Assalamu Alaikum ma abota karatun Hausa nazo maku da wani littafi labarine ɗan kaɗan mai ma ana sosai inafatan kuna marahaba lale da labarina.
*SANDACE*
*Story and written by Dr Zarah Lg*
*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(Sarki da Sarauniya writers)*
https://facebook.com/groups/1756414801245712/
*Short story*
*TSOKACI*
*Dagudu tashiga dokar daji babu abinda take falfalawa saigudu saita nufi wani icce dogo babba taje tajingina dashi ta ba'ce bat'*
Yanacan yarude' Yana tunanin wace amsa zaiba iyayenta insun tambaye shi wane hali zaishiga insukaji abinda yafaru natahowa dayayi da ita hanyar daji . .......
WhatsApp number 09078772252/or call 09167352441
*Comment*
*WhatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/D6TzXYv1kSwF7EFMWwegqM
*SANDA Ce*
*Story and written by Dr zarah Lg*
*Short story*
🅿️1
*Sadaukarwa ga Abdul king article*
*KIND AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(Sarki da Sarauniya writers*
*We Rule the World of Writing*
https://www.facebook.com/profile.php?id=100063945240173
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ALLAH madau'kakin sarki🙏
Bismillah Rahmnani Rahim
A wani ɗan karamin kauye anyi wani mutum maisuna Alhaji Bashir mai kuɗi ne irin kuɗin kauye gashi da kirki ga kyauta gashi yasan darajar mutane saidai yana cikin damuwar data hana shi sukuni ta rashin haihuwa ,matarshi ɗaya Haulatu yana son sosai kuma be kara aure ba sunkai shekara 10 atare tun anamatsamai yakara aure yakidai' yar da har angaji ankyaleshi,"
Alhaji bash Yana cikin tafiya yarasa mike damunshi yarasa ina zaisa kanshi ,kawai saiyaga wani mutum yana neman sadaka take yanke yafiddo kuɗi yabashi yayi godiya yawuce,mutumin nan nata kallon shi har yayi nisa,"
Assalamu Alaikum , wa Alaikumu Salam ,sannu da zuwa maigida yawwa Haulatu miyesa wai bazai bar tunanin nanba daga ganin idonki kinyi kuka kuma naga yamaki komai lokacine Arayuwa kikara hakuri Ubangijinmu nasane damu,badamuwa maigida,sai ga wani yaro yayi sallama yace? anakiran Alhaji yace? gashinan,
Dasauri yafita saiyaga wani tsoho atsaye jikinshi duk gashi buzu buzu cikin girmamawa yace baba gani amma yafara firgita dashi ,Ni bawan ALLAH ne Alhaji nasan bakasanniba inaso nataimakane nasan halin da kake ciki amma inaso nayi magana da matar ka dakai gabaki ɗaya yace yabashi yan' mintina bari yashiga yafada'mata yasanar da ita , yazo yashiga dashi yazaunar dasu yace shizai basu wani taimako insun amince mijin yaso yaƙi itakau duk tarude' haka kau akayi yafadi' masu yace subude' wani da'ki da basu amfani dashi sukabashi yafiddo wata sanda da duka tarazanasu ya ajeta ada'kin yace ?akulleshi sufita haka kau akayi,ya gindiyamasu sharuda' yatafiyarshi,'
Yau kwanaki sunja saikawai tazo zata wuce ta hanyar ɗakin taji kukan jariri da gudu taje tasanarma mujin yace tazo subude' sushiga anatafiya yana gaba tana baya harsuka isa da'kin sukabude' abinda taganine yasa ta gigice jaririya akwance cikin jini, taka sa ɗaukar ta mijin yace sudau'ka kowa da silar da abu zaikasance agareshi tamata wanka aka gyara ta yakira yan' uwanshi dayake Baga rinsu ɗaya ba kuma ita bayawan zuwa takeba saboda basu sonta waijuyace ,sunata mamaki wannan wane irin cikine saiwasu suce ikon ALLAH nan akazo akafara zaman Barka cikin walwala saboda daman rashin haihuwarne basu sonta kawai ,"
Yau ranar suna akasama yarinya suna shafa atu sunan kakarta za adunga cemata Yar' gata ,aiko haka akayi har mewankan jego yaɗauko.mata yana ganin kamarma dakanta tahaihu",
Akwana atashi yarinya tafara tasawa har ansata makaranta tafara zuwa yar'gatace sosai ko a school ba abugunta ga yarinyar akwai biyayya da hakuri da sanin Yakamata,"
Akullum sonta karuwa yake agaresu basu da abinda yawuce su sanyata farin ciki suga dariyarta,"
Yau Yar' gata takai shekara 18gata kyaukyauwa ajin farko ga masoya saikawo mata hari sukeyi uban na hanawa saidai wani saurayi daya like yaƙi rabuwa da ita nandai har mahaifin yabarshi sukasaba kamar ɗan gida kusan koda yaushe sunatare,"
Ayaune farin ciki tagama school ansha fidima sosai ankashi kuɗi yanzu takara zama budurwa sosai,"
Sabir nakara shigema yar'gata da soyayyarshi sosai har yake cemata zataje tagaida iyayenshi nan tafada'ma Mamanta ta Amince akan gobe zasu tafi ,........
To ma abota karatun littattafai na inakara mika' gaisuwa agareku sosai ina godiya ALLAH yabar tare🙏
WhatsApp number
09078772252/Call 09167352441
*Comment And share please*
*SANDACE*
*Story and written by Dr zarah Lg*
*Short story*
*Last*🅿️
*KIND AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(Saurki da Sarauniya writers*
*We Rule the World of writing*
https://www.facebook.com/profile.php?id=100063945240173
Sabiru yashirya tsaf yazo yace mata? sutafi,takauyi bankwana da Mamanta tama ta nasiha suka tafi , suna tafiya suna Labari nan hartakecemai tanaso yakaita gona?ba'ta taɓa zuwaba Abbanta yaki kaita yace kibari mudawo tukunnan?to badamuwa,"
Sun iso gidansu sabiru angirmamata sosai ambata kulawa amma ta kyaututtuka sosai suka fito suka taho akan zasuje yanunamata gonaki suna fara shiga cikin gona tafarko idonta yacanza Launi taji wani abu mara daɗi ajikinta tace mai sukoma yace bakince zaki ga gona ba yaƙi suka shiga ciki sosai suna shiga yaga takama nan nade' zani yace matar tawa yanzu Yar' guduce batakalleshiba balle ansa, yaga ta falfala da gudun indama yakasa gane hangota yanata kiran sunanta ina har taɓa cemai saikawai yaji wani iska yafisgeshi yana buɗe idonshi yaganshi agabanta yana tabata hakuri kallonshi kawai take tana matsema icce nan ta ɓace bat', yashiga ruda'ni mezaije yasanarma iyayenta ?
Sabiru ya iso gidansu jiki asanyaye yashiga direct Daman yakoma dan' gida suna tambayarshi tana ina saibinsu yake da kallo yazauna yazayyanamasu labari tas take Mama tasuma Abba ya watsamata ruwa ta farfaɗo, sun shiga tashin hankali a ranar sosai sukayi sallama da sabiru yatafi Mama tashiga halin rashin Yar' gata amma dayake masu danganane saisuka manta dakomai yawuce yazama tarihi daman ance kar abarta taje wurin icce ko ya yake gashi sunrasata,"
Mama da Abba sundawo normal soyayyar su kamar sabuwa ana cikin hakane watarana mama tace ma Abba cikin ta naciwo yakaita asibiti suna zuwa akasanar dashi yayi farin ciki sosai haka itama tayi godiya ga ALLAH sosai dayayi mata Wannan baiwar.... .
To masu sauraro wannan ka'geggen Labari ne ,narubuta wannan labarine dan mutane masu ganin ALLAH baibasu haihuwa ba su rude' kosu shiga wani hali , karkudamu komai lokacine Ubangijinmu nasane damu A kodayaushe saidai ƙaddarar mutum duk yarda tazo ya gaggawar riketa hannu bibbiyu bawa bai gama ganin ƙaddarar harsai ranar daya mutu ALLAH yasa mudace🙏
WhatsApp number 09078772252/call09167352441
*Comment and share*
0 Comments