TSOHO NE

                                                                



TSOHO NE
Story and Writing by Dr zarah LG
Bismillahir Rahmanir Rahim

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki

Da misalin ƙarfe goma na dare Amra ta fito daga Gidan Rawa tana tafiya kamar zata faɗi saboda tsabagen kayan mayen da tasha cikin rashin mutunci, tana shiga cikin motar ta tayar, anan ta fizga a guje kamar bazata tsaya ba,  waƙa ce ta kunna ta turanci ta tokare ƙara har ƙarshe, tuƙi take kamar zata tashi sama tana karkaɗa kai tanabin waƙar,  cikin rashin tsammani  saiga wani tsoho yazo zai tsallaka titi,  kaɗan ya rage ta makesa, sa ar da aka samu shine tayi saurin jan burki, anan motar ta tsaya gefen titi bayan ta karkace, da sauri mutane suka antayo ana salati, da ƙarfi ta buga ƙofar motar ta buɗe ta fito, anan ta tsaya a gabansu ta ɗan ja gilashin dake fuskar ta, ɗaga hannunta tayi ta wanke wannan tsohon da mari.
  " Kai wane irin ɗan ƙauyene? kana ganin mota bazaka iya jira tawu ceba? ko a garinku babu motocine? Kai bakasan odar mota bane tsoho dakai marar hankali! da ace nayi asarar ɓata motata da walaƙancin dazanma wallahi sai yafi wannan! tsohon banza dakai kawai. "
Duk mutanen wurin saida suka girgiza da marin data mashi, babu wanda ya tanka mata a cikin su, da yawan jama'ar dake wurin haƙuri suke baiwa tsohon, dan suna ganinta suka san irin yaran nan ne ɗiyan masu kuɗi marassa mutunci da zasu iya walaƙanta kowa basajin shakkar gaya ma naga bansu magana, a haka kowa yaja bakinshi yayi gum bai tanka mataba, ashe dagacan gefe wani na sauraronsu, cikin fushi ya taso ya wanketa da mari, wani ihu ta buga wanda ya girgiza mutanen dake wurin, dafe kunci tayi ta fara magana  cikin kuka:
  " Kai ɗan gidan uban waye dazaka mareni? bakasan waye babana Alhaji Balarabe Mai Kuɗi? To wallahi saikayi dana sanin marina." Nan take tayi latse latse a waya takira tace tana wuri kaza suzo susameta, anan kowa ya tsaya yana kallon ikon Allah, ba afi minti talatin ba saiga motar ƴan sanda.
 Motar ƴan sandan na tsayawa sai mutane suka fara guduwa, wani babban ɗan sanda ne ya fito yace " Hajiya lafiya miya faru?" nan take ta masa bayani shi kuwa wannan saurayin ko gizau bai yiba, anan ƴan sandan suka sakama saurayin ankwa daganan suka hau dashi motarsu, mutane sunata bada haƙuri  tayi ƙememe tamurje ido sai an tafi dashi, haka kuwa akayi, ƴan sandan suka tafi dashi itakuma tawuce gida. Tana shiga falo ta tarar da  Ammi da Abba suna fira, tana shigowa ta fashe da kuka taje ta rungumi Abba tana kuka, da yake akwai fitila mai haske wadda ta zagaye falon tako ina, anan yaga gefen fuskarta yayi ja, ɗagota yace " miya sameki Amrat?"  labarin abinda ya faru ta bashi. 
  " Ɗan gidan uban waye ya taɓa min ƴa ɗaya tilo, aiko sai ya gane kuskurensa."
  " Abba baɗan gidan kowa bane face ɗan gidan matsiya tane." Anan Abba yai lallashinta da kuma faɗa mata cewa gobe zasu tafi asibiti a duba fuskar nan, Ammi ma ranta ya ɓace sosai, da ƙyar suka samu Amra tayi shiru, rakata ɗakinta Abba yayi domin ta kwanta daganan ya lulluɓeta da bargo, Amrat kwance tana sharar baccinta hankalinta kwance, sai da safe misalin ƙarfe takwas ta tashi, daga tashinta sai ta fara jin wani iri a jikinta kamar ba itaba, ta nufi wurin madubi kenan abinda tagani a jikinta yasa ta ƙwalla wata ƙara har saida su Ammi suka jiyo, daga ɗakinsu suka nufo ɗakinta da gudu,jikinta ne yakoma ko ina gashi baƙi ƙirin, nan take ta fara warware kanta, anan gashin kanta ya fara zubowa kamar ana ɓanɓararsa,  Ammi da Abba suna tura ƙofar ɗakin, ammi dagudu ta juya cikin tsoron yanayin data ga Amra a ciki domin ita batayi tsammanin Amra bace ta koma haka, Amrat ce a gaban madubi sai faman soshe soshe take ga jikinta ya canza gwanin ban tsoro, Abba tambayar Ammi yayi  lafiya, da ajiyar zuciya ta nuna masa ɗakin ya shiga ya gani,  Abba na shiga ya ganta gaba ɗaya halittar jikinta ta canza, kulle ƙofar ɗakin yayi da makulli ita kuwa Amrat kasancewarta ba cikin hayyacinta take ba bata masan abinda ke faruwa ba, Abba da Ammi sunyi mamakin faruwar wannan lamari domin basuda masaniya akan abinda ya janyo hakan, anan Abba yakira  likitansu a waya, ba a fi minti talatin ba saiga likita ya iso, buɗe masa ɗakin sukayi shi kuwa ya shiga. Amra na ganin likita ya shigo sai ta sheƙo da gudu ta ɓoye a bayan Abba  tana taɓa hular kanshi tana dariya.
       Likita na ganin haka sai yace wannan ba aikin shi bane saboda haka a kira malamai, anan Abba yace ba damuwa zasuyi hakan, likita na tafiyarsa sai Abba ya miƙe tsaye da zimmar fita ita kuwa Amra riƙe shi tayi gam, akan dole Abba ya zauna ita kuwa Amra sai hauka take tana zagayarshi, ita kuwa Ammi a firgice take ganin wannan lamari dake faruwa, haka Amra taci gaba da hauka sai da ƙyar da lallashi Abba ya samu tayi bacci, da yaga tayi nisa a baccin saiya zameta a hankali daga jikinsa daga nan ya mayar  da ita ɗakinta, datse ƙofar ɗakin yayi da makulli, yana isowa falon sai  ya tarar da Ammi nata rusa kuka, zaunawa yayi kusa da ita yana rarrashi harta ɗan safka, koda aka gama abinci kowa tsoron shiga ɗakin Amra yake, Abba ne da kanshi ya kai mata abincin ta da kanshi, zai fita kenan ta riƙe masa riga, kallonta Abba yayi ya tuna Amrat da take yarinya kyakkyawa ƴar ƙwalisa amma gashi ta koma haka, hawaye suka zubomai, nan dai ya fara bata abinci tana ci tana dariya, daya tabbatar ta ƙoshi sai ya fito ya kulle ɗakin. Abba neman malamai ya farayi ruwa a jallo ba dare ba rana, da yaji labarin malami sa ya tafi wurinsa amma abin yaci tura domin duk malamin da yazo sai yace bazai iyaba domin Baƙin Aljanine saboda haka yafi ƙarfinsa, ita kuwa Amrat  sai bunƙasa takeyi a cikin wannan yanayi na hauka, yanzu har takai  ko abinci bata iyaci sai ruwa shima dole sai an mata ɗure kamar jaririya.
      Amrat ce a ɗaki sai maganganun hauka take faɗa, shi kuwa Abba yazo zaishiga ɗakin yajiyota, cikin tausayi ya duƙufa yana kuka ƙamar ƙaramin yaro, shiga ɗakin Abba yayi domin ganin halin da take ciki ai kuwa yana shiga Amra ta shaƙe masa wuya, sa ar da aka samu Ammi na kusa, masu gadi Ammi ta kira sai da ƙyar suka ƙwaci Abba daga hannun Amra, tun daga wannan lokaci da wannan abu ya faru Abba ya daina shiga ɗakinta, abinci kuwa sai dai a tura mata a taga shi kenan, kamar yadda Hausawa ke cewa mai nema yana tare da samu to haka Abba yaci gaba da bin manyan malamai har ya dace wani abokinsa ya haɗashi da wani babban malami daga Maiduguri, Abba ne ya shirya komi game da yadda malamin zai iso a cikin jirgi daga Maiduguri zuwa Katsina, bayan malamin ya iso Katsina sai Abba ya tura direba ya taho dashi daga can Filin Jirgi, Abba da Ammi sunyi maraba da malamin.

Ba yadda basu yiba domin malam ya huta kafin ya fara aiki amma yace yafiso ya fara da yake tun tuni Abba ya labarta masa abinda ke faruwa a cikin waya, anan malam ya fara ruƙiya wanda hakan ya tabbatar masa cewa sheɗani ne a jikin Amrat, anan sheɗanin ya labartawa malam abinda ya faru da kuma jaddada cewa Amrat itace ta janyo ma kanta wannan ciyo, wannan tsohon da take gani kamar ta mari banza ashe ba banza ta mara ba, masifa ce ta janyo ma kanta, sai da ƙyar malam ya roƙi sa shi kuma yayi alƙawarin zai fita kuma bazai ƙara dawowa ba, atishawa Amrat tayi mai ƙarfi daganan ta dawo hayyacinta, Abba da Ammi sun yiwa Malam goma na arziƙi kuma a wannan ranar ya koma Maiduguri a cikin jirgi, ita kuwa Amrat bayan iyayenta sun faɗa mata abinda ya faru sai tayi dana sanin aika aikar da takeyi, anan ta bugama ƴan sanda su saki wannan saurayin da tasa aka kama, bako shakka Amra tayi dana sanin tuƙin ganganci da takeyi kuma tayi dana sanin rashin mutuncin da take wa mutane wanda shine ya jefata ga wannan masifa data tsinci kanta a ciki, daga wannan lokaci sai Amrat ta dawo yarinyar kirki mutane garin sai mamaki suke ganin sauyi daga wurinta su kuma iyayenta sai albarka suke saka mata, haka dai Amra da iyayenta suka cigaba da rayuwa cikin jin daɗi na har abada.
                                                           ALHAMDULILLAH
                  





















Post a Comment

0 Comments