*TUNATARWA TUNATARWA*
Shin ko kasan cewa kuɗinka da jama arka ba bazasu iya baka lafiya da farin ciki ba, idan ALLAH yaga dama sai ya baka kuɗin da jama a amma kuma a jarabtaka da rashin lafiya da kuma rashin farin ciki, idan lafiya kaɗai aka baka to ka godewa ALLAH, Ya ALLAHU kabamu lafiya da zama lafiya ka dauwamar damu a cikin farin ciki na har abada, Amin Amin
*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*TUNATARWA TUNATARWA*
Kace kai musulmi ne amma baka ɗaukar salla da muhimmanci
Kace kai musulmi ne amma kana zina
Kace kai musulmi ne amma kana kallon batsa
Kace kai musulmi ne amma kana munafunci
Kace kai musulmi ne amma kana fifita chatting akan karatun ƙur ani
Kace kai musulmi ne amma kana ƙarya
Kace kai musulmi ne amma baka ladabta iyayenka
Kace kai musulmi ne amma kana sata
Kace kai musulmi ne amma kana mu'amala da waƙe waƙe masu cunkaso da kaɗe kaɗe
Kace kai musulmi ne amma kana aikata abubuwa na haramun barkatai
Shin ko kasan ma anar kalmar musulunci kuwa?
Yaku ƴan uwa muji tsoron ALLAH mu gyara yanzun mu kafin rashin mu ya tunakaromu
Ya ALLAHU kasa mu dace dace, Amin Amin
*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
0 Comments