QUNCI NA😭😭
PAID BOOK
STORY & WRITTEN BY SAADATU IBRAHIM BABALE
~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINQAI~
~INA ROQON ALLAH YA BANI IKON FARA WANNAN BOOK DIN LAFIYA KUMA IN GAMA LAFIYA AMIN YA ALLAH 🙏~
GODIYA!! ina godiya ga Allah subhanahu wata'ala
SAK'ON GAISUWA AGAREKU QAWAYENA DA 'YAN UWANA
ZAINAB ALIYU MAMMAN
ZAINAB JUNAID YARO
AYSHA ABDULLAH GHANA
AYSHA GARBA DDM
SADAUKARWA!! Na sadaukar da wannan littafin ga Ahalina guda biyu da nake Alfahrin fitowa daga dukka tsatson LATE ALH BABALE KANKI FAMILY da kuma SABON GARI FAMILY BAKORI ina fatan Allah ya k'ara hade kanmu gaba daya Amin ya Allah 🙏
jINJINA AGAREKI MAHAIFIYATA Allah ya qara maki lafiya da nisan kwana Amin 🙏
*FREE PAGE*
PAGE0⃣1⃣
Ciki da sanyin jikina kamar ko yaushe nake bude idanuna dake cike da bacci da kuma gajiya da sauri na kara bud'e idanun nawa ganin yadda hasken rana ya keto ta tagar dan qaramin dakin nawa cikin sauri na tashi daga kan 'yar yabudaddar katifar tawa da ko arziqin zanin gado babu ballantana rigar katifa, kaina na dafe dake tsananin sara min wanda nasan yanada Alaqa da gajiya da kuma rashin bacci wanda duk a cikin satinnan bansa mu nayi ba, take idanuwa na suka cika da hawaye tunowa danai yau na makara a aikin nawa a hankali cike da sanyin jikin da Allah ya min nake takawa har na qarasa bakin qofar dan matsatstsen toilet din dake cikin dakina na kama hannun qofar toilet din kafin na tura na shiga naji anbuga qofar dakina da mugun qarfi tsaye nayi kamar statue kafin naji can an qara bugawa kuma cike da bala'i muryar Aunty hamida naji tana cewa "ke AMAARA !bakijin ana nocking bazaki bude ba to wallahi mama tace tabaki minti biyu kizo idan kuma bakizo ba to abinda zata miki kin sani basai na fada ba"take hawayen danake ta riqewa suka silalomin bisa fuskata da sauri na sa hannu na share banshiga bandakin ba na qara sa bakin qofar dakin nawa na bude ko gama bude kofar banyiba naji an finciko ni da qarfi ta jawoni waje tareda yimin wani ranqwashi a kai mai zafin bala'i da sauri na dafe imda ta ranqwashe nin "au da kinaji iskanci ne yahanaki budewa ko mi? Kiyi haquri Aunty wlh yanzu na tashi makara nayi ko sallah ma b..... Ban qarasaba ta qara kaimin wani ranqwashin tareda cewa lallai ma yarinya kinsamu wuri har bacci ma kike da damaryi Alhalin baki fito kinyi Aikin dake gabanki ba ko? Toh muje wurin maman zaki sani" nidai shiru nayi tana jana kamar wata baiwa har muka fito daga lungun da dakina yake muka biyo ta madai daiciyar farfajiyar gidan, bayan mun qarasa falon gidan inda mutanen gidan suke Aunty hamida ta tunkudani na fadi a gaban mama dake zaune kan kujera tana karkada qafafuwan ta wanda Alamu suka nuna cikin fushi take" ina bude baki zanyi magana ta buge bakin tana cewa ke Yanzu kin girma ko wato kina ganin har 7 ta kusa amma baki tashiba kina can kina bacci saboda kin samu guri ko? Kwana biyu ban dukanki shiyasa kike nema ki fi qarfina to mu zuba ni da ke tashi ki bace min da gani munafuka!Har na tashi na nufi hanyar kitchen sai kuma na juyo nace dan Allah mama kiyi haquri inyi sallah "bazaki wuce kije kimana Abinda zamuyi breakfast ba ni na hanaki tashi da wuri kiyi sallar?
Cike da tsoron ta da nakeji na qarasa kitchen din ina goge hawayen da suka zubomin domin hanani sallar da tayi ba qaramin batamin rai yayi ba, tunowar da nayi yau monday yasa naji hankali na ta kwanta tunda ba wani breakfast mai wahala zanyi ba tea ne soyayyar doya sai toasted bread with egg
Ina cikin fere doyan naji motsi cikin kitchen din ko ban juyo ba nasan kowacece saboda ita kadaice ta damu da lamarina duk gidan qarasowa kusa dani tayi tana min murmushi sai nace mata Zarah ya akayi? Ba komi yah Amaara kinyi sallar ko in dauko maki hijab da carpet a daki sai ki koma can gefe kiyi ko? Wani dadi naji ya rufeni nace mata da sauri yauwa qanwata yi sauri ki kawomin da sauri ta juya, Aikina na cigaba dayi ba'a dade ba sai gata ta dawo da sauri na fita ta qofar baya dake cikin kitchen din Akwai toilet a bayan can naje nayi tsarki da Alwala ina zuwa nasamu daga gefen kitchen din nayi sallata bayan na gama sallar a gurguje na kammala hada masu breakfast din na jera masu a dining table din dake palourn sannan na tafi dakina da sauri nashige bathroom don yin wanka,
Bayan na fito daga wanka katifa ta na daga na dauko uniform dina dake a linke waini ina son suyi karin guga dukda uniform din nawa sun tsufa sosai amma a wanke suke, sai da nagama shirin tafiya school dina tsaf sannan na dauki dan turarena da zarah ta bani tsarabarta data dawo daga hutu gidan wan babanta,
A hankali nake takawa har na shiga palour inda na iskesu suna cin abinci ni sai lokacin ma naji cikina yana kukan yunwa qarasa wa nayi gaban mama nace "mama nagama zan tafi school" school kuma lallai ai yau babuke babu zuwa school saboda gobe RADIYA zata dawo daga London dan haka shirye shiryen Abinda za'a tarbeta gobe zaki fara babu inda zaki school din takuma da ba'a komai ko kina ganewa? Ta tambayeni cike da izgili" mama dan Allah kibar ni inje wlh Qualifying examination zamu fara kuma idan banci ba bazan yi WEAC da NECO ba dan Allah kib... Kafin na qarasa ta yunquro kamar zata dakeni da sauri na matsa baya qwafa tayi tareda cewa ai da kintsaya ni kin raina ni ko har ina magana kina bani amsa toh babu inda zaki tashi ki wuce kitchen ki duba duk abinda babu kiyimin list dinshi in bada asiyo,
Haka na ina ji ina gani banje makaranta ba duk da ba wannan ne karo na farko ba da aka hanani zuwa ba amma wannan sai na samu kaina da rashin jin dadi sosai haka ina aiki ina kuka
Sai bayan magariba sannan nasamu damar dawowa dakina cike da gajiya dan kuwa na aikatu yau gyaran dakin Aunty RADIYA duk shi ya idasa gajiyar dani don kuwa ta dade bata nan, koda na shiga dakin ban zauna ba bathroom kawai na shige dan yin wanka, da Alwala dan ma Allan ya taimakeni ba'a bina bashin sallah ko daya
Sai da nayi har sallar isha'i sannan na dauko wata roba ta takeaway dana zubo Abinci wanda babu wanda yasan na dibo dan da mama ko aunty hamida sun sani sai sun dakeni bayan nagama cin abincin
books dina na dauko munkusa fara exams inyi karatu..
*Washe gari*
Tunda na tashi da asuba bayan nayi sallah na tafi cikin gida na fara 'yan Aikace aikacen da zanyi ance karfe goma na safe flight dinsu zai sauka dan haka nake son kafin lokacin nagama,
Aikuwa tara saura minti 5 nagama komai na Abinci da abinsha dan kuwa abinci kala biyar nayi ina ta mamakin yawan Abincin dukda yin abinci kala biyar ba sabon abu bane a wurina dan idan Daddy (babansu Aunty hamida) zai dawo har fiye da biyarma yinake.
Koda mama tazo ta duba taga komi lafiya lau sai tace in wuce in tafi tunda nagama, ina shiga dakina da sauri na janyo wata leda da nake Ajiye kayan abincin danake dan dafawa a kan electric stove dina dake dakin wanda wata sauran spaghetti (taliya) ita na dauko na dafa ina cikin cin abincin ko gamawa banyi ba naji am turo kofar dakina zarah ce ta shigo "yaya AMAARA sannu da aiki kinsha aiki bata tsaya da maganarta ba ta cigaba da cewa wai yaah Amaara miyasa baki dibo abinci a cikin gida sai dai kisaya ki dafa kema fa 'yar gida ce kuma ke kike dafa abincin kullum amma baki diba kuma sai ki zauna a d'aki ke kadai babu kowa" murmushi na mata bance komai ba harta gama surutunta tace min ita ta tafi taje ta shirya don zasuje dakko Aunty RADIYA,
Bayan fitar zarah shiru nayi ina tunanin duniya da abinda ke cikinta da dai naga da sauran lokaci kafin a k'ara kirana a cikin gida sai kawai na kwashi kayana da suke da datti na fito dasu don in wanke saida na ajiye bakin pampon dake kusa da dakina sannan na tuno da banda sabulu dan haka hijab na zura na nufi hanyar gate dan in sayo sabulun a kantin dake bakin layin ina bude k'ofar naji nayi karo da mutum qamshin wani turare naji mai shegen dadi wanda ni nasan duk irin qamshin turaren 'yan gidannan to wannan ya fisu sosai yanayin k'amshim ma ba daya ba subhanallahi naji an fada da wata irin murya wadda tunda nake a gidan bantaba jin mai irinta ba da alama dai baqo mukayi a gidan, baki ganin gabanki ne naji mamallakin muryar ya fada be tsaya ba ya wuce kawai ina juyawa sai naga mutumin ya shige dakin baba maigadi da idanu na bishi ina tambayar kaina shin ko ankawo sabon mai gadine tunda ance baba garba mai gadinmu na da bashi da lafiya fita nayi a gidan dan inyi sauri in siyo sabulun inzo inyi wankina,
Sanda nadawo sai kawai naga wannan bawan Allah'n a zaune inda baba mai gadi yake zama niko da shegen shiga ukku da ban masan ina da shiba kawai na qarasa gaban mutuminnan nace sannu bawan Allah
Dago da kansa yayi ya dubeni,
Tundaga k'asa yake k'are mata kallo dazun ta bige shi amma bai tsaya kallon yarinyar ba sai yanzu shin ko 'yar aikin gidannan ce duba da yanayin suturar dake jikinta ko kadan batayi kama da 'yan gidan ba dukda bawanda yasani a gidan sai hajiyar
A hankali ya bude bakinshi yace "lafiya?
Nikam da nake tsaye mamakin yadda yake qarema kayan jikina kallo nike tunda shima kayan jikin nasa baqaramin jin jiki sukayi ba Amma gwara shi dani tunda nashi a wanke suke kuma ana jin tashin qamshin turaren da sukeyi nikuwa fa kamar wata mabaraciya haka na fito Amma ko kadan banji kunyar kallon kayana dayake ba na amsa shi da cewa " ina baba garba naji ance bashi da lafiya kuma dansa yazo kaine dannasa?
da kamar bazai tanka mata ba sai kuma a d'an shaqe yace da ita" yana gida yana samun sauqi"
Toh dan Allah kace mashi idan kaje AMARA tana gaidashi ni zan shiga gida
AMAARA ya maimaita a cikin ransa sai kuma yace taci sunanta AMAARA yanayin ta daya da sunan,
Harna juya sai kuma na dawo naxe dashi " bansan sunanka ba"
Aransa yace tacika surutu sai kuma yace mata "RIDWAN"
To yaya RIDWAN kaci abinci ko na kawo maka? Girgizamata kanshi yayi kawai beyi magana ba,
Uhhhm kaji zakaci abincin in kawo maka... Kafin yabata amsa sukaji hucin mota a bayansu da sauri ya tashi yaje dan ya bude gate din,
Sauke glass din motar akayi mama ce zaune zaune a gidan baya itada Aunty hamida sai Aunty RADIYA danaga ta zama kamar baturiya itama ta qara kyau abinta zarah kuma na gaba kusa da driver,
K'arasa sawa nayi nace sannunku da zuwa mama Aunty RADIYA sannu da dawowa a dan ya tsine ta dago daga danna wayan data ke ta kalleni sai kuma ta dauke kanta mama kuma tace uban me kike yi a wurin mai gadi wato dan kinga bani nan shine kika fito neman maza ko har wani jijjiga jiki kikeyi kinga namiji a gabanki to mu shiga gidan zaki yimin bayani
Mama na siyo sabulu ne zanyi wanki shine.. Shine ina magana kina bani amsa Amaara bana hanaki ba wlh yau sai na goge rainin daya shiga tsakanina dake, take idanuwana suka cika da hawaye " sada shiga muje"
Sai da na bari suka shige sannan nima na shiga ta qaramar kofar gate din ina ganin sa nayi sauri na share hawayen fuskata sai da nazo zan wuce shi naji yace
" ke me aka miki kike kuka haka?da kamar bazan tsaya ba sai kuma na tsaya nace mashi wai dan na tsaya ina tamabayarka zakaci abinci shine mama tace zata dake ni"
Toh ke waye yace kitsaya tambayata ce miki akayi ina buqatar Abincinki(toh fa 🤔 daga taimako)
Daga can kuwa mama tsayawa tayi tana kallon ikon Allah lallai Aamaara ta gama raina ta Aunty hamida ce tayi qarfin halin qwala mata kira ke!! Amaara bakiji abinda mama tace maki ba!
Da sauri na juya na tafi inda suke 'ya' yan cikina na juyawa.....
comment and share pls.. ✍️✍️

~QUNCI NA 😭
~✨STORY & WRITTEN BY Sa'adatu Ibrahim babale ✨💕
Free page✍️✍️
0⃣2⃣
Ina k'arasawa mama batayi wata wata ba kawai ta janyoni gabanta ta rufe da duka tana fadin "mi na gaya maki dan kin rai na ni shine nayi maki magana ko a jikinki ko har kina qara tsayawa gurin wancan mai kama da Aljanun yarinya dake sai shegen kafiya da baqin halin da kikayi gado gurin uwarki da ubanki,
Idan nace ban daku ba nayi qarya dan kuwa mama qarfinta tasaka kawai tana dukana dukda a gurina ba baqon abu bane amma yau nad'an ji jiki saboda an kwana biyu rabon da ta dakeni
Tunda yaga an fara dukanta ya shige dakinsa daya shiga kuma sai ya kasa zaune yaka tsaye tunda koma minene saboda shi aka daketan amma bazai taba iya zuwa ya karbeta ba haka nan sai ya tsinci kansa da zuwa ya tsaya bakin window'n dakin nashi yana kallo bayan tagama dukanta kuma ta tunkuda ta tafadi k'asa sannan ita kuma maman ta wuce hanyar Apartment dinta
Na dade a wurin ina kuka ba dukan yasani kuka ba dankuwa duka dai ai ba sabon abu bane kawai cewa da tayi wai nayo gadon baqin hali gurin iyayena iyayen da ni ban ma sansu ba ko suna raye ko sun mutu? da sauri wata zuciyar tawa kuma tace to ai da suna raye da bazasu barki a nan ba, wannan tunanin danayi ne yasa naji wasu hawayen sun zubo mani nasan da ace iyayena na da rai ai da bazasu kawoni gidan mama ba sai na samu kaina dayi masu Addu'a ALLAH KA GAFARTA MA IYAYENA, sai da nagama kukana sannan natashi na tafi dakina.
A cikin gida kuwa mama tana shiga ta iske Aunty hamida ce kawai a palour kallonta tayi tareda cewa ina RADIYAn take " tashiga ta watsa ruwa har kin gama dukan kenan ai da baki daketa ba mama kika sani suruki kikayi ta fada hade da yin dariya" hmmm hamida kenan dan tayi saurayi shine har ina mata magana dake ta rainani har qara tsayawa take wurinsa shima ai zan sameshi yaron ni ko yama sunansa"mama kuma baiyi kama da malam garba ba"
Suna nan zaune suna magana jefi jefi har RADIYA ta fito sanye take da wata Armless data kawo mata k'asan gwuiwa babu dan kwali a kanta sai wayarta kirar IPhone13promax sai earpods shima na Apple dake maqale a kunnenta cike da yanga ta iso wurin tana zuwa kawai ta rungume mama tana cewa mamana nayi kewarki sosai mama tayi dariya tareda cewa nima haka babyna ya London an kuma gama school saura aure da sauri ta saketa tana b'ata fuska aure kuma mama ai ni ba yanzu ba mana tace to sai yaushe "uhmm sai hamida tayi" hamida dake jinsu ta d'an harareta tare da jan dan karamin tsaki "mama kin ganta ko daga nayi magana shine hadda min tsaki" kyaleta tashi muje kici Abinci ko in kira AAMAARA tayi serving dinki?
No mama wannan dirty girl din da bata wanka ma maybe kawai muje kiyimin da kanki ta fadi haka tareda tashi tsaye ita ma maman mikewa tayi suka dunguma wurin dining din.
****
Koda na koma dakina sauran kayan dazan wanke na dauko na fito na fara wanki na so nake na gama da wuri sai in tafi islamiya Allah dai yasa yau kada mama ta hanani zuwa islamiyan,
Zuwa wajen qarfe hud'u da kwata 4:15pm na fito tsaf cikin shirina na zuwa islamiya part din mama na shiga babu kowa a parlourn dan haka sai na haye sama inda dakin mama yake a hankali nayi nocking jikin k'ofar muryan mama naji daga ciki tace waye?
Nice mama zani islamiya ne na fadi haka ina maimaita hasbunallahu wa ni'imal wakeel a cikin raina aiko Addu'a ta ta amsu dan cewa tayi intafi amma in dawo da wuri zan mata tuwo nace to tareda juyawa nazo sauka kenan mukayi karo da Aunty RADIYA ita kuma zata hawo saman da sauri na matsa gefe kafin tace na bangajeta kallona naga ta tsaya yi sai kuma tace min zokwuce,
RADIYA kuwa cikin ranta kissimawa take dama haka yarinyar nan keda kyau OHhh my G lallai mama bata san kadara take neman kashewa ba kalli jikin ta (dake yanzu tayi wanka) uhhhmmm ta fadi haka tareda dan lasar lips dinta na qasa mai dauke da siriryar huda hadda bari ma ta silver mai kyau.
Oho ni ban masan tanayi va dan da sauri na fito daga part din na nufi hanyar waje dan na kusa makara
Har na zan fita daga gidan sai naga banga Yah Rid ba(an cusu😀) da sauri na koma baya na dan bubbuga kofar d'akin naji shiru babu motsin mutum sai kawai na juya na tafi
Yana kallonta tunda ta fito daga lungun d'akinta har shigarta part din mama da fitowarta da zuwanta dakin sa ta bubbuga yana sane yaqi budewa dan ya lura kamar ta manta da dukan da tasha dazun Aranshi kuma yayi murmushi tunawa da yayi saboda shi aka daketa she is very beautiful ya fada cikin ransa da sauri kuma ya bata rai tareda dan dauke kansa kamar tana gabanshi.
****
Ana tashi daga islamiya ban tsaya komi ba dukda dai daman ba tsayawar nakeba tunda ba qawa ke gareni ba nima kuma inba hudda ta karatu ba babu da wanda nake magana
A kofar gida na iske RIDWAN yana Alwalar sallar magrib gaidashi nayi ya amsa ciki ciki na lura kamar haka yake maganar sa da kamar ince dazu na buga dakinsa naji shiru sai kuma nayi shiru nace araina ko ina ruwana ma dashi nida na sansa jiya jiyannan.
12:45am
Radiya ta kasa bacci sai juye juye take ita kadai a dakinta zuwa can kuma naga ta tashi zaune tareda yaye qaton duvet din da ta lullube sai kuma ta zuro da k'afa fuwanta kasa sannan ta miqe tsaye bata tsaya daukan lullubi ba kawai tayi waje da sand'a ta bude k'ofar dakin ta fita can waje ta fita sai kuma tayi hanyar d'akin Aamaara tana zuwa ko ta tura dakin taji dakin a bude yake da sauri ta shige ta maida kofar ta rufe da sauri ta k'arasa kan katifar ta d'an zaune cike da qyanqyami hannu ta kai ta fara tab'a mata jiki,
Yau dake da daddare nasha aiki sosai shiyasa ko k'ofar dakina ban tsaya rufewa ba inayin sallah na kwanta cike da gajiya dan gobe ina son inje school ina tsaka da bacci na naji ana tab'ani da farko na dauka mafarki nake sai da naji abun babbane sannana na bude idona dake cike da bacci kawai sai naga Aunty RADIYA da sauri na tashi zaune ina fadin Aunty lafiya?
Bata amsani ba ta k'ara kawo hannunta jikina da sauri na tashi tsaye ita sai ta tashi ta jawoni jikinta na k'wace tareda yin baya ina jin tashin hankali na bijiromin cikin zuciyata,
Aamaara dan Allah ki taimakamin mutuwa zanyi kibari inyi ko mi kike so wlh zan baki har waya ikina so zan siya miki amma dan girman Allah kibarni kinji kanwataaa ta qarasa cike da muryan tausayi(kamar wata ta Allah)
Wani kuka ne ya kufcemin ban ma iya cemata komi ba sai da naji ta qara kai hannunta jikina sannan na buge hannun nace "haba Aunty radiya kina mace kina wannan abun kin san kuwa hukuncin meyin wannan abun da kike shirinyi dan Allah nidai ki taimaki rayuwata da maraici na ki kyaleni bana buqatar wani abu naki dama can bada taimakonki nake rayuwa ba dan haka bana buqata Allah ki bari zan rinqa yimaki Addu'a Allah yasa ki daina dan... Haba mana Aamaara bakijin roqone wai please sister am in need of your help if not mutuwa zanyi ta k'ara kaimin cafka garin in kauce kawai na bige da bangon dakin Amma ba ta bigewar na ke ba Addu'oin tsari kawai nike maimaitawa har Allah ya bani sa'a na ingijeta na fita a dakin da gudu ina fita nayi tuntub'e da wani abu da bansan kominene ba kawai na fadi qasa warwas kafin in yunqura in tashi Aunty radiya ta fito daga dakin aikam ina ganinta na tashi da gudu nayi hanyar gate hankalina a tashe,
RADIYA kuwa ganin Aamaara tayi gate yasa kawai ita kuma tayi sauri ta shige part dinsu cike da bak'in cikin rashin samun biyan buqata,
Nikuwa ina zuwa gate rasa mima zanyi nayi dan na bala'ina tsorata da sabon halin na Aunty radiya ina nan tsaye ina hawaye har naji na gaji da tsayuwa sai kawai natafi bakin qofar dakin baba maigadi tunda akwai baranda na zauna ina cigaba da kukan bak'in ciki da takaici duniya babu masu tsoron Allah in banda bala'i da tashin hankali ace wai 'yar uwarka mace tana nemanka inna lillahi wa inna ilaihiraji'un ya Allah kasa Aunty radiya ta dena.
Tana nan zaune tana kuka har bacci ya dauketa bata sani ba,
A hankali yake bud'e' yar karamar kofar dake jikin gate din har ya shigo ya maida qofar ya rufe idanunsa ya qara budewa shin kodai gizo suke masa kamar mutum yake gani bakin k'ofar dakin yana k'arasawa kuwa ya ganta ta d'an kishingida tanata baccin ta abunta da kamar ya tadata sai kuma ya fasa ya tsallaketa ya shige dakinsa yana shiga yayi sauri yafara cire kayan jikinsa ya shige dan toilet din dake cikin dakin ya d'an jima kafin naga yafito daureda wani light blue towel da alama wanka yayi yana fitowa da sauri ya cire towel din ya fara goge jiki shi kafin ya janyo wata 'yar jaka ya fiddo Abubuwan ciki body lotion ne na la prairie Switzerland da kuma cream dinsa shafawa ya farayi a jikinshi kafin bayan yagama kuma ya dauko tureransa na tomford da kuma dior savage sai da yaga ma komi dayake naga ya dakko wata system ta Apple ya bude ta,
Har ya fara aikinsa kawai kuma tunanin yarinyar nan yayi mashi tsaye a zuciya shin miya korota daga dakin ta ta dawo nan wata zuciyar kuma tace ina ruwanka kaidai kawai kayi abinda ke gabanka haka nan ya share ya cigaba da abinda yakeyi sai wajen 2:30am sannan ya gama abinda yake maimakon ya kwanta sai ya sake shiga toilet ya dauro alwala ya fito ya tada sallah ya dade yana Addu'a bayan yagama sallar kafin ya dauko qur'ani ya fara karatu yana nan zaune aka fara kiran sallar Asuba sai da yaji za'a tada sallah sannan ya rufe qur'anin ya tashi ya fita yana fita yaci karo da ita yanzuma tsallaketa yayi abinshi ya tafi masallaci,
Aamaara kuwa da baccinta take hankali kwance dukda uban sauron dake ta cizon ta ga sanyin asuba daya fara sauka,
Sanyi danaji yana shiga jikina ne yasa natashi ina tashi kuma naji ana sallame sallar asuba gari ma ya dan fara shan iska da sauri na tashi har na nufi hanyar dakina sai na tuno da Aunty radiya na ciki baya na dawo da sauri na leqa dakin baba maigadi ganin babu kowa dakin yasa kawai na shige da sauri ina shiga kuma direct toilet na nufa qamshin wasu irin sabulai naji toilet din nayi dukda bawani toilet din azo agani ba dan sumintine kawai aka shafe bayin dashi amma a wanke yake tsaf
Fitsari na farayi kafin nayi sauri nayi Alwala ina gamawa nafito da sauri kada in makara sallah dakin nabi da kallo bayan fitowata a gyare shima dakin yake da alama dai yana da tsafta na Ayyana haka a raina wani abu nagani kamar laptop bisa table din da sauri na qarasa gurin ina matsawa idanuna suka gane min abin tashin hankali inna lillahi na bani na kawo kaina wani tashin hankali ne ya dirarmin shikenan kwana na sun kare wayyo Allah na ni RUQAYYA wani tsautsayi yasani na shigo dakinnan ina juyowa yana bude dakin ya shigo
Tsaye yayi yana kallonta cike da b'acin rai dakuma mamakinta lallaima yarinyar nan yau zaiyo maganinta kuwa
Nikuwa da nike tsaye kallonsa nike nima cike da tashin hankali da kuma tsoro to tsoro mana na tabbata duk wanda yaga abinda na gani k'ila wani har zawo sai yayi dan koni da ina da dama qila da zawon zanyi....
Comment and share please.. ✍️✍️✍️
💫QUNCI NA 😭 😢
STORY and WRITTEN by✨
✨Sa'adatu Ibrahim Babale 💕
Free page
PAGE 3⃣&4⃣
K'arasowa yayi cikin dak'in tareda matsowa inda table din 'yar qaramar bindigar dake kai wadda itace ta tsorata Aamaara ya d'auka yana dauka ya saita kanta da bindigar tare da d'ana kunamar bindigar ya saita ta da ita tare da fadin
"miya kawoki dakina har kina yimin bincike "ya fada tareda dauko wuqar da suke ajiye tareda bindigar,
Niko da tuni zufa ta gama jik'e ni sharkaf jikina in banda b'ari ba abinda yake da qyar na iya hadiye wani kakkauran miyau daya cika min baki tsabar tashin hankali sannan na bude bakina nace "dan Allah yaya ridwan kada ka kasheni wlh ba bincike nake maka ba Alwala kawai nayi ni ban masan ko minene ba ..
Ohhh yanzu ai kinganta ko?
Miya hanaki kwanan a d'akin ki kika zo nan?
Y
a qara jero min wata tambayar kafin na amsa waccan
" Uhmm babu komi kawai tsoron d'akin nakeyi, dan Allah kayi haquri kada ka kasheni na fada tareda hade hannuwana biyu alamun roqo"(🙏)
Sai kuma yaji tadan bashi tausayi amma duk da haka bari ya qara tsorata ta wuqar ya dakko ya nuna mata tareda cewa kinga wannan knife d'in " da sauri na daga mishi kaina cike da tsoron sa daya kamani"
Idan nasake naji labarin kin fadawa wani cewa kinga bindiga da wuk'a a d'akina sai nasa wuqar na yanke bakin ki sannan in cire maki idanu kafin daga baya in harbeki da bindigar wuce kiban wuri kafin na can za ra'ayi,
Kafin kace mi tuni na fice a d'akin ko waiwayensa banba ina ganin kaina a tsakar compound din gidan kawai nasa gudu sai d'akina sai da na shiga d'akin sannan ma na tuno da Aunty radiya kallon d'akin nayi naga bata nan sai naji dad'i toilet na shiga na sake dauro Alwala ina fitowa a gurguje nayi sallah ina gamawa na fita cikin gida danyi musu breakfast,
Kamar kullum yauma babu kowa sai yarinyar dake yin shara da goge bata tanka min nima kuma bana tanka mata dan haka kitchen kawai na shige na fara sabgar gabana.
Yau na d'an makara wurin shirin makaranta dan haka a gurguje na shiga nace ma mama na tafi Allah ya taimakeni bata hana ba banga Aunty radiya ba Amma abinda tamin yana nan tsaye cikin raina abu goma da ishirin ga d'an kidnapping har cikin gidanmu sannan kuma ga wannan bala'in na Aunty radiya daurewa kawai nikeyi a haka na tafi school dinmu dake da nisa tsakanin gidan mama Amma saboda ina son in lallaba 'yan sauran kudina na wannan watan yasa na tafi a k'afa wannan dalilin yasa na qara makara sosai ina zuwa ko na iske an tare sai da aka dakeni dan zalinci ma irin na prefect din datayi taren sai da ta qaramin bulalan wai ai ni kusan kullum sai na makara,
Ina cikin class ana mana lesson Amma hankali na yana gurin tunanin abinda Aunty radiya tayi min jiya Nakasa fidda abin daga raina haka har aka tashi daga school dake bawani koyarwa ake ba sosai tunda munkusa fara exam, yanzuma a k'afa na tafi gida.
Cikeda bala'in gajiya na qara so k'ofar gidanmu a bakin gate naganshi zaune bisa bencin da baba mai gadi ke zama yasha iska wanda yake k'asan babban bishiyar mangwaro dake qofar gidan,
Da sauri nayi wuff na shige cikin gida ko bari idona ya kalli inda yake banyi ba sai da na ganni a tsakar compound din gidan sannan nasaki wata Ajiyar zuciya,
Ina shiga d'akina cike da gajiya na fada bandaki don yin Alwalah,
Bayan nayi sallah ne naji cikina yana qugin yunwa sai lokacin na tuno da rabona da wani abinci tun jiya gwara d'azun a school da akayi break na siya awara ta talatin naci da pure watern goma Amma kaman banci abinci ba dan cikina yamutsawa kurun yakeyi,
Tashi nayi na dakko wata ledata ta ajiye ajiye na bude da sauri na rufe ganin babu komi cikin ledar sai wani dan kakkaben garin kwaki wanda ko cokali biyu bazaiyi ba amma ban damu tunda nasan zai ragemin yunwa,
Bayan nagama shan garin kwanciya nayi dan indan huta kafin lokacin aiki yayi.
2:25Am
A hankali ta bude kofar Palourn su ta fito tsakar gidan direct dakin Aamaara ta nufa tana zuwa kam ta taki sa'a dan tana budewa qofar ta budu ta shiga da hanzarin ta Abin mamaki tana shiga ta iske ta zaune bisa darduma da qur'ani a hannun ta tana karatu,
Yau tunda zan kwanta naje rufe k'ofar d'akina Amma yaqi rufuwa bansan dalili ba haka nakasa bacci dan dana rufe idona zanga Aunty radiya haka dana bud'e kuma zanji kamar ana tab'ani danaga dai zanyi asarar darena sai kawai na dauro Alwalah na kama sallah dana gama na dauki qur'ani maigirma na fara karatu take naji hankalina ya kwanta,
Ina nan zaune naji tana shigowa d'akin cikin raina Ayyanawa nake yau koni ko ita inajin tsayuwarta Amma ban ko dago kaina na kalleta ba karatu na kwai na cigaba dayi
Sai da takusa minti talatin a tsaye ita bata zauna ba sannan naji kawai an dauke qur'anin dake gabana a ajiye,
Da sauri na dago na kalleta nace "malama lafiya?
RADIYA tayi d'an murmushi tace" lallai ma yarinya ni kike d'aure ma fuska dan na shigo wannan akurkin d'akin? Toh bari in tuna miki tunda kin manta nan gidanmu ne bana ubankiba dan haka inada ikon shiga duk inda nake so a gidannan sannan kuma jiya ni kika so tona ma asiri ko kika tafi wurin me gadi dama kullum da daddare wajensa kike zuwako?
Da sauri na girgiza mata kaina zuciyata na tafasa
Ta cigba da cewa to bari kiji in fad'imaki wani abu da baki saniba shine ked'in nan baiwar gidanmu ce dan siyenki mukayi a lokacin da uwarki ta gujeki hakama ubanki daya gudu ya barta da cikin ki baiji tausayinta ba balle ke da kike cike uwata itace taji tausayinta ta kawota gidannan amma a haka tacimata amana ta koma tana neman mijinta duk wannan baisa ta koreki a gidanta ba a lokacin da ita mahaifiyar taki ta gudu ta barki kina 'yar shekara ukku a duniya haka mama ta barki a gidanta har kika girma amma shine dan tsabar butulci har ni diyar wannan matar data taimake ki keda mahaifiyar ki ta baki wurin zama a gidanta ina neman alfarma a wurinki bazakiyimin ba haba Aaamara shin kema butulu ce kamar mahaifiyar ki?
Ni ko tun fara maganar Aunty radiya nake kuka shin da gaske guduwa iyayena sukayi suka barni to miyasa? mina tsare musu?sunsan bazasu iya riqeni ba miyasa suka haifeni?
Allah sarki ni kullum cikin begensu nake ashe sune suka yanke Alaqarsu dani...... ✍️✍️
Comments and share please 👈
https://chat.whatsapp.com/BVqOy4UJveaDh5ZhJOEW5T
💫QUNCI NA😧😢
✨STORY and WRITTEN by sa'adatu Ibrahim babale ✨
This page was dedicated to my little brother HAMZA IBRAHIM BABALE (REIHAN)💕 Allah ya Albarka ceka duniya da lahira Amin🙏
Free page
PAGE 5⃣&6⃣
Dama kin daina wannan kukan da kike dan kuwa maganata haka take mahaifiyarki ta karbi kud'in mama ta gudu dasu ta barki a hannun mama a madadin kud'inta kinga kenan siyar dake tayi kinzama baiwar gidanmu kuma ita baiwa komi aka umurceta tayi yitake babu gardama balle musu,
Harta kai k'arshen maganarta ban dago ba ballantana in kalleta kuka na kawai nakeyi "shin da gaske ne kenan siyar dani ummana tayi? Toh miyasa kuma ai mama tace ummana 'yar uwarta ce dama d'an uwa be rik'on d'an d'an uwansa ne sai da kudi? Ko kuma dai a kaina aka fara nida banida gata hmmm koma dai minene ina sonsu a haka tunda har suka haifeni"
Tashi nayi in barmata d'akin dan bazan jure jin ana muzanta min iyayeba koda kuwa yankan naman jikina sukeyi suna ci,
Kamar tana jira dama in tashi tsaye kawai ta rungumeni tsam a jikinta tana fad'in
"haba qanwata ki tsaya mana muji dad'inmu na miki Alqawari indai kika tsaya tohh zaki daina yin duk wani aiki a gidannan zan dauko mai aiki dazata rinqayi ina biyanta ki yadda dani i promise to you Aamaara"
Tsanar ta naji tana zubowa cikin zuciyata mai tsananin gaske k'ok'arin qwatar kaina na fara Amman ta riqeni sosai tunda yanayin jikinmu ba daya ba sannan kuma ta fini shekaru "hasbullahu wa ni'imal wakeel da innalillahi wa inna ilaihiraji'un" nake ta maimaitawa cikin raina har Allah ya ban sa'a tayima rungumar sakwa sakwa aikuwa na fizge na fita waje da gudu har nayi hanyar gate saina tuno da kashedin da RIDWAN yamin na zai harbeni sai kawai na rab'e jikin wani dan lungu na zauna a gurin ina kuka mai sosa zuciya..
(ohhh poor Aamaara 😢)
****
Ina nan wurin har akayi kiran sallar farko zuwa lokacin na daina kukan sai ajiyar zuciyar da nike ta saukewa akai akai inaji har aka tada sallah Amma tsoron shiga d'akin nakeyi tunda nasan Aunty Radiya na ciki,
RADIYA
Turetan da Aamaara tayi yasa ta bugu da bangon d'akin take kuwa ta sume a wurin sanyin Asuba daya sakko ya farkar da ita tana tashi ta ta dafe goshinta dataji yana mata zafi tana tab'awa ko taji ya kumbura sosai saida gabanta yad'an fad'i tunowa datayi mama tana iya tambayarta dalilin jin ciwon tashi tayi ta fito daga d'akin da sauri tana waige waige taga ina Aamaaran ta b'oye sai da ta hanga ko'ina bata ganta ba sannan ta shige part d'insu....
Nikam sai dana tabbatar da ta shige part d'insu sannan na fito daga lungun dana b'oye dake ina ganinta ita ce bata ganina d'akina nakoma dan inyi sallah inajin zazzab'i yana neman rufeni
Da qyar kuwa nayi sallar saboda zazzafan zazzab'in daya rufeni rijib wata tsohuwar hijabina da zarah tabani kwance na janyo na lullub'e jikina.....
****
08:07am
Zaune take ta hakimce bisa d'aya daga cikin kujerun da sukayima falon qawanya girgiza k'afa take cike da b'acin rai tana k'ara kallon tamfatsetsen agogon dake parlourn,
"Hamida, hamida!"
Na'aam! Itama ta amsawa uwar cikin qufula "kai mama wannan irin kira haka sai kace nice Aamaaran?gani mizan yimaki ta fada cike da rashin d'a'a
Kije d'akin 'yar iskar can ki tadomin ita dan kuwa indai ni naje toh wlh sai na sabauta ta
"hummm aikece kike kyaleta kwana biyu tana abinda taga dama dan samun wuri ace har 8 tawuce Amma ba' ayi breakfast ba a gidannan ballantana gyaran d'akunan mu" hanyar fita ta kama tana mitar irin abinda Aamaara takeyi yanzu har takai qofa komi ta tuna sai gata ta dawo ta shige kitchen can kuma ta fito riqeda wani d'an qaramin bucket kallonta mama tayi tace "mi kuma zakiyi bacin ga abinda na saki can bakiyi ba"
Kaiii zuwafa zanyi Amma sai mita kikeyi sai kace tsohuwa (😱)
"Toh naji tafi"
Tana fitowa direct bakin tap din dake jikin wasu flowers ta nufa bud'e tap din tayi ta d'an tari ruwa kad'an cikin bucket d'in hannunta sannan ta ajiye bucket d'in qasa ta d'auko qanqarar pure water wadda ta d'auko a kitchen fasa qanqarar tayi ta zuba ta cikin ruwan data d'iba a bucket d'in sannan ta nufi d'akin Aamaara tura qofar tayi taji ta bude sannan ta shige tana shiga ta ganta kwance bisa 'yar yaloluwar katifarta tab'a ruwan tayi taji sanyinsa beyi mataba sai ta dakata sai da taga qanqarar tad'an narke sannan ta kwarama Aamaara ruwannan mai tsananin sanyi...
Ina kwance bacci yad'an fara fizgata har yanzu jikina rawar sanyi yake dan wani bala'in sanyi nakeji ina nan kwance kawai naji saukar wani ruwa mai sanyi sosai" a firgice na farka na yaye hijab d'in dana lullube dashi tsaye naga Aunty hamida riqe da bucket a hannunta kafin na tashi zaune ta idasa kwaromin sauran ruwan dake cikin bucket take jikina ya qara rikicewa da rawan sanyi"
"Dan kin raina mutane shine har yanzu kina nan kina bacci bakije kinyi aikin ba ko dan tsabar samun wuri irin naki to ki tashi mama tana kiranki kafin tazo ta sabautaki"
A hankali na bud'e bakina da qyar nace "dan Allah Aunty hamida kibawa mama haquri wlh banida lafiya bazan iyayin aikiba"
toh miya shafeni da ciwonki ko mutuwa zakiyi sai kin fito kinyi mana bauta dan haka tashi muje kafin na fara janki a qasa
Jin tace haka ne yasa na tashi a hankali jiri na d'an d'ibana na fara kokawar cire kayana dan sun jiqe jagab
"nufinki wai ina nan tsaye ina jiranki zaki canza kaya? Toh baki isaba wuce muje a haka baki canja kayan sai dai in mutuwa zakiyi"
Haka inaji ina gani ban canza kayan ba nabita a baya muka nufi part d'in mama,
Muna shiga na qarasa gaban mama dake zaune bisa kujera ta cika tayi fam ina qarasowa kuwa ta rufeni da duka tana buguna tama fad'in "raini ya shiga tsakanin mu ko da bazaki zo kiyi mana aikiba dame na rageki shin ban biyan ki kud'ine yadda ya kamata ko minene"
Ban samu damar magana ba har ta gama dukana kasa tashima nayi zaune saboda jikina dayayi ligiligi ko yatsana banjin zan iya d'agawa balle har ayi batun tashi tsaye
"zaki tashi ko saina dawo dan na lura kamar baki buguba yadda ya kamata"
Mama dan Allah kiyi haquri wlh bazan iya tashiba ban da lafiya tab'a jikina kiji da qyar nake yin maganar,
Ko ciwon Ajali kikeyi yau RUQAYYA sai kin tashi kin yi aikin nan tunda bazan biyaki a banzaba kinji na fada maki ta fadi haka tana hayewa sama dan ta dubo RADIYA taji bataji motsinta ba gashi kuma yau zata aiketa bank,
Da jan jiki na shiga in kitchen d'in rasa yadda zanyi in tashi nayi dankuwa jikina ciwo sannan ga wani Mugun sanyi inaji (ban tab'a yadda ni marainiya ce ba sai yau) kuka nakeyi a hankali har naji kamar motsin mutum ya shigo kitchen din da sauri na yunqura na tashi zaune da qyar ashe zarah ce ta shigo da sauri ta qaraso inda nake ta rungumeni tana kuka tana cewa
"kiyi haquri Aunty Aaamaara wata ran sai labari kinji bari inyi miki aikin mi za'ayi yau?
Da k'yar na bud'e baki nace a'a zarah ki barshi zan iya kawai dai ki wanke min wake k'osai za'ayi
"toh tace sannan ta tashi da sauri ta shiga store debo waken dazata wanke min,
Bayan ta wanke saida ta markad'a sannan ta daura ruwan kunu duk ina kwance tsakar kitchen d'in sai ga kuma Aunty hamida ta shigo "uban mi kikeyi a nan zarah shiga uku ko toh wlh ko ki fita ko kuma yanzu nan namiki shegen duka kuma in fadawa mama" da sauri zarah ta fita tana zumb'ura baki gaba itama hamidan binta tayi a baya,
Samu nayi na tashi jiri na d'iba ta haka na daure na dora frying fan din da zarah ta zuba mai bisa gas ban samu damar buga k'ullin kokonba na fara tuya ina cikin tuya Aunty Radiya itama ta shigo kitchen d'in da kumburarren goshi tana qarasowa gaba kawai ta ingiza ni baya man dake bisa gas ya b'aro min a qafata,
Wata gigitacciyar k'ara ta saki da duka gidan saida ya amsa.....
😟😟😟
Sa'adatu Ibrahim babale ('yar mutan bakori)✨
Comment and share please... ✍️✍️✍️
https://chat.whatsapp.com/BVqOy4UJveaDh5ZhJOEW5T
💫QUNCI NA😢😥
✨ STORY and WRITTEN by sa'adatu Ibrahim babale ✨
Free page.. ✍️✍️
PAGE 7⃣&8⃣
Ihun data kwantsama ne ya jawo hankalin mama da hamida dake zaune parlour suna jiranta ta gama hada breakfast suje suci (dan hamida bata iya komai ba na aikin gidama ballantana girki wannan na d'aya daga cikin abinda mama bata koya masu ba su duka sai zarah wadda itama tsabar nacin da takema Aamaara ne yasata ta iya wasu abubuwan)
Suna shigowa kitchen d'in suka isketa duqe a qasa tana kuka RADIYA kuma na daga tsaye gabanta wurin suka qaraso suna tambayar RADIYA "baby minene ke faruwa ne?"
Uhmm mama kalli fuskata kigani,
Kallonsu suka maida kan fuskar take kuwa suka zaro idon su duka ganin yadda goshin RADIYAr yayi uban tsini sai kace tayi karo da babbar mota "RADIYA minene ya sameki haka Kodai fitar da kikayi jiya da daddare kinyi accident ne amma baki fadamana ba?
RADIYA da daman tana sane ta boye kanta a bathroom d'azu dan kada mama taga goshinta ta tambayeta dalilin jin ciwon shiyasa ta boye amma yanzu plan d'inta yatafi yadda take so cikeda shagwab'a ta kalli maman tace
"mama dan kin daketa tayi laifi shine ta rama a kaina nazo ina mata magana shine ta tureni na bige da bango nikuma danaji zafi nima na tureta ashe kusada mai take shine fa man ya zubar mata a qafa maybe ta k'one"
Mama data gama sauraron RADIYAn ne ta maida kallonta kan Aamaara dake duqe k'asa ta dafe k'afar da man ya zubar mata
"Aamaara saboda kinyi laifi na hukunta ki shine kike neman ki nakasa min yarinya mitayi miki ne ai kaina yakamat ki rama tunda nice na dakeki"
Da qyar cikeda da tsananin zazzabi da ciwon jikin da ya kamani na bud'e baki zanyi magana amma mama ta dakatar dani ta hanyar kamo k'afar da man yazubar min ni ban ma san lokacin da ta duqa ba
"hamida zoki kama min ita wlh saina rama ma baby yau ba sai gobe qunar nan zata tashi tunda kema bakida mutunci" rirriqeni Aunty hamida tayi mama kuma ta kama qafata mai qunar ta mirza bata saki ba tacigaba da murza min qafar wai dole sai ta tayar da wutar,
Hummm idan nace maku ga irin zafin da nakeji to nayi qarya dan kuwa ba qaramar azaba nashaba ko bakin yin ihu banda shi haka suka gaji suka sakeni
Kama radiya mama tayi suka bar kitchen d'in tana cewa "muje in kaiki hospital baby ayi dressing ciwon"
****
Tana nan kwance batasan ina kanta yake ba har Allah ya kawo zarah da daman jira take su maman su tafi asibiti sai ta taimakawa Aamaaran,
Tana shigowa ta ganta kwance a k'asa ga kuma gas yana ta ci danma Allah yasa kad'an yake ci ruwa ta dibo cikin cup ta zubamata Amma taga bata kawo numfashi ba take hankalinta ya tashi dan ita babu abinda yazo ranta face Aamaaran ta mutu dan haka hanyar waje ta nufa da sauri,
tana fitowa harabar gidan taga bataga drivernsu ba dan haka tayi gate da gudu ta bud'e gate din ta qaramar k'ofa ta fita
Yana zaune kamar kullum shiru shi kad'ai yaga zarah ta nufo inda yake da gudu tana zuwa cike da sheshsheka ta ce mashi "dan Allah mai gadi ka taimaka min su mama sun kashe Aunty Aamaara"
Da sauri ya d'ago ya kalleta sai kuma yace mata "waye ya mutu?
Dan Allah kazo ka taimakeni wlh ta mutu bata numfashi!
Da sauri ya tashi yabi bayanta suka shiga gidan
Kitchen suka nufa inda Aamaaran take kallo d'aya yayi mata ya d'auke kansa saboda yadda fuskarta itama take a kumbure qarasa yayi ya durqusa zuciyarsa na bugawa da sauri hannunta ya kamo yaji pulse dinta sai kuma ya saki hannun ya kalli zarah yace " bata mutu ba tana da rai miya sameta?
Cikin kuka zara ta fada mishi abinda ya faru da kuma zubamata man da radiya tayi,
Take jijiyoyin kansa suka tashi idanuwansa suka kad'a sukai jajir da sauri yasa hannu ya dauketa yayi hanyar fita waje, itama zarahn mara mai baya tayi,
Fitowa sukayi daga gidan still tana hannunsa yana zuwa waje cikin ikon Allah saiga wani mai napep ya taho da Alama wani ya sauke tsaida napep d'in yayi ya shiga da ita tana rugume a jikinsa kaman baby zarah kuma ta shiga gaban napep din wanda ita bata taba ma ko shiga keke napep ba barantana gabanta Amma yau ko tunowa da hakan batayi ba ta shige sai da ma mai keken yace ta riqe karfen sannan ta riqe,
Fadamishi inda zasu yayi wato Asibiti
"megida asibitin kud'in kona gwamnati inji me napep d'in,
Cikin b'acin ranshi da yakasa boyewa yace ma me napep d'in ya kaisu private hospital mekyau,
Da sauri zarah ta kalleshi dan kuwa dukda ita d'in ba wata babba bace amma tasan private hospital dole sai mai kud'i to shida yake gadi ina yaga kud'in kai wani asibitin kud'i shima yana fama da kansa,
Shi hankalinsa baya kanta har suka isa asibitin suna zuwa Security d'in bakin gate suka so hanasu shiga dan kuwa asibitin ta masu kud'ice sosai sukuma sunga suturar jikinsu daga shi har Aamaaran sai a hankali gwara zarah ita doguwar Abayace had'e da veil dinta tayi rolling dinsa,
Da qyar ya iya danne b'acin ransa ya yabasu haquri akan su taimaka su barsu su shiga inba hakaba patient din da suka kawo zata iya mutuwa
Wani ne a cikin security d'in yaji tausayinsu yasa aka bari suka shiga suna shiga cikin asibitin akace dole sai ya biya kud'i kafinma likita ya duba ta barinsu yayi da zarah ya tafi inda ake biyan kud'in ya biya sannan fa akayi emergency da ita,
Can kuma saiga doctor d'in ya fita ya kira RIDWAN d'in yace yazo,
wajen doctor d'in yanufa yana zuwa kam yace
"miya faru da yarinyar da aka kawo"
A gajarce yayima likitan bayani aikuwa likita yayita masifa yana cewa shi baima yadda ba waya sani ma ko shid'in mijin ta ne kuma shine yayi mata wannan mugun ta'addancin dan kuwa da ganin fuskarsa zai iya amma shine yakeson ya raina masu hankali to gaskiya bazasu dubata ba sai ankira police dankuwa a duniya babu uwar da zata iya yima 'yar cikinta wannan dukan (shifa duk zatonsa mama ce ta haifi Aamaara dan a haka RIDWAN yace mamanta dan shima baisan yasuke da maman ba)
Danne zuciyarsa yayi yace"babu buqatar zuwan police kawai ka duba ta"
Take fa doctor ya zage ya fara zubamai rashin "m" yana fadin wai soyake yayi iko dashi komi toh bari ya kira security su fiddashi daga asibitin gaba d'aya,
Gani nayi yana nunama doctor din wani abu da banga ko minene ba sai kuwa likitan ku yakoma d'akin da aka shiga da Aamaara..
****
Sai da aka b'are qunar akayi dressing sannan aka samata drip da wasu Allaurai a ciki bayan an shafe fuskanta da wani gel na cire radadi sannan suka fito aka canza mata d'aki daga A&E zuwa d'akin hutu
Zarah dai tana ganin ikon Allah a ranta take cewa "ko ina yasamu kud'in biyan babban d'aki haka kodake maybe yana tara kudinsa ne daman"
Shi dai yana nan zaune shiru har doctor yazo jikinsa na rawa yace mashi an canza mata d'aki zasu iya zuwa su ganta sannan kuma akwai fever a jikinta da kuma alamun yunwa sosai a tareda ita,
Jinjina masa kai kawai yayi ya miqe zuwa inda d'akin yake itama zarah binshi takeyi bakin k'ofa ya tsaya yana qaremata kallo ta qara haske sosai saboda ciwo kanta babu dankwali gashin kanta da babu kitso ko kyan gani babu dan a cukurkud'e yake shaddar jikinta babu datti Amma ta koma fara fat dan tsabar kod'ewa,
Shi mamakin kansa ma yake yanda ya shiga cikin Al'amarinta yayi qabe qabe itace mace ta farko daya fara shiga lamarinta idan aka cire mahaifiyar data haifesa itace ya fara kai hannunsa jikinta sannan kuma har ya damu da lamarinta shin wai mike damunsa wata zuciyar kuma tace saboda taimako ko haka ka barta ka taimaka mata ai,
Jiyake kamar ya tafi ya barsu tareda zarah Amma kuma bazai iyaba saboda ko suna buqatar wani abun haka nan ya daure Amma duk yana jinsa ya takura,
Haka suka jira har ta tashi daga baccin sannan drip d'in ya qare kuka kurin takeyi daga ita sai zarah a d'akin zarahn ce ta lallabata tayi shiru sannan ta fadi mata wanda ya kawota asibitin
Shiru nayi zuciyata na bugawa dan kuwa dukda ina cikin ciwi ban manta abinda ya had'ani dashiba ina cikin tunanin ya shigo d'akin tareda doctor da Alama sallamata za'ayi dan naji yana cewa a rinqa kawoni ana min dressing din wutar inba hakaba zan samu matsala
Har aka sallamemu ban samu nayi magana dashiba haka muka fito bakin gate d'in asibitin muka samu taxi din da ta dauke mu ta kawomu gida dayake ciwon ba'a tafin qafa bane sai yazam zan ita d'ingisa qafar amma bazansa ruwa ba dokar likitace wannan,
Saida muka fito sannan na d'an kalleshi a dan tsorace nace
" nagode Allah ya saka da mafificin Alkhairi"
Kallonta yad'anyi sai kuma ya dauke kai ya maida kan zarah dake gefe tana kallonsu su duka biyun cemata yayi kada ta fadawa kowa shine ya kai Aamaara hospital yazama sirri a tsananin su sannan ta fadawa mama kada a bari tanayin aikin da zaisa ta tab'a ruwa saboda kada qunar yaqi warkewa
Toh tace dashi sannan ta matso na dafata muka shifa gidan direct d'akina tayi dani ina shiga na kwanta ita kuma ta hau dan gyaramin d'akin bayan ta gama tace bari ta samomin wani abu inci,
****
Koda zarah ta shiga parlourn zaune ta iske mama Aunty RADIYA tayi pillow da cinyarta "daga ina kike zarah maman ta tambayeta"
Naki Aunty Aamaara hospital ne an dubata
"ubanwa yace ki kaita ko ko neman suna?
Mama tana cikin tsananin neman taimako shine na kaita sannan kuma sai da aka kira police shine nace masu wani ne ta daketa har mai ya zubar mata a qafa ta qone Amma ya toh yanzu dai police din sun karb'i Address din nan gidan zasuso bincike dan haka mama wlh a shawarce kada a qara bari tayi wani aiki inba haka ba zasu gane kune kuka daketa,
Ba mama kad'ai ba har RADIYA da hamida da shigowarta parlourn kenan sai taji tsoro dan kuwa in 'yan sanda suka kamasu toh fa sun kad'e dan ita mama hango igiyar aurenta take tana lilo dan idan babansu hamida yasan abinda ya faru tabani tunda indai sukai waya dashi sai yayi mata fad'an ta daina saka Aamaaran aikin da zai wahalar da ita dan akwai ranar da Aamaaran batada lafiya bata fito tayi breakfast ba lokacin yana gari shine mama ta daketa har tayi targed'e a hannu shine fa yai ta fad'a ya kuma yi mata rantsuwar indai wani abu makamancin haka ya sake faruwa to abakin aurenta toh ina ga ance masa RADIYA ta qona Aamaara kuma tasan dole yasani indai police d'in sukazo gidan.....
Toh faahhh mama a tsaka mai wuya(🙆)
Sa'adatu Ibrahim babale... ✍️✍️
https://chat.whatsapp.com/BVqOy4UJveaDh5ZhJOEW5T
💫QUNCI NA 😢😥
✨ STORY and WRITTEN by sa'adatu Ibrahim babale ✨ 💕
Free page
PAGE 9⃣&🔟
Kallonsu su duka zarah tayi taga lallai ta sakasu jin tsoro sannan ta nufi kitchen dan samarwa Aamaaran Abinda zataci,
Ba'a dafa komi ba kamar yadda tayi tsammani dan dukansu har maman son jiki bazai barta tayi Abincin ba,freezern dake kitchen din ta bude ta d'auki fruit aciki kankana ne sai Ayaba da kuma paw paw yankasu tayi da d'an girma cikin wani d'an bowl sannan ta zaba sugar kadan da madara sai ta maida cikin freezer ta fara kiciniyar hadamata tea,
Leqowa tayi tagani haryanzu suna parlourn taga suna nan zaune kowa yayi shiru komawa tayi tabi ta qofar baya ta fice zuwa d'akin Aamaara
Da qyar na iya shanye tea d'in sannan zarah ta matsamin saida nasha fruitsalad d'in kad'an wannan shine shana dashi na farko Amma dake ina cikin ciwo ban wani ji dad'insa ba
Sai da zarah ta tabbatar da nasha magungunan da aka bani a hospital sannan tafita ta barni ni kadai a d'akin dama na saba zama ni kadai sai banji komi ba.
****
Da daddare da qyar na lallab'a nayi sallah ko tashi banyi ba daga wurin zarah ta shigo d'akin hannunta riqe da plate d'in noodles shima da qyar ta sani naci Amma cikin raina Addu'an gamawa da duniya lafiya nake yimata dan kuwa itace mutum ta farko a duniyar nan data fara nuna min qauna,
Sai da nasha magani sannan ta qyaleni ta tafi nikuma daga nan bacci ya d'aukeni mai cike da fargabar zuwan Aunty Radiya
Toh bata ma zoba d'in kamar yadda nayi tsammani....
****
Sai da nayi sati ina jinya kuma har lokacin ban sake saka RIDWAN a idona ba haka ma su mama babu wanda nagani sai zarah kawai datake dawainiya dani,
Jin jikina da qarfi yasa yau na koma aiyukan da nakeyi na gida kamar baya dan na warke sosai wutar ce kawai bata qarasa k'ame wa ba Amma batayin ruwa tunda ni da zarah munje hospital din sau biyu anayiman dressing an bani kuma maganin da zai sa ta warke da wuri Amma har muje mu dawo bana ganin RIDWAN,
A gefen RIDWAN kuwa yana kan sani yake b'oye kansa da ganin Aamaaran kullum cikin tunanin ta yake yayi fama ya cire Abun a ransa amma ya kasa babu Abinda yake tunowa sai sanda tana kan gadon Asibitin nan yanda tayi kyau kamar ba ita ba sai kuma lokacin da taga bindiga a d'akin sa yanda duk ta tsorata wannan abun ya tsaya mai a rai sosai..
Yana zaune daga cikin dakinsa dayake bakin window yake zaunen saikuwa ya hangota ta fito daga part dinsu mama tayi hanyar d'akin ta sosai ya qureta da kyawawan idanuwansa masu kama da na 'yan qasar turkiya ta rame sosai Amma kuma ta qara haske doguwar rigace jikinta ta Atamfa Amma ko zanen Atamfar ba'a gani saboda azabar kod'ewar da tayi kafarta ko takalmi babu amma haka take tafiyarta babu ruwanta
Cikin ransa yake magana "shin wai ita miyasa d'akinta a waje sannan kuma minene had'inta da 'yan gidan tunda ya lura ba aikatau takeyi ba sannan kuma batada sutura ne? Wata zuciyar tace ina ruwanka gashi nan yanzu daga taimako tazo tayi maka tsaye a qahon zuciya wannan tunanin da yayi ne yasashi jan wani munafikin tsaki da ko karshen tsakin be kaiba yaji wayar jikinsa na vibration tashi yayi daga bakin windown yakoma kan katifa sannan ya fiddo wayar kangawa yayi a kunne beyi magana ba sai daga can bangaren akace " GAGO ya kake" a taqaice ya amsa da lafiya lau "toh ya gadin? ya fada cike da shaqiyanci shidai RIDWAN be tanka sa ba har yaci gaba da cewa
" munyi waya da oga yace yanata kiranka baka d'aukaba dama batun operation d'in da za'a fita anjima ne toh yanzu yace abari sai nan da kwana biyu saboda akwai rashin tsaro yau kada ma kafita ko'ina dan gudun problem"
Hmmm ya d'an sauke ajiyar zuciya kafin yace shikenan Allah ya kaimu lafiya daga can bangaren ya amsa da Amin kafin yace dan Allah GAGO kada ka fito dan gudun matsala,Amsashi yayi da naji tareda katse wayar yana jan dan gajeren tsoki....
****
Bayan na gama komi daya kamata inyi a cikin gida sai nadawo d'akina na zauna na rafka tagumi dan kuwa yunwa nakeji kamar zan mutu ruwa kawai nakesha tun safe komi nawa ya qare gashi banda kud'i sannan kuma har yanzu mama bata sallameni ba kuma ni bazan iya tambaya kada in dama ma kaina salalan tsiya haka nan na haqura na kwanta da yunwar...
****
A bangaren RIDIYA kuwa tunda taga Aamaara ta fito tayi Aiki tasan ta warke kenan dan haka ta qurduta yau saita cimma burinta shiyasama tunda dare yayi taqi zuwa ta kwanta har mama dasu hamida da zarah suka shige d'aki suka kwanta sai da ta tabbatar da sunyi nisa a barci dan lokacin qarfe shabiyu tayi har da kwata sannan ta tashi ta haye upstairs d'akinta ta nufa ta d'auko wani abu kan mirrors cikin wata qaramar container tana d'auka ta fice daga dakin ta sauko qasa fridge din dake parlourn ta bude ta dauki wani tamarind juice ta hada da cup din dake saman fridge din ta fice daga parlourn da sauri kamar tana tsoron wani ya ganta hanyar d'akin Aamaara ta nufa tana zuwa bakin qofar ta tsaya ta durqusa ta bud'e juice din ta zuba cikin cup ta ajiye gefe sannan ta dauko container ta bude wasu 'yan qananun drugs ta dibo guda biyar ta zubasu cikin cup d'in sai data tabbatar da sun narke a cikin juice d'in sannan ta saka hannunta ta juyashi a ciki yazamana ta motso na qasan sun hade da juice din kafin ta miqe tsaye ta shige d'akin
Kwance ta isketa kan 'yar yagalgalallar katifarta ta rufa da wata hijab wadda itama bata da banbanci da tsumma qarasawa tayi tana tada ita dan so take dole tasha juice din inba hakaba da matsala..
Ina cikin baccina me hade da muguwar yunwa naji ana tashina daga bacci cikida magagin baccina daya fara nisa na farka mutum nagani duqe tana miqomin cup dake yunwa nakeji sai kawai na miqa hannuna na karb'a dan duk a tunanina zarah ce ko kusa ban kawo zuwan Aunty RADIYA ba dan tun ranar da ta qonani ban sake ganinta ba ko da'zu dana shiga aiki ban ganta ba dan haka sai nayi tunanin zarah ce da zuciya daya na kai cup din bakina.... ✍️
Note:Assalamu Alaikum readers QUNCI NA littafin kud'ine kamar yadda kuka gani a jikin book cover d'in naira 300 kacal zaki biya ki karanta dan free pages ya kusa qarewa
Nagode🙏
Sa'adatu Ibrahim babale ('yar mutan bakori)
✨ ✍️
https://chat.whatsapp.com/BVqOy4UJveaDh5ZhJOEW5T
💫QUNCI NA 😧😥
✨STORY and WRITTEN by sa'adatu Ibrahim babale ✨ 💕
Free page
PAGE 1⃣1⃣
Sai da na kurb'i kadan a bakina har zan shanye sai na d'ago da niyyar yimata godiya kawai naci karo da fuskar Aunty radiya take na furzo da juice d'in bakina ya kuwa feshe mata kyakkyawar fuskarta take naji tsoro ya cikani shin minene nasha haka me zaqi da d'aci da kuma tsami? Kafin na bawa kaina amsa naji saukar wani mari kai bal'ain zafi da sauri na dafe kumatuna ina kallonta da mamakin abinda nayi mata da har zai sa ta mareni
Radiya kam data maretan ko alamar nadama babu a tattare da ita saima cemata da tayi "wlh baki isa kisakani yin asara ba dan UWARKI dole ki shanyeshi ta fada tana kokowar kai cup d'in bakin Aamaara"
da sauri na matsa baya ina koqarin tashi in barmata d'akin kamar yadda na saba aiko ta danneni da iya qarfinta nanfa muka fara kokowa toh dake nice a qasa sai nafita shan wahala daga kokowa kam naji Aunty radiya na laluben wasu sassa na jikina take hankalina ya qara tashi na shiga maimaita duk Addu'ar da tazo raina babu ta yanda zanyi ihu dan ta matse min baki da hannun ta daya tanason by force insha wannan abun dake cikin cup wanda ni ban masan minene ba,
Allah ya ban iko ta cire hannun data rufemin baki kafin ta maida na qwala ihun da saida d'an qaramin d'akina ya amsa da qarfi na ke fadin "wayyo Allah a taimakeni innalillahi wa inna ilaihi raji'un a taimak... bata bari na qarasa ba ta rufemin baki ganin zan tona mata asiri dukda baza'a tab'a jinaba a part d'insu...
Yau tunda dare yayi yake zagayen gidan dan hakanan yaji ajikinsa kamar wani abu zai faru dashi dan gabansa fad'uwa kawai yakeyi ya kasa bacci shiyasa ya fito yana zagayen cikin gidan kamar daga sama yaji muryarta tana ihu da neman taimako har yayi hanyar sai kuma ya daina jin ihun zai juya kenan yaji kamar gurnani da sauri yayi hanyar d'akin ya shiga,
gabansa ne yayi wata irin muguwar faduwa ganin RADIYA d'are d'are bisa Aamaara suna kokowa
Radiya da taji motsin shigowa d'akin da sauri ta d'ago kai cikin tsoro sai kuma taga wannan qazamin mai gadin nasu na yanzu tsaki taja tace masa " malam lafiya zaka shigoma mutane haka" ko kallonta beyiba ya qara so bakin katifar yana danne fusatarsa dan idan yace zai tanka mata to ba makawa sai ya KASHETA to yanzu dai bai shirya wannan ba tukun maybe sai nan gaba idan ya cimma burinsa be tsaya wani tunani ba yasa hannu ya finciko RADIYA ya wurgata gefe ya dago da Aamaaran da tuni ta dad'e da sumewa saboda rufe mata bakin da tayi harma da hanci wannan dalilin yasa ta sume, daukarta kawai yayi yabi hanyar fita d'akin ko takan radiya dake kwance qasa tana ganin ikon Allah bebi ba ya fice da ita daga d'akin tana rungume a hannun sa sai kace baby 👶 ,
Bayan ya fito da ita daga d'akin sai kuma ya rasa ina zaiyi da ita gashi tana riqe a hannun sa dan haka sai kawai yayi hanyar d'akin sa da ita yana shiga ya shimfid'eta a kan lallausar katifarsa dake d'akin, zaune yayi yana qare mata kallo sai kuma yayi sauri ya kauda kansa tareda tashi zaune ya shige tiolet d'in dakin ya dauko ruwa cikin wata qaramar buta yana zuwa ya d'an tsiyayi ruwan a hannu kafin ya duqa ya shafa mata a fuska,da sauri ta kawo numfashi mai qarfi,
Waige waige na farayi ina kallon inda nike gashi wani irin kamshi ya cikamin hanci mai dad'in shaqa dan lumshe idanuna nayi ina shaqar qamshin da na rasa ina na sanshi wani tunani ne ya zomin a rai da sauri na d'aga kaina had'a ido mukayi dashi da sauri na sauke idanuna qasa na fara himmar tashi zaune sai da na tashi sosai na zauna sannan na qarayin qasa da kaina cikeda kunyarsa da ta kamani dan na tabbatar da yaga abinda Aunty RAADIYA ta tayimin shiyasa har ya tsareni da idanuwansa masu kama dana mage a zuciyata nace qilama kallon abinda Aunty Radiya tayimin yake take naji na muzanta,
Uuhhmmm ya d'anyi gyaran murya sannan yamin tambayar data sakani d'agowa na kallesa a mugun kid'ime
" INA IYAYENKI SUKE SANNAN KUMA MINENE DANGAR TAKARKI DA MUTANEN GIDAN NAN, KUMA ITA WACCAN DA TAKE ZUWA DAKINKI MI TAKE ZUWAYI?
ga nin tana kallonsa yasa yace " inason kibani amsar duk tambayoyinnan danayi miki yanzu!
Ya qarasa fad'a a kausashe,
Cikin muryarta mai sanyi kamar komi nata ta fara" kamar yadda ake haihuwar ko wani mutum a duniyar nan haka nima "RUQAYYA AL QASEEM G" aka haifeni sai dai kuma bansan su wanene sukayi silar zuwana wannan duniyar ba mai cikeda da tarin QUNCI da damuwa harma da tashin hankali,
Kawai na tashi ne na ganni ina rayuwa a wannan gidan a kuma cikin wannan d'an d'akin,
Ban san kowa ba a duniyar nan bayan mutanen nan gidan matar da a da can nake tunanin mahaifiya tace ashe ba itace ta haifeni ba a cewar ta wai ita d'in qanwar mahaifiya tace wadda bansani ba kamar yanda kaji na fad'a da farko bansan waye mahaifiyata ba ballantana kuma mahaifina haka na tashi ina rayuwa ni kad'ai a d'akina idan safiya ta kuma in shiga cikin gida in yi masu aikace aikace kamarsu girki gyaran d'akuna da sauransu,
A bangaren abinci kuwa dama ni ban isa inci Abincin gidan ba wanda nice ke dafashi komi rintsi duk kuwa azabar rashin lafiya bana fashin aiki sai idan BABA yana nan ne yake hana asakani aiki idan bani da lafiya kud'i ake bani naira dubu takwas sune kud'inda ake bani a wata in sayi abinci da sabulun wanki da sauran buqatuna yau da kullum kamar siyen magani idan banda lafiya da kuma idan ana buqatar kud'i a school dan ma ba wani masu yawa suke nema ba
BABA shine ya d'aukeni ya kaini makarantar islamiya da boko wanda the a lokacin da girma na shekarata bakwai da wani abu sanda ya kaine makarantar boko sunso suqi karbata Amman dake ta kud'ice kuma ya basu kud'i enough take kuwa aka sakani primary one wanda duka 'yan ajin na keresu a girma da tsayi,
Bayan na kammala primary ne zan tafi J. S. S one Aka can zama baba wurin aiki sai yazam baya zama nan sosai yakan dad'e ma bai zoba dake yana da mata a can inda yake,
Kafin ya tafi sai da ya bada komi nawa na tafiya secondary school amma bayan tafiyarsa da za'a kaini madadin a kaine inda yace sai naga an kaini makarantar gwamnati bandamu tunda inason inyi karatun amma babban qalubalen da na fara fuskanta a fannin karatun shine hanani zuwan da akeyi wataran dan sai mama taga dama take bari na inje, a fannin karatu ina d'an ganewa babu laifi sosai abin yake damuna
ina zuwa islamiya shima sai anga dama ake barina zuwa Amma haka nake nacewa da karatun har nike fahimta babu laifi wanda Alhmdllh babu laifi ina d'an ganewa....
Bayan baba babu wani wanda ya damu da lamurana a gidannan sai zarah itace ke bani suturar sawa idan banda lafiya ta kula dani Amma bayan ita babu kowa shiyasa nima a duniya da ita kad'ai na saba itace tacemin mama qanwar mahaifiyata ce Amma da bazan tab'a yarda ba...
Ban tab'a jin ina kewar IYAYENA sosai ba kamar ranar da RADIYA ta fara shigo min d'aki da mummunar d'abiarta wanda a ranar nayi kukan rashin uwa harma da uban dukda ance wai guduwa sukayi suka barni ko kad'an banjin haushinsu koba komai sune sukayi sanadin zuwana duniya Amma kuma tambayar da har yanzu na kasa yima kowa ita itace minene yasa suka tafi suka barni minayi musu ne?
Ta qarasa tana fashewa da wani kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro,
(wayyo Allah 😢😢)
Shima kad'an ya hanashi fashewa da kukan Amma ya daure zuciyar sa dan ya yadda da kansa shid'in namiji ne namijin ma mai da kakkiyar zuciya dan haka ya had'iye abun da ya tokare masa a wuya wanda take jijiyoyin kansa suka yi rud'u rud'u
Rasa yanda zaiyi ya lallasheta yayi dan haka yayi shiru yana kallonta tana kukan nata dan an tono mata inda ke mata qaiqayi dan tunda take bata tab'ayin wannan maganar da kowa ba sai yau itama bata san dalilin dayasa daya tambayeta ba har ta iya bashi labari....
****
RADIYA kuwa da akan idonta RIDWAN ya fice d'akin riqeda Amara tana nan kwance inda ya hambarar da ita har ta gaji ta tashi da sauri ta fice daga d'akin ko ta kan robar qwayoyin da ta ajiye bakin qofa bata biba tayi part d'insu cikeda baqin ciki da kuma tsoron kada wancan qazamin ya kira babanta ya fada masa abinda tayi tuno da hakan da tayi ne yasa taji gabanta yayi wani mugun fad'uwa haka ta shigo parlourn su cikin fargaba ganin wutar palourn a kunne tana shiga kam taga zarah zaune da ruwa a hannunta da alama ruwan ta sauko ta sha dama,
Kallon RADIYAn zarah tayi tace "Aunty Radiya ina kikaje da daddarennan?
Radiya da daman take cikin takaicin rashin cikar burinta aiko ta hayayyaqo ma zarah tana cewa" ban sani ba uwata uban minene ruwanki dani koko gulma da kinibibi da munafurci" a'a Allah ya baki haquri zara ta fada tana miqewa ta haye sama ta bata wuri dan dama ba wani shiri sukeyi ba sosai(sako sako☺️lols)
Itama RADIYAn hayewa tayi ta nufi d'akinta tana shiga ta nufi side lockern dake jikin gadon ta tabude ta d'auko syringe da wata injection cikin kwali ta fasa ta zuqo sannan ta cakama hannunta tanayi ta yadda syringe d'in da kwalbar Alluran ta kwanta kan gado... ✍️ ✍️
Aamaara tana ga nin IYAYENTA kuwa ko dai sun mutu,
RAADIYA fa tana cimma burinta kan AAMAARA kuwa ko kuwa haqura take,
RIDWAN fa minene a ransa??
Shin kuna son sanin wannan Amsoshin?
Duk mai so ya biyoni 'yar mutanen BAKORI dan jin yadda zata kaya a cikin lattafin QUNCI NA
Second to the last free page kenan in baku manta ba daman nace maku QUNCI NA paid book ne mai son karantawa zai jiya naira 300 ta wannan account d'in
👇
1673082483 SA'ADATU IBRAHIM ACCESS BANK sai shedar biya ta wannan numbern
08145299097...
Masu comments da sticker dan Allah su bari kawai da words nake so in bazakiyi da typing ba toh ki barshi kawai bawai a turomin stickers ba a madadin.
💫QUNCI NA 😥😢
✨ STORY and WRITTEN by sa'adatu Ibrahim babale ✨ 💕
<UNDER THE PENS OF SARATU IBRAHIM MAITAMANIN (Jaririyar writers) and SA'ADATU IBRAHIM BABALE (bakori girl 👧) >
KING 👑 AND QUEEN 👸 WRITING CHAMBER.
PAGE 1⃣2⃣
Yanata kallonta tana kukan amma yakasa lallashinta saboda bai iya ba besan taya zai lallashetan ba
"Kibar kukan nan haka ya isa"
A hankali naji nutsuwa tana shiga saboda yau ne rana ta farko da wani babba mai hankali ya kula da lamari na in aka cire zarah,
Share hawayen nayi sannan na tashi tsaye na nufi kofar fita daga dakin bai hanata ba har ta fice yana binta da ido ba ko kyaftawa
Dakina na nufa ban damu da ko Aunty raadiya na nan ba ko bata nan na shiga d'akin banyi mamakin rashin ganinta a d'akin ba tunda abinda ya kawotan bata samu ba dama ai tafiya zatayi inma banda mugun nufin da ke tare da ita nasan ban isa ko hanyar d'akina ta kalla ba, ban kwanta ba Alwala nayo nazo na fara kai kukans ga mahalicci mai kowa da komi,
****
Kasan cewar ban kwanta da wuri ba shiyasa na tashi a d'an makare da sauri na shiga bandaki inyi brush kafin a zo nemana ina ciki naji an turo kofar dakina an shigo dan haka da sauri na qarasa kuskure bakina na fito Aunty hamida kamar yadda na sani,
Harara ta zabga min kafin tace "uban minene yasa baki shigo kiyi aikin ki ba kokuwa salon a dakeki kiga kamar an zalunceki alhalin kece azzalumar tunda duk wata ana baki haqqinki amma ke sai lokacin da kika ga dama kike yimana aiki"
Sai da nabari ta kai qarshe sannan nace "wlh Aunty ban tashi da wuri bane amma yanzu zanzo"
Bata tanka min ba ta juya ta fice daga d'akin,
Ta fito d'akin kenan zata wuce sai taga container mai dauke da drugs yashe a kasa kallon container tayi sosai ta tabbatar da itace kokuwa durqusawa tayi ta dauka hadda juice d'in da shima yake a wurin cikin tashi container bude ta drugs d'in tayi taga tabbas sune aikam jikinta na rawa tayi hanyar part d'insu tana shiga taga mama zaune kan kujera tana jiran azo ayimata breakfast dan office zata,
A mugun rud'e ta qarasa inda maman take tazauna hadeda miqa mata robar,
Da kallo tabi roban kafin kuma tasa hannu ta karba sannan ta bude ganin kwayoyin dake ciki yasa ta zaro ido sosai sannan ta maida kallonta kan hamida dake saqe saqe cikin ranta "ina kika samu wannan abun hamida?
Sai da tad'an yamutsa fuskarta kamar yanda ta saba yima maman sannan tace" a qofar d'akin Aamaara na gani ban san kuma ko nawaye ba"
Kallonta mama take sosai kamar wata makauniya kafin ta bude baki tace hamida kodau yarinyar nan shaye shaye takeyi bamu sani ba? Ban tunanin haka mama ina taga kud'in siyen wa'innan tsadaddun abun kinsan kud'in su kuwa sai dai idan samari tayi suke bata amma dai kam bata iya sayensu"hummm mama ta sauke nannauyar ajiyar zuciya sai kuma tayi wani murmushi mai kama da na qeta ita dai hamida kallonta take da mamakin murmushin na fuskar tata amma dai bata ce komai ba,
Kamo hannun hamidar mama tayi kafin cikin wani farin ciki daya zo mata yanzu tace "hamida zanso ace da gaske yarinyar nan shaye shayen take da kuma bibiyar mazan nasan ko da wannan na barta maybe in kusa hucewa da abinda uwarta tayi min"
Hamida bata tab'a jin tana tausayin Aamaara ba sai yau da sauri ta fizge hannunta daga na mama da ta riqe wani kallo take yimata mai kama da Harara sai kuma tace haba mama ki rinqa tunanin mutuwa mana dake da mahaifiyar Aamaara fa jininku d'aya wannan abun da kike shirin aikatawa ba daidai bane wlh da sauri mama ta katseta ta hanyar daka mata tsawar da tunda take bata tab'a yimata ba dan kuwa tsakaninsu da mama sai dai lallab'awa bata son ma taga suna fushi gwanda ma zarah wataran tanashan zagi saboda ita tana shiga lamarin Aamaara sosai"ke! Hamida nice uwarki ko kece kika haifeni da zance ga yanda za'ayi kicemin a'a kinsan irin baqin ciki da tashin hankalin dana shiga ta dalilin uwarta kinsan abunda akayimin duk saboda ita toh wlh babu uban daya isa ya hanani abunda nayi niyya in kuma zaki iya toh bismillah ga fili ga mai doki saura sukuwa kuma wlh ko babanki naji kin fadawa wannan maganar sai ranki yayi mummunan b'aci ballantana kuma kiyita da wani wlh sai na tsine miki Albarka tana fad'in haka ta tashi ta haye sama da sauri dan farin ciki ma yasa ta daina jin haushin makarar da Aamaaran tayi dan Allah Allah take taje office suyi maganar da Aminiyarta,
Da kallo hamida tabi mahaifiyar tata kafin ta wai bayan ta jin motsin mutum Aamaaran ce tashigo cike da sanyin nan nata idanuwanta sun d'an kumbura saboda kukan da tayi jiya da kuma rashin isashshen bacci,
Sosai nayi mamakin da Aunty hamida bata cemin komiba har na shige kitchen na dai lura da yanda take kallona sosai ni dai Aikin gabana na kama ina cikin yi naji fitar mama daga gidan zuwa office na cigaba da aikina ban fita a kitchen dinba sai da na kammala komai na jera a madaidaicin dinning table din dake parlourn bayan na gama ne na fito zan nufi dakina kawai muka had'a ido da Aunty RADIYA dake zaune kan daya daga cikin kujerun dake parlourn waya ce kare a kunanta da Alama wata take ni dai da sauri na fice na nufi d'akina dan inyi shirin tafiya school,
Da wani mayataccen kallo RADIYA tabi Aamaara sai da taga ficewarta sannan ta wani lashe lips d'in ta daga can bangaren da take wayan ne aketa "hello babe kinajina hello" heyy babe ina jinki kaya nagani shiyasa kika jini shiru yarinyar nance da nake fada miki tazo wucewa kadan ya rage bata tafi da rayuwa ta ba wlh, daga can bangaren tace uhm kedai zanso inga Aamaaran nan da kike kodawa haka ace duk haduwar sandra da kalpana Amman kice ta fisu... Katseta RADIYA tayi da cewa kinsan bana qarya ko soffy wlh tunda har na bibiyeta kinsan kam ta hadu qazama ce fa amma haka nan nake haquri ina bibiyar ta amman kuma yadda kikan san wata RIHANNA ko CARDI B haka yarinyar nan ke wulaqanta ni, kina sakar mata kud'i kuwa cewar soffy kenanda har ta gama hasaso kamannin Aamaara a idanuwanta, Amsa RADIYA ta bata da ban fara bata ba tukun Amma yau zan gwada dan ma jiya wancan kucakin mai gadin yayimin cikas ai da yanzu zance ya qare anjima ki shigo mana ki kwana sai mu aiwatar da shirin mu tare, da gaske aiko zanzo ta fada cikeda murna tareda kashe wayan,
Bin wayar tayi da kallo kafin ta tashi tayi hanyar dinning..
A wurin mama kuwa tana zuwa companyn da take aiko office din Aminiyarta ta nufa Amma bata nan waya ta daga ta kirata ashe bata zoba tana gida dan haka hanyar fita kawai ta nufa batareda tunanin daukar excuse ba dan tasan ko ta nema baza'a bata ba itakuma a halin yanzu tana da buqatar ganawa da Aminiyar tata,
Tana isa gidan tayi horn mai gadi ya bude mata gate ta kutsa kai cikin farfajiyar dake gidan ko parking din kirki batayiba ta fice tayi hanyar da zai sadaka da babban parlourn su tana shiga taga bata ga kowa ba dan haka direct d'akin matar gidan ta nufa tunda gidan ba baqonta ba ne tana zuwa ta tura qofar bedroom d'in ta shige
Wata 'yar lukutar matace zaune kan stool d'in mirror tana kwalliya baqace Amma ba sosai ba sanye take da wata hadaddiyar Grand super light purple sai zanenta black da golding jikin atamfar tayi kyau ba laifi kallon Aminiyar tata tayi sannan tace hajiya ta hajiyan nera, dariya mama tayi sanin kirarin da qawar tata kemata kenan ita kuma tace na gode da wannan kirarin hajiya binta falgore kune kud'i kabewar kan kabari baqin cikin mai taushe tare suka kwashe da dariya gaba d'ayansu sannan hajiya binta falgore ta ce " kince zamuyi magana ina jinki ko dayake bari in fara kawo maki ko juice ne da cake kici" a'a kinga ni ko breakfast ma banyi ba kuma bazan ba sai mun gama maganar nan da takawoni na koma kan abincin"toh ina saurarenki qawa,
Akan 'yar gidan Aysha ne dake wajena wato RUKAYYA Aamaara,
Toh hajiya miya faru kota samu mijine?
Wane irin miji kekuma ai kinfi kowa sanin yanda na tsani Aysha da' yarta yanzu idan ta samu miji ai sai zuciya ta ta buga tunda ban dauki fansa ba kan abunda akayimin, wlh bacin mahaifina yace bai yafemin ba ko bayan ransa idan ban riqe Aamaara ba toh da wlh sai dai tabi titi kokuma tabi bola kamar yanda uwarta tayi, toh naji yanzu gayamin maganar,
Ba wani abu bane kinji ta fara bata labarin qwayoyin da hamida ta nuna mata sannan ta dora da Aminiya so nike yarinyar Aysha ta zama gawurtacciyar KARUWA kuma MAI HULDA DA MIYAGUN KWAYOYI ta hakane kawai zan fara rage radadin abunda uwarta da kakar ta su kai min dan har Abada bazan tab'a manta rashin arziqin da sukai min ba..... ✍️ ✍️ ✍️
Toh fa tashin hankali kenan dame Wannan baiwar Allah zataji ga RADIYA ga kuma mama da hajiya BINTA FALGORE 🙆
KWANA BIYU KUNJI NI SHIRU Abubuwane suka min yawa Amma yanzu Alhmdllh..
💫QUNCI NA 😥😢
STORY and WRITTEN by sa'adatu Ibrahim babale ✨ 💕
<UNDER THE PENS OF SARATU IBRAHIM MAITAMANIN (Jaririyar writers) and SA'ADATU IBRAHIM BABALE (bakori girl 👧) as in identical twins >
KING 👑 AND QUEEN 👸 WRITING CHAMBER.
PAGE 1⃣3⃣
Kallonta sosai hajiya falore takeyi ganin yanda Aminiyar tata ta fusata dan gyaran murya tayi hmmm
"hajiya ta kwantar da hankalinki mana duk kinbi kin fusata kanki sai kace wadda Aka cemaki ga Ayshan can tana walwala da jin dad'i ki natsu mana muyi magana ta hankali"
Ajiyan zuciya mama ta sauke sannan tace qawas ina jinki ya za'ayi
Gyara zama hajiya falgore tayi ta kalli maman tace ki kwantar da hankalinki wlh na miki Alqawarin in dai ina doron duniya sai na tayaki daukar fansar Abinda Aysha tayi miki yanzu kinsan mi nake so dake? Da sauri ta girgiza kanta tana mai qosawa taji abinda qawar tata zata ce dan tasan bata maganar banza,
Abinda nake so dake shine daga yau ki fara janta a jikin ki ki dai na nuna mata tsangwama ki bari ta sake dake sosai sannan sai kizo in fad'i maki plan B Amma fa idan kinji baza ki iya daina tsangwamar ba akwai wani plan d'in
Shiru mama tayi tana tunanin shin anya zata iya danne zuciyar ta har ta nunama yarinyar Aysha qauna? Hmmm gaskiya bazan iyaba Aminiya Amma mizai hana tunda yarinyar tsoro na takeji sosai mizai hana in tursasa mata abinda nayi niyya ince mata idan batayi ba zan koreta daga gidana kinga tunda bata da inda tasani kaf garin nan dole tabi umarni na ko dan ta zauna a gidana ya kika gani,
Wowww gaskiya qawata kin kawo shawara mai kyau haka za'ai ma kawai yanzu akwai wani wanda zan fara had'a ta dashi wlh zai duk kud'in da ta samu kuma ki amshe kinga ko a nan kinyi riba biyu na farko zaki dauki fansar Aysha na biyu kuma kin samu hanyar samun kud'i ta fada tana kashe mata ido d'aya
Da sauri mama ta rungume hajiya falgore cikeda farin ciki "kai gaskiya qawata kinyi a rayuwa aini tun tuni wannan tunanin bai zomin ba da tuni sunan Aamaara ya shahara a duniyar karuwai,
Kin manta nice hajiya binta falgore Aminiya ki da kullum kanta baya kullewa sai ma sabon abubuwa da nike zaqulowa a duniyar nan qawasa mune fa duniya mune manyan matan da a yanzu ake jidasu a garinnan kinga kam bazan tab'a bari kaina ya kulle ba,
Toh nagode da wannan shawara yanzu tashi mu koma office dan ni ko permission ban dauka ba nayo nan,
****
Yau inason zuwa islamiya tunda banje boko ba dan haka da wuri nake son in gama aikina in tafi ga yunwa inaji saboda komi nawa ya qare gashi har na gama girki Aunty hamida na palour zaune babu halin na diba in tafi dashi dan haka na koma kitchen na dibi abincin na faraci a tsaitsaye ina cusawa na cinye nasha ruwa na goge bakina na fito har na wuce Aunty hamida batayi min magana ba nayi mamaki sosai dan ba haka take ba indai zan wuce tana nan toh sai ta sakani aiki kona wankin undies d'in ta ne amma yanzu abun mamaki ko kallona batayiba haka na wuce dakina ina tunanin ko dai bata da lafiya ne,
Sai da nagama shirina cikin uniform d'in islamiya ta da suke brown colour Anma sun koma farare tsabar kod'ewan da suka yi wuyan hijabin kuwa yasha d'inkin zare da Allura saboda azabar yagewan da yakeyi idan mama ta kamoni nayi laifi zata dakeni data kama sai ya yage dama kuma ya gama shan omo,
Ina cikin fesa dan turarena daya kusan qarewa ina tunanin zarah kwana biyu bana ganinta a gidannan ko ina taje ina cikin tunanin naji an turo qofar dakin da qarfi juyowa nayi muka had'a ido da Aunty RADIYA kallona tayi sosai sannan tace mama na kirana yanzunnan tana gama fada ta juya ta fice nima ajite turaren nayi nabi bayanta ina cewa a raina har ta dawo yau da wuri ita da bata dawowa sai gaf da magarib, haka dai na shiga ina Addu'an Allah yasa kada ta hanani zuwa islamiyan yau,
Kamar ko yaushe yauma hakimce take kan three seater radiya tayi pillow da cinyoyinta sai kace itace Autar yau babu Aunty hamida a zaman sai su biyu kawai da bowl din fruit a gabansu kan centre table, a hankali na qaraso na durqusa ina gaida maman ta amsa a shaqe kafin tacemin "yau ki haqura da zuwa islamiyan nan ki wuce bathroom dina akwai undies dina ki wanke min" kallonta nayi kamar zan fashe da kuka amma bata ko kalleni ba ta dora da fad'in waike baki da hankali baki san kije ki duba ba kigani miya kamata kiyi min sai dai kiyi ta yin abu kamar mai toshewar qwalwa dallah tashi ki wuce kafin nayi ball dake"
Da sauri na tashi ina danne kukan daya tahomin na biqin cikin hana ni zuwa islamiyan da tayi dan ni wankin bai bata min raiba kamar hanani zuwan kusan kwana nawa banjeba, sama na haye na shiga dakin maman ina shiga na wuce bathroom d'in naga kayan ba undies bane kadai hadda nighties d'in ta haka na fara wankin hankalina yana wurin tunanin ina zarah ta shige ne yanzu ma banganta ba.
Sai dab da mangariba na gama wankin na shanya su nan ciki na fito zaune na samu mama a dakin tana waya kallona tayi sannan tamin Alamar in tsaya in jirata jiranta nayi har ta gama,
Kallon Aamaara mama tayi sosai tanajin wani annashuwa na ratsa zuciyar ta wasu kaya dake gefenta ta dauka ta miqo mata "karbi wannan kayan kiyi wanka kisaka su sannan ki tabbatar da kinyi wanka sosai idan kinsaka kayan kizo nan ina jiranki"
Batareda dana tambayeta ba na karbi kayan na juya dan bani da damar tambayan ina fitowa harabar gidan na hangoshi zaune bisa kujeran roba da wani littafi da alama karatu yakeyi tun sheranjiya da mukayi magana ban sake ganinsa ba sai yanzu ina ganin zai dago kansa na wuce da sauri,,
A gurguje nayi wanka na fito nayi sallah sannan na dauko kayan da mama ta bani na bude su da kyau da sauri na wurgar da su ganin yana yin kayan wlh ko qara ganinsu bani son yi saboda muninsu tsallajesu nayi na janyo Ghana most go dina data gama yagewa da yagalgalewa bude ta nayi na dauko wasu kayan na saka sannan na fita kallon dakin mai gadi nayi na ganshi a rufe sai driver kawai zaune a inda na ganshi dazun Apartment din mama na nufa wata zuciyar na cemin ko ina ruwanki dashi da kika damu haka dan baki ganshi ba ina ruwana kuwa kawai dan yana da kirki ne shiyasa kawar da tunanin nayi sanda na tsinci kaina a gaban mama dake min wani irin kallo mai kamada na wulaqanci "ke ina kayan dana baki nace kisaka? Dago da idanuwa na nayi na dan kalleta sannan na mayar da kallona zuwa qasa ina maida hawayen da suke neman zubo min nace mata" mama baki ga kayan ba irin na 'yan iska ne kuma.... Kuma mi wlh ki kiyayeni ki tashi kije ki saka nabaki 5mnts inba haka ba wlh sai kinyi da nasani ta fada kamar zata kawomin duka da sauri na goce tare da miqewa na fice ina fashewa da kukan da niketa dannewa tun dazun,
Haka nan inaji ina gani nasako kayan da marabarsu da tsirara kadanne ina shigowa palourn da idanun Aunty radiya dake zaune gefen mama na fara cin karo ta qureni da kallon da ita kadai ce tasan ma'anar sa,
Mama ma kallon yarinyar take sosai dama haka jikinta yake da kyau wata doguwar gown ce irin mai shine shine dinnan silver colour sai siririn veil dinta black data yane kanta dashi ba qaramin kyau tayi ba duk da ba makeup ko digo a kamilalliyar fuskarta Amma sai taji tana kishinta dan ita a ganinta Aamaara taso tafi yaranta kyau dan haka dole ma rayuwar ta ta gurbata dan kada ma a samu matsala tayi wanna tunani a cikin ranta a fili kuma kallon Aamaara'n tayi tace jeki dakin zarah kiyi makeup sannan kisa turare akwai wani black takalmi da handbag ki dauko idan kin gama sai kizo nan kisameni,
Hanyar dakin zarahn na nufa ina son in tuno dalilin da zaisa mama tace insaka wannan kayan har ma dayin makeup bugu da qari kuma hadda sabon takalmi da sabuwar jaka ina ta tunanin dai har na shiga nayi abunda tace na fito haryanzu radiya na nan zaune ina fitowa ta qureni da ido ni kaina nasan nayi kyau sosai dana kalli kaina a mirror sai da nace ashe dai ina da kyau (lols☺️)
Kallon Aamaara dake tsaye riqe da jaka da takalmi tayi taga yanda tayi kyau jitake kamar kada ta bari su hadu da Alhaji SIDI KAN DAWA(Wanda hajiya binta falgore takeson ta had'a da Aamaara) Amma tuno irin tarin dukiyar da zata samu yasa tayi wani mugun smiling maida dubanta tayi gurin radiya dake qarema Aamaara kallo qasa qasa tana lashe baki kamar tsohuwar mayya "radiya dan bani guri inji mama kenan dake kallon radiyan da dan mamakin ganin yadda take rufe ido kamar maijin bacci tashi tayi batareda tace komi ba ta haye sama abunta,
Kina jina ki fita waje wani mutumi na nan cikin mota zaki karbar min saqo
Toh mama bari na dauko hijab dina a daki "hijab din mi ai a haka zakije wuce muje ma in raka ki ta fada tana kama hannunta tana janta har suka fito suka zo bakin gate sannan ta sake ta tace fita ga motar can ki sameshi"
A hankal nake tafiya ina kuka ina kare jikina da yake nunawa sosai a cikin gown din da nasa har na qarasa jikin motar gani nayi an bude min back seat duk a tunani na a nan saqon yake dan haka sai na zura kaina cikin uwar jikina na waje nufina kawai in dauka saqon ba sai na shiga motan ba... Ji kawai nayi an fizgoni tareda rufe qofar ihu na qwala da qarfi ina Ambaton innalillahi wa inna ilaihiraji'un juyowa nayi inga waye yakeson sace ni ga mamakina naga macece sanye cikin wasu baqaqen kaya tana da qaqqarfan jiki sannan ta rufe rabin face dinta da mask,
Baiwar Allah minayi maki da zaki sace ni dan Allah.. Ban qarasa ba naga ta dauko bindigar dake gefenta wadda ni ban ma lura da itaba tsabar rudewan da nayi "kina sake magana sai na tarwatsa qwalwarki" ta fad'i da wata qatuwar murya shirun nayi kamar yanda tace Amma ban daina hawaye ba,
Sai da muka kusa barin gari sannan naga mun shiga wata kwana sai gamu gaban wani d'an madaidaicin gida mai gadi ya bude gate aka shige, muna shiga wannan matar ta fita ta zagayo inda nike ta bude ta fiti dani a hankali take tafiya dani har muka shiga dan madaidaicin palourn gidan nidai Addu'a nake tayi a raina ina tunanin mi na aikata wa mama da zata siyar dani.. Tunani ya katse sanda nayi arba da wani shirgegen mutum zaune kan kujera babu kaya jikinsa sai 3quater da singlet
"sir ga yarinyar nan ina fata tayi maka kalleta da kyau"
Hhhh yayi dariya sannan yace tayimin gaskiya ta falgore ta iya zabe zo nan babyna ya fada yana mai tashi tsaye da qyar saboda azaban qibar sa
Hankali na naji yayi mummunan tashin da bai tab'a yiba innalillahi sai yanzu na gane dalilin bani kayan nan da mama tayi shin minayi mata haka da zafi da ta zaba min wannan rayuwar? Ban ankara ba naji an riqo ni kawai naga wannan mutuminne da sauri na qwace nayi hanyar fita Amma kafin nakai har wannan matar takai fita tayi ta rufe qofar daga can waje ihun neman agaji na fara "hhh yarinya dama kiyi shiru dan babu wanda zai jiki ko an jikima babu wanda zaizo taimakon ki"
Wani floor vase ta dauko tace wlh kana zuwa saina kasheka ta fada tana qara fashewa da kukan baqin ciki
Yana zuwa ta daga zata buga mai ya riqe hannunta ya murdeshi baya ya amashe sannan ya fara qoqarin had'a jikinsa da nata wani irin ihu ta qarayi tana cewa dan Allah kayi haquri ka qyaleni wlh ni ma rainiya ce kaji qan maraicina dan Allah babana...ina ai Alh SIDI KAN DAWA baya jin zai iya qyaleta dan yarinyar ta tafi da imaninsa rigar jikinta ya fara qoqarin yagawa har yaci nasarar.... ✍️ ✍️
💫💫
💫QUNCI NA😥😢
Story and written by Sa'adatu Ibrahim babale (bakori girl 👧)
(Under the pens of saratu Ibrahim maitamanin and sa'adatu Ibrahim babale)
K
ING 👑 AND QUEEN 👸 WRITING CHAMBER.
✨Page 1⃣4⃣ ✨
....qaran harbin bindiga daya karade gidan shine ya dakatar da Alh SIDI KANDAWA daga qoqarin yage rigar jikin Amaara wadda ita tuni ta dade da fita a hayyacinta tsabar tashin hankali, jin Abun bana wasa bane yasa baisan lokacin da ya wurgar da ita ba ta fada kan flower vase din da ya fashe a wurin take kuwa kwalban ya cake ta a goshinta shikuma Alh hanyar wani corridor yanufa da niyyar ya dakko nasa bindigar kafin yakai yaji wani qarar harbin da aka ma qofar palourn wanda yasa gaba daya qofar da dama ba wani qwari ne da itaba ta fado cikin palourn wanda yayi harbinne ya shigo cikin wasu baqaqen kaya da bulletproof jacket a saman kayan jikinsa sai mask daya sanya a face dinsa shiyasa ba'a ganin fuskar daga bayansa wasu suka shigo su kusan biyar suma riqe da bindiga sannan irin shigarsu daya da na gaban wanda ya fara shigowa inda Alhaji yake tsaye ya daga hannuwansa sama Alamun surrender suka nufa suna zuwa basuyi wata wata ba suka bigeshi ya fad'i na farkon wanda shine kamar ya fisu fusatasa ya fara dukanshi ba qaqqautawa har saida yaga ya daina motsi sannan yasa sauran yaran suka daukesa sukayi waje dashi inda suka ajiye sauran yaran gidan da masu gadi shikuma ogan yayi Aaamara take kwance a sume bata numfashi....
****
PITIÈ SALPÊTRIÈRE HOSPITAL PARIS,FRANCE.
Dakin da naga ansa Salle de théâtre (theatre room)jan hasken dake cikin dakin ne ya dauke ya koma green zuwa can kuma k'ofar ta bude wani black doctor ne ya fara fitowa da alama shi babban doctor ne a hospital din bayansa sauran turawan doctors din suka biyo tareda nurses din,
Tunda suka fito ya tsura masu Idanuwansa masu tsananin haske da kwarjini sanye yake cikin long sleeve da trouser masu hade da jacket na fendi black colour sai sandal shima fendi ne black jacket din ajiye gefensa hannunsa kuma riqe da waya amma idanunsa da hankalinsa duka suna kan DR AMMAR dake qarasowa inda yake yana zuwa ya bashi hannu sukayi shaking fuskarsa da d'an fara'a yace " ka kwantar da hankalinka sir insha Allah nan da 4to6 hours zata iya farkawa kumu muna saran aikin da akayi mata yazamana yayi dai dai insha Allah"
A hankali ya bude bude bakinsa yace Alhamdulillah wanda bacin doctor Ammar yasan halinsa ciki da bai to ba lallai ya gane abinda yace ba juyawa dr Ammar yayi zuwa office dinsa,
Rasa wama zai kira yayi sai kawai yayi dialing numbern da aka rubuta MAMYNA💖 yayi wayan na fara ringing aka yi picking daga can bangaren muryar wata matashiyar budurwa tayi magana "hello ai Assalamu Alaikum yaya mamyn bata nan taje bama Alhaji Maganinsa" ok kawai yace ya kashe wayan sai kuma kawai yatashi ya nufi hanyar fita daga wurin gaba daya.
****
Zaune take a cikin palourn ta sabanin kullum da take hakimcewa kan kujera yau a qasa take zaune ta tasa plate din Abincin da hamida ta kawomata tun dazu wanda shi Abincin ma tuni ya dade dayin sanyi tayi wujiga wujiga ta dan rame babu wani gayu a tattare da ita kamar ba mama ba ga wani uban tagumin da ta rafka sai kace wanda akace RADIYA ta mutu ko hamida ko. Zarah (😁 lols) hawaye ne ke zarya akan dan lututin kumatunta mai kama da Alkubus din dayaji bugu ya tashi sosai(😛) itama haka fuskanta ya koma saboda tsabar kukan da yau kusan sati biyu kenan tana ai kin yinsa
Hamida ce da tun dazun take tsaye bakin qofar kitchen tsaye wanda itama ta rame sosai saboda Aikin da takeyi yanzu a gidan tunda dai meyin batayi zarah kuma babansu ya dauketa daga gidan RADIYA kuwa ita ba'a sakata ma a zancen dan yanzu bata zama a gidan ma sosai kullum tana yawon bin qawayen banza basu wannan club din basu wancan dan ita tunda taga halin da mama take ciki itama ta kama kanta,
K'arasowa inda mama take hamidan tayi cikeda rashin kuzari tace "mama dan Allah kiyi haquri ki cire damuwan komi a ranki komai zai wuce.. Zai wuce fa kika ce hamida anya kuwa kina da hankali? Ko ko bakiji barazanar da mahaifinku yamin ba kafin ya bar garinnan ta fada cikin kuka wanda muryanta ma baya fita da kyau saboda tsabar kukan da takeyi a kwanakin "hmmm hamida ta sauke wata nannauyar Ajiyan zuciya ta cigaba da ba mama baki akan tayi haquri " hamida ni yanzu babban tashin hankalina shine sanin inda AAMARA take gashi an kama ta falgore da Alhaji sidi ballantana insa ta inda zan fara nemanta gashi babanku wata d'aya yabani naci 2weeks saura 2weeks yanzu ya zanyi sannan ga RADIYA data zama abunda ta zama itama yanzu rabonta da gidan nan tun shekaran jiya abu ya hademin goma da ishirin gashi babu Aminiya ta wayyo ni Allah na ta qarashe fade tana kukanta da bashi da Amfani"
Kiyi haquri mama dan Allah abinda hamida take cewa kenan kafin kuma ta miqe tayi sama zuwa dakinta dan ita kam jitake kukan maman na bata haushi ai har shawara ta bata amma taqi ji taqi gani.
****
Abinda yafaru bayan shigowar mutanen da tuni dama suke neman ALH SIDI KAN DAWA shine bayan sun kamashi da sauran yaran gidan mata da maza cike kuwa harda RABI HAJIYA FALGORE (na canza sunan ta saboda wasu dalilai na) hadda ita suka kama wanda su AAMARA basu jima da ahiga gidan ba itama ta shigo tazo yin nata hidimarne,
Bayan an gama kwashe su Alhajin RIDWAN wanda dashi akayi operation dinne yayi kan AAMARA wadda bata ko motsi ga uban jinin dake zubowa daga kanta da alama taji ciwone a gurin daukarta kawai yayi yai waje da ita inda suka ajiye motocinsu da suka zo dasu, kallonsa duk abokan Aikin nasa sukeyo ganin shi rungume da yarinya ga jinin dake zubowa a kanta wanda bacin baqaqen kaya ne ajikinsa to babu abinda zai hana a ga jinin daya daga cikinsu ne daya kasa yin shiru yace GAGO ina kuma zaka da ita nan baga hilux dinda aka sa sauran can ba? Bai juyo ya kalleshi ba ballanta yasaran samun Amsa illa ma qarasa wa gaban motar da yayi yasa hannu daya ya bude back seat yasata da dan hanzari ya rufe ya zagaya driver seat ya shige tareda yima motar key yaci da gudu sauran ma ganin ya fita yasa suma suka shishshiga mota suka fice daga gidan suka bar wasu da zasuyi gadin gidan,
Babban asibitin dake garin ya nufa yana zuwa basu tsaya komi ba suka amshe ta emergency bayan dogon bincikensu sun gano sanadiyar buguwar da kanta yayi a qasa ta samu matsala da kan nata dan haka a sharwarce kawai idan da hali a fita da ita qasar France suna da babban likitan qwalwa a can babu wani jan lokaci aka gama komi hatta da Aaamaran da bata san waye ke a kanta ba an gama mata komi na marasa lafiya kuma aka hadasu da babban likitan wato dr Ammar,
Sai da komi ya kammala sannan suka tafi Abuja dayake ta can jirgin su zai tashi hospital akayi da ita shikuma gidansa dake maitama phase 1 ya nufa gidane babba wanda idan akace maka mallakin wannan mai gadinne ko sama da qasa zata hade bazaka yadda ba bayan drivern daya dakkosa daga Airport yayi parking da sauri wasu security majiya qaqqarfan jiki sukazo suka bude masa ya fito cikeda sassarfa ya nufi hanyar wani part da wanda daka shigo gidan zakaga yafi ko ina kyau yana zuwa yasa security din kofar ta bude ya shige woww masha Allah dan kuwa wani qayataccen palour ne irin na sarakunan larabawa nan da masu kudi royarls ne a palourn wanda suka amsa sunansu royarls wanda masu ruwan zuma komi na palourn kalar ruwan zuma ne amma mai haske wanda ya haska palourn yayi kamar na prince hammad dan sarkin dubai(😁 lol) sama ya nufa direct inda nan ma wani palourn ne sanna sai bedrooms guda ukku na tsakiyar ya nufa nan ma sai da yasa security sannan qofan ya bude yashige qayataccen bedroom din da shina yagaji da haduwa bayan yayi wanka ya kimtsa ya fito palour ya iske tuni cook dinsa ya shirya masa table dan cin abinci Amma shi yanzu ma bata wannan yake ba ta yanda zai fadawa iyayensa abunda ke faruwa yake zama yayi kan daya daga cikin kujerun wayansa a hannunshi yana kira saida ta kusan tsinkewa kafin aka daga cikin nutsuwa da kamewa irin tashi yace "Assalamu Alaikum mamyna" Amin wa Alaika salam habibi muryar wata kamilalliyar mata ta amsa"kun wuni lafiya ya kowa na gidan ya jikin Alhaji? Kowa lafiya lau RIDWANUL JANNAH ya aikin har yanzu baku gama ba yaushe zaka dawo gidane wai? Dan gajeren murmushi yayi jin sunan da mamyn tashi ta kirashi da kuma yanda ta dagw tana jeromai tambayoyi sai kace wata Alqali"na gama mamy kuma zan dawo dan ma wasu 'yan matsaloli suka riqine da tuni na dawo ai"
Subhanlallahi wace irin matsala kuma Allah yasa dai lafiya dama naji muryanka wani iri " hmm Mamy daddy na nan ina son zanyi magana daku ku duka" Jitai gabanta ya dan fadi Allah yasa dai ba wani abune ya samu yaron nataba amsa tabashi da eh gashi nan yana jinka ta fada tana kallon daddyn da shima zuciyarsa ke tsinkewa akan dannasa cikin kamewar da RIDWAN yayi gado gunsa yace ina jinka habibi mike faruwa"
Cike da rashin qarfin jiki ya basu taqai taccen tarihin Aaamara wanda yasani da kuma matsalar da tasamu a kanta amma ya boye masu a inda yaganta (wato tareda Alh sidi kandawa) wannan idan Allah yayi ta farfado ta bashi labari ko da kuwa da tsiye ne (toh fa🤔),
Ajiyar zuciya suka sauke dukansu cikeda jimami dan ita mamy hadda hawayenta na tausayin Aaamara dan kuwa lallai tana cikin QUNCIn rayuwa ace baka san su waye suka yi sana diyar zuwanka duniya ba kuma ba mutuwa suka yi ba sannan kuma Allah ya jarabceta da Azzalumar qanwar uwa wannan wani irin zumince haka daddy ne yadan bata baki kafin yaceda RIDWAN "lallai ka cika dan Halak Allah yayi maka Albarka ya kuma tsare gabanka da bayanka Allah ya baka mata ta gari"
Amin dad nagode Allah ya qara girma ya amsa cike da fara'ar da inba da iyayen nasaba baka ganinta a kamilalliyar fuskarsa "toh yanzu gashi ka samin matar tawa kuka daddy ya fada cikeda tsokana wanda sai da yaba mamy dariya itama Albarka da Addu'oi ta yimasa kafin tace"zan turo maka HANAN ta zo kodan saboda gudun lalura tunda ba lallai bane su masu asibitin su rinqa yimata komi ba bayan ta warke koya kagani daddy shima daddyn ya yadda da shawarar mamy koba komi ai Aaamara din ba muharramarsa bace ba"
Toh shikenan mamy yanda kika ce mu gobe zamu tafi "toh Amma inajin HANAN bata taba zuwa France ba dan haka zata dan dauki time kafin tazo Amma insha Allah zamuyi kokari tazo da wuri" toh nagode muku dukka Allah ya qara girma" da amin suka Amsa kafin kuma suka cigaba da wafa firar data shefesu,
****
WASHE GARI,
Washegarin ranar qarfe 9:45 na agogon Nigeria da Niger Cameron da chad jirginsu ya daga zuwa qasar faransa.....
Toh sai dai muce a sauka lafiya RIDWAN & AAAMARA.. ✍️✍️✍️
BAKORI GIRL 👧
💫 QUNCI NA 😥😢
Story and written by Sa'adatu Ibrahim babale (bakori girl 👧)
(Under the pens of saratu Ibrahim maitamanin and sa'adatu Ibrahim babale✨ )
KING 👑 AND QUEEN 👸 WRITING CHAMBER.
Hasbiyallahu la ila ha illa huwa Alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul Arashil Azeem 🙏
PAGE 1⃣5⃣
✨✨✨✨
Back to story...
Bayan Awa shida (6)
A hankali take bude idanuwanta da sukayi mata nauyi sosai harta budesu fesss
Akan matashiyar budurwa fara tass sanye da blue jeans da red bady hug da kuma jibgegiyar rigar sanyi a sama wadda ta kai mata har k'asan guiwarta farace sosai kuma kyakkyawa ta ajin qarshe hannunta riqe da waya samfurin iPhone 13promax da farko na tsorata dan sai naga kamar RADIA Amma dana kalleta sosai sai naga ba ita bace gizo ne kawai idanuna suke min kwallan tausayin kaina ne ya zubo min ina tunanin toh yanzu kuma ina suka kawoni ni RUQAYYA shin wai mina aikatama mamane da zata hadani da wa'innan miyagun mutanen?
Motsin da Aaamara tayi shine ya maido hankalin HANAN dake tsaye wadda zuwanta asibitin kenan kallon Aaamaran takeyi sosai ganin hawaye na bin gefen idonta yana zuba kan pillown da take kwance da sauri ta juya zuwa waje kiran dr dan ita a tunaninta ko an samu matsalane tunda taga tana hawaye,
Da kallo na bita harta fice daga dakin idanuwana na kan qofar lokacin da Dr Ammar ya shigo d'akin bayansa kuma wata nurse ce sai HANAN itama qarasawa bakin gadon yayi ya kashe na'urorin da aka sanya mata nurse din kuma na cire na jikina sai da suka gama sannan likitan ya fara min tamboyoyi cikin harshen hausa nima cikin mamaki nake Amsa shi sai da ya tabbatar komi normal sannan yayi rubuce rubucen sa kafin ya dago ya kalli HANAN wandda har yanzu take a tsaye kamar ta hadiyi tabarya(😁 lols)
Miss GAGO ki sameni a office zanyi magana dake "okay doctor" ta fada calmly kamar yanda yake dabi'arta,
Nidai ina kwance ina ganin ikon Allah dan sai yanzu na san a asibiti nake, nurse din da suka shigo da dr ne ta shiga bathroom din dake cikin dakin zuwa can kuma ta fito magana take min cikin harshen France Amma ni ban masan abinda take cewa ba danni ko turanci ma ba ji nake sosai ba bare wani fransanci haka nan ta gaji da magana ta kamani zuwa cikin bathroom din wanda kamar ba na asibiti ba tsabar yanda yake da kyau fitowatayi bayan ta nuna min ruwan data tara cikin bathtub mai zafi sosai,
Wankan nayi da ruwan da yamin dadi sosai dan nagasa jikina da nakeji kamar ba nawa ba jina nake fayau kamar zan fad'i, yanzu kan wata 'yar kujera naga hanan tana ganin na fito ta taso tazo ta kamani tana min sannu nikuma ina amsawa da kaina, bayan na zauna ta miqo min wani lotion na shafa sannan ta dakko wata' yar jaka ta fiddo kayan ciki ta bani ita kuma ta fice daga d'akin da waya kare a kunnenta,
Saida na gama shiryawa cikin free gown din data bani sannnan ta sake shigowa tea ta hadamin mai zafi ta bani da qyar nasha rabin tea din dan bakina bana jin dadin sa da taga nasha da yawane ta fara bani magungunan da dr ya bata sai da taga duk na shanye sannan tace min "sannu Allah ya qara lafiya yayanmu yaje ya dawo nasan anjima zai dawo ta fadi haka tana kallona"
bance komi ba illa kafetan da nayi da ido to waye take magana wane yayan nasu kuma
"waye yayanku?"
na tambayeta cikin rashin sani, itama kallona tayi da dan mamaki sai kuma tace"wanda ya kawoki nan da bakida lafiya"
"toh minene ya faru dani wancan ranan na tambayi kaina(bakida mai baki Amsa tunda itama wannan d'in bata sani ba) inji wani bangare na zuciya ta daya bani Amsa
Dukan mu munyi shiru sai zuwacan ta jeho min tambayar "ya sunanki?"
"RUQAYYA"masha Allah RUQAYYA" "nikuma HANAN" murmushi nayi jin sunan nata na sake maimaitawa a raina sunan yamin dad'i nima saida aka jima sannan nace mata "bada RUQAYYA ake kirana ba AAMARA ake cemin a gida" wowww AAMARA sunanki duka akwai dad'i akwai wata friend dina 'yar Pakistan ce sunanta kenan hala kema kina da relatives a Pakistan dan kina kama dasu hanan ta fada da dan dariya a fuskanta (ita hanan tsakaninta da Allah Aamara tayi mata kama da Pakistanis ne),
shiru Aamara tayi zuwa can kuma ta girgiza kai tana dan gajeran murmushi dan hanan ta bata dariya ina ita ina Pakistani?
Bata qara magana ba tayi shiru ganin tayi shiru ne yasa hanan ta fara bata labarin sanda take school a America sosai Aamara ta saki jinta tana jin dad'in labarin sosai
****
zaune yake kan daya daga cikin sofas guda biyu dake dakin ya miqar da kafarsa kan sofa din da pillow kan cinyarsa sai system din Apple daya dora kan pillown aiki yake sosai Amma tunaninsa na wani wurin daban tunani yake kota farka Amma yasan da ta farka dr Ammar zai kirashi ya fada mai HANAN nacan Amma itama ai hanan bawata babba bace dama yasani UMMY ya kira da ita da kanta zata zo ba aike ba yayi nisa cikin tunani ne yaji wayarsa na neman agaji da qyar ya iya motsawa ya dauko ta HANAN ce ke kira,
A nutse yayi picking tare da kaiwa kunnensa "Sai da tafara sauke ajiyar zuciya dan batayi tsammanin zai dauka ba ganin harta kusa tsinkewa wayar, Assalamu Alaikum yah RID ina wuni" saida ya Amsa mata sallamar sannan ya amsa gaisuwarta da tambayar yanda suke "lafiya lau ta farka" ta fada kamar bata son yaji,da masha Allah Alhamdulillah ya take normal ko Amma dr bai kirani ba
Kila aiki ne ya masa yawa ta fada ma yayan nata haka
da okay ya amsa mata kafin ya dora da fad'in" ki kula da ita sosai idan tana buqatar Abu kiyimata kafin na shigo anjima "
toh tace masa tana danne dariyar data taso mata (wai ta kula da ita lallai ma) ta fada cikin ranta tare da kashe wayan.
Kiran hanan na yankewa sai ga wani kiran yana shigo mai ganin wanda yake kiran ne sai da yaja qaramin tsaki kafin ya daga yakai kunne yayi shiru beyi magana ba sai wancan daya gaji ya tanka"uhhmm su gago manya ai nayi tunanin yauma bazaka daga kiran nawa ba saboda ka sace yarinya ka tafi da ita shin wai ina ma ka kaita ne?
Mitsss Abbas idan baka da abinyi ni inada shi dan Allah kuma maganar yarinya ba abinda ya shafeka bane balle ka shiga mitsss ya kashe wayan gaba daya tareda wurgi da ita kan kujeran dayake zaune system dinma tureta gefe yayi ya tashi dan ya gaji da aikin shi yanzu ma ji yake kamar yayi tsalle ya ganshi a Cikin dakin da take Amma dai ya danne ma zuciyarsa.
😁
****
Tana kwance a kan gadon HANAN na zaune kan kujera kusa da gadon tun dazun take lallashinta akan ta tashi taci abincin da tayi order tundazun wanda ba mai nauyi ba ne ba amma taqi tashi saima cema hanan din datai wai bata iya cin komi
"Aunt HANAN wlh banda appetite bazan iya ciba qila anjima idan na qara jin sauki zanci kinji"
Amma ko fruit ne kisha kinji qanwata ta fada cikin murayanta mai sanyi kuma cikin lallashi
Sai naji wani ban barakwai wai yau nice ake lallabawa akan cin abinci?nida wata ran ma ko wanda zanci bana samu Allah sarki rayuwa sai naji hawaye masu dumi sun silalomin,
Da sauri hanan ta tashi daga kan kujeran ta koma gefen gadon da Aaamara take zaune "eyya Allah sarki baby girl ashe haka kike da shagwaba bansani ba"hanan ta fadi haka cikin barkwanci"
dan murmusawa nima nayi cikin raina nace Aunty hanan kenan ni ai da nasamu wanda zan ma shagwabar ma da naji dadin duniyar nan ina 'YAR AIKI da shagwaba shin to ma wazan mawa(ZARAH mana' yar uwarki) wata zuciyar ta ban Amsa "toh ai kuma kanwata ce"
Wake nan? Hanan ta tambayi Aaamara da tayi maganarta ta qarshe a fili batareda ta sani ba
Uhmm ba kowa wani tunani nakeyi kum...magana ta katse lokacinda naji an turo qofar dakin an shigo da sallama ciki ciki sai kamshin dior savage da ya cika dakin sosai,
Tsurama kofar shigowan ido nayi zuciyata na bugu da qarfi dan wannan qamshin kam ban manta sa ba,
Sosai zuciyar ta ta kusan fitowa daga qirjinta lokacin da mukayi ido hudu da RIDWAN mai gadin gidanmu sannan dan KIDNAPPING....
toh fa🤔 ga RUQAYYA ga kidnapper 😁😁
Bakori girl 👧ce✍️✍️✍️
Comments and share please.
https://chat.whatsapp.com/BVqOy4UJveaDh5ZhJOEW5T
💫QUNCI NA😥😢
Story and written by
Sa'adatu Ibrahim babale
(bakori girl 👧)
(Under the pens of saratu Ibrahim maitamanin and sa'adatu Ibrahim babale)
"LA HAULA WALA QUWATA ILLA BILLA"
PAGE1⃣6⃣
Sosai naji tsoro da tunanin anya ba gizo bane ba Amma kuma dana dan mintsini kaina a hankali sai naji zafi sai na tabbatar da gaske ne ba mafarki ba,
A nutse yake takowa cikin dakin duk takunsa d'aya sai zuciyar AAMARA ta buga harya qaraso bakin gadon yaja kujeran da hanan take zaune d'azun kafin ta koma bakin gado baya yad'an ja kafin ya zauna yana kallonta k'asa k'asa ganin yanda duk tabi ta firgice kamar taga wani Aljani
Gaidashi hanan tayi ya amsa mata sannan ya kalli inda AAAMARA take
"ya jikin" ya tambayeta idanuwansa akanta,
A d'an daburce ta amsa masa "da sauqi Alhamdulillah"
Shiru yayi bai sake magana ba sai ma kallon inda hanan take da ya sake yi
" kunyi magana da dr Ammar din"?
"Eh yaya yace idan kazo kaje yana son yin magana da kai"
Tashi yayi dan yaje ya sami dr Ammar din yaji ya yanayin jikin nata idan da buk'atar wani babba yazo sai ya kira ummy yasan zata zo
Bayan fitarsa shiru mukayi ita hanan chatting takeyi a wayanta AAAMARA kam tunanin take ta yanda RIDWAN ya daukota ya kawota nan asibitin dan daga gani tasan ba'a garinsu bane haka nan kuma taga duk yawanci nurses din Asibitin turawa ne(dan ita bata san ba'a Nigeria take ba haryanzu)
Amma bari yazo gaskiya ni gara ya maidani gida duk wahalar da zansha wurin mama zan jure toh shekara nawa ma ina jurewan?
Ai wlh da in zauna da b'arawo toh gara in koma cikin bauta,yunwa,da wahala duk su taru suyi ajalina sai kuma wata zuciyar tace (toh yaal zakiyi da RADIYA sannan ita kanta mama karki manta sharrin data ke binki dashi)
Hakanan zan koma inyi hak'uri
Na bawa kaina amsa.
****
Mama dai jiki yayi gaba dan yanzu sosai take ciwon na gaske ta wani kumbura saboda jininta da ya hau gashi hameeda tayi juyin duniya akan su tafi asibiti Amma tak'i yadda sai dai likita yazo har gida yana dubata duk bayan kwana biyu,
A hankali take fitowa daga bathroom dinta tayo wankan da sai da hameeda ta lallabata sannan tayi shi gaba daya har yanzu ta kasa kwantar da hankalinta ita yanzu babban tashin hankalinta shine kwata kwata babansu hameeda ya daina daukar wayan hameedan ma dan ita dama ba'a sakota a lissafi saboda ita ya daina daukar wayan hameeda kwata kwata,
Bakin gado ta zauna ta zabga taguminta daya zame mata d'an uwa a yanzu sosai ta rame ga damuwar rashin zaman radiya dan tun washe garin da abunnan ya faru ta daina zaman gidan kwata kwata
Hameeda ce ta shigo d'akin hannun ta rik'e da plate gaban maman ta k'araso tana mata sannu
Amsawa tayi itama cike da tausayin hameedan a kwanakinnan komi na gidan nan itace ke lallabawa tana yi duk da bata iyaba haka nan take k'ok'artawa tayi
"mama ga abincin ki samu kici ko kad'an ne sai kisha magani" hameeda ta fada tana mik'a mata plate din noodles wanda sai da tasha wuya kafin ta iya dafawa tunda koyo takeyi
Amsar plate d'in mama tayi ta kalli noodles din sosai da lokacin da AAMAARA take nan ne da wallahi bazata ko kalli irin wannan jagolgwalon ba amma yanzu haka nan zata ci kodan tasha magani,
Tana cikin cin abincinne suka ji an turo k'ofar d'akin tareda sallama wata doguwar matace fara sosai wanda ta sirka da d'an mai sosai take cikin kwalliya ta kece raini,
Kallon matar data shigo take cikin mamakin ganin k'awar tata da kusan shekara biyu kenan rabonta da ita da sauri ta ture plate d'in gaban ta tayi tare da tashi kamar ba mara lafiya ba ta nufi k'awar tata
"hajiya balaraba"! mama ta fad'a cikin tsananin murna da mamaki,
Sosai hajiya balaraba ke kallon mama cikeda mamakin yanda ta rame
" k'awata mike damunki haka duk kinbi kin tsofe kin rame"?
Da sauri tayi kicin kicin da fuska"haba balaraba ke kinsan yanda na tsani ace na rame ballanta na kuma ace na tsufa cin mutunci kikazo yiminne har gida?kin san kuwa cikin tashin hanakalin da nake ciki ne wallahi da kinsani baza ki cemin haka ba"
"Allah ya baki hak'uri hajiyata nasan damuwarki bata wuce na kama ta falgore da akayi ba toh ki kwantar da hankalinki tunda gani na dawo zanyi yadda nayi aka fiddota"
Hmmm mama ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya tana kallon hajiya balaraba kafin ta kalli hameeda da sauri hameedan ta tashi tafita bayan ta gayar da hajiya balaraba kallon k'awar tata mama tayi ta fara fad'a mata damuwarta
"ban da wannan ina cikin wadda tafi wannan tashin hankali nan fa mama taba hajiya balaraba labarin yanda suka tura AAMAARA wajen Alh sidi Kandawa wanda jami'an tsaro suka kamashi tare da hajiya falgore ita kuma AAMAARA ba'a ganta ba kuma bata hannun jami'an tsaron dakuma barazanar korar ta da baban hameeda yace zaiyi indai bata nemo AAMAARA ba"
Hajiya balaraba ta tausayawa k'awar tata sosai dan kuwa inda baban hameeda ya kori mama toh wallahi sai ta shiga cikin QUNCI na sosai
"ki kwantar da hankalinki HAJIYA indai dan wannan ne toh zan taimaka miki muje wajen wani tsohon malami na kafin in koma saudia shine yake min aiki ya iya aikinsa kamar yankan wuk'a haka yake kinga sai muje a toshe bakin baban hameeda ya bar maganar korar nan dan ita ke tadamin hankali nima"
"toh balaraba amma fa wallahi harda ita AAMAARAn nake son ayi ma kiranye dan har yanzu zuciyata bata huce akan abinda uwarta tayi min ba kuma kinsan a kanta nake son hucewa gashi kuma ta gudu ni ban huce d'in ba"
"Kedai ki kwantar da hanlinki uwarta ma ta biyu ballantana ita zata dawo ne idan ta dawo azabar da zaki rink'a yimata dan Allah tafi wadda kikai mata a baya dan ni na fiki tsanar A'ISHA wlh"
"Nagode balaraba Allah ya barmu tare"
inji mama da tuni ciwo ya tafi jini kuma ya koma yayi kwance tunda za'a wurin da za'a biya mata buk'atarta (wa iyazubillah Allah kasa mufi k'arfin zuciyar mu Ameen)
Nan fa su mama aka hau shirin tafiyar da zasuyi gobe tunda asubahi
(Sai muce a sauka lafiya hajiya mama)
****
Yana gama jin bayanin da dr Ammar din yayi masa fitowa yayi daga office d'in yasamu wuri inda aka tanada dan zaman masu zuwa dubiya nan ya zauna ya zaro wayarsa daga aljihu tunani ya shigayi shin wa zai kira MAMY ko UMMY?
Mamy ya fara kira Amma sai yaji line busy da alama waya takeyi ko kuma kiranta ake maida akalar kiran yayi kan ummy duk da ba yanzun yake son zuwanta ba Amma kuma dole ne ya kiratan ringing ukku tayi aka d'auka "Assalamu Alaikum ummy barka da yamma" ya fad'a cikin murna da farin ciki,
"Amin wa Alaika salam habeebi lafiya lau ya abubwa?"dagacan b'angaren muryar wata kamilallar mata ya amsa mashi
"Alhamdulillah ummyna daman wata 'yar Alfarma nake nema idan babu damuwa"
"toh fa katab'a jin alfarma tsakanin uwa da d'an ta?ai ita uwa ko yaushe cikin neman farin cikin yaranta take dan haka inajin ka d'an Albarka fad'amin abunda ke damunka"
Sosai yaji k'aunarta da tausayin ta na k'ara cikashi tunowar da yayi ita d'in har yanzu bata da d'an da zata nuna tace ita ta haifeshi da cikinta sai dai na 'yan uwa da abokan arziqi barin ma shi datake ganin kamar ita ce ta haifeshi
"dama ba wani babban issue bane ummy kawai dai wata baiwar Allah ce bata da lafiya toh batada dangi kuma tana asibiti a nan France toh hanan ce kawai a tareda ita mamy ta turo ta kuma hanan bazata iya jinyarta ba dan sai nan da 2 weeks zasu sallameta shine nake neman Alfarmar ko Abba zai barki kizo akwai buk'atar babba a kusa ni inada tafiya ne gobe ko jibi insha Allah"
"Allah sarki na tausaya mata rashin dangi babban QUNCI ne insha Allah zanzo kasan Abban ka bazai hanani zuwa ba Amma sai na nemi visa maybe na d'an dade tunda banta b'a shigowa france ba"
"Toh ummy nagode Allah ya k'ara girma da Arziqi da shekaru masu Albarka"
Ameen Ameen habeebi sai ka jini ta fad'a tare da kashe wayan
Bin wayar yayi da kallo yanajin wani dad'i akan zuwanta dan Allah kad'ai yasan irin son da yakema matarcan,
Tashi yayi ya nufi d'akin da AAMAARA take hanan bata nan tana bathroom sai patient d'in dake kwance tana bacci saboda Allurar da dr yazo yayi mata
Sosai yake k'are mata kallo ganin yanda ta koma kamar ba jinya takeyi ba tayi haske ta k'ara kyau gown d'in jikinta ta k'aramata wani irin kyau kamar ba itaba mai yawo da kod'add'iyar atamfa shi baima tab'a lura da tanada haske haka ba sai yau ko dai ciwonne yasatayin haske? motsi yaji a bayansa yana juyowa sukayi ido hud'u da hanan wadda tund'azun ta fito tana tsaye amma yayan nata baisan tana wurin ba
Saurin d'aure fuska yayi kamar bai tab'a dariya ba sannan ya juya ya fice daga d'akin,
Hanan kam duqewa tayi a wurin tana dariya dan ya bata dariya sosai.... ✍️✍️✍️
(Bakori girl 👧)
https://chat.whatsapp.com/BVqOy4UJveaDh5ZhJOEW5T
💫QUNCI NA 😥😢
✨Story and written by✨
Sa'adatu Ibrahim babale
(bakori girl 👧)
<under the pens of saratu Ibrahim maitamanin(jaririyar writers) & sa'adatu Ibrahim babale (bakori girl 👧) as in identical twins>
Allahumm a'inni ala zikhrikha wa shukhrikha wa husni ibadatikha
PAGE 1⃣7⃣
Duk'e suke gaban malam kindari malamin hajiya balaraba mama hankalinta kwance take fad'a masa damuwarta da kuma mik'a al'amuranta gareshi cikin gushewar tunani da saka ran shine zai yimata maganin matsalarta( wa iyazubillah Allah ya tsaremu daga fad'a wa a halaka) kallonta malam kindari yayi da idanunsa da suka sha kwalli ranbad'au ya mik'a mata wani abu cikin d'an k'yalle tareda cewa "wannan na maigidanki ne cikin abinci ake sakawa a motse idan har yaci wannan maganin toh ko kara kika sa bazai tsallake ba sai kin masa izini sannan ita yarinyar da kikeson a yima kiranye zan miki wani aiki akanta amma gaskiya yanada wahala za'ayi mata kiranye duk inda take a fad'in duniya sai ta dawo inda kike"
Sosai dad'i ya kama mama jin abinda malam kindari yace nisawa tayi sannan tace dashi"toh malam duknaji abunda kace yanzu kamar nawa zan k'aro da za'ayi min aiki kan yarinyar"
"ki bada kamar dubu d'ari biyar saboda zamu sayi bak'ak'en dabbobi muyi yanka sannan ana buk'ar wasu abubuwa da dole sai an kashe kud'i"
Dafe baki tayi jin irin zunzurutun kud'in daya ambato amma kuma da sauri muguwar zuciyar ta ta kauda mata tunanin yawan kud'in wata zuciyarma cemata tayi
"karki damu ai idan ta dawo finsu ma zaki mayar indai kud'ine kin mance k'udirinki a kanta ne"murmushin mugunta tayi tareda cewa
"Toh shikenan malam ba damuwa yanzu banida kud'in a hannu amma da sun samu zamu dawo nida balaraba sai ayi koma minene "
Bayan ya sallamesu ne da suka fito hajiya balaraba ta kalleta tace"yanzu k'awata yaushe zaki samu kud'in kinsan dai gara yarinyar nan ta dawo dan kuwa ita d'in kadarace dan ni tun dama can nake son in cemaki kiban ita muje tikari saudiya amma ganin yanda kike huce haushi akanta yasa nayi shiru" ta k'arasa maganar dai dai lokacin da suka kai bakin 'yar k' aramar motar hajiya balaraba dake Parker a wajen shiga hajiya balaraba tayi mama kuma ta rik'e murfin motar ita bata shiga ba kuma ta rik'e murfin ta saki baki galala tana kallon k'awar tata kamar tana neman wani abu jikinta bata ganshi ba
D'an duk'o da kanta hajiya balaraba tayi tana kallon mama dake tsaye kamar statue tayi "lafiya naga baki shigo ba?
Hmmm k'awata baki yimin adalci ba daman kinsan za'a iya tafiya da ita tikaranci shine baki fad'amin ba wallahi da kin fad'amin da na barki kun tafi nida babu abinda nafiso a duniya yanzu irin inga jinin A'ISHA da QASEEM ya wulak'anta!! ta k'arashe a mugun hasale,
Fitowa daga motar hajiya balaraba tayi ta zagayo inda mama take tsaye rik'e da marfin motar har yanzu dafa kafad'arta tayi ta fara mata magana cikin son kwantar mata da hankali "kwantar da hankalinki k'awata indai AAMAARA ta dawo nayi maki alk'awarin sai na kaita takaranci saudiya kuma wallahi ba k'aramin kud'i zata samo maki ba dan kinsan manyan larabawannan sun fi son yara"
"Kinyi Alk'awari balaraba? Nayi miki wannan alk'awarin indai ta dawo ko wata uku bata k'arawa sai mun wuce da ita saudiyya"
Rungume hajiya balaraba mama tayi ciki farin ciki da hango ma kanta irin Arziqin da AAMAARA zata kawo mata dab tasan duk duniya bata da kowa sai ita kuma a yanda tayi training d'in AAMAARA bata tunanin zata iya tsallake umarninta,
Cikin wannan farin cikin suka shiga mota suka kama hanyar gida...
****
WASHE GARI..
tun bayan dana tashi daga baccin bayan asuba naga Aunty hanan tazo sai da muka gaisa ta tambayeni yanayin jikina sannan ta saka ni nayi wanka na shirya ina zaune a kan gadon na jingina bayana ita kuma Aunty hanan tana zaune kan kujera tana amsa waya a hankali, nikam damuwa ce fal a raina dan kuwa jiya har mafarkin mama nayi tunanin irin dukan da zanci idan na koma gida nakeyi dan kuwa nasan babu mai amsa ta gashi yanzu na koma hannun d'an KIDNAPPING gaba d'aya a tsorace nake hankali na rabi yana wurin mama rabi yana kan yanda RIDWAN ya d'auko ni nake so nake kawai inganshi muyi magana amma kuma har yanzu bai zo ba sosai zuciya take bugu tuno irin dukan sakwarar da mama zata yimin sosai hawayen QUNCI da bak'in ciki suka zubomin tunowar da nayi inda mama ta turani toh mitake nufi dani KARUWANCI take son nayi komi?
Da sauri hanan ta matso inda take tana tambayarta lafiya ko wani abun nayi mata ciwo ne "AAMAARA mike damunki wani abu nayi miki ciwo ne"? ta fad'a cike da nuna tsantsar damuwa akanta
kallon hanan nayi ganin yadda duk tabi ta damu da lamurana karo na farko kenan da wani bayan ZARAH da RIDWAN a rayuwata da wani ya damu da abinda yake damuna ko kuma akasin haka,
"babu abunda yake damuna Aunt hanan kawai ina tunanin rayuwa ne da yanda take zoma kowa a duniya ta yadda ubangijin talik'ai ya tsarama ko wane bawan sa wani da dad'i wani ko akasin haka wato rashin dad'i wani da lafiya wani da ciwo wani da talauci wani da Arziqi kowa da yanda rayuwa take zoma sa kowa dai da IRIN TASA QADDARAR Aunt hanan a lokacin baya kad'an da ya wuce bani da burin da ya wuce inga mahaifiyata ko mahaifina amma a yanzu da wani abu wanda nasan daga cikin zanen QADDARATA yake ya faru dani sai naju takaicin kaina nason ganinsu dan nasan kona gansu d'in babu abinda zasu min tunda basa k'auna ta dankuwa da suna k'auna ta bazasu tafi su barni ba a lokacin da bansan kaina ba bansan wacece ni ba haka nan kuma basuji tausayin k'ank'anta taba suka gudu suka barni a lokacin da nafi buk'atarsu a rayuwata ba ta k'arashe cikin kukan daya kubce mata mai tsanani da kuma tausayi,
ita kanta hanan ba k'aramin ratsata maganganun AAMAARA sukayi ba ga wani tausayinta daya cika mata zuciya (ashe dama ita marainiya ce? hanan ta tambayi kanta)
Rarrashin AAMAARA hanan tayi "kiyi hak'uri AAMAARA dama haka rayuwa tak komi nufin Allah ne kuma dakanki yanzi kika gama fad'a kowa da yanda Allah ya tsara masa tasa rayuwar kiyi hak'uri ki daina kuka saboda kada aikin da akayi maki ya samu matsala kinji k'anwata"
Rungume Aunty hanan kawai nayi jin yanda take lallashina shirun nayi kamar yanda ta buk'ata,ina haka rungume a jikinta ina sheshshekar kuka mukaji ana knocking zame ni tayi daga jikinta ta shi dan bud'e k'ofar delivery ne daga restaurant d'in da tunda tazo ake kawo abinci dukda ni bana ci sai abu mai ruwa ruwa,
Amsar sak'on hanan tayi ta juyo zuwa inda AAMAARA take dama ita yunwa takeji dan yanzu kusan 9:30am tea ta fara had'a ma AAMAARA ta bata sannan ita ma ta fara nata breakfast d'in
A hankali nake shan tea d'in dukda idan ya shiga cikina inajin dad'in d'uminsa amma kuma banason sha dan raina cike yake da damuwa muna a haka mukaji an turo k'ofar d'akin tare da sallama ciki ciki da sauri na kalli k'ofar saboda k'amshin da naji ya bud'e ilahirin d'akin,
Had'a ido sukayi da sauri ta d'auke nata idon ganin yanda ya cika wajen gaba d'aya da kwarjininsa ya cika wajen sanye yake cikin body hug black sai black trouser ya d'ora jacket babba akan kayan jikinsa k'afarsa ma sanye take cikin black sneakers yayi kyau cikin black outfit d'in sosai suka yima farar fatarsa kyau a hankali kamar bazai taka k'asa ba yake takowa zuwa cikin d'akin har yanzu idanunsa na a kan AAMAARA wadda tun kallon farko da suka had'a ido bata sake d'ago kanta ba da sauri hanan ta tashi ta bashi kujeran ita kuma ta koma kusa da AAMAARA "Good morning yah RID" hanan ta fad'a cikin fara'a "morning ya ta k'arajin jikin nata?"taji sauk'i Alhamdulillah,
" Ina kwana" siririyar muryarta ta daki dodon kunnensa kallonta yayi suka had'a ido shine ya fara d'auke nashi kafin ya amsa mata gaisuwar a d'an dak'ile
"ya jikinki hope babu wani matsala ko"?
Nima a hankali na amsa shi dan gaba d'aya yayi min kwarjini kamar ba mai gadin gidanmu ba
Ganin yayi shiru bai sake magana ba yasa nima nace bari inyi amfani da wannan damar in tamyesa lokacin da zan koma gidanmu kallon Aunty hanan nayi naga gabad'aya hankalinta nakan wayarta sannan kuma tasa airpods a kunnenta kallon sa nayi dai dai ya d'ago kansa aiko muka k'ara had'a ido d'an turo bakina nayi (sai wani kallona yakeyi wannan ai wulak'anci ne)
"ya dai 'yan mata akwai magana ne"?ya fad'a haka yana k'ara nitsa idanunsa cikin nawa
Saurin janye ido na nayi sannan a d'an daburce na fara masa magana dan ko duk sai naji shakkarsa ta kamani "uhmm yah RID dama cewa nayi yaushe zan..kom..a gida ta k'arashe fad'a cikin nauyi
kallonta yayi sosai cikin mamakin ta to mamaki mana ita yanzu har yima kanta fatan komawa gidan nan takeyi
" ga hanya nan zaki iya tafiya ma yanzu ai kin warke amma kafin ki tafi ki fad'a min abinda kikaje yi gidan wannan mutumin sannan saiki tafi duk inda zaki tafi,ke!! bari ma kiji wani abu wallahi tallahi kinji na rantse to babu inda zaki bazaki koma gidannan ba idan kuma kina shakka ki jaraba fita daga cikin d'akin nan ma kiga yanda zanyi dake! ya na kaiwa nan ya tashi ya nufi hanyar ficewa daga d'akin da sauri kuma cikin tsananin fusata,
Nikam da idanuwana da suka tara k'walla na bishi cikin mamakin k'arfin halinsa wai bazan koma gida ba to shid'in waye a cikin rayuwata da har yake ganin kamar yanada iko akaina to wallahi bazan yadda ba koma mi zai faru sai dai ya faru ni bazan zauna da d'an fashi da makami ba..... ✍️✍️✍️
(😂😂😂 yarinya kina cikin kwale kwale)...
Bakori girl 👧 ce....
https://chat.whatsapp.com/BVqOy4UJveaDh5ZhJOEW5T
💫💫QUNCI NA... 😥😢
✨ Story and written by Sa'adatu Ibrahim babale (bakori girl 👧)
💫<under the pens of saratu Ibrahim maitamanin(jaririyar writers) and sa'adatu Ibrahim babale(bakori girl) as in identical twins>💫
KING 👑 & QUEEN👸 WRITING CHAMBER
(sarki da sarauniya writers association)
(RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRIN FAQIR)
PAGE 1⃣8⃣
Idanuna na kansa har ya idasa ficewa daga ward d'in, wani kukan takaici da bak'in ciki na fashe da shi "toh miya ke nufi dani satoni yayi koko mi wannan ai zalunci ne" ta fad'i haka cikin ranta dake mata wani irin suya
(toh fa ah lallai AAMAARA kin girma😊)
Hanan da duk tana jin yanda AAMAARA sukayi da yayansu kallon AAMAARAn dake kuka tayi sanin idan tacigaba da kukan zai janyo mata matsala a aikin da akayi mata dama gashi ko d'azun tayi kukan yasa ta d'an dafa kafad'arta tana mata magana cikin lallashi da tsantsar kulawa"haba baby girl ki daina kukan haka nan mana kinji ko kiyi hak'uri duk da bansan abinda ya had'aku ba da yah RID amma koma dai minene dan Allah ki daina kuka ko kinason ki samu matsala ne a aikin da aka miki?" da sauri ta girgaza kanta sannan ta share hawayen tana kallon hanan d'in da d'an sauran kuka a muryanta tace "wallahi Aunty hanan baki san irin tashin hankalin da yake son saka ni ba idan ban koma gida ba mama kasheni zatayi dan Allah ki taimaka min kinji" ta k'arashe fad'a tana had'a hannayenta biyu alamun rok'o d'an nisawa hanan tayi sannan ta kalli AAMAARAN da har yanzu take d'an matse hawaye "naji AAMAARA amma ki fad'a min mana ya akai kikaji ciwo a kanki har yayanmu ya d'auko ki ya baro NIGERIA dake kinsan yanzu haka kina k'asar france ne gida yayi maki nisa dan haka ki k'ara hak'uri har ki idasa warkewa sai ya maidaki wurin maman"
Take AAMAARA ta k'ara gudun hawayenta jin wai bata Nigeria tana france innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai AAMAARA ke maimaitawa wai tana france toh a yaushe kuma bata sani ba?
"AAMAARA ko bazaki fad'a min ba ta yanda yaya RIDWAN ya kawoki nan kuma ya akai baki sani ba?"hanan ta sake tambayarta dan itana so take taji yanda akai AAMAARA ta san RIDWAN d'in dan gaskiya tana mamaki yanda yayan nasu yake babu ruwanshi da sabgar kowama ballantana kuma wata mace bare wadda ba 'yar gidan su ba,
"wallahi nima bansan abinda ya faru ba kawai dai abinda nasani mama ta aikeni wani gida sai wani mutumi ya taso yana son tab'a..... kukane yaci k' arfinta tuno yanda sukayi da Alh SIDI KAN DAWA rarrashinta hanan tayi kanta cigaba da fad'a mata "Aunty hanan daga nan bansake Sabin abunda yafaru ba sai dai na farka na ganni a nan"
Shiru hanan tayi tana nazari shin taya akai ma AAMAARAn tasan RIDWAN? bata samu damar tambayarta ba doctor Ammar ya shigo tareda nurses guda biyu ganin tana hawaye yasa ya fara fad'a cikin harshen hausa
"miss hanan ya akai kika bari patient d'in take kuka za'a iya samun matsala a aikin da akayimata a kanta"
Kallonsa hanan tayi cikeda takaici sai kace itace ta sakata kukan da zai wani rufeta da fad'a sai kace shine yayanta RIDWAN "Dr nifa bani na sakata kuka ba nan ma daka gani lallashinta nakeyi tayi shiru tak'i tayi"ta mai damai a d'an fusace itama,
Kallonta yayi ya d'an girgiza kansa baice komi ya fara duba file d'in ta sai kuma ya juya ya fita nurses d'in na take masa baya, da harara hanan ta bishi sannan tayi k'wafa ta maido da idonta kan AAMAARAn da ta rage hawayen da takeyi d'aure fuska tayi ita ma ta fara yimata fad'an kukan da take yawanyi sai kace wata 'yar yaye"kinsan Allah ko AAMAARA idan baki daina kukan nan ba zamu b'ata wallahi in tafiyata in koma inda na fito kinajin dai Abinda Dr yace toh indai baki bari zanyi tafiyata na barki ke kad'ai" tana kai wa nan ta tashi ta d'auki handbag d'inta ta fice daga d'akin itama akabar AAMAARA ita kad'ai tana sauke ajiyar zuciyan kukan da tayi,
Daure wa nayi ban sake kukan tun bayan fitar Aunty hanan da nasan ranta ya b'aci ne da Dr yake ganin kamar itace ke sakani kuka Addu'a nakeyi cikin raina Allah yasa ta dawo kada ta tafi ta barni a k'asar da bansan kowa ba sai ita da wancan kidnapper d'in kallon T. V d'in dake dakin yayi naga 1:32 lokacin sallah yayi dan haka na tashi a hankali ina d'an jin k'arfin jikin yanzu bathroom d'in shiga nayo alwala dan in gabatar da sallah..
****
5
STAR HOTEL PARIS-MANDARIN ORIENTAL PARIS
Zaune yake kan coach d'in dake k'awataccen d'akin jikinsa d'aure da towel fari k'al da sake haska farar fatarsa mai d'aukar ido da k'yalli gaba d'aya ransa a b'ace yake da abinda AAMAARA tayi shin anya ma kuwa ma aikin da akayi mata yayi kodai ta samu tab'in hankali, toh idan ba tab'in hankali ba har a baro da ita daga gidan can mai kama da jahannama a wurinta amma kuma wai take son ta koma kai gaskiya ya kamata ya tuntub'i Dr Ammar ya k'ara duba ta anya bata samu tab'in hankali ba
(lols 😁 lallai RIDWAN naka wasa ne)
Wayansa dake ajiye kan centre table ne ta fara ringing can k'asa d'an gajeran tsoki yayi kafin ya mik'e ya nufi wayar da gab take da tsinkewa k'arasawa yayi ta d'auka wayan da sauri yayi picking ganin UMMY ce ke kiransa,
"Assalamu Alaikum habiby how are you"?
"Amin wa alaiki salam ummyna barka da dare fatan kuna lafiya keda Abba"
"Muna nan lafiya lau ya mai jikin hope ta ji sauk'i Allah ya bata lafiya"
"masha Allah ummy Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana mai jiki kuma tana samun sauk'i sosai"
"okay dama kiranka nai in fad'a maka gobe zan taso daga UK da asuba zan taso 7:00am kaga kenan 8:35am zamu yi landing dan haka kazo da wuri kayi picking d'ina a Airport kada kabar maman ka sanyi yayi ajalinta"ta k'arashe fad'a cikin dariya
Shima RIDWAN d'in murmusawa yayi yace "toh ummy na gode Allah yasaka da Alkhairi Allah ya kominke lafiya ummyna"
" Amin habiby bye"ta fad'a tana kashe wayan
Bin wayan yayi da kallo yana d'an murmushi sosai yaji dad'i zuwan ummyn dan daman jibi zai tafi NIGERIA ya k'arasa aikinsa, jiyayi ma duk wani bacin ran da AAMAARA tasaka shi a ciki ya b'ace b'at juyawa yayi ta baya ya fad'a kan gadon cikin tsananin farin ciki kona minene oho..
****
Bayan nayi sallah bacci ya d'auke ni a wurin da nayi sallahn batare da nasani ba,
Hanan ce ta shigo d'akin a hankali ganin hannunta rik'e da wata bag mai kyau ta shopping, AAMAARA na kwance a k'asa gashi garin akwai d'an sanyi sanyi yasa ta k'arasa tana tashinta ta koma kan gado ta kwanta idan baccin zatayi, tashinta ta farayi sai da ta farka sannan ta kamata suka koma kan gadon ta kwantar da ita kamar wata 'yar yarinya,
Har hanan zata juya taji an rik'e hannun ta kallon AAMAARA tayi data rik'e hannun "Aunt hanan baki tafi ba?" na tambayeta ina bud'e idono dasuke cike da baccin da na fara,
Dawowa hana tayi ta zauna tana kallon AAMAARA datake jin tsananin tausayinta "a'a baby girl ban tafi ba bazan iya tafiya in barki ba kawai dai raina ya b'aci ne da yanda wannan Dr Ammar d'in yake tayi min masifa Amma yanzu babu komi ai na huce gashi ka shopping nayo na siya maki abin dad'i oya wake up kizo kici"
"Toh Aunt hanan ni yanzu bacci nakeji idan na tashi zanci nagode Allah yasaka da mafificin Alkhairi ya baki miji na gari"
"Amin k'anwar Aunt hanan har kin tuno min da AFRAH k'anwata daga ni sai ita Auta itama kamarki haka take da shagwab'a kullum sai munyi fad'a da ita"
Dariya AAMAARA tayi tace "yanzu dai Aunty hanan tayi missing AFRAH kenan"
"Nibanyi missing d'inta ba nayi dai na mamy bari ma na kirata tayi miki ya jiki d'azun ta kirani tace na baki nikuma time d'in ina waje na fita"fiddo wayan ta tayi daga cikin handbag d'in ta na LV, wayan na fara ringing mamy tayi picking tare da sallama amsawa hanan tayi tace mama mamyn ga AAMAARAn zasu gaisa ta fad'a tana mik'ama AAMAARA wayan a kunnenta "Assalamu Alaikum mamy ina wuni ya gida ta fad'a cikin muryanta mai sanyi kamar yanda halinta yake"
Daga can b'angaren sai da gaban mamy ya fad'i sanda AAMAARA tayi sallama ji tayi kamar tasan voice d'in amma ta manta wurin wa amsawa tayi da "lafiya lou RUQAYYA ya jikinki"? Naji sauk'i Alhmdllh
" toh Allah ya k'ara lafiya kinji"
"Amin mamy nagode Allah ya k'ara lafiya" tana fad'in haka ta mik'a ma hanan dake kallonta sosai wayan cigaba da magana da mamy hanan tayi tana tambayarta Afrah da sauran mutanen gidan nasu kafin ta kashe wayan tana yima AAMAARA maganar ta tashi taci abinda ta siyo mata tunda ba wani abu bane mai nauyi zata iyaci ai..
****
NIGERIA 🇳🇬
tunda suka dawo daga wurin malam kindari take tunanin yanda zatayi ta samu kud'in aikin da za'ayi mata kan AAMAARA ta dawo amma ta rasa mafita sai kawai ta yanke shawarar saida d'aya daga cikin zinarinta tunda daman ita ba wata kadara gareta ba ballanta ta siyar ta amfani da kud'in amma tasaka ma ranta da AAMAARA ta dawo sun tafi saudiyya ita da balaraba tikaranci to ita kuma lokacin yin nata Arziqin yayi,
Ajiyar zuciya ta sauke tunda ta samu mafita tashi tayi ta lek'a kitchen hamida na tsaye tana wanke wanke duk tayi ma kitchen d'in kaca kaca can ruwa can plates ne data wanke ga uban shara ya cika dustbin kallonta tayi cikeda takaicin yadda bata iya komi ba irin na mata sai yanzu ne ma take koyawa kanta tunda 'yar aikin tasu bata nan ta tafi yawon iskanci,
Tsakin da taja yasa hamida da ko motsin mahaifiyar tata bata jiba sai da tayi tsaki sannan ta juyo tana kallonta da mamakin abinda take yima tsakin
"lafiya ko mama naji kina tsaki?"
Harararta tayi sannan tace "ba dole inyi tsaki ba hamida ace wai kece babba Amma babbar banza dubi dan Allah yanda duk kikabi kika k'azance kitchen d'innan haba gida sai kace na kutare duk yabi ya zama wani iri saboda azabar k'azanta irin taki"
Kallon mama hamida keyi da mamakin ta yanzu wannan uban aikin da takeyi a gidan nan idan ba'a gode mataba ai baza'a tsine mata amma shine mama duk bata ganin k'ok'arinta saima zagi data sha
"haba mama yanzu ni duk abinda nake yi banyi ba sai kin zageni toh ai gara ni da waccan banzar RADIYAn ita yau kwananta nawa rabonta dako kiranki tayi toh wallahi na gaji da wulaqancinki gaskiya zan tattara kayana nabi baba yafi kin da wannan abun da kikeyi"ta fad'a cike da rashin kunya da rashin Arziqi
Kuka kawai mama ta fashe da shi 'haba hamida dan saboda nayi maki fad'a shine har kike cewa zaki tafi ki barni toh idan kin tafi dawa zan zauna ZARAH bata nan radiya kuma ta zama abinda ta zama kema kuma sai kice zaki gujeni haba hamida
Dan turo baki gaba tayi tace "shikenan na hak'ura amma wallahi sai dai ki nemo 'yar aiki dan ni nagaji da wahalar gidan nan komi ni ko aike fa yanzu ni ake aike sai kace nice 'yar aiki gashi maigadi har yanzu bai dawo ba maybe ma ya gudu"
Kallonta mama tayi da sauri jin tace maigadi ya gudu da sauri zuciyarta ta k'issima mata anya va tare AAMAARA suka gudu ba da mai gadin nan tunda tana lure da yanda yake shiga lamarin yarinyar, cab lallai aiko dole yau ta nemo ina ne gidan asalin mahaifinsa wanda ke yimasu gadi da kafin ya fara rashin lafiya sai d'ansa yazo a madadinsa,
Da sauri ta juya tabar hamida tsaye tana mai binta da kallo ganin kamar uwar tata bata cikin hankalinta har zata bi bayanta sai kuma ta koma tana d'age kafad'u alamun babu ruwanta aikin ta tq cigaba dayi,
Mama kam mayafinta ta d'auko da purse sai key d'in motar ta kitchen d'in ta nufa ta cema hamida ita ta fita ta dawo da Allah ya tsare hamidan ta bita, tana fitowa tundaga nesa tayi unlocking d'in motar tana sauri ta k'arasa fatanta ace AAMAARA na gidan da shikenan kud'in ta sun huta ba sai ta siyarda zinarinta ba Amma kuma wallahi hukuma zata rabata da dangin masu gadin nan kamar yanda tasha wuya suma sai ta sakasu a uku balle ma yanda fulani ke tsoron 'yan sanda tasan ba k'aramin tashi hankalinsu zaiyi ba ita kuma AAMAARA saita yimata dukan da saita kasa tashi ta bata wahala kamar yanda itama tasaka ta kai da ace tana da halima da itama sai ta d'ora mata hawan jini kamar yanda tasa itama ta kamu dashi ta sanadiyyar guduwarta.....✍️ ✍️ ✍️ ✍️
(Bakori girl 👧)
💫QUNCI NA 😥 😢
STORY AND WRITTEN BY SA'ADATU IBRAHIM BABALE (bakori girl 👧)
💫QUNCI NA 😥 😢
STORY AND WRITTEN BY SA'ADATU IBRAHIM BABALE (bakori girl 👧)
KING 👑&QEEN👸WRITING CHAMBER 🔥
💫QUNCI NA 😥 😢
STORY AND WRITTEN BY SA'ADATU IBRAHIM BABALE (bakori girl 👧)
KING 👑&QEEN👸WRITING CHAMBER 🔥
<UNDER THE PENS OF SARATU IBRAHIM MAITAMANIN AND (jaririyar writers) AND SA'ADATU IBRAHIM BABALE (bakori girl 👧) as in identical twins 👩❤️👩>
{HASBIYALLAHU LA'ILA HA ILLA HUWA ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBUL ARSHIL AZEEM🙏}
PAGE 1⃣9⃣
.... Koda ta shiga unguwar da asalin mai gadin nata yake da k'yar ta iya gane gidan tana shiga tun a tsakar gidan da babu kowa ta iske mai gadin kan wata 'yar k'aramar tabarma ya kishingid'a yana sauraron radio yana ganin ta ya tashi zaune daga kishingid'ar da yayi jikinsa har rawa yake saboda baiyi tsammanin ganinta ba har cikin gidan sa kallonta yayi cikin jin d'an tsoro tsoro yace
"hajiya kece sannu da zuwa barka dai da zuwa ina wuni"
Duk ya jero mata wannan maganar a jere
A mugun harzuk'e mama ta taso mashi da masifa
"Ban sani ba kabiru nace ban sani ba ni ba wata munafukar gaisuwarka ta kawoni ba ina d'anka yake ya sace AAAMAARA ya gudu da ita dama ku talakawa haka kuke da shegen kai mutum ku baro shi indai ya kawo ku inuwa to insha Allahu ku rana zaku maidosa"
Jikin baba kabiru ne ya fara rawa dan yaji tsoro dan baiyi zaton asirinsu zai tonu ba nan kusa
"hajiya dan Allah kiyi hak'uri wallahi ban san abinda ke faruwa ba kuma ni ban masan inda yake ba dan rabona dashi tun satin daya wuce"
"Eh lallai toh wallahi sai ka fiddo shi duk gidan ubanda ya shiga"
ta fad'a a harzuk'e tana yin hanyar d'aki d'aya k'wal dake tsakar gidan yaye labulen buhun dake d'akin tayi sai dai babu komi sai tarkacen kayan mai gidan sakin labulen tayi ta dawo kan maigadin ta tsaya
Shi dai baba mai gadi kallonta yake cikin mamakinta
"tunda bazaka fad'a min inda yake ba bari na kira maka hukuma k'ila idan suka kamaka suka yima kalar tasu izayar ka fad'i inda yake"tana fad'in haka ta d'aga wayarta ta kanga ta a kunnen ta
Yana ganin haka ya tashi da sauri zuwa inda take tsaye ya durk'usa har kasa "dan Allah hajiya kiyi hak'uri karki had'a ni da hukuma wallahi gaskiya na fad'a miki bansan inda yake ba ni ban ma sanshi ba kawai yazo ne har kof'ar gidan ki ina zaune a waje kan benci yazo yasameni yace min zai bani million d'aya ince banda lafiya shi d'a nane zai rink'a zuma a nadadi na shine niku dama ina neman kud'in da za'a yima yarinya ta dashen k'oda aiki to ban samu ba daya wannan tayin sai na amsa kud'in shikuma ya zauna a matsayin d'ana kinji yanda akayi"
Sosai mama hankalinta ya tashi amma lallai malam kabiru ya cuceta
"innalillahi lallai kabiru ka cuceni toh wallahi dole hukuma ta shiga tsakanin mu" tana fad'in haka ta juya ta fice daga gidan motar ta shiga ta tayar sai police station..
****
Tun da dr Ammar yazo ya dubani bai k'ara dawowa ba sai nurses dai ke d'an lek'owa nida Aunty hanan dukanmu a kan gadon asibitin muke dake yanada girma pics d'in ta itada friends d'in ta turawa take nuna min hadda na Afrah tana cikin nuna min na mamy RIDWAN ya shigo da sallamar sa ciki ciki kamar bayaso duk gaidashi mukayi ya amsa mana da k'yar sai kace dole,
Wani iri nake jina dana d'ago kaina sai mun had'a ido dashi kuma hakan baisa ya daina kallon nawa ba nima sai na maida idon kan wayar Aunty hanan dake kallo a tiktok,
Tashi yayi ya fita batareda da yace mana komi ba, kallon AAAMAARA hanan tayi taga itama idonta na kan bayansa dayake ficewa daga ward d'in,
Nima tashi nayi ina d'an lallab'awa zan shiga toilet inyi fitsarin da ya matseni tun d'azun a hankali cikin taka tsan tsan har na shiga toilet d'in sai da nayi komai nazo zan fita kenan naji wani mugun santsi ya kwasheni zuwa k'asa,
K'arar da AAMAARA tayo da k'arfi yayi dai dai da shigowar RIDWAN da kuma Dr Ammar da RIDWAN d'in ya taso gaba wai yazo ya sake duba masa AAAMARAn
Da sauri sukayi hanyar bathroom d'in gaba d'ayansu har hanan ma Dr Ammar ne ya fara shiga sai RIDWAN a bayansa fad'uwa tayi k'asa har kanta ya sake buguwa da bangon toilet d'in showar gel ne ya fad'o daga kan d'an k'aramin mirrorn da akayi ma bathroom d'in kwalliya daya fad'i kuma ashe marfin ya bud'e shine yayi ta gangarowa har AAAMARA ta taka bata sani ba,
kafin Dr yakai hannunsa kanta RIDWAN ya rigasa cikin zafin nama dan hankalinsa ya tashi da yanda kanta ke zubar da jini,
D'aukarta yayi kacokam ya rungume a hannun sa yana ficewa daga bathroom d'in yana fitowa nurse da wata baturiya suna shigo wa da gadon da ake d'aura mara lafiya kan gadon ya nufa ya kwantar da ita jikinsa har rawa yake dan ko motsi batayi yana shimfid'eta kan gadon sai ya tsaya kuma yana k'are mata kallo cikin tsananin tausayinta fatansa d'aya kada ace ta sake samun wata matsalar a brain d'inta Allah yasa kada tayi formating ganin jini ta baka da hanci ga kuma uwa uba kanta daya fi ko'ina buguwa shima Dr Ammar yabama masu tura gadon umarnin barin ward d'in da ita zuwa A&E suna fita shikuma ya tsaya yana basu baki
"sir ku kwantar da hankalinku insha Allah zata tashi lafiya lou babu wata matsala tunda naga fad'uwan k'arami ne nasan insha Allah bataji wani ciwo sosai ba"
RIDWAN ma bai iya magana ya dai jijjiga kansa kawai dan gabad'aya jinsa yake cikin damuwa sosai idanunansa sunyi jajur jijiyoyin kansa duk sun tashi sunyi rud'u rud'u,
Hanan cema ta iya kallon Dr Ammar d'in dan ita ma sosai take cikin tashin hankali kuka take yi a hankali itama fatan ta bai wuce na tsoron kar AAMAARA tayi loosing memory d'inta ba dan taga yanda jini ke fita mata ta kanta da baki da hanci.. ✍️ ✍️ ✍️
Toh fa jama'a AAMAARA na bukatar Addu'arku, Allah yasa kada tayi loosing memory,
Ga kuma mama da malam kabiru mai gadi.
Na yau babu yawa😡
Bakori girl 👧.. ✍️ ✍️ ✍️
💫QUNCI NA 😥 😢
STORY AND WRITTEN BY
SA'ADATU IBRAHIM BABALE (bakori girl 👧)
<UNDER THE PENS OF SARATU IBRAHIM MAITAMANIN (Jaririyar writers) & SA'ADATU IBRAHIM BABALE (bakori girl 👧)>
A bisa jagorancin k'UNGIYA
KING👑 AND QUEEN👸
WRITING CHAMBER,
(sarki da sarauniya) 🔥🔥
[LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH]
PAGE 2⃣0⃣🔥
Sai bayan kusan 4 hours sannan Doctors da nurses d'in da suka shiga da ita suka fito,
Dr Ammar shine ya fad'a ma RIDWAN d'in su kwantar da hanlinsu zata warke insha Allah babu wata matsala sai dai sanandiyar buguwar data sakeyi sanda ta fad'i yasa dole sai da aka sake surgery din da akayi mata Amma a iya tunanin su da fatansu babu wata matsala insha Allah
Kai kawai RIDWAN d'in ya iya jinjina ma Dr Ammar sai hanan da itama take cikin tashin hankalin dan koda batayi sati d'aya bama da sanin AAMAARAAn amma sosai takejin k'aunarta cikin ranta, itama kwantar mata da hankali Dr yayi dukda yana d'an jin haushin ta kad'an
Bayan wucewar Dr suma haramar tafiya suka fara dake Hotel d'aya ya kama masu da hanan d'in shiyasa tare suka tafi kwata kwata baya tare da natsuwarsa sosai yake cikin zullumi,
Hanan d'akin ta ta shige shima ya nufi nasa ita kanta hanan d'in tausayi yayan nata ya bata da kuma uwa uba AAMAARAAn koda ta shiga d'akin wanka ta shiga tana fito wa ta shirya tayi sallah ko abinci bata nema ba saboda gaba d'aya itama bata cikin wata nutsuwar kirki Allah Allah take gobe tayi taje taga yanayin jikin AAMAARAA d'in,
****
Shima bayan shigarsa d'akin wanka ya shiga ya dad'e a cikin k'awataccen bathroom d'in sannan ya fito jikin sa na d'igar ruwan wankan yana kuma fidda k'amshin sabulan da yayi wankan dashi zama yayi kan stool d'in mirror yana goge jikinsa da wani d'an k'aramin towel bayan ya gama ya shafe jikinsa da lotions masu tsada dayake amfani dasu jallabiya ya zura ya shimfid'a carpet d'insa da yazo dashi dama saboda sallah, sallah yayi bayan ya gama kuma yayima patient d'in sa addu'a da fatan samun lafiya nan wurin ya zauna yana azkar d'in da bai samu yayi ba tun d'azu,
Yana nan kwance baccin gajiya ya d'aukesa shine bai tashi ba sai cikin dare daya tashi yayi sallah ya sake rok'a ma AAMAARAA lafiya wurin mai koma mai komi wato Allah mad'aukakin sarki anayin sallar asuba ya kwanta kafin lokacin da UMMY zasu sauka ya d'an samu baccin
Sosai yaji dad'in baccin 8:07 ya farka da sauri ya tashi yana addu'a a bakinsa a nutse ya fad'a bathroom yayi brush da wanka sama sama dan ma bazai iya fita ba tare da yayi wankan ba da bazai yi ba sanin ummynsa ta kusa sauka kuma tayi masa gargad'in kada ya barta tana jiransa da sauri ya shirya cikin shirt and trouser na fendi sai jacket itama fendi's ce kamar ko yaushe daman sune outfits d'in da yafi sakawa ko yaushe in dai fita ta kamashi wadda bata shafi aiki ba ko kasuwan cin sa
sosai yayi kyau jikinsa sai tashin k'amshin turarukansa masu tsada yake, har zai fita sai kuma ya daga waya ya kira hanan yace ta shirya zasuje Airport aiko da sauri ta shirya dukda bai fad'a mata wanda zasu dauko a Airport d'inba,
Itama cikin palazzo jeans da white balenciaga long sleeve ta shirya sai qatuwar jacket saboda sanyi sosai itama hanan d'in tayi kyau,
Suna fita dama already akwai motar hotel na jiransu tareda driver shine zai kaisu Airport d'in dan haka suna zuwa babu jira suka shige bayan motar ya ja suka nufi Airport suna zuwa ba dadewa su Ummy sukayi landing,
T
unda mutanen cikin jirgin suka fara fitowa yake qure wurin da kallo yaga ta inda zata bullo can kuwa sai gata tana sauko a hankali cikin kamewa da nutsuwar da Allah yayi mata fara tass mai d'an jiki daga ganin ta bazata wuce shekaru 45 zuwa 48 yanayin haskenta yayi kama dana indiyawa gashi baqar oman Abayan datasa ta qara fiddo ainahin kalar fatar tata kyakkyawa ce ta sosai kana ganin fuskar ta da yananin gashin girar ta daya kusan hadewa da zara zaran gaahin idonta shine zai nuna maka kamar zatayi tsawon gashin kai kyakkyawa ce ta qarshe tsayawa fad'in kyanta ma bata lokacine,
Tana hango tahowar RIDWAN da hanan ta qarasa saukowa da sauri ta tsaya har suka iso
Rungumeta hanan tayi RIDWAN kuma ya amsa d'an madaidaicin travelling bag d'in ta na DIOR kallon hanan tayi tace "masha Allah hanan yarinyata kece kika girma haka bazan iya tuna when last na ganki ba"
Itama hanan d'in da take kallon Ummyn tana son tuno da kamanninta dan kuwa tun tana 'yar 6 years mamy tace rabonta da ummyn gara mamy tana zuwa mata ziyara amma ita banda ita saboda school zuciyar ta na bugawa sosai saboda son tuno da wanda ummyn take mata kama amma ta kasa tuno wa har ummyn suka gama gaisawa da RIDWAN ita hanan d'in bata jiba ma saboda zurfin da tayi a tunani motan data kawosu suka nufa RIDWAN ya shiga gaba ummy da hanan na baya
Koda suka isa 5star hotel d'in dakin hanan ummy ta sauka dan taqi yadda a ansan mata wani tace zata zauna da hanan d'in,
Tunda tayi wanka ta koma bacci ko breakfast bata yi ba saboda ta kosa suje hospital d'in taga halin da patient d'in take ciki dan lokacin da hanan ta bata labarin kad'an daga rayuwar yarinyar da ta fahimta sai taji tausayinta yakamata dukda kuwa bata santa ba amma kuma sai taji tana son ganinta kodan ita d'in bata da yara ne wanda zata bugi kirji tace itace ta haifesu ba inba RIDWAN ba data kejin kamar itace ta haifesa, gashi ance kuma jiya ta sake fad'uwa kai wannan taga rayuwa hakanan da wannan tunanin ta kwanta kafin lokacin zuwansu asibitin yayi..
****
A bangaren mama kuwa data kai karar tsohon mai gadinta police station ce masu tayi tana suspecting dinsa da d'an sa akan laifin kidnapping din yarinyarta 'yan sanda kuwa masu neman ayi bala'i ballantana kuma gashi a hannu dan sai da ta tabbatar masu da lallai da gaske take aikuwa sukayo mota biyar dasu da makaman su itace agaba tana masu kwatance har suka zo gidan,
Suna zuwa ita tafara yin gaba suka fad'a ba sallama ba komi aikam suna shiga taga gidan babu kowa sai tarkace irinsu bucket na wanka buta sai tukunya da randar ruwa gabata ne ya dan fad'i amma sai ta danne ta kalli d'an sandan da shigo tare tace "officer ka duba can d'akin maybe nan ya shige ya boye tunda yaji siren" ta fada tana nuna masa d'akin data leka dazun neman AAMAARAA
Bude d'akin sukayi sai dai nan ma d'in babu kowa sai tarkacen dan kuwa ko kayan sakawarsa data gani yanzu bata gansu ba alamun dai ya gudu kenan,
Dora hannuwa akai mama tayi ta kurma wani uban ihun da sai da police d'in dake wurin suka toshe kunnuwansu,
"na shiga ukku ni halima yanzu nan shikenan sun cuceni bazan ga AAMAARAA ba balle balaraba ta tafi da ita saudiya wayyo Allah na"
ta qara fashewa da kukan takaici dan ita da har ta fara hangoma kanta yanda idan taga AAMAARAA ba zata kashe kudin ta ta kaima malamin da zai ma AAMAARAA kiranye wani tashin hankalin ne taji ya sake bijiro mata
Kallon ta police d'in sukeyi cikin mamakinta d'aya daga cikinsu ne yace ma macen dake tare dasu ya bata umarni akan ta sakama mama dake kuka handcuff saboda bazasuyi asarar mansu da suka qona ba a banza tunda karya takeyi ba wani suspect d'in da ke akwai a gidan maybe ma itace, kama hannunta Sargent Gwamma tayi tana ihu tana kururuwa tana komi tana tirjewa haka take janta har suka fice daga gidan inda suka tarar mutane sun cika kofar gidan kunsan mutanen mu da anga 'yan sanda ansan wani abun ne ya faru,
Wani daga cikin police dinne ya amsa key d'in motan ta ya shiga ciki yaja ya nufi police station d'insu da ita mama kuma a hilux aka jefata tareda Sargent Gwamma suka tafi suka bar mutanen wurin da tunanin abinda ke faruwa.
****
Bacci sosai UMMY da hanan sukayi dan itama hanan d'in bawanu baccin kirki tayi ba da daddare saboda tunanin jikin AAMAARAA koda suka tashi shiri suka fara a gaggauce sai da suka gama shiryawa sannan hanan tayi kiran RIDWAN ta fada masa sun shirya daman shi already yana hospital d'in dan tunda safe sukayi kiransa suka fad'a masa farkowan AAMAARAAn
Ai suma suna jin haka suka fito da hanzari bakamar Ummy data qagara ta ganta a asibin dukda ta wani bangaren zuciyar ta tanajin yana bugu sai ta alaqanta hakan da tunin yarinyar da bata da lafiyan
Suna isa ward d'in da aka maida AAMAARAAn kafin su kaiga shiga sai ga Dr Ammar da RIDWAN sun fito daga dakin kallon ummyn RIDWAN yayi yana mata barka da zuwa
"yauwa habibey ya ta kara ji hope dai akwai sauqi jikin" jin jina mata kai yayi alamun da sauqin
Dr Ammar ne ya gaida ita cikin harshen hausa ita ta amsa yace mata
"hajiya ai mai jiki ta ji sauqi sosai banyi zaton ma zata tashi haka da wuri ba dan kuwa gata can ma har tambaya ta tayi ina Aunty hanan" ya karashe fad'a yana kallon hanan da ta gimtse annurin fuskarta tunda ta ganshi
Sosai dadi ya kama ummy
"to masha Allah bari mu shiga"
Ta fad'a tana kama hannun Hanan sukayi pushing kofar d'akin
Da kallon tausayi RIDWAN ya bita da kuma tsananin qaunarta dankuwa ummy kamar mahaifiyarsa yake ganinta duk wani abu daya shafesa ko minene to tana sonsa ko ita d'in bata so to zata sauko saboda shi,
****
Tunda na farko daga d'an bacci nake sa idon ganin Aunty hanan Amma bata zo ba sai can da aka jima ina kwance Dr Ammar ya shigo sai RIDWAN a bayansa hada ido mukayi da shi ni na dauke nawa amma shi inajin nasa a kaina
Dubani Dr yayi ya tabbatar masa da babu komi ba wata matsala sannan ya fita ya dawo zaman shiru mukayi sau da aka dade sannan ya naji cikin husky voice d'in sa yana tambayata jikina
"ya kike jin jikin naku yanzu ya kanki yana maki ciwo"
Kallonsa nayi a karo na farko naji wani abu ya tsikari zuciyata a kaf fadin duniyar nan shine mutum na farkon bayan zarah da ya damu da lamari na shine ya fara kaini asibiti da bani da lafiya ya kula dani ya kula da lamura na har yaje ya ceto ni daga hannun ALHAJI SIDI KAN DAWA nasan bacin shi da yanzu wani labarin ake va wannan ba,
Amsa mashi nai da
"Alhmdllh naji sauki kaina ne kawai kamar an daure manshi"
"Eh zai daina shima inji Dr Amma sai kin rage wannan kukan da kikeyi na banza inba haka ba koni sai na bata maki rai in dai na qara ganin ki kina kuka"
shiru tayi batayi magana ba har Dr Ammar ya dawo ya sake sa mata drip sannan suka fito shida RIDWAN d'in shine suna fita sukaci karo dasu hanan,
Ina nan kwance da drip d'in naji an turo kofar an shigo Aunty hanan ce bayanta kuma wata wadda ban kai ga ganin fuskar ta ba Jinayi kamar in tashi zaune da naga Aunty hanan,
Dafe zuciyar ta ummy tayi lokacin da taga AAMAARAA da karfi ta furta "RUKAYYA AAMAARAA" tana sakin hannun hanan ta qarasa gaban gadon da AAMAARAA take tana zuwa ta riqe hannunta wanda babu drip d'in
"MY BABY RUKY wallahi itace wannan ALHMDLLH" ta fad'a cikin tsanin mamaki hadi da dimaucewa ma gaba d'aya
Ni kuwa AAMAARAA kallon matar nan nake da take kirana da ainahin sunana sannan kuma sai naga muna tsananin kama da ita to wacece ita?.... ✍️ ✍️ ✍️
Tohh fa jama'a bomb ya fashe yau ga mama hannun jami'an tsaro sannan kuma ga UMMY da take ikirarin AAMAARAA 'yar ta ce...
End of book 1
Zamu fara book 2 nan da 2to4 days insha Allah
Bakori girl 👧.... ✍️ ✍️ ✍️
0 Comments