SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
Bismillahir rahmanir rahim da Sunan Allah mai rahma da mai jin ƙai wanda cikin ikonsa,yardansa,amincewarsa tare da aron numfashin daya bani na rubuta wannan littafin SALON ƘADDARATA,bayan na kammala littafin UWATACE SANADI. Ya Allah ka tsare mini hannayena wajen rubuta abinda zai zamto cutarwa ga al'umman musulmai tare da tarbiyansu.
Anty Amina ma'aji(Maman Khairat)shugaba mai son cigaban na ƙasa da ita aduk inda ake maganar nagarta da kyawawan hali,itace mutum na farko take zuwar mini a rai. Wannan page ɗin na kine kiyi yanda kikeso dashi, inasonki fisabilillahi alkhairin Allah yaje miki har inda kike.
Oh my fans i'm back no more waiting,ku gyara zama dan ban dawo da wasa ba wannan salon na dabanne kamar yanda zubin labarin yake na daban kuma na mussamman, Hajiya kar ki bari ayi wannan tafiya ba ke ah to.
Page 0⃣1⃣
Duhune sosai ya mamaye dukkan ɗakin duhu irin na yanayin damina,cikin baccin daya fara saɗɗata nake jiyo tashin muryar Daada a hankali na ɗaga haƙarƙari na dayake mini ciwo sakamakon kwanan ƙasa na sauƙe idanuna akan Daada dake zaune saman sallaya hannayenta na sama tana addu'ar.Hasken walƙiyar da akeyi dayake hasko ɗakin shi ya bani damar ƙarewa Daada kallo har na hango hawayen da keta kai kawo saman kunci ta.
"Allah banida dabara akan kaina sai abunda ka yanke min,ya Allah ka haskaka rayuwar ƴaƴana kaɗaukaka su sannan ka tsaresu cikin ko wani hali na rayuwa da zasu riski kansu nan gaba,ka azurtasu da imani da tsoronka.Allah ga mijina nan kafi kowa sanin iri zaman da mukeyi da wannan bawan nan Allah ka shirya shi in mai shiryuwa ne inba mai shiryuwa bane Allah ka gaggata ɗaukar ransa".
Tana kawowa nan ta shafa addu'ar kalamanta suka ƙara sanya jikina yin la'asar,na koma na kwanta tare da jawo wayarta nokia ta na duba agogo ƙarfe biyu da rabi har ya gota,tun ƙarfe goma muka jiran dawowar Abba har bacci ya fara ɗaukata na sauke nauyayyen ajiyan numfashi ina runtse idona da ƙarfe.
Cirko-cirko muke tsaye daga ni har Daada dasu Sha'awa,yau ce ranar da Zulaihat zata koma makaranta ƴan kuɗaɗen Daada take tanadinsu domin yi mata siyayya mun nemesu sama ko ƙasa babu su babu dalilinsu,nida Sha'awa muketa ƙara dubawa Daada ta miƙe da tsohon cikinta nayi saurin faɗin"Daada ina zakije?".
Ba tare da ta juyo ba tace"ku cigaba da dubawa zan shiga banɗakine". Daga haka taja kumburarrun ƙafafunta da aka ce mata a asibiti rashin jinine ya haifar mata da kumburin.
Da kallo nabi bayanta har ta shige banɗakin na tabbatar kuka zata shiga tayi dan lokuta mafi yawa bata kuka a gabanmu mussaman akan baƙin-cikin Abba,dan bana raba ɗayan biyu kuɗin nama shiya kwashesu ya tafi caca dasu.
Na kalli Zulaihat data gama shirinta tsaf!duk mun fita haske nida Sha'awa. Dan ita kalar mahaifinta tayo,nice babba a tsakanin mu sai Sagir a lokacin Daada suka rabu da Abba,ta auri mahaifin Zulaihat yasota sosai sannan kuma ya inganta rayuwarta fiye da Abba Zulaihat na cika shekara ɗaya da rabi ya rasu.
Wata ƙaddarar haiho Sha'awa da kuma wannan cikin dake matuƙar wahalar da Daada yasata ƙara dawowa gidan Abba,ita kaɗai ne a cikinmu wacce take makaranta saboda dangin mahaifinta sun tsaya mata a fannin karatunta,nikam banajin ko takardan shaidar gama ƙaramar makarantar sakandiri inada ita dan ban gamata ba Abba ya cire mu nida Sagir,Daada ce ke surfe da wankau take biya mana Sagir kuwa yana talan pure water.
Bansan sanda hawaye ya fara zuwar mini ba sai ji nayi Sagir ya dafa kafaɗata cikin muryarsa dayake nuna cewa a buge yake yace"Antynmu meye yake faru a cikin gidan,nagan ku duk ƙarayin kalan tausayi kodai wannan tsohon ne ya ƙara dukan Daada dan na rantse da sarki dake busan numfashi nayi alwashin duk ranar daya ƙara dakar mini uwa sai na sauƙe masa dukkan hannayensa ƙasa da adda".
Sha'awa tayi saurin faɗin"A'a yaya Sagir kuɗin da Daada take ajiyewa domin yiwa Anty Zulaihat siyayya ne muka rasa su".
"Af ya ɗauke mana kuma kunsani ai basai an gaya muku,yanzu yana can wajen cacarsa anma cinye kuɗin".
Furcin Sagir ya kai ƙarshe yana tambayar Sha'awa ina Daada tace tana banɗaki,bata rufe bakinta ba Daada ta fito daga banɗaki tana tafiya daƙyar. Sha'awa da Zulaihat suka riƙota ta zauna saman tabarman da na shimfiɗa,kusa da ita Sagir ya tsuguna yace"Sannu Daadarmu".
Kanta kawai ta iya ɗaga mishi ya ɗaura da faɗin"Daada ki kwantar da hankalinki indai kuɗine duk idan suke a cikin garinnan yanzu zan fita na samo miki kona uban waye", yana kawowa nan ya miƙe Daada ta bishi da faɗin"Sagir ka dawo banason kana taɓa kayan mutane fa ".
Kota kanta mai biba yayi ficewarsa ya barta da faɗin"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un".Bazan taɓa manta ranar da Abba yayiwa Daada duka ba cikin ruwa ya koro ta daga ɗaki yace ta kwana a waje ciki tsakiyar daren ya hau ɗura mata ashar yana sauƙe mata kyawawan maruka babu abunda mukeyi sai kuka muna masa magiya,Sagir ya rarumi kujera ya bugawa Abba a goshinsa yana huci ya isa ga Daada ya ɗagota yana cewa"Daada ki daina kuka duk ranar daya ƙara dukanki zan rama miki kinji".Ranar Abba ya tsinewa Sagir ya kuma haramta masa tsayiwa koda a ƙofar gidan sane muna kuka muna masa roƙo da makiya akan ya bar Sagir ya zauna a gidan Daada tace ita zata tafi amma shi Sagir ya zauna tunda bashi da gurin zuwa daya wuce nan.
Haka Abba ya roki Sagir cikin wannan dare akan idonmu kuma ya mana zazzafar gargaɗin cewa daga ni har Sha'awa ko ƙofar gida muka bi Sagir Allah ya isa bai yafe mana ba.Tun daga wannan ranar Sagir bai sake kwana a gida ba mun nema duk inda muke tinanin zamu gansa amma babu ko mai kama dashi.
Wata rana aka kawowa Daada labarin cewa an ganshi yana shaye-shaye bamu yarda ba sai lokacin da da idona naga an biyo wasu ɓarayi hadda Sagir a ciki,ranar munyi kuka har muka rasa hawayen tsiyayarwa Sagir shi kaɗai ne namiji a tsakaninmu amma Abba ya buɗe masa ƙofar shiga duniya yayin daya yanka masa tikitin lalacewa.Sagir baya zuwa gida sai ya tabbatar Abba baya nan komai ya sato ko suka tare hanya suka yi ƙwace sai ya kawowa Daada dai-dai da rana ɗaya bata taɓa amsaba.maganan da Zulaihat ta farayi ya sani dawowa daga cikin duniyar tinanin danayi nitsu a cikinsa.
"Anty UMMUKURSUM nikam kawai bari na tafi kar na makara".Nayi saurin miƙewa na zato hijabina dake saman igiyar shanya ina ƙoƙarin sawa nace"To muje na rakaki".Daada ta miƙe haɗi da faɗin"Zulaihat Allah ya kiyaye dan Allah a maida hankali ayi karatu sosai kinji ko?"ta ɗaga kanta alamar taji da zamu fita nace Sha'awa ta ɗaura girki kafin na dawo sarai nasan bamuda ko ƙwayar tsabar hatsi a cikin gidan,kwana biyun nan ma zuwan Zulaihat datayi ne da wasu sauran shopping ɗinta na makaranta dabai ƙare ba muke amfani dashi,wani lokacin kuma Sagir yake shigo mana da abun kari.
Muna tafe cikinmu babu wanda ya furta koda kalma muka hangi Sagir ya nufo mu sauran ƴan tawagarsa suna biye dashi,ganinmu ya sashi dakatawa ya miƙawa Zulaihat ledar dake hannunsa yace"Ga wannan nasan zasu ishe ki,koda yake ke kam ma ai dundumarki da gata nasan yanzu an tanada miki komai na buƙata kawai zuba miki su za'ayi a mota driver ya kwashe ki sai makaranta ko?".Ta karɓa tana yalwata annurin fuskarta sannan tace"Yaya Sagir kenan nagode Allah ya saka maka da alkhairi". Yayi dariya sosai kafin yace"to amin"muka cigaba da tafiya duk cikinmu Sagir ya fimu son karatun bana mantawa kullum yana faɗawa Daada burinsa wataran ya saka uniform ɗin soja a rayuwa.
"Antynmu ya kikayi shuri ne kodai wani abunne?"na ɗago na kalli Sagir nace"Babu komai "ya matso ya ɗaura hannunsa a saman kafaɗata na turesa ina faɗin"Sagir banason shashashanci", ya juya ya kalli ƴan tawagan nasan da suke biye damu a baya yace suje su jira shi a kangonsu zai zo ya samesu babu musu duk suka watse.
Har mun kawo bakin titi muna jiran adaidaita sahun Sagir yace"kinga Zulaihat kiyi karatu sosai dan in naji labarin kin kula wani saurayi wallahi sai dai uwarsa ta haiho wani,tunda ke Allah ya sa zakiyi karatun to ki wakilce mu gabaɗaya.ni ɗin nan da kike gani inada buri a rayuwata a karatu amma nasan yanzu lokaci ya ƙure mini shiyasa kikaga duk lalacewata ina ƙoƙarin kare mutumcinku so nake Anty Ummu Allah ya bata Likita ta aura ita kuwa Sha'awa wani babban soja ke kuma an miki miji a gidanku daman".tayi saurin kai masa duka a kafaɗarsa ya zamewa yana dariya,daidai nan wani mai adaidaita sahu ya tsaya Zulaihat tace"Malam madina quaters zaka kaini"inda gidan mahaifinta yake kenan makaranta kuwa a jahar Jigawa take cikin birnin kudu tana karantan aiki koyan jinya(nursing).
Sai a sannan nace"nawa zamu baka ita ɗaya ne?"na kai ƙarshe ina since ɗaurin dake bakin zani ina fiddo da wata tsohuwar ajiyan naira saba'in ɗinta.Sagir ya miƙa masa naira hamsin ya fara gardamar cewa bazaije madina quaters tun daga nan wunti street na jahar bauchin yakubu akan naira hamsin ba,nan Sagir ya shiga yi masa barazana tare da jaddada masa shi ɗin wayena a kaf!cikin bauchi har wuƙa ya zaro daga ƙungunsa na riƙe sa.
Tsabar tsoron da mai adaidaitan yayi ya tafi yana bawa Sagir haƙuri yace bazai iya ba mu nema wani,wata uwar harara na cillawa Sagir nace"yanzu me kayi kenan?"ya langwaɓar da kai yace"Antynmu irin waɗannan sai ana musu haka".yana rufe bakinsa wata mota baƙa wukul tana tafe tana numfashi har ɗaukar ido takeyi ta faka dai-dai inda muke tsaye.
Aka zuge baƙin gilashin motar yana ƙare mana kallo tunda daga sama har ƙasa yace"ke Zulaihat wuce mu tafi".
"Yaya Abdallah daman yanzu ma tafiyan zanyi muna jiran adaidaita ne".
Wani kallo ya watsa mata daya sanya ta saurin cewa"Anty Ummu ni na tafi sai munyi waya ki gaida Daada yaya Sagir na wuce".Tana kawowa nan ta shige motar Sagir ya kinkime akwatinta zai buɗe boot ya saka mata Abdallah ya fito haɗi da daka masa wani uban tsawa"kar ka sake ka taɓa motarnan da wulaƙantattun hannuwanka,inko kayi zakayi nadama stupid".
A irin yanda nasan Sagir da zafin zuciya nayi tinanin zai mayar masa da zazzafar martani sai naga saɓanin hakan,murmushi kawai ya sakar masa yana ɗauke hannunsa daga jikin akwatin,Abdallah ya ɗauka yasaka cikin boot ɗin ya dawo mazaunisa yaja motar da mungun ƙarfi ya bule mu da ƙura.
Sarai na ganesa shine Abdallahn da Zulaihat ke bamu labarin ɗan wan mahaifinta mai matuƙar zafin nan,sannan shine Sagir yake tsokalar ta da cewa shine mijinta. Kasa haƙuri nayi sai dana tambayi Sagir meyasa bai mayarwa Abdallah raddi ba,murmusawa yayi yana zura hannayensa cikin aljihun wandonsa,yayi ƙasa da kansa ya ɗau lokaci kafin ya ɗago kana yace"UMMUKURSUM sufa irin waɗannan mutanan gani suke duk wanda yake rayuwa a cikin talauci shi yaso,ko kuma shiya tsarawa kansa haka.na ɗaga masa ƙafa ne albarkacin Zulaihat na wajen kar naja mata abun faɗa a danginta amma wallahi na rantse miki da sarkin da babu waninsa bacin haka da bai isa ya min wannan tsawan ban yanke masa harshe ba".
Na kallo shi sosai duk rashin mutumcin Sagir yana ƙare mana mutumcin mu da kuma nisantan duk abunda zai taɓa kimarmu,kafin nayi wata magana wani abokinsa ya nufo mu sukayi wani irin gaisawa na daban sannan yace"AJANI akwai wani harka fa wasu ƴanmatane ƴan hannu,inka naso na ajiye maka biy...".
Bai ƙarisa sakamakon dakatar dashi da Sagir yayi ta hanyar ɗaga masa hannu"Kaga nifa kafi kowa sanin duk lalacewana bana iskanci bana lalata ƴar kowa domin nima inada ƴan uwa mata wannan kuma sai dai ku,domin ni bakin Ubane kawai a kaina har yanzu uwata tana samin albarka".
"Hakane kuma fa mutumina to sai mu kaɗe ko?"suka ƙara tafawa Sagir ya lantayo wani mummunan ashariya ya jefa masa shima ya maido masa yana ɗagowa muka haɗa ido kunyata yasa shi ɗauke nashi idon,koni zan shaidi Sagir akan baya zina amma abubuwan shaye-shaye kam babu wanda baya sha har hodar ibilis nasha ganinsa da ita raina ya kai ƙololuwar ɓaci nace"Sagir yanzu abunda kakeyi ka kyauta kenan ko tausayin Daada bakaji dan Allah ka shiryu duk wannan harkan daban ka rabu dashi".
A raunane yace"Antynmu inama inaso na daina ku tayani da addu'a", Daidai nan muka ƙariso ƙofar gida zan shige ko sauraran Sagir banyi ba dan ya gama ɓata mini rai na tsinkayo muryarsa yana faɗin"Ki gaishe min da Daada wataƙil bayan sati ɗaya ko biyu na ƙara leƙowa na duba jikin natan".
Na waiwayo haɗi da cewa"ba zaka shigo kaganta kafin ka wuce ba?".
Har ya fara ja da baya yace"bazan shigo ba dan nasan wannan tsohon yanzu lokacin dawowarsa yayi bazan iya jure ganinsa tsaye a gabana zuciyata tana karato min irin tuzarcin da yakeyi wa Daada na tafi ban cire wani sashi daga jikinsa ba,kawai gwara na tafi zan ƙiraki a waya"yana kawowa nan ya gyara zaman hular facing cap ɗin dake kansa ya fara tafiya da matuƙar sauri kamar zai tashi sama.
A wajen na durƙushe ina bin bayan Sagir da kallo har ya ɓace mini shikenan Abba ya sanya katanga tsakanin ɗa da uwa?. Ya lalatawa Sagir dukkan burinsa akan karatu a rayuwa yayin daya ƙare a ɗan daban cikin unguwa da yin bangan siyasa, inajin SALON da ƘADDARATA tazo da shi mai wuyar fassarawa ne balle a misalta shi da kalamun da baki kan iya furtawa, lokata da yawa nakan zama nayi tinani inama ace Sagir shiryayye na tabbatar da wahalar Daada ta yanke a bayan ƙasa haka nan muma,ko Sha'awa bamu shaƙu da ita kamar yanda muka shaƙu da Sagir ba a hakansa a yanzu shi yake mana komai na sutura duk inda yaga atamfa yakan sayowa Daada koda bazata karɓa ba hatta pant duk wata shi yake saya mana nida Sha'awa.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
__________________________________
Page 0⃣2⃣
Na daɗe a wajen kafin naja ƙafata na shiga cikin gidan can ƙasan maƙoshina nayi sallamar wanda ba lale kowa yaji ba,nan na iske ƴar biyun Daada Anty Hussaina tazo na zauna kusa da ita ina ɗeban gaisuwa tare da karɓan ɗanta Musaddik na ɗaura akan cinyata idanuna suka sauƙa akan Sha'awa daketa faman iza wuta da mamakina nace"Sha'awa me kike dafawa haka?"ta washe baki kafin ta shiga faɗin"wallahi Anty Hussaina ce ta kawo mana taliyan murji kwano biyu".daga nan ba kuma cewa komai ba Daada ta tambaye ni na raka Zulaihat ɗin nace mata mun haɗu da Abdallah ma ya ɗauke ta.
"Yanzu Adda Hassana haka yaran nan zasu zauna babu karatu anya rayuwa zata yiyu a haka kuwa,in ya hana karatun ai ko aure ne sai a musu allabashi saci gaba da karatun a ɗakunansu".
Furcin Anty Hussaina kenan daya sanya Daada sauƙe wata ƙatuwar ajiyan zuciya tana zame hannunwanta daga tagumin data zabda hannu bibiyu"Maman Musaddik kenan kinfi kowa sanin rayuwar cikin gidan nan lamarin Malam sai dai addu'a".Daada ta faɗa amon muryarta kaɗai ya isa ya fallaso aihinin da zuciyarta ke a ciki.miƙewa nayi ina saɓa Musaddik a kafaɗata naje ɗakinmu na kwantar dashi saboda baccin da yayi,sannan na zare hijabin kaina na fito na fara share tsakar gidan.maganganun Anty Hussaina suka ziyarci kunnuwana"yanzu Adda shi kuma Sagir haka za'a zuba masa ido ya cigaba a haka,kwanaki fa a unguwarmu akayi sata shiya jagoranci tawagar ɓarayi,gaskiya Adda Hassana a nema masa taimako a wajen malamai".
"Nima ina tinanin haka amma sai dai kinsa dole sai Malam ya yafe masa,shi kuma yayi rantsuwar cewa har ƙasa ta rufe masa ido bazai yafe masa ba".
Jiyo muryar Abba tun daga bakin titi yara na biye dashi suna masa alalo,yasha ya bugu yana tafe yana faɗuwa yana tashi.Daada ta miƙe da hanzari tace"Maza Ummukursum je ku shigo dashi".na saki tsintsiyar da nake sharar da ita Sha'awa ta miƙo min hijabina daga ɗaki muka fita,yana tsaye daga shi sai ɗan kanfai duk kayan jikinsa an cinye shi a caca nayi saurin runtse idanuna da suka kawo ruwar ƙwalla.sai ɗurawa yaran da suka biyo shi ashar yakeyi Sha'awa ta ɗauki wani kara ta fara koran yaran ni kuwa na isa na kamo hannun Abba nan ya shiga kwaro mini aman burkutun daya shayo a jikin farin hijabina shi ɗayane ɗan sabo sabo a kaf!cikin kayana bai jima ba da Sagir ya kawo mini shi.
Sai daya gama wankeni da aman tun daga ƙirjina har kusan gwiwana yana ɗiga har saman ƙafata,hawaye suka shiga sintiri saman dakalin fuskana Sha'awa ta ƙariso muka ɗago shi tana riƙe da kafaɗarsa ɗaya ta saƙale saman wuyanta nima ina riƙe da ɗayar muka shigo ciki dashi.muna isa tsakar gidan ya zame ya faɗo ƙasa ya cigaba da kwararo amansa Sha'awa ta koma gefen Daada ta kifa kanta tana kuka mai tsuma zuciya.
Anty Hussaina keta basu baki har na fito daga banɗakin dana shiga,kaina a ƙasa na kasa ɗagowa tsabar yanda kaina yake sara mini,na wuce ɗaki na ciro wata doguwar rigan atamfa wanda tsabar koɗiya har baka iya bambamce wani launi ce.sai dana zarata a jikina ta sauƙa mini har ƙasa sannan na fito na kwashe tulin aman da Abba yayi nan muka barshi ya cigaba da kwanciyar dan Daada taci alwashin cewa bazai ƙara shigar mata ɗaki a cikin halin maye ba.koda Sha'awa ta sauƙe taliyar kasa ci nayi tsabar yanda zuciyata take lugudan tara-tara raina ya mini soya sosai.
"Adda Hassana akwai wani gida anan maƙwatanmu amarya ce aka kawo tana buƙatar ƴar aiki,shine nace ko UMMUKURSUM zaje tana maka".
Magananganun Anty Hussaina kenan da suka shiga mini yawo a tsakiyar ka,na ɗan tsagaita ina jiran amsar da Daada zata bata.
"Hussaina Malam bazai amince ba tun ba yau ba munsha yi makamanciyar iriyar wannan maganan amma ya nuna cewa ƴaƴansa baza suyi aikatau ba"
Fuskar Abba na zurawa idanu ina karato abubuwa da yawa da suke shimfiɗe a kanta,wani ajiyan numfashi na sauƙe wanda yayi dai-dai da tsananta bugu da ƙirjina ya soma yi lokaci guda a hankali na zame hannu daga cikin kwanon taliyar da mukeci nida Sha'awa nayi ɗaki kusa da Musaddik da har yanzu yake bacci na zauna ƙalbina cike da tausayin Daada wayata da take saman taga ta fara ruri na ɗauko tare da ɗaga ƙiran na kara a kunnena daga ɗayan bangaren Zulaihat tace"Anty Ummu na iso nace bari na ƙiraki na sanar dake".na cizo leɓɓana na ƙasa kana na shiga faɗin"to Zulaihat Allah ya taimaka".
"ya Daada fa da jikin natan an kaita asibitin kuwa?"sai dana zauna daga tsayiwar danayi nace"ba kaita ba amma Sagir yace zaizo sai mu kaita".ta numfasa kana tace"to Allah dai yabata lafiya".a raunane na amsa da amin sannan mukayi sallama ko gama katse ƙiran banyi ba na fito a harzance har ina tuntunɓe da dakalin ƙofa sakamakon ruwar ashariyar dan jiyo Abba na zazzago su.yana daga zaune inda yayi aman Daada na durƙushe a gabansa da ƙaton cikinta kanta na kallon ƙasa sai masifa yake yana faɗin"yanzu Hassana tsabaragen rashin mutumcinki kullum ƙara girmama yakeyi na shigo gidan nan amma ko ruwan da zan watsa a jikina baza a kai min banɗaki ba.wai Hassana me kike nufi dani ne in auren ne kika gaji dashi sai ki fito ki faɗa min na baki takardan ki".
"Malam yau na tashi banajin daɗin jiki nane amma kayi haƙuri yanzu Ummukursum ko Sha'awanatu sai wanin su yakai maka".sai daya tattaro miyau ɗin bakinsa ya fesa mata a fuska kafin yace"wallahi tir da ke Hassana ke nake aure ko su Ummukursum da anyi magana kice wai bakyaji daɗi to yanzu a duniyar nan waye yake jin daɗin".ruwar hawaye suka shiga ciko mini idaniya na basu basu damar tsiyayowa dan a wannan lokacin bani da wata dabara.Anty Hussaina data gama cika fam!da takaici ta miƙe tana faɗin"Haba Malam Nura ai ka tausaya mata a cikin halin da take ciki,jibi fa ciki ne a jikinta ga wannna kumburin da tayi amma duk waɗannan ababaɗen basu isa tausayin wannan baiwar Allahn ya darsu a ranka ba?".har yanzu mayen bai sake sa ya miƙe yana tangaɗi ya nufi inda Anty Hussaina take tsaya ya fara nunata da ƴar tsaya yana cewa"ke ki fita daga idona Hussaina bar ganin kinada aure wallahi sai na tattaka ki a cikin gidan nan"da zafinta Anty Hussaina ta yunƙura zata maido masa da martani Daada ta katse ta hanyar faɗin"Hussaina inhar na isa dake kar ki ƙara cewa komai kizo ki wuce ki tafi".
Bata kuma cewa komai ta gyara mayafi ya ɗauko Musaddik ta goye shi"wallahi kaci darajar ƴaƴanta"furcin data jefawa Abba kenan taaa ɗaukar hanyar ficewa daga cikin gidan Abba ya zabura zau bita nayi sauri isa gabansa na haɗa hannaye wajen ɗaya cikin kukan dayake shirin zuwar mini nace"Abba dan Allah kayi haƙuri kar ka bita"ina kawowa nan na zibe akan gwiwoyina ina sakin kukana ɗago ni Abba yayi yana washe mini rinannun hakwaransa da shan giya da burkutu suka dafar dasu yace"ki shuri ƴar leleta daina wannan kukan"na miƙe ina share hawayena tare da zuƙe majinar kukan daya zo mini na zame jikina daga nashi na wuce na ɗauka bokati naje na ɗebo masa ruwan wankan sai dana kai masa ruwan sannan nace"Abba an kai maka ruwan wankan"daga haka na wuce ɗakin wajen Daada da Sha'awa kusa da ƙafafun Daada na zauna ina ɗaura kaina akan cinyarta kamar yanda naga Sha'awa tayi duk suna kuka nima na jona su muka ɗaura daga inda suka tsaya mun daɗe a haka kafin nayi ƙarfin halin furta"Daada dan Allah ki daina sa damuwar Abba a ranki,inga kema ba ishashshan lafiya ce gare ki ba kuma ba'ason masu lalura irin naki su fiye ɗaga hankalinsu".
"Ummukursum duk abunda Malam yake min bai taɓa ɗaga min hankali ba,ni kune a gabana rayuwarku shi yafi komai muhimmanci a gare amma shi yayi fatali da hakan yanzu a irin halin sa wani ɗan na gari ne iyayensa zasu yarje masa ya auri ɗaya daga cikin ku matuƙar aka ga mahaifinku sai kuma gashi Allah ya bani ku dukka mata Sagir ne shi kaɗai ".furcin Daada kenan da ya sanya ni jin wani sabon kukan tausayin kanmu ya zo mini ina cikin shekaru ashiri da biyar Sha'awa kuwa shekarunta goma sha bakwai tun tasowa ta babu wani ɗa namijin daya taɓa furta mini kalmar so ko cikin sigar wasa balle akai ga maganar gemu da gemu.
"Daada dan Allah ki tausaya mana ki daina saka komai a cikin ranki,bamu san yanda zamu fara tinkaran rayuwa babu ke ba"ta ƙai ƙarshen zance tana ƙara riƙo hannun Daada cikin nata.a hankali Daada take shafa kanmu muna sauƙe ajiyan ɗaya nabin ɗaya mun daɗe cikin wannan yanayin har na fara yin baccin wahala ina farkawa ƙiran sallan Asr ya sauƙa a cikin kunnuwana nayi wata ƙarƙarfar miƙa tare da sakin salati na tashi daga kan lamutsatstsiyar katifar mu da bata da baraba da tabarma wajen kauri da tudu.kodana fito ban iske Daada da Sha'awa a tsakar gidan ba na wuce bayi sannan na fito na ɗauro alwala na koma ɗaki sai danayi Zuhr sannan nayi asr na daɗe ina addu'ar neman sauƙi daga wajen mahaliccinmu akan halin ƙuncin da muke ciki,sannan daga ƙarshe na ɗora da nemawa Sagir shiriya a sanyanye na shafa addu'ar cikin yanayi daya zamto mini ɗabi'un sannan na fito na fara share tsakar gidan da ɗazu ban gama ba sakamakon dawowar Abba ina gamawa na leƙa ɗakin Daada na iske ta tana kishingiɗe Sha'awa tana mata lausa a ƙafafunta na ƙariso na zauna bakina ɗauke da sallama Daada ta amsa haɗi da furta"Ummu har kin tashi?".
"E Daada na tashi har nayi shara ma"na faɗa ina gyara zamana kusa da Sha'awa ina bin ƙafar Daada da kallo sosai ya kumburu dan jiya da yau ko takalmi bata iya sanyawa na zagba tagumi Daada ta kallo ni kana tace"Ummukursum banason ganinki kina wannan tagumin menene?".na zame hannuna a hankali"Daada wallahi wannna kumburin ya fara bani tsoro gashi Abba ma ya nuna halin ko in kula akan hakan,ya kamata ace kije asibiti ki sama kulawar malaman lafiya".
"Haka ne Anty Ummu in yaya Sagir yazo sai mu sanar dashi ko zamu sama wasu kuɗaɗen daga wajensa"furicn Sha'awa kenan daya sanya Daada saurin miƙewa daga kishingiɗewar ta tayi tana faɗin"ban yarda ba bada yawu na zaku ƙarba abun hannun Sagir da nufin nema min lafiya ba,duk abunda zai fito daga hannunsa ya haramta a gare ni matuƙar bazai yiwa kansa faɗa yasan annabi ya faƙu ba".tunin Sha'awa ta fara sakin ruwan hawaye tana faɗin"Daada dan Allah ki sasautawa yaya Sagir a wannan matakin dayake jiki addu"arki yafi buƙata sama da komai wallahi shima ba a son ransa yake aikata wasu abubuwan.shiyasa inzai zo wajen ki ko tabar sigari baya sha kuma baya bari ki gani da idonki".sai da sauƙe ajiyan numshafi mai ƙarfi da kuma sauti kafin tace"Haka ne Sha'awa amma ya zama dole a nuna masa illar abunda yake yi,duk da ba kowa ya jawo hakan ba face malam".ta kai ƙarshen zance fuskarta tana bayyanar da raunin da zuciyarta ke a ciki.
Nikam nauyi bakina naji ya mini na kasa furta komai sai sauraran zantukansu nakeyi bana manta ranar da Sagir yazo Daada tace ya tafi taƙi buɗe ido ta kalli koda fuskarsa ne balle ta saurare,tayi fatali da kayan dubiyar daya kawo mata dan a lokacin bata da lafiya.haka ya fita waje yayi kuka sosai har yana buga kansa da jikin bangon gidan mu bazan iya ƙidaye awannin daya ɗauka a wajen yana kuka ba sai da dare danazo rufe mana ƙofa na tarar daya tafi.muna zaune cikin ɗakin aka ƙiran magrib duk muka miƙe mukaje mukayi sai da mukayi isha'i sannan muka zubo sauran taliyan rana muka ci sannan muka baje tabarma a tsakar gidan muka zauna Daada tana ƙara mana karatun al-qur'ani dan tayi sauƙa wajen mahaifinsu babban malamine mai almajiri sunansa aka sanyawa Sagir.sai da muka kammala karatun Sha'awa ta maida qur'anan ɗaki ta dawo ta zauna.
Na riƙo hannun Daada nasa cikin nawa ina ƙara yalwata annurin dake shimfiɗe akan fuskata nace"Daadarmu Allah ya sauƙe ki lafiya,Allah yasa namiji ne mu sama ɗan-uwa".Sha'awa tayi saurin faɗin"ni kuma mace nakeso wallahi"na galla mata hararar gefen ido"Nidai namiji nakeso tunda bamu dasu da yawa Allah ya amshi roƙo na".Daada ta murmusa har sai da kyawawan wushiryata irin nawa suka bayyana tace"Allah ya kawo masu albarka"muka amsa da amin.
Tana rufe bakinta Abba ya shigo kamar an jefo shi yana ƙwala mini ƙiran mafarauta,nayi saurin miƙewa na isa gabansa na tsuguna kaina na kallon ƙasa nace"Abba gani".yayi wata ƙazamar gyatsa mai wari na kawar da kaina hawaye na ziraro mini ta gefe da gefen ido."ki kasa kunne da kyau ki saurara abunda zan faɗa miki".bance komai ya ɗaura da faɗin"yau an saka caca mai zafi kowa sai saka abunda ya mallaka yake yi domin nuna bajinta da nuna cewa kaina ka isa,ni kuma naga banida wani abunda zan sanya mai daraja kamar ke UMMUKURSUM nace nasa ƴata inhar aka cinye ni to zan aurawa duk wanda ya cinye ni aurenta in taƙaice miki zance dai yanzu an cinye ni daman caca ta gada haka yau a cika gobe kaci waninka,yanzu ki tashi daga ƙarƙashin ikona ki koma ƙarƙashin ikon Buba uban ƴan caca ko yau ya kawo sadaki zan aura masa abarsa faƙat".tun daya fara maganar na tsayar da ƙwayar idona akansa har yakai aya bansa sanda na zube daga tsugunan da nayi ba sai jina nayi na tafi luuuu.....
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
________________________________
Page 0⃣3⃣
Sha'awa tayi saurin riƙeni Daada ta tashi da ƙyar tana gyara ɗaurin zaninta.
"Haba malam ina ka taɓa ganin ansa mutum sukutum a caca sai kace a garin gaɓa-gaɓa in dai ni na ɗauki cikin Ummukursum a jikina na tsawon wata tara nayi nishin naƙudanta kuma naketa haƙƙi akanta ban yarda da wannan haɗin ba,ko wasu iyaye zasu so aurar da ƴaƴansu izuwa ga nagartaccen miji domin inganta rayuwar gobensu amma kai malam ako yaushe burinka bai wuce ka wulaƙanta rayuwar ƴaƴanka".furcin Daada kenan ta ƙare zance cikin ƙaryewar murna kuka mai ƙarfi nake sarwa na buɗe dukkan muryata ina rero sa Sha'awa ta ƙara ƙarfin riƙon da tayi kafin takai ga furta abunda dake ɗauke akan leɓɓanta Abba ya soma faɗin"ince dai da kai da kaya ai duk mallakan wuyane da Ummukursum da Sha'awa dukkansu mallaki nane babu mai ƙarfi iko akansu sama da ni ɗin da kika raina.na yanke hukunci na bada auren Ummukursum ga Buba uban ƴan caca kuma tun daga yanzu da muke wannan maganar ko gobe ya kawo sadaki zai ɗauke ta su tafi,banda baƙin jini irin nasu ma ace har yanzu babu wanda ya taɓa zuwa ƙofar gidan nan da sunan yana neman auren ɗaya daga cikinsu".Maganar da Daada ta soma ya sanya Abba miƙewa tsaye ya shiga sauƙe mata kyawawan maruka hagu da dama.
Nan take naji wani sabon ƙarfi yazo mini nayi azaman tashi tare da fisge jikina daga na Sha'awa na isa ga Daada,da take tangal-tangal zata faɗi sakamakon marin da Abba ya mata na riƙe tsam!a jikina ina ƙara tsananta kukan danake yi naji wani abu tamkar garwashin wuta a fagen ƙuna ya soki ƙalbina,cikin muryata da take rawa da bayyanar da tashin hankalin dake tattare a cikinta na soma faɗin"Abba nayi biyayya ga umarninka kuma zan zauna inka ɗaura mini aure da ko wanene,na tabbatar duk wanda yayi riƙo da biyayyan iyaye basai taɓe ba nagode da ƙoƙarin sauƙe haƙƙinmu na aurar damu dayake kanka da kake ƙoƙarin yi".
Ina kawowa nan a zantukana naja hannun Daada da numfashinta ke sarƙewa yana fita da sauri-sauri mukayi ɗaki,sai dana zaunar da ita akan shimfiɗar mu sannan Sha'awa ta biyo bayan mu ina ɗagowa idanunmu suka sarƙe cikin na juna nayi saurin kawar da nawa gefe.
"Wallahi Anty Ummu bazaki auri wannan mutumin ba zanyi komai domin ganin an soke wannan auren koda raina nane zan bayar fansa.wallahi mutumin nan ba mutumin kirki bane kowa ya shaidesa akan hakan shiyasa tun muna ƙanana mukejin labarin yanda yake lalata da ƴaƴan mutane,shiyasa ya kasa samun matar aure amma Abba dayake baya kishin mu zaice ya baki shi ya sanya ki a caca"ta ƙara fashewa da wani kukan mai matuƙar sauti a hankali na duƙar da kaina ƙasa ina zaune kusa da ƙafafun Daada ashe kuka ma waje ya samo domin duk yanda naso na zubda hawaye ko zanji sausauci a sashin ruhina amma lamarin ya faskara.ji danayi Sha'awa ta faɗu jikina tana saki kukanta ya sanyani ɗago kaina sannan na riƙo hannunta"Sha'awa ki kwantar da hankalinki SALON ƘADDARATA ce haƙiƙa tsarkakekken zuciya bata fushi da ƙaddata Sha'awa ki tayani da addu Allah ya bani ikon cin wannan jarabawan".muka ƙara rungume juna mun daɗe a haka kafin na tsinkayo muryan Daadata tana faɗin"Ummukursum Allah ya muku albarka amma matuƙar ina numfashi bazan taɓa lamintan wannan lamarin da malam yazo dashi ba,akan hakan na gwammace ya sake ni".
"Daada ki kwanta ki huta dan Allah kar kisa wannan abun a ranki,kinga lafiya bata wadace ki ba"na ƙarishe zancen ina mata tausa a ƙafafunta Sha'awa ta soma ƙoƙarin yin wata maganan na dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu na ɗaura da cewa"Sha'awa mubar wannan maganar dan Allah"bata koma cewa komai ba ta koma can gefe guda ta takure cikin hijabinta,sannu a hankali nake yiwa Daada tausa har bacci yayi nasaran ɗaukarta.
Tsawon wannan daren bacci ya gagari idanuwa ƙiran assalatun farko kuwa kamar acikin kunnuwa akayisa na tashi nayi salla sannan na tada Daada da Sha'awa,ina ƙidar da nawa sallan nakoma na kwanta ban tashi ba sai wajajen ƙarfe bakwai na fito tsakar gida na iske Sha'awa tana wanke-wanke ta gaishe ni na amsa tare da leƙa ɗakin Daada na ga har yanzu bata tashi ba sannan nazo na fara aikin dana sabar da kaina dasu a kowacce safiyar duniya.
Tun daren jiya na ƙudurce a raina cewa zanje mu tattauna da Sagir akan wannan maganan shi kadai yazo mini rai kuma nakeda yaƙinin zai tsaya min tsayin daka.
***********************
Babban asibitine mai yalwan fili da shuke-shuke manya gini dogaye ne a cikinsa da aka yi masu gini dai-dai da tafiyar zamani mutane ne ta ko'ina ke wulgawa cikin compound ɗin asibitin manya manyan gate ne guda huɗu farare tas a asibiti da ko'ina yake ɗaure da nashi securities ɗin,a hankali ya danna horn ɗin motar gate man ya fito da ɗan saurinsa shima uniform ne a jikinsa yazo ya buɗe masa kasancewar yasan shi ɗaya ne yake shigowa ta wannan gate ɗin,ya zuge masa gate ɗin dayake ɗauke da sunan asibitin da manyan harrufa ZAYYAD EL-FAROUK SPECIALIST HOSPITAL gamayar hakan ya bada sunan ZAYFA HOSPITAL.
Yana ɗaya daga cikin manya-manyan asibitocin da ake ji dasu a kaf!faɗin jahar kaduna,sai daya dai-dai parking cikin ɗan madaidaicin parking space ɗinsa mai ɗaukar motoci biyu kacal sannan ya zaro ƙafafunsa da suke sitirce cikin baƙar covershoe, wajen mintuna biyar a tsakali sannan ya fito da sauran gangan jikinsa sanye yake cikin shigar nevy blue ɗin suit da light blue ɗin long sleeve a jiki necktie ɗinsa baƙi,hannunsa na dama wani farin zoben azurfa ne dayake ta ƙyalƙi ya murza zoben a hankali as he taking his step ya zagayo ya buɗe bayan motan ya ɗauko jakansa securityn daya taso domin karɓan jakan ya ɗagawa hannu alaman ya dakata sannan ya ɗauki hanyar da zata sada shi da ƙofar ofice ɗinsa.
Ƙoface aka fitar masa daga baya ta yanda babu wanda zaisan shigowarsa balle fitansa,shurun wajen zai sanya mutum tinanin ba cikin asibitin bane wani kyakykyawan garden na hango ya zubawa idanuwa dayake ɗauke da shuku-shuke korayen flowers da tsuntsaye,dogune sosai mai duhun launin fata baƙinsa har wani sheƙi yakeyi da ɗauƙar ido.
A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar tare dayi sallama wanda ya kasance ɗabi'arsa duk dayasan cewa ciki babu kowa amma yasan mala'iku zasu amsa,wani ni'imtaccen ƙamshi ne yake tashi daga ko wacce kusurwa daga cikin office ɗin sai sanyin AC dake tashi,komai na cikinsa Ash colour tunda daga kan kujeru,carpet da kuma dogayen labulayen office ɗin.
Kan kujerarsa dake fuskarta ƙofar reception ya zauna yana lumshe idanunsa,file-file ne sosai akan teburin gabansa da kuma laptop ɗinsa can gefe guda kuwa tarin lambobin yabo ne da karramawa daya samu akan aikinsa na likitanci da makeken photonsa a jikin wall ɗin office ɗin da aka haɗa aka gine tare dashi.gaban teburin sunansa ne a ajiye DR.ZAYYAD EL-FAROUK BAITA.
Ya daɗe idanunsa a lumshe sai da aka fara knocking a ƙofar office ɗin kafin ya fara ƙoƙarin ware idanunsa,can ƙasan maƙoshinsa yayi iznin shigowa PA ɗinsa ya shigo ya ladabtar da murya kafin ya gaishe shi kansa kawai ya ɗaga masa da wani azababben ciwon kai ya sauƙar masa.
"Sir matan nan mai ciki wacce za ayiwa Cs sun gama clearing komai kai kaɗai ake jira"
Gently ya miƙe yana gyara zaman suit ɗin dake jikinsa suka fito tare sai daya sauya shigansa izuwa na operation kafin suka shiga operation ɗin sosai matar ta kumbura ɗanne ya dawo ƙirjinta ya tokare mata successfuly akayi tiyatan aka ciro mata yaronta na miji one hour after the operation matar ta rasu a hankali ya zame face mask ɗin dake maƙale a fuskarsa ya zauna ya ƙarewa fuskar jaririn kallo yanda yaketa mirtsukuku yana ɗan sakin kukan yunwa ya ƙara karyar masa da ruhi.
A lokuta da yawa tausayin kansa ne yake zuwar masa a duk sa'in da mace ta rasu tabar jariri,a cikin irin wannan rayuwar maraicin ya taso ana haifan sa mahaifiyarsa ta rasu,ko ɗumin jikinta mai jiba bai rayu da mahaifinsa ba har sai da yayi shekara ashirin da biyar kafin yasan yanada mahaifi har da ƙanne.farin zoben azurfan dake hannunsa ya murza a hankali yana sadda kansa ƙasa kafin ya miƙe ya ɗauki jaririn ya ƙira masa salla acikin kunnensa na dama kaamar yanda addinin islama ya tanada.
Sai da nurses suka gyara jaririn suka sanya masa kayan sanyi saboda yanayin hunturon da akeyi a wannan lokacin suka mulkesa da man zaitun,da kansa ya ɗauki jaririn ya fito dashi izuwa ga dangin mahaifinsa,ya miƙa musu shi.
"A kula da rayuwarsa tarbiyarsa da ilminsa ku tarbiyantar dashi ya zamto sadaƙatul-jariya ga mahaifiyarsa a bayan ƙasa"yana kawowa nan ya miƙa musu jaririn tare da ƙara miƙa musu nashi saƙon ta'aziyar.
Sosai kansa ya ƙara sara masa saboda dogon maganan da yayi yana komawa office ya zare kayan tiyatan dake jikinsa yasa waɗanda yazo dasu ya fito ta ƙofar baya mota ya shiga ya mata key gate man ya buɗe masa da sauri ya fita.cikin Unguwar sarki ya nufa farkon layin ya tsaya bakin wani gate mai ɗaukar ido take kansa ya ƙara sarawa ya kai mintuna goma shabiyar kafin aka buɗe masa gate ɗin ya shigo yayi parking cikin parking lot.
Direct part ɗinsa ya nufa tun daga ƙofa yake jiyo sautin kiɗan daya ke tashi daga cikin falon ya ciro leɓɓansa na ƙasa sosai,sannan ya tura ƙofar falon ya shiga ƙannensa Haidar da Adam ne keta busa hayaƙin shishi ya karaɗe ko'ina da sauri ya koma da baya yana zaro face mask ɗinsa yana sawa saboda asthman dayake ɗauke da ita da sauri ya koma falon ya wuce ɗakinsa dayake farko acikin ɗakuna uku dasu ɗauke cikin falon.
Sai daya maida ƙofar ya rufe sannan ya jingina kansa a jikinsa yana kokuwa da numfashinsa dake barazanar ɗaukewa,inhalern sa ya ciro ya fara amfani da ita a hankali ya fara sulalewa zuwa ƙasa ya zauna yana fitar da numfashin wahala dariya da shewar dasu Haidar suka sakar masa dayake shigowa ya fara dawo masa.
Ya daɗe kafin ya miƙe ransa cike da tinani kala-kala SALON ƘADDARARSA yana tafiya da abubuwa daban-daban da sukafi ƙarfin kwakwalwa.bathroom ya shiga yayi wanka sannan yafito ya shiga cikin manya kaya shigar jamfa yayi fari sol mai santsi,dan baya iya zuwa gaban Hajiyarsa da shigan ƙananan kaya.ya maƙala agogonsa da kuma gilashinsa dayake ƙara masa ƙarfin gani ya saka sannan yamaida face mask ɗinsa ya fito.
Bai tarar da kowa a falonsa ya fito wajen motarsa ya shiga ya fice daga gidan kansa tsaye cikin karamar hukumar zaria yanufa cikin samaru.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
______________________________
Page 0⃣4⃣
Sosai yake zuga gudu akan titin har ya isa cikin zaria Atiku flyover dake samaru ya nufa bakin wani gate yaja burji dai-dai lokacin numfashinsa ya fara sarƙewa anan waje ya bar motar ya fito ya shiga cikin gidan gate man ya taso da sauri ya iso gareshi yana tambayarsa lafiya kansa kawai ya gyaɗa masa yana ɗaukar hanyar da zata sadashi da ƙofar falon.
A nutse ya murɗa handle ɗin ya shiga bakinsa ɗauke da siririyar sallamar daya tsaya iya kan laɓɓansa,zaune take akan cushion mai aikinta tana mata tausa jin sallamarsa ya sata saurin miƙewa ta nufo shi tare da riƙo hannunsa suka zauna akan carpet kwantar da kansa yayi akan cinyarta yana sauƙe ajiyan numfashi akai akai hannunta tasa cikin sumar kansa tana shafawa a hankali.
Cikin muryarta mai cike da kamala da dattaku tace"Ubana meyake faruwa ne waye ya kuma ɓata maka rai kuma,meya faru acan gidan nakun?,a dunƙule ta jefa masa tambayoyin sanin da tayi ko yaya ransa ya ɓaci sai ciwonsa na asthma ya tashi.
Sai a sannan ya ɗago idanunsa da sukayi jajir jijiyar kansa sun fito raɗau yace"Hajiyata bansan meye na aikata mata ba da batason ganin nayi farin-ciki a rayuwata,hatta ƴaƴanta basa sona basa min kallon ɗan-uwa mahaifina bai damu da sanin halin danake ciki ba rayuwar kasuwancinsa shine gaba da komai a gare shi.Hajiya KECE MADADI(sunan littafina mai fitowa in sha Allahu)dukkan wani farin-ciki a rayuwata har izuwa yanzu".
Yana kawowa nan ya ƙasa cusa kansa akan cinyarta yana sauƙe ajiyan zuciya,sosai maganganun Zayyad suka ƙara narkar mata da zuciya shi ɗin amanar hajiya Shamsiyya ne a gareta lokacin da zata haife shi Alhaji baya ƙasar da ita sai mahaifiyar su Haidar,Hajiya Amina ƙiyayyar Hajiya Amina ga Zayyad tun yana cikin cikin uwarsa domin ita Allah bai bata haihuwa.
Tayi yunƙurin kashe Shamsiyya da abunda yake cikinsa sau babu iyaka Allah bai nufeta da samun nasara ba,ranar da za'a haife shi tace likita ya kashe shi yana fitowa zata bashi ko menene a duniya jin haka ya sanyan Shamsiyya guduwa daga gidan tare Shatu(Hajiya)a hanyarsu ta barin cikin kaduna Shamsiyya ta haihu ta damƙa amanarsa a hannun Shatu tare da cewa ta nisanta shi daga gidan ubansa har sai ya mallaki hankalin kansa kafin ta dawo dashi.Awa ɗaya bayan haihuwarsa Shamsiyya ta rasu haka Shatu ta rungumi Zayyad tun daga ranar ta koma ƙauyensu dashi iyayenta suka koro ta ganinta da jariri sabon haihu duk yanda taso fahimtar dasu kasa fahimta sukayi ta dawo Zaria ta sama aikin wanke-wanke da shara a wani gida da wannan kuɗi ta cigaba da ɗaukar ɗawainiyar rayuwar Zayyad har izuwa lokacin daya isa shiga makaratanta alhajin da take aiki a gidansa ya sashi har ya gama secondary ya sama scholar ship yaje ƙasar syria yayi karatun likitanci sai daya dawo sannan Shatu ta sanar dashi labarin yanada mahaifi harma da ƙanne kuma ta maida shi ga mahaifinsa kamar yanda taɗaukarwa mahaifiyarsa alƙawari.
A hankali ta ɗago kansa daga kan cinyarta takai hannunta tana goge masa ruwan hawayen dayake yi kafin tayi ƙarfin halin furta"ya isa haka Zayyad komai na rayuwar nan mai wucewa ne wataran sai labari ka cigaba da haƙuri hakaa mahaifiyarka tayi wannan haƙurin har ta koma ga Allah"kansa kawai ya ɗaga mata ta miƙar dashi suka nufa dinning area ta zuba masa abinci ta fara bashi da kanta a baki sosai ya zaki ransa inda abunda yake saurin kawar masa da damuwa da sanya shi shauƙi bai wuce ya gansa gashi ga Hajiyarsa ba.
Ji yake bashi da tamkarta duk faɗin duniya shiyasa ya ɗauke mata komai ma'aikata ya zuba mata a gidan sosai zuwanta aikin hajji da umra kuwa bazasu irgu ba,komai ya samu dalilinta ne domin wahalan da tasha akansa tamkar zanen da aka yishi akan dutsi ne baya gogewa a cikin kwakwalwarsa saboda shi har yau bata taɓa aure ba.
Sai data cika masa cikinsa tam!kafin suka dawo falo suka zauna suka cigaba da hirarsu.
Sai dare sosai kafin yayi niyar dawowa cikin kaduna har jikin mota ta rakosa tare da dafa kansa yana masa addu'a kamar yanda ta saba,ya riƙo hannunta tare da manna mata kiss ya marairaice murya yace"Hajiyata inasonki"murmushi ta sakar masa tace"inasonka ɗan amana na".
"Ki shiga ciki sai naga shigarki zan tafi"murmusawa kawai tayi takoma ciki dan tasan hakan ɗabi'arsa ne,tana shiga ya wuce wajen ma'iakatan gidan yana ƙara jaddada musu akan su kula sosai da aikinsu su kuma guji dukkan abunda zai baƙantawa Hajiya.yana gamawa wannan jawabin ya bi kansa da naira dubu ashirin-ashirin ya taba musu sannan ya koma wajen motarsa ya data ita ya tafi har ya isa cikin kaduna yana waya da hajiyarta sai daya shigo cikin gidan kafin sukayi sallama.
Part ɗinsu ya nufa ya wuce bedroom ɗinsa kai tsaye yayi wanka sannan ya ɗauro alwala ya fito ya tada sallan nafila yana iddawar yafara karanto alqur'ani cikin ƙwarewa da fitar da haƙƙin ko wani harafi.kamar jira su Haidar sukeyi ya fara karatun sunka fara shan shishan su take jikinsa ya fara rawa ya tsani warinsa kamar mutuwarsa yatashi da sauri ya nufi bathroom ya fara kwata amai sosai yake aman sannan ya wanke fuskarsa ya fito ya kwanta akan bed idanunsa suna kallon ceiling.
Tun zuwarsa gidan Nenne data fahimci yana ɗauke da wannan ciwon tasa Haidar da Adam dawowa part ɗin da aba basa,koda Alhaji ya nema jin dalili sai tace saboda suna kula dashi koda ciwonsa zai tashi,wanda a zahirin gaskiya ba haka bane wani mummunan nufine ƙasan zuciyarta da ta barwa kanta sani.ko gaisuwarshi bata amsa balle ta mishi kyakykyawan kallo shi kuwa Alhaji bai fiye zama a ƙasar ba.
Wayarsa dake kan site drawer ne ta soma ringing ya mirgina ya ɗauka tare da ɗaga ƙiran ganin sunan Alhajinsu ya bayyana cikin screen ɗin wayar.
Cikin sanyin muryasa yayi sallama haɗi da gaishesa ya amsa tare da tambayar sa yanayin jikin nasa da kuwa asibiti duk ya amsa da alhamdulillah yana gyara kwanciyarsa.
"Son ina fatan dai komai lafiya su Haidar basa takura maka tunda Hajiya tace su dawo part ɗinka hankalina bai kwanta ba"sai dayayi nisa kafin yace"babu komai Daddy nima ɗin nafi jin daɗin suna kusa dani".Alhaji ya sauƙe ajiyan zuciya sun ɗan taɓa hira kafin sukayi sallama ya cilla wayar gefe yana fitar da numfashi ɗai-ɗai babu jima bacci yayi gaba dashi.
Ina zaune kan dakalin ƙofar ɗakinmu na zabga tagumi hannu bibiyu maganganun da mukayi da Sagir suna dawo mini cikin kwaryan kaina,yaci alwashin matuƙar Abba ya aura mini Buba uban ƴan caca sai ya kashe shi kuma ya kashe kansa.
Da sauri na runtse idona da suka kumbura tsimtim sakamakon rashin baccin danake fuskanta cikin kwanakin nan,tsirarun hawaye suka shiga gangaro min ta gefe da gefen fuskana nayi saurin miƙewa na shige ɗaki na zaro hijab ɗina na fito na ɗaga labulen ɗakin Daada tana kwance ƙafafunta sun koma kumbura na tsuguna kusanta"Daada bari naje gidan Anty Hussaina".
Ta sauƙe wani wahalanlan numfashi tace"dan Allah karki ɗade ki gaishe ta inkin je".
"Anya Daada kina shan jiƙonki kuwa?".
"Ummukursum wannan cikin ban taɓa ɗaukar ciki mai wahalar saba,inajin kamar na tafiya ne".furcin Daada ya sani sauri matso hawayena na soma faɗin"Daada ki daina faɗin haka in sha Allah zaki haife wannan cikin kamar ko wanne ki haifo mana santalelen ƙanninmu".nakai ƙarshe ina riƙo hannunta na sakar mini tauttausan murmushi har sai da wushiyarta suka bayyana na miƙe na fice daga ɗakin ina yarshe ƙwallar da suka taro mini a cikin ƙwayoyin idona.
Ina fitowa na tafi adai-daita sahu yakai ni unguwan Anty Hussaina ina sauƙa na miƙa masa naira hamsin ɗinsa,wani matashin dayake cikin adai-daitan yace"kije kawai zan bashi".ban tsaya dogon magana dashi ba na gabatar masa da godiya na tsallaka titi na shige gidan Anty Hussaina.
Sallamar dana shigo da ita ya sata washe baki tana mini sannu da zuwa kafin ƴarta Humaira ta shimfiɗa mana tabarma muka zauna na gaisheta ta amsa kafin ƴaƴanta Humaira dasu Musaddik duk suka gaishe ni na amsa cikin sakin fuska.
"Ummukursum ya jikin Adda Hassanan?"na numfasa kafin nace"to da sauƙi dai zamu ce dan har yanzu bamuje asibiti ba Sagir ne daman yace zai kaita ranar dayaso kuma akayi rashin sa'a ya tadda Abba a gida ya kore sa".ta tafa hannu gami da rafka salati da sallami ta riƙe haɓa"lamarin malam Nura sai dai addu'a,mutumin nan bansan abunda yake damunsa ba gashi ya ɗauke ki ya sanya ki a caca tsabar rashin sanin darajar iyalinsa".na jijjina kaina kawai ina rusunar da ido Humaira ta fito cikin shirinta zata tafi makaranta tana jami'ar Abubakar tabawa ɓalewa babban yayansu kuwa yana can kogi state yana kataru sai Musaddik ƴaranta kenan.
Sallama tayiwa Anty Hussaina sannan nima ta min tare da bani saƙon gaisuwa inkaiwa Sha'awa,na bita da kallo yayin da take fice daga cikin gidan rayuwar auren Anty Hussaina da mijinta yana burgeni yanda ya damu da rayuwar ƴaƴansa da karatunsu.maganar da Anty Hussaina ta somayi ya sani dawowa cikin hayyacina daga tinanin dana faɗa.
"Mezai hana kizo nan Ummukursum kiyi zamanki har izuwa lokacin da Abbanku zai janye maganar auran nan,kafin nan Abban su Humaira ya dawo sai yaje ya masa magana ko zaiji".
Wani murmushin takaici na saka lokaci guda nace"Anty kenan gwara dai na zauna acan ɗin hankalina zaifi kwanciya kusa da Daada"ta kalloni da tsabar idanunta da tausayina ya shimfiɗa cikinsu kafin min taje kitchen na dafa abunda zanci na miƙe na nufi kitchen ɗin.
Doya na soya sannan nayi stew naci sai yamma lilis sannan nayi haramar tafiya ta haɗa ni da naira dubu biyar tace mukai Daada asibiti duk abunda ake ciki na ƙirata a salula na sanar da ita,ragowar abincin ranan da na mana ta juye min tace na taho dashi.
A hanyata ta tafiya gida na hango Abba a rumfar cacarsu tare da Buba uban ƴan caca na ƙara saurin danakeyi ƙafafuna har harharɗewa sukayi,kaɗan daga cikin aikin Abba ne yanzu ya kwala min ƙira ya fara nuna ni ga abokan cacarsa.ina samun adai-daita ko ciniki bamuyi ba na hau zuciyata tana mini zafi sosai mussamman dana gano irin abincin da Abba yake ci a waje.
Shinkafa da wake da miya hadda yankan naman sa ɗaya da goran kunun aya a gefe,hawaye suka zubo min yau kusan sati biyu kenan da ɗoriya Abba bai kawo mana ko ƙwayar tsabar masara cikin gidan nan ba kullum cikin babu yake.ta cikin madubin adai-daita sahun mai adaidaitan ya kalloni haɗi da faɗin"Lafiya kuwa yayata?"nayi saurin kai hannayena na kawar da hawayen dake gudana saman dandamalin fuskana nayi jarumtar furta"babu komai muje kawai".
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
________________________________
Page 0⃣5⃣
Ina sauƙa na zaro naira ɗari biyar daga cikin kuɗin da Anty Hussaina ta bani ya zari kuɗinsa ya bani canjina nayi gaba sai dana tsaya a soro na dai-daita nutsuwata tare da ƙaƙalo murmushin dole na yaɓa akan fuskata kafin na shiga cikin gidan bakina ɗaure da sallama.
Sha'awa na iske zaune a tsakar gidan tare da Daada tana ƙara mata karatu na kai mazaunaina na zauna kusa da inda Daada da miƙar da ƙafafunta sai dana ƙare mata kallo raina cike da tausayinta kafin na mata ya jiki ta amsa da alhamdulillah,kolulin abincin da Anty Hussaina ta haɗo ni dashi na diresu a gaban Daada tare da kora mata bayanan yanda mukayi da Anty Hussaina na ƙarishe zancen ina miƙa mata dubu biyar ɗin data bani da zummar akai Daada asibiti.
Jim tayi kamar mai nazarin wani abu kafin tace"an gode yanda take ɗawwainiya damu Allah ya tashi ƴaƴanta suma su mata".
"Amin amin"muka haɗa baki da Sha'awa wajen faɗi kafin na miƙe nayi ɗakinmu jin kaɗan na fito na wuce banɗaki nayi wanka sannan na ɗauro alwalar sallan magrib da aka fara ƙira,ina zara kayana na tada sallan na daɗe akan sallaya ina addu'ar nemawa kaina sauƙi sai danayi isha'i sannan na zare hijabin daga kaina dai-dai zan fito wayata ta hau ruri na koma na ɗauka ganin sunan Sagir ya bayyana cikin screen ɗin wayar ya sani na koma na zauna sannan na amsa ƙiran.
"Ya ake cikine ya janye ko kuwa?".
Muryarn Sagir kenan da suka dira a cikin kunnuwana na sauƙe ƙatuwar ajiyan zuciya ina ƙara lankwashe ƙafafuna waje guda"Sagir bazai janye ba ƘADDARATA CE a haka wataƙil bama daga cikin bayin da Allah ya ƙaddara zamuji daɗi a duniya,idan mukayi haƙuri sai mu tarar da babban rabo a can"hawaye masu ɗimi suka gangaro daga idaniyata.
Inajin yanda shima ya sauƙe tashi ajiyan zuciya kana yace"Ummukursum wallahi matuƙar ina numfashi a bayan ƙasa,bazaki auri wannan mutumin ba in sha Allah sai kin auri mijin da zai zame miki haske a cikin rayuwarki ki zuba ido kiga yanda zamuyi da Abba koda tsiya sai ya janye Buba uban ƴan caca sai yayi dana sanin zuwarsa duniya".yana kawowa nan a zancen sa ya gimtse ƙiran ya barni da faɗin"Sagir kabi komai a hankali".
Jin ya kashe wayar ya sani zareta daga kunnena cikin mutuwar jiki,nafi minti ashirin a zaune a wajen ina tukfa da warwara cikin raina waye zan tunkara da damuwar dake ƙasan ƙalbina?,waye zai dakatar da Abba daga haɗa wannan auren?.
Na zame hannuna daga tagumin danayi saboda karatun da zuciyata ta karanto mini babu wanda zai hana Abba abunda yayi ra'ayi,jiyo muryar Daada tana kwaɗa mini ya sani dawowa cikin hayyacina na fito da sauri.
"Wai me kaka tsaya yine a cikin ɗakin?"
"Daada Sai danayi sallan isha'i ne"na faɗa ina sanya takalma na sannan na ƙariso ga Sha'awa da take cin abinci na zauna nasa hannu muka fara ci Daada kuwa tayu sirkin kamu tana sha muna gama cin abuncin Sha'awa ta tattare kwanunkan takai ɗakin da muke jibge tarkacenmu a cikin.
Ta dawo ta zauna na fara soma leɓɓana da nufin furta kalma,Abba ya faɗo gidan yara suna biye dashi kamar kullum suna rera masa waƙar yayi marisa yasa banson.Sha'awa da take fitar da ƙwallan takaici ta tashi ta koresu tare da rufo ƙofar gidan.a ƙasa Abba ya zauna tanada wasu zantuka marasa kan gado kafin daga bisani ya ciro tabar sigari daga aljihun gaban rigarsa da nufin kunawa na jawo muryata da ƙarfi na soma faɗin"Dan Allah kayi haƙuri karka shata anan".ya ɗago ya kalleni kamar bazai mayar ba sai kuma ya mayar yana sakin wani shu'umin dariya yace"na mayar ƴar lelen Abbanta".
Na duƙar da kai ƙasa,Sha'awa ta miƙe tana saka takalmanta tace"Daada na tafi gidan Anty Sakina ɗazu ta turo kina banɗaki wai naje na tayata kwana,mijinta yayi tafiya".
"To Sha'awa ki gaisheta,dan Allah karki tsaya a ko'ina kinji ko".kanta kawai ta ɗaga bayan tayiwa Daada a kwana lafiya ta fice daga cikin gidan.
Na daɗe a wajen hadda Daada ta tashi ta shiga ɗaki ta barni zaune a wajen,na lura yanzu ta jima da nemawa kanta sauƙi ta hanyar yakice damuwar da ta danganci Abba daga ranta.
A hankali na miƙe bayan ƙatuwar ajiyan zuciyan dana sauƙe nace"Abba mu kwana lafiya"ban tsaya sauraran abunda zai faɗa ba na faɗa ɗaki tare da maida ƙofar langa-langan na rufe.kayan jikina na fara zarewa na ɗaura zani ɗaurin ƙirji na kwanta ina ƙarewa rufin ɗakin kallo tunin nayi nisa cikin tinanin danakeyi naji an fara sakin ruwan sama na kallo tagar ɗakin yanda ruwan yake zuba kamar da bakin kwayar.
Tinanin Sagir ya faɗo mini a rai tamkar faɗuwar adaru,yanzu ko a ina zai fake oho,wani tsohon kango ne suke rayuwa a cikinsa ko rufi babu,wani kuka mai ƙarfi ya biyo bayan numfashin dana sauƙe.
Figigi na ɗago kaina jida nayi an hankaɗo kofar ɗakin an shigo,idanuna tar!suka sauƙa akan fuskar Abba nayi azaman mikewa na rarimi hijabina na saka ina cewa"Abba lafiya?".
"Lafiya ƙalau ƴar leleta har yanzu bakiyi bacci ba?"ya faɗa yana ƙara nufo inda nake tsaye na dalle idonsa da tocin wayata dana kunna nace"e yanzu nakeso nayi".har ya zauna akan katifar yace"zauna muyi magana"zuciyata ta harba da mungun ƙarfi sakamakon kallon dayake mini yana tanɗe baki na zauna a tsorice kafin na ankara naji hannayensa a saman ƙirjina na zage iya ƙarfina na kurma ihu ya toshe min baki da takufan hannayensa.
Hawaye masu zafi suka fara rige-rigen fitowa daga idona na ƙwace jikina daga nashi nayi nisa ina faɗin"Abba kaifa mahaifina,shari'a ta haramta mana abunda kake ƙoƙarin aikatawa dani yanzu,Abba meyasa baka tausayinmu?ka fara sanya zuciyata kokotan anya kains mahaifina".yaɗan fara waige-waige ya kuma nufo nina kauce tare yin azaman ɗauko kwalban da muke ɗaura maganin sauro akai na runtse idanuna ina faɗin"Abba ka fita wallahi ka cigaba da tsayiwa anan zan iya yiwa kaina illa,zan kashe kaina kowa ya huta"..
"A'a Ummukursum sauƙe makamin ƙasa".na ƙara daka masa tsawa ina faɗin"Abba ka fita ko na kurma maka ihu".kafin na buɗe idona har ya fice daga ɗakin nayi saurin maida ƙofar na rufe ina sulalewa na toshe bakina ina hana sautin kukana fita"Ya Rabb ka kawomini haske cikin rayuwata".take jikina ya ɗauki rawa sanyin da ake busawa yana ratsa ilahirin gaɓoɓina na miƙe ina ƙara matse jikina waje guda naje kan katifarmu na zauna na saka kai cikin gwiwa ina kuka da takaicin hayayya irin na Abba har akayi ƙiran assalatu ban rutsa ba zuciyata ta kasa nutsuwa tinanin nake da zaran na rutsa Abba zai iya dawowa.
Ina iddar da sallan asuba na kwana akan sallayan baccin wahala ya kwashe ni,bansan awannin danayi ina kwance ba ina buɗe idona naga har rana ta fito nayi miƙa ina kamo sunana Allah cikin bakina na miƙe a hankali abubuwan da suka faru daren jiya suka fara dawo mini ƙoƙon kaina jikina sanyaye na fito na iske Sha'awa tana dama koko.Daada kuwa tana zaune akan tabarma tana karatun al-qur'ani.
Kusa da ita na zauna sannan na gaisheta,ta amsa kamin Sha'awa ta gaisheni na amsa tare da tambayarta inda ta samo gasaran da take damawa,tace anty Sakina ce ta haɗota dashi hadda ƙosai ta min nuni da wani ɗan madaidaicin kola.
"Ummukursum lafiya kuwa,ba ɗabi'arki bace komawa bacci bayan sallan asubahi ko baki da lafiya ne?".Daada ta jefo min tambayar data tarwatse min tinani nayi jarumtar furta"Daada kaina ne ke min ciwo".sai data rufe qur'anin dake hannunta kafin tace"Allah ya sauwaƙe,daman ni danaga baki fito ba nacewa Sha'awa wataƙil bakya jin daɗi ne karta tashe ki.yanzu kije ki kwanta inta gama dama kokon sai taje ta amso miki magani".
Tunin idona suka kawo ruwar ƙwalla tausayin Daada ya mamaye rai da ruhina,bazan iya sanar mata Abba na nema ba domin nasan babu shakkar hakan zai kai ruhinta ga kushewa duk sanin dana mata tanada matuƙar takwakali.
Duk gaɓoɓin jikina sunyi sanyi ƙalau na miƙe nayi ɗaki bansan hawaye ya zubo min ba sai jin Daada nayi tana faɗin"haba!Ummukursum yanzu ciwon kan kikeyiwa kuka?".bance da ita uffan ba na wuce ɗaki dan ji nayi kalaman baki sun gaza wajen fallasa damuwar dake ƙasan ƙalbina.
A hankali yake driving akan shimfiɗaɗɗiyar titin dake cikim unguwar sarki,a nutse ya lumshe fararen idanunsa yana sauƙe numfashi a lokaci guda kewar Hajiyarsa yana ziyartar rai da ruhinsa,dai-dai nan ya iso gate ɗin gidansu horn ɗaya yayi gateman ya fito ya buɗe masa a hankali ya gaida mai gadin nasun da ya manyanta sosai ya amsa cike da fara'a wani bangare na zuciyarta na cike da tausayin rayuwar irin ta Zayyad.
Sai daya tura hancin motar cikin sannan ya fito yazo ya rufe gate ɗin,lallausan murmushi ya sakar masa kana yace"Baba banajin daɗi naga kana buɗe mana gate da girmanka,shiyasa nakeson ayi providing wasu masu gadin kaima ka huta".
"ZAYYAD kenan,dukkan tausayi babu inda baka gado mahaifiyarka ba Hajiya Shamsiyya,Allah ya maka albarka yakuma kyautata rayuwarka ya haɗaka da mace ta gari".
Sai daya rusunar da kansa ƙasa kafin yace"Amin".kafin ya rufe bakinsa ƴaƴan Baba mai gadi Nana da Iman suka rugo da gudu yana ganinsu ya zube kan gwiwoyinsa tare da ware musu hannayensa suka faɗo jikinsa.
Site kiss ya mannawa Nana a chick suna masa sannu da zuwa tare da bashi labarin abunda aka koya musu a makaranta.mahaifiyarsu ta biyo bayansu bayan su gaisa da Zayyad ta ɗaura da faɗin"Nana ku duba kuga duk kun ɓata masa riga da datti".sai a sannan ya kai kallonsa ga gaban rigarsa da duk suka ɓata masa da datti.Baice uffan ba yaja hannayensu zuwa inda ya parking motar sa yabuɗe ya ciro manyan ledodin chocolate guda biyu ya damƙa musu.
Suka cika da murna suka ruga wajen mahaifiyarsu bayan sun masa godiya,kyakykyawan ajiyan zuciya ya sauƙe yana karantar farin-cikin daya lulluɓe fuskarsa.haka Allah yayi ruhinsa dason yara shiyasa tun dawowarsa gidan daya lura basa zuwa makaranta ya sasu ya kuma ɗauki nauyin karatunsu,motar ya koma yaje yayi parking ɗinta cikin parking space sannan ya ɗauko jakar labtop ɗinsa ya nufi part ɗinsa har yakai ƙofar part ɗin ya jita a rufe ransa yake ƙololuwar ɓaci ya nufi part ɗin Nenne neman su Haidar.
A hankali ya murɗa handling ɗin motar falon Nenne can-can yayi sallama yashiga babu kowa a ciki kansa tsaye ya nufi ɗakin su Haidar dan sunada ɗakunansu a part ɗin.har ya wuce ya dawo da baya ya kafe ƙofar ɗakin Nenne da kallo sakamakon nishin dayake jiyowa yana tashi daga cikin ɗaki,da sauri ya runtse idanunsa da lokaci guda suka rikiɗe kansa ya sara da matuƙar ƙarfi.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
_______________________________
Page 0⃣6⃣
Ya daɗe yana tsaye a wajen yana sauraran sumbaton da Nenne takeyi yayin aikata baɗalarta,ya nan a wajen aka rufo ƙofar ɗakin ko matsawa baiyi ba balle tinanin barin wajen.ƴar aikin da aka ɗauka last 3 mounth ya gani ta fito daga ɗakin cikin zungumemen hijab har ƙasa wani ƙazamin kallo ya watsa mata da rikiɗaɗɗun idanunsa tayi saurin duƙar da kansa ƙasa.
Kansa kawai ya girgiza ya wuce yabar wajen yana isa ɗakin Adam ya shiga ya kuwa hangi key ɗin a saman mirrow ya ɗauka ya fice ransa har wani soya yake masa,yana buɗewa ya wuce bedroom ɗinsa toilet ya faɗa yayi wanka ya fito yasaka long jallabiyarsa har ƙasa fari sol.ya kwanta akan bed yana sauƙe ajiyan numfashi tinaninsa kaf!ya taro waje guda ya rasa meyasa Nenne take aikata wannan alfashan da ƴan aikinta.
Jin numfashin sa ya fara cunkushewa waje guda ya sanya shi tashi ya ɓalle maɓallin wuyar rigan ya ɗauki wayarsa da labtop ɗinsa ya fice daga ɗakin sai daya kulle part ɗin kafin ya wuce cikin garden akan wasu shiryayyun kujeru da suke fuskantar juna ya zauna ya buɗe labtop ɗin ya fara latsawa,bai daɗe da zama ba wata house maid tazo wucewa ta durƙusa ta gaishe shi har tayi gaba ya kirata.
"Wannan ƴar aikin da aka kawo watannin uku da suka wuce,nakeson ki ƙira min ita menene ma sunanta?".
"Sa'ida".
"uhmm what ever ita zaki ƙira min".
Ta miƙe da saurinta taje ta ƙira masa ita,a hankali take takowa zuwa inda yake zaune yana operating system ɗinsa zuciyarta na mata lungudan tara-tara,tana isowa ta tsaya cikin rawar murya tace"ranka ya daɗe gani".wani firgitantan tsawa ya daka mata yana faɗin"zaki zauna ko zaki cigaba da tsayiwa min aka"ba shiri ta zube kan gwiwoyinta ya kafeta da ido yana zare gilashin dake saman karan hancinshi sautin kukan da takeyi ne kawai yake fita ƙasa-ƙasa.
"Meyasa kika amincewa Nenne kuke aikata abunda daga ku har ni muka san haramune,me kike tinanin zaku fuskanta idan har na sanarwa Daddy?".da hanzari ta shiga faɗin"Dan Allah karka sanarwa Alhaji wallahi da wannan aiki na dogara dagani har mahaifiyata,tirsasa min tayi har barazanan tabani da rayuwata tayi inban amince ba shiyasa na amince saboda da kuɗin wannan aikin nake jinyar mahaifiyata".
Miƙewa yayi ya sauƙe mata lafiyyayyun maruka biyu a kuncinta,yana huci yana faɗin"ke wata irin daƙiƙiyace,dole ne aikin da har zaisa ki manta da cewa mahaliccinki yana kallon duk abunda kike aikatawa,ko kina tinanin ita mahaifiyar taki intaji abunda kike aikatawa zakayi farin-ciki da hakan?".cikin ɗimuwar marin da bai gama sakinta ba ta jijjiga kanta alamar a'a sai daya naɗe hannayensa a bayansa dukka wannan wata al'adace dayake ɗabbakata a duk lokacin da ransa ya ɓaci ya ɗaura da faɗin"Na daɗe da sanin Nenne na aikatawa wannan abun but this is the frist time da nayi magana akan hakan let me warn you,daga yau kinbar wannan aikin inma mutuwa zakiyi sai dai ki mutu ki shirya gobe zaki kaini wajen mahaifiyar takin".
Yana kawowa nan ya kuma ya zauna ta rarrafo ta iso gabansa zata soma magana ya ɗaga mata alamar bayason jin komai"Abeg malama tashi ki tafi kar kisa min ciwon kai".sai data gama kukanta kafin ta miƙe tabar wajen rufe labtop ɗin yayi ya tashi ya tafi masallaci sai wajen ƙarfe tara sannan ya dawo ya wuce part ɗinsa wanka kawai yayi yasa kayan baccinsa ya kwanta dan bayajin sha'awar cin komai yanajin su Haidar suna knocking yazo ya buɗe mus yayi banza dasu dasuka uzura masa ya danne kana da pillow.
Washe gari da wuri ya shirya ya fito ya kaika aka ƙira masa Sa'ida ko kallon inda take baiyi ba yace"kije ki shirya kizo mu tafi"ta gwalo ido waje "ranka ya daɗe ina zamuje?".kallon daya watsa mata ya sanyata cinye sauran kalamanta a cikinta taje ta ɗauko hijab ɗinta ta fito a mota ta sameshi ta shiga muka fara tafi tunda ya tambayeta sunan unguwansu ta faɗa masa take kuka.ya faka motar ya daka mata tsawa"ke malama ki rufe min baki kafin na miƙa ki gun sojojin nan"tayu saurin rufe bakinta sannna yaja motar suka tafi.
Suna isa cikin unguwar ya nuna masa gidansu yace ta fita tace ana sallama da mahaifiyarta cikin kuka tace"bata da lafiya ko tafiya bata iya yi"yace to taje tace tayi baƙo zai shigo ta fita ta shiga ciki sannan ta dawo suka shiga tare.
Tsuganawa yayi kan ƙafarsa yanawa mahaifiyartatan sannu kafin ya ɗaura da faɗin"Inna ta sanar dani saboda kula da jinyar take wannan aikin,idan akayi la'akari da ƙarancin shekarunta wannan aikin yafi ƙarfin shekarunta.nizan ɗauki nauyin jinyarki sannan na mayar da ita makaranta".godiya mahaifiyarta ta masa sosai kafin Sa'ida ta sanar da ita cewa yaron gidan da take aiki ne ya galla mata harara yace ta shiryata su fito su tafi asibitin.
Yana mota suka iskeshi suka shiga yaja motar izuwa ZAYFA SPECIALIZED HOSPITAL,ganin motar akayi saurin zuge masa gate ya shiga suka fito ya ƙira wani Doctor a waya ya masa bayanin ciwon natan tare da umartar yayi handling case ɗin,yana kashe wayar Doctor ɗin ya fito ya shiga dasu har zai shiga mota ya jiyo muryan Sa'ida na faɗin"Ranka ya daɗe mun gode da taimakon daka mana baza mu taɓa mantawa dakai ba,yanda ka yaye mana damuwarmu Allah ya yaye maka naka".
"Look badan ke nayi ba"yana kawowa nan ya faɗa motar ya tafi bai cika son yawan magana haka ba,mussamman da mace yanda yakejin ransa baya jin yau zai iya zaman office gida kai tsaye ya wuce tunda Baba mai gadi yake buɗe masa gate yake shaida masa Nenne tace tana nemansa da zaran ya dawo.ciki-ciki yayi tsaki dan ba ƙaramin tsanar ganin fuskarta yayi ba yana gama parking ya shiga part ɗinta tana tsaye sai safa da marwa takeyi,Adam da Haidar suma suma tsaye sai ƴar aikin da jiya ya aika ta ƙira masa Sa'ida.
Sai daya iso tsakiyar falon kafin yace"Nenne gani ance kina nemana"sau data dako gabansa kafin tace"Zayyad bansan me kakeson ka maida mu acikin gidan nan ba,jiyaka ƙi buɗewa su Haidar ƙofa yau da safe kuma ka ɗauki Sa'ida kun fita tun sassafe yanz kuma ka dawo babu ita.ina kukaje ina kakai ƴar mutane".
Adam ya karɓe zance da cewa"tambaye shi dai Nenne a haka ya nuna kamar yafi kowa sanin Allah"
"Nenne na maida ita ga mahaifiyarta,tabar aikin daga yau a nemo wata ta maye gurbinta"ya faɗa har yanzu kansa yana kallon ƙasa.ta hanzuƙa"Meye dalilinka na koran min ƴan aiki,kai ka kawo min koko?".sai a wannan sa'in ya ɗago kansa ya sauƙe idanunsa tar!akan fuskarta"Nenne dalili kike tambayata?,saboda tsamuta daga halakan da kike ƙoƙarin jefa rayuwarta aciki ba tare da tausayi ba".
Yana kawowa nan a zancensa ya fice daga falon yana hucin ɓacin rai,tunin jikin Nenne ya ɗauki mazari ta fara gaskata hashashen zuciyarta kardai Zayyad yasan abunda take aikatawa a ɓoye?,dole ne tasan ta hanyar da zata ɓullo masa gudun tonuwar asirin da ta daɗe tana lulluɓewa.
"Nenne lafiya wai meye magana akai ne,wani halaka zaki jefata"?furcin Adam kenan daya sanyata ƙara ruɗewa"Babu komai to ni ina zan sani"ya hau upstair da sauri ta nufi bedroom ɗinta.ya zama dolr tasan yadda zata katse da rayuwar Zayyad abayan ƙasa kamar yanda ta katse na mahaifiyarsa.
Tana isa part ɗinsa ya wuce bedroom kulle kansa yayi,yayi kwanciyarsa yanajin yanda kansa yake sarawa da ƙarfi har jijiyoyin kan su fito raɗau-raɗau.cikin ransa yana girmama ƙarfin halin Nenne da har ta iya masa wannan tambayar.
Tun ranar da Abba ya shigo mini ɗaki ban ƙara sa shi cikin ƙwayoyin idona ba,haka nan nabar abun a maƙele acikin raina duk lokacin dana yunƙuro da niyyar faɗa mata sai naji kamar an ɗaure mini baki
Bai ƙara zuwa gidan ba haka nan muma bamu damu dasanin halin dayake ciki ba,tashin hankali ya yawaita a gareni saboda jikin Daada daya matsa mata kwana biyu duk ta kumbura kamar zata fashe ga jinin dayake zuba daga jikin wanda ba musan dalilinsa ba.
Sagir na ƙira na sanarwa da kuma Anty Hussaina a ranar Anty Hussaina tazo ta dubata tare da tsareni da tuhuma akan kuɗin data bani akai Daada asibiti,nima naso ace munkaita asibitin amma ita ta nuna batason zuwa duk magiyar dana mata amma ta ƙi haka mukasa kuɗin a gaba muka cefane acikinsa,sauran kuwa Sha'awa ta karɓo mata magani a chemist dashi.
Ina zaune ina wanki duk jikina babu kuzari banji shigowarsa ba sai ganin sa nayi tsugune a gabana,numfashinsa dab dani.na ɗado na watsa masa harara kafin nace"Kai Sagir wai meye haka zaka faɗo mana gida babu sallama".
Bai damu da hararar danake jifansa dashi yace"Afuwan Antyna ya jikin Daada ina take?".
"Tana ɗaki"na faɗa ina karantar yanayin fuskarsa kafin na ƙara da wani abu ya ajiye mini baƙar leda a gabana"gashi wannan a dafa mata taci sannan akwai magani a ciki na ƙarin jini shima tasha,dan Allah kar kice mata ni nakawo dan nasan inta sani bazata ci ba".
Yana zuwa nan ya miƙe zai fice muryar Daada data bugu dodon kunnuwanmu yasa shi tsayawa cak!ba tare daya waigo ba.
"Sagir duk abunda zai fito daga hannunka ya haramta a gareni,domin bata hanyar halal ka same shi ba".furcin Daada kenan daya sanya Sagir juyowa ƙwalla suka ciko masa idaniya rabon danaga hawaye a fuskarsa tun ranar da Abba ya kore shi daga gida sai kuma yau.
Kan gwiwoyinsa ya zube har yanzun hawaye na zuba masa yace"Daada dan Allah ki sausauta fushinki a gareni wallahi yanzu a duniya gabaɗaya babu abunda yake sanya ni cikin ruɗani da tashin hankali kamar fushin ki a gareni".
Kalaman Sagir sukayi nasaran wargaza zuciyata haka ya rarrafo gaban Daada ya durƙar da kansa ƙasa yace"Daada ki samin albarka kamar yanda ko wacce uwa takeyiwa ɗanta,ki min addu'a".
Shuru ya biyo bayan maganansa zuciyata ta faɗa cikin tinanin Daada zata cimishi albarka koko na sauƙe ƙatuwar hamdala danaga Daada ta dafa kansa tana masa addu'o'i cikin ranta wanda bama iya jiyo abunta take furtawa.
Kamar mutumin da aka zare masa laka haka Sagir ya miƙe daga gaban Daada dazai fita muka haɗa ido ganin hawayensa ya sanya nawa tsiyaya na isa ga Daada na rungumeta munayi tare.
SALON KADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
_____________________________
Page 0⃣7⃣
Tunda daga ranar Sagir bai ƙara zuwa ba kona ƙirashi a waya baya shiga haka nan Abba tun ranar nan ban kuma sanya shi cikin ƙwayoyin idona ba,Anty Hussaina kullum tana hanyar gidanta zuwa gidanmu da gumi tayi gumi har wajen cacansu Abba,nida Sha'awa mukaje neman Abba aka shaida mana wai yayi tafiya can kudu.
Buba uban ƴan caca ya fara washe mini baki kamar gonar auduga,na harkace na hau cilla masa harara da zamu tafi ya taso yana mana maganan dana kasa tantance abunda yake furtawa ya miƙawa Sha'awa naira ɗari biyar wai mu hau abun hawa takarɓa mukayi gaba.sai da mukayi nisa da wajen nahau zazzage mata masifar dana ƙunshe a raina akan meyasa ta karɓa kuɗinsa.
"Anty naga dai kuɗin nan buƙatarsa muke koba kome ma haɗa mukai Daada asibiti".nayi gum da bakina ban koma faɗin komai ba har muka isa gida wani rashin sa'an cikin satin akayiwa mijin Anty Hussaina canjin wajen aiki koma duk tare zasu tafi dan a yanda take sanar da Daada har gida aka bashi acan haka suka tafi kullum muna waya da Anty Hussaina.
Ranar duk tsawon dare bamu runtsa ba Zulaihat da Anty Hussaina ma awa bayan awa suke ƙiran wayata,tun ina cikin halin dazan iya ɗauka har muyi magana har hakan ya gagara.jikin Daada ya rikice sosai sai zubar da jini takeyi tun muna saka tsumma hadda muka fara saka suturunmu ta gabailata ƙarfinta ya fara gazawa kuma har yanzu bata haihu ba makwabciyar mu Anty Sakina ita Sha'awa taje taƙira tazo guba Daada tace kawai mu tafi asibit zataje ta taro mana abun hawa saboda yanzu safiya ce basu fara fitowa ba.
Tsirarun kayayyakin da Daada ke tanadinsu domin rana irin ta yau nahau dannasu cikin leda ina kuka ina gamawa naje na tsuguna gaban Daada"Sannu Daada bari mu tafi asibitin yanzu ko?"
Tayi hanzarin riƙo hannuna na koma na zauna muryar da take magana acikinsa kaɗai ya isa ya fallasa irin raɗaɗin da takeji cikin jikinta.
"UMMUKURSUM"ta faɗa cikin jawo numfashinta daya fara nisa sannan ta ɗaura da faɗin"Ki kula da ƙanneki amana ce a gareki,har hayayyen mahaifinku ya sanya ku kuskuren kasa bashi hakkinsa a matsayinsa na ubanku.komai runtsi komai wuya ki tsare mutumcinki"ta maimaita min wannan kalmar sau har yanda muryarta ta daina fita.
Cikin wani irin hargagin kuka daya taso mini cikin sa'i guda nace"Daada in sha Allah zaki haife wannan cikin lafiya kamar yanda kika saba haihuwa".
Daga haka kukan danakeyi ya ƙara zuwar mini dana tina wai munada mahaifi amma bai damu da rayuwar muba balle ta mahaifiyarmu ya tsallake mu cikin wannan yanayin yayi tafiyarsa duk danginsa babu wanda muka sani domin Daada ma tace batasan kowa nashi ba a wajen ƙanin mahaifinta ya karɓa aurenta bayan iyayenta duk sun rasu.rashin iyaye da rashin gata da kuma rashin tsayayye da ƴanci yasa aka aura mata shi batare da son ranta ba.
Buba uban ƴan caca kawai muka sani a matsayin wani nashi,cikin wannan tinanin dayake faman jefa zuciyata cikin cakwakiya naji Anty Sakina ta dafa ni ma daɗo na kalleta.
"Ummukursum ba kuka zaku mata ba ki tashi mu tafi asibitin ga can mai adai-daitan yazo".
"Anty Sakina bamu da komai ko kuɗin da zamu bayar a asibitin bamu dash......".ban kammala ba ta rufe min bakina tana ƙara maimaita min cewa"babu abunda zai gagara tashi kawai muje".
Na miƙe da ƙyar inajin zafin ciwon da Daada takeji kamar a jikina na fito muka shiga adai-daitan muka bar Sha'awa a gida.asibitin koyarwa na Abubukar tabawa ɓalewa muka nufa muna isa Anty Sakina ta biyashi hadda mana Allah ya sauwaƙe kafin yaja nafef ɗinsa yayi gaba.ina riƙe da kafaɗar Daada Anty Sakina nariƙe da ɗaƴa muna ta aikin jero mata sannu muna shiga cikin harabar asibiti wasu nurses biyu suka taso suka riƙe Daada suka shiga da ita ɗakin ƴan haihuwa.
Muna tsaye mukai mari mukai bango wata nurse ta fito tace mu bada takardan zuwanta awu,nan fa ido ya raina fata sai data ƙara maimaita mana tambayar kafin Anty Sakina tace"kinga baiwar Allah maganar gaskiya bata zuwa awo kinsa mutanen da basu wani yarda dahaka ba da zuwa asibiti ba".
Wani kallon uku saura kwata ta mana tun daga ƙasa har ka kafin tace"Aikin banza daman haka kuke bazaku kawo mace asibiti ba tayi awu ba,sai kuma lokacin da ta galabaita ta kasa taɓukawa kanta komai ku jajiɓota.mezamu mata bayan ko katin zuwa awo bata dashi tunda haka kuka zaɓaaa kanku sai ku ɗauketa ku tafi da ita,kuma ina tabbatar muku babu asitibin da za'a karɓeta babu katin zuwarta awu".
Tana kawowa nan ta fara tafiya tana ta ƙananun suturutai ban gama gaska abunda ta faɗa ba sai dana ga sun fito da Daada babu ko tausayawa suka ajiye dirsham a ƙasa,duk wani kusurwa daga jikinta yana tsatstsafar da gumi leɓɓanta na ƙasa take cizowa tana fama jijjiga kanta nayi saurin isa gareta saboda faɗuwar da take shirin yin na rungume tsam!a jikina.
Anty Sakina ta fara bawa ma'aikatan asibitin haƙuri da kuma magiya wata daga cikin nurses ɗin ta daka mana rikitaccen tsawa daya sanya ni runtse kumburarrun idanuna.
"Dalla malamai ku fice mana daga nan kuma wannan jinin data ɓata wajen dashi,ku tabbatar kun goge shi mutanen banza kawai".
Anty Sakina tabi bayanta tana ƙara bata haƙuri bansan yaya suka ƙare dasu ba,naga sun dawo tare sukaje a shiga da Daada suka shiga da ita,na ɗago kumburarrun idanuna na sauƙe su akan Anty Sakina bakina cike da tambayoyin danake son furta mata mana babu damar hakan wani sashi na zuciyata yana ayyana mini wani irin kalmomi zanyi amfani dasu wajen godewa Anty Sakina.
"Ummukursum kinsa komai sai da dabara wani abun na basu,suka yarda zasu yanko mata katin awo yanzu kuma su cike mata".kaina kawai na jijjina ina girmama lamarin ƙasata.
Muna zaune a wajen wata nurse ta kuma fitowa wai mu kawo kuɗin safan hannu Anty Sakina ta zara ta basu ta koma ciki.tun muna tsaye har hakan ya gagare mu muka zauna har aka fara ƙiran sallan zuhr sai a sannan suka fito sukace mana wai bazata iya haihuwa da kanta ba saboda ɗan ya mutu mata a ciki kuma ƙarfinta ya ƙare sai dai a mata operation a cire ɗan.
Tunin ji da ganina suka ɗaure zuciyata ta shiga harbawa da mungun ƙarfi,can ƙasan leɓɓana nake ƙoƙarin furta kalmar"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"a ƙoƙarin samarwa kaina nutsuwa.
Anty Sakina ce tayi ƙarfin halin furta musu cewa su ɗaga mana ƙafa zuwa gobe muga abunda hali zaiyi,ko kallon arziki bamu ishesu ba sukayi gaba suka barmu tsaye sololo a wajen.kukan danake dannawa ne ya fito da matuƙar ƙarfi.
"Ummukursum bazan hana ki kuka ba kiyi abunki,kai rayuwa abun tsoroce wallahi sakayyan wannan baiwar Allahn ma kaɗai ya isa ta hana malam Nura samun nutsuwa a rayuwar duniya".
Bance mata ko kanzil ba tayi ta gama muka miƙe izuwa ɗakin da Daada take ciki a ware ta izuwa wani ɗakin daban ko gado babu sai ƴar tabarman da aka shimfiɗa wanda shima yayin da muke shigowa sukace gobe muzo da tabarman mu.
Wani kukan ya fara yunƙurin taso mini na kawar dashi raina yana mini zafi na isa ga Daada dake shimfiɗe kamar gawa na mata sannu kanta kawai ta ɗaga min duk da yanayin raɗaɗi da ciwon da take ciki sai da tayi ƙoƙarin sakar mini wannan murmushinta mai taushin a ƙoƙarin taga ta kwantar min da hankali.
Na rige hannuwanta ina reru kukana wiwi ya karaɗe ɗakin da sautin kukan,nida kaina na ɗago kaina na tashi nace"Anty Sakina bari naje gida na ɗauko mana kayan buƙata".
"To Ummukursum nima ki shiga gidana ina Abban Amira ya dawo ki sanar dashi halin da ake ciki".
Na ɗaga mata kai na cire daga cikin ɗakin da ƙafa na taku tun daga cikin asibitin har wunti street saboda ko naira ɗaya bana magani,Sha'awa na tarar zaune a tsakar gidan ta haɗa kai da gwiwa tanata kuka nayi saurin isa gareta,ina tambayenta menene cikin muryar dake bayyanar da ta daɗe tana kukan ta soma faɗin"Anty Ummu yaya Sagir ne an kamasu suna police station, wai anyi fashi a gidan wani jiya shine ake tsargin sune".
Zuciyata ta buga da wani sautin gam-gam sabbin hawaye suka zo min na kawar tare da jarumtar furta"shikenan ya isa haka kibar wannan kukan,idan basu bane suka aikata ai za'a sako su mu mishi addu'a.sannan ki shirya mu tafi asibiti an bawa Daada gado".
Tayi saurin watsu mini idanunta tace"ta haihu ne?"na giggiza kaina ta ɗaura da cewa"Anty Hussaina da Zulaihat ma sai ƙira sukeyi nace baku dawo daga asibitin ba.hankalinsu duk ya tashi".
"Uhmm"na faɗa ina karɓan wayata daga hannunta na wuce ɗaki na ɗaukowa Daada wasu kayan da kuma tabarma da wasu tsumman zannuwanmu.nayi sallan sannan muka rufe gidan muka shiga gidan Anty Sakina muka iske ƴaƴanta Abdallah da Amira,a Abdallah muka bawa sallahun cewa in Abbansu ya dawo su sanar dashi muna asibiti sannan muka ɗauki hanyar asibitin a ƙafa.
Muna isa shida har ta gota muka wuce ɗakin da aka warewa Daada,Anty Sakina ta takure a gefe ta zuba tagumi ina sako ƙafata ɗakin na fara da tambayarta ya jikin Daada.sai da tayi nisa kafin tace"Ummukursum sai dai addu'a dan inaga kaman borin haihuwa zatayi,gashi kuma likitotin ma sunƙi kulata naje na musu magana babu iyaka ko kallona basayi".
A wajen na daskare yayin da Sha'awa ta isa ga Daada tana jera kukanta,Anty Sakina ta fita waje ta samu mana ruwan da mukayi alwala mukayi sallan magrib dashi sannan muka canzawa Daada tabarma da kuma wani shimfiɗar.Anty Sakina tace gobe sai mu wanke musu tasu tabarman.
Bayan isha'i mijin Anty Sakina yazo hadda kayan dubiya ya kawo mana bayan duk mun gaishe shi ya shiga ƙarewa Daada kallo yana faɗin"kai malam Nura bashi da imani ace iyalinka suna cikin wannan halin,amma ka tsallakesu ka tafi.wallahi ire-iren sune suke jawowa al'umma fushin Allah kuma in abun yazo ya haɗa da kowa".
Duk mukayi shuru kamar ruwa ya cinye mu har yayi ya gama yace Anty Sakina ta taso su tafi,tana miƙewa nabi bayanta ina ƙara mata godiya ta dafani tare da faɗin"Ummukursum mahaifiyarku mutuminyar kirkice,komai na mata ban faɗi ba domin nima kaman uwa take a gareni".
Mijinta yaya Aliyu ya karɓe da faɗin"kwarai kuwa,bansan ko kun sani ba Sagir ma yana hannunmu ina ƙoƙarin handling case ɗin in sha Allah ko jibi za'a sako su,dan ya amsa basu sukayi matuƙar kuwa su kayi wannan fashi Sagir zai faɗa dan baya shayin ɓoye laifinsa".
"Mungode yaya Aliyu,Allah ya saka maka da mafifin alkhairinsa,ya raya muka ƴaƴanku"na faɗa cikin rawar murya.
Duk suka amsa da amin kafin suka hau mashin ɗinsa suka fice daga cikin asibitin bayan yaya Aliyu ya bani dubu biyu.na dawo ɗakin muka zubawa Daada idanu tsawon wannan dare bamu iya runtsawa ba gashi wayata ta mutu balle Anty Hussaina ko Zulaihat insun ƙira su iya samuna.
SALON KADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
______________________________
Page 0⃣8⃣
Zaune yake a gaban teburinsa a office yana singing akan wani file,yana gamawa ya ɗago ya miƙawa nurse ɗin dake gabansa ya karɓa ya fito.dafe kansa yayi yana sauƙe numfashi da sauri da sauri wayarsa ya ɗauka ya shiga dialing numbern Hajiyarsa.
Bugu biyu ta ɗauka ya langwaɓar dakai kamar yana gabanta cikin sanyin voice ya gaisheta ta amsa tare da tambayar ya aiki.
"Lafiya ƙalau Hajiyata ina kewarki".
Sai data ɗan murmusa kafin tace"ABEENA kaci abinci kuwa nasan halinka bakason cin abinci"sunan da take ƙiranshi dashi kenan tun yarinta.
Kwantar da kansa yayi saman teburin ya tallafa kuncinsa da hannayensa kafin yace"Hajiyata kinsa bana iya cin abincin da ba naki ba,inna tashi daga aiki zanzo".Addu'a ta masa sosai kafin sukayi sallama haka kawai ya tsinci kansa cikin farin-ciki.
Wayar ya zubawa ido son Hajiyarsa na ƙara girmama cikin ransa,har ya miƙe shigowar ƙiran Daddynsu ya shigo wayarsa ya koma ya ɗauka tun kafin su gaisa yace"Zayyad duk abunda kake ka bari yanzu kazo gida ina nemanka".yana kaiwa nan ya kashe wayar.
Tsura wayar yayi cikin aljihunsa ya fito ko rufe office ɗin baiyi ba ya faɗa motarsa ya figeta da gudu,yana isa baba mai gadi ya buɗe masa ya shiga.kansa tsaye part ɗin Daddy ya nufa da sallamar yana ƙara ware manyan idanunsa akan Daddy dake tsaye ya naɗe dukkan hanayensa a bayansa.gabansa ya taku tare da rusunar dakai yace"Daddy gani".
"Zayyad inason nasan gaskiyan lamarin da Hajiya ta sanar dani,menene tsakaninka da Asiya ƴar aikin gidan nan?"cikin kakkausar murya yayi maganar yana ƙara haɗe rai.sai a sannan Zayyad ya ƙarewa mutanen falon Nenne ce zaune gabanta Asiya tana durƙushe sai Asiya sai Adam da Haidar da suke aikin taya Nenne huci.
A hankali ya fara furta"Daddy bansan komai ba hasalima babu wata alaƙa a tsakaninmu".
Nenne ce ta fara magana cikin sheshsheƙar kuka"Alhaji daman sai danace a rufe wannan maganan babu amfanin tarashi,abunda ya faru ya riga ya faru amma Zayyad ka kamu kunya".
Cike da rashin fahimta ya kuma gwalo idanu waje asking"Nenne me kike faɗa haka mena aikata?".
Wani zazzafar mari Daddy ya sauƙe masa tana faɗin"kanaso kace bakasan tana ɗauke da cikin daka mata ba,an sanar dani kullum sai kun keɓe da ita,Zayyad ka bani kunya kai danake yaɓa da salla sai ka kasa alwala".
Sunkuyar da kansa yayi ƙasa ransa yana masa zafi,yasan duk shirin Nenne akan abunda ya mata ran.
"Daddy bazan taɓa baka kunya ba Allah ya tsare zuwar wannan ranar a cikin rayuwata,Allah ya huci zuciyarka"yana kawowa nan ya fice daga falon bayan y watsawa Asiya idanunsa da suke bayyanar da ƙololuwar ɓacin ran dayake a ciki.
Part ɗinsa ya wuce ya shiga bedroom kayan jikinsa ya fara cirewa yayi wurgi dasu,sannan ya zauna bakin bed yana kokuwa da numfashinsa dake barazanar nisa dashi.gani numfashinsa ya fara sarƙewa ya sashi ɗauka inhalern sa yafara using dashi sannan ya kwanta lamau akan bed ɗin yana runtse idanunsa a hankali sirarun hawaye suka fara biyo gefen fuskarsa ya daɗe a haka kafin ya tashi kamar ɗan maye ya faɗa toilet yayo kwanta.
Yana fitowa ya shirya cikin manya kaya kamar yanda ya saba inzai ziyarci Hajiyarsa,idanunsa har ya rufe tsabar ɓacin ran dayake aciki ya faɗa mota kota kan su Nana da Iman dasuke magana bai biba.Da gudu ya figi motar ya fice daga gidan ya ɗauki hanyar zaria yana ganin wayarsa dayake ringing sunan Daddy yana bayyana cikin screen ɗin wayar,kashe wayar yayi ya cigaba da driving ɗinsa.
Yana isa ya wuce gidan Hajiyarsa acikin garden ya sameta,ya isa gareta yana sunkuyar da kansa akan cinyarta hawaye na zubo masa a hankali ta fara cusa hannunta acikin sumar kansa.
"ABEENA menene ya faru?".
Shuru yayi kusan 5 mint kafin yace"Hajiyata Nenne ta tsane ni sharrin zina ta min kuma Daddy ya yarda".runtse idanunta tayi da ƙarfi na tsawon lokaci kafin tace"Zayyad ka daina damuwa akwai Allah komai zai wuce ka daina damun kanka dan Allah ABEENA".
Ajiyan numfashi kawai yake sauƙewa ɗaya nabin ɗaya ya daɗe a haka kafin yace"Hajiyata zanje Bauchi bazan iya komawa gidan ba,zanje wajensu Ammie".
Sai datayi nisa kafin tace"shikenan Abeena ka gaishe dasu amma karka sanar dasu dalilin zuwanka,yanzu ka tafi mu shiga ciki kaci abinci kafin ka tafi".kansa kawai ya ɗaga mata taja hannunsa kamar yaro suka shiga ciki sai data cika masa cikinsa sosai da abinci har yaɗan saki ransa kafin ya fara shirin tafiya bauchin yakubu wajen dangin mahaifiyarsa.
Sosai ya sama addu'o'in Hajiyarsa da kuma albarkarta sannan ya tafi har yanzu wayoyinsa duk a kashe suke,dan bayajin zai iya amsa ƙiran kowa a halin dayake ciki.yamma sosai ya isa cikin bauchi ya wuce G R A,duk mutanen gidan suka tarbesa da farin-cikinsu kakarsa Ammie da jikokinta su kenan a gidan.part ɗin Ahmad ya sauƙa wanda yake kusan sa'ansa suna shiga ya kwanta akan bed yana sauƙe numfashi kuncinsa inda Daddy ya sauƙe masa mari ya shiga masa raɗaɗi ya runtse idanunsa da suka ƙara,ƙanƙancewa tsabar gajiya yana tino zargin da Daddy yake masa na aikata zina.
Sai da Ahmad ya taɓo ƙafaɗarshi kaɗan yana ƙiran sunan shi"Hamma Zayyad lafiya kuwa?".
Ƙaramar tsaki ya saka kafin ya tashi daga kwanciyar da yayi yana birkita sumarsa yace"Nifa banzo da kaya ba wanka nakeso nayi ka rakani na sayo wasu",dariya kawai Ahmad yayi dan yasan halin Hamman nasun.
Sai da yayi wanka ya mayar da kayan dake jikinsa suka fita masallaci tare da Ahmad,anan sukayi magrib har da isha'i sannan suka dawo suka wuce part ɗin Ammie.
Kusa da ita ya zauna yana kwantar da kansa akan cinyarta,ko damuwa dasu Salima da Ramla da suke masa dariya baiyi ba,haka yata zubo masa shagwaɓarsa son ransa tana biye masa.domin yana cikin jikokinta mafi soyiwa a gareta sai bayan shekara ashirin da biyar da haihuwarsa tasan fuskarsa tasan tanada wani jikan.
Nan sukaci abinci sannan suka taɓa ɗan hira kafin kowa yaje ya kwanta,Salima da Ramla suka masa sai da safe sannan suka wuce ɗakunansu,shima sallama yayiwa Ammie zasuje su kwanta da Ahmad.gargaɗi sosai Ammie tayiwa Ahamd akan ya kula da Zayyad inko bazai iya ba a share masa wani part ya koma can.
Dariya yayi kana yace"Ammie kenan ki kwanta da hankalinki zan kula miki dashi sosai".
"Nasan halinka ne ai da shiririta har ciwonsa ya tashi cikin dare kai kanata,sharan baccinka"ta faɗa yana poiting ɗin Ahmad da hannu.har bakin ƙofar falon ta rakosu dai-dai zasu fita idanun Zayyad suka sauƙa akan family picture ɗin dake maƙale acikin wall ɗin falon,hadda mahaifiyarsa dan hoton da daɗewa akayishi irin na da ɗin nan ne.
Ruwar ƙwalla ne yaji sun ciko masa kwayar idonsa,yayi saurin kawar dasu yana yiwa Ammie sai da safe suka tafi da Ahmad wanka kawai yayi ya kwanta.
Kamar yanda ya saba ƙarfe uku dai-dai ya farka ya shiga bathroom yayi ɗauro alwala sannan ya fito ya fara sallon nafila,yana iddarwa ya kara karatun al-qur'ani.lokaci ɗaya ruwar sama ya barke kamar da bakin kwarya,a hankali ya rufe qur'anin yana ajiyewa saman site drawer sannan ya miƙe yana rufe labulayen ɗakin tare da kashe Ac yana ƙara matse jikinsa waje ɗaya.duk gaɓoɓin jikinsa sanyin yake ratsawa ya hau bed ya kwanta yana rufe jikinsa da blaket yakai kallonsa ga Ahmad dayake ta kwasar baccinsa hankali kwance.
Yaune ranar da aka bamu a asibiti akan mu tattara mutafi,tunda mun kasa biyan kuɗin da za'a yiwa Daada aiki,tun daren jiya sukace mu tafi har aka fara ruwan nan muna waje cikin wajen ajiye motoci suka kwantar da Daada,Anty Hussaina ce ta turo mana dubu ashirin ta account ɗin mijin Anty Sakina yaya Aliyu muka biya kuɗin wasu kananan abubuwa har aka ƙara mata jini leda biyu,kullum sai munyi waya da Zulaihat har wasu daga cikin ƴan-uwanta sunzo duba Daada suka kawo mana goma ta arziki.haka Anty Sakina ma da mijinta suna ƙoƙari akanmu don kullum kwanon abincin mu yana gidansu.
Wani abun ƙarin takaicin har wajen Buba uban ƴan caca mukaje akan ya ƙira mana Abba ya sanar dashi halin da muke ciki,don ko mun ƙira layinsa tafiya.Daada tace kar mu ƙara zuwa wajensa gwara ta mutu cikin halin da take ciki akan Buba uban ƴan caca ya taimaka mana.
Zaune nake nida Sha'awa kusa da Daada daren jiya nayi kuka har na godewa Rabbi,wani zazzaɓi mai zafi ya sauƙa mini saboda ruwan da akayi jiya daya dake mu.muna zaune naga shigowar motar babban likitan asibitin na tsirgar da ƴar tsaki ina tina wulaƙancin daya mana da muke roƙansa akan ayiwa Daada aiki daga baya sai mu kawo kuɗin.
Shi ya fara buɗe ƙofar motar ya fito yana riƙe da rigarsa ta likita,sannan aka buɗe ɗayar ƙofar ɗan zaman banza aka fito sanye yake cikin shigar blue ɗin jeans da white ɗin t-shirt ya ɗaura blue ɗin cargidan akai,ya rufe fuskarsa da face mask kansa da black ɗin facing cap,har suka wuce ta gefenmu bai ajiye wayar dayaƙe saƙale a kunnunsa ba suka shiga office ɗin likifan.
Nabi bayansu da kallo ina sauƙe ƙatuwar ajiyan numfashi har suka shige ofishin,a raina ina ayyana meyasa masu kuɗinmu suke ɗaukar talaka ba a bakin komai ba,haka muka cigaba da zaman jiran Sagir.
Suna shiga office ɗin,Ahmad ya wuce kujerarsa ya zauna shi kuwa Zayyad ya tsaya a jikim window yana leƙo cikin compound ɗim asibitin sai daya gama waya da Hajiyarsa sannan ya dawo ya zauna akan kujerar dake fuskantar Ahmad yana miƙa masa wayarsa.
Kallonsa Ahmad yayi yana kallon numbern da ya ƙira yace"Hamma kai meya sama taka wayar,naga tunda kazo baka ko kunnasu ba?".
Jingina kansa yayi da jikin kujerar yace"banason wani ƙarin damuwan ne"kafin Ahmad yayi wani magana ya kuma cewa"Yauwa waɗancen da muka wuce a cikin compound kamar majinyaciya ce dasu ko,meyasa kuka barsu haka?".taɓe baki Ahmad yayi yana cewa"mahaifiyarsu ce za'ayiwa aiki so basu biya kuɗin aikin ba shine kawai yau muka sallamesu mun gaji da ajiyansu".ware idanunsa sosai Zayyad yayi akan Ahmad yana mamakin furcinsa sai kace ba likitan dayasan makaman aikinsa ba.
"Look Hamma take it easy,bafa laifin mu bane we treat them the way it suppose to be,su suka kasa haɗu kuɗin aikin".
"Afara shirin shiga da ita aikin,zanyi payment komai".Zayyad ya faɗa yana miƙe izuwa reception da kallo Ahmad ya bishi har ya dawo ya jefa masa takardar shaidan biyan kuɗin aikin dayayi yace"oya a shiga da ita aikin".
Miƙewa Ahmad yayi yana zara wayarsa a aljihu sannan ya ɗauki takardan ya fice daga office ɗin.
Munata ƙoƙarin ɗaga Daada zamu shiga da ita cikin adai-daitan da Sagir ya samo mana wata nurse ya taho da saurinta tace muje doctor yanason ganinmu.
SALON KADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________
Page 9⃣
Muka haɗa ido da Sagir muka zaunar da Daada cikin adai-daitan na juyo na kalla Sagir wanda shima niɗin yake kallo nace"Mu tafi kawai Sagir meye kuma zasu mana bayan wulaƙancin da suka mana?"ina kawowa nan hawaye suka shiga wanke mini fuska.Sagir ya tako gabana yana ɗan langwafar dakansa ta yanda tsayinmu zai daidaita yace"Anty Ummukursum muje muji abunda zasu faɗa mana".
Na sauƙe numfashi nace "sai dai kai kaje".yabi bayan nurse ɗin suka koma cikin asibitin ni kuma na shiga cikin adai-daitan kusa da Sha'awa dake riƙe da Daada.mun ɗau lokaci muna jiran Sagir kafin ya fito tun kafin ya iso na watsa masa harara da mamakina naga ya washe bakinsa yace"Afuwan Antyna wallahi Allah ya karɓi kukanmu wai wani bawan Allah ne ya biyawa Daada kuɗin aikin da za a mata,shine suka tsayar dani nasa hannu akan takardar aikin".
Mamaki,farin-ciki,murna da al'ajabi bansan wanda yazo mini a wannan lokacin ba nayi sauri zagayowa muka fito da Daada daga cikin adai-daitan tare da Sha'awa nursess suka fito da wani gado aka ɗaurata akai aka shiga da ita duk muna biye dasu a baya sai da suka shiga da ita ɗakim tiyatan suka dakaran damu a waje.muka zauna raina cike da ta'addujin wanene wannan wanda ya biyawa mana waɗannan maƙudan kuɗin?,menene alaƙarmu dashi?.hawaye suka shiga gangaro mini Sha'awa ta damƙo hannuna cikin nata tace"Anty dan Allah ki daina wannan kuka,gashi fa an shiga da ita wannan aiki,addu'armu kawai take buƙata a yanzu,inta sauƙa sai mu ƙara gwada layin Abba kozai shiga a sanar dash.....".
Wata girgitacciyar tsawan da Sagir ya daka mata ba ita kaɗai ba hatta ni sai da hanjin cikina ya kaɗa ransa yana matakin ƙarshe a raci yake maganar"Idan na ƙarajin bakinki yayi kuskuren furta sunan Abba wallahi,saina tattaki anan wajen inaso ku sa a ranku cewa daga yanzu bamu da wani mahaifi mu kaɗai zamuyi rayuwarmu da Daada,zan zame muku uba sannan zan samar muku da duk wani abunda uba yakan samarwa ƴaƴansa".sirarun hawaye suka biyu bayan kalamansa na ƙarshe.
Duk muka kayi shuru har izuwa lokacin da wayata ta fara ringing tana hannun Sagir dan haka shiya ɗaga ƙiran yana sanar da Anty Sakina halin da ake ciki,tace itama gatanan zuwa,tun muna daga zaune har zaman ya gagaremu muka miƙe muna safa da marwa a ƙofar ɗakin da aka shiga da Daada.ganin fitowar Dr Ahmad ya samu miƙe da hanzari muka isa gareshi suna rige-rigen jefa masa tambayar ya jikin Daadan?.
Ya share gumin dake tsatstsafowa daga goshinsa kafin yace"An cire mata ɗan amma sai dai baizo da rai ba sakamakon,aikin ƙarfin da tayi da kuma rashin zuwanta awu ana duba lafiyarta dana abunda ke cikinta".
"Innalillahi wa'inna ailahir raji'un"shine kalmar dayake fita daga bakunan mu dai-dai nan Anty Sakina da yaya Aliyu suka shigo wajen yaya Aliyu ya ƙarisa da Dr Ahmad ya ƙara masa bayanin abunda yake wakana,nan aka fito mana da gawar yaro babu abunda ya rabi na kama da Abba,yaya Aliyu da Sagir suka fito domin nema waɗanda zasu shirya shi.
Ina tsaye inda nake duk yanda nakejin zafi a ƙalbi da ruhina amma na kasa fidda hawaye,kuma na gaza lallashin Sha'awa daga kukan da takeyi Anty Sakina tana tayata.sai da sukayi mai isharsu sannan muka miƙe muka shiga ɗakin da ka maida Daada domin hutawa,tana kwance hannunta saƙale da robar jinin da aka ƙara mata tana bacci numfashinta yana fita can ƙasa-ƙasa.
Muka zauna kusa da ita kukan nakeson nayi amma hakan ya gagare ni,sai na zuci nakeyi wanda yake ƙona mini rai sosai,Anty Sakina ce ta ƙira Anty Hussaina da wayarta take sanar da ita sannan ta ƙira Zulaihat itama ta faɗa mata.
Yana zaune a office ɗin yana murza farin zoben azurfan dake ɗan yatsarsa nz tsakiya a hankali,Ahmad ya shiga his face show so wrong Zayyad ya ɗaga masa gira"What's up anyi mata aikin?".
Sai daya zauna a kujerarsa yana zare safan hannun dake hannusa kafin yace"unfortunately ɗan ya tarasu a cikinta baizo da rai ba,itama tana under critical condition".
Gyara zamansa Zayyad yayi yana fuskanto Ahmad yana faɗin"Look Ahmad try your best a samu a ceto rayuwarta inma ana buƙatar wani kuɗin nan i'm ready to spend everything idan bazasu iya bane kuma,na ɗauke ta zuwa asibitina".
Tasowa Ahmad yayi ya dafa kafaɗarsa yace"calm down Hamma in sha Allah na ɗaukar maka alƙawarin ko bayan ka tafi zamu kula da ita".lumshe idonsa yayi yana cewa"Ahmad na tabbatar danada ƴaƴa banason su taso cikin rayuwar maraici kamar yanda na taso shiyasa nakeson ku kula da ita please".ya ƙarishe maganar cikin sanyin murya da karaya.
Shima kansa Ahmad ɗin sai da jikinsa yayi sanyi ransa cike da tausayin rayuwar Hamman nasan,miƙewa yayi slowly ya ɗauki hanyar fita daga office ɗin yace"ina jiranka a mota inka gama kazo ka maida ni gida bazan iya driving ba".bai jira amsar da zai maido masa ba ya fice yaje cikin mota yayi zamansa tare da lumshe idonsa yana shafa kuncinsa inda Daddy ya mare sa.
Muna zaune kusa da Daada har yanzu ƙarin jinin da aka mata bai ƙareba haka nan kuma bata farka ba,maganan da Anty Sakina ya sani zame hannu daga tagumin dana zabga.
"Ya kamata muje wajen likitan,ya faɗa mana wanda ya biya mu masa godiya ko?".Sha'awa ta karɓe zance tare da ɗaurawa da cewa"Gaskiya ne kam Anty ya cancanci godiyarmu".
Miƙewa sukayi har sunkai bakin ƙofa Sha'awa ta juyo tana faɗin"Anty baza ki taso bane?".
"Kuje kawai hajijiya nakeji inna tashi".basu kuma furta komai ba suka fita suka nufin ofishin Dr Ahmad.a hankali na ɗago kaina saboda ganin Daada ta fara ware idanunta nayi azaman ƙara riƙo hannunta cikin nawa cikin muryata da take rawa nace"Sannu Daada,sannu yajikin ina ne yake miki ciwo?".
Ta maida idanunta ta rufe gam!haka ya sanya ni ƙara maimaita tambayar a karo na biyu,na ɗaga min kanta na ƙara saurin furta cewa"Daada an miki aiki kin haihu Daada".sai kuma naji shuru tinawa da nayi ɗan baizo da rai ba maimakon naga tashin hankali akan fuskarta sai naga saɓanin haka,tayi ƙoƙarin sakar mini wannan murmushin natan kamar tasan abunda ya faru tace"Ya rasu ko,ban haife shi da rai ba ko?"a hankali na ɗaga mata kaina ina kifa kaina jikin ƙarfen gadon.
Ta fara lallashina kamar nice wacce nayi naƙudan,a haka Sha'awa da Anty Sakina suka shigo suka iske mu.bayan sun gawa jerawa Daada sannu Anty Sakina ta ɗaura da sanyawa wannan bawan Allahn daya ɗauki nauyin aikin da akayiwa Daada.
"Wanene shi ina yake?"Dadda ya jero tambayoyin a jere Anty Sakina ta karɓe zance da cewa"Daada kinsa masu kuɗinnan basu fiye son in sunyi alkhairi ayita yaɗa sunan su ba,likitan yace mana yace basai an sanar damu wanene shiba,kuma daga yanzu har a sallame mu ya ɗauki nauyin komai".
Daada ta fara yunƙurin tashi na taimake ta ta kishingiɗa da pillow tan rufo idonta cike da wahala tace"Allah ya masa albarka ya bashi rayuwa mai inganci,yanda yaye mana wannan damuwar Allah ya yaye masa nasa ranar ƙiyama,Allah ya shiga lamuransa ya kuma bashi waɗanda zasu masa".
"Amin-amin"itace kalmar dake fitowa daga bakunan mu.
Yana tsaye a baƙin ƙofar ɗakin hannunsa yana kan handle ɗin ƙofar,addu'a'in da ake masa acikin ɗakin wanda ya kasa tantance mai yinsa ya sanya shi dakatawa bai shiga ba,wani sanyin ya tsirka masa sashin ruhinsa sai daya lumshe idonsa yana cizon lower lips ɗinsa da ƙarfi kafin yace"Amin".jin an dafa kafaɗarsa ya sashi waigowa yana ware idanunsa ɗaga masa gira Ahmad yayi as he asking him if there is something wrong?.
Kawar da kansa gefe yayi"Muje kawai daman kai nazo dubawa ka wani shanya ni a mota ina jiranka".
"Sorry Hamma ban gama aikin bane,but inkanaso ka dubata ne sai mu shiga ai ɗazu ma sunzo office suna ta godiya tare da tambayar wanda ya biya musu kuɗin,nace yace kar a bayyana sunansa"Ahmad ya faɗa yana tsaida ƙwayar idonsa akan Zayyad kansa kawai ya ɗaga masa slowly ya furta"Good".
Sannan yayi gaba Ahmad nabiye dashi a baya,shi yayi driving har suka isa gida ya zagayo yana knocking a Zayyad ganin har yanzu bai fito ba,sai daya furzar da iska daga bakinsa kafin ya buɗe ƙofar ya fito ya wuce part ɗin Ahmad ya kwanta.tinani ne cunkushe a ƙasan ransa bai san meyesa ba zuciyar ta take wajabta masa taimakon wannan baiwar Allahn mirginawa yayi gefen gadon yana kallon ceiling dole zai nemesu ya kuma sanya sunansu cikin jerin mutanen da zai taimakawa ƙarƙashin kungiyarsa ZAYFA FOUNDATION da kuma STAND FOR NEEDERS wanda Hajiyarsa take gunadar dashi,don tallafawa mata da ƙananan yara.
Muna zaune a ɗakin Daada tana waya da Anty Hussaina,Sagir da Yaya Aliyu suka shiga na amsa sallamar da suka shigo da ita,sai da Daada ta ƙare wayar kafin yaya Aliyu ya gaisheta tare da tambayar yanayin jikin natan,ta amsa da alhamdulilliah cikin yanayin sakin fuska.
Langwaɓar dakai Sagir yayi yana isa ga Daada"ya jikin nakin ina ne yake miki ciwo yanzu?".sosai ta sakar masa murmushi tana dafa kansa tace"babu inda yake min ciwo,ganinku kusa dani shima ƙara min wani kuzarin yakeyi".duk muka saki murmushi saɓanin da da duk muke cikin jimami Daada ta kuma cewa"Babana wannan gashin kan nakan ka aske shi,inko ba haka ba sai dai tana yawo da hula".
Ya kunsuyar dakai ƙasa yana ɗan shafa ƙeyarsa yana faɗin"yanda kikeso haka za ayi Daadata".
Wani daɗi yabi dukkan sassan jikina cikin raina ina ƙara godiya ga Allah da kuma nemawa Daada lafiya mai ɗaurewa maganar Anty Sakina ya katse mini hanzari.
"Abban Amira yaushe za ayi jana'izan?".
"Bayan sallan magrib in sha Allah".duk mukayi shuru da aka fito da gawar jaririn aka kawowa Daada shi ta rungume shi a ƙirjinta,na tsawon lokaci kafin ta miƙa shi ga Sagir suka fice dashi tare da yaya Aliyu.Anty Sakina ta bisu da faɗin"Allah yasa mai ceto ne"muka amsa da amin.
Daren ranar wasu daga cikin ma'aikatan asibitin da suka mana wulaƙanci,sukazo da borin kunyarsu wai sunzo su bawa Daada haƙuri.basu san munada alaƙa da Dr Ahmad ba nikam ko kallo basu ishe ni ba haka nan ma Anty Sakina da take aikin banka musu harara haka sukayi suka ja jikinsu sula fice.washe gari Anty Hussaina ta iso bata sama zuwa da wuri ba sakamakon faɗan rikicin ƙabilancin da akeyi a jos ɗin,hakan ya sanya aka rufe garin.nida ita muke kwana a wajen Daada Sha'awa kuma takan bi Anty Sakina su koma gida washe gari su dawo haka nan ma Sagir.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
__________________________________
Page 1⃣0⃣
Tsaye yake a falon ya naɗe dukkan hanayensa a bayansa yana kai kawo acikin falon,Nenne dake zaune ta kalloshi tare da taɓe baki lokaci guda ta shiga furta"Haba Alhaji wai wannan damuwar ta mecece,ai shi Zayyad ɗin ba yaro bane da za'a nemesa a rasa da yake shi gashi ɗan golden ba a isa a masa faɗa ba sai yasa ƙafa yabar gida".
Ko ta kanta Alhaji Faruok Baita bai biba sai ma zaro wayarsa da yayi daga cikin aljihunsa yana ƙara dialing number ɗin Zayyad kamar kullum yanzu ma a kashe take,amma hakan bai hanasa dakarawa daga ƙira ba har sai daya gaji dan kansa ya zauna yana sauƙe numfashi kamar wanda yasha gudu a fagen tsere.
"Alhaji ni banga abun damuwa akan wannan al'amarin ba,ko'ina yaje ai zai dawo kuma kaima zaka iya rayu ko babu sh......."saurin dakatar da ita yayi yana watsa mata idanunsa da suka rikiɗe suka koma jajir"Hajiya ya ishe ki ya zama dole na damu da sanin inda Zayyad yake kodan mu warware wannan al'amarin,mu tabbatar da gaskiyan wayen uban cikin da kikace Asiya na ɗauke dashi".da wani irin kallon mamaki Nenne take bin Alhaji har yakai aya ya miƙe ya hau upstairs kanta ta jinjina tana faɗin"Lalle akwai jan aiki a gabana".
Koda Alhaji Farouk Baita ya fito wuce Nenne yayi ya fice bayan ya wurga mata wani kallo,zaria ya nufa gida Hajiya yana zuwa na sanar da ita abunda ke tafe dashi domin yasan ko Zayyad bai sanar da kowa inda zashi ba ita kam bazai ɓoye mata ba.
Sai da tayi nisa kafin ta sanar dashi yana bauchi amma ya bari zata masa magana da kanta akan yazo cikin kadunan,sosai suka tattauna akan lamarin Zayyad ɗin sannan ya tafi.
Kodaya dawo bai kula Nenne ba balle ya sanar da ita yanda sukayi da Hajiya,haka ya wuceta zaune a falo inda ya barta yayi bedroom ɗinsa.
Adam da Haidar suka shigo kusa da Nenne Haidar yana laluɓo tabar sigarinsa daga cikin aljihunsa,zai kunne Nenne tayi sauri buge hannunsa tana aika masa da harara"Wai kai Haidar wani irin mutum ne,ban hanata sha min wannan abun a falo ba?".Kwaɓe fuska yayi yana maida sigarin bayan fatan kunnensa,yana faɗin"Nenne wasu kuɗi nakeso za'ayi birthday ɗin abokina Mubarak next two days a bauchi".
A karo na biyu da Nenne ta ƙara watso masa wani hararan tana faɗin"bani dasu bazan baka ko sisi ba wai ku meyasa bazakuyi hankali bane,kuna haka ta yaya zamu cika burinmu".
"Shikenan Nenne ba daman na tambaye ki kuɗi sai ki fara min wannan karatun nakin,wai yaushe zamuyi hankali.to shikenan wallahi duk abun naja miki ke kika jawa kanki ai shi waccen ɗan golden ɗin ko nawa zai tambaya ba'a masa shamaki tsakaninsa da kuɗin sai mu"ya faɗa yana miƙewa zai fice daga falon,Nenne ta dakatar dashi ta hanyar ƙiran sunansa kafin ta shiga faɗin"shikenan kaman nawa zai ishe ka?".ya juyo yana ƙara haɗe ransa yace"500K".
Miƙewa tayi tana shurin Adam da ƙafa da tun shigowarsu ya zube a wajen yana bacci,cikin maye da bai gama sakin saba ya buɗe idonsa takaici ya cika Nenne.ta wuce bedroom ɗinta Haidar yana biye da ita ya karɓa kuɗin ya fice.
Kwanan mu biyar a asibitin muna samun cikakken kulawar malaman asibitin,awa bayan awa suke shigowa duba jikin Daada cikin faran-faran.tare da Sagir muke zantawa akan wanene wannan wanda ya taimaka mana shine mai asibitin koke menene,har tambaya mukayi ko shima likitane a asibitin suka ce mana a'a domin Dr Ahmad shine babban likitan asibitin.
Haka muka kawar da maganan sai dai aduk lokacin da muka ɗaura goshin mu a ƙasa da sunan bada farilla yana cikin addu'o'inmu,wani abunda ya ƙara jefa zuciyoyinmu cikin wani tarin baƙin cikin shine har yanzu Abba zaizo ba,kuma bai kira ba Anty Sakina da yaya Aliyu suke tsaye akanmu sai kuma Anty Hussaina.izuwa yanzu kam nima na fara amanna da furcin Sagir gwara sabarwa kanmu rayuwa tamkar yanda marayu marasa iyaye sukeyi domin bambamcinmu dasu ƙalilan ne.
Muna zaune ina zuba masa abincin da Anty Sakina ta taho mana dashi da safe a cikin yalwataccen firantin silba tana sanar mana matar ƴaƴan Yaya Aliyu ta rasu yanzu ma can zasu wuce cikin azare,duk muka musa ta'aziya tare da rakasu da addu'ar Allah ya sauƙe su lafiya.Sagir na zaune gefen Daada,Sha'awa kuwa ta raka Anty Hussaina gida za suje su dawo.
Ina gama zubawa na turo mana kwanon abincin gabanmu muka faraci a baki Sagir yake ɗaukar lomar abincin yana bawa Daada a baki har sai da ta ƙoshi kafin mukaci nida shi.muna gamawa na fita waje na wanke kwanonka na dawo na kimtsasu babu jimawa Anty Hussaina da Sha'awa suka dawo sun ƙarin wani girkin sun taho dashi Zulaihat ta ƙira wayata na miƙawa Daada ina ficewa daga ɗakin naje nayo alwala na tada sallan magrib ina iddarwa na ninke sallayan ganin har yanzu Daada basu gama wayar da Zulaihat ba ya sani cewa Anty Hussaina"Anty bari naje gida nayi kwanta na dawo daman jira nake ku dawo ".
Ta kallo ni tana gyara zaman Musaddik akan cinyanta tace"To amma dan Allah kar ki ɗade kinga garin da hadiri har ruwan nan ya sauƙo ya same ki".
"To"na amsa dashi ina lakuto kuncin Musaddik na fice nabar cikin asibitin ina tsaye a bakin titi ina jiran abun hawa amma babu ko alamarsu dan a lokaci an shiga salla hakan ya sa na fara takawa da ƙafata,ina tafe aka fara iska sosai na ɗan tsagirta ina waiwaige ko zanga abun hawa,cikin sa'a na sama adaidaita ko tsayawa ciniki banyi ba na shiga ina faɗa masa wunti street zai kaini,bamu ɗau lokaci ba muka isa na bashi naira ɗari biyu ya bani,canji sannan nasa ɗan mukulli na buɗe gidan duk da tunda daga yanayin gidan yake bayyanar da matsagaicin ƙarfin mutanen da suke zaune a ciki,amma komai tsab-tsab.
Na fara da zare hijabin dake kaina sannan ɗauki bokatin ƙarfe na cika da ruwa nakai bayi,nayi wanka sannan na ɗaura da alawa na fito ina ƙara matse jikina waje guda saboda sanyin daya sauƙa a garin alamar ruwan sama yana gab da zubowa na wuce ɗaki sai nada mulke jikina da mai kafin na sauya kaya izuwa wata doguwar baƙar atamfa ta nayi salla sannan na saɓa hijabina a kafaɗata na fito ina jawo ƙofar na rufe da makulli haka nan ma ƙofar gidan na rufe.
Na ɗauki hanyar da zata sada ni da bakin titi da ɗan saurina kar ruwa ya sauƙo,nafi minti biyar ban saba abun hawa ba ina tsaye wata mota ta galle ni da hasken fitollinta nasa tafukan hannuna ina kare idona sai da motar ta iso dab dani kafin na iya jiyo sautin waƙar dake tashi cikinta nakai duba na mutanen cikin motar matasa ne su biyu ɗaya yana driving ɗaya kuma yana zaune a kujeran ɗan zaman banza.
Bana iya ƙarewa fuskansu kallo saboda babu wutar lantarki a lokacin,ga kuma duhun damunan daya mamaye wajen.cikin wannan tinanin daya fara nisan kiwo a cikinsa na jiyo muryar ɗaya daga cikinsu wanda bazan iya tantance waye yayi maganar ba.
"Yan mata shigo mun kaiki mana,ga ruwa yana shirin sauƙowa".nayi banza dasu nayi na cigaba da tsayiwa ta ina waiwaige-waiwaigen gefen titin ko zanga wulgawan wani duk da bana gani komai a wajen saboda duhu, ban ankara ba naji sun buɗe ƙofar motan sun zagayo gabana"wannan jan ajin nakin ba burge mu zaiyi ba,dan mun saba ganin matan da suka fiki class in zaki shiga kawai ki shigo ko ruwan nan ya sauƙo ya miki duka".
Kalamansa suka ƙara tunzura ni na hayyaƙo da bala'ina muryata har sarƙewa takeyi nace"to daman wani ya tsayar daku da bazakuyi tafiyar kuba,koko ce muku nayi ina neman taimakonku da har zaku gaya mini magana".naja wata gajeruwar tsaki ina ɗaukar hanyar barin wajen izuwa gidan sai an gama iskan sannan na fito kozan sama abun hawa ina tafe ina ƙananun suturaina.
Naji wani daga cikinsu yayi sama dani cak!ya saɓa a kafaɗarsa,na fara ƙoƙarin kwace jikina ina kai masa duka da cizo tare da ƙwala ihun neman agaji,cikin motar ya dure ni ya rufe ƙofar kafin nayi wani yunƙuri suka ja motar suka fara tafiya.
"My man dawo nan kayi driving ɗin,zanyi maganin rashin kunyarta".
Na zaro idona saboda wannan murya tayi daban da wanda naji ɗazu,sukayi canjin waje shi ya dawo bayan motar inda nake nayi azaman kaama murfin ƙofar zan buɗe dan na gwammace na ka faɗo na karairaye akan su cigaba da tafiya dani.naji an yiwa hannuna mungun kamu wanda yasa ko ƙarƙauran motsi na kasayi,shuru ya ratsa cikin motar naji wani ɗan ƙara tsut!kujeran danake kai ta fara baya har ta kwanta dukkanta kamar tabarma hawaye ya gangaro mini cikin rawar murya nace"dan Allah kuyi haƙuri ku kyale ni mena muku?"ya ɗauke ni da kyakykyawan mari saitin idona na hagu ji kake tassss!na saki wani ƙara mai matuƙar sauti ya fara keta mini hijabin dake jikina har zuwa rigar na gallawa hannunsa cizo ya kuma ɗauke ni dawani marin dayafi na ɗazu na miƙe jikina duk ya ɗauki mazari kamar anjona mini wutar lantarki na fara kokuwa da ƙofar zan buɗe na jita a rufe kafin nayi wani motsin naji yakuma dawo nayi baya yana ƙara sakar mini mari tare da danne ni na kasa taimakawa kaina.cikin wahala da maida numfashi da ƙirjina dake lugudan tara-tara nace"dan girman Allah na haɗaku da girman ubangiji kuji tsoron Allah ku sani yana ganinku duk inda kuka shiga,sannan kuma akwai malaiku a tare daku da suke rubuta aikunku shin bakya jin kunyarsu yayi aikata ɓarna.mene muku ku barni nayi tafiyata karku rabani da mutumcina na ɗiya mace".na gwammace na koma yi musu wa'azi don naga duk kwalalan da nakeyi babu mai jina balle a kawo mini ɗauki.
Kota kan magiyan danake musu basu biba naji ya rabani da duk suturar dake jikina na runtse idona ina ƙiran sunan mahaliccina ina ƙarawa da faɗin"Wayyo Daadata kizo ki taimake ni",daga nan ban koma sanin inda kaina yake ba tunda daga sa'in danajin ƙalbina ya buga da matuƙar ƙarfi yana watsa wasu sabbin saƙonni ga sauran sassan jikina da suka bar aiki.
Sanyin asuban da ake busara ya sanyani buɗe idanuna da sukayi wani mungun kumbura,har inajin sun mini nauyi,na fara waiwaige waiwaige domin tantance inda nake inda nake jiyo tashin murya wasu maza sun fito daga masallacin sallan asuba ya sani kai dubana garesu,banyi ƙoƙarin matsawa daga wajen ba kamar yanda har yanzu zuciyata bata aiki yanda ya kamata,har suka wuce basu lura da niba danake kwance cikin sabon kwalbatin da aka fara aikinsa a ƙofar gidanmu,da suka yatsar dani.
Bana buƙatar sai an sanar dani dan na tabbatar fyaɗe suka mini ko ince ya min wani kuka mai ƙarfi ya biyo bayan wannan tinanin dayake shirin tarwatse ƙwaƙwƙwalwata into part- part,dana tina irin gargaɗin da Daada ke mana a lokuta da daman akan mu tsare mutumcinmu duk tsanani.
SALON KADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
________________________________
Page 1⃣1⃣
Ganin an shiga sallan asuba ya sanya ni ƙoƙarin miƙewa ina dafe kaina dake mini azababben ciwo idona yana gani bibiyu ina ƙara gyara zaman yageggen hijabanin dake lulluɓe a jikina,makullin dana yatsar lokacin da suka tosani cikin motar na ɗauka na buɗe gidan da sauri na faɗa ina maida ƙofar na rufe kirif!.
Kamar jira nakeyi na saki kuka sosai dayake fitowa kai tsaye daga ƙasan raina, tausayin Daada ya kwashe kashi mafi yawa acikin raina yaya zata ɗauki wannan al'amarin?.ƙirjina ya kuma bugawa da ƙarfi dana tina na rasa budurcina,waye shi?,mena aikata masa?,meyasa ya lalata mini rayuwa illa mafi muni da cutarwa?.Ko fuskarsa banga niba balle na duƙufa wajen neman sa na masa Allah ya isa na masa addu'ar Allah ya dawwamar dashi cikin baƙin cikin kamar yanda a yanzu akalan tawa rayuwa take shirin sauyawa.sautin muryarsa suka dira acikin dodon kunnuwana tamkar diran mikiya.
"My man ka dawo nan kayi driving ɗin,zanyi maganin rashin kunyarta".
Na ƙara runtse kumburarrun idanuna cikin muryata da ta dusashe amonta baya fita nace"Allah ya isa!Allah ya isa!!Allah ya isa!!!".bazan taɓa mance amon muryarsa ba duk da tana bayyanar da cewa a cikin maye yake.
Yanda muka rabo da Daada daren jiya ya fara dawo mini cikin lissafina,nayi azaman miƙewa ina dafe gefen da gefen gina na miƙe akan ƙafafuna da suke karkarwa,sai a yanzu na ƙarewa kaina kallo babu komai a jikina dangin suturu sai yagaggen hijabina da suka yaga min,ƙafata ko takalmi babu ga jinin daya biyo cinyoyina har ƙasan duga-dugaina duk halittun fuskarna sun canja sakamakon marukan daya dunga sauƙe mini.
Ba shiri na koma na zube a waje ina mai cigaba da wani sabon kukan,cikin raina ina addu'ar Allah yasa babu wanda yaga shigowata gida balle yanayin dana shigo.na daɗe a wajen kafin na kuma miƙewa ina taka ƙafafuna cikin tafiya ta data koma kamar na yara masu koyan tete,na tasafa ruwan zafi nakai banɗaki na gasa kaina duk yanda yake ƙona ni ban fita ba har sai daya huce sannan nayi wankan na fito salla na farayi ina ƙasƙastar da kaina a gaban mahaliccina.
"Ya Allah kai ka tsara mini rayuwar dazan gudanar tun kafin nazo duniya,kuma ka sanya ƙaddara da jarabawa suka zamto abubuwan da suke bibiye da rayuwar kowani mumuni,ya Allah ka bani ƙarfin gwiwan fuskantan wannan al'alamarin da na tsinci kaina a ciki ka sanya ni cikin bayinka da zasuyi nasarar ciye jarabawar da zaka musu.ya Allah ka ɗaiɗaita rayuwarshi kamar yanda ya lalata tawa rayuwa ka haɗashi da musifa da bala'in ka hanashi kwanciyar hankali a duniya.ya Allah bamu da ƙarfin da zamu shiga kotu dasu amma na kawo wannan shari'ar kotunka,inda ba'a bada cin hanci balle rashawa babu batun wanene kai ko su waye mahaifanka,balle abunda ka tara.Allah ka bimin haƙƙina".
Ina kawowa nan na shafa addu'ar ina ƙara kifa kaina cikin gwiwoyina ina ƙara saƙin wani sabon babin kukan,da nakejin tamkar ana watsa mini garwashin wuta a sashin ruhina.na daɗe a haka ji da nayi an fara bugun ƙofar gidan kamar za'a ɓalle shi ya sani ɗagowa a firgice ƙirjina na bugun tara-tara.na miƙe na nufi ƙofar ina faɗin"waye ne?".
Daga ɗayan bangaren na tsinkayon muryan yaya Aliyu yana faɗin"nine Ummukursum ki buɗe,lafiya kuwa?".
Nakasa amsa masa tambayar har sai daya maimata a karo na biyu,na isa ga ƙofa na buɗe inaja da baya ya shigo yana bina da kallon tuhuma yana mai cigana da faɗin"Ummukursum lafiya kuwa Sagir ya ƙirani jiya baki koma asibiti ba,sunyi ma tinanin ko Sakina ce ta dawo kuna tare da ita.jiyan kuma nazo nata bubbugawa baki buɗe ba".
Jikina ya shiga rawa kamar mazari nayi jarumtar harhaɗo kalaman dazan furta cikin bakina nace"ina jiran a gama ruwa ne sai na koma sai kuma bacci ya ɗauke ni,banji ma lokacin da kake buga ƙofar ba bacci yaci idona yanzu kuma na tashi da zazzaɓi".
Ya kalloni sosai kafin yace"to Allah ya sauwaƙe duk hankalinsu ya tashi,ki shirya sai muje asibitin ina jiranki a waje".
Naɗa masa kaina ina jawo gefen hijabina ina rufe fuskana sakamakon kallon daya bina dashi,kamar yanason ya gane wani a tattare dani.sai daya fita na mayar da ƙofar na rufe na ɗauko babban hijabi na saka wanda ya sauƙa mini har ƙasa.awarware nakeyin tafiya na fito waje na iske shi zaune a saman saman mashin ɗinsa na hau muka tafi asibitin.
Muna isa na hango Sagir yana fitowa ganinmu ya sashi nufo mu,na sauƙo daga mashin ɗin muryar Sagir suka yiwa kunnuwana dirar mikiya"Antyna Lafiya kuwa duk hankalinmu ya tashi,munyi zato kuna tare da Anty Sakina ne ma sai kuma yaya Aliyu yace mana ta dawo ba tana can azaren".
Na ƙaƙalo murmushin dole na maka a fuskana kana nace"lafiya ƙalau Sagir kawai bacci ne ya ɗauke ni kafin a gama ruwan sai kuma yau dana tashi da zazzaɓi".
Ya jinjina kai yana cewa"Ayya sannu mu shiga sai ki karɓa magani".nayi gaba yana biye dani a baya shida yaya Aliyu muna shiga ɗakin idanuna suka sauƙa kan Daada nake naji wani rauni ya zo mini na kasa riƙe kaina na isa gareta.na gaisheta da kuma Anty Hussaina da suke ɗakin ta amsa tana ƙarewa fuskata kallo kamar mai nazartan wai abun akan ta.
Mintuna biyu a tsakani sannan ta jefo mini wani tambayar data sanya hancin ckina haɗawa"Ummukursum lafiya kuwa?".maimaikon na bata amsa sai kawai na fashe da kuka tare da kifa kaina akan cinyarta,mamaki ya cikasu suka cigaba da tambayata lafiya nayi shuru babu amsa.
Sai Sagir ne ya ɗanyi murmushi yana takowa ya iso inda nake a jikin Daada ya ɗago ni tare da yalwata fuskarsa da annuri yana faɗin"Haba Antyna kuka kuma meye haka a gabanmu,dan baki da lafiya kawai".Anty Hussaina ta tsirkar da guntuwar tsaki haɗi da faɗin"Lalle Ummukursum zanga ranan da zaki girma yanzu a ciwon kike yiwa kuka?".Sha'awata saki dariya sosai na galla mata hararan da ya sanyata ƙunshe raguwar dariyar.
Daada ta kamo hannuna tana faɗin"Ku ƙyale min uwata,yanzu dai ki tashi ki shiga banɗaki ki wanke fuskarki kizo Sagir ya raka ki wajensu ki karɓa magani".na miƙe a hankali ina ƙoƙarin dai-daita tafiyata har nakai ga ƙofar banɗakin maganan da Anty Hussaina ta soma yi ya sani tsayawa cak!.
"Ummukursum tsaya tukunna meyasa ma tafiya naga kina yinta wani irin?".duk idanun mutanen ɗakin ya dawo kaina,na rusunar da kaina ƙasa dan bazan iya jure kallon cikin tsabar idon Daada na furta ƙarya ba nace"jiya ne dazanje gida,muka faɗi da adaidaita shine na ɗan buge".duk suka shiga jera mini sannu na juya zan shiga banɗaki muryar Daada ta dakatar dani"Amma meyasa baki ƙira waya kin sanar ba?".
Kafin nayi wani yunƙurin bata amsa Sagir ya karɓe zance da cewa"Daada kin manta ta bar wayarta anan,ai wajena ma wayar ta kwana".
"Haka fa na manta ne ki hanzatar ki fito kije su dubaki".na kama hannun ƙofar banɗakin na shiga na maida ita na rufe ko ban juyo ba nasan duk idanunsa yana kaina har na shige banɗakin.wani tuƙiƙin baƙin ciki ya taso mini lokaci guda na tabbatar yarda da kuma yaƙinin da Daada ke dashi a kaina shiyasa ta yarda da duk abunda na faɗa mata.wani kuka ya somin nayi saurin kai hannuna na toshe bakina a ƙoƙarin hana sautin kukan fita.
Wanke fuskana nayi kawai na fito ba tare dana ɗago na kalle kowa daga cikinsu ba nace"Daada bari naje na amso maganin",ta bini da toh.kallon da Anty Hussaina da yaya Aliyu suke bina dashi ya tabbatar mini da cewa basu yarda da yanayina ba zargina suke.
Ina tafe ina wannan tinanin naji sautin ƙafan takalman mutum a bayana,na waiga naga Sagir ne ya min alama da hannunsa akan na jira shi nayi kamar ban gansa ba na ɗauke kaina gefe,dan a halin yanzu nafiso na kaɗaita kaina da mutane ban ankara ba naji har ya iso dab dani.
Ban kulashi ba har mukaje nayiwa nurses ɗin bayanin abubuwan dake damuna suka rubuta mini magani,na karɓa takardan na fito Sagir yana biye dani hannuna ya kamo da ƙarfi ya fara jaana ina turjewa da masifar faɗin ya sakeni banason hauka,kota kaina bai biba har sai daya jani izuwa bayan ɗakunan asibitin ya sarka mini hannu.na hayayyaƙo cikin zallar masifa nake faɗin"wai Sagir meye haka ne,ka raina ni fa".na fara ɗaukar hanyar barin wajen yakuma riƙo hannuna"Ummukursum akwai abunda kike ɓoyewa menene ya faru,nasan baki kwana a gida ba sannan nasan duk abunda kika faɗawa su Daada ƙarya ne domin ko idanunki sun bayyanar da hakan.a ina kika kwana ina kikaje,sannan meya faru dake meyasa kikayiwa Daada da sauran mutane ƙarya?".
Ƙirjina ya buga tare da bada sautin dam-dam na juyo da sauri"Sagir ban gane me kake faɗa ba me kake nufi da ban kwana agida ba?".
Cike dason tabbatar mini da zancensa yace"kwarai kuwa nasan baki kwana agida ba domin lokacin da aka gama ruwan lokacin nabar cikin wannan asibitin,na wuce gidan na samu a rufe nata bubbugawa amma baki buɗeba.ganin hakan ya sani tsallaka gini na shiga na tarar bakya cikin gidan,nayi tinanin ko saɓani mukayi sai yanzu kuma Sha'awa take cemin baki kwana a asibitin ba".sirarun hawaye suka zubo mini nace"Sagir babu komai babu abunda ya faru dan Allah ka daina tambayata".ina kawowa nan nayi gaba zan bar wajen cikin sauri naji yace"UMMUKURSUM hawayen da kikeyi su kaɗai sun isa su tabbatar da min cewa akwai abunda ya faru,kodai Abba ne ya ƙara zuwar miki?".
Nayi saurin juyowa ina ƙarewa fuskarsa kallo yaya akayi Sagir yasan da wannan al'amarin domin ko Daada da Sha'awa basu sani ba,ban taɓa faɗawa wani mahaluki cewar Abba na nema na da lalata ba cikin rawar murya nace"Sagir waya faɗa maka haka,yaya akayi ka sani".yayi murmushi dake bayyanar da takaicin dayake a ciki kafin yace"ki fara amsa mini tambayata tukunna".
"Sagir duk abunda kake tinani cikinsu babu wanda ya faru,kuma karka sake min wannan tambayar sannan wannan maganar ta tsaya a tsakaninmu banason ko Daada ce taji".ina gamawa wuf na juya na wuce cikin sauri har ƙafafuna suna harɗewa na koma ɗaki. nasha maganin na nema waje na suƙure ina tino irin kallon da yaya Aliyu ya bini dashi dazan shigo ɗakin sam yanayinsa ya gama bayyanarwa da cewa shima bai yarda dani ba.
Haka na wuni banida cikakken walwala duk yanda naso sakar jikina lamarin ya faskara,ko yaya naƙi yarda na haɗa ido da Daada ita kuwa tausayina ya cikata saboda ƙaryan rashin lafiyan danayi ta hau kai ta zauna.
Cikin dare ina kwance idona arufe amma ba bacci nakeyi ba abubuwan da suka wakana suna dawo mini ɗaya bayan ɗaya,naji Anty Hussaina na tashina a hankali tare da ƙiran sunana,na miƙe ina fuskanto ta sai data ƙare min kallo tsaf ta naɗe hannayenta waje guda tace"UMMUKURSUM".
"Na'am"na amsa muryata tana rawa sannna ta ɗaura da faɗin"kiji tsoron Allah kisani komai kika aikata yana kallonki ki faɗa min menene kike ɓoyewa".zuciyata da buga dam nace"Anty babu komai sannan babu abunda nake ɓoye ki yarda dani"na ƙarishe maganar ina raurau da idanu ta ƙara kalleni tsaf kafin tace"shikenan koma ki kwanta".
A hankali na maida haƙarƙarina akan tabarma danake kwance a kanta ina mai runtse idanuna,ta yaya zan fara fuskanta Daada na bayyana mata wannan al'amarin.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"na furta can ƙasan maƙoshina ina roƙo Allah ya sada ni da mutuwata ko zanji sanyi da huta da wannan fitittunun.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
_________________________________
Page 1⃣2⃣
Kwance yake rigingine yana kallon ceiling wanda hakan ya fara zamtowa ɗabi'arsa,jin an turo ƙofar bedroom ɗin am shiga ya sashi sauƙe idanunsa akan ƙofar shigowar ya hango Ammiey ɗauke da tray yayi saurin miƙewa yana karɓan tray ɗin dake hannun natan ya ajiye akan stool,a bakin bed ɗin ta zauna yayin da shi kuma ya zauna a ƙasa kusa da ƙafafunta yana ɗan jingina kansa da jikinta shafa kansa tayi a hankali kafin ta shiga faɗin"Ga abinci nan kaci da kaina na dafa maka shi" .ta ƙarishe tana ƙoƙarin zuba masa abincin yayi saurin riƙe abunda ya fara zuba sai daya gama ya turo mata plate ɗin gabanta alamar ta basa.
Ta fara bashi da kanta har sai daya kusa cinyewa kafin ya ture plate ɗin,ya kwantar da kansa jikin ƙafafunta yana sauƙe numfashi,shi kansa bazai iya fasalta abunda ke damunsa cikin kwanan nan ba.ya kasa sakin jikinsa da kowa balle har ya iya zama ya tattauna damuwarsa da wani.
Ya daɗe haka duk maganar da takeyi da kai kawai yake amsa mata,har ta fice daga ɗakin tana matso ruwar hawayen tausayinsa daya cika ƙalbinta,a wajen ya kwanta yana sakin numfashi ɗaɗɗaya tinani suka shiga masa yawa aka wani sashi na zuciyarsa yana ayyana masa irin wautan da yayi na gujewa gida ba tare daya tsaya yayi binkice ba.yana kewar kaduna da kuma aikinsa,haka ya wuni a ɗaki koda Ahmad ya dawo daga asibiti yanaso ya tambaye shi wannan patiens ɗin tasa amma bakinsa yayi nauyi har suka kwanta.
Cikin kwana biyun nan duk nafita daga hayyacina nayi wani masifar rama na ƙara bushewa,kullum cikin rashin walwala nake da kuma tsarguwa da kaina ga Anty Hussaina da yaya Aliyu da suka sanya mini ido sosai haka nan ma Sagir,kwanan mu goma sha ɗaya a asibitin wanda yayi dai-dai dakwana huɗu da faruwar wannan lamari aka sallame Daada muka haɗa kayanmu tsaf!Sagir da yaya Aliyu suka ƙarayiwa Doctor Ahmad godiya sannan muka nema adaidaita muka wuce gida ina riƙe da Daada muka sauƙa muka shiga cikin gidan na buɗe mana ɗakin muka shiga ta kwanta sannan Sha'awa ta shigo da sauran kayanmu,tare dasu Anty Hussaina.Anty Sakina kam gidanta ta wuce akan da yamma zata shigo.
Na shiga banɗaki naci kuka har na godewa rabbi,na fito fuskar duk ta ƙara kumbura ina fitowa sallamar Sagir ta sauƙa a kunnuwana muka haɗa ido nayi saurin kawar da nawa na wuce ɗaki yana biye dani.kusa da Daada ya zauna yana mata sannu tana amsawa cikin sakin fuska.
Anty Hussaina ta miƙe tana faɗin"Adda nikam bari naje gida,yau Abban su Musaddik zai dawo".Daada ta fara faɗin"to Hussaina ki huta gajiya nagode shima ko gaishe shi".
Ta amsa da to kafin Sha'awa ta miƙe ta mata rakiya,suna fita nima na miƙe ina koma ɗakinmu nayi kwanciyata.cikin tinanin dana fara dulmiyewa acikinsahar hawaye ya fara tsiyayo mini naji shigowar Sagir.ban kula shi ba kamar yanda banyi ƙoƙarin kawar da hawayen dake kai koma tsakanin kuncina da saman haɓata.sai daya zauna kusa dani yace"UMMUKURSUM menene yake faru wallahi na fahimci duk takunki,ki sanar dani ko kuma na nemo da kaina kinsa dai zan iya ko inada mutanen dazan sa ku min hakan".
A yau kam nayi ƙudirin sanar da Sagir komai koda bazai rufa mini asiri ba,wataƙil naji sauƙi daga tsananin danake ciki na ɗago kaina nace"ina Daada?".
"Na fito na barta tayi bacci".
Na miƙe naje na tura ƙofar ɗakin na dawo na zauna ina fuskantar sa ta ina zan fara sanar dashi wannan lamarin ba shiri naji kuka ya zo mini na bashi damar zuba sai da nayi mai isha ta sannan na fara faɗin"Sagir zan sanar da kai komai domin kai ɗan-uwana ne wanda bani da tamkar ba koda kuwa zaka fallasa sirrina ga duniya".
Na tsagaita anan naci kuka sannan na ɗaura da cewa"Fyaɗe aka min Sagir na fito zan koma asibitin ina jiran abin hawa suka ganni suka min tayin shiga su kaini inda zani,na nuna musu banaso daga haka suka sani cikin motar suka keta mini haddi nayi iya ƙoƙarin taimakon kaina amma na kasa har sai da suka cimma burinsu akaina".
Na kuma sakin wani kukan Sagir da idanunsa suka rikiɗe izuwa launin ja ya tallafo haɓata yana faɗin"ya isa haka ki faɗamin zaki gane shi?".
Na jijjiga kaina haɗi da ɗaurawa da"banga fuskarsa ba bazan iya tantance kamanninsa ba muryarsa kawai naji kuma itama,tana bayyanar da cewa a cikin maye yake.Sagir ya rabani da mutumcina na ɗiya mace ya rabani da abunda duk wata mace take taƙama dashi ya cutar da rayuwata ta yaya zan fuskanci Daada da wannan lamarin a wannan halin da take aciki yanzu?". Ya riƙo hannuna gam!cikin nasa jikinsa duk ya fara rawa tsabar ɓacin ran da firgicin da yake ciki kusan mintuna biyar tsakani cikinmu babu wanda yacs uffan can yace"kuma kina ganin cewar ba Abba bane ya turo su?".
Ba tare dana tsaya wani tinani da zuciyana ba nace"A'a komai lalacewar Abba inada tabbatacin bazai aikata haka ba".
Ya kuma yi shuru na tsawon lokacin kafin yace"Antyna tabbas dole ki shiga firgici amma meyasa kikayi Daada ƙarya,zuciyarki tana shakkan akan ta ne?".
Nayi saurin girgiza masa kaina"bana shakka akan Daada sai dai iyaka ina tsoron halin da hakan zai sanya ta a ciki,wataƙil ma Abba ya wuye laifin dukka akanta na gwammace na rayuwa da wannan baƙin-cikin har yayi ajali da ace a silata Daada ta faɗa wani hali".wani kukan da kai tsaye yake bayyanar da raunin danake tattare dashi ya kuma zuwar mini,izuwa yanzu kam hatta Sagir ma shima kukan yakeyi yayi ƙarfin furta"Kiyi haƙuri tabbas ƙaddara bawa bata tsalake kan maishi,sannan babu wanda yasan sanda ƙaddarar mutum zata riske shi.domin muna gudanar da rayuwa ce tare da ƙaddararmu.haƙiƙa raywuwarmu abar tausayi ce ga kuma ƙarin wani abun yanzu na fara zargin kaina anya ba abunda nake aikatawa bane Allah ya fara nuna min ishara,abunda Abba yakeyi ne yau akayiwa ƴarsa baƙin-cikin dayake sanya iyayen yaran da yake ketawa haddi yau iyalinsa ne zasuji kwatankwacin hakan.yayi ƙudurin lalataki da kansa amma hakan bai samu ba har yanzu zuciyata ta kasa yarda da cewa bashi ya aiko su ba".
Duk yanda naso na ƙaryata hasashen zuciyarsa,bakina yaki bani haɗin kai wajen furta hakan sai kukan dana tsananta yinsa sosai.
Haka nacigaba dayi Sagir yana tayani mun ɗau tsawon lokaci a haka sallamar Sha'awa da mukaji ya sanya Sagir fara goge min hawayen fuskana yana faɗin"Shikenan ya isa haka ki daina wannan kukan,yanzu ki faɗa min ko lambar motar baki gani ba?".na ɗaga masa kaina alamar eh sannan yace na faɗa masa inda abun ya faru na sanar dashi komai.
Har yakai ƙofar fita ya juyo yace"kar ki sanarwa kowa bayan ni ko Anty Hussaina da Sha'awa balle Sakina,kibar komai a hannuna duk inda suka shiga zan nemosu kuma kome suke taƙama dashi".na ɗaga masa kaina sannan ya fice daga ɗakin inajin yanda yake tarban Sha'awa cikin daɗin rai duk dan ya kawar musu da zargi daga cikin ransu akaina.komawa nayi na kwanta lamau raina ya kasa yarda da cewa Abba zai iya turowa a mini ahaka.
Bansan sanda bacci ya kwashe ni ba ina farkawa naga garin ya lumshe alamar gajimare suna dab da sakin ruwa,gabana yayi mummunan faɗuwa sakamakon muryar Abba dasuka dira a kunnuwana yanata zazzago masifa,na fito da sauri har ina tuntunɓe nan na tarar da kowa a tsakar gidan Daada tana durƙushe a gaban Abba Sha'awa kuwa tana jikin Anty Hussaina ta ɗaura kanta a saman ƙafaɗunta wanda nake kyautata zatona kuka takeyi.
Jikina ya ƙarayin la'asar sosai na iso tsakiyar gidan ina tsaye kusa da Sagir.yaya Aliyu ne ya fara magana nayi saurin kai idona kansa a ƙoƙarin son fahimtar abun dake faruwa.
"Haba malam Nura mutumin nan fa kawai taimakama yayi,ya biya kuɗin wannan aikin da akayi koma bana tinanin kudana wani alaƙa dashi akwai taimakone don har muka baro asibitin bamu ganshi ba,ya nema a ɓoye sunansa".da wani wutar bala'in dake ruruwa acikin ran Abba ya hayayyaƙowa yaya Aliyu"Da yake duk kun maidani mahaukaci haka kawai siddan!bakusan mutum ba ya ɗauki kuɗi ya biya muku ko,mutane nawane suke neman taimako bai taimaka musu ba sai ku sannan kuma ku cemin baku da wata alaƙa dashi".
"Haba malam Nura ai kuwa dai mutumin nan inda ba gode masa ba bai cancanci aga aibun saba".
Furcin Anty Hussaina kenan.Sagir ya miƙe daga jingina bayansa da yayi a jikin gini ya iso inda Daada take durƙushe a gaban Abba hannunta ya riƙo yana faɗin"Daadata ki daina wannan kukan lokaci yayi daza ki daina damuwa da abunda ya shafesa baga mu ba ai mun ishe kiko,yanzu ki tashi kije ki kwanta ki huta".ya miƙar da ita hannunsu yana sarƙale cikin na juna Abba yayi azaman janye shi gefe guda da ƙarfin tsiya ya wancakalal"ke ban hanaka shigo min gidaba meya kawoka,ka fita min a gida".
Ina ganin yanda Sagir ya cizo leɓɓansa na ƙasa idanunsa suka ƙara rikiɗewa yace"nazo ganin mahaifiyata ne".
Yaya Aliyu yacewa Sagir yayi shuru kawai yaja hannun Daada suka wuce ɗaki Sha'awa da Anty Sakina suka rufa musu bayan yaya Aliyu ya bara bawa Abba haƙuri.a suƙure na bara jan jikina zan shiga ɗakin muryan Abba ta dakatar dani.
"Ke kuma mekikeyi anan munafukar banza munafukar wofi,yanzu zan wuce wajen Buba ko babu sadaki a ɗaura ya ɗauke ki yasan duk yanda zai yi dake".wasu hawaye masu ɗumi suka fara rige-rigen zubo mini na basu wannan damar,ɗakinmu na wuce saɓanin sauran mutanen da duk ɗakin Daada suna fama bata baki.
Kuka naci na fitar hankali har sai danaji numfashina yana sarƙewa,Sha'awa tashi shigo wai nazo mu gaida da mijin Anty Hussaina yazo duba jikin Daada.cikin rashin walwala na fito muka gaisa na koma ɗakin ya jima a gidan dan ina iya jiyo tashin muryarsa dasu yaya Aliyu da Sagir suna tattaunawa,sai da dare ya ɗauki Anty Hussaina suka tafi gidansu.
Sagir ya shigo ya ƙara kwantan mini da hankali duk maganar sai ya sanya cewa na ɗauki hakan a matsayin ƙaddara da kuma rubutacciyar al'amari acikin littafin rayuwata.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
________________________________
Page 1⃣3⃣
Ranar da lamarin zai faru tun safe na tashi da tsinkewar zuciya,ina zaune ina wanke-wanke jikina tamkar wacce aka zarewa laka Abba ya shigo ya watso mini wata harara da ta sanya ni firgicewa na masa sannu da zuwa ko kula ni bai yiba balle yasan da zaman mutum a wajen,ya wuce banɗaki yayi wanka tare da sauya shiga sannan ya fice yana ƙoƙarin kunna sigarinsa,ba tare da ya tambaya inda Daada take ba balle ya damun dason jin halin da take ciki.
Na sauƙe ƙatuwar ajiyan zuciya ina kinkimar kwandon wanke-wanken dan shigar dashi ɗakinmu najiyo tashin muryan Anty Hussaina suna tattaunawa da Daada na dawo da baya ina sauraran abunda suke faɗa,duk da ba komai suka faɗa nake iya jiyowa ba.
"Adda gaskiya zuciyata ta kasa nutsuwa da halin da Ummukursum take ciki ba,duk daman ita ba ta da wargi amma ta ƙara kaɗaita kanta daga shiga cikin mutane,bama wannan yafi damuna kamar rashin lafiyan daya ƙi barinta kullum tana cikin jinya haba gaskiya da alamar tambaya".
Daada tayi nisa kamar mai nazarin wani abun kafin tace"Nima na fara karantar wasu sauye-sauye daga gareta,amma yanzu meya kamata ayi?".Kamar jira Anty Hussaina takeyi tayi saurin furta"Muje asibiti kawai a dubata musan abunda ke damunta".
"To shikenan ku shirya in Sakina ta shigo sai kuje tare".
Furcin Daada kenan da sanya hawayen idaniyana tsiyaya nayi saurin barin wajen ina jin yanda jikina gabaɗaya ya ɗauki rawa kwandon hannuna yana ƙoƙarin zubewa ƙasa.
Na faɗa ɗaki na ajiye kwandon na zube kan katifa ina sakin kuka ciki-ciki"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un ya Allah ka kawo mini ɗauki"na furta cikin muryata da take shaƙewa.
Wani tinani yazo kaina nayi saurin miƙewa zaune ina lissafi da yatsun hannuna yau kwana goma sha bakwai kenan da faruwar wannan lamarin tun shekaran jiya ya kamata naga al'ada na amma baizo ba har yau,wani kuka ya ƙwace mini ina komar dakaina na ciro ɗan kwalina ina toshe bakina dashi.
Kamar an tsigara mini allura na koma tashi ina jawa wayata ina dannawa Sagir ƙira na ƙira,sau babu iyaka baya ɗauka nayi cilli da wayar na komar da kaina kaina pillow,cikin kukan daya fara cin ƙarfina na tsinkayo muryar Sha'awa a tsakiyar kaina tana faɗin"Anty Ummi wai inji Daada ki shirya zakuje asibit da Anty Hussaina".na ɗaga mata kaina alamar naji sannan tafice na cigan da kwanciyata banida niyyar tashi naji Anty Hussaina ta fara ƙwala mini ƙira na tashi na ɗauko hijabi sai dana goge hawayena sannan na fito ina saka hijabin akaina.
Na iskesu tare da Anty Sakina kaina a ƙasa nace"gani"Daada ta kallo ni sosai kana tace"ki tashi kuje asibiti".ban koma cewa komai ba sukayi gaba ina biye dasu baya tausayin Daada ya tsaya mini a ƙoƙon raina,meyake shirin faruwa dani?.tambayar dana jefawa kaina kenan ina ƙoƙarin samarwa kaina amsarta naji Anty Sakina ta taɓoni haɗi da cewa"Tinanin me kikeyi shigo muje mana".nasaka ƙafata cikin adaidaitan na zauna Anty Hussaina ta jijjiga kanta kawai tana faɗawa mai adaidaitan asibitin da zai kaimu.
Har muka isa asibitin hankalina baya ga gangar jikina Anty Sakina ta koma taɓo ni na sauƙo suka bashi kuɗinsa sannan muka nufa cikin asibitin,gabana yayi mummumar faɗuwa muka yanki kati sannan muka hau layi,yana isowa kanmu na shiga nayiwa likitan bayyani abubuwan da nakeji ya tura mo muyo test ɗin fitsari naje aka min sannan muka fito muna zaman jiran result.
Wani tinani ya shigo lissafina na fiddo da wayata daga cikin hijabina,na shiga danna code ɗin cin bashin layin MTN nayiwa Sagir text na sanar dashi abunda yake faruwa da kuma asibitin da muke ina rubuta text ɗin hawaye suna ciko mini kurmin idona na kawar dasu,Sagir shi kaɗai zai iya kawo mini ɗauki a halin da nake ciki yanzu raina yana ayyana mini cewa kamar farin-cikin da zanyi a rayuwata tazo ƙarshe.
Nurse ta fito tace mu shiga zuciyata da buga tamkar zata faso fata da nama na ta fito,su Anty Hussaina suka fara shiga ina biye dasu muka zaune,likitan yana ƙarewa result ɗin dake riƙe a hannunsa kallo a hankali ya zare gilashin dake zaune saman karan hancinsa tare da cewa"ina mijinta?".
Anty Hussaina ta amsa da"Likita bata da miji hasalima budurwace bata taɓa aure ba".yayi shuru na tsawon daƙiƙun da bazasu gaza goma ba sannan yace"result ɗin ya nuna tana ɗauke da juna biyu na tsawon sati biy...."bai ƙarisa ba sakamakon salatin da Anty Hussaina da Anty Sakina suke rige-rigen furtawa.
"Ciki! wani irin ciki yarinyar dako rana ba'a sa mata ba balle aure ace dana ɗauke da cikin har na tsawom satikar biyu".tana kawowa nan kuma ta fashe wani kuka mai tsuma zuciya.likitan ya ɗago yana bina da kallo kafin ya maida idonsa ga Anty Hussaina yace"Abunda result ya nuna kenan idan kunada tantama zasu iya zuwa wani asibitin na daban a mata gwaji".
Ko result ɗin basu tsaya ɗauka ba duk suka fice likitan yace"ke kuma kin kyauta garin yaya haka ya faru?,kina yarinya dake ki ɓata rayuwarki da bin maza har ta kaiki da ɗaukar ciki kina tinanin wannan hawayen da iyayenki suka zubar akanki Allah zai barki ne,dalla ɗauki result ɗin ki fice min daga office ki saurarin kuma yanda Allah zaiyi dake".
Na kasa ɗago kaina balle na kalli bangaren da yake banyi ƙoƙarin ɓata kalamaina wajen yin masa bayanin cewa fyaɗe aka mini ba,domin nasan zaiyi wuya ya fahimta na ƙara gaskata furcin malam bahaushe nacewa"Duk abinda namiji yayi adone".gashin a tashin farko kowa laifina yake hangowa.Haka na tashi duk gaɓoɓin jikina sunyi laushi na fice daga offishin na isa ga inda su Anty Hussaina suke tsaye ta cakumo ni da dukkan ƙarfinta tana faɗin"wuce muje wani asibitin a mana wani gwajin ban yarda da aikin wannan asibitin ba".hawaye suka gangaro mini ta cigaba da jan gefen hijabina suna ƙoƙarin fita daga cikin asibitin mukayi kiciɓus da Sagir yana sauƙa daga adaidaita ya sallame mai adadaitan da sauri ya iso mu yana tambayar Anty Hussaina lafiya.
"Ba lafiya gyara ka bani waje mu wuce"ta faɗa tana tsayar mana da abun hawa Sagir ya zauna a gaba har muka isa cikin asibitin asalam hawaye bai bat gudana daga idaniya ba,muka shiga aka mini gwaji result ɗin ya kuma nunawa ina ɗauke da juna biyu na tsawon sati biyu.haka muka ƙara gangarawa wani asibitin Anty Sakina ta haɗa mu da wani abokin yaya Aliyu ya mini gwajin shima ya tabbatar mana da ina ɗauke da ɗa acikin cikina.yana gama sanar mana Anty Hussaina ta saki salati tana sakin Musaddik zai sulale daga kan cinyarta Anty Sakina tayi azaman tare shi.
"Ummukursum kin cuce kanki,waya miki ciki meyasa kika bada kanki da wanda shari'a bata halalta muku junanku ba ko tausayin wannan baiwar Allahn mahaifiyarku bakyaji ba yayin da kike aikata wannan baɗalan?.duk faɗi tashinta domin taga ta rayuwarku ta inganta ne amma abunda zaki saka mata kenan dash..."bata ƙarisa sakamakon wani kukan daya zo mata ta fara rerosa nima kaina na kasa hana nawa hawayen gudana na rarrafo na iso inda take zaune na kama ƙafarta cikin muryata da take bayyanar da ƙololuwar tashin hankali da firgicin da nake aciki nake cewa"Anty wallahi ba laifina bane,nayi iya ƙoƙarin kare kaina nayi ƙoƙarin guje musu amma sunyi nasara akaina".wani kallon data watso mini ya ƙara jefa ni cikin wani sabon babin firgicin na kasa ɗauke ƙwayoyin idona daga kan fuskarta har izuwa,lokacin da tasa ƙafa tayi shuri dani na faɗi gefe guda ta miƙe tana fama sakin huci tace"Ba komai Ummukursum kije ai duniyace ta ishe kowa riga da wando, wanda bai zo bama tana nan tan jiranshi balle ke da kike cikinta".tana dasa aya anan tayi gaba ta fice daga ofishin yayin da Anty Sakina da yaya Aliyu suka rufa mata yaya bayan yaya Aliyu ya gama ƙare mini kallon gurilla ya jijjiga kai ya fice shima.
Nan na duƙufa ina rero kukana da sautinsa ya cika ofishin,Sagir yazo ya ɗago ni muna haɗa ido shima nashin idon ya kawo ƙwalla suka zubo lokaci guda yana furzar da zazzafar iska daga bakinsa har sai da ɗuminta ya sauƙa akan fuskana ya kamo hannuna muka fita bayan ya juya yayiwa likitan magana wanda bana cikin hayyacina dazan iya tantance abunda ya faɗa mishi can muka gano su Anty Hussaina suna tafe tana kuka Anty Sakina tana lallashinta yaya Aliyu ya tare adaidaita zasu hau,muka ƙara sauri nida Sagir don mu cimmasu nazo zan shiga cikin nafef ɗin Anty Hussaina ta daka mini wani gigitaccen tsawa daya sanya ni saurin kwantar da kaina a jikin Sagir.
"Ina zaki shiga,wai kina tinanin tare zamu koma gida ki bari wannan labarin ma kaɗai na tabbatar ya isa ya haifawa Adda wani damuwar basai ki bimu kin ƙarisa,kasheta ba na roƙe ki dan Allah karki rabani da ita.ita kaɗai ta rage min a duniya"takai ƙarshe tana haɗe hannayenta wuri guda alamar roƙo,Anty Sakina ta kallo yaya Aliyu da yake ta jijjiga Musaddiq daya ɓarke da kuka,tana masa alamar yace wani abu ya ɗauke kansa tamkar baisan da zamanta awajenba.
Wanda nake kyautata zaton cewa ɓakin-ciki da kishine ya turniƙe shi suka taru suka masa yawa,tun ba yau ba yaya Aliyu ya nuna mini alamomin soyayya ban bashi fuskaba saboda mutuncin dake tsakaninmu da Anty Sakina,kuma bansa a raina shima zai aureni ba saboda babu uban dazai amincewa ɗansa ya aure ni,matuƙar ɗabi'un Abba sun isa ga kunnuwansa.Figigi nayi na dawo daga wannan lissafin da ƙwaƙwƙwalwata ta antaya ina bin bayan adaidaitan da su Anty Hussaina suka hau yanda ya bule wajen da hayaki,yaya Aliyu ma yazo ya wuce mu kan babur ɗinsa.ba shiri na koma na zubewa a wajen duk zafin ranar kan kwaltar bai hanani yin zaman ƴan bori ina sakin wani hargitsantsan kukan da sautinsa baya fita ba.
Sagir ya zauna dab dani har muna iya jiyo bugun numfashin junanmu kallona kawai yakeyi,sirarun hawaye suna sauƙa daga dandamalin fuskarsa izuwa saman haɓarsa naji ya fara share mini hawayena bakina ya fara ƙarƙarwa kamar sabuwar haihuwar kazan da ruwan damina ya mata mungun bugu na soma faɗin"Sagir kun tafi kaima ka tashi ka tafi,dan Allah inkaje ta nema mini afuwan Daada ka sanar da ita yanda komai ya wakana sannan tayi ƙoƙarin lallashin zuciyarta ,dan nasan abunda na aikata mata ya isa yakai ruhinta ga kushewa" .
Ya kamu hannayena yana ɗagoni tsaye yace"haba Antyna ki daina wannan kukan tare zamu tafi gidan muje wajen Daada kumz mu mata bayanin komai".cikin wani rauni irin na ɗiya mace nace"kaima fa kukan kakeyi ta yaya zan daina,Anty Hussaina ma kukan take yi.yanzu nasan Daada ma tacan tanayi duk a dalilina kaico na".yayi saurin share hawayensa yace"shikenan kinga na daina".daga haka ya tara mana adaidaita muka hau muka nufa gida ƙirjina yana bugun tara-tara sau tara.
SALON KADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
Daga gobe in sha Allah zamu gama free page hilis a antayo ayi payment
_______________________________
Page 1⃣4⃣
Tacan farkon layinmu mai adaidaitan ya ajiyemu muka tako da ƙarfarmu cikin layin,muna karyo kwana idanuna suka sauƙa akan Anty Hussaina da suke shiga gida,raina ya ƙara yi mini wani soya tamkar zai tarwatse Sagir daya lura da sauyin yanayina ya damƙo hannuna yasa cikin nasan,har muka isa cikin gidan ban ankara ba naji Zulaihat ta taso ta faɗa cikina tana rungume ni na taba jikina daga nata ta langwaɓar dakai tace"Ayya Anty Ummukursum yanzu mukazo Daada take cemin bakiji daɗi ba kunje asibiti,ya jikin yanzu?". Ciki-ciki na amsa da"Alhamdulillah".Sannan na rusuna ina gaida matar babanta da kuma wata ƙanwar mahaifinta sai babbar ƴaƴarsu,duk suka amsa babu yabo babu fallasa. Na miƙe zan wuce ɗaki muryar Daada da suka sauƙa acikin kunnuwana suka sanya ni tsayawa cak ba tare dana waigo ba haka nan lokaci guda naji na tsani kaina da kaina dana kasa tabbatar da yaƙinin Daada akaina.
"Ummukursum ya jikin kun dawo ince dai lafiya naga Hussaina da Sakina sun shigo sun wuce ɗaki duk rai babu daɗi?". Na shiga harhaɗa kalamomin da zanyi amfani dasu wajen bata amsa cikin bakina,kafin nayi wani motsi Sagir ya karɓe zance yana ɗaurawa da "Daada lafiya ƙalau sai dai kin shigo ciki sai na miki bayani".
Ya kai ƙarshe yana ƙoƙarin ɓoye damuwar da ta fito ɓaro-ɓaro akan fuskarsa ta hanya ƙirƙan murumushin da ta tsaya iyan leɓɓansa.
Nayi saurin zara ƙafafuna cikin ɗakinmu saboda kallon da dangin Zulaihat suke bina dashi da kuma Zulaihat da Sha'awa har nakai ga tura ƙofar ɗakin nayi an jawo bayan hijabina da ƙarfi an jefani gefe guda na bugu da randar ƙasan dake tsakar gidan,idona suka koma cikowa da wasu hawaye na ɗago domin ganin wanda ya mini hakan idona suka sauƙa akan fuskar Anty Hussaina da take tsaye tana ta fama hucin tsayiwar da tayi sai hakan ya ƙara bayyanar da tsantsar kaman su da Daada a matsayin ƴan biyun da suka rayu a haifa guda.ƙololuwar baƙin-cikin da take a ciki ya sanya idaniyarta rufe ta manta da baƙin da suke zaune a wajen,Anty Sakina sai raɗa take mata a kunne wanda bana raba ɗayan biyu tana bata haƙuri ne akan ta rufa mini asiri sai baƙinsun tafi sannan.
Sagir ma ya isa gareta yana bata baki shima ta tureshi gefe tana nuno min da ƴar manuniyar yatsarta,jikinta har karkarwa yakeyi take faɗin"Wannan wannan za'a rufawa asiri wacce bataji kunyar watsar da mutumcinta a titi ba".Daada tayi saurin tasowa duk ta fara daburcewa take cewa"ke Hussaina wai menene kike faɗa haka menene Ummukursum ɗin tayi? meya faru a asibitin?".
Result ɗin ta fiddo ta miƙawa Daada ta karɓa hannunta har rawa yakeyi ta buɗe ta koma cewa"Hussaina kya bani a rubuce bayan kinsa ba ganewa zanyi ba faɗa mini menene yake faruwa?".
"Adda ciki ne a jikin Ummukursum har na tsawon sati biyu bamu da masaniyarsa". Luu Daada ta fara ja da baya zata kife Sagir da Zulaihat sukayi saurin ta reta,salati da sallami suka cika wajen da suke fitowa daga bakin dangin Zulaihat tsam suka fara miƙewa suna zara takalmansu ƴaƴar Zulaihat wacce naji suna ƙira da Hajja Fati ta finciko hannun Zulaihat tana faɗin"wuce muje ai bamu ga ta zama ba,uba mashayi ƴa kuma ta buge da yawon karuwanci". Zulaihat ta saki kukan yayin da suke janta suka fice daga cikin gidan.
Sagir ya ƙara gyara Daada a jikinsa ya shiga da ita ba tare daya kallo ko inda nake ba,zaunar da ita yayi sannan ya fara mata bayanin komai tiryan-tiryan kamar yanda na faɗa masa yanda abubuwan ya wakana,Anty Hussaina tace na tashi na shigo ɗakin na miƙe da ƙyar Sha'awa ta taho zata taimaka min Anty Hussaina tace karta kuskura ta taɓa ni,haka na shigo ɗakin kaina a ƙasa don banajin zan iya jure haɗa ido da Daada na zauna a ƙasa sautin kukan da nakeyi yana fita a hankali,shi muka ta saurara kafin na tsinkayo muryar Daada tana faɗin"Ummukursum meyasa kika ɓoye min faruwar wannan lamarin,kina tinanin zaki iya yiwa kanki magani ne ko kuma saboda ban kai naji damuwar ki ba?"nayi saurin jijjiga mata kai alamar a'a ta ɗaura da faɗin"Uwata faɗa mini menene ya faru?".
"Daada wallahi ki yarda dani fyaɗe ya min nayi iya ƙoƙarin taimakawa kaina amma hakan ya gagare ni har sai da yayi nasara akaina,cin ƙarfi yamin ko fuskarsa ban gani ba muryarsa kawai naji dan Allah Daada ki yafe mini". Na ƙarishe ina jan gwiwoyina na iso gabanta na kifa kaina a jikin ƙafarta, ban sani ba ko abunda na faɗa ya sama matsuguni a cikin ranta ko kuma itama zargina takeyi akan ni na bada kaina akayi amfani dani. Karo na farko da Anty Sakima ta tsuma bakinta "Daada wallahi zuciyata ta gamsu da duk abunda Ummukursum ta faɗa duk da ba a gabana hakan ya faru ba".Ta faɗa itama tana zubda nata hawayen Anty Hussaina ta kau da kai gefe tana taɓe baki na lura da ita lafiyar Daada da halin da zata shiga shi yafi damunta.
Jin Daada tayi shuru tana bina da kallo ya sanya ni ƙara furta"Wallahi Daada fyaɗe ya mini,fyaɗe aka min". Nakai ƙarshe ina ƙara tsananta sautin kukan danake yi. Sha'awa da duk ta gama kiɗimewa ta miƙe tana haɗa hanya kamar ƴar maye zata bar ɗakin har ta ɗaga labule ta sake tana zare idanunta da taci kuka dasu har ta godewa Rabbi,ganin irin tsoron da yayi ƙawanya a fuskarta ya samu duk muka maida idanunmu a bakin ƙofar ɗakin,ganin Abba yana tsaye ya naɗe dukkan hanayensa a bayansa yana fitar da wani hucin ɓacin rai ya tilastawa zuciyata ta shiga lugudan tara-tara na dafe saitin ƙahon zuciyata inajin wani abu yana bin gaɓoɓin jikina wanda na rasa da wasu kalmomi zanyi amfani wajen fasaltashi.
Da wannan tinanin da yake neman tarwatsa mini kunyar kaina naji an finciko ni da matuƙar ƙarfi aka yatsar dani a tsakar gida,wani tsohon katakon gadon Daada.Abba ya ɗauka ya hau dukana dashi ta ko'ina tun ina iya kare kaina ta hanyar rufe jikina da tafukan hannayena har ƙarfin yin hakan ya gagareni na kwanta lamau tamkar matacciya ina fitar da numfashi ƙasa-ƙasa.babu wanda yayi wani yunƙurin dakatar da Abba daga dukan da yake mino har sai da yaya Aliyu ya shigo sannan ya karɓe katakon daga hannunsa cike da zafin rai irin nashi dana sanshi dashi tun fil azal yake faɗin"Haba Malam Nura me kake aikatawa haka,idan rai ya ɓaci ai bai kamata ace hankali ya dushe ba kana tinanin inka kasheta hukuma zata barka ne bar ganin cewa ƴarta kace wallahi sai doka tayi aiki a kanka".
Wani kallo Abba ya gallo masa yana ƙara kawo mini wani dukan yaya Aliyu ya tare sai a sannan Sagir yazo ya ɗago ni daga durƙushewar da nayi ina ƙoƙowa da numfashina da yake ƙoƙarin nisa da barin gangar jikina.na kwantar da kaina a jikinsa ashe kuka ma waje ya samu domin duk yanda naso nayi abun yaci tura sai na zuci nake yi,a hankali na ɗago idona ina satar kallon Daada wacce take tsaye tana ƙoƙarin kawar da hawayen da suka ciko mata idaniya,Sha'awa kuwa ta kifa kanta a jikin Anty Hussaina tana nata kukan haka nan ma Anty Sakina.
"Ummukursum ciki!ciki a cikin gidana wallahi bazaki haifa mini ɗan shege ba maza kibar min gida kije ki nema ubansa"furcin Abba kenan da suka sanya zuciyata daina yin aiki sai ajiyan numfashin da nake sauƙarwa da ta ƙaru.Daada tayi jarumtar furta"Malam kayi haƙuri wallahi nima bani da masaniya sai yanzu da sukaje asibiti da Hussaina da Sakina aka tabbatar da hakan".Wani kallo ya watso mata da suke bayyanar da ruruwar wutar tafasar da ruhinsa yake yi cikin ƙwayoyin idonsa kana yace"Dalla rufa min baki munafukar banza munafukar wofi,duk bada bakin akayi komai ba duk abunda yarinar nan ta aikata kina sane kawai lalacewar danayi a idon ki ne bakya ganin kimata kika ƙi sanar dani.to wallahi wallahi rantsuwa kenan ko baza ƙara awa guda acikin gidan nan ba dan bazan rena ɗan shege ba".
"Malam Nura har kanada bakin da zaka furta waɗannan kalaman,kai ƴaƴa mata nema ka lalatawa rayuwa ta irin wannan hanyar,yara nawa ka jefasu cikin fushin iyayensu a dalilinka.ƴaƴa nawa ka raba da iyayensu,ƴaƴa nawa kayi sanadiyar shigarsu duniya.alƙawarin Allah baya haɗuwa ƙasa matuƙar kayi to kaima sai an maka na tabbatar abunda kake aikatawa ne Allah ya fara nuna maka ishara akan Ummukursum don ka ɗanɗana irin raɗaɗin da iyayen ƴaƴan daka ɓata suke ji,wasu sanadiyar haka har sukan rasa rayuwarsu gabaɗaya".furcin Anty Hussaina kenan tana jawo ni izuwa gaban Abba tana masa nuni dani har izuwa yanzu hawaye basu bar gudana a fuskarta ba.jikin kowa yayi sanyi a wajen mussamman Abba wanda duk idanuwa suka dawo garesa.baiji kunyar ƙara furta cewa na bar masa gidan sa tare da cikin shegen dake maƙale cikin mahaifata.
Daada ta tako har gabansa tan faɗin"Dan Allah Malam kayi haƙuri a duba lamarin nan,ayi bincike tunda ga Aliyu ɗan sanda ne sai su gudanar da bincike irin nasu har a gano waɗanda suka aikata mata wannan abun".ya daka mata wani tsawa yana ɗaura da cewa"Hassana kika ƙara furta wata kalma a bakin AURENKI,daga yau inna isa da gidan nan kuma na tabbata jagora kuma shugaba a gareku to na rufe babin Ummukursum ku manta da ita sannan ko maganarta banason ayi.ki tashi ki fice daga gidan nan tun kafin dare ya miki".yakai ƙarshe yana mini nuni da hanyar ficewa daga cikin gidan.
Nayi saurin ƙanƙame ƙafafunsa cikin kukan daya gama cin ƙarfina na soma faɗin"Abba dan Allah kayi haƙuri ku yafe min wallahi fyaɗe aka min ko fuskarsa ban gani ba muryasa kawai naji ku yarda ni,wallahi ka haramta mini zaman gidan nan bansan inda zan nufa a duniya ba dan Allah karka rabani da Daada koda zaka sanya min katanga tsakanina dasu".yayi saurin shure ni da ƙarfasa yana nuno ni da ƴar tsarsa manuniya yace"Kika ƙara kuskuren ƙirana da Abba sai na tsine miki albarka kibi duniya".
Ba shiri na miƙe duk na daburce na juyo ga Daada nace"Daada ki yafe min dan Allah sannan kimin fatan alkhairi tare da addu'ar Allah ya sadani da wanda ya aikata min wannan abub kodan na masa wata tambaya ɗaya tal!,mena aikata masa da ya rabani da farin-cikin da nake riritawa a rayuwata,meyasa sanda ya gama aikata min abun bai kashe ni ba ya barni na cigaba da rayuwa?".Daada ta rungumeni tsam!a jikinta duk muna kuka Sha'awa ma tazo ta rungume mu duk har Anty Hussaina da Sakina suma ba'a barsu a baya ba.Abba yazo ya finciko ni daga tsakaninmu ya fara jana izuwa tsakiyar titi ya warɓar,Daada da Sha'awa zasu fito yace kar wacce ta fito Sagir da yaya Aliyu suka fito Sagir ya ɗago ni yana goge min hawayen fuskana.
Kana yaya Aliyu yace nazo na shigo gidansa saboda mutanen da suka fara taruwa a titin a ƙoƙarin son jiyar da kunnuwarsu abunda yake wakana,Abba ya zaburo yace"Aliyu ka fita idona ban amince kowa ya taimaki Ummukursum ba a cikin unguwan nan ku barta tayi rayuwar data zaɓawa kanta,dubeta tsimi-tsimi da ita kamar batasan komai ba amma har ta iya biyewa saurayi ya ɗirka mata ciki".zuciyata tayi nasara buga wanda tun ɗazu ta daina harbawa sai yanzu nagane abunda yake ƙara tunzura Abba hadda ƙin amincewa da nayi dashi.
"Babu wanda ya isa hana ni taimakon Ummukursum dole ne ayi bincike har a gano gaskiyar abunda ta faɗa,kafin akai ga yanke mata hukunci don ka koreta daga gidanka ni zan ɗauki nauyinta da kuma abunda take ɗauke dashi a cikin cikinta har ta haifeshi".furcin yaya Aliyu kenan da suka sanya ni ware kumburarrun idanuna da nakejin sun har sun mini wani mungun nauyi Anty Sakina ta ciro hannuna daga cikin na Sagir ta riƙe gam!muka shige cikin gidanta,sanin yaya Aliyu hukuma ne ya sanya Abba yake ɗaga masa ƙafa a wasu lokutan.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
Allah yayi mun gama free page ga mai buƙata zai iya tuntuɓata ta wannan lambar 07038908713 yayi payment akan naira N300
______________________________
Page 1⃣5⃣
Tsawon daren wannan ranar bacci ya gagari idanuna sai kukan da har na rasa hawayen tsiyayarwa Anty Sakina da yaya Aliyu suna ta aikin lallashina tare da nutsar dani cewa kowani bawa da hanyar da Allah yake jarrabarsa a rayuwa,na ɗauki wannan a matsayin SALON ƘADDARATA.da ƙyar na iya tashi washe gari saboda ciwon da ilahirin gaɓoɓin jikina suke mini na tarar da Anty Sakina a kitchen tana haɗa abincin karyawa na gaisheta sannan nayiwa su Amir da Abdallah wanka na shiryasu cikin uniform ɗinsu yaya Aliyu ya kaisu.Na koma ɗaki nayi kwanciyata zuciyata da buga da ƙarfi tana bada sautin dam-dam,sakamakon muryar Anty Hussaina da nake jiyowa daga cikin ɗakin don katanga ɗaya yake da gidanmu,duk da kunnuwana basa iya tantance dukkan abubuwan da take furtawa amma na tsinci wasu daga ciki.magana ce akan rashin lafiyar Daada.
Zumɓul na miƙe tsaye ina rarimar hijabina na fito daga ɗaki,Anty Sakina da yaya Aliyu da bansan sanda ya dawo gidan ba.kota kansu ban bi ba na ɗauki hanyar da zaka sadani da barin cikin falon ban ankara ba naji Anty Sakina tasha gabana ta fara magana wanda bana ita tantance abunda take faɗi,don a wannen lokaci ji da ganina sun dushe abu mafi soyuwa a gareni shine nasan halin da Daada take aciki a halin yanzu.
"Ummukursum menene,ina ne zakije?"ta faɗa tana kamo ni jikinsa saboda na fara fizgewa kamar wacce aljanu suka yiwa mungun kamu tayi ƙoƙarin,dawo dani cikin falon tare da zaunar dani bayan musha kokawa da ita na fara sakin numfashi tamkar wacce ta shari gudu a fagen tsere.a hankali na fara jin ɗumin hawaye suna rige-rigen gangarowa daga idaniyata,yaya Aliyu ya durƙusa kusa dani mintuna biyu a tsakani yana ƙarewa fuskata kallo kafin ya furta"UMMUKURSUM"cikin kaukausar muryar ya faɗi hakan wanda ya tilas ta mini sauƙe ƙwayar idon a kansa kana na rusunar da nawa idon kasa.ya cigaba da faɗin"Ina zakije kin manta furcinsa na ƙarshe a gareki cewa idan kika taka izuwa ƙofar gidansa,tsinuwa ce zata shiga tsakaninku ki kwanta da hankalinki yanzu zanje na sama Sagir sai naji halin da ake ciki,kinji ki daina wannan kukan banaso".kaina kawai na iya ɗaga masa wasu hawayen suna ƙara cigaba da gosilo a tsakanin kuncina da saman haɓata.
Ya miƙe yana cewa Anty Sakina bari yaje yaji meyake faru,sannan ya fita ita kam har da hawayenta ta bishi waje ta ɗan daɗe kafin naga ta dawo ta zauna kusana tana ta lallashi da ƙoƙarin nuna min cewa babu wani abunda ya faru da Daada na ɗan tsagaita kukan da nakeyi badan na yarda da kalamanta ba.na kasa gusawa daga wajen har yaya Aliyu ya dawo ganinsa ya sanya ni saurin miƙe ina jefa masa tambayar ya jikin Daadan,don a lokacin zuciyata tafi ayyana mini cewa mutuwa ma tayi.
Yaɗan sunkuyar da kana ƙasa yana murza yatsunsa har sai da Anty Sakina ta ƙara maimaita masa tambayar a karo na biyu,sannan ya ɗago kansa yana faɗin"ba wani abu bane hawan jini ne kawai kuma kafin naje ma Sagir da Anty Hussaina sun kaita asibiti,jikin natan dai yanzu da sauƙi".yana isowa wannan gaɓar take naji na daina fahimtar abinda yake faɗi numfashina ya harɗe waje guda na fara kokawa dashi daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba,sai farkawa naji na ganni shimfiɗe akan gadon Anty Sakina na tashi da ƙyar ina dafe goshina da nakejin kaina tamkar zai tsage gida biyu.
Son ganin halin da Daada take cikin ya hana ruhina sukuni na tashi na fito daga ɗakin ina tafe ina haɗa hanya kamar ƴar mayen da tasha tayi tatil,nazo dai-dai ƙofar falo naji yo tashin muryar Sagir da Yaya Aliyu naja da baya ina jingina baayana da jikin gini ina sauraran abubuwan da suke tattaunawa.
"Gaskiya tana cikin wani hali mai wuyar fassarawa wanda a irin ƙarancin shekarunta,zai iya haifar mata da matsala ha lafiyarsa me yiyuwa ma ta iya kamuwa da ciwon hawan jini ko makamantansa,dole gobe mu kaita taga Daada kuma mu ƙara mata bayanin akan abunda ya faru".kalaman yaya Aliyu kenan da suka sanin tuna abunda suka faru ɗazu ashe suma nayi maganar da Sagir ya farayi ya sani saurin kawar da wannan tinanin daga lissafina ina sauraronsa."Gaskiya a yanzu Daada tana buƙatar hutu ga zuciyarta,a bar maganar zuwa wani ɗan lokaci in lafiyar jikinta ya kuma inganta sannan a ɗaura daga inda aka tsaya".can na jiyo muryar Anty Sakina ta ɗaura da faɗin"Hakane kam ya kamata abi komai a sannu har a gano bakin zaren,har izuwa lokacin da Allah zai sauƙe ta lafiya ta samu miji tayi aure".
"Anty Sakina ai yanzu kam aure ga Ummukursum sai dai wani ikon Allahn waye zai aureta bayan yaji wanene mahaifinta sannan kuma yaji cewa tayi ciki kafin a kai ga shafa mata fatiha".kamar jira Anty Sakina takeyi naji tayi hanzarin furta"ALIYU zai aureta kuma inada yakinin shi bazai mata gori ba balle har ya ƙamaceta".daga haka nayi saurin barin wajen na koma ɗakin su Amir na zube akan gado kamar jaka naci kuka har na godewa Rabbi,sai dana nayi mai isata kafin na miƙe naje banɗaki na ɗauko alwala nazo na gabatar da sallan zuhr da asr a tare na daɗe akan sallayan ina addu'a kafin na shafa wanda yayi dai-dai da shigowar Anty Sakina ɗakin tana riƙe da hannun Amir yana game a wayarta,bakin kafitar ta zauna tana fuskanto ni tace"kin tashi kenan?"na ɗaga mata kaina inayin tasbihi da yatsun hannuna bata koma cewa komai ba har sai da taga na kammala sannan ta ɗaura da faɗin"Aliyu yake asibiti duba Daada jikinta da sauƙi".nan ma ban bata amsa ba na ɗaga kaina ta cigaba da cewa"Ummukursum ki kwantar da hankalinki itafa rayuwar nan komai mai wucewa ne,in sha Allahu komai zai daidaita yanzu bari a kawo miki abinci kici yanzu dole ki ringa kula da kanki domin bake ɗaya bace".
Wani kuka mai ƙarfi ya zo mini nayi saurin mayar dashi,ina ƙar ɗagawa Anty Sakina kai don tayi sauri ta fice daga ɗakin na sama damar sakin kukana.haka ta fita domin ɗauko mini abincin na saka kaima cikin gwiwoyina ina kukan da yake ƙona mini rai da ruhi a lokaci guda,har na manta da wani abu wai shi abinci tsabaragen tashin hankalin da nake a cikinsa.duniyar gabaɗaya ta min zafi badan sanin da nayi akan cewa duk wanda ya kashe kansa makomarsa itace jahannama ba wallahi dana rataye kaina na huce takaicin raina.Amir ya dafani cikin maganar da bai gama ƙwarewa ba ya fara tambayata lafiya nayi ƙoƙarin maida masa da murmushi sannan na goge idona koda Anty Sakina ta kawo min abincin kasa ci nayi duk da yanda ta matsa mini burin raina a yanzu shine naga halin da Daada take a ciki.
Koda dare ya tsala yauma bacci ya gagari idanuwa sai juyi nake ta faman yi ƙiran assalatun farko kuwa tamkar ƙofofin kunnuwana ladanin yayi ƙiran sallan idona tar!na tashi nayi nawa sallan sannan na tada Abdallah da Amir suma sukayi,na sauƙe wata wahalallan ajiyan numfashi nacewa Abdallah ya bani fefa da biro daga cikin jakarsa ya miƙo mini na fara rubutun cikin hausar da taban gama ƙware a rubutun taba.sai dana gama tsaf!na ƙara karantawa sai kuma na fashe da kuka mai matuƙar sauti ba shiri na goge hawayena sannan na miƙawa Abdallah fefar dana ninkata biyu nace in mamansa ta fito ya bata na fice daga ɗakin.
Nayi sa'a kuwa na sama ƙofar gidan a buɗe wanda nake kyautata zaton cewa yaya Aliyu ne ya buɗeta ya tafi masallaci,don sanda na fito naga an shiga sallan asubahi a ƙofar gidanmu na tsaye ina sauƙe ajiyan numfashi mai ƙarfi sosai nakeson ganin Daada koda hakan zai kasance saduwar mu ta ƙarshe kamar yanda raina yake saƙa mini,wata zuciyata ta ayyana mini kawai na shiga na ganta kome zai faru ya faru,har na ɗaga ƙafata ta dama sai kuma nayi saurin maida ita sakamakon gargaɗin Abba a gareni daya fara yawa cikin kaina.
Can ƙasan maƙoshina nake furta"Daada ki yafe mini wallahi fyaɗe ya min ko fuskarsa ban gani ba muryasa kawai naji,zan tafi dominna tabbatar ganina zai iya haddasa miki wani ciwon na daban bayan wanda kike tare dashi,in fatan wataran gaskiya tayi halinta ku gane cewa fyaɗe ya min dan Allah Daada ki yafe min wallahi bansan inda zan shiga da nauyin fushin a gareni nasan ko mutuwa ne ta riske ni a cikin wannan halin Allah bazai gafarta min ba".ina isowa nan wani kuka ya suɓɓuce min yanda nake maganar ka ɗauka cewa ina gaban Daadan ne kamar sabuwar shiga hauka haka na fara tafiya ina waige-waige saboda lasifikan masallaci da naji har sun kammale sallan.sosai nake tafiyar tamkar zan tashi sama har sai da gari ya fara haske na iso bakin wani titi ƙarancin yawan mutane a wajen ya tabbatar mini da cewa na fito bakin gari duk da ban taɓa barin ko cikin garin bauchi ba ko ƙauyukan dake kewaye da ita balle kuma wani jahar daban.na nema wani waje na zauna kan dakalin aikin sabon titin da akeyi a wajen,ina sauƙe wata shirgegiyar ajiyan zuciya kuka mai ƙarfi da kubce mini na bashi damar fitowa.
A guje yake jan motar kallo ɗaya zaka masa ka gano damuwar dake shimfiɗe akan fuskarsa,rashin lafiyar Hajiyarsa ba ƙaramin sanya shi yake a cikin damuwa ba,banda haka babu abunda zai komar dashi kaduna,Da ƙarfi hancin cikina suka murɗa tamkar ana sanya hannu ana damƙo mini su,na miƙe jiri yana neman yatsar dani da ƙasa na nufa gefen titi kozan hangi gida na shiga na roƙa koda ruwa ne na jiƙa maƙoshina,an ankara ba na ji ban bugeni da mota na faɗi ƙasan sumammiya,da ƙarfi ya danne burki da ƙarfarsa ya tsayar da motar yana gangarawa gefen titi ya fito dana isowa kaina dishi-dishi idona suke iya gano fuskarsa ya fara jera mini sannu daga haka ban ƙasa sanin inda kaina yake ba.
Sai buɗe idona nayi na ganni a gadon asibiti na tashi zaune da ƙyar saboda matsanancin ciwon da jikina yake mini,ina ƙarewa ɗakin kallo jin kamar za'a shiga ɗaki nayi saurin komawa na kwanta don a wannan lokacin nafi buƙatar cigaba da zama a asibitin don in suka sallame ni ban san inda zan nufa ba, kaina suka tsaya duk da bana ganinsu amma ina jin abunda suke faɗa.na kanne idona ɗaya ina kallo fuskokinsu ƙasa-ƙasa.
"Alhamdulillah jikin natan ma da sauƙi kuma anyi sa'a cikin dake jikinta bai zube ba,da zaran ta farka ma za'a iya baku sallama don Allah sai a rinka kulawa yallaɓai"furcin likitan suna yin musabaha har zai fita ya juyo tare da faɗin"zamuje kayi sing ɗin tunda kace matarka ce,sai a sallame ku".ya ɗaga masa kai alamar yaji sannan likitan ya fice shi kuma ya zauna a kujerar dake kusa da gadon yana tallafo fuskarsa da hannayensa.
"Buɗe idonki ki kalle ni domin nasan ba bacci kike yi ba".amon muryarsa suka daki kunnuwana nayi saurin maida idona dana buɗe kaɗan na rufe,ya ƙara maimaitawa cikin tsawa ba shiri na tashi na zauna ya tsura min ido wani kuka ya zo min da bansan dalilin sa duk da wani sashin raina ina farin-ciki akan rashin zubewar cikin nayi alwashin rainarsa har na haifesa yazo duniya na kuma fuskan ci mahaifinsa dashi duk da zuciyata tana raya mini cewar bazan taɓa ganin sa ba.maganar daya soma yi ya katse mini tinanina.
"A wani unguwa kike na maida ke gida?"nayi shuru na kasa bashi amsa saboda kukan daya ci ƙarfina sai ajiyan zuciya nake ta faman sauƙewa,ya miƙe tsaye yana zura dukkan hannayensa a cikin aljihunsa alamar sanyin AC ɗin ɗakin yana ratsa shi yace"kina ɓata min lokaci ki ƙira mijinki ki shaida masa asibitin da kike".shuru ya ratsa ɗakin na daƙiƙun da basu gaza goma ba kafin nace"ban fito da wayata ba"ba tare daya juyo ba ya min nuni da wayar dake ajiye kan kujeran daya tashi,na gane nufinsa don haka nace"Bani da lambar a kaina".
ya juyo da saurin yana ware idanunsa a kaina na ƙara maimaita masa ya sauƙe ajiyan zuciya yana bina da wani kallon da yake bayyanar da zargina daya fara ɗarsuwa a cikin ransa ya ɗaga kafaɗarsa alamar bai damu ba sannan ya ɗauki wayarsa ya ajiye min wasu kuɗaɗe ya fice daga ɗakin.
Na lumshe idanuna na tsawon lokaci kamar an tsigara mini allura na miƙe ina yafa hijabina tare da cire ledar ƙarin ruwan da aka mana,na ɗauki kuɗin daya ajiye na fice daga asibitin cikin sauri sai a sannan na karanta sunan asitibin ANNOOR SPECIALIST HOSPITAL,asitibi ce data amsa sunan ta a cikin garin bauchi ina gamawa wani jiri ya ɗebe ni idanuna suka rufe ɗif!na faɗi a wajen,da sauri ya fito daga cikin motar daman tun fitowar ya tsaya don ransa ya fara zargin wani abu.ware idanuna da suke mini wani zafi-zafi nayi ina ƙoƙarin tashi zaune ina bin wajen da kallo zumbur na miƙe tsaye ina ɗan waige-waige saboda kasa tantance inda nake da nayi wajene fegi guda ɗakine koko masana'anta ne?.
Can na hango shi yana rubutu akan wani file nayi saurin isa gabansa cikin muryata da take rawa nake faɗin"Malam ina ka kawo ni nan,ka barni na tafi naje naga halin da Daadata take a ciki".ya ɗago yana kallona sannan ya cigaba da cike-ciken file ɗin dake gabansa na ƙara maimatawa cikin kushashewar murya,a daƙile ya furta"Kaduna"na zaro idanu ina faɗin"Kaduna kuma meya kawo ni nan garin yaya nazo don Allah ka kaini bauchi wallahi inason ganin Daadata".na durƙushe a wajen ina cin kukan da ya haifar min da cushewar numfashi.
Yana kammalawa ya miƙe zai fice nayi saurin isa gabansa ina masa makiyan ya maida ni gida,kota kaina bai bi ba ya fice ina ji yana dannawa ƙofar key.na koma na cigaba da kukana wata zuciyar tace min wataƙil ma ɗan yankan kaine shikenan na kawo kaina ga halaka.
Yana fita ya faɗa motarsa ya fice daga cikin asibitin da gudu ya nufi gida,ya rasa abunda yake masa daɗi a ransa,wani irin lalacewa al'ummar musulmai tayi da har ace wannan yarinyar tasan tayi ciki ba tare da miji ba,wata ƙaramar tsaki yayi yayin da yake danna hancin motar cikin gidan yana gama parking ya fito,da sauri ya nufi part ɗinsa don baya son kowa yaga shigowarsa.hannunsa yana kan handle ɗin ƙofar ya kasa shiga saboda maganganun su Haidar daya ke tashi daga cikin falon.
"Wallahi Adam tun ranar na kasa samun rukuni kuma ko fuskarta ban gani ba,a Faisal tayi wa rashin kunya ni kuma kawai na faɗa mata a hanyar mu ta baro cikin bauchi".
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjan Iyam
_________________________________
Page 1⃣6⃣
Wani ɓacin raina ne ya taso masa lokaci guda yawun bakinsa har yana ɗaukewa,ya tura ƙofar ya shiga ganinsa bai sa sun canza ma'udin akan abinda suke tattauna ba,haka nan ko kallo bai ishe su ba.har yakai ga ƙofar bedroom ɗinsa maganar da Adam ya soma yi ya sa shi dakatawa.
"Kai nifa shiyasa bana ɗaurawa kaina wannan wahalar,ina dai rage zafi ta hanyar yan dabaru irin namu ta yadda basai yarinya ta ɗauki ciki ba".Haidar ya gyara zamansa yana ƙara lankwashe ƙafafunsa wajen guda yana zuƙar shishan dake hannunsa yake faɗin"Baza ka gane ba akwai ban taɓa taɓo kazar da ta tsaya min a rai bane kamar wannan gashi ko fuskarta bazan iya tinawa ba".Adam yayi saurin furta"To ka tina fuskarta a wani dalilin,yanzu suna can ana ƙoƙarin rufe maganar daga ƙarshe kuma a nema wani a aura masa ita,kasan irin wannan mutanen basu da ƙarfi da zasu iya shiga da ƙara ma".suka saki wata shewa suna tafa hannu.
Wani mari Zayyad ya sauƙewa Haidar a saitin idonsa yana ƙara masa wani,ya miƙe da sauri suna shiga Bedroom ɗinsu Adam yana biye dasu,ƙoƙarin control ɗin kansa yake yi don ya fara barin cikin hayyacinsa zai iya aiwatar da komai ƙofar bedroom ɗin ya zubawa ido na tsawon lokaci ya tsani zina ya tsani mai kusantar sa ko waye yafar hannunsa yayi yana kaiwa cushion duka kafin ya shige bedroom yana maida ƙofar ya rufe da ƙarfi.bathroom ya nufa yana sakewa kansa ruwa ya ɗau lokaci a haka sannan ya fito ya shirya cikin shigar manyan kaya ya fito har yanzu ƙofar ɗakin su Haidar tana fito ya jijjiga kansa yayin da yake ficewa daga falon.
Rashin ganin motar Daddy acikin parking space hakan ya tabbatar masa da cewa bai dawo ba,don haka ya isa inda yayi parking motar zai shiga ya hango Asiya tana fitowa daga part ɗin Nenne,yana tsaye a wajen ya riƙe ƙofar motar ba tare daya shiga ba,har tazo ta wuce ta shige part ɗinsu bai ɗauke idanunsa daga kanta ba.
Sosai tasha jinin jikinta don kallon da yake mata na tuhuma ne,sai daya furzar da iska daga bakinsa kafin ya faɗa cikin motar yana maida ƙofar motar ya rufe jingina kansa yayi da kujerar motar yana sakin numfashi ƙasa-ƙasa can ƙasan maƙoshinsa yake furta kalmar"Innalil lahi wa'inna ilahir raji'un"wasu irin mutane Allah ya jefo shi yake rayuwa a cikinsu?,babu wanda zai iya fahimtar damuwarsa ba tare da yayi amfani da kalamai wajen furtawa ba sai Hajiyarsa.haka nan ya taso ko abokai ba shi dashi saboda gudunsa da akayi ana cewa ba shi da uba kuma Hajiya ba mahaifiyarsa bace.Allah ne shaida yana son ƴan uwansa matuƙa sai dai ya daɗe da fahimtar cewa babu ƙaunarshi ko ɗigo acikin rayukansu dukiyar mahaifinsu ne kawai suka ɗaura idanunsa akai.
Ganin numfashin sa yana ƙoƙarin sarƙewa ya tilas ta masa buɗe idanunsa yana sauƙe ajiyan zuciya mai ƙarfi,kafin yayi wa motar key ya fice daga gidan ya nufi cikin zaria wajen Hajiyarsa.dai-dai kiran sallan zuhr ya isa ya same ta a falo mai aikinta tana mata tausa ganinsa ya sanya ta saurin miƙewa tana nufosa,kamar yanda ya saba ya kwaɓe hular dake kansa yana rusunar da kansa ƙasa ya iso gabansa ya dafa kansa yana masa addu'a.
Sannan ta miƙa masa hannunta yayi kissing suka ƙariso cikin falon kallon fuskarsa take yi sosai kamar mai nazarin wani abu kafin tace"ABEENA lafiya kuwa kaje can gidan nakun ne?"wasu hawaye suka gangaro masa ya matso yana kwantar da kansa a jikin kafaɗarta shi kansa ya san cewa yana da rauni kamar mace a wannan bangaren.
"ZAYYAD"ta ƙira sunan cikin muryarta da take cike da sanyi da kamala,ya ɗago kansa yana kallonta yasan duk lokacin da ta ƙira ainihin sunansa magana ce za suyi mai muhimmanci.
"ABEENA ita rayuwar nan cike take da tarin ƙalubale,duk wani cikakken mumuni baya fushi da ƙaddara faɗa mini menene yake faruwa?".sai da yayi ƙasa da kansa yana murza zoben azurfan dake ƴar yatsar ta tsakiya a hannun hadunsa,kafin ya soma faɗin"Hajiya bazan iya zaman gidan ba,bazan iya jure ganin mumanan halayan ƴan-uwana ba,kuma banida ikon dazan iya dakatar dasu zan dawo nan kawai na zauna tunda tafiyarku jibi ne".
Tun kafin ya ƙarisa Hajiya ta fara jijjiga masa kai tana ɗaurawa da faɗin"ABEENA zaman a nan bazai yiyu ba domin mahaifinka yazo har nan munyi magana shima yana bukatar kusa dashi,ka cigaba da haƙuri shi fa duk wanda ya rungumi haƙuri baya faɗuwa a rayuwa".ajiyan zuciya ya sauƙe ya najin wani sanyi yana ratsa sassan jiki da jijiyoyin jikinsa,ya langwaɓar dakai yana cewa"Madalla da samun nagartaccen uwa da ta kasance sanyin idaniya ga ƴaƴanta,bani da abunda zan iya biyan ki dashi a duniya koda zan bada raina fansa Allah ya ƙara ɗaukaka da nisan kwana mai amfani".ta sakar masa da lallausan murmushi sai da haƙorin makkan dake maƙale a bakinta ya bayyana tana shafo sumar kansa tace"Amin ubana nima ina alfahari dakai".
"Zanyi missing ɗinki sosai"ya faɗa yana shagwaɓe fuska kamar mai shirin yin kuka ta ɗan harare shi tace"Nima tare naso muje amma ka nuna aiki ya maka yawa don haka Umra tare zamu je kamar yanda muka saba".murmusawa yayi yana komar da kansa kan cinyarta yana faɗin"Hajiya nima naso hakan amma zamuyi bikin cikar kungiyarmu shekara uku da kafuwa,dole wasu abubuwan sai na tsaya akai".
Daga haka ta fara tambayarsa labarin su Ammiey yace suna lafiya duk suna gaishe ki daga haka suka cigana da hirar su,koda wasa Hajiya bata tambaye akan cikin da Nenne tace Asiya na ɗauke dashi kuma take alaƙanta ciki da Zayyad don tasan hakan kan iya cife shi cikim wani yanayi na daban mussamman yanzu da ta fahimce cewa baya cikin nutsuwarsa.
Anty Sakina ce tsaye a kitchen tana haɗa abin kari Abdallah ya shigo ya miƙa mata takardan dana bashi,karɓa tayi tana juya takardan a hannunta tare da jefa masa tambayar ta mecece,ya sanar da ita jikinta nan take ya ɗauki rawa ta ware naɗin da nayiwa takardan ta fara karantawa,tana gamawa ta fara sulale ƙasa tare da kurma ihu wanda ya sanya Yaya Aliyu saurin fito daga ɗaki cikin shigarsa ta aikin ƴan sanda ya iso yana tambayar lafiya.
Takardan ta miƙa masa ya karanta yana sauƙe salati shuru ya ratsa kitchen ɗin sai sautin kukan Anty Sakina da yake tashi,ya ɗago ta suka dawo falo.
"Na shiga uku yanzu ta yaya zan fuskanci Daada da wannan maganar,innalil lahi wa'inna ilaihir raji'un! ya Allah ga baiwar ka nan ka tsare ta a duk inda take ka amintar da ita cikin amincewarka"abinda Anty Sakima take ta faman maimaitawa kenan yaya Aliyu ya riƙo hannunta ganin yanda duk jikinta yake rawa kamar ana jona mata wutar lantarki ya soma faɗin"Sakina ki nutsu mana kina cikin wannan halin ta yaya zamu zamar da hanya mai ɓullewa"bata kula shi ba illa tsananta kukan da tayi sallamar Sha'awa ta sanya yaya Aliyu haɗiye kalaman da yake shirin furtawa.
Cikin falon ta iso tana binsu da idanu yaya Aliyu yayi jarumtar cewa"Sha'awa lafiya kuwa ko jikin Daadan ne?".ta girgiza masa kai tana ɗaurawa da cewar"Daada ce tace a ƙirayo mata ita yanzu".suka yi saurin kai kallonsu ga junansu nan Anty Sakina ta ƙara fashewa da wani kukan Sha'awa da ta fara ruɗewa ta fara tambayar Anty Sakina inda nake"Anty ina Ummukursum ɗin menene ya faru da ita,don Allah ta fito muje Daada na buƙatar ganinta tana can kwance babu lafiya".ganin cikin su biyun babu wanda ya bata wata gamshashshiyar amsa ya sanya ta nufar ɗakin su Abdallah ta duba har ɗakin Anty Sakina da kuma kitchen babu inda bata duba ba amma ba ta kai ga samun abunda idanunta suke buƙatar tozali dashi ba.
A guje ta fito ta wuce yaya Aliyu da Anty Sakina da suke zaune har yanzu inda ta barsu ta fice yaya Aliyu yayi saurin bin bayanta,bai cimma ta ba har sai da ta isa cikin gidan ta zauna kusa da shimfiɗar da aka yi wa Daada a tsakar gidan tana sakin kuka,duk idanu suka dawo kanta Anty Hussaina tace"Meye ya faru,ina ita kuma Ummukursum ɗin?".tayi shuru tana mai cigaba da kukanta sai da Sagir ya daka mata tsawa sannan ta fara ƙoƙarin furta cewar"bata gidan naje ban same ta,na tarar da Anty Sakina sai kuka take yi".tana kawowa nan yaya Aliyu ya shigo.
Daada ta miƙe da ƙyar tana isa ga yaya Aliyu"ban gane abunda Sha'awa take faɗa ba ina ita Ummukursum ɗin?".baya jin zai iya haɗa ido da Daada don wani nauyinta gami da kunyarta ne ya mamaye birnin ƙalbinsa don haka ya rusunar da ƙwayar idonsa ƙasa,Sagir da ya lura da farar takardan dake riƙe hannun yaya Aliyun ya miƙe ya karɓa takardan ya buɗe ya fara karantawa a fili kamar haka.
---NASAN LOKACIN DA WANNAN TAKARDAN ZAI ISKE KU NAYI NISA DAGA GARIN NAN,DAADA KI YAFE MINI BAZAN IYA ZAMA INA KALLON HAWAYENKI NA ZUBA A SANADIYATA BA,BAZAN YAFEWA KAINA BA SABODA BAKI CANCANCI WANNAN SAKAYYAR DAGA GARENI BA,NA ZAƁI NA TAFI CAN WANI WAJEN HAR NA HAIFE ABUNDA YAKE CIKINA NA MIKI ALƘAWARIN RIƘE MUTUNCINA A DUK INDA NA RISKI KAINA KAMAR YANDA KIKA TARBIYYARTAN DAMU AKAI.ZAN CIGABA DA ROƘON ALLAH DAYA BAYYANA GASKIYA KOWA YA GANE CEWA FYAƊE AKA MINI KO FUSKARSA BAN GANI BA.DON ALLAH HAR KU CIRE NI DAGA CIKIN ADDU'O'IN KU,ALLAH YA SADA FUSKOKINMU DA ALKHAIRI.------
Yana kawowa nan Daada tayi saurin fizge takardan daga hannunsa ta juyo da Humaira ƴar Anty Hussaina da sauri take faɗin"Ungo Humaira karanta min takardan nan da kyau,ke kin fishi sanin ilmin boko yaje sai shirme yake karantowa".sai da ta cakomo hannun Humaira ta damƙa mata takardan ta farata shi tsaf!kamar yanda Sagir yayi.
Kalmar"Innalil lahi wa'inna ilaihir raji'un"ita ce abunda take fitowa daga bakunan mutanen dake wajen,sallamar Anty Sakina ya sa yaya Aliyu ɗago kansa daga sunkuyon da yayi suka haɗa ido.nan ta tsaya tana nata kukan gidan ya koma kamar gidan makoki.
"A'a ba Ummukursum bace nasan Ummukurusm ɗina baza taɓa tafiya ta barni ba,Aliyu don Allah kace na yafe mata ta dawo na ganka na yafe mata"daga haka ta tafi luu zata faɗi Sagir da Anty Hussaina su kayi saurin riƙe ta.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
_______________________________
Page 1⃣7⃣
Akan shimfiɗar ta suka kwantar da ita tana sauƙe numfashi kowa kuka yake yi a wajen,banda Sagir da yake ƙoƙarin ƙarfafa zuciyarsa yana lallashin Daada.
"Tashin hankali wai na zaune ya faɗi,ita kuwa Ummukursum ina zata a duniya daya wuce nan,wa take dashi daya fimu?"furcin Anty Hussaina kenan tana ƙara sautin kukan da take yi.
Da hannun Daada tayi wa Anty Sakina alama akan tazo ta taso kuwa ta matso kusanta,suka riƙo hannun juna"Ɗago kanki ki kalle ni".Anty Sakina ta ɗago suna kallon juna sannan Daada ta ɗaura da faɗin"Ki nutsu ki sanar dani yanda abun ya faru".
"Daada yau tun asuba banga wulgawar ta ba,nayi tinanin ko gajiyace ta hana ta fitowa,shiyasa ban leƙa ba na fara aiyukana ina kitchen Abdallah ya kawo min wannan takardan wai ita ta bashi tun asuba ta fice daga gid-gid-gida-gidan"ta ƙarishe maganar cikin rawar murya.wani shirgegen ajiyan zuciya Daada ta sauƙe lokaci guda tana runtse idanunta tana ambatan sunayen mahaliccinta dari ba ɗaya aciki ƙoƙuwar ranta.ganin har yanzu bata buɗe idon ba ya sanya Sha'awa taɓo kafaɗarta kota suma ne take ayyanawa a ranta.
Da mamaki suka ga murmushi akan fuskarta,tabbas na sani Daadata jaruma ce ko a cikin jarumai mata tayi zarra,domin zai yi wuya ka iya gane damuwarta ƙoƙarin miƙewa ta fara Sagir yayi saurin riƙe ta"Daada ki zauna jiri fa ɗeban ki yake yi".
Anty Hussaina ta taso tana faɗin"Adda don Allah ki koma ki zauna kinga lafiya bata ishe ki ba".
Murmushi ta mayar musu tace"Babu amfanin zaman bazai samar mana da mafita ba,duk ku tashi kuyi alwala mu yi sallah mukai kukanmu ga wanda zai iya da alamuranmu".duk jikin su ya ƙara yin sanyi laƙau wannan murmushin nakan fuskar Daada kaɗai ya isa ya fallasar da cewaa duk sanda tayi shi ƙona da raɗaɗi ranta cike a ciki.duk suka miƙe suka yo alwalan yaya Aliyu ya musu limanci suka gabatar da raka'a biyu tare addu'o'i sosai,kanɗa kanta Anty Hussaina tayi wasu hawayen suna gangaro mata take faɗin"Duk ni naja komai gashi na jefa rayuwar wannnan yarinyar cikin garari,da mun rufa mata asiri tare da gudanar da bincike".
Yaya Aliyu yayi gyaran murya tana ƙara langwashe ƙafafunsa waje guda yana faɗin"Ita ƙadddara ta riga fata baza mu canza taba sai dai mu kiyaye gaba,shiyasa akeson idan rai ya ɓaci to kar hankali ya gushe.duk muna da laifi amma Malam Nura shine babban ummul ba'asin faruwar komai".shuru ya ratsa wajen na tsawon daƙiƙan da basu gaza biyu ba kafin ya ɗaura da faɗin"in sha Allah zan sa yara su bazu ko'ina acikin bauchi har Allah ya bayyana mana ita".
"Yanzu haka zamu rayu babu Anty Ummu acikin gidan nan,don Allah yaya Sagir ka nemo mana ita"furicn Sha'awa tana kwantar da kanta a jikin Humaira,izuwa yanzu kam hatta Sagir ɗinma hawaye yake fitarwa ya tare su da hannunwansa Daada ta musu alama da hannunta akan su matso duk suka isota ta rungumesu a jikinta.
Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya bazu lungu-lungu a cikin unguwar mu,cewar nayi cikin shege kuma an neme ni an rasa,masu son ganewa idonsu da kuma son yaɗa lamarin har gida suke zuwa ana yiwa Daada jajen abunda ya faru.da Buba uban ƴan caca labari ya isa ga kunnuwansa ya tilastawa Abba akan cewa sai ya biya sa kuɗinsa tunda a kai ga ɗaura auren ba.
"Ɗan kuka shike jawa uwarsa jifa"inji masu iya kalami haka Abba ya ɗauki laifin dana aikata kacokam ya ɗaura shi akan Daada,kamar kullum tana durƙushe a gabansa yana faɗin"Tir da irin halayyaki Hassana bana raba ɗayan biyu cewar ki nada masaniyar inda yarinyar nan ta shiga,kawai so kike ki tozarta ni kuma burinki ya cika tunda ga Buba uban ƴan caca ya uzura min akan na biya shi kuɗaɗansa,don haka gidan nan zan sayar na bashi gidan ke kuma kyasan inda dare ya miki tun da wuri".
Anty Hussaina ce tayi gaggawar furta"Haba Malam Nura bangane tasan ida dare ya mata ba,ko ka manta har yanzu tana ɗauke da igiyoyin aurenka har uku akanta,sannan ƴaƴan ina zata kaisu?".Harara ya galla mata tare da faɗin"Ƴaƴa ta barsu duk inda taga ya mata,ai duk cikin su babu wanda bai mallaki hankalin kansa ba zasu rayu ko ba uwa da uba,ƙarshen zance ma ake haihuwar yaro a lokacin uwar ta mutu kuma ya cigaba da rayuwa,ya baku nan da zuwa yamma ku tashi ku bar masa gidansa don ni daga nan ikko na nufa".
"kasan ba inda shari'a ta amince maka,ka tsallake iyalanka ka tafi ka barsu ko muhalli babu".furcin yaya Aliyu kenan daya sa Abba ya waigo haɗi da faɗin"Aure ko?,ince dai sai ina aurenta sannan za'a kallafa min wannan dokokin,to taje na sake ta saki uku kuma Allah ya isa tsakani na da ita da ta lalata min tarbiyar ƴa".Sagir ya cakumo kwalar rigarsa da ƙarfi idanunsa suka rikiɗe izuwa jajir duk jikinsa ya ɗauki rawa tsabar ɓacin ran daya ke ciki har kana iya jiyo yanda haƙwaransa suke kararɗiya da juna.
Da wani irin hanzari Daada ta miƙe daga durƙushewar da tayi,tana ɗauke Sagir ya wata kyakykyawar mari tare da hankaɗe shi gefe guda,Sha'awa tayi saurin isa gareni tana riƙe shi da ƴatsarta Daada ta shiga nuna shi haɗi da cewar"Sagir tarbiyan dana baku kenan,ko ka mana cewar shi ɗin mahaifinka ne?".tana kawowa nan ta juyo da kallonta izuwa fuskar Abba sosai take kallon fuskarsa abunda bata ɓata yi ba kenan a tarihin zaman aurensu haɗa ido da Abba koda wasa yake magana to idonta a ƙasa inko a tsaye yake to tana durƙushe a gabansa,wasu hawaye suka biyo gefe da gefen fuskarta a iya sanin da na iya Daada a rayuwata macece mai matuƙar dauriya da shanye komai a cikinta.
Sai da ta ƙara taku ɗaya ta iso gaban Abba"Nura nagode da duk abunda ka min a cikin tsawon shekarun da muka yi muna amsa sunan miji da mata,Allah ya sani kuma kowa zai yi shaida na akan hakan banida burin daya wuce na lulluɓe asirinka cikin wannan ƙirjin nawan akwai tarin damuwa marar adadi,amma ba komai idan a cikin zaman mun na ha'ince ka to kasani AKWAI ALLAH kuma baya bacci,zamu bar gidan kamar yanda ka buƙata zan tsaya tsayin daka naga na bawa ƴaƴana tarbiya,sai dai kasa a ranka cewar daga yau sun daina amsa sunanka a matsayin ubansu".ta ƙarishe maganar tana nuna shi da ƴar yatsarta,Abba duk da kalaman sun sanyaya masa jiki amma wani tsaki mai dogon zango kafin ya fice daga gidan.
Daada ta cigaba da faɗin"Sha'awa ki tashi ki fara haɗa mana kayanmu Sagir kaje ka nemo mota".
"Adda ina zakuje waye muke dashi daya rage mana a duniya banda junanmu?".tambayar da Anty Hussaina ta jefa mata kenan suna rungumar juna,yaya Aliyu ya miƙe tsaye yana faɗin"Daada ba inda zakuje zanje wajen shi Buba uban ƴan cacan muyi magana dashi ko haya ne sai mu kama"yana dasa aya yaja hannun Sagir suka fice daga.
A hankali yake driving ɗin motar zai koma cikin kaduna kasantuwa da Hajiyarsa shine babban abunda yake samarwa rai da ruhinsa nutsuwa,iska ya furzar daga bakinsa yana karya kwana ya tina da yarinyar daya ɗauko daga bauchi tana can ya rufe ta a cikin office ɗin,wata tsiririyar tsaki yaja bazai iya barinta a asibitin ba kamar yanda yaji zuciyarsa tana wajabta masa taimakon dason jin abunda ya taro ta daga gida,da kuma uban cikin dake maƙale cikin mararta.
Yana isa cikin kaduna ana ƙiran sallan magrib sai da ya tsaya yayi sallah sannan ya nufa asibitin,ta ƙofar baya ya shiga kamar yanda ya saba yayi parking dai-dai nan ƙiran Hajiyarsa ya shigo wayarsa murmushi yayi har sai da kyawawan wushiryan dake tsakankanin haƙwaransa suka bayyana,da yake bai cika fara'a ba sai murmushin ta ƙara bayyanar da cikar haiba da kuma kwarjininsa.ya ɗaga ƙiran tare da furta sallama.
Tunda ya fita ya barni nake durƙushe jikin ƙofar ina sakin kuka,sashin ruhina tamkar ana watsa mini garwashin wuta tun ina iya fidda sautin kukan har ƙarfin hakan ya gagare ni,baccin wahala ya sure ni koda na tashi a firgice na farka ina kamo sunan Allah sunan Daada yana biyo baya,saboda gigitaccen mafarkin dana yi akanta sai dana ƙara duba inda nake na kuma bawa kukan da yake shirin zuwar mini damar fitowa,sai dana yi har na godewa Rabbul-izzati sannan na miƙe ina dafe goshina saboda sarawar da kaina ya min na fara waige-waigen ina zan gano ruwa nayi alawala nayi salla don ina iya jiyo ƙaran lasifikan ana ƙiran sallan duk bana iya bambamce cewar sallan mecece akayi,amma nasan ko zuhr ban yi ba.
Ko ina a rufe bana iya hango waje balle na nema agajin wani ko wata,jin kamar za'a buɗe ƙofar ya sani saurin komawa bayanta na ɓoye ana turowa na runtuma a guje zan fice naji an kamo ni,na fara watsil-watsil ɗin ƙwacewa aka maida ƙofar aka rufe,don kaina na miƙe daga faɗuwar da nayi ina ƙara jijjiga ƙofar.
Shi kuwa kansa tsaye ya wuce izuwa mazauninsa yana riƙe da waya a kunnensa duk da ba komai yake faɗa nake fahimta ba,saboda cikin harshen turanci yake magana amma dai na tsinta kalmar BYE daga haka ya zare wayar daga kunnensa.
Yana tusa hannunsa cikin sumar kansa baisan meyasa ya kasa sanar da Hajiyarsa batun wannan mahaukaciyar yarinyar ba,wata zuciyar ta raya masa babu ma amfanin sanar da ita kamar yanda baiga amfani cigaba da tsare yarinyar ba.a fusace na iso gaban teburin cikin kukan daya taso mini sabo dal!na shiga faɗin"Malam ka buɗe min ƙofa na tafi,baka da hurumin tsare ni anan".ganin yayi shuru ya sanya ni maimaitawa a karo na biyu,nan ma yayi banza dani na buga hannuna akan teburin ya ɗago kansa yanda naga idanunsa sunyi jajir yasa ni nasha jinin jikina cikin raina ina furta na shiga uku wataƙil ma ɗan yankan kaine ko kuma bai sha jini.
"Taimakon ki zanyi na cire miki cikin dake cikinki don na rage miki wahala".furcinsa suka sauƙa cikin ƙofofin kunnuwana,na ƙara firgita ina cewa"Bazan ƙara ɗaukarwa kaina wani laifin ba bayan wanda yake wuyana yanzu,bazan cire wannan cikin ba koda hakan yana nufin zai zamto ajalina sai na haife sa bayan haka babu abunda yasha maka kai dangane da cikin nake ɗauke dashi a jikina".idanu naga ya tsura min babu ko iftawa so yake ya gwada yarinyar shiyasa ya mata wannan tambayar amma ta tsallake tarkonsa don haka dole ya barta ta tafi,don daman tsoronsa shine kar taje a cire mata cikin duk har yanzu bai gama tantancewar na shege ne ko ko na halali.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
______________________________________
Page 1⃣8⃣
Ganin yayi shuru yana bina da ido ya sani faɗin"Malam ka buɗe min ƙofa na fita,nasan war haka hankalin Daada ya tashi saboda rashin gani na".
"Wacece Daada,uwar karuwan da suke rabo ku daga gidajen iyayenku su sanya ku a layin karuwanci?".
Take wani ƙarfi ya zo mini wanda bansan ina dashi ba a wannan lokacin na cakumo wuyar shaddar dake jikinsa,tamau na shaƙe masa wuya ina kallon ɓakar fuskarsa cikin muryata da ya fara hargitsewa nake faɗin"Ka kiyaye harshenka daga furta duk wani kalmar ɓatanci ga mahaifiyata,zan jure komai amma banda cin mutuncinta akan idona".
"Mahaifiyarki?,tunda har zaki iya tsallake ta ba ki fito da ciki ki nema shiga duniya ai bak...".ban barshi ya ƙarisa ba na ƙara ƙarfin riƙon da na yiwa kwalarsa ina hucin tamkar saniya zakai bugu.
Na sake sa na zauna gefe guda ina saka kaina cikin tsakankanin gwiwoyina ina fitar da wani hargitsatstsan kuka,da sautinsa yake bayyanar da raunin da ƙalbina yake a ciki. Meye mutumin nan yake nufi da ajiye ni anan?,ta yaya nazo kaduna?.duk raunin da nake a ciki ya zama dole na ƙarfafa kaina ko don na fuskanci rayuwata ta gaba.
Na daɗe ina kukan har sai da naji ƙarar an buɗe ƙofar an rufe sannan na ɗago kaina ina binsa da kallo,na jinjina kaina ina miƙewa na fara shige da fice a wajen ganin na sama ruwan da zan gabatar da alwala,har na fara sarewa ina saƙawa cikin raina kodai ba musulmi bane ace duk faɗin wajen ba'a tanadi wajen alwala ba,tabo sallan dana gani a fuskarsa yasa ni share wannan hashashe na zuciyata,can na hango wani ɗaki na tura a hankali ina baza ido na saƙalo ƙafata ciki.
Idona suka sauƙa akan mayukan wanka dana gyaran gashi da aka jeresu a gaban mirron dake maƙale cikin ginin banɗakin da ƙyar na iya kunna famfon don ina tsoron kar ya jani ganin kamar shima lantarki ne ina kammala alwalar na fito santsin kan talis ya nakani da ƙasa na zube a wajen,ina riƙe ƙuduna cikina ya murɗa wani balaƙeƙƙen yunwa ya taso mini har na manta ran da naci wani abu dangin abin ci kona sha tun gabannin wannan tashin hankalin a riskeni.
Murtsukuku na farayi a wajen daga bisani naja jikinsa ina ware ɗankwalina na shimfida na fara sallolin da suke kaina,ina iddarwa na shiga zubo kirari ga mahaliccina maƙagin rayuwata ina gamawa na fara jefo addu'ar nemawa kaina sauƙi ina faɗin"Ya Allah kai ce mu nema a wajenka zaka bamu,ga bawarka nan mai nema a gareka ina ƙasƙantar da kai a gabanka tare da roƙanka daka jiɓanci lamuran rayuwata,ka haska mini hanyar za zanbi ka ƙara min haƙuri,juriya da kuma dangana.ya Allah kaine kaɗai shaida ta babu wanda ya fahimce ni balle nakai ga furta musu cewar fyaɗe yamin cikin duhun dare,ya Allah kar ka ɗauki rayuwaka ba tare da nayi ido huɗu dashi ba na damƙa masa ƴarsa ko ɗansa.na tsine masa albarka na kalli cikin idonsa na masa Allah ya isa".ina isowa nan naji muryata ta ƙara rawa sosai na tsagaita tukunna na bawa kukan dama sannan na ɗaura da faɗin"Ya Rabbul-samawati ka bawa Daadata haƙurin rashina da kuma magaganun da za'a faɗa mata da kuma zargin da za'a jefe ta dashi,akan irin tarbiyar data bamu.ka sanya mata dangana a cikin ranta ka kuma bata ikon cinye wannan jarabawar".daga haka na shafa addu'ar.
Ina cigaba da sauraron yanda ƴaƴan hancin cikina suke kukan yunwa ga ciwon kan daya tsananta a gareni.
Tsaye yake bakin ƙofar ganin sallaya a hannunsa ya sani tinanin ko daga masallaci ya dawo,ɗauke kaina nayi daga gareshi don nabi shawarar da zuciyata ta ɗaura ni akai,bazan gudu ba yayi komai dani nafi su ya kashe ni ta hanya mai sauƙin-sauƙaƙawa na huta da wannan rayuwar.
Daskarewa yayi awajen ya kasa gaba ya kasa baya wannan addu'ar da yaji ta nayi,ya fara ƙoƙarin sa ruwa yana wanke hasashen zuciyarsa akan na kodai cikin shege tayi ta guje gida ko kuma auren dole aka mata ta gudo tare da cikin ta baro mijin ta shigo duniya.
"FYAƊE kenan aka mata?"ya jefawa kansa tambayar daya kasa samarwa kansa da amsarta,ina ɗago kaina naga har yanzu niɗin dai yake kallo na ƙara wani zargin akansa ina faɗin to ko kuma maye ne koko irin mutanen nan da suke tsafi da sassan jikin bil-adama.zuciyata da buga da ƙarfin wandaa hakan ya sani runtse idona.
Ya tako har gabana ya ɗan tsuguna gabana sannan kuma naga ya fiddo da waya daga aljihunsa,yayi ƙira cikin harshen turanci babu ɓata lokaci aka fara ƙwanƙwasa ƙofar ya tashi yaje ya buɗe ya karɓo take-away biyu da ruwar roba ya dire su a gabana.tun kafin ya buɗe ƙamshin abincin ya daki ƙofofin hancina ko ban gan girkin da yake ciki ba zan iya bada shaidar cewa ya amsa sunansa girki na kece raina.
Ganin ban kula ba ya ƙara turo min gabana yana cewa"ci".nayi ɗauriyar cewa"banajin yunwa".
"Ba don ke nake yi sai don,abunda yake cikin ki kici abincin nan".a dake na bashi amsa kamar yanda ya shima yake min maganar nace"Bazan ci ba idan kuma dole ne to sai mu gani".
Ya maka mini wani gigitacciyar tsawa daya haifar mini da rawar jiki yana faɗin"Oya take it kici kafin ki hassala ni".
Ba shiri na jawo abinci gabana da naga zai bani matsala wajen buɗe take-away ɗin na yaga shi kawai,na hau ci ina sauƙe ajiyan zuciya ɗaya nabin ɗaya.
Miƙewa yayi yana zura dukkan hanayensa a aljihu,tare da furzar da iska daga bakinsa,a rayuwar sa bai iya lallashi ba balle lallama ko don shima haka ya taso bai same su bane oho.daga bisani naga ya koma kan kujerarsa ya zauna yana buda wasu file can ya tashi yana buda agogon dake ɗaure tsintsiyar hannunsa,naga ya fita duk abincin da nake ci ya tsaya mini a wuyana tosawa kawai na keyi ganin ya fita na zage ina cin abincin har ina ƙwarewa na ɗaga robar ruwar ina kwanwaɗa,sai dana kusa shanyewa tas!kana na sauƙe cikina yayi wata iriyar damƙa da ƙarfi amai ya taso mini na rasa yanda zanyi na miƙe hadda ƴar guduna na shiga inda nayo alwala.
Nan fa na fara raba idanu na rasa ina ne makwarari inda zanyi aman,gashi sai taso min yake yi na ƙunshe shi a bakina ya burtso ya faɗa jikin fararen talis ɗin dake banɗakin na dunga amayo shi tamkar zan amar da duk kayan cikina.
Na galabaita matuƙar ga wani jiri da kasalan daya sauƙa min lokacin guda,na lumshe idona a hankali na miƙe na buɗe fanfo ina tara a hannuna ina wanke wajen don idona basu gane mini buta ko kuma kofi a duk cikin banɗakin ba,haka sai dana gama na fito na kwanta lamau akan ɗankwalina dana shimfiɗa na gudanar da sallah akai.bansan sanda hawaye suka fara biyo saman kuncina ba sai jin su nayi suna sauƙa har izuwa wuyata,sosai raina yake cikin buƙatuwar ganin Daada da kuma sauran ƴan-uwana tun daga yanzu nadamar gujewa gida ya fara ta'azzaran rai da ruhina amma ya zama dole na nisanta kaina dasu,yau na gani a inda bansan kowa ba haka zalika babu wanda ya sanni babu dangin uwa balle na uwa.tun da buɗe idona na ganni anan banga rana ba bana iya bambamce tsakanin dare da yini ko lokacin salla ma sai dai na ƙiyasta shi da kaina,duk da makeken agogon bangon da yake wajen amma ban iya amfani da shi ba.
Ina ɗago kaina naga mutum a tsaye akaina yana mini kallon gwarilla,nayi ƙoƙarin tashi na zauna ina jingina bayana jikin bango tare da ƙara rufe wuyana da hijabina,bai ce dani komai ba ya shiga wani ɗaki naga ya canza shiga izuwa wasu,ya cire waɗanda ya shigo dasu irin wanda ake sanyawa idan za'a shiga ɗakin tiyata,yayi waya da wayar dake kan teburinsa ba jimawa aka kawo masa shayi mai zafi yaje ƙofar ya karɓo don har ina iya ganin tiri-tirinsa ya ɗaga yana kurɓa a hankali lokaci bayan lokaci yana danna laptop ɗin dake gabansa.
Na ƙara takurewa a cikin hijabina ina jin wani zazzafi yana neman rufe ni ga sanyin kan tile's ɗin da yake ratsa ni tun daga tafin ƙafufuna,bakina har karkarwa yake yi naji an lulluɓa min wani mayafi na ɗago naga ashe rigarsa ta likitocine ya sanya min ya tsuguna akan ƙafarsa,yanda yayi zaman sai ya tina min da Sagir kullum haka zamansa na sadda kaina ƙasa wanda hakan ya bawa hawayen da suka ciko mini idaniya damar tsiyaya.
"Ɗago ki kalle ni,menene sunanki?"sautin muryarsa suka sauƙa cikin kunnuwata ba tare dana ɗago ba nace"UMMUKURSUM"ya ɗanyi shuru kafin yace"Ina iyayenki,meyasa basu neme ki ba har yanzu banji ana sanarwa a gidajen radio ko na television ba ko kuma wata kafar sadarwa ?".wasu hawayen ma'abota zafi da ƙona suka shiga rige-rigen fitowa daga idaniyata ƙasa ƙasa nake maganar don ji nayi kamar an ɗaure min maƙoshina"Bamu da ƙarfin da zasu shiga gidan radio bada cikiyata".
"Ko kuma saboda abunda kika jawa musu na kunya shiyasa baza su neme ki ba wannan daga ciki?".nayi hanzarin ɗago kaina ina kallon cikin ƙwayoyin idonsa wanda shima ɗin ni yake kallo dasu,ya ɗaga min gira alamar yana buƙatar amsar sa.idona kawai na ɗauke daga cikin nasa ya cigaba da faɗin"Meyasa ba kiyi ƙoƙarin guduwa ba duk da na baki damar yin hakan,kin saba kaɗai da maza kenan tun kafin wannan lokacin?".raina ya ƙara tunzura na ciro leɓena na ƙasa da ƙarfi duk da inason na mayar masa da zazzafar martani amma bakina yaƙi bani haɗin kai wajen aiwatar da hakan kaina kawai na jinjina ina kawar gefe.
Koda da ban juyo ba amma nasan har yanzu idonsa yana kaina,ya fara faɗin"Well bazan barki ki tafi ba daga nan har sai kin haife abinda yake cikin cikinki,don ban yarda dake ba baki da imani balle suffar tausayi zaki iya zuwa ki zubar dashi".Na watso masa idanuna da har yanzu basu gushe ba suna zubar da kwalla shima ya ware nashi idon a kaina yana cewa"Yes tunda har zaki iya tsallake iyayenki more specially mahaifiya ki nema shiga duniya,kuma ko yanzu kika haihu bazan bari ki kalla koda fuskar jaririn ba,zan ɗauke shi daga gareki domin kar ya taso cikin ƙazantacciyar rayuwarki a goranta masa akan hanyar da kika bi kika samar dashi".
Yana dasa aya nan ya miƙe da hanzari ya fice daga office ɗin inaji yana danna ma ƙofar key,na bi ƙofar da kallo ina sakin wani murmushi daya fi kuka ƙona da raɗaɗi,bani da damar dazan hana duniya jefa na da kowani irin kalamai akan wannan cikin da nake ɗauke dashi wanda zan iya ƙira da SALON ƘADDARATA.
SALON KADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
_______________________________________
page 1⃣9⃣
Gudu yake zugawa sosai akan titin kasancewar dare ne titin yayi shuru ,yana isa ya fito ya buɗe gate ɗin da kansa ya shigo da motar sai da yayi parking kafin ya fito ya nufo izuwa inda Baba mai gadi yake takalmansa sau ciki ya fara kwaɓewa sannan ya zauna akan tabarmar dake shimfiɗe a wajen ya zauna yana gaishe da Baba mai gadi tare da matarsa dake zaune a wajen.
"Lafiya ƙalau Zayyad,lafiya yau ka daɗe a wajen aiki?",sai a sannan ya kai kallonsa kan agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa wanda yake nuni da ƙarfe sha ɗaya saura na wannan daren cikin nutsuwa yace"Wallahi na tsaya yin wani aikine,wata matace zata haihu to hakan ya gagara sai da aka mata aiki aka ciro ɗan".kabara Baba mai gadi yayi sannan ya ɗaura da faɗin"Walahi wannan aikin nakun yana bani sha'awa yanda kuke ƙoƙarin,taimakon rayukan mutane Allah ya sada muku da gidan aljanna".
A zuciyarsa ya amsa Hajja ta tashi ta zubo masa damenmen fura a ƙwayar ta ajiye masa a gabansa,tana tattare kwanukan abincin da Baban Nana ya gama dasu ta shiga ciki dasu,ɗago kansa yayi daga wayarsa da yake latsawa yana turawa Hajiyarsa saƙon sai da safe yace"Baba ina su Nana fa,tunda na dawo bamu haɗu ba?".
"Sun shira dawowarka shuru har suka kwanta".kansa kawai ya jinjina yana buɗe furar ya fara sha a hankali,kallon fuskarsa sosai Baba mai gadi yake yi kamar mai nazartar wani abun kafin daga bisani yace"Alhaji ya shigo tun ɗazu,yace inka dawo komai dare ace maka yana nemanka don ko a gabana ya ƙira wayarsa baya samunta".furar daya ɗago zai kai bakinsa ya ajiye yana sauƙe ajiyan numfashi.
Baba mai gadi ya dafa kafaɗarsa yana faɗin"Zayyad komai zai wuce matuƙar akayi haƙuri,nasan irin zaman da kake yi da ƴan-uwanka da kuma mahaifiyarsu a cikin gidan nan,naji duk abunda ya faru na ƙazafin zina da tayi maka duk wani mahalukin dake cikin gidan nan zai shaide ka akan kamewa da ƙoƙarin kiyaye dokokin ubangijinka.ka kammala kaje ƙiran da yayi maka kaji yarona".kansa ya ɗaga masa yana jin ruwar ƙwallar da suka ciko masa kurmin ido,sam ya kasa shan furan duk da ƙaunar dake tsakaninsa da ita.
Turewa gefe yayi yana maida marfin ya rufe ya miƙe ƙasa ƙasa yace"Baba bari naje sai da safenmu"
Shima miƙewa yayi haɗi da faɗin"ZAYYAD"ya amsa yana rusunar da kansa cike da girmamawa sannan Baba mai gadi ya ɗaura da faɗin"Kar kayi kuskuren amsar laifin da kaba sanshi ba kuma baka aikata ba,ta hanyar yarda da cikin da Hajiya take iƙirarin Asiya na ɗauke dashi?".
"In sha Allah Baba nagode".ya faɗa yana saka takalmarsa ya nufi part ɗin Daddy,da kallo Baba Lawan yabi bayansa har ya shige part ɗin Daddy.tausayin Zayyad ɗin ya kwashe kaso mafi yawa daga cikin ransa tabbas yaron yana cikin matsananciyar damuwa da kuma tinani ga cutar maraicin da har yanzu yake azabtar da ruhinsa,babban abun babu wanda zai tsaye ya ji matsalarsa balle ya samar masa da mafita Hajiya ce kawai sanyin idaniya a garesa ita ma kuma Alhaji ya haramta masa kwana agidanta sai dai kullum yaje ya dawo.da wannan tinanin da shige ɗaƙi.
Cikin sanyi yanayin daya fara zamtowa ɗabi'a a garesa ya tura ƙofar falon haɗi da sallama,babu wanda ya amsa sallamar sai idanu da suka zuba masa kamar zasu cinye shi ɗanye,gaban Daady da yake zaune yana kallon labaran dare na BBC a kallo ɗaya zaka fahimta cewa tinaninsa baya ga kallon gabaɗaya,tsunagawa yayi a gabasa kansa yana kallon ƙasa yana murza zoben azurfan dake hannunsa na hagu yace"Daddy sannu da hutawa,saƙonka ya iso ni cewar kana nemana cikin gaggawa".
"Ina kasa wayarka na ƙira bata tafiya?"ya tambaya ba tare daya kallo shi ba,ya amsa tare da faɗin"Na barta a cikin office mun shiga operation banga ƙiran bane amin afuwa".sai a sannan Daady ya juyo yana fuskantarsa sosai yace"Menene ya shiga tsakanin ka da ƴan-uwanka?"cike da rashin fahimta ya ɗago kansa yace"Daady babu abunda ya faru".
Carab Nenne ta karɓe zancen tana ɗaurawa da nata"Dole ka musanta mu ai,yaran nan dai naga yanda kake taƙama da uban nakan suna ba shegu bane ubansu ne amma sai a ringa nuna musu bambaci gaskiya da sake,haka siddan zai kama yara da duka bazan laminta ba sai dai a bawa kowa part ɗinsa".sai a lokacin ya lura da Haidar da Adam da suke tsaye gefen kujeran da Nenne ke zaune ya komar da kansa ƙasa,duk shi ake saurara yace"Daddy nayi tinanin na isa dasu Haidar ta yanda a duk lokacin da na ga suna ƙoƙarin kwauce hanya,zan iya tsawatar musu shiyasa".shuru Daady yayi yana nazarin kalaman Zayyad babban burinsa a yanzu shine ya haɗa kan ƴaƴansa waje guda amma wankin hula yana neman kai sa dare.
"Hakane ka isa dasu da duk wani wanda yake cikin gidan nan,gobe ka shirya za muje asibiti ayi gwaji domin a tabbatar da cikin dake jikin Asiya akwai ko babu".kansa kawai ya ɗaga yana miƙewa yace"Allah ya kaimu mu kwana lafiya Daddy"da kallo Daddy ya raka shi har yakai ƙofa ya dakatar dashi ta hanyar faɗin"Ka tsaya kaci abinci"
Cak!ya tsaya jin wannan furcin na Daddy ƙara rusunar da kansa ƙasa yayi yana faɗin"Abbu naci a office kafin na taho".
"Ok take care my son a tashi lafiya"ya amsa da amin yana ficewa daga falon yana jin sautin wata doguwar tsakin da Nenne ta rako shi dashi,furcin Daddy ya ƙara dawo masa wai tambayarsa yake yi ya tsaya yaci abinci,tun zuwan sa gidan ba'a abinci dashi balle har a nema ra'ayinsa akan abunda yake son ci.hawayen da suke shirin zubo masa yayi saurin kawar dasu ya ɗauki hanyar part ɗinsa da sauri a falo ya yada zango yana lumshe idonsa a yanayin dana tsinci kansa a halin yanzu jin muryar Hajiyarsa ne kaɗai zai sanyaya masa ruhi.
Wayarsa ya zaro daga cikin aljihunsa ya fara ƙoƙarin dialing lambar Hajiyarsa,idonunsa da suka sauƙa kan agogon wayar da yake bayyanar da cewa ƙarfe ɗaya da mintuna bakwai ya tilasta mishi katse wayar yasan yanzu ta riga da tayi bacci.wani zazzafar iska ya furzar daga bakinsa lokaci guda kansa yana sarawa da matuƙar karfi.
Kamar ɗan maye haka ya miƙe ya shiga bedroom bayan yayi key a ƙofar falon,zare kayan dake jikinsa ya fara yi ya canza su izuwa wasu ɗan nauyi windows ɗin ɗakin duk yabi ya rufe saboda iskar da take karaɗawa yanayin garin ana dab!da zubar ruwan sama ga sanyin daya yiwa garin ƙawanya yana bin ƙashi da ɓargonsa yana rasa,da ruwan ɗimin daya jona a kitil yayi alwala don ji yake bazai iya mu'amala da ruwan sanyin ba a cikin wannan yanayin.shimfiɗa sallaya yayi yana fuskantar alƙibi ya tada kabbara yana gabatar da sallah dukkan nutsuwarsa yake sallan sai wajajen ƙarfe ƙarfe biyu da rabi sannan ya kwanta sam bacci yaƙi ziyartar idanunsa sai faman juyi yake yi.
Tashi yayi ya buɗe drawern dake kusa da gadon ya ciro wani hoto na mahaifiyarsa da kuma Ammiey wanda yake makake a falon Ammiey,ya kai aka kwanke masa shi yake kallo hawaye ne suka fito masa yana shafa hoton a hankali yayin da wutar soyayya da begen mahaifiyarsa ke wargaza zuciyarsa,yaso yayi rayuwa da ita yaso ya sama kulawarta a lokacin daya fi buƙatar hakan,ya taso cikin rayuwar maraici da kaɗaici har ake shifar sa da kalman ta SHEGE tun bai san ma'anar kalmar ba har ya fahimci ma'anar ta.
Da sauri da sauri numfashinsa yake fita ya dafe ƙirjinsa yana ƙara mimmiƙewa akan gadon,yana lalumar inhalernsa da baya nisa da ita,ya fara using da ita lamau ya kwanta idonsa yana kallo ceiling har baccin wahala ya ɗauke shi.ko sallan asuba a makare yayi ta yana tashi yaga missed call ɗin Hajiyarsa a cikin wayarsa,ko wacce asuba shike tashinta sallan asuba tun ƙarfe biyar zai ƙirata tayi salatul fajr amma yau ya makara.
"Subhanallahi"ya faɗa yana nufar bathroom cikin sauri ya ɗauko alwala yazo ya gabatar da sallan a makare sannan ya fara karatun alƙur'ani,ya daɗe yana yi sai da gari ya fara haske sannan ya rufe qur'anin yana jinjina kansa a jikin bed wayarsa ta hau ringing ya jawota yana ƙurawa sunan da yake yawo cikin screen ɗin wayar kallo.
Har sai ƙiran ya katse sannan yabi bayan ƙiran da sallama ta amsa ƙiran yayi shuru ta ƙara faɗin"ABEENA lafiya kuwa yau naji ka makara?".
"Hajiya ban sama bacci da wuri bane".ya faɗa ya ɗan lumshe idonsa ya katse masa hanzari da faɗin"Ina fatan dai lafiya ko ya naji muryarka haka?".ɗan shagwaɓe fuska yayi yana turo bakinsa gana kana yace"Hajiyata babu komai fa,kawai gajiya ce ta min yawa sai kuma kewar ki da na keyi".tabbas tasan dole da wani abun amma dole ta kawar da maganar sanin halinsa na zurfin ciki bazai sanar da ita ba har sai yayi niyya.
"Zan zo yau da dare kafin gobe ku wuce"ya faɗa don ganin shurun da tayi ta amsa da to tana ƙara jaddama masa akan yaci abinci kafin ya tafi office sannan suka yi sallama,yau gabaɗaya baya jin sha'awar fita ko'ina akan dole ya tashi yayi wanka yazo ya shirya cikin manyan kaya shadda ce fara sol an mata aikin surfani da golden ɗin zare,haka nan yabar kansa ba tare daya saka hula ba.inhalern sa ya ɗauka tare da wayarsa da kuma makullin ɗakinsa ya fito yana nufar part ɗin Daddy sanda ya shigo babu kowa sai ƙaran Ac da tv da suke aiki ya nema waje ya zauna yana danna wayarsa,yafi minti ashirin a wajen kafin Daddy ya fito ya durƙusa suka gaisa,Nenne yana biye dashi a baya ta riƙe masa jakarsa itama ya gaisheta fuskarta ta ɗan ƙara tsukewa sannan ta amsa.
Daddy yace taje ta ƙira Asiya ta fito su wuce asibitin Zayyad ya auna da kansa a gano gaskiyar lamarin.
"Abbu basai muje asibiti ma zamu iya aiwatar da hakan anan gida gaban kowa,in kuma ka naga zuwa asibitin zai fi samar da kwanciyar hankali da mafita sai muje ba wai na raina tinanin ka bane",ya faɗa har yanzu kana yana ƙasa.
"Ba komai Zayyad bari dai tukunna ta fito ɗin".shuru yayi bai kuma furta komai ba har Nenne ta dawo tana faɗin ta duba ɗakinsu bata ga Asiya ba kuma ta tambaya sauran ƴan aikin duk sunce basu ganta ba,nan da nan Daddy yasa aka tara duka ƴan aiki yana tambayar su ɗaya bayan ɗaya duka amsar da suke bashi ɗaya ce shine basu ga ganta ba har Baba Lawan aka tambaya yace bai ga fitar taba.
Sosai Nenne ta sauƙe ajiyan zuciya tana lumshe idonta cikin farin-cikia duk abubuwan sun tafi yanda ta tsara,fita Daddy yayi yakai rahoto ofishin ƴan sanda akan ɓatan Asiyar,shima Zayyad ficewa ya soma yi daga falon yabar Nenne da keta aikin gallo masa harara.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
______________________________________
Page 2⃣0⃣
Ina kwance a ƙasa na takure waje guda na rasa inda zansa kaina don bala'in sanyin da ake busawa,na kasa gane yanda zan kashe fankan dake aiki a wajen ina jin yanda aka sheƙa ruwa a daren ranar zazzafi mai ƙarfi ya lulluɓe ni na shiga rawar sanyi ko sallah na kasa iya tashi nayi rigarsa na jiya daya bar mini ita,ita na duƙunƙune a cikinsa sai kuma hijabina dana shimfiɗa kan tiles ɗin dake malele a wajen.
Wani kuka yazo mini a wahalce na sake sa inason ganin Daada da kuma sauran ƴan-uwana,amma dole tasa na nisanta kaina dasu nasan izuwa yanzu na jazawa Daada masifa da kuma abun kunyar dana tarba a ciki,da bala'in tsegumi da gulman mutan unguwanmu,wani lokacin har wanko ƙafa suke su zo gida suna tambayar Daada wai yaushe zata aurer da mu duk mun girma ba'a bambamce waye matar gidan a cikinmu.idanuna suka fara rufewa dana tina irin nasihar da Daada take mana akan mu tsare mutumcinmu komai rintsi.
Ni daban taɓa tsayiwa da ko wani ɗa namiji ba,ban taɓa kula kowa ba balle ya kaimu ga mun sauƙa layi.yau nice nake ɗauke da ciki tun kafin akai ga shafa mini fatiha wani kukan ya koma karyo mini dana tino ko uban cikin bansa ni ba da wani irin ido zan kalla abinda na haifa a yayin daya titsiye ni akan wanene mahaifinsa,banji shigowarsa ba balle ƙaran buɗe ƙofar sai ɗago kaina nayi na gansa a tsaye a kaina,nayi saurin ɗauke nawa idonun don ba kaɗan ba Allah ya bashi kwarjini da cika ido zai yi wuya ka iya jure kallonsa ido cikin ido.
Tausayinta ne yaso maka shi yanda yaga duk ta nannaɗe cikin rigar tasa,ga kuma Ac da fankan da suke bada iska a cikin office duk da dukkan windows ɗin a rufe suke amma sosai office ɗin ya ɗau sanyi,kai kallonsa yayi ga agogon da yake maƙale cikin wall da hatimin sunan asibitin a jikinsa yana duba lokaci wanda ya nuna ƙarfe goma saura mintu biyar.sai daya kashe Ac ɗin yabar fanka yaan Ƙara tsuke fuskarsa yace"Ki tashi nan ba wajen kwanciya bane".kalamansa suka sani nayi hanzarin ɗago idanuwa da har yanzu suke fitar da ruwar kwallar,duk tsanar sa sai ta kama ni rashin tausayinsa a fili yake bayyanar da ita,dama masu kuɗin nan duk haka suke.
Maganar daya ƙara yi ya katse mini hanzari"Malama ki tashi nace ko,ki bani rigata"na tashi zaune sannan na miƙa sama rigar ya karɓa yana riƙe ta da yatsunsa biyu kamar yana ƙyanƙyaninta yace"Wannan ai bazai saku ba,domin najasan jikinki duk kin shafa masa"yana kawowa nan ya cillata kan kujerun da aka jeresu jeras a cikin office da alama wajen hutu ne da kuma karance-karance saboda yawan littattafan dana gani suna a jere cikin tsari.
Duk da kalamansa sun soki raina amma bance da shi ko kanzil ba nayi jarumtar miƙewa akan ƙafafuna duk da jirin da yake ƙoƙarin kadani,na shiga inda jiya nayi alwala nayo sannan na fito yana tsaye inda na barsa yana waya yana kaiwa da kawowa,na wuce sa na shimfiɗa ɗankwalina na tada sallahn raka'a ɗaya kawai na yi a tsaye ɗayan kuwa a zaune nayi ta saboda jirin da yake ɗibata,ina iddarawa na ɗaga hannuna ina addu'ata cikin faɗin"Ya Allah ka bayyanar mini da haske acikin rayuwata ka kawo mini mafita ka yafe mini laifin dana aikata ka ƙarawa Daadata haƙuri da juriyar guje mata da nayi don alfarman annabinka Muhammad sallallahu alaihi wa sallama"ina ƙarishewa na shafa addu'ar ina lumshe idona,maganar da ya fara yi ya tabbatar mini da cewar ba a zuciya nayi addu'ar ba kamar yanda na zata.
"Ai baki ga komai ba,badai iyayenki zaki butulcewa ba wallahi sai Allah ya ƙasƙantar dake tun a nan duniya".yanda yake maganar kaɗai ya isa ya bayyanar da ƙololuwar ɓacin ran da yake ciki,a rayuwarsa ya tsani zina ya tsane mai kusantarta domin yasan irin raɗaɗin da ƴaƴan da aka haifa cikin zina suke fuskanta,rayuwar ƙuruciyarsa bata da mara ba da wannan domin ansha jifarsa da kalmar shege.Babu mai fahimtar zafin da wannan kalmar ta SHEGE take ɗauke dashi,sai ire-irensa waɗanda suka taso cikin maraici.
Duk yanda tausayin halin da take ciki da kuma son taimaka mata daya kwashe kaso mafi girma a cikin ƙalbinsa amma ya kasa tausasa kalamansa a garesa ƙyamar abunda ta aikata yake har ita kanta ma.
Runtse idona nayi da ƙarfi saboda kalamansa sunyi tasiri wajen tarwatsa zuciyata,wasu hawayen da suka gangaro min idona har wani zafi zafi yake mini na buɗe su tar!a kansa ina faɗin"Kar kayiwa ƘADDARAR wani dariya ko kayi ƙoƙarin karkatar da laifin kansa ba tare da bincike ba domin kaima bakasan wani irin guzuri rayuwa ta maka tanadi ba.nagode da taimakon da ka mini na kaini asibiti lokacin daka buge ni da motarka ko ba komai ka taimaka wajen ceto abunda yake ciki wanda bazan su na rasa shi domin shine hujjata a gaba,bazan juri kama alaƙanta kuskuren dana same ni ga mahaifana ba don taimakon ka ba zai zamto wajibi ba"ina kawowa nan na miƙe ina rarumar ɗankwalina danake zaune a kai na ɗauki hanyar ficewa daga wajen naji ƙofar a rufe na fara jijjigata na juyo da nufin furta masa cewar ya buɗe min naga yama juya min baya.na dawo haɗi da faɗin"Malam ka buɗe mini ƙofa na fita ko na kurma maka ihun ɓaraw....".ban ƙarisa ba sakamakon wani jirin daya ɗibe ni ya buga da ƙasa.
Zaune Daada take a ƙofar ɗaki Sagir yana mata tausa a ƙafafunta can gefe kuwa Sha'awa ce da Anty Sakina suna wanke-wanke sallamar da akayi ya sasu kai dubansu izuwa ƙofar shigowa gidan Zulaihat ta shigo da kukanta tana jan akwatin kayanta,da kallo suka ta binta har ta iso ta zauna Sagir yana tambayarta lafiya Anty Sakina da Sha'awa suma duk suka taso.
"Daada wallahi bazan iya zaman gidan ba,sun hana ni zuwa in duba ki yanzu kuma wai za'a ɗaura aurena da yaya Abdul wallahi banason sa zan iya kashe kaina aka aura min sh..."saurin kai hannu Daada tayi tana rufe mata baki ki ruf!ta jawo ta jikinta tana kwantar da kanta akan cinyarta a hankali ta soma bubbuga bayanta haɗi da faɗin"Shikenan ya isa kiyi shuru,amma maganar kashe kai banason na ƙara jinta a bakin ki kinji ko?".
Cikin shashsheƙar kuka tace"Naji Daada amma wallahi bazan koma gidan ba,gwara nayi zamana a nan".kafin Daada takai ga furta wata kalmar Sagir ya amshe zancen yana faɗin"To shikenan kiyi shuru mana ƙanwata,yanzu ke wannan santalelen saurayin ne bakya so ko dai ko dai"saurin kai masa duka tayi a kafaɗarsa tana ƙara cuno baki,ya saki dariya yana ƙara lallashinta har ta saki ranta,ita da Sha'awa suka ɗaura girki suna kammalawa ana ƙiran zuhr duk suka je suka yi Sagir ya fita masallaci suka dawo tare da yaya Aliyu,Anty Sakina ta zubo musu abincin sannan na juye musu sauran a faffaɗan tiran silba suka fara ci duk suna ankare da Daada da take juya cokalin kawai har yanzu bata kai abincin bakinta ba.
Sagir yazo gabanta ya tsuguna yana riƙo dukka hannayenta kallon tsakiyar idonta yake yi yace"Daada ba zamu iya bayyana miki yanda kike da muhimmanci a cikin rayuwar mu ba,kece komai namu a wannan duniyar bamu da wacce ta kaiki balle ta fiki.farin-cikin ki shine namu don Allah ki cire duk wata damuwa daga cikin ranki Allah ya sane damu kinji Daadata?"shafo sumar fuskarsa tayi tana sakar masa wannan murmushin nata mai taushi da sanyaya ruhi tace"Allah ya muku albarka yarona"ɗaura hannunsa yayi saman nata yace"Amin Daada,nasan kina damuwa ne akan halin da Ummukursum take a ciki,ina take taci abinci to ma waye zai bata ina zata zamu balle har taci waye zai bata,sannan kuma yanzu ga matsalar Zulaihat da kuma suturun da yaje kawo a cikin unguwa".
A karo na biyu kenan tun bayan faruwar lamarin da Daada tayi hawaye,daman burin Sagir kenan ko yaya ne tayi kukan akan ya taru mata ya tokare mata zuci,Sha'awa ta faɗo jikinta tana faɗin"Shikenan yanzu haka zamu cigaba da rayuwa a cikin gidan nan babu Anty Ummukursum,wayyo Allah Daada wallahi zuciyata tana cikin wani hali duk dare inzan kwanta sai naga kamar zan ganta a kusa dani haka nan idan na tashi meyasa Abba bai damu da rayuwar mu,meyasa Abba mai damu da damuwarmu don Allah Daada ki sanar damu anya shine mahaifinmu?".
Shuru karaɗe wajen na tsawon wasu mintunan da baza su gaza goma sha biyar ba,Daada ta ƙara matse idonta da ƙarfi wasu sabbin hawaye suna rige-rigen zubowa tayi ƙarfin halin furta"Sha'awa shine mahaifinku shi ya haife ku".
"To Daada meyasa bai damu da rayuwar mu shin daman haka ko wane uba yake ɗaukar lamuran ƴaƴansa koko tamu SALON ƘADDARAR ne haka?".
Ganin kukan da Sha'awa take yi ya fara wuce kima yanda take jawo numfashinta da ƙarfi,wanda hakan yake nuni da aljanunta suna dab da matsowa,yasa yaya Aliyu tasowa yana karanta mata ayatul-kursiyu a hankali a dai-dai kunnuwanta wani irin gargagi ta fara yi cikin muryarta da ta gama dushewa tana yago gashin kanta,haka suke matuƙar wahalar da ita a duk lokacin da suka motsa ciccire gashin kanta take yi sai dai kai ka tausaya mata.
Zulaihat da Anty Sakina suka taso suka rirriƙe tana cigaba da mata karatun,har tayi laushi sai numfashinta da yake fita da wani irin gargari daga haka baccin wahala ya ɗauke suka shigar da ita ciki,da kallo yaya Aliyu yabi bayansu har suka shiga suka kwantar da ita suka fito ya gyara zamansa saman tabarma yana fuskantar Daada da ta kasa ƙwaƙwƙwaran motsi daga wajen.
"Daada ya kamata a ƙara sanya mata kula sosai tana ƙara kusanta kanta da karatun alqur'ani,akwai wani malami wajen aikimu in sha Allah zan tuntunɓe akan laluranta".shuru tayi don dk jikinta ya gama mutuwa har inda babu gaɓa,ya ɗaura da faɗin"Sai kuma maganar kuɗin gida,naje wajen shi Buba uban ƴan cacan mun gama magana zan saya gidan yanzu na bashi rabin kuɗin.akwai wasu kuɗin da nake sa ran samunsu da zaran su iso sai na cika masa sauran maganar Sagir kuma na yanke shawaran zan bashi mashin ɗin na y fara fita yana yin acaɓa dashi don zama haka bazai yiyuwa".
Sai a sannnan Daada ta daɗo kanta haɗi da faɗin"Haba Aliyu inka bashi mashin ɗin to kai kuma fa?"ɗan murmusawa kawai yayi yace"ba komai Daada kar kiji komai,Allah zai kawo yanda za'a yi".
"Mun gode Aliyu yanda kake ƙoƙarin kulawa damu Allah ya baka masu maka,ya raya muku naku ƴaƴan su zamto sanyi idaniya a gareku da kuma al'umma gabaɗaya Allah ya ƙara buɗi da kuma ɗaukaka ya buɗa maka hanyoyin nasara a rayuwarka mun gode kaji ɗan nan".
Amin amim ita ce kalamar da take fitowa daga bakuna duk jama'ar wajen kafin Sagir shima ya gabatar da nashi jawabin na godiya,sai yamma sosai da yaya Aliyu zai koma wajen aiki Daada tace ya maida Zulaihat gidansu kuma ya musu bayanin kamar tazo ta maka don su nemo mafita.
SALON KADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________
Page 2⃣1⃣
A wahalce na fara wangale idanuna ina sauƙe numfashi ƙirjina tamkar an mini ajiyar wani abun mai nauyin gaske,na fara ƙoƙarin tashi zaune sarawan da ƙoƙuwar kaina yayi ya tilasta mini komawa na kwanta ina ƙoƙarin tina abunda ya faru amon muryarsa suka sauƙa a kunnuwana.
"Kiyi a hankali drip ne a jikinki".ban buɗe idona ba na cigaba da kwanciyata ina sauraron yanda zuciyata take harbawa da sauri-sauri.
Tinawa banyi salla ba ya sani koma tashi na zauna da ƙƴar saboda juyawar da kaina ya shiga yi,aka kwankwansa ƙofar ya miƙe yaje ya buɗe ya tare bakin ƙofar ya dawo riƙe da wasu file ya sa hannu ya koma ya miƙa ya rufe ƙofar,lumshe idona nayi ina ƙara girmama ɓakin halinsa yanda fuskarsa take baƙi har zuciyarsa
A hankali na fara zaro ƙafata ƙasa bayan na fige robar ƙarin ruwan da aka maƙala mini na diro ƙasa da ƙyar nake taka ƙafafuna da na jisu tamkar da basa cikin gaɓoɓin jikina na ɗauki hanyar banɗaki,ko ban waigo ba nasan idonunsa suna kaina na shiga banɗakin nayo alwalan sannan na fito komai na cikin wajen a hankali nake binsa gudu kar na taɓo wani abunda zai jani don na lura komai da suke wajen da lamtarki suke amfani.
Koda na fito daga banɗakin ban iske shi a wajen ba don haka kaina tsaye na wuce na shimfiɗa ɗankwalina na fuskanci alƙibla na tada kabbara,ina iddarwa na zubawa agogon bangon idanu a ƙoƙarin son fahimtar duk juyarwa da yayi na daƙiƙa ko sakan meye hakan yake nufi,inaso na fahimta kodan nasan lokutan salla tunda ko rana bana gani bana iya bambamce tsakanin dare da yini wani kuka mai tsananin sauti ya suɓɓuce mini na saka kaina tsakankanin gwiwoyina ina rero sa da dukkan muryarsa cikin muryata da ta tsaya tsakanin maƙwolantona da kan ganɗata nake faɗin"Daada ki yafe min,ki yafe min ko zanji sanyi a raina ".
Figigi na ɗago kaina jin sauƙan abu a gabana yana tsaye ya sanya dukkan hannayensa cikin aljihunsa ya juya mini baya yace"Ki ɗauki abincin nan kici a akwai magani a ciki ki sha".
Haka nan kawai naji raina yana mungun tafasa na yunƙura na tashi duk da jirin da nake ji nace"Kaga Malam banason duk wani abunda zai fito daga gareka da sunan taimako,ka buɗe mini ƙofa na fita don baka da hurumin da zaka tsare ni anan kaji ko".
Ba tare da ya waigo ya kalle ni ba yana daga tsaye idanunsa suna kan window ɗin wajen yace"Ba don ke nake yi ba,don abunda yake cikin ki nake yi don ke baki isa na tsaye ina musayan kalamai dake ba,banza karuwa wacce zata iya yaudaran kowa ciki hadda iyayenta".Raina ya ƙara tunzura na matso dab dashi sai na ganni na dawo gajeruwa a gabansa don ko cikinsa ban kai ba,na saka ƙwayoyin idona cikin nasa kana na soma faɗin"karuwa!karuwa!!karuwa!!!"sai da na maimaita kalmar sau uku a cikin bakina sannan na ɗaura da faɗin"Bazan hana ka jifa ta da ko wani irin kalama ba,domin nasan ko ba kai ba wasu zasu faɗa sannan bazan yi asaran kalamai na wajen fahimtar da mutum irinka marar tausayi da sanin darajar mace ba". Ina kawowa nan na nufi ƙofar fita ƙirjina yana lugudan tara-tara a yanda nake jin raina yana mini zafi zan iya shaƙe sa ba tare da nadamar aikata hakan ya zo mini ba.
Ina isa na fara jijjiga ƙofar da iya ƙarfina ban sani ba ko a rufe take ko ko nice ban iya buɗewa ta ba,nayi nayi har na fara sarewa na durƙushe a wajen ina bawa ƙwallar data ciko mini kurmin ido damar zubowa,a hankali na sata kallonsa yana tsaye inda na barshi har yanzu bai juyo ba haka nan bai ɗauke idonsa daga kan tagar ba,sosai nake sakin kukan don a halin yanzu shi kaɗai ne hanyar da zan iya bayyanar da girmar damuwar dake kwance kane-kane ƙasan ƙalbina.
Lumshe idanunsa yayi a hankali yana furzar da sanyayyan iska daga bakinsa,har tsakiyar kwakwkwalwan kansa kukan yake ratsa sa,inama ace shima zai sama wannan damar nayi kukan ko zaiji sausauci daga ciwon dake zuciyarsa da yake ƙoƙarin nisanta numfashinsa da gangar jikinsa,ina ma shima zai iya zama ya faɗo damuwar dake ransa,ina ma ce shima zai sama irin wannan ƙarfin gwiwan da zai bayyanawa tabbas yasan yana da rauni a wannan fanni.
Ware idanunsa yayi ya tako a hankali har izuwa bakin ƙofar,jin ƙaran takunsa ya sanya ni ƙara ƙanƙame idanuna don bana ƙaunar ganin wannan baƙar fuskar tasa maganan daya fara yi cikin rawar murya ya hatse mini hanzari ya ɗan sunkuyo ƙasa da kansa kaɗan dai-dai fuskata yana faɗin"Zan ƙara maimaita miki cewar baki da hurumi akan ɗan da yake cikinki,domin nasan ko yazo duniya zai nisanta kansa dake matuƙar yaji hanyar da kika same shi daga ranar da kika haife shi ko sanya shi a ido baza kiya ba sannan a lokacin zan barki ki tafi ko ƙarshen duniya ne idan ki naso"muryan da yake maganar da ita kaɗai ta isa ta fallasar da ɓacin ran da yake matakin ƙarshe a cikinta.
Ko kallon arziki ban masa b hasalima idona suna lumshen nace"Kayi ƙarya kuma wannan ka raba ni da ɗana baka da wannan damar".iskar day furzar daga bakinsa har sai dana ji ɗuminta akan fatar fuskana kana yace"Better kinsa wannan acikin kanta ba zaki rayu dashi ba a cikin irin rayuwar karuwancin da kika saba"yana dasa aya anan ya fice daga wajen na buɗe idona ina bin bayansa da kallo kafin wani kukan ya karyo mini.
Cikin parking space ya nufa yayin da securities da sauran ma'aikatan asibitin keta zubewa suna gaishe shi,ƙwayayen wutar lantarki sun haske ko'ina.masallaci ya nufa bayan yayo alwala aka shiga sahu ya jasu jam'in zuhr kamar kullum ƙarin karatu da kuma wasu tambayoyin da ya tsaya amsawa a mutane suka sa shi daɗewa a cikin asibitin a ar sai da yayi sallan Asr kafin ya fito mutane suna biye dashi sai gaigaisawa ya suke,wasu suna kawo ƙoƙon baransu na neman taimako wajen PA ɗinsa yake tura su suje su amshi takardar da zata basu damar shiga hall ɗin da za'a gabatar da murnar cika shekaru uku da kafa ƙungiyarsa.
Har wajen motarsa suka masa rakiya yana shiga ya mata key ya fice daga cikin asibitin cikin Zaria ya nufa a hankali yake driving ɗin yana bin sautin karatun sheik Ahmad Suleiman da yake tashi cikin motar yana karaton suratul Yasin,sai sama isowa da wuri ba yana shigowa ana ƙiran sallan magrib sai da ya tsaya yayi ya jira isha'i sannan ya nufi gidan Hajiyarsa yana gama dai-daita parking ya fito wata yunwa tana nuƙurkusan kayan cikinsa har wani dishi-dishi yake gani rabonsa da abinci tun ruwan shayin da yasha daren jiya,har yakai ga ƙofar falon wayarsa ta soma ringing ya fito da ita daga aljihunsa saurin ɗaga ƙiran yayi ganin sunan Ammiey ya bayyanaa ɓaro-ɓaro cikin screen ɗin wayar,yana dafe kansa
Shaf!ya manta da ƙiranta tun sanda ya baro bauchi basu yi waya ba yasan dole zai sha faɗa,daman kullum ƙorafin shine yafi bawa Hajiyarsa muhimmanci fiye da kowa da komai cikin sanyi yayi sallama yana ɗan shafa cikinsa daya lamushe kamar babu kayan ciki a cikinsa.shuru tayi ba tare da ta amsa sallamar ba wanda hakan ya sa shi faɗin"Ammiey na kina jina?".
"Zayyad ka kyauta,nace ka kyauta sau nawa ina ƙiran wayarsa baka ɗauka sannan kuma baza ka ƙira ba".
Rusunar da kansa yayi kamar yana gaban ta yace"Afuwan Ammiey wallahi aiyuka ne suka sha min kai,ga batun tafiyar Hajiya saudiya gobe ga kuma murnanr cikar ƙungiyar mu shekara uku da za'a gudanar sati mai zuwa".
Kawar da maganar tayi ta hanyar faɗin"ya jikin nakan ka tafi ka barmu cikin tararradi".
"Alhamdulillah jiki yayi sauƙi".
Cike da kulawa take faɗin"Zayyad don Allah in ka sama lokaci ka dunga ƙira ana jin lafiyar juna,ko Ahmad na tambaya yace kun daɗe ba kuyi waya ba"sosai jikinsa yayi sanyi ya ɗan lumshe idanunsa tabbas ko shima kansa yasan baya kyautawa don yakan shafe biye da satikai biyu ba tare daya ƙirasu,haƙiƙa yasan bashi da wasu masoyan da suka fisu bayan Hajiyarsa bai san meyasa ba a duk lamarin da ya saka da Hajiyarsa a ciki baya iya yin adalci.
"Ammiey amin Afuwa in sha Allah zan gyara nasan banida wasu masoyan da suka ɗara ku a rayuwata nagode da soyayyarku a gareni bani da abunda zan iya saka muku face na dawwama cikin yi muku addu'ar gamawa da duniya lafiya,Allah ya kara nisan kwana da lafiya mai amfani"wasu siraran hawaye suka biyo bayan furcinsa na ƙarshe ita ma Ammieyn sosai jikinta yayi ƙalau tace"Zayyad shikenan ya isa ka daina kukan kaji yaro na".ɗaga kanaa yayi yan ɗan ƙoƙarin sakin murmushi duk shi ba gwanin yinta bane yace"Inasonku Ammiey na,a gaishe min dasu Ramlat kafin na ƙirasu".yana kawowa nan ya gimtse ƙiran numfashinsa yana fizga da sauri sauri, ya dafe ƙirjinsa hawayen suna cigaba da zubo musu duk yanda yaso dakatar dasu don kadda Hajiyarsa ta zargi wani abu kasa hakan yayi.
Cikin wannan yanayin ya shiga cikin main falo masu aiki sai hidama suke yi,ya zauna a ƙasa yana kifa kansa cikin kujerar wana yayi dai-dai da sauƙowar Hajiya daga upstains da hanzari ta iso gare shi tana ɗago kansa ta ɗaura kan cinyar ta sosai tsoro ya darsu a ranta ganin yanda yake kokowa da numfashinsa da yake sarƙewa,a rikice ta furta"Abeena ina inhaler ɗinka?".nuni ya mata da aljihun rigar don halin da yale ciki bakinsa ya mutu tasa ka hannu ta ɗauko sannan ta fara bashi ita.
A hankali yake sauƙe ajiyan zuciya na tsawon zamani sannan ya ɗago kansa hawayen da Hajiya take yi ya sauƙa saman fuskarsa,hannunsa yasa ya fara share mata hawaye yana ƙoƙarin faɗin"Hajiya ki daina don Alllah ki tausaya min,domin a duk lokacin da naga hawaye akan fuskar ki sai naji tamkar na gaza baki kula kamar yanda kika bani lokacin da nake cikin zanin goyo,sai naji tamkar na kasa sakawa zuciyarki ne akan irin son da take nuna min".
Murmushi ta ƙirƙiro tana yaɓawa saman fuskarta don yanda ƙirjinsa yake harbawa har tsoro abun ya bata"Abeena menene ya kuma faruwa kuma banason ganin ka cikin irin wannan yanayin,ina tsoron na rasa a wannan duniyar".miƙewa zaune yayi tare da riƙo hannunta yace"Hajiyata babu komai kawai na fara kewar kine tun daga yanzu,amma babu abunda ya faru kinga ciwon ma na daina ji ina kwaɗayin na riga ki mutuwa kodan na sama wanda zai na tinawa dani a bayan ƙasa ".
Saurin ture sa tayi daga jikinta haɗi da faɗin"Zayyad bana son jin wannan maganar tashi muje kaci abinci sannan kasha magani"ya miƙe tana riƙe da hannunsa har dinning area yana ƙara girmama muhimmaci tare da tasirin Hajiya acikin rayuwarsa.
SALON KADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
____________________________________
Page 2⃣2⃣
Sosai ta cika masa cinsa da wainar farar shinkafar data girka da hannunta dominsa sai da ta tabbatar ya ƙoshi sannan ta ja hannunsa suka koma falo kwantar da kansa yayi saman kafaɗarta yana sauƙe wani wahalallen numfashi tare da lumshe idanunsa,so yake ya sanar da ita batun wannan yarinyar amma ya rasa meya ke dakatar dashi bai saba mata ƙarya ba har ya kai yana ɓoye masa damuwarsa duk da wani lokacin yana da matuƙar zurfin ciki tare son alkinta wasu ababaɗen a cikin ransa amma cikin ƙanƙanin lokaci take gano manufarsa.
Wani sashin zuciyarsa ta shiga raya masa ya bari kawai sai ta dawo daga aikin hajjin da zata tafi sai ya sanar da ita kafin lokacin yana sama zata haihu ya karɓi ɗan ya kawo Hajiyarsa tare da buɗe mata bayanin komai.jin ta taɓo kafaɗarsa ya sashi saurin ɗago kansa.
"Abeena na lura da yanayinka kamar akwai abunda kake ɓoye min kodai na fasa tafiyar ne inda wata matsalar?".rusunar da ƙwayar idonsa ƙasa yayi don ba zai iya jure kallon cikin idonta ya faɗa mata ƙarya ba cikin sanyin yanayinsa yace"Babu komai Hajiyata akwai gajiyace ta aiki sai kuma missing ɗinki da zanyi".shafo kana tayi ranta yana cike da maƙil da tausayin rayuwarsa tace"Ka daina damuwa Abeena shiyasa ai tun farko nace muje tare kace wai aiki ya mak yawa".
Ɗan ƙaramin bakinsa ya turo gaba tare da ɗago kansa yana kallonta kana yace"Hajiyata naje sau kusan bakwai aikin hajji haka nan ma umra ai inga izuwa yanzu na sauƙe farali,sai kuma ayi ƙoƙarin biyawa wanda basu da ƙarfin zuwa".jinjina kanta tayi maganganunsa suna ratsa duk gaɓoɓin jikinta.ganin tayi shuru ya sashi komawa ya kwanta a jikinta haɗi da faɗin"Gobe bazan sama damar zuwa na raka ki airport ba don inada operation ɗin da zanyi by 8".
"Ba komai Abeena Allah ya taimaka yasa ayi a sa'a".ciki-ciki ya amsa da amin yana ƙara gyara kwanciyarta akan cinyarta tunin bacci yayi gaba dashi.sosai take bin fuskarsa da kallo wanda kallo ɗaya zaka mata ka hangi tsantsar damuwar da yake ta'azzarar ruhin mai ita wasu siraran hawayen tausayinsa suka biyo gefen kuncinta,bata mance ranar da mahaifiyarsa ta rasu ta damƙa mata shi cikin jinin haihuwa yana tsala ihun wahala.ta bata amanarsa tun daga haihuwarsa runtse idanunta tayi da wani irin ƙarfi goshinta yana tsatstsafo da wani zuffa mai maiƙo zuciyarta tana harbawa da sauri da sauri.
Da ta tino irin zargin da mutanen ƙauyen su suka jefe ta dashi akan samuwar Zayyad duk juyin duniyar nan da duka,tsangwama da kyaran da ta fuskanta taƙi sanar dasu asalinsa da kuma yanda ta same shi don tayi alƙawari ga mahaifiyarsa akan cewar sai yayi shekaru ashirin da biyar sannan zata bayyanarwa duniya da asalinsa da kuma mahaifinsa.
A hankali ta zame jikinta daga nashi ta miƙe ta nufi bedroom ɗinta site drawern dake kusa da makeken bed ɗin dake ɗakin da yaji adon bedsheet,ta zuɗe tare da zaro wani farin mayafin da yake a tsaftace an ninke shi gami da goge shi rungume mayafin tayi tana shaƙar ƙamshin jikinsa tare da tsananta kukan da take yi.
Wannan mayafin shine mafarin ƙaddararta shine mayafin da mahaifiyar Zayyad tayi amfani dashi yayin data haife shi ta sanya shi a jiki ta miƙo mata amanar shi.
Sosai take kukam abubuwan da suka faru a baya suna dawo mata cikin kunyar kanta.
"Shatu ga wannan yaron bansan mena haifa ba amma in macece ki sa mata sunan mahaifiyar Alhaji watau Khadiya,in na miji ne ki sanya masa sunan mahaifina ZAYYAD.ki kula da tarbiyarsa tare da bashi kyakykyawan tarbiya banason kowa yasan dashi koda mahaifiyata ce ki ɓoye shi har sai yayi shekaru ashirin da biyar a duniya sanna ki damƙa shi ga Alhaji masa bayanin komai,ki sanyawa jaririn wannan zoben azurfan da zaran ya fara kawowa girma".
Furcin mahaifiyar Zayyad sa'in da take gangaran mutuwa tana yi mata wasiyya suka shiga yi mata yawo cikin tsakiyar kanta yana ƙara birkita mata tinani da lissafinta.ba taji shigowarsa ba balle tsayiwar da yayi a kanta sai jin numfashinsa tayi dab da nata tayi saurin ɗago kai tan kallonsa tare da ƙoƙarin kawar da hawayen idaniyarta,kallo kawai ya tsare ta dashi kafin daga bisani ya karɓa mayafin dake hannunta zuciyarsa ta bada sauti mai ƙarfi,baya iya jure ganin zubar hawayen Hajiyarsa.
Rungume juna suka yi suna kukan da ba mai rarrashinsu har sai da suka yi mai isharsu kafin Hajiya ta ɗago sa daga jikinta shi ya fara share mata hawayen fuskarta kafin itama ta fara kawar da waɗanda suke gudana a fuskarshi.
"Shikenan Abeena ya isa haka kaji".ta faɗa tana ɗan sakar masa murmushi.har muryarsa ta fara sarƙewa yau daya sama damar yin kuka sai yaji ɗan sanyi a ransa ko ba komai yaji sallama cikin ruhinsa"Hajiyata banasan bani da wacce ta kaiki a cikin duniyata balle ta fiki shiyasa na zaɓawa kaina na rayuwa cikin hidimta miki da ƙoƙarin samun albarki".
Shafo sumar fuskarsa tayi kana ta shiga faɗin"Zayyad wasu abubuwan har mu koma ga mahaliccinmu dafinsu da zafinsu ba zasu bar ruhinmu ya zauna cikin sallama ba,amma dole ne mu manta dashi yayin da raɗaɗinsu ya tashi ta hanyar zubda hawaye ne kaɗai muke iya rarrashin zuƙatan mu".
Shuru yayi bai amsa mata ba illa ajiyan zuciyan da yake sauƙewa ɗaya nabin ɗaya kamar wanda ya share tsawon awanni yana kukan,ta ɗaura da faɗin"Abeena banason ganinka cikin wannan damuwar,yanzu kaga dare yayi ka tashi ka koma gida tunda kace gobe kana da aiki".
"Hajiyata zanyi kewarki sosai Allah ya kaiku lafiya".ya faɗa yana ƙara marairaice fuskar kamar mai shirin yin wani kukan murmushi ta kuma sakar masa a karo na biyu haɗi da faɗin"nima zanyi kewarka Abeena muje na raka ka".slowly ya miƙa kamar ba ya son tafiyar ta riƙo hannunsa cikin nata har suka fito falon sosai fitillon ƙwayayan wutar lantarki suke gaske harabar gidan tamkar ba dare ba sai da ta kawo shi har jikin motarsa sannan ta kalloshi tace"To Abeena a sauƙa lafiya don Allah a tafi a hankali banda tuƙin ganganci"ta ƙarishe maganar tana kamo hannunsa tare da ɗan matsawa.
Yarfa hannu ya fara yana saki wani ƙara "wash!wash!! Hajiya ai sai ki tsinke mini kunne".yanda yayi maganar yana ƙara turo bakinsa gaba ya sanya ta sakin dariya haka nan shima.
Sai daya shiga motar ya fuskanto ta sosai yana faɗin"A tashi lafiya Hajiyata".
"Allahumma amin sannan ina fatan kana sane da maganar mu?".turɓuke fuska yayi kamar hadirin gabas yace"Nifa Hajiya don Allah ki janye wannan maganar wallahi bazan iya raba hankalina gida biyu ace na ajiye mata sannan kuma ga ki ba,don ina gujewa kaina tarin zunubin da zanje gaban Allah dashi na kasa sauƙe haƙƙinta dake kaina wannan dalilin yana ɗaya daga cikin abubuwan da suke sanya ni nake ƙara janye jikina daga mu'amala da ko wacce mace".idanu ta tsura masa cike da mamaki na tsawon lokaci kana tace"Zayyad aure ya zama wajibi da duk wanda yake da halin yinsa,inda kana da aure zaman gidan mahaifinka ma baza kayi shi balle har a jefe ka da zargin aikata zina".
Runtse idanunsa yayi da ƙarfi kalaman Hajiya suna masa yawo cikin ƙwakwkwalwarsa miƙewa yayi ya fito daga cikin motar tare da riƙo hannunta ya sumbata yana ɗaurawa da faɗin"Banason kina yawan magana Hajiyata kije ki kwanta gobe akwai tafiya a gabanku,sai da safenmu".
Yana dasa aya a nan ya koma cikin motar tare da jayo murfin ya rufe yana ɗaga mata hannu har ya fice daga cikin harabar gidan,da kallo ta raka shi har ya tura hancin motar ya fice ta sauƙe wata gigitacciyar ajiyan zuciya,dole zuciyarta take wajabta mata cewar ya zama dole ta nema masa abokiyar rayuwar da zata zamto duk wani haske a cikin rayuwarsa.
A nutse yake driving ɗin har ya isa cikin kaduna ya nufi unguwar sarki da fitillun sololin da yayi ƙawanya a unguwar yake haske kan titin dal!a hankali ya danna horn yana kai dubansa kan agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunwa wanda yake nuni da ƙarfe sha biyu da mintuna hamsin da biyu,ganin ba'a buɗe gate ɗin ba ya sanya shi turowa ya buɗe sannan ya shigar da motar ya dawo ya rufe,ko wani part an kashe wuta sai Nenne ne kawai da haske wanda yake bayyanar da cewar mutanen cikin basu yi bacci ba.
Wani baƙin cikine ya tukare masa ƙirjinsa kansa ya sara da ƙarfi, ya nufi part ɗinsa cikin sauri ƙafafunsa har harɗewa suke yi yana shiga ya wuce bathroom ya watso ruwa tare da ɗauro alwala sannan ya fito yana zara doguwar jallabiyarsa wacce ta sauƙar masa har ƙasa.sallaya ya shimfiɗa yana fuskantar alƙibla ya tada kabbara sai ƙarfe biyu sannan ya tsagaita ta kwanta tare da kamo sunayen mahaliccinsa ɗari ba ɗaya cikin bakinsa har bacci yayi nasarar ɗaukarsa.
Washe gari da wuri ya gama shirin fita asibiti sakancewar yana da operation ɗin da zai yi ƙarfe takwas,ya fito ya nufi part ɗin Daddy cikin garden ya tsaya yana waya da Hajiyarsa sai da su kayi sallama kafin ya kunna kai cikin falon Daddyn,zaune ya zame shi yana karanta jaridar AMINIYA labaran safe a nutse ya tako har gabansa yana ƙara ladabtar da murya ya gaida shi.
Sai daya yalwata annurin fuskarsa sannan ya amsa gaisuwar,Nenne dake zaune kan dinning tan breakfast ya kallo yana bata nata gaisuwar ko kallo bai ishe ta ba ta ɗauke kanta gefe guda,a hankali ya miƙe yana yiwa Daddy sallama ya fice daga falon yana kokawa da numfashinsa da yake cushewa waje guda.
Cikin parking lot ya nufa kansa yana kallon ƙasa kamar me neman wani abu jin warin tabar sigari ya ziyarci ƙofofin hancinsa ya tilasta masa saurin ɗago kansa yana baza idanunsa inda warin yake tashi,cak!ya tsayar da idonsa akan Haidar dake cikin garden ɗin yana busa hayaƙin tabar izuwa sararin samaniya cikin ƙwarewa yake zuƙo hayaƙin yana fesarwa.
Sosai ransa ya koma tafasa jikinsa ya ɗauki mazari ya nufi cikin garden ɗin gadan-gadan jin rurin da wayarsa take yi ya dakatar dashi ya ciro ta daga aljihunsa yana karata a kunnunsa bana iya jiyo abunda ake sanar dashi daga ɗayan bangaren,sai dai nasan ba ƙaramin abu bane zai dakatar dashi daga cimmawa Haidar da yayi niyya sauƙe wayar yayi ba tare da ya furta ko kalma ba ya shiga motarsa tare da zaburarta da mungun ƙarfi wanda hakan ya sa Baba mai gadi binsa da ido yana addu'ar Allah yasa lafiya don ba ƙaramin abu bane zai sanya Zayyad ɗin bayyanar da ɓacin ransa a sarari haka.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
________________________________________
Page 2⃣3⃣
Asibiti ya nufa yana isa ko office bai wuce ba ya nufi ɗakin tiyatan sai daya sauya kayansa izuwa na aiki sannan ya shiga awonin biyu cur!suka kwashe cikin ɗakin wanda daga ƙarshe su kayi nasarar ceto rayuwar magidancin da yake matakin ƙarshe a cutar daji,sosai yake sauƙe ajiyan zuciya tare da yin hamdala cikin ransa akan nasarar da suka yi tunin sauran likitocin suka fara miƙo masa hannu suna taya sa murna,a dole ya saki fuskarsa yana maida musu da murmushi duk da wani sashin ransa shima cike yake da farin-cikin.
Fitowa yayi ya sauya kayan jikinsa izuwa wanda ya zo dashi yana tafe tana dialing lambar Hajiyarsa,har ƙiran ya tsinke bata ɗaga ba ya mayar da wayar cikin aljihunsa yana murzar da iska daga bakinsa a hankali ya shafa cikinsa da yunwa take bin ƴaƴan hancinsa yana nuƙurƙusan su,ko office bai shiga ba ya wuce parking lot ɗinsa ya faɗa motarsa tare da figarta da gudu ya fice daga cikin asibitin cikin unguwar dosa ya nufa inda foundation ɗinsa yake daga farko ya faka motarsa saboda cincirindon jama'ar dake mamaye a wajen slowly ya jingina bayansa a jikin kujerar motar tare da lumshe idanunsa da ba komai a cikinsa face gajiya.
Cab ƙasan leɓɓansa yake furta"ya Rabbi ka bani ikon yayewa waɗannan bayin nakan damuwar su".wayarsa da ta fara ringing ta tilasta masa wangale idanunsa da suka fara masa zafi ya ƙurawa screeb ɗin wayar na jiyamun sa yana kallon Sunan Hajiyarsa dake yawo cikin screen ɗin har sai da ƙiran ya tsinke sannan ya jawo wayar ya shiga danna mata ƙira ringing biyu ta ɗauka.
Shuru yayi ba tare daya furta mata komai ba sanin halinsa da ɗabi'unsa,ya sa faɗin"Abeena ka koma gida lafiya jiya".
"Lafiya Hajiya an tashi lafiya?"ya furta yana ɗan wasa da wani box dake gabansa maganan da ta ɗaura dashi ya sa shi ƙara narkewa jikin kujerar yana fitar da numfashi ƙasa-ƙasa.
"Abeena in the next 30 min jirgin mu zai tashi ka kula da kanka Zayyad don Allah domin wannan tafiyar da zanyi gangar jikina ne kawai zai gusa,amma ruhi da tinanina suna nan a tare da kai ka kula da kanka da kuma lafiyarka da cin abinci akan lokaci".shuru ya biyo bayan furcinta na ƙarshe mintuna biyar ƙwarara a tsakani kana ya shiga furta"In sha Allah Hajiyata zan yi ƙoƙarin yin hakan sai dai nasan bazan iya kulawa da kaina yanda kike kula dani ba amma zan ƙoƙarta,Allah ya kai ku lafiya ya tsare hanya in kun sauƙa zan ƙira".
"Amin amin Abeena Allah yayi albarka"can cikin zuciyarsa ya amsa da amin yana zare wayar daga kunnensa sakamakon ƙwallan da suka ciko masa kurmin ido ya lumshe idanunsa yana sauƙe ƙatuwar ajiyan zuciya.
Jin ana bubbuga gilashin ƙofar motar ya sa shi fara buɗe idanunsa yana fuskantar PA ɗinsa dake tsaye daga waje,wayarsa kawai ya ɗauka ya fito daga cikin motar yana miƙawa PA ɗin hannu suka yi musabaha yayi gaba yana biye dashi a baya.cikin dandazon jama'ar ya ratsa bayan ya maƙala facemask a fuskarsa har ya kai ga shiga ofishinsa rauni ne ya mamaye ruhinsa ganin jama'ar dake zaune saman jiran tallafinsa yana ƙara godewa Allah da ya bashi abunda zai taimaka musu.
Suna shiga ya wuce izuwa da mazauninsa yayin da PA ɗin ya kwaso masa wasu file ya juye a gabansa yana masa bayani akan su,duk sunayen mutane ne masu neman taimako da suka cire sharuɗan ƙungiyan,wanda zasu taimakawa yayin gudanar da bikin murnar kafuwar ƙungiyar shekaru uku cur!tana bada tallafi ga al'ummar jahar kaduna tare da kewayanta ba tare da gajiyawa ba.
Sosai yake bin sunayen da kallo tare da buƙatar da suke nema daga garesu,kusan rabin sunayen duk marayu ne a yanda suka bayyana sai da yayi wa abun duban tsanaki sannan ya rufe yana miƙawa PA ɗin.
"Duk wanda sunansa yake cikin wannan list ɗin kuma kuka tabbatar da cewar sun cike dukkan sharuɗan ku basu kati,su hallara a taron jibi".ya ƙarishe yana miƙa masa file ɗin.
Cike da alamomin girmamawa yasa hannu ya karɓa yana faɗin"Sir akwai waɗanna su kazo tun safe suna jiran ka,sune ka tarar a waje nasu matsalar lalura ce ta jinya".
Kansa ya gyaɗa masa sannan ya miƙe suka fito tare ganin sa ya sa mutanen fara tattasowa saboda shigar sa ɗazu fuskarsa a rufe take,ma'aikata suka sa su layi suna zuwa ɗaya bayan ɗaya suna faɗan damuwar su,wasu da lalurar ba tayi tsamari ba magunguna ya rubuta musu wasu kuma yayi rubutu ya tura su ZAYFA HOSPITAL domin a ƙara inganta lafiyarsu.
Sai yamma sannan ya gama sallamar mutane,ma'aikatan suka taro yayi musu limanci suka gabatar da salla sai da ya ƙarawa wasu karatun wasu littattafai sannan ya koma suka fara tattaunawa akan yanda taron zai gudana manyan ɓaki suka gayyato sosai ciki hadda sarakuna da kuma malamai,katin gayyatar da suka buga ya amshi guda talatin zai kai wa Daddy sai da suka gama tsara komai hadda hall ɗin da zasu yi taron sannan suka fito dai-dai lokacin da ladani yake ƙwala ƙiran sallan magrib.
Masallaci suka nufa yayi musu limanci har sai da suka yi sallan isha'i kafin ya fara sallama da su, su ka mishi rakiya har jikin mota suna ƙara gaisawa sannan ya shiga ya ja ya bar wajen a hankali yake driving ɗin don duk jikinsa babu ƙarfi tamkar an zare masa laka.
Yana isa gida ko tsayawa danna horn bai yi ba ya ga Baban Nana(Baba mai gadi),ya taso ya fara ƙoƙarin buɗe masa gate ɗin.saurin fitowa yayi ya iso ya kama gate ɗin suka buɗe tare sannan ya shigo da motar cikin sai da yayi parking ya fito ya dawo inda ya bar Baban Nana yana tsaye murmushin dole ya ƙirƙiro yana lulluɓe damuwar dake shimfiɗe kan fuskarsa kafin yace"Ayya Baba na hana ka bacci ko,wallahi mun tsaya tattaunawa ne akan taron da zamu yi?".
"Ba komai yarona ai aikina ne hakan dole,nayi shi da ƙarfina kodan naci halal ɗina.wannan aikin da kuke yi babu wanda zai biya ku sai dai muyi fatan Allah ya biya ku da gidan aljanna ya jiƙan mahaifa".
Sanda kansa ƙasa yayi yana ɗan murza zoben azurfa dake hannunsa yace"Amin Baba bari na shiga daga ciki mu yi sallama da Daddy".
"To a fito lafiya"Baban Nana ya raka shi dashi,sai da ya buɗe bayan motarsa ya ɗauko katin gayyatar sannan ya nufi part ɗin Daddy tun kafin ya iso yake jiyo kururuwar Nenne cikin bala'i da masifarta"Allahumma ajirni fi musibati"ya furta can ƙasan kanɗansar yana murɗa handle ɗin ƙofar ya shigo da sallama ɗauke a bakinsa Daddy ne yayi saurin waigowa tare da amsa masa sallamar.
Cikin nutsuwa ya ƙariso cikin falon ya tsuguna akan ƙafafunsa kansa yana kallon ƙasa yace"sannu da hutawa Daddy lafiya kuwa?".
"Lafiya ƙalau Zayyad,ai duk wanda ya ɗai bo da zafi bakin sa wai yanzu ake sanar dani cewar an kama Adam sun haɗa kai da wasu abonkansa su saci mota.don haka banza je ba in sunga dama su yi ƙuli-ƙulin kubra dashi ba zai yiyu da girma na ana ganina ina zuwa station ba yayi zamansa a can har izuwa lokacin da zasu tura su kotu"Daddy ya faɗa cikin ƙololuwar ɓacin rai da tafasar zuci caraf Nenne ta amshe zannce tana ɗaura wa da faɗin"ai dole ka faɗi haka tunda da Zayyad ne aka ce maka yana station da ka daɗe da tafiya can,da yake su ba'a ƙaunar su a cikin gidan dole kayi kunnar uwar shegu da maganar".
Sosai kalamanta suka ƙara tunzura Daddy ya nufo ta yana pointing ɗin ta da ƴatsar shi"kar bakin ki ya ƙara kuskuren dangata Zayyad da ƴaƴanki"
"Mtswee zamu gani ai idan tusa yana huta wuta shima ɗin dai idan da za'ayi bincike akansa to sai an haƙa rami an ɓoye wuƙar tsabar muninta kawai don nasu ya fito fili shikenan sai a ɗauki karan tsana a ɗaura musu,kuma wallahi ko zan tafi tsirara zai na tabbatar maka cewar rayuwar su Adam ɗin dai da baka ƙauna shima Zayyad ɗin sai ya faɗa".
Da sauri Daddy ya yunƙuro zai kai mata duka ta hauce tayi bedroom,dafe ƙirjinsa yayi sanadin tarin da ya sarƙe shi cikin lokaci guda Zayyad yayi saurin miƙewa yana tallafo shi jikinsa ganin ƙafafunsa da ke ƙoƙarin kasa ɗaukar nauyin gangar jikinsa.zaunar dashi yayi akan kujera yana aikin jera masa sannu tare da ɓalle masa maɓallin rigarsa ta yanda zai samu sakekken iska.
Goran ruwar dake ajiyen kan teburi ya ɗauka ya kafa masa a baki kaɗan ya sha ya ture gefe tana sauƙe ajiyan zuciya cikin muryarsa da bata gama daidaituwa ba ya shiga faɗin"Zayyad kayi haƙuri,in sha Allah wataran sai labari bata isa ta maka abinda Allah bai rubuta shi cikin littafinka ba"ya ƙarishe maganar yana dafo kafaɗarsa.
Duk yanda ransa yake masa zaf sai yaji ɗan sanyi ya tsiga shi saboda yanda Daddy yake masa maganar cikin kwantar da karshe, da tausasawa kansa kawai ya gyaɗa masa yace"Ba komai Daddy daman katin gayyatar da muka bugo ne na kawo maka ko akwai wanda zaka gayyata daga bangarenka".
Katin ya tattaro ya miƙawa Daddy ya karɓa yana maƙala gilashin ƙara ƙarfin ganin da yake using da shi sosai ya sanya masa albarka gami da tabbatar masa da cewar shima zai halalta taron,sai da safe Zayyad ya masa sannan ya fito yana dafe ƙirjinsa da yaji tamkar an mishi ajiyar wani abu mai nauyin gaske da ƙyar yake iya jan sanƙararrun ƙafafunsa da yale jinsu kamar basa jikin gangar jikinsa izuwa part ɗinsa.
Yana shiga ya maida ƙofar falon ya rufe yana jingina bayansa a jikinta,a hankali ya fara sulalewa izuwa ƙasa yana dafe da ƙirjinsa da yayi masa bala'in nauyi tamkar faɗuwar aradu haka furcin da Nenne tayi iƙirari a kansa ya fara dawo masa cikin kunyar kansa.lokaci bayan lokaci yake sauƙe ajiyan numfashi da yake jawo da kyar cikin sa'i ɗaya numfashinsa ya fara ƙoƙarin sarƙewa inhaler ɗinsa ya ciro daga cikin aljihunsa ya fara using dashi.
Tsawon lokaci ya shafe zaune a wajen kafin ya iya miƙewa akan ƙafafunsa da suke rawa,yayi bedroom kwaɓe kayan jikinsa yayi ya faɗa bathroom ya sakewa kansa ruwa duk da sanyin ruwan da yake ratsa dukkan gaɓoɓin jikinsa haka ya gama wanka ya fito,ina jin kayan cikinsa da suka kukan yunwa doguwar rigar jallabiya ya saka ya wuce izuwa fridge ya fito da robar fura ganin yayi ƙanƙara ya sashi barin ta sake sannan ya fara shanta.
Kaɗan yasha yaji cikinsa yana ƙullewa ya ture robar gefe yana kwantawa akan bed,wayar da ya ajiye sanda zai shiga wanka ya jawa missed call ɗin Hajiyarsa shi ya fara cinkaro dashi,duk da a cikin halin da yake ciki yanzu muryarta ne kaɗai zai samar masa da nutsuwa amma bazai iya ƙiran ta ba gudu kar ya tada mata da hankali.dafe saman goshinsa yayi da ƙarfi yana ciro lower lips ɗinsa yana jin yanda zafi da dafin maraici yana bin ko wacce sassan jikinsa.
SALON KADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________
An hanzarta yin payment an sanbaɗa ku a payment group daga page 30 zaku ji ni ɗin. Daga lokacin labarin zai fara, a nuna mini ƙauna a sama mutum ɗaya da zai saye littafin nan
Page 2⃣4⃣
A hankali numfashin da ya saura a gangar jikina yake fita na duƙunƙune cikin hijabina saboda sanyin da yake ratsa ni ga kuma zazzaɓin da ya lulluɓe,jikina haka karkarwa yake yi kamar ana jona mini wutar lantarki.ƙoƙarin miƙewa nayi domin naje banɗakin na kwankwaɗo ruwa domin jiƙa maƙoshina da ya daɗe da bushewa jiri ya layyayani ya maka da ƙasa nayi zaman ƴan bori.
Wani kukan wahala da baya fitar da sauti ya zo min na bashi damar fitowa ba zan iya ƙayade rabon da nasa abinci a cikin cikina ba,don tun ranar dana suma ya karta mini baƙar magana tare da jifa ta da kalmar KARUWA,har yanzu ban sake sanya cikin ƙwayar idona ba.
Sautin kukan nawa ya daɗa ƙaruwa duk wajen ya ɗauka ina ƙara bin wajen da kallo daki-daki,tun da ya shigo dani wajen ban ga koda wulgawar wani mahaluki ba sai shi kaɗai,bana jiyo hayaniya balle takun mutane har na iya kururuwar neman taimako ko agaji.
"Wayyo Allah na ka kawo mini ɗauki ka fitar dani daga wannan ƙangin rayuwar,meyasa SALON ƘADDARATA ya bambamta da na sauran mutane,meyasa alƙalamin KADDARATA yake mini zane akan dutsi wanda ba zai taɓa goguwa ko shafewa a cikin tarihin ƙazantacciyar rayuwata ba?.mezan faɗa wa ɗan da nake ɗauke da cikin a cikin mahaifata idan ya diro duniya ya buƙaci ya san wanenen mahaifinsa?,da wani irin ido al'umma zasu kalle mu ni dashi?".
Shuru nayi ba tare da na kai ga furta sauran furcin ba da suka maƙale a maƙoshina,sakamakon wani sabon kukan daya karyo mini na sake shi da ƙarfi ina rerasa wiwiwiw.
Cikin dursashewar muryar da take fallasar da raunin da ƙalbina yake a ciki na ɗaura da faɗin"Ya Allah ka nuna mini fuskarsa kafin ranar mutuwata ta iske ni,ka nuna mini fuskarsa ko dan na yi masa Allah ya isa kuma na roƙa masa bala'i da masifa a rayuwarsa kamar yanda ya jefa tawa rayuwar izuwa garari".
Sosai jikina yake rawa saboda tsantsar yunwar da take cin ƴaƴan hancin cikina har wani ƙu ƙu suke yi na damƙe cikin da ƙarfina,ina kuka tabbas yunwa ya kusa yin ajalina tunin ji da gani na suka ɗauke na wucen gadi na ƙara yunƙurin tashi zanyi salla sai rarrafe nayi na shiga banɗakin nayi alwala nazo nayi sallan a zaune na kwanta akan sallayan ina jiran sa'i na ya cika.
Tsakanin jiya da yau sosai abubuwa suka masa yawa ko office baya samun shiga, gida ko baya ma sha'awan dawowa don da zaran ya doshi gidan ɓacin rai ne yake maye duk wani gurbin farin-cikinsa,furcin Nenne yaha na ruhinsa sukuni har sai da PA ɗinsa ya fara gano yana cikin damuwa haka nan ma Baban Nana duk da gano yanayin farin-ciki da damuwarsa abu ne mai wuya sakancewar bai cika sakin fuska da fara'a ba,ko Hajiya ya kasa sanar da ita zance ya barwa ransa muradinsa shine da zaran an gama bikin taron yai fuskanci Daddy da buƙatar son komawa sabon ginin gidansa ya da gama dake cikin unguwar rigasa.
Duk da yasan abu ne mai wuya amincewar Daddyn amma zai gwada hakan,zaune yake gaban Baban Nana suna zagaye gidan hannunsa duk ya naɗe hannayensa a ƙasa haka nan ma idanunsa suna kallon ƙasan.
"Ni kuwa Zayyad ya maganar Adam,ya kamata Alhaji yaje a shiga maganar ai hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar".
Ɗago kansa yayi kana yace"Baba bana tinanin Daddy zai je domin kuwa ya ɗau zafi,zanyi wani abu akan maganar in sha Allah".saurin faɗin"A'a"Baban Nana yayi yana ɗaurawa da cewar"A'a Zayyad kasan ta maka iyaka akan shiga lamuran ƴaƴanta,har kasa kanta a wannan al'amari daga ƙarshe azo ran kowa yana ɓaci tunda Alhaji ya janye hannunsa mu ma sai mu zama ƴan kallo.ai inda ake yi da kai nan ake cusa kai".
Taƙaitaccen murmushi Zayyad ya saka kana yace"Baba bata da ikon da zata min iyaka ko taba ni da ƴan-uwana,ni ne babba a tsakanin su dole na yi ruwa da tsarki akan matsalar su,saboda su ɗin jina na ne ko a ina".
Dafa kafaɗarsa Baban Nana yayi haɗi da cewar"Haka ne yarona Allah yayi albarka ya kuma bada sa'a".
Cikin ransa ya amsa da amin dai-dai nan suka kawo bakin part ɗin Baban Nana,su Iman dake cin abinci suka rugo da guda suka faɗa jikinsa hannu ya ware duk ya runguma so yana haɗa su da ƙirjinsa.Allah ya sani yana son yara a rayuwar sosai,shi yasa ya lashin takobin tsayiwa domin inganta rayuwarsu.
"Kai Nana bakwa ganin zaku ɓata masa jiki ne?"murmushi kawai ya saka ya ɗan duba gaban farar t-shirt ɗin dake jikinsa da duk ya ɓaci da miya,ya miƙa yana riƙo hannunsa har izuwa kan tabarman da suke cin abincin.zama yayi ya kallo mahaifiyarsu Hajja dake tsaye yace"A ƙaro mana mu ci tare dasu yau anan zan ci abinci".
Sosai ta ƙawata fuskarta da annuri don rashin nuna ƙyaman da bai yi ga abincin da ta girka ba balle kuma ƴaƴanta,duk da tasan cewa shi ɗin na daban ne a cikin gidan,kwanon ta ɗauka taje ta ƙaro musu wani sannan ta ajiye mususai da duk ya sa su,su kayi addu'ar cin abincin sannan suka fara cin abincin.
Baban Nana dake tsaye yana kallonsa har ƙwalla yayi don tausayin Zayyad ɗin da ya maƙale masa a ƙasan rai,ina ma mahaifiyarsa zata dawo duniya domin taga irin alkhairin da haiho ga al'umma.saurin kawar da hawayen yayi da hannun rigarsa ganin Zayyad ɗin ya miƙe ya wanke hannunsa su Iman suna biye dashi suna faɗin zasu bishi mota ya basu sweet.
"Baba bari na shiga don gobe taron da zamu yi kar na makara"ya faɗa yana ƙara ƙarfin riƙon da yayi wa hannun Nana cikin nasa.
"To Zayyad Allah ya tashe mu lafiya".sai da yayi wa Hajja sallama sannan yaje mota ya bawa Nana da Iman sweet ɗin suka masa sai da safe sannan suka koma.ko part ɗin Daddy bai shiga ba ya wuce nasa part ɗin a falo ya yada zango yana dialing lambar Ammiey sosai ya sake sula yi hira wanda hakan ya haifar mata da jin sanyi a cikin sashin ruhinta,har su Ramlat yace a bawa su gaisa kafin suka yi sallama.
Ya ƙira Hajiyarsa tana ɗagawa yayi shuru kamar yanda ya saba tace"Abeena jikina yana bani wani abu yana faru menene shi?".tun kafin ya kai ga bata amsa ta yi saurin faɗin"ko dai jikin kane ya tashi?".
Tausayinta ne ya so ƙaryar masa da ruhin ganin yanda ta rikice lokaci guda tana jefo masa tambayoyi ɗaya na bin ɗaya,sai da ya lanƙwashe ƙafarsa wuri guda har sai da tayi wata ƴar ƙara kafin yace"Hajiyata lafiya ƙalau kawai kewar ki ne da yake addaba ta".yana jin yanda ta sauƙe wata shirgegiyar ajiyan zuciya kafin ta kai ga faɗin"Zayyad nima nan ina kewar ka,amma lafiya jiya nayi ta ƙiran wayarka baka ɗagawa?".
"Lafiya ƙalau Hajiya lokaci muna meeting ne nasa wayar a silent,sai da na iso gida na gani kuma dare yayi shiyasa ban bi bayan ƙiran ba".
Sai da ta ɗan yi shuru na tsawon daƙiƙun da baza su gaza uku kana ta ɗaura da faɗin"to ka ya gidan nakun ina fatan ba wata matsala kuma kana kula da kanka?".
Sai da ɗan murmushi ganin yanda take jefo masa tambayoyi tamkar wani ƙaramin yaro yace"Lafiya ƙalau Hajiya babu komai,kuma ina kula da kaina an sauƙa lafiya".haka nan suka cigaba da hirar su da take bayyanar da tsantsar ƙaunar da suke gwadawa junan su sai ƙarfe goma sha ɗaya saura sannan suka yi sallama ya gabatar da sallan nafilansa kafin ya kwanta.
Tun ƙiran asubahi bai koma ba sosai sanyi ya lulluɓe garin yanayin yana nuni da ruwan sama kan iya kecewa a ko wani hali,sai da ya tafasa ruwa a heater sannan yayi kwanta tea kawai ya haɗa mai kauri ya ɗumama hanjinsa dashi sannan ya fitto da kayan da zai sa.shadda ce fara da aka yiwa aikin surfani da ash ɗin zare a wuyar rigar da kuma hannayen ta,ta cikin ya fara ɗauka ya saka ta da wandonta kana ya koma gaban dressing mirror.
Sama-sama ya murza mai a fatarsa sannan ya gyara sumar kai da kuma wanda yayi ƙawanya ga tsukekkiyar fuskarsa sai daya feshe jikinsa,da turaren laylatul sahara sannan ya ɗauki babbar rigar ya saka tare da ɗaura hula a kansa sai rantsi-rantsin Ash a cikin ta agogo ya ɗaura a tsintsiyar hannunsa.sannan ya ɗauki wayarsa da kuma key ya fito.
Yana fitowa ya wuce part ɗin Daddy ya shiga da sallama kamar yanda ya saba babu kowa a falon sai ƙamshin turare da kuma sanyin Ac da ya sanyaya falon,a hankali ya kalli agogon hannunsa da yake nuni da ƙarfe takwas da mintuna ashirin,ɗaukar hanyar fita yayi don yasan Daddy baya tashi a irin wannan lokacin caraf!idanunsa suka sauƙa akan katin gayyatar da ya kawowa Daddy a daren jiya.
Ƙura musu idanu yayi ko gusar dasu ba ayi ba daga inda ya ajesu balle yasa ran cewar an rabasu da mutane,ɗan murza zoben hannunsa yayi yana ficewa daga falon saurin ja da baya yayi ganin Nenne ta turo ƙofa falon zata shiga ya bata hanya rusunar da kansa yayi yana gaishe ta"Nenne an tashi lafiya".
Wani mummunan kallo ta watsa masa da duk da bai ɗago ya saka idanu cikin nata ba,sai da tsikar jikinsa suka tashi ba ta kula shi ta ƙeta tare da gefensa tayi wucewar ta shima ficewa ya soma yayi maganganun da ta fara ya sanya shi kasa ɗauke hannunsa daga kan handle ɗin ƙofar da yake shirin turawa ya fita.
"Inaso ka sanar da ita wacce take ɗaura ka akan wannan gwadaben da yake baka damar yin ruwa da tsaki a cikin al'amuran rayuwar ƴaƴana,asirin da bokanta yayi na kusa na karya shi da kuma shi Alhajin da yake ɗauke maka gindi duk a tafin hannuna kuke,dukiyar da kuke hari kai da ita sai dai ku mutu akanta domin zan iya yin komai akan hakan koda kuma hakan yana nufin zan rasa numfashina ku yi kaɗan kai da ita ku zo kuyi kane-kane akan dukiyar Alhaji waya sani ma ko ba jinin sa ba anbi boka da Malam an rufe masa baki "
SALON KADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
____________________________________
Page 2⃣5⃣
Cak! ya tsaya ya najin ɗumin wasu hawaye masu zafi suna shawagi tsakanin kuncinsa da saman haɓarsa,numfashinsa ya fara kokawa dashi da yake carkewa sosai kalaman ɓatancin da ta danganta Hajiyarsa dashi suka daki ransa gami da tarwatsa raunanniyar zuciyarsa jan jikinsa yayi a hankali ya fice daga falon yana jin tsakin da ta raka shi da shi yana masa kururuwa cikin kunnuwansa.
Yana fitowa ya wuce cikin parking lot cikin motar ya jingina kansa don da ƙyar ya iya kawo kansa wajen,saurin da zuciyarsa take yi wajen harbawa shima kansa yasan ya wuce kima wasu hawayen da bai shirya musu ba suka ƙara kwaranyo masa ya kawar dasu da hannunsa tare da ciro hankerchief a cikin aljihun rigarsa yayi wiping fuskarsa.hango Baban Nana yana ban ruwa ga shukoki tare da sauran ma'aikatan gidan ya dakatar dashi daga shiga motar wajen su ya nufo tare da sallama sannan duk ya gaishe su.
Cikin sakin fuska duk suka amsa masa kafin Baban Nana ya shiga faɗin"Masha Allah yau sai ka kuma fitowa a cikakken mutum ɗinka,ai irin wannan shigar ya fi na al'ada amma wancan kayan turawan a ɗaure ƙungu wuya ma a ɗaure shi ina".sauran ma'aikatan duk suka bushe da dariyar maganar Baban Nana,drivern Daddy Malam Habu yace"To ai Baba wannan shigar yanzu sune ake yayi na zamani mussamman ga su Zayyad matasa".
Duk maganar da suke yi bai ce dasu uffan ba illa tsayar da idonsa da yayi akan Haidar da yake shigo cikin gidan,yana tafe yana haɗa hanya alamun a buge yake.wani sabon baƙin-cikin daya share wanda yake ciki a fagen girma da raɗaɗi ya ƙara mamaye zuciyarsa.
Ta gefen su yazo ya wuce ko kallon su bai yi ba balle yasan cewa da bil-adama a wajen,ya wuce part ɗin Nenne a hankali Zayyad ya runtse idanunsa yana kamo sunan mahaliccinsa rayuwarsa kuma wanda ya tsara masa SALON KADDARARsa ta zamto mafi munin ƙaddarar da ya taɓa ji.rabon da yasa Haidar a cikin idonsa tun ranar da Nenne tace a raba musu part kowa a bashi nasa sai kuma yau tabbas yasan cewa ba gida ya kwana ba zuciyarsa ta buga da wani irin gigitaccen sauti kar dai wata ƴar ya kuma yiwa fyaɗe kuma furcin da yaji rannan suna maidawa junan su shi da Adam akan cewar yayi wa wata yarinya fyaɗe a bauchi ya wargaza lissafin ƙwaƙwalwansa.
Jin Baban Nana na taɓa kafaɗarsa ya sa shi dawo daga tinanin da ya rukfa"Zayyad lafiya ana ƙiran wayarka amma baka ɗauka ba?"saurin fito da wayar da take ta ruri yayi daga aljihunsa ganin PA ɗinsa ne yake ƙira ya sa shi katse kiran yana maida ta aljihunsa tare da faɗin"Baba bari naje jiya na sanar da kai yau zamu yi taron ƙungiya suna jira na".
Sai da ya faɗaɗa fara'ar dake ɗauke saman fuskarsa da tsufa ya fara bayyana akan ta kana yace"To yarona Allah ya baku sa'a ya sada ku da ɗimbin nasarori".
Sai da ya sunkuyar da kansa sannan ya amsa da amin kafin sauran ma'aikatan ma suka ɗaura da mishi nasu salon addu'o'in,wajen motarsa ya koma ya shiga sannan yaja ta ya fice daga cikin gidan sosai yake sharara gudu akan kwaltar da zata sada shi ga GOFF 10 HOTEL inda za'a gudanar da taron babban fili suka kama a wajen ta yanda zai ɗauki ɗimbim jama'ar da suka halallata,parking motarsa yayi cikin compound ɗin hotel ɗin yana maƙala face mask a fuskarsa sannan ya fito.
Ya hango PA ɗinsa Umar yana nufo sa musabaha suka yi sannan duk suk ɗauki hanyar isa wajen ,sosai wajen ya cika da jama'a komai anyi shi a cikin tsari wanda kallo ɗaya zaka yi ka tabbatarwa kanka cewar tafiyar ta masu ilmi ne wajen masu neman taimako daban,wajen manyan ɓaki sarakuna da masu madafan iko ma daban sai kuma wajen zamansa tare da sauran ma'aikata da kuma iyayn taron.
Sai da yabi ya gaigaisa da duk ɓakin da suka hallara sannan ya zauna a nashi gurbin,ƙarfe goma dai-dai aka fara gudanar da taron buɗewa da addu'a tare da gabatar da nasiha da fayyace muhimmancin taimako a addinin musulumci da kuma irin tagwanjin shi da Allah yayi wa masu irin wannan aikin,malaman da aka gayyato su kayi sai kuma tarihin ƙungiya da aka saurara daga bakin PA umar da irin nasarorin da ta cimma cikin shekaru uku daga nan uban taro DR ZAYYAD EL-FAROUK BAITA ya miƙe domin bata taimako ga mabuƙatan da suka taro a wajen tafi ya ɗauka ta ko'ina.
PA yana karaton masa sunayen yana bada taimakom har ya ƙare,wakilin sarkin bichi ya miƙe yayi nashi jawabin tare da bada naira miliyan uku ga ƙungiyar Kabbara ce aka saka da ƙarfi a wajen tare da addu'ar Allah sanya alkhairi,shigowar Daddy da ya gani tare da masu take masa baya ya sanya Zayyad saurin miƙewa ya iso gare su don har ya cire rai da zuwan sa ganin har taron yana neman tashi bai zo na,yana zuwa ya wuce kan munbarin jawabinsa na farko saƙom taya Zayyad ɗin da sauran ma'aikatansa murna cikar ƙungiyan shekaru uku yayi sannan ya ɗaura da addu'ar nema musu tsari da Allah ya ƙara karkato da hankulan masu kuɗin mu da suyi koyi dashi.
A ƙarshe ya bada naira miliyan biyar ga ƙungiyar matsayin nashi gudumawar sa tunin ƴan jaridu da masu camera suka masa rufgudu tare da mamaye shi da tambayoyin yaya yake ji a duk lokacin da yaji an yabi Zayyad akan wannan aikin da yake gudanarwa.amsar da ya basu ya sa kwalla cikowa Zayyad kurmin idanu ɓai taɓa sanin yana da wannan muhimmamcin a zuciyar Daddy ba.
"Tabbas samun ɗan kamar Zayyad abune da ko wasu iyaye za suyi alfahari da haka,ina alfahari da shi kuma ina ƙara ƙarfafa mishi gwiwa akan ya cigaba da hakan ni kuma na shirya bada daga naira ɗaya har naira miliyan ɗari domin taimakon jama'a".
Ba shiri Zayyad yaji zuciyarsa tan ingiza shi ya isa ga Daddy ya rungume tsam!a jikinsa yana hawaye tunin wajen ya ƙara rikicewa da sowa wasu saurin kuka iri na tunin suka fara,ɗago shi Daddy yayi yana sakar masa murmushi"Keep up the good thing my son,in sha Allah zan tsaya maka".
Kansa kawai ya ɗaga masa sannan ya raka Daddy har cikin mota ya tafi,tsayawa yayi yana amsa tambayoyin da ƴan jaridu suke masa kafin ya dawo ya fara sallama da ɓakin da suke shirin tafiya sai ƙiran sallan Asr sannan taron ya watse masu kemarori suka shiga nasu aikin sai hasko shi akeyi a hoto.
Cilli Nenne tayi da remote ɗin dake hannunta tana kurma wani irin ihu da ya sanya ma'aikatan gidan hallara a gabanta cikin rawar jiki,ido ta kuma ƙurawa Tvn tana fitar da hucin tafasan da ranta yake yi ganin ana haska yanda taron murnar cikar ƙungiyar ZAYDA FOUNDATION da #STAND FOR NEEDERS ya kasance,wai Alhajin da da safen nan suka sha arbatu dashi akan tana buƙatar miliyan biyu domin case ɗin Adam yace bashi da su bashi da dalilinsu shine ya ɗauki miliyan biyar ya bawa ƙungiyar Zayyad tallafi.
Kama ƙugi tayi da hannu ɗaya,ɗayan kuma tana dafe goshinta da yake tsatstsafo da maiƙon zuffa ta fara safa da marwa a cikin falo,tsawa ta dakawa masu aikin da sai yanzu ta lura da tsayiwar su a wajen "Ku kuma meye kuke yi anan,dalla ku ɓace mini a gani tun kafin mummunan hukuncin da raina yake saƙa min na aiwatar dashi akan ku".
Cikin rawar jiki har suna karo da junan su suka fara nufar ƙofar da ta shigo dasu falo,wayarta ta ɗauka tan dialing wani lamba sai da ƙiran ya kusa tsinkewa sannan a ka ɗaga bana iya jiyo abunda ke furtawa daga ɗayan bangaren sai ji nayi tana faɗin"Hajiya Jummai akwai matsala ba aikin nan bai ji ya,abubuwa sai faru suke yi".
"To shikenan ina jiranki sai kinzo"ta kuma faɗa ina gimtse wayar tare da cillata kan kujera tana ƙwalawa sabowar ƴar aikin da tasa a kawo mata bayan tafiyar Asiya,Mariya ƙira cikin sauri ta bayyana a gabanta tare da durƙushewa.
Kallo sosai Nenne take binta dashi kafin tace "tashi ki shiga ɗaki ki jira ni".tunin Mariya ta soma ruwar hawaye haɗi da faɗin"Don Allah Hajiya kiyi haƙuri nasan kisan Allah ya haramta wannan abunda kike ƙoƙarin sani na aikata tare dake ya kuma tanadi azab...."bata ƙarisa ba sakamakon kyawawan marukan da Nenne ta ɗauke tashi hagu da dama tana zaro idanunsa da suka yi jajir gami da ƙanƙance tsabar jaraba tace"ni zaki gayawa maganar banza wuce nace tun kafin na lahanta ki".wucewa ɗakin Mariya tayi Nenne na biye da ita a baya sai da ta rufe ƙofar falo sannan ta rufe na ɗakin ma ta shiga aikata badaƙalar ta wanda in tana yi bata ji bata gani.
A gajiye yake driving ɗin motar tsabar gajiya da yunwar da yake ji idanunsa har wani zafi-zafi suke masa,yau kam zai iya bugin ƙirji gami da alfahari kamar yanda ko wani ɗa yake a karom farko a rayuwarsa yau yaga tsantsan soyayyarsa a cikin idanun Daddy,kuma yau ya sama kulawar iyaye kamar yanda duk ɗa yake samu.Farin cikinsa ba zai misaltu ba saboda adadin mutane da ya ga farin-ciki akan fuskar su yau a ta sanadiyarsa addu'o'in neman gafara da suka dunga zubowa Mahiafiyarsa ya sanya shi lumshe gajiyayyun idanunsa yana buɗe su tare da ɗaura su akan titi.duk da yayi rashin Hajiyarsa a wajen da tana nan yasan abun sai yafi armashi tun kafin a tashi daga taro yake samun ƙira daga Ammiey da kuma Ahmad.
Wani wawan birji yaja yana gangarawa da motar gefen titi yayi parking,sai yanzu tinanin cewa ya ajiye wata a office ya faɗu masa a rai kwanansa uku ƙwarara rabon da yaje office"Innalillahi wa'inna alaihir raji'un"ya fita a firgice tunawa da cikim dake cikinta da kuma halin da ya barta na rashin lafiya har ruwa ya ƙara mata ranar yana da yaƙinim cewar babu wanda zai buɗe masa office inba shi yaje ya buɗe ba ko cleaners basa shiga office ɗinsa,shiyasa ya kaita nan don yafi masa surru .
A guje ya figi motar ya ɗaura ta akan titi yana nufar asibitin,ko shigowa da motar bai yi ba ya barta a waje ya buɗe securities suka buɗe masa gate ɗin baya ya shigo hadda gudu ya wuce izuwa ga office ɗin sai da ya kawo bakin ƙofar office ɗin ya ɗagawa securityn da ya biyo bayansa yana tambayar sa tafiya.
Key yasa ya buɗe office ɗin ya shigo tare da maida ƙofar ya rufe ya fara rarraba idanu,ganin babu alama mutum ya sanya shi fara zagaye office ɗin zuciyarsa tana wani irin harbawa kar fa ace guduwa tayi,tambayar da yayi saurin jefa wa kansa kenan yana tuhumar kansa akan laifin kasa bawa halitttan da ubangiji da kansa ya girmama sa
Jgo ni tare da tallafo kafaɗata yana buɗe ƙofar muka fita muna isowa dai-dai tsakiyar wajen na zube a ƙasa jikina gabaɗaya ya ɗauki mazari sake ni yayi na sulale ƙasa ina birgima sakamakon ƙugin da cikina yake yi.
Daga haka ban ƙasa fahimtar komai ba balle abubuwan da yake faɗa,da sauri ya iso yana ɗan buga hannunsa akan tile's ɗin son furta sunanta yake son yi amma ya manta sunan,ganin hakan bazai fishshe shi ba ya sanya shi ɗaura ni akan gadon duba marar lafiyar dake cikin offishin robar ƙarin ruwa ya fara maƙalawa tare da saisaita bugon zuciyata.
Yana gamawa yaji wani kakakin ama yana yunƙuro masa da ɗan sauri ya nufi banɗaki ya fara kwararowa,sai da ya gama ya kwanta fuskarsa ya fito duk tsigar jikinsa yana tashi in ba kwanta yayi ya sauya suturar dake jikinsa ba.ba zai sama nutsuwa ba don ji yake yi gabaɗayar jikinsa najasa ne.
A wahalce na soma ƙoƙarin buɗe idona lokacin guda ina sauƙe ajiyan numfashi,wasu hawayen da bansan dalilin kwaranyowar su a wannan lokacin ba suka zubo mini.ganin inda nake ya sanya kukan nawa ƙara ƙarfin gudu kan dandamalin fuskata naso a ce mutuwa ce tazo mini a wannan lokacin.
"Wayyo Allahna meyasa mutuwa bata zo mini a wannan lokacin ba,meye rayuwata bata katse a nan ba na huta da tarin matsalolin raina".na ƙarishe ina ƙara sakin wani kukan da bazai gyara ɓarakar da nayi a baya ba wanda yake cike da tausayin SALON KADDARATA da ta tarwatsa dukkan farin-cikin rayuwata,ta tabo ni da iyaye da ƴan-uwa ta cillo ni duniyar da babu dangin uba balle na uba.
Jin amon muryarsa suka dira a ƙofofin kunnena ya shayar da ni tsagwaron ruwan mamaki don a zatona a zuci nayi maganar.
"Meyasa kike yiwa kanki fatan mutuwa,bayan sanin da kika yi cewar duk mai rai da numfashi ba zai tsallake ta ba kar matsalolin rayuwa ko jarabawa ta saki ki ƙara kauce hanya domin duk inda muminin ƙwarai yake to fa sai Allah ya jarabce shi domin gwada imaninsa".
Miɗik!na haɗiye sauran kukan da yake taso mini yana tsaye ya saƙale hannayensa cikin aljihun shigar manyan kayan dake jikinsa farare tas! saɓanin ko yaushe yau dai ni yake fuskanta,ganin robar ruwar dake jikina ya ƙare ya sanya ni ɗagowa na jefa idona cikin nasa nace"Kire mini nayi sallah"babu musu yazo ya cire min ya sauƙo jiri yana ɗibata na shiga banɗakin na ɗauro alwala na fito duk jikina yana rawa saboda ruwan dana taɓa ya ƙara taso mini da wani azababben zazzaɓin.
Banyi gigin kallonsa ba na wuce na shimfiɗa ɗan-kwalina na tada sallah,ya ƙura min na jiyamu har na iddar yace"Malama gari ya daɗe da wayewa ki lissafa sallolin kanki ki biya su,koda yake ma ku ka....."ban san meya hana shi ƙarisawa ba yayi shuru tare da ficewa daga wajen da idanu na raka shi har ya fice kana na miƙe na cigana da sallana.
A wajen na zauna bayan na kammala sallan ina tasbihi da gaɓoɓin hannuna,sai yanzu na lura da yankewar da nayi a hannun lokacin dana faɗi a banɗakin na sauƙe wata shirgegiyar ajiyan zuciya da ta tafiyar da kukan danake yi lokaci guda.tabbas nasan na takfa babban kuskure a rayuwata na gujewa iyayena da nayi amma har yanzu zuciya tana kan bakan ta wajen ayyana mini cewar gwara na fuskanci ko wani irin wahala ne a nan akan na ga hawayen Daada na kwaranya a sanadiyata jin kamar za'a buɗe ƙofar ya sanya ni tsaida idona akan hanyar shigowar,sai daya shigo ya maida ƙofar ya rufe manyan ledodin dake hannunsa guda biyu ya dire a gabana kafin ya shiga faɗin"Ya jikin?".cikin tantausan muryar yayi maganar da tasa na ɗago na kallesa sannan na kawar da nawa idon gefe ina amsawa da Alhamdulillah.
"Ga abinci kici sannan kisha magani".ya kuma turo min ledar gabana na ɗan ɗure na zaro tufa ɗaya na fara ci ina taunarta a hankali tana wuce ta cikin makwororona,duk da bakina babu ɗanɗano amma naji daɗinta sosai na raɗawa kaina kodan ba'a saba haɗuwa bane oho.
Sai da naci shida ɗaya nabin ɗaya kafin na buɗe ruwar gorar na ɗan zuƙa na rufe ina hamdala,ya taso ya ɓalla min wasu magunguna ya bani na runtse idona kafin na watsa su cikin bakina na bisu da ruwa.Muƙwut!haka suka wuce ta hanyar wuya na kallon da yake min ya sani tsarguwa da kaina.
"Meye sunan ki ma kika ce?"yace dani a sanyaye nace"Ummukursum".ya ɗan yi shuru kafin ya katse shurun da faɗin"Cikin dake cikin ki yana da uba?".
Tambayar tazo min a sigar yana raina mini hankali ko kuwa wani irin kallo da yake min na danna abunda yakw tasowa cikin raina nace"Yana dashi ko ka taɓa ganin idan mace ta ɗauki ciki ba tare da namiji ba?".ya watso mini idonsa nima naƙi ɗauke nawa sai shi ya ɗauke nasa.
"Wanene mahaifinsa sadaki ya biya iyayen ki suka ɗauƙi aurenki suka damƙa masa ,mutane suka shaida koko yaya?".
Ba tare da tsoron komai ba nace"Babu ko ɗaya sai dai nima ina burin naga mahaifinsa ko don na masa tambaya ɗaya rak!".har yanzu idanunsa yana kaina ya kuma faɗin"Karki gaskata hashashen zuciya da take faɗa min ta mummunan hanya kika bi kika same shi,amma yanda naga kike son cikin yake share mini wannan tantaman".
Sosai nayi dariya wanda rabo na da ita tun gabanni wannan tashin hankalin ya riske ni"Tabbas zuciyarka ta hashasho maka dai-dai a wannan karan duk tinaninka a kaina suna kan hanya".nayi ƙudirin yau zan zazzagar masa da abun dake cikina akan wannan cikin dake jikina ko da hakan zai ƙara rura wutar tsanar da ya min koma ya kasa fahimtar inda na dosa.
Idanunsa ya ƙara warewa a kaina ya jawo kujerar zamansa ya kafa saitina tare da naɗe hannayensa a ƙirjinsa"UMMI"ko ya ƙira sunan duk da suna nane amma babu wanda ya taɓa ƙira na da hakan na ɗaga masa kai wanda ya bashi damar cigaba da faɗin"Inason nasan komai dangane da cikin dake cikin ki".
Duk da na ƙarfafa kaina lokacin amma dai da naji hawaye sun ciko kurmin idaniyata nayi ƙoƙarin danne su,amma bani da iko akan su sai da suka zubo na ja dogon numfashi kafin na fara masaa dalla-dalla cikin faɗin.
"Kamar yanda na faɗa maka sunana Ummukursum muna zaune a cikin garin bauchi cikin unguwar wunti stree,mu uku ne a wajen mahaifinmu ina da ƙanne biyu.Mahaifinmu gawutaccen mashayi ne ƙanina kuwa fitaccen ɗan bangan siyasa a kaf!cikin garin mu da kewayen ta,ba muyi zurfi a karatun zamani ba domin tun muna matakin primary mahaifinmu ya cire mu ƙanwata kuwa ƙaramar Sha'awa ko sata ba'a yi ba.
Mu kasance masu ƙananan ƙarfi ta yanda cin yanzu ma gagararmu yake yi balle na anjima har mu sai rai da samun na gobe,tun muna da ƙarancin shekaru mahaifiyarmu take aikin ƙarfi wajen ganin ta cinyar da mu da halaliyarta tunda mahaifinmu yayi nuna halin ko in kula akan lamuran rayuwarmu da ta mahaifiyarmu gabaɗaya.ba musan daɗin rayuwa ba domin SALON ƘADDARAr mu tazo ta daban kuma bai wahalar fassarawa da kalmomin da bakin kan iya furwata,sai dai ba mu nada wadatar zuci ta yanda muke neman na kanmu.ranar da Daadar mu ta haihu a asibiti zan koma gida ɗauko mana wasu kayan a hanya ta ta dawowa asibitin wannan ƙaddarar ta faɗa mini da zan iya ƙiran ta da SALON ƘADDARATA,ya raba ni da mutumcina rabuwa ta har abada ya mini tabo wanda babu ruwan da zai goge min shi a duniya banga koda fuskarsa ba sai dai sautin muryarsa da nayi haddansa a cikin kwakwalwata.
Nayi ƙoƙarin barin abin a cikin raina koda baƙin-cikin hakan zai zamto ajalina,ashe lamarin ya wuce ƙaramin tinanin kwakwalwata sai da alamominsa suka bayyana har asirin da nake ƙoƙarin bulawa ƙasa na birne ya fito,ranar naga tashin hankalin da bana fatan Allah ya ƙara kwatanta mini makamancin sa".
Ina isowa nan na dakata sakamakon kukan da yaci ƙarfi abubuwan ina ganinsu a cikin idona tamkar yanzu suke faruwa,sai da nayi har na godewa rabbil-izzati kafin na ɗaura da faɗin"Akan idonmu Abbanmu ya karkata dukkan laifa kan Daadarmu ya kuma haramta mini ƙara yin wani rayuwar a cikin gidansa tare da tsigare ni daga cikin jerin ƴaƴansa.babu wanda ya tsaya ya fahimce ni balle maganganun bakina har na kai ga iya furta musu cewar fyaɗe yamin cikin duhun daren da ko fuskarsa ban gani ba,bazan iya jure ganin zubarwa hawayen halittar da taso ni fiye da kowa da komai a duniya,bazan iya jure haɗa idanu da ita ba gwara na tafi inda babu wanda ya sanni balle a gorantawa abin dana haifa idan ya diro duniya".
Tiryan-tiryan na faɗe masa komai naga ya tsura mini idanu ba buri na ya yarda da abunda na faɗa masa ba,illa iyaka na fitar da abunda dake raina wala-allah naji sausauci.
Duk yanda wani sashin zuciyarsa yake jinyayi akan tausayinta da kuma halin da ta tsinci kanta a ciki yanzu amma haushin ta da kuma abinda ta da aika ta kasa barin mizanin tausayinta yayin jinyayin zuciyarsa.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________________
Page 2⃣7⃣
"Ba zai zama lalle ka yarda da abinda na faɗa ba,domin hatta Daada ma bata yarda dani ba".
Iya abinda na faɗa kenan cikin raunanniyar muryar kukan da nake yi tare da sauƙe ajiyan numfashi wata na bin wata saboda kallon tuhumar da naga yana jifa ta dashi.
Ba shiri naji ya ɗauke ni da kyawawan maruka uku!ras da sautin su ya amsa a cikin wajen tas!.a gigice na sakin wata ƙara mai rikicarwa ina dafe kuncina,miƙewa tsaye yayi yana riƙo ƙungunsa da hannunsa ɗaya,ɗayan kuma ya dafe goshinsa da jijiyoyin kansa suka fito raɗau-raɗau shimfiɗe a goshinsa.
Sosai kansa yake sara masa ya juyo ya fuskanto ni,ƙwayar idonsa kaɗai dana kalla na sanya jikin ɗaukar tsimi don yanda ya ƙara ƙanƙancewa kuma suka yi jajir muryar da yale maganar tana bayyanar da zahirin baƙin-ciki da takaicin dake ransa ya ce da ni.
"Waya gaya miki ana gujewa iyaye mussaman UWA,guje mata da kika yi sai yafi sanya ta damuwa fiye da girman laifin da kika aikata mata domin shi takan iya yafe miki.bansan meyasa wasu da Allah yayi wa gatar rayuwa tare da iyaye biyu uwa da uba amma suke sakaci wajen faranta musu,wani lokacin har sune za suyi sanadin zubar hawayen iyayen nasu kinyi kuskure mafi girman kuskure a rayuwarki wanda ba zaki iya canza shi ba kuma haƙƙin mahaifiyarki ba zai taɓa barin ki ki rayu cikin salama ba a duk inda kika shiga cikin faɗin duniya".
Yana dasa aya anan ya ƙara dafe goshinsa tare da furzar da zazzafar iska mai ɗumi daga bakinsa,mazauninsa ya nufa ya zauna yana tallafo fuskarsa da hannayensa runtse idanunsa yayi da ƙarfi yana sauƙe numfashi a lokaci guda,tabbas da Allah ya ƙaddara masa gunadar da rayuwa da mahaifiyarsa cikin wanga duniya da ya ƙara da lokutan rayuwarsa wajen faranta masa.
"Wasu suna neman iyayen da zasu farantawa wasu kuwa har guje musu suke yi".abinda yake faɗi kenan cikin ransa.
Wani gigitaccen kuka na saka har ina neman shiɗewa na fara jin jikina yana rawa kaina yana sarawa da ƙarfi ya mini nauyi har idanuna suna ƙoƙarin rufewa naji numfashinsa dab da ni nayi jarumtar wangale murfin idona na masa kallo ɗaya kafin na maida su na rufe gam!don ji nayi ko iska ne bana buƙatar ya fura su balle naga wani haske dasu.
"Ina buƙatar alqur'anin don Allah"na furta wasu hawaye suna ziraro mini bai amsa mini ba naji ƙaran takunsa yana barin wajen mintuna biyu tsakani ya dawo ya miƙa min alqur'anin na karɓa sannan na fara buɗewa a tsanake suratul Anbiya'i yana ja burki na fara karantowa cikin tsantsan kushu'i da fitta da wa ko wani harafin haƙƙinsa.
Har cikin kwakwalwarsa sautin karatun yake ratsa dukkan jijiyoyi da gaɓoɓin jikinsa,lumshe idanun sa yayi ya tsawo daƙiƙu kafin ya buɗe su yana duban agogon wayarsa ya miƙe tare da ɗaukar rigar likitotin dake saƙale saman kujerar tasa wanda na fara zaton cewa likita ne musamman da naga ya iya sanya drip da kuma cire ta ya fice cikin wajen.
Na cigaba da karatuna har izuwa lokaci da na fara jin sashin ruhina ya fara sanyaya na sauƙe gawutaccen ajiyan zuciya,na ɗau tsawon lokaci ina karatu har na samawa kaina nutsuwa ta hanyar karata zance na gaskiya.yunwar da take ƙwaƙwular hancin cikina ta kuma murɗowa na jawa ledar gabana na buɗe wata take away da yake ɗauke da shinkafa da yanka nama na fara ci hannu baka hannu kwarya sai da na fara jin amai yana taso mini kafin ya ture shi gefe na ɗaya goran ruwan dana sha magani da shi na zuƙe sauran.
Na tashi na wanko hannu na sannan na ɗan tattare wajen na shirya kayan cikin ledar na ajiye gefe guda,na zauna kan ɗankwalina don ko kan ƴar ƙaramar carpet ɗin dake yashe a tsakiyar wajen mai launin ruwan toka ban taɓa zama akanta ba balle kujerun da suke shirye a wajen.a hankali na sha cikina maganganunsa suna yi mini wayo cikin kunyar kaina tabbas nima nasan haƙƙin Daada ba zai bar ni ba,amma ya zama dole na nisanta kaina da ita a cikin irin wanga lokacin kamar yanda zuciyata take karanto mini da manyan harrufa.kur'anin na rungume a ƙirjina ina jin son ɗa ko ƴar dake rayuwa cikin mahaifata yana bin dukkan sassan ruhina.
Inason ko sau ɗaya ne naje asibiti awu domin sanin halin da yake ciki ko dan na kaucewa irin halin da Daada ta tsunguma yayin da tazo haihuwa ba tare da shaidar zuwarta awu na.amma ta yaya zan fara fuskantar da wannan zancen wasu hawayen suka ciko mini kurmin idaniya da na tina ikirarin da yayi akan ina haihu zai ɗauke yaron ko fuskarsa bazai bani damar kalla ba balle na ji ɗuminsa a jikina.
Kukan da nake dannewa ya suɓɓuce mini na shiga rerosa wiwi ina rungume da kur'anin a ƙirjina.
Bansan sanda wahaltaccen baccin ya sure ni ba sai jin naji ana bubbuga inada na kwantar da haƙarƙarina a hankali,nayi figigi na farka tare da rarimo hijabin ina yiwa ƙirjina shinge da shi,yayi saurin tare kur'anin da yake neman sulale ya ɗauka tare da nema masa matsuguni na mussamman ya ajiye shi ya dawo ya jawo kujera ya zauna ya ɗaura idonsa a kaina na tsawo mintuna kamar ɗan sandan dake nazartar wani mai laifi,jin idanunsa a jikina duk na kasa sukuni gami da nutsuwa har lokacin daya furta.
"Amshi wannan MPn kina saka karatun a ciki mussamman suratul Yusuf,ana son duk wata mace mai juna biy tana yawaita sauraronsa ta zama a ko yaushe abokiyar hirar ki domin yana sa a haifi yaro mai farin jini da kwarjini".
Yanda yake mini maganar a yau ta bambamta da ko yaushe banyi musu ba na miƙo hannu na amsa duk da naga wannan ɗin tayi daban da MPn da na saba gani a gidan Anty Sakina,wannan ƴar ƙarama ce kamar tocila na ɗan jujjuyata a hannuna kafin na ajiye ta gefe guda.
"Kiyi wanka domin naga tunda kika zo cikin wannan kayan kike".
Na buɗe idona dana runtse su sanadiyar sarawan da kaina yake yi,nayi ƙasa da kaina tare da faɗin"Ban iya amfani da kayan cikin banɗakin ba naga kamar komai na lantarki ne,famfon dai kawai na iya kunnawa".
Kansa kawai naga ya ɗan jinjina kafin ya miƙe ya shige gaba ina biye dashi a baya har izuwa cikin banɗakin,yanda ake kunna shower ɗin ya fara nuna mini wanda ita ma take daban a gare ni duk yanda nake ga kyau da kuma arzikin gidan Anty Sakina da yaya Aliyu sai naga ashe ma ko matakin farko baza a sako su ba inna haɗa wannan banɗakin da gidan su kaf!.
Figigi na dawo daga tinanin saboda maganar da ya soma"ki dai bi a hankali don in kikayi wasa kuma ki taɓo wani abunda ruwa zai ja ki".ya ƙara tsora ta ni da wannan maganar har na tina wata mummunar gobarar da aka yi a unguwar mu gidan wata amarya aka ce heater ɗin cikin banɗaki ne ya haifar da gobarar.
Haka har ya gama koya min na tsinci wasu abubuwan sannan ya fita ya bar ni a banɗaki domin nayi wanka,ya miƙo mini towel da kuma wata rigar abaya.kaya na na fara kwaɓewa a farkon banɗakin da yake shima wani ɗaki ne mai zaman kansa da ya amsa sunan sa sai ka wuce shi kana ka shiga inda zaka gudanar da wanka,wajen fitsari da sauran biyan buƙata shima sashin sa daban.
Kamar yanda ya koyar dani a aikace haka na kunna showern nayi wankan ba tare da soso ko sabulu ba sai dana kammala tsaf!sannan na hangi sabulon a can gaban mirrion dake cikin banɗakin na fito ɗaure da towel ɗin a jikina izuwa cikin farkon banɗakin inda na kwaɓe kayana,sai dana ɗan tsaya ruwan jikina ya tsamtsame kana ya zara doguwar rigar abayan da ya haɗu ni da ita ta sauƙa mini har ƙasa na tattaro shi na tuƙuiƙuye a hannuna sannan na maida hijabina tare da ƙunsho kayana da na cire a hannuna na fito.
Kaina a ƙasa na fito na wuce inda na shimfiɗa ɗankwalina na ninke kayana dukka na ajiye a gefe sannan na zauna ina ɗan wasa da yatsuna.sautin karatun da yake tashi cikin sifikon MPn ya mamaye ɗakin,daɗi ya ɗan tsirka ni don daman ban iya kunna ta ba.
"Ina fatan kin tanadi kalaman da zaki faɗawa ɗan dake cikin cikin ki,idan ya buƙaci sanin waye mahaifinsa?".bai bani damar amsawa ba ya ɗaura da"Lokacin da lamarin ya faru kun shigar da ƙara wajen jami'an tsaro domin a bi muku haƙƙinku".
Sirarun hawaye suka biyo gefen kuncina kafin nace"Bamu shigar ba domin a lokacin duk hankulan mu yana tashe bamu yi wannan tinanin ba".
"Bauchi kika ce kike ko,wani unguwa ma?".nayi saurin faɗin"wunti stree muke".
Ya miƙe haɗi da faɗin"Ki daina kwanciya a nan,ga gado ki kwanta akansa ni zan tafi sai gobe zan shigo sannan ga abinci ga kuma magani kisha".
Nayi saurin katse shi da faɗin"Don Allah ina ne nan,a ina nake?".
Ya ɗan dakata daga hanyar ƙofar daya ɗauka ya ce da ni" Kaduna".ganin zai fita ba tare da na sama gamshashshiyar amsa ba nayi anzarin furta"ka sanar da ni wannan abinda nake son sani shine ina ne nan,domin tunda ka shigo da ni lokacin bana cikin hayyacina babu wanda nake gani balle naji motsin wani halitta babu wanda yake shigowa sai kai ɗaya".
Ya juyo ya ɗan kalle dungun da nake kafin ya kawar da kansa gefe ya ce dani"Bana tinanin wacce zata iya barin gidan iyayenta ta zaɓi shiga duniya zata yi fargata ko kuma tsoron zama a duk inda ta tsinci kanta".
Bance dashi kanzil ba sai ma dana sanin tambayar sa da nayi,don yau kaɗai naga fuska mai kamata na wuce iyaka ta ba.bansan wani tinani yayi ba ya koma dawowa da faɗin"Nan asibiti ne kuma cikin ofishina a nan zaki zauna har ki haife abinda yake cikinki har kuma izuwa lokacin da zan ɗauka wajen gudanar da binkice akan sanhihancin labarin da kika bani".
Gifff!yaja ƙofar ya rufe ƙaran ya sanya ni saurin rintse idanu da suke nason hawaye,ina tausayin kaina da kuma SALON ƘADDARATA a yanda ta zo.yana fita ya wuce masallaci saboda ƙiran sallan asr da aka zoma alwala yayi sannan yaja su sallan bayan sun kammala yayi musu ƙarin karatu,kafin ya wuce izuwa parking lot ɗinsa ya shiga mota ya fice har ya isa gidan yana waya da Hajiyar tana ƙara jinjina masa akan namijin ƙoƙarin da yayi wajen ganin bikin taron ƙungiyar ya tafi bisa turban tsari,sallama suka yi ya kashe wayar ya fito kansa tare da tsagayowa kujerar zaman ɗan banza ya ɗauki babbar rigarsa ya fito yana tafe yana waya da Barristern da ya ɗauka akan case ɗin Adam.
Hango Nenne da yayi tana fitowa daga cikim garden ya sa shi zame wayar daga kunnensa,kallon daya ƙura mata ya sanya ta shan jinin jikina ta yi saurin ɓoye wuƙar da ta haƙa rami ta burne layan a bayanta,sai da ya iso kusan ta kafin ya ce"An wuni lafiya".taɓe baki tayi haka nan shima bai tsammace samun amsa daga gare ta ba don haka kansa tsaye ya nufi part ɗinsa da rabon sa da ita tun ranar taron bai dawo gida ba yana asibiti.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________________
Page 2⃣8⃣
Zaune Daada take a tsakar gidan da yasha shara ko'ina tsaf!duk da simitin duk ya faffashe amma babu ƙarazanta a gidan mu Sagir yana mata tausa sai kuma Sha'awa da take wanke-wanke.
"Dadda lafiya kuwa naga kinyi shuru?".Sagir ya ce da ita yana ɗan sausauta tausar da yake mata a ƙafa sai da ta sauƙe ajiyan zuciya kana tace"Babana lafiya kawai ina tinanin kamar mun ɗaurawa yaron nan Aliyu nauyi da yawa tunda ko kuɗin,hayar gidan nan shi yake biya da kuma Sha'awa da ya maida ta makaranta.ya kuma ɗauki mashin ɗinsa ya bada kana ɗan sahu dashi,ya kamata mu ma ko wata sana'ar da zamu dogara da kanmu.
"Haka ne Daada nima aiki ne yanzu babu ciniki saboda tsadar man fetur da ake fama dashi."
Kusa da Sagir,Sha'awa ta zauna tana goge ruwan hannunta a jikin zanin ta bata tsoma baki cikin tattaunarwa ba illa bin su da ido da take yi.
"Babu abunda zamu cewa Aliyu da Sakina sai dai Allah ya saka musu da gidan aljanna,ya kuma raya musu zuri'arsu".duk suka amsa da amin kafin Dadda ta ɗaura da faɗin"Kaima Sagir ya kamata in abubuwa suka warware ka koma makaranta tunda,kana da burin karatun".
Sai da ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa yana dariya kafin ya ɗago da haɗi da faɗin"Daada kenan yanzu ina da ku a gabana ai kuma babu batun makaranta,na iya samar muku da ingantaccen rayuwa yanzu shine buri na a rayuwa,karatu yanzu ai sai Sha'awanat...".
Saurin haɗiye sauran maganganun yayi a ƙoƙarin son furtawa Sha'awa kalmar"Lafiya"sabida hawayen da suka fara gudana akan dandamalin tudun fuskarta.
"Ke lafiya kuka kuma na meye ƙanwata?"ya kuma jefa mata tambayar jikinsa ta kwanto tana faɗin"yaya Sagir mafarki jiya nayi da Anty Ummukursum na ganta cikin wani irin yanayi,tana roƙo na akan na nema mata yafiyar Daada".a nitse ya sauƙe ajiyan zuciya yana tallafo ta jikinsa sosai tare da bubbuga bayanta da ɗayan hannunsa.
"Sha'awanatu ai shi mafarki ba gaskiya bane,ki daina damun kanki akan wannan duk sanda kika yi irin wannan mafarkin to ba'a faɗawa kowa sai dai ki tashi ki mata addu'a kinji ko?".kanta ta ɗaga masa kafin ya kai ga furta wata kalmar ta katse masa numfashi da faɗin"Yaya Sagir yanzu ko ƙofar gida na fita,sai ayi ta nuna ni ranan nan yaran gidan su Khadija masu awara har bina su kayi suna faɗin wai yayata tayi cikin shege ta gudu.Abbanmu ya saki Daada sai yaya Aliyu ne da na haɗu dashi ya kore su ya raku ni gida yace in daina kuka insu na tsokalata kuma kar na sanarwa Daada".
Gefen fuskarta ya ɗan shafo a hankalin yanda yake tana maganar jikinta yana rawa tana yi tana jawo numfashinta ya ce da ita"Gaskiyan sa ki daina kula su ko suna yi,sannan ai yanzu kin girma ba ki gani bane yanda kika yi tsawo ko aure fa yanzu za'a iya miki".saurin kai masa duka tayi a kafaɗarsa tana tashin daga kwanciyar da tayi a jikinsa tare da cuno baki"Haba yaya Sagir kai maganar ka ɗaya kace wai aure aure,to ni yanzu wa ma zai aure ni gwara na daina yauradar kaina tare da ɓatawa kaina lokaci.ya fi min nayi zamana da Daada muyi rayuwar mu lamarin aure ya fita daga raina don inaga kamar duk maza irin halayyana Abba ne gare su".
A sanyaye ta ƙarishe maganar,Sagir yayi shuru yana ɗan satar kallon fuskar Daada ta kamar bata jin abunda suke tattaunawa tun farkon maganar tasu."subhallahi"ya furta yana ƙara matsowa dab! da Daada ganin hawaye a fuskarta.
"Daada kema kukan zaki yi don Allah yaya kuke son ni nayi da raina ne,danne nawa nake yi domin faranta muku fa don Allah Daadata ki cire damuwar komai daga ranki ki miƙa komai ga Allah,SALON KADDARAR mu ace mu kuma haka sai muyi ƙoƙarin cinye jarabawar koda ba ji daɗi a wannan rayuwar ba ma ji idan muje can".ya ƙarishe yana riƙo hannunta cikin nasa dai-dai lokacin da Anty Hussaina da su Humaira suka doko sallama.
Sha'awa ce tayi ƙarfin hali amsa sallamar tana ƙara ware musu tabarmar ta yanda zai ishe su,su ka zauna kafin Anty Hussaina ta shiga faɗin"Haba Sagir kai da zaka kwantar mata da hankali kuma kaima kake taya su kukan,duk kuka zama ɗaya"tana dasa aya a nan ta dawo kusan Dadda tana share mata hawayen.
"Dan Allah Adda ki daina ki mayar da komai ba komai ba,Ummukursum yanzu addu'arki a matsayin uwa shi tafi buƙata ba wannan kukan ba tare muke da Abban su Humaira zaku gaisa zai koma wajen aiki yau".
Sagir ya miƙe ya fita suka shigo tare Sha'awa ta ɗauko sallaya ta shimfiɗa masa ya zauna yana riƙe da Musaddik akan cinyarsa,ya gaida Daada tare da mata jajen abubuwan da suka faru ta amsa tana ɗan sakin fuskarta.
Kusa dashi Sagir ya zauna yaya Auwal ya dube shi cikin yanayin zolaya yace"Ɗan acaɓa to ya garin?".
"Lafiya ƙalau yaya Auwal gari fa yaci wuta ku kuke riƙe da garin"ya ƙarishe yana ɗan sosa ƙeya,Sha'awa da Humaira suka saki dariya a lokaci guda kafin yaya Auwal ya ɗaura da faɗin"Mama Humaira ta sanar dani cewar mashin ɗin bana kaba bane ko?".Sagir ya ɗaga masa kai alamar e yana gyara zamansa sosai.
"Ka tambayo nawa ne kuɗin sabuwar mashin ɗin sai muga yanda za'a yi ka mallaki naka kaima".
"Ai sabuwar tana kaiwa dubu tamani zuwa da biyar haka"Sagir yayi hanzarin furtawa bakinsa har kunne.lalume ajihunsa yaya Auwal yayi ya ciro wasu kuɗaɗe ya lale ya irga kafin ya miƙawa Sagir yace"To ga dubu casa'in sai kaje da Aliyu ya duba maka mai kyau,ai shi sana'a tana da daɗi mussamman ga ire-iren ku matasa".
Godiya Sagir ya shiga zabga masa kafin Daada ma ta gabatar da nata da kuma wasu addu'o'in suna biye dashi,Sha'awa da Humaira da Anty Hussaina ma ba'a bar su a baya ba duk sai da suka taya Sagir godiya.
Yaya Auwal ya ciro wasu kuɗin ya miƙawa Anty Hussaina yace ta bawa Daada suyi cefa ne sannan in suna buƙatar wani abun a sanar dashi,Daada ta yita zubo godiya Sagir da Sha'awa na taya ta,sallama yaya Auwal ya mata Anty Hussaina da su Humaira suka raka shi jikin motar sa ya tafi.
Sannan suka dawo Anty Hussaina ta miƙawa Daada kuɗin da ya bayar a bata,ta karɓa tana faɗin "Hussaina shi kuwa Abban su Humaira hadda ɗaurawa kai nauyi haka,ke da kwana biyun nan kike faɗin rashin kuɗi ne ma ya hana sa komawa wajen aikinsa akan lokaci ya ɗeba kuɗi maka ya bada Sagir?".
Ɗan murmusawa Anty Hussaina tayi tana cewa"Adda lokacin dan sanar masa halin da kuke ciki ne,ya yi alƙawarin sayawa Sagir mashi shiyasa ya dakatar da komawar da zai yi har sai da kuɗin ya haɗu".
Jinjina kanta Daada tayi cikin ranta tana ƙara gaskata wannan karin maganar nan ta masu iya magana da suke faɗin cewar"Naka naka ne ko yaci namarka ba zai tauna ƙashinka ba".
"Allah sarki!Allah ya saka masa da mafifin alkhairi ya raya masa zuri'arsa" .
Amin amin ita kalmar da take fitowa daga bakunan su,kafin Daada ta aika Sagir yaje ya ƙira mata yaya Aliyu ta yi masa bayanin komai tiryan-tiryan tare da umartansa akan gobe suje kasuwa su duba mashin ɗin,ta amshe kuɗin daga wajen Sagir ta damƙa masa.
Sauran wanda Anty Hussaina ma ta bata duk ta haɗa masa tace ya riƙe a wajensa tunda komai shi yake musu,cefene ne dai wataran in Sagir yayi ciniki yake taho musu dashi da wasu ƙananan abun da ba za'a rasa ba.fir yaƙi karɓan kuɗin,kuɗin sayo mashin ɗin dai ya amsa amma wancan kuɗin yace ta riƙe a tare da ita suyu wasu buƙatar dashi shi domin Allah yake kyautata musu ba don su biya shi ba.
Haka ya tafi ba tare da ya karɓi kuɗin ba,Anty Hussaina ta bishi da idanu yayin da yake ficewa ta ce"Daada wannan yaron da matarsa suna ƙoƙari akan mu,Allah dai ya saka musu da alkhairi da ace ana samun makwabcin irin su da al'umma ta zauna lafiya".
"Aliyu da Sakina kam ai ba daga nan ba".daga haka suka cigaba da hirar su har Daada ta saki ranta ta fara jefa magana ɗaya biyu a cikin zancen.
Kwance yake a cikin bedroom ɗinsa ya ƙurawa ceiling ɗin ɗakin kallo wanda ya zama shamaki tsakaninsa da sararin samaniya,Tvn ɗin dake aiki cikin ɗakin ya saka sautin karatu sheik Afif Muhammad ya karaɗe dukkan ɗakin.yana karanto suratul Nisa'i yana bi a hankali ba tare da yake kallonsa izuwa ga tv ɗin ba.
Wayarsa dake kan ruwan cikinsa ta fara ruri bai bi ta kanta ba har ta tsinke,don baya tsammanin ƙiran kowa a irin wannan lokacin sai da aka ƙara ƙira a karo na biyu sannan ya jawo ta ganin lawyern da ya ɗaura akan case ɗin Adam ne ya sa shi picking ɗin call ɗin tare da manna ta da kunnuwansa.
Daga can bagaren aka yi sallama ya amsa sannan suka gaisa,ya fara shaida masa da sun gama case ɗin ba sai aje gaban kotu ba yanzu kawai sa hannunsa ake buƙata kafin a bada ballin shi Adam ɗin.
"Gani nan zuwa"ya amsa dashi yana kashe wayar tare da tsirtar da wata siririyar tsaki kasancewar yau weekend ko asibiti bai yi niyyar leƙawa ba saboda son huta gajiyar da ya ɗebowa jikinsa,a dole ya miƙe ya shiga bathroom yayo wanka sannan ya shirya cikin shigar ƙananan kaya farar t-shirt da blue ɗin jeans ya saka,wayarsa da key ɗin motarsa ya fice daga bedroom ɗin haka ya bar tvn yana aike ya fita ya rufe part ɗinsa tare da zara key ɗin a cikin aljihunsa.
Kansa tsaye ya wuce cikin parking space ya faɗa motar ya fice,ya nufi station ɗin yana zuwa ya tarar da lawyern a waje yan jiransa suka shiga tare kasancewar sa sananne yasa duk ƴan sandan dake bakin aikin taso wa suka gaisa kafin suka gabatar masa da takardan da zai sa hannun yayi sign ɗin sannan ya fito tare da lawyern don baya son Adam ya ganshi ball e har yasan shi ya tsaya masa akan case ɗin.
Musabaha suka ƙara yi da lawyer ɗin tare da ƙara jaddada godiyarsa a garesa,sannsn ko wannensu ya faɗa motar sa kansa tsaye ya wuce gida don baya sha'awar shiga asibiti yau.
Yana turo hancin motar ya hangi Baban Nana yana nufo sa,don yau ba shi bane akan aiki ɗayan gate man ɗin ne da yake yi na rana,ganinsa ya sanya shi faka motar ya fito ya isa gare shi ganin kamar baya cikin nutsuwar sa.
"Baba lafiya kuwa?".
"Lafiya amma ba lau ba Zayyad,ina zagaye ne naci karo da wannan layar a cikin garden karnuka sun tone shi kuma daga yanda naga alamun wajen mutum ne ya burne shi. Shine duk na faɗa tinanin mezai shiga da mutum cikin gidan nan har ya burne laya ba'a ganshi ba".
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________________
Page 2⃣9⃣
Karɓan layan yayi tare da bismillah,sannan ya fara warware ƙullin dake cikin ta farar takarda ne a cikin da aka nannaɗe ta ya ware ganin sunansa ya bayyana cikin manyan harrufa wanda yake ɗauke jikin takardan ya sanya ƙirjinsa bugawa da sautin dam-dam.
Runtse idanunsa yayi kafin ya ware su akan Baban Nana wanda shima ɗin shi yake gani yace"Baba kace a ina ka samo layar?".
"A cikin garden na samo ta na kusa da bangaren ka karruna sun tone ta,menene a cikin naga kamar rubutu ne ko?".
Saurin naɗe takardan yayi yana cunkushe ta cikin hannunsa kafin ya ce"Baba babu komai kar ka samu shirme kawai a cikinta,watakil iska ne ya shigo da ita bari naje na ƙona ta".
Duk da Baban Nana bai yarda da abinda Zayyad ya faɗa masa akan babu komai,ya amsa da to tare da ɗaurawa da Allah ya kyauta.a wajen Hajja Zayyad ya karɓo ashana ya cinnawa layar wuta ta cinye ƙurmus sannan ya kwashe tokar ya watsar duk Baban Nana yana tsaye yana kallonsa.
"Baba bari na shiga ciki"ya faɗa yana ƙarkaɗe hannayensa yana rufe bakinsa Adam yana turo gate ɗin gidan ya shigo yana haɗa hanya sai da ya iso dab! dasu ya ƙare musu kallo tsaf kana ya tsirgar da wata tsaki mai dogon zango yana ɗaukar hanyar part ɗin Nenne.
"Allah dai ya kyauta".
Iya abunda Baban Nana ya furta kenan yana ɗaukar hanyar barin wajen yaje ya tufe gate ɗin da Adam ya wangale,a hankali yake ɗan murza zoben azurfan dake ɗan ƴatsarsa ji yo ihun da Adam yake kurmawa ya sanya shi ɗago idanunsa yana sauƙe su a kan sa.
"Nenne!Nenne!! gani na dawo".
Har kusan faɗuwa Nenne take tsabar saurin da ta ɗebo ta fito tana nufo inda Adam yake tsaye ta rungume shi,tana bayana ƙeyarsa Haidar ma ya fito suka rungume juna shi da Adam kafin Nenne ta shiga faɗin"Allah nagode maka da ka dawo min yarona gida cikin ƙoshin lafiya,su kuwa ƴan baƙin-ciki da son ganin bayan mu sai a mutu".
Ta ƙarishe maganar tana aikin cillawa Zayyad da yake tsaye a wajen kamar an dasa shi,ya kasa motsi balle yunƙurin barin wajen wani marayan murmushi ya saka taƙaitacce ta gefen bakinsa yana jin yanda ruwar ƙwala ta ciko masa idaniya ya sunkuyar da kansa ƙasa wanda hakan da yayi ya bawa hawayen damar tsiyayowa saman fuskarsa.
Har cikin ransa yake jin wani farin-ciki yana fuzgansa ganin yanda dawowar Adam ya haifarwa Nenne irin wannan farin-ciki hadda godiya ga Allah.a hankali ya ciro handkerchief daga aljihunsa yana kawar da hawayen fuskarsa tare da ɗago idanunsa yana tsayar dasu akan Nenne da keta faman rungumar Adam da Haidar a jikinta.
Murmushi ya ɗan saka irin wanda hausawa suke yiwa kirari da yafi kuka ciwo da ƙona,kafin ya ɗauki hanyar part ɗin sa a falo ya zube kan kujera tare da lumshe idanunsa yana ji yo sautin karatun da ya bar Tv tana aiki yan ratsa cikin kansa ya daɗe cikin wannan yanayi har sai da ya fara jin ladani yana ƙwala ƙiran sallan magrib kafin ya miƙe ya fita izuwa masallaci tare da Iman sai da aka yi sallan Isha'i sannan ya dawo saɓe da Iman a kafaɗarsa da tunin yayi bacci.
Hajja ta karɓe shi ta kwanta,kusa da Baban Nana ya zauna yana ɗan laƙwashe ƙafafunsa waje guda "Zayyad kun dawo"kansa kawai ya ɗaga masa ya cigaba da faɗin"Zayyad ni kam maganar layar nan ta tsaya mini a rai,mussamman da na yanzu naje na tarar da karen da ya tone layar ya mutu wani irin kumfa yana fita daga bakinsa abun ba kyan gani".
Sosai jikin Zayyad ya kuma jin sanyi ƙalau duk yanda yaso hana zuciyarsa zargin komai ko kowa akan samuwar wannan layar,amma yanzu furcin da Baban Nana yayi ya share wannan daga cikin ransa dole ya tsorita da lamari tunda cikin garden ɗin part ɗinsa hakan ya faru.
Babu wanda yake shiga part ɗinsa hasalima tun bayan raba musu part,da aka yi dasu Haidar ko'ina zai je sai ya tabbatar da cewar ya kunne sashinsa.ko ƴan aiki basa shiga part ɗinsa su gyara masa kamar yanda suke a ko wani part ɗin cikin gidan Nenne ta hana shi mu'amala da kowa a cikin gidan hatta ƴan-uwan shi ma tana ƙoƙarin raba shi dasu.
Maganar da Baban Nana ya soma yi ya sashi saurin dawowa daga tinanin da ya fara nisa a cikinsa,"Zayyad ya kamata ka ƙara dagewa da addu'a domin kowa yasan cewar Hajiya da ƴaƴanta basa ƙaunar ka bana shakkar faɗin ko dama ta samu zata iya kawar da kai daga bayan ƙasa".
Numfashi ya shiga sauƙewa ɗaya na bin wata kafin ya ce"Baba kowani bawa da irin salon yanda ubangiji yake jarabtarsa domin ya gwada matakin imaninsa da ƙadaita Allah a cikin ko wani irin yanayin ya iske kansa.SALON ƘADDARATA ne a haka Baba abunda nake buƙata daga gare ka shine ka cigaba da min addu'a Allah ya bani ikon cinye wannan jarawaban".
Shuru ya tsara wajen na tsawon daƙiƙun da basu gaza goma ba kafin Baba Nana ya dafa kafaɗarsa yana faɗin"Zayyad kana da kyakykyawan zuciyar da ba kowa yake dashi ba,Allah ya ganar dasu su fahimta cewar sunyi kuskuren cutar da kai da su keyi har su dawo kan dawo madaidaiciya,Zayyad shiga cikin case ɗin Adam da aka yi ya faranta min rai domin ko ba komai shi ɗin ɗan-uwanka ne kuma ba'a canzawa tuwo suna Allah yayi maka albarka".
Can ƙasan maƙoshinsa ya amsa da kalmar amin,kafin ya miƙe tare da yi masa sallama ya wuce part ɗin tun a falo ya zare rigar dake jikinsa wanda yake jin ta taƙura masa wajen fita da mayar da numfashi yanda ya kamata kan three siter ya kwanta yana sauƙe numfashi wata na bin wata.ya daɗe a haka wasu irin tinanin nika suna ziyartan kwakwalwarsa saurin dafe ƙirjinsa yayi jin irin bugun da take yi wanda ya wuce misali.
Dim!ya faɗo daga kan kujerar ya fara birgina a ƙasa yana kokuwa da numfashinsa da yake curewa waje guda,azaman ciro inhaler ɗinsa da baya rabuwa da ita yayi daga cikin aljihunsa ya fara using dashi cikin ƙanƙanin lokaci duk jikinsa ya sake ya fara tsatstsafo da zuffa daga kowacce sassan jikinsa.
A hankali ya miƙe kan ƙafafunsa da suka fara butulcewa ɗaukar nauyin gangan jikin,yana dafe gefe da gefen ginin falon ya shiga ɗaki kansa tsaye ya nufi bathroom bayan ya zare ragowar kayan dake jikinsa ya shiga yana sakewa kansa ruwan dumi, har sai da ya ji ya fara samun nutsuwa sannan ya fito ɗauke da towel a jikinsa doguwar rigar jallabiya ya saka sannan ya kwanta yana lulluɓe rabin jikinsa da blanket.
Ya furza da iska mai zafi daga bakinsa kansa yana sarawa a karon da ba adadi,tabbas ya zama dole a gare sa ya bincika labarin yarinyar nan ya tabbatar da sahihancin zancen da ta faɗa masa a matsayin labarin rayuwarta.dole zuciyarsa take wajabta masa akan ya hukunta akan laifin gujewa iyayenta da tayi ba tare da tinanin halin da zasu faɗa ba.
"Ita kenan da take dasu ma amma bata san darajar su ba,ire-iren mu da suka taso a cikin ƙunci da raɗaɗin maraici su suka san muhimmanci iyaye".
Furcin da ya gama saƙawa kenan cikin ransa yana gyara kwanciyarsa tare da runtse idanunsa saboda wani masifaffan ciwon kan da ya sauƙo masa.sunan mahaliccinsa ɗari ba ɗaya ya fara ambata cikin bakinsa har bacci yayi nasarar kwashar sa.
Tun ƙarfe uku da ya farka bai koma rintsawa ba ya ƙira Hajiyarsa suka yi waya kafin ya fara shirin tafiya asibiti,cikin farin suit ya shirya da ɓaƙin long sleeve a ciki haka nan ma neck tie ɗinsa jakar laptop ɗinsa da wayarsa da key ya ɗauka ya rufe part ɗin sannan yaje cikin mota ya ajiye jakar laptop ɗin ya nufi part ɗin Daddy.
Da sallama ya tura ƙofar falon yana tusa kai ciki,yana zaune yana sauraron labaran safe yana skipping coffe mai zafi ya iske shi ya tako har gaban ya durƙusa ya ladabtar da murya yana gaishe shi.
"Lafiya ƙalau Baban an tashi lafiya?".
Sai da ya ƙasa rusunar da ƙwayoyin idonsa ƙasa kana ya amsa da"Lafiya ƙalau Daddy jiya da dare ban shigo da wuri ba,daman wata magana ce nake neman alfarma akan ta".
Sosai Daddy ya bashi hankalinsa yana sauraron sa ya ɗaura da faɗin"Daddy ina so inka amince min tunda na kammala gini na,na koma can al'amuran zasu fi zuwar min da sauƙi tunda gidan yana kusa da asibiti".
Sai da Daddy ya kalle shi tsaf kamar mai nazarin wani abun kafin yace"wannan kaɗai shine dalilinka".
Jin haka kaɗai ya sanya shi yarda da cewar ƙorafinsa bai sama matsuguni a zuciyar Daddy ba,yasan daman abu ne mai wuya ya amince kansa kawai ya ɗaga masa zai ɗaura da wani maganar Daddy ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu yana faɗin"ya isa ba sai ka ƙara faɗin komai ba,menene yake faruwa a cikin gidan da har kake sha'awar barin cikinsa?".
Saurin ɗago kansa yayi ya ce"Daddy babu abunda ya faru kawai dai ina nemawa kaina sauƙi,saboda yanzu aiyuka sun min yawa sai dare nake dawowa shigowan dare bashi da daɗi sai wani ma ya zarge ka akan hakan".
Kansa Daddy ya jinjina na wani lokaci kafin yace"Zayyad bazan maka lamanin komawa wani wajen da zama ba a yanzu,ko don ciwon da kake ɗauke dashi kana buƙatar kulawa da sanya ido sosai.ban bar ka ka koma ne kaɗai lokacin da ka fito da mata kayi aure sai ku yi tafiyar ku amma ba yanzu ba".
Ba zai iya musayan kalamai da Daddy ba don ko haɗa ido har sai ta kama yake iya jefa nashi cikin nasa,don haka ya ce"In sha Allah bazan ƙara tada wannan maganar ba nagode da kulawar ka a gare ni,a tashi lafiya ni zan tafi asibiti".
"To Zayyad Allah ya kiyaye,na ji yanda kayi ruwa da tsaki cikin case ɗin Adam har sai dai kaga ya dawo gida".
Cak!ya tsaya daga ƙoƙarin tashin da yake son yi babu mahalukin da yasan shi ya fito da Adam daga cell,daga Baban Nana sai Lawyern dake kan case ɗin.yayi imanin Baban Nana bazai taɓa faɗin duk abinda ya surranta ba to yaya akayi Daddy yaji wannan labarin?".
Tambayar da ya jefa kansa kenan da ya kasa samarwa kansa da amsar ta yafi muryar Daddy sun bugi dodon kunnuwansa.
"Kana mamakin inda naji labarin ko?"saurin ɗaga kansa yayi alamar eh,Daddy yayi dariya sosai kana yace"Babu komai ka kyauta kuma hakan da kayi ka ƙara tabbatar min da cewar ko bayan raina,bani da fargaba domin zaka kula da ƴan-uwanka jeka kar ka makara zuwa wajen aiki".
Duk Daddy ya gama shayar dashi ruwar mamaki haka yayi masa sallama ya fita,ya wuce cikin parking lot yayi wa motar key ya fice izuwa asibiti.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________________
Page 3⃣0⃣
Ina zaune na cusa kaina tsakankanin gwiwoyina nayi nisan kiwo cikin kogin tinanin da kwakwalwata ta dulmiya,sautin karatun suratul Yusuf yana tashi cikin sifikar MPn da take aiki.
idan lissafina yayi daidai a yau satina uku da kwanaki biyar a cikin wannan wajen wanda hakan yake nuni da cikin dake jikina yayi wata biyu da kwana biyar.
Sautin kukana ya ƙaru da na tina Daadata da kuma sauran ƴan-uwana,Allah kaɗai yasan irin halin ƙuncin da take a ciki daga Abba da kuma sauran mutanen unguwar mu bana buƙatar sai an faɗa mini domin nasan izuwa yanzu wataƙil Abba ya ɗaura mata dukkan laifin da daga ita har ni bamu san hawa ba balle sauƙa.
Kaina ya koma sarawa wanda hakan ya tilasta mini runtse kumburarrun idanuna,ina jin yanda zazzaɓi yake ƙoƙarin rufe ni ga balaƙaƙƙen yunwar da nake ji tun sanda na farka duk abincun da ya bar mini na cinye shi tas!wani irin ci na fitar hankali cikin ya saka ni.
Na ɗan shafa ƙasan marata sosai cikin ya fara ɗago rigata,jin kamar za'a turo ƙofar a shigo ya sani buɗe idona da na runtse su ina kafe hanyar shigowar da kallo.
Caraf!idanun mu suka sarƙe cikin na juna nayi saurin kawar da nawa gefe guda,ina ƙara takurewa cikin hijabina mazauninsa ya wuce kansa tsaye ya zauna yana dafe goshinsa da jijiyoyin kansa suka fito raɗa-raɗa tun daga inda nake zaune ina iya jiyo yanda sautin numfashinsa yake fita da wani irin ƙara gu!guu.
Na sata kallonsa na ga har yanzu bai ɗago kansa ba,na share shi ina cigaba da tufka da warwara a cikin raina don ni kaf! tinanina masu kuɗin nan basu da wata matsalar rayuwa da take damunsu.
Ƙaran buɗe ƙofar naji yayi ya fice na bi bayansa da kallo ina sauƙe ajiyan zuciya,bai ɗau lokaci ba ya dawo hannunsa riƙe da ƙatuwar leda yazo ya dire ta a gaba na.
"Ɗauki kici zamu yi magana tunda naga alamar ke ba'a koya miki gaishe da na gaba dake ba".
Muryarsa suka yiwa ƙofofin kunnuwana diran mikiyi na ɗago na kalle fuskarsa da ya ƙara tsuke ta,nikam zan iya rantsewa akan cewar ban taɓa ganin annuri akan fuskar ba sa tun da SALON ƘADDARATA ta haɗa ni dashi,cikin sanyin yanayi na ce dashi.
"Ina kwana an tashi lafiya".
Bai kula ni ba illa juya mini baya da yayi,na jawo ledar gabana na fara ci hannu baka hannu kwarya saboda yunwar da take ƙwaƙwular hancin cikina sai da naji na kai geji sannan na kwankwaɗi ruwar roba mai sanyi har kashe haƙuri yake yi na fara tsile yatsun hannuna ɗaya na bin ɗaya.
Ina gamawa muka haɗa ido dashi juyuwar sa kenan na rusunar da nawa ƙwayoyin idon saboda kunyar da ta zo mini a lokaci,na tattare take-away ɗin na ƙunshe cikin ledar sannan na shiga banɗaki na ɗauraye hannuna na koma na zauna ganin ya ƙi min magana ya sani faɗin.
"Na gama kace za muyi magana".
Sai da ya ƙare wayar da yake yi,wanda ko lura da ita ban yi ba haka nan ban tsinci komai daga ababaɗen da take faɗa ba saboda cikin harshen turanci yake yin maganar na sake baki ina bin yanda yake motsa leɓɓansa idan zai yi maganar.watau shi fa mai ilmi duk inda yake abin ban sha'awa ne take naji raunanniyar zuciyata ta kuma tarwatsewa ina ma Abba ya goya mana baya munyi karatu,ina ma ya tsaya mana akan harkan karatun mu kamar yanda ko wani uba yake yi wa ƴaƴansa.
Ban san sanda na fara sakin ƙwalla ba sai ji nayi yana faɗin"Malam ba kuka nace ki sa ni a gaba ki min".cikin zafi yake maganar wanda ya sa ni saurin haɗiye raguwar kukan da suke shirin fito mini ba shiri.
"Menene kika ce sunan ki?".
Ciki-ciki cikin kukan da bai gama saki na ba na ce"UMMUKURSUM".ya jinjina kansa yana zama kan kujerar da take fuskanto ni dukka hannayensa ya naɗe a ƙirjinsa kafin yace"Wunti stree shine unguwar ku a cikin Bauchi haka ki ka ce ko?".
Kaina na ɗaga masa saboda kukan da yake ƙoƙarin taso mini,saboda sunan unguwar da ya faɗa ya tino min da irin rayuwar da na gudanar cikin unguwar a nan rayuwata ta soma har izuwa lokacin da ƙaddara ta rabo ni dashi.
"Zanyi bincike akan labarin da kika bani,zanje bauchi sannan zan je unguwar ku idan na sama saɓanin abunda kika faɗa min to kiyi kuka da kanki".
Dakatawa yayi a nan wanda hakan da yayi ya antaya kwakwalwata izuwa duniyar tinani,gargaɗi yake mini koko kashedi ban kai ga samarwa kaina wannan amsar ba na kuma jin sautin muryarsa a cikin kaina.
"Zan kai ki gidan mu ki zauna a can har izuwa lokacin da zan kammala bincike na,sannan ba zaki kula kowa ba balle har ki saki jiki da mutanen gidan zama ne zaki yi na ɗan wani lokaci sannan zaki je ne a ƴar aiki koda wasa kar kiyi kuskuren furta cewar kin san fuskana kafin nan.duk abinda na faɗa kar ki ƙarya ta shi kuma kar wanda ya tambaye ki labarin ki ko kuma cikin dake cikin ki,ki faɗa masa kina ji na".
Ya ƙarishe maganar yana daka mini wata gigitacciyar tsawar da ta sani daburcewa lokaci guda,na ɗaga masa kaina alamar naji kuma nayi hadda duk sharruɗan da ya shimfiɗa min.shuru ya ratsa wajen na wasu daƙiƙar kafin ya kawar da shurun ta hanyar faɗin"Idan kika yi yunƙurin guduwa ki sani zan nemo ki a duk inda kika shiga matuƙar kina wannan ƙasar".
"Bazan gudu ba koda zaka dunga tsaga naman jikina ne,na shirya fuskantar ko wani irin ƙalubane akan wannan cikin domin shine ƘADDARATA da ya yanke mini duk farin-cikin rayuwata yake ƙoƙarin kifar da rayuwata izuwa duhun baƙin ƙunci".
Nayi jarumtar faɗa cikin sigar ƙarfafa kaina sai da ya ƙare mini kallo tsaf!.
"Baba buƙatar jin komai daga gare ki,domin babu wata kalmar da za kiyi amfani da ita wajen wanke kan ki daga kallon dattin da nake miki,tashi mu tafi ina da aiyukan da zan yi".
Magana ya yaɓa mini cikin azanci tabbas kalamansa sun yi nasarar tarwatsa ƙalbina har sai da hawayen da nake gujewa fitowar su suka kwararo akan dandamalin fuskana,suna kai kawo a tsakanin kunci da saman haɓata.na ciro leɓɓana na ƙasa da ƙarfi tare da rufe idona ruf!.
Sannan na miƙe tsaye ina gyara zaman hijabina a saman kafaɗata,na riƙo ɗan kwalina a hannu ya wuce gaba ina biye dashi a baya ya fita ta ƙofar da yake shigowa ba wanda ake masa bugu ya buɗe ya fita ba.
Rana ya saito saitin fuskana ina shaƙar iskan ƴanci ina ƙara baza idanuna a wajen shuke-shuke koraye shar-shar dasu,an gyara su cikin tsari ta hannun dama da hagu.kamar na ruga da gudu haka na ji naje na ga Daadata ko da daga nisa ne na hango to na cimma muradin raina na sauƙe wata gwauruwar ajiyar numfashi dai-dai nan muka iso gaban wata mota.
Farar ce sol motar,sunkuyar da kaina ƙasa da nayi ya bani damar gano tayonta da suma suke a tsaftace a jikina naji cewar idonsa yana kaina don haka na ɗago ya ƙara ware min idon yana faɗin"Komai zai an faɗa miki shiga mana".a ɗan zafafe yayi maganar hakan ya ƙara wulla tsanar halayyarsa a cikin kogon raina.
Na jawo murfin ƙofar motar na shiga gidan baya sannan na ga shima ya zagayo mazaunin driver ya zauna ya gyara mirron dake gaban motar yana hasko ni.
"Ina fatan kinji abunda na faɗa miki babu buƙatar sai na maimaita?".
"Naji".
Na amsa dashi a taƙaice cikin muryar kukan da ke ƙoƙarin ƙara zuwar mini,waya ya ɗaga yana faɗin"An aiko clearnes sun gyara min office ɗina kafin na dawo a buɗe take".
Yana kawowa nan ɗif!ya katse wayar yana ajiye ta gefe guda naga ya ɗaura belt sannan ya ta da motar aka buɗe masa gate ɗin ya fice ban lura da inda ya taɓa ba sai ji nayi wani sanyi mai ratsa jiki ya fara shiga na ya saka faifayin saket ɗin karatun sheik Afif Muhammad a cikin radion motar.
Ina yawan ganinsa a cikin Tv in naje gidan Anty Sakina,saboda kusan kullum naje sai na tarar da ita tana sauraron karatunsa muryarsa ta ƙira'a tana mini daɗi da muka sanyin yanayinsa gami da nutsuwar da yake yayin da yake jero karatun littafi mai tsarki.don haka na ƙuƙuta na tara ƴan kuɗaɗena na bawa Sagir na ce ya sayo mini memory card na kai aka turo mini karatunsa sosai a cikin kullum ya zamana shine abin ji da sauraro na har yanayin karatuna ya koma irina nashi.
Wani wawan burki ya taka wanda ya sa ni yin luu! na wantsilo na yo gaba sannan na koma da baya,ta cikin mirron ya gallo mini harara tare da faɗin"Malam ki saka belt ɗin kujerarki".
Take na fara kiciniyar ƙwaƙumawa kaina belt ɗin na ɗaure jikina da ita,ni kaina nasan ban saka dai-dai ba amma haka nan na bar ta.na maida hankali a titin sai wuce shataletale muke yi ga dogayen solar a ko'ina tabbas nasha kallo kuma na ƙara gaskata kyawun garin kaduna a raina.
Bakin wani ɓakin gate naga ya ja ya tsaya wajen shuru kamar unguwar bai tara mutane ba da yawa,aka wangale masa gate ɗin ya tura hancin motar izuwa cikin farfajiyar gidan cikin wani ɗan rumfa naga ya saka motar sannan ya kashe ta.bai yi magana ba haka nan bai bani umarnin fita ba don haka nima na dake cikin motar ina ƙara more sanyin cikinta.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________________
page 3⃣1⃣
Bazan iya ƙidaye mintunan da muka ɗauka a haka ba,bai ce dani ko kanzil ba haka nan nima ban yi gigin furta wata kalmar ba sai can naga ya since belt ɗinsa ya tura murfin ƙofar ya fita nima kuwa nayi caraf!na bankaɗo ƙofar na fito.
Ya watso mini idanunsa da suke matuƙar sanya ni cikin firgici da ruɗewa, ina jin sautin da siririn tsakin da ya saka ya bada na ƙara takure kaina cikin hijabina da ya sauƙa mini har ƙasa ya fara tafiya ina biye dashi a baya har izuwa cikin wani fili mai yawaitan sirrai masu ɗaukar ido da kuma sanya nishaɗi.
"Baba sannu da aiki".
Ya furta yana ɗan sakin fuskarsa wanda ya ƙira da Baban ya ɗago tare da faɗin"Yauwa sannu yarona an dawo?",ya faɗa yana bi na da idanu.
Kansa naga ya ɗaga masa yana ɗaurawa da faɗin"Baba ga wannan ƴar aikin da Hajiyata tace a samu mata ne shine yau wacce take kawo ƴan aikin ta ƙira ni akan an samu wata,shine na kawo ta nan kafin Hajiya ta dawo daga saudiyya".
Kalle ni yayi tsaf! har sai dana tsargu da kaina na lura shima sai da ya tsargu da kansa ganin kamar bai yarda da maganar ya da faɗa masa ba.nayi saurin zubewa ƙasa ina fa ɗin"Ina wuni".
Ya ɗan murmusa kana ya ce dani"ina kwana dai ko yanmata".
"In-in-ina kwana".
Na furta maganar a rarrabe kamar mai koyan magana,yace dani lafiya kaina har yanzu yana ƙasa na jikina ya fara rawa ina ƙoƙarin samarwa kaina nutsuwa naja dogon numfashi na fesar sannan na ɗago idona saboda maganar da ya fara.
"Baba bari na shiga da ita".
Ya ɗago yana kallonsa sannan ya ce dashi"To ZAYYAD a fito lafiya,yarinya sannu ko meye sunanki?".
"UMMUKURSUM"na faɗa ina ɗan ƙara rusunar da idanuna ƙasa tare da ƙara maimata sunan da ya ƙira shi dashi zayyad a cikin raina,yau ne karon farko da naji sunansa.ganin ya fara tafiya yasa ni miƙewa ina biye da shi a baya kamar jela duk inda ya sauƙe ƙafarsa zan saka tawa har izuwa wani sashi mai girma har mun kai ga ƙofar sai kuma ya juyo yana kallo ni,wanda hakan ya sanya ni ja baya da taku biyu.
"Ina fatan kinji abubuwan da na faɗa miki,har ki kuskura ki sanar da wani ko wata a cikin gidan nan labarin rayuwarki.ni zan tsara komai kuma kowa ya tambaye ki haka zaki faɗa kinji ko?".
Nayi sauri gyaɗa masa kaina ya jinjina mini kansa sannan ya murɗa mariƙin ƙofar tare da tura ta,ya shiga ina take masa baya babban waje ne sosai don na bawa idona abinci ta hanyar ƙarewa duk wata kusurwa kallo.gaban wani farin dattijun da alamon manyanta suka fara bayyana a kan fuskarsa mai cike da kamala ta hanyar farin gashin da ya fara lulluɓe masa fuska,naga ya zauna nima na ƙariso zan zauna naji an daka mini tsawar da ta sanya hantar ciki kaɗawa.
"Ke!Baiwar Allah dakata bakya ganin dattin da ke cikinki ne zaki hau min kan carpet dalla tsaya a tsaye ko ki fice ki jira shi a waje".
Tsam!na miƙe jikina kamar mazari sai a yanzu na lura da zamanta a cikin falon,tana zaune tana fuskantar makeken talabijin ɗin dake maƙale cikin bango yana aiki a kallon ɗayan da na mata na gano fatarta da tayi jajir duk ta mele alamar ta gaji da jin mayukan bleaching.ta ƙarishe maganar tana wulla mini wani irin kallon tsana da ƙasƙanci wani na bin wani.
"Haba!Hajiya Aisha shi fa ɗan adam ba abun wulaƙantawa bane domin Allah da kansa ya girmama shi,kinsan me yake tafe da ita ne ko ko kinsan dalilin da ya sanya ya shigo da ita?".
Ko kallon arziki bata mishi illa ɗauke kanta da tayi tana maida shi izuwa ga kallon da take yi,kansa kawai ya jijjiga kafin ya dawo da gubansa izuwa ga Zayyad yana faɗin"Zayyad wacece wannan?".
"Abbu mai aiki ce da Hajiyata ta sa a nemo mata shine aka kawo kuma ta tafi saudiyya,shiyasa nace bari na kawo ta nan ta zauna kafin ta dawo".
Idanu naga duk sun zubo mini kamar zasu cinye ni kafin shi Abbun yace"ƙwarai nasan ta tafi saudiyya don ta ƙira ni ta sanar dani, ba matsala sai ta zauna ɗin a nan kafin ta dawo amma naga kamar yarinya ce ƙarama wacce ya kamata ace yanzu tana gaban iyayenta tana makaranta".
Lagwanshe yatsun hannayensa yayi har sai da suka yi wani ɗan ƙara kash!,kana ya soma faɗin"Abbu bazawara ce sannan kuma marainiya ce,mijin ya rasu ya barta da ciki shiyasa ta fito neman wannan aikin".
Shuru ya ratsa wajen kafin Abbu ya katse shurun ta hanyar faɗin"Allah ya musu rahama sai ta zauna ɗin har lokacin da zata dawo,Hajiya sai a kaita part ɗin sauran ma'aikatan ta zauna a can".
Caraf!ta karɓe zance ta hanyar miƙewa tsaye tana faɗin"ta zauna a ina wai mace har da ciki aikin me zata iya yi,domin kuwa indai zata zauna a cikin gidan nan dole ne tayi aikace-aikace".
Ganin Abbu sai mayar mata da martani ya sani saurin faɗin"Hajiya zan iya shiyasa na fito nema".koda da ban ɗago idanuna ba a jikina ina jin yanda take bina da wani irin mungun kallo muryarta da suka sauƙa a kunnuwana suka katse mini hanzari.
"Ɗauko kayana ki,ki biyo ni".
"Bani da kaya ban zo da su ba".
"Ke anya kin shirya wannan aikin kuwa?".
Ta kuma jefo mini wata tambayar kafin na kai ga bata amsa Abbu yace"wuce ki tafi kinji ƴata".
Na ɗauki hanya ina bin ta a baya muka fice ta wani ƙofa da ya sada mu da wani sasi ɗan madaidaici ta ƙira wata wai ita SARAUNIYA tace mata ta kai ni ɗakin su Mariya.
"Zayyad Ammieynku ta ƙira ni tana sanar da ni auren Ahmad ya kamata ka shirya muje gabaɗayan mu hadda Hajiya da su Haidar".
A hankali ya ɗago kansa yana ɗan murza zoben azurfan dake hannunsa yace"E Abbu nima ya sanar dani shi Ahmad ɗin".
Gyara zamansa Abbu yayi yana ajiye jaridar dake hannunsa kafin yace"zamu tattauna kafin lokacin,inka fita sai ka sayo yarinyar nan suturar da zata sauya tunda tace bata zo da su ba".
"To in sha Allah Abbu a huta lafiya".ya faɗa yana miƙewa tare da barin cikin falon sosai ya sauƙe wata shirgigiyar ajiyan numfashi ya lumshe idanunsa da suka ƙara ƙanƙancewa ganin tsayiwar ba zata haifar masa da ɗa mai ido ba ya sanya shi jan ƙafafunsa da suka yi nauyi kamar basa jikinsa yayi part ɗin ganin ƙofar falon a buɗe tun daga nan ya san ba lafiya ba bayan yasan da hannunsa ya kulle ƙofar da safe kafin ya tafi office.
Saurin isa cikin bedroom yayi ganin yanda aka hargitsa ko'ina a cikin falon,yana isa ya fara rarraba idanu tare da ƙara sanƙarewa a wajen ya kasa gaba ya kasa baya.ko'ina an hautsilashi alamar dai an shigo ɗakin an yi masa bincike hoton mahaifiyarsa da ya gani an yasar a ƙasa ya sanya shi ƙarisa shigowa ya ɗauka hoton tare da rungumewa a ƙirjinsa ya sulale ya zauna a wajen.
Da sauri-sauri zuciyarsa take harbawa dif!dif!!ya runtse idanunsa yana jin yanda wani irin abun da ya kasa fasalta shi cikin kalma guda yana bin duk jijiyojin jikinsa.kamar an tsigara masa allura haka ya miƙe yana nufar site drawer ɗin dake kusa da gadon ganin duk kuɗin ciki an ɗebe su ya sashi dawowa ya zauna yana sauƙe wata ajiyen zuciyan wata na bin wata.
Tabbas yasan takardun kaddarorin da Abbu ya bashi ajiyar su,su aka biyo domin kwashe su a ɓata shi a idon Abbu da duniya gabaɗaya.
"Wallahi baza ta saɓu ba bingida a ruwa ai ba shi kaɗai bane ɗa acikin gidan,da za'a ɗauki duk dukiyar a mallaka masa"
Kalaman Nenne kenan sanda Abbu yake jaddada jawabin cewar ya sanya sunan Zayyad akan duk kaddarorinsa,ko bayan ransa shine magajinsa sune suka fara dawo masa cikin lissafin kansa, da ya haifar masa da matsanancin bugun zuciya.
Ya daɗe a cikin wannan yanayin kafin ya ja jikinsa ya fara tattare ɗakin sai da ya gama kimtsawa,sannan ya koma falo shima ya tattare komai wanka ya shiga ya sakewa kanda ruwa yana ɗan runtse idonsa yana fitowa ya zara doguwar jallabiyan da ya sauƙa masa har ƙasa ko amai bai tsaya shafawa ba ya fito zashi masallaci gabatar da sallan zuhr sai da ya biya part ɗin Baban Nana ya ɗauko Iman suka tafi tare.Sabon masallacin da ƙungiyarsa ta ɗauki nauyin ginawa wanda za'a fara salla a cikin ta yau ya nufa.
Shi yayi musu limanci yayin gabatar da sallan sannan ya tsaya aka buɗe masallacin dashi aka yi mubaya'a aka sanya shi limamin masallacin,sai da ya tsaya har aka yi sallan asr sannan ya dawo gida bayan ya tsaya a wani katin yayiwa Iman siyayan Sweet da chocolate ɗin da yake saya musu domin zuwa makaranta.
Suna isa ya wuce sashin Baban Nana Hajju kawai ya samu ya gaishe ta sannan ya sauƙe Iman,tana masa godiya tare da tambayarsa akan sabuwar ƴar aikin da Baban Nana yake faɗa mata an kawo.
Kawar ta maganar yayi ta hanyar faɗin"Bari na shiga ciki,anjima zan koma asibiti ta juyu a can zan kwana".
Sanin halinsa ya sanya ta amsawa da to sannan ya wuce yana jin Iman da yake ta bata labarin an bawa Uncle Zayyad limanci.
Cikin garden ya nufa ya zauna akan shiryayyun kujerun plastic dake shirye a wajen,ya ɗaga wayarsa yana ƙiran sarkin gida akan yaje sashin mata ya ƙira masa sabuwar ƴar aikin da ya zo da ita yau.
Ina zaune cikin ɗakin da aka kawo ni,na kasa sakin jikina nayi wargi kamar yanda sauran suke yi duk motsin su ina bin su da kallo ne amma hankalina sam baya tare dasu yana ga tinanin da nayi nisan kiwo a cikinsa naji ana ɗan taɓo kafaɗata nayi figigi.na ɗago kaina naga SARAUNIYA CE kamar yanda naji sauran suna ƙiran ta dashi kuma sunan ya dace da, ita saboda yanda take zuba mulki a sauran ma'aikatan a ɗan awannin da nayi cikin gidan na fahimta ita komai yi mata akeyi tana daga zaune ta hakimce.
"Kije magajin Alhaji na neman ki".
Na tsura mata rinannun idanuna cikin rashin fahimta nace"waye haka?".ta ɗaure fuska tamau kana tace dani"Zayyad yana cikin garden dalla malama ki tashi kafin ranki ya ɓaci".ta ƙarishe zance tana zaro mini ido kamar mayya.
Na yunƙuro na miƙe ina ƙara hijabina sannan na taɓo wata da naji ɗazu Sarauniya ta ƙira ta da Mariya nace"Don Allah ina ne garden ɗin ban sani ba".ta maido mini da murmushi sannan ta fara kwantanta mini na mata godiya sannan na fito.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________________
Page 3⃣2⃣
Kwantance da ta mini na bi har nayi nasaran hango shi zaune akan kujera ya jawo ɗaya gabansa ya ɗaura ƙafarsa a kai,na ƙariso cikin wajen da sallama ya amsa ba tare da ya buɗe idonsa ba balle ya mini kallon kirki na iso na durƙushe a wajen kafin nace"Gani ance kana nema na".
Yayi banza da ni ba tare da yace dani uffan ba har na fara gajiya saboda zaman da nayi akan ƙafafuna sai naji duk sun sanƙare,na gyara ina ɗan langwashe su tare da runtse idona saboda zafin da naji.sai a sannan na ga ya ɗago kansa a wannan karon ɗin ma sakamakon rurin da wayarsa ta shiga yi ne yayi saurin ɗaga ƙiran yana karawa a kunnensa ya tashi ya ɗan yi nisa dani yana yin wayarsa.
Har na fara gyangyaɗi naji muryarsa a tsakiyar kaina yana faɗin"Magana nace zamu yi ba bacci nace kizo kina min ba".
Na mirtsike idanuna ina ɗan gyara zamana ya dawo ya zauna a mazauninsa na ɗazu yana fuskanto ni tare da haɗe hannunsa waje guda ya ɗan matsa su suna ƙara wanda daga ɗazu zuwa yanzu na fahinmci cewa hakan ɗabi'ar sa ne.
"Wani ɗaki kike?".
Na ɗan yi jim tare da ɗaga kaina sama ina ƙoƙarin tinano sunayen mutane ɗakin,can nace"naji dai sunan ƴan ɗakin akwai Sarauniya da kuma wata wai Mariya".ban sani ba ko kunnensa bai jiye masa abunda na faɗa da kyau bane ko meye oho!dan ganin nayi ya birkita ya mini wani kallo sannan ya ɗauke kana yana maimaita sunan Sarauniya can ƙasan leɓɓansa.
Na ƙara guƙar da kaina ƙasa ina ƙanƙanme jikina da sanyin wajen yake ratsa ni yana shiga cikin gaɓoɓina,har wani zazzaɓi nake ji yana ƙoƙarin lulluɓe ni.
"Bazan cigaba da maimata miki ba kar ki kuskura,ki saki jiki da kowa a cikin gidan nan balle har ki bari su shiga jikinki.duk wanda ya tambaye ki labarin ki to ki kar maganar da zaki yi ya bambamta da wanda nayi a gaban Nenne kina ji na ko?".
Nayi gaggauwan ɗaga masa kaina ina jin ɗumin wasu sirarun hawaye suna biyo gefe da gefen kuncina,wanda nima kaina a lokacin ban san dalilin zubar su ba.na ɗan sata kallonsa naga ya miƙe ya juya mini baya ya dafe goshinsa da hannunsa ɗaya mintuna biyar a tsakani bai ce dani ko kanzil ba har zaman ya fara dungura na ga kuma zazzaɓin da yake saɗɗata.
Sai da ya dawo ya zauna ya tallafo kuncinsa da duk hannayensa kana ya ɗauki wayarsa ya shiga dannawa,cikin baccin da ya fara fisgana na jiyo muryasa yana faɗin.
"Kace wa Sarauniya ina neman ta yanzu".
Iya abinda kunnuwana suka jiye mini kenan na ga ya ajiye wayar gefe guda,ba a ɗau wani lokaci ba na hango Sarauniya ta nufo wajen ta iso ta rusuna tan faɗin"Yallaɓai gani ance kana nema na".
Shuru yayi kamar bai ganta ba,sai da ya ƙarishe izzarsa kafin ya shiga faɗin"Ina fatan an sanar da ke cewar wannan ba mai aikin gidan nan bace,ta gidan Hajiyata ce na wani ɗan lokaci zata zauna a nan".
A hanzarce ta amsa da faɗin"e yallaɓai naji wannan labarin bakin Hajiya".
"Don haka bana son tayi ko wani irin nau'in aikin cikin gida,ko fita daga ɗaki bana so ta yi ki kula da wannan saboda yana ɗauke da juna biyu".
Ya ƙarishe zancen yana watso mata idanunsa,kanta ta ɗaga masa tare da basa tabbacin zata kula da hakan kafin na ga ya turo wasu kuɗaɗe daga aljihunsa ba tare da ya irga ba ya miƙa mata,jikinta har yan rawa ta matso kusa ta karɓa sannan tace mini na taso mu tafi.
Na miƙe jiri yana ɗiba ta na tafi luu! tayo kaina ta riƙo ni ta mini shinge da jikinta,ta shiga jera mini sannu tare da ƙara riƙo hannuna.
"Kije da ita zansa sarkin gida ya kawo mata magani".
Har muka isa sashin ƴan aiki yana riƙe da ni,muna isowa bakin ɗakin ta hantsilo ni daga jikinta nayo ƙasa na faɗi,nayi saurin ɗago kaina ina kallonta da raina cike fal da mamaki saboda yanda ta nuna mini kulawa a gaban Zayyad.
"Ke ki kasa kunne da kyau ki saurari abinda zan faɗa miki,gidan nan ba'a huto sannan kar kisa rai da samun taimakon kowa dole ki yi aiki tunda kika shigo cikin gidan.juna biyun da kike ɗauke dashi babu abinda ya sha mini gaba dashi ".
Idanu na tsura mata cikin zallan rashin fahimtar da ta bayyana ɓaro-ɓaro akan kumburarriyar fuskata,na zaro mini idanunta manya sosai da suka sanya hantar cikin kaɗawa.
Ƙas!ƙas!! shine sautin da taunar chewgum ɗin da take yi yake badawa,ta zara kuɗin da ya bata cikin rigar mamanta sannan ta shige cikin ɗaki ta shure mini ƙafata na gwaru da jikin ƙofan na runtse idona ina ƴar yarfa hannuna cikin azaban da nak e ji a cikin jikina.
Duk yanda naso na tashi daga wajen amma zuciyata ta ƙi bawa gangar jikina haɗin kai,wajen aikawar dashi haka na zauna a wajen a yashe har izuwa lokacin da sallamar da sarkin gida yake dokawa suka sauƙa a ƙofofin kunnuna na ɗago kaina na masa kallo ɗaya sannan na kawar da idona gefe.
Da sauri ya iso gare ni yana salati tare da tambayata abunda ya faru,maimakon na bashi amsa sai tsananta hawayen da nake yi nayi,tabbas rayuwa ta juya mini juyi-juyi mafi tsauri da wuyar jurewa yau nice na tsinci kaina a wani rayuwar da ko a mafarki ban taɓa tinanin samun kaina cikin sa ba.
Na ɗauki ciki a jikina na kuma sinci kaina cikin wasu irin mutane da na gaza fahimtar wata alƙibla suke kanta.balle har sun fahimce ni.
Maganar da ya kuma yi ya sani dawowa cikin tinanina, nayi figigi na ɗago ina kallon fuskarsa,bakinsa kawai nake gani yana motsi amma ko za'a sanya mini wuƙa a wuya bazan ce ga abinda yake faɗa ba.
Ya miƙe ya shiga ciki suka dawo tare da Mariya tayo kaina da saurin ta,tana ɗago ya mini matashi da cinyoyinta.
"Ki shiga da ita ciki ga maganin nan sai ki bata ta sha".
Ya faɗa yana miƙa mata ledar dake hannunsa da ya shigo da ita a tare dashi,ya taɗo ni muka shiga cikin ɗakin ta kwantar dani saman katifar ta sannan ta ɗebo mini ruwa ta ɓallo min maganguna ta miƙo mini.na ɗan ɗago kaina na karɓa maganin na bi bayansu da ruwa sannan na koma na kwanta ina sauƙe numfashi wata na biyo bayan wata.
Ta fita ta dawo ɗauke da tray a hannunta,ta dire a gabana tana faɗin"ga abinci ki daure ki tashi kici".
Bana jin ko nayi yunƙurin furta wata kalma bakina zai bani haɗin kai wajen jin hakan,don haka na gyaɗa mata kaina alamar bazan iya saka komai cikin cikina ba a halin yanzu.
"Dan Allah ki daure kici abincin nan,naji ɗazu Sarauniya tana cewa kece sabuwar ƴar aikin da aka kawo mai ɗauke da ciki,ko dan ɗan da yake rayuwa a cikinki ya kamata kici".
Ta ƙara faɗa a karo na biyu da ya sani yunƙura na fara ƙoƙarin tashi zaune,ta taimaka mini ta hanyar saka min matashin a bayana inda don ta ni ne kam bazan ci wannan abincin ba,amma tun daga lokacin da na fahimci cewar sai naci sannan ɗan cikina shima zai samu yaci ya zama mini dole na tusa abinci ko bana jin daɗinsa.
Tray ɗin na jawo gabana na fara ci a hankali,naci ba kaɗan ba sannan ya ajiye gefe ta kallo ni da fara'ar da ya fito fara-fara akan fuskarta ta ce dani"Yauwa yanzu ko ke fa,amma ko sunan ki ban sani ba".
"UMMUKURSUM".
Na faɗa a taƙaice saboda maganar ma tana son ta gagare ni ta ce"ni kuma sunana Mariya kinga sai muyi ƙawance kafin ki tafi".
Na gyaɗa mata kai don tun ɗazu naji sunanta a bakin Sarauniya ita ta ɗauke ragowar abincin da na bari ta fitar,bata dawo ba har bacci ya fara ɗauka ta.
Zaune yake cikin garden ɗin ya kasa taɓukawa kansa komai tun lokacin da Sarkin gida yazo ya sanar dashi a halin da ya same ta a ciki,cusa hannayensa yayi cikin sumar kansa yana birkita su tare da furzar da wani zazzafan iska daga bakinsa.tabbas ya aikata babban kuskuren da bai taɓa aikatawa ba a tarihin rayuwarsa bai taɓa yiwa Abbu ƙarya ba sai yau kuma ƙarya har ya sa ko da sunan Hajiyarsa a ciki.
Duk da yasan ba lalle bane Abbu ya ƙira Hajiyarsa ya tambaye ta a game da yarinya,ko shakka babu yasan dukkan sun ɗaura yarda mai tarin yawa,a hankali ya zame hannunsa daga cikin sumarsa yana ɗan karkaɗa kansa dole zuciyarsa tak ayyana masa akan ya binciko labarin rayuwarta lokacin da yake dashi wajen gudanar da bincike kuwa kafin Hajiyarsa ta dawo daga aikin Hajji ne zai yi komai ya gama yana sa ran kafin lokacin ma ta haihu duk da kuwa har yanzu bai san adadin watannin cikin ba.
Dole yaje bauchi tunda auren Ahmad ya matso kuma dole ta sanya matakan tsaro akan yarinya kar yayi gudun gara kuma ya tar da zago, don yasan matuƙar Adam ko Haidar suka san da zamanta cikin gidan sai sunyi ƙoƙarin kawar da ƙishiruwar su akan ta.a hankali ya zame hannunsa daga cikin sumar kansa,yana tallafo kuncinsa da shi ya ɗau lokaci cikin wannan yanayin dashi kansa ya kasa fasaltawa cikin kalma gudu, kafin yayi azaman miƙewa ya ɗauki hanyar part ɗinsa yana dialing numbern Hajiyarsa har ƙiran ya tsinke taba ɗauka ba.
Yana isa cikin part ɗin ya yada zango a falo, kan doguwar kujerar three siter ya zauna yana sauƙe wata ƙaƙƙarfar ajiyan zuciya yana daga zaunen ya jawo remote ya kunna Tv ya sanya ƙira'ar sheik Muhammad afif lumshe idanunsa yayi yana jin sautin karatun yana ratsa ko'ina a cikin jikinsa.
Ban zan iya ƙayyadai tsawon lokacin da na ɗauka ina baccin ba, sai jiyo sautin kuka nayi na farka a firgice da ni da sauran mutanen da idanuwana yayi mini tozali dasu a cikin ɗakin suna zazzaune kuma fara rige-rigen fitowa daga ɗakin domin kashe ƙwarƙwatar idon mu ta hanyar ganin abinda ke gudana.
Wata budurwa na hango Sarauniya tana jan ta da ƙarfin tsiya,tana kuka haɗi da jeranta mata magiya amma ko ta kan hakan bata bi ba,har ta fice da ita daga cikin wajen duk muka bi su da idanu cikin babu wanda yace dasu uffan balle yayi ƙoƙarin ba wa Sarauniya haƙuri.can ba gano Mariya a aikin rarraba idanu da na shiga bazawa a wajen na isa gare ta,itama ganin na nufo ta yasa ta ɗaukar hanyar da zai sada ta dani.
"Mariya menene yake faruwa ita kuma wannan ina za'a kai ta haka?".
Tambayar da bakina yayi gaggawar furta mata kenan,duk har yanzu gangar jikina ta kasa sakewa da yanayin gidan balle mutanen da suke rayuwa a cikinsa,ta ɗan yi jim ba tare da ta amsa mini tambayata ba ganin bata da niyyar amsawa ya sani ƙara maimaitawa a karo na biyu.
"Wajen Hajiya za'a kai ta domin ta ɗebe mata kewa, ko wani dare ana kai mata mutum ɗaya daga cikin mu".
Shine abunda ta furta mini cikin rawar murya sakamakon ruwar kwallan da suka ciko mata idaniya. fuskana fal! ɗauke da mamakin da ya kasa ɓoyiwa na kuma cewa da ita"wani irin kewa Mariya ban fahimta ba?".
A wannan lokacin sai da kwallar da suka ciko mata idaniya suka kwararo, ban sa ni ba ko tambayar da ba mata ne har ya kai mizanin da zai soki zuciyarta har ya haifar mata da fitar kwallar ta amsa mini cikin faɗin.
"Ɗebe kewa kamar yanda take faɗa, ta hanyar saduwa tsakanin mace da mace".
Sakeke nayi ina bin ta da kallo kamar ina ƙidaye duk wani ɗigon ruwan hawayen da yake zubo daga idaniyarta.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________________
page 3⃣3⃣
Muryar Sarauniya da naji ya ratsa har cikin ƙoƙuwar kaina, ya tilasta mini ɗauke idona daga kallon ƙurillan da nake yi wa Mariya.
"Ku kuma me kuke aikatawa anan, ke Mariya ki kwana da shirin gobe ke zaki je sashin Hajiya".
Furcinta suka ratsa ƙofofin kunnuwana sautin kukan da Mariya ta saka ya sanya jikina ɗaukar rawa, tsakanin kuka,mamaki,takaici,baƙin-ciki na kasa bambamcewa wannan zan iya a dai-dai wannan sa'in.ban ankara ba naji Mariya ta cafko hannuna tare da jan sanƙararren jikina muka nufa ɗaki muna shiga ta sake ni ta faɗa kan katifarta tana sakin kukan da ya karaɗe dukkan ɗaki.
Can gefe guda na nema na zauna saboda ƙafafuna da suka fara butulcewa ɗaukar nauyin gangar jikina,na sauƙe wata gauruwar ajiyan zuciya da ta ba wa kukan da yake maƙale ƙasan maƙoshina gaban tsiyaya kamar yanda nima ban yi wani ƙudirin hana su zuba ba.
Ɗaƴar ƴar ɗakin da naji ɗazu Mariya ta ƙira ta da suna Zainab, ta shigo kallo ɗaya da na ɗago kaina na mata na hango irin tashin-hankali da yake tattare da ita.kusa da Mariya ta zauna sannan ta fara abinda ni na kasa yinsa watau ba wa Mariya haƙuri tare da lallashin zuciyarta.
"Mariya yanzu nazo wucewa nake jin,ƴan ɗakin su Amira suna faɗin wai Sarauniya tace gobe ke zaki je sashin Hajiya haka ne?".
Kanta kawai Mariya ta ɗaga mata, tana ƙoƙarin miƙewa zaune daga kwanciyar da tayi Zainab ta soma share mata hawayen da yake gudana akan dandamalin tudun fuskarta tana ɗaurawa da faɗin"Mariya dan Allah ki daina wannan kukan ya isa haka, haba! ai wannan abun idan sabo ya kamata ace yanzu mun saba ƘADDARAR mu ce mu kuma tazo a haka dole sai mun aikata hakan kafin mu kai ga samun abincin mu".
Sai a sannan Mariya ta yi magana saɓanin da, da take bin bakin Zainab da kallo tana furta zantukanta daki-daki.
"Zainab wallahi na rasa yanda zanyi da rayuwata, na rasa ina zan nutsa kaina a wannan duniyar naji daɗi.ko Ummanmu ina je mata da wannan maganar sai tace naje na cigaba da aikina kuɗaɗen da Hajiya ta nika mini na albashina sun rufe mata ido".
Ta ƙarishe zancen cikin raunanniyar muryar da take bayyanar da rauni har cikin zuciyarta ne,suka rungume junansu suna kukan sun ɗau lokacin a haka kafin Zainab tayi nasarar ɓanɓare Mariya daga jikinta, ta tallafo fuskarta da hannunta kana tace"Mariya mun cigaba da haƙuri wata rana sai labari, in sha Allah komai ya kusa wucewa bari naje ina da aiki a ƙasa".
Tana kawowa nan ta miƙe ta fice daga ɗakin tana sharce ragowar ruwar ƙwallan da suke akan fuskarta,sai a sannan nayi yunƙurin jawo jikina amma gangar jikina yaƙi bani haɗin kai wajen aiwatar da haka, na rarrafo har na iso bakin katifar na riƙo hannunta nasa cikin nawa sannan na cilla ƙwayoyin idona da suke ganin dishi-dishi har wani zafi-zafi suke mini cikin nata.
"Mariya yau ne farko shigowata cikin gidan nan,ko kwana ban yi ba amma na fuskanci ababaɗe masu tarin yawa game da yanda rayuwar gidan take gudana. menene ɗebe kewa kuɓa menene maƙasudin yin sa?".
Ta ɗan yi jim kamar bata da niyyar amsa mini tambayar, sai can ta ce dani"Ummukursum duk wata ƴar aikin da kika gani a cikin gidan nan, ko sai Hajiya ta sadu da ita saduwa tsakanin mace da mace. duk ba'a son rayukan mu bane amma babu yanda muka iya kuma abu mafi ban mamakin shine kamar ta ɗinke mana baki domin bama iya tattauna maganar da kowa balle har mu samawa kanmu mafita, bata barin mu mu riƙe ko wacce irinyar waya balle mu sama damar sanar da wani namu halin da muke ciki in zamu yi waya sai dai muje wajen Sarauniya".
Sai da ta tsagaita saboda kukan da ya taso mata mai matuƙar sauti da amonsa ya amsa ko wacce kusurwa ta ɗakin,sai ta dayi mai isher ta har ta godewa Rabbil izzati kana ta ɗaura da faɗin"Duk wacce ta amince da ƙudirin Hajiya to, ta kan ninka mata alabashinta sau biyar kuma zata bambamta daga cikin sauran ma'aikatan ta hanya bata nata ɗakin ita ɗaya da kuma wasu abubuwan more rayuwa".
Mutuwar zaune naji a wajen, na saka motsa ko wani gaɓa daga jikina hannuna da ya sanƙare kamar dutsi nayi nasarar jawowa ina toshe bakina.gaɓoɓin jikina suka ƙara yin sanyi ƙalau duk suka mutu ina jin su tamkar basa jikina duk yanda labarin da ta bani ya taɓa mini zuciya game da ratsa ilahirin gaɓoɓin jikina duk yabi ya kashe su amma na kasa zubda koda ɗigon ruwar ƙwalla ne.
Na runtse idanuna saboda yanda zuciyata take mini soya kamar garwashin dake ƙasan tukubar tsire, tabbas nasan cewar a wannan lokacin kukan zuci nake wanda yafi ƙona da sanya raɗaɗi ga mai yin shi. hannunta kawai na ƙara damƙowa cikin nawa na riƙe gam! na kasa furta mata komai.
"Ku kuma wani sabon salon munafircin kuke ƙullawa a nan,Mariya naga ke rawar kanki ƙara hauhawa yake yi a kullum to ki kasa kunnuwa ki saurari abunda zan faɗa miki. ki fita harka wannan yarinyar dole ita ba zama ya kawo ta ba".
Furcin Sarauniya kenan da muka jiyo shi kamar a tsakiyar kanmu tayi shi,kafin na yunƙura nayi wani ƙwaƙwaran motsi Mariya har ta miƙe ta zare hannuwanta daga cikin nawa.abu ɗaya da na kuma lura na hankalta dashi a wannan lokacin shine sun matuƙar tsoron Sarauniya da kuma bin duk maganar da ta shimfiɗa kamar wahayi daga Allah.
"Sarauniya ba-ba-ba babu abinda muke tattaunawa,daman nazo na tashe ta ne tayi salla saboda naga lokaci zai ƙure".
Mariya ta furta cikin muryarta da jikinta da yake rawa kamar mazari,sai da ta ƙare mana tanadi tsaf! daga ni har Mariya ta hanyar bin mu da kallon tuhuma kafin taza wata doguwar tsaki mai dogon zango tana ficewa daga ɗakin.
"Ga can banɗaki ki shiga kiyi alwala lokacin salla yayi".
Iya abunda ta faɗa mini kenan tana ɗaukae hanyar ficewa daga cikin ɗakin,na bi ta da idanuna da suka ƙeƙashe ruwan cikinsu ya ƙafe ƙarƙaf na sauƙe wata gigitaccen ajiyan zuciya ina saƙala kaina cikin gwiwoyina.
Na ɗau tsawon mintuna a haka ba tare da na motsa daga inda ta bar ni ba, kafin nayi na ɗago kaina ina tsaida idona akan tagar ɗakin naga garin yayi duhu alamar magriba ta daɗe ta wucewa na miƙe da hanzari cikin kuzarin da nima kaina ban san ina dashi ba a wannan lokacin.
Na shiga cikin banɗaki, kayan jikina na soma kwaɓewa na watsa ruwan a jikina sannan na ɗauro zanin a jikina tare da sako hijabina na fito ina riƙe da sauran kayan a hannuna,wajen ledar da nake kyautata zaton cewar kayana ne da aka ce sarkin gida ya kawo mini tare da magangunan. na nufa na fara fiddo da kayayayyaki ina gani har na iso kan wata doguwar riga baƙar da adon stone masu ɗaukar ido a jikinta da kuma ɗan kwalinta a ƙulle a jikinta na ware ɗan kwalli sannan na zara doguwar rigar na maida nawa wanda na cire cikin ledar sannan na tada sallan magrib da isha'i a tare na yi su kasancewar na makara.
A kan sallayan na zauna tinanunnuka marasa kan gado suna ta ziyartar ƙwaƙwƙwalwata,lalle na ƙasa gaskatawa cewar kowa ka gani cikin wannan rayuwar da nashi damuwar wani dauriya kawai ya fika shiyasa ba'a gane nashi. a hankali na fara sulale ina ɗaura haƙarƙarina akan sallayan nayi matashin kai da hannuwa wasu sirarun hawaye suna biyo gefe da gefen kuncina da suka sani jin wani sanyi yana ratsa ni sai naji sauƙi da na jin na tsiyayar da ƙwallar.
Zaune yake a cikin part ɗinsa yana kallon ceiling ɗin bedroom ɗin da ya zaɓa shamaki tsakanin sa da sararin samaniya,hannunsa riƙe da wayarsa yana waya da Hajiyarsa a handsfree ya danna ƙiran.
"Lafiya ƙalau Hajiya sai kewar ki da taƙi bari na".
Ya faɗa a kasalance,kafin ta kai ga bashi amsa yayi saurin cewar"Yauwa Hajiyata kunyi magana da Abbu ne, akwai wata ƴar aikin da na saka a samo miki saboda naga yanzu Iya girma ya fara kama ta wasu aiyukan ba zata iya aiwatar dasu ba, shiyasa na saka aka nemo wata sai a haɗa ta da Iya ta koya mata abubuwan da kika fiye ci na gargajiya tunda kince kinfi son girkinta".
Sai da ta murmusa sosai har ya fara zarguwa da kansa ko dai ta bugu jirgin nasan ne,maganar da ta soma yi ya sa shi kawar da wannan tinanin gefe guda.
"Abeena kenan,ni wace ƴar aiki kuma yanzu nake da buƙata ai kawai kar ni da Iya nafi jin daɗin zama da ita".
"Kina nufin Abbu bai ƙira ki ya miki magana akan sabuwar ƴar aikin ba?".
Tambayar da yayi gaggawar watsa mata kenan yana gyara zamansa,cike da zaƙuwar son jin amsar da zata ba shi,zuciyarsa ta shiga bugun tara-tara.
"Ya ƙira ni amma bai min maganar wata ƴar aiki ba, Zayyad ko akwai wata matsalar ne kake ɓoye min?".
Cikin hanzari ya shiga jijjiga kansa kamar dashi ga ita kana ya soma faɗin"Babu wata matsala Hajiya, amma tabbas na aikata kuskure babba da nake jin nauyin sanar dake a halin yanzu".
"Abeena menene yake faruwa ka sanar dani ko menene".
Sai da ya fesar da dogon numfashi mai zafi yana naɗe ƙafafunsa wajen guda, kafin ya ce da ita"Hajiyata na bada cikiyar nemo miki ƴar aiki ba tare da na sanar dake ba, har aka kawo ta na karɓe ta na kawo ta gidan Abbu akan in kin dawo sai na gabatar miki da ita ba.zuciyata ta ka sa samun sukuni akan hakan idan nayi la'aƙarin da tun tasowa ta bana iya ɓoye miki komai da ya shafe ni".
Shuru ya biyo bayan jawabinsa na tsawon daƙiƙu kafin tace"Zayyad duk inda ɗan ƙwarai yake to kai, ka kai ina alfahari da kai a ko yaushe sannan ina so la samarwa kansa nutsuwa domin wannan abunda ka aikata bai kai har ka ƙira shi da laifi ba Abeena".
Tabbas yasan akwai yarda mai ƙarfi da zai yi wuya wani abu ya iya zuwa ya shiga tsakaninta, ko ya raba ta, koko ya share ta tsakanin sa da Hajiyarsa haka nan zuciyarsa take ayyana masa cewar ɓoye mata labarin wannan yarinyar da yayi kamar SALON ƘADDARARsa ce take ƙoƙarin juya akalar rayuwarsa.bata cancanci yayi mata shamaki da komai da ya danganci rayuwarsa ba.
"Ummata".
Ya furta ya furta cikin sanyin jiki,bai yi zato taji ba kasancewar cikin muryarsa da bata fito sosai ba yayi maganar. sai ji yayi ta amsa da faɗin"Na'am ɗan Umma".
Dariya yayi sosai wanda rabon sa da yin sa har ya mance bai sani ba ko ire-irensa waɗanda suka taso cikin zazzafar cutar maraici su ƙaɗai suka san ɗacin rashin ƙiran su da ƴaƴa da ake yi.Sosai ya saki ransa tana jansa da hira har duk damuwoyisa suka kau
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________________
Page 3⃣4⃣
Sanyin asubahin da naji ana busawa yana ratsa dukkan gaɓoɓina, ya tilasta mini wangale idanuna da suka kumbura tsim tim. Na yunƙara zan tashi gangar jikina ya ƙi taimaka mini na kwantar da kaina lamau ina irga numfashina da yake fita ɗaɗɗaye.
Ganin kwanciyar ba zai amfane da komai ba, ya sa ni jan jikina na miƙe na nufa banɗaki sanyin ruwan ya hana ni watsa shi a jikina, alwala kawai nayo na fito ina zara hijabi na tada sallah sosai na jero addu'o'i cikin sujadata ta ƙarshe kafin nayi sallama ina shafa addu'ar na kwaɓe hijabin daga kaina na zauna akan sallayana.
Na daɗe zaune a wajen ban ga kowa ya shigo ɗakin ba, har na fara tinanin ko cewar basu tashi bane ko kuma su Mariya ba'a ɗakin suka kwana ba don tashi na ban ga wata alamar da zata alamta mini cewar wani ya kwana a ɗakin bayan ni ba.
Na miƙe ina saka hijabina a kaina na fita daga ɗakin,na ƙarewa sashi kallo tsaf!ɗakuna ne da suka kerewa ganina a jajjere suna fuskantar junan,na Sarauniya shine a farko na lura kuma nata yafi sauran girma don shin fetinsa ma da alama sabo ne. Ban haɗu da kowa a tsakar wajen ba don haka kaina tsaye na fice daga cikin sashin na fito ainihin tsakiyar gidan na fara tsil-tsila idanu ina ƙarewa girman gidan kallo da ya fara son zarce tinani da lissafin ƙaramar curin ƙwaƙwalwan dake cikin kaina.
Na sake baki hangalgal! gani motoci ma da nasu sashi da aka ware musu mussamman don adana su, iya kan filin wajen ajiyar motocin da yafi filin gidan mu girman ta fannin tsayo da faɗi. ganaɗaya filin gidan kuwa da idanuna suka yi nasaran hangowa daga bakin gate ɗim shigowa zuwa inda nake tsaye ya kai rabin girman unguwar mu.
Tsaye yake cikin sabon filin da ya sa aka gyara cikin gidan domin dawakan da ya bada ordern a sayo masa, sosai aka gyare filin tare da yi masa fasali mai ɗaukar hankali tare suke da sarkin gida da kuma Baban Nana suna ta yabon kyawun wajen ana ɗaure dawakan da aka kawo, ya fito ganin su Baban Nana suke yiwa wanda ala ɗauko domin kula su jawabi.
Shi kuwa Zayyad kansa ya ga wayar salularsa da yake latsawa suna chart da Ahmad akan maganar bikinsa da ya rage saura kwanaki goma,sosai Ammiey da Ahmad ɗin suka kafa masa ƙahon zuƙa akan lalle yazo yana da nashi ƙudurin zuwa bauchi ko ba don wannan auren ba don ya binciko wannan lamarin da ya tokarre masa a ransa akan labarin da wannan yarinya ta ba shi.
A karon farko da ya ɗago kansa daga kallon wayan da yake yi, tun lokacin da Sarkin gida da Baban Nana suke zantukansu caraf! idanunsa suka sauƙa akan Adam da yake fitowa daga part ɗin su za shi part ɗin Nenne.
Ɗauke kansa yayi daga kallo da ya masa ganin irin shigar da yake sanya a jikinshi, gajeren wando ne da ya tsaya masa dai-dai gwiwarsa jikinsa babu ko sigileti balle riga gashin ƙirjinsa sun mimmiƙe masu sanya tsikar jikin mu tashi.tun yana ƙaramin sa yake ƙoƙarin alkinta tsiraicinsa tun lokacin da ya kawo munzalin balaga ko Hajiyarsa ba zata ce ta taɓa ganin sa babu riga a jikinsa ba.
Kamar an ce masa ya ɗauko kansa, yama ɗagowa idanunsa suka sauƙa a kai na juyowa ta kenan idanuwan mu suka sarƙe cikin na juna,sosai na ga yana kallon inda nake tsaye wanda hakan ya sanya ni rusunar da nawa ƙwayoyin idanun na tsawon daƙiƙu na ɗan sata kallon naga har yanzu dai ni yake kallo.na yi saurin juyawa da baya zan tafi na ci karo da mutum nayi hanzarin kaucewa daga hanyar ina bashi waje.
Yanayin da na gansa ya haifar mini da rawar jiki don tunda uwar Daada ta haife ni zan iya rantsuwar cewar ban taɓa yin mummunan gani irin na yau ba.
"Ke me kike yi a nan wajen, waya shigo dake cikin gidan nan?".
Gabana yayi mummunan faɗuwa wanda hakan ya haifarwa ƙalbina,dakan lugudan tara-tara nayi jarumtar wulla nawa idanun cikin nasa muryarsa ta fara yi mini yawa cikin kunyar kaina tare da dawo mini da abubuwa da yawa da sula faru.yanda nasan cewar ba zan taɓa mance ranar da na gujewa gidan iyayena ba haka nan nayi amannan cewar amon muryarsa ba zata taɓa gogewa daga cikin kaina ba, domin nayi mata kyakykyawan haddan da har ranar da ajalina zai riske ni bazan iya mance shi ba a tarihin rayuwata.
Da wani irin sauri ya miƙe yana nufar inda Adam yake ganin irin kallon da yake mata cikin maye yake zai iya aikata komai,yana isa ya riƙo hannun Adam tam! cikin nasa tare da kwantar dashi a jikinsa.kafin ya watso mini wani kallo ban san sa'in da hawaye suka fara gudana saman fuskana ba sai jin muryarsa nayi ta ratsa shimfiɗa-shimfiɗar ƙofofin kunnuwana.
"Me kika fito yi nan, hala ban ja miki kunne akan ki zauna a can cikin part ɗin ku ba?".
Shuru nayi jikina ta ɗauki tsimi na kasa furta ko da kalma ce,tabbas wannan muryar mutumin da ban san ko wanene ba yayi kamanceceni da muryar da jinta ya zamto ranar da dukkan tanadin da na shafe tsawon shekaru ina yiwa rayuwa,yayi kama da muryar wanda ya raba ni da abin da duk wata mace take taƙama dashi BUDURCI, kuma take alkinta shi tare da burin kai shi inda ya dace watau gidan mijinta.
"Ummiiiii".
Naji ya kuma faɗa cikin kausassiyar murya nayi saurin dawowa cikin hayyacina,ina tare hawayen da suka ƙara ciko mini idaniya naga sarkin gida da kuma Baban Nana har su ma sun iso wajen.na duƙar da kaina ƙasa saboda ganin duk sun tsura mini na jiyamun su.
"Zayyad ka shiga dashi naga kamar baya cikin hankalinsa,ita kuma bari na kaita wajen Hajja".
Furcin Baban Nana kenan ya wuce gaba na soma bin sa a baya jikina duk yayi laushi ƙalau!.sai da ya ga shigewar mu sashin su Hajja don ko ban waigo ba jikina yana bani cewar har yanzu idanunsa suna kanmu.
Tallafo kafaɗar Adam yayi yana ƙara gyara masa kwanciyarsa a ƙirjinsa kafin ya kallo Sarkin gida ya ce dashi.
"Bari na shiga ciki inna fito zan nema akwai maganar da nake son muyi da kai".
"A fito lafiya".
Sarkin gida ya faɗa yana barin wajen,shima Zayyad ya nufi part ɗinsa yana riƙe da Adam da har yanzu giyar mayan bata gama sakin sa ba.suna isa ya zaunar dashi a falo sannan ya wuce wajen fridge ya ɗauko maltina da peakmilk masu sanyi,ya tsiyaya a kofi ya kafawa Adam a bakinsa sai da yasha sosai kafin ya zare masa kofin daga bakinsa ya miƙe ya shiga bedroom ya barshi ya huta.
Wanka yayi a gurguje don asibiti zai wuce,ya shirya cikin light blue ɗin long sleeve da navy blue ɗin suit a saman ta sai neck tie ɗin da ya ɗaura baƙi.sama-sama ya murza mai a fatarsa ya ɗaura agogonsa sannan ya ɗauki wayarsa da key ɗin motarsa ya fito falon har yanzu Adam yana bacci don hakan ya tsaya daga tsaye yana dialing lambar Hajiyarsa.
Shagwaɓe fuska yayi kamar dashi ga ita tana gaishe ta, ta amsa tare da tambayarsa yanayin jikinsa shi kam ma dariya taso ba shi don yanzu wani lokacin har mantawa dake da yana da asthma don kwana biyu ya daina matsa masa. duk tattaunawarsu akan maganar auren Ahmad suka yi ta don ita kam ma za ayi bata ƙasar.
Ganin Adam ya fara buɗe idonsa yasa shi sallama da Hajiyarsa akan in ya isa office zai ƙira ta,maida wayar yayi cikin aljihun wandonsa kana ya iso wajen Adam da sauri ya tsuguna gaban shi.
"Adam baka ji na?".
Ya faɗa yana tsayar da idonsa akan fuskar Adam ɗin,ya amsa masa ta hanyar ɗaga masa kansa sannsn ya ɗaura da faɗin"Hamma ɗazu naga wata yarinya a cikin compound wacece don ban taɓa ganin ta ba?".
Sai da ya gyara tsugunan da yayi yana ƙara fuskanto shi sosai sannsn ya ce dashi"Adam babu wata yarinyar da ka gani, idonka ne kawai yake nuna maka haka kasan fa ba'a cikin hankalinka kake ba shiyasa a ko yaushe nake muku faɗan ku guji shan miyagun ƙwayoyin,yanzu idan ba'a yi sa'a ba to kwakwalwarkace ta fara samun matsala shiyasa kake ganin abinda babu shi".
Cike da tsoro Adam yace"yanzu Hamma kana nufin haukacewa zanyi kenan?".
"A'a Adam baza ka haukace ba amma matuƙar baka raba kanka da shan ƙwayoyin ba,kana dab da rada hankalinka".
"Hamma yanzu kenan kana son kace mini babu wata wacce na gani a waje?".
Ƙara fukanto shi yayi sosai ganin haƙarsa tana ƙoƙarin cimma ruwa,saboda ganin yanda maganganunsa suka yi tasiri wajen kama hankalin Adam,kana yace"A zahiri babu wata wacce ka gani daman irin haka yana faruwa inda mutum yana cikin maye to yana rasa lissafinsa ne gabaɗaya,shiyasa wani in yana cikin maye yana iya aikata komai fyaɗe,cin zarafi da wasu abubuwan da sai daga baya za'a zo ana da na sani".
Shuru Adam yayi yana nazarin maganar Zayyad tabbas yaga yarinyar amma dole ya share abin tunda babu wanda ya ganta sai shi ɗaya,jin Zayyad ya riƙo hannunsa ya sanya shi dawo da kallon sa izuwa gare shi.
"Tashi yanzu muje ka samu kayi wanka sannan ka daina fitowa haka koda kuwa a cikin gida ne,domin akwai waɗanda ba muharraman ka bane".
Dariya Adam ya saka sosai yana faɗin"Hamma su waye muharramai?".
"Kana nufi bakasan su waye muharramai ba a gare ka?".
Zayyad ya maido masa da tambayar cikin tsan-tsar mamakin da ta bayyana akan fuskarsa.
"Ban sani ba".
Amsa da Adam ya bashi kenan da ya sanya shi jijjiga kansa,lalle akwai aiki babba a gaba ganin lokaci zai ƙure ya sa shi riƙo hannun Adam suka fito sai da ya kulle part ɗinsa sannan suka nufa cikin parking lot.
Ya buɗe motar ya zaro wasu kuɗaɗe ya ba wa Adam dubu ashiri haka nan ma ya damƙa masa na Haidar yace ya kai masa.
"Wohoho oh Allah!Hamma sai da kai wallahi ai da kana irin wannan da mun zauna lafiya".
Riƙo kunnen Adam yayi sosai yana matsawa yace"kuma kuɗina bana sayan kayan shaye-shaye bane,sannan bana son naji wannan maganar kayi ta da kowa akan wai kaga wata".
"Hamma ai wannan maganar anan mun burne ta".
Abinda Adam yake maimatawa kenan har ya sake masa kunnensa ya shige motarsa ya fice daga gidan,idanunsa akan part ɗin Hajja har ya fice da motarsa Allah ya taimaka basa waje.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________________
Page 3⃣5⃣
Tun lokacin da Baban Nanan ya kai ni sashin su,muka iske matarsa da naji ya ƙira ta da sunan Hajja tana wanke-wanke sai ƴaƴansu biyu mace da na miji da na musu kallo ɗaya na ɗauke kaina suna wasan guje-guje a madaidaicin filin tsakar gidan.
"Hajja ga ta za ta zauna a nan kafin Zayyad ya dawo".
Miƙewa tayi ta nufo ni nayi saurin rusunawa ina gaishe ta, ta amsa cike da annuri a fuskarta kafin ta ja hannu muka nufa cikin uwar ɗakin ta.na zauna ina taƙure kaina cikin hijabina ta fita domin ta gama aikin tsakar gidan jim kaɗan da fitar ta ƴar su ta shigo ciki-ciki na amsa sallamar da ta shigo ɗakin dashi ta ajiye kwaryan fura a gabana sannan ta fice na bi ta da kallo ina hango tulin gashin kanta da aka tufke mata shi cikin dankwali ya ɗan fito ta bayan ta.
Wata ƙaƙƙarfar ajiyan zuciya na sauƙe mai ƙarfi ina runtse idona, yayin da muryan wannan mutumin da ban san ko wanene ba ya shiga yi mini yawa cikin kunyar kaina tabbas muryarsa tayi kamanceceniya da wanda ya keta mini haddina ta hanyar ta raba ni da rigar mutuncina.
Kaina ya kuma sarawa a karon da ba adadi duk gudun da falfelan fankar dake aiki a cikin ɗakin take hakan bai hana kusurwar jikina tsatstsafar da gumi mai maiƙo ba a saman goshina,zuciyata ta mini nauyin gaske tamkar a mini ajiyar dutsi raina yana soya kamar garwashin wutar da yake ƙasan tukubar tsire.
Numfashina ya fara cushewa waje guda jikina ya ɗauki mazari kamar ana jona mini wutar lantarki,nayi ƙoƙarin jawo numfashina da ta fara nisa da gangar jikina a wahalce.
Na saka kaina tsakankanin gwiwoyina ina fitar da numfashi wani na bin wani,wasu hawaye masu zafi gami da raɗaɗi suka shiga wanke mini fuskana ranar da abin ya faru ya fara ziyartar tinanina.
Bansan san da na saki wani gigitaccen ihu ba da sautinsa ta amsa duk wata kusurwar ɗaki,saboda gaskata hashashen zuciyata tabbas muryar tayi dai-dai.
Naga Hajja da Baban Nana duk sun shigo ɗakin, Hajja ta zauna kusa da ni tana riƙo hannuna sannan ta fara faɗin abinda ba na iya tantance abinda bakinta yake faɗi sai gani nayi yana motsi.
"Riƙe ta na mata addu'a naga kamar bata cikin hayyacinta".
Muryar da naji ta a tsakiyar kaina kenan wanda na kasa bambamcewa cikinsu waye yayi ta,sai gani nayi Baban Nana ya miƙe ya fara karanto mini wasu addu'o'i yayin da Hajja ta ƙara ƙarkon riƙon da ta yiwa hannayena.
Duk jikina yayi laushina na kasa taimakawa gangar jikina ko da da motsa ƴar yatsata ne, nayi jarumtar motsa wuyana na kwantar da kaina akan kafet ɗin dake shimfiɗe a ko'ina a cikin ɗakin.numfashina ya na sauƙa a hankali da kallo kawai nake bin su duk da ba komai da suke faɗa kunnuwana suke iya jiyo mini ba saboda nauyin da idanu da kunnawana suka yi mini.
"Malam ka ƙira Zayyad ka sanar dashi halin da take ciki, don naga kamar bata cikin hayyacinta kuma ga juna biyun da take ɗauke dashi ya kamata ace tana samun kulawa".
"Haka ne bari na ƙira Zayyad ɗin".
Tsaye yake a cikin office ɗinsa yana sign akan form ɗin operation ɗin da zasu shiga by 2:00 na rana,yana gamawa ya miƙawa nurse ɗin dake tsaye a gabansa ta karɓa ta fita,zara hannuwansa yayi a aljihunsa yana fuskanto windown office ɗin sai da ya sauƙe ajiyan zuciya yana furzar da iska daga bakinsa mai zafi.
Tabbas yasan cewar yayi babban sake da ya bari har Adam ya san da zaman wannan yarinyar da a yanzu zai iya siffanta ta da SALON da ƘADDARARSA tazo dashi domin a kanta ne ya fara yiwa Abbu da Hajiyarsa ƙarya da sauran mutanen da suke kewaye da shi,dole yasan Adam zai bibiye yarinyar da kuma zaman ta a cikin gidan.
Haka kawai yake jin cewar ba zai iya tafiya bauchi ya barta ta zauna a cikin gidan ba,domin hankalinsa ba zai kwanta ba,bai san meyasa ta ruɗe da taga Adam ba abinda da yake masa yawo a cikin kansan kenan.
Jin wayarsa da take ringing akan teburinsa ya sashi ɗauke idonsa daga kallon windown da yake yi,yana watching movement ɗin mutanen dake shige da fice a cikin harabar asibitin.har ƙiran ya tsinke ya kasa zuwa ya ɗauki wayar har sai da aka ƙara ƙira a karo na biyu sannan ya isa gaban teburin ganin sunan Baban Nana ya bayyana cikin screen ɗin wayar ya sa shi ɗaga ƙiran tare da yin sallama a sanyaye aka amsa daga ɗayan bangaren, sannan aka ɗaura da faɗin.
"Zayyad kana ji na?".
"Ina ji Baba".
Ya faɗa yana zaman kan kujerarsa kafin Baban Nana ya ɗaura da faɗin"Kayi maza kazo gida wannan yarinyar ce ba lafiya,sai wasu abubuwan da take kamar gabaɗaya bata cikin cikakken nutsuwarta kazo dai gida yanzu".
Ƙarƙarfar ajiyan zuciya Zayyad ya sauƙe yana zame wayar daga kunnansa yana ƙura mata kallo,tusa hannuwansa yayi cikin sumarsa yana barbazasu kafin yayi azamar jawo key ɗin motarsa tare da wayarsa ya fice daga office ɗin ta ƙofar baya da sauri ya isa ga motarsa sannan ya tada ta ya fige ta da gudu ya fice daga cikin asibitin.
Cikin mintuna ƙalilan ya iso gidan a waje ya faka motar, ya buɗe ƙaramar ƙofar cikin gate ɗin ya shiga kansa tsaye ya nufi inda ya hango Baban Nana yana gyaran flowers,tun kafin ya isa shima ya nufo shi yana faɗin.
"Zayyad har ka iso?".
"Na iso Baba tana ina ne?".
"Tana ciki muje ka ganta".
Gaba yayi yana bin sa a baya har suka shiga cikin sashin.
Bansan sanda baccin wahala yayi gaba da ni ba, sai daina jin tattaunawar da su Hajja suke yi nayi.cikin baccin da nayi nisa a cikin sa nayi wani mummunan mafarki wai Allah ya nuna mini fuskar wanda ya min fyaɗe har nayi jarumtar luma masa wuta a ƙirjinsa sai da nayi masa suka bakwai duk a ƙirjinsa sannan na zube a ƙasa ina rungume abinda na haifa cikin jinin haihuwa.
Figigi nayi na farka ina toshe bakina da tafukan hannayena,saboda ihun da yake ƙoƙarin suɓuce mini babu shiri naji mutum ya riƙe ni na ɗago idaniyana da suke ɓarin hawaye naga Hajja ce sannan na fara bin mutanen ɗakin da kallo Zayyad ne sai Baban Nana yana faɗin.
"Subhanallahi! kaga irin ta ko Zayyad tun ɗazu haka take yi da ta sama baccin sai ta farka cikin wannan yanayin".
Bai ce dashi uffan ba ya tako har gabana kaina yana ƙasa sai ƙafafunsa da na gani, kafin yace da Hajja.
"Hajja ki kama mata kanta dai-dai goshinta sai kina maimata addu'ar da zan faɗa".
Hajja ta kamo goshina kamar yanda ya faɗa,sannan ta shiga maimaita addu'ar da yake karantowa sosai na sauƙe ajiyan zuciya ina jin nauyin da murafan idona suka mini sun fara raguwa.
"Zayyad ya kamata tana samun kulawa tunda ciki ne a jikin ta, wannan halin da take ciki zai iya haifar mata da matsala da kuma abinda yake cikinta ko kuma kawai ta koma can gidansu in Hajiyar ta dawo daga saudiya sai taje can kawai gidan Hajiyar".
Furcin Baban Nana kenan ya ƙarishe zance yana tsayar da ƙwayoyin idanunsa akan Zayyad ɗin, da yayi ƙasa da kansa yana ɗan murza zoben azurfan dake hannunsa.shuru ya ratsa ɗakin har sai da Baban Nanan ya taɓo kafaɗarsa kana ya ɗago kansa tare da faɗin"Baba da zaka min wata alfarma,ta zauna a nan tare da Hajja har izuwa lokacin da Hajiyar zata dawo don hankalina bai kwanta da zaman ta a can sashin ƴan aikin ba,mussamman yanzu da Adam ya ganta".
"Babu komai Zayyad sai ta zauna a nan ɗin".
Daga haka naga duk sun miƙe shi da Baban Nanan suka fita can Baban Nana ya dawo shi kaɗai ina jin sanda yake sanar da Hajja cewar shi Zayyad ɗin ya wuce office sai dare zai dawo.
Tsawon wunin wannan ranar haka na ƙarisar dashi cikin rashin kuzari da walwala haka nan ko sashin su Mariya ban leƙa ba,Iman da Nana sai shigowa suke yi wajena amma rashin ganin fuska daga gare ni yake hana su zama.ina zaune saman sallayan da na iddar da sallan isha'i ina jan carbin da Hajja ta bani tinanin Daada da su Sagir ya baƙuncin birnin ƙalbi na ba wa kukan da nake maƙale shi damar fitowa sosai nake rero sa da dukkan ƙarfina wiwi!wiwiwi!!.
Hajja ta shigo tayi ta lallashina tare da bani baki,amma na kasa tsayar da kukan haka nan ma Baban Nana har yayi ya gaji ya fice wai zai ƙira Zayyad.ina zaune a ɗaki na jingina kaina jikin ginin ɗakin ni kaɗai duk sun fice sun bar ni muryata har ta dushe sautin kukan baya fita amma ban fasa yin sa ba.naji an turo ƙofar ɗakin na kai kallona ga hanyar shigowar yana tsaye jikin ƙofar cikin shigar da ya fita da ita ɗazu sai dai yanzu ya kwaɓe rigar saman saura iya ta ciki.
Ƙura min ido yayi na tsawo daƙiƙu kafin ya tako ya shigo cikin ɗakin, ya ajiye ledar da ya shigo da ita yana tsugunawa akan ƙafafunsa a gabana ina iya jiyo sautin da ajiyan zuciyan da ya sauƙe ya ba da.
"Ban san ke wacce irin marar tausayi da imani bane,jaririn da yake rayuwa cikin cikinki ma bai tsira daga zaluncin ki ba sai ki wahalar da shi,menene alfanun wannan koke-koken da kike yi da zama da yunwa ko dan kinji cewar sai kinci kafin abin cikinki shima ya ci".
Shuru nayi ban amsa masa ba saboda a zafafe yayi maganar,bai bani damar amsawa ba ya ɗaura da faɗin"oya yanzu ki ɗauki abincin nan kici".
"Ba-ba-ba-ba na jin yunwa".
Nayi jarumtar faɗa saboda tsoron da yayi mini lulluɓi a wannan sa'in,ya daka mini gigitacciyar tsawa"ki ɗauka nace kici ba wai neman jin ra'ayinki nake yi ba".
Nayi hanzarin jawo ƙwaryan furan da Hajja ta ajiye mini na fara sha,ina yunƙurin amaryawa ya kuma gilla mini wata tsawar.
"Karki sake ki min amai anan".
Muƙut!sautin haɗiyar da nayi wa furan kenan,haka na dunga tura shi har nasha ya kai rabi sannan na ture gefe bai ce da ni ko kanzil ba ya ɗauki ledar da ya shigo da ita ya fara ɓallo mini magani ya miƙo min na karɓa ina watsa su a bakina tare da bin bayan su da ruwa.
"Zaki cigaba da zama anan tare da Hajja,sannan zan ƙara maimaita miki cewar ko ƙofar ɗaki kadda ki kuskura ki fito sannan idan kinga dama har ki kuma cin wani abincin but let me warn you duk abinda ya sama ɗana da yake cikinki ki shirya fuskantar ko wani irin hukunci".
Yana dasa aya nan wuf! ya miƙe zai fice ya barni da juyayin maganganunsa cikin raina ganin da gasken fita zai yi nayi saurin dakatar dashi ta hanyar amayo masa da tambayar da take nuƙurƙusan ruhina.
"Dan Allah inason sanin wanene wancan mutumin da ɗazu na gan shi da safe?".
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 3⃣6⃣
Cak ya tsaya ba tare da yace da ni uffan ba, haka zalika bai waigo ba kamar yanda nima na kasa ɗauke idona daga kansa. Tsawon mintuna muka ɗauka cikin haka kafin ya saki handle ɗin ƙofar ya waigo tare da watso mini wani kallo da rikitattun idanunsa nayi gaggawar rusunar da nawa idanun.
Ina jin takun tafiyar sa ya iso har gabana ya tsuguna akan ƙafafunsa yana fuskanta na sosai yace da ni"Shin kin san shi ne a wani wajen, ko kuma wani abu ya taɓa haɗa ku dashi don naga matuƙar kaɗuwa akan fuskarki yayin da kika yi tozali da shi".
Wasu siraran hawaye suka biyo gefen fuskana nasa hannu na kawar da su, maganar ta mini nauyi wajen furtawa wata zuciyar tana raya mini to meyasa ma zan sanar dashi alhali har yanzu bai yarda da cewar fyaɗe aka mini ba, yafi karkata laifin gare ni da tinanin cewar ni na bada kaina ga maza har na ɗauki cikin dake jikina.
"Tambayar ki nake malama kin min shuru, a ina kika taɓa sanin sa?".
Muryarsa suka bugi dodon kunnuwana bakina ya shiga karkarwa ƙasa-ƙasa cikin amon muryata da bata fita sosai nace"Ban san shi ba".
Na lura tabbas amsar da na ba shi kamar ƙara fusata shi tayi,ya miƙe tsaye yana riƙe ƙugunsa tare da jijjiga kansa yana cizo leɓɓansa da ƙarfi ya fara zagaye ɗakin kamar mai kaiwa da kawowa. Tass! naji ya sauƙe mini gigitaccen mari a ɓarin fuskana ta dama tsabar azabar da ta sauƙa min na kasa ko da kuka sai hawayen da na tsananta yin su.
Shuru ya karaɗe dukkan ɗakin sai sautin ajiyan zuciyan da nake sauƙewa a kai a kai,har yanzu yana tsaye ya kasa zama yana aiko min da wani irin kallo mai cike da tuhuma.
"UMMI".
Naji ya furta sunana a karo na biyu kenan tun bayan haɗuwana da shi, duk da nasan cewar Ummi ɓangaren sunana ne amma sai naji wani iri don ba wanda yake ƙira na da hakan, ban ɗago kaina ba ya matso kusa da ni ya yiwa kansa mazauni yana faɗin"Tambayar ƙarshe zan miki a ina kika san Adam sannan menene ya taɓa haɗa ku dan sanda kika ganshi kin ruɗe, idan kuma kika bari na gano da kaina to lalle zaki yabawa aya zaƙinta".
Numshafina ya fara cushewa na shiga kokawa dashi na tsawon daƙiƙu, ya miƙo min kofin ruwan da na sha magani dashi na kafa a bakina na ɗan sha kaɗan sannan na cire na sauƙe wata gwauruwar ajiyan zuciya kana na soma faɗin.
"Ban san shi ba hasalima yau ce ranar farko da na fara ganin fuskarsa".
Ban ƙarisa ba ya katse ni da faɗin"ki tafi kai tsaye ga tambayar da na miki".
"Muryarsa da naji ta min kama da murya mutumin da ya tarwatsa mini rayuwata ya rabo ni da duk wani jin daɗina. Wallahi ko rantsuwa nayi babu kaffara a kaina muryarsa tayi dai-dai da waccen wanda yayi mini fyaɗe".
Idanu ya tsura mini babu ƙiftawa haka nan bai ce mini komai ba, hakan ya bani damar kwararar da ƙwallarta son raina. Sosai ƙirjinsa yake bugawa ya runtse idanunsa da suka fara rufewa yana ambato sunan haliccinsa cikin ransa tabbas hashashen zuciyarsa ta tabbatar don daman tinaninsa shine lalle ta san shi a wani wajen yanzu kuma sai ya tarar da abinda ya girmewa tinaninsa ta yaya muryar Adam zata yi kamanceceniya da wanda take ƙikirarin yayi mata fyaɗe?.
"Look ki nutsu ki ƙara tinani anya kuwa kinji muryarsa dai-dai don a lokaci shima ba a hayyyacinsa yake ba".
A ruɗe yayi maganar don har yaso ya fini ruɗewa, sai da na zuƙe majinar kukan da yazo mini kana na amsa mishi da faɗin"Wallahi naji ta da kyau kuma nayi dai-dai da muyar wancan mutumin da ya mini fyaɗe".
Kansa kawai ya jijjiga yana yarce gumin da ya tsartsafo masa a saman goshinsa, ya gyara zamansa yana ƙara lankwashe ƙafafunsa tabbas in abunda ta faɗa ya zamto gaskiya lamarin zai ƙara cakuɓe masa indai ta tabbata cewar Adam ne ya mata fyaɗe ƙaryar da yayi wa Abbu da Hajiyarsa sai ya fito ya warware ta.
"Ki kwana ana gobe da safe zamu gama maganar".
Ya faɗa yana miƙe ya fice daga ɗakin ya barni da sakin wani kukan da ya tukare mini ƙirjina,na sake shi sosai anan na kwana tare da su Imam da Nana a ɗayan ɗakin da nake kyautata zaton cewar ɗakin yaran ne.
Yana fita ya iske Baban Nana a wajen dawakan da aka kawo, isa wajen yayi ya masa sai da safe sannan ya wuce part ɗin sa cikin sauri don a yanzu yafi son kaɗaita kansa fiye da komai. yana isa ya saka key ya rufe ƙofar falon ya ware neck tie ɗin dake wuyansa sannan ya zube a kan kujera ajiyan zuciya ya sauƙe mai nauyi yana jin sanyin Ac da fankan da suke aiki a cikin falon suna ratsa dukkan gaɓoɓinsa.
"Innalillahi wa inna alaihir raji'un".
Ya furta can ƙasan maƙoshinsa tare da roƙon Allah yasa ba Adam bane wanda yayi mata fyaɗen, domin idan har ta tabbata shine to hukuncin da zai ɗauka akan sa sai duniya tayi tinanin cewar bai taɓa haɗa wata danganta dashi ta jini ba. Yasan cewar Adam yana shan duk wasu nau'o'in kayan maye kuma suna fitar da mutum daga hayyacinsa har ya aikata komai a sanda ya sha su.
Meya kai Adam jahar bauchi, har suka haɗu da ita, meye dalilinsa na yi mata fyaɗe?.
Tambayar da ya watsawa kansa kenan yana miƙewa tsaye,Haidar ne ya fara faɗo masa a ransa domin shi yafi shiga shirgin mata fiye da Adam shi dai barshi da shaye-shayensa da sata.
Dafe goshinsa yayi sakamakon wani azababben ciwon kan da ya sauƙo masa,ya wuce cikin bedroom kayan jikinsa ya kwaɓe ya shiga bathroom ya sakewa kansa ruwa ya daɗe kafin ya ɗauro alwala ya fito ya zara doguwar rigar jallabiyansa, agogon da yake manne jikin wall ɗin ɗaki ya kai kallonsa gare sa da yake nuni da ƙarfe goma da mintuna bakwai.dole ya kuma ya zauna don yasan yanzu Abbu ya kwanta.
Ya miƙe ya shimfiɗa sallaya ya tada kabbara raka'a biyu yayi ya sallame ya fara karatun qur'anin yana karanto suratul Muhammad yana kai ayar ta uku wayarsa ta fara ringing da take kusa dashi ganin sunan Hajiyarsa ya sashi ɗaga ƙiran ya cigaba da karatunsa.sanyin daɗi ne yake tsirga dukkan jikinta jin yanda yake karanto zancen Allah cikin cikakken nutsuwa da fitar da hakkin ko wani harafi.tayi shuru tana sauraronsa har ya gama karanto sural,sannan ya rufe qur'anin ya saka wayar a kunnansa.
Sallama yayi mata ta amsa sannan suka fara tattauna akan maganar auren Ahmad, sosai shi kam yaji daɗi da baza ta sama halaltar auren ba tinaninsa shine da zaran an gama aikin Hajjin zai yi mata visa ta tafi Madina ta zauna can. sun ɗau lokaci suna wayar kafin daga bisani suka yi sallama.
Kasa tashi nayi da asubahi saboda kukan da na kaɗaita kaina nayi a daren jiya,duk haluttun fuskana sun sauya ya kumbura idanuwana kamar zasu fito sosai cikin dake jikina ya fito wanda yanzu yake cikin wata huɗu don haka na kallafawa kaina zama ko yaushe cikin hijabi.
Ina iddar da sallan asubahi bacci yayi nasarar ɗauka ta sai da gari ya waye tar!, kafin na tashi naga har an kimtsa ɗakin na shiga banɗaki na wanko fuskana na fito falo ban tarar da kowa ba don haka kaina tsaye na fito tsakar part ɗin,na hango Hajja tana tarar ruwa a fanfo na nufo ta ina gaishe ta, ta ƙara yalwata annurin da yake kwance akan fuskata ta ce dani.
"Ummikursum kin tashi?".
"E wallahi na tashi na maraka ne ma, ina su Iman fa?".
"Sun tafi makaranta ai tun ɗazu".
Daga hakan ban ƙara faɗin komai ba, ruwan da take tara ya cika na miƙo hannu zan ɗauka mata ta yi hanzarin faɗin"A'a barshi masu juna biyu da ba'a son suna ɗaukar abu mai nauyi,na hutar dake kije ki zauna na kawo miki abin kari".
Maganganunta suka sanya ni jin kunya, ta ɗauki ruwan ta kai wajen wanke-wanke sannan ta kawo mini abinci bayan ta shimfiɗa mini tabarma ɗan caccakalan abincin nayi nace na ƙoshi ta miƙo mini wayarta babban ƴar latse.
Na bita da mamaki domin girmar wayar da na gani ta zauna kusa na tana murmushi tace"Kinga wayar babba ko?".
Na gyaɗa mata kaina domin mamaki bazai barni nayi magana ba, ta ɗaura da faɗin"Zayyad ne ya sayowa su Nana suna kallo a cikin yana kuma koya musu abunda ake musu a makaranta duk ta cikin wayar.nima a haka har na koya danna ta na saka mata memory na kai ake turo min littattafan hausa naji da na karantawa ina ji".
Na jinjina kaina ta karɓa wayar ta lallatsa ta shiga mini wajen littafan hausan,bayan ta tambaye ni naji ko na karantawa nake so na zaɓa na karantawa ta kai mini na gan su rututu.na sake baki tana faɗin"ni kam ma nafi son na sauraran domin ban iya karatun hausan ba".
Murmushi kawai na mata, ta miƙe ta fara wanke-wanken ni kuwa na fara jan littattafan har nazo kan wani littafi GIDAN MARAYU na danna kansa ya shiga ya watso mini rubutun.
Sunan marubuciyar idona suka fara yin tozali dashi an rubuta da manyan baƙi *AMINA MA'AJI*.
Sannan na faɗa cikin karatun gadan-gadan duk da wasu kalaman suna mini wahalar karantawa,saboda gurɓataccen hausata da bata gama nuna ba nayi nisa sosai a cikin littafin na sauƙe ƙatuwar ajiyan zuciya ina runtse idona sosai littafin yayi tasiri a zuciyata saboda yanda marubuciyar ta baje fasaha wajen zaƙulo irin rayuwar da maruya suke yi.tabbas littafin yaci sunan sa GIDAN MARAYU.
Sai naji raina ya ƙwaɗaitu ina ma ace nima marubuciya ce ta yanda zan rubutu SALON ƘADDARATA, a matsayin littafi ya isa ga ɗimbin jama'a don ya zama izni ga wasu mussamman masu halayya irin ta Abba.
Ina ma ace labarin rayuwata ya zamto ishara ga waɗanda basa gaskata ƙaddara.take naji raina ya mini zafi na kasa jurewa har sai da ƙwalla ta kwarara daga idaniyata.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
_____________________________
Page 3⃣7⃣
Naji hannun Hajja a saman kafaɗata ta dafo ni tare da faɗin"Ummukursum lafiya?".
Nayi hanzari kawar da hawayen da suke shawagi a saman fuskana kana na ce da ita"Lafiya wani abu ne ya shigar mini ido".
Sannu ta shiga jera min kafin ta koma ta cigaba da aikinta ta bar ni da sauƙe wata gwauruwar ajiyan zuciya na kasa cigaba da karanta littafin tausayin kaina da rayuwata su kayi yiwa ruhina dabaibayi.
Tinanin Mariya ya diro mini a rai furcin da Sarauniya ta yi akan cewar ita zata je sashin Hajiya yau domin ta ɗebe mata kewa, take naji ina son sanin halin da take a ciki rabo na da shiga sashin su tun jiya da safe.
Har Hajja ta gama wanke-wanken ta koma kusa da ni ta zauna na fuskanto ta haɗi faɗin"Hajja bari naje sashin su Mariya na ɗebo kayana".
"Kul! Ummukursum tunda Zayyad yace ki zauna a nan, to kiyi haƙuri ki zauna a nan ɗin shi yasan dalilin da yasa ya rabo ki da can ɗin".
Nayi shuru na wasu daƙiƙu kafin nace"Hajja ni kuwa na ga wata irin rayuwar da su Mariya suke yi, wanda ban hane masa ba wai ɗebe kewa suke ƙiran shi..."
Ban ƙarisa ba naji Hajja ta rufe mini bakina da tafukan hannayenta tare da cewar"Kul! Ummukursum ki tara kanki da wannan lamarin domin yafi ƙarfin tinaninki, Hajiya ta wuce duk lissafin kanki tayar keke ce wacce baka gane gaban ta balle bayan ta,kowa ya san tana lalata da ƴan aiki ba amma babu wanda zai iya garajen sanar da Alhaji domin bayan ka rasa aikinka har rayuwarka ma tana iya salwanta. wannan dalilin ya sanya Malam ya min hani da shi cikin gida iya ka ci na wannan sashin sai kuma tsakar gidan ko su Nana basa shiga".
Tunda ta fara maganar nake bin bakinta da kallo yanda take bayyanin daki-daki,sai naji son ƙara ganin fuskar Hajiyar ya ɗarsu a birnin ƙalbina gashi dai a fuska kamar ta Allah har tabon salla take dashi a goshinta.ta fara jana da hirar da hankalina baya garesa a ƙoƙarinta na kawar da maganar Hajiya da na kawo.sallamar da Baban Nana ya shigo da ita ya sani haɗiye sauran maganganuna.
Na ɗago kaina na kallosa tare yake da Zayyad shigarsa ta yau ta bambamta domin alkabba ce a jikinsa, baƙa da rantsin ruwar ƙasa a jikinta sai farin rawanin da yayi wa kansa da kuwa siririn sajen da ya kewaye tsukakken fuskarsa.
Kallo ɗaya na masa na ɗauke kaina gefe guda ina gaishe da Baban Nana ya ama mini cikin sakin fuska, sannan na fuskanto shi cikin faɗin"Ina kwana an tashi lafiya".
Bai kula ni ba kamar yanda nima daman ban sa raina da samun amsa daga gare shi ba, ya tsuguna yana gaishe da Hajja ta amsa tare da tambayar sa wannan shigar fa?.Baba Nana n ya amshe zancen cikin faɗin.
"Kinsan sabon masallacin da aka buɗe a can tsallake wajajen gefe da mu?".
Ta ɗaga masa kanta alamar ta gane hakan ya bashi damar ɗaurawa da faɗin"To shine yau zai yi limancin sallan juma'a masallacin, yau za'a yi addu'ar buɗe masallacin yana cikin manyan malaman da aka gayyata".
"Alhamdulillah! Allah ya sanya alkhairi yayi jagoranci".
Da amin suka amsa shi da Baban Nana ni kam na yiwa kaina ƙiyaman layli na ja bakina na tsuke,Hajja ta gabatar masa da abinci ya ce sai ya dawo don yana son ya tafi masallacin da wuri.
Har ya miƙe ya kallo ni yace"Ki shirya monday zaki fara zuwa awo".
Na masa wani kallo ido cikin ido domin na zata maganar waccen mutumin zai mini, amma sai na ga ya watsar da maganar ban amsa mishi ba sai Hajja da tace"To Allah ya kaimu".
Na amsa da amin can ciki, ta miƙe ta bi bayan Baban Nana da yace ta kawo masa ruwa a buta zai yi sallan walha, hakan ya bani damar faɗin"Dan Allah ka sanar dani wanene wannan mutumin ko zan sama nutsuwa".
Yana daga tsaye ya daku gabana da taku uku sannan ya ja tsaya, ya naɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa yace"ki dama dukkan tinaninki zuwa anjima zan kawo miki wasu muryoyi sai ki tantance su".
Yana ƙarishe zancen yana ɗaukar hanyar ficewa daga sashin na bi bayansa da kallo, yana tafiya a hankali har ya fice hawaye suka ciko mini kurmin idona na matse su har izuwa lokacin da Hajja ta dawo ta zauna ko sallamar da ta iso wajen dashi ban iya amsawa ba saboda rawar da muryata take yi.
Sai da ta zauna kana tace"Ummukursum wannan kukan nakin ya fara wuce misali, abinda yake cikin ki zai iya samun matsala ba a son masu juna biyu suna yawan damuwa ki cire komai a ranki ki miƙa lamuran ki ga maƙagin rayuwarki".
Hawayen da nake matsewa suka shiga rige-rigen zubowa daga idona ƙirjina ya mini nauyi tamkar an mini ajiyar dutsi, na kallo Hajja da ita ma ɗin ni take kallo nace"Hajja nagode da shawara in sha Allah zan yi ƙoƙarin aikata hakan".
Ta kamu hannuna cikin nata"Ummukursum tabbas mutuwar miji abu ne mai nauyi mussamman in akwai ƙatuwa a tsakanin ku dole ya zamo abin tinawa a gare a ko yaushe, amma idan kika yarda da ƙaddarar da ta faɗa miki sai komai ya zo miki da sauƙi".
Idona na cilla cikin nata ya bushe wankitak! hawayen ma sun daina tsiyaya nace"Hajja ba kowa bane yake ɗaukar ƙaddarar wasu a matsayin ƙaddara, da yawa suna ɗauka zaɓin rai ne yasa ake yi wa ƙaddarar ado a bisa son rai".
"Haka ne Ummukursum amma duk zuciyar da mai ta ya sanya mata dangana da haƙuri to kwaɓarsa bata yin ruwa".
Kaina kawai na kwantar akan cinyarta ina mai cigaba da sakin wani kukan, bata fahimce irin raɗaɗin da nake ji a cikin raina ba domin kuwa duk a tinaninta cewar aure nayi mijin ya mutu ya barni da wannan cikin har na fito neman wannan aikin.
A hankali take shafa kaina har izuwa lokacin da na tsagaita kukan da nake yi, na tashi na zauna ina goge fuskana dai-dai lokacin da su Iman da Nana suka yi sallama suka shigo nayi ƙoƙarin ƙago murmushi na dasa akan fuskata saboda ganin sun nufo ni da gudu suna rige-rige, suka faɗo jikina dukkaninsu.
Sannan suka gaishe ni na amsa tare da tambayar su ya makaranta suka amsa min da kalmar alhamdulillah.kafin suka miƙe suka je cire kayan su Imam ne ya fara fitowa cikin shirin tafiya masallaci yazo ya ɗauki buta yayo alwala, sannan Nana ma ta fito ita kam wajena tazo ta zauna. na sake mata fuska sosai tana bani labarin abubuwan da aka musu a makaranta.
Baban Nana ya fito dai-dai lokacin da Imam ya iddar da alwalan,ya riƙo hannunsa suka tafi masallacin bayan ya mana umarnin da mu ma mu tashi muyi sallan, muka miƙe muka yi alwala sannan muka shiga ɗaka muka yi sallan.
Ina zaune a akan sallaya har na iddar da tawa sallan na jiyo lasifikan masallacin ta amsa limamin yana karanto suratul juma'a cikin kakkausar murya gami da kushu'i. na shafa doguwar addu'ar da na ɗauka ina zare hijabin dake kaina na tsaya a gaban madubi ina kallon kaina sosai wasu ƙasussuwan wuya suka fito mini kamar a malala ruwa ya kwanta na saka hannuna ƙasan rigata ina shafo ƙasan marata, sosai cikin ya ɗago rigar wasu hawaye suka gangaro mini na kasa bambamcewa tsakanin farin-ciki ko akasin sa wanne nake yi a wannan lokacin.
Jin taku kamar za'a shigo cikin ɗakin nayi hanzarin kawar da hawayen na fito waje, na kamawa Hajja aiyukan da take yi tare muka kammala abincim rana muka ci sannan nida Nana suka haɗa wanke-wanke muka yi saannan muka yi shara.
Sai da aka yi sallan asr sannan ya baro masallacin tsawon wunin wannan ranar ko asibiti bai leƙa ba, a gajiye ya dawo gida don da ƙafarsa ya taka kasancewar babu wani nisa tsakanin su da masallacin. ko da ya iso bai iske kowa a bakin gate ɗinba hakan ya bashi damar wuce kai tsaye izuwa part ɗinsa yana isa ya rage kayan jikinsa kana ya faɗa bathroom wanka yayo ya sauya shiga izuwa wasu marasa nauyi, tea ya haɗa ya fito dashi hannu yana sha yana sauraran tashar NTA suna haska labaran yamma.
Sai da ya gama zuƙe tea ɗin sannan ya fito ya nufi part ɗin Abbu,da sallama ɗauke a bakinsa yana saƙalo ƙafarsa kafin gangar jikinsa. ya ƙariso cikin falon tare ya iske Abbu da wani amininsa tare da iyalansa gabaɗaya sai Nenne dake zaune a kusa da Abbu.Durƙusawa yayi ya gaishe su suka amsa masa cikin sakin fuska kafin aminin Abbun ya fara yaba masa akan ƙoƙarin da #STAND FOR NEEDERS FOUNDATION take yi.
Miƙewa yayi zai fice daga falon muryar Nenne ta dakatar dashi"Zayyad baka ga Rufaida bane tun ɗazu suka zo tana jiran ka".
Kallo ɗaya ya mata kana ya ɗauke kansa yana maida kansa izuwa ga Nenne yace"Nenne yanzu ina sauri ne ma gaisa wani lokacin".
Yana kawowa nan ya fice daga falon ransa yana masa wani irin zafi, bai san meyasa ba Nenne take son naniƙa masa wannan yarinyar mussamman a gaban Abbu. kawar da tinanin komai yayi daga kansa ya nufi part ɗin su Adam.
Tun kafin ya shiga cikin falon yake jiyo hayaniyarsu har ya shigo cikin falon basu san da shigowar sa ba.duk hankalinsu yana ga cacar da suke bugawa sai da yayiwa kansa mazauni akan ɗaya daga cikin kujerun da suke falon kafin suka ankara da shigowar sa, tsaki Haidar ya saka yana miƙewa zai bar falon Zayyad yayi saurin miƙewa ya cafko hannunsa.
"Zauna magana nake so muyi".
"Wata magana ce tsakanin mu da kai malam,ko wani iri ce ka faɗe ta ana haka ina jinta daga tsayen".
Kamo hannunsa Zayyad yayi ya ƙariso dashi har cikin falon kana ya zauna yana ciro wayarsa ya danna recording sannan ya mayar da ita cikin aljihunsa.
"Daman wata magana ce ta kawo ni domin mu tattauna ta da ku, a matsayin mu na ƴan uwa bai kamata ace muna irin wannan zaman ba,yanzu dai wata riba na samu na bussiness ɗin sarrafa gyaɗa shine nake son ko wanne daga cikin ku yayi tinanin wani sana'a zai yi tunda kun ƙi karatu sai na bashi jari".
Kallon- kallo Adam da Haidar suka shiga aikawa junansu kafin Adam yace"To wai kuɗin har nawa ne?".
Taƙaitaccen murmushi yayi yace"miliyan talatin ne".
"Ina fatan ba daga cikin dukiyar mu da take hannunka take wannan fatalin ba, kar daga baya kuma ace daga cikin gadon mu ne tunda shi wannan tsohon ya tattara dukkan dukiyar ya damƙa maka".
Miƙewa yayi ya tako har gaban Haidar kana yace"wannan kuɗin halalina ne".
"To munji kaje zamu yi shawara tukunna".
Murmushi yayi kawia ya fice daga falon har sai da yaiso cikin parking lot, kana ya zaro wayar daga aljihunsa yana sauraran recording ɗin da yayi. sosai muryoyinsu suka fito ganin su Abbu sun fito domin zuwa masallaci ya sanya shi binsu izuwa masallacin sai da suka yi sallan isha'i kafin suka dawo.
Tunda na iddar da sallan isha'i tinanin Mariya ya gallabi ruhina a ɓoye na tambayi Nana ta nuna mini sashin Hajiya,don na mance shi na saki jikina bayan naga shigewar Hajja banɗaki na nufi sashin Hajiyar.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________
Page 3⃣8⃣
Ina tafe ina waige saboda bana son wani ya ga shigewata sashin Hajiyar,sai da nazo dai-dai part ɗin da suke su uku suna a jere tsakanin biyun da ɗayan garden ne kawai nan fa ido ya raina fata na mance wanda Nana ta nuna mini domin sai da na iso dab! dasu naga duk gini da fantin su irin ɗaya ne.na kusa da garden ɗin na nufa ƙirjina yana dakan lugudan tara-tara tamkar zai faso fata da namana ya fito waje amma duk da hakan baisa na dakata daga nufar sashin da nayi gadan-gadan ba.
Na ɗaura hannuna akan mabuɗin ƙofar na tura a hankali naji ta a buɗe take,na fara leƙo da kaina sannan ƙafafuna gangar jikina ya biyo baya na maida ƙofar na rufe, na iso cikin falon na fara yan waige-waige na dafe ƙirjina da yake harbawa da matuƙar ƙarfi na ƙarewa falon kallo tsaf! na dai tabbatarwa kaina cewar ba nan bane sanda ya kawo ni gidan ya shigo dani.
Ina ɗago idona suka sauƙa akan makeken hotonsa da yake maƙale a jikin bango,cikin shirya likitoti tare da wasu mutane masu jajayen kunnuwa.gabana yayi mummunar faɗuwa duk jikina ya ɗauki karkarwa na juya da hanzari zan fice naci karo da mutum na ja da baya da sauri.
Ko da, da ban ɗago da nawa idanun ba amma jikina yana bani cewar nashi idanun suna kai na, na fara sakin hawayen ban kai ga cimma abinda ya fito dani ba, gashi na ƙara jefa kaina cikin wata masifar. sautin muryarsa da na tsinkayo suka dawo dani daga tufka da warwaradr da nake saƙawa a cikin zuciyata.
"Meya fito dake, ta yaya kika shigo nan meya kawo ki?".
Na gama ruɗewa ainun nace"na-na-na-na fito zani sashin su Mariya ne na ɗauko kayana ina son nayi wanka".
Ya tsura mini ido cikin tuhuma yace dani"sashin su Mariyan ne hanya ta biyo dake ta nan ko meye?".
"A'a sashin nasu ne ya ɓace min".
Bai ce dani uffan ba ya ƙariso cikin falon ya zauna akan rantsatstsun kujerun da suke a jere a falon masu launin ruwar toka kamar dai na ofishinsa, hakan da yayi ya bani damar nufar ƙofar ficewa daga falon ya dakatar dani da faɗin.
"Malam tambayar ki nake yi meya fito dake".
Cikina ya bada wani ƙara ƙululu! nayi tsuru da idanu har sai da ya ƙara maimata mini a karo na biyu a zafafe.
"Na fito ne zanje na duba Mariya naji Sarauniya tace yau ita zata je sashin Hajiya ta ɗebe mata kew...."
Bai bani damar ƙarisawa ba ya ɗauke ni da wata kyakykyawan mari a gefen fuskana na bangaren hagu, da ya sanya ni sakin wata gigitacciyar ƙara ina jin kamar marin ya tafi min da idon gani na na gefen.
Sosai nake kukan har ƙafafuna suka fara butulcewa ɗaukar nauyin gangar jikina, na durƙushe ya iso dab! dani haɗi da faɗin"Me kika sani akan abinda kike faɗa sannan yaushe kika ji tana faɗar hakan?".
Tsoronsa ya hana ni taɓuka komai illa kukan nawa da na tsagaita yinsa, na lura kamar ya fara fusata nace"Ranan ne naji Sarauniya tana faɗa tace yau Mariya ce zata je".
Yayi shuru bai tanka mini ba ya kallo ni yace"shine kika fito yin meye yanzun kenan?".
"Na fito ne domin na dakatar da Mariya daga zuwa sashin Hajiyar".
Na faɗa ina ƙoƙarin danne tsoron da ya taso mini a wannan lokacin, ya kafe ni da idanu na tsawon daƙiƙu kana ya miƙe jijjiyoyin kansa suka shimfiɗa raɗa-raɗa a saman goshinsa. ya dafe goshin yana runtse idanunsa ba tare da ya buɗe idanunsa ba yace"kina fusata ni da yawa akan wannan taurin kanka da kike dashi, har kina sani aikata abinda ban yi niyya ba watau ɗaura hannuna akan mace da sunan duka".
Ban kula shi ba domin maganar sa sai ta mini kama da wannan karin maganar da ake cewa daga baya kenan wai anyi sadaka da karuwa,na share hawayena na katse shuru da faɗin"Har yanzun baka sanar dani wanene wannan mutumin ba".
Yayiwa kansa mazauni akan kujerar ya naɗe hannayensa a ƙirjinsa, kana ya ɗauko wayarsa da take ajiyen a saman teburin gilashin da yake tsakiyar falon, ya shiga latsawa ya kallo ni yace"ki saurara kiji waɗannan muryoyin da kyau".
Na ɗaga masa kaina sannan ya danna wani abu cikin wayar sai ga sautin murya ya fara fita,na ƙara baza ƙofofin kunnuwana ina sauraro,muryar dab! da na ƙarshe ya sanya ni miƙewa babu shiri jikina ya ɗauki mazari tamkar tsohuwar ƴar borin da taji tsimi tabbas muryar mutumin ta yi dai-dai da muryar wanda ya mini fyaɗe.
Ƙafafuna suka fara ƙarƙarwa na tafi da baya nayi luu! daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba,sai tashi nayi na ganni kwance shame-shame a ƙasa na wangale marafan idona da suka mini nauyi ina kallon wajen dishi-dishi idanuna suka iya hango mini bangaren da yake tsaye ya zara dukkan hannayensa cikin aljihunsa.
Na tashi zaune daga kwanciyar da nayi ina ƙara gyara zaman hijabina da ya tattare a saman kafaɗuna, wani kuka na saka mai ban tsoro saboda yanda sautin sa yake amsa ko'ina a cikin falon har muryata ta fara dishashewa numfashina yana cunkushewa waje guda.
"Ki tabbatar wannan muryar ita ce na wanda ya miki fyaɗe?".
Tambayar da ya jefo mini kenan haka nan ta zamo abun farko da kunnuwana suka fara ji bayan suman da nayi na farfaɗo, na ɗago jajayen ƙwayoyin idanuna na sauƙe shi a kansa cike da wani irin jarumta da ƙarfin yarda da kai nake faɗin"Tabbas wannan ita ce muryarsa domin tana ɗaya daga cikin abubuwan da baza su taɓa gogewa a cikin tarihin rayuwata ba, wallahi wannan muryarsa ce dan Allah ka nuna mini shi na tabbatar ko kashe shi nayi ba zanji sanyi daga uƙubar da ya jefa rayuwata a ciki ba".
Yayi shuru na wasu mintuna kafin yace"tashi kije ki zan neme ki idan na kammala bincike na".
Na rarrafo har gaban sa cikin kukan da ta fara galabaitar dani nake faɗin"Don girman Allah da soyayyar ka da iyayenka ka nemo mini shi, inason ganin fuskarsa ko da shine abinda zan gani na ƙarshe a rayuwata, ina son ganin fuskarsa na masa kallo ido cikin ido don na tambaye sa laifin da na aikata masa da na cancanci hukuncin da yayi mini zan damƙa masa abinda na haifa ba tare da na ƙara waiwayarsa ba".
Na ƙarishe maganar cikin raunanniyar murya tare da ƙaryewar zuciya,na lura da lokacin da shima ya saka hannayensa ya tare hawayen da suka ciro masa kurmin idanu yace dani"Nace ki tashi kije zan neme ki idan na gama binciken da nake yi, sannan gargaɗi na ƙarshe da zan miki kadda ki ƙara kuskuren fitowa waje kinji ni ko?".
Na ɗaga masa kaina ina ƙoƙarin miƙewa zan fice yace"inason ki cire kanki daga lamarin Mariya ki kuma goge duk abinda ƙwaƙwalwarki ta miki hadda akan furcin da Sarauniya tayi".
Ban amsa mishi ba saboda nauyin da bakina ya mini na fice daga cikin falon,da ƙyar nake jan ƙafafuna da suka sanƙare tamkar dutsi ƙwayayen wutar sola tana hasko ko'ina.
Kwance Nenne take a kan bed ɗinta ta lulluɓe rabin jikinta da blanket, tana sauƙe wahalallen ajiyan zuciya don ba kaɗan ba yarinya ta wahalar da ita. sai Mariya dake takure can ƙarshen ɗakin ta haɗa kai da gwiwa tana nata kukan duk suturarta Nenne ta raba ta dasu don haka ta tuƙuiƙuye kanta tana kare ƙirjina da hannayenta.
Tashi Nenne tayi tana jawo blanket ɗin tana rufe jikinta dashi, zata shiga bathroom domin tayi wanka siririn tsaki ta saka in ba jaraba ba ma irin nata ina ita a matsayin da take dashi har ta haɗa jikin da maƙasƙanciyar ƴan aikinta. tazo dai-dai windown ɗakin da yake facing part ɗin Zayyad taga fitowa mace daga part ɗin tayi saurin watsa idanunta a wajen tabbas ba idanunta bane suke mata gizo macen ce da gasken gaske.
Wayarta ta ɗauko da sauri ta danna video ta shiga ɗauka a wayarta, hasken ƙwayayen wutar solabda suke haska ko'ina a cikin gidan ya bata damar ƙarewa fuskar yarinyar kallo. sai da tayi yanda ya ishe ta kafin ta katse vidoen.
Tana ƙara kallo tare da son tina idan ta taɓa ganin fuskar yarinyar,tabbas ita ce wacce Zayyad ya kawo a matsayin ƴar aikin Hajiyarsa wani murmushin gefen baki tayi wanda ita kaɗai tasan ma'anar da kuma dalilin yin sa.da wannan videon zata yi amfani wajen tirsasa shi da ya mallakaka mata komai ita da ƴaƴanta da suka danganci dukiyar Alhaji da yake hannunsa,domin ta san ba zai so Alhaji ya ga wannan videon ba don yana matuƙar kiyaye yardar da Abbu yake dashi a kansa.
"Lalle a fuska kamar na Allah, ya nuna yafi kowa sanin Allah da tsoron sa ashe har karuwa zai ɗauko ya kawo cikin gida da sunar ƴar aiki tana shiga part ɗinsa duk daren duniya suna aikata badaƙala waya sani ma ko cikin dake jikinta na shine".
Tana ƙarishe zance ta wurgowa Mariya wani kallo tana ɗaurawa da faɗin"Dalla malama tashi ki wuce, ki bar mini ɗaki kin cika min kunnuwa da kukan banza".
"Hajiya kayana zan ɗauka".
"Ba zaki ɗauki kayana ba haka nake so ki fita tsirara".
Wani kukan Mariya ta kuma sakewa domin tasan tunda ta faɗa,sai ta aikata shi knocking ɗin da aka fara yin a ƙofar ɗakin ya sanya Nenne faɗin"waye?".
"Nenne ki buɗe nine, Abbu ne ya aiko ni ƙiran ki yana falo".
Adam ya faɗa yana barin bakin ƙofar tun kafin ya ji amsar da zata bashi,juyowa tayi ga Mariya tana faɗin"Allah yaso ki bazan barki ki fita a haka ba, domin Alhaji yana falo tashi ki ɗebi kayanki ki fice min".
Tashi Mariya tayi ta kwashe kayanta ta mayar jikinta sannan ta fice daga ɗakin,kanta a ƙasa ta yiwa Abbu sannu da hutawa ta wuce shi a falon ta koma nasu sashin.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
__________________________________
Page 3⃣9⃣
Sai da ta fito waje sannan ta saki kukan da take ƙunshe sa a cikin ranta saboda zaman da Abbu yake a falon,jin mutum tsaye a kanta ya sata saurin ɗago kanta cikin firgici kafe ta shima yayi da ido yana ƙara gaskata maganar ashe har yanzu Nenne bata watsar da wannan mummunar ɗabi'arta ta ba.
"Daga ina kike?".
Shuru Mariya tayi tana ƙoƙarin daidaita nutsuwarta, kana cikin rawar murya tace"daga sashin Hajiya nake naje yin aiki".
Furzar da iska yayi daga bakinsa ya tsani a masa ƙarya a rayuwarsa, mussamman akan abinda ya sani kawai tabbatarwa yake son yi fuskanto ta yayi sosai yace"Look Mariya na riga da nasan komai daga ina kike?".
"Daga sashin Hajiya nake".
" Me ya kai ki cikin wannan daren?".
Maganar ce ta mata nauyin furtawa tayi shuru sai da ya ƙara maimata mata tambayar sannan tace"ƙira na tayi ta aikata abin.....".
Kasa ƙarisa maganar tayi saboda kukan da ya taso mata, ta sake shi. Gigitaccen ajiyan zuciya ya sauƙe yana riƙo ƙugunsa tare da dafe goshinsa, ransa yana masa soya sosai yawun bakinsa ya ɗauke cak! SALON da ƘADDARArsa tazo tashi na daban ne wasu lokuta ya kan zauna ya tambayi kansa wani laifi ya aikatawa mahaliccinsa da ya jefo shi cikin wannan ahalin.
"Ya isa haka kukan yanzu ki wuce ki koma part ɗin ku,gobe za muyi maganar amma bana son kiyi ta da kowa kinji ni ko?".
Kanta ta ɗaga masa sannan ta raɓa ta gefensa ta wuce nasu sashin, part ɗin Nenne ya ƙurawa idanu yana jin wani irin tsanarta da halayyanta da suke ƙara girmama a cikin ransa.yayi tinanin tun lokacin da ya kama ta akan Sa'ida ta watsar da lamarin ashe bata canja zani ba.
Cikin garden ya nufa ya zauna akan kujerun plastic da suke jere a wajen, tallafo kuncinsa yayi da hannayensa yana runtse idonsa kansa kamar zai fashe izuwa gida biyu haka yake ji.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un".
Ya furta a hankali yana buɗe idonsa yana kallon yanda bishiyoyin wajen suke kaɗawa, saboda iskan da ya taso tare da wani baƙin hadiri mai haɗe da iska mai ratsa jiki.
Duk yanda sanyin yake ratsa jikinsa ya kasa jan jikinsa ya bar wajen, haka ya daskare a wajen kamar an dasa shi har sai da ruwar ya fara sauƙa kaɗan-kaɗan ya lumshe idanunsa. tinani ne barkatai a suke masa yawon cikin curin kansa ya rasa wannan zai farayin nazari akansa,lamarin yarinyar nan da Haidar ko ko ƙaryar da yayi wa Hajiyarsa da Abbu ko kuma lamarin Nenne da ƴan aikinta.
Fitowa Baban Nana yayi domin duba dawakai ya hango shi cikin garden ɗin yana zaune, hasko shi yayi da tocilar dake hannunsa sannan ya nufo shi har ya ƙariso wajen bai sani ba sai da ya dafa kafaɗarsa sannan ya buɗe idonsa tar! a kansa.
"Zayyad lafiya kake zaune a nan ga ruwa ya sauƙo?".
Ciro leɓɓansa yayi da ƙarfi kana yace"Baba lafiya kawai gajiya ce take damuna sai ciwon kai kuma da ya saka min".
Sai da ya ƙare masa kallo tsaf! shakka babu ya san cewar,abinda yake damun Zayyad a halin yanzu ya wuce matakin ciwon kai kamar yanda yake faɗa domin fuskarsa ta fallasa dukkan abinda zuciyarsa take ƙoƙarin burnewa.
"To yarona Allah ya kawo sauƙi, ka tashi ka shiga ciki mana har wannan ruwar ya saka maka wani ciwon, kai da ciwonka ba sanyi yake so ba".
Murmushi ya ɗan saka yana miƙewa yace"Yanzu nake son tashi sai kuma ruwan ya sauƙo, sai da safen mu a tashi lafiya".
"Allah ya kaimu yarona".
Da amin ya amsa dashi yana ɗaukar hanyar barin wajen ya doshi part ɗinsa sai da ya biya ta wajen dawakan sannan ya wuce.yana isa ya maida ƙofar ya kulle da key sannan ya zube a falon yana sauƙe numfashi.
Tun sanda na fito daga sashin nashin,na nufi sashin Hajja shigowata tayi dai-dai da ɗagowar Hajja tana tattare abubuwan amfanin da bata son ruwa ya sauƙo ya taɓa mata su.
Ganin ta ya sani shan jinin jikina na faƙaici idonta na goge ragowar hawayen da suke fuskana, ta kafe ni da kallo har na ƙariso gaban ta nayi yaƙe nace"Hajja kina nan".na ƙarishe ina karɓar tabarmar da take nannaɗewa.
Ganin har yanzu tana kallona ya sani faɗin"Ina su Nana fa ko har sunyi bacci?".
Ta ɗauke idonta daga gare ni kana tace"Ummukursum ina kika je?".
Na soma daburcewa cikin ƙiƙƙina nace da ita"Hajja na ɗan fita waje ne, na sha iska yanayin garin ya sanya ni nishaɗi".
Na dasa aya ina ƙara yin wani yaƙen, jijjina kanta kawai tayi tace"to ki shige ciki kar ruwan nan ya taɓa ki".Daga haka tayi gaba ta barni sololo na bita a baya har sai da muka isa cikin falon na iske Baban Nana yana cin abinci ya tare ni da tambayar"Ummukursum ina kika je ne haka?".
Kafin na kai ga bashi amsa Hajja ta amsa mishi cikin faɗin"wai ta ɗan fita waje ne, shan iska saboda yanayin yayi mata daɗi".
"Hakan yayi yana da kyau tana samun hutu ta hanyar kaɗaita kanta".
Sai da safe na musu kawai na shige ɗaki ina jin Baban Nana ya na faɗin zaije ya dubo dawakai saboda hadirin da ya gangamo.
Bacci yaƙi ziyartar idanuna sai juyi nake yi akan katifar, Nana na kwance kusa dani shi kuwa Imam an masa nasa shimfiɗin. tar! idanuna duk yanda naso na zubar da ƙwalla hakan ya gagare ni tinanin Daada ya baƙunci ruhina.
"Daada ki yafe mini nasan na saka ki cikin wani hali da kuma sauran ƴan-uwana, haƙƙinki bazai taɓa bari na, na rayu cikin salama da kwanciyar hankali ba"
Na faɗa raina yana mini soya na bala'i, na tashi zaune na jinjina bayana da pillow tare da lumshe idanuwa da suka soye muryar mutumin da yayi mini fyaɗe tana dawo mini cikin kunyar kaina tabbas wancan muryar nasa ne ko rantsuwa nayi babu kaffara a kaina.nayi saurin watsawa kaina tambayar da na gaza cimma amsarsa.
"To shi kuma Zayyad a ina ya san shi, har ya naɗi muryarsa menene haɗinsa da wancan mutumin da na gani jiya?".
Kwantar da kaina nayi lamau ina fidda numfashi a wahale daki-daki,ranar ba don bacci ya cika cikakken ɓarawo ba da ba zai yi nasarar ɗauka ta ba saboda matsanancin tashin hankalin da nake ciki ƙirjina ya mini nauyi yana zafi.
Washe gari haka na wuni kamar marainiyar ƴar kwikwiwon kariya,duk jikina babu kuzari Hajja ta wuni tana jeranta mini tambayar meyake damuna. Na amsa mata da babu komai har ta haƙura ta share ni sai can da yamma idanuna suka yi tozali dashi ya shigo ya gaishe da Hajja ta amsa sannan ya ba wa Nana ledar kayana yace ta kawo mini na tashi na shige ɗaka na sauya kayan jikina don tunda nayi wanka sune a jikina ban canza ba.
Koda na fito na iske Hajja tana karanta masa cewar yau tun safe bani da walwala,yace ta barni wai daman masu juna biyu suna samun kansu cikin irin wannan yanayin. ban kula su na ja gefe na zauna titirin tafasan da miyar da Hajja take ta rana ya bugi ƙofofin hancina na yunƙura na mike da sauri naje makwarari na fara amai sosai nayi sa kamar zan amar da duk kayan cikina, Hajja tana riƙe dani tunda na fara har na gama ta kawo mini ruwa na wanke fuskana sannan ta shigar dani ɗaki na kwanta.
Kasancewar yau asabar bashi da niyyar zuwa asibiti, ya ɗauki ɗaya daga cikim dawakan da aka kawo ya fita dashi filin polo cikin ƙwarewa yake yin rinding ɗin har izuwa lokacin da ya bar dokin ya huta shima ya zauna akan kujerun da suke a jere a wajen robar ruwa ya ɗauko daga cikin jakar da ya taho da ita ya ɓalle marfinta ya fara zubawa fuskarsa sai da ya juye gabaɗaya sannan ya lumshe idanunsa yana furzar da iska daga bakinsa.
A hankali yake murza farin zoben azurfan dake hannunsa, ransa yana masa wani iriyar ɗaci izuwa yanzu kam ya gama ƙure tinani da basirarsa zarginsa gabaɗaya ya koma kan Haidar. amma ta yaya zai gaskata hashashen zuciyarsa, ta yaya zai sanya Haidar ya sanar dashi abunda ya faru. a cikin satin nan zai tafi bauchi sannan yayi ƙudurin ba zai dawo ba sai ya gano komai game da yarinyar, rayuwarta ta baya da kumaa iyaye da ƴan-uwanta har da dalilin da ta rabo ta dasu.
Miƙewa yayi ya zaro wayarsa daga cikin aljihunsa yana dialing ɗin lambar Ahmad ringing ɗaya ya ɗauka, suka gaisa sannan ya ɗaura da faɗin"zan shigo cikin bauchi may be wednesday don zan riga su Abbu shigowa, akwai wani bincikan da nake son nayi inason goyan bayanka".
"To shikenan Hamma sai ka zo ɗin, ai daman kai kam ya kamata kazo da wuri don kai kaɗai ne a dangi baku taɓa haɗuwa da ita ba".
Cikin sauri yace"ita waye kenan?".
Ahmad ya saki murmushi kana yace"ita amaryar tawan mana".
Kit! ya kashe wayarsa yana mayar da ita aljihunsa,sannan shi ɗaya ya soma sakin murmushi wai Ahmad ƙanin bayan sa shine zai yi aure. shi kam da aure sai randa ubangiji ya zartar domin matsalar rayuwarsa ta fi komai a wajensa da har take sashi mantawa da wani abu wai shi soyayya ko aure, ba ya jin akwai wata macen da zata iya zama dashi a yanda yake kuma ta iya bashi kulawa kamar yanda Hajiyarsa take yi.
Haka nan kawai yau ya tsinci kansa cikin annashuwa da farin-ciki mussamman in ya tina yanda fuskar mahaifiyar Mariya take bayyanar da tsantsan farin-ciki da godiyarta ga Allah da ya dawo mata da ƴarta, duk da da farko taso yin gardama tare da kafewa akan dole ita ƴarta tayi wannan aikin saboda dashi suka dogara hakan da tayi ya ƙara tabbatar masa da abunda Mariya ta faɗa akan cewar mahaifiyarta bazata amince ta bar wannan aikin ba kuma ta sanar da ita lalatar da Nenne take yi dasu amma duk da hakan tace ta cigaba da aikin.
Sai da ya ajiye mata wasu kuɗaɗen tare da yin alƙawarin zai ɗauki nauyi ci da shan su, har ma da karatun Mariyar sannan ta amince.
Sai gab! da magrib ya bar filin polon ya wuce gida wanka kawai yayi ya fito ya tafi masallaci, sai da aka yi sallan isha'i ya tsaya ƙarawa mutane karatun wasu littattafan addini. a matuƙar gajiye ya dawo ga yunwar da take ƙwaƙular hancin cikinsa tun dare jiya rabon sa da sanya wani abu a cikinsa dangin abinci tun tea ɗin da ya sha daren jiya.
Part ɗinsa ya wuce ko sai da safe bai yiwa Abbu ba,tea ɗin ya kuma haɗawa mai kauri yasha da bread take jikinsa ya shiga tsatsafar da gumi ya kwanta a wajen yana tausayin irin rayuwar da Allah ya tsara masa ace wai shi da gidan ubansa amma bashi da kwanon abinci a gidan.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
Page 4⃣0⃣
_______________________________
Yau ta kasance monday ranar da za muje asibiti domin fara yin awu, Hajja tace na shirya da wuri nayi hakan kuwa su Nana suna fita makaranta ya shigo ya shirya tsaf! cikin shirgarsa ta zuwa aiki na. na sata kallonsa sai ya fito mini sak! ranar da ƙaddarata ta fara haɗa ni dashi.
Ya tsuguna ya gashe da Hajja, ta amsa masa tare da gabatar masa da abin kari yace yana azumi. nima na tsoma baki cikin maganar tasun nace"Ina kwana an tashi lafiya".
A taƙaice ya amsa mini da faɗin"Lafiya ƙalau".
Rashin ganin fuska ya sani yiwa bakina linzami na tsuke shi.
"Ki fito ina jiran ki a cikin mota".
Ya faɗa yana miƙewa ya fice, nima na tashi na shiga ɗaki na ɗauko hijabina na saka nayiwa Hajja sallama na fita. a bakin sashin na hange shi tsaye a jikin motar na isa wajen da sallamata, sallamar kawai ya amsa ya shige ganin haka nima ya sani jan murfin ƙofar motar zan shiga gidan baya yace na shigo gaba.
Na buɗe ƙofar na shiga sannan ya ja motar muka fice daga cikim gidan, ya saka faifayin kaset ɗin karatun sheik Ahmad Suleiman har muka isa cikin asibitin ya shiga ta babban gate mai ɗauke da hatimin sunan asibitin da manyan ɓaƙaƙe.
Cikim gurɓataccen hausata da bata gama zama a bakina ba, na haɗa sunan asibitin *ZAYYAD EL-FAROUK HOSPITAL*.
Mai gadi ya zuge gate ɗin ya tura hancin motar ya shiga da ita cikin, ya faka motar sannan ya kashe ta ya fita nima na fito naga ya ƙwaƙwumawa kansa takunkumi ya wuce gaba ina biye dashi a baya har izuwa cikim asibitin.
Yayi wa wata ma'aikaciya magana cikin yaren turanci, nikam na sake baki ina bin su da kallo saboda yanda ya rikiɗe cikin ƙanƙanin lokaci ya kuma kamar bature.sai da ya mini magana na dawo cikin hayyacina daga kallon nurse ɗin da nake yi ta bani sha'awa sosai na saki murmushi ƙasa-ƙasa da na tina cewar nan da wani lokaci ƙadan Zulaihat ma zata fara sanya kayan likita ko haka na tsaya na cika wani sashi daga cikin burin da nake dashi na karatu domin yanzu kaɓ nasan lokaci ya ƙure mini.
Muka shiga wani ɗaki tare da nurse ɗin bayan yace mata in an gama ta kawo ni office ɗinsa, awun ta fara mini kana ta mini nuni da wani gado take na kwanta ta kuma cewar na kwaɓe hijabina na cire sannan ta ɗan ɗaga rigata ta fara gabatar da aikinta bayan ta saito mini wani naƙura yana fuskanto ni, tace mini ina kallo zan ga abinda yake cikina. na ƙurawa na'urar idanu cikin zaƙuwa.
Ta fara goga mini wani abu akan cikina wal! hoton abinda yake cikina ya bayyana cikin na'urar. na soma gigituwa ganin yaron cikina yana ta watsil-watsil so nake na tambaye ta akan yanda naga yaron kamar ya rabu biyu koko haka na'u'in na'urar take oho.
Sai da ta gama tsaf! kana na tashi na zauna na jawo hijabina na mayar jikina, tun kafin na kai ga guntsar mata da tambayar da nake son fesarwa ta kallo ni tare da washe bakinta tace"congratulation Madam abinda yake cikin ki suna lafiya, kuma suna kwance a inda ya dace sai dai jinin ki ya hau a gwajin da na miki. dole ki rage saka damuwa a cikin ranki saboda ba'a son mace mai juna biyu tana saka damu a ranka ya kan haifar mata da ciwon hawan jini da zai bata matsala yayin da tazo haihuwa".
Kafin na ɗaura da wani abun, ta koma cewa "Gashi ƴan biyu kike ɗauke dashi a cikinki, dole kina samun kyakykyawan kulawa ko dan ƴaƴan da suke cikin ki".
Na rasa me zanyi tsakanin mamaki ko murna kawai na saka kuka, ta dafo kafaɗata tana bani haƙura tare da nusar dani cewar ba kuka ya kamata nayi ba godiya ga Allah zanyi. ban ce da ita uffan ba ta kamo hannuna muka fito har izuwa ofishinsa yana tsaye jikin window yana riƙe da kofin shayi a hannunsa.
Ba tare da ya juyo ba, ya amsa sallamar da nurse ɗin tayi ta mini nuni da kujera tace na zauna na zauna. ina mai cigaba da kukana sautin kukan da na shigo dashi ya sa shi waigowa ya tsubawa nurse ɗin ido yace"kinyi mata duk abinda nace?".
"Yes sir duk nayi mata har scanning, sannan ga result ɗin da ya nuna yana ɗauke da ƴan biyu".
Ta ƙarishe tana miƙa masa result ɗin, ya karɓa yana duddubawa ya ɗauki mintuna biyu yana dubawa kana yacewa nurse ɗin taje. ta fita ya dawo mazauninsa ya zauna ya ajiye result ɗin a gabana.
Ban ɗago kaina na kalle shi ba, zuciyata tana harbawa da gudu- gudu Allah kenan wai ashe yanzu ƴan biyu ne suke rayuwa a cikin cikina. na tsananta kukana da na tina bani da abinda zan faɗa musu a sanda suka diro duniya suka nema sanin waye mahaifinsu.
"Ina fatan ta miki bayanin komai, ƴan biyu kike ɗauke dasu a cikinki sai dai wani lokacin shima kana scanning ɗin baya zamowa gaskiya domin Allah ne kaɗai yasan gaibu da kuma abunda mahaifa take ɗauke dashi"
Kukan da nake yi ya hanani samun damar amsa mishi, na shiga sauƙe ajiyan zuciya tausayin yaran da suke cikina ya mamaye ruhina tun kafin su zo duniya.
Har cikin kansa yake jin sautin kukan natan yana ratsawa, wani tausayin ta ya hana shi motsa koda gaɓa daga jikinsa. dole ya ajiye fushi da kuma zafin ransa ya bata kulawa mussamman da yanzu zarginsa ya karkata ga Haidar. miƙewa yayi yace"tashi mu tafi".
Na tashi jikina duk yana rawa ya fice ina biye dashi, har jikin motarsa na ɓalle marfin na shiga sannan shima ya zagayo ya zauna ya tada motar ya fice daga cikin asibitin. jin ya takawa motar birki ya sani ɗago kaina ina watsa idona akan titin ya fice ya shiga cikin wani babban shago ya ɗau lokaci kafin ya fito da wasu samari biyu a bayansa suna riƙe da ledodi niƙi-niƙi ya buɗe musu booth suka zuba kayan sannan ya shigo ya ja motar.
Rufe idona nayi har sai da na kuma jin ya danna birki, wanda hakan ya tabbatar mini da cewar mun kawo gida ne na buɗe idona naga saɓanin haka domin gefen titi ya faka na ɗan kallo shi naga ya sunkuyar da kansa yana danna wayarsa kamar saƙo yake aikawa.
"Jibi zan tafi bauchi, sannan bazan dawo ba sai na tabbatar da labarin da kika bani inason ki mini kwantance gidanku da unguwan ku".
Zuciyata ta kuma yi mini nauyi fasalin gidan mu ya fara dawo mini cikin kunyar kaina, da kuma irin rayuwar da muke gudanarwa a cikinsa tare da Daadarmu da sauran ƴan-uwana. na ba wa ƙwallar da suka ziyarci idona damar tsiyaya sai da nayi kuka sosai ya miƙo mini wani farin handkerchief yace na goge idona banyi musu ba na amsa na share hawayen fuskana kana na muzguta ina faɗin.
"Kamar yanda na sanar da kai cewar sunan unguwarmu wunti stree a nan cikin jahar bauchi, gidan mu ba ɓoyayye bane domin da kaje unguwar kaje kana neman gidan da ake surfe da wankau za'a kai ka gidan mu".
Na ƙarishe ina sakin wani kukan, mintuna biyu tsakani bai ce dani uffan ba kafin yace"Shikenan in sha Allah zan je ɗin".
Daga haka ya tada motar ya ɗaura ta akan titi muka bar wajen, sai da muka iso gida ya faka dai-dai sashin su Hajja zan fita na juyo haɗi da faɗin"idan kaje ka gaishe mini da Daada ka nema mini afuwa da yafiyarta sannan karka ɓoye mata halin da nake ciki ko hakan zai sa ta yafe mini ƙuncin da na saka ta a ciki".
Ina dasa aya anan wuf! na ɓalle murfin motar na fice, na wuce Hajja dake zaune a tsakar gida tana tsintar shinkafa ta bini da kallo tana cewa dani"Ummukursum lafiya ina shi Zayyad ɗin?".
Ban tsaya bata amsa ba domin ko na tsaya bakina ba zai iya furta mata komai ba, shigowar Zayyad ɗin ya dakatar da ita daga yunƙurin biyo baya na da tayi niyya.
Sarkin gida ya shigo da kayan masarufin da ya lodo a bayan motarsa, ya fake su gefe guda sannan ya fice.
"Zayyad lafiya ita kuma ta shigo tana kuka daga zuwa asibiti, ko an auna anga da wata matsalar ne?".
Sai da ya zauna saman tabarmar kafin yace"Hajja babu wata matsala, an dai yi mata scanning ne an tabbatar da cewar ƴan biyu take ɗauke dasu".
Kalmar Alhamdulillah Hajja ta shiga faɗi cikin bakinta, tare da mini fatan Allahu ya raba lafiya. kayan da ya sayo yayiwa Hajja nuni dasu tare da faɗin"jininta yayi ƙasa dole tana samun kulawa da kuma cin abincin da zai gina mata jiki, shiyasa na kawo wannan kar na ɗaura muku nauyi da yawa".
"La! Zayyad wallahi ba komai Allah dai ya sauƙe ta lafiya, itama ta kama aikinta".
Shuru yayi yana rusunar da kansa ƙasa, duk mutanen da suka yarda dashi yarda mai tsanani yayi musu ƙarya tare da ɓoye musu haƙiƙanin gaskiya game da yarinyar.a hankali ya miƙe ya fice ya wuce sashinsa.
Tun daga ranar ban kuma sanya shi cikin idona ba, sai dai ina samun ririta da kulawa mai tarin yawa daga Hajja kamar zata maida ni ciki haka take ji da cikin da yake cikina.
Yau ta kasance ranar da zai tafi bauchi tun asuba suka yi waya da Hajiyarsa ya sanar da ita,zaune yake a gaban Abbu yana faɗa mishi cewar yau shi zai wuce insun zo sai su dawo tare fatan sauƙa lafiya ya masa tare da faɗin ya gaishe dasu Ammieyn kafin ya iso.
Wani murmushin da Nenne take sakar masa gabaɗaya ya ƙulle masa kai, ita kuwa nata nufin daban domin wannan vidoen da take ɗauke dashi shi zai zame mata tamkar makamin da zata yi amfani dashi wajen mallakar duk dukiyar da yake hannunsa, bayan ta karɓa kuma ta bayyanawa Abbu vidoe tasan dole zai ɗau ƙwaƙwraran hukunci akan sa. wani dariyar ta kuma sakewa saboda shiryawan da zuciyarta ta mata akan wataƙil ma ya kore shi daga gidan.
Miƙewa yayi ya fice daga part ɗin yana mai cike da mamakin Nenne a cikin ransa, jiya ya kwana da tinanim cewar Nenne zata fuskance shi akan dalilin da ya saka ya ɗauke Mariya ya mayar da ita ga Mahaifiyarta. amma sai yaga saɓanin tinaninsa.
Cin karo yayi dasu Haidar da Adam suka tsaya, ɗauke kansa yayi kamar bai gansu ba suka nufo shi.
"Jiran fitowarka muke yi".
Haidar ya faɗa cikin gatse ya juyo ya kalle shi cike da fusata yace"gani na fito menene?".
"Akan maganar jarin da kace zaka bamu ne, to mun gama shawarar".
"Yanzu tafiya zanyi zamu tattauna maganar, bayan na dawo".
Ya faɗa ba tare da ya ƙara kallonsu ba,sashin Hajja ya nufa ya mata sallama lokacin ina banɗaki ina wanka naji muryarsa, yana bada amanata a Hajja tare da faɗin Nurse zata dinga zuwa gida tana duba lafiyata sosai tayi masa addu'o'i sannan ya tafi.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
Page 4⃣1⃣
_________________________________
Sai da ya fara biyawa ta cikin zaria yaje gidan Hajiyarsa, ya duba yanda ma'aikatan suke kula da gidan kafin ya wuce don tunda ta tafi bai sama damar zuwa ba sai yau.
Ƙarfe huɗu da mintuna bakwai kamar yanda agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya nuna ya iso cikin garin bauchin yakubu, a masallacin da yake kusa da unguwarsu Ammiey ya tsaya yayi salla sannan ya wuce gidan.
Tunda ya ƙira ya sanar da Ammiey cewar ya iso take compound tare da su Ramlat tana jiran dawowar, shigowar motar sa ya sanya su miƙewa a tare ya ƙariso da motar yayi parking cikin parking lot sannan ya fito.
Ya ƙariso ga su Ammiey cire hular kansa yayi ya rusunar da kansa a gabanta, ta dafa kansa tana sanya masa albarka sannan ya juya ga sauran ƴan-uwan mahaifiyar tasa su mahaifiyar Ahmad da Ramla da kuma sauran. duk ya gaishe su cikin girmamawa suka amsa masa fuskarsu tana bayyanar da tsan-tsan ƙaunar sa.
Gidan a cike yake sosai da dangi na kusa da na nisa,duk da cewar bikin sai ranar juma'a za'a ɗaura part ɗin Ahmad aka buɗe masa yayi kwanta ya sauya shiga bai tarar da Ahmad ɗin ba domin ya ji Anty Khadija ƴaƴar mahaifiyarsa ƴar Ammiey ta farko tana faɗin ango yana wajen aikinsa bai dawo ba.
Yana kwance yana waya da Hajiyarsa, Ammiey ta aiko ƙiransa sallama yayi da Hajiyarsa ya katse ƙiran ya fito duk suna zaune a falo ya iske su yazo ya zauna gaban Ammiey kwantar da kansa yayi a jikin ƙafarta ko damuwa baiyi da tarin ƴaƴa da jikokinta da suke wajen ba. suka saka dariya wanda yasan cewar dashi suke yi amma bai damu ba.
Dawowar Ahmad ya sanya su Ramlat faɗin"ga angoya dawo".
Ya iso cikin fara'a yama kwasar gaisuwa ƴar hararar Zayyad ɗin yayi da ya toshe kunnuwarsa da earpieces yama sauraron karatun al-qur'ani.
"Hamma ashe har ka ƙariso shine baka ƙira ni, kuma babu wanda ya faɗa min".
Ahmad ya faɗa yana ɗan shurin ƙafar Zayyad ɗin, da hakan ya sanya shi zare earpieces ɗin da yake kunnensa cikin gajiya yace"Ban daɗe da isowa ba, nazo lokacin kana asibiti".
"Wallahi ina can ina ta tinaninka kar ka canja ra'ayi ka ƙi zuwa".
Bai kula shi illa mayar da earpieces ɗin da yayi kunnensa da hakan ya sanya Anty Binta sakin tsiririn tsakin tana ɗaurawa da faɗin"Aikin banza kowa yana son yin hira da kai amma ka wani toshe kunnenka".
Murmushi Ammiey tayi domin tasan halin mitar Binta sarai,ƙiran salla ya sanya Ahmad da Zayyad miƙewa izuwa masallaci sai da akayi sallan isha'i sannan suka dawo abinci suka ci as one family cikin so da ƙaunar juna, sannan ƴan matan suka fara tattaunawa akan walimar da za'a gudanar gobe da yarda Allah.
Miƙewa yayi ya riƙo hannun Ahmad zasu hau sama, Anty Khadija ta dakatar su ta hanyar faɗin"ku kuma ina za kuje duk ana hira zaku wani tashi ku tafi, dalla ku kuma mini ku zauna".
Komawa suka yi suka zauna har sai da aka gama sannan Ammiey tace, kowa yaje ya kwanta saboda tashin gobe. sai da yayi wanka sannan ya ɗauro alwala sanda ya fito ya iske Ahmad yana waya wanda yake kyautata zaton da amaryarsa yake yi saboda yanda take wani lumshe ido alamar yana jin daɗin wayar.
Sallaya ya shimfiɗa ya tada kabbara ya fara yin nafila, har ya iddar ya fara karatun alqur'ani ya kammala sannan yayi addu'o'insa ya shafa. ya kallo Ahmad da har yanzu wayar yake yi kansa kawai ya jijjiga yana mamakin abinda take faɗa masa ya da sanya shi kasa ajiye wayar har yanzu.
Dawowa yayi ya zauna a bakin bed ɗin yana jiran Ahmad ya gama wayar suyi magana, lokaci bayan lokaci yake tsirgar da tsaki yana duba agogon wayarsa ganin Ahmad bai da niyyar ajiyar wayar ya sashi fizge wayar ya kashe ta ya ajiye a gefe.
"Haba Hamma da kayi haƙuri ma fa mun kusa yin sallama".
"A hakan ne zasu yi sallama ai banga alamar hakan bane, in ba rashin haƙuri bama saura kwana nawa ne".
"To yanzu dai daka kashe wayar wani magana zamuyi?"
Gyara zamansa yayi yana fuskanto Ahmad sosai sauƙe ajiyan zuciya yayi kana yace"Ahmad zan sanar da kai abunda na kasa sanar da kowa, hatta Abbu da Hajiya bansan meyasa ba zuciyata ta amince da ina fallasar da kai abunda na alhinta a cikin raina ba".
Tashi Ahmad yayi ya zauna ya kamo hannunsa cike da kulawa yace"Hamma faɗa min ko menene nayi alƙawarin matuƙar bai fi ƙarfina ba zan yaye maka damuwarka".
"Ahmad inason ya zama sirri a tsakanin mu ko Ammiey bana son ta ji".
"In sha Allah kayi, gaggawan sanar dani don Allah zuciyata ta sama nutsuwa".
Zame hannunsa Zayyad yayi daga riƙon da Ahmad yayi masa kana ya miƙe tsaye, ya zura dukkan hannayensa a cikin aljihunsa kana yace"Ahmad na sanar da kai cewar zanyi wani binciken da nake buƙatar goyan bayanka".
Tsura masa ido Ahmad yayi kana yace"in sha Allah Hamma zaka sama dukkan goyan bayana".
"Wancan zuwan nawan bauchi sanda zan koma kaduwa lokacin da Hajiyata tayi rashin lafiya, na ci karo da ƘADDARATA na buge wata yarinya a take a wajen ta suma. na ɗauke ta na kaita asibiti aka duba ta aka tabbatar da cikin da take ɗauke dashi ba'a rasa shi ba, na bata damar ra ƙira ƴan-uwanta ko iyayenta ko kuma mijinta amma ta nuna mini nayi tafiyata kawai zasu zo saboda halin gaggauwa da nake ciki a wannan lokacin ya sani barinta a asibitin na tafi duk da ta dasa miin zargi a cikin raina akan yanda fuskarta ta bayyanar da rashin gaskiya yayin da nace ta ƙira iyayenta. na dakata a cikin asibitin sai naga ta fito ta faɗi wajen na duba ta da kaina sannan na ɗauke ta muka tafi kaduna".
Dakatar dashi Ahmad yayi a dai-dai nan yana zaro ƙafafunsa ƙasa daga kan gadon, yace"Hamma bangane ka tafi da ita kaduna ba ka kaita ina kenan?".
Sauƙe ƙatuwar ajiyan zuciya yayi ya juyo yana kallon Ahmad da ya tsura masa ido, cikin son jin amsar tambayarsa yace"Ahmad wannan shine babban matsalar, sai dai akwai wata matsalar da yanzu ta kunno kai fiye da wannan".
"Hamma ka fara amsa min tambayata, tana ina yanzu".
Sai da ya zauna kana yace"Na tafi da ita kaduna na ajiye ta a cikin office ɗina, sannan na gwada na tabbatar da akwai cikin a jikinta na tambaye ta uban cikin amma ta shaida min cewar bata taɓa aure ba fyaɗe aka mata mahaifinta ya kore ta daga gidan shine dalilin da ya ta baro gida. yanzu na kaita gidan Abbu kuma nace masa cewar ƴar aikin Hajiya ce inta dawo daga saudiyya zata koma can gidan Hajiyan bansan meyasa na kasa sanar da kowa haƙiƙanin gaskiyar lamarin ba, tace taga fuskar wanda ya mata fyaɗe ba amma muryarsa kawai ta riƙe taji muryar Haidar kuma tayi yaƙinin cewar shine wanda ya mata fyaɗen wannan dalilin ya kawo ni bauchi domin na bincika gaskiyar labarin da ta bani domin a labarin da ta bani tace a bauchi take".
Shuru Ahmad yayi kamar mai nazarin wani abun mintuna tsakani yace"Hamma tabbas ɓoyewar da kayi laifi ne domin dole wataran zaka maida ga iyayenta, inta haihu amma yanzu ta ina zaka fara nemar gidan su a cikin bauchi?".
Tallafo fuskarsa yayi yana furzar da iska daga bakinsa ya ma rasa abin faɗin can yace"Ahmad ban sani ba amma na ƙuduci bazan koma kaduna ba, sai na gano iyayenta".
Tasowa Ahmad yayi ya dafo kafaɗarsa kana yace"Hamma ka kwantar da hankalinka, in sha Allah zaka gano iyayenta ka kuma miƙa musu ita gobe idan an gama walima sai muje mu unguwar da ta faɗa maka ɗin".
Kansa kawai ya jijjina masa sannan ya tashi yaje ya kwanta,lulluɓe jikinsa yayi da blanket Ahmad kuma ya shiga wanka.
Washe gari tun asuba babu wanda ya kuma runtsawa a cikin gidan, har gari ya waye tar! shigar manyan kaya yayi shi da Ahmad da kuma sauran jikokin Ammiey samari da suka sama damar halallata.
Dukkansu farar shadda suka saka suka murza hula shuɗiya, shi kuwa ango golden ɗin shadda ya saka da hular mai tsantsin kalar ruwar toka. su Ammiey da ƴaƴanta mata kuwa laffaya suka sa su Ramlat suka yi shigar abaya da sauran ƴan matan.
A filin gidan Ammiey aka shirya walimar a zamanance, tare da dangin amarya shirgar ya zamto abin jan hankali da ƙawatarwa domin ita ma shigar laffaya tayi fari mai tsantsi-tsantsin golden a jikinsa kwalliyar fuskarta very light marar hayaniya da takura. Manyan malamai walimar ya sama damar halalta gaba ji karatun qur'ani daga bakin Amarya haka nan ma ango zallar nasiha da wa'azi aka gabatar a wajen tare da nunawa ma'auratan haƙƙin junan su sannan taron ya watse bayan ɗaukar hotonan da aka yi tare da dangi.
Tunda aka fara walimar yake zaune tare da wasu ƴaƴan Anty Binta maza, da zai zarce su a shekaru ganin yanda suke shigewa ƴan matan wajen, yaso bashi tsoro duk da hankalinsa yana ga tinanin da kwakwalwarta ta dulmiya kansa kamar zai fashe ga numfashinsa da yake ɗaukewa saboda yawan cunkoson wajen. bana gamawa dai-dai ana ƙiran sallan magrib don haka ko gida basu shiga ba suka wuce masallaci sai da aka yi isha'i sannna suka dawo.
Part ɗin Ammiey suka wuce don a can duk dangi, suka sai hira akeyi suna shiga aka sanya guɗa ana ga angon ga angon. gaisuwa suka fara kwasha sannan suka ci abinci suka fito.
A motar Ahmad suka fita tunda suka fito ya shiga motar ya lumshe idanunsa, yana jin yanda ƙirjinsa yake harbawa.har sai da suka iso cikin unguwar kafin Ahmad ya taɓo shi yace"Mun iso fa".
Sai a sannna ya buɗe idonsa ya fito daga cikin motar, sannnn Ahmad ma ya fito daga farkon layin suka bar motar muka shigo cikin layin da ƙafarsu. ya maƙalawa fuskarsa face mask sai da suka yi tafiya mai ɗan tsayi kana suka tsaya a wajen wani mai shayi suka yi tambayar gidan kamar yanda ta kwantanta masa.
Yace su ƙara yin gaba kaɗan sai su tambaya, hakan su kayi kana suka sama wasu suna cin abinci suka musu, sallama kana suka tambaye su gidan da suke neman.
Kallon-kallo suka shiga aikawa junansu kana ɗaya daga cikinsu yace"Gidan da ake wankau da surfe gidan su Sagir fa kenan".
Ɗayan yace"wanda ƴaƴar su tayi cikin shege kuma ta gudu ba, wancan ne gidan na gefen mashin ɗin can".
Ya ƙarishe maganar yana musu nuni da gidan, kalle su Zayyad yayi tsaf! kana Ahmad ya gabatar musu da godiya suka nufi ƙofar gidan.
Sosai Zayyad yake ƙarewa gidan kallo wanda yake bayyanar da ƙarancin ƙarfi da wadatar masu gidan, saboda rabin ginin gidan ya faɗi aka kewaye da langa-langa. Jawo hannun Ahmad yayi da ya nufi gidan gadan-gadan.
"Bari kawai Ahmad tunda munga gidan, gobe ma zo yanzu dare yayi".
Ya ƙarishe maganar yana jin yanda juwa yake ƙoƙarin kada shi da ƙasa, ga matsanancin ciwon da kansa yake masa idanunsa har rufewa suke yi.
Saurin saka shi a jikinsa Ahmad yayi ganin kamar zai faɗi sannan suka nufa inda suka ajiye motar yana aikin jera masa sannu.
Wata mashin ne ta nufo layin da ta dalle su da haske ta, sannan ta faka a gefe wani saurayi ne ya sauƙo ya nufo su bayan sallamar da yayi ya taya Ahmad riƙe Zayyad har suka shigar dashi cikin motar.
"Mungode fa sosai bawan Allah, anan unguwan kake ne"?.Ahmad ya faɗa yana kallon saurayin, dariya yayi kana yace"A nan nake".
Ahmad ya ciro kuɗi ya miƙa masa ya ƙi, karɓa fatan samun sauƙi kawai ya musu yaja mashin ɗinsa ya tafi.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________
Page 4⃣2⃣
Ahmad ne yaja motar har suka isa gida, ya fito sannan ya zagayo ya buɗewa Zayyad ɗin da ya kwantar da kansa jiki kujerar motar tare da runtse idanunsa.
A hankali ya sauƙo da ƙafafunsa sannan sauran gangar jikinsa ta biyo baya, Ahmad ya riƙo shi suka wuce part ɗinsa saboda nan ne kawai babu hayaniya part ɗin Ammiey kam a cike yake haka nan ma nasu Anty Binta dasu Ramlat. Har cikin bedroom ya kai shi ya zauna yana dafe kansa da yake masa ciwo sosai cikin tangaɗi ya miƙe ya shiga bathroom ya watso ruwa a jikinsa sannan ya fito ya saka kayan bacci very light marasa nauyi da takurawa.
Har ya fito Ahmad yana zaune inda ya bar shi,ganin ya fito ya sanya shi tashi ya ɗauko masa magani da ruwa ya ɓalla masa babu musu ya karɓa ya sha. Sannna ya zauna yana sauƙe ajiyar zuciya kafin muryar Ahmad ta dira a ƙofofin kunnuwansa.
"Hamma wani irin alaƙa ce tsakanin su da mutanen unguwan su, da suke jifan su da irin waɗannan kalmomin. lafazin su yana nuni akan cewar kowa yasan cikin shege tayi wanda dalilin hakan yasa ta gujewa gida".
Gyara zamansa yayi domin maganganun Ahmad sunyi dai-dai da saƙa da warwarar da take yi a cikin zuciyarsa, ya furzar da iska daga bakinsa kana yace.
"Nima abinda nake tinani kenan wata iriyar alaƙa ce tsakanin su da ƴan unguwan, amma kasan irin wannan unguwan dole a sama masu yaɗa maganganu any how because they don't care whether it's truth or not, but we have to find out everything. Gobe nasan kana busy ba zamu sama zuwa ba next tomorrow sai muje gidan or i should go alone".
"No Hamma in sha Allah i will try to make my self off, so that sai muje jibin".
Kansa kawai ya jinjina yana jin kamar ana ɗaure masa jijiyoyin kansa saboda raɗaɗin da yake ji, wayarsa ya ɗauka ya turawa Hajiyarsa saƙo akan ya iso lafiya saboda jiya ya ƙira wayarta bai samu ba. Yana gamawa ya jona wayar a caji sannan yace"Tashi muje part ɗin Ammiey nasan duk suna can".
Tashi Ahmad yayi yabi bayansa har suka isa part ɗin Ammieyn kamar yanda suka zata kuwa duk suna falon, sai hira ake yi wasu kuma suna yin ƙunshi da kitso. kusa da Ramlat ya zauna bayan yayi wa Ammiey da su Anty Binta da kuma wasu manyan matan da bai shaida fuskokinsu ba sannu da hutawa".
Ahmad shi yake amsawa Anty Binta tambayar da ta tsare shi dashi akan ina suka je tun ɗazu ana neman ango, amma babu shi babu Zayyad. Dauke kansa Zayyad yayi yana jin ƙaryar da Ahmad yake kitsawa Anty Binta akan cewar ya raka abokansa ne da suka zo wajen walimar.
Karɓan ledar ƙunshin yayi daga hannun Ramlat ya fara zana mata a hannu, da hakan ya sanya sauran ƴan-matan yin wata shewa Nafisa ƴar Anty Binta ta uku tace"Hamma wannan fa lalle ne, ba aski bane irin naku balle kace ka iya ka barmu kawai muyi abun mu".
Ko kallon ta bai ɗago kansa yayi ba ya cigaba da zanen da yake yiwa hannun Ramlat, yana tina zamanin ƙuruciyarsa yana yawan ganin Hajiyarsa tana yiwa mutane na kuɗi domin ta rufawa kansu asiri kafin ta sama aikin wanke-wanke da sharar da mai gidan ya ɗauki nauyin karatunsa. yawan ganin da yake yi ya sa shi shima, wataran gwada zanawa Hajiyarsa a hannu kuma yayi kyau.
Sai da ya gama sannan ya ɗago ya kalli fuskar Ramlat yace" i'm done".
Murmushi tayi cikin faɗin"Thanks Hamma it look so beauty".lakato kan hancinta yayi yana miƙewa daga wajen ya koma kusa da Ammiey.
"Ammiey yunwa nake ji tun safe ban ci abinci ba".
Yana faɗa yana ɗan shafa cikinsa, Anty Khadija ce ta saka aka kawo masa abincin da aka girkawa Ammiey don iya sanin da ta masa yafi son abincin gargajiya fiye dana zamani
Tuwon acca ne da miyar ɗanyen kuɓewa da ta sha ganda da nama, sai kunnun tsamiya ita da kanta ta jawo hannunsa gabanta ta fara bashi abincin da kanta yana ci.
Sosai take kallon fuskarsa da shi kam yafi maida hankali ga abincin, sosai fuskar mahaifiyarsa Shamsiyya ƴar-uwarta ya bayyana akan nashi fuskar hatta yanayin shape da gashin da yake kwance har saman goshinsa. Hawaye ne ya ciko mata idaniya tina rabuwarsu ta ƙarshe da ita tunda cikin Zayyad daga wannan lokacin basu sake haɗuwa ba, sai gawarta da aka tsinto a cikin daji aka kawo musu sai bayan shekaru suka sama labarin abinda ta haifa ta bari yana raye a wannan duniyar.
Ganin ta ƙura masa ido ta daina bashi abincin ya sa shi faɗin" Momma". A sanyaye yayi maganar ganin hawayen da yake sauƙowa daga idonta hakan ya jawo hankalin Ahmad, Ammiey da sauran mutanen dake falon.
"Maman Ahmad lafiya meya faru?".
Anty Binta ta faɗa tana tasowa ta iso wajen, share hawayenta Anty Khadija tayi kana faɗin" ba komai akwai Shamsiyya na tina yanda rabuwar mu ta ƙarshe ta kasance".
Shuru ya biyo bayan zancenta na ƙarshe kowa jikinsa ya mutu, a hankali shima ya sunkuyar da kansa yana murza zoben azurfan dake hannunsa kafin ya kai ɗayan hannunsa yana tare hawayen da suka ciko masa idaniya. Ammiey ta taso ta jawo shi jikinta ya kwantar da kansa akan cinyarta.
"Haba Khadija yaya da girman ki da komai zaki nayin irin hakan, shin baki ga halin da wannan yaron yake ciki bane tun zuwarsa jiya bashi da wata cikakkiyar walwala haka nan rayuwarsa kullum a cikin maraici mu da ya kamata inya raɓe mu yaji sanya, mu kuma zamu na sanya shi kuka".
Shuru ya kuma ɗaukar falon, sai tashin sautin kukan da yake tashi a hankali hatta su Ramlat da basu santa ba ma yau sunyi kukan rasuwarta jin yanda Anty Binta take basu labarin yanda aka kawo musu gawarta a wulaƙance. Sai da Ammiey ta taka mata birki sannan tayi shuru saboda rawar da jikin Zayyad ɗin ya ɗauka wani azababben zazzaɓi ya lulluɓe jikinsa.
A hankali ya ɗago kansa da ya masa nauyi sosai daga cinyar Ammiey yace" Sai da safe Ammiey a tashi lafiya, zan kwanta bana jin daɗin jikina".
"Zayyad".
Ta ƙira sunansa cikin muryarta mai bayyanar da dattako da kamalar da take ɗauke dashi, a hankali ya amsa cikin muryasa da bata fitowa sosai sannan ta ɗaura da faɗin.
"Zayyad kowani bawa da kake ganin cikin duniyar nan da nashi ƙaddarar, ka cigaba da haƙuri da fawwalawa Allah komai in sha Allah wataran haske zai bayyana cikin rayuwarka".
Kansa ya jijjina ya miƙe bayan ya mata godiya ya nufi part ɗin Ahmad, yana tafiyar yana haɗa hanya kamar wanda yasha ya bugu ganin haka ya sanya Ahmad bin bayansa.
A ƙofar shiga part ɗin Ahmad ya cim masa zai riƙe shi, ya ɗaga masa yana faɗin" i'm ok". Daga haka ya shige ciki kansa tsaye ya wuce cikin bathroom yayo alwala sannan yazo yayi nafila raka'a biyu yayi addu'ar nemawa mahaifiyarsa gafarar Allah ya shafa, wayarsa da ya bari tana caji ya ciro ya cikaro da missed call ɗin Abbu da Hajiyarsa.
Call ɗin Abbu ya ƙara shigowa yayi saurin ɗagawa, gajeruwar gaisuwa suka yi kafin Abbu ya shiga tambayarsa ya isa lafiya kunya ce ta kama shi saboda tunda ya iso bai ƙira Abbu ba.
"Lafiya ƙalau Abbu".
"To madalla muma gobe in sha Allah muna hanya".
"Allah ya kawo ku lafiya".
Daga haka suka katse ƙiran bayan tambayoyin wani na bin wani da Abbu yake masa akan yaya jikinsa, sai da ya ƙira Hajiyarsa suka yi waya sosai sannan ya kwanta.
Washe gari kamar jiya haka suka yi tashin sassafe, gidan ya cika da hayaniyar jama'a daga ko'ina. Ƙarfe goma da mintuna suka kammala shirin su shigar bakar shadda yayi da aka yiwa aikin surfani da golden ɗin zare a hannu da kuma wuyar babbar rigar, haka nan ma hular kansa ɓakar ce mai sheƙi da ɗaukar idanu yana tsaye a gaban mirrio yana feshe jikinsa da turare. Ahmad ya shigo tare da wasu abokansa kallo sa yayi cikin yanayin barkwanci yace" Masha Allah, Hamma ai sai ace ma kaine angon irin kyau haka".
Ya ƙarishe maganar yana kashe masa ido ɗaya, marfin turaren Zayyad ya wullo masa yayi saurin gucewa yana dariya sannan suka fito tare da zurgar abokansa suna rufa musu baya. Part ɗin Ammiey suka nufa aka fara haska hotuna kana suka wuce masallacin da za'a ɗaura auren dai-dai sauƙowa daga sallan juma'a aka ɗaura aure tsakanin Ahmad da amaryarsa Fatima.
Ana tsaka da ɗaura auren su Abbu suka iso mota guda suka ciko, tare da su Adam da Haidar sai kuma Baban Nana. Ya miƙe ya iso gare su ya rusuna ya gaishe da Abbu da Baban Nana yana ɗagowa da nufin yi musu jagora izuwa cikin masallacin idanunsa suka sauƙa akan Haidar da yake faman cika yana batsewa tamkar dole aka masa zuwa bikin.
Cak! yawun bakinsa ya ɗauke cikin lokaci ƙanƙani, ya nema nutsuwarsa ya rasa har cikin ransa yake jin tsanar ganin fuskar Haidar ko ba don abinda yake zarginsa a kai ba, yasan cewar kafin ita ma ya lalatawa yara mata da yawa kamanninta rayuwa. Domin a yanzu bincikensa kawai yake jira ya kammala da zaran ya kammala ya gano gaskiya to toshe kunnansa zai yi daga jin duk wanda maganar da zata taso.
Gaigaisawa Abbu ya shiga yi da mutane yayin dashi kuwa ya koma gefen da su Ahmad suke, ana gamawa suka wuce gida tare dasu Abbu har cikin part ɗin Ammiey ya shiga aka kwashi gaisuwa kuma daman an daɗe ba'a sadu ba.
A yammacin ranar Abbu ya koma tare dasu Haidar da Baban Nana, shi kam yace zai ɗan kwana biyu kafin ya koma Abbu ya lamince masa akan hakan.
SALON ƘADDARATA
©Maimunah Tijjani Iyam
____________________________________
Page 4⃣3⃣
Tun bayan da aka gama bikin ya dawo gida bayan ya raka su Abbu ya bar Ahmad tare da abokansa, cire kayan jikinsa yayi tsaf! yayo wanka sannna yayo alwala ya fito ya sauya wasu marasa nauyi sannan ya tada sallan Asr yana iddarwa ya jingina kansa jikin bed ɗin yana kallon ceiling ɗin ɗakin da ya zamto shamaki tsakanin sa da sararin samaniya.
Inda har abunda mutanen unguwan su suke faɗa akan ta ya tabbata to tabbas ya zama dolensa ya tono komai, ji yake yi kamar yayi fiffige yaje gidan domin ransa ya ƙagu da son ji daga iyayenta duk da ba kai tsaye zai bayyana musu yana tare da ƴarta su. Dole sai ya haɗa cikin siyasa da dabara har ya shiga jikin su ta yadda baza su ɓoye masa komai ba.
Lumshe idanunsa yayi a karon da ba adadi, sannnan ya miƙe saboda bugun da ake yiwa ƙofar falon, ya fito ya buɗe bai tsaya ganin wanene ba yayi gaba ya koma ɗakin. Ahmad suka shigo tare da zugar abokansa da suke ta faman tsokalarsa.
Biyo bayansa Ahmad yayi, ya zauna a gefensa haɗi da faɗin"Hamma lafiya ka taho daga wajen ɗaurin auren da wuri, ko jikin nakan ne?".
Kansa kawai ya ɗaga masa don hakan ne kaɗai zai sa ya ƙwaci kansa daga tambayoyin Ahmad.
"Ina taya ka murna, Allah ya bada zaman lafiya".
"Amin Hamma ai zaka yi rakiyar ango ko?".
Murmusawa yayi yace"in sha Allah".
Har Ahmad ya miƙe ya dawo da faɗin"Hamma ya maganar zuwa gidan su yarinyar kuwa, yau dai kam bazaka sama kaina ba".
Musgutawa Zayyad yayi yace" i decide to go tomorrow, amma ina tinanin dole sai mun haɗa da siyasa don ba zai yiyu ace tashin farkon mun sanar dasu ƴarsu tana tare damu ba".
Kansa Ahmad ya jinjina kafin yace"This is a good idea".
Daga haka ya koma wajen abokansa, Anty Binta ta saka aka kawo musu abinci suka ci sannan suka fara shirin event ɗin da aka yi na yarensu kanuri da yammaci.
Shigar manyan kaya suka yi marron colour ango kuwa nashi fari, suka murza farar hula ta yare shi kuma ango tashi marron. Su Ammiey suka sha laffayo na ban girma su Ramlat da sauran ƴan matan kuwa kamfala suka saka marron da gyale manɗil shi kuma red.
Ƙarfe huɗu dai-dai aka fara gabatar da event ɗin wushe-wushe, sosai taron ya ƙayatar an ƙawata hall ɗin da adon ballons fari da marron shigowar ango da amarya ya ɗauki hankali kemarorin suka shiga haska su. Ɓalle bakin aljihunsa Zayyad yayi ya shiga yiwa ango da amarya ruwan sabbin nairori zubin ƴan dari biyar biyar.
Anci an sha, sannan aka shiga rabon savours da yake ɗauke da hoton ango da amarya a jikinsa ansha hotuna sannan taro ya watse kowa yana son barka.
Sosai kansa yake sarawa har wani jiri ne yake ɗeban shi, ya dawo gida a motarsa ya dawo tare da Ramlat da Nafisa su kaɗai suke hirar su a cikin motar har suka iso gida. Cikin motar ya fito ya barsu ya wuce part ɗin Ammiey cikin bedroom ɗinta ya wuce yayi kwanciyarsa yana dafe da goshinsa yana karanto"Hasbulallahi wa ni'imal wakil" a ƙoƙarin samarwa kansa nutsuwa da daidaituwar harbawar zuciyarsa. Kafin daga bisani ya danna ƙirar Hajiyarsa.
Ya daɗe da dawowa sannan su Ahmad suka dawo motar su Anty Binta yana biye dasu, Ahmad da abokansa part ɗinsa suka wuce daman gudun hayaniyar su ya sanya shi dawowa part ɗin Ammiey.
Yana jiyo tashin hirar da suke yada zango suna yi a falon, yana kwance yana wayar har ya gama sannan ya taso yana jin sauƙin ciwon kan. Yana zaune bakin gadon ƙiran Ammiey ya shigo wayarsa bai ɗaga ba illa miƙewa da yayi ya fito
"A'a daman kana ciki ne?".
Kansa ya ɗaga mata yana ƙarisowa cikin falon da Ahmad yake ɗurkushe Anty Binta tana karanta masa rayuwar aure dole sai an haɗa da haƙuri da tausayawa juna mussamman irin zaman da ake saka ran da mutuwa ce kawai zata raba.
Zama yayi yana sauraron furcinta har ta gama Ammiey ta ɗaura da nata, Sannan Ahmad ya miƙe su Ramlat sai tsiya suke masa akan ya bar ɗan Ammiey ya koma na Anty Fatima. Bai ce dasu kanzil ba face murmushin da ya wadata fuskarsa dashi Zayyad ya miƙe suka fito tare.
Mota ɗaya suka shiga sai babban ɗan Anty Lauratu Mahmud da ita sai jiya tazo tare da mijinta ƴaƴanta kam sun daɗe a nan daman ƴaƴanta biyu ne daga Faisal sai Nasifa duk kuwa suna wajen Ammiey, shi yake jan motar sai kuma wani abokin Ahmad ɗin da yake zaune a kujerar ɗan zaman banza.
Su kenan a cikin motar sai wata mota da take biye dasu ta sauran abokan nasan, suna isa gidan suka ga motocin da suka je ɗauko amarya har sun iso parking suka yi cikin parking lot ɗin da aka tanada a cikin gidan kafin suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya. Suka saka angon a tsakiya bayan sun yi layi biyu yana daga tsakiya suka jero suka shiga cikin gidan.
Aka saki guɗa mai ƙarfi, anan falon suka tarar da amarya da sauran danginta da ƙawaye addu'a a kayi kafin aka biya ƙawayen amarya kuɗin sayan baki aka bar ango da amaryarsa. Mahmud da Faisal ƙanin Ahmad ɗin su suka yi jigilar maida ƙawayen amarya gidajen su.
Sauran abokansa suka wuce hotel ɗin da aka kama musu shi kam dawowa gida yayi cikin motar da suka tafi da ita. Kansa tsaye ya wuce part ɗin Ahmad ɗin kwantawa kawai yayi yayi salla sannan ya kwanta tsabar gajiyar da take ratsa duk gaɓoɓinsa.
A makare yayi salla asuba yayi karatun al-qur'ani ƙarfe goma ya koma ya kwanta, bai tashi ba sai lokacin da yaji bugun da akeyi ƙofar part ɗin kamar a cikin mafarki ya mirgina ya tashi ya nufi ƙofar ya buɗe ta Mahmud ne tsaye ya gaiseh shi ya amsa sannan ya sanar dashi saƙon Ammiey akan ta aiko shi ne yazo ya duba lafiya har yanzu bai fito ba.
Agogon bangon falon ya kalla da yake nuni da ƙarfe ɗaya da mintuna arba'in, umarni ya ba wa Mahmud akan yaje yana zuwa. Wanka yayi ya fito yana tsame ruwar jikinsa sannan ya wuce ya mulke jikinsa da mai ƙananan kaya ya kasa farar t-shirt da blue ɗin jeans sannan ya ɗaura blue ɗin jaket akan rigarsa saboda sanyin da yake ji kamar asthma ɗinsa yana dab! da tashi.
Wayarsa ya ɗauka kawai ya fito, yan tafe yan dialing ɗin lambar Baban Nana ringing dab da na ƙarshe sannan ya ɗaga ya ladabtar da murya tamkar yana gaban sa ya gaiseh shi ya amsa yana ɗaurawa da faɗin"an gama biki lafiya?".
"Lafiya ƙalau Baba ya gidan yasu Nana?".
"Duk lafiya ƙalau yarona Ummukursum ce ma jiya ta kwana tana amai yanzu ma ina hanyar sayo mata magani ne".
Ɗan shuru yayi daman tambayar da yake son yi masa kenan yaya jikin natan, sai kuma ya riga shi furtawa tusa hannunsa yayi cikin sumar kansa kana yace" Zan turo nurse tazo gidan ta duba ta, amma Dan Allah kar kowa ya sani".
"In sha Allah yarona sai tazo ɗin to".
Daga haka ya gimtse ƙiran yana mayar da ita aljihunsa ya shiga part ɗin Ammiey gaishe ta yayi sannan ya gaida, ƴan-uwan mahaifiyar tasan guda uku Anty Khadija, Anty Lauratu da kuma Anty Binta sannan dangin mahaifin Ahmad da suka zo biki.
Abinci Ammiey ta kawo masa yaci sannan ya zauna yana mata tausa, yana jin wayarsa tana ruri wanda yasan Ahmad ne amma ya ƙi ɗagawa domin yasan maganar da zai yi masa, dole ya barshi yaci amarcinsa gobe sai suje gidan su yarinyar. Nan ya zauna har sai da aka yi ƙiran sallan zuhr sannan suka fita tare dasu Faisal izuwa masallaci sai da akayi sallan asr sannna suka dawo ya tsaya yana yin waya yana ba wa nurse ɗin umarnin zuwa gida ta duba ta.
Tun ranar da ya shigo yayi wa Hajja sallamar tafiyar sa bauchi, daren ranar na kwana da zazzaɓi mai zafi a jikina saboda tinanin Daada da rayuwata ta baya da ya hana mini sukuni notikan kaina duk suka kunce. tun ina kukan amon sa yana fita har ƙarfin hakan ya fara gagara ta, ganin na gaza samun nutsuwar zuci ya sani tashi na shiga banɗaki na ɗauro alwala nazo na tada salla har sai da ƙafafuna suka yi sanyi sannan na ɗaga hannayena sama ina jero addu'o'i da na sani na neman sauƙi da taimakon maƙagin raina.
Ina shafa addu'ar na baje akan sallayar bacci ya sure ni, hannuna yana kan cikina. Sai da gari ya waye tar! sannan na tashi ina miƙa tare da kamo sunan haliccina cikin bakina da yawun cikinsa ya ɗauke kamar anyi kwashe ƙaf!.
Na tashi na shiga banɗaki na wanke fuska da bakina, sannna nayo alwala nazo nayi salla a makare sai da nayi wanka na saka doguwar riga marar nauyi cikin jikina ya bayyana sosai hakan ya sanya ni ɗaura hijabi akan rigar sannan na fito. Na iske Hajja a tsakar gida tana yiwa Nana tsifa na kai mazaunaina akan tabarmar da take shimfiɗe a wajen na zauna ina gaiseh da Hajja ta amsa tana ɗaurawa da faɗin.
"Na leƙa ai naga baki tashi ba, nace Nana ta barki wataƙil baki sama bacci bane daren jiya".
Murmushi kawai na mayar mata don a lokacin bana cikin yanayin magana, ta gabatar mini da abinci nace"Hajja bar shi sai zuwa anjima yana jin daɗin jikina da zan fita na sha iske zan ware".
Ta ɗan yi shuru na ɗan lokaci kana tace"Amma Ummukursum kar kiyi nisa dan Allah ki tsaya iya can sashin nan".
Kamar jira nake yi wuf! na miƙe saboda yanzu sam bana ƙaunar zama waje ɗaya nace"to Hajja in sha Allah nagode".Daga haka na fice daga sashin ina ɗan zagayawa cikin lambu da suke da yalwar shuke-shuke can na hango shigowar wata mota na ɗan fito ina kafe ta da kallo.
Naga matuƙin motar ya fito ya buɗe ƙofar baya, Hajiyar gidan ta cikin shigar alfarma da ƙasaita ta fito tasha ɗanyen leshi ɓaki ga fatarta da ta gaji da jin mayukan bleaching. Na kasa jan jikina na bar wajen saboda naga ita ma ni din ta ƙurawa ido jikina ya soma rawa har ta iso ni na kasa wani kwakwkwaran motsi balle nayi yunƙurin janye jikina daga wajen.
Ta zame zaman ɓakin gilashin da yake saman karan hancinta, sannan tace dani" Ke me kike yi a nan?".
"Na-na-na na fito zagayawa ne".
Ta taɓe baki yana bina da kallo kafin tace"Yayi kyau yaushe ne zaki tafi gidan Hajiyar?"..
Nayi tsuru hantar cikina tana kaɗawa nace" ban sani ba amma ance in ta dawo daga saudiyya".
Ta matso ni da taku biyar na saka idona ƙasa saboda mazarin da jikina ya ɗauka, ban ƙara dulmiyawa cikin ƙololuwar firgici ba sai da naji hannunsa a saman mazaunaina da cikin dake cikina ya kumbura ni suka fito sosai.
Nayi hanzarin cilla ƙwayayen idona cikin nata ta sakar mini murmushin da na gaza, gano ma'anarsa.
"Jeki huta yayi kyau".
Daga haka ta barni tsaye a wajen tamkar an dasa ni, sai da nasha fama wajen daidaita fitar numfashina sannan na janye jikina na koma sashin Hajja. Tun daga wanna lokacin raina yake cikin ɗimuwa murmushi da ta mini ya tsaya min a ƙololowar raina, zazzaɓi mai ƙarfi ya lulluɓe ni ina duƙunƙune cikin bargo ko waje bana iya leƙawa cikin haka naji wai Baban Nana zasu je bauchi aure a ranar da yamma na fito ina kwarara amai ya dawo.
Ina kwance a ɗaki naji sallamar Hajja tare da wata ma'aikaciyar asibiti, na bisu da kallo yayin da suke shigowa suka zauna bakin kafitar Hajja tace dani.
"Zayyad ne ya aiko ta, ta duba yanayin jikim nakin".
Ta fara aikinta na tana gwaji a jikina sannan ta saka mini drip ta mini gargaɗin akan ina ci abinci don zama da yunwa zai galabaitar da abinda yake cikina.
SALON ƘADDARATA
© Maimunah Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 4⃣4⃣
Zaune yake a gaban Ammiey suna breakfast suna kammalawa, su Ramlat suka tattare wajen sannan suka fito tare da su Nafisa zai kai su gidan Ahmad tare da Mahmud suka tafi.
Yana gama dai-daita parking suka fito suka nufa cikin gidan, wayarsa yana manne a kunnunensu suna waya da Abbu ya shigo cikin falon dai-dai sanda suka yi sallama ya maida wayar aljihunsa.
Akan 2 ceater da Mahmud yake zaune a kai ya zauna yana faɗin"Ango mijin amarya, amarya gabaɗaya ta ɓoye ka"
Rusunawa Fatima tayi tana faɗin" ina kwana an iso lafiya".
Sai a sannan ya kallo ta yana daga zaune a tsakanin su Ramlat, ya amsa mata cikin faɗin"lafiya ƙalau amarya yau dai naga amarya da kake ɓoye min ita".
Dariya mai sauti Ahmad ya sauƙe sai da ya tsagirta kana yace"To ai Hamma kai ne tun yaushe nake maka tayin zuwa wajenta kake kaucewa".
"A'a malam ni kar ka haɗi da madam fa".
Duk suka koma sakin wata dariya saboda yanda yayi maganar cikin wasa da barkwanci ba kamar yanda fuskarsa take a kullum cikin ɗaurewa da rashin fara'a ba. Hirar suka shiga yi bayan Fatima ta gabatar musu da ruwa da abin taɓawa lokaci zuwa lokaci yake saka bakinsa cikin maganar tasu idan sun sako dashi har izuwa lokacin da ya miƙe yana faɗin.
"Amarya inaso a bani aron angon nakin, zai raka ni wata unguwa".
Murmushi Fatima ta saka kafin tace"Hamma an baka".
Godiya ya mata yana kamo hannun Ahmad suka fice bayan yace wa su Ramlar su jira shi zai dawo ya maida su gida, a motar Ahmad suka fita suka nufa unguwar wunti stree kamar ranan tun a farkon layin suka ajiye motar suka fara takowa cikin lafin da ƙafarsu saboda cakwamin da kwancancen ruwan sama da ya kwanta a cikin layin.
Dai-dai ƙofar gidan da samarin suka musu nuni dashi, suka tsaya suna kokonton anya nan ne kuwa.Saboda lokacin da aka nuna musu dare ne, ganin wani yaro zai gilma ta gabansu ya sanya Ahmad ƙiran shi yace"Dan Allah ɗan samari gidan nan muke so ka shiga kayi mana sallama da mai gidan".
Riƙe haɓarsa yaron yayi kana ya shiga faɗin"Lalala! Abbansu yayi wa Ummarsu duka ya roke ta daga gidan, shi kuma yayi tafiyarsa basu da baba ya tafi ya barsu".
Mamaki ne ta sa suka yi mutuwar tsaye dukkan su a wajen ɗan mitsitsin yaro kamar wannan har ya iya zaro zance haka kamar ana buɗe cikin kansa ana zuba masa, Ahmad ya tsuguna gaban yaron yace"Kai waya yake sanar da kai duk wannan, a ina kaji?".
"Umman muce nake ji tana faɗa idan tayi baƙi, kuma duk yaran unguwan nan an hana su shiga gidan saboda har Abbansu yace muzo muje ya cire mana kayan mu yayi wasa damu. Ummanmu tace kar mu yarda inya ƙira mu muje".
Bin yaron Zayyad yayi da kallo tsaf! yana mamakin ƴan unguwan, wacce irin halayya gare su da har zasu zaunar da ƴaƴansu masu ƙarancin shekaru suna saka musu irin wanna maganar a kansu har suyi haddarta.
"To shikenan jeka abinka, amma kar ka ƙara gayawa wani wannan maganar da Ummarka ta faɗa maka babu kyau kaji ko?".
Kansa kawai ya gyaɗa masa yaron, yana kaɗa motarsa ta kara ya bar wajen. Ahmad ya waigo ya kallo Zayyad da ya sanƙare a wajen kamar gunki tunda yaron fara jawabi filla-filla bai ce komai ba.
"To Hamma kaji fa, wata sabuwa kuma abinda yaron ya faɗa wai an hana su shiga gidan".
Sauƙe wata gigitacciyar ajiyan zuciya yayi mai nauyi yace"Ahmad to yanzu ban san yaya zamu yi ba, don a labarin da ta bani bata sanar dani cewar mahaifinta ya rabo da mahaifiyarta ba".
Ganin dosowar wani yaro ya nufo gidan yana ɗauke da hular abinci a hannunsa, ya sanya Ahmad haɗiye maganar da yake son furzowa gaiseh su yaron yayi zai shige cikin gidan Ahmad ya dakatar dashi da faɗin"Abokina gidan nan zaka shiga ne?".
"E nan zani Ummata ne ta aiko ni na kawo abinci".
Tsugunawa Ahmad yayi a gabansa yace"Good dan Allah sallama muke son ka mana da masu gidan nan".
"Wajen yaya Sagir kuka zo, abokansa ne ko?".
Saurin ɗaga masa kansa Ahmad yayi yana ƙarawa da faɗin"E wajensa muka zo inka shiga ka mana sallama dashi".
"To".
Kawai yace ya shige cikin gidan, Ahmad ya rakashi da kallo yana miƙewa daga tsugunan da yayi yace"Finally Hamma mun sama wanda ba'a hana shi shiga gidan ba".
Idanunsa da ya lumshe su Zayyad ya buɗe yana kafe Ahmad dasu ya jijjina masa kansa ,shuru cikin su babu wanda ya ƙarayin wata magana har izuwa lokacin da yaron ya fito yace" wai ance baya nan ya fita da mashin ɗinsa".
"To Mama fa tana ciki?". Ahmad yayi gaggawan faɗan sanin indai suka bar wannan yaron ya tafi to zaiyi wuya su kuma samun wani yaron da zai shiga cikin gidan.
Cike da rashin fahimtar maganar nasan yaro yace"waye Mama kuma gidan nan babu Mama, sai dai Daada".
"E ita ɗin kace an sallama da ita".
Komawa yaron yayi domn isar da saƙon babu jimawa ya fito yace"wai ance ku shigo".
Hamdala Zayyad ya sauƙe don har ya gama tinanin cewar ba zasu samu abinda suka fito nema ba a yau. Gaba yaron yayi, yayi musu jagoranci izuwa cikin gidan tabarmar da suka ganin an shimfiɗa a madaidaicin tsakar gidan suka zauna.
Dattijuwar matar dake zaune sanye cikin hijabi yaluwa, idanunsa suka fara yin tozali dashi kasa ɗauke idonsa yayi daga fuskarta da take ɗauke da tsantsar kama da yariyar da neman labarinta ta fito dashi.
"Samari kune kuka neman Sagir?".
Jin muryata ta sauƙa a kunnansa ya tilasta mishi ɗauke idonsa daga kallon ƙurillan da yake yiwa fuskarta, sunkuyar da kansa yayi kusan a tare shi da Ahmad suka ce" ina kwana Hajiya mun samo ku lafiya".
"Lafiya ƙalau amma ban shaida ku ba?".
Sha'awa dake zaune ƙofar ɗaki ne ta amshe zancen cikin faɗin" Daada baki gane sa bane, shine fa likitan nan da yayi miki aiki a asibiti lokacin da wani Alhaji ya biya miki kuɗin aikin baki gane shi ba?".
Kallo su Daada tayi tace"Sha'awanatu ban gane shi ba, wanene daga cikin su"?.
"Daada wannan ne fa mai farar rigar".
Kallo Ahmad Daada tayi kana tace"Ayya yaro yi haƙuri ban shaida ka bane, da yake lokacin bamu haɗu ba. Ƴaƴana sun sanar dani komai irin ƙoƙarin da kata yi damu a lokacin mungode Allah ya saka maka da alkhairi yanda ka yaye mana damuwar mu, Allah ya yaye maka damuwarka a ranar da babu wani mai iko sai Allah".
Wasu zuffan da suka tsatstsafowa Ahmad a goshi ya kawar da hannayensa kana yace"Amin amin ya jikin fa ban sama damar dawowa ba har suka bar asibitin".
"Jiki alhamdulillah yayi ƙarfi".
"Masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi".
"Amin".
Sha'awa da Daada suka amsa dashi kafin Ahmad ya ɗaura da faɗin" Daman wannan ɗan-uwana ne, ƴaƴae sannan kuma shine wanda ya biya kuɗin aikin da aka miki, yazo shine yake tambayar matar da aka yiwa aiki munsha wahala kafin muka sama gidan shine na kawo shi kafin ya tafi".
Saurin ɗago kana Zayyad yayi yana kallon Ahmad da ya zage yan shiryo ƙarya daki-daki, riƙo hannunsa Ahmad yayi cikin nasa yana hana sa maganar da yake son furtawa.
Kallo Zayyad, Daada tayi sosai sallamar da Anty Sakina ta shigo dashi ya dakatar da ita daga maganar da take son amaryawa. Gaishe dasu Anty Sakina tayi kana ta iso ta zauna kusa da Sha'awa, tana tambayar Sha'awa wanene waɗannan mutanen a hankali, raɗa Sha'awa ta mata a kunne tan faɗin.
"Likitan da yayi wa Daada aiki ne yazo tare da wanda ya biya kuɗin aikin".
Maganar da Daada ta soma yi ya katse musu hanzari"Yaro mungode! mungode Allahu ya saka maka da mafifin akhairinsa, ya sada ka da nasarorin rayuwa ya katse gabanka da bayanka. Ya baka kaima ƴaƴan masu albarka da zasu samo sanyin idaniya a gare ka".
Duk jikinsa ya kama mutu, zuciyarsa take ta karye ya amsa da "Amin". Ciki-ciki yana tino ranar da aka mata aikin da yaje shiga cikin ɗakin yana jin tashin muryarta da yake tashi, tana masa addu'o'in alkhairi.Allah ya sani bai taɓa kawo cewar wannan matar itace mahaifiyar UMMUKURSUM ba, ta yaya zai fuskanci wannan matar da addu'o'inta suke tasiri ga rayuwarsa duk da babu wani alaƙa tsakanin su.
Sallamar da aka yi ya sanya su watsa idanunsa ƙofar shigowa gidan, yaya Aliyu tare da Sagir suka shigo akan tabarmar suka zauna suna yin musabah kafin Ahmad yace" kamar kai muka haɗu dashi rannan ko?".
Ɗan murmusawa Sagir yayi yace"Nine doctor ai tun a lokacin na gane ka, kawai da naga kamar baka shaida ni ba kuma kana da marar lafiya shiyasa ban ja maganar ba".
"Ayya ai a lokacin ma gidan nan muke nema".
Kallon Ahmad, Zayya yayi ido cikin ido yama watsa masa wani kallo mai kama da warning, domin yaga maganarsa ta fara yawaita zai jawo masa ruwa. Ya kamata ya taƙaita zancensa daidai wadada har su cimma abinda ya kawo su. Jin muryar wacce ɗayar budurwar ta ƙira da Daada wacce yake kyautata zaton mahaifiyarsu ce yaji a tsakiyar kansa.
"Aliyu ga wanda ya biya mana kuɗin aikin nan, da aka yi a asibiti".
Ƙara miƙa masa hannu yaya Aliyu suka ƙara gaisawa kana yace"Allah sarki bawan Allah mungode fa mungode wallahi tun a lokacin munso yi maka godiya na mussamman, amma sai aka ce kace a ɓoye sunanka mungode Allah ya biya ka".
"Amin".
Ya amsa dashi yana jin ruwar hawayen da suka ciko masa idaniya da ya rasa dalilin su, jiyo muryasa Ahmad sun bugi dodon kunnensa ya sanya shi saurin ɗago kansa yana girmama ƙarfin hali irin na Ahmad.
"Hajiya ni kuwa nace ina ita yayar tasu naga, lokaci kamar matan su biyu ne?".
SALON ƘADDARATA
© Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________
Page 4⃣5⃣
Ganin duk sunyi shuru cikinsu babu wanda ya amsa tambayar da Ahmad yayi, ya sanya Zayya kallo shi with lower voice yake faɗin"Ahmad ya isa haka maganan".
"Haba Hamma inba ta hakan ba ta yaya, zamu sama abinda muke so".
Maganar da yaya Aliyu ya soma yi katse Zayyad daga maganar da yake yiwa Ahmad.
"Am-am ta ɗan fita ne, bari a sayo muku lemo".
Ya ƙarishe maganar yana zaro naira ɗari biyar daga aljihunsa ya miƙawa Sagir haɗi da faɗin"Amshi nan kaje ka karɓo musu lemo".
Karɓa yayi ya zara takalmarsa ya fice idonsa suna kawo ruwar ƙwalla, gyara zama Ahmad yayi yana karkacewa ya kuma faɗin" Tana min kama da wata sister nace da ta daɗe da rasuwa, tun muna ƙanana shiyasa na tambaye ta menene sunanta kuwa?".
"UMMUKURSUM shine sunanta".
Yaya Aliyu ya amsa mishi dashi da ya sanya Zayyad saurin sadda kansa ƙasa, bai gama gaskata hashashen zuciyarsa ba sai yanzu da yaji sunan da suka ambace ƴarta su, duk da tun a shigowarsu ya gano kamar dake shimfiɗe a fuskar Daada da ita Ummin hatta wushiyar dake tsakankanin haƙwaransu yayi dai-dai.
"Tabbas nan ne, nan ne asalinta kuma tushen rayuwarta".
Abinda ya faɗa kenan cikin zuciyarsa da take harbawa da ƙarfi da ƙarfi tamkar zata yago fatarsa ta fito waje, Amir da yake zaune kan cinyar Anty Sakina yazo wajensa ya zauna. Ɗaukar shi yayi ya azashi kan cinyarsa kafin muryar Daada suka sauƙa a kunnuwansa.
"Allah sarki! Allah ya jiƙanta da rahama".
Kallon Ahmad yayi da yake amsawa da amin har da sauya yanayin fuskarsa alamar yana cikin jimamin, rasuwar ƴar-uwarsa da ya faɗa wanda shi dai kam bai san yana da wata ƴar-uwar da ta rasu ba. Sallamar Sagir ya sanya shi kawar da idonsa daga kan Ahmad yana wasa da Amir.
Ajiye musu lemon yayi kafin ya musu bismilla dashi suka nuna sun ƙoshi, sai da Daada ta tsoma baki sannan suka ɗauka suka sha suka ajiye. Miƙewa su kayi Sagir yace" Har zaku tafi?".
"E wallahi zamu koma amma in sha Allah gobe zamu zo sai na duba jikin Daadar ma".
Ahmad ya faɗa yana saka takalminsa sau ciki, godiya sosai yaya Aliyu da Sagir suka musu Anty Sakina da Sha'awa suna taya su.
Zara hannuwansa Zayyad yayi cikin aljihunsa ya ciro bandir ɗin kuɗi ya ajiye a gaban Daada cikin sanyi yake faɗin"Daada ga wannan ko kwayi wata buƙatar da, ita Allah ya ƙara ƙarfin jikin".
"Allah yayi maka albarka ɗan nan, Allah ya saka maka da alkhairi duniya da lahira halinka na ƙwarai ya bika. Madalla da iyayenka da suka jajirce wajen baka tarbiya da ɗaura ka akan tubalin da ya dace, ace matsahin saurayi kaman ka yasan abinda ya dace tare da zuciyar tausayin na ƙasa dashi ai wannan abin alfahari ne ga ko wasu iyaye, Allah ya maka albarka".
Kansa ya ƙara sunkuyarwa a gabanta bai san meyasa ya kasa jure kallon cikin idanunta ba, a hankali ya motsa leɓɓansa yace" Amin nagode zamu tafi".
Rako su Yaya Aliyu da Sagir suka yi har jikin motarsu, har yanzu yana riƙe da hannun Amir da ya bashi wayarsa yana wasa da ita(game).
"To Alhaji mungode Allah ya saka da alkhairi".
Murmushi ya maidowa yaya Aliyu da shima fuskarsa take tamkar gonar audugu, Ahmad yace"Sunan sa DR ZAYYAD EL-FAROUK BAITA mamallakin Zayfa hospital da kuma ƙungiyar #Stand for needers da zayfa foundation. Ni kuma sunan Ahmad".
Ɗaga kansa Sagir yayi kana yace"Lalle muna jin sunar ƙungiyar, labarin alkhairinta ga jama'a yana iso kunnuwanmu Allah ya ƙara girma da ɗaukaka".
"Amin tare da ku".
Zayyad ya amsa dashi yana ƙoƙarin dasa fara'a a fuskarsa, kafin ya maida kallonsa ga Amir haɗi da faɗin"yarona zamu tafi sai kuma gobe idan muzo ko".
"To Uncle sai anjima ka gaida Mamanka".
Tsura masa idanu Zayyad yayi yana jin wani abun da ya gaza samun kalmar da zai fasalta shi dashi cikin kalma ɗaya yana bin jini da jinjiyar jikinsa yana ɗaurewa tamau, wani murmushin ya kuma saka da ake masa laƙani da yafi kuka ciwo da raɗaɗi kana ya shafo kan Amir yace" Yarona ni Mamana ta rasu in kayi salla kana taya ni yi mata addu'o kaji".
"To naji zan yi mata, Anty Ummun gidan su yaya Sagir tana koya mana addu'a hadda wanda ake yiwa in anje birne mutum, da kuma na zuwa masallaci duk na riƙe su".
"Good boy to mu mun tafi".
Iya abinda ya faɗa kenan yana miƙewa daga tsugunan da yayi gaban Amir, yaya Aliyu ya katse mishi hanzari da faɗin" Ayya yallaɓai Allah ya jiƙanta da rahama yasa ta huta".
"Amin- amin".
Suka shiga faɗa shi da Ahmad kafin suka ƙarayin sallama suka isa ga motar su, wajen zaman ɗan banza Zayyad ya buɗe ya shiga Ahmad ya shiga mazaunin driver ya tada motar suka bar cikin unguwar.
Duk maganganun da Ahmad yake yi jin su kawai yake kamar suna yawa a cikin iska, don baya iya tantance ababaɗen da yake faɗi. Lumshe idanunsa kawai yayi yana gyara zamansa ya kwantar da kansa a jikin kujerar motar yana tino addu'ar da Daada ta masa. Ba yau ne karo na farko da ya fara jin addu'arta gare sa ba, tun kafin su sadu da juna tana asibiti yaji addu'ar da take masa.
Jin Ahmad ya faka motar ya sa shi buɗe idonsa tare da tinanin ko sun iso gida ne, ganin gefen titi ya faka motar ya sanya shi watso masa idanunsa da suka fara rikiɗewa izuwa jajir. Tun kafin yayi magana Ahmad ya tari numfashinsa yace"Hamma magana nake son muyi akan wannan yarinyar Ummukursum".
Gyara zamansa Zayyad yayi yana fuskanto Ahmad kana yace"Ahmad yanzu bana cikin yanayi amma abunda yake ɗaure mini kai shine, wani irin alaƙa ce tsakanin su da mutan unguwansu da ya zamto babu jituwa tsakanin su balle su yiwa juna fatan alkhairi. Labarin da ta bani yaso bambamta da abinda idanuna suka gane min, domin bata sanar dani cewar iyayenta sun rabu ba".
"Hamma wataƙil sai bayan barin ta gida hakan ta afku, kai fa kake ce min tace maka mahaifinta mashayi ne. So kasan kuma babu abunda mashayi ba zai iya aikatawa ba, ko kuma abinda ta aikata shi ya tunzura shi har ya sauwaƙewa mahaifiyarta ta".
Sauƙe numshafi Zayyad yayi mai ƙarfi yana furzar da zazzafan iska daga bakinsa kana yace"Dole sai na shiga jikin su sosai, kafin na cimma muradin abinda nake son sani".
Dafa kafaɗarsa Ahmad yayi haɗi da faɗin"Hamma in sha Allah, zaka sama dukkan goyan bayana".
Kansa kawai ya ɗaga masa saboda matsanancin ciwon kan da ya sauƙa masa cikin sa'i guda, a hankali yake sauƙe numfashi ɗaɗɗaya. Sannan Ahmad ya figi motar ya ɗaura ta akan titi suka bar wajen.
Koda suka iso sai da ya taɓo Zayyad ganin bai da niyyar fitowa daga cikin motar, sannan ya fito yana jin ƙirjinsa da yake masa nauyin gaske tamkar an masa ajiyar wani abun a cikin ƙirjinsa. Basu iske kowa a falon ba sai Mahmud yana kallo zama suka yi, ya kwantar da kansa a jikin kujerar tare da lumshe idonsa. Ahmad ya zauna kusa dashi Mahmud yana musu sannu da zuwa Ahmad ne ya amsa yana cewar"Mahmud ina ƴan matan fa suka shiga?".
"Yaya Ahmad duk suna kitchen suna haɗa lunch, nima yanzu na fito na ɗan sha iska".
Dariya Ahmad yayi haɗi da faɗin"Lalle yaron nan kace dai kaga abin yafi ƙarfinka".
Shima Mahmud ɗin murmushi ya maida masa mai sauti yace" Wallahi yaya Ahmad ka tambaye su duk ni nayi aikin, saura ne kawai na bar musu suna ƙarisawa shine na fito nan".
Wayarsa Ahmad ya ciro yana latsawa har izuwa lokacin da Fatima tare dasu Ramlat suka fito suka jere abincin akan dinning, Nafisa ta hararo Mahmud tana ɗaura da faɗin" Kai dai Mahmud bakinka baya kunyar faɗin abinda bai faru ba, tun shigowar su Hamma nake jinka kana faɗin wai duk girkin kai kayi kai da yankan albasa ma kasawa kayi ka fito nan".
"Ke kuma banza wacce ba'a sirri dake to ina yanzu hankalinki ya kwanta da shegen suturun ki parrot mouth".
Murguɗa masa baki Nafisa tayi suna ƙarisowa cikin falon suka zauna, suna yiwa su Ahmad sannu da dawowa. Ramlat da ta lura da yanayin da Zayyad yake cikin duk maganar da su Mahmud suke yi bai sanya bakinsa ba balle yayi ƙoƙarin wangale idonsa.
"Hamma lafiya kayi shuru haka ko baka da lafiya ne?".
Kyakykywan ajiyan zuciya ya sauƙe da zummar buɗe idanusa da suka masa nauyi, murmushi yayi ƙoƙarin wanzarwa akan leɓɓansa wanda iya kansa kan fuskarsa bai kai ga zuciyarsa ba. kana yace"Lafiya ƙalau kawai stree ne, da kuma ciwon kai haka amma da zarar na kwanta in sha Allah zai daina. Ahmad ku tashi mu tafi masallaci lokaci yayi".
Yana kama faɗin haka ya miƙe ya fice daga falon, kamar yasan unguwar sai da ya kai bakin gate sannan su Ahmad suka cimma masa. Masallacin kusa yake suka taka da ƙafarsu suka isa sai da suka yi alwala sannan suka shiga masallacin suka gabatar da sallan kamar yanda suka saba sai da suka yi sallan asr sannan suka koma gida.
A gate suka iske ƙannen Fatima suka gaisa sannan suka shiga cikin gidan tare, abinci suka ci sannan aka kafa dabar hira cikin raha da walwala. Keɓe kansa yayi a cikin compound ɗin gidan ya rasa gane kansa gabaɗaya sai safa da marwa yake yi cikin yalwataccen filin gidan. a hankali ya kai gubansa izuwa agogon da yake ɗaure a tsintsiyar hannunsa, da yake nuni akan ƙarfe biyar da mintuna sha biyar wayarsa ya fiddo daga cikin aljihunsa ya danna ƙiran Mahmud yace" oya ku fito mu tafi".
Daga haka ya kashe wayar yana maida ta cikin aljihunsa, mintuna ƙalilan a tsakani duk suka fito Ahmad ne ya fara isowa ya rungume shi yace" Hamma naga yanayinka duk ya sauya, ka kwantar da hankalinka in sha Allah everythings will be okay".
Kansa ya ɗaga masa yana kallo inda Fatima take tsaye tare dasu Ramlat yace" To madam mu zamu tafi sai kuma wani lokacin".
"To Hamma mungode Allah ya kaiku lafiya".
"Amin".
Ya amsa dashi yana shigewa motar, sannan su Mahmud ma suka shiga ya tada motar suka tafi. Suna isa su Ramlat suka wuce part ɗin Ammiey shi da Mahmud suka wuce masallaci sai bayan isha'i sannan suka dawo, suka nufi part ɗin Ammiey yawan jama'ar yau kam sun ragu saura ƴan-uwa kawai kusa da Faisal, Mahmud ya zauna shi kuwa ya zauna kusa da Ammiey bayan ya gaishe ta amsa ta ɗaura da faɗin" Zayyad lafiya naga kamar baka da kuzari?".
"Lafiya ƙalau Ammiey gajiya ce kawai, inaso na kwanta sai da safe daman nazo miki".
Sannu su Anty Binta suka shiga jera masa kar ya miƙe, ya fice daga falon ya wuce part ɗin Ahmad kayan jikinsa ya rage ya shiga ya watso wanka, da ƙyar ya iya jawo ƙafarsa ya fito ya saka kayan bacci marasa nauyi.
Sosai jikinsa yake rawa yana jin wani irin masifaffen sanyi, yana ratsa dukkan gaɓoɓi da ƙashinsa. Sallaya ya shimfiɗa ya tada kaffara yana kaiwa ruku'u ya ɗago ƙafafunsa suka fara rawa, sulalewa yayi ƙasa ya baje akan sallayan numfashinsa yana fita sama-sama.
Lalumar inhaler ɗinsa ya fara yi, wanda tana cikin kayan da ya cire kafin ya shiga wanka. Sosai numfashinsa ya fara cushewa idanunsa suna rufewa babu abinda yake hangowa sai duhu.
SALON ƘADDARATA
© Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________
Page 4⃣6⃣
Numfashinsa daya fara butulcewa bin umarnin ruhinsa, ya fizgo da matuƙar ƙarfi tare da yunƙurin sake tashi a karo barkatai hannunsa ya yi ƙoƙarin jawo wa gangar jikinsa ya ƙi basa haɗin kai wajen aiwatar da hakan. A wahalce yake sauƙe numfashi ɗaɗɗaye yana runtse idanunsa can ƙasan maƙoshinsa yake jiƙa harshensa da sunayen mahaliccinsa ɗari ba ɗaya, ƙara mimmiƙewa yayi kan sallayan duk jikinsa ya sake yana ƙara bajewa akan sallayan.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un".
Iya abinda zai iya tinawa kenan yayi nasarar fitowa tsakanin hakwaransa da suke karafɗiya ya faɗa, daga haka numfashinsa ya tsaya cak! bai ƙara sanin inda kansa yake ba sai buɗe ido yayi a hankali yana ƙarewa inda yake kallo, sai da ya bi ko'ina da kallo sannan ya sauƙe zazzafar ajiyar zuciya yana ƙara tabbatar da sahihancin abinda idanunsa suka gane masa saɓanin abinda zuciyarsa take ayyana masa na cewar mutuwa yayi, amma ganin inda yake yanzu ya tabbatar har yanzu da rabon sauran shan ruwarsa a bayan ƙasa.
Dishi-dishi idanunsa da suka kumbura har wani zafi-zafi suke masa, suke iya hango masa Ahmad da yake tsaye bakin window yana waya gefe kuwa Faisal da Mahmud ne suna zaune. Yunƙurin tashi yayi hakan ya gagari kuzarin jikinsa dole ya tilasta masa komar da kansa kan pillown ya kwanta.
A tare Mahmud da Faisal suka lura da tashin da yayi duk suka iso garesa suna jera masa sannu, kansa kawai yake iya ɗaga musu yana ƙoƙarin tinano abinda ya faru dashi har ya kwantar dashi haka, robar ruwar da yake saƙale a hannunsa ya kai kallonsa gare sa tare da lumshe idonsa yana jin kansa tamkar zai tarwatse saboda ciwon da yake masa sanyin ɗakin ne yaji yana ratsa ƙashi da ɓargonsa hakan ya haifar masa da rawar ɗari.
Dai-dai lokacin da Ahmad yayi hanged up ɗin wayar da yake yi ya iso wajen, ɗaura hannunsa yayi saman goshin Zayyad ɗin haɗi da faɗin"Hamma sannu ina ne yake maka ciwo yanzu?".
Bai yi yunƙurin amsa mishi da kalaman baki ba, domin yasan ko yayi ƙoƙarin aikata hakan ba zai sama haɗin daga bakinsa da yake jin yayi masa nauyin gaske ba, kansa kawai ya ɗaga masa tare da wangale idanunsa da ya lumshe su ya buɗe su tar! akan Ahmad.
Ganin yanda jikinsa yake rawa ya sanya Faisal miƙewa ya kashe fankar dake aiki cikin ɗakin, sannan ya rufe windows ya dawo ya zauna, Ahmad ya kalle su ɗaɗɗaye kana yace" kuje falo ku jira ni".
Basu yi musu ba duk suka miƙe suka fice daga cikin bedroom ɗin izuwa falo, sai da Ahmad yaha fitar su kana ya zauna kusa da Zayyad hannunsa marar drip ɗin ya kamo ya sanya shi cikin nasa kana ya fara bin fuskarsa da kallo kamar mai son karanto abinda da ya ƙunshe ƙasan ƙalbinsa.
"Hamma menene yake damunka, menene ya maka zafi cikin wannan duniya da har kake ƙoƙarin sanya rayuwarka cikin halaka. Tun daren jiya Ammiey ta ƙira take sanar dani baka da lafiya basu sani ba sai da suka ga baka fito sallan asuba ta aiko Mahmud yazo ya tashe ka suka iske ka cikin mummunar hali, Hamma athsmar kace ta tashi amma kuma har jininka ma ya hau don Allah menene damuwarka ka sanar damu, yanzu ga can Ammiey tun jiya take kuka da ƙyar yanzu ta sama bacci ta hana a ƙira Abbu a sanar dashi".
Gigitaccen ajiyan zuciya Zayyad ya saka, wanda lokaci guda ya canza bugun zuciyarsa, shuru yayi na wucen gadi har sai da yaji Ahmad ya ƙara ƙarfin riƙon da yayi wa hannayensa kana ya ɗauke kansa daga kallon da ya ƙurawa ceiling ɗakin cikin sanyi yake faɗin"Ahmad bazan ɓoye maka domin izuwa yanzu na fahimce cewar kana daga cikin mutane ƙalilan da zuciyata, take girmamasu tare da fallasa musu dukkan abinda yake cikinta ba tare da ɗar ko wani shakka ba. Nayi alƙawarin sanar da kai damuwata amma ba yanzu ba sai lokacin da ya dace kowa ya sani yanzu babban abinda da yake damuna shine na sada wannan yarinyar da iyayenta".
Shuru Ahmad yayi na tsawon daƙiƙun da baza su gaza biyar ba kafin ya shiga faɗin"Hamma haƙiƙa duk mun shiga tsananin damuwa aka halin da muka iske ka a ciki, koda bamu kai matsayin da zaka sanar damu damuwarka ba amma don Allah roƙo ɗaya zan nema a wajenka shine kayi ƙoƙarin cire komai daga cikin ranka ko dan lafiyarka tunda akan taimakon wata can daban zaka iya jefa rayuwarka cikin gagari".
Yana dasa aya a nan ya zare hannunsa daga cikin nasa tare da miƙe daga zaman da yayi kusa dashi, da kallo Zayyad ya bishi yanayin fuskarsa ya sanya shi tinanin kamar bai ji daɗin maganar da yayi masa bane don haka yace" kama ni na tashi ka kaini naga Ammiey".
Riƙo Ahmad yayi da kafaɗarsa ya tashi ya zauna, sannan ya zare masa robar ƙarin ruwan da aka masa har suka fito falo yana riƙe dashi, ganin fitowar su ya sanya su Mahmud miƙewa suna aikin jera masa sannu ɗaya na bin ɗaya har suka isa part ɗin Ammiey.
Su Ramlat suka iske a falon tare da Nafisa suna haɗa breakdast sallamar da suka shigo da ita, ya jawo hankalan su izuwa gare su, zaunar dashi Ahmad yayi akan saman doguwar kujerar 3seater ya jinjina bayansa da jikin kujerar yana lumshe idanunsa tare da sauraron yanda zuciyar dake ƙirjinsa yana harbawa.
Zama kusa dashi Ramlat haɗe baki suka yi da Nafisa wajen faɗin " Hamma sannu yaya jikin?".
Ba tare da ya buɗe idonsa yace"Alhamdulillah ina Ammiey?".
Yana rufe bakinsa hakan yayi dai-dai da sauƙowar Ammiey daga upstain, tare da Anty Binta tar ya buɗe idanunsa akan ta har ta sauƙo ta zauna yaje gabanta ya zauna yan ɗaura kansa akan cinyarta. tare da lumshe idanunsa jikinsa yana ɗaukar rawa har cikin jijiyoyinsa da ɓargonsa yake jin yanda azababben sanyin da yake ratsa jikinsa. Shafa kansa ta fara yi a hankali tace" ya jikin nakan na ƙira Mahmud yace min ka tashi shine nace, Binta ta fito da ni naje ashe ma har ka fito".
"E Ammiey jikin ma ai da sauƙi sosai ki kwantar da hankalin ki".
Sauƙe ƙarƙarfan ajiyan tayi tana ɗaurawa da faɗin" Gaskiya yanayin da muka ganka a ciikin mun shiga cikin kaɗuwa sosai, shiyasa muka gaggauta ƙiran Ahmad yazo".
Kansa kawai ya ƙara kwantarwa a jikinta yana jiyo muryar Anty Binta da Anty Khadija da suka haɗa baki wajen faɗin" Allah dai ya baka lafiya, asthman ne tana wahalar da kai".
Duk jama'ar dake falon suka amsa da amin, kafin su Nafisa suka sauƙo da breakfast ɗin ƙasa da ƙyar ya iya zuƙar ruwar tea shima don Ammiey ta matsa masa ne.
Yana gamawa Ahmad ya kawo masa maganinsa ya sha sannan ya wuce ɗakin Ammiey yayi kwanciyarsa ganin baccin ya ƙi ziyatar idanunsa ya sanya shi danna ƙiran lambar Hajiyarsa.
Tunda Sagir da yaya Aliyu suka dawo daga rakiyar da suka musu, yaya Aliyu yake sanar dasu cewar mutumin da ya biya kuɗin aikin da aka yiwa Daada shine mamallakin tagwayen ƙungiyoyin nan na, #Stand for needers da Zayfa foundations. Mamaki da al'ajabi suka mamaye zuƙatarsu.
"Menene aikin ƙungiyar ni ban ma taɓa jin su ba?".
Daada ta faɗa tan tsayar da ƙwayoyin idonta akan yaya Aliyu da yake ta faman bayyanin, aiyukan ƙungiyar tiryan-tiryan. Gyara zama yayi yana fuskanto ta yace" Daada ƙungiya ce ta taimakon al'umma mussamman masu ƙananan ƙarfi mata da ƙananan yara, hatta kayan ɗakin suna bayarwa ga marayu suna haɗa aure tsakanin samari da ƴan mata sannan suna raba jari ga matasa, sannan suna tsayawa matan da aka keta masu haddi watau fyaɗe har sai sun ga anyi musu adalci domin suna aiki da ƙwararrun lauyoyi ".
Tunda ya fara bayyanin Daada take binsa da kallo har ya kafa aya ta ce"Lalle Allah ya saka masa da alkhairi kuma duk shi ɗaya yake ɗaukar nauyin komai?".
"Daada likita ne fa shi ɗin kuma babban a fannin fiɗa watau tiyata, ina yawan ganin labarai akan sa da kuma ƙungiyarsa a kafar sada zumunta".
Sha'awa tace"Allah ya saka masa da alkhairi, amma Daada ai da mun masa maganar Anty Ummu akan abunda ya faru ko zai taimaka mana".
Shuru Daada tayi haka nan ma su yaya Aliyu da Sagir kam da tun ɗazu yaja bakinsa ya tsuke, Anty Sakina tace" Haka ne kam nima tinanin da nake kenan cikin raina mu gwada tuntuɓarsa da maganar tunda, sun ce gobe zasu zo su duba ki".
"Sakina wata shaida muke dashi da zamu tunkare shari'a dasu sannan uwa uba ma ita wacce ake abun akanta bata nan babu wanda yasan inda take balle har mu gabatar da ita a matsayin makamin da zamu yi riƙo dashi".
Kusa da ita Sagir yazo ya riƙo hannunta ya riƙe sannan yace" Daada in sha Allah, duk inda Ummukursum take zata dawo gare mu ina jin haka a jikina wataƙil Allah ne ya amsa addu'o'in mu ya turo mana wannan mutumin a matsayin wanda zai share mana hawayen mu, mu gwada tuntuɓarsa da maganar wataƙil yasan wani babba da zai iya shige mana gab har ayi mana adalci".
"To shikenan tunda kun matsa in sunzo sai mu tare sa da maganar, ga wannan kuɗin da ya bayar Aliyu ka riƙe a wajenka sai ayi kuɗin makarantar da Sha'awa zata soma".
Karɓar ƙudin yaya Aliyu yayi suka fice tare da Sagir, jim kaɗan suka dawo suka fake kayan abincin da suka sayo yaya Aliyu ya ɗauki dubu goma ya ba wa Daada ta riƙe a wajenta ko zata yi wata buƙatar dashi, da farko ta ƙi amsa amma da ya matsa sai ta karɓa raguwar sauran kuɗin wajensa dashi za'a amfani wajen biyan ƙudin registration ɗin Sha'awa na makarantar sakandirin da ake nema mata.
SALON ƘADDARATA
© Maimunah Tijjani Iyam
______________________________________
Page 4⃣7⃣
Tun bayan ranar da ma'aikaciyar asibitin tazo har gida ta mini ƙarin ruwa ban ƙara lafiya ba. Har i yau wani azababben zazzaɓi ya mamaye jikina ya ɗauki zafi gau! ga kumburin da na zabga abin gwanin tsoro da al'ajali. Cikin dake jikina za'a yi tsammanin ya kai watannin takwas da ɗauriya, amma watansa biyar ne kawai,Cikin kwanakin nan na dasawa kaina wani hali na zaman ɗaka kullum ina cikin kuka tamkar matar mamaci duk na zabge nayi wata mungun rama marar daɗin kallo a ido.
Ko tsakar gida bana fitowa iya kaci na tsakanin cikin ɗaki da falo, duk tambayar da Hajja zata jero mini akan meye yake damuna bana bata amsa haka nan ko Baban Nana zai ƙarar da kalaman bakinsa wajen son jin dalilin kukan bana amsa mishi domin nima kaina ban san meya damuna ba kuma san so na sani.
Haka nan kawai jikina yake yawa ayyana mini cewar wannan cikin dake jikina bazan haife shi ba, na aljali ne hakan ya taimka wajen ƙara jefa raunanan ƙalbina cikin wani sabon babin tashin hankali muradin raina a yanzu bai wuce naga Daada da sauran ƴan-uwana ba ko don na nema afuwa da yafiyar su akan abin kunyar dana jawo musu.
Kukan da nake yi ya tsana dana tina irin rayuwar da muka taso a cikinsa babu kulawar uba, Daada ita ce komai a duniyar mu Allah ne shaidarta akan cewar ta tafiyar da amanar mu da ya bata akan kyakykyawan tubalin da ya dace. Ni kaina wani lokacin ina neman rasa tinanina wai ni Ummukursum ce nake ɗauke da cikin da ban san waye mahaifinsa ba, a cikin mahaifata na ƙara gaskatawa tare da tabbatar da cewar shi fa bawa yana wuce ƙaddarar rayuwarsa a ko'ina yake zai ta afka masa wala khairan ko akasin hakan.
Sai SALON ƘADDARATA tazo cikin mummunan fuska da yanayi da ya tarwatsa dukkan gini da foundation ɗin da na yiwa rayuwata tanadin sa cikin kwanakin da basu gaza ashirin ba.
Ina zaune can ƙuriyar ɗakin na ƙunshe kaina cikin hijabina ina sharɓar kukana son raina, duk zaman gidan ya gunrine ban ƙi ba na sama wata hanya komai hatsarin zan ɗauka na fice daga gidan. Banji shigowar ta ba balle saman da tayi kusa da katifar da nake zaune akai sai jin hannayenta nayi saman kafaɗuna, hakan ya tilasta mini saurin ɗago idona na mata kallo ɗaya na kawar da kaina gefe guda ba tare da nace da ita ko kanzil ba.
"Ummukursum don girman mahaliccinmu ki sausautawa kanki daga wannan kukan da kike faman yi, ma'aikaciyar asibitin nan dai ta sanar dake cewar yawan zama cikin damuwar da kike yi zai sanya jini ya hau wanda hakan zai haifar miki da matsala yayin da kika zo haihuwa, don Allah na roƙe ki ki daina kinji ɗiyata".
Wata gwauruwar ajiyan zuciya na sauƙe ƙaƙƙarfa, da ta canza bugun da ƙirjina yake yi ya ƙaru ɗif! ɗiff!! haka sautin yake fita, na karkato da kumburarran fuskana da duk halittun fuskan duk sauya saboda kukan da na sha har na godewa Rabbul izzati.
Ƙarfi hali nayi cikin fizgo numfashina da nake ji tamkar ana shaƙe ni nace da ita"Hajja ban san meye yake damuna ba, sai dai ina jin jikina yana bani cewar bazan haife wannan cikin ba wallahi duniyar gabaɗaya ta mini zafi na rasa ina sanyan kaina".
Na ƙarishe zancen nawa ina kwantar da kaina saman cinyarta, a hankali ta kai hannunta tana bubbuga bayana, ita ma tana taya ni ɓarin hawayen don ina jin su. Suna sauƙa bayan wuyata tsawon mintuna muka ɗauka a haka kafin ta ɗago kaina tare da tallafo haɓarta tace" Ummukursum ki zama cikin bayi masu kyautata zato a ko da yaushe, in sha Allah zaki haife wannan cikin. Nasan ko wacce mace in ta tsinki kanta a cikin yanayin da kike na rashin miji kuma ya barka da cikin ɗansa ko ƴarsa a cikinka dole kaji kai ma kamar bin sa zaka yi, amma idan kika yi takwalkali kika miƙa dukkan lamuran ga Allah kuma kika yarda shine matsarin komai a rayuwarki to sai kiga komai naki ya zo miki da sauƙin da bakya tsammanin samun sa".
Maganganunta suka bugu raunannan ƙalbina da ya kusa tarwatsa izuwa part-part, nayi jarumtar wulla idanuna cikin nata. Tausayina na hango muraran a cikin idaniyarta nayi saurin ɗauke nawa idon daga cikin nata ina jin wani kuka mai ƙarfi da yake shirin kubce mini.
Tabbas ta cike duk wasu sharruɗan zama masoyi na haƙiƙa a gare ni, macece mai matuƙar sanin ya kamata,dattako da kuma farar zuciya kamar yanda fuskarta take kullum cikin walwala da annashuwa. Ban san meyasa ba na kasa jure kallon cikin idanunta na kasa tantance cikin waɗannen biyu wannan ne nake yi a halin yanzu.
Kunya ce ko ko nadama nake yi akan ƙaryar da muka mata, na cewar mijina mutuwa yayi ya barni da wanna cikin. Kukan da nake ta ƙunshewa ina hana fitowar sautinsa waje ne ya fito babu shiri na sake sa da matuƙar ƙarfi tare da buɗe dukkan muryata ina rero sa wiwi.
Hajja ta ƙara kamo ni jikinta ta riƙe tsam! kamar wani jariri ɗan wata uku da haihuwa, sautin ajiyan zuciyar da nake sauƙewa a kai- a kai kamar wacce ta shari gudu a filin fage ya sanya Hajja ƙara manna ni a jikinsa na lumshe idona ina ƙoƙarin daidaita kaina a ƙoƙarin samarwa kaina nutsuwar zuci da taimakon Hajja, na miƙe na shiga banɗaki na wanke fuskana sannan tace na fito waje na sha iska ban mata musu ba na biyo bayanta izuwa tsakar gidan tun kafin na fito na iske Nana ta shimfiɗa mini tabarma. Duk da damuwar da take dawainiya da ruhina nayi ƙoƙarin dasa murmushin yaƙe akan fuskana tare da sakin jiki muna hira da su Iman da Nana.
Wuni ranar motsi kaɗan nayi sai Hajja ta tambaye ba'asinsa, har na fara ware jikina da yammaci ma'aikaciyar asibitin tazo ta duba ni, idona yana lumshe nake jiyo tattaunawar da suke yi da Baban Nana akan Zayyad ɗin ko ya ƙira wayarsa taba tafiya, ita haka yake daga nata bangaren domin tace sun daɗe basu yi waya dashi ba.
Magungunan da ta ambace su dana ƙarin jini ta lodo mini kana suka yi sallama da Hajja ta tafi.
Tsaye yake cikin falon Ammiey ya zara dukkan hannayensa cikin aljihun jamfar dake jikinsa, wanda tsayinta ya tsaya masa daidai gwiwarsa, hoton mahaifiyarsa tare dasu Anty Binta ya ƙurawa idona ƙaƙƙafar ajiyan zuciya ya saka a lokaci guda yana gyara tsayiwarsa, kafin ya kai hannunsa saman hoton yana shafawa a hankali. Murmushi ne ɗauke a kan fuskarta take zuciyarsa ta bada wani zazzafan sauti da ya sanya sa runtse idanunsa yana jin wani wutar so da kewarta tana mamaya a cikin rai da ruhinsa.
Meyasa tashi ƙaddarar ta jefo cikin maraici ta raba shi da mahaifiyarsa tun yana cikin zanin goyo, hawayen da suka ciko masa kurmin idanu ya kawar. Ƙaran sauƙowar mutum daga upstain ya sanya shi mai da kallon sa ga wajen, Ganin Ammiey ce tare da Ramlat ya sanya shi isa gare su, rungume Ammiey yayi yana ɓoye ƙwallar idonsa cikin muryarsa da ta fara rawa yace" Ina kwana an tashi lafiya".
"Lafiya ƙalau Babana ya ƙarfin jikin nakan?".
"Da sauƙi".
Shafo sumar kansa tayi kana tace"to muje kaci abinci sai kasha magani ko?".
Ɗago kansa yayi yace"Azumi nake yi nasha maganin tunda asuba, wajen Ahmad nake son naje".
"To amma ai daka sanar sai a maka abincin sahur ɗin, kuma kai da baka da lafiya ma ai da ka bari sao kaji sauƙi tukunna".
Cike da kulawa tayi maganar da ya sanya shi wanzar da murmushi a fuskarsa kana yace" karki damu Ammiey nifa lafiya ƙalau ki kwantar da hankalinki, na tafi zanje na sama Ahmad a asibiti".
Addu'ar neman tsari ta masa sannan ya saka kai zai fice daga cikin falon muryar Ramlat da suka yiwa kunnuwansa dirar mikiya, ya sanya shi dakatawa.
"Hamma an tashi lafiya ya jikin?".
Bai kula ta ba illa tsiririyar tsakin da ya saka yana murɗa handle ɗin ƙofar falon ya fice, da sauri ta bi bayansa bata cimma masa ba har sai da ya kusa isa ga motarsa sannan ta sha gabansa shagwaɓe fuska tayi tana riƙo kunnuwanta tare faman faɗin" Hamma please kayi haƙuri wai menene tun jiya inna maka magana baka amsa ni?".
"Abeg malama matsa na wuce, banda time sauri nake yi kwanana nawa a cikin gidan nan bani da lafiya kin taɓa buɗan bakin kin tambaye ni yaya jiki, sai yau da kika ganni zaki tambaya".
Haɗe hannuwanta tayi wuri guda tace"Hamma kayi haƙuri wallahi kullum in zaje, sai Ammiey tace a ƙyale ka ka huta".
Kansa ya ɗaga mata haɗi da faɗin"naji ya wuce". daga haka ya ɗauki hanyar parking lot har jikin motar ta raka shi sai da ya fice daga cikin gidan kana ta juya zata shige ciki, ganin Mahmud dake tsaye yana kallonsu ya sanya ta wurga masa harara shi kam dariya ta bashi ya sake dariyarsa har da riƙe ciki.
A ƙulafuce tace" Sai kayi ai tunda aiki ne bai ishe ka ba".
Sai da ya dai-daita kansa kana yace"kece dai aiki bai ishe ki ba, wai ke anan haka son Hamma kike yi ko, to wallahi gwara ki sani iska ce kawai take wahalar da mai kayan kara domin Hamma Zayyad kam ƴan matan da suke fi ki cika mace ma basu ishe shi kallo ba balle ke ƴar mitsitsiya da ke".
Ya ƙarishe maganar yana ƙara tuntsirewa da wata dariya, duka Ramlat ta kai masa yayi saurin gocewa kana tace"To sai ka nashi auren nawan, wallahi kana cikin gidan nan sai na baka mamaki".
"Ai kuwa dai ina nan ina jira".
Kalmar da Mahmud ya raka ta dashi kenan ta shige part ɗin Ammiey bayan ta gama aikin murguɗa masa baki, shima ya wuce part ɗin Ahmad saboda Ammiey tace yaje ya gyara part ɗin kafin Zayyad ɗin ya dawo.
Yana fita daga gidan ya wuce asibitin da Ahmad yake aiki, a gate ya tsaya ya zaro wayarsa yana danna lambar Ahmad ɗin bugu ɗaya ya ɗaga yace". Ina waje am waiting for you".
Yana ƙarishe maganar ya datse ƙiran tare da jingina bayansa jikin kujerar motar, ya rintse idanunsa. Yau haka nan ya tashi da kewar mahaifiyarsa dukka bai rayu da ita ba ko na sakan ɗaya a rayuwarsa shigowar Ahmad ya sanya shi buɗe idonsa yana gyara zamansa.
Bai kula shi yaja motar suka fara tafiya, Ahmad ya kallo shi sannan yace"wai ina zamu je?".
Sai daya ƙarya kwana kafin yace"Wunti stree zamu".
SALON ƘADDARATA
© Maimunah Tijjani Iyam
_____________________________________
4⃣8⃣
Shuru Ahmad yayi masa ganin baya cikin yanayin jurar yawan magana, ya zaro wayarsa ya fara latsawa jin da yayi ya faka motar ya sanya shi ɗago idonsa yana watsa su akan titin. A inda suka saba fakin ɗin motar ya ajiye ta suka fito suna dosar cikin layin.
Wayarsa da ta fara ruri ya sanya shi haɗiye maganar da yake zo guntsawar Ahmad, ya zaro wayar ganin sunan Hajiyarsa da yake yawo cikin screen ya sanya saurin ɗaga ƙiran yan karawa a kunnensa bayan sallaman da yayi mata shuru yayi, yana sauraran yanda take maganar cike da damuwa ƙarara a tattare da muryarta da har rawa take yi.
"Abeena wai meyasa baka tausayin kanka ne, Ammiey ta sanar dani cewar kwana biyun nan ciwonka ya tashi har ƙarin ruwa aka maka, amma baka ƙira ni ka faɗa mini ba. Menene yake damunka ka sanar dani yanzu?".
Kyakykyawan ajiyan zuciya ya sauƙe yana maida hannayensa cikin aljihunsa, kana yace" Hajiya ki kwantar da hankalinki ba fa wani sosai bane ciwo, kuma kinga yanzu kam ma am feeling better gani ma na fita unguwa tare da Ahmad".
Shuru ya biyo bayan zancensa na ƙarshe ganin shurun yayi yawa ya sanya shi, zare wayar daga kunnunesa yaga ko ta kashe ne yaga har yanzu ƙiran yana kan layi.
"Hello kina jina?".
Yana iya jiyo yana ta sauƙe numfashi mai ƙarfi kana tace"Zayyad hankalina ba zai taɓa kwanciya ba har sai naga ka sama mata kayi aure, ka sama wacce kaima zata na kulawa da kai wacce zata zamto sanyin da zaka fake a lokacin da jikinka ya ɗau zafi. Wannan shine kawai samun kwanciyar hankalina lokaci yayi da kaima ya kamata ace ka zama cikakken mutum Abeena".
Furzar da iska yayi daga bakinsa dai-dai lokacin da suke karya kwanar da zata sada su da gidan, ya ɗan saci kallon Ahmad da shi kam ma hankalinsa yana ga kan titin.
"Hajiya wannan ba maganar da zamu yi a waya bace, in kin dawo ma yi ta".
Magana ta soma yi ya katse ta, ta hanyar faɗin"Ga Ahmad ku gaisa".
Daga haka ya miƙawa Ahmad wayan suka fara gaisawa, tare da masa addu'ar samun dawwamamman zaman lafiya a rayuwar aurensa, suka tsaya wajem wani mai sayar da lemo da kankana suka saya sannan suka wuce, sallama Ahmad suka yi da Hajiya ya miƙawa Zayyad wayar shima suka yi sallamar sannan ya katse wayar ya mayar aljihunsa.
Kallonsa Ahmad yayi tare da sakin murmushi ƙasa-ƙasa wanda hakan ya sanya Zayyad ware idonsa akan sa like asking him what?, Giggiza kansa Ahmad yayi yana tsagaita dariyar da yake yi yace"Hamma gaskiya a wannan lokacin da zafinta ta tazo akan maganar aurenka, ka fito da mata ko mu maka auren dole ehenn".
Hayaniyar da suka jiyo shi ya sanya Zayyad haɗiye furcin da yake da niyyar furzowa waje, suka isa wajen da hayaniyar take tashi yara ne sunyi dandazo suna tsokalar wata yarinya hadda masu ture ta bokatin markaɗen dake kanta ya zube ƙasa duk ya ɓata mata jiki, hankaɗo ta suka yi suna faɗin.
"Ahayye aga aga, aga wacce yayarta tayi cikin shege ta gudu daga gida, aga wacce Abbansu yake dukan Ummarsu".
Taro ta Zayyad yayi daga faɗuwar da tak shirin yi saboda hankaɗar da suka mata, ta faɗo jikinsa tare da kwantar da kanta tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Take idanunsa suka kaɗa har wani ruwa-ruwa suke kawowa ya kai ƙololuwar ɓacin rai mussamman da ya ga wasu dattawan da suke zaune daga gefe suna ganin yaran amma basu yi wani yunƙurin dakatar dasu ba.
Ahmad ne ya kori yaran har suka watse suka bar wajen sannan ya ɗauki bokatin markaɗen da suka kwaɓar mata, saura kaɗan a ciki duk ya zube ya saka marfin ya rufe sannan ya kallo Zayyad da har yanzu yake riƙe da ita bata tsagaita da kukan da take yi ba.
"Hamma muje kawai na lura gabaɗaya, mutanen unguwan nan basu san ya kamata ba".
Shima cikin matuƙar ɓacin rai yayi maganar, ɗago kanta Zayyad yayi yana tsayar da idonsa akan fuskarta Ahmad yayi saurin faɗin "Sha'awa!".
Cikin rawar baki yayi maganar yana ƙara matsowa kusa tare da ɗaura da cewar"Hamma ƙanwar Sagir ne fa".
Riƙo hannunta Zayyad yayi ya isa har gaban wannan dattawan da suke zaune suna fira, sai da ya ƙare musu kallo tsaf sannan yace"Baba bani da shakkar faɗin cewar cikin ku, babu wanda bashi da ƴaƴa in ma bashi da shi yana da ƴaƴan ƴan-uwansa, bakwa yin tinanin cewar ita ƙaddarar bata bambamce tsakanin wannan ko wancan kan mai ita kawai take faɗawa. A kan idon ku waɗannan yara suke tsokalar yarinyar nan tare da faɗim magangu marasa ɗa'a amma baku yi wani ƙoƙarin taka musu birki ba, kuyi tinanin idan ƴarku ne yay zaku ji?".
Ɗaya daga cikin su ya ɗago ya watsa masa wani kallo, sannan suka kalli junansu suka taɓe baki kana ɗayan yace"Yaro yanzu kai inba rashin ta ido ba mu nan ba muyi sa'annin ubanka bane, zaka tsaya kana gaggaya mana magana. To mu muka saka yaran su tsokale ta ko ko ƙage aka mata basu yi cikin shegen kuma ta gudu ba, ƴaƴa mata nawa ubansu ya lalata a cikin unguwar nan ƴaƴa nawa ya raba su da gidajen iyayen su ya jefa rayuwarsu izuwa rayuwar bariki, kai yaro banda lalacewar zamani har kamar kai ya isa ya kalli idonmu yana gaya mana magana son ransa".
"To ai babban shi yake sayawa kansa ƙima, babu yanda za'a yi kuna a haka kuma kuyi tinanin samun girmamawa daga mutane ba".
Ahmad ya faɗa yana watsa musu kallo ido cikin idon, dafa kafaɗarsa Zayyad yayi yace"mu tafi kawai Ahmad babu amfanin mayar musu da magana mu ma sai mu zama kamar su".
Ɗaukar bokatin markaɗen Ahmad yayi suka wuce suka bar wajen, har suka isa gida bata daina kukan ba, suna isa tsakar gidan Sha'awa ta zare jikinta daga nasa ta ruga cikin ɗaki da gudu wajen Daada.
Tsayiwa suka yi a tsakar gida, Zayyad yana dafe goshinsa da jijiyoyin kansa suka shimfiɗa raɗau-raɗau, Ahmad ya riƙe shi yana cewa" Hamma lafiya kuwa?".
Kansa ya ɗaga masa dai-dai lokacin da Daada da Sha'awa suka ɗago labulen ɗakin suka fito, Anty Hussaina da Anty Sakina suna biye dasu a bayansu, tabarma Anty Sakina ta shimfiɗa musu suka zauna sannan ta gabatar musu da ruwan sha.
Ladabtar da murya suka yi suka haɗe baki wajen gaiseh da Daada, ta amsa sannan suka fara bin Anty Sakina da Anty Hussaina da nasu gaisuwar suka amsa cikin sakin fuska.
"Wai lafiya Sha'awa ta shigo gida tana kuka, ashe ma tare kuke?".
Anty Sakina ta tambaya tana kallon Sha'awa da har yanzu take kukan, kallon juna suka shiga aikawa junansa shi da Ahmad kafin Ahmad yayi ƙarfin halin faɗin"Daman mun shigo cikin layin ne muka tarar da yara, suna tsokalanta har da masu hankaɗe ta gashi duk markaɗen sun zubar mata".
Shafo kan Sha'awa, Daada tayi da ta kwanta lamau a jikinta tace"Ɗago ki faɗa mini menene suke tsokalar taki?".
Sai da ta zuƙe majinar kukan da ya zo mata kana ta shiga faɗin"Daada na dawo daga gidan markaɗen ne shine na kaɗu da ƴaƴan gidan Dije masu awara suka fara tsokalanta, wai Anty Ummu tayi cikin shege ta gudu daga gida kuma wai Abbanmu yan dukan ki har kan titin".
Ta ƙarishe maganar tana ƙara fashewa da wani sabon kukan, Daada ta rungumeta jikinta tana shafa bayanta a hankali shuru wajen ya ɗauka cikin su babu wanda ya kuma cewa komai har izuwa lokacin da Zayyad yace "kinga Sha'awa zo nan".
Tashi tayi ta matso gabansa yace"Ki daina kuka kinji a duk lokacin da wani ya tsokale ki, baki ga yanzu kin girma ba kiyi wucewar ki kawai kar kina kula su".
"To".
Kawai ta amsa dashi ya ɗaura da cewar"Ok good girl ki tashi kije ki wanke fuskar ki".
Tashi tayi ta shige banɗaki, Anty Hussaina ta matso tana tambayar Anty Sakina wanene su, raɗa ta mata a kunnenta tana faɗin"wancan shine wanda ya biyawa Daada kuɗin aikin da aka mata shine mai ƙungiyar nan ta bada agaji, sannan shine wanda muke son sanar dashi labarin Ummukursum ko zai taimaka mana akan lamarin, ɗayan kuma shine likitan da ya mata aikin".
Jinjina kai Anty Hussaina tana ƙara binsu da kallo, ganin yaro ne matashi sai abin ya bata mamaki don tayi tinanin babban mutum ne sai taga saɓanin tinaninta. A tare yaya Aliyu da Sagir suka shigo suka zauna sannan suka fara gaggaisawa, tare da mu su sannu da zuwa suka amsa cikin faran faran kamar sun daɗe da sanin juna.
Sannan Ahmad ya matso yana duba jikin Daadan abun ma'aunin gwajin hawa da sauƙar jini, ya ɗaura mata a damtsen hannunta yana gwada hawan jininta sannan ya cire mata tana mayar da abin cikin gidansa, kana ya kalle ta yace"Alhamdulillah Hajiya jinin ki ya sauƙa ba kamar yanda kika baro asibiti mu ba, amma har yanzu akwai buƙatar ki rage damuwa sannan zan rubuta miki wasu magagunguna da zan ɗaura ki akan su zasu taimaka".
"To Daada kinji dai da kunnenki ko, in ni ne na faɗa miki sai kice mena sani a boko gashi dai yanzu ɗan bokon da kansa ya faɗa miki".
Sagir ya faɗa yana lagwashe ƙafafunsa waje guda, murmushi Daada tayi Anty Hussaina ta amshe zance cikin faɗin"Kai dai Sagir Allah ya shirye ka naga ranar da zaka yi hankali ka mayar da mu kamar kakanninka".
"To ai yanzu kune iyayen kuma sune kakannin duka".
Leɗar da suka shigo da ita Ahmad ya gire ta a gaban Daada ta shiga sanya masa dozin-dozin ɗin albarka da amin yake amsawa sauran mutanen wajen suna taya sa amsa wa har ta kai aya kana ya masa damar amayar da maganar da ta tokare masa ƙirjinsa.
"Daada wacce wannan Ummukursum ɗin, da yara suke tsokalar Sha'awa da ita akan tayi cikim shege ta gudu?".
Shuru duk suka yi suna aikin aikawa junan su da kallon da yake cike da ma'anonin da su kaɗai suka barwa kansu sani, sai a sannan Zayyad ya ɗago kansa yana ƙarewa fuskokinsu kallo tare da som karantar abinda yake cunshe cikin zuƙatansu.
Miƙewa Daada tayi, tayi ɗaki tana tare guntun hawayen da ciko mata idonta Anty Sakina da Sha'awa suka rufa mata baya.
Yaya Aliyu ne ya katse shurun da yayi mamaya a wajen ta hanyar faɗin"Ummukursum ita ma ƴa ce ga Daada yayar su Sagir ce".
Jinjina kansa kawai Ahmad yayi daga haka bai ƙara cewa komai ba, suka miƙe zasu tafi Anty Hussaina tayi saurin dakatar dasu da faɗin"Muna neman taimakon ku akan lamarin ta hanyar ƙungiyar ku ta taimakon al'umma".
Gyara zamansa Zayyad yayi yana langwako ƙafafunsunsa waje guda, yana ƙara fuskantar Anty Hussaina da ke jawabin.
SALON ƘADDARATA
© Maimunah Tijjani Iyam
0 Comments