ƳAR ARO

  


    'Yar ARO Complete By Kulsoom Ismail Idris Mrs Baba Bello Abubakar 


Bismillahir Rahamanir RAHIM

Da sunan Allah me Rahama mejin kai.

Yauma gani dauke da wani littafi wanda zai fadakar da ku ya ilimantar daku ya nishadantar daku.

Wannan Littafi na sadaukar dashi ga ku fans dina,dan jindadin yadda kuke ruwan comment,maganin damuwa,maganin tunani,in kika karanta wannan Norvel zakiji kin watstsake garau dake.

23/8/2023

       'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Page 1_2


Katsina State

Tsiga

Wani kauye dake Katsina State,garin manoma suna da tarin albarkar noma,yahada hausawa da fulani.

Wata 'Yarinya na hango tsaye take da zabgegiyar bulala ahanun ta,dagawa tai ta zugawa wata yarinya abaya,gantsarewa tai tare da fashewa da Kuka,dan Allah 'Yar Aro kimin rai kiyi hakuri bazan sake tsokanar ki ba,harara wadda aka kira da 'Yar Aro ta maka mata,harni Hanne zaki rainawa hankali,in kinga na hakura to sai kin goyani,daga nan zuwa can,zaro idanu Hanne tayi,taya zan iya goyaki haba 'Yar Aro,waike baki san a hadaki da Allah ba kamar shedaniya,kan kuturun bala'i ni kika cewa shedaniya,saurin jijjiga kai Hanne tai,ba dake nake ba,baki nane ya subuce amma nidin banza zance miki shedaniya,shiru 'Yar Aro tai kin tabbata badani kike ba?Allah shine shaida ba dake nake ba,kin fanshi kanki,da yanzu nai miki asuwaki da kasa.

Daga yau sai yau Hanne karki sake tsokana ta ki gudu,tunda ni ba haukaciya bace,gyada kai Hanne tai fatanta tabar hannun 'Yar Aro,biyoni abaya,haka 'Yar Aro tai gaba Hanne na take mata baya,tanatsine mata azuciyar ta,tunda babu halin furtawa afili,duk inda suka zo wucewa sai an ambaci 'Yar Aro jikar Dada,washe hakora take wanda suka dafe da miyar Kuka,datti dai ba amaganar sa.

Kare mata kallo nake tundaga sama har kasa,wasu riga da sket ne,sun kode sun side amma dan jaraba irinta 'Yar Aro taki daina sasu.Lawwali me kifi data hango ta karasa wajan sa,har gyara tafiya tai saboda karya ankara da ita,Hanne dake binta abaya kamar bindi ta watsawa harara alamar ta daina binta,cikin bin umarni Hanne ta tsaya daga can baya.Gaba daya hankalin Lawwali baya kanta,yana can ya juya baya yana gabzar shinkafa da wakensa,hannun sa dauke da redio yana Jijjiga kai.Murmushin samun nasara 'Yar Aro ta saki hankalinta kwance ta karasa,kifine abude tarwai kudaje sai celebration sukeyi akansa.Wata katuwar jela ta dakko can wani lungu ta maqale,saidata cinye tas tana gyada kai,kara lekowa tai taga har yanzu ba kallon wajan sana'ar sa yake ba,guda biyu ta kara zara ta buya ta cinye.Hanne dake kallonta tana hafiyar yawu ta wurgawa harara,da sauri Hanne ta sunkuyar dakai,kamar dai baiwa da Uwar dakinta.Saida 'Yar Aro ta cinye mai kifi jela biyar kafin ya ankara da barnar datake masa.Kayyasa ashe shegiyar kin durgo banganki ba,a sittin yabiyota,takewa tai da shegen gudu tana tikar dariya ko banza taci bulus.Ganin inya biye mata zai asarar kayansa a banza ya tsaya yana haki.

'Yar Aro kinci Allah ya isa,bazan taba yafe miki ba,kinji nagaya miki,ko saura nikadai zanfewa kishiga Aljannah Allah bazan yafe miki,shegiyar yarinya mekama da ruwan aska,gaki 'yar firit amma kinfi shedan iya shedanci.Lawwali kome zakace ka fada amma naci dubu sai ceto,ni jikar Dada saidai aganni akyale ni,ni kadangaran bakin tuluce.Babu Abunda ka isa kaimin,ai ance komai na Allah ne,in kanasan abu kaji ranka ya biya ka dauka kawai.Ganin zata bata masa lokaci ya gyada kai alamar zasu hadu,ransa bace ya karasa wajan kifin sa,yana ayyana Abunda zayyiwa 'Yar Aro inya kamata a hannun sa.Munafuka ke kuma da kika tsaya kina kallon mutane,innaji labarin mazan gidammu sun san naci kifinnan na lahira saiya fiki jindadi.Bazamma fada ba,kima fada kinsan wacece 'Yar Aro ai bana barin kota kwana balle tai tsami.


"Wani babban gida suka fada duk da haka Hanne bata daina take mata bayan ba,,gidan babbane da alama irin gidan yawannan ne,dakuna ne birjik kamar gidan haya,ga yara nan da manya kowa yana harkar gabansa.A Uzubilllahi ga annoba nan ta dawo,ja 'Yar Aro tai ta tsaya tare da rike kugu, tana zabagawa me maganar harara,ni kike cewa annoba Innar Saminu?na fada da ke ba annobar bace,ni wllh tun sanda kika duro Gidannan nasan an kawo mana irin masifa haba,yarinya badare ba rana baki barmu mun huta da masifar ki ba.Aiko zakiga Annoba Innar Saminu dan wllh yau keda bacci saidai kiga anayi, zan tabbatar miki dani guguwa ce bana ragawa kowa inna tashi yin sharata.Saina kala miki sharri da bazaki iya kare kanki ba,zanga karshan surutunki,tunda kika shiga gonata yau babu ke ba zaman lafiya.

"Tsaki wadda aka kira da Innar Saminu tai,aikekam baki isa ki hanani baccin dare ba kinyi tsararo,wata Dariyar mugunta 'Yar Aro ta fashe da ita,muje zuwa Innar Saminu kamar bakisan 'Yar Aro ba,wucewa tai tana sakin dariya tana karkada kugu kamar na sauro.Kofar wani daki ta tsaya sai data shirya tsaf ta gyara muryarta kafin ta takarkare ta fashe da Kuka,yadda take tsala Kuka saika dauka dukanta akeyi,dukamma bana wasa ba,da gudu wata dattijuwa ta fito fara ce tas me tsananin kama da 'Yar Aro.Ke me akai miki kike wanann kukan nashige su,,sake tsugewa da kuka 'Yar Aro tai,ai Dada da kinsan irin cin mutuncin da akaimin acikin Gidannan sai kince na kara karfin kuka na.

"Gaba daya Fuskar Dada baci tai jin abunda 'Yar Aro ke fadi,,daya bayan daya take kallon matan gdan da suka zagaye su,wace metsautsayin ce acikin ku tataba min 'Yar Aro,shiru sukai kowa yana tsoron masifar Dada,ko bakuji magana ba,caraf 'Yar Aro ta cafe,haba Dada kema banda abinki wazaiyi laifi kuma yace shi yayi,ni yakamata ki tambaya basu ba.Da sauri Dada ta kallo 'Yar Aro,kuma fa hakane maza diyar Albarka gayamin abunda akai miki yanzu na dauki mataki."Fyace hanci 'Yar Aro tai ta kara rushewa da sabon Kuka,Dada ba kowa ya muzantani yau agidannan ba sai Innar Saminu"ido cikin ido ta kirani da Annoba,ke catai sanda aka haifoni ma a hannun shedanu na fado shiyasa nake da shegiyar fitina,tunda aka zo dani ta kyalla ido taga yadda muke kama dake tasan bazanyi girman arziki ba,Saboda atarihin rayuwar ki haka kika dinga zalinci,kincuci mutane ba adadi,,tasan makomarki wuta ce,a wuatar ma cancikin wani kwari da jahannama ma neman tsari take dashi nan za'a tsulluma ki.Kuma baza'a taba fitowa dake ba,wadanda kika cuta bazasu yafe miki ba balle a fito dake akaiki Aljanna.Tare kuma za'a hada dani dake asaka mu,tunda duk Abunda nakeyi ke kike sakani,azanarma tare zamu shata.Ashe Innar Saminu ba kaunarki takeyi ba Dada,bata son mekaunarki ma,tunda ni mekaunarki ce shiyasa wutar ma saidai mushata tare.


"Sake sakin Kuka 'Yar Aro tai,wannan maganar itace ta dakeni Dada"ita ta sani wannan kukan"Dada data dora hannu aka tana sauraron 'Yar Aro idanun ta nakan Innar Saminu data dafe kirji tana jinjina kaidi da sharri irin na 'Yar Aro hawaye ne ya fara zuba daga Fuskar Innar Saminu dan tana da tabbacin yau Dada saita tsinke igiyoyin Auranta......

    Hmm tofa Lallai 'Yar Aro ta cika shu'uma kuma shaidaniya kamar yadda Innar Saminu ta ambace ta,ashe hartafi haka sharri.....
    Kubiyo ni fans danjin yadda zata kaya.....
     Taku har Kullum.
    Mrs 🌹 Baba Bello Abubakar
        .......✍️✍️✍️✍️


         'YAR ARO

(Funny and romantic)

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

ING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Paid book 200 only


Page 3_4

"Wani shegen kallo Dada ta watsawa Innar Saminu,munafuka algunguma"yau sai kin gayamin agidan ubanwa na dinga cutar mutane da zaki dangatani da shiga cikin wuta,ashe Zulai bakya kaunata ban sani ba,ashe kaf garinnan baki da makiyi sama dani,rushewa da Kuka Dada tai tsakanina dake Allah ya isa,kuma yau saikin bar gidannan tunda babu gadon Ubanki aciki.Innar Saminu dukawa tai gaban Dada tana bata hakuri akan tai mata rai karta saka asake ta.Wallahi Dada ban fada miki haka ba kowani naji zaifada miki haka saina hukuntashi,balle ni da kaina.Rushewa taida kuka tana kama kafar Dada.Janye kafarta tayi ai saki ma ya zama dole,ni zaki jawowa alkaba'i,mena tsare miki,da kika ce ahannun shedanu 'Yar Aro ta fado kece shedaniyar ko,ke yazama dole ma kitafi,da ace ni kadai kika taba zan iya hakura amma tunda kika hada harda 'Yar Aro babu Maganar hakuri.

'Yar Aro da take murmushin mugunta tana kada idanu kamar fara,dan ya mutsa fuska tai,Dada ki kyaleta tunda har tace ta tuba to kiyi mata afuwa,amma fa da sharadi,sharadimme ne Dada ta kalli 'Yar Aro,sharadin shine da safe saita cikamin langa da 'yar tsala sai naci na ture tukunna in har ta yadda da wannan sharadin nawa,da sauri Innar Saminu ta Jijjiga kai na yadda wllh,matukar Dada zata barni naci gaba da zama, murmushi ta kara saki,kin fanshi.kanki,Dada a sakar mata mara tai fitsari haka abarta tasha Iska,shikenan tunda kinyi belinta amma ni so nai tatafi Gidan su zatafi ganin ki da Mutunci."Baruwana da wani mutunci Dada tunda bukatata zata biya nacin 'yar tsala mutuncin nan asashi agefe,kallon matan gidan 'Yar Aro tai kowa ya ware yaci gaba da harkar gabansa.

"Cikin rawar jiki kowacce tabar wajan cike da tsoron sharrin 'Yar Aro,sun tabbatar wanann yarinya guguwar masifa ce,bata kyale kowa ba hatta mazan gidan basu sha ruwa ba."Dakin Dada ta fada tana fadawa kan gado"wash nagaji Dada abani Abinci,to kyatashi kiyi sallah ai tukunna, gskiya Dada nagaji kibari cikina ya dauka,bazaki ci Abincin nan ba sai kinyi sallah, yarinya kamar me kwankwamai aka,ayi ayi kiyi sallah saiki dinga kawo wasu uzuri can daban,kinga ina goya miki baya akan komai amma banda kinyin sallah."Tana Kuka sàida Dada ta jata waje har bakin rijiya ta kaita tare da zuba mata ruwa abuta,in har bazakiyi ba ki zauna,nikuma bazan baki Abinci ba,banbancin kafiri da musulmi ai sallah ne,in bakiyi ba ai kinzama su."Tana alwala tana kuka, babban bacin ranta ace dole saitayi sallah,wannan abu yana tsaya mata a kahon zuci,sallar ma bunbuga ta tai tana idarwa taja katuwar langa cike da danwake.

"Sài dana zaro idanu ganin uban abincin da 'YAR Aro ta tashi dashi,sai gyatsa take kamar saniya,mikewa tai tana lasar hannu yadda kasan bataci ba,kokadan cikinta ashafe yake kamar batasa komai acikin sa ba.Labule ta bankado tafito idanun ta ya fada kan Auwal da yake cin dumaman tuwo,kambu dama da akwai tuwo aka hanani,aiko wllh saina ci,bazato yaga ta dauke kwanon ta kwasa da gudu,binta yayi abaya yana kuka dan Allah ta bashi tuwonsa amma fir tahanashi."Karshe ma ficewa tai daga gidan tana cin tuwon tana gudu tsabar dan ta wahalar dashi,karo sukaci da Salame tuwon kuwa yayi tsalle ya tambade akasa.Tsabar bakin ciki 'Yar Aro bata san sanda ta kwarfawa Salame mari ba,dafe kunci Salame tai tana kallon 'Yar Aro wadda take mata kallon ko zaki ramane,agirme Salame ta girmeta"amma tsabar tsaurin ido tai mata wannan marin,cikin shammata Salame ta dauke ta da shegen mari hagu da dama,Salame irin yarannan ne masu murdaddan jiki,jikinta gagau yake,sabanin 'Yar Aro da take kamar sillan kara."Ni kika mara?na mareki hegiyar yarinya me kafirin rashin ji,to duk fitsarar ki atafin hannuna kike."Kukan kura 'Yar Aro tai ta shako wuyan Salame,kokawa suka kacame da ita,dan danan 'Yar Aro ta fara ji ajikin ta,bakaramin duka take shaba,amma taurinkai ya hanata barin fadan.

"Mutane 'yan kallo sun zagaye su,sai sowa ake ana dariya,yawwa Salame kici mana Ubanta,yau dai munga faduwar 'Yar Aro,hakan ya bawa Salame kwarin guiwar yi mata shegen duka,saiga 'yar Aro da fasashen baki.Kasa Salame ta diba ta cika bakin'Yar Aro dashi,ta jibgu iya jibguwa dakyar take maida martani,amma idanun ta kamas babu koda digon hawaye,zuciyarta kamar zatai bindiga,tayi alkawarin saita shayar da Salame mamaki,saita addabi rayuwarta.Dada ce ta shigo tsakiyar filin tana masifa,wata bangaza taiwa Salame data hau ruwan cikin 'Yar Aro tana jibga kamar Allah ya aiko ta.Amma kekam Salame anyi tambadaddiyar yarinya,jikartawa zaki yiwa lahani,to daganan har gaban megari bazan taba yadda ba."Mutanan wajan tafi suka ci gaba dayi,yau munga faduwar 'Yar Aro,'Yar Aro me idon biri,me hancin kada,kazama,me warin jaba,me kwarkwata 'Yar Aro.Da masu waka da masu amshi,tsanin bakin ciki ya saka 'Yar Aro fashewa Kuka kamar ranta zai fita,da wuya kaga abu ya sata Kuka amma yau dai gata tana kukan bakin ciki.

"Da kyar Dada ta rarrasheta suka koma gida,ita kadai tasan kudurin data dauka azuciyarta,dan wllh sai sunsan ita sukayiwa dariya harda waka."Tana shiga matan gidan suka fara dariya da yaran Gidan,oh yau kuma su 'Yar Aro anji jiki,dama in kayiwa wani ka kwana lafiya,wani inkai masa saidai ka kwana aciki,fashewa suka sakeyi da dariya.Kedai bari Innar Auwalu,zalinci tai ina ganin sanda ta dauki tuwon Auwalu tai waje,ashe merabon shan duka ko ana muzuru ana shaho saiya sha.Shewa suka kara sawa,Dada tana jinsu yau bata da Lokacin su shiyasa bata tanka musu ba.Haka kunnen 'Yar Aro duk ya tariyo mata abunda suka fada jijjiga kai tayi zamu gauraya.

Ranar bakin ciki kamar zai kashe'Yar Aro,babu inda ta sake fita tana daki tana dacin rai,da sakawa da kwancewa.'Yar Aro 'Yar Aro wani babban mutum daya shigo yake kwalla mata kira,jiki na rawa tafito kamar mutuniyar arziki,gani baba,Harara ya watsa mata,ya akai kika je kika ciwa Lawwali kifinsa har gammo biyar,zaro idanu tai,wllh baba karya yakeyi,taya zan iya cinye kifi gammo biyar kafar wata kura.Hambari ya kawo mata da wacece inba kurar ba.'Yar Aro ki kiyayeni kin san Allah duk ranar da kika shigo hannuna bazakiji da dadi ba.In ka kamata kakashe ta kaji,Dada data futo daga daki take fadin hakan kamar ta rufeshi da duka.

"Yanzu Dada yarinyar nan bazaki mayar musu da 'Yar suba,hakanfa kamar zalintar su kikai,haka kawai kin dakko musu yarinya,bafa susan sanda kika dakkota ba,wayar gari sukai basu ganta ba.Kuka Dada ta fashe dashi, Innalillahi Baban Saminu yanzu ni kake cewa barauniya,dama dazu matarka tagama cemin 'yar wuta kaima gashi yanzu ka kira ni da barauniya.A'ah Dada ni wllh ba haka nake nufi ba,dama ganinai gwara ki mayarwa da Yaya 'yarsa hankalinsa zaifi kwanciya,zan yarfa maka mari Mamuda ni zakadinga fadawa namaida 'Yar Aro to bamga wanda ya isa ya rabani da ita ba,ko uwarta da Ubanta basu isa ba,balle kai dabakasan zafinta ba.Shiru yayi ganin yadda Dada ke masifa yarasa wani irin so takewa 'Yar Aro.Da zai samu dama saiya saceta ya mayar da ita wajan iyayanta,amma muje zuwa ya jijjiga kai tare dayin waje,ai dukana zaka zo kayi mara mutunci.

'Yar Aro da farin ciki ya kamata Dada tazo ta ceceta, rungume Dada tai ina sonki Dada ta, karki bari arabamu,to da wazai rabamu ai banganshi ba."Cikin dare 'Yar Aro ta tashi duk baccin dayake idanun ta ta wartsake tsabar neman masifa.Bokitin karfe ta dakko dasu baho,dan yau ta rantse babu wanda zaiyi bcci agidannan.Iya karfinta ta dage tadinga kida baji ba gani,duk masu bacci sàida suka mike,afirgice sukayo waje,tsayawa kawai sukai suna kallon 'Yar Aro data zage tana buga kida taba waka,tsabar bacin rai ya hanasu Magana.Huwaila data kasa jurewa afusace ta fusgota daga kan tiemin data zauna,waike wace irin yarinya ce da bakyasan zaman lafiya,yanzu da kika hanamu bacci mene ribarki.Cikani Innar Basira karkisa na huce haushina akanki,wani matashine daya fito a fusace ya wanke Fuskarta da mari,kanya dauke Dada ta yarfa mai mari shima,uwarme tai maka?katan saurayi balagagge ka sauka akan jaririyar Allah to ahir dinka mesunan Malam.Kaci sàa amma da ace bakai bane bansani me zamma ba.Tashi ke kuma mu tai daki karba sharara miki duka,ganin fuskar Dada babu wasa yasata mikewa tana cuno baki sukai daki.Daya bayan daya suka dinga shiga daki,banda me sunan Malam da bakin cikin duniya ya tare masa a kahon zuci,mezaiwa'Yar Aro ya huce shikuwa,badai zata makaranta ba gube,saiya bata gwale gwale zata gane shayi ruwa ne.

"Washe gari sassafe 'Yar Aro tatashi,katuwar langa ta dakko ta zauna,duk yadda bata tashi da wuri ranar saigashi tatashi danwuri.Innar Auwalu data fito da kullunta na kunun sayarwa da takeyi ta ajiye a madafi,duk abunda takeyi 'Yar Aro na kallon ta,wani shegen murmushi ta saki na mugunta,har Lokacin bakinta be sace ba,yana nan a kumbure.Daki Innar Auwalu ta koma dan karasa shirin fara sana'ar ta.Zaram ta mike ta dakko fitilar su ta kwai,irin wadda ake zubawa kalanzir dinnan da irinta suke Amfani.Wuf ta fito dauke da fitilar,sai data dauke Numfashi ta tabbatar ba motsin kowa,sadaf sadaf ta karasa gaban katon botikin da akalla yaci hatsi kwano biyar.Fitilar ta bude ta dagata tas tajuye kalanzir din ciki'.Hankali kwance ta koma daki bayan ta gama hautsina kullun tas,zuciyar ta fes ta koma dakin Dada.Kan gadon karfe ta haye ta babbaje kamar me baccin Gaske.

"Kusan karfe 8 an gama dama koko"masu saya sai layi sukeyi,ga kuma Innar Saminu dake tuyar yar tsala da kosai.Wata azababbiyar tsohuwa ce ta shigo,ina Innar Auwalu hauka akeyi zamusha kamu yana warin kalanzir,narantse sai anbiyani kudina bazan yadda ba,nan hayaniya ta kaure abun mamaki saiga wadanda suka siya daya bayan daya suna dawowa da Innar Auwalu,wadda tai sakare ta rasa abun fada,tasan babu abunda ya hada kullun kamunta da kalanzir.

🤦🤦🤦Batasan 'Yar Aro ta gamayi mata aika aika ba...

    Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
         ......✍️✍️✍️✍️
    
    
          'YAR ARO
    
   
Funny Girl 🧕

 Written and Narrated
    
    By Kulsoom Ismail Idris
    
   *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Paid book 200 only
 
Page 5_6
    
    
    "Fada fa yakici yaki cinyewa,Innar Auwalu da sai rantse rantse takeyi,akan babu abunda ya samu kokonta,wata matace ta miko mata na hannunta,tunda minyi miki karya kisha wannan ko kuma ki dauki na bangajin da Kuka dama ki sha kiji.Dukawa tai ta debo a ludayin duma takai bakinta,kasa hadiyewa tai tsabar yadda warin kalanzir din ya bata kokon,furzar dashi tayi tana goge bakinta,to kinji ba,ai gashinan ba karya mukai miki ba,dan haka babu kira babu abunda zaici gawayi.Kwarai kuwa jama'ar wajan suka dau hayaniya.Babu yadda Innar Auwalu zatai haka ta dauki kudin su ta dinga basu."Tunanin ta wazayyi mata haka,'Yar Aro mana zuciyar ta tasanar da ita,girgiza kanta tayi kai àah gaskiya bazata iya wannan zalincin ba duk fitinarta kuwa."Koda wasa ma bataga fitowarta ba,tasanta sarai da jarabar baccin tsiya.Duk abunda akeyi akan kunnan ta,dariya kamar zata kasheta,tayi dariya kamar zata zauce,Dada da bata dakin batasan da tashin taba ma,tanacan tsakar gida tana rabon fada,da bawa masu sayan kunu hakuri.
    
    "Mutsutstsuke idanun ta tayi yayi jawur alamar lokacin tatashi daga bacci,tana fitowa ta zari buta,kewaye ta shiga kafin ta dawo ta zauna ta fara Alwala,kusan karfe 9 sai yanzu zatai sallah.Babu wanda ta kalla a tsakar gidan balle ma a zargeta,fuskatai ta wuce ranta ahade alamar ba wasa.Tana idar da sallah ta dakko langa babu wata magana ta mikawa Innar Saminu,kyan alkawari,cikawa inji Dada dake tsaye,kallon Innar Auwalu tai data dafe kai tatasa kunun ta agaba tana sharar hawayan takaici da bakin ciki.Wata dariya ce ta tahowa 'Yar Aro tai jarumtar tare ta.Innar Auwalu sai kace wanda aka aikowa da sakon mutuwa irin wannan tagumi haka,harara ta watsa mata batare data tanka mata ba,ke ta ina zata iya magana kemadai banda abinki shalele,ai ibtila'i ne ya fada mata,kamun ta aka samu wani debebben ya watsa mata kalanzir a cikin kamu,dafe kirji 'Yar Aro tai tana fiddo idanu waje,garinya haka tafaru,da ace na kama wanda yayi miki wannnan aika aika dasai inda karfina ya kare,ai nasani dama ke diyar Albarka ce cewar Dada da take kallon su.
    
    "Innar Auwalu dai batace ci kanki ba,Innar Saminu ce ta miko mata 'yar tsalar kusan rabin langar data miko mata,gaskiya Innar Saminu kidinga jin tsoron Allah yanzu saboda ALLAH bazaki cikamin ba,harara ta watsa mata batare da tace komai ba,bakaramin haushin 'Yar Aro suke jiba,gaba daya ta zame musu masifa da bala'i,Allah ya kawo Lokacin da zata bar musu garin ma baki daya.Karba tai tatafi tana murguda duwawu, hankalinta kwance.
    
    "Yar Aro duk wannan kinji da fitinar da takeyi bata wuce sharu goma ba,amma yadda kasan uwar mata haka ta addabi Jama'a,ta hanasu sukuni,kowa Addu'a yake Allah ya kawo silar barinta garin gaba daya."Tas tagama cinyewa kafin ta mike tasha ruwa aranda,cikinta yayi kat,kayan bokonta ta dakko wanda suka sha sukuizin gaba daya sun tatatare,sun cu kuikuye.Jakarta tabdakko da litattafan ciki sun gama yagalgalewa kamar ba school ake zuwa dasu ba,takalmi ta sharba na Dada tafice daga gidan.Bawata tafiya ce me nisa tsakanin suba da makarantar.Sanda taje anfito break dama sabonta kenan,bata tashi zuwa sai amfito break.Nera goman da Dada ta bata taje ta sayi rake,gefe ta koma babu wanda ta kula,haka suma ba wanda ya kulata.Ana komawa aji ta samu wajan data saba xama ta harde,fuskarnan a bace.Uncle Sulaiman ne ya shigo kowa ya mike dan gaidashi amma banda 'Yar Aro,tsayawa yayi yana kallon ta,tsawa ya daka mata,ke stand up,kememe taki tashi yi taima kamar bata jishi ba.
    
    Ai kasan sunana ba ke aka samun ba,kuma Allah bazan tashi ba,ni kaf garinnan babu wanda zai firgita ni.Bulalar hannun sa ya zabga mata Iya karfinsa amma kamar ya daki dotse haka tai kikam,saida yayi mata bulala Goma yadda kasan sosa mata baya yake,kuma tanajin zafin dukan,wai dan karya rainata yaga gazawar ta,dan kansa y gaji ya kyaleta yafara tunanin yarinyar nan ba kalau take ba.Sukan su 'yan class din sun kara tsorata da taurin kai irin na Fatima Habib Sadauki.Asalin sunan ta kenan amma bata amfani dashi a cikin garin su.Har akatashi tana zaune tana kallon yan class din dai dai,tana yatsina Fuska,in banda shegen tsami babu abunda takeyi.Ana tashi bata tsaya wasa ba ta fada gida ko sallama babu.Tsaki Hajjo taja tana maka mata harara,yar gadon masifa kin dawo,cak 'Yar Aro ta tsaya kafin ta juyo da baya,ke Hajjo ai gwarani babu wanda ya taba ganina da Namiji,amma ke tsabar iskan ci dan Lami saunawa ina zuwa kwar gidannan,ballagaza kawai me kula maza,matsowa Hajjo tai da nufin kamo ta ta fyalla da gudu.Hajjo zatakai sharu sha Uku sune wanda Za'a aurar wannan banar,sune yammata agarin.
    
    "Da ki tsaya mana,tasan Hajjo sarai shegen karfi ne da ita kamar Talauci.Bata kara bi takan Salame ba,badan ta manta da abunda tai mata ba tana sane.Bayan sallar isha'i dayake lokacin sanyi ne,ana daka kowa yana shan dumi,karan da aka gama girki 'Yar Aro ta dauka,kaitsaye gidan su Salme ta fada,Shiru babu kowa kamar anyi shara,runbun da suke ajiyar abinci ta nufa,karan ta jingina ajikin rumbun da yake cike da kayan Abinci,ficewa tai babu abunda ya dameta,tana shiga daki ta fada ta nannade acikin bargwanta.Kusan mintuna biyar ta farajin hayaniya,temako wuta ta kama,dandanan makwafta suka firfito dan kawo dauki,anriga an makara ganganga wutar take ci,da kyar aka samu aka kashe wutar,baban Salame saida aka rike shi,ya shiga tashin hankali ganin kayan Abinci da yasha wuya wajan nomawa ya kone.Innar Salame da Salame sai kuka sukeyi.
    
    "Babu wanda be tausayawa Malam Hadi ba ganin yadda ya shiga mawuyacin hali,kaf yan gidan su 'Yar Aro babu wanda be fito ba ana jimanta tawa,banda ita da yake tasan tsiyar data shuka sake gyara kwanciyar ta tayi tana jan munshari.Washe gari ko kadan bata nuna tasan abunda ya faru ba,tana jin yadda ake maida magana,amma ci kanki bata ce ba,ita tasan abunda ta shuka,ko banza ta kunsawa su Salme fiye da dukan da tasha a hannun ta."Yamma lis taci kwalliya suka nifi dandali ita da kawayan ta,kamar sarauniya da bayinta haka.suke take mata baya,tana tafe tana tafiyar kasai ta.Hanne da Lantana sai Biba sune daman kawayan nata,ta dole suka koma yi mata biyayya.

"Tunda aka hango ta howarta samari kowa ke gyara zaman rigarsa,da hular sa da ya saka,amma ko daya bata kalli inda suke ba,tsakiyar fili ta tsaya,'Yar Aro badai san rawa da waka ba,kida aka farayi mata na musamman ita kadaice a tsakiyar fili,wata shegiyar rawa take tana gatsarewa tare da kada kugu,sai tafi ake mata ana sowa da kara zugata taci gaba da rawar.Samari ne aka fito ana nuna bajinta,daga me lika mata biyar sai me Goma,ahakan wai anyi mugun kokari.Wani dan kwalisa ne yanshigo da mikakkun naira ashirin,yana shiga aka fara ihu sai habule,nan ya karkace kai ya fara likawa 'Yar Aro da take girgijewa a tsakiyar fili.Habule wani saurayi ne bazai haura 18years ba,ahakan wai Aure za'ai masa agida yake neman matar Aure.Matan kuwa basa wuce 12 in sun dade be zasukai 13 an aurar dasu.

Ana tashi daga dandali 'Yar Aro tayo hanyar gida,lokacin har anyi sallar isha'i ana can ana raye raye.'Yar Aro ya kira sunan ta,hadda wani marairaice fuska,yatsina Fuska tai tana kallon sa sama da kasa,ya akayi?cikin rainin hankali tamai tambayar.Dama akan maganar soyayyar mune nace yaushe za'a zo a tambayar min,harara ta watsa masa,kaga Habule kafita daga idanuna na,kaga nayi kala da wadda za'a yiwa Aure yanxu,kiyi hakuri 'Yar Aro namiki alkwarin zan kaiki birni mu wataya can,wata Dariya ta sheke da ita,ai sàidai na kaika,ko ka manta ina da dangi acan,kaga da inason zaman birni da tuni Dada takaini.

"Hakane amma ki duba yadda nake sonki,tsaki taja,wai Habule anya kai ba maye bane,to in ba maita ba kaitabin mutum yana gudunka,ka kyaleni ni bayanzu za'a min Aure ba.Gaba tai tabar Habule atsaye kamar zai rushe da kuka.Tana komawa gida kan gadon ta tahaye,dan kar Dada ma tajita tace sai tayi Sallah."Washe gari ma sai karfe 9 tatashi,tana tashi babu wanka ta dakko kayanta ta turmusa ajiki,kafar nan kamar antonota daga rami,sàida taci dumaman ta tai nak kafinta figi jakarta.

Yau kam ba'a fito ba ana cikin aji ana karatu,kowa zaka ganshi tsaf tsaf amma banda 'Yar Aro yadda kasan me motsi aka haka zakaga shigarta,hakan kuma be taba damunta ba,ko a kwalar rigarta.Uncle Bashir data hango yasa gabanta faduwa,tana shakkarsa kwarai da Gaske,inya tashi duka baya yin na hankali,ta window ta sadada zata dira,duk Abinda takeyi yana kallon ta.Tana dirowa sukai ido biyu dashi,yadda taga Fuskar sa,ba alamun rahama da sassauci yasata fara matsar kwallah.Dan Allah Uncle kayi hakuri,bazan sake ba,tunkan yayi mata magana ta fara bashi hakuri,ko kallon ta beba yaci gaba da karatun sa.Saida ya gama tsaf kafin ya kalli mazan ajin,ku dakko min ita,yana da tabbacin yace ta biyo shi office guduwa zatai.

Dama Haushin ta suke ji,Mutum ukune suka taso kafin tasan abinyi sukai mata daukar Amarya,duk yadda take fisge fisge kin sakinta sukai,sai Kuka take su sauke ta amma fir suka ki sàida suka kaita staff room.Dan mugunta suna zuwa nikar da ita sukai akasa,sàida kashin bayanta ya amsa.Uncle da besan abunda sukai mata ba wanda ya sata Kuka ya dalle mata baki,yiwa mutane shiru yau zakiji ajikin ki.Mike ki biyo ni,haka ta mike ta bishi,sashin toilet suka nufa.Toilat ne guda 12 kowannen su bukatar wanki yakeyi,maza nagansu kal kal kamar tamgaran.

"Bokiti ya miko mata yana tsaye akanta,saita jawo ruwa a rijiya kafin ta dakko ta kawo ta wanke,kuka take tana wankewa gaba daya kafafunta yadda kasan su karye,bayanta kamar ba ajikinta yake ba,hawaye da majina sun hadu sun dame awaje daya."Ko kadan be ji tausayin ta ba,sài data gama aikin daya saka ta,da kyar take daga kafafunta kamar zata kife akasa."Sanda ta koma har ankusa tashi,zubewa kawai tai tana Kuka ba kakkautawa.'Yan class din sai ALLAH ya kara sukeyi mata,sai dariya suke mata da masu yi mata gwalo.Sanda aka tashe su da kyar takai kanta Gida,gaba daya duniya juya mata take.....

   🤣🤣🤣🤣Nima dai ko kadan ban tausaya miki ba 'Yar Aro....

    Ana nan ana cigaba da biya.Karku bari wannan kayataccen Labari ya wuce ku.Wadda take son biya taimin magana ta prvt.Karku manta naira 200 ne kacal.😁😁 

Mrs Baba Bello Abubakar
       .....✍️✍️✍️✍️

        'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

Paid book 200 only

   *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Free Page 7_8


"Gaba daya Fuskarta tayi jajawur,a tsakiyar Gidan ta zube tana maida numfashi,zagaye ta sukai batare da sun tambaye ta abunda yake damunta ba,amma da alama dai koma me ya sameta taji jiki.Dada da fitowarta kenan daga kewaye taga yadda yara da matan gidan sukai tsaye suna kallon wani abu,ita ma tahowa tai ta bawa idanunta hakkin sa.Hango 'Yar Aro abaje akasa yasata yarda butar hannun ta,da sauri ta karasa ta dago ta.Nashige su meya sameki,wanene ya bige ki,shiru tai batare data tankawa Dada ba.Ita kadai tasan abunda zataiwa Uncle Bashir.Tunda take babu wanda ya taba bata wahala kamar sa.Dada data gaji da tambayar ta daki ta kinkimeta ta kaita,dama abace kamar sillan kara.Ranar da zazzabi ta kwana,sai rawar sanyi take,jikinta ba karamin ciwo yake mata ba.Saida Dada ta bata magani tasha kafin ta samu relief bacci ya dauke ta.

"Washe gari da safe tana tashi ta wanke baki,tayi garau kamar ba ita ce take neman shekawa lahira ba.Bakinan ya dafe alamar ya dade bega wanki ba,gashin kanta kuwa ko tsagarsa ba'a gani saboda tsabar dadewa,taki yadda ko kadan ai mata sabon kitso,farar fatar ta duk ta dafe.Babbar Langa ta dauka saidata sako tuwo gutsire 6 miyar Kukar da tasha daddawa da wake ta kamfa to,dakin Dada ta shigo ta nemi waje ta mimmike kafa,yajin daddawa ta jawo ta gambaza,tana ci tana gyada kai kamar kadangaruwa."Kanna farga ta tashi da tuwon tas kamar ba ita ce ta cinye ba tayi mirsisi azaune.Kayan makarantar ta ta yayi ba tasaka,ta dauki jakarta ta buhu.Dada kudin makaranta,kai ni dai nagaji da wannan cacar kudin da kike sani 'Yar Aro, kullum sai nayi kashin kudi kuma ni har yanzu banga abunda kike koya ba,bata rai tayi haba Dada ya kike nema ki zageni,dakikiya fa kike cemin,toda mece kanki gaba daya ya dafe da miyar Kuka,kukan takaici ta saka,yanzu Dada ni kike fadawa haka,anya bawanine yashiga tsakanin mu ba.

"Babu wanda ya shiga aike dince bakyajin magana sai shegiyar tsokana,saura kadan na daina tare miki fada,nidai ba wanann ba kiban kudin natafi,babu yadda Dada ta iya haka ta ciro kudin ta bata.Ficewa tai daganan ba makarantar tatafi ba,wajan mesuyar awara ta tsaya,abani ta naira goma,miko hannu tai bani kudin,to kifara zubamun mana sai kace wadda zan gudu,babu musu matar ta dakko leda ta zuba mata guda biyu,mika mata tai,yawwa Allah yayi miki Albarka Harira,bangane Allah yayi min Albarka ba bani kudi na,zoki kwata,ficewa tai aguje tana dariya,Harira data harzuka mikewa tai tabi bayan ta,gudu suke ci 'Yar Aro tayo kwana,wajan awarar ta dawo,tagama cika wani farin bokiti ta sunkuya ta dauke awarar gaba daya.Tana gudu tana cin a warar tsabar bakin ciki Harira zama tai ta fashe da Kuka"ganin irin asarar da 'Yar Aro keyi mata.

"Tsayawa tai daga nesa tanai mata gwalo tana murguda mata duwawu,Harira wata bazawara ce datake suyar awarar ta danta rufawa kanta asiri,amma yau wannan mara mutuncin tai mata rugu rugu da jarinta,data sani da bata bita ba,ta kyaleta taci iya ta goman."Sake yunkurawa Harira tai zata bita tataka da gudu,jakar makarantar ma ta yadda ita ahanya tsabar tsokana."Tsokana gaba daya ta rufe mata idanu ko kadan bataga mota agaban ta ba,atakaice ma batasan da zuwanta ba,cikin sauri ya taka wani wawan birki saura kadan ya taka ta.Bakaramar tsorata tai ba,botikin awarar sàida yayi sama ya tar watse,in ran Harira yayi dubu to ya baci."Afusace ya balle murfin motar ya fito beyi wata wata ba ya dauke Fuskar 'Yar Aro d wani shegen mari,sàida tayi katantanwa kafin ta tsaya akan kafafunta,gaba daya kunnuwanta daina aiki sukai na wucin gadi,ta maru ba kadan ba."Kafin ta gama dawowa hayyacin ta yayi mata wata damka kamar kaza haka ya bude sit din baya ya watsata aciki,sàida kanta ya bigi murfin motar,bam yaja ya rufe motar.

"Juyawa yayi kan Harira,kudi ya zaro a aljihunsa ya mika mata,hannu na rawa ta karba,zuciyar ta cike da tsoro wanene wannan daya zo ya sace 'Yar Aro.Yana bata kudin ta ta juya harda hadawa da gudu.Motar yayiwa key a zafafe yaja wani reverse sàida kura ta tirnike wajan fisgar motar yayi ya juya aguje.'Yar Aro da take zare idanu abayan mota Kuka ta fashe dashi tana kururuwa wayyo nashiga uku,dan yankan kai ya saceni,wayyo ni Jama'a kuzo ku ceceni,amma ina babu mejin ta gaba daya glass din motar azuge suke,tsawa ya daka mata duk bushewar zuciyar ta saidata jijjiga,shiru tai tana zare idanu gaba daya ta gama firgicewa tasaki fitsari a wando.Harira ce tashiga gidan su 'Yar Aro da gudu,sàida taje tsakiyar tsakar gidan kafin ta fashe da Kuka,aguje matan gidan suka zo suka zagaye ta,Harira lafiya kike Kuka haka,wanene ya rasu,wani me motane yanzu yazo ya sace 'Yar Aro.Dada ce ta rafka salati aka sace 'Yar Aro kafin ta kece da Kuka nashiga Uku ni Fatsima yanzu ina zansa raina,gani sukai Dada tatafi luuu zata fadi,da sauri suka taro ta.Ciccibar ta akai aka kaita dakin ta,gaba daya 'yan gidan jikin su yayi sanyi,duka yadda suke so ta barmusu gidan su,amma bazasu taba so asace ta ba.
    

"Tun 'Yar Aro na Kuka harta gaji tai shiru,tai tsuru yau ta tabbatar kwananta ya kare,daganin Fuskar wannan mutumin ba imani zaiba,tun ana wuce da zuzzuka gari gari,har bacci ya dauke ta.Sake farkawa tai yunwa ta addabi rayuwarta.Yunwa nake ji wayyo ciki'na,wata leda tagani a kusa da ita,da azama ta jawota kanmshin daya bigi hancinta yasa tabude ledar da sauri.Bamkararriyar kaza ta gani sai kyalli take tana maiko,sai gurasa da tasha kayan hadi.Babu wata damuwa ta fara dannawa abakinta,acewarta gwara taci kafin ajalinta ya risketa.Duk abinda takeyi yana kallonta,tana gama ci ta kora da juice ta kara bingirewa tana bacci.Sai kusan La'asar ya shiga garin ABUJA.Tsakanin katsina da ABUJA ba karamin nisa bane,ahakamma yayi sauri.

Batasan adadin awa nawa ta shafe tana baccin ba.Wani shegen duka taji andaka mata a firgice ta mike tunkan tasan ina ya kawo ta ya fusgota daga cikin motar sa,janta yayi kamar wata shara wani katafaran parlo ya nufa da ita,ko sallama be samu damar yiba saboda yadda ransa ke bace,tsakiyar parlourn ya wurgata tatafi suuu zata fadi,dabas ta koma ta zauna tana zazzare idanu.Gaba daya mutanan parlourn zuba mata idanu sukai kamar yadda ita ma take kallon su ko kiftawa batayi.Yadda kasan Almajira haka 'Yar Aro ta koma,yadda nai duba da mutanan parlourn gaba dayansu kyawawane,gogaggun 'yan boko ne,daga gani boko ta ratsa su.

Fita daga parlon yake kokarin yi,Sadauki muryar wata mata ta ambaci sunan sa,cak ya tsaya ba tare daya juyo ya kalle ta ba,karkacemin Hamna ce ta dawo haka,idanun ta nakan 'Yar Aro take wannan Maganar,itace Mammah,sakai yayi yafice batare da yakara cewa komai ba.Wata mata daga can gefe tunda aka wullo 'Yar Aro ta kafeta da idanu,idanun ta da suka kada sukai jajir take kallon diyar tata,wani zafi da kuna takeji a kirjinta,anya zata yafewa Dada kuwa,kalli yadda ta mayar mata da yarinya yadda kasan mahaukaciya mebin bola,hawayan da take kokarin rikewa ne ya sulalo batare data san da zubar saba.Jin an dafa kafadarta yasata dagowa dan ganin wadda ya dafatan tan.Mima ce wadda take tsananin kama da wadda aka kira Hamna((🙄🙄mudai da 'Yar Aro muka santa))kiyi hakuri Ammi ba gashi ta dawo ba,girgiza kai tayi,anya ki kalli halin da take ciki' kuwa Mima,nagani Ammi amma mune zamu canza ta,zata dawo kamar yadda muke san ta zama,goge hawayan ta Ammi tai tana kara duban 'Yar Aro da take zazzare idanu kamar ammata rinton uwa.

"Fashewa tai da kuka ta fara birgima tsakiyar parlourn,wani irin ihu take na rashin mutunci,ni wllh saikun maidani wajan Dada wayyo Dada kizo ki tafi dani zasu kashe ni,ni bazan zauna da kuba,bana son birnin ni nafison wajan Dada,kuka take bilhakki,tanajin duk wanda ya dakkota ya kawota gidannan ba karamin makiyin ta bane,Mamma ce tataso ta ruko hannayanta,fisge hannun tai tare da ja baya,ni karki shafan dauda,duk yadda mutanan parlourn ke cikin Alhini sàida suka dara wai kar ashafa mata dauda,bayan ita kanta ita ce daudar.Ita kanta Mamma sàidata dan dara,to naji Hamna taso muje naimiki wanka,tana jin Mamma amma tai mata banza kamar bata jita ba.

"Babu yadda Mamma batai da ita ba akan tai mata wanka firtaki yadda.Bayan Mamma da Mima babu wanda ya nuna yasan da zaman Hamna a wajan,wata mata da yaranta 'yammata dake gefe sai ya mutsa fuska suke yi suna kallon Hamna,farin ciki fal ransu tazama abar gudu awajan kowa,suna da tabbacin babu wani abu da zaisa aso wannan mahaukaciyar, murmushin mugunta suke ta saki.Ammi tana kallon dukkan motsin su.Murmushi ta saki me ciwo tana girgiza kanta,dauke kanta tai daga kansu har yanzu bataiwa Hamna magana ba,ita ma kuma.bata dago ta kalli kowa dake parlourn ba.Babban bacin ranta yadda aka rabota da rayuwar 'yanci,rayuwar da babu me saka mata ido,amma yau saiga wani dan iska yazo ya satota,tabbas saita kaishi kara dan wannan satota yayi.

"Kamshin turaran daya gauraye parlourn shiya tabbatar musu da dawowar sa,tsit parlourn yayi kowa yana maida Numfashi cike da shakkar sa.Kallon ta yayi inda ya ajiyeta tana nan azaune,tsawa ya daka mata wadda ta hautsina dukkan tunanin ta,batasan sanda ta mike tsaye ba cikin rawar jiki,Hanya ya nuna mata babu musu tai hanyar barin parlon,binta yayi abaya,gaba yayi ta bishi abaya kamar jela,ta tsine masa yafi cikin kwando.Tunkan su shiga part din ya juyo tare da watsa mata harara,kwabe wannan kayan haukan dake jikin ki,sakare tai tana kallon sa da kasa fahimtar me yake nufi.Wani shegen rankwashi ya sakar mata,zaki abunda na saki ko zaki zauna kina kallona me kama da mayya kawaii.Duk da yarintar ta saida taji wani dum wai ta cire kayan jikin ta.

"Dam kota yake niyyar yi tai baya da sauri,bazaki shigar min part da dattin kazan taba oya kwabe kayanki anan,babu yadda ta iya haka ta cire kayan tana matsar kwallah,tankada keyarta yayi har cikin bedroom din sa, toilet ya wuce ya tara ruwa a bathtub,hankalinta tashe take kallon yadda ruwan ke tururi kamar wadda za'a yiwa wankan jego,tunani take a zuciyarta na yadda za'ai ta faki idanun sa ta sheqa da gudu.

Lallai ga Sadauki ga Hamna.Jama'ar wannan Gida harna tausaya Muku,matukar kuka shiga komar 'Yar Aro bazakuji da dadi ba.

   Masu korafin Mrs Baba meyasa zaki ce sai munbiya 200 zamu karanta.Nima ba asan raina nace kubiya din ba,amma yanayin yadda abubuwa suka sanja,ga zaman typing ga siyan data.200 nace ba 500 nace ko 1k ba.Ahakan na sauka ka matuka,saboda ku din na sauka ka.

Allah ya bawa kowa ikon biya.Masu kukan baku da 200 Allah ya baku.

Account number
6113314982
Ummakursim Idris Ismail
Opay bank.

Duk wanda ya biya ya turon shedar ya biya.

 Mrs Baba Bello Abubakar
        .....✍️✍️✍️✍️
    
    
       'YAR ARO
    
    Written and Narrated
    
    By Kulsoom Ismail Idris
    
      *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Paid book 200 only


Page 9_10
    
    Kamar yasan abunda ke zuciyarta ya juyo yana kallon ta,kallonta yake daga sama harkasa,yadda kasan wadda aka tuno daga rami,kafarta futu futu,wani shegen pant ne ajikin ta wanda yarasa gane wane color ne,shiba maroon ba shiba ash ba,shiba black ba,ya dafe ya dakal kale,ya mandake,tsaki yaja metsayi,kokarin juyawa take yayi caraf ya damkota,kamar kaza haka ya dagata ya tsullumata acikin ruwan,kuka ta fashe dashi jin yadda zafin ruwan yake ratsa fatar ta,da bayan hannun sa ya gwabje mata baki dan dole tai shuru tana sheshshekar kuka.Nade hannun shaddar sa yayi babu makawa saiya dirji jikin wannan me kama da fatalwar,mamaki be gama kashe 'Yar Aro ba saida taga ya dakko soso da sabulu kamar Allah ya aiko shi haka ya dinga dirzar ta,dandanan ruwan kumfar ya dafe kai daga karshe ma kinyin kumfa yayi tsabar dauda.Kusan sabi 10 yayi mata tun tanajin dadin wankan har fatar jikinta tafara radadi da zugi.Kuka take shabe shabe,amma dan tahalukinnan be barta ba saida yaga ta dawo hayyacinta.Tsamota yayi ya dire ta akasa,bursh ya dakko da kansa ya dirje shegen bakin daya gama dafewa,kanta ya kalla,tallake mata keya yayi kazamar banza Kawai.Duk yadda ya dirji kan ganin sa yake be fita ba.Karamin towel ya dakko ya daura mata,iska medadi ce take shiga jikin ta,sai kallon kanta take yadda taga ta kara haske kamar ba ita ba,amma zuciyar ta fal bacin rai dole tadauki fansar abunda yayi mata.

Jan hannun ta yayi sukai fice daga toilet din,duk abunnan da yake ko saudaya bataga hakoransa da nufin yin murmushi ba,anya ma wannan yana dariya.Tabe baki tai tare da hararar sa Karaf suka hada idanu,waro idanun sa yayi yana kallon ta,da sauri Hamna ta kawar da kanta sosai taji shakkarsa a zuciyar ta,duk rashin jinta taji wannan tana shakkar sa.Wani bedroom suka shiga,komai na dakin ya tsaru, pink ne kayan dakin dagani dakin yara ne,dakin ya birgeta matuka, wardrobe ya bude,wata gown ya dakko mata iya guiwa ta tsaya mata fara ce sol,da kansa ya saka mata kayan,kamar yadda ta kira shi da dan iska harta pant shiya saka mata,haushi kamar zai kashe ta ya ham kalle mata jikin ta.Veill ya dakko dan karami yayi mata rolling saiga 'Yar Aro tatashi ras da ita,gaban mirror ta karasa tana kallon kanta,hakoranta ta bude ganin yadda suka fara washewa,ita kanta tayi sha'awar kanta,ashe dai zaman birni akwai dadi,to gaskiya bazata sake bin Dada su koma kauye ba(🤣🤣🤣haba 'Yar Aro da wuri haka).Turarukan data gani akan mirror din ta dauka baji ba gani ta dinga fesawa,ganin abunnata bana hankali bane ya kwace daga hannun ta.

"Bece mata komai ba yaja hannun ta suka koma maine parlour,har Lokacin suna zaune,sai zuba idanu suke suga ta inda zasu bullo,zuba mata idanu sukai yadda sukaga Lokaci daya yarinya ta fara canzawa,'Yar Aro kuwa cakewa tai tana kare musu kallo daya bayan daya,face a tsine take kallon su kamar taga kashi,abun ba karamin haushi ya basu ba,sun lura Hamna ba karamar mara kunyar yarinya bace,aiko zasu gyara mata zama.Idanun tane ya sauka akan Ammi da take kallon su ita da saudauki daya bayan daya yake karantar fuskokin Mutanan parlon,wani dadi ne ya Ziyarci Ammi,ganin yadda Sadauki ya gyara mata yarinya tas da ita,tarasa wace irin kauna Sadauki ke mata ita da 'ya'yan ta.Amma koda ta tuna wacece Hamna awajan sa sai batai mamakin hidimar da yayi agare taba.

"Mima ce ta mike ta kamo hannun ta, Little Sister,kauda kai Hamna tai tana cono baki,gaba daya haushin mutanan Gidan take ji,bama yadda taga wasu 'yammata nai mata kallon hadarin kaji,abin sai yakara bata haushi,kusa da Ammi Mima ta kaita,Ammi bakiga yadda Hamna tai kyau ba,nagani Ammi ta fada tana kallon Hamna,amma babu ruwana da ita bakiga ko kallo bamu isheta ba,rashin Kunya kikaje kika koyo acan kenan,shiru Hamna tai tana kallonta,sarai tasan ita ce Mamanta,amma ita bata saba gaida mutane ba tuncan baya,yanzu ma bazata iya gaida suba.Cikin kuluwa Ammi ta kawo mata duka,sabon salon Iskanci ne hakan inai miki Magana kina jina,kumbura fuska tai ni bazanyi Magana da kowa ba sai naga Dada ta,amaidani kauye."Hajiya Jamila da tuntadazu batai Magana ba itace ta magantu,ai dama dacan kika dace,ni bansan kitifin dayasa akaje aka jajibo ki ba,muna zaman zamanmu.Babu wanda ya tanka mata,sai 'Yayan ta dake cika suna batsewa,nima Abunda nagani kenan Mom,kome yahada dan kauye da birni oho.Momma ce ta mike tare da rike hannun Hamna sukai part dinta,tanaiwa Mom fatan shiriya,tarasa me Hamna ta tsare mata,tun sanda aka haifeta ta dora idanunta akanta bata barta ta huta ba,ko Kuka take ta dinga jaraba kenan an haifa musu me Kuka zata hanasu sukuni.

  Dada ita ce Mahaifiyar su,wadda Asalin sunan ta Fatima,su 'yan Katsina ne dukkan mahaifar su,iyayan su da kakannin su duk suna can.Mahaifinsu Allah yayi masa rasuwa tun basu da wani karfin da zasu Iya daukar dawainiyar Mahaifiyar su da sauran kannan sa.Matan Baban su Uku kowacce tana da 'Yaya agidan.Yaran Dada Akallah zasu kai su goma,guda Uku sune anan ABUJA suma aiki ne ya kawo su,babu yadda basiyi da Dada ta dawo Wajan su ba amma firtaki,tace bazata Iya rayuwa awannan garin ba,bakinciki ne zai kashe ta,duba da yadda take ganin wasu masu bingilalliyar riga da siketi,haka suka gaji suka kyaleta.Gidan da Alhaji Habib ya tanfatsa part hudu yayi shi,biyu  na 'Yan uwansa,sai guda daya na Dada da nashi,amma sai dadan taki dawowa.Dukan su a yanzu babu wanda baida iyali Big Dady shine Mahaifin Sadauki, sai Abbah shine Baban 'Yar Aro,sai papi shine Mijin Hajiya Jamila.A zahiri zaka ce suna zaman lafiya,amma in kazauna da su zaka tabbatar abun ba haka yake ba,kawai kowacce ta iya takun tane,amma ko akan yara sunsha cacar baki,musamman sanda 'Yar Aro ta fada rarrafe tasha kirba awajan Hajiya Jamila.

"Sanda Dada tatafi da ita ai tafi kowa farin ciki,daga yaye Dada tace zatai kwana biyu shikenan taki dawowa da ita,babu sintirin dasu Ammi basiba akan ta basu Hamna amma firtaki bada ita,Ammi tai Kuka kamar zata shide ganin inda Dada take nufin rainar mata diyarta.Ammi ba anan kasar take ba,daga can Germany  Abbah ya Auro ta,tunda Dada ta kyallara ido taga ya Auro Baturiya acewar ta,tunda acan aka haifi Ammi,amma asalin su Fulani ne,aiki yakai mahaifinta can,gaba daya rayuwar su saita koma kamar ta turawan.Dada tasha sababi akan taya zai dakko mejan kunne,taya zatai tarbiyyar yaransa,shidai yaji ya gani da kyar ya shawo kan Dada tadan sakko,amma da yadda ta tsani mutuwarta haka ta tsani Ammi,wadda asalin sunan ta Aisha ne,suke cemata Ammi.

Ita ma Ammi din da kyar iyayanta suka bawa Abbah Auranta,basa son ko kadan tayi nesa dasu,dan dai babu yadda zasiyi ne shiyasa suka yadda da Auran,Abunda diyar su take so shi suke so,ita kadai Allah ya basu shiyasa suka dauki son duniya suka daura mata.Tunda tazo gidan Momma ce kadai take kaunarta takuma jata ajiki.Momma yaranta Biyar Omar shine Babba suna kiransa da Sadauki,sai Yusuf,Basma,Najma,Khairat itace Auta.Hajiya Jamila wadda suke kira da Mom yaranta Biyar itama,Khalid,Sumayya,Bilkisu,Sauda,Musaddik.

Haihuwar Ammi ta farko ta haifi Khadija suke kiranta da Mima,haihuwa ta biyu ne ta haifo Fatima suke kiranta Hamna.Haihuwa ta uku akasa mata Aliyu suba kiransa Munib.Sunan Dada a kasa,aiko Dada tayi matukar farin ciki,sanda aka haifi Hamna lamar diyar Larabawa,fara ce tas kamar su daya da Ammi kamar antsaga kara,tun sanda Sadauki ya dauke ta yaji tayi matukar birge shi,Lokacin yana final year a digree dinsa na farko a fanni Lafiya.Daya dawo part din Ammi yake wucewa,duk ko da yadda yara basu dameshi ba,amma akan Hamna baya gajiya da daukar ta.Tun Ammi na hanashi daukar ta Saboda karya kayar mata da ita harta gaji ta kyaleshi.In tana fadin nidai Sadauki karka yardamin ita,sàidai yayi murmushi kawai,wadda bakowa yake ganin murmushin saba.Kaf 'yan gidan suna matukar shakkar sa,in kayi laifi duk girmanka zai zanema jiki,musamman yaran Mom da sukafi Kowa rashin ji.Shiyasa tasu sam bata zo daya da Sadauki ba,ba karamin haushinsa take jiba,yana tsaye a kahon zuciyar ta.

"Shima gaba daya Mom batai masa ba,hakanan yaki jininta,Saboda macece me shegiyar karya,ga son 'ya'yanta batason ko kadan ai musu fada,damma papi yana taka mata birki.Kula da Hamna kusan komawa hannun sa yayi,data ganshi zata fara daga masa hannu tana bangala masa dariya,inko ya tafi school sai tayi ta kuka tana nemansa,harsai ya dawo za'a ga Dariyar ta,harta Ammi kasa rarrashin ta takeyi.Haka Mima zatai tai mata wasa amma bazata taba dariya ba.Shekarar ta daya da rabi Abbah ya turashi can Germany yaci gaba da karatun sa acan,babu yadda zaiyi haka ya tafi yana dagawa Hamna hannu da batasan meyake yi ba,atunain ta school zaije ya dawo.Tun tana Kukan rashin sa har tagaji ta hakura.Sanda aka yaye ta Dada tazo ta dauke ta ta gudu da ita,babu wanda ya sanar Dashi antafi da Hamna kauye,ana da tabbacin zai iya biyo jirgi ya taho,babu makawa kuma saiya dakko ta.

"Sàida ya shafe shekaru biyar acan,Gidan su Ammi nanne masaukin sa,mutane masu karamci da Mutunci,kamar Ammi haka suka dauke shi a jikansu,babu abunda basa yimasa,har so suke suji yana da wata bukata suyi masa.Yadade be hadu da mutane masu karamci irin su ba,saiya karajin Ammi ta kara girma azuciyar sa,tabbas mutunci badaga sama ta same shi ba,agidansu taga anayi.Bayan shekaru biyar ya dawo,ananne yaji Labarin abunda Dada ta aikata,ta dauki Hamna ta fece da ita,tun Lokacin yaso zuwa ya dakkota koda tsiya da tsiyatsiya,amma Big Dady yaja masa layi,inya kuskura ya batawa Mahaifiyar su rai shima sai ransa ya baci,kamar zai hadiyi zuciya haka yaji,Ammi ce ta dinga lallashin sa da bashi baki,duk da itama daurewa takeyi Abun yana cin zuciyar ta.Sosai Sadauki yayi fushi da Dada ko kadan taki zuwa inda take,yana takaicin yaje yaga yadda Hamna ta koma,ga wani suna data lika mata wai 'Yar Aro wannan suna na bata masa rai."A wannan karon ne yayi alkawari zuwa ya dakko ta,kome Big Dady zaice masa zai jure.

   Wannan Kenan.

  Wannan shine Last free page maza ki hanzarta ki biya 200 dinki Hajiya,kada kibari wannan kayaraccen Labarin ya wuce ki.

Labari ne me cike da Nishadi.
Soyayya.
Tausayi.
Butulci.
Dama sauran abubuwan da bazasu Laiisafu ba.Yanzu ma aka fara.



 Account number
6113314982
Ummakursim Idris Ismail
Opay bank.    

Mrs Baba Bello Abubakar
           .......✍️✍️✍️✍


        'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

Page 11_12

"Abinci Ammi ta zuba mata,tunda tazo bata sani ranta ba saidata ga Abincin,amma ahakamma tanraina shi Kawai dai shiru tai kar ace tacika zalama.Kan carpet ta zauna ta mimmike kafa zata faracin Abincin,tankwashe kafarki Ammi dake kallonta tai maganar,dagowa tai tana kallon Ammi ko kadan babu fara'a afuskar ta,shakkar Ammi ta faraji ganin kallon datake wurga mata,Ammi duk da tana da sanyin hali amma nata wasa wajan tarbiyyar yaranta.Babu musu ta tankwashe kafar ta fara kai Abincin bakin ta,tana ci tana karkada kai,sosai Abincin ke ratsata.Saidata cinye tas kafinta dago kanta,ganin yadda Mima da Kanin ta Munib suka zuba mata idanu yasata bata rai,kallon me kukemin haka,daga kafada Mima tai nothing,Munib ta kalla ta watsawa harara ganin yadda yake kunshe dariya yana buya abayan Ammi.

"Ita kanta Ammi dariya ke cinta ganin Uban abincin data cinye kamar jaka,lallai akwai yaki agabanta dolene tasan yadda zatai da Hamna,ya zama dole ta dawo da ita hayyacinta.Gorar ruwan dake gabanta ta dauka saidata shanye tas kafin ta wullar da gorar,oya dauke kikai inda ya dace dashi,mikewa tai takai plate din kiching kafin ta fice daga part din gaba daya.Tana fitowa harabar gidan ta hango Mom da tawagarta,da alama dama zancanta sukeyi,dariya taga sun saka suna kallon ta,mutanan kauye har amfara gyagijewa amfara shan jarmiya.Bilkisu ce tatabe baki,ni wllh hakanan banji dadin dawowar yarinyar nan gidannan ba,naso ace a kauyem aka barta taje can takarata,har ina shirin nanda 2years mu ware bikinta,amma dan bakinciki yaje ya dakko ta.Sumayya datafi kowa jin haushin Hamna ta yamutsa baki,ni kyanta nema yake batan rai,yarinya kamar aljana,da sa'ar kice wannan bazaa kalle mu ba,ita za'a dinga yiwa layi.Ita awa cewar Sauda da take watsawa Hamna harara,aini wllh bana ganin kaina ba kyakykyawa ba,a sahun farko nake ajiye kaina,ta inama zanfinga kai kaina baya,da manyan mata nake gogayya bada jaririya ba.

"Fada musu dai abunda Mom ta fada kenan,gaba daya sunbi sun tada hankalin su akan wannan ficiciyar Yarinyar.Musaddik da yake sauraron su kallon mamaki yakeyi musu,yarasa wane irin.mutanene sukam, ba'a damu da suba amma su sun damu da mutane.Allah ya shirye ku wllh,ina ruwanku da ita daga zuwan yau amma zaku gallabe ta,kudai ku canza hali,kuma Mom duk laifinki ne,yanzu Gashi kin dasa musu hassada da kyashi acikin Zuciyar su.To kanin Aisha zoka rufeni da duka,nifa Musaddik bazaka birgeni ba,saika koma dakin Aisha amatsayin kasake uwa.Nan gaba muka jera da ita ina da tabbacin zakace banice uwarka ba itace.Allah ya baki hakuri ni gaskiya nake gaya muku.Musaddik shekarar sa 15 yana da hankali da sanin yakama ta.Mikewa yayi yana sakarwa Hamna murmushi,duk maganar da sukeyi taji su sarai,kenan basa santa,aiko zama agidannan ya zame mata dole,ada ta fara tunanin in Dada tazo tafiya da ita tabita,amma yanzu tafasa zataga shegen dazai fita da ita daga gidan.

"Wani murmushi ta saki wanda ita kadai tasan ma'anar sa,azatan Musaddik dashi take saiya kara fadada fara'ar sa.Hannun ta ya kama zo muje mubuga boll Hamna,babu musu ta bishi tunda taji rashinji za'a je ayi.Da harara suka rakasu,oho basuma san suna yiba.Wani babban filine anan suke buga boll,kayan boll dinsa ne dama ajikinsa,nima ina nawa kayan, murmushi yasaki kina so ne,gyada masa kai tayi alamar eh,to zan siyo miki inna taso daga school gobe,so nake muciwo cup din duniya.'Yar dariya ta saki batace komai ba.Fara wasan su sukai hankali kwance,babu abunda take tsinanawa sai gudu datake yi,boll dinka bata iya riketa saboda tai mata nauyi balle kuma aje ga bugata.Saidata gaji dan kanta tace ta gaji,kwanciya tai tana maida Numfashi kamar yadda shima Musaddik din yake maida Numfashi.Kasa mikewa tai sàida ya mika mata hannu takama hannunsa kafin ta mike,gaba daya ta hada gumi,zo muje part dinmu,make kafada tai,bana zuwa inda ba'a kaunata,ba'a maraba dani.Kunya ce ta kama Musaddik ganin ashe ta gano Abunda Mom din sukai mata,sunkuyar da kansa yayi bece mata komai ba ya wuce.

Ita ma wucewa tai tana ayyana irin rashin mutuncin da zata shukawa su Mom din.Su Big Dady basu dawo ba sai kusan Sallar isha'i,Indai mutan gidan suka saba tattaruwa yauma suna parloun,kowacce da tawagarta agefenta,Momma da Ammi waje daya suke zaune haka yaran su.Mom da ko yaushe take ware kanta daga cikin su ita da yaranta suna ta kus kus alamr wata gulmar sukeyi.'Yar Aro na can gaban TV kamar zata fada ciki sai dariya take tana buga cinya,dariyar tace tasa suka Lura da ita,da Mamaki Papi yake kallon ta,kamar mamana nake gani,eh itace papi cewar Najwa,ina Dada yaushe suka zo?Mom ce ta caraf ai Dada ma batasan anje an satota ba,yanxu haka Allah kadai yasan halin da take ciki',cikin takaici Mom ta karasa magana,yadda kasani 'Yar Aro akanta take."To tsohuwar munafuka,nifa nalura tunda nazo Gidannan bakya kauna,to babu Inda zanje zama daram,sàidai ki mutu wllh.'Yar Aro ce ke wannan maganar cikin jin haushin Mom.

"Gaba daya tsit sukai aparlon Musamman Mom wadda wuta ta daukewa,sosai kalaman Hamna suka kona mata rai.Abbah ne ya kalle ta,kinci Gidan ku Hamna,maman taki kike fadawa haka,niba mamana bace Abbah tunda bata sona nima bana santa.Big Dady har yanzu bece komai ba, kallonta kawai yake yadda ta koma ta gwafe agaban tamfatsetsiyar plasma.Papi watsawa Mom harara yayi ta fara kaishi bango da halinta na banza da wofi.Wanene ya dakko ta,cewar Big Dady wanda ko baa fada ba yasan aikin wanene wannan din.Numfashi ya sauke,amma ko ba komai yaji dadin ganin ta,dama yasan shikadaine wanda zai iya kwato Hamna daga hannun Dada.

"Su Ammi suna jinta,mamakin tashin kunyar Hamna suke,da kuma saurin gano abubawa,yanzu harta gano Mom na adawa da dawowarta.Ammi taso yin Magana Mamma ta girgiza mata kai alamar tai shiru da bakina.Big Dady ne yayi Magana,maxa taso mamana,batace komai ba tatason ajikinsa ta kwanta,Big Dady ài bakwa sona,kundena kawan alawar nan medadi da kuke kawon,Dada tana fadamin zaku zo kukawon amma kuka daina zuwa.Shafa kanta yayi to kiyi hakuri yanzu kafin ki koma zakisha sweet ki koshi.Na koma ina?wajan Dada mana,wata 'Yar karamar dariya tasaki,aini Big Dady bazan sake komawa wajan Dada ba,ashe ni cutata kukeyi,kuna nan kunacin dadi ni kunbarni acan ina shan wahala,nazo kenann.Allah ko Dada zata mutu bazan kuma ba,tafada tana Murguda baki.

"Dadar taki kikewa fatan mutuwa Hamna,aiba nufina ta mutu ba,ko zata mutu nace,amma in Lokacin ta yayi ai kaga bazan riketa ba dole tatafi.Abbah ne ya wurga mata harara,uwar tamu kikewa fatan mutuwa,ko bammata ba dama zata wuce,Abbah mikewa yayi ya tabbaatar Hamna ta gama sangarcewa,yadda kasan wawiya haka take sam bata iya magana ba,bayajin zai kara yadda yabawa Dada ita su tafi kauye,tadawo kenan.Ammi ma takaici ne ya tsaye mata awuya,ganin gaba daya yarinya babu kwaba,komai fadarsa take kanta tsaye,shiyasa mutane da yawa suke gudun rainon kaka,to ita dai gashi yadda 'yarta ta dawo.Mikewa tai rai bace tai part dinta,ko ganin gabanta batayi saboda takaici.Tana shiga parlon su ta tarar da Abbah ya zuba tagumi,gaba daya abun Duniya ya isheshi,yana tsoron rigimar Dada inyace bazai bata Hamna su koma ba,Allah kadai yasan abunda zatayi.Shima din Ammi Haushin sa take ji, tagaban sa tazo zata wuce ya rike hannun ta."Kukan dayake cinta tun da rana shine ya kwace mata,zubewa tai kan sofa tare da fashewa da kuka.

"Abbah Kallon ta yakeyi,tabbas duk abunda yasa Aisha kuka ba karamin cimata rai yakeyi ba,bubbuga bayan ta yadinga yi alamar rarrashi,yanzu saboda Allah Abbah anyi min adalci kenan,kalli yadda Hamna ta dawo babu kwaba komai furtawa takeyi,bata kallon kan kowa da gashi,tunda Sadauki ya kawo ta taki gaida kowa acikin gidannan,shiru Abbah yayi bashi da bakin bata hakuri.Kiyi hakuri Aisha komai me wucewa ne,bazan kara bada yarinya ta akoma da ita kauye ba kaji na fada ma,fuuu tatashi ta fada bedroom din ta tare da murzawa kofarta key dan karma ya biyota,ayanzu batasan damuwa ko kadan."Sai kusan karfe 11 kowa yatashi dan zuwa yayi bacci, Lokacin tuni 'Yar Aro ta jima da wucewa Lagos,sai jan minshari take kamar rago."Mima ce ta fara tashinta,amma kamar dutse kin tashi tai."Yaya Musaddik dan Allah dakko min ita muje mu kwanta,mikewa yayi daga inda yake zaune,idanun Mom kamar zasu fado tsabar hararar datake watso masa,sarai yasan kallon da take masa shiyasa ma be yadda yakalle ta ba.Ciccibar Hamna yayi ashema bata da nauyi ya ayyana azuciyar sa.

"Har part din Ammi ya kaita bedroom din Mima anan ya kwantar da ita,sàida safe Yaya Musaddik Mima ta fada tana murmushi,Allah ya kaimu Mima.Rage musu hasken dakin Mima tai kafin ta kwanta.Kusan karfe 2 na dare Hamna ta lancaba uban fitsari,lallai ashe har fitsarin kwance take na iya shege."Sàida asuba Mima tatashi da nufin yin Sallah ta ganta tsamo tsamo acikin fitsari,da alama ba saudaya tai fitsarin ba,kamar zata rushe da kuka take kallon wulakancin da Hamna tai mata."Daka mata duka tai wanda yasata tashi a firgice,cikin hasala Mima take watsa mata harara,ashe dama fitsarin kwance kikeyi Hamna,kincuceni wllh da kikazo kikamin fitsari a bed,to Allah bazaki sake kwanar min a room ba saidai abaki naki kije can ki karata."Saboda nayi fitsari kikaimun wannnan dukan,nayi miki ko zaki rama ne,aiko wllh saina rama,sakkowa tai daga kan bed din,azatan Mima da wasa takeyi,batasan 'Yar Aro bata fadar abu bata aikta ba.

"Bazato taji ta rufe ta da shegen duka yadda kasan 'yarta haka ta zage ta dinga dirkar Mima kamar Allah ya aiko ta......

     Mrs Baba Bello Abubakar
     ......✍️✍️✍️✍️


         'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

Paid book 200 only

  *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Page 13_14


"Dambe suka kacame dashi,duk da Mima ba wani karfi ne da ita ba,amma ita ma ta jibgi Hamna ba karya,sai haki suke kamar wasu zakuna,Hamna da takaicin duniya ya isheta na yadda tatasheta daga bacci ta kara kaimata duka,hannun tarike tare da murdewa,wata kara Hamna ta sanya ba karamin zafi taji ba,Ammi da.fitowar ta kenan tajiyo.karar da sauri ta fado dakin,bin dakin take da kallo sun hargitsa komai garin dambe,ga zarnin fitsari daya ke tashi a dakin.Kai mene haka zakusa mutane gaba kunai musu fada,menene ya hadaku,cikin kuka Mima take fadin Fitsari taimin Ammi,dannai mata magana shine ta rufeni da duka,fitsari Ammi ta maimaita tana kallon Hamna datai fiki fiki tana zare idanu.Hamna fitsarin kwance kikeyi dama,iskancin naki harya kai kamarki ki saki duwawu kiyi mana fitsarin kwance,ai bacci nakeyi,kuma shi me bacci ai besan abunda yake aikatawa ba,yimin shiru kazamar banza,tashi kije kiyi wanka ki cire Wannan kayan,kuma kayan shimfidar da kika bata babu me.wankewa ke zaki wanke kayan da kika bata.

"Kamar zata fashe haka ta fada toilet tana ayyana Abunda zataiwa Mima,kai bama ita kadaiba harda Ammi din sai sunsan sun taba ta.Watsa ruwa kadai tayi ta fito daure da wani towel,kallon ta Ammi tayi babu alamar wanka.ajikinta, ÀLLAH ya shiryeki, blanket da bedsheet din Ammi ta dauke,ana idar da sallah kifita dasu can bayan Gida ki wanke,Inba haka ba kinsan sauran."Kuka Hamna ta fashe dashi ni ban iya wanki ba,saidai kijira Dada tazo ta wanke min,gwabe mata baki Ammi tai,yimin shiru mara kunya kawai,dakko mata kaya Mima ta saka tai Sallah,zanga wanda zai tsaya yana wanke fitsarin gardiya.Tana Kuka tana sallah,ga takaicin ansata sallah,gana tashinta daga bacci da akai,ga kayan fitsari dake jiranta,abu goma da ashirin.

"Mima ma sàida tayi wanka saboda yadda jikinta ke tashin zarni,yadda kasan ita ce tai fitsarin.Karfe 7 Ammi ta tankada keyarta dauke da kayan fitsarinta a hannu sai Kuka takeyi,sàida sukaje har harabar part dinsu,Inda suke wanki anan sukaja birki,wani katon baho ta dakko maza zuba su aciki,zubawa tai ta dakko mata kilin ki tabbatar kin wanke su yadda ya kamata.Komawa tai tabarta anan,zubewa tai ta fashe da Kuka,wayyo Dada kizo kitafi dani,gwara na koma kauye,akan nadinga wankin kayan fitsari na,saidai muzauna tare anan kidinga wanke min,Kuka take kashir ba,tun sanda tafara Kukan ya shigo part din,dama zuwa yayi yaga abunda take aikatawa,fitsari ya maimaita azuciyar sa.Jin a dungure da kafa ta mike afusace dan ganin wanda yayi mata haka,Ganin Sadauki tsaye akanta,ya zube dukkan hannayan sa a aljihun wandon sa,da sauri tamaida hannun ta data dunkule dan kaiwa wanda yayi mata haka duka."Ya kika mayar,kiyi abunda yake ranki mana,shiru tai tana zare da idanu,wannan mara dariyar tana matukar jin shakkar sa,amma wai wanene shi ma,ya akai bata san shiba tunda take zuwa Gidan.Kazama kawai me kwarkwata,abunda ta tsana kenan ace mata me kwarkwata,Kuka ta fashe dashi,ni dai banda kwarkwata,duk abinda kukeyimin yana rubuce akaina Dada nake jira tazo na zayyane mata.

"Bece mata komai ba,da hannu ya nuna mata kayan wankin ta,babu yadda ta iya haka ta sunkuya tana wanke kayan tana matsar kwallah,sàidata wanke tas yana tsaye akanta,ashe dama ta iya Iskanci ne irin nata.Shanyawa tai kafin ya juya yashiga part din,abaya ta bishi tana kumbura fuska.Ammi tana kiching tana hada break saboda masu tafiya school.Har kiching din ya bita.Good Morning Ammi, morning big brother, murmushi yayi inta kirashi da wannan sunan,ita ma murmushi Ammi tayi,tana matukar kaunar Sadauki kamar kanin ta haka take jinsa.Kaga Mutuniyar taka awaje,um kawai yace tasan miskilancin sa,bata sake magana ba ta juya taci gaba da aikin ta.Tana tsaye a Inda ya batta,kamshin da take ji gaba daya ya cika mata ciki,sai bude hanci takeyi,burinta kawai azubo mata wannan abun da ake girkawa,yawunta ba karamin tsinkewa yakeyi ba.

"Bece mata kala ba yaja hannun ta sukai part din Mammah,sai kalle kalle take,gidan yayi matukar birgeta sosai,ta jima bata zo ba,duk anyi canje canjen abubuwan da bata san dasu ba.Mamma tana parlour azaune da azkhar a hannun ta.'Yammatan ta gaba daya suna Kiching suna hada breakfast,haka take dama,babu abunda bata koyawa yaranta ba,tajima da daina girki saidai idan basa nan.Murmushi ta saki ganin su tare da Hamna,uhm na Hamna har anje andakko ta kenan, murmushi kawai yayi yana zama kusa da Mamma,hararar daya zuba mata ne yasata tsugunnawa batare data shirya ba.Ina kwana ta furta kamar anai mata dole,lafiya lau Hamna kin tashi lapiya,gyada kai tayi alamar eh."Maza ga yayyanki can kije ki taya su aiki,mikewa tai babu musu,yadda kamshi yake tashi dole nema taje taga abunda suke dafawa yake tashin kamshi haka.Su biyu ne a kiching din Basma da Najma Khairat tana can tana shirin school,sa'annin ne ita da Mima,su Basma sunyi Candy result suke jira."Murmushi suka saki ganin yadda HAMNA ta tsare su da ido,kamar su daya kamar wasu 'yan biyu ta ayyana azuciyarta.Hamnan Yaya SD shigo Mana,shiga tai hankalin ta nakan food flacks din dake ajiye akan kanta.Dariya Najma tai Hamna kodai ta bahuwa kike ji,irin wannnan hadiyar yawu haka."Babu abunda nakeji akoshe nake,tafada wai dan karsu rainata, Murmushi Basma tai dama magana bata dameta ba,kidai fadi gaskiya Hamna,in kina so yanzu za'a san yadda zaai ko tabin gishiri ne kifarayi,dan jim Hamna tai,tunda kun matsa kubani na fara dandanawa.Dariya Najma ta saki 'yar rainin hankali waimu zaki mayar bugaggu,ai tunda kikace ba yunwa kikeji ba saiki jira sai angama.Kamar Hamna zatai Kuka take kallon Najma,ashe bakin haline dake natsaya nake sakar miki fuska,Allah daga yau bazaki sake ganin hakora na ba,daga kafada tai ke kika sani,abinci ne dai bazaki ciba ba sai mungama.

"Fitowa tai daga kiching din takaici kamar ya kasheta.Sadauki tunda tafito ya kalleta yasan Akwai abunda kai mata, Mammah ce ta tambaye ta,yadai Hamna ko wani abu akai miki,girgiza kai tayi alamar àah,daga can gefe ta koma ta zauna."Cikin karadi da masifa Dada take zabga sallama,salamu Alaikum gani nazo ina mara mutuncin nan yake daya je har gida ya satomin yarinya,tun wuri Wllh afitomin da 'Yar Aro kafara kafarta,zumbur Hamna ta mike jin muryar Dada jikinta har rawa yake wajan ficewa daga part din,hannunta taji an ruko,juyowatai suka hada idanu da Sadauki,bece mata uffan ba ya ja hannun ta,ta part din Mammah yabi ya shiga part dinsa tana jaye a hannun sa.Murzawa kofar key yayi danya rantse Dada bazata sake tafiya da Hamna ba."Kamar Hamna ya raushe da Kuka haka take binsa,sàida yakaita har bedroom dinsa kafin ya saketa,zaka yayi abakin bed dinsa ya a dafe kansa,tsaye tayi tana zabga masa harara,da taga zai dago saitai sauri ta kawar da kanta.

Matsamin daga ka karna tattakaki,can gefe ta matsa kamar zatai bindiga, parlo ta fito idanun ta ya fada kan wani prime me kyau, kyakkyawar baby tagani abun sha'awa,gashin ta luf luf kamar diyar Larabawa,tashaga da kallon prime din tana tunanin wacece Wannan ajiki.Sai Lokacin ta lura kusan duka parloun Irin wannan pick din babbyn ne birjik.Ko wacece wannan oho,tafada tana tabe bakin ta.Stoll din mirror ta sadada ta dakko batare daya ganta ba,ajewatai tare da rike kugu tana tunanin wanda zata fara dakkowa tagani."Idanun ta ne ya tsaya kan wani pic dayayi masifar kyau,babyn ta fara girma tana tsaye da tady dinta ahannu,face dinta dauke da murmushi,ga wasu hakwara guda hudu kasa biyu sama biyu,abun ya Matukar kayatar da ita.Kitson da akaiwa babyn ibrane gashin baki sidik an daure nata shi a tsakiyar ka.Daga gani tafiyar ta batai kwari ba,alamar akwai wani agefe wanda yake mata wasa tana bangala dariya Ahaka akai pic din.Kayan jikin babyn Maroon color ne,sun amshi farar fatar ta.

Duk cikin mintuna biyu tagama karewa pic din kallo.Daddafawa tai ta hau kan Kujerar mirror din,duk da haka tsayin ta bekai ba sedata hada da dage.Saidata dakko prime din tsaf kafarta ta gurde,sakin phone tai aiko yana fadowa Glass din ya bada wasi sauti alamar wani abu ya fashe,duk yadda taso karta yadda ya fado abun ya gagara,gaba daya kafafunta suka dira akasa,abun tsautsayi glass daya fashe akasa sai farta daya ta sauka akansa.Wata kara da tasaki wadda ta tilastwa Sadauki futowa,kafarta ta rike tare da sakin Kukan azaba.

"Wani kalar radadi take ji a kafarta,tuni kafar ta fara bleeding jini har tsartuwa yake,da sassarfa ya tsugunna agaban ta,sai Lokacin ya lura da aika aikar da tayi masa,kallon sa ya maida kanta,yadda idanun ta har sun kankance sabida azabar datake karba.Bece mata komai ba,mikewa yayi ya dakko box din sa,tana inda ya barta tana aikin kuka,kafar ya rike kwalbace ta shigar mata kafa sosai.Da kyar ya samu ya cire mata bakaramar azaba tasha ba,tunkan agama zazzabi ya rufe ta me zafin Gaske.Dressing yayi mata yasa bandeji ya nade mata kafar.Dauketa yayi daga wajan ganin kayan jikinta basu baci ba ya dorata a bed dinsa, blanket ya lulluba mata ganin yadda take rawar sanyi,ga kuka ga zugin da kafar keyi mata.Maganin ya dakko harzai bata maganin ya tuno batayi break ba.Fridge ya bude ya dakko mata yogurt me sanyi,a cup ya tsiyaya mata,tashinta yayi zaune,da kansa ya bata,ganin bazata iya sha da kanta ba.Da farko taki sha sàida ta kalli face dinsa ba alamar wasa tukunna takarba tasha.

Toilet ya fada yayi wanka,ya jima aciki kamar me wankan jego,daure da towel a kugunsa ya fito,Lokacin Hamna ta jima dayin bacci,saboda yadda kafar ta rage yimata radadi.Kananan kaya ya saka sai p-cap daya dora aka,sosai kayan sukai masa kyau.Sadauki farine tas,kamar kataba jini ya fito,yana da dara daran idanu,sajan face dinsa luf luf,yanada tsayi da jiki,jikinsa a murde yake.Sai miskilanci nakin karawa,yan gidan na matukar shakkar sa,kananan sa hatta matan gidan suna shayin sa.

Key dinsa ya dauka ya fice daga part din baki daya,murzawa kofar key yayi yana da tabbacin maganin daya bata zai sata bacci sosai."Motar sa yayi wa key wadda ta wanku kal sai daukar idanu takeyi.
      
     Mrs Baba Bello Abubakar

......✍️✍️✍️✍️✍️


                 'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris


  *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Page 15_16

"Jiyo hayaniyar Dada yasa gaba dayansu suka fito,suna jan kalu Innalillahi,suna da tabbacin yau bazata barsu su sha ruwa a gidannan ba.Yana ina nasan babu tsageran dazaije ya dakko min Yarinya saishi,ashe ni ina can zan kashe kaina abanza,amma tunda nasake kiran Harira ta siffatamun shi,sarai nagane ja'irin canne da fuska kamar ta kosai,Wllh yazo yabani 'Yar Aro mujuya,ba zama nazo yiba."Sannu da zuwa Dada,Big Dady ya furta yana matsowa kusa da ita,rashin lafiya nake zakadinga min sannu,tunda an hada baki dakai ansatomin jika aidole kamin sannu.To Wllh baxan sararawa kowa ba sai ambani Yarinya na koma da ita."Kiyi hakuri ki zauna Dada kinshawo hanya,cewar Abbah da yake kallon ta,Habibu karka sake batamin rai,nasan kaima da hadin bakin ka,Saboda na dauki 'Yarka ka tura wancan mara kunyar ya satota.Wai yana inama yabarni sai babatu nakeyi.

"Ammi ce ta karaso tanaiwa Dada sannu da zuwa,hararar da Dada ta watso mata yasata sunkuyar dakai,birinki ya cika Aisha an kwato miki 'yar ki,to ki sani bazan lamunta ba,rukon Fatsima ahannuna ya dace,bazaki Iya bata tarbiyya kamar yadda ni zan bata ba,shiru Ammi tai tana hadiye wani abu medaci azuciyarta,tarasa meyasa Dada bata kaunarta,ta haifo 'yar acikinta tadinga cewa wai bazata iya tarbiyyar taba,kwallah ce ta ciko idanun ta,da sauri ta juya jin yadda kuka yake kokarin kwace mata.Harara Mima ta watsa mata,sosai takejin Haushi Dada duk sanda tazo gidannan saita kunsawa Ammin ta bakin ciki,Mima shekarunta sha'uku da Hankalin ta ras,tasan kiyayya tasan kauna,bin bayan Ammi tai bataga abunda zata tsaya tai awajan Dada ba.

"Kowa Zuciyar badadi akan abunda takeyiwa Ammi,banda Mom zuciyar ta kal,sai murmushi takeyi,aduniya babu abunda take so bayan taga damuwa akan fuskar Ammi,haka nan taki jininta,kuma tsabar hassada ce ganin tafita komai,tafita kyau,ilimi,dukiya,nasaba,gaba daya ta kereta shiyasa Mom Jamila abun ya tsaye mata azuciya.Mammah ce ta magantu,ki zauna Dada in yaso sai ayi Maganar a tsanake,to da yake ita ma tagaji da tsayuwar ga yunwa na addabar ta,saita samu sofa ta hakince,sai kada kafafuwa take tana hura hanci, murmushi papi yasaki Dada 'yar rigima."Cikin kisisina Mom Jamila ta duka har kasa tana gaida Dada,da fara'a Dada take amsawa,dan kaf gidannan tafi ganin mutuncin Mom,saboda intazo yadda kasan Mom ta kwanta tadinga bi takanta tsabar biyayya."Sannu Jamila ya hidima kuma, Alhmdlh Dada,bari akawo miki kayan kari,yawwa ina jira,dama cikina ya zazzage,amma kalli dayake basu dauke ni da muhimman ci ba,babu wanda ya dakko min abun kalaci,da Uwar Aisha ce tazo da yanzu ancika gabanta da kayan tande tande(uwar Ammi take nufi)babu wanda ya tanka mata,sai Mom data sake sakin murmushi,wane ita ai Dada kece kike da iko da gidannan,abunda kike so aishi za'a yi,ke da kika samu tarbiyya kenan,cewar Dada da take watsawa Mammah harara,ita ma tafarajin haushinta ayanzu.Mammah kauda kanta tayi,Lallai Jamila makira ce,ga yadda take sunkuyar dakai,bayan abayan fage ba kaunar Dadan take ba,ita kuma Dada har yanzu takasa gane wanda yake kaunarta tsakani da Allah.

"Mom ce ta dakko food flaks din"Sumayya da Bilkisu suka dauko tea flaks da cups."Har kasa suka duka suna gaida Dada,amsawa tai tana tambayar su yaushe zasu futo da mijin Aure,Shiru sukai,sai Mom ce tace nan bada jimawa ba Dada,to Allah ya kaimu.Ga kanwar su nan ma nanda shekara biyu zamma ta Aure,bakiga yadda samari suka fara yi mata layi ba,danma bata da wayo taki saurarar su, Mom abun nema ya samu,dariya kamar ta kashe su,ashe Dada min kusan zuwa biki,kwarai kuwa,min kusan kiranku kwana kusa.Su Abbah da suke sauraren su basu ce kala ba,tab lallaima ai bazasu taba yadda da wanann Auren ba, har nawa Hamna take da Dada ke mata xancan Aure kwanan nan."Sàida Dada ta gama cin Abinci tai kat,taji kwari ajikinta sannan ta kara dira masifa,kowane part sàidata shiga ta duba babu 'Yar Aro,ta tabbata boyeta akai,su Abba sunga tijara,abakin get ta zauna tana jiran taga ta ina Sadauki zai bullo."Bashi ya dawo ba sai kusan 12  yana danno hancin motar sa ya hango Dada azaune suna hira dame gadi,zumbur ta mike tana watsa masa harara,ranta bace ta matso kusa da motar tana leka kanta ciki ko zataga Hamna aciki,ganin bata ciki Dada ta kara fusata,gidan Ubanwa ka kaimin Yarinya?ko kallo bata ishesa ba ya kauda kansa,face dinnan yayi cidin cidin da ita,sai hura hanci yakeyi.Ai ko iska zaka tayar saika fitomin da 'Yar Aro."Yana gaba tana biye dashi har maine parlo,da yake weekend ne gaba daya suna gida.

"Kai gaya masa ya bani 'Yar Aro mutafi tunda kai kahafeshi zaifi jin Maganar ka,shiru Big Dady yayi yana kallon Sadauki,wanda ransa ke bace.Ina Hamna,Big Dady ya tambaye shi yana kallon sa, Numfashi yadan sauke bacci takeyi,agidan uwarwa take baccin,zaka tashi ka fitomin da ita ko saina makeka, murmushi yadan saki jin wai zata make shi.Sadauki jeka dakko ta,cewar Abbah daya gaji da fadan da Dada keyi,kodai ita ce tai nakudar Hamna sai haka."Mikewa yayi Dada mikewa tai zata bi bayansa,karki sake kibiyo ni,abunda yace kenan yayi gaba ya barta atsaye,cikin takaici Dada ta koma ta zauna,tasan halinsa tana binsa to bazai fito mata da Hamna ba."Saidaya shiga part din ya tuna da barnar da Hamna tai masa, glass din data fasa yana wajan, bedroom din ya shiga bata ciki, toilet ya leka nan bata nan,mamaki ne ya kamashi to ina tatafi,fitowa parlon yayi sai Lokacin ya hangota,kamar bera tana makale abayan sofa, Apple din fridge dinsa ta jido sai ci take tana lumshe idanu, murmushi kawai ya danyi,jin alamun an tsaya akanta yasata bude brown din eyes dinta,saurin yadda Apple din hannun ta tayi tana zare idanu."Bayan rashin kunya har sata kikeyi,kuka tafashe dashi,wllh bana sata,yunwa nakeji shine na dauka nake ci,bakiji me kika ce ba,kika dauka kinga aiba baki nayi ba,ya zama dole kibiyani Apple dina.Zan biya ka,ta yaya?a part din Ammi zan dakko,keda baki girmama Ammi din,ko bakisan ita ce tai nakudar ki ba,harta kawoki wannan Duniyar,amma shine kika hada kai da Dada kike bata mata rai.

"Nadaina"Allah ko?saurin gyada kai tayi,ai matsalar ke ba abar yadda bace Hamna,tuban muzuru gareki,yanzu matsaya guda daya,in kikai hakan na tabbatar kin gyara kura kuranki na baya,in har Dada tace zata tafi dake kiki yadda ki bita,kallon sa kawai take,ko bazakiyi ba,zanyi,dama ancema ni mahaukaciya ce zan sake komawa kauye,good girl,oya tashi muje,in ko kikai sabanin haka nidake ne."Mikewa tai tana dingisa kafa,tana gaba yana biye da ita abaya,zuba musu idanu mutanan parlourn sukai,sabanin Dada data rafka salati,mezan gani haka,meyasa meki akafa 'Yar Aro,tana riketa take wannnan Maganar.Cikin jindadin ganin ta Hamna ta rungume ta,oyoyo Dada ta,keni ba wannan ba,shine yaji miki wannan ciwon ko yaya,kallonsa tai ganin bama ita yake kallo ba,fadowa nai shine na taka kwalba,ke fadamin gskiya,dagaske nake Dada,au na aza mugunta ce tasa yayi miki haka.

"Ai yau dinnan zamu juya tunda nema akeyi a kashemun ke"dago kanta tai suka hada idanu da Sadauki,kallon dataga yayi mata na gargadi yasata saurin girgiza kai,aini Dada bazan koma kauye ba gaskiya,ke menakeji kina fada haka,bazaki bini mukoma ba,eh sàidai kema ki zauna anan muzauna tare.Tafa hannaye Dada tahauyi, Innalillahi nashige su kodai farraku akai mana eh,shiru 'Yar Aro tai dan batagane menene farrakun ba.Duk wanda ya shiga tsakanina dake ban yafe masa ba ko wanene,in kuma munafukar Uwarki ta saki zanji.Sosai Hamna taji haushin furucin Dada gaskiya Dada karki sake cewa uwata munafuka takarasa fada tana murguda baki,ni zakiyiwa rashin kunya,ni gaskiya na gaya miki zamu iya samun matsala dake,Dada data rasa bakin magana tai shiru tana al'ajabi.

"Sadauki kuwa darya yakeyi a zuciyar sa"su Abbah ma sunyi mamakin Maganar Hamna,kuma sunji dadi data ce bazata sake bin Dada kauye ba,sabanin su Mom da bakin ciki yayi musu kum azuci.Cikin jin haushin Hamna Mom ta fara magana,dama Hamna baki da kunya yanxu Dadar kike fadawa haka,saboda sa'ar kice ko yaya,harara Hamna ta watsa mata,ana babbakar giwa wazaijiyo kaurin zomo,ni bana shiga harkarki kidaina shiga tawa,Dada ce ta gwabe mata baki,ina rabaki da rashin kunya bakiji,to Dada bakiga ba harkata ta shiga,kuma Allah kodan saboda ke bazan koma kauye ba,saina addabe ki,kamar yadda na lura bakya sona nima bana sanki."Kul Hamna naki kinkara fadar wannan Maganar,itama mamanki ce,kallon Big Dady tai daya gama yi mata fada yanzu,daga kanta kwai tayi amma badan ta yarda ba.

"Babu yadda Dada bata da ita tabita su tafi fafur taki,Ammi tana jinsu ko kadan bata sa baki ba,haka Mammah Mom ce bakin ciki yake cin zuciyar ta,kamar ta rufe Hamna da duka haka takeji.Daga karshe dai Dada Zuciya tai tace aranar zata juya,rarrashin duniya taki zama annuna mata iyakarta akan Hamna."Direba aka sa ya dauke ta tana matsar kwallah, aduniya Dada na matukar kaunar Hamna."Dada na tafiya Hamna ta rushe da Kuka,sosai take kaunar Dada kamar yadda take kaunar ta.Mammah ce ta rarrasheta, Mom kuwa fuuu ta shige dakin ta kamar zatai bindiga,sam takasa boye kiyayyar da takewa Hamna,ko meyayi zafi oho.

"Satin Hamna biyu ta warke garau,zuwa lokacin tasan saki da lungu na gidan,tasan masu santa da masu kinta, Sadauki da kansa ya dauke ta yakaita makarantar su Mima,sanda akazo yi mata interview ansha dariya,kannan babu abunda tabsani,da kyar suka sakata a primary 2 matar da take kokarin shiga js a kauye.Uniform da komai a aljihunsa yayi mata,su Abbah suna jinjina kaunar da yakeyi wa Hamna,komai zai mata aduniya bayajin ya fadi,hakanan yakejin kaunarta acikin jinin sa."Fara zuwan Hamna makaranta babban tashin hankali ya zame musu,kullu yaumin saita fashewa dan mutane kai,akawo karar ta,ko andaketa bata jin duka,gaba daya ta addabi makarantar da rashin jinta,cikin gaggawa me makarantar ya rubuta mata takardar sallama ganin yadda iyaye ke yunkurin cire 'Ya'yan su.Hankalin su Abba ya tashi matuka,anyi nasihar abanza,andake ta abanza,ammata barazanar abanza.

"Bawan Allah haka Sadauki ya sake canza mata makaranta,nan ma bata sake zani ba,cikin wata Biyar ancanza mata school sau biyar,taki yadda ta zauna da kowa lafiya.Uban wani yaro har police ya dakko saka makon cirewa dansa hakora guda biyu data yi,da kyar aka sasanta case din,daganan kuwa aka sallami Hamna,abu takeyi tamkar me motsi aka,in tana rashin ji bata ji bata gani saita gama aiwatar da abinda akai niyya.

      Mrs Baba Bello Abubakar
       ......✍️✍️✍️


         'YAR ARO

Funny Girl 😁

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris
  *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "


Page 17_18

"Yauma tunda aka dakko ta daga school din ta makale a harabar gidan,sai zazzare idanu take tasan tsiyar data shuka,ganin tsayuwar bazatai mata ba yasa ta shiga part din su kamar wata mutuniyar arziki hadda sallama."Ammi dake zaune tana kallo ta bita da kallo,tunda taga tana sunkuyar dakai tasan akwai tsiyar data shuka,ke zonan,kamar ta rushe da kuka haka taji sam bataso Ammi ta ganta ba,babu yadda zatai haka tataho kai asunkuye,gani Ammi,harara Ammi ta watsa mata,wannan sunkuyar da kan da kikeyi fa,kamar kin shigo gidan surukan ki?babu komai Ammi idanune basa san ganin haske,au hakane,gyara kai tayi alamar eh,mene Wannan kike boyewa a hijab dinki,pepa ce,mugani Ammi ta miko mata hannu.Amana aka bani Ammi,kece xaa baki amana, mahaukaci ne kadai zai baki Amanar kayan sa,ke kanki baki rike Amanar kanki ba balle abaki amanar wani abu.Bani tunkan kisha mari,mika mata tai tana matsar kwallah,Sàida Ammi tagama karantawa tsaf kafin ta dago ta kalle ta,mari ta kawo mata tai saurin dukawa,kin kyauta Hamna yanzu abunda kika kara jawowa kenan,zanga wanda zai kara canza miki school tunda kin maidamu sakarkaru."Bari yayanki ya dawo zakiyi medalilin,fashewa tai da Kuka dan Allah Ammi karki gayawa yaya Sadauki yace saiya ballemin kafar baya,to ni da zai balle miki ma da ba an huta ba,ya hadda hadda hannun ya karairaya.

"Tashi kiban waje karki fusatani na dakko cable na zaneki wllh,mikewa tai tana rasu Kuka yau tasan tabani ta lalace a hannun muguncan kamar yadda ta samasa suna.Bedroom dinta ta shiga tuni aka raba musu room da Mima Saboda tsabar fitsarinta,tana bude dakin zarni Yayi mata welcome,gaba daya ta hautsine dakin sai tashin tsami yake da zarni.Har yau tananan da fitsarin kwancen ta,saidai aimata Addu'a shiriya.Atsakiyar dakin ta wullar da jakar hannun ta,gashinta daya sha gyara ta barbaza,zuwa yanzu du wata Sadauki yake tisata suje ai mata wankin kai,shiyasa zakiga gashin ta Kullum tsaf tsaf.A tsakiyar dakin ta wullar da school bag dinta,shoe ta kwabe shika ta wullar,haka 🧦 anan ta wullar da ita.Bed dinta ya fada,da yake tashin zarni."Tun tana kwance tana tunani har bacci ya dauke ta.

"Sai bayan La'asar Sadauki ya dawo,a gajiye yake yau ba karamin Aiki ya shaba,sosai ya jigata,yau hospital din Kamar an akaro musu yawan mutane,duk da prvt ne haka ake tururuwar zuwan sa.Part dinsa ya wuce,sàida yayi wanka yayi sallar La'asar kafin ya fito,part din Ammi ya zarto yawanci yafi cin abinci awajan ta."Bata parlor zama yayi yana sauke Numfashi.Mima ce tafito saga kiching hannun ta rike da plate,sannu da zuwa Yayah,kamar beji taba haka ya share,da yake sun saba da halinsa bata wani damu ba.Ammi fa?tana bedroom,ina Hamna,bacci takeyi,zai kara mgana Ammi ta sakko daga sama,aah Likita bokan turai,dan murmushi ya saki,kamar kasan yau mutuminka nayi,sinasir nayi kuma saboda kai nayi shi,godiya nake Ammi, murmushi tadan saki, kiching din ta wuce,sai data debomai a wani vowel me kyau,miyar sai tashin kamshi take,ga namanan zuku zuku akai."Zaune takai bayan ta dire masa Abinci,ina Hamna Ammi,tayi Sallah kuwa,gaba daya face din Ammi canzawa tai,tana dakin ta tana bacci,takara halin nata,Wllh Sadauki nagaji da halin Hamna,gwara a tattarata a maida ita kauyan,inya so Dadan tayi mata Auren.Shiru yayi yana sauraron Ammi,ace yarinya bataji gaba daya,kamar wadda akaiwa baki,magana taki shiga kunnan ta,nagaji wllh,cikin bacin rai Ammi ta gama magana.

"Bece Komai ba sàida yagama cin Abincin sa,haushi ne ya kara cikata,ganin tanai masa magana kamar bashi take gayawa ba.Mikewa yayi ya haura dakin Hamna,yadda zarni ya daki hancinsa yasa yayi saurin toshe hanci,yana Mamakin fitsari irin na Hamna.Dakin baja baja da kayanta,takawa yayi a hankali har bakin bed din,tsayawa yayi yana kallon yadda tabaje tana mun shari,kayan makarantar ne ajikinta bata cire ba.Daka mata duka yayi,azabure takai duka tayi tunanin Mima ce,caraf ya rike hannun yana watsa mata Harara,wata alkafura tai ta wuntsulo daga kan bed din.Yadda yake kallon ta kadai ya isa ya sanar da ita babu sauki ba sassauci.Kiyi wanka kiyi sallah ki sameni a part dina,juyawa yayi ya fice,ajiyar zuciya ta sauke.Da sauri ta afka toilet tai wanka tare da dauro Alwala,dadduma ta shimfida tai sallar azahar da La'asar.

"Saboda yadda cikinta ya duri ruwa kojin yunwa batayi,wasu riga da wando ta dakko ta saka sai hula data makale aka.Tagaban su Ammi ta wuce sai matsar hawaye take tunkan ta isa, Mima ce ta daga murya adawo lafiya,tana sakin dariyar mugunta,ko kallonta Hamna batai ba, murmushi Ammi tai tasan Sadauki shine maganin Hamna.Ahankali tashiga tana rarraba idanu,yana zaune akan sofa, Laptop ce akan cinyar sa daga gani wani aiki yake me muhimmanci.Gani Yaya,ko kadan be dago ya kalle ta ba,kneel down,dan Allah kallon daya dago yayi mata ne yasata saurin dukawa,daga hannayanta sama tai,sunkuyawa yayi yaci gaba da aikin sa,saidata kai 30mnt tana kneel down fuskarta tai kaca kaca da hawaye,kafafunta kamar zasu tsige saboda gajiya,sai haki take tana sheshshekar Kuka,stand up da sauri ta mike,amma tsayuwar ta gagare ta,komawa tai ta kwanta plat tana haki,yana kallon ta duk abinda take yi.

"Fita gaba daya fulawowin Gidannan ki zuba musu ruwa,mikewa tai kamar wata yar kaciya haka take tafiya sai tangadi takeyi.Bakin pampo ta karasa mesa ta zira abkin pampon ta data aikin daya sata,sai data zagaye Gidannan tana aikin tana kuka shabe shabe,su Bilki da Sumayya sai dariya suke sheka mata,koda wasa bata kalle su ba taci gaba da aikinta zata juyo kansu suma."Sài data gama tukunna ta koma part dinnasa,nagama yaya tafada gwanin ban tausayi,dago da kansa yayi yana kallon ta, marairaicewa tai saboda yaji tausayin ta,murmushin gefen baki ya saki,zonan,da rarrafe ta karaso inda yake,rasama abunda zai ce mata yayi gaba daya Hamna batajin fada da nasiha.Nasan abunda zai dace dake, boarding school zan kaiki anan na tabbatar zakiyi hankali.Kuka ta fashe dashi dan Allah Yaya kayi hakuri kar akaini,banza yayi yana kallonta.Nagama magana tashi kiban waje.

"Mikewatai ta fice tana gursheken kuka,kan cinyar Ammi ta fada,bata tambayeta Meyasa ta kuka ba,saidatai me isarta kafin ta sarara.Ammi kiba Yaya hakuri ni banasan boarding school, Murmushi Ammi ta saki,aini wllh da zai kaiki ma danafi kowa jindadi ko zakiyi hankali kafin ki dawo,sake barkewa tai da Kuka,ni Ammi bazanje ba,aiko saikin je,kinsan yayanku magana daya yakeyi,babu makawa sai kinyi boarding school gwarama kisawa ranki salama.Mikewa tai ta nufi part din Mammah,da Najma taci karo tana kokarin fita daga part din,Meyasa sameke Hamna?wai Yayah ne zai kaini.boarding ni banzan jeba,au ashe keda Yayah Sadauki ne,bazan shiga wannan fadan ba yafi karfi na,sakinta tayi ta fice daga part din,gaba Hamna tai ta fada parlour lokacin Mammah na zaune ita da Khairta.Subahanallahi kukamme kike Hamna, Mammah ta furta tana mika mata hannu,Yayah ne zai kaini boarding, boarding kuma,Mammah ta maimaita,kodai kinyi halinne,kinsan yayanki yayi miki warning in aka aka sake koroki zai dauki mataki,nadaina Mammah,kinyi laifin kenan.Ni yanzu bani data cewa tun asali laifinki ne Hamna,saunawa ina zaunar dake inai miki jan kunne amma kika ki ji,yanzu saiki rungumi kaddara acan dai kikai wasa zane ki zasu yi.

"Khairat ce ta dafa kafadar Hamna,kiyi hakuri sis duk lefinki ne,saunawa anai miki kashedi amma kinki ji,yanzu dan Allah wa gari ya waya gashi sai Kuka kike za'a kaiki boarding school.Nadaina Anty Khairy,dariya Khairat tayi sabon salo,lallai Hamna baki son Boarding yau ni ake cwa Anty, Murmushi Mammah tai nima naga alama ai.Amma kici gaba da Addu'a Allah yasa Yayah ya canza shawara,Ameen ta amsa tana goge hawayan fuskarta."Big Dady yana dawowa ta kara kai karar Sadauki,dariya yayi mamana wannan ai duk lefinki ne,amma zan bashi hakuri ko Allah zaisa ya hakura,matukar zanyi hakan saidai da sharadi,zanyi Big Dady sharadimme ne?sai kin daina rashin ji,doke doke,fitsarin kwance,rashin kunya,matukar kika daina wadannan ni nasan yadda zan bullowa yayanki ya janye maganar sa,shiru ta danyi tana nazari,in baki yadda ba tashi ki tafiyar ki, a'ah na yadda Dady, Murmushi ya saki to yanzu harkallah a fada,amma.innaga sabanin haka bake ba zama agidannan saikin nufi boarding school.

"Cikin Farin ciki' ta baro part din Mammah sai sakin Murmushi takeyi,cin karo tai da mutum gaba tai zata fadi Allah ya taimaketa bata fadi ba,dagowa tai dan ganin dan rainin wayon da yayi mata haka,Khalid ta gani tsaye yana kallonta Kamar yaga kashi,turbine face tai tare da tsuke dan karamin bakinta,yadda ta tsani kutuwar ta haka ta tsani yaran Mom Jamila.Mahaukaciyar ina ce ke zaki bige ni kina tafiyar,ko dan uwar ki bata koya miki tarbiyya ba,cikin bacin rai ta watsa masa harara,uwar ka dai,ita ce wadda bata koyama Abun Arziki ba gata can adaka,wanda ya sha nonon tsiya kawai,waro idanun sa yayi yana Kallon ta,ke dan Uwarki ni sa'an kine,badai uwata ba ta fada tare da murguda masa baki,daga hannu yayi zai kashe ta da mari,karka fara yaji muryar Saidauki ta daki dodon kunnan sa.Dagowa yayi idanun sa jajir yana kallon Sadauki,kallon kai awa yake masa.

"Tsakanin Khalid da Sadauki babu wani yawa shekarar Sadauki 30 cif shekarun Khalid 28,Yusuf shekarun sa 26 dama su ukune manya maza agidan,zaka tare mata ne,kai awa zakace karna dake ta,ke ya nuna Hamna da yatsa,saina babballaki wllh,sainayi miki illah ki kiyayi haduwa ta dake next time."Ko kadan maganar bata shiga kanta ba balle harta dame ta,amma maganar ta tsayawa Sadauki matuka a kahon zuciya,sai maimaita sainayi miki illah yake a ransa,jin Abun zai damesa ya watsar badan ya manta dashi gaba daya ba.Hannun ta yakama sukabar Khalid atsaye yana hura hanci,sosai yake jin tsanar Sadauki a zuciyar sa,Kamar yadda Mom ta samu nasarar cusawa 'ya'yanta kiyayyar 'yan uwan su.Musaddik ne kawai ya fita zakkah shine har yanzu ya gaza daukar hudubar Mom na cewa iyayan su maza sun fi san sauran 'ya'yan su akan su,kuma karin bakin cikin ta,sunfi 'ya'yan ta kyau,musamman Khalid da take kwatanta masa shida Sadauki kisan kansu daya amma shine mefada aji agidan,sabanin shi dako zancan sa ba'a yi,hatta da Mahaifin za papi yafi nuna kaunarsa akan Sadauki,wannan ne ya hadu ya kara rura wutar kiyayyar Sadauki azuciyar sa.Cizon yatsa yayi ganin sun tafi sunbar shi atsaye kamar wani tababbe.Girgiza kansa yayi yana cije lebe.

 Tofa Lallai akwai kura,amma Mom bakiyiwa kanki adalci ba,kin gurbata tunanin yaranki da hannun ki.Dukkan Uwar da take da burin munana wani a idan 'ya'yan ta,to tasani kanta take dabawa wuka,tabbas ita ma bazata ga da kyau ba.Allah yasa mufi karfin zuciyar mu.

      Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
           .......✍️✍️✍️✍️✍️

        'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

 *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 19_20

"Ransa bace ya fada part din su, Mom dake,zaune tana kallo ita kadai ce,'yammatan ta nacan kowacce na makale da waya tana hira da saurayi."Yadda yake huci yasa ta dora dukkan nutsuwar ta akansa,ya akai Khalid?wa yabata maka rai haka?ajere take jeho mai tambaya,ko kallon ta beba ya samu waje ya zauna,zuciyar sa ajagule yake ya mutsa sumar kansa daya tara ta him kamar gammo.Dafa kafadar sa tayi kasa hankalina yatashi son ka sanar dani matsalar ka.Tsaki ya danja yana zukar Numfashi,nidai wancan banzanne,tunda ya fadi haka ta gane dawa yake,menene ya hadaku haka,harni zai hana na daki waccan kwailar Yarinyar,taimin rashin kunya zan hukuntata ya hanani,wai akan Hamna kake magana,aini na dade da.gane cewar san wannan me kama da balbelar yake yi,tsaiyayi da ransa yana kallon ta,kin tabbata Mom abunda kike fada hakane,kwarai kuwa na tabbata."Wani murmushi ya saki wanda shikadai yasan ma'anar sa,na gano ta hanyar da zan kuntata masa fiye da yadda yake tsammani,sainasa zuciyar sa ta buga ta daina aiki gaba daya,taci gaba da.kiwatata sannu ahankali.

"Mikewa yayi yana kallon Mom,part dinsa ya nufa da yake bangaran Mom din,binsa tai da kallo tana tunanin maganar sa,ganin zata batawa kanta Lokaci ta watsar da.maganar taci gaba da kallon ta,koma menene su shawo ta acan,ta dade da sànin Khalid baya daukar rainin hankali,in akai masa saiya maida martani,shiyasa yake masifar birgeta,take kuma Alfahari dashi."Part dinsa ya wuce da ita kafin su zauna a sofa,Hamna mene matsalar ki, school din ce bakya so ko yaya?shiru tai tana rattaba idanu, Girgiza kai tayi alamar à'ah,rankwashi yayi mata atsakiyar ka,bude baki kimin magana,ina so yaya ta fada cikin kuka,ko yaushe Hamna ta zama raguwa oho,amma yanzumma ba mamaki kukan karta take yi."Amma kika ki yadda ki zauna da kowa lpy.Wannan shine Last warning kinsan Allah nakara camza miki day baki zauna ba, boarding zan kaiki,ko na kaiki can gidan rainon yara mara sa jin magana irin ki,na yadda Yayah bazan kuma ba Allah,tsaki yaja kima sake.

"Fitowa tai tana washe baki,jin ya hakura zai barta bazai kaita boarding school ba.Harzata wuce tajiyo ana kus kus a wani dan lungu,Kamar muryar Mom take jiyowa, Ahankali ta sadada ta makale,Dariyar Mom tajiyo tana fadin,ai Hajiya Zaituna tuni na dauki takaddun nan na boye, original da dauki na barshi da photo copy,kuma yun duniya hardani za'a dinga neman su."Ai kimmin dabara,gobe sassafe zanzo na kawo miki ta kaddun asan yadda za'a yi,ki adana mum su Lokacin amfanin su yana nan zuwa,sai nagama tatike shi tas tukunna zance ya salleme ni,af karkiji komai,nicefa Jamila gagara badau,ai akan takaddun nan har wajan malam zamuje arufe bakinsa ruf,ta yadda bazai taba bude baki ya gayawa kowa ya nemesu ya rasa ba.

Jin zata juyo yasa Hamna saurin buya tana sakin ajiyar zuciya,yatsa ta ciza,aiko yasin nima saina sace ta kaddun nan,gwara kowa ya rasa,badai takaddun school din wani zaki boye ba,nima zan dauka na boye.Ganin tayi part din papi ya tabbatar mata bazata dawo part dinta ba,da sauri ta nufi part din Mom din,part din dako kadan be taba bata sha'awa ba,ahankali ta tura kofar jinta abude yasa tai ajiyar zuciya,dakunan su Bilki ta kalla duk suna ciki sun kulle dakunan su.Taking steps tafarayi cikin taka tsantsan, bedroom din Mom ta fada tana zare idanu,sai hada gumi takeyi bata saba ba,jitake kamar sata zatai anya zata zama barauniya akan wasu takaddun banza ma."Kamar zata fita saidai wata Zuciya tace gwara ki dauka ko dan ki kuntatawa Mom.

"Dube dube ta fara yi"sai data shafe mintuna 10 bataga komai ba,har zata hakura ta fito ta tuna bata daga katifa ba,kamar dole haka ta fara kici kici da katifar Mom,da kyar ta samu ta daga sai haki take tana hada gumi,tana dagawa ko saiga takaddu a kasan katifar,da sauri ta dakko su ta ajiye agefe,maida katifar tai ta mayar,gyara bed din tayi kamar yadda ta gashi."Fitowa tai cikin farin ciki harzata wuce dakin ta,saitai tunanin bari ta kaiwa Sadauki ya boye mata,saita bawa Mom wahala sannan zata bata kayanta."Yana bedroom din sa,kwanciyar sa kenan kusan 12 na dare kowa ya kwanta banda Hamna.Hango shi da tai akan bed tayi wajansa da paper a hannu,tunda ka shigo yaji motsi ya buds idanun sa dan ganin wanda zai shigo mai part d daddaren nan."Sosai yayi mamakin ganin ta kamar wata aljana,kan bed din tahau tana jan blanket din daya rufe jikin sa,ganin tana neman yimai tsirara yayi saurin rike blanket din,daga shi sai boxer ajikin sa.

"Kwanciya tai akan kirjinsa tana dariya,Yayah boyemin takaddun nan adakin Mom na dakko su,ita ma yaya bana ta bane shine nima na dauke saina bata wahala zan bata kayanta,mikewa yayi da ita ajikinsa tana jan tsaki,kincika matsala Hamna me zanyi da wasu takaddu adarennan,dan Allah Yayah ka ajiyemin karka ce àah,har bazai karba ba,saidai ya karba,idanun sa yakai kan paper din,sàida yaji wani shork ganin Abunda suka kunsa,kagani ko Yayah,jinai tana waya zata kai ajiya shiyasa nace aiko saina bata wahala kafin nabata,shiru yayi yana kallon ta,gaba daya batasan mene ajikin takaddun ba,tayi hakanne dan tsokana da neman masifa,amma hakan datai ya zame musu Alkhairi.

"Numfashi ya sauke,tare da dai daita Fuskar sa dan karta gano wani abu,murmushin karfin hali ya saki,kin kyauta amma karki sake babu kyau daukar abunda ba naka ba,ai Yayah ba abinci na dauka ba,takadda ce fa,kuma ita ma bakaga satar su tayi ba?bece mata komai ba,ok karki fadawa kowa kin dakko kinban ajiya,sanda naga ya dace na baki kimayar zan fada miki.To Yayah.Oya tashi kije ki kwanta,zan kwanan anan,harara ya watsa mata,Allah ya tsaren kizo kimin fitsari tashi ki fita,zumbura baki tai ta sauka akan bed din,sàida safe,fita tai da dan gudunta,Numfashi ya zuka ya fesar,sauka yayi ya bude jakar da yake sa laptop dinsa ya zura takaddun aciki."Sosai mamakin Mom ya kamashi,me take shirinyiwa papi?zata kashe shi taci dukiyar sa ko yaya take nufi.Ya jima yana kwancewa da sakawa,gaba daya kansa ya dauki charge sosai abun ya tsaya masa azuciya.

"Washe gari sai kusan karfe 9 tatashi"brush tai ta zura doguwar riga ta atamfa,Sanda ta fito maine parlour babu kowa,ranar weekend ce babu tashin wuri.Part din Mom ta nufa tana saka muguntar da zatai mata,harta gota kiching tadawo da baya,leda ta dakko ta zuba yaji da Uban gishiri,kullewa tai ta damke a hannun ta.Mom da yunwa ta korota tana kiching tana hada tea,cup din tea din sai tururi yakeyi,tunowa da tabar wayar ta a sama yasata Fitowa da sassarfa ta haura sama,da sauri Hamna dake labe ta fito ta afka kiching din,gishiri da yajin gaba daya ta antaya mata aciki,teadin daya sha hadin kauri saiga shi ya canza kala,da sauri ta fita daga part din tana Dariyar muguntar,koda Mom ta dawo sam bata kalli cikin cup din ba,samun waje tai ta zauna aka sofa,kai cup din baki ta tai,wata muguwar zuka taimasa yadda zaifi dira acikin ta da gaggawa,hankali tashe ta furzo da wanda ta dura abkinta,saidai ina yariga ya tafi wulli tai da cup din tea din tare da wayar hannun,dafe kirji tai jin yadda yajin yake haurawa har can cikin kirjinta,kanta harya fara sarawa,dan danan idanun Mom suka sake yowa waje,dama abunka da tubarkalla tana da manyan idanu,kai kanka babba idanunta firgita ka suke balle yara.

"Yara ansha zuwa dasu Gidan da sunyi arba da Mom zasu canyare da kuka,idanun ta ke razana su,gani suke kamar idanun zasu fado."Dama gata da ulcer sai ciwon kirjin ya taazzzara,wurga idanu tayi babu kowa akusa balle ya agaza mata,Hamna dake makale tana Dariyar mugunta,da gorar ruwa tashigo a hannun ta me shegen sanyi, Mom na hangota ta dinga yimata nuni ta bata ruwan,Dariya Hamna ta dingayi tana zagaye Mom tana zubda ruwan akasa,ai wllh Jamila saidai ki mutu Indai nice zan baki ruwa, murgudawa Mom baki tai,wadda batama san tanayi ba,jin za'a fito yasata shekawa da gudu tabar part din."Sumayya ce ta sakko daga ita sai wani sket iya guiwa,sai yamutsa fuska take kamar kashi,hango Mom yashe akasa ya sata tahowa da sauri,idanun Mom data kalla sàida tai saurin kauda kanta,sunyi jajawur kamar gauta,tama kasa magana tsabar wahala.Bilkisu kufito Mom da gudu suka fito khaled da Musaddik har suna bugun juna,sosai abun ya daure musu kai ganin Lafiya kalau suka ganta dazu."Bari na kunna mota kuyi sauri ku kamota,da sauri ya fice,da sauri suka hadu suka ciccibeta suka mikar da ita.

"Hijab suka zira mata suka kakkamota suna faman nishi,da kyar suka sakata amota,babu wanda suka fadawa ganin halin da take ciki, Hospital din da Sadauki ke aiki suka kaita,da gaggawa suka karbe ta,wata allura sukai mata wadda zata rage mata radadin dake damun ta.Papi suka kira suka sanar masa,sosai yayi musu fada da basu sanar da kowa ba."Su Ammi dan danan suka hallara a hospital din anaiwa Mom bya jiki,wadda ta sami kanta da kyar,abunda Hamna tai mata yana zane a zuciyar ta,saita ci Uban Hamna wllh,abunda take ayyanawa kenan aranta.

Yamma Lis aka sallami Mom,abunda ya bata bakin ciki ko saudaya Sadauki be shigo dan suba ta ba,duk da yana cikin asibitin,kin yadda yayi ma ya zauna a office dinsa,yasan Ammi saita tisa shi agaba yaje ya duba jikin Mom din.....

🤣🤣🤣Mom ya da farawa a gadon Asibiti,muje zuwa.


       'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

 *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 21_22

"Sanda suka dawo Hamna na can tana buga boll ida da Munib,babu abunda ya dame su sai wasan su suke yi.Ammi ce ta kwalla mata kira,da gudu ta tataho da boll din ahannun ta,kitson da akai mata doka sunyi mata matukar kyau,manya akai mata,wasu sunyo gaba wasu sunyo baya,saita koma fillon ta sak.Kayan boll ne ajikin ta, yellow and black.Me kikeyi haka Hamna,ga mom dinku bata da lafiya ke kina can kina wasa,ya mutsa face tai wace Mom din ce bata da lafiya,Mammah kike nufi ko ke,rankwashi Ammi takai mata,zakice baki gane wadda nake magana akai bane,kusan haka Ammi,girgiza kai Ammi tai Allah ya shiryeki Hamna,Ameen Ammi,aini in bake ko Mammah ba bani da wata mama agidannan.Kuma Ammi ni kidena ma hadani da ita waccan bazan iya nunata matsayin uwata ba,bakiga idanun taba kamar na mayu,da sauri Ammi ta toshe mata baki tana kallon bayan ta,ganin babu wanda ya yajita tasaki ajiyar zuciya.Hannun ta ta fizga sukai part din su,har cikin bedroom Ammi ta shiga da ita kafin ta sake ta.

"Hamna bakyason na zauna Lafiya ko?kinsan kalmar maita kuwa,akan wanann kalmar tsaf zaki iya tafiya prison dan haka ki iya bakin ki.Wallahi ki iya bakinki na gaya miki,hannun ta yana hannu Ammi ta murde ta karasa yi mata fada,hawayan azaba take sharewa kamar Ammi zata tsige mata kunne.Cikin kulata fara magana,ni wllh Ammi bana sonta na tsane ta, Innalillahi, Ammi ta dafe kai tana kallon Hamna,nashige su yanzu Hamna bazaki gyara kalaman ki ba,to zan hadaki da Yayan ki shine zai gyara miki zama agidannan kinfi karfina Hamna,kuma yanzu kije kiyi mata yaji ki.Shiru Hamna tai tana matsar kwallah ko bakiji ni ba,fuuu ta fice ita fa wllh bata son Mom gaba daya har 'ya'yan ta bata so, Musaddik kadai take so acikin yayan ta.Suna zaune a parlo sanda ta shiga.Fuska aturbune ta tsaya akan su,sannu ya jiki tafada tana kallon Mom da take mata wani kallo data kasa fassara shi."Ban sani ba,zuwa kikai kiga ko na mutu kici gumba ko,tabe baki tai da kin mutu aida tuni labarin mutuwar ki ya isa kunnena."Yanzu ma baasan raina nazo duba ki ba,Ammi nace ta sakani,kinsan nikuma ammin tarbiyya in aka fadamin ina ji,sabanin wasu da ba'a isa asa su suyi ba.

"Zaburowa Bilkisu tai,ke dan Uwar ki wanene sa'anki anan,ah dama babu sàa na Acikin ku,abi wani sarkin,in ko har kikai tabani zakiyi nadamar tabani wllh,karasa fadatai tana sakin murmushin mugunta.Sauda ce ta mike Allah Mom kibarnin na tattaka Yarinyar nan,kyaleta Mom ta furta tana kallon Hamna,fitar min daga part ko nasa si miki lugudan duka,kodai mudaki juna ba,ta fada tana murguda baki,ficewa tai tana raira waka, zuciyarta fes tana da tabbacin Mom batai lura da bacewar takaddun taba."Sumayya da haushin Hamna ya kamata matuka tai kwafa,ni wllh Mom bana son yarinyar nan gaba daya,Mudaddik da yake jin su da Mamaki ya kalle ta, akamme bakya sonta,hassada na lura kukewa yarinyar nan kamar wata saar ku,shiyasa gaba daya tabi ta rainaku.To uban shishshigi cewar Bilki,wai kodai san yarinyar nan kake bamu sani ba,waya sani imma sannata nakeyi ko zaki hana ne,aiko wllh baka isa ba cewar Sumayya da take dankara masa harara, murmushi ya saki yana kallon su, Lallai baku da aikinyi,na kara tabbatar da Hassada tana daf dasa Zuciyar ku ta buga,akan wadda bata damu daku ba.

"Mom ce ta nuna masa hanyar fita,tashin ka fita Musaddik tun kafin ranka yayi mummunar baci,Mikewa yayi Allah y baki hakuri Mom nidai gaskiya nake fada muku,karike gaskiyar ka bana bukata.Bece komai ba ya fice suka bishi da harara.Mom Mikewa tai tabar wajan,ita kadai tasan yadda take jin tsanar Hamna,ta so am barta acan kauye,amma wancan munafukin ya dakko ta."Kai tsaye part din Mammah Hamna ta nufa,su Basma da Najma suna zaune kusa da Mammah,oh Hamna shine bakije hospital duba Mom ba,tabe baki tai tana kallon Najma,inje in duba wa,ai wllh Anty Najma ko mutuwa tai sai dai nace Allah ya jikanta amma bazanyi asarar hawaye na ba,dakuwa Mammah tai mata,ungo wannàn Hamna,banace kidaina nuna kina kin Jamila ba."To ai Mammah ita ma bata sona,gidanku bana so nakarajin wannàn Maganar abakinki.

"Shiru Hamna tai tana turo baki"nifa Mammah banga laifinta ba,Allah haka kawai nima bana kaunar Mom dinnam ni tsoroma take ban,narasa me papa ya gani ajikinta ya kwaso mana ita.Duka Mammah ta kawowa Najma datake kora jawabi,bari inya dawo sai kije ki tambaye shi,dariya suka saka gaba daya.Hamna ce ta fada kan cinyar Najma yawwa Anty Najma naji dadi da kikace baki son ta kema, murmushi Najma ta saki,cigaba aikai da hirar su suna biyewa shirman Hamna,labarin kt take basu,yadda tadinga tsokanar mutane sai dariya suke shekawa."Kamshin turaransa ne ya farayi musu sallama dan danan suka nutsu kamar basu ba,Hamna harda sunkuyar dakai tana kif kifta idanu.Idanun sa ne ya fada kanta, tabe baki yayi kalleta kamar wata mutuniyar arziki.Yayah barka da dawowa suka hada baki wajan furtawa,yauwa ya amsa daga haka ya tsuke bakin sa.

Kusa da Mammah ya zauna yana sauke numfashi,kallon sa tayi da murmushi a face dinta,uhm da alama kagaji da yawa, murmushi yadan saki yana gyada mata kai,zurum Hamna ta mike hannun sa ta rike Yayah xomuje na hadama ruwan wanka, kallon ta yayi kaji yarinya waita hada masa ruwan wanka,su Khairat kunshe dariya sukai ganin kallon da yake watsawa Hamna,ba shiri ta sakar masa hannu tana rarraba idanu, Mammah ko nayi laifi ne, àah bakiyi ba Hamna maxa kije ki hada masa ai aikin lada zakiyi,baki ta washe tare da ficewa da sauri."Haba Mammah kin samfa Hamna ba hankali ne da ita ba,barna zataje taimin,to banda abunka ai Ahaka zata koya,shiru yayi bece komai ba.

"Hamna kuwa ranta fes ta fada bedroom din sa,sai data karewa room din kallo kafin ta fada toilet, bathtub din tagani acike da ruwa fari kal sai daukar idanu yakeyi,jitai kamai tana sha'awar shiga,ko cire kayanta bataiba ta dunbula cike,sanyin ruwan sosai yake ratsata,saboda yanayin zafi da akeyi,kwanciyatai aciki tana kyalkyala dariya,sam batasan da shigowar saba ta shagala da wasa da ruwa,kallon ta yake zako kici Ubanki,abunda kika zoyi kenan,hannu daya yasa ya figo ta kafin ya dire ta akan kafafunta,tuni ta fara zare idanu tana kif kifta ido,abunda kika zo yi kenan,dama ni nasan badan Allah kikace zaki hadan ruwan wanka ba,rankwashi ya kawo mata,kazama me tsarin kwance ki shigarmin bathtub,oya zubar da ruwan ciki ki wanken shi fes,na baki mintina 3,matse hawaye ta fara,ko bazaki yi ba,da sauri taja baya zanyi yaya karma kiyi.Fita yayi yabarta aciki,haka ta zubar da ruwan ciki ta wanke masa tas,tsayuwa tai tana tunanin yadda zata fito da jikakkun kayannan nan ma yayi mata masifa,cire kayan tai da dakko towel ta daura,gashin kanta da Ammi ta gama shan wuyar gyaransa dazu gaba daya ta tuje shi.

"Kanta asunkuye ta fito"yana zaune yana shan coffee,tsayawa tai tana satar kallon sa, murmushi ta saki ya zama dole Yayah Sadauki yasan wacece ita,dan wllh saita shirya masa mugunta, murmushin da takeyi ne yaja hankalin sa,nazarinta yayi tabbas akwai Abunda take sakawa azuciyar ta,bece mata komai ba ya tashi ya fada toilet,in yatsaya kula tama ya batawa kansa time.Kallon dakin take yi sako da lungu,wani 'yar akwati data hango ta leko ta kasan bed ta sunkuya ta dakko,kiciniyar budewa tahauyi,samu tai ta bude wasu yari da sarka ta gani na Gold masu azabar kyau,sai walwali sukeyi da sheki,sai wasu zubuna guda biyu wadanda ta rasa ma'anar abunda aka rubuta ajikin su.Akan mirror ta daura akwatin sarkar,sarkar tabdakko tana washe baki ta saka awuyan ta,dai yari data makala,sosai tayi mata kyau,awarwaron ta dakko ta saka sai gashi ya fado da kansa saboda yayi mata yawa,haka zobunan data gani summata yawa.

"Jujjuyawa take agaban mirror tana kallon kanta,sai murmushi take saki,Allah yasa Yayah Sadauki ita ya siyowa sarkar nan,karar bude kofar dataji yasata juyowa tana sakin murmushi,sam yamanta ma tana dakin ya fito daure da towel a kugunsa,da dan gudunta taje ta fada jikin sa,saidaya razana gaba daya ya manta ita,kara kankame sa tayi tana dariya,Yayah naga sarkar daka siyomin tayi kyau sosai,rasa Inda maganar ta ta dosa yayi,tashi tayi tana nuna masa wuyanta kaga yaya dana saka tamin kyau,kallon ta yake daga sama har kasa,gishinsa ya dafe wai Hamna wace irin yarinya ce ita.Ke nace na siyowa da kika dauka kika saka,ai Yayah nasan ba wanda zaka siyowa saini,kaji yarinya ya fada azuciyar sa,to bake na siyowa ba,wanann ta wife dina ce,dan haka maza ciromin tunkan ki shafa mata dauda,kwabe face tai dan Allah Yayah,shishsh ya dora hannun sa akan bakin sa,bakiga ta manya bace ko kece wife din tawa,da sauri ta daga kai nice Yayah Allah zan zama wife din nima saika barmin kaga,'yar dariya ya saki ganin da gske saita zama wife din dandai kawai ya barmata sarka,batasan mene ma'anar wife din ba amma ta dage saita zama.

"Ok naji amma ai aikin wife ke bakya yinsa gaba daya,mene aikin Yayah daga yau zan dingayi,zuwa gaidani da safe,kawo min breakfast da bani abaki,yimin shara da mopping ako wane Lokaci,gudun bacin raina duk kankantar sa,kawo min coffee kowane dare,ina har zakimin haka to kin zama wife dita.Kai Yayah ashe aikin ma ba wahala,duka zan dingayi maka,amma zaka barmin sarkar,ba yanzu ba saikin girma kizo zan baki hannu da hannu, murmushi ta saki har dimpul dinta na lobawa,nayadda  Yayah,to yanzu coromin kayana,babu musu ta curo ta mika masa ya karba.Jan hannun ta yayi suka shiga bedroom din da kayanta suke,wata jar yar kanti ya saka mata,har powder ya shafa mata,gwara a ramawa kura aniyar ta,tunda zaki dingamin hidima yanzu munzama friend murmushi ta saki,eh Yayah munzama,hannu ta kawo mukullah,kullawa sukai sun zama abokai,saidaya gyarata tsaf,sweet ya dakko ya bata,maza kije kiyi wasan ki,fita tai tana Nishadin ta.

"Jikin Ammi ta fada tana sakin dariya"kallon ta Ammi tai kekuma wadannan kayan daga ina,Yayah Sadauki ne ya sakamin, murmushi Ammi tai daga can kike kenan,eh Ammi yace na zama Wife din sa,shiru Ammi tai tana sauraron maganar ta,jin gaba daya shirme ne yasa tace,to Allah ya tayaki ruko tunda kun zama friend ai shikenan,gyada kai tayi,amma Ammi yace sena girma zai bani sarkar da nazama Wife din,Allah y kaimu Ammi ta fada Hamna bata gajiya da surutu kamar aku.

               Mrs Baba Bello Abubakar

  ......✍️✍️✍️✍️✍️


                    'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

 *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 23_24


"Kwana biyu da dawowar Mom ta warke garau,yau kuma ta shirya zuwa Gidan Zaituna dan kai ajiyar ta,kwalliya ta dauka kamar ba Matar Aure ba,matar Auran ma me shirin Aurar da 'ya'ya.Makullin motarta ta dakko ta daga katifarta,takaddun suna nan yadda ta ajiye su,ajiyar zuciya ta sauke tana sakin murmushi,sai data dauka ta tabbatar da sune ta,bude hand bag dinta tayi tayi musu kyakykyawar ajiya.(Saidai na zaro idanu Ganin takaddun to ya akai haka,kodai Hamna ba takaddun ta dakko ba dama)"Taking steps ta fara tana karkada mukullan motar ta,idanu suka hada da Sadauki,sàida gabanta ya fadi,amma da yake cikakkiyar yar duniya ce saita maze,kakaro murmushi tai a'ah Babban yaya yau kaine a part din Mom dinka,wani murmushi ya saki wanda shi kadai yasan ma'anar sa,nine Mom canai bari na shigo na gaishe ki da jiki,sanda Kuka je hospital din mu bana kusa shiyasa baki ganni nazo ba."Murmushin jindadi ta saki,hanya mafi sauki ta samu,yanzu ne zata jashi ajiki yadda zata cutar dashi ba tare da kowa ya farga ba,Allah sarki aiko ka kyauta son.Sauda ta kwalawa kira,tsawon mintuna biyu sanann ta sakko,Sauda sa'ar Mima da Khairat ce,bazasu wuce 14years ba."Rashin kunya take niyyar yi suka hada idanu da Sadauki,da sauri ta gyara bakin ta tana susar kai,Yayah Sadauki ina wuni,lpy ya amsa batare daya kalle taba,ki kawo masa ruwa,no mom zan makara,zanje wajan Munir ne dama,mikewa yayi saina dawo Mom,to Allah ya tsare hanya,yana ficewa ta bishi da harara tare dayin kwafa alamar zamu gauraya.

"Yana fita ya fada motar sa,ko jiran driver be tsaya yi ba,yafi ganewa yayi driving da kansa,yana tafe yana sauraron karatun Alkur'ani."Bejima da fitaba Mom ta fito ana taku dai dai,driver ne yake janta,har kofar gidan Hajiya Zituna ya kaita,hon ya danna get man ya wangale musu get suka kutsa kai,fita tai batare da tace da Habu direba komai ba,ko kallo be isheta ba dama.Hajiya Zaituna na zaune hakimce a katafaran parlourn ta, murmushi ta saki Ganin Mom tana shigowa parlourn,zama ta gyara,sannu da zuwa Aminiya,yawwa Aminiya Mom ta amsa suna sakarwa junan su murmushi.Zama Mom tai tana sauke numfashi,kinji wai Tafiyar nan danai harna gaji, Lallai Jamila an sangar ce,kamar bamu ke tallan goro ba,hannu taba Mom suka kashe,to ke wane yace damu bamu ba,tunda muka rantse sai munyi arziki ai sai munyi,ki bari kawai Zaitun gashi yanzu min taka matsayin da bama zato,shewa suka kara sawa kamar wasu yara."To ya ake ciki' andace ko yaya,kema kinjiki tun awaya na sanar dake andace,zuge bag tai ta fito da takaddun tana mikawa Zaitun,amsa tai tana jujjuyawa yes taiwa Mom jinjina.

"Nifa Jamila ina mamakin wannàn abu,duk wani abu da kikasa agabanki sai kinga kin kawar dashi,gaskiya ba karamar sa'a kike da ita ba, Mom sake maida dankwalinta tayi gaban goshi,wani dadi ke ratsata jin ana wasa ta ana yabon ta.Aikema Zaitun me sa'a ce,kalli fa wannàn katafaran gidan da kike ciki' kamar ba a Nigeria ba,ga miji a hannun ki,wai ina wanann 'Yar wahalar kishiyar taki,tsaki Zaitun taja tana nan sai yadda nai da ita,shiyasa kike birgeni,barima na kira "yan iskan nan su dakko miki Abun motsa baki,kinsan tuni na kori 'yan aikina suke komai Acikin gidannan suda uwar su."Ke Raudah Siyama,da sauri suka shigo parlourn har suna gware da junan su.Allah sarki kyawawan yara ne bazasu wuce 8yers ba da alama tweens ne kamar su daya,gamu Mom,a tsiya ce ta kalle su,wasu ko daddun kaya ne ajikin su,ko 'yan aikin Gidan sunfi karfin sa wadannan kayan balle su, munafukai sai ankira ku kudinga wani sunkuyar da kai kamar mutanan arziki,mena fada muku da nayi baki kuyi sauri ku kawo abunda ya kamata.

"Kiyi hakuri bamusan kinyi baki ba,suka fada cikin Kuka,ga wata azababbiyar yunwa da suke ji, Mom ce ta kalle su gaskiya yarannan ya kamata ki sassauta musu Zaitun tunda ni banga laifin su ba,da Uwar su kike kishi ba su ba,da alama ma yunwa suke ji,harara Zaitun ta watsa mata,kinga Jamila zamu samu matsala dake,yaushe imani ya sauka.a zuciyar ki,ah shawara fa na baki,da zaki adana su hakan yafi,amma tunda baki yadda ba shikenan.Wani hambari Zaitun ta kawo musu kitashi ku ficemin da gani,ni wllh kallon yarannan ma na tsaniyi,saboda bana kaunar su ko kadan,badan nasan hukuncin wanda ya kashe wani ba da yanzu nakai su bar zahu.

"Kirji Mom ta dafe ah to gaskiya Zaitun kin fara bani tsoro,mene na kawo maganar kisa,kibar wanann zancan dan Allah haka kawai ana zaune kalau,ke kika sani cewar Zaitun.Jujjuya takaddun hannun ta take,tana ayyana yadda zatai sama da fadi dasu,ba dake suka dace ba Jamila dani wannàn dukiyar ta dace,zan kumayi duk me yiwuwa danganin na mallake su((Lallai dara zata ci gida kenan,sata ta saci sata,to ke Mom saiki daura damarar kwatar kadarar da kika sato kema)).Amma azahiri murmushi Zaitun ta saki,yanzu bari na tashi na adana takaddun nan kinsan da zafi zafi akan bigi karfe,gaskiya ne 'yar Uwa,mikewa tai bari na haura sama,tashi tai tabar Mom tana karewa Gidan kallo.Hmm ai wllh papi yana mutuwa mijin Zaitun zan Aure,saina fiddake Zaitun na Aure Mijinki,dani wannan Gidan ya dace ba keba,🤣🤣Lallai kowa da burin da yaci akan dan uwan sa,Allah ya karemu da sharrin Zuciya.

"An canzawa Hamna school"ba laifi tadan rage fitina ba kamar daba"aikin da Saudaki ya nata kuwa ba kama hannun yaro tafara ririta shi kamar baby,ta bashi Abinci abaki,hatta gugar takalmi ita ce take masa,wanann sarka ta kwallafa rai akanta,shi abun nata ma dariya yake bashi ganin bilhakki aiki take da zuciya daya."Kullum saita tambaye shi Yayana ya batun sarkar zaice da sauran Lokaci."Tafiya ce tataso wadda Abbah zai wakilta kan harkar business dinsa,bazai samu zuwa har yayi 3years ko 4years ba,yana da iyali bazai iya nesa da Ammi ba,hakan yasa ya shirya musu tafiya Germany da Ammi Mima Hamna da Munib,sosai Ammi ke murna zata koma kusa da iyayan ta na wasu shekaru."Bangaran Sadauki gaba daya ya shiga damuwa,sosai Hamna ta sangar tashi ko yaushe yana zaune zatai masa abu,shan coffee tun ya daina wahalar da kansa,ita ke kawo masa.

"Abinci ma abaki take bashi tsabar sangarta,ya dinga zuba shagwaba kenan Hamna na lallaba shi."Yauma tana gabansa tana matsar hawaye,Yayana kazo mutafi tare karka canza Wife kafin na dawo kabata sarkar nan,shiru yayi yana kallon ta,ita ta sarka ma takeyi bashi zatai kewa ba,hade fuska yayi,ke ta sarkama kikeyi ba tani kikeyi ba ko,kenan bazakiyi missing dina ba,zanyi mana Yayah amma saina fi Missing sarka ta,kamar ya mangare ta dan haushi,ya yadda har yanzu Hamna bata da hankali,abunda yakeji akanta ita sam babu wannnan acikin kwakwalwar ta.Aiko zan baiwa wata sarkar tunda sarkar kadai kike so banda ni,da sauri ta zaro idanu,kwanciya tai ajikinsa,Allah Yayah ina sonka,sàida yaji maganar har tsakiyar kansa, Lumshe idanun sa yayi yana sakin murmushi,koda bada wata manufa ta fada ba hakan ya sanyaya ransa,yaji dadi matuka.

"Sake kankame shi tai"yaushe zakazo ka ganni in munje,ni bazan zoba,make kafada tai,um um nidai Yayah sai kazo, murmushi ya dan saki,to kimin alkawarin bazaki kula kowane Namiji ba,baki ta tura gaba,ni Yayah kaga ina kula namiji ne dama?hannun sa ya miko,kimin alkawarin kawai,naima.yayah bazan kula kowa ba, good girl.Hamna a halin yanzu shekarar ta 12 ta kara girma ba kamar baya ba,tsabar kyaune da ita kamar aljana."Harabar gidan ta fito ta hango Sumayya tana zance da wani saurayin ta dan kwalisa,yaci wanka sai karya kai yake kamar tarwada,dariya ta saki yanzu zan tarwatsa ku yasin.Tuno watai a duniya ba abunda Sumayya ke tsoro sai mage,part din Ammi ta wuce dama sune suke da mage,dakko ta tai ta boyota kar Ammi ta ganta,sadaf sadaf ta tataho babu wanda yaga tahowarta acikin su.Saidata saita magen ta tabbatar wajan su zata nufa ta cilla musu ita,bafa dira akan kowaba sai kanciyar Sumayya.

"Razana tai ta kwalla kara,dama.shima irin matsoratan samarinnan ne,tashi tai tana ihu,ga takalmin kafarta me shegen tsini,ita ma.magen kamar tasani ta makale a jikin Sumayya,gaba daya ta gigice ta kalmin ya gurde ta rim ta fadi bakinta ya bugu,amma sam bataji zafin faduwar ba,kamar zata shide take Kuka tana gudu,cin karo tai da bango karamar buguwa tai agoshi ba."Saurayin nata tuni ya ware bazai iya wannan tashin hankali ba,da rarrafe Sumayya tai hanyar part dinsu,yanayin yadda sket dinta ya matse ta ya hana ta gudu yadda ya kamata,gaba daya ta daddauje guiwa,Hamna tana biye da ita tana tikar dariya har kwanciya tai saboda tsabar dariya.

🤣🤣🤣🤣 Sumayya 'Yar Aro ta juyo gareki.

             Mrs Baba Bello Abubakar
                  .......✍️✍️✍️✍️


                  'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

 *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 25_26

"Mom data fito cikin sauri har tana tuntube"hango Hamna da mage a hannu tana cigaba dabin Sumayya,wadda gaba daya ta fita daga hayyacin ta ya fusatata,sam Hamna batai san da tahowar Mom ba tsulum ta ganta agabanta,daga hannu tai da niyyar marinta ta daka tsalle tai baya,wani dutse dake kusa da ita ya harde kafar Mom wajan yunkurin binta,ji kake rim ta fadi,tsabar azaba ce tasa ta kwalla kara,akan hannunta ta fada,ga aba ba kadan ba,sàida hannun nata yayi wani kas alamar ya samu wata gagarumar matsala,Hamna can nesa taje tana cigaba da dariya tana girgiza musu kugu,farin ciki fal ranta.

"Saurin rugawa part din su tai ta dakko karkashi,Dada ce ta kawo musu shi dan suyi miya,tsabar sauri a cup ta ambulashi ta zuba ruwa,tsallake Mom tayi wadda ta kasa tashi,kofar part din Mom ta nufa ta kwara karkashin a kofar parlourn,duk abunda takeyi Mom na kallanta,tsanar Hamna ta kara dira a Zuciyar ta.Sai data kammala aikinta tsaf ta dauke cup din ta boye,hannu ta dora aka ta runtuma ihu, wayyo Mom tafadi kuna ina,Bilki ce da Sàuda har gware suke wajan saukowa daga sama,ganin Mom bata parlon suka yo hanyar fitowa daga parlourn Inda sukejin kururuwar Hamna,shima Khalid dake dakin sa ya fito cikin sauri,akusan tare suka dora kafafun su akan karkashin,gaba daya sun rigada sun ajiye karfinsu,zuuuu sukaji sun tafi,hatta Khalid da yake Namiji kasa tasyuwa yayi,rim Bilkisu tayi mummunar faduwa saiga hakorinta daya ya fice fit,Sauda akan hannun ta tafada ba karamar azaba ce ta ziyar feta ba,Khalid kuwa kafarsa ce tai wata irin lankwashewa,sàida tayi wani kas,duk jarumtar sa sàida ya kwallah kara ta tsananin azaba.An rasa wanda zai tashi ya taimakawa wani acikin su,Hamna dake makale a bayan kofa sai tillikar dariya takeyi.

"Fitowa tai tana kyakyata dariya kamar mara hankali"binta sukai da kallo cikin mamaki,Allah sarki sannu iyalan hassada da bakin ciki,zanga wanda zai taimake ku yanzu,bana gaya muku ba'a shiga harkata akwana lafiya ba,wannan punishment din danai muku somin tabi ne,naso ace bazamu bar kasar nan ba da ina tabbatar muku saina canza muku kamanni,gayyar na ayya gayyar tsiya,gaku ga uwar ku babu me taimakon wani,ku zauna ahaka,so nake karaya da targadan da kukai sai sunyi tsami tukunna za asan daku azo a gyara muku."Khalid ta kalla ta yamutsa fuska,kai namafi tsanar ka akan kowa wllh,tunda bakason Yayana nima bana sonka na tsaneka, murguda masa baki tai,kalli kanka dan Iska dakai ma,wace ma zata Aure ka,dariya ta saka saina biyo dare nayima kwalkwal yasin.Kai bana tashi ina da ayyukan yi,'yayan Jamila aci gaba da hutawa,sai min sake haduwa,next time,idanu ta kanne musu ta dauki magen ta tai gaba."Tsantsar bacin raine ya bayyana afuskokin su gaba daya tattara abubuwan da zasu aikatawa Hamna sukeyi,saita gwammace batayi musu wannan muguntar ba, musamman Khalid daya fi.kowa daukar zafi,yana ayyana irin abunda zaiyiwa Hamna matukar ta shiga hannun sa,saiya wulakanta ta,saiya kassarata,sai yayi mata rugu rugu da rayuwar ta,zatasan shi dan halak ne ba shege ba,matukar nonon Mom yasha saiya dauki fansa akanta,ba ita kadai harda Sadauki,in ya tabata kamar ya taba shi ne.

"Sumayya Kuwa da kyar takai kanta daki,zubewa tai tana numfarfashi,ji take kamar har Lokacin magen tana jikin ta,jikinta in banda karkarwa babu abunda yake yi,tayi Kuka harta gaji,tun tana sa ran ganin su Mom harta fidda."Hajiya Zaitun ce tafito daga mota cikin takama,part din Mom ta nufa,dama in tazo ko kallo su Ammi basu isheta ba.Turus taja ta tsaya ganin Mom azube kamar kayan wanki,idanu sun yi jajir kamar gauta,nashiga uku Jamila me zangani haka,ina yaran duka barki azube kamar kayan wanki,da sauri tai hanyar parlon Mom tabita da kallo,yadda tashiga tana kwalla musu kira gaba daya bata lura dasu a yashe a qasa ba.Sai data ji santsi ya debe ta ta dawo hayyacin ta,ihu ta kwalla gaba daya ta tafi rim keyarta tai wata shegiyar buguwa,aijitai kamar kanta ya fice fit,gaba daya jitai duniya tana juya mata.Duk halin da suke ciki sàida ta basu dariya,sam ta kasa motsawa ga kugunta da yayi muguwar buguwa,yadda kasan zai balle haka take jin sa."Babu me temakon wani, Zaitun ta gama saddakarwa bazata kara moruwa ba ajalinta ne ya kawo ta,rushewa tai da kukan bakin ciki ganin bazata cika burinkan ta na duniya ba zata wuce kiya ma,saiga Zaitun ta fara kalmar shahada,anufin ta in mutuwa tazo ta mutu da imani.🤣🤣🤣tab lallai Zaitun kina da aiki.

"Najma ce ta shigo part din Mammah ta aiko ta wajan Mom,da sauri ta karasa gaban Mom ta duka, Innalillahi Mom meyasa meki haka,babu bakin magana in banda ido da take binta dashi,da gudu ta juya, Mammah na zaune ta fada parlourn ke lafiya,aiko Mammah ba lafiya, Mom nacan azube,tai riki ca kamar wata tirella,dakuwa Mammah tai mata,da sauri suka fita,halin da sukaga Mom ba karamin tsoro ya basu ba,kwalkwal su Sumayya kira suka hauyi shiru,hanyar parlon sukai da Mom bayan sun ciccibeta da kyar,ja sukai suka tsaya hango wasu yashe akasa,ke jeki kira Ammin ku,da sauri Basma taje takira Ammi,tare suka taho Mima da Hamna,dariya kamar zata kashe Hamna.

"Amma da yake Hamna shedaniya ce"a gaban su ta duka, Innalillahi meya sameku haka,kamar wadanda sukai hatsari ajirgin sama,karasa fade tai tana kashe musu ido batare da kowa ya lura ba sai sukadai.Tsabar tsanarta take hangowa acikin idanun su,gaban Khalid ta matsa kamar me abun arziki,tana sane da karsa daya fada akanta,cikin mugunta ta jawo kafar,wata kara ya kwalla jiyayi azaba har cikin kwakwalwar sa,dai dai kunnan sa ta matsar da bakin ta,kadauka nidin ta wasa ce ko,duk wanda ya hana na zauna Lafiya wllh shima bazai zauna ba,in sha Allah ma sai ayanke shegiyar kafar nan taka,sainaga dame zakai yawon,dama na dade da gano kai dan iskane,har bin mata kake awaje,kaga in aka yanke ma kafa ai bazasu kula ka,Khalid gurgu za'a na kiranka,dariya ta fashe da ita hangosa yana cangala kafa,gaba daya kallon ta sukai cikin mamakin dariyarta.

"Amma da suka tuna wacece Hamna"dama ba hankali ta cika ba sai suka juya basu wani maida abun serious ba.Tsantsar bacin rai Khalid ya kara riskar kansa aciki"da ace ba mutane awajannan wllh saiya murdewa 'yar iskar nan wuya ta mutu kowa ma ya huta."Sàida aka nemo taimakon get man kafin a dauke su a komar dasu gefe,babban bacin ran Bilki yadda hakorinta yayi fitar burgu,gashi abun bacin rai na gaba ne ya cire,fashewa tai da kukan bakin ciki da takaici,ga bakin ya haye yayi suntum,yadda take kukan sai wawulan ya kara fitowa,da sauri Hamna ta matso gabanta,wata shegiyar dariya ta kece da ita,Billy gayu ya haka kuma naganki da wawulo abaki,wallah har kinban tausayi,yanzu babu ke babu murmushi acikin Jama'a.Kunnan Bilki ta matso,wananna sumin tabi nai miki,na bankwana ne,kinsan gwara na barmuku abunda zaku dinga tunawa dani,inna tafi haka kamar bammuku adalci ba,bankuma cika tantiriya mara mutunci ba kamar yadda kuke fadi."Af na cika ki da surutu,bari na kyale ki haka kar zafin yayi miki yawa.

"Babu wanda zai dauka ba sannu take musu ba"saidai aga sunyi sakare suna kallon bakin ta"Sauda ta kashewa idanu da take kallon ta"Sauda "yan mata,yanzu ina gayun"ina kwalisar"aini da acema zaki karye da naji dadi"zanga ta iyayi,wanann shegen abunda ya fito miki da zai yanzu da sauna sa wuka na yanke dan Iska,kirjinta ta nuna,ba karamin haushin Sauda take jiba,yadda in tana tafiya tana bankaro kirji wai ita yar Iska,tana nuna mata ta girma,Sauda dai ayau babu bakin magana sai zare idanu takeyi."Hajiya Zaitun da aka kasan ciccibarta tana nan rikica kamar kayan wanki,gabanta ta duka,dama aminai kuke,indadi yazo ky raba in wahala tazo kuraba,karfa kiji badadi,kinsanni bana Munafurci,kinga faduwar nan da kikai nice nan na zuba muku karkashi kuka taka,sannu Mama tafada tana sakin Murmushi.Zuciyar Zaitun ta farfasa ta kamayi,dama wannan yarinyar ce ta saka tai wannan mummunar faduwar,ina so ki adana dukkan fushinki,akwai wani babban sirri naki ahannuna,wllh Matukar kikace zaki dau mataki akan abunda nai miki,zanyi miki zagidir a idanun duniya,ni Hamna inna dauki niyya bana ji bana gani,kamar mahaukacin da ya fito daga turu haka nake,yana gudu kar akama shi amayar dashi,yadda zanyi gudu haka zanta jan rayuwar ki akasa,in kunne yaji,kama kunnan ta tayi tana sakin Murmushi.Zaitun da hankalin ta yayi mummunar tashi tunanin ta daya wani sirrine da ita haka wanda wannan tsinanniyar tasan dashi.

"Su Big Daddy aka kira aka shaida musu halin da ake ciki"babu shiru suka baro ayyukan su suka taho,yadda suka ga halin da suke ciki sosai hanlakin su ya tashi babu bata Lokaci akai hospital dasu.Sadauki na zaune a office din sa,gaba daya baida walwala yanxu,Munir yayi tambayar harya gaji,Jin anbude masa kofa babu neman excuse ya sashi bude idanun sa,tana tsaye tana washe masa hakora,waro idanun sa yayi tana sake kallon ta,to meya kawo ta,da sauri ta karaso ta tsaya agaban sa.Yayanah lumshe idanun sa yayi yana kallon ta,meya kawo ki hospital dimmu,baki ta kara washewa muda su Ammi ne duka gidan muka taho,saurin gyara zaman sa yayi ya kama hannun ta,fadamun meya faru,ai Yayah Mom ce da 'ya'yan ta suka samu wani dan karamin hatsari,kallon rashin fahimta yake yi mata,hannun sa taja zo muje kagan su,babu musu yabi bayanta,room din da aka kaisu su kadai ne aciki.

"Kare musu kallo yake"Mom ya kalla yadda tai jage jage da hawaye,gyaran hannu ake mata,sai ihu take tana Kuka,yadda kasan zata zauce,tsagewar kashi ta samu a hannu,Sàuda ma targade tayi,Zaitun kuwa keyar ta tai wani shegen tsini,ga kwankwason ta daya ke azabar ciwo,ana zatan shima targadan ya samu.Bilki dai tana nan da dogon baki,yayi him kamar balo,Khalid dai karaya ya samu akafa,yana can dakin dori yana karbar azabar sa."Hamna tana bayan Sadauki tanai musu gwalo, Mom kamar zata sume saboda yadda hannun yayi tsami,haka Sàuda sai kururuwa take,gaba daya sun cika asibitin da iface ifacen su.

🤣🤣🤣Allah sarki su Mom karku damu bankwana Hamna takeyi daku,zaku sha iska kanta dawo....

        Kuyi hakuri rashin charge ya sanya jiya baku jini da yamma ba.

Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar.
         ......✍️✍️✍️✍️✍️



         'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail

Page 27_28


 *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

"Sàida kyar suka bari aka gama gyaran targaden nan,su kansu Nurse din sun cika musu kunne,dandai family din Sadauki ne shiyasa suka daga musu kafa,da sunsha ruwan masifa kuwa."Baccin wahala ne ya dauke Mom, Sadauki na tsaye ya harde hannayan sa akirji yana kallon su daya bayan daya"Hamna ya juyo ya kalla,hada idanu sukai tanaiwa su Bilkisu gwalo, rankwashi ya sakar mata aka,da sauri ta dafe kan tana kukan tabara,kauda kansa yayi daga kallon ta."Ammi ya kalla,meyafaru dasu haka?wllh Sadauki muma bama ceba,tsautsayi ne kawai,amma bamusan musabbabin abunda ya faru ba,shiru yayi yana nazarin maganar ta,idanun sa ya dora kan Hamna da take ta rarraba idanu,kinyadda tayi su hada idanu tasan sarai zai karanto abunda take boyewa.

Juyawa yayi ya fice daga room din"ko karin binsa takeyi Ammi ta damko ta,bakisan yana da tarin ayyuka ba zaki zo ki dame shi da surutu,zauna anan Ammi ta zaunar da ita akusa da ita,kamar zata fashe da kuka,taso tabarta ta bishi,dalili wani inibi data hango akan fridge dinsa,amma Ammi ta kwafsa mata,fir ta hanata taje office din sa."Gaba daya Family din suna cikin damuwa Saboda rashin lafiyar su Mom,babban wanda yafi kowa jin jikima Khalid,an samu an dora kafar tana sakale asama,bakaramar azaba yake shaba,shikadai yake ayyana irin fansar da zai dauka akan Hamna.Kwanan su Mom biyu suka warware aka sallame su,amma banda Khalid,kullum suna zuwa wajan sa,Yusuf ne ke jinyar sa,dan Sadauki ba kunya ya sanar da Abbah bazai iya jinyar Khalid ba anemi wani,sanin 'yar tsamar sake tsakanin su yasa bai takura masa ba,yana sa tabbacin koshi Khalid din Sadauki ya karye bazaiyi jinyar sa ba.

"Duk sanda za'a zo da Hamna ake zuwa"saita bari kowa ya fita zata cangale kafa tana nuna masa yadda zai koma tana sheka masa dariya,da ace yana da damar tashi babu abunda zai hana be ballata ba,saidai yayi dacin ran ya gama,akwai sanda Mammah ta taba kamata tana tsokanar sa,murde mata kunne tai tanai mata fada karta sake yayanta ne ta bashi girmansa,taji Mammah ne kawai badan ta yadda ba.Mom bacin rai goma da goma,saima ta kalli Bilki yadda hakorin gaba ya cire abun ke sake dafa zuciyar ta,haka Bilkisu ko san ganin mirror batayi,duk rawar kanta da iyayin ta 'yan class din su sun sami lafiya,ranar da suka lura da bakinta sun tsokane ta kamar tai kukan dan bakin ciki,dariya ta shara,mazan ajinsu da takewa iyayi da feleke tasha wulakanci a wajan su."Sai aji yayi tsit wani aciki zai daga muryar sa,da kudina bazan Auri me gibi ba ba wanann maganar,sai a kyakyace da muguwar dariya.Haka suka dinga yi har aka tashi ranar,da kuka ta dawo gida wurjanjan,ai Mom jitai ina wuta ta jefa Hamna,Hamna kuwa bata masan suna yiba tuni ta tattara su ta zuba akwandon shara.

"Sàida Khalid yayi kusan 3weeks kafin a sallamo shi,daya ke yaci sa'a dorin yayi kyau sai dan danan ya dan fara zagayawa da sanda ahannun sa,haka Hamna zata dinga binsa abaya tana sheka masa dariya, Yayah Khalid yaushe za'a siyoma robar bara,baya cemata kala,sai wani lokacin inta kure shi zai fara danna mata zagi kamar bamaguje,saidai tayi dariya,tayi rawa da waka,tabarshi anan yana sababi."Zuwa Lokacin shakuwar ta da Sadauki ta kara Yawa"bata iya bacci saitaje taga yayi bacci,shan coffee dinsa ya dawo hannun ta,kome taci sai tace da Ammi na Yayah Sadauki,tun Ammi na mamaki harta gaji ta daina,ta zuba musu na muniya shi da ita.Duk yadda yake daure dauren fuska baya iya yiwa Hamna,kullum tsarabarta da bance.Tafiyar su sai kara tahowa takeyi yanzu saura sati biyu su tafi,shirye shirye sun kammala,hatta Visar su ta fito,shiri sukeyi sosai,duk yadda Hamna ke dokin tafiyar inta tuno zata tafi tabar ya Sadauki sai taji kamar tace ta fada tafiyar.Su Mom ba kamar murna sukeyi da tafiyar ba,Anno ba zata tafi kosa sarara,suji dadin rayuwar su."Bangaran Sadauki shima kamar mara lafiya haka ya koma,awannnan tsakanin duk wanda yayi laifi duk kankatar sa jibga yake sha,babu ragayya,zafin zuciyar sa ya karu,kamar zaici babu haka yakejin zuciyar sa,yarasa abunda ke damun sa, zuciyar sa acunkushe take da tsantsar bacin rai da takaici,ba komai ya jawo hakan ba sai tafiyar Hamna,ya riga ya saba da ita,baya fatan abunda zai nesanta shi da ita,amatsayin ta na kanwar sa,amma fa injisa.


"Yau ma tunda ya shigo yake huci shikadai,hango Sumayya yayi taci wasu matsatstsun kaya yadda kasan zasu yage ajikin ta,wani siririn mayafi ta dosana awuya, hills din takalmi ne akafar ta,an caccaba mata kwalliya a face dinta,da alama biki zataje ko wani party na musamman."Saidata zo giftawa ta kusa da motar sa wanda sam bata lura dashi ba,balle murfin motar yayi ya fito yana kallon ta,sai Lokacin ta lura dashi,ras gabanta ya fadi,cikin rawar murya take fadin sannu da zuwa Yayah,shiru yayi bece kala ba,kallon ta yake daga sama harkasa.Ina zaki je?cikin rawar harshe take fadin am dama Biki zanje,da wannan kayan zakije bikin?shiru tai tana kallon kasa,tsawa ya daka mata Answer me,saurin gyada kai tayi alamar eh,mari ya kawo mata,wanda sai dataji kunnan ta ya amsa,sake fella mata mari yayi wanda ya sata zaman 'yan bori,kukan ma kasawa tayi gaba daya ya gigita rayuwar fuskarta."Kuka ta fashe dashi daga baya,dan Allah Yayah kayi hakura bazan sake ba.

"Hambari ya kawo mata babu shiri tai shiru tana sharar hawaye,harabar gidan ya kalla,ganin ganyayyaki sun faffado,kalli nan,saurin daga kai tayi,oya banso naga ko tsinke awajannan,sàida gabanta ya bada ras,ita ce zatai picking din,zaki tashi kosai na ballaki,da sauri ta mike,takalaman kafarta ta cire,tana sunkuyawa zip din sket dinta ya bada wani fek ya balle da kansa,saurin kauda kansa yayi bacinrai na kara sakko masa,yanzu data fita haka zataje tayi akan layi,sosai hankalin Sumayya ya tashi ganin wata lukutar masifar data kara samun ta,wanann karamin gyalan ta kwanto ta daura a daidai kugun ta."Biyo ni"tunkan suje part dinsa ta fara Kuka da tausayawa rayuwar ta ayau,part din sa ya wuce tana biye dashi,sàida ya tabbatar ta shiga parlon ya saka key,dan Allah Yayah kayi hakuri sharrin shedanne,ai yanzu zan fitar da wannan shedan din daya makale ajikin ki.

"Belt din kugunsa ya kunto,nannade shi yayi ya lafta mata abaya,ihu ta saka ba karamar azaba taji ba,yadda kayan suka dameta saiya bawa bulallar dadin kwanciya ajikin ta,saidaya yimata dan iskan duka babu mejin kukan ta kafin ya kyale ta,nan ya barta tana kukan azaba, bedroom dinsa ya wuce yayi wanka,da gashi sai singlet da boxer ya fito.Tashi ki fitar mun a part,da kyar ta mike ta fita jiri na dibarta,bakaramar dakuwa taiba."Da kyar takai kanta part din su,sai rusa kuka take,jikinta yayi rudu rudu,da sauri Mom tafito har tana tuntube,ke mezan gani haka,meyafaru kike Wannan kukan,ubanwa yayi miki wannan dukan kamar jaka,Cikin masifa Mom ke tambayar ta."Yah Sadauki ne"what Mom ta fada tana zazzare idanu,Sadauki,shine yayi miki wannan dukan,saboda ke jakar Uwar sace,Wllh be daki bamza ba,saiya biya bashin wannan dukan da yayi miki.

"Hhhh Abun Dariya,sai kumfar baki takeyi,amma takasa Zuwa ta sami Sadauki akan dukan da yayiwa 'yarta.Papi yana dawowa ta sauke masa kwandan masifa,kayiwa dan dan uwanka Magana,ba ruwansa da 'ya'yana,ya barsu suyi rayuwar da suke so,shi inya fita wayasan tsiyar da yake shukawa,sai 'ya'yana zai sakawa idanu.Kingama papi yace da ita,kinga Jamila ina rabaki da raba mana kan yara,ke meyasa wai bakyason azauna lafiya,yanzu bashi da ikon da zaiwa kannan sa magana,sai kihau balokoko,kina kumfar baki,bafa nasan irin wannan halayyar take,rai bace ya karasa magana halin Mom yana matukar damunsa,shi kadai ne beyi sàar mata ba acikin 'yan uwansa.Aiko sake kuluwa tai damma tana shakkar papi da ba karamar raina shi zatai ba.

"Tashi yayi yabar mata parlour gaba daya,yagaji da bacin ran da Jamila take kunsa masa,zai dauki mataki akanta kwanan nan kuwa.

        Mrs 🌹 Baba Bello Abubakar
         ......✍️✍️✍️✍️✍️✍️


         'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

 *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 29_30

"Satin da zasu tafi ya kama,Dada tazo kamar zatai Kuka,bata son wannan tafiya,acewarta jikokinta za'a lallata mata su,Ammi najinta batace komai ba."Sai sababi take tana lallaba Hamna karta yadda atafi da ita,tab Dada taya za'ai naki tafiya gaskiya sai naje,haushine ya ishe Dada ta ture ta daga jikin ta,ja'irar banza saikije kiyi ta tafiya,na lura uwar ki ta hure miki kunne bakya kaunata gaba daya,ni dai Dada Ammi na bata taba cewa karna soki ba, Innalillahi yanzu 'Yar Aro ni kike mayarwa da Magana,ai gaskiya na fadamiki,ta fada tana murguda baki.Ai kingan ta nan wannan yarinyar bata da kunya Dada,Aisha ta gama batata da sangarta ta,ina da tabbacin ita ce ta hanata zama awajan ki,cewar Mom cikin hassada da bakin cikin tafiyar da Ammi din zatayi,to ai tayi ta banza,nida takwarata mutu karaba takalmin kaza.Babu makircin da Mom batai ba kar aje da Ammi Dada ta hana tafiyar nan da ita,amma Dada batai hakan ba,gaba daya haushin Dada ya kama Mom,ji take kamar ta rufe ta da duka.

"Ganin ba riba zataci ba,ya sata mikewa tabar Dada awajan,binta tai da.kallo tana sakin murmushi,tsaf tagama karanatar Jamila,tana da matukar bakin ciki da kyashi,bata son taga wani ya samu wata daukaka ya zartata,Allah ya shirye ki cewar Dada.Hamna da take bin Dadan da kallo cikin mamakin furucinta,Dada me kikagani,shiru Dadan tai bata bata amsa ba,ba maganar ki bace kiyi shiru da bakinki cewar Dada tana mikewa tare da barin wajan.Mikewa tai ita ma tabar wajan ta nufi part din Ammi.

"Tashin safe sukai,gaba daya gidan aka dunguma raka su airport,su Najma har Kuka sukai na raubuwa da Ammi,suna matukar jin dadin zama da ita, Mom bakin ciki ne ya hanata rakiyar,tana gida tana dacin rai,hadda Dada aka tafi kaisu airport din,gaba daya idanun Sadauki sunyi jajir,sosai yakejin badadi na rabuwa da Hamna,sanda aka fara kiran matafiya, rungume Sadauki Hamna tayi,hadda kukanta zatai kewar sa sosai,daurewa yayi shima saura kadan yayi kukan amma ya dake.Abba ma ji yayi kamar karya rabu da 'yan uwansa da mahaifiyar sa,su Dada hadda sharar kwallah sosai take kaunar Abbah.Mamamh da Ammi rungume juna sukai sunan jin kewar rabuwa da zasuyi,suna ji suna gani su Ammi suka shige cikin jirgi,sàida suka ga shigar su tukunna suka dawo zaciya sam babu dadi,kowa da abunda yake sakawa azuciyar sa.

"Can Germany kuwa,iyayan Ammi sun kasa zaune sun kasa tsaye,shiri na musamman suke na tarar tilon 'yar tasu,ma'aikatan gidan su kansu sun shaida yar gata ce zata zo ganin gida,sabbin kaya Alhaji Ishaq ya canzawa ma'aikata gaba daya,da yake turawa ne ma'aikatan sket ne iya cinya da farar riga ajikin su,babu ruwansu haka suke yawo tsingil tsingil.Hajiya Sadiya tana cikin farin ciki ita ma,abokan arziki da suke nan duk sun hallara dan tarbar su Ammi.Sanda jirgin su Abbah ya dira a airport na Germany su Hajiya Sadiya suna wajan,sai baza idanu suke yadda zasuga yar su da jikokin su."Sunan fitowa sukai arba dasu sai washe hakora sukeyi,Hamna dai tasha kauyanci acikin jirgi,yanzumma sai zare idanu takeyi,har tsoron taka kasa take ganin ko ina tar kamar tangaran babu alamar turbaya,mamaki sosai ya kamata,anya ba Aljannah suka zoba?abunda take ayyanawa kenan,mutane daban daban take gani da masu kyau da akasin haka.

"Abbah ne ya danko hannun ta ganin tana neman tai wata hanyar tsabar kauyanci,ko Munif beyi abunda takeyi ba.Alhaji Ishaq wanda Ammi ke kira Abie da sauri ya rungume Abbah yanai musu barka da zuwa,Hajiya Sadiya da suke kiranta Amma Ammi ta rungume farin ciki na mamaye ta,sakinta tayi ta rungume su Hamna da Mima,sunji dadin zuwa kasar ba kadan ba.Dunguma sukai suka shiga tsala tsalan Motocin da Abie yazo da su.Hirar yaushe gamo sukeyi,Ammi dai kamar zata shige cikin Amma ba karamin kewar ta tayi ba,sai murmushi takeyi bakin ta yaki rufuwa.Abbah sakin murmushi yake tayi ganin farin ciki a fuskar matarsa habibiyar sa."Tara ta musamman akai musu,har wata kwarya kwaryar Liyafa Abie ya shirya musu.Sanda suka shiga harabar makeken gidan Hamna ba karamin diriri cewa ta karayi ba,sai karewa gidan kallo takeyi.Kayataccen parlon suka shiga,komai ma sha Allah,maid sai welcome suke musu.

"Sàida suka baje a parlo tukunna Hamna ta samu bakin magana,Ammi wannan kasar bazan koma Nigeria ba anan zan zauna,Amma ce ta shafa kanta da nayi farin ciki da hakan,ko Abban ki zai barmana ke?ta fada tana kallon Abbah, murmushi kawai Abbah yayi bayajin zai iya barin Hamna a ko ina.Yunwa nakeji nidai Ammi,oh Hamna sarkin ci har yanzu kina nan da cin ki"ai Amma wannan bazata canza ba,ci ne da ita kamar gara, murmushi Amma tai tana shafa kan Hamna,ai lafiya ce gwara taci,yanzu ku farayin wanka tukunna sai kuci Abincin,babu musu suka mike amma Hamna ba haka ta so ba,wane irin wanka kuma,ita da cikin ta ya zazzage a jirgi.Saida sukai wanka suka nutsu kafin su hallara a kan dining table,babu me Magana kowa cin abincin sa yake yi,dokar Abba ce dama sun sani in ana cin Abinci ba'a magana.

"Sàida suka kammala cin Abinci sannan Hamna suka fita harabar gidan,hira suka zauna yi tare da Abba,babu ruwan su da zancan surukin sune kamar dan su suka dauke shi,part guda suka warewa su Ammi zasu fi jindadin zama tare dasu.Kwanan su biyu da zuwa Abba ya fara fita aikin daya kawo shi,in Ammi ta gama ayyukanta na part din su sai ta taho wajan Amma susha firar su.Hamna dama a bangaran Amma take kwana,sosai take son Hamna."Watan su daya da zuwa sun canza sun kara kyau da haske, musamman Hamna, school me kyau Abie ya sama musu ita da Mima,anan ma bata daura zani ba,kullum Hamna cikin tsokana take,sàida Abie ya tashi tsaye akanta ganin nan ba Nigeria bace zata iya samun matsala.Ammi na nasiha haka Amma ahankali ta fara rage rawar kai da fiti na,saidai in ta dawo Gida in abu ya hada su da Munib ta jijjibgesa,saidai yayi Kuka ya share.

Nigeria

"Duniya fa tayiwa Sadauki zafi,ko yaushe bashi da walwala,Mammah tayi mitar harta gaji ta zuba masa idanu,hatta big Dady yasan ya canza,sam be kawo tafiyar Hamna ce tasa shi komawa hakan ba,daga antabashi sai fada,hatta a hospital ya kara zama miskili na gaske ko yaushe face dinsa a turbune kamar hadari."Mom tana nan da bakin halin ta,burinta yanzu ta mallake dukiyar papi wanda take ta hari tun tuni, Zaitun na kara dorata akeken bera tana kara hure mata kunne."Khalid ya warke garau amma Abunda Hamna tai masa yana ransa,ko shekara dari zatayi kan ta dawo saiya dauki fansar abunda tayi masa.Yanzu ma yana zaune shi kadai yake murmushin mugunta tuna irin abunda zai yiwa Hamna,wanda zata tabbatar shi dan halak ne ba shege ba,zata tabbatar nonon Jamila yasha.

"Yana duke a gaban Dady shida Khalid,kallon su yake daya bayan daya ganin yadda babu me kallon dan Uwansa,gyaran murya yayi suka kara Nutsuwa agaban sa,wai menene matsalar ku kaida shi,meyasa bakwa jituwa da junan ku,ina san ku sanar dani gabar dake tsakanin ku,shiru sukai kowa da abunda yake ayyanawa a ransa.Babu komai Big Dady,Sadauki ke wannann maganar,kaifa ya kalla Khalid,nima babu,tunda haka ne,karna sake ganin wani sabani a tsakanin ku.Sannnan ya ka mata kowannan ku ya nemo matar Aure,kusan kun girma,duk kun mallaki hankalin ku,kusan abunda ya kamata,nabaku nan da wani Lokaci kankani ku fadda matar Aure.Babu wanda yace kala,tabdi Khalid ya fada a zuciyar sa,kaji tsoho da Munafurci,ni kamar ni ace zanyi Aure yanzu ai bazama ta sabu ba,shidai Sadauki bece komai ba.

Tashi sukai suka fita,babu wanda ya kalli dan Uwansa acikin su.part din Mom ya wuce sai faman hura hanci yakeyi, Mom dake zaune ta hakimce a parlo ta kalle shi,yadai naganka ranka abace,Aidole kiganni haka,kamar ni waccan tsohon zai cewa zaimin Aure,bazata taba yiwuwa ba,kai zancan wasa kake ko na gaske kintaba ji naimiki irin wannan maganar.Tab to da sake wllh har yaushe kai girman da za'a yima maganar Aure,yayiwa dansa shi kadai amma banda kai,yanzu naji magana Mom,ki hana faruwar hakan,tsaki taja ai wannan ma maganar banza ce,irin ta mutanan wofi.

Hmmm Lallai Mom kina ruwa.

       Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
          ........✍️✍️✍️


         'YAR ARO

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

 *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 31_32

"Yau Hajiya Zaitun ce ta kawo mata ziyara,kallon Mom takeyi kamar tana nazarin wani abu ajikin ta,wai lafiya Zaitun irin wannan kallo haka,Numfashi ta sauke,wai yanzu bakya sha'awar irin fantamawar da nakeyi Jamila,sosai nake sha'awa har mamakin yadda kike kwakular kudi a hannun Alhajin ki nake yi, murmushi Zaitun ta saki,wannan wani sirri ne megirma wanda in har kikaji shi zakiyi mamaki,mamakin me kenan,akwai wani boka waishi me kankat,matukar kika kai sunan mijin ki wajansa angama magana,keda talauci saidai kiga anayi,dan da kin tambayi mijin ki kudi angama magana jiki na rawa zai baki.Shiru Mom tayi kina ganin haka zan dinga tatsar Abban su Khalid kwarai kuwa.Aini yanzu Zaitun bama wanann ne ya daman ba,waccan 'yar iskar yarinyar nake so aimin maganin ta,wa kenan Hamna mana aina dauki alkwarin saina wulakanta rayuwar ta.Dariya Zaitun ta saki,in har wannan ne ai baki da matsala,amma kuma yarinya ce me zaisa zaki kullace ta haka,ai wannan yadda kikasan kumurcin maciji haka nake ganin ta.Buri na amakanta shegiya,zanga da idanun da zatai rashin kunya,sannan akurumtata,gata dai da rai amma bata da Amfani.

"Baki da kyau Jamila,abun ai saiyayi mara yawa,saidai ki ,zabi daya,kamar kurum fatan zaifi tunda da bakin take miki rashin kunya,kuma kin kawo shawara,yaushe zamuje,ni ko yau nema muje na matsu naga faduwar waccan yarinyar."Kamar yadda duka tsara awashegari haka suka nufi wajan wani boka,can dajin falgore sukai tafiyayya dan sabwa Allah,kamar yadda sukaje mai da bukatar babu ja,yayi musu Alkawarin kurumtata nan bada jimawa ba,zai tura mata aljani dan kurma,shine wanda zai shiga jikin ta,ya toshe mata dukkan kunnuwanta,bazata sake jin ko wane iron sauti ba,haka bazata karayin magana ba,saidai taga anayi."Cikin farin ciki Mom ta dawo gida ranar kowa ya tabbatar tana cikin farin ciki.Saboda tsabar Munafurci Mom har kiran Ammi tai wai zasu gaisa,matar da tunda suka zo ko saudaya bata kira su ba,boye mamakin Ammi tai suka gaisa,tambaya tayi yaya yara,lafiya lau Ammi ta ce da ita,abunda ya daga mata hankali jiyo Muryar Hamna radau tana zuba surutu,ba shiri ta yanke kiran ta kira Hajiya Zaitun.

"Zaitun wane irin aiki me kankat yayi mana,ga shegiyar yarinyar can baki radau kamar ca kwaikwaiwa,Haba dai karki damu aishi aikin sa a hankali yake tafiyar dashi,zakiga aiki nan bada jimawa ba,shikenan amma gaskiya ni dai harnaji na fara sarewa,abunda ko sati ba'ai ba shine zakice kingaji kina da aiki Jamila,kin cika gaggawa.Haka sukai sallama da Zaitun sam hankalin ta ya gaza kwanciya.Bayan sati biyu.

Germany

"Karfe 7am Hamna Hamna Amma ke kiranta ganin yau tana neman makara a school,bude kofar dakin ta tayi tana kallon ta,tana zaune a tsakiyar gado Hamna ta kara kiran sunan ta,amma kikadan batai alamar zata amsa ba,karasawa Amma tai ganin sabon iya shege da take damun Hamna yau.Dafa kafadar ta tayi sai Lokacin ta dago da sauri,hawaye tagane sharkaf a fuskarta,Cikin mamaki Amma take kallon ta,kukan me kikeyi Hamna,ko wani waje nayi miki ciwo,babu amsa sai kallon bakin Amma da takeyi,dan tantance abunda take Magana akai,amma harta gama magana bata gane me take cewa ba.Hannun ta taruko tashi kije kiyi wanka kizo ki shirya zaki makara,har kofar toilet din ya takaita kafin ta juya ta futa,sam bata lura da yanayin Hamnan ba ta dauka iya shegen tane yau ya motsa."Bangaran Hamna kuwa tana cikin tashin hankali,duka yadda taso tai magana abu ya faskara,saita bude baki zatai magana sai taji kamar ansa wani abu an toshe makogaranta,kunnan ta batajin komai,ko wace irin kara ta daina jinta.Haka tai wanka ta futo da tunanin wace larura ce ta kamata haka.

"Zama tai daure da towel ajikin ta,tajima azaune kafin ta mike ta saka uniform dinta,cikin dauriya ta sakko daga room dinta,part din Ammi ta nufa,shiga tai ba tare da sallama ba,Ammi ce ta kalleta,mene haka Hamna shigowa ba sallama koma kiyi sallama,tsuru tai tana kallon Ammi batajin abunda take fada gaba daya."Sake kuluwa Ammi tai ganin tayi mata banza,magana zata sakeyi Abbah ya dakatar da ita,kiyi mata ahankali mana,kinsan Hamna batai taba shigowa sai tayi sallama,to yaudimma bamu san dalilin ta nakinyin sallama ba.Zonan Hamna,ya fada yana yafitota da hannun hakan yasa tagane meyake nufi.Ahankali tatako inda yake,idanunta yayi jajir,ita kadai tasan yadda zuciyar ta take tafarfasa."Kusa da Abba ta zauna,shafa kanta tayi,ya akai Mamana,shiru babu amsa,sai kallon su da take tayi kamar ayau din ta taba ganin su."Ammi ce ta kalli Abbah ka gani ko yau wani sabon wulakanci tatashi dashi,kana yiwa yarinya magana tana kallon ka,babu gaisuwa ba komai,kallon bakin Ammi tai hakan yasa tagane Ammi fada take mata.

"Hawaye ne ya wanke mata Fuskarta,ganin Ammin ta na magana amma ta kasa jin sautin maganar ta,haka.Ammin ta na magana ta kasa jin sautin muryar ta.Sakare sukai suna kallon ta,jikin Ammi ba karamin sanyi yayi ba ganin hawaye a fuskar Hamna,yarinyar da bata taba yarda aga faduwar ta,to me akai mata haka.Kusa da ita Ammi ta koma ta zauna,meya sameki Hamna."Da sauri ta mike ta dakko school bag din ta,pepa ta dakko tai rubutu ajiki,mikawa Ammi tai,kurawa rubutun idanu Ammi tai,gani take kamar ba daidai take karantawa ba.Banajin me kuke fada Ammi.Mikawa Abbah tai shima ya karanta,kurawa Hamna idanu sukai suna shiga tashin hankali,yadda take kallon su haka suka suke kallon ta."Yanzu Hamna bakyajin abunda muke fada Innalillahi wa'inna ilahirraji'un,Ammi ta fada hawaye nabin kuncinta,meyasa meki haka Hamna,fashewa da kuka Ammi tai tana kallon Abbah,dakko ta mutafi hospital ko wani kwaro ya fada mata akunne.

"Cikin sauri Abbah ya mike sosai hankalin sa yayi mummunar tashi shima,Mima dake tsaye tana sauraran iyayan mata,hawaye ya wanke mata fuska itama,gaban Hamna ta tsaya tare da rike hannun ta, sister bakyajin magana ta kike nufi yanzu,babu amsa sai kallon bakin ta da takeyi,sakin ta tayi ta juya da gudu wajan Amma da Abie ta nufa,suna zaune suna mitar Hamna taki zuwa tai break taje tai zamanta.Kallon Mima sukai ke lafiya,ina lafiya granny,Hamna ta kurmance ta saina ji,ta daina magana,da sauri suka mike tare da dafe kirji,kika ce me?da sauri sukai hanyar part din su Ammi har sun fito zasu tafi hospital.Amma ce ta ruko Hamna bakyajin maganar mu Hamna Innalillahi,wane irin abune ya sameki haka,cikin sauri suka fada mota da yake akwai mayafi dama ajikin ta.

"Gaba daya babu me magana acikin su,sunyi jugum jugum kowa da abunda yake tunani azuciyar sa,gaba daya zukatan su bugawa sukeyi na abunda za'a sanar dasu a hospital din,suna karasawa babu bata Lokaci Doctor Leena ta fara dubata,dakin gwaji aka kaita babu irin binciken da Doctors din basiyi ba amma bash gano Abunda yake damun ta,lafiyar ta kalau shine abunda Sakamakon ya nuna Musu.Kallon su Abbah Doctor Leena tai cikin tausayawa,Kallon Hamna ta sakeyi ganin yarinya karama ta hadu da babbar cuta.I m sorry sir saidai kuyi hakuri,munyi Iya kokarin mu yarinyar ku bata da wata matsala,bamusan daga ina matsalar take ba,abunda binciken ya nuna mana lafiyar ta kalau.Shiru su Ammi sukai sanajan Innalillahi a zulatan su,idanun Ammi tayi jajir tunda suka zo take Kuka,abun yayi matukar damun ta,yau ace Hamna tayi awa one batai magana ba kasan akwai damuwa,balle gashi ta shafe awoyi masu yawa.Doctor Leena rarrashin su ta karayi,da dora Hamna akan magani hakan zai taimaka mata,haka suka dawo gida guiwar su a sanyaye,ko ruwa sun kasa sawa acikin su,gaba daya zuciyar su babu dadi.

"Duk yadda Hamna take cikin damuwa tafi damuwa da iyayan ta,ganin irin halin da suka shiga musamman Ammi,da hannu take musu nuni suyi Murmushi,fashewa Ammi tai da Kuka ya tabbata Hamnan ta tazama kurma kenan,gashi harta fara maganar kurame,babu wanda be share Hawaye ba,ganin yadda Hamna take murmushi Hawaye na zuba a idanun ta,wai dan dai ta kwantarwa da iyayan ta hankali take hakan.

    Allah sarki Hamna koni ma na tausaya miki,saidana share guntun Hawaye na tsananin tausayin ki.
    
         Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
              ..........✍️✍️✍️✍️✍️
    
    
               'YAR ARO
    
    
    Funny Girl 🧕
    
    Written and Narrated
    
    By Kulsoom Ismail Idris
    
    *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

 Page 33_34

"Tsahon kwana biyu babu wani sauyi da aka samu,sun kara komawa asibitin nan madai shiru kamar anshuka da dusa,babu ji babu magana,abu fa ya hadu yayiwa Ammi yawa ta sanya damuwa azuciyar ta.Allah sarki Hamna tun tana damuwa akan rashin maganar ta harta gaji ta hakura.Ahankali rayuwar ta ta sauya,saidai ta zauna ita kadai ta kurawa waje daya idanu,wannan kiriniyar da wasan duk babu,saidai tai jugum tana kallon nau'ikan tsuntsayen da Abie ke kiwo,sune suka zamo.abokan hirar ta,in kaga tana murmushi to tana tare da sune,zakaga hakoran ta."Mutan Nigeria sun samu labarin abunda ya samu Hamna,sosai abun yayiwa Mom dadi,ranar kamar ta Zuba ruwa akasa tasha,amma kannewa tai kamar babu abunda ya dame ta.Sadauki fadar irin tashin hankalin daya shigama bazai misaltu ba,yaso ta howa Abba ya hana shi,cayayi yayi zaman sa Addu'a Hamna take bukata.Badan yaso ba haka ya hakura,amma sam hankalin sa ba akwance yake ba,tana ta tunanin abunda ya samu Hamna wanda yasa ta rasa ji da ganin ta.

"Haka su Najma sun shiga damuwa matuka,sanda Dada taji Kuka ta rushe dashi shikenan Hamna ta nakasa,Yanzu garin yaya tadaina ji da magana,tsakanin ta da wanda yayi silar ciwan Hamna Allah ya isa,sanda take wanann abun Mom na zaune fuskarta da lamar Alhini,ta zabga tagumi kamar gaske,hatta da 'ya'yan ta duk yadda sukejin haushin Hamna sunji badadi,amma banda Khalid ko ajikin sa,saima Allah ya kara daya ce,aga ta bakin surutu.Mom bayan ta shiga daki dariya ta fashe da ita harda kwaso shorky sosai take cikin farin ciki."Shiryawa tai tatafi gidan Zaitun, àah kodai andace ne had naga kina faman yashe bakinnan da alamar akwai wata akasa,uhm kedai bari Aminiya ai aiki yatafi yadda ya kamata,hannu ta bata suka tafa,kice Allah,ai nagaya miki dama aikin me kankat kamar yankan wuka ne,sha yanzu magani yanzu,shewa suka saka aiko na tabbatar yanzu,oh ashe ga magani na zauna yar banza tana batan rai.Yanzu bagashi kinyi maganin ta ba, murmushi tasaki aike dai bani da abunda zan bigaki sai godiya kawai,bakomai aikedai karki damu anzama daya.

Cigaba sukai da hira suna ci gaba da kulle kullen su na sharri,Allah ka rabamu da bakar zuciya wadda ba imani acikin ta Ameen.

"Ahaka Hamna taci gaba da zuwa makaranta,Sadauki na kiran video call saidai ta kura masa idanu,kamar yadda shima.yake.kura mata nasa idan,babu damar magana tunda baji takeyi ba,saidai ya dinga yimata nuni da hannu ko taimasa nuni da hannu,ahaka sukeyin hirar,saidai kaga tana ta sakin murmushi,in suna hirar Ammi takan zauna tana kallon ta,tarasa wace irin shakuwa ce tsakanin ta da Sadauki,in kaga ta jima tana fara'a to dashi takeyin magana.Sosai rayuwa ta dinga canzawa,al'amura da dama sun faru,zuwa yanzu su Abbah sunyi 3years a Germany.Aikin da yake sa ran zai kaishi 5years sai gashi a 3years ya kammala shi,har sunsa ranar tafiya nan da 2weeks.

"Shekarun Hamna 15 ta zama budurwa kyanta ya kara futowa,makerin yammata ci ya fara kerata,yayi da Mima take da shekaru 17,da yake Hamna nada tsayin kafa kansu kusan daya da Mima."Tana cikin farin ciki matuka da komawar su Nigeria saboda taga Yaya Sadaukin ta,sai Farin ciki take tana walwala,Ammi murmushi kawai take saki tasan musabbabin murmushin nata.Sun shirya tsaf sai tafiya kawai,sosai Amma suka fara kewar su, musamman Hamna duk da ba magana take ba,suna matukar jindadin zama da ita,tana da shiga rai,ko yaushe zaka sameta cikin fara'a koda kuwa akwai Abunda ke damunta tana boye hakan.

"Karfe 8am a airport tai musu, rungume juna Ammi da Amma sukai,hawaye suka goge saboda tunanin zasu sake haduwa ko bazasu sake haduwa ba,daya bayan daya tabisu ta rungume su,sàida sukaga tashin su sanann suka juya gida.A can ABUJA kuwa,Mammah sai aiki yakeyi na tarar baki,haka su Najma sun kasa zama sai shiri sukeyi,saura 1months Auran su,su Biyar za'a hada.Najma da Sumayya,sai Basma dama sune manya,sai  Sadauki da Khalid wadanda Big Dady ya takurawa sàida suka futo da matan Aure,badan Sadauki yaso wannan Auran ba,babu tsarin Aure a tare dashi,yarinyar da zai Aura Jawahir ta dade tana sonshi,ganin baya nata Fuska yasa taja baya dashi,da yake Allah yayi matar sace sai gashi ya nemeta,tayi matukar farin ciki,haka mamarta Hajiya Sarah sosai taji dadin wannan Aure.Tana matukar son abunda 'ya'yan ta ke so,matsalar ta daya bata son laifin yayan ta,ko laifi yayanta sukaima to in kanasan zaman lafiya saidai ka zauna akaine mara gskiya,in ta kama ma kabawa yarta hakuri Yawwa sai azauna lafiya.

"Yau wankan daya dauka shikan sa yasan yayi matukar kyau,farar shadda ce kal ajikin sa, fuskar sa dauke take da annuri.Besan iya adadin turarrukan daya sanya ajikin sa ba,bakar hula ya dakko ya saka sosai ya fito ras ba karamin haskawa yayi ba.Yana futowa sukai Kicibis da Khalid kallon sama da kasa yayiwa Sadauki,ya jijjiga kai tare dayin gaba,ko kadan Sadauki be nuna yama san da wanzuwar sa awajan ba yayi gaba shima.Tare da Mammah da Dad da papi suka dunguma dakko manyan baki, Mom dai tana gida burinta taga kurma yaya ta kare."Tunda jirgin ya gama dai daita kasa suka fara zuba idanuwa,musamman Sadauki,wadda ya matsu yaga Hamna,hannun sa na harde a kirjinsa,idanun sa kyar akan kofar da zasu bullo.Ahankali matafiya suka fara sakkowa,Abbah ne a gaba Ammi na bayan sa,sai Mima sun bala'in kara kyau,ga wani fresh da suka karayi,ga hasken da suka kara,mika wuta yaci gaba dayi burinsa ya hango Hamna."Sanda yayi arba da ita saida numfashin sa ya kusan daukewa,ashe ba komai yake gani a video call da sukeyi ba.Ta kara kyau,haske,yammatancin ta sai ya sake fitowa fiye da yadda yake ganin ta,gown ce maroon color ajikin su ita da Mima,ta karbi farar fatar su musamman Hamna.

"Dago kanta tayi tana hangen 'yan uwanta,iyayan ta,da yayyan ta,idanun ta ne ya fada kan Sadauki da yake sakar mata kyakykyawan murmushi,kamar bashi dinnan ne miskili ba,ita ma murmushin take sakar masa,idanun ta ne ya ciko da kwallah tuna yanzu fa bazata iya magana da kowa ba,saidai nuni da hannu.Kara sawa tai gaban sa,gaba daya dama hankalin ta na kansa,agabansa ta tsaya fararan hakoranta na sake budewa, hugging dinsa tayi cikin Farin cikin ganin sa.Murmushi yayi tare da jan kumatun ta.Iyayan su kallon su sukeyi cikin jindadin yadda suke son junan su,hannun ta ya kama ya sakata a mota,babu wanda ya jira acikin su yaja motar ya fice daga airport din,bin su sukai da Kallo baki sake,kallon juna sukai kafin su saka dariya,kajimu da yaro yama manta damu,da yake ya dauki kanwar sa sai yayi tafiyar sa.

"Murmushi Big Daddy ya saki jin yadda suke ta yiwa Sadauki tsiya.Abbah ne yace kunga ku kyalemun yaro kunsan tsakanin sa da Hamna ayi tsiya ayi dadi, Lallai kuwa inji papi,nima abunda nagani kenan,mota suka dunguma gaba dayan su,sukai Gida."Sanda Sadauki yayi parking a harabar makeken gidan,dai dai Lokacin Khalid ya fito zai fice daga gidan,Hamna ya kurawa idanu,kallon kurilla yakeyi mara daga sama har kasa,wani mugun yawu ya hadiye,ganin yadda yarinyar ta cika tako ina,wani murmushi yasaki wanda shikadai yasan maanar sa,hade fuska Hamna tai haryanzu ta tsani Khalid sosai takejin Haushi sa,saima ta kalli askin kansa yadda kasan ba musulmi ba,ya tara uban gashi a tsakiyar ka kamar rakumi,ya aske gefe da gefe,babu yadda Big Daddy baiyi dashi akan yayi aski ba amma yaki zuwa yayi,saboda mom ta daure masa kugu,saidai yayi abunda yaga dama.

Jan hannun ta Sadauki yayi suka wuce shi,ganin irin shedanin kallon da yake bin Hamna dashi,sam beyiwa Sadauki dadi ba,ransa sosai yayi mugun baci,baya san kulashi ne suyi sa'insa shiyasa ya shanye ya jata sukai gaba.Mom tana main parlou ta cakare kamar me zuwa gidan Biki,ba Komai yasata wanann kwalliyar ba,sai yadda burinta yau zai cika,zata ganewa idanun ta yadda yar iskar yarinyar can ta koma,idanun ta kyar abakin kofa ta dora kafa daya kan daya,tana jiran taga ta ina zata bullo...


     Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
        .......✍️✍️✍️✍️


                     'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

    *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 35_36


"Da sauri Mom tata so,kamar wadda taga diyar ta,oyoyo my daughter tare da rungume Hamna,oh Allah sarki Hamna,ba karamin missing dinki nayi ba,kin dawo lafiya,shiru ba bayani,face din Hamna adaure take haryanzu bawai daina tsanar Mom tai ba, àah tsanar na nan azuciyar ta."Hawaye nagani yana zuba a idanun Mom Shar shar,wanda na rasa Lokacin data kakalo shi,baki hangame nake kallon ta,lallai makircin Mom yakai Inda yakai,kedai Allah ya baki Lafiya,da dane da yanzu maganar ki ta karade gidan nan amma yanzu kaji shiru,lallai me lafiya dan gata,suna tsaye sun zuba mata idanu,duk da Hamna batajin abunda take fada,amma yaga yadda take sharar hawaye,tunanin ta yaushe Mom ta fara kaunarta da har zatayi Kuka akan ta,anya wananna kokan nata na gaskiya ne,hakanan taji kukan be kwanta mata ba,tabe baki tai suka hada idanu da Saidauki,wanda ya kame yake ganin tsantsar makirci irin na Mom,ko kadan bai yadda da wannan munafikin kukan ba,kar yake kallon ta,wannan kukan farin ciki take bawai kukan damuwa da bakin ciki ba.

"Murmushin gefen baki ya saki yana bin Mom da wani shegen kallo,sàida ta tsargu ganin wani malalacin kallo dayake mata,amma mannewa tai bata nuna afuskarta taga yanayin kallon ba."Kaita bedroom dinta ta huta,kafin azo aci Abinci,babu musu yaja hannun Hamna,wadda take bin Mom da kallo kamar wawiya."Wani banzan kallo ta raka bayan su dashi,sanda taga kulewar su tsaki taja me sauti,hmm angaya miki ana taba Jamila akwana lafiya,yanzu sainaga bakin rashin kunya da futsara,mara Mutumci kawai,kadamma kika gani indai nice, ba'a tabani awanye lafiya."Part din Ammi ya kaita"ba tare daya ce komai ba ya cika hannun ta ya juya cikin sauri,bin bayansa tayi da kallo tana tunanin abunda ya canza yanayin sa Lokaci daya."Karewa part din nasu kallo take da aka kara kawata shi da abubuwan more rayuwa,an sake hyarashi fiye da yadda suka tafi suka barshi.

"Kafarta tasa a cikin parlon daddar Iska me dadin shaka da kamshi na musamman ya daki hancinta,ko shakka babu wannan Aikin Mammah ne, Mom bazata taba yin wani abu na azo agani ba.Kan sofa ta fada tana Lumshe idanun ta da bcci ke fisgar su."Ahankali ya fada kan bed dinsa,wani abu yakeji akan Hamna,wanda yake gwagwarmaya dashi a zuciyar sa,abun kunya ne agare shi ya fito da abunda yake damun zuciyar sa tsahon shekaru."Kyakykyawar fuskarta da akullum take masa gizo a farke ko ido biyu yake kallo, murmushi ya saki wanda shi kansa besan ma'anar saba,komai nata burgeshi yake yi,tunowa da Jawahir haka nan yaji ransa ya baci,sam bata daga cikin jerin matan da yake so,amma matsawar Dady yasa ya nuna ta matsayin abokiyar rayuwar sa."Mom kamar ba ita ba sanda ta amshi su Ammi,kamar zatai goya su akokarin ta na nuna farin cikin dawowar su,Ammi tayi mamaki sosai,amma data tuna wacece Jamila zulwajahaini,sunan data rada mata kenan,sai batai Mamaki ba,ta iya badda kama,ta yadda bazaka taba gane ainihin taba,kullun caccanzawa take kamar wahainiya.

"Tunda Hamna ta kwanta,sai bayan Sallar La'asar ta farka,Addu'ar tashi daga bacci tai a cikin zuciyar ta, ahankali ta sakko fararan kafafunta tamkar bata taka kasa,wanka ta shiga fitowa tai daga ita sai karamin towel,ni kaina sàida nace ma sha Allah,ganin yadda Hamna ta zama cikakkiyar budurwa,kamar ba ita ce'Yar Aron Dada ba kirji ashafe kamar faranti,yanzu kam babu wanann tako ina ta cika,ga shinta da take ja yasha gyara,kwayar idanun ta brown ce tamkar ta Sadauki,idanun su iri daya ne,suna tsananin kama saidai ta nuna masa hasken fata kadan.Idanun su kullum alumshe suke kamar masu jin bacci,idanun su biyu zaka dauka bacci suke yi.

"Help gown ta saka mara nauyi,hular net ta dauka ta saka,babu abunda ta shafa sai lipstick data dan goga,sai takara yin wani fresh Kamar baby haka take,har yanzu bata da kiba,tana nan lange lange da ita."Part din Sadauki ta tafi."Baya parlour sanda tashiga,bata tsaya ba ta shige bedroom din sa,ganin baya room din a zauna abakin bed tana jiran fitowar sa.Phone dinsa ce ta fara kara,sauka tai dantaga wanene akan layi,Jawahir taga anrubuta,kurawa sunan idanu tai kamar mesan ta tantance wani abu,harta katse bata daga ba,sake kira akai a karo na,tome zatace inta daga,ita da ba magana takeyi ba."Kawai jitai bari ta dauka,ko dantaga wacece take kiran yayan nata."Picking tai babu wani sauti da taji akunnan ta,hawaye taji yana sauka akan face dinta,ko zata kara ji ko bazata kara jiba bada ta da masaniya akan hakan."Tunda ya fito ya tsaya abakin toilet din yana kallon ta,hawayan ta dake zuba jiyake kamar yana zuba a zuciyar sa.Ahankali ya tako har gabanta,zare wayar hannun ta tayi sai Lokacin tasan da fitowar sa,kauda kanta tayi ganin sa dagashi sai towel da ya daura a kugu.Kokarin goge hawayan ta takeyi,da sauri ya duka agabanta,face dinta ya kamo yana kallon idanun ta,saurin lumshe idanu tai ganin yadda idanun sa ke mata wani irin kwarjini,da hannun sa yasa yana goge mata hawaye.Alama yayi mata Meyasa take Kuka,da hannu take nuna masa Saboda batajin abunda aka fada a phone dinsa,zata kara ji kamar kowa kuwa?ba karamin tausayi ta bashi ba,gyada mata kai yayi alamar zataji radau kamar da can baya,yayi mafarkin hakan agare ta,ta warke sosai, murmushi ta saki fararan hakoranta suka bayyana,shima murmushin yayi ganin murmushi akan face din ta.

"Wacece take kiranka awaya?matata wadda zan aura Kwana kusa,idanu ta dan bude tana kallon sa,wife kake nufi,gyada mata kai yayi alamar eh, murmushi ta saki tana kallon sa,kenan kaima zaka zama Dady Maman Baby,mamaki ne ya kamashi yana kallon ta,dariya ta kyalkyale da ita har tana kwanciya akan bed din sa, murmushi yayi ganin wai tsokanar sa take yi,mikewa tai ta dauki karamin flow ta saka acikin ta,kwatanta masa tai alamr haka matar zata koma da katon ciki, murmushi kawai yake saki,ya tabbatar Hamna fahadin farin cikin sa ce.

"Ta jima tana tsokanar sa kafin ta zauna tana maida Numfashi."Kallon sa tai ina sarkata,wadda kace ta zama tawa,hararar ta ya danyi,saidai in zaki zama maman babyn da za'a haifomin kinga shikenan,make kafada tai alamar a'ah,ni kawai ka bani sarka ta,minyi alkawarin innagirma zaka bani,mikewa tai tana jujjuyawa agaban sa,wai ya kallah tayi girma yanzu,yadda take jujjuyawa yasa yaji wani abu na tsirga masa,da sauri ya kauda kansa yana korar shedan."Murmushi tai kafin ta wuce wardrobe dinsa,dubawa tai tana son gano inda sarkar take,ta dauke abarta tunda Alkawari ya cika ta girma."Ganin bata ganta ba yasa ta juyo tana bata fuska, murmushi kawai ya saki ya isa gaban mirror din sa."Shafe shafe ya zauna yi tana kallon sa,hakanan taji Yayan nata ayau yana matukar birgeta,sai binsa take da kallo alamar ta yaba da wankan nasa."Kaban kaya ya saka kafin ya feshe jikinsa da turarruka masu kamshin gaske.Alama yayi mata akan tazo,babu musu tataso ta kara so gaban sa, phone dinsa ya dauko ya fara kashe musu selfie,sosai sukai selfie cikin Nishadi da walwala,sunyi masifar kyau,wasu yayi hugging dinta,wasu ta dafa kafarsa,wasu ya goyata tamkar Larabawa haka sukai matukar kyau.

  "Kama hannun ta yayi suka nufi maine parlour,gaba daya sun hallara dan fara cin abinci,tunda suka shigo kowa ya zuba musu idanu"sosai sukai masifar machine sai sakin murmushi sukaeyi,abunda da wuya ka ganshi a face din Sadauki,amma yau da wowar Hamna sai murmushi yake saki.Iyayan su zuba musu idanu sukai suna kallon su, murmushi dauke akan face din su,tabbas sun hango wani abu tare da yaranna su........

        Mrs 🌹 Baba Bello Abubakar
             .......✍️✍️✍️✍️


                'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

   *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 37_38

"Kusa dashi ya zaunar da ita kafin shima ya zauna,ganin yadda ake binsu da kallo yasa ya gimtse face dinsa,gaida iyayan su sukai atare,kafin su fada cin abincin su,sàida suka kammala,sannan yayi mata alamar tazo tai masa rakiya, kallon Ammi tai tana sanar da ita abunda Sadauki yace,gyada kai Ammi tayi alamar sai sun dawo,mayafin rigarta datai rolling dashi suka fice,duk abunda  suke Khalid na kallon su,takaici kamar ya kashe su,komai nasu daya hatta kamannin su,yana jin haushin wanann abu sosai."Sit din gaba ya bude mata da kansa,shiga tai ta zauna kafin shima ya zagaya ya bude,shiyake driving din,babu bakin surutu shiyasa motar tai tsit babu me Magana acikin su."Wata babbar unguwa ya nufa da ita daidai wani babban get ya danna hon,da sauri get man ya wangale masa kofa sanin wanene shi Agidan."Fitowa sukai tana karewa gidan kallo,babban gidane sosai daga gani mutan gidan sun tara sosai."Kallan sa tai da alamar tambaya,Wajan Antynki na kawo ki,dan ki gaishe ta,bata ce komai ba,wayar sa ya dakko yayi Maganar minti one kafin ya gyara tsaiwar sa.

"Tsaiwar kusan mintuna 5 sukai suna baza idanun ganin ta inda Jawahir din zata bullo,kamshin ta ne ya isar da sakon zuwan ta,tundaga nesa take kallon su kamar yadda suma suke kallon ta."Idanun ta akan Hamna ya fada,sàida gaban ta yayi mummunar faduwa,ganin wata me tsananin kama da Dear din ta.Daurewa tai ta fata sakin murmushi,Hamna haka nan taji Jawahir din batai mata ba ko kadan,dinke face dinta tai ta kauda kanta daga kallon ta."Cikin karairaya Jawahir ta kara so"fada ce amma ba sosai ba ta kara da kai,tana da kiba wata shirim da ita kamar kayan wanki,takaici ne ya kama Hamna ganin aba saikace dorinar ruwa,yanzu Yayanta ya rasa wadda zaiso sai wannan Abar.Asslamu Alaikum Jawahir tayi sallama,dan a ka idar Sadauki ya karanta mata abunda baya so tun farkon haduwar su.Kara tamke face Hamna tai ta kauda kanta gefe,ko kallon barin da suke ma batasan kallo gaba daya basu dace da juna ba."Dear kanwar muce wanann amma,gyada mata kai yayi alamar eh,da kyar Hamna ta daidaita kanta ganin irin kallon da Sadauki yakeyi mata,da hannu tai mata alamar gaisuwa,zatan Jawahir iyayine,kaji shegiyar yarinya ni zayiwa wannan abun.

"Katse mata tunani yayi wannan ce Hamna da nake baki labarin ta bata ji ba kuma tayin magana,alamun alhini Jawahir ta nuna afuskarta,Allah sarki ashe bata ji,amma azuciyar ta,cewa take gwara haka,wannan yarinyar da tana magana daga gani zatai rashin ji.Daga haka Hamna bata kara kallon su ba,saman motar ta haye tana kallon yadda tattabaru me shawagi asama,shima suna gama gaisawa yayi mata sallama,kallon Hamna yayi tataho su tafi."Mota ta shiga ko kallon Jawahir batai ba,wadda tai tsaye tana kallon ikon ALLAH.Sanda suka fara tafiya ya kalli yadda ta turbune fuska,bece mata komai ba,suna zuwa gida ta fice daga motar be ankara data fice din ba,goshinsa ya dafe yana tunanin abunda ya fusatata haka."part din mommah ta nufa,suna zaune ita da Big Dady suna hira."Jikin Momma ta kwanta,kallon ta sukai ganin yadda ta canza kamar ba ita ce ta fita da walwala ba.

"Yadai mamana,Mikewa tai tana kallon Dady da Mommah,yanzu nake naga matar da Yayana yake cewa zai Aura,wata katuwa,me katon kai,me budareren hanci,bana santa Mommah a sake wata,ni natsaneta ma,bataimin ba,akwai kanana kamarni,asako wata,amma banda wannan."Tunda ta farayi musu nuni sukai sakare suna kallon ta,baki hamgame ganin yadda take kuka,tana sake maimaita musu bata san Jawahir tare da Yayan ta."Kallon juna suke Mommah da Big Dady,sake maida kallon su sukai kan Hamna,wadda ta zuba musu idanu taji hukuncin da suka yanke."Murmushi Dady ya sakar mata,mika mata hannu yayi alamar tazo,da sauri ta mike ta karasa him sa,zama tai tana sake matsar kwallah."Dafa kanta yayi,mamanah kodai ke zamu bawa yayan naki,ni ta nuna kanta,gyada mata kai yayi alamar eh,ni kadai amma banda wancen katuwar,in har ni kadaice na yadda Dady,dama nice wife dinsa."Labarin binsa bashin sarkar da takeyi tai masa,dama can baya yace ita wife dinsa,to yanzu aje Gidan su waccan lukutar,har kwatantawa take,wai me kama da Mom dinnan,ace yayanta ta fasa,ita zata zama wife awajan sa.

"Dariya kamar zata kashe Mommah takara tabbatarwa har yanzu Hamna batai hankali ba,15years amma babu ruwanta bata boye abunda yake xuciyar ta, murmushi Big Dady yayi,ki kwantar da hankalin ki,abunda kike so shi za'ayi Mamana,yanzu kije ki fara shiri kema Amarya ce,Dariya ta kyalkyale da ita,tana nuna kanta wai da gaske yake an fasa da waccan?gyada kai yayi alamar eh,da sauri ta mike ta fice da gudu cikin matukar farin ciki."Jitai anjawo ta da mugunkarfi,saidata razana,can lungun Gidan su ya jata,kiciniyar kwace kanta takeyi amma ya kasa bata damar hakan,gaba daya ta firgice gane a hannun wanda take din,daddagewa tai ta gantsara masa cizo,babu Arziki ya sake ta,da sauri ta fito daga lungun tana kallon sa,tsantsar kiyayyar sa ke sake mamaye zuciyar ta."Khalid da cizon da taimasa yayi masifar kona masa rai ya tsaya yana kallon ta,kai dan Iska ne dama,kana tabani,ni ba 'yar iska bace saina fadawa Ammina Abbah na da Yah Sadauki,hararar sa tayi tai tafiyarta ta barshi anan,rakaicin duniya ya ishi Khalid kamar bakin ciki zai kashe shi.

"Part din Ammi ta wuce farin cikin da take ciki yasa ta watsar da Maganar Khalid din,Ammi Jitai kawai an fado ajikin ta,wash Hamna zata karya ni,Dariya ta kyalkyale da ita,yau ina cikin farin ciki Ammi,ina Abbah,nuna mata tayi yana sama,da gudu ta mike,yana zaune yana aiki a laptop din sa.Jin Karar bude kofa yasashi daga kansa,shigowa tai tana murmushi,kallon ta yayi shima yana murmushi abunsa,kusa da shi ta zauna,ajiye laptop din hannun sa yayi yana kallon ta.Abbah yau ina cikin farin ciki,name?yayi mata tambaya,Dady yace nice Amarya,Amaryar Yayana,banason waccan matar tasa,ta cika girma,wata katuwa da ita bana sonta,Dady yace na kwantar da hankalina nice Amaryar ba ita ba,har da wani yamutsa Fuska.

"Kallon ta Abbah yake yana nazarin maganar ta,shirme ya dauki zancan nata,natayaki farin ciki daga haka yaci gaba d aikin sa,yasan shirman Hamna,shiyasa bema bi takan maganar taba.

   Hmmm Hamna fa da gaske take wannan Maganar,tirka tirka ya za'a kare tsakanin Sadauki da Jawahir,acikin Hamna da Jawahir wacece zata samu nasarar mallakar sa.......

       Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
         .......✍️✍️✍️✍️


          'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

 *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 39_40

"Jawahir rai bace ta shiga kayataccen parlon su, Mom dinta dake zaune taci uwar kwalliya,macece yar kwalliya ko yaushe zaka sameta tas tas da ita,taki yadda ta kowani hali Alhaji Saminu yayi mata kishiya,ta dauke hankalin sa daga kan kowa ce Irin mace,ita kadai yake gani,atakaice ma yanaji aransa bazai taba iya zaman da wace mace ba bayan ita.Shiyasa takecin karanta babu babbaka,ta kafa uban dauri aka."Jawahir take kallo tunda ta shigo,yanayin face dinta kawai ta kalla ta gane akwai damuwa.Ke Jawahir lafiya?ya zaki fita da farin ciki ki dawo kina dacin rai,kara tamke fuskatai."Mom dole ki ganni haka,wata yarinya Sdk yazo da ita,bakiga yarinyar nan ba,kyau kamar ita tayi kanta,kamar su daya da Sdk,abunda ya batan rai yadda yarinyar nan ta dinga min kallon hadarin kaji,gaba daya fa Mom bakiga yadda ta kalline ta watsar ba.

"Wace yarinya ce wannan?wacece ita awajan sa,yadai cemin sister dins ce"koma wacece wannan tabbas tana da Babban matsayi a zuciyar sa,tunda har ya kasa tsawatar mata,kuma yana ganin kalar kallon da take miki."Nima abunda nake tunani kenan,Hajiya Sarah muskutawa tai tare da sakin tsaki,shiyasa tun farko nace ga samari nan bila adadin kina dasu,ga Kamal yaronnan yadda yake matukar kaunar ki,amma haka kawai kin nacewa wanda be damu dake ba."Tunda kuke ya taba cewa bari yazo ya gaisheni,matsayina na Uwar ki,kinga bakya gabansa kwata kwata,zan baki shawara matsayina na Mahaifiyar ki,ki saki wannan yaron ki kama dahir,ni naji araina ma ba Aurar ki zaiba tunkafin Lokaci ya kure miki ki sake shi ki kama wani nadai gaya miki."Shiru Jawahir tai tana tunanin abinda Mom dinta take cewa,kome ta fada gaskiya ne,ita kanta ta san Sadauki be damu da ita bag gaba daya,ayadda ta lura da wanann kanwar tasa ta hango kishin sa akwayar idanun ta,ai ita bag yarinya bace tasan me takeyi.Mikewa tai jikinta asanyaye ta haura dakin.

"Saura 3weeks Biki yanzu"Mom ta kasa zaune ta kasa tsaye zata Aurar da 'ya'ya biyu,Khalid da Sumayya.Mammah kuma Sadauki da Najma da Basma,Hamna sune kannan Amarya sai shige da fice akeyi,duka abun da akwaiwa amare ita ma saitace sai ammata,haka Mommah take hakura da rigimar ta aimata,ko yayyan ta Mima da Khairat basa cewa sai ammin su sai ita."Gaba daya zuciyar Sadauki a jagule take, zuciyar bata san wannann Auran amma babu yadda zaiyi ne,gidan su Jawahir ma ana ta shirin Biki tako ina za'a Aurar da 'yar gata, Hajiya Sarah babu zama kullum tana waje ana shirin Biki."Event guda hudu aka shirya,Momma da Ammi sun tsaya tsayin daka ganin anyi komai na harkar girma,Dada ta diro gidan Biki da tawagar ta,mota guda sukayo saura 2weeks Biki,gaba daya sun gigita rayuwar Gidan,babu shiri Dady ya bude musu part din Dada suka koma can,shine aka samu salama.

"Duk kayan da Saidauki ya dinka"to yayiwa Hamna irinsa,komai iri daya yake yi musu,ko Amaryar tasa baya tunawa da ita Hamna ce kawai agaban sa."Angama hada lefen Khalid da Sadauki,rana daya akai niyyar kaiwa,gidan su Jawahir sukace Al'adar su sai ranar daurin Aure ake tafiya dashi,hakan yasa aka bar nasa aka dauki na Khalid,itama yar manyan mutane ce,gidan su babu kwaba,kowa rayuwar dayaga dama ita yake yi.'Yan uwan Hajiya Kudrat din gogaggun 'yan duniya ne masu idanu atsakar ka,akwati 8 aka kai musu a yatsine suke kallon kayan,babu sannu da zuwa haka suka zurawa su Ammi idanu,kallon hadarin kaji suka dinga jifansu dashi.Ammi da Mommah sai dada abun ba karamar kular dasu yayi ba.

"Basu gama shan mamaki ba"sàida wata busashshiya tafito,tana rangwada,kananan ya sha attached tasha uban mai,ba gaba ba baya tasa wani wando pencil da wata yar riga.Feedo Amarya,kara so ga kayan da dangin miji suka kawo,cewar wata daga cikin yan karbar kayan,idanu su Ammi suka bude ganin wai wannnan ce Amaryar,ikon Allah kadai suke kallo,Dada da hannun ta ke kirjinta tana bin wadda aka kira Feedo da idanu, lallai akwai gagarumar matsala."Zama  agaban kayan,ah bari na kalli kayan Aure na,koya kuka ce guys dariya suka.sa kwarai kuwa,to na wanene in baki kalla ba wazai kalla Autar Mom,Hajiya Kudrat ce tai wannan maganar."Babu wani abu aranta ta zauna tana daga kayanta,daya bayan daya saidata gama kallon su.Amma gaskiya ni Mom nayi zatan 24 za'a kawon saboda ganin yadda nake dinnan kamar nafi karfin akwati 8,amma bakomai zanyi manej."Sai Lokacin ta kalli barin dasu Dada suke,gaba daya fuskokin su a turbune suke,ganin irin gidan da suke neman hada zuri'a dasu.

"Hi Granny Feedo ta fada tana dagowa Dada hannu,ran Dada sake baci yayi,mikewa tai ta kallo su Ammi,kai kutashi mutafi ashe bagidan masu mutunci Khalid yaje ya nemo Aure ba,kalli wai wanann amarya ce,shegen nono kamar silifas ko nawa Albarka,fa rashin tarbiyya daga uwa har dangi,to shikadai zai dakkowa kansa,dan wannan me kama da maburgin bazaki zo kifagawa Mutane hankali ba,gayyar tsiya kawai."Hajiya Kudrat ce ta mike, a'ah tsohuwa wllh karkija abunda zai sa mu nada muku na jaki,daga abun arziki min baku yar mu shine zaku zo har Gida ku fadawa Mutane magana."Anfada muku,cewar Rakiya daya daga cikin surukan Dada ne,yawwa gaya musu Rakiya,Rakiya 'yar rigima ce bata barin kota kwana,Innar Auwalu ma mikewa tai,wllh Dada ki barmu mununa musu komu aslalin suwanene,yanzu da 'yar tasha za'a hada zuri'a.Wannan gaba daya Munafurcin Jamila ne,ninasan tasan halin wadannan masu kama da arnan farko.Cacar baki ce ta kaure ana neman abawa hammata Iska.

"Feedo ce ta mike"wllh da sake Bazan yadda da raini daga dangin miji ba,bayan ma tsiya ni babu abunda zai hadani da dangin miji,naso ace uwar sa ma ta wulla tuntuni,ta wulla gidan uwar wa,wata kanwar Mom Jamila ta fada,duka rashin kunyar gidan su yau sunga wadanda suka dame su.Dan suma gidan su Mom ba baya bane wajan rashin tarbiyya da rashin kunya."Ina kuwa zata wulla can Lahira nake nufi,kanta rufe baki rasheeda kanwar Mom ta kaimata wata mahangurba a fuska,kokawa ce ta kaure tsakanin rasheed da Feedo,shegen attached din kanta ta jawo saiga gashi kamar na jarirai anyi wasu kananan kalba aka."Rakiya dama babu wadda tafi bata haushi irin Hajiya Kudrat daurin dankwalin kanta ta tuje, sosai suke dukan juna,su Ammi ne masu rabon fada,Innar Auwalu ma wata kawar haj Kudrat suka fara casuwa.

"Dada samun kushin tai ta kame tana kallon yadda ake casar su Hajiya Kudrat ranta fes,harsu zasu kawowa Iskanci,saidata tabbatar jikinsu ya gaya musu tukunna taiwa su Rakiya magana su barsu haka,dauke kayan lefen su sukai akan bazasu yadda da wannan Auran ba,sosai su Feedo suka sha shegen duka.Haka su Dada suka.dawo rai bace,suna dawowa Mom tafito ta rar su,ganin kowacce fuska cunkushe yasa ta tsaya turus tana kallon su."Ko dakko kayan dake mota basi ba suka dunguma cikin parlon gaba daya."Lafiya Dada na ganku gaba daya ranku bace,ina kuwa Lafiya Jamila kin daurewa danki kugu yaje ya dakko yar tasha,yanzu sàida akaci uwar sabada kafin mu baro Gidan.Yana ina shi Khalidun wllh baza'ai wannan Auran ba,inko yace sai anyi to saidai ku karata ke dashi,kome tai muku babu me zuwa ya tare muku fada nagaya miki.

"Sai Lokacin kowa bakinsa ya bude,Innar Auwalu da taketa haki har Lokacin fadi take aini bantaba ganin tanbadaddun mutane irin wannan gidan da Khalid yaje ya dakko Aure ba,amm ko Yanzu sun tabbatar babu abunda zasu ci ajikin mu,saidai su sha duka abanza,tsaki rakiya taja,kibari Innar Auwalu mu har za'a gaya mana rigima ne,ai gidan suka tarar wllh,wannan da anan garin nake sai sunga ikon Allah,gidan zan koma bayan anyi bikin da tamin abunda bai gamsheni ba zanja hegiya na zaune,dama gatanan kamar an tsoma kaza aruwan zafi,dariya suka fashe da ita.

"Mom fa tana tsaka me wuya,haj Kudrat kawar Zaitun ce kut da kut yanzu in har tace anfasa wanann Aure zata samu matsala.babba dole tai wani abu akai....

           🙄🙄🙄Lallai Mom kina ruwa tsamo tsamo..

         Daga Alkalamin Kulsoom
          ......✍️✍️✍️✍️


            'YAR ARO


Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris


 *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 41_42

"Abunda ya hanata yadda da hukunci Dada kenan,sanda Khalid ya shigo Kamar Dada zata rufe shi da tsinannan duka,fada takeyi Kamar zata ari baki,yanxu karasa Inda zakaje neman Aure sai Gidan karuwai,ni wannan Uwar tata daga gani irin yan tuwo tuwonnan ne da suke yawo atasha,to ahir dinka,inko harka dage saika dakko wannan me kama da sauron,saidai ka karata acan kai da ita."Tunda Dada ta fara magana yake kallon ta,ya mutsa fuska yayi,ke kuma fa,ni zakicewa wai na hakura da Auran Feedo,ita ce Yarinyar data kwantamin duk garinnan,ko waccan kurmar kike so ki hadani da ita,lalala bazan Auri ra gowar wani kato ba."Babu wanda be dago ya kalle shi acikin parlourn ba,hatta Mom bataji dadin yadda yayi subul da baka ba,bata so ace sun fito da kiyayyar su afili ba."Cikin hargagi takai masa mari,kai baka da mutunci ko,kanwar taka kake jifa da wanann mummunar kalmar,ahir dinka,karna sake jin wanann maganar abakin ka.

"Zayyi magana ta kifta masa idanu,da yake rainon tane tuni ya gane inda ta dosa,ka bace min dagani mara kunyar banza,ficewa Yayi daga part din gaba daya.Juyowa tai tana bawa  Dada hakuri wadda ko ci kanki batace mara ba."Tana fita daga part din Dada ta wuce part dinta,hango Khalid azaune ya sata karasawa da sauri,kai wane irin yaro ne me shegiyar kiriniya,so kake ka tona mana asiri ko kuwa,komai ana yinsa asirran ce amma kai banda kai."Yanzu Mom menayi wai da kike tamin shouting aka,cikin jin haushi Mom ta dalla masa Harara,dole kace haka mana.Yanzu Abunda nke so dakai awane matsayi kaajiye Feedo,tananan a na wadda zan Aura.Good dama nima ban yarda ka rabu da ita ba,kasan dai yadda muke da Zaitun,ba nason ko kadan kayi abunda zai lalata zumuncin mu.Kuma ni maganar da duka fadama sam banyarda da ita ba,inada tabbacin su dada ne basu da gaskiya.Sune na cewar Khalid da yake faman hura hanci,Feedo ta kira shi ta gaya mai karya da gaskiya yahau y zauna."Ni Mom ba gudu ba ja da baya inason kayata ahaka.

"Nima daman ba nufina afasa ba"kaje kaci gaba da shirin ka"in yaso ko da kankane kadauki kayan lefen ka mayar musu,hakan ma za'ayi Mom."Babu wanda ya kara bi takansu da maganar dasa biki,kowa ya zuba musu idanu.An kawo lefen Basma da Najma da Sumayya,akwatunan Najma 10 na Basma 8 na Sumayya 5,wayyo ai ranar Mom jitai kamar zuciyar ta zata babbake tsabar bakin ciki,taya zaai akawowa 'yarta akwatuna gida Biyar,da sake amba me kaza kaida kafa."Agabanta tasa Sumayya ta kira Faisal din ta kora masa jawabin kaya sunyi kadan,babu musu tabi umarnin Mom ta kirashi."Babu kunya ta dinga gasa masa maganganu akan kayan,aiko yayi mata wankin babban bargo,dayake shima dan haune haka yadinga cusawa uwarta zagi,sosai hankalin Mom ya tashi jin yadda surukin nata yake daman zazzaga fada in har basason kayan su bashi abun sa."Ganin za'a bata goma daya bata gyaru na,sai Mom ta amshi wayar ta fara rarrashin sa,da kyar ta samu ya sakko aka daidai ta,ta tabbatar masa kuruciya ce irin ta Sumayya amma yayi hakuri hakane bazata sake faruwa ba.

"Sumayya dake risgar Kukan takaici da damuwa, Mom Gaskiya na fada Wannan Auran,kallon baki isa ba Mom take mata,so kike ki tona mana asiri wannan Auran babu fashi na gaya miki,haka Sumayya ta wuni tana Kuka,gaba daya Auran Faisal ya fita daga zuciyar ta,ya zama dole awanann karan ta nunawa papi shine Mahaifin ta,ta dade tana biyewa Mom suna tsula tsiyar su tare,ta manta da papi shidin me Matukar kaunar sune da sasu ahanyar dai dai,yau arana ta farko ta gane Mom ba tarbiyya ta basu ba,ruguza rayuwar su ta dingayi da hannun ta."Karfe 9 ta isa dakin papi,yana zaune yana karatun Alkur'ani ta zube agaban sa,cikin mamaki yake kallon ta,gaba daya tafita daga hayyacin ta,idanun ta sunyi luhu luhu alamar ba karamin Kuka tasha ba."Saida yakai matsaya kafin ya juyo ya kalle ta,fashewa tai da Kuka tare da ruke dukkan hannayan sa,lamarin daya kara daure masa kai kenan."Sumayya me akai miki kike irin wanann Kukan,papi na fasa Auran Faisal bashi da tarbiyya,besan daraja ta,data iyaye na ba.

"Dukkan abunda ya faru adazu ta sanar dashi Komai,,shiru yayi yana kallon ta,ai shine dai dai dake Sumayya,irin tarbiyyar ku daya ta rashin sanin girma da daraja na gaba daku,anan wajan na kiraki naja miki kunne ki rabu da Faisal ba yaron Arziki bane mekika cemin,kunya ce tai Matukar kamata sunkuyar dakai tayi dan tuna irin maganganun data fadawa mahaifinta batare da taji wani shakka ko dar azuciyar taba,ayau din sai ta gane babban kuskuran data tafka,hawaye tashare kayi hakuri papi.Murmushi ya saki mefadi Addu'a sa a kullum Allah ya shirya masa yaransa,yanzu ya kike so ayi,hawayanta tashare tana kallon sa afasa kawai papi daga baya Allah zai kawon wanda zai Aure ni,ni ina da wanda zan baki matukar zaki zauna lafiya kiyi biyayya agareni.A shirye nake papi da karbar dukkan umarni daga gareka,ina da yakinin bazaka taba kawon abunda zai cutar dani ba,Allah yayi miki Albarka, murmushi tasaki Ameen papi,mikewa tai cikin Farin ciki tabar dakin zuciyar ta fes.

"Bangaran Hamna babu zama"kullum tana tare da Saidauki ita ce babbar abokiyar ango,gaba daya bata tabikin yan uwanta saita bikin yayan ta,kome zaisiya tare suke zuwa su suyo shi, Munir yasha yiwa Sadauki cari wanann alakar tasu tayi zafi dayawa babu wanda ya cancanta ya Aura sama da Hamna,basar da maganar Munir din yake saboda yana fama masa wani rami ne dake zuciyar sa."Amfara gudanar da Biki cikin kwanciyar hankali,tako wane bangare shan shagali sukeyi,duk wani event da suka shirya babu Jawahir babu dalilin ta,kin zuwa tai gaba daya,shima Sadauki ba damuwar sane taje ko kar take ba.

"Kwalliya ta musamman ya dauki Hamna ya kaita,Sàida ya gigice sanda yaga tsabar kyawun tayi,kaya iri daya suka saka ba karamin dacewa da juna sukai ba,ko wajan party din tare suka shiga,babu wanda beyi.mamakin ganin Hamna ta haye kujerar Amarya da Ango ba, selfie aka dinga haska su."Khalid daya kalli Hamna ya kalli Feedo sai yaga babu ma hadi,wani abu yadinga ji azuciyar sa,da yasan hakane da ya nemi Auran ta,ta yadda zaici Ubanta babu wanda ya sani,amma yanzu ma be makara ba zai kara da ita,saita zo ata biyu.....

  Tab Lallai Khalid kana ruwa tsunduma....

       Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
         .......✍️✍️✍️✍️


        'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

 *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 43_44

"Kwana hudu akai ana shan shagalin Biki."Yau take Lahadi ayau ne kuma za'a daura Auran Amare da Angwaye,gida jan surukan su mata suka fara zuwa dan adaura Auran Sadauki da Khalid,kamar yadda suka ce sai ranar daurin Aure za'a tafi da kayan lefan Jawahir haka akayi,amota su Abbah suka saka kayan aka dunguma zuwa Gidan su Jawahir,amma sai me abunda ya matukar basu Mamaki,sunan zuwa sukaji andaura Auran Jawahir da wani can daban ba dan su ba,ransu ya baci sosai ganin tozarcin da akayi musu,Mahaifin Jawahir sosai ya basu hakuri da sanar dasu ba laifin sa bane,basu ce masa komai ba sukai Addu'ar Allah yasa ya zama Alkhairi agare su baki daya.

"Daurin Auran Khalid suka wuce ana daurawa suka yo hanyar gida kowa da abunda yake sakawa azuciyar sa,gaba daya Sadauki besan abunda ke faruwa ba sàida Munir ya kora masa jawabi,ajiyar zuciya ya sauke dan kokadan beji wani rashin jindadi a zuciyar ba,saima wani farin ciki daya dira acan cikin zuciyar sa."Daurin Auran Sumayya aka farayi da Angon ta Abubakar,kamar yadda papi yayi mata alkawari,wani yaran abokin sa ya Aura mata,sai Najma da Angon ta Mukhtar,Basma da Angon ta Nura.Adaka ta za'a daura wani Auran.Big Dady ne ya kalli Abbah kawo sadakin danka,cikin mamaki yake kallon Dady bece komai ba ya karkace ya zaro 200k Andaura Auran Umar da Fatima akan Sadaki naira dubu dari biyu lakadan ba ajalan ba."Kowa abazata yaji wannan daurin Aure, musamman Sadauki da ya rasa awace duniya yake,wani mahaukacin dadi ne ya dinga sauka azuciyar sa.Munir ne ya daka masa duka,dan iska munafuki ashe kasan abunda ka kulla amma kaki sanar dani abunda ke faruwa."Bece da Munir komai ba sai sake gimtse fuska da yayi waishi alallai kar ace dama yana san abunda akai din.Dady sake kallon sa murmushi kawai ya saki ya yadda Sadauki Namijin duniya ne,wai shine zai boye abunda ke ransa.

"Khalid ji yayi kamar an watsa masa ruwan zafi,arasa wanda za'a bawa Hna sai Sadauki,yarinyar da tunjiya yagama tsara yadda zai huta da ita amma wadannan tsofaffun sun cuce shi."Acikin gidama labari ya karade An daura Auran Hamna da Sadauki,babu wanda beyi shork ba,duba da yadda Hamnan nawa take kuma ga larurar data sameta,abun zai mata yawa ga kurum ta,ga yarin ta,ga Aure."Ammi gaba daya jikinta sanyi yayi,wayyo zuciyar Mom kamar bakin gawayi haka ta koma ita data gama tsara komai babu wanda zai zo yace yanasan kurma,amma gashi lokaci daya an shammaceta."Mommah kamar ta zuba ruwa akasa tasha,Dada ma rangada guda tai ta tsananin farin ciki yau Allah y nuna mata Auran Hamnan ta.

"Ammi ce ta kalli Hamna wadda gaba daya batasan me akeyi ba,tadaiga yanayin fuskokin su fara'ar su ta karu.Ammi ta tambaya farin ciki name suke yi,na Auran ki da yayan ki,ni amsa da waccan katuwar,gyada mata kai Ammi tai eh dake kadai aka daura,wani ihu tasa da tsalle,kan Ammi tai wani abu da fyalla da gudu,part din mommah ta nufa,tana tsakiyar kawayan ta ta fado dakin,babu abunda ya dame ta har kusa da Mommah ta karaso bakinnan kamar zai yage.Mommah wai ni ce Amaryar Yaya ba'a daura da waccan ba,gyada mata kai Mommah tai tana sakin murmushi,dariya Hamna tai farin ciki ta rasa inda zatasa kanta.Kawayan Mommah da yan uwanta gaba daya driya sukeyiwa Hamna,Allah sarki yarin ta."Fita ta sakeyi ta koma part din dakinta ta fada kan bed dinta ta fada tana dakin Numfashi,yanzu ta zama Amarya,rufe fuskarta tai wai kunya take ji.🤣🤣🤣daga baya kenan Hamna.

"Tun Ammi na damuwa harta watsar akaci gaba da shagalin Biki,Sadauki gagarumar walima ya shirya da abokan sa,sai Amaryar sa daya gayyata da kawayan ta,hhh Hamna Amarya sai rawar kafa takeyi,sai zumudi take taga yayan nata,burinta kawai ya bata sarkar ta,tunda dai gashi ta zamo wife din tasa."A part din Dada ya hada walimar,Hamna tasha kwalliya,dunkin bikin da yayi masu iri daya aciki ta dauki wata pple din shadda,tasha aiki me kyan gaske,farin mayafi aka yafa mata,hakoranta gaba daya sunki rufuwa."Sa'annin ta wanda ta gayyato bikin yayanta sune suka take mata baya,ganin yadda take zirgilli Khairat ta damko ta,nuna mata tai wai taja ajinta,sai yayan ma ya rainata,ya mutsa fuskarta ita babu ruwan ta da wani jan aji,ai yayanta ne,cikin takaici Mima da Khairat suka hambare ta,ke ana koya miki abu na mata amma kinki yadda,Make kafada tai alamar taki din.

"Sanda suka shiga part din ya kawatar da su an qawatashi da waso balo,ga kujeru da aka zuba awajan,tana shigowa Sadauki yana shigowa su Munir na take masa baya,da sauri Dada ta karaso ta ruko Hamna ganin yadda take rawar kafa zata tafi wajan Sadauki,hararar ta Dada tai,ke rufe bakinnan saukin jama ya rainaki,sai washe Biki kike kamar me tallan mackilin,bats fuska tai."Kara sowa wajan yayi wai Dada meyasa kike takurawa yarinyar nan ne,tsaki taja to kadai mataki mana,wuce kije ki zauna ke kuma,babu musu daje Inda aka tanadar mata ta zauna.

"Wani babban malami Sadauki ya gayyato,to amarya dai babu abunda take ji,haka aka tashi daga walimar bataji ko alifun ba.Anci ansha,hatta Mommah tazo wajan,Ammi ce dai taki zuwa, Mom ma bata zoba, hassada tana neman tsinka zuciyar ta."Magariba nayi aka fara shirin kai Amare,an je dakko Amarya Feedo abun maki Amarya harta kai kanta ita da tawagar kawayan ta,abunda ya kara jawo ce ce kuce kenan aka fara hayaniya,anan ma dai ankusa bawa hamta iska,tsakanin su da haj Kudrat,da kyar aka rabu."Sauda aka kai dukkan Amare Sadauki na zuba idanun akai masa tasa,amma shiru wai Malam yaci shirwa.Amarya Hamna tuni ta kwanta bacci ta mantama da wani Aure akanta.

"Suna zaune dukkanin su Sadauki ya shigo kansa asunkuye,gaida su Abbah yayi,ah Ango ya mukaga kanata yawo,ina Amaryar taka,sosa kansa yayi ai ba'a kaita ba Abbah,kallon Momma yayi ya akai haka.Dada da take musu kallon sama da kasa jan tsaki tai,kai wa kuke cewa za'a akai,aiba yanzu zankai Hamna ba,bazai je ya durawa yarinya ciki ba,saita warke garau ta kara girma zan bashi ita,babu wanda beji kunyar maganar Dada ba,kowa bakinsa kullewa yayi,shikan sa Sadauki wata matsanan ciyar kunya ce ta kama shi,Dada ta gama dashi.....
🤣🤣🤣.

     Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
       ......✍️✍️✍️✍️✍️



          'YAR ARO

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

Page 45_46


 *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


"Da kyar Sadauki ya mike yana sunkuyar da kansa,munafukin banza,ka lallabo abaka yarinya ka taushe,tsit parlourn ya sake yi,sai jarabar Dada da take ta tashi,Ammi da Mommah Kamar su nitse dan kunya,ita kuwa babu Abunda ya dame ta."Kamar ya biya ta dakin Hamna Kawai dai ya share,kallon part din nasa yayi,yadda ya kara shan gyara,anzuba sabbin kujeru da labulaye,anan part din dama aka shira masa zama da matar sa,shima Khalid akwai sabon part da Big Daddy ya gina masa,amma yace shi bayanzu zai zauna ba saiya gama cin amarcin sa,awani gidan da abokin sa ya ara masa,babu wanda yace masa kanzil suka barshi yaje ya gama cin amarcin nasa."Washe gari da safe Hamna bayan ta idar da Sallah dakin Ammi ta shiga,da murmushi take kallon Ammi din,ita ma ita take kallo."Gaida Ammi din tayi da yanayin yaren da zata gane na kurame,amsawa Ammi din tai tana shafa kanta,shiru sukai na wani Lokaci kafin Ammi din ta kalle ta,kungaida yayan ki kuwa,girgiza kai tayi alamar àah,to maza tashi kije ki gaishe sa amma karki dade,daga kai tayi alamar to.

"Fitowa tai suka ci karo da Mommah,kokarin shigowa part din Ammi din takeyi,da sauri Hamna ta duka tana gaida ita, Mommah kafadar ta tarike ta mikar da ita,tashi abinki aike Amarya ce 'yar gata, murmushi Hamna din ta saki,tare da rufe idanun ta,wai taji kunyar abunda Mommah din ta fada akan ta."Murmushi Mommah tai tana sakin hannun ta,part din Dada ta fara shiga dan gaishe ta.Mikewa tai Dada ta kalleta,ina zakije,zanje wajan Yaya na gaishe shi,uwar azarbabi Dada ta fada,to.saura kije ki zauna gargadi tai mata tare dajan kunnan ta,batace komai ba tafice tai hanyar part din Yayan nata."Yana kwance sanda tashiga room din sa,wani bacci ne ya kwashe shi,mafarkin ta yake yi dama,zama tai a bakin bed din nasa, kyakykyawar face dinsa ta zubawa idanu tana kallon sa, murmushi take saki gaskiya Yayan ta kyakykyawa ne,sai Yanzu take kara hango kamannin su,sajan fuskarsa dayayi luf ta mika hannu tana shafawa,farkawarsa kenan ya ganta zaune agaban sa,yaki motsawane yanai mata kallon kasan idanu,sanda ta miko hannun ta duk yana kallon ta.


"Yadda ya fara shafa masa sajan yasashi dan motsawa,dan zaro idanu tai ganin ya damke hannun nata,janyo ta yayi gaba daya ta fado jikin sa,kallon Cikin ido sukewa juna,yanayin yadda ta zare idanun nata ba karamar Dariya ta bashi ba,lakace mata hanci yayi,ita ma Dariyar tayi tana kallon sa."Kayan jikin ta ya kalla, sleeping dress ce iya guiwar ta,sai hula data sanya akanta,wani yawu ya hadiya,waishi Dada zata cewa sai ta kara girma za'a kawo masa matar sa."Ganin yadda ya kurawa kirjinta idanu yasa tai saurin zagayewa da hannun ta tana nata Fuska,basarwa yayi kamar bega abunda tai din ba,kokarin tashi take daga jikin sa,kin bata damar Hakan yayi yana kallon ta da rikitattun idanun sa."Kiss ya manna mata agoshi mikewa yayi daga shi sai boxer,bata taba jin kunyar ganin sa a hakan ba irin yau."Saurin rufe idanun ta tayi da barin kallon sa, Murmushi ya saki yana shafa sumar kansa,lallai yarinyar nan zaki sani.

"Toilet ya fada,hakan ya nata damar ficewa daga part din nasa,gaba daya ma ta manta abunda ya kawo ta."Sanda ya fito yaga bata dakin girgiza kansa kawai yayi yaci gaba da shiryawar sa."Part din Mommah ya soma zuwa ya gaida su,kafin ya wuce part din Ammi,Cikin jin kunyar juna duke gaiswa,Ammi jitai gaba daya ta kasa dakewa bakamar baya ba,dole dama zata ji wani abu na kunya agare ta."Kamar bazai shiga part din Dada ba amma sai yayi jihadi ya fada part din,tana zaune ta baje a parlon ta,'yan Biki kowa ya kama gaban sa,ta so binsu amma ta fasa saboda gadin Hamna,sosai tai shirin sanya Musu idanu,ta yadda sai nan da 2years zata bashi matar sa.

"A yatsine take kallon sa,hakane yasa ya gimtse face dinsa,ya tsani rainin hankalin da Dadan take masa.Au harka tashi,sannu da tashi,inma wani maganin jarabar kaje kasha tunwuri ka nemi makarin sa,kaida Hamna sainan da shekara biyu she,gaba daya takaicin maganar ta kamashi yayi,ya rasa Dada wace kalar mata ce da baa gasa mata baki ba,kallon tara saura kwata yayi mata,wani murmushi ya saki wanda shikadai yasan ma'anar sa,zai tabbatar mata dashi tsohon jarababbe ne kamar yadda take yi masa ikirari."Murmushin Uwar me kake yi mesunan Malam,rai bace yake kallon ta,karki sake cemin me sunan malm nifa na tsani wanann sunan,aiko saina fada,saina fada nace mesunan Malam."Ganin zata bata masa rai ya fice ya barmata part din gaba daya.

"A can Bangaran Ango Khalid Kuwa"Kwana akai ana gabza masifa Tsakanin sa da Feedo,yadda ya zaceta ba haka yaji taba,yadda kasan ya fada rijiya haka yaji ta,gata salam kamar kazar da ba gishiri ba magi."Suna tashi da safe suka dora daga Inda suka tsaya."Kallon raini da wulakanci Feedo din ke masa,lallai Khalid me kake daukar kanka,ni da kai kwaryar sama ke dukan ta kasa,abariki muka hadu,da kana tunanin kaji ni dam kamar budurwa,yadda kadinga sasakar yayan jama'a nima hakan aka dinga sasakata,wani mari ya kawo mata,wllh Feedo baki isa ba,bazanyi asarar kudina na Auran kiba,dama ke rikakkiyar 'yar iska ce,ko da nahadu dake agidan gala ai ban dauka kin gama tambadewa haka ba.

"Wannan Gidan dana shirya mana miyi rayuwar Amarci na fasa,dan banga Abinda za'a ci ajikin naki ba,narantse da Allah yanzu basai anjima ba sai kinkoma family House dimmu,acan zaki zauna tunda karya ce ke!!!"cikin karaji ya karasa magana,karka kuskura kasake cemin  karya,yanzu zan nuna maka ni cikakkiyar 'yar tasha ce wllh,wata kwalbar turare da aka jera mata akan mirror ta raruma,tunkan yasan abunda zatai dashi ta rotsa masa aka,dafe goshinsa yayi da yake masa wani azabar zafi,kafafunta ya kwarfo gaba daya sai gata tayi baya,muguwar faduwa tai saiga bakin ta ya tashe.

"Goshinsa dake zubar jini ya dafe,dankwalin sabuwar atamfarta ya daure kansa dashi,daga ita sai wata ya loluwar doguwar riga,shegen kirjin da Dada tace kamar nata ba mamaki na Dadan yafi abun arziki🤣🤣keep ya jata,sai harbi take kawo masa amma yaki saki ta.Hijab ya dakko a kayan da aka kai mata na lefe da kyar ya zura mata,megadi dake zaune yana jin redion sa hango Ango najan Amarya ya sashi mikewa cikin mamaki,Khalid beyi wata wata ba ya watsa Feedo amota,saida kashin hakarkarin ta ya amsa.Maida murfin yayi ya rufe ya sawa kofar lock ta yadda bazata iya fitowa ba,zaginsa take yi kamar zata ari baki,ko kadan be kalle ta ya koma,akwati daya ya dakko ya saka a boat,afusace yaja motar,ransa ajagule yake tukin.

"Get man daya ji ana danna masa uban hon da sauri ya tashi ya bude kofa,da gudu Khalid ya shigo da motar sa,tana gama daidaita parking ya fito,bude back sit din yayi ya fusgota,tsabar yadda ya buga baki adazu ta kasa magana,bakin ya haye suntum sai zare idanu takeyi, zuciyar ta banda tafasa babu abunda takeyi.Anci sa'a babu kowa a harabar Gidan,makullin part dinsa na hannun sa dama,budewa yayi ya tankada keyar Feedo,zubewa yayi akan sofa yana maida Numfashi,kallon banza ya watsa mata,in kinga dama zaki iya nemar naki bedroom din,amma koda wasa kika sake rabo Inda nake saina kakkaryaki wllh,mikewa yayi ya barta sake da baki tana binsa da kallo jar uba,ashe za'a kona gidan saboda bala'i.

   🤣🤣🤣Mom ki shirya ga masifa nan tana tunkaro ki,Bacci be kama ce ki ba Mom.....

        Mrs Baba Bello Abubakar
        .......✍️✍️✍️✍️


         'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 47_48

"Dada da fitowar ta kenan ta hango part din Khalid dake garkame a bude,to wa ya bde wannan part din,anya kodai Angonne ya zo daukar kayan sa,tabe baki tai ta koma part din ta,da dai Kamar ta karasa taga wanene aciki,amma saita basar ta koma taci gaba da harkokin ta."Feedo ganin tsayuwar nazatai mata ba ta zabi bedroom ta fada,bakin ciki da bacin rai Kamar ya kashe ta na wulakancin da Khalid yayi mata,aiko yayi da 'yar halak wllh saiya san ita ya tozarta haka.

Gashi bata dakko wayar taba balle ta kira Mom din ta,da kyar taja jikin ta tafada toilet,sai data gasa jikin ta sosai kafin ta fito,tana fitowa tai arba da akwatinta daya dakko mata,kwafa tai ganin bata sameshi adakin ba,da sun dora daga Inda suka tsaya,in zasu Kwana suna masifa bazata gaji ba,kallon kanta tayi a mirror tayi wani uban muni,bakin ta yayi wani zungurere kamar zumbutu."Parlo ta fito cikin ta ya fara kiran curoma,zaman tai tana ayyana abubuwa da dama azuciyar ta.

"Hamna data fito shawagi ta hango part din Khalid a bude,tsayawa tai kodai ya dawo ne,bari taje taga wanene aciki,babu wata damuwa ta doshi part din nasa,tayi wanka tasa pakistan dinta,sosia tai kyau,sai dan karamin mayafi data yane kanta."Part din ta shiga kafin ta fada parlour,tana shiga tai arba da fuskar Feedo,idanu ta zaro tana kallon ta,wata dariya ce ta kwace mata wadda gaza rike kanta,dariya ta fashe da ita shine dalilin daya sa Feedo tasan da wanzuwar ta."Sakace Feedo tai tana kallon ta,zaman dirshan Hamna tai tana kallon ta,tsagaitawa tai tana nuna ta,kece Amaryar Khalid,Feedo bata san me take magana akai ba,watsa mata harara tai ganin ta maida ita mahaukaciya zata sata gaba tanayi mata dariya.

"Khalid ne ya fito rannan bace"arba yayi sa Hamna wadda ta kura masa idanu,goshinsa da yayi tsini shiya ja hankalin ta,inta kallo Feedo saita kalle shi,gaba daya ta kasa rike dariyar ta,ta tabbatar wadannan kwana suka suna bala'i,mikewa tai tana kallon su,tabe baki tai irin ko ajikin ta,nuni tai masa shi da matar sa sun sami rabin hankali ne,ina Amarcin da yace saiya gama ci zai dawo Gidan su,tana Tambayar sa tana dariya babu abunda ya dame ta,bakin ciki ne ya sake kama Khalid,kallon Hamna yake tana jin dacin da abokin hamayyar sa ne ya samu nasarar wuff da ita,ganin babu me bata amsa acikin su ta juya tai ficewat ta,ranta fes Gwara da Allah ya dawo da Khalid,shida wancan fatalwar matar tasa bazasu taba shan ruwa agidannan ba.

"Part din Dada ta ruga dan kai mata rahoto,Dada sake ninke kayan ta ta kalli Hamna wadda tashi afujajan,ke lafiya ke da bakya tafiya a hankali, murmushi ta saki tana zama agaban ta,nuni ta farai mata,Khalid da Amaryar sa suna can sun farfashe kawunan su,zaro idanu Dada tai,dagaske kike Hamna,daga kai tayi alamar eh,da sauri Dada ta mike dan ganewa idanun ta.Sanda suka shiga atsaye suka yadda Feedo da Khalid ana kokarin baiwa hammata iska,sunyi cirko cirko kamar zakaru,kowa haushin dan uwan sa ya kama shi,yadda kasan zakuna haka suke huci,dan tasha ya hadu da 'yar tasha."Kai mezan gani haka,ina cin Amracin ko har gama cinye shi,dama Allah na tuba ko makaho ya shafa wannan ai yasan anyi biye biye,yanzu meya hada ku kukayi wannan muzu muzu din,babu wand ayayi magana acikin su,tsaki taja ai yanzu ma Kuka fara gani,zo mufita Hamna in suka huce maji abunda ya dame su.

"Jamilah Jamilah Dada ta kwallawa Mom kira,da sauri Mom ta sakko tana kallon Dada,sannu da zuwa Dada,yawwa,ta amsa a ya tsine,ina fatan kinsan akwai manyan baki agidannan,kallon rashin fahimta Mom take mata,baki kuma?wane bakin?surukar ki da danki mana,gasu can sunyo gudun hijira,dan haka saikije kiga halin da suke ciki,ina zatan danki ne yayi wa 'yar mutane rugu rugu.Dafe kirji Mom tai tana kallon Dada,da sauri tai hanyar part din Khalid din,tana can gefe ya samu waje ya zauna,Feedo kuwa tana tsaye ta Jijjiga kamar balbela.Subahanallahi Khalid meyafaru Kuka dawo da sassafe haka,ina gidan naku,sai Lokacin ta lura da yadda gaba daya kowa da nasa tabon ajikin sa.

"Feedo take kallo cikin mamaki,meya sameki haka,Wani banzan kallo Feedo ta watsawa Mom,tambayi danki aibani ya kamata ki tambaya ba,baki sake Mom take kallon Feedo,rai bace Khalid ya mike,ke uwa ta sa'ar kice,aini uwar kama batakai sa'a taba,taimin kadan nayi gogayya da ita saidai wadda tafita."Mari ya kawo mata tai saurin rike hannun kayi kadan ka sake marina anyi na farko anyi na karshe, Mom da hankalin ta yayi mummunan tashi ganin abun take kamar a mafarki,zage zage suka farayi Mom na tsakiya,kadan suke jira su kara dakuwa."Da kyar Mom ta samu ta janye Khalid tai part dinta dashi,zaman tai kanta na saraw kamar zai tsage,kallon Khalid din takeyi, Aure kwana daya amma harya rame ya fige sai idanuwa awaje.Khalid ya akai haka ta faru,tsaki yaja,taya zakimin wannan tambayar,ashe kinsan Feedo tambadaddiyar ce kika goyamin Naya na Aure ta,to wllh sakinta zanyi."Aiko baka isa ba,papi dke fitowa daga daki ya ambata,sanda akace karka Aure ta ba hada kai kukai da mahaifiyar kaban,to yadda Kuka fitittike baku yadda a fasa ba,yanzu ma babu saki ba yaji,ba jeki ki dawo,saiku raba wahalar tare."Ke kawar ki ce tayi hanyar Aure ko,yanzu sai kisan yadda zakiyi.

Amma ina tabbatar miki baza'a saki wannan Auran ba."Shiru Mom tayi gaba daya kanta ya kulle ta rasa tunanin da zata dauka tayi guda daya,kanta ya dauki zafi,ta rasa ma mezata ce sai muzurai take,da na sani yana zagaye zuciyar ta."Ganin ba mafita zata samar masa ba ya mike yabar part din gaba daya.

     Mrs Baba Bello Abubakar
        ......✍️✍️✍️


                   'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 49_50


"Babu shiri Mom ta fada Kiching"Girki ta dora gaba daya zuciyar ta acun kunshe"wane irin Aure ne wannan Kwana daya har za'a fara samun matsala,gaskiya da sake bari zata kirawo Zaitun tafita sanin halin Hajiya Kudrat,dole ta tambaye ta dama bata da kamun kai ne da Kunya ko yaya."Saboda gudun samuwar matsala da kanta ta dauki Abincin ta nufi part din Feedo,tana zaune kafa daya kan daya tana kada kafa,koda Mom tai sallama ko kallon ta bataiba balle tasa ran zata amsa.Mom taso tankawa amma ta basar bata ce mata komai ba ta aje kayan tafice daga part din,da harara Feedo ta raka ta,ita atsarin ta bata son Uwar Miji,ta so ma ace tuni tana lahira,amma Saboda tsabar danta ya raina mata hankali yazo ya hade ta da Uwar sa,kwafa tai tare da jan mugun tsaki,ita kadai tasan rashin mutunci da zata tatawa Khalid,kai bama shima ba gaba daya gidan,zasu san wacece Feedo.

"Hamna part din Ammi ta shige,sai dariya take tana buga kafa,in ta tuno bakin Feedo da keyar Khalid ba karamar dariya abun ke bata ba.Ammi da Mima da suka tsira mata idanu da mamakin dariyar me takeyi haka,Ammi ce ta tatabo ta tana tambayar ta dariyar me take yi,dariya ta sake saki,kafin ta kora masa bayani yadda zasu fahimce ta.Ammi dan zaro idanu tai,kai Hamna banda karya,Allah kuwa Ammi ba karya nake ba,jan hannun Ammi tai,zo muje kiganewa idanun ki, àah sake ni aini ba Uwar bamza bace,koma me ya had su Allah ya daidaita su,amma ace Aure kwana daya anyi fashe fashen kai."Mima ce ta mike zo muje Hamna ki rakani,harara Ammi ta dallah mata,to babbar banza,ke yanzu sai kitasa kanwar ki kutafi gulma,karna ji karna gani,kai Ammi gaida Amarya zanje fa,in dai Amarya ce aiga kanwar kinan gaishe ta,bata face Mima tai kai Ammi,sai kuma kiyi.

"Konawa tai ta zauna tana jin takaicin yadda Ammi din ta hana ta fita.Hamna dake zaune kanta taji ya fara sarawa, ahankali ta lumshe idanun ta da suka fara canza launi.Mikewa tai ta haura dakin ta,tana shiga ta fada bed dinta,fashewa tai da kuka aduk sanda taka yan uwanta na magana batajin me suke fade hakan na matukar damun ta, akullum tana rokon Allah ya bude mata kunnan ta,ta koma ji Kamar da,ranar batasan irin Farin ciki da zatai ba,zatayiwa Allah Allah godiya,ta dauki alkawarin har azumi uku zatayi,na godiya da ni'imar da Allah yayi mata.

"Mom Zaitun ta kira"wadda ke zaune yaran kishiyar ta nai mata tausa"ta kafa uban dauri ta caba ado Kamar me zuwa gasar daurin kallabi."Aminiyar na'am Zaitun ta amsa,gaisawa sukai da tambayar ya gajiyar Biki,ai kinganni ma na shirya gidan Amarya zamu wuce yanzu haka,haj Kudrat nake jira,dafe kirji Mom tayi wace Kudrat din uwar Amaryar kike nufi?ya mutsa fuska Zaitun tai kamar tana gaban ta,kwarai kuwa zata je taga lafiyar diyar ta mana,tabjam Mom ta ambata,bangane me kike nufi ba Jamila?ai abunne naji shi banbarakwai wai Namiji da suna Hajara,ban taba jin Inda uwar Amarya taje washe garin kaita ba."Kinga da kata Jamilah ko kina cikin iyayan mijin dake sawa matar dan su idanu? àah fa Zaitun ni ba haka nake ba,kawai dai maganar taki ce na jita kamar al'amara,to yanzu saiki dainajin haka, agaske nake sanar dake tare da Uwar Amarya zamuje duba 'yar ta."Kema in zakije bamu hana ki ba,ah wani bana cikin wannan layin da hankali na,kut mu kike cewa mahaukata?Jamila yaushe kika wajan bacci na haka?nice mahaukayar,kin sanni sarai warki ce ni dai dai nake da kugun kowace shegiya wllh,kin san bani da kyau Jamila,karki ja abunda zaki nadamar sanina a rayuwar ki.

"Cikin sauri Mom ta katse ta,dadi na dake bakya cin ribar zance,abunda yasa na kiraki daban,ke kuma maganar da kike daban,me yasa kika kirani,?dama zan sanar da kene ga Firdausi anan gidan mu,tunda safe ya kawo ta,mikewa Zaitun din tayi,bangane Inda kika dosa ba,kina nufin ya rabota daga Inda muka kaita jiya?kwarai kuwa.yamzu gatanan bansan abunda ya hado su ba,amma daga gani tashin hankali sukai kafin su dangana da gidanan."Tirka shi,yanzu shi danna ki kwaya yasha ko kuma wiwi,daga kawo masa Amarya jiya jiya har sun fara samun matsala,to wllh ina me tabbatar miki Kudrat bazata yadda da wanann Iskancin ba,dan tasa gajeran wando su daku da danki ba wani abu bane awajan ta."Dama kinsan bata da tarbiyya kika kara karfafa Auran,saboda ke fa na yadda da wanann Auran Zaitun,saboda Amintar dake tsakanin mu."Tabe baki Zaitun tai,naji saboda ni kika yadda da Auran,nina haifeta ko kinana ce ita,kawance ya hadani da Uwar ta,Kinga maganar kice ma saboda ni nata taso ba, tabdi wannan shine anyi ba'ai ba,kit Mom ta katse kiran tana zagaye a parlon ta,babu abunda ya tsaya mata arai face bata ki tasa gajeran wando su daku da sirikin nata ba,lallai ta kara tabbatar da yan bariki Allah ya hada ta dasu.

"Ba'a shafe awa daya da wayar ta da Zaitun taji dirar motoci atsiya ce,fuska cunkushe Kudrat ta fito tare da tawagar ta,burinta kawai taga diyar ta, Zaitun ta gama fesa mata komai harda kari.Zaitun da yake tasan part din kai tsaye nan suka nufa,Feedo tana kan dining tana break,amma tana hango uwar ta ta taso da gudu ta fada jikin ta,cikin karawa wuta fetur ta fashe da Kuka,Mom dan Allah nidai ki tafi dani, Khalid baya kauna ta,jiya kwana yayi yana kirbata kamar kubewa,kalli bakina,gaba daya zubawa bakin nata idanu sukai,yadda yayi sin tim har wani kyalli yake yi."Ashe yau akwai rotse rotsen kai Agidanan,yana ina matsiyacin yanzu zan tube mu daku wllh,jaka na kawo masa da zai kamaki yayi miki wannan dukan, ba'a haifi uwar saba ba shi ba."Jakar ta zuge ta nemo number sa,ring biyu ya daga,nazo gidan ka kazo ka saman,abunda ta ce kenan ta yanke kiran."Zaitun dake kallon Feedo daga sama harkasa cikin jimami ta bude bakin ta,hama aiko abariki bayayi miki wanann dukan ba,balle agidan Auran ku na sunna,barshi Zaitun zan tabbatar masa dani uwar zamani ce wadda ba'a taba yaranta azauna lafiya.

"Tana rufe baki ya fado parlon fuskarsa kamar hadari haka ya tsaya yana kallon su awulakance,yadda yake kallon su haka suke kallon sa."Kina ganin kallon da yake mana kuwa Zaitun nagani,ai in beyi haka ba to ba nonon Jamila ya sha ba.Ke tsohuwar kilaki karki kuma jiran sunan uwata,kaf din ku nan babu sa'an ta,wllh uwata tafi uwarka,cewar Feedo da take zabga masa harara.Kudrat zatai magana Zaitun ta kifta mata idanu,shiru tai dan batasan shirin Zaitun din ba,kunga Duk wannan Abun bana tashin hankali bane,gaba dayan ku yayan mune,muna da ikon da zamu tsawatar Muku,ke Feedo kece baki da gskiya,kece akasa tunda kece matar sa,I wani laifi yayi miki saiki bashi hakuri a zauna lafiya."Duk Zaitun ce me kora wanann jawabin kamar mutuniyar arziki,Kudrat kanta kallon Zaitun take tana jinjina makircinta,tabbas akwai abunda ta tuna shiyasa tai saurin yiwa tufkar hanci.

"Mom da shigowar ta kenan sosai taji dadin Maganar Zaitun,yawwa Aminiya ni dama nasan zuwan ki zai sasanta komai,shiyasa nazo din ai ta fada tana sakin wani murmushi,yanxu dai kuzauna,babu musu suka zauna."Khalid ta kalla,kai yanzu meya hadaku,ku kayiwa juna wannan ragargazar,ko so kuke makiya siyi mana dariya."Rai bace Khalid ya jefawa Feedo harara,ki tambaye ta,yadda kasan bakin rijiya haka na same ta,sàida wuta ta dauke musu,duk yadda suka kai da bariki sàida zancan yayi musu dum,cikin mazewa da waskewa Zaitun ta kalle shi."Banda abunka Khalid yanzu bakasan kaddara ba,Feedo tun tana wata bakwai aka samu wani mara imani ya shiga har gida yayi mata fyade,wannan shine dalilin daya sa kajita haka,a wannan Lokacin babu wanda yasan zata rayu,amma da yake Allah yayi da shan ruwan ta gashi har munga Auran ta.

"Kallon tara saura kwata yake yiwa Zaitun din, Kudrat data karkace kai tana jin yadda Zaitun ke zabga karya abun ba karamin dariya ya bata ba,Feedo ma kallon ta kawai take wai tana wata bakwai akai mata fyade tab."Kinga Zaitun kike ko Ruman,kinganni nan idanuna kyar suke,karki rainamin hankali kimai dani sha sha sha,aiko makaho ya shafa wanann yasan tayi biye biye acan baya babu wani ba wata,dama kayan lefena yana hannu na to bazan bawa bazawara wanann kayan ba,ke bazawarar ma kome 'ya'ya goma bazatakai wannan ba,in zata zauna ahaka fakat in Bazata zauna ba kutafi da ita,ko kaunar ganin ta banayi dama.

"Mom Zaitun ta kalla,kina jin abunda danki yake fada,tabe baki Mom tayi,bashi zai zauna da ita ba,tunda yace ga sharadin sa ai she abishi,zakici Ubanki kuwa Zaitun ta fada azuciyarta ta,to shiekenan hakan ma yayi,Allah ya baku zaman lafiya,ko kala bece ba ya fice rai bace."Mom ita ma mikewa tai bari na fita zan dan je na kwanta na huta,binta sukai da wani shegen kallo,kallon juna sukai duka su Ukun,tirkashi,kina ganin zasu Maida mu bamusan abunda mikeyi ba,wllh nayi Alkawarin saina sanya Jamila kuka da idanun ta,har ni zata kawowa Iskanci,tatashi tabarmu wai zataje ta huta, murmushi ta saki,huta Jamila Lokacin kine yanzu kafin na waiwayo kanki."Kudrat da Feedo da ba su san me take nufi ba binta sukai da kallo.

"Me zaki aikata agare ta?Kudrat ta kalle ta danneman karin bayani.

      Mrs Baba Bello Abubukar
       ......✍️✍️✍️✍️


        'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 51_52

"Tashi mutafi,Feedo mikewa tai ina zakuje zaku tafi kibar ni,ina zamuje kuwa,ke dama nan ai gidan Mijin ki ne dan haka kiyi zaman ki, Kudrat mekewa tai ki kara hakuri munanan dawowa."Suna fita suka fada mota,ganin Zaitun tana niyar barin gari Kudrat ta kalle ta wai Zaitun ina zaki kaimu, murmushi ta saki,Jamilah zannuwa kuskuran ta ayau basai gobe ba.Ai kinsan wata 'yar facalar ta Hamna?gyada kai tayi eh wata 'yar farar yarinya,kwarai kuwa inace kinji ance kurma ce,gyada kai tayi naji har naji mata takaici,da ace tana da baki wannan Allah kadai yasan irin samarin da zata tara."Af ai harda ita akaiwa Aure,haba dai wanann yarinyar kwarai kuwa,to ba kowa ya kurmantata ba face Jamila."Dafe kirji Kudrat tayi,ke dan Allah da gske,zammiki karya ne,ko nataba yi miki maganar ta banda yau, àah abunne ya dake ni,to me ya tare mata, hassada ce kawai."Ni kuma yanzu zanje na sashi ya kwance duk wani sihiri dake jikin yarinyar,kanta za'a maida shi kenan,af wane irin kanta ai banci ribaba kenan,saita dandani zafin da iyayan ta suka ji,acikin yaranta zansa akurmanta wanda tafi so da kauna acikin su.

"Kuma kinyi magana me kyau,yanzu wa tafi so a yaran nata,wa kuwa in banda wannan yarinyar me kai kamar bishiyar giginya,dariya suka saka,wata me dogon wuya kenan,aina lura bata da kunya dama,rannan ina ganin ta a wani mall tana zagin wani tsoho,zanga da bakin da zatai zagin yanzu ai."Haka suka dinga hora har suka isa dajin Falgore,tun kusan kar fe 9 basu suka je ba sai kusan La'asar,saboda shegen nisa."Tun da boka ya hango su yake babbaka dariya,dara taci gida,mata kaidin ku ko shedan ya sara muku,kirari sukai masa kafin su shige bukkar tasa,wani tsamurmuri ne,sai idanu kwala kwala,kamar zasu fado kasa,bakikkirin dashi,yayi duku duku da kazan ta."Zasu fata magana ya daga musu hannun sa,nasan abunda ke tafe daku,buge bugen sa yayi saiga wata guguwa tana tashi."Sàida guguwar ta dade kafin ta lafa,Aljani durkus,asaki wannan yarinyar,aikimmu ya kare akanta,kasa ya kara bugawa saiga hoton Bilkisu,tana wajan birthday din kawar ta,sai casar rawa take yi,dariya bokan ya kyalkyale da ita wannan bazata bamu wahala wajan aiki ba.

"Saime ke tafe daku"maganar 'yan biyun waje na,daga mata hannu yayi,tuntuni na sanar dake aljani bazai iya shiga jikin wadannan ya ranba,ina son ki cire su daga zuciyar ki,bazasu taba zama wasu ba aduniya,gyada kai tayi badan taso haka ba,burinta da za'a kashe su ma suda uwar su haka take so."Sai maganar mijin Feedo muna so a mallake mana shi,mita tatsarsa babu halin yayi mana musu,angama wannan me sauki ne,shima baya Addu'a ya shagala da duniya kamar ku dinnan,ku tashi ku bani waje aikina kamar yankan wuka yake,kuyi jiran lokaci."Kudi Zaitun ta dire masa kafin su mike.Har suka kai mota babu wanda ya kara magana.Dariya Zaitun tayi ta buga sitiyari,zan so naga yadda Jamila zata haukace in taga diyar ta ta kurum ce,nasanta da son yayan ta,Jamilah banda kyau sanin hakanne kawai bakiyi ba,tafasa sukai ita da Kudrat ran su fes.

"Ranar Hamna har kusan 11 suna General parlo suna kallo,hamma ta farayi hakan yasa ta mike tanai musu sàida safe,Dada mikewa tai ta raka ta har dakinta,duka abunda take yi Sadauki yana kallon ta, murmushi kawai ya saki,lalli Dada aiki ya same ki."Mikewa shima yayi ya wuce part din sa."Karfe 6 Hamna ta farka da yake yau bata sallah shiyasa bata tashi sallar asuba ba,kamar da wasa taji Iska me dadi na ratsa kunnan ta,sakare tai tana san tantance wa,ga kuma karar AC da take ji tana sauka a dodon kunnan ta,bude baki tai ta fara magana,sautin taji yana dira akan kunann ta,babu shiri ta diro daga kan bed din ta,Ammi ta furta sautin tangararau a kunnan ta,zubewa kasa tai ta fashe da kukan farin ciki.Sujudushshikur tayi dan nuna godeyar ta da Allah ya bata lafiya,badan ta isa ba,saidan ikon sa da rahamar sa,da jin kan bayin sa.

"Da gudu ta kwasa ta sauko zuwa parlon Ammi,Ammi Abbah Mima Munib haka ta dinga kiran sunayan su,kamar amafarki Ammi ta dinga jin muryar datai shekaru tana san jinta,tai shekaru tana gurfana gaban Ubangijin ta tana rokon sa Allah ya bawa diyar ta lafiya."A sukwane Ammi ta mike,har hijab dinta na neman kayar da ita,kamar hadin baki Abba shima ya fito daga dakin sa, bibbiyu suka dinga taka step hango Hamna atsugunne ta bude dukkan hannayan ta,alamar su taho gare ta,hawaye sai tsiyaya yake akumcin ta.Abbah yanzu ina ji Ammi ina magana,kuna jin magana ta kuma?abunda take nanata musu kenan,farin ciki ya hanasu motsawa gani suke kamar mafarki suke yi,da sauri Mima data fito daga room dinta ta tsugunna agaban ta."Kanwata dagaske muryar ki ta dawo,gyada mata kai Hamna keyi, rungume ta tayi suka fashe da kukan farin ciki,su Ammi da Abba matsowa sukai suka rungume Hamna,Abba har hawayan farin ciki ya goge batare da kowa ya lura da hakan ba."Fadi yake Alhmdlh Hamna Allah ya bawa Hamna ta lafiya,mamana ta warke,Allah shine abun godiya,sake rungume ta yayi yana shafa bayan ta."Mikewa tai bari na fadawa Dada ta,da gudu tai hanyar part din Dada tun kafin ma suyi magana."Dada da bacci yadan fara fusgarta Hamna sàida taje dai dai kunnan ta ta kwallara mata kara, afirgice Dada tai wani allan dungure,kyalkyalewa da dariya Hamna tayi,Dada murya ta ta bude,Dada da ta hamgame baki tana kara karkatar da kunnan ta,jin kamar mafarki takeyi,kan cinyarta Hamna ta fada shine dalilin da wowa hayyacin ta,Dada da gaske ne ba mafarki kike ba,sake zare idanu Dada tai kanta fashe daku ka,dama da rabon zan sake jin muryar ki takwara ta,kai Alhamdlh Allah shine abun godiya,kai ma sha Allah dole ne yau ayi sadaka agidanan."Mikewa tai daga kan cinyar Dada bara na dawo Dada,kiranta Dada keyi amma ina ta kyalla da gudu.

"Part din Sadauki ta fada,ya zama dole Yayan ta yasan wannan abun farin ciki daya sameta."Yana kwance yana bacci yaji fadowarta ajikin sa,Yayana ka tashi na warke,jin muryar ta ya sashi saurin bude idanun sa,fes ya sauke su akanta,bakin ta na daidai nasa,tana kara jaddada masa ta warke ya tashi Yagana ta,gaba daya yayi mutuwar kwance,mafarkin da ya dade yanayi Hamnan sa ta warke ya tabbata,besan sanda ya rungumeta yana sakin dariya ba,ita ma Dariyar take yi,Yaya na kaga na warke ko,daga mata gira yayi yana sakin Murmushi."Sake kankame ta yakeyi kamar wanine zai kwace mai ita yake yi."Wash Yayana zaka ballani,sassauta rukon yayi mata."Yawwa Yaya tunda naji sauki ka bani sarka ta,kallon ta yayi yana mamakin nacin Hamna,zanyi maganin ki,sarka kike magana akai,da sauri ta gyada kai,kin shirya karbar ta yanzu,sosai ma,kawai ka dakko min, murmushi ya kara saki,kindai tabatta kin shriya,tsaf ma kuwa ta fada tana kumbura fuska ta matsu ya bata abarta.Dariyar dake cinsa ya gimtse,sai kin zama wama bace sarkar ta zama taki?inna zaman wife kuma na zama,haka Ammi ta fadamin yanzu ni matar ka ce.Alhamdulillahi tunda har kinsan da haka,yanzu dai kin shirya karbar matsayin mijin ki,gyada kai tayi tana kallon sa,dariya ya saki yana kallon ta,ashe ni yau zan zama Ango ita ma Dariyar tai ehman yaya.

"Yawwa yanzu yaya zai dakkomun sarka ta"har wani sake gyara kwanciya take him tana jiran ya tashi ya dakko mata."Jin bakin sa kawai tai acikin nasa,zare idanu tai tana kallon sa,kokarin zamewa take ya riketa yadda bazata iya kwacewa ba,ya mutsata ya farayi cikin salan da yasan bazata razana ba,hawaye ke zarya a fuskarta,gaba daya ya yamutsa mata gashin kanta,iya kiss kadai ya tsaya amma Hamna gaba daya ya gigita,jin saukar hannun sa akan kirjinta yayi masifar razana ta,kokarin ture hannun sa take yi amma hakan ya gagara,banda jamai Allah ya isa babu abunda Hamna ke yi🤣🤣🤣da wasa Sadauki ya so razana ta,amma saiga abu yana neman zama gaske.

"Muryar Dada ce ta katse masa dukkan wani hanzarin sa, ahankali ya fara dawowa nutsuwar sa,kallon sa ya Maida kan Hamna,wadda tai Kuka harta gaji ta zubawa sarautar Allah idanu,da sauri ta runtse idanun ta,bazata sake zuwa part dinnan ba, tun da yayan nata ya zama dan Iska.Hamna wai kina ina,ubamne kake mata wai,bazaki fito ba sai ranki ya baci,motsawa tai zata tashi yayi saurin rike ta.

"Tsurawa kirjin ta idanu yayi sake bayyane tuni ya cire maballan rigar ba tare data sani ba,ganin inda yake kallo yasata kallon wajan, zabura tai tai rubda ciki,Kuka ta kara sakar masa, murmushi ya saki me sanyi,jikin sa na kara mutuwa,Dada ta gama cutar sa,yaso ya kashe boss din saiyaga abunda Dada zatai,amma tazo ta cuce shi."Rai bace Dada tabar part din kodai bats ciki ne,tunanin da take kenan kai bata ciki ma,ai da tayi magana, hankalin Dada ne ya kwanta ta koma part din ta."Mikewa yayi yana shafa kansa, toilet ya fada,wannan mitsitsiyar yarinyar ta tayar masa da hankali,wanka ya kamashi, murmushi kawai yake saki.

"Sai data tabbatar ya shiga toilet din ta mike,idanu jajir ta kalli kanta a mirror,lebanta ta kalla kamar ya sake tsini,gashinta yai buxu buxu,tattare dashin tai,saidata kalli kanta kafin ta fice daga part din baki azumbure."Momma da Ammi kallo daya sukai mata suka kauda kan su,kai masa basu da kunya,ya zama dole tafara gyara Hamna waccan me idanu atsayen bazai saurara mata ba, Mommah ke wannan tunanin,ganin yadda duk ta diririce yasa suka nuna kamar basu ganta ba,wuff ta haura sama, murmushi kawai suka saki kowa bakin sa dauke da magana,saidai sunyi shiru sun barwa zukatan su.

  🤣🤣🤣Hamna wife ta fara aikin ta tukuru.....

      Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
        .... ✍️✍️✍️✍️



          'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 53_54

"Hamna kuwa tana shiga dakin ta ta murza key"kan bed dinta tafada tana shiga blanket"gani take kamar yabiyo ta"kankame jikinta tayi tana sake bata fuska"bata taba zatan Yaya Sadauki haka yake ba"wayyo shikenan ya gama da ita"barkewa tai da Kuka,wazata dafawa wannan maganar,Dada Zuciyarta ta sanar da ita,ya zama dole ta sanar da Dada tashiga tsakanin ta da Yayan nata,dole ne taja masa kunne batasan irin wannan wasan,ko kuma Big Daddy zata sanar hakamma za'ayi,shikansa in yaji Abunda ya aikata mata sai yayi masa fada sosai."Tajima akwance tana sake sake kin fita tayi dan kar su hadu da Sadauki.

"Shiko a bangaran sa yana wanka yana sakin Murmushi shikadai,shafa kansa yake jin wani farin ciki na ratsa shi,babynsa ta girma,Dada zakiga tsiya kuwa,badai ni kikewa rashin mutum ci akan hakkina na,wani murmushi ya saki."Daure da towel ya fito"shafe shafen sa ya tsayayi"pyjamas ya saka farare tas,silifas ya zura akafar sa,bayan ya feshe jikin sa da turarruka masu Matukar kamshi."Ammi da Mommah har lokacin suna zaune,yana shigowa suka bishi da kallo,gaba daya sai yaji ya tsargu,bare kallon da Mommah ke masa,kamar kallon tuhuma yaga tanai mai,basarwa yayi ya karasa zama yayi akan carpet tare da tankwashe kafafun sa."Ammi kunyar hada idanu ma take ji dashi,hakan yasa ta dauke kanta daga kallon sa."Barka da Safiya Ammi,min tashi lpy,tafada da kyar tana danne Abunda take ji,lafiya lau, Mommah dake kallon yadda Ammi ke wani runtse idanu dariya ta bata."Kallon sa ya maida kan Mommah data kuramai idanu,mara kunyar banza kalli yadda yake wani tsare gida,kamar ba yanzu ya gama matse mata yarinya ba."Gaida Mommah yayi ta amsa a ya mutse,yanzu ka tashi daga bacci hala,eh ya gyada mata kai,xata sake Magana Ammi ta matse mata hannun ta,alamar karta ce komai,sarai tasan halin Mommah zata iya tuhumarsa yanzu."Hadiye maganar tai ta kalle sa,to zaka iya tafiya, Mommah ta fada tana hararar sa,mikewa yayi koma dai menene shidai bazai daina ba,ya gano akamme Mommah din ke hararar sa 

"Kururuwar Mom da suka jiyo ita ta sasu mikewa batare da sun shirya ba,har bangazar juna suke wajan shiga part din nata."Hamna ma dake daki sàida kururuwar ta shiga kunnan ta,a sukwane ta mike tai side din da tanan takejin kukan."Suna tsaye suna tambayarta amma taki cewa komai tana rungume da Bilki wadda Kuka take ita ma kamar ranta zai fita,sai zare idanu take tana kallon bakin kowa."Tsaki Feedo taja wadda sai Lokacin ma suka ganta,taci wasu riga da wando yadda kasan an daurawa biri igiya,babu shape haka take ashafe,wata dariya ce ta tahowa Khairar da Mima amma suka maze."Su Ammi Kansu dariya ke cin su,sungane sarai,tabbatacciyar Amarya mara Kunya."Kinga in bazaki fadi meke damunki ba kowa saiya kama gabansa,kawai sassafe kisa mutane agaba kina kuka kamar wadda akace uwarki ta rasu."Tsit parlon yayi hatta Mom din sàida maganar ta dake ta,afusace ko ta mike ta kawowa Feedo din mari,saurin kaucewa tai karki kuskura wllh,babu kunya zan daga hannuna na rama.

"Khalid ne ya shigo hakan ya bawa Mom damar sake rushewa da.kuka,kanajin Abunda matar ka ke fada akaina?zagina fa ta gama yi."Kallon ta yayi ya kalli Feedo din dake,zabga masa harara,maida kallons ya sakeyi kan Mom din,wai to akamme kike wannan kukan,haba sassafe kidinga yiwa mutane Kuka,wannan dai be dace ba gskiya,kuma abinda  Feedo ta gaya miki ai Gaskiya ne babu ja amaganar ta, Mom data dora hannu aka tana tunanin wace masifa ce ta same ta haka,hawayan fuskarta ya kafe kaf,bata dawo daga hayyacin ta taga yaja hannun matar sa sun bar mata part din."Kallon kallo aka shigayi a parlon,mamaki ya kashe su a tsaye,me ya hau kan Khalid."Dada ce taja mugun tsaki,Kinga Jamila in baki da abun fade zami gaba wllh,to danki ma ya tafi yabar ki balle mu 'yan karere,ta karasa fade cikin jin haushin Mom din.

"Bilkisu ce ta kurman ce,bata ji ta karasa tana sakin kukan bakin ciki.Hamna ce ta saki wata shegiyar guda tare da fashewa da dariya,gaba daya zuba mata idanu sukai yadda take dariya tana buga kafa,gaban Mom din ta karaso ta tsaya,Kinga yanxu shikenan'yar ki ta zama kurma ke kuma babar kurma."Tsantsar mamaki yasa Mom shako wuyan rigarta,yaushe koka warke kika fara magana,ya akai hakan ta faru?zubawa mom idanu sukai ganin yadda ya fita daga hayyacin ta,ahakku da kokon to ya shiga cikin zukatan su,wannan maganar abayyane take,tasan musababbabin kurmancewar Hamnan kenan kome.

"Dada ce cikin tabbatar da zargi ta ta kalle ta,ke Jamilah wace maganar banza naji kinayi,in Hamna zata samu sauki sai anyi shawara dake dama,ko kina da hannu akan kurmancewar tata mu bamu sani ba?sai loakacin Mom ta dawo hayyacinta,ko daya Dada kawai abunne ya dake ni,ta yadda har Hamna ta samu sauki babu wanda ya sanar dani shiyasa abun yayi min ciwo."Babu wanda ya yadda da kalaman ta,musamman Mommah da Ammi, sunsan wacece Jamilah zatai abunda yafi haka ma."Tabe baki Dada tayi to Allah ya sauwake ya bata lafiya,saiki dauke ta kikaita asibiti,babu wani yawon asibiti da zamu tafi wllh,sanda Hamna ta kurmance iyayanta kadai sukai wahalar ta,kema yanzu saikiyi ta 'yar ki.

"Kama hannun Hamna tai suka bar side din,haka Mommah da Ammi basu ce komai ba suka fice, Mima da Khairat ma bin bayan su sukai,daga mom sai Saudat da Bilkisu aka bari sai Musaddik bawan Allah yana tsaye yana kallon su."Zuciyar sa banda bugu babu abunda takeyi,kardai Mom din tana da hannu akan ciwan Hamna,amma wannan maganar kamar a bayyane take,bece komai ba ya juya shima ya fice,bazai iya wannan jegon jakar ba,gwara ya fice ya tafi harkokin sa,Saudat ma warewa daki tai ta fada kan bed din ta.Daga Mom sai Bilkisu,kuka Mom take tana kiran nashiga uku,da gudu ta haura dakin ta,wayar Zaitun ta dinga kira,tana kallon ta taki dauka tasan kwanan zancan harta karaci kira bata dauka ba."Kamar zata zare haka ta koma.

"Su Ammi haka suka zauna jugum jugum kowa da abunda yake sakawa a zuciyar sa,suna ji aran su kamar kaikayi koma kan mashekiya ne,tundaga shi Hamna ta warke 'yar ta ta kurman ce."Hamna mikewa tai tai part din mommah,da sallama ta tsaya a kofar parlon Big Dady,amsawa yayi yana bata izinin shigowa."Da murmushi yake kallon ta Mamana baki ya bude, murmushi tayi ita ma eh Dady."Kaiwa zaune tai tana kallon sa,gaidashi tayi kafin tai shiru tana murza hannayan ta,yadai Mamana,shiru tai idanun ta na cikowa da kwallah,hannayan ta ya rike fadamin matsalar ki."Um am dama karar Yaya Sadauki na kawo, murmushi yadan saki me kuma ya hadaki da Yayan naki,kashiga tsakanin mu karya sake taba ni."Maganar girma tai masa,amma ya kanne yadan kalketa wannan ce matsalar ki,gyada masa kai tayi alamar eh,to zanko ja masa kunne zai kiyaye,baki ta washe to Dady."Da murna ta mike tafice,binta yayi da kallo yana girgiza kai yaro yaro ne, murmushi ya saki yana shafa kansa, Sadauki shiya gado komai na Dad yana yi shima,hatta yanayin muryar su daya ne.

    Uhm Hamna manya.
    
       Mrs Baba Bello Abubakar
         ......✍️✍️✍️✍️


          'YAR ARO

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 55_56


"Mom ganin komai yana neman kwabe mata ta bazama gidan boka,ga Bilkisu da take ta zuga kuka batajin komai sai dindim acikin kunnan ta,ga bacin ran yadda mutanan Gidan babu wanda yayi ta kanta,kowa yayi biris da halin da 'yar ta ke ciki."Tashin farko ya sanar da ita wadda tasanya awarware aiki,wayyo zo kuga yadda zuciyar Mom take babbaka tana ci da wuta,har ita Zaitun zata ciwa amana,tasa boka ya karya aikin ta ya mayar kan 'yar ta.Babu bata lokaci ta zube masa makudan kudade,da neman a warware dukkan wani kulli da Zaitun din tayiwa mijin ta,ta yadda yake shakkar ta,yake wulakanta matar sa akan ta,babu wani jan magana ganin ta ajiye masa bugun ABUJA babu musu ya fada buga aikin sa,ya tabbatar mata da komai Zaitun din ke takama dashi ya lalata shi,cikin farin ciki ta kalle sa,saura na kurmantar mata da 'yar ta da yayi,wanna kuwa ca yayi bazai karayu ba ayanzu,saita shafe shekarun da Hamna ta shafe batajin komai a kunnuwan ta,Kuka mom ta fashe dashi,tana rokon sa yayi wani abu akai,tsawa ya daka mata wadda ta shiga taitayin ta,gargadi yayi mata kafa ta sake rokon sa,saboda shi baida tausayi baida imani.

"Jiki na rawa tabaro tsaunin sa"rai ajagule ta fada mota driver ya jata."Babu wanda yasan inda taje,koda ta dawo kusan Sallar magari ba babu wanda ya tambaye ta,har taje ta koma Bilki kuka takeyi,idanun ta sun kumbura,babu sallah ba salati haka take zaune,dama sallar ba wani damun ta taiba sai taga dama ta keyi."Tana ganin Mom ta rungume ta,tana kara saki Kukan takaici da bakin ciki,kawayan ta da abokanta sai zabga mata kira suke,amma ina! Babu bakin magana,saidai ta kalli kiran ta sake rushewa da kuka,haka ta wuni ko abinci taki ci,Sauda babu yadda batai da ita bag amma fir taki ci,gajiya tai ta kyale ta,tunda ai ba jaririya bace da zata dinga bata lokacin ta akan ta.

Papi sosai ya shiga damuwar halin da Bilkisu ke ciki,haka Abba da Big Dady,adaran yasa Sadauki ya duba ta,amma duk binciken sa bega komai ba."Washe gari haka aka sake daukar ta zuwa asibiti ammata gwaje gwaje amma shiru babu baya ni,sai idanu da take bin mutane dashi abun tausayi."Haka suka dawo gida a General parlo suka zauna,kowa yayi jugum da abunda yake sakawa azuciyar sa."Muryar da suke juyowa ana zage zage taja hankalin su,kamar mahaukaciya haka ta fado parlon,gadan gadan kan Jamilah tayo wadda ta mike tsaye ita ma tana kallon Zaitun din,wadda bayan shaidar maruka da tasha da bakin ta fake fashe baka ganin komai afuskarta sai tsananin fusata da daukar fansa."Wata shaka ta kawowa wuyan Mom din wanda yasa muatan parlon mikewa cikin mamakin me kuma ya hada aminan yau,dan sun san Zaitun da matsayin ta na Aminiyar Mom din.

"Shigiya Annamiyaya,harni zaki sa awarwarewa aiki,yanzu gashi mijina ya dankaramin saki har uku,yadda kika saka aka sake ni wllh kema sai an sake ki,da kyar su Dada suka taru wajan banbare Mom da taji kamshin mutuwa."Sake zabga wata ashar Zaitun tayi,kinsan Allah Jamilah yau ko ni ko ke,cikin Masifa da tashin hankali Mom ke kallon ta,ubamme nayi miki da zaki biyo ni har gidan Mijina?tafi Zaitun tayi tare da shewa gidan Mijin ki lika ce?aiko yadda na bar nawa Gidan mijin kema haka zaki barnaki,dan yanzu zan kwance dik Wani kulli da kika kulla,saina warware shi kowa ya jiki."Kirjin Mom ne yayi masifar bugawa,wani tsalle tayi ta naushi bakin Zaitun,azabar da taji ya sata fyallawa Mom wani shegen mari,kafin ta jawo ta ta zaune ta kirbar Mom take kamar Allah ya aiko ta,tako ina take dukan ta, Mom din na kokarin kare kanta.

"Shigowar Yusuf yasa Dada nufar sa yawwa raba wannan fadan,dan wllh bazan je a naushe ni a banza ba,bansan sanda suka kulla tsayar su ba na kare agadon asibiti, Yusuf da dawowar sa kenan daga school ya tarar da wanann rikici,su Mommah ya kalla yadda suke haki kamar wadanda dasu ake fadaan,basu saba,gashi sunyi rabon abun yaki rabuwa."Da kyar ya samu ya janyo Mom wadda aka zaune sai numfarfashi take yi,ai wallhi Jamilah yau sainai miki sintiri agidannan."Daidai lokacin su Abbah suka shigo,kallon Mamaki suke musu yadda sukai cirko cirko ga Mom a ya mutse bakin ta na zubar da jini."Cikin san karawa wuta fetur Zaitun ta daga murya,daya ke ke munafuka ce,ai da befi da ba,shine danna je nasa boka ya warware asirin da kika sa aiwa Hamna ta kurmance ya koma kan 'yar ki,shine zakije kisa mijina ya sake ni,maganar ba karamin dukan su tayi ba,kowa hannun sa akan kirji yake kallon Mom,gaba daya sai taji ta muzan ta,cikin borin kunya da san kare kai Mom ta kama zage zage,harni zaki yiwa sharri Zaitun,kije ALLAH ya isa tsakanina dake bazan taba yafe miki ba.

"Big Dady ne yayi karfin halin kallon Zaitun wai me yake faruwa ne?kiyi mana bayani yadda zamu gane,da sauri kuwa Zaitun ta gyara tsayuwar ta,karkace kai tayi tiryan tiryan ta basu labarin abunda ya faru,amma batai maganar ta kaddun da takai mata ajiya ba,dan wadannan tuni Zaitun ta cinye su,bata kuma da niyyar bayarwa."Salati kowa ya dauka a parlon,mmaki da tsoro ya shige su,Hamna dake gefe fashewa tai da kuka,dama Mom har haka ta tsane ta bata sani ba?dama bata kaunar ta harda zata sa ana kasa mata rayuwa,batajin zata yadda saita dauki fansa akan ta.Ammi da Mommah ma share kwallah suke yi, Sadauki da tun dazu yake tsaye yana sauraron su,kallan tsana yakew Mom dama tuncan ya gane bata kaunar Hamna,ashe kiyayyar harta kai haka."Kuka Mom ta fashe dashi tana rantse rantaen sharri tai mata,yi mana shiru munafuka,ai maganar da wannan ta fada gaskiya ne,dama kalar ku daya kalar karuwai 'yan tasha,papi ta kalla wanda bakin ciki ya kusan kashe shi atsaye,'yar dan Uwansa matar sa taiwa haka?kagani ko,dama shiyasa tun sanda na fara ganin ta naga batai min ba,amma ka nace kai sai ita,ai gashinan tai mana aika aika,abun kuma ta qare akan 'yar ta.

"Kasa cewa komai yayi,ransa ajagule yake,tsanar Mom ta zauna daram a zuciyar sa,dama tuni ya dade da fitar da ita daga zuciyar sa,ba karamar wahalar zama yasha da ita ba."Ganin Zaitun na niyyar barin parlon mom ta falfala ta cafko ta,wuyan ta ta shake kamar zararriya,bani ajiyar dana baki,dan wllh bazan sake ki ba saikin sanar dani Inda kika kaita."Fadane ya sake kaurewa atsakanin su,ai wannan takaddu sun zama nawa na cinye su."Murmushi Sadauki ya saki wanda yake kallon su,tuni ya gane akan me suke magana."Dama kundaina wahalar da kanku wadannan takaddun duk basa hannun ku,kowa juyawa yayi yana kallon sa baki sake,jin yasan akamme suke magana,tsayawa sukai da kokwar su kansu suna kallon sa,wani makirin murmushi ya saki,ya dora idanun sa akan Hamna,wadda ita ma kallon sa take,amma sam bata gane akan wasu takaddu ake magana ba.

"Kayi mana bayani dammu gane"Abbah ne me wanann maganar."Gyara tsayuwar sa yayi yana kallon su,ashekarun baya da suka wuce Hamna ta tana dakko min wasu ta kaddu adakin Mom,wadda a wautar ta tayi ne dan Mom din taita nema daga baya saita bata in ta gama wahalar da ita."Dalilin jin wayar da tayi da kawar ta,nacewar ta samu nasarar dakko ta kaddun nan,sanda ta kawon na girgiza ba komai bane bayan kadarorin papi,kowa kallon sa yake baki bude,hannun Mom akan kirjin ta."Nagargadi Hamna karta sanarwa kowa,bata kawo komai aranta ba tuni ma ta manta da Maganar,kamar yadda Hamna ta shiga ta dakko su,adaren nayi photo copy yadda babu yadda mutum zai gane ba original bane,Inda Mom ta ajiye nan naje na ajiye mata na bogin.

"Kuka Mom ta fashe dashi,amma ka cuceni Sadauki kaida Hamna saidai nace Allah ya sakamin cutar da kukai min,papi ne ya zaburo zai kamota ya kakkaryata kozai huce zillewa tai,runtumawa sukai da gudu ita da Zaitun din,kafin papi yace get man karya bude musu kofa har sun fice,cikin fitar hayyaci suka hai kan titi,wata mota data shararo tai sama dasu jikake tim sun fadoooo......

😳😳😳Lallai Mom da Zaitun kuna ruwa....


        Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
               ......✍️✍️✍️✍️✍️


                  'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

Page 57_58



*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


"Gudun da me motar keyi yasa ya kasa taka birki,saida yayi ciki dasu tukunna motar ta tsaya,jina jina haka suka fado cikin mummunan yanayi,na rayuwa da mutuwa,me gadi daya biyo su ganin yadda suka sheka a guje akan Idanun sa komai ya faru,da gudu yayi cikin Gidan,Alhaji hajiya mota ta kade su suna can kofar Gida,koda wasa papi be motsa ba,su Abba ne suka fita asukwane,har mutane sun fara taruwa,wanda ya kade sun tuni yaja motar sa ya gudu."Motar Abba aka saka su, Mom da tsabar azabar da take ji a kafafunta ya sata suma,Zaitun Kuwa Kamar ma babu rai ajikin ta."Hospital din su Sadauki aka kaisu,cikin gaggawa aka amshe su, emagency akai da su dan suna bukatar kulawa ta musamman.Abba da Big Daddy su suka tsaya akan komai,su Dada ma kin zuwa asibitin sukai sosai abunda mom din tayi ya dake su,ya kuma basu tsoro da Mamaki.

"Sàida sukai Kwana biyu,da kyar Abba ya rarrashi Dada suka zo asibitin,duk wanda yaga yadda suka koma saiya tausaya musu, Mijin Zaitun da ka sanar dashi cewa yayi babu ruwan sa,ba shi da alaka da ita ya sake ta,iyayan ta ya taima ya kira babu bata Lokaci suka bayyana a hospital din,sanda suka ji abunda suka aikata sunyi Kuka da Allah wadai da hayyar su,haka iyayan Mom duk yadda babarta keda masifa da zafi da son 'ya'yanta wannan karon taga laifin Mom din."Kafar Mom ta kumbura bazata sake moruwa ba Sàida aka yanke,sanda ya farka ta ganta da kafa daya kururuwa ta dingayi tana zambarwa,sai da kyar aka samu akai mata allurar bacci,tukunna aka samu lafiya.

"Duk yadda Hamna kejin zafin ta data zo ta ganta sai taji ta yafe mata duk wani abu data aikata mata."Mom ta kwantsame Kamar ba ita ba,sai idanu awaje da take zarewa Kamar ta fara samun tabuwa a kwakwalwar ta,papi yaso ya sake ta su Abbah suka hana shi,be kamata ya sake ta tana wannan halin ba,dan dole ya hakura,amma babu Maganar santa azuciyar sa,ya tsaneta ba kadan ba.Khalid ma tuni ya shiga taitayin sa Feedo kanta tayi laushi ta tsorata ganin yadda su Mom suka koma,hatta Haijiya Kudrat sai data ji tsoron Allah ya shige ta."Sai da mom tayi Wata daya a asibiti aka sallamo ta,tare da sandar ta guragu,tai Kuka Kamar ranta zai fita,tayi nadamar abun data aikata abaya."Sai gashi wadda ta tsana din tana taimakon ta,sautari in tana san wani abu ita ce take mika mata,Hamna ta basu matukar mamaki ashe haka take da tausayi da sanyin zuciya,duk wani laifin data aikata mata ta shafe shi,bata marmarin ta tuna shi.

"Bilkisu an kira malamai sunyi mata addu'a da rukiyya,da kyar aljanin jikin ta ya fita,sai gashi ta dawo magana ras,tuni ta sanya nutsuwa a jikin ta,duk wani rawar kai ta ajiye shi agefe,Mom har kunyar hada idanu takeyi da jama'ar Gidan,idanun ta kullum yana kasa tana sharar Hawaye."Har wannan Lokaci Dada ta hana shi matar sa,su Mommah sun zuba musu idanu shida Dadar,gyara dai Hamna tana shan sa,tayi fresh ta kara kyau over.

"Yau da wuri ta wuce dakin ta,wani mugun bacci ne a idanun ta,tana ganin kiran Sadauki amma ta share,daga karshe ma kashe wayar tai tayi kwanciyar ta,kusan 11 ya murdo kofar ahankali,tana kwance tana sharar bacci,gaba daya gashin ta ya tar watse a fuskarta,rigar ta ta yaye ta dawo iya cibi,makwat ya hadiyi wani mugun yawu,gefanta ya samu ya kwanta,dan yasin yayi alkwarin ya daina kwana shikadai,kwanciya yayi ya rungume abar sa,cikin dare zatai juyi taji ta makale ajikin mutum,babu shiri ta bude idanun ta,akan kyakykyawar face din sa ta sauke idanun ta,kura masa idanu tai tana kallon sa,Yaushe to ya shigo mata daki,duk abunda takeyi yana kallon ta.Lips din ta ya ya shafa da hannun sa,dan zaro idanu tai tana kokarin juya masa baya,saurin juyo da ita yayi,ai yarinya baki isa ki juyan baya ba,wllh saina fadawa Dada kashigomin daki,kanta karasa ya hade bakin su waje daya,wani princess kiss yake sakar mata,tuni Hamna tai tsit tana sakin numfashi,jin Abunda yake mata ya wuce tunanin ta ta saka masa kuka,dan dole ya rabu da ita karta tara masa mutane.

"Ana kiran farko ya fice daga dakin.Tun daga wannan ranar tare suke kwana,Dada nacan shanye da baki bata taba sànin Abunda yake faruwa ba."Ammi tana yawan kokon to akan Hamna,ganin yadda komai nata ya kara fitowa,ta kara girma da gogewa,idanun ta kyar,Sadauki ya gama goge mata hadda,bayan karatun sa babu Abunda ke kanta akarance tsaf,ko yaushe tana manne dashi ya gama fitsarar da ita."Dada yau tunda ta fito take Kallon ta,wai takwara kodai wani maganin uwarki ke baki,kalli yadda kirjinki sukai ritsi ritsi kamar zasu tsokanewa mutum idanu,nifa cikin wata daya naga kin kara wanann girman,bata fuska Hamna tai,haba Dada wai me duk salan kibawa mutum kunya kin iya,yanzu kuma da wani yaji fa,ke banson mita,bazan fadi Abunda ke raina ba haka kawai.Zumbira baki tai ta tashi tabar part din Dadan."Clashing sukai ita da Sadauki,saura kadan ta fadi ya taro ta,matseta yayi yana Kallon ta,Kallon sa tai da sauri,yaya muna kan hanya fa,so kake sai wani ya gammu,daga mata gira yayi to mene,ko haram mukai,nidai sake ni,ci kata yayi ta kwasa da gudu, murmushi yayi tana Shafa kansa,shiyasan Abunda ya shirya.

"Karfe 9 ya shigo Gidan,kai tsaye part din sa ya wuce hannun sa rike da ledar,sai walwala yake yana murmushi.Kajine masu zafin gaske,kamshi sai tashi yake yi,yau babu maganar daga kafa saiya angwance,kome ze faru sedai ya faru.

  🙄🙄🙄Lallai Hamna harna tausaya miki.

     Mrs Baba Bello Abubukar
     ......✍️✍️✍️✍️
         


                  'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris


*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 59_60


Bedroom dinsa ya shiga da ledar rike a hannun sa"kayan jikin sa ya rage ya dade kafin ya fito daga toilet din,farar jallabiya ya zira data tas,bayan ya feshe jikin sa da turarruka masu dadin gaske."Sallah ya tayar ya dade azaune yana lazimi,agogon bango ya kalla,karfe 10pm mikewa yayi ya zira silifas din sa mataushi."Kai tsaye part din Ammi ya nufa, Ajiyar zuciya ya sauke jin kofar part din abude,ahankali yake takawa baya son kokadan asan da shigowar sa,room din Hamna ya fada,tana kwance da alama bacci ba karamun dadi yake yimata ba."A hankali ya tako gaban ta, sleeping dress dinta da suka zauna das ajikin ta kamar dan ita aka yi su,betsaya wani tunani ba ya dauke ta cak yayi hanyar barin room din da ita.

"Hamna badai nauyin bacci ba,sam batasan bikin da akeyi ba,sàida ya shiga da ita bedroom din sa,tsakiyar bed dinsa ya kwanta da ita,da baya koma ya rufe part din gaba daya."Sake komawa yayi ya zauna kusa da ita,tausayin ta na tsirgawa azuciyar sa,kamar ya hakurar da kansa akanta,amma kash bazai iya hakan ba,yana cikin matsalar da bazai iya jurewa ba."yan yatsun ta ya fara ja ahankali,cikin magagin bacci ta fara bude idanun ta,biji biji ta soma ganin sa,ahankali ta mike zaune tana kallon sa,maida kanta tai tana kallon inda take,kallon sa ta sakeyi da alamar tambaya a fuskarta,yaushe ya kawo ta nan din,haka an taji tsoron sa ya darsu azuciyar ta."Kokarin mikewa take ya ruko hannun ta,Yayah kasakeni na tafi na kwanta bacci,tana maganar tana lumshe fararan idanun ta."Murmushi yadan saki,nima yau anan zamu kwana aramawa kura aniyar ta,kullum ni nake zuwa tayaki kwnaa,nima yau saiki taya ni,kwabe fuska tai kamar zatai Kuka,idan Ammi tasan anan na kwana fa?"yadda tamaida fuskarta shima haka yayi,nima da Annin taganni fa da nake zuwa, murmushi tayi ganin yadda ya koma kamar wani baby.

"Saidaya jata da hira ta warware kafin ya rike hannun ta,kinyi wanka da zaki kwanta,daga kanta tayi alamar eh,jeki dauro Alwala,nayi sanda zan kwanta,kisake wata,wannan ta karye tunda kinyi bacci,babu musu ta mike,rigar jikinta iya guiwace,hakan ya bawa kafafuwanta dogaye damar fitowa farare tas dasu."Cikin mutuwar jiki ta dauro Alwalar,gaba daya jikin ta babu dadi ga faduwar gaba data dame ta,daurewa kawaii tayi tafito,hijab ta tatar ya ciro mata,dama tana da kaya a part dinsa,wanda ta rasa meyake yi dasu har haka.

"A bayan sa ta tsaya, raka'a biyu sukai ya jima yana kwarara musu Addu'a,shafawa sukai tana kokarin mikewa ya ruko hannun ta,kancinyar sa ya daura bayan ya zare hijab din jikin ta,ajiye hijab din yayi agefe kafin ya maida idanun sa kanta,gaba daya tsoron sa ya fara cika zuciyar ta,tarasa wane irin lallabawa yake mata a cikin darannan kamar zata rusa Kuka haka take ji."Ledar daya shigo da ita ya jawo,sai plate da knife daya dakko,kazar ya bude wani kamshi ne ya daki hancin ta."Sai data hadiye yawu,Hamna akwai san nama.

"Yankowa yayi ya dinga bata,babu musu ta dinga karba,saida taji cikin ta yakai geji kafin ta kauda kanta,shima ci yayi kafin ya jata toilet,brush sukai ita ce ta fara futowa bacci ne Kawai yake fisgar ta."Hayewa bed din tai tare da jan blanket har kanta,koda yafito kallon ta yayi ya karasa gaban mirror,sàida ya kara shafe shafen sa kafin a hankali ya karasa kan bed din ya zauna."Sàida ya gama tofe ta da Addu'a kafin ya rage hasken dakin ya kwanta."Jikin ta ya jawota,rawa jikinta ya dauka,dariya ma taso bashi wata sabuwar gulma."Zazzafan romance ya gara bin kowace gaba ta jikin ta,tun tana tureshi har jikin ta da ruhinta ya fara amsar sakwannin sa, ahankali yayi fatali da dukkan kayan jikin ta,haduwar fatar su waje daya ya kara susuta shi."Hamna gaba daya rudewa tai ta gigice,be taba yi mata abunda yake mata ayau din ba, kwakwalwar ta nema take ta buga,saboda abunda yake yawo akan ta.

"Dadin da take ji ne ya koma wuya,tuni ta dawo daga hayyacin ta,jin wani bakon abu megirma agareta,wata azaba take ji wadda bata taba jintaba,kokarin kwace jikinta take amma ina gogan yayi nisa sam bayajin kuka da rokon da take masa,tun tana Kuka hartagaji taishiru,hawayan ma yaki fitowa ko kadan,tun tana sanin me yake aikata mata har tadaina gane komai."Tsahon awa biyu yana abu daya gaba daya ya manta dawa yake tare,kankameta yayi ajikinsa tana sakin numfashi,wani hawayan farin ciki yaji yana sauka kan kuncin sa,wanda ya rasa gane na menene ne.

"Shafa kanta yake ahankali,sai Lokacin yaga jikin ta ya saki gaba daya,da sauri ya mike yana lalubar abinda zai kare jikin sa,dagota yayi gaba daya ajikin sa,yaraf ta zube ajikin sa,da hanzari ya daga ta tsam yayi toilet da ita,ruwan zafi ya tara kafin ya tsullumata,wani numfashi taja kafin ta zabura zata mike,cikin azaba take neman kwacewa daga rukon da yayi mata,Kuka take sosai idanun ta da fuskarta sunyi jawur,haka idanun ta sun kumbura.

"Sàida yagama gasata,sannan yayi mata wanka,nadota yayi a towel idanun ta arufe ko san ganin sama batayi,kan sofa ya kwantar da ita, bedsheet din ya cire ya sauya wani,dakko ta ya sakeyi,kaya masu kauri ya saka mata,lullubeta yayi kafin shima ya koma ya tsaftace jikin sa,cikin wani irin farin ciki yakejin zuciyar sa."Blanket din daya lullube ta yashiga shima jin jikinta zafi zau yasashi tashi,box dinsa ya dakko ya dauki magani,ruwan dake dire a side drower ya dauka,saidaya ballo kafin ya dakko ta da kyar tasha maganin Kuka take ba kakkautawa,jijjigata ya hauyi yana fada mata kalamai medadi,ahaka bacci ya dauke ta.

"Fuskarta ya kurawa idanu yana jin matsananciyar kaunar ta,Hamna danja,shafa kansa yake yana sakin Murmushi,shikadai yasan irin dadin daya ji agare ta,yayiwa Ammi Addu'a ba kadan ba da tahaigomai mata kamar Hamnan sa."Har gari yayi haske basu motsa ba,kukan Hamna ne ya tashe shi,kara daukarta yayi ya gasata sosai,taji dadin jikin ta babu laifi,kaya ya canza mata,azaune tai salla gaba daya kafafuwanta sun kasa daukar ta,tafiyar ma atattale takeyi ko ina najikin ta ba dadin sa take jiba.

"Kujerar mirror ya jawo ya dora ta, murmushi ya sakar bata,ko kadan batai kokarin mayar masa ba,fuska aturbune take kallon sa."Wardrobe dinsa yasa key ya bude,wani kit ya dakko me kyan gaske,a kusa da ita ya zauna,budewa yayi wata sarka ce me azabar kyau ta kashe mata idanu,wadda ylta ninka wadda tataba gani.awajan sa,kyau da tsada ta ninnin kata."Mikewa yayi ya zagayo bayanta,sarkar ya dakko ya saka mata,ba karamin kyau tai mata,dan kunnan ma da.kansa ya samata,awarwaro da zobe,harda abunda ake sawa a hanci,dana tsakiyar gashi,kai yadda kasan indiya haka ta koma,duk yadda take fushi dashi dataga wannan sarkar sai taji ta huce.

"Kallon kanta tai a mirror ta kalle shi,daga mata gira yayi,anyi 50 50 ba cuta ba cutarwa,an zaman wife na bada sarka,rufe fuskarta tai,dariya ya dan saki yana lakace mata hanci, gaskiya Yayan nan baida kunya,ta ayyana azuciyar ta,amma hakan bazai hana ta kaishi kara wajan Dady ba,amma tace yayi mata me?gaskiya bazata iya fada ba,ita kadai take zancan zucin ta."Daukar ta yayi suka koma parlor,ranar da kansa yayi musu girki,sunan kule a part din sa yana tattalin matar sa.

"Ammi tunda tatashi bataga Hamna ba tai shiru da bakin ta,haka Mommah babu wadda ta tanka, Dada ce kadai ta dinga sababi ina Hamna tatafi,babu wanda yace kala,saidaya tabbatar sunbar parlon Ammi din yakai ta ya zaunar da ita,kamar sarauniya haka ta koma,ya tsantsara mata kwalliya,har Lokacin sarkarta na jikin ta,wani sari ya saka mata golden sai yabi farar fatarta ya lafe."Mima da sakkowar ta kenan ta hango Hamna,har neman faduwa take wajan sakkowa dan ganin wace ba indiyar ce ta ziyar ce su,turus ta tsaya tana karewa Hamna kallo,mamaki kamar ya kashe ta,ganin yadda tai wani masifar kyau."Hamna,ta gifta sunan ta, na'am Hamna ta amsa bakin ta dauke da murmushi.

"Ammi zo kiga yadda Hamna ta koma,sakkowa Ammi tai tana kallon Hamnan ita kanta tayi mamakin yadda taga Hamnan tayi sharshar da ita, murmushi Ammi din tai,bata tambayeta waya bata kayan jikin ta ba,amma zuciyar ta tacika da farin ciki ganin yadda Hamnan tayi wani kyau namusamman."Mommah shigowar ta kenan ta hango su tsaye,matsowa tai ita ma tabawa idanun ta hakkin sa,ita kanta kallon Hamnan ta tsaya yi wadda ke washe baki tana san daure ciwon da takeji ajikin ta,yadda Hamna take da.kiriniya sukaganta ta nutsu waje daya,kallon juna sukai ita da Ammi,kasa dakai Ammi tai tana barin wajan.....

🌹🌹🌹🌹Hamna ta zama amarya,Hamna ta zama.'yar gata💃💃💃.

    Mrs Baba Bello Abubakar
       ......✍️✍️✍️✍️



         'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 61_62

"A hankali Mommah takarasa inda Hamna ta kame ko kwakwkwaran motsi batasan yi,kamo hannun ta Mommah tai batare da tace komai ba,duk yadda taso ta daure takasa,sosai wajan yayi mata tsami, fashewa tai da kuka bayan Mommah ta mikar da ita tsaye,ajiyar zuciya Mommah ta sauke,hasashan su ya zama gaskiya kenan."Daure Hamna,cikin tausayawa Momma take kallon ta,da kyar ta kai kanta parlon Mommah, toilet ta jata gashi me sunan gashi tai mata,Kuka ta tinga rusawa, Mommah ganin barnar daya yiwa Hamna abun bakaramin fusatata yayi ba."Saidata tabbatar bazata sami wata matsala ba kafin ta kyaleta haka,kamo hannun tayi jikin ta daure da towel,sosai taji dadin jikinna ta.

"Bedroom Mommah ta wuce da ita tana ayyana saita wanashi kafin ta bashi matar sa."Kaya masu kauri ta saka mata,tea me zafi ta hado mata,da kanta ta dinga bawa Hamna abaki,badadin sa takeji ba,haka Mommah ta dinga cusa mata."Magani ta bata ta kwantar da ita,babu dadewa bacci yadauke ta."Mommah kallon ta take tana ayyana irin kaunar da take yiwa Hamna,mikewa tai ta fada kiching dan fara aikinta,saita kara gyara Hamna ciki dabai."Sàida Hamna tai sati biyu ahannun Mommah,gyara take sha tako ina,Sadauki kamar yayi hauka ya roki Mommah ta bashi matar sa,amma ko kallonsa batai ba,sai data tabbatar tawarke ras kafin tabarta ta koma part din Ammi."Babu katya ita ma tai missing din Yayan nata,sai duk ta damu saboda fushin da yayi ya daina zuwa rokon Mommah.

"Karfe 9 ta salallaba ta shige part dinsa,yana zaune yana aiki a laptop din sa,duka yadda yaso shareta kasawa yayi,hannu ya mika mata,cikin wani salon taku najan hankali ta karasa gaban sa,dandanan ta susutashi,kamshi ya riga ya zauna ajikin ta,matseta yayi yana sakin numfashi,shiru tai ajikin sa,tayi missing dinsa ba kadan ba."Tundaga wannan rana suka kara dinkewa,soyayya suke kwasa sun manta da kowa da komai."Dada duk abunda ake bata da labari,tana can hankali kwance sai nan da shekara zata bashi matar sa."Ammi tana ganin Abunda ya isheta yanzu babu kunya Sadauki zai zo yawuce ta ya fada dakin Hamna,abunda ya isheta hada kayanta tayi ta kaita har part din sa,jankunne tai mata karta sake ganin kafarta a part dinta,bazasu maidata mahaukaciya ba."Abun yayi musu dadi sai sika kara baje kolin soyayyar,suke cin karan su babu babbaka.

"Watan Hamna biyu ta fara wani Zazzabi me zafi,sanda zazzabin ya rufeta tana kwance dakin Dada,zuciyar ta tashi take kamar zata amayar da 'ya'yan cikin ta,sosai hankalin ta ya tashi,ruko Hamnan tai ta gyara mata jikin ta."To ni Fatsima wane irin Zazzabi ne wannan,ba mamaki maleria ce tai miki mugun kamu,ganin zazzabin nagaba harta daina game wanda ke kanta hankali tashe suka kinkimeta sai Asibiti."Munir Dada ta kira ya duba Hamna,kallo daya yayi mata yasan abunda ke damun ta."Tes yasa akai mata, fitsarin ta ya nema Dada ta fara sababi me za'ai da fitsari daga maleria ta kamata,babu wanda ya tanka, Mommah ce ta kamata sukai toilet,kawowa Nurse din tai ta kara maida Hamna ta kwantar."30mnt result ya fito,su Dady asibitin suka yo jin labarin Hamna babu lafiya."Zama Munir yayi yana kallon su da murmushi,daidai Lokacin Sadauki ya shigo hankali tashe,ganin Iyayan sa awajan yasa shi dan dakatawa.

"Shigo mana Munir ya fada yana sakin Murmushi, congrats ina tayaku murnar karuwa da kuka samu,Hamna nadauke da juna biyu na sati Biyar,dum kowa yaji kansa yayi amma banda Mommah da Ammi sunsan kwanan zancan,Dada da take masa kallon mahaukaci,Manniru lafiyar ka kalau kuwa,anya baka fara shaye shaye ba,shiru yayi yana mamakin furucin ta,banda Iskanci irin naka yarinyar da bata tare dakin mijin ta ba, za'a yiwa maganar ciki."Dada wannan aiki nane tabbas haka maganar take,a tsorace ta juya tana kallon Hamna,wadda kunyar duniya ta gama kamata,kallon kurilla Dada keyi mata,maida kallon ta tayi kan Sadauki,Nayadda kai tsohon jarababbe ne,yanzu wannan ta tsitsiyar kabi ka danne ka durkawa ciki,kowa kasa yayi da kansa ba karamar kunya ce ta kamasu ba.

"Kema Munafuka,ni zaku ha'inta to bani kika cuta ba kanki,Dada banda masifa babu abunda takeyi,mikewa tai,bazan zauna jinyar asara ba,tunda kikasan hanyar dakin miji ai sai ka zauna kai jinyarta ka karasa shanye roman,ficewa tai afusace su Mommah suka take mata baya,abun ya masifar bata haushi,wai ciki sun shammace ta.

Har sukaje Gida fada take,su mommy sai data zage su tas da hadin bakin su,hakuri suka dinga bata amma kamar zugata sukeyi.Ahankali ya karasa gaban ta,ganin yadda take kuka sai ya shiga damuwa ko cikinne ba kyaso?, Girgiza kai tayi alamar a'ah,to menene?Dada tai fushi dani.Ajiyar zuciya ya sauke,karki damu indai Dada ce zata hakura kinji,to ta amsa, rungume ta yayi kamar zai maidata ciki."Ganin taji sauki suka koma Gida,sosai yake tattalin ta kunyar kowa takeji agidan shiyasa take makakewa a part din su taki fitowa,su Mommah ganin tana wasan buya sai sauka rabu da ita,sai dare take zuwa gaishe su,tasha tsokana wajan su mima,ansa ranar Auran suma.

"Mom me kafa daya haka ta cangalo tazo duba Hamna ta nuna murnarta sosai na samuwar cikin,ta jima wajan Hamna,tana sake koya mata dabarun zama da Miji,oh lallai su Mom an saduda."Gaba daya tayi laushi kamar ba Jamilah 'yar kwalisa ba,ta koma ustaxiya karfi da yaji."Zaman Khalid da Feedo sai ahankali haryanzu ana nan ana bugawa,amma ba kamar daba,ayi tsiya ayi dadi."Hamna na samun kulawa ta kowane bangare tun Dada na fushi hatta sakko ta fara tattalin cikin,ajika wancan aba ta ajika wannan, Sadauki sunsha fada da Dada akan tadaina durawa matarsa magani tace saita dura."Cikin Hamna ya fara fitowa tayi kyau ta kara girma,ta kama mijin ta ram ahannu,katafaran gidan su nanan saita haihu zasu koma."Ammi ma tana bata tata kulawar Haka Mommah kamar ta goyata,su Abbah ma kowa da tsarabar da yake kawo mata,ta ko ina Hamna bata da wata sauran damuwa.

Yauma tana zaune da tirtsetsen cikin ta,ta shiga watan haihuwarta, tana wajan Dada saboda kar nakuda ya tasar mata,goba ce ahannun ta tana ci suna hira da Dada da su Ammi,wanda suka maida part din Dada dandalin su,hatta Mom tana zuwa hira tare da yaranta,ayanzu kawunan su a hade yake,babu nuna banbanci tsakanin yaran su,Feedo ma na zaune ana hira jefi jefi."Hamna jitai kamar an mintseneta ta share,bayan tane ya fara amsawa nan ma takanne ta dauka abun nawasa ne,gyara zamanta tai gobar hannun ta ta ajiye tare da cire dankwalin kowai zataji Iska,nan ma ba canji,mararta da tai wata irin murdawa batasan sanda ta zabga salati ba,abunda ya jawo hankalin su kenan suka yo kanta.

🏃🏃🏃To fans kuta ho mu karbi haihuwar Hamna.

           Mrs Baba Bello Abubakar
              ...  ✍️✍️✍️


         'YAR ARO

Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*

Page 63_64


"Wani salati ta kara zabgawa hankali tashe suka yo kanta,Hamna suke ambatar sunan ta,wani ruko taiwa Mommah saida kashin hannun ta Yayi kara, Ammi tana zaune amma zuciyar ta cike take da tausayi 'yar ta,ta kanne ta dake ne dan kar ace bata da kara,ku kikkimota mutafi asibiti,tare suka ciccibeta,Mom ma sandar ta ta dogara tashige mota."Wayyo Allah Dada bayana zai balle aciremin ciwonnan dan Allah Dada,Dada sai share hawaye take na tausayi,haka Mommah,su mima kuwa Kuka suke ka shirban,suna ayyanawa aransu sun fasa Auran,dama haka akeji in Za'a haihu?tabdijam.

"Suna marasa hospital Nurse suka amsheta,sanin matsayin mijin ta a hospital din room na musamman aka kaita."Da sassar fa Sadauki ya fada dakin,tana hangoshi ta miko masa hannu,babu baki Yanzu sai ido,abunda takeji yanzu ya wuce bakin ta ya furta,wata Irin azaba take ji tana ratsa dukkan sassan jikin ta,tayi zuru zuru kamar ba ita ba.Hannun ta ya kama cikin tsananin tausayi,sosai jikinsa yayi sanyi ganin yadda kamannin Hamna suka sauya(Allah ya sakawa iyayan mu,da mafificin Alkhairi.Allah kayi musu tukuici da Gidan Aljannah).kusan awa daya Hamna ta kwashe babu wani Labari sai bakar wahala da take sha,su Dada nacan waje ana ta zagaye ana salati,ko wacce kagani zuciyar ta cike take da zullumi.

"Dr muhseen shawara ya Sadauki aimata cs dan tsira da rayuwar ta da ta abinda me cikin ta,kasa sa hannu yayi sai Abba ne yasa,yana zaune ya rasa abunda yake masa dadi,wani gumin tashin hankali ne yake tsatstsafo masa."Ana shirin kaita dakin operation nakudar ta kara tashi,da karawa sukai suka fara yi mata temakon gaggawa,cikin hukuncin Allah sai ga kan baby,kara jawo shi sukai,babyn na fadowa Hamna ta suma sabida wahala,ga jikin ta da yayi lauahi."Kukan babyn karade dakin yayi ya ware muryar sai canyara Kuka yake,na waje ma na jinsa,Hamdala su Mommah keyi.

"Sadauki bata baby yakeyi ba,saidaya tabbatar da matarsa ta farfado yana ganin numfashin ta hankalin sa ya kwanta."Gyara baby sukai tsaf,baby boy ne me tsananin kama da iyayan sa,dama kamar su daya komai nasu iri daya me."Dan danan asibiti ya cika da 'yan uwa da abokan Arziki."Hamna ma angyara ta,bayan tasha dinki Saboda karuwar da tai,yarin katoto kamar ba ita ce ta haife shi,sanda nurse suka kira su Abba su shigo kowa jikinsa rawa yake ya fara daukar babyn.

"Big Daddy ne ya fara daukar sa,tsananin kaunar yaron ta mamaye kirjin sa, Addu'a yayi masa,mikawa Abba yayi shima ji yayi soyayyar yaron ta lullube shi,yadda kasan Hamnan sa sanda aka haife ta."Babu wanda be dauke shiba,Dada data dauke shi kinbadashi tai yana hannun ta,ta kwakume shi kamar wani zai gudu dashi."Hamna baccin ta take hankali kwance,jitai kamar ancire mata kaya haka taji,bata farka ba sai bayan magari ba,sannu sukai mata Gyada kai kawai take har yanzu bakin ta akulle yake.

"Mommah ce tai mata wanka tare da gasata,sai taji jikin nata yayi sauki,kaya ta canza mata ta kamota ahankali take ta kawa,Saboda radadin azaba da takeji."Tea Mommah ta hada mata me kauri,sai data sha sanan ta miko mata baby,kunya ce ta kamata ta rufe fuska,dariya suka saka kaji wata gulma,sanda kika dinga bin ubansa daki bakiji kunya ba sai yanzu,shiru kowa yayi suna jinjinawa bakin Dada da baya haila."Karbar sa tai soyayyar sa ta dura acikin zuciyar ta,wani irin so taji tanai masa wanda bata taba yiwa wani shiba, rungume shi tai tafi sukai suna sakin dariya,dariya tai ita ma.

"Sadauki shigowa yayi ba karamin birge shi sukai ba."Oh yau naga rashin kunya,tunda Yarinyar nan ta haihu sai faman zarya kake na gane take taken ka,to dakina zan mayar da ita,sai kaje can kaci jarabar ka kaikadai."Harara ya wurga mata zai magana suka hada idanu da Mommah,harara ta watsa masa,shiru yayi yana sosa kai,amma yaso nawa Dada amsa dai dai da lafaxin ta."Ficewa sukai suka bashi waje,amma Dada cewatai babu inda zata je,zaka tai kusa da Hamna babyn hannun ta ya amsa ya rike ahannun sa,kwantar dashi yayi ya janyota jikin sa,Dada dake tsaye ganin iskancin nasa yayi yawa ficewa tai babu shiri, murmushi ya saki dama dan ya kore ta yayi haka.

"Kiss ya manna mata agoshi yana kallon babyn, ngd my princess, murmushi ta saki dan jin dadin abunda ya fada mata,kalaman soyayya yaci gaba da fada mata kalaman soyayya.Dada da taji shiru dawowa tai ta tasa keyar sa agaba,ita ce ta kwana da ita,sanda zata fara bawa baby Mama Kuka ta dingayi saboda zafin da take ji,shiko babu ruwansa hankalin sa kwance yake sha,Dada fada ta dingayi mata ai kowama da haka ya saba,washe gari aka sallame su."Su Innar Saminu tuni aka hallara,da Innar Auwalu,idan ta tuna abunda ta dingayi musu har kunyar hada idanu takeyi dasu."Sunan Abbah aka saka Habibullah zasu dinga kiransa da junior."Kaya dai wannan baby ya sha kaya,ga ta babansa da kakkanin sa,hatta Mom ba'a barta abaya ba sàida tai masa kaya na gani a yaba,dashi da Hamna babu wanda bataiwa ba,kowa ya shaida shiryuwar Jamilah.

"Ranar suna ansha shagali anci ansha an raba kayayyaki,babu wanda zai kushe sai makiyi."Dada ce taci gaba dayi mata wanka,gyara take sha tako ina Sadauki dai saidai ya hangeta daga nesa,Dada tai kane kane,ta kankane komai,bata yadda ko nan da can ta matsa,tana lura da take taken sa,shiyasa ta hanashi sukuni da sakewa da matar sa."Bangaran Hamna ita ma batason Sadauki ya kusantota a yanzu,haryanzu bata mance radadin da taji na haihuwa ba,tana jin aranta ba ita babu kara haihuwa."Sàida tai arba'in aka fara shirin tarewar su sabon gidan su da Sadauki ya dankara,amma Dada tace sai sunje kauye sun zagaye dangi,ji yayi kamar ya kama Dada ya zane mata jiki,ya gama shirin tarbar matarsa amma ta bata masa shiri,fita yayi daga harkar su gaba daya,har Hamnan daina ganinsa tai,abun saiya fara damun ta,Dada kuwa ko ajikinta,catai yaje zai gama fushin nasa ya dawo.

"Hamna dai zuciyar ta taki kwantawa batason ko yaya yayi fushi da ita."Ammi basu sa musu baki ba,sun zuba musu idanu,antaba haka ki rikewa mutum mata saboda zagaye wani dangi akauye,sananin halin mitar Dada yasa sukai shiru basu tanka ba....

     Mrs Baba Bello Abubakar
       ......✍️✍️✍️✍️




         'YAR ARO


Funny Girl 🧕

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

Page 65_66

"Hamna kamar tai kuka ganin yadda Yayan ta ya banzatar da ita,washe gari Dada ta tisa keyarta suka tafi kauye,tunda driver yayi parking yan garin suka zubawa motar idanu ,da tunanin wadda zai fito daga cikin ta,Dada ce ta fara fitowa rungume da Junior a hannun ta,yara ne suka fara tsalle ga Dada ga Dada sannu da zuwa Dadah,nan hankalin mutane yayo kansu,manya da yara suka dungumo danyiwa Dada sannu da zuwa."Fitowar Hamna cikin wani tsadaddan less dinkin bubu yasasu dakatawa suna kallon ta,wannan wace balarabiyar Dada tazo da ita,sai binta suke da kallo kamar sunga TV."Murmushi ta sakar musu,abundariya saigashi sumà sun awashe jajayen hakoran su.

"Baku game taba 'Yar Aro ce fa,kallon Dada suke alamar basu yadda wannan 'Yar Aro bace,tsaki Dada tai kar Allah yasa ku yadda ke wic mushiga."Suna shiga suka tarar da mata da yaran Gidan ana jiran shigowar su Dada,kan Hamna suka yo anaimata oyoyo,kamar ba Hamnan da ba'a kaunar ta dawo daga yawo ba,Saboda inya shigo kowa saiyaji ajikin sa,yau sai gashi ita ce ake dokin ganin ta da marmarin ta."Sannun ku da zuwa har rige rigen gaisheta akeyi,sai amsawa take da fara'a a fuskarta,su Innar Auwalu baki yaki rufuwa sai kallon Hamna suke,kamar ba ita bag ta canza tayi matukar kyau.

"Kaji aka kama dandanan aka yanka su guda Uku,girki akai musu medadin gaske,tuwon dawa aka mullika musu,miyar kubewa bushashshiya,ga man shanu da aka zuba ya wadatu,ga nama aciki,kai abun ba'a cewa komai."Hamna zama tai ta kwashi abincin,tayi missing din abincin kauyan,ba karamin dadin sa taji ba,haka Dada aka kalmashe kafa ana wullla tuwo baki,haba yanzu nasan naci abinci,amma haka kawai aita baka kayan fulawa kana ci,ba dole basir ma ya kama ka ba,yaushe rabon da naci tuwo,nifa Hamna kina tafiyar zan tattaro na dawo kauyennan nafijin dadi da rayuwa ta Anan.

"Hamna da take dariya ganin yadda dada ke warba loma,ai yanzu Dada ba zaki iya rayuwar kauyanan ba,canfa kin saba da AC babu duhu kullum kina cikin haske,ga babu sauro,nan Kuwa ai kanki kara sabawa za'a dade,shiru Dada tai tana nazari kuma fa hakane,gaskya in tadawo kauyannan akwai matsala,gwara ta zauna acan,amma sai tayiwa Hamna shiru dan kartai mata dariya.

"Sai washe gari suka fara zagaya wa gidan 'yan uwa da abokan arziki,bayan tataburazr da aka sha da junior kan yayi bacci saboda zafin daya dameshi,yasha Kuka ya hana kowa sukuni,sai 'yar karba karba aka dingayi ana goya shi."Duk inda Hamna ta zaga san ganin ta akeyi,kowa burinsa yayi magana da ita,ta zama tauraruwa acikin kauyannan."Satin su biyu suka juyo Gida,bayan taje gidan kawayan ta,yanzu Hanne yaranta biyu,amma duk ta tsofe kamar ba ita ba,saboda wahalar kauye,kiyi daka,kece surfe,kece debo ruwa kullum matan su na tafe a kan hanya.

"Su Ammi sunsha tsaraba,washe gari su Hamna zasu tare a sabon gidan su,baccin gajiya sukai sosai, Junior hankalin sa kwance yasha baccin sa."Washe gari gyara n musamman Mommah tasa aka zo hargida aka sakeyiwa Hamna,fatarta sai sheki takeyi kamar tarwada,ta kara haske da cika,tadanyi jiki ba kamar daba,kunshi da kitso aka yarfa mata,tayi masifar kyau,duk inda ta motsa kamshi ke tashi ajikin ta."Karfe 8 aka kawo motar tafiya,yadda kasan za'a kai Amarya haka aka jere motoci,Munir ne da wannan aikin gogan yana can yacika kamar zai fashe."Kowa ma sha Allah yake furtawa ganin yadda gidan yayi kyau.Plat ne me kyau madaidaici,babu hayaniya haka akai tsarin gidan.

"Muhadu a parlo ne,sai dakuna guda biyar dake cikin kayataccen parlon,komai pink ne a parlon,sofa da labulaye,sunyi kyau,ankashewa Hamna kudi kaya set biyu akai mata,Abba da Big Daddy sun mata."Karfe 8 kowa ya kama gabansa,daga Hamna sai Junior dayake ta wasansa,yana kalle kalle,yafara wayo sosai,watan su biyu cif da haihuwa."Wanka ta sakeyi ta mulke jikin ta da turarurruka masu sanyin kamshi, sleeping dress tasaka masu kauri,saboda yanayin garin yadda yadan fara sauyawa, junior ma kayan ta canza masa da masu kauri.

"Zaman jiran Yayan ta tayi,harta fidda ran zaidawo,sai kusan 10pm taji tsayuwar motar sa,da sauri ta mike ta kara kallon fuskarta,kafin ta kara faffeshe jikinta da turare,silifas ta zira ta fice Parlo."Bayan labulaye ta buya,yana shigowa ya Lumshe idanun sa,jinwani sanyi da yake ratsa zuciyar sa,karewa parlon kallo yake ta ina zai ganta,saiya tuna ma fushi yakeyi da ita."Ahankali ta fito beyi auneba yaji ta rungume shi ta baya"jiyayi kafafunsa na neman kasa daukar sa,da sauri ya zayo da ita gaban sa, murmushi da take sakar masa ya kara hautsina shi."Duk wani laifin d tai masa ya nmeshi ya rasa,yayi kewarta ba kadan ba,kiss ya fara aika mata,gaba daya sun rikita juna,ganin abun babbane ya sun kuci matar sa sukai bedroom.Asuba tagari 'Yar Aro.

"Washe gari da kyar ya barta,taji jiki bakadan ba,saboda gyaran data sha bana wasa bane,sàida yaga ta saka mai Kuka ya lallashi zuciyar sa ya barta."Tasha gashi sai Lokacin tadanji dadin jikin ta,shine ya shiga kiching break ya hada musu,da kansa yayi feeding din ta."Tana kwance ajikin sa sai shagwaba take zuba masa,mutumin sai kara rikitashi takeyi,ganin take taken sa yasa ta faki idanun sa ta sheka daki dagudu,key ta murza ta lura abunnasa bana wasa bane,baya ji baya gani.

"Magiya yayi tai mata ta bude amma taki budewa."Rayuwa sukeyi cikin jindadi da farin ciki,anyi bikin su Mima, Bilkisu ma Anyi Auran ta, Mom ta kara zama shiru shiru.Papi ya kara Aure,wata bazawara ya Aura Aisha me kirki, Mom bata nuna komai ba duk da kishi nacin zuciyar ta."Yanzu hankalin wannan family akwance yake,Feedo ma ta rungumi mijin ta,zaman lafiya sukeyi ta haifi diyarta mace, Hajiya Kudrat ma an zama saliha Duk wani rawar kai ta dena shi."Zaitun dai daga karshe rasuwa tai cikin mugun yanayi,Allah yayi mana kyakykyawan karshe.

     3years Ago

"Gidan Hamna na sake lekawa,suna zaune aparlo ita da Sadauki sun kara wani irin girma da kyau,kamar ba Hamna ba,ta zama babbar mace, junior ya zaka dan saurayi sai wasa yake da keken sa,bayan keken akwai zukekiyar yarinya yar kimanin shekara daya,sai bangala dariya takeyi suna wasa da yayan ta.Su Hamna sai kallon yaran su suke cikin so da kauna,kallon juna sukai tare da sakarwa juna murmushi,kashe mata ido daya yayi,fakar idanun yaran sukai suka fada daki.

    "Nima anan naja tunga na tsaya.
    Anan nake cewa Alhmdlh godiya ta tabbata ga Allah me komai me kowa,daya aramin Numfashi na karasa wannan Littafi cikin koshin lafiya.
    
    Abunda na fada dai dai Allah ya bani ladan sa,kuskura danai acikin sa Allah ya yafe mini.
    
    Ina Godiya agare ku fans bazan manta daku ba,inai muku fatan Alkhairi.
    
    Allah ya karawa Annabi Daraja.
    
    ALHMDLH ALA KULLI HALIN
        
         TAMMAT










       
    



Post a Comment

0 Comments