JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 1&2
Wata yarinya na hanga sai sauri takeyi sanye take da uniform green wando da farar riga sai green din hijabs sai sauri take yi tana daga kai tana kallon yanayin garin da ruwa zai iya balle wa a ko yaush,saurin da take ne yasa ta hango wasu masu irin uniform dinta kara sauri tayi ta iske su
Deejah shine kuka taho kuka barni ko wadda aka kira da deeja ce naga ta kalleta eaa sai me dan mun taho ke dai bakin tsaya iyayi ba shiru tayi bata tanka ba suka wuce suka nufi hanyar gida.........
Dai dai bakin wani katon gida naga sun nufa zasu shiga ita da Deeja sai wasu yara su biyu kana nu kofar gidan zagaye yake da flowers ga wani gate mai kyau shi kadae ma kyalli yakeyi Knocking Yarinyar ta farayi amma shiru ganin haka yasa yarinyar da aka kira da deeja dazu ta daka mata tsawa wai ke jannat baki da hankali ne tinda ba a bude ba ki jira mana kallon ta jannat tayi ni kike cewa bani da hankali ko nafa girme ki tsaki taja kawae yaran wajen ne daya ta kalli daya ke zee kalli ita deeja kullun fada da wannan dariya sukayi ki ma dae kin fada niima wallahi dariya suka sa dai dai lokacin aka bude gate din..............
Deejah ganin an bude da sanenta ta bangaje jannat ta huce sauran yaran su ka bi bayanta kallonta kawae jannat tayi ta huce sai da suka gaisa da mai gadin sannan ta shige ciki wow gida har gida da kaga wannan gida kasan an zuba kudi wajen parking din mota ma gashi nan motocin wajen sunfi sha biyar ga wani garden daga gefe tafiya kadan zakayi ta sadaka da babban falon gidan....
Katon falo ne mai dauke da kujeru sai wani katon dining dake gefe mai dauke da kujeru wannan gida akwae jama'a wata mata nagani ta harde tana dannan waya kar kuyi tinanin wai budurwa aa babbace zata kai irin shekara 40 din nan tana zaune jannat ce ta fara shigowa hangota a zaune yasa ta karasa ta gaisheta amsawa tqyi cike da fara'a tana sa mata albarka sannan ta huce wani side...............
??JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 3&4
Deejah shiru ganin basu kulata ba yasa ta mike wai ku aunty kunajin mutum ya dawo gida amma ba wanda zai kulasa daya daga cikin su ce ta dago ohh sannu fa tsaki ta ja fuu naga ta shige wani daki.............
Sanye take da doguwar riga mai tsantsi yadin blue ne tayi matukar yi mata kyau abinka da farar mace sai karamin hijab data dora ta tada sallar magariba sai da ta idar harta shafa addua ta jiyo kuka da sauri ta fito ta gansa shi kadae yana hangota ya fara dariya yaron bazai huce irin shekara 2 ba cikin gwaranci yake mata magana tana amsa wa hade da dariya i love you my ammar nah......
Deejah kuwa tana shiga falo ta ga matar sarai amma tai furr ta wuce tana waka kallonta matar tayi a ranta tana mamakin halin deejah da uwarta ita ma falon ta shiga kamar yadda jannat tayi sai dai mai tin kan ka karasa wani wari na tashi tin daga bakin kofa zaka ci karo da bola iri iri ledoji abin takeaway kazanta dai........
Dik da wannan kazantar bata hana wasu manya zama ba a wajen sun mike kafa suna danna waya Deejah na shiga tai hanyar wani daki,dakin sak irin na jannat amma tsabar dauda da kazanta tasa dai dai da tiles din sunyi matuqar dafewa ga wani ruwa dayake zubowa dubawa nayi naga ashe daga toilet din dakin yake zuba lalle wulla jakar tayi kan gado yama na mahaukata sannan ta fito ta wulla hijabi kan kujera ta koma daya ta zauna tana kallon masu dannan waya ba wanda ya kulata......
??JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 5&6
Dauko ammar tayi suka fito falon a lokacin kowa na cikin gidan ya hallara ana dinner zama tayi kan dining ta rungume ammar mamanta ce ta zagayo ta zuba mata abinci tana mata magana akan halinta na kin fitowa da wuri murmushi kawae tayi tana ya hkr ammynah nadaena ta fara cin abincin jin wata bangaza da akayi mata ne yasa ta sauri rike table din wajen tare da furta ammy daga kai suka suna kallonta ganin wata mata nayi jibgegiya sai hura hanci take kamar bijima mama ce tai magana ke yanzu mansura me yasa kina abu kamar ba babba ba ke hajiya mama ki rufen baki ko nasa dake ne tana yi tana gatsina fuska murmushin takaici tayi ai shi kin kyauta mansura juyo da kanta tayi kan jannat ke dan kaza kazarki sauka daga kan kujeran nan bata musa ba ta sauka ta koma gefe tana zare ido zama tayi tare da janyo kunenta ke dan uwarki wannan ba kujera ta bace shiru tayi wani bakin ciki ne ya cika mansura ta gaura mata mari ta hankada ta.........
Kallon su mahaifiyar jannat tayi tace maman deejah yanxu menene haka tsakani da allah ke dallah dakata min na tureta din cewar mansurah sai me nace sai me wallahi Salma ki kiyaye ni ke ma zan gaura miki marin naga mai zaki iya shiru salma (mahaifiyar jannat ) tayi taci gaba da cun abin cinta yayin da mansura ke cin abinci cikin nutsuwa wata shewa ce ta tashi can gefen su......
Gaba daya hankalin su ya koma inda suka jiyo shewar abinne ya basu mamaki wasu yammata nagani su uku sai shewa suke suna tafi mansura ce ta daga baki wae ku wane irin yara ne dan ubanku kuzo kuci abinci ko sai anciye shashashun banza taso wa sukai suka kallesu sunka ya mutsa face suka tako da sanen su daya ta take wa jannat hannu jannat ta sani amma sai tai shiru hajiya mama ce ta miko mata plate tai mata alama ta dawo kusa da yarinyar ta hidaya tashi tayi ta dawo.........
??JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 7&8
Da haka kowa ya watse suka nufi dakinsu jannat da ammynta sai ammar a hannun Salma suna zaune a falonsu suna zaune suna kallo cikin kallon ne jannat ke tambayar ta ammy wae dad bai dawo ba juyowa tayi ea jannat bai dawo ba sai gobe zai dawo toh ammy allah ya kaimu kallon agogo tayi wash ammy dare yayi ni zan je na kwanta murmushi ammy tayi yo nima jannat mai zan zauna nayi ki kashe kayan kinji ta nufi dakinta ita ma ta kashe wutan dakin ta nufi dakin ta........
??ASALIN LABARIN??
Alhaji Jalaluddeen Habibu babban dan kasuwa ne a cikin garin Abuja yana daya cikin mutanen da suke kasuwancin su kasa kasa alhaji Jalaluddeen an haife shi a garin abuja anan ya tashi ya yi karatu har ya girma tin yana karami mahaifinsa ya rasu sai mahaifiyar sa wadda ta rage masa tana gidan dake anguwar garki......
Alhaji Jalaluddeen Habibu yana da mata 4 sun hada da Naseeba (Hajiya mama) Sai mansura mahaifiyar su deejah sai salma mahaifiyar jannat sai kuma Fatema ita ce amarya ko wannensu yana da yara dan akalla yaran sa zasuyi 30 suna zaune cikin rufin asiri......
Hajiya mama tana da yara 11 akwae Naseer sai habibu (alhaji) Muhammad Abubakar Usman sai Munnira Ruqayya Umar Zahra Araf sai zeeyah babban danta naseer yana aiki ne anan garin abuja shima kasuwanci yake yana da mata sai yarinya 1 mai suna naseba suna ce mata (Oummu) sai Alhaji inda yake a kano Sai Muhammad da yayi graduate usman kuma yana makaranta sai kuma munnira da tayi aure ita da ruqayya sai umar zahra(Hidaya) araf zeeya da dik suna zuwa makaranta.....
??JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 9&10
Sai Mansura mai yara 6 dika mata Raidah ce babba sai Zainab Zulaihat Muhibbah Maymun Khadija dikansu ba wadda aka aurar amma zainab da raidah sun gama degree dinsu suna jiran ayki sai zulaihat maymun da muhibba dake karatu a Kano (B.U.K) Sai deejah da suke makaranta daya da jannat wato (Pace setters schools Abuja). Mansura ta kasance mace ce mai bala'i wadda bata jiran ko ta kwana bata da mutunci dik yaranta mai saukin kai ma ita ce maymun bata da rigima amma sauran kama akwae bala'i especially Raidah da deejah.......
Mace ta uku a matansa itace mahaifiyar jannat Wato Ummussalama suna ce mata salma yara kuma maman jannat ke kiranta Mace mai hakuri da sanin ya kamataace mai saukin kai sam bata nuna damuwa akan ko wane irin abu raidah tasha kama jannat ta daketa amma ko kallo koda jannat ta kawo kara sai dai tace tayi hakuri salma tana da yara biyu kacal data haifa sai kuma tana da cikin na 3 Jannat ce ta fari ta da de bata samu hai huwa da wuri ba sai lokacin data haifi ammar shekarunsa 2 cal a dunia........
Sai matarsa ta hudu wato amarya kenan Ameena tana da yaranta Uku ita ma dika mata Muhseenah Sai Farida sai fadila su din twince ne dik cikin gidan nan mansura sun fi dasawa da ita ko meye dalili oho.........
??CIGABAN LABARI??
Washe gari tin karfe 6:30 Jannat ta tashi sai da ta kammala komai sannan ta fito kitchen ta shiga ta tarar da hajiya mama har kasa ta tsugunna ta gaisheta cike da fara'a ta amsa gefe daya kuma ta hango hidaya dake wanke wanke matsawa tayi kusa da ita tana tayata wanke kwaninka suna hirar makaranta a haka suka gama sai da ta taya mama ayki ta gama sannan suka fita ita da hidaya kowa yay hanyar dakunsu.......
??JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 11&12
Karfe 7:20 dai dai lokacin motar School ta faka a kofar gidan su motar su jannat ce dan haka sanye na hango jannat da farar riga a ciki mai gajeren hannu sai a samanta ta dora wata riga tazo mata gwiwa irin mai kamar kasan turmi a kai ta baje but iya kwari riga ta tsaya dark blue ce mai zane zane sai farin wando sai black School shoes sai kuma hijab karami sai tap a wuyan a jiki an rubuta JANNAT JALALLUDDEN HABIB Sai karamin pic dinta da sunan class sai registration number tayi kyau sosae abinka da farar mace yanda naga shigarta haka naga ta hidaya ta fito itama sai deejah da ko hijab bata saka ba sai araf da Muhseenah sanann suka fito suka shiga school bus sai school.........
A bangare daya kuma wani kyakkyawan saurayi ne mai matukar kyau gashin kannan a taje suma luf luf a kansa sanye yake da jallabiya a jikinsa a kwance yake ya juya baya sallamar da akayi ce tasa shi ya juyo wow masha allah kyakkyawa karamin lips manyan idanunawa kai dik wani shika shikan kyau mutumin nan ya hada haidar lafiya yau baka fita ba cewar wata tsoh da suke matukar kama da shi kamar an tsaga kara tashi yayi Mah?? dama yanzu nake shirin tashi na shirya sai na fito nai break Ok shikenan haidar ka fito da wuri murmushi yayi insha Allah Mah......
Tana fita ya janyo wayar hannunsa yana dannawa lokacin yasata a kunne ba abnda naji sai kawae karar da yayi done sannan ya katse ya shiga toilet 20 minutes sanye yake ta kananan kaya masha allah iya kyau ya hadu gayen ya dau wanka iya wanka zama yayi a dining yay break sannan yayi Mah sallama ya tafi tana mai masa addu'ah.......
??JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 13&14
Mansura ce ita da ameena suna hira abinsu kai kace kawaye ne gaba daya gidan shiru kakeji kowa ya kama gabansa in banda su ra'ida da zainab da kullun suna gida sai dai watarn su fita wataran su zauna a cewar su wae idan dad ya dawo ya nemar musu aiki......
Ameena ce ta numfasa wallahi mansurah banga laifinki ba ko nice bazan yadda a aurar mun da yara ba wallahi ba tare da sun sami aiki ba murmushi mansura tayi tace ai dama shisa nima na dage nace wallahi sai sun gama makaranta ke har da aiki kuma wallahi hakan sai ta faru dai dai nan sukaji karar waya tashi tayi binta ameena tayi da murmushi mugunta a hankali ta furta Zaki gani ko ba ni ba........
Bai zame ko ina ba sai wani katon gidan gona mai cike da shuke shuke har sai ka fara barin gari sannan zaka iske shi horn daya an bude masa yayi doguwar tafiya a ciki sannan ya sauka ya shiga wani daki wata dariya ce ta kubce masa yayin da yayi arba da abokanan sa tare da wani katon kwali a ajiye........
A makaranta kuwa yanda ta kasance ana Ajiye su kowa ya kama hanyar ajinsu yayin da jannat da hidaya suka tafi nasu deejah tana shiga ajinsu 'yan aji suka fara shewa..
??JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 15&16
Matsowa gefe yayi ya kalli daya daga cikin friends dinsa da suka kawo masa kwalin ya komai yana ciki daya ne ya kallesa eaa Haidar komai yana ciki kamar irin look saurara basai ka lissafa ba bayan lissafin da mukayi a waya kawae ka duba na tura maka kudin dik wannan maganar haidar ne ke yi cike da izza da sarauta ok haidar shikenan yanzu sai ina kallonsu yayi su biyu ne dika bakomai kawae kowa ya wuce zamu hadu a hall ok shikenan haidar, haidar ne ya kallesa amma kafin nan Adam saka mini kwalin a mota ka karasa ladanka......
Ba abinda ke tashi a class din sai shewa dan ganin deejah ajin gaba daya maza da mata sai tafi suke cike da farin ciki na ganinta dai dai lokacin wata aunty ta shigo dik da sun ganta amma basu fasa shewar da tafin ba Shutup abinda ya fito daga bakin malamar anan suka saurara suka nutsu kallonsu tayi rai a bace ta bara fada can ta juya ta fara topic din daya kawota amma me tana juyowa ba kowa a ajin dik sun fita sun barta.....
Karfe 1:00 dai dai School bus ta saukesu a kofar gidan su kamar kullun shiga sukayi kowa ya kama gabansa karfe 2 kowa ya fito sanye da uniform din islamiyya yayin da kowa ya nufi makaranta deejah sunyi nisa suka ga ta sauya hanya hidaya ce tai mata magana juyowa tayi to ina ruwanku dani ku tafi makarantar ku mana jannat ce tace kinga hudaya zo mu tafi kawae....
??JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 17&18
Shigowa yayi ta kwalin ta kofar baya yabi ya shiga dakinsa da katon kwalin wata loca ya buda ya saka sannan ya wuce bandaki dimin watsa ruwa a ransa yana kiccifa yanda zai karar da wannan kayan domin gaskiya yau sai ya dau chaji da haka ya fito....
Wani katon hall suka sauka yayin da kida yake tashi kai da gani kasan hall din na masu hannu da shuni can wani table na gani haidar ne sai adam sai abokin su na dazu gaba daya suna zaune suna jiran waiter kallon haidar dayan abokin yayi haidar ya kamata ka rage wannan dabi'ar ta shaye shaye mana haba kaganmu nan dik da muna sha bata nuna mu ba kamar yadda ta nuna ka kar fa tai maka lahani haidar kai dallah dakata mana cewar haidar Kaiwa Salees meye matsalar ka ina ruwanka da rayuwata kaga dan allah kabari mana ko zaka nuna wa ubana kudine kai din mai ma wai salees wallahi adam ne ya rikesa sorry haidar plz calm down but ai nasiha yayi maka to bazan dauka nace bazan dauka ba wato kaima adam ka koma bangaren sa ko wallahi zanyi maganinku...
Zanyi maganinku daya bayan daya especially ma kai salees wallahi wallahi sai nayi maganinku a haka yana ban bami ya tashi ya dau hanyar gidansu bai zame ko ina ba sai dakin sa wata drawer ya bude shakare da dik wani launi na kayan maye wani abin ma ni ban taba ganinsa ba janyo drawer yayi sai gashi ta taho kamar faranti a kasan cushion ya zauna ya fara aikin........
Zaune suke ana ta shira bayan sun gama lunch dika falon kowa ya hallara dama haka al'adar gidan take hira ake cike da so da kaunan juna a wasu fuskokin Alhaji jalaluddeeen ne yayi gyaran murya...
??JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 19&20
Juyowa yayi kowa ya nutsu magana ya fara hade da kallon su alhaji Ya min magana akan aurensa hajiya ya miki zancen kuwa murmushi tayi ea alhaji munyi magana dashi akan zai turo kudi sai muje ko ni da ammyn jannat ne muje muyi masa siyayya dan gaskia nafi ganin sai dai ma mubi flight wata harara mansura ta wulla musu su bayin allah bama su gani ba shikenan zuwa nan da wani week din gaskia dan ya kamata a fara magana lokaci sai gabato wa yake kai kuma pa Muhammadu ka dade da gama graduate kai ba ga auren ba kai baga aiki ba sosa kai yayi am daddy wallahi dama inaso nai ma magana kuma na dan sha'afa ne na nemi aiki a federal ministry kuma sun bani insha Allah nan da 1 weeks zan fara zuwa zaro ido ra'ida tayi a hankali ta furta kuttt lalle ma.......
Zainab ce tace kema dai mu bamu samu aiki ba amma ki duba shi yanda ya samu da wuri ke ra'ida juyowa tayi ya zancen mu daku ne shiru sukayi jin zasu raina masa hankali ne yasa ya shi yi musu tsawa ba su ba dai dai da mutanen dakin sunyi shakkar tsawar nan am daddy dama dama, ke Raidah saurara ni zaku mayar karamin mutum wallahi kun sani bana magana biyu ku tabbata kun fitar da mazajen aure nan da 1 month Domin so nake na hada auren ku dana Alhaji.....
Mansura kamar wadda aka mintsina ta mike wallahi alhaji ina hakan ma bazai yiwuba wallahi yarannawa ka dubesu dikansu sun gama degree kuma sun fara neman aiki akan me za a ce za a musu aure to wallahi ban lamince ba wallahi ba a isa ba ehee ke mansurah firgigit ta dawo kan kujera ta zauna dan dik iskancinta tana shakkar alhaji domon baya mata ta wasa.....
??JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 21&22
Mansurah kin sani bana magana biyu na riga da na yanke hukunci idan kuma kikace zaki jayayya da wannan hukuncin wallahi zan matukar baki mamaki dom kin sani kinsan halina ku kuma na baku nan da 1 month ku tabbatar kun kawo min mijin da zaku aura ku tashi ku bani waje shashashun banza ido tsilli tsilli suka tashi mansura ce ta tashi tana tafe tana maganganu nifa alhaji bazaka zagarmin yara ba wallahi akan me ka zage su su lalace yana jinta yayi banza da ita ta wuce.....
Jannat wadda ke zaune da littafi a hannunta sai pen da alama rubutu take kallonta mahaifiyar ta tayi jannat ki tashi kije ki kwanta kinga dare yanayi ko murmushi tayi sai alhaji ya dago aa ki barta ta karasa rubutunta mana ko jannat murmushi tayi wanda ya kara fito mata da dimple din bakinta tace eaa daddy ai nakusa gamawa ma tambayar ta yake makaranta nan pa ta samu waje ita da hidaya sukai tai masa surutu har sai da su mom suka korasu sannan suka tafi....
Wata katuwar kwalbar giya ce a hannunsa gefe daya kuma cigarette yana shaqa sai da ya ya tabbatar sigarin ta kare sannan ya fara dube dube kamar me neman wani abu can naga ya saki murmushi ya janyo wata fara abu a hannunsa kwalbar giyar ya ajiye tare da furta yes ashe gata nan ma nadauka ai kin buya shikadae sai surutai yake can kuma ya yage ta ya juye sai da ya gama yi mata dik wani Design irin nasu na masu sha sannan ya shaka take ya fara bubbuga kansa yana babbaka dariya....
??JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 23&24
Haidar Haifaffen dan garin Abuja matashi mai ji da dukiya da kudi ga kyau ga wanka sai dai matsalar sa dan shaye shaye ne na a mutu mahaifin sa alhaji attahir Shamsudden Yana cikin garin abuja babban dan siyasa wanda akeji dashi a kasa dan haka komai ya tara sunan matarsa Saudatuh ta haifi aliyu shine suke kiransa da haidar Ya taso a sangarce sakamakon gatan da iyayensa suka nuna masa tin yana karami a gabansu yayi primary inda yana shiga secondary mahaifinsa ya daukesa ya maidashi u.s acan yayi karatu tin daga secondary har degree 2 a can ya koyo wasu dabi'u marasa kyau...
Yana da abokai biyu Adam da salees wadan nan sune abokansa gashi baya kula mata dik maitar budurwa sai dai ta hakura tin yana u.s ya tsani mata a cewar sa shi mai zai dasu babban jin dadinsa kawae yasha ya shayu wannan kenan...
Yau ta kama weekend ne ba makaranta kowa yana gida a zauna bangaren su mansura kuwa zaune take tayi shiru gefe daya kuma zainab ce sai Ra'idah sun sata a gaba zainab ce ta matsa wai amma ya zamuyi da hukuncin daddy dan allah amma ki fada mana dogon numfashi taja sannan ta sauke zainab Ra'idah kawai ku fito da miji kafin nan da 1 month wata uwar ashar ce ta fito daga bakin Raidah lalle ma ammah kenan kina goyon bayan daddy wallahi ni bazan aure ba ehee sai na sami aiki na faracin gashin kaina wallahi tabb ammah wallahi kin raina mu ma shiru masura tayi can ta nisa tace ku saurareni da kunnan basira ba wai ina nufin kuyi aure ba ku zaina din din din ba aa banaso ya aura muku wanda ba kwaso ne ya cutarmun da ku kara ku fito miji yayi muku aure sabida kyawawan yara dole sai yaran masu hannu da shuni amma kafin ayi bikin na tabbata sai nayi wani abun wallahi dariya suka saki yawwa amma shisa muke sonki uwa tagari....
??JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 25&26
Hajiya mama ce sai mahaifiyar jannat suna magana akan tafiyarsu dubai siyayyar danta alhaji kenan sun gama komai sun ma sa ran ranar Monday zasu tafi dayake da alhaji zasu tafi shi zai huce Poland...
Jarumar taku sanye take cikin blue jallabiya mai wani kyalli kyalli tayi mata das sai mayafin rigar data dora gashin kanta sai da ya fito dik da ta nadesa kai da gani kasan tana da jibi da fulani ga wani shahararren kamshin tirare daya cika dakin jaka kawae ta fincika ta fito tana kwalawa sauran kira Hidaya deejah zeeyah Muhseenah fadila farida Ni'ima wai kuna inane kunsan ziyarar mu dayawa pa sai kuma ta juyo tana murmushi ganin hajiya mama tana kallonta tana mata dariya tsugunna wa tayi tana kallonta aa jannat har kin shirya eaa wallahi mama su hidaya nake jira amma bara naje na kadosu mutafi salma ce ta rike haba jannat ki kadosu kuma kamar dabobi da dariyarta ta bar wajen dakin su hidaya taje har sun shirya zeeyah suka tura waje sukuma suka nufi sauran part din....
A bangaren deejah suna shiga ba kowa take hudaya taja da baya jin wani wari dayake fitowa daga dakin da alama toilet ne akai using ba a wankeba jannat ce ta riko ta wae ke meye hakan ne zaki wani juya malama haka zaki daure muje da haka suka nufi falon da suke zama cike da sallama suka iske su sai da suka gaishe da kowa dik da raidah da zainab tin kallon farko suka watsar da ita gefe jannat ce tai jarumtar ammah ina deejah daddy yace da ita za aje pah dagowa tayi to bazata ba nace bazata ba wallahi jannat zanci uwarki zaki huce ki bani guri ko sai na tattakaki shegiya mai zubin aljanu shiru tayi suka fito basu yarda sun bi ta falo ba sai sukabi ta baya hidaya ce ke bata hakuri kawae murmushi tayi hidaya ai nasaba bakomai wallahi......
A haka suka fito kowa cike da farin ciki yau suna da yawo da haka suka nufi unguwar garki....
??JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 27&28
Jannat na fita Ra'idah ta juyo wai ammah wannan yarinyar meyasa ta fiklmu kyau ne shegiya kullun kara kyau take kamar sai kuma tayi shiru ammah ce ta dago zan aikeku anjima ku shirya zaunab ce tace to ammah ina zamu je ne banza tayi mata ta tashi tsaki Raidah taja ni abinda ke ban haushi kenan sai dai kullun tace zata aikeka amma taki gaya ma inda zaka zainab ce tace dalla rabu da ita (wai mahaifiya sukewa haka kuduba lamarin pa mahaifiya ba abin wasa ba)...
Haidar ne zaune akan sofa sai hajiya saudatu da mahaifinsa suna shirin yin break kamar kullun sanye yake da t-shirts sai wando harder iya gwiwa kenan abinci suke ci Hadadden cous cous ne yaji farfesun ganda wadda ta alama tasha wuta sai kananan lemuka da ruwa alhaji attahir ne ya dago haidar ya ambaci sunan sa amsawa yayi ka shirya gobe kaje gidan aminina murmushi yayi to abeeh zanje hajiya saudatu ce tace anji zakaje amma karkaje da irin wannan banzar shigar kaji ko murmushi yayi to mah zan gyara da haka sukaci gaba da break dinsu....
Su jannat basu dawo ba sai bayan sallar magariba.jannat tana shiga dakinsu wanka tayi tai sallar tana idarwa ne taji an tada sallar isha'i kawae yi tayi ta fito a falo ta tarar da ammynta zama tayi tana ta bata labari gidan da sukaje da abinda suka gani jannat ce ta dago ammy yaushe zaku tafi dubai eaa yauwa jannat dama inaso na miki zancen na sha'afa ne ranar Monday zamu tafi dan allah jannat ki kula nasan mansura ba abinda bazata iya miki ba jannat ki kula kinji murmushi tayi kai mom karki damu zan kula kinji da haka suka tashi suka fita zuwa lunch...
??JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 29&30
Yau tin safe jannat take guga ko fita batayi ba tana dakinta ko break a daki tayi saboda acewarta yau shine last a wannan weekend din sai da taga ma tai gyaran wardrobe sai wajen 3:00pm ta gama wanka tayi ta saka wani material doguwar riga tasha dauri sai karamin veil da takalmi kamar wadda zataje unguwa fitowa falo tayi ta tarar ana zaune ana hira harda daddy idan ka cire mansurah da ahalinta basa nan itama zama tayi aka fara da ita basu dade ba akai kiran sallah kowa ya watse....
Mansura ce ita da ameena tana zaune a dakun amina tana gaya mata shiru amina tayi kema karki damu dan wannan abin karki damu akwae yanda zanyi zan baki number wata kawar kawata ce ki kirata ki gaya mata damuwarki zata taimaka miki kinji shiru tayi shikenan bani number ta ta amsa tayi ta huce amina ce ta kalleta banza shashasha kawae....
Jannat hidaya zeeyah Muhseenah suna falo suna wasa rabi kallo rabi wasa sai dariya suke karar television ta cika dakin ga ihunsu sallama yayi amma shiru ba wanda yasan dashi deejah ce ta taho falon yana kallonsu deejah da sanenta ta takewa jannat dan yatsa da sauri ta dago idanunta har sun kawo ruwa ke deejah me nai miki kika takeni tsaki taja ke dallah jaka rufemin baki ko naci uwarki tashi jannat tayi wallahi ba uwata ba sai dai taki shakota deejah tayi ni kike zagi dan waka zaniyarki shegiya kawae ganin fadan zai girma yasa haidar karasawa yana rabonsu jannat ta kyaleta sannan ta ruga dakinsu taje ta sanar mata sunyi bako....
Ganin jannat ta tafi sunsan mai zata yi suma kowa fita yayi banda deejah data zauna ta harde tana taunar chewing gum tana latsar wayar mansura......
??JANNAT??
Written And Narrated
By Auntynmu??
*Page 31&32
Jannat ce tafe gefe mahaifiyar ta tin daga nesa salma ta gane kowaye da fuskarta da fara'a ta karasa wajen ta zauna a daya da kujerun falo suna cikin gaisawa ne sai ga su ra'ida da zainab suka shigo har zainab tayi gaba raidah ce ta furta wow so cute zainab kalli wani hadadden gaye juyowa sukayi yayin da suka zuba masa na mujiya hajiya mama ce tashigo suna gaisawa yayin da Jannat ta tashi salma ce ta kalleta jannah kawo wa yayan naku ruwa mana shiru tayi ta nufi kitchen a can ne suka hade da ra'ida daata kokarin jera komai a tray Raidah ce ta juyo ke dan uwarki wayace ki shigo nan ok saboda baki da hankali turo baki tayi aunty ra'ida ki daena zagina da sauri ta karaso wajen ke jannat ni kike zagi wani wawan mari ta sakar mata dafe wajen tayi wayyo ammy fitowa tayi tana kuka.....
Gaba daya falon kowa ya hallara daidai da daddy yana zaune suka jiyo kukan jannat tana tahowa haidar kuwa kallonta yayi ya tabe baki a zuciyarsa yana wannan yarinya karasowa tayi hajiya mama ce ta matsa ta dauke mata hannunta abinka da farar fata sai ga sawun 'yan yatsu hudu a kan fuskarta kuma ga baki a fashe wuff zainab tayi wallahi jannat kin cika jan fada yanxu kuma wa kikaiwa laifi banza tayi mata sannan alhaji ya kalleta yaata nuni ta dawo kusa dashi ta zauna batai musu ba ta zauna....
Ra'ida ce dauke da tray ta taho sai karairaya take tana tafe tana taunar chewing gum daidai kan center table din gabansa ta ajiye tray din Daddy ne ya mata alama da ta ajiye sannan ta zauna...
Jannat ganin kowa sun gaisa da ya haidar yasata tashi gaban ammy tazo ammy ni zanje haraba kallon ta tayi shikenan jannah ki kula kinji tana fita yaran suka bita yuu suna jannat banda deejah data dora kafa daya kan daya har yanxu tana latsa waya..........
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
*Page 33&34
Haidar kam zancen zuci yake yana tsinewa raidah shegiya sai wani abu take ni kam ba sanki nake ba me zanyi dake fuska dik bleaching shashasha mara kamun kai maganar jannat ce ta dawo dashi gaisawa suka kara yi sosae ya dan jima sannan ya tashi zai tafi sallama yayi musu nan aka kira jannat da sauran yara sukai masa sallama sannan suka zauna a falon kamar ance duba jannat ta hango wayar sa daya bari dauka tayi ta ruga isj sa tayi zai kunna mota knocking din glass din tayi tare da furta ya haidar ka manta wayarka da murmushi a fuskarsa ya amsa nagode jannat bakomai ka gaishe da mah dariya yayi ganin yanda ta fadi sunan da haka ya tafi.....
Karfe 8:00 bayan tafiyar su jannat makaranta su hajiya mama sukai sallama da mutanen gida da masu aiki akan tafiyarsu dubai faran faran akai sallama suna tafiya Mansura ce ta koma dakinta number da amina ta bata ta fara dialing kira daya aka dauka bayan gaisuwa ne ta gabatar da damuwar ta banji mai Akace ba aka kashe wayar da murmushinta a fuskarta ta fara shiri mayafi kawae tasaka ta dauki jaka tai hanyar fita daga dakin ne zainab ta shigo ammah ina zaki zainab zani unguwa ne ku kula da gidan bazan dade ba ok ammah sai kin dawo muma zamu fita zamuje shopping shikenan sai kun dawo amma kudawo kafin yaran nan su dawo toh ammah da haka ta tafi....
Haidar ne zaune a dakinsa yana aikin daya sa ba wayarsa ce ke ringing yana kallo yaki dagawa sai da ya maku gaba daya hankalinsa ya gushe anan ya kwanta yana bacci sai gurnani kamar tsohon zaki saudatu ce tai knocking jin shiru yasa ta juyawa tana mai bakin cikin wannan hali na haidar allah ka shirya min shi......
Dai dai wani katon mall suka tsaya shiga sukai basu fi 30mint ba suka fito dauke da leda niki niki sai wasu samari da suke biye da su a bayan boot din motar suka tsaya sai da suka saka sannan suka juyi suka fuskance su fuskar su dauke da murmushi yayi kyau mungode pah aa ai ba komai ni sunana Muazzam Saleh kefa ya nuna Raida murmushi tayi Raidah jalaluddeeen wow nice name exchanged number sukayi hakance ta faru a bangaren zainab Ita da Jafar Mukhtar.......
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
*Page 35&36
Jannat gida suka shigo sunata dariya dayake suna labarin wata a mota da haka suka shiga suna shiga suga su raidah kallinsu sukayi ko wacce tai hanyar dakinsu jannat sai da ta shirya tsaf sannan ta fito kitchen ta nufa ganin ba komai yasa ta dawo falo aunty ra'ida ina abinci na tsaki Zainab taja wato da kin dauke mu kin yi iskar karan mahaukaciya damu sai yanxu da buqatar kanki ce to bamu dafa ba sai me shiru tayi idanunta har sun kawo kwallah wallah aunty ra'ida yunwa nakeji tsaki taja ta tashi ta wanketa da mari wata wayar cable ta ciro sai da ta zaneta suna ji tana ihu ba wanda yayi gigin fitowa saboda sun san tsaf zata hada dasu kallonta ta yi ki min shiru shegiya mai siffar aljanu tashi nasaki girki kuma wallahi idan bakiyimin mai dadi ba sai jikin ki ya gaya miki...
Jannat jikin sai zugi yake ta dago aunty zainab dan allah kuyi hakuri raidah ce ta hayayyako jannat ki rufe mana baki shegiya ki surara kiji ina miki magana kina min banza inajinki pa aunty so nake ki dafa min Basmati rice tare da banana milkshake kina jina da sauri tace eaa aunty sai ki hado min da fruit salad shikenan to har ta tashi Zainab ta fincikota ke dallah dawo ni naga ya miki abinda zaki dafa mini ne ki dafa mini spicy peppered chicken sai orange mocktails nikuma danbun cous cous nakeso to ta amsa ta tashi ta nufi kitchen tana ta zauna nashiga uku ni yanzu ya zanyi da wannan masifaffun kuka ta rushe dashi...
Gani bani da kowa a dangin mahaifiyataa allah ya jiki kanku ya gafarta muku...Haidar bashi ya fito ba sai 5:00 na yamma zama yayi a falo hajiya saudat na zaune sai da suka gaisa har ya tashi sai kuma ta zaunar dashi nasiha ta shiga yi masa yana amsawa sai da tagama ya tashi ya fita sai inda ya saba zuwa wato party tin daga kofar guy far hall din kakejin kara....
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
*Page 37&38
Mansura ce ta shigo falon ganin jannat na gyara yasyasa tashige dakinta ra'ida ta gani sai zainab sai karar ruwa da alama deejah ke wanka sallama tayi ta zauna da murmushi a fuskarta ku ya samarin kun daidaita wata zabura sukai suka dago ammah ya akai kika sani....
Ku dallah karku maidani shashasha mana ke ya raidah ba sunansa muazzam ba ke kuma jafar shashashu kawae ai nasan komai akansu zainab raidah ajiye wayoyin sukayi ammah please taya kika sani ki fada mana murmushi tayi zan fada muku amma ya kamata daddynku yana dawowa ku gabatar dasu dan banason ya muku auren da bakwaso dagowa sukai shikenan ammah zamu fada masa.....
Jannat na gama gyara falo kitchen ta shiga sai da ta dafa jellop mai rai da lafiya tasha busasshen kifi sai kamshi take sannan ta juye ta a flask ta wuce dakin su tana zuwa tasa key tare da furta wash naga wanda zai kara sani aiki basai kun ganni ba mugaye kawae da haka ta shige.Mansurah najin kamshi ya karade gidan ta ce wayyo dadi zainab maza jeki zubo mini abinci tabe baki tayi ta tashi tana shiga kitchen.....
Haidar zaune a falo yana danne danne waya dagowa yayi mah yaushe dad ya tafi bansani ba kallinsa kawae tayi ta ce kana can kana baccin asara kaga ni tashi zan aikeka kallonta yayi kai mah ni kuma ina masu aikin gidan nan ne su bazaki aikesu ba ne murmushi tayi haidar kenan kace dai bazaka ba aa Mah ni bance bazani ba allah dariya tayi shikenan tou.....
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
*Page 39&40
Kwana 2 komai ya faru a ciki har da dawowar su hajiya mama da salma mahaifiyar jannat sai jannat da sun fara exam ta fita daga matakin secondary wato waec sai kuma shakuwar raidah da zainab ga samarinsu jafar da muazzam har an fara gabatar dasu a wajen daddy da zarar ya dawo yau suke sa ran dawowar sa dan haka kowa ka gani zaka ga yana cikin walwala da farin ciki especially ma Mansura da ita kadae tasan me take kullawa.....
Bangaren Haidar kuwa abu sai abinda ya turewa buzu nadi kullun shine party shaye shaye mai makon abu yayi baya kullun gaba yake ga yaro matashi mai jini a jika amma ya bata wayonsa saboda sangartar da iyayensa sukai masa....
Haidar ne zaune akan sofa yayin da alhaji attahir ke zaune akan kujera shi da matarsa saudatu alhaji attahir ne ke fada sama sama haidar bazaiyu dan na sangarta ka ba ya zama kuma nazuba maka ido banason iskancin banza haidar ka shiga taitayinka shiru haidar yayi sai kuma ya numfasa to dad kana nufin bazani karin karatun ba alh ne yace bafa ina nufin bazaka ba ne ba amma kuma ina da sharadi guda 1 shiru yayi cikin sexy voice yace inajinka dad numfasa alhaji yayi ya zama dole da matarka zaka tafi ina nufin zan maka aure ehh wata zabura yayi dad aure kuma a wannan lokacin ni kuma mah kinaji pa kinaji kallonsa tayi kaga haidar abinda mahaifinka ya fada hakane nima ina goyon bayansa kallarka a kalla yanzu kana da shekara 29 a haka kake tinanin cigaba da zama ne watan gobe fa zaka cike 30 amma kana cewa bazakai aure ba to wallahi indae kanason ka tafi America ka samo mata in ba haka ba ni zan nemo maka zancen banza kawae saudatu ce ta tashi tana ta fada ta huce dakinta....
Dad ne ya numfasa kaji toh mahaifiyar ka kanta tadau zafi akan maganar nan dan haka ka fitar da mata nagaya maka har ya tashi sai kuma ya juyo ka tabbata nan da 1month ka fito da ita in ba haka ba ni zan aura maka wadda naga dama.......
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
*Page 40&41
Haidar gaba daya kansa ya kulle ya dau zafi kara kawae ya saki ya tashi ya yi dakinsa wayyo allah na yana shiga ya zauna ya fara daga kwalba kafin wani lokaci ya gita daga hayyacinsa sai surutai yake....
Daddy zaune kowa a falo ya zauna inda anan ne aka yanke ranar da za a kai laife dik da hajiya mama tace dad ya samu yabawa su alhaji attahir kawae subi flight sukai shima yayi na'am da wannan zancen akan wannan lamari yace zai nemi alhaji amma sai yaje gidan nasa zuwa gobe juyowa yayi kan su raidah ina jinku ina muka kwana da zancen mu ne zainab ce tace dad sunce gobe za su zo ma ok yayi kunyi kyan kai yawwa raidah tambayar ki nakeson yi ji tayi wani dumm gabanta ya fadi a zuci ta furta wayyo me ya hadaki da jannat har kika mareta ranar da haidar yazo shiru tayi tsawa ya daka mata jannat ce ta matso aa daddy komai pa ya wuce wallahi kuma ma ai tabani hakuri dama bisa kuskure ne ko aunty ra'ida ai ya wuce dad ne yace shikenan da haka aka tafi wani labarin....
Haidar yinin yau yana daki daga wannan sai wannan sai karfe 5:00 ya fito daga dakin leqawa yayi harabar gidan yana kwala kiran saleh da gudu ya taho sanye da kayan aiki dika blue yana ta washe hakora alhaji gani kaje ka gyara dakin murya na rawa ya fara toh toh karamin alhaji yanxu kuwa da haka ya huce zuwa dakin shikuma yayi part din mah yana mai sallama....
Yanzu jannat basa dawowa da wuri dan haka ta ajiye makaranta islamiyya a cewarta sai sun gama exam zaune take ita da ammynta suna hura jefi jefi ita kuma tana duba littafanta sai ammar daya na can gefe yana kallin Tom and Jerry sallamar dad ce ta katse musu hirar yayin da jannat ta dawo kasa ta basu wuri sai da suka gaisa sannan ta fara masa zance jin surutun zai yawa yasa shi cewa kinga yi karatunki kinji........
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
*Page 42&43
Zaune ya tarad da ita kan sallaya tana wuridin yamma zama yayi har sai da tagama tsaf sannan ta juyo garesa haidar lafiya dai ko matsowa yayi kusa da ita ya kwantar da kansa kan jinyarta tasan sarai me yake nufi sai ta sharesa da cewa lafiya dai ko haidar kallonta yayi ido cikin ido yana mah please yanzu sai nayi aure zan tafi America yes son ta basa amsa a takaice mah amma kuma idan nafasa tafiya America pa shima son sai kayi aure wannan shine hukuncin da muka yanke idanun sa ne suka kawo ruwa moh to ni ina zan samo yarinya mah kinsan bana kula kowa a cikin 'yammata ganin zai sa mata kuka yasa ta fara kwantar masa da hankali a haka har yayi shiru.....
A bangaren alhaji jalaluddeeen da alhaji attahir an shirya kai lefen nasa inda zasu hada wakilai cewa sukayi zasu fara sauka a gidan alhaji karami sai washe gari su kai laifen nasu a haka aka tsayar da shawara........
Bayan sati 2 yau gidan cike yake kowa ka gani kasan yana cikin fara'a 'yan uwa da abokan arziki sun hallara sai hidima ake domin kuwa yau akasa rana ta auren ra'ida da zainab nan da 1 month shima na habeeb an kara sa saboda ayi bikin tare a gama. jannat ce sanye da uniform din ta na boko ta shigo ita da hidaya sai deejah jerowa sukayi kowa ka gani kagansa a gajiye ammar ne ya rugo da gudu ya rungumota yana kiran addah addah murmushi tayi tadaukesa tare da basa chocolate yana ta dariya abinsa....
Gaba daya haidar ya daena fita nan da can kullin yana daki daga daki sai falon sa kullin sai dai yasha yayi mankas ya dawo ya bugu yayi ta surautai wani lokaci kuma sai dai yayi alwala yayi sallah dan dik iskancin sa baya wasa da sallah.....
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
*Page 44&45
Jannat ce zaune kasan cewar gobe zasu gama exam sannan zasuyi graduation washe garin ranar gashi tana buqatar kudi Domin zataje siayaya hidaya ce tazo tana ta mata sallama amma bata ji ba sai da ta tabata firgigit ta dago hidaya zauna mana da murmushi a fuskarta kina nan a zaune kaka tazo sai tambayarki take washe baki jannat tayi allah yaushe muje toh hidaya ce ta kalleta ke tsaya wai me kike tinani ne jannat ce tace sis kudi nakeso amma na sa ran da zan tambayi dad kuma baya nan ko kin tina da rigar da aka fito laaa wallahi sis namanta amma muje yanzu idan mungama da kaka sai muje wajen mama muyi mata magana ko da haka suka tafi......
A bangaren su raidah tin lokacin da akasa rananr bikinsu suka fara zuwa wajen gyaran jiki basa fita ko nan da can kullin suna cikin AC ba laifi sun danyi kyau fuska ta murmure zaune suke da ammah su tana musu hudubar da kullin ta saba na kan kowaye ya taka ku kuma ku takashi kunji banason yarana su zama ragwage kuma bance dan anyi aure ba ku tsaya namiji ya rainaku banaso raidah ce ta matso karki damu ammah insha Allah bazamu baki kunya ba tabe baki mansura tayi kuma dai yawwa zainab yaushe zulaihat da maymun zasu dawo ne dagowa tayi yawwa ammah munyi magana sunce wani week din zasu taho......
Zaune yake a mota cikin kasa kasa da murya adam kasani ni bana kula mata and Abeeh yace sai fitar da mata kamin natafi America gashi na matsu na tafi saboda anan bana sararawa ko ina sa ido ka taimake ni yanzu ya za ayi shiru adam ne yace gaskia bansan ya zan yi da kai ba haidar amma shawara ka barwa iyayenka zabi mana kamar ya adam me kake nipi murmushi yayi ina nufin baka taba soyayya ba mai zai hana ka bari su daura ma aure da ko wacece mana daga baya sai kai rainan soyayyarta a can America shiru haidar yayi daga baya yaja motar sa....
Jannat a gaban Mama suna fada mata abinda ya faru ta fuskance su shikenan jannat karku damu amma dama baku kai kudin ba hidaya ce eaa mama bamu kai ba ni na manta ma jannat ce ta tina min shiru can kuma tace yayi ina zuwa ta tashi ta shige ciki bata dade ba ta fito da kudin nasu ta bawa jannat dayake ta girmesu idan kunje kije kiyi muku payment godiya sukai tayi mata.....
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
*Page 46&47
Bayan kwana 2 jannat sanye take da uniform dinta na school ta fito ita da hidaya sai dariya take daga makaranta sun tsaya bakin gate daya ke yau ba School bus ce zata mai dasu gida ba tsaye suke suna jiran taxi suna hira jefi jefi yayin da deejah ta koma gefe sai yauki take tana taunar Chewing gum kass kass dai dai lokacin wata bakar mota ta tsaya a gaban su ba wanda ya bi ta kanta sai deejah data taho ana bude glass din motar idon ta ya sauka akan wa haidar ne gefe daya kuma adam.....
Adam ne ya jiyo haidar ya dai naga ka tsaya bai kallesa ba yace Ina zuwa kagane wadan nan yaran babansu abokin abeeh na ne amma kuma naga kamar sun rasa abin hawa ne shine zanfita naji ok shikenan fitowa haidar yayi ya gyara tsayuwar sa kusa da su ya matso dai dai nan jannat ta dago har ta mai da kai sai kuma ta tina fuskar dagowa tayi cike da murmushi daya kara fito da asalin fuskarta laah yaya haidar kaine ko wata kazo dauka ne murmushi shima yayi aa naganku a tsaye ne shisa na ce bari natsaya ko kuna buqatar taimako jannat shiru tayi yayin da jannat ta kutso kai yawwa ya haidar dama mun rasa taxi ne shin zaka kaimu gida bai musa ba ya bude musu mota suka shiga bayan sunyiwa wasu na kusa da su sallama.....
Tafe suke motar shiru jin Shirun yayi yawa ne yasa haidar yayi magana yawwa jannat baku bani labarin graduate din ba murmushi jannat tayi ta bude baki kenan deejah ta fara surutu jannat ce ta juya suka hada ido da hidaya suka taba baki, Haidar badan yaso ba yake biye mata dan kwae ba yanda zai yi ne yana kaisu bakin gate ya ajiye su jannat tayi tayi ya shigo amma yace sauri yake da haka sukai sallama tana ta masa godiya....
Adam ne ya kalli haidar bayan tafiyar su wai haidar waccan tsigigiyar mai kama da muciya sai shegen surutu kamar aku murmushi haidar yayi kai kanka kace ni ga wadda naso tayi magana amma kuma ga wadda ta da me ni da haka haidar ya ajiye adam a gida ya huce gida shima......
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍😍
48&49
Dik abinda akasawa rana to dole yazo ti da gashi bikin yaran alhaji JALALLUDDEN HABIB ya zo inda yau akesa ran saura 1 week sai shirye shirye ake amare sai shiri akeyiii biki ya zama biyu ga wani a kano ta dabo ga wani kuma a abuja tin ana sauran 1 week Kaka tsohuwa ta garki ta iso gidan inda gaba daya yan uwa da abokan arziki suka iso Naseer ma yazo da kuma maymun da zulaihat.....
Gaba daya family sun taru akan maganar auren daya zama biyu tinda habeeb ya dauko hanyar zuwa abuja Zaune suke alhaji ne yayi gyaran murya ya gabatar da abinda ya tarasu kamar yadda nafada ni zan tsaya anan abuja domin daurin auren raidah da zainab shi alhaji attahir shi zai je kano domin auren Alhaji kallon kaka yayi inna hakan ai yayi ko da murmushi a fuskarta tace ea banki ta taka ba hakan ma yayi allah dai ya kaimu ameen suka amsa ....
Sannan kuma kowa na bashi kudin da zasu isheshi na wannan sabgar da kuma dinkin da zaku saka nariga dana ba kowa da haka yayi sallama ya tashi.....
Raidah ce da zainab ce suka ce wa yaran kowa ya zauna zainab ce tace da fatan kowa ya karbo ankonsa dan kunsan bama san latti yawwa kuma karku manta ranar Laraba zamuyi bridal sai dinner sai Ladies day sai kuma walima dan haka ku nutsu kusan abinyi tashi sukayi suma suka tafi yayin da jannat ta furta kanku akeji sai iyayin masifa...
Jannat zaune akan kujera bangare daya salma ce suna shira,Jannat ce ta ce ammy nipah wannan bikin nasu wallahi bazan zauna ba sai ranar daurin aure zan dawo saboda kara na bi hidaya kano, Salma ce tace ai shikenan dama nima inaso nai miki zancen,Yawwa ammy na suna cikin hira suka tsinci maganar deeja na fadin ke dallah jannat kizo......
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍😍
50&51
Jannat ce tai banza da ita taci gaba da zancenta salma ce tai mata magana jannat ba magana ake miki ba Shiru jannat tayi sai kuma tace yanxu ammy ace bamu isa tai mana sallama ba kuma katse ta salma tayi ya isa jannat ki tashi ki tafi kawae ba dan taso ba ta tashi ta nufi falon.....
A falon mansurah ta tarar akan kujera tana zaune sai hura hanci take jannat tana zuwa ko sallama bata yi ba a tsaye tace gani kallonta mansura tayi sama da kasa sannan ta dauketa da mari aikin banza kawae wato jannat kinyi tsaurin ido ko ina zuwa mikewa tayi ta wuce zuwa dakinta bata dade da shiga ba mansura ta fito rike da katuwar dorina daga wa tayi ta zabga mata a gadon baya wani uban ihu ta saki daya sa gaba daya mutanen gidan fitowa yayin da salma ta zo wajen ta tana kokarin janye jannat amma ina sai zabga mata dorina take daga nan alhaji ya fito amma Mansura bata fasa dukanta ba.....
Alhaji ne ya tsayar da ita ke mansurah lafiya kina dukanta dagowa tayi haba alhaji yanzu ace kamar jannat ni zan sata aiki tace bazatayi ba ita har ta isa kuma har tana min kunkuni lalle ma alhaji kana nufin na barta haka ina wallahi aalhaji aa amar wani solobiyo ya tsaya yana kallonta daga karshe sai ya koma dakinsa gaba daya dakin kowa yayi mamakin wannan hali na alhaji mansurah ce ta saki dariyar cin nasara a kansa sannan ta ci gaba da fukanta da kyar hajiya mama da salma suka kwace ta a hannunta dik ta kumbura mata fata.....
A daki suke sunyi shiru ammy ni wallahi ban zageta ba allah kuma bata sani aiki ba kawae dan nashiga ban mata sallama ba shine har da mari salma ce ta juyo to ke jannat meyasa baki mata sallama ba kuka ne ya kubcewa jannat haba ammy kuma daddy yana kallo ko magana bai mata ba da kyar salma ta ta lallaba ta ta shi ta shiga toilet wanka tayi ta gasa jikinta,Salma ce zaune tana tinanin wannan hali na alhaji lokaci guda ya chanja da wannan tinanin ta tashi ta nufi dakinta......
Jannat tana fitowa wata yololuwar riga ta saka yellow har ta kwanta sai kuma ta tashi ta fara hada kaya a kit dan ta tina gobe zasu tafi kano dan jibi za a daura auren ya zama dole ta hada komai a haka har dare yayi ko lunch bata fita ba a daki tayi.......
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍😍
52&53
Alhaji attahir ne zaune a falo hajiya saudatu ya aika ta kira masa haidar knocking takeyi a dakin nasa bai wani bata lokaci ba ya bude cike da mamaki hajiya saudat ke kallonsa yau wace rana haidar ka bude kofa da wuri kallonta yayi mah sannu shigo mana takaitaccen murmushi tayi aa haaidar fito Abeeh na son magana da kai,Murmushi yayi to mah muje ko....
A bangaren su Jannat sun shirya su da hidaya da zeeyah sai ango habibu sai muhammad,Abubakar sai jannat da alhaji attahir da haka suka tafi don ta gidan alhaji attahir zasu biya sai da sukaiwa kowa sallama sannan suka tafi.......
Haidar ni zan tafi kano daurin auren habibu murmushi yayi ea abeeh nagane sa dan gidan baba ko,eaa haidar shi dan allah haidar ka kula da kanka kaji ka kula min da gidan nan kaji ka rage wannan shaye shayen naka plz sunkuyar da kai yayi abeeh insha Allah zan gyara kaji zan daena abeeh inaso na daena shan komai amma nakasa abeeh narasa yadda zanyi yana magana yana hawaye tasowa alhaji attahir yayi ya rungume sa yana masa addua da haka sukaji sallama.....
Su jannat ne Hajiyaa saudatu ce musu lale lale ku shigo mana da fara'a suka shigo aka gaggyasa da kowa haidar ne ya dago suka gaisa da su habeeb jiyo da kansa yayi yau ke kuma dake za atafi dariya jannat tayi ea mana ya haidar ko so kake na zauna a abuja ne kullun dariya shima yayi anan suka bude babin fira kafin abeeh ya shirya mah mamaki take da ganin haidar ya sake da jannat ana haka alhaji attahir ya fito sai da sukai wa kowa sallama sannan suka dau hanyar Kano tin a hanya zazzabi mai zafi ya rufe jannat sai karkarwa taje tana rawar dari sai da habeeb ya bata panadol tasha kafin su isa kaduna sai a tsaya a asibiti......
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
54&55
Zainab da raidah ne aka kama katon hall na yin Ladies party iya yammata ne kawae masu ji da wanka amare ne zaune akan wata kujera ta alfarma sanye suke da wani material mai kyalli black ne sai daukar ido yake yayin da angwaye suka yi shigar white shadda ga wani shahararren kamshi daya ke tashi kide kide ne ke tashi a wannan hall din ansha pictures can na hango muku deejah tare da gayyar kawayenta sai kutsa kai suke sanye take da ankon material ne Ash sai suka daura black din dankwali......
Sai da suka tsaya a asibitin an gwada ta maleria ne sun bata magunguna da haka suka ci gaba da tafiya har suka isa garin kano kai tsaye unguwar sharada suka sauka a wani katon gida suna shiga aka fara yi musu lale lale masauki akai kaisu dika katon part ne amma kuma dakuna 3 ne a ciki rabawa akai akabawa su jannat daya sai ango daya sai alhaji attahir ya dauki daya suna sauka habeeb ya fara kiran abokansa na garin kano yana sanar dasu daurin auren sa gobe.....
JANNAT a daki suka zauna yayin da aka kawo musu abinci tsaki jannat taja ke ni sai na huta zanci abincin hidaya ke dai kawae ki ci kinji....
Jannat ce zaune a falon dakin suna gaisawa da mutanen dakin mutane masu karamci faram faram aka amsa amaryace ta matso kusa da su jannat ta jasu zuwa dakinta sai wajen karfe 10 sukai sallama kowa ya nemi makwanci.......
Washe gari jannat ce sanye da take da shaddah brown ga wani dinki mai kyau da fitar design fitowa tayi ta shiga falon inda kowa ke break gaisawa sukayi da mutanen dakin kallon mahaifiyar amarya fatima tayi amma mama ina su hidaya da fara'a a fuskarta tace ai kuwa suna tare da su hidaya kije dakinta kinji to mama.....
Karfe 01:00 aka daura auren Habeeb JALALLUDDEN HABIB tare da amaryarsa Khadijah Munnir saleh bisa sadakin naira dubu 80 alhaji attahir suna dawowa gida suka dau hanyar tafiya abuja da amarya domin sai sunje an hadasu da amare su raidah an musu nasiha tashar flight sukayi wanda zai kaisu abuja....
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
56&57
Suna shigowa cikin garin Abuja direct gidan alhaji JALALLUDDEN suka nufa ida a bangaren hajiya mama amarya ta sauka sai kuma su jannat da kowa ya kama gabansa....
Raidah da zainab sanye suke da wata pink gown wadda kana ganin shatin jikinsu andau Makeup karfe 8 suka tafi dinner ba su suka dawo ba sai 10 na dare ameena na hanga bayan compound din gidan tana tsaye ta kara waya a kunne banji me akace ba sai cewa tayi shikenan bakomai allah ya kaimu dan wallahi dole sai ta bar gidan nan shegiya da haka ta katse wayar ta juya ganin baata ga kowa ba yasa ta kama hanyar dakinta......
Dad ne zaune akan kujerar falon hajiya mama sai amarya khadija da angonta a gefensu da hajiya mama cikin wa a zi dad ke magana alhaji kasani wannan amana ce allah ya baka kai zaka kula da shanta cinta tufatar da ita da kuma rashin lafiyar ta alhaji kasani a ranar gobe kiyama allah zai tambaye ka akan wannan amana daya baka sannan ke kuma khadija ki zama mai hakuri da nuna kawaici nasan dik abinda zan fada miki an riga anfada miki shi tun a gida ina fatan allah ya baku zuri'a dayyiba amma alhaji kubari sai gobe idan za akai su raidah da haka ya tashi ya nufi part dinsa......
Washe gari gidan alhaji jalaluddeeen cike yake da yan uwa da abokan arziki maza da mata can na hango jarumar taku wato jannat sanye take da wani lace white da ratsin blue tasha riga da skirt dai dai jikinta sai blue veils mai matukar kyau sai kyalli take fuskar nan fes ba wani alamun Makeup sai karamar jakarta blue da takalmi ta fito.......
Karfe 11:00am aka daura auren Raidah jalaluddeeen habeeb da angonta Muazzam saaleh sai zainab jalaluddeeen habeeb da angonta jafar Mukhtar wanda ya samu hallarta mutane da dama domin cikin Masallacin gidan an rasa waje masu pic nayi masu video nayi ma aikatan gidan tv kuwa sai video suke cikin salo har liman ya tashi dai dai nan alhaji attahir ya tsayar da shi liman ka manta akawae daurin auren mutum daya.....
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
58&59
Haidar na hango sanye da farar shadda tasha dinkin zamani bari daya abokanan sa ne adam da salees suna tsaye da angwaye ana hotuna kamar daga sama sukaji sanarwar wani daurin auren a massalacin cikin mamaki wanann ya dubi wannan wannan ya dubi wannan to wai shin daurin auren wa za a yi......
Liman sai da aka gama addua sannan ya furta an daura auren Aliyu Attahir Shamsudden da amaryarsa jannat jalaluddeeen habeeb a bisa sadaki naira dubu 60 lakadan ba ajalan ba dai dai lokacin da liman ya ambaci aliyu attahir lokacin haidar ya kusa faduwa take kansa ya fara juyawa da taimakon adam suka koma gefe suka zaunar dashi yayin da sauran mutane sai jansa suke suna aa ashe harda naka shine ka boye mana ganin mutane sunyi yawa yasa shi kokarin fita daga gidan abin mamaki kowa ya kagani kaga yana taya sa farin ciki da kyar ya samu ya shiga mota a wannan yanayin ya nifi hanyar gida....
Cikin gida kuwa ba abinda yasan me ke faruwa kawae kowa sabgar gabansa yake kowa ka gani kagansa cikin farin ciki jannat ce zaune a dakinta ita da ammar tama sa masa shaddar sa babbar riga da hula tana gamawa suka fito 'yan daurin aure ne suka shigo suna allah sanya alkhairi anan sukaci karo da jannat tsayawa sukai mata allah sanya alkhairi abim ma mamaki ya bata cikin inda inda tace ai ga su aunty raidah can suna daki ku shiga mana daya ne ya kalleta kina nufin ke banda ke murmushi yake tayi eaa mana su aunty raidah ne gasu can kina nufin banda ke ya tambaya amma kuma ke aka daurawa aure a masalaci wucewa jannat kawae tayi tana cewa ni da ko saurayi bani da shi kuna kiramin aure harabar gidan ta fito...
Muhammad ne ya matsa kusa da ita jannat amsawa tayi naam yaya muh'd dad yace mu samesa a dakinsa yanzu to tace ta kama hanyar dakin yayin da Muhammad ke binta a baya....
Yana isa gida motocin mutane ya gani birjik mamaki yake to wadannan motocin me sukeyi kuma bayan shi mah batace masa zasuyi baki ba dai dai nan ya tina da daurin auren da akayi fitowa yayi ya fara kwala kiran mah mah da haka ya shige gidan......
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
60&61
Gaba daya mutanen gidan ta gani idan ka cire daga kan hidaya abinda yayi kasa suna zauna jannat kusa da mahaifiyar ta taje ta zauna tayi shiru tana zaune sai ga shigowar alhaji jalaluddeeen sai da aka gabatar da addua sannan dad yayi gyaran murya abinda yasa na tara ku anan shine bayan daurin auren su raidah dana gabatar na yanke shawarar daura auren jannat ita da haidar dan gidan abeeh wani tashi jannat tayi idon nan ya kawo kwallah dad ni dad ka dauran aure dad banason wannan auran ni bazan iya ba dad bakace min zakai min aure ba yanzu dik wannan maganar a tsaye take yinta yayin da hawaye ke zuba a idonta......
Mansurah na gefe tana dariya ciki ciki shegiya allah ya kara kwara ma daya aurar dake kona huta haba yarinya sai kyan masifa maganar dad ce ta katseta kimin shiru jannat ki sani na isa dake ne shisa na yanke wannan hukuncin a matsayinki na yarinya mai tarbiyya sannan ki sani ba anan zaku zauna ba America zaku tafi wata kara jannat ta saki ta fadi a wajen sumammiya.....
A dakinta ya tarar da ita mah ya furta zaune take sai kannen ta su biyu suna hurarsu ta 'yan uwa zuwa yayi ya tsaya mah wai me ake ne naga mutane da waya da murmushi a fuskar saudatu ta dago bikinka mana haidar mah bikina fa haba mah haba mah ya zaai kai kaga haidar saurara mana ai dama abeeh ya baka zabi da baka bi zabinsa ba yasa ya yanke wannan hukuncin dan haka fitarmun daga daki ganin ba wasa a fuskar saudatu yasa shi fita yayi hanyar dakin sa yana kuka yana shiga tasa key gaba daya ya rasa me zaiyi......
Jijjiga ta salma take amma ba alamun motsi a fusace salma ta dago shikenan ai gashinan kun kasheta kun huta haba alhaji haba alhaji yaza ka yanke wannan hukuncin akan jannat ka tina jannat yarinya ce ba ta da wani wayo haba alhaji da kyar Muhammad ya janye ta yay hanyar fita daa ita yayin da salma ta durkushe a wajen tana fitar da hawaye.....
Family hospital suka nufa basu dauki 5mint ba suka isa shi da habeeb sai maymun data biyosu a baya tana hawaye suna isa aka basu gado kasancewar a sume take shiga sukayi da ita da sunfi awa 3 akanta da kyar sukai kokarin ceto rayuwarta.....
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
62&63
Salma ce zaune daga ita sai alhaji attahir da alhaji jalaluddeeen cikin sanyi murya take magana alhaji meyasa kayi haka dan allah jannat yarinya ce shiru yayi ya kasa magana alh attahir ne yayi gyaran murya salma kiyi hakuri ba nayi haka bane dan na bata rayuwar jannat Salma kin sani bazan cutar da jannat ba hasalima ni na nemar wa dana aurenta salma ina mai baki hakuri idai hakan bai miki ba wallahi zan iya kunce wannan auren daga hannu salma tayi banaso ko mai zai faru ya faru wannan itace kaddararki jannat kiyi hakuri komai mai wucewa ne juyowa tayi bakomai allah ya sanya alkhairi da haka ta tashi ta tsallake yan biki suna ta magana amma bata kula su ba fita tayi taiwa driver magana suka fita zuwa asibiti......
Tana isa aka nuna mata icu jannat ta hango kwance sanye da inhaler sai fitar da numfashi take kallo daya zaka mata kasan tanajin jiki salmace ta tsaya sai safa da marwa take maymun ce ta taso ammy sannu da zuwa ki zauna sunce sai nan da awa 2 zata farka murmushi kawae tayi shikenan maymun sannu da kokari amma yakamata ki tafi gida kinji saboda 'yan uwanki suna can suna nemanki zama maymun tayi to ammy nai musu me vayan ga mara lafiya a gidan mu ni gaskia ammy bazan koma ba......
Haidar yana tsaye tin shigowar sa sai tsaki yakeja gaba daya haushin kansa ya ke yanzu ni aka daurawa aure jannat wannan yarinyar aka auramin to me zan da ita wannan wata zuciyar ce tace masa ai dai kyakkyawa ce gyada kai yayi naji da kyanta amma kuma ina ni ina ita nafi karfinta wallahi tsaki yaja kawae yaje ya haye gado yayi rubda ciki......
Jannat ce ta farka sai da likito ci suka shiga suka dubata sannan suka dawo salma ce ta tashi dr Sagir zamu iya shiga ne eaa zaku iya shiga amma kuma karku dameta da surutu domin
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
64&65
Salma ce zaune daga ita sai alhaji attahir da alhaji jalaluddeeen cikin sanyi murya take magana alhaji meyasa kayi haka dan allah jannat yarinya ce shiru yayi ya kasa magana alh attahir ne yayi gyaran murya salma kiyi hakuri ba nayi haka bane dan na bata rayuwar jannat Salma kin sani bazan cutar da jannat ba hasalima ni na nemar wa dana aurenta salma ina mai baki hakuri idai hakan bai miki ba wallahi zan iya kunce wannan auren daga hannu salma tayi banaso ko mai zai faru ya faru wannan itace kaddararki jannat kiyi hakuri komai mai wucewa ne juyowa tayi bakomai allah ya sanya alkhairi da haka ta tashi ta tsallake yan biki suna ta magana amma bata kula su ba fita tayi taiwa driver magana suka fita zuwa asibiti......
Tana isa aka nuna mata icu jannat ta hango kwance sanye da inhaler sai fitar da numfashi take kallo daya zaka mata kasan tanajin jiki salmace ta tsaya sai safa da marwa take maymun ce ta taso ammy sannu da zuwa ki zauna sunce sai nan da awa 2 zata farka murmushi kawae tayi shikenan maymun sannu da kokari amma yakamata ki tafi gida kinji saboda 'yan uwanki suna can suna nemanki zama maymun tayi to ammy nai musu me vayan ga mara lafiya a gidan mu ni gaskia ammy bazan koma ba......
Haidar yana tsaye tin shigowar sa sai tsaki yakeja gaba daya haushin kansa ya ke yanzu ni aka aurawa jannat wannan yarinyar aka auramin to me zan da ita wannan wata zuciyar ce tace masa ai dai kyakkyawa ce gyada kai yayi naji da kyanta amma kuma ina ni ina ita nafi karfinta wallahi tsaki yaja kawae yaje ya haye gado yayi rubda ciki......
Jannat ce ta farka sai da likito ci suka shiga suka dubata sannan suka dawo salma ce ta tashi dr Sagir zamu iya shiga ne eaa zaku iya shiga amma kuma karku dameta da surutu domin batasan hayaniya wucewa dr yayi sukuma suka shiga kwance take kallo daya zakai mata kasan tanajin ana jin jiki yau daya ta rame tayi wani haske fayau cikin dakushewar murya ta furta ammy....
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
66&67
Mansura tin bayan fitarta dakinta ta nufa ta shige dakinta ta kulle dariya ta babbake da ita ahayye yau anayi inajin dadi allah nagode maka allah ya kara ai wallahi raina fes dama nace sai an aurar da ita gashi kuwa ta tabbata wayar ta tazaro ta shiga dialing number.....
Jannat na kwance tace ammy yanzu da gaske dad ya dauramin aure a yaya haidar ammy ni banason wannan auren wallahi banaso nashiga uku ammy shiii tayi mata alamun tayi shiru kama hannunta tayi mara drip din tace kai jannat shin baki dauki kaddara ba jannat so kike kiba mahaifinki kunya ko jannat shin dad dinki bai isa da keba ki sani jannat tin kafin kizo duniya allah ya tsara miki hakan dan haka jannat kiyi kokarin cinye wannan jarabawar kinji haka dai tai ta lallashinta har ta saki jiki da ita suka fara hira maymun ce ta tashi ya Muhammad tinda ya habeeb ya tafi kaini gida nasamu na kawowa jannat abinci dagowa jannat tayi nagode addah maymun shafa kanta tayi tare da murmushi......
Maymun na shiga gida ana kokarin kai amarya zulaihat ce ta matsa ke maymun kizo mutafi kai amarya tsaki maymun tasaki to naji bara na shirya fakar idon mutane tayi ta shige kitche ta dorawa jannat abinci Muhammad kai tsaye wajen hajiya mama ya nufa yayi mata bayanin komai na jikin jannat...
Haidar ne zaune sai saudatu da alhaji attahir haidar ne yayi magana abeeh meyasa meyasa kazaba mini wannan yarinyar a matsayin mata abeeh ni banasonta wallahi indai itace nahakura da auren ni zan saketa kawae sai na samo wata wani wawan mari ya sakar masa ji kake tass ashe baka da hankali aliyu dik kallon da nake ma ashe kai mahaukaci ne bansani ba wallahi kasake ka saki jannat bani ba kai alhaji attahir ne ya wuce dakinsa juyowa haidar yayi haba mah na girmi pa jannat a kalla yarinyar nan zan bata 15 years amma kuma ita aka auramin saudatu ce tace ya isa haidar eaa ita aka daura ma ka aure da ita ba dae kaki fito da mata ba to wallahi kasani yanzu haka jannat na asibiti a ta dalilinka ka tabbata kaje dubata kuma ina maka kashe da dik ranar daka saki jannat sai dai kanemi wata uwar badae ni ba tashi tayi ta bashi a wajen...
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
68&69
Haidar mikewa yayi yan kunkuni ya wuce dakinsa yana shiga ya janyo kayan aikinaa ya fara durawa cikinsa ko yaji saukin abinda yakeji a zuciyarsa yana kallon kiran adam amma yaki dagawa.....
Bata dade ba Muhammad suka koma maymun ce tashiga da sallama ta ajuye kulan salma ce ke mata godiya yayin da jannat tayi bacci sai wajen 10 maymun ta koma gida ita da Muhammad dakinsu ta nufa har yanzu da mutane amma dai dai kowa ya watse wasu kuma sun tafi kai amarya kashe fitilar dakin tayi ta dukunkune a bargo take baccin gajiya yayi gaba da ita...
Dr sageer ne ya shigo dakin tareda magunguna salma ce ta mike likita me yake damun ta dan allah ka fada min murmushi dr sageer yayi bakomai dama damuwa ce sai jininta daya hau amma mun samu ya sauka yanzu haka tafita daga hadari zuwa gobe insha Allahu zamu iya sallamar ku da haka sukai sallama shi kuma ya fita...
Alhaji attahir ne a daki sai fada yake ni zai maida karamin mutum wallahi bai isaba wannan auren ya dauru saudatu ce tashigo tana cewa ya hakuri mana abeeh shi ya isa ya sauya wannan maganar yanzu kira jalaluddeeen din muji jikin nata ya yake
Alhaji jalaluddeeen din ne yayi sallama a lokacin salma tana sallah ita kuma jannat idon ta biyu jin muryar mahaifinta yasa tai kamar bacci take dan tasan tabbas tayi masa abinda bai dace ba dazu zama alhaji jalaluddeeen yayi cike da jin tausayin yarinyar tasa shafa kanta yayi cikin kulawa karar ringing din wayar sa ne yasa shi kallon wayar dake hannunsa.....
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
70&71
Daga kiran yayi da akai saving number da aminina yasaka a kunne gaisawa sukayi alhaji attahir ne ke tambayar sa jikin jannat kallon jannat jalaluddeeen yayi da sauki attahir karka damu da komai na tabbata jannat bazata bani kunya ba jannat yarinya ce mai hakuri mai daukar kaddara dik cikin yarana nafisonta saboda bata saba wa umarnina yau ma abinda yasa kaga haka ta faru saboda ban nemi shawarar kowa ba nayi haka sallama sukayi da alhaji attahir dai dai nan dr sageer ya shigo dakin da leda a hannunsa....
Mansura tana kwance ranta fes kallo daya zaka mata kasan tana cikin farinciki dik da darene amma haka kawae take murmushi mikewa tayi ta nufi dakin su zulaihat komai take nema ohoo tana shiga ta iske maymun da sai bacci take sharawa,kallonta tayi a yamutse sai kuma tafara tashinta ke maymun ke maymun tashi cikin murya bacci maymun ta amsa da ammah yadai wata uwar ashar ta saki take maymun ta wartsake ammah lafiya cewar maymun......
Jannat juya kai tayi a lokacin da dr sageer ya shigo da kuma idar da sallar salma dik da idonta biyu amma taki ta bude idonta saboda kunyar mahaifinta da abinda tayi masa dazu sai ta tabbata yayi sallama ya tafi sannan ta tashi ta shiga toilet alwala ta dauro ta dawo ta fara jero salloli sannan ta roki allah alkhairi sannan ta tashi ta dawo kan gadon yayin da salma ta mika mata abinci ba musu ta amsa domin wata mahaukaciyar yunwa takeji.....
Maymun kina nufin baki tafi kai amaren ba shiru maymun tayi hankali a tashe ta duba agogo ammah karfe 10:30 amma har yanxu basu dawo katseta Mansura tayi tambayar ki nake maymun cikin inna inna tace ea..am..mah to meyasa mansura ta kara jefo mata wata tambayar shiru maymun tayi mansura a kufule ta tashi wato maymun nagane kin tsaya wajen waccen dakikiyar ko jakkar wadda batasan inda kanta yake ba maymun wallahi akan jannat zan iya saba miki ke wallahi saima na tsine miki dago kanta maymun tayi tare da furta nashiga uku ammah jannat pa dakata maymun ki rufemin baki shashasha banzar wadda batasan ciwon kanta ba hanyar fita tayi sai zage zage take yayin da kuka y ma kwacewa maymun.....
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
72&73
Washe gari karfe 8:00 alhaji jalaluddeeen yayi sallama a dakin da aka kwantar da jannat,h annat zaune take tayi shiru jin sallamar mahaifinta ne yasa ta sunkuyar da kanta zama yayi ya juya sai da suka gaisa da salma sannan ya kalli jannat,jannat ce tace dad ina kwana da murmushi a fuskarsa yace lafiya lau jannat ya jikin dagowa tayi dad da sauki alhamdulillah allah ya kara sauki jannat,jannat ce ta amsa ameen ameen dad......
Tashi yayi bara naje nadauko muku abincin na mantashi a mita wallahi fita yayi bai jimaba ya dawo dauke da basket babba ajiyewa yayi a kan drawer wajen sannan ya kalli agogo salma ni zan wuce ina da meeting amma insha Allah zan dawo salma ce ta juyo to shikenan alhaji sai ka dawo idan kuma mun koma gida sai na kiraka nagaya maka da haka sukai sallama.....
Karfe 9:00 jannat zaune akan gadon da abaya a jikinta kallo daya zaka mata kaga ta rame sallamar da akayi ce ta katse mata tinani tare da dagowa hajiya mamace sai hidaya da zeeyah da fara'a jannat ta amsa tana kwala kiran ammy data fita shan iska zama sukayi yayin da salma ta shigo dauke da fara'ar ta suka fara gaisawa hidaya ce ta matsa kusa da ita bayan ta mata yajiki suka bude sabon shafin hira dr sageer ne ya shigo dubata har yana mamakin wannan cuta janta yake ita dae jannat murmushi kawai tayi masa kara ma hidaya ta biye masa....
Hajiya saudatu sai alhaji attahir sun fito da shirin su na tafiya asibiti domin dubo lafiyar jannat abin mamaki haidar ne zaune a falo sanye da ash din yadi dinkin jamfa Kai ko hula babu sai da ya Taje sumarsa yana hangosu ya tashi sai da sukazo ya tsugguna ya gaishe su sannan yace abeeh muje na rakaku da murmushi a fuskarsu suka nufi waje......
Bangaren amare yau antashi a gidan aure raidah ce kwance akan gado sai jan tsaki take aikin banza aikin wofi wannan ai iskanci ne in banda rashin mutunci mutum idan yasan yayi barna ba sai ya gyara ba wallahi wallahi zai dawo ne bani ba shi dik jarabarsa sai dai yayi juyawar da zatayi sukai ido biyu da muazzam zaro ido tayi ganin ya nufota daga shi boxer a hankali ta furta na shiga uku bakina yaja mini......
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
74&75
Jannat sai hira suke zubawa ita da hidaya dr sageer ne daya gama duba jannat ya tabbatar ba matsala ya basu sallama nan da karfe 10 zasu tafi shisa hajiya mama ta tsaya su tafi kawae sallamar abeeh ce ta katse musu hirar ta su da fara'a salma ta amshesu kujera ta basu suka zauna aka fara gaishe gaishe jannat ce ta juyo wajen saudatu da abeeh ta gaishe su cike da kulawa suka amsa sallamar haudar ce ta katse musu hirar.......
Dakin ya shigo yayin da kan jannat ke kasa tana wasa da 'yan yatsun hannunta cike da fara'a haidar ya gaishe da hajiya mama da salma suka amsa shiru yayi ana kallon kallo salma ce tace ke yanzu jannat kina ganin mutane shine ko gaisuwa da kyar jannat ta daga kanta kadan ya haidar ina kwana amsawa yayi lafiya lau jannat ya jikin da sauki ta bashi amsa saudatu ta tashi ta basu wuri ita da mijinta ganin haka yasa hajiya mama da salma mikewa jannat aka bari daga ita sai hidaya ganin hidaya na kokarin mikewa yasa ta riketa dagowa hidaya tayi ta furta a hankali ke toilet zan shiga pa sakinta tayi aka bar su a dakin dagashi sai itasai karar ac dakin dake aiki.......
Zainab zaune akan kujera a falonta fitowar jafar ne yasa ta kara kwanciya akan kujerar jafar ne ya matso honey kin mana breakfast ne tabe baki zainab tayi kut ni zan maka girki yau kwana na 1 acikin gidan nan Wallahi beb inma zaka samu mai mana girki ka nemo dan ni ba'a kawo maka ni dan nai maka bauta ba ehee kallinta jafar yake cike da mamaki wucewa yayi yana murmushi lalle yarinyar nan sai na fito miki da asalin kalata wallahi zaki gane......
Jin shirun yayi yawa ne yasa haidar fadin ya jikin naki da sauki har ma anbamu sallama anjima zamu koma gida gud kawae yace sai kuma ya kwantar da kai a kan kujerar da yake kai ya na tinani can kamar wanda aka zabura ya dago jannat kina da passport ai ko daga kai tayi take idanunsu suka makale da juna wajen 20sec jannat ce tai kokarin janye idanunta tare da bashi amsa ea ya haidar da haka ya kara ce mata allah ya sawwake amma ki shirya nan da ranar Wednesday zamu tafi America ki shirya dagowa tayi tace ya haidar kallonta yayi tare da furta yes!! Da haka ya fice........
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
76&77
Bayan tafiyar su haidar jannat ce ke kuka wiwi harda tirza kafa nashiga uku ammy wai ina zai kaini ne ni wallahi bazan bishi ba,ba inda zanje,shi din wa ma zan bisa haba ammy wayyo allah na zan tafi na barki ni gaskiya tsawar da salma tayi mata ne yasa ta yin shiru cike da zafi ta fara fada ke jannat wai yaushe zaki hankali shin baki yadda da kaddara bane kisani wallahi wallahi jannat zanci mutuncinki yanzu pa ba da bane nagaya miki wallahi hajiya mama ce ta fara bata hakuri da kyar tai shiru a haka suka fara shirye shiryen tafiya gida jannat ce ta kalli hajiya mama amm hajiya yau ba monday ba murmushi tayi eaa mana jannat lafiya dai koh daga kai kawai tayi.......
Raidah ce zaune akan dining tana breakfast ba abinda ke tashi karar tv datake dakin knocking din data ji ne yasa ta sakin tsaki cike da masifa tace ko ma waye yashigo mana turo kofar akai su maymun ne da zulaihat sai deejah cike da fara'a ta tashi ta tarbesu harda tsalle maymun ce ta tsaya tana kallonta yayin da zulaihat taja ta gefe wai ke raidah bakya jin zafi ne shine kike tsalle washe baki raidah tayi wane irin zafi bayan wancen jarababben ya gama dani ke ni pa maganin da ammah ta bani ya mini aiki wallahi shewa suka sa suka tafa ita da zulaihat........
Jannat harsun dawo gida zaune take a dakinta tayi shiru ta saka wancen da kunce wannan sallamar da akayi ce tasa ka ta dagowa da sauri domin rabon da taji wannan murya a dakinta tin tana karama tashi tayi tana fadin dad sannu da dawowa alama yayi mata ta zauna zama tayi akan drawer gefe shikuma ya zauna akan gado jannat ya ambaci sunanta dagowa tayi jannat karkiga kamar ban miki adalci ba jannat,tabbas ina sonki kuma nafisonki dik cikin yarana saboda kece yarinyar da kike da hakuri ba kya kula kowa koda wani yayi miki abu jannat kina cewa a rabu dashi jannat ki taimaka min jannat karki ce bakyason wannan auren jannat saboda nasan na isa dake ne kuma nasan cewa tabbas zaki min biyayya amma kiyi hakuri jannat shiru jannat tayi dagowa da zatayi ne yasa ta ganin kwallah a cikin idanunsa rungume sa tayi tana kuka kayi hakuri dad na maka alkawarin bazanki wannan auren da ka dauramin ba dad na yadda dakai nasan bazaka Cutar da ni ba amma ka daena kuka a haka sai da suka gama kukan su sannan yasata dariya suna ta hira waya ya janyo yace jannat sai kuma ya fasa maza dakko hijabinki ki rakani yi sauri tashi tayi ta saka suka fito a lokacin karfe 7pm......
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
79&80
Zulaihat basu suka baro gidan Raidah ba sai 7pm shima mijinta ne ya kawo shi kuma ya wuce uzurinsu suna shiga direct part din su suka nufa suna shiga kowa ya jabe akan daudar da ba mai gyarawa sai maymun da kwana nan dakin ya danyi haske dawowarsu......
Jannat ce biye da dad mota suka shiga bank suka nufa a take a wajen aka bude mata account zuwa nan da 24hrs su dawo su karbi atm ita dai jannat mamaki takeyi sun fito jannat ce ke tambayar dad meyasa ka budemin account kuma dariya yayi yace saboda kawae akwai abinda zan saka miki da haka suka nufi katon shop na sai da wayoyi da laptops ciki suka shiga ya jata dai dai wajen wasu wayoyi ya tsaya yana dubawa kallonta yayi tou duba kizabi daya cike da dariya tace allah dad nazaba gyada mata kai kawae yayi cike da zumudi ta dauko wannan ta maida ta dauko wannan ta maida da kyar ta zabi wata iphone modern design silver sai ya tabbatar tayi mata sannan suka tafi wajen payment ya biya a wajen har powerbank ya siya mata shima silver har ya fito sai kuma yayi wani tinani cike da kula yace shiga mota gani nan yanzu zan dawo .......
Bai fi 2minut ba ya fito rike da wani Katon kwali sai wani karamin kwali guda biyu shiga dasu yayi dika ya mikawa jannat,jannat tsayawa tayi tana kallo tana rmta dariya can sai ga hawaye tana daga katon kwalin dad ka siyamin laptop harda sims dad allah ya buda maka a koda yaushe yaja min da ranka kaji dad na amsa mata yayi da ameen ganin basu dauki hanyar gida yasa ta cewa dd mutafi gida mana ko siyayyar ta isa haka dai dai wani boutique aka tsaya jannat ce ta riko hannun alhaji jalaluddeeen dad please kabarsu haka ka kashe kudi dayawa dad ina da kayan sawa da yawa dad kallonta yayi yace jannat kisani yanzu kin fita daga hannuna kinyi aure jannat dan haka komai zan miki ban fadi ba jannat fito muje badon tasiba ta fito suka shiga a kalla sai da ta zabi kaya sets 20 sannan ya biya suka taho gida suna sauka yayi hanyar dakin sa juyowa jannat tayi dad to kazo muje kagani mana cike da murmushi yace toh karki damu gani nan ke ma ki sallah kinji toh tace tashige falonsu ganin ammy yasa ta zube mata kayan ta wuce dakinta.....
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
80&81
Tana idar da sallah ta fito tana ta dariya salma ce ta kalleta tace aa ni da wash dik murnar siyan kayan ne jannat ce ta matso ea mana ammy haba dad ya kashe kudi mom tsaya ki gani ta dauka kenan ta hango ammar ya taho kiransa tayi ammar zo ka gani kaima wayar ta bude har daukar ido take karba salma tayi tana dubata salma ce ta bude sim din tasaka sai kuma ta bude kwalin laptop din cike da murmushi take kallonta silver mikawa salma tayi ammy kalli kiga karba tayi sai suka gama gani sannan suka dawo kan kayan nata salma ce bayan haka ta zauna tai mata nasiha mai shiga jiki a haka dad ya shigo ta kara nuna masa daga karshe tai masa addua da godiya ta hade kayanta tayi dakinta......
Haidar zaune akan gado hannu daya cigarette ce kesha tsaki yaja sai kuma ya tina gobe zaije yayi wasu cike cike jibi su bi flight din dare su isa America tashi yayi ya dauko giya ya koma gefe yasha yasha ganin kan yaki daukar chajine yasa shi dauko hodar wiwi ya fara shakwa kankace kobo ya fita da hayyacinsa......
Washe gari jannat bata fito ba sai 9 har tayi wanka fitowa ta tarar da kowa a falo zama tayi itama ta zuba abinci ta faraci mansura ce ta kalleta ta watsar can ta budi baki ke kuma ya jikin kallonta tayi tace ai naji sauki da haka aka gama kowa ya watse jannat ta nufi daki.....
Akwatinta ta janyo ta fara zabar kayan tana yi tana hawaye domin tafison ta zabi komai kan lokaci ya kure mata sallamar haidar ce ta katseta ji tayi suna gaisawa da ammy shiru tayi a zuciyarta tace me yakawo sai maganar salma tajiyo tace tana daki ka shiga mana haidar da haka ya nufi dakin yana shiga ya ganta ta juya baya tana linki sallama yayi mata amsawa tayi tare da juyowa jannat ce tai masa sannu da zuwa ya haidar ka zauna ta nuna masa wata 1 setter dake dakin haidar ne ya zauna ita kuma taci gaba da linkinta wasu ta zuba a akwati wasu kuma a wardrobe.....
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
82&83
Maganarsa ce ta katse ta wannan kayan kuma da kike hadawa pa shiru tayi kamar bazatayi magana va can kuma ta dago ya haidar dama kacemin gobe zamu tafi ne shisa nake hada kayan tabe baki yayi tare da cewa allah ya kyauta jannat ya ambaci sunanta dagowa tayi naam ya haidar kiyi hakuri kinji dagowa tayi ya haidar da me kuma kawai tashi yayi yace ni zan tafi gobe zan zo idan mun tashi sai mu wuce dai dai lokacin idonsa ya sauka akan bed dinta waya yagani da labtop matsowa yayi yagani dagowa yayi jannat waya saya miki cike da mamaki tace daddna yace allah sanya alkhairi ya wuce abinsa......
Raidah ce zaune akan kujera knocking ake tashi tayi taje ta bude me zata gani kannen muazzam ne tsaki taja kawae tace ai sai ku shigo ba wanda yace ta tafasa suka shige sai da suka zauna sannan suka fara gaisheta....
Zama yayi akan kujerar falon tare da furta wash allah mah nagaji daga kai saudatu tayi ta kallesa yayi kyau kaje wajen jannat din sosa kai yayi eaa mah daga can nake shikenan ka kyauta haidar allah ya sanya alkhairy ameen ya bata amsa tare da tafiya daki yana sosa kai......
Washe gari jannat ce zaune akan gado tayi shiru shivowar ammy ce tana cewa yau jannat ki shirya mana me kike haka dagowa jannat tayi sai ga hawaye sharr a idanunta da sauri salma ta nufeta lafiya jannat me ya faru jannat ce ta rungume salma ammy banaso natafi na barki ni nafasa tafiya ammy dan allah ammy toh kizo mutafi mana dagota salma tayi kai jannat ki kula mana yanzu tashi kije ki wanka yanzu maza tashi.....
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
84&85
Haidar kwance yana sharan bacci akan bed wani juyi yayi yaji muryar mah tana knocking badan yasoba ya tashi ya nufi kofar budewa mata yayi ta shigo a falonsa ta zauna shima zama yayi haidar karfe nawa yanzu dube dube ya fara ta dakatar da shi da cewa karfe 12:00 amma kana kwance kana baccin asara wai haidar mai kataka ne ba yau zaka tafi America ba amma me ka kwanta kai ta bacci ko dan nasani kaje kayi shaye shayen naka shine kazo kana bacci ko haidar dagowa yayi yana kallonta ka hada kayanka shiru yayi yana kifkifta ido kamar munafiki cikin daga murya ta kara tambayar sa aa ya bata amsa ok gud haidar ka kyauta tashi ka bani guri kafin nan da 2:00 ka tabbatar ka gama komai magana zaiyi ta dakatar dashi tare da tashi ta fita.......
Salma zaune a falo tayi shiru jiran fitowar jannat take bata tsinkaya ba taji muryar jannat tana ammy kidaina kuka kinji dan allah kidaina kuka da sauri ta goge hawayen fuskarta tare da kakalo murmushi tana kallon ta kinyi kyau sosae my jannat allah ya baku zaman lafiya kinji yanzu dira mayafin aka zamu je wajen dadynki kinji toh tace tare da yafawa suka tafi bangaren alhaji.....
Huduba alhaji jalaluddeeen yayi mata mai ratsa jiki da kuka suka rabu dashi sannan kuma hidaya ta tako tazo ta kama hannuta mama bara muje sauran part din ko shikenan kuje hidaya cewar ammy part din mansurah suka shiga neman wajen zama sukai suka rasa ba wanda ya kulasu kasabcewar maymun bata nan da haka suka tafi part amina ita ma dai ai sha,ani tafi dai mansura...
Karfe 4 jannat tsaye a gaban mota sai sharar kwallah take tana kewar ammynta da suke makale da juna da kyar dad yayi wa salma magana da taimakon maymun suka rabu da juna sai kuka suke da haka jannat da haidar sai yan rakiya suka nufi hanyar filin jirgi a can ma din jannat bata fasa kukan ba cikin idanunta sunyi jawur da haka lokaci yayi suka tafi tare da alkawarin zasu zo ba dadewa ba jannat tana tafiya tana waiwaye a haka harta bace musu....
Jannat kuka take sosae ganin haka yasa haidar janta gefe tare da daka mata tsawa jannat zan mareki wallahi me nayi miki kike bina kina kuka ko namiki dole sai kin biyoni ga hanyanan zaki iya wucewa ki koma mana haba yarinya sai kafar kai wucewa yayi ya barta yayin data tsagaita da kukan harta juya sai ta tina da maganar mahaifinta da sukai jiya ala dole ta huce ta bishi lokacin har ya nemi wajen zama duba kujera take anan taga wata kusa da wata ta zauna a haka suka daga sai America.........
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
86&87
Zainab ce kwance akan sofa gefe daya wasu yara ne suke kirina sai magana take musu sunyi banza da ita sun ci gaba a zuciye ta miki ta ciro soket din gefenta ta janyo tayo kansu ta fara zabga musu soket din nan sai da ta zanesu dik ta farfasa musu jiki....
Jannat ce rike da akwatinta tana kokarin ajiyeta a dakin da haidar ya nuna mata nata tsayawa tayi kallon daki ta shagala kawai taji kiransa ba yadda ta iya ta fito tazo a zaune ta gansa itama zama tayi a daya da kujerun dakin numfasa wa yayi wannan shine gidan namu sannan baki san kowa ba ya zama ki zauna anan banda yawo jannat sannan banason bin makwaftan nan nasan wasu dik hausawa ne yana zuwa nan ya tashi yayi ficewarsa bata damu ba ita ma ta tashi ta fara zagaye gidan.......
Karar motar jafar ce taja hankalin zainab tsawa ta daka musu take suka rufe bakunan su sukai shiru shigowar jafar yayi dai dai da nufo kofar yana shigowa ta rungume sa hade da kiss murmushi yayi mata tare da nufa hanuar dakinsa ko ta kan yaran bai bi ba....
Jannat bayan ta zagaye gidan dakinta ta koma sai da takira ammy suka sha hira sannan ta kashe har ta ajiye wayar sai tatina da number maymun wayar ta dauka tai dialling number bugu daya ta dauka sai da suka dan taba hira tare da bata shawarwari gareta musamman kan mijinta da yadda zata kula dashi sannan sukai sallama tana ajiye wayar karar shigowar haidar taji tashi tayi ta fita rike yake da leda a hannunsa zuwa tayi ta karbi leda tayi masa sannu da zuwa sannan ta tafi kitchen din data gani dazu ta dauko plate sannan ta fito sai da sukaci abincin sun dan dade a zaune haidar ne ya tashi tare da mata sai da safe itama tashi tayi ta kashe tv din ta nufi nata dakin............
Jafar ne ya fito ganin yaran a shiryene yace musu ku taho mu tafi koh bai kula da abinda zainab tayi musu ba haka suka tashi sumi sumi suka fita suna fita zainab ta tabe baki wallahi bazaiyu ba ban haifi yara ba suzo su takuramun daga yanxu dik yaran daya kara kawomin wallahi haka zan musu eheee babbakewa tayi da dariya ta tashi........
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
88&89
Washe gari jannat ta tashi sai da tai wuridinta kamar yadda ta tashi sai wajen 9 ta fito kitchen ta shiga sai da ta hada breakfast mai rai da lafiya sannan ta shige dakinta sai da tai wanka ta saka daya daga cikin kayan da dad ya siya mata sannan ta fito har 10 haidar bai fito dakin nasa ta nufa a hankali ta bude kofar ta leka a dunkunkune ta tarad dashi gefensa ta koma ta leka fuskarsa ganin bacci yake sosai ne yasa ta fara kokarin tashinsa juyawar da zaiyi ne ya ganta a kansa tashi yayi ya fara balbala mata masifa ke angaya miki ana tashina ne wallahi daga yanxu indai ki ka kara shigowa dakin nan batare da izinina ba wallahi sai na saba miki dallah tashi kifita stupid girl jannat kwallah dake kokarin boye wa ce ta gangaro mata tana kokarin tashi wato kuka ma kike ko daga miki magana wallahi zaki kuka mai dalili ko ba ni ba ita dai jannat fita tayi......
A haka rayuwa tana tafiya kenan da auren su jannat n hanga a kitchen ba laifi ta rame amma ba sosae ba sai wani fari datayi zaune take shigowar haidar ne yasa ta tashi cike da murmushi amma me ganin yana tangadi yasa ta ja dabaya tare da cewa ya haidar kace fa kadaina wannan dabi'ar bai saurareta ba yayo kanta tsalle tayi ta gudu dayan gefen kuka ne ya kwace mata dole ta matsa kusa dashi tana taba sa yaya haidar please why ya haidar kace min kadaina taya haka kuma kukan ne ya kwace mata kallonta yayi ya tallafo fuskarta yana kallonta cikin muryar maye ya ce nifa inasonki jannat kawai bazan iya daina wannan shaye shayen ba jannat ce tace ya haidar zaka iya mana zaka iya jin shirun dayayi ne yasa ta dagowa a kwance ta gansa alamun yayi bacci zama tayi anan tana kuka tana tina shawarar da ammynta ke bata gashi tanasin komawa makaranta yanzu ya zatayi.....
Yau tin safe jannat na falo a zaune tana jiran fitowar haidar yana fito sanye da shirinsa na fita ganinta ne yasa ya nufo falon ya zauna gaisawa sukayi cike da fara'a har ya tashi zai nufi dining jannat tace yaya haidar ya zancen school din murmushi yayi ya juyo ea ni na manta ma kuma bara naduba email dina nagani dubawar da zaiyi ne ya gani anyi approved kallonta yayi yace jeki shirya kinga sunyi approved tin jiya da daddare da murna jannat ta mike hade da 'yar kara laa ya haidar rungume sa tayi sannan ta sakesa ta wuce dakinta ta shiryo ta fito......
Breakfast kawai sukayi suka dau hanyar makarantar tasu ba nisa da gidan nasu dan a kasa ma zata iya zuwa ta dawo a kasa har wajen shugaban makarantar ya kaita yayi masa bayani sannan yayi mata registration suka fito cike da murna jannat ta kama hannunsa thank you ya haidar thank you so much allah ya taimake ka yaya da haka sukai sallama ita kuma ta nufi ajinsu na mass communication.....
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
90&91
Ammy kuwa kullun sai sunyi waya da yarta alhaji ne suka yanke zuwa America shi da amininsa attahir sai matayensu murna wajen salma kamar ta matso da ranar......
Jannat a hanyar ta ta dawowa daga school ne taji wayar hannunta tayi kara dubawa tayi ashe alert din kudine daga mahaifinta cike da murna ta kirasa a waya bayan sun gaisa take gayamasa taga kudi Murmushi tayi kawai tace nagode daddy allah ya kara Budi dad ina hanya ne idan nakoma zan kira ka kashe wayar tayi kit tai gaba.....
Salma sai shirye shirye take komai ta samu jannat bayan kwana 2 suka hau flight dirar bazata zasuyi musu dan ba wanda yasan ma zasu zo a cikinsu jannat na zaune taji knocking iya saninta tasan idan haidar ne zai bude kawai ya shigo batare dal tinanin komai ba tana budewa tayi turus tana kallonsu ganin kamar mafarki take tasa ta kara murza idanunta murmushi salma tayi to jannat matsa mana hanya mu wuce mana cike da fara'a ta matsa suka shige su dika sai murna take ta rasa ina zata saka kanta idan tayi nan sai ta dawo tayi nan ko zama batayi ba sai da ta kira haidar ta sanar masa da zuwan nasu batare da bata lokaci ba haidar ya iso cike da fara'a shima.....
Sai da suka gaisa da su dad sannan haidar ya kalli saudatu mah ya hanya dafatan komai lafiya lokacin jannat ta shiga kitchen salma kuma tana can wajen 'yar ta suna hirar yaushe gamo su kuma su alhaji attahir sun fita daga gidan sun tafi uzurinsu.. Jannat ce ta kalli salma ammy wai shi ammar wannan wane irin bacci ya tara ne har yanzu pa bai tashi ba salma ce ta kau da maganar da jannat ya zaman gidan kinajin dadinsa kuwa dagowa tayi da dan murmushi eaa ammy ya haidar yana kulawa dani dafata tayi jannat tabbas kin dau hudubar da nayi miki allah yayi miki albarka kinji allah ya baku zuri'a dayyiba a haka suka gama jannat ce ta shirya su a dinning din dakin sannan taje ta tashi ammar yana kallonta yana dariya laa addah dariya tayi masa sai da tayi masa wanka ta shiryasa sannan suka dawo falon a lokacin alhaji attahir sun dawo sannan aka zauna ana cin abinci......
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
92&93
Jannat ce zaune tsakiyar salma da ammar sai hira suke sallamar alhaji ne ya katse su yasa jannat tashi ta koma wata karamar kujera ta zauna tare da gaishe da dad tayi masa godiya sosai dariya yayi jannat ya makaranta dad ina zuwa kuma ina gane karatun shikenan jannat allah ya kara basira ya zaman gidan fatan ba matsala eaa dad ba matsala komai lafiya lau dad kuma ya haidar yana kulawa dani kaga shi ya kaini makaranta kullun shi yake kaini ya dawo dani dad ba wata matsala jannat ce ta janye hirar tare da tambayar 'yan gida.....
Saudatu ce ta matso kusa da shi yanzu haidar baka fasa wannan halin ba haba haidar haba haidar ya kakeso muyi kuma kaduba jannat yarinya mai hankali hakuri da mutunci yakamata ka gane haidar amma har yanzu kanayin abinda kake ya allah alhaji attahir tashi yayi ya bar wajen cike da bacin rai saudatu saida tayiwa haidar nasiha mai shiga jiki sannan sukayi sallama ta tafi dakinsu da aka basu.........
A bangaren jannata fitowa tayi tare da yiwa su dad sallama tana fitowa ta fara sake saken to yau akeyinta yanxu ina zan dosa kenan tana wannan tinanin ne ta karaso falo a zaune ta tarad da haidar yana hawaye matsowa tayi tana tambayar aa lafiya jin shiru ne yasa tace haba ya haidar kamar ba na miji ba kaadaina kuka komai akwai lokacin sa kaji dagowa yayi tare da kallonta mai ya fito dake dariya tayi ya haidar su ammy ne a dakin pa yanzu sai dai nakwana a falo kai kaje dakinka kawai kamar ya ya tambayeta eaa mana ai kace nadaina shiga dakinka ta bashi amsa shiru yayi can yace tashi muje ki kwanta yau na yadda dariya tayi ta tashi dakin suka shiga bargo ya dauka ya haye katuwar kujerar dake kusa da gadon ita kuma jannat ta haye gado tare da jan dogon numfashi tana shakar kamshin turaren sa saboda haidar badai tsafta ba.....
Ganin dakin a rufe ne yasa jannat tafiya duniyar tinani wai shi yaya haidar baya da feelings ne wata zuciyar ce tace mata yana dashi mana amma mai yasa baya nunawa tsaki taja jin tinawa da lafazin da yayi mata cewa ita yarinya ce mai zai tsinta a wajen ta tsaki taja da yayi sanadiyar maganar haidar lafiya dai ko jannat eaa ta bashi amsa da haka bacci ya saceta.....
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
94&95
Washe gari can na hangi jannat sai hada kaya akeyi iya kayan sawarsu karfe 11 sun bar gidan sun shiga mota wata unguwa suka nufa tafi wadda suka baro kyau da tsaruwa hatta gidajen unguwar daban suke abin sai wanda yagani nakasa kwatanta muku wannan gida dai dai kofar gate din mai kyau karami motar ta tsaya......
Zainab ce rike da jaka a hannunta tana janta ta baya tana kallon hajiya mama a falo tai banza da ita ta wuce ta doshi falonsu tana shiga Mansura ta tarar dai dai nan mansura ta dago ta ganta da akwati budi baki tayi zatayi magana zainab ta zauna da kyar mansura tace mai ya dawo dake ammah ni nagaji da zaman gidan can karshe ma kinga yace ya sakeni dafa kirji mansura tayi saki kuma zainab har nawa daya ta bata amsa tare da hawa kujerar wajen ta kwanta abinta tana karkada kada........
A cikin sati daya komai ya faru a haka har da dawowar su daddy daga america bayan sun chanja musu gida hade da bawa Jannat mota zuwa school amma bata iya ba dan haka tashiga makaranta koyar da mota kullin idan ta dawo daga Makaranta nan take zuwa alhaji jalaluddeeen ko da dawowar sa ya iske zainab a gida dalili ya tambayeta kafin rayi magana mansura ta mika masa takarda hade da balbalesa da bala'i kallonsu yayi kin kyauta amma duniya ce zaki gani mansura zatayi magana ya tashi ya bar mata wajen.......
Bayan wata daya a lokacim jannat har ta iya tuki kullin a motarta take zuwa ta dawo a motarta kamar kullun yau tana cape tana shan lemonade aai kuma ta fada duniyar tinani yanzu ace watan mu 5 da aure ba abinda ya shiga tsakanina da yaya haidar to ko bashi da lafiya ne tsaki taja da furta no no ba haka bane to kodan yana smoking ne yasa baya bata karasa ba ta tashi tare da daukar karamar jakarta ta fito ta shiga mota kenan wayarta tai kara number haidar ce tagawa tayi sai ji nai ta ambaci wane asibiti katse wayar tayi ta nufi hanyar asibitin......
Ra'ida ce zaune akan kujera da kayan ciki a gaba kai kace yayi wata 7 din nan katoto muazzam ne a gefe yana chatting a wayarsa kallonsa tayi ta tabe baki can kuma tace darling ka manta ne dagowa yayi na manta da me pah kace pa zamu fita cewar ra'ida shikenan ya furta tashi kije ji shirya ki fito kinji amaryata murmushi tayi ta tashi........
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
96&97
Tana shiga asibitin reception ta nufa aka fada mata number dakin da yake sannan ta tafi dakin a kwance yake kansa nade da bandage sai hannunsa shima da bandage sai kananan ciwuka a jikinsa kwallah ce ta zubo mata dai dai nan nurse ta gaya mata doctor na nemanta a lokacin ta shiga office din.....
Bata dade ba ta fito ta shigo dakin tama rasa ya zatayi fitowa tayi daga asibitin a gaggauce ta tafi gida sai da ta hada komai na abinci sannan ta dawo har lokacin bai farka ba amma sai taga doctor a kansa har likitan ya wuce sai kuma sukaji motsinsa waigawa likitan yayi sannan ya juyo good sannan ya wuce ita kuma ta karaso ta rike hannun sa wanda ba bandage tana murzawa a hankali tana mai ambata masa sannu to yace a lokacin ne ma wayarta tayi ringing cikin nuna dakiya haidar yace karki gayawa kowa cewa ina asibiti kinji my jannat please shiru tayi tana shafa masa suma sai ga hawaye sharrrrryana zubowa alama yayi mata da zai tashi murmushi tayi kawai ta gyara gadon zaune yake yana mai rarrashinta.....
Kwanan haidar 4 aka sallamesa a lokacin suka koma gida gaba daya jannat ta dawo dakinsa ta tattare shi kansa haidar baya san ganin jannat tayi nisa dashi ko kitchen taje sai ya bita wata sabuwar soyayya ta shiga tsakaninsu cike da kulawa da shakuwa yayin da haidar ke ta samun sauki da kulawar jannat abin mamaki yanzu ya daina wannan shaye shayen da taimakon addua jannat tina maganar likita ne yasa ta debe kayan dika ta zubar dasu haidar kuwa ko ta kansu bai kara bi ba da zarar lokacin sallah yayi haidar zakiga yayi alwala ita haka kuma jannat........
Bayan wata hudu jannat na hango a falonsu sai guje guje suke tayi kyau ta kara fari tayi kiba fuskarnan kamar ka mintsina jini yafito yayin da haidar ke binta a baya da kyar haidar ya kamata ya rungumota yana cewa yesss nakamaki bani abuna turo baki tayi to ya haidar ka sakeni mana zan baka ai dariya yayi tabb my jannat ni zaki yiwa wayo ko to wallahi baki isa ba bani abuna da kyar ta samu ya saketa suka zauna akan kujera sunata dariya can haidar ya kamo hannunta tabbas jannat ke alkhairi ce a gareni ina matukar kaunarki sumbatarsa tayi a kumata ta tashi ta fada daki binta yayi a baya.......
Zainab kuwa maganar sabon aure takeyi zata auri wani soja shikuwa dad cewa yayi yanda tagani a haka aka daura aurenta da sojan aka kaita gidanta.......
JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
98&99
Cikin bargo na hango jannat yayin da haidar na tsaye gaban mirror yana taje sumarsa juyo yayi jannat yadai ki yashi mana y mutsa fuska tayi kaida kawai kaje ni sai anjima zanje school kallonta yayi kenan yau ko rakiya babu juya masa baya tayi karasawa yayi ya janyota lafiya dai ko jannat kallonsa tayi ta sumbace sa a goshi bye mijin jannat kiss yayi mata ahima ya fita ita kuma ta juya ta lumshe ido tana tina rayuwar da tayi a baya......
Zainab ce tsugunne akan gwiwowinta tana raba ido belt ta hango a hannun sale ya nufota tin kan ya karaso tasan yau kashinta ya bushe dukanta ya fara yi dik inda ya daka sai jini ya taru sai da yayi mata mai isarsa sannan ya kalleta gobe ki karamin girkin da bance kiyi min ba shashasha kawai ficewa yayi ya fita ya barta waya ta dauko tayi dialling number mansura......
Haidar har ya dawo jannat ko tsinke bata daukeba tana kwance tanda ya barta cikin bargo ganin tana bacci ne yasa haidar yi mata aikace aikacen harda girki sannnan ya tasheta taba jikinta yayi yaji zafi da kyar ya lalkabata tana rigima ya dauketa suka tafi asibiti gwajin farko ya tabbatar da tana da ciki zo kaga murna wajen haidar da jannat suna dawowa gida haidar ya dauki waya dakatar dashi jannat tayi ya haidar mai zakayi fadawa mah zanyi jannat ce tace aa kabari muyi musu surprise koh ya haidar eaa kuma fa hakane my soul lumshe ido tayi ta zauna yanzu mai zaki ci ne.........
Raidah ce zaune a gadon asibiti gefe kuma yarinyar tace da ta haifa jiya mai cike da kyawu da kaganta kaga ubanta dangi ancika dakin kowa fuska dauke da farinciki.....
Zainab kuwa wuya takesha a gurin sale yau kuwa ganin hannunta nayi a sale ta kone wajen ya tashi gashi ta rame dik ta zuge dik iyayin zainab babushi ga daula har daula amma ba kwanciyar hankali tana daki a zaune take zuciyarta take tino abinda ta aikata ta tabbata alhaki ne wannan........
🍃JANNAT🍃
Written And Narrated
By Auntynmu😍
100
Bayan kwana 7 yarinya taci sunan ta Hannatu suna mata lakabi da hannah raidah ta nemi yafiyar salma mahaifiyar jannat saboda ta gane kuskuranta ta dawo da cewa ita sai ta sami aiki...hidaya kuwa anan take karatu a wata private university ita da deejah.....
Bayan watanni 8 jannat ce zaune a gadon asibiti tana sharar bacci gefe kuma haudar ne rike da jariri sai kallonsa yake sak yaran kamarsa ya dakko ba abin da ya bari nasa gadon naga ya nufa ya ajiyesa kusa da wani mai kama dashi din yana shafa yaran karar wayarce yasa shi fitowa reception abin mamaki mah ce da salma fuskarnan cike da annuri dakin suka shiga inada alokacin jannat ta farka taga amminta yaran suka dauko tare da furta masha allah allah ya raya mana mah ce ta kalli haidar tace kamarku daya.....
A ranar aka sallami jannat bayan kwana 4 suka koma Nigeria anan za ayi nadin suna a ranar suna yara sukaci Attahir da jalaluddeeen za a na kiransu da Abeeh(junior) da Daddy(junior) raidah sai da tazo wajen jannat ta bata hakuri matuka akan abinda ya faru jannat ce tace ai bakomai aunty raidah komai ya wuce kuma ni ai na yafe miki ma tin a lokacin da haka mutane sukai ta shigowa barka zo kaga bakin ciki wajen mansura ga zainab jabe a gida ta gudo daga gidan soja gashi ya biyota ma da takarda ta tasaki abin duniya ya ishi mansura daga baya kuma tzo tasaki fuska akai komai a cikin kwanciyar hankali......
Jafar ne zaune gaban Dady yana basa hakurin abinda ya faru dad ne ya numfasa bakomai jafar hakan da kayi shine dai dai insha Allah anjima za a daura auren karka damu bai shawara da kowa ba yana fita sallar isha'i aka mayar da auren zainab da jafar sai da yazo yake fada musu karkaga farinciki wajen zainab da mahaifiyar ta.....Washe gari tin da safe zainab aka maida ta dakinta yayin da haidar ya sa ranan da zasu komai America saboda karatun jannat dashi kuma da sikeso su karasa.......
Bayan shekara Biyu jannat na hango sanye da kayan lawyer a cikin gidan ta gefe kuma wasu yara na su biyu wadda tafiyar tasu ma baymtayi kwari ba sai haidar da yake tayi mata hoto tana dariya cike da farinciki da annushuwa tana dariya matsowa yayi kusa da kunenta ya rada mata my soul yakamata yau pa bai karasa ba jannat ta hade rai dole ya fasa wani yaro ne ya taho cikin gwaranci yake magana bazan ce ga abinda yace ba.......
Tammattt anan nakawo karshen wannan littafi har kullin nice taku Auntynmu ga masu buqatar wasu zafafan littatfan ku tuntubi wannan number kai tsaye 08067574868
Ina godiya ga wanann kungiya king and queen writing chamber har kullin ina godiya ga abdulkingarticle da kuma kawata kulsoom Ismail (mr baba bello abubakar)
Wannan littafi na sadaukarsa ne ga masoyana masu bibiyana har kullin ina alfahari daku......
0 Comments