UWATACE SANADI





UWATA CE SANADI


       ©Maimunah Tijjani Iyam




Bismillahir rahmanir rahim ina Mai farawa da sunan Allah mahaliccina Wanda cikin ikonsa,amincewar sa,yardar sa tare da Aron numfashin daya bani na rubuta wannan littafin nawa UWATACE SANADI.ya Allah ka tsare min hannaye na wajen rubuta abin da zai zama cutarwa ga al'umman musulmai tare da tarbiyarsu.

              GARGAƊI
Ban yadda wani ko wata suyi ƙoƙarin sauyamin littafi ba,ba tare da iznina ba Duk Wanda yayi ƙoƙarin aikata hakan ALLAH YA ISA BAN YAFE MASA BA.


UWATACE SANADI

            Tsarawa/Rubutawa

           ©Maimunah Tijjani Iyam

______________________________

Page 0⃣1⃣


Littafin ƙaddarar rayuwa ta cike yake da babi-babi na ƙuncin dana taso,na tsinci kaina a cikin tun kafin nasan kaina.
Kamar yanda jini yake yawo cikin duk wata sassan jikin ɗan adam misalin yanda ƙunci yayi kane-kane cikin rayuwa ta.
Kowani ɗa yafi kusanci da mahaifiyar sa saɓani nida ta wa uwar take ƙoƙarin nisan ta kanta dani,rashin dace da samun nagartacciyar uwa shi yaja ragamar rayuwa ta izuwa ga ƙunci da baƙin ciki. 
Bansa menene farin-ciki ba,bansan ya ake yinsa ba,bansan inda ake samun sa ba,wasu lokutan nakan zauna nayi kuka da hawaye anya akwai mai irin ƙaddara ta kuwa?.


Tabbas kowani bawa da irin tashi salon ƙaddarar da kuma yanda take zuwa masa amma tawa ta fita daban.
Suna na Hibba labarin rayuwata Mai matuƙar girgizarwa ne,firgitarwa,gami da kiɗimarwa.
Duk wata zuciyar da Allah ya dasa imani acikin ta sai ta raunana domin jin labarina,yayin da idanuwa da yawa zasu zubda hawaye yayin da suka saurari labarin rayuwata.
Nice ɗiya ta farko a wajen mahaifina ta bangaren mahaifiyata kuwa ta kasance, ta taɓa aure kafin mahaifina ɗanta ɗaya da tsohon mijin nata YAYA FAWAS,amma duk tare muke zaune dashi.
Mahaifiyarmu haj.Juwahir ba inda munanan halayyarta basu jeba kowa ya shaideta da rashin ta ido wato kunya,ta bangaren Abbana kuwa juya shi takeyi son ranta kasancewar ta fishi abin duniya.
Duk dawainiyar gidanmu ita takeyi,Abu daya daya ke rushe mata wannan aikin alkhairin shine gori domin ko ruwa. 
Ta saya a gidan nan sai ta wuni tana yiwa Abba gori,ta gaza fahimtar nauyin igiyoyin aurensa uku dake kanta, ta wofantar da nauyin tarbiyanmu dake kanta ta zaɓi duniya sama da inganta lahilarta.
Yanda ake dama koko a cikin kowani gida na kirki haka Umman mu ke dama giya a tsakar gidanmu wai da sunan Sana'a.
Safiya ce datake cike da sanya nishaɗi yayin da faffaɗan bishiyar tsamiyar dake dashe,a madaidaicin filin tsakar gidan mu ke kaɗa iska ko'ina.Yanayi ne mai tafiyar da zuciya kasancewar daren jiya kwana akayi ana zabga ruwa,hakan ya sanya garin ƙara sanyaya.
 Zaune nake a madaidaicin ɗakin yake mallaki na,katifa ce wacce take yashe a ƙasa sai kuma bahon kaya daga can gefe guda su kenan a cikin ɗakin.
Shirin tafiya makaranta nakeyi ina saka safa yaya Fawas ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, da fara'a a saman fuskata nake amsa sallamar.A gefena ya zauna tare da karɓan safan dake hannuna ya fara ƙoƙarin sanin yana cewa.

"My cute angle har yanzu baki gama shiryawa ba ko so kike muyi latti?".

Cikin murmushi nace"A'a yayaa Fawas ai nakusa gamawa ma fa ka shigo".

"Ba wani kin kusa gamawa bayan kullum sai nazo na taya ki shiryawan".
Yana gama sanin safan ya riƙo hannuna muka fito,A kwance akan tabarma muka hango Umman mu ta lumshe idanunta kamar mai bacci, a hankali muka ƙariso inda take cikin ƙasa-ƙasa da murya yaya Fawas ya kamo kunne na yana cewa,

"Ƙanwata mu tashe tane ko kuma mu tafi?".


Nace "yaya Fawas inmuka tashe ta faɗa zata mana gwara mu tafi kawai".

"To".


Kawai yaya Fawas yace tare da ƙara riƙo hannu na muka dauƙi hanyar fita daga gidan.
Kamar daga sama muka ji muryan Umma ta daka mana tsawa a firgice dukkaninmu muka juyo yayin,da lokacin ɗaya jikinmu ya ɗauki rawa bansan sanda nasaki wani razanannan ƙara ba saboda duk na tsorita inda abin dayake saurin gigitani to tsawa ne.
Kamoni yaya Fawas yayi sosai cikin zubda ƙwalla yace "kin nutsu ƙanwata kinji".
Cikin wani tsawan umma ta cigaba da magana tana cewa,"Munafukan banza ina da kuke shirin tafiya yan iska jarababbu salon kujawa mutum abin magana a gun wannan sakaran uban naki ko?".
Cikin raunanniyar murya yaya Fawas ya shiga faɗin "Umma dama munga kina bacci ne kuma bamason mu tashe k......"

Wani tsawan ta kuma dakawa yaya Fawas Wanda yasa shi yayi shiru ba tare da ya ƙarisa maganar da yakeyi ba.
Cikin zafin rai Umma take maganan tamkar zata kaiwa ya Fawas duka take cewa"Dalla rufe min baki munafikin banza, Ku wuce kuje Ku ɗauko abinci kuci kafin Ku tafi".

A hankali na wuce kitchen naje na ɗauko mana abincin, hawaye tunin ya fara wanke min fuska muka fara cin abincin.
Ai kuwa kamar jira Umma takeyi mu fara cin abincin.Muna kai spoon ɗin farko ta fara zazzaga mana gori.Wani dariyar ƙeta tayi sosai har sai da idanunta suka kawo ƙwalle kafin tace,"Uhm abin da kuka iya kenan daga Ku har lusarin uban naki shine ci kudai sai dai infita innemo muku,in dafa,in baku Ku zauna Ku hau ci ko? daman shine aikin.ba komai ai Allah yana ganin duk abin da sule yakemin a cikin gidan nan duk ɗawainiyar gidan nan ya gibge shi a kaina tsabaragen lusaranci irin nasa".


Sai data numfasa sannan ta cigaba da faɗin"Bashi da aikin sai yawo a cikin unguwa daga wannan masallacin sai wancen".
Da  hawaye fal a idona na takaicin furcin Umma na miƙe daga cin abincin cafko hannuna yaya Fawas yayi shima idonsa cike da hawaye yace"A'a ƙanwata ki zauna mugama cin abincin kar ki ja  mana wani abin maganan".
Tabbas akwai wata irin so da shaƙuwa tsakani na da yaya Fawas,a lokuta da dama nakan mance dacewa ba mahaifinmu ɗaya da shi domin ko Kaɗan Abba baya nuna bambamci a tsakaninmu.

A hankali na dawo na zauna tare da ɗaura kaina akan cinyar yaya fawas ina kuka.Mukam wacce iriyar uwa Allah ya bamu,kullum tinani na shine wani irin laifi muka aikatawa umma datake nuna mana wannan zallar kiyayya tamkar ba ita ta haife muba.


Shafa kaina yaya Fawas yayi cikin Ƙarfi hali yace"Ya isa haka Hibba ki tashi mu tafi kinga ma munyi latti".


Tashi nayi na fara tattare kwanukan abincin na kai kitchen.Umma nake kallo yayin da ita kam ma hankalinta ba'a kanmu yake ba sai al'amuran gabanta takeyi.
Wasu hawaye ne naji sun shiga ambaliya a fuska na wato ita kukan damukeyi ma bai  dameta ba,.kitchen na shiga domin ajiye kwanukan daidai lokacin daxan fito daga kitchen din najiyo muryan yaya Fawas yana cewa."Umma xamu tafi".


Cikin ɗaga murya Umma tace" to Fawas Dan zaku tafi me kakeson namuku kenan?na goya Ku nakai Ku makarantar ko kuma yaya kake son na muku?".


Cikin sanyin murya yaya Fawas yace" A'a Umma dama kuɗin nafef zaki bamu kinga munyi latti".

Harara Umma ta watsa masa sannan tace" nizan baku kuɗin nafef ɗin? Ai da niyyar ficewa kukayi daga gidan ba tare dakun sanar dani ba indai sai nabaku kuɗin nafef sai dai, Ku fasa zuwa makarantar ai dama ba dole bane".


Tana kawowa nan ta cigaba da abinda ke gabanta.Fitowa nayi daga kitchen ɗin na nufi inda yaya Fawas ke tsaye riƙo hannun shi nayi ina cewa"Yaya na mu tafi kar muyi latti".

Durƙusawa yaya Fawas yayi tare da ƙara riƙo hannu na dukka biyu hawaye nabin fuskar sa yake cewa"Hibba ko zamu haƙura yau da zuwa makarantar,kinsan da nisa in mukace zamuje da ƙafa bazamu isa akan lokaci ba,gashi kuma Abba baya nan balle inyana dashi ya bamu".

Wani marayan murmushi nasaka Wanda iyaka cinsa fuska dan baikai har ga zuci ba kafin nayi ƙarfin halin furta.


"A'a yaya Fawas muje kawai".


Shima murmushin ya saka yana cewa" Ƙanwata mu tafi da ƙafa bazaki gaji ba?".kaina na ɗaga masa alamarar e.


Share hawaye fuskan shi yayi tare da riƙo hannu na muka tafi.A hankali muke tafiyar kamar babu laka a jikin mu,tunda muka fito daga gidan cikinmu ba Wanda yayi magana. 
Kowa da abinda yake tinani acikin ransa.Muna cikin tafiya muka hangi Abba zaune a bakin wani masallaci,ya zabga tagumi hannu bibiyu.


Hannunsa riƙe da carbi yana tasbihi amma kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar wa kanka,cewa hankalinsa ba akan tasbihin daya ke yi yake ba.


Ina hango Abba  nasaki wani nauyayyan ajiyan zuciya nasan wahalar mu ta ƙare matuƙar yana da kuɗi zai bamu.
Mu ƙarisa makarantar ƙafafuna har jinsu nakeyi tamkar ba'a,jiki na suke ba dan tsabar gajiya kawai,daurewa nake har ya fawas ya gane hakan.
Da sallama muka iso inda Abba ke zaune,a hankali ya ɗago kansa daga tagumin da yayi yana binmu da kallo yace"Hibba Fawas me kuke yi har yanxu Baku tafi makarantar ba?".
Tunin idanuna sun kawo ruwan ƙwalla nace "Abba wallahi Umma ce tace bazata bamu kuɗin abin hawa ba wai sai dai mu tafi da ƙafa,Ko kuma mu fasa zuwa makarantar".
"inna lillahi wa inna ilaihir raji'un!wannan wani irin rashin tausayi ne haka,tun daga nan zaku tafi har makarantar kuma da ƙafa?".
Jijjiga kansa yayi tare da ciro naira ɗari biyu daga aljihunsa,ya miƙawa yaya Fawas tare da faɗin"Ga wannan Fawas ko hau nafef,Ku tafi makarantar".Karɓa yaya Fawas yayi tare da yi masa godiya sannan muka tafi.




UWATACE SANADI


     Tsarawa/rubutawa


 ©Maimunah Tijjani Iyam


__________________________ 

Free page



Page 0⃣2⃣


Asalinmu

A jahar yobe muke da zama ƙaramar hukumar potiskum, unguwar tandari.

Asalin sunana Fatima naci sunan kakata ta wajen abba shiyasa Abba yake ƙirana da Ummul-khair.

Abba Dan asalin kano ne cikin ƙauyen gano, kasuwanci ya kawo shi potiskum.A lokacin ya mallaki komai najin daɗin rayuwa kafin Allah ya jarabce shi da karayan arziki,auren soyayya sukayi da Umma amma tun daga lokacin da karayan arziki ya sameshi komai ya canza na daga zaman dasuke yi.


Anan garin potiskum suka haɗu da Umma lokacin ta fito daga gidan mahaifin yaya fawas.A wajen kakarta take saboda iyayenta sun daɗe da rasuwa,bayan wani ɗan lokaci ma Allah yayiwa kakarta ta rasuwa.

A haka Abba ya aure ta ya kuma riƙe  yaya fawas tamkar ɗan daya haifa.

Abba baya wasa akan duk wani lamarin daya  shafi harkan karatunmu tun muna nursery school suke private school har kawo yanzu,duk da halin dayake ciki na babu bai taɓa gajiyawa,ba ko nuna gazawa wajen biya mana kuɗin makaranta ba.

Burinsa ɗaya ne a duniya shine muyi karatu ta yanda zamu tsaya Da ƙafafunmu ko bayan bashi.Ina jss 3 ya Fawas yana ss 2 a unity model school dake nan cikin potiskum.


Yau kam idan nace na gane abinda aka mana a makaranta to nayi ƙarya,dan tun da muka isa hankali yake ga tinani,har aka tashi muka dawo.


Tun daga nesa muke hangi mutane keta shige da fice a gidanmu,wani baƙin ciki ne naji ya tsaya min a raina dana tino mummunar sana'ar Umma na sayar da abinda da Allah ya haramta.

Manyan mutane,yan siyasa da ma'abota dukiya suke siyan giyan da umma keyi da sunan Sana'a.

Da sallama muka shiga cikin gidan amma ba,Wanda ya kula da shigowarmu cikin gidan balle musa rai ga za'a  amsa sallamar da muka shigo da ita.Gidan cike yake da mata da maza, karuwai da kuma ƴan daudu kowa abin da ke gabansa shi yakeyi.


Ga wani mummunar shigar da matan sukayi,Umma na zaune a kan garduma tare da wasu mutane biyar uku maza biyu mata.Suna buga caca riƙo hannuna yaya Fawas yayi sosa tare da rufe min idona da tafukan hannunsa wai dan kar na kalli abin da Umma keyi.


Muka wuce muka shiga ɗaki yaya Fawas yace."Kiyi wanka kihuta kafin lokacin islamiya yayi kinji ƙanwata "



"To yaya Fawas".

Fita yayi ya nufi daƙinsa,wanka nayi sannan nayi salla na kwanta ina kwanciya yaya Fawas ya shigo.


A gefena ya zauna yana cewa" Hibba kinci abinci kuwa?".


"A'a yaya Fawas kaima ai nasan baka Ciba"na faɗa ina tsaida idanuna akan fuskar shi.

Ajiyan numfashi yasaka kafin yace,"Hibba inason muyi wani magana dake".

Gyara zamana nayi ina cewa" to yayana inajinka".

Cigaba da magana yayi yana cewa "ƙanwata kinga irin rayuwar da mahaifiyar mu ta zabawa kanta ko?" jinjina kaina nayi alamar ina fahimtar maganan tasa,sannan ya ɗaura da faɗin.



 "To Hibba banason koda wasa ne koda ace ni da Abba bamu numfashi cikin duniya,wataran kiyi sha'awar irin rayuwar da kikaga umma nayi,my cute angle kinga ke macece".

Cikin nutsuwa nace" In sha Allah yaya Fawas zan nisanta kaina daga dukkanin ɗabi'un da umma take aikatawa.Amma abinda yake damuna shine in har tasan baza ta so mu ba to  meyasa ta haifemu?".

Gyaran murya yaya Fawas yayi kafin yace "Hibba Umma tafi karfin musata acikin jerin maƙiyanmu,ita tayi silar zuwanmu duniya ta nuna mana dukkanin ƙauna tinda har ta haifemu kuma bana son na ƙarajin,ki furta cewa Umma bata son mu kinji my cute angle?".

" To ya Fawas in sha Allahu bazan ƙara ba".


Shafo kaina yayi yana cewa" yauwa my cute angle nizan tafi shago in lokacin islamiya yayi ki shirya ki tafi kinji ko".


Turo baki nayi kana nace" yaya Fawas ban iya hadda ba bazan jeba".


Murmushi yayi Wanda sa ka fararen jerarrun hakwaran sa suka bayyana, yaya Fawas badai kyau ba dan mahaifinsa buzu ne ɗan nijar. 

"To shikenan amma in Abba ya dawo yasame ki a gida ba ruwa na" yana gama faɗin haka ya fice.

Kallo nabishi dashi yayin da take ficewa daga daƙin,ina ƙara jinjina irin shaƙuwar dake tsakaninmu da yaya Fawas komawa nayi kwanciyata.

Sai dab da magriba sannan na tashi nan  naji gidan gaba ɗaya yaɗau kiɗa ta ko'ina sauti ne kawa ke tashi.

A hankali na buɗe ƙofan ɗakin na fito wajen,dan gane ma idano na meyake faruwa.Maza da mata ne sun haɗe sai tiƙar rawa suke babu ko kunya,gefe guda  masu shan taba sunayi,masu sha wiwi sunayi,mai shan shishi nayi.
Can gefe kuwa masu caca ne suma sun haɗa nasu daban sunayi.


Umma kuwa tana ta dama giyarta ga masu saya sun mata cirko-cirko akanta,sai sauri take taga ta sallame su lokaci ɗaya muka haɗa ido da ita.
Sauri nayi na kawar da kaina gefe tare da share hawayen dake shirin zubowa daga idona.



 "Yauwa Hibba zo ki sallame waɗannan".

Tunin ƙwalla suka fara bin fuskata nace"Umma alwala zanyi fa an ƙira salla".

Ashar Umma ta shiga ɗuramin masu nauyin maimaitawa sannan tacigaba da cewa"Ƴar iska Mai halin ubanta ni zaki cewa salla? zakiyi ko muɗin ce miki akayi bama sallan,zaki yi gadon tsiya matuƙar kikace zaki gado halin ubanki wuce ki bani waje shashasha".

A hankali nake daga ƙafata na wuce naje nayi alwala sannan na koma daƙi nayi salla.

Ina iddarwa na kwanta akan sallayar wani azababban yunwa nakeji har sai da naji kamar zazzabi yana neman rufe ni,lokaci ɗaya jikina yaɗau rawa tashi nayi nashiga banɗaki nayi wanka sannan na dawo kan sallayata na,kwanta bansan sanda wani baccin wahala ya ɗauke ni ba.

Sai bayan sallan isha'i sannan Abba da yaya Fawas suka shigo kamar night club haka gidanmu yake a kowani dare,suna shigowa suka hango Umma ta zage sai buga caca yakeyi,ga wani sautin daya ke tashi cikin ko wata kusurwa acikin gidan.

Kai tsaye Abba ya nufi inda Umma take yace."Juwahir taso innason magana dake".

Ko ɗago kai batayi ta kalle shi ba balle tasan da mutum awajen ta cigaba da cacan ta.


Cikin zafin rai Abba ya sake magana a karo na biyu" Juwahir wai ba magana nake miki bane".

A harsale Umma ta juyo tana cewa,"Haba!sule wai ya kake son nayi da rai nane kazo ka tarar dani ina Abu to  ba sai kayi wucewar ka ba".

Ɗaga hannu Abba yayi da nufin zabga mata mari,cikin sauri yaya Fawas ya riƙe hannun Abba cikin muryar kuka yace."Dan Allah Abba kayi haƙuri taci alfarma mu".


Cike da takaicin daya gama cika Abba yace,"Juwahir Allah ya shiryeki" sannan ya wuce daƙin sa.

Yaya Fawas ya shigo daƙi na kwance akan sallaya ya tarar dani a hankali ya zauna gefe na,mafici ya ɗauko ya fara min fifita gani yanda naketa haɗa gumi.


Wani wahalallan ajiyan zuciya na saka lokacin,dana ji iskan na ratsani hijabin dake kaina ya fara ƙoƙarin ciremin.

A hankali nafara buɗe idona ganin yaya awas ne yasa na fara,sakin murmushi yayin da nake ƙoƙarin tashi.


Da fara'ar sa yace "my cute angle yunwa ce tasaki baccin nan ko?".



UWATACE SANADI


        Tsarawa/rubutawa

     ©Maimunah Tijjani Iyam

________________________________________


Free page


Page 0⃣3⃣


Sunkuyar da kaina ƙasa nayi ina cewa"A'a yaya Fawas naci abinci".

Ɗago kaina yayi yana cewa,"Hibba ko wani motsi kikayi nasan me hakan yake nufi baki ci abinci ba ko ƙanwata?".

 A hankali nace" e ya Fawas ban Ciba".


Wata Leda ya miƙo min wacce ya shigo da ita yace."Gashi kici Abba ne ya taho mana dashi".

Jawo ledan nayi gaba na na buɗe ƙosai ne a ciki Wanda baifi guda bakwai ba,tunin na fara hawaye na buɗe baki zanyi magana kenan yaya Fawas ya dakatar dani ta hanyar cewa.

"Nasan bazai ishemu ba kici ke ɗaya kinji my cute angle".

Bai jira amsar dazan bashi ba ya fice daga daƙin.

Inaci ina hawaye haka har na gama na tashi naje nayi alwala sannan nazo nayi sallar isha'i,ina iddarwa yaya Fawas ya shigo yace Abba na ƙira na.


Cikin sauri na miƙe nabi bayansa muka nufi daƙin Abba.Yana zaune akan sallaya muka sameshi wuri muka nema muka zauna,gyaran murya Abba yayi kafin yace "Ummul-khair da Fawas".

Cikin nutsuwa dukkaninmu muka amsa sannan ya cigaba da maganar.

"Kunsan halin da muke ciki a wannan gidan abinda yake damuna yanda ƙiyayyar da juwahir kemin har ya shafeku,amma bana son kusa wannan damuwar a ranku har akai ga wataran kun ɓata mata rai,a cikin ko wani yanayi kar Ku na mantawa da cewa ita ce silar ku nazuwa duniya babu abinda zaku yi mata Wanda zai biyata wahalar nishin naƙudar ku datayi.Tsakanin Ku da ita sai addu'a Allah ya shirya mana ita".


"Amin "duk kaninmu muka amsa dashi.

Nasiha Abba yake mana sosai akan irin girman hakkin da umma take dashi akanmu.


Muna cikin haka umma ta bankaɗo labulen daƙin tare da shigowa daƙin tsaki ta saka kafin tace.


"Haka dai ka iya sule baka da aikin yj sai  dai ka tara yaran nan kana tusa musu ƙiyayya ta a cikin ransu.Wa kai a hakan kafi kowa son su bayan ba ɗaya daga cikin ɗawainiyar, su Wanda kakeyi sule kai kam ka tsoraci ranan da Allah zai tambaye ka irin kulawar daka bawa iyalinka".


A hankali Abba yace" ummul-khair da fawas Ku tashi kuje Ku kwanta".


Duk jikin mu yayi sanyi  muka tashi muka fita bayan munyi wa Abba sai da safe.


Miƙewa Abba yayi tare da faɗin"Juwahir nagaji da abinda kike min a cikin gidan nan,daga rana mai kaman ta yau indai na amsa sunana na matsayin miji a gareki to kin daina wannan sana'ar,sannan kuma bazaki ƙara taramin maza a gida na ba".


Wani shewa umma ta saka kafin tace"Sule gidanka ko gidana? kai ko kunyar faɗa bakayi ba?kuɗin hayan dani nake biyansa".


Cike da takaici Abba yake faɗin "juwahir ni kike gaya haka koda yake bazan yi mamaki ba domin Ku mata kunada saurin manta alkhairi,kin manta lokacin dana auro ki duk da kasancewar dangi na basuyi na'am dake ba juwa".


Cikin matuƙar ɗaga murya wanda ya zamto ɗabi'ar ta,a duk sa'in daza tayi magana tace.

"Na faɗa ma sule nace na faɗa ɗin yo sule da miji irinka a gwara babu,idan ka cika dan halak a cikin iyayenka ka ficemin daga gidana sai sanda ka sama zuciyar neman na kanka sa ka dawo,mu cigaba da zaman yanzu kai idan za'a lissafo maza za'a saka a cikine sule".


Kallon ta kawai Abba yakeyi yama rasa me zaice mata a hankali yace.

"Juwahir duniya ce ta tafi gabaruwa iya jima kije kiyi inkina ganin zai haifar miki da ɗa mai ido".


Ficewa yayi daga daƙin ya shigo daƙin yaya fawas har yayi bacci ya same shi,juyowa yayi ya shigo daƙina inajin shigowar sa amma na rufe idona kamar bai bacci dan duk abinda yake faruwa inajinsu.


Zama  yayi gefen lamutsatstsiyar katifa ta kallona yake yi sosai yana shafa kaina yana hawaye yace.


"Mama na Allah ya muku albarka keda ɗan-uwanki inason kasancewa tare daku amma dole zan barku".

Addu'o'i yashiga min yashafa min sannan ya fice daga daƙin.

A hankali nabi bayansa da kallo ina ƙoƙarin fahimtar inda maganganunsa suka dosa,umma na tsaye a ƙofar daƙin ta lokacin da Abba ya fito daga daƙina.


Yatsina fuska tayi kana tace "Dan Allah sule inka tafi karka dawo har anaɗe duniya,inka tafi ma ai ni wahala ka ragemin umma ta gaida aisha a sauƙa tsiya lafiya".


Ficewarsa yayi ba tare da ya kalli ko inda take ba,tsaki tasaka tare da komawarta daƙi.


Tsawon Daren wannan ranan ban runtsa ba kamar yanda ban iya,tsayar da ruwa hawayen da ido ke tsiyarwa ba. 

Washe gari da wuri muka yi shirin tafiya makaranta, umma na zaune a ƙofar daƙin ta muka fito as usual tare da yaya fawas hannunmu saƙale cikin na juna.


Durƙusawa muka yi muka gaishe ta amma ko ɗago kai batayi,ta ganmu ba balle tasan da mutum awajen.


Miƙewa nayi na ɗauko mana abincin mu a kitchen cikin sauri mukayi muka gama ci.



"Yaya fawas yau tinda na tashi banga abba".


"Haka ne nima naje daƙin sa da asuba mu tafi masallaci amma da mamakina sai ban ganshi ba,amma karki damu my cute angle akwai kuɗi a wajena sai muyi amfani dashi mu tafi makarantar".


"To yaya na" na faɗa tare da sakin murmushi.


Sallama mukayi a umma muka tafi ƙarfe uku saura muka iso gida bamu sama umma a gida ba amma gidan a buɗe muka same shi.

Cire uniform ɗina nayi, nayi wanka nayi salla sannan na shirya cikin uniform ɗin islamiya na fito.

Ina fitowa ma yaya fawas ya fito zai tafi shagon da yake zuwa koyan ɗinki,murmushi na jefa masa cike zolaya ina faɗin.


"Allah my yaya irin kyau haka anya ka duba madubi kuwa kaga irin kyan da kayi?".

Na ƙarishe maganar tare da kashe masa ido ɗaya.

Matsuwa yayi ya shafo ƙuncina  tare da faɗin.

"Haba!hibba ta kyau ya wuce wanda kikayi a yanzu na tabbatar ko gasar kyau kikaje,a haka babu abinda dazai hanaki ki cinye gasar".

Turo baki nayi tare da kai masa dukan wasa a kafaɗunsa nace.

 "A hakanne zanci gasar kyau yaya fawas?".


Na ƙarishe maganar ina duban uniform ɗin jiki na da har canza launi,suka yi daga ainihin kalar su saboda tsabar tsofan dasukayi.

Ganin yanayi na daya sauya yasa yaya fawas cewa "Sosai ma kuwa ƙanwata".


Dariya mukayi sosai kafin muka fito a tare sa daya rakani,har islamiyar sanna ya wuce  shagonsu.

ƙarfe Biyar muka tashi daga islamiya sanda na iso gida har izuwa lokacin umma bata dawo ba,uniform ɗina nacire nayi wanka sannan na fito.


Na fito na shiga kitchen na fara dube-dube kozan sama abinda zanci amma babu komai a ciki,fitowa nayi na nufi daƙin umma amma  ƙofar daƙin a rufe yake.


Wani nauyayyan ajiyan zuciya na saka na fito ƙofar gida ina jiran dawowar Abba da yaya fawas.


Can na hango ya fawas cikin sauri na isa gareshi tare da karɓan ledan dake hannun sa, cikin sakin fuska yace.


"Ƙanwata umma bata dawo bane naganki a waje?".


Ya tsina fuska nayi nace" e ya fawas bata dawo ba,Abba ma kuma mai dawo ba".


Kallo ni yayi yana murmushi ya riƙo hannuna  kafin ya shiga faɗin.


 "Karki damu zasu,dawo ai dare ma baiyi ko ummul-khair ɗin abban ta".


Murmushi nasaka ina sunkuyar da kai na ƙasa daya kira ni da yayi da  ummul-khair sai naji kamar Abba ne,domin shi kaɗai ne ke ƙira na da wannan sunan.


Da haka muka ƙarisa cikin gidan tabarma na ɗauko na shimfiɗa mana,sannan na shiga kitchen na ɗauko Kofi na juye kunnun da yaya fawas ya taho mana dashi.


Sannan muka fara sha muna hira,muna zaune umma ta shigo tamkar bataga ƴan Adam awajen ba tasa kai zata shiga daƙinta.


Yaya fawas ne yayi saurin cewa" umma sannu da dawowa".


A hankali ta juyo tare da ƙare mana kallo sannan tace.


"Yauwa fawas sannun ku har ka dawo daga, shagon kenan?".


Cikin jin daɗin yanda umma take masa magana yace"E wallahi umma yau da wuri na dawo".

Nima da fara'ata nake faɗin"Umma tun ɗazu da muka dawo daga makaranta muka samu bakyanan".

Cikin sakin fuska tace "wallahi na fita wata unguwa ne hibba ya makarantar taku?".


Cikin nishaɗi na amsa mata da  alhamdulillah umma.


"Yauwa maman abbanta Allah ya taimaka" dukkaninmu muka amsa da amin.


Tashi tayi zata shiga ɗakinta cikin sauri, maganar da yaya fawas ya fara ne yasata juyowa.

"Umma wai yau ina Abba yaje ne tun safe baya gidan nan?".

Kamar bazata amsa ba sai data jima a tsaye kafinta dawo ta zauna tare da faɗin.


"Amma fawas ai kasan gidan nan bana sabane ko?".

A  hankali yaya fawas daya jinin jikinsa ya amsa da cewa.


"Kiyi haƙuri umma nasan,da haka dama kawai na tambaya ne naga tun safe baya nan".


Sai data turo ɗaurin ɗan kwallin ta irin ɗaurin da akewa laƙabi da ture kaga tsiya,izuwa gaban goshin ta wanda in tayi hakan ƴan daudun ta da sauran tarin,matan datayi silar rabasu da gidan iyayen su.

Suke mata kirari da"Magajiya kinci dubu sai ceto,kinfi ƙarfi yaro walla sai  dai baban yaro ƙadangaren bakin tulu kike abarki ki lalata ruwa,a kashe ki a fasa tulu".


Chewgum ɗin dake bakin ta ta tauna da ƙarfi,sai da tayi wata ƴar ƙara kash!.


Sannan ta fara warware mana zare da abawa  abinda ya faru a daren jiya,wasu hawaye marasa control ne nayi sun shiga ambaliya daga idona yana sauɗa akan fuskata.


Harara umma ta watsa min tana faɗin.

"Dalla kaji banza marar tinani to dan ya tafi sai me?,Dama meyake tsinana miki a cikin gidan?".


Kuka yaya fawas yake yi sosai muryansa Ƙasa- Ƙasa yake cewa"Haba!umma Meyasa bakya tausayawa halin da muke ciki ne?, umma mufa ƴaƴankine Abba kuma mijinki ne amma Sam k....."


Watsa masa mari umma tayi hagu da dama ta ɗaura da faɗin.


"Shashasha fawas har kai ka isa ka faɗamin abinda ya dace na aikata?.Gida dai nice mai biyan kuɗin hayan nan dan haka duk wanda baiji daɗin hukuncin,dana yi ba to shima sai yabar min gida".


Tana kawowa nan ta miƙe ta shige ɗakinta.


Ɗaura kaina nayi akan cinyoyin yaya fawas tare da sakin wani irin wahalallan kuka,mai cin rai kuka nake da iya ƙarfina ina faɗin.


 "Wannan wani irin rayuwa ne yaya fawas?,Meyasa mu kuma ƙaddarar mu take zuwa a haka?,Meyasa Abba zai tafi ya barmu?,Meyasa umma zata mana haka yaya fawas meyasa yaya fawas?".


Ɗago kaina yayi idanunsa taf! da ƙwalla cikin sigar lallashi yake cewa.


"Hibba ƙanwata ki daina kuka kinji,kukan ki na ɗagamin hankali sannan yana karyar min da zuciya naji tamkar bazan iya ba dan Allah ki daina".


Muryana can ƙasa-ƙasa nace" yaya fawas shikenan fa Abba ya tafi kenan?".


Komar da kaina nayi kan cinyarsa na cigaba da kukana,shima yaya fawas hawaye basu daina zuba daga idanunsa ba haka muka kwana a wajen muna kuka.




UWATACE SANADI

        Tsarawa/rubutawa

        ©Maimunah Tijjani Iyam

________________________________________

Free page


Page 0⃣4⃣



Washe gari na tashi da matuƙar zazzaɓi ko makaranta bamuje ba,yaya Fawas ya sanar da Umma halin danake ciki,naira hamsin ta bashi wai yaje ya siyo min paracetamol.


Jikinsa sam babu kozari ya karɓa kuɗin cikin sanyin murya yaya Fawas yace "Umma inaso muyi wani magana dake".
Tana daga kwance tace,"menene inajinka Fawas?".

Sai daya sauƙe ajiyan numfashi kafin ya shiga faɗin.
"Umma dan Allah inason nasani ne ke kika haife mu?, kuma wani laifi muka aikata miki a cikin duniyar nan wanda yasa bakya sonmu?".


Cike da mamaki Umma ta juyo tana watsa masa wani irin kallo kafin tace"Fawas kamar ya bani na haifeku ba?banason surutun banza,ka wuce ka je ka sayo mata maganin".
"Amma Umma muka fa ƴaƴanki ne, amma ko kaɗan mu a rayuwar mu,bamusan daɗin uwa ba haba um....."


Tsawa Umma ta daka masa sai da jikinsa ya ɗau rawa,cikin zafin rai take faɗin" kafice min daga ɗaki Fawas".

Jiki a sanyaye yaya Fawas ya fito daga ɗakin.gefe na yazo ya zauna cike da kulawa yace"Ƙanwata kiyi haƙuri yanzu zanje na siyo miki".
Gyaɗa masa kai kawai nayi sannan ya fice.Haka rayuwa tacigaba da zuwa mana da ƙalubale iri-iri,ga tsangwaman da umma take mana Kullum hau-hawa yakeyi.


Nikam kullum cikin kuka nake,rayuwa duk ta mana zafi gashi bamu da dangi a kusa balle muje wajensu.
Duk dangin Abba a kano suke da zama,ita kuwa Umma duk iyayenta sun rasu inna (kakarta) ma ta Daɗe da rasuwa.


Yaya Fawas kuma dangin mahaifinsa ƴan nijar ne,koda sukazo nigeria a   azare suke na jahar bauchi.
Haka muka cigaba da rayuwa abinci ma umma sai jifa-jifa take bamu, ahaka har yaya Fawas ya gama secondary school lokacin ni kuma  zan shiga ss 2.


Cikin ikon Allah yasama admission a university of Maiduguri (unimaid),course ɗin daya kasance burinsa cikin ikon Allah shiya samu mass communication.

Nan Umma tace"ita bazata iya cigaba da mana dawainiyar karatun muna,sai dai ɗaya daga cikinmu ya haƙura ta cigaba da biyawa ɗaya".

Yaya Fawas yace "shi ya haƙura zai cigaba da zuwa shagon dayake zuwa koyan ɗinki ni ta cigaba da biya min".

Ranan nayi kuka daya zarce a misalta shi na yadda naka sai naka.Nace" A'a yaya Fawas nina haƙura da karatun kai kayi".


Kamo hannu na yayi yana hawaye yana faɗin"A'a Hibba ke kiyi burin Abba ne,muyi karatu duk da kasancewar Abba ba mahaifina ba amma bai taɓa nuna bambamci tsakani na dake ba,sai yanzu dan bayanan zan shiga tsakanin ki da burinsa my cute angle kiyi karatu ki cikawa Abba burinsa kinji Ummul-khair ɗin Abbanta".


Kallon shi kawai nakeyi ƙwalla nata  gudana a saman kunci na, bakina na rawa nace"Nagode yaya Fawas In sha Allah bazan baka kunya ba zan maida hankali ga karatu na".
Shafo fuska na yayi tare da sakin wani murmushi wanda yafi kuka ciwo da raɗaɗi yace "yauwa ƙanwata".


Haka yaya awas ya sadaukar,da burinsa nayin karatu saboda ni nayi.
Burin yaya Fawas ɗaya ne a duniya ya zama dan jarida dan haka,nasa a raina matuƙar ina numfashi a cikin duniya sai na tabbatar da wannan,burin bai mutu ba cikin zuciyar yata Fawas ba.


Lokacin da mukayi jamb mass communication na zaɓa a matsayin course ɗin danake son karanta,a duk choice huɗu na zaɓar institution da jamb ɗin ke bayarwa.


Haka yaya Fawas ya cigaba da zuwa shagon ɗinki,har shima ya gware a sana'ar.
Haka na gama secondary school na cikin ikon Allah na sama admission a yobe state university (YSU),na koma sama course ɗin danake so.

Murna wajen Rabin jikina yaya fawas ba'a magana,dan lokacin tafiyata jami'a tayi,kusan komai yaya Fawas ne ya siyamin hatta sutura sai daya sauya min.Dan yanzu alhamdulilla yana samu sosai a shagonsu.


Ranar dazan tafi tun safe na gama shiri na,na fito da kayayyakina ƙofan gida
Ina tsaye yaya Fawas ya shigo fuskarshi da fara'a yace" A'a ysu student har kin fito"?.
Murmushi na saka nace"E wallahi yaya fawas umma ma nake jira,ta dawo muyi sallama dan tun ɗazu data fita har yanzu bata dawo ba".


"Haba!ƙanwata kinsan sai  dare zata dawo,inki kace zaki tsaya jiranta zaki bata lokacin ki tafi kawai inta dawo sai na faɗa mata kin tafi".

Yaya Fawas ya faɗa yana riƙo hannu na. 
Nace " To  ya fawas amma Abba fa.....".


Cikin sauri yasa hannun sa ya rufemin baki,yana faɗin"Hibba Abba zai dawo gare mu inajin haka ajikina".


Wata leda ya Ciro daga aljihunsa, ya miƙamin Hannuna na rawa na karɓa na buɓe ledar,sabuwar wayace dal! ƙirar Android, kallon shi nake.
Ina tambayar ta waye? Murmushi ya saka kafin yace"Ƙanwata naki ne kwanan nan muna samu ɗinkuna sosai a shago,shine na tara kuɗin da'ake sallama ta na haɗa da wanda umma ta bayar na biya miki registration sannan na miki wannan siyayyar,shine sauran na saya miki wannan wayar dan inki tafi in dinga jin muryarki my cute angle ko bakya so ne?".


Bansan sanda hawaye suka fara zubomin ba,wayar ta burge ni duk da ba wata mai tsada bace hugging ɗin sa nayi cikin kuka nake cewa.

"Nagode yayana Allah ya ƙara buɗi Allah yasaka maka da gidan aljanna,Yaya  Fawas kai kaɗai nake dashi a duniyar nan bayan abba na,ina sonka yayana".


Ɗagoni yayi yana faɗin"Hibba nima inason ki,inki tafi ki kulamin da kanki".
Sausauta muryar shi yayi sannan ya cigaba da cewa"Ki rufamin asiri Dan Allah hibba kiyi abinda ya kaiki makarantar nan kinji my cute angle?".


Yanda yayi maganar sai danaji tausayin sa nace" In sha Allah yaya Fawas bazan baka kunya ba"


"Yauwa ƙanwata sannan banda biyewa samari kiyi abinda yakaiki".


Murmushi nayi nace "Yo a ni yaya fawas ko aure zanyi,to sai wanda ka zaɓar min balle har na fara kula wani ba tare da Sanin ka ba".
Shima murmushin ya maido min saboda yanda nayi maganar cike da shagwaba.
Kuɗi ya Ciro daga aljihun sa 10k ya miƙo min tare da faɗin"Hibba ga wannan ki riƙe a wajenki".


Wasu hawaye ne suka cikomin ido nace "nagode yayana".
Share min hawayen ya farayi da hannun shi yana cewa."Ƙanwata ki daina kuka da kinsa yanda nakeji a zuciya na idan naga hawaye na zuba daga idanun ki,to dakin tausayamin ki daina,inki na haka sai naji kamar na kasa riƙewa Abba ke.Yanzu ki tashi ki tafi har yamma ta miki akwai yayan wani abokina lecturer ne a  school ɗin munyi magana dashi zai ringa kulamin dake,ga numbern sa bari nasa miki".


Wayar daya bani ya karɓa ya kunna ta yasamin number sannan shima yasamin nasa numbern daman ya sama min sim a cikin ta 
Har motor park yaya Fawas ya rakani sannan ya juyo.
Ina isa cikin ysu na kalli fuskar wayata Wanda ya nuna ƙarfe goma da mintin arba'in.


Lalle kam jami'a(freedom life),jama'a kala-kala kowa sai harkan gabansa yakeyi.
Hostel naƙarisa daman yaya Fawas yagama min komai na registration, nashiga room ɗinmu.
Mu huɗune a room ɗin tima,zubaida sai shahida zubaida ƴar gombe ce tima kuwa ƴar geidam ce shahida ce kawai ƴar potiskum.
Sannan itace department ɗinmu yazo ɗaya da ita,Dan tima chemistry department take zubaida kuwa tana political science department.

Sa yamma muka fito zamuje cafterian dake cikin school ɗin,makarantar babba ne sosai Dan nasha kallo.


Tare muka fito dasu tima,indomie mukayi order cikin nishaɗi muka faraci inka ganmu zaka rantse mun jima da nisanin juna.

Cikin haka yaya Fawas ya kirani hira mukayi sosa kafin mukayi sallama.
Hostel muka wuce damuka gama Dan a lokacin  bamu fara  lectures ba.
Sai da mukayi kwana uku da zuwa sannan muka fara lectures.

Ranar da wuri muka shirya nida shahida muka fito,dan munada lectures ɗin 8:00 to 10:00am sannan zamu  fito daga lectures ɗin.
Sosai na maida hankali ga lectures ɗin, lecturer ɗin macece hakan nan kawai naji ta burge ni muna fitowa.

Wayata na ciro daga cikin jaka ta na shiga dialing numbern lecturern da yaya fawas ya bani.

Sai da kiran ya kusa tsinkewa sannan ya ɗaga,gaishe shi nayi ban masa wani dogon bayanin ni wacece ba,yace ya ganeni dama sunyi maganar da yaya fawas ya kwantamin office ɗin sa yace nazo.


Tare da shahida mukaje sai  damukayi knocking sannan ya bamu iznin shigowa,yana duba wasu takardu sanda muka shigo.

Zama muka yi har ya gama sannan ya dago ya kallemu,sunan sane ajiye kan teburinsa DR.BASHIR MUHAMMAD AUWAL.

Gaishe muka karayi ya amsa sannan yace "Hibba ko?"
 "E itace".
Sannan ya cigaba da cewa"Muyi magana da fawas so duk da ni ƴan a chemistry department,nakewa lectures amma duk abinda ya shige miki duhu ki sanar dani in sha Allah zan yi iya ƙoƙarina".
A nitse nace "nagode".
Cikin yanayinsa na barkwanci Dana karanta yace "sunana bashir".

Taƙaiceccen murmushi nayi kafin  nace,"To nagode yaya bashir".


Sannan muka fita,Haka rayuwa ta cigaba da tafiya nidai karatu na nasa a gaba baji ba ƙwauƙwautawa.

A lokuta dama ina tuna furcin ya fawas"HIBBA DAN ALLAH Ki RUFAMIN ASIRI KIYI ABINDA YA KAI KI".

Sam samari basa gabana Dan Bana ma sakar musu fuskar da har zasu min magana,kullum su tima cewa suke.

 "Wallahi ke hibba har yanzu baki waye ba".


Bana damuwa da abinda suke faɗi dama wasu daga cikin course mate ɗin mu da suka ganin kamar,girman kai ke sakani yin haka.

Na tabbatar dasun san irin ƙalubalen dana fuskan ta kafin su ganni a cikin wannan jami'ar,da bazan sumin wannan maganar ba. 


Bazan taɓa manta wani safiyar asabar ba,tin daga wannan ranar ƙaddarar  rayuwa ta sauya.

Ina kwance a hostel shahida tace inrakata ta sayo recharge card doguwar rigar abaya ce ajikina.

Gyalen rigar nayi  rolling akaina muka fito,muna tafe muna hira har muka isa wajen.
5 hundred shahida ta Ciro daga Jakarta ta mik'awa Mai shagon tace,"Gashi a bamu card na mtn na Dari bibiyu".


Kallonta nayi nace"Kedawa na ɗari bibiyu?A'a wallahi shahida kibar kuɗin ki karki ɗaurawa kanki wata wahala".

"Haba Hibba babu wata wahala,kedai sai dai inkin Rena ne to".Shahida ta faɗa,Murmushi na saka kafin nace,"To nagode".
Wata mota ce tazo ta wuce ta gefenmu, tayi parking cikin parking space aka tanada cikin compound ɗin school.
Buɗe ƙofar motar akayi tare da sauƙo da ƙafafunsa waje sannan shima ya fito
Milk ɗin shadda ne ajikinsa,tsayin rigar dai-dai gwiwar sa ya ɗaura brown ɗin agogo a damtsen hannun sa.


Kansa babu hula yayin da tarin sumar fuskar sa wanda tasha gyara sa sheƙi takeyi,haka nan sun kwanta luf a saman fuskarsa.

Idanunsa sun boye cikin wani farin glass,sai wani ni'imtaccen ƙamshi ne yake tashi daga cikinsa.

A hankali yake tafiya cikin cikakken nutsuwa ya nufo inda muke tsaye.
ƙamshin shine ya bugi hancina, nan take na juya domin ganin Wanda yake tafe da wannan ƙamshin.
Karaf muka haɗa ido dashi,sai a wannan lokacin nasama damar ƙarewa halittar fuskansa kallo.


Round face gareshi skin color ɗinshi black ne amma mai irin kyau ɗin nan ne.Dan kowani mai farin fatan bazai nuna mishi kyan skin ba.

Idanunsa manya ne ma'abota haske,yanada yalwan gashin eyes lid da eyes lashes bakin nashi Dan dai-dai.

Yana da madaidaicin tsayi,lumshe idona nayi yayin da ƙamshin sa ke ƙara tsara ƙofofin hancina.

Da sallama ya ƙariso wajen,a hankali yake motsa dan wannan bakin nasa yana tambayar mai shagon  akwa  recharge card na airtel?.Da rawan jiki Ma shagon yake cewa e akwai.


Tsaki na saka nacewa shahida wacce ta naga shagalta da kallon wannan guy ɗin"Dan Allah ki karɓa chanjin mu tafi".

Sai a sannan ta ɗauke idon ta daga kallon dake mishi Tace" Malam bamu chanjimu mu tafi".


"Wallahi ba canji, sai dai kuje anjima sai Ku dawo Ku karba".Mai shagon ya faɗa lokacin dayake yagowa wannan guy ɗin recharge card ɗin.

Dafe goshin ta shahida tayi tace"to ai zamuyi amfani da canjin ne yanzu ya za'ayi?".

Sai a lokacin sannan guy ɗin ya ɗago kai daga latsa wayarsa da yakeyi,ya kalle mu murmushi yayi cikin sanyin voice ɗin sa yake cewa mai shagon


"Kaga malam ka basu kuɗin Nasu kawaesai ka haɗa kuɗin card ɗin,da suka saya da nawa zan biya".


Cikin fara'a shahida tace,"Mungode bawan Allah".
Taƙaitaccen murmushi kawai ya saka sannan ya maida kallon sa ga wayarsa ba tare da yace da ita komai ba.

Miƙowa shahida five hundred ɗin ta Mai shagon yayi,karɓa tayi tare da ƙara cewa,"mun gode bawan Allah".


Sai a wannan karon ya ɗago kansa a  hankali yana cewa"karki damu amma ita ƙawarta ki bata magana ne?".


Washe baki shahida tayi Shahida  tace" La!hibba ai wallahi haka take bata da yawan magana".


Maimaita sunan kawai yakeyi Hibba!Hibba!!"Sunan ya burge ni ni kuma sunana habib bari nabaku complementary card ɗina".


Wani card ya Ciro daga aljihunsa mai ɗauke da sunanan sa da phone numbernsa,ya miƙawa shahida karɓa tayi tare da ƙara yi masa godiya sannan muka bar wajen.

Tsaki shahida tasaka tana faɗin"Wallahi hibba halinki yana bani mamaki ke Sam a rayuwarki bakya sakewa mutane  fuska,to  a haka wazai ce yanasonki?".

Murmushi nayi kafin nace"Shahida kenan inda ace kinsan irin ƙalubalen dana,fuskanta kafin nazo nan da bazaki min haka ba karatu nazoyi ba sakewa samari fuska ba".


"Amma fara'a ma ai wani abune, ko at list ki nuna mishi godiyanki akan alkhairin daya mana".


A harsale nace,"shahida wai rokansa muka yi ne, ra'ayin kansa ne fa".Shiru shahida tayi dan tasan halina.


UWATACE SANADI

Tsarawa/rubutawa
     
     ©Maimunah Tijjani Iyam


________________________________________

Free page


Page 5⃣


Hostel muka wuce,nasa recharge card ɗin da shahida ta saya mana na kira yaya Fawas.
Ringing biyu ya ɗauka cike da so da kuma ƙaunar juna muka gaisa.Nace "ya Umma?".


"Umma lafiyanta kalau yanzu ina shago,inna koma gida da dare zan haɗa Ku Ku gaisa". Cewar yaya Fawas


Ajiyan zuciya na saka kafin nace,"yaya Fawas har yanzu Abba baizo gida ba?".
Shima ajiyan zuciyar ya saka yana cewa,"Hibba har yanzu babu labarin Abba,yau kusan shekara uku kenan har baffa na kira ko yaje wajensu a kano amma suka shaida min bai zoba".


A hankali naji hawaye yana bin fuskana.
Bakina na rawa nace" Yaya  Fawas yanzu shikenan ba zamu sake ganin Abba ba kenan na shiga uku nikam yaya Fawas".


Wani kuka Mai ƙarfi na saka tare da kifa, kaina akan pillow ina fitar da numfashi a hankali.
"Hibba ki daina kuka,matuƙar Abba yana numfashi a ciki duniya zai dawo garemu komai daren da daɗewa ki daina kuka kinji ƙanwata kukan ki na ɗaga min hankali"yaya Fawas ya faɗa cike da kulawa.


Cikin dushashewar murya nace "Na daina yaya Fawas na daina kaji yayana".Cikin jin daɗin furci na yace,"yauwa ƙanwata".
Yayin dayake hana hawayen dake cike fal a idonsa zubowa.
Da haka muka cigaba da hirar mu,har sai da aka kira sallar magrib sannan mukayi sallama.

Alwala nayi na gabatar da sallan magriba ina zaune kan sallayata shahida ta shigo tana cewa,"Hibba Dan Allah ina wayarki?".


"Ga tanan meza kiyi da ita?".Matsowa tayi ta ɗauki wayar daga gaba na tana faɗin,"Wani waya zanyi mai muhimmanci wayata kuma ta mutu babu caji".


Ban bata amsa ba, na cigaba da tasbihin da nakeyi yayin da ta koma    ta kwanta akan gado tana wayanta.
Suna na naji Shahida tana kira hibba!hibba!! Hibba!!!a harzance na juyo ina faɗin lafiya?.


Ƙarisowa tayi gaba na tare da miƙamin wayan Tace,"Gashi HABIB ne zaku gaisa".


Cike da rashin fahimta nake tambayar ta  "waye kuma HABIB?".
Tsaki ta saka kafin tace"Habib mana wannan guy ɗin daya saya mana recharge card ɗazu.


Harara na watsa mata ina cewa"Haba Shahida daga haɗuwa da mutum sau daya shine har zaki kirashi wannan wani irin tusa Kaine?to  nidai bazan gaisa da kowa ba".
Inajinsa daga cikin wayar yana cewa, "just leave her alone,kar ki takura mata just extent my greeting to her".


Bansan sanda nasaki wata doguwar tsaki bana,Fizge wayata nayi daga hannun Shahida "Daman wannan shine kiran dazakiyin har kike kiran sa mai muhimmamci?".


Juya idanunta tayi cikin wani nishaɗantaccen murmushi tace"Hibba bazaki gane bane,guy ɗin ya haɗu over nake gaya miki he is very nice and cool".


Cike da takaici nace"Shahida kinyi nisa Allah ya taro ki ".

Ta bangaren Habib kuwa yana kashe wayar ya cilla ta kan bed ɗinsa sannan shima ya kwanta,yana ƙarewa ceiling ɗin bedroom ɗin nasa kallo.


Da ƙarfi ya cije lips ɗinsa tare da shafa sumar fuskarta,sannan ya dafe ƙirjinsa saboda matsanancin bugun da take masa.

Wayarsa ce ta fara ringing gani sunan DR BASHIR ya bayyana cikin screen ɗin wayar yasa shi sakin tsaki sannan ya ture wayar gefe.

Ƙara kira akayi a karo na biyu,sai da ƙiran yakusa tsinkewa sannan ya ɗaga Koda ya ɗaga shiru yayi baiyi magana ba.

"Afuwan mutumi na,wallahi fita ce ta same ni ta gaggawa shiyasa daka zu baka same ni ba".cewar Bashir


A hankali cikin yanayinsa na rashin son yi magana mai tsayi  yace"uhmm".
Dr bashir yace "To yanzu yaushe zaka wuce katsina nan?".


" Next tomorrow in sha Allah"ya faɗa yana gyara kwanciyar sa.


"To Dan Allah gobe ka same ni a cikin school wallahi banason ka koma katsinan nan ne Baku haɗu da maryam Ba".

Cikin ƙosawa da sauraron surutun sa Habib yace"okay Allah yakaimu goben and then if u wish ka ƙara ficewar ka nazo ban sameka ba kaga mezai faru".


Yana kawowa nan ya kashe wayar yana sauƙe numfashi,can ya tashi ya shiga bathroom yayi wanka yayi alwala sannan ya fito ɗaure da towel a waits ɗinsa sai kuma wani ƙarami yana goge kansa dashi.


Doguwar bakar jallabiya yasaka da hular ta,sai ka rantse da allah balarabe ne.
Masallaci ya fito yaje nan ya zauna sai da akayi sallan isha'i sannan ya dawo wani part naga ya shiga Wanda yafi nasa girma.


Da sallama ya shigo cikin palon Wanda aka ƙawata shi da abubuwan more rayuwa,kallo daya zaka yiwa furnitures ɗin dasuke falon Masu launin shuɗi ka tabbatar da an narka kuɗi wajen ƙawata falon.


Wata matace zaune akan lausassun kujerun  wacce zata kai kimanin shekaru shitta da biyar a duniya,ta amsa sallamar cike da fara'a.
Kusa da ita ya zauna yana faɗin"Sannu da hutawa Granny".


"Yauwa Babban mutum ga can abincin ka can akan dinning".


Ya tsina fuska yayi yana ƙoƙarin ciro wayar sa daga aljihun sa Yace,"Bashi Granny banajin yunwa sa zuwa anjima zanci".


Ba ta kula shi ba ta miƙe izuwa dinning arean ta zuba mishi abincin a plate,masa ne na farar shinkafa da miyar alayyahu Wanda yaji nama da kifi.
Sannan ta tsiyaya mishi sanyanyan lemon kunnun a'ya a Kofi.


A gabanshi ta dige plate ɗin ta zauna tana cewa" To  gashinan oya kacinye mishi gaba ɗaya".

Zaro idanunsa yayi yana faɗin,"Granny ina zankai dukka wannan abincin?".


Ganin bashi da niyyar ci yasa ta fizge wayar sa ta ajiye a gefe.
Da kanta ta dinga bashi abincin sai da tabbatar data cika mishi cikinsa sannan ta kyale shi.

Sun ɗan taɓa hira da ita kafin ya tashi ya tafi part ɗinsa ya kwanta, bayan ya gama jero nafilfilinsa.


WANENE HABIB?


Habib Abubakar Galadima shine cikakken sunansa.
Mahaifinsa alhaji Abubakar sanannan ɗan kasuwa ne bama a iya Nigeria ba gaba ɗaya faɗin Africa sunan sa ya zaga,kusan watace jaha a Nigeria yana company a jahar.

Kasuwanci shine gadon gidansuSu uku ne a wajen mahaifansu Abubakar shine babban su,halima sannan suraj.
Halima tun tana primary school Allah yakarɓi abinsa.
Sun taso cikin kulawar iyayensu alhaji Galadima da Haj.hauwa wacce suke ƙira da Granny.

A bangaren business Abubakar yayi karatum sa shi kuma suraj engeering ya karanta.Bayan kammala karatun sune suka dawo gida Nigeria.


Inda Abubakar ya cigaba da kula da companies ɗin mahaifinsu.A nijer ya haɗu da mahaifiyar  Habib ya aure ta Suka dawo Nigeria da zama.


Bayan wani lokacin Allah yayiwa alhaji Galadima rasuwa,sunyi jimami sosai da wannan babban rashin dasukayi.
Nan fa kula da kasuwancin mahaifinsun ya dawo hannun abubakar.
Bayan wani lokaci Suraj ma yayi aure a katsina ya zauna da matarsa,kasancewar acan yake aikinsa.

Amma shi Abubakar a damaturu yake tare da mahaifiyar su.
Habib ne ɗansu na farko Wanda yaci sunan kakan sa na wajen uwa, daga shi kuma haihuwar ta tsaya.
Tun haihuwar Habib aka haife shi da wannan cutar ta CARDIOMYOPATHY ma'ana raunin zuciya.


Hakan yasanya tausayin sa a zukatan kowa,tashi ƙaddaran kuma kenan a yanda tazo.
An mishi aiki a zuciyarsa aka bashi wasu magungunan dazasu taimaka wajen saisaita bugun zuciyar tashi.
Sosai ahalin nasan suke kiyaye duk wani abin dazuka san sai ɓata masa rai.

Simple life Habib ke yi dan sanin dayayi masu cuta irin tashi basu fiye tsawon rai a duniya ba,an masa aiki a zuciyar sa tare da jaddawa iyayen nasa suka kasance suna,masu Samar masa da farin-ciki  Sosai duk ahalin suke gwada masa ƙauna.

Suraj kuwa ƴaƴansa biyu sayyid Wanda yaci sunan Abubakar,sai kuma Yasira Wanda taci sunan mahaifiyar su.
Habib yana da shekaru huɗu,Allah yayi wa mahaifansa rasuwa,a hanyar dawowarsu daga nijer.

Nan riƙonsa tare da tarbiyar sa suka dawo hannun Granny.
A jami'ar Abubakar Tabawa Ɓalewa ta jahar bauchin yakubu yayi karatun sa fannin kasuwanci,yana dawowa kuwa ya karɓi ragaman kasuwancin family ɗin nasu.


Wannan kenan.


UWATACE SANADI

Tsarawa/rubutawa

        ©Maimunah Tijjani Iyam

________________________________________

Free page


Page  6⃣


Washe gari bamu da lectures ɗin safe sai na ƙarfe goma.
Ina zaune a hostel inna duba hand out,waya ta ta fara ringing, sunan yaya Bashir ne ya bayyana cikin screen ɗin wayar.


Naɗaga wayar tare da sallama ya amsa,sannan na gaishe shi ya amsa min.
"kizo office ɗina akwai sakon da fawas ya aiko miki sai kizo ki karɓa,Dan fita nake son nayi".


" To"kawai na amsa dashi sannan na kashe wayar.
Gyalena na  ɗauka milk color na bulluɓa a kafaɗa ta,Shigar atamfa ce a jikina simple ɗinki aka mata bamai taƙurawa ba.
Yaya Fawas da kansa ya ɗinka min ita, an mata adon black stone a jikin ta.


Wayata na ɗauka na fito izuwa office ɗin yaya Bashir,lokacin Dana kusa office ɗin shi kuma yana fito wa da sauri.
"Sorry Hibba ki shiga ki jirani ina zuwa,akwai  wani aboki na  dazan taro shi yanzu".Dr Bashir ya faɗa lokaci dayake wucewa.


Office ɗin nashiga na zauna ina latsa waya ta.Ta bangaren Habib kuwa Daren jiya dakyar ya samu ya runtsa.

Washe gari kuwa sa wajajen 9:00 na safe ya samu ya farka.
Yana tashi ya faɗa bathroom wanka yayi,as usual ya fito ɗaure da towel a waits ɗinsa da kuma wani ƙarami yana goge sumar kansa dashi yana dumping ruwan jikinsa.
Gaban dressing mirror ya nufa ya fara shafe laulausar fatar sa, da mayuka gyara sumar sa yayi tare da shafa musu mai ai kuwa tunin suka hau sheƙi.

Wata dakakkiyar shada baƙa ya fito da ita wacce aka yiwa aikin surfani,da Golding ɗin zare ɗinkin ya ƙawatu sosai.

Ya saka sannan ya saka hular sa ma baƙa ce da rantsin Golding ajiki sannan  ya saka a tsintsiyar hannunsa .
Sannan ya feshe jikinsa da daddaɗan turare,kallon kansa yayi a cikin madubin Wanda kayan daya sa suka ƙara fallasar  da sirrin  tsan-tsan kyan halittarsa shi kanka yasan yayi kyau ba ƙarya.


Phone ɗinsa ya ɗauka da key ɗin motar sa,ya fito ya nufa part ɗin Granny bai iske ta a falon ba.

House maid ɗinta ne kawai suke ta gyare-gyare.
Suna ganinsa Duk suka zube suna gaishe shi cike da girmamawa,kanshi kawai yake gyaɗa musu.
Ɗaya daga cikinsu wacce tafisu manyan ta ya zubawa ido.A hankali yake motsa Dan ƙarami bakinsa yake cewa

"Haba! Iya Bana hanaki Duk wani aikin wahala ba a cikin gidan nan ki bari sauran ma'aikatan suyi mana,saboda haka fa na ƙaru wasu ma'aikatan".

Murmushi tayi wacce ya kira da Iya tana ƙara jaddada nutsuwa da sanin ya kamata irin ta Habib ɗin.


"Babban mutum banason zaman haka ne,shiyasa nace gwara ina Dan motsa jikina".cewar Iya


Langwabar da kai yayi yace,"To iya nidai banason kina wahalar da kanki,ina Granny?"


Ta amsa masa datana ɗaki.Direct upstairs ya nufa inda ɗakin Granny yake.
Tana kan sallaya ta iddar da sallan walaha kenan,ya shigo kusa da ita ya zauna cikin sanyayyiyar voice ɗinsa ya gaishe ta ta amsa.

Kallo ta tsare shi dashi yayin da taga fuskar mahaifinsa ya bayyana akan fuskar tashi.

Turo baki yayi ganin irin kallon datake masa yana cewa,"Tsohuwa wannan kallon fa?to nifa kar ki lashe ni".


Murmushi tayi kafin  tace,"ina zuwa haka?"


"Zanje cikin YSU ne wajen Bashir,jiya naje ban same shi ba".

Yana gama faɗar haka ya miƙe zai fita
Muryar Granny ne ya dakatar dashi daga fitan.

" Breakfast ɗin ka fa?"

Yana shirin murda handle ɗin kofar ɗakin yace,"A kaimin part ɗin,sai na dawo zanci".

Har zai fita sai kuma ya juyo da faɗin,
"Yauwa Granny Dan Allah banason iya ta sake wani aiki a cikin gidan nan,Bana jin daɗi inna zo naganta tana wasu aiyukan buda da irin shekarunta".


"Nima ba yanda banyi da ita  ba amma ta ƙi dainawa amma karka damu zan ƙara mata magana".cewar Granny


"To"Yace yayin da yake fita daga ɗakin.
Fitowa yayi ya nufi parking lot,wata sabuwar mota dal ƙiran range rover ash color ya shiga,yayin da gate man ya kwangale masa gate ɗin ya fita.


Yana shiga cikin YSU yayi parking mota sa,sannan ya buɗe ƙofar motar ya saƙalo ƙafafunsa wajen,ba tare da ya fito ba.
Wayar sa ya ɗauka ya shiga dialing numbern bashir,ringing ɗaya ya ɗauka yana tambayar yana inane?

yace "gani a parking space".

Kashe wayar yayi dai-dai lokacin daya hangi bashir,ya nufo shi sannan ya fito daga cikin motar.
Da fara'a Dr bashir ya iso,suka rumgume juna suna farin ciki Office ɗin Dr bashir suka nufa.

Yayin da Duk inda suka wuce mutane ke bin habib da kallo,yan mata kuwa kowacce da rawan kanta suka fara tasowa suna gaishe da Dr bashir da kuma habib,Dr bashir ne kawai Mai amsawa.

Har suka isa office ɗin,turo kofar suka yi tare da sallama a bakinsu,nan take naji zuciya ta ta fara bugawa da ƙarfi sallamar na amsa,


Sannan suka ƙarisa shigowa cikin office ɗin.
Dr bashir ya zauna a kujerarsa shi kuwa habib ya zauna a kujerar da take facing ɗina.

Tunda ya shigo office ɗin zuciyar sa take bugawa,muna haɗa ido kuwa bugawar zuciyar tashi ta tsananta.
Kallo na yake yi da sexy eyes ɗinsa masu kashewa mutum jiki.


Dr bashir yace,"Sorry hibba na barki kinata jira".


Sunkuyar da kaina nayi saboda izuwa yanzu na fara tsorita da irin kallon da yakemin nace,"La ba komai yaya bashir".

"Bari na ɗauko miki saƙon na bari a mota".Dr bashir ya faɗa yayin dayake ficewa daga office ɗin.

Kamar na ƙwala ihu naji da yaya bashir ya fita,ya barni dashi.

Na daure nace"To yaya bashir"Sannan ya fita yana cewa.

"Abokina sorry fa bari na ɗauko mata saƙo".Yana kawowa nan  ya fita.

Kamar jira yake yi yaya bashir ya fita yayi magana,cikin sanyayyiyar voice ɗinsa da na ji ta,tun daga toe ɗin na har cikin head ɗina Yace ,"Sannunki".

Ba tare Dana dago na kalle shi nace,"Yauwa sannu".

Kallona ya cigaba dayi hakan, ya ƙara tsorita ne.cike da tuhuma na ɗago kaina nace,"malam lafiya irin wannan kallon?".


Murmushi yayi Wanda sai da fararen haƙwaransa suka bayyana.

"HIBBA ko? Shine jiya gaisawa ma muyi a wayar shahida kika ƙi ko?".


Cike da faɗa na ke cewa"Meye haɗina da kai da har zamu gaisa".


" Amma ai ke musulmacce addinmu ne ya haɗa mu".


Harara na watsa mishi na cigaba da kallon wayata.
Shigowar yaya bashir,ya dakatar dashi daga maganar daya yi niyya.


Ledodi yaya bashir ya shigo dashi ya ajiye a gaba yana cewa,"Yauwa hibba ga saƙon naki".

Godiya nashi sannan na ɗauki ledar zan fita.Ina ɗaga ledar ta tsinke nan kuwa kayan ciki suka zubo ƙasa,kayan tea ne da abubuwan da dan makaranta kan iya buƙata na yau da kullum.


Kamar na fasa ihu haka na fara tattare kayan,A hankali ya miƙe daga inda yake zaune ya  fara tattrare kayan shima.

Wata Leda yaya bashir ya miɗomin na zuba kayan aciki na fita.

Hostel na wuce raina Duk baya min daɗi,Ina isa na ƙira yaya fawas ina mishi godiya har umma yabawa wayar muka gaisa da ita sama-sama.duk da bawani magana mukayi da ita sosai amma naji daɗi rabo na dajin muryan ta tun bayan zuwa na school.


Hira mukayi sosai da yaya fawas nan yake faɗamin shima zai jona FCE potiskum dan yanzu alhamdulilla yana samu sosai a sana'ar sa na ɗinki,fatan alkhairi na mishi sannan mukayi sallama.


UWATACE SANADI

Tsarawa/Rubutawa

      ©Maimunah Tijjani Iyam


______________________________


Free page


Page 7⃣ 


kallo yabi bayana dashi har na fice daga cikin office ɗin,kallon shi Dr bashir yayi tare da sakin murmushi,sannan ya kawar da kansa gefe.
Dan hararan shi habib yayi yace, "Wai meye ne haka malam?".


 "To ai kai zan tambaya habib".Ajiyan zuciya habib yasaka kana yace"kaga malam ka tashi mu tafi inda zamuje,tun kafin na canja ra'ayi kuma".


Cikin sauri Dr bashir ya mik'e suka fita.Ina zaune a hostel shahida,ta shigo Dan harararta nayi tare da gyara kwanciya ta, sannan nace,"ɗazu naga mutuminki a office d'in yaya bashir".


Washe baki tayi tace "Ayya my Prince,kin tinamin ma bari na kira shi".

Tima dake zaune tana cin abinci,tace "wai ke shahida wanene wannan habib d'in?".

Juya idanunta shahida tayi Wanda izuwa yanzu,na tabbatar haka tana yin shine a Duk lokacin da take cikin farin ciki.


"ina ruwanki yar sa ido". Cewar shahida

Taƙaitaccen murmushi Tima ya saka kafin tace,"To Allah ya ki hakuri bani na kar zomon ba rataya aka bani".

Nidai dariya nake ta musu.cikin kwanacin nan muka fara exams sosai na maida hankali ga karatu.

Ana haka habib ya koma katsina gidan ƙanin mahaifinsa suraj,Dan anan katsina ta dikko ɗakin kara manyan companies ɗinsu suke.

Tun daya tafi ya kasa sukuni,kullum sai ya kira wayar hibba  yayin da ita  kuma bakin ta a baya fasa fadɗa masa,baƙaƙen maganganu.

Nayi tinanin ina tura mishi numbern shahida, zai daina kira na Dan a zato na ya ɗauka wannan layin tane,Dan da shi ta kira at a first time dasukayi waya.sauran mu exams biy malamai suka tafi yajin aiki.

Sosai nayi takaicin haka ma students da dama,duk haka muka fara tattare kayayyakin mu.



     ____________KATSINA__________


Zaune habeeb yake a office ɗinsa, yana duba wani file dake gabansa.
Ajiyan zuciya ya saka mai ƙarfi tare da dafe ƙirjinsa saboda matsanancin bugun da take masa.

Numfashi ya furzar tare da dafe kansa,tabbas ko shi kansa ba zai iya fasalta irin yanayin da shiga ba saboda wannan yariyar ba.


Wayar sa ce ta fara ringing, ba tare daya duba Wanda ya kira ba ya kara wayar a kunnensa.
Shiru yayi baiyi magana ba,gada dayan gefen Dr bashir ne ke ce"Mutumi na yane?".


Kamar ba zai iya buɗe bakinsa yayi magana ba yace,"normal bashir ya school ɗin naku?".


"Normal abokina mun shiga strike ai gobe ma,students za su watse wallahi". Cewar bashir


Kamar an zabure shi ya miƙe da cewa"Okay nima zan zo damaturun kafin goben".


Bai jira amsar da bashir zai bashi ba ya kashe wayar,key ɗinsa ya ɗauka  ya fito daga office ɗin da sauri.


Parking lot ya nufa yayin da drivern sa ya taso da wuri ɗaga masa hannu yayi yana cewa,"No ni kadai zan fita".


A guje ya figi mortar yanufi gida gida,yana isa direct side ɗinsa ya nufa ya faɗa bathroom,a gurguje yayi Wanda ya fito  dumping ruwan jikinsa yayi.


Yasaka kayansa brown ɗin shadda sannan ya fito,side ɗin matar uncle suraj(ummi)ya shiga.


Tana zaune a falo da sauri-sauri yake cewa,"Ummi zanje damaturu yanzu".


Juyowa tayi tana fuskantar sa tace," Habib lafiya da yamman nan?".

Cikin ƙoasawa dasan ya tafi ɗin yace,"lafiya kalau ummi akwai wannan company na groundnuts oil ɗin nan, da zamu buɗe,nake son naje naga yanda abubuwan suke tafiya".

Fɗaɗa fara'ar ta ummi tayi kafin ta shiga faɗin"To habib Allah ya kiyaye hanya,ka gaishe min da grannyn inka je".


"To"Kawai yace lokacin da yake, ficewa daga falon yana jin yasira nacewa,"Hamma habib zan rakaka".Amma ko ta kanta baiyi ba ya fice.

A guje yake driving motar,ƙarfe sha ɗaya da wasu mintina ya iso cikin garin damaturu duk da gudun dayake zugawa,bura-bura estate ya nufa inda gidan granny yake.

Yana isowa ya nufi part ɗnsa wanka yayi ya fito yayi sallolin  da ake binsa,sannan ya jawo wayarsa jawo dialing numbern da yayi saving da HIBBA ya shiga yi.


Ina zaune a hostel ina harhaɗa kaya na,wayata ta fara ringing na ɗaga,shiru yayi baiyi magana ba.


Nace" hello".Sai a sannan yayi magana yace, "Yakike?"."Lafiya" na amsa dashi.


Daga nan bai sake cewa komai ba,komai bai kashe wayar ba.

Tsaki nasaka nace,"Dan Allah malam in baka da abin fad'a to ni ina da abunyi".


Zaffafar Ajiyan zuciya ya saka sannan yace,"Okay  sorry gobe zaku tafi ko?".


Sanyaye na amsa da  e,


"Ayya  Dan Allah goben before Ku tafi inason magana dake".Ya faɗa yana ƙara sau-sauta muryar sa.

"okay"kawai  nace tare da kashe wayata,na cigaba da haɗa kayana.

Ajiye wayar yayi kan bed,sannan shima ya kwanta nan kuwa bacci yayi gaba dashi ko part ɗin granny bai samu ya leka ba.

Washe gari da wuri ya tashi,wanka yayi ya shirya cikin nevy blue ɗin shadda wacce tasha aikin surfani da light blue ɗin zare,hular kansa ma da rantsin blue ajikin sa.

Gyara sumar sa yayi tare da shafa musu mai sannan ya feshe jikinsa da turaren sa na lalatul sahara.


Wayar sa ya ɗauka da key ɗinsa ya fito ta shiga part  granny.tare da iya ya same ta ya shigo da sallama a bakinsa,
Suka amsa suna Washe baki granny tace,"A'a Babban mutum yaushe a garin?".


"Sauƙan jiya da dare"ya faɗa yayin dayake zama kusa da ita.Nan ya gaishe su suka amsa da fara'ar su,sannan ya dubi iya yana cewa,


"
Ƴar tsohuwa me kuka jagwalgwala ne yau a gidan?Dan nasan ba wani iya girki kuka yiba".


Dariya suka saka kana iya tace"sinasir ne da miyar kubewa sa kuma kunnun gyaɗa".Yatsina fuska yayi yace,"A kawo min kunnun gyaɗan".

Iya ce  ta tashi zata kawo masa yayi saurin cewa,"A'a tsohuwa yi zaman ki bari na ɗauko da kaina".

Ya miƙe ya nufi kitchen ɗin.(iya amintacciyar ma'aikaciyar gidan ce tun yana yaro granny tace masa ita take renon sa kuma tana masa wani irin so mai tarin yawa,kasancewar bata taɓa haihuwa ba.shiyasa shima yake jinta ta daban acikin ransa).


Daga kitchen ɗin ya fito dauke da cup a hannunsa yana shan kunnun,yasha sosai Dan ba ƙarami daɗin kunun yaji ba.

Miƙewa yayi yace"Granny zanje wajen bashir,yanzu zan dawo kiyi min addu'a allah ya bani sa'a".


Bai jira amsar da zasu bashi ba ya fice daga falon.Tun wajen 9:00 na gama shiryawa,ina jiran habib amma har yanzu ana neman 11:00 bai zo ba,har su tima da zubaida sun tafi Shahida kuwa tare zamu tafi da ita.

Lokaci zuwa lokacin nake duba agogon dake ɗaure a hannu na,tare da sakin tsaki da shahida ma ta shanya ni tun ɗazu wai taje sallama da wasu class mate ɗinmu yan Zaria.

Shigowar motarsa na hango yayi parking dai-dai inda nake tsaye tare da kayan mu,Ya fito ya iso inda nake tsaye langwabe kai yayi yace"Afuwan na barki kina jira".


Ban kula shi ba illa ƙara ɗaure fuska danayi."Sai murna ake za'a tafi gida ko?".

Bansan sanda nasaki, dariya mai sauti ba nace, "e mana".Shima sai daya murmusa kafin yace, "may Almighty Allah tackle us this unnecessary strike".


Da amin na amsa mishi dashi,sannan yaɗan fara Jana da hira duk na lura akwai abinda yakeson faɗa amma bansan meyake dakatar dashi ba.
 
Ƙiran sallan da aka farayi yasa mukayi sallama ya tafi.ƙarisowar shahida ne yasa na dawo da kaina daga kallon motar sa danakeyi har tabar cikin school ɗin.


Hararar ta nayi ina cewa"wai me kika tsaya yine?".

"Wallahi hira muka tsaya yi dasu rukayya sunusi".Shahida ta faɗa tana ɗaukar akwatin ta.

Motor park muka je muka shiga motar potiskum.Dai-dai kiran sallan la'asar muka shigo garin potiskum,ni na biya mana kuɗin motar.


Godiya tayimin sosai sannan kowa ya ɗauki hanyar unguwansu,kasancewar shahida a old army barrack take.

Ina sauƙa daga nafef na hango,yaya fawas yana fito wa daga cikin gida,da Sauri na sallame mai nafef ɗin na sauƙo da akwati na.

A guje naje na isa ga  yaya fawas ina cewa,"nayi kewar ka yaya na" riƙo hannu na yace, "Nima haka my cute angle".

Sannan ya ɗauka min akwatina muka shiga cikin gidan.


UWATACE SANADI

Tsarawa/Rubutawa

©Maimunah Tijjani Iyam


Book one free 
        Book 2 paid @N300

_______________________________


Page 8⃣ 


Umma na zaune a tsakar gida tana sauraran radio,cike da farin ciki naje na faɗa kan cinyar ta.
Itama fuskar ta ba yabo ba fallasa tace,"Wai ke ummul-khair yaushe zakiyi hankali ne?".


Cikin yanayin zolaya yaya Fawas yace"Umma sai ranan darayi aure zatayi hankali".


Cike dajin kunyar maganan yaya fawas,na miƙe ina cewa bari naje nayi wanka.

Ɗakina na shiga nayi wanka, dama yaya Fawas inna sanar dashi zuwa na ya gyara min ɗakin.

Ina fitowa Tima ta kirani na ɗauka kafin nayi magana tace"mutanan potiskum harkun isa?" "wallahi mun isa".
Mun Dan taɓa hira kafin muyi sallama
Na fito naci abinci sannan muka zauna,da yaya Fawas ina bashi labarin jami'a da yanayin mutanan cikinta,shima yana bani labarin gida bayan tafiya ta.
    

      _________________Habib__________________


Yana isa yayi parking motar sa ya fito ya shiga part ɗinsa.
Direct bathroom ya nufa, ya sakewa kansa ruwa sannan ya ɗauro alwala ya fito.
Doguwar jallabiyar sa fara Sol ya saka ya fito ya tafi masallaci.
Yana dawowa ya koma part ɗinsa,canja shiga yayi izuwa shigar wani maroon ɗin yadi,tsayin rigar dai-dai gwiwarsa key ɗin sa da wayarsa ya ɗauka ya fito ya shiga part ɗin granny.
Tana zaune a falo ta iddar da salla kenan,tana ninke sallayar ya shigo.
Karɓan sallayar yayi ya ninke,sannan ya ajiye shi a muhallinsa Duban sa  tayi tace"To har dawo?"



"E granny katsina zan koma",Da mamakin ta take tambayar sa lafiya yaushe ma kazo?.
Langwabar da kai yayi yace,"Granny zan tafi ne akwai akin Dana baro a can ɗin".
"To ka gaishe min da sauran yan uwan naka".Har parking lot ta mishi rakiya sai jero masa addu'o'i takeyi.

Shikuwa ya figii motar sa ya fita,duk ransa babu daɗi,dukan sitiyarin motar yayi tare da furzar da iska daga bakinsa,gefen hanya ya samu yayi parking tare da ɗaura kansa akan sitiyarin motar.


Ransa duk a jagule,a hankali ya furta "ya rabb wani irin al'amari ne yake shirin faruwa da zuciyata?".


Yafi 30min a haka wayarsa da tafa ringing ne ya sashi ya ɗago kansa.a hankali ya kara wayar a kunnensa yace "bashir yane?".

Daga ɗayan bangaren bashir yace,"normal fa mutumina,yanzu Nazo gida granny take cemin kazo har ka koma tace min jiya ka shiga cikin YSU shine ko ka nemeni sannan ma wajen wa kaje a cikin school ɗin?".



Ajiyan zuciya yasaka yace,"bashir I am on my way now if I reach home I Will call you,"

Yana gama faɗin haka ya kashe wayar, sannan ya zaburi motar ya hau titi.


Yana isa cikin katsina direct office ya wuce,yayi locking kansa a office ɗin.


Ƙiran sallan magriba da aka farayi ne,ya tilasta masa fitowa ya tafi masallacin da yake cikin companyn,sai da akayi isha'i sannan ya tafi gida.

Yana isa ya shiga part ɗin Ummi,gefen ta ya zauna yana sauƙe numfashi ƙasa-ƙasa ya ɗaura kansa akan kafaɗarta.


Dubanshi tayi tace,"A'a Habib har ka dawo baka min waya, ka sanar dani ba?".


" Ummi tafiyar ce tazo ba tsammani".ya faɗa yana gyara kwanciyar sa akan kafaɗata.


"To ya ka baro su Granny ɗin?"."Lafiya kalau tana gaishe ku, musamman this parrot".

Ya ƙarishe maganan yana nuna Yasira da take zaune a falon.


Cuno baki Yasira tayi tana cewa"Hamma Habib bana ce zan bika ba ka ƙi kulani".Yace "to school ɗinfa kiyi yaya dashi?".
"Ayya Hamma naga ba daɗewa zamuyiba".Miƙewa yayi tare da faɗin"Ummi akawomin abinci na part ɗin"yana kawowa nan yafita daga falon.


Bazan taɓa manta wata ranan alhamis ba,lokacin kwana na biyu da dawowa daga makaranta tun daga wannan ranan ƘADDARAR RAYUWA TA ta sauya.

Da yamma muna zaune a kofar gida ni da yaya Fawas Muna shan iska,wata farar mota ƙiran Mercedes tayi parking dai-dai kofar gidan mu.

Drivern dake jan motar ne ya fito ya buɗe bayan motar wani mutum ne ya fito,naso ace wannan ranan ta zama mafarki wannan ranan shine sanadin rubuta labari na tamkar a mafarki idanu na suka sauƙa akan fuskar Abba dake fitowa daga cikin motar.


A zabure na miƙe domin tabbatar da abinda idona ya nunamin domin na saba irin wannan mafarkin,Bansan sanda hawaye suka zubo daga idanuna ba.


A guje na nufi inda Abba yake tsaye na rumgume shi ina kuka,yaya Fawas ma zuwa yayi tare da rumgume shi.


Riƙo hannuna Abba yayi muka ƙarisa cikin gidan,Umma tana fitowa daga wanka sukayi ido huɗu da Abba.


Sake bukatin ɗin dake hannunta tayi cike da mamaki gami da jimami da son tabbatar da abinda ta gani tace,"Sule!sule Kaine wannan?".

Abba yace"kwarai kuwa Juwahir nine".
Tabarma na shimfiɗa mana muka zauna yayin da driven Abba ya shigo da wani akwati ya ajiye a gaban Abba sanna ya fita.
Ruwa Umma ta kawowa Abba ta ajiye masa tana cewa tana tafe tana faɗin,"Sule kai kuwa meyayi zafi haka?zaka tafi abinka ko waiwayen mu bakayi ba".


Abba yace"juwa kenan bagashi yanzu na zoba".yaya  Fawas ya gyara zaman sa yana ƙara fuskanto Abba yace,"Amma Abba Duk tsawon lokacin nan ina kaje?".


Murmushi Abba yayi tare da buɗe akwatin dake gabansa,ya Ciro waya guda biyu ƙiran iPhone 12pro max ya miƙawa yaya fawas ɗaya sannan nima ya miƙomin ɗayan yana faɗin"Mama na kema ga naki".

A hankali nasa hannu na karɓa ina masa godiya,zannuwa ya Ciro ya mikƙawa Umma har ƙasa Umma ta zube tana masa godiya.

Dubu ɗari ya miƙawa yaya Fawas yace ya riƙe koda wata buƙata Zara tazo Umma ce tayi saurin cewa"Sule kodai arzikin Kane ya dawo?".


"Juwahir kinsa ikon Allah yafi gaban komai,shike azirta duk Wanda yaso a lokacin daya so kuma a sanda yaso".yana gama faɗin haka ya miƙe,Cikin sauri nace" Abba ina kuma zakaje?".



"Ummul-khair inason na shiga cikin unguwane mu gaisa da mutane kinsa an Daɗe ba'a haɗu ba".

Har ƙofar gida muka raka shi sannan muka dawo,kowa acikin mu jiran zaman dawowan Abba yake domin amsa mana tambayoyin da suke bakin mu akan dukiyar daya zo da ita.


Muna zaune har aka kira sallan magrib yaya fawas ya fita masallaci,ina iddar da sallah waya ta ta fara ruri na ɗaga.


Mun Dan yi hira da Habib sama-sama  Dan ba kowani magana nake bashi amsar,bata sai dai nace masa uhmm da haka mukayi sallama.

Mu na nan zaune har ƙarfe 9:00 na dare  Abba bai dawo ba,har bacci ya fara ɗauka na Washe gari duk muka tashi da mamakin,rashin dawowar Abba har makwabtan muka tambaya ko yaje wajen su kamar yanda ya faɗa amma kowa yace bai ganshi ba.


Kullum da sa ran dawowar Abba muke kwana acikin ranm ,har izuwa wata Daren ranan juma'a,yaya Fawas da Umma suna zaune a tsakar gida.


Yaya Fawas kayan mutane yake ta yankawa ita kuwa umma sana'arta takeyi wato dama giya.


Ni kuwa ina ɗaki ina waya da habib, kullum sai ya kirani a kalla sau biyar  a yini,yana tambayar lafiya ta tun bana biye masa har na fara sakin jiki dashi.


Sosai mukayi wani shaƙuwa mai ƙarfi da habib,har nakan iya sanya shi a cikin,jerin mutane mafi muhimmanci a gare ni acikin kwanakin nan har yaya Fawas ya fara fahimtar wani Abu.


Sallama mukayi da Habib akan cewa zai shiga wanka inya fito zai kirani.Fitowa nayi waje na zauna kusa da yaya Fawas inna kallon yanda yake yankar kayan.


Ina zama Abba ya faɗo cikin gidan a firgice,cike da tsoro halin da muka ganshi duk muka miƙe muna faɗin lafiya?.


Bai kai ga bamu amsa ba motocin yan sanda suka zagaye gidanmu sannan wasu suka shigo ciki,wani jami'i ne ya ƙarisa  kusa da Abba ya daka masa tsawa yana cewa"Be on ur kneel."

Tunin Abba ya durkushe a wajenSannan jami'in yasa masa handcuff a hannun sa,suka ɗauke shi suka fice dashi duk cikin mu babu Wanda Allah ya bashi damar tambayarsu dalilin tafiya da Abba domin mamaki ya gama cikamu.


Wasu hawaye masu zafi naji suna zubowa daga idanuna,wani ƙara na saka mai ƙarfi tare da zubewa a ƙasa ina wani irin kuka mai ban tausayi,durƙusawa yaya fawas yayi a gefena cikin kuka yace,Hibba kanwata ki daina kuka wallahi kukan ki yana ɗaga min hankali".


Muryata can ƙasa nace "Haba!yaya Fawas taya bazan yi kuka ba kana ganin abinda ya faru fa Abba suka kama".



Na ƙara fashewa da wani kukan rumgumo ni yaya Fawas yayi ya riƙe ni gam muka cigaba da kukan mu Umma kuwa sai safa da marwa takeyi.


UWATACE SILA

Tsarawa/Rubutawa

       ©Maimunah Tijjani Iyam

_____________________________



Page 9⃣


Haka muka kwana yanda mukaga rana haka muka ga dare,cikin mu ba Wanda ya runtsa.

Washe gari kuwa tun da sanyi safiya muka tafi police station,abinda ke tafe damu muka bayyana musu suka ce mana ba,nan aka kawo shi ba saboda laifinsa babba ne,damaturu aka wuce dashi tun Daren jiyan.

Umma tace"wa meya aikata ne haka shi kuwa?".

Sai da police ɗin ya zabga mata harara kafin yace"Kinason kice baki San sana'ar mijinki ba,na haɗa kai ga masu GARKUWA DA MUTANE?".

Dam-dam ƙirji na ya bada wani jiri naji yana ɗebata nan take na faɗi awajen sumammiya.

Cike da tashin hankali yaya Fawas ya riƙoni,yana kiran sunana Umma tace,"To Dan Allah bawan Allah inmukaje damaturun zamu zama ganisa".

Yace mata bashi da tabbacin zamu sama ganinsu Dan daga damaturun abuja za'a wuce dasu.


Salati umma ta saka,tana faɗin"Sule ka cucemu ka cuci kanka sule mai ya kaika wannan aikin?.


Wani police ne Wanda babu tsausayawa acikin ƙwallar idonsa ya dakawa yaya fawas tsawa,Yana cewa"Ku fice mana daga nan mutanan banza kawai".


Ɗauka na yaya Fawas yayi nuka fito,muka nema nafef mukayi gida.tunin labari ya baza unguwarmu masu zagi nayi masu tsausaya mana suma nayi.


Buɗe idona nayi a hankali,ina ƙarewa wajen kallo a zabure na tashi ina faɗin Abba!Abba!!Abba!!!.yaya Fawas ne ya kamoni ganin bana cikin hayyacina kuka yake matsananci yace, "Hibba kiyi hakuri abba zai dawo".



A hankali na kwantar da kaina a ƙirjinsa ina kuka,haka muka yini muka kwana Abu ɗaya.


Tabbas naga tashin hankali Umma matuƙar awannan lokacin tabbas tsakanin miji da mata sai Allah.


Nikam ba abinda yake sake sani kukan zuci,kamar ina tuna umma ce ta kori Abba daga gida har, shaiɗan ya rinjaye shi ya aikata wanna aika-aikan.


Tabbas UWATACE SANADIn duk wani ƙuncin rayuwa dana shiga,itace silar zubar hawaye na.


Washe gari muka ƙara komawa police station ɗin,cikin rawar murya Umma tace,"Dan Allah bawan Allah ka sanar damu shin zamu iya ganinsa inmukaje damaturun?".



Cikin zallar masifa yace,"wai Ku wasu irin mutane ne? nan fa aka sanar daku laifin wannan mutumin, to wallahi laifin,da mutumin nan ya aikata kuma cire rai da dawowarsa baza ku gani ba Dan wallahikashe su za'ayi".


Salati Umma ta saka tana faɗin"Na shiga uku ni juwahir naga abun da ya isheni.


Ni kuwa wani jiri ne naji yana ɗebata,da ƙyar na iya tsayawa akan ƙafafuna,riƙoni yaya fawas yayi idanunsa taf da ƙwalla yace,"Umma muje gida".


Muna isa gida na wuce ɗakina na kwanta,wani nauyi naji zuciya tamin da sauri-sauru  take bugawa tamkar zata fito daga cikin ƙirjina.


Inajin wayata tana ringing nasan habib ne,sai dai bana cikin yanayin da zan iya ɗaukar waya a yanzu.Haka muka shafe kwanaki biyar cikin wannan tashin hankalin.



A cikin rana ta shida, wani makwabcin mu ya shaida mana,da yankewa su Abba hukuncin kisa ta hanyar harbewa da bingida,kuma har an zartar musu da hukuncin.


Har video yanuna mana a wayarsa, gasu nan kafin a kashe su suna fitowa daga kotu yan jaridu sai tambayoyi suke musu.


Su goma sha ɗaya ne dukkaninsu matasa ne da bazasu ɗara shekaru ashirin da biyar  ba a duniya,Abba ne kawai dattijo a cikinsu.


Yana gama sanar da mu umma tace  yaya fawas yaje police station,Dan tabbatar da gaskiyar wannan videon.

Can ɗin ma da yaje suka bayyana masa da kotu ta yanke  musu da hukuncin kisa kuma,har anzarta da hukuncin akansu.


Dan acikin Wanda suke da plan ɗin yin garkuwa dashi har da ƙwararran engineer ɗin nan masu kamfanin kayan masarufi GALADIMA'S NIG LIMITED wato ENGINEER SURAJ GALADIMA.

Duk abin da suke faɗa yaya fawas baya fahimtarsu yace.

"To gawarsa fa ko zamu samu mu mishi sutura kamar yanda addini ya tanada?".


Suka ce masa basa bada gawar irin waɗannan mutanan,birne su akeyi tare da sauran yan garkuwar a rami ɗaya.


Lokacin danaji yaya fawas yana sanar da umma wannan labarin,ji nayi tamkar babu rai a cikin jikina.


Tsayawa nayi cak!ba abinda yake motsi a jikina sai ido.

Yayin da numfashi na ya fara barazanan barin gangar jikina,faɗuwa nayi a wajen ba wani gaɓa a jikina Wanda yake motsi.


Cikin wani irin kuka mai bayyanar da tsan-tsan tashin hankali,yaya fawas ya iso inda na faɗi yana jijjigani umma ma sosai take kuka fuskar nan duk ta kumbura.


Tunin gidan mu ya cika da taron mata, har yan daudun umma sunzo,sai kuma maza dasuke waje.


Har yan-uwan Abba sunzo ƙaninsa(baffa) tare da matarsa hajara,sai kuma mahaifiyarsu inna dama suke nan suka ragewa Abba a duniya a matsayin dangi.


Kowa yazo sai ya tambayi gawar Abba, umma takan ce musu a can aka masa jana'iza ba'a kawo gawar gida ba.


Ina kwance da kan cinyar yaya  fawas,a ɗakin umma.Dan tunda na faɗi yake riƙe dani ko gaisuwar dasu baffa ke karɓa a ƙofar gida ba jeba shi.


Hannuna yana saƙale a cikin nasa yana murzawa a hankali.Inna na tofin addu'a a cikin ruwa tana shafa min a fuska.


A Hankali na fara buɗe idona dana jisu sumin wani irin nauyi.Ina ƙarewa mutanan wajen kallo,wasu hawaye ne masu matuƙar zafi suka shigo rige-rigen tsiyayowa daga idona.magana ma ya gagare ni.

Tashi nayi daga jikin yaya fawas,na matso kusa da inna na kifa kaina akan cinyarta ina kuka,bubbuga bayana takeyi a hankali da hannayen ta ita ma tana kukan.


Har cikin ranta umma take ɗaurawa alhakin abinda Abba ya aikata,Lokaci daya naji kaina yamin wani irin nauyi,ko idona bana iya buɗewa ga wani azababben zazzabi daya sauƙa a jikina haka na yini cikin wannan halin ina maƙale ajikin inna.


Da dare mutane sun safara watsewa,ina kwance har yanzu a jikin inna.

Izuwa yanzu kam hawayen ma sun kafe sai dai kukan zuci,wayata ce ta hau ringing inaji har kiran ya tsinke aka sake kira a karo na biyu.shima banbi ta kansa ba sai da aka kira a karo na uku.

Sannan inna tace,"wayar wayene wannan aketa kira?".

Muryata har bata fitowa sosai nace"Tawace".


"To  ki ɗaga mana".

nace"ki barshi inna ai kiran ma ya katsa".

Ina rufe bakina aka wani Kiran yasake shigowa,ɗauka nayi tare dayin sallama bai amsa sallamar ba Duk dayasan muhimmancinta a addinance.

Illa ajiyan zuciya da ya saka kafin yace,"Hibba for how many days nake kiranki bakya ɗauka?".


UWATACE SANADI

Tsarawa/Rubutawa

    ©Maimunah Tijjani Iyam

_________________________________

Page 1⃣0⃣


Kuka ne ya kubce min,a razane Habib yace,"Hibba lafiya?meya saki kuka?".

Ajiye wayar nayi yayin da na kifa kaina akan gwiwata ina kuka.

"Hello kina jina?"

Shine abinda yake ta maimaitawa a cikin wayar,ganin haka yasa inna ta ɗauki wayar.

Sallama tayi habib ya amsa tare da gaishe ta cike da ladabi da girmamawa,sannan inna tace,"Bawan Allah kayi haƙuri hibba yanzu bata cikin hayyacinta,bazata iya magana da kaiba".


"Dan Allah meye faru da ita".




Nan fa inna(baki ba sakata)ta shiga bayyana mishi duk abinda ya faru, sai dai bata sanar dashi irin mutuwar da Abba yayi tadai ce masa abba na ne ya rasu yau.

Wani irin tausayi ne da kuwa abinda shi kansa baisan menene shi ba,suka ƙara shigewa zuciyar habib a lokaci guda,yasan zafi da kuma raɗaɗin maraici domin nasa iyayen bai taso a cikin su ba.


Hawaye yaji suna gudana a fuskarsa,a hankali ya share su yace,"Dan Allah ko zakimin kwatancen gidan?".

Nan inna ta shiga kwatanta mishi gidan,duk da ita ma ba wani sanin potiskum ɗin tayi ba ta'aziya ya mata sannan sukayi sallama.


Washe gari bayan sallan zuhr,ina zaune a tsakar gidanmu yayin da mutane keta zuwa gaisuwa,yaya fawas ya shigo ya kirani gefe muka tsaya sannan yace.


"Hibba kinyi baƙo a waje tare suke da bashir yayan abokina Faisal".


"Ni yaya Fawas ba Wanda mukayi dashi zai zo".


"Kije ki sanarwa inna da Umma zasu shigo su gaisa"cewar yaya Fawas.

GefenUumma na tsuguna ina faɗa mata,ina rufe baki na kuwa sallamar habib ya sauƙa a cikin dodon kunnena,tare yake da yaya bashir da kuma ƙanin yaya bashir ɗin Faisal.


Ɗaya bayan ɗaya suka gaida mutanen wajen, tare dayin ta'aziya wa umma da inna miƙewa sukayi yayin dana bin bayan su muka tsaya daga jikin motar yaya bashir Dan na lura da ita suka zo duk sunmin ya haƙuri.

"Mun gode Allah "sannan suka tafi na amsa dashi.


Wani abin takaici ranar da Abba yacika kwanaki uku da rasuwa a ranan Umma ta cigaba da sana'arta.
Ranan bani ba hatta Inna da Baffa sun sha kuka mai isarsu.
Wasa-wasa  Abba ya cika wata biyu cur! da rasuwa, a ranan inna dasu baffa sukace zasu koma umma tace"Ita ta sama miji aurenta zatayi tana gama idda dan haka dani da yaya Fawas kowa zai koma wajen dangin mahaifinsa,saboda mijin da zai aure tan yace bazai riƙe mata ƴaƴanta ba".

Yaya fawas yayi kuka tamkar ransa zai fita a ranan.
Ya roƙi umma data barni na zauna,a wajenta kodan karatu na,amma umma tace"Ai  daman,ba ita takeda hakkin kula damu ba dukkanin mu wajen dangin mu zamu koma ni zanbi su inna mukuma kano shikuwa yaya Fawas daman dangin mahaifinsa a azare suke Dan haka shima zai koma can da zama".


Rabuwa da yaya  Fawas,jinsa nayi tamkar ƙarshen numfashi na kenan a cikin duniya.
Abba ya tafi tafiyar da ba waiwaye balle dawowa,yanzu kuma ga rabuwa da yaya fawas.
Jinayi komai na rayuwar duniya ya fita a raina,meyasa mu kuma tamu ƙaddarar take zuwa mana a haka?meyasa umma bata tausayin halin da rayuwar mu zai shiga?meyasa Umma bata mana kallon ƴaƴa?.
Tambayoyin dana kasa samawa kaina amsoshin su kenan.
Duk mungama shirya kayanmu nida yaya Fawas muka fito dasu kofar gida, kuka muke tamkar bazamu sake ganin juna ba,riƙo hannuna yaya fawas yayi yace"Hibba ki daina kuka,kukanki na ɗaga min hankali my cute angle ko ina kika tsinci kanki,ki riƙe mutuncinki sannan ki riƙe addininki kinji ƙanwata?".



 "Yaya Fawas ajikin nakejin kamar bazamu sake haɗuwa ba".Hannu yasa yana share min hawayen fuskana.

 
Kafin ya shiga faɗin"Hibba ki daina faɗin haka in sha Allah zanzo har inda kike my cute angle kinji ki daina kuka". 

Muryata har ya dushashe nace" yaya Fawas yanzu karatuna shikenan ya tsaya kenan?".
"Hibba zaki cigaba da karatu domin shine burin Abba, ga kuɗin da Abba ya bani dashi akayi amfani wajen saya abinci da wasu abubuwa dubu talatin ne ya rage gashi yanzu zan baki ki riƙe a wajenki koda zaki buƙaci wani Abu".

"Yaya Fawas ba abin dazan buƙata a yanzu sama da kasancewa tare da kai,amma Umma ta hana hakan yiyuwa"


Muna cikin haka Umma tafito tare dasu Inna,Hajara da kuma Baffa Umma tace"Hibba Fawas sai dai kuyi haƙuri domin ba kuka ba komai zakiyi bazai sa na canza ra'ayi na ba".


Cikin sauri Inna tace"Ashsha ashsha haba Juwa,ki barsu da baƙin cikin da kika sanya su aciki ma ya ishesu basai kin faɗa musu wadannan kalaman ba".


Baffa da duk haushin Umma ya gama cika shi yace"Inna mu tafi".

Ƙarisuwa Inna tayi tare da Ciro hannuna daga cikin na yaya Fawas ta riƙe muka fara tafiya.
Tafiya nake amma bansan inda nake saka ƙafafuna ba,numfashi na sama-sama yake fita har muka isa tasha muka hau motar kano.
Yaya Fawas kuwa inda nabarshi,nan ya tsaya yana wani irin kuka mai tsuma zuciyar Mai sauraro,sai da yayi Mai isharsa sannan shima ya nufi azare.


Ƙauyen gano dake cikin karamar hukumar kano,muka nufa inda su inna suke da zama.
Gidan ƙarami ne Mai ɗauke da ɗakuna biyu,ɗaya na Baffa da matarsa ɗaya kuma na Inna.

A ɗakin Inna na ajiye kaya na saboda anan zan zauna muna isa na kira yaya fawas amma wayarsa a kashe.

Kwana na biyu a gidan na fahimce irin rayuwar gidan nasu.Inna bata isa ta faɗawa Baffa,magana yaji ba yayin da matarsa Hajara take tsula tsiyarta son ranta wa Inna.

Ranan ina shara Habib ya kira wayata,na ɗauka tare dayin sallama ya amsa sallamar tare faɗin"Hibba yanzu Bashir yake gayamin school ɗinku,sunyi resuming daga strike ɗin dasuka tafi.amma yace min ke baki komaba ko lafiya?".


Hawaye suka ciko idona a hankali nace"Banida lafiya ne,amma in sha Allah innaji sauƙi nima zan koma".

A kiɗime yace "Subhanallahi! tun yaushe?".


Bansan sanda bakina ya furta"Tun last week"ba
Cike da nuna damuwar sa yace"To Allah yaƙara lafiya "
"Amin"
Mun Dan taɓa hira har yake sanar dani tsautsayin dayaso ya faɗa ga uncle ɗinsa,na yan garkuwa dasu ka so kamashi.


Na jajanta masa tare da addu'ar Allah ya kiyaye gaba Mun Dan tab'a hira kafin mukayi sallama.

Na cigaba da sharan danakeyi,ina gamawa na nufi ɗakin Hajara sallama nayi aka amsa sannan na shiga.

Baffa na zaune na shigo na zauna can gefe cikin nutsuwa nace,"Baffa sannu da hutawa"

Ba tare daya ɗago ya kalli ni ba yace"Yauwa Mamana".


"Baffa daman mun koma makaranta ne daga hutun da malaman makarantar sukaje shine nima nake son wani sati na koma".


Sai a sannan Baffa  ya ɗago ya kalle ni yana faɗin"Hibba kya bari dai abubuwa su dai-dai kafin kizomin da maganar komawa makaranta".

Nace" Baffa makarantar nan shine burin Abba Dan Allah kar ka han......."
Tsawa ya daka min cikin faɗa yake cewa"Wai ke Hibba wace iriyar mara hankali ne?,a halin damuke cikin inna mukaga ƙarfin ɗaukar nauyin karatunki. bayan ba abin da Sulen ya bari sai ɓata mana suna da yayi a gari to karatu dai wanda kikayi a baya Allah ya albarkace shi".


Hawaye tunin sun fara wanke min fuska,na tashi ina fita daga ɗakin ina kuka na shiga ɗakin Inna.
Yaya Fawas da Abba kawai nake tunawa Allah sarki mutuwa Mai tunan asiri.
Wayata na ɗauka na shiga  dialing numbern yaya Fawas yana ɗauka kuka nasa Mai ƙarfi nace "Yaya Fawas karatuna Baffa yace banzan cigaba ba".

Da mamaki yaya Fawas  yace"Meyasa yace haka?Baki gaya mishi burin Abba bane kiyi karatu?"

" Na faɗa mishi yaya Fawas".


Ajiyan zuciya yaya Fawas ya saka kafin yace"To shikenan my cute angle ki daina kuka na faɗa miki kukanki yana daga min hankali ko,ƙarshen watan nan zanzo sai muyi magana da Baffan ko?".


Cikin sheshshekar kuka nace "to yaya Fawas".
Haka muka cigaba da hirar mu kafin daga bisani mukayi sallama.
Sati na biyu tare da su InnaBrannan baffa ya shigo yace a kirani.Hajara tazo tace min Baffa yana kirana naje na durƙusa a gaban shi nace" Baffa gani".


Gyaran murya yayi kafin ya shiga faɗin"Mama na  zamanki a haka bazai yiyuba sabida haka nasamo miki MIJiN AURE  aure zan miki".
Wani ras!naji gaba na yana faɗuwa,a kiɗime nace "Baffa aure kuma?"na faɗa maka fa ni karatu zanyi domin shine burin Abba Baffa inna gama sai ayi maganan auren".



"Na dai gaya miki kenan,matuƙar kina ƙaunar ki cigaba da zama a gidan nan to sai kin auri NAZIFI".


Idona fal da hawaye nace, "To ni wallahi bazan auri kowa ba".
Mari baffa ya sauƙe min hagu da dama Yana faɗin "Shashasha to ki kasa kunne ki saurare ni, wallahi  ko ubanki ne Sule ya dawo duniya bai isa ya hana aurenki da nazifi ba".
Inna ce ta fito daga ɗakin ta,tana cewa "Adamu dan Allah kabar yarinyar nan haka,ka hana ta cigaba da karatun ma ai ya isa".


"Haba!Inna wai  ke  ba daman  anyiwa yarinyar nan,faɗa sai kita mita to wallahi aure zan mata koda son ranta ko babu".


Hajara ce  ta karɓe zancen tana faɗin"Haba!Inna meyasa kike ɗaurewa yarinyar nan gindi ne,in batayi aure ba to mezatayi?".


Ajiyan zuciya Inna ta saka kafin tace"Hibba kiyi haƙuri taso ki shiga ɗaki".


Na tashi na shiga ɗakin Inna na faɗa kan katifa ina kuka Bayan kwana biyu Baffa yace in shirya nazifi zaizo kaina na kallon ƙasa nace"Baffa bana jin daɗi bazan iya fita ba".
Cikin zafin rai yace "Hibba ko mutuwa zakiyi wallahi sai kin auri nazifi".

Da kukana na miƙe na shiga ɗaki naci kukana har na gaji na tausayawa kaina na daina.


UWATACE SANADI

   Tsarawa/Rubutawa

        ©Maimunah Tijjani Iyam

______________________________

Katsinawa wannan page din nakune bazan manta da karamcinku ba a rayuwata.


Book 1 free

       Book 2 paid @300

______________________________



Page 1⃣1⃣


Gashi wayata ta mutu,balle na kira yaya  fawas domin babu wutan nefa a gidan baffa kuma ya hana ni fita ko'ina balle na sama waya nayi kira.


Inna da hajara kuwa basu da waya baffa ne kad'ai  mai ita,Ina zaune akan sallaya ina roƙo mahaliccina,daya sassauta min tsananin danake ciki.


Bazan zargi umma da laifin jefa rayuwa ta cikin ƙunci ba,amma tabbas UWATACE SANADIn sanadiyar kuka na.
Hajara ta shigo tana cewa,"kizo baffa yana kiranki"Miƙewa nayi nabi bayanta.A hankali kamar mai ciwon baki nace"Baffa gani"


"Kije ki shirya nazifi na jiranki a waje".

Miƙewa nayi jikina a sanyaye na fita wajen sallama kawai,nayi masa naja gefe na tsaya ina masa wani irin kallo mai cike da tsana.
"Ina fatan an sanar dake dalilin zuwana?".Cewar nazifi
Hararan na watsa masa ne  ya sanya shi saurin ɗauke idonsa daga kallon daya kemin yacigaba da cewa"Maganar aure ne yakawoni amma bari na fara da gabatar miki da kaina.Sunana nazifi Sana'a ta noma ina noman dankali dawa Masada da kuma barkono sannan ina kiwon tattabaru ina aure k.........".


Tsawa na daka masa ina cewa "Kaga malam kama daina  mafarkin aurena Dan bazan taɓa aure mutum irin kaba, gwara ma tun kafin lokaci ya ƙure maka ka janye wannan maganar."


Ban jira amsan dazai bani ba na koma ciki Baffa na tarar zaune a tsakar gida,ko kallonshi ban yiba nasakai zan shige ɗaki naji muryan baffa yana cewa.

 
"Ya kukayi da nazifin?."


Ya dakatar dani daga shiga ɗakin a  dake nace"Baffa ni baimin ba kuma bazan taɓa aurensa".
Mari naji baffa ya sauƙe min ta gefen fuska na sai dana jijiri  na ɗebata.
"Billahillazi koda gawarki ne,sai na ɗaurawa nazifi aure da ita kinsa alkhairin da yaron nan kemin kuwa?".

A raina nace ina kuwa zan sani karo na biyu da baffa ya sake maimaita min. 
"MATUƘAR KINA ƘAUNAR  KI CIGABA DA ZAMA ACIKIN GIDAN NAN SAI KIN AURE NAZIFI,


"Yanzu ke kina tinanin har kina da wani ƴancin akan kanki ne ai hibba ko mai ya faru dake a rayuwarki to  babu wanda zakiyi,kuka dashi face MAHAIFIYARKI domin ita ta zaga yi miki abinda uwa take yiwa ƴaƴanta".
A guje na shiga ɗaki ina kuka,kuka nayi na fita hankali naci kuka mai isa ta bamai bani haƙuri saboda inna batanan daman ita ce mai kwantar min hankali.Tashi nayi na zauna tare da share hawaye na,ina kara tino furcin baffa.


"MATUƘAR KINA ƘAUNAR KICIGABA DA ZAMA A CIKIN GIDANNAN SAI  KIN AURE NAZIFI AURE ZAN MIKI NA HUTU".

A hankali nace "Baffa zan bar maka gidanka na gwammace nabi dunyia akan na auri nazifi,matuƙar ina numfashi a cikin duniya sai na cika burin Abba sai na cimma ƙudurin yaya fawas na zama yar jarida".


Ina cikin haka inna ta dawo,fara'a na ƙirƙiro na tashi na tarbeta.
Kallo ta tsareni dashi tace "Hibba idonki kamar kuka kikayi ko?".
Wani maraniyar murmushi nasaka tare da karɓan ledan dake hannunta nace,"A 'a inna kaina ne kemin ciwo kawai"


"To Allah ya sauwake" nace "amin".


Kwana nayi ina tufka da warwara a cikin raina,ko yaya fawas bazan Sanar mishi zan bar gidan baffa ba domin nasan shakka babu ba zai goyi bayana ba akan hakan ba.
To ma ina zan nufa inna bar gidan baffa?,wanake dashi dazan nufe shi da matsalolina a halin yanzu?umma ce ta fara faɗu min a raina.
Amma nasan ko hauka nakeyi basan nufi wajen umma ba domin baza ta karɓe ni ba.Wata zuciyar tace min to ki shiga duniya mana.
Haka na kwana ban runtsaba,washe gari kuwa na shiga tinanin hanyar dazan bi na fita koda Ƙofar gida ne domin baffa ya hana ni fita ko'ina.
Muna zaune da inna ina tsince mata wake,hajara ta fito daga ɗaki tana ta jaraba.Cewar wai gidan ba ruwa ga shi baffa ya fice abinsa ba tare daya nemo yaron dazai ɗeboba.


Cikin hanzari nace"Bari naje na ɗebo ruwan".
Inna tace "A'a hibba kar kijawa kanki abin magana,adamu yazo yata miki faɗa ki bari ya dawo ya nemo Wanda zai ɗebo ruwan da kansa".
"To inna ki barta ta ɗebo mana daman,aikin metakeyi a cikin gidan".hajara ta faɗa tana wurgo min wata uwar harara.
Cikin sanyin murya inna tace "To hibba kije amma Dan Allah karki daɗe"

"To" 

Kawai nace, hijab ɗinna na ɗauka da waya ta sannan na ɗauki bokatin ɗebon ruwan  na fita.
Ina fita na ajiye bokatin a kofar gida,na nufi tashi duk daba wani sanin garin nayi ba.
A ƙafa na ƙarisa tashan  wani shagon saida wayoyi na hango a gefen tashar
Na shiga na saida waya tavsannan na dawo cikin tasha.
Ajiyan zuciya nasaka yayin da hawaye ke zubowa daga idona,ina zan nufa yanzu?wanake dashi dazan je wajen sa?inama-inama ace innaje wajen umma zata fahimci irin raɗaɗin danake ji a cikin raina ta karɓe ni?.
Share hawaye na nayi dai-dai  lokacin da wani mutum ya ƙariso Inda nake tsaye yana cewa "Hajiya KATSINA ne?".


Lokacin ɗaya naji bakina yace "E",ba tare da yayi shawara da zuciya ta  ba.
"To bismilla ga can motar a can"
Na shiga motar daman mutum ɗaya ya rage motar ta cika ina shiga kuwa direban ya ja motar.
Tinda muka hau titi nake kuka har muka isa cikin katsina ta dikko ɗakin kara kunya gare Ku badai tsoro ba.
Tabbas mutanen katsina sunmin karan da bazan taɓa mantawa dashi ba a tarihin rayuwa ta.
Yaron Motan ne ya shiga tattaran kuɗin motan,yana isowa na zara daga cikin kuɗin waya ta dana sayar na bashi.
Sannan na fita daga cikin motar,ina ƙarewa wajen kallo a duk cikin rayuwa ta ban taɓa ko mafarki zuwa katsina ba,sai gashi yau a dalilin maraici nazo.


Mahaifiyata ta kasa janmu a jikinta ta riƙe mu duk daɗi Duk wahala,yayin da dangin uba suka Gaza Samar min da kwanciyar hankali.


Haƙiƙa maraici cuta ne musamman na uba.Furcin baffa na tino"MATUƘAR KINA ƘAUNAR KI CIGABA DA ZAMA A CIKIN GIDAN NAN TO SAI KIN AURE NAZIFI".


A hankali nace yayin da hawaye kebin fuskana "Baffa nabar maka gidan ka".


Sannan wani kuka Mai ƙarfi ya kubce min nan na zauna cikin tashar naci kuka mai isa ta.

      ________________________________________

Inna tana zaune har tagama tsintar waken bani ba alamata tace"Hajara ko zakije ki dubo hibba ne kar,adamu ya dawo bai sameta a gida ba kinsan faɗansa".


Harara Hajara ta cilla mata kafin tace"Kiji min inna da wata iriyar magana,hibban ƙaramar yarinya ce da inta fita sai annemota?Allah yasa ya dawo bai same ta ba komai ya mata ita ta jawa kanta".


Tana rufe bakinta Baffa ya shigo riƙe da bokatin dana fita ɗebo ruwa dashi.


Hamdala inna tayi tana faɗin"Adamu yana ganka da bokatin ita kuma hibban ina ka baro ta?".
"Inna a kofar gida fa,naga bokatin na shigo dashi ita hibban ina taje?". Cewar Baffa
Cike da jimami Inna tace"Tun safe ta fita ɗebo ruwa har yanzu ba ita ba labarinta".

A harsale Baffa yace "uban wa yabata iznin fita?".
" Inna ce sai danayi nayi,a bari sai ka dawo ka nema mai ɗebo ruwan amma ta dage akan zataje".Hajara ta faɗa tana cillawa Inna  wata hararan.


Tsaki Baffa ya sake tare da ficewa daga gidan.Bai Daɗe ba ya dawo inna da duk ta gama rikicewa tace"Adamu aganta?".
Ajiyan zuciya ya saka kafin yace "inna Hibba butulu ce,Hibba ba ƴar mutumci bane a yau nayi mamakin kasancewar ta ƴar yaya Sule domin ko kaɗan bata gado halinsa ba".
"Adamu meya faru yimin yanda zangane meye Hibban tayi?".



Sai da Baffa ya numfasa sannan yace,"Inna Hibba guduwa tayi yanzu dana fita wani yake shaida,min ya ganta a tasha kuma yaga shigarta mota".
Salati inna ta saka tana kuka tana faɗin"Adamu kagani ko sai dana gaya maka ka haƙura da maganar auren da yarinyar nan amma kaƙi,to yanzu ga abinda kajawo mana marainiyar Allah ta'ala".
Cike dajin haushin maganar inna hajara tace"Haba!inna ya zaki daura masa laifin daba nasaba taje ai duniya ce tafi gabaruwa iya jima".




 *********************************


Tunda na sauƙa a tasha dana gama kuka na,na tashi na hau tafiya.
Har aka ƙira sallan la'asar mai tallan pure water na tsayar na saya domin nayi alwala nayi salla,gefen zani na na since zan bata kuɗin ruwanta.
Naga babu kuɗi salati nasaka tare da sake dubawa amma babu kuɗin ba alamar sa.
Miƙa mata ruwan nayi ina cewa,"Kiyi haƙuri banga kuɗin nawa ba".
"La ki riƙe kawai ba komai ki bar kuɗin",nace "nagode".


Tafiya na cigaba dayi ina tinanin a ina na jefar da kuɗin nan,ga wata masifaffiyar yunwa dake nuƙurƙusa na.
Hawaye ne suka fara tsiyayowa daga idona saura kiris wani Mai keke ya bugeni,sai daya rurrugamin ashar kafin ya wuce.
Hawayen danake yi ne,suka tsananta gefen wani shago saloon na zauna nayi alwala sannan na shimfiɗa ɗan kwalina nayi salla akai.


Na kuma cigaba da tafiya bansan inda zan nufa ba.Yunwa nakeji tamkar zan mutu ga wani masifaffen ciwon kai daya dameni ina tafiya ina haɗa hanya kamar bugaggiya,ina zuwa dai-dai wani gidan cin abinci na faɗi na suma.


Nan jama'a suka cika a kaina aka shiga dani cikin gidan abincin,aka bani abinci naci sannan na soma dawowa cikin hayyacina.


Wata matace Mai gidan abincin tace"Baiwar Allah ya kikejin jikin yanzu?"

"Alhamdulillahi nagode da taimakon ki amma naso ace kin barni na mutu".



Cikin sauri tace,"Subhanallahi! baiwar Allah meya miki zafi cikin dunyia har kike wannan fatan akanki?".


Hakanan kawai naji zuciya ta bata nutsu da in samar da ita labarin rayuwa ta ba.


Shiru nayi tare Sunkuyar da kaina ƙasa,ta dafa kafaɗa tare da faɗin"Ƙanwata ki sanar dani abinda ke damunki ƴar-uwar ki ce ni mace".

Idona fal da hawaye nace,"Ki taimaka min domin Allah badan nasanar dake labarin rayuwa ba ta".
"Wani irin taimako kike so?".

"Wajen dazan zauna shine damuwata a yanzu."na faɗa inajin wasu sabbin hawayen nabiyo kunci na.
Sai datayi Jim kafin tace,"Zan taimaka miki zamuje dake gidana in mijina ya amince ki zauna shikenan".
"Nagode Allah yasaka da alkhari".

"Amin ya sunanki?"

Nace" HIBBA" ita kuma tace "sunan ta Amina".


Haka muka zauna a shagon har yamma sannan muka tafi gidan ta dake unguwan fayamasa.
Tun kafin mu isa ta shaida min tanada abokiyar zama balaraba da ɗanta ɗaya kabir tamin kashedi sosai,akan na kiyayi shiga harkan Balaraba da kuma ɗanta Kabir.
Muna isa gidan muka tarar da mijin anty Amina yana tsakar gida yana alwala saboda ƙiraye-ƙirayen sallan magrib da aka fara.


UWATACE SANADI

Tsarawa/Rubutawa

        ©Maimunah Tijjani Iyam


______________________________


Page 1⃣2⃣



Da sallama muka shigo ko sallamar bai amsa ba,yace"amina wannan kuma wacece?".

Nan anty amina ta shiga bashi labarin yanda muka haɗu.Miƙewa tsaye yayi tare da ƙwalawa baralaba ƙira yana cewa"fito ki tayani ganin ikon allah".

"Malam meye faru?",ta faɗa tana fitowa daga ɗakin.

" Amina ce ta kwaso mana wata gayyar tsiya dubeta".ya ƙarishe maganar yana mata nuni da inda nake tsaye.

kallona balaraba ta farayi from toes to head.Kafin tace"baiwar allah ina iyayenki?".

A hankali nace"suna nan",

"To maza-maza ki fice daga gidan nan kinada iyaye ki,barosu ki zauna damu.malam wannan yarinyar nan ba mamaki cikin shege tayi iyayen suka koro ta",


Wani zafi naji a raina furcin balaraba sun soki zuciya ta,bansan sanda hawaye suka fara gosilo a fuska na ba.

Roƙon sa  anty amina ta shiga yi daya barni na zauna,sai daya kafa mata sharuɗa kan zata ɗauki nauyin ci da Sha na.


Ta yadda itama balaraba kashedi tamin akan,kar nasake na shiga harkan ɗanta KABIR, ɗakin anty Amina muka shiga.
Kallo ni tayi tana cewa" Hibba na roƙe ki dan girman allah ki dubi darajan taimakon dana miki ki kiyaye kanki daga shiga harkan balaraba da ɗanta,har ki zamo silar tarwatsewar aure na".


"In sha allah Anty zan kiyaye haka".


"Yauwa ki tashi kiyi alwala kiyi salla".


 Ta nunamin banɗakin dake cikin ɗakin na shiga nayi alwala nafito nayi salla.


Ina zaune a inda nayi sallan nace"Anty Dan allah zanyi ƙira da wayanki inbazaki damu ba?".

Cikin sakin fuska ta miƙomin wayar sannan ta fice daga ɗakin.


Numbern yaya Fawas na saka daman na haddace ta akaina,na shiga dialing numbern.

Inna ƙira caraf!yaɗaga inajin muryansa na fara hawaye to ma mezan faɗa mishi?nace masa na baro gida kenan saboda baffa zai aurar dani?ko kuma ince mishi na shiga duniya?saboda za'amin auren dole ko kuma saboda baffa ya dakatar min da karatuna?.

Kashe wayar nayi ba tare dana mishi magana ba,muryarsa ma kaɗai danaji yasamar min da kwanciyar hankali.

Kaina na kifa akan gwiwowina ina rusar kuka,tare da tinanin rayuwar dazan tsinci kaina anan gaba.



__________________HABIB__________________



Ta bangaren habib kuwa rashin samuna a waya,da kuma rashin dawowata makaranta da bashir ya sanar dashi ban yi ba yasashi cikin tashin hankali.

Kwance yake akan bed ɗinsa a part ɗinsa a gidan uncle suraj,yana dialing numberta kamar kullum yauma switch off aka ce masa,cigaba yayi da dialing numbern har izuwa lokacin da yasira ta shigo ɗakin.ko ƙaran shigowarta  baiji balle sallamar data shigo dashi.


Gefenshi ta zauna tana bubbuga pillow daya ɗaura kansa a kai tana cewa"hamma!hamma!!hamma!!!".


Figigi ya tashi ya zauna ya haɗe rai yana cewa" wai ke ban hanaki shigo min ɗakin ba sallama ba".

"Ayya hamma wallahi nayi sallama sai dai inbaka ji dan na shigo na tardaka tanata tinani". Yasira ta faɗa tana ƙoƙarin zaman gefen shi.

Dafe kansa yayi tare da furzar da iska daga bakinsa.

Sosai yasira ta fuskan ta akwai abinda ke damunsa tace" hamma kana cikin damuwa meyake damunka hamma na?".


"Ba komai ƙanwata gajiyace kawai"

A nitse tace" hamma zanfi yadda inkace min bankai inji damuwarka ba akan kace min ba komai".

Cike da ƙosawa da sauraron surutunta yace" yasira nace miki ba komai ko",


Miƙewa tayi tana cewa"okay tinda bazaka faɗa min ba hamma bari naje na faɗawa ummi watakil ita ka iya sanar da ita".

Riƙo hannunta yayi yana cewa" zauna".


Ba musu ta zauna tare da cewa" to inajinka hamma meye damuwarka?".

A hankali ya dogo idanunsa dasu ka rikeɗe suka koma jajir ya zuba mata tare da cewa da ita ba komai.

Ajiyan zuciya ta sauƙe kafin tace "hamma nasan ni bazan iya maka maganin damuwarka ba amma ban iya tayaka da addu'a,please hamma na meke damunka?".

Nan fa ya sanar da ita komai har da yanda ya daina samun na a waya,gashi Dr bashir yace masa ban dawo school ba sannan sun sa Faisal ya ƙira.yaya fawas amma wayarsa shima kullum a rufe.

Ya ƙarishe maganar tare da sassauta muryarsa sannan ya cigaba da cewa.

"Yasira bazan boye miki ba,Innason hibba kuma zuciya bazata iya jure tashin taba duk ban furta mata ba,ina tsoron duk abinda zai sanyan ku tashin hankali mussamman ace nine sanadinsa,ina tsoron na rasa hibba domin muddin hakan ya faru zaku iya rasani".

Tun daya fara maganar ba abinda yasira,take yi illa hawaye tabbas ta tausayawa ɗan-uwan nata matuƙa.


Cikin kulawa tace" hamma kaje gidansu mana".

" Yasira naje sau babu iyaka amma aka ce min sun tashi tun bayan rasuwar babanta".


Riƙo hannunsa tayi tace"hamma bi'izininlahi ta'ala zata bayyana sannan zata amshi soyayyarka".


Ajiyan zuciya sannan yace"allah yasa hakan ƙanwata,Dan ina fargaban saku iya rasani matuƙar na rasa hibba".


Haka tayita kwantar masa da hankali har tasamu ya fito yaci abinci.


Haka abubuwa suka yita tafiya duk weekend habib sai yaje damaturu yayin dashi da Dr bashir zasu garzayo potiskum,amma kullum bacigaba.


Harsu shahida suka tambaya ko muna waya dasu,suka ce tun gaishewar rasuwar Abba dasu min basu sake samuna ko a waya ba.

Ranan habib yana office ya dafe kansa ga tulin files ɗin dasuke gabansa,amma ya kasa dubasu,shigowar PC ɗin sane  ya  sashi ɗago kansa.

"Sir waɗannan turawan masu company sarrafa alkama a chine ɗinnan sun iso har na shirya meeting ɗin". PC ɗin ya faɗa yana kallon shi.

Miƙewa habib yayi ya nufi ɗakin taron nasu koda yaja ma yakasa tsinana wani abin kirki,a haka suka tashi gida ya nufa.

Yana isowa ya nufa direct part ɗinsa ya shiga ya wuce bedroom kan bed ɗinsa ya faɗa yana sauƙe numfasha a hankali.


Yakai kusan 30min a haka sannan ya tashi ya shiga bathroom yayi wanka, sannan ya fito ko mai bai shafa ba ya zara doguwar rigar jallabiyarsa fara tas! sannan ya fito ya shiga part ɗin ummi.


Tare da uncle suraj yasame su sai yasira data zubawa makeken tv ƙiran plasma dake manne a cikin wall ɗin  parlon, ido tana kallon wani series(hawas Maya)da ake haskawa a mbc Bollywood.

Yana shigo da sallama ɗauke a bakinsa,ummi ta amsa sallamar gefen yasira ya zauna yana yiwa uncle suraj sannu da hutawa.

Sai daya tambaye shi ya companies ɗin?yace" alhamdulillah daddy komai yana tafiya yanda akeso".

"Masha Allah I hope kana shan magungunan ka". Daddy ya tambaya cike da kulawa

Sai da yayi ƙasa da kansa sannan yace" E daddy Ina sha".

Kallon yasira yayi yanda ta zubawa tvn ido ko kiftawa babu,da alama tana enjoying kallon series ɗin.


"Wai ke  yanzu kinajin abinda suke faɗa ne kika wani zuba ido haka?".

Dariya tayi sosai sannan tace" hamma ina ganewa mana,kaima inkana kalla yau da gobe zakana fahimtar me suke faɗa".ta ƙarishe maganar tana mai da kallonta ga tvn.

Murmushi yayi kafin yace"Gobe sayyid zai dawo ai munyi waya dashi ɗazu yake faɗamin sun sama hutu zaiyi maganinki inya dawo ai kinsan halinsa sarai".


Sayyid lecturer ne a freedom college of nursing and midwifery kano,ita kuwa yasira tana shekaran ƙarshe a alƙalam university dake cikin katsina nan.inda take karantan biological science.

Zaro idanu yasira tayi tana faɗin "na shiga uku hamma kawai kace mugun zai dawo".

Nan ta miƙe ta nufi upstairs tana ta faman gunaguni.

Dariya habib yayi sosai  irin shirmen yasira wasu lokatan sukan mantar dashi damuwar dayake ciki,suma su ummi da daddy dariyar suke kafin ummi tace.

 "Zai dawo zaki maimaita a gabansa".

Miƙewa daddy da habib sukayi,saboda ƙiran sallan magriba da'aka farayi,habib na Miƙewa yaji kamar wani Abu ya tukare masa zuciyarsa.

Nan da nan yaji ƙirginsa ya masa nauyi da wani jiri dayake ɗibarsa,tangal-tangal yayi kamar zai faɗi daddy ya riƙi shi da sauri yana faɗin"habib lafiya?".


Wani tari Mai ƙarfine ya sarƙe sa cikin ƙanƙani lokaci Duk yafita hayyacin sa.

Ummi ta kawo masa ruwa,daddy ya basa sannan tarin yaɗan lafa daddy yace.

"Tashi mu tafi asibiti habib". Ya faɗa yana ɗago habib ɗin

"A'a daddy ai naji sauƙi ma".


Badan sun so ba haka suka barshi dan basa son takura masa.

 
Haka suka tafi masallaci suna dawowa ya wuce part ɗinsa,wanda ya sama rakiyar daddy.

Sam bacci yaki ɗaukar sa har aka kira assalatun asuba,yanda yakejin jikinsa  bai jin zai iya tashi balle har ya fita.
A bedroom ɗinsa yayi,salla a zaune ma ya yita sannan ya koma ya kwanta kan bed ɗinsa.
ƙarfe 9:00am dai-dai na safe Sayyid ya dawo cike son ɗan nasu Daddy da Ummi suke amsa gaisuwar dayake musu,ita kuwa Yasira tana maƙale jikin Ummi kamo kunnenta Sayyid yayi yana cewa.

"Wato kin gani shine ko gaisuwa babu?".


Tunin Yasira ta saki ihu tana yarfa hannu,tana faɗin "A'a Hamma Sayyid kayi haƙuri,wayyo Ummi zai tsinkemin kunne".


Saketa yayi yana dariya tare da faɗin" ina hamma fa?".
"Yana part ɗin sa" cewar ulUmmi
Part ɗin Sayyid ya nufa yana tura kofan bedroom ɗin,ya hango shi kwance a ƙasa cikin jini da duk alamu aman jinin yayi.

A kiɗime ya nufoshi yana kiran sunansa,da ƙarfi"Hamma!Hamma!! Hamma!!!".


Wayarsa  ya  ɗauka ya kira wayar Daddy yana faɗa masa halin dayazo yasama Hamma Habib ɗin a ciki.


Dukkaninsu suka shigo bedroom ɗin, ɗaukar shi Daddy da Sayyid sukayi  suka wuce asibiti dashi.

Emergency aka shiga dashi yayin da Yasira keta shirga kuka hakama uUmmi,sun kai kusan 1 hour suna jira,kafin likitan ya fito yace.

"Daddy da  Sayyid su same shi a office".


Ummi da Yasira kuwa ɗakin da'aka shiga dashi suka shiga,yana kwance yana bacci ansa masa robar ruwa.Fuskarsa tayi fayau da ita sai ɗan raman dayayi.


Kallon likitan Daddy yayi yace" doctor meyake damunsa?".

Sai da likitan yayi Jim kafin yace,"Damuwa ce ta masa yawa kuma matuƙar ya cigaba da zama a haka zuciyar sa tana cikin barazana,dan zata iya bugawa ako yaushe".

Sai da likitan ya numfasa sannan ya cigaba" Akwai abinda yake so Wanda bai same shi ba".


Mamaki ne ya cika daddy fal! yana maimata,furcin likitan "wai damuwace ta masa yawa".
Miƙewa yayi ya fice, ba tare daya ƙarisa jin sauran maganan da likitan ya cigaba dayi ba.
Sayyid ma fitowa yayi daya gamajin sauran maganan da likitan ya faɗa musu yabi bayan daddy. 

Ɗakin da'aka kwantar da habib suka shiga,har yanzu bai farka ba.


Gefenshi Daddy ya zauna,ya riƙo hannun sa sannan ya shiga faɗin.


"Habib meyeke damunka a cikin wannan duniyan?mena gaza maka Wanda uba yake yiwa ɗansa?Habib ban barka kayi maraicin iyayenka ba domin na maye maka gurbin su?".
"Wai meyake damunsa ne?,meye likitan yace?".uUmmi ta shiga jero tambayoyin a lokaci guda.

 
Nan Sayyid ya faɗa mata komai.Kuka ta saka mai sauti tana cewa" innalillahi!da wani ido zan kalli Granny na gaza samarwa Habib farin-ciki"

Da ƙarfi ta furta "Habib meke damun zuciyarka?".
Dukkansu kuka sukeyi bamai bawa wani haƙuri.Fita Daddy da Sayyid sukayi masallacin dake cikin asibitin,nan kuwa yasira ta sama damar faɗawa mmi komai game da damuwar Habib ɗin.
Ta tausaya mishi matuƙar,su Daddy suna dawowa kuwa suma ta faɗa musu.
Tunda Sayyid ya sanarwa Granny ta ɗaga hankalin ta sai datazo,


Nan fa Daddy ya dage sai an fitar dashi waje domin sama masa ingantaccen lafiya acewar sa zuciya ba wasa bace.
Likitotin sukace masa ba sai an fitar dashi ba suma zasu bashi kyakykyawan kulawa.
Amma Daddy ya dage sai ya fitar dashi,dan tunda sukazo asibitin yau kwana uku kenan sau ɗaya yayi magana.
Nan ya shirya musu tafiya malesia domin kula da lafiyarsa,tare da Daddy da sayyid aka tafi.
Yasama kyakykyawan kulawa daga likitotin kasar,amma sun shaidawa Daddy cewa zuciyarsa ta taɓo.Dan haka a kiyaye ɓata masa rai.

Kwanan su goma sha shida aka sallame su,tare da kafa musu sharaɗin duk bayan wata uku Habib ɗin zai dinga zuwa ana duba lafiyar zuciyar tashi.

Yasama kulawar  ahlin nasa sosai har ya fara dawowa hayyacinsa,ƙoƙarin sa shine ya manta da hibba kodan farin-cikin iyayen nasa.

Daddy kuwa tunda yasira ta faɗa musu nice sanadiyar damuwar Habib ɗin.Ya kira Bashir suka tattauna akan zance,nan Bashir yasake sanar dashi wasu abubuwan daya sani dame dani.

Nan fa Daddy ya zubawa gidan TV da radio kuɗi anata cikiyata.dan a nasu zaton tare da Umma da kuma yaya Fawas muka tashi daga gidan.


   ___________________________________



Ina zaune a tsakar gida ina wanke-wanke,anty Amina kuwa ta tafi shago.

Kabir ya shigo tare da wasu abokansa uku."Ke ki kawomin abincina ɗaki". Ya faɗa da tsan-tsan izza.
Ko kulashi ban yi ba na cigaba da aukina,ya ƙaracewa "bakya jinane?,nace kikawomin abinci ko".

 
Sai a lokacin na ɗago tare da faɗin,"Amma ai kasan niba yar aikinku bace dazaka sani aiki ko?".

A harsale Kabir yayo kaina "ke ni kike faɗawa haka?",


"An faɗa maka ɗin".na faɗa ina ajiye soson wanke-wanken dake hannu na.


Mari ya shiga sauƙe min hagu da dama yana faɗin" shashasha to ko ita wacce ta kawoki gidan bata isa ina faɗa tana faɗa ba balle ke wawuya kawai,wacce zaman gidan iyayentaya gagare ta".


Yana gama faɗin haka ya shiga ɗakin sa yayin da  zugan abokan nasu suka rufa masa baya.

Dafe kuncina nayi ina hawaye, a hankali na maimaita furcin kabir"WACCE ZAMAN GIDAN IYAYENTA YA GAGARE TA".


Share hawaye na nayi cikin sanyin jiki na ƙarisa wanke-wanken sannan na dawo ɗaki nacigaba da sana'ata wato kuka,sai daf da magriba sannan anty amina ta dawo ko kaɗan ban bari ta fahimce wani Abu ba.


Washe gari da wuri anty Amina ta tafi shago,sannan nima na fito na kama aikin dana san ko sharafar mutuwa nakeyi sai nayi wannan aikin.

Share gidan sannan nayi wanke-wanke na wanke banɗaki.

Na koma ɗaki na kwanta,a hankali naji ɗumin hawaye nabin fuskana.Ajiyan zuciya na saka tare da kwantar da kaina akan pillown.

Haƙiƙa kowa da irin tasa ƙaddarar a rayuwa,mutuwa ta rabani da Abba ƙaddara kuma ta rabani da yaya Fawas.

"Ya rabb ka nufeni da cimma abinda na fito nema wato karatu,na cika burin Abba sannan na cimma ƙudurin yaya Fawas". Na faɗa ina share hawayen dake bin fuska ta.

Kamar daga sama naji balaraba na kwaɗa min kira,cikin sauri na miƙe na fito nace" gani".

Ba tare ta kalle inda na keba tace"ke hibba saboda tsabar rashin mutunci shine baki sharewa Kabir ɗakinsa ba?,bayan nasanar miki kullum kina tashi kizo ki share masa ɗaki".


Sanyayyan ajiyan zuciya na saka sannan nace"naga bai tashi daga bacci bane shiyasa ban shiga ba".

Muryan Kabir naji yana cewa yayin dayake fitowa daga ɗakin nasa yana faɗin" munafuka ni tun yaushe na tashi,zaki wani ce wai ban tashi ba".



"Yi shirunka basai ka ɓata bakinka ba ni nasan halinta tsabar munafurcine".


Cikin sanyin murya nace"kabir kaji tsoron Allah yanzu fa ka tash........."

Ban ƙarisa maganar ba Balaraba ta rufe ni da duka tana faɗin"shegiya munafuka acikin mu yawake miki ƙarya?".


Duka na takeyi tamkar tsohuwa ta sama shantu,tun ina bata haƙuri har maganar ma ta gagareni.

Anty Amina ce ta shigo tare da sakin salati,ta dakatar da balaraba daga dukan datake min ta hanyar cewa.

"Haba! Balaraba meye baiwar Allahn nan ta miki a dunyia?,karki manta fa itama ƴace ga wasu sannan ƘADDARA CE(littafina mai zuwa in sha Allah) ta rabota da iyayenta".


Cikin matuƙar ɗaga murya Balaraba take cewa,"To ni ina ruwa nace ina ruwa na.dakike cewa wai ƙaddara ce ta rabota da iyayenta, wayasan abinda ya rabota da iyayen nata".ta ƙarishe maganar tana wani huci.


Ɗagoni anty Amina tayi ta riƙo hannuna tana faɗin"sannu hibba",

A hankali na miƙe idona cike da hawaye nace"anty Balaraba Allah shine shaida na ban taɓa aikata,abinda kike zargina dashi ba sannan bashi ne silar barowata gida ba".

UWATACE SANADI

     Tsarawa/Rubutawa

          ©Maimunah Tijjani Iyam
           
 _____________________________



Page 1⃣3⃣


Taɓe baki Balaraba tayi tare da cewa, "ke akwai abinda zaki faɗa Wanda zan yarda shine, kuma wallahi yau ko sharafar mutuwa kikeyi a cikin gidan nan,sai kin sharewa kabir ɗakinsa."

Cikin zafin rai anty amina ta shiga faɗin" ya isheki haka balaraba ina so kisani daga ke har ɗanki HIBBA ba baiwa na kawo muku ba".


Tana gama faɗin haka taja hannuna muka shiga ɗaki.


Zaunar dani tayi akan kujera tare da riƙo hannuna,dukka biyu tasa cikin nata tace.


"Hibba ina mai baki haƙuri akan irin abubuwan da abokiyar zama take miki ita ɗanta ki cigaba,da haƙuri wataran sai labari".


Cikin kuka daya ci ƙarfi na nace"anty Amina zamana a gidan nan,inaga kamar ina ja miki magana nagode da taimakon da kikamin Allah ya saka miki da alkhairi,amma ni inaga kamar inna tafi rayuwar gidan aurenki zaifi samun kwanciyar hanaki".


Dakatar dani tayi da cewa"hibba ki daina faɗan haka,tun kafin kizo haka nake zaman haƙuri a gidan nan nidai ina mai baki haƙuri" ta ƙarishe maganar tare da sharemin hawayen dake bin fuskana.

Buɗe baki nayi da niyyar yin magana amma anty Amina ta hanani wannan damar.


"Tashi kije kiyi wanka,bari na haɗa miki ruwan zafi ko"anty Amina ta faɗa tana ƙoƙarin tashin daga kan kujerar damuke zaune.

Toilet ta shiga ta haɗamin ruwan zafi sannan ta fito,tana cewa "kije kiyi wankan ko sai kiyi salla kici abinci".


A hankali na tashi duk wata  gaɓa a jikina ciwo yakemin na shiga banɗakin,rufe ƙofar nayi na jingina kaina ajikin ƙofar ina wani irin kuka mai raunana zuciyar mai sauraro.


Shin haka daman rayuwar kowacce mace,yake cike da ƙalubale?ko kuma tawace kawai haka?.Allah sarki mutuwa ta tona min asiri,ta rabani da Abba.umma tagaza janmu a jikinta.


A lokuta da yawa ina tinanin,anya umma tun da muka bar gidanta ta taba tinaninmu kuwa?.Dalilin maraici yau gani a inda bansan kowa ba.


Ashe duk macen da bata gaban iyayenta, kallon ƴar iska ake mata kamar dai yanda balaraba take min?.


Nayi kuka sosai sai dana,tausayawa kaina na daina fuskata duk ta kunbura saboda dukan danasha da kuma kukan danayi.

Wankan nayi sannan nayi alwala nafito,anty Amina  natarar tazabga tagumi hannu bibiyu.


Cikin nutsuwa nace"Anty lafiya?"

A hankali ta ɗago kanta  tare da faɗin"hibba lafiya wani tinani nayi nace ko zamu fara fita shago tare".


"To anty" na faɗa ina barin wajen


Cike da farin cikin amsar Dana bata tace" yauwa hibba kinga duk zaki rage wannan tinane-tinanen da kikeyi".


Wucewa nayi ba tare dana amsa mata ba  nayi salla,sannan ta kawomin abinci tunda nasa abincin a gabana na kasaci.akan sallayan na kwanta nan take wani baccin wahala ya ɗaukeni.


Tamkar a mafarki najiyo muryan mijin anty amina,sai zazzaga masifa yake yi,a firgice na tashi na nufi wajen na tsaya daga bayan labulen ɗakin ina jiyo abinda yake faɗa.

Cikin matuƙar bala'i yake cewa"Amina na faɗa miki,tun ranar da yarinyar nan tazo gidan nan kar ta shiga harkan kabiru amma bataji bako?".


"Malam baka fahimce abinda ya faru bane yarinyar nan ba f.....".


Dakatar da ita yayi da cewa" to mezan fahimta ko ita balaraban data gayamin,zata miki ƙarya ne?nidai na faɗa miki ta fita harkan kabiru,dan wallahi in irin haka ya cigaba da faruwa to billahillazi a bakin aurenki".


A firgice anty Amina tace"saki kuma malam meyayi zafi?".


"Komai ma yayi zafi kabiru shi kaɗai nake dashi bazai yiyu ba yarinya tazo har gidan ubansa,tana cin arziki sannan ta nema ta takura mishiba,Ke baki haifamin ba kuma a nema kashe min Wanda nake dashi".


Kukan anty Amina ke dannewa ne ya sama nasarar fitowa"malam,amma kasan ai haihuwa ta Allah ce ko?kuma nima bai manta dani ba".


Tsaki ya sake yayi shigewarsa ɗaki,cikin sauri nima na koma na kwanta,inajin shigowar anty Amina ɗakin na rufe idona kamar mai bacci.

Zama anty Amina tayi tana kuka,inajinta amma na kasa tashi inbata haƙuri.

A hankali nima hawaye suka fara bin kuncina,Matar data taimake ni a lokacin danake matuƙar buƙatar hakan,ta ɗauke nauyin ci da Sha na lokacin da uwata ta gaza yin hakan a gareni,ta zauna dani zama na domin Allah duk da kasancewar bata san labarina.


Yau a ta dalilina,take zubda Ƙwalla,a hankali nace"ya Allah ka bani abinda zan sakawa wannan baiwar taka dashi.


       ___________ GANO________


Zaune baffa yake,a kofar gida wani Mai mashin yazo ya faka dai-dai kofar gidan.


Yaya fawas ya sauƙo daga mashin ɗin,ya nufo inda baffa ke kishingiɗe.bakinsa ɗauke da sallama.

Durƙusawa yayi ya gaishe da baffa cikin sakin fuska baffa ya amsa tare da cewa"mutan bauchin yakubu yaka baro gidan naku?".


Washe baki yaya fawas yayi kafin yace "baffa duk lafiya suna gaisheku".


"Madallah ka tashi ka shiga ciki kasha ruwa inna ma tana ciki".baffa ya faɗa yana ɓantarar guntun goron sa


Cike da rashin fahimta yaya fawas yace"baffa hibba fa?".

Gyaran zamansa baffa yayi kafin ya shiga faɗin " fawasu yau kusan wata biyu hibba bata cikin gidan nan".


Cike da rashin fahimta yaya fawas ya kuma tambayar sa"Baffa ko ta koma makarantar ne?Dan kullum ina ƙira wayarta,bana samu shiyasa ma nace bari nazo naga ko lafiya?".


Gyaran muryan baffa yayi,tare da bayyanawa yaya fawas duk abinda ya faru.

Wasu hawaye ne suka shiga zubowa daga idanun yaya fawas nan take ya suma a wajen,miƙewa baffa yayi yanata doka salati ya shiga gida ya ɗauko buta ya zuba mishi ruwa.


Dogon ajiyan zuciya yaya fawas yasaka baffa ya riƙeshi yanata jera mishi sannun har suka isa cikin gidan,hajara ta shimfiɗa musu tabarma suka zauna.


Cikin wani irin yanayi Mai matuƙar ban tausayi da wahalar fassarawa,yaya fawas yace.

"Kuma baffa duk an bincika wajen sauran dangi bataje wajensu ba?".

Caraf inna ta amshe zancen da cewa" gashi nan ba yanda banyi dashi akan ya haƙura da maganar nan ba amma yayi burus da maganata ai yanzu kaga abin daka ja mana".


"To inna to karatun nata fa?"furcin yaya fawas


Sai da inna ta gyara ɗaurin zaninta kafin tace" Adamu shine silar duk abinda hibba ta aikata sannan ka shirya fuskantar ubangijinka da laifin kasa sauƙe hakkin marainiyar da aka barma".

Sai data numfasa sannan ta ɗaura da cewa"Adamu sanin kan Kane ka ƙuntatawa,rayuwar  hibba dakai da matarka".

Ajiyan numfashi baffa yayi cike da nadaman abinda ya aikata yace.

"Inna ban taɓa tinanin hukuncin dana zartar akan hibba,zata iya barinmu saboda wannan ba".

Cikin zubda ƙwalla murya can kasa,yaya fawas ke cewa" baffa baka kyauta min ba,shin baka tinanin halin da hibba zata shigane?,ko baka tausayin tane?,jinin kace fa ita ƴar ɗan-uwanka ce fa".


Dafa kafaɗunsa baffa yayi yana cewa "fawasu ka kwantar da hankalinka in sha Allah duk inda,hibba take tana hannu mai aminci.Daga nan  ka wuce wajen mahaifiyar ku ka tambaya ko can hibban taje".


"Baza taje ba baffa kuma ko taje ma umma baza karɓe ta ba".cewar yaya fawas.


Ɗaga hannanyen sa sama yayi,ya shiga faɗin" ya Allah ka tsare min ƴar-uwata aduk inda take acikin duniya,ka amintar da ita cikin amincewar ka dawo mana da ita cikin aminci".


Yana gama faɗin haka,ya kifa kansa akan gwiwowinsa yana wani irin kuka Mai cike da tausayawa.

Miƙewa hajara tayi tana cilla musu harara tayi shigewar ta ɗaki..



  ______________HABIB_______________


Zaune yake akan kujera a cikin bedroom ɗinsa,na gidan granny sunzo gaishe ta tare dasu ummi,riƙe da wayarsa  yana dialing numberna.


Kamar kullum wayar a kashe yajita,dan uncle suraj har a companyn mtn ya bada numbern da zaran ansa layin akan waya zasu sanar dashi.


Cilla wayar yayi kan bed ɗin sannan ya kwantar da kansa,akan hannun kujerar.


Dafe ƙirjinsa yayi saboda bugun da zuciyar sa take masa,da sauri-sauri.

Lokaci guda yaji numfashinsa yana ɗaukewa,tari ne ya sarke shi sosai ƙirjinsa yaƙara dafewa da ƙarfi.


Tari yake yi sosai,har da jini ga numfashin sa daya ke barazanar barin gangar jikinsa,faɗowa yayi daga kan kujerar.


Dai-dai lokacin da ummi ta shigo ɗakin  salati,ta saka tana nufo inda yake a ruɗe ɗaura kansa tayi akan cinyarta sannan ta riƙo hannunsa tana murzawa.
ƙwalla nabin fuskarta,ta fara kiran sunansa "Habib!Habib!!Habib!!!".


UWATACE SANADI

    Tsarawa/Rubutawa
       ©Maimunah Tijjani Iyam

________________________



Page 1⃣4⃣


Lumshe idanu sa yayi a hankali muryansa can ƙasa-ƙasa yace"Ummi zan mutu zuciya na ciwo yake min".


Ummi da duk ta rasa nutsuwar ta tace "A'a Habib bazaka mutu ba,ciwo bashine mutuwa ba".
Wani razanan ne ihu tasaka ganin Habib  ɗin ya daina motsi,hakan yasa su Granny,Sayyid,Yasira da  kuwa iya shigowa.

Dan dama  sunzo  gidan  Granny ne dukkan sunzo gaisheta,Daddy kuwa yayi tafiya Japan.


Asibiti suka wuce dashi GENERAL HOSPITAL dake cikin garin damaturun emergency aka  shiga dashi.


Wayarsa dake hannun sayyid ne, ta fara ringing ganin sunan bashir ya bayyana cikin screen ɗin wayar.

Yasashi ɗaga kiran,nan yake sanar dashi halin da habib ɗin yake ciki,tambayarsa yayi"wani asibitine?"sayyid ya gaya masa.


Granny keta safa da marwa kofan ɗakin da'aka shiga da Habib,Yasira da Ummi kuwa sai kuka suke iya nata lallashinsu.


Within 15min Bashir ya iso cikin asibitin,Sayyid ya ƙira ya fito ya shigo dashi bangaren da aka kwantar da habib ɗin.


Zama Granny tayi,tana sauƙe ajiyan zuciya kafin ta shiga faɗin"Ban shirya nasaka ba Habib da farko na rasa halima,nasara mijina sannan na rasa dukkanin iyayen ka Habib a lokaci guda.ya Allah ka ɗauki rayuwa domin na tabbatar bazan iya jure rashin Habib ba".
Dafa ta Sayyid yayi yana cewa"haba! Granny inkina faɗin haka mu kuma ai sai  ki karyar mana da zuciya, In sha Allah Hamma bazai mutu ba ki daina kuka".ya ƙarishe maganar yana zama kusa da ita
 Yana rufe bakinsa likitan dake duba Habib ya fito,cikin sauri suka ƙariso gare shi suna tambayar ya jikin Habib ɗin?.
"Ku kwantar da hankalinku,Gajiya Ku biyo ni office".iya abinda likitan ya faɗa kafin ya wuce office ɗinsa
Binsa sukayi a baya har izuwa cikin office ɗin nasan.
Zama yayi tare dayin gyaran murya sannan ya fara faɗin"Hajiya Habib yana da wata damuwa a cikin ransa ko kuma ince akwai wani abu dayake so wanda bai samu ba,advice ɗin dazan baku a matsayinku na makusantan sa,Ku zauna dashi Ku tattauna ya faɗa muku damuwarsa inba haka ba hajiya I'm sorry to say za'a iya rasa sa gaba ɗaya".


Ajiyan zuciya Mai nauyi Granny ta sauƙe tare da cewa "to doctor ko zamu iya ganinsa?".


"E you can see him amma please kar ayi hayaniya dan hakan zai iya sa jinin sa ya hau".


Fita sukayi suka nufa ɗakin, da aka kwantar da habib ɗin.


Yana kwance yana bacci zama sukayi duk suna kallonsa, fuskar sa kaɗai ta isa mutun ya iya fahimtar girman damunwan dake cikin zuciyarsa.


"Yanzu yakuke ganin za'ayi?" Cewar granny.


Ummi tace " hajiya nidai gaskiya a tinani na,yabar ƙasan nan gaba ɗaya, dan inyaga ya nisanta da ita koyaga ya dena samun wasu labaru akanta hakan zai taimaka wajen rage tinaninta dayakeyi".

Tana rufe bakinta habib yafara buɗe idanunsa a hankali.


Dafe kansa yayi saboda wani irin nauyi daya yi masa,yana faɗin "wash!".


Cike da nuna kulawa Granny tace "sannun babban mutum,inane yake maka ciwo?".


Cikin ƙarfi hali yace"Granny kaina kaina ciwo yakemin".

Ƙara riƙo hannunsa tayi tana murzawa tace "sannu".

Bashir yace" Granny bari naje,na sanarwa doctor ya tashi daman yace inya tashi a sanar dashi".ya na gama faɗin haka ya fice.


Sannan suka dawo tare da doctor ɗin duba shi yayi sannan ya bashi maganinsa ya sha,cikin ƙanƙanin lokacin ya sama bacci.



Sai da dare sayyid ke sanar da daddy halin da habib ɗin yake ciki, faɗa daddy yayi sosai akan me  za'a ajiye shi a asibitin 9ja?.


Bayan yanada likitansa na mussamman dayake duba lafiyarsa a malesia.


Tun kafin ya dawo ya gama shirya fitar da habib izuwa malesia.


Haka kuwa akayi yana dawowa,ya ɗauke sa suka tafi malesian tare da sayyid wannan karan hadda granny kwanan su biyar suka dawo.



Amma shi habib ɗin acan suka bari shi daman sugama magana da granny akan zai zauna acan.Na wasu lokaci kafin likitotin sun ƙara tabbatar da samuwar lafiyar zuciyarsa.


Watansa uku acan bikin bashir ya taso da ƙyar granny ta amimce masa yazo.


________________________________________



Ina kwance a ɗaki anty Amina ta fita,unguwa naji balaraba na ƙwala min kira.


Na fito nace"gani".

Wasu tulin kayan wanki ta nunamin,tana cewa.


 "Ga kayan kabir nan yanzu ki wanke masa sannan inki gama kizo,zan aikeki kasuwa kimin cefa ne".


"Anty balaraba waɗannan kayan,ai bazan iya wanke su ayau ba Sai dai na raba su yau nayi,gobe ma nayi". na faɗa ina ƙarewa yawan kayan kallo.



Harara ta ɓalla min tana faɗin"ke zan sharara miki mari fa,ki kiyaye ni fa,a yau zaki wanke kayan nan gabaɗaya".

Nauyayyen ajiyan zuciya na sauƙe, kayan na ɗauka na fara wankin.


Tun safe har bayan la'asar ban gama ba gashi saboda anty Amina bata nan,ko abinci banci ba dama itace mai bani kuma yau bata nan.


Haka na wanke kayan tas!ko sannu  balaraba batamin ba balle tace min madalla.


Ina shara anty Amina ta dawo,nabar sharan naje na karɓi ledan dake hannun ta ina mata sannu da zuwa.


Cikin fara'a take amsa min,sannan muka nufa ɗaki.

Tsawa balaraba ta daka min tana cewa "munafuka inazakije?baki gama min aikin dana saki ba?".


Jikina na rawa nace"anty balaraba innayi salla zan fito na ƙarisa".


"Yimin shuru wato kinga ta dawo ko shine zaku shige ɗaki kuyi sana'ar taku ta gulma ko?".cewar balaraba


Ajiyan zuciya anty Amina ta sauƙe kafin tace"hibba shigo ɗaki kiyi salla,sannan kici abinci dan nasa tun safe baki ciba".


Cikin ɗaga murya anty balaraba tace,"Yo daman wa kika ajiye acikin gidan dazai bata abinci?".


Ba mu kulata ba,muka shige ɗaki anty Amina ta bani abincin data sayo min a hanya.


Naci sannan nayi salla,na fito na ƙarisa aikin.na zaune kan sallaya bacci ya ɗauke ni.


Washe gari anty Amina ta tashi da ciwon kai,don haka ko shago bata fita ba.


Kamar kullum ina tashi na fara wanke-wanke nayi shara sannan na wanke banɗaki.

Ina gamawa zan shiga ɗaki kabir yana fitowa daga ɗakinsa,wani harara ya cilla min mai cike da tsana lokacin da muka haɗa ido dashi.


Ƙofar ɗakin balaraba ya nufa,yana faɗin"mama!mama!!mama!!!".


Fitowa tayi tare da malam habu tace"lafiya kabir?".

Marairaice murya yayi kana yace" mama dan Allah kiga wani irin wankin da yarinyar nan tamin duk basu fita ba salon kawai ta dafarmin da kaya".


Kamar jira  malam habu yakeyi ai kuwa ya  rufeni da faɗa tare da cewa" ki ɗauki kayan nan yanzu ki kara wanke su.


Wasu hawaye masu zafi suka shiga rige-rigen fitowa daga idanuna,kayan na kwatsa na fara wankesu, inayi ina hawaye har kiran sallan azahar ban gama ba.


Fitowa anty Amina tayi tace "hibba kibar wankin nan ki tashi kije kiyi salla sannan kici abinci".


Miƙewa nayi naje nayi alwala sannan nayi salla,Anty amina ta ɗebo min abinci inasa abincin a gabana naji muryar balaraba sai ashariya takeyi.


Tana cewa "malam fito,kagane min ikon Mai sama yanzu na sauƙe abinci wani yazo ya ɗeba".


Malam habu yana fitowa yafara kiran anty Amina, tana fitowa ya hau ta da masifa.


Ta inda ya shiga bata nan yake fita ba,cikin sanyin murya anty amina tace "ayya malam a hibba fa na ɗebawa,naga tun safe take aiki acikin gidan nan kuma ban fita ba balle insayo mata shiyasa na ɗeba mata".


Zabga mata mari malam habu yayi hagu da dama,sannan ya ɗaura da jaddada mata cewa.

"Shin Amina ban faɗa miki nauyin ci da shan yarinyar nan yana kanki ba tun lokacin dakika kawo ta?,maza-maza ki wuce ki dawo da abincin nan".


Ina zaune a inda anty Amina tabarni ta shigo ta ɗauki abincin, daman ko hannu na ban saba.


Sannan ta dawo tace"hibba kiyi haƙuri,bari na baki ɗari biyu kije ki sayo wani abincin".


"A'a anty kibar shi ma banajin yunwar".


Bata kulani ba ta ɗauko kuɗin ta miƙomin ban mata musu ba na karɓa na fita.


Ina tafe ina hawaye wannan wani irin rayuwa ce?,komai ya faru dani UWATACE SANADIn zubar hawaye na.


Ina cikin tafiya wani Mai mota yayo kaina,kafin na kauce masa har ya iso gareni.


Fitowa yayi daga cikin motar yayo kaina cike da faɗa ya fara zagina.


Wata macece zaune agaban motar wacce bazan iya faɗin matarsa ce ko ƙanwarsa ba,ta fito tana ƙoƙarin hana shi zagi na.Ni kuwa ina tsaye na kasa ko motsi sai hawaye danakeyi.


Wani mummunan kallo ya jefomin yace "dallah dube ta fa ko haƙuri bata iya badawa ba".hannu ya ɗaga niyyar sauƙe min mari.


Cikin sauri na runtse idona,jin banji sauƙar Marin ba yasa na buɗe idona.


Wani mutum ne ya kama masa hannun daya ɗaga da niyyar mari na.


Ɗago kaina nayi da niyyar, gani ko wanene caf" idanuna suka sauƙa akan fuskan HABIB.


Zaro idanu nayi bakina narawa nake furta" habib".

Kallo ya tsareni da shi a hankali lips ɗinsa suka motsa tare da furta"HIBBA kece".

Juyawa yayi yana bawa Mai motan haƙuri, ni kuwa cikin sauri na tsara ta cikin mutanan dasuka fara tarowa a wajen na bar wajen.

UWATACE SANADI


      Tsarawa/Rubutawa
            ©Maimunah Tijjani Iyam


_________________________

Page 1⃣5⃣




Bayan wani shagon aski,na tsaya ina hangen habib sai bawa Mai motan haƙuri yakeyi.

Yana gama bashi haƙurin ya juyo inda yabarni tsaye sai dai,bai ganin awajen ba waige-waige ya farayi.

Tambayar mutanen wajen ya shiga yi ko akwai wanda yaga fita ta daga wajen?.

wani yace masa "ai ta daɗe da barin nan dama tare kuke ne?".


Da sauri-sauri zuciyarsa ke bugawa,tamkar zata fito daga cikin ƙirjinsa jingina bayansa yayi a jikin motarsa.


Sannan ya fara zamewa a hankali har yakai ƙasa ya zauna.


"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!".

Ya furtawa a hankali badan mutumin daya shaida masa yaga wucewa ta ba,tabbas da zaice gizo idanunsa ke masa.


Wayarsa ya ciro daga cikin aljihunsa ya ƙira drivern sa,ya faɗa masa inda yake yace yazo ya ɗauke sa,dan a yanda yake jin kansa yanzu bazai iya driving ba.


Ina tsaye bayan shagon naga tafiyar habib, wasu hawaye masu zafi suka fara bin kuncina.


Tabbas bayan Abba da yaya fawas,banida wani masoyi kuma jigo kamar habib,amma bazan iya bayyana masa kaina a halin danake ciki yanzu ba.


Da kyar nake ɗaga kafata har na isa gida kabir na iske a ƙofar gidan sai daya dallo min harara sannan yace.

"Ke kuma lafiya zaki dawowa mutane gida kina kuka?".


Ban kulashi ba nayi wuceta cikin gidan,anty Amina tana tsakar gida tana haɗa murhu na wuceta zan shiga ɗaki.



Muryar tace ta dakatar dani tana faɗin "hibba lafiya meya faru?".

Ban kulata ba dan ji nayi bakina ya kasa furta komai na shige ɗakin.


Ina shiga na ƙara sakin wani Sabon kuka,anty Amina ta biyo ni ɗakin.


Dafa ni tayi tare da faɗin" hibba lafiya ko kabir ne ya miki wani abun?".


Kai na girgiza mata alamar a'a,tace "to menene?",faɗawa jikinta nayi nacigaba da kuka na itama tana tayani.



Mucin kuka Mai iskar mu, Kafin anty Amina ta ɗagoni daga kwanciya danayi ajikinta.Hawaye fuskana ta fara share min tace "ya isa haka hibba meya saki kuka?".


 "Babu komai"na faɗa cikin kukan dayake shirin sarƙe ni.


Miƙewa tayi tana cewa"shikenan hibba tinda bakai naji matsalarki ba,sai ki cigaba da kukan".cikin sauri na riƙo hannun ta.

Nace"anty kiyi hakuri ki zauna".

Zama tayi tana fuskanta na tace "inajinki menene?".

Ajiyan zuciya nasaka yayin da hawayen danake ya tsananta.


"Anty tabbas ki riƙe ni amana zan sanar dake labarin rayuwata,inkiga zaki iya zama dani a haka zanso hakan in kuma bazaki iya ba nagode da taimakon dakika min a rayuwa".


Nan na sanar da ita,komai game dani ita kuka ni kuka ba mai bawa wani haƙuri.Har nagama hawaye bai bar zuba daga idanuna ba.

Anty Amina tayi ƙarfin halin faɗin" tabbas rayuwa cike take da jarabawa kala-kala,ban taɓa jin labarin irin naki ba hibba.Ban taɓajin inda uwa ta aikata irin abinda ummanki ta miki keda ɗan-uwanki ba Allah yajiƙan abbanki".


A zuciya na amsa da amin saboda kukan danakeyi yaci ƙarfina jin abubuwan nakeyi kamar yanzu suke faru,mussamman ranan da Abba ya rasu da kuma ranan damuka rabu da yaya fawas.

Kamo hannuna tayi,tasa cikin nata sannan tace.


"Hibba zan tsaya miki ki cigaba da karatunki,duk dama nima bawani ƙarfi ne dani ba gidan abincin na watace nake tsaye mata akai, amma gobe zanje gidanmu zan sanarwa mahaifiya ta inada dabbobi acan sai na tsayar nabaki kuɗin kiyi amfani dasu ki koma makarantar".



Kuka na saka Mai sauti,nace"anty nagode Allah yasaka da alkhairi".


"Ba komai hibba ai mun zama ɗaya yanzu".cewar anty Amina


Ranan kwana nayi ina kuka washe gari anty Amina ta shirya,zata tafi gidansu dake karamar hukumar daura.


Tare tace zamu je amma sai na tashi da matsanancin ciwon kai,hakan yasa ta tafi ita kaɗai.


Ina kwance a ɗaki ina rawar ɗari balaraba ta banko labulen ɗakin sannan ta shigo tana cewa.

"Nizan fita ki ɗaura min girki sannan kabir yana gida,duk abinda yace kimishiki tabbatar kin mishi".



Ban damu na sanar da ita halin danake ciki ba dan nasan,hakan bazai sa ta basa aikin da tace nayi ba.Dan nasan ko sharafar mutuwa nakeyi sai nayi aikin nan kamar yanda ta saba faɗa min hakan.


A hankali nace" to adawo lafiya".Bata kulani ba illa ficewa datayi  daga ɗakin tare dajan wani tsaki mai dogon zango.


Ina kwance naji kabir na ƙwala min ƙira da kyar na tashi na fito ina cewa" kabir lafiya?".


Harara ya watsa min tare da cewa" ki wuce ki ɗaura min ruwan wanka".yana gama faɗin haka ya koma ɗakinsa.


Wuta na haɗa na ɗaura masa ruwan sai daya tafasa sannan,na juye a bukati na nufi ɗakin kabir Kasancewar banɗakin sa acikin ɗakinsa yake.

A ƙofar ɗakin na tsaya ina cewa" ga ruwan wankan".

Daga ciki naji yana cewa "ki shigo ki kaimin banɗaki".


Ban kawo komai a raina ba na shiga ɗakin, kasancewar irin jan kunnen da balaraba tamin kafin tafita,koma yanzu banason na ƙara jawa anty Amina magana awajen malam habu.


Har kofar banɗakin na ajiye masa bukatin ɗin.Na juya zan fita naji kabir ya riƙo hannuna, firgice duk jikina ya ɗauki rawa na juyo.


Bakina na rawa na furta" kabir meye haka?".na fara ƙoƙarin ture shi daga jikina. 


Manna bayana yayi jikin bango ɗakin tare da riƙe dukkanin hanneyana biyu cikin hannunsa ɗaya,yayin dayasa ɗayan hannun nasa ya cire min hijabin dake kaina.


Zani ne ajikina kaɗai ɗaurin ƙirji kaina ko kwali babu,muryata na rawa nake faɗin.

"Dan Allah kabir kayi haƙuri ka barni da mutumcina".


Bai kulani ba illa wani irin kallon daya tsareni dashi da idanunsa da suka rikiɗe suka zama jajir.


Bakina narawa na ƙara cewa"kabir kayi wa girma Allah kayi haƙuri,na haɗa ka da girman allah karka ketamin haddina".


Duk magiyan danake mishi hakan baisa ya barni ba,cillani yayi kan gado yafara nufoni.


Kuka nake ina masa magiya ina ja da baya har na iso ƙarshen gadon,ina waige-waige na hango kwaskon turaren wuta cikin azama na ɗauko kwasko.


Kabir yana yiyowa kaina na buga masa kwaskon a goshinsa,cikin jin azaba yadafe goshin nasa da hannunsa.


Nan take kuwa jini yace salama alaikum ya fara zuba kamar da bakin ƙwarya.

Ɗago kansa yayi yana kalloni da idanusa dasukayi jajir,gashin kaina ya damƙo da ƙarfi ya cillani ƙasa daga kan gadon.


Ɗago ni yayi yafara wankeni da mari hagu da dama,sannan ya hankaɗe ni kaina ya bugu da window glass ɗin windown ya sari hannuna.


Wani ihu nasaka mai ƙarfi saboda azabar danaji.Dai-dai lokacin balaraba ta turo ƙofar ɗakin,daman kabir a buɗe yabarta.


Salati tasaka tare da jefawa kabir,wani irin kallo Mai cike da tuhuma ganin jinin dake ta zubowa daga goshinsa.

Cikin sauri kabir yace"wallahi mama ban mata komai ita ta shigo har cikin ɗakina".


Cikin zafin rai da wani irin hucin ɓacin rai balaraba ta nufo inda nake durƙushe.


Ɗago ni tayi tare da rufeni da duka ta ko'ina dukana takeyi tana faɗin.


"Hibba Allah ya isa tsakani na dake ɗan nawa ƙwalli ɗaya shi kikeson ki lalata min?".


Tana juyawa ta hangi bukatin  ruwan zafin dake ajiyen ƙofar banɗakin kabir.


Tureni gefe tayi na faɗi yayin da ita kuma taje ta ɗauko bukatin ruwan zafin.


Ina kwance a ƙasa ina fitar da numfashi sama-sama naji sauƙar ruwan zafin a jikina,wani irin azababben ihu na saka lokacin dana kejin ruwan zafin na ratsa duk ilahirin sasan  naman jikina.


"Munafuka daman ki shigo gidan da nufin lalatamin yarone?to Allah yafi ƙarfin ki,ki tashi kibarmin cikin gida kafin na illata ki".


Ƙafafuna na karkarwa na fara ƙoƙarin tashi,hijabina na saka sannan na tashi ina tafiya ina faɗuwa har na fita daga cikin gidan.

Wani irin azaba nakeji acikin jikina ƙafata ko takalmi babu haka nake tafiya.

Ga raɗaɗin da hannuna yake min inda glass ɗin ya yanke ni,idanuna basa ganu min komai sai baƙin duhu.duk gaɓoɓin jikina jinsu nake kamar ana sassara minsu.


Faɗuwa nayi daga nan bansake sanin inda kaina yake ba sai buɗe ido nayi na ganni a gadon asibiti.

Wani masallaci ne a cikin unguwan suka haɗa kuɗi suka ɗauki nauyin jinya ta.

Ina fita daga gidan su kabir balaraba ta kira malam habu yana isowa,ta fara cewa"malam Amina ta cucemu ta kawo mana annoba cikin gida".


"Balaraba meya faru?" Ya tambaya cikin zaƙuwa dason jin abinda zata faɗa masa.

Nan ta faɗa masa ƙarya da gaskiya wai inason na lalata musu yaro,har neman kashe shi naso nayi na fasa masa goshi.


A take a wajen malam habu,ya kira anty Amina a waya ya mata saki uku sannan suka wuce da kabir asibiti.



____________________HABIB______________


Tun lokacin da drivernsa ya ja motar suka nufi gida, tun acikin motar yaji zuciyarsa ta masa wani nauyi.


Suna isa ya wuce part ɗin ummi, tana zaune tare da yasira wacce yanzu dawowarta daga makaranta.

Driver ya shigo dashi,cikin Sauri ummi ta miƙe tana tambayar ko lafiya?.

Zaunar dashi driven yayi sannan yace "hajiya kirana yayi nazo na ɗauke shi saboda bazai iya driving ba, amma sai naga kamar bashi da lafiya shine na taimaka masa na shigo dashi".


Ummi  tace " mun gode".

Sannan ya fita kusa dashi ummi ta zauna tana cewa "sannu habib ina ka ajiye maganinka yasira ta ɗauko ma kasha?".


A galabaice yace"yana bedroom ɗina cikin fridge".

Cikin sauri yasira taje ta ɗauko maganin sannan ta ɗauko masa ruwa yasha.

Yana sha ya sama bacci kallonsa ummi takeyi sosai tabbas yana matuƙar azabtuwa.

Wayar tace ta fara ringing ganin sunana Granny ya bayyana cikin,screen ɗin wayar yasa ta ɗauka tare da kara wayar a kunnenta.

Cike da girmamawa ta gaishe ta amsa tare da cewa" ya jikonki nawa?".

 Ajiyan zuciya ummi ta saka kafin tace"Hajiya duk lafiya habib ne dai yanzu ciwon sa ya tashi amma yanzu alhamdulillahi harma ya sama bacci". Ummi ta faɗa tana kallon fuskar habib ɗin.

Salati Granny tasaka kafin tace,"ni daman tun farko banso wannan zuwan nasa da yayi ba,shine dai ya dage sai yazo auren bashir ɗinnan nafiso.Yayi zaman sa acan malesian a cigaba da duba lafiyarsa, yanzu ga irinta nima gobe zan taho katsinan".

UWATACE SANADI

Tsarawa/Rubutawa
      ©Maimunah Tijjani Iyam

________________________




Page 1⃣6⃣



Tun da Ummi ta sanarwa Daddy, ya taho Sayyid kuwa tunda Yasira ta faɗa masa halin da Hamman nasu yake ciki.


Yace shima zaizo amma Daddy yace "masa yayi zamansa,jikin nasa da sauƙi daman ciwo ne na lokaci guda kuma yanzu da sauƙi".

Nan yadage har sai da Daddy ya barshi nazo.
Granny kam fafur taƙi yadda da maganar da Daddy yake ce mata,na jikin nasa yayi sauƙi.
Sai datazo jikin Habib yayi sauƙi alhamdulillah,suna zaune akan dining sunayin break fast.
Daddy yayi gyaran murya sannan yace" Habib duk ganinka cikin jinya yasa mun mance bamu tambayeka abun daya tayar maka da ciwonka,wai meya faru ne?".

Ajiye spoon ɗin dake hannun sa habib yayi kana a sanyaye yace"Daddy ranan dana fitane naga hibba,da farko na zata gizo tamin kamar yanda kullum hakan take faruwa dani amma dana tambaye mutanen wajen,sai  Ku shaida min dasuga lokacin datake barin wajen".


Ummi tace"hakan yana nufin tana cikin nan katsina kenan?".


"To ya kamata naje na sanar da ƴan sandan dana bawa aikin binciko ta,su binciko ko'ina domin tana cikin nan katsina"cewar Daddy.
"Amma Daddy ko photon ta fa bamu dashi taya kenan insun ganta zasu ganeta?".

Kurɓan tea ɗin dake gabansa Daddy yayi kafin  yace"mama na munje wajensu da Habib, an ƙira Mai zane yana siffantar mishi ita shi kuma yana zana photon ta,to izuwa yanzu dai munada photon ta".


Ajiyan zuciya Granny ta sauƙe wacce daman tun zuwanta bata koma ba tare da faɗin" to Allah ya bayyana ta",dukkanin su suka amsa da amin.
Suna gama cin abincin Daddy ya biya ta station ya sanar dasu sannan ya wuce office.
Saura kwana uku auren Bashir Habib ya shirya tafiya damaturu,Tare da granny da kuma Yasira suka tafi.
Anyi wasu event kafin ɗaurin auren,ana ɗaura auren kuwa Granny tace Habib ya koma malesia.
Hakan nan ya koma sosai Daddy,Granny da Ummi suka masa faɗa akan yawan tinanin dayakeyi,har rubutu Granny tasa a dunga masa yana sha.
Daga can ya cigaba da kula da companies ɗinsu.


_____________________________


Nasha jinya sosai a asibiti tamkar bazanyi rai ba.
Wannan kuɗin da'aka haɗa mina masallaci dashi limamin masallacin ya cigaba da kulawa dani,dan nace musu "ni marainiya ce bansan kowa ba a garin".
A haka aka sallame ni daga asibitin sosai nayiwa liman godiya tare da matar dasuke ta dawainiya dani.

Sun tambaye daga nan ina zanje?,nace "musu zanje wajen dangina".

Fatan alkhairi suka min sannan na tafi,matarsa har da bani dubu biyu wai nasha ruwa a hanya. 

Ina tafe ina tinani bansan inda zan nufa ba,bansan sanda hawaye yafara bin fuska naba.

Izuwa yanzu kam nasan na jazawa Anty Amina, bala'i da masifa a rayuwar aurenta watakil ma izuwa yanzu malam Habu ya sake ta.
Wani kuka mai ƙarfi ne ya kubce min WAYYO ALLAH.wai shin tunda muka rabu da Umma ta sake tinanin mu kuwa?.
Ban ankara ba naji mota ta kwashe ni,Wasu maza biyu ne,suka fito daga cikin suna min sannu.

Tare da tambayata"ko naji  ciwo?"banji ciwo sosai ba kurjewa ne kawai,a hannuna da kuma ƙafata.
Asibiti muka wuce, akamin dressing wajen dana ɗan ji ciwon.
Ɗayan magidanci ne wanda nake kyautata zaton mahaifin saurayin,dasuke tare ne.
Sukaje zasu kaini gidansu na huta tukun sai  sukaini gidanmu,a gate ɗin wani tankamemen gida motar ta tsaya.


Ya dannan horn gateman ya fito ya wangale musu gate motar tashiga.
Cikin parking lot tayi parking fitowa sukayi,nima nafito a hankali ina ƙarewa girman gidan kallo.

Wasu mata biyu na hango sun nufo inda muke tsaye.
Tace"alhaji wannan itace yarinyar da sayyid ke gaya min a waya,kun bige da mota?".


"Itace wallahi".


Ta  kalloni cike da tausayawa  tare da faɗin "Ayya sannun ko".

A hankali nace"yauwa sannu ina wuni".ta amsa tana cigaba da cewa "YASIRA Ki kaita tayi wanka,tayi salla sannan kikawo ta taci abinci".


Wacce aka kira da Yasira ta amsa da" to Ummi",sannan ta riƙo hannuna muka shiga cikin gidan.
Wani ɗaki muka shiga ta nunamin banɗaki nashiga nayi wanka,Sannan ta bani doguwar rigar material na saka nayi salla.


Sannan muka fito falo ta kawomin abinci naci.
Cikin jimami yYsira tace"yaya Sayyid a ina abin yafaru".Nan ya faɗa mata komai.

Mahaifinsu yace"baiwar Allah a wani unguwa kike mu kaiki gida?".
Kaina na sunkuyar ƙasa nace"ni ba ƴar garin nan bace".
"To inane garinku?".Ummi ta tambaya

Har yanzu kaina na kallon ƙasa nace"ni ƴar potiskum ce na jahar yobe".

Ummi ta kuma cewa" To a ina iyayenki suke?".

"Mahaifina ya rasu mahaifiyata kuma bama tare da ita".na faɗa ina danne ruwan hawayen dake shirin zubo min.

Cike da tausayawa Ummi ke faɗin" Allah sarki baiwar Allah ko sanar damu labarin ki bamu da niyyar cutar dake".
Haka kawai naji zuciyata ta gamsu dana sanar dasu labarin rayuwa ta a karo na farko,anan na sanar dasukomai akaina.

Tun Dana fara sanar dasu Ummi ke hawaye,Yasira kuwa kuka  take sosai har da shashsheƙa.

"Innalil lahi wa'inna ilaihir raji'un", mahaifin nasu ya faɗa.

Sannan ya cigaba da cewa"baiwar Allah haƙiƙa labarin rayuwarki yana cike da darrusa masu yawa,amma kinyi kuskure dakika gujewa danginki domin ita mace a gurare uku ya kamata a sane ta gaban iyayenta,ko gidan mijinta inko ba'a same ta a ɗaya daga cikin waɗannan biyun ba to a same ta a kabari.zamu zauna dake tsakani da Allah
bamu da nufin cutar dake ni sunana ALH.SURAJ,ga mata HAJ.AISHA.Sannan ƴaƴanmu Sayyid da Yasira sai kuma yayansu yana malesia".



Ummi ta ɗaura da cewa"meye sunanki".

"Sunana Hibba".



Share hawayen fuskar ta Yasira tayi kafin tace "Ummi nima yanzu na sama ƴar-uwa,daman yaya Sayyid da Hamma  sai suyi ta haɗemin kai".


Dariya sukayi kafin  alh.suraj wanda naji suna ƙira da Daddy ya ɗora da cewa.

"Zamu zauna dake har izuwa lokacin da kike tinanin danginki,zasu haƙura akan maganar wannan auren da zasu miki sai mu maidaki garesu,ke kuma ki nema yafiyarsu na bujirewa umarninsu dakikayi,kuma in sha Allah za kicigaba da karatun ki".


Cikin zubda ƙwalla na matso na durƙusa a gabansa ina masa godiya.
Ummi tace"yasira ki kaita ki nuna mata ɗakin dazata zauna".


A hankali na Miƙe nabi bayan Yasira,ɗakin dake gefen nata muka shiga tace" Anty ga ɗakin ki sai ki duba inda abin da bai miki ba,sai ki faɗawa Daddy".
Murmushi na saka nace"ɗakin yamin".
"To masha Allah bari na barki ki huta".tana gama faɗin haka ta fice daga ɗakin.


Yasira ta girmeni sosai amma koda wasa bata taɓa kiran suna na kai tsaye ba,sai dai tace min Anty haka nan nima nake Kiran ta da anty.

Haka na cigaba da rayuwa,ƙarsashin kulawar alh.Suraj da iyalansa,babu tsangwama balle kyara.
Sosai na maida hankali na ga karatuna domin shine burin yaya Fawas ne a rayuwa zamantowa  ɗan jarida,dan haka na jajurce naga na zamto ƴar jarida.


Nacigaba da karatuna a Alƙalam university lokacin kuwa Yasira ta gama.
Kullum cikin maganar Hamman su sukeyi amma nikam ko a photo ban taɓa ganinsa,sai dai naji lokuta da yawa suna cewa suna matuƙar kama da Yasira.
Sau da yawa insuna waya da Yasira takance min nazo mu gaisa,nace "kibarshi kawa Yasira wataran zamu haɗu".

Bazan taɓa manta wani safiyar ranar litinin ba.
Tun safe muka tashi da shirye-shiryen dawowar Hamman nasun, girki kuwa munyisa babu iyaka.

Ƙarfe biyu Daddy da Sayyid, sukaje airport domin ɗauko sa.
are da Yasira mukayi arranging dinning table ɗin sannan muka wuce ɗakina mukayi wanka.

Ina fitowa daga wankar nawuce gaban dressing mirror, nafara shafe jikina da Mai,sannan na Zara doguwar rigar atamfar da daddy ya mana anko nida Yasira.
Ina ɗaura ɗan kwalina Sayyid ya shigo ɗakin yana cewa"hey ladies Hamma has arrived."
Da gudu Yasira ta fice tabi bayan Sayyid.Ina gama ɗaura ɗan kwalina feshe jikina da turare,sannan na wuce kitchen na ɗauko fruit salad ɗin damuka haɗa.

Na ɗaura akan tray sannan na nufi falo bakina ɗauke da sallama,Ummi ce ta amsa sallamar sannan cikin farin,-cikin daya kasa buyiwa a saman fuskan ta tace"To Hibba yau dai ga ɗan nawa kingan shi nan".


UWATACE SANADI

    Tsarawa/Rubutawa

           ©Maimunah Tijjani Iyam

_____________________________

Page 1⃣7⃣


Ɗauko kaina nayi ina satar kallonsa yana zaune agefen yasira ya lumshe idanunsa,yayin da yasira keta gabza masa surutu.

A firgice na saki trayn dake hannuna ya faɗi ƙasa nan take ya tarwatse.

Sayyid yace" Hibba lafiya?".A hankali Habib ya buɗe idanunsa dan ganin meyake faruwa.
Lokaci daya muka haɗa ido a razane  shima ya miƙe tsaye baki na rawa ya shiga faɗin  "HIBBA".


Hawaye nabin fuskata yana wanke hodar dana shafa nace "Habib".
Miƙewa Ummi  tayi daga inda take zaune tana cewa" Habib daman kasan Hibba ne?".
Wasu hawayen farin-ciki,ne suka fara zubowa daga idon habib yace"Ummi itace fa".
Sayyid cikin zaƙuwa  yace"hamma itace Wa?".


"Hibbata Sayyid itace".
Cike da al'ajabi dukkaninsu suka kallo ni ummi kuwa da murna da mamaki ya gama,cika fuskar ta tace"Habib kana nufin Hibba itace yarinyar dakake so?,wacce kayi jinya a sanadin soyayyarta?".


" Ummi itace".


Rungumoni Ummi tayi tana jero godiya ga Allah"Alhamdulillah Allah yakawo mana,sauƙin jinyar Habib har gida".shi kawai take mai-maitawa.
Runguma Habib ɗin sayyid yayi,yana faɗin na tayaka murna hamma.
Kallo ya tsareni dashi yana sakin ajiyan zuciya,dafe ƙirjinsa yayi da sauri tare da runtse idonsa da ƙarfi.
Ummi ta ke duban sa tace" habib lafiya?".
Ƙara dafe ƙirjinsa yayi da ƙarfi yana cewa"Ummi zuciya na yamin nauyi".
Cike da nuna kulawa dukkaninsu suke,masa sannu zaunar dashi Sayyid yayi ya kwanta akan kujeran tare da ɗaura Kansa akan cinyar Ummi.
Yasira na zaune akasa kusa da kujerar dayake kwance akai ta riƙe hannunsa.
Sayyid kuwa yana zaune a gefen Ummi sai sannu suke jera masa,cike da kulawa Ummi take kallon sa tare da faɗin" Habib anya kana shan maganinka kuwa?".


Cikin sanyin voice ɗinsa,marar hayaniya yace"Ummi ina sha".
"To yanzu ina maganin?".

 "Yana cikin akwatina".yabata amsa
Akwatin na gefena inda nake tsaye Ummi tace"na buɗe na ɗauko masa maganin".Na buɗe na ɗauko sannan na ɗauko masa ruwa.Na miƙawa Ummi dakanta ta bashi maganin yasha.Tashi yayi ya zauna tare da ɗaura Kansa akan,kafaɗun Ummi yana kallona yana sakin murmushi ƙasa-ƙasa.
Dai-dai lokacin da Daddy ya saƙo daga upstairs sanye da farar jallabiya,Dan tunda suka dauko Habib daga airport ya shige bedroom ɗinsa sai yanzu ya fito.
Tun kafin ya zauna,Yasira tace"Daddy I have a gist for you".


 "To inajinki auta ta".

"Daddy Anty itace wacce Hamma yakeso ɗinnan".cewar Yasira wacce bakin ta ya kasa rufuwa tsabar farin-ciki.
Zaro idanu Daddy yayi yana cewa"hajiya wai maganan Dasira haka yake?".
"Kwarai kuwa", Ummi ta faɗa tana shafo kan habib ɗin dake kwance  akan kafaɗar ta.Godiya Daddy ya farayiwa Allah, kafin ya shiga bayyanawa Habib yanda suka haɗu dani.

"Tabbas tun ranar dana  fara ganin hibba,nayi zargin itace domin a yanda habib ya siffanta ta,aka zana hoton ta kama ce sosai".
Take a wajen Daddy ya kira Granny yasanar mata tayi farin-ciki matuƙa.
Dining area muka wuce muka fara cin abinci spoon ɗin kawai naketa,juyawa a cikin abincin nakasa ci Ummi dake ankare dani tace" Hibba lafiya?".


Murmushi nasaka kafin nace"mmi lafiya kalau".Ina ankare da Habib sai satar kallona yakeyi,amma naƙi yadda mu haɗa ido dashi.
Muna gama cin abincin muka dawo falo yasira tace"Hamma ina tsaraba ta?".
Murmushi ya mata yace,"Ƙanwata tsarabarki nanan ɗauko min akwatin can".
Ya mata nuni da wani pink ɗin akwati taje ta ɗauko ta ajiye a gabansa.
Zungurin kanta Sayyid yayi tare da faɗin"kekam naga ranar dazakiyi hankali,mutumin dayaje jinya ina batun wani tsaraba kuma".

Tuno bakin  tayi tana matsowa kusa da Hamma Habib ɗin.Buɗe akwatin yayi ya fara Ciro dogayen rigunan abaya yace"Ƙanwata ga tsarabar ake kaɗai na sayo amma yanzu na fasa baki a wat.........".
Sai kuma yayi shuru tare da sunkuyar dakansa ƙasa yana ɗan Sosa ƙeya.
Cuno baki Yasira ta marairaice fuska kamar mai shirin, yin kuka tana cewa"Ayya Hamma na kayi haƙuri ka bani ".
Murmushi ya saka yayin dayake cigaba da ciro kayan yace"sai kiyi kuma nidai  na riga na faɗa miki".
Wasu turarurruka ma'abota tsada Habib ya ciro tare da matsowa kusa da Daddy, ya ladabtar da murya ya shiga faɗin" Daddy ga naka tsaraban".Cike da happy karɓa  yana sanya masa albarka.
Ummi kuwa mayafai Habib ya sayo mata ta karɓa cike da farin-ciki,shi kuwa Sayyid wani danƙareren agogo Hamman nasa ya sayo masa.
Sannan ya tura akwatin gaban Yasira wacce tun ɗazu take ta rarraba idanu ganin, Hamma ya kusa gama rabon kayan ita baice ga nata ba.
Wani murmushi mai sauti,ta saka tare da ƙara jawo akwatin gaban ta tana kara duba kayan.Kallo ni tayi tare da faɗin"Anty zoki ga kayan mana".


"A'a basai na ganiba kaya sunyi kyau masha Allah".na faɗa ina sadda kaina ƙasa
Kafeni Habib yayi da ido,ko kiftawa bayayi da sauri-sauri ƙirjinsa ke bugawa.Na ɗauke idona daga cikin nasa,yana ɗago kansa suka haɗa ido da Ummi.

Wata iriyar kunya ce ta lulluɓeshi cikin sauri ya tashi ya nufi upstair yana murmushi.Haka na wuni ranan duk banida kuzari maganar Ummi ce ketamin yawo cikin kwakwalwata"yarinyar dakeso,wacce kayi jinya domin soyayyar ta".
Washe gari ina kitchen ina haɗa breakfast.Habib ya shigo yana sanye da farar jallabiya har ƙasa,a ƙofar kitchen ɗin ya tsaya yana kallona.
Nikuwa sai aikina nakeyi,don bansan akwai mutum awajen ba.Ajikina kawai naji ana kallona,ina juyo wa kuwa muka haɗa ido da sauri na sunkuyar dakaina ƙasa nace"ina kwana".


"Lafiya".

Ya amsa yayin dayake shigowa cikin kitchen ɗin,yana cigaba da cewa" bari na tayaki aikin".

Ban kulashi ba nacigaba da aikin danakeyi.Wuƙa ya dauƙa yafara yanka albasa yana cewa" Hibba I see like kamar bakiji daɗin ganina ba?".
Ajiyan zuciya na saka kafin nace"na isa nace haka kai da gidanku,ince banji daɗin dawowanka ba."
Fuskanto ni yayi sannan a hankali ya shiga faɗin"Nasan jiya kinyi mamakin furcin Ummi ko?".


Kaina na ɗaga masa alamar e,Sannan ya cigaba da faɗin "Hibba" cikin kakkausar murya ya kiran sunan wanda hakan,ya sanyani ɗago kaina na kalle shi sannan na maida idona ƙasa.
"Basan ina sonki ba sai,lokacin dana dena samunki a waya na cigaba da ɓoye hakan a raina har izuwa wani lokaci,yayin da hakan yamin babban lahani a cikin zuciya dalilin hakan iyaye na suka turani malesia.Dawowa ta kenan nazo auren Bashir shine ranan muka haɗu dake duk lokacin dana tinaki sonki ƙara dawowa sabo yake a cikin zuciyana,dan Allah ko sau ɗaya ne ki furtamin kina sona".
Tsare shi nayi da ido hawaye nabin fuskana kamar yanda zuciya ta tasha faɗa min,tabbas yau na ƙara gaskatawa banida wani masoyi a cikin duniyan nan da ya wuce Abbana da yaya Fawas sai kuma Habib.
A hankali nace" Habib wataran zan furta hakan a gareka."
"Meyasa sa wataran?,sai bayan cutar sonki dake addabar zuciyana ta kasheni sannan ki furta, min Hibba meyasa bakya tausayi nane?" Yaƙarishe maganar tare marairaice fuska.
Ɗauke kaina nayi kamar yanda,shima naga ya ɗauke kansa daga gare ni,sannan ya maida hankalinsa kan yankan albasan dayakeyi.
Ajiyan zuciya na sauƙe tare da goge hawayen dake bin fuskana nacigaba da aikina.
Yana cikin yanka albasan wuƙan ya yanki hannunsa,sakin wuƙar yayi ta faɗi ƙasa.
Cikin sauri na iso inda yake sai yarfa hannun yakeyi first aid box na ɗauko masa yayi dressing wajen.


Ɗago kaina nayi ina kallonsa nace" sannu".

Cikin halin ko inkula yace"riƙe sannunki ai daman ba tausayina kikeji ba".yana gama faɗin haka ya fice daga kitchen ɗin.
Da kallo nabi bayansa yayin dayake ficewa daga kitchen ɗin,A haka na gama girkin na jeresu akan dining sannan na koma,ɗakina nayi wanka doguwar rigar material nasaka maroon color sannan na fito falon.
Sayyid na tarar zaune na gaishe shi ya amsa cikin sakin fuska,sannan na zauna tare da ƙurawa tv kallo.
Muna zaune Yasira ta shigo tace "ayya Anty harkin gama break fast ɗin shine baki tasheni na tayakiba?".
" Ba komai Anty Yasira ai naga kina baccine".
Sauƙowar Habib daga upstair,shi ya dakatar da yasira daga maganar dazatayi.
Sanye yake cikin shigar shadda Navy blue, hular Kansa ma da rantsin blue ajikintaSajen fuskarsa ya ƙara kwanciya luf asamar haɓarsa.A hankali yake sauƙowa daga upstair ɗin yana ɗaura agogo a tsintsiyar hannunsa.
Gaishe shi Yasira da Sayyid sukayi a tsare yake amsa gaisuwar tasu nikam daman mun gaisa a kitchen.
A tare Ummi da Daddy suka fito,dukkaninmu muka gaishe su suka amsa sannan muka wuce dining muka fara break fast.
Tun da muka fara cin abincin babu Wanda yayi magana,sai Habib da yace "Sayyid ka shirya zamuje wajen Granny".


 " To Hamma"cewar Sayyid ɗin.



Da haka muka gama cin abincin har compound muka musu rakiya,sai wani cin magani yakeyi ko kallon inda nake baiyiba suka tafi.
Suna isa cikin garin Damaturu direct new bura-bura estate suka nufa gidan Granny.
Wangale musu gate,gateman yayi suka shiga sukayi parking sannan suka fito suka nufi cikin gidan bakinsu dauƙe da sallama.
Ba kowa a falon sai house maid ɗin,Granny tana goge-goge ta rusuna ta gaishe su.


Sayyid yace "Granny fa?"tace "tana ɗaki tana salla".



"To in ta fito,kice mata mun tafi masallaaci".


Da to ta amsa sannan suka juya suka fita.
Masallaci muka nufa saboda ƙiraye ƙirayen sallan  la'asar da aka farayi.suna dawowa suka wuco part ɗin Granny tana zaune a falon suka tarda ita.
Cikin farin-ciki ta tarbe su tana faɗin"lale da mutan malesia zance ko katsina".


"Granny yanzu kam sai dai mutan damataru"
Gaishe ta sukayi ta amsa tare da tambayar su mutan gidan,suka amsa mata da duk lafiya.
Dinnig suka wuce ta zuba musu dambu wanda yasha kayan lambu da mai,ga lafiyayyan yaji.sosai sukaci abinci dan ba ƙaramin daɗi ya musu ba.
Suna gama ci suka dawo falo kwanciya sayyid yayi akan ɗaya,daga cikin kujuren falon ai kuwan nan baccin gajiya ya ɗauƙa shi.
Kusa da Granny habib ya zauna tana mata tausa a ƙafarta,kallon shi tayi kafin tace"Babban mutum Suraj ya sanar da ni yanzu haka,kuna tare da wannan yarinyar cikin gidansa sannan ya sanar dani labarin rayuwarta ko wannen mu shaida ne akan irin son dake mata,amma ba musan manufar ka  akan hakan ba.Babban mutum nasan  halin kane kyautatawa dan girman Allah ka riƙe yarinyar nan da amana sannan kuma ka daraja ta".
Sosai maganganun Granny suka ratsa ƙalbinsa a hankali yake furta.

"In sha Allah Granny zaki same ni mai biyayya da dukkanin  umarnin ki".

"Za muyi magana da Suraj ɗin,yanzu kam tunda mun samo maslaha ga matsalar sai  a maida ta ga dangin ta mu nema maka auren ta,a yi abun nan hankali kowa ya kwanta"cewar Granny.


Sosai Granny ta masa nasiha sannan ya fita yaje gidan Bashir nan,yake sanar dashi maganar dasu tattauna da Granny ɗin.Sosai Bashir ya masa murna tare da masa fatan alkhairi sai da yayi sallan magrib a can sannan ya dawo.
Part Granny ya wuce nan ya tarda ta,zaune ita da Sayyid zama yayi yana cewa Sayyid."Ka tashi kenan malalaci kawai daga katsina,zuwa damaturu shine duk ka wani gaji haka".

Murmushi Sayyid ya saka kafin yace"Hamma kawai kwantawa nayi na huta shine fa,baccin ya sace ni".
Shima Habib ɗin murmushi ya saka haka nan ma Granny,sosai suka yi hirar su sannan suka ci abincin suka kwanta da gobe da wuri zasu koma zai ajiye Sayyid a kano sannan shi ya wuce katsina.
Washe gari da wuri suka shirya  sukaci ɗan waken da Granny tayi musu,nan Habib yake tambayar Iya dan tun jiya dasuka zo bai ganta ba.
Granny tace"tayi wata tafiya ce  zuwa ƙauye,ƙanin ta yana aurar da ƴarsa".
Sun sama rakiyan Granny tare da kyawawan addu'o'i ta musu,a kano Habib ya sauƙe Sayyid domin aikin sa daya bari a can ɗin sannan ya wuce katsina.
Koda ya iso office ya fara wucewa sai da tashi sannan ya wuco gida,part ɗin sa ya wuce direct ya nufi bathroom tare da sakewa kansa,ruwa sannan ya yasa kaya mara nauyi sannan ya kwanta nan kuwa baccin gajiya tayi awon gaba dashi.
Sai dab da magrib ya tashi alwala ya ɗauro  ya fita izuwa masallaci,nan ya zaune har akayo isha'i sannan ya dawo ya wuce part ɗin Ummi.

Ina zaune ina karatun exam wanda muke dab da farawa cikin kwanakin nan,ya shigo falon ya zauna gaishe nayi ya amsa cikin sakin fuska yana faɗin"karatu akeyi  ne?".

nace "e".Yayin dana fara harhaɗa littattafaina zan koma ɗaki,na cigaba da karatuna  muryar sa ce ta dakatar dani  yana cewa"Fatima tsaya inason magana dake".


Wani iri naji duk nasan Fatima suna na ne,amma ba kowa ke ƙirana dashi ba.ba tare dana juyo ba nace"inajinka".

UWATACE SANADI

     Tsarawa/Rubutawa

      ©Maimunah Tijjani Iyam

______________________________

Page 1⃣8⃣



Tashi yayi ya iso inda nake tsaye,yana fuskanta ta sannan ya naɗe hannayen sa a bayan sa.


"Munyi magana da Granny yau sannan izuwa yanzun na tabbatar da sunyi maganar da Daddy,akan maganar zuwa gidan ku nema min auren ki.Banason na tirsasawa zuciyar ki domin nafi son ta amshe ni cikin daɗin rai shin kina isona?zaki iya aure na?".
Baki nane ya soma rawa na shiga faɗin"Habib idan nace banason ka to nima nasan ƙarya ne,amma yanzu  karatuna shine mafi muhimmanci a gare ni ,mu jingine wannan maganar sai zuwa wani lokaci"ina faɗin haka na wuce  ɗaki na barshi tsaye a wajen.
Koda na koma ɗakin gagara na karatun yayi,hakan yasa na rufe littafin na lula izuwa duniyar danafi samun nutsuwa a cikin ta wato tinani.Ina zaune a haka Yasira ta shigo tana cewa"Anty kina nan ashe ke muke jira ki fito mu ci abinci.
Tashi  nayi nabi bayan ta muka fito tare,muna gama cin abinci muka tattare wajen tare da Yasira,zan shige ɗaki Daddy yace"na zauna ya nason magana dani".dawowa nayi na zauna.
Ajiye jaridar dake hannunsa  yayi sannan ya shiga faɗin"Munyi magana da hajiya kuma gobe in sha allah muke son muje gidan ƙanin mahaifinki da kika labarta mana yana zaune a kano,domin nemawa ɗan mu Habib auren ki.Dan haka muke son kimana kwantance duk dacewa ke zamu je".
Wani zazzafar ajiyan zuciya na sauƙe kafin nace"Daddy ina neman alfarma a ɗan jinkirta zuwan har izuwan lokacin da zan kammala karatuna".
"A'a Hibba aure baya hana karatuna,kamar yanda karatun baya hana aure.Na miki wannan alƙawarin zaki cigaba da karatun ki koda bayan auren ki da Habib ne,sannan ni zan kashe miki ko nawa ne har sai kin cimma burin ki"cewar Daddy.

Ummi ce ta ɗaura da cewa"Hibba muna neman alfarmar ki ki taikama mana wajen cero rayuwar Habib amincewar ki muke nema domin baza mu miki dole ba".
Da mai zan sakawa waɗannan bayin allahn,wanda suka bada gudumawa wajen cikar buri na?zuciyata tace kawai ki amshi buƙatar su ki auri Habib hakan zai zamto silar samuwar farin-ciki a zuƙatan su,domin na lura farin-ciki sa shine nasu.


A hankali nace"na amince Ummi,nagode Allah ya saka muku da mafifin sakayyar sa".
Habib da tun ɗazu yake jiran amsar dazan bawa tambayar Ummi,ya sauƙe ajiyan zuciya yana hamdala.
Sosai Daddy da Ummi suke samin albarka,sannan suka shiga tattaunar maganar tafiyar da zamuyi goben.Nidai tashi nayi na koma ɗaki a hankali nake sauƙe numfashi sama-sama yayin da wani kukan da bansan na menene ba ya kufce min.
Ɗan kwalli na na jawo na toshe baki na dashi,ina ƙoƙarin hana sautin kukan nawa fitowa tashi nayi na rufe ƙofar ɗakin sannan na dawo na kwanta na cigaba da kukan.


Da wasu idanun zan kalli Inna?,mezan cewa Baffa?,banida ƙwarin gwiwan zan iya haɗa ido da yaya Fawas.watakil ma su zarge ni akan rayuwar dana yi a ba gida ba.
Naso sai na kammala karatuna na zamto  cikakkiyar ma'aikaciyar aikin jarida,sannan zan koma musu shiyasa ma ban taɓa yiwa su Ummi maganar son zuwa wajen su Baffa ba.
Kuka nayi sosai har ina ƙoƙarin shiɗewa ganin  haka ya sanya ni tashi nayi alwala sannna nazo na fara gabatar da nafila,ina iddarwa na shiga neman sau-saucin ƙuncin da zuciya take ciki a wajen mahaliccina,anan kan sallayar bacci ya kwashe ni.

Washe gari duk muka shirya dan hadda su Ummi da Yasira zamuje Sayyid kuwa zamuje mu ɗauke shi a kanon,tunda muka hau titi nakejin faɗuwar gaba ban san abinda zanje na tarar ba a gano.
Muna isa cikin kano muka wuce,freedom college inda Sayyid ke koyarwa muka ɗauke shi dan daman Daddy ya sanar dashi game da tafiyar.
Muna isa cikin garin gano nafara kwantatawa Daddy gidan Baffa har muka,ƙofar gidan bansan sanda hawaye suka fa bin fuska na ba sai  da naji Ummi ta dafa kafaɗata tana cewa"Hibba yanzu ba lokacin daya dace kiyi kuka ba ki share hawayen ki mu shiga".


Share hawaye na nayi sannan muka fito muka shiga cikin gidan dukkanmu har dasu Daddy,Inna muka tarar tana shiƙar wake,sallamar damuka shigo da itane ya sanya ta ɗago kanta tare  da sauƙe idonta kan ƙofar shigawa cikin gidan.
Sake kwaryar dake riƙe a hannunta tayi,tana waro idanunta wajen tare son gaskaka abinda ta gani bakinta na rawa ta shiga faɗin"Hibba ce koko mafarkin dana saba neyi ne?".
Nima tunin hawaye suka fara kai kawo a fuskata nace"Inna nice"na ƙarisa wajenta muka rungume juna.
"Hajara fito fito kiga abin al'ajabi"Inna ta faɗa tana ƙara rungumo ni jikinta.
"Haba!Inna wai meye ne kike ta wani kwaɗa min kira haka".Hajara ta faɗa tana fitowa daga ɗaki tare da gyara ɗaurin ɗan kwalin kanta.


"Wa idona ke nuna min kamar Hibba?wato kin gama yawan duniyar nakin shine yau kuma,kika tino inda muke ko bayan kinsa ƙafa kin fice babu wanda ya ƙara saki a kwayar idon sa".Hajara ta faɗa tana tsaida idanunta akaina.
Cikin mu ba wanda ya kula ta,tabarma Innaa ta ɗauko ta shimfiɗa mana muka zauna sannan suka shiga gaisawa dasu ummi.

Inna tace"Hibba waɗannan fa ban shaida su ba".
Kafin na bata amsa Daddy yace"Inna alkhairine ke tafi damu,amma kafin mukai ga sanar dake zanso ganawa da shi ƙanin mahaifin natan".

"Adamu tun farar safiya ya tafi gona,amma yanzu duk inda yake nasan yana hanyar dawowa"cewar Inna.
Tsaki Hajara ta saka sannan ta tashi tayi shigewarta ɗakin bayan ta gama cillo mana harara.
Muna zaune a wajen Naffa ya dawo muna haɗa ido ya saki fartanyan dake saƙale a kafaɗarsa yana cewa"Mamana ke ce koko gizo idanuna kemin?".
Tashi nayi naje na durƙusa a gaban sa hawayen nabin fuska na nace"Baffa nice  Baffa na dawo gare ka,ka yafe min na rashin bin umarnin ka nayi".

Nuni yamin da hannunsa kan na tashi daga durƙushewar danayi sannan yace"Hibba na yafe miki nima ki yafe min ƙuntatawa zuciyar danayi nasan nine silar komai daya faru dake,kaico! na dana gaza fahimta ƙuncin dana jefa zuciyar marainiya a ciki".


"Baffa na yafe maka",riƙo hannuna yayi kuka zauna akan tabarman sannan suka gaida dasu Daddy.
Nan Daddy ya shiga labarta masa yanda haɗuwar mu dasu ta kasance,har kuma da irin alaƙar dasuke son ƙullawa da dangin su.Sosai Baffa da Inna suka tausayawa irin rayuwar danayi a gidan Anty Amina.
Nan wajen suka tsaida magana akan yanda aure zai kasance suka sanya watanni biyu,Inna ce ke sanar da ni bayan bari na gida yaya Fawas yazo.Nayi kuka sosai lokacin da Inna ke faɗa min irin mawuyacin hali  daya shiga.
Baffa na roƙa nace ya kira shi yace masa yana neman sa,amma kar yace masa na dawo hakan kuwa akayi a wajen Baffa ya kira yana sanar dashi yanason ganinsa gobe.
Sosai Inna da Baffa suka yaba da  kamalar Habib da kuma halin dattaku irin na iyayen sa.Sai yamma sosai su Daddy sukayi shirin komawa amma nida Tasira zamu zauna muyi kwana biyu a wajen su Inna.
Muna zaune a ɗakin Inna nida Yasira munacin kwaɗon zogalen da Inna ta mana,Sayyid ya shigo ɗakin tare da faɗin"Hibba kije Hamma Habib yana kiran ki yana ƙofar gida".
Hijab ɗin na saka na fito shi kuwa Sayyid ya zauna ya faracin kwaɗon shima,a tsakar gidan na tarar da Inna da Ummi sunata firar su kamar dama can sun sa juna.
Yana zaune akan benci na hango shi na ƙarisa na zauna nisa dashi,wata leda dake kusa dashi ya miƙo min yana cewa"gashi waya ce ki riƙe a hannun ki dan kwana biyun daza kuyi a wajen su Baffa indinga samunki".
Kaina na kallon ƙasa ina wasa da yatsun hannuna waɗanda suka sha jan lalle wanda Ummi tasa aka mana kafin tahowar mu,nace"A'a nagode ka bashi bana buƙatar sa".
Tun farko zuwa na gidan su Habib Ummi ta saya min waya,amma na ajiye ta bana amfani da ita dan banda ma wanda zan ƙira da ita.
Ajiye min ledar yayi kusa dani sannan yace"gashi nan dai na ajiye miki,kuma nasa miki sim aciki na kuma samiki lambobin su Ummi da Sayyid a cik.....".
Saurin ɗago kaina nayi ina kallon shi wanda hakan ya sanya shi kasa ƙarisa maganar daya ɗauko.
Yaya Fawas na tino lokacin da ya sayo min waya ranar dazan tafi jami'a,irin kalmaman Habib ya furta min yana cewa"ya samin sim a cikin wayar kuma yasa lambarsa".
Saurin mayar da hawayen dasuka ciko idona nayi nace"nagode allah yasaka da alkhairi".
Sai daya saki taƙaitaccen murmushi kafin yace"amin ".
Wayarsa ce ta fara ruri ya ɗaga da sauri ganin sunan Granny ya bayyana cikin screen ɗin wayar.


Sai suka gaisa sannan take tambayar sa sun "iso lafiya?"don ta kira Daddy bai ɗaga ba"lafiya kalau Granny"ya amsa mata dashi.
Nidai maida hankalina nayi akan wayar da Habib ɗin ya sayo min,suka  cigaba da hirarsu ban ankara ba naji ya miƙo min wayar yace "ga Granny zaku gaisa".


A hankali na karɓi wayar na kara a kunne na duk kunya ta rufe ni,sallama nayi ta amsa sannan na gaishe ta shima ta amsa sannan ta shiga faɗin"Mun gode sosai kan irin halaccin da kika gwada mana,na amincewa ki auri Habib haƙiƙa kin ceto rayuwarsa a lokacin data dace Allah ya miki albarka".


A sanyaye nace"amin"sannan ta cigaba da cewa"Kuma duk sanda ya ɓata miki kizo gidan kiyi zaman ki abinki".
Dariya Habib yayi sosai kafin yace"Granny tun yanzu zaku fara haɗe min kai?".A hankali nace"nagode nima hajiya sosai allah yasaka muku da mafificin sakayyarku".
Da "amin",ta amsa dashi sannan mukayi sallama na miƙawa Habib wayar shima ɗin sallamar yayi mata sannan muka cigaba da hirar mu.
Har izuwa lokacin da Daddy da baffa suka fito,inna kuwa tanata ƙara jero wa Ummi godiya sai Yasira da Sayyid dasuke bayansu sosai Yasira ta yaba da yanayin garin.Tasowa nayi daga wajen Habib cike da kunya,naso wajen Ummi ina musu addu'ar Allah ya kiyaye hanya hakan nan ma Inna da Baffa ke musu bendir ɗin kuɗi Daddy ya ciro  daga aljihun sa ya miƙawa Baffa duk yanda yaso Baffa ga karɓi kuɗin ƙi yayi.Haka suka tafi akan bayan kwana biyu Sayyid zaizo mu koma katsinan tare dashi inna kuwa ta haɗawa Ummi tarkacenta,irin na tsofaffi su bushshen kuɓewa da kalwa Ummi ta karɓa tare dayi mata godiya.
Sai da muka daina ganin motar tasu sannan muka koma cikin gidan,ɗakin Inna nida Yasira muka shiga yayi da Innar ta shiga banɗaki,Baffa ma ɗakin Hajara ya shiga tana tsaye jikin ƙofar ya same ta sai huci takeyi.
"A'a Hajara na zata ai bacci kikeyi,shiyasa ban ganinki ba a waje ashe idonki biyu?"Baffa ya faɗa yana zame babbar rigarsa.

A wulaƙance ta kallo shi tare da faɗin"To mezan zo na muku?,Malam yanzu da hankalin ka ka ɗauki auren Hibba bakawa waɗannan mutanen?,wayasani ma ko dashi wanda aka fake da cewar anzo nema masa auren nata dashi suke yawon taziba.......".

Bata ƙarisa ba sakamaton marin da Baffan ya sauƙe mata a gefen fuskarta,ba zato ba tsammani.


UWATACE SANADI

     Tsarawa/Rubutawa

©Maimunah  Tijjani Iyam

_______________________________

Page 1⃣9⃣


"Hajara izuwa yanzu kam,bazan jure ba sannan bazan ɗauki duk wani ɓatancin da zaki gandanta hibba dashi ba.A da na kuskuren jefa ta cikin ƙunci amma bazan ƙarayin mai-maita wannan ba"cewar baffa.


Dafe kuncin ta hajara tayi tana faɗin"malam ni ka mara? ".

"E sannan ba ma keba duk wani mahalukin dazai tsaya a  gaba na,yana jefar hibba da mummanan kalami to irin hukuncin daya cancance shi kenan".

Yana gama faɗin haka ya fice daga ɗaki,alwala yayi kafin ya leƙo ɗakin inna yana cewa"ku tashi kuyi salla an kira".

Sannan ya wuce masallaci domin ƙiran sallan la'asar da aka farayi.

A tare muka fito da yasira muna cikin alwalan,hajara ta fito sai data tsaya ta dallo mana wata uwar harara sannan ta fice tare da sakar mana tsaki.ba wanda yace da ita daga uffan muka kammala alwalar muka shige ɗakin inna.

Hajara na fita gidan wata yayar taje wacce itama take aure a cikin ƙauyen ganon,tana zaune a tsakar gida tana tsintar yakuwa haraja ta shigo.

"Ƴan-uwa rabin jiki,hajara kece tafe da yammacin nan?".


Ƙarisowa hajara tayi ta zauna kafin tace"Adda barira wallahi nike tafe kuma matsalace ta kawo ni".


Ajiye yakuwar dake hannunta adda barira tayi gefen guda kafin tace"to hajara kekuwa wace matsala ce ta ɗago ki cikin wannan sakaliyar yammacin?".


"Wallahi adda kinga yau kawai muka wayi gari inna wannan yariyar da take ƴar wan malam ta dawo,bayan tsawon watannin data shafe bata gidan kuma wai harda wanda zata aura tazo tare da iyayen sa,shine fa daga nacewa malam ni ban yadda da dawowar wannan yariyar ba ya bincike ta shine ya wanke ni da mari nan a kunci na".


Hajara ta faɗa tana gyara zaman akan tabarmar kaban salati adda barira  ta shiga yi tare da faɗin.


"Oh ni barira ƴan iska basa ƙarewa a duniya,yanzu shi adamun ne ya mare ki akan wannan maganar?".


"Wallahi kuwa adda ni yanzu ma zuwa nayi ki haɗani da ɗaya daga cikin malaman da kuke hulɗa su,a mallake min shi ta yanda ko kara na ajiye zaiyi shakkar tsallake ta,tunda gashi yanzu tun ba'aje ko'ina ba ya fara mari na".cewar hajara.

Dafa kafaɗarta adda barira tayi sannan ta shiga faɗin"haba!ke kuwa ƴar-uwa sai kace ba jini taba ai ita wacce ya miki abun a dalillin ta,ita za ayiwa bashi ba sawa zamuyi asa mata tsanar shi yaron data kawo zata auren,taji duk duniya babu wanda ta tsana sama dashi sannan daga baya zai mu dawo kan adamun.Yanzu ki tashi kije gida zanzo nima".

Murmushi hajara ta saka kafin tace"yauwa adda ta".

Nan suka cigaba da hirar su,sai da akayi sallar magrib sannan hajara ta komo gida.

Muna zaune a tsakar gida hajara ta shigo kamar bataga mutane ne a wajen ba tasa kai tayi shigewarta ɗakin ta.ranar sosai mukayi hira da inna da kuma baffa.


Washe gari tare da yasira muka gyara gidan tsaf!sannan muka ɗaura girkin shinkafar da baffa ya  sayosai da muka gama komai sannan mukayi wanka,muna zaune a ɗakin inna ina karatun jarabawa wanda da zaran mun koma zamu fara.


Inna ta ɗago labulen ɗakin sai data washe baki sannan ta shiga faɗin"ku fito munyi baƙo".

Sai dana rufe littafin sannan muka fito tare da yasira.

Turus nayi ganin yaya fawas zaune a tsakar gidan shida baffa,sai a sannan na tina da cewa daman yau zaizo a hankali naji ɗumin wasu hawaye masu zafi suna bin kunci na.Shima ni ɗin yake ganin bakin sa na rawa ya furta"hibba".


"Yaya fawas".


Yunƙura yayi zai tashi sai kuma ya koma ya zauna,da ƙarfi ya runtse idanun sa hawaye na zubowa kusa dashi na tsuguna ina kamo hannun shi ya fusge.


"Yaya fawas dan Allah  ka yafe min kar  ka azababtar da zuciya ta ta hanyar yin fushi dani".

Numfashi ya saka mai ƙarfi wanda ya tafiyar da kukan daya ke kafin yace.


"Ummul-khair kin sani cikin wani hali,a ko yaushe zuciya ta kan nuna min kamar na gaza riƙe ki a matsayin amanar da abba ya barni,karki manta ranan da wannan iftila'in ya faɗawa abba abinda yace dani shine "ka kula da ƙanwar ka".wanda hakan ya zamto furcin sa na ƙarshe a gare mu".


Sai daya numfasa sannan ya ɗaura  cewa"Ina kika shiga?".

Ɗaura kaina nayi kan ƙafarsa ina cewa"yaya fawas zaɓi ne ya ƙare min,a lokacin banda zaɓin daya wuce hakanamma haƙƙin ka danasu baffa bai barni nayi rayuwa cikin farin-cikin ba yaya na ka yafe min".



Sunkuyar dakansa yayi wanda hakan yabawa hawayen dasuka ƙara ciko idonsa damar tsiyayowa sannan yace.

"Na yafe miki my cute angel ki daina kuka kinji,kukan ki na ɗaga min hankali".

"Na daina yayana,na daina ka gani"na faɗa ina share hawayen dake bin fuskar yana sauƙar har izuwa wuya ta.

Sai a sannan yasira ta gaishe shi,ya amsa mata yayin dayake ƙoƙarin tsayar da hawayen sa,inna ce ta mishi bayani wacece ita.

Sannan baffa ya sanar dashi komai daya sani game da habib da kuma ahlinsa,sosai yaya fawas yayi murna sai fatan alkhairi yake min amma baffa yace"ba za'a sanar da mahaifiyar kuba sai tukunnan abubuwan sun ƙara kamkama,dan kar tace wani abun kuma".


Sosai inna tayi na'am da zance baffa haka nan ma yaya fawas,wuni mukayi muna hira da yaya fawas tare mukaci abinci wanda rabon mu dayin hakan tun kafin bayan rabuwa.


Anan yaya fawas ya kwana dan dama tare dashi zamu koma katsina a cewar inna yaje ya gano wajen.kwana nan mu huɗu a gano sannan muka fara shirin komawa domin jarabawar da zamu fara.



Tunda mukazo ba kallon arziki tsakanin mu da hajara,hakan nan zaman lafiya yaƙare tsakanin ta da baffa.


Ranan ana gobe zamu koma katsina muna zaune a tsakar gida muna taya inna tsintar wake,baffa da yaya fawas kuwa sun tafi goma Adda barira ta shigo.

Washe baki inna tayi kafin ta shiga faɗin"lale maraba da zuwa barira kece tafe?".


"E wallahi inna nice tafe hajarar tana nan kuwa?"ta faɗa tana daga tsaye.


"E ki shiga tana daga ciki".


Gaishe ta mukayi a tare nida yasira ta amsa tanabin mu da wani irin kallon dana kasa fassara meyake nufi,mamaki ko al'ajabi.

"Inna wannan ce yarinyar da ake tayi da ita a cikin garin nan ko?,ta sa ƙafa tabar gida tsawon lokaci ba wani makalukin daya sata a idon sa.Oh ni bariratu naga ikon mai mana ruwa da iska,abin mamaki baya ƙarewa a duniya inda ranka kuwa kasha kallo".


Sai data bina da wani irin kallo mai cike da tuhuma,tana jawo kujerar da inna ta miƙo mata ta zauna sannan ta ɗaura da cewa.


"Ke kuwa yarinya duk tsawon wannan lokacin ina kika shiga?,inna kika je?,wajen wa kike zaune?".



A dunƙule ta jefo min tambayoyin tana ƙara kafe idon ta akaina.


Hawayen danake ƙoƙarin hana fitowar sune suka biyo kunci na,yasira da ta lura  da hakan ta kamo hannun na tana jijjiga min kanta tare dayi min alamar nabaryin kukan.


Inna ce tayi saurin cewa"Ashsha haba!barira da girman kike biyewa maganar mutan garin nan haba".


Fitowar hajara ne ya katse adda barira daga maganar da tayi niyyar amayar da ita.


"Adda ki shigo mana kika tsaya daga waje"hajara ta faɗa tana daga tsaye ƙofar ɗakin.


"To ai shikenan allah ya kyauta"cewar adda barira yayin datake miƙewa tayi ɗakin hajara.

Sosai na sakin kukan danake dannewa duk mutane irin kallon dasuke min kenan?,meyasa zasu yanke min wannan hukuncin ba tare da bincike ba?,watakil inna jewa umma ma ita ma kallon hakan zata min wacce taje yawon duniya.



"Anty kiyi haƙuri ki daina wannan kukan bashi da amfani,kuma kisan komai kikayi sai mutane sun sama abin suka acikin sa"yasira ta faɗa cikin sigar lallashi.


Sannan inna ta ɗaura da  nata"gaskiya ne maganar yasira domin yanzu kisan an daina kiyon dabba sai dai ta mutum".


Share hawaye na nayi sannan nacigaba da gyaran wanken ba tare danace dasu uffan ba.

Domin raɗaɗin da zuciya take ciki kalmomin baki sunyi kaɗan wajen furta shi.

Adda barira na shigowa ɗakin hajara ta mayar da ƙofar langalanga ɗakin ta rufe.


Ƙaran da ƙofar tayi ta sanyani juyo na ganni ƙofar sannan na maida kaina ga aikin danake yi.


"Oh ni bariratu yau idona sun gane min abin mamaki,hajara ki dubi irin suturun da ke jikin wannan yarinyar sannan babu alamar wahala ko yunwa a tattare da ita.Sannan ace ba  yawon karuwanci taje ba?".adda barira ta faɗa tana zare hijab ɗin dake kanta.

Sai da hajara ta saki ajiyan zuciyawanda hakan,ke nuni  da irin ƙuncin da zuciyar take cikin akan maganar sannan tace.


"Ai adda baki gama komai ba,sai ma kinga yanda malam yake ririta kamar jariri ɗan wata uku".

"Ai kuwa yau komai zaizo ƙarshe"adda barira ta faɗa tana since gefen zanin ta.

Ƙullin magani ta ciro tare da riƙon hannun hajarar tana damƙa mata kullin tana faɗin.


"Kinga wannan kullin shi zaki barbaɗa mata a cikin duk wani,abu nau'in ababen sha kamar kunu da dai sauran su.Bi'izinillahi indai tasha to sai dai a yi wani labarin amma ba wannnan ba domin ita da wannan yaron har abada zuciyar ta zatayi dakon tsanar shi,da duk wani abu daya dangance shi ki fara aiwatar da wannan kafin mu juyo kan shi adamun".


Karɓa hajara tana ƙara damƙe ƙullin cikin hannunta tana faɗin"nagode adda ni daman nasan ba wani matsala tawa dazan kai miki ki kasa magance min ita".


"Haba!ke kuwa ƴar-uwa nayiwa wasu ma balle ke".


Haka suka cigaba da ƙulla mumanan manufofin su,muna zaune inda  ta barmu suka fito ni kuwa ina zaune kan dakalin ƙofar ɗakin inna ina waya da habib.

"To inna ni na wuce allah ya bamu alkhairin sa"cewar adda barira.


"To a gaida mutan gidan"inna ta faɗa tana ɗaukar buta zata shiga banɗaki.

Rakata hajara tayi sannan ta dawo "Ana ta abun kenan".


Ta jefo min maganar yayin datake wucewa kusa da inda nake zaune tayi ɗakin ta,tana sakin wani yalwataccen murmushi.



Da kallo nabita ina ƙoƙarin fassara manufofin dake dunƙule cikin wannan dariyar tata,jin Habib yana ƙiran suna na a cikin wayar yasa ni sakin wannan tinanin.


Ko dasu Baffa suka dawo,nan muka zauna muna ta shan hira Yasira sai faɗi takeyi"zarayi missing ɗin kwaɗon zolayan  inna".

Da mamaki na naga Hajara ta fito ta zauna cikin mu,abinda da tun zuwan mu banga tayi shibada ita ake ta hirar.

Baffa kuwa sosai ransa ya masa daɗi ganin hajara ta watsar,da komai daga ranta har ta fito ta zauna cikin mu,ana wasa da dariya.

Washe gari da wuri muka shirya kayan mu muna jiran zuwar Sayyid,muna tsakar gida Yasira sai hoto take ɗauka mana da yaya Fawas da kuma su Inna da Baffa tana faɗin inmun Koma zata bayar a wanke mata su muryar Hajara dana tsinkaya ne ya katseni,daga sheƙa dariyar danake yiwa Yasira.

"Hibba har kun fito kenan?,daman fura ce kingan ta mai kyau na dama miki ita".

Ta ƙarishe maganar tana miƙomin kwaryar furan.


UWATACE SANADI


       Tsarawa/rubutawa

       ©Maimunah Tijjani Iyam

___________________________

Page 2⃣0⃣ 


Karɓa nayi sannan nace"Ayya Anty Hajara da baki wahalar dakan ki hakan ba nagode".


Sai data marairaice murya kafin ta shiga faɗin"Haba!Hibba kedai ki sha ko kaɗan ne ai zanji daɗi nima,tunda kuka zo fa ban samu na muku wani abu ba sai wannan".

Inna ce ta amshe zancen tana faɗin"haba!Hajara suda zasuyi tafiya kyabasu fura salon ta kashe mata jiki".
"Haba!ilnna furace fa kawai,kuma kingan ta ba mai yawa bace".
" To ai shikenan"shine iya abinda Inna ta furta.


A hankalin na kurɓa furan sosai tamin daɗi dan haka nake shan ta sosai,kaɗan na rage a cikin kwaryan ina tanɗe baki.
Nan Yasira tace zata sha guntun da wani mungun hanzari Hajara ta karɓa ƙwarya daga hannun Yasira tace"Bari na zubo miki naki ta mussamman".

Sannan ta karɓa ƙwarya taje ta zubo mata tas!Yasira ta shanye.

Sallamar Sayyid ta   sa dukkan mu kallo shi yaya Fawas ne ya amsa sallamar,sannan ya sukayi musabaha sayyid ya gaida Baffa da Inna suka amsa tare da yalwata fara'ar dake ɗauke a saman fuskokinsu.
Kayan mu muka fito dasu muka sasu a motar sayyid sannan muka shiga yin ban kwana gasu Baffa.sosai yake mana addu'ar Allah ya tsare mu ya kuma kaimu lafiya haka nan ma Inna da hajara yaya Fawas kam daman dashi zamu tafi Sannan muka tafi.


Muna shiga cikin katsina muka wuce gida a compound muka same su suna jiran isowar mu,cike  murna Ummi take mana sannu da zuwa sam bakinta ya kasa rufewa.
Yaya Fawas gaisawa sukayi da Daddy sannan ya gaida Ummi ma musabaha sukayi Habib sannan muka shiga,ko da muka shiga ƙara gaisawa muke tayi mussamman yaya Fawas da Daddy yake ta masa bayanin akan Habib ɗin.


Ɗaki muka shiga da Yasira bayan Ummi tamin umarnin dana kaiwa yaya Fawas kayansa cikin part ɗin Sayyid,wanka mukayi sannan mukayi salla muka fito mukaci abinci,Habib kam tunda muka dawo yakejin kansa cikin wani farin-ciki na mussamman.


Haka muka gama cin abinci muka dawo falo muka cigaba da hirar mu,haka nan kawai naji zuciya ta ta kasa nutsuwa da irin kallon da Habib kemin,miƙewa nayi ina cewa"Ummi ina zuwa"sannan ya wuce ɗaki cikin sauri.


Sai a sannan Daddy yake sanar musu da sunsa bikin nanda wata biyu shi da Baffa sosai Ummi take bayyanar da farin-cikin game da haka.Haka nan ma Sayyid da yaya Fawas, Yasira kam miƙewa tayi da gudu tana nufo ɗakina.
Ina kwance rufda ciki na rungume matashi na,Yasira ta shigo ɗakin kaina ta faɗo tana cewa"Anty nataya ki murna ansa auren ki da Hamma nanda wata biyu".


Ras!naji  gabana ya faɗi tureta nayi daga jikin na sannan na juya mata baya"Anty Yasira ki barni na gaji inason na huta".


Nan ta fara lissafin kalolin event ɗin da za'ayi,ni dai kam bance da ita komai ba dan ji nayi duk raina ya jagule na rasa gane kaina haka na wuni.


Da yamma ina kitchen ina haɗawa Ummi fruit sallad waya ta ta hau ringing,ko ba a faɗa min ba nasa Habib ne ɗagawa nayi na kara a kunne na ba tare da nace komai ba.


"Please inba abinda kikeyi kizo inna jiran cikin garden".Bance mishi komai ba na kashe wayar tare da ajiye ta gefe guda.


Sai da gama abinda nakeyi na kaiwa Ummi fruit sallad ɗin sannan na wuce ɗaki nayi kwanciya ta,wayar tace ta fara ringing tsaki na saka sannan na miƙe na saka hijab ɗin na har ƙasa sannan na fito.


A cikin garden ɗin na hange shi yana zaune kan kujerun plastic da aka shirya su a wajen,da sallama na isa gare shi ya amsa sannan na zauna.Shuru ne ya ratsa wajen ina ɗago kai muka haɗa ido dashi saurin ɗauke nawa idon nayi daga cikin nasa yayin na naji,wata iriyar tsanar ganin fuskar sa ya shige ni tun daga yatsun ƙafata har tsakiyar kaina.

"Amaryan Habib da yaddan allah"ya faɗa yana ƙare kafeni idanu.


Sai  dana haɗiye wani yawu mai  ɗaci,wanda naji ɗacin sa ya wanzu cikin ko'ina a baki na kafin nace"Angon Hibba",Ba ƙaramin jarumta nayi ba wajen wannan haɗa waɗannan kalaman.
Sosai ya saki murmushi sannan yace"Munyi magana da Granny tace inkun gama jarabawa nakai mata ke ku gaisa".


"To Allah ya nuna mana nima zanso haka".na faɗa ina ƙara takurewa cikin hijabi ta.

"Amin".ya amsa dashi sannan ya cigaba daja na da hira,dauriya kawai nakeyi nake amsa masa amma duk sa'in da sautin muryarsa ta bugi dodon kunne na tsanar shi ne take ninkuwa cikin zuciya.

"Zan shiga ciki kaina yafara min ciwo"na faɗa ina ƙara takurewa.

"Suhbanallahi!Allah ya sauwaƙe muje na baki magani"ya faɗa yana miƙewa.


Tashi nayi muka jera dashi muka shiga cikin gidan maganin ya ɗauko mini nasha sannan ya taraka ni har ƙofar ɗaki,sai daya ga shiga ta sannan ya koma.

Koda na shiga kwanciya nayi yayin da ƙaryan ciwon kan danayi ya zama gaske,domin ji nake tamkar an ajiye min wani abu mai nauyi a tsakiyar kaina.Bansan ta yadda zan fara tunkarar Daddy ba nace masa a fasa wannnan auren domin jinake da a ɗaura wannan auren gwara akai  ni kabari.


Kuka na saka mai ƙarfi ta yaya zan butulcewa mutanen dasuka zame mini gata a lokacin dana rasa hakan daga kowa,suka dawo min da  farin-cikin dana yanke tsammani dashi,sannan suka bada gudumawa wajen cimma buri na.


Ana cikin haka muka fara jarabawa kullum Habib shike kaini kuma ya dawo dani,a cikin haka yaya Fawas ya koma tare da Sayyid suka tafi wanda shima ya koma makaratan.kamar na bishi haka nakeji amma saboda jarabawar damukeyi nayi shuru.


Cikin haka muka gama jarabawar Ummi na roƙa akan inason naje daura gidan su Anty Amina dan cikin,kwanakin nan sosai nakeyi mungaye mafarkai akan ta.

Tare da Daddy Ummi suka tattauna maganar ya amince min,naje tare da Yasira da Habib haka washe gari muka shirya muka ɗauki hanyar daura muna isa muka tambaye gidan malam Mahiru mai ɗan kara anan kuwa aka nuna mana.Domin Anty Amina ta taɓa cemin mahaifinta babban malamin addini ne a cikin daura kowa yasan shi.


Muna isa ƙofar gidan Habib yayi parking sannan muka fito nan naji kamar an sauƙe min wani abu mai nauyi,a cikin ƙirji na da sallama muka shiga cikin gidan akan anty Amina idona suka fara sauƙa wacce take zaune a tsakar madaidaicin gidan nasun tana wanke-wanke.

Sallamar damuka shigo da ita yasanya anty  Amina ɗagowa tare da amsa salllamar,sakin kwanon siban dake hannun ta tayi yayi da idonunta sukayi tozali da fuska ta.

Miƙewa tayi tana faɗin"Hibba kece".

"Nice anty Amina "na faɗa ina isowa gare ta.

Rungume juna mukayi muna sakin kuka,wanda hakan ya sanya mahaifiyar anty Amina fitowa daga ɗaki ganin mu datayi haka yasata faɗin"Amina lafiya?,Waye waɗannan ɗin?.

"Umma itace Hibba wacce nake baki labarin ta"Anty Amina ta faɗa tana zuƙar majinan kukan daya zo mata.

Salati Umma ta saka tana ƙara jaddada iko irin na illahi,sarkin da ikonsa yake akan komai sannan tace"Baiwar Allah kullum Amina cikin zancen ki take safe da yamma,ko yaushe tinanin ta wani irin hali rayuwarki zaka faɗa?,duk sa'in data ɗaura goshinta a ƙasa da sunan salla kafin tayiwa kanta addu'a to sai ta nema miki tsari daga dukkan abin ƙi".


Tabbas Anty Amina ta zame min tamkar garkuwa a rayuwata ta baya,sannan itace ta fara bani taimako a lokacin danake matuƙar buƙatan hakan,wannan dalilin yasa nima a ko yaushe take cikin addu'ata.
Duƙusawa nayi ƙasa inacewa"Anty Amina nasan nayi miki silar lalacewar auren ki,ban saka miki da irin alkhairin da kika min ba sai dai ma igiyoyin auren ki da a sanadiyata tsinkewar su,ki yafe min anty Aminaa"na ƙarishe maganar take da jan  furcin ƙarshen.

Ɗago anty Amina tayi kafin ta shiga faɗin"Hibba ban taɓa sanyawa a raina wai kece kika kashe min auren ba daga ni har iyayena,abinda nasa a raina kuma nake tina shi a ko yaushe shine ƙaddarar bawa ba taɓa tsalle shi,dukkan mu a wannan duniyar kuna rayuwa ne tare da ƙaddararmu.Sannan ba zamu taɓa guje mata ba kamar yanda bazamu iya gujewa inuwar mu ba".


"Anty Amina nagode,ga wanda zan aure wannna kuma ƴar-uwar sace"na ƙarishe maganar tare dayi mata nuni da su Habib da Yasira.

Tabarma ta shimfiɗa mana muka zauna sannan suka shiga gaisawa da Habib.

Muna zaune a wajen mahaifinta anty Amina malam Mahiru ya shigo,sai daya zauna sannna Umma ta shiga masa bayanin komai,jinjina kansa yayi kana yace"Tsarki ya tabbata ga sarkin daya ƙaddara saduwa tsakanin mu dake ".

Sosai malam Mahiru ya mana bayanin yanda malam Habu yayiwa Anty Amina sakin wulakanci a waya tare da jifan ta da zargi kawoni domin na lalata musu rayuwar ɗa.
Nayi kuka sosai da har sai dana rasa hawayen tsiyarwan sannan na shiga kukan zuci,abubuwan dasuka faru tsakani na da Kabir a ranan da Balaraba ta kore ni daga gidan ne,ya fara min yawo cikin ƙwaƙwalwata tamkar yanzu suke faruwa.

Nan na sanar dasu ainihin abinda ya faru tsakanin mu da Kabir a ranar,inayi ina ƙwalla haka ma anty Amina,Yasira Umma da kuma Habib daya sunkuyar da kansa yana tare hawayen dasuke shirin zubowa daga idonsa.
A duk cikin rayuwar sa ba halittan dayake girmamawa gamin da darajawa irin mace,wannan dalilin yasa aduk lokacin ya ga wata mace cikin matsala yake mata kallon ƴar-uwa ta jini,kuma yaken shiga lamarin ta mussaman irin waɗannan aka ketawa haddi har sai anmusu adalci.


"Ba komai akwai Allah,kuma akwai ranar tsayuwa a gabansa domin yiwa kowani bawa hukunci dai-dai  da abinda ya aikata".cewar malam Mahiru wanda hakan ya dawo da mu daga duniyar tinanin da mukayi nitso a cikin sa.

UWATACE SANADI

     _Tsarawa/rubutawa_
         ©Maimunah Tijjani Iyam

________________________________

Page  2⃣1⃣


Ƙiran sallan zuhr da aka farane ya sanya malam Mahiru da Habib fita masallaci yayin da mu kuma mukayi alwala sannan Anty Amina ta shigar damu ɗakin mukayi salla.
Tunda na iddar da sallan nake zaune kan sallayar,ni kaina bazan iya fasaltar irin tsanar danayiwa Habib ba cikin kwanakin wanda shikuwa kullum burin shi ya kyautata min tare da neman hanyar da zai dawo min da farin-cikin dana daɗe da rasa shi.

Shigowa anty Amina tayi ta dire mana kwanon ɗan-wake a gaban mu,maganar da Yasira tayi ne ya katse anty Amina daga tata maganar datayi niyya fiddawa.

"Anty inso nayi waya da Ummi,naga missed call ɗinta amma ba services".
"Wallahi muna fama da matsalar service a gidan amma da zaran kin fita ƙofar gidan kikayi tafiya kaɗan zaki samo sai kiyi wayarki"cewar anty Amina.

Gyalenta dake kafaɗarta Yasira ta gyara sannan  ta fita tana cewa"Anty Hibba bari naje wajen".
Kaina kawai na ɗaga mata sannan ta ƙarasa ficewa.Zama anty Amina tayi kusa dani tana fuskanta na kafin tace"Hibba na kula da fuskan ki tabbas akwai abinda yake damunki menene?".


Nauyayyan ajiyan zuciya na sauƙe sannan nace"Anty Amina wallahi ina cikin matsala babba,bazan ɓoye miki ba wallahi banason wannan auren na Habib domin na gwammace akai mishi gawata ko ganinsa banason yi zaman gidan gabaɗaya ya fice min a rai.Shiyasa na roƙi Ummi ta barni naso nan".
Duk abinda yake raina na fitar daman ba  wanda na sama damar yin maganar dashi sai yanzu danake gayawa anty Amina,ko yaya Fawas bamuyi maganar dashi ba.


"Hibba tabbas a yanda kika bani labarin zaman ki da mutanan nan,basu cancancin suzo miki da buƙata ki kasayi musu ba maƙutar kinada damar yin hakan,ni wallahi ma tausayin Habib ɗin nake saboda ciwon dayake ɗauke dashi.Ki dage da addu'a ba abinda ya gagare Allah kita sanar dashi damuwar ki bi'izinillahi komai zai wuce amma kar ki sake koda wasa kiyi wannan maganar da kowa kinji?".


Kaina kawai na gyaɗa mata domin naga Anty Amina bazata fahimci irin saurin da zuciya take iya ba wajen zana min tsanar habib da manyan harrufa a ko'ina a ciki taba.
Shawarwari Anty Amina ta bani sosai tare da wasu addu'o'i,muna haka Yasira ta shigo sannan mukaci abincin.

Mukayi sallan Asr kuwa muka yi shirin bari daura sosai Habib yayiwa malam Mahiru sha tara ta arziki,sai dana karɓa lambar wayar Anty Amina sannan muka tafi.
Tunda muka fara tafiyar zuciya ta take min zafi ɗan wuni da nayi a wajen Anty Amina jina nayi saƙayau kamar ɗaurarran daya masa  ƴanci.

A hankali na lumshe idanuna sannan na kwantar da kaina kan seat ɗin motar ina maimaita "Hasbunallahu wa ni'imal wakil".

Habib daya lura da yanayi na yace"Fatima lafiya?".Cikin kwanan kin nan kuma sunan daya tsiri kira dashi kenan.
Kamar ya watsa min wuta haka naji lokacin da na tsinkaye muryar shin ya sauƙa cikin kunne na,sai dana harhaɗo jarumta kafin nace"Lafiya kalau kawai gajiyace".

"Daga cikin katsina zuwa daura shine har kin gaji?,To next tomorow da zamuje damaturu fa sannan mu biya ta wajen su baffa"ya faɗa yana sakar min murmushi.

Shagwabe fuska nayi ina ƙara lumshe idona nace"nidai ba inda zanje sai na huta".

Murmushi ya ƙara sakar min a karo na biyu kafin yace"Haka ne kam tawan ba wanda zai ta kura miki"ya faɗa yana maida ga kallonshi ga titin.

"Allah dai ya nuna mana lokacin bikin nan"Yasira ta faɗa sai a sannan na tino da ita dan tunda muka,shigo motar sai yanzun tayi magana da amin ya amsa mata.
Muna isa gida nida Yasira muka wuce part ɗin Ummi yayin da shi kuma ya wuce part ɗinsa sosai hakan ya min daɗi.Zaune da Daddy muka tardasu muka gaishe su suka amsa mana tare da tambayar mu ya hanya."Alhamdulillah!na amsa musu dashi sannan na tashi zan shiga ɗaki.

Inajin Ummi nacewa"To Hibba hankali ya kwanta yanzu dai ko,kije kin gano ta"murmushi kawai nayi na shige ɗaki.
Anty Amina na ƙira na sanar da ita mun iso lafiya sannan na kira yaya Fawas sosai mukayi hira dashi wanda shikam zancen sa duk akan bikin ne,wanda yanzu saura sati huɗu.

Washe gari kuwa da yamma ina kwance a ɗaki ummi ta aiko ƙirana,a falo na iske ta tare da yasira.


"Hibba zo kiga kayan lefenki ne kafin gobe a wuce dashi gidan granny"ta ƙarishe maganar tana min nuni da akwatinan dake jere jeras a gabanta.

Set uku ne masu launukan maroon,ash da kuma golding,ko wani set guda huɗu ne sai ƙaramar jaka a cikin sa.

Sunkuyar dakaina ƙasa kawai nayi ina cewa"Ummi basai naga ni ba,sunyi Allah ya saka da alkhairi".


Dafa kafaɗata tayi tare da faɗin"Amin hibba Allah ya miki albarka".
A sanyaye nace"amin"sannan na koma  ɗaki koda Habib ya dawo ya aiko ƙira na ƙin zuwa nayi,daya matsa kuwa Ummi ce tace ya barni kunya nakeji kar ya matsa min.
Washe gari kuwa Ummi tajeta damaturu tare da kayan lefen a gidan Granny aka ajiye su,sannan suka wuce gano ita da ummi da kuma iya suka kaiwa su Inna lefen kamar yanda al'adar hausawa take dangin ango suke kaiwa lefe gidansu amarya.
Ranan rasa inda zatasa kanta Inna tayi dan tsabar murna,sosai Baffa ya musu tarban azirki.
Koda suka tafi Hajara rasa inda zata sanya kanta tayi dan baƙin-ciki,sam ta kasa zaune ta kasa tsaye.fargaban ta shine kar dai aikin nan baici ba.
Gidan Adda Barira taje ta shaida mata,kwantar mata da hankali Adda Barirar tayi tare da cewa su bari dai suga nanda wani lokaci in ancigaba,dayin batun auren sai su san matakin da zasu ɗauka.

Ummi kuwa kwananta uku a damaturu sannan ta dawo.Haka nan cikin kwanakin nan,da bikin keta matsowa kullum nake cikin kuka duk lallashin da Habib zai min bana kula shi,haka ko kalaman bakin Yasira zasu ƙare wajen tambaya ta abinda ke damun na bana tanka mata.Domin nima kaina zanso sanin abinda ke damun nawan.

 Ummi ce wasu lokutan kance dasu daman ko wacce,mace in lokacin bikin ta ya ƙarato takan tsinci kanta cikin fargaba.
Tun ana saura sati biyu bikin Ummi ta sa akemin gyaran jiki sosai fatata ta murjewa ta ƙarayin,haske da kuma kyau.Cikin kwanakin nan kuwa wasan ɓoya mukeyi da Habib dan koda wasa bana yadda mu haɗu dashi.

Ana saura kwana biyar bikin na koma gano tare da Yasira,dan acan za'a  ɗaura.Ana ɗaurawa kuwa tare da waɗanda sukazo ɗaurin auren zamu juyo katsina.
Guɗa Inna ta shiga rangaɗawa yayin da muka iso,ƴan-uwa da abokan arziki tunin sun fara cika gidan.Sosai Baffa da Inna sukayi farin-cikin zuwana.
Washe gari kuwa yaya Fawas shima yazo,ranar wuni mukayi Baffa da Inna suna min nasiha haka nan ma Yaya Fawas.

Da kanta Inna tasa aka zanzara min ƙunshi tare da Yasira,ana gobe ɗaurin auren da daddare ina tsakar gida ina waya da Habib Inna da yasira kuwa suna ɗaki.
Hajara ta fito daga banɗaki taɓe baki tayi yayin datake ajiye butar dake hannun ta kafin tace."Oh ni Hajara duniya sam babu tsoron Allah a zuƙatan bayi,daga mutane sun taimaka miki shine kuma bari a aure ɗan gida,yo wayasan irin abinda aka bashi ya sha a kunu da shayi aka mallake shi".


Ajiye wayar nayi ba tare danayiwa Habib sallama ba nace "Anty Hajara wai dani kike wannan maganar?".

Sai ta dallo min harara kafin tace"A akwai wani dazanyi dashi bayan ke".

Lokaci ɗaya naji raina yana mungun tafasa a harzuƙe nake faɗin"To ki buɗe kunnuwanki kiji abinda zan faɗa miki ni Habib baya cikin raina sannan da kike maganar wai na mallake shi,ni ko yanzu banƙi a fasa wannan auren ba baya gaba na balle kuma abin daya  mallaka".
Ina gama faɗin haka wuf na juya na wuce ɗaki,na barta tsaye a wajen.
Kodana shigo ɗaki Inna na tarar zaune akan gadon ƙarfenta irin Nada mai rumfa,ta zabga tagumi hannu bibiyu.Yasira kuwa na kwance gefen ta tana bacci.
Kallo ɗaya nayiwa Inna yanayin ta,ya tabbatar min data saurarin maganganun da mukayi da Hajara.

Ɗauke kaina nayi na fara gyara inda zan kwanta muryartace ta katse ni.

"Hibba inason ki tabbatar min da abinda kika faɗawa,Hajara shin da gaske bakya son Habib?".

Gefen ta nazo na ɗauki pillow,ina cewa"Inna  karka ki damu kanki fa,amsa ce kawai na bata dai-dai da tambayar data min kuma ai daman hakan takeson ji daga gare ni".na faɗa ina ɗaura kaina akan pillow na.

"To kul Hibba kar na ƙarajin kinyi irin furcin nan,yanzu yanda gidan yake cike da jama'a da wani ya jiki fa ki daina irin haka banaso".

Sai dana murmusa kafin nace"Inna kenan basai a fasa ba".


Cikin sauri tace"A fasa meye ɗin".


"Auren mana".


"Allah ya shiryeki Hibbatu,ki kwanta kar gobe ki kasa tashi da wuri".
Hmm Tabbas farin-cikin dangina shine abin daya zama abin tattali da riritawa a gare ni.Basan iya tunkarar ɗaya daga cikinsu in sanar dasu zuciya batason Habib ba,na gwammace in rayu cikin baƙin-ciki matuƙar nasu farin-cikin zai cigaba da wanzowa.
Hajara kuwa nan inda na barta nan daɗi ya ishe ta,ɗaki ta koma fuskarta na bayyanar da tsan-tsan farin-cikin da zuciyarta ke ciki.

"Alhamdulillahi madalla da Adda Bariri,wannan farin-cikin danake ciki haka Allah yakaimu gobe in fiddoshi waje".ta faɗa tana rufo ƙofar ɗakin.

"Amin Hajara da alama dai akwai babban abun dakika shirya goben nan?".

Tambayar da baffa ya wurgo mata wanda yasa hanjin cikin ta kaɗawa.
Ya faɗa yana ƙara duban kayan dasuke gaban shi,wanda yaya Fawas ya ɗinka mishi,wanda zai sa ranar ɗaurin auren.

"Ah Ah Malam daman kana ciki ne?,wallahi kasan duk wani masoyin mu yana farin-cikin ganin rana irin ta gobe.Ranar dazaka aurar da Hibba izuwa gidan mutumci,na tabbatar yaya sule zaiyi farin-cikin da hakan".


Sai daya murmusa kafin yace"Haka ne maganar ki Hajara"A takaice ya faɗi maganar.
Washe gari kuwa data kasance ranar juma'a ranar dake mafi daraja da falala daga cikin jerin kwanaki,dai-dai sauƙowa daga sallan juma'a aka ɗaura auren.
Tun ƙiran assalatun farko Hajara ta tafi gidan Adda Barira,duk abinda ya wakana tsakani na da ita ta kwashe ta faɗa mata.

"Adda ni yanzu so nake koda an ɗaura auren ya zamana ta kasa zaman gidan,hankalin ta ya kasa nutsuwa waje ɗaya.Ta yanda da ƙafarta zata baro gidan" Hajara ta faɗa fuskarta na bayyanar da tsatsan ƙiyayyarta gareni.

Shewa Adda Barira ta saka kafin tace"Sha kuruminki ƴar uwa yanda kikeso haka nan za'ayi,kinga yanzu ma tashi zamuyi daga nan mu wuce wajen Malamin nan mu sanar dashi buƙatar mu".


"Yauwa Addata tashi mu tafi,kafin Inna ta farka ta ga bana nan ta tsareni da tambayar ina naje".
Hajara ta faɗa yayin dasuke miƙewa, fitowar kishiyar Adda Barira daga ɗakin tane yasa su tsayawa.

Ɗaga labulen ɗakin tayi ba tare da ta fito gaba ɗaya ba,tana tsaye daga bakin ƙofar tace"Haba!Yaya ita kuwa yariyar nan meta tare muku  a doron duniya?,meta aikata muku dahar kuke bibiyar ta da waɗannan munanan sharrukan?,Meye ribar ku indan kuka hana ta zaman gidan auren ta?.Shin bakwa tsoron ranar da Allah zai kamaku da laifin zaluntar wannnan baiwar tasa?.


Tsawa Adda Barira ta daka mata,yasa ta shuru ba tare data ƙarisa maganar data ɗauko ba.

"Laure ki kiyaye ni wallahi wato laɓe kike mana kenan ko?Ina ruwan ki da maganar mu meya shafe ki,muzaki nunawa kin fimu jin tsoron Allah".

"A'a Yaya Allah ya baki haƙuri"cewar laure tare da sakin labulen ta koma ɗaki.

Tsaki Hajara ta saka tare da faɗin"wallahi Adda ke kikayi sake har wannan matar take gaya miki magana son ranta haba!".

"Kyale ta ƴar-uwa zanyi maganinta"cewar Adda ta faɗa tana gyara zaman mayafin ta a kafadarta sannan suka fita.

UWATACE SANADI

      Tsarawa/rubutawa

          ©Maimunah Tijjani Iyam

_______________________________

Page  2⃣2⃣



Gidan malamin suka wuce suka zayyana musu buƙatarsu bayan Adda Barira ta aje masa kuɗin aikin dana yankan daya ce za'ayi.
Sosai ya basu tabbacin cewa ita da zaman gidan aure lafiya sai dai da wani,ɗa namijin amma ba Habib ba sai taji ta gwammace ta shiga duniya akan ta zauna a gidan sa.
Sosai suka masa godiya sannansuka tafi gidan ta,Adda Barira ta wuce akan cewa zatazo anjima sannan Hajara ta wuco gida.


Hakan nan ji zuciya ta,ta kasa sukuni tun da Habib ya ƙira ni yake shaida min nazama mallakinsa.
Cikin wani tsadadden atamfa na shirya mai launin shuɗi,ɗinkin doguwar riga ne daya sauƙa min har ƙasa yayin da aka ƙawata ɗinkin da adon stones masu ɗaukar hankali.
Tare dasu Sayyid da sukazo ɗaurin auren Ummi ta haɗo su da mai make-up.
Sosai kwalliyar ta zauna a fuska na,sannan ta ɗaura min ɗan-kwali sannan na yafa gyale na daya kasance fari marar nauyi da kuma kauri haka nan kuma bashi da  duhu.
Yasira kuwa anko ta saka wanda harsu Inna ma sunyi shi,ko dana fito nan gidan ya ɗauki guɗa ta ko'ina.
Yasira ce tashiga yiwa Inna magana a kunne,bansan meta faɗa mata ba sai gani nayi Habib ya shigo Sayyid na biye dashi a baya.Tare da tarin zugar abokansu.

Wata guɗar aka sake rangaɗawa,wata tsohuwa na faɗin"Ga angon ga angon".
Gaishe su sukayi sannan suka miƙe zasu fita bayan Sayyid ya sanar da Inna cewa yanzu za'a wuce da amarya.
Dam!zuciya ta ta bada,duk da Ummi ta sanar dani daman da zarar an ɗaura zamu taho,amma ban zata abin zaizo min a haka ba.
Bansan sanda hawaye suka fara bin fuska na  ba,sai jin Habib nayi dab da inda nake tsaye yana share min hawayen.
Kamar ana watsa min tafashashshen ruwan dalma,haka nakeji a duk inda hannun Habib ya sauƙa a fuska na.

"Ki daina wannnan kukan fati na banaso kinji ko?"ya faɗa cikin raɗa,kaina kawai na ɗaga masa alamar naji.

Nan kuwa abokansa suka fara hasko mu,da kemarurin wayoyinsu suna mana hoto.
Sai a sannan na tino a inda nake,saurin matsawa gefe nayi ina sunkuyar da kaina ƙasa cike da kunya.

Shi kam ko a jikinsa fita yayi yana ɗan sosa ƙeya.
Yayin dasu Sayyid suka rufa masa baya ɗaki na koma na faɗa kan gadon ƙarfen Inna ina kuka,shigowa Inna tayi tare da zama dab dani tana faɗin"Hibba ba yanzu ne lokacin daya dace kiyi kuka ba,ki share hawayen ki inna da kyakykyawan zato akan Habib zai riƙe ki bisa amana".

"Inna nima banida tantanma akan Habib Inna,kukan danake Inna wai yau ake ɗaurin aurena amma mahaifiyata bata damu da tazo ba balle sanin yanda za'a gudanar da bikin".Na ƙarishe maganar ina cusa kaina a cikin pillow.

Ajiyan zuciya Inna ta sauƙe kafin tace"Hibba Fawas yaje sanar da mahaifiyar ku,amma ya samo ta tashi daga gidan kuma ba wanda yasan inda ta koma, ba wanda za'a tambaya cikin unguwan domin daman ba zaman mutunci sukayi ba".


Cak!kukan danake yi ya tsaya yayin da zuciya ta min nauyi sosai.
Numfashi na dayake sarkewa yasa ni tashi na zauna Inna ce ta fara ƙoƙarin yi magana,Amma na katse ta ta hanyar faɗin"Inna shikenan basai kinci komai ".

Ina rufe baki na Baffa da yaya Fawas suka shigo ɗaki sai da suka zauna kafin baffa ya shiga faɗin.

"Hibba dan girman Allah da manzonsa in an kaiki ɗakin ki kiyiwa mijin ki biyayya sau da ƙafa,ki riƙe dangin mijinki tamkar ƴan-uwa".

Sosai Baffa kemin nasiha kafin yaya fawas ma ya ɗaura da nashi.

Saida suka kammala sannan baffa ya ɗauko wata alkebba,ya lulluɓa min wanda ta sauƙa min har ƙasa.

Ta da ce alkebba dan hatta ɗinkin ta na hannu ne da mata keyi a wancan lokacin,gyara min zaman alkebban inna tayi.Tana rufe min fuska na dashi sannan ta riƙo hannu na muka fito waje.

Tunin motocin ɗaukar amarya sun hallara,sallama mukayi da  irarun ƴan-uwan inna da sukazo sannan muka fito waje hannu na damƙe cikin na yaya fawas.

Da Inna da hajara da kuma wata ƴar ƙanwar inna(shatu),dasu zamu tafi sai kuma yasira.Motar dake tsakiya yaya fawas yasaka ni ƙara damƙe hannunsa nayi yayin da ranar da umma ta rabamu ya dawo min cikin ƙwaƙwalwa ta.


A hankali ya zame hannun shi daga cikin nawa,sai daya sakar min taƙaitaccen murmushi sannan yace"Allah ya bada zaman lafiya ƙanwata".


A Zuciya na amsa sannan ya rufo mufin ƙofar,ta ɗayar ƙofar yasira ta shigo yayin da su inna suka shiga sauran motar.

Muna shiga cikin katsina gidan ummi muka fara zuwa har yanzu kaina na lulluɓe da alkebba,Inna na riƙe dani muka shigo falon ummi wanda yake cike da mutane maƙil.

A ƙasa na zauna yayin da ƴan-uwan mahaifiyar habib mutan ƙasar niger suka shiga feshe ni da turare.

Ummi kuwa tsabar murna ma ta kasa zaune ta kasa tsaye,da an tambaya amaryar habin zatace"gata nan ƴar albarka".

Muna cikin haka habib ya shigo ya sauya shiga izuwa wata farar yadi,Wacce aka iyawa aikin surfani izuwa yanzu kam na lura da cewa yana matuƙar son aikin surfanin.

Ƴan-uwan mahaifiyar sane suka fara tasowa,yayin da wata tsohuwa daga cikin su ta ta kamo hannun sa har izuwa inda nake zaune.

Tafukan hannunsa ta buɗe ta fesa masa turaren sannan ta umarce shi daya haɗa hannunsa da nawa,hakan yayi kafin ya miƙe ya fara min karin ƴan dubu-dubu ina daga zaune.


Tunin gidan ya ɗauki shewa sai  fatan zaman lafiya kowa ke mana,sannan aka wuce dani part ɗin habin ɗin su kuwa su inna nan part ɗin ummi sukayi zaman su.

Tun ina sa tsammanin zuwarsu inna part ɗin har na daina,dan a zato na a nan zamu kwana tare dasu.

Wata munguwar gajiya ce ta sauƙar min,da azababben ciwon kan daya sauƙa min lokaci  guda sakamakon kukan  danayi.

Tashi nayi na faɗa bathroom nayo alwala sannan na fito kayan,akwatin na buɗe na ɗauka hijab nayi salla sannan na koma kan gadon na zauna.

Ina zama suka turo ƙofar,a firgice ta gyara zaman danayi ina ƙara lulluɓe fuska ta da alkebban dake jiki na.

Tare da sayyi da kuma Dr bashir suke sai kuma wani abokinsu ɗaya,zama sukayi kafin Dr  bashir yace.

"Amarsu ta ango to a buɗe mana fuskan mana".

Ƙara sunkuyar da kaina ƙasa nayi ina sakin murmushi muryar habib datayi wa kunnuwa na dirar mikiya ne ya sanya murmushin,danakeyi gushewa yayin danaji  zuciya ta tamin wani irin zafi.

"A'a malamai ban fa gane wai ta buɗe muku fuskaba,kuyi abun zakuyi ku tafi"Habib ya faɗa yana ware idonsa akan Dr Bashir.


Dariya dukkaninsu suka yi kafin sayyid yace"Shikenan Hamma zamu tafi tunda daman kowa a gidansa sarki mu kaga tafiyarmu,bazaka ƙara ganin mu ba sai ka neme mu".


"Kyale shi sayyid Yau ai ranar sace"cewar ɗayan abokin nasu ya faɗa yana ajiye ledar dake hannunsa akan site drawer.

Murmushi Habib ya saka sannan ya shiga faɗin"E dai kuyi tafiyar ku,mun gode".

Miƙewa sukayi kusan a tare suna faɗin"To amarya mun bari ki lafiya".

Tashi habib ɗin yayi ya rakasu tamkar na fasa ihu kozan sama rangwamen irin raɗaɗin da zuciya takemin,haka naji hawaye suka fara gosilo a saman kunci wanda nima bansan dalilinsu ba.

A hankali naji ana yaye alkebban dana rufe fuska ta da ita.

Ƙara sunkuyar da kaina ƙasa nayi yayin da yashi kuma ya zauna a bakin gadon,da ido ya tsare ni har sai na fara tsarguwa da kaina.

"Ya isa haka kukan nan fatima ki daina kinji,yanzu ki tashi ki wanke  fuskar ki kizo muyi salla mu nunawa Allah godiyar mu a gare shi,daya nuna mana wannan rana a cikin rayuwar mu".


Maimakon na taƙaita kukan saima tsanan tashi danayi.

"Hibba Ya isa nace miki,ki daina kukan nan kodan lafiyar ki"ya faɗa cike da kulawa.

Sai daya tsazaita sannan ya cigaba da cewa"Baki da lafiya ne?,Meyake damun ki?".
Ya faɗa yana ɗaura hannun sa a saman goshi na,sosai jiki na  ya ɗau zafi rau.
Sosai yake jera min tambayoyi ɗaya nabin ɗaya na cewa Meyake damu na?.

Ganin irin yanayin daya shiga,sosai naji tausayin sa mussamman da na tino irin cutar da yake ɗauke da ita ta raunin zuciya.

A hankali nake furta"Habib mahaifiya ta na tino yau har anyi bikina amma babu ita cikin mahalalta wajen aure na,Ina kewa ta inason na ganta koda daga nisa ne inason jin muryar ta inason mu zauna da ita muyi magana da ita irin ta ƴa da uwa".

Duk da a wannan lokacin tinanin umma ba shi yafi sanya ni cikin damuwa ba,domin tsanar habib dayake girmama a cikin zuciya ce a wannan lokacin shine babban damuwa ta.


Amma na ɗaukarwa kaina alƙawarin cewa zan bar abin a raina ba tare dana sanar da kowa ba,koda kuwa hakan zai zamto silar salwantar rayuwa ta.

Sai daya sauƙe ajiyan zuciya sannan ya matso kusa da inda nake zaune,hannu na ya riƙo ya sa cikin nasa.

Wasu hawaye masu zafi naji suna rige-rigen fitowa daga ido na,hannu na daya riƙe jinayi tamkar ya watsa min garwashin wuta.

"Fatima ki miƙa dukkan lamuran ki izuwa ga Allah domin kuwa shine sarkin da baya kuskure a cikin lamuran sa,Ki godewa Allah ke kin taso kinsan wacece mahaifiyar ki,kin rayu da ita na tsawon lokaci domin baiwa ce ga duk wanda ya rayu tare da iyayensa  biyu uwa da uba".

Sai da yayi shuru na wasu daƙiƙu,Hawayen dasuka ciko masa idanu  ya tare su da hannayen saSannan ya ɗaura da faɗin.

"Ni ban taso  tare da iyaye naba,na rasa su tun inada ƙarancin shekaru na rasa su a lokacin danake da tsananin buƙatar su,rashin iyaye ciwo ne da raɗaɗinsa baya misaltuwa haka nan kalaman baki sunyi kaɗan wajen furta su.Kiyiwa Umma kyakykyawan zato sannan ki dage da Addu'a komai zai dai-daita da izinin Allah yanzu ki tashi kiyi Alwala muyi sallah".


UWATACE SANADI

      Tsarawa/rubutawa

©Maimunah Tijjani Iyam


Page 2⃣3⃣



Duk da yanda zuciya ta take min soya,ɗaurewa nayi na tashi yayin daya riƙoni har izuwa ƙofar bathroom ɗin dake cikin ɗaki.

Tare muka shiga mukayi alwala,sannan muka fito Salla muka gabatar raka'a biyu sannan muka shiga kirari ga mahaliccin mu kafin muka fara Addu'a.

Nikam ta bangare na addu'a nakeyi Allah ya kawo min ɗauki da sauƙi a cikin damuwar dake damun zuciya ta,Ina tsoron ranan da Allah zai kamani da haƙƙin habib na aure dana tauye,Domin izuwa yanzu tsanar shi na rinjayar soyayyar da zuciya ke masa.

Shikam ta bangare sa sosai yake mai ƙasƙantar dakai ga mahaliccin sa, yana  roƙon ubangiji daya bashi damar zamantowa alkhairi ga rayuwar hibba sannan ya dawo mata da farin-cikin data rasa a cikin rayuwar ta.


Muna iddar da sallan ya jiyo inda nake,kaina ya dafa sannan ya shiga min addu'a.

Abincin da ummi ta sa a kawo mana da kyar naci abincin cokali uku nayi, shima kasa ci yayi sai tambayar  da na lura baya gajiya dayin ta.

Na tambaya ta lafiya ta nace kaina ke min ciwo,kasa cin abincin yayi yasani gaba yana min sannu.

Alama yamin da hannunsa akan na matso kusa dashi,ba musu na matso jawo ni jikinsa yayi.

Runtse idona nayi da ƙarfi sannan na jawo ɗan kwali na na toshe bakina dashi,saboda kukan danaji yana ƙoƙarin kubce min.

Duk cikin naman jiki na ji nake tamkar yana watsa min tafashashshen ruwan zafi,Haka na ɗaure tare da ƙara runtse idanu na.

Ina sakin ajiyan zuciya akai-akai ganin haka ya sa habib tinanin cewa nayi bacci,zame jikinsa yayi sannan ya gyara min kwanciya ta,ya ɗauko blanket ya lulluɓa min anan wajen.

Baiyi niyyar tashi na na hau gado ba,dan yanda jikina ya ɗau zafi sosai ya zata zazzaɓi ke damu na kuma da kyar na samu bacci.

Sai daya min Addu'a ya shafa min,kafin ya tashi ya shiga bathroom alwala ya ɗauro sannan ya fara gabatar da nafilfili.

Washe gari da matuƙar ciwon kai da kuma zazzaɓin daya sauƙa a jikina tun dare jiya na tashi,magani nasha kodan damuwar da habib ya shiga a dalilin hakan ya sani daurewa na nuna mishi naji sauƙi


Duk da inajin kwana ɗaya danayi a cijin gidan habib matsayin matar sa,duk na nema nutsuwa ta na rasa amma zan zamto masa mace ta kwarai.


Da taimakon sa na shirya cikin shigar laffaya,sannan muka shiga part ɗin ummi.

Ƴan-uwan mahaifiyar dasukazo muka fara gaishewa wata daga cikinsu ne ta shiga faɗin.


"Oh duniya!Allah ya jiƙan zainaba yau ake bikin ɗanta amma bata duniyar rayuwa kenan".

Da Amin dukkaninsu suka amsa dashi,lokaci guda na lura da yanayin habib daya sauya.


Ɗakin da aka bawa su inna muka wuce muka gaishe su sosai inna ta ƙarayi  masa nasiha.


Sannan muka wuce part ɗin ummi ita nasihar ta ke mana sosai masu ratsa jiki da ƙwaƙwalwa.



Ɗakin granny muka wuce sosai fuskar ta ke bayyanar da farin-cikin dake ƙasan zuciyar ta na ganin mu tare da tayi,Anan mukaci abinci sannan muka zauna tare da ita dakuma yasira data shigo yanzu.

Da kuma matar Dr bashir maryam daman tare suka zo da ita,sosai muke shan hirar mu kamar dama can munsan juna

Nan granny take sanar dani cewa ta faɗawa su Inna ma,da yamma za'a wuce dani gidan habib bazamu zauna anan ba dan dama ya gama gininsa.

Da yamma kuwa da kanta ummi ta shirya ni cikin,shigar laffaya mai tsantsi da granny ta bani.

Falon Daddy muka taro dukkanmu nasiha shima yayi mana,sosai tare da sanya mana albarka da fatan Allah ya bamu zaman lafiya.

Granny da Inna dasu muka tafi gidan dake cikin unguwar Dutsen safa low-cost behind M&M pharmacy a nan cikin katsina ta dikko.


Gidan babba ne sosai dan har yaso yakai na su ummi girma,part biyu ne dasuke kallon juna sai kuma wani ɗaya daga gefe wanda bai kai sauran girma ba.

Ciki muka shiga har cikin ɗaki su granny,suka kaini sosai ɗakin ya ƙawatu da furniture masu launin ruwan toka.

Muna zama habib ya shigo sanye yake cikin shigar manyan kaya kamar kullum,shadda ce fara sol wacce aka ƙawata ɗinkin da ado na zaren golding.

A wuya da kuma hannun rigar,Inna ce ta amsa sallamar daya shigo da ita sannan ya ƙariso ya zauna akan ɗaya daga cikin sofan dake ɗakin.

"Ga matar ka nan babban mutum amana ce da iyayenta suka duba kamala da kuma cancantar ka,suka ɗauke ta suka baka Idan kaci wannan amanar kasani kai da Allah kuma yana kallon ka ko mu ka ɓoye mana".

Sai daya gyara zaman sa kafin ya shiga faɗin.

"In sha Allah baza kuji wani abu marar daɗi ba tsakanin mu da yardan Allah".

"Haka muke fata"cewar inna.

Miƙewa sukayi dasu tafi nan inna take sanar dani gobe suma zasu koma gano.

Sallama mukayi dasu sannan na musu fatan sauƙa lafiya habib ya raka su.

Suna fita na sauƙe kuka mai ƙarfisosai zuciya ta take min suya,kamar na tashi nabi su haka nakeji dan bazan iya zaman gidan ba.

Banji shigowar saba sai jin sauƙar numfashin sa nayi dab dani.

"Ya isa haka Fatima tabbas nasan rabuwa da ƴan-uwa sai dole,amma duk wata ƴa mace da kika gani a cikin gidan  aure ta fuskanci rana irin wannan ki daina kukan nan banaso kinji?".

Kaina kawai na gyaɗa masa alamar naji,sosai yake amfani da duk wata kalamar dayasan zai kwantar min da hankali cikin furcinsa.

Ƙiran sallan magrib ya tilasta mishi fita masallaci,nima tashi nayi nayo alwala sannan nayi salla.

Sosai nake tausayin kaina da kuma irin rayuwar da zanyi cikin gidan habib.

Ina zaune akan sallayar aka ƙira isha'i sai danayi sannan na ɗauko qur'ani na fara karantawa ko zanji sanyi cikin raina.

Ina zaune wajen habib ya dawo zama yayi kusa dani,sannan ya jawoni jikinsa muka cigaba da karatun tare.

Sai wajajen ƙarfe goma sannan muka ajiye qur'anin abincin da su granny suka taho mana dashi mukaci sannan muka fara shirin kwanciya.

Ina zaune akan gado na lulluɓe ƙafata da blanket ya fito daga toilet shiryawa yayi cikin kayan bacci,3quarter ce tsayinta dai-dai gwiwarsa da t-shirt marar nauyi.

Yaune karo na farko dana fara ganinsa,da ƙananan kaya sosai kuwa kayan suka amshe shi.

Akan site drawer ya zauna yana fuskanto ni yace.

"Ki kwanta ki huta nasan kin gaji ko gimbiya ta?".

Murmushi nasaka tare da gyaɗa kaina,addu'a yamin ya shafa min sannan na lulluɓa min blanket ɗin.

"Sai da safe fatan nishaɗantaccen bacci".ya faɗa yana kashe wutar ɗakin.

"Allah ya kaimu"

"Amin"ya faɗa yana ficewa daga ɗakin.

Da kallo nabi bayan shi dashi yayin dayake ficewa sannan na sauƙe ajiyan zuciya.

Sosai raina yamin daɗi danaga zai kwana a ɗakin sa,dama tun ɗazu fargaban danakeyi kenan dan bazan iya haɗa shimfiɗa dashi ba.

Washe gari da wuri na tashi na haɗa breakfast sannan nayi wanka,ina tsaye a  gaban mirro ina ɗaura ɗan kwalli ya shigo.

Ta cikin madubin da hango shi yana tsaye bakin ƙofar ɗakin ya naɗe hannayen sa a ƙirjinsa.

Juyowa nayi tare da gaishe shi ya amsa yana ƙarisowa inda nake tsaye,riƙo hannu na yayi muka wuce dinning.

Da mamaki shimfiɗe kan fuskarsa yake tambaya na yaushe na tashi na haɗa wannan breakfast ɗin?.

Murmushi kawai nasaka na cigaba da zuba mana abincin,wani lokacin inyana magana na tankamasa ma yakan zama min mayuwacin abu.

Jallof ɗin taliya ne sai dai bansa vegetable sosai ba,kasancewar nasan habib ɗin baya ta'ammalin da duk wani abu green kamar alayyahu da dai-dai makamantarsu saboda lafiyar zuciyar sa.

Sosai mukaci abincin suna  ci muna hira cikin nishaɗi.

Ummi ce ta ƙirashi ya ɗauka ladabtar da murya yayi ya gaida ta, ta amsa sannan tace ya bani wayar.

Sai dana gaishe ta ta amsa tare  da tambaya ta ya kwanan baƙunta nace.

"Alhamdulilla"

Na faɗa ina ɗagawa habib ido ɗaya irin abun nan dake nuna dako lafiya? Sakamakon kallon danaga ya tsare ni dashi.

Wanda izuwa yanzu na fara karantar hakan na daga cikin ɗabi'arsa,muryar ummi ce ta katse min hanzari.

"Anjima yasira zata kawo min kayan da dangin mahaifiyar habib suka miki".

"To Allah ya kawo ta daman inada faɗa da ita".

Sallama mukayi sannan na miƙawa masa wayar shima ɗin sallamar sukayi.

Muna gamacin abinci ya  miƙe tare da faɗin"Akwai wasu abokaina dasukazo a hotel suka sauƙa so innaso naje wajen su kafin su wuce".

Kamar banji saba nayi na miƙe ina tattare kwanonka,izuwa yanzu kam na fara tsorita da irin tsanar da zuciya ta kewa habib ko muryarsa banason ji balle kuma na ganshi kusa da ni.

Riƙo hannu na nayi tare da tsaida idanunsa cikin nawa.

"I'm sorry Tawan wallahi daga nisa sukazo ne shiyasa zanje muyi sallama kafin su tafi,badan haka ba inna tabbatar miki babu abinda zaisa in fita a irin wannan ranar".

"La!ba komai hamma habib na fahimta"na faɗa ina kashi masa ido ɗaya cikin sigar zolaya nayi maganar sannan na raba hannu na dan nasa.

Gwalo idanu waje yayi kafin yace"waye hamman nakin?".

"Kai mana"

Sai daya murmusa kafin yace"zan dawo ai zamu gamu".

Sosai na saki dariya sannan ya fita key ɗin motar dake ajiye akan dinning ɗin na ɗauka nabi bayan sa.

Har jikin motar na rakashi tare dayi masa kyawawan,addu'ar sauƙa lafiya sannan yaja motar ya tafi.


Sai da naga ficewar motarsa daga gidan sannan na sauƙe wata zaffafar ajiyar zuciya,yayin da wani nishaɗi ya sauƙa min lokaci guda ciki na dawo.

UWATACE SANADI

       Tsarawa/rubutawa

           ©Maimunah Tijjani Iyam

_____________________________

Page 2⃣4⃣




A falo na tsaya ina ƙarewa falon kallon,furnitures set biyu ne a ciki da masu launin shuɗi da kuma golding.


Sai makeken Tv plasma dake manne cikin wall ɗin falon.

Lokaci guda idanu na suka sauƙa akan hotunan mu na bikin dake ajiye gefen Tvn sai kuma wasu da aka kafesu a cikin wall.

Matsowa nayi ina bin hotuna da kallo wasun ma bansan lokacin da aka ɗauke su ba.

Waya ta data fara ringing ne,tasani barin cikin falon na wuce dinning.

A hankali na ɗaga kiran tare da kara wayar a kunne na daga ɗayan bangaren habib yace.

"I forget to tell you i love you,shine na ƙira na faɗa miki".

Wasu zuffa ne suka keto min lokacin guda bakina na mungun rawa nace"me  too"na faɗa ina dai-dai nutsuwa ta.

Sosai nakejin sautin dariyarsa kafin yace"ki kula min da kanki kinji".

"Uhmm kaima haka".

Ban jira amsar dazai bani ba na kashe wayar,dawowa falon nayi na kwanta akan ɗaya daya cikin kujerun ina lumshe ido na.

Bansan sanda na fara hawaye ba sai jin ɗuminsu nayi sunabin kunci na,Arazane na tashi jin ana bubuga hannun kujerar danake kwance akai.

Ganin Yasira yasa na watsa mata harara ina ƙoƙoarin tashi na zauna tare da share hawayen dake fuskana.

"Anty lafiya kike hawaye,ina shi hamma Habib ɗin?".

Yasira ta faɗa  tana bina da wani kallon tuhuma.Ban kulata na fara gaishe da mata biyu da sukazo tare wanda suke ƴan-uwan mahaifiyar Habib,amsawa sukayi suma suna ƙara tambaya ta dalilin hawaye dasu gani a fuska na.

"Ba komai wallahi,wani abu ne ya shigar min cikin ido"na faɗa ina miƙewa domin ɗauko musu abin sha.
Yasira kam nomban Habib ɗin,tashiga dialing  ringing biyu kuwa ya ɗauko.

Nan ta sanar dashi halin dasuka zo suka same ni,da mamakin ta sai taji ya saki dariya sannan yace.

"Wai ba dan na fita ne wajen wasu abokaina da sukazo daga malesia yau zasu koma shine nakega dalilin wannan kukan".

Murmushi ta saka kafin tace"Au hamma kace kukan daɗi take?".

Shima murmushin ya maido mata dashi sannan sukayi sallama,ina shigowa falon hannu na ɗauke da tray.

Kallo ni tayi yayin da take maida wayar cikin jakar ta tace.

"Anty lalle hamma na shagwaɓa ki da yawa dan ya fita shine kike kuka".

Sai da na galla mata harara sannan nace"Anyi ɗin"na faɗa ina juya idanu na.

Anan suka wuni yasira take sanar dani su inna tun asubar fari suka tafi.

Sai yamma sosai sannan suka tafi,bayan na musu rakiya sannan na dawo falon ina duba kayan dasu zo min dashi.

Zannuwa ne da kwaraye wanda aka ƙawatasu da launuka,da zane masu ɗaukar hankali irin dai na ƴan mutan niger.

Sai kuma kwaskon turaren wuta,suma sun ƙawatu da zanuka da kuma turaren wutan.

Sosai kayan suka burgeni duk da ba wani yawa gare su ba,amma naji daɗin wannan kyautar tasu gare ni.

Ƙaran shigowar motar habib danaji ne ya kawar da annurin dake fuska na,nan take naji raina yayi baƙi ƙirin,kamar na fita da guda haka nakeji.

Ina zaune ya shigo miƙewa nayi na iso gareshi tare da karɓan ledan dake hannunsa,Inajin yanda zuciya ta take tsananta bugu.

Rungumo ni yayi muka ƙariso cikin falon,saurin raba jiki na nayi da nashi.

"Bari na kai maka ruwan wanka sannan ka huta"na faɗa murya ta na rawa haka nan ma jiki na.

Ban jira amsa dazai bani ba na juya cikin sauri na wuce bedroom ɗinsa,Bathroom na nufa na haɗa masa ruwan wankan sannan na fito.

Ina fitowa yana shigowa ɗakin kayan jikin sa na fara rage masa.

"Jinki nake a ko'ina a cikin raina shiyasa bazan daina yiwa Abba addu'a ba,Allah yakai haske kabarin sa daya haifo min ke".


"Amin ya Allah"na faɗa ina cire masa safan dake ƙafansa.


Miƙewa yayi ya shiga toilet ɗin,kaya na ciro masa na ajiye masa akan bed ɗinsa sannan na fita.

Sannan na fito na buɗe ledar daya shigo da ita,kaza ce da kuma rufaida yogurt ɗayan ledar kuwa fruit ne.

Kitchen na wuce na zuzzuba komai a mazubin sa sannan na jere su akan dinning.

Waya tace ta fara ringing na ɗaga da sauri ganin sunan yaya fawas,daya bayyana cikin screen ɗin wayar ina murmushi.

Sai da muka gaisa nake tambayar sa yaushe zai zo gida na?.

Sosai yake sakin dariya kafin yace"Haba!ai sai kin shekara tukunna"


"Kai!yaya fawas ai kuwa ni zanzo".

"Kul ban yadda ba kiyi zaman ki a ɗakin ki daga yin auren har zaki fara zuwa gida"ya faɗa yana ɗan ƙara sautin muryarsa.


Fitowar habib ya sani haɗiye maganar,da ke maƙoshi na fuskar shi ɗauke da murmushi ya nufo inda nake zaune.

"Ina habib ɗin fa".

Tambaya da yaya fawas ya jefo min wanda ya sanya ni dawowa daga duniyar tinanin danayi nutso cikin sa.

Miƙewa habib ɗin wayar nayi,ya karɓa tare da karawa a kunnensa ba tare daya tambayan waye ba.

Sosai sukayi hira kafin daga bisani sukayi sallama,dinning area muka nufa mukaci abincin.

Fruit ɗin kawai habib yake sha ni kuwa sosai nake yagar kazar ina bin bayanta sanyanyan rufaida yoguth.

Sai danaji ni nayi ƙatti sannan muka  tattare wajen,wata hamma na saka ina lumshe idanu na.



"Bacci ko?".


Gyaɗa kaina nayi yace"to ki tashi muyi salla sai ki kwanta ko?".


Ya faɗa yana riƙo hannu na sai da muka gyara dinning ɗin sannan muka ɗauro alwala muka gabatar da sallan magrib.


Muna zaune akan sallayar aka ƙira isha'i mukayi .


Miƙewa yayi  ya kamo hannu na muka nufi ɗaki,wanka na shiga na fito nayi shirin kwanciya.


Sanda mafito yana zaune akan sofa yana aiki a lapton,ɗinsa kayan dasu yasira suka taho min dashi na ɗebo su na nuna masa.

"Masha Allah kaya sunyi kyau"ya faɗa yana guban lapton ɗinsa.


Rufe lapton ɗin nayi na cuno baki ina faɗin.

"Hamma magana fa nake maka kana kallon lapton".

Naɗe hannayen sa yayi a ƙirjin sa yana sakin murmushi yace.


"To shikenan inajin ki ".

Kayan na turo mishi gaban sa inna ce "kaga kayan sunyi kyau ko?"na faɗa ina tsaida idona akan sa.

"To yanzu ke mezakiyi da wannan kwaryan haka da yawa".

Ɗan hararar sa nayi ina cewa"ba ruwanka nidai inason abina".na faɗa ina tattare kayan.

Saurin kamo ni yayi ya manna da jikinsa na fisge,kayan naje na ajiye a store tura ƙofar nayi sannan na jingina a jikin ƙofar.


Da sauri-sauri hawaye dake ambaliya akan kunci na,zuciya ta na bugawa da tsananin ƙarfi.

Dafe goshi na nayi ina karantu duk wata addu'a darazo baki na.

"Ya Allah ka fini sanin kaina ya Allah ka sausauta min wannan tsananin danake ciki,ka nuna min ƙarshen shi ina tsoron ranar da zaka kamani akan laifin kasa bawa habib, hakkinsa na aure dana take a gaban dukkan halittunka Allah ka kawo min sauƙi ".


Na ƙarishe maganar ina sulalewa ƙasa daga jikin ƙofar.

Duk yanda naso kyautatawa habib,tsananin tsanar da zuciya ta ke masa wanda inada tabbacin ko a mizani,aka sashi sai ya rinjaye soyayyar danake masa.


Shike hanani kyautata masa duk da yanda shi yake buri da kuma ƙoƙarin sauya rayuwata izuwa cikin dauwamemman farin-ciki.

Kamar an tsigara min wani abu haka na zabura na tashi wanke,fuskata nayi a kitchen sannan na koma ɗakin.


Yana zaune inda na barshi yana waya da granny,gefensa na zauna ina ƙurawa fuskar shi kallo sosai fuskar tamin baƙi ƙirin a idanu na.

Saurin kawar da kaina gefe nayi,ina ƙoƙarin maida idona ga TVn dake aiki a cikin bedroom ɗin.


Sai daya bani wayar muka gaisa da granny tare da ƙara,roƙo na dana kula da lokutan shan maganin habib ɗin Sannan sukayi sallama ya ajiye wayar.

Sosai yake jana da hira duk yanda zuciya ta take min soya,haka na danne na ke bashi amsa cikin walwala.

Saukar ajiyar zuciyan danakeyi neya tabbatar masa da nayi bacci kan bed, yakaini sai daya min addu'a kamar yanda ya saba sannan ya rufa min blanket.

Shafa goshi na yayi a hankali yake furta"Hibba inason ki so mai tarin yawa".

"Nima haka hamma habib".na faɗa ba tare dana buɗe ido na ba.


Murmushi ya saka sannan ya kashe wutar ɗakin ya fita.

Washe gari da wuri na haɗa mana breakfast,a gurguje habib yaci kasancewar yanada baƙi a office.


Sanda zai fita har da ƴar hawaye ta,sosai ya shiga aikin lallashi na yana cewa"ba daɗewa zaiyi ba zai dawo".

Sai dana mishi rakiya tare da masa addu'o'i sannan ya tafi.


UWATACE SANADI

        Tsarawa/Rubutawa

    _Maimunah Tijjani Iyam_


_________________________


Page 2⃣5⃣




Ranar wuni nayi na rasa abinda dake damuna,kamar na fita a guje daga cikin gidan domin zaman gidan ya gundure ni.

Alwala na ɗauro na fara jera salloli,sai dana iddar sannan na ɗauki Al-qur'ani na fara karantawa.
Sosai na farajin sanyi a cikin raina na daɗe ina karatun sai danayi sallan zuhr sannan na tashi na fara haɗa abincin rana.
Simple girki nayi dan na lura Habib ɗin,yafi son abinci marasa nauyi da kuma sauƙin sarrafawa.

Ina gamawa na jere su akan dinning,dai-dai lokacin da waya ta fara ringing.
Sai dana faɗaɗa fara'a ta sannan na ɗaga ƙiran ganin sunan Anty Amina ya bayyana.
Sosai mukayi hira da ita take tambaya ta yanayin zaman namun.


Sai dana sauƙe ajiyan zuciya kafin nace"Anty Amina gashi nan dai wallahi ba abunda ya sauya,sai ma ƙara tsanani dayake yi".
Na ƙarishe maganar ina sharar ƙwallan dasuka ciko min idanu.Itama ajiyar zuciyar ta sauƙe sannan tace"Hibba ki cigaba da addu'a akwai wasu ma zan kawo miki,in sha Allah komai zai wuce tamkar mai komai bai taɓa faru ba.Meye ne bai faru ba a zamanki a gidan malam habu tsohon miji na?,amma ba gashi ba yanzu kamar ba ayi ba".


"Haka ne Anty Amina amma nikam har na fara tinanin ko,inace masa ya sauwaƙe mi....".


Saurin katse ni Anty Amina tayi ta hanyar faɗin"Kul Hibba wannan shine kuskuren daza kiyi mafi muni a rayuwarki,ki dubi irin karamci na iyayen Habib sune sanadiyar cigaba da karatunki,su suka maida ki ga dangin ki sannan suka miki babbar sutura ta hanyar yarjewa ki auri ɗansu."

Sai data numfasa na wasu daƙiƙu kamar mai nazarin wani abu, kafin ta ɗaura da faɗin"Hibba aure shine rufin asirin ko wace ɗiya mace,idan kikace ya saki ki yanzu wani hujja kike dashi dazai zame miki madogara?,Da wani idon zaki fuskanci iyayen ki da kuma Fawas?".


"In sha Allah Anty Amina zanyi yanda kika ce zan koyar da zuciya ta haƙurin zama inuwa ɗaya da Habib".na faɗa yayin danake bawa ƙwallan dasuka ciko min idanu damar zubowa.
Ba kaɗan ba Anty Amina take kwanta min da hankali gami da bani wasu addu'o'in.
Ƙiran sallan Asr da aka farayi yasa mukayi sallama bayan tamin alƙawarin kawo min ziyara,dan lokacin da akayi aure tayi tafiya shiyasa bata sama damar halalta ba.
Sai dana gabatar da sallan,bayan nayi addu'o'in da Anty Amina ta bani na dawo falo.

Wayata na ɗauka na shiga dialing nombar Habib katse ƙiran yayi sannan ya ƙira ni.

"Ranki  ya daɗe "ya faɗa cikin muryar da take bayyanar da tsananin gajiyar dake tattare dashi.
Sai dana jefa masa tambaya na ya office ɗin?ya amsa da Alhamdulillah sannan na ɗaura da faɗin"Hamma yaushe zaka dawo?,wallahi nidai tsoro nakeji "na faɗa ina ƙara sausauta murya ta.

"Kinga wallahi yanzu muka fito daga meeting,so innayin sallan magrib zan dawo".

Ɗaukewar da wutar bob ɗin dasuke haska ko'ina na cikin falon sukayi,sakamakon ɗauke wutar nepa da akayi.Kafin kuma sola ta fara nata aikin yasanya ni ɗago kaina ina sauƙe idanu akan bob ɗin kafin nace"To shikenan tunda kace salla zakayi,amma dazaran ka iddar ban yadda a tsaya a ko'ina ba sai gida".


Sai daya murmusa kafin yace"Consider is done ranki ya daɗe".
Nima darawa na yi kafin daga bisani mukayi sallama,Ina zaune akam sallaya na iddar da sallan isha'i kenan naji ƙara shigowar motarsa,saurin shafa addu'ar dana keyi nayi sannan na miƙe tare da cire hijab ɗin dake kaina na cillashi akan bed na fito.

Sanda na fito yana dai-daita parking  cikin harabar gidan da ƙwayayen wutar lantarki suke hasko ko'ina kamar ba dare ba.
Ƙarisowa gare shi nayi ya riƙo ni muka shigo cikin gidan,sai na rakashi bathroom ɗinsa yayi wanka sannan muka fito abinco mukaci,sannan muka cigaba da hirar mu.


Ranar duk yanda zuciya ta take ƙara ayyanano min tsanar Habib kawarwa nayi na zage mukayi hirar mu.
Haka rayuwa ta cigaba da juyawa,lokaci na tafiya yayin da duk wani bugun ko wani daƙiƙa na agogo tsanar Habib dake sake hayayyafa a cikin zuciya ta.
Ana haka muka koma makaranta,idan na fita ji nake kamar kar na dawo cikin gidan.
Mota Habib ya saya min sannan ya ɗauko min drivern da zai dinga kaini kafin nima na koya.

Tun ranar da aka kawo ni gidan Habib,bamu taɓa haɗa ɗaki dashi ba har izuwa wannan lokacin.
Sau ɗaya yayi ƙoƙarin aikata hakan bayan  mu kwanta sosai nake,sakin kukan duk yanda naso dannesu kasa yin hakan nayi sai da suka fito.

Tashi yayi tare da kunna wutar dake kan site drawer a gefan shi yana cewa"Hibba lafiya?,meya same ki?".

Rasa abin faɗi nayi sai tsananta kukan danake yi danayi,matsuwa yayi tare da kamo hannuna.

"Meya ke damunki,ki sanar dani "ya ƙara tambaya a karo na biyu.

Sauke ajiyan zuciya nake a hankali cikin kuka nake faɗin"Kayi haƙuri Habib wallahi ban iya kwana tare da mutum ba ɗaki ɗaya ba,balle kuma ace gado ɗaya".banida da abunda zan faɗa a wannan lokacin daya wuce haka.Ƙara matse hannuwa na dake riƙe cikin nasa yayi da ƙarfi,sai da hannu na yayi wani ɗan ƙara.

Manyan idanunsa daya ƙara waresu ya kafe ni dasu, sai a sannan naga wauta na ƙarara bai dace a matsayinsa a gare ni ba faɗa masa wannan maganar ba.
Saurin sunkuyar da kaina ƙasa nayi ɗago haɓata yayi da hannunsa.

"Duk wani abunda zai zamto silar wanzar da  farin-ciki a fuskar ki,ki sani ina sonsa koda kuwa hakan na nufi nizan cutu"ya faɗa yana ƙara kafe ni da ido.


Wasu hawaye ne suka biyo gefen kunci na,nan baki na ya ɗauki rawa haƙware na har ƙara sukeyi kamar mai rawar ɗari nace"Habib dan Allah ka tayani addu'a Allah ya kawo min sauƙi cikin gaugauwa".

"Ko yaushe kina cikin addu'a na hibba matuƙar ina cigaba da numfashi a goron duniya bazan daina miki addu'a ba".

Ya faɗa yana lumshe idanunsa sa ya buɗe su yayin da yake miƙewa,Magana na fara ƙoƙarin yi amma yayi saurin dakatar dani da faɗin"Ya isa haka bana buƙatar kice komai,kuma wallahi har ga Allah banji haushin ki maganar ki nasan daman dole kiji abun wani irin,saboda rashin sabo".
Kaina kawai na ɗaga masa alamar ina sauraron sa"Ki kwanta yanzu kar gobe ki makara zuwa school ko?".
Ya faɗa yana rufa min blanket ɗin,sai daya min addu'a ya shafa  min sannan ya fita.
"Hamma inasonka"na faɗa ina bishin da kallo.


"Nima haka Hibbatuu"

Ya faɗa tare dajan harafin ƙarshen,hakan ya sa na tino da Inna a lokuta da yawa haka take ƙira nada hHibbatu.
Duk yanda naso nayi bacci kasa zuwar min yayi tashi nayi,naci kuka har na godewa rabbana.
Sosai kaina yake sarawa,tashi nayi na ɗauro alwala nazo na fara salla ina iddarwa na fara karatun qur'ani.
Sai wajen ƙarfe uku sannan na samo bacci asuba ma a makare nayi sa.

Sannan na haɗa breakfast nayi wanka,nayi shirin tafiya makaranta na fito.
Har ana neman ƙarfe takwas,Habib bai fito ba ɗakinsa na nufa na tura ƙofar a hankali.
Tare da rangaɗa sallama yana kwance akan sofa daga yanayin,sa na tabbatar da dakyar yasamu baccin.


Matsowa nayi na tsaya kusa da kujeran dayake kwance kallo ɗaya nayiwa fuskarshi na ɗauke kaina tare da runtse idanuna da ƙarfi.
Sosai fuskar shi ta ƙara baƙancewa a idanuna  ƙwayar idonsa,da haƙwaransa sune kawai nake ganinsu da haske.


A jikinsa yaji ana kallon sa a hankali ya fara ware idanunsa saurin maida hawayen dasuke shirin zubo min nayi.


"Hamma ka tashi lokaci fa ya ƙure"na ɗaure na faɗa yayin da wani miyau mai ɗaci ya taro min a baki na.


"Subhanallahi!"


Yana faɗa yana ƙoƙarin tashi,tare da sauƙe idanunsa akan agogon dake maƙale cikin wall ɗin bedroom ɗin.


Toilet na shiga na haɗa masa ruwan wanka sannan na fito,towel na basa sannan ya shiga wankan.


Sai danaga shigar sa sannan na saki kukan dayake nuƙurƙusa na cusa kaina nayi cikin gwiwoyi na.

Tabbas nasan ina cutar da Habib amma bayin kaina bane nima.Na kasa tabbatar da yaƙinin da iyayen habib suke dashi akaina,na zan samarwa ɗannasu ɗan gaban goshi farin-ciki.
Jin kamar za'a buɗe ƙofar banɗakin,ya sanyani sauri goge fuska ta.Na fara  ciro masa kaya shadda ce nevy blue.

Wacce taji aiki sannan na ciro masa hula da agogo,taimaka masa nayi na shirya sannan muka fito falon.
A gurguje mukayi breakfast ɗin kasancewar inada lectures ƙarfe tara,sai dana bashi maganin sa yasha sannan muka fito.

"Yau fa nizan kaiki school"ya faɗa yayin da muke nufar cikin parking lot ɗin,yana karkaɗa key ɗin dake hannun sa.


Kallo shi nayi tare da sakar masa murmushi sannan nace"A'a Hamma na yafe kar kayi lattin zuwa office".


Sai daya ɗan hararo ni sannan ya shiga faɗin"Aikin me nakeyi dahar zai hanani kaiki school na yau kawai?,to drivern ma tsallamar sa za'a yi,daga yau nizan na kaiki kuma ina ɗauko ki "


"To ranka ya daɗe yanda kake so hakan za'ayi".


"Yauwa dan abin ya fara motsawa"ya faɗa yana buɗe min ƙofar motar.


"Meye kenan?"na jefa masa tambayar tare da tsaida idona akan sa ina jiran amsa ta.

Sai daya juya idanunsa kafin yace"kishi mana".Sosai ya bani dariya yanda ya juya idanun nasan,kamar wata mace.


    UWATACE SANADI
             Narh
     _Maimunah Tijjani Iyam_

______________________


Page 2⃣6⃣




Har muka isa cikin makaranta bamu daina hira ba,ba tare da san rayukan muba mukayi sallama.
A wajen na tsaya ina bin bayan motar da kallo,yayin da yake ficewa daga cikin harabar makarantar.
Nauyayyen ajiyan zuciya na sauƙe ina ma-inama ace farin-ciki zai ɗaure a zaman mu,ina ma ace zamu rayu kamar ko wasu ma'aurata,zanso na zamewa habib  abokiyar rayuwa ta ƙwarai incike duk wani giɓin dake cikin zuciyarsa.


Ta yanda bazai nema komai,daga gareni ya rasa ba ko badan soyayyar dake nuna min a aikace ba.Dan ya cancancin hakan daga gare ni.Nasha jin ana faɗar cewa "zuciya nason wanda yake kyautata mata".
Amma narasa gane tawa zuciyar wata iriyar zuciya ce,marar godiyar Allah da duk yanda habib ke kyautata mata hakan ya kasa tasiri wajen canzuwar ta.Bansan sanda na fara hawaye ba sai ji danayi wata ƴar department ɗinmu Limat Auwal ,ta faɗa kafaɗuna tare da faɗin"Fatima suleiman lafiya kike tsaye ana ke ɗaya kina hawaye?,gashi har an kusa shiga lectures".

Saurin ƙirƙiro murmushi nayi na yaɓa a fuskata kafin nace"Lafiya kalau wallahi kawai,yau na tashi banajin daɗin jiki nane".Na ƙarishe maganar ina share ƙwallar da bakin hijabi na.

Kallon da take bina dashi,ya tabbatar damin da bata yadda da abin dana faɗa mata ba.Gaba nayi na ɗauki hanyar dazai sadani,da department ɗinmu ina cewa"Kinga kizo mu tafi,kinsa halin lecturer ɗin nan inya rigamu shiga ba barin mu  zaiyi mu shiga ba".
Biyo baya na tayi da ɗan saurin ta kasancewar duk makarantar ba wanda baisan halin prof A.S karumi ba,matuƙar  ya rigaka shiga class to saidai kayi zaman ka a gindin bishiya dan bazaka shiga ba.
Ƙarfe sha biyu muka fito,masallaci mukaje mukayi sallama sannan muka saya abinci mukaci.Sannan muka koma lectures wanda muke dashi ƙarfe biyu,sai ƙarfe huɗu sannan muka fito.

Habib na ƙira na sanar dashi baifi mintuna goma sha biyar ba yazo.Gidan Ummi muka nufa ya sauƙe ni kan zai dawo anjima ya ɗauke ni,A falon ummi na tarar da duk mutanen gidan hadda daddy.

Cike da farin-ciki suke amsa gaisuwar tawa,yasira kam kamar ranar ta fara gani na tana maƙale gefe na tana faɗa min yanda tayi missing ɗina.Nan muka zauna muka sha hirar mu,hadda sayyid dan shima yazo gida lokacin.

Sai bayan magrib sannan habib yazo,muna zaune nan a falon ya shigo da sallamarsa ummi ta amsa.

"Ango mijin  amarya sai yau aka tino damu"Sayyid ya faɗa yana duban wayarsa.

Ɗauke kansa yayi kamar baiji abinda ya faɗa ba,ya ƙariso ya zauna ya gaida Daddy da Ummi,sannan yasira da Sayyid ma suka shiga gaishe shi.
Amsawa yayi tare da yiwa Yasira ishara da hannunsa akan tazo nan kuwa ta dawo kusa dashi ta zauna."Kai kuma meka dawo yi?,Sayyid kana wasa da aikin nakan nan fa"cewar Habib.
Ajiye wayarsa da yake latsawa tun ɗazu Sayyid yayi sannan yace"Haba!Hamma ni shikenan kuma bazan so gida ba,haba satina nawa acan Hamma ka dubi fa duk yanda na rame".


"Kai dai kam,Sayyid sai shiriyar Allah yanzu ne lokacin dayafi dacewa ace ka ƙire aikinka da muhimmanci".
Daddy ne yayi saurin amshe zancen ta hanyar faɗin"Gaskiya ne abinda Habib ya faɗa,ni na rasa me kake zuwayi gidan nan yanzu yaushe ka tafi har ka dawo,suma makarantar dasuke barinka kakeyin son ranka".


"Yanzu dani ne da ya fara cewa ni malalaciya ce kullum sai zaman gida"Yasira ta fada tana watsa masa idanunta.
Miƙewa Sayyid yayi tare da shurin Yasira da ƙafa,sannan ya zauna kusa da Ummi tare da kwantar da kansa akan cinyar ta.

"Ummi kinajin su ko wai hadda wannan parrot mouth ɗin ma duk sun saku ni gaba,Dan Allah inbanzo na  ganku ba ina zanje".ya ƙarishe maganar tare da shagwaɓe fuska.


Ummi tace"Haka ne Sayyid duk ka kyale su ko yaushe kazo zan buɗe maka ƙofa".
Dariya muka saka sosai,nikam hadda riƙe ciki sai da mukayi sallan isha'i anan mukaci abinci sannan mukayi azamar tafiya.Kamar nace masa ni ana zan kwana,sai kuma naga kamar hakan dazanyi zan cutar dashi da yawa kuma zaisa su ummi suyi zargin wani abun.

Haka muka tafi bayan Yasira ta mana alƙawarin zuwa tunda muka fara tafiyar bance uffan ba shi kaɗai yake ta surutunsa.
Muna isa kowa na wuce ɗaki wanka nayi sannan na fara shirin kwanciya,ta cikin madubi na hango shi yana tsaye bakin ƙofar ɗakin,kamar ko yaushe ya naɗe hannayensa a ƙirjinsa.

Tashi nayi na ƙariso gare shi sai dana ɗaga kaina sama kafin nake kallon fuskar shi nace"Hamma inason naje wajen su Inna,wallahi ina kewarsu daga nan sai ka kaini na gaida Granny".

Murmushi yayi tare da riƙo hannu na muka dawo cikin ɗakin,sai da muka zauna bakin gado sannan yace"To in sha Allah gobe zan kaiki matuƙar hakan zai saki farin-ciki".

"Na gode hamma".

Na faɗa ina ƴar tsalle ta,sannan na tashi naje na ɗauko masa maganinsa da ruwana bashi ya sha.

Mun ɗan taɓa hira kafin kowa yaje ya kwanta.Nikam tsabar zumuɗin da son ganin su baffa na da Inna kasa baccin arziki nayi.Assalatun farko kuwa na tashi,tsaf na gama shiryawa na nufi ɗakin Habib.
Yana zaune dawowarsa daga masallaci kenan."Yanzu nake shirin zuwa na tadaki kiyi salla ashe ma har kin tashi".

Sai da ɗan rusuna sannan na gaishe shi ya amsa,tare da cigaba da faɗin"Ya naganki haka da shirin ki?".

"E na shirya ne".


"Kin shirya zuwa inna kenan?"ya sake jefo min tambaya.

Cikin ƙosawa da mu tafi ɗin nace"Hamma zuwa gano mana".

Dariya ya saka mai sauti sai dayayi mai isharsa sannan yace"Kin duba agogo kuwa ƙarfe bakwai ma fa batayi ba".


"Nidai mu tafi da wuri tunda daga can har gidan granny zamu wuce".Na faɗa ina ninke sallayar daya dawo daga masallacin da ita.
Ganin zai fara wata maganar ya sanya nayi,sauri na faɗa toilet na haɗa masa ruwan wanka na fito sannan na fara ciro masa kayan da zaisa.
Ganin da gaske nake yasa ya  shiga wankan bai ɗau lokaci ba ya fito,dumping ruwan jikinsa na masa sannan ya shirya muka fito.Sosai  driven yake sheƙa gudu da motar,kafin ƙarfe goma kuwa muka iso cikin gano.

Wani farin-ciki,nishaɗi ko murnar dana kasa bambamce,a cikin ukun nan wane nakeyi naji suka mamaye birnin zuciyata.Tun kafin drivern ya gama dai-dai parking,a ƙofar  gidan baffa na fito daga motar da gudu na,na shiga cikin gidan ina ƙwalawa Inna ƙira.


Itama da murnar ta ta fito daga ɗaki nan kuwa na rungume ta,tare da Adda Barira wacce tunda Habib ya ƙira Baffa yake sanar dashi da zuwan namun.

Hajara ta faɗa mata nan gidan tazo dan aiwatar da umarnin malam dan dole sai da taimakon ta,abin zai tafi ba tare da amsama mishkila ba.
Sallamar Habib yasanya Inna raba jikin ta da nawa,sannan ta ɗauko sabuwar tabarmar kaban ta ta shimfiɗa mana.

Sai da muka zazzauna kafin,muka shiga gaida Inna ta amsa tana mai sanya mana albarka.A hankali nakai dubana ga ƙofar ɗakin,Anty hajara wanda tun fitowarsu sukayi cirko-cirko suna tsaye a wajen nace musu.

"Ina kwana nan ku".
Sai a sannan suka dawo daga kallon mu nida Habib,da suka shagala dayi mussamman Adda Barira dan wannan ne karo na farko data fara ganinsa.
"Lafiya kalau mutan katsina"Cewar Adda Barira sannan ta ƙariso,bakin tabarmar ta zauna cikin salo na gwanancewa a munafirci.

Itama Anty hajarar kujera ta,ɗauko ta zauna tana ta faman washe baki.Ladabtar da murya Habib yayi kafin ya shiga gaishe su suka amsa ba yabo ba fallasa.

"Lafiya kalau yaro,kuna nan dai lafiya ko ina fatan ba wata matsala?"cewar Adda barira.

Ko ni da har yanzu ƙuruciya bai gama bari na ba sai dana sha jinin jiki na,ga duk mai hankali wannan tambayar tana cike da manufofi balle kuma Inna.Dan yanda tayi maganar sai nake tinanin kamar ko ta ganu irin zaman da mukeyi da Habib ɗin ne.

Shigowar Baffa shiya katse Habib daga,maganar da zaiyi.Washe baki Baffa yayi kana yace"Lalle da mutan katsina ta dikko har kun iso?".

"E wallahi Baffa dayake tun a lokacin danake sanar dakai ma zuwan namu a waya har mu taso".

Habib ya faɗa yana miƙewa tare da Ƙarɓan fartanyan dake hannun baffan,ya ajiye gefe guda.Zaman Baffa yayi nan kuwa muka  shiga gaishe shi yama amsawa.

Kwaɗon zogala da Inna tayi ta kawo mana,sosai mukaci har muna rige-rigen kai loma nida Habib.Ganin haka yasanya Baffa faɗin"ko a ƙaro muku ne?".

"A'a Baffa sai dai anjima,yanzu kam mun ƙoshi"na faɗa ina suɗar yatsa.

Tashi Habib da Baffa sukayi suka koma ƙofar gida,yayin da muka kafa hirar mu nida Inna lokaci bayan lokaci Hajara take jefa baki a cikin hirar tamu.

Adda barira kam izuwa yanzu na gama fahimtar so take ta kaini ga bango,domin duk tambayar da zata min sai ta sako.


 "Yaya zaman ku da Habib ɗin ina fatan kuna zaune kalau ko?".

Murmushi kawai nake sakar mata,ko kaɗan ban yadda nayi maganar zaman dake da Habib da ita ba.

Ƙiran sallan zuhr  da aka fara,ya sanya Inna tashi tayi alwala sai data iddar da alwala tata sannna tace"Hibba ki tashi ki ajiye wayar nan,kiyi salla ".ta faɗa tana gyara ɗaurin zanin ta mai launin ruwan ɗaurawa.

"To Inna ta yanzu nima zan tashi nayi ".

Na ƙarishe maganar tare da sakin dariya,dan chart muke da Yasira ta what's app ina gaya mata munzo Inna ta mana wannan shegen kwaɗon zogalan nan natan mai daɗin tsiya.
Ajiye wayar nayi sannan na tashi,na ɗauki butar da inna tayi alwala dashi na zubo ruwa na farayi.

Ina cikin shafar kai Adda barira ta fito daga banɗaki.

"Haba!Hibba dubi kanki,sai kace bana amarya ba duk kitso nan ya tsufa".

Nidai nasan kitsona bai tsufa ba,duk da cewa kuwa tun na biki nane da aka min.Amma ina gyara shi sannan bana wasa da kula da gashi na duk da ba wani gashin kirki gare ni ba,amma ina tattalin abina.


 UWATACE SANADI


        Tsarawa/rubutawa

     ©Maimunah Tijjani Iyam

________________________

Page 2⃣7⃣


Nikam ma dariya taso ta bani,bance da ita uffan ba na cigaba da alwala ta ina gamawa nayi ɗakin Inna.
"Inna wallahi wannan matar ta cika iyayi da yawa,to ni yanzu ina ruwanta da kitson kaina?".
Na faɗa ina shimfiɗa sallaya  Inna tace "Ai Hibbatu da gaskiyar ta har yaushe zaki bar kanki haka ki tsefe shi kafin ku koma sai a miki wani".

Sai dana fuskanto inda take zaune a bakin gado taya saƙar hula nace"Inna muda yanzu  zamu tafi,kuma ma to inna tsefe wa zaimin?".


"Hajara mana ai ta iya kitso,duk yawancin makwabtan mu nan suke zuwa ta musu".

Ta faɗa tana tattara zaren a ɗan yatsar ta.Nidai bance uffan ba ko lokacin danake gidan Baffa ko kaina zai dudduge Hajara ba  ta taɓa cewa in tsaife zata min ba.

Kawar da tinanin komai nayi a raina,na tada kabbara na farayin salla ta.Inna iddarwa ƙiran Habib yana shigowa waya ta,katse ƙiran nayi sannan na ɗauko maganin sa dake cikin jaka ta,na fita ina cewa"Inna bari yanzu zan dawo sai nayi tsifar".


Ƙofar gida na fito nan kuwa na hango shi zaune cikin mota Baffa kuwa na zaune bisa tabarmar dake shimfiɗe ƙofar gidan tare da wani baƙo.

Sai dana gaishe su sannan na wuce wajen Habib ƙofar motar na buɗe na shiga,ina shiga kuwa drivern ya fita.Magananin na shiga balla masa,sannan na ɗauko goran faro dana hango cikin motar na miƙa masa.

Runtse idanunsa yayi sannan ya saka maganin cikin bakinsa,kafin yabi bayansu da ruwa.

"Nadai lura yanzu kin maida hankalin ki wajen ganin inasha kwayoyin nan,ba tare da miss up ba ko?".

Sai dana murmusa kafin nace"E mana alƙawari fa na ɗaukar wa Granny,so kake inmuje taga ɗan jikallen nata ya rame tace bana kula dashi".

Sai daya ƙara kora ruwar sannan yace"to ai waɗannan maganin basu zasu hanani mutuwa ba in lokaci na yayi".

Sosai gabana ya  faɗi kamar faɗuwar aradu,cikin mintunan da basu gaza ɗaya ba idanu na ya kawo ruwar ƙwalla.

"Baza ka mutu ba Habib ka barni da tarin zunubin kasa sauƙe haƙƙin ka dana tauye,inna maka addu'ar tsawon rai ina fatan zuwar ranar dazan sauƙe haƙƙin ka da suka rataya a wuya.Bana son naje gaban Allah da wannan laifi mai girma".

Ina gama faɗin haka na fice daga motar,ko Baffa dayake tambaya ta lafiya ban saurara ba na wuce cikin gidan.
A soro na tsaya na goge hawayen fuska na,sannan na ƙarisa shiga ciki.
A tsakar gidan na iske Inna,Hajara da kuma Adda Barira.Kan tabarmar dana gani shimfiɗe a wajen nakai,mazaunaina na zauna tare da zare hijab ɗin dake kaina.

Nan Inna ta fara min tsifar tana gamawa Hajara ta miƙo min mataji na taje sannan ta fara min kitson.
Runtse idanuna nayi da ƙarfi ina faɗin"wash!kiyi min guda  goma".
Saboda zafin kitson dayake ratsa ilahirin kaina,har sai da jijiyoyin kaina suka fito raɗa-raɗa.

Kamar yanda na faɗa guda goman tamin dukka baya.Godiya na mata sannan ta miƙe tayi ɗakinta yayin da Adda Barira ta rufa mata baya.

Nikam a wajen nayi kwanciya ta,riƙe da waya ta ina ƙiran yaya Fawas.

Sai da Hajara ta rufo ƙofar ɗakin,tare da sake labulen sannan taja hannun Adda Barira suka zauna akan ledar data rufe ko'ina acikin ɗakin.

"Adda kinga rabo ko?,ƙarshe dai gashi mun samo gashin kanta".

Hajara ta faɗa tana ɗaga matajin dake riƙe a hannun ta,wanda yake ɗauke da gashin kaina a cikinsa.

Taƙaitaccen  murmushin gefen baki Adda Barira ta saka kafin  tace"Yo ai daman keki tsaya sanya har kike ganin bazaki iya samowa ba.Ai ƴar-uwa ina tabbatar miki tunda wannan yarinyar ta zamto silar da Adamu ya ɗaura hannunsa akan ki da sunnan duka,abin dabai taɓa faru a cikin tarihin aurenku ba wallahi sai tayi kuka da idonta kai wataran ma sai ta nemi hawayen tsiyayarwan ta rasa,Ke kaɗai kika rage min a duniya babu iyayen mu,babu dangi tsayayyu akan mu,muba ƴaƴa ba ba jikoki ba bazan taɓa iya zuba ido wani ya zamto sanadiyar shigarki damuwa ya kwana lafiya ba".


Ta ƙarishe maganar tana tino irin faɗi tashin dasukayi a rayuwa,da yanda dangi suka wofartar dasu bayan rasuwar iyayensu.

Karɓan matajin dake hannun Hajara tayi,sannan ta cire gashin dayake cikin tare da ɓallo bakin matajin tasa cikin wani ƙyalle ta ƙulle su.

Miƙewa tayi suka fito waje,muna tsaye muna sallama da Inna da kuma Baffa.
Har jikin motar suka mana rakiya hajara da Adda Barira ma ba'a basu a baya ba.


Muna tafiya Adda barira itama sallama tayiwa Inna sannan ta miƙe izuwa gidan malamin.
Yana zaune akan kilisa ta iske shi,zama tayi dan daman ba'a masa sallama inza'a shigo wajen sa.

"Allah gafarta malam ga abubuwan daka buƙata,mun samo su".cewar Adda Barira tana miƙa masa ƙullin.

Ƙullin ya karɓa sannan ya ware gashin ya ɗeba kaɗan a hannunsa ya watsa  cikin kwaryan dake gabansa,wanda yake cike da ruwa sannan ya shafa saman ruwan yana faɗin"Matso ki gani wannan itace?".

Matsowa Adda barira tayi ai kuwa hoto nane ya bayyana cikin ruwan,gani nan cikin mota muna tafiya har mun kusa barin cikin ƙauyen gano.

"Kwarai kuwa malam itace".

Sai daya bushe da wata iriyar dariya marar daɗin,sauraro sannan ya shiga ƙulunboton sa da sauran gashin.

Sai daya gama sannan ya buɗe idanunsa,dasuka rikiɗe suka juya kamar garwashin wuta.
Ciki wata iriyar murna mai tsananin, sanyawa duk wani wanda aka yiwa magana da ita firgici da tsoro yace"Daga yau ba ita ba kwanciyar hankali sun raba hanya dashi zata tsane shi fiye da komai a cikin duniya,sannan zamu aika mata da aljani ɗan mama ya hanata samun nutsuwa a cikin gidan".

Sai daya numfasa sannan ya ɗaure fuskarsa,kamar bashi yayi wannan dariya ɗazun nan ba.

Sannan ya ɗauko wasu layu guda biyu ya miƙa mata tare da faɗin.

"Ki sama tsohuwar rijiyar da ruwan cikin ta ya kafe,aka daina amfani da ita ki binne waɗannan layu a bakin rijiyar".

Kamar an sauƙe mata wani abu mai nauyi daga ƙirjin ta,haka Adda Barira taji ranta ya mata fes zuciyar ta ƙal.

Miƙewa tayi tare da ajiye masa kuɗin daya buƙata ta fice sai da ta binne layu sannan ta wuce gidanta.

Yamma sosai muka iso cikin damaturu rabona da garin tun ranar da muka bar YSU.Direct gidan granny muka wuce sosai bakinta ya kasa rufuwa saboda murna,mussamman dataga Habib ɗin kamar hankalinsa yanzu a kwance  yake.

Iya kusa ransa inda zata sani tayi saboda tarairayar da take min.Anan muka kwana washe gari kuwa sai da mukayi sallan zuhr kafin muka fara shirin tafiya.
Granny kam cewa tayi ya barni a wajen ta nayi kwana biyu,ya nuna mata bazai yiyuba saboda ina zuwa makaranta.

Haka muka tafi bayan muje gidan Dr bashir matar shi nada tsohon,ciki haihuwa ko yau ko gobe.Sai wajajen ƙarfe goma da wasu mintinu muka isa cikin katsina,a gajiya muka isa gida.

Ina shigowa na wuce ɗakina kayan jikina na rage nayi wanka na kwanta,ko jiran shigowar Habib banyi ba.

 Washe gari kuwa bamu da lectures sanin hakan yasa nasha bacci na,sai wajen ƙarfe takwas na farka.A gurguje nayi wanka na fito ban shafa komai a fuskana ba na fito na nufi kitchen.
Ganin Habib danayi  yana fere dankali yasa na tsaya,sannan nayi saurin cewa"Hamma kaika kanka kake wannan aikin?".
Na faɗa ina ƙarisowa gareshi tare da karɓan wuƙar hannunsa na fara fere dankalin.
Sai  daya kama waist ɗinsa,yana sharar zuffar data taru a saman goshin sa sannan ya ce"Yau dai kawai nace bari na mana girkin na hutar dake,sai kuma naga abin na neman gagara nafi 20min ina fere dankalin nan".


Murmushi na sakar masa ina cewa"to ai daman ba aikin ka bane,yanzu dai na hutar dakai bari naje na haɗa maka ruwan wanka,har kayi lattin tafiya office".

Shima murmushin ya maido min dashi tare da faɗin"A'a nima na hutar dake zan haɗa ruwan wankan dakaina".ya faɗa yana ficewa daga kitchen ɗin.
Cikin sauri nagama suya dankalin sannan  na haɗa tea,na jeresu a dinning ina tsaye a wajen ya fito.

"100 percent hamma kayi kyau kamar a sace a gudu".

Nafaɗa ina ƙarisowa cikin falo domin ɗauko masa maganinsa,sai dana ɗauko sannan na dawo dinning area ɗin.

"To ai ni bazan satu ba"ya faɗa yana jawo min kujera sai dana zauna na ɓalla masa maganin na miƙa masa da ruwa yasha.

Muna gama yin breakfast ɗin muka tattare wajen tare,sannan na masa rakiya har wajen motarsa.

Da mugun sauri drivern ya taso ganin fitowar habib ɗin,sai daya gaida mu sannan ya karɓa jakar habib ɗin dake hannu na.

"Jiya dana dawo malam Idi mai gadi yake sanar dani matar ka ta haihu har yau suna shine baka sanar dani ba".


Cewar Habib yana nuna kansa da key ɗin motar dake riƙe  a hannunsa.

Ƙoƙarin magana driven ya fara ya katse shi,ta hanyar zara hannunsa a aljihu ya miƙa masa wasu kuɗaɗe da bazasu gaza dubu ɗari ba.

"Ga wannan kayi hidimar suna dasu, sannan ka koma gida sai jibi sannan ka dawo aikin,iyalanka suna buƙatar kularwa a halin yanzu".

Sosai drivern yake godiya yana ƙara ɗurƙushewa a wajen,ɗaga masa hannu habib yayi alamar ya tafi.

Addu'o'i na shiga masa sannan ya tafi,na juya na koma a falo na tsaya na kunna kallo.

A hankali kunnuwa na suka fara jiyomin kamar ana ƙiran suna na a cikin bedroom ɗin Habib,wanda kuma na riga nasan cewa ni kaɗai ce a cikin gidan sai su malam idi dasuke waje.


UWATACE SANADI

         Tsarawa/rubutawa
 
     ©Maimunah Tijjani Iyam

____________________________

Page 2⃣8⃣


Rage volume ɗin kallon danakeyi,nayi sannan na kasa kunne kozan ƙaraji amma banji komai ba.Miƙewa nayi na ajiye remote ɗin dake hannuna,na nufi kitchen zan ɗauko ruwa.
Sosai gaba na ya faɗi ji danayi a wannan karan an ƙiran sunan nawan da ƙarfi kuma muryar yarace.
Tunin jikina ya ɗauki rawa duk da yanda zuciya ta take bugu hakan,bai hanani dakatawa daga hanyar ɗakin Habib dana nufa ba.
Sai dana runtse  ido na da ƙarfi,baki na na rawa na shiga karantu bismillah sannan na buɗe ƙofar ɗakin.
Wayam babu kowa kuma babu alamun ma wani ya shiga ɗakin,Sai dana lalleƙa har cikin bathroom amma babu kowa.

Dawowa falon nayi na wuce na ɗauko ruwar na dawo hannunane,ya shiga karkarwa tunin na sake kofin tangaran ɗin dake hannun na ya faɗi ƙasa ya tarwatse.
Wani ƙaton ƙadangare na gani akan kujerar falon inda na tashi ,irin masu jajayan kai ɗin nan.
A guje na fice daga falon na nufi bangaren malam Idi mai gadi ina ƙwala masa ƙira.

Tare da matarsa Hajja suka fito,kusan a tare suke tambaya na lafiya?.

"Malam Idi dan Allah ƙadangare ne ya shigo min falo,ka fitar min shi".na faɗa ina waigen falon.

"To".


Kawai yace sannan ya nufi hanyar falon bai daɗe ba ya dawo yana faɗin"Hajiya nifa banga komai ba wallahi,na duba ko'ina a cikin falo".

Sai dana dai-daita numfashi na dayake fizga tsabar kaɗuwar danayi sannan nace"Yana nan akan kujerar farko kana shiga zaka ganshi".

"Wallahi Hajiya babu komai sai dai muje dake ki nuna min".

Gaba yayi muka bishi a baya nida hajja muka nufi falon.Rarraba idanu na shiga ina duba inda naga ƙandagaren tabbas anan na barshi amma kuma yanzu babu ko alamarsa.

"Hajiya to kindai gani,gaskiya nan kam babu wani abun".cewar Hajja

Muryarta ne ya tsinkayo ni daga duniyar tinanin dana lula,figigi nayi ina cewa"to shikenan amma nidai tabbas na ganshi".
Fita sukayi sannan na rufe ƙofar na koma bathroom ɗina sai dana ɗauro alwala sannan na kwanta bayan na kunna  karatun alqur'ani a wayata.
Sai wajen ƙarfe biyu sannan na tashi,salla nayi sannan na wuce kitchen na haɗa tea kawai nakeda sha'awar sha.
Dan ba girki zanyi ba kasancewar Habib sai yamma sai dawo,ina buɗe ƙofar kitchen ɗin idanu na suka sauƙa akan wannan ƙadangaren,yana gefen gas yayin dayake fuskanto ƙofar kitchen ɗin.
Saurin maida ƙofar nayi na rufe inajin yanda ƙirjina yake dukan tara-tara.

"Innalillahi wa'inna alaihirraji'un".

Kawai bakina yake iya furtawa,shi na cigaba da nanatawa har na tsawon wasu minti na.
Nayi jihadi na buɗe ƙofar a hankali na shiga ware idanuna,ina sauƙesu dai-dai inda na ganshi yanzu wayam babu shi.

Da wani mungun hazari na fice daga kitchen ɗin,ɗan madaidaicin part ɗin malam Idi mai gadi na kuma  nufa.
Nan na iske matar shi Hajja tana wanke-wanke,gani na datayi cikin wannan yanayin yasata miƙewa tare da faɗin.

"Hajiya lafiya".

Ta ƙarishe maganar tare da nauraye hannuwan ta,da ruwar ɗaurayar wanke-wanken natan.

"Wallahi tallahi na ƙara ganinsa wai hajja bakwa ganin sa ne ni kaɗai nake ganinsa kenan?".

Na faɗa ina sakin wani kuka mai matuƙar ƙarfi,ƙarisowa gareni tayi tasa hannu tana goge min hawayen dake sintiri a samar fuskana kafin tace"Kidaina wannan kukan Hibba,bari Malam ya dawo sai yaje ya ƙara dubawa kozai gansa".
Kaina kawai na gyaɗa mata ina wucewa naje na fara mata wanke-wanken hawayen dake gudana a idona basu daina ba,kamar yanda nima banyi wani ƙoƙarin hanasu zubowa ba.
Dan a wannan lokacin,ina tinanin su kaɗai ne zasu sani naji sauƙi daga irin raɗaɗin da zuciya take ciki.
A nan part ɗin su Hajja na wuni koda malam Idi ya dawo Hajja,ta sanar dashi dayaje ya duba baiga komai ba.Sai gabda magrib Habib ya dawo,malam Idi dayaje buɗe masa gate nan yake sanar dashi ina bangaren su.

Sannan ya ɗaura da sanar dashi abinda ya faru,ina takure akan tabarma na tisa kwanon dambum tsakin masaran da Hajja ta kawo min.
Malam Idi suka shigo tare da Habib ina ganinsa naji wasu hawaye masu zafi sun shiga kwaranyo min.Gefen tabarmar yazo ya tsuguna tare da faɗin"Meyake faruwa ne duk na ganki haka,nata ƙiran wayanki bakya ɗagawa shiyasa ma na dawo yanzu dan ba kaɗan ba hankali na ya tashi,sai kuma malam idi yake sanar dani cewar wai ƙadangare ne ya shigar miki  falo".


"Wallahi Hamma duk inda na duba shinake gani,kuma su Hajja sunce basu ganshi ba".

Na ƙarishe maganar ina tsaida ƙwayar idona dayake cike fal! da sabbin ƙwalla,akansa cikin son  tabbatar masa da maganar tawan.
Handkerchief ya ciro daga aljihunsa ya miƙo min,na karɓa na share hawaye na sannan ya riƙo hannun na na miƙe tsaye.

"Malam Idi  bari muje na gani da kaina"
Ya faɗa yayin da muke ficewa daga part ɗin nasun,koda muka shiga ba inda habib mai duba ba amma babu wannan ƙadangaren.

Hakan ya ƙara tabbatar min dacewa ni kaɗai kenan nake ganinsa,ranar kota kan abinci bamu biba muka kwanta.
Sosai muka raya mafi yawa daga cikin,dare da nafilfili sannan muka fara karatun alqur'ani.
Ranar Habib a ɗakina ya kwana yana gadina,amma duk da haka na kasa runtsawa.
Haka muka waye gari na kafe kan Habib bazai fita ko'ina ba,Sosai ya shiga lallashi na tare da bani haƙuri akan cewa akwai baƙin da zaiyi daga Morocco,da zaran ya gama dasu zai dawo.
Haka ya tafi sannan na dawo ciki nikam daman ranar bazanje makaranta ba.
Saboda ana training na censors a department ɗin,tun ƙarfe takwas ɗin safe suke farawa zuwa shidan yamma,ko munje ba lectures za'a mana ba.


Ɗakin Habib na shiga na sama wani babban MP nasa memory card ɗin a ciki na kunna karatun qur'ani,na ƙure volume.
Da wuri Habib ya dawo inayin sallan isha'i na kwanta saidai,na kasa baccin haushin karnuka nakeji ta ko'ina a cikin kunnuwana.

Kamar karnukan a cikin ɗakin suke,tashi nayi na zauna ina karatu duk addu'ar datazo bakina.
Habib yana kwance kan sofa,yana bacci har nayi niyyar tashinsa sai kuma na fasa.
Daga jiya zuwa yau baya samun ishashshen bacci,dan sai da asuba yake kwantawa indan na tashi.
Ga kuma wuni dakeyi a office cikin kwanakin nan,alwala na ɗauro nazo na tada salla.

A hankali na farajin na dainajin haushin,ana kan sallayar na kwanta ina fitar da hawaye.
Wai sai yaushe zan sama farin-ciki ne a cikin rayuwa ta?,sai yaushe zan rabu da tarin damuwa da ƙunci?,sai yaushe nima zanyi rayuwa kamar yanda sauran,mutane sukeyi cikin farin-ciki da walwala?.
Da waɗannan tarin tambaboyin dana gaza samun,amsarsu bacci yayi gaba dani.Haka rayuwa taita juyawa yayin da ko yaushe gane-ganen danakeyi suke ƙaruwa,ko Habib inna faɗa masa cemin yake baya ganin komai.
Wai  kawai nasa abun a raina nane nima shiyasa nake yawan gani.Cikin kwanakin dabasu gaza bakwai ba,nayi wata mungun rama duk wanda yasanni sai yace na rame.
Ko makaranta daina zuwa nayi,indai ba fita mukayi da Habib ba bana samun nutsuwa,muna dawowa kuwa komai zai cigaba.

Koda Habib ya faɗawa Ummi rubutu tasa aka amso min ina sha sannan tace in daina sauraron kiɗe-kiɗe.
Daddy yace"Yasira tazo ta tayani zama kafin suga abunda Allah zaiyi".

Haka Yasira ta dawo gidan da zama,daga zuwanta da kuma rubutun da Ummi take karɓo min na rage gane-ganen.
Saidai hankali na yakasa kwanciya da Yasira a gidan sosai tasa mana ido.Inna tsoron ranar da zata ganu cewar,ba ɗaki ɗaya muke kwana da Gabib ba.
Haka kullum muna rigata kwanciya duk juyin duniyan nan dazan mata nacewa taje ta kwanta.Murmushi kawai take sakar min tare da faɗin"Anty kuje kuyi kwanciyar ku,niba yanzu zan kwanta ba".

Haka nan zamu tashi mubarta a falon,har sai taje ta kwanta sannan Habib zai koma ɗakinsa.

Ranar na dawo daga makaranta Habib ya ɗauko ni,muna tafe muna hirar mu.Yasira muka iske a falo tana kallo,sannu da zuwa ta mana sannan muka zauna.
Ruwan rubutun da Ummi ta aiko dashi ta ɗauko min nasha sannan na wuce ɗaki na.

Wanka nayi sannan na canza shiga,izuwa wata doguwar rigar material marar nauyu na fito.
Hakan yayi dai-dai da fitowar Habib daga ɗakinsa,dinning area muka nufa wanda Yasira da jere shi abincin data grika mana.

Sosai naci abinci rabona da abinci tun safe,muna gamaci Habib ya tafi masallaci.

Muma tashi mukayi mukaje mukayi sallan,sai da akayi isha'i sannan Habib ya dawo.Tashi mukayi mukaje muka kwanta,sai dai koda  muka shiga ɗaki zama mukayi.Muna jiran Yasira takoma ɗakinta shima ya tafi nashi ɗakin.
Sai wajen sha ɗayan dare sannan ta kashe kallon,tayi ɗakinta sannan Habib ɗin ma yafita bayan yamin sai da safe.

A hankali ya fito daga ɗakin ya shiga nasa dayake ɗan nisa kaɗan da nawa.Yasira wacce tazo ɗaukar wayarta data barsa yana caji a falon taga  fitowarsa.

Wayarta ta cire tana ƙarabin ƙofar ɗakin da kallo,tafi minti talatin a wajen tana jiran taga fitowarsa amma bai fito ba.
Komawa ɗakinta tayi tana tinanin to ko wani saɓani muka samu ne?.
Da safe da niyyar yi mana maganar  ta tashi,amma ganin mu datayi babu wani sauyi daga yanda muke,ya tabbatar mata da ba wani matsalar da muka samu.
Tare da Habib muka fita ya sauƙe ni a makaranta sannan ya wuce  office,sai ƙarfe huɗu muka fito na ƙira Habib na faɗa masa bai ɗau lokaci ba yazo,ya ɗauke ni muka dawo gida.
Muna zazzaune a falon bayan munyi salla munci abinci sosai nakejin bacci amma Yasira ta kasa ta tsare a  falon nan.

Ɗan satin datayi a gidan sai naji dukna matso ta tafi.Miƙewa Habib yayi bayan ya amsa ƙiran da aka masa a waya.

"Bari nakai matar malam Idi asibiti bata da lafiya".
Ya faɗa sannan ya fice cikin sauri,fatan samun lafiya muka mata.Sannan nima na tashi zanyi ɗakina,"Anty bari nabiki nima"cewar Yasira.
Ban kulata nayi wucewata tabiyo ni,hira mukeyi sosai muna kallon hotunan bikin mu da Habib.
Sai ƙarfe gowa da wasu mintina,mukaji ƙaran shigowar motar Habib.

"Anty ga mijin ki ya dawo bari na tafi".cewar Yasira ta faɗa tana tattare hotunan.

Murmushi  nabita dashi dai-dai lokacin ta Habib ɗin yake shigowa ɗakin,matsa masa tayi sai daya shigo sannan ta fita.
Sai nada tambaye shi jikin Hajjan?,yace da sauƙi hawan jini ke damunta,harma an basu gado.

"Allah ya sauwaƙe".
Da amin ya masa sannna muka ɗan taɓa hira kafin yamin addu'a yafita.Yasira dake tsaye a cikin falo ta naɗe hannayenta,a ƙirjinta yau kam ta ƙudurce a ranta sai ta tabbatar da zargin ta.

"Hamma".

Ta ƙira sunnan shi a hankali ya juyo sai daya bita da wani irin  kallo kafin yace"Me kikeyi har yanzu baki kwanta ba?".

Sai data iso dab dashi sannan ta shiga faɗin"Hamma wani irin zama kukeyi da Hibba?,waɗannan abubuwa duk meya kawo su bakwa kwana ɗaki ɗaya,sannan kuma ba wai saɓani kuka samu tsakanin ku ba?".

Dam-dam ƙirjinsa ya bada hannunta ya kamo suka nufi ɗakinta.

UWATACE SANADI

        Tsarawa/Rubutawa


    ©Maimunah Tijjani Iyam

_________________________

Post a Comment

0 Comments