DANGINAH BY KULSOOM ISAMA'IL IDRIS MRS BABA BELLO ABUBAKAR OUM ANEESAT &NIHLA
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
Da sunan Allah mai RAHAMA maijin kai.
Wannnan Littafin Nawa kirkirarrene banyishi dan cin Mutuncin wani ko Wata ba.
Ya kunshi abubuwa da dama.
Tausayi
Juriya
Biyayya
Butulci
Soyayya
Da sauran su.
Na sadaukar da wannan Littafi ga kawayena na Amana
Aisha Abubakar Muhammad
Salamatu Assadi Adam
Firdausi Auwal Khalid
Fatima Yusha'u
Sa'adatu Sani
Suwaiba Mansur
Bilkisu Mansur
Nabila Abubakar
Ramlatu Muhammad
Hassana Abubakar
Sai kawata abar kaunata abar Alfaharina Fatima Abubukar Ina rokon ALLAH daya gafar tamata yasa tahuta ALLAH ya sanyata cikin rahamarsa Ina rokon ALLAH ya raya abun da tabari.
Nafara Rubuta wannan Littafi kamar haka.
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 1_2
KADUNA
Unguwar Kadaure
Unguwace wadda tatara mutane kala kala mutane daban daban, akwai masu hannu da shuni da masu karamin karfi."Wata babbar unguwa na fada gaba daya manyan gidaje ne, wannan yana wane wannan" dan kam layin ya cika da Motoci mutanene birjik kowa kaga fuskar sa cikin jimami take da alhini, wasu najan carbi wasu dai gasunan a tsaye.
"Gidan danaga ana shige da fice da alama anan abun ya faru cikin gidan na kutsa kaina, matane dan kam da masu Kuka da masu matsar kwalla kowacce dai da abunda take yi"maine parlo na zarce gawar mutane biyu ita ce shimfide atsakiyar parlon, sai wata kyakykyawar budurwa bazata haura 14years ba ta kan kamesu ajikinta Kuka take kamar ana yankar naman jikin ta.
Dan Allah Abbana da Ummina ku tashi karku tafi kubarni, meyasa zaku tafi alokacin dana ke tsananin san zama tare daku,ku kadai nake daku, kune takama ta ako da wane lokaci.Abbah Ummi kutashi na roke ku!!! sake fashewa da Kuka me tsuma zuciyar wanda yake sauraron ta da yawan mutanen parlon Kuka suke.
Wasu matane suka shigo su biyu hannun su aka suka fasa kuka, nashiga Uku ni Baturiya dan Allah yaya Idris katashi, Anty Sadiya kitashi ya zamiyi da rayuwar mu, kuntafi kun barmu wayyo Allah na ni Baturiya munyi babban rashi,wanda suka shigo tare ce ta karba Baturiya ninafiki yin babban rashi ni nasan wanene yaya wajan kyautatawa gashi yanzu mun rasa shi ya zamiyi fashewa da Kuka suka sakeyi.
Wannan budurwa cigabatai da kukanta, baji bagani mazane suka shigo daukar mamata, makara guda biyu aka shigo da ita, nan fa aka fara kokawa da wanann yarinyar, sai Kuka take tana zillewa kar adaukar mata iyayanta, Ummi na waya kashe ku ni banyadda mutuwa kukai ba ku sakeni na bisu!!!.
Wani daga cikin masu kokarin saka Alhaji Idris amakara ne ya riketa, haba Ansariyya kin manta kina damu muma iyayanki ne kiyi musu Addu'ar Allah yasa can tafi nan,bajin sa take ba ba kuma sauraron sa take ba.
Sanda akazo fita da su faduwa tai ta suma, Allah sarki rayuwa kenan,sàida aka yayyafa mata ruwa tukunna ta farfado, kukan ma ta kasa yinsa, kallon kowa takeyi kamar tababbiya haka ta koma, Ladidi ce ta jawota ta rungume kiyi hakuri Ansariyya Addu'a ce tamu Allah ya jikan yaya sake rushewa tai da Kuka.
Haka aka dinga karbar gaisuwa wannan yashigo wannan yafita, duk wanda zaizo gaisuwa saiya dunkule kudi me tsoka ya bada abin sadaka 'yan uwan Abba sune masu karba baba Yahaya da Baba Gali. 'Yan kauyan su mota guda sukai suka zo gaisuwa ranar sadakar Uku suka juya, mahaifan su sun riga sun mutu tuni sai dai dangi na kusa.
Sai da aka kwana 7 ana zaman makoki, ba kananan kudade aka tara ba amma babu su ba alamar su, Yahaya da Gali sunyi sama da fadi, su wanann mutuwa wata hanyar samuce ta bude musu. Su Hajiya Baturiya ma ai anci kasuwa yadda ya kamata, Allah kadai yasan kudin da suka samu shiyasa sukai bake bake wajan zaman makoki, basa yadda su matsa ko nan da can, kai har sallah sunsha hadawa azahar La'asar magari ba dan karma sutashi wani abun alkhairi ya shigo basa kusa.
Babu dangin Ummin ta ko daya dayake dama Ummi tsintar ta akai babu wanda yasan iyayanta mahaifin Alhaji Idris shiya tsinceta daga baya Abbah yaji yana kaunar Ummi, beji kyamarta ba haka ya nunawa Malam Usman yana san khadija, wato Ummi aiko ba wata jayayya haka ya aura masa ita sunyi zama na amana da kaunar juna.
Sun dade Allah be basu haihuwa ba,akallah sunyi sheru goma kafin Allah ya azurta su da Ansariyya, aiko Ummi tasha gori wajan su Hajiya Baturiya akan juya ce ga rashin asali, sàida Abba ya tashi tsaye ya taka musu burki kafin ya samu su rage abunda suke yiwa matar sa.
Anan Kaduna ya dankara katafaran gidan sa, abun hannun sa be rufe masa idanu ba, ko yaushe cikin kyautatawa 'yan Uwansa yake kai hatta jama'ar gari sunsan halin taimako na Abbah.
Uwar su daya Uban su daya da su Hajiya Baturiya Hajiya Ladidi Alhaji Yahaya da Alhaji Gali, babu wanda be mallakawa gida acikin su ba basu da nisa da shi betaba gajiyawa da dawainiya da suba.
Ansariyya tasha gata iya gata, hakan besa ta sangar ce ba sun bata tarbiyya dai dai gwargwado, sosai su Hajiya Baturiya suke nunawa Ansariyya kauna, tasha zuwa tai kwanaki agidajan su, kamar su goyata haka suke ji da ita, basu da wani 'ya'ya sosai Hajiya Baturiya bata taba haihuwa ba, yanzu ma bata da Miji, haka Hajiya Ladidi haihuwarta biyu Mijinta ya rasu bata kara Aure ba.
Baba Yahaya shine me 'ya'ya Biyar baba Gali me 'ya'ya Uku sai Abba me 'ya daya wato Ansariyya.
Lafiyar Allah suka kwanta, bayan sun gama hira da Ansariyya, babu ciwon kai ba komai salin alin suka kwanta,sai gawar su aka tarar, babu wata alama dazata nuna ga wata rashin lafiya data samesu lafiyar Allah.
Faduwa Ansariyya tai ta suma ba karamin tashin hankali tashiga ba na rashin iyayanta.
Anyi kusan kwana goma kowa ya watse tunda aka fashe, babu idan mutane su Hajiya Baturiya suka daina rarrashin Ansariyya, da taci da kartaci uwar su daya Uban su daya, sun mimmike kafa sai caskar dadi sukeyi, kajin da suke cikin fridge kullum gasawa suke suna ci, bayan farfesun da suke caska suna jindadi.
'Yan aikin Gidan tuni suka sallame su, akan aikin su ya kare sai ansake haduwa ta wani fannin, su kansu ma'aikatan sunyi kuka sosai, sunyi rashin Hajiay da Alhaji mutanan arziki wadanda suka san mituncin dan Adam.
Ranar kwana 11 da rasuwar Abbah, Baba Yahaya yazo da wasu mutane sunsha rawani,azuwan alkalaine sune masu raba gado, babu wanda yace àah dama kowa jira yake azo araba, sun manta yana da 'ya ita ce ahakku wadda zata fara cin gado,wani irin rabon gado akai na zalinci, baba Yahaya ne ya tashi da wannan katafaran gidan da suke ciki ahalin yanzu, sai baba gali da aka bashi gidaje da filaye, haka su Hajiya Baturiya aka rarraba musu gidaje da filaye, tas sàida suka gama rabe gadon atsakanin su.
Ansariyya na zaune agefe tana ganin ikon Allah, motocin Abba da kamfanin sa guda biyu, da wasu gidajan sa na ABUJA su baba Yahaya ya dage gadon Ansariyya ne, kuma ahannun sa zasu zauna, tunda shine babba, ankusa abawa hammata Iska akan wannnan gado, dayake yafi su fawa sàida yaci nasara akan su.
Aranar suka watse cike da farin ciki sun samu ganima, ranar Ansariyya ita kadai ta kwana agidan, tayi kukan da bata taba yiba hatta me gadi an sallame shi, washe gari iyalan Abba Yahaya suka dawo, matarsa Mama Saudat me matukar karamci da mutunci, haka taja Ansariyya ajiki bata taba nuna mata banbanci tsakanin ta da yayanta, haka suma 'ya'yan suna son Ansariyya, akwai sa'anninta acikin yaran shiyasa tasu tazo daya.
Ba arufe wata biyar ba, Abba Yahaya ya fara muzgunawa Ansariyya, kyara da tsangwama babu Abinda baya yimata, kullum Mama tana nusar dashi, amma yayi nisa bayajin kira, yanzu takai ta kawo yaji aransa bazai iya cigaba da rike Ansariyya ba.
Asafiyar yau ya kira Abba Gali akan yazo yana neman sa, koda yazo Ansariyya ya hadashi da ita taje tai kwana biyu
Da yake yaji ba dadewa zatai ba ya yadda ya tafi da ita, kaya kala uku Mama ta hada mata tunda ba dadewa zataiba badan ranta yaso ba tabi Abbah Gali, aiko taga wulakanci awajan Anty Zee kamar almajira haka ta mayar da ita, bata bata abinci saitaga dama, kwananta uku ya tattaro ta da kayanta aleda, jakar kayanta ma Anty Zee kwacewa tai.
Suna shigowa Abbah Yahaya ya mike, me kadawo da ita taimin? ai tunda ka karbeta ka karbeta kenan bazata dawo cikin gidannan ba, ka koma da ita nabarma ita halak malak.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 3_4
"To!!wallahi Yahaya kaji narantse yarinyar nan bazata zauna awajena ba, nima nawa yaran sun isheni, haka kawai ina fama da kaina ace saina dauke ta, sam hakamma bazata sabuba ehe"
Au haka kace!? nafada Yahaya saidai ta zauna gidanka amma ba gidana ba. Ke!!! Daka mata tsawa Abbah Yahaya yayi saidata razana, dauki kayanki kibishi yadda kuka zo wallahi haka zaku koma, dan baki da gurbi acikin Gidannan.
Haba Alhaji kaji tsoron Allah yanzu duk halaccin da mahaifin yarinyar nan yayi muku amma idanunku sun rufe, kun manta, cikin karaji yake fadin Saudat!! Kinsan girman ALLAH kika sake magana abakin Auranki.
Shiru tayi tana bin Ansariyya da kallo, sai rusar kuka takeyi, amma tsabar rashin imani an rasa wanda zai riketa acikin su, Gali kodai ka dauketa kona dauketa dakai da ita nahadaku na watsaku waje, tunda bawani shege ya ginan gidanba.
Damkar hannun Ansariyya yayi kiiiii yajata kamar kayan wanki yayi hanyar waje da ita, tana tirjewa tana komai kememe yaki sakinta,Gali ne yai wuff ya rike hannunta, kasan Allah bazata fita agidannan ba, sanda Ubanta yadinga baka kudi kana amshewa waya sani, ai yanzu sai aramawa kura aniyarta.
"Kuma banda kai tsohon Munafukine ubanwanene ya amshi gadonta,ko angayama mun manta,to inma bacci kake ka farka Yahaya"
Kai bana son munafunci kai be baka ba, ko bansan duk sati saiya turama kudin cefane ba, shine zakace yabani wani abu to matukar yabani, kaima yabaka, Allah na tuba har nawa ma naci abunda betaka kara ya karya ba.
Jani inja suka dingayi da ita, gaba daya nema suke su karya mata hannu, sai Kuka take kamar ranta zai fita ganin irin wulakancin da suke mata kamar basu hada komai da ita ba.
Saida Yahaya ya samu nasarar futo da ita, be wata wata ba ya hankado ta waje ita da Galin, saigata akwata tinjim, da kyar ta samu tafuto daga kwatar saboda rashin imani yana tsaye yana kallonta tana kici kicin futowa ko ajikinsa, baba Yahaya tuni ya koma ya datse kofarsa, cikin jin haunshi Alhaji Gali ya maka mata duka aka, shegiya mujiya me shegen bakin jini, wuce mutafi gidan Ladidi ko ALLAH zaisa ta karbe ki.
Haka tatashi baiwar ALLAH jikinta duk kwata, haka ta dauki dan buhun kayanta tabishi abaya, tafiya me nisa sukai kafin su iso gidan Ladidi, suna shiga ta toshe hanci kai da kata!! ina zakuje haka kamar wadanda aka koro.
Gaskya ku tsaya anan dan bazaku bata mun gida ba, tsayawa sukai nan Gali ya fara kora mata jawabi, Ladidi dama gani akai kece baki da yara da yawa, mukuma kinsan ga iyali sun tarar mana, shiyasa mukace bari mukawo miki ita,tunda ya fara magana take masa wani kallan sama dakasa, bangane me kake nufi ba nufinka wai nice zan riketa.
Bangaji asara ba, kai kanka kasani, duk abinda bazanci ribaba bayinsa nakeba, so kake gaba daya jarina mutaru da ita mucinye kome kake nufi.Hanyar waje ta nuna mai kaga nan tanan kuka bullo, to kujuya kasan banda mutunci wllh tun kafin nai maka dibar Albarka, haka kawai dama can bashiri nake da iyayan taba, baki bude yake kallanta, haba Ladidi kiji tsoran ÀLLAH jinake wannan gidamma Ubanta ne ya siya miki.
To gori zakaimin, dadinta dai bakaine kasiyan ba balle kace zaka kwace, ran kwashi ta sakar mata aka me ido irinna Uwarta, daina kallona ni Gida dai bazaki zauna acikinsa ba sai ayi waje.
Sanin rashin mutuncinta yasashi fita gaba daya ransa abace yake, ya rantse shima bazai maida ita gidan saba, kamar ya rufeta da duka haka yakeji, Yarinya ta zamar masa masifa kowa ya gudu yabarshi da ita, sai fama yake da jaraba fuuuu yayi gaba Allah sarki saita bishi abaya.
Wani matsakaicin Gida ya shiga bako sallama tana zaune tana kirga kudi, ganinsa yasa tai saurin boye kudinta, bata fuska tai meye hakane haka kawai zaka fadomin Gida kamar wanda kake bina bashi, eh ai kusan hakanne bashin da kikaci shine Lokacin biyansa yayi, ina fatan kin shaida wannan? kare mata kallo tai tare da mutsa fuska, naganeta mana, menene zakazo min da ita Gida, ko gaisuwar danai acan bata isaba saika sake biyoni Gida.
Ke!!! Baturiya da kata ba wannan ne ya kawo niba, zuwa nai da wannan yarinyar ta zauna a wajanki, ke kadai yafi da cewa ta zauna tare dake, tunda ba da ba jika kinga bazakice an dora miki wahala ba,tunda ya fara magana take kallon sa shekeke, shekewa tai da wata shegiyar dariya maida dan kwalinta tayi gaban goshi Gali Gali yaro besan wutaba saiya taka.
To ai tsaya na fada maka, ko su Inna ne zasu dawo daga Lahira basu isa su sani na dauki wannan yarinyar ba, ni kaga arayuwata duk abunda zaisa na kashe sisi bana kaunarsa wllh, to kaga rukon 'yar wani ai ba nawa bane. Kallon ta yayi cikin Masifa bangane 'yar wani ba har yaushe uban nata ya mutu da kika zare shi daga jikinki kema 'yarki ce.
Mekewa tai afusace, kaga to kai ka dauketa mana, wai ana dole ne, eh kana da gida ina da gida kaje ka kaita wajan matar ka mana, ni Baturiya nace bazan rike Ansariyya ba fakat, duk wanda zakaje ka fadawa kaje ka fada masa nace bazan riketa ba,kofa ta nuna masa kufitar mun daga gida kasanni sarai banda mutunci wllh kaje ka kaita dangin uwarta mana su zasu iya rike ta.
Rai bace ya dakawa Ansariyya tsawa wuce shegiya annamimiyar yarinya, me kafirin bakin jini, kai bantaba ganin me bakin jini kamar kiba, kowa baya kaunarki.Allah sarki Ansariyya babu abunda takeyi sai Kuka wani daci takeji a zuciyarta, meyasa kowa zai gujeta ya juya mata baya, alokacin da take bukatar taimakon su, idan ta tuna yadda suka kaunace ta abaya, abun yana bata mamaki yadda kasan kwai haka suke lelenta, ashe dama sabo da abun hannun mahaifinta suka nuna mata kauna.
"Dirka mata duka yayi abaya, ubamme kike tunani sai magana nake miki kin maidani dan iska, wuce ni me farar kafa"
Bawani nisane tsakanin su ba, ko sallama beba haka ya fada gidan sa, babban gidane get da get ,karewa gidan kallo nai harda 'yan aiki amma a kasa rike mutum daya, a kofar falon ta tsaya kanta asunkuye danjin tsoron abinda zaije ya dawo inta kuskura ta shiga da kwata ajikinta.
Anty Zee dake hakimce a parlor hango Ansariyya ya sata mikewa tana kallon Gali dayake rarraba ido, kallon tuhuma take masa rai bace take nuna Ansariyya, ya mukai dakai ba cewa nai karna sake ganin ka shigomin da ita cikin gidannan ba, koba haka mukai dakai ba.
Kiyi hakuri zee wadancan 'yan iskan gaba daya sunki karbarta, kinga ai ba'abarta ta dinga garari awaje ba.
To seme dan tayi garari awaje, ina ruwana, ta kama daki asabon garima niba matsala ta bace, haka kawai bana kaunar wanann yarinyar tuncan jinina be hadu da ita ba. Idanun Ansariyya ne suka ciko da hawaye wannan gidan yana daya daga cikin gidajan da Abban ta ya bari, sunshiga sunmike kafa amma take fadin wai dama can bata kaunarta, ashe dama makashinka yana tare dakai, in kana dashi baka taba gane makiyinka sai randa ka talauce, ko mutuwa ta dauke ka ananne zaka ga tsantsar wulakanci.
Ke!! taji muryar Anty Zee kina jina!! gyada kai Ansariyya tai, matukar zaki zauna acikin gidannan kisani saidai na sallami 'yan aikina baki daya, kece zaki dinga ko wane irin aiki, ke hatta tura get kece me wannann aikin, matukar zaki iya wannan ba matsala bace.
Zan iya Anty, abunda ta furta kenan hawayanta na sake kwarara, kin nemawa kanki maslaha, yau basai gobe ba zan sallami masu aiki da me gadi bazan dinga ciyar dake abanza ba.
Ko ajikin Gali bashi da damuwa tunda har ta yadda zata zauna Agidan, koma wane irin aikine taita sata, bashi da matsala da wannan. Sannan abu nagaba kannatashi daga bacci ki tabbatar kinyi wa Amir da Ameera wanka, ki shiryasu kisa musu uniform driver ya kaisu school.Ke driving dimma da kin iya kece zaki dinga kaisu,dan baki da wani amfani.
To Anty ta kara amsawa gwanin ban tausayi, maza wuce kije toilet din me gadi ki wanke jikinki ki canza kaya, karki yadda ki shigomin parlo da kwata ajiki.
Juyawa tai a sanyaye da 'yan kayanta aleda binta da harara Anty Zee tai kamar idanunta zasu fado,zama tai kaima nadawo kanka karnaji karna gani, karka yadda nakama ka kana kula wannan yarinyar, ban yadda ahada kulawar 'ya'yana da kowa ba, 'Ya'yan dana haifa acikina su kawai nasani nadai gaya maka.
Murmushi ya saki, Zainab kenan kina zatan zan dinga barnatar da kudina a aikin banza ne, ba haka nake ba ni dinnan da kika ganni nasan zakin kudi, bazan taba yadda na barnatar da su abanza ba,ah to yanzu naji magana cewar Anty Zee.
Allah sarki Allah ka rabamu da maraici.Maraici akwai ciwo musamman kakasa samun marika na gari, Allah kabarmu da mahaifammu wadanda nasu suka rasu Allah kayi musu Rahama.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
Kulsoom Ismail Idris
Page 5_6
Kamar yadda ta umar ceta haka ta shiga toilet din me gadin, yana daga zaune da redion sa ya hangeta, sàida yaji wata kwalla ta ciko idanun sa, Allah sarki rayuwa kenan cike da tsananin tausayin Ansariyya, inya tuno irin gata da kulawar data samu abaya amma kalleta ta dawo tamkar almajira, inama ace Allah zai masa arziki, babu abunda zai hana be rike ta ba sake sake yake tayi azuciyar sa.
Kayan data cire ta nufi bakin panpo da su, tarawa tai babu omo haka ta fara wanke su da ruwa kadai,gani tai ana miko mata kilin dan 30 dagowa tai tana kallon sa, idanun ta cike da hawaye take kallon Malam Audu, tun sanda ta rasa iyayanta babu wanda ya taba tausaya mata sai shi, murmushi ya sakar mata dafa kanta yayi Allah yayi miki Albarka, da sauri yabar wajan idanun sa cike da hawaye.
Binsa tai da kallo Allah ya saka mai da Alkhairi,Addu'a ta shigayi a zuciyarta,zazzagawa kayan tai sai data wanke su tas ta dauraye ta shanya a wata igiya can bayan Gidan. Ledar kayanta ta dauka kanta asunkuye ta shiga parlon da sallama, babu wanda ya amsa acikin su sai binta da kallo da sukai, akasa ta zauna nagama Anty Zee.
Ya mutsa face Anty Zee din tai ok, wata mata ta kwallawa kira Talatu, da sauri wadda aka kira Talatu ta fito kallonta tai kikarawo Jummai da Hansai, to ta amsa sanin rashin mutunci irin na Zee tsaf zata iya zageta bazata ga girmanta da shekarun ba,cikin sauri suka fito,gamu Hajiya, yawwa kunga wannan, kallonta sukai tana nan yadda take kanta asunkuye, sarai suka gane ko wacece eh mungane ta Ansariyya ce.
To me warin baki ban tambayeki sunan ta ba, shiru Hansai tayi ranta ya matukar baci,yau zan sallame ku tunda game aiki tazo Allah ya hutar damu bama dinga barnatar da kudinmu a aikin banza ba, daga yau itace zata karbe ku yanzu kuje ku fara hada kayanku ayi gaba akoma kauye kuma.
Kala basu ceba suka mike cike da Mamaki, wai itace zata dinga yi musu aiki in har ba idanun sune ya makance ba wannan ai Ansariyya ce yar gatan Abban ta da momin ta, amma yau ace ita ce zata zama house girl.
Amma wannan mutane bazasu ga dai dai arayuwar suba, maraniyar Allah bata jiba bata gani ba ku hadu kudinga zaluntar ta, Allah sarki rayuwa Talatu ce me wannan maganar,hmm Jummai tace aini nama kasa magana, wai yanzu arayuwar nan inbaka da iyaye sai yadda Allah yayi dakai, matukar dangi babu Allah aransu sai su manta baya.
"Jibi dai yadda uban yarinyar nan ya gatanta su, waishi me 'yan uwa yasha kaisu saudiyya ke kasa kasa babu inda baya tura su kasuwanci, amma shine bayan ransa ga abinda suke saka masa dashi" Uhm kedai Allah ya rabamu da mummunar kaddara dan wannan kaddara ce cewar Hansai, dorawa tai da fadin aini namaji dadin barin gidannan dama nagaji wllh, haba wanann jaraba haka babu damar kayi motsi sai ahauka da zagi da fada kamar wani karamin yaro.
Kikaji dadi ko naji, dama shirin yin sallama nake yi inji Talatu, saima gashi da kanta zata sallame mu kaf suka hade yan kayayyakin su.
Inda suka barta anan suka tarar da ita, duk sanyin kasa ahaka take zaune tatakure waje daya, hirar su sukaci gaba dayi kamar basu san da zamanta a parlon ba,mun fito Hajiya, kallon su tai daga sama harkasa, badai wani abu da kuka daukar mana ko,ci kanki babu wadda tanka mata 15k ta watsowa ko waccan su gashinan kudin aikin ku na rabin wata kwayi kudin mota.
Kwashe kudin sukai suka mike, au baku iya godiya ba,Jaummai ce ta juyo azafafe Godiyar me zamiyi, tunda ba kyauta aka bamu ba hakkin mune kinga kuwa ai babu wata godiya da zamu zauna yi, da dai da mutum cine mayi Godiyar ayi sallama cikin mutunci.
Wata ashar Zee ta lailayo tare da mikewa, harkin isa ina magana kina magana ke awa,jan hannunta Talatu tai dan Allah kizo mu tafi, ya zaki zauna kina haushi ai saiku zama daya keda ita,fita sukai suka bar Zee tana zage zage.
Ke kuma munafuka tashi ki dauki kayanki ki koma dakin da suka bari, da sauri ta mike dama zaman wajan ya isheta, dakin ta fada dakin ba laifi da girmansa, katiface guda uku irinta 'yan bording sai fanka datake juyawa aka sa, sai net dake daure a saman katifa, da alama su Talatu ne suka bar mata guda daya.
Akwai toilet acikin dakin dan madaidai ci, yanayin tsaftar su shiyasa bai lalace ba, suna kula dashi sosai share hawayan face dinta tayi, rayuwa kenan wai ita ce a wannan halin, ko amafarki tai mafarkin ta ganta a Wannan mummunan halin zata karyata mafarkin ta, sai gashi agaske ne ido bude take cikin wannan halin, amma bakomai akwai Allah shi kadai ne wanda zai mata magani.
Ta dade awajan tana Kuka, bata da wani gata sai Allah Allah shine gatanta,kiran sallar azahar aka farayi mikewa tai ta dauro Alwala tana idar da Sallah Anty Zee na kwala mata kira, da sauri ta fita har tana neman faduwa, tana hakimce a parlo Ameer da Ameera ne suka rugo da gudu oyoyo Anty Ansariyya.
Kai!! Anty Zee ta daka musu tsawa agidan ubanwa ta zama Antyn taku, ku dawo ku zauna karna tashi nai muku shegen duka,turus sukai suna kallon Maman tasu cikin mamaki Ameer ya kalleta Anty ko baki gane ta bane, na ganeta sai akai yaya ku dawo ku zauna ga cartoon nan anayi kuci gaba da kallo.
Komawa sukai a sanyaye suka zauna, Ameer yana shekaru 7 Ameera zatai 5years, tsurawa Ansariyya idanu sukai suna tunanin meyasa Maman su ta hanasu zuwa wajan ta, kuma ai tasaba zuwa Gidan su siyi ta wasa,ke kallon ya isa haka wayasanima ko uwarki mayyace, danni wllh idanun ki kama dana mayu yake,sunkuyar da kanta Ansariyya tayi,jin zuciyarta na zafi da kuna,nacin mutuncin da takewa mahaifiyar ta,alhalin tana cikin kabari.
Wuce ni kibani waje,kifita harabar gidannan duk wani ganye daya fado, ki sunkuya ki dauke shi,ban yadda kisa tsintsiya ba saikin tsince tas,sannan kidauki tsintsiya ki share,karki yadda na fito naga ba daidai ba,gyada kanta tayi hawaye na shatata afuskar ta,tana futa durkushewa tai akan guiwowinta fashewa tai da kuka me Azabar ciwo da radadi,daga hannayanta tayi dan taroki ubangiji ya kawo mata dauki,amma sam takasa furta hakan,jujjuya kanta kawai take cikin tsananin tausayin kanta.
Wace irin rayuwa zatai anan gaba,shine tambayar da takewa kanta,ashe haka maraici yake da ciwo,ashe haka dangi suke da butulci,ko dai ita ce batai sa'ar dangi ba,tabbas ita ce batai sa'a ba,tajima tana Kuka kafin ta mike,cikin jarumta yunwa takeji kamar zata fadi,amma tasan ba abincin zata samu ba,kallon harabar gidan tai yadda ganyayyaki suka fado sukai kaca kaca,yanzu wannan duk itace zata kwashe.
Sun kuyawa tai ta fara tsincewa,Lokaci lokaci tana sharce hawayan fuskarta,gajiya iya gajiya ta gaji,bazata iya wannan aikin ba,saidai yau kome anty Zee zatai mata tai mata,amma wannan aikin yafi karfinta ya girmi shekarunta,zubewa tai a wajan tana maida numfashi,bakinta ya bushe cikin ta tamkar ya hade da bayan ta,lumshe idanun ta tayi sama sama takejinta kamar ba aduniya take ba,ba zato taji saukar ruwa ajikinta,ruwane cikin bokiti Anty zee ta juye mata shi aka.
Eh lallai ma daga cin arziki agidana, nasakaki aiki amma ki kiyi ki samu waje ki kwanta,ina wllh da sake matukar bazan moreki ba waje road zanyi dake, Jijjiga take tana huci kamar wadda take dambe da sa'ar ta,da kyar ta mike jikinta na sake daukar rawa,kasa tsaiwa tayi akan kafafun ta,kiyi hakuri Anty yunwa nake ji,dakyar takai karshan furucinta,dau ta dauke Fuskar Ansariyya da mari,Ubanki ne ya kawo abuncin,ko mataccen Ubanki ne ya siyo mana kayan Abincin.
Girgiza kai tayi alamar àah,to kuma shine kike bude kazamin bakinki kike cemin yunwa kike ji,saboda raini ko saboda me,kikoma can gidajan sauran 'yan uwan ubannaki mana su baki Abincin,kai ni wllh amma cuceni da aka kakaba min ke,ba dangin iya ba na baba,wadanda suka zama dolenki basu dauka ba ni ambarni da wahala,zuwan ki yau kadai kinfara sani haushi kamar karya, tsaki taja karna sake dawowa na tarar dake baki fara Abunda na sakaki ba.
Bige zaninta tai tabarta awajan adurkushe,kanzo ta hango wanda Megadi yake shanyawa,kudaje sun gama binsa harya fara bushewa,da rarrafe ta isa gaban kanzon,zaman dirshan tai agabansa,leda ta hango da rarrafe taje ta dakko ta,gaba daya mikewa ta gagareta,zubawa tai aledar bakin panpo ta nufa tarawa tai ta wanke shi tas, hannunta har rawa yake ta fara diba tana dannawa abikin ta,tanaci tana Kuka saidata cinye tas tasha ruwa.
Wata nutsuwa ce ta fara saukar mata,Allah sarki jin cikinta ya dauka saita mike taci gaba da aikin ta,saidatakai magariba tana wannan aikin,tana gamawa tabawa fulawa ruwa,atakai cedai hada salloli tayi tundaga La'asar har isha'i,cikin bakin ciki take sallar hawaye bebar zuba akan face dinta ba,tunda take bata taba hada sallah biyu ba, balle uku sai yau,jitai gaba daya ta tsani ahalinta,tatsane su dan basiyi mata rana ba.Fatan ta Allah ya kawo mata dauki,Allah ya bimata hakkin ta,bata da karfin da zata iya kwatar kanta daga gare su,kukan taci gaba dayi har bacci ya dauke ta.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrates
By Kulsoom Ismail Idris
Episode 7_8
Ke!! kina ina! taji muryar Anty zee tana kwalla mata kira cikin dan baccin daya fara daukar ta,cikin sauri ta futo dukawa tai gani Anty,a wulakance ta kalleta wani dan yafifin abinci ta dangware mata,wanda 'ya'yanta sukaci suka ragene suka gama jagwalgwalawa,saiki dauka kar kije kina yawo dani bana baki Abinci,dauka tayi tana kokarin mikewa, fusgota tai tadawo dabar ba karamin zafin faduwar taiba,kimma isa na taimake ki,na baki Abinci haka kawai saiki mike babu nagodi bare Nagode.
Kama kunnanta tayi ta murde,kara ta saka,jin tana barazanar tsige mata kunne,da sauri Ameer ya rike Anty Zee,dan Allah kicikata,wai meyasa Mama yanzu kika daina santa,kin manta abaya intazo bakya dukanta,bakya sata aiki,komai take so kinayi mata,meyasa kika tsaneta yanzu,yana zubar da hawaye yake tambayar mamar tasa,to kanin ubanta,akanta kazauna kana zubar da hawaye,uwarka nai mata ko intai laifi bazan hukuntata ba,ko bakaga tarbiyya nake bata ba,so kake ta lalace,ta sangarce ace laifinane.
Kallonta yake yana kasa yadda da maganganunta,sam be gamsu da bayanin taba,duk da karancin shekarun sa,ai yasan mugunta,ko zalinci,wannan ba daidai bane Mama,mu meyasa bakya yimana abunda kike mata,ita ma badan iyayanta sun mutu ba na tabbatar bazasiyi mata haka ba, malamin mu na islamiyya yana gaya mana,duk wanda ya zalinci maraya makomarsa wutar jahannama.
Tsawa Anty zee ta daka masa, Innalillahi yanzu ni Ameer akan wannan me kama da mujiyar kake cewa wuta zan tafi,saboda ta lashema kurwa,metake baka da har kafi kaunarta akai na,na tabbatar da Ameera ce ko Najwa bazasu fadan haka ba,amma kai dayake ba hankaline da kaiba kake jawomun bala'i akan wannan,maka mata duka tayi daga zuwanki har kinsa dana ya fara kalubalantata,kinfini awajansa kenan,shiru Ansariyya tai tana share hawayan idanun ta.
Ameera ce tataso daga Home work din da takeyi,nima Mama ina bayan Yayah Ameer ina son Anty Ansariyya kidaina dukanta,muna santa Mama,bakin cikine ya hana Mama magana kamar ta hadasu su Ukun tai musu dukan kawo wuka,au kema bin bayan Ameer din zakiyi,daga kai tayi alamar eh,gyada kai kawai Mama keyi kamar kadan garuwa,wani kallo takewa Ansariyya wanda ta kasa tantance na menene,ita fa aduniya bata so danta ya rabu da kowa,ko uban su bata cika so taga suna shige masa ba,tafi so komai ita ce agaba.
Mikewa tai tabar wajan kamar zata tashi sama,dawo da kallon su sukai kan Ansariyya,Ameer ne ya matso gabanta,hannunta ya rike yana murmushi,kiyi hakuri Anty riyyah indai Mama tai abinci zan dinga satowa ina kawo miki, murmushi ta saki tana shafa kansa, àah Ameer ba kyau sata,kuma karka sake cewa Mama bata sona,tana sona yanzu ma laifi nai mata shiyasa takemun fada,laifin me kikai mata riyya, àah sirri ne kai kuma kayi kankanta da jinsa,abunda nake so kudage da karatu kunji.
Gyada kai sukai suna murmushi dukan su,Ameera ce ta kalleta Anty riyyah amma malamin mu ya gaya mana bakyau zalinci,ita kuma Mama bakya laifi take dukan ki,ki koma gidan ku wajan Ummenki naga ita bata dukanki,hawayan idanun ta tashere,ai basanan Ameera sun tafi sun barni da yanzu ina gidammu nima,kiyi hakuri Anty riyyah zasu dawo innai Sallah zanta Addu'ar Ummi da Abbanki su dawo suzo su tafi dake,kinga babu wanda zai sake dukanki, murmushi riyyah ta saki,kumatun Ameera taja to nagode Ameera.
Abincin da aka sammata shita dauka ta wuce dakinta,binta da kallo sukai,sosai Ameer yakejin zafin maman sa,ya tabbatar muguwace ita,tunda take dukan riyyah dinsu, Home work din ma kasa karasawa sukai gaba daya jikin su yayi sanyi,dakin su suka wuce,kowa yahau gadon sa ya kwanta.
Washe gari bata manta kashedin Mama ba,karfe 6 ta futo daga daki,dakin su Ameer ta wuce,suna kwance suna bacci da alama ko tashi basiyi ba,bubbuga kafar Ameer tai,dan bude idanu yayi ganin riyyah yasashi tashi,ku tashi Ameer zaku makara,hannun sa ta ruko muje naima wanka,sakkowa yayi yabita abaya,tas ta gama yimasa wanka,Ameera tazo tashi dakyar tatashi saboda nauyin baccin da take dashi,wanka tai mata ita ma, cikin sauri ta shirya su.
School bag dinsu ta goya musu,ta saka musu 🧦 da shoe dinsu,hannayan su ta ruko suka dawo parlo suka zauna,basi zaman 5mnt ba hakimar ta futo,taci wanka ta baza uban turare indai wajan kwalliya ne gwana ce,kallon su take daya bayan daya,ganin babu wata makusa a shirin datai musu yasa bata tanka ba,ina kwana Anty kamar bata jita ba haka ta basar,ana gaidake Mama Ameer ya furta yana kallon mamar tasa,to bazan amsa ba,ko dole ne sena amsa uban iyayi,da feleke,kaga Ameer ka kiyayan wllh bani da kyau,karka yadda kashigo komata,zan rufe idanuna naima tsinannan bugu,wanda sai kaji ajikin ka.
Shiru yayi tare da sunkuyar da kansa, dining ta nufa,ganin sa wayam yasa ta tuna tafa ta kori masu girka mata,tsaki taja tana shafa goshin ta,kallon riyyah tai da kanta ke sun kuye,zaman me kike wai ko aikin wani dan iska zai miki,kalli parlon nan babu abunda kika dauke,ba mopping haka uwar take ta koya miki,Girgiza kai tayi alamar àah,tabe baki tai koda yake dama ba'a sababa,tsintacce Allah na tuba wayasan rayuwar sa ta baya,duk yadda riyyah taso rike hawayan ta kasawa tai.
Au kuka kike,kaji annamimiyar Yarinya,dukanki nayi da zaki kama yimin kuka,ko salon ayi baki agidannan ace zaluntar ki nake,ko ki share hawayan ki ki tashi ki fara aikin daya wajaba akanki,ko jikinki yayi tsami sai kiyi medalilin,da sauri ta mike, tsintsiya ta dauka,dakin su Ameera ta fara sharowa tai mopping,sannan ta wuce dakin Mama ya hadu matuka, parlon ta dawo zuwa sannan harta dafa musu tea da indomie sunci sun tafi,ita kuwa ko oho babu abunda aka rage mata,sai wani bakin tea akasan cup,gakamma abude yake yayi sanyi karara.
Bakaramar wahala tasha ba kan tagama aikin parlon,sai haki take ga yunwa,ga jikinta be saba da wahala ba,kofar parlon Mama ta tsugunna,nagama Mama,saidata mula dan kanta,kije ga tea dinki can,to Angode ta furta kamar mabaraciya,kan dining din taje,anan taga tea din hardasu Abin bread aciki,haka tasha babu yadda zatai,babu inda yaje mata kamar ma bata shaba.
Harabar gidan ta fita,sharewa tai tas ta baiwa fulawa ruwa,tsugunnawa tai jin jikinta yana wani mahaukacin ciwo,rarrafawa tai ta jingina da bango tana maida numfashi,Lumshe idanun ta tayi tana tunanin iyayan ta,ababan so da kaunarta,kariyarta,garkuwarta,ta tabbata yanzu bata da wani bango da zata jingina,bata da wani gata,bata da wanda zata nuna tace me kaunarta ne,sai Ameer da Ameera tasan tabbas suna kaunar ta,sai Mama Saudat da 'yayan ta,daga su batasan sai wanene yayi saura amasoyan ta ba.
Yauwa Audu dama kiranka nai zan sallame ka,zan canza sabon megadi,Allah ya sada mu da Alkhairi,shiru yayi yana auna maganganun ta, Hajiya ko nayi wani laifine,a kaskance take kallon sa,kamar taga wani kashi no bakaimin komai ba,karshan zaman kane yazo agidannan,na samu sabon get man,wanda kyauta babu ko sisi zai gudanar da aikin sa,ai kaga kudi ya huta ajuyashi ayi wani Amfanin dashi,zuge jarakta tayi ta dauko 20k ga kudin aikin ka,karba yayi jikin sa asanyaye.
Ficewa yayi tinani kala kala akansa,hangota da yayi a rakube yasashi nufar inda take, Ansariyya me kikeyi anan,bude idanun ta tai wadanda suka rine da wahala da kukan datasha,bakomai baba hutawa nakeyi,cike da tausayawa yake kallon ta,kudin hannun sa ya bude,3k ya zara ya bata gashi ki boye kin kinji yunwa kidinga siyan ko biskit ne kina ci,kallonsa take da Mamaki a fuskarta,dama dan uwanka yana iya gudunka bare yayi maka rana,Girgiza kai tayi kabarshi baba,bata fuska yayi ni nabaki ai amma ki boye kinji.
Hannunta na rawa ta karba,godiya ta fara zabga masa,ba komai ai da nakowa ne,ni matsayin jikata na dauke ki,kici gaba da hakuri watarana sai labari,share hawayan ta take wasu na korar wasu,ni zan tafi Allah ya sake sada fuskokin mu da Alkhairi,saurin mikewa tai baba ina zakaje,zan tafi garimmu Hajiya ta sallameni kiyi hakuri da rayuwa,duk inda kika samu kanki kirike mutuncin ki kinji,gyadakai take tana Kuka,ji take kamar wani dan uwanta ne shidin,gatan ta zai tafi kenan ina zata sa kanta,tana ganin ya fita da kullin kayansa ta fashe da kuka.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 9_10
Sai data gama kukan ta share hawayan ta,da kyar ta mike ta shiga maine parlourn ba kowa sai karar AC,dakin ta wuce kan katifarta ta fada,wani irin bacci takeji ga azababbiyar yunwa kamar zata kasheta,tana kwanciya bacci yayi awon gaba da ita,Mama ce take kwala mata kira taji shiru afusace ta bankado dakin nata,iye lallai mecin arziki be Iya samun waje ba,bacci kan balastin koni matar Gidan ban kwanta nai bacci ba saike,aiko zakici Ubanki.
Parlo ta koma cable ta ciro ta kara dawowa dakin,saidata daddage iya karfinta ta tsula mata acinya,wata alkafura riyyah tayi cikin tsananin azaba,bata kyaleta ba ta bita da duka kamar ta samu jaka,shegiyar yarinya daga na rufa miki asiri,dakiyi yawo irin na uwarki na samu na baki wajan kwana shine abun ya zama iskanci,dan Allah Mama kiyi hakuri bazan kara ba,kima kara,ninasan mezan yi miki.
Tsayawa tai da dukanta sai haki take, riyyah Kuka take tana kallon jikinta yadda ya daddaye kamar wadda ta kone,da kika kwanta kina bacci wa kika barwa bakin get din,daga yau sai yau na haramta miki zama acikin daki,kamar yadda get man ke kare rayuwar sa awaje kema haka zaki kare taki,ke in baki wasa bama dakin sa zaki koma da kwana,tashi kifita karki kara fusatani nai miki dakan sakwara,da sauri ta mike jiri na dibarta ta fice daga parlon baki daya.
In da baba Audu ke zama akan benci nan ta zauna,kallon jikinta take ga azabar radadi daya zagaye dukkan jikin ta,a yanzu hawayanta sun gama kafewa,sai tafasa da zuciyar ta takeyi,anya bazata gudu ba,to ina zataje inta gudu,wata sani wajan wa zataje,shine tunanin daya cika zuciyar ta,hijab dinta tasa ta goge hawayan ta.
Bata jima da zama ba taji anfara danna hon alamun mota zata shigo,tashi tai da sauri danta bude get din,da kyar take turawa sai haki take tana nishi,yakai mintuna biyar tana kici kici da get din kafin ta bude gaba daya zufa ta gama wanke mata fuska,mamaki ne ya kashe habu driver,ganin macece kuma ta koma bude get,asanyaye ya shigo yayi parking,su Ameer ne suka futo suna kallon riyyah datai tsamo tsamo tana hada zufa,hannun ta take murzawa jin irin radadin da yake mata.
Komawa tai tana kokarin sake maida get din amma ta kasa,saboda yunwa da jirin dake dibarta,da sauri habu yazo ya tura mata get din al'ajabi ya cika masa zuciya,tabbas ya gane ta,ita ce wannan Yarinyar da mahaifinta ke zuwa da ita,kamar masu Gidan zasu goyata dan so,amma wai yau itace ta koma megadi,amma ALLAH wadaran wadannan dangi masu kafurar zuciya,da rashin tsoron Allah.
Nagode ta furta sanda tazo wucewa ta kusa da habu,kin kallon su Ameera tai bata bukatar ko wace tambaya daga gare su,zata amshi kaddarar ta da hannu bibbiyu,bata bukatar taimakon kowa,zata tsaya da kafafunta,tasa aranta bata da wasu DANGI,tanaji aranta bayan iyayanta babu kowa aduniyar ta,kamar yadda suka nuna basa kaunarta ita ma ta zare su daga ahalinta,da ace jinin su zai fita daga jikinta data raba kanta da duk wani abu daya dangana tasu.
Wani irin karfin Zuciya taji,bazata sake zubar da hawayan ta asabo dasu ba,zata mikawa Allah dukkan lamuranta,zata rayu aduk inda kaddara ta juya ta,goge gumin fuskarta tayi ta koma kan bencin ta zauna.
Da kallo suka bita gaba daya,Ameer zuciyar sa ta karaya na tsananin tausayin ta,inama ace ya girma daya dauke Anty riyyah ya gina mata gida sun koma tare,shima baya son maman sa tunda muguwa ce ita batason riyyah,ta tsaneta,hannun Ameera ya kamo suka wuce maine parlour,tunda suka shigo take sakar musu murmushi dayi musu oyoyo,amma babu wanda ya kalleta acikin su kowannen su rai bace suka wuceta.
Sototo tai da baki ganin lokaci daya 'yayan ta sun canza halayyar su,sun canza daga yadda suke nuna mata kauna,tatashi daga masoyiyar su ta zama abokiyar gabar su, hankalin tane ya tashi meyake shirin faruwa da ita,in bata manta ba tun ranar da riyyah ta sako kafafunta cikin Gidan yaranta suka sauya baki daya,tab aiko da sake dole ne ta dawo dasu kan hanya,harsu suka fita sanin abunda ya dace,dan sufa takeyin komai.
Ranar koda wasa bata dawo Gidan ba,tana bakin get tasa aranta wanann shine duniyar ta,awajan take sallah intaji antada sallah a masallatai,wajan karfe 4 su Ameer suka fito zasu tafi islamiyya,da murmushi a face dinsa ya matso inda take, murmushi tai masa ita ma,da sauri ya zuge jakarsa,abincin daya boyo kusan rabin bakar leda ya dora mata akan cinya,Ameer ruwa ta dakko daga tata jakar ta dora mata akan cinya,da sauri suka bar wajan gudun Mama ta leko ta samesu awajan.
Bin su tai da kallo cikin wata irin kaunar su,ta tabbatar sudin masu santa da kaunar tane,abincin daya dora mata akan cinya ta kalla,jikinta har rawa yake wajan budewa,shinkafa da taliya da miya,sai naman kaji fika fiki da cinya akai,hannu tasa ta fata dannawa abaki,saidata cinye tas ta kora da ruwa,wata irin nutsuwa ce tadinga saukar mata,tunda tazo gidan bata taba koshi ba saiyau,ledar data gamaci ta dauka,kofa ta bude ta wurgar,pampo ta wuce ta wanke hannunta,tanaiwa Allah godiya.
Sai kusan karfe 6 Mama taga dama tadan yafito mata Abinci ko dan yaye ba isarsa zaiba,karba tai ta ajiye har Lokacin a koshe take jinta,ranar sai kusan 12 ta baro bakin get,Abba Gali shine karshan shigowa,kodaya ganta abakin get babu abunda ya dameshi,yana daidaita parking ya kwashi ledojin daya zo dasu ya shige gida,binsa tai da kallo tana tunani daban daban a zuciyarta.
Sanda ta shiga babu kowa,sun gama ciye ciyen su sun wuce dakunan su,nata dakin ta wuce toilet ta wuce tai wanka,yan kayanta ta dakko ta canza,kwanciya tai bayan ta tofe jikinta da Addu'a, hankalin ta kwance take sharar baccin ta,dan tayi alkawarin cire ko wace irin damuwa daga ranta,zatai rayuwarta cikin farin ciki,bazata kashe kanta abanza ba,in ta mutu dama basu da asara,dadi ma zasuji sun rabu da wahala,in sha Allah kuwa ba zasu taba ganin mutuwarta ba,babban fatanta taci gaba da karatun ta.
Tana j's 2 Abbanta suka rasu,tasan ko akan kudi Abbah Gali da Abba Yahaya suke kwana bazasu taba maida ita makaranta ba,ko acikin gadonta tasan bata isa ba balle ace su fitar da nasu,to gadon natama yana ina,sun riga sunyi sama da fadi sun cinye,sàidai Allah ya bimata hakkin ta amma bazata taba yafe musu ba,sake saken da taitayi kenan har bacci ya dauke ta.
Taku ko yaushe....
Kulsoom Ismail Idris
.......✍️✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 11_12
Haka taci gaba da rayuwa kamar mara galihu,Anty Zee sam bata da tausayi,ba ragayya haka take azabtar da ita,ta kara ramewa sai idanu awaje,tayi baki zaka iya kirga kasusuwan dake jikin ta,ga aikin gida gana bakin get duk ita kadai,ko wata babbar macen bazata shanye abunda riyyah ta shanye ba,danma ahakan su Ameer na debo mata Abinci ba tare da sanin uwar ba.
Yau ma tana zaune akan bencinta data saba da zama akansa,batajin dadin zama a ko ina inba kansa ba,jin ana danna hon tai saurin mikewa zuge get din tai tana jiran ashigo,motoci biyu ne suka shigo masu kyau,maida kofar tai ta rufe ko kallon wadanda suka zo din bataiba,dan ba hurumin ta bane tayi iya aikin ta,tun da tashigo take kallon ta,idanun ta kamar zasu fado,tsoro da razani sune suka.cika kwanyar kanta da zuciyar ta.
Kallon ta kusa da ita tai,itama riyyah din take kallo,Mama wai dagaske idanuna gaske suke nunamin riyyah ce abakin get, riyyah ce ta zama haka, riyyah 'yar gata gaba da baya suka maidata haka,anya Mama su Abbah zasuga Annabi,marainiya ce fa,bata da kowa sai su,ita din suke wulakantawa,inama inada gida Mama,da ayau zan dauke riyyah bazasu sake ganin taba,saina ginata,saina daukaka darajarta,alokacin zata kalubalance su zata nunawa duniya suwa nene su.
Bazan taba la'akari harda Mahaifina ba,zan tsaya tsayin daka wajan kwato mata hakkinta,wace irin rayuwa ce Wannan,Fatima kenan itace me wannan sharhin 'ya ga Abba Yahaya,hade hannayanta tayi tana kallon Mama Saudat dan Allah Mama ki taimake ta,ki kaita dangin ki,na tabbatar zasu sota,zasu kaunace ta,zasu zama gatan ta,ayau naji na tsani Mahaifina,na tsani halayyar sa,damme zasuyi son zuciya,ita dinfa macece me rauni,mace abar atausaya mane ba abar awulakanta ba.
A sanyaye Mama Saudat ta futo daga motar,har kusa da riyyah ta tsaya amma batasan da tsayuwar taba,tunani ya aureta,yazama abincinta,yazama abin shanta,ko yaushe acikinsa take,dafa kafadarta Mama tai, firgigit ta dago idanun ta,sauke su tai akan Mama Saudat,matar nan data taba nuna tausayi agare ta,matar nan da bata banbantata da 'yayan cikin taba,har yanzu tana tuna karamcin ta,tana tuna jajircewarta,tasha fada da Mijinta duk akanta.
Murmushi ta sakarwa Mama,wadda take zubar da hawayan tausayin ta, Lallai tashigo dangin azzalumai,ta tabbatar da wani acikinsu zai sake mutuwa,haka zasu rufe idanun su,sukwashi ganima kamar yadda suka kwasa akan dukiyar Abban riyyah,me kikeyi anan riyyah?kaudakai Ansariyya tai,aiki nake Mama,nan shiyafi dacewa dani,kin manta niba kowa bace,bani da kowa Mama,kuma bani da komai,hakan ma cin arziki nake,kuma ngode da wannan karamcin da sukai agareni.
Kin manta sauran basimin haka ba,suka nunawa Duniya nidin ba kowa bace,suka nuna dama can ba kaunar mu suke ba, cali cali fa aka dingayi dani Mama,sai nan din na samu na fake,damme zanji haushi ko nadamu,koba komai sun bani wajan fakewa,da yanxu inabin bola Mama,na rokeki asabo dani karki rasa Auran ki,kin manta abun daya fada miki abaya,in kika sake yunkurin taimakona abakin Auranki,damme zanyi silar mutuwar Auran da tunkafin asan za'a haifeni aka gina shi.
Murmushi Mama Saudat ta saki, Ansariyya ina jinki kamar diyar dana haifa,ashirye nake na rasa igiyar Aurena wajan taimakon ki,me ake da zama da irin Abban ki,meyasa zakice naci gaba da zama akarkashin inuwarsa,kinaso yaci gaba da cidamu da haram,nidai Mama bana so kirasa Auranki akaina,bata kara magana ba tajuya cikin gidan suka shiga ita da Fatima.
Tana hakimce a parlo,taci kwalliya kamar me zuwa gasa,Anty Zee akalla zatai shekaru 38 matashiya ce meji da kanta,meji da ado da kwalisa,me takama da kanta,bakace sai dai shafe shafen datai yasa tai haske,atakaicema allura take zuwa aimata duk wata,kudade take kashewa jikinta ba kadan ba,ganin su Mama Saudat yasata sakin fuska,dan duk wanda zai bata anan tafi kauri.
Sannu da Zuwa Hajiya Sauda,da kyar Mama ta amsa da yawwa,wani kallo take watsawa Anty Zee daya fara kular da ita,maida kallon ta tayi kan Fatima wadda take mata kallan tsana karara,jitake kamar tatashi ta shaki wuyan Anty Zee kowa ma ya huta,ke wanann kallon da kuke keda uwarki na menene,Mama Saudat numfasawa tai,amma Zainab kin bani kunya wllh,kin nuna cewar bakisan ciwon dan wani ba,baki damu da dan wani ba inba naji ba,to tsaya na gaya miki wani abu,kaso naka duniya ta kishi,kaki naka duniya ta soshi,ina tabbatar miki saikinyi nadamar abunda kike aikatawa akan marainiya,wadda bata da kowa awannan duniyar,sai Allah dashi kadai ta dogara.
Dakata guntsugulu,harni zaki zaunar kinaiwa wa'azi,in baki sani ba bari na gaya miki,tunda na fara wayo aka sani a islamiyya nai sauka nai hadda,sittinne kyan kyan akaina,kinga kuwa in sànin Allah ne ai baki kaini ba,Mijinki ya kamata ki fara zaunarwa ki karantawa wannan zancan naki,shine dolenta,ni kuwa fa,babu Abunda muka hada,hakanan bazan ajiyeta ina ciyar da ita ba tare dana moreta ba,karyane wllh,ki dauke ta kikaita gidanki mana,zaki zauna kina asambulan hakora,kin wani tasani agaba yen yen yen sai zubu magana kike,kamar zabiya.
Fatima ce ta kalli Anty Zee ya kuma isheki karki sake ki zagi uwata,dan wllh yanzu zan tube mu daku ni da ke,nice dai dai dake ba uwata ba,shewa Anty Zee tasaka ahayyee nanaye,dama na kwana biyu ban wasa kashina ba,zamu iya bugawa aga wanda zai kwashe,kuma kutsashi kubar min gida,tunkan nasa ai waje daku,gidanki ko gidan riyyah,ina tabbatar miki akwai ranar da ko gidan leda bazaki samu arzikin zama acikin saba,duk abunda Mijinki ya kwasa sai yadawo dashi,matsiyaci futuk zasu koma dukkanin su.
Mama ce ta gwabewa Fati baki kul karna sake ji,iyayan kine karki sake jifansu da muguwar kalma,tashi mutafi,kallon Anty Zee tai ke kuma Allah ya shiryeki ya ganar dake hanya madaidaiciya,ke za'ai wa wannan Addu'ar Sauda,keda kanki yake bakar ledar,haka kawai kin dauki damuwa kin dora akan 'yar facala,nidai bazan taba canzawa ba,ina nan akan ra'ayina,indai ba barmin gidana taiba to bazaman lafiya,ita dataji sanyi da sassauci,inaga sai akabarinta.
Girgiza kai Mama Sauda tai taja hannun Fatima,dan taga Maman Ameer tai nisa batajin kira,tana inda suka barta,kanta asunkuye da alamar Kuka take,sun tayar mata da mikin daya dade a zuciyarta, riyyah Fatima ta dafa ta,dagowa tai da rinannun idanun ta,murmushin yake ta sakarwa Fatima, na'am Anty Faty,hannunta ta ruko taso mutafi gidammu,zare hannun ta tayi daga na Faty,a'ah Anty nan din shine daidai dani,kisa aranki baku hada komai dani ba,dan Allah kuyi rayuwarku nayi tawa, hade hannayanta tayi alamar roko.
Hannayanta Mama Sauda ta rike,amatsayina na uwa,wadda tasan ciwon 'ya'ya da zafin haihuwar su,tayaya zan barki acikin wannan kaskancin,ki biyoni na tabbatar Abbanki bazaiki karbarki ba, murmushi me ciwo Ansariyya ta saki,wane Abban nawa kike nufi Mama? ni Abbana ya dade da rasuwa,dama shikadai nake da,yanzu kuma yatafi ya barni,akaf duniya babu wanda zan nuna nace shine Abbana,babu Mama ta karasa cikin Kuka.
Idan har Mama kika matsa na biki,zan gudu daganan bazaku sake jina ba har abada,zanje nayi rayuwata nikadai,zan goge sunan ahalina,daga Abbana sai Ummina su kadaine bazan goge sunan su daga Zuciyata ba.Idanun ta Mama Sauda ta kalla tabbas dukkan abunda ta furta daga Zuciyarta yake futowa,ta hango kiyayyar danginta kwance a kwayar idanun ta,taya zata zama silar fadawarta duniya,hannun wa zataje,hannun wa zata fada,goge mata hawayanta tayi,shikenan riyyah na barki anan din,amma kimin alkawarin bazaki taba watsi da tarbiyyar da Ummin ki tai miki ba,dora hannun ta tayi akan na Mama nayi miki Mama,dan rungume ta Mama tai tanajin tsananin kaunar ta.
Tare da Faty suka tura get din har suka fita suna daga mata hannu,daga musu tai alamar bye,komawa tai ta zauna,zamanta ke dawuya ta hango Anty Zee afusace........
Duk group din da sukaga na dainai musu posting basa comment ne,na tace na tankade ina gaf da daina sa muku Littafin nan da alama be muku ba.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrates
By Kulsoom Ismail Idris
Page 13_14
Sai huci take kamar kububuwa,sai da cikin riyyah ya murda,hannunta ta kalla Wata shegiyar dorina ce,musamman dan ita aka siye ta,dan kafa da kafa Anty Zee ta nufi kasuwa sàida tasa aka shafe mata ita da manshanu,yadda zatafi shiga jikin ta,tana zuwa batai wata wata ba ta rufe ta da azababban duka kamar wadda tai kisan kai,tun tana Kuka tana bata hakuri har muryarta ta dashe,sàida tai mata jina jina kafin ta kyaleta.
Ke har kin isa akan ki azo har gida ana fadamin maganar banza,daga na taimakeki abu yana neman zama tsiya,zanga shegiyar matar data kara zuwa taimin magana akanki,ranar na lahira saiya fiki jin dadi,sama sama riyyah take jinta,jitake duniya tana juyawa da ita,idanun ta har rufewa suke,saboda tsananin masifar da take ciki,hancinta sai zubar da jini yake,tsaki taja ta halbeta da kafa ta tsallake ta,ni ko mutuwa kikai ma ina da asara,ni da zaki mutuma dana huta wllh.
Tayi kusan awa daya akwance gaba daya batasan inda kanta yake ba,hadari ne agarin gari yayi bakikkirin,suk wani me gata yana zaune agida,sakaye acikin daki,amma ita gata awaje,awajanma cikin mugun yanayi,yayyafi aka fara kafin ruwan ya tsuge da mugun karfi,bazata iya koda motsa ya tsunta ba,balle ta samarwa kanta mafaka,zubar ruwan ajikinta yana fama mata ciwukan da Antyn taji nata yanzu,zuciyarta ta bushe,bataji a yanzu akwai wata masifa da zata bata tsoro wadda ta zarta wadda take ciki ayanzu.
Batasan iya adadin lokutan data kwashe ba,ahankali tafarajin sanyi na kadata,motsa hannun ta tayi wanda takeji kamar ya karye,da jan jiki ta rarrafa ta leka parlon,babu kowa hakimar tana nade a bedroom dinta,haka ta lallaba ta shige dakin ta,kwana tai batai bacci ba,saboda Zazzabin daya rufe ta,ta matukar jigata,numfashin har sakewa yake.
Daya ke yau weekend babu wanda ya tashi da wuri,kusan karfe 10 Maman Ameer ta fito daga bedroom dinta,tundata fara sakkowa ta hango parlourn a hargitse,yadda suka barshi haka yake,rike baki tai lallaima wanann yarinyar ta samu waje,harni zakiyiwa gyaran Gida,taje ta samu waje ta kwanta,dakin riyyah ta wuce rai bace,tana kwance ta kudundune da zaninta,bata da arzikin da za'a bata bargo ta rufa.
Janyo zanin tayi,bude baki zatai ganin yadda take rawar sanyi yasata yin shiru daga kwandan masifar da tazo sauke mata,ke! ta dungure ta kafa,mene hakan zaki zo ki kwanta,kowa ya tashi ke isashshiya kina kwance lakadan,batama san tanayi ba,tsaki Maman Ameer taja tai waje,aikin banza yarinya sai kalatowa mutane aiki,yanzu da kika shargabe akwance wanene zai dauki nauyin yi miki magani.Abbah Gali ne ya fito da kayan shan iska ajikin sa,kallon Anty Zee yayi ke kuma mitar me kikeyi tundaga daki ina jiyo ki.
Tsaki ta karaja,dawa zakaji ina hayaniya inbanda waccan wahalar daka hadani da ita,nidai wllh Gali bakamin adalci ba,duk fadin Kaduna arasa wanda za'a kakabawa ita saini,ba dangin dangiro,wai akan Ansariyya kike magana,harara ta wurga masa da kanwa zanyi har zaka dinga tambayata akan wa nake,yanzu kuma metai miki,gatacan akwance dan Munafurci sai rawar sanyi take,kalli gida kaca kaca ba gyara,ni rashin lafiyarta be damanba ta aikina nakeyi.
Ameera ya kalla,jeki taso ta,mikewa tai tanajin badadi a zuciyarta, Anty riyyah tadan bubbuga kafarta,jin jikinta zafi rau kallontà Ameera tai cikin damuwa,baki da lafiya,kizo inji Abbah,tanajin maganar Ameera amma yadda jikinta ke matukar ciwo ya hanata motsawa,da kyar ta samu ta mike,tana hada hanya suka isa parlon,zama tai danjin yadda jiri ke barazanar kayar da ita,tundata fito yake hararar ta,wai yanzu nufinki baki da lafiya ni zan fitar da kudi nai miki magani.
Kanta daya ke Azabar sarawa ta sunkuyar,ko kaunar kallon fuskokin su batayi,dan ganin su take kamar bakin maciji,kai Ameer shiga daki ka dakko mata panadol ta kora,ahakama zataji sauki ina zaman zamana bazaki jawomun asara ba,rai nace Ameer ya tashi dakin Abbah yashiga ya dakko panadol din,kallon Abban yayi ai bataci Abinci ba Abba,harara suka wurga masa atare,waikai wannan yaron wane irin dane me shegen san iyawa,kafimu sanin daidai ne da zakace ai bataci Abinci ba,kai ci kai da kake zancan wata bata ciba.
Kumbura fuska Ameer yayi ai sai abari agama sannan sai tasha maganin,da kuwa Abba yayi masa,ungo naka nan ana magana kana magana,wai meyasa ka zama me gaddama yanzu,tambaya ma kake ga wadda ta koya masa nan, shegiyar yarinya tunda tazo ta baddalamun kan 'ya'ya basajin magana ta,tsawa ta dakawa Ameer bata tasha ko natashi naima shegen duka,in bataji sauki ba taya zata koma bakin aiki.
Assalamu Alaikum sukajiyo sallama daga bakin parlourn,amsawa sukai gaba dayan su,shigowa parlourn tai babbar macece me cike da kamala,sannu da zuwa Umma gaba daya suka hada baki sunai mata sannu da zuwan,da fara'a take amsawa,samun waje tayi ta zauna,har kasa Abba Gali ya duka yana gaida ita,inaga in uwarsa ce bazai mata wanann ladabin ba,amsawa tai kadaran kadaham,suna kama da Anty Zee da alama Mahaifiyar tace.
Sannu da zuwa Umma,fuska daure take amsawa Maman Ameer din,idanun tane ya fada kan riyyah da take rawar sanyi azaune,wata irin haijijiya take ji kamar zata fadi daga zaunen,maida kallon ta tayi kan su gaba daya,dama danku nazo gidannan a wannan Lokacin, kallon ta sukai da alamun tambaya a fuskokin su,kwarai ta gyada kai,ina zaune agida na samu mummunan labarin kun maida marainiya me gadi,bari na fara ta kanka Gali,kai yanzu yarinyar da dan uwanka ya rasu ya bari shine kabarta sasakai kowace shara ake juyewa a kanta.
Abunda nake so na fadama kaji tsoron Allah,kasani zaku tsaya kai da ita agaban ubangiji ranar gobe kiyama,sai Allah ya fitar mata da hakkinta,ke kuma na dawo kanki mutuniyar banza,yanzu Zainab da hankalin ki da ilimin ki,zakiyi wanann aikin jahilcin,to kowadda bata zauna ko saudaya a aji ba bazatai wanann abunda kika aikata ba,inamai tabbatar miki matukar baki gyara ba wllh zamu raba hanya dake,idan 'yayan kine zaki musu haka,sanda Ubanta yake da rai ji nake nan nan kike da ita,ashe duk na Munafurci ne.
To mahaifinki yaban sako matukar bega canji ba yace na tabbatar miki bake bashi,duk ranar daya sake yaganki agidan sa,saiya rugurguza miki kafa,bacin rai ya hana Mama magana sai huci take,akan riyyah Ummanta zata sata agaba kamar wata yarinya tanai mata fada,haka Abba rai bace yake hararar riyyah a kaikaice batama san suna yiba,kanta na cikin cinyo yinta.
Su Ameer kuwa dadi kamar ya kashe su dama Ameer ne yaje ya fado musu abinda Maman sa keyi azo ai mata fada,ke Ansariyya zo nan,Umma ta kirata,da kyar ta mike harta iso gaban Umman,jikinta ta taba taji zafi zau kamar wuta, jijjiga kai tayi kun kyauta,kama hannun riyyah tai suka fice daga parlourn gaba daya,bin su da kallo sukai da tunanin ina Umma zatakai riyyah din.
Kai tsaye Umma hospital ta kaita,abubuwan da aka lissafo akanta sàida suka sa Umma zubar da hawaye, lallai ta tabbatar diyarta da mijin ta basu da imani,siyayya taiwa riyyah datake binta da kallo,tun acan ta siyo mata tea me zafi tasha ta bata magunguna,dan danan saiga gumi ya fara sakko mata, murmushi Umma ta sakar mata Allah yayi miki Albarka,hawaye ne ya cika idanun riyyah zata iya kirga iya a dadin bakunan da sukai mata wannan fatan.
Nagode Umma,girgiza kai Umma tai kull karki sake godemin iyayanki dun can canci ai miki komai saboda su,sudin mutanan kirki ne,har suka dawo gida tana rarrashin ta,da kwantar mata da hankali,da nuna mata muhimmancin hakuri,saitaji Ahankali bacin ranta yana zagwanyewa,zata kara hakuri akan wanda take dashi,basa parlo sanda suka dawo,sai kamshin girki dake tashi a parlon,kwalawa Maman Ameer kira Umma tai,sai gata ta fito daga bedroom dinta,tana hada idanu da riyyah ta bata rai,tare da hararar ta.
Kin dawo Umma,mun dawo dai ko bakiga bani kadai bace,zubo mata Abinci ta kara ci ta kwanta ta huta,kamar Maman Ameer zata zabga ihu haka taji wani bacin rai na taso mata,fakewa tai ta juya kiching din,Abincin ta zubo mata cikin plate Albarkacin idanun Umma,tana kawowa tabar wajan dan batason ganin kayan takaici,duk da riyyah bata da lafiya haka ta zage taci Abincin,dan bata da tabbacin zata kara samun Abinci ayau din,saidata ji tana shirinyin amai tace da Umma ta koshi,kin tabbata,eh ta gyada mata kai.
To tashi kije dakinki ki kwanta,Allah ya kara sauki,Ameen ta amsa tana mikewa,wai wayan Umma take har tashige dakin ta.
Maman Ameer ce ta sake futowa,Umma bana kawo miki Abinci, àah nagode,ni da cin abincin gidan ku kadanne bazance har abada ba,ga wadda ta zama dole ba'a bata ba balle ni,mikewa tai kuma karnaji karna Gani,zan kara dawo naga irin abunda kike aikatawa,shiru Maman Ameer tai tana bin Umma da kallo,to wai wane munafukinne yaje ya fadawa umman tata abinda take aikatawa,kodai Mama Sauda ce kwafa tayi koma wanene zatasa kafar wando daya dashi,bata kawo aranta Ameer zai iya kai karar taba.
Dako saitayi masa duka na fitar hankali.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 15_16
Kwana biyu ta samu tadan sarara,ba akara tayar da maganar bakin get ba,har ankawo sabon get man,saidai ayyukan gida da take shansu ba laifi, "Alhmdlh jiki yayi mata sauki sosai"saidai karfin jiki da bata dashi"jitake kamar iska zata fadar da ita".
"Tana zaune a harabar gidan ta gama bawa fulawa ruwa taga an zuge get,mota daya ce ta shigo tasha wanki har wani daukar idanu take"Hajiya Baturiya ce ta fito tasha wani uban less,ta cokala dauri,Fuskar nan ta dauki mai,yadda kasan budurwa haka ta koma."Cimgom ne abakin ta,kas kas take taunar sa,tasha hills ko kunya bata ji"hand bag dinta ta rataya,tana kada mukullin motar dake hannun ta,"idanunta ne ya fada akan riyyah data zuba mata ido tana kallon ikon ALLAH.
Harara ta watsa mata,dena kallona yar banza me idanu kamar balo,sun kuyar da kanta tai tana wasa da hannun ta,biyoni,mikewa tai ta bita abaya,Mama tana zaune a parlo ita ma taci nata gayun,tana ganin Haj Baturiya ta fadada fara'ar ta,sannu da zuwa yauwa ta amsa itama da tata fara'ar,maida kallon ta tayi kan riyyah da take binta abaya Kamar jela,ke kuma da kike binta zugui zugui fa,àah kyaleta nice na kirata,shiru maman Ameer tai taso ta sauke mata kwandon masifa.
Zuwa nai dama na tafi da ita,ras gaban riyyah ya fadi zata sake komawa wata ukubar kenan,dan bata face Maman Ameer tai,dan sosai takejin dadin yadda riyyah ke mata aiki, amma gashi lokaci daya za'a ce anzo tafiya da ita,kikai shiru Zainab,wai dama da ambar min ita anan din kamar zaifi,tunda yace tun farko kune ku kaki kar barta shiyasa ya kawon ita,gashi na saba da zama da ita.
Wani kallon Baturiya ta watsa mata,ke dakata kilbabba har yaushe kike mata rokon mutunci balle ki saba da ita,sarai labarin abunda kike mata ya zagaye garinnan da kewayan sa,shine yanzu zaki cemin kin saba,nabi sabon da gudu ba riga,shiru Maman Ameer tai tasan wacece Baturiya duk bala'in ta tafita, riyyah ta kallah,ke kuma wuce ki hado kayanki sai wani rarraba idanu kike,asanyaye ta mike ta hado kayan nata.
Dama ba wasu kaya bane a yar leda ta zubo su,mikewa Baturiya tai,to zamu tafi sai gani na gaba, riyyah ko kallon inda Maman Ameer take batai ba dan Bazata taba mantawa da abunda tai mata ba,sai Allah ya saka mata irin zaluncin datai mata arayuwa,back sit ya bude ta shiga,get man ya wangale musu kofa,tafiya sukai me tsayi kafin taga Baturiya ta tsaya dai dai wani gida dan madaidai ci,harda me gadi,zuge musu get yayi suka shiga.
Sai data dai daita parking kafin ta bude ta fito, mukulli Baturiya tasa ta bude parlon wanda ya kawatu, Mamaki ya hana riyyah Magana,Lallai arziki yaci uban nada,yaushe Baturiya ta gina wannan Gidan harda kayan alatu aciki,zama tai aka carpet gudun magana,ajiye mayafi da key din hannun ta tayi,wani dan madaidai cin daki ta nuna mata kishiga nan,ki hura kafin anjima,gyada kai tayi ta mike da kayanta ta shige room din.
Dan madaidaicin daki ne bed da wardrobe acikin sa,sai toilet shima madai daici,zama tai tana karewa dakin kallo,Allah yasa dai Anty Baturiya bazatai mata mugunta ba, ALLAH yasa tausaynta yasa ta dakko ta,kwanciya tai a bed din,yaushe rabon data kwanta akan bed harta manta,sai data ci baccin ta ta koshi kafin tatashi,wanka ta sillo ta dauro Alwala,Sallah ta kabbara tana idarwa taji Baturiya na kwala mata kira,da sauri tatashi tana amsawa,parlon ta fita,ta tarar da ita da bakuwa,daganin ta kasan yar duniya ce,idanun ta sun riga sun gama budewa.
Tunda riyyah ta fito take binta da kallo kamar me son ta hango munin ta,gaishe su tayi suka amsa,nuna mata plate tai shake da Abinci harda nama akai dauki kije kici,da sauri ta dauka tai gaba.Amma dai Baturiya kin kusa ki cuci kanki wllh,yanzu kina da wannan yarinyar kika kusa yin wasa da damar ki,ni wllh har kin batamun rai,ni yanzu har Akwai wani da daza'a kawon nace wai bazan dauka ba,haukama akeyi.
Ai Hajiya Zulfa bazaki gane bane gaba daya lokacin kainane ya toshe,ashe ni haja aka kawon amma na kusan yiwa kaina asara,dariya suka sa tare da tafawa,yanzu wannan yarinyar shekarar ta nawa dan nazarin Baturiya tai zatai 14yers,yawwa tayi yadda ake bukata,amma Hajiya Zulfa wani hanzari ba gudu ba,Namiji fa ake nema ba mace ba ko kin manta,sake gyara dan kwalinta tai,ina sane kuma ba'a cikin maye nake ba.
Har nawa yarinyar take,kinganta fa kirji ashefe kamar allon sha,ai maida ita Namiji ba abun wahala bane,kai abunda kamar wuya fa Zulfa,ke kike ganin haka,in kuma so kike wannan arzikin ya wuceki to,naga sai dari dari kike da harkar nan kamar bata kwanta miki ba,haba harka ta kwanta min nidai burina naji dumus,kaji yar gari amma sai nuna miki hanya nake kina gocewa.
Aike yarinyar nan ta rabu da Gidan Dan Barno ai mun warke,ance babban dan sane baida cikakken hankali,duk wanda aka kawo dai yayi masa mugun mutuwa,ke har karya wasu yasha yi,shiyasa ake kawo masu kula dashi daban daban,duk wanda aka kawo guduwa yake karce,ga uwar sa da mugun hali bata yadda akawo mace ba sai Namiji,ke jin kishin dannan nata take kamar me,ke nifa nafara tunanin kodai ita take son ta Aure shi,dariya Baturiya ta saka,ke kin taba ganin inda uwa ta Auri danta,to bagashi ina gani ba Baturiya,na taba ganin wannan tashin hankali,kinki bari kowace mace ta rabi danki saike kadai.
To wannan ita ya shafa mudai amsar kudine namu,cewar Baturiya,wallahi fa,yanzu dai ta gama cin abincin zamu tafi wajan wata kawata indai wanann fannin ne ita tasan yadda zata shawo kan lamarin,ko dan banzan gashinne ma sai a aske in zai kawo mana matsala,ai bazata kai ga haka ba wane irin a aske mata gashi,ai ina samun abunda na samu agidan Dan Barno zan canza sana'a Nasan kan lokacin ta zama cikakkiyar budurwa,wata dariya suka sake saki ALLAH ya Kyauta.
Kaf maganar da suka tattauna akunnan riyyah,hawaye take kashirban jin yanzu kuma Namiji za'a maida ita,gadin mahaukaci zata tafi,ta mutu kota rayu basu da asara,abincin dabata karasa ciba kenan,dama kishi taji ta fito zata dauki ruwa,taji irin kulalliyar da suke mata,akwai Allah.
Tana gama ci suka sata agaba,tafiyar da sukai babu wani nisa,wata barkekiyar mata ce,tashi shirim akan sofa da murmushi ta tare su,kaga manyan hajiyoyi,wanda taurarin su ke haskawa,shewa sukai sa kafin su bata hannu suka tafa,kallon riyyah tai tare kuke da ita,gyada kai Baturiya tai tare muke,yar yayanace daya rasu,Allah sarki ashe ita ce,to Allah y jikansa Ameen suka amsa baki dayan su,koba komai riyyah taji dadi an yiwa iyayanta Addu'a.
Ko ita ce Yarinyar da za'a kai Gidan AA? Kwarai kuwa ita ce,dan jim matar tai anyi baza'ai kasada ba,nina dauka kauye kikaje kika mannawa iyayanta wani abu,amma wannan yarinyar kamar bazata cancanci asata a hadari ba,dan bata rai Baturiya tai kinga kefa matsalata dake kenan Zaituna,kamar ke kikafi kowa sanin Allah,ba zancan haka bane Baturiya gani nai amanarta aka barmiki,to in bata fita ta nemi kudi ba taya zanji dadin kula da ita,in zakiyi mata abunda ya dace kiyi,in kuma yine bazaki ba mu nemi wani,Cikin fushi Baturiya takai karshan zancan ta.
"Kefa matsalata dake saurin fushi"mene abun fusata acikin nan,ah to ai kece da abun haushi"za'ai harkar arziki kina neman yi mana baki tunkan ma afara"shikenan maida wukar ainaga daman ba wata budurwa bace bazata bada wahala ba wajan badda bami"haba ko kefa Zaituna yanzu naji magana,kuma jikina yayi kwari,yar dariya suka sa gaba dayan su, riyyah tana gefe tai tsuru tana jin yadda ake shawarar maida ita Namiji, alhalin tana mace,kai wannan wulakanci da tozarci da ake mata har ina.
Zonan Zaituna ta yafito ta,a sanyaye ta matsa inda suke,dafa kanta tayi kinajina ko,gyada kai kawai tai dan inta bude baki to Kuka zata fashe dashi,kinga mamanki Baturiya hanyar da zaki nemi arziki take san doraki,akwai wanda zakije jiyya,ba wani abu zaki masa ba kula dashi zaki nayi,amma ba'a bukatar mace a wannan aiki sai Namiji,shiyasa mukaga ya dace mukaiki tunda kece tamu ai da arziki agidan wasu gwara agidan ku,koba haka ba,hakane suka hada baki,cigaba da tsara riyyah tai duk tana jinsu badan ta yadda wai san cigabanta za'ai hakan ba.
Tadai jisu ne da tunanin Allah yasa can din tafi mata nan,tsaida magana akai nanda jibi za'ai mata dressed na yadda babu wanda zai gano macece ita,har suka baro Gidan Zaituna bata ce uffan ba, Baturiya ce keta janta da hira wai dan ta saki jikin ta,a kwana biyun nan taga gata wajan Baturiya farfesu ta dinga yi mata,ita ma batai gaddamar ciba,tasa aranta Allah ne ya kwato ya bata,sai tattalin ta take,sabulai masu kamshi dasu takeyin wanka,awannan lokacin aka dage da koya mata yadda zata dinga acting din maza.
Kayan Maza aka siyo dai dai nata,amma basu kamata ba sun mata yawa masu kyau da tsada haka aka aje boutique aka siyo mata,takalma tsala tsala na maza suma aka hado dashi,so ake taje a yadda baza'a raina ta ko aganta da kazanta ba,shiri sosai akai mata wata hula aka samu kalar fatar ta,bayan ammata kitso kanana ta yadda bazasu taba fitowa ba, kirjinta da sai lokacin ta fara kirgar dangi aka daure shi tamau yadda bazai kawo cikas ba.
Pad aka siya mata saboda tsaro,can kasan kayanta aka sata kafin a loda kayan sawarta aciki,Baturiya da kanta ta shirya ta tsaf,cikin wata t shirt da jeans masu kyau da tsari,cap aka dora mata aka daigata ta dawo Namiji sak,kallon kanta tai amadubi kalar fatarta saita dace da kalar kayan da akasa mata,dimpul dinta dake lobawa ya kara taimakawa wajan kyawun fuskarta.riyyah tana da kyau me sanyi da shiga zuciya, black beauty ce,ba baki canba amma batakai chocolate ba.
Tana da dara daran idanu,kwayar idanun ta brown ne,tana da eye lashes masu tsayi,tana da kirar jiki mekyau,tafi su Baturiya suka saka ganin yadda ta dawo sak wani dan matashin yaro za'a ce dan baza'a kirata da saurayi ba,ke danyi tafiya mugani,tafiyar ta farayi yes Haj Zulfa tai mata jinjina wannan yarinyar bazata bamu kunya ba.
Kinsan wane suna zaki koma amsawa a yanxu, girgiza kai tayi alamar a'ah,yawwa dama sunan ki riyyah ko,eh ta gyada kai to daga yanxu kin koma rayyan kinga ai ba'a wahalar da shari'a ba,jinjina baturiya taiwa Zaituna shiyasa nake sonki Aminiya kanki yana masifar ja,yanxu in muka nufi meduguri sainan da karfe nawa zamuje,kamata yayi abari gobe mufita da asussuba banason tafiyar dare gaskiya,cewar Baturiya da take kallon su hakan ma yayi,amma mutum dayane zai kaita bama dunguma ba kamar masu rakiyar amarya.
Sun dade suna kara tattaunawa na yadda za'a bullowa lamarin,washe gari asubar fari Baturiya ta sata agaba,tare da jakarta daya agoye daya ahannu,bafa kananan kudi Baturiya ta kashe mata ba,tasan zata samun minikin banin kin din su a Gidan Dan Barno.
Motar haya sukai hau bazata iya tuki ba daganan har maiduguri,basu sauka ba sai karfe daya na rana,yanayin motar da suka samu sam bata gudu yadda ya kamata,mashin ta tare musu ta fadamai sunan unguwar da zai kaisu New GRA ya nufa dasu,Unguwar masu hannu da shuni,get din wani katafaran gida anan ya tsaya suka sauka.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 17_18
Bin gidan riyyah take da kallo,ya Matukar kawatuwa,kwankwasa get din Baturiya tai,get man ya leko dan ganin wacece,wa kike nema ya tambaye ta,wajan haj Fannah nazo,jin cewa wajan hamshakiyar gidan tazo kuma ya kalle su bega alamar wahala ajikin su ba saiya bude Musu suka shiga,babban gidane na gaske, part part kusan 6 ne agidan ya kawatu matuka,amma gidan tsit da alama mamallaka gidan sun kule acikin part din su,saboda yanayin zafi da.ake zugawa,dama maiduguri badai zafi ba,rana kamar zata silalaka.
Waya ta ciro daga jakarta dan rasa wajan da zasu nufa,tana kokarin kira taga wata mata tafi to daga wani part,karasowa tai wajan su cikin mutuntawa suka gaisa,dama wajan Haj Fannah muka zo,ko kece wadda tace zaki kawo yaro gyada kai tayi da sauri eh nice gaba daya ta kosa tabar cikin wannan ranar me azabar zafi,Kubiyo ni,gaba tai suka bita abaya part na biyun karshe shita shiga dasu, Numfashi suka dinga saukewa jin sanyin AC ya bigi Fuskar su bayan sun shiga maine parlo.
Ku zauna,zama sukai akan wasu lintsima lintsiman kujeru,ash color da ratsin black ajiki sunyi kyau matuka sun kawata parlon,wani corridor sukaga tabi ko ina zataje oho,sunyi kusan zaman 15mnt ko kuda basuga yazo ya gifta ta kusa da suba,ran Baturiya ya fara baci da wanann wulakanci na Fannah sai kace wadda suka zo bara,tsaki take ja azuciyar ta,wani kamshi sukaji ya baibaye kofofin hancin su,tana tafe tana rausayawa tamkar daweesu.
Lallai wannan matar tanaji da gayu,abunda Baturiya ta ayyana kenan aranta,kokarin sauka riyyah take Baturiya ta maka mata harara,ganin tana neman bada su,yadda ta zauna ta kame haka suma suka kame,kare musu kallo tai,idanun ta ya sauka akan riyyah,hakanan taji gabanta ya fadi akallon farko dataiwa riyyah,kauda kanta tayi daga kallon kurillar datake mata,barka abunda tace da Baturiya kenan,cikin kwarewa da gogayya da kowane taku ka fuskanceta dashi tamaida mata amsa dai dai yadda ta furta mata,barka dai,tsut Baturiya taja bakinta ta tsuke,tayadda wannan matar yar rainin wayo ce.
Sai data sha kamshi ta fesar da Numfashi kafin ta kara kallon su,kece Zulfa ta turo,gyada kai Baturiya tai dan akule take da Fannah,ok fatan tai miki bayanin Aikin da nanema akawo yaro,eh taimun bayani gashinan na kawo shi,dan kallon riyyah ta dadayi,ya sunan ka,rayyan ta furta cikin muryar ta me sanyi,duk da ahakan wai ta gyara ta zama ta maza,sake kallonta Fannah tayi a kaikaice,rayyan tasake maimaitawa azuciyar ta,sunan santa kenan,basarwa tai.
Ya kwalo ta kwallawa wata kira,da sauri wanann matar datai musu rakiya ta futo,gani hajiya,a basu Abun motsa baki,daga haka ta mike ta komai inda ta fito,Allah kadiran ala manyasha'u Baturiya ta furta bayan ta bi bayanta da kallo,eh inda ranka kasha kallo kaji mata,aiko matar sarki sai haka,aikin banza ta kara jan tsaki,ya kwalo ce tai Murmushi itama mulikin Hajiya Fannah yana bata mamaki,mace sai san dagawa da nuna isa,kamar ita kadaice da mijin.
Cika gabansu tai da kayan ciye ciye da lashe lashe, Baturiya aje mayafinta tai agefe,waman taraka bati siddan wllh sainaci nayi kat bazanyi wahalar banza ba,zagewa tai saidata ci komai da yake wajan, riyyah kadan taci ya dauke hannun ta,wasu abubuwan ma ba cimar su bace bata taba ganin suba,sàida Baturiya taji cikin ta yana neman fashewa ta hakura,kwashe kayan ya kwalo tai ta mayar kicking,wani daki ta nuna musu suyi Sallah kafin Hajiya ta kara sakkowa.
Basi gaddama ba dama sun gaji,ga gajiyar mota,dakine shima tsararre me kyau, toilet riyyah ta wuce ta dauro Alwala, Baturiya kuwa ai bajewa tai akan bed tagaji sai cikinta ya sassauta tayi sallar,saidata sakata gudan kar wani ya shigo kafin ta dauki mayafin Baturiya ta nada,kabbara Sallah tai,tadade tana Addu'a kafin ta shafa,kan stoll din madubi ta zauna bayan ta bude dakin, Baturiya take kallo wadda ta bude baki tana bacci haikan aziman.
Ya Kwalo ce ta shigo,kuzo Hajiya ta sakko da to suka amsa,bata dauki kayan taba tafi tunanin nan ne dakin kwanan ta,ta canza sabuwar shiga ta kafa dauri,babbar macece meji da gayu meji da kanta, black beauty ce hutu ya ratsa fatarta,hannun ta Gold ne awarwaro da zobe,haka wuyanta wata dankareriyar sarka ce me matukar kyau da tsari.
Manna soket din su sukai akan kujera,munyi maganar Albashi da Zulfa dan haka baku da wata matsala,zaki barshi anan zai kula mun da mara lafiya,saboda banda time din zaman jinya nima abubuwa sun isheni,shiyasa na nema akawon yaro Namiji,banason kowace mace ta rabi dana,matukar ba nice na yadda da hakan ba,kallon juna sukai riyyah da Baturiya, Baturiya fadi take azuciyarta zakici kundugurun Ubanki,aikuwa ga mace nan saidai kiyi hakuri hajjaju.
Kai kuma rayyan duk abunda zai maka banda fushi,dan bashi da lafiya ne da Lafiyar sa kalau bazaiba hakane ba,gyada kai riyyah tai har fargabar haduwa take da wannan mahaukaci,to mahaukaci mana tunda ance har karya Jama'a yasha yi,cikinta har wani murdawa yake,akwai me zuwa yi masa wanka,aikinka shine bashi Abinci da lura da lukutan shan ganin sa,da tayashi wasa aduk sanda ya bukaci hakan.
Assalamu Alaikum wai ina jama'ar gidanne,wata tsohuwa ce me karadi ta shigo parlon,sai data wurwurga idanu sannan ta hango su,goran hannun ta takara bantara,tabbatacciya ashe kianan kina baza shegen hanci kamar gajeran wando,tunda ni ba Uwar ki bace dole ki kalleni ki watsar ai,Haj Fannah bata rai ta karayi ganin yadda Iyyani kesan zubar mata da kima,maida kallon ta tayi kan su Baturiya da suke kallon ta da tunanin wacece ita,au baki kikai ma kenan daga ina,wanda zai dinga kula da Babagana ne.
Ina wuni riyyah ta gaida Iyyani,nashiga Uku ni Fatsima yanzu ke Fannah bayan dibar Albarka har yan daudu kika koma dakkowa,nidai in kunne nane bejimin daidai ba kamar muryar mace nakeji, Baturiya kamar ta shaki wuyan Iyyani kai wanann tsohuwa da jarabar surutu take,kamar ta kone aka,sake karewa riyyah kallo tai,kai ya sunan ka,rayyan ta furta cikin tsoron sake magana,washe baki Iyyani tai ALLAH sarki kaji suna medadi,sunan mijina kenan kai sannu da zuwa,aikai bakon Alkhairi ne,duk wanda ya tabaka agidannan kazo ka sanar dani,gyada kai riyyah tai.
Bata kara cewa komai ba ta jiya,da harara Fannah ta bita, Iyyani tana shigarmata hanci da kudun dune tarasa meta tsare mata,dogon tsaki taja wanda yasa suka kalleta.Zuge jaka tai ta fiddo rafar kudi ta mikawa Baturiya,kyayi kudin mota,karba tai ta zira ajaka ko sisi nata baiwa riyyah ba,kai kuma gobe da safe zaka fara aikin ka,dakin da kuka fito yanzu anan zaka kwana,kafin gari ya waye,to ta amsa kamar zata fashe da kuka,mikewa Baturiya tai da dauki hand bag dinta,ni zan wuce Hajiya sai gani na gaba, gyada kai tayi batare da tace mata uffan ba.
Mikewa riyyah tai kamar tasa Kuka,duk da ba sabawa tai da Baturiya ba amma batason tatafi ta barta, hawayene ya fara sauka afuskarta,kallon ta Baturiya tai,haba ta rike au rayyan kukanme kuma kake kamar wanda bazaka sake ganina ba,kaza kashare hawayanka zan dinga kiran waya sai adinga hadani dakai muna magana kaji,gyada kai riyyah tai,yawwa ko kaifa share hawayan ka,goge fuskarta tai,tana ji tana gani Baturiya tatafi ta barta.
Dakin da aka sauke ta nan ta nufa Fannah ta bita da kallo,nazartar ta take anya wannan yaron zai iya aikin nan ki yadda yake tafiya kamar za'a busheshi ya fadi,dage kafada tai inma bazai iya ba shiyasa ni,ita dai tunda ta biya kudin aikin sa dole yayi mata aiki.
Key ta sawa kofar kafin ta kwance daurin da akaiwa kirjin ta,har yafarayi mata zafi,jin iska na shigarta ba karamun dadi taji ba,kwanciya tai tana tunanin rayuwarta,yadda take garawa da ita,kowane Lokaci sabuwar kaddara na kafada kafada da ita,tarasa wanann wace irin rayuwa take,inama tare da iyayanta ta mutu,da yanzu ta huta da wannan wahalar,saidatai Kuka me isarta kafin bacci ya dauke ta.
Kiran sallar magariba ne ya tashe ta, Alwala ta dauro,boyayyan hijab dinta ta zaro wanda ko su Baturiya basu san ta sako shiba,sawa tai ta kabbara Sallah,bata motsa daga wajan ba har akai sallar isha'i,tana idar da sallar tatashi ta gyara tamaida kayanta na maza,sanann ta bude kofar gudun kar wani yazo ya buga bata shirya ba.
Ko zaman mintuna biyar batai ba taji ana noking yes come in,tura dakin akai aka shiga,Ya Kwalo ce face dinta dauke da murmushi take kallon riyyah,itama murmushin tai mata,dan dukawa tai tana gaida ya Kwalo,amsa tai cikin dakin fuska hakanan taji yaron ya birgeta,gashi kyakykyawa,ya sunan ka ne,sunana Rayyan,rike haba tai kai kace sunan Uban masu Gida ne dakai,gaskiya zaka sha gata wajan Iyyani,saboda tana kaunar wanann sunan,duk wanda ya tabaka bazata yadda ba saita rama maka,dan murmushi ta saki,dimpul dinta suka koba,tsai Ya Kwalo tai da ranta,kai wannan da mace ne daya fi haka kyau,hakan take ayyanawa a zuciyarta.
Kazo za'ai Dinner kuma Iyyani tace nakira ka,kaima ka zama dan Gida,ni dama nai Mamaki danaji ta matsa sai na kiraka,muje ko,mikewa tai tabi bayan ya kwalo,fita sukai daga part din Fannah baki daya,ai kullum a part din Iyyani ake Dinner wanann dokarta ce,tafi so ta hada kan ahalin ta waje guda,ta lura Ya Kwalo tana da surutu.
Ganin takalma birjik saida kirjinta ya buga da mugun karfi,hadaddun shoe ne gasunan birjik na manya dana yara, Addu'a ta fara karantawa azuciyar ta,matukar ana kallon ta jitake kamar zata fadi,idanunta har sun fara cikowa da kwalla,da sallama suka shiga duk da tata za'a iya cewa a makoshi ta makale,kamar yadda ta zatane tana shiga kowa ya zubo mata idanu,jitai wata hajijaya na neman kayar da ita,sunkuyar da kanta tayi,tsayawa tai daga bakin kofar dan batasan inda zata nufa ba.
Tundaga sama har kasa suke kallon ta kamar sun samu TV,sun sami labarin zuwanta amma basu dauka zasu ga wannan figaggen matsayin me kula da Babban yaya ba,tab lallai wanann yaron yana da aiki,haka suke ayyanawa azukatan su.
Hmmm lallai Rayyan saika daura damara,danna lura wannna aikin ba karami bane.Na tausaya miki riyyah.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 19_20
Kara so mana,Iyyani ta furta fuskarta dauke da murmushi, ahankali ta fara takawa kusa da ita taga tana nuna mata,dukan su suna kasan carpet dining yayi musu kadan,daya bayan daya ta gaida su,akwai sa'annin ta,akwai wadanda suka haifeta,akwai iyaye aciki,wata Babbar mace data dago zataga tana kallon ta,sunkuyar dakai tayi tarasa wanann kallon na menene,karfa ta gano ainihin wacece ita, murmushi Matar ta saki hakanan taji tana kaunar yaron.
Ya sunan ka,dan dago idanun ta tayi wanann Matar ce,kan ta bata amsa Fannah tai caraf ta cafe,waike yagana menene hadinki dani,yaron nan dai nice na kawo shi,baki da hurumin da zaki tambayi sunan shi,babu abunda ya hadaku akarkashin ikona yake,tabe baki Yagana tai dan ke kika kawo shi sai kuma akace mu bazami Magana dashi ba,wai dan Allah Fannah meyasa bakyason azauna Lafiya.
Tsaki taja,aini tsakanina da kishiya babu zaman amana wllh,babu riwanki da harkata,Iyyani ce ta watsa mata harara,sannu Fannah tunda kece me zuciya akirjinki,ita ance miki bata kishinki,amma dayake Yagana yar arziki ce ta iya takunta,saike ballagaza da ba'a gasa miki baki ba,komai sai kinyi Magana akai,ki kiyayeni Fannah.kin girma bakisan kin girmaba,to bayan ma Iskanci kizo kisamu mace da mijinta,daga an auro ki kici arziki abun saiya koma Iskanci kuma.
Cikin sababi Iyyani taci gaba da magana kamar zata ari baki, Fannah fa iya kuluwa ta kulu,sai girgiza kafa take tana bankawa Yagana Harara,Wadda sam bata gabanta,batama san tanayi ba,cigabatai da cin Abincin ta cikin kwanciyar hankali,kiyi hakuri Iyyani abinci kike ci be kamata kidinga magana ba,wani dan matashin saurayi ne ya furta hakan,bazai wuce sa'an riyyah ba sai dai yafita tsayi da kadan,shikenan Asad tunda kayi magana banai shiru.
Gaba daya riyyah tana jinsu,dan zuwan datai ayau ta fuskanci Haj Fannah fitinanniyar mata ce wadda bata san zaman Lafiya,bataso hannunta ta fado ba wanann Matar ba mutunci zatai ba,saida aka kammala cin abinci aka zauna zaman hira, riyyah na gefe Asad da yake nazartar ta tsam ya taso daga wajan zaman sa yazo gaban riyyah,da murmushi afuskarsa ya mika mata hannu su gaisa,nan fa ake yinta saida cikin riyyah ya murda ganin namiji ya miko mata hannu wai su gaisa,babu yadda zatai hannu na rawa ta mika masa hannu suka gaisa.
Kallonta ya danyi,ya sunan ka, murmushin yake tai Rayyan,kai babban suna,sunan Babban Yayammu ne kuma kaga ai bazamu fada ba,yaken ta karayi yaja hannunta ya rike yaki saki,Iyyani ya kalla da take kallonsu tana murmushi,koba haka ba Iyyani ya kamata acanza masa suna yadda kowa zai dinga fada masa,tunda sunan Babban yayane dashi,ai wannan aikin nakane Asad daga yau ma na kulla abota kai dashi,washe hakora Asad yayi aiko naji dadi Iyyani nasa masa Bomboy kowa da haka zaina kiransa.
Dariya 'yan parlon suka saka banda Fannah da bakin cikin Duniya ya kare mata aka,ta tsani ta kawo abu taga wani ya rabe shi,tafi sukaji anyi wata matashiyar Budurwa ce,cikin dariya take fadin yes Asad wannan sunan ya dace dashi gashi kyakykyawa dama macene da kawata zaizama,dariya sukai,banda abinki Humaida ai yanzumma zaku dinga gaisawa,mikewa tai tana washe baki Allah Yaya Asad,hararar ta yayi kaji Munafurci yaushe rabon da kicemin Yayah sai yau.
Gaban riyyah ta tsugunna,hannu ta miko mata mugaisa abokina Bomboy, murmushi riyyah tai ta mika mata hannu,daga yau nima kawar kace kamar yadda Asad zai zama abokin ka,jinjina kai riyyah tai,tana mamakin saukin kansu,kyawawane sosai black beauty,suna da gashi baki sidik me santsi da laushi,yawancin su ba dan kwali akansu,sai mayafi medium da sukai rolling dashi,ta fuskanci suna ji da gayu ahalin gidan,duk wadda ka gifta kamshi ke tashi daga jikinta.
Mikewa Fannah tai saika tashi mu tafi ai,mikewa riyyah tai,Asad ne ya kalli Fannah Ayya Mami kibar manashi ya kwana a dakin mu,harara ta watsa mai,tunda danku na dakko shi mezai hana ban barmuku shiba,wuce mutafi kaikuma me shegen cusa kai, daga zuwanka har kasamu sake ka sarara,gaba riyyah tai ita bataga abun fada anan ba.
Da yake ta gane part din da sukai fito nan ta nufa, maine parlo nan ta shiga shiru babu kowa,dakin da aka sauketa nan ta wuce,tanajin sanda Haj Fannah ta shigo tare da hayaniyar wasu tana tunanin wagartace ta hado kan su,kwanciya tai bata da abunda zatai,sai data tabbatar babu motsin kowa tatashi ta murzawa dakin key,kwance abunda aka nannada mata tayi kafin tankwanta,tana sakin Numfashi jin iska na shigarta tako.ina.
Tayi baccin data dade batayi irin saba,dayake ta saba da tashin wuri akan kunnenn ta akai kiran sallar asuba,mikewa tai ta dauro alwala,kabbara sallah tai har gari ya fara haske tana zaune,wanka ta fada sosai ta wanke jikin ta fes,zuge zifdin jakarta tayi wasu riga da wando ta dakko masu kyau,sun mata das tsayawa tai tana kallon kanta a mirror,dan murmushi kawai ta saki kafin ta koma bakin bed ta zauna.
Dan kwankwasa mata kofa akai,shigo turo kofar Ya Kwalo tai,da ladabi riyyah ta duka tana gaida ita,amsawa take cikin yaba tarbiyyar da iyayansa suka bashi,kazo Haj na kiranka,to ya amsa,kataho da dukkan kayan ka zaka koma part din babban yayan su anan zaka dinga zama,gyada kai tayi ta dakko jakun kunan ta guda biyu,kirjinta sai bugawa yake na abunda zataje ta tarar acan.
Tana kishingide a kan sofa kamar wata sarauniya,kallon riyyah tai ganin yayi fes ba wata matsala,dan batason kazanta,bata son agogawa danta wani datti ko kadan,dukawa tai tagaida Fannah,tsabar takama da kyar take amsawa kamar an sata dole,Ya Kwalo ta kalla rakata,nasan yanzu lokacin baccin sane be tashi ba,ka zauna kusa dashi har saiya farka,to riyyah ta amsa.
Ya Kwalo ce agaba riyyah na bayanta,gaba daya fargaba ta cika Zuciyarta da ruhin ta,kofar parlon suka tura,wani sanyi ne ya bigi hancin su,saidai riyyah tadan lumshe idanun ta,ya matukar kawatuwa tunda tazo bataga part me kyansa da tsaruwar saba,kujerun parlon pink and white ne sun haska parlon matuka,ga tamfatsetsiyar plasma nan amanne kowa yake kallon da ita oho.
Taking steps Ya Kwalo ta fara data juyo taga riyyah bata binta,tsayawa tai taho mana rayyan,kwallar idanun ta ne suka tsiyayo gaba daya tsoro ya kamata,duk wannan makeken part din ace anan zata zauna tare da mahaukaci me duka,asanyaye take taking steps din jitake kamar kirjinta zai fado saboda razana,duk sanda ta tuno yasha karya maza balle ita datai badda kama tana mace ta zama namiji tasan duka daya zai mata saidai ta wayi gari akiyama.
Kayi hakuri rayyan inya saba dakai zakaji dadin zama dashi bashi da matsala,amma da farko zakasha wahala kaji,gyada kai tayi ba tare da tayi magana ba,wani daki ya kwalo ta tura kafin su shiga nan dinma pink color ne da alama mamallin part din yana masifar son color din,kallon riyyah tai anan zan tsaya rayyan amma kashiga daga ciki inya farka zaka mai brush kabashi break yanzu zan kawo,meyi masa wanka zai iso nanda ajima,babu abunda riyyah tace ya Kwalo tajuya ta fice daga part din.
Dakunan da tagani ajere sunkai hudu,na farkon ta tura dan neman Inda zata ajiye kayanta, bedroom ne me girma ya kawatu sosai,wasu fish ne acikin glass sai yawo suke",sai suka hadu suka bada wani color me kyau,sai makeken bed shima ya kawatu,sai wardrobe mirror cike yake da turarruka kamar dakin mace,ajiye kanta tayi kafin ta shiga Inda ya Kwalo ta nuna mata nanne dakin mara lafiyar.
Wani kamshine ya daki hancin ta,warware idanu tai tana hangen a ina zata ganshi,can tsakiyar gado ta hango wani ingarman Namiji,gashin kansa take hange yayi luf kuf baki sidik,ahankali take takawa cikin sanda dan gudun karya tashi,har gaban bed din ta tsaya,saida kirjinta ya buga tasbihi taiwa Ubangiji daya halicci wannan kyakykyawar halittar,fari ne tas kamar balarabe gashin girar sa ya kusa hadewa sa dan uwana sa,sajan fuskarsa ya matukar kawata face din sa,duk da bataga fuskar saba tagane yana da dara daran idanu.
Dagashi sai vest da boxer da alama wannan shine kayan baccin sa,takasa dauke kanta daga kansa,ya masifar tafiya da tunanin ta,bata taba zatan akwai masu kyau irin wanann ba,shi wannan duk yafi 'yan gidan kyau kamar shi yayi kansa,furucin ya subuce daga bakinta ba tare datasan ta furta hakan ba,dan toshe bakin ta tai tana kallon bayanta kartaje wani ya jita,ajiyar zuciya ta sauke ganin ita kadai ce adakin.
Adarare ta zauna agefen bed din dan jiran tashin sa,ta lula cikin duniyar tunani gaba daya hankalinta ba akansa yake ba, ahankali ya fara bude idanun sa yajima akwance kamar me hankali,sai daya jima kafin ya karkato da kansa inda riyyah take,turbune Fuska yayi da tunanin wane yazo ya hau masa abun kwanciyar sa,tashi yayi zaune sai daya dunkule hannun sa ya daddake ya saita bayan riyyah wani shegen dundu ya sakar mata,tsabar zafin da taji sai da tayi alkafura ta fado daga kan bed din,jitai kamar ya burma mata baya.
Afusace ya sakko ganin Fuskar dabe santa Agidan su ba,da rarrafe riyyah ta fara ja da baya yadda kasan bijimin sa haka taga yayo kanta gadan gadan.
🙆🙆🙆🙆
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Isma'il Idris
Page 21_22
Hawaye tuni ya wanke mata face ganin yana tunkarota,wata damka ya kawo mata wadda tasata kwallah ihu,da kafa ya kawo mata duka,sàida kanta ya daki mirror,kukan wahala ta sake saki,shigowarsa kenan yaji kukan mutum asama,yasan halin Canal tsaf zai targada duk wanda yazo hannunsa,da gudu ya karaso dakin ,sarai yasan halinsa bayason yaga bakuwar fuska,ya daga kafarsa kenan zai talitse riyyah da gudun gaske yayi azamar janye ta daga saitin kafarsa,tyls ya daka sàida ya bada wata kara,fitsari ne ya kufcewa riyyah ganin mutuwa kiri kiri,ganin ta tsira da gudu ta fita daga bedroom din,gaba daya sauka tai daga sama, maine parlour ta koma tazauna,jikinta har lokacin rawa yake.
Tatsinewa Baturiya ba adadi,ta tabbatar ko ita bazata iya kula da wannan gan samemen katon ba balle ita,ta tabbata bata da gata bata da galihu,hawaye tana goge wani wani na zubowa,takai kusan 40mnt sai lokacin ta lura da breakfast din da aka jera akan dining,ta gumi ta zabga,inama tana da iko da ayau zatabar gidan nan tun kafin ya halaka ta a banza.
Jin karar tafita ya sata daga kanta sama,baki sake take kallon yadda yayi masifar kyau,kamar me hankali,yasha wanka, Three quatar ne ajikin sa,sai t shirt da ya saka masa fara tas,kansa yasha gyara,yana rike da hannun sa,matashin saurayi ne shima,kusan kansu daya da Babban yaya,sàidai babban yaya ya nuna masa kyau da aji, Murmushi ya sakar mata na karfafa mata guiwa,ganin yadda yaron duk ya firgice abun dariya.
Zaunar dashi yayi akan dining kafin shima ya zauna,zo mana,mikewa tai kamar ta fashe da kuka gaba daya bata kaunar abunda zai kara hadata da Babban yayan nasu,tsayawa tai daga nesa tana muzurai,gani,dan murmushi ya saki,ya sunan ka,Rayyan ta bashi amsa,kai nice name,kace babban sunane dakai,sunan ku daya dakai da wannan ya nuna mata babban yaya dayake cin magani yana hararar ta.
Canal kaga wannan,kallon me maganar yayi sannan ya kalli riyyah,shine zai dinga kula dakai da baka abinci,bana son ka sake dukan sa kaga yaro ne karami,kawai kallon bakinsa yake batare daya fahimci me yake fada masa ba,ni sunana Sadik babban Aminin Canal fatan zaka tsaya ka kula da abokina yadda ya kamata,gyada kai ta sakeyi ta matsu ya sallame ta ta tafi.
Amma abun takaicin sai taji yace zo kai sarving dimmu tun yanzu zaka fara gabatar da aikin ka,babu yadda zatai haka ta matso gaban dining din,tea ta fara hada musu,kafin ta zuba musu wainar kawai da dankalin da suke ta tashin kamshi,barin wajan take kokarin yi ya dawo da ita,kaima ka zauna kayi break tare damu,babu yadda ta iya haka ta zauna tea kawai ta hada,da kyar take hadiyar sa,tsabar hararar da canal ke mata tana cinye musu abinci.
Tea din da Sadik ke bashi yake furzo dashi yana watso mata afuska,gogewa take batare da tace komai ba,bacin ransa be santaba kawaii tazo ta zauna kusa dashi.
Sadik dai sai kunshe Dariya yake zaiga yadda canal zaiyi da wannan yaron,tunda uwarsa bata yadda da kowa ba,kaf ahalin gidan takasa bari su kula dashi,saidai ita ta nemo da kanta,Yanzu wannan yaron ya zaiyi da canal,amma inya saba dashi ya tabbatar bazai dinga dukansa ba.
Tana gamawa ta mike kan sofa ta koma,gaba daya jinta take atakure bata taba zama da Namiji kamar haka ba,amma kalleta tsamo tsamo acikin maza,sanda ya gama bashi break din kan sofa suka koma suka zauna,tv ya kunna musu zaman kurame akai Canal yana kwance kamar me bacci.Karfe 9 wani dattijo me Matukar kamala da haiba ya shigo,yana kama da yaran gidan,da murmushi a face dinsa yayi sallama,cikin girmamawa suka amsa,kasa Sadik ya zamo yana gaida mutumin.
Ita ma saita sakko daga sofa tana gaidashi kamar yadda taga yayi,haka canal ya sakko ya duka kamar yadda sukai batare dayace komai ba,kansa dattijon ya shafa,idanunsa na kawo kwalla,ganin jajirtaccen dansa,me dakawa maza gumba afilin daga,amma ayau kalli yadda rayuwa ta juya dashi,ya koma tamkar karamin yaro Abunda yaga anyi shiyane kwaikwaya.
Allah ya baka lafiya Rayyan,Ameen Sadik ya amsa,kallon riyyah yayi ko kaine me sunana Canal da akace ankawo,tunjiya Iyyani take bani labrin ka,gyada kai tayi eh nine,dan murmusawa yayi to dan Allah ka kula dashi sosai kaji,da to ya amsa,dattijon ya dade tare dasu kafin ya mike yayi musu sallama,ficewa yayi daga part din suka bishi da kallo.
Hakimar kuwa ko takansa batabi ba ta shiga mota tai tafiyarta aiki,wainan da sunan sansa take shiyasa bataso kowa ya rabe shi.Daya bayan daya yaran gidan suka dinga shigowa suna dubashi Asad,Haj Yagana itama tashigo wadda suke kira da Umami kishiya ga Haj Fannah,tana matukar kaunar Canal ji take kamar itace ta haife shi,da mahaifiyar sa zata bata dama da babu Abunda zai hana bata kula dashi ba,amma saidai kash uwarsa bata yadda da kowa ba,abinda yaga dama shi takeyi.
Umami bakiga Bomboy ba, murmushi ta saki ta kalli riyyah data sunkuyar da kanta kasa,Bomboy kunyar me kake jine kamar wata mace,dan dagowa tai ta kalli Umami ina kwana,lafiya lau Bomboy haka kawai Asad ya kakabama suna ga sunan ka medadi Rayyan,Dariya suka saka,wani saurayi dake gefe ya kalli Asad ai Umami kinsan Asad badai shishshigiba,kuma yasan Halin Mami na tabbatar taji haushin sunan daya radawa wanda ita ce take da ikon fadar yadda za'ai akan sa.
Kumbura fuska Asad yayi haba Yaya Kamal aikai da kaya duk mallakar wuyane,injiwa ya fada maka haka,caraf Humaida ta cafe hakane yaya aiba laifi dan munsa masa suna,daga kafadar sa yayi ku kukasani,Sadik ya sake mikawa hannu Allah ya bashi lpy ameen ya amsa kafin yayi waje.
Sun jima anan kafin daya bayan daya su tashi su fita,Umami mikewa tai bana wuce zan danyi aiki yau aikin night ne dane shiyasa ban fita ba,ok Umami na dauka yau kina off danaga baki fita ba, murmushi ta saki aah Sadik zanfita amma sai karfe 8pm ok Allah ya taimaka,Ameen ta amsa,kallon riyyah tai,Bomboy ka kulamun da yaro sosai,to ya amsa,fita tayi,shima Sadik mikewa yayi agogon hannunsa ya kalla,zan wuce Bomboy sai yamma zan sake lekowa,ka kula dashi karyayi banna.
Kamar ta rushe da Kuka dan takaici,ganin za'a barta daga ita sai shi, murmushi Sadik ya saki,meyasa kake da tsoro kamar ba jarumi ba,mace aka sani da tsoro amma kaga kai Namiji ne,kasani nan gaba har filin daga mudinga tafiya dakai,idan Canal yaji sauki sosai,yawu ta hadiye da kyar karfi da yaji,ta koma Namiji rayuwa kenan, murmushi ta kakalo ba tare da tace komai ba.
Canal ta kalla yadda taga sai zazzare idanu yake,da alama Akwai Abunda yake son yi,tsam taga ya mike,wani daki taga ya shiga,batasan me zaiyi acikiba,tana zaune taka ya bude kofar kayan wasa tagani ahannun sa,kamar wani yaro ya dinga jido kayan wasa,su tady, mota,jirgi,boll saidaya gama dibosu tas sannan ya zauna atsakiyar parlon,wasa ya fara haikan aziman kamar yadda yara keyi.
Boll ya dauka ya fara bugawa in ya buga boll din kamar tashin duniya sai riyyah ta razana,haka ya dinga maka mata boll din tana gudu yana binta,shi awajansa wasa yake,besan dun sanda ya dirka mata boll din azabar zafi takeji,har Kuka sai datai san takaici,karbar boll din tai aiko zakaji ajikinka kaima,yadda ya dinga binta yana buga mata boll din haka.itama ta dinga binsa tana ramawa,duk da ba iyawa tai ba,bayan kujera ya buya,abun ba karamin Dariya ya bata ba.
Saidata kwanta tai dariya iya san ranta, lekawa tai bayan kujerar hangoshi tai sai muzurai yake,dariya ta sake saki,hakanne yasashi daga kansa ya ganta ta leko tana tsokanarsa,bata fuska yayi yana hura hanci,zagayawa tai ta tsugunna,toya gaji kadauka kaikadai ka iya mugunta,kallonta kawai yake, hannun sa ta rike tana janyo shi amma ko motsi beba,fito kaci gaba da wasan ka,kasa jawo shi tai,sai ita datake wahalar da kanta.
Sakin sa tai tarike kugu,tana kallon yadda parlon ya hargitse,ya jika mata aiki,sunkuyawa tai ta tattare kayan wasan baki daya,room din dataga ya debosu nan ta maida su,ashe suna da yawa ba duka ya dakko ba,saidata gama maidasu gaba daya,sannan ta dawo ta gyara parlon,komai ya koma dai dai.
Kwanciya tai tana maida numfashi,haka.kawai takejin nishadi azuciyar ta,wannan wasan datai ya sata matukar farin ciki.
Mrs🌹Baba🌹Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 23_24
Sai da ya dade kafin ya fito dan kansa,gefe daya ya koma yai shiru kamar bashine ya gama guje guje ba,tsura masa idanu tai,tausayinsa taji ya dirga azuciyarta,to me ya zamar dashi haka,kodai aljanu sun shiga jikinsa yake abun yara,mikewa tai har gabansa ta tsugunna,kura mata idanu yayi yana kallon ta,face dinsa babu alamun fara'a,wannan ko sanda yake da lafiya dagani baya dariya,murguda masa baki tai ganin irin kallon da yake mata tamkar ya santa.
Kauda kansa yayi daga kanta cikin cinyoyin sa ya tura kansa,mikewa tai daga gabansa takoma ta zauna tana hangensa,duk wani motsi dayake akan idanun ta yake yinsa.Jitai jikinta duk badadi yana bukatar wanka,mikewa tai dakin data ajiye kayanta nan ta nufa dan tai wanka,tura kofar tai kafin ta mayar ta rufe ba tare datasa key ba, toilet din ta wuce hankali kwance ta cire kayanta tas,sànin babu wanda zai shigo nan din ko anzo part dinma tasan a parlo za'a zauna.
Shower ta kunna sanyin ruwan na ratsata,wankanta take cikin Nishadi,gaba daya bataji sanda aka shigo toilet dinba,kumfar data mulkawa idanun ta ta wanke,caraf idanunta ya fada kan Canal dayayi kuri yana kallon ta,ihu tasaka tare da durkushewa akasa,shikansa sàida ya razana da ihun data saki,kukan takaici ta fashe dashi naganinta da yayi ba kaya,tunowa da ai bashi da hankali taji zuciyarta tai sanyi,tana tsaugunnen ta janyo towel ta daura jikinta duk kumfa.
Harara ta zabga masa kamar ta kifamai mari,hannun sa ya daga yana kokarin cire rigarsa shima tai masa wankan,batasan sanda tai wata sufa ta kankame shiba hankalinta tashe,yanzu Inya cire kayansa ya zatai dashi,tsayawa yayi daga kokarin tube kayan da yakeyi yayi tsuru yana kallon ta,jin yadaina yunkurin cire kayan ta sake shi,ruko hannun sa tai ba musu ya but zugui zugui.
Kofa ta bude zoka fita,make kafadarsa yayi kamar wani baby,idanun ta tawaro tana kallon abunda yake, bubbuga kafa ya hauyi alamun bazai fita ba,kara bata rai tai,matsowa tai danta kamashi ta tura shi waje,matsawa ya dingayi shifa bazai fita ba,dariya abun yabata nema yake ya maida ita tababbiya kamar sa,zagaye dakin suka farayi tana son kamashi yana guduwa,gajiya tai ta kyaleshi,yana bata mata Lokaci,tana shiga ta murzawa kofar key tasan zai iya dawowa,aiko kamar tasani tana fire kofar yana karasowa bubbuga kofar yake alamar ta bude masa.
Tanajinsa tai masa bamza saurin karasa wankanta tai ta fito tsaf,dama kan tashiga ta dauki kayan da zata saka tsaf ta fito ashirye gudun kar wani yazo ya ganta,sanda ta fito baya dakin tabe baki tai gwarama daka fita.
Bangaran Canal tunda riyyah ta rungumeshi yakejin kamar wani abu na yimai yawo ajiki,haka kawai abunda ya gani akirjinta ya tsaya masa arai,har daga rigarsa yayi ko yana da irinsa amma sam bashi da irinsa,aiko ya samu abun wasa,dan shi atunanin sa wani kayan wasanne a jikin riyyah,🤣🤣🤣tab lallai akwai kura.
Parlo ya koma ya zauna ya nutsu yana kallon tv,tana fitowa ya mike yana kallonta,akan kirjinta ya sauke idanun sa amma abunda ya bashi mamaki bega wannan boll din daya gani dazu ba,ashafe wajan yake abunda ya harzukashi kenan damme zata boye masa kayan wasan sa,ganin kallon da yake mata sàida hanjin cikinta ya murda,dandanan taga idanunsa sunyi jajawur ran yammaza fa ya baci,jikinsa har karkarwa yake tsabar fusatar da yayi,makwat riyyah ta hadiyi yawu da kyar,babu abunda yafi razanata sai kallon dataga yanai mata,kamar na muguwa azzaluma irin ta cuceshin nan.
Gaba daya batasan ya karaso gabanta ba,saijin wani lafiyayyan mari tai a kuncinta,sàida ji da ganin ta ya dauke na wucin gadi,kanta farfado ya kara kai mata wani marin agigice tai baya santsi ya debeta tim tafadi akasa,kuka ta fashe dashi ganin yadda Canal yake huci kamar mayunwacin zaki,rarrafawa tai da.nufin fita daga parlon tsabar azaba ko ganin gabanta batayi,gaba daya Fuskarta ta haye idanun ta har yayi taruwar jini,kuka take kamar ranta zai fita.
Ragowar 🍞 din dazu ya dakko,damka daya yayiwa ledar ya yage ta,wani kato ya gutsuro ya damko riyyah ya cusa mata abaki ta karfin tsiya,ashe shima ya iya mugunta dan kartai kuka yayi mata wanann muguntar rankwashi ya sakar mata aka riyyah fa tana halin ha'ula'i,dafe kan tai babu bakin magana ya danna mata bread abaki sai ruwan hawaye dayake.tsiyaya kamar an bude pampo.
Iyyani ce ta fado parlon kamar an koro ta,dafe kirji tai hango irin muguntar da yakewa Bomboy,da dan gudunta tataho kai kaci ubanka sakar musu da kasheshi zakai,nashigesu da banzo ba saidai aga gawar wannan yaron, dunkule hannu tai ta narka masa abaya amma karshe itace ta bige dajin zafi,mikewa yayi afusace yayo kan Iyyani dam taji kirjinta ya buga,amma tsabar karfin hali tsayawa tai taga mezai mata, cable din jikin tv ya fusgo a miliyan Iyyani ta juya suka kasa tsere.
Innalillahi nashiga uku,ya salamullahi yau nayi gamo,dama soja duk inda yake ai saiya zalunceka tana gudun tana kumfar baki,ganin zata tsere masa yayi wani tsalle ya daddage ya tsula mata cable din abaya,wani ihu Iyyani ta saki,Allah ya bata sa'ar fita daga part din anan ta bar zanin ta daya subale batare data sani ba,daga ita sai sket dan kwalinta ma ya cire,hannun ta dafe abayanta ta karasa part dinta,gidan shiru kowa ya tafi harkar gabansa dakyar takai kanta daki,gani take kamar ya biyo bayan ta,key ta murza kafin ta zauna tana maida Numfashi.
Riyyah tana ganin yabi Iyyani ta mike da kyar ta fada daki,bayan ta murza key sai data sa sakata,zama tai abakin kofar da kyar ta fito da katon bread din daya danna mata abaki,rarrafawa tai ta karasa gaban mirror gaba daya Fuskarta ta haye tai suntum,fashewa tai da kukan bakin ciki haka kawai wani kato yazo yana laftar ta abanza,tabbas wataran zai iya murde mata wuya kuma ya kashe banza.
To in sauran sun gudu ai sunsan inda zasuje,ita yanzu inta gudu ina zataje bata da wani gata sai awajan Allah,ko giyar wake tasha bazata koma kd ba tabbas Baturiya sai ta kusa tsireta,dan danan Zazzabi ya rufeta me zafin gaske,anan kasan carpet ta kwanta Abun duniya ya hadu ya kacame mata,lallai ta yadda Canal rikakken mahaukaci ne,me tai masa daya kamata yayi mata wannan muguntar,baccin wahala ne ya kwasheta batasan yadda suka kwashe da Iyyani ba.
Sai la'asar ta farka,jikinta wani mugun ciwo yake mata,dakyar ta rarrafa tai Alwala,tana idar da sallah taji ana buga mata kofa,shiru tai kirjinta na bugawa tunanin ta Canal ne ya dawo, Bomboy ka bude mana,jin kamar muryar Namiji me hankali yasata mikewa, ahankali ta zare sakatar kafin ta murza key din ta bude,Sadik ne atsaye abakin kofar kallonta yake baki bude kamar wadda mota tabi takan fuskarta,dariya ke cinsa amma ya gimtse, Bomboy me yasameka haka,dama me neman Kuka ne aka jefeshi da kashin awaki.
Kuka ta fashe dashi me cinrai,abokinka yamin haka,idanu ya zaro tabbas yasan abunda yafi hakama yasha yiwa mutane,da kafarsu suka dinga guduwa,hannun Bomboy ya kamo fito muje tirjewa tai kar ya kaita wajan Canal,ba abinda zai maka babu yadda zatai haka ta biyo bayansa,amma zuciyar fal tsoro,yana kwance a kan sofa yana sharar bacci kamar bashi ya gama aika aika dazu ba,kaga bacci yake kuma.yana tashi ya manta abunda ya hadaku har yayi ma hakan,gyada kai riyyah tai badan ta yarda da maganar saba.
Ga lunch ankawo kaje kaci,banaci ta fada da kyar, àah ya za'ai ka zauna da yunwa kaje kaci sai kasha magani,batasan musu da babba shiyasa ta mike,farfesun kaji ne,sai frid rice sai tashin kamshi take,da flas din tea,tea din kawai tadan sha kamar wadda take shan magani,mikewa tai tabar dining din tana zama canal na farkawa,agigice riyyah tai bayan sofa ta buya,Abun ba karamar Dariya ya bawa Sadik ba, gaskiya Bomboy kana da matukar tsoro,haba jarumin maza cikin Dariya Sadik yake tsokanarta.
Kafito babu abunda zai maka, ahankali ta fito amma bata yarda tazo Inda suke ba,kura mata idanu Canal yayi sai kallon fuskarta yake da tunanin meye a fuskar ta, ahankali ya mike sam batasan yazo gabanta,hucin numfashinsa kawai taji a fuskarta,saurin matsawa baya tai ya sake biyota,hannu yakai zai taba fuskarta ta bige hannun,fuskarsa ta nuna rashin jin dadi akan abunda ya sameta,juyawa yayi yana kallon Sadik dan yabashi amsar da yake bukata,kaine kai masa wannan dukan kamar ka kama me Laifi.
Duk da begane meyake fada akan saba amma ya fahimci shine yayi laifi,maida kallon sa yayi kan riyyah datake watsa mai harara cikin tsabar jin haushin sa,kamar ta rufeshi da duka, sunkuyar da kansa yayi bayaso yaga ana hararar sa,tashi yayi jikinsa asan yaye ya koma.ya zauna,dan murmushi Sadik yayi lallai da alama Baomboy zai iya canza Canal tunda gashi harya san ayi fushi dashi aki yimai dariya.
Kayi hakuri Bomboy ka daina fushi dashi,a stage din da yake ba'a son ya dinga yawan tunani me zurfi akin zai kara dawowa baya,ana so adinga debe masa kewa ahankali abubuwan daya manta zasu dinga dawowa kwakwalwar sa,gyadakai riyyah tai tana san tambayar sa me yasame shi amma sai taga wannan din ba hurumin ta bane,shiyasa tai shiru da bakin ta.
Kama hannun sa Sadik yayi suka wuce dining,fir yaki karbar abincin,duk yadda Sadik yayi kin ci yayi,haka ya hakura ya kyaleshi, riyyah na kallon su duk abunda sukeyi,tausayinta sosai ya kara kamata kodai baida Lafiya ne,tundaga safiya zuwa yanzu bataga yayi dariya ko saudaya ba,anyama yana dariya kuwa?bata dame bata amsa.
Sai karfe 5pm Mami ta dawo daga banki anan take aiki,tana shiga maine parlour ta gan su a zazzaune,ga Iyyani datake sababi kamar bakinta zai tsinke,hango Mami ya sata kara fusata,tsaki Iyyani taja,amma kedai Fannah anyi shakatafin mace,ace aikinki yafi danki,kullum kina yawo ahanya da sunan aiki,ni banga tsiyar da kike tsinanawa ba.
Ahaka kike tafa jijiyar wuya ke kina son danki kar wanda ya rabe shi,yau nima sai daya tabbatar mun da rashin hankalinsa yakai Inda yakai,ya daddage ya tsula mun bulala kamar sa'ar Uwar sa,da niyyata akanki zan rama wllh,amma yarannan suka hadu sukaban hakuri,ko kala Mami bata ce mata ba,au ina magana zaki maidani 'yar iska,yanzu da uwar kice zaki mata haka,iya bacin rai Mami tayi shi,batason tai abunda zai tsinke igiyar Auran ta,amma da saita nunawa Iyyani tabbas ita din ba Uwar ta bace kamar yadda tasha fade.
Fita tai daga part din Iyyani gaba daya tana dana sanin shigowar ya.Haba Iyyani dan Allah kidinga sassautawa zuciyar ki,naga ba ita tasaka yayi miki hakanba,hasalima batasan anyi ba sai yanzu,kefa uwar miji ce dole ki koyi yadda zaki zauna da kowa Lafiya.Eh lallai Hafsa ni kike fadawa haka,ubanwa ke yahanaki zama anaki gidan Mijin,jinake koro ki akai,shine kike da bakin shigarwa wata,ala baki hakuri ni tunatarwa nai miki,bazan hakura ba nace bazan hakura,mikewa Hafsa tai ta barta awajan,tasan inta zauna wannan fadan bazai mutu ba.
Mrs 🌹 Baba 🌹 Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 25_26
Afusace ta karasa part dinta, Iyyani tana masifar bata mata rai,komai zatai bata iya ba,ta dinga kusheta kenan duk abunda zatai bata gani,bazata taba daina neman kudinta ba,ai ba debowa zatai ta dinga bata ba,amma kullum sai kwaroro to da take mata,wannan abu ya fara isarta wllh,naga ga kishiyar can na zuwa aiki,kodan ita ce zabinta yasa bata ganin fitar da take,har kwana take awajan aiki bata taba magana ba sai akanta, tsaki take ja ajejjere kamar tsaka,me zatai masa da zata dinga zama awajan sa kamar wani yaro goye.
Humaida ce ta shigo ganin yadda ran Mami ya baci yasata juyawa,zo nan,a sanyaye tajuyo,munafuka me kika boyoni zaki min,tunda kin sami wata uwar bayanni ai banga abunda zaisa ki biyo ni ba,kiyi hakuri Mami,yimin shiru dan Ubanki,daga wannan part din ki fada wancan ni gani asarrarriya me takashin haihuwa na haifawa duniya kuko,girgiza kai tai idanun ta na cikowa da kwallah,kika yadda hawayanki ya zubo sai kinga abunda zan miki.
Kuma na sami labarin kin dakko wata kawarki tazo duba yayanku,awane dalili? me muka hada da ita,da zaki jajjibota tazo dubiya,ko in bata zo ba zaiki warkewa ne, girgiza kai tayi kamar zata fashe da Kuka,wai meyasa Mami bata son ko wace mace ta rabi yayan su,Maganar Mami ce ta katse mata tunani,koda wasa kika kara dauko wata yar iska tazo dubamun dana,saina zaneki daga ke har wadda kika gayyato,nasha sanar daku banason naga kowace mace akusa dashi sai wadda na yadda da ingancin ta,na yadda da qualityn ta,na yadda daga wane gida tafito,na tace na tankade,na rairaye,ba kowa ce kara da kiyashi ce zata zauna tare da dana ba.
Jan kunnan Humaida tai saidata saki kara,da mugunta ta sake murde mata kunnan,gargadi na karshe zammiki karna sake ganin kin dakko kowace kucaka indai da sunan wajan Rayyan tazo kinjini,gyada kai take hawaye nabin idanunta,wani dundu Mami ta sake dirka mata,uwar shishshigi fitarmun apart karma na fito na ganki,ki koma wajan sabuwar uwar da kikai,dan Allah nono na da kisha tasa sirinji ta zikeshi ta dura miki nata,shine karshan so,dakinta tai da sauri Humaida ta fice tana zubda hawaye.
Part din Umami ta nufa,tana zaune da azkar a hannunta taga Humaida ta shigo tana kuka riris,ajiye azkar din hannun ta tai tana kallon Humaida,me ya faru kike wannan kukan Humaida,batace komaiba takwanta akan cinyarta,shafa kanta Umami taitayi harta samu sassauci azuciyarta,ajiyar Zuciya take saukewa,me akai miki,hawaye tashare kafinta kalli Umami,yanzu Umami mene laifina dan kawata tazo duba yayammu,shine Mami ta kamani take ta mun fada harda murdemin kunne.
Murmushi Umami ta saki,to shine abun kuka Humaida,kuyi mata biyayya,ku bita ayadda take so tunda batason ko wace mace ta rabi yayanku,kubarta kubita kan tsarinta, Mahaifiyar kuce ita ya zama dole kuyi mata biyayya,gyadakai Humaida tai amma badan taji Maganar Umami ba,ko gobe kawarta ta sake cewa zata zo duba yayansu saita rako ta,ai arzikine ma asan dakai,har ace za'a zo duba naka.
Bayan karfe 8 Umami ta shirya tsaf dan tafiya asibiti, part din Canal ta kara lekawa ta gano jikin nasa,tana shiga ta hangi Mami ta dora kafa daya kan daya,ga riyyah a gefe Canal yana kusa da ita,abinda ya batawa Mami rai kenan ganin yadda ya makale ajikin riyyah ko mitsawa yaki yi,wannan abu ya tsaye mata arai,harara nau'i nau'i take watsawa riyyah,wadda ta sunkuyar dakai tsabar yadda hararar me razanar da ita,kamar Umami ta juya saboda batason wata hayaniya amma saita karasa.
Sake tamke Fuska Mami tai,kai amma dai wllh kedai Yagana badai naci ba,ko tare mukai nakudar Rayyan sai haka,nace kifita a harkar dana kinki,sauran kin lashe musu kurwa suna hakura nabar miki,wannan din shima bazaki barmin ba, murmushi Umami ta saki da wuya kaga fushi akan fuskarta,kiyi hakuri Fannah ni akan Canal baki isa kisamin doka ba,saboda Mijina yake min komai,da kuma daukata da yayi amatsayin Mahaifiyar sa,bantaba banbantashi da sauran 'ya'yana ba,son da nake mai yanzarce wanda nakewa yayan dana haifa,wannan kuma hukuncin Allah ne bazan daina kulawa dashi ba kamar yadda kike bukata,kowa zai iya fita daga harkarsa amma bandani banda 'ya'yana kome zaki ina jiranki Fannah.
Iya kuluwa Mami ta kulu,sai yanzu na gane inda kikasa gaba Yagana,cikin danginki kike so ki lika masa ya aura,to kar nake kallon ki,dana ni zan zabo masa Matar Aure ba dangin yuyu yuyu zan kwaso masa ba,ran Umami ya soma baci da maganganun da Mami me mata,dan karamun murmushi ta saki,da ace ina da sha'awar hada zuri'a dake da nayi hakan kuma baki isa ki hana ba,amma ki sani ina neman tsari da duk Abunda zaisa jinina ya Auri danki,bazaki birgeni ba Fannah sai agobe muji sanarwar kin daura masa Aure,shine zan tabbatar da kedin kincika Mahaifiya me zartar da hukunci ba tare da uban daba.
Dama bata zauna ba ta kasa kai ta fice,tabar Mami da cizon yatsa,har ita kishiya zata zauna tana fada tana fada,ita fa arayuwarta ta tsani kishiya sai gashi mummunar kaddara tasa ta Auri me mata,ahakamma Mijin wata ba ita akazo aka samu ba,inta tuna wanann abu yana bata mata rai,kwafatai ta sake watsawa riyyah harara da ita da Canal din daya nuna be santa ba ya makale ajikin wannan figaggen Yaron. Hmmm Mami muje zuwa yarinya dai ba yaro ba.
Mikewa tai tabar part din baki daya.Kallon yadda ya wani mamike mata ajiki tai gaba daya ba'a hangota ya tashi ya matse ta ajikin sofa,motsawa tai ya kara matsawa kamar ta gaura masa mari,tarasa wane kalar Iskanci ne wanann zai dinga mamukarta,ko abincin dare ya hanata ci,dakyar ta samu ta mike zumbur ya mike shima gaba tai yabi bayan ta kamar yaron da yake bin uwarsa.
Dining ta jama sa kujera yana tsaye be zauna ba,saidata zauna shima ya zauna,tuwon shinkafa akai yaji naman rago da man shanu da yajin daddawa sai tashin kamshi yake, plate ta dakko ta zuba musu malmala daya,sai miyar kubewa datake tashin kamshi,kallon tuwon yake kamar be taba ganin saba,zakaci tatambayeshi,har Lokacin fuskarta bata sabeba,akwai kumburin marukan data sha ahannun sa.
Debo Abincin tai takai bakin ta,ganin yana kallon bakinta ta nuna masa plate din shima yaci,amma kin sa hannunsa yayi kamar me kyankyamin ya taba miyar,sake debowa tai da hannu ta nufi bakin sa ta zata nazai karba ba saitaga ya bude bakin ya amsa,haka ta dinga ci tana bashi saidata tabbatar ya koshi sannan ta kyale shi,mikewa tai tasan ko bata ce ya taso ba zai biyo ta,hakan kuwa akai binta yayi abaya, kicin ta shigo ta wanke hannun ta kafin ta kara fitowa.
Hannun sa ta rike gaba daya tagaji da wanann bibiyar tata da yake,so take ta warware daurin dataiwa kirjinta ko zatasha Iska amma sai binta yake kamar bindi,jan hannunsa tai suka haura sama,ta tabbatar shima ya fara jin bacci yadda taga yana lumshe manyan idanun sa,magungunan sa da Sadik ya nuna mata dazu suta babbala ta bashi kowanne aciki,saidaya dade azaune kafinta kaishi ya kwanta,amma fir yaki kwanciya ganin bata kwanta ba,yadda take atsaye yana tsaye yaki yadda ko zama yayi,kamar ta fashe da Kuka take kallon sa,wai me zammaka kuma ka kyaleni na huta haka,oho bema san tana yiba kallon bakinta kawai yake.
Zama tai ta dafe kanta,shima zaman yayi sun kusa awa zaune amma tsabar naci yaki kwanciya,idanunsa sun hadu Sunyi ja alamar be saba kaiwa wanann lokacin be kwanta ba,bata da zafin daya wuce ta kwanta muddin baso take su kwana azaune ba,tana kwanciya kuwa ya kwanta abayan ta,rufe danunta tayi kamar me bacci,saida aka shafe 30mnt tafarajin saukar numfashin sa,ajiyar Zuciya ta sauke a hankali tatashi,dan jim tayi kafin ta tattofa masa Addu'a taja masa blanket ta kashe masa kwai tai waje.
Inda taiwa kanta masauki nan ta shiga,wata ajiyar Zuciya ta sauke jin ta samu freedom babu me binta abaya,murzawa kofar key tai kafin ta fada toilet,wanka ta feso kafin ta fito daure da towel,kayan baccinta ta zura wata doguwar rigace wadda kowa zai iya sawa ko mace ko Namiji, Baturiya ce ta hado mata da ita saboda tsaro, Addu'a ta tattofawa jikinta kafin ta rage hasken dakin ta shige cikin blanket,lumshe gajiyayyun idanun ta tai, ahankali taunanin iyayan ta ya fara mamayar zuciyar ta.
Da ace tana tare da iyayanta da yanzu tana tsakiyar su akwance harsai tayi bacci suke daukarta sumaidata dakinta,dakinta babu abunda Abbanta be zuba mata najindadin rayuwa ba,rayuwarta take cikin farin ciki da nishadi da kaunar iyayanta,ko bata furta tana son abuba Abbanta baya bari saita furta da bakinta,iyaka soyayya da gata ta shasu,amma yau kalleta ta bige da gadin mara lafiya,wanda ako wane lokaci ciwon sa ya motsa zai iyayi mata illah,batasan hawaye ke gudu a face dinta ba saidata shafa fuskarta,hatta flow din data dora kanta ya fara jikewa.
Murmushi ta saki mematukar ciwo da sukar zuciyar ta,babban burinta arayuwa ta zama Doctor amma wannan birin mata ya ruguje rana daya ya rushe,bata da wanda zai tsaya mata,tasawa ranta bata da wani dan uwa aduniyar nan,haka tunannika suka dinga addabar Zuciyar ta,har gwanin iya sata yazo ya sace ta.
Washe gari tun asuba tatashi saboda tasaba da tashi dama,wanda in bata tashi bama bada baki ake tashin taba sai taji ajikinta,Anty Zee tasha kwara mata ruwan fridge me mugun sanyi wanda harsaita shide saboda sanyin daya ratsa kashinta,hakan yasa harta saba da tashi duk yadda Anty Zee ta kullo muguntarta sai dai tazo ta tarar tatashi,girgiza kai riyyah tai rayuwa kenan.
Tana idar da sallah taje tai wanka ta shirya tsaf,kayan data sassaka ta wanke acikin toilet din,akwai wajan shanya shiyasa bata wahalar da kanta ba ta shanya a toilet din tunda basu da yawa,dakin Canal ta nufa yana kwance yadda ta barshi jiya da alama ko kuyawa beba,fitowa tai ta dawo maine parlourn ta zauna,tashi tai ta fata sharar parlon tai mopping dinsa fes har daukar ido yake,ko ina sai data bi ta tsaftace shi kafin ta koma ta sake zama.
Karfe 7:30 Asad ya shigo goye da school bag dinsa, murmushi ya sakar mata kai Bomboy harka tashi,gyada kai tayi tana dan sakin murmushi abun yana taba zuciyarta,sai taji dama itace zata tafi school a halin yanzu,eh natashi Asad,hannu ya miko mata ta noke hannun itafa bata son hannun abun,kallonta yayi ya haka Bomboy ko bazaka gaisa dani ba, àah jiya na bige yanamin ciwo ne,ayyah Allah ya baka lafiya,idan Umami ta dawo anjima ka fada mata zata baka magani,to ya amsa ta matsu ya tafi bata son doguwar magana,kamar yasan meke zuciyarta ya mike bari na tafi Bomboy naga kamar bakason abota dani,saurin girgiza kai tayi meyasa kace haka Asad,naga nikadai nake neman ka kai baka taba zuwa nemana ba,ko haryaushe nazo gidan,ta ayyana azuciyarta,kuma ina macema zan wani tafi neman ka,amma azahiri saita saki fara'a kayi hakuri kaga ina tare da mara lafiya shiyasa,sakin fuska Asad yayi kuma hakane fa dakaimin bayani saina gane,amma ko Yaya Sadik ne yazo saika dinga fita muna buga boll zaka rage zaman kadaici,to zan dinga zuwa amma ban iya boll ba.
Rike haba Asad yayi kai amma Bomboy kana da son jiki,nifa naga saika dinga lankwasa jiki kamar mace,duk sanda suka ambaci tana kama da mata saitaji kirjinta ya buga karfa wataran su gano ita din macece,tasan daga ranar tata takare zasu tuhumeta akan meyasa ta canza kama ta shigo musu gida me zatace musu?.
Fans kubata amsar me zata ce musu?
Mrs 🌹Baba 🌹 Bello Abubakar.
........✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 27_28
Bubbuga kafadar ta yayi ganin kamar bata hayyacinta, Bomboy mekake tunani haka, murmushin yake tayi, a'ah bakomai,to shikenan saina dawo yau da yamma akwai wasa,kuma kaine gola abakin raga zan ajiyeka natabbatar bazasu samu damar ciba,makwat ta hadiye wani mugun yawu bata samu damar bashi amsa ba Asad ya juya ya fice daga part din,binsa tai da kallo hantar cikinta na kadawa jin yanason jajibo mata wata masifar tana zaman zaman ta.
Jikinta asanyaye tatashi jitake kafafunta sunyi mugun sanyi,sama ta haura direct sakin canal ta wuce,ta kintata daidai yana zaune yana zare ido,hararar sa tayi jishi wani kato amma baya sallah,tunda ta taho ya zuba mata idanu kamar yau ya taba ganin ta,tayadda da abunda Sadik ya fada mata,da yasaba da ita zai daina yimata mugunta,gashi yanzu ta tabbatar da maganar sa,mika masa hannu tai alamar ya taho,kamar mejin tsoron wani abu ya dora hannunsa akan nata,kansa take kokarin yi ya mike amma kamar gungume ko motsi beba.
Gajiya tai ta sakar masa hannu tana maida numfashi,katashi kayi brush,kamar yaji abunda tace ya mike,gaba tai ya bita abaya.Toilat ta shiga brush ne ga sunan ajejjere sabbi kal,guda daya ta dauka ta bare makilin ta matsa masa ta bashi a hannun sa,rikewa yayi besan abunda zaiyi da shiba,dafe kanta tai waishi wanann babu abunda aka koya masa aiko Bazan zauna kana wahalar dani ba komai koyama zanyi,daukar brush tai tasa abakinta,duk abunda yaga tayi shi yakeyi,suna gamawa taga yana kokarin cire boxer aguje tai hanyar fita ya rufa mata baya dan besan akan abunda take gudu ba.
Hhhhh wandon yana hannun sa yadda Allah ya taimaka rigar ta kusa zuwa guiwa,Hankalin ta yayi kololuwar tashi ganin duk inda tasa kafa nan yake maida tasa,tsabar tashin hankali yasa ta fara fitsari atsaye batare data sani ba,fuskarta kuwa tayi jage jage da hawaye,kai riyyah taga masifa,tuntana gudun da kwarinta harta gaji da wanann zagayan da sukeyi,zama tai tana haki tare da fashewa da Kuka,kayiwa Allah kamaida wandon ma,narokeka hadda hada hannaye alamun roko,tsuru yayi yana kallon ta,shibesan akan me take magana ba.
Zuwan Sadik kenan yaji parlon tsit,da dan saurinsa irin na Soja daya samu trening ya hauro benan,yana tura kofar ya hango riyyah tana yiwa Canal magiyar ya maida wandon sa,besan sanda dariya ta kufce masa ba,tsabar dariya saidaya zauna dirshan,wayarsa ya dakko ya fara yi musu vidio batare da riyyah tasan da zuwan saba,dan gaba daya hankalinta baya bakin kofar yana kan Canal da tunanin abunda zai aikata mata.Saidaya gama shan dariya kafin ya fada parlon sai Lokacin tasa da zuwan sa.
Da gudu ta mike tayo bayan Sadik tana yayi masa magana ya maida kayansa,abun dariya yadda ta buya abayansa haka shima canal yazo ya buya abayansa aka kara gauraya da juna,da sauri tai baya tana tunanin wace irin jaraba ce Wannan Namiji zai dinga binta,hanyar waje tai da sauri canal yayi niyyar binta Sadik yayi saurin cafko hannun sa,dariya kamar zata halaka shi,juyowa Canal yayi yana bata fuska akamme Sadik zai rikeshi.
Tsabar jigatar da riyyah tai kasa zaman tai akan sofa,kan carpet ta baje tana maida numfashi,har time din hawayan fuskarta na nan,akalla takai 30mnt akwance tana maida numfashin wahala,tunda suka fara sakkowa yake kallontà,yau sun matukar bashi Nishadi,sosai abun yaki barin idanun sa,yadda yaga ana dauki badadi tsakanin Canal da Bomboy.
Sannu Bomboy Sadik ya furta cike da tsokana,an tsallake rijiya da baya,tashi zaune tai sai lokacin abunda tai ya bata kunya,sunkuyar da kanta kawai tayi tana dan murmusawa."Yar dariya Sadik ya saki,wai meyasa Bomboy kake da matukar tsoro,tsoronka na bani mamaki wani zubin,amma innai duba da yanayin shekarunka sai naji babu wani abu dan kaji tsoro,shiru riyyah tai bata tanka masa ba.
Ranar Sadik wuni yayi dasu har yamma yana part dinsu,data gaji da zama dakin ta ta fada tasaki,bacci tasha zuwa karfe 4.Wanka ta karayi tasa kaya,tana fitowa ta jiyo hayaniyar Asad da su Ammar duk yan gidanne,su Biyar ne suka shigo duk kusan kansu daya,hango riyyah da Asad yayi ya washe baki,kunga Bomboy nasan yau zakusha kashi a hannun sa,bazai baku ko wace irin dama ba,sai yayi raga raga da tim dinku.
Dariya suka saki,kai Asad kallemu da kyau kasan munfi Bomboy auki bawani abu dazai firgita mu danya tsaya abakin raga,haka kukace,kwarai kuwa,dukan kafadar riyyah yayi wani shegen zafi ya ziyarceta amma ta kanne, Bomboy karka bani kunya duk yadda za'ai karka yadda ka barsu suci,murmushin yake riyyah ke saki,kayan boll ya cillo mata ta cafe ihun murna Asad ya saki kaga ko ai nafada muku Bomboy bazai bani kunya ba,kayan take kwallo kirjinta kamar zai tsage,wandon iya cinya zai tsaya mata sai riga data sakko ciniya, yellow da black shine rashin rigar.
Number 1 tagani ajikin rigar, Bomboy ka saka mu fasa ka basu kunya,harwani yaji yaji takeji a idanun ta,tsanar su Baturiya kara shiga Zuciyar ta tayi,ganin an maida ita jinsin daba nata ba,juyawa tai bari na saka kayan,kai Bomboy yanzu bazaka tsaya kasa anan ba,gyada kai tayi alamar eh da sassarfa ta wuce dakinta maida kofa tai ta rufe,fashewa tai da kukan daya fara taso mata,kallon kayan take sakeyi da sunan wai ita zata saka wayyo ni riyyah,ta furta cikin tausayin kanta.
Saidata gama kukanta,jin muryar Asad na kwalla mata kira yasata fadawa toilet ta wanke Fuskarta,kayan jinka ta cire tasa kayan,kamar yadda ta fasalta yadda zaai mata hakan sukai mata,kallon kanta tayi takoma Namijin sak,hatta da bular kunnan ta ansa abunda babu wanda zai gane akwai wanzuwar bula awajan duk bin kwakwkwafinsa,sakewa tai ta fita ranta ahade,tana fita suka hau tafi hatta Sadik saidaya taba,gaskiya da alama Bomboy bazai bada kunya ba irin wannan cin mazu haka, murmushi tadan saki.
Boll aka wullo mata,dakyar tai jarumtar cafe ta bayan ta sauka akirjinta,daya fara yimata ciwo saboda yadda yasha matsa,kamar ta kurma ihu haka taji amma babu hali dan dole ta shanye azabar.
Katon filine Inda yaran gidan ke boll,dama.wajan dan haka aka yishi,harda kujerun 'yan kallo,wasa aka fara gudanarwa tun daga fara wasa aka fara lallasa su Asad,dan Bomboy fa ba labari in aka bugo boll kan tatare ta isa raga,ganin Bomboy zai kaisu kasa akai musaya takoma fili wani ya koma bakin raga,dakyar sukai ci biyu,hatta boll din Bomboy be iya bugawa ba,gaba daya kafafunta ciwo suke mata kamar zata fadi har wani duhu duhu take gani,ganin zata kashe kanta abanza tazo ta samu waje ta zauna,da sauri Humaida ta miko mata ruwa dama shi take bukata.
Allah sarki Bomboy aboki gaskiya kasha wahala,dama baka iya boll ba,da kyar ta gyada Humaida kai,har aka gama wasa bata san me yake wakana ba,sama sama takejin muryar Asad akanta,amma dai Bomboy ka bamu kunya wllh,duk zugakan danai amma kakasa abun arziki,kasa bude idanun ta tayi ta kalle shi,balle ta bashi amsa.
Haba Asad wai bakaga halin da yake ciki bane Inagafa sam be iya boll ba,nawan Allah kalli yadda kukai masa jina jina ko bude ido ya kasa yi,sai Lokacin Asad ya kalleta,ganin yadda fuskarta tayi ja kafafunta sun fara kumbura duk da akwai takalmin boll akafarta,Allah sarki kuma kinada gaskiya Humaida kinga yadda lokaci daya ya koma,bubbuga kafarta yayi Bomboy kayi hakuri,ko motsawa batai ba jitake kamar dukkman kasuwan ta basa tare da ita.
Taso muje ka huta kan aikiran sallah,duk yadda taso mikewa kasawa tai,Asad da Ammar ne suka ciccibeta har part din Canal,a kan sofa suka kwantar da ita,gaba daya Numfashinta baya fita da kyau,jikinta bai sababa,Sadik ne ya watsa musu harara,meyasa zaku dauki dan mutane baku da tabbacin ya saba da wannna kiriniyar taku,gashi yanzu ko motsawa ya kasayi.Ai yaya Sadik bamu san be iya ba,Asad ne me wannan maganar,ai dama bazaka sani ba,duk wane da giggiwa yazo.ya jajibe shi In ba kaiba,karna sakejin kamaimaita irin wannan kuskuran,gyada kansa yayi gaba daya jikinsu yayi sanyi daga yin wasa saika dangabe Kamar wanda ya shekara yana rashin lpy.
Tun suna jira bomboy ya tashi har akai magariba suka fita Masallaci,ranar riyyah ba ita ta samu kanta ba sai kusan karfe 9 ta farka,jikin taji dama damansa,babu kowa aparlon sai ita kadai,da kyar ta mike ta haura sama,dakin Canal ta fara lekawa har yayi bacci tasan aikin Sadik ne,dakinta ta wuce ruwa me zafi ta hada,tadade aciki ba Laifi ta jarajin dadin jikin ta,sallah tayi magrib da isha'i,yunwa takeji hakan yasa ta kara saukowa taci abinci,tana gama tsakura ta mike dakinta ta kara komawa tasa key kafin ta kwanta sai bacci.
Washe gari makara tai sai kusan 8 ta farka taga gari ya waye tangararau,da sauri ta fada toilet,sai datai wanka ta dauro Alwala,shiryawa tai tasa kayanta,dakin Canal ta leka yana kwance be tashi ba,sauka tai fita tai daga maine parlo tana zazzaga part din gaba daya,sai lokacin tasan yadda yake sosai ya kayatar da ita,jitai jikinta ya dada warwarewa sannan ta koma parlo.
Tv ta kunna ko zata rage mata kewa shiru ita kadai babu dadi.
Yau weekend bame fita aiki acikin su kowa yana gida yana hutawa.Misalin 12pm wasu 'yammata guda biyu suka shugo acikin wata dalleliyar mota,sunsha wanka da ganin su hutu ya ratsa fatar jikin su,suna daidaita parking Kamal na fitowa daga part din Umami,da fara'a ya tare su,manyan gari 'yar dariya sukai ina zamuje Kamal munzo duba Canal ne,kasan jiya dana dawo daga Cairo Mom take sanar dani abunda ya sameshi,shiyasa kaganni hankali tashe nabazamo dubiya,babban abokina baida lafiya,gaskiya ne kuzo muje nakaiku ku dubashi.
"Ok suka bishi abaya"sanda suka shiga tana zaune akusa da riyyah yana zazzare idanu,ja sukai suka tsaya ganin hararar dayake watso musu,murya na rawa sukai masa ya jiki,babu amsa sai kallon su dayake ya fara fusata damme zasu zo inda yake,ledar hannunsu ta dubiya suka ajiye,kallon riyyah sukai data tsura musu ido itama,dan batasan ko suwanene ba,dan murmushi ta sakar musu ina wuninku,amsawa sukai da kyar dan irin kallon da canal ke musu akwai damuwa,kuma labari ya isar musu har duka yake.
Riyyah rike hannunsa tayi ganin yadda yake son tashi ya kore su,tsam suka mike suka kwashi takalmansu,ina zasu tsaya wani kato ya jibge su abanza,har gware suke wajen kokarin fitowa daga parlon,'yar dariya kamal ya saki,wai mene kuke wannan rawar jikin,harara suka watsa mai tambayar muma kake,dariya ya saki gaskiya Salma kuna da shegen tsoro,kai tsoro halak ne haka kawai ana zaune kalau dan wata yazo ya jibgemu,da hakan zata faru uwarsa Allah ya kara zatai mana,gimtse face Kamal yayi bakuma.nasan cin fuska agabana kuke neman zagin uwata,uwar wasu dai dan ko akiyama nasan bazata taba nuna tasanka ba,besan sanda dariya ta kufce masa ba.
Part din Innayi suka shiga tana zaune tana goro,wanda ya zame mata jiki in bataci ba har Zazzabi take,dan washe baki tai.su Salamatu ne bata fuska Salma tai nifa Iyyani abunda ke hadani dake kenan mene wata Salamatu ko dadin ji babu,dan Allah karki kara,inna kara mezakimin,mataki zan dauka,iyee wato rashin kunya kika karo awaccan kasar ta masu jajayen kunnuwa,ni dama sàida nace da Ubanki karya kaiki amma dayake taurinkai gareshi kamar ganda sàida yakaiki,fashewa sukai da dariya wai kamar ganda.
Kawai Innayi kice min bakin ciki kike da cigaba na,inba haka ba ina riwanki dani,nikuma narasa wanda zanwa bakin ciki saike ala kiyaye,ci gaba sukai sa tsokanar juna cikin Nishadi da farin ciki.
Salma jikar Innayi ce,gidan su na Shuwari 5,suna matukar dasawa da Canal duk gidan da ita kadai suke shiti,wannan abu yana bata ran Mami gani take Canal san Salma yake shiyasa ko yaushe yana makale da.ita,shi kuma sam babu wannan azuciyar sa,hankalin ta da dabi'unta yasa suke dasawa badan wani abu ba.Itama a bangaranta babu wannan a zuciyarta,tana da tabbacin Umminta ko duk garinnan za'a hadu bazata taba yadda ta Auri Canal ba,saboda mugun halin uwarsa tsaf zata maida mata 'yarta bazawara.
In za'a daka ta Ummin ta Haj Ramla Canal bazaije gidan su ba,amma tana jin kunyar tanuna masa kamar bata kaunar sa,shiyasa tai shiru tare da jawa 'yarta kunne,da gargadi akan Canal din kartaji karta gani,atsaya iya zumuntar shiyafi,matukar Fannah ta taba yarinya to kuwa za'ai tashin hankali da ita bazata taba lamunta ba.
Kamar ko anjeho Mami saigata tashigo fakan fakan fuskarnan ahade kamar zata babbake,tuni labari ya isar mata Salma ta dawo gata ma acikin Gidan,yadda ta hade rai haka suka.kowa ya canza fuska,zamatai tana karewa salman kallo kamar ta rufeta da duka dan takaicin yadda take bibiyar danta,ina wuni Mami dakyar ta amsa.
Innayi ce taja tsaki kai Allah ya sawwake wannan mugun halin naki,ni Fatsima ban taba ganin wannan masifa ba,waini Fannah kodai me zaki Auri dannaki,yo inba haka ba ki hana zuciyarki sakat saboda kishin masifa irin naki,wai uwa da kishin danta,hmm kina da aiki,zaki debo ruwan dafa kanki kuwa zanga matar da zaki zabo masa,kikalli jikata tsaf tafi karfin danki inmma tunani kike za'a hadasu to ki kwantar da hankalinki,uwarta ko giyar wake tasha ba zaku hada sarakuta da ita ba,saidai mummunar kaddara.
Hmmm Lallai Mami kina ruwa,aiki ya sameki,kina can kina hauka kindakko macen da hannunki,kin damka danki ahannunta.
Mrs🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 29_30
Jijjiga kafa Mami take takaici Innayi na kara kamata, muskutawa tai kamar bazata ce komai ba,yanzu Innayi laifi ne dan natsaya tsayin daka wajan zabowa dana mata 'yar gaske,wadda nasan zataimun biyayya tabi abunda nake so,ni bazan lamunta wata ta dinga mulkar dana ba.
Kura mata idanu Innayi tai,gyada kai take àah banga laifinki ba Fannah,kici gaba da lullube danki,da laluba masa matar data dace dashi tunda shi makaho ne,daga haka taja bakinta ta tsuke.Wata hirar suka fada suka bawa banza ajiyar ta,gajiya tai ta mike ta fice suka bita da kallo.
Wannan kenan.
Wata hamshakiyar mata ce zaune awani katafaran parlo,hannu da kafa Gold ne ke walwali ajikinta.Sannu a hankali tafara sakkowa cikin takun kasaita,siririya ce me matukar kama da matar dake hakimce a parlo,jin takun takalmanta yasa matar daga kanta tasan babu wani atare da ita inba Sahar ba, kyakykyawa ce ajin farko,fara ce tas kamar katabata jini ya fito,irin wadanda ake cewa wanke hannu ka taba,yadda kalar fatarta take haka kalar launin Mom dinta yake.
Hajiya Hadiza kenan wadda ta juku da naira,taiwa talauci mummunan tsere wanda ba lallai ya kamota ta dadi ba,tunda Sahar ta fara sakkowa take sakin murmushi,tana matukar kaunar 'yarta ta,su biyu ta mallaka aduniya,Shiyasa take matukar lelensu,daga ita sai yayanta Ubaid.Tsaddaiyar shadda ce ajikin ta tagani ta fada wadda tasha hadaddan dinki kaida gani ba kananan kudi aka narka ba.
Kusa da Mom dinta ta zauna,kwabe fuska tai kamar zatai kuka,yanzu Mom kawai sai natashi naga ba kowa atare dani,kinsan fa ko kadan bana san motsa jikina,kanta tashafa I'm sorry pretty kinsan Mom dinki akaf duniya ba wanda take so sama da 'ya'yanta,ko yayane ina tare dake murmushi Sahar ta saki,gashinta daya sha gyara har tsakiyar bayanta.Shikenan Mom na yadda da zancan ki,amma kar asake maimaitamun irin haka, murmushi Mom ta saki,angama sarauniyar da babu kamarta.
Gyara zama Mom tai, niko pretty ina son nai wata magana dake,dan kallon Mom din tayi alamar tana sauraronta.Kinsan kawata Fannah ai,tunani tadan tafi kafin ta tinano wacema Fannah,dan ya mutsa face tai nagane ta,yawwa dama mun jima dayin Alkawari da ita zamu hada 'ya'yammu Aure,wata muguwar dariya Sahar ta saki kafin ta tsagaita.
"Anya Mom lafiyarki kalau kuwa"kalau nake, me zaisa ki dakko wani village Man kice wai an kulla alkawarin Aure tsakanin ke da uwarsa,gskiya Mom kikoma yadda kukai wannnan maganar ku kwanceta,ni bamtashi Aure yanzu ba,ban gama jindadin rayuwata ba,so bana so namiji yazo ya takuramin,sànin kanki ne abunda nake so shinakeyi,bazan taba yadda da umarnin kowa ba,shiru tai tana sauraron abunda Mom zatace.
Sahar kenan banda abinki wazai takura miki kowa yayi rayuwarsa,Abinda mahaifiyar sa ke so kenan karta samu wanda ya damu da danta balle ya malllake mata shi,tsurawa Mom idanu tai kina nufin wai tana kishin danta ne?kwarai kuwa kishin da take nunawa akansa ko ubansa albarka,ko ubansa bata nuna wannna zafin kishin akansa,ni kaina ina mamakin abunda take gudu,wanda yasa bata so a mallake danta,Dariya Sahar ta kyalkyale da ita,indai haka Fannah take na yarda da butarki Mom.
Hmmm biyayya zata sameta,bazan taba nuna na damu da danta ba,amma daga ranar dayazo hannuna ya dainaji maganarta har mahadi ya bayyana,wanene dannata? Canal Rayyan Attahir Rayyan.Idanu Sahar tadan zaro wai kina nufin shine dan nata,kwarai kuwa kin sanshi kenan gyada kai tayi amma batace komai ba,wani irin bacin raine ke sakko mata, guy din daya takarkare ya zabga mata mari,adalilin buguwar datai tahau kan titi tana gudun wuce sa'a,ya kirata da ballagaza kuma jaka dakikiya,kuncinta ta shafa,ta dade tana neman tawace hanya zata rama abunda yayi mata,yanzu ga hanya me sauki.
Kai tayi alkawarin hatta danginsa saita gigita su bama uwarsa ba,hukuncin Fannah yafi nakowa tsauri,sai taga ubanda takewa kishi,saita rabata dashi,ganin sa sai Lokacin da taga dama,iska ta zuka ta fesar, Mom na amince amma bana bukatar ganin sa ayanzu,ki nuna mata bamdamu da danta ba,yadda take bukata haka zamu kasance,ita ce 'yar wasan ayanzu mukuma damu zatai wasan,amma mu zamu cinye wasan,gira ta dagawa Mom,dukan kafadarta Mom tai alamar jinjina,ni dama nasan bazakiban kunya ba pretty tabbas Mom,baki haihuwar banza ba.
Mecece matsalar ki?kudi Mom ta ambata yar Dariya pretty ta saki,meyasa Mom kike da azabar san kudi,kefa kike mulkar gidannan gaba daya dukiyar Abba ahannunki take,amma har yanzu kudi be isheki ba? pretty kenan aini har abada bazan gaji da karbar kudi ba,saboda yadda nake so adama dani aduniya har yanzu sunana bekai nan ba,dan murmusawa pretty tai Mom kenan,daga haka bata kara cewa komai ba.
Sahar matashiyar yarinya ce meji da kanta,takama da kyau da dukiya,mahaifinta Ambassador ne ya tara dukiyar dabe san adadin taba,bazata wuce 27 ba aduniya,amma muguwar hatsabibiyar yarinya ce,in ta sakoka agaba saita tatseka tas zatai gaba,manyan kwari take bi bawai kananan 'yan tasha ba,sai kana da lasisi take hurda dakai,shaye shaye take na tashin hankali,hatta cocaine bata dauketa akomai ba, wine kuwa ta maida ita tamkar ruwan shanta,dama bata sallah tun tana shekara 15 rabon data kalli gabas da sunan sallah.Allah ka tsare imanin mu.
Ahankali rayuwar riyyah ta dinga garawa,ayanzu babu wadda Canal yake yarda dashi sama da riyyah,duk inda tai yana binta abaya,tsakani da ALLAH take kula dashi,jinsa take ya zamo wani bari na rayuwarta,yayanta abokinta amininta,duk tabashi wannan matsayin,tun Fannah na bacin rai akan yadda ya fifita riyyah akan kowa harta watsar tunda ba Lafiya ce dashiba,tasan yanajin sauki zai watsar da bombay daganan aikinsa ya kare saiya hada kayansa ya ware.
Yau tunda ta farka da safe wani azababban ciwo cikinta yake,kamar ana hura mata wuta, Canal na gefenta da sassafe ya tashi,ya tsiri wani abu saiyaki kwantawa da safe tana tashi sallar asuba zai farka,tsabar nacinsa yasa tafara kwana adinsa,yana kan bed tana kan sofa wata guda daya akasa a bedroom din data kasa sanin amfanin ta,akai take kwana,data motsa zatai sallah zataga ya mike kamar an mintsine shi.
Da kyar ta daddafa tai sallah saboda yadda cikin ya dameta da ciwo,kallonta yake tayi kamar me tausayin ta,yadda yaga tana ta yarfe hannu tana hawaye,intashare wani,wannan ya biyo baya,zamewatai ta kwanta tare dajan bargo ta kudundune har kanta,tatsani kallon kurillar da Canal yake zaman yimata kamar me hankali,tagaji da boye boye in zata kwanta kwance takunkumin dasu Baturiya sukai mata takeyi ta kwanta ta bararraje.
Tunda ya kyalla ido ya gani,shikenan ya daina baccin safe,har alla alla yake ya farka yaga abunda yake tsunemai idanu,yana Matukar jin haushi da rana inya kalla yaga babu,koda rana yadinga kallon kirjinta kenan yadda kasan wanda zai tambayeta ina abunda yake gani amma ba dama,sàidai kallon,har Sadik mamakin yadda yake kallon bomboy din yake,shidai baya ganin abun kallo amma saiyaga Canal ya zuba ido kamar zai cinye ta.
Ganin ta kudundune ta barshi,kansa ya dora adaidai kirjinta azubure ta mike tana sakin kara,sosai kirjin ke mata ciwo dama gashi yazo zai fama mata,Adam tsorace ya dagata yana kallon ta,harara ta wurga masa ta kara kwanciya,be kara kwanciyar ba ya zauna kamar me gadin ta,cikin dan baccin daya fara figarta ta farka harwani gumi ke tsatstsafo mata,ciwon da takeji ya tsanan ta,rike cikin tai tana.yarfe hannu,jin kamar tana fitsari azaune yasata mikewa tai toilet da gudu.
Rufa mata baya yayi ta danno kofar dan dole ya tsaya, tsugunnawa tai dan yin fitsarin,bakon lamarin data gani tattare da ita yasata gane abunda ya sameta,itako ta shigo Uku ya zatai,pant din jikinta ta cire ta wanke saidata tabbatar ta wanke masa toilet sosai tukunna ta fice,yana tsaye Inda ta barshi wuce shi tai ta shige dakinta,key ta murza kafin ta dakko bag dinta,pad din da aka hadota dashi ta dakko saidata shirya kanta tas kafin ta fice.
Kasa ta sauka tayi ayyukanta tana gamawa Umami na shigowa,hakanan taji kirjinta yayi muguwar bugawa,wani mugun yawu riyyah ta hadiye,kallon da Umami ke mata shiyafi komai daga mata hankali, murmushi Umami ta sakar mata,menene ya saki wannan rawar jikin,jin fitsari yana neman kufce mata atsaye da sauri ta tsugunna,ina kwana Lafiya lau,hannayanta ta ruko acikin nata,dakin datasan natane nan Umami ta jata,sàida Umami ta murza key adakin sannan ta fuskanci riyyah da gaba daya bata hayyacinta.
Zaunar da ita Umami tai kafin ta tsura mata idanu,sunkuyar dakai riyyah tai tashin hankali na rufto mata aka.
Meyasa kike sha'awar jinsin daba naki ba,shin kinmanta Allah ya tsinewa wanda yayi kamanceceniya da namiji,haka Namijin da yayi da kamanceceniya da mace,ban zaci hakan daga gareki ba,meya birgeni da ha'intar mutanan da suka yadda dake,shiru riyyah tai hawaye na tsiyaya a idanunta.
Sake rike hannun ta Umami tai,nidin uwace wanda nasan yanayin halittar jinsin mace haka jinsin Namiji,no Doctor ce tun ranar dana fara ganinki na kwana ina nazari akanki,tabbas baki kama da namiji ba,amma yanzu inason ki fadamin dalilinki,matukar sun gamsar dani ashirye nake dana taimaka miki,inko basu gamsar dani ba kinsan sauran.Kuka riyyah ta fashe dashi me tsuma zuciya lallai Baturiya ta sata amasifa,ni din ba kowa bace Umami kuma banzo gidannan dan na cutar da kowa ba,hasalima bantaba sanin da wanzuwar ku ba.
Labarinta ta bata gaba daya,kanta gama bata labarin Fuskar Umami ta jike da hawayen tausayinta,wata irin kaunar yarinyar taji azuciyar ta,tabbas danginta azzalumai ne,yadda suka sa rayuwarta acikin hatsari, bubbuga bayanta Umami take ta kasa magana,dama akwai dangin da zasu aikatawa maraya haka,lallai dan adam butulu ne,in sha Allah saita taimakawa riyyah iyakar iyawar ta,zata tsaya tsayin daka wajan ganin rayuwarta ta inganta.
Nayadda da dukkan bayanan ki riyyah,daga yau Inaso ki dinga yimin kallon mahaifiyar ki wadda ta tsugunna ta haifeki,wllh riyyah tun ranar dana fara ganin ki Naji matukar kaunarki,ashrye nake dana taimakeki,farin cikin riyyah ya kasa boyuwa,zamowa take kokarin yi dan godiya agareta,riketa Umami tai babu wannan atsakanin mu riyyah.
Share mata hawaye tai,ina so kici gaba da boye kanki,ki kumayi taka taantsan da Rayyan ako yaushe zai iya dawowa hayyacin sa,daga lokacin daya warke zan daukeki daga gidannan matukar uwarsa ta gano macece ke,bansan wane irin hukunci zata yanke miki ba riyyah,gyada kai ta dingayi junta take cikin farin ciki,razanin da take ciki na tonuwar asirinta yanzu yakau daga zuciyarta.
Tabbas da Iyyani ce ta gano riyyah na miji ce da sai kowa yaji,da ayau zata bargidan ayanayin da bazata tantance kanta,jan kunne Umami taci gaba da yiwa riyyah kafun su fito parlo saboda tsaro.
Riyyah ni kaina na tayaki farin ciki.Na samun new Mom.
Mrs🌹 Baba 🌹Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 31_32
Suna zama Sadik yayo sallama,da fara'a Umami ta amsa,riyyah sunkuyar da kanta tayi gani take kamar kowa yariga ya gano ta,yadai Bomboy ba gaisuwa,murya na rawa tace ina kwana,lafiya lau yame jiki da sauki Allah ya kara sauki,ameen suka amsa gaba dayan su.Dan kallonta ya sakeyi kodai yauma ya dakeka ne kamar kayi Kuka,Umami ce ta amshe maganar ko daya kasan jiki da jini gajiya ce tai mata yawa,gaskiya dole akwai gajiya shekariun sa sunyi karanci aturoshi wannan aikin,gyadakai Umami tai Hakane amma kasan kuwa da yanayin rayuwar Gidan su,ta yiwu shi Agidan su wannan ba komai bane,hakane Umami Allah yasa mudace ameen ta amsa.
Mikewa tai ni zan wuce saina dawo,adawo lafiya sukayi mata ta fice daga part din,bari naje na gano mutumin mikewa yayi ya haura sama.
Dan Lumshe idanun ta tayi,cikin farin cikin dake zagaye zuciyar ta,yau ji take kamar an sauke mata wani kaya dayake saman kanta,kaunar Umami na kara huda zuciyar ta,ayau ta samu uwa kamar Ummin ta,taji tana kaunar Umami kamar jininta ahalin ta,kai tamafi ahalinta tunda su bamzatar da ita sukai,batasan lokacin da suka sakko ba sai ganinsa tai tsaye akanta.
Saidata dan razana,bata fuska tai itafa wannan Kallon nasa ya fara isarta,idanunsa kadai razanar da ita suke,tamkar wani mejin bacci haka yake kallonta,sakin fuskatai tunawa da halinsa yanzu zai iya zama ya manne mata matukar yaga ranta ya baci.Hannunsa Sadik ya kama yakaishi dining amma fir yaki karbar abincin da yake bashi,ciwon kai me tsanani ke damunsa,hatta jiniyar kansa tatashi amma basu lura da hakan ba.
Da kyar riyyah data bashi ya karba shidinma kadan yaci,magungunan sa suka bashi yasha,zama yayi shiru kamar bashi ba,haka ya wuni sukuku, riyyah har boll dinsa ta dakko masa suyi wasa amma ko kallanta beba,daga karshema kwanciya yayi ya Lumshe idanun sa.Gaba daya sai taji ba dadi,Canal ya zamo wani bari na jikinta,ya zamar wani sashe na zuciyarta,sosai take jinsa aruhinta,tunani ne ya aure ta,ganin abokinta yau baya walwala da sukuni.
Da daddare ma kin kwanciya yayi yana zaune aparlo,gajiya da zaka riyyah tai ga yadda cikinta ke ciwo daurewa kawai takeyi,kama hannun sa tayi suka haura sama,har kan bed dinsa takaishi saidata tabbatar ya kwanta taja masa blanket.
Barin dakin tai gaba daya,dakinta ta fada saidatai wanka ta canza pad din jikinta,kayan bacci ta saka doguwar riga,ranar jitai tana bukatar bude kanta yasha iska,hular da aka samata ta cire da kyar, Lumshe idanun ta tayi jin wani sanyi na ratsa tsakiyar kanta,kanta ta kalla amadubi kitson da akai mata yana nan yadda yake sai tsufa da yayi duk da a kunshe yake,nadeshin da akai ta warware har tsakiyar bayanta jelar takai,idanun ta ne ya ciko da hawaye yaushe rabon data ganta kamar haka,kamar kowace mace sai yau.
Goge hawayanta tai ta sauka kasa ko dan kwali bata daura ba to Inama ta ganshi,saidata rufe ko ina kafin ta haura sama yana kwance yadda ta barshi da alama bacci yakeyi menauyi,kamar yadda ya saba tana tottofa masa addu'a yauma hakan tayi masa,sai data dauro Alwala kafin ta kwanta bacci.
Karfe 2pm ya dafe kansa da yake matukar sara masa,yadade awannan halin kafin ahankali ciwon ya fara lafawa."Ahankali ya fara bude manyan idanun sa da sukai masa matukar nauyi,lumshewa yayi ya kara budewa,tabbas wannan dakin sane,dafe kansa ya karayi meyasa meshi haka,a barrack ya kamata ya tsinci kansa amma kalle shi anan,tariyo abubuwan da suka faru ya dingayi daya bayan daya".
Kautar da kansa yayi idanunsa caraf ya fada akanta,tana kwance ta baje tana sharar bacci,kitson dake manta saiya kara mata kyau,ras gabansa ya fadi mace yake maimaitawa a zuciyarsa,meyakawo wannan yarinyar part dinsa bama a parlou ba har bedroom.Ahankali ya mike kamar me tausayin kasa akanta ya tsaya yana kare mata kallo daga sama har kasa,yama rasa mezeyi mata,haryakai hannun sa da nufin fincikota saiya janye,aikuma bansan wacece ita ba,bansan dalilin zuwanta inda nake ba,haka yake Ayyanawa a zuciyarsa,ya kamata na tsaya naga menene shirinta akaina da har dan rashin kunya ta shigomin part da daddare.
Zama yayi yana tunanin abunda ya sameshi abaya,abunda zai iya tunawa motarsu data dake wani babban dutse daga hakan bazai iya tuna komai ba.Awannan daran kasa runtsawa yayi tunani ya addabi zuciyar sa,har akai kiran farko be runtsa ba."Bakinta dauke da Addu'a ta farka,ka'idar ta dama kiran farko take farkawa,saidata gama karantawa tukunna tatashi zaune,idanunta takai kansa idanun sa alumshe yake duk abinda take yana kallonta.
Dan bata fuska tai ganin ya yaye rufar datai masa, ahankali ta mike takarasa gaban gadon jan blanket din tai ta lullube shi,iya kansa kawai tabar masa awaje,sai zabga uwar hamma take alamun bacci be isheta ba.Toilet dinsa yaga ta afka,abunfa ya matukar daure masa kai,lallai wannan ko wacece tana da kwarin guiwa tashigo mai part kamar nata,shi abunda yafi bashi haushi mezai kawo wannan kwailar yarinyar inda yake,zai tsaya yaga musababbin zuwan ta.
Yananan kwance yaga tafito da alama Alwala tai,duk da tana period tasaba dashi hakane yasa tatashi ta daura Alwala,zama tai tana lazimi akan kunnan ta akai assalatu,tun yana jiran yaga ta kabbara sallah shiru kake ji har aka idar da sallah tana zaune,shikuma dannaci yaki tashi inhar zai tashi hakan na nufin zata gane yaji sauki.
Saida gari ya fara haske yaga ta fita daga dakin,dakinta ta fada tsaf tai wanka ta maida kayanta,saigashi ta koma Bomboy dinta,yananan kwance yaga dawowarta idanu ya zaro ganin wani Namiji daban acikin dakinsa,shiru yayi kamar me bacci,dan tsayawa tai akansa,wai yau Canal meyasa kaki tashi,tasaba da tashin wurin da yake yau kuma taji shiru yaki tashi,tirkashi.
Bubbuga kamarsa tai ko zai tashi,bude idanun sa yayi kamar me baccin gaske,rike kugu tai tana kallon sa,yau kuma wata gulmace ta sameka aida naga kakoma tashi dawuri,murguda masa baki yayi fakare yayi yana kallonta,shifa kamar yarinyar dazu yake gani agabansa amma kuma ya akai ta koma Namiji.
Hannunta tamika ta ruko hannunsa,jansa tai alamar ya tashi haka ya mike yabi bayanta,brush yaga ta dakko ta mika masa,ba musu ya karba itama guda daya ta dauka,kayi kamar yadda kaga nayi,nagaji da wahala akanka kai kullum aita fadama abu baka ganewa,shiru yayi yana jinta tana mita,kamar yadda ta nema haka yayi suna gamawa ta kara kama hannun sa, aparlo ta zaunar dashi.
Aikinta tafara babu wata damuwa tattare da ita,duk inda tabi binta yake da kallo,in har wanann yarinyar itace takemai wanka amma kuwa da ta cuceshi kuma dole yadauki mataki akanta."tana gama mopping ta debomai kayan wasan sa,gashi kayi wasa kan Sadik yazo yayi ma wanka,karamar ajiyar zuciya ya sauke jin ba itace take masa wankan ba,kallon kayan data jeremai yayi da kallo,wasa waikodai ciwon hauka yayi be saniba, Innalillahi kawai yakeja azuciyar sa.
Kamar yadda ta fada mai,basu jima da zama ba Sadik yayi sallama,amsawa tai tana gaidashi yame jiki Bomboy da sauki, Bomboy ya maimaita sunan azuciyar sa,yau mutumin ya tashi da wuri kenan,eh yatashi,dukan kafadar Canal yayi Allah ya baka lafiya abokina,ta tabbata kenan ciwon da yayi ba karamin cuta bace,lallai Sadik masoyinsa ne na hakika,amma ina 'yan Uwansa da suka kasa kula dashi, Mami ya furta amakoshinsa,tabbas yasan bazata taba yadda su rabe shiba,ya rasa wane irin rayuwa ce Wannan ta hanashi sukuni kwata kwata.
Hannunsa Sadik ya kamo muje kayi wanka,ba musu ya bishi abaya koda wasa be nuna masa ya warke ba,sanda suka fito har ankawo musu abinci dining suka nufa,yau riyyah ce ta dinga bashi abaki haka ya dinga amsa saida yaji cikin sa ya dauka ya kauda kansa gefe.
Mekewa sukai daga dining din,saiga yan hayaniya nan su Asad sun shigo,dan runtse idanun sa yayi ya tsani wannan hayaniyar tasu,kai tsaye wajan riyyah suka nufa,kai Bomboy anji jiki,dariya suka saka wllh mundauka sai ankaika emagency, murmushi kawai take,ashe baka iya boll ba mukai zabon timin dare,ni dama tunda naga kana tafiya kai kadaiba kamar zaka fadi balle wata boll nasan dole Asad yasha kasa,dariya suka kara sawa,fada masa dai Ammar shifa gani yake Bomboy dinann wani jarumine gashinan kunsha kasa.
Kaf maganar da suke akan kunnan sa,daya bayan daya yake auna maganganun su,amatsayin Namiji tazo kenan, landing ya karayi a sofa saiyaga iya gudun ruwanta.
Sunjima atare dasu kafin kowa ya kama hanyar sa.Kwana biyu kenan da samun lafiyar sa,tsaf ya karanci wacece riyyah,rayuwarta kawai take da tunanin ai baida lafiya bazai gane jinsin taba.Haka ya gane suwanene ke zuwa dubashi suwane basa zuwa,tunda yaji sauki ko saudaya bega Iyyani ba yayi mamaki sosai yasan bata yadda zaai taki zuwa wajansa,tabbas akwai dalilin daya hanata zuwa.
A yaune ya shirya tsaf dan sanar da ita yafa ganta amatsayin mace.
Tana gama yimasa brush ta fice daga dakin,dayake ta saba baya biyo bayanta yanzu bata saka key ba,saidaya tabbatar ta dade dashiga sannan ya bita,yana shiga ya murza key a kofar,dakin yake karewa kallo, Lallai ma har wani dakine da ita a part dinsa,kwata yayi kafa daya kan daya ya dora kafarsa yana jiran fitowar ta.
Hannunta rike da towel,ta dauro wani iya cinyarta ya tsaya,kanta ta wanke duk da bata tsefeba,saidata san razana ganinsa datai a dakin,bata fuskatai ta harare shi,bama ce kadaina biyo niba,tashi ka koma parlo kokarin ruko hannunsa take ya rike hannun,hada idanu sukai ras taji gabanta ya fadi,wani irin kallo yake mata data kasa tantance shi,betabayi mata irin wanann kallon ba.
Kokarin janye hannun ta tayi ya cika mata,haka kawai tasha jinin jikinta da irin kallon dayake mata,mikewa yayi yana sakin wani munafukin murmushi,hanlin riyyah ba karamin tashi yayi inhar ta kalla daidai murmushi fa yake mata,matsawa ta farayi yana binta,har jikin bango ta dangana,hawaye tuni ya wanke Fuskarta,bakinta rawa yake takasa furta komai,hannunsa ya dafe jikin bango dashi gaba daya bata ganin komai sai faffadan kirjinsa daya rufeta dashi.
Karfin kukanta ne ya karu,yaushe hakan ta faru,yaushe ya warke,dama yadade da warkewa bata sani ba?sake barkewa da kuka tai kamar wadda yake duka,lumshe idanun sa yayi kukan natama dariya yake bashi,shiiiiii ya dora hannunsa akan abakinsa,takasa rike kukan gaba daya,yau tata takare ta tabbatar Canal sai yayi kuli kulin kubra da ita.
Wacece ke!!? tsit kukan da take ya tsaya jin dakakkiyar muryarsa a dodon kunneta,shiru tai tana rawar jiki,kallonta yake kallan kasan ido,jintayi masa shiru tana zare manyan idanun ta da suka kara kyau saboda razanin da take ciki.
Mika hannunsa yayi batare data ankareba ya fizgo towel din dake daure ajikinta,fasa wata gigitacciyar kara tai gaba daya tafada jikinsa batare datasan ta aikata hakan ba.
Hhhhh hehehe ga Rayyan ga Riyyah.
Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
.....✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrates
By Kulsoom Ismail Idris
Page 33_34
Runtse idanun sa yayi abazata ta fado jikinnasa,gaba daya hannunta tasa ta zagaye shi,kukanta na kara hauhawa,banbareta yake sonyi amma fur taki sakin sa,huci me zafi ya furzar daga bakin sa,cikani matukar baso kike nai miki abinda bazaki taba mantawa ba har karshan rayuwarki,matuka maganar ta daki zuciyarta to mexe yimata,kin sakinsa tai,sakinsa na nufin yagama da ita,duk wani mutuncinta ya gama gane mata shi ina bazai taba yiwuwa ba.
Bawai dan bazai iya yin hakan agare taba,danka daya zai mata yafigeta daga jikinsa,amma gaba daya takwance masa duk wani lissafin sa,cije lebansa na kasa yayi towel din dake yashe akasa yasa kafarsa ya dakko,fara kokarin daura mata yayi,abun ba karamin haushi ya bashi ba,daka mata tsawa yayi batasan sanda ta sake shiba hawaye na tsiyaya a idanun ta,tsaki yaja cike da takaici,uwarme zangani kike wannan kukan me kike dashi ma da kike boye boye,abinda be wuce kiyi yawo ba riga ba.
Maganganun sa bakaramin takaici suka bata ba,kara damke towel din daya daura mata tai,gaba daya jitake kamar ta nutse ga wani tsoronsa daya dirga azuciyarta,oya sit nuna mata gefen bed yayi bata da zabi wanda ya wuce ta zuba din.Yakai kusan mintuna 5 batare da tace komai ba,kallon kasan ido yake mata gaba daya tatakure agefe,jinta take Ita da tsirara basu da banbanci,fesar da hucin bakin sa yayi,zaiyi magana kenan yaji anfara norking.
Dagudu riyyah tatashi ta fada toilet harda sa key tsabar yadda ya kadu kamar zatai fitsari awando.Kamar bazai bude ba saidai ya murza key din,tsaye tayi abkin kofar tana kallonsa da Mamaki,meya kawo shi dakin riyyah harda murza key,tsura masa idanu tai kamar yadda yake kallonta, murmushi ya sakar mata,Matar nan da yake ganin kimarta sa karamcinta gare shi,yana Matukar jin Umami azuciyarsa,yakanji inama ita ce ta haifeshi,saboda kyawawan halayanta.
A hankali ya tako har gaban ta,dukkan hannayanta ya rike murmushin nan nasa mematukar tsada da ba kowa yake ganinsa a face dinsa ba.Umami ya furta cikin muryar da ita kadai tasan shi da ita.Rayyan ta furta idanunta na cikowa da hawayan farin ciki, rungume shi tai farin cikinta ya kara karuwa,tana Matukar kaunar Rayyan,hakanan takejin kaunar sa da tausayin sa,tana matukar tausayin halin Mahaifiyar sa,wadda kanta kawai ta sani bata damu da damuwar sa ba,inta yanke hukunci akansa be isa ya sauya ba.
Nagodewa Allah daya nunamin ranar daka warke Rayyan ina matukar farin ciki da samun lafiyar ka,goge mata hawayan fuskarta yayi wanda batasan yana zuba a face din nata ba.
Dakin take bi da kallo bataga riyyah ba,kallon tuhuma take binsa dashi tana ina,dan ware idanu yayi akanta,dama dake aka hada baki aka kawota part dina,kasan wace jinsi ce kenan,girarsa ya sosa yana kallon Umami da take kallonsa,kamar kin manta nime kamo me laifine Umami, murmushi tadan saki wannan din ba irin karatan daka saba kamawa bane,itadin Acikin alfarmata take,diya tace halak malak nidin zan zamo komai agareta.
Kallon fuskar Umami yake tabbas duk abinda take fada daga zuciyarta yake fitowa,wacece ita? meyasa kake son sani?kamar hakan zaimin Amfani,bazai amfaneka ba Yayan su,rabar inda take tamkar ka dakkowa kanka dala da goran dutsene,wani yawu ya hadiye mematukar daci,tabbas Mamin sa macece me matukar san kanta shi kansa yasan da hakan.
Hannunsa ta jawo tamaida kofar ta rufe,zama tai akan stoll tana daga tsaye yana kallonta,zan sanar dakai wacece ita,amma hakan ya kasance sirri atsakanin mu,gyada kansa yayi burinsa tasanar dashi menene ya kawota gidan su.Kamar yadda riyyah ta bata labari haka ta bashi bata rage masa komai ba,gaba daya idanun sa sun canza launi,dama akwai masu hali irin nasu Gali,lalai dole saiya hukuntasu amma ta wace hanya,ita dakanta zata hukunta danginta abinda ya ayyana kenan.
Riyyah Umami tadaga murya wajan kirani sunan ta, ahankali ta fito fuskarta ta jike sharkaf da hawaye,dan zaro idanu Umami tai ganin daga ita sai towel iya cinya,ga Big bro dayake binta da kallo kamar yau ya soma ganin ta,dan hade face Umami tai ta nuna masa hanyar waje ba musu ya juya dan shima yana bukatar hakan.Kallon riyyah tai data tsaya tana wasa da yatsun hannun ta,harara Umami ta wurga mata,haka kika tsaya agabansa riyyah katuwar budurwa ki tsaya gaban Rayyan tik dake,matse kwallah riyyah take be ganni ba,aini makauniya ce davanga yadda yake binki da kallo ba.
Wuce kishirya kanki ina jiranki aparlo,gyada mata kai tayi,kamar babu laka ajikinta ta fara shiryawa,kayanta na maza ta mayar sabbi kal bata taba saka suba sai yaudin,fitowa parlon tai ta zauna.Umami ce ta saki murmushi ganin yadda ya kame azaune kai kadauka Namijin ce yadda kayan suka amshe ta.Wani azababban kamshine ya daki hamcin su gaba daya suka daga kawunan su sama,Canal ne cikin wani tattausan yadi fari kal,hatta vest din dayasa aciki ana ganin ta,kannan yasha gyara kamar ba wanda ya tashi daga rashin lafiya ba,hakanan taji tana san kallon sa,bakaramin kyau yayi mata ba ashe haka yake da matukar kyau.
Selfie Umami ta fara daukar sa bakinta kamar zaiyage,bakaramin kyau taga yayi ba,wow carkwadidi malladidi,gaskya yarona me tsadane dole bazan bayar dakai afarashi me rahusa ba,dan murmushi kawai ya saki,yana gama sakkowa Sadik yayi sallama,idansa akan Canal ya fada,ware idanun sa yayi cikin tsananin Mamakin ganin yadawo hayyacin sa.Da sassarfa Sadik ya karaso suka rungume junan su.
Dude da gaske kai nake hani akan kafafunka,tunanin ka na baya yadawo,gyada masa kai yayi kamar yaron goye,girma da kimar Sadin yana mara shiga zuciyar sa,yatabbata shidin abokine na gari.Mungode Sadik Allah yayi Albarka Allah yasa abotarku ta amfaneku har Aljannah,ameen suka amsa.
Bomboy yau kaga megidanka ya warke ko,dan murmushi ta saki tana gyada kai alamar eh,Umami murmushi kawaii tayi suka hada idanu da Canal kauda kansa yayi daga kanta.Muje part din Iyyani nasan Mamin ka tafuta tun sassafe,ok dunguma sukai har riyyah babu kowa agidan masu aiki sun fita masu school sun fita.Tana zaune aparlon ta tana kallo,jin alamun tsayawar mutane tai abakin kofarta,dago idanu tai karaf ya sauka akan Canal wanda yake mata kallon kaikaice,nashiga uku biyoni kai har dakina ka zalinceni ko kuwa,mikewa tai har zaninta na neman tadeta,da gudu tashiga kiching dinta tadakko katuwar tabarya,taho yau ai nashirya tsaf ubanka zanci.
Duk yadda yaso kinyin dariya sai daya dara,haka su Umami sosai Iyyani ta basu dariya,cikin dariya Umami kefadin haba Iyyani yanzufa ba dukanki yazo yiba,gaisheki yazo yi,ansamu cigaba matuka yanzu megidanki ya warke,kallon Umami tai kafin tamaida kanta kansu,wai Yagana ni sa'ar wasanki ce zaki fadan gaskiya ko sai ranki ya baci,kallon Canal Umami tai jeka taga zahiri.
Ahankali ya tako har gaban Iyyani datake zazzare idanu,fuskarta awashe yanzu ta tattabar jikanta ya samu lafiya,tabaryar hannunta ya karba ya ajiye agefe,hannun ta ya kama gaba daya,idanunta har cikowa sukai da kwallah.Yanzu Soja da gaske ka warke,gira ya daga mata,duka takai masa kai wane irin salan iskanci ne zaka dinga dagan gira kamar Budurwarka, murmushi yadan saki,ita ce ai ko kinmanta kece Uwar gidana, murmushi tasaki tabbas tayadda Rayyan dinta ya samu lafiya.
Kai zo muzauna nakara kallon ka sosai,hango riyyah tai ta tsakure agefe,washe hakora Iyyani tai kai Rayyan zonan kaima ga abokin naka ya warke,kallon wanda takira Rayyan yayi,wanann yarinyar har sunan sa ta sata kuma,kwafa yayi alamar zasu gauraya.Da dan murmushi a fuskarta ta matso inda suke hade hannun riyyah dana Canal tayi,yauwa kaga wannan yaron yabaka kulawa sosai daga yanzu ya zama kaninka shima,banda cin zalin daka dinga yimai sanda baka da lafiya duk kawamke lefinka,ni da iyayanta zasu yaddama da sun barmanashi wllh ina son sa,takara fuskarta tana bayyana abundake Zuciyarta.
Caraf Umami ta dauka aiko bazasu barmanashi ba,zuwa zasi sutafi da dansu,kema Iyyani wazai baka kyautar da awannan zamanin,to in since sun barmana kice bazai zauna ba,wai Yagana kodai bakin ciki kikene da zaman sa,haba Umami ta rike nina isa tata zanyi bakin ciki akan abunda kike so,ah to yanzu naji magana,nadauka kema kinbi sahun waccan me fala falan kunnan, Fannah take nufi,yar dariya sukai sun rasa mene tsakanin Iyyani da Fannah gaba daya jinin su be hadu ba.
Abbu ne yashigo part din Iyyani danya gaisheta,yayi matukar Farin cikin tashin dansa,mafi soyuwa agare shi, rungume juna sukai suna masu Farin cikin sake haduwa da juna.Shafa kansa Abbu keyi,Mazan fama dagaske ka warke, murmushi ya sakar masa yana gyada kai yana matukar ji da Abbun nasu, Alhmdlh Allah shine abun godiya.
Tabe baki Iyyani tai,andaiji butur babu kara agabanmu kake kwakumarsa kamar zaka maidashi ciki, murmushi yadan saki,bece komai ba,dukawa yayi yana gaida Iyyani dakyar ta dinga amsawa wai saidaya fara da dansa kafin ya gaisheta,shidai hakuri ya dinga bata.
Duk wanda ya shigo yaga Babban Yaya a parlon Iyyani da gudu yake zuwa ya rungume shi mazansu da matansu,yaudai Canal babu daka tsawa ya saki ransa na wucin gadi.'Yar mulkin sai kusan azahar ta dawo tana parking Humaida tataho tana washe baki kamar gonar auduga,kallontà Mami tai kekuma Farin ciki me kike, albishirinki Mami goro ta amsa.
Yauammu ne ya warke garau Mami tunda kika fita da safe,kallon bakin Humaida take maimaita kalmar safiya take,amma arasa wanda zai kirata,ita da danta bata isa dashi ba,rai bace ta wuce part din Iyyani cike yake da jama'a sai zuwa Barka da Arziki ake,abun da yaka bata ranta kenan ganin har can bare sunsan da samun lafiyar sa banda ita Mahaifiyar sa.
Tunda ta shigo kowa ya zuba mata idanu ganin sai huci take,ansan rashin mutuncin data saba zatai,idanun ta akan Canal ya fada wanda yake sakar mata murmushi,harara ta watsa masa cike dajin haushin be dauketa da muhimmanci ba.Sannu Fannah angama zagayan garin andawo,sake kuluwa tai kamar ta rufe Iyyani da duka,zoki dakeni Fannah koba gaskiya na fada ba,tun safe danki ya warke amma kinacan kina neman kudi,wane shege kika ajiye dazai kiraki,nadai san haushin da kike ji kenan,to wllh saidai ki mutu,nan gaba ko Auran 'Yarki za'ai bakyanan kintafi wanann shegen aikin maki,kullum kisa wani bakin sket ki fice saidai kizo kiga munkaita dakin mijinta aha.
Zatai Magana suka hada ido da Canal kallon tayi shiru yake mata,tarasa meyasa idanunsa suke kassarata aduk lokacin da zatai.wani abu shiyake fara dakatar da ita,shiyasa aduk sanda zata yanke masa wani hukunci bata yadda ta kalli idanun sa,hakane zai iya karya dukkan wata kwarin guiwata,ficewa tai ba tare data firta abunda ke kan harshan taba,mara kunyar banza da kifadi abunda ke ranki mana.
Mikewa yayi yasan halinsa sarai yanzu Allah kadai yasan tijarar da zatai masa,binsa da kallo Iyyani tai tana ala wadarai da halin uwarsa.Tana zaune sanda ya shiga kamar zata fashe,dama yasan za'a rina tunda yashigo take jefamai harara,har gabanta ya karasa ya zauna,hannayan ta ya ruko yana kallon ta,Mami ya furta cikin sanyin murya,dan runtse idanun ta tai,muryar datai watanni masu yawa bata jitaba, ahankali fushinta ya fara sauka,tana matukar kaunar danta,shiyasa bataso kowa ya rabe shi.
Kiyi hakuri Mami na,kunsan me kadaice sanyin idaniyata,tunda nabude ido ke nake mararin ganin,sedai kash asanda nake neman ki bakya atare dani Mami,shiru tai tana kallon sa dukkan wani laifinsa ya wanke shi,tunda yace tunda ya farka ita yake.mararin gani,shafa kansa tai,yau ina cikin Farin cikin tashin ka Rayyan,dan kallontà yayi jin ta ambaci asalin sunan sa, murmushi tadan saki batace komai ba,shiru sukai basu da abun fada,sam babu shakuwa atsakanin su,tsakanin ta dashi bada umar nine bayan wannan babu wani abu,amma ko yaushe maganarta daya kar azo kusa da danta.
Ganin babu Amfanin zaman sa ya mike,harya fice tana binsa da kallo da hasaso irin matar dazata Aura masa.
Wayarta tajawo tai dialing din wata number,ring biyu aka daga,cikin Murmushi tai sallama,daga daya barin aka amsa,Haj Hadiza manyan gari yar dariya tasaki wane mu,yame jiki kuwa,ai jiki yawarke,kai ma sha Allah,naji dadi Allah y kiyaye gaba Ameen haj.Ina Sahar ayya ai tatafi islamiyya kinsanta kullum tana hanyar makaranta,fadada fara'a Mami tai shiyasa take birgeni.
Zamu zo da ita gobe muduba mejiki,Allah ya kawo ku Ameen ta kashe kiran.Kallon juna sukai suka fashe da dariya gskya kema Mom kina da wani abu,yanzu kamar ni kice natafi islamiyya,rabon danaje tun ina shekara 10 aduniya,dariya Mom din tai ai sàida haka,tunda abinda take so kenan saimu bita ahaka zaifi,dan tabe baki pretty tayi ita tasani.
Bangaran Mami cikin Farin ciki ta sauke wayarta,tabbas danta zaiyi dacan mata,aduk sanda zata kira sai ance Sahar tatafi makaranta wannan abu yana sata karajin kaunar Sahar din,gashi abun farin ciki ance batason aiki,babu wani aiki da zata dinga fita sàidai ta zauna agida hakan yayi mata 100% hmmm Mami kenan.
Msr 🌹Baba🌹Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 35_36
Washegari kamar yadda Mom din pretty ta fada hakan ce ta kasani ce,tunda safe Mami take shirin tarbar su,babu wanda yace mata kanzil ita kadai ta dinga budirinta,Abinci kusan kala 5 ta girma,banda snacks data bata Lokaci wajan yin sa,tana kammalawa ta fesa wanka ta kashe dauri,sam bata san harkar karanta,data motsa kamshi ke tashi daga jikin ta.
11am a harabar gidan taiwa su Sahar, driver ne ya fito ya bude mata kofa,tana sit din gaba ta hakimce,fitowa tai tana zukar iska,dan Lumshe idanun ta tayi tana karewa harabar gidan kallo,tabbas ta yadda suma ba kananan mutane bane,ba Laifi bazataji kunyar ambatar gidan matsayin gidan surukanta ba.Wani makeken mayafi ta nannade kanta acikin sa,banajin ko Mom dinta tataba yafashi,fuskarta fayau babu kwalliya ko kadan,farine kal mayafin sai sheki yake da walwali daganinsa me tsadar gaske ne.
Tunda Mami taji dirar motar su ta leko ta window dinta,ba karamin farin ciki taiba hango Sahar cikin kamala da Mutunci,ta tabbatar babu wanda zai kusheta,ga kyau,ga ilimin addini dana boko,ga nutsuwa da kamun kai,ga dukiya iyayanta suntara,ita kanta batasan irin dukiyar da Sahar din keda ita ba,ta tabbatar abun hannun danta bazai tsone mata idanu ba,bama agabanta yake ba.
Ya Kwalo ta kwallawa kira,da sauri tafito har tanacin tun tube gani Hajiya,yawwa angama kimtsa komai,sosai Hajiya komai sai san barka,wannan kayan da muka hada ko first lady ce zata shigo bazata kushe ba, murmushi Mami ta saki aikinki yana kyau ya Kwalo,aje ga bakin can ashigomin dasu,angama Hajiya,jiki na rawa ya Kwalo tai hanyar waje.
Har Inda suke ta karasa da fara'a suka tarbeta,sannun ku da zuwa Hajiya kishigo,ok suka bi bayanta tamkar basu san wani abu wulakanci ba.
Oyoyo Mami take fadi sannu da zuwa diyar Alkhairi, murmushi Mom ta fadada ganin yadda Mami ke nan nan da pretty,kamar zataiwa Mami sujjada haka ta zube agabanta,karantse da Allah jakadiya ce kanta asunkuye take gaida Mami wadda kanta ya kara kumbura ta samu sirikar Arziki 🤣🤣🤣kayya dai.Haba Sahar taso mana ainima Mamin kice amma ina fur Sahar taki zama akan sofa,lallai Sahar tacika 'yar duniya.
Kayan tande tande ta gabatar musu amma Sahar ta kafe bazata ciba Saboda tsabar kunya hatta fuskarta a lullube take,hmm ai Fannah indai Sahar ce kya gaji kunya ce da ita,inzaki kwana kina magana bazataci abincinnan ba,nidai zanga lokacin da pretty zata daina wannan kunyar,'yar dariya Mami tai ai banga laifinta ba kunya adon macece kuma tayi matukar birgeni,tabbas yarona yayi sa'ar mace tagari,irin Matar dana dade ina roka masa akan Allah ya azurtashi da ita,sai gashi Allah ya karbi Addu'a ta.
Gyada kai Mom tai tabbas kinsan Addu'ar uwa bata faduwa kasa banza,gashi Allah ya cika miki burinki,nima na dade inaiwa Sahar Addu'ar samun miji Nagari,saigashi ta samu fatana dai Allah yasa su daidaita kansu,zama su daidaita Son baida matsala baya taba tsallake Umarni na,caraf Mom ta cafe haka Sahar matukar muka nuna munasan abu ko bata so biyayya take mana,kai Alhmdlh kinga bazamu sha wata wahala ba hali yazo daya.
Dukkan tattaunawar da suke akan kunnan Sahar wadda take kunshe dariya,tabbas Mami Addu'ar ki ta karbi,danki ya fado hannuna kin zama sorry,abunda take ayyanawa kenan azuciyar ta.
Tsaf suka kammala cin Abinci kafin tace suzo takaisu wajan Innayi su gaida,ba musu suka bi bayan ta.Tana zaune aparlo sai Umami da riyyah dake can gefe kome suke tattaunawa oho.Da kallo suka bisu tunda suka shigo,baki bude Innayi take kallon su,kasa yin shiru tayi,ikon Allah Amarya kika kawomunne,yar dariya Mami tayi kishiya na kawo miki, Sahar ce wadda Rayyan zai Aura,gaba daya zubawa Mami ido sukai,hakanan riyyah taji kirjinta ya harba,idanunta ta sauke akan wadda ta lullube fuskar caraf suka hada idanu,wanda hakan yasa kirjinsu bugawa alokaci guda,kamar hadin baki kowacce ta kaida kanta, Sahar jitai tatsani wanann yaron ita kanta bata san dalili ba,bangaran riyyah nanata kalmar matar Rayyan take azuciyar ta.
Au ashe Allah yayi cewar Iyyani da take rike haba,tabbas kuwa ga Amarya nan 'yar gaske gata da kunya kin iya zabe Fannah, murmushi suka saki ita da Mom jin yadda Innayi bata kushe Sahar ba,karo na farko kenan da Innayi tataba karbar wani abu daga gare ta batare data kushe ba, jindadin abunda Innayi tayi yasa ta nunawa Sahar Umami akan Itama ta gaishe ta,ba musu kuwa ta gaida Umami cikin girmamawa,da fara'a take amsawa haka suka gaida da Mom din Sahar amutunce.Basu jima ba suka.mike ganin Innayi taja bakinta ta tsuke gadai magana abakinta amma tazabi tai shiru tana ta kokawa da harshanta,sallama sukai wa Innayi rafar kudi Sahar ta direwa Innayi wadda ita kanta batasan adadin su ba,hakan fa ya kara kankaro mata mutunci awajan Mami tabbas wannan in danta ya Aure ta gaba ta kaita kullum kudi bazai yanke mata ba.
Ba yabo ba fallasa Innayi tayi godiya har suka fice tana binsu da kallon dana kasa fassarashi,haka Umami ta bisu da kallo wani abu na taba Zuciyarta,tana matukar kaunar Rayyan dukkan wani abu da zata hango wanda zai zama silar rushewar farin cikin sa bata fatansa,ajiyar zuciya ta sauke jin muryar Innayi ta daki dodon kunnan ta.Hmm dadina da gobe saurin zuwa lallai Fannah zatai babban kuskuran tura kanta ramin damisa,nikam bazan ce komai ba nawa ido dantane,kamar yadda tasha fadar ita ce zata zabamai matar Aure gashi ta zabi din Allah ya ara mana rai da lafiya,daga haka Innayi taja bakinta ta tsuke,gaba daya Zuciyarta ba dadi.
Bazakuje ku duba Rayyan din ba,kara sunkuyar dakai Sahar tai,da sauri ta kara gaban motar su alamun bazataje ba,dariya Mom ta saka,kemadai Fannah kamar bakisan Sahar din ba,ai bazata taba zuwa ba,nima daganan zamu wuce kinsan mara lafiya yakamata adinga barinsa yana hutawa,zan dawo zuwa na musamman na duba shi,to shikenan Mom pretty saina jiki,kan lokacin ma zan turo shi su fara ganin juna,babu damuwa muna maraba da zuwan sa,har bakin mota tara kasu tanai musu Godiya,tana tsaye driver ya jasu suka fice.
Tunda suka shiga mota Sahar ke babbaka dariya,cilli tai da mayafin daya addabi rayuwarta,tunda uwarta ta haifeta bata taba yafa wannan zunfumemen abun ba,kai ita atsarinta ma bata fita da mayafi,takura mata yake bazata iya dakon wahala ba,gaskiya Mom da kina film ba kamar star zaki zama ba fannin makirci,dariya Mom din tasaka,to kinga laifina mene dannace kina da kunya,ni kam Mom karma ki sakoni awannan sahun banajin kunyar uban kowa,wanann tsugunnan da kika ga nayi zan fanshe agaba banyi abanza ba,ina tabbatar miki kamar yadda na duka agabanta wllh Itama saita duka saita bini,cike dacin alwashi ta furta hakan,nasan zakiyi fiye da haka baki tsotsi nono na abanza ba,yes Mom.Dukkan maganganun da suke driver na jinsu fatan shirya yake musu azuciyar sa,yana mamakin bakin hali irin nasu kamar bazasu mutu ba.
Bayan sallar isha'i ta jawo phone dinta,ring 3 aka dauka cikin muryar kamala tai sallama,daya barin aka amsa,Umami ta furta cikin sanyin muryar ta,dan murmushi Umami ta saki, na'am Fareeha,kuna lafiya yasu muniba lafiyar su kalau.Kinsan yayanku yaji sauki kuwa,ihun murna ta saka dagake Umami,zammiki karya ne,amma meyasa ba'a sanar dani ba,dama zamu zo nan da 1 week Abban Muniba ya samu hutu, murmushi ta saki faduwa tazo daidai da zaka,dama zami wata magana dake ne amma tunda zaki zo ba damuwa inkinzo mayi Maganar atsanake,Allah ya kaimu Umami.
Hirar su suka ci gaba dayi tana sanar da ita cigaban da Mijinta ke samu a USA ga yaranta ma sha Allah suna karatun su sai san barka,hakan ba karamin dadi yayiwa Umami ba tasan hannun da zata damka riyyah bazata taba Kuka da Fareeha ba tana sa kwarin guiwa akan 'yar tata.Sallama sukai ita kadai take sakin murmushi,abubuwa da dama take ayyanawa a zuciyar ta.
Tunda ya koma part dinsa yake akwance,gaba daya ya rasa abinda yake damun zuciyar sa,dayaji motsi saiya dauka ita ce ta dawo,me take nufi bazata dawo ba kenan,dan yaji sauki ai bagama warkewa yayi ba,kamata yayi tazo ta karasa aikin ta,tsaki yakeja tun yamma har dare be dena ba,haka kawai yaga part din yayi masa girma,kamar kewar wani abu yakeji azuciyata sa,to kewar wa zaiji kenan,amsar da zuciyar sa ta bashi yayi saurin kawarwa hakamma bazai taba faruwa ba.Bangaran riyyah wani iri takeji da yau bata tare dashi,ta saba dashi matuka,dukkan wani motsinta yana biye da ita,ko toilet zata shiga yana bakin kofa kamar me gadinta,ta saba da rikicin sa,wasan da yake akowace rana hakan na sata Nishadi,in har tace bata kewar sa taiwa ranta karya,jitake kamar taje inda yake.Kamar Innayi ta shiga Zuciyarta kai kuma dan yaji sauki shine bazakaje inda yake ba,tashi katafi dare yayi,kamar ta doka tsalle haka taji azuciyarta,dama jira take zaram ta mike,yadda Allah ya taimaketa Umami bata part din da tabbas zata kirkiro abunda zai hanata komawa.
Har sauri take dan kar si kicibus ahanya,tana karasawa part din ta sauke ajiyar zuciya sosai tai missing din part din kamar ta shekara bata cikin sa.Akan idanunsa ta shugo,dan Lumshe idanunsa yayi wani sanyi na kwarara a zuciyarsa,meyake damunka ne Rayyan akan wannan ficiciyar yarinyar,abunda ya tambayi kansa kenan,sam bata lura da wanzuwar sa awajan ba,zamatai akan sofa tana maida numfashi kamar wadda tai tsere,murumushine kwance akan face dinta,dimpul dinta sake lobawa ya tsurawa idanu,abun da yake matukar so ga mace arayuwar sa kenan,ajikinta taji ana kallonta,caraf idanunta ya sauka akan sa,bazaka taba gane kallonta yake ba,dan ware idanunta tayi akan kyakykyawar fuskarsa,wadda babu fara'a ko kadan acikinta,hakan kuma be hana bayyanar kyawun dayake dashi ba.
Daina kallona,taji yanfurta abazata dan ware idanunta tayi,da sauri ta rufe fuskarta gaba daya kunya ta kamata ganin yadda ya kamata dumu dumu tana kallon sa.Besan sanda murmushi ya subuce masa ba arayuwar sa yana son mace me kunya,duka da karancin shekarunta amma tasan kunya saita burgeshi matuka,takara samun fada azuciyarsa,yana jinta kamar jinin sa kanwar sa.
Um um dai Canal muje zuwa.
Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 37_38
Sake saka kanta tayi tsakanin cinyoyin ta,kunyarsa ta keji matuka,tarasa Meyasa in tana tare dashi takan tsinci kanta cikin Farin ciki,kodan bata da iyayene kannne da yayye takejin hakane,tunowa da Abbanta da Ummeen ta ya canza yanayin fuskarta,dago kanta tayi ta jingina bayanta jikin sofa,takan tuna maganar Ummee a koyaushe.(Riyyah ina fatan Allah ya ara mana tsahon rai,banaso kiyi maraici kamar yadda na taso acikin sa,nakasa manta radadi da dacin da naji asanda bani da kowa,ina alfahari da mahaifinki,ina rokon ALLAH ya bani ikon yi masa halacci) ashe haka Ummen ta taji,ashe haka maraici yake da daci,ita kadai takejin kanta,tasa aranta bata da kowa,kullum zuciyarta na kuna inta tuna butulcin danginta,babban fatanta tazamo abunda basa son ta zama,tana so ta nuna musu iyakar su,Allah ne da rayuwarta basu ba,tabbas sunso kasheta da wahala Allah ya tsallakar da ita.
Tunda fara tunanin yake kallon ta,hawayan da yaga yana sauka akan face dinta ya kara daukar hankalin sa,tausayin ta kara narka zuciyar sa yake,yana da tabbacin ta tuna iyayanta,tana da kananun shekarun da zata kasa rike hakan,bata cancanci haka daga wajan ahalin ta ba."Tsam ya mike ya tako har Inda take zaune,tayi Matukar nisa a tunanin ta,tattausan hannun sa yasa yana share mata hawayan da batasan da zubar saba,dago jajayan idanun ta tai ta zuba akan sa.
Bayan Mama Sauda da Baba megadi,babu wanda ta hango tsantsar tausayin ta akwayar idanun sa sama da gwarzan matashin nan dake gabanta,badan ya hadu da larura ba tasan babu yadda za'ai ta zauna kusa dashi balle hartai magana dashi.Ya tsinci kansa da rashin san zubar hawayan ta,yana da Matukar tausayi akan mace,ba yaso ko yaya yaga hawaye na zuba a fuskar diya mace,mata suna da wani girma da kima a idanun sa,matukar kinason lagonsa to sanda zai miki hukunci kikama Kuka tabbas zai iya yafe miki laifin da kikai agareshi,kuma bazai kara waiwayawa yayi duba da laifin ba har abada.
Dan murmushi yasakar mata daba kowa yake samun hakan daga gareshi,daga Umami sa Innayi da Abban sa,hatta Mami bata fiye ganin wannan murmushin nasa ba,saigashi ya tsinci kansa da yiwa riyyah.Kura masa idanu tai,tuni ta manta da kukan da takeyi,farin ciki takeji yau ta samu wanda ya damu da damuwar ta,kamar wanda aka tsikara ya mike daga gabanta,gaba daya haushin kansa ya kamashi wai meyake damun sane? bashi da amsa.
Binsa riyyah tai da kallo harya bacewa ganin ta,dan lumshe idanun ta tai tana shakar daddadan kamshin turaran daya barmata,tajima awajan kafin ta lallaba tashige dakin ta,dama yasan Bazata zo dakin saba,shima be yadda da hakanba,wanka tai ta sauya kayan jikinta zuwa kayan bacci,tana rokon Allah ya yaye mata sa kayan mazanann da take fama dashi,yaushe zata samu 'yanci bata sani ba,koma babu rana hakan take Ayyanawa azuciyar ta,kwanciya tai taja Blanket har kanta.
Washe gari Mami ta aiko Humaida kiran riyyah har part din Canal sàida kirjinta ya buga dan tunanin wane irin kira take mata wannan.Jikinta asanyaye ta shiga part din Mami tana zaune taci kwalliya,gaba daya bata gajiya da kwalliya,Kullum jin kanta take matashiyar Budurwa mejini ajika.Tunda suka shigo ta zubawa riyyah ido gani tai kamar yakara girma ya kara kyau,wannan yaron da macene da anyi kyakykyawa,da babu tsautsayin da zaisa ta kaishi part din danta,ita kanta kyan yaron na daukar Hankalin ta,balls kuma namiji,yadda Allah yaso ba macen bane yaje can ya karata da kyansa.
Harta tsugunna agabanta batasan da isowar taba, Mami ga Bomboy din,cewar Humaida naganshi ai ko tashi zanyi na goya shi, girgiza kai Humaida tayi hanyar waje Mami ta nuna mata,barin part din tai gaba daya Zuciyarta na tafasa ta rasa abunda yasa Mami batason su rabeta kamar ba itace ta haife su ba.Maida kallontà tayi kan riyyah,kaikuma sannun ka,gidannan dai koda kudin ubanka aka hada aka gina sai haka.
Sàida riyyah ta dago ta kalle ta,ranta ya gara baci jin tana zagin Ubanta dayake cikin kabari,idanunta harya ciko da kwallar bakin ciki,ka kalleni da kyau,ta silata kazo gidannan amma ban isa kazo Kullum ka gaishe niba,saidai Kullum kana tare da mahassadana,bini bini katafi wajan waccen me fuska biyun Yagana,in kuma kun hada dangantaka da ita saika fadamin nasani,girgiza kai riyyah tai alamar a'ah,au tsanar kwadayine irin naka,to uwarme take baka inkaje wanda ba'a baka a part din dana.
Tuni Hawaye sun wanke mata fuska,kunnanta takama saidata sa kara saboda azbar da taji,yau basai gobe ba zan kira wadda ta kawo ka,aikin dakazo yi ya kare dama,sai akara gaba ni wllh haka kawai naji jininama be hadu dakai ba,kullum kana sunkuyar dakai kamar kaga surukarka,wannan yana daga cikin alamun Mutum munafikine wadda bayaso ya dinga hada idanu da mutane,shiru riyyah tai batace komai ba,amma a badini hankalinta amatukar tashe yake jin za'a maidata hannun Baturiya,bata mance abunda taji suna tattaunawa akan taba,tana gama wanann aikin zata mikawa alhazai ita,tana da tabbacin zata zama muloniya.
Tunawa da hakan yasata fashewa da kuka,data koma hannun Baturiya gwara daganan tashiga Duniya,tasan gashin kanta zata ci,bazata taba yadda ya koma hannun ahalin ta ba,zatai ne yiwuwa ganin ta gudu daga gidannan gaba daya zataje can tayi rayuwa Inda babu wanda ya santa.Eh lallai samun waje tafiyar ce bazakai ba kake wanann kukan,batace mata komai ba,haka Mami taita banbamin masifa,wayarta ta jawo afusace kai Allah ayauma zaka bar gidannan tunda abun naka ya zama Iskanci.
Number ba turiya ta dannawa kira,ko tashi daga bacci Baturiya batai ba,tana gefan wani Alhaji a hotel sun gama sheke ayar su tamkar bazasu mutu ba,rai bace ta dakko wayar dan ganin wanda zai takura mata da sassafenan,ganin number Mami yasata saurin tashi zaune,duk inda harkar samun kudi take Baturiya batai sanya.
Ko amsa sallamar datai Mami batai ba,yawwa wa kike da suna Turai kike ko Baturiya,to komadai inyamura ce kizo kidauki danki yagama aikin sa,yau kuma nakeson kizo ki tafi dashi,wanda yazo aikin dominsa ya warke.Fuska Baturiya ta washe faduwa tazo daidai da zama,jiya jiyannan dama akazo mata da wata harka, za'a fitar da kananan yara can kasashen ketare bakaramin alheri zata samu ba,dama da takaicin sulmiyewar kudin ta kwana sai gashi komai yazo mata dai dai.
Zanzo yau kuwa,batare da Mami ta tsaya ba ta sauke wayarta daga kunne,yanzu sai kace bazaka tafi ba,zanga dani dakai waye megidan tashi kaban waje ka hada kayanka tas tana zuwa sai tafiya.Mikewa tai kanta na barazanar tsagewa,in akwai abunda ta tsana a ambaci sunan ahalin ta,ko ganin gabanta batayi karo taji taci da wanda yake gaban ta,baya tai zata fadi yayi saurin tarota,gaba dayan ta tafado jikin sa,idanun ta kadai ya kallah yasan bata hayyacin ta,part din Umami yafi kusa cak ya dagata yayi part din da ita,babu kowa a parlon kan sofa ya kwantar da ita,daga part din Mami ta futo yanada tabbacin akwai abunda tai mata.
Ajiyar Zuciya take saukewa ajejjere,idanunta yayi jajawur,tsura mata idanu yayi yana kallon ta,tausayin ta yakara kamasshi matuka.Fitowarta kenan daga bedroom ta hango Canal a parlon ta,sai data sakko ta lura da riyyah sake kwance akan sofa,da sauri ta karasa gaban ta,me akai mata son dan furzar da iskar bakinsa yayi,nima bansani ba,maida kallon ta tayi kan riyyah da idanunta ke rufe amma Hawaye ke gangarowa ta gefen kunnan ta.
Kaimun ita bedroom dina,ba musu ya kara daukarta kamar baby,tanajin dukkan abunda ke faruwa,amma nauyin da idanunta yayi ta kasa budesu,har kan bed din Umami ya kwantar da ita,ficewa yayi daga room din dan bata damar dubata,zamatai kusa da riyyah hannayanta ta rike tausayin yarinyar na kara kamata,tayi kankanta da shiga irin wannan tashin hankalin.Batace mata komai ba ta gyara mata kwanciya, blanket ta lulluba mata kafin ta fice daga room din.
Kasa ta sauka baya part din.part din Iyyani ta nufa danta gaisheta,anan ta tarar da Mami taje gaida Iyyani,kadaran kadaham Iyyani ta amsa gaisuwar Mami,ganin Umami yasa Iyyani sakin fuska,abunda yake batawa Mami rai kenan yadda take nuna banbanci akan ita da Yagana,tarasa ubamme yaganar ke bata data fifitata akanta( abunda Mami bata sani ba abun hannun Umami be rufe mata ido ba,duk watan Duniya ta dauki Albashi akwai kason Innayi Acikin,bayan haka yadda take girmama Innayi Mami bata girmama ta haka,duk da akwai 'yan aiki amma Umami da kanta take wanke kayan Innayi wannan ya kara dasa kaunar Umami azuciyar Innayi.Kowa ce zuciya tana son me kyautata mata).Harara Mami tabi Umami da ita tare dajan tsaki,saurin kallontà Innayi tai Allah yasa dai badani kike ba.
Kumbura fuska Mami tai kamar Yarinya,kinji nace dake nake,wadda tasan da ita nake ai sakon ya isa gare ta,dan murmushi Umami ta saki,to yanzu naji magana,da ace dani kike da saidai yau Attahiru ya zaba koni ko ke,shiru Mami tai tana hura hanci.Kallon Umami Innayi tai wai ina yaronnan Rayyan,caraf Mami ta karbe dazu Munyi waya da mamarsa zatazo daukarsa yau,kodai ke kika kirata,nasan bakin halinki Fannah ko yaya bakyason kiga bako ya shigo gidannan,ke muma da kinada dama da yanzu kin koremu daga gidannan,kema kayanki akulle yake ko yaushe zaki iyayin gaba kidaibi ahankali.
Bandama masifa irin ta Namiji,haka kurum kaje ka dakko wata guzumar mace,ni ina tunanin ma kingirme shi,duk yadda Umami taso rike dariyarta kasawa tai,haka Hafsa 'yar Autar Innayi ce tana daga daki tana tikar dariya,dama shirin futowa take daga dakin,tana futowa kuwa Innayi tai arangama da ita.Sannu Hafsa kina daka amimmike ni gani awaje,wllh kin bani kunya kin kuma cuceni bakiyo halina ba,wai kishiya ce ta hanaki zama agidan Miji,inna tuna wannan abu da kikai Hafsa jinake kamar nahau kanki da bugu wllh.
Ni har Akwai kishiyar data isa nabar mata mijina."Akwai sanda babanku ya raba auran wata fitsararriyar mata wai harni zata sakowa 'yar shimi da buje tafito tana jujjuyawa atsakar gida,nace hmmm bakisan wacece Fatsima ba,batasan nafita sanin takan duniya ba,saidana dai daici Mijina ya dawo,ina hangota tafito tana rausaya agabansa waidan da burgeshi.Dana tashi tabbatar mata nafita tashanci dagani sai dan kanfai da rigar Mama na futo bayan naci gayu na gyare gashi na,ai da gudu ta koma daki taga wadda tafita iya shege.
Fashewa sukai da dariya baki dayansu hatta Mami da ranta ke bace, gaskiya duk wadda tai zaman kishi da Iyyani tayi matukar kokari.Aidaga ranar nai maganin 'yar banza daga karshe da kanta ta hada kayanta,har daki ta boyoni tana ban hakuri da alkawarin tabarmin mijina,dama yaga baya ta ita,kuma ni bankore taba kishiya dai bata isa ta hanani kula da mijina ba,amma ke dayake sha sha shace kishiya ta koro ki,kinji kunya Hafsa takarasa fade tana wurgawa Hafsa harara.'Yar dariya Umma Hafsa tai kamar yadda yaran gidan ke kiranta,haba Innayi kinsan kowa fa da kaddarar sa,kaddara kin kwanta ba dole kaddarar tabi ta danneki ba,ai Allah yace tashi na temake ka solobuyo kawai.
Umami mikewa tai hankalinta nakan riyyah dole su san abinyi bazata taba yadda tabada riyyah atafi da ita ba,hakan na nufin gurbacewar rayuwarta,zata cika alkawarin data dauka na kulawa da ita muddin rai.Kamar yadda Baturiya ta alkawarta kudi sun zauna mata,jirgi ta biyo karfe 12 napep ya sauke ta akoafar gidan dan Barno.Wannan karan bata tsaya sai an shigo da ita ba,part din Mami ta nufa kai tsaye tana zaune tana kallo Baturiya ta shiga da sallamar ta,ta dau wanka ba karya,ta cokala uban dauri,dayake ba jigatar mota kamar lokacin tai kwalliyar fuskarta.
Da mutunci Mami ta karbe ta,taganta fes dagani tanacin na kanta, hannayan ta yasha zanen lalle baki da ja,saiya kara futowa da farar fatar Baturiya data kara haskakata da mayuka.Kayan motsa baki tasa aka jere mata,bataiwa kanta mugunta ba sai data ci tai kat.goye da jakarta ta shigo abayanta,washe baki Baturiya tai kai Rayyan haka kakara girma dakyau,Mami ta kalla gaskiya Hajiya nagode Allah ya saka da Alkhairi, murmushi Mami ta saki,Ameen ita kanta ta kara hango kyan da riyyah ta kara,ta kara haske ta murje.
Kusa da baturiya riyyah ta zauna,Fuskarta dauke da murmushi tagaida baturiya cikin sakin fuska take Amsawa,tana ayyana irin makudan kudadan da zata samu ta hanyar riyyah,a da sauran kadan ta cuci kanta nakin karbarta datai,yanzu ko ita kadai zataci gajiyarta,tunda sauran dama sunnuna basa bukatar ta,hatta Ladidi bazata san inda riyyah take ba.
Baturiya ke wannan dogon lissafin.
To!! zamu gani zakici nasarar tafiya da riyyah ko zakiyi biyu babu.
Mr🌹 Baba 🌹 Bello ABUBAKAR
........✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 39_40
Kudi masu yawa Mami ta zaro daga jakarta,mikawa riyyah tai,gashinan nakane wanann karike ahannun ka,kara zaro wani tai ta mikawa Baturiya kwayi kudin mota,godiya sukai tare da mikewa,bari naiwa Iyyani sallama,ok Mami ta furta,dakin Iyyani riyyah ta shiga,kwalalo idanu tai tana kallon riyyah da mamakin ganin ta da jaka,ina zakaje da wannan kayan badai Tafiyar zakai ba,kamar yadda waccan me kodaddiyar fuskar ta ambata adazu.
Murmushi riyyah ta sakar mata,eh Iyyani zan tafi,oh nashige su yanzu da gaske Tafiyar zakai bazaka zauna ba,gyada kai tayi alamar eh,yaran gidanne suka dinga shigowa,Asad harda matsar kwallah zasu rabu da bombay,Humaida Kuka tadingayi shabe shabe kamar karamar yarinya,bataso bomboy ya tafi,sun Matukar sabawa dashi,babu yadda suka iya,aikuwa shatara ta arziki suka dinga bata,har mamaki tai dama yaran gidamma suna da kudi haka.
Driver akasa ya kaisu tasha a mota zasu koma,dan Baturiya bazatai jigilar saka riyyah ajirgi ba,haukama take yi tab,sàida yakaisu har inda suke bukata godiya sukai masa suka fice,gyara parking dinsa yayi yana kokarin juyawa,daidai lokacin wayar Baturiya tai kara,ganin sunan Zulfa yasata saurin matsawa gefe ta tabbatar samuwa ce akan maganar tafiyar riyyah waje ne,sai data bada tazara tsakanin su dan batason riyyah taji komai akan tafiyar,wannan damar riyyah ta samu ta kara fadawa motar da suka fito daga cikin ta.
Cikin bin umarnin da aka bashi yaja motar da mugun gudu kamar walkiya suka bace daga titin bat.Bangaran Baturiya sai data gama waya fuskarta washe da murmushi ta nufo inda tabar riyyah sàidai me wayam babu ita ba labarin ta,tun tana zatan abun nawasa ne saiga karamar magana ta zama Babba,bazama tai cikin tashar tana neman riyyah amma ba ita ba alamunta.Hankali tashe ta fara tambayar mutanan wajan ko sunga wani yaro magana dayace basu ganshi ba kuma basusan inda yayi ba.
Gumin tashin hankali ya fara tsatstsafo mata,akalla takai awa daya tana bulayin neman ta Matukar jigata,ga zafin rana da kishi daya addabe ta,makoshinta har wani daci yake,fuska taji rana har wani ja tai tsabar wahala.Babban bacin ranta asarar da zatai ita bag batanne ya tayar mata da hankali ba,taga samu tana neman rashi.Station ta nifa ta bada report din batan danta,anan sàida suka karbi kudade ahannun ta,da alkawarin za'a tsanan ta bincike akan neman sa,kamar Baturiya ta dora hannu aka haka takeji,asara goma da goma,kudin data kashe bata samu wata ribaba saima nata daya shiga ciki.
Kudadan da 'yan gidan suka tattarawa riyyah yana hannunta,dama jira take su fita daga mota ta kwace saigashi ta bata da makudan kudade ajikin ta,kai ko yanzu taga riyyah saitaci Ubanta ba karamar wuya ta bata ba.Ba abun takira gidan da suka baro ba konan ta koma tasan batasan hanya ba babu yadda za'ai ta koma gidan,akwai dai Abunda ya faru,kodai gudawa tai,nan ma zuciyar ta bata gamsu ba,akamme zata gudu bayan yanzu zata samu 'yanci ta wataya zata dawo ainihin macen ta.
Kin tafiya Baturiya tai,hotel ta nufa anan zata kwana kafin taga Abunda zai faru zuwa gobe.
Kai tsaye Shuwari 5 ya wuce da riyyah,wannan din shirin Umami ne,tana sane tasa driver ya kaisu tasha hakane zai basu damar dauko riyyah batare da shan wata wahala ba,sun gama magana da haj Ramlah mahaifiyar Salma akan riyyah zata zauna anan kafin Fareeha tazo suwuce US.Babban gidane amma bekai gidan su Canal ba suna zuwa get man ya wangale musu get,kutsa kai sukai cikin gidan daya gaji da haduwa.
Mom Ramlah da kanta tafito dan tarbar riyyah, murmushi ne shimfide akan fuskarta,tunda ta taho riyyah ke kallon ta,ta Matukar burgeta da alamun zatai saukin kai da mutunci,cikin girmamawa drive ya gaisheta,amsawa tai fuskarta asake,hannun riyyah ta ruko batare da tace komai ba,tausayin yarinyar ya cika mata Zuciya,ganin Yarinya ma sha Allah amma an canza mata jinsinta da wani daban.Sama suka haura,dakin salma ta kaita jeki wanka,gayada kai tayi dakin yayi mata kyau sosai komai pink color ne adakin.
Wardrobe din Salma ta bude,dayake itama ba wani jikine da Salman ba tasan kayan bazasiwa riyyah yawa sosai ba,arabian gown ta dakko mata ashe color,tasha adin stone sai walwali takeyi,sai sabon pant akan bed din ta ajiye mata kafin tajuya tabar dakin.Ta dade tana wanka har kanta ta wanke,wata Iska ke shigarta tako ina,tana fitowa ta hango kayan da Mama Ramlah ta ajiye mata,daga kayan tai idanunta na cikowa da hawaye,yau she rabon da tasaka kaya mai tsada irin wannan tun Abban ta na raye,share hawayanta tai ta zura kayan,kallon kanta tai amadubi,tabbas duk ayadda Allah ya halicce kafi kyau a wannan jinsin,ganin yadda kyawunta ya kara fitowa tai,datai shigar mata,kallon kanta take tana tuna abubuwa da dama azuciyar ta.
Mayafin rigar ta dauka,babu Abinda ta shafa duk ko da jerin kayan shafe shafen dake kan mirror,bide kofar tai,karar bude kofar ya jawo hankalin Mama dake zaune tana waya,zubawa yarinyar kallo tai tana yaba kyawunta,yarinya nitsatstsiya amma ake so acutar da rayuwar ta, murmushi Mama take sakar mata nuni tai mata akan ta zauna kusa da ita,babu musu ta karasa inda take zaune,hannun ta taruko ta zaunar da ita kusa da ita,babu musu ta zauna tana wasa da yatsun hannun ta.
Tana katse wayar ta maida kallonta tai kan riyyah,sannu da zuwa Ansariyyah,sàida riyyah ta kalleta jin tafadi cikakken sunan ta,'yar dariya Mama Ramlah tai ko kin dauka bamsa cikakken sunan kiba,mamanki Yagana ta sanar dani komai,kuma in sha Allah nima zan bada gudummawata wajan kulawa dake iyakar iyawa ta,tumdata fara magana riyyah take kallonta,duk harafin daya fita daga bakinta dukan dodon kunneta yake,wata murya takeji wadda ta dade bata jita ba,muryar Abar sonta da kaunar ta,Ummeen ta jitake kamar muryar tanai mata gizo tana rikida zuwa ta Ummeen ta, rungume ta Mama tai,wata irin nutsuwa riyyah taji wadda ta dade bataji kwatankwacin ba,kara lafewa tai ajikin Mama Ramlah wadda hakan har mamaki ya bata ganin lokaci daya ta saba da ita.
Inama Umami zata barmata riyyah data riketa awajanta,amma tasan bazata taba barmata ba saitazo ta karbe ta.Tashi muje kici Abinci rana tayi kama hannunta tayi suka wuce dining,dambun shinkafa tai hadadde wanda yaji zogale da gyada,yaji attaruhu da albasa sai tashin kamshi yake,sai kunun gyada data dama fari kal dashi,sai dinja data dakko a fridge cup din har raba ke zuba saboda sanyin da yayi.Allah yasa dai kina cin abincin gargajiya,gajeran murmushi riyyah ta saki yana daga cikin abunda tafiso arayuwar ta,duk ranar da Ummee tace zatai dambu tunsafe take damunta yaishe za'a dora.Cika mata plate Mama tai tatura mata agabanta,sai kunun gyada data zuba mata acup taje ta fata shansa ahankali ta dinga sha bakaramin dadi yayi mata ba,ba laifi taci dambun saidata kai bakinta ta kara tabbatar da dadinsa,har kifine aciki bakaramin dadi yayi mata ba,bata fargaba tatashi da wanda Mama ta zuba mata ba,kunyace ta kamata azatanta ko rabinsa bazata iya cinyewa ba sai gashi tatashi dashi.
'Yar dariya Mama Ramlah ta saki,in baki koshi ba na karo miki,nima Maman kice ki saki jikinki,gyada kai tayi fuskarta dauke da murmushi mikewa tai ta koma kan sofa.Saida Mama ta kammala tataso kusa da riyyah ta sake zama tana janta da hira,balaifi tadan saki jikin ta sunyi hira takuma ji dadin hakan sosai, Mama Ramlah wayayyar macece,bata da duhun kai ko kadan,haka bata daukar wargi ko kadan shiyasa basa shiri da Fannah sam basa zama a inuwa daya.
Kar 4 Salma ta dawo daga unguwa,ganin Mama da bakuwa yasata sakin fuska, Mama ba kuwa kikayi ne,ba bakuwa bace 'yar gida ce,kai Mama amma ban santa ba,kallon riyyah tana mika mata hannu sugaisa ba musu ta mika mata nata,ta ganeta itace sukaje duba Canal,kai Mama kamar nasan wannan Fuskar tafurta hakan tana kallon riyyah,saidai amafarki kika santa amma wannan da kike gani daga kd take,dan dafe kirji Salma tai kai ashe tafiyayya tayi amma naji dadin zuwanta Mama.Anan gidan zata zauna amma,waya gaya miki badadewa zatai ba,dan batarai Salma tai dan Allah kice ta zauna anan,dariya Mama kawai tai surutun Salma yayi yawa.
Ruko hannun riyyah tai taso muje dakina,mikewa tai tabi bayanta,dukda akalla taba riyyah shekaru 5 Salma shekararta 20 riyyah 15 amma atsaye riyyah ta kamo ta.Dankin da tabaro dazu nan suka koma,zauna mana anan zamu dinga kwana tare,Allah yasa abarmana ke,kinga gidannan bayamin dadi nikadaice mace sauran duka maza ne,ba damar nayi laifi zasu taru su zaneni,dariya riyyah ta saki,Babba dake suke dukan ki,hmm tab bakisan yayyena ba basa dariya kamar Babban yaya,dan jim riyyah tai tasan wanda take nufi tundazu takejin kewar sa,ko zata sake ganin sa anan gaba,ko bazata sake ganin saba.
Jajjiga kafadarta Salma tai tunanin mekike, firgit ta dawo daga tunanin da tajeyi,bkm bari naje nai wanka,to riyyah ta amsa tana binta da kallo ashe haka take da saukin kai,kallon datai mata da farko bata zata bata da girman kai ba,ashe class ne kawai da kuma yanayin hutun da take ciki,koya ta motsa kamshinsa takeji a hancin ta,tarasa Meyasa takejin kamshinsa atare da ita,gaban mirror ta karasa tana shin shina turarukan dake wajan ko zataji kamshin aciki amma babu ko kadan,komawa tai ta zauna daidai lokacin Salma ta fito daure da Babban towel,sorry riyyah na barki ke kadai azaune,batace komai ba sai murmusawar da tayi.
Ranar wuni sukai tare,tasaki jikinta sosai,har magariba suna tare,Mama ta ce gobe ko jibi zasuje da Salma atsefe mata kannan awanke mata shi,dama duk karshan wata Salma na zuwa,ai mata wankin kafa,wankin kai,gyaran farce,wankin hakori haka take wannan jigilar bata gajiya,kamshin turare ya riga ya kama jikin su,ko basu shafa komai ba kamshi sukeyi.Ko bata fada ba Mama Ramlah ta gano bata sallah,hakane yasa tatashi da kanta ta hada mata abubuwan da sukeyiwa kansu da 'yayan su in suna period,sanda Mama ta nuna tasan bata sallah kamar ta nutse awajan haka taji,ashe duk Abunda take tana lura da ita,batai musu ba ta karbi abubuwan data hada mata Salma nai mata dariya tayi kankanta da farawa.
Babu ruwansu haka suke rayuwar su da mamanta kamar kawaye,hakan ya burge riyyah sosai,kamar ita da Ummeen ta,babu Abunda Ummee bata koya mata ba,ba kuma tajin kunyar tasanar da ita abunda bata sani ba.Sanda Abee ya dawo yaga riyyah da fara'a ya tare ta,bakuwa mukai ne, Aah Abee ba bakuwa bace,wajan Umami tazo shine ta kawo mana ziyara cewar Salma uwar karadi,to Madallah ya manyan suna lpy,lafiya kalau riyyah ta amsa tana yaba mutuncin familyn dan Barno.
Adaidai sanda su riyyah ke sharar bacci, Baturiya bacci ya gagare ta,sai safa da marwa take da tunanin inda zaagano mata riyyah,tayi alkawarin saitai mata tsinannan duka,tana zaman zaman ta tasakata asara bataji ba bata gani ba,tayi tunani akan batanta ta kasa samun matsaya guda daya wannan abu ya dugunzuma hankalin ta,ga wayar da zulfa take zabga mata Alhajin daza'a dan kamasa riyyah yayi alkawarin daukar nauyin zuwanta kasar,wannan fa shine ga koshi ga kwanan yunwa,abunda ya kara tashin hankalinta kenan jin ko kudin jirgi badaga lalitarta zai fita ba.
Awannan dare baccinta ragagge ne,sassafe ta doka sammako sai station,amma abun haushin babu wani cigaba da aka samu,saima yun kurin kara karbar kudinta suke,dutse ahannun riga aka rabu da Baturiya rai bace ta baro station din, riyyah ta gama cutar ta,ta ha'ince ta,ta rasa da abunda zata saka mata sai guduwa.
Haka ta juya Kd cike da dana sanin kawo riyyah garin maiduguri.lokacin data koma haj Zulfa na gidan tana jiran isowar su, za'ai wa riyyah hoto aturawa da Alhajin danya tabbatar babu cuta ba cutar wa,da murna Zulfa tatare ta tana kallon bayan ta amma bata kome kama da riyyah ba,yana ganki haka ina riyyah din,batace da Zulfa komai ba ta wuce parlon ta zauna,sauke mayafin kafadarta tayi tana sauke numfashi me zafin gaske.Waiya zaki maidani bugaggiya Magana nake miki fa kinmin banza,cikin kuluwa Baturiya ta kalleta,me kike so nagaya miki tunda bazan sakota ajakata na shigo da ita ba.
Bangane me kike san sanar dani ba,kina nufin kin biyoki tai ko masu gidanne suka dauketa aiki,duka babu daya aciki riyyah dai ta bace bat,bangane ta bace ba kamar wata laya,kamar yadda kikaji haka nake nufi,bayani tai mata dalla dalla tafa hanni Zulfa tai tayi,amma wannan yarinyar ta cucemu,ai Baturiya bake ba koni sai na dangwali arziki akan riyyah,wannan abun dama ahiryashi akai taya yarinyar da batasan ko ina ba za'ace ta bata,kodai sace ta akai ko takoma inda aka dakko ta,shiru Baturiya tai tana tunani kumafa zai iya yiwuwa haka,dakko wata tai bari nai kiran haijiyar naji.
Saidata katse ta kara kira kafin Mami ta daga badan bataga kiranba tana gani ta share,mene hadin su kuma bayan ta basu dansu.Sallama Baturiya tai rai abace haka itama Mami ta amsa rai bacan,yadai lafiya jinake munrabu mene kuma na kara kirana, Numfashi Baturiya ta sauke,yaron dana taho Dashi tun a tasha na neme shi na rasa,gidan ku ya dawo ko an hada baki da wani ansacemun yaro,ke!! dakata karki gayamun maganar banza, yaro kisa keyarsa agaba kutafi kicemun ya bata,wannan keta shafa be shafan ba,kije can kinemi danki,daga rana me ka tayau karki kara kirana akan maganar danki,Inba haka ba ranki zaiyi mummunan baci,kit Mami ta kashe waya tanajan tsaki.
Jiki asanyaye Baturiya ta sauke wayar daga kunnan ta,kindai ji da kunnan ki tabbas naji ajikina sace riyyah akai,amma suwanene suka sace ta?ina zasu kaita?bamu da wannan amsar.
Mrs🌹 Baba🌹 Bello ABUBAKAR
......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 41_42
"Amma wannan anyi 'yar iskar yarinya ta jawo mana asara"ni babuma wadda nake tausayawa sama dake Baturiya"wannan zuwa Barno be mana dadi ba."Takaici ya hana Baturiya Magana,takaici goma da goma,ba riyyah babu kudinta,tayi babun ba dinuhu"ga maganar haj Zulfa kara bata mata rai takeyi"tsam ta mike ta barta a parlon tunkan maganganun ta susa zuciyar ta tabuga".Har tayi gaba ta dawo kusa da Zulfa"kuma yanzu Alhajin bazai amshe ni ba,dani sai naje da kaina"dariya Zulfa ta kunshe tana karewa Baturiya kallo,matar da kowa ya kwashi rabon sa,ruwan jikinta duk ya kare take maganar ko zata iya zuwa."
Dan ya mutsa fuska Zulfa tayi, gsky Baturiya ba irinki yake soba"yarinya me jini ajika ake bukata"ammake yanzu ai kin fada tashi daga aiki"adai lallaba anan din tunda customer na zuwa"ba karamun zafin maganar Baturiya taji ba,mudai ci gaba da lallabawa anan zakice Zulfa"ba kiware kanki ba,ai kwaryar sama ke dukan ta kasa"afusace ta wuce Zulfa datake kyalkyala mata dariya,,,,,zama tai tayi dariyarta san ranta"bakaramar dariya Baturiya ta tabata ba,wai ko itace zataje hmmm ta Girgiza kai".
Kwanan riyyah biyu agidan su Salma"ta saba da 'yan gidan sosai,mazan gidan ma basu da wata matsala,saidai basa san raini ko kadan"Abunda yasa suke jibgar Salma kenan son girma ne da it's,,,sakonta Aryan bazatace masa yaya ba"shi kuma Abunda yake jin haushi kenan,,,har so yake fada ya hada su ya mazgeta san ransa"Wai bazaku tashi ku shirya ba,,,yanzu zamu tashi Mama"kallon riyyah tai data sake tamkar gidan su,,,tashi ki shirya riyyah in har bazata jeba aryan ya kaiki,,,,mikewa riyyah tai ta haura dakin su.
Biyo bayanta Salma tai,,ke yanzu riyyah har akwai wanda zai shiga tsakanin mu,,'yar dariya riyyah tasa waye ya shiga tsakanin namu,,wancan dan bkin cikin dazu da Kuka hade kai meyake gaya miki,,,wa kenan?ai kinsan kowa nake nufi nifa banason ma na ambaci sunan shi",,,'yar dariya riyyah ta saka gaskiya nidai Anty Salma ba gane ba,,,hura hanci Salma tai kanta ya kara fashewa,,,tunda riyyah ta fara ce mata Anty farin ciki kamar ya kashe ta,,,tunda kikacemun Anty bari na sanar dake" Aryan nake nufi"dariya ta gimtse dazun data gansu suna kus kus gulmarta sukeyi gashi yanzu ta tambaye ta",,,Anty Salma ba wani abu muka tattauna ba,tambayar sa yanayin university nake yake karamun haske"harara Salma ta watsa mata ni meyasa baki tambaye ni ba"sai abokin fadana,,gaskiya karki sake min irin haka,,,gyadakai riyyah tai tana rike dariyar dake cinta.
Fes suka shirya cikin riga da sket na atamfa,,,dama akwai kayan data dinkawa 'yar yayarta aciki ta debarwa riyyah kala biyar"acikin kayan Salma Wadanda sukai mata kadan duk ta hada mata"zuwanta gidan yanzu akalla tana da kaya kala15 bayan hijab da mayafan da Mama tasa aka siyo mata sabbi fil.Saukowa sukai Mama Ramlah ta bisu da kallo"aryan ne ya fashe da dariya yana kallon Salma,,,bata fuska tai tasan raina mata hankali zaiyi yanzun nan"nuna ta yayi yana kara sakin dariya,,, Mama Ramlah ce ta wurga masa harara mene zaka samun yarinya agaba kana sheka mata dariya"yanzu Mama bakiga yadda Salma ta dumbuza hoda afuska ba"tasa wani jan janbaki kamar akuya ta dumbuli dusa,,,,kallon ta Mama tai ita bataga abunda kwalliyar taiba wulakancin Aryanne kawai.
Kuka Salma tasaka na takaicin abunda Aryan ya fada mata,,,kyaleshi tabiyun auta tunda riyyah tazo take cewa Salma ta biyun Auta"riyyah ce Autar ta,,,yanzu Mama bazaki dauki mataki akan saba"au mataki kikeson dauka bari na tashi,,, cable din dake hannun ta tamike tabi Aryan Dashi,,,da gudu ya fita yana dariya"haba Mama taya zan zauna kijibgeni akan wannan yarinyar,,,gaba dayansu dariya suke ganin yadda Mama da Aryan ke zagaye aparlo"gajiya mama tai ta kyale shi,,kunga kuwuce kuitafiyar ku,,zaizo ya sameni ina zaune,,sallama sukai mata suka fice,,duka da haka Aryan be kyale Salma ba, har bakin motarta ya bita yana tsokanar ta"banza tai dashi taiwa motar key da gudu tai kansa kamar zata take shi,,,tsalle yayi ya koma gefe riyyah nai musu dariya,,,ba kananan 'yan drama aka hada agidan ba,,zuwanta cikin su sun koya mata surutu"dan dole take biye musu aita hayaniyar da ita.
Wani hadaddan salon takai riyyah"dagani wajan na manya ne se kana da 'yan canji"tsefewa riyyah kai akai duk da ya basu wuya wajan tsifa"saboda yadda ya dankare.Tas aka wanke mata shi"gyara sosai akayi musu dukan su,,kan riyyah har wani kyalkyali yake yana sheki"har bayanta ya sauka baki sidik,,,haka salma keda gashi,ga cika ga yawa,sabanin na riyyah baida cika sai tsayi.Basu dawo gida ba sai kusan azabar"sanda suka shigo ba kowa a parlo sai tv dake burarin ta ita kad'ai"daki suka wuce dan yin sallah,,,,suna idarwa suka sauko yunwa ta fara rarakar cikin su.
Lumshe idanun tayi jin kamshin daya kasa barin hancin ta,,,ya kasa barin kwakwalwarta,,,wadda missing dinsa yakasa barin ranta,,,zuciyarta,,,da gangar jikin ta.Kofa ta kallah caraf suka hada idanu dashi"sai data d'an zabura sam batasan zata kara ganin shi arayuwar taba"kauda kanta tai jin kaifafan idanun sa akanta"Salma ce ta dago dan ganin wanene yake shigowar,,,idanun tana ya fada kan Canal Rayyan ma'abocin kwarjini da haiba"fadada fara'ar ta tayi,,,oyoyo Big bro"kadaran kadaham fuskarsa take,,,gaba daya besan yazo inda suke ba,,,yaya baka gani ne zakabi takan riyyah,,,cak ya dakata da tafiyar da yake.
Maida kallonsa yayi kanta,,,kanta na sunkuye tana wasa da yatsun hannun ta,,,,kawar da kansa yayi,,gani yayi ta kara kyau da girma,zuba musu idanu Salma tai tana karantar su"yayammu ka santa ne?hade rai yayi yana hararar Salma,,,zo ki matse bakina na fada miki,,, murmushi ta saki ni na isa yayammu na matsema baki,,,daga kafadarsa yayi ke kika sani.Barin wajan yayi ya samu wake kan sofa ya zauna"gaba daya duk wani motsinta yana kan idanun sa,,kamar me bacci ya Lumshe jigatattun idanun sa,,,.Mama ce ta sakko daga sama,, a'ah wa nake gani kamar mazan fama,,,sakin fuska yayi yana kallon ta,,,zama tai tana kallon Canal,,,sannu Rayyanun Iyyani"d'an murmushi ya saki yana kallon ta,,zamowa yayi yana gaishe da it,,,fuskarta dauke da fara'a take amsawa,,,yasu Innayi da su Umami,duka suna lafiya,,,ashe kana ziyara dama"sosa kansa yadanyi dama wucewa nazo yi shine nace bari na shigo mugaisa,,,ah kako kyauta ALLAH ya saka da Alkhairi.
Aijiya jiya da naje baka nan"Innayi take sanar dani abun alkhairi kasamu matar Aure"tsam yayi da ransa yana auna maganarta"kasamu matar Aure,,,,,Abunda ya tsaya masa a zuciya"ganin yayi shiru itama taja bakinta ta tsuke,,,katashi kaje kuci abinci tare da kannan ka,,,,girgiza kai yayi alamar ya koshi"gaba daya maganganun ta yawo suke mai aka"Lumshe idanun sa yayi yana sakin ajiyar zuciya"tagama cin Abincin amma hakanan ta kasa tashi,,,,wai bazaku tashi haka ba sai cikinku ya fashe,,,, Mama ce ke wannan maganar,"mikewa sukai gamunan Mama,,kusa da ita suka zauna,ina wuni ta furta cikin sanyin muryar ta,sarai ya jita amma ya basar kamar beji me tace ba,, yayammu riyyah na gaishe dakai,,,ko motsawa beba balle tasa ran zai amsa,,,sanin halinsa yasa riyyah bata damu ba,,zaman datai dashi ta gane mugun miskiline.
"Basu kara bi ta kanshiba suka ci gaba da hirar su,,,Mama ce ma mesako sakoshi acikin hirar,hankalinsa nakan riyyah,yadda take komai nata anitse birgeshi takeyi"ajikinta taji yana kallon ta,,amma kin daga ido tai ta kalle shi,,,har suka gama hirar su suka bar wajan yana kwance,,kamar wanda aka daure."Sai magariba yabar gidan,,lokacin basa parlon suba dakinsu ita da Salma.
Bayan sallar isha'i suna zaune da Abbah Mami gyara zaman tatai tare da muskutawa,, kallon ta Abbah yayi Fannah da alama akwai magana abakinki,, murmushi ta sakar masa tare da gyada kai,,kamar kuwa kashiga zuciyata,,dama magana ce akan yayan su,maida dukkan Hankalin sa yayi kanta,,ina jinki,,dama na zabo masa matar Aure ne,,dan jim tayi tana jiran jin amsar Abbah,,matar Aure ya maimaita,,haka yace miki ya rasa matar Aure ne dasai kinnemo masa,,wani yawu Mami tahadiye,,tasan halin Abbah da kafirin taurin kai,,kome za'ai Bazata sauka daga kan zabinta ba.
Ai Abbah ba Lallai saiyace na nemo masa ba,,amatsayina na Mahaifiyar sa ina da right din da zan zabo masa Abinda naga ya dace dashi"gyada kai Abbah yayi tabbas kece me cikakken right kuwa,,,cikin jindadin maganar sa ta washe baki,,ai abunma na gida ne,,ina kawata Hajiya Hadaza Ambassador,,to 'yar wajan tace Sahar Yarinya me tarbiyya da kamun kai,,ga kunya shine abunda yaja hankalina nayi sha'awar hada zuri'a da ita."Tundata gata magana Abbah ke mata wani irin duba na lallai Fannah baki da hankali.
"Ni kuma amatsayina na Ubansa in zabinki bemin bafa,,,bata Fuska tai tana hura hanci,zaima yima,,menene aibun zabin danai masa,,wai anya Fannah kinsan wadda kike kokarin makalawa danki,,bana son Abinda zaisa daga baya kizo kina dana sanin,,,kinji wallhi rantsuwar dan musulmi duk abunda ya biyo baya babu ruwana acikin sa,,,iya kuluwa Mami ta kulu,,babu ma abunda zai biyo baya sai Alkhairi,,Allah yasa,,zan kara baki dama ta karshe kije kisake bincika wacece wadda kike ikirarin kawar kice.
Mikewa yayi yabar mata wajan,,ransa amugun bace harshi zata kalla tacewai tayiwa danta mata,, shikenan zai barta da zabinta,,tunda hartai maganar right tabbas zai barta da right dinta.Binsa da kallo tai tana tabe baki,,,ai bayau nasani hadizan ba,ba kuma jiya ba,,matar arziki ga kyauta abun hannun ta be rufe mata ido ba,,haka kawai bazan yadda ya dakko wadda zata mallake shi ba,,ni kuma ko oho Bazata sabuba,,,ita kadai take mita tana sambatu kamar zautacciya.
Wai waye Adon tafiya......
Alhaji Rayyan shine asalin sunan mahaifinsu,sai Mahaifiyar su Hajiya Fatima(Innayi).Rigimammiya ce tunkan takai haka tsufa,,,Allah ya azurtasu da haihuwar 'ya'ya guda biyar,,Biyu maza uku mata.Attahir shine Babba,sai Alhaji Muttaka mahaifin Salma,Hajiya Falmata tana Aure anan Meduguri,Hajiya Raihana tana Aure a sudan,sai Auta Hafsa 'ya'yanta biyar yanzu haka tana zaman gida.
Allah yayiwa Alhaji Rayyan tarin dukiya(Lakabin sa Dan Barno).Sun taso cikin so da kaunar iyayan su,Attahir sanda ya gama karatu ya fada kasuwanci,ana haka ya Hadu da Yagana(Umami) yarinya ce mehankali,ganin farko Innayi taji Yagana ta kwanta mata,anyi biki amarya tatare adakinta,tun sanda ya hadu da ita dama tana karatun ta,bayan sunyi Aure be hana taba taci gaba da karatu.Sunyi kusan shekaru shida ba haihuwa,,,hakan ya tashi hankalin Yagana ta dinga Kuka ya kara Aure bataso afarayi mata gorin haihuwa,,,daidai da rana daya Innayi bata nunawa ko afuska ta damu darashin haihuwar taba.
Ana haka Allah ya hadashi da Fannah,,tun sanda ya Kawo Fannah matsayin wadda zai Aura taji batai mata ba sam,,,dalilin banzan kallon da taga tana bin Yagana dashi,,,ga tarbiyyar Fannah bata gama yimata ba,,,hakan yasa Innayi ta tubure batasan Auran,,,sosai Alhaji Rayyan ya dinga rarrashin ta hatta sakko,,,,koda akai Auran bata shiga sabar Fannah ko kadan batason taga taje part dinta,,,hatta Auran su Falmata daya tashi Yagana ta dora akan komai,,,abunda ya kara fusata Fannah kenan tasa aranta Innayi bata kaunar ta.
Bata shafe wata Biyu ba saiga Fannah da ciki,,,babu bakin ciki haka Yagana tatayata Murna,sai hura hanci take itace me haihuwa,,,babu wanda ya kalleta cikin Yagana da Innayi kamar madai Innayi batai farin ciki da wannan ciki ba,,,,watan cikin ta biyar Allah ya azurta Yagana da samun ciki itama,,,zo kaga Murna wajan Innayi kamar zata taka rawa dan farin ciki,har sadaka tatara yara ta babba su,,,sam Fannah bataji dadin cikin da yagana ta samu ba,,,ba haka taso ba,taso ace har abusa kaho kar Yagana ta haihu saidai ita kadai taita haihuwa.
Wata tara Fannah ta santalo santalelen danta Namiji,,,,aiko ba karamin dadi taji ba ganin ta haifo magajin gida,,,tunda Yagana ta dora idanu akansa taji tana matukar kaunar sa,,,ranar suna Alhaji Rayyan ya maida sunan sa Rayyan,,,abun sam bewa Fannah ba sunan babanta taso Sawa amma ankama ansa mata sunan Uban Miji,,,aiko Innayi sàida tayiwa Fannah wankin Babban bargo, labari ya isa kunnanta,,,,sàida Mami tai danasanin nuna bata son sunan,,,,daga wannan kinda Innayi kewa Fannah sai ya kara habaka,,,.
Watan Rayyan hudu Yagana ta haifo santaleliyar 'yarta me kama da Innayi sak,,,kanjiki kan karfi Innayi tadinga hidima ranar suna yarinya taci sunan ta Fatima,,,suna kiranta Batool,,,tare suka taso da Rayyan wanda suke kira da karamin megida,,,yadda kasan 'yan biyu haka suka tashi sun shaku matuka,damma Mami bata barin Rayyan yadade tare dasu,zatazo ta dauke danta.
Bayan Rayyan ta haifi Beenazir Ammar,,,Huzaifa,Humaida,,Yagana ta haifi,,,Kamal,,Fareeha,,Asad,,Muhsin,,Ridwan.
Haka rayuwar su taci gaba da garawa,,gaba dayansu abisa karkashin kulawar Umami suka tashi,,duk da tana fita hospital hakan besa ta kasa kulawa da suba,,,sabanin Mami ta haife sune kawai amma batasan yadda zata kula da suba,,,sai in magana tatashi tadinga gadara 'yayanta ne,,,.Tunda suka taso suke kiran Rayyan Babban yaya ko sune Yayammu,,,Botool suna kiranta da Anty Babba,,,tunda ya taso yake sha'awar zama soja,,tun suna wasan yara a matsayin soja yake fitowa,,,ganin yana da interes akai yana gama primary Abbah ya kaishi makarantar sojoji dake nan Meduguri.
Botool kuma low take san karanta kowanne aka bashi damar zabar Abunda yake so.Suna js 3 kakansu ya rasu Alhaji Rayyan da kyar aka rike Innayi sanda za'a futa dashi har suma ta dingayi ana yayyafa mata ruwa........
Allah sarki Innayi.
Mrs 🌹 Baba 🌹
Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 43_44
Sosai ahalin suka shiga tashin hankali ganin itama suna niyyar rasata"musamman 'yayan ta,,hankali tashe akai asibiti da Innayi,,da kyar Allah ya taimaka tafarajin sauki,,amma kullum cikin kuka take,,ba karamin son mijinta takeyi ba"sunyi zama na amana da mutunta juna"tana san kayanta yana son ta,,ahaka ta dangana ta barwa Allah lamarin sa"bayan Lokacin saita kona shiru shiru,,kamar ba wannan Innayin ba wadda bata gani ta kyale,,jajircewar Umami yasa ta fara dawowa kamar da,,,bangaran Fannah dadi taji da Innayi ta daina yawan surutun,,,yanzu hankalinta kwance yake babu meyi mata ciwon baki"sàida Innayi ta shafe shekara kafinta dawo normal.
Ahaka suka ci gaba da rayuwar su cikin jin dadi da kwanciyar hankali,,tun a primary Rayyan yake tare da Sadik har girmansu suna tare,,shakuwa ce sosai atsakanin su,,babu me iyawa da halin Rayyan sai shi,,tsakanin sa da Mami bada umarnine,,babu ruwanta dame yaranta suke so,,suna da damuwa ko basu da ita"ko menene Umami ke share musu dukkan hawayan su,,sai sukafi sabawa da ita,,,wannan abu yana konawa Mami rai ganin yadda komai Yagana ta kankame,,ga mijin ma ahannun ta yake,,muddin Umami zata fadi Magana baya tsallakewa,,,amma duk abunda zata kawo saiya hango kuskure acikin maganar ta"hakan yasa ta kara daukar zafi da Umami,,ta tabbatar tashanye mijin da 'ya'yanta.
Kuma har wannan lokacin akan wannan tunanin Mami take,tsakaninta da kishiya ba ragayya ba sanayya,, abokiyar gaba ce awajanta.
Cigaban Labari...
Bari mu leka Kd
Mama Sauda ce zaune a parlo,sai Abba Yahaya dake gefanta,news suke kallo,,kamar saga sama yaji ana neman marayun da suka rasa iyayan su,,gwantin garin zata dauki nauyin komai nasu,,,tare da taimakawa marukansu da makudan kudade,,tsai Abba Yahaya yayi da randa,,riyyah ce ta fado zuciyar sa,,tabbas lokacin amfaninta yayi,,ashe yarinyar nan Alkhairi zata zame mai,,daya sani be barwa Gali ita bag"amma yanzumma ko da tsiya saiya kwato ta"mikewa yayi kamar ammasa allura,,key din motarsa ya laluba,, Mama Sauda na tambayar sa ina zaije,amma ko kallonta beba,,babban burinsa ya dira agidan Gali...
A guje ya figi motar,,wani mahaukacin hon yake dannawa kamar wanda aka biyo shi abaya"da sauri Get man din ya wangale masa kofa,,yana gama daidaita parking ya fito yana saba babbar riga"kai tsaye maine parlo ya nufa yana zabga sallama,,babu kowa a parlon fadawa yayi yana kara rangada sallama,,Gali ne ya fito yana amsawa da fadin wai wanene yake damun mutane da ihu,,hada idanu sukai da Abba Yahaya dake tsaye a parlon babban burinsa yayi ido hudu da riyyah.
Wai dama kaine kake ta wannan sallamar kamar wanda kake bina bashi",tsaki Abba yaja kaga ba wannan maganar ce ta kawo ni ba,,ina yarinyar nan take?"wace yarinya kake nufin?"harara Abba Yahaya ya watsa masa,,akwai wadda zanzo nemane banda Ansariyya"kallonsa Gali yayi fuskarsa dauke da Mamaki,,anya Yahaya kasan wadda kake nema kuwa"kamanta abinda kace har abada bazaka taba nemanta,,dan babu abunda zata tsinana maka,,meyasa tunkafin aje ko ina ka sauke makaman yakinka,,tsaki Abba yaja kai banason maganar banza zaka kiramin ita,,ko dogon surutu zaka tsaya yimin"dariya Gali ya saka wadda ta kara fusata Abba.
"Ganin baida niyyar kiran riyyah ya fara kwallah mata kira,,ke Ansariyya kina ina ne"shiru babu amsa"ba magana nakeba kina ina innashigo zanci ubanki"Anty zee ce ta sakko daga sama,,ganin su curko curko yasata ja ta tsaya,,,lafiya kuwa naganku a tsaitsaye,,yawwa Zainab shiga kifitomin da Ansariyya nazo tafiya da ita,,wace riyyah din ai bata gidannan,,asukwane ya dago yana kallonta,,bangane inda kika dosa ba"Allah ya rabamu da alakakai ai Baturiya tazo tatafi da ita,,hankali tashe yace Baturiya,,ubanwa yasa da tazo kibata ita batare dakin kirani ba"wata dariya tasaka,to nakiraka matsayinka nawa,,Sanda akazo da ita gidannan daga gidanka ka korota fa,,kuma dannice me kwakwalwar kifi sauna kiraka dannasamu me daukarta"tana hannun uwarta Baturiya saikaje can kuyi wadda zakui,,rai bace ya juya tare da nufar gidan Baturiya.
"Tana parlo abun Duniya ya isheta,kamar ancilloshi haka ya fado mata parlon,,,kamar zararre ya tsaya akanta ke Baturiya tana ina,,,dama neman wanda zata huce haushinta take yi,,,mikewa tai cike da masifa,,,haba yaya saikace gidan arna zaka fadomin gida babu neman izini babu sallama,,,ke dalla yimin shiru,,awane gidan zanyi sallama,,,ko ance miki bansan garadan da kike kawowa gidan ba,,,saini danna shigo kikemin ihu,,,dankwalinta ta turo gaban goshi,,eh lallai Yahaya ni zakayi wa sharri,,,nayi miki zan tattakaki Baturiya,,,ba wannan maganar ce ta kawo niba,,,rayuwar kice keje kiyi abunda kikaga dama,,,banda matsala da hakan.
Ansariyya nake tambayar ki tana ina?"hura hanci tai tana karkada jiki kamar 'yar dambe,,nima bansan inda take ba ta bata,,kwalalo idanun sa yayi,,wata ashariya ya dura mata,,shikansa besan inda ya koyo taba,,,ni zaki rainawa hankali,,marainiyar zaki dauka kikaita wani waje,,,wai komadai yawon karuwancin da kike kika dorata ita ma?dakata gaskiya karka kara kirana da karuwa,,tsaf zan runtse idanuna naima rashin mutunci,,,ni kike fadawa wannan maganar koki fito da riyyah konaci Ubanki acikin gidannan.
Kamar yadda na gayama tabata a meduguri,me kikace Ubanki ne a medugurin da kika kaita,, Baturiya kinsanni banasan rainin hankali,,,zanyi biji biji dake,,,yarinya tana zaune kalau agidan Gali saboda munafuka ce ke kije ki dakko ta,,,yanzu duk gidan Uban da kika kaita ki kawo min ita,,babu fa Indai zanje neman ta,,,sama ko kasa anrasata kamar aljana ta bace bat,,, bansan ranar da za'a ganta ba,,,wata kilama 'yan mafiya ma sun kamata,,,kanta rufe baki taji saukar zazzafan mari a fuskarta,,dan baki da mutunci ni zaki jawowa asara,,ni zakiyiwa bakin ciki,,,dafe kunci tai ni kamara,,ko zaki rama,,, babbar rigarsa ya tube,,yau in ban faffasa miki ba Baturiya niba dan halak bane.
Kanta ce wani abu ya rufeta da azababban duka tako ina,,kuka take tana kururuwa ko sauraranta beba,,sàida yayi mata lilis kafin ya haure ta da kafa,,,nuna ta yayi da dan yatsa nabaki nanda awa 24 ki kawon riyyah har gabana,,,inba haka ba kinsan sauran,,,daukar babbar rigarsa yayi ya fice kamar zuciyar sa zata babbake,,,yana jawa Baturiya Allah ya isa ta cuceshi ta ha'ince shi.Dakyar Baturiya ta mike in banda zugi babu abunda jikinta yakeyi,,,rabon da adaketa tun tana karamar yarinya,,sai gashi yau wani katon gardi ya zage ya narketa,ya zama dole ta rama akan riyyah,,,tunda Yahaya yafi karfinta,,duk randa sukai ido hudu da riyyah sainaci Ubanta.Da kyar taja jiki ta fada daki cike da bakin ciki da takaici.
🤣🤣🤣🤣Allah ya kara Baturiya.
Maiduguri
Yana durkushe a gabanta saidata gama shan kamshi dan kanta ta magantu,,,nakira kane badan na baka shawara ba,umarnine kai tsaye daga ni Mahaifiyar ka,,shiru tayi kafin ta dora,,nice nai nakudarka na haife ka,,tsahon wata tara kana mun bige bige da naushe naushe aciki,,,duk da haka ban gajiya ba nai nakudarka na haifoka,,,kashi da fitsari duk na shanye,,dan haka ina da ikon da zan zaba maka abunda nake so,,,dan haka na zaba maka matar Aure kaje ku daidaita kanku,,,itama yarinyar bata da matsala,,,yarinyace me tarbiyya da kamun kai,,,na tabbatar zakaji dadin zama da ita....
Tunda Mami ta fara magana,,gumin tashin hankali ke keto masa,,zuciyarsa har tururi take jin lafuzan dake futa daga bakin Mahaifiyar sa,,,meyasa Mami batasan Farin cikin sa,,,meyasa bazata bashi damar ya kawo wadda yake soba,,,meyasa tafiya fifita farin cikinta akan na 'yayanta,,idanun sa yayi jajawur,,gaba daya jijiyar kansa tatashi,,abunka da farar fata Fuskar tai ja ta yamutse,,,bece komai ba ya mike ko ganin gabansa ba yayi,,,binsa tayi da kallo kamar tai kiransa sai ta fasa,,tabbas yanayinsa ya taba Zuciyarta,,saidai hakan bazaisa tabkarya kudurin taba.
Part din Umami ya wuce yasan acanne kawai zaiji sanyi a zuciyarsa,,,tana zaune dawowarta kenan daga aiki taga shigowar sa,,,zuba masa idanu tai tana karantar sa,,tunkan ya karaso ta isa gareshi,,,gaba daya hannayansa ta ruko,,ganin yadda jikinsa ke rawa ta tabbatar ransa ajagule yake,,kuma yana daf da sume mata matukar batai wani abu akai ba,,,haka yake matukar ransa zai koluluwar tashi to suma yake sai ansha fama kan numfashin sa ya dawo gangar jikin sa.
Kan sofa ta karasa dashi,,,da sassarfa ta isa fridge ruwa me sanyi ta bude ko cup bata dauka ba takafa masa abki,,,sàida ya shanye tas ya fada jikinta, rungume shi tai cikin tsananin kaunarsa da tausayin sa,,,tarasa Mami wace irin macece da take son halaka danta da hannun ta,,,duk sanda wata damuwa zata kaishi gadon asibiti itace sila,,,wace irin uwace wannan me matukar san zuciyar ta,,,ahankali take shafa kansa,,ajiyar zuciyar yake daukewa idanun sa alumshe,,kallon sa take tana ayyana abubuwa da dama,,, matukar Mami bata sonsa tofa ita tana sansa,,,kuma ashirye take ta nemo masa farin ciki ko a inane matukar befi karfin su ba.
Haba gwarzan Umami,,,Yayan Botool,yayan Fareeha,Aminin sadik shalelen Umami me dakawa maza gumba afilin daga,,dama akwai abunda zai dinga tashin gwarzona,,dana abun tunkaho na ako yaushe,,,kaine fa babban su sa maza gudu balle mata,,,haba jikan Iyyani jaruma agidan Mijin ta,,gwarzuwar kakarka.me tsayawa adukkan lamuranka,,duk muna zagaye dakai mezai dameka harya dagama hankali,,,haba Rayyan jikan Rayyan,Bansan gwarzona da saurin fushi ba,,ranka yayi fari dan Umami ni koda yaushe ina tare dakai,,dan fatan Abban sa,,dan gatan Abee da Mamah Ramlah,amini awajan Salma,duk fa muna tare dakai Canal dina.
Tunda ta fara magana yake jinta, ahankali fushinsa ke sauka,,kaunarta girmanta nakara samun fada azuciyarsa,,ina inama tajikinta ya tsago ya fito,,mace me karamci,mace me mutunci da sanin ya kamata.Jin yayi shiru tai Murmushi tana kallon sa,haba Canal kana bani tsoro kaida zaka zauna da mace kana saurin fushi wataran zaka iya illa tata,,mikewa yayi ya zuwaba Umami ido,,kallon tuhuma yake binta dashi.Hardake Umami kallon rashin fahimta take masa hardani me,,Auran da Mami ta sanar dani ta zaban matar da zan Aura,,,shiru tai tana girgiza masa kai,,,bandani yayansu,amma kasani Mahaifiyar kace dole kayi mata biyayya,,kayi abunda take so,,rashin amincwarka zai jawo ma matsala babba,kayi hakuri kai mata biyayya bazaka taba tabewa ba.
Shiru yayi yana sauraronta,,saidata tabbatar Abinda take fada masa yashiga cikin kunnan sa,,tukunna ta kyaleshi.Tsahon kwana biyu Mami na kasa kunnan zaije amma shiru ko afuska be kara nuna mata yana sane da maganar taba,,,,yau Mami ta same shi har part din sa,,bakaramin bacin rai ta nuna akan watsi da maganar sa da yayi ba,,hakuri kawai ya bata da fada mata uzuri ya hana shi zuwa,,,gargadi me zafi ta kara yi masa kan karya wuce gobe bataji kyakykyawan Labari na zuwan saba,,,sun kuyar da kansa kawai yayi yana hana kansa bacinrai da fusata.
Koda wasa Abbu be kara tayawar da Mami maganar datai masa ba,,,haka be nunawa Canal ya san da hakan ba,,,ya zuba mata idanu ya batta tayi yadda take so matsayinta na wadda tai nakudar sa,,,bakin cikine ya hadu yayiwa Canal yawa daga karshe ya tattara kayan sa ya koma barrack ko zuciyarsa zata sanyaya,,,hatta Sadik ya gane yana cikin bacin rai be tambaye shi Komai ba yana da tabbacin bazai sanar dashi damuwar saba,,,gaba daya tattara maganar Sahar din yayi yasaka agefe ganin kan wata banza can zai hana kansa sukuni,,,lamarin ya kara harzuka Mami ta tabbatar da bata da iko dashi be kuma dauke ta abakin komai ba.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 45_46
TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!
Aneesat DATA SERVICE
Kuzo kusai Data me lasting me sauki da rahusa.Cikin Aminci zaki samu Datar ki.Karki bari wannan gara basar ta wuce ki
Data A vailable all networks
MTN AIRTEL
500MB_150. 500MB_150
1GB_300. 1GB_300
2GB_500. 2GB_500
3GB_750. 3GB_750
5GB_1,400. 5GB_1,400
10GB_2500. 10GB_2500.
GLO. 9MOBLE
500MB_200. 500MB_150
1GB_350. 1GB_250
2GB_600. 2GB_450
3GB_800. 3GB_650
5GB_1500. 4GB_850
10GB_2800. 5GB_1200
Duk abunda ke faruwa Innayi tana da masaniya,,,amma taja bakinta tai shiru,,kamar yadda uwarsa ta nuna su bakomai bane sai taja gefe sun zama 'yan kallo,,bangaran riyyah tunanin Canal yayi mata da baibayi,,ko yaya ta rufe idanu shi take gani,,,duk da batasan meyasa ta damu dashi ba haka kawai takejin tausayin sa,,,ganin da gaske zai watsa mata kasa a idanu ta kirashi a yammacin cikar satinsa daya da barin gidan.
Yana dauka ta lailayo masa wata ashariya,,saidaya runtse idanun sa jin zagin data antayo masa,,,nagode Rayyan daka maidani ba abakin komai ba,,,to zan kara jaddada maka matukar gobe bakaje gidan Ambassador ba sai ranka yayi mummunar baci,,zangani kuma na isa dakai ko ban isa dakai ba,,,kit ta kashe wayar,bin wayar yayi da kallo yana runtse idanun sa,,,zuciyarsa kamar zata fashe tsabar yadda take bugawa,,,adaran ranar beyi bacci ba,,yayi alkawarin koma wacece wannan da Mami ke san dagula masa lissafi akanta saita gwammace bata sanshi ba"sai yayi mata wulakancin da bata taba zata ba,,,saiya sanar da ita bata da wani gurbi azuciyar sa,,da wannan alwashin Canal ya kwana.
Adaran ranar Mami ta kira haj Hadiza akan gobe Canal zaizo suga juna shida Sahar"sosai ta nuna farin cikin ta cikin jindadi Mami ta yanke wayar ta,,,kallon Abban Sahar tai da yake kallon ta,,kanajin abunda aka sanar dani yanzu,,ina ko zan sani tunda ba a handsfree kika saka wayar ba,,,to Albishirinka,goro fari kal,yar darya Mom tai,ka kusa yin siriki,,kallon ta yake da neman karin bayani,,kwarai kuwa gobe wanda yake san Sahar zaizo su daidai ta,,,dan gidan Alhaji Attahiru Dan Barno shi kesan Sahar din,,, murmushi Abbah ya saki kai ma sha Allah,,naji dadin kwarai da gaske,babu wanda bazai so hada zuri'a da wannan gidan ba.
Dariyar farin ciki Mom ta saki,,nima abin ba karamin dadi yayi min ba,ganin Sahar zata shiga hannun mutanan kirki,,Allah yayi mana jagora cewar Alhaji Abbas Mahaifi ga Sahar,,bari ma kaga na mike ba'abori da sanyin jiki,,mikewa tai ta nufi dakin Sahar.Tana zaune tana zukar shisha,idanun ta sunyi jajawur,dago idanu tai tana kallon Mom data fado mata daki,,,dan bata fuska tai,wai Mom saunawa zan fada miki kedaina fadomin daki babu neman izini,,dan zan shigo dakinki sai na nemi izini,,bazaki gane ba Mom kowa yana bukatar sirri a harkokinsa,,so please kidaina ahigarmun rayuwa.
Shiru Mom tai tana kallon Sahar,is ok nima haka kawai ai bana zuwa dakinki sàida dalili,,,fadi dalilin ki cewar Sahar datake bade Mom da hayakin bakin ta,,yanzu mukai waya da Fannah gobe Rayyan zaizo kuga juna,, murmushi Sahar bra dan saki,,badamuwa Mom dukkan shiri yana hannun ki,kayan da zansaka a tabbatar an zabarmin kalar data dace dani,ba yanzu zan nuna masa ainihin kalata ba,so nake saina shiga gidan sa, alokacin ne zan nuna masa nidin ba karamar tantiriya bace kamar yadda ya kirani.
Gyada kai Mom tai kamar kadangaruwa,tabbas banga laifinki ba Sahar dole a hukun tashi fiye da laifin daya aikata miki,,,daga wa Mom hannu tai alamar zata iya tafiya,tamkar itace Uwar haka tabi umarnin Sahar ta fice daga dakin,,hmmm Allah ya kyauta.
Tunda ya tashi ya kasa tsinanawa kansa komai,,Sadik daya zuba masa idanu yana kallon sa takaicin sa na kara kamashi,,wai dude daka kirani gadinka zanyi kome,,,nifa bana san wannan halin nka in baka data cewa zanyi gaba,, lumshe idanun sa yayi yana kallon Sadik da yaketa hura hanci yana girgiza kafa,,murmushin gefen baki kawai ya saki da kyar ya bude bakin sa,,zamuje unguwa anjima,,daga haka yaja bakinsa ya tsuke,,ina zamuje kuma wace unguwa,,daga kafadar sa yayi alamun shima be sani ba,,sanin kansane tunda yayi masa haka bazai taba fada mai Inda zasu jeba shiyasa yayi shiru be kara tanka masa ba.
Karfe 4 a kofar gidan su Sahar tai musu dake old GRA wangale musu get akai suka kutsa hancin motarsu cikin gidan,,Sadik ne ke drive din yana gefansa kamar an aiko masa da sakon mutuwa,,kamar bazai fitoba da kyar dai ya fito,,,da kakkiyar shadda ce ajikin sa dark blue,,,dan kallon sa Sadik yayi yana kunshe Dariyar sa ganin yadda yake ta huci kamar kububuwa,,jingina yayi da motarsa yana fesar da numfashin bacin rai da takaici"wata dattijuwa Mom tasa tashiga dasu dakin baki,babu musu suka bi bayan ta,har dakin baki ta kaisu,,dan kallon su tai da murmushi akan fuskarta kuzauna kafin Sahar din ta zo,babu musu suka zauna,,badan ganin girman matar ba,babu Abinda zai sa Canal ya zauna.
Tsaf Mom ta gama shirya Sahar cikin atamfa riga da sket,,sun bala'in matseta kamar zasu yage ajikinta"Mayafi midium ta dauka ta yafa akafada,,aganin ta wannàn shine karshan shigar mutunci wanda zata iyayi,,ta boye ainihin kalarta,,farar fatar ta tasha zanen lalle baki da ja,,wanda a dazu Mom ta dakko meyi mata,,aiko ya zanu kamar an manna mata shi,,,turare kusan kala 10 ta hada ta faffesa saboda tsabar kamshi har hawar wa mutum kai yake,,tsahon mintuna 15 babu Sahar ba Labarin ta,,sai kayan kwalam da makulashe bacin rai ya hana Canal magana.Arayuwar sa ya tsani jira,sam bayason ya zauna yana jiranka ka shan yashi kamar wata shara.
Kallon agogon hannun sa yayi,ganin irin time din daya bata akan wata banza kucaka,,ko 'yar shugaban kasa ce sai haka,,badan yana tuna gargadin Mami ba babu Abunda zai hana be tashi yayi tafiyar sa ba.Kamshin da sukaji ya doso inda suke ya tabbatar musu akwai wanda ke yunkurin shigowa parlon.Da sallama abakin ta tashigo tana taku kamar bazata taka kasa ba,ko kallo bata ishi Yayammu ba Sadik ne ya amsa mata sallamar yana kallon ta,,lallai kyakykyawa ce dole taja aji wannan shanyar datai musu ba abanza ba,,gogan kuwa kara turbine fuska yayi kamar hadari.
Zama tai akan sofar da take fuskantar su,barkanku da zuwa,tafurta cikin yanga kissa da kisisina,,barka Sadik ya amsa da fara'ar sa,,amma kuma munsha shanya harmun bushe, murmushi tadan saki afuwan ban kammala shirya wabane,,bakomai dama sarauniya ai sàida jan aji,,jitai kanta ya dada girma,takaici ne ya kama yayammu kamar ya tashi yasheke wuyan Sadik,,duk surutun da suke yana jinsu kamar me bacci ya Lumshe idanun sa,,satar kallon sa tai,,tabbas shine irin mijin data dade tana fatan ta samu,,sai gashi komai yazo mata cikin sauki,,gashi kyakykyawa uwa Uba kudi da ilimi,,babu inda bazata shiga dashi ba daga kasar Nigeria har kasashen ketare.
Mikewa Sadik yayi bari zan amsa kira,,yayi hakanne dan ya basu damar ganawa da junan su,,ficewa yayi daga parlon baki daya."Shiru ne ya ratsa parlon batace masa ba shima bece mata ba,,ranta soma baci yayi ganin yazo su daidaita amma yayi mata banza,,shanyewa tai tsam tamike daga wajan zamanta,cup ta dauka ta tsiyaya masa jus me sanyin gaske,,cikin karairaya ta karasa Inda yake,ahannun Kujerar da yake zaune ta zauna,,kamshin daya ji ya kara cika masa hanci ya sashi bude idanun sa da har Lokacin bacinrai be fita daga cikin su ba.
Idanun sane ya fada kanna Sahar mummunar fuskar da baya fatan ko amafarki ya kara ganin ta,,afusace ya mike yanai mata kallon tsantsar tsana,,makoshinsa har wani daci yaji yana yi,,nuna ta yake da dan yatsa amma ya gaza furta komai,,zuba masa shanyayyun idanun ta tai,,wadanda daganin su kasan ba daidai takeba akwai Abunda tasha,,,kece Sahar din da nazo gunki,daga masa gira tai alamar eh,,mikewa tai ta nufo bakinsa da nufin ta bashi jus din hannun ta,wani shegen mari ya kashe fuskarta dashi saboda tsananin azaba batasan sanda ta zuba kara ba,,jida ganinta daukewa yayi na wucin gadi,,cup din hannun ta ya warta ya watsa mata afuska.
Cikin huci ya nuna ta da dan yatsa,,to ina so ki tabbatar da cewar ni Rayyan bazan taba Auran 'yar tasha irin kiba,'yan iskan da kika gama rabarwa jikinki atiti su yakama ta kije can ki Aura bani Rayyan ba!!! Cikin karaji yagama fadar hakan,,ni ba mazana ci bane dan haka bazan Auri mazinaciya ba,,ina so ki farka daga baccin da kikeyi bazaki taba samuna ba,nai miki nisa sàidai ki hangoni daga nesa, stupid kawai,,bangaje ta yayi yafice daga parlon a fusace.
"Kamar gunki haka ta kame atsaye hawayan bakin ciki da bacin rai na zuba akan fuskarta datai ja saboda marin data sha awajan yayammu,, durkushewa tai akan guiwowinta,,yau ita wani namiji ya mara,,yau ita wani ya ciwa mutunci ita da maza keyi mata layi,,Maza da suke binta tana gudun su,marifa kamar ita asamu wani ya daga hannun sa ya watsa mata mari a kan Fuskar da take tattalinta da tunkaho da ita,,mezatai masa itako ta huce dame zata rama,,,kara fashewa tai da Kukan tashin hankali,,ya bata mata tarihin rayuwar ta na namiji bai taba daga mata ya tsaba,,sai gashi yau ansamu me marinta,,wayyo ni Sahar na shiga uku!!! Kara barkewatai da sabon Kuka.
"Ko ganin gabansa ba yayi tsabar yadda zuciyarsa ke tururi,,harwani hawayene ya taru a cikin kwayar idanun sa,,idanun sunyi jajawur fuskar ta hadu tayi ja,, hankali tashe Sadik yake mai magan amma ko kallan sa beba,,da kafarsa ya fice daga gidan,,,tsana me sunan tsana ya tsani Sahar,,,tun sanda ya hadu da ita ya tabbatar bata da cikakkiyar tarbiyya,,shine yanzu mahifiyarsa take kiran wannan ame tarbiyya da kunyar,,,anya batai mata gurguwar fahimtaba?"da kyar Sadik ya samu yahau motar gaba daya kansa ya daure meya batawa Canal rai haka,,tajima bega yayi Irin wannnan fushin ba,,yana shiga motar ya runtse idanun sa ganin abun yake tamkar amafarki,,bayajin zai yadda da hukuncin Mami taya zai Auri wadda tagama tanbadewa awaje,,ya aureta yace ya Auri wa...
Ihun tane ya fito da Mom daga daki,,a sukwane take sakkowa daga sama,,hango pretty baje a parlo har lokacin hannunta yana kan kuncin ta,,tsabar yadda marin ya shigeta hatta barin idanun ta yayi taruwar jini,,,ke me zangani haka meya sameki pretty ki sanar dani,,, Mom dama akwai wani Namiji dazai iya kallona ya gayamin maganganu masu daci da muni,,,ni zai wulakanta karshe ya tsinkamin mari ya zubamun jus ajiki,,mari fa kika ce daga kai tayi alamar tabbatar wa,,,kan Uba yazo har cikin gidan Ubanki ya mareki,,bari nakira Fannah naji idan itace ta turo shi yayi wannan rashin mutuncin..
Wayarta tafigo rai bace ta dannan wayar Mami,,,ring biyu ta sauka,,sallama take kokarin yi Mom ta dakatar da ita,,,rike sallmarki Fannah,,,dama ashe danki mahaukaci ne bamu sani ba,,,Gwara da Allah ya nuna mana tunkan mu bashi yarinyar mu yaje ya illatata,,,shiru Mami tai tana sauraron yadda Mom ke zazzaga masifa kamar zata hadiye harshan ta"wai Hadiza duk akamme kike wannan fadan kin kasa tsayawa kiyimin bayani,,dama taya zan iya tsayawa nai miki bayani,,,kin turo danki ya zage akan karamar yarinya batasan hawa ba batasan sauka ba ya zage iya karfin sa yadinga dukanta kamar Allah ya aiko shi..
Gatanan akwance duk ya faffasa mata jiki,,magana guda daya Fannah wannan Aure bazai yiwu ba,,yadda yake mahaukaci bazan bashi 'yata ba,,,kit ta kashe wayar tabar Mami da waya ahannu,,,mikewa Mami tai tana zagaye parloun ta,,dama abinda yaje ya aikata kenan,,,ya wulakanta ta ya kunya tata,waime ya dauki kansa haka,,me kuma yake damun kwakwalwar sa,,,wayarsa ta kira amma kira uku ba amsa,,abunda ya kara fusatata kenan yadda ya bata mata rai shima ransa saiya baci fiye da nata,,, number Sadik ta kira dayayi parking a hanya ya zubawa Canal idanu yadda yake fidda zazzafan huci...
Tausayinsa na taba Zuciyar sa,, ring din dayaji wayarsa nayi ya zarota,, number Mami daya gani yasashi daukar wayar,, Sadik ina abokin ka,, kallon barin da Canal yake yayi,,,bayajin dadi Mami yanzu haka yana kwance magashiyan Zazzabi ya rifeshi,,,shiru tai tana sauraron sa,,karka rainamin hankali Sadik kabani shi in yana kusa dakai,,baya kusa Mami kamar yadda nagaya miki na kaishi Gida baya cikin hayyacin sa,,,duk wata masifa da tayi niyyar sauke masa saitaji tana raguwa ahankali,,ka tabbatar gskiya kake fadamin,,gaskiya nake fada miki Mami,,,ok in ya tashi kasanar dani ina memansa,,in sha Allah.
Duk abunda suke Canal yana jinsu yana sauraran su,,,Sadik bece Komai ba yaja motar,, barrack ya mayar dashi,,da kyar ya daddafa ya shige gidan sa dake cikin barrack din,,,yana budewa ya fada kan sofa kansa ya dafe wanda yake azabar ciwo kamar zai rabe Gida biyu,,,hannunsa yasa ya dafe kan dayake barazanar tsagewa.
Tsahon kwana biyu yayi yana jinyar kansa da zuciyarsa,,yayin da abangaran Sahar da Mom sukaci alwashi akansa,,kota halin kaka saiya aureta,,da mahaifiyar sa zasu fara amfani a yanzu babu makawa sai anyi wannan Auran.Misalin karfe 8 na dare yashiga gidan su,,babu laifi yadan samu sauki amma daka kalli fuskar sa zaka san yana cikin tsananin damuwa,,,kai tsaye part din Innayi ya nufa,,gaba dayansu suna zaune a parlo anata hira da Innayi,,muryarta kadai kakeji tana karadi,,,shigowarsa ya sasu yin dif,,babu wanda yaji sallamar da yayi aciki ciki yayi kayarsa.
"Innayi da bakinta baya shiru itace ta magan tu,,,oh ni naga takaina,,kamar kashigo gidan arna bazakai mana sallama ba,,mutum sai kafurin miskilanci,,,Allah ya shirye ka to,,nidai ba halin mijina kaiba,mijina dan Aljanna,,babu inda yake shiga babu sallama,,ko kallontà beba yasamu sofa ya lafe,,daya bayan daya suka dinga gaisheshi suna ficewa,,amma babu gaisuwar wanda ya amsa,,tunda yashigo Innayi ke nazartar sa,,ganin yadda yayi wata irin rama lokaci daya..
Tausayin sane ya kamata,, ahankali tataso ta zauna kan sofar da yake kwance,,,kansa ta dauke ta dora akan cinyarta,,,zafi rau taji kansa ya dauki zafi,,tsura masa ido tai tana tunanin abinda ya same shi.....
Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 47_48
💦KULSOOM DATA SERVICE💦
Kuzo kusai Data me lasting me sauki da rahusa.Cikin Aminci zaki samu Datar ki.Karki bari wannan gara basar ta wuce ki
😍😍Muna arha muna hana bashi.
Data A vailable all networks🔥
MTN AIRTEL
500MB_150. 500MB_150
1GB_300. 1GB_300
2GB_500. 2GB_500
3GB_750. 3GB_750
5GB_1,400. 5GB_1,400
10GB_2500. 10GB_2500.
GLO. 9MOBLE
500MB_200. 500MB_150
1GB_350. 1GB_250
2GB_600. 2GB_450
3GB_800. 3GB_650
5GB_1500. 4GB_850
10GB_2800. 5GB_1200
Cikin muryar rarrashi take shafa kansa,,shi bawa mumini duk inda yake anason ya yadda da kaddara mekyau ko marar kyau,,kayadda dama Allah ya kaddaro maka shiga wannan halin,,shiyasa Allah ya hadaka da mahaifiya kamar Fannah,,koda baka gayamun ba nasan ita ce musababbin damuwar ka,,mezai hana kayi hakuri kasaba da halayyar ta,,tsahon shekaru da zata canza data canza kafin girmanku,,amma tana nan akan halayyar ta,,kayi hakuri kayi mata biyayya zakaga Amfanin hakan,, Aljannarka tana karkashin kafafunta ka daure ku rabu Lafiya..
Jin saukar ruwa a hannunta yayi matukar girgiza Innayi,,Kuka Rayyan yake akan wani dalili,,abin ya matukar girgiza ta,,rabonda taga kukansa tun yana yaro karami,,,take ta karajin zafin Fannah,,aduniya ta tsani Abinda zai bata ransa ko yaya ne,,saigashi yau yana zubar da hawaye ta tabbatar abin ba karamun abu bane,,Kuka Rayyan ta ambata cikin rawar murya,, tsantsar tausayinsa na dawainiya da ita,,banason damuwarka Rayyan ashirye nake nayi komai saboda farin cikin ka,,amma bazan baka goyan bayan ka bijirewa umarnin Mahaifiyar kaba,,ko wace yarinya kake so afadin Duniyar nan zan tsaya maka saika sameta,,alokacin zan nunawa Fannah bata isa ba zannuna mata muma muna da iko akanka,,amma kayi hakuri ka karbi zabinta,muma zamu baka zabimmu..
Bece komai ba ya Lumshe idanun sa,, wace mace zai nuna afadin garinnan yace ita yake so,,be taba soyayya ba hasalima baya shiga sabgar mata ko kadan"badan bai samu masu sansa ba,, à'ah yana dasu har office sunsha binsa,waya kuwa saida yadaina kiran bakuwar number,,yanaji aransa haka zai kare bazai taba Auran soyayya ba."Bama wannan ne yafi damunsa ba illah matar da Mami ke ikirarin zai Aura,,inya tuna wannan abu yana dagula masa lissafi.
Tun zuwan sa gidan tasan da zuwan sa,,amma abinda ya bata mata rai bezo wajanta ba saiya zarce wajan kakarsa,,safa da marwa takeyi tana kallon hanya amma shiru babu shi babu dalilinsa,,,afusace tai hanyar dakin Innayi taje taga uban da yakeyi,,kamar kububuwa haka ta fado parlon,,cin birki tayi ganin sa akan cinyar Iyyani,,kafa mata idanu Iyyani tai tana hararar ta,,to rasa kunya zuwa ko zuwa kikai ki rufeni da duka saboda yazo wajena bezo inda kike ba,,,shiru Mami tai tana kunkuni,,hannu Innayi tatafa ni kike zagi Fannah,,ai da wannann abunda kike min gwara ki ware murya kimin zagin sosai,,ashe karyar futsara kike tunda bazaki fitar da abunda ke Cikin ba"shiru Mami tai tana girgiza kai kamar zata shako daga ita har Canal din taita duka.
Yau na kara tabbatar da Attahiru ya dauko mara tarbiyya Wadda batasan mutuncin kanta ba balle tasan na wani,,kije indai duniya ce ta isheki riga wando,,bace min daga daki tunkan namike na nuna miki ni na haifi Tahir kamar yadda kike tutiya ke kika haifi Rayyan,,tasan wacece Innayi tsaf zata iya sawa ai waje da ita,tadade da gane Innayi ba kaunarta take ba,,dogon tsaki Innayi taja haushin Fannah na kara kamata Jahilar banza kawai Innayi ta furta cike da takaici..
Duk Abinda suke yana jinsu Ahankali ya mike duk da jirin dake dibar sa,,binsa da kallo tai tasan wajan Uwarsa zai nufa,,kamar yadda ta hasaso nan din kuwa ya shiga, zuciyar sa acunkushe,,dama awuya take yana shigowa ta sauke masa yatsunta biyar akan kuncinsa,,tana sauke hannunta Abbu ya tsinka mata kyakykyawan mari sàida kanta ya amsa saboda tsananin zafin marin daya ziyar ceta,,tsantsar mamaki da tashin hankali ne ya bayyana akan fuskar Mami,,koda wasa Abbu be tama yunkurin marinta da sunan wasa ba balle da gaske.
"Cikin bacinrai ya nuna ta da yatsa,, Fannah bansan dakikancinki yakai har haka ba,,bazan taba zuba ido akan san zuciyar ki ki kashemun dana ba,,dan kin haifeshi bayana nufin tsarin yadda zai tafiyar da rayuwar sa a hannun ki yake ba,,akan wata 'yar iskar mata cen tabbadaddiya ki nuna min wa kikasani ahalinta akaf fadin garinnan,zaki dakko bara gurbi ki kawon cikin zuri'a ta,,wai anya Fannah kanki daya kuwa,,wannan ce rana takarshe da zaki sake daga hannu ki mareshi akan wannan Auran,,matukar kika kara yunkurin hakan nikaina bansan me zanyi miki ba,dan haka ki kiyaye,,jan hannun Canal yayi suka wuce part dinsa.
Binsu tayi da kallo hannunta dafe akan kuncinta,ba zafin marinne ya dame ta ba,kafa tarihin da marin yayi abunne ya tsaya mata azuciya,,zuciyarta har wani bugawa take kamar zata tsago tafito.Umami da tazo shigowa jin maruka na tashi hakan yasata juyawa ba tare da sun ganta ba,,dama biyo Canal tai dan taga ya jikin sa yake,tana mamakin yadda Mami ta dauki yaddarta ta bawa Hadiza bayan dan adam ba abun yarda bane,Allah ya kyauta cike da jimami Umami ta koma part dinta.
Abun duniya fa yayiwa Mami yawa,,ga wayar Hadiza akan komai ya wuce awajan su ranar ma rantane ya baci shiyasa ta fada mata magana,,hakan ya kara birge Mami ganin sun san sunyi kuskure gashi har afuwa suke nema,,tabbas Hadiza Mutuniyar arziki ce afa fadar Mami,,wannan hakurin da suka bata sai yasa ta kara jin san Auran ya shiga zuciyarta,,dukkan fafutukar ta saiya koma naganin yadda zaai Auran ya tabbata,,abangare guda kuma Hadiza na kara kwantar dakai da sake kulla dankon abotar su,,kudi kuwa duk sati sai Mami taji alert wai daga wajan 'yarta Sahar ta samata albarka,,ai Mami saita kara sakankancewa tabbatas wannan surukar arziki ce.
Ganin Abbu yaki kulata,,haka Innayi taki cewa komai saita wanki kafa tatafi wajan Abee har Kuka tayi akan ba'a maidata abakin komai ba,ai Mahaifiyar sace ita bazata taba zaba masa abunda zai cutar dashi ba,Abee ya karbi bukatar ta da alkawarin zaiyi bincike da kansa,,taji dadin wannan lamari hakan yasa ta koma gida da kwarin guiwarta.Abee takanas ya wanko kafarsa yazo wajan yayansa,,akan ya bata damarta ita ma,,abun ba kan kowa zai fada ba sai Canal din,,in har Mahaifiyar sa tayi fushi dashi akwai babbar matsala,,anyi ja inja da Abbu kafin daga baya ya Aminci zai tabbatar ya bata cikakken right dinta kamar yadda ta fada.
Anje neman Aure kamar yadda al'ada ta kasance,,babu wani jani injaka akai komai aka gama da tsayar da lokacin biki nanda sati uku,,hakan kuwa ba zabin kowa bane face zabin amarya Sahar hatta abunda Abban nata zaije ya fada wajan bakin ita ta zauna ta tsaramai a takadda,,ko kadan bataso ya kwafsa mata,,ya kuma baro da darajarta,,tafiso komai ayi harkar arziki bata tsiya ba"da yake angama dashi sai abunda haj Hadiza tace dashi babu musu ya zauna yayi nazarin takardar da aka damka masa,,duk da zuciyarsa kuna take kamarshi 'yar sa zata zauna ta tsarawa abunda zai fada,amma haka ya cije ya kanne dan tsira da Mutuncin sa.
Naira dubu dari biyu suka kai kudin Aure,,a lalitar Abbu kudin ya fita dan Canal ya rantse bazaisa kudinsa ya auro ragowar karti ba,,sanda aka kaiwa Mom kudin masifa ta balbale Ambassador da ita ai 'yarta ba saniya bace da za'a kawo kudin dari biyu kacal"babu yadda zaiyi haka yadinga bata hakuri,,tamkar danta haka tasashi agaba har kokarin tsokanemai idanu takeyi tsabar yadda take kumfar baki da numfarfashi,,hatta Amaryar ba'a barta abaya ba wajan gayawa mahaifinta magana akan kudin daya karbo ko ita zata iya sadakar su lokaci guda.
Dayake so suke a rurruma ayi Auran sai basu tada wata fitina ba,,ko saudaya Canal be shiga cikin lamarin Auran ba Sadik ne akan komai,,hasalima ya tattara zancan yamaidashi gefe harkokin gabansa kawai yake yi,,'yan uwansa sai dokin bikin suke shiri suke tako ina,,tun Innayi na fushi hatta gaji ta sakko da fadin Allah ne ya kaddara matar sace dole tasa hannun ta acikin lamarin bikin,,,Mami fa buri ya cika danta zai auro mace tagari,kamila gata da Addini,dukiya dama bata danta zata dinga hariba indai kudine Ubanta ya tara.
Bangaran riyyah abun Duniya yabi ya isheta,,Kallon salma kawai take da yaketa rawar duwawun bikin yayansu,,taja gefe dama 'yar kallo ce ita,,amma tarasa meyasa takejin haushin Auran da zaiyi,,tayiwa kanta wannan tambayar amma babu amsa,,takara haske tayi fresh ayanzu bata da wata damuwa inba tunanin canal ba,,danginta ta dade da shafe babin su acikin rayuwar ta,,sai tunanin Iyayanta data rasa wadannan abubuwan sune babbar damuwar ta.
Bikifa ya kankama takanas Mami da kansawar Adda suka nufi Japan hado kayan lefe,,Mami zuge jaka tai duk wani tattalin arzikin ta da take boyewa saidata juye shi awannan bikin,,batason harkar karanta akwatuna 15 suka tantso da kaya nagani na fada,,sati daya sukai suka juyo nigeria,,duk wanda yaga kayan sai san barka,amma me da aka kai kayan ankusa bawa hammata Iska,,abunda ya basu Mamaki uwar amarya da danginta ca sukai su basa karabar akwati kasa da 24.
Cikin takaici Batool ta mike in bakwaso yanzu zamu juya da kayan mu,,fadane ya kusa kaurewa tsakanin su da dangin Mom ko nace kawayanta,gaba daya wasu gogaggun 'yan duniya ta tara sune masu karbar kayan lefen,,waya Beenazir ta kira Abbu ta sanar dashi abunda ke faruwa,,cayayi su dawo da kayan suma dama basan Auran suke ba.
Anty Babba ce tallesu kudebo kayan mutafi dama ni tunda naga gidan da dan uwana zai dakko Aure naga babu tarbiyya acikin sa,,kamar uwa kamar 'yarta na tabbatar yadda kike haka 'yarki take koma ta fiki,,dama Anty Babba sam tatsani raini batason wulakanci ko kadan(wato Batool sakuwar Rayyan itace Anty Babba)mikewa su Fareeha sukai,gaba dayansu bikinne ya kawo su,ganin da gaske tafiya zasi Mom ta hau borin kunya ai ita bacewa tai akoma dashi ba.
Suma awannan Lokacin sukace basu san zance ba Aure mafa sun fada dakko dangin jaraba,,sàida Ambassador ya shiga cikin lamarin ganin girman mutumin da dattakonsa ya sasu hakura suka bar kayan,,amma ko tukuicin da aka basu kin amsa sukai haka suka dawo gida rai a tsananin bace,,dama Umami catai bazata jeba,ranar da Rayyan dinta zai Auro mace 'yar gaske awannan lokacinne zata nuna bajintar ta,,bazata wahalar da kanta a aikin banza ba.
Hakan yaso hada su fada da Mami,,har part din Umami ta bita tana gasa mata magana,,ashe dama karyar son dannawa kike tunda gashi kina bakin ciki da samun karuwar sa,,in Allah ya yadda wanann Auran Alkhairi zai zame mana duk masu bita da kulli saidai su gani akwaryar shan su,,batace mata cikanki ba haka ta gama rashin mutuncin ta tafuta.
Sanda suka dawo kai tsaye Beenazir daki tabi Mami dole ne ta amayar da abun dake cikin zuciyar ta.
Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar.
.....✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 49_50
💦KULSOOM DATA SERVICE💦
Kuzo kusai Data me lasting me sauki da rahusa.Cikin Aminci zaki samu Datar ki.Karki bari wannan gara basar ta wuce ki
😍😍Muna arha muna hana bashi.
Data A vailable all networks🔥
MTN AIRTEL
500MB_150. 500MB_150
1GB_300. 1GB_300
2GB_500. 2GB_500
3GB_750. 3GB_750
5GB_1,400. 5GB_1,400
10GB_2500. 10GB_2500.
GLO. 9MOBLE
500MB_200. 500MB_150
1GB_350. 1GB_250
2GB_600. 2GB_450
3GB_800. 3GB_650
5GB_1500. 4GB_850
10GB_2800. 5GB_1200
Beenazir Zurawa Mami ido tai ,kallon me kikeminne kamar wadda na canza kamanni,,Girgiza kai tayi bakomai Mami kawai dai ina mamakin gidan da Yayammu yaje ya nemo Aure,,daga mata hannu Mami tai kifito kifadi abinda ke ranki kina mamakin Inda naje na nemo masa Aure,,to nina san menakeyi gidan mutumci naje na nemo masa Aure,,ni Mahaifiyar sace yadda naga dama haka zanyi,,babu wanda zai canza min ra'ayina,komdai menene ya hadoku na tabbatar kune baku da gskiya,,tunda kin biyewa wadancan da suke bakin ciki da wannan Auran,,kije kici gaba da zama awajan su suna kara hure miki kunne,,nasan zakui Alfahari da wannan Auran.Tunda Mami ta fara magana Beena take kallontà, jijjiga kai kawaitake ta tabbatar Mami tayi nisa batajin kira."Gargadin da zanyi miki nakarshe matukar kinsan ba Alkhairi zaki fada ba,,to! Kija bakinki kiyi Shiru,,hanyar waje ta nuna mata tanan kika biyo dama dauki'yarki kiyi waje,,'yarta ta saba tai waje,,gaba daya zuciyarta ba dadi,,,tana matukar jin haushin halayyar Mami da bata taba karbar gyara arayuwarta,,abunda tai niyya shitakeyi,,Allah ya kyauta ta furta cikin sanyin jiki...
Part din Umami tawuce,,sallama dauke abakinta,,amsawa sukai dukkanin su,,kowa daka ganshi ransa bace yake,,maimakon ai murna da Aure sai bacinrai ke biyo baya,,,saitaji babu dado,,kunya na neman kamata,,a tashin su duk wata fitina Mami ce ke fara kunno ta,,tazama Kamar wata shedaniya,,gaba daya batasan zaman lafiya,,, Innayi da takaicin Mami ya kume ta,, Addu'a take Allah yasa Fannah ta gane shayi ruwane akan wannan Auran,,tagirbe abunda tadade tana shukuwa,badai ita sankanta ba zasuga ta karshan san zuciya da shegen kwadayi.Wai ni narasama zaman me mukeyi anan,,indai bacin ran Fannah zamu rike azukatammu to kuwa zata kaimu ta baromu,,,tsaf cuta zata iya kamamu a aikin banza dana wofi,,sai sukaga tabbas maganar Innayi gaskiya ce gwara kowacce ta kama abunda zai fishsheta,,Umami dai na gefe takaicin duniya ya isheta,,ga number Canal takira sau ba adadi yaki dauka kwata kwata.
"Kamar yadda Innayi ta basu shawarar su saki ransu hakan sukai abunda yafi karfinka saika maidashi wasa,,,biki aka cigaba da shiri wani gidan Abbu dake Shehuri south babbane sosai babu abunda babu aciki,,nan ya bawa Canal din su zauna da matar sa,,,sanda yake masa maganar gidan babu abunda yace,,ko Angode becewa Abbu ba shi bashi aka bawa gida ya zauna ba,,bega abunda zai sashi yaje gidan ba."Hatta dunkin biki a hannun Sadik yake shi yayiwa Yayammu komai,,shidai nashi ido,,satin biki ya zo,,kowane bangare babu zama,musamman bangaran Mom gyara namusamman akeyiwa Pretty,,cikin magungunan gyara da Mom ke dura mata,,cikin dare wani azababban ciwon ciki ya killeta babu shiri aka kwashe ta sai asibiti,,abunda ya matukar tayar da hankalin su,,suna kaita sukaga anyi dakin 'yan haihuwa da ita,,aguje Mom ta bisu tana tambayar ina zasu kaimata 'yarta,,Hajiya yarinyar ki zatai bari ne,,cikin jikinta ya lalace,,wani mugungane yadinga ketowa Mom da Ambassador,,ya tsinewa Mom azuciyar sa ba adadi,,amma azahiri ita yazo yana rarrasa,,dayi mata nasiha tayi hakuri kaddara ce,,,duk yadda takai da sanin hayyar Sahar bata taba zatan har maza take biba,,kan wannan ciki ya fita sàida aka kai ruwa rana,,kamar Sahar zata mutu da kyar da sidin goshi aka samo rayuwarta.
"Washe gari da safe Mom ta nemi sallama dan rufuwar asirin su,,duk da doctor yaso rike Sahar din saboda yanayin jikinta kamarma jini be wadace taba,,amma Mom taki yadda da tsarin sa,,bashi da ikon hanata 'yarta dan dole yabata ita suka tafi,,,amota ba wanda yake magana kowa da abinda yake sakawa azuciyar sa,,Allah sarki Ahaji Abbas idanun sa har kwallar bakin ciki take tarawa,,yana matukar dana sanin bijirewa umanin iyayansa na Auran Hadiza,,alokacin babu irin nasiha da jan kunne da nuna masa illar Auran Hadiza amma yakiji yanzu gashinan tana sashi a masifu kala kala."Suna zuwa gida Mom ta wuce da Sahar part din Ambassador batasan kowa yaganta awannan halin,,Indai kai ba makaho bane kana kallonta kasan nejego ce,,ga 'yan Biki sun fara hallara gida ya fara kacamewa,,suna shiga dakin ta yarfawa pretty shegen mari me tsinannan zafi,,dan Ubanki ashe baki da hankali,ni zaki tonawa asiri agarinnan dan uban wanene yayi miki cikinnan shiru Sahar tai bata kuma da alamun zata furta komai"cigaba da masifa Mom tai bakinta har kumfa yake ba karamin bata matarai Sahar din tai ba,,tana dafe da kuncinta tana kallon Mom,, murmushi Sahar din tadan saki,,kina neman wanda yamin wannan cikinne,,to nikaina ban sani ba,,,ban kumasan wanene uban cikin ba nikaina bazan tantance nawane din ba,,inko har kina san sani zan lissafo miki samarin nawa,,wata kila su sunada amsar da zasu baki,,kuma da kike tamin ihu aka ance miki wannan shine cikina na farko,,dariya tadan saki àah Mom,,kinyi babban kuskure na sakarmin ragamar rayuwata ahannuna,,kefa kika bani lasisin komame na aikata kinada hannu aciki,,,banga dalilin da zaki dinga tuhumata ba,,,wannan marin da kikaimun ya zamo na karshe gaskiya,,ayanzumma danna kai Zuciyata nesa ne shiyasa ban rama ba,,ido bude Mom take kallonta tunda tafara magana,,,kirjinta har wani dagawa yake tsabar yadda maganganun Sahar din ke dukanta.
Rai bace Mom din tasake kallon ta,,dama kindade kina cin amanata,wannan ce tarbiyya danai miki,,dana sakar miki rayuwarki aibacewa nai kije ki lalace ba,, abun da kika yimin kema Allah yayi miki,,'yar dariya Sahar din ta saki,, Mom yada harzuka haka,,,kiyimin abunda ya kamata na warware na dawo normal,,kinsan kinyin hakan na iya fitowa damu tsakiyar rana,,,afusace Mom ta fada toilet kamar ta rude pretty da duka,,,sanda ta fita ana tai mata yame jiki,dole tadinga yaken dole,aitaji sauki Zazzabi ke damunta,,Allah ya sawwake suka dinga yi mata,,fatan samun lafiya.Paty da pretty ta shirya ayau ita da samarinta da kawayanta masu kalar halinta,,dik da yadda takejin jikinta sàida tafita partyn aranar ba agida ta kwana ba sunacan suna cashewa,,sunyi rawa sun cake kamar masu tabin hankali.
Bangaran Ango dama babu wani program da suka shirya,, Mami ce tashirya walima da kawayanta,,takanas Mom din Sahar ta kira Mami akan Sahar tace babu wata bidi'a da zatai,,walima zatai Malama zasu dakko taiwa amarya nasiha,,ran Mami sai ya dada fari fat,,tafinga sawa Sahar din Albarka da kara jinta azuciyar ta,,sanda Mami take sanar da Innayi abunda Mom din ta fada gyada kai kawai tai sunyi kyan kai kuwa,,sun kyauta hakan nada kyau,,gwara da ba'a kara gayyato shedan ba,,shedan da shedan suka hadu ai ba'a san mezaifaru ba agaba,,tunda Innayi ta fata magana Mami take kallonta da son auna maganarta amizani,,amma sam takasa gane me Innayi take nufi,,, murmushi Innayi ta saki jiki magayi wai yaro yaji danyan kara,,daga gobe dai komai zaizo karshe Allah ya basu zaman lafiya,,ameen Mami ta amsa tana ficewa daga part din,,binta da kallo Innayi tai tana girgiza kai,,kome take tunani oho.
Yaune dubban al'umma suka shaida daurin Auran Sahar Abbas da Angonta Rayyan Attahir Rayyan akan sadaki naira dubu 100.Lumshe idanun sa yayi da har wani yaji yaji suke mai,,wannan Auran jinsa yake kamar an doramai wani nannauyan abu akansa,,kansa ya dafe da yake azabar sara masa,,Abbu da Abee suna lura dashi bakaramin tausayi ya basu ba,,hannunsa Abbu ya kama suka bar wajan daurin Auran,,shida Abee suka sashi agaba suka dingayi masa nasiha har suka karasa gidan Abee din,,babu kowa duk suna gidan Biki sai riyyah da take dakin su akwance,,gaba daya batajin dadin Duniyar yau,,dama bata ce zataje bikin ba,, Salma babu nacin da bataiba tazo suje tace à'ah,,,sàida Mamah Ramlah tasa baki akan ta kyaleta,dan sunyi waya da Umami akan karta taho da riyyah ta barta agida,,hakan yasa Salma tatafi afusace tanajin haushin riyyah.
A parlo ya kwanta bayan su Abee sun gama yi masa nasihar da bayajin zaidauki ko daya daga cikin su,,zaman dakinne ya isheta tamike dan tafito ko kallone tayi tarage zaman kadaici,,sanin ba kowa agidan sai ita kadai,,yasata fitowa hankali kwance,,doguwar rigace ajikinta irin 'yar saudiyyar nan bata kama jiki ko kadan,gashinta da yasha gyara ta tufkeshi atsakiyar kanta,,tafiya take kamar bazata taka kasaba,,wai itama ta zama 'yammata,,tunda ta fara sakkowa yake kallontà,,wani abu da yatsaya masa amakogwaro a hankali yaji yana bacewa.
Bacin ransa kaso 100% 50% ya ragu adalilin ganin riyyah,,yarinyar yana jinta matuka azuciyar sa,,labarinta ya tabashi sosai shiyasa yakejin tausayin ta,,samun waje tai ta zauna sai Lokacin hancinta ya shinshino mata kamshin turaran sa,,dan Lumshe idanun ta tai da sakin murmushin da batasan saboda me tayi shiba,,tunowa da tai yayi Aure amma ko yagayyaceta yasata bata rai kamar tana gabansa,,duk abunda takeyi yana kallon ta,,ita kadai take harare harare da mugunjin haushin Canal din,,,har yazo kusa da ita bata san da zaman shiba,,jin anzauna kusa da ita ta zabura cikin tsananin tsoro zata zabga kara,,,hannuta ya fusgo gaba daya ta fado jikinsa,,toshe mata baki yayi da tafukan hannayan sa,,,ido waje take kallon wadda yayi mata wannnan aikin,idantane ya fada cikin nashi da har Lokacin basu washe ba,,zaro idanu tai ganin shidinne,yaushe ya zoto,,kici kicin tashi take daga jikinsa amma ya riketa gam yaki bata damar hakan.
"Ina zakije ko kinmanta ni mara lafiyar kine,,saboda me kika gudonan kika daina aikin ki,,yanzu duk zan huce zaki biyani asarar tattalin da kika dingakin abaya yau saikin fanshemin kayana,,tunda yafara magana take zare idanu ba karamar Dariya ta bashi ba,,wani Nishadi ya dinga ji dayake tare da ita,,,gira ya daga mata,amma baki da adalci riyyah!!! Wani yar taji yana zagaye jinin jikinta,,jitai ba wanda ya iya furta sunan ta daidai saishi,,harwani lumshe idanu tai ta kara narkewa ajikinsa batare da tasan tayi hakan ba.Ana can ana cin uwar sabada abikina amma ke kina gida meyasa baki jeba,,jitai ranta ya baci da yayi mata zancan bikinsa,,kallon yanayin ta data sauya lokaci guda yake harwata kwallah ya hango kwance acikin kwayar idanun ta.Murmushin gefan baki ya saki,yana sosa girar sa guda daya,bakinsa ya kawo daidai nata,kara ware idanu tai hankali tashe,,,,,,,,
Hmmm mudai bazamuce komai ba.....
Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar.
......✍️✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 51_52
💦KULSOOM DATA SERVICE💦
Kuzo kusai Data me lasting me sauki da rahusa.Cikin Aminci zaki samu Datar ki.Karki bari wannan gara basar ta wuce ki
😍😍Muna arha muna hana bashi.
Data A vailable all networks🔥
MTN AIRTEL
500MB_150. 500MB_150
1GB_300. 1GB_300
2GB_500. 2GB_500
3GB_750. 3GB_750
5GB_1,400. 5GB_1,400
10GB_2500. 10GB_2500.
GLO. 9MOBLE
500MB_200. 500MB_150
1GB_350. 1GB_250
2GB_600. 2GB_450
3GB_800. 3GB_650
5GB_1500. 4GB_850
10GB_2800. 5GB_1200
"Razanar da tai ba karamin bashi dariya tai ba"lakuce mata hanci yayi matsoraciya kawai janye face dinsa yayi daga daidai tata,, maida kansa yayi kan sofa ya jingina,, dining ya kalla yaga babu komai akai,,dan yamutsa fuska yayi sai Lokacin yakejin wata yunwa,,dole yaji yunwa kam yamanta rabon da ya zauna yaci abincin arziki,tunkan Mami tai masa zancan wannna kaddararran Auran."Mezan samu taji ya furta ahankali kamar bashi ba,,dan kallon sa tai da alamar tambaya,,yunwa nakeji ya kara furtawa,,dariya ya bata ganin ya koma kamar baby,,sake yunkurawa tai wannan karan ya saketa,,da sauri ta fada kiching jingina tai da bango ya dafe saitin zuciyar ta,,,wani irin bugu take kamar zata fado"samun kanta tayi cikin farin ciki.
Abu simple ta zaba wanda tasan bazai bata mata Lokaci ba,,yana daga parlo yaji kamshi ya bade masa hanci,,ba laifi zuwanta gidan su Salma ya kara sa ta iya girki ba kamar daba,,dan Mama Ramlah bata taba yadda tana kiching danta yana nannade da kafa yana hutawa,kafarta kafar su hatta mazan bata barsu ba saidata koya musu girki.(Hakan na da kyau ga kowace uwa ta jajirce wajan koyawa yaranta girke_girke kala kala,ba kina ta aiki 'yarki na kalmashe da kafa ta dauki waya ta kame kamar ita ce matar Gidan.'Yammatan mu na yanzu ya kamata kucire kyuya kudinga taimakon iyayan ku)sai data jera komai a dining kafin ta karasa Inda yake,,rasa ta yadda zatai masa magana tai,,ta maza tai a hankali kamar me tsoron tai masa laifi,Yayammu food is ready,,yana jinta amma ya nuna kamar bacci yakeyi,,ganin kamar yana bacci tayi niyyar juyawa,,caraf ya ruko hannun ta hakan yasa ta tsaya cak.
Kin juyowa tai kallon idanun sa nasa tajita wani iri"idanun sa summata girma in yana kallon ta takura take ako wane lokaci,,wane yayammu,,hannunta na rawa da yake cikin nasa,,kai mana,,ta furta muryarta na rawa,,bakisan sunana bane,,da sauri ta juyo tana kallon sa,,ni zanfadi sunan naka,yadda taidin ya bashi dariya,,eh ko bazaki fada ba,, àah aika girmeni ni bazan iya fadar sunan kaba,, murmushi kawai yayi ya sakar mata hannun da sauri tabar wajan har tana tuntube.
"Kan dining din taje ta zauna,dama yunwa takeji amma bazata iya ci agaban yayammu ba,,sàida ya shafe mintuna kafin ya karaso kan dining din,,sunkuyar da kanta tayi gaba daya jinta take atakure,,zama yayi yanai mata kallon Kasan ido,,yana ayyana irin kyan da Yarinyar nan zatai inta kara girma,,jiyayi kishi ya rufe shi daya tuna lokacin yasan samari har layi zasu dinga yi mata,,basarwa yayi ya danne zuciyar sa,,oho bata masan yana yiba"jallop din taliya tayi musu sai arish da kifi zuku zuku,wani kamshi na musamman ke tashi daga cikin ta,,sai jus data hada musu medadin gaske,,zuba masa tayi acikin plate ta tura gabansa,,zuba mata idanu yayi,sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannun ta,,ai baki gama aikin kiba kamar yadda kika dinga lura dani sanda banda lafiya irin wannan nake so kiyimin yanzu.
Zaro idanu tai tana kallon sa,,ko bazakiyi ba,saurin girgiza kai tayi alamar àah,nina manta irin yadda nake baka abinci,,kuma yanzu aika warke,,kamar zatai kuka ta karasa fadar abunda yake Zuciyarta,,Harara ya watsa mata,,gayamun abunda ya kamata zakiyi ni bansan daidai ba,,in bazaki bani ba kawai ki fadamin,,bata rai tayi harda kumbura fuska tana hura hanci,,dariya ce taso kwace masa amma ya gimtse,,tunanin ta ta ina zata fara bashi Abinci bayan yanzu da hankalin sa garau,,time ya kalla in nakirga uku baki fara ba ni nasan abunda zanyi miki,,1_2_zaice 3 tai saurin debowa ta nufo bakinshi,,ashe hannun ta hancinsa ya nufa ganin tana kokarin cusamai abinci a hanci yayi saurin rike hannun,,dariya ce ta kamshi tsabar tsoronsa tana neman samai abinci a hanci.
"Kallon hannun ta tayi da yake cikin nasa,,motsa hannun tai amma ya rike yadda bazata iya kwacewa ba,,jawota yayi saigata akan cinyar sa dare dare,,zabura tai zata sauka ya riketa,bari aramawa kura aniyarta,yaudai nima na baki da kaina kamar yadda kika dinga bani abaya,,ni dai na yafema saboda Allah nai maka,,idanunta cike da kwalla take gaya masa,, tsoronta daya kar wani yazo yaganta akan cinyar sa aimata wata mummunar fassara ta daban,,bake kika sani ba nine nayi niyyar rama miki,,inta kama har toilet din da kike rakani nima saina rakaki ai,,fashewa tai da kuka jin abunda ya fada,,dariya yasaki ganin bilhakki take kuka kamar ya bita toilet din"kinga ya isa inhar kinci Abincin babu waccan maganar amma matukar bakici ba dole abunda na fada ya tabbata"babu yadda zatai haka ta zauna acinyarsa yana bata abinci"yana sane ya kashe duka wayoyinsa dan yasan za'a neme shi.
Kamar ko yadda ya zatane"Mom din Sahar abunda yayi ya masifar kona mata Zuciya"ana tajiran Ango yashigo gaida iyayan Amarya kamar yadda aka saba amma shiru babu shi ba abokan nasa"ga 'yan uwan Ambassador suna ta magana harda masu yimata dariya daga gani angon basan 'yar tata yake ba,,abunda ya kara bata mata rai kenan ganin anata gulmar ta,,da wadanda tasu ta fito fili da wa 'yanda suka rike tasu a Zuciya.Mami ta kira tana sanar da ita Rayyan fa bezo yagaida dangi ba,, hakuri ta bata da zummar zata kirashi yanzu,,amma bugun Duniyar nan bata samu wayar saba,,daga karshe Sadik ta kira akan ya bata Rayyan din amma yace shima nemansa yake.
"Mami ta tabbatar yana sane ya kashe wayar sa"Mami fa uwar ango sai shiga ake ana fita,,danginta dana Abbu sun cika gidan ba masala tsinke sai hada hada akeyi,,ta rataya katuwar jaka sai karbar gudummawa take tana dannawa ajaka,,bangaran Umami ma tasha wankanta,cikin atamfarta holland gaba daya ta damu da sanin halinda Rayyan yake ciki,,amma ta kasa samun wayar sa,,shiyasa hankalinta ya gaza kwanciya."Bangaran Amarya Sahar suna daki ita da kawayan ta,sai hira suke sunata shewa,,duk da har Lokacin tana jinjiki bawai ta dawo daidai bane,,anje anwa amarya jere nagani na fada sosai Ambassador ya kashe makudan kudade wajan yi mata kayan daki,haka Mom ta kashe iyayan kudin wajan yimata kayan kiching.
Anan ya shantake wuni sukai tare da riyyah wadda ya hanata sukuni,,tana can gefe so take tafaki idanun sa ta kwasa daki aguje,,kamar yasan abunda take son yi ya Lumshe idanun sa kamar yana bacci,,sadaf sadaf ya dinga tafiya sàidata tabbatar tayi nesa dashi tattare rigarta ta tsula da gudu,,duk abunda take yana kallon ta,,dariya kawai yayi ya girgiza kai."Sàida yayi sallar La'asar kafin ya fita daga gidan,sai Lokacin ya kunna wayoyin sa,ko walimar da barrack dinsu sukai niyyar shirya masa cayayi subarshi baya bukata."Sanda suka hadu da abokansa yasha jaraba awajansu na nemansa da suka dingayi,,banza yayi dasu bece musu komai ba,,su kyaleshi ma yaji da abinda ya dame shi.
Karfe 5 Motocin daukar Amarya sukai jerin gwano akofar gidan su Sahar,, lokacin tana dakin Mom sai banka mata magunguna take dan asamu asiri ya lullubu,,sun shirya abunda zata gayawa Canal ayau din,,tasu san ko kallo ba isarsa zatai ba balle wani abu ya hada su,,daga dangin Ango mutane biyu suka zo daukar Amarya,Mama Raihana da Adda kanwar Mami sune suka zo karbar Amarya.
Tasha lullumi cikin laffaya fara kar tana gaban Mom tana kukan munafurci,nan kuwa tsabar makircine idanun ta kamas take kallon kowa, Mom harda matsar kwallah 'yan nasihu tai mata wanda baza'a rasa ba,,cikin mutunci su Adda suka karbi amarya daganan gidan su Canal akai da ita,,wajan Innayi aka kaita tasha sabon dinkinta sai zuba kamshi take kamar ba tsohuwa ba,,an damka mata amanar Sahar a hannun ta,, kadaran kadaham ta karbe ta,da Addu'ar Allah ya saba halaye.
Ko sisi Innayi bata fitar ba na sallamar amarya catai kudinta ba hakosu takeyi ba,,haka suka tashi suka fito dakin Mami aka kaita,,kamar zata kwantawa Mami tsabar yadda ta nutsu ta sunkuyar dakai kasa sai sheshshekar Kuka take kamar gaske,, Mami sai samata Albarka take,,tukuici me kauri ta dauka ta bawa amarya,,daganan wajan Umami aka kaita itama tankarbeta da mutunci koba komai tazama 'yar ahalin su,,,kuma duk abunda zatai dan Rayyan dinta zatayi,,tabada nata tukuicin daganan aka dunguma akai gidan Amarya.
Gidan ya kayatar sosai har bedroom aka kai Sahar,wadda zuwa wanann lokacin ta fara isarta,,so take dangin Rayyan su fice tacire tasha iska,,kamar ko sun sani babu jimawa kowa yadinga tafiya daya bayan daya aka dinga kwasarsu zuwa gida,,hatta kawayanta ba wacca ta zauna kowacce tatafi since suna da wajan zuwa,,saidata ji gidan yayi tsit kafin ta yaye laffayar jikinta,,kwanceta tai gaba daya tai wurgi da ita,wannan shine na karshen sa kayan nauyi awajan ta,,bata kara nade kanta ba kamar gawa.
Wata atamface ajikinta wadda akaiwa dinkin rashin mutunci,,,gaba daya gaban rigar a fafake yake dukkan ilahirin kirjinta awaje suke,,suna cikin bra rakwacam kaida gani kasan maza da yawa sun kwashi ganima akansa,,,harwata nan karwa ce ta fito baro baro akansa,,haka bayan rigar yake shima a fafare,,sket din daya matseta saiya kara fito da asalin siran takarta,haka take kamar one duwawun nan kamar akuya ta mike tsaye.A takaice dai bata da abunda zatai takama dashi amatsayin ta na mace"sai kyan Fuska da farar fatar amma babu kyan zuciya dana jiki.
Parlo ta fito tana zazzagayawa ganin irin dukiyar da aka kashe mata yasata farin ciki,,ko bakomai zata kawo kawayanta hankali kwance Susan cewa fa eh yadda Ubanta yake da kudi haka ta Auri me kudi gashi handsome ajin karshe"Toilet ta fada ta kara silla wanka turaruka ta shafe jikinta dashi masu dadin kamshi,,wasu matsiyatan sleeping dress ta dakko tasaka,,dasu da babu duk daya,,irin kayannan ne da ake kira baka da shamaki Oga"zaman dirshan tai tana jiran Canal ya dawo amma har ta karaci zamanta babu shi ba labarin sa,,har bacci ya kwasheta akan sofa batare data sani ba,,sai da gari ya waye ta ganta kwance akan sofa zumbur ta mike tana karewa inda ta kwana kallo"wani kululun bakin cikine ya tokare mata awuya,,tana Amarya guda wadda zaaiy tattalinta da dokin ta,,amma kalli a inda ta kwana,,rai bace ta koma dakin ta.
Bangaran Yayammu be shigo gidan ba sai kusan karfe 1 na dare,,yana shigowa da ita yaci karo a parlo,,sau daya ya kalli kayan jikinta ya kauda kansa,,dama yasan wadda aka aura masa zatai fiye da Abunda tayi a yanzu,,babu wata yarinyar arziki da za'a kawota gidan Miji ayau sannan asameta da irin wannan shigar,,tsaki yayi ya barta awajan ya haura dakin sa,, hankalin sa kwance yasha bacci bashi da wata damuwa dan yayi alkawarin mantawa da babun wata Sahar acikin Gidan.
Kusan 8:30 aka fara norking a kofar parlon,, Sahar ce ta fito wannan karan atamfa ta saka dinkin balaifi ammasa na Mutunci,,sanin baki Zasu zo babu mamaki hadda dangin Canal din shiyasa tai wanann shigar,,bude kofar tai,,Asad ne atsaye da kula a hannunsa,,ganin kamannin su da Canal yasata sakin Fuska,,shima dan sakin fuskarsa kadan yayi,,gaida ita yayi ta amsa da fara'a,,kwandon hannunsa ya mika mata gashi inji Umami tace na kawo muku,,karba tai kace mata angode,amma bazaka shigo ba,, àah ina sauri ne sai anjima juyawa yayi ya barta tsaye awajan,,tabe baki tai kowa yake ciccijewa oho,,yayan naka ma zan maganinsa balle wani kai.
"Kan dining ta jera food flaks din,daki ta koma ta dannawa Mom kira kamar jira take ring daya ta dauka,,tunkan Sahar din tai magana cikin zakuwa take fadin,yadai Sahar ina fatan babu wata matsala komai yatafi dai dai kin nuna masa period kike,,wani dogon tsaki Sahar taja,,ai waccan dan taurin kaine Mom dole akai sunan sa wajan gobe da nisa,,kina ganin ko kallo be isheni ba,,zan samu nafito nan bada jimawa ba ayi min maganin sa,,ajiyar zuciya Mom ta sauke aidama wanann daganin idanun sa za'a sha fama amma bakomai kiyi duk yadda zakiyi in ankwana biyu kizo muje da zafi zafi ake dukan karfe.
Oum Aneesat
........✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 53_54
"Gaba daya ranta a dagule ta dawo parlourn ta zauna,,bata san awane babi take ba,,ina Canal ya tafi,,shine tambayar da take yiwa kanta,,kamshin dataji ya cika mata hanci yasa ta daga kai da sauri,,caraf idanun ta ya fada kan nasa daya ke sakkowa hankalin sa kwance,,babu wata damuwa a tattare dashi,,fuskarsa ta kara wani kyau da haske,,kura masa idanu tai tana jin son kara zama dashi,,dasan kasancewa dashi a kowane Lokaci,,tunda ya fara sakkowa yaji idanu akansa,,ya tabbatar itace,,sanin ko wacece a parlon yasa koda wasa be nuna yasan da zaman taba,,ganin da gaske fa ficewa yake kokarin yi yasata mikewa da sauri tasha gabansa,,,cak ya tsaya tare da ja baya kamar yaga wata muguwar halitta,,hakan da yayi ya kona mata rai sosai amma ta kanne,,cikin kissa da kisisina take kallonsa da mayaudaran idanun ta,,kwalla ta matso daga cikin idanun ta wadda bansan lokacin data kwakukulota ba.Duk yadda ya tsani yaga kukan mace beji hakan akan Sahar ba,,saina wani tarin tsanarta data kara taso masa azuciya,,ganin kara da kiyashin da aka ajiye masa acikin gidan sa da sunan matarsa ta sunnah.
Wani shegen kallo yake mata wanda ta kasa gane na menene,,dukkan wasu kalamanta saita nemesu ta rasa,,kwarjinin sa ya hana ta furta abunda yake Zuciyarta,,haka kawai ta tsinci kanta da tsananin shakkarsa,,idanunsa daya zaba mata sune suka karya dukkan kwarin guiwarta,,zagayeta yayi ya wuce ganin zata bata masa lokaci abanza."Binsa tai da kallo kamar zata hadiyi zuciya,,bacin rai yasata zabgawa kanta mari dan haushin kanta da kanta ya kamata,,me kikeyi hakane pretty,meyasa zaki canza Namiji guda daya shine zai firgitaki haka,,kamar zararriya takewa kanta da kanta fada,,Abun dariya har dungure kanta take da hannun ta.
Bangaran gidan Mami kuwa yau kwanan farin ciki tai Allah ya cika mata burinta,ta zabowa danta mace tagari,,zuciyarta fes bata da wata sauran damuwa.Fareeha dake gaban Umami tana kora mata bayani akan riyyah tai shiru tana sauraran ta,,Anty Babba ce tashigo ganin sun kule adaki ta kalle su da mamaki,,to me uwa da 'ya suke tattaunawa ba'a so muji,,'yar dariya suka saki sirri ne bama son bare sujimu,,hmm aiko sainaji koma me kuke kullawa nima akulla dani, Murmushi Umami ta saki,,kuma hakane,zaka tai agefan Fareeha.Dan Allah kuyi sauri kusanar dani kusanni akwai san labari,,to wanann ba wani labari bane medadin ji,,nidai ku fadamin awuce Wajan.
Bayanin riyyah Umami ta sake maimaitawa Anty Babba,,shiru tai nawani dan lokaci,,amma gaskiya Umami nidai ba'a kyautamun ba,, wannan maganar tawace bata Fareeha ba,,sanin kanki ne tafini yara da yawa,yaranta uku yarinyata daya kinga ni yaka mata ana Saboda Allah fa,, Fareeha dake sauraran yayar tata dan bata fuska tai,, gaskya Antymmu ni zaa bawa ita,tundaga US da shirin tafiyarta nazo kiyi hakuri kibarmun ita,,gaddama ce ta kaure tsakanin Antymmu da Fareeha daga karshe dai Antymmu tasamu nasara akan Fareeha Saboda hujjojin data kawo kuma Umami ta yadda dasu matuka,,kamar Fareeha zatai kuka dan ta kwallafa rai akan daukar riyyah tunda Umami ta sanar da ita labarinta taji zuciyarta ta cika da kaunar ta.
Umami ce ta kalle Fareeha gimtse dariyar ta tayi ganin yadda take matsar kwallah,,karamar Dariya Antymmu ta saki,kiga fa wai kuka takeyi akan na kwace yarinya damafa batazo hannun kiba,,amma tsabar neman magana kizauna ki kama kuka bari na kira yara suzo suga Ammin su na kuka,, Murmushi tadan saki, Antymmu bazaki gane ba kinsan ina dasa abu arai nasa maganar azuciyata shiyasa,,har Abban Sajjad munyi magana dashi ya kuma bani goyan baya akan hakan amma yanzu gashi kin karyamun budget,,dafa kafadar ta Antymmu tai Fareeha bankwace ta daga hannun kiba Saboda wani abu,,naga yafi dacewa ta zauna anan din tundaga Zuhura zasuyi komai tare,,yanzu kafin aimata cuku cuku atafi da ita wata kasar akwai jan lokaci,,nayi muku alkawarin zan riketa na kula da ita kamar nice na haifeta.
Banajinki Antymmu kuma na gamsu da bayanin ki,, Allah ya tayaki ruko,, Murmushi Batool ta saki Ameen kanwata,, Murmushi Umami tai tana jindadi azuciyar ta yadda suka hade kawunan su,,da ace ba maganar sirri bace hadda Beenazir za'a yita,,amma tana tsoron kar wataran dadin hira ya debeta ta gayawa Fannah halin da ake ciki.Yanzu dama jibi zan wuce Abuja gobe in ALLAH ya kaimu zamuje gidan Abee daganan sainaga yarinyar,,gyada kai Umami tai Allah ya kaimu,,Allah ya yimuku Albarka,,Ameen suka.amsa gaba dayansu.
Amma yaushe zakuje gidan yayanku,,ya mutsa fuska Antymmu tai ni wllh Umami jinai wanann Sahar din batai minba natsaneta,,kawai dai babu yadda zanyi ne,dan yayammu zanje badan ita ba,, Fareeha ce tai caraf kamar kin shiga Zuciyata Antymmu nima wllh batai minba,kaini gaba daya dangin nasu ma basu kwanta min azuciya ba,ni gani naima kamar nasan fuskar Amaryar a US kodai ba ita nagani ba,tabbas kamar hatta baci,,tabe baki Antymmu tai koma dai yayane ita tasani nidai Allah ya karemun dan uwana,Botool ta fada cike da jimamin wanann Aure.Wayar tace ta fara kara cirowa tai tana kallon screen din,, Murmushi Antymmu ta saki kafin tai picking,,ango kasha kamshi,,bansan meyafada mata adaya bangaren ba,ok ganinan fitowa.
"Mayafinta ta dauka ta yafa,,ina zuwa kuma,,zandan fitane yanzu zan dawo Yayammu yayi kirana nasameshi akofar gida bayason shigowa gidan yanzu,,gyada kai sukai kafin tafice daga part din baki daya,,kamar yadda yace yana kofar gidan daga can gefe,kwankwasa glass din motar tai kafin ya bude mata sit din gaba,, murmushi ne shimfide a fuskarta take kallonsa,babban kanina,,hararar ta yayi dariya tadanyi dama intana san tsokanarsa tana cemai kanin ta,,yana jin haushin hakan sosai,,ganin fuskarsa serious itama saita gyara tata almar ba wasa."Numfashi ya sauke kafin ya sauke idanun sa akanta,,dan kawar da kanta tayi yayansu na matukar yimata kwarjini,,hannayanta ya ruko gaba daya hakan yasa Antymmu kallon sa,,ta tabbatar maganar dazai gaya mata ba karamar magana bace,aduk lokacin da yariko hannun ta lokacin dazai fada mata wata magana tana daukar maganar da girman gaske.
Numfashi yadan furzar daga bakin sa."Zaki karbi Amanata?"kallon rashin fahimta tai masa,,Amanarka yayammu tame?"kamar bazai tanka ba harta fidda rai da cewar sa,,Amanar new sister,kaimun bayani yadda zan gane,abunda Umami ta sanar da ita adazu shi ya kara maimaita mata,,jijjina hannunta dake cikin nasa yayi,, please Botool nasan zaki iya riketa amana banson rayuwarta ta kara fadawa garari,kimin alkawarin zaki kula da ita kamar mamanta,,tsuru tai tana kallonsa,,karantar sa take duk wani harafi dayake furtawa tana tankade shi ta sashi a ma'aunin hangen nesa,,idanunsa kadai sun sanar da ita abunda ke damun sa,,abunda yake dawainiya dashi wanda besan dashi ba,,rabonda ya zauna yayi magana da ita me tsaho tun suna secondary school,,saigashi yau ya shage 30mnt yana kora mata bayani.
"Murmushi kawai take saki zata so taga wanann wace yarinya ce,,yayanta ya sucece akanta idanunsa suka rufe,,amma duk da haka kira yake tausayinta yakeji,,dama mana ai dole yaji tausayinta,,ganin tana ta zabga Murmushi yasashi dakatawa da abunda yake fada mata,,gimtse face dinsa yayi yanai watsa mata harara,,kunshe dariyarta take kokarinyi amma hakan yaci tura,,tuntsirewa tai da dariya hannunsa sake cikin nata ya murde,,kara ta saki tana magiyar ya cikata,,saidata ji ajikinta kafin ya saketa,,tabe fuskatake tana yarfe hannun ta,, murmushi ya saki tuna lokacin da suke yara,,in yanajin mugunta akan ta dama yake saukewa,,haka zata zauna agabansa taita Kuka,,in kuma awaje aka daketa saiya rama mata.Cikin jin haushin dariyar data mai yake kara maka mata harara,,,mekika gani ajikina da kikemun dariya,,babu kawai jindadin Amanar daka banine,,dajin dadin yadda ka tsallake kowa ka dam kamin wannan Amanar,,kyautar dan mutum kaimunfa dole naji dadi nai farin ciki Yayammu,,hawaye ne ya sulalo daga cikin idanun ta,,tuna shekarun data shafe tana fafutukar taga Allah ya basu haihuwa,,saidaga baya Allah ya azirtata da Zuhura,,saiga wasu sun sami diya amma suna wulakantata da tozartata aduniya,,jin yana share mata hawaye ta dago tana kallon sa.
Kyaleni Yayammu ina kukan farin cikine,,kasan daci da zugin danaji kuwa alokacin da ban haihuba,,nakan kwana na wani ina kuka batare da naji sanyi araina ba,,duk da mijina bai tafa sauyan fuska ba amma hakan yasa na kasa sakin jikina,,nadage sa Addu'a ba dare ba rana har sàida Allah ya azurtani da haihuwa.Labarin yarinyar ya tsumamun Zuciya,,Zumuncin yanzu ya zama daga kwauri sai guiwa kowa nasa yake so,,zan riketa kamar yadda zan rike Zuhura nama alkawari,,dora hannun ta tayi akan nasa,, murmushi ya saki yana kallon Botool din,soyayyar ta dabance kaf acikin 'yan uwansa,,tana da hankali da sanin ya kamata,,uwa Uba gata da ilin Addini dana bolo,,cikakkiyar likitar matace ta kware akan aikinta,,ina Alfahari dake kanwata,dariya ta saki,,nifa yayammu da wata 4 kagirmeni nima kamata yayi kadinga cemun Antymmu,, murmushi kawai ya saki yana shafa kansa.
Kallon agogon hannun sa yayi,,fitar mun amota zan tafi,,ok anjima da yamma zamuje ganin Amarya,,gimtse face yayi kamar bashi ne yagama dariya yanzu ba,,ganin yanayin sa ta fice daga motar tasan halin muguntar sa tsaf zai iya sata kuka da girmanta.Kamar yadda ya sanar dashi da yamma suka dunguma sai Gidan Amarya,,da mutuntawa ta karbe su,dandanan ta cika gabansu da kayan tande tande,,su Humaida ta sa siyi mata girki,,dama babu abunda ta iya inbanda tafasa ruwa,,ko dahuwar indomie bata iya ba,,zagewa sukai sukai mata hadaddiyar frid rice taji kayan hadi.
Babu Laifi su Antymmu sun dan saki rai bakamar yadda suka shiga gidan ba,, Beenazir duk hirar da suke bata samusu baki,,Kallo take karewa Sahar tana fahimtar wasu abubuwa daga gareta,,haka Fareeha take kallon ta tana san tabbatar wa zuciyarta abunda ya dade yana sukarta akahon zuci,,tabbas ita din ta gani a USA ba wata ba,,bawai bata kai taje can bane inda tagantan shine abun damuwar,,mamakin ta taya Mami zata dage akan wanann Auran,mene abun burgewa ajikin wannan silinda din,,bangaran Sahar tana ta kokarin ta rufe ainihin kalar ta,,bayanzu zata bayyana musu ita wacece ba,,sai dan uwana su yazo hannun ta,,zata ci gaba da pretending har sai burinta ya cika.
Sàida sukai sallar magari ba suka baro Gidan,,shatara ta arziki ta had musu,,'yammatan kuma ta basu kayan kwalliya,,sun nuna bazasu karbaba ta dage da magiya.harsai da suka karba,,har bakin get ta rakasu Antymmu ce ke driving din tana daga musu hannu har sàida suka fice tukunna ta dawo jikinta sanye da zumbulelen hijabi.
Mu hadu a next page.
Daga Alkalamin.
Kulsoom Ismail Idris
......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 55_56
Sanda suka koma gida Mami taga irin kayan da Sahar ta basu,,hakan ba karamin dadi yayi mata ba"saita sakankance ita ma tata kyautar tananan tafe"ranar Canal kin zuwa Gidan yayi sai waya kira ya gaida su"Mami taso yin korafi amma ta basar saboda ko gajiyar biki ce ta hana shi zuwa.
Kamar yadda suka tsara washegari suka dunguma gidan Abee,, Antymmu da Fareeha sai Umami sune suka kaiwa Mama Ramlah ziyara,,sanda sukaje riyyah tana kiching tana karasa girkin da suka fara,,Alkubus take turarawa sai tashin kamshi yake"zama sukai suna gaggaisawa kiran riyyah Mama tai akan ta kawo wa su Umami ruwa,,amsa wa tai da to,,dauke da plate ta fito ahannun ta,,goguwar rigace ajikin ta,,tayi mata kyau haka dinkin ya dace da atamfar,,fuskarta fayau babu kwalliya ko kadan"gashin ta data tufke yana ta reto agadon bayan ta"tunda ta fito su Antymmu suka zuba mata idanu,,tabbas yarinyar kyakykyawa ce,, murmushi Antymmu ta saki dole yayansu ya rikice akan wannan yarinyar,,nan gaba inta kara girma yakenan zai zama.
Umami sai washe baki take ganin yadda riyyah tai fes alamar Hankalin ta akwance yake"saidata ajiye ruwa da drinks din data kawo ta lura da Umami dan ita kadai ta sani acikin su"fuska ta washe sosai tai missing din duka 'yan gidan musamman Humaida da Asad dama sune abokanta"har gabanta tazo kafin ta tsugunna tana gaisheta da fara'a take amsawa"kallon Mama tai lallai Maman Salma kin iya kiwo kinga yadda 'yar tawa ta kara zama budurwa"dariya suka saka"Mama ce takalli Umami ke kuwa ainidin bata wasa bace"meyasa bazaki barmin ita ba"wllh bakiji yadda nasaba da ita ba"juyawa tai ta gaishe dasu Antymmu fuska washe suke amsawa suna yabawa da nutsuwar yarinyar.
Umami itace wannan"gyada kai tayi itace 'yar taki"farin Antymmu kara yawaita yayi hannu ta hudewa riyyah zo diyata naji dumin ki"duk da riyyah bata gane mesuke nufi ba haka ta matsa jikin Antymmu rungume ta tayi tana sakin Murmushi"kan kameta Antymmu tai tana dariyar farin ciki"ba'a taba yimun kyautar data farantamin rai kamar wannan ba Umami"bakiji yadda zuciyata take taka rawa ba"dariya suka saka to ai mu bazamu gane ba,inba gani mukai kina taka rawa atsakiyar parlon nan ba,dariya tasaka ALLAH zan iyayin rawa Indai akan samun new dota ne,, murmushi kawai suka.saki suna kallon su gwanin birgewa.
Raba ta tai da jikinta tana kallonta"mene asalin sunan ki"sunana Ansariyya"murmushi Botool ta saki ma sha Allah suna medadi"kamar yadda nake kaunarki ina fatan kema zaki kauna ceni ko rabin haka ne"gyada kai tayi da murmushi a fuskarta ta"dafa kanta Antymmu tai Allah ya yimiki Albarka"Ameen suka amsa gaba dayansu.gaskiya da sake amba me kaza kai da kafa"ni kuma a tutar me zantashi ina zaman zamana azo aimun kwacen yarinya"Umami ce tai caraf banda abinki Maman Salma ajiya fa aka kawo miki"ranar da akazo karba saika dakko kabayar salin alin"Uhm Mama Ramlah tadan murmusa batace komai ba"tana jin badadi azuciyarta na rabuwar da zatai da riyyah"balle kuma Salma da komai tare sukeyi yanzu"tana matukar jindadin zama da riyyah"zama acikin maza yasa ta fara koyar surutu irin na salma"dan samarin gidan badai surutu ba"amma sai tsare gida su basa san raini.
Mikewa tai bari nakarasa girkin Mama"to maza jiki karasa juyawa tai suka bita da kallo"ajiyar zuciya Mama Ramlah ta sauke wadda sàida suka juyo suka kalle ta,,wllh haka kawai nakejin yarinyar acikin jinina,,ban taba haduwa da wani mahaluki nai masa irin wannan kaunar ba"komai nata yana min kamanceceniya da nawa"na rasa meyasa nake ganin kamannina a fuskarta"shiru sukai suna sauraran Mama da take kora musu jawabi fuskarta dauke da damuwa"kinsan ance kowa yana da me kamarsa aduniya ta yiwu ta hakan kukai kama"kuma hakane Allah yasa dai mudace Ameen suka amsa."Wata hirar suka fada,tana gama abincin ta dakko akan carpet suka baje sunfijin dadin zaman kasan akan su hai dining area.
Sai yamma lis suka tafi da kara jaddadawa riyyah ta shirya da wuri zasu wuce ABUJA a goban"da to ya amsa tana jin wata irin kewar ahalin gidan da zata bari sam batajin dadin tafiyarta wani waje na daban ba"tasa ba da nan din"sun mutum tata sun daraja ta bata taba ganin annuna mata banbanci ba tun zuwanta gidan"ko wani abu Abee ya siyo saiya kirata ta fara zaba wai ita ce Auta"haka zasi ta fada da Salma suna 'yar ture turen dauka su Mama si tai musu dariya.Ranar haka ta kwana tana tunanin Salma juyawa tai ta zuba mata ido tana baccinta hankali kwance"da kyar bacci barwo ya sace ta tana da saurin sabo da mutane."Sàida safe Salma ta samu labarin tafiyarta Kuka riris ta dingayi"Abee ne ya dinga lallashinta"ita kanta Mama jitake kamar ta fashe da Kuka"haka mazan gidan gaba daya basuji dadin tafiyarta ba.
Sanda driver Antymmu ya sauketa a harabar gidan da Salma ta leka ta hangota kara fashewa tai da Kuka"sosai takejin riyyah azuciyarta tanaji kamar kanwarta ce yakini"bata taba banbanta matsayinta da 'yan gidan ba."Kan kame riyyah tai tana rokon abar mata ita"ita ma riyyah Kuka take na kewar da zatai na ahalin gidan"da kyar Salma ta saketa, Mama taje ta rungume saidatai da gaske ta rike hawayan ta"Allah ya kiyaye hanya riyyah ina fatan bazaki manta damu ba"bazan taba mantawa daku ba Mama"wajan Abee ta karasa tai masa sallama dafa kanta yayi Allah yayi miki Albarka Ansariyya"hawayan fuskarta ne ya kara karfin gudu a face dinta saitaji kamar Abban tane ya samata Albarka.
Har bakin mota suka raka su"jakar kayanta aka saka mata aciki"sai kudi da Abee ya bata tasha ruwa ahanya"taso kin karba ya dire mata acinyarta"haka ya kirgo ya mikawa Botool da take kalllon su"tanajin badadi da zata raba su da riyyah"saidai babu yadda za'ai dole anisanta riyyah da maiduguri zuwa wani dan lokaci.Har suka fice daga harabar gidan suna tsaye suna daga musu hannu"suna fita Salma ta zube akasa tana Kuka da birgima"sai da kyar Abee ya lallasheta suka koma gida.(Allah sarki sabo tirken wawa"bako raba ne duk yadda yakai da dadewa agidan ka wataran zai tafi").Ranar Salma kincin abinci tai saboda bakin cikin tafiyar riyyah.
"Tsahon sati daya kenan duk yadda Sahar taso jawo hanlin Yayammu abunfa ya faskara"babu kalar shigar da batai ba dan ta jawo ra'ayin sa amma kamar dutse"tarasa Canal wane irin Mutum ne anyama lafiyarsa kalau kuwa"abunda bata sani ba ko kadan jikinta be taba burgeshi ba saima tsananin kyamarsa da yakeyi"abun duniya yayi mata zafi sosai kullum cikin kiran Mom take dayi mata korafin halin da take ciki"saidai Mom ta rarrashe ta"duk safiya saita kira Mami ta gaida ita"tana washer baki da samata Albarka zakaji tana Amsawa"musamman ta tura mata da 50k wai tasaiwa yara alawa"ranar kamar Mami tai hauka dan dadi"sai gashi ta fito tsakar gida tana shelar abun arzikin data fara samu daga Sahar"murmushi Innayi ta saki batare data furta komai ba.
"Yau Sahar tatashi da kudurin tafiya gidan gobe da nisa"har daki tabi Canal ta sanar Dashi Mom ba lafiya zataje ta gaishe ta"Allah ya sawwake ya furta daga haka be kara kallon inda take ba"bata damu ba dan tana da tabbacin zataje inda za'a share mata Hawaye"ai mata maganin matsalar ta"dama ta gama shiryawa mayafinta ta saba da makullin motar ta"bata zame ko ina ba sai kofar gidan su"dama yadda suka shirya da Mom ba saita shigo ba itace zata fito su tafi"tana daidaita parking ta kira Mom kanta fito"babu jimawa kuwa Mom ta fito taci gayu kamar me zuwa gidan Biki"fita Sahar tai ta koma back sit driver yashiga ya jasu,wani daji suka yanka tafiya kamar bazata kare ba"tun ana tafiya a marmarce har Sahar ta kosa ta fada yiwa Mom mita itafa gaskiya tagaji wannan wace irin wahala ce"balle kuma driver dayake tsine musu Albarka azuciyar sa"haka kawai sun jawo su matattarar aljanu"yana da yakinin akwai gagaruman aljanu awannan dajin.
Akalla sàida sukai tafiyar awanni uku acikin dajin"ba gida gaba ba gida baya"sun matukar gajiya musamman Sahar da bata saba da wanann gajab gajab din na mota ba"Inda bazasu iya shiga da motar ba anan suka tsaya suka fito daga cikin motar"wai Mom ina mutumin"numfashin wahala Mom ta sauke waike atunaninki anan zamu ganshi sai min shiga ciki"tsaki taja gaskiya nidai danasan hakane daban biyo kiba"to aiyanzumma saimu koma danwa nake wannan abun inba keba"shiru tai suka nausa cikin dajin"kunga wancan tsaunin wani tsauni Mom ta nuna mata tsininsa kawai suke iya hange to can zamuje"kamar Sahar ta dora hannu aka haka taji,,amma bata tanka ba"zasuje bazasuje ba yadda kasan baya ake mayar dasu"tsantsar gajiya tasa Sahar zubewa akasa tana numfarfashin wahala,,kafafunta ta kalla sunyi taruwar jini tsabar masifa"bayanta kuwa kamar zai tsage ga kishin ruwa daya addabeta"daure ki tashi Sahar mu karasa min kusa zuwa.
"Bata da yadda zatai haka ta mike suka dora daga inda suka tsaya"(hhhhh Allah ya kara gwara kuji ajikinku kuma)sun shafe wasu mintunan kafin su karasa gaban tsaunin"suna kokarin shiga sukaji andaka musu ta zananniyar tsawa"Sahar batasan sanda ta saki jakar hannun ta ba ta kankame Mom"daga can kuma sukaji ankece da wata mahaukayar dariya"cikin wata murya mara dadinji kamar ana buga ganga"(Barka da zuwa iyalan shedan"abokan tafiya wutar jahannama"kun zabi Duniya kamar yadda muka zaba"zaku samu Duniya kan muje can kuci ubanku"dama abokan tafiya muke nema kuci ga tururuwa jakadan shedan"saini gobe da nisa ko shedan haka ya ganni ya kyaleni"ni tsinanne uwata tsinanniya"sake shekewa akai da wata shegiyar dariya)"tashin hankaline yasa Sahar sakin fitsari batare data sani ba"abunda yafi komai daga mata hankali bata ganin me maganar magana kawai suke ji.
Hmm tofa Anzo dai dai wajan"Allah ka rabamu da tabewa,Ubangiji ka tsare mana imanin mu.
Mu hadu a Next page dan jin yadda zata kaya."Taku Mrs Baba Bello Abubakar.
......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 57_58
Ke!!! Tsohuwar kilaki banji kirara na natashi ba,,shigo da baya da baya"alama taiwa Sahar su juya baya kan su shiga kogon da yake cikin tsaunin,takalman su a hannu suka juya baya fuskar Sahar tai jajawur kamar a ce kyat ta zura da gudu"sàida suka shiga kogon kafin su juyo Mom ce ta fara zabga masa kirari"(Sai kai mugu dan muguwa,tsinanne dan tsinanniya,kai la'ananne uwarka la'ananniya"kafi fir'auna kafurci,ko shedan tsoron makircin ka yake"babammu maganin kukammu kaine me share mana hawaye"mugu dan muguwa)babbakewa aka sakeyi da dariya kafin ya bayyana akan wata katuwar kujera da na gaza gane akasa take ko asama take"wani shirgegen kato ne ko nace aljani gaba daya suffar sa ta banbanta data bil'adama,,ban sani ba ko tsabar sabon Ubangiji ne ya maidashi haka"zubewa sukai akan guiwinsu"madallah da 'yan uwana batattu"kun yarda kunyi amanna kunzabi nan akan can"shiru yayi yana zare kwala kwalan idanun sa,,tsananin tsoro ya hana Sahar dagowa ta kara kallon wannan halittar da ko a mafarki bata fatan Allah ya hadata da shi.
Meke tafi da ku! Zabura Sahar tai alagabarta Malam"kanta karasa ya zunduma mata wata uwar ashariya tunda tazo duniya bata tabajin wannan zagin ba"cikin fushi ya nunata da shafcecen hannun sa"karki kara karki kuskura ki kara kirana da wannan sunan"wannan sunan da kika kirani dashi kamar kinkaskantar da nine"nine asaman Kowa bana son faduwa ko yaya take ki kiyaye"afuwa guda daya zammiki wannan ne karonki na farko zuwa neman biyan bukata inda muke"tsohuwar ki nacika dukkan sharudammu shine afuwar da kika samu daga gareni"sunana mugu dan muguwa!!! cikin tsawa ya karasa fada mata hakan,,harta Mom data saba zuwa wajan ayau ta kara razana"ta sake gasgata hatsabibancin gobe da nisa.
Bude baki Sahar tai zata sake Magana ya daga mata hannu nasan meke tafe dake"sandar hannun sa ya nuna bango da it's"kamar walkiya saiga hoton Canal ya fito baro baro"yana zaune a barrack.din su yana aiki acikin laptop dinsa"cikin Mamaki Sahar ke nunashi,shine wannan,,dariya ya sheke da ita kin kawo shi Inda za'ai maganin sa"zaki juya shi sai abunda kike so zai aikata,ko kara kika saka masa bazai iya tsallakewa ba matukar baki bashi umarnin hakan ba"ya zama naki har abada"Farin ciki ne ya kama Sahar tunda tazo wajan batai dariya ba sai yanzu haka fuskar Mom kamar gonar Auduga.
"Amma da akwai matsala"zuba masa idanu sukai suna kallonsa danjin abunda zai sanar dasu"karki yadda wata mace ta shiga cikin rayuwar sa koda wasa"akwai wata yarinya da zata shigo cikin rayuwarsa inhar kikai sakaci"shigowarta daidai yake da rushewar dukkanin aikin ki"wannan yarinyar tamkar garkuwa haka zata zame masa"duk yadda nai kokarin gano wace yarinya ce madubi na yaki bani damar hakan.Sosai abun ya daki zukatansu sanin wanene gobe da nisa"duk hadarin aiki kazo gunsa zai aiwatar dashi amma gashi wannan karon ya kasa ganin wata 'yar karamar alhaki.
Jiki asanyaye Sahar ta daga kai zan kiyaye haka mugu dan muguwa"babu ta yadda za'ai tabari wace mace tarabe shi"zatayi duk me yiwuwa danganin ta hana faruwar hakan"aciki bata dauke har uwarsa ba saita yimata katanga dashi(tirka shi Mami kin debo ruwan dafa kanki)."Wani garin magani ya cillo mata"ki tabbata kinsamai wannàn Acikin abinci matukar yaci bazai kara gaddama da dukkan maganar ki"zamu tura masa aljani mantau"zai manta dukkan iyayan sa ko ahanya ya hadu da su saidai ya wuce batare daya gane suwanene ba"turare ya wulla mata wannan turaran shi zaki fesa shine mafarin aikin ki"gaba daya kayan ta tusa ajaka cikin kwarin guiwa jitake aiki ya kammala.
"Abunda zaki biya Aljani mantau"za'a yanka masa bakaken kare guda biyar"bakiken dan taure guda biyar"sai shanu manya guda biyar"wannan shine ladan aikin sa"ayimun afuwa na bada kudin kayan aikin"wannan bamu da matsala kudinki ya biya miki bukata"fito da kudi tai ita kanta batasan ko nawa bane"zubewa tai agabansa"babbakewa yayi da Dariya Abokiyar tafiya kin yanki ticket mun kara Yawa"ihu yasa yana yiwa kansa kirari"ku tashi kufita ansallame ku"babu musu suka tashi suka fice da baya da baya kamar yadda suka shigo."Wannan karan Sahar bataji wahalar tafiya ba tunda aikinta ya kammala"burinta na daf da cika"suna zuwa suka fada mota driver yaja suka tafi"basu suka dawo ba sai bayan magari ba"tana shiga ta zarce bedroom dinta hannunta rungume da jakarta,kamar me tsoron karta gudu.
Wanka ta fada"tana futowa ta zura riga Iya cinya ta tsaya mata"kanta ta kara gyarawa kafin ta dakko turaran gobe da nisa ta feffesa"bashi da dadin kamshi kwata kwata,har hawa mata ka yake saboda rashin dadin sa"dining ta wuce ganin food flaks a jere ta tabbatar Mami ce ko Umami takawo musu abinci"ta Kwana gidan sauki,,zuwa tai ta dakko mganin ta barbade kan miyar tukunna ta mayar"sàidata tabbatar komai yayi daidai kafin ta koma kan sofa ta dora kafa daya kan daya tana jiran Canal."Ranar sai akaci sa'a karfe 9 daidai driver ya daidai ta parking a harabar Gidan"yajima kwance a back sit din hakanan bayajin dadin jikin sa"laptop dinsa ya dakko sai hilarsa daya rukota a hannu"tunda ya shigo idanun sa ya sauka akanta wani bacinrai yaji yana taso masa"kauda kansa yayi daga kanta ya karasa shigowa parlon"tasowa tai cikin karairaya tana jifansa da wani irin Murmushin mugunta"har gabansa ta karaso hannu ta mika danta karbi jakar laptop dinsa yayi niyyar bige hannun ta ya shaki kamshin turaran data ambula ajikin ta"jiyayi kansa ya azabar sarawa harsai daya runtse idanun sa ya sake budewa akanta"samun kansa yayi da sakar mata jakar batare daya furta kowa ce kalma ba.
"Kashe masa idanu tai tana sakin dariyar farin ciki da'alama hakanta na daf da cimma ruwa"hannunsa ta kamo ya bita zee kamar jela"bedroom dinta ta shiga dashi ruwan wanka ta hada masa duk abunda takeyi sai binta yake da ido"zuciyarsa zafi take amma ya kasa control din kansa akan yafice yabar mata dakin"dan samun waje irin na Sahar da kanta ta silleshi tai masa wanka"taso komai ya kankama tun a toilet din amma yadda kasan dutse haka yako mata binta kawai yake da kallo"duk wata hanya datasan tana tashin hankalin Namiji tabi wannan hanyar amma shiru kakeji wai Malam yaci shirwa"ranta bace ta fito daga toilet din ta barshi aciki"taso tun yanzu ta fara dandanar zumar sa amma sai kace ita ce"kwafa tai ta fice daga bedroom din.
"Sanda yafito yaga bata dakin"bedroom dinsa ya wuce ya canza kaya"kwanciya yayi saboda yadda kansa yake ciwo har wanann lokacin"ganin shiru shiru be fito ba ta kwaso kayan abincin"sakwara ce da miyar kwai tayi masifar haduwa sai tashin kamshi take"hangoshi akwance ta karasa ta jere mayan agaban bed din"Baby Baby ta bubbuga kafafunsa"dan bude idanun sa yayi da sukai jajir"tashi kaci abinci,,ji yayi sam bazai Iya musu ba da kyar ya yunkura ya mike"abaki ta dinga bashi dan yafi ci da yawa"balaifi yaci kam"lemu ta tsiyaya mai mai sanyin gaske wanda yasha magani aciki"karba yayi ya shanye ya maida kansa ya kwanta'murmushi ta saki aiki ya kammala"awannan dare Canal beyi bacci ba saboda yadda yaji wani abu kamar ya danne masa zuciyar sa"bakinsa ya kulle yakasa ko wace irin Addu'a sai juyi kawai yake.
Washe gari da safe garau ya tashi babu wani abu dayake da munsa"sau tsananin kaunar Sahar da yaji Lokaci daya ta cika zuciyar sa"jin yunwa na neman halakashi ya shiga kiching ya iya girki tea ya dafa musu sai dankali da kwai daya soya musu"dining ya jera kafin ya wuce dakin Sahar tana zaune tana mutsutstsuke idanu murmushi ya sakar mata wanda ya kara narka zuciyar ta"sweet kin tashi"jitai kanta ya kara kumbura hannu ya miko mata ta dora nata akai"rungumeta yayi yana sakin ajiyar zuciya"hope kina lafiya"gyada kai tayi tana kara kankame shi abunda ta dade tana mafarki yau sai gashi azahiri.
Tsahon sati daya akai ana shan soyayya"ya manta da duk wani nasa sai Sahar da Mom sukadaine aduniyar sa"hatta Sadik daya kira Canal danjin lafiyar sa Sahar ce ta daga kan yana lafiya in tai ra'ayi zata sakeshi ya fito"sanda take wayar yana zaune a gefanta yanajin kuma abunda tasanar da Sadik din"wayar yabi da kallo yana tunanin wane irin sauyi aka samu haka lokaci guda"wayar Canal a hannun Sahar anya babu wani abu akasa"saurin kauda wannan zancan yayi daga ransa ko da dai ai matar sace zai iya yiwuwa sun sasanta"murmushi ya saki yana girgiza kai.
"Tun ana zuba idanun cin amarci ya hana Yayammu zuwa gida har lamarin ya fara basu tsoro"tsahon 2weeks bashi ba Labarin sa"tun abun baya damun Mami har hakan ya fara taba zuciyar ta"taka nas ta wanki kafa dan zuwa ganin Amarya taga ko Lafiya gadai wayarsa na ring amma ba'a picking daga karshema in sun kira basa samun sa"ashe Sahar a balack list duk ta dura su"Humaida ce tai mata rakiya Mami harda guzirinta na kayan gyara🤣🤣."Ganin su get man ya wangale musu get sanda suka karasa maine parlour babu kowa sai karar AC da tv dake kunne ita kadai take burarin ta.
Sallama suka dinga zabgawa amma babu amsa"ke muzauna kodai bacci takeyi matar gidan"Inaga Mami tunda munyi sallama munji shiru madan jira muga ko zata fito"akallah sàida suka shafe 20mnt kome kama da Sahar basu gani ba"anya tananan kuwa Mami ta kalli Humaida gaba daya zaman ya fara gundurar ta."Tun sanda suka fara sallama tana jinsu amma tai kunnan uwar shegu dasu"saima kara gyara kwanciyarta da tayi taci gaba da chart dinta da samarinta"jin anci gaba da damunta ta mike rai bace ta fara taking steps tunda ta fito suka zuba mata idanu daga ita sai vest da wani dan guntun wando"wai wanene yake damuna da sallama in ba'a amsawa mutum ba basai ya koma ba"ni wllh na tsani naci arayuwa ta."Ido bude suke kallon ta da tsananin mamakin furucin ta"Sahar kin gane wadanda suka zo kuwa"sai Lokacin ta dora idanun ta akan na Mami"wani malalacin murmushi Sahar ta saki"au ashe kece aida bangama tantance ki ba sàida kikai min bayani"kinsan akwai 'yan maula da suke damuna na dauka ko daga cikin su ne.
Murmushin dake kan fuskar Mami bacewa yayi bat"Zuciyarta bugawa take kamar zata fado"haka Humaida tai mutuwar zaune tana maimaita kalmar 'yan maula"samun wajan zama tai babu abunda ya dame ta da kayan jikin ta"to ya gida Mami tunda kika haifamin miji dole akwai girmamawa tsakanin mu"Talatu ta kwallawa wata mata dattijuwa da aka samo mata dan ayyukan gida"yawwa ga baki nan ki kula dasu abasu suci su koshi"mikewa tai toni zan koma ku gaida gida"gaba tai tabar su azaune gumin tashin hankali na ketowa Mami idanun ta har yaji yake saboda yadda Zuciyarta take bugawa kamar zata tsage biyu.
Jiki magayi Mami yanxu ma aka fara bakiga komai ba.In
kinki sharar Masallaci zaki ta kasuwa.
.....Mrs Baba 🌹 Bello Abubakar.
......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 59_60
"Mikewa Mami tai ko ganin gabanta batayi"neman faduwa take Humaida tai saurin ruko ta"Talatu binsu tai da kallo tana da tabbacin,'yan uwan me gidanne tunda taga irin wulakancin da Sahar din tai musu"back sit Humaida tasaka Mami da zuciyarta take suya da tafarfasa"me kenan haka halin Sahar yake ko aljanune suka shigar jikinta"ko kuma dama lullubin biri haj Hadiza sukai mata"an nannade kura da fatar akuya"babban tashin hankalinta rashin ganin danta"awane halin take sai yanzu ta tabbatar ba Alkhairi ne ya boye shiba akwai wata akasa"gumin fuskarta ta share.Sanda suka koma gida Mami kin yadda tai asan halin da take ciki"dan aganin ta bekamata a fara yimata dariya tun yanzu ba"haka ta daure tana yake dole"suna shiga Innayi ta taresu da tambayar ina Rayyan dinta yana lafiya kuwa"wani abu medaci Mami ta hadiye yana lafiya Innayi"aiki aka turasu shiyasa bama samun wayar sa"haha koda naji nidai nasa da hankalin sa da lafiyarsa bazaiki zuwa gidannan ya gaida mu ba"to Allah ya dawo dashi lafiya"Ameen Mami ta amsa Kuka nason kwace mata.
"Kallo daya Umarni tai mata ta karanto tsantsar tashin hankalin da take ciki"tasan wacece Fannah in tana cikin farin ciki tasan abunda takeyi"da tasamu yadda take so ayadda taje gidan danta ta dawo saikaki tana yada habaici da nuna musu abunda ta samo"amma babu ko daya shiru takame bakinta."Tsam Mami ta mike ta karasa bedroom din ta"saidata shige canciki kafin ta fashe da kukan dayake taso mata tun adazu"kuka take tana tsinewa Hadiza data cuceta ta bata diyarta mara tarbiyya"Indai ita tahaifi Rayyan ya zama dole ya saki Sahar(hmm àah Mami anya hakan zai yiwu)saidata gama kukanta babu wanda ya lallasheta tagaji tai shiru.
"Tunda Humaida ta fara sanar da ita abunda ya faru hankakinta yayi mummunan tashi"abunda ta jima tana tsoro ya tabbata"Fannah ta kashe rayuwar danta da kanta"Umami bata furta komai ba gaba daya harshanta yayi mata nauyi"kwallar tausayin Canal ta ciko a idanun ta"ajiyar Zuciya ta sauke kafin ta kalli Humaida"wannan din yazama sirri karnaji kinfadawa kowa wannan Maganar ko Innayi bana son ta sani zaa shawo kan lamarin in sha Allah"gyada kai Humaida tayi zuciyar ta babu dadi ba Mami ta tauyawa ba"Yayan su take tausayi dan Mami kome tagani ita tajawa kanta.
Bangaran riyyah ta samu tarba ta musamman a wajan Zuhura"tayi matukar murna da zuwan ta"Mijin Botool me kudi ne sosai babban Gida ne dagani kasan ankashe nera kafin ginin wannan Gida"shi kansa Yayi murna da dawowar riyyah gidan sa ko ba komai 'yar sa tasami 'yar uwa dama ita kadai take rayuwa acikin gidan babu abokin hira"dakin Zuhura ne ya zama nasu su biyu komai tare sukeyi"sa'anni ne ita da Zuhura shiyasa suka karajin dadin zama da juna.Makarantar da Zuhura take zuwa nan aka saka riyyah ss one aka kaita"ranar riyyah har kukan farin ciki tayi ashe Allah zai cika mata burinta"dama ance bayan wuya sai dadi.
"Tafiya ta mika yanzu Sahar mulkinta take zubawa"bata da shamaki da fita a duk sanda taga dama"ko yaushe tai raayi zata dauki mukulli tai waje koda Yayammu yana nan bashi da kata bus sai Abunda matar gidan take so shi za'ayi"bakaramar damuwa Sadik ya shiga ba ganin yadda rayuwar Aminin sa ta kasance"ko hanyar gidan su baya son bi kai atakaice madai ya manta da su"har barrack Abbu ya biyo shi saboda ya kasa jure rashin sa"amma Abunda ya girgiza Abbu tsayawa yayi yana kallon sa gaba daya bema gane shiba"sàida Abbu yayi da gaske kafin ya iya rike kansa da kyar yakai zaune"dan babu wani shayi Canal ya rufe idanun sa ya dinga zazzagawa Sadik masifar kamme zai shigo masa da bako batare daya nemi izinin sa ba"Abbu kallonsa yake kamar idanunsa zasu fado tsantsar mamaki da kaduwa sun hanashi motsawa daga zaunan da yake.
"Idanun sa na kan Canal still shiyake kallo ganin sai huci yake kamar zai rufe su da duka"Abbu bece komai ba yamike ya fice daga office din tsaf ya karance shi tabbas wannan ba dansa bane wanine daban yake gani amma ba zahirin dan sa bane."Sadik da idanunsa suka ciko da hawayan tausayin Abbu ya kauda kansa daga kallon Abbu yayi matukar bashi tausayi tabbas ya tabbata Akwai Abunda sukaiwa abokin sa"har mota Sadik ya raka Abbu da yakejin Numfashinsa na kaikawo a makoshin sa"cikin karfin hali ya sakarwa Sadik murmushi da dan dukan kafadar shi."Jan motar driver ba yayi Sadik ya bisu da kallo yana furzar da zazzafan huci"tsabar Sahar na zagaye dukkan ilahirin jini da jijiyar"yayi alkawarin saiya tarwatsa mata dukkan shirin ta"saiya gano Abunda taiwa abokin sa.
"Mami ta matukar ramewa ta kode ta fige tsananin damuwa tai mata yawa"Kiran Hajiya Hadiza tai sukai kaca kaca zagi in zaga sukai atsakanin su"fada sosai sukai kowa ranta bace ta sauke wayarta"ayau dai Mami ta kasa jurewa zubewa tai akan guiwowinta ta fashe da kuka me tsuma zuciya"hatta aiki yanzu intaje bata iya tabuka komai daga karshe sai sallamar ta akai saboda basa san wasa"lallai Hadiza sun shammace ta sun matukar bata mamaki"Abbu daya shigo yanzu kallonta yayi damuwa cunkushe a zuciyar sa"ganin tama kara bata masa rai yayi ko kukan jini zatai bazai taba jin tausayin ta ba"samun waje yayi ya zauna jin jiri na neman kayar dashi"Lumshe idanun sa yayi hango dansa daya haifa acikinsa ya manta dashi kwata kwata kamar betaba ganin sa sai ayau din.
Rarrafiwa Mami tai ta kama kafafun Abbu dake zaune"dan Allah Tahir ka rufamin asiri ka nemomin dana"nayi nadamar kuskaran dana aikata wllh yanzu na gane hanyar gaskiya"ashe dama yaudarata sukai suka kaini suka baro"na hada ka da girman Allah kayi wani abu akai zuciya ta na daf da tarwatsewa."Zuba masa idanun ta yayi yana watsa mata wani irin kallo rai bace ya janye kafafunsa daga hannun ta"bantaba sanin cewa baki da kunya ba sai yau"har yaushe akai daran balle garin ya waye"right dinki na baki da ko kin mance"kici gaba daga inda kika tsaya"kamar yadda kika nema abaya na barki kikai son ranki to haka yanzu ma zan zuba miki ido ki girbe Abunda kika shuka da hannun ki.
"Ko kin manta 'yar gidan tarbiyya jika zabo masa,,ga kunya,,,ga Addini,,,ga kudi ga kyau,,,ga kuma uwa Uba kunya bayan wadannan me kuma kike nema kin riga kin samu dan haka kici gaba da cin sharafinki Fannah ga 'yar gidan tarbiyya can kinkai gidan danki yanzu saiki haifi wani dan a mayar miki da suna Rayyan amma ba waccan wanda kika yiwa Aure ba"banajin zai kara dawowa karkashin inuwarki da mulikinki"bance miki har abada ba amma ba anan kusa ba."Kofarki abude take right yana hannun ki''mikewa yayi ya zagaye ta yabarta tsugunne a wajan sake rushewa tai da kuka nadamar maganganun data fadawa Mijinta akan wata can"ashe macuciya ce azzaluma bazata taba yafewa Hadiza da tsinanniyar 'yarta ba.(🤣🤣🤣daga baya kenan,,lallai abu ya ta azzara yau Mami ta tsinewa zabinta Sahar)."Ba wai ita kadai take wannan halin ba hatta Umami da Innayi suna cikin halin damuwa kai kaf ahalin dan Barno hankulansu a tashe yake ganin gagarumin shirin da sahar tai akan Rayyan ba karamun shiri tai akan sa ba.
Yau dai Mami kasa jurewa tai sai taje ko ita ko Sahar din"babu wanda ta sanar zataje gidan ta dauki kafa tatafi"sanda ta dai daita parking tajuyo karar kida na tashi ga hayaniya da take tashi tun daga cikin gidan har parking space"balle murfin motar tai ko rufe motar batai ba tai gaba zuciyarta na azalzalarta taje taga abunda suke aikatawa acikin gida"tsayawa tai cak a kofar shiga parlon zuciyarta na tsananin harbawa"kare musu kallo take kamar yadda take kallon su"kowacce su sigari ce a hannunta tana busa hayaki,,ga kwalaban wine nan sunsha wani an tsiyaya a cup yadda kasan jus suke sha"karasa shigowa parlon tai tana kankance idanu sai Lokacin idanun ta ya fada kan Sahar da take zaune ta hanya kara hudu ta biyar ce a hannun ta.
"Cikin zafin rai ta karasa gaban Sahar din cikin shammata ta takarkare ta kashe face din Sahar da wani shegen mari"shirune ya ratsa parlon gaba daya sun tsaya da abunda suke suna tunanin wacece wannan"kan Mami ta gama daidaita hannu ta taji an yarfa mata mari hagu da dama"saidatai luuu kamar zata fadi tai ta maza ta tsaya akan kafafunta"dago idanu tai dan ganin wanda yayi mata hakan Sahar ce tsaye a kanta tana huci da jijjiga jiki"nuna Mami tayi da dan yatsa"wannan kadan nayi miki na gargadine,,matukar kika kara daga kazamin hannun ki kika mare ni,, murmushi Sahar ta saki aranar zan tabbatar miki danidin ko wacece zan manta da matsayin da kike dashi"ke kina cire wannan daga zuciyar ki kisa aranki danki ya mutu tuni an binne shi,,kisawa zuciyarki hakuri ya zama mallakina ni kadai"babban kuskaran da zaki karayi arayuwarki shine kara yunkurin taba lafiyar fatata"ko Mom ta mareni ayanzu babu abunda zai hanani ramawa balle wata ke"kallon kawayan ta tai da suke parlon kunsa wace wannan a'ah saikin fada"dariya ta sheke da ita to hawan jinina ce"kunsan badan murigayiya na aura ba"dariya suka fashe da ita.
"Mami bata san sanda hawaye ya dinga sauka daga idanun ta ba"hawayan bakin ciki da takaici hawayan damuwa da nadama"hawayan kaico data tirsasa danta ya auro bara gurbi."Baby Sahar ta bude murya wajan kwallawa Canal kira ashe duk drama din da ake yana kiching yana girki"futowa yayi ya karaso inda suke"tsayawa yayi batare da yayi magana ba"tunda ya fito Mami take kallon sa"yaushe rabonda tasashi a idanun ta tun befi kwana 3 da Auren kaddara ba."dafa kafadar sa Sahar tai kasan wannan nuna Mami tai tana dariya kasa kasa"girgiza kai yayi alamar àah"yanzu da za'a ce tsakanin nida ita kazabi wadda kafi so wazaka zaba"ke mana"ihu suka saka da tafi kiss Sahar ta manna masa akumatu''aikin ka yana kyau mutumina maza aje aci gaba da aiki"babu musu ya juya ko kallon Mami bata ishesa ba.
"Fannah kinga irin karfin ikona ko"shiyasa na baki shawara me sauki kije ki dage ki takarkare ki haifo wani dan sai asaka miki Rayyan amma wannan ya zama na Sahar ita kadai,,yauwa zaki iya fita tunkan na fitar dake"wuyan rigar Sahar Mami ta damka yau koni koke saina sauke dukkan rashin kunyar da take damun ki"nida dana uwar kice ta haifarmun yaron cikin fitar hayyaci Mami ke furta hakan"ba karamar shaka taiwa Sahar ba hakanne yasa ta fara kakarin mutuwa"da guda kawayan ta suka zo suka fara dukan Mami tako ina dakyar suka samu suka banbare hannunta daga wuyan Sahar aiko yayi jajawur."Sahar batai wata wataba ta dauki kwalba ta rotsawa Mami aka dandanan jini ya wanke mata fuska"jirine ya fara dibar ta tun tana gani dishi dishi har ganinta ya dauke kunnuwanta suka daina dakko mata maganganun su.
*Tsoro ne ya kama su karfa tazo ta mace musu su shiga uku kallon kallon suka farayi atsakanin su.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 61_62
Teena ce ta tsugunna agaban Mami munshiga uku bata Numfashifa"Sahar da gumi ke keto mata duk iskancinta tana tsoron ace tayi kisan kai"duk da tasan ubanta yana da kudin da za'a iya rufe case din"amma sanin wadda ta tabadin sun dafe madafan iko suma yasa hankalin ta kara tashi"jiki na rawa ta kara hannunta a hancin Mami shiru babu wani labari"sallama suka ji anayi a kofar parlo"gaba daya yawun bakin sune ya kafe kaf kallonsa ya mayar kan wadda ke kwance a tsakiyar parlourn"ganin Mami ya sashi afkowa cikin parlon"Sadik ne Allah ya jehoshi a wannan lokacin dalilin wayar da sukai da Canal akan wani aiki daya taso yanemi yazo su tattauna"karfa kuce abota suke kamar baya a'ah yaro ne da ubangidan sa"wannan amintakar da shakuwar da sukai a baya Canal ya mantata yadda kasan anyi nasa wankin kwakwalwa haka ya manta da kowa da komai sai Sahar da iyayanta.
Kallon tsana da kyama ya watsa musu musamman Sahar sàida zuciyarta ta girgiza"tsantsar tsanarta ta hango kwance a idanun Sadik din haka kawai taji tana matukar shakkarsa da shayin sa"cak ya dauki Mami yayi waje da ira"duk abunda ke faruwa Yayammu be sani ba yana kicking yayi kace kace yana girki"Numfashi suka sauke ganin an dauke ta sai lokacin hankulansu ya kwanta"amma ba wanann ba ta mutu ko tana raye shine abunda basu sani ba"ko kuma nace abunda bata sani ba dan itace aruwa"daya bayan daya suka dinga daukar jaka da takalman su suna fita"dama ba'a zancan mayafi baya daga cikin tsarin su"tas suka gama guduwa suka bar Sahar ta runtuma uban tagumi"gumi sai tsatstsafo mata yakeyi."Wani prvt hospital yakai Mami cikin gaggawa suka karbe ta"dalilin ganin kakin daya ke sanye ajikin sa"dukufa sukai wajan ceto rayuwar Mami.
Wayar Umami ya kira bayason dagawa Abbu hankali"halin da ake ciki ya kora mata salati ta saka tare da fashewa da Kuka tabbas suna ganin jarrabawar rayuwa"suruka ta daki surukarta ta kara tabbatar da Sahar ba 'yar arziki bace."Bata sanar da kowa ba ta taho asibitin hankali tashe,,dakin da aka kwanta da Mami ta wuce kanta yasha katuwar plaster goshinta ya kumbura sosai"tausayin tane ya kama Umami kowace uwa tana san danta amma dannewa take tayi hukunci da abunda ya face"amma wagari ya waya garin kishin danta ta dauko musu masifar datafi karfin su"wasa wasa Mami har yamma bata farko ba hakan ya tashi hankalin Umami da Sadik dan dole suka sanar da Abbu halin da ake ciki"zuga sukayo suka taho asibitin hankali tashe sanda sukaga yadda Fuskar Mami ta haye sàida suka zubar mata da hawaye"sanda sukaji wadda ta aikata mata hakan sun matukar fusata ainun.
"Kaitsaye sukai zuga mazan su da matansu Kamal Asad Ammar Humaida da sauran kannan su akalla zasiyi su goma suka nufi gidan Yayammu da kudurin sai sunyiwa Sahar tsinannan duka"sanda sukaje megadi yaso hana su shiga amma suka nuna sam saisun shiga babu yadda zaiyi haka ya bude musu"hakimar tana kwance akan kujera tana kallo tana babbaka dariya"tuni ta manta da abunda ya faru a dazun"basi wata wata ba suka janyota daga kan sofar sàida kanta ya bugu da kasa"arazane ta mike taga suwa nene sukai mata wannnan aika aikar saidata razana ganin sun jere agabanta babu alamun sassauci ko kadan a fuskokin su kallon tsana da kyama suke mata"bude baki tai zatai magana Kamal ya tsinka mata mari hagu da dama"rufe ta sukai da azababban duka sàida suka tabbatar sun luguiguita mata jiki baki da hanci sàida suka fasamata shi"ko Numfashi bata yi sannan suka kyaleta hakamma badan sun huce ba.
"Talatu me aiki tana daki tana Allah ya kara dama itama dazu ta gama zageta tas da girmanta da komai tayi jika da ita amma bata gani ba"godiya tai ga ALLAH da suka taru sukai mata rufdugu suka ci Ubanta ko za'a samu bakin rashin kunyar ya mutu"ficewa sukai babu wata damuwa a tattare da su sai da suka koma suka tarar da Mami ta farfado sai kuka take bakin ciki kamar zai tarwatsa zuciyar ta."Duk yadda Innayi take jin zafinta saidata tausaya mata tasan tabbas abunda ciwo matar danka ta dake ka"Abbu yana tsaye be tofa tasa ba shifa har yanzu be farajin tausayin Fannah ba kowa yasai rariya yasan zata zubda ruwa"yanzu da abu ya kwabe mata shine zata zo ta sasu agaba tana Kuka.
"Sanda ya dawo ya hango Sahar yashe a tsakiyar parlourn ammata jina jina hankali tashe ya kinkimeta sai asibiti"saidata sha karin ruwa da allurai kafin ta dawo hayyacin ta"Kuka ta dinga rusawa babu ji ba ganin"tambayar duniya taki magana ranta yayi kololuwa wajan baci"saidata gama kuka kafin ta sanar dashi wasu bata garine wanda bata sani ba suka zo har gida suka zaneta"kamar Zuciyar Yayammu zata babbake an taba masa mata daya san suwanene wadannan babu abunda zai hana be hukunta su da hannun saba amma yanzumma zaiyi bincike akai basu daki banza ba.
"Kamar yadda yayi alkawari saidaya binciko su aiko har kofar gidan Abbu motar sojoji ta taka"Lokacin an sallamo Mami daga hospital tana kwance a parlo zuciyar ta na bugawa"megadi ne ya shigo har parlon ya sanar dasu ga sojoji can akofar gida"gaba daya suka dungumo suka fito harabar gidan"bayani sukaiwa Abbu cewar Oga ne yace a zo a tattare kaf yaran gidannan a binciken daya gudanar ya gane sunje har gidansa sun lakadawa matar sa duka"ba laifin tsaye babu na zaune"gaba daya wuta ce ta dauke musu bakin su har rawa yake wajan tambayar wane ogan nasu Canal Rayyan Attahir Rayyan"kallon kallo aka farayi atsakanin su Mamaki da alhini na dada mamye dukkan zukatansu"yayansu ne ya bada umarnin azo a tafi dasu"Abbu kallon sojojin kawai yake sunkai su 30 kamar wadanda suka zo kama gagaruman 'yan ta adda"gaba dayan su kansu a sunkuye yake zukatansu sam ba dadi sanin su wanene sudin awajan ogan nasu"amma babu yadda zasiyi matukar suka sabawa umarnin sa Zasu shiga cikin matsala"suna Mamakin yadda ya manta da sudin suwanene agarshe har yake Jayayya dasu yake son jefa ahalinsa acikin matsala"a yadda suka lura akan matarsa tabbas har kisa zai iya yi batare dayaji komai a zuciyar saba.
"Daya bayan daya yake kallon 'ya'yan nasa da sukaje suka jawo musu masifar suna zaman zaman su"cikin dakiya da nuna jarumta ya basu umarnin tafiya dasu Kamal din"hatta Humaida sàida aka tattara harda ita aka dura amota tana kuka tana tirjewa haka aka tafi da it's"Mazan kuwa ko kadan basu ji wani abu a zukatan su ba ko banza sàida sukaiwa matar tasa jina jina"in basu aikata laifinba shine zasuji haushi da an hukunta su amma tunda sun aikata babu wani abu dazai taba Zuciyar su"idanun Mami tsiyayar da hawaye yake ganin asanadinta yau 'ya'yan su zasu tafi barrack matsayin masu laifi"Umami da Innayi tsabar damuwa sun kasa furta ko kalma daya sun tabbatar Sahar ba karamin tsafi taiwa Rayyan ba amma bakomai akwai Allah.
"Sanda a kaisu gabansa duka yayi musu na fitar hayyaci hatta Humaida sai data sha matuka ahannun sa"ya tabbatar musu saiyaga wanene ubansu a kaf garin maiduguri dazasu je gidansa su dakar masa mata"ba dukan da yayi musu ne ya razanar dasuba sai furucin sa basai yaga wanene ubansu me yake nufi da wannan maganar"kuri sukai suna kallon yadda yake zazzaga masifa daga karshe yasa awatsa su a dakin horo duk yadda Kamal yake da dakiya da juriya sàida yayi hawaye"yayan su me tsayawa adukkan lamarin su yau shine yasa aka kaisu dakin horo meyake shirin faruwa da rayuwar yayan su.
"Hankali tashe Sadik ya shigo barrack din danjin mummunan labarin abunda ya faru"tuni garin ya dauka Canal Rayyan ya haukace tunda har yaje ya yayibe 'yan uwansa ya dannasu a cell"duk wata hanya da Sadik yasan zaibi wajan fitar dasu abu ya gagara"zazzafan gargadi ya yiwa yaran Canal kan wanda ya sake ya sake taba su"Abbu tunda aka tafi dasu bece komai ba tsahon kwana biyu"da kokarin Sadik dana Abee suka isa gaban General cikin gaggawa yayiwa Yayammu waya da nuna zallar bacin ransa akan ya saki yaran daya kama"bakaramin jin zafin hakane Yayammu yayi ba bashi da yadda zaiyi haka ya sake su saboda umarnine daga sama"lokacin da suka koma gida ba karamar kaduwa sukai da sukaga yadda su Asad suka rame ma sunyi baki musamman Humaida ta kara gogewa"ahakan wai tana karkashin kulawa Sadik yayi me yiwuwar ganin ba'a sake taba su ba"kai tsaye wajan Umami suka wuce sosai sukejin zafin Mami koma menene ita ce ta jawo musu"hatta Humaida bata tafi wajan Mami ba jikin Umami ta fada tare da fashewa da kuka"shafa kanta Umami tai batare da tace komai ba tana hadiye wani abu me mugun daci aranta.
Malamai Abbu ya samu yadinga basu sadaka ana saukar Alkur'ani"masallatai ya dinga kai sadaka adafa abinci a gida araba sadaka dandanan asirin da akaiwa Canal ya fara sanyi"a yanzu sam baya shayin Sahar fada suke sosai in tabashi Umarni ya daina bin umarnin ta"gashi ya masifar sama idanu ya hana kowace 'yar iska shugo masa gida"yawo dai bai hanata fita ba gaba daya bayajin kishinta a zuciyar sa,,hankalinta fa inyayi dubu ya tashi bazama sukai suka koma wajan gobe da nisa"ananne ya tabbatar musu aiki na daf da lalacewa matukar iyayansa suna raye bazasu taba barin sa haka ba,, shawara daya saidai a shafe dukkan tunanin sa daga zukatan su.
Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubukar
......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 63_64
"Kallan juna sukai ita da Mom dinta"ayi abunda ya dace dasu mugu dan muguwa"dariya ya sheke da ita"ina son Mutum mara imani kamar ni"tabbas kedin dake da uwarki kun tabbata marasa rabo baku da rabo"fashewa ya sakeyi da dariya ko ajikinsu burin su bukatar su ta biya"wannan Aikin babban aikine wannan karan jinin dabba yayi kadan awannan aikin rabashi da kowa da komai ba karamin yaki bane"saboda iyayansa sun rike Addu'a koda yaushe cikin bautar Allah suke"aikin da zanyi akansu ni kaina sai nayi taka tsantsan"ban cemiki bazasu taba tunawa dashi ba har abada"amma ki kiyaye faruwar hakan"kiyi duk yadda zakiyi adauke shi daga garin a canza masa wajan aiki"yayi nesa da dangin sa da 'yan uwansa"matukar suna haduwa tofa akwai lokacin da tunanin sa zai dawo zukatan su ki kiyaye wannan.
"Gyada kai ta dingayi kamar kadan garuwa tab lallai yazama dole ta rabashi da kowa nashi"dukkan dukiyar ta dawo karkashin ikon ta"bata son taga kowa acikin Duniyar ta daga ita saishi"naira dubu dari takwas ta fara dire masa kafin alkalami kafin aciko ragowar"farin ciki fal zuciyar su suka dawo gida."Cikin sati daya da fara aikin gobe da nisa mummunan sihirin daya shirya akansu ya fara tasiri ahankali suka dinga mantawa da Rayyan acikin ahalin su"hatta sunan sa ya bace babu wanda ya kara tunawa dashi balle ciwon ran rasashi da sukai harma siyi wani motsi akan taimakon sa"sàidai cikin zukatan su sunaji kamar andanne musu zuciya da wani irin dotse me nauyin gaske"suna ji aransu sun rasa Wani muhimmin wani abu acikin rayuwar su"gaba daya ahalin sai suka tsinci kansu da saina walwala duk wanda zaka gani to babu wani farin ciki akan fuskarsa.
"Bangaran Canal ma haka yakeji tabbas akwai wani abu daya rasa to menene wannan abun meya rasa"in ya zurfafa tunani yanzu ne kansa zai fara azbar ciwon"bangaran zaman sa da Sahar ayanzu sam bayajin wani abu akanta yanaji tamkar akan dole yake zama da ita"dukkan wani aiki daya saba yi mata abaya yanzu ya daina yinsa kullum fuskarsa a hade"tsahon wata Biyar da Auran su amma har Lokacin babu wani abu daya taba shiga tsakanin su"Sahar kamar tai hauka duk yadda takai da sha'awar sa da kwadayinsa hakan ta ya gaza cimma ruwa"har Asibiti ta tisa sashi suka tafi dan abinciki lafiyar sa magana daya ce lafiyar sa kalau babu kuma abunda yake damunsa"duk sanda suke tare kamar abun arizi sai ankama harka rimi rimi amma da anje bakin border al amarin zai tsaya cak,,alokacin ne makaman yakin zai kama bacci lakadan ko alamar motsi bazai karayi ba duk zulamar Sahar tana ji tana gani abu ya gagare ta.
Hakan saiya haifar masa da azababban ciwon mara me tsanani wanda ya dangana shi da gadon Asibiti"abinci ken da sukai suka gano sparm ne ya dankare masa kuma hakan zai iya jawo masa matsala"akan magani suka dorashi wanda zai taimaka masa wajan raguwar halin da take ciki"Sahar ko kadan bata ji wani abu akan rashin lafiyar tasa ba can ta matse masa tunda tana da Masu biya mata bukata a gefe yama mutu bata da asara"halin da yake ciki saiya kara sawa ya dawo mugun miskili ko kadan baya fara'a babu wata magana datake hadashi da kowa"ana haka akai masa sauyin wajan aiki zuwa ABUJA sosai Sahar taji dadi dama babban burinta yabar garin maiduguri sai gashi faduwa tazo dai dai da zama.
"Zuwan su ABUJA saiya kara gogar da idanun Sahar ta kara sanin takan duniyanci"manyan Alhazai takara samu take shan sharafin ta"a bangare guda damuwa na kara cin zuciyar Rayyan yakan kurawa wayarsa idanu kamar zuciyar sa nason tuno akwai wasu muhimman mutane daya ke kira da ita abaya"amma suwanene gaba daya ya bincike contact dinsa daga number wajan aikin su"saita Haj Hadiza da Sahar su kadai ya gani aciki"(Abunda be sani ba gaba daya Sahar ta dura su a blacklist shine dalilin da baigansu ba)haka rayuwar taita garawa a hankali"Sahar kasashe take fita duk inda taga dama"zuwa tai aka daure mata mahaifarta sabida kar ta na daukar ciki azo asami matsala takara sakankancewa tana cin karanta babu babbaka"tana murza naira yadda take so ATM din Yayammu a hannun ta yake duk wani kudi dazai shigo tasan da zaman sa.
3years Ago
"Cikin takun kasaita da aji kyawawan 'yammatan suke takowa tamkar bazasu taka kasaba"tundaga nesa Abbah da Ummi suke sakar wa 'ya'yan nasu murmushi hannu Ummi ta bude musu cikin matukar farin ciki suka fada jikinta baki dayan su"dago fuska daya daga cikin su tai"saidana koma baya na kara ware idanuna akanta"Ansariyyah na furta cikin tsananin Mamakin yadda ta goge ta murje ta zama cikakkiyar budurwa mejini ajika"mecin shrafinta da ganiyar kuruciyarta"murmushi ta sakarwa Abbah dayake kallonta hannu ta mika masa I'm missing you Abbah"murmushi ya saki yana shafa kansu ita da Zuhura natayaku murnar kammala karatun ku."Juyawa nai kare wanann matar kallo sai lokacin na lura ashe Antymmu ce ta murje takara zama babbar mace me aji"kyau da kwanciyar hankali sun zauna ajikin ta"Uhm kaji wata shagwaba Secondary school fa kuka gama amma sai wani hura hanci kuke kamar wadanda kuka gama university"dariya sukai Abbah ya kalleta kodai bakin kike musu"ya za'ai yara na su gama babbar makaranta amma kidinga ba wani abun arziki sukayi ba"tabe baki Antymmu tai wadda suke kira da Ummi nikam inhar ba digree sukai ba baza su birge ni ba.Murmushi kawai sukai suka dunguma suka shige mota.
"Zubewa sukai a parlo suna maida Numfashi"dan Lumshe idanun ta tayi zuciyarta babu dadi duk da tana farin ciki da wannan rana amma babu ahalinta ko mutum daya"babu Ummin ta da Abbanta"masoyan ta ababan kaunarta"sai kuma mutum daya daya kasa barin zuciyarta ta kuma kasa mantawa dashi yana nan zane daram akwayar idanun ta",ya samu matsugunni mai girman gaske a zuciyar ta"Zuhura ce ta dafa kafadar ta"sis tunanin mekikeyi haka"murmushin yake ta kakalo tana duban Zuhura babu komai sister ina tunanin Abba da Ummi ne naso ace sunga wannan babbar ranar amma saidai kash basa cikin Duniyar nan ahalin yanzu"hawayan daya bata mata fuska ta goge amma bazan taba butulcewa rahamar Allah da yayi min ba"yabani iyaye kamar Abbah da Ummi na tabbatar abunda iyaye na zasumin shi sukai min ahalin yanzu babu abunda zanyi musu sa Addu'ar Allah ya basu Gidan Aljannah.
Murmushi Zuhura ta saki tana sharewa riyyah Hawaye"ni sister tunda kikazo gidannan bantaba jin muna da banbancin matsayi ni da ke awajan su Ummi ba"sun zama iyayaenki tun tuni ki dauka dama can su suka haifeki"murmushi riyyah ta saki tana gyada kai alamar taji abunda Zuhura ta gaya mata."cikin dariya Zuhura take kallon ta amma ba wannan damuwar ce ita kadai take damunki ba"anya bakya boyemin wani abu?hararar ta riyyah tai tana ya mutsa fuska"tunda kina tunanin na boye miki wani abu basai ki gano da kanki ba"uhm dan dai banga dama bane amma da tuni nagano abunda kike boyewar kinsan dai ina da saurin ganiya"to nabaki gari matukar baki canko ba zakisha maruka awajena"idan kuma na canko fa? Zuhura ta tambaya"kafada riyyah ta daga saikiyi hakuri,,,haba dai ai wllh nima mari zan feffellamiki hagu da dama,, murmushi riyyah ta saki to ke kika sani nidai nabaki assignment kije ka lalubo abinda yake damunnawa.
Mikewa tai kinga tafiya ta,nagaji bacci nakeji sai kin taho,sama tahau tabar Zuhura a zaune tana cigaba da tsokanar ta."Kan bed dinsu ta fada tare da rungume flow a kirjinta,,Lumshe kyawawan idanun ta tayi masu matukar kyau da tsari,, kyakykyawar fuskarsa take gani acikin idanun ta"tsayin shekaru bata ganshi ba tana matukar san ganin sa,,saidai ta wace hanya yaushe zata ganshi"zuwan su Uku maiduguri amma kome kama dashi bata gani ba"abunda ya daure mata kai ko sunan sa babu wanda yaji yana ambata sosai lamarin ya daure mata kai"amma ba mamakin ko baya kasar ne baki daya wannan tunanin tasawa Zuciyar ta."Bata face tai tare dajin haushin kanta riyyah ina ruwanki da shi wai yana can tare da matar sa suna shan soyayyar su"sai taji ranta ya baci har wani daci makoshin ta yake,,tana jin sanda Zuhura tashigo tai lif kamar bacci take nan kuwa idanun ta biyu,,tunaninnika sun Aure ta matuka.
"Barrack ne babba yana da katukar girma da kawatuwa"aciki akwai Makaranta da gidajan su har kasuwa ce acikin barrack din babu abunda bazaka samu ba"Wani babban Office na hango wanda a kalla sojojin dake tsaitsaye a kofar office din sunkai su dari layi layi sukai sun kame kamar gumaka"da alama suna jiran mamallakin office din ya fito,,saman office din na kalla baro baro aka rubuta Major Rayyan Attahir Rayyan,,ido waje nake kara karanta abunda nagani mamaki na kara kasheni yaushe ya tashi daga Canal ya koma Major"karar bude kofarsa ya sasu kara nutsuwa"cikin kakin sa na soja ya fito kansa sanye da hula gaba daya hannayan sa zube suke a cikin wandon kayan"in garman matashi me jini ajika dan kimanin shekara 35 ya kara kyau da haiba,,amma face dinnan babu fara'a ko kadan tsayawa yayi agaban su sara masa sukai suka kara kamewa.
"Kamar bazai ce komai ba tsahon mintuna goma yana karantar yanayim su"gyaran murya yayi kafin ya sauke numfashi mezafin gaske gaba daya Zuciyar sa a cunkushe take"bayajin kowane irin farin ciki acikin rayuwar sa"sai tsantsar damuwa."Abinciken damuka gabatar harin da a ka kaiwa R A R Store ayau ma akwai yiwuwar zasu kara kawo wannan harin na fashi da makami"ina so ku kara kulawa yadda ya kamata kusa idanu akan masu shige da fice kumasan ce a nakare yes sir suka hada baki tare da sara masa,,juyawa yayi ya fada office dinsa wanda ya gaji da haduwa,,kan kujerar sa ya koma tare da lumshe idanun sa da suke dauke da matukar gajiya.
"Misalin karfe 4 su riyyah suka shirya tsaf dan fita siyayya"cikin fasifa Zuhura take fadin wai dan Allah riyyah kekam kin cika nuku nuku kishafa wancan kin goga wannan amma bazaki hakura ba"harara riyyah ta watsa mata kinga barni in kuma acan zan hadu da mrs no name dariya Zuhura tasaka"lallai aiki ya sameki dik samarin da suke binki anan bakiga wanda ya miki ba sai munje can zaki samu to zan zuba idanu naga ko za'a hadu dashi"aiko zakisha Mamaki naji araina yau zan hadu da no name aha,,murgudawa Zuhura baki tai takarasa daura dan kwalin shaddarta."Shaddace ajikin su iri daya peach color sunyi matukar yin kyau"sai mayafi takalmi da jaka suka yafa,,turare suka feffesa kafin su fara sakkowa kasa"tunda suka fara sakkowa Ummi take musu tafi àah kaga 'yammatan Ummin su"irin wannan kashe kala haka anya yau ba surukai zanyi 'yan gaske acikin gidannan ba"dariya suka saka"Zuhura ce tai caraf zatai magana riyyah ta toshe mata baki"Allah kika fada saina miki rashin mutunci"àah me ake hanata ta fadamin nima kar ayi babu ni afadamin abunda ake boyewar cewar Ummi"fakar idanun riyyah tai ta kwasa da gudu ta buya abayan Ummi"riyyah biyota tai tana son toshe mata baki karta fada Ummi ta rike riyyah yauwa yanzu fadamin Zuhura"Ummi cewa tai yau zata hadu da gwarzan zuciyarta"dariya Ummi ta saki wannan shine abun boyewar"bubbuga kafa riyyah ta farayi Ummi ta cikata ta damko Zuhura,, Zuhura na can nesa tanai mata gwalo"nan kuma Ummi tana rarrashin riyyah tayi hakuri ta kyaleta.
Hmmm yanzu ma aka fara Sahar kinyi babban kuskure,,,,,,,!!!
Mrs 🌹 Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 65_66
Asslm Alaikum sisters,,ina godiya da nuna kauna ina fatan Alkhaiti agareku Allah ya bar zumunci."Sakamakon rashin Lokaci da nake samu bako yaushe zaku dinga samun posting sau biyu ba.Nagode
"Sàida Ummi tagama lallamar ta kafin ta hakura tana kara jefawa Zuhura harara data rike kunnan ta alamar neman afuwa"make kafada riyyah tai alamar bazata hakura ba"marairaicewa Zuhura tai alamar ita din"yadda tai dinne yabawa riyyah dariya harta tuntsure da dariya"murmushi Ummi ta saki tana karajin kaunar yarinyar a zuciyar ta"zuwan ta gidan ya saka su acikin Farin ciki"bata taba ganinta cikin damuwa saita wanzar da murmushi akan fuskarta"duk da tanaji a jikinta ta rabu da wani bangare na jikinta amma menene ta rasa"tana matukar jin kewa da kadaici"kamar tarasa wani abokin shawarar ta acan baya"jin hawaye na neman zubo mata tai saurin hayewa sama tana daga musu hannu da fadin karsu dade awajena"ficewa sukai batare da sun lura da yanayin taba"jingina tai da kofar dakin ta,,hawayan da take rikewa ne suka balle a kyakykyawar fuskarta,,daga karshe fashewa tai da kuka tabbas ta rasa wani abu tana jin zafi da kuna acikin zuciyarta"amma tunaninta yagaza kaita inda abunda ta rasa yake"mena rasa aruwata!! tai furucin tana watsar da kayan dake jere akan mirror dinta"Abban Zuhura da tun shigowar sa yake kallon ta"tsantsar tausayin ta ya kamashi"tsahon shekaru uku tana cikin wannan halin"Inama yana da damar dazai nemo mata abunda ta rasa din"abunda ta manta dashi din acikin rayuwarta"bama ita kadaina har ahalin ta"lamarin yana jijjiga zuciyar sa"alkawari ya dauka saiya tarwatsa dukkan shirin Sahar saiya dawowa da matarsa Farin cikin ta."Abinda Antymmu bata sani ba yana sane da rasa Rayyan acikin rayuwar su ya maida su wasu irin mutane masu zafin ziciya"jin wannan kadaici da damuwa yasa suka yanke alaka da kowa basa shiga harkar kowa.
"Rike hannayan ta tayi da take shirin fashe madubi"haba mar'atussaliha meyasa kika canza Fatima"ina wanann hakurin naki da tawakkalin dana sanki dashi"nasha sanar dake aduk sanda kikaji irin haka addu'a itace mafita"haba Batool din Innayi nafa sanki da tawakkali da kuma ruko da Addu'a"kici gaba da Addu'a da sannu zaki tuna da abinda kika manta"gyada kai tayi tana sakin ajiyar zuciya.
"Cikin Nishadi suke tafiya suna yiwa iliya driver hira sai babbaka dariya yake yi"labarin sanda kadangare ya shigar musu class suke bashi"yadda Zuhura ta takarkare ta saki fitsari awando"Zuhura ta cika fam sai darya suke mata."parking lot ya daidata tsayuwar sa"sai shige da fice akeyi a cikin store din"har park ne a ciki iyaye sai kawo yaron su suke suna wasa.
"Zuhura ce ta kalli riyyah yau dai muhau lilon can yana burgeni innaga yara da manya na hawa"tabe baki riyyah tai kije ke kihau amma babu wani lilo dazan hau dan maida kai baya kamar wata yarinya"harara Zuhura ta maka mata,,to da mece ke Inba yarinyar ba,,18years shine kike wani bude hanci ke Babba,,,hura hanci riyyah tai kinga Zuhura karki kure ni nai miki biji_biji kan mutafi gida Allah,,,dariya Zuhura tasa tab sannu Anty babba sai san girma kamar gyambo,,kije ki tason girman wama yake son shekaru yanzu haka kawai kazo ka mutu,, murmushi riyyah ta saki kece kike gudun mutuwa amma ni yanzu ko abun mutuwa nagani bazan gudu ba saboda yadda zuciya ta ta cika da imani Aljannah kawai nake hangowa.
"Wani shegen kallo Zuhura tai mata Allahu Akhbar kaga limaman saudiyya,,wato kin shirya tsaf mutuwa kike jira,,gira ta dagawa Zuhura alamar kwarai kuwa,, murmushi kawai Zuhura ta saki Allah ya kawo abun gudu inga kin gudu kin shiga uku awaje na,,daga kafada riyyah tai yazo din kiga inzan gudu ni yanzu har akwai wani abu dazan ji tsoron sa ai babu,, kyalkyale wa da Dariya Zuhura tai a'ah karfa ki cika baki inga ba haka ba,,'yar sa ido babu ma abunda zaki gani."riyyah ce ta kalli Zuhura wai me muka zoyi store dinnan nifa babu abunda zan siya,,kallonta Zuhura tai amma kinci uwar rainin hankali dama bakisan abunda zaki siya ba muka shigo eh man,,cab dijam,,sai kizo mu karasa bakery kinsan akwai aciki fanni fanni ne kome kike so zaki samu,,me zamu siya acan din riyyah ta tambaye ta,,ko 🥧 ne agasa mana ai bami zuwan banza ba,,ok muje tafiya suke a nutse sai surutun Zuhura dake tashi,,har suka shiga suka fito da ledoji guda biyu ahannun riyyah.
"Taku daya biyu sukai aka saki wata razananniyar bindiga da take shirin kashewa mutum dodon kunne"cikin kaduwa da tashin hankali riyyah ta jefar da ledar hannun ta ta damki hannun Zuhura ganin yadda mutane suke gudu,,kowa babban burinsa yafita daga store din amma kofa an datse ta,,wasu manyan bundugu ne a hannun 'yan fashin fuskokin su rufe cikin bakar hula"yadda mutane sukai riii dan ficewa haka suka kara dawowa aguje,, riyyah dan kwalin kanta da mayafinta tuni sukai hanyar su amma duk da haka bata saki hannun Zuhura ba"Kuka suke shabe shabe babu inda baya rawa ajikin su.
Wani office suka hanga basi wata wata ba suka afka cikin office din sudai kona wanene ma gwara sun shiga sun buya,,yana zaune a cikin office din ta CCTV 📷 yake ganin duk abunda ke faruwa"jin an bude kofar anrufe garam ya sashi juyowa amma kafin ya tantance suwanene su riyyah sun shige karkashin table din dake ajiye a gaban sa,,luf sukai aciki ko kyakykyawan motsi basa son suyi"tsai yayi da ransa yana mamakin wasu yarane wadannan amma yanzu dai bata su yake yiba,,wayar sa data dauki ruri ya dauka"yaransa yabawa Umarnin fitowa cikin kayan gida suka fito suka zagaye kowane lungu da sako na store din"ta haka yadinga basu umarni ba karamin bata kashi akai da 'yan fashin ba kafin asamu nasarar cafke su"su biyar ne biyu daga cikin su sun samu nasarar guduwa an kama guda uku"uamarni ya basu su wuce barrack dasu afara tambayar su tun yanzu"cikin girmamawa suka amsa umarnin sa kafin su tattare su su dura amota bayan an buga musu ankwa hannu da kafa."Sàida ya tabbatar da fitar su kafin ya juyo kan yaran dayaga sun fado office din"cikin dakakkiyar murya yake fadin kai kufito kuma,,shiru kamar anshuka dusa aruwa dan riyyah ta kankame Zuhura tana girgiza mata kai karta fita.
"Tsawa ya daka musu tsabar kidima basu sanda suka yo waje ba,,Kuka riyyah ta fashe dashi tayi kace kace da hawaye da majina abar dariya kamar ba ita tagama kuri dazu ba"rarrafawa tai har gabansa ta rike kafafunsa na hadaka da Allah ka rufa mana asiri muna fita zasu kashe mu"tunda ta fara magana zuciyar sa take mahaukacin bugu,,ji yake kamar yasan wannan muryar kamar ya taba jinta alokutan baya,,janye kafafunsa yayi daga hannun ta,,mikewa yayi da nufin ya bar mata office din dan zuciyar sa gab take da tarwatsewa saboda bugun da takeyi,,wuff ta mike ta rungume shi ta baya zagaye hannunta tayi akan cikin sa da nufin ta hanashi fita daga office din"dif wutar kansa ta dauke zuciyar sa tana kaikawo yayin da numfashinsa ya fara wahalar fita daga makoshin sa.
"Cak kukan da take ya tsaya dalilin shako turaran datai shekaru tana mararin sake jin kamshinsa,,babu Inda bataje dan samun turare irin sa amma hakan yaci tura,,ko bacci take kamshin takeji acikin hancin ta,,yau saiga me irin turaran atare da ita ya zama dole ta rokeshi ya sanar da ita sunan turaran"gama wanann tunanin tai sauri sakin sa tare da zagayowa ta gabansa ta tsaya"atare zuciyoyin su suka buga da azabar karfi,,musamman Major Rayyan saidaya dafe saitin zuciyar sa,,kallon Fuskar ta yake yana san tuna inda yasan wanann Fuskar yanajin wani abu na fusgarshi zuwa gare ta"amma kamar ana dawo dashi baya ne da nufin hana zuciyar sa isa gare ta"bangaran riyyah duk wani tashin hankali datake cikinsa daukewa yayi ganin sa kadai ya wanke mata zuciyar ta ya fitar mata da duk wani tsoro dayake cikin zuciyar ta.
"Cikin rawar murya take nuna shi da hannun ta Yayammu"kansa ya dafe jin sunan data ambace shi dashi"wasu muryoyi ya fara ji mabanban ta da suke maimaita sunan Yayammu acikin kwakwalwar kansa,,nuna kanta take ni nice Yayammu riyyah,,kallonta yake da jajayan idanun sa,, Lumshe idanun sa yayi cikin zafin nama ya zagayeta ya fice daga office din tabbas yaci gaba da tsaiwa wanann yarinyar kasheshi zatai"anya mutum ce kuwa,,ko karin binsa takeyi Zuhura tai caraf ta riketa,wai riyyah baki da hankali wanene wannan din har kike rungumar sa kike kiran sa da yayanki,,kuri riyyah tai tana kallon Zuhura da tsantsar mamaki da al'ajabin daya cika mata Zuciya ya kuma jijjiga tunanin ta,,wai wanene wanann?wai meyake faruwa ne Zuhura tana nufin tace batasan Yayammu ba"girgiza kai tayi a'ah hakanma bazai taba faruwa ba ai bayau aka haifi Zuhuran ba tasan Yayammu farin sani.
"Jin zuciyarta na neman bugawa taja hannun Zuhura sukai waje bat baya wajan tuni tawagar motocinsa sun bace daga harabar wajan,,zubewa tai akan guiwowinta ta fashe da kuka ta ganshi gashi ya kufce mata"yanzu aina zata nemo shi tana da tarin tambayoyin da take so ya amsa mata"ganinsa ne kawai zai warware mata abunda ya kulle mata kanta,,baki bude Zuhura take kallon yadda take Kuka kamar wadda ta rasa wani dan uwanta,,cikin jin haushi Zuhura take fadin Allah in baki tashi ba zan tafiyata,,akan wani can sai Kuka kikewa mutane me muka hada dashi"rai bace riyyah ta watsa mata harara bansani ba nace bansani ba,,Iliya ne ya rugo da gudu yana haki,,Allah nagode maka tun dazu nake nemanku hankalina ya matukar tashi sosai"kallon riyyah yayi tai wujiga wajiga idanu yayi jajir zuciyar ta har tafasa takeyi saboda kufce mata da Yayammu yayi,,to kukan me kike tunda dai 'yan fashin suntafi kiyi shiru haka,,batace kala ba ta mike sai lokacin ta lura da kanta ko dan kwali da Mayafi babu ajikin ta,,Ganin babu kowa awajan kowa yayi takansa tunda mutane suka samu suka fice kowa ya cika bujensa da iska ya ware,,mota suka fada iliya yaja su.
"Suna komawa gida a parlo suka zube"Ummi da Abba hankali tashe suke tambayar su me yasame su haka"Zuhura ce tai musu bayanin ibtila'in da suka hadu dashi"riyyah kuwa tsabar tashin hankalin dake dankare azuciyarta ta kasa magana"hawaye ke zuba a face dinta wani na korar wani,,tambayar Duniyar nan tayi magana amma taki sai sharar hawaye da takeyi"bakin cikin dake cinta yafi karfin ta musaltashi"yafi karfin ta bayyana shi"gajiya Ummi tai ta rabu da ita daga baya tafada mata abunda take yiwa kukan"barin parlon sukai suka shige daki Ummi tashiga kiching riyyah da Abbah ne kawai a parlo.
"Aljihun wandonta ta laluba ta dakko wayarta,,gallary tashiga tana kallon hotunan Yayammu awayar Ummi ta dauka"kara fashewa tai da kuka tare da rungume wayar akirjinta,,zuba mata idanu Abbah yayi yana karantar yanayin ta"kusa da ita ya zauna kafin ya mika hannu ya zare wayar hannun ta,,hoton Yayammu daya gani a screen din wayar ya bashi Mamaki matuka,,bece mata komai ba ya kama hannunta tare da mikar da ita,,janta yayi suka bar parlon baki daya,,gaiden suka wuce saidaya zaunar da ita kafin shima ya zauna.
Shiru yayi na wani dan Lokaci,, Numfashi ya sauke tare da kallon ta"Ansariyya wanene wannan kike kuka adomin sa,,kike asarar hawayanki akansa? Menene alakarki dashi? shiru tai tare da sunkuyar da kanta kasa,,wasa take da yatsun hannun ta tome zatace dashi"um um dama saiyayi shiru tana tunanin abunda zata gayawa Abbah,,dama me,,idanun sa still yana kanta" Yayan Ummi ne,, murmushi Abbah ya saki na tsantsar farin ciki,,kina sane dashi baki manta dashi ba riyyah,,daga kai tayi alamar eh,, Alhmdlh ya furta cikin jindadin lamarin,,saboda me kike kuka akansa,,shiru tai batace komai ba,,kara murmusawa yayi nasan bazai wuce ganin yadda ya manta dake be ganeki ba ko,,ya fadi hakanne danyayi mata dabara."Jijjiga kai tayi alamar eh,um ya furta bekara cewa komai ba,,ki huta zami wani aiki tare dake,tabbas kece wadda zata taka rawa awannan aikin matukar dagaske 'yar gatan Ummin ce to zaki so ganin farin cikin ta,,tsuru riyyah tai tana sauraron kalamansa,,kanta ya dafa Allah yayi muku Albarka,,Ameen riyyah ta amsa.
Abbah Babban mutum ne,,ba Ummi kadaice matar sa ba,, Ummi ita ce ta Uku amma kowaccen su gidanta daban babu ruwanta da wata,,tana da 'yaya samari da aurarru,baida wata matsala ta kowane fanni yana matukar son Antymmu,,ko sanda bata sami haihuwa da wuri ba shine ya dinga karfafar guiwarta,,Alhaji Mansur shine asalin sunan sa yaransa suke kiransa da Abbah.
"Tunda ya fada mota idanun sa ke Lumshe"sunan Yayammu na sake mai amsa kuwwa,,yadda riyyah ta rungume shi hakan ba karamun tasiri yayi azuciyar saba,,da yadda ta nuna tasan shi hakan ya tsaya masa arai,,ba barrack yasa a maidashi ba,,yana bukatar hutu gaba daya kansa ya dau charge,,gidan sa dake cikin gari aka wuce dashi"agajiye yake takowa parlourn"hamshakiyar tana zaune taci riga da wando kannan sai sheki yake,ta kara kiba da fari,,hannu da wuyanta gold ne sai walwali take,,tunda ya shigo take binsa da wani mayataccen kallo,,tana bacin rai data kasa samun sa har yanzu matsayin Mijinta,,larurar sa tabaya har ilayau tananan saima abunda yayi gaba,,yanzu hartakai ta kawo ya daina yadda ko kadan ta rabeshi,,hakan ba karamun cutar dashi yake ba tunda ba biyan bukata"kokarin rungumesa take yayi saurin daga mata hannun fuskarnan a turbine,,wani mugun shayinsa ne yake kamata akwanakin nan."Kewayeta yayi ya bude part dinsa da key dan yafi ganewa ya kulle din baya so ki yaya Sahar ta shigar masa part.
"Tana tsaye kamar andasata ya bude ya shige ciki"maida kofar yayi ya murza key dan baya son damuwa kokadan,wasu zafafan hawaye ne suka fara sakkowa daga idanun ta,, tarasa wannan wane irin Aure ne babu biyan bukata saidai wasu agefe da suke biya mata bukarta.Zuciya a cunkushe ta koma tazauna tare da rafsa tagumi.
Kadan ma kenan Sahar.
Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 67_68
"Kwanciya yayi tare da rufe idanun sa"ita dindai yake gani"yayanmu nice riyyah baka ganeni ba"maganar dake masa yawo kenan aka"riyyah ya sake maimaita sunan acikin zuciyar sa"ganin yana batawa kansa lokaci ya mike ya fada toilet"ya dade aciki kafin ya fito daure da towel ajikinsa"babu abunda ya tsaya shafawa ya zura jallabiyya fara kar ya fito dan zuwa masallaci an fara kiraye kirayen sallar magariba."Tana zaune har Lokacin kamar wadda aka daure ta bata da niyyar tashi tayi Sallah duk da yadda taji ana kiraye kirayen sallah hakan besa ta tashi dan dauro alwala ba"harya gotata ya dawo da baya yana kallonta"sallar ce bazaki ba"ya watsa mata tambaya"dagowa tai da nufin zuba masa rashin mutunci amma hada idanun da sukai taga irin kallon daya ke wurga mata saita kasa cewa uffan"mikewa tai batare data furta kalmar data makale mata a makoshi ba.
"Tsaki yaja ya barta awajan dan wani mugun haushinta yake ji"gaba daya baya son ganin ta kamar wata halitta me cutarwa haka yake jinta aransa"duk da tanajin sautin tsakin nasa hakan besa ta waigo ba ranta ajagule ta fada daki"maimakon tayi alwala kamar yadda ya bata umarni saita rarimi wayarta dake kan mirror,, number Mom ta daddana tare da karawa akunnan ta"tunkan Mom tai magana Sahar ta fashe da Kuka cikin damuwa Mom ke tambayar ta menene yafaru wanene ya rasu"Mom nashiga uku Rayyan yanzu baya shakkata ko kadan akwayar idanun sa na hango tarin jin haushina,,da rashin son zama tare dani"Idan aikinnan ya lalace nashiga uku ya zanyi Mom"kara rushewa da kuka Sahar tai"kinga ki kwantar da hankalin ki ninasan aikin gobe da nisa inyayi baya warwarewa har ranar mutuwar wanda aka yiwa"ki kwantar da hankalin ki kedai kici gaba da lallabashi ina maganin dayace kidinga samai a Abinci"yananan Mom yaushe rabon da nabashi wani abu yaci"dama kinsan ban iya girki ba shi kuma yace matukar bazan girka da hannuna ba to bazai kara cin abincin 'yan aiki ba.
"Dafe goshi Mom tayi kinga abunda nake gaya miki ko Sahar yanzu da kin iya girkinnan aida duk haka bata faruba"yanzu menene mafita Mom?mafita daya zanyi magana da gobe da nisa duk abun da ya sanar dani zan kiraki na gaya miki"to ya amsa tare da kashe wayar kodai Major yafara kala 'yanmata ne batare data sani ba"ras taji gabanta ya fadi tunawa da maganar boka inhar ta yadda wata mace tashigo rayuwar sa tofa aiki ne zai lalace gaba daya"fasa shiga toilet din datai niyya tai,,futowa tai ta fada dakin sa ajiyar Zuciya ta sauke ganin room din abude,,wayoyinsa dake ajiye a kan wardrobe ta dauka tasan password din daya saka"bincike tafara yi masa amma babu number mace ko daya a contact din sa,,sai Lokacin zuciyar ta tasamu salama jin wani azababban kishi ya tokare mata awuya,,ajiye wayar tai tana kara samun nutsuwa dajin cewa babu wata mace data isa ta rabar mata mijinta.(um um Sahar saidai kar akuma).
"Mami dake zaune adakin ta ta zabga uban tagumi"tayi sanyi da laushi kamar ba Mamin nan ba 'yar gayu 'yar kwalisa"gaba daya ta rame damuwa saicin zuciyar ta take batare data san musababbin damuwar tata ba"jin hawaye na gangaro mata tai azamar sharewa tare da lumshe idanun ta"Innayi ce ta shigo parlon Mami ta hangota awanann halin"kai nikam naga takaina ni Fatsima wai yanzu saboda ALLAH Fannah bazaki sanar damu abunda ke damunki ba"jiya jiyannan fa kika fito daga asibiti"kuma agabanki likita yace kirage tunani shi yahaifar miki da hawanjini kina zaman zamanki kin dorawa kanki masifa"babu abunda Mami tace sai tsiyayar da hawaye"kinyi hakuri Innayi nikaina bansan me yake damun Zuciyata ba,,amma tabbas abun yana matukar sukar Zuciyata,,fata na ki tayani da Addu'a Allah ya yaye min abinda ke damun Zuciyata.
"Shiru Innayi tai tana kallon Fannah"fadin rai da jiji dakai yanzu duk ya zama tarihi,,komai na rayuwarta ta baya ta ajiyeshi agefe,,gaba daya Duniyar bata yiwa Mami dadi,, Numfashin Innayi ta saki shikenan Fannah amma kisani wannan fadan da muke miki sabida lafiyar kine"Allah ya yaye mana dukkan da muwarmu,,Allah ya sassauta miki zuciyarki ko zakiji dadi da salama,,Ameen Mami ta amsa cikin sanyin murya.
"Tsahon sati daya kenan da haduwarta da shi kullum Addu'a take Allah ya kara hadata dashi ko tasan inda yake babu abinda zai hana ta zuwa wajansa,, Ring din wayar tane ya katse mata tunani ganin Abba ke kiranta tai saurin dauka"sallama tai kafin ta gaishe dashi cikin girmamawa"kusameni a lambu to Abba ta amsa tare dasa hannu ta dauki hijab dinta tasaka,,sanda ta sakko ba kowa a parlour kai tsaye ficewa tai tundaga nesa ta hango Abbah dauke da jarida yana dubawa,,sallama tai ya amsa fuskarsa dauke da murmushi,,tsugunnawa tai tana gaida shi,,ina wuni Abbah lafiya lau riyyah,,maza tashi ja xauna kujerar dake facing dinsa ya nuna mata,,sàidata daidaita zamanta kafin ya ajiye jaridar hannun sa."Kinsan abinda yasa nakira ki? Girgiza kai tayi alamar a'ah,,nakira kine akan maganar Rayyan"saurin dagowa tai tana kallon sa,,gyada mata kai yayi alamar tabbatarwa,,kamar yadda na sanar dake a kwanaki zamu aiki tare dake dan tsamo ahalinsa dashi kansa cikin halin da aka jefa su,,kuri tai tana kallon sa,,wane aikine wannan Abbah murmushi yadan saki halin mantuwa da akasa ka ahalinsa shine zamiyi kokarin ganin mundawo dasu hayyacin su da yardar Allah.
"Bayanin abunda yake faruwa da Rayyan da su Innayi yayi mata"sosai take kuka jin irin rashin imani na Sahar ko ba'a fada ba tana da tabbacin wannan aikin tane"tsananin tausayin Yayanmu ne ya kamata"tayi alkawarin zata zage damtse wajan ganin ta taimaka musu"in sha Allah zata rama musu halaccin da sukai mata arayuwa"bata da abunda zata ce da wannan Ahali sai Addu'ar fatan Alkhairi"maza goge hawayan ki riyyah yanxu ba lokacin Kuka bane tunda muka gano bakin zaran,,yanxu abunda nake so dake zaki bi Mubarak barrack din su ya tabbatar mun yana daga cikin yaran Rayyan din"Mubarak yana daga cikin 'ya'yan Abba shima soja ne kuma yana karkashin Major Rayyan ya sanshi farin sani.
Gyada kai riyyah tai alamar ta fahimta"akwai ruwan rubutu dana karbo zaki dinga yi mas agirki a kullun tsawon kwana 7 zakije amatsayin kanwar Mubarak"duk wata hanya da zakibi dan Abincin ya isa gareshi wannan aikin na bar miki shi ke kikasan yadda zakiyi"murmushi kawai tadan saki kunyar Abbah na kara kamata"rufe fuskatai ganin yadda yake mata Dariya gaba daya ya gama karantar abunda ke zuciyar ta"yaran zamani ya girgiza kansa."Agogonsa ya kalla yanxu zanje na karbo ruwan maganin zan kawo miki shi ki zauna cikin shiri daga gobe zaki fara aiwatar da aikinki"zan kiyaye Abbah yawwa Allah yasa mudace sai kin kula sosai riyyah saboda nasan wanene Rayyan sam bashi da yarda arayuwar sa.
"Ta dade azaune tana sakawa da kwancewa duk da zuciyarta tana farin ciki da sake ganin sa,,to ammafa tana tunanin cin abincin da zaiyi anya zai yadda ya amsa kuwa tasan wanene Yayanmu azaman datai dashi ta karanci halayan sa,,mikewa tai jikinta asanyaye ta koma dakin su"kamar yadda Abbah ya sanar da ita hakan tatashi kusan karfe 10 ta shiga kiching"shiru tai tana tunanin abunda zatai masa wanda tasan yana matukar so bazai iya tsallake tarkon da zata dana masa ba"sakin murmushi tai tunawa da yana matukar son funkaso babu wani bata lokaci ta fara kokarin kwabawa tana gama kwabawa ta rufeshi kafin ya tashi ta kama suya.
"Ummi ce ta fito tana kallon yadda riyyah tai kace kace tana aiki rike haba tai kaini wannan wane irin kamshine yake tashi"murmushi riyyah ta saki abun dadi nakeyi Ummi"budewa tai tana rike haba kai gaskiya har yawuna ya tsinke"aiko yanzu zan dora Ummi da saukaran aiki amma dan danan zan gama"bari na tayaki miyi sauri dandanan ta rayata suka kammala komai"miyar tasha naman rago ya dahu yayi tibis yadda zaiyi dadin tauna"sàida suka gama kammala komai Ummi ta fita daga kiching din"rubutun da Allah ya kawo mata ta dan diba ta debi daidai miyar da zata ishi Yayammu ta zuba aciki"kan gas ta dora miyar ta kara dahuwa kafin ta sauke ta zuba acikin food flacks"kwando ta dakko me kyawun gaske ta jera kayan aciki kafin ta ajiye agefe guda"futowa tai daga kiching din tana yarfe gumin dake tsatstsafo mata agoshi.
Wanka ta fada shape shape tafito,, kwalliya tayi simple material ta dauka ta saka yayi mata kyau sosai"mayafi medium ta dauka tai rolling sai plate din takalmi sai hand bag dinta data dauka tasaka wayarta aciki"kamar yadda Abbah ya sanar da Ummi akwai mara lafiyar da riyyah zata na kaiwa abinci hakan ta sanar da Ummin ita ma"dan kar Zuhura ta bita Abbah ya manna mata aikin dazai hanata bin riyyah din koda tanason hakane"sallama taiwa Ummi akan tatafi har bakin parlon ta rakata tana tagaida mejiki.
"Tana fita dama iliya driver ita yake jira, back sit ya bude mata tashige bakinta dauke da Addu'ar samun nasara."Kin barinsu shiga barrack din akai sàida ta kira Mubarak yayi musu bayanin kanwar sace koba yauba inta zo abarta tashigo"parking lot suka wuce sàida iliya ya daidaita tukunna tafito hannunta dauke da kwandon abincin"murmushi ta sakar masa yaya Mubarak,,shima murmushin yayi na'am kanwar yayanta"yar dariya tasaki amma wanann barrack din naku ya birge ni,, murmushi kawai yayi saboda yanayinsa na mara son magana"office dinsu ya wuce da ita balaifi duk da bawani babba bane su ukune acikin office din bana mutum daya bane.
"Zama taj tana sauke numfashi"dan kallonta yayi badai kin gaji ba"shagwaba face tai alamar hakanne"waike meyasa muguwar lazy ce ke,da kuma har ina cewa zan kawo ki kiyi trening din soja,,kwalalo idanu tai badai niba wllh aida sedai kuzo ku dauke ni a kakkarye,,dariya ya fashe da ita haba kamar ba kanwar soja ba,,kuma kika sani ko kizama matar soja,,basar da maganarsa tayi kamar bataji meyace ba,,mikewa yayi taho muke binsa tai abaya,,ba wata tafiya sukaiba suka karaso katafaran office din wanda ko daga waje kasan ya hadu daga ciki,,hakanan taji gabanta na faduwa amma ta daure ta cije.
Norking Mubarak yayi kusan 3mnt baiji an amsa ba"kamar daga sama sukaji maganar sa yes come in,,kafafunta har rawa suke wajan kutsawa cikin office din.Yana kishingide idanun sa alumshe"Oga yaji muryar mubarak a saman kansa,,dan bude idanunsa yayi caraf suka fada cikin na riyyah da take kallon sa kamar yaga sabuwar halitta,,zuciyarsa ce ta buga,,ya salam ya furta Inaga wannan Aljanna ce,,kallonta ya karayi ganinta dare dare akan kujera ya bashi Mamaki waya bata izinin zama"ya bude bakinsa kenan Mubarak ya tari numfashin sa kanwata ce wannan yallabai ina yawan bata kabarinka,,mutuncinka,da taimakon ka Shiyasa yau tayi takakakkiya dan zuwa ganin ka,,alasa dai banyi laifi ba aimun afuwa yallabai,,hadiye maganar da yayi niyyar yi yayi,,yana hadiye fushinsa koba komai macece zai iya yimata ko wane irin uzuri.
"Mubarak ne ya kifta mata idanu akan ta gaishe shi"cikin sanyin muryarta data samai kasala ta gaidashi"kara landing yayi akan sofa jin yadda muryar ta saukar masa da kasala,,be amsaba sai daga mata hannu da yayi alamar ya amsa,,atunanin sa tashi zatai ta fita saiyaga ta kara gyara zaman ta still idanun ta na kansa sam bata gajiya da kallon Yayanmu.
"Mubarak juyawa yayi ya fita ganin yadda Yayanmu ke watsa masa harara a kaikaice"shiru ne ya Ziyarci office din wayarta ta dakko ta fara game sai dariya take intaci tai darya da tafi in bata ciba ta bata rai"yana ayadda yake yana kallonta sosai ta burgeshi ganin bata da wata damuwa arayuwarta Nishadi kawai take,, kyakykyawar fuskarta yake kallo duk sanda kuma tunta suka loba sai yaji wani iri acikin zuciyarsa"wani shaukine yake fusgarsa yana jansa izuwa gareta"wayarsa ce tai kara saidata katse aka kara kira kafin ya duba me kirarn"ganin sunan Sahar baro baro ya sashi jan tsaki kome zata fada masa oho"ajiye wayar yayi yana sakin tsaki"sàida riyyah ta dago ta kalle shi.Kwantar da kansa yayi akan sofa still ta kara kiransa dagawa yayi rai bace tunkan yayi magana ta saki kukan kissa da makirci.
"My Soja na ka dawo gida yau zamma surprise nayi maka daddan girki da hannu na na girka kadawo kaji irin yadda yayi dado"dan Allah karkace àah shiru yayi yana sauraronta okay abunda ya furta kenan ya yanke kiran"kan bala'i riyyah ta fada azuciyar ta ai wllh babu Inda zakaje duk wayar da sukai akan kunann ta"bangaran Sahar daka tsallan murna tai dama maganin gobe da nisa ta kara barbade kan abincin dashi"inyasan wata besan wata ba,,badai yace shi sai ita zatai girki ba"wata mata ta dakko haya tana gamawa ta biyata kudinta tai gaba.
Ganin ya mike ya sata kallon sa da tunanin kardaifa tafiya zai wajan matar tasa"tana tunanin zuci haryazo daf da ita yana kokarin gotata ta ankara da abunda yake shirinyi"caraf ta ruko hannun sa"cak ya tsaya zagayowa tai tana kallonsa dan taci alwashin bazai fita ba saiyaci nata abincin"wata shagwaba ta fara zuba masa wadda ita kanta batasan tanayi ba"bubbuga kafafu take tana kukan shagwaba"gaba daya tsugar jikinsa ce ta fara tashi ganin yadda albarkatun kirjinta ke kaikawo a cikin rigar data lafe ajikin ta"saurin kauda kansa yayi yana hadiyar wani mugun yawu.
"Yayammu taya zan kawoma abinci kaki ci katafi ka barni dashi kasan dai bazan ji da dadi ba"please Yayanmu kaci koda kadanne,,samun kansa yayi da fadin ai baki bani abincin ba"murmushi ta saki wanda ya kara tafiya da numfashin sa jawo hannun sa tayi ta zaunar dashi akan sofa"da sauri ta dakko kwandon da tazo dashi ta ajiye agaban sa"futo da food flacks din tai tajere agaban sa sai plate data dakko da spoon."dan karamin table dinsa ta janyo ta jere kayan kafinta budi mai yaga abunda ke ciki wani kamshine ya daki hancinsa,,abunda yake matukar so arayuwar sa yazama dole yaci funkasonnan yawunsa har tsinkewa yake.
Hhh kaka kakara kaka ga Sahar ga riyyah zamuga wanda zayyi winning acikin su.
Mrs 🌹 Baba 🌹Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 69_70
Zuba masa tayi da kanta ta tura gabansa"yadade yana kallon abincin kamar yaci kamar karya ci"yadda yake kallon abincin haka ita ma ta zuba masa idanu"fuskarta akwabe kamar zatai kuka"hannun sa tasaka ya gutsuro zaikai bakinsa tai saurin rike hannun sa"kallonta yayi yana neman karin bayani"bakai bismillah ba"shiru yayi yana nazari yaushe rabon da yayi bismillah dan zaici abinci"shi gaba daya ma ya manta da anayin bismillah"ahankali ya motsa bakinsa yayi bismillah murmushi ta saki good aikinka na kyau Yayanmu kallonta yayi ta kashe masa idanu tana karamar Dariya"hade face yayi karfa yarinyar nan ta raina shi ji yadda take kashe masa idanu kamar wani sa'anta"tashi tai ta bude fridge dinsa ta dakko wani sumamman lemo da glass cup ta ajiye agabansa"tsiyaya drink din tai tamika masa be karba ba yayi mata alamar ta ajiye masa hakan kuwa akayi ta ajiye akusa dashi.
"Wayarta ce tai kara cirota tai saga hand bag Ganin Ummi ce akan layi tayi saurin packing"Asslmu Alaikum Ummina"wa'alakissalam wai wace irin dubiya ce wannan riyyah kodai kece kike jinyar mara lafiyar tundazu nake jiran kidawo amma kinje kin makale"dariya ta danyi to Ummi kika sani mara lafiyar ko akarkashin kulawa ta yake"hakan ma bazata faruba cewar Ummi kinga na baki nan da 20mnt naganki acikin parlon nan"angama ranki yadade dariya Ummi tai yarinyar nan kin maidani kakarki Nidai kinji abunda na gaya miki"angama uwa tagari murmushi Ummi tasaki tana dariyar shakiyancin riyyah.
"Tunda Ummi tai magana ya tsaya dacin abincin dayake jin muryar kamar ya santa awani shidaddan lokaci"tabbas muryar ta daki zuciyar sa saiyaji yana son ganin mamallakiyar muryar"bakinsa ne ya subece wajan furata wacece wannan?"dan juyowa riyyah tai tana kallon sa yadda yayi zugudi yana kallonta sai ya bata tausayi"Ummi nace ko kanasan ganin tane"Jijjiga kansa yayi alamar à'ah tare da hararar riyyah din"mene hadina dake da zanje ganin mamarki"niko muke da hadi dakai tunda gashinan nayi maka girki ka lamushe kana neman hadawa da plat din batare dakai ankare ba"saurin kallon plat din dayake ta mamuka hannunsa yayi wayam ashe harya cinye batare daya sani ba"murmushi ya saki yana shafa kansa shikansa abun ya bashi dariya na yadda ya cinye besan da hakan ba"drink din data tsiyaya masa ya kora"Alhmdlh ala kulli halin ya furta ahankali yana yagar tishu ya goge bakinsa"bowel ta dakko tare da ruwa tatara masa ya wanke hannunsa tas.
"Tana kammalawa tamike ta tattare kwanukan ta"kona barma anjima kakarashe abincin ka"kamar zaice bani amma miskilanci ya hanashi fadar haka dan sam abincin begaji da cinsa ba"gaba daya ma be yadda itace tai girkin ba yasan bazata iya irin wannan abincin medadin gaske ba"hand bag dinta ta saba tare da daukar kwnadon hannu ta daga masa alamar byee sai gani na gaba"binta yayi da kallo kamar yace ta dawo haka yake ji acikin zuciyarsa amma ya kame fuskarsa kai bazaka taba karanto wani abu acikin ta ba.
"Tana fita office din Mubarak ta wuce tare dayi masa sallama gaba daya hankalinta yayi gida,,iliya yana nan azaune akan wani benci ya sai rake sai gabza yake yana gyada kai hangota yasashi mikewa yana yashe baki"Hajiya riyyah harkin fito"eh rabashi amsa,,to wai nan din wajan wa kika zo"kai iliya kacika tambaya lallai saikaki"to aikin san ance matambayi baya bata"to wanann ka bata iliya ina raba ka dabin kwakwkwafi"garin shegiyar kwakwarka wataran zakaje ka gano Abunda zai hanaka baccin dare"dariya yayi babu wanann maganar aini haka nake bakina baya shiru yadda kikasan ba'a gasan baki ba haka nake da surutu"to Allah ya shirye ka ameen,dama shiriyar muke nema ai ganin zai maidata kalarsa yas atai masa shiru bata kara tankawa ba.
"Tunda ta shigo parlon Ummi take harararta"ajiye kayan hannunta tayi ta tsugunna ta rike kunann ta alamar ta tuba"duk yadda Ummi taso kartai dariya sàida tayi"ke ko ta nuna riyyah duk sanda zakiyi laifi kinsan kalar ban hakurin da kike bayar wa ko"murmushi riyyah ta saki ai Ummi banaso kokadan naga kina fushi da nine sainaji duk duniya tamin zafi"ai Ummin kima bata fushi dake yauwa Ummi."Ina Zuhura"ai basu dawo ba kin manta Abbanku ne ya tafi da ita office wai akwai wasu ayyuka da zata taya shi"dafe goshi tai nafa manta hakane"amma daga yau ba sake komawa hospital din zakiyi ba"ai Ummi sainan da sati daya za'a sallami mara lafiyar kuma kunga ni Abbah ya wakilta na wakilceshi nadinga kai abinci tsahon kwana bakwai.
"Haba Ummi ta kama nina rasa wane mara lafiya ne wanann da Abbah ya damu dashi haka to Alalh ya bashi lafiya"Ameen Umami banaje nadan kwanta nagaji"ai dole.kigaji kawai an kallafa miki aikin da ba naki ba"murmushi riyyah ta saki bakomai Ummi ai aikin ladane kuma kece kike gaya mana kada mu raina aikin Alkhairi duk kankantar sa miyi sauri mu aiwatar dashi"murmushi Ummi ta saki kama kumatun riyyah tai"Madallah da samun diya ta gari kamarki"Allah yayi muku Albarka Ameen Ummi"mikewa tai Ummi ta bita da kallo sosai take jinta aranta.
"Yayanmu be koma gida ba sai bayan magarib duk yadda Sahar ke zabga masa kira kin dauka yayi"sanda ya shiga ta cika tayi fam kamar zata fashe amma saboda sanin takan tuggu saita saki ranta kamar babu wani abu dayake damunta,, soulmate tun dazu naketa jiranka nayi maka daddan abinci da hannuna"waje ya samu ya zauna akan sofa bece mata komai ba"sai binta da kallo yake mini sket ne ajinta sai have best data saka ta gyara gashin kanta ta tufkeshi atsakiya"tayi kyau sosai amma daya tuno riyyah saiyaga duk wanann kyan nata ya disashe baya ganin sa"kokarin zama take akan cinyar sa ya daga mata hannu"na kwaso gajiya ki kyaleni na huta"shiru tai tana kallon sa tana san danne bacin ranta"cikin dauriya ta furta"bari na kwaso maka abincin tunda naga ka gaji sai kaci anan din.
I'm not hungry"what ta juyo a hautsine take kallon sa,,bude idanunsa yayi yana kallonta jin yadda ya razana,,saurin gyara yanayinta tayi waidama naga na bata lokaci wajan yima girkine am kace bakajin yunwa tome kaci"kamar zata fashe da Kuka ta karasa maganar banza yayi mata kamar beji abunda ta fadadinba,,ganin zata takura masa mikewa yayi yabar parlon binsa tai da kallo hawayen bakin ciki na zubo mata akan kwalliyar data bata lokaci wajan yinta"oho bemasan tana yiba tuni yakai dakin sa ya fada kan bed dinsa zuciyar na harbawa yarasa meyasa yakejin faduwar gaba haka.
"Daga wannan rana riyyah ta daura damarar kai masa abinci,,sannu ahankali shakuwa tashiga tsakanin su"wanda in Lokacin zuwanta yayi baya so ko kadan wani aiki yagifto atsakanin"in tana tare da ita yakanji dukkan wata damuwa tashi ta yaye kamar yana tare da wani ahalin sa.A wannan kwanaki inhar tayi girkin tare da mutanan gidan take hadawa suma suci irin abuncin da ake kaiwa Yayammu"hatta lemu da suke hadawa da ruwan Addu'ar take hada musu gaba dayansu suke sha duka gidan."Ance dare mahutar bawa amma banda awajan Major Rayyan kwana yayi kansa na Matukar ciwo da mafarkai marasa dadi daya dingayi da zarar ya rufe idanun sa"bacci gaba daya ya kauracewa idanun sa"mikewa yayi ya dauro Alwala yadinga jera sallah tare da neman sassauci awajan Sarki meduka,,Sarki mejinkan bayin sa.Har akai assalatu babu alamun bacci atare dashi yana kan dadduma,,saidaya yayi sallar asuba kafin ya kwanta bacci medadi ya dauke shi.
"Tunda ya kwanta yake mafarkin riyyah cikin kyakykyawar shiga"hannun ta dauke da farantin kayan marmari sai kashe shi take da kayataccen Murmushi yana sakar mata murmushi shima"farkawa daga bacci yayi ya samu kansa yana sakin murmushi"yayi mamaki matuka kodai agaske yake ganin ta ba mafarki yayi ba."Tsahon sati Biyu kenan taga bashi ruwan maganin ya shanye amma duf babu wani labari"Sosai hankalin ta ya tashi ganin har wannan lokacin sun masa dawowa cikin hayyacinsu,sun kasa tunawa da junan su"tasha buya tayi kuka dan kar Zuhura taganta take buya inta gama ta wanke Fuskarta"Abbah ta samu ta sanar dashi har Yanzu fa basu dawo daidai ba"murmushi kawaii yayi,,kanta ya dafa Ansariyya manya,,ai shi ciwo ta farat daya yana iya kamaka amma sauki sai ahankali, Addu'a zamuci gaba dayi Allah ya dafa mana in sha Allah ina ji ajikina sun kusa dawowa kamar da"karki manta sihirin da yake jikin su ba karamin mushirki ne yayi wannan aikin ba"dan haka dolene mu kara dagewa da Addu'a.
Saukar Alkurni Abbah yasa aka dingayi da bawa yara kanana sadaka badare ba rana haka suka dage da Addu'a gaba daya sun sadaukar da lokacin farin cikin su, zuciyoyin su akan wannan ahalin"Allah gafuturrahim Allah mejinkan bayinsa saigashi sunga nasara Allah ya amshi Addu'ar ya dubi kyakykyawar niyyar da take azukatan su('Yar uwa kisani dukkan wata damuwa da kike ciki babu wanda zaiyaye miki ita face Ubangiji madaukakin sarki.Shiyace muroke shi zai yaye mana dukkan damuwar data addabe mu.Ko acikin jindadi kike kiyi masa godiya saiya karo miki wannan ni'ima da yayi miki.Ba inya biya miki bukata ba daga ranar ki mimmike kafa ke ai bukatarki ta biya,karki kasance sai kina cikin wata masifa zaki fuskanci Ubangiji wai sai alokacin kika tuna shine zai yaye miki dukkan damuwar ki, à'ah ko kina cikin ni'ima kici gaba da godiya agare shi).
"Karfe Ukun dare Abbu ne ke zaune akan daddumar sa Addu'a yake yana kai kukansa wajan Ubangiji akan ya yaye masa dukkan kunci da damuwar dake damun zuciyar sa"wani irin sanyi ne yadinga kwarara azuciyar sa"Ahankali sunan Rayyan ya fara kaikawo a Zuciyar sa sunan daya shafe shekaru batare daya tuna ba"sunan daya dinga fafutuka danganin yasan sunan wanene a cikin ahalinsa,,yau sai gashi dukkan tunanin dannasa ya dawo kansa"fashewa yayi da kuka kodai mafarki yake ba'a gaske ya manta da dannasa ba mafi soyuwa agare shi"kasa zama yayi ya mike cikin sassarfa ya fita daga part din Mami"kai tsaye part din su Kamal ya nufa"norking ya dinga yi musu har saidai Asad ya tashi yana tambayar wanene,cikin rawar murya Abbu yake fadin nine Asad bude mun"da sauri Asad ya bude jin muryar Abbu har nema yake ya fadi wajan fadowa dakin"bubbuga kafar Kamal yayi da sauri ya tashi yana kallon wanda ke tashinsa atsakiyar daran nan"Ganin Abbu yasashi mikewa yana Abbu Lafiya meyafaru?ina kuwa Lafiya zo muje kakaini gidan yayanku nagano halinda yake ciki"ras gabansu ya buga atare jin sunan da Abbu ya ambata Yayanmu,,take jikinsu ya fara rawa sunan yayan nasu na dawowa ciki kwakwalwar su"duk wani bacci sake cikin idanun su gaba daya babu shi ayanzu mikewa sukai hankali tashe tunani suke yaushe rabon da suje gidan yayansu ko suganshi har sun manta Allah yasa dai Lafiyar kalau,mota biyu sukai suka fice daga gidan sukai gidan Yayanmu.
Alhmdulillahi Ala kulli halin.
Sahar karyarku takare.
Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar.
......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 71_72
"Sanda suka dauki hanyar gidan Yayanmu garin tsit sai kukan karnuka dayake tashi tako ina"tafiyar 20mnt sukai suka karasa gidan"saidai Abunda ya jijjiga tunani su hatta kwadon da aka garkame gidan dashi yayi tsatsa alamar andauki tsahon lokaci ba'a bude gidan ba"Abbu dake tsaye da tarin damuwa afuskarsa yana dannewa ne saboda karya tayarwa da yaransa hankali"Shiru sukai suna nazarin tsahon lokacin da aka dauka batare da mamallakan gidan sun wanzu acikin sa ba"rariyar gidan suka haska kamas babu alamun ruwa acikin ta."Jin ana kokarin bude wani Gida dake jikin na Yayanmu suka maida hankalin su kan gidan"saida megidan ya tazama ya dauka wasu mugayan mutannan ne suka shugo Unguwar su"saidaya ham.nazarin su Abbu Kamar yadda shima suke kallon sa"matarsa ce ba Lafiya ya bude kofar dan ya kaita asibiti.
"Ganin kamar yanajin tsoron matsowa kusa dasu Abbu ya matsa yayi masa sallama"jin muryar kamilallan dattijo yasa mutumin dakin ajiyar zuciya"hannu Abbu ya mika masa sukai musabiha"Jim yayi yana kallon Abbu danjin me zai tambaye shi"am dama dan Allah mazauna gidannan muke nema"dan jim mutumin yayi kafin ya tuno da wadanda ma suka taba zama agidan"gaskiya ankai kusan shekaru uku da tashin su indai ba mantawa nai ba"gaban Abbu ne ya yanke ya fadi yana maimaita shekaru Uku"Innalillahi wa'inna ilahirraji'un yake maimaitawa azuciyar sa"wani gumi me yanko masa ganin mutumin da hankalin sa tabbas bazaiyi masa karya ba kamar yadda ya fada musu yasan haka Abun yake"hannu Abbu ya mika masa tare dayi masa Godiya"bece da su komai ba ya wuce su Kamal dake jiran cewar Abbu amma be tanka musu ba ya fada mota.
Shiru sukai an rasa wanda zaiyi magana har suka koma gida"ko kadan Abbu be runtsa ba awanann daran burinsa gari ya waye ya kira Sadik dan yaji ina Yayanmu yake shine kawai zaisa hankilin sa ya kwanta."Kamar yadda yayi aniya hakan ce ta kasance ko ruwa ya kasa sawa acikin sa sàida ya kira Sadik"cikin girmamawa ya gaida Abbu tambayar daya cillo masa ita tasashi zabura ya mike kamar wanda ya farka daga bacci yake maimaita Rayyan"baki hangame Abbu ya rike waya yana jiyo yadda Sadik ke jera Innalillahi,,sai hankalin Abbu ya kara tashi yana ta hello amma tuni Sadik ya yanke kiran ya bazama office din Canal Rayyan"saidai daya shiga office din kome kama dashi be gani ba"sabanin shidin wani daban ya gani a office din.
"Kai tsaye wajan ogan su ya tafi danya tambaye shi ina Rayyan yake"murmushi Major Farouq ya saki Canal ko Major kamar ba abokinka ba kana nufin kace kamanta ammasa karin matsayi"gumi Sadik ya share tare da kakalo yaken dole"hakane sir na dan shiga wani yanayi ne"fita yayi daga office din Farouq din"cikin bindiddigi ya samu labarin barin Rayyan barrack din gaba daya tsahon shekaru Uku"dafe kai Sadik yayi to kodai mutuwa yayi ya dawo Inba haka ba taya Canal zai bar barrack dinnan batare daya sani ba"wai ya tashi daga canal ya zama Major yaushe din?yana me."Besare da neman bayanai akan Yayanmu ba harsai da ya samu cikakken address din inda yake tabbas zama be gansu ba"Abbu ya kira ring daya ya dauka dama kiran yake jira tun dazu yake kiran wayar sa be daga ba"Abbu bawan Allah gaba daya ya fice daga nutsuwarsa daga gani kasan yana cikin damuwa amma yana boye hakan.
"Sunan gama waya da Sadik ya kira Abee akan yayi shiri zasu bi jirgin karfe 12 zuwa ABUJA babu wani Jayayya Abee ya amsa da Allah ya kaimu"duk wani abu Sadik shine ya tsaya har komai ya daidaita,,befadawa kowa Inda zaije ba yadai shirya kamar kasuwa zai tafi.
"Asad ne ya fado parlon Innayi da take zaune tana azkhar"zama yayi kusa da ita Innayi wai ya akai kika manta da Yayanmu"cak Innayi ta tsaya da abunda takeyi Rayyan ta ambaci sunan kamar me koyon magana"zumbur ta mike kai aini namanta dashi ja'iri tunda yayi Aure tsahon wata daya kaga ko kirana be karayi ba"kuma baya zuwa inda muke mikon wayata naji an yasa ya manta damu"tsuru Asad yayi yana kallon Innayi mekiran wata daya"kai anya ba daga gidan mahaukata aka sallami su ba"begama wanann tunanin ba Mami ta fado dakin har haki take wajan tambayar Asad ina yayansu tunda suka fito daga gadroom sunyi waya dashi kuwa"cikin jin haushi Innayi ta watsawa Mami harara"ke tafi can duka wanene ya kawo mana wannan masifar Inba keba"kiduba yadda yasa akaiwa yara jina jina ai bedaki banza ba jira nake ya dawo sai ransa ya baci"inma matar tashi ce ta sashi zan ji ai"jawo Asad tai tana duba inda yaji ciwukan jikinsa amma bat tanemesu ta rasa"kara ware idanun ta tayi akan Asad din"kai kodai ba mutum bane kai dazu a dawo daku jina jina amma yanzu naganka kamas kamar wanda akai maka susa babu ciwo babu alamar sa.
"Shidai Asad shiru yayi bashi da abunda zai amsa mata tambayar da take cillo masa"ke Fannah kodai idanuna ke min gizo duba min kigani"ita ma Mamin mamaki ne ya kamata ganin babu wani tabon ciwo ajikin sa"nima banga komai ba Innayi"kwallawa su Humaida kira ta hauyi daya bayan daya suke shigowa duk wanda yashigo saita kamashi har rigarsa take lekawa amma babu ciwon"da tazo kan Humaida ganin Innayi na neman cire mata riga a bainannasi tai saurin rike mata hannu"wai Innayi lafiyarki kalau kuwa haka kawai zaki ciremun riga"ina ko Lafiya gaba daya naga kun warke ba dazu aka dawo mana daku yayanku yayi muku shegen duka ba,,kamar wadanda akaiwa format akwakwalwarsu saiyanzu abubuwan suka dinga dawo musu ka"kallon kallo suka shigayi atsakanin su Yayanmu suke maimaitawa a zukatansu"ai be kara zuwa ba Innayi tunda aka dawo damu suka hada baki wajan sanar da ita"tsaki taja ta nemi waje ta zauna to bari na zauna najirashi inanan azaune zaizo ya saman kukuma kowa yayi tafiyarsa,,kun wani cunkushe min adaki sai zarnin fitsari kukeyi,,driya sukayi kafin su juya su fice"zuciyar Innayi dai sai kaikawo take sai watsawa Mami harara take a dakilinta aka dakar mata jikoki"abun shekara uku jinsa suke kamar bedade da faruwa ba ahalin da suke ciki yanzu.
"Tunda ya tashi yau yakejin faduwar gaba"Addu'a yake Allah yasa Alkhairi ne"cikin danyan boyel fari tas ya fito daga bedroom din sa"kansa saye da bakar hula zanna bukar da bakin takalmi"daddan kamshin turaransa na tashi."Tunda yafara sakkowa ta kafa masa idanu take kallon sa har hadiyar yawu take ba kadan ba take san Rayyan" babu inda bazata shiga dashi ba mijin nunuwa duniya ne"murmushi take sakar masa amma a tasa face din ko kadan ba alamun fara'a saisake shan kunu da yayi"cikin karairaya tataso tana kokarin karbar jakar laptop din sa,,kaucewa yayi batare da yace uffan ba" rafar 500 ya dakko daga aljihunsa ya ajiye mata yayi gaba"binsa tai da kallo takaicinsa na kamata" ko kadan ta tsani wannan miskilancin nasa,,wai bazai bude baki yayi mata magana ba sai bakin rai ya iya,,tsaki taja tana hararar kudin daya ajiye mata"duk yadda takai dasan kudi wannan be birgeta ba haurawa tai tabar kudin awajan.
"Kallon wayar sa yake yana tunanin inya kirata me zaice mata"kasa control din zuciyar sa yayi ya danna mata kira"riyyah na zaune a bakin bed dinsu ta tafka uban tagumi gaba daya tunanin Major ya cika mata Zuciya,,jin wayarta tahau neman agaji ta kaikata kallonta kan screen din"sunan data ganine ya bata Mamaki"tunda ya amshi number dinta be taba kiranta ba inba yanzu ba"cikin farin ciki ta daga kiran amma saita waske kamar babu wani annuri a fuskarta"sansanyar muryarta dake masa sallama ya sashi lumshe jigatattun idanun sa"a kasan makoshi ya amsa yana ya mutsa face kamar bashi yayi kiranta ba"wanene ta tambaya cikin nuna bata nasan me magana ba"cire wayar yayi daga kunnan sa ya kara mayar wa,,shi zatacewa ma wanene"in baza'ai magana ba zan kashe wayata"Numfashi ya zuka ya fesar wanda tanajin hucin numfashinsa"dif ya yanke kiran yanajin haushin kansa meyasa ya kira wannan yarinyar"murmushi ta saki dam tasan zai iya yanke jiran"hauka.takema zata nuna tasan shine ya kirata yama rainata kenan yace ai ta damu dashi har seving din number sa takeyi"bangaransa lumshe idanu yayi jin muryarta kadai yasa yaji sassauci amma bazai taba nuna mata yasa ita ya kira ba"yana kwance yana wannan zancan zucin yaji anmasa norking yes come in,,maida kansa yayi ya kwantar ko.wanene ma yazo zai dameshi a halin yanzu.
"Tsaiwa sukai a bakin kofar suna kare masa kallo idanun Abbu cike taf da kwallah haka Abee yake kallon da yayan nasa cike da kauna da soyayya"Sadik ji yake kamar ya falla da gudu yaje ya rungume shi"amma dakewa sukai suka aro jarumta suka yaba a fuskokin su"suna mamakin yadda ya kara samu wannan matsayin batare da sun sani ba"tabbas sunyi nesa da juna koma wanene ya shiga tsakanin su Allah ya fishi."Jin shiru babu alamun za'ai magana ya dago idanun sa ya dora akan su"haka kawai yaji gabansa ya fadi kallon su yake kamar yadda suke kallon sa"wani busashshen yawu ya hadiye jin yadda bakinsa ya bushe"dauke kansa yayi daga kallon su kallon da suke mai ya fara damunsa matuka har tsakiyar zuciyar sa yakejin kallon"jikin su asanyaye suka karasa cikin office din sukaiwa kansu matsugunni"kansa yana sunkuye yana danna laptop din dake gaban sa.
"Meke tafe daku?ya wulla musu tambayar a bazata"kallon kallo suka shigayi atsakanin su,,to ganesu ne beba ko kuma kama suka canza"kai tabbas akwai wata akasa"ALLAH sarki Abbu share zufar data wanke masa fuska yayi ganin yadda dansa ya manta dashi kwata kwata be gane suba"da zaisan wanda yayi musu wanann zalincin tabbas bazai barshi ba."Abee zai magana kenan aka turo kofar bakin ta dauke da sallama tashigo yau ba girki tai masa ba snacks ta debo masa tasan yana da jus saita hada dashi"rannan nata ahade dan karma ya dauka san ganin shi takeyi Shiyasa tazo inda yake.
"Tunda tashigo gaba dayansu suka zuba mata idanu sam bata lura da suba harta karasa gaban table din sa"wani shegen kallon kasan idanu yake mata"murguda masa baki tai tare da fari da ido"besan sanda ya saki murmushi ba hakan yasa ta zaro idanu ta nuna shi"tare suka sa dariya ita dashi wadda besan sanda ya koyi yin dariyar ba"in yana gabanta yana mantawa da matsayin sa gaba daya"ficiciyar yarinya ta susu tashi baki daya"kujera ta jawo ta zauna Yayanmu ga snacks nai maka medadin gaske"kallon ledar datake miko masa yayi batare daya karba ba."Sunan da sukaji ta kira na Yayanmu ya sasu kara ware idanunsu akan ta,,a ina tasan wanann sunan haka"gaba daya hankalinta ba'a kansu yake ba kallon agogon hannun take satar fita tai batare da Ummi tasan tafita ba"mikewa tai nidai Yayanmu na tafi dama aikena akai nabiyo tanan"daga masa hannu tai ta fice daga office din suka bita da kallo"shima gogan binta yayi da kallo face dinsa asake"kallon juna Abbu da Abee sukai dan mamaki ya gama kashe su azaune."Basu da tacewa sai kawai suka mike batare da sunce mai kala ba sukabar office din yazama dole suyi gaggawar karya wanann sihirin dake jikinsa.
"Kaitsaye gidan Antymmu suka nufa sugano awane hali take ita kuma"sanda suka isa gidan Zuhura ce a parlo ganinsu yasa ta daka tsalle ta dane Abbah tana kwalawa Ummi kira tazo taga manyan baki"aiko da sauri Ummi ta fito daga dakin ta bakinta kamar zai yage dan farin cikin ganin su.Sannu da zuwa take jera musu zama sukai suna sakin yaken dole"riyyah data fito daga toilet tajiyo kwaroroton Zuhura yasata fitowa taga suwanene suka zo."Taking steps ta fara tana tambayar Zuhura suwanene suka zo"tundata fara sakkowa suka kara cika da Mamaki tabbas ita suka gani to ya akai tasan inda yake?"ido hudu sukai da Abee washe fuska tai dadan gudunta ta karaso"Abee sannu da zuwa murmushi yasaki yawwa riyyah.
"Tsuru Sadik yayi yana kallonta tabbas yasan wannan Fuskar amma aina?........kubashi amsa fans.
Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 73_74
"Sai Lokacin idanun ta ya fada kan Abbu dayake kallonta cikin nazari da mamakin Inda suka hadu dazun tabbas tasan wani abu kenan"tsugunnawa tai ta gaishe dasu"Abee ina Salma yaushe zata zo nan"murmushi yayi Salma tana nan kullum cikin zancanki take bikinta ya kusa"washe hakora tai kai ashe zamusha Biki"cikin dariya Ummi tace kika sani ko za'a hada da naki"saurin rufe fuska tai tana murmushi"Zuhura ce ta daka mata duka munafuka ana so ana kaiwa market"banza riyyah tai da ita kamar bataji abunda take fada dinba"Ummi ce ta mike maza taso riyyah mushiga kiching"mikewa sukai dukansu suka dunguma kiching.
"Kallon juna Abbu da Abee suka sakeyi"kaga abunda na gani"cewar Abbu gyada kai Abee yayi nagani Yaya bakaga na kasa furta kowace kalma ba"amma taya suka hadu awannan garin shine abunda yake min yawo a Zuciya cewar Abee"shiko Abbu dama be santa ba be kuma san da zamanta ba Bomboy ya sani ba riyyah ba"kuma koda yaganta be kawo aransama ya santa ba"yayi tunanin 'yar uwar Abbah ce.Wayar da Ummi takira Abbah ta shaida masa zuwan su Abbu ya sashi dawowa da wuri"parlon sa ya kaisu cikin girmamawa suka gaisa bayan Sadik ya gaida Abbah yamike ya fice dan basu waje su tattauna.
"Abbu ne ya gyara zama yana kallon sirikin nasa,,niko bilyamin wani abu nagani wanda ya daure min kai Agidan ka"gyara zama Abba yayi me kakagani Abbu"wannan yarinyar dana gani dazu da mukeje office din Rayyan ita nagani"ALHMDLH Abbah ya furta fuskarsa dauke da murmushi"yanzu kana nufin kun tuna da Rayyan daga masa kai Abbu yayi alamar tabbatar wa"fara'ar fuskarsa ce ta karu,,sanar dashi wacece riyyah kamar yadda matar sa ta sanar dashi da irin rawar data taka wajan ganin sun dawo hayyacin su"tunda Abbah yafara nagana suke kallon bakinsa kaunar riyyah nashiga kowane sako da lungu na zuciyar su"gyada kai kawai suke suna jinjina lamarin ubangiji Allah ya cillota ahalin su dan tai taimako agare su"suma in sha Allah zasu saka mata zasu sata farin ciki.kamar yadda take fatan ta gani afuskokinsu.
"Hakika ina matukar Godiya abisa yadda ka jajirce wajan ganin ka tsamomu daga cikin halinda aka jefa mu"bazamu taba biyanka wannan kokari dakai agaremu ba"murmushi Abbah ya saki babu Komai matsalarku matsala tace"idan ina da iko zanyi iya bakin kokarina wajan ganin na magamce Muku shi"amma tunda harkace haryanzu be shaida kuba tabbas akwai aiki agaba saidai mu daukeshi mukaishi wajan malamin ganinsa zaisa yasan ta yadda za'a bullowa lamarin"amma wani hanzari ba guduba tawace hanya zai yadda ya bisun"nazari suka shiga yi"Abbah ne ya numfasa ni abunda nake gani ta inda aka hau tanan ake sauka ta hanyar yarinyar zamu kara janshi gidan Malam din"sun gamsu da shawarar Abbah sosai dole saidai su kwana dan baxai yiwu su koma ayau dinba"waya Abbah ya kira ya sanar da Malam halinda ake ciki'"yayi naam da maganarsa sai ankawo shi zaisan abunda ya kamata ayi masa.
"Abbah bayan magarib ya kira riyyah duk yadda za'ai ya sanar da ita,,ita ma taji dadi koba komai tana so taga ya koma cikin ahalinsa"tana so taga Murmushi akan fuskar Ummi tana sane da yadda take shiga matsananciyar damuwa duk adalilin rashin sa,,ta bawa Abba tabbacin zatai iya bakin kokarinta wajan ganin ta kawo shi gidan Malam Yakub din Albarka ya saka mata kafin ya sallameta"tana futowa suka hada idanu da Sadik kunu tasha dan kallan kurillar dayake mata ya fara bata haushi"Murmushi kawaii yayi ya shafa kansa harta kule yana binta da kallo.
"Bayan sallar isha'i watar tace ahannun ta sai jujjuyata take tarasa wata karya zata shirga masa harta samu ya yadda ya biyo ta gidan Malam din"addu'a tai kafin ta danna kira"yana zaune a parlo yana kallo"Sahar na gefansa"tare suka kai idanun su kan wayar amma da yake beyi seving din number ba shiyasa batagane wanda yayi kiranba"amma shi sarai yagane number jadda ce take akansa"dai data katse kafin ya kirata da kansa kara gyara kwanciyar sa yayi tare da lumshe idanun sa"kamar tasan tunaninta yakeyi"daddar muryarta ce ta daki dodon kunnan sa"Asslmu Alaikum Yayanmu"akasan makoshi ya amsa sallamar"am dama kame kame riyyah ta soma yi dan karya ba aikinta bane saita rasa mezata ce masa"in baki da abun fada na kashe wayata"abunda ya fadane ya jawo hankalin Sahar ta gane da mace yake waya"kan Uba ta ambata harsai daya juyo yadan kalleta"tuni duk wani annurin fuskarta ya dauke har wani huci take tana Girgiza kafa wace 'yar iskar ce ta kira mata mijin ta."Dama Yayanmu laifi mukai a makaranta akace kowa yazo da Babansa ko yayansa"kuma in aka sani agida za'a daken please kataimaka kazo muje dan Allah"shiru yayi yana sauraronta"saboda ni kika raina bakya tsorona shine ni zaki gayamun"ayyah Yayanmu bafa haka bane kaga kai yayana ne kuma abokina zakafimin sassauci akan su"besan sanda Murmushi ya subuce masa lallai yarinyar nan waishi zataiwa wayo"gaba daya ya manta da wata Sahar ai zuwa Lokacin harta mike ta rike kugu zuciyar ta har daci take tsabar masifar da take cinta.
"Shagwaba ta dinga zuba masa tanai masa dadin baki harsai daya yadda zai futo sutafi karfe 9 na safe"cikin farin ciki ta sauke wayar tana daka tsallan samun nasara"rai bace Sahar take kallon sa da wace 'yar iskar kake waya agabana dan cin Fuska kake waya da wata awaje"ko kadan be nuna yasan dashi take ba"tashi yayi tsam ya barmata wajan sai sababi take tana kumfar baki ko kadan be bi takanta ba ya wuce ta zuciyar sa fes.
"Awanann daran Sahar batai bacci ba tsabar yadda zuciyar ta take bugawa idan ta tuna gargadin boka na karya yadda wata mace ta rabeshi sai hankalinta yayi matukar tashi"taci alwashin gobe kafarta kafarshi bazata barshi yafita shikadai ba."Tara saura kwata ya fito sanye da kananan kaya gashinsa yasha gyara sai sheki yake"sajansa ya kwanta luf luf"Sahar tana zaune tunda dazu dama shi take jira tana ganin yayi hanyar waje ta bishi ta rataya wani ziririn mayafi a kafadarta dashi da babu duk daya"yana kokarin shiga mota yaga ta bude sit din gaba ta shige tsayawa yayi yana kallon ta dauke da Mamaki"me lafoyarki kalau kuwa ina zakije"Fuska ahade race binka zanyi naga wadda take bibiyar ka yau koni ko ita"eh sai yanzu na tabbatar da jahilcin dayake damunki"daga jin nayi waya saiki dauki abun kimakala akanki,aiko kina da babban aiki,,batai tsammani ba taji ya jawota daga motar har kanta yana bigewa da murfin motar ya dangwarar da ita akasa yayiwa motarsa key yabarta a yashe awajan.
"Da gudu ta mike zata boyo shi amma ina har an rufe get kamar zararriya haka ta fada motar ta da gudu tayo bakin get din gadan gadan,,da sauri masu gadi suka wangale mara get din a haukace ta fice daga unguwar barrack ta nufa amma abin bacin ran tundaga bakin get aka sanar da ita bezo ba"dafe kanta tayi tare da fashewa da kukan bakin ciki ina yatafi!! Buga sitiyarin motar take kamar zata tada bori."Bata hakura ba tadinga garari ahanya kome kama dashi bata gani ba,,rai bace ta koma gida da alkawari saita gano wace shegiyar yarinyar ce take bimata Miji.🤣🤣🤣ai Sahar kin riga kin makara lol.
Inda ta sanar dashi zasu hadu adai dai wajan ya tsaya motar su Abbu nadaga nesa da sauri ta bude back sit din dayake zaune batare ya ankara daga inda tafito ba shidai ya hangota ta bullo cikin uniform din ta na Makaranta"harda goya jakarta abaya itafa a lallai makarantar zasu tafi,,tunda ta taho ya kafeta da idanun sa masu matukar yimata kwarjini"yadda take tafiya da komai nata burgeshi yakeyi"da sallama ta shiga motar tana dan murmusawa"gaida shi tai kafin ya watsa mata harara"ni sa'anki ne da zakice nazo nakaiki school kinyi laifi"kunnan ta takama alamar ban hakuri tana kwabe fuska kamar zatai kuka"kauda kansas yayi jin wani abu na tsirga masa"tada motar yayi tana nuna masa hanya"dai dai kofar gidan Malam Yakub tasa ya faka"dan dafe goshi tai kash yayammu kaga nan gidan kakannina nane kuma ina bawa kakata labarinka tace tana son ganin ka kazo mushiga ka gaishe da ita.
"Hade rai yayi ke futowa gaishe gaishen danki nai ko makaranta zan rakaki"kai Yayanmu kaso me sonka gaisawa fa kawai zakui marairaicewa tai kamar zatai Kuka"harara ya dada watsa mata kafin ya balle.murfin motar ya fita"Murmushi ta saki tana godiya ga Allah daya yadda zai shiga gidan"Abbah taiwa text gasunan zasu shigo"dama ta hango motarsu sun rigasu zuwa kenan.Haka kawai yaji baya son shiga gidan amma wani bari na zuciyar sa na sanar dashi in kaki shiga bazataji dadi ba,,suka shiga tsakiyar gidan Malam Yakub dama ya tanadi turaransa da gaushi me yawan gaske sai daya tabbatar yashigo sosai ya zuba turaran dandanan Yayanmu yaji kansa ya sara idanun sa sun kada sunyi jajir jin yadda kansa ya dauki zafi"ko taku daya kasa karawa yayi idanun sa sukahau lumshewa tafiya yayi zai gadi riyyah ta taroshi"gaba daya suka zube akasa kan riyyah ya bugu da wata tukunya ga yadda Yayanmu ya kwanta mata ahannu ihun data sane yasa su Abbu futowa aguje"dauke Yayanmu sukai suka shiga dashi wani saki"kafin Abbu ya dauki riyyah da take Kuka shabe shabe tana tana dafe da hannun ta"waje aka samu ta zauna jitake kamar hannunta ya karye amma yanzu burinta taga Yayanmu ya warke.
Malam Yakub karatun Alkur'ani ya kunna cikin wata katuwar mp gaba daya kararta ta cika dakin daidai kunnan Yayanmu aka kawo mp din"ga hayakin maganin dake tashi adakin"jin azaba taiwa aljanin dake jikin Yayanmu yawa ya fara surfa ihu yana kuraruwar ana konashi"babu wanda ya saurare shi sàida suka tabbatar ya jigata ya kokkone kafin aka saurara da karatun"Malam Yakub ya nemi ya sanar dashi wanda ya aiko shi yace shima umarni kawai me gidansa ya bashi besan aikin na wanene ba"kuma yayi alkawarin yanzu zai fita yabar jikinsa,,sàida Malam yayi masa gargadi zazzafa kafin abarshi ya fice"ajiyar zuciya suka sauke suna furta Alhmdlh.
"Gaba daya fuskokin su awashe suke suna taya juna murna"riyyah ma na gefe tana sakin murmushin jindadi,,kusan 30mnt yana bacci kafin Ahankali ya fara bude idanun sa"lokacin su Abbu suna dakin Malam Yakub suna kara tattaunawa sai riyyah dake zaune ta kura masa idanu tana kallon shi,,a kanta ya sauke idanun sa yana kara kallon dakin da yake me yakawo shi wannan dakin kuma.....
Bansamu damar yin typing me yawa ba kuyi hakuri da wanann.
Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
.....✍️✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 75_76
"Tashi yayi yana dube dube"kallon riyyah yayi da take sakin Murmushi ya watsa mata harara"ke ni sa'an kine ina ne kika jawo mu"batace mai komai ba"Yayanmu ma gane ni?cikin mamakin tambayarta yake kallonta"kinsan daga makanta na warke ai"dariya ta saki tana kallon sa"Abbu Yayanmu ya farka"har tuntube suke ci wajan shigowa dakin"Zuba musu idanu sukai suna Addu'a Allah yasa dai ya warke,,Abbu inane nan"ajiyar zuciya suka sauke gaba dayansu tare da fadin ma sha Allah.Yanzu ma ganemu Rayyan Abbu ya furta cikin rawar murya mamaki kara kasheshi yayi jin wata tambaya da suka kara jefo masa,,daga kansa yayi dan baida tabbacin Abunda ya same shi"daya bayan daya suka dinga rungumarsa jiyake kamar yayi nisan zango ya dade be jisu akusa dashi kamar Yau din ba.
"Godiya sukaiwa Malam sosai"tambayoyine cunkushe a zuciyar sa amma ya barta sai sunkoma gida yayi musu tambayar"kai tsaye mota suka fada Gidan Ummi suka wuce ayau zasu koma gida basai gobe ba"suna shiga harabar Gidan ya shaida gidan Antymmu ne"ya akai ya manta da gidanta bayan yana cikin ABUJA ya Allah ya dafe kansa da har wanann lokacin bedaina yi masa ciwo ba.Tana parlou ita da Zuhura sanda suka shiga zumbur suka mike suna washe baki"Ummi harshanta har rawa yake wajan furta Yayanmu,, Murmushi yake sakar musu Zuhura da gudu ta fada jikin sa,, Yayanmu kadade bakazo gidan mu ba"shafa kanta yayi batare da yace komai ba,,zama sukai dan danan Ummi ta cika gabansu da kayan tande tande da lashe lashe.Zaman hira sukai Ummi da takejin wani irin farin ciki wanda ta dade bataji kamar saba sai sakin Murmushi take ita kadai.
Kamar yadda su Abbu suka tsara bazasu furta komai ba sai sun dangana da maiduguri"Abbah sanar da Ummi yayi su shirya akwai taron family da Innayi tashirya gaba daya tana son Ganin su"babu bata lokaci suka hau shiri"riyyah dai tana zaune hannun tafa ya fara damunta amma haka ta daure tana cijewa"karfe 2 suka daga maiduguri gaba daya yamanta Allah yayi ajiyar wata Sahar acikin Abujan sam ya manta da babunta.2:30 suka shiga harabar Gidan dan Barno sai akaci sa'a dama 'yan gidan gaba dayansu sun hallara saboda kayan Auren Salma da za'a kawo agobe"mazan su da matansu"hatta su Fareeha sun zo da sauran kannan Abbu da suke Aure a wasu kasashe da garuruwa.
Suna parloun Innayi suna shan fira harda Mami data zubar da makaman yakinta tana cikinsu ana hira,,Umami tana gefe tana saka baki jefi jefi"Ganin su Abbu sun fara shigowa yasa su yin shiru sunai musu Sannu da zuwa,,wanda ya shigo akarshe ne yasasu yin tsit zukatansu na bugawa da sauri da sauri musamman Mami data kasa zama saidata mike,,ganin yadda ya canza musu ya kara girma da kwarjini"alamar hutu ya ratsa fatarsa ya dagani hankalin sa akwance yake baida wata damuwa.
Yayanmu suka hada baki wajan furtawa wata annashuwa yakeji tabbas yaji aransa yayi rashin su na tsahon lokaci."Muryar Innayi ce ta katse wajan kaji ja'iri dama nace zakazo ka saman ina zaune"yadda kasa aka dakarmin jikoki akan busashshiyar matarka saina rama mata"kallonta kawai yake yana mamakin abunda take Magana akai din"hannunsa Abbu ya kamo suka karasa shiga parloun daya bayan daya suka dinga gaida shi fuskokinsu dauke da fara'a da farin cikin ganin sa.
"Idanun sa ne ya fada kan Mami da take sharar hawaye tsantsar farin cikine ya mamaye zuciyar ta,,Umami ya kalla wadda take sakar masa murmushi da tarin kauna agare shi,,sàida komai ya lafa kafin Abbu yayi gyaran murya kowa tsit yayi yana sauraron abunda zai fada.
"Sallama yayi musu irin ta Addinin Musulunci Abee ya bawa dama ya bude taro da Addu'a"Kamar yadda na taraku anan to bakomai bane face miyiwa Allah godiya da Allah ya tsamomu daga cikin ibtila'in da kuskuran wasu ya jefa mu"kamar yadda kuka sani abaya yayanku yayi Aure ko nace shekaru uku da suka gaba ta"tsugul Innayi ta furta kai dannan karka maidamu sakar karu mana Auran dako shekara ba'aiba kake kiran shekaru uku"murmushi Abbu ya saki kamar yadda kikaji nafada to hakanne Innayi shine ayanzu zan sanar daku abunda ya faru"kowa kasa kunne sa yayi danjin yadda har akai shekaru uku batare da sun sani ba.
"Tiryan tiryan ya basu labarin duk abunda ya faru ashekarun bayan"babu wanda be zubda hawaye ba acikin su,,zukatan su sun dauki zafi da taantsan tsanar Sahar da dukkan ahalinta kuka Mami take riris tana ji aranta duk itace ta jawo wannan matsala.Numfasawa Abbu yana nuna riyyah hakan be kasance ba sàida taimakon wannan yarinyar,,gaba daya suka zubawa riyyah ido wadda ahalin yanzu fa tafarajin garin yana juya mata hannunta na cikin mayafinta ya kumbura sosai dalilin da babu wanda ya lura da hannun."Shikansa Uban gayyar zuba mata idanu yayi yana karajin matsayinta na karuwa azuciyar sa"Innayi ce tataso Allah sarki ammako Allah yayi miki Albarka,,runguma ta kawowa riyyah wadda ta sata tsandara ihu sàida Iyyani ta razana tai baya nashige su kai ko bata da lafiya ne.
"Hannunta ta rike wayyo hannuna"babu wanda yasan sanda yayanmu ya tsallako ya zauna agaban riyyah da take kuka shabe shabe"Ummi ita ma har turereniya suke wajan isa gare ta"Abbu ne yace ashsha tabbas dazu naga sanda take kokarin taroka ma fada mata ahannun banyi zaton zataji ciwo ahannun ba,,ayyah Allah sarki cewar Innayi ashema kaine kaji mata ciwon saika gyara mata hannun ko akira megyara ya gayara mata"haka kawai yaji baya bukatar wani kato ya rike mata hannu danyi mata gyara"gaba daya sannu sukewa riyyah gaba daya fuskokinsu sun cika da tausayin ta"Umami da Ummi kamar siyi mata kuka Mamah Ramlah na gefe tanai mata firfita Salma na rike da daya hannun tana matsar kwallah yadda kasan me nakuda haka suka jere sunai mata sannu.
"Ganin idanun da suka zubo masa ya mike bayasan kallo kokadan kinkimarta yayi yayi hanyar part dinsa da ita Innayi masifa ta hauyi kai sauke ta banason iskancin banza yarinya na cikin jama'a kasunkuce ta katafi da ita to kafata kafarka dan Namiji ba abun yadda bane"dariya suka saka gaba daya ganin yadda Innayi sai balbalin fada takeyi tana binsa abaya"Ummi ma bin bayansu tai sai Umami data kasa tsayawa a kan sofa ya dora ta kafin ya zauna agaban ta,, kallon su Ummi yayi yadda suka jere agabansa kuriketa mana"harara ya makawa Innayi sai aukin surutu amma kintsaya kinkasa katabus"oho kodai me zakace kafada nadai biyo sahunka.Murmushi su Umami keyi ganin yadda Innayi ta kasa ta tsare."Sosai tasha Kuka harda majina Ummi hartayata kuka tai ganin yadda take zanbarwa daga karshe fadawatai jikinsa tana kokarin rike hannunsa da daya hannun shikansa zuciyar sa ta cika da tausayin ta ashema shine ya jawo mata wannàn wahalar batare daya sani ba.
Baccin wahala ne ya kwasheta ajikinsa bayan angama gyaran targadan data samu"to sauketa kaje can ka rungumi kedarar matar ka"banza yayi da ita danya kara kular da ita kara gyara mata kwanciya yayi ajikin sa,,kara kuluwa Innayi tai ta dunkule hannu ta duma masa abaya sauke ta dan ubanka niyau naga jaraba"nina san Abunda zanyi wllh Kayi da 'yar halak fuuu Innayi tai waje tana kumfar baki,, Murmushi kawai su Ummi sukai suka juya sukai bi bayan ta."Zuba mata idanu yayi yana kare mata kallo intana bacci tafi kyau haka ya ayyana azuciyar sa.
Sanda riyyah ta farka ita kadai ta gani Acikin parlon mikewa tai tabbas tagane wannan part din,,part din yayanmu ne,,hannunta ta kalla da kumburin yadan sauka,,kamshin dataji a hancinta yasa ta dagowa ta kalli Inda takejin kamshin"ido hudu sukai da yayanmu dayake sakkowa cikin shadda ash color yayi kyau sosai sai Zuba kamshi yake,,Harara ta watsa mai tare da kumbura baki"mikewa tai sànin Abunda tai masa inya kamata zata ji Jiki,,da gudu ta falla ta fice daga part din kallo kawai ya bita dashi yana shafa kansa,,face dinsa dauke da Murmushi.
Part din Umami ta nufa suna zaune aparlo Ummi Fareeha Beenazir suna kara tattauna yadda al'amarin ya faru"sunkuyar da kanta tai jin kunyar su ta kamata,,shugo mana riyyah,,a hankali tataka kusa da Ummi ta lafe tana boye fuskarta"dariya suka saki kodai surukanki zamu zama irin wannàn sinne kai haka"Ummi ce tai Murmushi to ku baku gane ba aini tuni naje gano kunsannni akwai kamo sabuwar tasha"dariya suka kara sawa"Umami ce ta harare su kunga karku samun yarinya agaba ai Kunya adon macece"Beena ce ta kalli Ummi wai Antymmu aina kika samo yarinya ne"yarinya tace baki gane taba kenan saunawa muna zuwa gidannan da ita koda yake ke bakya zuwa sosai shiyasa baki santa ba,,gyada kai tai hakane,,ni yarinyar ce ta burgeni dama kanin Mijina yace na samo masa yarinya me hankali ina ganin ta naji ta cancanta.
"Antymmu ce ta kalleta to ai ita wannàn da kike gani tun tana karama aka riga aka kama layi"naci kudi amatsayina na Uwar amarya kinga yanzu bana dawo na hana ba,,kai Antymmu kudinwa kika ci,,kunsan shi amma gida be koshiba ai ba'akaiwa dawa ba,,dariya Fareeha tai kai anya ba ubangayyar kikewa tanadi ba"kaji 'yar gari banmu kashe mika mata hannu tai suka tafa.Umami dai na jinsu suna firar su,,maza kije part din Mami su Humaida na can babu musu ta mike suka bita da kallo.
Sanda ta shiga part din Mami tana zaune ita da Mama Ramlah"Lallai riyyah idanun ki kenan ni babu Abunda zakice min"baki zuwa gidammu amana batace haka ba"Murmushi ta saki ta zauna ajikin Mama Ramlah kai Mama kefa ta dabance taya zan manta dake,,kinsan in munzo bama dadewa muke tafiya amma kina Zuciyata"um um fa banasan dadin baki dagaske Mama to na yadda"cikin so da kauna Mami ke kallon riyyah tun kallon farko d suke zuwa da Antymmu taji yarinyar ta kwanta mata ashe itace silar farin cikin su(🤣🤣🤣har yanzu Mami bata san Bomboy bane ya juye ya koma riyyah)Allah sarki nima kaina yarinyar tana burge ni cewar Mami,,ai Hajiya Fannah riyyah akwaita da dadin zama"gasu Humaida nan a dakin sama jeki same su to ta amsa tare da haurawa sama.
"Kwanan su biyu agidan kowa ya gane Inda yayanmu ya dosa akan riyyah"yasha cari kuwa wajan Sadik kan sun gano Abunda yake damun sa"sosai su Abbu sukaji dadin wannan lamari dama.abunda suke shawartawa kenan atsakanin su"babu Abinda zasu sakawa riyyah dashi face daya daga cikin 'yayan su ya Aure ta."Sahar cikin kwana biyunnan Kamar tayi hauka takira yayammu yafi saudari amma koda wasa bedaga kiranta ba"babu shiri ta bazamo meduguri"Abunda yasanar da Mom ya daga mata hankali tarasa Inda zata tsoma ranta gaba daya tunanin su be basu asirin da sukaine ya karye ba dan boka ya basu tabbacin bazai taba karyewa ba.
"Wajan gobe da nisa suka bazama saidai abun tashin hankalin hatta tsaunin dayake kai ya kone kurmus,,zubewa sukai suka fashe da kuka kai kace wani jinin sune ya mutu"kai a kalla sunkai 1hour suna gursheken kuka gatansu ya mutu,,kamar zararru haka suka koma Gida komai ya jagule musu komai ya kwabe"Zazzabin tashin hankali ne ya rufe Sahar yanzu dai batasan a wane babun take ba"Rayyan ya dawo hayyacinsa ko wajan wani bokan zasu canza......
Lallai su Sahar fa sunyi nisa basajin kira.
Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubukar
......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 77_78
"Kallon Sahar tai yanzu abunda za'ai tashi zakiyi kije gidan matsayin kinje gaishe su,,ta hakanne zaki gano abunda yake faruwa,,danjim Sahar tai tana kallon Mom anya wanann shawara mekyau ce kuwa,,kwarai kuwa kiyi kitashi kishirya zanyi tunanin wajan malamin dazamu tafi in kika dawo"ok Sahar ta ambata tare da mikewa,,dandanan ta shirya ta dauki wanka"kudi ta saka ajaka wanda batasan ita kanta ko nawa bane."motar ta sabuwa dal tadauka wanda wani kwartonta ya saimata ahalin yanzu kasar Marocco yake yi musu shirin tafiya zatai masa rakiya.
"Fuskarta akame ta shiga harabar Gidan babu kowa a harabar sai kukan tsuntsaye da suke shawagi awajan"riyyah, Salma,da Zuhura da Humaida ne suka fito daga part din Umami suna tafe suna hirar su suna dariya"ganin Sahar kawai sukai agabansu tana sakar musu Murmushi,,sak sukai suna kallonta dama basu santa ba"tsaf Humaida ta gane ta wani dogon tsaki taja tare da watsa mata harara,,kai dallah kuzo mutafi ni duk makircin mutum hakan bazaiyi tasiri akaina ba"babu musu suka bita face dinta dauke da damuwa ta bisu da kallo"me Humaida take nufi data furta hakan agareta"cikin sanyin jiki ta karasa parlon Mami,,su Uku ne azaune Mama Ramlah da Mami sai Beena dake gefe suna hira jefi jefi."Tunda Sahar ta shigo suk wani annurin fuskar Mami ya dauke yadda kasan taga mala'ikan mutuwa haka take kallonta"Sahar dai bata karaya ba fuskarta sake ta karasa har gabansu"tsabar Munafurci har kasa ta duka tana gaida su"ganene ko wacece yasa kowaccen su ta hade girar sama data kasa"shiru Sahar tai gaba daya idanunsu sun fara damunta"munsameku lpya Mami dakyar Mami ta amsa lafiya lau daga haka taja bakinta ta tsuke.
"Innayi ce ta shigo dankwalinta ahannu tuni Humaida taje ta fesa mata ga Sahar nan tazo"Annamimiya kingammu lafiya sumul yadda Kuka so ganin mu keda uwarki ba haka kika samemu bako,,ke bandama rashin Kunya harzaki iya shigowa cikin gidannan,koda dai dama ina kikaga Kunya ai tabar gangar jikinki tuni,,Kunya ma ai tame imani ce,,Innayi cikin Masifa taci gaba da fadin aini bansan ke dangin jaraba bace Sàida aka auroki me fararkafa kawai,,shigowarki zuri'armu kika fara janyo mana Masifa,,ni bayanma ubansa yace karya sakeki ai wllh saki uku zansa ya rubuta miki amma kije dan kanki shegiyar farar fuska kamar kosai.
"Duk yadda suka so kamewa saida Murmushi ya subuce musu"ke kalleni,, Sahar da kanta ke duke hawaye na shatata na tsabar bakin cikin wata kucaka tazo tanai mata haushi aka,,banda kaddara ma ai ita matar shugaban kasa ce amma tabige a auran dan su"hanya Innayi ta nuna mata tanan kika biyo maza tashi tunkafin nasa garadan gidannan siyi miki jini da majina,,sai ranar da aka gallo sabuwar amarya 'yar gaske tukunna za'a sammiki inda zaki zauna,,duk maganganun Innayi basi mata ciwo ba kamar maganar Amaryar nan data ambata,,rai bace ta mike Innayi na binta abaya tana kara silleta.
"Tsaki Innayi taja mara mutuncin banza,,ai duk kaifinkine Fannah haka kawai kin jajibo mana masifa,,da abun akanki kadai ya kare ma bazanji komai ba,,amma sai abun ya hada harda mu,,sai hakuri Innayi saimu godewa Allah tunda Allah ya takaita mana wahala"kibari kawai Ramlah ai kinfi wanann hankali ta nuna Fannah kafin ta fita tana cigaba da mita,,kai Innayi badai mita ba cewar Beenazir da take binta da kallo,,Mama Ramlah ce ta kalleta intajiyoki ta dawo kyasan yadda zakiyi da ita,, Dariya Beenazir tasaka kai haba Mama ai bayanki zan labe,,dariya Mama Ramlah tai badani ba kuwa.
"Hannu ta aka tashiga parlourn su Mom dake tsaye tana cacar baki da Ambassador suka bita da kallo,, wayyo nashiga uku Mom wai Major kishiya zaimin wayyo naga ta kaina,,Dad ne ya daka mata tsawa shiru tai tana zare idanu tunda take da Dad koda wasa betaba daga murya da sunan fada ba balle tsawa,, Alhmdlh nagodewa Allah da zaimiki kishiya yanzu ita ma uwarki sanar da ita nake zan mata kishiya inyaso saiku mutu karku zauna da ita,,wallahi Abas karya kake kace zakaimin kishiya ni Hadiza bazan zauna da kishiya ba tunda kuruciya ta banyi zaman kishi ba,,yanzu ma bazan fara ba,,aiko saidai kifita daga gidannan ita tashigo,,keda zaki fitama wllh haka nake so badan Hajiya ta ta hanani ba da yanzu zan sakeki kibarmun Gida,,natsaneki Hadiza bansan kaddarar ma data hadani dake ba,,gaba daya kin lalata min 'ya'yana Allah ya isa tsakanina dake wllh kije keda Allah."Bantaba zatan hajiyarka munafuka bace saiyau,,kanta rufe baki Ambassador ya dauke ta dawani gigitaccen mari hagu da dama,,mahaifiyar tawace munafuka kinacin darajarta kina zaginta,,to wanann ce rana ta farko kuma ta karshe in kika sake zagin kome sunan tace ba ita bama ninasan Mezan miki,, ballagaza kawai."Kan Sahar ya dawo kekuma inbaki shiga hankalin kiba wllh zan miki mummunan duka na karairayaki inga ubanda zai tuhumeni akan haka,,karnaga kafarki taje ko kofar Gida sai Mijinki yazo naji awane matsayi kike yanzu awajan sa,,shiru sukai Mamaki yagama kashe su yau Ambassador acikakken megida yake bada umarni cikin kwarin guiwa,,wai meke shirin faruwa da sune,,(nidai nace karshen kune yazo)haka suka zauna yadda kasan masu zaman makoki kowa da abunda ya dame shi,,amma fa sundauki alkawarin bazasu zauna da kishiya ba koda wasa.
"Umami zubawa riyyah idanu tai yadda take Kuka,,haba riyyah yanzu laifine dan mun tambayeki ina dangin Abbànki suke,,kisani mu bamu da ikon yimiki Aure dole sai mundagana gare su haka addinin musulunci ya tanadar"numfasawa Umami tayi kafinta dora tabbas sudin masu laifine agare ki amma hakuri zakiyi yansu bagashi Allah ya sauya miki da mafi alkhairi ba,,kisani riyyah wllh ba wani abu Yasa muka tambayi danginki ba hakkin su zamu basu duk dasu sunkasa sauke naki hakkin,,munatare dake jinki muke kamar daga ahali daya muka fito kidaure kidaina wannan Kukan"tunda har bakyason zuwa gunsu nabar zancan"mikewa Umami tai zata fice daga dakin"da sauri riyyah ta ruko hannunta kiyi hakuri ni bana nufin haka Umami"bazan taba tsallake umarnin kuba,,kudinfa kune kuka tallafamin Lokacin da kowa ya gujeni"Lokacin da nawa ahalin suka nuna basa bukatar rayuwata"damme zankasa yimuku biyayya akan duk abunda kuke so,,zan kaiku har gaban ahalina Umami zankaiku,,sake fashwa tai da kuka aduk sanda ta ambaci ahalinta ranta suya yake,,juyowa Umami tai yawwa ko kefa kishare hawayanki kafarki kafarmu,,bazamu taba tahowa mubaroki acan ba.
"Shiri sosai suke na tafiya Kd,, Salma Humaida Zuhura har kuka sukai akan zasu bisu"da kyar Mami ta rarrashi Innayi harta hakura aje dasu Amma da cewa tai in anje dasu to saidai ita tafasa zuwa,,itafa batason harka da yara,,da kyar dai aka lallameta ta hakura,,duk wannan dokin da suke riyyah hankalinta atashe yake wace irin tarba zasiyi musu"bata fatan takaisu a wulakanta su,,sunada wata kima da daraja a idanun ta,,in hakan tafaru dawane ido zata kallesu ita kuwa.
"Wadanda za'ai tafiyar dasu Abbu, Abbah,Abee,Yayanmu,Sadik, Umami,Innayi, Antymmu, Beenazir,,Mamah Ramlah,Salma,Humaida,Zuhura,su Asad ma sunso su bisu Yayanmu yace babu inda zasu je."Tafiyar asussuba sukai saboda yanayin hanya,,sosai suka dinga sheka gudu riyyah tana takure akusa da Ummi Zuciyarta inbanda bugawa babu abunda take yi."Basu suka shiga Kd ba sai karfe 3 na rana sosai suka gaji da zaman mota,,Musamman Innayi sai mita take yasin bazata koma amota ba saidai ashiga jirgi wannan shegiyar wahala har ina,,babu wanda ya tanka mata sunjigata ainun"Gidan Abbu dake Kd anan suka sauka,,babban gidane sosai ya dade da siyanshi tun wani aiki daya taba kawo shi Kd daya kama haya ya gwammata yasayi Gida gaba daya,,Akwai masu zuwa su share sa duk bayan kwana biyu shiyasa yake fes babu wata kura,,a parlo suka zube suna maida Numfashi,,su Salma sai zare ido akeyi basu saba da tafiya menisan haka a mota ba,,sàida sukai sallah kafin Yayanmu da Sadik su fita kayan Abinci suka jibgo kamar wadanda zasi sati agarin,,su Zuhura da riyyah sune a kitchen zagewa sukai suka sheka musu girki,,jallop din shinkafa suka shirya taji wadataccen kifi sai tashin kamshi take,,jus dan zobo suka dafa bayan sun yanka abarba aciki da cucumber da kayan kamshi,,kowa yawunsa tsinkewa yakeyi,,kansu gama girkin sun sashi acikin fridge yadda suna gama girki sunsan yayi sanyi sosai.
Sanda suka gama Abincin kusan biyar da 'yan mintuna,,tsit parlourn yayi kowa yana harrakawa,,Ummi ce ta kalli riyyah ina na Yayanmu da Sadik,,yana kiching Ummi,,to haka ake kula da Miji dama dauki kikaimasa saiki dawo kici kema,,badan tasoba ta mike batason ko kadan ta hadu dashi kunyarsa takeji ga irin kallon da yake mata mesanya jikinta ya saki gaba daya."Part din da suka sauka ta nufa norking tai taji an amsa daga ciki,,tura kofar tai Sadik ne kadai azaune yana Kallo,, Murmushi ya sakar mata Amaryar mu,,rufe idanu tai kunya ta kamata,,ni ina tawa Amaryar bakizo da ita ba wannan sankai ne,, Murmushi ta da saki,,wacece Amaryar taka,,rike haba yayi yanzu duk yawon kamfen din da nke da yada manufata har yanzu ba'asallama min ba,,dariya ya bata,,ai yaya Sadik mu bamusan wannan karatun ba,,kafuto amutum kabayyana mana kudurinka,,daganan saimu tantance ka,,dariya ce ta kufce masa besan haka yarinyar nan take da surutu ba,,to shikenan tunda abun yazama haka nima baza'abar kd ba sai an tabbar da kuri'ata,, Murmushi kawaii tayi,,tunda suka fara surutu yana jiyo su daga bedroom din" wani azababban kishi ne yake taso masa,,jin yadda ya bude baki tanaiwa wani kato dariya"wata zuciyar tace dashi Sadik nefa Amininka,,to dan Aminina ne ai shima namiji ne,,jin zuciyar sa zata tafi wani abu daban yayi a uziyya yakori shedan.
"Jin alamun za'a bude kofa ta falla dagudu ta fice,,batason su hadu a yanzu batada sukuni azuciyarta,,tana tsoron abunda zai biyo baya in sukaje gaban su Abba Yahaya.Sanda ta koma da yawan su sun kammala cin Abinci,,kadan tadan tsakura jin cikinta ya cushe bata bukatar wani abu kuma."Anan suka kwana sai washegari karfe 10am suka nufi gidan Abba Yahaya,,Hon sukai amma shiru ba'a zo anbude bade ba,,sàida suka leka sukaga kome gadinmma babu,,fita driver yayi ya tura get din kafin su samu damar kutsawa cikin gidan"babu kowa shiru duk fulawawin dake gidan sun bushe kai kayau kayau yadda kasan filin yaki,,babu mota ko daya acikin Gidan"futowa sukai suka tsaitsaya suna kallon riyyah da takebin gidan da kallo tana zubar da Hawaye,,tuno rayuwar jindadin da sukai ita da umminta da Abbanta,,amma jiba yadda gidan ya fita daga hayyacin sa,,kutaho matanne suka bita abaya,,mazan tsayawa sukai sai an basu izini tukunna.
"Sanda suka shiga parlourn sunsha Mamaki ganin ko kujeru babu ansaida komai sai wani carpet da aka samu aka dan shimfida a tsakiyar parlourn"sallama suka rangada kafin suji an amsa,,wata matace ta fito ta cokala Uban dauri,,fuskarnan tasha mai dganinta dai tsohuwar 'yar bariki ce sai taunar cimgom take"àah baki mukayi ku shigo mana shiga sukai,, riyyah sai tunane take wannan kuma wacece,,bayan sun gaisa riyyah take tambayar ta Abba Yahaya,,oh wai waccan mara Amfanin kuke nema,,kallon kallo suka farayi jin abundata ambata,,bude muryatai Yahaya,, na'am ya amsa jikinsa har rawa yake wajan fitowa hannunsa duk kumfa da alama wanki yake tika,,gani Hajiya yawwa ga bakinan sunce kai suke nema Allah yasadai ba bashi kaje kaciba yanzu ranka ya baci"kallon su yayi daya bayan daya,,wllh Hajiya ni bamma sansu ba,,toku kunji bayin Allah yace bema sanku sai dai in batan kai kuka yi,,wuce kaje kaci gaba dayin abunda na saka,,juyawa yayi yana kokarin tafiya muryar riyyah ta doki dodon kunnan sa,,Abba,,cak ya tsaya yana tunanin ina yasan wannna muryar,, ahankali ya juyo ya sauke idanun sa akanta,,ko shekaru nawa yayi bazai taba iya mantawa da riyyah ba,,kullum da tunaninta yake kwana da fatan Allah ya nuna masa ita koda saudaya ne ya nemi yafiyarta,, Ansariyya ya ambata Hawaye na zuba akan fuskarsa.
"Dama kina raye riyyah nakima ina nemanki danna nemi yafiyarki amma abun yaci tura dan Allah kiyafemun laifukana riyyah batace komai ba,,kallonsa kawai take ya rame ya zuke saikace me cutar kanjamau"tare muke da baki awaje"dan jim yayi yana satar kallon wannan matar ko wacece awajansa oho"saidai kuzo muje gidan Gali babu musu suka mike duk yadda matar nan ke watsamai harara haka ya shige gaba suka bishi wata shegiyar kodaddiyar shadda ce ajikinsa taji jiki ba kadan ba"yadda kasan zai fadi haka yake tafiya kalau kalau dashi."Mikawa su Abbu hannu yayi yace suzo suje gidan kanin sa babu musu suka koma mota tafiyar mintuna biyar ta kawo su kofar gidan Abba Gali"to dama dama shi haryanzu akwai me gadi sàida suka daidaita parking suka fito Abba Yahaya cayayi su biyoshi abaya.
"Tunda suka doshi parlourn suke jin muryar Anty zee sai zazzaga masifa take ta gaji dashan koko tafiya zatai bazata iya wannan masifa ba,,banza Abba Gali yayi mata amma duk da haka batai shiru ba kwalarsa ta rike da niyar yaga masa riga"daga hannu yayi ya wanke ta da mari,,waike Zainab wace irin macece ke mara hankali"kedai ba Matar rufin asiri bace yanzu bazaki tausaya min halinda nake ciki ba suwa suka.cinye kudin Inba ke da 'ya'yanki ba,,karkaimin maganar banza to bazan kara yadda kasake daukar wani abu agidannan ba saidai na hada kayana na tafi gidammu.
"Jin ana sallama akofar parlon ya sasu waigowa ganin Abba Yahaya da tawagar mutane yasasu yin shiru suna tunanin suwanene wadannan sudai basuga wahala ajikin su ba,,kushigo Anty Zee ta ambata ganin da alama za'a samu mamora atattare dasu,,bayan sun zauna akai gaishe gaishe.Abba Yahaya ne ya kalli Gali nasan baka shaida su ba,,gyadakai Gali yayi dan wata azababbiyar yunwa yakeji kamar zata kashe shi"to Ansariyya ce"ware idanu sukai suna kallon ina Ansariyya din sàida sukai da gaske suka gano ta,,ta kara kyau ta kara girma hutu da jindadi sun zauna ajikinta"wata irin kunya ce ta kama Abba Gali,,Anty Zee kuwa bakin ciki da hassada ne ya cika Zuciyarta,,duka yadda taso riyyah ta wulakanta amma kalli yadda ya kara samun daukaka dajindadi"jin an ambaci riyyah Ameer dake daki ya fito har yana cin tuntube"idanun sane ya sauka kan riyyah da take sakar masa murmushi,,cikin jin dadin ganin ta ya matso Inda take Anty riyyah,,tsugunnawa yayi agabanta yana kwalawa Ameera kira tazo taga Anty riyyah dinsu ta dawo,,Ameera data tashi daga bacci fuska duk yawun bacci,,yanzu Ameer shekarar sa 14 Ameera shekarar ta goma,, rungume riyyah tai Anty riyyah ina kika tafi sanda kika tafi Yayah Ameer yayi ta kuka yana nemanki,,Mama ta dinga dukansa wai bashi da hankali dan Allah karki sake tafiya ki barmu"kan su ta shafa to ai gani na dawo yanzu"kin sakinta sukai zama sukai akusa da ita dan karta sake tafiya batare dasun sani ba.
"Abbu ne yayi gyaran murya kowa saiya nutsu dan yaji abunda yake faruwa,,kora musu jawabi yayi akan abunda ya kawo su wajan su,,shiru parlon ya dauka sai muzurai suke na rashin gaskiya,,mun baku Auran ta Inda Ansariyya ce"Abba Yahaya ne ya juya gare ta dan Allah riyyah kiyi mana afuwa kiyafe mana laifukanmu"yanzu dai kinga halinda nake ciki bani da komai gidan da kiganni acikima waccan matar annobar ta kwace shi"bansan haka zalinci yake ba sàida na hadu da Zulai tashi daya tasa naiwa matata korar kare tare da 'ya'yana sai maganarta kadai nake sauraro saidata tabbatar ta kwace komai nawa"da dukiyarki dana handime da tawa gaba daya ta hada ta tattare ta koma hannun ta,,ban isa nayi magana ba,,tundaga sannan na gane hakkinkine yake bibiyata,,lallai nayadda zalinci duhu ne kuma Allah baya taba barin wanda yazalinci maraya kiyafe min riyyah.
"Abba Gali dai shima neman yafiyar yake yi,,cikin jin haushi Anty Zee takalle su wai me akai mata da kuke ta bata hakuri,,ciyar da ita da muka dinga yi fa aiba abanza zamu bata taci tai kashi ba,,ke dallah yiwa mutane shiru ana Maganar masu hankali wayake zancan ki,,kedama ai babu Allah aranki saikije can kici gaba da dakon hakkinta akanki dankinfi kowa zaluntar ta cewar Abba Yahaya da Anty Zee din tai kular dashi,,eh naji bazan nemi yafiyar ba daganan katafi gidan redio ka sanar naki neman yafiyar wanann faratun.
"Babu wanda ya tanka mata acikin su gaba daya sungane hassada ce take damunta,,awajan Ansariyya tace ta yafe musu sosai sukai mata godiya har mota suka rakasu dayi musu kwatancan Inda suka sauka."Kudi Yayanmu ya debo ya damka musu aiko sai godiya suke suna shimasa Albarka.
Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
.....✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 79_80
"Kwanan su biyu a Kd aka daidaita komai sun nemi Aure har can garin kakanninta na Uba suka je,,acan akai komai aka gama sun bada dukiyar Aure harda sa rana wata 3 aka saka dai dai dana Salma"sosai Yayanmu yayi farin ciki kan Lokacin kowa zai shirya ashirya amare yadda ya kamata,,riyyah dan kunya kasa kallon su Umami tai tadaina yadda ta zauna tare da su,,sanda suka tashi tahowa Abba Gali harda mezai hana abarta anan gidan sa,,kallon sa kawai tayi Innayi ce tai caraf ALLAH ya sittiri bukui,,aida ganin waccan matar taka har yanzu na hango kin riyyah a kwayar idanun ta,,dama duk wanda yace baya sonka ai Naya sannaka,,kafarmu kafarta,,sunyi na'am da maganar Innayi itama riyyah koda wasa bazata sake yadda abarta awajan su ba,,tabbas Anty Zee zata iya cutar da ita dan bata da imani ko kadan.
"Bayan kwana biyu da komawar su ta matsawa Ummi yaushe zasu tafi dan tagaji da abunda Yayanmu ke mata,,babu dama ta fita saiya ce taje ta sako hijab bata ganin da maza agidan,,tana mamakin furucinsa taga dai duk kannan sane agidan amma dan bansan kishin sa ya hana ya gane hakan."Shima awannan Lokacin Sadik ya nuna yana san Humaida kai komai dai ma sha Allah dan danan iyayan sa sukazo nema masa Auranta ankuma basu"gaba daya ahalin yanxu wannan ahalin zagaye suke cikin tsantsar farin ciki.Mama Ramlah ce ta debe su dan sukje su kwanar mata kansu koma ABUJA haka nan Allah ya dora mata kaunar riyyah tana matukar santa"babu musu ita da Zuhura harda Humaida suka bita,, ubangayyar dai be soba sai nata rai yake baya son kokadan riyyah tai nisa dashi amma sai basarwa yake baya son yara su kawo masa raini.
"Karfe 8 na dare gaba dayan su suna parlo suna kwasar hira da Mazan gidan yayan Salma kenan,,lura Mama Ramlah tai babu riyyah acikin su,,harzata share saidai ta mike dan zuwa taga abunda ya hanata fitowa kodai bata da lafiya ne"tasanta da san hira da yanzu tana cikin su ana kwasar hirar da ita."Sanda ta tura kofar dakin riyyah tana zaune a kan bed dinsu rungume da wasu hotuna idanunta na zubar da hawaye"da sauri Mama Ramlah ta karasa kusa da riyyah,,subahannallahi meya sameki riyyah?ko wani waje na miki ciwo"fashewa ta sakeyi da kuka tana kara kankame hutunan akirjinta,,babu kowa Mama na tuna da Abba na da Ummi,,naso ace suna raye"nasa da yanzu suna cikin farin cikin da basu tabayin Kamar sa ba,,da ace nasan dangin mamana nasan zasu nunamin wannàn kaunar,,wanake dashi yanzu duk babu jinina,,nasan kuna matukar kokari akaina ba butulci zammu ku ba"amma abun da akwai ciwo Mama,,sake fashewa da kuka riyyah tai haba riyyah muna tare dake akwai wani abu da zaisaki a damuwa,,bazamu taba daina kaunarki ba"nasani Mama ta fada tana goge hawayan fuskarta wani na zuba.
"Rarrashinta Mama Ramlah taci gaba dayi tare dayi mata nasiha me ratsa jiki da Zuciya,,harta mike zata futa idanun ta ya sauka akan hoton dake kasa,,wanda sam riyyah batasan da faduwar saba,, tsugunnawa tai tana fadin gashunan kin yarda pic din Ummin naki,,idanunta takai kan hoton sàida zuciyarta ta harba da mugun karfi'kare ware idanun ta tayi tana kallon wadda take gani ajikin pic din"murya na rawa ta ambaci Khadija,,da sauri riyyah ta dago danjin sunan data ambata,,cakumo riyyah tai jikinta na rawa wacece wannan tana nuna mata hoton hannun ta,,Ummi nace riyyah ta furta cikin Mamakin yadda jikin Mama ke rawa"kina nufin kice wannan ce Ummin taki data rasu"gayada mata kai riyyah tai dan bakaramin ruko Mama taiwa hannun taba"abinda ya kara daure mata kai yadda taga Mama ta fashe da Kuka tare da rungume riyyah ajikin ta.
"Yanzu da gaske kanwata kin rasu,,Meyasa zakiyi mana haka Dija,,saboda me zaki tafi kibar mu,, zumbur ta tashi hannunta tuke da hoton gudu gudu ta fice daga dakin su riyyah ta fada nata dakin"wayarta ta raruma tai dialling wata number,,ana dagawa ta fashe da kuka hankali tashe wadda takira din take fadin Lafiya Ramlah"Innalillahi wanene ya rasu"Ummu naganta naganta wllh"cikin damuwa Ummu ke tambayarta wa kika ganni"Dijam mu Ummu"gaba daya Ummu riki cewa tai tana tambayar Mama akan tai mata bayani amma takasa yi sai kuka da take,,kit Ummu ta kashe wayar kallon yayar Mama Ramlah tai"anya Zaliha Ramlah tana Lafiya kuwa hankali yakasa kwanci tashi muje gidan nagano halin da take ciki banason itama na rasata kamar yadda na rasa 'yar uwarta"cikin damuwa wadda Ummu takira da suna Zaliha ta mike in sha Allah ma babu abunda ya same ta.
"Sàida suka futo ainihin harabar gidan naga ashe babban gidane part part ne akallah sunkai goma ginine duk iri daya"wata matace ta futo daga wani part zatai sa'ar Ummu koma tafita manyanta"Ina zuwa haka naga kuna ta sauri kamar babu lpy"gimtse face Ummu tai àah Lafiya kalau zamu dan fita unguwa ne"kodai wanine baida Lafiya,,babu wanda baida Lafiya kowa garau yake"zata cilla mata wata tambayar Ummu tai gaba ta barta awajan ta lura Iyami bata da aikin yi"ta gane sarai bugun cikin su take taji inda zasu je"binsu da harara Iyamin tayi gayyar na ayya gayyar tsiya haka zaku kare cikin wahala indai ina raye ,,🙄🙄🙄tofa ita kuma wannan wacece?.
"Zaliha ke driving sun kosa su karasa gidan Mama Ramlah,,sanda suka shiga su Salma suna zaune har Lokacin suna hira,,da gudu Salma tatashi ta rungume Ummu,,ke cikani karki kadani katuwar budurwa dake,,jikin Anty Zaliha ta fada sannu da zuwa Anty,,aini baruwa na dake tunda sai yanzu kika ganni,,kai tuba nake Anty.Kinga ba wannan ba ina mamanki tana sama Ummu,,ok haurawa sukai Anty Zaliha ce ta leka tana ambatar sunan Ramlah Ramlah.Jin kamar ana màgana a room din Salma yasa suka nufi dakin"Mama na mamike da riyyah sai rusar kuka take jin Dijan su ta rasu"riyyah dai ji take kamar amafatki haryanzu takasa gasgata me kunnan ta yake juyo mata.
"Da sassarfa suka shigo dakin"da sauri Ummu takarasa tana taba Ramlah,,ke lafiyarki kuwa kukanme kikeyi,,wacece kika rungume haka bayan mun baro salma a parlo"jikarki ce Ummu tafada cikin raunin murya,kallon kallo suka farayi ita da Anty Zaliha kiyi mana bayani yadda zamu gane Ramlah kin barmu aduhu"saikin riyyah tai ta dago fuskarta data baci da hawaye"dawa tai miki kama Ummu"tsurawa riyyah idanu sukai cikin sauri Ummu ta matso Fuskar Kadija ta nake gani a fuskarta,, Murmushi mama.tasaki,,to 'yar Kadija ce wannan din jinin muce Ummu,,jininmu ke yawo ajikin ta,,miko mata hoton hannun tayi suka karba har gware suke ita da Anty Zaliha wajan leka mene acikin photon"Ummu ce ta fashe da Kuka tabbas wannan Kadija ta ce ko zanyi shekara dubu ban gantaba bazan kasa gane yarinyata ba."Allah ya isa tsakanina da duk wanda ya rabani da diya ta,,bazan taba yafe masa ba ko wanene shi.
"Sauri zama tai a kusa da riyyah datake binsu da kallo daya bayan daya"tsantsar kamannin Ummin ta ta gano a fuskokin su"barimma Ummu yadda kasan Ummin ta take kallo saidai wannan Fuskar tafi ta Umminta manyan ta,, rungume ta Ummu tai ya sunan ki ina Kadija dan Allah tashi muje kikaini inda take"shekaru na shafe ina kukan rashin ta,,kewa da damuwa da ita ta sun kasa barin zuciya ta ta huta,,shiru riyyah tai ganin yadda gaba dayan su suke kuka alamar akwai abunda ya taba zukatan su,,akwai wani miki da aka fama.musu,,girgiza riyyah Ummu ta sakeyi tashi muje naganta,, girgiza kai riyyah tai tana share hawayan ta,,Ummi na bata raye shekaru 4 kenan da barinta duniya ita da.Abbana,,shiru ne ya ratsa dakin kafin Ummu ta sake rushewa da kuka Innalillahi Yanzu Autata ta rasu wayyo Allah ina zansa kaina,,sambatu Ummu take tana kuka shabe shabe,, riyyah dai na kallon su wani haushine ya turnike zuciyar ta,,da sunsan suna santa suka.kasa nemanta har tsayin wannan Lokacin.
"Ni wanann kukan da kukeyi gaba daya ba burgeni kukai ba"meyasa naku nemi Ummi ba saidata rasu yanzu zaku kama Kukan rashin ta"kuna zatan kun mata adalci Ummi ta shafe shekaru cikin damuwa da kuka,,nasha kamata tana Kuka amma inna tambayeta sai cemin bakomai,,duk yadda naso Ummi ta sanar dani suwanene danginta,,alokacin zanga bacin ranta tasha gargada ta baruwana da tambayar danginta tunda nasan nawa dangin tona kyaleta sanin danginta bashi da amfani."Hakan da Ummi ke gayamin nasa araina tabbas danginta sun cutar da ita wanda bata fatan takara haduwa dasu duk da suna cikin zuciyar ta takasa mantawa dasu"ku ansamin tambayata me Ummi na tai muku Kuka bamzatar da rayuwar ta,,ta mutu cikin bege da kewar ku,,kuna tunanin Allah zai barku,,kunsan yadda ta kaunace ku kuwa?tai musu tambayar tana binsu da kallo cike dajin haushin su"sam batai farin cikin data dauka zatai intaga dangin Ummin ta ba,,sunkasance masu san kansu tunda tsahon shekaru basu sake waiwayar taba,,basu sake tunanin taba sai ayanzun zasu fara wani kuka mara amfani,,share hawayan ta tayi tana kokarin mikewa tabar musu dakin,,bama.dakin kadai zata bari ba gidan zata bari gaba daya.
"Da sauri Anty Zaliha ta ruko hannun ta,,kina tuhumar mine akan abunda bamu da laifi akansa,,kinsan shekaru.nawa Ummu ta kwashe tana kukan rashin 'yar ta,,tun shekara daya da Kadija tabar gida Ummu ta fara nemanta,,tasha kwanciya agadon asibiti adalilin rashin ta,,aduk cikimmu munsani kowa yasani Kadija ita ce mafi soyuwa awajan Ummu da Abbu suna matukar kaunarta,,shin kina zatan iyaye zasu haifi da acikin su su bamzatar dashi suna sane"àah hakan bazai kasance ba musamman uwa,,Uwa ta dabance riyyah,,Mahaifi zai iya juyawa dansa baya amma Mahaifiya koda tayi fushi tana saurin sakkowa ta rungumi 'ya'yanta,,ki zauna ki saurari uzurimmu ki tabbatar da cewa munfiki kaunar Kadija munkuma shafe shekaru muna nemanta."Maganganun Anty Zaliha sun sanyaya jikinta hakanne yasa ta koma ta zauna.
"Hannayan ta Ummu tarike muryarta na rawa tafara magana kamar haka.....Shakaru 30 da suka wuce"Unguwar Kaleri nanne inda tunda mukai Aure da kakanki wannan gidan aka kaini"naje na tarar da facaloli matan yayyan mina,,ga kuma surukaina awanann lokacin atakaice dai gidan yawane,,saidai kowacce da bangaran ta babu ruwan wata da wata,,amma duk da hakan ana samun sabani dan akwai 'yan sa ido da hana ruwa gudu.Muna zaman lafiya nida Mijina Alhaji Badamasi babu mejin kammu"sabanin sauran mutan gidan da lokaci lokaci zaka dinga jin hayaniyar su da mazajan su,,wani lokacin harsai surukammu sun shiga lamarin,,ganin ba'a taba jin kammu da mijina ba sai abun ya tsayewa wasu arai,,oho banmasan suna yiba nidai da zuciya daya nake zaune dasu,,bana kuma nufar kowa da sharri.
"Duk gidan munfi da sawa da Bilkisu muna kiranta da Maman Arif komai kusan tare muke yinsa saboda halinmu ya zo kusan daya"ita ma baka taba jin kanta da Mijinta komai zasu kashe su rufe atsakanin su sai tamu tazo daya da maman Arif,,hakan saiya kara harzuka sauran matan yayan mijina damme Maman Arif zata zama kawata,,awanann lokacin Ubanta kusa ne acikin siyasa,zatansu tarayyata da ita wata tsiya take dauka taban,,basu san Allah yayimin wadatar zuci ba,,nima kuma.iyayana masu kudine,,babu abunda zanne ma basiyi minba.Haihuwa ta fari 'yan biyu ba haifa aka samu Hassan da Hussain,,surukaina sunyi matukar farin ciki haka mijina da sauran masoyana ciko harda maman Arif sosai akai shagalin suka aka watse"sai Hajja da Alhaji sunan da muke kiran surukaina kenan suka dauki so da kauna suka dorawa Hassan da Husaini wannan abu ya kara jawon bakin jini musamman a wajan Iyami"matar data doramun tsana bansan abunda na tare mata ba haka kawai ta tsangwameni,,tasha kai gulmata wajan Hajja karshe saidai Hajja ta zageta tas tas koro ta,,ganin ta kasa samun wannan saita dawo wajan Maman Arif da tarabamu nanma bataci nasara ba,,saita koma wajan 'yan gidan anan dai taci nasara suka hade min kai,,innaiwa mijina magana akan menai musu suke ware ni,,saiyace na rabu dasu duk hassada suke min da bakin ciki hakan kuwa akai na rabu dasu.
"Bayan Hassan da Husaini na haifi Umar,sai Zaliha,sai Mariya,sai Ramlah,sai Kadija Auta,,min dauki so mun dorawa Kadija komai take so zamiyi mata,,gata da farin jini tun tana karama ake kawon kayan gaisuwa wai ana kamun ta,,saidai nayi dariya kawai dan kyau ma sha Allah Kadija na da kyawu sosai,,duk da ba fara bace amma kyanta yadda kasan irin black american nan haka fatarta take,gashinta har gadon bayanta bata da hayaniya ko kadan haka take da sanyin hali.Laokacin data gama Secondary school sai kanin Maman Arif Tajuddeen ya nuna yana santa,,nayi farin ciki matuka sanin ahalin Maman Arif basu da wata matsala,,haka Tajuddeen nitsatstsen yaro ne me hankali,,magana fa tai karfi har ankaiga tsaida ranar Aure sosai suke kaunar junan su,, Lokacin ne mahassada na suka dawo da duk wata kiyayyata da sukeyi kan Kadija,,tako wane bangare hari suke kawo mata dan ganin anfasa wannan Aure akarshe dai sukai nasara wajan kulla mata babban makirci wanda ta kasa tsallakewa.
"Hawaye Ummu tashare haka suma suke sharar hawaye,,bakar rana agaremu itace ranar wata Asabar,kowa yana gida tunda hutun ma'aikata ne dama babu wanda yake fita,,kururuwar Shema'u 'yar Iyami mukaji tana fadin kwarto adakin Kadija,,asukwane mukai dakin abunda muka gani ya jijjiga zuka tammu,,Kadija tace rungume jikin wani kato babu suttura ajinta,,sai bacci take lakadan babu wani abu daya dameta,,Kuka na fashe dashi nai baya zan fadi saboda tashin hankali dana shiga,,da sauri Alhasan ya taro ni nafada jikinsa,,abundaya daure mana kai kafin mu ankara wannan kwarto ya gudu sama ko kasa aka rasashi ta wace hanya ya fita babu wanda ya sani"nan fa hayaniya ta kaure sai awanann lokacin Kadija ta farka,,ganin yadda aka cika mata daki abun ya bata mamaki jikinta ta kalla ganin babu komai ajikinta ta kwalla kara tashige cikin bargo,,tsantsar tashin hankali abunda yake faruwa ta kasa Kuka,,munafuka annamimiya cewar Iyami ni dama na dade ina zargin yarinyar nan ashe kyan dan maciji tayi yau Allah ya Toni asirinki.
"Mahaifinta ba wani bun ba'asi ya fisgota yadinga narkarta kamar ya samu jaka saidaya yimata jina jina,,lokacin babu wanda yaji aransa abunda muka gani ba gaskiya bane,, Iyami ita ce me bakin magana sai kara hura wutar take,, Allah sarki Kadija hancinta na zubda jini haka Mahaifinta ya watso mata kayanta ya bata nanda mintuna biyar ta fitar mai daga gida,,wani shegen murmushi naga Iyami na saki wanda na kasa gane ma'narsa,,gashi dai inaji araina Kadija bazata aikata hakanba amma bakina ya kulle,,inason naje na rungume 'yata hakan ma yagagara,,muna gefe muna Kuka,,munaji muna gani Kadija tabar gidan har juyowa tai ta kalleni da neman dauki agareni amma nai saurin kauda kaina daga kallon ta,,batasan kowa ba saimu gashi rana daya ankore ta.
"Tunda tatafi nake jin ciwo da radadi amma nakasa magana akanta,, Tajuddeen yazo kamar yayi hauka ya bazama neman ta amma ina babu ita ba Labarin ta,,yadda kasan zai cinnawa gidannan wuta haka yadinga tashin hankali ya gigita duk wanda yake cikin gidan,,yayi rantsuawar sharri akaiwa Kadijan sa,,awata rana ne Iyami ta kirashi wai mezai hana amaida Auran kan shema'u 'yarta"wata matsiyaciyar shaka yayiwa Iyami wadda ihunta ya jawo hankalimmu hankalimmu yayi mummunan tashi ganin yadda yake kokarin kisan kai,,da kyar muka kwaci Iyami wadda ta fara jin kamshin Mutuwa,,nuna ta yayi da dan yatsansa,,munafuka azzaluma ni dama ke nake zargin kinwa masoyiyata sharri ina tabbatar miki na kammala bincikena na gano kece na lahira saiya fiki jindadi,,kowa tsaurawa Iyami idanu yayi tayi fiki fiki tana zazzare idanu gashi ta kasa kare kanta,,ai kamar Taj yayi mana wankin kwakwalwa sai Lokacin muka tuna da baunda ya faru,,sai kuma muka bazama neman ta bayan lokaci ya kure mana,,mahaifinta Kuka ya fashe dashi da tunanin ya akaima ya kore ta,,wane tsautsayin ne ya kaishi ya koreta."Rayuwa fa tai mana zafi da kunci,,gari gari haka Mahaifinta yadinga bi dan cigiyarta amma babu ita,,nayi Kuka kamar zan rasa raina haka maman Arif ketayani aduk sanda nake kukan,,ta tabbatar min alokacin tagane makirci aka hadawa Kadija amma takasa furta hakan dan jitai kamar anrike mata baki,,hakanne yasa na tabbatar wanda ya shirya hakan akwai wani abu daya kulla mana muma,,harka wo yau da kika ganni bancire rai da ganin Kadija ba,,ashe tarasu batare da munnemi yafiyar taba,,nasan muncutar da ita,,munkuma zalince ta hakika Allah bazai barmu da hakkinta ba.Wannan shine abunda ya faru da Mahaifiyar ki.......
Allah sarki Rayuwa Allah ka hadamu da Abokan zama Nagari......
Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 81_82
Nima dai yajin aiki zan tafi,,,kamar yadda nepa suka tafi yajin aiki.🏃🏃🏃🙋
"Shiru sukai sai kukan riyyah daya ke tashi adakin jin irin kazafin da akaiwa Ummin ta,,komawa yayi mata wannan sharrin da sannu za'a gano shi,,dafa kafadarta Anty Zaliha tai bamu labarin rayuwar Ummin ki bayan rabuwar ta damu."Gayara zama tai ta kwashe duk irin rayuwar da Ummi tai,,da irin gararin data shiga bayan rasuwar Ummin ta da Abbanta,,sosai suke kuka saboda tsananin tausayin riyyah,, rungume ta Mama Ramlah tai wahalarki taxo karshe riyyah shiyasa tun lokacin dana ganki naji kaunarki acikin zuciyata,,ashe 'yar kanwata ce ke,,mafi soyuwa agare mu,,tabbas dangin Mahaifinki sun cutar dake,,amma Allah ya fisu tunda Allah ya wulloki hannu Nagari.Babu abunda zance da Umami da Batool saidai matukar Godiya agare su,,sun daukeki batare da sun san kewacece ba,,basu taba banbanta ki da 'ya 'yan su ba,,tsakani da Allah suka kaunarki,,babu abunda zammu su saidai Addu'a fatan Alkhairi.
"Hakane Ramlah cewar Ummu,,lallai kinyi sa'ar samun abokan zama nagari,,Allah ya saka musu da mafificin Alkhairi,,Ummu cikin farin ciki tadinga kiran waya tana sanar da Jama'a anga no diyar Kadija,,hatta su Umami da Ummi Mami Innayi sàida suka dungumo gidan dan jin wanann abun Alkhairi daya faru,,sunyi matukar farin ciki,,sun kuma godewa Allah daba wulakanta riyyah sukai ba yanzu da dawani idon zasu kalli Mama Ramlah da Ummu,,yayyan Ummin ta su Alhaji Hassan da Alhaji Hussain haka suka.kwaso iyalansu rungume ta sukai suna jin tamkar Autar su ce agabansu Kadija,,saboda.tsananin kamar da sukai da riyyah,,kai farin ciki fa yayiwa riyyah yawa ganin yadda al'umma suke ta barkowa dan kawai suzo su ganta,,ashe haka take da dangin jingim amaiduguri batare data sani ba,,lallai taga karamcin Kanuri tun kafin su san wacece ita suka riketa hannu bibbiyu,,kukan farin ciki tasaki ganin yadda kowa yake burin ta zauna kusa dashi a dangin Ummin ta,,ina ma ace Umminta na raye da wani irin farin ciki zatai ayau,,tabbas tasan yadda Ummi ta kaunace iyayanta da 'yan uwanta ta tabbatar da ayau zatai kukan farin cikin data dade batai kamar saba,,Allah jikanki Ummina da Abbana,,,Ameen suka amsa gaba daya batasan afili tai Addu'ar ba.
"Kakanta Alhaji Badamasi duk da baya kasar amma asatin yace zai dawo dan kawai yaga jikarsa,,yasa an hadashi da ita awaya farin cikin sa ya gaza boyuwa,,sai tambayar ta yake mezai kawo mata,,sai yashe baki da take ganin yadda kowa burinsa ya kyautata mata,,catai duka abunda yaga yadace da ita to yakawo mata tana so,,aiko zakiga tsaraba Amarya ta,,kisanar da wannan lusarin mijin naki tunda ya kasa ni ganinan zanzo nine wanda zanyi wuff dake,,dariya riyyah ta kyalkyale da ita,, àah kam ni gwarzona jarumi ne,,kai yanzu aka.kaika filin daga ai sàidai akwaso ka shukuwa fa saidai makiya suji tsoro su dare suna gudu hadda fitsari.awando,,cikin Dariya Alhaji Badamasi ya furta iyeee hakane abun zan baki mamaki bari in zai fita filin dagar zamu tafi tare,, aah gaskiya bazan so ai rugu rugu da kasusuwan kaba zakai kin wani Amfanin,,cikin barkwanci da tsokana suka gama wayar,,tana dago ido caraf suka fada kanna Yayanmu zaro idanu tai gaba daya batasan sanda yazo kusa da ita ba.
Kallon ko ina tai ba kowa sai ita kadai azaune tana shan iska,,marairaice fuska tai Yayanmu amma bakaji abunda nace ba,kauda kansa yayi yana sakin Murmushi jiwani kama kai,,ana so ana kaiwa market,,ashedai yarinyar ta mato akaina,,😒hararar wasa ta cilla masa,,da sauri ya dafe saitin zuciyar sa na karbi wanann salon,,dariya ta saka ganin yadda ya dafe kirjinsa kamar gaske,, murmushi yayi yana kallonta,,dariya ba karamar kyau take mata ba,,dan karamin bakinta yake kallo jiyake kamar yayi 😘 din sa,,ya matsu ayi a shafa akai masa matar sa,,ai yayi mugun kokari ma,,amma sai ja masa rai akeyi shigani yakema gaba daya lokacin baya tafiya,,ganin yadda yake matso da fuskarsa kusa da tata batare daya sani ba tai saurin saka hannun ta a tsakiyar face din su,,sai Lokacin ya lura da abunda yake shirin yi,,kwabe face tai tanai masa nuni da ido akan ya matsa,,make kafada yayi alamar yaki."Baya tai da fuskarta ya kara biyota narai narai tai da idanu kamar zatai kuka,,dariya yadan saki kafin ya mike ya zauna inya ganta acikin tsoro idanun ta bakaramin burgeshi suke yiba.
"Mikewa tai tana kokarin guduwa ya ruko hannun ta,,haba matar jarumi ina zaki je kibar gwarzan zuciyar taki,,rufe fuska tai tana dariya gaba daya kunya ta kamata,,kunyar me zakiji jawota yayi sai gata akan cinyar sa,,zabura tai zata mike ya komar da ita hade face yayi kamar bashi yagama dariya yanzu fa."Nifa matata banason naga tanamin duhun kai,,so nake miyi rayuwa tamkar bamu taba zaman nigeria ba,,in muna gida bana so naga ko nan da can kin matsa ko yaushe nafi so najiki ajiki na,,wata magana ya rada mata akunne zaro idanu tai kafin tasa kukan shagwa dariya yakeyi dan yasan abunda ya fada mata,,nidai Yayanmu ka bari banaso,,ko naje nasamu Innayi na sanar da ita kana son iskanta ni,, murmushi ya saki to bari nayi medalilin kawai,,zip din rigarta ya fada laluba kamar zai zuge zumbur ta mike ta fanna da gudu yabita da kallo yana dariya,,shafa kansa yayi sai shegen surutu amma ga tsoro.
"Alhaji Badamasi daya dawo tasha tsaraba can family house din su suka dunguma"gagarumar walima ya hada danshi jiyake kamar Dijan sace ta dawo,,gaba daya 'yan gidan su Major kwansu da kwarkwatar su sun dunguma gidan Ummu,,su Innayi sune agaba wajan gudanar da walima kaya iri daya ya dinka musu Zuhura Salma Humaida riyyah kala daya ya dinka musu wata dakkiyar shadda,,doguwar riga akayi musu dinki bubu bakaramin kyau sukai ba,,an tsantsara musu kwalliya sai suka fito kusan kansu daya,,sàida suka shigo wajan walimar ta lura da yayanmu da suka sha nasu Ankon iri daya da nasu Alhaji Badamasi yayi musu shida Sadik da Saurayin Salma,,suna hada idanu ya kashe mata ido da kumbura fuska yana nuna mata mutanan wajan tarufe mai jikinsa sosai,, murguda masa baki tai alamar taki,,bakinsa ya datse alamar zata zo hannun sa.
"Walima anci ansha dangin su Ummu sun hallara ancika gidan makil,Allah sarki Tajudden sanda yaga riyyah rungume ta yayi yana tunawa da Abar kaunar sa Kadija itama riyyah taji tana matukar kaunar sa sosai tunda ya kaunaci Ummin ta,,ya zama cikakken magidanci da kyar aka samu yayi Aure shekaru goma da suka wuce,,ansha fama kafin ya amince da Auran hadda matar sa ya yaransa biyu suka zo"yakoyi sa'ar mata me kirki da mutunci,,tun sanda ta Auri Taj ta tabbatar san Kadija yayi nisa azuciyar sa,,shiyasa tataya shi san abunda yake so,,hakan data nuna shiya fara jawo hankalinsa zuwa gareta,kuma har zuciyarta take Addu'a Allah ya bayyana musu Kadija bata da damuwa Indai mijinta zai samu farin ciki to bada da bakin ciki da bayyanar Kadija (Allah sarki kaji masuyi dan Allah,,🙄🙄kufa dauki darasi akan Sumayya kuso abinda Mijinku keso karnaji karna gani lol)har gift yazowa da riyyah haka Sumayya itama da nata gift din."Taro fa komai yayi dai dai,,komai yatafi yadda akeso saidai ace Alhmdlh.
"Duk da wannan bidirin da akeyi Iyami nadaki kamar zuciyar ta zata babbake,,ganin yadda Kadija bata wulakanta ba harda Aure takasa zaune ta kasa tsaye,,dukkan ahalin Ummu ta tsanesu matukar tsana,,daya daga cikin 'yayanta ne ta shigo hannunta dauke da ledar take away sai washe baki take tana kai walima tayi dadi Alhmdlh munci munsha wanda beje ba shi yayiwa kansa,,cikin bacin rai Iyami take kallon Sajida da take cike da farin ciki,,nikam Sajida kodai ancanza min ke a asibiti ban sani ba,,yanzu dan rashin zuciya sàida kika je wajan walimar nan,,meza'a baki wanda ba kyacin irin sa,,to Umma abunda nakeci dan ambani ai bawani abu bane babu wanda baya son ihsani arayuwar sa,,nidai bazan fasa shiga sabgar Ummu ba gaskiya saidai kiyi hakuri,,kuma ni da hankali na da ilimina mutane babu abunda suka takan sai nadauki gaba dasu bazan iya ba wllh,,ni gidan mijina ma zanzo na wuce Allah ya huci zuciyar ki Umma,,yarinayrta dake bacci ta saba ta goya kafin ta dauki mayafinta da hand bag dinta tafice tabar Iyami sake da baki tana binta da kallo.
"Wata ce ta kara shigowa again fuska taci mai duk yadda takai ga feleke daga ganin fuskarta ansan ba yarinya bace,,kallon Iyami tai dake tsaye kamar andasata,,Iyami tsayuwar me kike kamar wadda akaiwa gorin zama,,sai Lokacin ta farga da shigowarta,,tundaga sama harkasa take kallon ta,,yanzu ke shema'u daga gidan ubanwa kike,,tun safe kika fice daga gidanan amma sai yanzu zaki dawo,,wai meyasa kike son takura min Iyami saboda ALLAH in ban fita na zazzagaya ba ko Allah zaisa na sami mijin Aure so kike na.zauna.agida a manta dani,,kas ta cigaba da taunar cimgom dinta,,haba shema'u wace maganar banza kike fadamin haka,,yanzu shekarunki nawa akalla kinyi shekaru 35 har yanzu babu wani daya taba zuwa yace yana sonki ni wllh nafara gajiya ga kannanki babu wanda beyi Aure ba amma banda me,,Kuka shama'u ta fashe dashi yanzu Iyami ni kikewa gorin Aure,,kin manta harna sami tsayayyen saurayi yana shirin turo iyayansa kika huran kunne ke Tajudden kike so na aura,,duka da kinsan kanwata yake so a wannan lokacin,,tun banyadda da hudu barki ba harna yadda da Abunda kika fadamin,,yanzu duk kinmanta to bari na fada miki Iyami,,gaba dayammu hakkin Kadija bazai taba barin muba,,yadda kikai sanadin barinta gida shiyasa Allah yake hukuntani da wanann zunubin da muka aikata,,wllh nayi nadamar bin shawarar ki yanzu kinkaini kin baro ni megakinan daram adakin Mijinki,,ni kuma ina nan ina gararamba agari narasa mashinshini,,kwarton da kika nemo kika samata adaki shikadai sai Allah ya saka mata,,nida bani na kawo kwarton bama kallo irin sakayyar dake bibiyata balle kuma ke da kika nemo shi da kanki wllh Allah bazai barki ba Iyami,,duk fa wannan maganar cikin Kuka Shema'u take korawa Iyami jawabi"daga hannu tai zata yarfawa shama'u mari taji ance kul Iyami kika sake kika daki yarinyar nan,,ashe dama ke Mutuniyar banza ce,,abunda kikai aikata dama shekara da shekaru kenan,,a tsorace Iyami take kallon mijinta Alhaji Ishaq cikin bacin rai da tsantsar tsana yake kallon ta,,kamar yadda 'yarki ta fada ne ita kinyi.silar rasa nata masoyin to.kema yanzu zaiyi sanadin rasa igiyoyin Auranki,,da gudu Iyami ta duka agabansa dan Allah Alhaji kayi min rai wllh natuba dan Allah karka sakeni nashiga uku wayyo Allah na,,kukan da Iyami ke rusawa shi yajawo hankalin jama'ar gidan dan danan suka taru a part din Iyami danjin abunda ke faruwa."Cikin fusata ya fisge kafarsa kar wanann kazamin hannun naki ya kara taba ni keje nasake ki saki Uku nidake har abada Iyami"salati mutanan wajan suka dauka"Alhaji Badamasi ne ya matso kusa da yayan nasa haba Yayah yaza'ai ka yanke wannan danyan hukuncin akan matar ka,,shekara da shekaru kuna tare sàida kuka.manyanta zakui irin wannan rabuwa,,kyaleni Badamasi bakasan tsahon bakin cikin da wanann matar ta cusa minba,,tunda na aureta ban huta ba haka nake hakurin zama da ita,,amma Abunda naji ta aikata ayau naji tabbas bazan iya ci gaba da zaman da ita ba,,daka.mata tsawa yayi munafuka kiyi mana bayanin yadda abun yafaru,,kukan bakin ciki Iyami ta fashe dashi asanadin iyalin Ummu ta rasa Auranta ita ko tashiga uku.
"Dan Allah kuyi hakuri wllh sharrin shedanne,,kuyi hakuri kuyafe min,,Innayi.da bakinta baya shiru tai caraf ke dallah kiyi mana bayanin abunda kika aikata kafin musan mizanin da zamu dora ki,,dama nice na kawo wanann kwarton dakin Dija,,salati suka saki suna kallon Iyami da take rusar kuka,,Kuka Ummu ta fashe dashi wllh Iyami kin cutar damu bazamu taba yafe miki ba har abada kuwa,,kuma kije keda Allah ni bana son jinma yadda akai kika kawo shi cikin gidannan kije dan kanki,,wadda kikaiwa kazafin bata raye in kinje can zaki girbi abunda kikai shuka wllh,,juyawa.Ummu tai dan wllh ji take intaci gaba da tsaiwa zata iya yiwa Iyami lahani,,tabe baki Innayi tai kaji tsiyar mugun abu sanda zaka aikta bakajin komai sai ranar nadamar da bata da amfani ka.ishi mutane da koke koke,,kowa fashewa yayi ya barta tana durkushe tana rusar Kuka,, shama'u na tayata koda dai kowa da abunda ya dame shi azuciya,,catai zama daram babu inda zataje zaman 'ya'yanta zatai."Ummu kuka take sosai haka riyyah da sauran 'ya'yan ummun,,bata taba sani haka Iyami take kinta ba tunda harzata iya yiwa 'yarta wannnan mummunan kazafin.
Alhaji Badamasi shima karfin hali kawai yake amma yaji dacin abunda Iyami ta aikatawa diyarsa ba kadan ba,,ya shanye ne ganin irin hukuncin da Mijinta yayi mara dama ai Allah ba azzalumin bawan sa bane,,saidai shi bawan ya zalinci kansa,,gashinan tun yanzu ta fara ganin illar abunda taiwa 'yar su,,ga 'yarta nan yayar Kadija ce amma haryau ta kasa auruwa dama ance inzaka gina ramun mugunta gina shi daidai dakai wataran kai zaka rufta acikin sa.
"Bayan Sallar isha'i su Umami suka dauki hanyar unguwar su tunda angama walima ancinye,,anan suka bar riyyah danta kara sabawa da dangin Mahaifiyar ta,,aiko Ummu taji dadin haka koba komai zasi mata gyara na Musamman."Tattali da kulawa sosai take samu tako wane bangare,,Ummi hargidan ta biyota tazo sutafi,, Ummu ta lallaba ta tayi hakuri tabar musu riyyah ta kara kwana biyu,,sun tabbatar mata da cewar bazasu taba kwace mata riyyah ba 'yar tace halak malak,,badan Antymmu taji dadi haka ta hakura,,sun roki data bar musu Zuhura su zauna su Uku har salma batai musu ba dan tasan inta tafi da Zuhura ma kaya zata zame mata,,zata dameta da maganar riyyah ta dawo ko Aikin arziki bazata yi mata ba.
"Gyara aka ake musu haikan aziman,,kundai san Kanuri ba daga baya ba wajan gyare 'ya'yan su tsaf,,sai gashi sun kara wani fresh Sunyi matukar kyau tako ina kamshi ke tashi ajikin su,,Humaida Gidan ta dawo tare ake gyara su ciki' da bai,,da sun giftaka kamshi ke tashi tako ina,,haka angwaye sukai ta sintiri Ummu tace batasan zancan ba babu wadda Zasu gani Acikin su,,hatta wayoyin hannun su kwacewa tai dan kar su hilace su siyi Musu wayo,, Yayanmu kamar zaiyi hauka dan takaicin hanashi ganin riyyah da akai,,har Gidan Mama Ramlah yaje akan ta bada baki abarsu suga matansu tace babu ruwanta,,shima fushi yayi ya kyalesu aidai dole akawo musu matansu.
Saura wata daya Biki aka kawo kayan lefan su,,Humaida akwati 8 akai mata,,Salma akwatuna 6,, riyyah 12 akai mata,,kayane nagani na fada aciki komai sai san barka,,'yan uwa sai faman tururuwa suke ganin kaya,,can dangin babanta da akai musu waya ca sukai abar kayan anan in za'a taho daurin Aure a taho musu dashi sugani.
Wai ina labarin Sahar ne.
Sahar fa abubuwa sun cude musu komai yayi musu zafi,,ga Ambassador dayayi watsi da lamarin su,,Mom dai kamar zatai hauka haka takejin bakin cikin wannnan Auran,,part guda ya ware yake shekawa amarya gini na haduwa,,sosai ya bude bakin Aljihu sa,,wannan abu ya daga musu hankali,,ga Sahar da batasan ababin da take ba damma Saurayin ta yana debe mata kewa,,yanzu sun shirya tsaf zasu cale kasar Marocco,,sosai Sahar ta kara gyara kanta,,kayan mata ta dinga dirka saikace tare da Mijinta zasiyi tafiyar.
"Sati na zagayowa tabi saurayin ta mesuna Alhaji Barau suka cale danyi masa rakiya.......
Mrs 🌹 Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 83_84
"Sanda suka isa Marocco wani babban hotel suka sauka,,Alhaji Barau ya jibgo kayan kwalam da makulashe,,sunci sunsha kafin su fada masha'ar su,,wanann tafiya Sahar ba karamin dadinta taji ba,,kudade ta same su haka Alhaji Barau ya sakar mata bakin Aljihu,,duk abunda ta nuna tana so babu musu yake siya mata,, account dinta ita kanta bata san nawane aciki ba,,taci alwashin da sun dawo daga wannan tafiyar zata samo hatsabibin bokan dazai tarwatsa ahalin Rayyan,,saita mallakeshi ta yadda bazasu kara iya kubutar dashi daga sharrin ta.
"Yauma tana kwance jikin Alhaji I ya saki uban tunbi"amma a hakan sai karairaya take masa"masoyi ta"na'am Alhaji na murmushi ya saki,,in kikace Alhajinnan naki wani dadi nakeji,,saina dinga jina na dawo yaro danye sharaf,,dariya ta dan saki irin ta yaudara kafin tai fari da ido"to aini Alhaji na tamkar Jariri haka nake kallon ka,,washe baki yayi yana shafa dogon gashin ta daya sha gyara,,kishirya bayan La'asar akwai surprise din dana dade da tanadar kimi"babbar kyauta ce wadda na tabbatar bazaki taba mantawa da ita ba har karshen rayuwar ki,,wani irin dadi ne ya mamaye zuciyar Sahar lallai haduwarta da Alhajin nan zai zamo mata Alkhairi."Cikin yaudara ta kalle shi harkasa nafarajin zumudin zuwa inda ka tanadar mana"ai kisha kurumin ki masoyiya dama dan ke kadai na tanadi wajan,,cikin farin ciki ta manna masa kiss tana ayyana irin yadda zata zama babbar Hajiya me fada aji.
"Kamar yadda ya sanar da ita karfe 4 ta gama shiryawa,,cikin wasu matsatstsun riga da wando,,kanta ko hula babu ba mayafi haka ta dauki hand bag din ta,,fatata taje aka saka mata ga eye lashes data je aka manna mata,,face dinnan tasha makeup ta fito caras da ita.Hannunta na cikin na Alhaji Barau suka fada mota,,daidai wani kyaraccen gini suka tsaya unguwar shiru sai manya manyan gine gine na alfarma,,sai kallon wajan Sahar take da tunanin irin kyawun da wajan yake dashi,,jan hannunta yayi haba ke ko masoyiya taho mushiga mana,,keda zaki shiga cikinsa kisha kallo,, murmushi ta saki ai wajanne ya kayatar da ni my man,,kama hannunta yayi aka zuge musu get suka shige,,wasu gansama gansaman samarine majiya karfi me gadin kofar,,sàida gaban Sahar ya fadi ganin yadda suke muzurai babu alamun wasa a tatare dasu,,mazewa tai dan karta bada kanta ta dake"duk da zuciyarta rawa takeyi.
Makeken gida ne sassa daban daban tsit wajan yake kamar mutuwa ta gifta,,inane nan Alhaji ta tambayeshi ganin yadda suke kutsawa babu alamun akwai mutane acikin Gidan,,gidan wani abokina ne daga haka yaja bakinsa yayi shiru,,kofar wani dankareren parlo suka tsaya,, password yasa ajikin kofar kafin ta zuge kanta,,wani sanyine ya bigi fuskar Sahar har sadata lumshe idanu,,sàida suka je tsakiyar parlourn ta lura ashe akwai mutane akalla sunkai su 7 kowanne kansa yasha tankwal sai kyalli kawunan suke,,tunda suka shigo taga yadda suke kallonta kamar tsofaffun mayu haka kawai taji mutanan basiyi mata ba,,samun waje sukai suka zauna,,canza wani yare sukai wanda ko kadan bata jin abunda suke fada,,dagani dai jayayya sukeyi tsakanin su da Alhaji Barau,,dukannan su dai 'yan Arewa ne amma tarasa gane wannan wane kalar yare ne.
"Wata Baturiya ce tafito dauke da jus sai glass cup da doro akan plate,,kai tsaye gaban Sahar ta ajiye tare da tsiyaya mata jus din,,ganin wannan baturiyar ya hankalin kwanciya koba komai taga mace 'yar uwarta,, ahankali take kurbar jus din saidata shanye ta kara tsiyayar wani ba karamin dadi yayi mata ba,,wata irin kasala ce ta fara baibaye dukkan gabobin jikinta,,tun tana kokarin shan jus din har hannunta ya gaza haka,,gashidai idanunta abude amma jikinta ya daina motsawa,,kallon juna mutanan parlourn sukai kafin su saka dariyar keta.Hankalin Sahar ba karamin tashi yayi ba ganin gaba daya alhazan nan sun mike atare zuwa kanta sukai suka zagaye ta kamar sun sami TV.Alhaji Barau suka kalla aikinka yayi kyau kwaro,,dariya fashe da ita kundauka nidin na wasa ne,,ai Indai bazasu daina kwadayi ba to bazasu daina haduwa da irin muba,,nidai naci nawa rabon kowa saiyasa Albarka,,komawa gefe yayi ya zauna yana kallon su.
Daya daga cikine ya fara kici kicin cirewa Sahar dukkan kayan jikin ta,,sàida sukai mata tik zuwa lokacin Sahar hawaye take amma babu damar ta motsa ko ina"ba kunya ba tsoron Allah haka mutanann.sukai rik agaban junan su,,babu abunda ya dame su,,daya bayan daya suka dinga Saduwa da Sahar,,hatta ta dubura sàida kowannen su ya kwanta da ita,,tayi kuka ta suma azaba ke sata farfadowa,,duka Iskanci ta bata taba yadda Namiji ya shiga ta duburar ta saigashi yau har mutum bakwai sunyi sukuwa akanta,,babu dugon imani a zukatansu duk yadda sukaga jini na fita daga jikinta nasu kyaleta ba sàida sukai mata kaca kaca,,bayan sun gama abunda zasiyi wani farin kyalle suka dakko kowa ya goge gabansa kafin itama su goge mata.
"Sahar sam babu Numfashi atattare da ita,,wani daki suka jata suka watsata aciki kamar shara,,ficewa sukai daga gidan suka barta,,Sahar bata tashi farkowa ba sai cikin dare Kuka ta fashe dashi jin bala'in da takeji akasanta,,saidata roki Allah dama be halicce taba da dai taga wanann masifar,,motsa hannunta tayi taga ya motsa,,kokarin mikewa tai amma ina kafafunta sukace basu san wannan ba,,da kyar ta daddafa ta mike tsaye kamar kasanta ya zazzago haka take jinsa ga wata Iska datake shigarta,,nadamar da bata da amfani ce ta lullubeta,, toilet taja jiki tafada ruwan zafi tatara abaho tashiga cikinsa,,ihu ta zunduma jin tako ina azaba ce ke ratsata,,tayi Kuka kamar zata mutu,,haka ta dinga gasa kanta saidataji dama dama.Rabon data kalli gabas da sunan zatai sallah harta manta"yau saiga Sahar hadda dauro alwala,,batasan gabas ba,,gashi ba mayafi ko hijab ajikin ta,, towel babba ta dakko ta dora akanta,,haka ta kabbara sallah tanayi tana kuka,,tana idarwa taji anturo kofa sàida gabanta ya fadi,,wani kato ne ya shigo dauke da plate din Abinci sai ruwa guda daya batare dayace mata komai ba ya dangwarar mata yafice daga room din"kuka tafashe dashi ganin yadda take awulakance da gatanta da komai,,tatsinewa Barau babu adadi,,haka tahakura taci abincin ba karamar yunwa take jiba.
"Haka rayuwar Sahar takasance cikin tsanani da azaba,,su Alhaji Barau ba kyaleta sukai ba kullum sai sunzo sunyi amfani da ita harta baya,,ta suma ta farka saboda tsanani a zaba,,gaba daya Sàida suka tabbatar bata da wata mamora hatta tutu tadaina iya rikeshi sannan suka sata abut din motarsu suka fita da ita can bular garin suka wullata,,karnukan kasar da suka ganta sundauka wata halittar ce nan suka hauta da cizo da yakushi harsada sukai mata kaca kaca suka tabbatar ta daina motsi tukunna suka kyaleta,, Sahar dai a wulakance tamutu da ma'aikata suka zo kwashe shara aka hada da ita,,wama yasan tana ciki.(Allah kayi mana kyakykyawan karshe gadai yadda Sahar ta gama cin duniyarta da tsinke ga yadda karshan ta yakare,,in har ka zalinci dan uwanka kasani tunkafin kamutu Allah zai fara hukuntaka,,ta manta da lahirarta ta zabi duniya akan Lahira"yanxu gashi tayi mutuwar wulakanci). Wannan kenan.
"Iyayan biki su Umami ba zama tako wane bangare shiri akeyi,,in kaga yadda su riyyah suka zanzare,,suka kara wani sihirtaccen kyau zaka sha Mamaki,,duk inda suka juya walwali sukeyi"ayanzu riyyah bata da wata damuwa dangin Ummin ta babu Abunda basayi mata,,takan biya tai kuka tana yiwa Allah godiya akan ni'imar da yayi mata."Bangaran Yayanmu Gidan sa dayake dankarawa a Federal low cost nan za'a kai masa tauraruwar sa,,dan yaci alwashin bazai zauna inda Sahar ta zauna ba,,ya tsani dukkan wani abu daya shafeta.Unguwa daya suka kera gidajan su da Sadik mijin Salma da yake shima abokin sune duk basu da nisa da juna,,amma gidan Yayanmu yafi girma nesa ba kusa ba.
"Can Bangaran su Abba Yahaya shiri sukeyi dai dai nasu dan yanzu babu abun,,saidai a lallaba kawai,,yanzu gashi ya zalinci marainiya wata 'yar isaka daban tazo ta kwashe Kudin,,yauma fadane ya hadashi da matar kaddarar tashi,,dama haushinta yake ji,,duk wani tsoronta da yakeji ya daina ji kwata kwata,,zage kwanji yayi ya lafceta san ransa,,ta daku iya dakuwa sannan ya dankara mata saki biyu,,babu wata damuwa a fuskarta danya saketa dakinta ta wuce danta hada kayanta,,fuskarta fal murna ki banza ta yagi Abunda ta yaga,,binta yayi abaya dan gaba daya beyadda da itaba,,yadade yanason gano Inda ta boye mai kudade da ta kaddun kamfanunuwa,,gidaje da filaye,,ahankali ya tura kofar har bedroom ya bita,,karkashin gado yaga ta leka ta jawo wasu manyan jakunkuna guda uku,,zugewa tai saidaya zabura ganin kowace jaka shake take da kudi,,takaddun kadadarorin sa dana riyyah taba daya ta futo dasu tana dariyar mugunta,,awata jaka ta adana su kafin ta mike,,ficewa yayi ya samu waje ya zauna a parlo zaiga ta gidan Uban da zata fice da dukiyar sa.
"Fuska ahade tafito jaye da jakun kunan tana matsar kwallah"mikewa yayi gidan uwar wa zakije da wadannan jakunkunan,,in bantafi da kayana ba kai zan barwa,,nade hannun rigarsa yayi ashe yanzu zan dira akanki nai miki shegen duka,,ganin yadda yayo kanta gadan gadan yasata arcewa da gudu,,tunda tasan takaddun dake hannun kobata tafi da Kudin ba tasha,,,rufa mata baya yayi kanta fice ya cafkota,,wani shegen mari ya sakar mata sàida taga taurarin azaba,,baji bagani yadinga kirbarta,,saida yakara yimata lilis kafin ya kwace jakar hannun ta,,janta yayi ya watsata waje,,dawowa yayi ya dannawa kofar sakata,,kamar ranta zaifita take ihu tana tsine masa ko ajikinsa ya wuce ciki cikin farin ciki zai komawa riyyah da dukiyar ta,,haka dai yadda tazo a tsiyace haka tatafi inda tafito a tsiya ce🤣🤣🤣 Allah ya kara.
"Anty Zee ce kwance a parlon ta sai mata guguwa take sanadin wani azababban ciwon ciki daya takura mata,,sai birgima take ita kadai tasan azabar da take karba,,su Ameer sun zagayeta sunai mata sannu"Abba Gali na gefe yanaimata sannu dan gaba daya dan Abunda yake dashi ya kare wajan wannan ciwon nata,,wayyo nashiga uku!! Gali kayiwa Allah ka kaini asibiti,,zammutu,,yanzu Zainab ya kike so nai miki kinsan da ahalin yanzu na samu karayar arziki,,banda kudin da zanji da wannan ciwonnaki,,sanda kikaje akadinga miki allurar bleaching din kin sanar dani,,yanzu wa gari ya waya kin debowa kanki cuta,,cancer tai miki mummunar illah a mahaifarki,,ina ranar farin da kikai,,kalli fatarki ko kyawun gani baki dashi,, Zainab kingama cutar da rayuwar ki,,a sanda nake miki nasihar kizauna yadda Allah ya halicceki hawa kaina kikai da zagifa,,in kinmanta na tuna miki,,kece kika dinga zugani akan karna kula da riyyah,,yarinyar nan kwana nke da tausayinta amma saboda masifarki nake kauda kaina akanta,,aitunda na dakko ta na kawota gidannan kinsan ina kaunarta,,sanda kowa ya gujeta naji ni bazan iya barinta akan titi ba,,ko kinmanta cewa kikai in sabon gari zataje ta kama daki baki da damuwa,,wannan masifar da kike ciki wllh akwai hakkin zaluntar ta da kika dingayi,,kedai Zainab ba Matar arziki bace,,tunda bazaki taimaki Mijinki yayi aikin Alkhairi ba,,saidai ki dorashi a mummunar hanya,,yanzu saiki girbe Abunda kika shuka,,akan ciwonki bazan je naciwo bashin mutane ba azo a daure ni,,kade rigarsa yayi yafice daga parlon.
"Kuka Anty Zee ta fashe dashi,,Ameer da ke gabanta kauda kansa yayi,,ya dade yanajin zafin Mahaifiyar sa akan riyyah,,yana sane dama Allah bazai barta ba,,irin sakayyar daya guje mata kenan,,amma takiji,,dukda yana yaro yasan zalinci babu kyau,,amma tasha dukansa akan ya fada mata gaskiya,,Allah ya baki Lafiya Mama,,mikewa yayi ya dauki school bag dinsa yayi waje,, Ameera ma mikewa tai Allah ya kara sauki Mama tata school bag din ta goya tabi Ameer har sun fara late,,yanzu akafa suke tafiya basu da ko keke agidan balle mota,,binsu tai da kallo zuciyarta haryau ta kasa yaddar mata zaluntar riyyah tai balle ta nemi afuwarta,,Allah ka rabamu da kekashashshiyar zuciya"wadda bata tunatar damu sharrin mu,,sai daidammu.
"Wai ya labarin Baturiya,,abubuwa sun mata yawa aka,,ta rame ta kanjame,,Ladidi dake gefanta azaune tunda tazo take kare mata kallo,, Baturiya mezan gani haka,,ko dama abinda ke yawo agari kin kwaso kanjamau gaskiyane"kings yadda kika koma kuwa,,kalli wasu jijiyoyi da sukai miki kawanya,, Baturiya da bakin cikin Duniya yayi mata ko kala bata ce ba."Numfasawa Ladidi tai karki manta na 'yar uwar kice kisanar dani dukkan damuwarki,,daga mata hannu Baturiya tai kinga Ladidi banason Munafurci da tsugudidi badai kinzo kinganni ba,,ruwanki kifadi koma mezaki fada akaina,, 😒 banason bin kwakwkwafi,,dama ina ganin ki nasan badan Allah kikazo gidannan ba,,banda haka yaushe rabon dana ganki acikin gidannan.Tabe baki Ladidi tai,,to nidai bani nakar zomanba,,ratayarma ba'a bani b,,dama xuwa naiyi na sanar dake bikin 'yarki,,wace 'yartawa? riyyah mana ko harkin manta da ita,,to tana can meduguri Allah yayi mata gyadar doguwa harta hadu da dangin mahaifiyar ta,,wadda muka dinga yiwa gorin vata da asali,,ashe danginta har sunfi namu asali da tushe ga kudi,,aini wllh saiyanzu nakejin kunyar riyyah tabbas min aikata babban kuskure,,sam yaya be cancanci miyi masa abunda mukai masa ba."Tundata fara bayani wutar kan Baturiya ta dauke,,kallon bakin Ladidi kawai take amma gaba daya bajinta take ba,,dama 'yar isakar Yarinyar nan ba saceta akaiba guduwa tai,,amma ko ta cuceta da yanzu tana da tabbacin ta zama shaharriyar mekudi,,agidan ubanwa ta hadu da dangin uwar tata,,baki bide Ladidi yake kallon Baturiya da Hawaye ke zuba a fuskarta batare data sani ba,,ke Baturiya ko hassada kike mata da bakin ciki bamu sani ba?narantse da Allah da nasan zuwanta meduguri zai sadata da danginta daban kaita ba,,ashe ni gata naimata batare dana sani ba,,wannan yarinyar ta cuceni ta gama da rayuwata."Kinga Baturiya bangane inda kika sa gaba ba,,taya akai kika kaita meduguri al_halin bamu da kowa acan"aikatau na kaita shine da zanje tahowa da ita ta gudu"salati Ladidi ta saka tare da dafe kirji,,amma Baturiya kincika mara imani,,yanzu ki rasa abunda zaki sakawa yaya sai kai 'yarsa aikatau.Ladidi!!! Baturiya ta furta sunan ta afusace,,karki fusatani wllh,,ke kinkara tunani akanta ne ballantana ma kisan halin da take ciki,,ba Gwara mani na tuna da itaba,,harnai mata gata na kaita aikatau dinba,,ke kuwa fa ko saudaya baki kara danganta kanki da ita ba,,tashi kibarmun gida tunkan na tabbatar miki da abunda kike zargi na rayuwar bariki danai,,sanin rashin mutuncin Baturiya yasata daukar mayafinta,,to ai shikenan nadai isar da sako sati mezuwa shine biki,,anan Za'a daura Aure adunguma can meduguri asha shagalin biki,,in kina da interest akan zuwan zaki Iya magana dani,,ficewa tai tabar Baturiya dafe dakai,,yanzu abunda ya matukar damunta arayuwa sanyin da take ta kwaso,,in kaikayin nan ya taso mata ko agaban wanene daita zura hannu a zani tahau susa,,tayi maganin harta gaji babu wani sauyi da ake samu,,ga wasu kuraje da suka feso mata a prvet pant dinta,,gaba daya batajin dadin rayuwarta,, customer tuni sun kama gaban su,,bata da wani amfani yanzu,,Kuka ta fashe dashi tana nadamar halin data santa kanta,,duka a dalilin kawaye tabbas Zulfa ta cuceta,,tana zaman zamanta ta kwadaita mata harkar bariki,,yanzu gashi ta kaita ta baro tana can tana sharholiyarta,,harta mance rabon data ganta,,gwara zeenatu dama harkar bariki ba damunta tai ba,,bata mantawa sanda zata kai riyyah ta nuna hakan be face ba,,tana gidanta tana business hankalinta kwance.(Allah ya hadamu da abokan zama Nagari).
Kubiyo ni fans danjin yadda zata kaya.
Ka kasance me shuka Alkhairi akowane Lokaci,,matukar ka shuka kishirya kasan makomarka,,yanzu dai gashi suna girbar dukkan abunda suka shuka.
Manzan Allah (S A W ) ya fadi gwaggwaban lada ga duk wanda ya ciyar da Maraya da Bazzawara.'Yan uwa adage kar wannan Lada ya wuce ki matukar kika taimaki maraya kema Allah zai taimakeki.Babu wanda yake da tabbacin zai rayu da 'ya'yan sa muddin rai,,inka taimaki wani kaima Allah zai taimake ka.
"A wannan zamani zumunci ya lalace,,kowa gani yake inya dauki dan dan Uwansa aiya daurawa kansa wahala ne,,daga kauri sai guiwa kowa kansa ya sani,,mudage mu karfafa zumuntar mu.Zumunta akafa take basai kin bada wani abuba ko zakije aimiki kallon banzan kije ai kinsauke naki hakkin.Akwai masu wannan tunanin in akaga ina zuwa sai ace kwadayi naje,karki tunani akan wanann kije dai kinfita har agurin Allah.Basai kin zauna kin wuni ba mintuna biyar ya isheki inma ana tunanin kwadayin kikaje ki nuna baki damu da komai nasu ba,,ta hakan sai ataru azauna Lafiya.Allah ka kara mana zumunci.
Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 85_86
"Biki bidiri bire de"yau za'a fara Biki,, gagarumin Kamu da walima haj Ummu ta shirya tata ta kanta,,tun ranar Laraba aka fara shan galin biki babu kama hannun yaro,,tsararriyar fulawa da kunshi aka shekawa a maran,,sai walwali suke da sheki.Briden shower suka farayi ranar Laraba,,kawayan su kwansu da kwarkwatar su sàida suka gayyato su,, riyyah bata da kawa ko daya gaba daya 'yan uwanta ne sai kawayan Salma dana Humaida."Ranar Alhamis Arabian night suka gabatar sunsha ankon arabian gown maroon color sai Farin mayafi da sukai rolling."Yau Friday shine Kamu da walima da Ummu ta shirya a harabar Gidan ta."Amare sunfita tamkar ammusu wanka acikin inji musamman riyyah da fatar ta takara wani irin kwanciya,,tsabar hutu da gyara yazauna akan fatar tata.
"Can Bangaran Mami ita mafa ba'a barta abaya ba,,tata walimar ta hada ta musamman.(🤣🤣🤣 dagaske fa Mami ta canza tana farin ciki da abunda danta yake so,,lallai Mami anyi laushi da yawa.)'yan uwa da abokan arziki sun cika gidan makil Fuskar Mami kamar zata yage,,har zuciyarta takejin kaunar riyyah da yadda aranta yanzu danta zaiyi Aure dan gaske.
"Walimar ta kayatar sosai saidai san barka,,ta Ummu data Mami babu wanda batai kyau ba da kuma.ma'ana,,Ummu Malamai ta dakko suka yiwa amare wa'azi akan zaman takewar Aure,,da yadda zasu yiwa mijin su biyayya,iya girki,iya tafiya,iya magana,tsafta,yi nayi bari na bari,in sukai haka sun kame mazajan su tsaf a hannun su babu boka ba Malam.Gaba dayan su Laffaya suka saka,,daga Amaran har 'yan gayya.Iyami tana daki tana kuka ganin ko waje takasa fita,,tana fita take ganin irin kallon tsanar da mutanan gidan ke aiko mata,,gata kamar mayya taki tafiya wai zaman 'yayanta take,,mijinta ada ya tabbatar mata Aure zaiyi kuma ya zama dole ta fitar masa daga gida,,sosai sukai rigima da Iyami cewarta zama daram,,dakyar 'yan uwansa suka shawo kansa ya bata daki falle daya daga can hanyar harabar gidan,,nan dimma taso tace bata yadda ba,,ya tabbatar mata matukar bazata zauna anan ba saidai ta bar masa gidan sa,,babu yadda zatai haka ta hakura ta koma tana Kuka tana komai,,tsanar Ummu ajininta take,,sauran 'ya'yan ta shiga sukai akai warkajami dasu,, shama'u dai ta kasa sakin jikina sai rabe rabe take,,to duk sa'annin nata sun zama iyaye harda 'yammata gare su,,sai cikin yaran mata tashiga jefi jefi take dan saka baki a hirar da suke yi.
"Ranar Asabar Shine ranar Dinner,,kayataccen event,,tun safe ake kara tsama su da kayan gyara iri iri,,Angwaye kansu ya dauki charge sai zirga zirga suke tare da abokan su,, Yayanmu ma babu zama damma su Kamal sun tsaya akan wasu al'amura,,tunda Sadik shima ta hidimar Auransa yake dashi zai tsaya akan bikin Yayanmu.Karfe biyar na yamma aka fara tsantsara musu kwalliya,,Saboda makeup akwai cin lokaci,,kwararriya aka dakko har gida tazo ta tsara musu kwalliya tagani ta fada.Material suka saka iri daya,, purple and white ba karamin kyau sukai yiba,,head aka daura musu sai net da aka makale ajikin head din,,sai kyalkyali suke suna bada wata kala ta daban.Amota daya aka sanya Amaran haka Angwayan a mota daya suka zauna,,wannan tsarin Umami ne ta lura da yadda suke ta rawar kai akan matan nasu,,shiyasa ta shirya musu wanann tsiyar,,aiko ba karamin haushi abunya basu ba musamman Yayammu,,kayansu iri daya suma,,kalar kayan Amaran su kalar nasu.
Gidan Ummu yayi tsit yara da manya babu wanda be tafi ba,,haka gidan su Major hatta Mami ba'abarta abaya ba,,su Innayi kuwa ai sune agaba,,in bataje ba wazaije.Abbu dai da Abee cewa sukai babu Inda zasu je sun barmusu,,In kaga yadda Antymmu ta cakare zaka dauka itace amaryar sosai ta dauki wanka.Yaran Abokan zaman ta babu wanda be hallara ba."Sanda Motocin su suka tsaya a event din su Yayanmu ne suka fara futowa fuska aturbune sukaja suka tsaya,,dan ganin yadda zaai yanzu badai an hana su ganin matan su ba,,zasuga yadda za'ai yanzu.
Murmushi Umami ta saki ganin yadda suke ta kumbura musamman Yayanmu,,Lokacin da aka fito dasu riyyah kallon su suke,dan kowa ya tantance tasa,,kallo daya Yayanmu yayi wa riyyah ya gano itace,,duk da kansu asunkuye yake ba karamin kyau ya hango ta kara ba,, lumshe idanun sa yayi yanayiwa Allah godiya daya mallaka masa riyyah a matsayin mata."Ummi ce ta kama hannayan su kowacce takaita kusa da Mijinta,,gaba su Umami sukai suka barsu atsaye,,ana satar kallon juna,,kallon kasan idanu Yayanmu ke aikawa riyyah,,gaba daya jinta take a takure kamar ta zura da gudu,,mazewa tai tana wasa da yatsun hannun ta,, hannun ba karamun daukar Hankalin sa yayi ba,,yasha jan lalle yayi maroon yafito radau.
"Kaga Malam kallon ya isa haka,,kataho mutafi ko mubarka Anan,,sai Lokacin ya farga ashefa basu kadai bane,,shafa kansa yayi yana sakin Murmushi,,tare suka jera kawayan amare da abokan angwaye sun sasu a tsakiya.Suna shiga aka saki wakar tarar amarya da Ango,, event din acike yake sai kawunan bil'adama kake hange yana tashi,,mikewa sukai dan giramamwa ga Amare da angwayan su.
Wasu yara aka jera maza da mata reras sunaki su 20 kaskon turaran wuta ne a hannayen su"kamshi nan fa ya fara tashi,,sune agaba ba karamar bada kala yaran sukai ba.Tunda suka shigo aka fara manna musu kudade kamar ba nemansu akai ba,hakosu akai akasa,sam Mami bata kalli Humaida ba su Yayanmu ta dinga zazzagawa rafas din 'yan dubu dubu,,yakan ba karamun faranta ran 'yan wajan yayi ba,ganin lokaci daya Mami ta canza kamar ba ita ba,,su Umami ne sukewa Humaida da Salma liki,, Mamah Ramlah ma su Yayanmu takewa liki dan tasamu masu yiwa 'yarta kara.Mc yaga ruwan kudi sai kirari yakewa amare da angwaye musamman Yayanmu,,wanda yaga gaba daya rabi da kwatan kudin su aka likawa shida Amaryar sa.
"Biki fa yayi biki dakyar aka barsu suka karasa wajan zaman su,,kowa kaga table da yake zaune zagaye ya ke da kayan Abinci kala kala,,karya kake kace kazo wanann taron bakaci ka koshi har ka barshi ba,,naman Kaza,Naman sa dana rago tsire babu abunda babu awajan."Kara kiran Amare akai nanna sunsha liki,,sai fareti da barrack suka shiryawa Yayanmu ba karamin kayatar dasu yayi ba.Innayi ma ba'abarta abaya ba sosai tayi liki anci ansha saidai ace Alhmdlh.
"Ba'a tashi daga wajan Dinner din ba sai karfe 11 yadda aka kawo mutane haka aka dinga dibar su,,a komawa gida ma Umami tasa keyar Amaren tai suka shiga mota tare,,nan tabar su Yayanmu da cizon yatsa."Sassafe suka wuce Kaduna can dangin Abban ta."Jirgi suka hau ita da Ummi da Abba sune suka farayin gaba,nan makarfi anan dangin Abbanta suke,Sanda suka isa su hajiya Ladidi sun hallara,,Gidan kakanninta nan aka sauke su,sai gidajan sauran dangi duk dai akusan unguwa daya suke,,taga gata haka suka dinga rungumarta,,gidan dankam yake da Jama'a sai shige da fice akeyi.Baturiya kin yadda tayi su hadu da riyyah kunyarta Sosai takeji,,tana tunanin dawani ido zata kalle ta.
"Karfe 11 tawagar Ango ta iso,,tundaga bakin unguwar maroki ke kwaroroton yana zabga kirari,, soldiers ne birjik dagani kasan abun nasu ne,,tsaf unguwar ta dinke da Jama'a,,ba masaka tsinke a masallaci Juma'a aka daura auren,,sadakin riyyah dubu dari biyar tare da key din mota,,ana shafa fatiha yayanmu ya lumshe idanunsa,,jin wani sanyi yana kwarara tundaga kasan zuciyar sa,,sabanin Auransa da Sahar da yaji wani tashin hankali ya rufto masa aka,,tare da wani dunkulalllan bakin ciki,,a yau wannan Abinda ya tsaya masa amakoshi yaji yafada cikin cikin sa.....
Mrs 🌹 Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 87_88
Acikin gida kuwa ana cewa andaura riyyah ta fashe da Kuka,,tare da fadawa jikin Ummi,,jitai kamar andaura mata wani nauyi,,gaba daya jikinta yayi sanyi kalau.'Yan Uwan Abban ta daya bayan daya suke tai mata nasiha."Ango sun shigo tare da zugar Abokansa,wadanda me take masa baya,,tana jinsu takara mannewa ajikin Ummi,,sun girmama danginta kwarai,,Abba Yahaya da Abba Gali sunsha fararan shadda harda babbar riga,,kowa ya hallara abikin,amma banda Anty Zee gaba daya hassada da bakin ciki ta gama cinye zuciyar ta.Karfe 1 sukai shirin tafiya da Amarya,,jirgin kafe 1:30 zasu bi,,mutum goma aka ware wadanda zasu raka amarya,,sosai su Abbah Yahaya sukai mata nasiha irin wadda Uba keyiwa 'yar sa in za'a kaita gidan Mijin ta.
"Kuka sosai riyyah takeyi,,tanaji Inama Abbanta na zaune acikin kannan sa,,ko ba komai taji dadin irin kaunar da suka nuna mata,,haka matan suka taru wajan yi mata nasiha ta zauna lpy da mijin ta,da danginsa,,tare da Haj Ladidi za'a tafi,, baturiya dai catai bazata jeba ita kadai tasan halin da take ciki.Sai tsoaffi guda biyu da kuma yaran mata,hadda Ameer da Ameera za'a tafi kai riyyah,farin ciki kamar ya kashe Ameer ganin yadda rayuwar riyyah tayi gwanin burgewa.Ko acikin jirgi tana kusa da Ummi Yayanmu nadagan can get shida abokansa amma gaba daya hankalinsa yana kan riyyah,,jiyake kamar ya taso ya rarrashe ta,,ganin yadda har lokacin taketa kuka.Sanda jirgi ya sauke su a airport motocine akalla sunkai 20 suka.zo tarar su.Kai tsaye gidan Ummu aka wuce da ita sai yamma za'a zo kai Amare.
"Motar su na tsayawa aka fara sakin guda,,wata zabiyar mekidan kwarya suka dakko tundaga cikin gida har waje anajin yadda take taita wakoki,,da dukan kwarya ita da mukarraban ta,,gidan ba masaka tsinke ana fili ana cashewa,,ana shiga da ita gidan tsakiyar fili aka jata,,liki sosai sukai mata kafin a karasa da ita part din Ummu dan ta huta,,tamatukar gajiya amma haka ake walagigi ita."Ansha biki yadda ya kamata Biki kuma ya kayatar sai san barka.
"Abbu da Abee da kansu suka nufi gidan su Sahar dan jin yadda aka kwana da maganar ta,,sanda suka je Ambassador yana gida,,gaba daya damuwa ta mamaye ransa,,tsawon 3weeks kennan ba sahar ba labarinta,, Mom tayi Kuka kamar ranta zaifita,,gashi basu san inda yatafi ba balle su tafi nemanta,,tun suna daukar Abun wasa ne gashi yana neman zama gaske.Babu wani boye boye ya sanar musu suma neman ta suke ruwa ajallo,,babu Inda be bada cigiyarta ba,gidan 'yan uwa da kawayanta babu Inda beje ba babu ita ba alamar ta.Sun matukar jajanta masa da Addu'a ALLAH ya bayyana ta,,kowannen su da Abunda yake sakawa a zuciyar sa.Mom bakin ciki biyu ya hade mata,,gana batan 'yarta ga na kishiya da za'ai mata,,kuma taci alwashin saita hana wannan Auren((Har yanzu fa Mom batai nadama ba))haka su Abbu suka dawo jiki asanyaye,,dan sun rasa wane kalar tunani zasiyi akan batan Sahar din,,basu sanar da Yayanmu komai ba,,sun bari sai bayan biki komai ya lafa sayi maganar da zasiyi.
"Karfe 6 aka fito da Amarya riyyah an nannadeta a cikin laffaya golden ba karamin Kyau tayi ba,,da kyar tasaki Ummu,,tayi matukar saboda su dan zaman datai a wajan su."Gidan su Major aka fara kaita Innayi sai rangada guda take,,yanzu mukaga Amarya 'yar gaske,, Amarya 'yar dangi,,wajan Mami aka fara kaita farin ciki ya hana ta magana saita fashe da kukan farin ciki,,tana tuna cutarwar da Hadiza da diyarta sukai mata,,ashe zabin Allah shine zabi,,ba zabin da kaiwa san zuciyar ka ba,,Allah ya baku zaman lafiya riyyah,,ina fatan zaki dauke ni tamkar mahaifiyarki,,ni ba surukar ki bace uwa nake agare ki,,Allah ya yi miki Albarka,ya sanya Albarka acikin Auran ku.Ameen suka amsa baki dayan su,,su Ummu sunji dadin yadda Mami ta karbo riyyah da hannu bibbiyu,,tare da Humaida ta hadasu tai musu nasiha kafin amike dasu.
"Part din Umami aka kaisu ita ma dankare yake da 'yan uwanta nasiha tai musu itama,,taso binsu kai Amare amma su Ummi sukace tai zaman sun wakilceta taji da bakin gida,, motoci baka ganin karshan su,,gaba daya layin ciki yayi da Motoci masu kyau da tsada.Humaida aka fara kaiwa Gidan iyayan Sadik ammusu karba ta mutunci hajiyarsa sosai takara yi musu nasiha,,haka Salma ita ma aka mika ta gidan Surukanta,,suma sun karta da mutunci komai sai san barka,,daya ke unguwa daya za'a kaisu sai aka dunguma akai hanyar unguwar su.
"riyyah aka fara kaiwa katafaran gidan ta,,wanda yagaji da haduwa,,kamar ba a nigeria ba in kashigesa,,komai antsara shi,,dagani ba karamar dukiya aka narka agidan ba,,komai na maine parlo bulu ne yayi matukar kyau da tsari,,kafar benan wani style akai mata,,kowa masha Allah yake furtawa ganin yadda gidan yake daukar idanu.Kaya akai mata nagani na fada,,Dangin Abban ta,su Abbah ya haya sun mata kayan daki,,Abbu shima yayi mata yace itama 'yarsa ce,,haka Abba shima yayi mata amatsayin sa na marikinta,,Alhaji Badamasi shima yayi mata kayan daki kowannen su daga kasashan ketare akai order su,,atakaice dai riyyah tatashi da kayan daki set hudu,, riyyah fa tazama 'yar gata gaba da baya,,gidan tashin kamshi yake lungu da sako kamshi yariga ya kama gidan baki daya.
"Kowa santin gidan yake yana yaba irin tsarin da akaiwa gidan,,Inda aka sa kayan su Abba Yahaya nan aka shiga da ita,,komai pink ne adakin,wasu kwayaye ne suke kawowa masu matukar daukar hankali,,kan katafaran bed dinta aka zaunar da ita,,sanda za'a fita dasu Humaida rungume juna sukai suna kukan rabuwa dukkan nanin su,,da kyar aka banbare su daga jikin riyyah aka fita dasu dan kaisu nasu gidajan.Sai bayan sallar isha'i gidan yayi tsit alamar kowa ya tafi,,daga Antymmu sai Zuhura,Anty Fareeha Anty Beenazir su aka bari sàida suka kara gyare mata ko ina,,wanka suka sata tai tas tafito kafin Ummi ta dakko mata sabuwar atamfa dinki ya zauna das ajikin ta,,ba makeup sukai mata ba,,sai turare da suka kara bulbula mata,,mayafi suka dakko suka lulluba mata,,nasiha suka karayi mata sunajin tsayuwar motar Yayanmu suka mike,,rike su tai tana kuka karsu tafi su barta,,da kyar ta sake su suka fice,,ita da Zuhura kuka suke sosai itama Antymmu daurewa takeyi dan Kuka ne yake taho mata.Tayi matukar saboda riyyah dan dai Aure shine cigaban ko wace mace,,da bazata yadda riyyah tayi nesa da ita ba.Shikadai suka gani yasha babbar riga sai Zuba kamshi yake,,fuskarnan asake yau babu turbune fuska.
"Anty Fareeha ce ta rike haba Yayanmu ina abokan naka,,sun tafi gida mana,,ai bekamata kashiga kai kadai ba,,yanzu inna shiga nikadai kizo ki fito dani,,dariya suka.saka ah Yayanmu me yayi zafi,,kudai kuka sani,gwara da Allah yasa kukaiwa karatun ta nutsu Kuka fito,,dama ina shiga zan tarkato ku.kuyi waje,,kingama yimin Amfani,,yanzu fagen nawa ne,,uhm suka ce suka fada mota dan matukar akaja zancan nan su zai bari dajin kunya,,yana tsaye suka fice daga gidan suna daga masa hannu,, murmushi yayi suma ya daga musu hannu.
"Murmushi yake ta saki,,wata iska ce me dadi take shigar sa,, Maine parlo ya shiga da sallama duk da yasan ba kowa,,sanyin AC da kamshi medadi ne ya daki hancin sa,, Lumshe idanun sa yayi masu dauke da gajiya,,wata babbar leda ce ruke a hannun sa,, taking steps ya fara kafin ya karasa part din dayake tunanin nan aka ajiye masa Amaryar sa.Tsarin yadda suka ajiye mata kayan yayi,,set biyu asama,,set biyu aka sa,,duka Inda suka ga dama zasuje su iya kwana basu da matsala da wani."Jin motsin za'a shigo yasa ta kara komawa can kuryar gado,,sake lullube kanta tayi acikin mayafin ta,,ajiyar Zuciya ya sauke hango ta da yayi sai kara mannewa take da jikin bed,,dariya tabashi kamar wadda aka zo kamawa har Lokacin kuma kuka takeyi.
"Lumshe idanun sa yayi tuno auransa na baya,,yana shigowa yayi arba da Sahar taci kayan bacci na futsara,,tundaga ranar ya kara tabbatar wa kansa tantiriya aka aura masa,,an lullubewa Mami kura ne da fatar Akuya."Ahankali ya karasa bakin bed din yana sakin ajiyar zuciya,,babbar rigarsa data dameshi ya cire ya ajiyeta a gefe,,Numfashi ya kara fesarwa kafin ya mika dogayan hannunsa masu cike da gargasa,,jawota yayi batare datasan lokacin daya miko hannun nasa ba,,zabura tai da nufin zillewa amma yayi mata rukon tsauri bazata iya kwacewa ba,,agefansa ya ajiyeta yana jin yadda takejan ajiyar zuciya.Murmushi ya saki kafin ya dauke mayafin datake ta kudundunewa ajikinsa,,runtse idanun ta tayi da sauri,jin wata kunyarsa na mamaye ta,,dago fuskarta yayi,,zara zaran eye lashes dinta ya jike da hawaye,,ba karamin kyau takarayi ba,,yarintar ta saita kara futowa,,dan bakin nan acone dan mitsil dashi,,share mata hawayan face dinta yayi.
"Zaunar da ita yayi kafin ya sakko ya duka agaban ta,,gaba daya hannayanta ya kamo yana yana kallon kyakykyawar fuskarta,, ahankali tadan bude idanun ta caraf suka fada cikin na Yayanmu,,saurin rufewa tai tana kokarin boye fuskarta,,um um Amarya tasha kamshi,,yanzu bazaki bude idanu ki kalli Angon naki ba,,kinfada haryanzu dama bangama warkewa ba,,maganin da yakamata ace andade da bani gashi ban samu ba,,ina fatan zan samu daga gare ki,,gyada kai tayi alamar eh,,duk da bata gane abunda yake nufi ba.'Yar dariya ya saki good jarumar matata,,gaskiya da alama ashirye kike tsaf da tarbar angonki,,kallonsa ta danyi ya dage mata gira tare da kashe mata idanu,, zumburo baki tai tana hura hanci abun ba karamar Dariya ya bashi ba.
"Lakuce mata hanci yayi kafin ya ja hannun ta,,mikewa tai yajata suka fice daga room din baki daya,,muje muzabi daki na musamman,,sai wanda yafi kyau da tsari anan zamu ci amarcimmu,,saurin daukar daki tayi tana rintse idanu kai Yayanmu bashi da kunya,,daga kafadar sa yayi,,kinmanta abunda nagaya miki kenan,,nifa banason wanann kunyar dan zata hanani baje koli na ne,,batace mai komai ba suka ci gaba da zagaye gidan,,bakaramin kyawu yayi mata ba,sai sakin Murmushi take batare data sani ba wai wanann duka gidan tane,,Alasa kar Matar sa ta dawo,,batasan afili ta furta hakan ba,,daga zuwa sai kwacan Miji,,saurin dafe bakinta tayi tana zaro ido ashe yajita,,dariya ya saki,,aikin shine zai bada tabbacin yiwuwar da wowarta da rashin dawowarta,,saiki dage ki zage damtse,,dan Mijinki ba ragon Namiji bane,,ganin bama fahimtar zan cansa take ba yayi shiru da bakin sa.
Sàida suka zagaye gidan saidaya tabbatar ta warware sai janta da wasa yake yi,,dama danta sake dashi tadaina jin tsoron sa yace tazo su zagaye gidan su,,sàida suka gama zagaye suka koma sama,, wani part daban ya jata,,komai na part din black and ash bakaramin kyau yayi ba,,akan sofa ta zube tana maida numfashi alamar tagaji,,kallonta yayi lallaima yarinyar na ke raguwa ce harkin gaji,,to bari nai miki tausa,, zumbur ta mike,,aah Yayanmu na daina jin gajiyar,,dariya ya saki shikenan kinwa kanki,,sunkuyar da kanta tai tana wasa da yatsun hannun ta........
Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
🌹🌹FATA NA 🌹🌹
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 89_90
Last page 💃💃💃💃
"Yayanmu bacci nake ji,,yayan su dai,,kallon sa tayi nikuma,,mijin ki ne ni ba yayanki ba,,kodan har Yanzu ba tabbatar miki da matsayina ba? Batace komai ba,,zan tafi dakina,, murmushi ya saki aibaki da daki wanda ya wuce wannan anan zamu kwana,,rau rau tai da idanu,,kaifa Namiji ne gaskiya dakina zan tafi tafada Kamar zata rushe da Kuka,,to da a mata maza kike son kiganni bari na tube kisan ni cikakken Namiji ne,,kokarin kwance tsazuge yake ta ruga da gudu ta kankame shi,,dan Allah kayi hakuri karka cire tsoro nake ji kabari please."Ai bemasan me take fada ba tundata rungume shi yaji wani irin shork kara kankame ta yake yana fitar da zazzafan huci,,da kyar yayi control din kansa,,ok sakeni da sauri ta sake shi kunya na kamata ashe wai kankame shi batare data sani ba,,lakace mata hanci yayi daga baya kenan.
"Kan sofa ya jata ta zauna kafin ya fice daga room din baki daya,,ajiyar zuciya ta sauke tana shinshina jikinta,gaba daya kamshin turaran ta ya hade da nasa saiya bada wani kamshi na musamman."Dawowa yayi hannun sa dauke da leda,sai plate guda dire wa yayi kafin ya zauna shima,sakko watai ta jawo Ledar gaban sa,,dan anasihar da akai mata harda basai ya furta tayi masa wani abuba ko yaushe ta kasance ankare da abinda yake bukata.Murmushi ya saki yana sakar mata budewa tai wasu manyan kaji ne sai kamshi sukeyi me matukar dadin guda daya ta dauka ta dora akan plate,,wani plate din ta mike dan dakkowa yabita da kallo,,bata jima ba ta dawo tare da knife a hannun ta."Dai dai wadda zasu ci ta yanka tabar sauran agefe gabansa takai plate din ta zauna tana wasa da yatsun ta,,dakko wata tsoka yayi ya nufi bakin ta,,taso tai gaddama amma yadda ta kalli fuskarsa ahade yasa tai saurin bude bakinta ta karba,,haka yadinga ci yana bata saidaya tabbatar ta koshe sanann ya kyaleta.
Oya jekiyi wanka ki brush,,in kuma nai miki to,,saurin mikewa tai ta fada bedroom din tana rufe fuska,,dariya yadan saki yana shafa kansa."Tana shiga toilet ta fada ta jima aciki kafin ta fito daure da Babban towel,,kaya ta hango akan bed din fararen sleeping dress ne masu Matukar Kyau,,ajiyar zuciya ta sauke ganin yadda suke da dan kauri da sauri ta saka dankar ya dawo ya kara samun ta,,turarurrukan da Ummi ta bata ta dakko ta shafa kowanne,,kamshi medadin gaskene yadinga tashi daga jikin ta,,kan bed ta haye blanket ta janyo ta shige ciki,,can karshan bed din ta matsa,,jera floor tai a tsakanin su,,dan tana da tabbacin sai ya dawo,,ko mintuna 2 bataiba taji shigowar sa,,ido daya tadan bude tana kallon sa,,duk abinda takeyi yana kallon ta,, murmushi kawaii ya saki,,in zaki kalli mijin ki sosai ki kalla,,saurin rufe idanun tai kunya ta dabaibaye ta,,fararan kaya ne ajikin sa shima kala daya da nata,,ban ban cin ita na matane shi kuma nasa na maza.
Saidaya gama shafe shafen sa yahau kan bed din,,watsar da floor din yayi akasa kafin ya mika hannun sa ya jawo ta,,sake narkewa tai kamar tana bacci,,cakulkuli ya fara yimata,,dan dole ta fara dariya,, murmushi ya saki dama dariyar tata yake so,,shiru yayi yana shinshina kanta dayake fitar da sansanyan kamshi,,shiru tai jin yadda yake busa mata Numfashin sa me matukar dumi tsigar jikinta har tashi take,,hannunsa ya fara yawo Dashi asassan jikinta,,da sauri ta rike hannun sa tana sakin kuka,ni bacci nake ji,,yana jinta yayi mata shiru,,sàida yagama jagwalgwala ta tukunna ya kyaleta,,ko kimin shiru ko nayi abunda kike tsoron awuce wajan,,tsit tai tana sauke numfashi,, Numfashi yake saukewa cikin wahala,,gaba daya ya kunnowa kansa wuta amma haka zai daure zai barta tadan huta."Ahaka bacci ya sauke riyyah shidai sam kasa bacci yayi saida kyar bacci barawo ya sauke shi tana kwance ajikin sa.
"Shiya fara farkawa wajan karfe 4 mararsa tai azabar daurewa,,jikinsa yayi zafi sosai da kyar ya yunkura ya sauketa daga jikinsa,,da yake bata da nauyin bacci dan danan ta farka,,ganin ta farka ya tayar da ita zaune,,da kyar yake magana shikadai yasan hakin da yake ciki,,Zuba mara idanu yayi tausayinta na kamashi,ganin ta wata 'yar tsugul agabansa,, Numfashi ya sauke amma in yabarta hakan na nufin zai jawowa kansa matsala babba,,hannun ta yaja ya mikar da ita,,muje mu dauro Alwala,,bata kawo komai aranta ba ta.mike tunanin ta kiyamul laili zasu yi,,tare suka shiga suka dauro Alwala,,hijab ya bude wardrobe ya dakko mara har kasa,,jan su sallah yayi raka'a biyu,,dafa kanta yayi ya dinga kwararo Addu'a,,tayi Mamakin yadda taji yana karanto Addu'a ashe yana da ilimin addini haka."Tare suka shafa,mikewa yayi ya dakko mata fresh milk mara sanyi mika mata yayi ta Girgiza kai alamar bata sha,,kisha kawaii karna dura miki babu yadda zatai haka ta karba ta kafa kai ta sha da yawa,,mikamai tai alamar ta isheta beja da yawa ba ya karba ya mayar Inda ya dakko ta.
"Dawowa yayi taga tana kokarin fire riga da sauri ta sunkuyar da kanta,,sam batasan yazo kusa da ita ba,,jitai cak ya daga ta,,bedire ta ko ina ba sai kan bed din,,sakar masa nauyin sa yayi,, Yayanmu zaka karya ni,, murmushi yadan saki kafin ya rage nauyin daya aza mata,,hannunsa ya fara yawo dashi asassan jikinta,,tun tana kaucewa sàida yakashe mata jiki gaba daya ta kasa hanashi abun da yakeyi din,,sosai ya birkice ganin jikinta me Matukar daukar hankali,,jiyake kansa har hayaki yake tsabar irin dadin dayake ziyartar sa,, riyyah jin abun bana wasa bane ta fashe da kuka bema san tana yiba saidaya tabbatar yamaida ita cikakkiyar mace,,tasha kuka kamar ranta zai fita,, Yayanmu sai Albarka yake saka mata,idanun sa kwance da hawayan Farin ciki,,dai yanzu yake yiwa Allah godiya daya tsare shi dayin rayuwar Aure tare da Sahar.Allah shikadai yasan abunda ya boye.
"Karfe 9am nakara yiwa gidan dirar mikiya,,suna zaune a parlo gaba daya tana narke ajikinsa sai Aikin lallashi yake tana kara tabarewa,,tasha wankan less me Matukar Kyau da tsada,,ya kara haskaka fatar ta,, breakfast yake ta lallabata akan taci amma fur taki ci sai koke koke da takeyi,,duk yadda yake lallashin ta taki amsa,,dakewa yayi ya turbune fuska ganin babu alamun wasa yasa ta karba ta fara ci,,saidaya tabbatar ta koshi kafin ya kyale ta.
"Ajikin sa bacci ya dauke ta,,kurawa kyakykyawar fuskarta idanu yayi,,santa da kaunar ta na kara huda zuciyar sa,,yana Matukar san riyyah akallon farko yaji ya kamu da santa,sai gashi Allah ya mallaka masa ita,,tana jikinsa baya son yayi wani motsi ta farka,,shima ahaka bacci ya kwashe shi,,sai kusan 11 ta fara bude idanunta ahankali ta zube su akan Fuskar sa ma'abociyar kwarjini da haiba,,tadade tana kallon sa kafin ta motsa ahankali jin motsinta yasa shi farkawa,,zube idanunsa yayi akan ta,,saurin rufe idanun ta tayi saboda wata kunyarsa ke kamata,,murmushin gefen baki ya saki."Mikewa yayi da ita ajikin sa wanka ya kara yimata tare da kara gasata dakyar ta tsaya,,nadota yayi kamar baby tana lafe ajikin sa.
"Tsaf ya gama shiryata,, yanayin tasowar da yayi acikin mata yasa ya iya harkar mata sosai,,atamfa ya dakko ya saka mata,,doguwar riga ce wadda taji tsadaddan dinki,,zaunar da ita yayi ya gara tsantsara mata dauri,,kallon kanta tayi a mirror bayan ya gama,,ba karamin kyau daurin yayi mata ba,, murmushi ta saki,, Yayanmu a ina ka iya dauri,,lakuce mata hanci yayi Ummin kima ninake mata dauri awajan ta na koya,, murmushi ta saki kai amma yayi.kyau sosai,,wayarsa ya ciro to bari miyi selfie, pick suka fara kala kala,,sai gashi riyyah ta ware kamar ba ita ba tana ta sakin dariya,,pics din sosai sukai kyau da tsari."Nan suka shashance wajan yin selfie sai ji sukai ana norking,,kallon juna sukai which din hannunsa ya kalla sai Lokacin yaga ashe sun shafe lokaci me tsayi suna tabara batare daya sani ba,karfe 1:20 dan shafa kansas yayi yana tuanin yadda Yarinya karama ta susu tashi haka.
Sakinta yayi yaja hannun ta,,daukowa sukai Ganin yadda take tafiya ya dauki kayar sa,,kan sofa ya dire ta kafin ya karasa bakin door din ya bude,,araba yayi dasu Ummi su kusan goma sai faman rarraba idanu yake,,gimtse face yayi mene na zuwa gidan Amare da sassafe haka,,Ummi ce ta harare shi,,ni yanzu matsayin surukarka nake dole ne kadinga girmamani,,dariya dan saki bece komai ba,,to Mama Batool shigo daga ciki,,dariya suka saka yadda yayi Maganar ya basu dariya,,ganin harda Ummi yasa riyyah saurin buya aka bayan sofa Sosai takejin kunyar su a yanzu,,kaji wata sabuwar gulma,,kinga fito ni Uwar zamani ce,,in be gasa ki yadda ya kamata bama yanzu zan cire mayafina na gasheki,,dariya suka saka,,harara ya watsa mata ki kuma iya bakin ki,, Yayanmu yanzu fa na kora ma jawabinnan bazai yiwu na baka Yarinya ta sukutum da guda ba,,ajiya Allah kadai yasan garar daka kwasa kuma daga bisani kafito kana daurin min fuska a matsayin kaine babba bazata yiwu ba na kwace wannan girman,,ganin zasu tubura shi yasa yabar gidan babu shiri,,hadda su Hajiya Ladidi suna ta santin gidan,, riyyah tasha tsokana wajan Zuhura,,saidata ga zatai kuka ta rabu da ita.
"Kafin su tafi shawarwari suka kara bata Sosai yadda zata kara kame zuciyar Yayammu,,aiko komai ta nadeshi akanta,,wasu fitinannun kaya Ummi ta siyo mata masu azabar kyau,,wanann kayan sunan su gigita megida."Sai yamma suka tafi bayan sun kara gyare mata ko ina,,har kuka tai sanda suka tafi suka barta,,daganan gidan Salma da Humaida suka je,,suma sun kara basu shawarwari yadda zasu zauna da mazajan su lafiya.
"Soyayya ake ci kamar ba gobe,,dan danan Yayanmu ya gama fitsarar da riyyah,salo salo na nunawa megida saidaya koyar da ita,,tuni ta debe karatunsa akanta,,koyaushe tana makale ajikinsa Matukar yana gida,,yanemi transfer an kara Dawowa dashi barrack din Maiduguri Sosai wannan abu yayiwa riyyah dadi,,ba tason ya matsa ko nan da can,,dan danan ta kara wani girma da haske fatar ta kamar tarwada haka ta koma."Watan su biyu da Aure Mami tazo taga tarba taban girma ba Irin wadda Sahar tai mata ba,,rasa Inda zata ajiyeta riyyah tai dandanan ta cika gaban ta da kayan tande tande,,da tatashi tafiya shatara ta arziki riyyah ta hada mata har parking lot ta rakata tana daga mata hannu,,zuciyar Mami fes ta koma gida,,hatta mutanan gidan sun san yau Mami tana cikin Matukar Farin ciki.
"Mom fa duk da haka bata daddara ba,,anyo mata tsaleliyar amarya bazawara ce Yarinyar ta daya,, Ambassador tuni ya tattare ya koma wajan ta ya samu inda za'a kula dashi yadda ya kamata,,hakan ya kara fusata zuciyar Mom da Sahar da take ta bulayin nema,, Ambassador tuni ya samu Labarin mutuwar ta,,yayi kukansa shikadai dan wannan abun ala wadaraine ace 'yar tatafi karuwanci da Auranta can wata kasa,,ko Mom be fadawa ba yasan koma me Sahar ta aikata ita ce ta daura ta akan hanya,,daga Hajiyar sa sai Yan Uwansa na kusa suka san abunda ya faru,,sun girgiza matuka tare da ala wadarai da Auran mace Irin Mom."Yau can wani jeji ta nufa inda wata kawar ta kwatanta mata anan wani hatsabibin boka yake,,ba bata lokaci Mom ta fantsama tatafi,,aiko a hanyar da wowa wata tirela tai gaba da motar,,wani rami ta fada,,dakyar mutane suka taru suka ciro motar,,saidai ina Mom tayi rugu rugu acikin motar,,sanda labari ya iske Ambassador hankali tashe yazo Inda abun ya faru,,babu damar ai mata wanka,,sai yayyafa mata ruwa akai akai mata sallah da 'yan tsurarun mutane aka kaita makwancinta na gaskiya.((Shiyasa ake so mutum ya kasan ce yana aikata Alkhairi,besan sanda mutuwa zata riske shi,gadai yadda karshan Mom ya kare)).Allah yasa mudace.
"Bangaran Anty Zee dai cuta sai gaba takeyi,,babu kudin da za'ai mata aiki,,likitoci sun tabbatar mahaifarta ta gama lalacewa sai an cire,ga brest cancer data kamu da ita dik asanadin alurar bleach,,Abba Gali bashi da wannan kudin da za'ai mata aikin shiyasa ya zuba mata idanu,,iyayanta ne keta dawainiya da ita,,kullum taita ihu tana kuka saboda tsabar Azabar da takeji a dukkan sassan jikinta,,duk wanda ya ganta saiya tauyamata ta dawo kamar aljana."Mama Sauda ta dawo bayan Abba Yahaya yaje biko can gidan su,,da kyar ta yadda zata dawo amma da sharadin ya tattara dukiyar riyyah ya bata abarta,,ya yadda da Abunda ta fada din.
"Watan riyyah Biyar da Aure ta duro Kd dan ganin dangin Abbanta,,gidan Abba Yahaya ta sauka,,gidan dai har yanzu sai ahankali yana dan juya Iya dukiyar sa,,dukiyar riyyah wasu daban ya dora akai,,sunyi farin cikin ganin ta,,Itama haka tai farin ciki da ganin su kamar zasu goyata,,anan ta samu labarin rashin lafiyar Anty Zee,,babu wata damuwa ta dauki nauyin aikin da za'a yi mata,,yan uwan ta haka suka dinga yiwa riyyah Addu'a."Baturiya ma babban asibiti tasa aka kaita dan abun kara gaba yake manyan kudade ta fitar aka dinga lura da Baturiya saiga sauki yana samuwa,,sanda Abba Yahaya ya bata takaddun kadarorinta sam kin amsa tai tace ta bar musu su raba shida Abba Gali,,sun sha mamaki ganin yadda duk wanann uwar dukiyar tace ta bar musu,,tabbas tana da kyakykyawar Zuciya irinta iyayanta.
"Ko kadan kudin be burgeta ba,,babu abunda bata samu daga wajan mijin ta,,yanzu ita kanta batasan abunda ta samu dashi ba,,saidai Alhmdlh."Bayan ta dawo ta fara Zazzabi da ciwon kai,, hospital Yayanmu ya dauketa ya kaita gwajin farko doctor ya tabbatar musu tana da ciki wata Biyu,,farin cikin da yayanmu ya nuna ba'a magana,,haka su Mami gaba daya sukadau san duniya suka dorawa cikin,,watan haihuwarta na kamawa ta santalo tsaleliyar 'yarta mace me kama da babanta sak,,kamar an tsaga kara,,washegarin data haihu Salma ita ma ta haifo mace,,kwanan su Uku da Haihuwa Humaida ta haifi mace gaba daya wanann family sun cika da murna da farin ciki."Ummu ce tatafi da riyyah badan Yayanmu yaso ba,,tare aka hada akasha suna.'Yar riyyah aka samata suna Khadija sunan Umminta kenan suna kiranta Amna,yar Salma Aisha,,'yar Humaida safiyya.
"Suna yin arba'in aka tarka to ta aka dawo da ita bayan tasha gyara kamar bata haihu ba haka ta koma.Cigaba sukai da rainon Amna tana matukar samun kulawa tawane bangare.A yanzu riyyah bata da wata damuwa kullum kara ganin cigaba takeyi,,ahalin yanzu Yayanmu ya mayar da ita Makaranta,,ta zama babbar mace me takama da juyi agidan Mijin ta."Saidaga baya suka samu labarin mutuwar Sahar ko ajikin su babu wanda ya damu.Innayi tana nan daram da bakin surutun ta,,shekarunta sun kara ja sai rikicin tsufa take musu.Anyi bikin Zuhura anan maiduguri ita ma aka dire ta.Zumuncin Yayanmu da Sadik sai abunda yayi gaba.
Wannan Family na dan Barno babu abunda zasu ce saidai Alhmdlh.
Nima anan nace ALHMDLH.
Anan na kawo karshan Littafin FATA NA ina fatan sakon da nake so na isar ya isa zuwa gare ku.
Yabo da dukkan Godiya su tabbata ga Ubangijin talikai.Ina yiwa Allah Godiya daya aramun rayuwa har na kawo wannan lokaci,na kammala wanann littafi Lafiya.Dukkan kukuran dake ciki Allah ya yafe mini.
Ina mika jinjinar bangirma ga masoyana masu bin rubuta na akowane lokaci Allah yabar zumunci.
Sai mun sake haduwa a sabon Norvel dina na gaba.....
ALHMDLH ALA KULLI HALIN
TAMMAT BI HAMDULILLAH
0 Comments