ba,
balle abinda ya shafe mu.
wai tunda an nuna masa iyakar shi.
Alhali lokacin da baban mu ke raye, yana cikin wadanda suka fi kowa cin moriyar shi,
wai yau shi ne har dakin mu
Fakare na yi, in ji da wadda ya zo.
Bayan sun gama gaisawa da innar mu,
muka gaishe shi
"Ashe Amina kin zo?
Ta ce "Eh baba."
Ya ce
" Ai jiya ban shigo gidan da wuri ba,
don na je mani,
da na dawo kuma na tsaya hira a layin barankaci."
Ta ce
"mun same ku lafiya?
Lafiya kalau,
ya mai gidan da iyayen shi?
"Ta ce duk suna Lafiya lau,
tare ma muka zo." To.to madallah
, ai ladi ta bani tsaraba, har da ita dani da yara duka.
"Ta ce "Ai bako mai Baba.
Ta sa, ummu ta miko mata jakarta ta hannu
ta amsa ta zaro Bandir din 'yan Dari biyu
ta mika ma baba,
"Ga shi ba yawa, baba ayi cefane
Godiya ya shiga yi
har yana 'yar kwalla,
wai ya tuna dan-uwan shi
mahaifinmu
, niko dariya nake a zuciyata,
Ina cewa
"kudi masu gida rana,
ba wuya sun ruda mutum.
Allah ya dora mu kan kudi,
kowa san su yake
kamar me,
dan idan baka da su, sai ka karan rogo ma ya fi ka amfani. Sai na tuna wani malamin mu
da ke mana karatun tauhidi a islamiya
in da yake ce mana yana daga cikin hikimar
Allah ta'ala da ya turo kowane manzo
zuwa ga mutanen sa da mu'ujiza.
Ga abinda manzon ya zo da shi
kuma mu'ujizar manzon
tayi dai-dai da abinda mutanen sa suke akai,
dan mutanen su gaskata mu'ujizarsa,
dan bijiro da imaninsu da cewa
lallai wannan daga Allah ta'ala yake,
kamar Annabi musa
(A.S) mafi yawanci a zamanin sa sihiri ne
kuma suna gasgata masu sihiri,
sai Allah ya aiko shi da mu'ujizar data ruda duk masu sihiri,
kamar kuma Annabi isa( A. S).
Allah ya aiko shi ne a zamanin likitanci da ma'abota ilimin dabi'a
Sai ya zo masu da mu'ujizar data dace da wannan
, ya kasance
yana warkar da makafi da kutare
da tayar da matattu da izinin Allah,
amma manzon mu Annabi Muhammad (S.A. W)
an aiko shi a lokacin fasaha da balaga ta magana
, sai ya zo masu da mu'ujiza dawwamamma, ita ce Al-kur'ani.
Sai malamin namu ya ce
da ace a yanzu za'a sake turo Annabi, da me kudi za'a turo,
dan mutanen yanzu ba abinda suka fi ganin kimar shi irin naira
To haka dai baba ya gama matse-matsen shi, ya tafi
, ni kuma na tashi na gyara dakin.
Ummu ta kwashe wanke wanke za tayi.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: 🌟🌟 CHANJIN BA ZATA⭐⭐
by
MARYAM IBRAHIM lITEE
Malumfashi
Babi na uku
Innarmu tana kan kekenta Amina tana waya,
da na gama sai nayo wanka,
na ƙara tsaftace bayan gidan, na kai ma Anty Amina ruwa,
duk da dai gidanmu duk yawanmu Allah yasa mutane gidan suna da tsafta, da wuya ka ga abinda za ka ce tir!
mai na shafa
na murza hoda
nasa atamfa(deluxe) baƙa,
me ratsin yellow - yellow, na aje hijab dina gefe.
Amina ta fito wanka,
sagale nayi Ina kallon kwalliyar da take yi, dauko wannan
(body spray), fesa
, goga wannan, shafa wannan, (body lotion), fuskarta wata 'yar hoda, ta dan shafa,
nan take fuskarta tadauki sheqi,
(wet lips)kawai ta shafa ma labbanta
Ta shiga sa kaya,
wani tsalelen leshi mai matuƙar laushi da rashin nauyi,
kalan shi ruwan Zuma, yana da stones.
Ta gyara dogon gashinta,
ta kama shi da wani tafkeken ribbon,
duk da tsawonta,
wani (high hill shoes) tasa
da jaka da gyale, duk kalarsu ɗaya,
(white). Sai tasa sarƙa da dan kunnenta suma ( white) Sai daukar ido suke yi, hannunta bangul ne da sai agogo,
Na ce
"Daga jiya, zuwa yau
kin mai da mana ɗaki
na 'yan gayu, saboda qamshi.
ba tayi magana ba,
murmushi tayi
"Bari in shiga ɗakunan mutanen gidan,
in gaishe su,
sai mu wuce".
Ɗaga kai nayi.
Ta bi daki ɗaki kowa kuma abinda Allah ya tsaga rabon shi shi ta ba shi.
Sannan ta zo muka fito tana ce ma ummu
"Ke ba za ki gidan yayar tamu ba?
ta kaɗa hannu
"Ina da hidimomi da yawa,
Idan na kammala da wuri za ku gan ni"
Muna zuwa ƙofar gida na ga tana murmushi
na kai idona in da na ga take kallo
Mijinta ne zaune gaban motar shi ya zuro kafar shi ɗaya waje,
ya fito ya rufe motar
Yau har ya fi jiya kyau
Wata dakakkiyar shadda ce sky blue da tayi matukar dacewa da hular kansa, agogon (Fiaget) ɗaure a hannunsa.
Fuskar shi ɗaure take
Na tsaya a in da na ke
Ta ƙarasa gaban sa,
"Ba ka wuce ba? "
Ya yi shiru
Ta ce
" likitana ba ka ji na ne?
nan ma bai tanka ba
"Kama kunnuwanta ta yi
"Na amsa laifina. "
Ya ɗan saki fuska,
"Dama tunda na ji kin hanani zuwa na san yawo kike son zuwa"
Rage murya tayi
"Yi haƙuri Dr,
Nan gidan yayarmu za ni kawai, daga nan sai gidan hajiya sai abi dokar oga sorry sir!
Ta sara ma shi
Wani malalacin murmushi ya saki irin nasu na miskilaye
"Mu je in gaishe da su mama, zan wuce Ina da Appointment da Dr Sada"
Ya duba agogon hannunshi.
Gaba na suka wuce gaisuwar da nayi masa ma lafiya kawai ya ce ya wuce,
tun anan na shaƙa, me ma ake da mutum miskili
Ita ta ji zata iya ni kam Allah ya tsaran da auren miskili,
na ɗan jima a tsaye kafin suka fito,
Shi ya buɗe mata
ta shiga
Kafin shigarta sai da ta buɗe min baya
Ban san me ya ce mata ba
Ta ce masa
"Ba ka gane ta ba? shuhainarmu ce.
Wani kallo ya min wanda ya ƙara min takaici, kamar in ce ban zuwa dan ni duk miskili ba wai shiri nake da shi ba, dan ban san wulakanci
Yafito ni tayi
"Shiga mana Shuhaina"
Na kama murfin ƙofar na shiga na rufe,
ya tada motar
Mun fara tafiya ya dube ta,
"Me zan bar maki ne?
Ta ce
"kamar me kenan?
ya ce
"Wai ko kina buƙatar kuɗi"
Ta gyara zama
"Yanzu dai kam akwai wasu,
sai dai ka san hidimar biki,
ban san ko za su isa ba"
nuni ya yi mata da wurin da yake ajiye kuɗi a gaban motar,
"Akwai kuɗi a ciki ki kwashe su, idan kina da matsala sai ki kira ni,
In tura maki".
Godiya tayi masa,
Muna isa ƙofar gidan yayarmu ni na fara fita,
A sauka lafiyar da nayi ma shi ma kamar yana ciwon baki ya amsa,,,
Tabe baki nayi a zuciyata
n ce "Ka ci arzikin kana auren yar'uwata, da ko kallon ka na bar yi. "
Wuni me daɗi muka yi gidan yaya Azima,
Inda tayi mana danbun shinkafa da kunun aya,
Sun yi daɗi ba kaɗan ba,
Har mijinta ya dawo shi kam me sakin fuska ne, sai da ya jajjamu da wasa, sannan ya fita.
Yamma sosai muka tafi sai muka biya gidan hajiya, sannan muka gangaro gida.
...................................
An shiga hidimar biki ba kama hannun yaro,
Bajinta sosai Anty Amina tayi wajen bikin,
An daura aure an ci me daɗi an sha me dadi.
Ran wuni na dawo daga gidan Amarya dama can na kwana, lokaci zai kama sha biyu da rabi na rana.
Yan biki suna ta hidindimunsu,
Haj Zinatu ce hakimce kan wata kujera nayi imanin idan aka kira ta da zinaru zata iya amsawa dan saboda Adon gwal ɗin da ta sha sai sheƙi take
ga wata marokiya gefenta tana mata kirari da mata biyu sun fi ƙarti goma.
shi kaɗai na riƙe cikin kirarin da take mata"
Kusa da ita na matsa Ina gaishe ta, ta amsa da fara'arta
Ta ce "Ashe ba ki gidan shuhaina?
Na ce mata "E na kwana gidan Amarya ne, yanzu kuka iso?
Ta ce
"E jiya direbana baya nan"
Na ce oho
Dakin kishiyar innammu na shiga
na gaida jama'ar da na samu a dakin sannan na wuce uwar dakanta
In da Haj laila take zaune
Itama kamar yar'uwarta ta sha kwalliya ba magana amma ita jiya ta zo,
Na gaishe ta
Ta ce min anjima za ta wuce.
Na ce
"Haj ai ba ki gano ɗakin amaryar ba.
Ta ce
"Za mu biya da direbana in zan wuce."
An yi buɗar kai,
Kowa ya ga ɗakin Amarya zai ce ma sha Allah ɗaki ya yi.
Washegari tun da safe nake haɗa ma Anty Amina kayanta, dan mijinta yayo waya direba na hanya.
Kafin ta tafi sai da ta saya ma innarmu waya,
ta gaya wa Yusuf ya yi ƙoƙarin neman Admission,
ya fara karatu,
za ta ɗau nauyin karatun shi.
Da za ta wuce da iyakacin ƙarfinmu mu ke mata godiya a bisa dinbin alherin da ta baibaye mu da shi, ita kam ƙwalla tayi tayi.
Bayan kwana uku da tashin biki aka ba Yusuf kudin adashin shi,
wanda ya yi zuciya ya ƙi karɓan kuɗin,
sai da innarmu ta kashe wutar ta karɓa,
Wannan kenan.
Na ci gaba da zuwa makarantar islamiya har hutun mu ya kare.
Wata ranar alhamis ba islamiya dan haka nayi niyyar zuwa ma Haj yammaci
Zama nayi na gyara jikina Ina kamshi wasu riga da siket nasa cikin irin kayan da Anty Amina ta kawo min
Na kalli kaina a madubin da ke rataye a uwar ɗakinmu,
Ko ba'a gaya min ba nasan nayi kyau,
sai dai ni kam Allah ya zuba min kunya, ganin yanda ta toni asirin ƙirjina kamar in cire,
sai dai na bar ta, takalma marasa tudu nasa na zura hijabi,
Sallama nayi ma innarmu na bar gidan.
Sannu a hankali nake takawa har na isa,
Ginin gargajiya ne bulo da bulo shafaffe da siminti, a tsaftace ba ka cewa me shi ɗin tsohuwa ce,
sannan an ƙayata shi sosai da kayan alatu.
Sanda nayi sallama tana lazimi dan haka wucewa kawai nayi na zauna,
na ce
"Wash tsohuwar nan ki na jin daɗinki, ki ci kaji ki sha sanyin raɓa me ya fi ranki?
"Ai kam babu "
Ta faɗi tana miƙewa
"Kema ki fiddo miji ya ɓoye ki a gida ko kya huta da wannan tafiye tafiyen ".
Baki na kama
"Lallai ma, ba laifin ki bane,
Samu kika yi Ina zuwa gaishe ki,
"Kuma wa ya ce maki ma na isa aure?
Hararata tayi
A wannan cika da kika yi idan ba'a yi maki aure ba sai yaushe?
Ɓata fuska nayi
"Wai ke duka nawa nake, na ma gama makarantar ne?
"Duk a yan'uwanki wa ya yi cikarki a yanzu haka?
Na ce
"Kin ga dai ki raba ni da labarin cikar nan, mu dawo maganar gaskiya
wanda nake so mutum ɗaya ne,
to inda matsalar take, me shige min gaba nake tunani,
In kuma za ki je ki zo min da shi ko gobe ba matsala"
Ta faɗaɗa fara'arta
"Ke kuma waye wannan, har sai an je an zo maki da shi?
Ai indai yana sanki sai in yi hakan ai ba kaɗan ba nake son in ga kema an kauda ki, zan ma je in samu uwar taku"
na ce "Ita za ta min auren?
Ta ce "To ko waye sai in je, waye baƙona?
Ina kallonta ƙasa ƙasa na ce
"Ai sai ki hanzarta,
amma wanda nake so malam musa ne".
(Mijinta da ya rasu)
Zuba min ido tayi
"Ja'ira ".
ni kuma na kwashe da dariya.
Ta ce
"In kin gama shakiyancin sai ki isa kitchen akwai farfesun kayan ciki,
ki zubo ki zo ki ci,
ki ji daɗin shakiyancin".
na miƙe
"Inda nake sanki ƴar tsohuwar nan,
me wuya mutum ya zo ba ki ba shi abin daɗi ba"
Bayan na zubo na zauna
Ta ke ce min an ce takwara ta ciki ne da ita ko?
na ce
"E har ma da ummu".
Ta ce "Ma sha Allah, ubangiji ya raba lfy".
Na ce Amin
Ta ƙara da cewa
"Ke kuma kafin su sauka in sha Allah kina ɗakinki"
na dafe kumatu
"Kai ni kam ko bisa kanki aka ɗora ni iyakarta kenan, kin tasa ni gaba kamar cikin fari ni ba ki san bamma san meye son ba, duk wanda zai ce yana sona ɓata min rai yake"
Ta ce
"Ba an ce mutum uku sun zo sun tanbayi babannin naki ba,
ai sai su zaɓi wanda ya fi hankali a ba shi,
fatanmu dai wanda za'a zauna lafiya. "
Baki na turo
"Da yake an ce maki zamaninku ne,
In ma barci kike gara ki wartsake, ni ban ma yin auren idan ba samo saurayi kika yi ba ayi mana tare. "
Kwafa tayi
"Taƙadara ki tsaya ayi maganar gaskiya sai ki ta sako shakiyanci,
ni cire wannan hijabin da ba ki gajiya da shi kamar matar liman ki ɗora min tuwo, talatu abincin rana ta bar min,
kin san kuma na fi san sabon abinci"
Na ce "Ina Talatun ta je?
"Marabar ƙanƙara duba jikanta da ya sha fama da baƙon dauro"
Na tashi na shiga kitchen ɗin Ina cewa
"Tsohuwar nan ki dai ta da mutane tsaye,
amma wani abincin kirki kike ci."
tana ta mitar na ƙi cire hijabi, na yi shiru ban ce da ita komai ba.
Watan cikin
Anty Amina bakwai, kullum sai tayi waya
tayi mita da magiya
innarmu ta zo
ta ga ɗakinta,
ita kuma sai ta ce sai an kwana biyu.
Rannan dai ba masaniya sai ga ta tana tura cikinta, da ya yi tamkar ba na fari ba dan tsananin girma.
Direba ya kawo ta ta ce kwana ɗaya za tayi
dan mijin nata ma baya nan,
Ya je aiki ibadan,
dan yanzu ya kama aiki da babban asibitin Abuja,
(National hospital)
A matsayin shi na ƙwararren likitan mata da ƙananan yara.
Ta tasa innarmu har kuka tayi kan su juya tare
Innarmu ta ƙi
Ta ce "To innarmu ki bani shuhaina in tafi da ita, idan na haihu sai ta dawo"
Ta ce "Hauka kenan, sai ta je ku zauna kanku ɗaya."
ta ce "Kai innarmu shuhainar ce ta kai ni?
ta ce
"Tsawo kawai za ki gwada mata, amma bata fi ki cika ba?
Ni dai
Ina zaune ina saurarensu
a raina na ce
"Ai ni kuma na bani da wannan cika da ake ta yayata min"
Inna tayi mata alkawarin tana haihuwa za a zo da ni,
Saboda yanzu akwai makaranta.
Ta ce "In kika bani ita sai in sa ta wata a can"
ta ce
"A'a indai kika haihu bayan yan suna sun zo nima zan zo maki"
Da za ta tafi ta bani waya
Infinix Hot 10 nayi ta murna.
Da watan cikin ta ya tsaya Gwoggo Rakiya kanwar babanmu Ita ta tafi ta zauna mata.
A lokacin ne ummu ita ma ta dawo haihuwa, dan an maida mijin aiki katsina, ga gida ita kaɗai
ji da ita muke, ban bari tayi komai na ƙosa ta haihu in rinƙa mata reno.
....................................
Ranar wata juma'a aka yo waya Anty Amina tana ɗakin haihuwa, za a yi mata aiki.
Mota guda suka cika mutanen gidanmu hada innarmu suka tafi.
Na kira su dan mu ji halin da ake ciki, wayar Haj kishiyar innarmu na kira, abinda take gaya min yasa ni wurgi da wayar, jikina na rawa.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: 🌟🌟CHANJIN BA ZATA 🌟🌟
By
MARYAM IBRAHIM LITEE
Babi na hudu
Na fasa kuka, Ummu da ke zaune ta tasa cikinta gaba
take tanbayata,
Taa... aa rasu! Ummu mun rasa Amina, Amina ta rasu Ummu".
Sai da nayi da na sanin gaya wa ummu dan halin da ta shiga ga tsohon ciki".
Kwanakin da suka biyo baya sun zo mana a tsanance kwarai,
Koda yaushe za ka same mu shiru da ummu da salma,
wani lokacin kuma mu yi ta kuka,
Gamu mu kaɗai a gida,
Sai da aka yi sati sannan mutanen gidan su ka dawo, ciki har da yayarmu,
Mutuwar ta taɓa kowa a gidan,
dan lokaci zuwa lokaci za ta aiko mota cike da kayan abinci a raba duka gidan, hatta sutturu zata aiko ta ce a raba wa masu bukata,
Hadda kuɗi aba magidantan su yi cefane.
Wani zance mara daɗi ana zaman makokin aka sace kit ɗin ta da take adana gwala_gwalanta
Sai na riƙa tuna zuwanta na ƙarshe in da ta ce ma innarmu
"In sha Allahu innarmu in dai na rabu da cikin nan lafiya
ya zama dole
in sai da wasu gwala gwalaina,
in zo in bada aikin gyaran gidan nan".
Ban mantawa innarmu murmushi tayi
Ta ce
"Ke ai da wuya kuɗinki su yi auki, kullun kuɗinki na cikin hidimta mana,
ubangiji dai ya yi albarka
ya raba ku da cikin nan lafiya,
tare da kowace musulma
me ɗauke da shi".
Su innarmu basu dawo ba, babanshi ya roƙi su zauna har tayi arbain
dan ƴan gaisuwar kullun ƙara zuwa suke,
ga mijinta ya shiga ruɗani mai yawa
Su biyar ne zaune can hada Haj ƙanwar kakarmu
Ranar da tayi arba'in
ƙannan babanmu maza
suka yi mota guda
suka nufi Abujan
da niyyar su ƙara ma juna gaisuwa,
sai su taho da su Innarmu
Haka kuwa akayi Washegari sai ga su sun dawo,
Kallo ɗaya za ka yi wa innarmu ba za ka so ƙarawa ba,
Yadda duk ta bi ta yamutse.
Uwar ɗakanta kawai ta wuce ta hau gado, rufe ta muka yi muna ta kuka masu shigowa yi mata gaisuwa suka yi ta bamu haƙuri.
A ranar cikin dare ummu ta haihu cikin ƴar gajeruwar naƙuda
ta samu santalelen yaro,
Innarmu ta fita ta taso Haj kishiyarta
da Baba Rakiya,
dan da nan suka gyara me jego
da ɗanta.
ƙarfe biyu suka yi sallama kowace ta koma ɗakinta.
Da safe me jego kamar ba ita ta haihu ba,
Allah kenan me yin yadda ya so
Ita Amina ko haihuwar ma bata kai ga yi ba,
Allah ya amshi abinsa.
Da safe mutane suna ta shigowa barka
har dare,
Uban ɗan ma a ranar ya iso daga katsina.
Cikin dare na farka na ji motsin innarmu da na saurara sai na ji sautin kukanta a hankali,da sauri na tashi na zauna kusa da ita
Innarmu me ya same ki ?
Shiru tayi da farko
sai da na maimaita
na ce
Innarmu ki yi haƙuri duk mai rai mamaci ne,
Ina so akan wannan ma ki sa haƙuri".
Ta ja numfashi ta share hawayen da ke gudu kan kuncinta,
Ba mutuwar uwata nake ma kuka ba,
Ina kukan al'amura da dama,
Muhimmi cikin su shi ne rasa mahaifinku da na yi a lokacin da na fi kowa bukatar shi, musamman kasantuwar ƴaƴana mata ne,
Ina da buƙatar shi kusa da ni".
Na ce
Ki yi haƙuri innarmu
Ke ɗin ma ai jaruma ce, da ki ka fi wasu mazan tsayuwa a kan Ƴaƴan su."
ta ce
"Shuhaina ki yi haƙuri saboda ke na ke wannan kukan".
na rufe baki
"Na shiga uku! Innarmu me na yi maki?
ta ce
"Ki yi haƙuri, amma ba ki yi min komai ba,
abinda nake so da ke,
idan har ni ce mahaifiyar ki,
Ina kuma da ƙima a wurinki,to
ki yi haƙuri da abinda zan gaya maki,
kuma ki rungumi ƙaddara".
Na ce
"Na ji,
In sha Allah kuma zan yi yadda kike so".
duk da dai cikin ƙarfin hali nake,
gabana faɗuwa yake,
dan na san abinda zai sa ta kuka ba ƙaramin abu ba ne. ta ce
A jiya da hantsi za mu taho an hallara a falon mahaifin Ahmad ana ƙara wa juna gaisuwa sai Babanku ya'u ya matsa kusa da shi ya ce
"A madadina da yan'uwana mun yanke shawarar ba Ahmad ƙanwar mariganyiyar,
uwarsu ɗaya Ubansu ɗaya,
kuma watanni kaɗan suka rage ta kammala karatunta."
nan da nan Alhajin ya shiga godiya,
Ya ce idan ba damuwa a faɗi sadakinta tunda akwai jama'a sai a ɗaura,
Babanku ya faɗi sadaki Dubu hamsin,
nan take Alhajin ya biya, aka ce jama'a su shaida
aka ɗaura maki aure da mijin ƴar'uwarki."
Ya zuwa lokacin da ta kawo nan
kuka nake iya ƙarfina,
ina fyace hanci
Na buga kaina a bango
Ina cewa yau na san ni marainiya ce, na rasa mahaifina,
dan da shi ne nasan ba zai min haka ba,
ya ba wanda bai ce
yana so na ba.
Ihu nayi da ƙarfi
Ina
"Wayyo na bani ya ma za'a yi in auri mijin Amina?
Ban ankara ba sai dai na ji Innarmu ta make baki na.
"Yi mana shiru, ba ki da hankali?
Ba ki san dare ba ne, ki tado mana jama'a?
Ashe ke ba za ki yi haƙurin da kike cewa in yi ba?
Ba sai mu bar wa Allah komai ba ya warware mana?
Daga haka Alwala tayo ta haye Sallayarta,
Ni kuma zama nayi na jingina da bango
na haɗa kai da gwiwa,
Kuka na ke
wanda zuwa safiya fuskata ta kunbure,
ko kokon da na dama ban sha ba,
ban ma da niyyar zuwa makaranta.
Baba ya'u ya yi sallama a ƙofar ɗakinmu,
sai da ya zauna muka gaishe shi ya gaisa da Innarmu,
ya ce "Fatima ba ki ce
komai ba kan sadakin shuhaina".
wani ɗan murmushin da bai kai zuci ba tayi,
"Ni kuma a taƙaice wace hujja gare ni ta cewa a bani sadakinta?
ya ce
"In na lura Fatima sai in ga kamar fushi kika yi".
ta girgiza kai
"Ko ɗaya,
tunda an riga an ɗaura to me kuma zaka ce?
ya ce
"Ato bare duk wanda rai ya yi wa daɗi baran me shi ne,
Na ga wannan gata ke nayi mawa,
don idan ta samo kan ta tuna da ni sai ta fara kawo maki,
yanzu ba ga Zinatu ba wane faɗi tashi ne ban yi ba kafin yuwuwar auren ta?
amma yanzu wa ta sani idan ba uwarta ba,
har makka ta kai ta
ni kuwa ko sansanin alhazan ban je ba".
Innarmu ta tari numfashinsa,
"Abinda nake so ka gane,
kar mu sa wani hange cikin wannan aure,
mu riƙe shi da zuciya ɗaya,
Mu yi addu'ar Allah ya sanya masa albarka
Amma wata niyya tamu ta daban ba wannan ba,
za ta iya janyo mana
matsalar da idan ta zo ba za tayi mana daɗi ba".
Ya ce
"Haka ne"
ya tashi ya fita
Ummu ta dafe baki, "Yanzu fa shi kenan ya riƙe sadakin nan ba zai bayar ba? "
Innarmu ta ce
Uhum! kawai
Baba sani ya shigo yana ta ba Innarmu haƙuri
Ya ce
"Shi tsoron da yake ji masu kudin nan ba'a yi masu irin wannan
karan tsayen.
ta ce
"Ba komai Allah ya sa hakan ya zama alheri".
Ranar suna yaron Ummu ya ci suna Najib.
Na ci gaba da zuwa makarantata.
Satin Ummu uku da haihuwa
Baba ya'u ya shigo gidan cikin sauri, ya ce a ba shi tabarmi ga uban Ahmad nan da mutane.
Ya ɗan jima da zuwa
aka kira Innarmu
su gaisa, ya yi mata godiyar karamcin da aka yi masu,
Ya ce ya zo ne ya ƙara yin godiya, kuma a account ɗin Amina, an samu dubu ɗari biyar da ashirin,
Mijinta ya ce ya yafe
Sai suturunta duk an zo da su,
Kuma shi ma Ahmad ɗin wai yana nan zuwa
dan yanzu haka ba ya ƙasar,
kan wani aiki da ya taso masa,
kuma ya ce kar a sayi wani kayan ɗaki, dan ba zai iya zama gidan da ya zauna da Amina ba, ya koma cikin asibitin da yake aiki nan za'a kai ni.
Ina jin muryar Baba ya'u ya na cewa "Ina Shuhainar ta gaida surukinta?
Karkashin gado na shige.
Ya shigo har ciki yana ce wa Ummu
"Ina shuhainar?
ta ce
"Ai ko ta fita"
Tsaki ya ja ya juya,
Mahaifin Ahmad ya cika mutanen gidan da kudi
sannan ya tafi,
Zo ka ga fara'a wurin Baba ya'u, ya samu abun san shi.
Har Ummu tayi arba'in ta koma, ba Ahmad ba labarinsa, ga gulmar da ta fara yawo a cikin gidanmu,
Wai ai dama kwaɗayi ne,
In ba dan an ga kuɗi ba
Ƴaƴa take da su,
ballantana ace zata riƙon su,
Ko shi bai santa ba? ba za a jira ya ce yana san ta ba.
A yanda ma ake bada labarin wai Innarmu ce ta roƙi ya aure ni,
Wata aminiyar ta ta ƙut da ƙud
Haj baraka ta zo tana tanbayar Innarmu gaskiyar maganar,
ta ce mutanen gidanmu ke zuwa gidansu da labarin idan an tabbatar da ba ta nan,
Ita kuma idan ta dawo sai mutan gidan su su gaya mata.
Daga ni har Innarmu mun shiga halin takura a cikin gidan,
Ina dai zuwa makaranta ne, amma gani nan ne
Har muka fara zana jarabawar (WAEC) ɗinmu, da ƙyar na sa ma zuciyata salama na fuskanci jarabawar,
Ranar da muka kammala paper karshe ina dawowa gida,
Sujjada nayi ma ubangiji
da na ɗago idona na malalar da hawaye,
Innarmu wadda ke zaune tana yankan ɗinki ta dube ni,
"Ki yi haƙuri Shuhaina
kowane bawa da irin ƙaddarar shi a rayuwa,
haka idan Allah ya shirya rubutaccen al'amari baya kankaruwa,
an ɗauke alƙaluma kuma takardu sun bushe,
Matar mutum kabarinsa."
Daga haka ta ci gaba da yankanta.
Wasa wasa sai da aka ƙara wata guda,
Ranar na dawo islamiya da hantsi
mota na gani galleliya
tana ta sheƙin ɗauke ido,
cikin hasken ranar da ya fara ɗagawa,
Ƙwarai na yaba kyan motar a raina,
Na wuce cikin gida,
abinda na lura mutanen gidan sai kallona suke,
ban damu ba, na wuce ɗakinmu,
Innarmu na samu kan sallayarta,
na san ita ɗin ma'abociyar sallar walha ce,
"Innarmu na dawo,
Yusuf ɗin ya kawo cefanen kuwa?
Ina son yi da wuri ,
gidan ummu za ni
in gano Najib."
Cikin sanyin murya ta ce
"Bar girkin nan Shuhaina,
je ki yi wanka".
Na ce
"Nayi kafin in tafi makaranta".
Ba tare da ta dube ni ba
ta ce
"Na ce ki je ki ƙara yi"
Ban saba musu da ita ba sai na wuce,
Sai da na dawo wankan, ta ce in yi kwalliya me kyau,
zama nayi nayi kwalliyar
ta ce in ɗauko kayana sababbi in saka,
Ba musu nayi yanda ta ce,
Hijab ta umartan in saka
Gwoggo Rakiya ta leƙo
"Yawwa ta kammala?
Sai ta juya,
tare suka dawo da hajiyar mustafa kishiyar innammu,
Suka ce ma Innarmu "Sai ki sa mata albarka dan suna jiranmu su yi mata faɗa".
ta ce
"Allah ya yi maki albarka, ya bada sa'a"
ta sa kai ta shiga uwar ɗakanta,
Sai sannan na fahimci abinda ke shirin faruwa da ni,
Kawai sai na sa kuka.
Za su kama ni mu fita na ce
"Zan ɗauki wayata"
hada ƙaramin Al-ƙur'anina na
na ɗauko,
da hisnul muslim,
ɗakin gwoggo ladi aka kai ni,
Inda muka samu duka ƙannen babana sun hallara, faɗa suka yi min, da nasihar in bi aure.
Baba ya'u ya ce
"Duk mun fita,
bin mu aka yi,
aka ce mu zo,
Mijinki ya turo mota a tafi da ke.
A raina na ce "Ka ji wai direba dan rashin galihu".
Da muka fito direba ya taso da sauri ya buɗe ƙofofin motar,
Mu huɗu ne a baya,
Baba ramu a gaba, da yake ita tana da jiki,
Ƙannen babana duk suna tsaye,
Mutanen gidan ma duk sun leƙo suna ta ɗaga hannu,
Wani ƙududu na ji ya taso ya tokare ni,
ko ƴan'uwana ba a bari sun zo
mun yi sallama ba,
dai dai da salma bata nan,
Yusuf kuma cikin dare ya iso daga kano,
inda yake karatu,
bamu gan shi ba sai da safe,
leƙowa kawai ya yi ya gaida Innarmu,
ya ce
Bari ya je yayo cefane ya dawo,
ya ce min
"Akwai labari Shuhaina, bari in dawo. Kafin ya dawo na tafi makaranta,
Sai dai idan ya dawo ace mashi an tafi da ni.
Kuma dangin uwata ko ɗaya basu tsaya an ɗauka ba,
duk da yake sune dangin nata, amma ai da ko Haj an aika mawa.
Mun iso marabar jos, nayi ƙoƙarin tsaida hawayen da ke bin fuskata,
Na dubi su Baba Rakiya, barci duk ya yi awon gaba da su.
Tunanin babana yana ta bijiro min, da kuma tarihin shi da aka bani.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
———————————
CHANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE
Babi na biyar
MAHAIFINA
Mutumin Gora ne wani ɗan ƙauye da ke daf da malumfashi,
Sunan shi Umar
An ce mahaifinsu ya rasu tun suna yara su shida maza biyar mace ɗaya. ita ce Gwoggo Rakiya ita ce ta uku,
riƙonsu ya koma hannun ƙanen mahaifinsu wanda bai taɓa haihuwa ba,
Sai bayan ma ya cire rai aka haifa ma shi Innarmu,
ya tura babanmu karatun allo meduguri ya samu karatu me zurfi,
Ya'u da ke bi ma shi ya tura kano, amma saboda laulayinshi
Ya dawo da shi,
Bai kuma ƙara tura kowa ba,
Babanmu ya dawo gida da zancen auren wata shuwa Arab,
Ƙanin tsohonshi ya tsaya ma shi,
Sun kashe dukiya me yawa
aka ba shi ita.
Ita ce Haj Hauwa
mahaifiyarsu Haj Zinatu
da Haj laila sai ƙaramin su mustafa,
ya ware masu ɓangaren su daban,
yana shiga kasuwar malumfashi ya yi saye da sayarwa,
Cikin ɗan lokaci Allah ya buɗa masa,
har ya sayi fili a malumfashi ya gina,
Ya so tasowa da iyalinsa
Ƙanin tsohonshi ya hana, dan haka sai ya sayar
ganin ya samu alheri
Sai ya ci gaba da sayen filaye yana ginawa ya sayar,
tuni har an yi wa Rakiya aure, ƙannan shi biyu ma sun yi aure,
Ya ƙara sayen fili makeke ya gina
Ya kuma ƙara roƙon ƙanen mahaifinsu da ya koma,
wannan karon bai hana shi ba
Nan da nan suka tare,
Daga baya ne ya roƙe shi
Ya ba shi auren tilon ƴar shi Fatima,
Murna sosai tsohon ya yi
Ya ɗaura masu aure
In da duk shekara biyu sai ta haihu
Da Azima ta fara,
sai Amina sunan ƙanwar mahaifiyarta Haj kenan,
Sai Yusuf
Sai Ummu
Sai ni,
Sai haihuwar ta tsaya
har sai da na shekara biyar, sannan ta samu cikin salma,
Watan cikin bakwai
Allah ya yi wa mahaifin mu rasuwa
A sanadiyar hatsarin mota.
Iyalanshi da ƴan'uwansa sun ji mutuwar sa
Dan tun Innarmu na goyon Azima
Mahaifinta ya rasu,
Duka yan'uwansa ya nemi su dawo gidansa,
Hidimar Ƴaƴansu kaf shi ne me yi,
Gwoggo Rakiya ma tun mutuwar aurenta na farko
ta shiga yi yana mutuwa karshe ta watsar
tayi
zamanta a ɗakin da aka dawwama mata.
Tun daga nan Innarmu ta shiga wahala,
dan mahaifiyarta ma ta rasu
Tun tana goyon ummu.
Kanwar mahaifiyarta Haj ke tallafa mata, dan tana da ɗa me kudi yana zaune a katsina da iyalin shi.
Gidan da muke ciki babanmu
tun yana da rai ya ce ba shi cikin abinda za'a raba gado,
duk dan'uwanshi me sha'awar zama ya zo ya zauna,
Mun ci gadon wani gidan babanmu da gonaki biyu
an sa yan haya ana ɗan samun na cefane,
gonakin kuma akan ba manoma noma tashi su ɗan bada wani ubu,
Ƴaƴan Haj Hauwa mutanen gidan suna ce mata hajiyar mustafa, mustafan tsaran ummu ne,
Ƴaƴanta sun yi aure tuni Haj Zinatu tana kano Haj laila na sokoto dukansu masu hali suke aure,
Suna matuƙar hutawa
Suna taimakawa mahaifiyarsu,
dan duk gidan babu me jin dadinta kowa sai ya fita zai samo na masara.
Yusuf tun soma girman shi ya ga yanda innarmu ke shan wahala kafin mu ci abinci ya dage da neman kuɗi duk abinda ƙarfin shi zai iya
tana saida kayan miya wanda ba su zuwa ko ina ake cinye jarin, in ta samu ɗan kudi sai ta ɗora,
tana dinki sosai.
Mutanen gidan mu duka suna girmama Hajiyar mustafa wanda ko makaranta bata dame shi ba
sai dai ya wanke goma ya tsoma biyar
Suna gulmar ta kan wai ƴaƴanta suna badawa ta ba mutanan gida ita ke dannewa.
Ana haka aka tashi auren Azima,
wata uku ya rage bikin
Amina ta raka Haj biki katsina,
anan Ahmad ya gan ta
ya kuma manne mata
dan bikin na gidan abokin shi ne
na ƙut da ƙut Abdullahi,
Kannan babanmu sun ce ba yanzu za su yi mata aure ba na yayarta za su yi tukun,
ya nace har sai da mahaifin shi ya zo
Wanda babban mutum ne,
ya roƙi alfarmar su ɗiyar kawai suke so,
ana ɗaurawa a basu ita
Dan shima karatu yake yi bai shirya yi mashi aure ba,
duka a lokacin shekarun sa ashirin ne da bakwai
hutu ya zo,
za a yi mata biza sai ya tafi da ita
ta ci gaba da karatunta acan.
hakan akayi
ana ɗaurawa aka wuce da ita Abuja gidan mahaifinshi,
daga can suka lula England.
Mahaifinshi ƙusan gwamnati ne da ya riƙe muƙamai daban daban a ƙasar nan, ya mallaki matan aure uku
Mahaifiyar Ahmad ce ta biyu.
Idona biyu har na yi tozali da dutsen Abuja,
Wayar da direban ke yi yasa na kalli in da yake,
"E ranki ya daɗe mun shigo yanzu".
Ya saurara
Kafin ya ce
"An gama ranki ya daɗe".
Babban asibitin Abuja National Hospital
Muka yi wa tsinke rukunin gidajen ma'aikata
direban ya nufa da motar,
A gaban harabar gidan wanda ya ƙayatu da shuke shuke masu ban sha'awa ya tsaida motar,
wasu mata guda biyu suka tare mu tare da yi mana jagora zuwa ciki,
Gwoggo Rakiya ke riƙe da ni.
"Shiga da bismilla".
ta raɗa min,
Yayin da ƙafata ta taka tattausan kilishin da ke barazanar shanye min ƙafa
dan tsananin taushinsa.
Wani ni'imtaccen sanyi da ƙamshi suka ratsa ni,
Zaunar da ni da Gwoggo Rakiya tayi bai sa na buɗe fuskata ba.
Lale lale suke ta yi da maraba
suka gaggaisa
kafin suka gabatar masu da abinci,
sallah suka fara yi.
Matan biyu suka yi sallama da su gwoggo
bayan sun nuna masu akwatuna
masu ɗauke da kayan aurena,
suka ce za'a kawo mota
a tafi da mu gidansu Ahmad,
Wucewarsu
su Gwoggo ladi suka zuba abinci. Haj ta miko min nawa
na ajiye a gefe sun yi nisa da ci
Baba Ramu ta ɗago ta dube ni
Ki ci abincin mana shuhaina. "
Na jawo shi gabana
nayi cokali biyu sai na ajiye.
Duk da daɗin abincin
da kasantuwar ban taɓa cin abinci
me daɗin shi ba
ji nayi yana shaƙe ni,
Saboda halin da nake ciki
na ruɗani da tausayin kai, Gwoggo Rakiya ta dube ni,
"Anya shuhaina ba za ki ci abincin nan ba?
To mu dai ci zamu yi
gara ke yanzu za ki soma ci,mu kuma gobe gida zamu koma".
shiru na mata
Sai dare sannan Ahmad da abokinsa Abdullahi suka zo
suka gaida su gwoggo,
wani abincin aka kuma kawo masu me rai da lafiya,
Suka ƙara ƙona yatsu
ga kaji suka karya ƙashi
Da safe duk da halin da nake ciki
sai da na kusa dariya,
akwatunan auren da aka gaya masu
suke son gani,
Sai dai an rasa wadda zata ko matsa kusa da wardrobe ɗin
da suke ciki,
Wardrobe ɗin gadon ce bango guda
Gwoggo Rakiya ta kama baki
"To abu ne duk gilasai ka ce za ka buɗe ina zaka taɓa? ka je kayi masu barna?.
Da jin wannan zancen nata ban san sanda nayi dariya ba,
kallona tayi
"Ja'ira kike min dariya,
to tashi ke ki buɗe mana".
Sanin halinta bata wasa da yara
yasa na miƙe
sai da na gama kallonta tsaf
Sannan
na buɗe masu
Na koma inda na tashi
suka firfito da akwatunan
Ina jin su
suna ta mamakin yawan kayan
da kyan su.
Sai da suka gama
aka yiyyi wanka
tsaye nayi cikin bathroom ɗin
ina kallon tulin turarukan wanka da aka jibge,
a rayuwata
Ina matuƙar san kamshi
dan haka ban cuci kaina ba,
zuzzubawa nayi a ruwan wanka
na kwanta cikin bahon wankan,
na wanke jikina fes
na fito ina ƙamshi,
Gwoggo Ladi ta turo min akwatin
da kayan kwalliya suke,
"Ki yi kwalliya da su".
Ban musa mata ba
na tsinci na tsinta
na ɗora su kan tsalelen dressing morrow
da ke fuskantar gadon
na yi kwalliya,
ita ta miƙo min kayan da suka cire min na akwatin,
Atamfa ce da mayafi
zuwa su sarƙa da ƴan kunne,
hada takalmi na shirya tsaf,
Kamar jira
aka yi masu magana direba ya zo,
ba motar jiya ba ce,
sai dai direban shi ne
Ya kwashe mu zuwa gidan su Ahmad.
Tarba me kyau muka samu daga jama'ar gidan,
Sashen mahaifinshi aka soma kaimu,
Wanda ya yi ta godiya kamar ba babban mutum ba,
da suka miƙe ya cika su da kuɗi,
Daga nan sai sasan uwargidan shi Haj Babba, ita ma ta cika su gwoggo da kuɗaɗe sai sasan amaryarshi da na ji an ambata da Haj Asmau, itama da suka miƙe kyautar kuɗaɗen tayi masu,
Sasan Haj Hadiza mahaifiyar Ahmad ne ƙarshe
ta karɓi su gwoggo da mutuntawa,
Sun ɗan zauna aka ce su fito,
turamen zannuwa ta basu
da kuɗaɗe su yi ɗinki,
Su gwoggo suka tafi
suna ta godiya,
ta dawo daga rakiyarsu
ta samu ina share hawaye.
Zama tayi tana ta rarrashina
ƙarshe ta ƙare da gaya min maganganu masu daɗi
akan Amina,
na irin halayyarta
da daɗin da suka ji
basu ni da aka yi bayan rasa ta.
Ko ba komai zuciyata tayi sanyi,
a yabe ka bayan ba ka ai ba ƙaramin dace bane,
Ina tare da ita har dare
Ta sani nayi wanka ta bani wasu kayan na sa
Sai takwas da rabi Ahmad ya zo,
Ce ma shi tayi
ya je tare da ni
wurin mahaifinsa,
Nasiha ya yi mana
Da muka miƙe kuɗaɗe ya ba Ahmad
ya ce ya riƙe min,
Ina biye da shi kamar wadda ƙwai ya fashe mawa,
har inda ya ajiye motarshi,
sai da ya shiga ya rufo na ƙaraso
na dan tsaya jim
ganin ba shi da alamar ce min ci kanki,
yasa na kama ƙofar baya na shiga,
har muka soma tafiya
bai yi ko tari ba,
illa ƙira'ar sudes da ta ke fita cikin taushi.
Da muka isa sai da na ga ya fita
nima na balle murfin na fice,
ban gan shi a falon ba
Kofofi uku ne a falon,
ɗaya wadda za ka shiga ta kai ka ɗakina,
ɗayar kuma kitchen
za ta kai ka,
dan da safe nan na ga
me ma shi aikin gida
da ban ruwan fulawoyi yana karakaina,
ɗayar nake kyautata zaton ɗakin shi ne
nawa ɗakin na shiga,
na cire kayan jikina
katafaren gadon na haye,
duk da niimar da ke cikin dakin
be hana tunani ya dabaibaye ni
na yan'uwana da innarmu,
Wani ɓarayin kuma tsoro ne taf
a cikin raina na kwanan da zan yi ni kaɗai,
saboda sabo da gidan mu na yawa.
Na raba dare
kafin in samu gwanin iya sata
ya yi awon gaba da ni.
Asuba nayi
lokacin da na saba tashi
sai na farka,
addu'a a bakina
na miƙe
na kewaya
na ɗauro Alwala
Na haye pray mat
na tada sallah,
da na idar
nan nayi ta zama
nayi azkar
da karatun Al-ƙur'ani,
ƙarshe na haɗa kai na da gwiwa
Ina tunanin gidanmu
da al'amuran mutanen gidan.
Ina nan zaune har gari ya waye sosai,
Ba zato na ji an murza ƙofar ɗakin,
hantar cikina ta kaɗa,
ta da kaina nayi na dubi ƙofar, ya yi kyau har ba magana,
Cikin ƙananan kaya
farar riga ce da bulun wando,
Agogon dura king ɗaure a hannunsa,
Sumar shi ta sha gyara sai sheƙi take,
cikin abinda bai gaza sakan ashirin ba
Na ƙare masa wannan nazarin.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/FCGolden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
———————————
🌟🌟CHANJIN BA ZATA🌟🌟
By
MARYAM IBRAHIM LITEE
6
Maida kaina nayi ƙasa na ce
"Ina kwana?
Ya amsa kamar bai son yin magana
"Kina iya shiga kitchen a duk sadda kike buƙatar hakan,
akwai komai a ciki. "
A sanyaye na amsa da "To"
Ina ƙara takurewa
"Tonny yana gyaran gida ne
da kula da shukoki,
har falon nan yana gyarawa,
da kuma kitchen.
"To. "
na kuma cewa sai
ya juya
Sai da na tabbatar da barin shi gidan
Sannan na fito
duk da falon ba shi da datti
an daɗa tsaftace shi,
Sai tashin ƙamshi yake
Kitchen ɗin na nufa
Kamar yanda na zata, kitchen ɗin ya tsaru da na'urorin zamani kala kala,
Akwai manyan Deep freezer guda biyu a ciki
Kayan amfani babu wanda babu.
Lallaɓawa nayi na jona kettle
tayi zafi
Na haɗa tea me kauri
sai na koma falon
nan na zauna
ina kurɓa
ina kallon
tashar Aljazira
da na samu tana yi,
da na gama
sai na koma kitchen ɗin
na ɗauraye cup ɗin, Window kitchen ɗin na leƙa
in da na hango Tonny
yana ta aikin sa
na gyaran fulawoyi,
Ɗakin na koma nayi wanka na gyara jikina,
Sha biyu na rana Tonny ya kawo min wasu cooler guda biyu ɗaya shaƙe take da danbun nama ɗayar kuma cake ne
Bayan ya gaishe ni cike da girmamawa ya ce
"Saƙon daga mahaifiyar oga ne, ta ce a kawo min direban gidan ya kawo
Godiya nayi sai sannan na tuna da kuɗin da aka bani jiya dan jakar tawa ma a motar na bar ta da wayata ma a ciki,
hango jakar nayi saman wani ɗan tebur,
Na yi saurin ɗaukota na buɗe har da kuɗin duk suna ciki,
Na ce "Ina direban? ya ce ya wuce
ɗibar masa nayi yana ta godiya
Naira dubu na ba shi guda ɗaya
Na ce ya sawo min katin MTN na kuma ba shi wata
na ce ya sawo min na etisalat
Shi kuma na ba shi ɗari biyar
na ce ko zai sa
Ba'a ɗauki lokaci ba ya kawo min
Na karɓa
nayi zaman sawa na sa MTN
Etisalat ɗin kuma na tura wa innarmu,
Na yi ta try ɗin samunta
amma wayar ta ƙi shiga
ƙarshe na hakura.
Na miƙe dan gabatar da sallar Azahar
Danbun naman shi na ci
a matsayin abincin rana
Na ɗauko madarar hollandia na haɗa.
Cikin sati guda abinda ke faruwa kenan
zai shigo da safe idan zai fita
ina kwana nake masa ya ce lafiya
Daga nan idan ya fita sai kuma wata safiyar ni da kara ganin shi dan nima da na fahimci lokacin dawowar shi ina ganin ya kusa zan koma dakina in rife
Tun ina tsoron kwana
ni kadai har na saba
ga kadaici
na saba da gidan mu
na yawa
Na hutar da Tonny gyaran falo da kitchen
zan gyara ko ina fes
tare da fesa room fresheners din da na ga yana fesawa
Na kan kira Innar mu da sauran yan'uwana lokaci lokaci
Suma suna kirana
har na wartsake
Na kan shiga kitchen in ta gwada girke girken da aka koya mana a makaranta
dan littafi guda ne da ni
Sai in ga kuma ya yi fiye da zato na.
Na'urorin kuwa da karanbani na iya amfani da su
Yin girkin ya kan dauke min zaman kadaici
wa'azuzzukan malamai da ke cikin wayata
suma ba kadan ba suke debe min kewa
Duk bayan kwana uku Tonny zai same ni
Ya ce madam oga ya ce
Idan akwai abinda babu ki fada min in je in sawo
Idan akwai abinda nake bukata
sai in fada masa
Momi mahaifiyar sa tana kirana ta tanbaye ni ina da matsala?
Sai in ce babu komai
Kuma bata gajiya da yi min aike
dan haka na cire komai a raina
Iyaka dai jira nake ya gama wulakancin shi ya sallame ni
ai dai shi kenan ko?
Tunda ba kwantai nayi ba ni ba mummunar kama ba.
.....................................
Ranar da na cika wata guda
da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare,
Kamar wasa na ji ana ƙwanƙwasa ƙofata sai da nasa hijab sai na buɗe kofar,
Yana tsaye fuskar nan tashi ba walwala kamar kullun,
"Ki zo falo ana kira"
"To"
kawai na ce
Sai ya juya
na ɗan tsaya Jim
Sai kuma na bi bayan shi,
Abdullahi ne abokinsa zaune,
wanda na san
Ba shi da Aboki sama da shi,
Sallama nayi a hankali
ya amsa
na gaishe shi ina tsaye rashin sanin abinyi,
ya ce
"Ki zauna mana
In dai ba fushi kika yi ba,
wata guda ban zo na kwashi gaisuwa wurin amaryarmu,
Tafiya nayi saukata kenan ɗazu da rana".
Ɗan murmushi nayi
"An dawo lafiya?.
Na faɗa ina zama a takure,
"To ya gidan?.
na ce "lafiya lau"
"Ya amarci da baƙunta?
Shiru nayi
"Ko da yake kin zama ƴar gida".
Ya kai glass cup ɗin da ke hannunshi kan wani ɗan stool ya dube ni
"Ba ku rage komai bane a gidan?
shi wannan baƙin baturen sai lemo kawai ya kawo min?.
Na ce
"Ba za'a rasa ba"
ina mikewa
Kitchen na wuce
Tuwon shinkafa miyar agushi nayi,
Miyar ta ji tantaƙwashi,
Tuwon kuma ya yi danƙo kwarai,
Na shiryo a babban tire
Na kawo masa
Zan juya,
Ya ce
"Zama za ki yi muyi hira."
Na saci kallon Ahmad wanda ya zura ma TV ido
tamkar baya wurin.
Yana ci yana cewa
"Gaskiya ba kaɗan kika iya girki ba,
In dai zan riƙa samun abincin gargajiya irin wannan, anan zan riƙa yin Dinner,
matuƙar ina gari
Kin san abin ka da gwauro"
Ganin ban tanka ba yasa shi cewa
Ni fa daurewa za ki yi ki saba da ni
dan ni ɗin wan ki ne,
daga bakatsine nake kamar ke,
ko ba ki san masanawa ta katsina ba?
Na ce
"Ina jin sunanta dai,
dan ban taɓa zuwa katsina ba. "
Baki ya rufe
"Ashsha ashe ki ce kifin rijiya ce,
to yi shiru kar wannan ya ji ya yi mana dariya".
ɗan murmushi nayi
ya ci gaba
"Ko da yake na kusa barin gwaurantakar nan dan na kusa angwancewa
Saura watanni uku, duk da ba tarewa za tayi ba
tana karatu ne".
Na yi ƙarfin halin cewa
"Allah ya sanya Alheri".
"Amin, sunanta khausar
Sai ki bani lambarki in bata kwa riƙa gaisawa kafin ta iso".
Na ce "Zan bayar"
Hamma nayi
ya ce
"Ki je ki kwanta na gode da hira da kuma abinci"
Ɗan murmushi nayi
Sai na kwashe kayan abincin
na kai kitchen,
na je ɗaki na rubuta lambar, zan kawo masa.
Tana bada baya ya dubi Ahmad,
"Me nake shirin gani?
A tsanake ya dube shi
"Kamar me?
Ya ce
"Kamar komai ma,
daga ganin yarinyar nan ba ka janye ƙudirinka ba,
dan sam ba alamar ta saba da kai".
Shima ranshi a haɗe ya ce
Duk abinda ya kamata na ci ko sha ba wanda bana ƙoƙarin wadata
ta da shi,
to me kuma kake son in mata bayan haka?
Ya ce "kwarai gaskiya ne baka da abin mata,
dama wannan shi ne maƙasudin auren,
Ka yi dai dai yanda ka yin...
Katse shi ya yi "Kai malam abinda fa kake nufin in yin,
ba fa zan yi ba,
Ka san na gaya ma wannan ba irin choice ɗina ba ce,
mace gajera maka malam,
bagidajiya
Kullun a lulluɓe
Ina cikin raɗaɗi na rashin matata,
dan rashin tausayi
Sai kawai kamar wani yaro
ace an bani ita ka....
Cikin matuƙar ƙufula ya katse shi
"Dakata malam, ina me tabbatar maka
Yarinyar nan ta wuce ka ci mata fuska,
dan ƙaryarka ka kira ta gajera,
na dai yadda matsakaiciya ce
Idan ma ƴan hotunan da ake kawo maka talla ke ruɗarka,
to ina me tabbatar maka
duk ƙyale ƙyalen banza ne,
ban ga kamar ta ba.
Allah ya yi maka baiwa kana nema ka butulce,
Yanzu gidanku ba matarka ake yabon halayenta ba?
Ina ce akwai matan kabir
amma ta ka ake yabo
ashe ba abun ka godewa Allah bane,
Bayan ka rasata an
ɗauki ƙanwarta an ba ka
ka yi dace da gida na mutunci
Masu tarbiya,
Wallahi abokina uba ɗan malumfashi ai ka dai san shi ?
Ko wancan weekend
ɗin mun haɗu a (Zone ll)
Muke Maganarka
Ya ke cewa ai ba ƙaramar sa'a kayi ba,
dan mahaifinsu dattijo ne mutumin kirki
Ƴaƴan shi suna da tarbiya,
Musamman ita wannan da aka ba ka.
Ya ce ko a abokansa yasan da yawa masu san ta,
Kawai kwarjini take wa maza
saboda kamun kanta
kullun za ka ganta cikin shiga ta kamala
Ka samu za ka wulaƙanta
sai ka auro falwaya".
Mikewa ya yi ya ɗauki key ɗinshi da ke ajiye
ya bar falon,
Sanin ya yi fushi yasa ya tashi ya bi bayan shi.
A ranar idan na ce nayi barci to sai dai ɓarawo ba sanin lokacinsa, dan tsabar baƙin ciki
Kuka nayi tayi
har na ji kaina yana ciwo,
Na yi da na sanin tsayawa na saurari maganar Ahmad, zantuttukansa masu kama da zubar tafasashshen ruwa a ƙahon zuciya.
Da safe ma key na sa ma ƙofata dan kar ya shigo
to shi ɗin ma bai shigo ba.
Wunin ranar nayi shi ne cikin baƙin ciki da tunanin mafita,
dai dai da wayata kashe ta nayi
na kasa sa komai a baki na,
Ko wanka ban yi ba sai biyar na yamma
Na yi tunanin Abdullahi zai zo cin abinci
Sai na yi ƙoƙarin shiga kitchen,
Dan ko ba komai ni kam ina girmama duk mutumin da ya nuna min mutuntawa,
kamar yanda na tsani ka wulakanta ni.
Lafiyayyen danbun shinkafa na yi
Wanda dama shi na yi niyyar yi,
Amma halin da na tsinci kaina
Yasa duk ƙamshin da yake yi bai sa na ji sha'awar cin shi ba,
sai kunun zaƙin da na haɗa masa nayi ta banka ma cikina.
Tonny ma da na zuba masa da ya maido kwanonin sai faɗi yake
"Madam abincinku na hausawa yana da daɗi"
Murmushi nayi
Sai da nayi sallar isha'i,
kamar jiya yau ma haka ya zo,
Sai dai ban yarda na zauna ba
wucewa nayi nayi kwanciyata,
tare da fatan barci ya dauke ni.
Yau da gobe sosai na saba da shi,
sai dai megidan ne na kasa sabo da shi.
duk da dai yanzu na tsinci kai na a wani hali na san ganin Ahmad da san jin muryar shi,
randa duk ban samu ya shigo ba
ko kuma Abdullahi bai zo ba da ƙyar nake samu barci ya ɗauke ni,
Wani lokacin sai dai in ta kuka
Ina me zargin zuciyata
da san wanda bai so na,
Sai in ce
shi kuma san
haka sharrin shi yake?
Ya saka san wanda bai ƙaunar ka?
Mun saba da khausar
wadda Abdullahi zai aura ta waya,
Idan mutum ya ji muna hira
zai sha mun shekara da sanin juna ne.
.............................
Ana gungurawa a haka nayi wata uku,
ranar wata talata
na kira Innarmu
mun gaisa da su yayarmu
da ummu,
Yusuf ne wayar tashi a kashe take.
Ina ajiye wayar a gefena
na ji ana danna ƙaraurawa a falo
daga in da nake zaune na amsa,
Wata haɗaɗɗiyar budurwa ce
ta shigo,
doguwa ce baƙa
irin black beauty ɗin nan,
tafiya take kamar iska na kaɗa bishiyar turare,
Cikin rausaya ta tako cikin falon.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
CHANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE
7
Faɗaɗa fara'ata nayi,
"Sannu da zuwa"
Cikin fara'ar ita ma ta amsa min.
Jin muryar ta yasa nayi saurin cewa
"Idan ban yi kuskure ba
Ina ganin khausar ce a gaba na".
Lallausan murmushi ta saki
"Of course"
Cikin zumudi na miƙe dan kawo mata abin motsa baki,
hira sosai muka shiga yi,
tare muka yi sallah,
na kawo mana abinci,
mun kammala ci ba ɗaɗewa ta ce
"To ni fa zan yi ta yan mota"
Ɓata rai nayi
"Ni ina ce wuni sosai za ki yi min"
Ta ce "Ki yi haƙuri ai zan dawo jibi,
akwai wuraren da zan ziyarta yau da gobe,
kasantuwar ba ɗaɗewa zan yi ba,
Dear na bai fada maki next week ne ɗaurin aurenmu ba?
na turo baki "Na sani,
bayan ba tarewa za ki yi ba, yayana ya huta
da zaman kadaici".
Dariya tayi
"Gara in kammala karatun shekara ce da yan watanni suka rage,
Ban da ya kasa haƙuri da sai na kammala sai a ɗaura a tare gaba ɗaya".
Sai bayan tafiyarta
na riƙa tunanin tarihinta
da ta bani,
mahaifinta babarbare ne mutumin borno,
Mahaifiyarta shuwa Arab,
Alh Muhammad bulama
Sunan mahaifinta,
ɗan boko ne wanda ke riƙe da muƙamin kwamishinan ilimi,
Mahaifiyar ta Haj bilkisu
Dr ce.
Ita ce ta uku wurin iyayenta,
Tana bin maza biyu, mata biyu na bin ta,
Abdullahi ma a nan Abujan suka haɗu
Saboda tana zuwa
Wajen ƙanwar mahaifinta
Anty Zara,
Ƙanin mijin Anty zaran abokin Abdullahi ne,
anan Abdullahi ya haɗu da ita.
Shi kuma Abdullahi
Ƙanin mahaifinshi neighbor ɗinsu Ahmad ne,
Kasantuwar ba shi da ɗa namiji a lokacin,
sai ya riƙa ɗauko Abdullahi,
har ya samu
ya rabo shi da katsina gaba ɗaya.
Tare suke da Ahmad tun primary har secondary,
har tafiyarsu England
Inda Ahmad ya zama kwararren likita
Abdullahi kuma cikakken lauya.
Tana karatun digiri ne a jami'ar maiduguri,
Inda take karanta
(Business administration)
Na yi murmushi na janyo ledar da ta kawo min tsaraba, irin turarukansu ne,
Sai wasu kwalabe da ke
ɗauke da wasu abubuwa kamar magani,
Na buɗe drawer na saka.
—————————
Washegari ne na tashi ina jin jikina ba daɗi
kaina yana sarawa,
tun ina daurewa
har ta kai ni kwanciya a falo,
wai ko zan ga Ahmad
idan zai fita,
in shaida masa ba ni da lafiya,
Shiru har na fidda rai,
da ƙyar na miƙe
na leƙa window,
Inda na hango Tonny yana ta aikin shi na kula da shukoki, na rasa yanda zan yi in kira shi ya ji ni ya zo ya sawo min magani
Kwanciya na ci gaba da yi kamar in kira wayar momi,
ganin yin hakan zai iya janyo tashin tashi na
ni kuma ba mai son in ta faɗar abinda ya dame ni bace Iamba ɗinshi na danna wadda na ɗauka a wayar khausar
har za ta soma ringing na
katseta,
kaina ya ci gaba da azalzala min,
ga shi ban ci komai ba.
Da dai na ga ba nayi,
Sai na kira wayar ta shi
har ta karaci ringing ta katse ba'a ɗaga ba,
na ƙara kira ba'a ɗaga ba kuma,
Sai na haƙura na ci gaba da kwanciyata,
Sai zuwa Azahar ya ɗan lafa,
Tea na haɗa na kukkurɓa sama sama,
na watsa ruwa
Sai nayi sallah na koma na kwanta,
Zuciyata na gaya min yanzu ko mutuwa zan yi
ƙarshenta kafin wani ya zo kaina,
gawata ta sandare.
Haka na ƙarasa wunin
a wuya ce,
cikin dare zazzaɓi ne ya rufe ni.
Da safe har goma
na ga bai shigo ba,
sai na san yau ma ba shi da niyyar zuwa
inda nake,
Hawaye ke bin idona ɗaya bayan daya,
Ina me tausaya wa kaina.
Ƙaraurawa a ke taɓawa
da ƙyar nayi maganar da aka jiyo ni,
ta bayyana cikin falon
Khausar ce,
Turus!
ta tsaya
"Me ya same ki?
A hankali na ce ba ni da lafiya
ta ce
"Tun yaushe?
na ce
"Tun jiya da safe"
"Kin sha magani?
na girgiza kaina
"Shi likita bokan turan bai sani bane?
nan ma ɗaga kai na yi
"Ya fita?
na ce "E bai daɗe sosai ba,
Waya ta ɗauko a jakarta
tana ƙoƙarin neman lamba
tana cewa,
Ko jiya a wurina suka yi hira shi da dear
Yawwa Dear ko za ka juyo
Sai mu shigar da shuhaina cikin Hospital ɗiin nan?
na same ta kwance ba lafiya".
Saurarawa tayi
"E" ta ce min bai ma sani ba, kuma bata sha magani ba".
ta kashe wayar ta juyo gare ni,
"Bari in haɗa maki ruwa,
sai ki daure ki yi wanka
dear zai wuce da mu cikin hospital ɗin".
Kaɗa kaina nayi,
Ita kuma ta ajiye mayafin ta ta wuce cikin sauri
"Taso to".
Umarnin da ta bani kenan,
Na miƙe ina dafe da kaina,
mai kawai na murza
na sa jallabiya da hijab,
A gidan baya na kwanta,
Abdullahi na ƙoƙarin barin wurin
Yana tanbayata abinda ke damuna?
nai masa bayani
Ya yi min fatan samun sauƙi.
Ya gyara parking a wurin adana motoci
Khausar ta ɗan rike ni,
Muna biye bayan shi
Wata ya tanbaya da alama stander ce
Doctor Ahmad na ciki?
Ta ba shi amsa
"E Yana ciki,
amma yana da baƙuwa"
Ji nayi gabana ya faɗi
Kai tsaye ya murda ƙofar
ya danna kai ciki,
muna biye da shi,
Office ɗin ba ƙaramin haɗuwa ya yi ba,
ga wani ƙamshi
da ya haɗu da
sanyin A.C
ya bada
wata ni'ima
ta musamman,
zaune yake
kan kujerar shi
teburin gaban shi
ya yi ma shi shamaki
da matashiyar
budurwar da
suke fuskantar juna,
Mikewa ya yi tsaye,
"Ran barrister ya daɗe".
Ya miƙo ma Abdullahin hannu,
Shi bai miƙa ma shi ba
Maimakon haka mur ya sha,
ganin su waye a bayan Abdullahin ya sa
shima ya sha mur,
illa dai sun gaisa da khausar,
Abdullahi ya ce
"Dama ba wani abu muka zo yi ba,
Matarka ce, bata da lafiya".
Ƙara tamke fuskar shi ya yi,
"Dan bata da lafiya
Kuma sai an biyo ni da ita?
Waya ya ɗaga stander ya kira,
ta shigo cikin hanzari.
Ya ce
"Ki je da su
wurin Dr sa'a,
In ji ni tayi treatment ɗin ta".
Ta amsa ta kuma juya,
muka rufa mata baya. Doctor sa'a ta duba ni
ta rubuta min magunguna
sai da tasa
aka kawo
magungunan
hada allura ta min da kanta
ta ce ba jimawa zan samu barci.
Mun nufi wurin motar,
Khausar na dafe da ni,
Sakamakon jirin da na ce mata ina gani,
Ahmad idona ya nuna min tsaye gaban wata Hommer jeep,
Yarinyar da muka gani a office ɗin shi,
Ita ma tana jingine jikin motar suna magana,
Duk da ciwon da ke damuna sai da na ji wani kullutu ya tsaya min, ya tokare ƙirjina.
Khausar na bude min bayan motar sai na kwanta,
Abdullahi ya ce yana zuwa,
Riƙe da ledoji hannu bi biyu ya dawo,
Sama sama na ke jin maganar da suke da khausar,
Idanuna a lumshe suke ina maida numfashi a hankali,
"Ka ga har ta samu barci
Na ji muryar ta sama sama,
"Wace ce yarinyar da ke tare da Ahmad?
Dan tsaki ya ja
"Wai ita yake son ya aura"
Gabana na ji ya yi wani irin bugu,
Tsaki ta ja
"Duka yaushe ya yi wannan auren,
har yake neman rakito wata?
Ya ce "Sun daɗe tare,
tun muna karatu a England,
Ita kuma a lokacin dadynta Ambassadan Nigeria ne a can,
ta nace masa.
Shi kuma bai damu da ita ba a lokacin,
wai sai yanzun kawai na gan su tare,
shi ne yake faɗa min
aurenta zai yi,
amma sai ya kammala ginin shi da ya fara,
na filin da ya saya,
bayan dawowarmu".
Taɓe baki tayi
"Lallai sai ta shirya zama,
ko ba gidan da na ji kuna magana ba?
Yana cewa daga turai ya zo da tsarin gininshi, yana son shi cikin nutsuwa,
dan ayi mashi
kamar yadda yake so.
Dai dai nan muka isa,
Da sauri ta ɓalle murfin motar,
ta zagayo baya
Sai da ta taɓani
sai na buɗe ido
"Za ki iya takawa
In riƙeki?
na ɗaga mata kai
Ta riƙeni muna takawa a sannu zuwa ciki,
kafin ta koma ta karɓo sayayyar da Abdullahi ya yo,
kamar jira sai barci ya ɗauke ni,
Na farka ne na ga khausar kan sallaya ta idar da sallah.
Ta ce
"Kin tashi?
Na ɗaga mata kai
Cikin sauri ta miƙe ta fita, sai ga ta ta dawo ɗauke da tray a hannunta,
"Ɗan daure ki wanko bakinki"
na yi kamar yanda ta ce
"Ya kike jin kan?
na ce
"Kamar an sauke min kaya ya yi wasai".
"Zazzaɓin fa?
Na sharo zufar da ke kan goshina,
"Ba ki ga yanda nake gumi ba?.
"Okey
to ɗan daure
ki cinye abincin nan,
ko kya yi saurin wartsakewa.
Ta miƙe ta ƙaro karfin A.C
ban san yi mata musu
dan ko banza ta yi min abinda ƴan'uwana za su yi min,
ga wanda na ke zaman shi ma
Indan shi sai dai in mutu.
ɗan tsakura nayi sai na cire hannu,
Mug ta miƙo min cike da kunun gyaɗa,
"Ɗan daure ki sha. "
Na sha shi fiye da zatona,
sannan na yi sallah,
a inda nake ina Addu'a
Na ji hawaye masu ɗumi
suna sauka bisa fuskata,
ban san khausar na lura da ni ba
Sai da ta kira sunana,
na yi maza
na share hawayen,
na amsa a sanyaye.
Ta ce
"Ko da ba ki gaya min aurenku
yana da matsala ba,
ni na san haka,
gabana ya ɗan faɗi
na dai yi zugum,
Ina sauraronta.
Ta ci gaba
"Kin san dai tsakanin
Abdullahi da Ahmad
Sai Allah ko?
Na ce
"Haka ne?
ta ce
"To amma saboda
wai hankali na
da dear
ya ce yana yabawa
Shiyasa
ya gaya min
halin da Kuke ciki,
kuma abinda ya tsara
tuni yake so in zo garin nan,
a ganin shi ke yarinya ce,
ba zan rasa shawarwarin
da zan taimaka maki da su ba".
ta ja numfashi
"Amma ke tun zuwanki
Wace hikima kika yi
irin tamu ta mata
dan ganin kin taimaki kanki?
na watsa mata idanuwana,
nuna alamar
ban fahimci
abinda take nufi ba,
"Nufina wane ƙoƙari kika yi,dan ganin kin taka masa birki?
Dan langabe kaina nayi
Maimakon magana sai hawaye,
Ban ko damu da share su ba,
ta dafa ni
"Ki yi haƙuri Shuhaina,
ba nufina in sa ki kuka ba,Kuma ba wai ina son
sai na ji sirrin zaman ki bane,
illa dai na san daga sanda Abdullahi ya faɗa min matsalarki na san ina tausaya maki,
daga sanda na haɗu da ke,
Sai na ji zuciyata tana maki so
tamkar ni da ke mun haɗa jini,
Ina sonki da zuciya ɗaya".
Na share hawayen,
"Ban taɓa sha'awar
Bayyana ma wani damuwata ba,
Ina dai gaya wa Allah ya yi min zaɓin abinda ya fi alheri,
dan Ahmad na haƙura da shi, ɗiyar tsohon Ambassador ya ke son ya auro ya haɗa da ni,
Ni da ba yar kowan kowa ba,ga shi ganina da ita na farko
Ya fara nuna min iyakata a gabanta.
Dama yana sona ne
da ɗan dama dama.
Sai da nayi kuka me isa ta,
sannan na ji zuciya ta ta
Aminta in bata labarin ko ni wace ce,
A kalla ko bata yi min maganin
Matsala ta ba
Zuciyata za ta yi sanyi.
Nan na gaya mata tarihina,
har zuwa yau.
maimakon kamar yanda nayi zato za ta tausaya min,
Saɓanin haka
wani kallo take bi na da shi, kamar za ta falla min mari.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
——————————
🌟🌟CHANJIN BA ZATA 🌟🌟
By
MARYAM IBRAHIM LITEE
8
Tana buɗe baki sai cewa tayi,
"Ai duk kuma halin da kika samu kanki, laifinki ya fi na shi yawa".
Saurin dubanta nayi
Kyawawan idanuwanta ta watso min,
"Ke yanzu kamar wacce ta fito daga dawa,
kin yi karatu dai dai gwargwado,
wanda za ki laƙanci rayuwa, amma bai maki amfani ba,
Aurenku kin san yanda aka yi shi,
gari ba zai waye ba
Ki yi wanka da kwalliyar ki me ban sha'awa,
ki je falon ki jira shi
Yana fitowa
ki gaishe shi,
Ah ah sai ki wani ƙunshe a ɗaka
In ba shi
ya ce maki ba
ke ba za ki ce
masa ba.
Kina ta fama da uban lulluɓi,
Sai ki gaya min
ta inda za ki ja
hankalinsa
gare ki.
Taɓe baki nayi
"Ai ko
sai dai mu shekara
a haka
Sai ka ce wata
ƴar iska
ni ce ma zan riƙa neman shi?
Ina ce idan ya ja ni
Jikin shi
Shi ne zan saba da shi,
Manzon Allah ma
Ya ce
Kunya bata zuwa sai da alheri,
nauyin shi nake ji,
Musamman idan na tuna
Shi ɗin fa
mijin yayata ne,
sai in kasa sakewa. "
To idan mijin yayarki ne haramun ne
Naku auren da shi?
Ina ce
koyi ne da fiyayyen halitta
yin hakan,
Sayyidina Usman
Allah ya yarda da shi
Yar manzon Allah
Rukayya,
wacce take
Mata ce
ga sayyidina Usman
da ta rasu,
Sai manzon Allah ya ƙara ba shi
Ummu khulsum,
Ita ma
Allah ya amshi ranta,
Sai manzon Allah ya ce
Bamu da wata yar
Ya Usman da mun
Kara ba ka.,"
Na gyaɗa kai
"Haka ne".
Ta ci gaba
Ba wai za ki riƙa kai kanki bane wajen shi
nake nufi,
za ki yi amfani
da waccan
dangantakar taku
Ki riƙa ba shi girma
kina nuna
Ke fa har yanzu kina ganin
Ke ƙanwar shi ce,
Yaya Ahmad sama da ƙasa,
ya zo
Zai fita
ki zo,
"Za ka
Fita ya Ahmad?
Babu abinda za'a yi maka,
Ki yi masa girki
Idan ya dawo
ki tare shi,
Sannu da zuwa
Ya Ahmad
ga abinci na yi maka,
Ki rika tsala kwalliyarki
tuni za ki ɗauke hankalin sa,
Shi da kanshi
zai nemi
canza mu'amalar taku.
ni ina ce ma mace
Komai ƙnƙantarta
da kissar ta ake
haihuwarta,
Kina da ƙirar da ba shi ba,
duk namijin
da ya zauna da ke
ba zai iya
kauda kai
matuƙar shi ɗin
lafiyayye ne?
Ki dubi kanki
Ina aka rage ki?
Sura me ɗaukar
hankali
Allah ya maki.
Ban ƙaryata ta ba
dan ba ita ce
farkon
wadda ta yabi
Kyan surata ba.
Dan Gwoggo Rakiya
ma
Idan ina tafiya
ta dinga
min faɗa kenan,
Wai wace irin
tafiyar karuwai
Nake yi,
Ina tafe
Ina kaɗa jiki,
mafari kenan
Na zaɓi zama
da hijab ko yaushe.
Na ce
"Ni da a tunanina
ya gama wulaƙancin
shi ya sallameni
ba shi kenan ba."
Wani kallo ta bi ni
da shi galala,
girgiza kai
tayi
Wai ma shekarunki nawa ne shuhaina?
Na ce
"Yanzun na shiga
ta sha takwas"
Ajiyar zuciya ta ja
A sanin da nayi
ke ɗin ba ƴar fari
ba ce,
ballantana
In ce sokoncin
ƴar fari ke damun ki,
Allah ya ba ki mijin
nuna ma sa'a
za ki wasa
da damarki,
ga shi inda suke burgeni
akwai riƙe addini,
na sani miskilayen
Maza,
Musamman waɗanda suke ganin
sun haɗu
ta fannin
kyawun
halitta
Uwa uba ga aljihunsu
Suna jin ya cika,
ga wayewa
ta ilimi,
to fa sai ka sa
Juriya da haƙuri me yawa.
Amma ina me tabbatar maki
da yar jamia
a ka ɗauko
masa
da sai ya raina
kansa,
Tsaf za ta yi
maganinsa.
Amma ko ke ɗin
kika bani
haɗin kai
za ki sha
mamaki
Sai ya gane
ba shi da
Wayo.
Wardrobe ɗi na ta ce
Tana son ganin kayan aurena
Na buɗe na ciro,
Ina buɗe akwatunan
tana kallo
Ganin dunkunan simple style ɗin kawai na yi amfani da su,
amma duk
daukacin fitted ɗin ban taɓa ba,
Cikin wani
takaicin ta dube ni.
"Su ma duk dan kar ya ga
Jikin naki
kika ƙi saka su?
Ɗaga mata kai
nayi
kwafa tayi
Ta duba in da
kayan make-up suke
Su ma wa'annan ba'a
taɓa ba?
Zunɓuro mata baki nayi
ta buɗe kit
ta ɗauko daga
Haɗaɗɗun sarƙa
da ƴan kunnaye
zuwa abin hannu
da agogo da zobuna,
ta ce
Su ma wa'annan
duk a banza?
na ce
"To wai ni
Ina ma nake zuwa?
Hararata tayi
"Yar kauye kawai"
Na ce
"Ah ah daina ce ma
garinmu ƙauye"
Ta ce
"Dole in ce
Masa daga kin
bada su a wajena"
Dan murmushi na yi
"Ni kuwa idan aka bar ni
Zan ce duk local Government ɗin Nigeria
bayan malumfashi suke".
Yar dariya tayi
Faɗi kike a wajen ki ba?
"Dama wajena mana daga ban da sama da ita"
Na kai hannu na yanki
Apple da ƴar wuƙar da ke hannuna,
na kai baki na fara
taunawa.
English wears ta fara
Warewa,
Ta riƙe kunnena har sai da
nayi ƙara
Na ce
"Wai ke kin manta
bani da lafiya?
ta saki kunnen
dan haka ma ta tsaya a jan kunnen da ranƙwashi
zan maki,
Allah kar kiji
batun wasa
matuƙar megidan yana nan wa'annan sune kayanki,
Cin abincin ma
Zan ce dear ya ɗaga ƙafa
har sai kun
ƙare amarci,
ko ya riƙa ai ko direba yana. amsar masa.
Kallonta nayi
"Ke ba ki ga ruwa ba za ki kama shuka,
Wannan kayan idan na sa a ina
zasu maƙale min
Ta ce
"Koma ina ne,
masu neman wuta ma
Suka sanya
Ballantana ke in
kin sa ka Aljanna kike nema.
Ta fara jera kayan kwalliya kan dressing mirrow
Tana yi tana mita
Bahaushe ya ce
In kana da kyau ka kara da wanka
Kin wani kimshe su
auren da aka ce yana neman yi idan bai
Maki sallamar da kike nema ba
Ciwon zuciya ya
Wuce da ke
Karara kishi ya bayyana
a fuskata
ko lura da hakan da tayi
Sai tayi saurin cewa
"Ba ki san yana neman
Wata tsaleliyar yarinya a
Maiduguri ba?
Kar ki so ganinta
Wata fara mai matsakaicin tsawo
tana da dan jiki haka kadan
amma ta fi a kasan ta maana daga mazaunan ta
Tana da kafadu waanda suka taimaka ma Brest din ta tsayawa cak
ko da suke manya
Tana da fuska me kyau da lallausan gashin kai. "
Dan tsaki na ja
ina tura baki
da na gane
Waskewa tayi
ta wayance
Da siffanta
'kirata
Bata san na
riga na ji maganar su
da Abdullahi ba
da alama subutar
baki tayi
Ina turarukan da na kawo maki
Na nuna mata lokar da na ajiye su
ta bude ta dauko ledar
ta shiga min bayanin su
Ba wai dan kamshi kawai ba
har da gyaran jiki,
ta jawo bunner ta jona
bayan ta zuba
wani turare sai da ya dau
zafi ta cire
Sa ta cikin zanen ki
Turirin na shiga gaban ki. "
Da karfi na ce
"Wai ke kin manta
ba ni da lafiya ne?
Ta ce
Yi hakuri ba wai ina nufin
yau za'a yi abin ba
kawai tsumaki zan yi
Na amsa na yi yadda ta ce
ta jika wani sassake kafin in tafi sai kin shanye shi
ganin kallon da nake
mata ya sa
ta ce
da kin san in da aka hado kayan nan
da ba ki masu gani gani ba
na musamman ne da aka hado min na gyaran amare
Ba mu ankara ba sai gani muka yi lokacin sallar magrib ya yi
Sai da ta fara Alwalar kafin na yi
da na idar na shiga wanka
na fito na samu ta
Ajiye min riga da wando
Irin na mutanen
India da gyalen su
Kwalliya na yi sosai ina kamshi
Sannan na sa kayan
kalar su pink ne
rigar ta kama ni
ta fidda surata da nake jin nauyi a rika dubana a haka. na yane jikina sa gyalen su
Ta ja ni zuwa falo
Tana zuba mana abincin
da ta yi ina barci tana gaya min irin kyan
da na yi
ni dai cikin dar_dar nake zaune dan na san mai wurin ya kusa dawowa
Gyaran muryar shi da muka ji
Yasa na soma
Mutsu mutsun neman gyalena wanda khausar ta take
na kuma san tana sane
Cikin faran faran suka gaisa
Ya ce
In zo kenan in kai
Amaryar mu gida
Ta ce
Ah ah ka huta kawai,
direba zai zo
dama 8:pm muka yi da shi
Zungurin da take min yasa na ce
Sannu da zuwa
Fuskar shi ce ta sauya
Ya dan hade fuska ya shige
Dai dai nan wayar ta
ta shiga ringing
Ta daga tana cewa
Za ta fito yanzu
Ta mike ta hada kayan abincin
Na ce
Dama kin bar su'
Ta ce
Ke da ba ki jin dadi
Sai da ta kai su
Kitchen ta dawo sai ta rataya jakarta
tare muka fito
Bayan tayi sallama da Ahmad
Da ta shiga motar
ta dan rage glass
"Ki kara hakuri
duk wanda kika ji ya ce
ya yi shi bai ci ribar shi ba
to kadan ya yi.
in sha Allah
komai zai zo iyaka. "
Na gyada kai
Haka ne,
na gode kwarai
Ubangiji ya saka da alheri
Allah ya bar kauna
sai yaushe?
Jibi
zan biyo ai
kafin in wuce,
Daga nan kuma
Sai Allah ya sake sadamu
Direba ya ja suka tafi
Na koma falo na same shi
News yake kallo
yana cin wani abu da ban
tantance
ko meye ba.
ban san yana kallona ba
sai da na murda kofar dakina zan shiga
Ya ce
Ya jikin?
Kamar me rada
ban waiwaya ba na ce
"Da sauki".
Na shiga na canza
kayan jikina
nayi addu'o'ina
na kwanta.
Da safe na tashi garas
Na yi wa Allah godiya
wanka na yi
na yi kwalliya da atamfa Holland dinkin fitted ne da ya zauna a jikina
Na kishingida kan kujera kwaya daya da ke dakin
Ban sha'awar cin komai
dan bakina ba
dadi
Karatun Al-kur'ani cikin suratu kahfi
na ji ya kunna daga falon
Idona a lumshe nake bin karatun,
Murda kofar da aka yi yasa ni daga kai
ganin shi yasa ni
saurin gyara zama
na shiga gaishe shi,
kamar kullun ya amsa
Ya ce
Ya jiki?.
Na ce
Da sauki
Abdullahi na falo
ya zo gaishe ki
To na ce
Na lalubi hijab dina na zura sai na bi bayan sa
Abdullahi tsokana ta ya fara yi
Ka ga mara lafiyar ta samu. "
Dan murmushi na yi
Alhamdulillahi
Na yi masa godiyar dawainiyar da ya yi da ni
Bai amsa ba
sai dai ya yi murmushi
Suka fita da Ahmad Ahmad
Ashe wai fitar nan da ya yi sokoto ya nufa
Sai Tonny ke gaya min
Kamar in yi kuka sai na ga to dan me in dai yi hakurin
In sha Allah ina sa ran ganin sakamakon shi ko ba yanzu ba.
Khausar ta zo mun yi sallama
In da na bata abinda na sa Tonny ya sawo min
Na ce ta kai wa mamanta
. mun rabu cikin begen juna
ta bar ni cikin kewar alherinta me yawa a gare ni.
Na ci gaba da amfani da magungunan da ta kawo min
dan na yi imani ba za ta cutar da ni ba
Sai da Ahmad ya yi mako guda ya dawo
Bai amsa sannu da zuwan da na yi masa ba
Abin sosai ya bata min rai
da na dawo daki na kalli kaina tsaf
Sanye nake cikin riga da siket na material
Sai na kawo doguwar hijabi na baka na sanya
Na zare hijabin
Na zauna bakin gado
tare da tagumi
hannu bi biyu
Ta waya nayi wa khausar murnar aurenta da aka ɗaura,
har take faɗa min
Ina ta ma angonki
tsiyar me yasa
bai taho min
da ke ba,
ya ke gaya min daga sokoto yake.
Ni dai uhum kawai na iya cewa.
Washegarin dawowarsa,
na tashi da wata matsananciyar yunwar da na riƙa ji
kamar an kwashe min ƴan ciki,
a daddafe na kai ƙarfe takwas kan sallayata,
kasa haƙuri na yi
in yi wanka,
Sai kawai na zare zanen da na ɗaura saman rigar barcina da zan yi sallah,
na zare hijab ɗin
Na fito haka, ba tare
da tunanin rigar barcin tawa guntuwa ce zuwa gwiwa,
Hannunta na shimi ne
kalarta baka me kama jiki.
Na isa kitchen na jona kettle,
Maimakon jira
Sai na fasa ƙwai
na soya,
Kamar in zauna kitchen ɗin in ci
Sai kuma na ga gara
In tafi ɗakina
kar Ahmad ya fito
Sai a sannan
ma na tuna da shi,
A faranti me faɗi na shirya komai,
Ina fitowa muka yi
Kacibis,
mugun gamo
in ji hausawa,
yA yi kyau kwarai cikin shigar suit
ƙamshin shi
ya mamaye wurin,
sosai ya burge ni, a
Kallon da na samu yi
masa sau ɗaya, na
sunkuyar da kaina.
Sai a sannan na tuna
yadda na fito
ƙafafuwana har rawa suke,
kamar zan kifar da farantin
dan tsananin ruɗewa,
muryata na sarƙewa, nayi ƙoƙarin gaishe shi.
By
Maryam litee
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
——————————
🌟🌟CHANJIN BA ZATA 🌟🌟
By
MARYAM IBRAHIM LITEE
9
Ya amsa cikin yanayin shi da har na soma sabawa,
ya wuce cikin sauri
A sanyaye na shiga daki
tare da dana sanin fitowa ta a haka
sai na nemi yunwar da na ke ji na rasa
Da kyar na karya
Wunin ranar sai na samu kaina da jin kunyar kaina
saboda tunanin yadda ya ganni
Sai da nayi sallar isha'i
sannan na shiga wanka
Kan stool na zauna ina
goge jikina da tawul
na busar da gashin kaina
da
(Hand dryer)
na mulke jikina da mayuka kala kala
Ina tuna khausar
Allah sarki masoyiya ta hakika
Alherin Allah ya kai ma ki.
Ina murmushi na fara shafa humrorin da ta kawo min masu
Matukar kamshi mai sanyaya rai jikina har ya kama kanshin
Na tsura ma jikina ido ta madubi,
Ko ba'a gaya min ba na san na samu sauyi me yawa
fatata ta dada gogewa tayi lukui lukui
Duk da dai dama
Fatar tawa me laushi ce
da wani sheki da
Kawayena ba su gajiya da tanbayata man da nake shafawa
In na ce
Vaseline babu me yarda
Sai su ce ban san gaya masu ne kawai
Mikewa na yi
na sa kayan barci na
riga da wando ne
rigar guntuwa ce
Iyakacin ta cibi wandon iya gwiwa
Skin tight ne
sun lafe da Fatar
jikina
na koma jikin window
ina leka yadda ruwan
sama ke sauka
kamar da bakin kwarya
ajiyar zuciya na saki
dan ni kam ina
son ruwan dare sai in ji dadin barci
na koma kan stool na zauna ina kallon
kaina ta madubi
Wai a haka khausar
ke son in rika fita gaban
Ahmad
Ba zan iya ba
na fadi a raina.
Jin turo kofa ya sa
gabana faduwa
Ahmad ne
cikin jallabiya fara sol
na dukar da kaina
na gaishe shi
Bamma yi tunanin amsawar shi ba
ban san me yake ciki ba
Ji na yi kawai an wurga ni bisa gado
Kan in yi yunkurin
mikewa
ya biyo ni
Ban san al'amarin babba
bane sai da na ji ya raba ni da kayan jikina
ban kuma tsinkewa ba
sai da na ji azaba ta ratsa ni, tabbacin
cewa abinda na ke ji
yana faruwa ga sauran mata
to ni ma ya iso gareni yau
Ban san iya lokacin da ya dauka yana abu daya ba
abinda na sani dai
Na yi kuka
har na ji ba dadi
Kafin ya hakura ya
bar min dakin
A haka na kai asuba
Ina tuna abubuwa kala kala
Sai da na gyara kaina bathroom
sannan na fito na yi sallar asuba
na koma na tattake
to rannan fa
ban tashi ba sai
sha biyu
shima yunwa ce ta tashe ni.
Gogan kuwa ya ma bar gidan
Tun kuma ranar ban kara ganin shi ba
Sai dai in ji shi
A yanzu sai takaicin shi ya fi yawa a zuciyata
Sau da dama zan ta zubda hawaye
Ina tuna abinda ya
faru tsakanin mu
Sai in rika tunanin
dama abinda ya kawo
shi wurina kenan
Yana samun biyan bukatar shi
dakin da nake ma bai ishe shi kallo ba
Ya cuce ni
ya maida ni
Second hand
wannan wace irin kiyayya ce
Ya ke min?
Ina yawan tanbayar kaina hakan
Mai zai faru?
Ana cika wata guda da faruwar hakan a tsakanin mu
Ba sai na tsinci kaina cikin wani irin lalaci ba
baki na ba dadi
Komai zan ci ba ya zama
sai zuciyata ta yi ta tashi
Abinda nake so
nake marmari tuwon dawa
miyar yauki.
Tonny shi ya yi aikin sawo ta da nikanta
ban jira kudin Ahmad ba
da na hannuna na yi amfani
Sai ko Apple da ban gajiya da cin shi
Idan na gama tuwon nan
Miyau na zan ji har yana tsinkewa
Kafin in fara ci
da haka na soma tunanin to wai meke damuna
Wani sashen na zuciyata na rada min ko dai ciki na samu
gabana ya yi saurin yankewa ya fadi
Na yi saurin ture zancen
tare da karfafa zuciyata da ba yanda za'a yi daga sau daya
hakan ta faru
Amma kuma ban ga al'adata ba
hakan ba damuwa ba ce
dan a gida na kan shafe wata hudu ban yi ba
Wancan watan kuma
na yi
dan in ban manta ba
kwana biyu ne da gamawa ta Ahmad ya shigo dakina.
Sai nake ta kara ma kaina kwarin gwiwa da cewa yanayi ne kawai na yau da kullun idan kana
yawan cin abu ka ji
ya ishe ka
Wata biyu bayan nan
Momi mahaifiyar Ahmad
tayo min waya
Kanwar Ahmad da suke uba daya ta haihu
Ita ce yar farko wurin Anty Amarya har jibi suna
In yi kokari ya kai ni
A suleja ta ke aure
Sai na ce
Ko za ta gaya masa
ta ce
shi kenan
Na aiki Tonny ya sawo min turmin zane da rigunan jarirai masu kyau guda biyu
zan kaiwa me jego
Gaskiya ba kadan nake gode ma Abdullahi ba
dan duk wani kudi
da zan kashe
Shi ke bani
Matukar ya zo gidan
Zai min Alheri
hakan ne ya taimaka min
yin duk abinda na ji
Ina bukata.
Ranar suna da misalin karfe goma na fito cikin kwalliya atamfa ce Aura sai na sa farin hijab da takalmi da jaka
A mota na same shi
Kamar an buge shi dan
Mugun hada ran
da ya yi
Ni dai na balle murfin motar na shiga
har muka isa
bai ko kalli wajen da nake ba
Waazin sheik jafar Adam yasa a CD motar
Gidan da muka je
Katon gaske ne
Irin na masu da shi
Sauke ni
kawai ya yi ya wuce
Abin shi.
Kamar ba gidan suna ba
Masu aiki ne kadai
Ke ta shawagin su
Daya daga cikin su
ta yi min jagora
Zuwa wani katafaren falo
ta ce
In zauna in jira hjy
bata fito ba tukuna.
Na zauna har zaman
ya gundure ni
Bakin ciki ya kama ni
dama ya san ba'a fara sunan da wuri ya kawo ni ya sanya?
Karfe daya na yi na nemi daya daga cikin yan aikin
ta nuna min makewayi
na zagaya na yi Alwala
na yi sallah a falon
Aka rika shigo da manyan kuloli
na abincin da aka yi oda dan bikin sunan a
Wata runfar shan iska
da ke harabar gidan
Wata cikin su ta
tanbayan
Abinda zan ci
Na ce
Idan akwai
tuwon amala
miyar yauki ta kawo min
Ta ce
Drinks fa
Na ce
exotic is ok
Ta hado min hada robar ruwan faro
Na ci fiye da tunanina
Kamar jira ake in gama
Me jegon ta fito
Sai yauki take
An sha kwalliya
Ko ta ina sheki take
Na ganeta
dan ta taba zuwa gida na
Kuma sunan da na ji Ahmad ya kira ta da shi
Rufaida
Sama sama muka gaisa
Na yi mata Barka
Da bata abin da na kawo
mata
da kyar ta motsa labbanta ta ce
Ta gode
Mun zauna zaman kurame
Mutane suka fara zuwa
Kowa ya zo bai dadewa zai juya
Ko ganin ba ni da niyyar tafiya
ta kira dan'uwan ta a waya
Ce mata ya yi
In har ba wanda zata sa ya kawo ni to ta bar ni nan
Yar dariya irin ta su ta miskilaye ta yi
Kai ma yaya ka nuna rashin bukatar ta bare ni
ni me za ta min
Ran roki masu tafiya
Wasu su dan sauketa
Abin ya Sosa min rai
Cin fuskar ya yi yawa
Mata kuma sun yi
biyar wa'anda ta yi wayar a gaban su
Wata hamshakiyar Hjy tayi ma magana
ta ce
Ba matsala
Matar me mutunci na yi na yi ta sauke ni bakin Asibitin
Ta ki sai da ta kai ni
har kofar gida
Na yi
mata godiya
ta ce
Ba komai
A ranar dai barci gaza daukata ya yi saboda bakin ciki
Da gari ya waye
Kirana ya yi
da miskilallar muryar sa
Ki shirya zan kai ki
gidan mu
Hakan aka yi
Sai da muka fara isa sashen mahaifin shi sannan na hjy Babba
Hjy Asmau anty amarya kenan
Maaikaciya ce ba mu same ta ba
Muna zaune gaban momi sai tanbayata take
Babu abinda kike bukata idan kun je can?
Duk da dai akwai abubuwan da na tanadar maki
Sai idan zaku tafi
sai ki wuce da su
Ni dai kaina a daure yake
To wai ma ina zamu?
Ta ce ma Ahmad
Su waye masu maku rakiya air port
Saurin cewa ya yi
"Jirgin safe za mu bi,
Na dai yi wa tunau direba
magana zai zo ya kai mu
dan haka mun hutar da kowa
Ta ce to ka kula da yar mutane amana ce a hannun mu
Suna ta firar su
Ina sauraren su
da ya tashi tafiya
Ya ce in tashi muje
Ta ce
Ah ah
Yi tafiyar ka zan sa a kawo ta
Bayan ta gama min wuni
Haka muka wuni tana ta ji da ni
Sai yamma likis ta sa aka mayar da ni gida
Na fito wanka ina daure da tawul guntu
daga kirji zuwa cinyoyi
rigar da zan sa in kwanta nake nema
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: CHANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE malumfashi
11
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
———————————
*BISMILLAHIRRAH-MANNIR-RAHEEM*
Ummu da Yusuf da yaya Azima suka haɗa kudi suka sayi ragon suna, ranar da na kwana biyar na tashi da ciwon nono ga zazzabi ya rufe ni, za muje kauyen dawo karɓo magani ganin yadda nake rawar sanyi Innar mu ta ce in kwanta bari ta je ita kaɗai ina nan kwance na tattake a kuryar gado
maganar mata na ji sun shigo falo, ban ko motsa ba illa kara kashe kunne da nayi ina jin hirar da suke ɗaya daga cikin su tana cewa;
To kwaɗayi yasa aka ja ma yarinya wahala ga shi nan ba'a samu abun duniyar da ake kwaɗayin samu ba an ja wa yarinya wahala sai ƴar da aka haifa, wacce marabar ta da shegiya kaɗan ne.
Gabana naji ya buga da karfi, ɗayar ta amshe, haka ne kuwa Asabe dan ko kare an ce bai leko ta fannin uban ya ce su ci kan su ba.
Sallamar Baba Gambo yasa su yin shiru, ta ce kuna ta jira ko ga shi har yanzu Innar su Salmar bata dawo ba
sai dai ashe Shuhainar tana ciki ni ban ma san ba tare suka tafi ba.
Eh tafiya ma zanyi idan ta dawo ayi mata barka.
Hankalina ya ɗaga kwarai da jin zancen su wunin ranar kuka nai
ta yi wanda Innar mu take ganin ciwon ne ke damuna sai ina tunanin ko meye dalilin Innar mu na kin sanar da iyayen Ahmad.
Ranar suna da yayar mu zata taho ta kawo min sabuwar Atamfa ta ɗinka, na ce; da baki wahalar da kan ki ba
ina da kaya.
Ta ce
Ai duk me jego sabo take sawa ran suna na kada kai daidai Ummu ta na ɗaukar yar ta ce Allah ya raya mana Antyn mu.
Yaya Azima ta ce amin.
Na cigaba da wanka da kula da Ƴata wacce nake ce wa Anty har muka yi arba'in, yarinyar ba ƙaramar ƙiba tayi ba, ga ta fara sol ga suma baka sidik
me lub- lib dan haka take da farin jini
ko bari na da ita ba'a yi, wannan ya ɗauka wancan ya ɗauka har makota.
Samun yarinyar a tare da ni
Sai ya dauke min hankalin tunani
ba ni da aiki
Sai gyaran a ba ta
Innar mu ba ta bari na zuwa ko ina
a cewar ta ai mijina ba cewa ya yi baya auren ba
Tafiya ya yi
kuma ya ce
Idan ya dawo
zai zo ya tafi da ni
don haka bata ga dalilin yawon ba
Ni dai ina jinta ne kawai sai in ga shi kam
ya yada kwallon
mangwaro ya huta da kuda
.......................................
A harabar kasaitacciyar makarantar da ke cikin
birnin Canada
Karkashin wata itaciya
zaune a kan kujera
Ahmad ne
A zahiri za'a ce
hankalin shi na kan
Mutanen da ke shawagi a wurin
sai dai a badini ba
haka ba ne
tunanin shi ya yi nisa
kwarai a kan matar sa
Wadda yake ganin
abin da ya yi mata
bai kyauta ba.
Abin ya zama masa
kamar wani sihiri
baya da ikon rufe idonsa
Surarta za ta rika ma sa gizo
Idan ya dawo daukar darasi
Ya kan fita harabar
makarantar
dan shan iska
duk matan turawan da
za su rika giftawa ta
gabansa
da fatan ko zai taya
Lumshe idanuwan sa
yake yi
cike da jin zafinsu
sai ya ga duk ba
wadda ta kama kafarta
sai ya shiga tunanin rana guda da ya kasance tare da ita
hakika yarinyar ta yi
Mace ce sosai
Wadda za ta gamsar da namiji har ta sa shi
mance sunan shi
a duk sanda ya tuna
al'amarin da ya shiga
tsakanin su
Lumshe idanuwan shi yake ya fada cikin
wani yanayi me wuyar fassara
Ina ma bai yi karyar ya taho da ita ba
da sai kawai yanzu
yasa ayi mata biza a
kawo ma shi ita wani irin murmushi ya yi tuna ba karamin morewa zai yi ba.
Dai dai da Abdullahi bai fada ma gaskiyar lamarin ba duk kiran da yake
ma shi ya na cewa khausar ce ke son
magana da Shuhaina
Sai ya ce
baya kusa da ita.
Watan Anty hudu wadda su Yusuf ke ce ma little
ta iya zama
ranar wata asabar ta
tashi da zazzabi
Yusuf da ya zo daga makaranta
ya sawo mata
magani
amma zazzabin nan
ya ki sauka
cikin dare ta ce ga garinku nan
na shiga wani hali
na rasuwar yarinyar nan
tuni na koma
halin da na fita sanadin samun ta
Kwananta biyar da rasuwa
Ina kwance a uwar daka
kan karamin gado
Littafin matanir risala ne
a hannuna
Na Ibn Abi zaidil kairawani
Innar mu
tana falon ta
tana yankan dinki
hayaniyar da na ji tsakar gidan ya dauka ne,
ana maraba da gaisuwa,
na gane an yi baki
Kofar dakin mu
ake sallama
muryar wadda na ji ta shigon ce
ya ba ni mamaki
sai dai ban motsa ba har suka gama gaisawa da innar mu
tanbayar ta na ji tana yi
Wai ina yar tawa
ba ta zuwa ta gaishe ni?
Ko nima laifin baba
Karamin
ya shafe ni?
Innar mu ko da ban ganta ba
na san murmushi tayi
Lamarin Yayan zamani ne, dan dan fari ya mutu
Ka dauke shi wani tashin hankalin da za ka ki ci ka ki sha
Cikin rashin fahimta a maganarta
Ta ce
Hala waye ya haihu?
Innar mu ta bata labarin
dawowar da nayi da ciki
har zuwa haihuwata da rasuwar yar kwana biyar
da suka wuce
Sai ga momi tana
hawaye
Innar mu tana bata hakuri
Ta ce
Wannan wace irin cuta ce
Ranar dai sai ga baban su Ahmad har dakin mu
da iyayena maza aka zauna
suka bada hakuri iya iyawar su
Baban shi ya ce
Yanzu zaman Shuhaina
ya dawo karkashin kulawata
zan sa ido dan ganin bai cutar da ita ba
Idan kuma abin ya gagara wanda ba'a fata
da kaina zan maido ta
Mahaifiyar shi ta karbe
tun bayan tafiyar su
Na fahimci akwai abinda
Baba karami yake boyewa
Koda yaushe
muka yi waya na nemi ya bata wayar sai ya ce
Baya gida
Na tada hankali
kan ina so in je
In gano
abin da yake boyewa
Sai Alh ya ce
In hakura da cewar da nake sai na je
a tura Najib dan wajen Amaryar mu
da Tunau direba ya ga lallai tafiyar za'a yi
Ya ce zai fadi yanda aka yi
amma dan Allah
ka da sunan shi ya fito
a wurin Baba karami
Ya ce
Gaskiyar magana oga shi
Kadai ya kai Air port
Matar shi gidan su ya sa ya kai ta
Ya ja kuma kunnan sa da kar ya fada wa kowa Jiya aka yi maganar nan
yau muka taho da Alh
ku yi hakuri ku
bamu shuhaina
kamar yanda Alh ya ce
zamu kula da ita
Zaunar da ni
Babannina suka yi
Ina kuka suka ce in tashi in hada kayana
Ta ce
Bar kayan ki zo muje
Baba karami zai gane
kuskuran shi da ni
Yake zancan.
ta kama ni
Muka fito,
Salma na biye da mu tana kuka.
mahaifin Ahmad
da momi suna baya,
ni na shiga gaba gefen direba na kudundune cikin hijab di ta.
.......................................
Bayan kara rabo ni
da gidan mu
a Karo na biyu
ba tare da sallama da
yan'uwana ba.
A mota ina kudundune
Ina sharbe
Ina sauraren su
daddy na
bayyana tsananin
bacin ran shi da abinda
Ahmad ya yi
Har muka shiga Abuja
zancen suke.
Momi dai na rike da hoton Amina ( little)
wanda ke cikin frame
Yusuf ya bata album
guda ya cika da hotunan
yarinyar.
Mun isa gidan su Ahmad
ana sallar magrib
Abba shi da Direba
alwala kawai suka yi
suka nufi masallacin
da ke cikin harabar gidan,
Muma muna shiga sashen mommy
Alwalar muka yi
muka bada farali,
Yan aikin gidan suna ta shigo wa mana barka da dawowa
Haj Babba ta shigo
da Anty Amarya
Suna ta maida maganar
Ina sauraren su.
Momi dai duk wanda ya
Shigo cikin yaran gidan
sai ta nuna masu
Pictures din little
su kuma sai ka ji sun ce
Wooow! Fine baby"
da kuma ta ce
"Ai ta rasu"
Sai su yi ta cizon yatsa
sun jima suna maida maganar
daga bisani sun bar sashen
suna fadin Allah shi kyauta.
Suna fita momi ta dube ni
"Sauko ki ci abinci "
da yake an shirya abinci a ledar cin abinci
da ta ga na zuba ina ta
juya cokali
Ta ce
" Ina nan fa har sai kin ci
Kin koshi
ko kya dawo yanda kike da gwanin ban sha'awa
Da safe momi ta ba danta daya daga cikin hotunan
Little
Ta ce
ya kai a yo lamination,
Farhan ya dawo ya ce
"Na kai momi, yacson din ya ce sai Friday
In koma in karba".
Ta ce "Allah ya kaimu ".
Sai ta shige bedroom dinta
Wayar ta da ke kusa da in da ta tashi ta shiga ruri
Farhan ya kai hannu ya duba da ganin sunan
Ya yi saurin mikewa
da karfi ya ce
"Momi yaya Ahmad a waya".
Daga ciki ta ce
"Kar ma ka karaso ce
ma shi ina gaishe shi"
Farhan ya yi turus da waya a hannu
Cikin sanyin jiki ya daga ya gaishe shi
Ko ya tanbayi ina momi ne
Ya ce
"Ban san dalili ba ta ce
ba sai na bata ba
wai tana gaishe ka
Kome yake gaya mashi
Farhan ya yi tsuru tsuru,
daga karshe ya kashe yana share zufa
Kallona ya yi yana tabe baki
Ni bamma je farautar ba ballantana ma in kashe zomon ko a kashe a bani rataya.
Ya kara da cewa daga fadar sako sai ya zama laifi?
Dan murmushi nayi ban yi magana ba
dai dai nan momi ta fito ta miko ma shi makullan motar ta
"Ku je Farhan ka rakata
gidan ta ta kwaso kayan amfanin ta
kafin in samu lokaci
sai muje kasuwa".
Ya amsa hada makullan gidan ta hada masa
Na mike na shiga dakin da momi ta ware
min
na dauko abaya
muka fito
yana gaya min
Momi bata bani motar ta
wai kar in je
in buga ma wani
sai yau
, dama ai an ce
Albarkacin kaza
kadangare kan sha ruwa a kasko"
Murmushi nayi dan na lura yana da san raha motar samfurin vibe
kalarta ruwan sararin samaniya sai walkiya take
Muna tafe yana
gaya min
"Wai saboda Allah ban isa mallakar mota ba?
Kallon shi nayi
"Haba dai in ji wa?
Abba mana ya hanani mota,
Na lura kuma hada
momi ke zuga shi
daga fa na taba buga ma wata mota sau daya
wai sai na shekara ashirin da daya
Na ce
"Suna da gaskiya ka ga
sannan ka kara hankali
sosai"
Kwafa ya yi
"Har fa sai nan da shekara biyu
Na ce
" To meye?
ba dai an sa lokaci ba?
Kar ka damu zai zo. "
Dan gajeren tsaki ya ja
"Sai dai in za ni school in yi wani 'kwam direba na ja na
ko kuma in wani ya ji kaina ya bani aro"
Maganar shi dariya ta bani
dana auna
sai na ga shi din sa'ana ne
Yana karatun Engineering a jami'ar Abuja.
Dai dai nan muka shiga Asibitin
Ya shiga gidajen ma'aikata
Zuciyata cike da tunanin abubuwan da suka shude a gidan.
A raina ina cewa
ko ina Tonny?
A falo ya jira ni
na shiga Bedroom komai na nan yadda na bar shi sai dai kura
Na hada kayan na fito
Ya dube ni
"Aunty kinga wata waya".
Na karba ina dubawa
Sai na ga ainahin wayata ce wadda Aunty Amina ta bani
da Ahmad zai tafi ya karbe
Dadi ya kama ni
har Farhan ya gane farin cikina
Ya ce
"Haba dai Aunty
ba girmanki bane
kina matar Dr Ahmad
ki rike wannan wayar
ni dai murmushi na yi
Da yamnacin ranar tare da momi muka shiga kitchen
dan girka abincin dare
na lura da kanta ta kan yi girki matukar ita ke da me gidan
duk da tarin maaikatan da ke gidan.
tunda kowace tana girkin ta a sasanta da masu aikinta
Saboda girman gidan
da kuma sashen kowa daban
sai kai sati ba ka ga mutum ba
matukar ba kafarka ta kai ka
In da yake ba.
Ina lura da yanda take sarrafa komai
aikina ta kan bani umarni
Miko min wannan, yadda wannan.
Kafin magrib mun shirya
Abinci kala kala
waanda suka cika sashen da kamshi.
Da daddare hada autan momi Abakar
me shekaru sha uku muka hau dinning dan cin abinci
Momi tana sasan Abba.
Da safe ma ina gefenta ta gama shirya komai
dagowar hantsi
muka fito, ina rike da jakar kayana waanda ba'a dinka ba
Farhan ya dube ta
Momi in zo muje?
Ta girgiza kai
"Na hutar da kai"
"Amma momi dan kin samu Aunty shuhaina ne ko?
Ta ce
Yi zaman ka,
idan lokacin shigar ka lecture ya yi
sai kayi tafiyar ka. "
gyada kan shi ya yi
ya maida kan shi ya cigaba da kallon da yake a TV.
Muka fito
Ta burgeni kwarai da bani sha'awa yanda take jan motar.
Muna tafe ina satar kallonta
har muka shiga harabar wani katafaren waje
Me hawa biyu,
Faka motar tayi wurin motor park din wajen
Muka fito
ta kulle kofofin
Ina biye da ita
Wani kanti ta shiga a hawa na daya
Yanda maaikatan wurin
ke gaisheta cikin girmamawa
na gane ba zuwanta na farko kenan ba.
Wurin zama aka bamu
wata cikin su wadda alamu suka gwada ita ce shugabar su
ta ce
Wannan yarinyar za ku gyara min. "
Yar dariya tayi
Haj zaku aurar da ita ne?
Ba tayi magana ba murmushin su na manya tayi
Matar ta bani umarnin in biyo ta
gyara sosai aka yi min cikin awanni tun daga gashin kaina har jikina da kafa da hannu.
na fito ina ta sheki,
ko ina nawa na fidda daddadan kamshi
Na samu momi in da na bar ta
na yi mata sannu
Aka bata list na kudaden gyaran ta biya muka bar wurin
Wani wurin muka shiga
In da ake sayar da kayan
kwalliya
Ta ce
In zabi wa'anda nake amfani da su
Nauyinta yasa na kasa daukar komai
Sai ita ta zabar min
ban tsinke ba sai da na ji yawan kudaden su da aka caje ta
Shagon masu dinki muka shiga
sun karba da alkawarin yin waanda zasu burge.
Mun fito ta dube ni
"Na gaji Shuhaina
bari muje gida na so saya maki English wear sai dai idan mun dawo. "
Sanda muka koma gida an yi la'asar
Farhan ne ya shigo
Mummy kina da labarin zuwan babban yaya?
Duban shi tayi
Kabir ya shigo kenan?
Ya daga mata kai
tayi fara'a
"Ban sani ba dan bamu dade da shigowa ba,
Kai baka wuce school din ba?
Sosa keyar shi ya shiga yi
Akwai sauran time,
Muhimmin abu kuma ina so yaya kabir ya ganni ".
Dan tsaki ta ja
"Allah kuwa ya kyauta maka,
Ni ban san sanda ka baci da shegen san kudi ba
To me ka nema da ba'a shigo maka da shi an ajiye maka ba?
Dan kada kan shi ya yi
Wai ma momi,
ai su kudi da sa nishadi suke ka juya ka ji aljihunka cike ba abinda ya fi shi farin ciki amma ina amfanin ka zauna duhu na dukan duhu bakin wando ba kwabo
Duban shi kawai tayi bata sake magana ba.
Kabir dan wajen Haj Babba ne
shi ne da na farko a gidan,
Matanshi biyu da yara biyar daga uwargidan shi Amaryar an ce banufiya ce bata haihu da shi ba.
Sallama akayi a kofar falon ya
Shigo mutum me dinbin fara'a da sakin fuska
Momi ta amsa cikin jin dadi
Tana fadin
Maraba da mutanen ikko"
na mike zan shiga ciki bayan na gaishe shi
Ta ce
"Hado ma yayanku abinci"
Na wuce yana cewa kamar ko kin san momi ban samu lokacin cin abinci ba saboda jama'a "
Sai da ya fara cin abincin suka shiga gaisawa
tana tanbayar shi iyalin shi
da wajen aikin shi,
Ina ciki yake cewa
"Momi ina kika samo yarinya me hankali?
Ta ce
" surukar ka ce"
baki ya dan rike
Amma Ahmad bai kyauta min ba,
ko a hanya na ganta ai ban santa ba.
Ta ce
Lallai kam,
bai kyauta ba,
sai dai idan ya dawo sai ya kai maku ita. "
Ya ce
"Allah ya dawo mana da shi lafiya dan ko jiya mun yi waya da shi akwai sauran kujeru biyu da suka rage
a wurina, ina ga aba surukar tawa daya ai an kyauta ko"?
Ta ce
Kwarai sosai aka yi halin girma,
Allah ya kara zumunci.
Yana kurbar lemo yana fadin
Amin
A dokance farhan ya iske ni
"Babban yaya ya baki kujerar zuwa saudiya"
Cike da jin nauyi na leko na yi ma shi godiya
Ya ce "Ba komai
Suka ci gaba da firar su
da ya tashi tafiya bai yarda ya tafi haka nan ba
Kudade ya bamu
ya ce mu raba ni da farhan da Abakar.
Farhan ya ce
Ki fito kudi sun zo
Ko in wuce school sai na dawo a yi kasafi?
Momi ta ce "Ah ah dawo ka bata kudinta
Na fito na zauna ina sauraren su
Ya ce
"Wai momi ina kika kai yar taki? sai sheki take tunda kuka dawo?
Ta harareshi
Ina ruwanka ko kawarka ce?
ya ce "Allah ya bada hakuri"
Sai ya koma zancen kudi
rafa guda ya miko min.
Karbi naki
in ji babban yaya
dan shi ba karanta
a lamarin shi,
Sai dai kuma ni ina namiji
nawa ba su kai nata ba,
ke kina ma tare da momi me za ki yi da kudi?
Momi ta rike baki
Ni Hadiza wannan yaro kamar ya yi modi da sarki,
zance sai ka ce dan kama
ina laifi karan ka ya kamo
Ya ce "kuma haka ne ana yi da kai
ya fi ba'a yi da kai
an cire ka
daga sarki
an baka me unguwa.
.
Na ce
" Wai kai me za ka yi da kudi ne,?
ga hausa bakin ka kamar jakin kano,
dama hausar ka karanta ".
Ya ce Aboki gare ni bakatsine,
kin san ku din in dai hausa ce karshe ne
ba shi da kowa sai tsohuwar kakar shi
duk fadi tashin nan
Shi nake temaka mawa
na zari dubu goma cikin nawa na kara ma shi
Sai da ya dubi idan momi ya karba
Ta ce
"maza bata kudinta"
Na ce
Bar mashi momi
na albishir din
da ya yi min ne.
Ya fita yana cewa
Kar ya makara
Momi ta dube ni
Ai ke da goshin ki kika dawo, jiya Alh ya ce
Ya yi wa Husna booking din kujera ga shi basu samu hutu ba har lokaci zai kure,
Ya ce a bar maki kujerar
ban kai ga gaya maki ba sai ga wata
Sai ki yi shawara wa za ki ba wa dayar?
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: CHANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE
10
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LfSQNGZy8Mz51VPphKpTjh
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
———————————
*BISMILLAHIRRAH-MANNIR-RAHEEM*
Ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, na gaishe shi ya ce ; ki haɗa kayan ki waɗanda kike ganin zaki buƙata zan yi tafiya ne zuwa course Ƙasar Canada na kimanin shekara ɗaya gobe zan wuce
ke kuma daga (Air port) direba zai wuce da ke gidan ku maybe sai na dawo zan zo in taho dake.
Kamar in buɗe baki in ce kawai ba ni takarda ta kayi tafiyar ka, amma kwarjinin shi ba zai iya barina in buɗe baki in yi wata doguwar magana a gaban shi ba, bare har in iya faɗa mashi mara dadi.
Ina wayar ki?
Ya tambaye ni, da hannu na nuna masa dan idan na buɗe baki kuka ne zai fita daga bakina, yasa hannu ya ɗauke ta.
Ban san kowa yasan ba tare dake na tafi ba, dan haka ki kiyaye ki iya bakin ki, bandir ɗin Kuɗi ya ajiye kan mirrow
har guda biyu, ki yi amfani da su".
Tun kafin ya bar ɗakin na fara sauke akwatunana, uku na cika ban kwanta ba sai ɗaya saura, idona kuwa ya ce bai san wani abu barci ba, saboda yadda zuciyata ke ɓace.
Ina idar da sallar asuba na shirya cikin sauri na ja akwatunana zuwa harabar gidan zama na yi na ta sa su, ba sai na fadi irin yadda suyar da zuciyata ke min ba.
Tonny nan ya fito ya same ni, yana gaishe ni tare da tambayata Madam lafiya kuwa?
Murmushin yaƙe nayi na ce lafiya lau.
Ya kama aikin shi ina nan zaune.
Direba ya zo Ahmad ma ya fito cikin shiri direban ne ya kwashe akwatunan yasa a boot, sannan ya ɗauko na Ahmad suma ya zuba su, Ahmed ne ya zauna a gaban motar kusa da Tunau direba ni kuma ina a baya.
.
Har muka isa Air port ɗin babu wanda ya yi ko tari.
Ya sauka ya ɗauki jakar shi, da ƙyar na danne zuciyata na yi masa fatan alheri.
Tunau direba na biye da shi a baya sai da suka ɗan yi nisa da motar suka tsaya magana yake masa shi kuma ya ɗan rusunar da kan sa cikin saurare.
Ya zo ya ja motar muka bar wurin, muna tafe zuciyata na sake-sake duka wata nawa da yin auren?
Ni kunyar yadda ƴan gidan mu zasu ji zancen ya fi damuna lokaci-lokaci ina share kwallar da ke sauko min.
Ana sallar Azuhur muka shiga garin Malumfashi ƴan gidan mu na ta oyoyo ga Amarya ga Amarya masu riƙe ni
na yi ni dai yaƙe kawai nake kokarina bai wuce in ga na isa ɗakin mu ba, Uwar ɗaka na wuce na haye ƙaramin gado duk wanda ya leƙo dan mu gaisa
sai Innarmu ta ce; ga ta can uwar daka ta tattake ko bata iso da lafiya ba?
Ko ruwa ta ki tashi ta sha wasa-wasa sai zazzabi ya rufe ni mai zafi
abin ne ya hadu da yunwa ga rashin barci.
A daren su yayar mu da Ummu suka zo ganina, halin da suka same ni
yasa su tafiya da sanyin gwiwa.
Yusuf ya sayo min magani amma da zazzabin na kwana, da safe sammakon asibiti muka yi ni da Innar mu wadda har ban san kallon ta
in na tuna duk da dadin da take ji
na ganina, amma tana jin yadda tafiyar take hankalin ta zai tashi.
Na ga likita ya yi min tambayoyi
kafin ya tura ni gwajin jini mun jima kafin nan aka fito da sakamakon likitan da kansa ya faɗa min ina ɗauke da juna biyu na wata biyu sai na sa kuka kawai Innar mu ganin ina kuka ta balbale ni da faɗa, to shege ne da kiike neman tara mana mutane? Ki samu a cikin zargi ga duk wanda ya ga kina kuka.
Dole na yi shiru amma kar ka tona zuciyata haka muka dawo gida.
Ranar da na samu kwana hudu na wartsake Innar mu ta tasa ni gaba
dan jin damuwata dan ta ce
Ya lura ba wai ciwon
kadai ke damuna ba
Ina da wata mas'alar ta daban
Ban yi ko dar ba
Na bata labari
dan an ce ba'a boyewa abokin kuka mutuwa
Sosai jikinta ya yi sanyi sai dai ta horan da in maida alamarina ga Allah
babu abinda ya gagare shi
Da safe ta kira kannen
babana ta mai da masu
Yanda aka yi
dukkan su alhinin su suka nuna
Illa Baba Ya'u da ya kwakwkwara min zagi
Wai an kai ni
In da zan huta
har suma su huta
Na yi halin tsiya an
koro ni
Ranar maganar ta kewaye gidan
wuni aka yi kowa na fadin albarkacin bakin sa
Tuni ni kuma na rasa nutsuwa da kuzari
da zarar na tuna cikin
da aka ce ina dauke da shi
sai in rasa in da zan sa kaina
Lokuta da dama
sai in rika zargin kaina
Kila da na bi shawarar
Khausar da ba wannan labarin ake ba.
Sai kuma inna tuna bawa bai kubce ma kaddarar sa.
Ga ciki me kwashe kwashe
yanzu kuma ya tashi daga san tuwon dawa
ya koma ina ganin
abincin mutanen gida sai in ji miyau na ya tsinke
ban ankara sai dai in ji miyau na na zuba kasa
sai ka ce wata mayya
sai in shige daki
duk da dama ba wani
fitowa na cika yi ba
Na samu Yusuf ya na cigaba da karatun shi
kudaden da aka ba innar mu na gadon Amina
Yahaya aka ba dan wajen
Baba sani
Wanda tun kafin rasuwar
Baban mu dan dakin innammu ne
Haka bayan rasuwar shi yana temaka mata da abinda ya samu
To yana da shago
Sai kudaden jama'a su ka karye masa.
sai ya zama dan abinda ya rage da shi ya biya mutane
Innar mu ta ce
Yusuf ya fito da kudin
A ba shi ya tada shagon shi
To anan ake samun na cefane,
shima ya yi hidimar iyalin sa
da yake yana da mata da
Yaro daya
Yusuf ma yana dan hidimar karatun shi
Kudin da na zo da su ma
bayarwa nayi aka kara ma shagon.
Kwanci tashi ciki na ya yi girma bai fito ba sai ya bi jikina
Innar mu duk yadda ta ga
na shiga damuwa
sai ta yi ta gaya min
kalaman kwantar da
hankali
har in samu nutsuwa
Sai dai lfy ta ki min
Ko da yaushe muna hanyar asibiti
Likitan ma sai da ya ce
ma Innar mu
Yarinya karama kamar wannan me ke sa ta
yawan tunani
ga shi a yanda ya nuna
jinin ta
yana gab da hawa
ga hawan jini hatsari ne
ga me ciki
Da kansa zai rika lallashi na
Su yayar mu ma basu
daukar lokaci suke zuwa duba ni
wai tausayi nake basu
Mutanen gidan mu kuwa
har mamaki suke ba ni
kiri kiri innar mu ta hakura da zaman
tsakar gidan
dan da ta zauna
za ka ji ana sakin maganganu
wanda duk me
hankali zai gane da ni a ke
A haka har cikina ya kai
watannin shi
ranar wata juma'a na
tashi da ciwo tun safe
ban samu kaina
ba
sai azahar
in da na samu santaleliyar yarinya
wanda duk ya ganta ya sai ya fadi tubarkalla
Kamar ta daya da
Anty Amina dan duk
wanda ya san
Amina sai ya jinjina
Kamar su
Kan ka ce me sun gyara ni ni da ya ta.
. cikin rufin asiri
Kwana biyar kafin
nan
ummu ta yo min
Sayayyar su kayan sanyi
Kayan jarirai
su pampers,
A duk sadda na zauna daki ni daya
Sai in ta kallon jaririyar Ina jin tausayin kaina ko yaya rayuwarta ta gaba za ta kasance?
Da innar mu ta tambaye ni Ko ina da sunan da nake so a sanya ma yarinyar sai na ce Amina jikin ta na ga ya yi sanyi ta fita dakin.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-1
CHANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE malumfashi
12
Oh!
Na ce cikin raina
Allah sarkin dadi
In ji barawon zuma,
cikin satin da ya gabata,
Idan an ce zan tsinci kaina
cikin farin cikin da na samu kaina yanzu
zan ce ah ah,
Amma da yake Allah babu
ruwanshi
baya dawwama ka a bakin ciki haka kishiyar shi
Sai ga shi wuni guda ya jefani cikin dadin da nake ji tunda na ke duniya
ban taba tsintar kaina cikin sa ba.
Motsin momi da na ji ya katse min tunani
Na ce "
Innammu zan ba"
Na shiga yi mata godiya
Da daddare na je nayi ma Abba godiya da Haj Babba
Ranar sai dai barci da yake shi barawo ne
ya samu nasarar sace ni.
Momi da kanta tayi wa innar mu waya ta shaida mata
zancan tafiya sauke farali.
Ranar da na cika sati guda da dawowa sai ga Abdullahi,
Ya zo gaida momi.
Kallon mamaki ya yi min da ya ganni
Ke kuma mutanen waccan kasar saukar yaushe? ba ko labari. "
Saurin fara gaishe shi na yi.
Momi ta fito, ya shiga nutsuwar shi ya soma gaisheta.
Ta ce
"Anya na amsa gaisuwar nan taka Abdullahi? dan na san duk tsiyar da abokin ka ya tsula ba zaka rasa sani ba. "
Cikin nutsuwa ya ce
"Momi me muka yi"?
ta ce "Kana nufin ba kasan abinda Baba karami ya yi wa matar shi ba?
Nan ya shiga rantse rantsen bai da masaniyar komai.
Na mike na shiga kitchen
na hada ma shi abun motsa baki, sanin shi din gwauro ne, sai na koma hada ma shi abinci.
na dawo momi na ba shi labari,
zan shige ciki ta kirani,
Zo ki yi zaman ki
har zufa ya rika yi "Wallahi momi ban san Ahmad ya yi haka ba, ina dai shan jinin jikina akwai abinda yake boye min,
sai dai duk tunanina na kasa gano komai. "
nan ya shiga bata hakuri
a madadin Ahmad suna neman afuwar ta,
na bata masu da aka yi.
Sun dan jima suna tattauna maganar
Daga bisani ta tashi ta shiga ciki.
Juyowa yayi yana fuskantata,
Hakuri yake bani murmushi kawai nayi
amma zuciyata cike take fal da kunci,
Sai na sunkuyar da kaina
a hankali na ce ma shi
" Ina Khausar?
"Tana gidan su"
ya bani amsa.
"Yaushe ne tarewar?
Ya ce
"Za su je aikin hajji da mamanta idan suka dawo za'a sanya rana.
Na fadi "Allah ya nuna mana"
Ya dubi hoton little Amina da momi ta kawo ma shi
"Allah sarki mun yi rashin beautiful baby wallahi Allah ya kawo masu albarka?
Shiru na ma shi
ya kammala cin abincin
kudi ya ajiye min
"Ki kara hakuri, in sha Allah ribar shi tana tafe.
gyada ma shi kai na yi sannan na ma shi godiya.
Ya yi ma momi sallama ya wuce.
Na kira khausar a waya ranar ban yi firar dare ba
duk da dama in momi
na wuri ban iya sakewa
Mun sha fira
na gaya mata halin da na shiga bayan rabuwar mu,
Daga muryar ta na gane ta shiga damuwa kwarai.
Ita ma hakurin tayi ta bani.
Da safe ne Ahmad ya kira momi a waya ta amsa radam kamar bata da wata mas'ala da shi.
da ta bar falon ne farhan ya ce
Humm lumbu lumbu momi ta ma shi, sai ya dawo zai sha masifa."
yar harara na ba shi "Momin ce zata yi masifar?
Saurin marin bakin shi ya yi
Au Allah na tuba fada zai sha fada "
Ni dai bin shi nayi da ido ina kara jinjina shakiyancin shi.
. Daga bita zuwa duk wani abinda ya danganci mahajjaci ya yi tare da momi muke zuwa,
dan tare zamu je
dan duk shekara, Abba na tafiya da daya daga cikin matanshi,
To wannan zuwan na momi ne,
An hada Innammu da wanda zai taimaka mata
Illa dai idan tashin ya zo za'a dauko ta mu tashi tare.
Kwanci tashi lokacin ya zo, kwana daya Innammu tayi aka kira mu
Aiki me dadi muka yi,
tunda tafiya ce da masu abun,
na dukufa gaya wa Allah Allah matsalolina idan aurena da Ahmad shi ne alheri Allah ya saukaka min al'amarin, idan kuma babu alheri Allah ya yi min canji da abinda ya fi alheri.
Mun kammala aikin mu, mun yi tsaraba sosai dan duk wanda ya dace in saya ma wa na saya ma shi
Momi ta saya min English wears masu yawa, wanda saboda yawansu da tsadar su sai nayi tunanin yar ta budurwa ta saya mawa,
Nan na kara yaba tsantsar alherinta a raina.
Sai da muka kwana biyu da dawowa aka sa direba ya mayar da Innar mu gida.
Sai ga Abdullahi ya zo mana sannu da zuwa
cikin kayan hannuna na ba shi hadaddiyar jallabiya da agogo na maza.
Yana dariya ya ce
"Ina na abokina? gane ba zan tanka ba ya ce
Na ma manta shi na shi special ne.
Ni mantawa ma nake ina da wani miji in ba maganar shi aka yi ba dan momi tayi kokarin ganin ta mantar da ni duk wata damuwata ta hanyar alherinta da karamcinta, kuma na san ban da momi ta hana shi da tuni ya guntsa ma Ahmad
Wani hantsi ina shirya ma momi kayan ta da me guga ya kawo, ta kirani na amsa sai na fito
Na same ta, a zaune take da takarda a hannunta
na ce "Gani"
Miko min takardar tayi
Foam ne na wata computer school da ke nan bayan mu
ki cike sai ki fara zuwa ko Diploma kya samu kafin mu ga abinda Allah zai yi,
zuwan zai rage maki zaman kadaici idan wannan uban shiriritar baya nan".
Na dubi gefen da farhan yake yana bata rai
ina ma shi murmushin zolaya
Na fadi "
Na gode momi Allah ya kara girma
Ba'a dade ba na fara zuwa, gaskiyar momi ne
fitar yana sani nishadi
da kafa nake zuwa na dawo a kafa.
Waya muke da khausar
nake ce mata
"Wai ku sai yaushe za ku tare
tace "Sha kuruminki an kusa, yanzu Dubai zamu ni da mommy na da Anty Rabi muna dawowa haka nan daddy zai hakura ya mika ni. "
Ina jinjina kai kamar tana kallona na ce
"Ah lallai ya ta rika"
dariya tayi
na ce Ina son zuwa bikin tarewar nan taku, amma ba zan iya tunkarar momi
in tanbaye ta dan ba kasafai take barina fita ba imma zan fita sai tare da ita yawanci ma wajen gyaran jiki ne. "
Ta ce "Iyee ki ce har an fara shirye shiryen taran sweet heart din?
dan tsaki nayi
"Ji ki da wata magana, kawai ta ce tana so in dawo da kyau na kamar da, wai ba karamar yamutsewa nayi ba.
cike da zolaya ta ce
"To kin yi kyan ko?
ba tare da na fahimci in da ta dosa ba
Na ce "Sosai ma kuwa"
dariyar ta kara "To ai shi kenan, amma ina ganin tunda ogan na bisa hanya dan ya kammala abinda ya kai shi, yana kuma san halartar bikin mu, kin ga kuwa ba zai bar abar shi ba.
Tsaki na kuma ja
Kan ki ake ji biki daurin aure sama da shekara a kudunduno ki a kawo kawai, ba sai an ba yayana wata wahala ba.
Wata irin dariya tayi me nuna abinda ba zai yuwu ba kenan.
Mun dade har credit dinta ya kare sai na kira ta muka kare maganar.
A kicin aiki ya kacame na abincin taron yayan momi da za su zo daga india, babbar yar ta ita Ahmad ke bi ma wa Anty Kubra wadda take aure a can,
da kuma Husna wadda ke zaune wurinta tana karatu,
kanwar shi ce ita ke bin shi,
amma a yadda Farhan ya bani labari tazarar shekaru me yawa ce a tsakanin su da Ahmad din.
Sai da na ga kammaluwar komai, sannan na wuce nayi wanka da kwalliya cikin shadda riga da zane wadda aka kayatata da hadadden dinkin zamani sai na dora after dress,
na fito falo in da farhan ke jirana, dubana ya yi
"Wannan kwalliya sai ka ce zamu taran yayanmu
harara na bi shi dan ita dan momi na wurin sai ban magana ba.
Zaman kimanin minti talatin muka yi kafin saukar jirgin,
mutanen da suka fito basu da yawa, sannan suka fito, kallo daya na yi masu na shaida su, dan duk na ga hotunan su wurin Farhan
Husna ce gaba wadda take doguwa suna fizgen kama da Ahmad dan dai ta dan dara shi gaske, wanda na san shi mahaifin shi ne sak,
Anty kubra na biye da ita ita kuma kamar an tsaga kara da momi matsakaicin tsawo da jiki gareta ga ta fara sol ga fara'a taro su muka yi da taimakon mu suka saka kayansu a boot
Mun yi nisa da tafiya Anty kubra ta ce wa Farhan
"Ina ka samo yar kyakykyawar budurwa?
da mamaki ya dan saki sitiyarin ya dube ni cikin murmushi "Surukar ki ce"
cikin mamaki ta ce "Dan Allah ? ashe da an yi abin kunya".
Da muka isa ba karamar murna momi tayi ba na ganin yayanta Husna dai bata cika magana ba, sai da suka gaido mutanen gidan aka zauna cin abinci, da aka kammala nayo ma yaran anty kubra wanka mata biyu namiji daya namijin take goyo tubarkalla kato da shi sai ganin shi ya rika tuna min little Amina,
daukar shi na yi muka shiga daki ina yi ma shi wasa yaron me suna Zayyad.
Tunda na ji momi ta fara ba Anty kubra labarin watsa masu kasar da Ahmad ya yi, Husna na kwance shame shame saman sopa tana wasa da wayar ta, daga Farhan har Abakar ba wanda ya shigo wai ball ake yi suna kallo a dakinsu.
Daki daya muka kwana da Husna da yaran Anty kubra, momi kuma ta kwana da yar farinta.
Washegari da da yan aikin momi muka hada abin karyawa Sannan na taya yaran suka yi wanka suka shirya, na sha mamaki danaji
Husna ta gaishe ni musamman kalmar Anty da tayi amfani da ita wurin gaisuwar.
Anty kubra kuwa sai sannu take min da aka hadu wurin karyawar, na dauki Zayyad wanda ya tashi a lokacin na cire ma shi pampers nayi ma shi wanka na ba shi abincin shi ina ma shi wasa yana dariya.
, naso tafiya da shi wurin computer momi ta hana ta ce "Haka nan ki je da shi ya hana ki abinda ya kai ki sauke mata danta ki yi tafiyar ki"
Da na dawo na sha mamakin tsarabar da Anty kubra ta bani riguna ne da wando da lullubinsu irin na mutanen can masu daraja., Husna ta bani abin hannu sirara na silver farare da ribbom na kama kai kala daban daban.
Na yi masu godiya.
sati guda da zuwansu .ba karamin sabo muka yi ba, Husna bata da saurin sabo amma kuma tana sabawa da kai mu'amala me dadi zakuyi.
Duk in da za su ziyara tare muke zuwa sai dai idan na je makaranta, har Bauci muka je muka kwana daya,
Satin Anty kubra uku ta koma Husna dai ce zata jima dan hutun nata dogo ne.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-1
CHANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE malumfashi
14
Shiru na ji har na fito kitchen din na jawo tebur na jera kayan abincin na saci kallon shi ya dafe kanshi da hannayenshi,
tabe baki na yi na yi wa momi sallama na wuce.
Da daddare ma kasa zama nayi a falon dan yana nan, kwance nake kan gado idanuwana suna kallon sama daddadan kamshin da ban iya manta mamallakin shi ya daki hancina, lumshe idona na yi ya zauna saitin kafafuwana kara rufe idanuwa nayi gabana na fat fat.
"Na zo ban hakuri ne Shuhaina" muryar sa ta ratsa dodon kunnena,
karo kuma na farko da na ji ya ambaci sunana
gabana ya tsananta bugawa
"Ki yi hakuri ki yafe min nasan na zalunce ki na kware ki tsawon zamana da ke ban kyauta maki ba, ashe har ciki na tafi na bar ki da shi ki ka yi wahalar shi ke kadai ki ka yi ta haihuwa ki ka dora ta reno, kika dandani zafin rashinta ke kadai ki yafe min.
Maida hawayen da na ji sun taho min na yi gami da kara kudundunewa.
Ya dade yana magiya amma bai samu na ce ko uffan ba.
Da safe da ya shigo ya ce ma momi yana son tafiya da ni bikin Khausar,
ta ce " Idan ta amince sai ku yi ta tafiya da zai fita ya yafito Husna tashi tayi ta bi bayan shi,
can sai ga ta ta dawo tana daga min rafa na yan dari biyu na ce "Iye wa ya baki kudi?
ta dan murmusa
"Lanbar wayar ki kadai na bayar aka bani"
dai na murmushin da nake na yi na tabe fuska na mike tsam na shige daki, kamar jira ake aka
kira wayata bakuwar lamba ce na daga hade da sallama ya amsa "Ranki ya dade roko nake ki zo muje gidan mu ki amshi tsarabar ki".
jarumta nayi sosai wurin ce ma shi "Ba sai na je ba ranar da ka samu lokaci ka kawo"
rage murya ya yi "Haba my baby ki daure mu je".
Ba tare da na amsa ba na kashe wayar, ba'a dauki dogon lokaci ba ya kuma kira kamar in share shi sai na amsa
Rokona yake da magiya in fito yana mota ganina kawai yake son yi"
Na ce ma shi To
Kashe wayar nayi gaba daya na haye gado barci kuma ya yi awon gaba da ni.
Da daddare ma yana gidan dan haka ban fito falon ba, rike nake da littafin hausa ina karantawa turo kofar dakin aka yi abinda ya sani kai idona kofar, Ahmad ne wanda ya sha kwalliya ta kananan kaya yana ta zabga kamshi, kujerar dressing mirror ya jawo ya zauna " Shuhainata kenan ba ko gaisuwa? kara rufe fuskata na yi da littafin ni sai yake bani mamaki kamar ba Ahmad din da na sani ba da wanda ban ishe shi sauraro ba, wata zuciyar ta ce ya gama tsula tsiyar shi yanzu lokacin ki ne.
Wayar shi ya ciro magana na ji yana yi, Abakar ya yi sallama kofar dakin da jakunkuna a hannun shi gaban shi ya ajiye, yaron na juyawa ya maida kofa ya rufe, ya fara bude jaka " Ginbiya tsarabar ki ce na rasa abinda zan sawo maki dan ban san komai naki ba abu daya dai na rike ke din ma'abociyar kamshi ce, dan duk sa'adda na shiga dakin ki zuciyata ta kan nutsu da daddadan kamshin da ke fita a ciki,
dan haka na sawo maki turaruka da kayan shafa.
Turo min ita ya yi ya kuma turo min sauran guda biyu babba da karama.
Yau ma haka ya gaji da magiyar in furta ma shi ko kalma daya ne ya gaji ya tafi.
Husna ce ta bude jakunkunan ta farko rantsatstsun takalma ne hade da jakunkunan su, sai ta biyu cunkus take da kayan kwalliya da turaruka masu matukar tsada, sai yar karamar sarkoki ne da yan kunnayen su wa'anda ba sai an gaya maka taadi me yawa aka yi wa naira kafin a mallake su.
Bayan mun kwanta ma text din shi suka yi ta shigowa yana fada min halin da ya fada na tsananin kaunata, na karshe shi ne yake shaida min zai shigo da safe mu je wajen tela ya gwada ni dunkunan da zan sa a wurin bikin Abdullahi yau ya sayi kayan.
Da ya zo kuma nayi mirsisi na ki zuwa gwada dinkin, sai Husna ce ta dauki rigata ta ba shi.
A daren bai zo ba sai nayi tunanin ya yi fushi ne, tara da rabi sai ga kiran shi wai ga shi a bakin get in fito mu shirya tafiya wurin bikin,
text na tura ma shi ba za ni ba na koma na cigaba da kallona.
Da safe bayan mun yi sallar asuba mun yi marajaa komawa nayi na kwanta sai dai na ji Husna na bubbuga ni cikin barci nake tanbayar ta meye?
Ta ce "Ba yau za ku tafi ba kika koma kika kwanta?
Maida kaina na yi "Sai in ki barci dan yau zamu tafi"
ban san iya lokacin da na dauka a kwance ba sai dai na ji an yaye bargon da na lullube saurin bude idona na yi tunanina Husna ce, Ahmad ne zaune gefena ya zura min ido saurin kankame jikina nayi saboda rigar barcin da ke jikina ba wata ta kirki ba ce, dan miskilallen murmushi ya saki tare da nuna kamar be san me nayi ba
"Barcin ya isa haka ki tashi mu wuce".
Dan tura baki nayi na ce " Ba za ni ba".
Ya ce "Kina so in shigo cikin bargon kenan? "
Zumbur na yi na duro na fada bathroom sai da na sa key sai na fara wanka
muryar shi na ji jikin kofa "Ga kaya nan ki zabi wanda za ki sa yanzu".
Daga ciki na ce " Ni fa in ba da Husna ba ba in da za ni"
Ya ce " In hakan kika fi so sai ayi hakan".
Na kara cewa" Idan ba ka tafi ba ba zan fito ba".
Ya ce "Na tafi"
Sai da na tabbatar da tafiyar shi na fito na fara shafa mai ina kallon kayan da ya zube bisa fado, na shiga duba su na rasa wadda zan zaba dan duk sun hade daga karshe na hakura da wata shadda ready made doguwar riga ce ta amsan ba kadan ba na zabi cikin sarkokin da ya kawo min na zabi jaka da takalmi ina daura dankwali ya shigo ta madubi na hango shi yana min kallon kasa kasa, bude jakar da ya kawo min ya yi ya ciro turare yana fesa min ni dai kaina yana kasa ya koma ya kwashe sauran kayan da ke zube a kan gadon ya maida cikin jakar ya rufe ya yi waje da jakar.
Na sami momi zaune na gaishe ta ta amsa tana cewa "Har an shirya kuma ba'a karya ba?.
Ladi cikin masu aikin ta ta fito da tire ta ajiye gabana tea na hada na sha sama sama, Husna ta fito ta sha kwalliya itama ba magana momi tayi mana fatar dawowa lafiya,
muka. fito muna taku a hankali, nesa na hangi motar Ahmad yana zaune cikinta yana shan waya, bayan motar muka zauna mu biyu waiwayowa kawai ya yi ya dube ta ta yi saurin fita ta bar motar, bayan ya dawo kusa da ni "Haba gimbiya ta dawo gaba mana " shiru nayi ina duban fuskar shi da ke nuna damuwa karara, "Dan Allah ki rika min magana wannan shirun ba karamin azabtar da ni kike ba, gara ki rika min magana ko da ba kalmomi masu dadi za ki gaya min ba ".
Yana rufe bakin shi wayar shi ta soma kara a hands free yasa ta muryar me kiran ta fito "
Kai malam mun fa gaji da jiranka
ya ce "Ina gaban gimbiya sai ta gama shiryawa ".
Ya ce " Yana da kyau amma ka kara minti ashirin sai dai ku taho kai da gimbiyar".
Daga can ya ce. "kuna iya tafiya"
Sannan ya kashe wayar ya koma lallashina in dawo gaba sai da na gama mishi yanga sai na koma ta waya ya kira Husna.
Cikin tawagar abokan su muka yi tafiyar Ahmad ke jan motar shi Abdullahi na gefen shi muna baya ni da Husna
Yamma likis muka isa, gidan babba ne amma ba masaka tsinke ko ina jama'a ne, rawa ake cashewa.
Khausar suka yi ma waya ta ce ta fita amma za ta yi waya a zo a yi mana jagora zuwa ciki daki guda aka bamu hatta da abinci an shirya mana salla muka fara yi sannan muka ci abinci,
Mun kammala muka kishingida har Husna tayi barci ni kaina cikin gajiyar nake, san ganin Khausar ya hana ni yin barcin da karfi aka turo kofar "Ina Shuhainar nima cikin jin dadi na tashi zaune na tare ta,
hannuna ta kama ta rike yanda na ga ta koma ya sani rike baki, na zuba mata ido a sanin da nayi mata ita din doguwa ce mara jiki sai na ga mata ta ajiye hips da cikar kirki, hure idona ta yi " Malama kallon fa lafiya?
"Ke kin fa bani mamaki kin ga yanda kika koma?
Ta kada ido " To ba dole ba, aure wasa ne?
Na rike baki "Aure? ai ba ki tare ba?
Ta yarfe hannu "Ba dai an daura ba? ai nan daf nake da juyewa"
Sai da na ji faduwar gaba jin zancen ta
" Ban gane juyewa ba? kina nufin ciki gare ki ?
Cire wai ana kai ni ban wuce three month ".
Kama baki nayi
"Ke yanzu Allah ya sanya Alheri za'a ce ko Allah ya raba lafiya?.
Kafada ta noke
"Duk wanda aka ce ai fata ne"
Na jinjina kai "Ashe yayana yasan abinda ya taka shi yasa ya daina wannan giringidishin ".
Ta ce "Da farko bai samu hadin kaina ba sai da ya dage"
"To da ya ji maganar cikin me ya ce?.
Me kuwa zai ce dadi hakan ya ma shi Wai hakan ya sa Abba na ya ba shi matar shi".
Na ce "Ko da yake da gaskiyar shi yayan nawa ya zama tuzuru, ina zai iya jira?
Ahmad shekarar shi nawa da aure? ko da yake na farko auren gata aka yi ma shi "
Ta rike baki "Wai me Ahmad din ya ba ki dawowar shi kike zaro zance haka?
dan ni dai Shuhainar da na sani idan an sa mata hannu a baki ba za ta ciza ba". Muka yi dariya ta ce "Yanzu ma Abba na da kyar ya yarda yasa ranar tarewar shi bai san rabuwa da ni, sai da momi ta ce ka ba shi matar shi in dai ba so kake a haife mana a gida ba".
Na ce Shi daddy bai san yar ta gaji da zama da su ba".
Dariyar muka sake yi daga karshe tashi muka yi ta kaimu muka gaisa da mahaifiyar ta.
Karfe tara na dare kowa ya gama shiri dan halartar liyafar da abokan ango suka shirya ma shi na hade tsaf cikin wando da riga na wanda ya yi min cif rigar daga sama zuwa ciki ta kama ni sai aka bude ta daga kasa tsawonta iya gwiwa
dan haka ta fidda surata, gyalen me yala yala ne wanda zugar Husna na bi na yafa shi in banda haka rufe jikina zan yi sanin zunubin da zan kwasa, wai so take in kara ruda yayanta da na ce mata akwai maza a wurin ba kyau ta ce " Yau ne kadai ta ma roki Allah ya yafe mana dan ta san hada ita za'a raba zunubin daga ita ta matsa min.
Dariyar maganar ta nayi
Na ce "Dama wani malamin mu ya ce mace ce in za tayi magana sai ka ji ta ce Allah na tuba memakon tun da ta tuba tayi shiru to maganar da za tayi wadda zata janyo mata zunubin ce".
Sarkar da nayi amfani da ita me kama wuya ce
takalmina me tsini ne da jakar shi Husna na tsaye rike da turare tana fesa min na rike hannunta "Bar ni haka in ji da wannan zunubin"
Ta ce "Duk da yaya Ahmad yake dan'uwana da nake so da girmamawa ya bata min rai kwarai da abinda ya maki dan kin san ciwon ya mace na ya mace ne, kuma ko ni aka yi wa abinda ya yi maki ba zai ji dadi ba".
Ban lalubi amsar bata ba aka kira wayata Ahmad yake gaya min ya so ya zo ya tafi da ni to amma dole ya kasance a wurin dan ganin tsaruwar wajen, amma ya turo a dauke mu, idan mun gama shiryawa.
An fara shirye shiryen da za'a yi muna kallon wajen zaune muke ni da Husna muna kallon juna mun sa tebur tsakiya Ina son kallon ango da amarya amma idon da Ahmad ya tsare ni da shi ya hanani sakewa ya sha duk da uban kwalliyar da ya sha yana daga gefen angon daga hagu amarya na a zama kowannen su ka duba ba'a maganar irin kyan da ya yi, abokan angon yan boko ne masu murza naira, yammatan amarya masu ji da kan su ne ko wacce ka duba sai shan kamshi take, fira muke kasa kasa tare da kallon abinda ke gudana a wurin, maza biyu suka tsaya kanmu da san yi mana magana Husna ta ce matan aure ne na ukun ne ya fi naci dan da kyar ta samu ya wuce na ce "Ai kin ga irinta"
Muna cikin haka ango da amarya suka shiga tsakiyar fili.
Wurin ya rincabe da jama'a ana masu liki naso zuwa ganin yawan mutanen yasa na saurara, Husna ta ce in bari su yi sauki sai mu je da suka ragu na mike ita kuma tana amsa waya, na ratsa mutane na soma likin kamar jira maza suka rufe ni da liki, gabana na ji yana harbawa na yi wuri wuri ina neman in da zan bi in sulale ina cikin haka ban san yanda aka yi ba sai dai na ji an finciki hannuna ja na ake da karfin tsiya, ban fahimci wanda ke min wannan aikin ba sai da muka fito harabar wurin da ake ajiye motoci wata mota ya bude ya tura ni ciki ya shigo ya zauna kusa da ni, ba sai na fadi irin razanar da na yi ba a takaice ji nayi kamar in saki fitsari a zaune ya dube ni da idanuwan shi da suka canza kala dan bacin rai, "Ke kin ga dacewar abinda kika yi? wannan shigar ita ce ta dace da matar da ke da igiyar aure a kanta ta fito haka?.
gaba daya hall din kallon ki ake kin san irin zunubin da kika kwasar ma kan ki?
Ya finciki yalolon gyalen da na yafa ya murde shi a hannun shi na yi maza na kare kirjina da hannuna biyu, kwafa ya yi me bayyanar da takaicin shi "Bayan kin gama nuna ma kattin banza. Kuka na shiga yi mashi ya ce "Yanzu dai kin gama Fatin bikin ma ban da na Abdullahi ne da gida na wuce da ke dan ba dan iskan da zai kuma ganin ki na ki ki hau high table dan kar a gan ki ashe ban tsira ba, dawo gaba in maida ki gida na ki motsi na ce gyalena" ya ce "Wato ni kadai kike jin kunya sauran duka yan iskan da suka gani ba ki jin kunyar su?.
mantawa ya yi da ni ya danna kira'ar Abba zaria sautin ya rika ratsa cikin motar, kwankwasa glass din motar da ake yasa ya tada kai ya sauke glass, "Lafiya" ya ce da matashin da ke tsaye, tsayuwa ya gyara "Wannan gimbiyar ta bayan motar ka na biyo, dan Allah ina son magana da ita."
"Yi hakuri malam ka kama gabanka matar aure ce".
Yar dariya ya yi "Nima mijin aure ne, ka dube ta fa ai ba alamar hakan a tare da ita. "
Tsaki me karfi Ahmad ya ja ya juyo ya dube ni " Kin ga abinda nake gaya maki ko".
Sannan ya juya wurin mutumin sa'ar ka daya ita ta yi shigar da ta kira ka amma ba dan haka ba, yayi kwafa "Idan an ce ga me irin fasalinta ba za ka yi marmarin kallo ba".
Daga haka ya finciki motar ni da ban shirya ma hakan ba har ina hantsilawa muna isa "sauka kawai ya ce min ganin ba fuskar tanbayar gyalena na fita na soma tafiya kamar wadda kwai ya fashe mawa kuma jikina ya bani ni yake kallo dan ban ji tashin motar shi ba.
Tana shigewa cikin gidan ya shafi dan lub lub din sajen shi gaskiya Allah ya yi halitta a nan yaso ya yi wa kan shi sakiyar da ba ruwa yana tuna yanda take tafiya komai nata na girgiza ko ta ina ta cika, ashe ba banza take faman lullube lullube a hijabi ba ta san abinda take boyewa.
har mamakin kanshi ya rika ji tun da ta shigo hall din ya rasa sukuni gani yake kowa a wurin ita kadai yake kallo, wanda ya san Amina tana yawan sa gyale shi ne ma lullubinta amma bai taba damun shi ba.
By
Maryam litee
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-1
CHANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE malumfashi
13
Aunty kubra tana ta fadin rashin jin dadinta na rashin dawowar Ahmad su hadu, dan rabon ta da kasar tun rasuwar Anty Amina.
Ta tafi da kwana biyu ranar ta kama litinin, na gama shirina tsaf cikin kyakykyawar shiga ta abaya kalar ta milk color,
gaban ta caccabe da kwalliya, mayafi me kyau na yane jikina da shi,
Takalmina flat ina rike da hand bag na fito.
Husna da farhan na samu dan farhan ya ce sai biyu yake da lactuce Abakar an tafi da su shi da yaran Haj Asmau Anty Amarya. dan duban su na yi,
"Barkanku da hutawa. "
a tare suka juyo suka dube ni Husna ta ce "Banda ban yi wanka ba ai da tare muka fita na wuce sallon".
Na ce "Ki bari idan na dawo sai mu je.
Kai ta daga Farhan ya ce
Anty Shuhaina daga kuma samun Anty Husna sai aka wancakalar dani".
Kallon mamaki nake ma shi "kai kam akwai daukar dumar magaji da nishi, yaushe aka yi hakan?
Husna ta ce " Kyale shi hala ni din kishiyar ka ce?
na ce " To yi hakuri tashi mu tafi in za ka
Ya kada kai "Yi tafiyar ki kallo nake. "
Na yi wa momi sallama sai na bar gidan.
Ko da na isa sai na samu kaina ban san yin komai kasala duk ta rufe ni, sai ina jin faduwar gaba.
a daddafe na kare zaman na taho hanyar gida ina ta sake saken ina isa kwanciya kawai zan yi.
Na yi sallama kofar momi na sa kai, abinda na gani ba karamin sani kaduwa ya yi ba, take gabana ya soma bugawa ya amsa sallamar da na yi yana zaune yana cin abinci a dinning
Ya kara wani irin kyau da gogewa sai annuri ke fitar ma shi, na bayyanar yana cikin jin dadi kananan kaya ne a jikin shi da suka yi matukar amsar shi daga idon da nayi a karo na biyu dan in kara tabbatar da shi din nake gani hada ido muka yi ya zare glass din shi ya dube ni, na yi saurin wucewa ciki a dakin wurgar da komai na yi na fada gado rub da ciki na kwanta, sai na samu kaina ina tuna abubuwan da suka shude, tun dawowar Anty daga zuwa rasuwar ta.
CANJIN da aka samu na BA ZATA wato aurena da Ahmad da irin zaman da na yi da shi har zuwa tsallake nin da ya yi ya tafi ya bar ni da dan tayin da bai ko san da shi ba, har haihuwata rasuwar yarinyar zuwa yau
Komai na ji ya dawo min sabo wani irin bakin ciki ya lullubeni.
Sai na samu kaina ina malalar da hawaye masu zafi.
Ban san iya lokacin da na dauka a haka ba sai dai muryar Abakar na ji
yana fada min Momi ta ce ya zo ya gani na dawo".
Na ce Eh
ya ce "Ta ce ki fito a ci abinci"
Kai na daga ma shi na tashi zaune ganin ya juya na mike na shiga bathroom wanke fuskata nayi na fito na mutststsuka mai da hoda sai na fito na same su a falon.
momi na yi wa sannu da gida,
duk yadda na so daurewa in ci abincin ya ki wuce min ganin Ahmad ya lalata komai sai juice na yi ta banka ma cikina
Ina lura da Momi hankalinta na kaina,
ko da ba ta ce min komai ba.
Da na gaji da zaman mikewa na yi na koma na yi alwala na yi sallah na dade a duk sujjadar da na yi ina neman agajin ubangiji kan kar ya kara maimaita min irin zaman da nayi da Ahmad na rashin yanci da ganin wulakanci,
Dan ni dai yanzu na san bani da wani yanci da zan ce bana auren shi in dai ba shi na samu ya ce ba ya yi ba.
Har dare ban kara jin motsin shi ba, ba kuma ji wanda naji ya yi maganar shi.
Husna dama ban same ta ba sai yamma sosai ta dawo,
Sai da aka kirani cin abinci ta lura bani da walwala,
Ta dubi farhan da ke gefenta,
"Wai make damun Antyn namu ne?.
tun da na dawo nake ganinta gata nan dai.
Ya noke kafada
"Ban san me ke damunta ba, amma kina da labarin dawowar yaya Ahmad a yau?
Ta ce " Abakar ya gaya min sai dai ban gan shi ba. "
Ya kada kai
" Yana falon Abba sun taram mashi, ni anya na taba ganin Abba yana irin fadan da na ga yana wa yaya Ahmad yau? "
Momi dai kwalla kawai take abinda ya kara tada hankalin yaya Ahmad, idan ka dube shi Allah sai ya baka tausayi. "
A natse take kallon shi jin ya kai aya ta ce
Sarkin tsurku, kai wa ya yi kiranka har ka gani? "
Ya bude ido " Ah ah ba tsurku naje ba Habu direba ya bani key na kai." "
Sai kuma ka tsaya ganin abinda bai shafeka ba?
Bai kara magana ba kujerar shi ya tura baya sai ya mike ya bar wurin.
Wayata ta dau tsuwwa na mika hannu na dauko
Anty Amarya ce
Ta ce " Shuhaina ki zo falon Alh yanzu. " gabana na ji ya buga
Na ce "To" sai na mike
Doguwar hijabi ta na zura
na ce ma Husna ina zuwa ta daga min kai
Na wuce kamar wacce kwai ya fashe mawa a ciki.
Cikin sassanyar murya na yi sallama kusada anty na rabe a kasa Abba ke kan doguwar kujera Haj Babba na zaune gefensa, momi na zaune kan kujera me zaman mutum daya Ahmad da na duba sau daya kan shi kasa yake sai zufa yake fitarwa.
Ko ni da ake mashi hukuncin domina zuciyata ta risuna.
Abba ya ci gaba da magana gargadi yake mashi me zafi da gindaya mashi sharudda a kaina.
Daga bisani ya sallami kowa ya rage daga ni sai Ahmad, nasiha ya koma yana ma shi cikin lafazi me taushi.
Hankalina ya dawo wajen yana cewa
" Ba zaka gane alherin da nake nema maka ba. Shi aure a gida na kwarai ribar shi ba ce, matukar ka rike wannan,
to in sha Allah za ka ga cin nasara a rayuwar ka.
Ni aka ba na kuma karbar maka ba tare da wani tunani ko shakku ba, duk wanda ya samu mace ta kwarai ya samu rabin addini sai ya nemi rabin,
Ina maka kwadayin samun alheri irin wanda na samu na auren matar kwarai irin mahaifiyar ka,
ba kai ba ma duk wanda ya sanni ya san ina girmama al'amarin ta,
bana wasa da duk abinda ya shafe ta, saboda tsatsaon da ta fito gida ne na mutanen kwarai
haka gidan da ka dauko wannan yarinya,
yar'uwarta har Allah ya amshi abun shi ka taba ganin abun ashsha a tare da ita?.
Sai da ya ji Abba ya yi shiru sannan ya ce
Na yi kuskure babba Abba, ban duba irin gatan da kuka yi min ba,
amma wallahi tun ban dawo ba nadama ta shige ni na shiga bakin cikin abinda na yi ina neman gafarar ku Abba,
tuni nake rokon Allah ya yafe min. "
Abba ya shiga shi mana albarka ya kara mana nasiha kafin ya sallame mu.
Ahmad bedroom din momi ya wuce ya dade yana bata hakuri kafin ya fito ya tafi.
Da safe da muka tashi
,da shi muka tashi duk rokon da ya yi mata ganin bata tanka ma shi ba ya fita limamin da ke jan sallah a masallacin cikin gidan shi kuma ke koya wa yaran gidan karatun addini.
Shi ya dauko wa momi
yana fara bata hakuri
ta ce Ita ba ita ya yi ma wa ba matar shi zai nema gafara
Ya ce duk da haka ita ma suna neman afuwar ta ta ce ta yafe.
Tun da na tashi yau ma haka nan nake raina babu dadi,
har Husna ta gaji da bi na da ido ta ce
Wai Anty Shuhaina har yanzu ba ki hakura ba? Ko ba ki gamsu da karbar yancin da su Abba suka yi maki ba?.
Na share hawayen da suka taho min
Na ce " Ba ki fahimce ni ba Husna amma Abba da momi bani da abin ce masu sai Allah ya yi masu sakayya da mafificin alherin sa, ya karbi rayuwar su cikin imani.
Dan tun randa aka daura min aure da Ahmad ba wanda ya nuna min ni ma ya ce me daraja, ba wanda ya dubi rashin adalcin da Ahmad ya yi min,
Mahaifiyata tana jin zafin halin da na shiga amma halinta na kawaici da kauda kai da hakuri yasa bata taba cewa komai ba, waanda ya dace su nema min yancin babannina ba su ce komai ba, sai Abba da momi suka tsaya kai da fata,
Sai dai abinda ke sanyaya min jiki yake sani jin tsoro.
Sai na yi shiru ina share hawaye
ta ce"Ina jin ki".
Na ce " Duk da ba wani uban shekaru gare ni ba na san ba karamin shiga garari bane a ce miji baya san ka sai iyayen shi ne ke san ka ina hange wa kaina wannan matsalar."
na lura itama jikinta ya yi sanyi
ta dan dafani in sha Allah Allah zai so ki kuma biyayya kika yi Allah ba zai wofintar da lamarin ki ba.
Na ce "Na gode Husna Allah ya shige mana gaba".
Ta ce "Amin" sai ta miko min mug wanda ta cika da kunun gyada "To shanye wannan ko fa karyawa ba ki yi ba".
Ta turo min flate din chips da kwai
Na kafa kai ina sha tana kara jan hankalina ta hanyar bani labarai
"Ke ai Anty ko dan kyakykyawar Surar da aka yi maki namiji ya soki ko bai shirya wa yin hakan ba, ballantana ma kina da kyan hali,
kin ganni ni ba me sakewa da mutane ba ce
Mu'amalar ki tasa dole na kasa share ki muke muamala me dadi,
ko momin mu abinda ya ja mata samun matsayi me girma a zuciyar Abban mu kenan".
Na yi saurin kallonta tare da yarda da abinda ta ce a zuciyata, dan shima Abban na ji ya fada da kan shi.
Ta ce "Yes Abban mu tare suka yi karatun jami'a da mama ( Haj Babba)School met din shi ce, har suka gama tare suna soyayya, tana yar masu mulki yana dan talakawa duk da kyawun sakamakon da ya fito da shi, bai samu wani babban aiki ba yana karamin ma'aikaci ita kuma yar masu da shi kuma jinin sarauta, kina dai kallon sai a wuni a kwana ba ki ji in da tayi magana ba, in ba ta kama ba,
Yan'uwan shi tun suna shaawar zuwa gidan shi har suka daina
Mahaifiyar shi kanta ta zo gidan shi sai dai ta nema wa kanta matsuguni, wannan ma ya rage kimar ta a zuciyar shi daga randa mahaifiyar shi ta ce ta sallama zuwa gidan shi hakan yasa ma shi sha'awar kara aure,
amma kuma yana gudun a kara maimaita yar gidan jiya.
Kusa da gidan su akwai wani kamilallen malami ko shi ya kan je daukar karatu wurin shi zamanin da yake jami'a da kuma ya fara aiki yana temaka mashi da Addu'a.
Yana yawan ganin yaran malamin har dai ya roki ya ba shi daya daga ciki.
Ya ce wane ina yaba hankalin ka kuma halayenka halaye ne da ko wane uban kwarai zai so hada zuria da kai, sai dai wani hanzari ba gudu ba ya ta babba a yanzu kwata kwata shekarunta 12 yanzu ta kammala karatun primary din ta.
Abba ya ce Allah ya gafarta malam in dai za'a bani ina so" ya ce" To abinda za'a yi ka turo malam Ahmad din muyi magana a kawo sadaki rana ita yau in sha Allahu zan daura maku aure da Hadiza a kai maka matar ka" godiya ya shiga yi
An daura auren kamar yanda Malam ya ce
Daki ya gyara a gidan su aka saka ta,
lokacin yana aiki a sokoto
Allah ya yi ta me kazar kazar kwata kwata bata da kasala, duk da karancin shekarunta ita take aiwatar da komai
na gidan sai dai abinda ya gagareta sai surukar ta ta yi dan tun tana hana ta har ta gaji ta kyaleta.
Idan ya tafi sokoto daga bauci sai ya yi wata amma ita ko a jikinta harkar gabanta kawai take yi
Allah da ikon sa tana cikin shekara ta biyu ta samu cikin Anty kubra wadda tsakaninta da yaya Ahmad wata ashirin ne da biyu, tana da karamin cikin yaya Ahmad Allah ya karbi ran mahaifin shi.
Sai gidan ya zama daga ita sai mahaifiyar shi sai kanan shi saurayi,
ta yaye Ahmad ba jimawa maman tashi ma ta rasu.
To anan fa ne hankalinta ya tashi ta gudu gidan su ta ce bata kara zama gidan.
Dole ya yanke komawa da ita sokoto yana kaita kuma makaranta ya jefata dan ya lura tana da hazaka tana kuma san karatun a zamanta bauci ta kan tsare kanen shi ka koya min karatu ka ga ni primary kadai na yi, wasa wasa ta samu karatu dan haka ss1 aka saka ta, Yayan ta kuma ya nemi me kula da su.
Dan a lokacin ya samu cigaba har motar kan shi ya mallaka, dawowar ta dangin shi suka dawo da zuwa, dan dangi ne da shi masu tarin yawa, duk wanda ya zo tana makaranta sai dai ta dawo ta iske shi tsakar gida daki za ta kai mutum ta ba shi abinci,
dam ma bata kara haihuwa ba, su yaran mama kyamar yan kauye suke momi ce me zuwa mama bata zuwa kauye".
Da haka ta kare sakandire din ta ta cigaba har ta samu Diploma a fannin girke girke duk dan ta burge cikin mijin ta, idan yan'uwan shi sun zo iya abinda take da shi zata zage tayi masu hidima da shi wanda kuma duk ya kawo kukan shi bata samun kwanciyar hankali sai ta ga ya yi masu, wannan ma ya kara mata matsayi me girma wajen Abba.
A kaduna ya auri Anty Amarya ita ma diyar masu da shi ce digiri ne da ita a lokacin shi ma kuma sannan ya kama kasa da su ake damawa a gwamnatin tarayya
Tsakani na da yaya Ahmad shekaru goma ne cif!
daga ni sai farhan sai auta abakar.
Mama yaranta shida yaya kabir babba sai mata hudu sai autanta sudais,
Anty Amarya yaranta biyar Rufaida ce babba sai Najib sai ummi sai yan biyun ta mata.
Dubana tayi ina fata kin fahimci dalilin ba ki wannan dogon labarin da abinda nake so ki fahimta?
Gyada mata kai na yi
dana duba flate din gabana sai na ga na ci sama da rabi ji na yi na dan samu nutsuwa
Dan haka mikewa nayi in shirya in wuce wurin computer.
Ina zuwa falon momi na samu da Ahmad sha'anin da da uwa fira suke, hoton Amina karama a hannun shi.
Na gaida momi zan wuce ta ce
Idan ba ki makara ba samo ma shi abin kari".
Da to na amsa na wuce kitchen ji na yi yana fadin "Da dai ace cikin da mina ta tafi da shi ta haife shi sai in ce diya ta ce da mina ta haifan min dan tsananin kamar su.
Ko dan ban gani ba na san murmushi momi ta yi wannan ma wata minar taka ce da Shuhaina ta haifa maka.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: CHANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE malumfashi
15
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*Bismillahirrah-mannir-raheem*
Ni dai da na samu na kai kaina dakin da aka sauke mu da kafafuwana da nake jin kamar ba za su dauke ni ba, na fada kan gadon ajiyar zuciya nake fiddawa tare da nadamar shigar da na yi ni kaina nasan ba tayi ba, istigfari na shiga yi. Ina nan kwance Husna ta shigo kamar an biyo ta, na ce "Lafiya".
Ta ce "Kin tafi kin bar ni da fargaba boyewa nayi tayi kar yaya Ahmad ya ganni, dan ban san yanda zai yi da ni ba karshenta ma ya ce ni na koya maki daga ya san ba ki yi. "
Na ce " Allah dai ya kyauta gaba amma ai ba karamin da na sani nayi ba".
Husna ta ce "Kai yau na ga kishi".
Na ce "Wurin wa?.
Kallona tayi mijinki mana".
Na ce "Haba dai kawai ya dai ga shigar bata dace ba".
ta murmusa shi ma din ai ya yi kasuwa a wurin, wasu taron yammatan amaryar da na boye a bayansu na ji suna ta maganarshi ba ki ji yanda suke kuranta shi ba kamar ba sauran maza. "
Wani abu na ji ya tsaya min dan haka ban kara magana ba,
mikewa tayi ta soma cire kayan jikinta ta mayar da na barci, ni kuma nayo alwala nayi shafa'i da wuturi, sako aka kawo mana ledoji biyu cike da kayan kwalama daga Ahmad.
Da muka kwanta na dade barci bai dauke ni ba yammatan amarya sai wajen daya suka shigo, hayaniyar da suke ta kara temakawa soyewar idona.
Da safe shirin wucewa da Amarya kawai ake, na shirya cikin farar super riga da zane da dankwali,
Husna da ta gama shiryawa tana murza daurin dankwali ta dube ni "Yau antyna ba matsewa?
Na kama baki "Allah ya tsaran haihuwa daya horon mahaifa".
Ahmad ya kira ni mu fito ana jiranmu, a natse muka fito a wajen gidan inda motoci suke tsaye suna jiran masu tafiya, hangosu muka yi Abdullahi yana kan bonet din motar Ahmad shi kuma yana tsaye da wani abokinsu yawancin abokan nasu duk suna cikin motocinsu, Abdullahi ne ya fara magana kafin ma mu gaishesu " Ran amaryarmu ya dade ".
A raina na ce "Kai kam dan dai ba mutumin da zan ba amsa bane da sai in ce duk zumudin angoncin ne ya ruda ka ko kuma dan ka san tsiyar da ka tsula shi yasa ba ka cewa matarka amarya ba,
Sai ni za ka turo wa amarci.
dan murmushi nayi muka gaishesu.
Husna ta koma dauko trolley din ta da ta manta.
Ahmad ya ce Airport za ka kai min sure. Dariyar shegantaka
Abokin ya yi "Ba za ta iya zaman mota ba?
amsar da Ahmad ya ba shi ta sani jin faduwar gaba
"Ai nima yau amarcin nan zan yi idan na bari mota ta gajiyar da ita ai ka ga ba kanta".
Dariya suka yi shi da Abdullahi shi kuma ya yi kamar ba shi ya fadi maganar ba, ni dai na sunkuyar da kaina.
Husna ta dawo abokin ya shiga ya tada motar, Ahmad ya leka inda yake " Kai dan iska nasan irin tukinka to ka ja min mata a hankali".
Ya ce "Allah sarki dadin abun ma matar nan nima ina da ita da yau haushi ya kashe ni".
Abokin nasu shi ya kaimu airport sai da ya ga tashin jirgin kafin ya juya, su Ahmad sai da suka ga tafiyar kowa kafin suka biyo jirgi.
A falon momi muka baje su farhan na cin kayan bikin da aka lodo mana,
Ahmad bai leko gidan ba sai washegari da yamma, suna gaisawa da momi ni kuma ina kitchen ina girki su Husna da Farhan sun fita shan Ice cream, ta kira sunana da na amsa ta ce in kawo wa pepper chicken din da na yi, ina shirya mashi a babban tire ina tunanin kaina ba dankwali calabar ce kaina Husna tayi min da rana ta kwanta kan kafadata, riga da siket ne jikina na atamfa dinkin cif jikina, na dai yi karfin halin sunkutar tiren na jawo ina gogewa dukawar da nayi gabanshi ashe rigata ta rabu da jikina tayi kasa ga shi bansa komai a kasa ba ashe na kunnan tashar shi, sai dai na ji maganarshi cikin kaina,
"Momi yaushe za ki bani yar taki ne?
Dan murmushi ta yi "Harka shirya ne"
Ya ce "Ai tun ban dawo ba momi an gyara gidan dama kuma Abdullahi na sawa a gyara ".
Ta ce " Ba damuwa amma ya ta ba za ta koma wannan gidan naka na asibiti ba."
Saurin dubanta ya yi ni kuma na gama jere ma shi na koma kitchen ina saurarensu, da sanyin murya ya ce "Saboda me momi?
Sai da ta dan jima kamar ba za tayi magana ba sai ta ce, " Saboda dalilai da dama ina sane da dalilin kai shuhaina wannan gidan, ko ba dan bata kai mace ba a wurinka?.
Idan ka gama tsararren gidan naka sai ka auro masoyiyarka wayayya kyankyasar inji?.
Ba Ahmad ba ko ni na sha mamakin yadda aka yi tasan haka, ya ce" Momi yin maganar nan yana nufin har yanzun ba ki yafe min ba. " ta ce "Ko daya so nake dai ta tare a sabon gidan da kake yi wanda na ga har yan'uwanka suna tayaka san shi suna ganin ya fi karfin Shuhaina ".
Namma mamaki na kara sha dan na gano abinda take nufi, dan kafin Ahmad ya dawo ina zaune yayan gidan mata masu aure suka zo wuni suna ta maganar ginin na shi, Sumayya yar wajen Haj Babba ta ce " Mun je ni da Alh mun gano ginin yaya Ahmad, wow gidan ya hadu".
Rufaida ta amshe "Eh Wallahi kamar ace ba wannan local din zai sa a ciki ba, ya samu diyar wata don ita ke dai dai da wannan gida".
Suka sa dariya.
ban san momi ta ji ba.
ya ce "Dama na bar aikin hannun wani abokina a nayi a hankali, yanzu kudina da muka hada hannu da Dr kasim muna turo magunguna sun fito mun samu alheri yanda ba ki tunani. " ta ce Allah ya sanya albarka ya ce " Amin" ta ce "Kai na ga fa Alert na makudan kudade na meye?
Ahmad ya ce " Irin kudaden ne momi ki sa albarka. " ta ce Allah ya yi Albarka".
ya ce "komai na gidan ya kusa kammala har ma na yi order kayan furniture's din da za'a sa".
Ta ce "Allah ya taimaka"
Ban ji motsin yaran nan ba ina suka shiga?
Ta ce " kasan sarakan shan zaki ne sun fita shan ice cream". ya ce " Ita yar taki bata sha?.
da gatse ta ce "Bata da kudi kuma kasan ba za su bata kyauta ba. "
ya ce "Kai momi tana tare da ke ne bata da kudi?
ta ce kudina daban naka daban ko tunda ka dawo ka bata nairarka?
ya ce "Ayi hakuri momi, na tanbayi Husna abinda za'a yi mata kan ta tafi ta ce min canjin mota take so gobe za'a zo a tafi da tata sai a kawo wadda take son,.
Nan ma momi addua tayi, suna ta firarsu ni dai da na samu na kammala daki na shige, ruwa na watsa, ina zaune kan morrow ina murza mai na ji turo kofa tunanina Husna ce dan haka ban damu da in waiwaya ba,
ta madubi na ganshi yana kare min kallo kamar ranar ya fara ganina rasa yanda
zan yi na yi dan daga ni sai guntun tawul takowa ya yi ya tsaya bayyana, ban aune ba sai dai na ji ya balle tawul din ratsa hannuwansa ya yi jikina abubuwan da yake yi ne yasa jikina daukar rawa, ya ja ni zuwa gado na rasa yanda zan yi da kyar na iya furta "Ka da Husna ta shigo".
sai ma na lura bai san ina yi ba, da kyar nayi kokarin kwace kaina na dauki tawul din na daura na bar ma shi gadon, na koma neman rigar da zan
sa.Na bar shi cikin wani yanayi da ni kaina ban ji dadin barinshi a hakan ba, to amma a ina za'a yi abinda yake nufin?
cikin lumshewar ido ya ce "Ki fadi abinda zan saya maki" shiru na ma shi kara maimaita min ya yi ya ce " Idan kuma ba ki yi magana ba tabbas zan tafi da ke sai kin kwana wajena".
Sauri nayi na furta laptop
tashi ya yi ya bar dakin bayan ya ajiye min bandir na yan dari biyar, na dade zaune ina maida numfashi sannan na shige bathroom tsarki na sake da alwala na fito na tada sallah, da na idar sai na fito falo Husna ta ce " Mun dawo ba motsinki ga ice cream dinki yana fridge na ce "Na gode"
Baba mai gadi ya yi sallama daga kofa ya ce" Haj Shuhaina na da bako a waje" Farhan ya ce
"Waye?
Ya ce " Na tanbaye shi ya ce Babangida ke da aiken" tashi na yi na fita na samu mutumin mun gaisa ya miko min laptop da kwalin waya ya ce in ji Dr Ahmad.
Ina shiga na mika ma farhan laptop din murna yake iya karfin shi "Wa ya bani?
ya tanbaya bayan ya tsagaita da murnar na ce "Yayanka"
ya ce "Amma da na ce mishi ya ban kudi zan saya wa abokina laptop fada ya yi ta yi min"
Momi tayi dariyarsu ta manya "Ba ka gane ba Farhan ita ta fada mashi sai ya saya maka"
Kallona ya yi " Ko dai ya take Anty na gode, Allah ya bar ki da yayanmu ke kadai, ya rufe idanshi kar ya hango wata"
dariya Husna ke ma shi, shi kam ko a jikinshi sai ma barin falon da ya yi yana kiran abokin na shi a waya.
Husna ta bude wayar sanfurin IPhone ce.
Kwana biyar tsakani muna zaune dariya muke na labarin da Farhan ke bamu wai kakar abokin shi ta basu labari wai a da idan an yi mutuwa a kauyensu tsofaffin da ke kwana wurin gawa kwana suke suna fadin ta tafi kenan ta tafi kenan sai wasu su amsa da mulumundu, mulumundu
a haka Ahmad ya shigo ya same mu, " Kai lafiya duk kun cika waje da surutu". tsit mukayi "Ina momi?
Ya tanbaya "Tana dakinta yaya" farhan ne ya amsa ma shi ta wayarshi ya sanar da ita zuwanshi ta fito ta zauna cikin shiri take da alama fita za ta yi ta ce "Sai ina haka ko zancan za ka?
Sai da na ji faduwar gaba jin maganar dan gaskiya ya hade cikin wani rantsatstsen farin boyel sai sheki yake hula da takalmin da ya sa sun shiga da juna
kamshinshi na ko yaushe na tare da shi, ya ce "Haba momi ba'a kada gizo ba ai ba'a cewa koki taso".
Murmushinta me kyau tayi
"Daga asibiti nake ina da patient sai na dubata, yanzu zamu tafi da yar ki ne a bude account din daga nan mu wuce ta ga tsarin gidan".
girgiza kai tayi "Na hada ta da farhan an je an bude a baka account no din?
Daga ni dauriya me yawa ya yi wajen cewa "E to momi ganin gidan fa?.
ta ce "Su shirya sai ku je" tana fadin haka Husna tayi tsalam ta mike ta shige ciki, Farhan ya ce "Yaya na gode da laptop A... kafin ya gama jero kalmomin godiyar da zai yi ya katse shi da cewa "Waye ya baka laptop" cikin dan tsoro ya ce Anty Shuhaina" ya ce "Ai bata gaya min kai zata ba ba da ban saya ba dan nasan wata shiriritar za ka yi da ita daga ta ka na nan". Momi ta ce min "Tashi kema ki shirya ba ki ga yar'uwarki ta tafi ba"
Mikewa ya yi
"Su yi zamansu"
Momi tayi dariya ta tashi ta bar falon, Husna ta fito farhan na son yi mata dariya yana tsoron masifar da za ta yi mashi, sai ya boye fuskarshi yana yi kasa kasa, ni kaina ta bani dariya ganin yanda ta sha kwalliya, Abakar dai babu ruwanshi sam yaron ba shi da hayaniya in dai ya samu ball shi kenan.
Haka suka yi ta drama da momi duk yanda yaso kebewa da ni sai ta san yanda tayi ta toshe,
misali sau daya ya iske ni wurin computer sai muka dawo tare to tun daga nan bata kara barina na tafi ni daya ba sai ta hada ni da Husna kome take sai ta bari mun tafi, shi kuma sai
sai ya tare gidan ko da yaushe in dai ba shi wurin aiki to yana gidan, ya kuma takura wa yayanta suna wasan ludo ya karba ya fasa idan yana zaune babu me kara tari ko kallo baya barinsu sai dai yasa masu waazi.
Muna waya da Amarya khausar ta ce "Ba ki da kirki" na ce "amarci kuke a zo karshe a takura maku, shi yasa na daga kafa ko da yake na mance amaryar ta zama kaya".
"Haba in ji wa? babu abinda za'a fasa ki zo ki yi course".
Na ce Ah ah ni ko na gani ba ruwana".
Ta ce "Sai ki tsaya kallon ruwa kwado ya rike kafar".
Mun shirya zuwa mata wuni ni da Husna, na gama shirina zan nade jikina da laffaya, Husna ta cire kanta jikin window ta dube ni " Anty Shuhaina ga mutuminki can jikin motarshi, ya dai zame wa momi dan zane na lura itama ya isheta karfin hali ne irin nata tayi mashi abinda yake so ko ta huta." Na ce "Me kenan kike nufi?. ta ce "Ina nufin ta sallame shi ta hanyar ba shi matarshi". uhum" kawai na ce
ta fara kwalliya tana cewa " Dan Allah cire laffayar nan aunty Shuhaina mu zolayi yaya Ahmad ".
Na ce "Me zan yi"
Ki sa cikin gyaluluwana me shara shara mu fita a haka".
Ido na zaro "Kin ga kar ki ja min fitina ranar nan har fitsari na kusa saki saboda razana ki kuma jaza min".
Husna bata bar ni ba sai da ta hilace ni tsaf na cire laffayar riga da siket ne jikina na material rigar karama ce ta kamani siket din ma ya min dam daga mazaunai dama ga shi da abun, dankunne da sarka fashion ne, kaina ya sha gyara, dan momi bata taba gajiya ba da tura ni gyaran jiki da kai dauri me kyau nayi.
Husna shadda tasa dinkin yan Mali ta kafe daurin dankwalinta ga gyalenta ta jefa shi a wuya ga kamshi na musamman muna yi
Kwas kwas sautin da takalmanmu ke fiddawa kenan wurin Husna na koyi saka takalmi me tsini.
Muka nufi wurin motar Husna waya yake yana kan motarshi ya juyo ya bi mu da kallo mun shiga cikin motar har tayi mata key sai dai muka ganshi gabanmu, daga mata hannu kawai ya yi ta kashe motar ya zagayo inda nake ya bude motar ya janyo ni ba shiri yana rike da hannuna ya yi sashen mazan gidan da ni.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: CHANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE MALUMFASHI
16
. ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*BISMILLAHIRRAH-MANNIR-RAHEEM*
Da hannu ɗaya ya bude ɗakin, wanda Farhan ya taɓa gaya min na shi ne tun yana saurayi. Ga mamakina kan luntsumemiyar katifar da ke yashe kan carpet ya wurga ni, ya naɗe hannuwanshi akan kirjinshi ya kafeni da ido, "Ke ba ki jin magana ko? taurin kunne ne da ke ko? Ya yi kwafa "Daga yau idan na ce bana son abu ba za ki yi marmarin ƙara aikata shi ba. "
Tuni jikina ya soma rawa har ban san sanda na soma fadar gaskiyar lamarinba. "Ka yi hakuri wallahi ga laffayata nan a jaka muna tafiya zan sa". Ok dama ni kenan ake so in ga kwalliyar, dama ai laifina ne da na sa maki ido shi yasa Momi taji daɗin riƙe min ke, da ta ga kina amai da zubar da yawu ai da ta bani ke ba gidan asibiti ba ko a ɗakin patient ɗin nake kwana". daga haka sai na ga ya fara cire kayan jikinshi, ya rage daga shi sai gajeren wando kallo ɗaya nayi ma katafaren kirjinshi na rufe idona ina salati da tunanin yanda zan yi in tsere, cikin nutsuwarshi ya shiga cire min kaya ina mashi kuka sai da ya min yanda ya ma kanshi abinda ya ga dama shi ya shiga yi dani, ba tare da na iya motsi ba ko ƙwace kaina, dogon lokaci ya ɗauka sai da ya gamsar da kan shi sannan ya tashi zaune, dafe kanshi ya yi da hannuwanshi biyu, ni dai ina kwance kamar matatta ya gajiyar da ni hannunshi yasa ya jawo ni na faɗa kirjinshi, magana yake gaya min kamar yana raɗa, "Na riga nayi wa kaina alkawarin zan ta yin hakuri ba zan taɓa kusantarki ba sai ranar da Momi ta hakura ta bani ke, sai dai in yi abinda zan rage wa kaina zafi na kwaɗayin ki da ke azalzalata".
leka fuskata ya yi, "Me Momi ke ba ki ne komai naki ya ƙaru? kin kara girma da kyau, amma kina gani Momi tayi min adalci in tafi sama da shekara ba mata in dawo ta yi min horo irin wannan?. A raina na ce ka ji wata magana ko kafin ka tafin mene ne?
ka san ma ka ajiye wata mace a gida.
Kara sunne kaina nayi a kirjinshi dan ba zan iya hada ido da shi ba.
Wani sha'anin ya shiga yi sai da ya gaji dan kanshi ya kyaleni ya fara maida min kayana, kuka na fara ma shi yana tanbayata mene ne?
da kyar na ce "Ni yanzu ya zan yi in koma wurin momi ta ganni"
dan murmushi ya yi " Fuska kawai za ki yi, ko in rakaki?
Saurin goge idona nayi na mike, ban ko kara komawa ta kanshi ba nayi waje da na kasa shiga sashen momi sasan Anty Amarya na wuce, na sameta zaune ita da yan biyunta.
Na dade sashen har farhan ya shigo neman Najib zai ba shi hand out, ya ce "Anty na nan kika sauka?
na daga mashi kai.
Ni ce ban tafi ba har sai da Husna ta zo ta ce Momi na kirana sai da muka je na ga momi ma bata sashen.
Washegari muka tafi sai dai Husna sauke ni kawai tayi ta wuce gidan yayarsu Aunty luba a maitama take aure, ta aiko tana nemanta.
Khausar din ce ta bude min da na yi knocking ta ce " Ai wallahi nayi fushi" da hannu na rika bata hakuri na ce "Kaina bisa wuyana Amarya "
tana murmushi ta bani hanya, na shige mamakin shigarta ya ishe ni kamar bame cikin wata bakwai ba duk da ya bi jikinta, wani damammen siket ne tasa sai bingilalliyar rigar da ta ka mata, kan nan ya sha gyara sai sheki yake. Na zauna muna gaisawa Abdullahi ya fito cikin shirin fita, gabanshi ta sha cikin wata kisinanniyar murya ta ce " Haba dear na ya zan shirya maka breakfast ka ce za ka tafi?
yana saka link din wuyan rigarshi yana fadin "laifin wa? wa ya sani makara?
ta karbi saka mashi link din, ya zauna cin abincin ya waiwayo inda nake " Kanwata ke ce yau a gidan namu ai sam ban ganki ba".
Na ce "Kasan an ce hankali ke gani". a raina kuma na ce " Ina fa za ka ganni ana maka wannan kwarkwasar?
da hanzari ya kammala ya mike, "Ai kanwata kina nan har in dawo ko?
na ce "Anya ban dai sani ba" ya ce " Haba ko shi Ahmad din ya zo ki ce na ce ya bar ki sai na dawo Lagos za ni."
Na ce "Allah ya kiyaye hanya" ya fadi Amin suka fita tare da khausar, da ta dawo ta canza kayan jikinta cikin doguwar riga me fadi, nayi yar dariya "Ban da dama rigima shigar da ta dace da ke a yanzu kenan".
kallona tayi "In ji wa?
Mazan nan da kike gani sai da haka dan ga matan nan birjik a titi jira suke ki koro mijinki ya iskesu, meye ki koroshi da zarar bai samu yanda yake so ba a wurinki kina mashi abinda zai dauke ma shi hankali daga kansu. "
tana gama fadar haka ta ce "Cire hijab din nan mu shiga kitchen. "
na ce "To"
Sai da muka fara kintsa wurin kafin muka sarrafa abinci daban daban muna fira, da muka gama ta jani bed room dinta. Ahmad ya yi min waya in jira shi zai zo ya dauke ni a raina na ce ko ina momi da ya samu wannan damar?
ina gidan har magrib har wanka na yi,
horn din mota mukaji ta ce " Ga mijinki nan"
shiru bai shigo ba ashe Abdullahi ne daga falo yake cewa yau ba'a tarata ta mike tana barin dakin sorry please my dear".
Sai da na basu lokaci kafin na fito dan in gaishe shi yana kan kujera ita kuma tana kan cinyarshi ganina sai ya ce dagani dama kanwata na ciki?. kinsa naji kunya, Ahmad bai shigo ba?.
Kai na daga mashi ina ma shi ya hanya, ba a kara minti goma ba wayar Ahmad ta shigo ya ce yana jirana a waje.
na shaida wa khausar ita kuma ta fada wa Abdullahi ya goge bakinshi da tissue sai ya mike ya rigamu fita, mun jero da Khausar ta ce "Yau gidan nawa ma ba za'a shigo ba? ya ce "Yi hakuri amarya momi na jiran yarta kar in shigo in dade. "
ya bude motar na shiga, Khausar ta ce "Ki yi min godiya wurin momi kafin in shigo".
na ce "Za ta ji"
Abdullahi ya ajiye min kudi kan kafa nayi godiya ya ja motar muka bar wurin, hannu daya ya rike sitiyari dayan yana cikin rigata, ni dai sai innalillahi nake fadi a raina mutumin da ke tuki me ya hada shi da wannan akin?
Allah dai ya rufa mana asiri yasa muka sauka lafiya bayan ya tsaya wani Mr bigs ya min sayayya, da ya tsaya da motar na ce ba za ka shigo ba?
Kallona ya yi har sai da na sunkuyar da kaina, saboda irin kallon da yake min "Ke kinga ya dace in shiga a irin wannan yanayin da nake ciki?
Ni kaina na gasgatashi, wani shaanin ya shiga kafin ya hakura ya sallame ni ya wuce.
Ina ta tunanin yanda zan shiga ciki, sam barka momi ita ke da Abba bata ma sashen, ajiye masu ledojin nayi na shige ciki dan yin shafa'i da wuturi.
Mun kwanta ya kira wayata sai da ya yi ta magiyar ko ba zan ce komai ba kada in kashe in saurareshi, sai da na ce ina jin barci ya kyaleni, na kashe wayar gaba daya na gyara kwanciya, "Har an gama soyewa?
Husna ta ce min tana murmushin shegantaka, ba tare da na dubeta ba na ce "Waye yake soyayyar?
murmushin ta kara "Miji da mata man, uhum dama abinda kesa maza suke more mana rauninmu, kinga yanzu har kin manta abinda yaya Ahmad ya yi maki kin yafe ma shi.
ta yi kwafa "Maza masu gari suna sha'aninsu".
tunanin da na shiga ne yasa ban ce mata komai ba sai na lumshe idanuwana.
Ranar wata juma'a da misalin karfe hudu da minti biyar na rana ni da Husna ne a kitchen, Momi ta sa ni hada mata salad, Husna zaune take kan wata kujera ina aikin muna fira, dukkanmu cikin kwalliya muke ta wani material da Momi ta bamu a safiyar ta ce muyi kwalliyar juma'a dinkin doguwar riga ne kowaccenmu ya zauna mata das a jiki, na Husna fari ne nawa pink kaina kitso ne guda biyu Husna ta kama min jelar ta sauka kan wuyana, sai na daura dankwalin.
Daga falo momi take kiran sunan husna ta amsa gami da mikewa, bata jima ba ta dawo
" Momi ta ce "Ki hada salad din hada ya Ahmad, ashe shi ne ya shigo ni sam ban ma dauki murya ba".
"Uhm" kawai na ce mata dan ni tun shigowar shi na gane muryarshi.
na ce " Ke wai tsakaninki da Allah ba za ki rika girki ba? ko har idan kinyi auren ba za ki rika girkin ba?
yamutsa fuska tayi "Idan ya rage three month aurena kawai sai in dauko kwararrun masu girke girke su koya min, idan momi ta ki koya min dan yanzu ma nasan fushi tayi ta daina kirana idan kuna yi, ko da yake gani ma da kwararrar ketchener a hannu kawai ma na huta da dauko kowa tunda ina da ke".
Shiru dukkanmu muka yi muna sauraron firar momi da danta. Shi ne ya ce " Momi gida fa ya kammala".
ta ce "Ma sha Allah, Allah ya sanya albarka yasa yawan rai aka yi mawa. "
Sai tayi shiru ya ce "To momi Shuhaina idan zakuje ganin gidan sai ku tafi da kayanta ko?
ta ce wane kayan?
ya ce "Na sawar ta mana".
"Kayan da har goyon ciki tayi da su tayi goyo ai sun tsufa" ya ce " Sai mu fita ko yanzu, idan ta shirya ta fito muje"
ta ce Yawwa ana gama dinkasu sai ku yi ta tafiya".
ta kara da cewa
"Ba ki kammala bane Shuhaina?
na ce na gama na dauko na momi
Husna ta biyoni da na Ahmad, zan shige ciki Momi ta ce " In ya kammala zaku fita, kema Husna dauko naki lullubin." dukkanmu muka ce To
Sai da muka jira ya gama ya fita Husna ta ce wa momi "So kike dai ya Ahmad ya hada sabon lefe. "
bata yi magana ba ta soma amsa waya.
Cikin abaya na fito ya bude kofar gaba na shige, Husna ta shiga baya karatun Al-kur'ani kira'ar Abba zaria ke kwarara cikin motar, yana burgeni saboda san sauraron karatun Al-kur'aninshi, dan kallona ya yi " Ginbiya yaushe za ki fara gaisheni? gyara zama nayi ban yi magana ba, "To ai ni sai in kwashi gaisuwar kin wuni lafiya"
a yangace na motsa labbana "lafiya"
bai hakura ba ya kuma cewa "Ko ke yanzu ba ki ga kin fi kyau ba da kika suturta jikinki? duban kaina nayi ban tanka mashi ba, haka muka kasance yana ja na da zance ina basarwa, har muka tsaya wani tankamemen wuri, gyara parking ya yi ya ce "Ku shiga Husna ta tayaki zabe, me wurin abokina ne duk abinda kuka dauka zan ji a wurinshi". daga mashi kai nayi, muna shiga wanda ke zaune wurin biyan kudin na farkon shiga ya taso da Sauri ya taremu da faraarsa muka gaisa " Ran amarya ya dade yanzu oga ya sanar dani za ku shigo". dubansa nayi ina tunanin inda ya sanni sai na gane wanda Ahmad ya taba aike ne ya kawo min waya.
Mun shiga zagayawa, ganin na ki daukar abin kirki Husna ta ce "Naki wasa ne ko in tayaki zabe ne?
na ce zan kuwa so haka dan ke din gwanar dressing ce".
ta soma jidar lesussuka na karshen da shaddodi atanfofi, na rike hannunta "Wai ke malama ba ki tunanin kudin?
Wani sakaran murmushi ta saki "Aunty kenan kina tausayin yaya Ahmad ne?
Na marairice "Ba ki ji ranar nan yana gayawa momi kudaden da gidan nan ya lashe, kuma ga shi an sakashi hada kaya, in dan tani wallahi da an barsu" humm kawaita ce "Aunty Shuhaina idan banza ta fadi kawai ki bi ta da yakushi ki tsaya kina tausaya wa namiji".
ta koma kan takalmi da jaka nan kam da gaske na riketa " Indai ba fahari abin zai zama ba duk waanda ya kawo min a kuma kara wasu?
ke to ba ki dauki komai ba?
Noke kafadarta tayi " No bani da matsala na ma kusa barin kasar karshenta ma in rigaki wucewa".
Na ce " Haba dai ki yi hakuri in tafi in ba ki sasan fadi zai min".
Muka koma wurin jakunkuna muka yi ta ruwan ido muka rasa na dauka. Cikin masu kula da wurin wani ya ce "Haj ko za ku duba wasu sabbin shigowa satin da ya wuce aka shigo dasu sai dai tsada"
gabadaya muka kai idanunmu wajen tabbas sun hade,
Mun fito ma'aikatan suka biyomu da kayan, wani wurin da ake siyar da kayan ball na shiga Husna ta biyoni tana tanbayata "Me kuma za ki yi a wurin saida kayan ball?
Abakar zan saya mawa? Ina dubawa nake bata amsa, Jc jc na dibar mashi sai kwallon na hada hada takalmin training, na bude jaka zan biya Husna ta ce "Ki bari in karbo kudi a wurin ya Ahmad".
Na ce "Ah ah zan biya ai ba shi ya sani ba". ta ce "Haka ne sarkin tausayin miji."
Muka fito muka shiga motar, dai dai wani wuri da aka rubuta Shawarma spot ya tsaya "Ko za ku ci shawarma?
ya tanbayemu Husna ta karba da sauri"E"
ya bata kudi ta fita zuwa amsowa
A raina na ce kila dan ba kasan kiran ruwan da muka yi maka bane sai ka ji bill din
Husna ta dawo muka wuce wurin dinki.
Sati daya bayan nan ya kawo dinkunan momi tana dagawa tana cewa lallai telolin nan naka ba kadan suka kware ba ga shi cikin sati har sun kammala, anjima za muje ganin gidan sati me zuwa sai ka zo ka dauki matarka". godiya ya yi mata ya tashi ya tafi ta umarcemu mu shirya, duka mutanen gidan muka tafi hada Haj babba da Aunty amarya, gidan yana cikin unguwar gwarumfa gidan farin gini ne da aka yi ma shi tsarin bature ya yi matukar tsaruwa a tsakiyar gidan aka yi ainahin ginin an yi shuke shuke masu ban sha'awa, har Gymnasium akwai, mun shiga ciki inda yaji kayan alatu komai an jereshi a tsare inda ya dace, da muka shiga bangaren da aka ce nawa ne dan wani kayataccen falo ne ya raba sashina da nashi ai kusan rudewa nayi sai na shiga tasbihi a raina a zuciyata ina fadin anya kana cikin wannan gidan za ka rika tunawa da mutuwa?
mun fita harabar gidan babu abinda ya fi burgeni irin daga kofar sashena ta baya aka dasa kujeru da tukwanen fulawa. Muryar Rufaida na tsinkaya cikin kunkuni da yake sun zo ita da sauran yan gidan na ma'aura. "Shi ya Ahmad nufinshi duk wannan gidan ginin mace daya zai mashi, dama matar tashi ma yar babban gida ce shi kenan am......
waiwayowar Ahmad wanda bai dade ba da zuwa ba suna tsaye shi da wani abokinshi suna magana kusa da inda muke, cikin daurewar murya ya ce "Ke me kike cewa?
Saurin ja da baya tayi tayi tsuru kamar ruwa ya ci ta.
Nayi kamar zan sa wannan cin fuska da ta yi min a raina sai na ga dan me to? Domin ni kam ina ganin kina mace kuma kina san cin mutuncin mace yar'uwarki to ki ta kanki dan ba ki yi komai ba, tunda ba ki tara sanin ke kuma abinda zai sameki ba. Kowa ya yi addu'ar fatan alheri a kayi ciye ciye da shaye shaye dab da za a tashi khausar ta zo ta ce Baki tayi daga meduguri shi ya hanata zuwa tun dazu.
A daren ranar ina zaune kan gado na riga na gama shirin kwanciya, Husna ta shiga bathroom tana wanka Momi ta shigo na kara shiga nutsuwata cup ta miko min "Karbi shanye wannan na amsa na shanye na mika mata wata yar karamar buta ta miko min "Ki rinka kama ruwa da ita idan ya kare sai ki zuba wani to na ce mata,. Tun kuma daga ranar kullun da abinda za ta bani wanda na tabbatar ko ita ta haifeni iya gatan da za ta min kenan, hakan yasa na kara ganin girmanta da kimarta. Akwai matar da ke zuwa kullun tana min gyaran jiki, ranar alhamis ana gobe zan tafi gidan Ahmad muka ziyarci sallon Husna tayi tayi dani a gyara min kai kawai
ni kuma na kafe na ce kitso nake so su min, an kuwa yarfa min shi abinka da gwanaye dan da nan fuskata tayi fayau, aka gyara wa Husna gashi.
Mun koma muka iske Wasu tsadaddun lesuka a kan gadonmu, Husna ce ta tafi tanbayo momi na waye ta ce Baba karami ya kawo su na Shuhaina ne"
Husna ta dawo tana ce min "To kin gani?
ke kina mitar kayan da na zabo sunyi yawa, to ga shi nan ya karo maki wasu".
ni dai na jinjina kai.
Mun zo kwanciya na saka lalle lallabe a kafata da yan yatsun hannuna, Husna tana mitar "Kin ki yadda a yi miki kunshin zamani kin wani tsaya yin wannan ordinary kunshin " na ce "Ni ban ga wani abin daukar dumi ba sai ka ce wata amaryar gaske har fa haihuwa nayi". wani malalacin murmushi ta saki "To haihuwa idan ba fadi kika yi ba wa ya san kin yita? da ba ki yi amarci ba dole yanzu kike amarya me kika karas da in ba ciwon zuciya ba?.
Ban magana ba na ci gaba da kunshina.
Da safe da na wanke ba karamin kyau ya yi ba hatta Husnar sai da ta yaba. tunani na shiga yi zuciyata na kara jaddada min kudirina abinda nake ganin ya dace in sulale in tafiyata malumfashi su shafa su ji bani, wani sashen na zugani Ahmad bai taba zuwa gidanmu ba tunda aka ba shi aurena bai je ya gaida uwata ba da Babannina ba ire iren tsegunguman da mutanan gidanmu suka yi tayi a zaman gidan da nayi dan haka na duro daga gadon na fada bathroom da sauri nayi wanka na fito na shirya cikin atamfa riga da zane na daura after dress takalmi flat nayi amfani da shi na dauki jakar da na sawa kaya kala biyu sannu kan hankali na tura kofar a harabar gidan ma ba kowa farin ciki na ji ya baibayeni hango get babu megadi.
By
Maryam Litee
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: CHANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE
17
*✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*BISMILLAHIRRAH-MANNIR-RAHEEM*
Na kusan ficewa sai naji motsi a bayana, wanda yasa ni jin faɗuwar gaba, barka da safiya Haj.
Muryar Baba me gadi ta ratsa dodon kunnen a, cikin karfin hali na waiwaya muka haɗa ido, " Barka dai Baba" na ƙara sauri dan in samu in fice, "lfy Haj da sassafe kuma a ƙafa? Na haɗiyi yawu, "Makaranta zani Baba ana neman mu ne". Na ciro Kuɗi na miƙa mashi ban kuma tsaya sauraron addu'o'in da yake kwarara min ba nayi waje, a ƙafa na fice unguwar kafin na samu abin hawa inda zan shiga motar Malumfashi na nemi ya kaini babu ta can saidai zuwa katsina ita na hau, gabana na ta faɗuwa a yayin da suke haɗa kudaden fasinja, bayan wani ɗan jira aka gama haɗa kuɗin mota, direba ya ɗau hanya mota tana ta shara gudu a titi ina kallon bishiyoyi, kukan da wayata ta ɗauka yasa ni saurin buɗe jakata na zarota Husna ce ban ɗaga ba illa sakon text na tura mata na kashe wayar gaba daya.
Cikin yardar Allah mun isa lafiya, a kwanar ABU na sauka, mashin na haye zuwa gida ina sauka na shige ciki, ina yin sallama mutanen gidan suka yo kaina da oyoyo har ɗakin mu, ni dai ido kawai nake wurgawa inga ta inda zan ga Innarmu ina cikin gaishe su ta fito daga uwar dakanta ashe mura take fama da ita, sai da ta ga kowa ya kama gabanshi ta tsareni da idanuwanta ina kokarin gaisheta bata kula ba, "lafiya wannan tafiya ta ki?
Dan murmushi na kakaro "lafiya lau"
tayi ta fama dani ta ji wani abu game da tafiyar na kafe na ce lafiya lau.
ta gaji ta ce "Shi kenan in ma dai wani abun ne ubannin naki suna nan, ko kowa ya kyaleki Baban Asiya ba zai dauki shegantaka ba. "( Baba ya'u)
Na ce "Bare ma innarmu ba komai"
muna nan zaune Aminu dan wurin Baba sani ya aiko Innarmu ta san mashi miya shi Innarsu miyar karkashi tayi baya shanta".
ta ce " Ka ce mashi kaza tayi kwanci kan murhun nawa".
Yaron ya juya, wani tausayi na ji ya kamani ina can cikin daula uwata na nan sai ta zauna bata dora abinci ba?
Na ce "Innarmu ina Yusuf?
Ta ce "Yana makaranta".
Na ce " Yahya fa? ya daina bude shagon ne?
Ta ce " Ya kwana biyu baya jin dadi, a rufe shagon yake"
Na marairaice "kuma sai ku zauna ba ku ci abinci ba ina Salma?
ta ce tana "Makaranta"
Mikewa nayi na kira Aminu
Kudade masu kauri na ciro na mika mashi lissafin kayan abinci na mashi ya tafi.
Na zauna ina kallon dakinmu fes yake ta malala hadadden carpet dinta da na saya mata a saudiya da labulayya.
Bayan Aminu ya dawo ya jide kayan abincin buhu daya na shinkafa na ce ya je da shi ya rabawa mutanen gidan, da tinkiya da nasa aka sawo aka gyara na ce ya raba masu kowace tayi miya.
Jallof din couse couse na dora wanda na sawa hanta da kayan lanbu dan shi ne zai dahu cikin sauri na gama na adana shi a warmers na kai daki, a kofar dakinmu nayi girkin sai wani kifi irin kifin ruwan nan ne da direba ya tsaya a hanya na saya, na wanke shi sai na tsane shi zuwa yamma in dafa.
Innarmu ta ce "Da kin cire wannan kayan kin samu wasu" na ce "To"
"Ni dai hankalina ya ki kwanciya da wannan tafiya taki, koma me ya faru da kin gaya min ya zan yi hakuri zan yi in ta fadin Alhamdulillahi alaa kullu halin, dama mu masu yaya mata ai bamu rufe kofa sai dai mu saya idan aka koro maka ka ce shigo".
Da naga hankalinta ya daga kwarai sai na gaya mata, fada tayi min sosai ta ce duk halaccin da uwarshi ta nuna maki bata cancanci wannan sakamakon daga gare ki ba.
Komawa wuri daya nayi ina mata kuka,
sai da ta gaji da fadan ta ce "Ki tashi akwai sauran kayanki da ban bayar ba ki canza" wata bulawus na saka na daura zane sai da nayi sallah salma ta dawo, tayi ta tsalle da murnar ganina.
Na idar da sallar la'asar ina buga miyar kukar da nayi wadda nasa aka sawo min kaza da ita nayi sanwar dan haka ban bata lokaci ba na dora farfesun kifina wanda na sawa attarugu da albasa da kayan kamshi da alayyahu, ina zaune gaban rishon a kofar dakinmu ya dauko dahuwa dan kamshin shi kawai ke tashi.
Ina ji mutanen gidan na ta gaisuwa alamar an yi Baki, ina juyawa wa zan gani Ahmad ne, ban kara mashi kallo na biyu ba na maida idona kan rishon gabana yana gama gaisawa da mutanen gidan ya tako kai tsaye zuwa kofar dakinmu, kallo ya kare min sai ya sa kai ya shige dakin.
Ina jinsu shi da Innarmu yana gaisheta da suka kare waje ta fito, an kwashi kusan minti bakwai ban shiga dakin ba sai da Innarmu ta rika yo min dakuwa daga inda take zaune, na tashi na shiga kai tsaye da niyyar dauko inda zan zuba kifina. Na dauko na fito zan yi waje naji an rike hannuna ido biyu muka yi sai na sunkuyar da kaina dan sosai idanuwanshi ke min tasiri ban cika juriyar hada ido da shi ba. Kallo yake kare min ni kuma ina kiciniyar kwace hannuna,
" Yi hakuri yammatana na gane kuskuren da nayi shi na biyo in gyara, duk wanda ya dace in nemi afuwarsa kan abinda nayi maki zan yi hakan, kin hakura?
Ya tanbayan yana leka idanuwana,
" Ko tashin hankalin da na shiga yau kadai da aka ce min ba a ganki ba kika rike a matsayin ramuwar abinda na maki ya isheki".
Jin ya sassauta rikon da ya yi min nayi saurin kwace hannuna nayi waje na juye kifin na cire na mutan gida na shigo da namu daki. Wuri na samu nesa da shi nayi tagumi, ya ce " Ba a yi dani ba girkin da aka yin?
Na tashi na kwaso su duka na ajiye gabanshi na hado da cokula da flate na koma inda na tashi, farfesun kifin ya zuba yana ci kallona yake "Banda ban ga su Baba ba da yanzu muka wuce "
Cikin dakewa na ce
Ni ba za ni ba". haka muka dauki lokaci yana kokarin shawo kaina
amma abu ya faskara har aka fara kiraye kirayen sallar magrib ya mike tsam dan tafiya masallaci, nima alwalar nayi na fara sallah.
Har aka idar da sallar isha'i ban kara jin duriyar Ahmad ba, sai dai naji bakin salma ta gan shi waje yana gaida Babannina. Asiya yar baba ya'u ita ce ta shigo ta ce Babansu na kirana".
After dress na dora saman wasu skin tight guntaye da na saka sai na daura zane sama dan garin akwai zafi.
Na same shi zaune yana cin tuwo, cikin girmamawa na gaisheshi
Ya ce "Yanzu muka gaisa da mijin naki a waje shi ne da na shigo ladi ke ce min tafiyar daban daban kuka yi ta ke kin zo da rana shi kuma da yamma, shi ne na ce da kyar ba wata shegantakar kika shirya ba, lafiya?
Na ce "lafiya lau"
Ya ce "Mijin naki ya bamu hakuri ya kuma roki san tafiya da ke gobe idan Allah ya kaimu, yana so ya koma ya je wurin aikinshi. "
Kuka na fara "Ni daga zuwa in bi shi gobe?
Dama shi mutum ne me saurin hasala nan da nan ya taso min, " Idan ba ki bi shi kun tafi ba sai ki gaya min uwar da za ki dauka nan din?
Kin ga Shuhaina ki fita idona in ba haka ba ina ganin sai na shige ki, sannan za ki nutsu ki gane abinda ake nufi, yanzu gaisheni kawai ya yi ga kudin da ya bani nan ko kirgasu ban yi ba, yan dubu dubu ne ga su nan lodi guda, yar banzar yarinya arziki na kiranki tsiya na hanaki.
Nan ya yi ta balbalin fadanshi ina sauraronshi har na shiga kuka, sai da ya kare ya ce in wuce in ba shi wuri.
Haka na shige dakinmu ina kuka, Innarmu ganin kukan da nake ta fita ta bar min dakin, ina cikin kukana naji muryar Ahmad a kaina, tsugunawa ya yi daidai kaina yana tanbayata abinda aka yi min, nayi banza da shi.
Da na gaji da lallashin da yake min na ce " Dama ka je ka gaya masu dan ba zan bi ka ko ina ba. "
Kasake ya yi sannan ya mike ki yi hakuri ki sameni mota sai mu warware matsalar ".
Na ce "Babu inda zan sameka".
kallona kawai ya yi yasa kai ya wuce bayan ya fadi "Ina jiranki" Ina nan wurin sai ga aikenshi yana jirana" na kori yaron. Ai kuwa Baban ne ya fito da kanshi kan in fice har saida ya dauke ni da wani gigitaccen mari, dan haka a guje na fice wajen, saida nayi waige waige kafin na hango motar tashi nesa kadan da kofar har ya bude min kofar ban da zabi sai kawai na shiga ina shiga nasa kuka me cin rai ya jawoni zuwa jikin shi.
Yi shiru bana san kukan nan".
Na ce " So nake ka sauwake min aurenka ka auri zabinka wadda kake so. "
amsa ya bani da cewa " Ai bani da wani zabi da ya wuce ke, saki kuwa tsakaninmu babu shi ina ganin ko za a daura min bakin bindiga ba zan iya furta shi a gare ki ba, zan dauki kowane irin bori da za ki yi min, babban burina ki huce ki so ni kamar yanda zuciyata ta hanani sakat saboda kaunarki, tun ban dawo ba aka jarabci zuciyata da san ki, ina kuma dawowa nayi arba da ke zuciyata ta dada sukurkucewa, na rasa duk wata jarunta a kanki,
sanki nake da dukkan zuciyata, ki yafe min laifin da nayi maki ko so kike in duka a gabanki dan ki fi gane irin nadamar da nayi?
Saurin cewa "Ah ah" nayi tare da kokarin kwace kaina ya kara matseni "Dan Allah ka barni Innarmu taso rufe dakinta".
"Ki bini masaukina ki bar mama ta rufe kofarta".
ya fadi yana kara mannani a jikinshi,.
Nayi saurin cewa "A'a"
Ya ce "To in kina son in kyaleki sai kin ce kin hakura".
Na ce "Ya wuce".
Ya ce "yawwa" yana kallona ina maida after dress dina da ya cire min
Na kauda kai Ba fa ka ci abinci ba?.
Ya ce " To ya na iya?
Tuwo nayi za ka ci
Ban cin abinci me nauyi da daddare amma daga babyna tayi zan ci je ki kawo min sai in tafi da shi.
Na shiga na zubo na kawo mashi,
Ya sallameni ya wuce.
A daren da tunani kala kala na kwana.
da safe ina ganin Baba ya'u ya shigo dakinmu na baro dakin na wuce dakin Gwoggo Rakiya na haye gadonta nayi kwanciyata, ita kuma tana ta kokarin fara tuyar waina dan dama tun sanin da nayi mata ita din kwararriya ce wajen waina da tana ta saidawa sai ta bari sai idan an bata aiki, yauma gidan wani attajiri da ke kusa damu ake biki. Kallona tayi " Hala shigar Baban Asiya ya koroki?
Na daga mata kai "Jiya fa har marina ya yi." Dan girgiza kai tayi "Ai yaya ba shi da dama jiya tunda aka ba shi kudin nan ya rasa inda zai sa kanshi, ko ni ya shigo dakin nan ya fi a kirga yana banbami, kin samu arziki za ki sa kafa ki shure, kuma gaskiyarshi, dan jiya gidan nan ba wanda bai shaida zuwan yaron nan ba, ya cikamu da abun arziki, Fatima kuwa sai Allah.
Nasan so take ta ji abinda aka ba Innarmu sai na ki gaya mata.
Nan ta fice ta barn.
Kamshin turarenshi ya fara cika hancina kafin ya bayyana cikin dakin, ya yi kyau matuka cikin dakakkiyar shadda sai maski take, annuri kawai ke fita a fuskarshi, shi ya nema wa kanshi wurin zama, ina zaunen na ce a hankali ina kwana ya amsa yana dan murmushi sama da kasa yake dubana "Wai a tafiyar da nayi ta shekara guda kika sauya waccan shuhainar da na sani kullun cikin rufe jikinta take amma wannan da ko wane irin kaya zama take ya kama rigar jikina yana lekawa hala daga ita ba ki sa komai a kasa ba ina kokarin kwace rigata aka yi sallama a kofa ya yi saurin sakina dan wajen Baba sani ne ya ce Gwoggo Rakiya na kirana na sameta kitchen inda take Suya kwanonin zuba abinci babba da karama masu kyau ta nuna min waina ce da miya wai in kaiwa Ahmad, bude ido nayi Baba ba aiki aka ba ki ba?
Itama idan ta bude min "Idan aiki aka bani fa?
Can gidan ma na aika na ce su bani miya surukina ne ya zo, ki duba miyar ta yi kyau ai ina ganin zai ci. na dauka na wuce dakinta me tsabtar tsiya, dan tsananin tsaftar gwoggo Rakiya ko bayi za ta bata yarda butarta ta taba kasar bayin.
Ya ci fiye da yanda na zata dan miyar ta sha tantakwashi da manshanu sai kamshi take.
Da ya kammala ya ce " Taimakeni kiyo wanka mu wuce ina so har in samu office, yanzu ma momi ta kira ni Husna kuma ta ce me ya samu wayarki dan tayi nacin in taho da ita".
Na mike naje nayo wanka na shirya kaina cikin shadda dinkin riga da siket, na tsuguna gaban innarmu, fada tayi min sosai tare da nasiha, Ahmad ya shigo yana mata sallama cikin sanyinta take mashi godiyar dawainiyar da ya yi.
Sai da nayi ma kowa sallama sai na same shi a mota, ya tasheta yana kallon fuskata hannuna daya cikin nashi yana cewa
"An min kitso dan ubansu, an min kunshi amma a bari akai min in gani sai kika gudo ke da zuwa sai dai in kin haihu raurau nayi da ido ya ce "A'a kar ki min kuka gaban momi zan kaiki tayi miki hukuncin gudun da kikayi ba saninta.
Gudu sosai yayi dan haka daya da wani abu muna Abuja, saukeni kawai ya yi ya juya kan motarshi ni kuma na rasa yanda zan yi in shiga ciki sai dai nayi ta maza
A falo na hangota zaune tana kallo "Oyoyo yan hijira ta fara fadi tare da tanbayar su Innarmu da mutanen gidan mu, nan na gane abinda nayin dai bai bata haushi ba.
Ta ce " Ki samu Husna a daki tunda ta tashi bata ganki ba bata cikin walwala sai ki zo ki ci abinci. na amsa da to Ina shiga Husna da ke kwance tana dago kai ta yi arba dani ta duro ta rungumeni muka fada gado " Su Anty yan dhniya"
Na ce "Ai sai ki fada min waye dan lahira " muka kwashe da dariya Ta ce
Jiya kin kada min ciki ba kadan ba, musamman ya Ahmad ba ki gani ba an dawo masallaci an sha kwalliya za a dauki amarya momi ta ce ai tun safe aka tashi ba a ganki ba"
tashin hankali ko ni sai da na tausaya mashi kawai sai muka ga ya zari key momi ta ce Ina za shi? Ya ce malumfashi ya gani ko can kika tafi, ai fa nan momi ta rufar ma shi Ai dama sa maka ido nayi in ga iya hankalinka tunda mutanan nan suka baka diya ka taka kafarka ka je kayi musu godiya ya gagara, ka dawo ka je kayi ban hakuri nan ma ba daya, yanzu ai sa ganka ta kyauta kwarai idan can din ta tafi. Ya fice falon na aika abakar zan bi shi ya koro shi na mashi text ba amsa. Na ce ya gaya min.
Da muka gama firarmu sai muka ci abinci
Husna ta shiga azalzalata in tashi in yi wanka in shirya nayi banza da ita, sosai nake cikin jimamin rabuwa da momi da yayanta, mun saba ba kadan ba, hausawa kuma suka ce sabo turken wawa, rai kuma ba abinda take so irin me kyautata mata. Husna ta hada min komai nawa ina kallonta.
Da na idar da sallar la'asar momi ta ce kiyi kokari ki shirya yana hanya.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: CHANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE malumfashi
18
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
Kwalliya nayi sosai cikin wani dandasheshen less golden color na yafa mayafi na koma bisa gado nayi zugum har ga Allah bana son rabuwa da mutanen masu dinbin karamci duk kuwa da san da nake wa Ahmad.
Kiran da momi take min ya dawo dani daga duniyar tunanin da na fada, na fito na zauna a kasa nesa kadan da ita, na ce "Ga ni momi" saitin inda na zauna Ahmad yake zaune, kallo daya ya min ya kauda kanshi, nasiha tayi mana ta kuma gaya min akwai dattijuwar da ta samo min suna da dangantaka da mahaifin Ahmad za ta zo daga bauci za ta rika debe min kewa, ta dubi Ahmad "kai kuma duk da haka ka ce a samo maku a nan, to nayi wa Haj Turai magana ta ce akwai me kawo masu masu aiki, tayi mata magana gobe za a zo da ita.
Ya ce "Allah ya kaimu" ta umarci Abakar ya kwashe kayana zuwa mota, muka je nayi wa su Haj Babba sallama da Aunty Amarya, Abba baya kasar tun kusan sati biyu da suka wuce.
Mun fito ina kokarin maida hawayen da ke taho min, dan na hango Husna a gaban sashensu tana nata hawayen, a hankali ya tashi motar yana leka fuskata, kuka kike kina san bata kwalliyar? Nayi mashi shiru shima daga haka bai sake magana ba, mun isa me gadi ya wangale get ya samu waje yayi parking, yana tafe ina biye da shi, khausar ce cikin sashena ta taremu da sauri tana fadin oyoyo Amarya. Juyawa ya yi mu kuma muka wuce daki mun zauna bakin gado ta ce
"Amarya kin sha kamshi"
Na ce "Ke ni fa Amaryar nan kunya yake bani".
"Dole kuwa a kiraki Amarya dan shima me gidan na ji suna tsiya da Dear yana cewa shi fa ango ne shi kuma yana ' Ina?
Akwai ma abubuwan da na zo maki dasu, ki dage wajen yin amfani dasu"
Kallonta nayi "Hala so kike ya kasheni dan ko Momi ban san iya abinda ta bani ba".
Ta murmusa "Ki ce Momi ta gyara wa danta wurin?
Na ce na " Na shiga uku" ina kai hannuna na toshe bakinta, " Wai ke wace iri ce?
cire hannun tayi "Daga zan fadi gaskiya".
Idona ya kai kan wani tsalelen show glass da ke aje gefe na ce " Amma kamar rannan da muka zo ban ga wancan ba?
Ta ce " E yanzu na zo da shi turaruka ne na maiduguri a gida nayi sako sai aka kawo min"
godiya sosai nayi mata. Ya shigo ya shaida min zai fita, Khausar ta ce " Ko zamu shiga kitchen?
Na ce lallai ma wannan maman biyun ba ki jin nauyin jikinki.
Sai da aka yi isha'i Ahmad ya dawo shi da Abdullahi, Abdullahi dai dariya kawai ya yi ya ce "Ya fi kowa murnar hakan" (daidaitawarmu) har mota muka rakasu na ce "Sai kin kiramu "
Haba ke kin fara kin zuwa har in haihu?
Ahmad ya ce " Amarya ta kan yi wata ko sama da haka kafin ta fara fita, ki dai yi hakuri har ki saukan.
Ta ce "lallai au haka ne?
Suka yi dariya.
Ina hanyar komawa ciki Husna ta kirani ta ce
"Ba ki ji part din namu ba ba dadi kin barmu cikin kewa. " na ce "Nima cikinta nake kar ki tona zuciyata ina farhan?
Ta ce ya ce zai kiraki. "
Kiranta na katsewa na shi ya shigo.
Karfe tara da kwata agogon dakina ya nuna zaune nake gaban dressing mirror ina tsala kwalliya na rika tunanin kayan da zan sa dan hudubar da zuciyata ke min duk da gargadin da yayar ke min zunubin da zan kwasa, matukar na aikata abinda nake nufin. Wata jar rigar barci da bata da maraba da babu nasa na saka jan pant na haye gado a buna ina taunar cingam ina jin dadin daddadan kamshin da ke fita jikina, tura kofar da akayi yasani daga kai, na amsa sallamar da ya yi cikin farar jallabiya yake, ya ce "Taso muje dakina ki dauko hijabinki" na ce " To"
Na daura zane saman rigar na zura hijab sai na bi bayanshi, muna tafe ina dariya a raina wannan shi ake cewa daga baya wai an yi sadaka da bazawara, ina shiga umurtata ya yi da in shiga toilet ya nuna min da hannu in yo alwala ban yi musu ba nayo na fito na same shi kan sallaya muka yi sallah da muka idar ya dade yana addu'o'i daga nan ya juyo ya kama kaina ya karanta addu'ar
Allahumma inni as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha ilaih, sau uku sai ya saki kan, ya rika tanbayata game da addinina ina ba shi amsa har sai da ya ga na fara hamma, ya ce " Na fa manta gwana ce wurin barcin wuri, to hau gado" ba musu na haye kallona yake amma barci da zane hada hijabi ya hawo gadon ya zare min hijabin da zanen sai ya shiga sha'aninshi bayan ya zare jallabiyar jikin shi, ban motsa ba nannauyar ajiyar zuciya yake fiddawa, sai da na fahimci ya kamu ba abinda yake so sai ni din, sai na shiga gunjin cikina tilas ya saurara min cikin wata Irin murya yake tanbayata abinda ke damunta, naki magana kuma na ki barinshi ya ci gaba da abinda yake, ina ji ya sassauta rikon da ya yi min sai na mike a guje na bar dakin na shige nawa na rufe, barcina na shiga yi lakadan ban farka ba sai asuba nayi sallah sai na cire keyn na koma na kwanta, sai dai na ji ana shafa fuskata, a hankali na bude idona zaune yake gabana " Taso muyi break fast"
"Ni fa banyi wanka ba" na fadi a hankali ya ce " Muje in taimaka maki"
Na ce " A'a" ya ce " To ina jiranki" na mike yana bi na da kallo, na gama na fito yana zaune inda na barshi, sai dai yanzu waya yake, a darare nayi shafar na zabi kayan da zan sa na koma bathroom na saka cikin less din da ya aiko mun ne kalarshi blue, na zauna daf da kafafuwanshi ina gaisheshi, ya amsa yana shafa gefen fuskata sai ya mike ina biye da shi har kan dinning, nayi mamakin wanda ya yi girkin kamar yasan tunanina ya ce "Albarkacinki momi ta aiko da shi ta ce har sai kin saba da zaman gidan, sai ki rika yi da kanki"
Kura ma fuskata ido ya yi har saida na sunkuyar da kaina, yasa hannu ya dago min fuskar sai na rufe idanuna ya ce "Me yasa kika yi min abinda kika yi jiya? kin kuwa san a halin da kika barni ba ki ji tausayina ba?
Shekara guda har da wasu watanni ina zaune haka sai jiya nasa rai za ki min haka. ni dai da nasan ban da abin cewa sai nayi shiru, da muka kammala danni sama sama na karya saboda ban taba cin abinci gabanshi ba,kama hannuna ya yi zuwa doguwar kujera ya kwanta sai ya kifani kanshi, yana gaya min kalamai masu dadi na yanda nake a ranshi, mun dauki wani lokaci a haka.
An kawo me aikin da momi ta ce za a kawo yau, me suna ma'u na nuna mata inda za ta zauna,wadda ta kawo ta ta tafi ya tara masu hidimar gidan ya gabatar mini dasu, akwai me gadi sai me kula da shukoki wanda Tonny ne ya dawo sai me wanki da guga sai direba wanda zamana zai yi sai cefane, ma'u kuma zata rika masu abinci.
Da rana Momi ta aiko da abinci me yawa muka ci har masu hidimar gidan.
Da daddare ma haka aka kwata nayi kwalliya ta jan hankali ya kawo kanshi nayi mirsisi naki.
Ranar laraba wadda na ci barcina na more sannan na tashi na ci abincin da momi ta aiko ganin ba a taba ba sai nayi tunanin bai dawo ba, na koma daki na watsa ruwa saboda ana fama da zafi, sai na dauko wata doguwar riga me taushi yadinta baki ne sai aka dan mata kwalliya da fari bata da nauyi kuma me kama jiki ce tsawonta ta gota gwiwa kuma me kama jiki ce hula nasa wa kaina, na zura silifas, baya na zagaya dan in sha iska, kan kujerar da ke girke ina zaune ina cin apple ina jin dadin daddadar iskar da ke kadawa kamar an ce in dubi wajen motsa jiki, Ahmad na hango kan mashin din motsa jiki, sai faman digar gumi yake, gani nayi ya sauna ya nufo inda nake daga shi sai gajeren wando kallo daya nayi mashi na sunkuyar da kaina
A hankali na gaisheshi, bai amsa ba kallona kawai yake ya zauna kujerar da ke fuskantata, "Je ki kawo min ruwa"
Na mike cikin jin kunyar rigar da ke jikina na wuce na hado mashi hada lemo da wani danbun naman da nayi na ajiye gabanshi,
kiran sunana ya yi na amsa ya ce "Me yasa ne wai ni ba ki iya kallona? Sai ki yi ta faman sunkuye sunkuye, na ga kin ki bani dama ne da kin amince min da yanzu na zame maki mutumin da za ki fi jin dadin mu'amala da shi sama da kowa. "
ya kai danbun naman bakinshi ya ce"Amma ba karamin dadi ya yi ba, momi ta aiko maki da shi?
Na girgiza kai
"Ni nayi"
Ya gama ci ya kara shan ruwa ya mike
"Zo muje daki ki tayani fira" nasan irin firar da yake nufi dan dai ban iya mashi musu na bi bayanshi har dakinshi
jagwalgwalani ya yi tayi ina mashi kuka, sai da ya gamsar da kanshi ya mike ya shiga wanka, saida ya gama shiryawa ya juyo inda nake kwance " Zan leka hospital akwai wani patient dina da zan kara dubawa".
Ya kamo hannuna muka fito har wajen motarshi, sai da ya bace wa idona sai na koma ciki raina cike da sanshi, sai dai ina jin ba zan iya sallama mashi kaina ba sai na ja ranshi ko na sati ne ya ji Irin takaicin dana dandana.
Wasa wasa sai da week din ya kare bai samu kaina ba duk ya zama wani mara kuzari ni kaina nakan tausaya mashi dan kullun nake shigar da zan tsokanoshi.
Yamma likis ya shigo wanka kawai ya yi na nemi ya ci abinci ya ce in bar shi in dauko lillibina kawai. "
cike da mamaki nayi yanda ya ce na same shi cikin mota, har muka bar unguwar bai yi magana ba duk da nasan a yan kwanakin nan ba shi da walwala amma yau kam ya fi kullun sai na ji nadamar abinda nake ta lullubeni dan nasan sarai zunubi nake kwasar ma kaina istigfari na shiga yi a hankali, unguwarsu ya shiga wanda sai na ji na samu kaina da jin faduwar gaba, jama'ar gidan muka fara gaisarwa sai muka dire sasan momi momi tayi murnar ganinmu amma ba kamar Husna na ce "Ba wani ai ba ki iya leko ni ba"
Ta ce "Yi hakuri Auntyna dazu ma direba ya kawo min sakonki ashe kina tafe na gode".
Murmushi nayi "Ina farhan da Abakar?
Ta ce "Sun nufi bauci dazu su da Abba"
Momi ta fita tana amsa waya, muna nan zaune muna maganar komawar da Husna za tayi makaranta gobe Ahmad ya shigo ya zauna, kallon Husna kawai ya yi ta tashi ta bar falon, kujerar kusa da ni inda Husna ta tashi ya dawo ya zauna kiran sunana ya yi na kara shiga nutsuwata kafin na amsa ya ce "Ban so ta kaimu da haka ba Shuhaina to ba yanda zan yi, na rasa abinda ke damunki a matsayinki na yarinya me tarbiya wadda tayi karatun islama, tasan addininta dan nasan kinsan abinda kike abu ne daya sabawa addininmu na islama, kina ganin yanda kika maida ni wani sukurkutacce da da ba ki kusa da ni na hakura amma yanzu ina ganinki gabana ina kuma sane da cewa ke din mallakina ce, ga shi an cika maki surarki ta yanda ba wani namiji lafiyayye da zai kauda kai daga gareki na rasa me zan yi ki gane irin kaunarki da ta kamani, ki bar ni ma in ji da radadin da zuciyata ke yi na zargin kaina da wofintar da matar da aka duba girma da mutunci aka bani har kika yi wahalar ciki wanda ni ne me shi kika yi ta haihuwa har abinda kika haifa ya rayu tsawon wani lokaci a matsayina na mahaifinta ban mata komai ba na hakkin diya akan mahaifinta hasalima ban taba ganinta ba".
A hankali na ce "Kama daina damun kanka dan hadisin manzon Allah ne abu uku an yafe wa al'ummata, na farko abinda akayi da kuskure, da abinda akayi da mantuwa da wanda aka tilasta mutum akanshi, ka ga kuskure kayi kuma ka gane ciki kuma ba ka san da shi ba. Ya ce "To ke kuma barin da nayi maki fa alhalin kina matsayin matata?
Na ce "Tuni na yafe maka dama kuma ban taba neman sakayya akanka ba. ya ce "Na gode amma hakan ba zai hana in gaya wa momi abinda kike min na rowar kanki. "
gabana ne ya yi mummunar bugawa jin zancenshi na fara mashi kuka, da wane idon zan dubi momi matukar ya furta mata wannan zance me nauyi.
Saurin sauka kasa nayi ina ba shi hakuri, ya ce "To goge fuskarki ya miko min hankachif din shi " Tunda kin daina kar momi ta zo ta nemi jin ba'asin kukan. " da sauri na amsa na goge fuskata.
Sai da muka ci abincin dare sai muka nufi gida da kyar ya bar ni na isa dakina nayi wanka, mai kawai na murza ina mutsutstsuka wata humra ta musamman ya shigo dakin daga ni sai tawul din jikina ya daga ni ina fadin ka bari in sa rigar barcina, bai ma san ina yi ba bai direni ko ina ba sai kan ni'imtaccen gadonshi bai tsaya wata wata ba salon kaunarshi ya shiga nuna min, wadda ni da kaina saida na fahimci irin wuyar da na ba shi, to ya fanshe dan na dandani kudata.
Ban samu wani isashshen barci ba sai asuba dan bamma san fitar shi ba, sai sha daya da rabi na farka yunwa ce ta addabeni text na gani daga gare shi jinjina yake min da yabo na irin farin cikin da na saka shi. Kunya na ji kamar yana wurin, Ma'u ta leko muka gaisa na tanbayeta sun karya ba matsala ko?
Ta ce "Babu"
Duk yadda naso in daure idan ya dawo in ce ya kaini muyi bankwana da Husna gajiya bata barni ba kara kwanciya nayi barci me nauyi ya yi awon gaba dani
Da ya dawo sama sama na ji yana tashina in ci abubuwan da ya shigo min dasu.
Ranakun da suka biyo bayan nan morewarshi yake yayinda nake jin jiki, shakuwa me yawa ta shiga tsakanina da shi, kullun kara san shi nake kamar yanda na lura yana ji dani.
Ranar wata alhamis na same shi da misalin karfe tara yana karyawa kujera na ja na zauna ina fuskantar shi, yana cin abinci yana bina da kallo har na rufe fuskata da hannuwana, na ce "Dama zuwa nayi dan Allah ka barni zuwa sallon a tsefe min kaina duk ya dameni, kullun na tanbayeka sai ka ce ba yau ba". ya ce " Idan kin shirya sai isa direba ya saukeki idan kin kare zan zo in taho da ke".
Godiya na yi mashi
Ya ce "Nawa ne kudaden da za a yi amfani dasu wurin gyaran gashin? na fada mashi, ya ce "Zan bayar kafin in fita" na mike ya ce "Ina za ki?
Na ce " Zan gyara maka dakinka ne sai in shirya" kai ya daga,
Sai da na kare shirin sai na samu isa direba muka wuce.
Sun tsefe min kan sannan aka wanke ana daf da kammala min kiranshi ya shigo wayata shaida min ya yi ya iso na ce "Zan fito ba dadewa, dan an kusa kammalawa. da aka gama na basu kudaden sai na fito a kofa mukayi kacibis da Rufaida ita da wata mun gaisa tana wani dauke kai, ta ce " Ke kadai?
Na girgiza kai
"Muje in gaisheshi"
na wuce suna biye dani, har inda ya ajiye motar ina jinta a bayana tana fadin samun waje har ya Ahmad ke kaita sallon ni dai dariya nayi a raina ina mamakin irin wannan kyashina da take ji, mun isa wurin motar suka gaisheshi daga ciki ya bude min gaban na shiga muka wuce su kuma suka shiga ciki, muna tafiya ya dan dubeni da idanuwanshi da duk suka canza "Wallahi a gajiye nake nayi aiki yau har na ji ba dadi, muje gida in watsa ruwa sai ki matsa min jiki na daga mashi kai.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.fIsacebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-1
CHANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE malumfashi
19
Ranar da na cika kwana talatin da biyar sati biyar kenan, muna kwance da daddare, kaina ya shafa "Har kin yi barci ne?
Na ce "A'a" "Akwai aikin da zan je yi ibadan ina sa ran zan yi sati biyu".
dan shiru nayi, jin ban ce komai ba ya ce "Ba ki yi magana ba? maimakon maganar sai na kama mashi kuka, rarrashi ya shiga yi ya ce "Kin fi san in tafi da ke? ba halin hakan ne, wadda momi ta samo maki za ta iso gobe kin ga za ta debe maki kewar zama ke kadai. "
"To" na ce mashi,
na dade barci bai dauke ni ba ina tunanin yanda zan kwashe tsawon sati biyu ban gan shi ba.
Da safe ina hada mashi kayan tafiya jikina duk ba kwari jawo ni ya yi muka zauna bakin gado, kalamai masu dadi yake gaya min, sannan ya mike tare da ni, ina rike da brief case din shi zuwa mota, mun dade cikin motar kafin ya sallameni ya wuce.
na tsaya ina goge yar kwallar da ta taho min duk da ya ce Isa direba yana dawowa ya kaini gidan momi, Baba kulu bata iso ba sai la'asar, a yanda na ganta za ta yi sa'ar mahaifiyata, sai da ta huta sai muka tafi, dan sau biyu Ahmad na kirana yana tanbayar na koma gida?
da na ce "A'a" sai ya kama min fada.
Kwana biyu da tafiyar ina kwance ina barcin safe, wayata da ke aje ta hau rurin neman agaji, cikin barcin da ke idona na kai mata wawura, ina mamakin wanda ke kirana a safiyar nan, dan Ahmad tunda ya tafi da asuba yake kirana ya ji na tashi.
Na kai idona kan fuskar wayar sunan Khausar ke yawo kan screen din wayar, da sauri na tashi zaune "Kin juye ne?
Na tanbayeta cikin zumudi, "Kamar kina wajen" ta amsa min.
Cikin murna na ce "Me muka samu?
Baby boy ne ga shi nan kwance ta kashe wayar ta bar ni ina ta murnata,sai da na gama shiri na tuna to wa na tanbaya?
kira daya ya daga na gaya mashi haihuwar da son da nake in tafi,ya ce A'a,ke da fita sai Allah ya dawo dani" rokonshi na shiga yi kamar Zan yi kuka,sai da ya gama ja min rai ya ce a dawo Lafiya.
Dakin Baba kulu na wuce na sameta tana jan carbinta,na zauna muna gaisawa na gaya mata zancen haihuwar da akayi na ce mata zan wuce, agogo ta kalla "
"yannann karfe tara za a bar gida? Nima na bi agogon da kallo "Ba damuwa Baba abokin Ahmad ne na kud da kud sun ma zama kamar yan'uwa"
Ta ce "Amma kya tsaya ki karya dan na taya wannan yarinya mun yi abun karyawa." na ce "Sannu Baba, ma'u ma akwai san aiki bata ko gajiya amma ni ku ci kawai zan karya a can.
Rike baki tayi "Kai wannan zumudi da yawa yake, sai kin dawo nima idan za ki koma zan bi ki muje in yi barka ki gaida masu jegon. na mike ina fadin "Za su ji Baba" na leka dakin ma'u muka gaisa na shaida mata zan fita
Na samu me jego sumul kalau ita da yaronta da aka shigo mata da farfesun kaza wanda ya dahu lugub yana fitar da kamshi,daga ji an sa daddawa sai na ji miyauna ya tsinke, na ce "me kuke da shi a gidan ban ko tsaya karyawa ba". ta ce "Ki isa kitchen din akwai kunun gyada yagana ta dama nasan mutuminki ne, idan kuma tea za ki sha akwai ruwan zafi" na isa kitchen din muka gaisa da yagana yar'uwar babanta, me aikinta ta gaisheni, na koma dakin ina cikin ci zuciyata ta fara tashi na ce "Ba ku da wani abu me dan daci da zan shashe baki" ta ce "Me ya faru?
Na yamutsa fuska " "Zuciyata ke tashi"
murmushi tayi "lallai Dr ko har ya cika aiki" harara na bata "Haba daga dawowata duka kwana nawa?
ta ce "Na sani ko dan gidan momi ne?
banza na mata, ta ci gaba " Dama tun shigowarki na ga canji a jikinki sosai nayi zaton haka". na mike ina cewa " Kya karaci sharrinki kin sani ma likita kika karanta karshen bin diddiki" na barta tana dariya nayi waje.
Kullun direba ke kaini gidan masu jego, ranar da akayi kwana hudu da haihuwar na samu wayar Ahmad ya ce "In samu Najib ko farhan wani cikinsu ya yi min rakiya zuwa kasuwa in yi ma me jego da baby sayayya, akwai kudaden da zai turo in biya banki dan ATM dina na da matsala in cire sai mu shiga kasuwar amma in kula da shigar da zan yi".
godiya na mashi
dan haka a washegarin ranar da na gama abinda zan yi na fito na sallami ma'u da baba kulu, direba ya saman ya ce ba isashshen mai a motar na ba shi kudi ya je ya nufi shan man.
Kujerun da ke harabar gidan na zauna jiran dawowar direba da zuwan farhan, na ciro wayata Yusuf na kira muka gaisa na tanbayi mutanen gidan ya ce kowa lfy sai dai innarmu da tayi fama da mura na ce " Har yanzu Murar?
Ya ce A'a ta samu sauki". Na ce ya karatun? Ya ce "Karatu yana nan muna bugawa" na ce "Ya shagon fa?
Ya ce "Yana nan amma kin san yau da gobe karatuna da abinda za mu ci duk shi muka zurawa ido" na ce Allah ya rufa asiri"
Ya ce Amin" na ce "account no dinka nake so ka turo min " yar dariya ya yi "Haba zancen yaushe shuhaina ai an rufe shi, me to zan kai bankin"
Na ce "To ba na wani da za ka turo min?
Ya ce "Akwai ta abokina Mahammadu sani zan turo maki".
Na ce "To ka hanzarta ina jiranka dan zan fita yanzu sai in turo maka idan ka cire sai ku karawa shagon kaya sauran ku sayi abinci, ka gaida innammu kwana biyu ban samunta a waya.
ya ce "Wayarta ta lalace amma na kai mata wurin gyara".
Na ce " Ka saya mata waya" ya ce "An gama ke dai godiya muke". Na kashe wayar Farhan ya karaso "Ke Hajiyata ina ta nemanki ashe kina nan".
Na ce E" muka jera ina tanbayar shi su momi, mun samu isa direba jikin motar ya dawo, farhan ya karbi key a hannunshi, mun bar gidan ina tanbayar shi "A me ka zo?
Ya ce acaba na hau"
na dan rike baki "Kamarka babban yaro kana hawa acaba ba girmanka bane, duk ina motocin gidan? ya ce Ba direba ko daya duk sun fice da motocin ai yaya Ahmad ba karamin gwangwajeki ya yi da wannan motar ai ta shiga tsara ce.
ni ne dai har na fidda rai, sai idan na gama karatuna sai ki ga na saya idan Allah ya taimakeni dan ba zan kara cewa a saya min ba.
ta wutsiyar ido na dubeshi "Kenan fushi ka yi?
kada kafadu ya yi "Kawai dai na ga sa ran da zaman jiran sai ammaka ba mafita bane, gara kayi fatan samun naka"
Na ce "Haka ne, kaima dan dai kana son motar da yawa ne ai ba cewa akayi ba za a saya maka ba, wani lokaci aka diba kuma idan muna raye zai zo, amma Abba mota nawa ya aje saboda ku?
muna firar har muka isa bankin sai da na cire kudaden masu yawa ya turo dan haka da na shiga kasuwa sayayya sosai nayi.
Ranar ban samu zuwa gidan masu jegon ba.
yaron ya ci suna Al'amin ranar suna shagali me kayatarwa akayi an tashi kuma lafiya.
Zamana da baba kulu ya debe min kewar zaman kadaici, mace ce me hikima da sanin ya kamata, idan muka zauna za ta yi ta bani labarurruka daban daban kwarai nake amfanuwa
Ranar da Ahmad zai dawo tunda safe ya yo min waya ya ce goma za su shiga meeting suna fitowa zai wuce air port.
tunda na tashi nake yan gyare gyare sai da na ji ko ina ya dauki kamshi me dadi, na sanya kira'ar Abba zaria wanda nima saboda zama da Ahmad ba karamin so nake wa karatun nashi ba.
na shiga kitchen nayi girke girke masu dadi sai da na adana komai a warmers ma'u ta gyara wurin, dakina na koma nayi sallah sai na dauko wata koriyar atamfa shar tana da dan ratsin fari, riga da siket ne waanda suka zauna min dam, sarka da yankunne fashion ne na burgewa. Ina feshe jikina da turare kala kala ina kara kallon kaina a madubi, na sa takalmi sai na isa kitchen na debi abinci, dakin baba na wuce na sameta tana lazumi yawan ibadarta kan tuna min Innarmu, sai da ta kammala sai muka gaisa
ina cin abinci muna fira. Rabin hankalina na kan firar rabi yana kan agogo Ina tunanin Ahmad, shiru har akayi la'asar, daki na koma nayi sallar na gyara fuskata sai na dawo zamana ba dadewa sallama kawai muka ji a kofar dakin, na dubi kofar wani irin dadi ya rufe ni samun wuri ya yi ya zauna suna gaisawa da baba kulu da kyar na ce sannu da zuwa saboda kunyar kallon da yake bina da shi ga shi ba mu kadai ba.
Mikewa ya yi "Bari in je in dan huta baba"
ta ce "Kwarai ai ya kamata". ya fice nayi dan jim ina jin nauyin bin shi, ta ce "Oh wane sakarci kenan? mijinki ya dawo tafiya ba za ki yi hanzarin isa wajenshi ki ba shi kulaw, maza mike ki gani.
na tashi na bi bayanshi, a dakinshi na sameshi yana cire kaya miskilallen kallon shi ya watso min "Sannu da zuwa ya hanya?
Na fadi ina kare fuskata da hannayena. dan murmushi ya yi "Bari in yi wanka sai in zo in ga irin sannu da zuwan da zan samu".
Wucewa nayi na hada mashi ruwan sai ya shiga, da ya fito ya kintsa kanshi zai cafkoni na fara rokonshi ya bari ya ci abinci a wurin cin abincin ma yana ci idan shi na kaina ya ga na rufe fuskata murmushi ya yi me fidda sauti, da ya kammala muka wuce dakinshi, a ranar dai Baba kulu bata ji motsina ba sai dare na fito na gasa mana kaza.
Da safe yake gaya min kudadenshi da suke hadin gwiwa da mijin Aunty Kubra na shigo da ingantattun magunguna sun fito, dan haka in fada mishi abinda zai mini, da na rasa abun cewa sai na ce "Ka sayawa farhan mota"
Na ki na ce bana farhan ba"
"Ai idan kayi mani alfarma ka saya mashi kamar ka yi min ne" dubana ya yi saboda me?
Na ce "Dan yanda nake son yan'uwana haka nake jin naka ma nawa ne, yaron yana son mota, kuma yana da nutsuwa ba wani yawo yake zuwa ba".
bai ce min komai ba ya tashi ya fita.
Bayan sati da yin maganar sai ga farhan ya zo yana murna
Aunty fito ki ga motata da yaya Ahmad ya saya min".
A baya nake biye da shi har inda ya ajiye motar na girgiza kai
"Lallai yayan nan ya burgeka, sai ka kula banda tukin ganganci Allah ya tsare" ya ce
"Ai da kyar Abba ya yarda aka bani key.
Ni da kaina na fahimci ina da shigar ciki, amma ban gayawa likita bokan turan ba, ban ma yi tunanin ya sani ba sai da cikin ya shiga wata na uku, dan bana laulayi komai ci nake.
Ranar wata monday ya dawo aiki zaune yake yana aiki a laptop din shi, ina kwance kan cushion tashar mbc nake kallo wani film suke haskawa me suna Blede Trinity Kira na ji ya shigo wayata na daukota na daga yayarmu Azima ce sai da muka gama gaisawa ta ce suna asibiti ummu ta haihu an sami budurwa. Cikin murna na ce bani ummun ta ce "Ai basu kaiga fitowa da ita ba.
Na ce zan kira anjima idan an fito da ita.
Kammala wayarmu da na rasa abinda zan yi in tabbatar da jin dadina sai na kama tsalle kamar wata yarinya, ni nama manta da mutum a falon.
Daga kanshi ya yi "Lafiya meye haka?
A sannan na maida hankalina kanshi na shiga nutsuwata, daure fuskarshi ya yi "Wace irin wauta ce haka?
kina ba ke kadai ba kina tsalle, so kike ki illata abinda ke cikinki?
cikin tsananin mamakinshi na shiga ba shi hakuri a raina na ce miskili ashe yasan da cikin kuma yana san shi amma bai taba nuna min yasani da shi ba. Tashi ya yi ya shige dakinshi ya barni zaune na rasa abinyi, ko wajen cin abinci ma kin sakar min fuska ya yi kuma ki ci kanki bai ce min ba, da ya kammala kwashe wayoyinshi ya yi sai ya bar gidan.
Sai goma ya shigo nayi ta sauraron ko zai nemeni jin shirun sai ya sani sake saken ko in bi shi ko kuma nima in share shi in ga iyakar gudun ruwanshi, tunda ban ga abinda nayi ya yi zafin daukar dimi haka ba. har na gama shirin kwanciyata zan hau gado amma na gaza barcin, har dai zuciyar da ke karfafani in je in same shi ko ba komai ni ce kasa da shi a karkashin ikonshi nake tayi rinjaye, na mike na sabule rigar da ke jikina na maida wata sakaryar rigar barci wadda da ita da babu duk daya, na fito na ratsa falonshi, na murda kofar dakin barcinshi wanda ya yi karara da sanyin AC fitilar dakin bata da wadataccen haske amma na hangeshi kwance saman gadonshi daga shi sai gajeren farin wando, ido ya dago duba daya ya min ya maida idon shi ya runtse na dan dade tsaye sannan na karasa na hau gadon na kwanta bayanshi sai na kankameshi, mun dauki wani lokaci kafin ya juyo ya rufeni da jikinshi sassauta muryata nayi na ce "Kayi hakuri ba zan kara ba".
Da safe nake gaya mashi haihuwar Ummu da san da nake ya barni in je suna, ya barni amma da sharadin kwana uku zan yi godiya na mashi, ana saura kwana biyu suna su Tonny suka rika shigowa da kwalaye wanda nayi ta bin su da ido, sai da suka gama jidesu suka ce aiken oga ne shi kuma da ya dawo aka shigo da wasu masu dauke da zannuwa, sai da safe yake ce min tsarabata ce da safe ma momi ta aiko da alheri me yawa ta ce in kaiwa Innarmu da me jego, a tsanake na rika shiryawa duk da murnar da ke cike da cikina dan na lura sai bi na yake da ido ya ga na nuna zumudi, ina dakina ya sameni kudade ya ajiye min, "Ki rike kuma ki kula da kanki bana son wauta zuwan ma banda ina ganin ya kama aje da ba inda za ki, naso in zo in taho da ke aiki ya yi min yawa, amma ki gaida su mama ki fada masu ina nan zuwa gaishesu. "
na ce "To"
Ina nan tsaye bayan labulai ina kallonshi sai da ya shiga motarshi na dawo na kammala shirina tuni su Tonny sun sanya min kaya a boot, dan haka jakar hannuna kawai na dauka. Malam Isa dama ni yake jira nayo ma baba kulu sallama ta biyoni tana ta min addu'ar sauka lafiya.ma'aikatan gidan sun taru gaban motar na raba masu kudade muka dau hanya mun yi nisa da tafiya na mika mashi plate din CD na waazin sheik Giro argungu yasa mana, ya ce Oga ba dama yana ta gargadin inyi tuki a hankali, bayan na san shi din gwanin gudu a mota ne, shi ne dai madam yake ji".
dan murmushi nayi na ce Malam isa ba dama ya ce "Allah kuwa Haj".
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: CHANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE malumfashi
20
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*BISMILLAHIRRAH-MANNIR-RAHEEM*
Uku da rabi muka shiga Malumfashi ya yi parking kofar gidan mu, wanda na rinƙa ganin kamar na ɗau wani dogon lokaci rabona da shi.
Cikin sauri na shiga gidan, gidan ya dau hayaniyar ganina abinka da gidan yawa, Innarmu tayi matukar murnar ganina, Yusuf ya shigo muka yi fira, sai da muka yi sallar magrib muka nufi gidan ummu ni da Yusuf da salma, mun samu yayarmu za ta wuce gida dan sun kammala aikin gobe suna, sai tara da rabi muka baro gidan inda ummu tayi tayi in kwana na ki na ce ta bari sai gobe yau zan yi fira da Innarmu.
Da safe da wuri yayarmu ta biyo min zuwa gidan sunan, na cire gudummawar me jego ina mikawa Innarmu nata da na sauran jama'a sai ta fara hawaye, ba sai mun tanbayeta kukan da take ba mun san Aunty Amina ta tuna muma sai kowa ya fara goge ido Yusuf ne me bamu baki, Sai da muka natsa sai muka wuce.
Yarinya ta ci suna Fatima sunan uwar mijin ne sai aka yi dai-dai muma sunan Innarmu kenan, nan na kwana na tayata kintsa gidan, yayarmu ta dawo da safe dan suyar ragon suna sai yamma sosai muka bar gidan
Da daddare muna fira a kofar dakinmu bayan kammala cin abincin dare, kiran Ahmad ya shigo wayata na mike na shige uwar dakanmu na haye gado, na ce " Da rana na kira na ji a rufe shi ne na yi zaton ko an fita rage rana ne kuma aka rufe wayar ka da irinmu mu dameku".
dan murmushi me sauti ya yi "Kishin kuma can ya kaiki? to maida wukar a sannan ina fama da wata me haihuwa ne kwananta bakwai tana bleeding sai da abun ya yi worse aka nufi asibiti da ita sai da ta kwana suka ce ba za su iya ba, shi ne akayo hospital dinmu da ita ina ma barci aka yo min waya ga Emagency an kawo, sai dazu da la'asar na samu nasarar janyo mata yarinyar ba tare da na fedeta ba.
Ajiyar zuciya na fidda.
Ya ce "To kin maida harsasan naki ko?
na ce "Wane irin harsasai kuma?
ya ce "Na yakata mana, na je wajen girl friend ko ba haka kike nufi ba?
dan murmushin kunya nayi jin ya gano ni, ya ce "Ni wanka ma nayi ina kwance kewarki na damuna, ina jin haushin kaina me yasa na barki har kwana uku?
dan murmushin jin dadi nayi "Na yau ne kadai gobe iyanzu muna tare in sha Allah". Ya ce "Ki yi kokari ku taho da wuri kar ya yi gudu da ke ku taho a hankali kin ga ba ke kadai ba ce ".
gyada kai nayi kamar yana kallona. mun jima kafin muka yi sallama sai na kwanta.
Da safe nayi ma Babannina alheri da sauran mutanen gidan, mun fita da wuri kamar yanda ogan ya bada umarni, Innarmu tana ta sa min albarka ni da sauran yan'uwana sai da muka biya gidan Haj kanwar kakarmu da gidan yayarmu sannan muka dau hanya.
Mun kusa shiga Abuja khausar ta kira "Maman twince kun shigo ne?
na ce. "Dan Allah bana son wani mmn twince mun kusa dai"
dariya tayi. "To amaryar Dr, idan kun shigo ki biyo ta gidana an kawo humrad da muka yi sako meduguri".
Na ce "To sai mun shigo"
Mun biya sai da nayi wa Al'amin wasa sai ta bani sakon.
Masu hidimar gidana sun nuna murnar dawowata, sai da na ci abinci nayi sallah muka zauna fira da baba kulu har da ma'u, Ahmad yayo waya mun iso na ce "E" ya ce Good Allah ya shi maki albarka zan shiga operation yanzu ina bukatar addu'arki".
nayi mashi fatan samun nasara, na kuma tura mashi text na kalamai masu dadi.
Sai yamma muka shiga kitchen muka yi girki na sha kwalliya cikin wata tsaleliyar shadda amma shiru ba Ahmad na gaji na cire na sa wata doguwar rigar barci me kalar ruwan goro shara shara ce na daure gashin kaina na sa wata mitsitsiyar hula na koma na mike kan cushion abinka da dama ina tare da gajiyar tafiya sai barci ya dauke ni. Sanyin da ya rika ratsa fuskata shi ya sa ni yin sheshsheka na dan bude idona tsugune yake gabana wanka ya yi sanyin ruwan hannunshi ne yake taba fuskata na yunkura na tashi zaune, "Sannu da zuwa ya aiki?
"Ke ke da sannu babyna ya hanya?
ya su mama da kowa da kowa?
Na ce lafiya lau" ya kewaye ni da nau'ikan abubuwan da ya shigo mun da su, na ce "Abincinka fa na kan dinning ya ce "Ok nayi tunanin gajiya ba za ta bar ki yin girki ba.
ya hau teburin ni kuma na soma cin abubuwan da ya shigo min da su sai da muka kammala sai muka kwanta.
Kwana biyu bayan nan wani yammaci na fito daga falona sai na isa na Ahmad har ga Allah ni ban san ba shi kadai bane, ashe bayan fitata su farhan da Najib sun shigo riga da siket ne jikina rigar fara siket din na jeans ne kalar shi blue sai nayi sallama kuma har sun fara gaisheni zan zauna kan masangalin kujera Ahmad ya daka min tsawa abinda bai taba min ba ya ce kuma in fita.
Na isa dakina ko gani ba na yi idona cike da kwalla ina faduwa kan gado na soma zubda hawaye, ban san iya lokacin da na dauka a haka ba na dai ji motsin bude kofa ban tada kaina ba muryarshi na ji fada ya rufe ni da shi kan shigar da nayi Ina sane akwai maza a ciki ya kare sai ya fice.
Ba abinda yake kara sani jin bakin ciki irin a gaban kannanshi ya wulakantani ya kore ni, da daga ni sai shi ne sai in ba shi hakuri dan dama zaman bauta nake daga aure ibada ne, muryar baba kulu na ji tana min magana daga kofar falo saurin tashi zaune nayi na fada bathroom na dauraye fuskata sai na fito na sameta "Tsaye kike baba ba ki zauna ba?
Na fadi ina kakaro murmushi "Na ji shiru ne ba ki fito ba uwar dakina"
na ce. "Kaina ne na ji yana dan sarawa shi ne na dan kwanta"
Bayan firar wani dan lokaci na bi bayanta a wurinta na ci abincin da suka girka ita da ma'u, ko da na ji dirin motarsa ban motsa ba har ta ce "Ba ki ji dawowar mijinki ba maza tashi" na ce "Bari baba in dan ga Karashen labarun nan".
ta ce "Can ma ai akwai talabijin din" muna cikin haka ya shigo gefen da yake ma ban kalla ba, suka gaisa da baba ya fita ta ce "Kin ga har ya biyo ki maza ki bi mijinki, ku yaran yanzu rashin dabara ke damunku, kika ga mijinki na sanki kema ita kokarin jawoshi jikinki kina kyautata mashi b...
ban ji karashen zancen nata ba nayi waje ko kallon sasanshi ban yi ba dakina na shige na datse kofar nayi kwanciyata, da safe sai da na tabbatar da fitarshi sai na fito na samu abincin da su ma'u suka yi na ci, da rana ma da nayi ajiye mashi kawai nayi.
Sai yamma na zagaya baya dan in sha iska na zauna sanye da riga da wando na English wear masu kama jiki ruwan madara, tafiya na ji sai gabana ya dan fadi dan ban tunanin akwai me zuwa wajen ba, sai dai in ka biyo ta falona ko na Ahmad kuma na rufo falona, waiwayawa nayi Ahmad ne na maida kaina na sunkuyar ina kallon yan yatsuna ya karaso ya zauna gabana, "Ke kunnen kashi ne da ke ko?
Ban daga kaina ba kuma ban yi magana ba "Yanzu wannan kayan idan wani ya shigo fa? dubi komai naki a bayyane yake fa".
ya kare maganar yana jan rigar kamar zai cireta na kwace rigata ta hanyar cire hannuns shi "Sai dai idan wulakancin ne bai isheka ba amma nan waye zai shigo am.... Sauran maganar ya makale saboda kukan da ya taho min da gudu na bar wajen.
Da daddare ina kwance a falo nayi rigingine ina kallon sama kayan ne jikina ban cire ba, ya shigo bai min magana ba wata katuwar leda ya ajiye sai ya juya ya fita, na tashi na rufe falon bayan kwanciyata ina ji yana buga kofata nayi banza da shi.
Sai da muka yi kwana uku a haka.
ran na ukun ne da hantsi
ranar ta kama asabar ina zaune ina kallo a tashar pox movies sallamar momi na ji na mike ina mata sannu da zuwa duk da na raya a raina zuwan nata yana da dalili dan ba kasafai ta cika zuwa ba.
Na shiga gaisheta cikin tsantsar ladabi kafin na shiga kitchen na kawo mata abin motsa baki, sai da na zauna ta ce "Wai ya akayi ne Shuhaina na zo in ji, mijinki ya ce kwana uku ba ki yi mashi magana daga ya yi maki fada haka ne?
maimakon in yi magana sai na fara mata kuka daidai nan ya shigo ya zauna "Abin yana bata min rai momi kowace irin shiga tayi haka take fitowa ko ina da baki da da farko ba haka take ba bata zama sai da hijab jiya ma na shigo mata da hijabai kinga ledar can ma ko tabawa bata yi ba".jin abinda ya ce sai na kara tsananta kukana ni wane bako ya yi na fito a haka?
leda kuwa ni ban ma taba ba bare in san meke ciki.
Momi tayi fada da nasiha ta tashi za ta tafi na bita har gaban motar inda direba ke jiranta sai da suka tafi na dawo falona na zauna shigowa ya yi "To zo mana"
kamar in yi banza da shi sai na tuna girman Momi da nake gani kuma ta ce ya wuce, sai na mike na bi bayanshi a bedroom dinshi na sameshi jawoni ya yi jikinshi har yana fitar da ajiyar zuciya, "Haba yammatana daga fada sai fushi yaki karewa?
har sai na dauko Momi, yi hakuri ban iya jurar ganin da wani zai maki ba ni ba kishi rufe min ido yake sai in ga kamar ke kadai ake kallo kar ma yanzu da kike da cikin nan..... rufe bakin shi nayi da hannuna yasa hannunshi ya cire hannun "Ban taba kishin wani abu a rayuwata yanda nake kishinki dan haka nake son ki kiyaye abinda zai tunzurani"
jin ya sake babi sai na fara kokarin kwace kaina kashi ya gwada min bai bar ni ba sai azahar inda muka yi wanka muka yi sallah.
Cikina yana girma dan ya shiga wata na bakwai, zaune nake gaban Dr na kafata yake matsawa dan ta dan yi kunburi, a bayan gidanmu muke zaune inda ya kan rakani in rika exercise idan na gaji mu zauna in huta, dan baya barina zuwa ko'ina hidimar cikin da kula da lafiyarshi duk shi ke yin kayanshi, sai dai ya sa min dokar da na ji ina da matsala ko baya nan in je asibitinsu.
Wayarshi ta shiga kara ya daga "Aunty Kubra ya gida?
Ina jin muryarta dan hands free yasa ya su Zayyad da babansu?
Kowa lafiya ya shuhaina?
Ya dubeni gata nan tana zama da kyar tashi da kyar" dariya tayi "Ka ce in hado kayan baby zan yi ya ko da, dama muna London ne mun zo ganin kanwar babansu Zayyad da ke aure a nan, idan na gama sayayyar zan turo.
ya ce "Zan turo maki kudi Aunty kubra sai ki yi wa madam dina nata sayayyar, amma masu kyau nake so.ta ce "Kar ka damu kai ka sanni ai magana ce ta iya kudinka iya shagalinka" dan murmushi ya yi "Na sanki ne Aunty kubra akwai iya business" ta ce. "Haba dai Allah ya kyauta in maka, har ciko zan yi idan ta kama. ya ce "Na sani Anty kubra ke din ai babba ce" dariya ta kara yi "Sai na ji ka" ta katse wayar.
Sati biyu bayan nan kayan suka iso da na duba akwatunan da ta shako da kayan baby sai da na jinjina sai ka ce wadda za ta haifi yan hudu, nawa kuwa nasan tabbas bata sa san rai ba wurin za bar min kaya.
Da safe Dr na ta shiri katsina za shi wajen wani taronsu na likitoci, ina zaune bakin gado na tasa katon cikina ina kallonshi na ce "Ji nake kamar ka tafi da ni ka sauke ni Malumfashi idan ka dawo sai ka biyo ka daukoni".
Yar harara ya bani "Ba ki da hankali a haka yanda kika zaman nan ina za ki ko an barki". na ci gaba da kallonshi yana saka safa fara kullun sai in ga kamar kara mashi kyau ake shigar farar shadda ya yi ya soma daura agogonshi citizen ya yi kyau har ban san dauke ido a kanshi na kai hannu zan dauki breaf case dinshi da ke gefena ya ce "No" ya dauka ya kuma miko min hannunsa na kama sai na mike muka isa wurin motarshi ya shiga ya zauna na sa hannuna kan murfin motar na ce "Allah ya kaika lafiya yasa ka dawo lafiya" shima ya fada cikin kwaikwayon muryata "Nima Allah yasa in dawo in iske baby na kamar yadda na bar ta".
ya leko da hannunshi ya shafi cikin ya yi dan murmushi na daga mashi hannu sannan na koma wurina na kwanta kamar yanda ya bani umarni.
Uku na ranar washegarin tafiyarshi na ji shigowar mota kamar in yi gudu in taro shi dan sosai nayi kewar tarairayar da yake min, sai dai katon cikina bai bar ni hakan ba, da nayi yunkurin mikewa sai kafar ta rike dole na zauna . sai ga shi ya shigo wa zan gani bayan shi Haj ce murna na kama yi na ce "Ashe gaskiya na kasa tashi ke ce kika rike kafar"
Yar dariya tayi "Ragwanta dai yarinya shi yasa na biyo megidan tunda kin tsufa".
Na ce. "Ai na ga alamar hakan ga shi daga isowarki na gaza tashi"
Na cicciba na tashi na umarci Ma'u ta kawo mata ruwa da abinci.
Na ce "Ina zuwa Haj"
Ta ce "Yi maza wurin mijinki na daukar mashi ruwa na wuce ina shiga janyoni ya yi ya zaunar na tsiyaya ruwan na mika mashi, "Ba ki ji ko? ba za ki bar girkin nan ba ko?
Exercise dinda kike yi ma is ok"
na ce "yi hakuri na ga kamar ba ka san girkin Ma'u ya ce " To ba lalura bane za ki tabbata ne a haka?
wanka kawai ya yi ya ci abinci sai ya dauki key dan bata rai nayi "Haba dan Allah daga dawowa ba ka bari ka huta?
kallona kawai ya yi sai ya bar gidan.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: CHANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE malumfashi
21
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*BISMILLAHIRRAH-MANNIR-RAHEEM*
Na koma wurin Haj na zauna muna gaisawa ina tanbayarta mutanen gida, na ce "Sam bai faɗa min zai ɗauko min ke ba hasalima ba muyi da shi zai biya Malumfashi ba" ta ce "Kuma kwanaki ya je garin sai ya yi wa uwar taku maganar zai zo ya tafi da ni dan in kula da ke, sosai Rakiya ta so zuwa tunda ta ji zancan, uwar taku kuma ta ce in barta ta zo duk da ta san zaki fi jin dadin ganina kusa da ke, to jiya ya biya ya ce idan ya dawo yau zamu wuto, to an yi rashin sa'a Rakiya tun jiya ta tafi Kankara gaisuwar ƴar aminiyarta da ta rasu sai yau din za su dawo. Yar dariya nayi "Wai ki ce mita na can yau idan Gwoggo ta dawo ". Muna ta labarummu har dare, sai na kaita dakin da za ta zauna dan ta samu ta kwanta ta huta. Kwarai na ji dadin zuwanta, ko ta ina ji da ni ake ga ta ga baba kulu momi ma kullun sai ta yi waya ta kan zo daga lokaci zuwa lokaci ballantana kuma ogan da ban san yanda zan misalta kular da yake bani ba, ya kan gaya min rasa yanda zan yi da ke nake Shuhaina idan na tuna kin taba dawainiyar ciki wanda nawa ne ni ke da shi ke kadai ba tare da na taimaka maki ba.
Wata safiyar talata na tashi da ciwon kai tunanina zai bari dan haka ban shaida wa ogan ba har ya fita da kyar na daure nayi wanka na ji bai bari ba, sai na kira Dr sa'a ta ce in hanzarta in zo dan tana cikin aiki ne da sai ta zo gidan. Na ce bari in nemo Dr a waya ta ce bai shaida maki zai shiga meeting ba?
na ce "Na manta gani nan zuwa "
Na fada masu Haj zan tafi asibiti har suna hada baki ita da baba kulu wajen tanbayata lafiya
na ce "Ba komai kaina kawai ke ciwo"
Haj ta ce "Ko in zo muje tare" na ce A'a zan je ni kadai
Dr tayi min tanbayoyi game da yanda nake ji tayi min duk abinda ya dace da na gama zan wuce ta ce "Dr ya fito ba za ki je ki fada masa abinda kenan ba? na ce "Haka ne fa bari in karasa" na wuce tinkis tinkis sanin wace ce ni stander bata tsaya yi min iso ba, ta dai gaisheni na murda handle din na shiga, me zan gani Ahmad ne zaune ya ma bar kan kujerar shi ta likita ya zauna kan kujerar me ganin likita kujerun guda biyu ne dayar wata ce zaune suna fuskantar juna, kallo daya nayi mata na shaida ko wace ce budurwar da muka
taba haduwa da ita a office dinshi lokacin da Abdullahi ya kawoni shi kuma ya wulakantani gabanta,lokaci guda na ji faduwar gaba dama har yanzu suna tare? na tanbayi kaina kare masu kallo nayi sai na juya na fice idona da kyar nake gani sai na ji ciwon kan ya dawo min sabo, na isa inda malam Isa ke jirana na fada motar ya ja sai muka bar Asibitin muna tafe ina waiwaye ko zan ga Ahmad ya biyoni to ko me kama da shi ban gani ba.
Sadadawa nayi kamar barauniya na shige dakina, zama nayi dirshan a tsakiyar gadona na dafe goshina da hannayena tunanin makomata a gidan Ahmad nake yi, ba zan manta ba ko in zolayi kaina da maganar da Abdullahi ya taba yi Ahmad ya yi wa budurwar tashi alkawarin aure da zarar ya kammala ginin gidanshi, ga shi kuma na gansu tare shaidar cewa suna tare, anya kuwa idan ta shigo ba zan raina kaina ba?
Ita da ya gani da kanshi yana so da ni da aka fi karfinshi aka ba shi.
na dade cikin tunani da na rasa mafita sai na kama hawaye turo kofar da aka yi bai sa na dago ido ba har sai da ya janyo kujerar madubi ya zauna gabana muna fuskantar juna, hannu biyu yasa ya tallafi habarshi ya zura min ido magana yake min a hankali,
"Yi hakuri ki daina kukan meye abin tashin hankali dan kin gan ni da mace alhali kin fi kowa sanin irin aikina, wannan da kika gani yar'uwarta ce ke labour.
na dago idanuwana da ke ta faman zubar hawaye na ce "Meye abun boyon hadaddiya me class wadda ba bagidajiya ba yar bokon karshen zamani da za ka aura, ai dama babban goro sai magogin karfe nima dama ai karanbanin akuya ne gaida kura, amma ai bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne, kawai ina kukan tausayawa kaina ne idan matan so suka shigo matar tushe kashinta ya bushe. "
Kara zuba min ido ya yi kamar me nazarin wani abu
"Duk wannan jerin maganganu naki wai me suke nufi ?
ni dai na cigaba da kukana ina share hawaye
shi dai rarrashina yake yana fadin in duba cikin jikina in kyale wannan soki burutsun ni dai nayi kunnen uwar shegu da shi da ya ga bani da niyyar shirun ya ce
"Indai ba so kike in hawo gadon nan ba to ki yi shiru, dan tausayinki yasa ban hawo ba, dan garin lallashin zan iya sauya babi.
Maganar Haj muka rika jiyowa nayi saurin sauka bisa gadon ina share hawaye sai na bude kofar ganin na fito sai ta zauna "Ke kuma haka ake sai ki dawo ba sanarwa mu kin barmu da tunanin ko yaya".
kafin in kai ga magana ta zuba min ido "Me kuma ya samu fuskarki? ko duk ciwon kan ne?
kai na daga mata ta ce "To Allah ya sawake da haka sai ka ga an rabu, sun ba ki magani ko?
kan na kuma daga mata sai a sannan ma na tuna da magungunan, Baba kulu ta shigo itama sannu tayi min sai suka fita tare.
Ahmad ya fito "Yaya kin hakura ko ni za ni in yi sallah ".
baki na tura banyi magana ba,
Da daddare ko da muka zo kwanciya juya mashi baya nayi nasa kaina wurin kafafuwanshi sai ya dauko pillow yasa bayana ya rungumoni ta baya yana rada min "Kin kuwa san hukuncin macen da ke juyawa mijinta baya? matukar ba ta nemi iznin shi ba amma ni na yafe maki daga nasan kina fama da kanki ne.
Haka muka tashi da safe tunda na gaisheshi ban kuma magana ba kujera na koma na zauna ya zo ya zauna kusa da ni "Yaya dai madam akwai damuwa ne? na girgiza kaina ya ruko kafaduna "Tunda nayi lallashin kin ki na baki to muje dakina" saurin girgiza kaina nayi "Ni ya wuce tuni" ya rage murya "Daga ganina da budurwa wannan irin bori haka ranar da zan kara aure fa sai yaya?
idanuwa na watsa mishi ya mike "Bari in yi shirin office muje ki tayani"
na mike na bi bayanshi.
daga nan aka bar maganar budurwar duk da dai da na tuna sai in ji kamar in ta kwarma ihu, sai in ta ganin har kamar ma ya aurota inda nake jin sauki daya ne idan na tuna ginin gidan na mace daya ne sai dai abinda na manta namiji sai dai idan baisa ma kanshi jarabar son kara aure ba, dan akan idona da wayauna cikin kannen babana akwai wanda ya saida dawar da ya noma suke ci da iyalanshi ya biya sadakin wata bazawara.
Kwana biyar tsakani na tashi da nakuda wadda ban bari Ahmad ya sani ba dan bai matsa mun ba sai bayan fitarshi Haj da baba kulu suna tare da ni, baba ta ce "Ko za a kira mijinta ne?
na ce "Yi hakuri baba mu kara gani tukuna ni a tunanina waccan a gida nayi. Wucewar awa uku Allah ya taimakeni ya saukeni lafiya na samu namiji mahaifar na fadowa baba kulu ta kira wayar Ahmad bata shiga ba na karba na nuna mata na ce ta kira min sister Rabi ai kam ban tashi daga inda nake ba ta iso ta karbi yaron a hannun Haj bayan ta kwashe min jini tayi min allura muka wuce Bathroom da Haj ta taimaka min dan jin da nake kamar iska zata daukeni saboda nauyin da cikin ya yi min yanzu kuma babu shi, ta fita ta dawo min da bagaruwa cikin wata container da ke jike da ruwan zafi sai da na gama na zuba a roba na zauna ciki na dade a ciki sannan ta kamoni na fito.
Na samu har su Haj Babba sun iso da anty amarya da yaran Haj Babba su biyu aunty luba da Aunty zainab khausar ma ta iso na wuce suna min sannu na zauna bakin gado, khausar ta miko min kayan shafa ina murza mai tana min sannu "Kin yi kokari wannan uban boxing baby da kika sullubo mana ai dole ki rika tafiya da kyar"
na ce "Zabo min zane da riga na atamfa me dinki me saukin sakawa" na sanya bayan na mutsutstsuke jikina da wata hadaddiyar humra, ta ce "Mutuniyar har fa kin fito nan da nan karfa ki sa angon karnin kyasawa idan ya iso" na ce lokacin da nake kwanciya, "Allah ya kyauta maki kina min wannan maganar tun ban gama dawowa hayyacina ba"
ta miko min cup da ta hada min tea na fara sha, Aunty luba ta shigo da kwanonin abinci a hannunta "Maza shanye ki ci abinci me jego"
na ce "Na gode Aunty luba "
ta fita sai da aka dan jima na ci abincin tuwon semo ne da miyar kubewa danya, duk yadda naso yin barci bai samu ba saboda jama'ar da ke shigowa.
Ahmad ya iso mutanen da ke dakin suka yi mashi barka suka fita, zama ya yi kusa da kafafuwana ni kuma ina kwance "Sannu da kokari, amma ya ba ki bari an sanar dani na zo munje hospital?
A hankali na ce "Kayi hakuri na ga abun da sauki ne a fada maka a daga maka hankali kana cikin aikinka".
Ya ce "Sister tayi maki komai ko".
Kai na daga mashi
"To tashi ki sha magani" ya shiga bude magungunan da shi ne ya shigo da su, na yunkura ya tallafoni na tashi zaune yana miko min magani ina sha yana bani ruwa da na gama sai na gyara kwanciya ina kallonshi yana tofe yaron da Addu'a ya ba shi zamzam ya gama kallonshi ya kwantar da shi kusa da ni "Bari in barki mata nasan shigowa ki ci abinci sosai zan gayawa khausar abinda za a dafa maki da za a barki ma da barci kika yi ki huta sosai. Sallama muka ji ya amsa nima na amsa a hankali Rufaida ce ta shigo ta gaisheshi ina mata maraba ya ce "Ku koma falo ku barta ta samu ta huta".
dan bata rai tayi ta dauki jaririn ta fita, shima ya fita ya ja kofar.
Washegari Aunty amarya ta dauki baby ta kaiwa Abba ya yi mashi huduba.
Ranar da muka yi kwana uku da daddare muna zaune mu uku ni da Haj da Baba kulu, yaron yana barci cikin gadonshi Baba ke cewa "Banda abin yayan zamani komai aka yi su ce canfi ai da an daura wa yaron nan maganin baki kowa ya zo sai ya tanka"
Haj ta ce "Yaron ne tubarkalla har ya fi iyayen kyau"
na dan tura baki
"Amma dai banda ni ni kam bai fi ni kyau ba"
Ta ce "Ke tafi can mijin naki ma bai fi ki kyau ba?
na ce "lala ke da kika ce sanda aka haifeni saboda kyauna da ban sha'awa idan kika yi min wanka kasa ajiyeni kike sai ki ji kamar ki saceni"
ta kama baki "Ka ji ni da Ja'ira yaushe kuma na ce har kamar in saceki?
ta jehoni da pillow muka sa dariya ni da baba, na ja abun rufa na ce "Ni dai na kwanta Allah ya bamu alheri".
Baba ta mike "Mu kwana lafiya bakon duniya"
ta fadi tana leka gadonshi, dama Haj tare
muke kwana tunda na haihu.
Ana jibi suna Aunty kubra ta iso wanda ban yi tsammanin zuwanta ba sam,
kayanta kawai ta ajiye ta iso gidana,
ba ta zo da yaranta ba
wata dandatsetsiyar sarka da ke ta sheki ta bani wai gift dina kenan
na haiho masu baby
na yi mata godiya
ta bani na yaranta
kowa da nashi
wai aba abokin danbensu
har da na mijinta,
na Husna ribbons ne kala kala sai mayukan gyaran gashi sai set set na kayan yaro
masu matukar tsada
sai turaruka designers,
na ce "Kin gama Aunty
dazu yaya kabir ya zo shi da Aunty Aisha (uwargidanshi) shi ya koma ita ta wuce gidansu na nan sai anyi suna akwati biyu suka kawo shima Abdullahi dazu khausar ta kawo nasu akwatuna, haka abokananshi duk wanda zai zo bai zuwa haka na kare da cewa ni kayayyakin sunyi yawa har firgitani sukayi"
yar dariya tayi
"Wa ya ce maki sun yi yawa?
ai dadin haihuwar kenan
ba ki ji kirarinta ba
ta kurya me gumin alheri?
sai ma ranar sunan
dan kila ba ki san waye mijin naki ba,
shi dai barshi da miskilancinshi amma mutum ne me alheri
ko cikin yan'uwa za ki ga kamar bai san me kake ciki ba,
amma da zarar abu ya sameka shi ne mutum na
farko da zai fara kawo
maka dauki,
har a cikin gidanmu ba shi da banbanci,
wajen aikinshi ma suna yabonshi na tsare hakkin aikinshi, sannan yana kyautatawa na kasa da shi.
na ce "Haka ne"
duk da dai ba komai na sani na halayen nashi ba,
ta katse min tunanina ta hanyar cewa
"Haka ya kabir ya taso kafin ya kwaso auren wata kabila
ta raba shi da kowa,
yanzu ma al'amuran sun yi sauki shi ne
har ya kan yi alheri,
uwargidan tashi ma dan tsaye take".
haka muke rufe firar
ta barni cike da tunanin waye mijina?
dan a gaskiya ko ni a farkon zamana da shi
kallon da nake mashi
Irin na yayan masu da shi dinnan
masu bakin girman kai da rashin ganin kimar jama'a,
sai da muka daidaita
na fahimci da yawa cikin zatona ba haka bane,
mutum ne mara san hayaniya miskili ne
dan miskili
ko ma'aikatan gidan ina yawan ganin
yana masu alheri
ba sai albashinsu ba,
me yawan kusanta kanshi da Allah ne
ta hanyar istigfari
ga yawan sauraron karatun Al-kur'ani
dan ban taba jinshi
yana sauraron kida ba,
har mamakin dadewar da ya yi a turai nake
yake kuma da wannan
kyawawan dabi'un,
yanayin aikinsu kowa
yasan ko wane irin lokaci
za a iya bukatarsu to
haka zai tsallakeni komai dare koda kuma me yakeyi a lokacin
ban taba jin ya yi korafi ba, mutum ne me kwazo kwarai akan aikinshi.
Kakkarfar ajiyar zuciya na fidda da kara ganin girmanshi a raina.
Na mike memakon in kwanta wayata na janyo data na kunna na shiga WhatsApp Husna nake son tura wa sako sai na gan ta online
dan haka na tura mata
"Barka da jin dadi yanmata"
ba a jima ba sakonta ya shigo
Barka dai Auntynmu to ya babynmu?
ya Ahmad ya turo min pics din babyn,
kwarai na yaba da kyautar da ubangiji ya yi mana na wannan tsalelen yaron Allah ya raya mana shi kyakykyawar rayuwa"
Na tura mata
"Amin ina
Ina godiya mutuniyar na ga sayayyar taki ta manya ce, Magyar ribbon hada ribbons ɗin naki" turo min ta yi "Ba ki da labari mutuniyar na tsinci dami a kala nake gaya maki wani dan canji na samu ba ki gan shi ba hand some wallahi ya mutu kaina duk da nima sosai na fada sanshi, a wani boutique muka hadu a birnin na Mumbai. Na tura mata "Dan ina ne? dan nayi tunanin ba'indiye za ki dauko mana" Ta turo "Kai haba dan garinmu ne Bauci, amma ya fi zama lagos"Me mata ne ko single ne? Matar yayanmu yar jarida dama Yayanmu ya barki kiyo karatun mass com shi ne dai dai da ke, yana da mata shekaru biyu kenan da aurensu suna da yaro guda, ganina ya ruda shi kamar yanda nima kaunarshi ta sa ni janye kudirina na kin auren me mata sunanshi Sagir Ningi, ina fata za ki tayani addu'ar Allah ya yi min zabi na alheri" na tura "Na tayaki murna Allah yasa Alheri.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: CANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE
Malumfashi
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
22
Na kashe datar na ajiye wayar, na gyara kwanciya, Haj tuni tayi nisa cikin barcin ta, babyn ba shi da rigima da zarar an mashi wanka to ya shiga barci kenan, hasken da na gani a wayata yasa ni ɗauko ta sakon Ahmad ya shigo zolayata yake in zo in taya shi kwana ni kaɗai yake jira, ɗan murmushi nayi na rufe wayar na ja bargo na rufe rabin jikina.
Da safe cikin nishad’i me yawa na tashi, saboda yau zan ga ƴan uwana a daki, isowar la'asar suka yi, motoci biyu suka zo masu aikin girki aka ɗauka bayan haka Aunty Kubra da Khausar na tsaye kan kula da komai, an karramasu da abinci da na sha nau'i nau'i, ƴan garin su Ahmad su ma sun zo suna gidan su Ahmad.
Sai dare muka kebe da ƴan uwana suka bani abinda suka kawo min na amsa ina ta jin dadi, harda yajin jego Innarmu ta dako min me dadi, suka ce Yusuf na min barka ya ce yana nan zuwa ganin yaron, mun raba dare muna fira.
Da safe yaro ya amshi sunansa Muhammad Khabir sunan yayan mahaifinsa, Ahmad ya shirya walima
inda jama'a da dama suka halarta musamman abokan shi da abokan aikin shi, aka ci aka sha sai aka tashi, zuwa goma na safe kamar ba a yi komai ba sai masu aiki da ke ta ƙoƙarin gyara wajen da aka bata,
na fito cikin kwalliyar atamfa nasa wacce ta ji kayataccen ɗinkin da ya karbe ni, wuyana da kunnuwa da hannu ko ina sheki yake dan an kayatasu.
Dakin me gidan na nufa, a hankali na tura kofar cikin siririyar sallama ya amsa yana zaune a bakin gadonshi, da dogon wando a jikinshi na ainahin shaddar da yasa da safe, rigar na rataye sai singlet fara a jikinshi.
Kallo ya bi ni da shi kafin ya mike ya ruko ni muka koma bisa gado ya dora ni saman kafafunshi ya zagayo da hannayenshi kan cikina ya dora kanshi kan kafadata, magana yake gaya min kamar me rada.
A yau na kara godewa Allah bisa baiwar da yayi min ya bani ke, na so in yi wa kaina, amma Allah da ya soni da rahma sai ya bani iyaye nagari suka tsaya min ban rasa ki ba, yayi maki baiwa da sirruka wa'anda duk namijin da aka baiwa ke, sai dai ya nemi lahira dan duniya kam ta samu, kamun kanki na daga abinda ya kara jefani cikin mayen sanki, a yau an wayi gari kin haifa min da me zan maki ne in kara nuna irin san da nike maki?
A hankali na ce "Ka ci gaba da sona, dan nasan halinku maza baku da tabbas, masu dauka da ajewa ne, yau ke ce gobe kuka kyallo wata kin zama bola, idan aka wayi gari ka juya min baya, ban san irin halin da zan tsinci kaina ba.
Da gama fadin haka sai na juyo na kankameshi dan idanuwana na ji za su fidda ruwa, shi kuma dama me kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, ai sai kawai na tsinci kaina tsakiyar gadon, nan fa idon me jego ya raina fata, na shiga rokonshi da magiyar ya kyale ni, sai da na kwaci kaina na koma gefe guda ina kallonshi.
Rigingine yayi ya tada kanshi da hannayenshi shima kallona yake ya ce
"Ba ki san wani abu da aka yi gabana ba, na ziyarci wani abokina Dr mu'azu a kano, ina tare da shi a office dinshi, yana duba marasa lafiya, wasu mata da miji suka shigo da yaronsu jaririn, result din da suka karbo na gwajin jini suka kawo ya duba ya rubuta masu magunguna hada waanda za su ba jaririnsu, mijin ya nemi sanin meye lalurar matarshi, likitan ya ce
Juna biyu ne da ita na kimanin watanni uku, sai matar ta fasa kuka likita na ta magana amma yin shirunta ya gagara da kyar ta ce yaronta ma watanshi uku, ita yanzu ta bani idan maganar cikin ta fito a kauyensu, daga karshe dai mijin wanda yayi zugum kamar ruwa ya ci shi ya ce
'Shi wallahi ranar suna ne tayi kwalliya (kinsan mutanen kauye ba wai kwalliya ta dame su bane, sai dai ayi ta zama haka, to wannan kwalliya ita ta dauke shi suka aikata abinda suka yi har rabo ya shiga mutanen sun zo ne daga wani kauyen jihar kano". Gyaɗa kai nayi na ce Allah ya kyauta, ni kam nan da wasu shekaru ma ban fatar shi. " zaune ya tashi ya ce "Me kika ce?.
Ai kam cikin sauri na nufi kofa dan na lura so yake ya kuma cafkoni,
na koma dakina na samu ana nemana baby ya tashi.
Haka na wuni cikin jama'a yan suna, wasu da yawa ma a ranar na soma ganinsu, na samu alheri me yawa daga kudi zuwa kaya abun ba magana.
Mutanen gidanmu washegarin suna suka koma amma yayarmu da Ummu sun kara min kwana biyu su kwana hudu suka yi, na sallame su da shatara ta arziki, Khausar ta dawo wanda ni na nemi ta dawo, muka hada uban kayan da na samu ta bani shawarar rage kayan dan sun yi yawa, kuma tana so ta fada min ko zamu hada hannu mu jaraba saro kaya sai mu bude shago, mu nemi wanda zai zauna mana.
Na ce "To zan shawarci Ahmad amma sai an kwana biyu. ta ce "Hakan ma yana da kyau dan gaugawa daga shedan take.
Farhan na kira na ba shi kudaden da na samu ya kai min banki.
Na ci gaba da wanka da kula da junior kamar yanda ilahirin family babanshi suke kiranshi, kafin arbain mun yi bulbul gwanin ban sha'awa, sannan Haj ta fara maganar ita fa in gayawa me gidan tana son komawa gida,
na ce "Kai Haj ni na sha zamammu za mu yi ki taya ni zama"
kallona tayi sosai "E lallai ke naki rashin hankalin babba ne, zaman auren zan taya ki?
ai da ni da ke sai a rasa wa yafi rashin hankali "
Na marairaice "Allah har fargabar ranar da za ki tafi nake"
ta ce "Allah ko?
to dama kin daina dan ina ganin nayi abinda ya kawo ni, zaman me zan yi in ta takurawa yaro".
Jin zancenta sai nayi shiru illa dai na fada mashi.
Sati ta kara bayan nan har muka je gidansu momi muka yi musu wuni,
Ranar da za ta wuce bani ba ma, Ahmad ma alheri me yawa ya mata yasa direba ya mayar da ita gida, munyi kewarta sosai ni da baba kulu.
Sai da nayi sallar la'asar na shiga kitchen, Ma'u na gefe tana temaka min,
kafin in haihu na megidan kawai nake yi, Ma'u da baba su yi na gida duka, yau sai na hada nayi duk gaba daya,
na kuma dage nayi nau'i nau'i masu gamsarwa.
Baba ta karaso kitchen din tana cewa
"Hala me jego yau ta shiga kitchen? ina daga zaune nake ta jin gidan ya kauraye da kamshi.
dan murmushi nayi ta samu wuri ta zauna muna fira ina aikina, sai da na kammala na bar Ma'u tana gyara wurin.
Daki na koma na sheka kwalliya cikin wani yadi me two color riga da wando rigar karama ce dai dai jikina, ina son mu'amala da kananan dinki matsatstsu dan na lura ba kadan ba suke dauke hankalin me gidan.
Na fito cikin daddadan kamshin da ko'ina na jikina ke fitarwa, inda nake jin maganar Ma'u Junior ta kawo min, dan tun yamma yake bayan baba ta goya shi, na karbe shi muka nufi falon da ya raba wurina da na Ahmad, na kwantar da shi
dan barci yake, Remote na dauka na kunna TV ina kallo sama sama ina tunanin abinda ya hana Ahmad dawowa har lokacin dan da ya sallami Haj Niger state ya wuce, kuma ya ce min in sha Allah zuwa magrib ya shigo, ban gama tunanin ba na ji sallamar shi cikin natsatstsiyar muryarshi, na mike ina amsawa yana sabe da Junior muka nufi wurinshi, sai da yayi wanka na gabatar mashi da abinci ya ce "Ba zan hau tebur dinnan ba kawo min nan kawai.
na shimfida ledar cin abinci kafin na jera mashi, na zuba mashi nima na zuba muna ci yana kallona, maganar da na ji ya yi ta sa ni dago ido ina dubanshi,
"Wata yarinya tana son kasancewa da mijinta ta ma tsohuwa wayau ta koreta"
Baki bude na ci gaba da kallonshi abinda za ka ce min kenan?
shi kenan ni da kai za a ga wanda ya matsu".
murmushi ya yi ya mike da junior a kafadarshi dan ya kammala
nima na kwashe komai sai na bi bayanshi.
Yaron yake kallo dan ya bude idanu, na karbe shi nasa mashi nono sai da ya koshi ya karbe shi ya kwantar bisa gadonshi, ya dawo kusa da ni
magana yake rada min, wadda ta sa ni runtse idona, halin da na ga ya shiga yasa nayi amfani da hakan na roke shi abinda na so tuntuni nake kuma tunanin sanar da shi cikin sanyin murya na ce "Dan Allah so nake ka bar ni in ci gaba da karatu".
bai tanka min ba ci gaba ya yi da abinda yake yi, shudewar lokaci ya tsallake ni zuwa Bathroom sanda ya fito har barci ya fara daukata, hada ni ya yi da jikinshi sai ya rufe mu "Me na ji dazu kina cewa?
faduwar gaba na ji ta same ni da kyar na maimaita mashi abinda na ce
Ajiyar zuciya ya yi "Ba zan iya ba Shuhaina, ban taba kishin wani abu a rayuwata yanda nake kishinki, ke wata aba ce me daraja a wurina, ba zan taba nutsuwa ba duk da ba wai ban yarda da ke ba ne, na san na so Amina amma ban taba jin irin kishin da nake maki a kanta ba, in kina san jari zan ba ki amma makarantar nan a hakura.
jin haka sai nayi amfani da damar na fada mashi yanda muka yi da khausar ya ce "Ba matsala, amma ni kam ba inda za ki wani yawon kasuwanci, idan za ta rika zuwa maku ko za ku nemi me maku duk daya".
nayi mashi godiya
Da asuba da nayi sallah komawa nayi na kwanta
saboda yanda nake cikin gajiya,
sai da na farka na lalubi Junior na ga wayam
na san babanshi ne ya dauke shi, dakina na koma nayi wanka na fito cikin less baki da akayi wa ado da flower ruwan goro sai aka ratsa fararen duwatsu.
Ahmad na samu zaune yana duba wasu takardu, gabanshi na zauna na ce
"Ina kwana?
"Ya gajiya?
ya ce yana duban cikin idona, na sunkuyar da kaina "Ina junior? ya ce "Na kai shi wurin Baba, tuni ta mashi wanka ta goya shi".
dafe goshi nayi "Shi kenan sai ta san abinda kenan, ni yanda ma zan hada ido da ita nake tunani".
Kada kafadunshi ya yi
"So what dan ta san abinda akayi, ai ko ita shaida ce kan hakurin da nayi, infact fa an yi two month, sai dai idan an dan saci jiki a dan yi min yan dabaru ana min korafin kada su Haj su gane".
na ce "Dama office ka tashi ka tafi kar kayi latti patient na can na jiranka".
kallo ya bi ni da shi
"Ai yau ba inda zan fita, ko kin manta ango nake, yau ai ke ce likitar, in ba gama dubani kika yi ba ba inda zan iya zuwa".
ban samu amsar ba shi ba muka ji sallama, Ma'u ce Junior ta kawo na tashi na fita na amso shi ta ce Baba ta ce a ba shi nono sai a dawo da shi
na koma falon na zauna ina ba shi nono,
Ahmad ya ce "Idan kin gama da Junior ina jiranki" ya tashi ya shiga ciki.
Sai bayan fitar shi na kira khausar na fada mata yanda muka yi da Ahmad ta ce
"Maganar ba ta waya ba ce kamata ya yi mu samu lokaci mu hadu, kodayake ba ma ki zo min yawon Arba'in ba"
na ce "Ki yi hakuri kinsan ogan wai amarci muke, ko zan fita sai mun gama"
shewa tayi yana da kyau hakan".
na ce "Amma daga gidanki ne nasan ba zai hana zan yi kokarin fitowa sai muyi maganar.
Da na tanbayeshi bai hana ba kamar yanda nayi zato, shi yama sauke ni da zai wuce wurin aiki, bayan mun tsaya ya sayawa Al'amin kayan wasa da carton na madarar da yake sha, mun sameta zaune Al'amin na wasa a cikin kekenshi na dauke shi kamar yanda ta karbi Junior tana fadin irin girman da ta ga ya yi mata, na zauna ina tanbayar Abdullahi tace
ya yi tafiya zuwa calabar, mun taba fira har muka
gangaro kan maganar da ta kawo ni.
ta ce akwai wani yaron gidansu tun yana karami yake wa mamanta aike almajiranci aka kawo shi daga wani kauyen kano, ya zama dan gida a gidanmu ba ki ganin shi ma yanzu ki ce ba dan gidan bane yana da amana ko sare saren Momina da yawan lokaci shi ta kan aika, to shi nake so musa ke kuma daga bangarenki sai ki samo mutum daya sai mu hada su, shi Idris yasan hanya ya kuma san takan komai, me kike gani ya kamata mu sa?
Na dan yi tunani na ce "Ina ga mu sa kayan mata zasu fi karbuwa".
Ta ce "Allah ya shige mana gaba".
ta wuce kitchen ta dubo girki ta dawo ta zauna
"Ke ban fesa maki ba".
Na ce "Ina jinki"
ta ce "Ashe wannan kanwar mijin taki yar rainin wayo da kika ce kin rasa ubanda kika kashe mata ta raina maki kura ashe budurwar Ahmad Zubaida kawarta ce".
tabe baki nayi
"Ke wa ya gaya maki?
ta ce "Shi yanzu nake son ba ki labari
na ce Ina jinki dama sunanta Zubaida?
daga kai tayi "Babbar yarinyar Aunty Zahra sun je bikin wata course mate dinta ita take bani labari a wurin dinner sun zauna kusa da wasu kawaye biyu firar da suka ji suna yi yasa su saurarensu, dayar tana fadin shawarar da ta yanke na rabuwa da Ahmad Tafida, kawar ta ce Ahmad sulaiman Ahmad Tafida kika samu za ki yi wasarere har damar da kika samu ta subuce, gayan fa ya hadu karshe sosai yake burgeni ina maki kwadayin samun sa dan akwai aji ita kuma marairaicewa tayi "Banda yanda zan yi ne, duk wata dabarata ta kare in ma na ci gaba da nacin bin shi sai dai in ta yaudarar kaina, dan farkon dawowarshi bayan rasuwar matarshi sosai yake saurarona, har ma ya ce in ba shi lokaci zai aure ni idan ya kammala ginin gidan da ya fara, duk da na razana da jin aurenshi da kanwar matar tashi, ya ce min kar wannan ya daman, Rufaida kuma ta ce min bai san yarinyar cusa mashi ita aka yi, kuma na yarda dan na je wajenshi muna tare a office dinshi abokinshi ya kawota bata da lafiya a gabana ya wulakantata sai na biyu a sunan Rufaida nan ma ina zaune ta kira shi ya zo ya tafi da ita nan take ya yi halin nashi, na samu kwanciyar hankali a wannan lokacin ina ganin na ma samu Ahmad na gama, duk da zuciyata na tuno min yarinyar natural kyau ne da ita duk hassada banga inda za a kusheta ba, ina ganin wata rana za ta shawo kansa daga mace take tana kuma da abinda ake so, amma Rufaida take danneni "Wai wannan gajar yar talakawa ce fa ta daina bani tsoro, to kwanaki mun kuma haduwa a office dinshi kin san me na gani? da tsohon ciki na gan ta, kuma kallonmu kawai tayi ta juya tunda ta fita kuma hankalin shi ya bar kaina, bai samu sukuni ba sai da ya tashi ya bar Asibitin, tun daga ranar bai kuma bi ta kaina ba wai ni nayi fushi ban sake neman shi ba, to ko ta waya bai nemeni ba.
Sumayya ta ce suna zuwa nan ko sun fahimci muna sauraronsu sai suka tashi suka bar wurin. "
tabe baki na kuma yi
"Hala recording ta yo maki?
Yar karamar dariya tayi
"Dadina da ke kishinki baya buya"
na ce "Ai ni wannan Rufaidar matsala za ta zame min matukar Ahmad na tare da wannan"
ta ce "Ai ba ki bari na kai maki karshe ba dear na ke gaya min Dr ya ce zuwan da kika yi kika same su ba karamin taimako ya yi mashi ba, dan dama neman hanyar rabuwa da ita cikin salama yake baya san su yi rabuwar baran baran dan saboda kaunar da ta nuna mashi baya san wulakantata". Ajiyar zuciya na fidda sannan muka ci gaba da maida zancen, wuni zungur muka yi mata.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: CANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE
Malumfashi
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
23
Sai da Junior ya yi wata hudu sannan na samu ya barni na tafi Malumfashi, a lokacin kuma har ya iya zama. Sannan ne aka sa bikin Husna da Sagir ɗin ta watanni bakwai masu zuwa, dan wata biyar ne ya rage mata ta kammala karatunta,
Sanda Junior ya cika shekara ya yi daidai da tura Ahmad America za su yi bincike kan wasu cututtuka, ba kaɗan yaso tafiya da ni ba nima haka, sai dai ba halin yin tafiyar ta mu tare ga bikin Husna da ke zuwa Momi ma cewa tayi idan muka tafi duka shi ba shi ni bani, nima kam ba zan so a ce bani a bikin Husna ba duk da na san ba karamar kewa zan yi ba ta rashin shi tsawon watanni bakwai zuwa takwas, na dai hakura, sai dai hakan bai hana ana gobe tafiyar shi na tasa shi nayi ta mishi kuka ba, tun yana rarrashina har ya rasa yanda zai yi dani sai ya sa min ido ya ce
"To ko daga tafiyar zan yi har sai an maki biza sai mu tafi tare?
na girgiza kaina ina share hawaye da bayan hannu "Na hakura sai dai ina tuna tsawon watannin da zan kwashe a gidan nan ba ka".
ya janyo ni ya kwantar sai ya kwanta rigingine ya dora kaina saman kirjinshi, kalamai masu dadi yake gaya min, har na ji na dan samu nutsuwa, daga lallashi abu ya zarce wanda al'amura masu tsayawa a rai suka faru tsakanin mu a wannan dare.
Duk da gajiyar da na ke ciki bai hanani tashi da safe na shirya mashi breakfast, sai da na ajiye komai inda ya kamata sannan nayi wa Junior wanka na shirya shi, wanda lokacin ya fara tafiya, na kai shi wurin Baba na dawo wajena dan in yi nawa shirin,
gyara kaina nayi na fito cikin kamshi na musamman, material na sa dinkin doguwar riga,
na same shi yana cin abinci, tunda na fito idansa na kaina har na ja kujera na zauna tafi nayi da hannayena ya dan ja ajiyar zuciya na ce
"Ya dai Yallabai?
ya ce "Tunani, anya zan iya tafiya in bar ki"
"Akwai ka da san maida zance baya na samu na rarrashi zuciyata za ka kuma jagula min ita".
Ya ce "Tuba nake madam dina, kin yi min kyau fiye da kullun".
dan murmushi nayi sai banyi magana ba na fara cin abinci yana tanbayata Junior
na ce "Yana wurin Baba"
ya ce "A kawo min shi"
na mike sai nayi wa Ma'u magana ta amso shi ana kuma kawo shi ya fara halin nashi na barna na ce "Ka ga irinta ko da ka kyale shi sai mun kammala".
mikewa ya yi da shi a kafadarshi ya ce "Ki hanzarta dan zan biya ta gida"
na ce "To"
takalmi da jaka nasa sai abaya na rufe jikina da na fito na samu har ya zauna a mota shi da danshi ga ma'aikatan gidan sun taru yana masu sallama har Baba tana wajen na matsa kusa da ita ta ce "Ubangiji yasa aje lafiya a dawo lafiya, Allah yasa a dace da abinda aka je nema, gaba salamun baya salamun.
nayi murmushin jin zancenta na karshe na ce "To Amin Baba"
na shiga baya kusa da shi, ya amsa sallamar ma'aikatan na shi da dinbin alheri da ya bi kowannen su da shi.
Direba ya ja motar muka isa gidansu, kowa ya yi mashi fatan alheri, muka fito da Najib da Farhan da ummi da Abakar suma za su yi masa rakiya, suka biyo bayanmu a motar Najib.
Wayarshi ta shiga kara ya daga jin maganar da yake na gane da Abdullahi suke waya
Sai dai mu hadu a air port dan har na fito na ma biya gida na sallami su momi"
ya dan saurara "Ok thanks " ya maida wayar inda take,
hannuna ya kamo ya rike cikin nashi ya kira sunana na amsa tare da kara nutsuwa dan sauraronshi ya ce
"Nayi niyya bana ni da ke zamu sauke farali, sai ga wannan tafiyar da ta same ni, dan haka kujera daya a baiwa mama, dayar kuma cikin babannin gidanku waye ya ce ma Abba an bani ke?
kallonshi nayi Baba Ya'u ne"
to sai a ba shi dayar "
Saboda tsabar murna ban san sanda na haye cinyarshi ba,
ban ankara ba ina ta munata sai da na ji ya cire min abayata na ce "Kai lafiya?
Ya ce "Ita ta kawo haka, ba ki san sanda kika hayeni ba?
cigaba ya yi da abinda yake yi dan har idanuwananshi sun soma sauyawa "Ke kuma da Momi za ku je umara idan ya rage two weeks sallah"
a kunnanshi na rika rada ma shi tsantsar farin cikin da ya sanya ni.
da muka isa sai da na goge mashi jambakin da na manna mashi a kumatu muka fito dan glass din motar tinted ne, na sha mamakin dinbin abokan shi da suka zo wurin karkashin jagorancin Abdullahi, bin su dai dai ya rika yi yana masu sallama hade da godiya, Junior na kafadarshi aka fara kiran matafiya ya zo inda nake tsaye ya miko min Junior feck ya bani a kunci "Ki kula da kanki, ki tsare min kanki, muyi wa juna fatan alheri, sai Allah ya dawo dani".
Ina share kwallar da ke taho min ina mashi Addu'a ya wuce mu ya shiga jirgi yana daga hannu.
Abdullahi ya karbi Junior motarshi ya sanya shi, ya ce zai kai shi wurin Al'amin su yi wasa sai yamma zai dawo da shi.
kai na daga mashi ba tare da nayi magana ba, na wuce motar da muka zo ciki, idona nata zubar hawaye, mun kusa gida na ji shigowar sako a wayata na duba wayar Ahmad ne zantuka masu sanyaya rai ya turo min, sai ga shi ina kuka kuma ina murmushi.
Muna zuwa gida dakina na wuce na hau gado kwanciya nayi rub da ciki, wunin ranar sukuku nayi shi.
Da yamma Abdullahi ya maido Junior tare da kayan ciye ciye da na wasa, ko da na bashi nono kamawa daya ya yi ya saki ya kama wasanshi a zuciyata na kudurta yaye shi, dan dama ba wani damuwa ya yi da shi ba ya fi san ya ci abinci kamar ba shekarar shi daya ba.
Dawowar Husna sati guda kacal da tafiyar shi na wartsake, dan kwananta guda a gidansu naje na tarkatota muka yo gidana tare muke komai da ita dan wai yanzu take son koyon girki, ana son burge oga Sagir.
Shirye shiryen bikin duk a gidana muka yi, kasuwa na shiga nayo mata sayayya ta makudan kudade.
Ana saura sati biyu bikin Aunty Kubra ta iso,
an sha shagalin biki irin na yarinya yar gata, me dinbin wayewa da tsagwaron ilimi, tare da dan da duniya ke yi da shi ta fannin abin duniya.
Komai a wurin bikin tare muke gudanar da shi da Khausar har mamanta ta zo, su yayarmu ma sun zo ita da ummu da kakarmu Haj, Yusuf ma ya zo daurin Aure, anan suke gaya min Innarmu ta ba yayarmu Azima kujerar makan da Ahmad ya bata, shi kuma baba wai zai zo godiya, na ce su gaya mashi ya hutar da kanshi, me kyautar ma baya kasar.
A legos aka ajeta.
Bayan gama bikin da kwana bakwai aka fara azumin Ramadan.
Sallah saura sati biyu muka wuce umara da Momi Junior yana wurin Baba,
ranar sallah muka dawo, tunda muka dawo nake kwance dan tun a can nake fama da matsanancin zazzabin dare daurewa kawai nake, ga kasala sam bana jin karfi da kaina na fahimci ciki ne dani dan nayi missing period dina tunda ogan ya tafi ban yi ba, text na tura mashi a take ya kira yana son in tabbatar mashi da gaskiyar maganar, na tabbatar mashi da gaske nake, ya umarce ni in je asibiti kar in sake in ta kwanciya na ce mashi "To"
Wani hantsi ina zaune a falo wa'azin Dr Isa Ali fantami nake kallo ina kuma saurare, jikina duk a mace yake murus dan wa'azin tashin alkiyama yake da aikin da ke gaban dan Adam,
Sai sallamar makociyata Zainab na ji na daga kai ina amsawa tamu ta zo daya, muna matukar mutunci,
"Manya manya karaso mana". na fada ina rage karar da remote din da ke gefena , ta zauna tana dan murmushi
"Wash! wallahi duk na gaji"
kallonta nayi "Me kika yi ya gajiyar da ke?
Form na je saye, direba ya fita shan mai na kasa hakurin jiranshi sai na tafi, kinsan ana dan wahalar man fetur ga zafin rana".
Na mike zuwa kitchen ina tanbayarta "Form dinme kika je sawo mana?
Na dawo da lemo da ruwa hada kofuna akan faranti, na ajiye mata na karbi form din a hannunta ina dubawa
ta ce "Tallar wata makaranta na gani cikin wata Magazine, Course ne kan harshen turanci tsantsa akwai tsada amma akwai biyan bukata, mallakar wasu masu jajayen kunnuwa".
na ce "Turawa kenan" ta daga kanta "Kwarai kuwa, saboda wannan kishiyar tawa nake son yin karatun, kin san ma'aikaciya ce"
kallonta nayi sosai, "Kamar ya?
ta ci gaba tana kai lemo bakinta "Ita da yaranta yan rainin wayo ne, wai su masu ilimi, tun ina karama mahaifina ke da burin ganin na yi ilimi me zurfi kasantuwata yar shi ta farko amma na sa shiririta na ki a shiririce na kare karatun sakandire, saboda rashin kyawun sakamakona dole sai da na maimaita shekarar in takaice maki sau biyu ina sake zana waec da neco duk bata canja zani ba babana ya yi fushi ya rabu da ni, sannan ne babansu walida ya fito neman aurena, ba a dau lokaci ba babana ya ba shi ni, shima farkon aurenmu babu yadda bai yi da ni ba in yi karatun naki fafur, sai yanzu na ga yadda idan muka hadu da kishiyar tawa take min salo yasa nake son karatun shi kuma ya hau dokin na ki. Wai sai yanzu ya gane ka dawo gida ka iske matarka ba abinda ya kai shi dadi,
dan ita ma'aikaciyar banki ce, shi ne da na ga wannan course din na makale ma shi da na ga wata shida ne kacal karshenta ya hakura ya bar ni in yi karatun idan ya ga a wannan din na bada himma. "
Jin tayi shiru yasa na dubeta cike da labarin da ta bani
"Ai ni Zainab banda ke da kanki kika gaya min haka da ba zan yarda ba dan ni aka ce min masters ne da ke yarda zan yi "
Yar karamar dariya tayi
"Saboda me?
"Saboda tsabar wayewarki da gogewarki"
ta ce "Ba mamakin hakan dan mahaifina ma'aikacin gwamnati ne, mun yi zaman garuruwa da dama, shima ogan me yawan tafiye tafiye ne, kuma ko'ina da ni yake tafiya ita bata samun dama saboda yanayin aikinta".
girgiza kai na yi
"Nima da Dr zai yarda ai da kin zo min da foam din na gaji da zaman kadaicin nan"
ta ce "Ki gwada sai mu rika fita tare"
ta kara kallona
"Kin fada sai dai kuma kin kara kyau"
yar harara na bata
"Kin manta azumin Ramadan muka kammala ga sittu shawwal na fara"
ta ce "Haka, amma ina sha sai da Dr ya dasa kwanshi ya wuce ya bar yarinya da aiki"
kallonta nake cikin mamaki ta mike tana dariya "Bari in shiga gida ruwa zan watsa in kwanta".
na ce "Farfesun yanciki na dora nasan kina so, ki tsaya" ta wuce tana cewa
"In kin kammala Ma'u ta kawo min" na rakata ta wuce na dawo.
Kullun sai Dr ya kirani dan jin yanayin jikina, ina son yi mashi maganar makaranta amma fargaba ta hanani, da kyar nayi kunar bakin wake sai na shaida mashi, ai fada ya rufe ni da shi har sai da na ba shi hakuri, na kuma tura mashi text ina kara ba shi hakurin bata mashi rai da nayi, na mashi bayanin gajiya nake da zaman gidan kadaicin rashin shi na damuna, Junior ma kullun momi ke aikowa a tafi da shi sai yamma a dawo da shi.
Har na manta da batun makaranta na cigaba da sabgar gabana, sai ga wani abokinshi a sanin da nayi mashi shi din lecturer ne ya kawo min foam din makarantar hada kudade in sayi hijabai in ji Ahmad, mamaki ya rufe ni.
Ba dadewa muka fara zuwa da Zainab, kwarai fitar da haduwa da jama'a ya dauke min kewar Ahmad da nake ciki, da kuma laulayin da ya sanya ni gaba.
Wata ranar asabar gidan Momi naje tana kallon yanda Junior baya barina sakat, ya haye ni ya yi ta tumurmusa ko kuma ya ce sai na goya shi, da muka tashi tafiya ya ce in dauke shi momi ta ce "Sauke shi, ki ma bar shi nan daga yau, ya barki ki ji da kanki, idan Allah ya saukeki lafiya ya dawo, Tunau zai zo zai amshi kayanshi. "
Kunya na ji ta rufe ni, sai na bar falon ganin da sauran lokaci gidan Khausar na wuce, jakata kawai na ajiye na iskota kitchen inda na ji motsinta, fridge na bude na dauki ruwa sai na zauna kan wata kujera da ke a kitchen din ta ce yar halas yanzu nake tunaninki, daga ina da yamman nan?
na ce "Daga gidan Momi, wai dama ana gane ina da ciki?
ta ce "Me ya faru?
na kwashe yanda muka yi da momi na shaida mata,
ta ce "Ai makaho ne kadai ba zai gane hakan ba, kin fa canja sosai da da farko ne kika yi rama sai kika yi kyau, yanzu kuma sai kika yi yar kiba me ban sha'awa, kallo daya za a yi maki a shaida hakan, ogan ya sani?
kai na daga mata tare da tanbayarta Al'amin,
ta ce sun fita da babanshi, kin kuwa leka shago?
na ce "Tun dai wani sati da na dawo makaranta sai na biya, sosai wurin ke ci gaba ai dace da samun mutum me amana ya tsaya maka kan harkarka ba karamin dadi ke gare shi ba.
murmushi tayi
na dan tura baki "Ai cikin ma da ke ya dace ba ni ba, kin fa huta. "
yar dariya tayi "Ba yanzu ba tukun, muna honey moon din da cikin shi bai barmu ba.
sai da na ci abincin da ta girka sai na isa gida.
A Kwana a tashi sai ga shi Ahmad ya kammala watanninshi, sai sa idon dawowarshi muke yi,cikina ya tsufa dan watanninshi takwas kenan na kammala course din da kwana shida ya dawo dirar ba zata ya yi min, dan bai sanar dani dawowar shi a ranar ba, zaune nake a falo ni kadai canjin Channel nake a talabijin, naji an rungumoni ta baya tsoro na ji ya kamani gabana ya fadi sai dai sassanyar kamshin da ba zai yuwu in iya manta mamallakinsa ba ya sani waiwayawa muna hada ido na kankame hannuwanshi da ya rufe min ido da su, zagayowa ya yi ya zauna kusa da ni yana dafe da ni ni kuma sai kallon irin kyan da na ga ya kara nake yi, sanye yake cikin suit bakake agogon police shima
baki daure a hannunshi, mun dade a wurin yana nuna min irin kewata da ya yi, kafin daga bisani ya mike tare dani zuwa bed room dinshi, ba yanda banyi ya bar ni in kawo mashi abinci ya ce
"In kyale abincin muyi abinda yafi abincin muhimmanci.
Dan haka kiran sallar magrib ya dawo damu daga duniyar da muka lula, cikin sauri ya zare jikinshi ya fada bathroom.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: CANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE
Malumfashi
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
24
Washegari muka je gidansu ya gaishe su sai muka taho da Junior, kwananshi ashirin da dawowa na haifi diyata kyakykyawa wacce ita da ubanta kamar an tsaga kara, tana fadowa ya ce Aminar shi ta dawo,
tare da shi muka yi haihuwar dan zan iya cewa shi ya yi komai muka yi tsaf ni da jaririyata, ko Baba Kulu sai da safe ta gan ni da baby dan ta dare ce, tayi ta kakkabi, "Ina gidan nan har ayi haihuwa ban sani ba? Tayi min fadan kar in sake mata irin haka na ce "To"
ranar suna yarinya ta amsa sunan Amina, ubanta ya hana in sake mata suna, ya ce in kirata da Aminarta.
Watanta hudu aka yi masa transfer zuwa babban asibitin Katsina, shi ya rigamu wucewa, satin shi guda da tafiya muka samu sakon haihuwar Anty Kubra, ta samu tagwaye mace da namiji, muna da zuwa New Delhi kenan zo ka ga murna wajena.
Sai dai Ahmad ya yo min waya in bari idan ayyuka suka yi masa sauki sai ya shirya mana tafiyar ni da shi, marairaice masa nayi ya bar ni in je ayi suna da ni, ta Lagos zamu tashi dab da haka saura kwana uku tafiyar na isa birnin Ikko ni da Aminata dan Junior Momi ta kuma karɓe shi, gidan Husna na sauka muka yi mata baƙunta na kwanakin kafin muka wuce.
Mun sha sunan yan tagwaye, inda aka bar su da sunan su.
Yan gidansu mata duk sun je, Rufaida bata sauya ba sai wani gani gani take min.
Mun sha yawo kasantuwar Husna ƴar gari, kwanaki goma muka share sannan muka yo ƙasar mu ta gado,cike da dinbin karamcin da Aunty Kubra ta yi mana ita da mijinta.
Muna dawowa Ahmad ya zo dan mu wuce ban so haka ba na so sai na je Malumfashi tukuna,dan har lokacin ban tafi ba tunda na haihu,
Mun yi parking din kayan amfaninmu daga ni sai shi a motar, direba kuma na janye da baba kulu da ma'u.
Na samu gidan me kyau,wanda aka ƙayata da kayan alatu,ya ji komai na more rayuwar ɗan adam,
duk da dai bai kai gidanmu girma ba.
Ban haɗa wata ba sai da ƴan gidanmu suka yo mota guda dan ganin inda na dawo,
Junior dai ya zama na momi dan har an jefa shi play group ta ce Amina ma da ta isa yaye da nan na bar mata ita.
Muna makotaka da wata Rabi mutuniyar kankiya mijinta ne dan Malumfashi, mun so juna ni da ita, ni dai ina sonta saboda mace ce me tsoron Allah, da san gaskiya, duk wani abu na sabon Allah za ka ga tana kyamarshi,
tana da kamun kai ƙwarai, yaranta biyar,
ita tayo min Register a makarantar islamiyar da take zuwa,muka riƙa tafiya tare,ina jin daɗin makarantar dan ina ƙaruwa sosai.
Wani hantsi ina zaune a falona ni da Yusuf,ziyara ya kawo min karon farko tun dawowata Katsina,
Ahmad baya gari yana Abuja, kasantuwar ƙarshen mako ne kuma ma dai a ɗan datsin nan duk weekend sai ya tafi saɓanin da da sai ƙarshen wata muke tafiya tare, yana cinikin wani fili wanda ya ce min yana son fara ginin asibitin shi ta kanshi,
idan ya kammala zai ajiye aikinshi sai ya rungumi tashi, riƙe yake da Amina wadda ke ta ƙoƙarin cire mashi glass din idonshi, na ce "Da ka ajiyeta ka sha lemon ba ta ji,ba za ta barka ba."
Ya ce "Haba kyaleta ai ni daɗi na ji da bata yi min ƙyuya ba, dan sabgogina basu bari ta san ni ba"
na ce "Ai kuwa kayi wuyar gani na je Malumfashi ya yi sau uku amma ban gan ka ba, sai innarmu ta ce min kana Kaduna,ni ina ta murna da Ummu ta ce min takardunka sun yi kyau sosai,ina cewa sai aiki, sai kuma na ji shiru".
dan tsaki ya ja
"Kin san komai kyan sakamakonka,sai kana da ƙafa,sha'anin ƙasar ne wa ka sani wa ya sanka ake yi,nayi fafutukar neman aikin har na gaji sai dai alƙawuran da aka yi min, Akwai wani abokina Sabi'u shi ya ce in zo muje Kaduna mu riƙa zama shagon yayanshi, dan shi tun gama Sakandire ɗinmu ya koma wurin yayan nashi,sai da ya tanbayi yayan ya ce Ba matsala ya zo da ni, kin ji yanda aka yi na koma Kaduna kuma Alhadulillahi na gane Kasuwanci na kuma san jama'a ina kuma samu gwargwado dan yayan nashi ba shi da mugunta,ciki har nayi wa innarmu aike, duk da cewar da take in sauƙaƙe wa kaina ba abinda ba ki yi mata".
Sai da ya ci abincin rana ya yi sallar azahar muka gama firarmu, sai ya yi haramar tafiya, ɗaki na shiga na fito da wayata, sai nayi mashi transfer,
jin shigowar sako ya ciro
wayar shi yana
dubawa,cikin rashin
fahimta ya ɗago yana
dubana, "Na mene ne
waɗannan makudan
kuɗaɗen da kika turo
min ?
Na ce "Ka yi amfani da su,kayi naka jarin, Allah
ya sanya albarka a ciki".
kallona ya yi cikin sauri
"Kin kuwa san nawa kika sa Shuhaina? kuɗaɗen suna da yawa fa"
Na ce "Na sani,fatana Allah ya sanya maka albarka a ciki".
godiya ya shiga yi min har na ji kunya.
Ahmad bai kai ga dawowa ba ya yi min waya an kammala cinikin,ya ma bari sai an sanya harsashin ginin kafin ya bar garin.
nayi murna ƙwarai tare da yi mashi fatan alheri,domin samun wurin ya ɗan ba shi wahala saboda yanayin wurin.
Rayuwa ta ci gaba da tafiya wanda tuni na yaye Amina,momi ta zo ta tafi da ita,daga ni har babanta rashinta kusa damu ya taɓa mu,dan yana matuƙar santa,muddin yana gida bata ƙara kallona, komai shi zai mata,baya taɓa gajiya da hidimarta ko wajen kwanciya tare suke tana manne da shi.
Ranar wata talata misalin ƙarfe uku da kwata na rana ogan ne ya shigo ina zaune kan carpet ina cin abinci,ɗago ido nayi na kalle shi tare da yi mashi barka da zuwa,na rage ƙarar TV, dubana ya yi yaya dai maman twince ba ki tanbayeni minata ba?
ɗan murmushi na yi sai ban yi magana ba,
ya ce "Na samu har ta zama ƴar gida,ta ƙwace wa junior fada har a wurin Abba,kowa zai fita ita ce ƴar rakiya,har mamaki ta bani tana tare da ni daga ganin Abba zai fita ta gudu wurinshi ta barni."
na ce "Ka san bata da wuyar sabo ko makaranta na je da ita ba a barina da ita sau da yawa sai an tashi zan amsota"
ya dai girgiza kai yana shafar sumarshi "Ina ruwan Minata"
ɗan lumshe idanuwansa ya yi ya watso min
"Albishir"
na ce "Goro"
ya ce "Wancan satin da ya wuce wani tsohon class mate ɗina a turai ya same ni yake gaya min mahaifinsa yana nemana,da naje sai mahaifin nasa yake gaya min contract yake son bani na shigo mashi da kayan aiki,dan ya gina ma ƙanwar abokin nawa asibiti,dan jin daɗin yadda ta tsaya tayi karatu saɓanin ƴaƴan shi maza da dukkan su ƴan shiririta ne,shi kuma harkokin shi sun yi mashi yawa bashi da lokacin bincike da tsayawa a shigo da abubuwan, da kanshi yake ce min ƴaƴan shi maza duk sun ƙi karatu sai dai su shiga cikin dukiya su yi ta facaka.
Ya ce "Ai kin san Alh Shuaibu me kadara?
na ce "Ina dai jin sunan shi a Abuja ko?
ya ce "Haka ne, amma mutumin Katsina ne uwargidan shi ke zaune katsina amaryar na Abuja tare da shi,ya shahara ƙwarai fannin dukiya sai dai rashin sa'ar ƴaƴa , abokin nawa tun rabuwarmu a makaranta sau biyu na ƙara haɗuwa da shi.
ajiyar zuciya na fidda nayi mashi fatan alheri.
Sati biyu tsakani muka bar ƙasar zuwa ƙasar China inda ya turo na'urorin, watanmu guda cif muka dawo,
Ahmad ya kashe min kuɗaɗe fiye da zatona
har na nuna mashi abin ya yi yawa,shafa kaina ya yi "Yarinya kin kuwa san miliyoyin da suka shige account ɗina?
girgiza kai nayi tare da cewa"Allah ya sanya ma abinda aka samu albarka"
ya ce "Yawwa kin ji abinda za ki ce"
A Abuja muka sauka sai da hutun da ya ɗauka ya ƙare sai ya koma ni na zauna sai da muka sha sunan Khausar wadda sai yanzu tayi wa Abdurrahim ɗinta ƙane.
Wani dare muna kwance wayar Ahmad ta hau ƙara, ɗaukarta ya yi tare da saurin yaye bargon da muka rufa, zaune ya tashi ina ganin tunanin shi nayi barci, ƙara lafewa nayi muryarshi ta ratsa dakin
"Wai ba ina hana ki wayar daren nan da kike yowa ba?
ɗan sautin dariya ya fito ta wayar
"Ran Dr ya daɗe tuba nake,amma meye laifina?
ya ce "Amma kin san a halin yanzu ina tare da iyalina,
yar dariya ta ƙara yi
"Kai dai ba ka da zance sai na wannan ƴar katsinawar taka,kamar daga ita babu sauran mata, lallai ta iya shafta dan ta samoka da yawa"
cikin gajiya da zancen za ka fuskanta daga muryarshi ya ce "Ya isa,idan kuma zancen matata za ki yi min idan kin kira to ki daina kiran dan ni ba sakaran namiji ba ne ".
cikin lanƙwasa murya ta shiga ba shi haƙuri, kashe wayar ya yi yana jan tsaki,ya dawo ya kwanta lamo na ƙara yi cikin tunani,dan tunda muka dawo ba daɗewa ya fara samun wayar dare kuma baya amsa ta gabana saɓanin da da zai ce in amsa idan yana wani aikin,kuma yana yawan fita idan ya dawo daga wurin aiki ba kamar da ba da idan ya shigo indai ba bukatar shi ake wurin aikinshi ba bai kuma fita,sai ko idan zamu fita tare dan akwai kyakkyawar mu'amala tsakanina da gidansu Abdullahi ina kai masu ziyara,
Ƙwaƙwalwata ta cika da tunanin to wannan wace ce?
kuma meye tsakanin su?
na daɗe barci bai ɗauke ni ba ba tare da na gano amsar tanbayoyin da suka cika min kwanya ta.
Sati guda da yin haka muna zaune da safe,wayarshi ta shiga ƙara ya ɗauka ya duba,fuskarshi ta washe da murmushi Hello ya kike?
ya faɗa yana wani lumshe ido , zuba mashi ido nayi dan na lura ya shagala ƙarshenta ma ya manta dani a wurin, "Yanzu zan fito, ok to ki ɗan jirani,bani 20minute zan iso in sha Allah"
Ya kashe wayar ya miƙe ya gyara zaman rigarshi, ya ɗauki breaf case ɗinshi kaina yana sunkuye ya ce "Na wuce"
A dawo lafiya na furta ban ko ɗago ba, a gurguje ya bar wurin.
Na miƙe gwiwata a saɓule na leƙa shi ta window har ya tada motarshi zai bar gidan
ban san iya lokacin da na ɗauka zaune ba takaici na cin raina da na fara gane bakin zaren
tsaki na ja tuna ni kaɗai ce a gidan bare in samu wanda za mu yi fira in rage zaman ɓacin ran,
Baba Kulu ta tafi garinsu jinyar ƴar ta da ke fama da rashin lafiya.
Bed room ɗinshi na shiga na gyara komai tsaf na fito na ƙwala wa Ma'u kira,ta iso cikin hanzari
na ce "Ki gyara kitchen da falo har zuwa bathroom ni zan shiga wajen maman Ihsan (Rabi) cike da ladabi ta amsa na wuce.
Ina zaune ɗakin maman Ihsan tana min fira,sai dai rabi da rabi nake fahimtarta har ta ƙare ta taɓa ni "Wai yaya ne maman twince ko har an fara tunanin labon?ƴar dariyar yaƙe nayi sai na miƙe "Haba dai, bari in je gida, ta ce "Tun yanzu? Na ce zan yi girki ne ta raka ni get, sai da na kammala girkin sai na sha wanka na ɗanɗasa kwalliya ina jiran Dr. Tunani kala kala nake yayinda nake zube mai da ido shi kuma yana cin abinci,ɗaga ido ya yi shima ya duban
"Yaya dai Shuhaina? Na ɗan narke fuska "Ka ce idan ka dawo zamu fita in sayi kayan kwalliyata dan saura kaɗan komai nawa ya ƙare". Ki yi haƙuri ina da appointment idan na samu lokaci sai muje." Ya goge bakin shi da tissue dama ya kammala sai ya miƙe "Bari in yi wanka" ya wuce ni na bi shi da kallo.
Ƙarar da wayarshi ta ɗauka ne ya dawo da ni hankalina hannu na kai na ɗauka Yasmin me kadara shi ne sunan da ke yawo kan screen ɗin, kamar in maidata inda na ɗauke ta amma zuciyata ta ƙi bani goyon bayan hakan, sai na samu kaina da ɗagawa "Hello Honey ina ta jiranka muyi lunch, kai fa ka ce idan ka tashi daga office nan za ka wuto mu fita tare. Ba zai yiwu in manta da mamallakiyar wannan zazzaƙar muryar ba, wadda tun da na soma jinta na kasa samun kwanciyar hankali. Latse wayar nayi na maida ita inda na ɗauke ta, kasa haƙuri nayi na kuma ɗaukota ɓangaren received call na shiga kiran da ake mashi da dare na ta ne na koma WhatsApp ai ji nayi kamar zuciyata za ta tarwatse dan wasu fitinannun text text da take tura mishi,kasa ci-gaba na yi da binciken wani kiran nata ne ya kuma shigowa na kashe wayar gaba daya na maida ta na aje tagumi na rafka da hannu bi biyu, fitowa ya yi cikin wata ɗanyar shadda army colour sai masƙi take ɗinkin half jamfa, bai sa hula ba sai kyakkyawar sumar shi da ke ta sheƙi shaidar ta sha gyara, agogon hublort ɗaure a hannunshi,fitinannen ƙamshinshi me narkar min da zuciya ke ƙara cika hancina,idan na ce ya yi kyau ya haɗu ƙarshe zai zama kamar ma ina ɓata bakina ne.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: CANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE
Malumfashi
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
25
Feck ya bani a kunci, ya shafi cikina "ina zuwa Shuhaina" ban samu ikon motsa laɓɓana ba ya wuce ni cikin sauri, bayan ya ɗauki wayar shi, ban an kara ba sai dai na ji hawaye na bin fuskata.
Bai shigo ba sai bayan isha'i. Tun daga ranar sai na tsangwami kaina ba hali in ga zai fita sai zuciyata ta raya min wajanta za shi,nayi nayi in kauda zuciyata kan abinda bani da ikon hanawa amma na kasa.
Ranar wata asabar kasantuwar ba aiki,Ahmad ji da ni yake tun safe muna ɗakinshi girki ma yana tare da ni nayi,ƙarfe uku ya dubeni
"Idan muka yi sallah sai mu fita kiyi shopping ɗin ko? ɗaga mashi kai nayi,
dan haka sai da muka sallar la'asar ɗin sai na sheƙa kwalliya,dan in ƙara janye hankalin shi, wani ƙanƙararren less na sa me ruwan hanta yana da duwatsu,na sa sarƙa da ƴan kunne na English gold,cikin irin waɗanda Ahmad ya saya min a China hannuna bangul ne sai ɗayan na sa agogo,wata haɗaɗɗiyar after dress na ɗora sabuwa dal,ga ƙamshi me sanyi ina yi mara tashi saboda sanin illar hakan,ƙamshin turarenshi na ji a bayana sai na waiwaya
"Oya fito muje" ya ce min,
yayi kyau cikin ƙananan kaya farar shirt ce da blue wando,sai na bi bayanshi.
Wani shopping mall muka je duk da ba yau ne farkon zuwanmu ba hasalima nan ne wurin zuwanmu idan za muyi sayayya irin wannan,wuri ya samu ya zauna na zagaya na zaɓi abubuwan da nake buƙata na iso wurinshi miƙewa ya yi sai ya biya kuɗin ta hanyar miƙa atm ɗinshi,muka jero yana riƙe min da ledojin,fira muke har inda ya ajiye motarshi gaya min yake
"Sai mun ƙara dawowa sai ki duba kayan sabon baby ko? sai da na dube shi sai na ce "Ka san Khausar ta fita mana sari nayi mata saƙo".
ya ce"Ok to ki yi min list ɗin kuɗaɗen da kika bayar sai in tura maki ta account ɗinki"
kai na ɗaga mashi,sai na ƙara waigawa inda wata matashiya ke tsaye jingine jikin wata rantsatstsar mota,tunda muka fito na lura da irin kallon da ta kafe mu da shi,haka nan na ji na tsargu da ita, buɗe min ƙofar ya yi na shiga sai da na zauna ya rufe ya zagaya ya buɗe ƙofar kenan daga bayanshi aka riƙa faɗin
"Ran Dr ya daɗe"
gaba ɗaya muka waiwaya,take na samu faɗuwar gaba,matashiyar da ke kallonmu ce doguwa ce fara wadda tsawonta ke tafe da jikinta,
daga ganinta ka ga gogaggiyar ƴar boko,wayayya wadda hutu ya ratsa,sanye take da riga da siket na atamfa kayan sun kamata tamkar tana yin tari zasu kece,sun tona asirin komai na halittar jikinta,
gabanshi ta tsaya tana wani rausaya jiki yanda take da ido ma kaɗai ya isa ban al'ajabi.
"Yaya dai Yasmin?
ya ce yana kallonta ta haske shi da wani ɗan iskan murmushi
"Shopping na zo yi mu shiga ciki mana".
kanshi ya girgiza
"Ina tare da madam ɗina,
ki leƙa sai ku gaisa".
ya leƙo "Shuhaina ga Yasmin me kadara,me asibitin Yasmin Hospital.
Gaisuwa muka yi kowa kamar bakinshi na ciwo
dan ni tun ban gan ta ba ina tsananin kishin muryarta me zaƙin tsiya.
Ya shiga ya yi wa motar key duk yadda yaso ja na da magana zuciyata cushewa tayi na kasa furta mashi komai,da muka isa ɗaki na shiga nayi ta kuka a haka ya shigo ya same ni ya yi tanbayar duniya me ya same ni na ƙi magana,har ya gaji ya ja min tsaki ya bar ɗakin.
Tun daga nan zaman mu ya ɗauki wani irin salo
na daina zuwa ɗakinshi shima bai nema na, kwata kwata ya ma daina zaman gidan,
A haka wani zazzaɓi me zafi ya kamani sai da na kwana na wuni sannan ya sani ya kula da ni ya bani temakon da ya dace a matsayin shi na likita amma duk da tsayuwar shi sai da na shafe sati biyu ina fama da jiki kafin Allah ya kawo min sauƙi,sai dai duk na lalace ban iya cin komai in ba dangin fruit ba,tunda yaga na samu sauƙi sai ya koma fitarshi.
Wani dare ina zaune tsakiyar gado na rasa yanda zan yi barci ya ɗauke ni,hawaye ke sintiri bisa fuskata ina sharewa da bayan hannuna,na ƙara kai idona bisa agogo, ƙarfe sha biyu saura minti goma na dare,komai ya yi tsit duk da dai dama unguwar koyaushe shiru take,har sannan Ahmad bai dawo ba,duk da dai tun sauyawar al'amuranshi ya fara kai dare bai taɓa kai sha biyu ba.dirin mota na ji da ƙyar na cicciɓa na sauka gadon saboda nauyin cikin da ke jikina na yaye labulen Ahmad ne ke shigowa na tsaya har sai da na ga ya kullo ko ina,
na kwanta hawaye na cigaba da tsiyaya min.
Bayan kamar wucewar minti arba'in na ji an murɗa ƙofar ɗakina,ƙara runtse idanu nayi dan na riga na gane ko waye turarenshi ya riga ya yi masa iso,ko ƙwaƙwƙwaran motsi ban yi ba har ya hayo gadon ya kwanta gefena,wanda na rasa dalilin hakan,dan rabon da ya zo ɗakina an kwana biyu.
Wayar shi ta shiga ƙara ya ɗaga gane da wacce yake magana yasa hawayena ya ƙaru,sun jima suna magana kafin suka yi sallama,ya shiga barcin shi,
ni dai ban san iya lokacin da na kwashe idona biyu ba.
Da safe sallah kawai nayi na koma gado barci na samu nayi har sai goma na tashi,na shiga wanka na fito na shirya kaina cikin jallabiya baƙa me gajeren hannu sai na shiga kitchen neman abinda zan ci,ban hango motar Ahmad ba,da yawan lokaci sai in ta ganin kamar ba shi bane wanda ya nuna min tsantsar so da kulawa amma yanzu kamar be sanni ba,na daɗe a kitchen ɗin kafin na fito,
Ƙarfe sha ɗaya Yusuf ya zo gaishe ni ba ƙaramar murna nayi da zuwan shi ba musanman yanda na ga ya canza dama ga shi kyakkyawa da gani ya samu hutu dan mun daɗe bamu haɗu ba,
shi kuma sai tanbayata yake wane irin ciwo kika yi kin ga yanda kika koma?
murmushi nayi "Ai na ma murmure"
muka shiga hira yana gaya min shagon da ya buɗe na sayar da kayan masarufi ya karbu sosai har ya sayi mota Honda Civic mai ƙofa ɗaya,na leƙa na gan ta nayi mashi addu'a ya ce kuma kamfanin jaridar New Nigerian da ya nemi aiki da su sun neme shi dan ba shi aikin zai tsaya a fannin computer ne dan ita ya karanta,
na taya shi murna.
Muna ta hira har na manta da halin da nake ciki ina yi ina duba girkin da na ɗora,ƙarfe ɗaya na kammala sai da ya fita zuwa masallaci nima na shiga ɗaki na yi tawa sallar ina idarwa hannuwana sama ina gayawa Ubangiji matsala ta tare da neman ɗauki daga gare shi, wayata ta hau kuka na miƙa hannu na ɗauka Ahmad ne
"Hello Assalamu" alaikum" shi na furta cikin sanyin murya,ya amsa sai cewa ya yi "Kar ki ga shiru ban dawo ba,aiki ya tsare ni".
na ce "To abincinka
fa?ko in ba direban su maman Ihsan ya kawo maka?
"No ki bar shi kawai,sai na dawo ko?
ya katse wayar
wani abu na ji ya tsaya min ƙwafa nayi na zuba ma wayar ido,abincin ma za ta fara janye shi ta hana shi cin nawa, "Allah ka kawo min agajinka" na faɗa ina miƙewa tsaye jin motsin Yusuf a falo
na gabatar mashi da abinci na zuba nawa, kallo ya bi abincin da shi "Dole ba za ki warware da wuri ba ai ba ki cin abinci".
Murmushi nayi sai na ƙara,ban ankara ba na ci fiye da zatona,da muka kammala ma'u ta kwashe kwanukan.
Tsayuwar mota muka ji na miƙe na yaye labulen sai na leƙa Aunty Luba ce yayar Ahmad sai Rufaida sai ƙanwarta Ummi ke fitowa daga motar,dama duk family ɗin su sun zo su kaɗai ne basu zo duba ni ba, har Husna ta zo daga Lagos.
Suka shigo ina ta masu maraba,ni da Ma'u muka cika masu gabansu da abinci da abin sha,
sai da suka yi sallah sannan suka fara cin abincin, Aunty Luba tana ta faɗin irin ramar da nayi, Rufaida dai abun na nan sai shan ƙamshi take,Ummi ma miskilar ce ba ta ƙara magana ba tun da ta gaishe ni.
A raina ina ta kakkaɓin abin, Haj Babba ita ce miskila magana ma wuya take mata, amma ƴaƴan ta ba wanda ya ɗauko ta duk ƴan faran faran ne, ita kuma Haj Asma'u Aunty Amarya da take da fara'a ƴaƴan ta duk ƴan shan ƙamshi ne.
Yusuf ya ce min zai wuce na raka shi har gaban motar shi kuɗaɗe na ba shi ya kai ma Innarmu da babannina,na ƙara mashi addu'a,sai muka yi sallama ya wuce,na dawo wurin baƙina sallar la'asar kawai suka yi suka ce za su wuce,
na ce "Kai Aunty na sha kwana za kuyi min,ga shi ko Ahmad ɗin ma baku gani kuka gaisa ba"
ta ce Jirgin yamma za mu bi,Ahmad kuma mun ta try ɗin nombarsa bamu same shi ba,ai weekend ɗin da ya wuce da ya shiga Abuja ya je gidana,idan ya dawo ki gaishe shi Allah ya ƙara sauƙi".
na ce "Amin na gode, ina zuwa na shiga gidan maman Ihsan na roƙi babban ɗanta ya zo ya sauke min su a airport,sai ya dawo min da motar hakan aka yi.
Da daddare da Ahmad ya dawo ko duba dinning ya yi ya ga wayam sai ga shi ya biyo ni ɗaki,
"Ina abincina?
na ce "Ban yi ba"
ya ce "Meye dalili?
na ce "Na ga na rana ma ka ce a bar shi so ban yi tunanin za ka ci ba".
ya ce "Zo ki bani na ranar dan yunwa nake ji".
na ce "Su Aunty Luba da Rufaida da ummi sun zo su na ba abincin da ka ce ba za ka ci ba"
Sai kawai ya rufe ni da bala"I,
ina sauraron shi har ya ƙare ban ce komai ba sai share hawaye nake da zanen jikina,
me kuma ya gani sai ya zauna bakin gadon jawo ni ya yi jikinshi yana lallashi, "Gaya min me yake damunki? dan na san ba ciwon bane dan kin warware, ba ki sakin jikinki da ni a duk ƴan kwanakin nan why?
shiru nayi "To tashi mu fita mu samo abinda za mu ci, dan kema na san ba ki ci komai ba".
ya shafa cikin "Ko baby ai ba zai bar ki barci ba idan ba ki ci ba"
miƙar da ni tsaye ya yi, da kanshi kuma ya nemo min hijab kan dole na sa wani mr bigs muka je ya yi saye sayen kayan ƙwalam muka dawo.
Ni dai shawarma na ci sosai sai na ɗora fresh milk sosai nake jin kuzari hakan sai ya sa ni gane hada ƙin cin abinci da nake yake sa nake ƙara rafkewa, har a shinfiɗa ranar ya nuna min kulawar sa,wanda har na manta rabon da hakan ya faru tsakanin mu, addu'a ita na riƙe ina neman ɗauki wurin me duka bisa ga wannan al'amari dan na san ba halin Ahmad bane shaiɗaniyar mace ya haɗu da ita,ita take son wargaza min rayuwar aure, Kuma duk yadda raina ya kai ga ɓaci da yanda yake ko oho da ni ban iya tarar shi in ce zan faɗa mashi mara daɗi, dan ina ganin mutuncinshi rashin kulawar shi gare ni kuma na san sharrin shaiɗanun mata ne da Allah ya haɗa shi da ɗaya daga cikin su,
Ina nan dai ina faɗa wa Ubangiji kuma na san shi assami'u ne me ji kuma almujibu ne me karɓar addu'ar bayin sa.
Muna nan a haka har watan haihuwa ta ya kama, zuwa lokacin idan ba farin sani kai min ba me wuya ka shaida ni saboda yanda nayi duhu na kuma rame, ni da Ahmad sai ido tun ina abinci in ajiye mashi har na hutar da kaina ma'u na kan bari tayi,
abinda kan haɗa mu duba lafiyar cikina dan da farko samuna ya yi
wai yana so in fara awon ciki a Yasmin Hospital, dan akwai ƙwararrun ma'aikata da za su duba ni yanda yake buƙata"
duk yanda nake ganin girmansa bai hanani galla masa harara ba dan takaicin maida ni sakarai da ya yi na ce
In dai ka gaji da yi min awon saboda ka fara gajiya da haife haifen da nake maka ba wai laifinka zan gani ba, amma ba inda za ni wurin wata banza awon".
na miƙe nayi tafiyata
biyoni ya yi cikin tsananin mamakina dan bai saba ina musayar magana da shi ba, sai wani gaya min ya yi
"Ina tunanin wani abu ne kan Yasmin ?
mutunci ne kawai tsakanin su,kuma ma ai ba ita za ta riƙa min awon ba"
ni dai in kai da baka nan ka tanka to nima na tanka.
Wani yammaci ina ɗaki yana zaune falo suna firarsu ta waya, tunanin shi barci nake, ni kuma saƙe saƙen abinda zan yi in taimaki kaina nake,dan na gaji da wannan zaman ƙuncin har daga ƙarshe na samo mafita inda na yanke ma kaina shawara, har na ƙagara gari ya waye, tun da wuri ya fita wanda nayi murna da hakan,
yana fita nima na fita zuwa gidan maman Ihsan, a falonta na same ta "Ah maraba da amaryar Dr "ɗan tura baki nayi a dai dai lokacin da nake zama ƴar dariya ta yi "Satin nan kwata kwata ba ki ko leƙa makaranta ba,ga shi za a fara Exam" dubanta kawai nayi na ce "Ke ba ki san ko na je ba daɗin zaman nake ji ba" bayan mun ɗan taɓa fira na ce "Zuwa fa nayi maman Ihsan in roƙi alfarmar direbanku ya kai ni Abuja idan ba takura" saurin dubana tayi "Abuja da wannan tsohon cikin, ke kuwa me za ki yo? na ce "Na gaji da zaman nan ɗin,gara na koma can idan na haihu sai in dawo" ta ce "Shi ne ba za ki jira Dr ba? Na ce "Ƙyale wannan aikinshi ya yi masa yawa" ta ce "Ba damuwa mu fita sai in ma direban magana, amma zan yi kewar ki wallahi" muka fito tana ma direban magana na wuce gidana na ci gaba da kintsawa.
Tare suka shigo da direban ya amshi key ya yi gaba, Ma'u ta riƙa fito da kayan mu maman Ihsan ko sai maimaita Allah ya sauke ki lafiya ina nan zuwa.
Muka shiga ɗagawa juna hannu har muka ɓace ma ganinta.
Sai da muka tsaya aka yi mana juyen baƙin mai sai muka ɗau hanya.
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: CANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE
Malumfashi
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-1
27
Ta jeho min tanbayar,
ƙara duƙƙad da kaina nayi,
na fara kuka,a hankali kuma na zayyane mata zamana da Ahmad tun daga samun kwangilar shigo da kayan asibitin Yasmin.
Ajiyar zuciya me ƙarfi ta saki,jin na kai ƙarshe,
ta ce
"Ki ƙara haƙuri,komai zai wuce in sha Allah,babu abinda ya gagari Ubangiji, kema kuma sai kin dage kina tashin dare dan kai ma Allah kukanki,
Baba ƙarami ni na hana shi shigowa tun a asibiti,
dan an ta neman layukan shi a rufe,
sai a kira na ƙarshe ni ce na kira kuma na samu amma muryar mace na ji,
shi yasa hankalina ya ɗaga da na ji abubuwan da kike faɗi,
ki yi haƙuri"
Ta tashi ta fita,
na cigaba da kukana mara sauti, ƴan yarana suka dawo,
dole na bar kukan na riƙa sauraron shirmen su.
Da azahar Khausar ta zo suka haɗu da Husna suna min hira,
sai na samu sauƙin zuciyata,
tafiyar Khausar ba daɗewa na ji an turo ƙofar a hankali,
ɗaga kaina nayi Ahmad ne,ya zauna kusa da ni,
hannuna ya kamo ya riƙe cikin nashi,
mun daɗe shiru yana bi na da ido har na kosa da zaman shirun, gyaran murya ya yi
"Ki yi haƙuri Shuhaina,na rasa ta yanda zan ba ki hakuri dan na san ban kyauta maki ba,amma dai ina rokon ki da ki yafe min"
Ni dai share ƙwalla kawai nake,
har ya gama gaya min kalaman sanyaya zuciya,
Sannan ya ce "Da safe zan koma wurin aikina,
na san ko na biyo momi ba za ta bar ni ganinki ba,
kuma sammako zan yi"
Da ƙyar na furta ma shi
"Allah ya tsare"
ya tashi ya fita.
Bayan an yi sallar isha'i ina ɗaki,Momi ta ƙwala min kira,na amsa sai na fito,zaune na same ta tana sanye da hijab,
ita da limamin gidan,
me koyawa yaran gidan karatun addini,
shima yana zaune,
na gaishe shi,
sai na zauna kan carpet,
suka kare maganar su ina sauraren su,
yana gaya mata kar ta damu,in sha Allah wannan ba wani abin damuwa bane za a gaya wa Allah za kuma a nemi temakon shi,ita ma kuma ta dage da addu'o'in da ya bata,
nima sai na daɗa warwarewa zai bani addu'o'in da zan riƙa yi.
Momi tayi ma shi godiya ya tashi ya tafi.
Nima na koma ɗaki ina tunani ita momi gani take asiri ke ɗawainiya da Ahmad, sai ka ce ta manta halin mazan zamanin nan, iya shegen su ya girmi asirin,asirin ma ai hali yake taddawa.
Na cigaba da zama da momi,
cikin tsantsar kular da take bani,
Dr da ta karbi haihuwata ita ke zuwa har gida tana dubani,hatta abincin da zan riƙa ci sai da momi ta nemi shawarar ta,
nan da nan kuwa na wartsake nayi mulmul,
sai dai matsala ɗaya Ahmad tun daga zuwan nan bai kuma zuwa ba,
sai dai ya kan kira waya ita ma sai jefi jefi,
cikin tashin hankali momi tayi ma malam magana,
ya ce ta kara hakuri sai a hankali in sha Allah komai zai dawo daidai.
Nima ya bani addu'o'i muka duƙufa ni da momi.
Sai dai wani abu da ke ɗaure min kai,
Ummi ƙanwar Ahmad ƴar wajen Aunty Amarya da ta tare wajena,
indai tana cikin gidan to za ka same mu tare, da ta ga zan yi abu za ta karɓa tayi,
ko kayan sawa ta ita ke zuwa ta dauko min.
shiri sosai muke yi har nayi arba'in.
Abba ya ce wa momi ta kintsa ni in koma ɗakina,
daga na warware ba da san ranta ba ta ce "To"
Na roƙe ta ina son in tafi malumfashi tukuna,
dan na san hankalin innarmu yana kaina,
hakuri da kawaici ne kawai irin nata shi ya hanata zuwa ganina,
ba tayi musu ba sai ma tsaraba da ta shiga haɗa min,
Wani ƙarin mamaki sai Ummi ta ce za ta bi ni,
hakan kuwa aka yi tare muka tafi,hadda Junior.
Ummi ke raɗa min ita bata ga wannan yayan nawa ba da suka gani a katsina,
na ce "Yana Kaduna"
Dan halak ɗin sai ga shi ya zo washegari,
tunda ya zo ta karɓi girkin dare,ita ke yi dama ga ta gwanar shi,dan shi ta karanta,wanda ba ra'ayinta bane, mahaifiyarta ce ta matsa mata kanshi.
Da kanta take shirya abincin da Yusuf zai ci,
Wani dare take gaya min
ita fa Wallahi san wannan yayan nawa take,
tun ganin da tayi ma shi a Katsina ta rasa yanda za ta yi da ƙaunar shi,
dan haka tana buƙatar temako na"
Na daɗe ina juya al'amarin a raina,
na ga Allah kenan,shi babu ruwan shi,
duk girman gidan su,
da ɗinbin arziƙin babanta,
da sunan da ya yi,
ta zo cikin gidanmu
ta ga yanda yake kuma ɗan cikin gidan take so,
So kenan ba ruwan shi.
Ana gobe zamu bar garin, muna zaune da Yusuf,yana cin abincin rana,Ummi sun tafi gidan Ummu ita da Salma,
loma ya kai bakinsa ya tauna sannan ya ce
"Ina amfanin macen da bata iya girki ba,girki ai shi ne mace"
duban shi kawai nayi
"Ai fa kam yayana,to ko za ka shiga wurin me girkin ne? ka ga shi kenan ciki lafiya baka lafiya".
Saurin kallona yayi "Kin kuwa san abinda kike faɗi?
wannan ƙanwar mijin taki ai tafi ƙarfina
"A'a mace bata fin ƙarfin namiji sai dai idan baka san ta"
ya ce "Sosai take burgeni,sai dai tunanin ajin rayuwarmu ba ɗaya bane shiyasa nake yakice abin a raina".
na ce"Kar ka ji komai faɗuwar gaba ai asarar namiji, kuma a rashin tayi akan bar arha".
ya shafa sumar kanshi
"Ban ƙi ta taki ba, amma hausawa na cewa "Yaro tsaya matsayinka ka da zancen ƴan duniya ya ruɗe ka".
na ce "Kai dai ka jaraba,dan ga alamu da nake gani itama kamar hakan take"
da sauri ya ce "A haba?
na ce "Kai dai gwada ka gani".
Da ta a dawo ya aiko kiranta,ba wani ɓata lokaci ta ƙara gyara fuskarta ta fita.
Washegari da za mu tafi,tana motarshi,tamu tana gaba suna bin mu a baya,
sai da muka iso Kaduna sai ta dawo tamu,
a hanya har muka isa zancenta ɗaya ne Yusuf.
A harabar gidan direba ya yi parking,idona Ahmad ya gane min zaune kan motarshi,
daga kallo ɗaya da nayi ma shi ban kuma ba,
muka fito direba ya biyo mu da kayan mu,
na samu Momi ta fita,
sai Abakar shi ya shaida min hakan,ya zo daga Ibadan inda yake karatu,
Farhan dai mutumina Abba ya cilla shi malesia can ya maida karatun shi.
Ban yarda na zauna ba sai da na gaido mutanan gidan,
Sai bayan nayi wanka nayi sallah yara suka shigo ɗaya daga cikin masu aikin momi tana biye da su da ledoji,
haye ni suka yi suna bani labarin yawon da babansu ya kai su,
Sai ganin shi nayi shima ya shigo,
kallon shi kawai nayi na ƙyale shi,
ya riƙa tanbayata mutanen gidanmu,
mun ɗan jima ya ce "Idan kin kintsa ki same ni mota sai mu wuce gidanmu".
kallonshi nayi galala
"Gida kuma?
momi ma kuma bata nan" ya ce "Ki bar saƙo idan ta dawo sai a faɗa mata"
A raina na ce "Wannan ma ya maida ni wata shashasha
da mamaki na dube shi
"Ba za a yi wannan rashin ta idon da ni ba"
daga haka ban kuma bi ta kanshi ba,kan akwatin talabijin na maida hankalina.
Ba a jima ba momi ta dawo,tayi murnar dawowar mu,
na faɗa mata akwai tsarabar da aka haɗo min in kawo mata,
tayi godiya,
Ahmad ya faɗa mata buƙatar shi ta san tafiya da ni,
ɗaure fuska tayi ta ce ba yau ba,
bai ce komai ba ya tashi ya fita,
bai daɗe da fita ba Abba ya yi kiran momi a waya,
ta ɗan jima can sai ga ta ta dawo "Ki shirya ku tafi,
dan Alh ya ce bai ga dalilina na riƙe ma shi mata ba, dan ya kai ƙarata, na so a ce kun tsaya dan wani temako na amso maku ke da mijin naki hada ƴaƴanku na sammu ne sai ku tafi da shi, dama na so ku gama amfani da shi, zan ba ki sai ki wuce da shi".
Na amsa mata cike da ladabi tare da gode mata
bisa karamcinta a gare ni,
ta sallame ni ta ce in je in yi sallama da mutanen gidan, har Amina muka tafi ɗan ta ƙi zama fafur.
Baba Kulu tayi murnar dawowata, dan da ta dawo gidanmu ta sauka, sai da na kwantar da yara a ɗakin su,na tofe su da addu'ar da Manzon rahma kan yi ma Hassan da Hussaini ita ce (A'uzu bikalimaatillahi tammat wa min kulli shaiɗanin wa hamma wa min kulli ainin lamma)
na bar su na je na gama shirina na hau gado,sai da na tofe jikina da ayatul kursiyu da ƙulaƙuzai sai na cika da (Allahumma ƙi ni azabaka yauma tub'asu ibadika) yayin da na ɗora kaina kan pillow sai ga Ahmad ya shigo, sha'anin miji da mata duk haushin
shi da nake ji kafin safiya ya mantar da ni,
mu'amala me daɗi muke yi kamar da kafin shigowar Yasmin cikin rayuwar mu.
Sati guda ya share a Abuja,har sai da na riƙa tuna ma shi aikin shi,
ya ce"To ya zan yi da ke?
kin ce ba ki komawa Katsina ni kuma yanda nake jin kin koma ko na tafi ba wata moriya zan yi ba,an ya ina zargin ba wani shiri da Momi ta yi maki?
baki buɗe nake kallon shi,
"Abin kuma hada momi?
ka da ka yi wa momi,wane shiri kenan kake nufi nufi za ta yi min?
maganganun da ya cigaba da faɗi ne suka sa ni tashi sai na bar ma shi wajen.
Da zai tafi sai ga ni ina kuka,dan kishi ke cin raina kuma baƙin cikin da na ƙunsa a Katsina yasa zaman garin ya fita raina.
Ba a ɗau wani dogon lokaci ba Abba yasa ranar auren Yusuf da ummi sakamakon ƙaunar da ta sarƙe a tsakaninsu,
babannina suka zo nema ma shi auren, ni kuma na haɗa ma shi lefe na gani na faɗa.
Mun sha biki,ni dai saboda zirga-zirga bani Abuja bani Malumfashi bani kaduna inda ya ajiye ta, flat hause ya kama me kyau a unguwar dosa, kafin ya kammala ginin
filin da ya saya a kinkinau, sai da na kwanta bayan biki nayi jinyar gajiya.
Kammala bikin da sati biyu na gama shirina tsaf,cikin ƙananan kaya riga da siket na English wear,sashen me gidan za ni dan yana gari ya zo weekend,na zo daf da shiga wurin shi na tsinkayi muryar shi da shi da wani da ban gane ko waye ba,sai na ɗan dakata jin maganar da wancan ɗin yake yi,
"To yanzu dai ita ta ce duk wannan maganar a bar ta, in dan ta ce ka aure ta ne, to ka dawo ku ci gaba da soyayyarku, dan ba za ta iya jure rashinka ba, sosai take sanka,ba ka ga yanda ta shiga tashin hankali ba,
ni idan ta kira wayata har rasa yanda zan ce da ita nake,ni ne kai Allah na tuba na samu wannan garaɓasar, ai kwantar da kaina zan yi in ta cin duniya ta da tsinke."
muryar Ahmad na ji ya amshe maganar
"Kai mutumina daga na samu Allah ya tsamo ni, ai ba zan yi gangancin komawa ba,
dama ni na san ba wani abu ke fizgata zuwa ga Yasmin ba sai sha'awar ta,ka san tana da manyan abubuwa,
ni kuma ba abinda ke ɗaukar hankalina a wurin mace irin su".
Dariya abokin ya yi shi kuma ya cigaba
Allah ya taimake ni na dawo daga rakiyar sheɗan,matata ta ishe ni dama bata rasa komai ba,kuma sosai nake san ta,dan ban taɓa san wata mace ba kamar yadda nake san ta".
Abokin ya amshe
"Ka dai duba lamarin yarinyar ta shiga wani hali saboda rashin ka,ko ka san ta dawo garin nan ta baro asibitinta saboda ta ji an ce ka ajiye aikin ka dan ka kammala naka asibitin?
Faɗuwar gaba na samu jin maganar shi, amma sai na ƙara fakewa in ji amsar da Ahmad zai bayar
"Ko zan buƙaci ƙara auren, bana jin zan iya aurenta dan yara ne waɗanda iyayensu suka basu lasisin lalacewa da sunan gata, ballantana na gaya maka matata ta ishe ni".
Barin wurin nayi dan yanda na ji gabana na harbawa,na koma wurina cike da tunanin waye kuma wannan me ɗaure wa ɓarna gindi?
wannan ma ai ba abokin ƙwarai bane,
daga labulai nayi ina hangen harabar gidan,
kallo ɗaya na yi wa baƙon nashi na gane shi,
wanda ke ƙoƙarin buɗe motarshi, Ahmad na bayan shi,
wani ɗan manyan ƙasa ne idanuwan shi kawai ka kalla za ka san ba ƙaramin ɗan duniya bane,sunanshi Jibrin,ya kan zo wurin Ahmad jefi jefi,na lumshe idanuwana
ina ta ma mijina addu'ar Allah ya kare shi daga faɗawa halaka da sharrin mugayen abokai, da kuma faɗawa saɓo kowane iri ne.
Tattausan hannunshi da na ji kan wuyana yasa na buɗe idanuna ina kallon shi, feck ya bani a kunci
"Kwalliya aka min haka shi ne ba a zo in gani ba?
"Na ga kana da baƙo ne
Coffee na miƙa ma shi dan dama shi na je kai ma shi na saurari zancen su,yana sha muna yar fira da ya kammala sai ya miƙe
"Sanya lulluɓinki,ki ɗauko Mina, sai ki same ni mota".
kallon shi nayi
"Ina zamu?
"Ki dai yi yanda na ce"
sai ya fice
wajen Baba na je na ɗauko ta,
a shirye take kodayaushe yarinyar kamanninta da ubanta ƙara bayyana suke, Junior dai tuni momi ta karɓe abinta.
Kama hannunta nayi zuwa wurin motar wadda bai daɗe da shigo da ita ba samfurin ANACONDA
baƙa wuluk.
Muna tafe ina ƙara tuna ma shi haihuwar Husna, yaushe zamu tafi?
dan Khausar ta ce min za ta je,ta wutsiyar ido ya dube ni "Ko ranar suna sai ku tafi"
Marairaice mishi nayi
"Yi haƙuri likitana"
ya ce "Amma kin san ba zai yiwu ki tafi ki bar ni ba"
ɗaga kaina nayi
mun daɗe shiru kamar ba zai yi magana ba
"sai ya ce
Ki shirya ana gobe suna sai ku tafi nima ranar zan wuce, in haɗo ya nawa ya nawa in dawo gaba ɗaya"
na ce "Na gode"
farking ya yi a harabar asibitin , wanda na ga an sa wa suna MINA Specialist Hospital,
rabona da zuwa wurin tun ginin bai yi nisa ba,muka zo tare da shi.
Cikin matuƙar girmamawa aka tarbe mu, sai zagayawa muke ko'ina cikin asibitin komai ya yi, wurin ya yi kyau ƙwarai, da gani ba tambaya ka san an narkar da miliyoyin kudi,
ba abinda ya fi burge ni
irin ƙayataccen masallacin da a ka tanfatsa a harabar asibitin.
Na yi ma shi addu'ar fatan alheri,sai muka bar wurin, mun tsaya wurin shan ice cream ya saya sai muka yo gida.
Muna zaune a falona muna magana kan asibitin,
Knocking aka yi na bada izinin shigowa,
Rufaida ce,da ganin yanayinta hankalinta baya kanta,
Kan carpet ta zube Ahmad na faɗin lafiya?
ta ce "Mijinta ne ya yo
mata auren wulakanci da cin mutunci, ko gaya mata bai yi ba."
Mikewa nayi zan bar masu wurin da na ga kamar sirrin su ne
Ahmad ya ce "Ke ina za ki?
[1/13, 5:25 PM] Maryam Ibrahim Litee: CANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE
Malumfashi
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
26
Tafiyar awanni kusan biyar ta kaimu Abuja, mun isa gidan bayan ya tsaya damu a wani Restaurant na sa shi ya amso mana abinci.
Sai da ya ci abinci ya yi sallah sannan na sallame shi da alheri me yawa.
Ma'u ta gyara ko'ina dan yarinya ce mara ƙyuya, Baba Kulu ta kirani ta ce
"Gobe idan Allah ya kaimu tana tafe, dan ƴar ta ta ta samu sauƙi" Na ce kawai ta wuto Abuja dan na baro Katsina. Muna sallama kiran Ahmad ya shigo yana shaida min ya yi tafiya zuwa ibadan in kula da kaina. Haushi na ji ya ƙara turniƙeni,sai nake ganin kamar tare da Yasmin ya tafi, na kira momi da Khausar na shaida masu zuwana.
Da daddare na kwanta kafin barci ya ɗauke ni naji abu na bi na,na tashi na ƙara hasken fitila, na duba sai na ga jini, hankalina ya ɗan tashi dan ban taɓa naƙudar jini irin wannan ba, can dai ina sauraron ikon Allah,abu sai gaba yake,zuwa can ciwo ya taso, na rasa wanda zan kira a wannan dare,da dai naji azaba sai na ɗauko waya Zainab maƙociyata na kira, ta ruɗe cikin shaƙaƙƙiyar murya take tambayata lafiya? Na ce "Labour nake,kuma ina cikin wani hali"
Aje wayar kawai tayi ba a ɗauki wani lokaci ba naji bugun ƙofa, ina tafe jini na zuba haka nan nayi ƙoƙari na buɗe,
ta rungume ni a jikinta tana"Ikon Allah da yamman nan da na shigo lafiyar ki ƙalau am.......
maganar mijinta muka jiyo daga waje yana cewa
"Memakon ki yi kokarin taimaka mata ku fito,sai ki tsaya surutu".
Da sauri ta wuce ciki,ta fito da zannuwa ta taimaka min na canza kayan jikina,ta kuma riƙe ni zuwa in da motar mijinta take.
Gaba ya zauna kusa da direba ni da ita a baya,
kai tsaye asibiti aka wuce da ni,da gaugawa suka karɓe ni,
ni dai kafin a shigar da ni na ɓata lissafina,
dan ban san kuma abinda ya ci gaba da faruwa ba.
Na farka na gan ni a ɗaki na musamman,dan ni kaɗai ce, sai mutane da na gani kewaye da ni,
na bi su da kallo kowa na
ta ƙoƙarin gaishe ni.
Khausar ta wuce da sauri dan kiran likita,
na dubi hannuna,wanda na ji ya yi min wani dundurumdin,ƙarin jini na ga an cire min,
na kalli ƙarfen da ke tsaye,wanda ke maƙale da ledar ƙarin ruwa ko jini, sauran ledar jini ke maƙale wurin,
sai na tabbatar da ƙarin aka yi min.
Ƙwaƙwalwata na ta tunanin har Husna na gan ta a wurin,
na shafa cikina na ji wayam,na lumshe idona ina tunanin ko ya Allah ya yi da shi ?
Likita ta zo ta duba ni,
ta ɗan jima riƙe da hannuna,kafin ta fita,
wani barcin ya kuma awon gaba da ni.
Washegari na farka da sauƙi ƙwarai, ganin har lokacin ba a ce min ga abinda na haifa ba sai na yanke wa kaina babu shi.
Can likita ta zo ta bamu sallama, kasancewar da safe ne,daga ni sai Momi,sai Husna da ta zo da safe,Husna ta shiga harhaɗa kayanmu, Husna na riƙe da hannuna muka fito, a harabar asibitin sai na hango Ahmad akan motar shi zaune, ganin fitowar mu ya yi saurin tasowa.
Ya iso wurinmu ya shiga gaishe da momi, ta amsa ba yabo ba fallasa, ya yi min sannu,ya ce "Momi ga motata"
ta ce "An gode, akwai mota".
Muka shiga yana biye da mu a tashi motar.
Ga mamakina sai na ga mun nufi gidan momi,
muna isa ɗakin da na zauna momi ta kaini, ɗakin na ta fitar da daddaɗan ƙamshi,
na haye gadon na kwanta, ta wuce bayi ta haɗa min ruwa,
ta umarce ni in shiga in yi wanka.
Na shiga na gasa jikina da kyau,na fito na shirya kaina, cikin wata doguwar riga da ta ajiye min.
Shigowa tayi da wani gasashshen naman kaza,
jin ƙamshin da ya bugi hancina yasa ni haɗiyar yau,
zama tayi tana yanko min,har sai da na girgiza kai,
ta miƙe da farantin bayan ta miƙo min ruwa,sai ta fice.
Na gyara kwanciya inda tunani barkatai yayi ta yawo a ƙwaƙwalwata.
Ƙarar buɗe ƙofa ya sa na kai ganina wurin, ashe Husna ce,ta zauna kusa da ni tana ƙara tanbayata jiki,
nan na samu nayi mata tanbayar da ke cin raina,
na kuma rasa wanda zan ma ita
na dai yi ƙarfin halin cewa,
"Wai Husna ya bayanin abinda ke cikina?
Idanta kawai na ga ya tara ƙwalla,
Aunty Shuhaina kin bani tausayi ƙwarai,dan da ƙyar Allah ya ba likitoci sa'a suka ciro abinda ke cikinki, yaro ne namiji,sai dai ko kuka bai yi ba,dan shima ya sha wuya har ya rasu a ciki,
ke kuma sakamakon jinin da ya zuba a jikin ki sai da suka nemi jini dan a ƙara maki,
hakan yayi daidai da isowar ya Ahmad, dan an ta shan wuya kafin a samu wayar shi,
a taƙaice dai jinin shi aka ƙara maki dan yayi daidai da naki,
Yau kwana huɗu kenan da haihuwar ki,
ƴan gidanku ma sun zo shekaranjiya suka tafi,
ƴan'uwanki sun bani tausayi da ƙyar suka tafi sai kuka suke.
Na runtse idanuna,saboda nauyin da na ji ƙirjina ya min dan baƙin cikin rasa babyn da na haifa wanda ko ganin shi Allah bai bani iko ba,
na share wasu hawaye masu zafi da suka taho min,na shiga maimaita
Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, Allahumma ajirni fi musiybatiy wakhlifniy kairan minha.
Ji nayi an haye jikina an maƙalƙaleni,na buɗe idon Junior ne da Amina,cikin uniform ɗin makaranta,
na ƙara rungume su ina jin daɗin ganinsu,
me kula da su ta zo dan tafiya da su ta cire masu uniform ta basu abinci,
da ƙyar ta samu suka bi ta,Momi ta sake shigowa da kwanonin abinci,ta zuba ina kallonta,
Cus cus ne da yaji haɗin hanta da ƙoda da kayan lambu sai ƙamshi yake,
ta miƙo min ban jin sha'awar cin komai dan yadda zuciyata take a ɓace,amma na miƙa hannu na karɓa saboda girmanta da nake gani na soma ci a hankali.
"Ga farfesun naman kai can ko zuwa anjima sai ki ci"
na ɗaga mata kai,
sai da ta ga na ci sannan ta miƙe ta fita da kwanonin, ta dawo Haj Babba ta shigo,
na gaishe ta ta gaida ni da jiki,ta ce ma Momi
"Ai ban san kun dawo ba,zan wuce asibitin direba ke shaida min dawowarku".
Momi ta ce "E an sallame mu saboda yanayin jikinta sai na wuto nan da ita".
Hajiyar ta ce "Ai hakan ya fi,ga ma mijin nata ba mazauni bane, Allah dai ya ƙara lafiya".
Momi ta amsa da "Amin"
ta fita, momi ta janyo kujara ta gyara zama
"Shuhaina" ta kira sunana
na amsa a hankali
"Meke tsakanin ki da Baba ƙarami?
ɗan shiru nayi kafin na ce
"Ba komai momi"
tayi duk ƴan dabarunsu na manya ina ce mata ba komai,
Can ta ƙare ta ce
"A ranar da kika haihu ba ki cikin hayyacinki kin ta faɗar abubuwa na zaman ki da Baba ƙarami,
Allah ya taimaka daga ni sai ke ne a ɗakin sai ko likitar da ta ƙarɓi haihuwar,dan na kira ta ta gane min abinda kike yi,ta ce min jininki ya hau sosai,dan sai ma da ya sauka aka samu ƙara maki jini, sai na danganta hakan da halin da kike ciki,
"Wace ce Yasmin?.
CANJIN BA ZATA
By
MARYAM IBRAHIM LITEE
Malumfashi
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
28
ME GARI YA WAYA
MARYAM IBRAHIM LITEE
(Labarin zaman kishin mata hudu, wanda ake ragargaza kishi a gwangwaje, abun sai wanda ya karanta)
"Ina za ki ne?.
Koma ki zauna".
Na koma na zauna ta cigaba tana fyace hanci, "Kamar ni kawai ya rasa wa zai auro min sai ƴar aikina,bai ko gaya min ba, sai dai ganin an kawo ta nayi" faɗuwar gaba na ji ta same ni jin abinda ta ce. "Wani wulaƙancin sashin shi aka ajiye ta, yanzu yasa gini kusa da sashena,wai idan ya kammala gini sai ta koma,na baro gidan na je gida Abba ya ƙi goya min baya,wai in koma gida zai hana mijina aure ne, na ce ni ba auren ya fi damuna ba ya rasa wa zai aura sai ƴar aikina.
Da na baro gidan gidan yaya Kabir na nufa Aunty Aisha bata nan, Sai amarya ina tunanin ita ta hana shi ya saurare ni, shima ban samu goyon bayan sa ba.
kwanana uku yau na taho nan".
Ahmad da ya yi tagumi tun soma maganar ta ya ce "To ke Rufaida ya za a yi mu hana mijinki aure, magana ta gaskiya ki koma ɗakinki ki yi haƙuri.
Yanzu ma shin ina yaranki? Ta ce "Na baro ma shi abin shi".
ya ce "In kin bar mata mijin kya haɗa har ƴaƴan ki? Ribar me kika ci to?
ta ce "Ni da in zauna da ƴar aikina gara auren ya mutu". Ya yi saurin cewa "Subhanallahi, ban san hauka. Kuje ciki Shuhaina,tayi wanka,ki bata kaya ta sauya,sai ta samu ta ci abinci zan ga mijin nata". Na miƙe tana biye da ni
har bed room ɗina, ta shiga wanka na ciro mata kaya, sai na fita.
An ɗan jima na dawo na samu ta saka kaya tayi tagumi kawai na ce "Ba ki yi make-up ba? Ta ce "Barni da kwalliyar nan, har na manta rabon da in yi ta" nan dai nayi ta bata baki har ta ɗan yi sama sama, muka fito ina ta tausarta har na samu ta ci abinci, ta koma ta kwanta rigingine idan ta na kallon silin.
Da muka zo kwanciya a bed room ɗina na ce ta kwanta na bata sabuwar sleeping dress kwanciya tayi tana kallona ina kwalliyar tafiya turaka, na gama nayi mata sai da safe na ja mata ƙofar,na wuce wajen mijina.
Wasa wasa sai da Rufaida ta shafe sati biyu a gidana, dan har sai da na je sunan Husna na dawo, sannan mijinta ya amince zai sake ma amaryar shi wani gidan cikin gidajen sa, ita kuma ta koma gidanta, ni yasa na rakata tana ta min godiya.
Na dawo gida ina ta kakkaɓin al'amarin, wato gaskiyar hausawa da suke cewa abinda ya baka tsoro wata ran shi zai baka tausai, yau Rufaidar da ke ganin ni ɗin ban cancanci zama matar yayansu ba,saboda Ni ba ƴar kowa ba ce, an wayi gari yau mijinta
ya auro me aikin ta, sun zama daidai a wajen shi in ta ɗauro ma ta fi ta a zuciyarsa, tun daga nan muka ƙulle da ita.
Wani hantsi zaune nake a ƙayataccen falon Innarmu, wanda na ƙayata mata shi, bayan na gyara gidan gaba ɗaya.
Dan ta ƙi komawa gidan da na gina mata.
Nasa an buɗe ɗakunan nata,an kuma yi mata kicin da bayi,tunda gidan yana da wadataccen fili.
Fira muke da Innarmu,ban daɗe da isowa ba daga Katsina, Maman Ihsan Rabi ta aurar da ƴar ta, ɗan da na haifa namiji Abdurrahman yana ta dabo a tsakar ɗakin, yayata Zinatu tayi sallama ta shigo sai da muka gaisa sai tayi min godiyar alherin da na aiko mata da shi na kayan abinci da kudaden cefane.
na ce mata "Ba komai" shekaru biyu kenan da aka cafke mijinta bisa ga kamashi da akayi ya shigo da haramtattun ƙwayoyi, komai nasu an karɓe, Ƴar'uwarta da ya kamata ta temaka mata itama yanzun sai a hankali, a kullum na dubi matsayin da take a da da kuma yanzu sai tayi ta ban tausayi ga ƴaƴanta basu san wahala ba, na kan ƙara girmama girman Ubangiji dama a cikin sunayen sa ya faɗa, ya girmama wanda yake so, ya ɗaukaka wanda yaso, ya kuma ƙasƙantar da wanda yaso.
Salma ta fito, kyakykyawar budurwa wadda da zarar na dube ta ban iya hana kaina murmushi ban gajiya da kashe mata kudade ina ƙara fiddo ta,
wani abokin Farhan ke neman aurenta,
mun gama firarmu muka kamo hanya,
saƙon Ahmad ne ya shigo, yana bayyana min irin matuƙar kewata da ya yi na kwanakin nan da bana nan, tare da bayyana zallar son da yake Murmushi nayi idona na lumshe nake gode ma Allah bisa bani miji irin wanda ya bani me sona da ƙaunata da tattalin farin cikina.
TAMMAT BI HAMDILLAH.
Godiya ga Allahu subhanahu wata'ala da ya bani ikon kammala rubutun littafin canjin bazata,abinda nayi daidai Allah ya haɗa mu a ladar,
kuskuren da nayi kuma Allah ya yafe min, Godiya ga masoya littafin nan,
a duk inda suke na gode da kauna
Musamman jama'ar Dandalin karatu ina godiya da ƙwarin gwiwa, Sai yan canjin bazata fans ina godiya da son littafin nan da kuke Ina barar ƙulhuwallahu Allah ya kai ladan kabarin mariƙiyata ya haskaka makwancinta😭 ga duk wanda ya ji daɗin labarin nan.
Nagode na gode na gode
Sai Allah ya sake sadamu
Taku ce MARYAM IBRAHIM LITEE
Malumfashi.
0 Comments