WA AT (Book 2)

            




 BY KULSOOM ISAMA'IL PART TWO

Na Sadaukar Da Wannan Littafin Ga Kanne na Da yayyena.

Banyadda wani ko Wata ba ya sauya mun Labari takowace siga.

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
Assalamu Alaikum.
Fans Barkanku Da Safiya Inayiwa Dukkan Daukacin Masoyana Masu Bibiyar Littafin WA'AT barka da Sallah.
ALLAH ya Maimaita mana.Saboda jindadin ku yau In ALLAH ya yarda Gani dauke da Cigaban Littafin WA'AT PART TWO Asha Karatu Lafiya.
               WA'AT

By Kulsoom Ismail
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
         PART TWO
Chapter 1
      "Suna shiga soro su kaci karo da Appa Cikin Sauri suka Duka har kasa Suna gaidashi kare musu Kallo ya tsaya yanayi ransa na sake baci sai hura hanci yakeyi Mtswww yaja tsaki da Kuka taho rikici rikici daga gidan Ubanwa kuke koko yawan maular Kuka tafi dan ansha gayamin kullum sai Uwarku ta turaku yawon Maula kwararo kwararo Lungu Lungu kuna Zubdamin Mutunci, ni wannan sauka ficikata Wallahi bazatai ciwon kaiba shinkafata ko kwaya daya bazanyi asararta Inda bazan maida asarata ba yadda Kuka taro Jama'a sai dai kuji kunya munafukan banza munafukan wofi kudinga sunkui dakai kamar Mutanan Arziki kini babbu"
     Ku tashini ganin kuma sake batan rai yakeyi kuma ko awajan sauka akace kununa Ubanku Kuka nunani Wallahi na Lahira saiya fiku  jindadi danma Malam ya takuramin mezanje nayi aikin banza kawai Dallah kubacemin agaba na WA'AT sarkin Kuka tuni Fuskarta ta gama jikewa da hawaye sosai Abun yake Mata ciwo wucewa suka zoyi ya daddage ya dirkawa WA'AT dundu abaya saidata saka kara dan sosai ya shigeta kuma abazata dukan Yazo Mata danshi Duk cikinsu ma yafijin tsanarta itace wadda tafara bude kofar a haifamai yara matan shegiya annamimiya yasake dukanta aka tuni taji kannata ya sara su Nusaiba ne suka sanya Kuka dan sosai suke kaunar yayar tasu da basu da kamarta.
       Mama tun karar farko tajiyo tundaga daki haka Umma har neman faduwa take jin Kuka asoro turus taja ta tsaya tana kallon Appa da yake huci kamar wani zaki kaikace da dan Uwansa Namiji zaiyi dambe hannu a dunkule ko naushi zai kaima waya sani.Tabe baki tai amma anji kunya Wallahi wai Dila ya shanye ruwan 'yan tsaki 
dama kaine asoronnan kazo katasasu agaba kana duka ni wllh na dauka yaran makota ke fada ashe wai kaine ALLAH ya kyauta dai nidai ahir dinka tabamin 'Yaya Wallahi ranar zaka gane Wacece Salamatu,kukuma kuzo kuwuce masu kama da 'yan ruwa.

    Karo na farko kenan acikin dukkan Rayuwarsu dazasu ce Umma tataba Taimakonsu dan badan tafito ba shirin kara kaiwa WA'AT duka yake dan duk wani Haushi dama akanta yake huceshi ko dukansu ya zoyi nata yafi na Kowa yawa Cikin Sauri suka wuce daki suka nufa Suna shiga WA'AT ta fada kan gadonsu Kuka take mematukar ciwo daga jinsa Kasan tundaga kasan Zuciyarta yake fitowa dan danan Zazzabi ya rufe ta.Mama tana Zaune ÀLLAH kadai yasan Halin da Zuciyar take ciki danji take dukkan wani hawayan 'Yartata yana dira acikin Zuciyarta.
    Ta hadiyene Saboda kartasa yaran nata a Damuwa batason ta rusa musu Farincikin da suke ciki ta kasa Magana gabadaya dan tabbas tana bude bakinta Kuka zata Fashe dashi shiyasa ta zabi tai shiru da bakinnata kan WA'AT din ta dora akan cinyarta ahankali take shafa kannata alamar Rarrashi agareta shiru kuwa tayi tanajin matsanan ciyar soyayyar Mahaifiyar tasu.

Magani ta balla ta bata dayake bata rabo da Magani ako yaushe Abincin Dare babu wanda yaci acikinsu Kowa Zuciyarsa a cunkushe ba dadi.
    
Karfe 7 Mama ta tattarosu tsakar gida kwado tasa ta kulle dakin Tunda dama Megidan yace baza ayi taro agidansaba taso tafiya gidansu ayi acan Malam ya hanata yace agidansa zaayi shine yanzu Zasu tafi can dan ko wanka basu tsaya yiba duk acan zasuyi.Shima Malam Yasan da Maganar Shiyasa yace Sassafe Subaro Masa Gidan Tunda ALLAH yasa bashi Kadai yake da Gida duk Fadin Zariya ba,sosai ran Malam ya baci dawannan dibar Albarka da Appa yakeyi danshi yake Zubdarwa da Mutunci Bawani ba.
                WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesa
              PART TWO
Chapter 2
    Kicibus sukai da Appa nanfa aka fara Kallon Kallo Ali yaga Ali tsakaninsa da Mama wani Kallo yaga tana yimasa daya gaza gane wane irine kamar kallon jin Haushi kamar na kiyayya.

Sai yaji ya kasa yimata Rashin Mutuncin daya fito domin sa daga daki,yasan yana Matukar son Aysha amma shifa wannan 'Yaya Matan data haifa masane bayaso Amma itandai yana sonta haryanzu babban Haushinta da yake ji haihuwar 'Yaya Matan datayi ne yake  mata dukkan Wani wulakanci dayake mata.

Kala bata ce Masa ba dan bata da Lokacinsa gaba daya inta tsaya ta Nuna mai taji Hashin Ma Abunda yayi Mata Ashema ta damu dashi shiyasa ko Uffan bata ce Masa ba sukai Gaba.
    
Kai tsaye gidan Malam suka wuce acan sukai wanka karfe 8 gida ya fara cika Dangin Mama dana Appa sai zuwa akeyi Inna kaya Kala Uku ta dinka mata Malam shima kala Uku Sai Inna Lami kishiyar Inna itama ba'a barta abaya ba Kala daya tai Mata, Mama tadinka mata Kala Uku Bakaramin Farinciki tayi ba sosai Mama taji dadin ganin Farinciki Afuskar 'Yartata Habibiyarsa Abar kaunarta Abar Sonta.

Uniform Suka sanya sabbi fil da yake Makarantar Babu ruwansu da Wani  Anko dokarsu Kowa yasaka Uniform dinsa na Makaranta.
   
 WA'AT acikin Hafizai tafito Uniform dinsu akwai Ban banci da Wadan da sauka kawai sukai Ba hadda ba sosai tayi kyau Cikin Uniform dinta Safar Hannu data Kafa haka tasaka saboda Lallen Hannunta Hijab dinsu har kasa koda Ban fada ba kunsan Zariya Hijabai Ba'a Maganarsu.
    
Karfe 9 Awajan Saukar tayi Musu Tare suka tafi da Jidda dasu Safna Harda Ammi duk tare Suka dunguma acikin Motocinsu Na Alfarma Mama tasha sabuwar Atamfarta da Sabon Hijabinta Fuskarta Kunshe da Fara'a itakadai tasan Irin dadin da takeji acikin Zuciyarta Babban Burinta yanzu taga ranar Auran Yarannata Musaman WA'AT datake Babbarsu.Wajan da Iyayan Dalibai suke Zama nan Sukaje suka zauna akafara gudanar da Sauka Cikin Tsari Gwanin burgewa.
    Ankira Dalibai sunyi Karatu Karatun WA'AT Bakaramin Jan hankali yayi awajanba muryarta Cikin sanyinnan nata tana fidda makarij daki daki wasu da yawa acikin wajan sunyi Fatan Inama 'Yar suce Lallai da sun kasance Cikin Masu Sa,a A Duniya Cikin Masu wannan tunanin Harda Ammi sosai taji Yarinyar ta matukar burgeta Lokaci daya taji kaunarta acikin Zuciyarta Inama wani abu da take tunani yakasance ita kadai ta saki Murmushi dan tuna Wani abu da tayi.
    Anty Juwaira ce tatabota ganin ita kadai tana Murmushi Lafiya kuwa Anty Ke kadai kidinga Dariya uhmm Bari Kedai Juwaira Wani abu nake tunani acikin Zuciyata akan waccan Yarinyar dabanma san sunan taba wakenan wadda take karatu yanzu.
    Murmushi tai Ayya ALLAH Sarki WA'AT kenan kawar Jidda ko nace miki Aminiyar ta nikaina Yarinyar nan Bakaramin kaunarta nake ba Wallahi da ace inada da Namiji Babba babu abunda zai hana ban nemar Masa Auranta ba Ammi ce tai Dariya to aiyan zumma kina dashi zaki iya Nemar Masa ware Ido tai Sosai A kan Ammi sai Alokacin tagane metake Nufi Dariya tayi kuma fa Wallahi Sai yanzu kaina ya Kawo Haske Lallai Dole ne nace Wani Abu a Wannan karan Nima Dariya sukai gaba daya.
   
 Inna da take bayansu duk tanajin Hirar tasu akan jikarta ita kanta tana Alfahari da ita sosai take jin Kaunarta kaf cikin Jikokinta tafi ji da ita saboda Nutsuwarta da Hankalinta da sanin ya kama tanta intai Wani abu kamar wata Babbar Mace haka take komai nata,tasan hakan yasamu daga wajan jajir tacciyar Uwa Wadda ya kamata ajinjina Mata tayi Sa'ar Suruka da kaf cikin Surukanta bataga Wadda zatai hakurin da take yiba akan danta.

Shiyasa a Kullum take rokon ÀLLAH daya kawo mata sauki adukkan lamuranta daya karkato mata da hankalin Mijinta da 'Yayanta Zatafi Kowa Farinciki Idan Appa ya dawo Mutumin kwarai Mutumin da zatayi Alfahari Dashi a matsayin danta.
         .......✍️✍️✍️
            WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
        PART TWO

Chapter 3 
    Kyaututtuka sun shasu awajan 'Yan siyasa da Manyan Masu kudin Garin Haka Makarantar Aka bata Wani Babban Fili za,a gina Musu Makaranta daga karshe wakilin Sarki ya tashi yayi Magana da yawunsa akan Ana Neman Mahaifin Fatima Kabir Nan fa aka fara kallon Kallo tsakanin Inna da Mama Malam da Appa bakunya Appa kokarin tashi yake Jiki har rawa yake Kiran Sarki aiba a banza ba ya tabbata Wani abun Alkhairin Zai samu.
    Koma Kazauna cewar Malam ransa ahade dama yajira yaga Iya rashin kunyar Appa kuma yagani ko bakaji Mahaifinta Akace ba kuma na tabbatar kai baka cikin Wannan Layin.

 Magana Yake son yi Malam Ya daga Masa Hannu cikin Bacin rai dole ya koma ya zauna kamar zai kurma ihu dan Bakin Ciki,Gefensa ya kalla inda Wan Appa yake azaune cikin shiga ta Mutunci da Kamala Tashi Kaje Usman Kallon Malam yayi da zummar ya rokeshi yabar Appa yaje Yadda yaga Fuskar Malama babu alamun sassauci A hade kawai tashi yayi guiwa a sanyaye Inna da Mama binsa sukai da Kallo Inna Murmushi tai kawai irnnasu na Manya dan bataga laifin Malam ba dole ne a hukun tashi ya girbe abunda ya shuka.
    
 Zuwa yayi ya tsaya Inda aka tanadar Masa dan tsayawa Lasifika aka bashi meze iya tofawa akan iyaye da suke banzatar da Rayuwar Yayan su Misali akan 'Yarsa dayai matukar kokari wajan ganin ya inganta Rayuwarta ya bata ilimi gashi harta taka Wani Babban Matsayi na Haddar ALKUR, ANI Mai girma.

Karbar Lasifikar yayi bayan yayiwa Annabi Salati da dukkan Ahalin Gidansa da Sahabbansa.Fara Jawabi yayi Cikin ilimi Aya da Hadisi haka yadinga Jawowa Na Hakkin Iyaye akan 'Yayansu ya dinga kwararo bayanai daki daki cikin Dattako da Kamala da sanin yaka Mata sosai Iyayan yaran jikinsu yayi sanyi suka karajin zasu sake zage dantse wajan kula da Rayuwar 'Yayansu bakaramin Burge Manyan baki yayi ba kama daga kan Iyayan yara da Malamai.
              
Wadanda sukasan Appa shine Mahaifin WA'AT abunfa ya daure musu kai tayadda sukaga befito ba amatsayinsa na Mahaifinta.Abun Mamaki dukkan wanda ke wajan saida jikinsa Yayi Sanyi da wannan Fadakarwa Amma banda Appa shi gaba dayama bacin ransa na abunda Za,a bayar ne WA'AT ita kanta share Hawaye take dan tasan sarai Baba Usman Saboda Appa Yayi wannan Fadakarwa Haka Inna da Mama sun san Saboda shi akai Amma kamar Wanda shedan yayiwa fitsari aka ko ajikinsa.
    Fatima Kabir Aka sake Maimaita kiran Sunanta akaro Na biyar sake fitowa tai ta tsaya Indai aka tana dar mata,Megabatar wane yafara Magana Kamar haka.

 Wani Bawan Allah da bai yadda Afadi sunan sa ba ya biyawa iyayanta Kujerar Hajji tare da zunzurutun Kudi Naira Million Biyar dan tallafawa karatunta Yayi ne dan ALLAH baya bukatar Afadi sunansa,sosai wajan ya kaure da Kabbara 'Yan Uwa da abokan arziki Farinciki ya cika zuka tansu Appa sai washe baki yake yana gyara Hula Duk abunda yake Malam yana Kallonsa kawai girgiza kai Yayi shiyasan tsiyar dazai shuka mai.
                  WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
            PART TWO
Chapter 4
     Haka Mama Sharar Hawaye take cikin Tsananin Farinciki yau Gashi asanadin 'Yaya mata aka biya mata Kujerar Hajji itako wace Irin Farar Haihuwa tayi haka babu abunda zatai sai Godiya Ga ALLAH daya nuna Mata wannan Rana.
    Addu'a akai akatashi daga wajan Sauka bayan an raba musu allon Sauka da Alkur,ani haka aka tashi cikin matukar Farinciki haka mutane suka zo suna ta gaisawa da Mahaifiyar Wa'at dan sosai suka jinjina mata wajan jajircewa datai tabawa Mahaifinsu gudummawa wajan Kulawa da Karatun 'Yayansu da Tarbiyyarsu Abunda basu saniba Duk kokarinta ne da Jikinta da Lokacinta rana zafi ruwa Iska baya hanata Neman Abunda zata biyawa 'Yayanta Kudin Makaranta damma tana samun temako daga iyayanta da Malam da inna babu Abinda zatace Dasu sai Godiya.
    Da Fara,a tadinga karbar kowa suna gaisawa cikin mutun tawa,gidan Malam suka dunguma babu kunya Appa yabisu kamar Jela wanda suka sanshi sai Alasanya alheri suke masa babu kunya yamatsa Kusa da Inna waidama Inna nace mezai hana awuce can gida ayi bikin saukar acan saboda kinsan Mutane sai suga kamar Wani Abu yasa ba'ayi Bikin saukar acan ba.
    Da ace ba Acikin Jama,a bane babu Abinda zaisa bata gaura masa mariba Wallahi har Ita zai kalla yayiwa wannan Maganar,mekuwa za'ace tunda ba agidan gala akaga zamuje miyi bikinba kaga kwantar da hankalinka babu wanda zai tunaninma kana da gidan da za'ai bikin saukar Aciki balle har azageka adauka Wani abune yasa ba'ayi anaka Gidan ba.
   
 Kaga can Juyawa yayi yana Kallon Yaya Usman Kamar Yadda suke kiransa abun bacin rai Gani yayi Manyan mutane sun baibayesa anata gaisawa dashi dayi masa Alasanya Alheri kallon kansa yayi babu wandama yasan dashi awajan balle ayi masa Alasanya Alheri,ina fatan ka ganewa idanunka babu ma wanda yasan da zamanka bare azageka ka kwantar da hankalinka.
    Ga Ubanta can kana Kallo shi akewa Alasanya Alheri aishi da dama basai ka haifeshi ba kake cin arzikinsa abun ALLAH sama taka yasamu Kujerar Hajji Dam yaji kirjinsa ya buga kanyayi wata Magana Inna tai gaba tabarshi anan gumina keto masa Abin ALLAH Gashi yasamu Kujerar Hajji to me Inna take Nufi shi aka bawa Kujerar ko yaya ai wannan Kujera tasace dole kuma abashi kayarsa tunda dai shine Ubanta sanda aka samu cikinta ba Uban Wani ya Haifar masa Ita ba ko ganin gabansa bayayi ya zarce gida.🤣🤣🤣🤣
    Yana shiaga ya tarar da Umma tana ta Masifa Zainab tatafi wajan Sauka bata gaya mataba tunda kanwar Uwar tace take saukar kamar hadin baki tai Sallama tashigo abunda saita dade batayi ba yau shine aka tuna mata.
    To ganta lalliya inbanda gulma Irin taki inake ina zuwa wajan Saukar su bayan ke da ALLAH yayiki baki da zuciya kare ya Lashe ,Appa ta kalla dayake ta faman Hada gumi kamar wanda kunama tashigewa riga Hhhh ta kwashe da Dariya aike Wallahi Umma anyi bake anacan ana rabon Kujerun Hajji bakije kinyi Kallo ba Inda ake harkar arziki bata tsiya ba abaka aimaka gori,dafe kirji Umma tayi ke mekike fada hakane kamar Amafarki nifa Banason karya nagaya miki.
    Au hakama zakice kitambayi Mijinki yafi kowa sanin Wadanda akaba ina tayaki Murna kishiyarki da wan Mijinki zasu cale Saudiyya Subar 'Yan bakin ciki A Nigeria aci gaba dacin gabza miyar kuka.

Kir Umma tayiwa Appa tana neman karin bayani wai Kabiru yazaka sani aduhu kuimin bayani yadda zan Fahimta baradai Umma nai miki yadda zaki gane Labari tabata tiryan tiryan Kam bala,i ina zaune Kishiyata abiya Mata Sa,udiyya tokai kaname kazauna baka tashi kaje ba.
    Shi Maganarta ma bata masa rai take Au namanta fa 'Yaya matane dole kaki tashi kam Amma ni nama godewa ALLAH daba'a bakaba dan Wllh yadda banje ba kaima bazaka ba gwaramani ina saran da Hajin bana dani zaaje dan Inada tabbacin Kamal zai biyamin kai bama niba harwani ma yace na kawo sunan sa kana Kallo ALLAH bazansa sunan kaba saidai na dagoma Hannu daga cikin Jirgi.
    Tsaki yayi yayi gaba danjin Irin Haukan da take Zubawa Ko agidan Ubanwa Kamal din zai biya mata Hajjin barin wajan Yayi gwara yaje ya samu mafita akan wannan Lamari dan bazai taba yadda ba.

Dan duk wacce za'ai saidai ayi Amma wllh bazai yadda abarshi Abaya ba shida Yarsa a kwacemai ita ina bazai yiwuba.
    🤔🤔🤔🤔 Tofa.
    .......✍️✍️✍️✍️
       
          WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
      PART TWO
Chapter 5

Lumshe Idanunsa yayi Jin har Lokacin Muryarta Na Amsa Kuwwa acikin Kunnu wansa Kamar A Lokacin take raira kira,ar sosai yaji wata Nutsuwa na sauka acikin Zuciyarsa Fuskarta yake Gani Tana Murmushin da yatafi da dukkan Nutsuwarsa Inama zai sake ganinta gyara kwanciyarsa yayi a Hotel din daya sauka dan ba wanda yasan da zuwansa yaso yayiwa Ammi Bazata datake cewa tasan ba Zuwa zeyi ba Gashi yayi Babban Katari da samun wadda Lokaci daya yaji tayi Masa dari bisa dari yarasa meyakeji game da ita.
     
 Burgeka kawai tayi abunda Zuciyar sa ta Ayyana kenan to wannan yarinyar ma dabata wuce sa'ar Safna ba mezeji agareta hazakarta ce kawai ta burge ni Abunda yasa aransa kenan.

Sosai Gidan Sauka ya dinke yan Uwa sai sake tururuwa sukeyi zuwa Alasanya Alheri duk wanda yazo kuwa baya tafiya hannu haka dan Malam da Inna da Sauran Yan Gidan sun shiryawa Wannan Saukar Appa ne kawai baya cikin sabgarsu dama basu kasa Dashi ba Jaka suka buga mata da Memo Kowacce Lemu da ruwa sai tek away dayake cike da kayan Snacks abun dai sai san barka.
   Karfe Hudu Jidda tashigo Gidan WA'AT taja gefe ke Ammi fa ta hada mana walima nagaya miki yanzu haka ga kayan da zamusa mu uku ni dake da Safna ganaki can tace nazo na taho dake,ware idanu tai akan Jidda Walima kai Jidda gashi Inayi Anan bata rai Jidda tayi kinga Abunda yake hadani dake kenan gaba daya ke haryanzu Ganina kike bare bakya sani acikin Danginki niba haka na daukeki ba ni Inaji araina kamar Uwa daya Uba daya muke Amma tunda kin nunamin iyakata shikenan,tafiya ta farayi da Sauri ta kamo Hannunta haba Kiyi hakuri niba haka nake Nufi ba.
   
    Toya kike Nufi duk sanda zannuna Inason wata Alfarma agareki bakya yadda naga nina damu dake bakomai dakyar ta rarrasheta ta sauko Wajan Mama sukaje Jidda tai mata bayani Dariya kawai tayi kai Amma itama da wahalar dakai take aida bata hada muku wata Walima ba Tunda gashi anayi Anan Amma naji dadi sosai ALLAH yabar Zumunci Kuje Amma banda rawar kai nagaya muku Dariya kawai sukayi Jidda ta sanar da ita Suna gayyatarsu gaba dayan su to zamuzo musa muku Albarka Hannun WA'AT taja suka futa.
    
    Gidansu Jidda suka shiga shima Gidan acike yake da 'Yan uwa wanda suka zo taya Murna Gidan babbane sosai a harabar Gidan aka zuba kujeru anyiwa wajan gyara na Musamman bakaramin Kyau yayi ba wajan Manyan baki daban Ga Kujerar Malama Wadda zata hau tayi Wa'azi wajan da Masu saukar Zasu zauna daban suma komai atsare haka aka yishi kai tsaye cikin Gidan suka shiga dakin Jidda suka Fada yan mata sun cika dakin anata hira masu shirin Walima har sun fara shiryawa.
     Me kwalliya dama tazo simple tai musu babu hayaniya bata cika musu Fuskaba sosai sukayi Kyau Dogayan riguna suka saka iri daya Maroon Colour bakaramin Kyau sukayi ba Rolling Tayi Musu sai gashi sun fito kamar wasu Larabawa Ammi ce ta leko kai kai Ma sha Allah haka Yammatana Kuka fito kamar akasar Larabawa kunyi Matukar Kyau kuzo na haskaku a Camera ta nizan fara has kaku.
    Kai Ammi aikin san Wadda ta haskamu ina Wani Kyau damukayi munsan da ita kadai kike dan duk itace ta cinye wannan Wankan Harararsu tayi saboda nice Zillaziyya ba to aikimma wuce haka nidai ba suruba kutashi na Haskaku kawai tayi Musu pics akalla kusan Kala goma sunyj Matukar Kyau adanasu tayi tukunna tasasu agaba suka fita wajan Walimar waje ya dinke da Jama,a kowa yasamu Kujera ya zauna komai anutse babu wata hayaniya.
    Babbar Malama suka Gayyato dazata gwangwajesu tai musu wa,azi me ratsa Zuciya bakowa bace face Malama ZAINAB JA'AFAR waje na musaman aka ware mata ita da Jama,arta da sukazo tare.Tako yi Musu Nasiha meratsa Zuciya dasa zubar Hawaye wajan Yayi shiru kowa baya kaunar ya motsa saboda kar Afadi Wani abun Bata jiba sai kusan Magariba aka tashi anci Ansha babu wanda zaice wannan Walima bata kayatar dashi ba.
    Sosai sukayiwa Malama Godiya da fatan ALLAH ya maida ita Gida Lafiya.
        ........✍️✍️✍️

               WA'AT
By KULSOOM ISAMA'IL IDRIS
MRS BABA BELLO ABUBAKAR
OUM ANEESAT

       PART TWO
Chapter 6
  Ammi ce da Anty Juwaira nidai Wannan Yarinyar tamin sosai Yanzu duk Wani kokari nabarshi a hannunki Juwaira tunda ni bana Kusa ina son Dan ALLAH kisake kokari akan hakan ga Yarinya yar mutunci kaf zuri'arsu banga Wanda yafadi aibunsu ba Mahaifiyarta kanta kina ganinta kinsan Mutuniyar Arzikice af ai Indai Maman Wa'at ce bata da matsala dan wannan Matar Baiwar ALLAH ce tana da Matukar Juriya da hakuri nan tabata Labarin abubuwan da Suke faruwa da ita tunda tai Aure Sosai Ammi ta Jinjina Lamarin oh ni Sadiya dama ana samun irin wadannan Mutanen Haryanzu.
     Nayi tunanin tun alokacin Jahiliyya da Musulunci yazo ya hana binne 'Yaya Mata da tsangwamarsu da cewa baza'a basu gado ba andaina irin wannan hmm cewar Anty Juwaira aikedai Sai Addu'a ina tabbatar Miki da awannan Lokacinma zai yiwu babu abunda zai hana be binnesu da ransu ba, toh ALLAH ya shiryeshi Ameen.Wallahi sai kika karasamin kaunar yarinyar da Mahaifiyarta In sha ALLAH zata zama Abar Alfahari Akwai randa zaiso anunata ace 'Yarsa ce zaiji dadin su fiye da yadda zaiji na 'Yaya Mazan daya kwallafa rai akansu.
     Anty Juwaira ce ta kyalkyale da Dariya Wallahi Ammi sai kika tunomin da Wata Drama nan tabata Labarin Sanda Umma ta barka Tutu Awando dan Dariya saida Ammi ta fado daga kan Kujera kai Juwaira nifa nasan Sharrinki ALLAH Anty da gaske nake miki ke kinji abu kamar a film Wallahi abunnan ya matukar bani Dariya harkinsa inason naga wannan Salame shakuruminki Anjima zakisa Mayafinki Muje Hargida kikara ganin Zahiri ALLAH ya kaimu kingama masan Juna da Maman Wa'at din Hakanne ALLAH ya kaimu Anjima.
       Karfe 12 suka isa Gidan Appa Mama tana daki tana ninke Sabbin kayan Wa'at wanda aka dinka mata akalla ta samu kaya kusan Kala goma sha Biyar 15 Zuciyarta wasai take jinta batajin Yanzu akwai Wani abu da Appa zai mata wanda ranta zai baci akansa duk Wani bacin rai tagama ganinsa ita
 Yanzu saidai tayiwa 
ALLAH Godiya da wannan Ni,ima da yayi Mata.

Sallama suka rangada Ummace ta bankado Labule tana Amsawa ganin Anty Juwaira yasa ta bata Fuska dan tasan ba wajanta akazoba.
     Harare Harare tafarayi Ammi ce takare mata Kallo Dariya Nacinta Dan Wallahi Sanda kudaje Suke binta kawai ta hango Hhhhh ta Kunshe Dariyarta da kyar uhm Sannu anwuni lafiya dakyar take Amsawa ita Alallai anzo gidansu, ALLAH kuma ya sanya Alkhairi da'a Kayi me Saukar 'Yarki Mana Y'arwa can gasu gada babu Abinda ya hadani da ita ga Uwar tacan adaki shiga kiyi mata dama nasan Maula taje Inda kuke ninan da Kuka ganni babu ruwana da Abun hannun Mutane inada wadatar zuci to Alhamdlh.

Anty Juwaira tsabar neman magana Hannu tasa ajaka rafar yan dari Biyar ta dauko to kinji fa ashema ita wannan ba ruwanta da Duniya akwai Zuhudu gaskiya kinkai duk Inda ake bukata bana maida kudina akwai mabukata awaje ALLAH ya hadamu dame wadatar Zuci itadai Ammi batace komai ba tuni Umma tafara zare ido ganin wannan Uban kudin Amma dai ALLAH ya tsinewa wannan baki nata dabaya iya gani saiya tanka Yanzu gashi tanaji tana gani zata cuci kanta.
    
 Aishi ihsani ko kana dashi in aka baka kana jin dadi kuma duk wanda ya kyautatawa Musulmi shiama ALLAH zai kyautata Masa, Kallon Juna sukai suka Fashe da Dariya cikin rada Anty Juwaira take fadin kinji Matar nan ashe Munafuka tasan babu kyau Muzgunawa Musulmi Amma ita take Muzgunawa wasu.To Mungode da tunatarwa ALLAH ya saka da Alkhairi gaba sukai sukabar Umma a tsaye tanajiran A miko mata kudin sarai sun gane metake Nufi sukai Fuska suka wuceta.
    Mama da take Kallonsu ta Window girgiza kai kawai tayi dan ita kanta abun ya bata Dariya yadda ta hango Umma tana Hada gumi daga Maida kudi jaka idanunta Kamar zai fado tasan Halin Anty Juwaira dama da tsokana ta girma batasan ta girma ba komawa tai ta zauna daidai Lokacin suka iso kofar dakin Mama.
          🤣🤣🤣🤣Koni Umma na tausaya Miki ga samu ga rashi dagayau kidinga gasa bakinki kanki Magana lol
        Taku Kulsoom Ismail
            .......✍️✍️✍️
        WA'AT
By KULSOOM Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesa
            PART TWO
Chapter 7

    Dakin Suka shiga tare da Sallama cikin Fara,a Mama takarbesu tanai Musu Sannu da zuwa waje Suka samu Suka zauna,gaisawa sukai cikin Mutunta juna Fridge tatashi tabude Kuma gashi yau Banyi Zobo da kunun Aya ba saboda kinsan Jiya ban samu zamaba,kai amma banji dadi ba nifa dama kwadayi ya kawoni gidannan dan randa su Jidda suka kaimin Zobonnan Kwana nai ina santi to aiko dai yau kindaki gurbi gashi baakusa kike ba balle nakai miki babu Komai ai zan sake dawowa sainazo hargida nasha.
    Sosai suke burge Mama baruwansu da Nuna Suna Dashi sam basu da Wulakanci dama zuwa mukai mi miki Alasanya Alkhairi Yarinyarki ta matukar burgeni Wallahi Wani dadi ne ya lullube Mama jin Ana yabon diyarta Nagode Sosai Allah yabar Zumunci cewar Mama.Anty Juwaira ce ta dora nida zaki bawa dana aida naji dadin hakan sosai Dariya kawai Mama tai ai 'Yarki ce inkin bashima bawani Abu bane.
    Ah to Godiya nake tunda aka bani wannan babban Matsayi haka nikuma bazan bada kunya ba haka dana Nasan ba Macen da zatace bata sonsa Banda dai sonkai cewar Ammi Ai wannan Abu a bayyane yake to nima 'Yata metsada ce sai wanda yakai zan bawa cewar Ammi to aikin san indai batun Love ne mudai ba baya bane kibamu mintuna biyarma ya isa munsace Zuciyar Yar taki sosai suke hira cikin barkwanci.
    Mama taji dadin Wannan ziyara da suka kawo mata dan danan suka saba da Ammi Dan Macece mesaurin sabo matukar ka zauna da Ita yanzune zaku saba.
    
    Tashi tai ta dora Musu girki Jallop din taliya tai Musu tun tana kan wuta kamshi ya bade Musu hanci bakaramin dadin girkin sukaji ba suka dinga santi hakan ya matukar faranta w Mama rai tasake gasgata karamcin su.Ruwa mesanyi ta dauko Musu tunda babu Zobo da suka tashi tafiya rafar yan Dubu Dubu guda Biyu Ammi taajewa Mama tata Gudummawar Mama cewa tai Bazata karbaba saida aka kai ruwa rana ta karba tana godiya.
    
    Tsakar gida suka fito abun Dariya Umma na zaune dirshan akofar daki kamar Megadi idanunta kyar akan kofar dakin Mama tana ganinsu kuwa tamike tana washe baki Au su Hajiya har zaku tafi eh Zamu tafi yanzu kuwa Mama Kallon Umma take tana Mamakin Kwadayi irin nata gaba daya bata Iya boye zilamarta akan abu.
    Anty Juwaira ce ta zuge Jaka kudin dazu tadauko dama tayi niyyar bata Hannun Umma har rawa yake bakinta kamar zai yage takarbe kudin kamar wanda zaakwace mata ta kankameshi abun ya basu Dariya sai Godiya take kamar Marokiya gaba sukayi dan sunga Godiyar tata bame karewa bace.
    Har Soro Mama ta rakasu tana sugaida gida sai dataga fitarsu ta dawo Umma tuni an Fada daki an adana kudi waidan kar Mama tasaraima zata sammata wayaga basa banba batasan abunda Mama tasamu ya ninnika nata.Mama data kirga kudin Naira Duba Dari Biyu cas sosai take Mamakin karamci irinnasu Ammi bata santa ba sai Awannan saukar Amma hartayi Musu wannan kyauta haka.
    Ajiye kudin tayi tana Ayyana abunda zatai dasu.
    Wai Ina Hajara Amarsu Ta Ango tun randa aka kaita tafara fuskantar kalu bale dan Kamal yana shiga zaiwa Hajiya Sallama ta mikomai Hannu ya bata Kajin Hannunsa haka ya mika mata bajesu tayi saidata kacaccalasu kai Hatta yan Aikin gidan saida ta raba wannan kaza dasu ga kajinan A cikin Fridge Amma wannan be mata ba kai jeka kira Matarka sukuti Yayi yana Kallon Hajiya ko bazaka bane.
    Futa Yayi jiki a sanyaye tana zaune adaki tacika tayi fam Sangal Sangal taganshi hannu wayam har leka bayansa takeyi koya ajiye ledar Hannunsa har Mamakin metake lekawa yakeyi yanaganka hannu haka injifa Amarya.
    Kizo Hajiya tana kiranki ni kuma take kira kota manta Amarya ceni yau aka kawoni wannan ne bansaniba saiki zo muje ki tambayeta abunda ya fada kenan Ransa abace ga Abinda Hajiya tai masa gashi Itama zatazo ta sake bata masa rai.
          .......✍️✍️✍️
         WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesa
         PART TWO
    Chapter 8
    
    Tashi tai rai bace suka tafi Suna shiga suka hango Hajiya ta baje Kaji kashi kashi yawwa kakirata ke zoki dauki naki kason dan ba'asaba ciba dan tabbas kikaci da yawa zata iya yimiki illah baki sake Hajara take kallonta kanta ma ya kulle tarasa me Hajiya ke nufi da Wannan Maganar ko bakyaci nakara rabeta haka taja kafa guiwa sake Hajiya fukafikin Kaza ta miko mata tsaywatai tana Jujjuya shi ahannunta wai Kajin Amarcin Natane aka gutsitsirasu haka.
    To saida safe zaku iya tafiya gaba daya kan Kamal shima ya daure me Hajiya take nufi dayin hakan dandai Mahaifiyarsa ce babu yadda zayyi da ita harsunje bakin kofa Yawwa kuma karfe 6 ake fara aiki kifito akan Lokaci aiki Tabdi ai Wallahi ba aiki tazo yiba Duk Yan Aikin nan ace saitazo anyi aiki da ita base ta ganta ba.
    
    A zafafe ta fada daki kamar zata rusa ihu zama Kamal Yayi ya dafe kansa yarasa ma mezai cemata sai girgiza kafa takeyi ,ni wllh bansan haka Uwarka take batada Tausayi da imani ba afusace yatashi tare da daka mata tsawa ke Mahaifiyar tawa kike fadawa haka nafada mata kai bakaga abunda tai minba saboda rashin imani kazar Amarcin nawa zata Kasa tasa agaba tacinye kamar tsohuwar Mayya Tas kake ji ya dauketa da Mari.
    
    Idan kika kuskura kika sake fadawa Hajiyata haka Wallahi sai ranki Yayi mummunan baci ga rashin Tarbiyya nan kina nunamin tunkan aje ko ina kinci Sa'a ina sonki Amma da sainamiki Mugun Duka adarannan futa yiyi daga dakin ya buga mata kofa Hajara Hannu ta dora aka tana rusar Kuka Wayyo Nashiga Uku Ni Kamal zai mara A daren Amarcina Wallahi saiya san ya Mareni haka tadinga Kuka Kamar hawayanta zasu kare .
    Wani kauri kauri tafara ji yacika dakin afurgice tadago kanta Kamal ne azaune ya harde kafa sai zukar sigari yake yana fesa Mata afuska tuni tari ya turniketa tari tafarayi babu kakkauwa dan danan idanunta suka furfuto Waje Cikin tashin Hankali take Kallonsa Kamal dama kana shaye shaye Amma baka taba fadamin ba.
    Dan Ubanki shi Yayanki daya fara shaye shaye fadawa Uwarki Yayi dafe kirji tai gani take Kamar ba Kamal ba kamar sanja mata shi Akayi Kamal din dayake tarairayarta ako yaushe bayason ganin bacin ranta yau shine Harda zaginta wata Muguwar zuka yayiwa sigarin Hannunsa yasake fesamata Afuska tuni hayakin yakai Mata ziyara har cikin Kwakwalwarta Fashewa tasakeyi da Kuka mai cinrai yau tana ganin Masifa.Dan Arayuwarta tatsani hayakin sigari.
    
Wata Dariya ya fashe da Ita irinta rikakkun Yan Duniya Hajara Hajara kina Mamakin nine koba nine bako to nidinne kuma ina tabbatar Miki da cewa sai kin gwammace baki taba sanina ba.Na dade da sanin Abunda yasa keda Uwarki Kuka shiga Kuka futa Saida kikasan Yadda Kuka rabani da abar kaunata cikin bacin rai yake magana dagaske nakejin kaunarta banje dan na cutar da ita ba Amam rana daya naji natsinci Kaina na tsaneta saike kawai nakejin soyayyrki kamar ta kasheni.
    Abunda bakusani ba Wannan Abunda kukai min beje ko ina ba ya karye alokacin dana gano aika aikar da kukayimin na rabani da abar kaunata nayi matukar bakin ciki nayi Kukan danai shekaru banyi shiba Nazabi na boye kalata harsai kinshigo Hannuna Dan Wllh nayi Alkawarin saina dandana miki azaba da nan gaba bazaki sakejin Marmarin Cin Amanar Wani ba Har Uwarki saitayi dana sanin sanina Arayuwarta  ina matukar tayaki Farinciki da shigowa Kurkukun Kamal saina tabbatar na maidake zautacciya saina gigita Rayuwarku keda Uwarki saina sabautaki sannan zan sakeki Saki Uku.
    Sai nayimiki Mummunar illah a rayuwarki sakamakon Mesan Zuciya kenan.
    Gaba daya Kukan Hajara ya dauke dif tuni tanemi kukan tarasa jida ganinta gaba daya daukewa sukai Yaraf tazube Akasa tai suma na wucin gadi Dariya ya sanyi tunkan Afara wasan harkin suma hmm tsallaketa Yayi yafice daga dakin gaba daya.
       🙆🙆🙆 Lallai Hajara tana cikin Masifar Rayuwa kubiyoni danjin Yadda zata Kaya.
         .......✍️✍️✍️
            WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
         PART TWO
Chapter 9

    Ruwa yaje ya dauko me shegen sanyi ya guza mata azabure tatashi tare da fashewa da kuka ai ba'a fara komai ba tunyanzu kin fara kuka Uwarki ce taja miki dabatai Miki Tarbiyyar Arziki ba koda dai itama ba Tarbiyya ce da ita ba inamai Tabbatar miki saina Maidaki Abar Kwatance a cikin Garinnan sannan zan sakeki Saki Uku rigis.ALLAH ya isa tsakanina dakai mugu Azzalumi kuma Wallahi saikaga wanda zaizo ya ramamin.
    Dariya ya fashe da ita basai kinfita zaki gayawa Wani bake bafita bashiga gadin Mahaukaci kina cikin gidannan harsai Lokacin dazan Sallameki yayi Na Tabbatar nayi miki Tarbiyyar da iyayanki suka Kasa yi miki Wallahi Duk Masifarka Dangina sun fika dan inka tabani kataba Masifa da bala,i to kinjifa kaf Dangin naki babu me hankali aciki Duk taran Matsiyata aka hada Makwadaita Masu hangen abun Hannun Wani.
 
"Gaka nan babban Matsiyaci ina arzikinnaku yake ni danasan haka kuke da Matacciyar Zuciya daban soka ba daganinku yan taka hayene,arzikin ba gadarsa akaiba aiko yaya Talaka yasamu kudi saiya fito da Talaucinsa Fili dan wanda yake dashi baya waiwayan baya.Aikin banza har nawa kakashemin dakake ta hakilo kana tada Jijiyar Wuya kayo Lissafi sai abiyaka ai,Kuma Wllh karka dauka inka tabani zaka zauna Lafiya Kakata kadai ta isheka dan saita tada Unguwar nan Gaba daya bama kaiba da masu goyama Baya"

Kyalkyalewa yayi da Dariya kardai kicemin Uwaliya Mezani Daya danna san Ita kike fade to daman wannan ai ba Mamaki zata Iya Abunda Yafi haka to kinga Dangin nakima Duk Mahaukata ne ke Kaf Dangin innasa aka rufemunsu har abusa kaho bawanda ya isa ya fito dasu inda zan kaisu be careful.

  Bude Baki tayi zatai Magana ya sake yarfa mata Mari dole tayi shiru tuna bakinta ya dade da Fashewa A wannan Dare dai Hajara babu bala,in dabata ganiba dan saida Kamal yai mata fata fata Sau uku tana suma amma dan Rashin imani irin nasa be bartaba azabace ke sata farfadowa 
Saida aka fara Kiran Sallah ya hakura dan acewarsa ya Fanshe Sadakinsa da kudin dasuka dinga cimasa.
   
 Karfe shida Kuwa Hajiya ta aiko yar Aikinta kan Hajara tafuto Aiki aiko bugun Duniya ba'a budeba Hajiya taje ta gayawa saiga Hajiya Afusace har neman faduwa take saboda Sauri Masiface kawai kevin Zuciyarta  Afusace tana tafe tana Masifar ita Zasu mayar yar Iska sushige daki sukulle kofa kuma sunsan dokar data saka ba taje taga Ubanda sukeyi Agidan Buga kofar ta dingayi Kamal ne ya taso ya bude rai bace ganin Hajiya yasashi Saurin sunkuyar dakai.
    
    Daga sama har Kasa take kare masa Kallo sannu tabbatacce Kasa ta adaki narasa Uban ma dakakeyi koka manta da dokata ne saboda nazama marainiyar wayonka aibataga ta hutuba aiki shiya kamace ta, kiyi Hakuri Hajiya zatazo yanzu tana ma ina hakimar tana zabga mai harara take fadin haka tana daki bangajeshi tai tawuce dakin afusace dan ta tanado rashin Mutuncin da zataiwa Hajara intashiga dakinnan.Tundaga tsakar dakin take binsa da kallo an hargitsa komai kamar filin Dambe kayan kan Madubin Duk sun tarwatse.
    
Kamar sokuwa haka Hajiya ta koma tana bin dakin da Kallo Kan Gadon ta kalla Hango Hajara tai eh Lallai 'Yar Talaka tasamu gado me Laushi dole tamike kafa taita bacci gadon ta nufa afusace.Harzata kama Bargon saita Fasa Fridge taje ta bude Hakamma bemata ba ta koma toilet ruwa ta debo abotiki batai wata wata ba tadaga ta Juye matashi aka gaba daya amma Abun Mamaki ko Motsi bataiba abunda ya sake batawa Hajiya rai kenan zako kici Ubanki yanzunnan daurin dan kwalinta hajiya ta Gyara ta Gyara daurin zaninta.

 "Batai wata wataba ta fusgo zanin gadon da take nade acikinsa daga Hannu tai da Niyyar ta Dirka Mata Duka hannunta ne yatsaya asama Ita bata sauke ba tayi kuma abunda tai Niyya ba"

Dam gabanta yai Mummunan Faduwa sake ware ido tai tana kare Mata Kallo sai Sannan ta lura ko Motsi batayi.
    Juyowa tai bayanta ganin Kamal tsaye yanata muzurai abun ya sake bata mata rai bezata ba yaji Wani Lafiyayyan Mari saidata Sauke mai Guda Uku a kuncinsa.
    Dan Arayuwarta Duk da tana da fada da Gudun Talaka Amma bataso taga anci zarafin Ya Mace Ashe Mahaukacine kai Bansaniba Kamal baka da imani da Tausayi toko aganimar yaki kaciyota kayi Mata haka sake Kai Masa Mari tai dauketa Dan Ubanka ka kaimin ita Toilat.

Sum sum ya ciccibeta kamar gawa yakaita cikin Kwamin wanka ya sakata runtse idanu Hajiya tayi ganin irin Aika aikar da dannata yayi.
    Zanin gadon ta nannade da gaba daya ya tashi daga Aiki wata katuwar Leda tasamu ta sakashi aciki bashi tai Fitar min da wannan Abun Toilat din ta fada Duk Wani taimako daya kamata taiwa Hajara tayi Amma a banza haryau Takasa Farfadowa sosai take yarfe Gumi kwalla Masa kira tai zoka maidata kan bed daukarta yasake zuwa yayi yamaidata kai danshi wannan Aikin da ake sashi ya fara isarsa.
    Hajiya da kanta ta saka Mata kaya saitaji Duk Wani Haushinta da takeji yanzu Babushi Phone ta dauka Likitarsu mace takira akan tazo da sauri akwai Mara Lafiya dan danan saiga Dr Feena da kayan Aikinta.
    ......✍️✍️✍️
         
           WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
    Chapter 10
    
    Bakaramar Wahala akashaba kan Hajara ta farfado daga dogon zangon data tafi babaki sai ido da take zarewa kamar wadda ta zautu Bayan dinkin datasha akalla yakai guda 5 Tsananin Azabar da takeji ajikinta ma bazai barta tai Kukanba jitake kamar ba itaba kamar wata sabuwar Halitta aka sauya daga jikinta Breast dinta tamkar basa Jikinta kamar anyanke matasu haka takeji.
    Dr Feena ce ta sharce zufar data tsatstsafo mata gaskya Hajiya da ace wannan Aikin bana gida Bane dole Hukuma tashiga cikinsa rashin Imanin yayi yawa yayi mata illa me tarin yawa ba Lallai ace nangaba ta sake jin dadin Aure ba saboda tun Farko annuna mata Rashin Tausayi hakan zai zauna acikin Zuciyarta Ina mamakin Maza masu Irin wannan Halin sidinga abu kamar Wadanda akace Za'a kwace musu matan wannan din ba daidai bane matasammu na yanzu sun dauka hakan wayewa ce kaje abokai suita zugaka suna durama Magunguna hakan zaka cutar da Yarinyar Mutanene.
    Gaba daya Jikin Hajiya ya karayin Sanyi Amma abun daya daure mata kai tasan duk da Kamal yana shaye shaye Amma yanada matukar Tausayi Musamman Mata baya taba yadda yaga ancutar dasu ya aikai hakan ta faru.Hmm Ngd Dr in sha ALLAH hakan bazai sake faruwa ba kuma yanzumma bazan kyaleshi ba dole ne na hukuntashi.
    Bakomai Hajiya ALLAH ya kiyaye gaba Magunguna ta rubuta Mata sannan da dokar sata A ruwan zafi da gargadin karya sake yasake neman Wani Abu daga gareta sainan da Wani Lokaci aibama saikin Fadaba Dr saiya ganta zai sake ai.

Sosai taiwa Dr Godiya tatafi Harara ta wurgamai Mutumin Banza Mutumin Wofi da yar Mutane ta mutu ina tabbatar ma dakaima kasheka za'ai.
    Kuma ka dauketa ka kaita bangare na acan zata zauna rai hade Hajiya ke wannan Maganar Daukarta yai kamar zayyi Kuka shifa haryanzu behuce daga abunda sukai Masa ba na rabashi da Masoyiyarsa dasukai Tsabar mugunta irinta Kamal Suna tafe yana mintsininta tana ji Amma bakinta ma bazata iya budewa ba dan harshi ba karamin Azabar zafi yake dan Har lebanta ya kumbura tai suntum😥 koni na Tausaya miki Hajara.
    Daki guda Hajiya ta ware Mata sosai ta dinga Kulawa da Ita ta zubar da makaman yakinta saita warke kozata dora acewarta Ahankali tafara samun sauki ko Muryar Kamal taji tadinga zabura kenan kota fashe da Kuka dan tatsaneshi ko san jin Muryarsa batayi bare kuma taganshi Kullum tana kulle adaki tawarke garau alokacinne ta dawo daidai kotaji Muryarsa ta daina razana da firgitar da takeyi.
    Nan ya takurawa Hajiya tabashi matarsa sukoma bangaransu Hajiya tace batasan zanceba dakyar ya lallabata ta yarda ranar Hajara jitai kamar maka barta Za'a Maida ita sosai take rusar Kuka Hawaye shabe shabe haka Hajiya tatisa keyarta tamayar da ita tundaga Wannan Lokaci takoma sabuwar rayuwa dan ba Azabar da Kamal baya bata badamar ya ganta azaune har wankin Bango sata yakeyi dandai kawai karta Huta tuni ta rame tafige tai baki.
    Can kuma Duk sati saiya kaiwa Umma kaya niki niki Aleda hankalinta kwance suke cin kayansu kodamuwa da rashin ganin Hajara batayi dan tasan hankalinta nacan Akwance da wannan ya sake siye Umma yayi hakanne tayadda kome Hajara zata fada mata bazata taba yadda ba.
Daga karshe ma haka yace Aisuntafi can garinsu tare da Hajiyarsa ai Umma aka sake sakan kacewa tadinga shiwa Kamal Albarka shiko Mugun sai Dariya yake Azuciyarsa Yasan Abunda yake Kullawa.Yana Matukar ganin Mama da kima da Daraja dan Sosai yake Girmamata inyaje gidan yayita hangen Hanya kozaiga Wa'at amma bata yarda Tafito harsai ya tafi.
   🤔🤔🤔Kunji Ja'iri.
         Taku Akoda yaushe.
         Kulsoom Isma'il Idris
        .......✍️✍️✍️✍️
       
            WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
          PART TWO
Chapter 11
    Yaya Abie bakaga pics din Saukar Jidda da mukaje ba Safna ke mikawa AA wayar dake Hannunta kamar Bazai karbaba saidai ya Amsa pic din yake Kallo daya bayan daya yana Kishingide sake mikewa yai Saboda ganin wadda yake kwana yake tashi Saboda tunaninta,Safna datai kuri tana Nazartarsa Dagawa Ammi gira tai Murmushi suka saki a tare alamar Jinjina Ammi tai mata.
    Yaya Abie Munyi kyaune sai Lokacin yasan kwafsawar da yayiwa kansa tsuke Fuska yayi Ina Wani Kyau anan Kun fente Fuska kamar Yayan Aljanu Haba yaya yanzu duk wannan Wankan da mukai bamu Burgeka ba ko mudai baka yaba ba aika yaba Na WA'AT dan bawanda bega irin kyan dataiba awajan Walimar nan dan wasu Maza dakyar aka rabasu Saboda dambe sukasha akan Suna Sonta.
    Besan sanda ya daka mata wata irin tsawaba tsalle tai takoma bayan Kujera Saboda tsabar firgita jiyayi gaba daya Wani Irin Kishi ya rufe Masa ido Zuciyarsa har Wani harbawa take tana barazanar darewa Biyu ita kanta Ammi tsawar ta razana ta Amma ta dake baki Bude take Kallonsa gaba daya idanunsa sunyi Jajawur Harwani Huci yake ikon ALLAH Abunda Ammi tafada a ranta kenan kafinta gimtse Fuska.
    Ya haka kawai daga Yarinya ta nunama hotunan sauka katashi ka buga mata wannan Uwar tsawa kamar wadda tagaya maka Wani Mugun Abu,sai asannan ya dawo Hayyacinsa sai kuma ya kama kame kame yama rasa Abunda zai kama yafada.To daga yau tadaina baka Duk Wani Labari tunda na lura basonji kake ba tsam ya tashi ya fita daga cikin parlon Part dinsa nagidan ya wuce da wayar Safna A hannunsa saidai ya shiga Bedroom ya sauke Wani Numfashi ya fesar dafe kansa yayi meyake damunsa haka ina ruwansa ma dan ance ana sonta da harzaiji Wani Damuwa akan hakan.
    Wayar Safna ya kurawa idanu Computer dinsa ya dauko ya kawashe gaba daya Photon dake Ciki dan sunsha hotuna dama Safna da Biyu ta dinga yimusu dan ta nunawa Yayan nata befitoba sai wajan karfe Biyar na yamma haka yafito yana ta Muzurai Shi Alallai ya tsare gida dan karma asake tadomai da wata Magana aje wayar kawai Yayi yadauki Key din Motarsa yayi Waje Ammi Binsa da kallo tai tana Murmushi dan tuni ta harbo jirgin dannata ya kamu.
    
    Anty Juwaira takira ta labarta Mata abunda ya faru sosai tai Farin ciki itama Ammi yanzu dai zanyi kokari duk yadda za'ai yazo Zariya sonake su hadu batare dasu kansu sunsan da hakan ba indai wannan ne ba Matsala dama akwai Wani sako daza akawo miki sainace shi zaikawo shikenan ma hakan yayi tattaunawa sukai Sosai akan nanda sati daya zata aiko shi in sha Allah.
    Gaskiya Ammi ina Matukar Farin ciki da wannan Auran Wallahi muje gidan Yaya Musakata Muwala Waccan Me duwawun kamar Akuya ta mike tsaye tadaina mana kallan Banza ba wajanta mukaje ba,duka Ammi ta Kawo mata karna sake ji ai matar Yayan kice Itama tazama Yayarki nagaya miki banason rashin Kunya to kiyi Hakuri Ammi taya zan hakura Alhalin ban tabbatar dakin daina ba Nadaina Ammi To shikenan.
         ......✍️✍️✍️
      
           WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
          PART TWO
    Chapter 12
    
    Harzai wuce dakinta Yaudai yaji yana bukatar ya leka yaga Lafiyarta dan duk da bayajin sonta kokadan yasan Hakkinta ya rataya A wuyansa tura kofar dakin yayi Wani hayaki ne ya bugi Fuskarsa gaba daya Dakin ya turnuke da hayaki saidaya dade atsaye sannan ya fara hangenta shisha take zuka Kaida Gani ta kware a zukar shishar kuma ba yau tafara ba ba jiyaba cikin Mamaki yake Kallon Fareeda yaushe tafara Shaye Shaye dama tanayi besani ba ko Yanzu ta fara tambayar dayakewa kansa kenan.
    Dago idanunta tayi dasukai Jajawur budewa take tana kullewa dagani ta bugu da alama ba iya shishar tasha ba Kwabe yagani Zube agabanta Shaye Shaye Abunda yake ta nanatawa kenan A Zuciyarsa shi yau Matarsa ke Shaye Shaye, binta kawai yake da Kallo da rinannun Idanunsa dasukai masifar yinja saboda tsananin Bacin rai Jinta kawai Yayi Ajikinsa Tana zantuka marasa kan gado daurewa kawai Yayi Amma gaba daya ita karan kanta wari takeyi.
    Dif yaji tayi saidaya duba yaga ashe bacci tayi daukarta yai ya ajeta a gado yama rasa wane hukunci zai yanke mata kamar Matacciya haka takejan Wani shegen Munshari Kamar rago yana daya daga cikin Abunda yasa yadaina kwana waje daya da ita kenan saboda Munsharinta da bashida dadinji saidai ka hakura da bacci katashi ka zauna bincike dakin yayi Duk wasu magani daya Gani saidaya kwashesu ya zubar sannan yayi hanyar barin dakin.

Cak ya tsaya hango wani jarka akasan Gado harzai gaba yaji yanason yaga mene acikinta dawowa yayi da baya ya sunkuya ya dauko ta Jujjuyata yake a hannunsa ganin wani Bakin ruwa aciki tinani yake mene wannan,saida yayi tunani me zurfi sannan ya gane menene rubutu.

Tome zatai da rubutu kodai bata da lafiya ne kai a'ah ba haka bane wani Murmushi ya saki tunawa da wani abu hmmm Yace tare da girgiza kansa sai Lokacin yayi tunanin sanda tayi Masa Bakin Farfesu abun Dariya yabashi Inda ya ganta sunkuyawa yayi ya ajiye tare da barin dakin.
     
Yana shiga Dakinsa zama yayi ya dafe kansa yana tunanin wai ita Fareeda wace irin Macace dabata da halayen kirki shitunanin sama ya akai ya Aure ta yaushe ma haryaji ya fara santa shidai yasan adacan ya tsaneta tsana metsanani kuwa saboda ballagazancinta yawo da Maza acikinta Harda na siyarwa,Lokacin da suka fara haduwa yafara tunawa.
    Shekaru biyu baya ya tafi tunani Wata ranane da safe yafita Motsa Jiki dan in yana wannan gudun kowane layima fadawa yake karfe 7 nasafe ya kutsa wani Layi shima Babban Layine dan da Manyan Gidaje Sosai Hayaniya Yafara jiyowa a kofar wani Gida saidaya kara Matsowa Wata Budurwa ya hango bamà Zai cemata Budurwa ba dan Akalla zasiyi Sa'annin Juna ita da wani Saurayine dayake tsaye cikin tsananin Damuwa.
    
Dan ALLAH Fareeda meyasa kike Wulakantani Danna ce ina sonki naga dai Talaucinnan ALLAH ne yaso yagammu Ahaka amma Har iyaye na kike zagi kawai danna nuna ina sonki kuma Auranki zanyi wani Kallon Sama da Kasa takeyi masa Fuskarta a yamutse tsaki taja kai yanzu ka kalli kanka ka kalleni ka kalli gidammu ta ina Muka hadu kai kasan Akwai Ban banci bayan tsabar tsaurin ido karasa wajan wadda zakazo kaf Unguwar nan saini.
    Aini ke Nake so ba suba to bana sonka me sonkama bana sonsa kaida ganina Kasan Munyiwa Talauci Tazara metarin yawa,kuma Wallahi gidannan bazaka sake shigarsaba daga cin arziki zaka zago Kace kana sona kama gama cutata Wallahi Magana Zai sakeyi ta hankadashi Saura kadan ya fadi takoma Gida ta bame Get din Gidan su.AA Wucewa yayi yabar saurayin a tsaye cikin bakin ciki da bacin rai ya dade a tsaye kafin yabar kofar Gidan.
   
 Haduwar su ta biyu ita da wani Alhaji ya gansu ta kyafe a Gaban mota gaba daya ita daban Motar daban Abun Ba karamin Dariya ya bawa AA ba gaba dayanta batai Kalar hawa Motar ba shopping dama ya shigayi Zai Saiwa Kannan sa sakon da suka bashi gam yaji sunyi karo da mutum yana dago kansa yaga Fareeda cikin Rashin Mutunci tadago zatai Magana Amma saita kasa ganin irin Kwarjinin da yayi Mata take taji tana Masifar Sonsa.
           ........✍️✍️✍️
    
              WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
          PART TWO
    Chapter 13
    
    Karkade jikinsa yayi yayi Mata wani Mugun Kallo danshi haka kawai yaji ya tsaneta Ya tsani Mace Mara Kumun kai Alhajinne ya taho Baby Meyake Faruwane yake kawai tayi tare da fari da ido bakomai Alhajina ba kunya takama Masa Hannu sukabar wajan Tanayi tana Waiwayen AA tare dacin Alwashin Duk Inda yake saita Nemoshi.

Mom Wallahi bakiga yadda Gayan nan yayi minba kuma daganinsa Iyayansa ba kananan Mutane bane Mom Washe Baki tai to Aidama irinsu Akeso yanzu tashi zaki Mutafi wajan nakan tudu Koma aina yake Zai binciko manashi Tsalletai kamar Wata Yarinya tafada daki Shiryawa tai cikin Wani Wando iya guiwa Kannan yasha kalba ta gashin doki.
    
    Basu zame ko ina ba sai wajan Boka Tunkan siyi Magana ya zayyane musu Abunda ke tafe dasu Wani koko ya dauko yayi Wasu sambatu aciki saiga Hoton AA ya bayyana cikin Zabura Fareeda tace shine yanzu me kukeso aimasa sonake ya mato akaina yaji duk Duniya babu wadda yake so saini kuma ni kadai Zai dingajin Maganata Angama indai Wannan nanne zaizo da kafafuwansa ki zuba ido.
    
    Fal Farin Ciki suka dawo Gida kwana daya biyu kamar Almara saiga AA harcikin Gidansu Kamar zaiwa Mom Sujjada sanda yake gaida ita dan Banza Yazo Hannu cewar Mom a Zuciyarta Fareeda kuwa shan kamshi ta dingayi masa tana jamai aji shikuma sai Lallabata yakeyi.

Abinci Mom ta girka da kanta yakarashan Maganin wajan Boka da Lemu nan ya zage yaci Abincin Duka daba dadinsa yakeji ba.
    Yana komawa Gida ya samu Ammi da maganar Ya samo Mata tayi Farin ciki Sosai Amma Abunda ya bata Mamaki yadda yaketa rawar kai yana Murna kamar Wani Shashasha gaba daya wunin abata Labarin Fareeda ya kareshi tuntanasan jin Labarin har abun ya isheta Amma kememe yaki dainawa daga karshe zuru tai tana Kallon sa Haka kannensa Safna da Marwanah dan Lokacin ba ai Auranta ba.
    Mahaifinsu AA ya jima da rasuwa Alhaji Abdulkadir Babban Mekudine Yaruke Mukamai da dama a cikin Gwamnati AA shine Babban Dansa Al-Ameen Abdulkadir Al-Ameen shine Mutane Ke Kiransa AA sai Marwana da Safna sukenan Yayan da suka haifa ya rasu a Wani hatsarin Jirgin Sama daya faru sunshiga Matsannancin tashin hankali Musamman Ammi da AA dan Alokacin yanagaf da Kammala karatunsa na Soja daya tafi shine yaci gaba da jan ragamar Gidan sai Dangin Mahaifinsu dasuka karbi Wani Ayyukan dayake suna da rukon Amana Dukiyarsu koyaushe kara habaka take dan Alhaji Abdulkadir Bakaramar Dukiya ya Mutu ya bari ba.
    
    Washe Gari AA ya garzaya Kaduna wajan Dangin Mahaifinsa Akan yasamo Matar da Zai Aura Jikinsa Harrawa yakeyi Kanin Baban nasa Alhaji Kashim zuba masa ido yayi yana Nazar tarsa ita Sadiyan ce ta turoka a ah Abba aibama tasan zanzo ba Jijjiga kansa yayi to ALLAH ya sanya Alkhairi Zamiyi Magana da ita tashi kashiga ciki tashi yayi Yashiga cikin Gidan su kansu yan Gidan sunyi Mamakin Ganinsa dan yana dadewa beje ba.
    Hajiya Sauda ce tace  Lallai Manyan baki saiyau ake ganinka uhm Wallahi yanxumma Maganar Aure nace ta kawoni danna sami Matar dazan Aura Wani Banbarakwai Hajiya Sauda taji kare Masa kallo takeyi ita sai Lokacimma taganshi duk afurgice kamar wanda aka koro yanzu zancan Aurnne ya kawo ka kenan Washe baki ya karayi kamar Wani Gaula eh Hajiya To ALLAH ya sanya Alkhairi Ameen.
    
    Daki tashiga waya takira Ammi bayan sun Gaisa take fadin kuma yau saiga Abie A Kaduna abun Sosai yaba Ammi Mamaki Kaduna kuma Wallahi Hajiya begayamin ba Ajiyar Numfashi ta sauke nanta labarta Mata komai shiru Ammi tai na Wani Lokaci Ni Hajiya gaba daya Nakasa gane kan Abie tunjiya gaba daya baya cikin Hayyacinsa anya babu Wata akasa nima Abunda nai tunani kenan Abie da magana bata dameshi ba Amma kimjiyoshi Yasa Kannan sa agaba yanata basu labarin Fareeda ni Wllh harnaji ma na tsaneta cewar Hajiya Sauda dan Wallahi daganin Wannan Son Bana ALLAH bane Amma Muci gaba da Addu,a.

      Aranar ya juya ABUJA dan inbega Fareeda ba jiyake kamar Zai Mutu Dan danan Karamar Magana tazama Babba dan cikin sati Biyu saida akaje aka nemo masa Auren Dangin Mahaifinta Mutum biyu suka bada Auran nata dan Mahaifinta shima ya rasu a Wannan Lokacin Ammi ta shaki Bakin ciki Gaba daya AA bashi da lokacin kowa saina Fareeda inbasa tare to suna makale awaya haka Ammi ta danne taci gaba dayi masa Addu,a.
     Lefe Ammi ta hada akwati 6 Amma ya ce shi sam wannan kayan sunyi Kadan Makudan Kudade ya fitar aka sake karo Wasu shidan aka kai gidansu Fareeda Party saidata hada kala Biyar kowanne kuma a Aljihun AA bakananan Kudi ya kashe Awannan Biki ba Ammi babu wanda ta gayyata dan wannan batajinsa Amatsayin Auran dazata tara Jama'a dan gaba daya Auran Bemata ba tana hangen Akwai gagarumar Matsala.

    Anyi biki Anwatse daga Amarya da sai Ango da yan Aikin ta tundaga sannan ya fara shiga Matsaloli saboda Auran Fareeda yaji sam ko hanyar gidansu bayasan bi kai Numbobin Ammi ma gaba daya gogesu yayi sai Abunda Fareeda tace Aduk sanda zata bashi hakkinsa saita yankamai Kudi ya biyata haka koda yaushe Matukar be biyata ba bazata taba Yarda ba ahakamma akwai lokacin da take bashi Lokacin yana cika zatace ya tashi yabar Mata daki.
    Haka Zai fita yadai koma kamar wani Yaronta su kansu yan Aikin Gidan sunsan Oga Yana cikin Matsala dan danan ya rame kamar bashi ba duk gayunnan yanzu babu shi ya susu ce ya fita daga hayyacinsa Wajan Aikinsu kwazonsa ya ragu dan Ogansu Har Magana yayi Masa akan meyake Damunsa Haka yace Bakomai.
    Sauke Ajiyar Zuciya yayi gama tunanin da yayi.

Sakejin tsanar Fareeda yayi dan akanta yarasa abubuwa da dama arayuwarsa bazai taba santa ba har gaban abada abinda ya ayyana aransa kenan.
        .......✍️✍️✍️

             WA'AT
By Kulsoom Ismail
Mrs Baba Bello Abubakar
Kim Aneesat
      PART TWO
Chapter 14

      Kamar Kazar da kwai ya fashewa aciki haka tashigo Gidan duk da Sabbin kaya tasaka Amma kallo daya zakai mata ka hango tsantsar wahala atare da ita,Ina wuni Mama Shiru Mama tai dan tafi tunanin kunnan tane beji daidai ba sake Maimaitawa tayi cikin Mamaki Mama tadago tana Kallonta Kare Mata Kallo takeyi ganin kamar ba Hajara 'Yar Gayunnan data sani ba duk ta kwantsame ta lalace tayi Wani baki.
    
       Lafiya Lau Hajara sai yau kika tuna damu cewar Mama Murmushin yake kawai Hajara tayi Sannu da Zuwa to Shiga Mana Umma ce yafito daga daki Sai Hura Hanci take hango Hajara datai da Mama Suna Magana abun ba karamin Haushe ya bata ba.To wai Ubanwa kike gaya mata da kika tsaya kuna Magana ko kuma tsarabar da kika kawo kike Juye Mata Zuwatai taja Hannun Hajara sukai gaba.
   
 Mama ce ta girgiza kai ALLAH ya kyauta Angirma Ba'asan Angirma ba bin Hajara da kallo Mama tai Wani Abu yana mintsinar Zuciyarta dagani tana cikin Wani Hali wanda ita kadai tasan Halin da take ciki ALLAH ya yaye miki koma meke damunki sunkuyawa tai tacigaba da Aikin ta.
    A dakin Umma kuwa kallon Hajara tai cikin takaici waini Hajara Aurenne yasaki kikai Laushi ko yaya ALLAH ya rufa miki asiri kinacan Gidanki hankali kwance kici kisha baki da wata Damuwa ga 'Yan aiki nan komai saidai aimiki.
    
Bakin Umma kawai Hajara ke kallo wai 'Yan Aiki to ai itace 'Yar Aikin Bawani ba, Fashewa tai da Kuka Umma sakin Bakitai tana Kallonta me yau naji Sabon iskanci Kukan me kike cikin gunjin Kuka take fadin Nidai Wllhi Umma bazan Komaba nagaji da wannan Auran da nasan hakane da banba ke Dallah yiwa mutane shiru Me akai miki yaro dan arziki Duk sati sai munci Kaji zaki mana bakin ciki yaro dan Mutunci.
  
  Eh Lallai Kamal ya cika mugun bawa dama Abunda ya shirya mata kenan Shiyasa datace zatazo gida be nuna wata damuwa ba yasan Abunda ya kullamata,Wallahi Umma dagaske nake miki Kamal mugune bashi da imani da Tausayi Kamar jaka haka ya maidani sake rushewa tai da Kuka cikin Hasala Umma kefadin waini yaushe ma kika lalace haka to Wallahi baki isaba saikin tafi nanda Anjima bazaki janyomun asara ba nafara jiyo kamshin tafiya Hajji.

 Duk yadda Hajara taso taiwa Umma bayani kememe taki saurararta tsakar gida tafuta tai zaman dirshan tana rusar Kuka ayau tayi Nadamar biyewa Umma gashi Abun Duniya ya rufe Mata ido Takasa tsayawa ma ta saurareta,yaune karo na farko dataji Nadamar Abinda tadinga yiwa Mama da kannanta gashi tunbaaje ko ina ba tafara ganin sakayya.

Tashi tai Jiki bakwari tanufi dakin Mama cikin Tsananin jin Kunya to intajema mezatace mata tsayawa tai a bakin dakin cikin sanyin Jiki tajuya zata koma dan bataga abunda zata gaya mata ba daga daki Mama datake kallonta tun tahowarta tace shigo mana Hajara,cak tatsaya juyowa tai da Sallama tashiga dakin Lallai su Hajara anji Maza yau itace harda Sallama Amsawa Mama tai babu Wani sauyi a Fuskarta.
   Zauna Mana zamatai tana wasa da yatsun hannunta gaba daya takasa Magana dakyar dai tayi kundun bala ta tattaro Abun fade Mama dama zuwanai nabaki Hakuri akan dukkan abubuwan danai Miki Agidannan Dan ALLAH kiyafemin tafada tare da rushewa da kuka.

Tsam Mama ta tsaya tana kallonta gaba daya taya mutse tayi baki wahala naneman kassarata tana yarinyarta da Ita dudu 21 take Amma jita takoma kamar yar 35,tambaya Mama ta jefo mata baki da lafiya ne Hajara tofa dama meneman kukane Akajefeshi da kashin Awaki sake bare baki tai tana Kuka Wallahi Mama gwarama Wani Mara Lafiyar yasan cuta yake koyaushe zai iya warkewa ALLAH zai kawo mai sauki nikam bansan ranar warakata ba.
            .........✍️✍️✍️

            WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
           PART TWO
Chapter 15

Cikin Nazarin Magan ganunta Mama take kallonta hannu ta mika mata alamar tazo kusa da ita da rarrafe Hajara ta karasa gareta kanta ta dora acinyarta alamar Rarrashi tana shafa kanta wasu zafafan Hawayene suka xubo daga idanunta Abunda Mahaifiyarta takasa yimata Ayau shine Wadda suka zalunta a baya take mata Wadda ta kawota Duniya ta gagara taji matsalarta saboda son Zuciyarta sabuwar Nadama ce ta kamata ta tabbatar sun tafka kuskure abaya Amma zata gyara koda zata Samu sassaucin halin da take ciki.
   
Saidai Mama ta Tabbatar tafara samun nutsuwa tashitai ta dauko Mata lemu me sanyi Cup ta dauko ta zuba mata mika mata tayi ba musu takarba dan dama abu mesanyin take bukata saidata shanye tas tafara sauke ajiyar Zuciya.Hannunta Mama takama tana kare Mata Kallo gaba daya Jikinta tabon dukane bawai iya Jikinta ba har Fuskarta dazaka Lura shatin yatsune A kwance kawar da kanta tai danjin Wani abu dayake sukar Zuciyarta.
 
 "Mecece Damuwarki"?
Nan Hajara tafara Labarin dukkan halin da take ciki na irin wahal walunda take Fuskanta dan itama Hajiya tun sanda taji sauki ta watsar da Lamarin ta inzatai sati bata gantaba bazata Tambayeta ba damar da Kamal yasake Samu kenan naci gaba da azabtar da Ita.
   Sosai Mama taji Lamarin Har Zuciyarta dan Kallon yaya take musu bata banbantasu da yayan data haifa.Nasiha Sosai Mama tayi Mata da kwantar mata da hankali da koya mata dabarun zama da Miji daina yimasa rashin kunyar da take Matukar zatabi wannan matakan babu shakka zataga canji.

Sosai Fuskarta ta fadada da Murmushi dan bakaramin jin Dadin shawarar da Mama tabata tayiba tashi Mama tai ta zubo mata Abinci Hajara har hadiyar yawu take dan rabon da taci takoshi tunkan bikinta yau kimanin wata biyar kenan.Hannu baka hannu kwarya takecin Abincin Tausayinta ne yasake kama Mama tana mata Addu,ar ALLAH ya kawo mata Sassauci cikin zaman Auranta.

Saidata cinye tas ta kora da kunun Aya sai Lokacin kunya ta kamata ganin Uban Abincin data cinye Murmushi Kawai Mama tayi danta Fahimceta babu kunya tsakanin Ya da Mahaifiyarta in har baki koshi ba saina karo miki Hajara. A ah nakoshi dama Aleda zaki zubamin inzan tafi saikiban naci da daddare to ALLAH ya kaimu tashitai tafuto daga dakin Zuciyarta wasai saitaji inama ace Mama ce Mahaifiyarta da Duk hakan bata faru a gareta ba.
    
Babu wata Maganar Arziki data sake hadata da Umma hartata shi tafiya Abun yabawa Umma Haushi ganin tazo hannu sake bata kawo mata komai ba Mama taje taiwa Sallama miko mata wata Leda tai Babba dagani kayan Amfanine ciki godiya tayiwa Mama kamar karta koma haka takeji Amma bayadda ta iya haka tatafi cikin takaicin Auran Kamal.
   
 Sake sunkuyar dakai yayi A Gaban Malam Kallonsa Malam yakeyi yaji dame kuma yazo sake muskutawa yayi um dama Malam cewanai yaushene tafiyar nan dan nafara shiryawa kar Lokaci ya kure.
    Cikin Rashin Fahimta Malam ke Kallonsa wace tafiya kenan dama akwai wata tafiya dazaai bansanta ba.Sake gyara murya yayi dama tafiya Saudiyya nake nufi nida Aisha da zamuyi A matsayinka nawa turus Appa yayi yanaiwa Malam kallon Rashin Fahimta.
    🤣🤣🤣Anfaxo daidai wajan
           .......✍️✍️✍️
    
            WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesa
           PART TWO
    Chapter 16
    
    Indai Maganar rakiya kake In sha ALLAH baza'a manta dakaiba dama za a gayya ceka,Malam kasani acikin Duhu ban gane Akamme kake Magana ba, Murmushi Malam yayi zaka gane yanzu kuwa mene alakarka da Wadda aka bawa kyautar Mahaifinta da Mahaifiyarta akace to kaikuma babu dayan da kake Ciki acikin wandana Lissafo to kaga kuwa dole nasaka acikin yan rakiya.
    Cikin rawar Murya Appa ke Fadin To ai nine Mahaifinnata iya sanina dai bansan kana da wata 'Ya mekalar sunan wanda akaba Kyauta ba sako kuma ya isa wajan Mahaifinta da Mahaifiyarta karkasake zuwa min da mgana Wadda hankalima bazai dauka ba zai sake Magana Malam ya daga mai hannu alamar ya sallameshi haka yatashi gaba daya kansa ya daure shida 'Yarsa ace batasa bace tab ai Wallahi baa isa ba.
    Malam binsa yayi kawai da kallo ALLAH ya shirya dan har yanzu be hango Nadama acikin idanunsa ba Abun Duniya ne yasashi fadin 'Yarsa ce taci Kyauta muje zuwa nidakai zanga wanda zai baka Kujerar balle harka tafi gida ya shiga.

Inna yake bawa Labarin Abunda yafaru Abun ma ya bata Dariya kabarni dashi Malam inyasan wata aibesan wata ba yanzu aka fara wasan babu Inda zaije yanaji yana Gani zai asarar wannan Kujerar Wallahi.
    Haryau beyi Nadama ba sai ranar dayayi Nadama zan masa Sassauci matukar beyi Nadama ba nima inakan bakata cewar Inna da take Magana cikin Bacin rai dan Sosai Kabiru ke kona mata rai tunda ta Haifeshi yake bata wahala daga yarintarsa har girmansa babu Wani canji saima kara tabarbarewa da yakeyi.
    Cigaba sukai da Tattaunawa Inna Lami ce tashigo Itama akaci gaba da zancen da Ita dansu atsakaninsu ba batun Wani kishi Tamkar yan Uwan Juna haka suka dauki kansu tundaga kuruciyarsu lafiya Lau suka zauna balle yanzu da girma yahau kansu Shiyasa Hankalin Malam akwance daga kansu be sake kara Aure ba daman.
    Ni yanxu babban burina naga Auran Yarinyar nan shine Mafarkina ako yaushe cewar Inna kinkusa Gani Aishi Aure Lokaci ne kuma Inaji ajikina lokacin ya kusa  In sha ALLAH.
    ALLAH ya tabbatar mana da Alkhairi Malam cewar Inna Lami Ameen Suka Amsa gaba dayansu.
           ******
    Gobe in ALLAH ya kaimu zan aikaka gidan Mamanka ta Zariya Inaso zaka kaimata Wani sako Zariyan kawai data Ambata saida yaji Wani ras Lumshe idanunsa yayi yana sauke wata boyayyar ajiyar Zuciya Inama zai ganta hakan yake Ayyanawa a Zuciyarsa,Duk abinda yake Ammi na lura dashi Murmushi kawai tayi ta basar zaka samu zuwa kona aika Bala Direba ya mutsa fuska Yai kamar gaske Ammi dakin aikashin ma inasa rai da Wani Aiki gobe to badamuwa ÀLLAH yakaimu saina aikashin.
    Bude idanunsa yayi yana kallon Ammi azatansa zata dage saiya je Amma sai yaji ta hakura da sauri haka tuni Zuciyarsa tafara bugawa maimaita Bala Direba yake a ransa aiko zaiga tayadda zaikai tashi yayi rai bace yafita Ammi tabishi da Kallo tana kunshe Dariya waishi irin jan ajinnan shi a Lallai bason Zuwa yake ba.
    ........✍️✍️✍️
     
            WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat 
       PART TWO
Chapter 17

 Karfe 6 Agidan Ammi tayi masa haka ya shigo sai Muzurai yake yana bata rai bakowa A Parlour Kowa yana can kwance yana hutawa ko yan Aikin ma basu fito ba Dan Ammi tace sudinga kwanciya Suna hutawa kar 7 sadinga fitowa sukama aikinsu sosai kuwa sukaji dadin hakan sun yaba da karamcin Ammi.

Sofa ya samu ya lafe gaba daya Jiya beyi Bacci ba Saboda Wani irin doki yakeji na zuwansa Zariya abunda betaba jiba shidai yasan shekara da shekaru yana zuwa amma be tabajin hakanba sai A wannan Lokacin.

Tundata sauko takejin kamshin Turaransa Amma tasan yanzu dai bazata taba ganinsa agidan ba sake shigowa parlon tayi sai asannan idanunta suka sauka akanshi tsam ta tsaya tana Kallonsa abun ma abun Mamaki yau shine da fitowar Sassafe to ina zashi haka,Zama tai akusa Dashi tare da bubbuga kafarsa Abie tunsanda tafito yasan da zuwan mutum parlon motsawa ne kawai beba.
    Tashi yayi ya zauna cikin girmamawa yake gaida Ammin tasa kansa ta shafa ina fatan katashi Lafiya Amsa mata yayi da lafiya kalau sake Kallonsa tai kamar Wani Sabon Ango yaci Uban wanka wata tsadaddiyar Gezna ce ajikinsa Fara kal da hula baka takalmi baki kai komaidai Ma sha ALLAH.Aduk sanda ta kalleshi tatuna dan tane tana riskar kanta acikin Farin ciki na samun gwarzon da danda ya maye mata gurbi masu Yawa.
    A Duk sanda ta kalleshi Fuskar Mahaifinsu take Gani a Fuskarsa dan Suna tsananin kama bata wasaba Girgiza hannun ta yayi ganin tatafi Duniyar tunani mekike tunani haka Ammi Murmushi kawai tayi tare da bugun kafadarsa Ina yiwa ALLAH Godiya ne daya Mallakamin da Kamarka danda kowace Uwa zatai Alfahari Dashi ina rokon ALLAH daya rabaka da sharrin Makiya sharrin Mutum dana Aljan sharrin karfe ALLAH ya kare munkai A duk Inda kake.
              
 Sanyine ke kwarara a cikin Zuciyar sa aduk Lokacin da Ammi ke masa Addu,a yanaji babu wanda ya kaishi sa'ar Mahaifaiya A Duniya sosai suke Alfahari da ita nazamtowar ta Mahaifiya Agaresu Ameen Ammina ALLAH ya kara Miki nisan kwana Murmushi kawai tayi masa.
    Wai Abie ina zakaje da sanyin Safiyar nan kallonta yake jin Abinda take tambayarsa kodai ta manta Inda tace zaije Ammi Zariyan Zan tafi baki bude Ammi ke Kallonsa eh Lallai Abun da gaske yake yinsa yamutsa Fuska tai aini da harna hakura da zuwannaka na aika Bala kawai yakai yanzumma na hutar dakai gwara kazauna agida kahuta.
   
 Gimtse Fuska yayi waiya Ammi take Masa hakane shikuma bayason ya nuna dagewa akan saiyaje zata Iya tunanin Wani Abu tunda nariga nazo kibani kawai saina kai mata tunda inason nai Mata Alasanya Alheri dama aranta Dariya takeyi ganin ya waske wai Alasanya Alkhairi zaije yayi mata Kaji Gulma To shikenan hira sukaci gaba dayi anan Sukayi Break tare sai 10 ya fita daga gida shikadai ya dau hanya duk yadda yaransa sukaso yimasa rakiya hanasu yayi.
    
    Sallama sukai suka shigo katafaran parlon Gidan yawwa Jidda kun dawo ai Wallahi Mami kinga dakyar tataho wai karya nakeyi bakice kina kiranta ba Dariya Anty Juwaira tayi kai kudai bakwa rabo da shashanci dama baki zamiyi shine nace takiraki kiyinmin Zobonnan da Mama takeyi da Kunun Aya da Fara'a A Fuskarta take fadin To Mami ALLAH nata karyarta ce dandai kawai nazo ne ashe kece da gaske aikuwa dai nice Wa'at yanzu dai ashiga Kiching Afara aiki to suka Amsa.
    Daka mata duka tai abaya Wallahi baki da mutunci harni zaki karyata kamar ni da hakorana guda Talatin Dariya Wa'at tayi Sannu wanda ta yankewa kasa Cibiya Auto dake baki saniba sai yanzu haba yarinya anbarki abaya ninan da Kika ganni naga jiya naga yau ehe to Sannu Kaka ta tsandauri Dariya suka kwashe da ita haka sukaci gaba da Aikin su Suna wasa da Dariya.
           ........✍️✍️✍️✍️
    
                 WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
         PART TWO
Chapter 18
      
    11:30 sun kammala komai kamshine kawai yake tashi ko ina fes fes dakin bakima sunje sunkara shareshi an fesheshi da turarruka masu dadin kamshi.

Yawwa to yanxu kuzo kuyi wanka saiku shirya kuma ai ba'azo aganku kaca kaca ba uhm aini Mami Gida zan tafi aibaki isaba inkinga kinbar Gidannan tofa baki sunzo suntafi ankara gyaran gida sannan zaki tafi gida,kamar zatai Kuka take Kallon Mami banza Mami tai da ita dan tasan halin naci Irin na WA'AT yanzu zata dameta da magiyat tabarta tatafi.
    Dakin Jidda suka wuce acan sukai wanka kaya iri daya Mami ta dinka musu riga da sket dunkin ba karamin kyau yayi ba kaida Gani kasan ansha kudin dinki das yayi mata kamar an Aunata mayafi Farare tas sabbi ta sake dauko Musu sai yari da sarka Mami da kanta ta zauna ta tsantsarawa WA'AT Kwalliya dan itama gwanace wajan tsara kwalliya koyaushe zaka sameta cikin kwalliya da Ado agidanta dan inbaka saniba bazakace ta haifi Jidda ba.
    
    WA'AT gaba daya Mamaki ya kamata wasu Irin bakine wannan dahar sai ammusu kawalliya dan zasuzo shirutai tabar Abun acikin ranta Jidda tundazu take kunshe Dariya dan tuni tasan Abunda ake kullawa Aminiyar tata harso take taga yadda wannan wasa zai kaya tanaso taga yadda za'ayi insuka hadu awaje daya fatanta dai tayiwa yayannta yaji ya mato akan son kawar tata zatayi Farin ciki mara misaltuwa.
    Tas tagama fente musu Fuska bakaramin kyau sukai ba dagwas dasu kamar 'Yan biyu haka suke itakanta WA'AT data Kalli kanta a madubi Gani tai kamar ba itaba dan Ita sam bata kwalliya haka take barin Fuskarta Akoda yaushe shiyasa da ammata kwalliya zakaga tayi Wani Irin kyau mesanyi duk wanda ya kalleta Dole ya kara.
    12 daidai Get Man ya wangale masa kofar Get yana Masa sannu da Zuwa cikin Mutuntawa suka gaisa da Baba Megadi dan tsohone sosai ya manyanta kudi yadebo ya mika masa sosai yake Godiya.

Mami da kanta tafito takaishi Masaukinsa bayan tagama yimasa carin baya zuwa Inda take Murmushi kawai Yayi dan Magana gaba daya Wahala take Masa Inkaga yana surutu to da Amminsa ne fita tai daga dakin data ajiyeshi dan a harabar gida kayataccen parlon yake.
    Yawwa kutashi kudebi kayannan kuje kukai to suka Amsa Wani Farantine me matukar kyau aciki aka jera kayan Abincin Cup din Zobo da Kunun Aya WA'AT ta dauko A Fridge yayi Sanyi har raba ke zuba Saboda tsabar sanyin da yayi cikin Wani kyakykyawan Faranti ta jera itama dauka sukai suka fita Jidda ce agaba WA'AT na bayanta.
    
    Wani kamshi taji ya bugi hancinta me matukar dadi da san yaya ruhi Lumshe idanu tayi sosai kamshin yayi bala,in tafiya da ita Da Sallama suka Shiga dakin yana kishin gide saika rantse bacci yake Amma yana Kallonsu ta kasan ido Zuciyarsa ce tai Wani Irin tsalle ganin wanda yake tunani akoda yaushe tunanin sa dama tana zuwa gidanne kodai gizo idanunsa keyi masa ajewa sukai dagowa tai da niyyar gaishe da bakin ido biyu sukai dashi.
    Wani Irin kwarjini taga yayi mata ga Zuciyarta datake Mahaukacin gudu gaba daya jitai kafafunta narawa dan har Lokacin tanajin kaifafan idanunsa ajikinta batasan sanda ta durkushe akan guiwoyinta ba danji take kamar ya daddaureta da igiya mekarfin gaske,Tuni Jidda tafice daga dakin tana tikar Dariya ganin yadda Mutuniyar tata tsaiwama ta gagareta Lallai abu ya gawurta.
    
    Idanunta aruntse suke ahankali tafara budewa kamar me ciwon wuya tasake kallo wajan da yake yana nan yadda suka zo suka sameshi Wani shegen kallo yake mata na kasan ido saurin kawar da kanta tayi sai alokacin ta lura da Jidda ta gudu tabarta cikin sauri tatashi jiki na rawa harcin tuntube takeyi wajan kokarin fita Hi taji yafada kamar beson magana cak ta tsaya awajan takasa gaba ta Kasa baya.
    Kamar zatai Kuka haka ta juya tuni Hawaye yafara sintiri akuncinta sake bude idanunsa yayi sosai akanta Kuka yafada akasan Makoshinsa tome yayi mata wanda zaisa ta tasasa gaba tanai masa Kuka Jiyai Wani Murmushi ya subuce masa ganin yarintarta tasake futowa kamar wata sokuwa haka ta fara shashashekar Kuka sosai abun ya kara daure mai kai Lallai wannan yarinyar yar shagwaba ce daga Mata Hannu yayi alamar taje tunkafin ta taramai Jama'a adauka Wani abu yake mata.
    Murmushi ya saki tuno Wani abu dayayi acikin Zuciyarsa.
    Kome yatuna Oho 
    Kubiyoni danjin yadda zata kaya Taku.
    Kulsoom Ismail Idris
    Yawan Comment dinku yawan Jindadin Labarin da kuke karantawa.
        ........✍️✍️✍️

             WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
         PART TWO
Chapter 19

Saidata tsaya tagoge Hawayan Fuskarta sannan tashiga Mami ce ta kalleta wai har kundawo daga kaiwa bakin Abincin Ina Jidda nima banganta ba dan Mami batasan Jidda tadawo ba Jidda ce ta futo cikin tsokana take cewa wai yanaga harkin dawo wane Irin tarbace wannan aida kintsaya kin tayashi hira ni cikinane ya murda shiyasa nafito.
     Harara ta maka mata tunda wajena akazo ba dole natsaya na tayashi hira ba waike Jidda Meyasa kikemin haka nifa banason Abunda kike yimin to Yanzu menai miki daga Abun Arziki Yayana nefa aikema naga ya zama yayanki Ko Mami tafada tana kallon Mami ah sosaima kuwa banda abinki Wa'at kamar Wadda za'a yankewa kai nifa Gani nayima kamar kinyi Kuka ko Wani abu yayi Miki.

Saurin Jijjiga kai tayi kamar kadangaruwa bemin komai ba Wani Abu ya fadan a ido Murmushi kawai Mami tayi batace Komaiba Jidda ce ta kwashe da Dariya sannu Aminiyar Gaskiya dagani wannan Abunda ya fada miki a ido kinsha wahala banza tayi Mata danta lura sotake tamaidata Mahaukaciya.

Zumbur tamike ni Mami zan tafi Mama tace nadawo dawuri Zanyi Aiki kai Yaushe akai haka ALLAH Mami Mama batace ta dawo ba to aishikenan tashitai ta debarmata Duk abunda suka suya tacika mata leda kin karba tayi Mami ta bata rai keni bana son wannan halin naki nibake na nabawa Mamanki zaki kaiwa sai Lokacin takarba tana Godiya ke Jidda jekice Abie yazo ya kaita gida.
    Jidda har tuntube take tsabar zumudi kai wannan Abu yayi mata dadi WA'AT datake tsaye tana rarraba ido tunani take wane kuma Wani Abie ko Sabon Direba sukayi.
   
 Yaya Mami tace kazo Muje mu Maida kawata gida Alhmdlh abunda ya fada aransa kenan dama tunanin da yake a ransa kenan ta ina zaisan gidansu amma yanzu tunda dama tasamu baya dama kawai.

Bata rai yayi keni sa ankune nida kawar taki dazaki ce nazo namaidata Gida dani nakawo ta,cikin Marairaicewa tamatsa Kusa dashi Dan Allah Yaya Kayi hakuri ka kaita kagadai Mami tace nazo nakira ka.
    Saidaya gama shan kamshinsa Sannan ya mike kai sekarantse Dole akai masa nanko Zuciyarsa Fal Farin ciki Mami har Bakin Motar tarakosu hada ido suka sakeyi Dam taji kirjinta ya buga kaddai Wannan ne zaimaidata Gidan Yanzu in aka ganta Amotarsa fa tace wanene shi Ita da yau tataba ganinsa ma.Yauwa Jidda Shiga kutafi tare saiku dawo keda Yayan naki.
    Sai Lokacin taji sanyi aranta jinda Jidda za aje bayan Mota suka bude da nufin Shiga harze Shiga ya dakata yana Kallonsu kai wane Direban ku dazaku shige baya ga dan iskan Direba kunsamu kuna baya a hakimce ana Janku ko wata tadawo gaba ko afasa tafiyar gaba daya kowa ya koma cikin Gida.Mami ce tai Caraf ke WA'AT koma gaba da sauri tadago tana Kallon Mami idanunta harsun ciko da hawaye itafa Wallahi batason tana zama tare da wannan tarasa metakeji tun Lokacin datai Masa Kallon Farko.
    Wani shegen Murmushi ya saki dadinsa da Mami kanta nakawo Wuta akoyaushe Mami na Ankare dashi dan tsilan Uwa tafada aranta Mami na tsaye saidata Shiga sit din gaba ta zauna sai bata Fuska takeyi takurewa tai kamar Wadda aka sato haka take zazzare ido yana Lura da ita Duk abunda takeyi Duk sanda zata dago idanunta saita kamashi yana satar Kallonta dayaga zata dago saiya sake tamke fuska Jidda dake baya sai kunshe Dariya takeyi ganin irin Wannan kallon kauna da Abie yake aikawa Aminiyarta dabama tasan yanayi ba.
    
    Suna fita tagano Malam a kofar Gida Hada idanu sukayi da WA'AT saurin sunkuyar dakai tayi gaba daya bataso Malam yaganta amotar Wani ba shima Mamakine ya kamashi to motarwa Jikar tasa takame haka agaba Saidaga baya ya hango Jidda datake daga Masa Hannu Murmushi yayi mata tsabar gulma Irin ta Jidda har nuni take masa da hannunta wai Ankusa daura Musu Aure girgiza kansa yayi dan yasan Halin Jidda shiko AA sam belura da Malam ba koda yaganshi ma ai besan wanene ba.
    
    Tafiyar 15mnt takawo su kofar gidansu Suna tsayawa Hankalin Jama'a yakawo kan Azababbiyar motar kaida Gani annarka kudade wajan sayota sai sheki take tana daukar ido tunkan ya gama tsaiwa take kokarin budewa kulle motar yayi gaba daya dan yaga Iya Gudun ruwanta Jidda dataga haka bude kofatai ta fice WA'AT tabita da kallo Juyowa tai taimata Gwalo tafada gidansu WA'AT tana Dariya.
         .......✍️✍️✍️
    
             WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
           PART TWO
    Chapter 20
    
    Kamar ya manta da ita a motar haka ya kwantar da kujera ya Lumshe idanunsa yarasa meyakeji game da yarinyar A kalla dai inbe haifeta ba ya Kusa haifarta danya girmeta nesa ba Kusa ba amma yar karamar yarinya tana neman ta susu tashi saidaya gama kallonta san ransa tayadda bazata taba zatonma kallonta yake ba saidaya mula dan kansa ya bude mata kofar dama jiran da take kenan ko waiwaye bataiba ta fada gida abunma dariya ya bashi.
    Tana shiga ta tarar da Jidda tabaje tana ta kwasar Fate sai tashin kamshi yakeyi harara tabita dashi tana shigewa Uwar daki Dariya Jidda ta fara tana Kallon Mama kai gaskiya da alama Yayana yayi Babban Kamu dan Mama bakiga Yayana ba ya hadu wallahi barama naje nace yazo yagaisheki dan asamu abunnan ya kara Albarka kedai Jidda ALLAH ya shiryeki yanzu haka kawaii saikije kice yazo ya gaisheni.
    
Tab to Mama haka kawaii nifa sonake  Aminiyar tai Wuff dashi bakiga matar saba abunma a yankata aboye wukar inkinga bakinta Kamar Bakin rijiya shegen Hanci Kamar na boto rami Lebe Kamar ganta kai ai Mama bakiga ba Duwawu Kamar Silifas shegen kirji Kamar Allonsha Me Mama zatai ba Dariya ba to yanzu kuma inya jiki ya zakifa ai bama Zeji ba.
    
    Ina zuwa Mama kishirya saifa ya shigo ya kwashi tabarraki su Hafsa cikin Jindadi aka tashi aka dauko turare aka sake fesawa adaki bakinsu washe Kamar zai yage Hijab Mama ta dauka ta saka sai kamalarta tasake fitowa.

Kwankwasa Glass din Motar tayi ahankali yayi kasa Dashi yana watsa mata Harara cikin Marairaicewa take fadin Afuwan yaya Abie dama zuwa zakai kugaisa da Maaman kawata kaga Mami dama Tabani sako inkazo ka shiga kagaisheta saboda kawar Mami ce ta Amana.
    Makullin Hannunsa ya wurga mata ke ina wasa dake Yaushe Mamin tace nashiga nagaishe da kawarta nan Jidda tafara rantse rantse ai Wallahi da gaske takeyi ba karya takeba haka akayi Ok Abunda yace kenan Futowa yayi daga Motar Nan ido ya dawo kansa kowa bakinsa fal da Magana sai kus kus akeyi dan basu taba ganin hadaddan Matashin nan a unguwar ba ga motar da yazo da ita ita kanta ta isa ta nuna cewar yayiwa Talauci nisan gaske yabashi tazara me tarin yawa.
    
    Umma na tsugunne zata fara Alwala kenan taji Sallama dagowatai tai arba da wanda yake shigowa gidan baki sake take binsa da kallo har kasa ya Duka yana gaida Ita Dayake bata ga Alamar tsiya ajikinsa ba da fara'a take Amsawa tunaninta gaba daya yatafi wajanwa ya zo Agidan sai Lokacin ta hango Jidda a bayansa Gimtse Fuska tayi gano wajan wadanda yazo bemasan tana yiba dan tuni Jidda tajashi gaba Umma kamar idanunta zai fado take Kallonsu gaba daya ta kifar da ruwan Alwalar batare data saniba.
    
Malafar Uba wajanwa yazo kenan to tasandai basu Hada Dangi dasu Jidda ba shiwanna kyakykaywan mene dalilin shigowarsa gidan.
    Saida yayi Sallama Mama ta bashi izinin shiga Yashiga tana zaune kanta akasa su Nusaiba ne aketamai Sannu da zuwa da Murmushi a Face dinsa yake Amsawa Sofa suka Nunamai kazauna anan Yaya Sosai yaran suka burgeshi ya hango kama afuskarsu data Wa'at kannan tane kenan haka ya Ayyana a Zuciyar sa Saida yazamo har kasa yagaida Mama Abunda yayi matukar Burgeta kenan.
    Da Fara'a tadinga Amsawa haka su Hafsa har kasa suka tsugunna suka gaidashi Wa'at kuwa na daki tana tunanin Irin Abunda zatayiwa Jidda kowa yasa tashigo musu dashi gida Oho.
    Jidda ta kalla Jeki dauko mai ruwa da Lemu tashitai ta debo amma besha ba yace ya gode Sallama yayiwa Mama hannu yasa a aljihu yaji besako Kudi aciki ba Jidda ya kalla zo muje Sallma sukai da Mama cikin mutunta Juna Umma na kofar daki tana Jiran futowarsa sallama yayi mata itama suka fice.
    
Motarsa ya bude Wani Waje ya danna saiga Kudi rafa rafa a ajiye rafa Uku yadauko ya mikawa Jidda jekikaiwa kannanta sasha Sweet karba tayi cikin jindadi danta kuntatawa Umma da gayya tataho da Kudin tana wasa dashi a hannunta aiko Umma tuni ta rikice ta hango bugun ABUJA cikin tsokana Jidda kefadin kai ALLAH dai ya rabamu da Matacciyar Zuciya yan ALLAH ya baku musamu fadawa dakin Mama tai.
    Kudin ta dorawa Mama acinya gashi nan yace kwasha Sweet kuma Mama bake yabawa ba danma karkice bazaki karbaba su Hafsa yabawa kantace Wani abu Jidda tafita da gudu tafada Mota jayayi sukayi gaba.
         ........✍️✍️✍️

            WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
            PART TWO
Chapter 21

      Daki ta fada cike da bakin Ciki tana zage zage kallo suka bita Dashi Zainab ce cikin sikewa da Al amarin Umman tace yanxu kuma me akai Miki Umma anya ba agidanku Fadar shedan take ba kuwa kofin hannunta ta willow mata agidan Ubanki yake shegiyar Yarinya Duk abinda nakeyi ba danku nakeyi ba ina Zaune Wallahi bazan taba yadda makiyana suji dadi ba wai Duk akamme kike tada Jijiyar wuyar nan inji Zubaida data zuba mata ido.
      Yauwa aike dama bakiyo halin wancan mebakin halinba nanta labar tamusu Abunda tagano atsakar gida, Kunga kuwa Aidole hankalina yatashi kuma kutafi Gidan hutu kamar yadda yar Uwarku tatafi Zainab ce tatabe baki shiyasa bakyaci gaba Wallahi Hassada tacika miki Zuciya to aida nayi Aure Irin na Hajara gwara na mutu banyi Aure ba Wallahi.
    
    Waike wace irin yar isakar Yarinya ce to kar ALLAH yasa Kiyi Auran ni inada Damuwa da hakanne aiga Magajiyata nan sai nayi hakillon akanta tundaki baki gaji arzikiba komai Akace saikin kawo naki batun saikije can kiyi,cikin kunkuni Zainab ke Fadin aishiyasa nagake kin gaji arziki gaba da baya.Wani Abu ta tuna tafashe da Dariya waime Naji kina Cewa ma Hajara tanacan gidan Daula kwarai kuwa tana babban Gida kuwa Gidan dabai mata Amfani ba Tunda tanacan ta zama baiwa.
    Futo da ido Tayi mekike Cewa ah ni babu Abinda nace sai Jikinta yayi Laushi tukunna dan Wallahi ko akasan silifas dina ban tausaya Mata ba Tsuntsun dayaja Ruwa shiruwa kan doka aidama ance kwadayi Mabudin Wahala.
    Wallahi Zainab natashi ranki Zai baci Matukar baki gayan ba aigani ya kori ji kije kigano da kanki Mana tafadi cike da Dariyar Mugunta kamar Anwa Umma Allura haka tamike Mayafi ta yayiba asaman kofa Kudinta dama yana Jikinta dan Matukar Zata aje kudi to banata bane saita nesu tarasa.
   
Napep be ajeta ko ina ba sai kofar Gidan Hajara konace Gidan suru kanta,Megadi ne yataso da Sauri ya tare hanya ganin tana neman shiga gida Hajiya wajanwa kikazo wajan yata nazo mana kallon sama da kasa yake mata danshi azatonsa yar aiki aka kawo Yarki acikin Wannan gidan kwarai kuwa ko bankai akawo yartawa bane kinga alabaki hakuri wuce ganin tana neman tara masa mutane.
    Gaba tayi tana mitar yaraina mata hankali yana Megadi zetsareta ya hanata shigowa.Ban garan Hajara tanufa Duk da zuwanta biyu Amma tagane hanya sarai kofar abude take kutsa kai tayi tana kalle kalle kasa kunne tai kamar Kuka take Juyowa ana kururuwa acikin parlo sake zura kunne tai tabbas Kuka take Juyowa kan Ubancan to me   yasamu Hajaran datake Wannan Uban Kukan wata kara taji ansaki batasan sanda ta afka Dakin ba.
    Zazzare Idanu tayi ganin irin tashin Hankalin data ganowa idanunta
    Tofa me Umma tagani daya nemi ya tsayar da Numfashunta.
    Kubiyoni Danjin Yadda zata kaya.
         ........✍️✍️✍️
    
             WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
             PART TWO
    Chapter 22
    
    Hango Hajara tayi magashiyan akasa gaba daya Jikinta yayi rududu da duka tana kwance Male Male Acikin Jini Face Face kai da alama ko Numfashi babu a tattare da ita Iya karfinta ta daddage ta kwantsama ihu tare da dora Hannunta aka sai Lokacin Kamal ya Lura da irin aika aikar da yayi ganin Halin da Hajara take ciki shikansa ya firgitashi cikin rufewar ido da tafasar zuci Umma ta rarumo wani Cup na Glass data Gani kan Fridge batai wata wata ba ta kwantsama Masa aka wata gigitar ciyar kara yasaki ya zube akasa asume.
    Karar data janyo Hankalin Hajiya da kannan Kamal asukwane sukayo bangaran turus suka tsaya ganin Umma atsaye tana Huci sukuma gasu akwance gaba dayansu babu me Motsi ajikinsu Cikin Kururuwa Hajiya take Fadin nashiga Uku takashe min dan Wallahi hukumace zata rabani dake bazan taba yadda ba nan kokawa ta kacame tsakanin kannan sa da Umma kai Har Hajiya ba'abarta abaya ba sosai suka Doki Juna ita dasu damma Umman Ba kanwar Lasa bace dasai summata jina jina.

Duk Wani abu me Amfani adakinnan sai da Umma ta Tabbatar ta ragargajeshi.
    Suna cikin Wannan Dambe Yan sanda kawai suka Gani kamar an cillosu Mata ne Mazan na waje dakyar suka raba wannan Fadan su hudun gaba daya aka tasasu akai waje dasu motar yan sanda aka durasu kowacce ranta bace dan yaune karo na farko da akataba sanyasu Amotar Yan sanda da Mutuncin su da komai aiko Duk Inda aka wuce dasu sai anbisu da kallo.
    Yan sanda da kansu suka debi su Hajara sai Hospital sosai tarasa Jini dan Bari tai naciki kimanin wata Hudu bakaramar wahala tasha ba bayan ta farfado daga suman datayi Kuka take me matukar daci da kunar Abunda Kamal yake mata Nan Duniya jitai ba wanda tatsana sama da Kamal ta tsaneshi ta tsinewa Auransa yafi akirga ko shine Autan Maza bazata sake yadda ta zauna Dashi ba Har abada kuwa.
    Wayar Nurse din takarba Numbr Umma tafara kira tanata Ring ba adauka ba Numbr Appa takira dan batada Numbr din Mama yana dagawa ta fashe da Kuka kala bece mata ba da abun ya isheshine ya buga mata tsawa tsit tayi tana sheshshekar Kuka ke Ubamme ne zaisa haka kawai kikirani kisani agaba kinamin Kuka dan iskanci da rashin Mutunci Ubamme akai miki.
    Cikin sheshshekar Kuka tafara fadamai tana asibiti ankwantar da Ita kuma bakowa awajanta ke dakata ina Mijinnaki dazaki kirani ina cikin kasuwancina Sake fashewa tai da Kuka Appa ai shine ya doken Har cikina ya bare Wallahi Appa bakaga yadda ya dakenba Yasameni kamar Jaka dan ÀLLAH Appa ka gayawa Umma ko Mama suzo.
    Ina fatan dai ba sakinki yayi ba cikin Mamakin Abunda ya Tambayeta takasa ma magana dan Wallahi in kika kuskura ya sakeki zanga gidan dazakije kizauna dan haka kawai ÀLLAH ya rabani da wahala bazaki dawon gida ki jibgemin ba kije can kikarata Aishi zaman Aure dama dan Hakurine kuma nasanma rashin arziki Irin naki tayiwuma rashin kunya kikamai ya ladabtar dake daga nan kina warkewa kiwuce gidanki na gaya miki kit ya kashe wayarsa.
     Tsayawa tai tana bin wayar da kallo gaba daya tunaninta ya tsaya cak anya Appa babu aljanu ajikinsa kuwa meyasa yake Fadin hakan akoda yaushe sudin matsalane takura ne nauyine Mazan daya keso ina suke jitake wahala suke bashi Amma haryanzu be sadudaba sai yaushe kenan.Share hawayanta Tayi towa zata kira Mahaifinta ma ya gujeta balle wasu kuma gashi bata da Numbr Mama kai Ita zata Iya Cewa ma Numbr din Mama betaba shiga wayar taba balle harta haddace.

Wasu Zafafan Hawaye tasake gogewa a sanyaye ta mikawa Nurse din dake tsaye tana kallonta kuma Duk taji abinda Appa ya gaya mata Mamaki take wannan wane irin Ubane dabai san Darajar Yayansa ba Zama tai Kusa da Hajara dafa kafadarta tayi kigayamin inane Gidanku ni zan aika azo da Mamanki harnan karki damu cikin Jindadi ta Goge hawayan Fuskarta Pepa da Biro ta miko mata Rubutamin Address din Anan.
     To Nanfa ake yinta dan Hajara inbanda sunanta babu abunda ta Iya rubutawa sai Alokacin tai Nadamar biyewa Umma da tayi taki zama tayi karatu tayi tunanin gata take mata ashe Cutarsu takeyi sai yanzu tagane hakan da Lokaci ya kure Mata.
    Fahimtar Hakan Yasa tace fadomin saina rubuta gayama Address din tayi ta rubuta Ina zuwa tashi tai tafita wani tasamu Cikin Masu yimusu shara ta bashi Address din dayi masa bayanin Abunda zai Mata karba Yayi ya nufi Unguwar su Hajara.
          .......✍️✍️✍️
    
                       WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesa
                      PART TWO
    Chapter 23
    
    Umma Yau sai gata abayan kanta gaba daya ta jigata sai faman zare ido take budesu akai kufito muje sai Hararar Juna ake kowa zuciya tana tafar fasa Office din DPO suka Shiga kowa bashi Umar nin zama akai zaunawa sukai daya bayan daya yake kallonsu,yanzu kowacce acikinku Za'a kira wakilinta dan muna zaune a office aka kiramu akan za'ai kisan kai mukammu bamu san wanda ya kiramu yabamu wannan bayani ba.
    Nisawa yayi tare da gyara Glass din Fuskarsa Mun baku nanda Mintuna Goma kowacce ta kira Wakilinta sai alokacin aka bawa Umma da Hajiya wayoyinsu dan ana sakasu amota aka amshe wayoyin Hannunsu.Numbr Appa tadanna Amma kiran duniya kememe yaki daga wayar dan yasan zancen Bazai wuce na Hajara ba tobase ya daga zatamai zancanba daga karshe kashe wayarsa yayi sakare Umma tayi da waya Ahannu ita yanzu babban tashin Hankalin ta halin da yarta take Ciki shitake tunani.
    Numbr Malam ta lalubo rabanta data kirashi anyi shekaru Biyar amma ya zatayi haka zata kirashi dan tasan Matukar ta kirawo wani a Danginta sai ankusan Kune Station dinnan saboda bala,in daza'a kwasa Bawan ÀLLAH Ring Biyu ya daga cikin Mutun tawa Umma take gaidashi shikansa Abun ya daure masa kai amma be nuna ba ya amsa cikin Kulawa,fyace hanci Umma tai nan tashiga koromai jawabin abunda ya faru cikin Sallallami Malam yake Fadin Ashsha abu beyi dadi ba yanzu shi Kabiru ne yaki daukar wayar taki Wallahi Malam daga karshema kashewa yayi.
    
    Shikenan yanzu zamuzo tare da dan Uwansa cikin Jindadi Umma ta kashe Wayar itama Hajiya wani kaninta takirawo yace gashinan zuwa.Cikin Mintuna Biyar kowannensu ya karaso zama aka sakeyi kowacce tafadi bayaninta Amma gaba daya sun kasa tsayawa siyi wani bayani gam sashshe gaba daya haya niya suke shirin tashi suke sukara dambatuwa saida wata Yar Sansa ta daka musu tsawa suka dawo nutsuwarsu.
    Nan ba Gidan Kallo bane da zakuzo Kusa mutane agaba kuna mana ihu aka Yallabai da alama haryanzu basiyi laushiba akara Mayar Dasu Bayan kanta inaga nan gaba zasu sake Nutsuwa tsit sukai dan sun tabbatar da bayan kantar nan ba dadi duk da badare bane Amma sunsha cizon Sauro ga zafi zarnin Fitsari kai babu abunda basu shako acikin wajannan ba.
    Umma aka ba dama tafara Magana Sake gyara zamanta Umma tayi tare da fadin.
    Yallabai Gidan Yata naje nasamu dan wannan Matar ta nuna Hajiya ya zage Iya karfinsa sai kirbarta yake kamar ALLAH ya aikoshi saboda baida imani harta Suma bekyaleta ba nikuma ganin 'Yata cikin Jini Nima idona ya rufe nadauki Cup din tangaran na rotsa masa aka Wallahi Iya gaskiya na Fada muku shine da yayi ihu Uwarsa da Kannan sa suka taho aguje suka hau kaina da Duka nima shine Narama dan nakare kaina.
    DPO ne ya kalli Hajiya haka akai eh Yallabai haka akayi nima ganinai tana neman kashemin da shiyasa nashigar masa,da masaniyarki dama yake dukan Matar tasa Nanfa Hajiya tai shiru tana share gumi banda Masaniya tunda ba waje daya muke zaune ba,amma aikina cikin Gidan hakane inanan Amma akwai tazara meyawa tsakanin mu.
    
    Amma Hajiya Abun Mamakin Sanda yake dukan Matar tasa gaba daya ALLAH be jiyar dakeba saida kikaji kukan danki dukko da tazarar da take tsakaninku sai gashi ALLAH ya jiyar dake tsit tai dan bata da Abun fade dan aduk lokacin da Hajara ke Kuka tana Jinta amma saitayi mirsisi taki zuwa ganin abunda yake faruwa,baki da abin fada ne babu nidai bana jin Sanda take kukan kasan Iska da dauko magana to iskace takwasa takaimin sautin kukannasa.
    Shikansa DPO din saidaya Murmusa jin abinda Tace wato dantane dan baiwa shikadai Iska ke kwasa takai mata kukansa.
    Yanzu zamu bada belinku saboda marasa lafiyar da kuke dasu a Asibiti amma kusani bawai mun Sallameku bane zaku dawo daku da Marasa Lafiyar dan kowa yagirbi abunda ya shuka Godiya sukai nan aka fada Musu kudin beli suka biya sannan aka basu damar tafiya tare da gaya musu asibitin da majinyatan suke.
           ........✍️✍️✍️

             WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
        PART TWO
Chapter 24

Kai tsaye asibitin suka nufa Umma Jikinta har rawa yakeyi saboda tanason ganin halin da Yarta keciki turus suka tsaya gaba daya su akofar dakin Suna kallon wanda ke cikin dakin Mama ce zaune harta yiwa Hajara wanka ta gyarata Fes,Abunda ya faru bayan wannan Nurse ta Aiki wanda taba Address din besha wahala ba yagane Gidan akofar gida ya kwada Sallama Zainab ce ta leko dan ganin wanene cikin rashin sani take Kallonsa.
    Dama wajan matar Gidan aka aikoni cewar Yarta Hajara tana kwance a Asibiti nazo na tafi da Ita to ai Umman tamu bata nan tatafi Gidan Hajarar tun dazu tonidai abunda aka fadamun kenan Wani tunani tayi ina zuwa Gidan ta koma kofar dakin Mama tatsaya to mezatace mata intaje itadako dakin bata taba shigaba batasaniba kotana Yarinya tashiga kundun bala tayi tashiga dakin suna zaune sunacin Abinci.
    Sunyi Mamakin ganinta Sosai Nusaiba ce tai zaraf to yaukuma ko batan hanya kikayi harara ta wurga mata ke Dallah Ba wajanku nazo ba kikamin rashin Kunya tattakaki zanyi Wallhi Mama ce ta kalli Nusaiba tare dai mata gargadi da ido dole ta hadiye abinda take nufin fada.Kallonta ta maida kan Mama dama Wani ne aka aikoshi wai Hajara na asibiti azo atafi da Wani kuma Umma bata nan.
    Subahanallahi cewar Mama mikewa tayi muje yamin bayanin me aka aikoshi Nusaiba kamar zata Fashe da Kuka haka tabi Mama da kallo Duk Wulakanci da sukai musu amma yanzu Shine Mama zata tafi abunsu da sune ko mutuwa zasi Umma bazata taba Zuwa ba.
    Bayanin daya yiwa Zainab shiyasake yiwa Mama.Ina Zuwa to daki takoma ta saka Hijab dinta kudi tasaka ajakarta Kula ta dakko ta cikata da shinkafa da taliya da miya sif dinta ta bude kayan WA'AT ta diba kala biyu sai Hijab tasaka acikin jaka Suna zaune Suna bin Mama da kallo baki bude tunaninsu ina zatakai wannan kayan.saidata gama hada kayanta tas harda Sallaya ta dauka sai Lokacin ta kallesu ganin sun zubo mata Idanu abunma Dariya ya bata.
    
    Ninatafi Asibiti yayarku bata da Lafiya kuma Ummansu batanan zanje kafin ta dawo kunjini ai to Mama kuma kukula banda fita ko ina dama yau ba Islamiyya to kuzauna agida Amsawa suka sakeyi har waje suka rakota kamar zasuyi Kuka Ita kanta Zainab Abun ya bata Mamaki Tarasa Mama wace irin Zuciya gareta dabata da ruko ko kadan tana da tabbacin da Ummansu ce Wallahi ko shure shure yayan Mama keyi batanan konkallonsu bazatai ba balle hartaje Inda Suke.
    Saitaji Maman tasake Wani girma acikin idanunta tasakejin kaunarta dan dama bata tabajin kiyayyarsu a zuciyarta ba batashiga harkarsu ne Kawai.
    Har dakin da take dan aiken ya nuna Mata da Sallama ta Shiga Hajara itakadai tsuru Abar Tausayi Kuka take kashirban tana dana sanin biyewa san Zuciya dakuma rashin Samun Uwa tagari da basiyi ba ta tabbata Umma tataka Muhimmiyar rawa wajan rugujewar rayuwarta gashi yanzu daga Suratul Fatiha dakyar zata Iya Kawai Alam Tara kaifa Babu komai akanta sai tsabar daki kanci.
    
    Sosai Mama taji Tausayinta ya sake kamata gaba daya ta gama lalacewa tayi bakikkirin da lallai ALLAH ne yaso yarta da RAHAMA dabe kaddara mata Auran Kamal ba dama Wani Hanin Ga ALLAH baiwane Itama tana mata fatan ta cinye Jarrabawar da take ciki.Ganin Mama ba karamin sanyaya mata rai yayi ba dan har ganin Maman saiyafi da dada mata akan ganin Umman nata.
    Kayan Hannunta ta aje toilet ta duba akwai pampo aciki ruwan zafine babu fita tai da buket a Hannunta Wani tasamu ta tambayrshi Inda zata samu ruwan zafi nuna Mata yayi siya taje tayi ta dawo toilat din tasake komawa kama hannun Hajara Kawai tayi Suka Shiga saida taimata wanka tas tagasata yadda ya kamata kayan WA'AT tabata tasaka kayan Jikinta sun tashi daga Aiki gaba daya aleda ta kullesu tafita can waje tayar.
    Ruwan zafi ta tsiyaya ta kullo madararta aleda suga da lipton hadamata tea tayi su Hajara andade ba ahaduba dan rabonta da tasha shayi me madara tun tana gidansu saiko Sanda Kamal Yayi Mata aika Aika shine fa Hajiya intaga dama take bata shayi da madarar saidata shanye tas tazubo mata abinci tas Hajara aka cinye saigata ta fara dawowa cikin hayyacinta.
    Zama mama tai tana binta da kallo anan Hajara ta fara labarta Mata abunda ya faru tana Kuka wai ashe ganewa yayi tana da ciki ya hauta da Duka shi bayason Haihuwa be shirya yanzu ba kuma kozai haihu ba da Ita ba shine yadinga naushin cikin saidaya ga tafadi ta suma jini na malala sannan ne fa ya tsure karyaje ta mutu.
    ALLAH kenan abunda Mama take fada aranta kenan shi Yaya matane bayaso gashi ALLAH ya hadashi da wanda shi haihuwar cema baya so gaba daya kuma ya gayamata Muddin zata samu ciki sau dubu sai ya zubdashi sau dubu Goge hayawan fuskarta Hajara tai dan Ita kanta Maman batasan Sanda Hawayan yafara zuba a idanunta ba tuno Irin tozarci da Wulakancin da Appa yayi mata har kwanan Yau Pant betaba hadashi da yayanta ba babu komai Danginta da nasa kemata tundaga ranar data haihu har kwanan yanzu bazata daga Wani abu daya kawo da sunan ya siyawa yayanta ba kosu yaran basu san da haka ba kuma bata fatan su sani Dan zasu iya rikarsa a zuciyar su.
     ......✍️✍️✍️

             WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesa
          PART TWO
Chapter 25

Tsayuwar sune ya katse mata tunanin data lula ganinsu Yasa tamike da sauri ganin Surukinta da wan Mijinta sannu da Zuwa tayi Musu Malam wani Farin cikine ya kamashi Lallai Samun mace kamar Aysha sai antona bata da ruko sam arayuwarta yana Alfahari da ita matuka Acikin Surukansa.Da Fara'a yake Amsa gaisuwar da take Masa Umma Tuni takara turbine Fuska dan ita tsakaninta da kishiya ba yadda ba Sassauci.
   
 Sannu ALLAH ya yimiki Albarka Ameen Malam Mama ta Amsa Cikin jindadin Addu,arsa agareta. Matsowa sukai sunawa Hajara Sannu datake Murmushin yake dan ita kadai tasan Damuwar dake cin Zuciyarta, ALLAH ya baki Lafiya Ameen suka Amsa gaba dayansu banda Umma da Bacin rai ya hanata Magana dan aganinta wannan ba hurumin Mama bane da zatazo tazauna mata da yarta kowama yaje ya gayyatota Oho.
    
    Kabiru ya sani kuwa ya sani Malam gaba daya Kallonsu suka koma dashi kanta to kuma ya akai haryanzu bezo ba Wasu hawayene suka sulalo daga kuncinta tuna tijarar da yagama yimata dazu barkewa Hajara tai da Kuka Cikin Kuka ta labar tamusu Abunda Appa yace mata dazu nacewar babu abunda yashafeshi da ciwanta sisinsa bazai kashe ba kuma karta yadda ta dawo mai Gida dan bazai Lamunta ba.
    
Tuni Umma tasake Kumbura yau ALLAH kadai zai rabata da Kabiru har ita zaiwa dibar Albarka yace yarta karta koma gida aiko gidan Zasu tafi zataga yadda za'ai yafita da ita.Malam shiru yayi yana Jajanta wannan Jahilci dayake damun Appa ya yadda Jahilci babbar cutace na yadda haryau girma yake yana kara Haukacewa.
    
ALLAH ya shirya abunda Malam yace kenan yanxu me Likitocin suka ce yafada yana kallon Mama ai Malam bandade da zuwa ba saidai Yanzu aje aji yadda za ai to ALLAH yayi miki Albarka Ameen nanfa Umma tasake kuluwa kamar ta rufe Mama da duka dan Haushin ita ko Kallonta beba bare ya samata Albarka.
  
 Futa sukai suka nufi Office din Likita basu izinin Shiga yayi Cikin mutunta Juna suka gaisa shima Babban Mutum ne wa Kuka kawo mune Yan Uwan Hajara Kabir Ok Wani File ya dauko yayi rubuce rubuce.
    Rufewa yayi tare da cire medical din idanunsa Numfashi ya Sauke tare da Kallon Malam da Baba Usman,a gaskiya Yarinyarku matukar ba'ai gaggawar daina barinta da yunwa ba Komai zai iya faruwa me ciki ba ason tadinga aikin wahala da daga abu me naunyi Amma da alamar Ita ta dauki abu me matukar Nauyi ga aikin Wahala datakeyi ga yunwa tattare da ita.
    Ulcer tai mata Mummunan Kamu Nayadda saura kadan ta taba mata Hanjinta a sakamakon aikinda ta dingayi na wahala dakuma Cikin da akafitar dashi ta karfin tsiya yasa Mahaifarta tayi Sanyin da nan gaba matukar zata sake daukar ciki sai ankula sosai dan zata Iya samun gagarumar matsala.
    Amma Alhmdlh Komai yazo da sauki Saboda ankawota asibiti Cikin gaggawa munyi kokarin dakire wannan Matsalar.Takadda ya miko musu ga magungunan dazaku siyo In sha ALLAH matukar munga ba Matsala Zamu sallameta a gobe in ALLAH ya kaimu bayan ammata wankin ciki karba sukai tare da mai Godiya suka fito daga Office din Cikin sanyin jiki.
    Toya akai hakan tafaru dama Yarinyar acikin Wahala take basu taba sani ba kome gaba daya yarinya ta gama kwantsamewa sai Idanu awaje kashin wuyanta kuwa ai ba'a maganarsa.
    Baba Usmanne ya siyo Maganin Bayan sunkai Musu Sallama sukai da zummar zasu dawo da Safe in ALLAH ya kaimu, Su Hajiya suka Hango a kofar dakin da aka kwantar da Kamal shiga sukai suka duba shi yasha Bandeji a ka idanun nan sun Kumbura sun shige Ciki yan Uwa da abokan arziki cike a dakin sunata zuwa Dubiya Duk wanda yazo sai anlabar tamasa Surukarsa tai masa wannan danyan aikin aiko Umma tanashan tsinuwa kwando kwando koda Wasa Hajiya bata gayawa kowa Hajara na asibiti ba abunda take fadin Surukarsa ta fasa mai kai dansun sami Wani dan sabani da Matarsa.
    
    Suna futa Itama Mama tadauki jakarta Hajara ta kalla toni zan tafi ALLAH ya kara Sauki dan sam Bazata Jure Kallon banzan da Umma take Mata ba Gwara ta kyaleta tayi jinyar Yarta Sam Hajara bataso Mama tatafi ba taso ace Itace zata zauna da Ita Amma Umma tazo ta Kasa ta tsare tanaji tana Gani Mama tatafi,Umma ta rakata da Harara tare da jan tsaki.
           .......✍️✍️✍️✍️
    
           WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesa
             PART TWO
    Chapter 26
    
    Abie dama kiran danai ma bana komai bane saina sanar dakai zanyi Aure zaka kara nan bada Jimawa ba kuma nice zan zaboma matar da zaka Aura dakaina wancan na barka kayi son ranka wannan karan Nima zanyi son raina zan zaba ma abunda nasan bazai taba cutar dakai ba.Tunda ta Fara Magana AA yake sharce gumi yanajan Innalillahi meyasa Ammi zatai masa haka saida ya fara jin soyayyr wadda aduniya bai tabajin son wata ya mace kamar taba kai shifa zai Iya Cewa ma sai yanzu yafara Soyayyar.
    
Amma Yanzu Ammi Duk zata rusamai wannan Ya ALLAH ya furta a Hankali yana dai daita Nutsuwarsa dan baya fatan Wani abu da zaisa Ammin tasa ta sakeyin fushi dashi koya sake bata mata yana sane da irin bakin cikin data kunsa Alokacin Auransa da Fareeda.

Kansa ya dago Duk yadda yaso boye Damuwarsa hakan tagagara tuni ta Hango tsantsar Damuwa acikin Idanunsa basarwa tai kamar bata gane Halin da yake ciki ba.
    In kuma kana da Wadda kake so zaka Iya sanar dani yanzu girgiza kai yayi alamar ba wadda yake so Miskili wato kai bazaka iya fadin abunda ke ranka ba aiko zaka san jan aji da Miskilanci zakaji ajikinka to shikenan komai ya zo da sauki tunda har ALLAH yasa ba wadda kake so take sonka ni inada ita tun tuni kuma tayimin bata da Wani Makusa.
    Ina Yar Baba Larai ta Birniwa Zulai to itace wadda na yaba da Hankalinta da nutsuwarta yarinya shiru shiru babu ruwanta Saliha zaku zauna Lafiya in sha Allah nanda wata shekarar ma ina sa ran zanga jikana Ammi take fada cikin dauriya dan ba karamar Dariya ce take cinta ba.

Gogan tuni idanunsa sun rune da Bacin rai Zulai yaketa nanatawa kamar me biya karatu wannan kucakar yarinyar da gaba daya kanta Duk kwarkwata hakwaran nan sun hadu sun dafe tuni yaji Zuciyarsa tafara tashi tuno Wani Mummunan wari da Mahaukaciyar nan tataba shakamai.
    Saidaya kwana Uku yana jin Wannan Warin A hancinsa dakyar ALLAH ya taimekshi ya dainaji shine Ammi take tunanin Auramai ita Kala bece ba ya tashi yafice Kamar zai kifa tsabar yadda Zuciyarsa take Hautsinawa aishi ko A Lahira baya fatan ALLAH ya hadashi da Zulai Saboda tsananin kazan tarta.
    Yana futa Ammi ta fashe da Dariya Dan Wallahi dakyar ta iya rike Dariyar ta bakaramin kokari tayi ba,Safna ce tafuto daga bayan Sofa da rarrafe har Hawaye take dan Dariya dama tana Bayan Kujera tana leken Yadda Lokaci daya Fuskar AA ta kacame Kamar me shirin Fashewa da Kuka.
    Cikin Dariya Safna kefadin kai Wallahi Ammi saura kadan na tona mana asiri bakisan yadda dakyar na hadiye Dariya taba kawai natuna Dramar Yaya Abie da Zulai ne Kinsan Ammi yana kwance ta dauka Bacci yake ta salallabo wai zatai masa abunda taga anayi A TV dan shima taga yana kama da indiyawa Kawai jin Bikinsa yayi a cikin Na Zulai Kamar a mafarki Dan Dariya saida Ammi ta sauka daga kan Sofa yanzu kuma ace za a Auramai Zulai aitasan da akwai Damuwa.
              *********
    Ko Kallon Fareeda dake jiransa Aparlo beba da bibbiyu ya dinga taka matattakalar Benan saboda tsabar Matsuwar yanganshi a BedRoom dinsa Toilat ya fada amai ya dinga kwarawa kai Duk Wani Nau'in warin da yaji awannan Lokacin Jinsa yake a hancinsa sosai yakejin tsanar Zulai aduk sanda ya tuna aika aikar datayi masa.
    
Sarai yaji shigowarta dakin amma ko kallo bata ishesa ba Bargo yashige ya rufe har kansa jin sanyi yana kadashi Duk yadda ya wuni yanajin zafi Amma yanzu Wani sanyine yake ratsashi tunani take takaraso kota koma dan yanzu sosai takejin shakkarsa gaba daya ya juye mata Gani takeyi kamar bashiba yasa mata dokar bashiga ba fita ko bakin Get belamunta tasake futaba shiyasa gaba dayanta takejinta kamar an sakata akeji tasaba tafita ta wataya duk Inda take so.
    Duk wata harka ta tsaya mata cak gashi yanzu gaba daya yadaina bata ko ficika kai ko kallo bata ishesa ba bare ya nemi Wani abun a wajanta ya tattarata ya watsar koma me take dashi taje ta rike abunta bashi da bukata ko Kusa da ita baya Kaunar yazo dan sosai yakejin kyankyaminta acikin Zuciyarsa.
           .......✍️✍️✍️
        
                 WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesa
            PART TWO
    Chapter 27
    
    Ammi fa dagaske take abunnata dan harta kira Baffan ninsa akan suje su tambayo mai Aure asatin kuwa suka Nufi Zariya Mijin Mami Baban Jidda shine yayi Musu Jagora cikin Mutunta Juna aka gaggaisa Bayanin abunda ke tafe dasu Sukaiwa Malam sosai ya nuna jindadinsa dayake Abun akwai sanayya dan danan aka Fahimci Juna Take awajan Malam yace ya basu sai suje su daidaita kansu.
    Wayarsa ya dauka ya kira Appa akan yazo yanzunnan yanasan ganinsa cikin 20mnt ya iso wajan gaisawa akai a mutunce dan baiga alamar Talauci ajikinsu ba dan garin kallon Motocinsu har tuntube yaci yana tunanin wasu Manya ne haka akai baki agidan.
    
Nuna bakin yayi Kasan wadanan A ah Malam Bansansu ba to Alhmdlh sunzo Neman Auran WA'AT ne nakira kane amatsayinka na kanin Babanta dan kaima abaka hakkinka Kallon Malam ya dago yanayi Fuskewa Malam yayi kamar be gane Kallon da yake masaba kanin Babanta kuma shidin dan Haka inason naji ta bakinka.
    Makwat ya hadiye Wani Mugun yawu ambasu ALLAH ya daidai tasu abunda yace kenan Zuciyarsa na tafasa kai shifa badan wadannan Mutanan daga ganinsu sunfi karfin Wulakanci ba da ayanzu za:ayita ta watse dan bazai taba yadda adinga maidashi baya ba katsemai Tunani sukai ganin sun ajewa Malam rafar kudi guda daya da fadin yaci Goro sam Malam cewa yayi bazai karbaba amma suka ce Lallai saiya karba.
    Appa dubu Hamsin suka mikamai yayi cefane ba kunya Appa ya amshe yana Godiya tuni ya manta da Wani bacin ran ancemai kanin Babanta saidaya daidaita zaman kudinsa a aljihu sannan ya samu Nutsuwa.
    Uffan Malam becemai ba Suna tafiya shima ya mike Amfaninka ya kare zaka Iya tafiya ko ajikinsa shidai tunda ya dafe aishikenan aijiyayi bama zai iya tafiya kasuwar ba dole ya tafi gida.
   
 Kamar an jehoshi haka suka ganshi ya fado gidan yau bacin Magani Fuska sake harda suyin Sallama ya shigo gidan dakin Mama ya nufa bakunya ba tsoron ALLAH haka ya Shiga dakin tana kan Sallaya idar da Sallar Walaharta kenan Sofa ya samu ya zauna to mekuma ya kawo shi tasandai arziki baya kawoshi dakin sai tsiya Indai zai shigo dakinnan to Wulakanci zaizo yayi mata Amma abunda ya bata Mamaki kamarfa Fara'a taga yana yi saidata shafa Addu'a tukun ta juyo tana Jiran taji dame yazo.
   
 Dama zuwa nai na sanar dake nayiwa Yata Miji kasa kunne takarayi tanai masa kallon Rashin Fahimta wace ya kake Magana akai danni kaf dakin nan bansan kana da 'Ya acikin saba yayana sukadai nasani.Bata rai yayi ya zakimin zancan banza ina magana  akan Yata kina neman kibatan rai bafa Maganar bacin rai bace abunda nasani shinake gayama ka.
    
To tunda yayanki ne kekadai saiki Nunan Ubansu inbani ba koke kadai kika Haifesu Nidai na gama magana nariga nabasu kotaso ko kartaso niban da Damuwa to aiko abinda bazai taba sabuwa bane Wallahi haka kikace zaki Iya sa Hijab kije kigayawa Malam be isaba yayi kadan yabada Yata.
    Eh to yanzu kayi magana ta hankali dan Malam ya isa ya dauki kowane ma ya bata amma ba can Wani ba dabe san ciwon Haihuwar Yayanba afusace Appa ya mike nine Wani can din kike nufi ko yaya Banza tai masa dan bataso ta kulashi su zama daya saidaya gama banbamin masifarsa ya fice daga gidan ma gaba daya.
    Ajiyar Zuciya ta sauke itadai ALLAH ya hada ta da mutum mara alkibla,wayar tace tayi kara Numbr Malam tagani da Sauri ta daga cikin girmamawa take gaidashi cikin Kulawa ya amsa.
    Aishatu Na'am Malam dama Wani Abun Alkhairi ya samemu gashi Kuma nai Gaggawa ban sanar dake ba Malam kome zakai acikin Lamarina bazaka taba yin ba daidai ba to Ma sha ALLAH nan ya koro mata bayanin abunda yasa ya kirata sosai ta nuna masa Farin cikinta dan tasan Malam bazai taba yin abunda zai cutar da itaba shime kaunarta ne Ako yaushe sosai tayi masa Godiya da Fatan Lafiya me dorewa yaji dadi Matuka Sallama sukai da Malam.
    Daga hannunta Sama tayi tayiwa ALLAH Godiya dan tasan Su Mami bazasu taba Wulakanta mata Yarinya ba abun ya matukar kwanta mata azuciya.
      Sallama tajuyo a tsakar Gida Lekawa tai Su Umma ta hango sundawo daga asibiti Ita da yan uwanta data kira Suka tayata zama sukusan shida ne fita tai tana musu Sannu da zuwa wasu aciki sun Amsa wasu kuma basu Amsaba abunma Abin Dariya kowaccensu tana fama da kudaddan zani daga Gani sunashan Bulalar Talauci shine har za ana musu Sannu da zuwa suna hura Hanci.
     Umma ma ko kallonta bataiba Hajara ce me amsawa cikin Fara'a dan wahala tasa Hajara ta dawo hanyar data fara karkacewa ta matukar ji ajikinta kai haryanzu batagama warware waba ko Yanzu Doctor saidaya sa mata dokar saita warke tas zata koma Gidan Mijinta to wanema Miji aiko Duniya zata hade bazata koma ba kome za'ayi Wallahi babu Inda zata saidai Appa yayi ya gama.
    Sallama yayi ciciki Kamar bayaso aiko yai Arba da Umma tanajan Akwatin Hajara da sukaje Suka dauko ke dakata ina zaki Juyowa akai ana kallon Kallo.
           
    Tofa Fans Meyake shirin Faruwa ne Appa zai yadda Hajara ta dawo Gidan sa ko Umma zataci galaba Akansa danjin Yadda zata kasance Kubiyo ni.
    
            WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
           PART TWO
    Chapter 28
    
    Kallon Juna suke kowa rai yana suya Gidan Ubanwa zakije da wannan Akwatin Gidan Uban da ya haifeta ko tana da Wani Uban da Bansan da shiba bayan kai,nunata yayi da danyatsa to Wallahi baki isaba bata isa ta zauna mun agida ba danna riga na Sallameta bata da Wajan zama acikin Gidana nadai gaya miki inba haka ba saidai kibita kutafi tare dankema nadade da gajiya dake dama.
   
 Eh Kabiru gwara daka fito Fili kagayamin Abunda yake Zuciyar ka na cewar kagaji da ganina to Wallahi zama daram kuma Hajara ma babu Inda zataje kai ko Yanzu Gidannan yazama nawa innaga dama zan Iya hado maka kayanka yanzu kafice min agida dan ya zama na Yayana Kallonta yake cikin tafasar Zuciya zaki fita koko saina fitar dake dan saidai kibita Zawarci badai agidana ba.
    
    In ka isa dan halak Kabiru zoka fitar dani kaga yadda ake tashanci dan Wallahi zan manta Duk Wata sanayya data ke tsakaninmu sainasa ammaka shegen Dukan da ba wanda zai iya gane ka daga Uwarka Har Ubanka Bismillah cin damara tayi tana huci tana hura Hanci.
    Gadan gadan yayo kanta dan inbe mata Mugun Duka ba bazai Huce ba Wata ce acikin Kannen Umma Itama yar zafin kaice tatare Appa karka kuskara ka dakarmin yaya dan Wallahi inka daketa katsonowa kanka bala,i da Masifar da bakasani Iya wahalar dazaka shaba dammu karo damu ba dadi dan in yaki zami dakai ko Ganin kasusuwanka baza agani ba.
    Wata ingiza ya kawo mata saida ta Kusa kaiwa kas ana Haka sukaji an zabga Sallama tuni Umma ta gane Muryar suwane awaje Yayyantane da kannan ta dasukai waya tun a asibiti zasuzo su duba Hajara.
    Hannu Umma ta dora aka tare da Fashewa da kuka hhhhh kai ALLAH ya rabamu da Kaidin Mata kan Appa ya ankara yagansu sun Afko cikin Gidan Umma na tsugunne tana rusar kuka tsabar Makirci irin na Umma harda Hawaye shabe shabe ko yaushe takakalo hawayan Oho Cikin Kuka take Fadin wayyoni Salame Kabiru kakasheni Kadokeni Aciki dan dai kawai nacema ina da Ciki kake Bakin Ciki zaka kasheni tun Lokacina beba Uwaliya kizo ki ceceni tunda bani da gatan da za'a ramamin sake rushewa tayi da Kuka.
    Kai kosu kansu yan uwannata Mata sun Jinjina Makirci irin na Umma bare Uban Gayyar daya kasa Magana kawai yana kallonta Wani Matashi ne acikinsu ya ce kai Abu takazar Uba harmu za'anunawa tashanci Wata tukunya ya hango da Umma take miya acikinta Wata me shegen Nauyi kan agama tantance Abunda zaiyi da ita jinta kawai akai Ya rotsawa Appa wanda saida ya zunduma Wata Uwar kara.
    Gaba daya Mazannan taruwa sukai Suka dinga Jibgar Appa Kamar ALLAH ya aikosu dama sunajin Haushinsa yaki zuwa asibiti sai Ubansane da yan Uwansa suke sintiri saida Suka tabbatar sun Huce Haushinsu Kansa Suka kyaleshi dan har Makota sunshigo rabon wannan Fada yaki rabuwa dan inkashiga tsakiya harkai ake hadawa dole kowa yaja gefe Appa ko yasha Naushi Hannu da Kafa ga kansa na zubar da Jini Hancinsa tuni ya Fashe kai Hatta kayan Jikinsa saida Suka yayyaga masa su.
    Aiko kasa tsayuwa yayi akan kafafunsa dan Wani jirine ya dinga daukarsa Umma na gefe tana Dariyar Mugunta da suna hada ido zatai Masa Gwalo,Ke kuma wuce kishiga daki kubar Matsiyaci anan Fyace Hanci tayi ai yaya yace nida Hajara sai Munbar masa gidansa shidin Banza kara Haurin Appa yayi da Kafa koda wasa kasake Cewa sufita agidannan Wallahi nidakaina zanzo da Matasa siyima daukar Amarya dakai da kayanka su watsaka waje kaida shigowa gidannan kuma Har abada nadai gayama Mutumin Banza kawai.
    🤣🤣🤣🤣Kunjifa Har kura ce zatace da kare Maye shine Mutumin kirki kenan.
    
    Umma gyara daurin dan kwalinta tayi ture kaga tsiya cikin Murguda Duwawu tazo ta wuce tagaban Appa har Wani tafiyar takama takeyi Suka shige daki sukabarshi Anan daya bayan daya kowa yadinga ficewa masu jajantawa Nayi masu Dariya da ALLAH ya kara Nayi wasu da yawa sunce Alhakin Mama ne yake Bibiyar sa.

Duk Abunnan da ake Mama tana daki ko saudaya bata leko ba dan babu abinda ya shafeta inzasu kakkaryashi shiyajawa Kansa Mutum kamar shedan kullum maganar sa daya kar adauramai wahalar yaya mata ALLAH ya kara dasuka zaneshi yasamu wadanda suka fishi sanin takan Iskanci.

Da kyar Appa yatashi ya Shiga dakinsa yana dana sanin Auran Umma da sanin Danginta da yayi ribarsa daya ta Haifo Masa Yaya Maza Amma Wallahi badan Haka ba da ya dade da sakinta dan ya gaji da wannan bala,in na Yan Uwanta gasu da shegen karfi kamar Dokuna gaba daya Jikinsa tsami yakeyi na dukan daya gama sha bana wasaba Godiyar da yayiwa ALLAH dabasu karyashi ba ko sun targadashi.
    Wajan da ya adana kudinsa ya duba sunanan Inda Suke kwanciya yayi cikin zugi da radadin jiki shida Gidansa Amma amfi karfinsa.
        .......✍️✍️✍️
    
             WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum ANEESAT
           PART TWO
    Chapter 29
    
    Shirye shirye Ammi ketayi na Wannan Aure datake Matukar so da burin Ganinsa tako ina shiri takeyi kai ba itaba hatta dangin Mahaifinsu ba'a barsu Abaya ba.
    
Inaso gobe in ALLAH yakaimu zakatafi Birniwa dan ku gana kaida Zulai jiyayi kamar ta buga Masa Guduma a tsakiyar ka kallon Fuskar Ammi yayi babu alamun wasa tadinke Face tsaf Kasa magana yayi dan Makoshinsa Har Wani daci daci yakeyi kai Ambatar sunanta Kawai sake bata mai rai yake batare ma daya ganta ba.
    
    Tashitai ta bar Masa wajan binta da kallo yai Zuciyarsa na tafarfasa bashi da zabi wanda ya wuce yafita shima gaba daya jiyayi gidan ya yimasa zafi Komai ya tsaya Masa kai Iska ma jiyayi kamar ba daidai yake shakarta ba.
    Waya ta kira Mami akan ta snar da Mama Gobe in ALLAH ya kaimu Abie zezo su gana da WA'AT sosai tai Farin ciki dan itama tunanin da yake Zuciyarta kenan gwarama yazo su dai daita ati awuce wajan Kawai.

Waya takira Mama tare da yimata Bayani sosai taji dadi itama sun shirya zaizo ya sameta Agidan Malam dakin bakinsa dake Soro anan Za'a Saukeshi.
    Mami da kanta tashiga gidan Malam Inna tayiwa bayani Inna rangada Guda tai da ALLAH ya nuna Mata wannan rana ranar da suka dade Suna Jira ALLAH ya tabbatar Musu da Alkhairi.Dakin tasa aka gyara tsaf dama ashare yake agoge turare na Musaman ta dauko ta feshe dakin dashi taja ta kulle.
    Washer Gari karfe 8 Ammi ta kirashi akan shifa Direba kejira yana bata Lokaci kamar ya fasa ihu haka yaji gaba daya Huci Yake kamar tsohon Zaki Gaba daya kayan kan Madubinsa tarwatsar dasu yayi tsabar Fushin da yake ciki Kamar bazayyi wankaba sai ya tuna Umar nin Ammi ne Dole yabi ko yana so ko bayaso Haka Yashiga yayi wanka tunanin Wasu kayan zaisa  wadanda ya tabbatar inyasa basa yimasa kyau.
    
Wata ash din shadda ya dauko atunanin sa Itace bazatai Masa kyauba amma abun haushin Duk wadda yasaka saiyaga tafito da ainihin kalarsa saiya cireta ya wullar akasa haka yaita saka Kaya kamar Zautacce saidaga karshe Yabar wata Shadda Lite Blue sosai taimasa kyau koTurare kin fesawa yayi amma daya ke Turaran ya kama kayansa da jikinsa saiyayi kamar ya fesa.
    Kowa Agidan kama kansa yayi dan sun tabbatar Oga Yau bakanta ransa abace yake dole kowa ya Shiga taitayinsa har uwar gayyar datake Jira ya fito ta silleshi saitaji Bazata Iya tunkarar saba dan tsaf zai nada mata na Jaki ya huce akanta Kala bece ba Back Sit aka bude mai ya Shiga kulle idanun sa yayi dan har bayason kowa yakalleshi balle ya gane halin da yake ciki ko gidan Ammi kin Zuwa yayi daukar Hanya kawai sukai abunda ya bashi Mamaki shidai baigayawa Direbansa Inda zasu jeba amma yaga ya dauki hanya.
    
Shiru yayi yaga Iya gudunsa yaga Inda zai kaishi kwantar da kujera yayi ya kwanta Wani baccine ya daukeshi dan jiya gaba daya be Runtsa ba Cikin Baccin yaji Direbansa ya tsaya sam kin bude idanunsa yayi Oga Mun karaso cikin bacinrai ya Murda kofar afusace yafito.
    
Turus ya tsaya  karewa Unguwar kallo in har ba gizo Gidan yake Masa ba wancan  ai Gidan Mami ne Meya kawoshi Zariya kuma kara dubawa yayi tabbas nan Unguwar su Mami ce Tuni Direba ya gyara Parking dan karyayi Masa Wata Tambayama yai Wuff ya fada mota.

Malam ne yafito Daga Gida Cikin Fara'a yake mai sannu da Zuwa Murmushin Yake kawaii AA yakeyi dan kansa ya daure shigo mana Daga ciki yashigo ina kenan Abunda yake Ayyanawa a Zuciyar sa kenan shidai yasan bashi da alaka da wannan Gidan.

Binsa yayi abaya kamar bindi dan yarasama mezece dakin ya bude tare da fadin Bismillah haka ya Shiga da Sallama abakinsa cikin girmamawa ya tsugunna yana gaida Malam sosai yayaba da hankalinsa Yaji aransa Jikarsa tayi Sa'ar Miji to tashi Kazauna ina zuwa bara aturota takawoma Abun Motsa baki Irin namu na Talakawa Murmusawa yayi dan tsohon ya birgeshi saboda Halinsa na dattako.
    Waza aturo kenan to konan gidan Zulan tadawo take Yaji ransa ya baci aiko zataci Ubanta dan Wallahi saiya mata Mummunan kashedi da takoma gida ta tabbatar tagayawa iyayansu bata sansa bata kaunarsa haka shima baya santa baya Kaunarta kwafa yayi yana jiran yaga ta Inda zata Bullo.
    Hakanan Yaji Murmushi ya subuce mai saboda tunowa da ita dayayi dolema yaje ya ganta to mezece ya kawoshi dan bayason Yarinya ta rainashi.

Inna Malam ya Samu tare da gaya mata bakofa ya iso Wa'at ta kwallawa kira Wadda tun safe Inna taikiranta akan zasiyi Wani Aiki,Kije cikin kwabata akwai Sabbin kayanki kidauko kisaka kizo yanzu ina jiranki to tace takoma dakin Inna Wata Atamfa ce See Green ta matukar haduwa tayi Kyau sosai sai Mayafi White ta dauka ta tasaka tana tunin ina zasuje da inna harda yimata Sabon dinki haka.
    
    Bawata kwalliya afuskarta yari da Sarkar data gani acikin kayan ta dauka tasaka tas tafito Turaran Inna ta dauka tashafa medadin kamshi ne Sosai,nashirya Inna saidata kalleta ta tabbatar babu Wani aibu ashigarta Tukunna Wani Katon tire ta miko mata Sabbin Kula ne akansa sai cup din Zobo da plate da spoon maza Kije kikaiwa bako dayake Soro wajanki yazo saura kije kiyi Masa Halin naki da kika saba wato Kuka.
    Tsaye tai da Farantin Ahannu takasa gaba ta Kasa baya wajanta kuma towane Wannan da zaizo wajanta fuuu tai gaba koma wane yanzu zai tashi ya tafi dan ba ita tagayyato shiba,dakyar tai Sallama saboda jin haushin bakon da akace yazo wajanta dungure Farantin tai akasa shima ko dagowa beba ya kalli Wadda tashigo amma abunda ya bashi Mamaki beji surutan Zulai yakama tashi adakinba.
   
 Tana tsaye itama rai bace kamar zatai Kuka ta gefen idon take Hararar wanda akace bakonta ne Jin tsayuwar tayi yawa danshi ya tsani atsaya mai aka cikin Jin Haushi Yamike daniyar yaga wace yar rainin Hankalice wannan itama Alokacin ta juyo taga Wani danji dakai ne wannan garam sukai karo baya yayi zaifadi da azama yaja hannunta kozata hanashi faduwar Gaba dayanzu suka Zube Akan Sofa saigata Dare dare Ajikinsa.
    🤣🤣🤣🙆🙆🙆🏃🏃🏃.
          Kubiyoni Danjin Yadda zata kaya Taku.
          Kulsoom Ismail Idris
             ........✍️✍️✍️✍️
         
                WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
                PART TWO
    Chapter 30
    
    Kici kicin tashi takeyi amma sam yahanata da matar hakan jin wani daddadan turare dayake dukan hancinsa tunawa da yayi Zulai cefa cikin sauri ya hankada ta daga Jikinsa tare da bata rai kamar bashine ba,fashewa Kawai tayi da kukan takaici tana jamai ALLAH ya isa A Zuciyarta haka Kawai yasa tazo tahau cinyarsa wannan daga ganinsa dan iskane cikin jin haushi ta mike zata tafi tabarmai daki caraf yarike hannunta duk yadda taso ta banbare hannunta ta kasa juyowa tai gaba daya tana kallonsa.
    Zaro idanu tayi ganin wanda yake gabanta saika rantse bacci yake amma kar yake kallonta gaba daya tinaninsa ya tsaya wannan din itace Zulai din dama ta canza haka kokuma Ammi ce takeso taga ta zautashi,tunanin da take itakuma meya kawoshi gidansu da har akace wajanta yazo yasamu daki yayi wani dare dare kamar agidansu sake motsa hannun tayi alamun ya sakar mata hannu sakinta yayi da sauri tayi baya.
    Kanta sunkuye gaba daya Kallon da yake mata takasa Fahimtarsa kawar da kansa yayi daga kallonta wani irin Farin ciki ne yake saukowa tundaga Zuciyarsa dama itace meyasa Ammi ta wahalar dashi haka.

Amma a Zahiri sake daure fuskarsa yayi kamar beji dadin Ganinta ba cikin kosawa da zaman da take adakin ta zumburo baki ga Abinci nan inji Inna tace na kawo maka.
      Ke ina yayartaki da akace nazo naganta kawai sainaga wata jaririya tafuto koda yake abinci kika kawon ngd hannu yasa a aljihunsa naira 50 yaciro yana mika mata gashi kyasha sweet ko.

Cikin takaici take kallonsa baki bude har ita zaicewa yarinya,au bakaga yara awaje da zaka shigo ba ni wllh ba yarinya bace nawuce haka nicema zance dana fito sai naga wani yaro mezanyi dakai Allah na tuba ga Mazan nan cada cada sai wanda na zama amma za'a hadani da tsoho.

Bata san sanda yazo kusa da itaba sai jitai ya murde mata baki cikin azaba take son ya sake mata baki amma yaki,gobema kisake rashin kunya nan gaba ba irin wannan hukuncin zammiki ba yanzumma saboda bazaki iya daukar karatunba na daga miki kafa next time ya kashe mata ido daya tare da sakinta.
     
     Wallahi saina gayawa inna dukkan abunda kayi min sai andau mataki akanka.
    
Banza yayi da ita kamar bejiba Kasa sukuni yayi dan Zuciyarsa wani irin duka take tsam ya mike dan tabbas yaci gaba da zama da ita adakinnan da akwai Matsala shikansa besan abunda zai iyayiba gwara yatashi tunkan yaje yayi aika aika ya zubda ajinsa agaban kanwar kanwarsa binsa tai da kallo tare da tabe baki ko ina zashima Oho tashi tai tafuta itama akofar gidan ta hangoshi jingine jikin Motar sa ya zubawa Gidan ido kamar mejiran yaga wani yafito.
   
 Malam ne ya fito ganinsa yasa yataho da saurinsa badai harka fito ba keyarsa ya shafa nafito Malam mun tattauna kuma min fahimci junanmu babu wata matsala toto ma sha Allah ai haka akeso, Amma tun yanzu zaka tafi kuma kashigo kugaisa da Mutanan Gidan harciki ya shiga yagaida su inna sosai hakan yayi musu dadi dazai tafi debo kudin da besan adadinsu yayi ba dakyar kuwa suka amsa.
   Kitashi kije kirakashi mana wai inna mene hadina dashi daza'ace narakashi uwaki ce zaki tashi kosai natashi kanki tashi tai ta futa Fuska aturbune yana shirin shiga Mota ya ganota ta taho fuska a hade shima hade tasa yayi aransa yana tunanin zaisha fama da wannan yarinyar dan ya lura bata tabayin Soyayya ba,zuwa tai ta tsaya inna tace nace kagaida Gida ware idonsa yayi akanta wai Inna tace kenan bama Ra'ayinta bane rakoshin da tayi.
    
    Tatsani yawan kallo shiyasa ta juya mai baya danji take kamar an daureta Awajan da sauri tayi gaba tunma kan yayi magana ta fada Gida hanyar da tabi yabi da kallo yana ganin Gidan Mami yaki shiga ABUJA suka wuce cikin matukar Jindadi ba kamar yadda ya taho rai bace ba lallai Ammi taimasa surprise.
    Gidan Ammi yasa ya zarce dashi da sallama yashiga Bedroom dinta dan bata parlo tayi mamakin ganinsa da wuri haka kamar wanda aka kora harya dawo fuskarsa kawaii ta kalla tasan ya yaba da zabin datai masa,mutanan Birniwa har andawo yaya su Zulai din ina fatan tayi maka besan sanda ya murmusa ba dan ya gane Ammi tsokanarsa kawaii takeyi uhm kawaii yace zama yayi akusa da ita.
    Nagode abinda yace mata kenan da akaime da zabin da kikayi min kana sonta kenan dama shiru yayi yana sosa kansa ya kayi shiru to nagane karatun bana kira Maminka Nasanar da ita yarinya fa bataimaba daga waya tayi kamar zatai kira da sauri ya rike hannunta yana marairaicewa kaifa kanuna bakasanta nifa Ammi ban fada ba Dariya tayi cikin farin ciki dan daganin dannata ya fada da yawa.

Cigaba sukai da firarsu gwanin ban sha'awa Macece da babu ruwanta tana jan yaranta ajiki shiyasa duk wata damuwarsu basa iya boye mata itace abokiyar shawararsu.
    
AA sam bashi da wasu Abokai dan tun yana karaminsa sosai Ammi takemai fada akan yawo da abokai shiyasa har girmansa abin ya zama jikinsa yanzu dai bazai iya nunama mutum daya yace wannan shine babban abokina ba ko wanda sukai schl ana gaisawa haryanzu amma acikinsu bazai ce ga wani babban abokina dayasan sirrinsa ba kowane sirri yanayine da Amminsa.
    Tundaga wannan haduwar magana tasakeyin karfi dan yanzu shirye shiryen kawo kudi akeyi Mama tana lura da WA'AT tana yawan zama taita tunani kokaga tasaki iurmushi ita kadai hmm yaran zamani kenan duk dabata furta tana sonshi ba ta yadda da Auran ita Mama tagano hakan shiyasa abun yayi mata dadi sosai.
                ........✍️✍️✍️
         
               WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
           PART TWO
    Chapter 31
    
    Yau za'a Kawo Kudin Auren duk wani abu da za'ai sunrigada sun tanada babu wanda yabi takan Appa koda acema yana da alaka mekyau da yayannasa bashi yakeda hurumin karbar kudinba tunda yana da yan uwa kuma Mahaifinsa naraye shiyasa ba wanda ya nemeshi dan daga Yayansa namiji kannansa Mata da Maza babu wanda bayajin zafinsa kowa yana alawadarai da wannan halin nasa.
    Karfe 12 Baffanin AA sukazo antarbesu cikin mutunci da mutuntawa cikin halin dattako akai komai aka gama dubu dari Biyu suka kawo kudin Aure tare dasu goro alawa cimgom suka kawo ansa rana wata Biyu masu zuwa kowa yayi masa dan babu wani Bangare da zaice beshirya ba dansuma su Malam Alhamdlh suna da rufin Asirinsu babu abinda zai gagaresu.
    Harda Mahaifin Mama shima yazo ankarba tare dashi anrabu cikin farin ciki kowane bangare yatafi da Zuciyarsa fes babu wani shakku da taraddadi bakamar na Fareeda da suka tafi suna tunanin wane irin Ahaline wannan da dansu yazo neman Aure dan kaf cikinsu babu wani Dattijon kwarai daza anuna ace me kamalane duk yan kama karya ne kai idan idanunsu ma yaga daidai kana ganinsu irin tsofaffin tashar nanne wanda sunyi shaye shayen har yagama dafar dasu angirma ba asan angirma ba.
    Amma wannan karan da kwarin guiwarsu suka tafi gida sun kira Ammi sun shaida mata komai itama tayi matukar farin ciki AA yana zaune kusa da Ammi sanda suke wayar murmushi kawaii ya saki yana lumshe idanunsa betabajin zeyi Aure ba sai awannan lokacin,to a lokacimma ina yasan zaiyi wani Aure komai da yakeyi jiyake a dole ake tirsashi.
    
    Wai Kafadawa Fareeda zaka kara Auren Kuwa wani Huci ya fesar duk Sanda za'a Ambaci Fareeda ransa baci yakeyi yarasa Kaddarar data sameshi harya Aureta duk matan garinnan intazo taganta Ammi sam ban yadda ba tana da hakkin da zaka fada mata tasani ko itama zatai shirshirye kuma ka kwantar mata da hankali Kasan mata ko yaya za'aimusu Kishiya abun badadi dole saika Lallasheta ka kwantar mata da hankali banason saurin fushinnan naka Abie nagaya ma.
    Shiru yayi yana sauraren Ammi yadai jitane amma shikam bazai zauna yana lallashin Fareeda ba dazatace zatai gaba ma daya gode mata data hakura da karta hakura duk daya shibashi da matsala da duk wani haukanta yana daidai da yasaita mata tunaninta.

Sallama yayiwa Ammi yawuce Gidansa yana fita harabar gidan ya fara yiwa ma'aikatan Gidan rabon kudi matansu da mazansu babu wanda be samu wannan alkhairin ba.
    Aiko sai zabga masa Addu'a sukeyi sosai ya faranta musu rai fatan Alkhairi Kuwa yashashi Ammi tana cikin Gida batasan eeyake faruwa ba saiganinsu tai suna shigowa yimata godiya sai alokacimma tasan abunda yake Faruwa murmushi kawaii tayi tana yiwa ALLAH Godiya daya azurtata da mai tausayin na kasa dashi akowane lokaci.
    Marwanah ce tai sallama tashigo daganinta agajiye take wash Ammi biki ake Agidannan ne naga su bala direba sun ware Mp suna cashewa abakin Get,rike haba Ammi tayi eh lallai abunnasu ya gawurta kice rawa suke tika dariya tayi wallahi Ammi baki gansu ba abun dariya da alama wani abun farin ciki ya samesu Yayankune yayi musu rabon kudi shinefa suke ta wannan murnar Yanzu suka fita harnan sukazo yimin Godiya ALLAH sarki Yaya Abie aina dabanne wallahi ALLAH ya kara Arziki.
    Ameen Aini wllh Ammi bakiji yadda nake Farin ciki ba zanga yadda wancan Matar tasa zatayi zanso ma agabana zai gaya mata naga haukan da zatayi dan wllh Yaya tsaf zai dawo da ita cikin Nutsuwarta uhm ALLAH dai ya kyauta abunda Ammi tace kenan.
     Yanzu ya maganar hado kayan Lefe munyi magana da Maminku sati mai zuwa zamuje Dubai acan nakeso a hado komai kitafi dani Ammi harararta Ammi tai toko Autata a Gida zan barta barike da kike da Miji babu inda zani dake ALLAH Ammi zai barni kinsan dai nafiku sanin takan kayan zamani iyee to Yarinya abunda mukasani ko rabinsa baki sani ba kufa yan dane Ammi kunsha Miya a'ah Taushe mukasha Dariya sukasa gaba dayansu.Cigaba sukai da hirarsu tsakanin uwa da Yarta.
           ......✍️✍️✍️
        WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Kim Aneesat
         PART TWO
Chapter 32
       Bamu waiwayi Kamal.
Kamal kusan sati yayi a Hospital aka sallameshi yakosha alwashin in harta dawo saita gane kuranta kuma saki nedai bazai sake taba haryanzu batakoma yadda yayi mata tanadi ba,agefe guda kuma Hajiya ta huramai wutar saiya saketa hakanan yaje ya dauko musu irin jaraba nan gaba ma Umma tsaf zata iya kashe mata dan shikuma ya kafe akan bazai saketa ba sosai abun ya batawa Hajiya rai to zanga nidakai waya haifi wani inma kafara santane to dole karabu da ita tunda ba tare na haifeku ba dan ubanka cikin tsabar jin haushi Hajiya ke wannan banbamin.
     Yayarsa ce tai tsagal to Hajiya kekuwa anwanke anbashi badole ya gaddame akan bazai rabu da ita ba lallai dole saikin tashi tsaye wallahi dan so suke surabaki da danki.

Sake hawa Hajiya tayi kibarni dasu dagashi har dangin wancan kekashashshiyar dan bazan taba yadda ba wallahi ALLAH ya kaimu gobe mukoma station dinnan dole arabaku nagaya ma tashi tai tabarmai wajan kowa da abunda yake ransa abunda yake ransa daban abunda suke nufi daban.
      
     Karfe 8 a station taimusu suna zazzaune akan benci suna jiran akirasu wani kurtu ne ya fito kushiga tashi sukai dangin Hajara da dangin Kamal sai hararar juna akeyi Hajara kosan kallan barin da Kamal yake bata sonyi dan Zuciyarta harwani zugi takeyi sosai takejin tsanarsa acikin ranta.
   
D.P.O be tsaya dogon wani bayani ba yayi sulhu kowannnen su saida akaci tararsa kan lefin daya aikata maganar ma'aurata kuwa cewa yayi suje gida su sulhunta kansu Malam gidansa ya bada umarnin tafiya badan su Hajiya sun so ba suka bishi, zama akai na musamman Kowa aka bashi damar ya fadi abunda yake ransa Kamal aka bawa damar magana gaba daya kame kame ne bayanin nasa.
     Itama Hajara damar magana aka bata tas saidata fadi dukkan abubuwan da yake mata duka rashin Abinci zagin tsamar Nama da yake mata babu abunda bata fada ba.Kai anyi haka kanyayi magana Hajiya tai caraf karya takeyi munafukar yarinya ko bakice ga abinda yayi miki ba aidama baza'a tashi daga wajannan ba saiya sakeki matukar Nono na yasha wallahi saiya rabu dake.
     Dama ance Talaka be iya samun waje ba cikin jin haushi Umma tace ALLAH na tuba ina arzikin yake sai karyarsa da akeyi abaki aiko baki fada ba dolensa ya sakarmin yarinya tunda bawani shege ya haifarmin ita ba kafata kafaryata babu inda zata koma bazaku kashemin yarinya a aikin banzaba takardarta zai bani cikin huci Umma take wannan hayagagar.
    
Aiko saidai Kutafi tare ina tabbatar miki yana sakinta gidanku zaki wuce cewar Appa da bakin ciki ya ishesa dan bakaramin haushin Umma yakeji ba yanzu au kace ubannata ma gudunta yakeyi shine za'alikawa dana to wallahi sai dai daganan tashiga Duniya amma bazata koma gidan dana ba matukar nima nina haifeshi anan zai rabu da ita.
   
 Gaba daya ran Malam ya gama baci babu ma wanda ya bata masa rai irin Appa yarasa wane irin da ALLAH ya bashi dayake da kafiya da taurin kai.
    Kai kuma Kabiru nasha gaya maka saidai kafita kabarmin Gidannan badaini natafi nabar makaba, to zangani kuwa tsakanin nidake wane megidan za'agani kuwa. 

Hajara nagefe tana rusar kukan bazata koma gidan Kamal ba cikin takaici Appa ya daga Hannu ya kifa mata wani mari da saida tadaina gani nawasu dakiku Kowa marin abazata yajishi shiru kake ji kuwa.
    
     Hajara ta fashe da Kukan zaba Umma ce ta dura wani ashar da saida Kowa ya girgiza yar tawa zaka kashemin Kabiru wallahi yau aKwai tashin hankali tas kakeji itama Umma ya dauketa da Mari kanya sauke nasa itama ta kifamai nata marin wani marin yasakeji Akuncinsa na hagu juyowa yayi yaga wanda ya mareshi.

Inna ya gani tsaye cikin Bacin rai take Kallonsa gaba daya ta kasa magana saboda bakin cikin da ya tsaye mata azuciya.
    Kwallace ta ciko mata ido duk yadda taso maida ita kasawa tayi zubowa sukai akan fuskarta Kabiru nagaji da bacin ran da kake sani narasa kai wane irin Mutum ne da bashi da Tauhidi bakasan kaddara ba gaba dayanka dukkan wata nasiha da za'ai maka ammaka ita Amma bata shiga Kunnan ka akwai ranar dazakai nadamar halayanka Ranar tananan zuwa ina kuma jiye maka tsoron wannan rana dazata waiwayeka ina rokon ALLAH daya nunamin wannan rana da zanganka durkushe akan Guiwowinka kana ba wadanda kazalinta  hakuri.
    Komawa tai ta zauna gaba daya Kowa Jikinsa sanyi yayi Malam ne yayi gyaran murya kowa sake nutsuwa yayi sosai yayi musu Nasiha me ratsa jiki,Kallon Hajara Yayi zaki koma dakin Mijinki tunda yace bazai sakeki ba saurin girgiza kanta tayi dan bataga Abunda zaisa ta sake yadda tazauna da Kamal ba kallonsa ya mayar kan Kamal kaji abunda matarka tace, ni ina sonta Malam ayi hakuri sharrin shedanne nayi nadamar abunda na aikata mata.
     Kuma dagaske har Zuciyarsa yaji zai iya zama da ita sosai Jikinsa yayi sanyi da irin maganganun da Malam Yayi Awajan.

Amma fur Hajara tace babu inda zata koma Malam cayayi a kyaleta yaje sudaidaita da Matar sa dan yasan Mata yan lallashine zata iya saukowa nan gaba kadan haka taro ya tashi ko kala Malam becewa Appa ba aishiruma Magana ce Amma fa game hankali.
    
    Yana Gani Umma tasa yarta agaba suka tafi babu yadda zayyi kowa tashi yayi yabar Appa awajan sai Malam wanda ya manta da ÀLLAH yayi ajiyarsa awajanma harkar gabansa yaci gaba dayi dan Kansa daya gaji da zaman yatashi yafita daganan bagida ya tafiba Kasuwa ya zarce zuciyarsa ba dadi.
    
Hmmm haryau fa da sauran Appa kome zesashi yin nadama Oho Kubiyoni danjin Yadda zata Kaya.
            ........✍️✍️✍️
                WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum ANEESAT
                PART TWO
    Chapter 33 
  
 Shirin Biki ya kankama har lokacin Amarya da Ango nasu kara Haduwa ba babu waya ahannunta bare ya kirata ko akwaima bakiranta zaiba yabari koma mene intazo zaisan tayadda zai koya mata soyayyarsa.
    "Tun dazu yake kallonta yarasa ta ina zai fara danshi ya tsani oguwar magana lumshe idanunsa yayi ya bude akanta gaba daya tazaku taji wace magana yace zai gaya mata tun dazu ya sata a gaba yaki yace mata cikanki Abun harya fara kular da ita"
    
Hannunta taji yariko tofa Lallai Maganar babba ce ita yaushe rabon AA yarike hannunta harta manta wani dadi ne ya cika mata Zuciya dan ta dauka aikin da Mom tace taje jiya anyi Kansane ya fara aiki harta fara kissima irin yadda zatamai rashin mutuncin daya dinga mata akwanakinnan gyara Fuskarta tayi tare da turbune ta ita alallai zata fara gwada sa'arta taga ko aikine yafaraci.
    Kaga dallah malam kazo kasani agaba kana kallona kamar wata TV inbaka da abun fada katashi kaban waje dama kayan wankina suntaru kadauko su yau kaine zakamin wanki.

Kallonta ya sakeyi da alama yauma tayi shaye shayen data saba Abunda yace kenan azuciyarsa danshi sam abun ma bebashi haushiba shitaya zai yadda ma Fareeda ta batamai rai yana cikin Farin cikinsa.
    Rarraba ido tafarayi ganin ko motsi beba gashi kuma yaki sakar mata hannu motsa hannun tayi danjin yana barazanar karya mata yan yatsu wata muguwar matsa da yayi mata batasan sanda tasa kara ba,Murmushin Gefen baki kawai yayi dan tsaf yagane inda ta dosa hmmm kawai yace duk abunda takeyi kar yake ganinta.
    "Cikin kularwa da bada takaici yace Anty Fareeda ware idanu tai akansa Anty nice Antyn"? eh man aike Anty nace dan natabbatar kingirmeni kinga dole nadunga baki girmanki matsayinki na babba wani kululu ne yazo ya tokare mata awuya abunda yakeson gani kenan dama, numfasawa yayi shiyasa naga ya kamata na kawo miki kanwa kinga gaba daya saiki hada kirainemo.
  
  Saurin fizge hannunta tayi tare da mikewa tsaye danta lura AA soyake ya maidata Mahaukaciya Yar iska menaji kana fadin wace Kanwa zaka kawo min.

Saida yayi wani shegen Murmushi tare ta shafa gemunsa tunda baki ganeba banai miki gwari gwari Kishiya zan kawo miki kema kanki zakifi jindadi kinga ALLAH ya taimakeki babu ko sisina za'abani hakkina kuma atarairayeni kekuma saikici gaba da adana kayanki kina sake tsumashi.
    
Kanne mata ido daya yayi tare da dage mata gira ina fatan wannan Kokarinnawa yayi Miki.

Kallonsa kawai take kamar wata sokuwa har ita zai kalla yadinga gayawa wannan maganar yaushe tai Lalacewar da AA zai mata haka, rasa Abunda zatai tayi kawai dora Hannu tai aka ta fashe da kuka kukan bakin ciki da takaici Kishiya ai wallahi bazata zauna da Kishiya ba duk abunda za'ai saidai ayi kuka take shabe shabe AA yana zaune yana tikar dariya abunda yakara kular da ita kenan kwalar rigarsa tazo takama tare da jijjjgashi.

Ameenu ni zakaiwa kishiya ka kalleni daga sama har kasa banyi kama da wadda zata zauna da kishiya ba amma matukar kace sai kayi Aurannan zanga ta yadda Amaryar zata shigo danko zan rasa komai nawa bazan bari ka Auro taba.

Numfawasa tai towaima yar gidan uban Wacece Agarinnan ba yar gidan kowa bace face yar gidan Mutunci da Tarbiyya dangin ta kaf babu me abun kunya.
     Wadda iyayanta suka koyar da ita sanin Muhimmancin na gaba da ita ina fatan Karatun yayi daidai da yadda zakiwa zancan fashin baki dallah dallah sosa kunnan sa yayi yana sakar mata Murmushin da yake sake kula da ita.
    Zare Hannunta yayi daga kan rigarsa ya zagayeta ya wuce dabar tazauna A tsakiyar parlour Zuciyarta wani tukuki take mata kamar kirjinta zai babbake haka takejin kishinsa na azalzalar Zuciyarta.

Samira ce suka Kalli juna daki suka fada kamar zasuyi me dan murna kaisu wannan abu ba karamin dadi yayi musu ba sosai Samira take kwaso Shoky danji take kamar ammata albishir da kujerar hajji Addu,ata ta karbu za'aiwa igiyar shanya Kishiya sunan da suka sawa Fareeda Kenan.
      Ta dade a zaune tana rusar Kuka dan ita ko tunanin Yan aikin Gidan suganta ma batayi ita tasan me takeji acikin ranta.Tashi tai ta fada bedroom dinta mayafi kawai ta dauka da key din Mota tai waje abun takaici tana zuwa zata fita sukace Oga yace kar abarta ta fita ko ina wannan fa shine duka biyu duk bala,in datai abanza kememe sukaki bude mata tai zage zagen kamar badasu take ba daga karshe dai haka ta koma gida rai bace.
         ........✍️✍️✍️
    
               WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
             PART TWO
    Chapter 34
    
    ALHAMDULILLAH tafiya tayi kyau su Ammi sunje Lafiya sun dawo Lafiya ba kananan kudi suka narka akayan Lefennan ba komai ma sha ALLAH sarkar Gold kadai sunkai Biyar acikin kayan kai inna tsaya baku Labrin kayan tsaf zan gama cika Littafina batare dana gama ba dan harkar ta manya ce.
    
Yan uwa da abokan arziki sai zuwa suke ganin kayan Lefe kawayan Ammi da yan uwanta kowa Yazo saiya Zuzuta Kayan sabida anbaje basira wajan zabarsu.

Sun sa ranar da zasu kawo kaya dan haka tuni an sanar dasu Malam matane zasu kawo Mami dai tana dangin amarya tana kuma dangin Ango kowane bangare tana bada tata gudummawar.
    Yaune za'a kawo kayan WA'AT angyare gida fes gwanin sha'wa wannan karon harda Hajara akeyin komai dan tadade da zubda makaman yakinta Umma dai haryau tana kan bakarta babu wani abu daya sauya yau dimma daza'a tona Zuciyarta ALLAH kadai yasan irin yadda Zuciyarta ke zugi da tukukin bakin ciki.

Aiko tacika tayi taf kamar zata fashe sai hura hanci takeyi.
    Yan uwan Mama dana Appa sai hada hada akeyi komai daya danganci wanda zasu ba baki sun tana da kowa kaga Fuskarsa washe take da Farin ciki yan uwan Umma duka sunzo ganin kwakwaf suna daki suna gulmar mutuminma dabai damu 'Yar ba ko saudaya baitaba zuwa ganinta ba aikasan Auran sadaka ne suna daka suna shewa haryanzu basu daddaraba.
    Ana cewa ga yan kawo kaya sun karaso suka fito gaba dayansu harda Umma dan tasan ba kayan arziki zasu gani ba harta tanadi bakaken maganganun dazata dinga saki awajan.

Shimfidu akai na tabarma babu wani karya da suka nuna komai dai dai su suka dauka basu dauka da zafiba babu kyama bakomai na cewa su masu kudine suka shigo gidan kai tundaga ganin suturar jikinsu kasan sunwa Talauci barazana tuni sunyi hannun riga dashi.
    Hamshakan Matane wadanda suka amsa sunan su kowaccen su kasan tanacin gashin kanta Fuskarsu dauke da Fara'a suka zauna wajan da aka tanadar musu Akalla sunkai su 7 harda Safna wadda ta nace sai anzo da ita saiko Marwana itama da akazo da ita kawo kayan.
    Wasu matasane suka fara shigo da akwatunan da alama dama tare suke Akwatunan kansu abun Kallo ne tun Umm nakirgawa saidata sare Akwatuna masu sunan Akwati ba gama gari ba saida aka shigo da guda 24 tuni Umma taji wata hajijiya tana neman kayar da ita takusa da itace tatarota dan neman kaiwa kasa takeyi jitai kamar aradu ta rufto mata aka metake shirin gani kam bala,i kenan.
    Su Anty Asma Kannan Appa kabbara kawai sukeja Farin ciki kuwa sun rasa inda zasu saka kansu Yarsu tayi Goshi Mama kanta ta Girgiza da yawan kayan wannan kaya ina zasu kaishi 

Gabatar da kayan sukai Safnace uwar rawar kai tatashi ta dinga bude akwatunan daya bayan daya komai dai sai sambarka Mahassada da masu bakin ciki da wadanda har zuciyarsa suke tayasu murna duk akwaisu awajan.
    
🤣🤣🤣Umma dai saida Rarrafe ta koma daki babu wanda ya lura da ita atsakiyar dakinta ta baje wani gumi ke keto mata na Tsananin tashin hankali gawanda ya kamata takama tarike ashe ita aikin banza tayi towaima agidan ubanwa suka hadu da wannan attajirin haka har ita za'a Munafurta aki gayamata tunda wuri.
    Hajara ce tashigo dakin jikinta a matukar sanyaye ALLAH kenan meyadda yaso gashi sun rabata da wancan ALLAH yayi mata sauyi mafi alkhairi gaba daya ayaudin tafijin zafin Umma fiye da koyaushe tana sane da hakkin Wa'at ne ya kamata tunda gashi adaran da aka kaita tafara girbar abunda ta shuka wllh Umma ta gama cutarta.
    Fashewa tayi da Kukan bakin ciki aduk sanda tatuno da Auran Kamal saitayi Kuka Ummace ta juyo ta kalleta Hajara ki kwantar da hankalinki matukar wannan ma yayi miki babu abunda zai hana banyi duk yadda zanyi Kamal ya sakeki ki Aure wannan ba bazan taba yadda wannan daular ta wucemu ba.
    Cak ta tsaya da Kukan da takeyi wai anya Umma kanta daya kuwa gasky tana tantamar haka.

Allah ya tatsareni Umma ni ALLAH ya yayemin cutar Hassada da bakin ciki da mugun nufi kan yan uwana kema ina miki Addu,ar ALLAH ya ganar dake tunkan Lokaci ya kure Miki,yanzu Umma duk halindana shiga besa kinyi Nadama ba sai yaushe zaki gane Gaskya nidai na godewa ALLAH daya farkar dani daga Nannauyan banncin da nakeyi.
    Kuma in sha ALLAH bayan iikin Wa'at zan koma Makaranta danna tabbata rashin ilimi babbar cutace mari Umma ta kawo mata dan ubanki nikike gayawa haka nice jahila banda ilimi kike nufi ni bance keba kawai ina magana tane haka kawai bazan tsaya kidakeni ba danna gaya miki Gaskiya kuma ko anjima ta kama nafada miki bazan fasa fada ba Wallahi.
    Dake da Appa kuguji ranar sakayya ranar da zaku girbe abunda Kuka shuka to har dan gwara kema bakiyi abunda yakeyi ba Amma Umma kisani ni me kaunarkice bazan taba gaya miki abunda zai cutar dakeba dan Allah kiyi hakuri kicanza halayanki dazu dana Fita duk indai nai bakar magana ake gayamin kuma kune sila kune Kuka jawo koma me akace.
      Umma sakare tai tana jinta da alama dai jikin Umma ya fara sanyi tunani tafada wai atsahon zamanta da Aysha metataba yimata da hartaji bata kaunarta Aurar miki Miji tai wani sashi daga Zuciyarta yagaya mata hakan.
 
   Mijin da besan darajar 'ya mace ba mene abun kishi akansa gaba daya jikinta ne ya kara sanyi tatafi dogon tunani tun sanda sukai Aure da Appa inkaji suna fada to akan ta haifo mace ne anya ma sumadin yana kaunarsu kuwa to ribar meyaci da haihuwar Mazan gashinan yarannata duk sun watse ko Umar saitai sati bata ganshiba tatabbata Alhakin Mama kadai sai ALLAH ya jarrabesu da Lalacewar Mazan da suka dinga tutiya akansu gwarama ita akan uban gayyar.
    Hajara ta lura jikin Umma fa yayi sanyi ciki Farin ciki ta zauna akusa da ita hannayanta ta kama duka biyun sosai taci gaba da bata misalai kala kala da tuni Umma taji Nadama ta kamata akan dukkan Abubuwan data Aikata in sha ALLAH zata gyara Kurara kuranta nabaya.
         Lallai ALLAH ya ganar da Umma gaskya saura Appa.
Kubiyoni dan kuji yadda zata kaya
         .......✍️✍️✍️✍️
             WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesa
        PART TWO
Chapter 35

A can tsakar Gida kuwa anyi komai cikin Mutuntawa da sanin yakamata sati uku masu zuwa Aka tsayarda ranar biki suna tafiya su Anty Asmi suka dinga rangada guda Mama kam Murmushi kawai take komai Ma sha ALLAH sai san barka akeyi.
Umma dai tana daki takasa Futowa dan wata kunya ce ta kamata dan bataso tafito su hadu da Mama adaki tai zamanta su Zainab Ana gaban Kaya ana bubbudawa babu wani damuwa atattare dasu.
   
 Sai Magariba kowa ya watse dakin su Yaya Umar aka zuba kayan dan babu wajan da za'a zubasu agidan kuma suna da tabbacin bazai taba dibar kayanba da dai Ameer yana nanne babu wanda zaiyi gangancin kai kayan dakin dan ansan amba kura ne ajiyar Nama.
  
  Appa ba kunya ya zauna agaban kayan yana kare musu kallo anya beyi Kuskure ba kuwa dayake kin Yaya Mata yanzu dai gashi Yar dayake gudu tatako sa'a zata tafi gidan manyan mutane shima tabbas yasan duk wata daula dole ne acita dashi.

Dakin Mama Yashiga Yau dan Gulma hardasu sallama Fuskarnan a washe babu bata rai ba komai.
    
Amarya Amarya wani banbara kwai Mama taji dan saidata jujjuya bayanta taga dawa yake kodai bakuwa sukai,bata rai yayi ya zakidinga juyawa baya Alhalin kinsan dai babu wata Amarya agidannan Inba keba,kuri tayi tana kallonsa anya Appa be fara zukaba shima batare da sun sani ba.
   
 Kawar da wannan zancan yayi yana gyara zamansa hannun ta yake shirin rikewa can baya ta Matsa tanai masa kallon karka kuskura haba Aysha wai mene kike guduna kamar wani Dodo aikafi dodo ma abinda tafada kenan A Zuciyarta.

"Kafadi abinda ke tafe dakai dama zuwa nai naji ya shirye shiryen Biki mezamu tsara"? Murmushi Mama tasaki iyayanta ai sune da magana sunacan sun gama tsara yadda abun zai kasance,bangane mekike magana akai ba ubanta dai nine.
    Ko bayanni tana da wani ubanne anzo wajan dama ranar datake jira kenan gyara zamanta tayi yadda zata gaya masa Maganganun da suka dade suna dankare a Zuciyarta.

Tana dasu kuwa dan sune komai nata ko inane kuwa dasu zatayi tutiya tabigi kirji ta nunasu amatsayin iyayanta matukar kaga annunaka awanda ake da sanayya dashine wato wanda muke haya agidansa wannan kuwa hakkin makota ne dole a lissafoka amatsayin makoci wanda ba'aji dadin zama a gidan hayar saba.
    
Dan haka kacire kanka dashiga abunda babu ruwanka wannan Maganace ta ahali kaikuma baka ciki to katsaya daga gefe kasha Kallo,in sha Allah shinkafar Biki dai nadau Alkawarin baza'a manta dakaiba goro da Alawa na daurin Aure duk zaka samu baya ga wannan baka da wani hurumi da 'Yayana ina fatan kagane karatun da nake nufi.
    Galala haka Appa yayi da baki yana kallonta rasa abun fade yayi kamar wani soko haka ya koma goro da Alawa tadebo ta dauramai akan cinya gana kanan na Hakkin Makwaftaka kada ALLAH ya kamani da Laifin rashin fita hakkin Makwafci.

Tashitai ta shige Uwar daki Zuciyarta na matukar Tafarfasa ba ason ranta takemai dukkan wata magana mara dadi ba saboda ko bakomai shidin Mijine agareta Kuma uban 'Yayanta,amma da bakinsa yasha maimaita shidin baya da alaka da 'Yayanta natane itakadai akoyaushe muryarsa nai mata amo acikin kunnuwanta niba 'Yaya na bane nakine.
    Karki Kuskura kinuna ko ahanya sun sanni banason wahala saboda bangajeta ba kirike su bana bukata,share hawayan Fuskarta tayi sosai abun yayi mata ciwo har ila yau takasa mantawa dashi anya zama ta manta Kuwa.

Badan Darajar iyayansa ba da tuni iyayanta sun raba wannan Auren amma Malam da Inna sun wuce haka agaresu sunwa diyarsu komai da kafin simata sau daya inna da Malam sun mata sau Biyar tunda sunfisu sanin halin da take ciki.
    Tana fatan Lokacin da zataga ya dawo kamar kowane Mutum mai Hankali dayasan abunda ya kamata zatai matukar Farin ciki kuma ashirye take data yafe masa matukar ya gane kuskuransa ya tabbatar da cewa yayi badai daiba.
    Wannan Kenan.
          ........✍️✍️✍️✍️
    
           WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
              PART TWO
    Chapter 36
    
    Amarya WA'AT dai tazama 'yar kallo kallon kowa take ganin yadda kowa burinsa yaga wannan ranar biki musamman yan ganin kwakwaf da yan maula makwadaita tuni Tauraruwar Mama ta fara haskawa dan wani girma na musamman Jama'ar Unguwarsu suka fara bata kowa faran faran take da ita dan kowa ya shaida Yarta ta tako arziki.
    Umma gaba daya takasa sakewa agidan kullum tunanin ta ta ina zata nemi yafiyar Mama tana da Tabbacin muddin ta furta neman yafiya agareta mutane da yawa zasu fassara hakan da kwadayi ne ya kaita ita yanzu ba wannan ne agabanta ba gaba daya tunaninta yatafi ta yadda rayuwar 'Yayanta ya tarwatse babban fatanta a yanzu tasan halin da Ameer yake ciki Amma tunda yatafi shiru kake ji kamar anshuka dusa aruwa.
    
Tuni Umma aka koma ga ALLAH Jam'i baya wuceta ko yaushe ka ganta da carbi tanajan istigifari kai kowa ya shaida Umma ta canza agidan za'a iya wuni ma ba aji koda tarinta ba koyaushe tana daki.Hatta Mama da bashiga harkar juna suke ba tana mamakin wannan sauyi na Umma.
    
Umma nacan Kuwa abun Duniya ya taru yayi mata yawa ga Hajara ansakota ga Mazan gaba daya babu wanda zata nuna tayi Alfahari dashi har gwara Umar tana ganinsa baya shaye shaye Amma fir yaki Makaranta tun yana karaminsa shima amma hakan sam be taba damunta ba sai awannan Lokacin gashi gaba daya baya ganinta da mutunci safiya bazata taba yiba yazo dakinta da sunan yazo gaida ita.
    Kai ita zata iya cewa ma basu tabayiba kaf 'Yayanta babu me gaida ita to bata koya musu ba kuma itama basuga tanayi ba dan Appa tun suna cin Amarci rabon data gaidashi saidai kullum cin Mutunci da zage zage atsakaninsu babu girmama juna shiyasa suma yaran gashinan abanza suke kallonsu to sungama zubda mutuncinsu agaban 'Yayansu.
    
Bikifa ya kankama dan Mami da kanta tadauko me gyaran jiki dan danan kyan Wa'at ya kara fitowa fatar nan tayi haske dama abarka dame kyau saita kara wani irin kyau me matukar sanyi,duk indata wuce kamshi ketashi gaba daya kamshi ya samu wajan zama ajikinta.
    Sako da Lungu gyaranta akeyi Kayan gyara kuwa tana shansu masu kyau da inganci tare da Jidda ake gyaran jikin dan itama tanace adinga hadawa da ita itama fatarta tasakeyin fes da ita.

Rabon IV ma Jidda ce sukai da wasu kawayansu na Makaranta aiko sunsha gayya dan duk wadda Jidda tasani saita gayyace sa.
     Kamu zasu fara sai walima saboda Malam yace bawata Bidi'a da zasuyi sai ranar da aka daura Aure zasu fita Dinner komai Mami ce ta tsara dan Malam yace karsu tsawaita Bidi'a komai dai Ma sha ALLAH.

Gidan Bikifa yasha fenti shindai Appa baza'ace ga yanayin da yake ciki ba Amma zamu iya cewa yana Farin ciki zai rabu da guda daya daga cikin 'Yaya Matan tunda wancan me kama da kaudar raken ta dawo bakaramin takaici yakeyi ya ganta ba.
    Ya dinka Sabbin Kayansa dal Amma duk wata Gayya yan uwansa ne sukayota ko Mutum daya be gayyata ba yace sai yatashi Aurar da 'Yayansa Maza za'aga gayya gari gari unguwa unguwa ba inda bazai Gayyato ba.
           *******
Bangaran AA shima shiri yake yi ba kadan ba ko yaushe soyayyar Wa'at sake ninkuwa take azuyarsa da ita yake kwana yake tashi Fareeda dukkan wani hauka tayi Amma babu ci gaba ko ajikinsa kowa ya watsar da ita acikin Gidan hatta yaransa murna suke taya Ogannasu dan bakadanba suke so suga Farin cikinsa su kansu sun yarda yana son wannan Amarya tasa.
     Kaf Ma'aikatan Gidan da yan Aikin Gidan Babu wanda be dinkawa sababbin kaya ba nacin Biki dan ya sanar da yaransa dukkan wani shagalin Biki dasu Za'ayi saiya kara wani irin girma da kima acikin idanunsu babu ruwansa da yafisu mukami ako yaushe yana kokarin daidaita Kansa dasu atakaice dai ya zamo Babban Yaya Agaresu.
     PART din Wa'at daban duk parlour daya ne amma ko wacce bangaranta daban irin gininnan ne muhadu A Parlour kowaccensu tana da ikon tafito babban Parlour ta zauna babu ruwan 'Yar uwarta da ita.
         ......✍️✍️✍️

            WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
        PART TWO
Chapter 37

Kaya na gani na fada haka akayiwa WA'AT babu ko sisina Appa bama ace mai kaci kanka ba ai shikam gaba ta kaishi,hardasu Safna akazo jere da takamarsu suka shigo gidan da kwarin guiwarsu ko kallan Fareeda basiba wadda ta kame a parlour tayi tunanin zasu kulata ayi hayaniya babu wanda yabi ta kanta babu kunya taki gaida Manyan da summa haifeta suma shiyasa babu wanda yayi mata magana dan danan akai komai aka gama dakunan ta sun Masifar haduwa ciki da Parlour ne Guda uku babu wanda ba asaka mata kaya ba.
    Kaya nagani nafada kafin nashiga da kunan akwai parlourn ta na Musamman babu abun da babu aciki Kichin Toilet zata iya wuni ma batare da tafito ba dan akwai abunda zata bukata komai akwaisa aciki.Dakin Megidan dai Yana sama duk inda yaga dama zai iya sauka,dayake basu sukayi aikinba komai Ma'aikatane suka daura nasu kawai su gaya musu gayadda zasu jera kayan.
    Abinci dagayya su Samira suka takarkare suka shirya Lafiyayyun Abinci masu shegen dadi dandai kawai su kara kular da Fareeda aiko sun kular dan tashi tai tana dura musu zagi ubanwa yace suyi girkin fatattakar su tayi daga Kichin din Marwana da kanta tazo tadebi kayan Abincin Fareeda na tsaye bayadda zatai da ita.
    
Suna gamawa suka kulle ko ina sukai ficewarsu suka batta da cizon yatsa dan taso sukula ta ayi tashin hankali sotai kayan dakimma ta Farfasashi.
    Alhamdulillahi taro fa anfarashi babu hayaniya bakomai badai kazo katafi kace katafi Hannu haka ba dan AA yasaki Kudi wadaka kawai ake da Nera harkar ta Manya ce tuni Su Hajara suka ware suka Shiga ana harkar Arziki dasu Ana damawa dasu,itama Umma ba laifi ta saki Jikinta Duk wadda yazo Zata karbeshi Hannu biyu har Sababbin Kaya ta dinka kala biyu wanda Zata ranar Biki.
    Kowa Mamakin Sauyawarta Yake wasu suce kwadayine wasu suce ÀLLAH ne ya ganar da Ita Gaskiya Musamman Dangin Appa dan dayawa sunce Tuban Muzuru Tayi mehali baya fasa halinsa kowa da abunda yake Fade.
                
Koda Inna tazo harkasa Umma ta duka tana gaidata kai itama Inna abun ya bata mamaki ya daure mata kai amma data tuna komai Lokacine ÀLLAH babu yadda baya Lamarinsa ÀLLAH yasa har zuci tai wannan tuban
      Mama kaya kala uku uku ta dinkawa Hajara Zainab da Zubaida suma suci Biki har godiya sukai mata dan sun zubda makaman yakinsu haka Umma har godiya tayiwa Mama,kowa kagani Abikinnan kasan Ma sha Allah bakinsa dumu dumu da maiko.Abinci kala kala sai kaci kabarshi.
     Har Walima sukai ALKUR'AN Hizib Sittin da sallaya da carbi duk wandda tazo Walimar nan ta samu Babbar Malamar nan dai Shahararriya suka sake daukowa dan sunji dadin Wa'azinta Lokacin sauka bakowa bace face Malama ZAINAB BINTU JA'AFAR MAHAMUD ADAM tako kwararo musu Bayanai masu matukar ratsa zuciya tayiwa Amarya nasiha sosai yadda zata zauna da Mijinta babu boka ba Malam sai tsabar Tsananin biyayya iya Girki Kwalliya iya Magana Tsafta komai saida tai masa Fashin baki akansa.
    Mata sai Kabbara akeyi Sosai sukàji dadin wannan tunatarwa ta Malama ZAINAB BINTU JA'AFAR.
    Amarya kuwa tasha Kuka Hijab ne ajikinta fari tas bakaramin kyau yayi mata ba sosai jikin Umma ya kara sanyi nayadda taji tana bayani akan Tarbiyyar yara Umma har sharar kwalla aka dingayi ganin yadda tayi sakaci da nata Tarbiyyar yaran amma ta daura damarar gyarawa tana fatan ALLAH ya bata Nasara da sa'a akan yun kurinta akaro na farko dan gyara Tarbiyyar Yaranta.
    Anyi Lafiya antashi Lafiya.
    Rana Lahadi yau take daurin Aure tun karfe 8 unguwar ta fara dinkewa da Jama'a agidan Malam za'a daura Auran manyan moto cine masu Numfashi suketa fakawa kama daga yan uwan Malam da abokan Baban AA da Baffaninsa kaf dinsu Abokansa sai jerin gwano akeyi da Motoci karfe 9 unguwar ta gama dinkewa da Jama'a wani maroki aka samu me zakin murya sai kirari yake xabgawa baji ba gani.
    Appa dai ansha Babbar riga shikansa saidaya firgita ganin irin manyan dayake gani wajan Bikin Yar tasa tuni yaji wani kwarin guiwa ya sake zuwar masa kaga inda ake harkar arziki cikin Mutane yadinga kutsawa sai washe baki yakeyi harsai da yaje kusa da Malam sannan ya tsaya yana rarraba idanu.

Kau dakai Malam yayi dan Wallahi jiyake kamar ya shararawa Appa mari idan ya tuna dibar Albarkar dayazo yayi masa jiya har gida akan shi ba'a daukesa abakin komai ba tundashi ko dinkin Biki ankasa yimasa.
    Wannan shine Mahaifin Yarinyar Malam ya fada dan bayadda za'ai su kankare shi daga zamtowa mahaifinta miko masa hannu Baffanin AA sukai aka sake gaisa haba tuni yaji kansa ya kara girma sai baza Babbar Riga yakeyi.

Karfe Goma daidai Jiniya ta karade Unguwar Motocine na sojoji akalla sunkai 30 kungiya guda sukayo dan taya Ogannasu murna dakuma manyan sa na wajan aiki suma ba'a barsu abaya ba Motar Ango an sakota atsakiya kai kanka mekaratu kaga yadda suka jero dole su burgeka.
                     .........✍️✍️✍️
 
                                   WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar 
Oum Aneesat
                    PART TWO
Chapter 38

Ango ne yafito kai ma sha Allah cikin wata dakakkiyar shadda kaida Gani ankashe kudade kafin atashi wannan wankan blue ce shaddar tayi matukar fito da farar fatarsa sai walwali yake da kyalli,abokansa ankon shadda sukai light blue gaba dayansu kowannen su yaci Babbar riga.

Malam Hamdala kawai yake aransa da Allah ya azurta jikarsa da samun Miji nagari dan yayi bincike akan ahalinsa sosai sai yabo daya jiyo beji sabanin haka ba saiko yan Hassada masu kawo suka wannan kuwa dama inhar baka da makiya da mahassada to baka cika mutum ba.Har kasa suka tsugunna suna gaida su Malam cikin Jindadi suke amsawa shima Malam Yayansa da Yan uwansa babu wanda baya wannan waje.

Babban Masallacin Juma'a dayake Unguwar Gaba Kadan nan aka dunguma dan Daura Auren,cikin yardar Allah aka Daura Aure kan sadaki Naira dubu dari Biyu da Makullin Mota nan muryar maroka tafara tashi tako ina busa sarewa akeyi me matukar dadi gidan Bikifa ya sake kacamewa dan gidan Appa jama'ane gidan Malam haka bikine akeyi na yangata 'Yayan Dangi.

WA'AT tana makotansu anan suke zama ita da kawayanta Kanwar Mama ce tashigo tana rangada guda tana shelar Andaura Wa'at Kuka kawai ta fashe dashi tuna zata rabu da yan uwanta da Mamanta mafi soyuwa agareta dakyar suka rarrasheta tayi shiru sake gyara mata fuska akai itama shaddar jikinta Blue ce tayi matukar yimata kyau.
    Kama Hannunta tayi suka shiga gida nanfa abokan wasa suka sakota gaba da tsokana har dakin Mama takaita,fashewa tasakeyi da kuka tuni harta fara tunanin Mamarta da kannanta sam bataso tayi nisa tabarsu,ita kanta Mama jitai hawaye na naneman zubo mata da sauri tajuya tashare.
     Yau ita ce zata Aurar da 'Ya batasan irin Godayar dazatayiwa Allah daya nuna mata wannan babbar rana ba Lallai Allah mabuwayine akan dukkan komai,gashi cikin sauki Allah yakawowa 'Yarta Miji babban fatanta Allah ya basu zaman lpy ya kade duka wata fitina atsakanin Mijin da abokiyar zamanta.
     Kusa da Mama aka zaunar ita kanta ta dora akafadar Mama tana sakejin rauni nasake mamayeta yanzu intatafi shikenan tadaina hawa cinyar Mama tadaina yimata shagwabar data zame mata jiki ajikinwa zata dinga kwanciya wazai kula da ita kamar Mamanta babu haka zuciyarta tabata amsa.
      Angone da tawagarsa suka shigo gaida iyayan Amarya sai guda ake saki kaida kaga Fuskarsa Kasan yana cikin Farin ciki mara misaltuwa.

Duk da be cika Fara'a ba Amma ayau Fuskar tadaban ce yana Murmusawa ko yayane sosai aka gaggaisa har dakin Umma sukaje gaisheta abun bakaramin dadi yayi mata ba,sai kunya ta kamata tuna sanda akai bikin Hajara koda wasa batace suje sugaida Mama ba Amma ita gashi har daki aka biyo ta.

Umma tasha sabon dinkinta komai nata sabone tashiga cikin aikin Biki kace kace kowa ya shaida yanzu fa ba Salaman da bace akwai banbanci,Mama sosai take Farin ciki da sauyawar Umma ya tabbata yanzu zata gyara kuskuran datai abaya na lalata Yaranta zata taimaka mata itama da yardar Allah dan Ganin sun zama nakwarai dakanta zata dauki nauyin sakasu A makaranta.
     (Kunjifa Masuyi dan Allah anaso kowane Musulmi ya kasance me yafiya merama Alkhairi in ammasa sharri.Allah ka kara dawwamar damu Acikin masu hakuri)

Biki yayi Biki Umma Yan kidan Kwarya ta dauki nauyin kawowa aiko masu kidan Kwarya sunzo sun gwangwaje 'Yan Biki sunsha liki kuwa haka Umma tabude bakin aljihu sosai taiwa Wa'at liki kai wannan Biki babu wanda zaice beji dadinsa ba haka su Hajara sunyiwa 'Yar uwarsu kara sun cashe cikin Farin ciki su Nusaiba kuwa ai ba'a Magana itace merukon Jakar Amarya sunyi matukar kyau ita da Hafsa.

Karfe 12 na rana Jerin gwanon Motoci suka zagaye Gidan Appa saboda tafiyar tasu akwai nisa kuma a Yau sai sunje can ABUJA za'atafi Dinner da Ammi ta shirya su Mami ne 'Yan daukar Amarya Wa'at saboda Kuka har shidewa take kam tarike Mama gaba daya Takasa yimata Nasihar da aka kawota tai mata fashewa tai da Kuka babu Abinda yataba rabata da 'Yarta yau gashi Aure zai rabasu.
  
  Dole ne tayi Kuka rashin Wa'at akusa da ita tamkar wani babban gibi ne acikin Rayuwarta Amma yazatayi dole ta hakura tunda cigabane Ganin kukannasu bana kare bane Mami dakyar ta banbaro Wa'at dakin Appa ta kaita Malam da inna su suka hadu sukai mata Nasiha meratsa zuciya,sukansu dauriya suke saboda zasuyi matukar kewarta.

Appa ALLAH yabada sa'a kawai yace daganan Uffan be kara tofawa ba haushine ya kama Inna suna fita da Wa'at ta makamai harara koba kaceba Ai ALLAH zai bata sa'a tunda uwarta tasa mata Albarka aikomai yayi Kyau.Kumbura Fuska yayi kamar wani yaro karami Waini Inna meyasa duk abinda nayi a ban iyaba nake saboda nafi kowa bakin jini yanzu muguwar Addu'a naimata kome.
     To saunawa kuma aidama duk wanda yace baya kaunarka to dagaske baya sonnaka ALLAH ya shiryeka inzaka shiryu Fuuu tafice Afusace binta yayi da Kallo uffan Malam bece Masaba ya tashi yafice yabar Appa da tunin waime yakeyi da kullum su Inna sai sunsashi agaba kamar wani yaro sunamai fada.
   Ankaita dakin Umma tayimata Nasiha Amatsayinta na Uwa agareta alokacinne tanemi yafiyarta akan dukkan wani abu datayi musu abaya ta Tabbatar mata data yafe mata Umma Hawaye ake shabe shabe,Inna ce ta saki Murmushi ganin ALLAH ya shirya Umma shikuma wancan ko me zaigirgiza zuciyarsa harya gane kuskuransa oho kwafa tai.
         .......✍️✍️✍️

               WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat 
            PART TWO
Chapter 39

Dakyar aka sakata amota dan dagewa tayi ita babu inda zataje abokan wasanta sai tsokanarta sukeyi,Inna da Umma sai Yayar Mama sune amotar kai Amarya sauran Motocin suncika dam dansu Nusaiba Hafsa Hajara ZAINAB Zubaida mota guda aka basu suka shiga.

Umar ma ba'abarshi abaya ba dan cayayi shima saiya je yasha Farar shaddarsa daya dinkata saboda Bikin sai wshe baki yake shi yayan Amarya gaban Motar dasu Hajara suka shiga nan ya shiga ya kame.

Matafiya sun dau hanya saidai ALLAH ya kaisu lafiya ya dawo dasu lafiya.
     AA tun 12 na rana jirginsu ya daga dan yaso abashi Amarya yafara yin gaba da ita Mami tace be isaba yadda akekai kowa cikin rakiyar danginsa itama haka za'akaita saidai yatafi shikadai zasu zo daga baya badan yaso ba ya hakura dan yasan Anty Juwaira akwai kafiya intace abu tofa da wuya ta sanja shida wasu daga cikin abokansa suka farayin gaba dan zuwa su sake tsara yadda Dinner din zata kasance.
       Kukan da Mama tasha saida tasha maganin ciwon kai tasamu takwanta sai bayan La'asar  data tashi taji tadan koma daidai haryau akwai Jama'a a gidan danginta dana Appa kai harda dangin Umma.
      🤣🤣🤣🤣Kai Hajiya Uwaliya dai itama ALLAH yayi  ta cale ABUJA ko banza zataje ta huce takaicin kajinta da bataci a Bikin Hajara ba taci sabuwar Atamfarta da sabon Hijab dinta saita fito ras da ita tunkan tashiga Mota Umma ke rokonta takame bakinta kartai abunda za'azo ana cewa tayi ba daidai ba haushi ko ya ishi Uwaliya Amma batason tayi hayaniya kar ace amfasa zuwa da ita danta rantse saitaje harda guzurin katuwar Ledarta.
    
 Karfe 4:00 Motocin sukai Jerin Gwano aharabar Gidan Ammi da kanta tafito Yan uwanta suka biyota abaya dan tarbar amarya Wani dakakken Les ne ajikinta yayi matukar yimata kyau hannu da wuyanta Daham ne masu matukar tsada hakoran Makan dayake bakinta masu walwali sai suka kara haskata.
     Oyoyi Oyoyo ina diyar Albarkar take nuna mata Motar da Wa'at take ciki akai da kanta tabude Motar ta kamo Hannayanta tana Fitowa da ita ta Rungumeta tana saka mata Albarka sosai take kaunar Wa'at yau tana cikin tsananin Farin ciki nashigowa Family dinta datayi su Inna abun ya matukar burgesu sun Tabbatar basu bada 'Yarsu inda za'a wulakantata ba sai suka sakejin kwarin guiwa.
    (Dama ance shinfidar fuska tafi shinfidar Tabarma,agareka da Fara'a da sakin Fuska yafi atareka da Naman Dawisu ana turbunema Fuska Hhhhh oh Su o'o nagafa anfara Hararata su dai gwanda abasu Dawisun Lol)

Har cikin Bedroom dinta takaita zaunar da ita tayi to abude Fuskar haka mana ko Kunyar Ammin taki kikeyi ni matsayin Mamanki nake ba suruka ba bude mayafin da aka rufota tayi ma sha Allah lallai haka kwalliyar kika dameta da Hawaye to adaiyi Hakuri ai nanma Gida ne kinji tanayi tana Bubbuga bayanta saiga Wa'at Anyi Luf share mata Hawayen fuskarta tayi.

Suma sauran bangare guda aka ware musu wanda zasu zauna nan fa Ma'aikata suka fara shigowa da Abinci kala kala wanda aka tanada saboda su kaji kuwa ai ba'a Maganarsu saidai kowa yaci ya ture hhhh Uwaliya dik nacinta da cin Kaza saidata barta sabida yadda taji cikinta babu masaka tsinke Drinks kala kala masu shegen sanyi haka suka dinga Korawa kai kowa yasan ya shigo gidan masu abun ba yantaka haye ba arziki kota ina.
     ALLAH sarki Hajara randa aka kaita nata Gidan Mijin ta tuno yadda tsabar wulakanci kazarma kin bata akai wai karta sata gudawa yau gashi asanadin kanwarta taci Kaza harta Ginsheta.

Goge Hawayan Face dinta tayi jitai Andafata Nusaiba ce ta tsira mata ido Anty Hajara wanine ya dakeki girgiza kai tayi tare da kakalo Murmushi a'ah kawai natuna da wani abu ne.
    Nata wani ya dokeki muje na rama miki abun Dariya yabawa Hajara saidata dara kallekifa kamar abusheki kifadi shine xaki ramamin aiko da kindawo da karyayyan kashi yarinya.
    Haba aini dinnan dakika ganni bakaramin karfi ne da niba tsayama nabaki labarin wata yarinya Amakaranta data ke tsokanata wai bakwaini fashewa da Dariya Hajara tayi Bakwaini kota dauka a bakwainin aka haifoki.
    Ai wllh rana daya dana kamata nai mata Brush da kasa bata sake tsokanata ba kinga kuwa aini mekarfice tuni Hajara taji duka wata damuwar dake ranta tatafi saboda nishadin da Nusaiba ta bata kumatunta taja nagode 'Yar Kanwata.
    Ammi kayan Abinci ta shigo dashi dakanta ta dinga bawa Wa'at abaki da firtaki karba saidata nuna mata bataji dadi ba sannan ta dinga amsa dama yunwa takeji saigashi tadanci balefi saitakeji kamar Mamanta dan haka take mata duk sanda takicin abinci Hawayene ya ciko a idanunta sarai Ammi taga Hawayan basarwa tayi dan tanayin magana ta Tabbatar Kuka zata saka mata.
    Iyeee Lalllai wato me 'ya ALLAH sarki ninawa dan babu wanda ya nemesa bare ya bashi Abinci to kema basaikije ki lalubosa ba wancan gansamemen zan tsaya nema har nabashi Abinci to Laifine dan Ammin kara an hada dashi aikuwa Lefine ga sabuwa nasamu me zanyi da tsoho af haka kikace aishikenan muma da ranarmu bari anjima tayi Dariya suka saka gaba dayansu Mami tafice daga Room din tana Murmusawa.
                ......✍️✍️✍️
      
                  WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
                 PART TWO
Chapter 40

Saida kowa yaci yayi kat suka dan kwanta bayan sunyi Sallar La'asar kowa yadan huta kan anjima acigaba da Biki dan shagalin yanzuma aka fara.
      Wai ina Fareeda ne.
Fareeda jitakeyi kamar ta amayo da Zuciyar ta tsabar tashin hankalin da take ciki ko wanka tagagara yi haka Mom dinta tasata a gaba da Lallashi sai rusar kukan takaici take da bakin ciki dan taci Alwashin saita nadawa shegiya duka koma wacece zata shigo mata Gida.

Yanzu ke Fareeda banda baki da wayo kikwantar dakai kita Amsar kudi ahannunsa da sunan zaki Gyaran Biki kema amma dayake ke shashashace kin tsaya babu wan babu kani ba kudi kuma ga Kishayar dai zata shigo.
 
Cikin takaici Mom take kallonta ni wllh bani kika gado ba gaba daya baki da wayo dakin samu kin karkarbi kudin aida munje wajan wani Malami da akace aykinsa kamar yankan wuka yake da kafarta zata fita,gaba daya kin sauraran Mom tayi dan Maganganuntama sake bata mata rai sukeyi,na tabbatar duk wadda zai kawo bazata fiki kyau da diri ba babu Namijin da bazai gankiba be susuce ba.
    Samira ce datazo kawo musu abinci ta kunshe bakinta aba kamar dorinar ruwa shine za'a ce babu wanda bazai susuce akantaba saidai makaho wanda baya gani.

Hanbari Fareeda ta Kawo mata shegiya Munafuka ubamme kike jira kuma futa kibawa mutane waje tabe baki tayi oho niyau babu abunda zai batan rai acikin Farin ciki nake burina yacika za aiyomiki Kishiya.
    Ma'aikatan Gidan kowa yasa sabbin kayansa iri daya yayiwa Maza haka matamma iri daya ya yimusu.
      Bayan sallar Magari ba aka fara shirye shiryan tafiya Dinner kowa burinsa yafi kyau da daukar wanka 'yammata sai goge goge akeyi da fente fenten Face ankon wani Material sukai mai matukar kyau da tsari duk wadda yasa saidai Ma sha Allah.

Jidda da Safna iri daya akai musu su biyu see green ya matukar yimusu kyau.
     Tabarakahhu ahsanul khalikin sanda aka gama tsantsarawa Amarya kwalliya Les ne ajikinta me matukar kyauda tsada hannu da wuya sarkar Gold ce take walwali jikinta kamar anyi mata barin turare kamshi kawai ketashi.Cupy ne da Golding anyi mata wani dinki me matukar kyau da tsari an dauramata hed golding takalmi da jakarta suma Golding tafito fes da ita color din yayi matukar zama akan Fatarta da take Chocolate.
       Sai bayan sallar isha'i Motoci suka fara fakawa babu wanda zaice be samu Motaba duk gayyarsu kuwa kowa saida yasamu waje.

Jidda da Safna sune suka nace saida Amarya zasu tafi Mami ce ta korasu babu wadda zata shiga daga ita sai Mijinta haka suka tafi amma sunci Alwashin bazasu shiga wajanba saida Amarya.
      Mami ce taruko Hannunta dan tuni itama Ammi tayi gaba da tata tawagar na kawayanta taci uban gwagwgwaro kaida gani kasan uwar Ango ce.

Suna fita harabar Gidan mota dayace tai saura wata hadaddiyar Motace Fara kal Tayota Prius har daukar ido takeyi saida Mami ta kwankwasa Glass din aka zugeshi Ahankali Direba ne kawai agaban dan tuni AA ya kora abokansa babu wanda zai shiga Mota daga shi sai wife dinsa abar adanawa ce da boyewa yasha tsiya kuwa kafin sutafi su kyaleshi.
    
 Bayan Motar ta bude tasakata sannan ta rufe gaban Motar ta bude tashiga tare da rufewa,tunda tashiga kamshin Turaransa da nata suka hadu suka bada wata kala me dadin gaske kare masa kallo nai yasha shadda Golding kamar yadda tai wanka haka shima kusan kaya kala daya suka saka wani kallan kasa kasa yakeyi Mata.
         .......✍️✍️✍️

             WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
                   PART TWO
Chapter 41

Gyara zamansa ya sakeyi gaba daya bata san da Mutum amotar ba tadauka daga ita sai Mami abazata taji anriko Hannunta sosai ta razana harta bude baki zata kwalla ihu saurin toshe mata baki yayi tuni idanun Wa'at suka fito waje tsabar yadda ta tsorata kirjinta wani Mahaukacin bugu yakeyi cikin kunnan ta ya rada mata are you okay.

Shi azatansa intaji shine zata samu nutsuwa kokarin fizge Hannunta takeyi danta matsa daga Kusa dashi mam ya ruketa.
       Dole tagaji dankanta ta Hakura da kokarin kwacewar datakeyi fatanta kar Mami taganta kusa dashi bama tasan mesukeyi ba gaba daya hankalinta yana kan wayarta.

 Hada ido sukai ya kashe mata ido daya saurin saukar da kanta tayi dan wani kwarjini yake mata aduk Lokacin data kalleshi.
     Zoban hannunta yake wasa dashi sosai kunshin hannunta ya tafi dashi gawani tsabar Laushi da hannun yake dashi kamar hannun Jariri,hancinsa kawaii taji a wuyanta yana sakar mata mani zazzafan huci saurin matsawa tai yasake dawowa da ita wannan karan gaba daya ajikinsa ya dorata Lips dinta ya kalla yasha jambaki Maroon gawani shining da yakeyi gwanin burgewa.
      Azabazata taji bakinsa akan Lips dinta tamkar zai tsinke mata Lips haka taji gaba daya idanu awaje take kallonsa saidaya tabbatar yashanye ya saketa hakanan yaji yana kishin wasu kartin banza su kalle masa Lips din Mata kamar zatai Kuka tai kasa da kanta danjin take gaba daya bakinta ya soma wani radadi saboda wuyar da sukasha a hannun AA.
     Kwantar da Kansa yayi shikadai yasan abunda yake zagaye Jininsa sosai ya kwantowa kansa Likin dayake ta kokarin ganin ya jure da sauri da sauri yake sauke Numfashi Motace ta tsaya da sauri ta sauka ajikinsa jinya saketa Mami bata tsaya jiransu ba ta fice.
     Su Jidda ne suka bude murfin Motar sai asannan yaji antsaya da bemasan wainar da ake toyawa ba maka musu harara yayi batare da yace musu komai ba gefe suka koma suna muzurai.
     Saida yafara fita ya zagaya ya bude mata hannunta ya kama dan dole ta hakura jere suka taho abun sha'awa 'yammata ne da samari suka fito suka jeru alayi MC sai babatu yake ga Amrya da Ango nan tafe wakar Amarya aka saka gaba daya wadanda suke Hole din sun zuba idon ganin Amarya da Ango.

Kememe AA yaki sakinta kamar wadda zata gudu kai daga karshema kugunta ya riko bakaramin dacewa sukai da juna ba.
     Ammi jaka kawaii ta zuge tunda suka shigo ake musu ruwan liki har suka zauna inda aka tanadar musu,kisaki ranki mana kamar wadda akaiwa Auran dole abazata taji maganar tasa saurin kallonsa tayi saika rantse bashi yayi maganar ba zumburo baki tai gaba wani munafukin murmushi yayi koki Gyara bakinnan ko yanzu na gyara mikishi saurin maida bakin tayi dan juyowa tayi ta kalleshi dage mata gira yayi.
      Da sauri ta dukar da kanta aranta take tunanin dama yana Magana.MC ne yake neman Amarya da Ango fadi yake duk wanda ya riga dan uwansa tashi to kalarsa za'ahaifa daga daya zuwa uku ya kirga zumbur Wa'at ta mike gaba daya ihu akasa da tafi shikansa AA abun ya bashi Dariya saidata mike taji kunya ta Lullubeta saukowa sukai daga steps din tsakiyar fili suka shiga.
      Wakar Biki yayi Biki aka saki nanfa masu kara suka shigo anyi Liki Nera tayi Kuka awannan Dinner anci ansha masu guzurin Leda ji sukai har basason kamshin Nama sai wajan 11 akatashi daganan za'awuce kai Amarya.

Tuni Wa'at tafara Kuka jin wai wucewa za'ai da ita gogan yana ruke da hannunta Kokarin cusata amota yake shima ya shiga jiyayi atalle masa keya to rasa kunya beran tanka zakabamu ita koko kaizaka tafi da ita.
       Kallon rashin fahimta yakewa Mami to Mami nizan tafi da Matata mana rike baki tayi iyeee Lalllai yaran zamani to inhar baka bimu asannu ba daganan gida zamu wuce da ita matsani kaban waje kaje kanemi wata Motar badai wannan ba tureshi tayi ta fada Motar tuni dama kowa yashige Mota ja akai sukabar AA bude da baki.
     Dukan kafadarsa yayi kai Ango wannan kallonta inka kwantar da hankalinki ai gidanka za'akaita Harararsa yayi yawuceshi yanamai dariyar shakiyanci.Motar abonkansa ya shiga bakaramin haushi yaji ba da aka rabashi da Matarsa.
      🤔🤔🤔🤔Kaji Wani iyayi uhm Maza Kenan.
     Tunda Fareeda taji Ana rangada Guda tadora hannu aka ta fashe da Kuka jitake kamar ta cinnawa bangaran Wa'at wuta sabida yadda kishi yake azalzalar zuciyarta yau ita za'aiwa kishiya kamarta Babbar Yarinya itakam gaba daya ajinta ya fado yanzu kawayanta zasiyi mata Dariya da take cika bakin ba ita ba Kishiya wace yar iskace wannan itadai uwarta ta haifo mata masifa Fyace hanci tai ALLAH sarki Fareeda ashe kinasan AA haka.
      Hhhh To Fans kuyo Gayya azo ararrashi Fareeda.
       Inkikaranta kidaure kiyi comment sister.
        Taku Kulsoom Ismail Idris
          ..........✍️✍️✍️

        
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
                   PART TWO
Chapter 41

Gyara zamansa ya sakeyi gaba daya bata san da Mutum amotar ba tadauka daga ita sai Mami abazata taji anriko Hannunta sosai ta razana harta bude baki zata kwalla ihu saurin toshe mata baki yayi tuni idanun Wa'at suka fito waje tsabar yadda ta tsorata kirjinta wani Mahaukacin bugu yakeyi cikin kunnan ta ya rada mata are you okay.

Shi azatansa intaji shine zata samu nutsuwa kokarin fizge Hannunta takeyi danta matsa daga Kusa dashi mam ya ruketa.
       Dole tagaji dankanta ta Hakura da kokarin kwacewar datakeyi fatanta kar Mami taganta kusa dashi bama tasan mesukeyi ba gaba daya hankalinta yana kan wayarta.

 Hada ido sukai ya kashe mata ido daya saurin saukar da kanta tayi dan wani kwarjini yake mata aduk Lokacin data kalleshi.
     Zoban hannunta yake wasa dashi sosai kunshin hannunta ya tafi dashi gawani tsabar Laushi da hannun yake dashi kamar hannun Jariri,hancinsa kawaii taji a wuyanta yana sakar mata mani zazzafan huci saurin matsawa tai yasake dawowa da ita wannan karan gaba daya ajikinsa ya dorata Lips dinta ya kalla yasha jambaki Maroon gawani shining da yakeyi gwanin burgewa.
      Azabazata taji bakinsa akan Lips dinta tamkar zai tsinke mata Lips haka taji gaba daya idanu awaje take kallonsa saidaya tabbatar yashanye ya saketa hakanan yaji yana kishin wasu kartin banza su kalle masa Lips din Mata kamar zatai Kuka tai kasa da kanta danjin take gaba daya bakinta ya soma wani radadi saboda wuyar da sukasha a hannun AA.
     Kwantar da Kansa yayi shikadai yasan abunda yake zagaye Jininsa sosai ya kwantowa kansa Likin dayake ta kokarin ganin ya jure da sauri da sauri yake sauke Numfashi Motace ta tsaya da sauri ta sauka ajikinsa jinya saketa Mami bata tsaya jiransu ba ta fice.
     Su Jidda ne suka bude murfin Motar sai asannan yaji antsaya da bemasan wainar da ake toyawa ba maka musu harara yayi batare da yace musu komai ba gefe suka koma suna muzurai.
     Saida yafara fita ya zagaya ya bude mata hannunta ya kama dan dole ta hakura jere suka taho abun sha'awa 'yammata ne da samari suka fito suka jeru alayi MC sai babatu yake ga Amrya da Ango nan tafe wakar Amarya aka saka gaba daya wadanda suke Hole din sun zuba idon ganin Amarya da Ango.

Kememe AA yaki sakinta kamar wadda zata gudu kai daga karshema kugunta ya riko bakaramin dacewa sukai da juna ba.
     Ammi jaka kawaii ta zuge tunda suka shigo ake musu ruwan liki har suka zauna inda aka tanadar musu,kisaki ranki mana kamar wadda akaiwa Auran dole abazata taji maganar tasa saurin kallonsa tayi saika rantse bashi yayi maganar ba zumburo baki tai gaba wani munafukin murmushi yayi koki Gyara bakinnan ko yanzu na gyara mikishi saurin maida bakin tayi dan juyowa tayi ta kalleshi dage mata gira yayi.
      Da sauri ta dukar da kanta aranta take tunanin dama yana Magana.MC ne yake neman Amarya da Ango fadi yake duk wanda ya riga dan uwansa tashi to kalarsa za'ahaifa daga daya zuwa uku ya kirga zumbur Wa'at ta mike gaba daya ihu akasa da tafi shikansa AA abun ya bashi Dariya saidata mike taji kunya ta Lullubeta saukowa sukai daga steps din tsakiyar fili suka shiga.
      Wakar Biki yayi Biki aka saki nanfa masu kara suka shigo anyi Liki Nera tayi Kuka awannan Dinner anci ansha masu guzurin Leda ji sukai har basason kamshin Nama sai wajan 11 akatashi daganan za'awuce kai Amarya.

Tuni Wa'at tafara Kuka jin wai wucewa za'ai da ita gogan yana ruke da hannunta Kokarin cusata amota yake shima ya shiga jiyayi atalle masa keya to rasa kunya beran tanka zakabamu ita koko kaizaka tafi da ita.
       Kallon rashin fahimta yakewa Mami to Mami nizan tafi da Matata mana rike baki tayi iyeee Lalllai yaran zamani to inhar baka bimu asannu ba daganan gida zamu wuce da ita matsani kaban waje kaje kanemi wata Motar badai wannan ba tureshi tayi ta fada Motar tuni dama kowa yashige Mota ja akai sukabar AA bude da baki.
     Dukan kafadarsa yayi kai Ango wannan kallonta inka kwantar da hankalinki ai gidanka za'akaita Harararsa yayi yawuceshi yanamai dariyar shakiyanci.Motar abonkansa ya shiga bakaramin haushi yaji ba da aka rabashi da Matarsa.
      🤔🤔🤔🤔Kaji Wani iyayi uhm Maza Kenan.
     Tunda Fareeda taji Ana rangada Guda tadora hannu aka ta fashe da Kuka jitake kamar ta cinnawa bangaran Wa'at wuta sabida yadda kishi yake azalzalar zuciyarta yau ita za'aiwa kishiya kamarta Babbar Yarinya itakam gaba daya ajinta ya fado yanzu kawayanta zasiyi mata Dariya da take cika bakin ba ita ba Kishiya wace yar iskace wannan itadai uwarta ta haifo mata masifa Fyace hanci tai ALLAH sarki Fareeda ashe kinasan AA haka.
      Hhhh To Fans kuyo Gayya azo ararrashi Fareeda.
       Inkikaranta kidaure kiyi comment sister.
        Taku Kulsoom Ismail Idris
          ..........✍️✍️✍️  
       WA'AT 
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
           PART TWO
Chapter 42
   
        Ankaita bangaran Fareeda dan abata amana bugun duniya taki bude kofarta haka aka gaji aka kyaleta cikin jin haushi Marwa tace ku kyaleta tunda anfita hakkinta bata budeba ita taga duhu.
      
  PART din WA'AT suka wuce saida Mami tasa tai Addu'a sannan tashiga da kafar dama gaba daya dakunanta ba karamin haduwa sukai ba kana shiga wani kamshi medadi ke dukan hancinka ga sanyin AC me sanyaya rai dasa nutsuwa a zuci,atsayar Bed Mami ta ajiyeta bawani dadewa sukaiba saida tasake yimata Nasiha itama Umma ta kara yimata fada dajan kunne ta zauna da kowa lpy.
      Da suka tashi tafiya Umma tarike gam tana Kuka dan ita take gani amatsayin Mamanta sai Inna data riketa gam dakyar aka samu ta cika su haka su Jidda sai matsar kwallah akeyi sun mata Alkawarin zasu dawo gobe kafin su wuce dan agoban zasu koma Gida.

Tsuru tayi bayan sun tafi gaba daya idanunta ya kumbura shikadai ya shigo dan cayayi babu wanda zai biyosa shima zai iya siyan bakinsa da kansa to dan iska muma muna da matannan bamu tafi wajansu haka suka dinga barkwanci.
         Sai daya rufe ko ina yayi Addu'a dakin Fareeda ya fara zuwa amma kememe taki bude kofar tafiya yayi yarabu da ita da sallama abakinsa ya shiga dakin Amarya Wa'at dakyar ta amsa saboda Kukan datake haryanzu, tsam yayi yana kallonta sai sheshshekar Kuka takeyi lallai Yarinyar nan.
     
Ajiye ledojin Hannunsa yayi tare da cire agogonsa da hularsa zama yayi agefen bed din yana kallonta zaburatai ta koma baya kamar wadda taga Dodo,ko kidaina wannan kukan ko yanzu nayi maganinki tsit tai dan yanzu sosai takejin tsoron sa dan har jikinta ya soma rawa daga jinsa adakinta.
      Mayafin dayake kanta ya yaye saida zuciyar sa tabuga gani yayi kamar tasake kyau datai Kukan Baby face dinta saita sake fitowa da Yarintar ta,runtse idanunta tayi dan bataso su hada ido wata kunyarsa takeji zare Mayafin yayi ya ajiye agefe 
          
Sata yayi agaba yana kallo hakan kadai Nishadi yake bashi.
    Jekiyi Alwala cikin rawar murya take fadin nayi sallah eh nasan kinyi jekiyi daganan kiyi wanka sannan ki daura Alwala to kawai tace ta sauka a bed din binta yayi da kallo yana ayyana abubuwa da dama akanta.

Tashi yayi ya fita bedroom dinsa ya fada saida yayi wanka sosai yayi shafe shefe kamar wani Mace ya feffesa Turaruka jallabiya fara kar ya dauko aledarta ya bare saka sannan yaja kofar da daddumarsa a hannu.
     Tuni tafito kayan jikinta ta mayar bece mata komai ba ya shimfida abun sallah wani karamin akwati ta bude taciro hijab dinta sallah ya jasu raka'a Biyu sosai yayi musu Addu'a tare da dafa kanta yayi mata Addu'a tayi Mamakin yadda ya san Addini sosai bata dauka yasani haka ba saitaji ya burgeta dan tanason Mutum me Addini.
       Suna shafa Addu'ar ya janyo Ledar gasassun kajin daya shigo da ita sai tashin kamshi sukeyi Kitchen ya shiga plate ya dauko da Knife saidaya zare kashin jiki wanda yasan zasu iya cinyewa ya turamata gabanta eat saurin girgiza kai tayi nakoshi nade hannun rigarsa yayi bazato taji yayi sama da ita bakaramin razana tayi ba saurin kankamesa tayi danjin yadda take barazanar fadowa.
      
 Dariya ta bashi amma ya gimtse akan cinyarsa ya dorata tuni Wa'at aka fara muzurai da zare ido dauko tsoka yayi ya nufo bakinta dashi kallon fuskarsa tayi babu alamun fara'a dan tabbas zai iya danneta ya dura mata dan dole tadinga amsa yanaci yana bata saida ya tabbatar ta koshi sannan ya kyaleta shima yaci yacika cikinsa.
     Fresh Milk me sanyi ya tsiyayo a cup ya samata abaki saidata sha da yawa ya kyaleta ya shanye ragowar.
         ........✍️✍️✍️✍️
        WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
           PART TWO
Chapter 43
  
Jeki brush tashitai simi simi kanta futo ya dauko wasu sleeping dress masu azabar kyau amma dasu da babu duk dayane farare ne kal turus tatsaya hango kayan datai akan Bed dinta da sauri ta karasa ta daga kayan da saurin sakin su tai dan  baza ta iya kallon suba sukansu kayan kallonsu abun kunya ne, bed din ta haye tana hamdala daya tafi dakinsa duk ya takura mata dama bargo ta jawo tarufe har kanta ko minti biyu batai da kwanciyaba taji ya bude kofar dakin ya shigo.
    
Kayan da ya'aje mata ya gansu yashe akasa girgiza kai yayi zakiga tsiya kuwa jitai an yayeta gaba daya bargon data rufa bawata magana ya tada ita zaune kici kicin zuge mata zip din rigarta yakeyi ta rike rigar tare da fashewa da Kuka tsayawa yai yana kallonta.

Ungo matukar bakya son nasaka miki da kaina kin amsa tai ganin zata batamai lokaci damka daya yayi mata takasa kwacewa saida yatabbatar ya gama samata kayan sannan yasake ta gaba daya shiyasan meyakeji ajikinsa ganin kyakykyawar surarta data gigita shi yafita daga hayyacinsa batare daya shiryawa hakanba.
    Ganin al-amarin yafi karfin ganina da tunanina da gudu nayo waje naja musu kofa asuba tagari  Amarya da Ango.
       Karfe 8 banzame ko ina ba sai dakin Amarya WA'AT gaba daya idanun nan sunkara fici fici AA nazaune dirshan yana aikin Lallashi da sanya mata Albarka sosai da sosai dan shikadai yasan irin ni'imar da ALLAH ya mallaka masa dole yayiwa ALLAH godiya daya azurtashi da samun mace tagari aiko iyayanta sunsha Addu'a da ita kanta.
    
Hhhhh kyauta kuwa ajiya har Ammi yace yabata kyautarta sai yanzu in wani abu yafado mata arai yake bata Dariya da kuma Kunya shida Kansa yasake silleta yayi mata wanka sosai take zuba shagwaba dakyar ta yadda bakaramin yaki yayi da zuciyarsa ba wajan rabuwa da ita Amma yana matukar jin tausayin ta danta dirzu ahannunsa bana wasa ba gaba daya kasa control din kansa yayi.
    Kai awannan rana ya dasa soyayyarsa me tsayawa arai acikin zuciyarta lokaci daya taji sonsa da kaunarsa ya mamaye dukkan zuciyarta saboda yadda yake Nuna tausayawarsa agareta da tattalinta.

Kichin Yashiga da kansa ya hada musu break sai da tace ya batta tayi amma fir yaki yadda tazauna ta huta kawai yace mata.
    
    Saida sukai kat sannan yaja hannunta suka nufi part din Fareeda tana zauna a parlour gaba dayanta a hargitse take danda alama bata runtsa ba.Sam bataji shigowarsu ba sai murya taji Anty ina kwana afirgice ta juyo saida Numfashinta ya kusa daukewa ganin Yarinyar dayaje ya dauko mata amatsayin Kishiyarta akalla wannan zata bata shekaru goma sha Biyar yarinya ce sharaf gata kamar diyar Larabawa duka acinkin minti biyu tayi wannan lissafin.
    
Bakiji ana gaidake ba juyo da kallonta tayi kansa hararar sa take kamar idanunta zasu fado harwani yaji yaji idanunta ke mata da ban kwana lpy ba zaku ganni Mtswww taja tsaki kuma zammuku gargadi na karshe karka sake dauko min wannan mekama da tsinken ashanar kazo min da ita bana bukatar ganinta hasalima natsaneta Wallhi.
    
Murmushi ya saki yana shafa gemunsa Kusa da ita ya matsa kamar abun arziki zai gaya mata daidai kunnan ta yakawo bakinsa.
    Uhm kingako tsinken ashana jiya ALLAH kadai yasan inda takaini na azama kinjiyo ihuna ashe ALLAH be jiyar dakeba kinsan yan cas cas sunfi abun bayarwa, bakudi zasu baka hakkinka sungaji arziki ba yan taka haye bane.

Sumana uku jiya ina farkowa dan koda wasa ban taba jina a irin wannan Duniyar ba kinsan akwai mata akwai muna mata to wannan cikakkiyar macece lambunta cike da niima da koramu.
 
Dagowa yayi fuskarsa dauke da Murmushin mugunta to uwar gida munbarki lpy tunda bakison ziyarar bana je nadora kinsan kogin da baya kafewa ba'a gajiyawa dashi da amfita ake sakejin marmarin kara shansa.
    Kada mata hannu yayi tare dayi mata byeee yakama hannun Matarsa sukai gaba baki sake tabishi da kallo tana tantance kalamansa daya bayan daya saidata gano bakin zaren tama rasa wane kalar tunani zatayi gaba daya kanta ya cushe tarasa madafa tana ji tana gani Mijinta yaja hannun wata Jaririya sunyi gaba.
    Cikin sanyin jiki tabishi gaba daya jikinta yayi sanyi ganin yadda Matar gidan tai mata  dagani saita hada da hakuri da juriyar zama da kowa agidan.Zata jure kamar yadda Mamarta ta jure dukkan wani kalubale.

Lura da hakan yasa yafara bata labarai da suke saka Nishadi saigashi ta ware tana ta Dariya bakaramin farin ciki yayi ba ganin Dariyarta duk da bayason magana metsayi haka ya daure yana sata Dariyar saidaya tabbatar ta ware sannan ya kyaleta.
    
Sai azahar su Jidda suka zo mata aiko tasha tsokana sunsha fira sosai ta nuna farin cikin ganinsu saidaga baya su Umma sukazo tare da Uwaliya dasu Nusaiba sunyi Farin ciki da inda Yayar tasu zata zauna saida sukai Girki suka sawa AA nashi sannan sukaci suka sake gyaramata duk abunda sukaga yana bukatar gyara.
    Sanda sukazo tafiya nan ma saidatasha Kuka dakyar ta bari suka tafi haka su Nusaiba sunyi Kukan rabuwa da yayarsu.
     Shatara ta arziki AA ya bisu da shi, haka Ammi kayan Biki babu abunda bata hada musu ba aka rabu cikin mutunci da mutuntawa leda guda ta cikawa Uwaliya da Naman kaji dan batasan ta ganta sanda take kokawar dura naman kaza aleda ba shiyasa tadau aniyar zata bata sosai kuwa Uwaliya ta dinga Godiya ko banza batazo ABUJA tatafi hakaba tasan tazo
             ........✍️✍️✍️
    
                         WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
                  PART TWO
    Chapter 44
    
    Soyayya fa kowa ya shaida ana shanta agidan sosai su Samira suke debe mata kewa tadaukesu kamar 'yan uwanta tuni AA yafara ajiye tumbi yakara zama wani babba kama larsa tasake futowa.

Fareeda tayi haukan babu wanda ya kulata haka Wa'at gaba daya bata shiga sabgarta danta lura kamar kanta da motsi tuni itama Wa'at takara fresh fatarta tasake gogewa harwata yar kiba tayi.
    Kullum tana kiran Mama da Umma da sauran yan uwanta susha hira dan credit a phone dinta baya yankewa tana yawan zuwa Gidan Ammi sun kara shakuwa da Ammi dan bata dauketa matsayin suruka ba a uwa ta dauketa.

Haka su Marwanah da Safnah yanzu hankali kwance suke shiga Gidan yayanna su.
    Mami ma ba'a barta abaya ba tana kiranta dasake bata wasu sirri kan na kula da Miji da yadda zata sake kameshi kam ahannunta aiko AA yasake matowa akanta ga tsafta biyayya iya Girki girmama danginsa da takeyi da daukar Mahaifiyarsa kamar tata saiyaji sonta kullum sake ninkuwa yake azuciyarsa.
    Kullum PART dinta tashin kamshi zaka jiyo hatta yaransa harso suke suci Abincinta tunda taiwa AA zobo da kunun aya ya makale mata kullum saitayi masa yayita santi.
    Shagwaba kuwa sai abunda tai gaba hakanan zata samai rigimar saiya fita da ita yawo haka bayadda zaiyi inta samai Rigima saidai inyayi maganinta da salon karatunsa da haryanzu takasa Gogewa tazama kamarsa amma tana kokartawa danta tabbatar da Mijinnata jarumine.
    Waiya Mutanan Zariya ne bamu leka.
    Umma tana Zaune tana tsintar shinkafa Mama na wanke kayanta sunata hirar su gwanin burgewa kamar basune abaya akai zaman doya da manja ba, yanzu basu da wata damuwa saita Mijinsu da saidai gyaran ALLAH hirar Wa'at kawai sukeyi Umma ke Fadin ai wllh yakamata Mamansu kije kigano dakin 'Yata bakiga yadda Gidan nan yatafi dani ba ga Mijinta dan Mutunci kaf dangin su babu wani me aibu.
    Murmushi Mama tayi to banda abinki Umman su aikin wakilceni ko zanje ba yanzu ba kefa andena irin wannan kunyar ta dan fari nasan kinason zuwa kawai ba kyaso muganene Dariya tayi kodaya zanje amma sainan gaba.
    Zainab ce daga daki take fadin Mama zammiki rakiya dan ALLAH kije dani Zubaida ce tai caraf kinma isa babu inda zakije da ita dani zaki.
    To nikuma ainice Babba dani yakamata kije Mama inji Hajara oh toke Hajara keda zaki koma Gidan Mijinki kema inake ina bimmu wani waje,bata Fuskatai nidai Mama bazan koma ba dakuwa Mama tayi mata ungo naki nan jiyama angayamin dayazo rashin kunyar da kikaimasa bara nagama wankinnan zankirashi da kaina yazo ina nemansa.
    Fashewa da Kuka Hajara tai Mama kefa kikamin Alkawari inhar banaso baza'a maidani ba to yanzu na janye magana ta sokike musa miki ido shiyace bazai sakekiba yayi Nadama kinki yafe masa kema Ummansu kisa baki kinki.
    Toni mene nawa aciki bayadda banyi da itaba kinsan Hajara da shegiyar kafiya da taurin kai nidai zan kyaleki da ita naga tafijin maganarki cewar Umma.
    Aiko zanyi Maganinta ALLAH ya temakeki yaro yayi Nadama har Uwarsa tabada hakuri ke kinki hakura gaya mata yanzu Ubanta wayataba bawa hakuri agidannan kome zema bazai baka hakuri ba ALLAH ya kyauta Mama tace tunda aka sako zancan Appa taji hirar tafita aranta.

Cikin Kuka take fadin wllh Mama dan bakusa irin abunda Kamal yamin bane har tsallan kwado yake sani yasani kamun kunne da bulalarsa yake zama dana dan tsaya zai zugakin kuga bayana yadda yayi shatin bulalai.Mama zata bude baki kenan taga shigowarsa ta hadiye maganar ta.

    Sallama yayi kamar Wanda akasa dole kowa gimtse fuska yayi boll yayi da wata buta daya ganta a bakin hanya yana muzurai dan yau beyi ciniki a kasuwa ba shine ya dawo rai bace.
    Umma tabude baki kenan zatai magana wasu dika dikan mata su kusan goma suka fara jerin gwanon shigowa gidan kowacce fuska tadau mai kaida ganinsu kaga cikakkun yan bariki cimgom ne abakinsu kas kas suke tauna nanfa aka fara kallon Kallo tsakaninsu da Jama'ar Gidan cikin ya mutsa Fuska dayar tabude baki tare da Fadin.
    To Ana wata ga wata .
    Suwanene wadannan Matan mesukazo nema  fuska ahade ba annuri.
    Toma wai wajanwa sukazo Kubiyo ni Fans danjin yadda zata kaya.
    Comment dinku nasake karfafamin guiwa.
    Kidaure Kiyi comment Sister.
    Taku Mrs BABA BELLO
            .......✍️✍️✍️

              WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat 
             PART TWO
Chapter 45
     
Kallon tara saura kwata sukewa jama'ar Gidan kallan kaskanci da rashin mutunci wata ce daga cikinsu ta dawo da dan kwalinta gaban goshi,cikin yamutsa Fuska take fadin wacece Salamatu kuma wane Kabiru,cikin kufula Umma kefadin yazaku shigowa mutane Gida ba sallama kamar 'Yayan arna.

Ke!!! dakata karki kuskura dan wllh yanzu zamusa gajerun wanduna miyi miki dukan kawo wuka.
     Tambaya mukai muna bukatar amsa amma da alama Kece Salamatu kai kuma ko ba'a fada ba nasan kaine Kabiru tunda kayi kama da dan Akuyan danka.
      Mama ce da abun ya isheta kallaonsu tai dan da alamu kome zai fito daga bakinsu ba Alkhairi bane,bayin ALLAH kusanar damu meke tafe daku dan ALLAH amma kunsamu aduhu in har bakui mana bayani ba tayaya zamugane meyake faruwa in babu damuwa kugaya mana.
    Wata figigiya ce acikinsu taka da baki tare da fadin tunda kince ALLAH bamu sanar dake abunda ya kawo mu tabbas ba Alkhairi ya kawo mu gidan nan ba hasali munzo ne komu koku dan hukumace zata rabamu abunfa yasake daure musu kai.

Appa ya gama kuluwa in bazaku fada ba kuficemun agida.
    Ahayye nanaye wata acikinsu tafada tare da tafa hannayanta ina Gidan yake wannan akurkin kajin kake kira da Gida to bakomai muka kawo muku ba sai results din da danka ya bari gasunan keyar wani yaro dayake rakube bazai haura 3yers ba suka tunkudo shi sai rarraba ido yake toga Kabiru nan watace acikinsu ta kyalkyale da Dariya kumafa yayi kama da kakannasa.
    Yaron suka kurawa ido abun Mamaki Appa ganinsa yayi kamar sanda Ameer yake yaro sak babu abunda ya rabasu kirjinsane yake wani mahaukacin bugu haka duk wanda yake wajan ya shiga shork da ganin eannan yaron.

Ke Lantana kwanto musu Salamatu aiko kamar jira takeyi ta tsigota daga baya ta dangware ta akasa Yarinyar ko ta fashe da Kuka bazata haura shekaru Biyu ba daganinta kodai ba'a yayeta ba ko anyayeta kwanannan kuwa.
 
Yarinyar sukabi da Kallo kamar sokaye haka suke bin Yarinyar dake tsandara Kuka gaba daya hannun Umma akan kirjinta yake jin numfashinta na barazanar daukewa.

Mufa bamu gane abunda kuke nufiba suwane wadannan yaran cewar Mama da gaba daya taji kanta yayi mata nauyi fatanta kar abunda take zato ya zama gaske,bara nai muku bayani tunda haryanzu kanku baya kawo wuta da alama nakarshen aji kuke zuwa a makaranta.
    Shewa suka sa suka tafa,basai sun taba zaman ajin bama kinsan da alama suma tsofaffin ansha fama.

Wannan yaron da kuke gani dumamai duka tai abaya jikankune wato Kabiru danku Ameer daya tafi yawon ta zubar kanwarmu tana zamanta  a lagos tana saida Abinci yadinga lallabawa yanai mata wayo saidaya dirka mata ciki,to mukuma a danginmmu wannan ba wani abun kunya bane dan an kara samun jari bayan ta haihu muka jamai kunne kan karya sake shinshina mana ajiya yace ya yadda.
    Wane Suna za'asawa Yaro yace Kabiru dan yana son yayiwa dagus dinsa takwara kunji daya kenan.
    Bayan shekara daya kwatsam muka sake ganin Zabba'u da ciki saida muka matsata tasanar damu cikin na shegen dankane wato Ameer muka dau alwashin matukar ta haihu zamudau mataki akansa wata Tara tahaifi yarta Mace Nanma muka tambayeshi wane suna za'asaka yace Salamatu sunan tsohuwarsa kenan muka rangada mata Salamatu aka yanka mata katon ragonta munsha shagali.
   Namu tabbatar da cewa danku dan bala'i bane sai randa muka farga da ciki na Uku ajikin Zabba'u  shiyasa muka kawo muku wannan kwa rage mana wahala madauki nauyin na cikinta tunda anyi anyi surabu sunki.
    Cak kowa ya tsaya dan bugun zuciyoyinsu tsayawa sukai gaba daya jinin jikinsu ya daskare Appa jiyayi kansa yana wata irin hajijiya kallon Kabiru da Salamatu kawai yakeyi dasuka fara wasansu Hankali kwance duhu ne ya mamaye idanunsa dif yadaina gane a Duniya yake Ko Mafarki yakeyi wane irin mummunan Mafarkine wannan.
    Faduwarsa kawai sukàji cikin azama su Hajara da Nusaiba sukai kansa ALLAH sarki ance da da Mahaifi sai ALLAH tuni hankalinsu yatashi ganin Affa baya ko motsi dukkan wata jijiya dake jikinsa tadaina harbawa.

Sai Lokacin Umma data tafi dogon suman tsaye tadawo hayyacinta wani tukukin Bala'i takeji ya tsaya mata azuciya gaba daya bakinta ya gauraye dawani azabar daci tuni idanunta sukai jajawur itakadai tasan yadda zuciyarta ke suya.
    Sam bata hayya cinta Zubaida ce ta girgiza Umma ganin kamar tazauce idanunta yana kan su Kabir takasa dauke idanunta daga kansu dukkan wani sako daya kai ziyara kwakwalwarta nanata mata Kabir da Salame jikokinku shine abinda takeji kawai yana amsa kuwwa akunannata.
    😭😭😭Gaskiya Umma na Matukar Tausaya miki wannan lamari beyi dadi ba.
    Fans kubiyoni danjin yadda zata Kaya.
    Inkin karanta Kidaure Kiyi Comment Sister.
           Mrs Baba Bello Abubakar
               .......✍️✍️✍️
    
              WA'AT
    By KULSOOM ISAMA'IL
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
               PART TWO
    Chapter 46
    
    Mama cikin razani tayi kan Affa ruwa suka debo an kuzamai amma shiru kake ji wai Malam yaci shirwa daki ta fada da sauri Number Malam takira cikin Kuka tashaida masa ga Kabiru nan kwance baya ko Numfashi ALLAH sarki iyaye dan danan hankalinsa ya tashi haka yace gashinan zuwa,tare da wansa da kannan sa suka taho dayake akwai masu Mota acikinsu basubi ba'asin komaiba suka kinki mesa suka sashi amota.
    Wani karamin asibiti suka fara kaishi Lamarin yafi karfinsu dan duk wata dabara sunyi babu wani cigaba dole suka daukeshi suka tafi shika dan danan aka karbeshi cikin gaggawa nan suka fara bashi agaji bakaramar  wahala suka shaba kafinsu samo Numfashinsa dakyar Oxygen suka saka masa shine yake taimaka masa wajan shakar Numfashi.
    Acan Gida kuwa Dangin Zabba'u ko ajikinsu haka sukai ficewarsu sukabar su Kabiru azaune a tsakar Gidan dagasu sai kayan jikin su tuni salamatu takwara ta barka kashi irin kashin hakorinnan takeyi.

Mama jijjiga Umma tayi ganin gaba daya idanunta yayo waje kamar wadda aka shake sam batajin Numfashinta yana fita yadda ya kamata Kuka suke gaba dayansu ganin irin halin da Umma keciki ana haka Umar yashigo da mamaki yake kallonsu ganin kowannensu Kuka yakeyi sun zagaye Umma wadda zuwa yanzu tafara wani irin haki na tashin hankali, yauwa Umar zoka taimaka kasamo mana Napep mukaita asibiti.
    Bece komaiba ganin halin da take ciki da sauri yayi waje ALLAH yasa yana fita wani zai juya ya sauke fasinja,shida Mama suka hadu suka ciccibo Umma datai wani azabar nauyi saboda gaba daya jikinta ya saki tare da Umar da Hajara suka tafi akabar su Zainab agida tare dasu Kabir takwara cikin jin tsanar yaran babu wanda ya kallesu acikinsu anan suka barsu suka shige daki zuciya badadi.
    Wani Asibiti suka kai Umma ankarbeta cikin Gaggawa jininta ne yayi mummunar hawa danda ba'akawota Asibiti da wuri ba da ansami gagaruwar matsala inda ace tafadi daga tsaye tabbas barin Jikinta zai iya shanyewa anmata taimakon Gaggawa dakyar aka shawo kan al amarin.
    Mamace tazauna kusa da ita tazabga tagumi gaba daya Rayuwar nan tsoro take bata yanzu gashi gaba daya suna kwance Gadon Asibiti sanadin da Namijin daya dinga fifitawa akan Matan da ALLAH ya bashi.
     Umma ce tabude idanunta bayan baccin da tasha sosai tunawa da abun da yafaru taji zuciyarta tayi wani irin rauni Lumshe idanunta tayi sai awannan Lokacin wasu zafafan Hawaye suka fara tsere a Fuskarta Mama sam bata hanata ba dan tasan Kukan shine zesa taji sanyin Zuciyarta saidatai Kuka ma ishi sannan Mama tadinga bata baki akan yadda da Kaddarar khairan au sharran.
    Kedin Jaruma ce aduk shekarun da kika dauka kina fuskantar bakin ciki da bacin rai daga garemu amma hakan betaba kwantar dake ba,hakika nasan munzalince ki ALLAH kuma zaimiki sakayya akowane irin Lokaci to ga ranar tazo ranar da muka dade muna shuka tsiyarmu batare da tunanin akwai ranar saka mako ba 
    Hannayan Mama takama Aysha nasan na cutar dake abaya inaso kidubi girman ALLAH kiyafemin na tabbata Alhakin kima bazai taba barina ba nashiga na fita na hanaki jindadin zama Gidan Mijinki duk da shima ya bada gudummawa wajan faruwar hakan amma tuni nayi Nadama wllh ga masifunan inata ganinsu daga wannan sai wannan Astagafirullah natuba ALLAH ka yafemin kurara kuraina.
     
Sake barkewa tai da kuka dana sani fal zuciyarta jitake inama bata haifi da Namijin ko daya ba.
    
 "Sake rike hannunta Mama tayi ni wllh Yaya bantaba rikonki araina ba wllh bazan taba kullatar kiba saboda anyimin abunda yafi naki shiyasa sam banajin zafin naki duk wadda aka Aurarwa Miji dole zatai Kishinsa"
     Share Hawayan da yake kwararo mata tayi da ace nasan wanene Mijinki dako jawoni akai aka kawoni wllh saina gudu dan ba Mijin Aure bane shine bana tunanin zan iya yafe masa abubuwan da yayi min asanadinsa nakamu da Hawanjini da saura kadan na nakasa ALLAH ya temakeni ya dubeni yakawo min komai cikin sauki danabi abunda Likita ya shimfidamin.
   
 "Kuri Umma tayi tana kallonta dama kina da hawanjini amma bamu taba sani ba"? Murmushi Mama tayi to aisanin naku baida amfani tunda ba magancemin zakuiba na tabbatar da kunji awannan Lokacin saina shiga bacin rai mara misaltuwa"
      Shiyasa na rike matsalata dagani sai iyayena hatta su Malam basu san da hakanba.
            ........✍️✍️✍️✍️

           WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
          PART TWO
Chapter 47

"Umma ke ayyanawa azuciyarta Lallai sun zalinci Mama cuta metarin yawa dole ALLAH ya Jarrabesu da wannan Lukutar masifa"
      Nidai ina neman Alfarmar kiyafemin dukkan abunda nayi miki da wanda nasani da wanda bansaniba kiyimin afuwa nayafe miki Duniya da Lahira ALLAH ya yafemu baki daya cikin jindadi Umma take zabga godiya.
      🤣🤣🤣Kamar wadda Kamal yayi mata kyautar Kujerar Hajji lol 🏃🏃🏃
       
 "Umar da Yayi sakare yana jinsu gaba daya sun daure masa kai,Mama yake duba wai meyake faruwa gaba daya kunsani aduhu kufitar dani sam nagaza gane inda maganarku ta dosa.

Mama ce ta bashi Labarin abunda yake faruwa sosai abun ya dakeshi dama Ameer abunda yakeyi acan kenan bayan shaye shayen harda bin mata duk yakeyi"
       Yanzu wane Asibitin aka kai Appa ina zamu sani cewar Umma cikin jin haushin Affa,wayarsa ya ciro daga Aljihu bugu daya Malam ya dauka bayan ya gaidasa yake tambayar inda aka kai Affan gaya masa asibitin yayi yace gashinan zuwa sun kawo Umma Asibiti salati Malam ya saki waini Umaru meyake faruwane zanzo yanzu Malam zakuji komai In sha ALLAH.
      
Doctor ne ya bawa su Umma sallama da sharadi tadaina sa damuwa aranta saida ya rakasu hargida sannan ya juya yatafi inda aka kwantar da Affa.
     Suna shiga da yaran sukaci karo Umma jitai kamar an buga mata guduma atsakiyar ka Fuuuu ta wuce su dan ko ganinsu tatsaniyi sunyi dama dama dasu duk sun bata jikinsu da ruwa da kasa karamar tayi Kuka harta gaji babu wanda ya kalleta.

Kaida ganinsu kasan yumwa sukeji tausayi suka bawa Mama aiba su da laifi dan babu ruwansu da asansune bata wannan hanyar za'a samar dasuba.
     Karamar ce tararrafo inda Mama take tana daga mata hannu alamun ta dauketa Murmushi ta kakalo dan ita kanta taga yaran bugun zuciyar ta karuwa yakeyi kamarsu daya da Affa kaiko 'Yayansa basu yo kamarsa kamar yadda wadannan yaran sukayo ba ALLAH kenan.

Nusaiba ta kwalawa kira futowa tai da sauri wadannan yaran da kuka barsu anan fa kuka shige daki Hajara ta kwalawa kira futowa sukai dukansu.
    Da kuka barsu anan suba mutane bane kenan aiba lefin su zaku gani ba basu da Laifi kudaukesu kuyi musu wanka yanzunnan badan sunso ba suka yimusu wanka dakin Mama suka kaisu dan suna shiga dakin Umma ta buga musu wata Uwar tsawa saida yaran suka firgita suka fashe da Kuka har huci Umma keyi dan bata kaunar ganin yaran nan kokadan wllh.
    Mama batace komai ba ta karbesu babban ta zubawa Abincin karamar bazata iya ci da kanta ba zama tayi dakanta tabata saida ta tabbatar sun koshi sannan ta kyalesu matsalar basu da kayan sawa dan kwalinta ta daddaura musu tasa Hafsa ta wanke musu kayan su ta shanya insun bushe tasaka musu.
    Yara sunji ciki ya dauka tuni suka hau Bacci Mama kura musu idanu tayi tana sake jin tsoron Rayuwar Duniyar nan.
   
 Sosai Wannan Family suka shiga cikin tsananin damuwa da wannan abu daya samesu ga Affa yau tsahon kwana Uku kenan besan inda kansa yake ba duka yaran sunzo dubashi babu wanda be tausaya maiba haka su Mama sunzo ita da Umma lallai merai ba abakin komai yake ba gaba daya Na'urorine ajikinsa.
    Duk yadda su Malam kejin zafinsa saida suka tausaya masa 'yan uwansa Maza ne awajansa dan Mama sam bata bada fuskarma ace ta zauna tayi jinyarsa ba bataji zata iya saidai suzo su koma.
    Wa'at sam kin gaya mata sukai dan kar hankalinta ya tashi dan akwaita da tausayi yanxu ne zata daga hankalinta saita zo.
    
Ammi duk sunzo dubashi tare da AA Doctor din yasamu akan abasu shi zasu canzamai Asibiti dan zuciyarsa ta kamu da matsannan ciwo ALLAH ne ya takaita takusan bugawa bawani jayayya suka samai hannu aka basu sallama cuku cukun tafiya India duk AA ne yayi su da kudinsa da Lokacin sa gaba daya ya bayar saboda surukinnasa.
    Sai ana igobe zasu tafi yake sanar da Wa'at aiko tasha Kuka dan kasa bacci tayi da daddare har Zazzabine ya rufeta takafa nacin saiya kaita ta suka nufi Zariya Asibitin suka wuce hankalinta duk atashe ta glass ake hango Affa sam ba abari ashiga dakin da yake Kuka ta fashe sosai ta razana da yadda taga Affan ya koma yayi fari ya rame tamkar wanda babu Jini ajikinsa.
    AA ne yake aikin Rarrashinta ba Kunya shi gaba dayama ya manta a inda suke watsewa akai aka barsu awajan dan sunga abun bame karewa bane saida yajuyo yaga wayam anan yasan abun kunyar daya tafka agaban surukansa.

Kowa ya ganta sai yayi Mamakin yadda tayi wani kiba takara haske Kamar ba ita ba su Inna sai san barka akeyi haka Mama tamatukar jidadin yadda taga 'Yartata.
            ........✍️✍️✍️
              WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello ABUBAKAR
Oum Aneesa
         PART TWO
Chapter 58

Karfe biyu dai dai jirgin su yandaga tare da Mama aka tafi bayan ansha fama da ita akan basai taje ba atafi da Umma,Umma sam cewa tai ba Inda zataje itama bukatar mejinyar ta takeyi dan dole Mama ta yadda.
Sai malam da Yaya Usman tare dasu aka tafi sai Fatan samun nasara da sauran dangi suka bisu dashi.

A babban birnin Dalhi suka sauka Wani babban Asibiti suka zarce dashi dama ansan da zuwan su dan akwai sanayya tsakanin su da AA Doctors ne suka dukafa akansa saida suka samo bakin zaran suka
 dora shi akan magungunan dazasu taimaka masa.
      Wani plat House aka sauke su na AA ne dan karamine amma yayi matukar haduwa acan suka huce gajiyar su dayake ba'a kwana awajan mutum Ma'aikatan ke kula da marasa Lafiyar su sai da safe mota tazo ta daukesu har gida takaisu Asibitin.

Alokacin Idanun Affa abude suke bedade da bude idanu ba ahankali yafara tariyo abunda suka faru take ya sake burkicewa tuni Na'urorin jikinsa suka fara kara.
    Kirjinsa na sama da kasa da gudu Likitocin suka rugo ansha fama kan abun yayi sauki jugum jugum suka zauna sai kallon shige da fecen da Doctors din sukeyi kowa Hannunsa ruke da carbi yanaja tare da Addu'a ALLAH ya bashi lpy ya tashi kafadunsa.
    Haka akaita fama awannan wunin daya farka zai tuno da abunda ya faru zai shiga mawuyacin hali dole tasa suka shirya yimasa aiki dan zuciyar tasa kara tabuwa takeyi adaran ranar akai masa Aiki Alhmdlh anyi aiki cikin nasara sai jiran farfadowarsa.
    
Karfe 9 nasafe ya farka idanunsa tar abude gaba daya hawaye kebin gefan Fuskarsa ya kurawa fankar da take juyawa ido Nadama ce me matukar yawa ta Lillibeshi 'yaya Mazan daya fifita shine yau ya Kawo masa sakamakon jika bata hanyar halal ba kuma tsabar tozarci yasaka sunansa shiko maiyafi wannan kuna radadi da tashin hankali agare shi.
    Aysha ya tuno yadda ya tsangwami Rayuwarta ya manta Ba ita tabawa kanta ba ALLAH ne yabata lallai ya tafka babban kuskure a Rayuwarsa anya zata yafe masa kuwa bazata taba yafema ba wata zuciyar tasanar dashi haka kansa yaji ya kara sarawa gaba daya yakasa gane ainama yake dan bayajin motsin kowa.
   Doctors ne suka shigo cikin Farin cikin Aiki Yayi kyau ganin ya farka babu wani matsala,wasu Alluran suka sake yimasa cire Na'urorin jikinsa sukai tare da turashi suka canzamai daki tun yanajinsu sama sama har bcc ya daukeshi.

Su Malam akace su shiga amma banda hayaniya.
    
Zagaye Gadon sukai suna kallanshi ganin yadda ya koma Lokaci daya Allah me yadda yaso da ba wansa Abinda Malam yace Kenan kujeru sukaja adakin zama sukai sukaci gaba da kallonsa,baccin da yayi beyi na awa daya ba ya farka ahankali ya fara binsu da kallo bedire akan kowaba sai Mama daba tasanma ya farka ba jiyayi Hawaye ya cikamai idanu duk Abunda yayi mata tazo Asibiti domin jinyarsa.
    
Wani sonta da Kaunarta yaji yana sake shiga zuciyarsa,katashi cewar Malam dayaga kamarma belura dasuba sai asannan Mama tasan ya farka waiwayowa tai suka hada idanu Gimtse fuska tayi kamar bata taba Dariya ba sannu ALLAH ya sawwake Abinda ta fada kenan tatashi tafita babu wanda ya dakatar da ita.
    Yaya Usman ne yayi masa sannu haka Malam tun yana zuba idon tadawo shiru taki dawowa tana sane taizamanta awaje komai dayake bukata Yaya Usman ne yayi masa hardare bata yadda ta dawo dakinba harsuka tafi,da safe ma cewa tai kanta ke ciwo taki biyo su sai akwana nabiyu taje tadaure ta temaka masa amma kome zatai Fuskarnan ahade take tamau.
   
 ALLAH sarki Affa kwana yake yana Kuka ya kasa kwantar da hankalinsa yan Nigeria sunata kiran waya da tambayar jikinsa.
   
 Satin su Biyu suka dawo jiki yayi kyau sosai suna shigowa da Kabir Yayi arba yana ganin Mama yataho wajanta alamun dai yagane ta dan zaman da sukai Salamatu kuwa tana daga zaune tana bangala Dariya da mika mata Hannu alamun ta dauketa kowa kauda kansa yayi cike da jimami jansu dakinta tayi yan Oyoyoyo sun zagayeta ganin harwani kyau takarayi.
   
 Tunda sukaiwa Affa sannu babu wanda yasake kulawa dashi dan sam babu wani shakuwa tsakanin su shiyasa tunda sukaga yaji sauki kowa yakama harkar gabansa Mama kam kamar zasu goyata Umma hardaki tazo tanai mata sannu da zuwa,Affa ma taleka tamai sannu tare da gaida su Malam dayi musu sannu da zuwa.
  
  Tomu zamu tafi Kabiru ALLAH ya baka lpy ga Matanka nan saci gaba da kulawa dakai ALLAH ya kiyaye gaba tashi sukai suka fita suma.

Nan fa yan dubiya aka dinga zuwa wai anzo dubashi nan kuwa duk munafurci ke kawosu babu wani dubiya da suke zuwa duk wadda yashigo saikaga yana hangawa kozaiga yara tuni Mama tasasu adaki danta lura ba dubiya suke zuwa ba tsabar Munafurci ke kawo su.
    ......✍️✍️✍️
           WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
            PART TWO
    Chapter 49
    
    Daga gaisuwar safe Mama bata yadda wani abu ya sake hadasu sai Umma itace take kulawa dashi itama ba sosaiba jikindai sai a hankali saboda damuwar da take dankare aransa idanunsa sunyi jajir.
    WA'AT tasake zuwa dan ya barta tai kwana Biyu murna takeyi sosai ita kanta tayi Mamakin yadda yaran ke kama da Affa abun yagirgizata sanda ake gaya mata tajinjina Lamarin ko AA bata gaya masa takame bakinta dan wannan babban abun kunya ne tare da su.
    
Har daki tabi Affa danta gaidashi cikin rashin saboda tagaidashi saiga Affa yana amsawa ba hantara bazagi,rasa abun fade tai bayan tamai yajiki tata so jikinta asanyaye tafuto binta yayi da kallo yana tuna abubuwan daya sha yimata abaya share hawaye yayi wanda ya wanke masa fuska batare daya farga ba.

Sassafe Inna da Malam suka dawo duba shi yana daki yaja sana'ar tasa wato Kuka tsayawa sukai suna kallonsa au kuka kake wai? cewar Inna tana tabe baki ai yanzuma ka fara kuka kakan Kabiru da Salamatu karshan me butulci kenan dama aina gayama matukar ka zalinci bawa tofa sai ALLAH ya saka masa.
 
   "Zama Malam Yayi yana kare masa kallo kamar bashine Duniya tadinga buga masa ganga ba"
    'Yaya matan da kake wulakantawa sai gashi Haihuwar su ce tai maka rana kaji kunya Kabiru wayonka bashi da amfani cikin bacinrai Inna ke wannan maganar tobara na gaya maka ita wadda kafi tsanarta akan kowa Mijinta shikaci Albarka cinta gari ya gari kasa ya kasa yadauki nauyin komai yafita dakai can kasashan masu jajayan kunnuwa aka nemama magani kagayamin kaf cikin danginka wazai bigi kirji yaimaka haka ko za'a kaikanma ina kudin.
    Fyace hanci tayi shiyasa shidan adam ba abun wulakantawa bane bakasan baiwar da ALLAH ya yimasa ba wllh matukar baka nemi yafiyar Aisha da yaranta ba ALLAH bazai barka ba nasha sanar dakai akwai ranar Nadama wllh nayi Nadama Inna haka Affa ya fada cikin gursheken Kuka kamar karamin yaro.
          
Rarrafowa yayi yarike kafafun Inna datake tsaye tana sharar hawaye aduk Lokacin data tuna irin yadda Kabiru ya wulakantata ya nunawa Duniya cewar ita ba wata aba bace agurinsa,Musaman  Lokacin Haihuwar Wa'at badan surukar tata yar arziki bace ai bazata sake ganinta da mutunci ba.
   
 Dan ALLAH Inna kiyimin aikin gafara wllh natuba nagane kuskurena kuma ashirye nake dana nemi yafiyar su kiyafemin fushinki BABBAR masiface agareni fusge kafarta tayi da baka san da hakan ba sai yanzu da masifa ta fada maka shine zakace na yafe maka ai wannan tuban naka ba domin ALLAH kayi shiba wahala ce tasaka tuban dole.
    
    Har Zuciyata wannan tuban nayishi saboda ALLAH.Da zaki shiga zuciyata kiga irin yadda nadama ta baibayeta da sai kin tausayan wah ALLAH ya tsareni da shiga zuciyarka ai kyakykyawar zuciya itace abar shiga.

 Gurin Malam ya rarrafa shima ya rike nasa kafafun dan Allah Malam kayi hakuri kayafemin nasan na bata maka tsawon zaman da kukai dani nasan nasaku magana na janyo muku magana kala kala kayafemin malam sharrin Sshedanne.
    Murmushi Malam ya saki dama xancan kenan kowa ya aikata Laifinsa saiya ce sharrin shedanne kaine shedanin kanka Kabir kaika fara bashi dama haryayi galaba akanka yaga Abunda ke kudurce a ranka shiyasa ya tayaka ya nunamaka hanya kaikuma kabi babu karkacewa.
    Amma tunda ALLAH yasa kagane kuskuran ka duk da Lokaci ya fara kure maka ALLAH meyafiyane amma baya taba yafe hakkin wanda ka zalunta matukar bashi yace ya yafe maka ba wannan ya rage naka kaje kanemi yafiyar Matarka kararrasheta dammu bazamu taba sa baki acikin Lamarinku ba kaidaka bata kaizaka gyara barnan da kayi nidai na yafe maka Duniya da Lahira haka Fatima tayafema dannasan bacin rai yasata kin yafema ayanzu.
   
 Affa sosai yayi Farin ciki jin Abunda Malam din yace sosai ya yayi musu Godiya Nasiha me ratsa zuciya suka hadu suka sake yimasa jikinsane ya kara sanyi.
   
 Mamace tai sallama sai Umma da take bayanta sunzo gaishe dasu Inna cikin Fara'a aka gaggaisa da tambayar su yame jiki suka amsa da sauki Idanun Affa kamar zasu fado saboda yadda yakebin Mama da kallo tashi sukai suka futa ko kallon Appa babu wadda tai acikin su daki suka koma.
    
Sai da ya tabbatar yaran basanan ya fito daga daki dakin Mama ya nufa ahankali yake tafiya dagani kasan badadi yake jiba Wa'at ma tatafi Gidan Mami daga Mama sai 'Yan biyun data samu suna kwance sunashan bacci abinsu.
     Da Sallama ya shiga dakin amsawa Mama tai tare da binsa da kallo kome yakawo sa Oho hakan ta Ayyanawa aranta,Maimakon ya zauna akan sofa gani tai Affa ya durkusa akan guiwoyinsa baki sake Mama take binsa da kallo.
     Kafin tai magana ya tari Numfashinta magana ya farayi cikin ranunin murya Aysha gani tsugunne agabanki kiyanke min duk hukuncin da kikaga ya dace da lefin dana aikata miki abaya wallahi nayi Nadama saurin daga masa hannu tayi tsaya dan ALLAH aini Kabiru babu abunda kayi min da har zakazo kanemi yafiyata ba kaimin komai ba kaga kuwa Maganar kace nayafema ai bata taso ba.

Katashi kafitar min adaki inkuma zaman hayar da nakeyine ya kare yanzu zan tashi na hada kayana nabar maka Gidanka,tashitai ta dauko wata katuwar jaka tabude sif zata fara dibar kayanta da sauri ya rike jakar dan ALLAH kiyi hakuri zan fita hanyar waje ta nunamai alamun yayi waje haka yanaji yana gani ya fita yana waiwayenta dama ance mehakuri be iya fushiba.
    Yana fita ta koma tazauna tare da dafe kanta lallai ta yadda wani Namijin ma bashi da Kunya haryana da bakin daz aizo yakalli tsabar idanunta yace wai tayafe masa yamanta alwashin dayaci akan bazai taba neman wani abu daga gareta ba kai bama ta da kimar dazai nemi wata Alfarma tata,tabbatar yanzumma badan Allah yazo neman ya fiyar ba.
    
    Wahala yagani haryanzu bata da tabbacin tuban gaske yayi ko tuban wahala nan gaba zai iya komawa bama wannan ba batajin zata iya yafe masa laifin daya aikata agareta.
    
    Yamma lis Ameer ya kwada sallama a tsakar Gida saida zuciyar kowa ta buga dan sarai sun gane me muryar hhhh abun Dariya sai gashi suna Leke ta window saida suka tabbatar babu wuka a hannunsa tukunna suka fara fitowa daya bayan daya.

Alokacinne su Kabiru karami suka fito daga daki Salamatu tana hannun Mama.
    Idanunsa ne ya Fada akan su wani ihu ya buga tare da dura wani Uban zagi sai gashi ana rige rigen fadawa daki dan ba karamin firgita su yayi ba, kirari yafara yiwa kansa ba kakkautawa saini dan Kabiru Uwata Salame Uban Kabir da Salame saini dakalin Majina Ahauni azame nahau Mutum na zauna daidai,saini kadangaran bakin tulu wanda yaje Legos ba tsara ba maza ya rako duniya.
    Mama!!! haka ya kwalla kiranta tuni cikin Mama ya fara kugi kuuuu tashin hankalinta kiranme yake mata wannan tashigesu yau itakam,

kinafa bala,in burgeni kinga yadda kika dauki Salamatu bakaramin kara mutunci kikai a idanuna ba suda naiwa takwara su yakama nazo nagansu ahannunsu suna lailayasu da shagwaba su.
    Nifa Mama sonai nazo naga Umma ana cashwa da ita akan layi yadda ta nunan gata ai yawane takiyiwa jikokinta haka haba nidai Umma kin batan raima gaba daya.
    
Wai Mama nace ba tsuru Mama tai ina fatan kayan su kaf an kawo miki dan ke zan bawa Amana nasan bame kaunata agidannan saike ina jakar kayan take ai ba akawo su da kaya ba me kikace ni za arainawa hankali banaje Gidan miyi wacca zamiyi.
    Naci Uwar rainin hankali Affa ne ya fito daga daki tsabar yadda ransa ke suya idanun nan sunyi jajawur birki yaja yana kallonsa.
  
  Fashewa yayi da wata mahaukaciyar Dariya yana nuna shi da hannun sa.

Dagus ALLAH dai yabiya wai yane naga duk kawani kwararrabe kasake tsofewa fatan kaga ta kwaranka ka kula dashi kamar yadda ka kula da ubansa.
    Dagus saboda irin son daka Nunamin shiyasa nima dana haifi dana naimaka halacci kasan ni dan halak ne bana manta halacci,babu sunan wanda nasa sai naka akula min dasu baba,cau cau Mijin Salamatu kakan salamatu saramai yayi.

Dif dif haka yafice daga Gidan kowa binsa yayi da kallo Umma ce ta rushe da Kukan takaici da bakin ciki zaman dirshan tayi tana rusar kuka kamar ALLAH ya aikota.
    
Affa jiyayi zuciyarsa tadauki wani irin zafi zugi da radadi neman faduwa yake da gudu su Zainab sukazo suka tareshi zaunar dashi sukai kirjinsane ya fara sama da kasa yana dafe da saitin Zuciyarsa sosai suka tsorata ALLAH ya taimakesu Umar ya fado Gidan dan angaya masa anga Ameer ya dawo yasan zai iya zuwa yayi musu aika aika shiyasa ya taho asukwane
            .........✍️✍️✍️
                         WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
                  PART TWO
Chapter 50

Cikin sauri ya dauki Affa dan tare dawani abokinsa suka zo acikin napep sashi sukai aka nufi asibiti,emagency suka kaishi cikin gaggawa akai masa abunda ya kamata Malm yakira akan jikin Appa yatashi dandanan suka garzayo hankali tashe dukkan kudin da ake bukata Malam ne ya bayar alokacin Wa'at ta dawo daga Gidan Mami ake sanar da ita.
     
Sosai abun ya tayar mata da hankali asibitin ta tambayi Mama suka gayamata dan danan sai gata duk kudadan da Malam ya kashe saidata maida masa harda kari komai itace ta dauki nauyin sa dan alokacin Wa'at tafara kama kasa kudi sun zauna Business take sosai Less Atamfofi kai kayadai na kwalliyar 'Yaya Mata babu abunda bata siyarwa dan AA jari me nauyi ya bata kuma ALLAH ya samata Albarka fidda kudi a wajanta bawani abu bane.

Haka beban tasu da Fareeda ba itama ya bata amma babu abin da take saidawa yarasa inda take kai kudi inya bata.
     
Ga Mijinta babu abunda baya yimata saidai ta godewa ALLAH haihuwace dai shiru haryanzu suna ta Addu'a ALLAH ya basu.
     Sai Yamma sosai Affa ya farka akan Wa'at yafara sauke ganinsa tuni yaji wata kunya takamashi tuna basu taba wata cuta ya kalle su ba balle yazo inda suke sai kyara da hantara atsakanin su amma yau sai gashi tana tsaye akansa cikin tsananin damuwar daya karanta acikin idanunta.
   
Da sauri ta sake matsowa ganin ya farka hawaye kawai ke zuba a idanunsa sannu Affa tafadi hakan tana sharemai hawaye da Mayafinta wani abu namaka ciwone bara na kira Likita juyawa tai da nufin tafiya taji ya ruko hannunta cak tatsaya,danjin yadda Zuciyarta ta tsinke dama Affa zai iya kusanta kansa dasu akwai ranar da zataga Nadama acikin idanunsa kamar yadda tagani yanzu.
     Hawaye ne suka ciko a idanunta asanyaye tajuya kur taga ya kura mata idanu yana kallonta wata kauna take hangowa a idanunsa tausayi da jinkai wanda bata taba gani a idanun Mahaifinta ba saidai taga anaiwa wasu amma yau hakan take gani a idanun Affa.
    
Affan nan dayace Haihuwar su asara ce babba agareshi Haihuwar su wahala ce bazai taba alfahari da suba sudin sun zame masa matsala anya idanunta ya gane mata daidai kallan kiyayya ya koma na soyayya,ta tabbata wannan Mafarkine bazai taba canjawa ba bata fahimta dai dai ba share hawayan da suka gangaro mata tayi dafata taji anyi juyowa tai ganin Malam tai tsaye abayanta fuskarsa cike da damuwa yake girgiza mata kai alamar tamatsa kusa da Affa.

Aduk taku daya jitake Zuciyarta tana tsinkewa bazata tuna sanda taje kusa da Mahaifin nata ba yau itace agabansa batare daya zageta koya doketa ba anya kuwa.
     Daf dashi ta tsaya idanunsa yana akanta Lumshe idanunsa yayi tare da budewa wasu Hawayan ke sake ambaliya a kuncinsa,dama haka 'Yayan suke haka suke nuna jinkai ga iyayan su ya tabbatar ba dan halinsa sukazo gareshi ba 'yaya Matan da yafi tsana aduniya yau suke tsaye akan sa da kudin su da Lokacin su duka sun bayar a saboda shi.
    Shinefa Ubannan da yagaza saya musu koda pant da suna Jarirai yayi watsi da rayuwar su su mutu ko suyi rai bashi da damuwa besan cin su da shan su ba wane irin Ubane shi lallai ya tafka babban kuskure A Rayuwarsa.

Kuka ya Fashe dashi tundaga kasan Zuciyarsa yakejin Nadama Me tsananin karfi yana me turr da halayyarsa da muguwar akidar daya samu sama taka dan be taso yaga anayi agidan su ba.
    
    Zuciyafa ta tsinke hankali kuma ya tashi Nadama ta samu mazauni acikin Zuciyarsa,Inna dake gefe share hawaye tayi irin ranar data take gudu kenan ranar Nadama ranar daukar fansa ranar dana sani agare shi inya mutu a yanzu meze ce da ALLAH wace amsa zai bayar akan kiwon da ALLAH ya bashi bashi da wata hujja,bakar Zuciyarsa takaishi ta baro shi.
    Cikin Kuka yafara fadin 'Yata jitai wani yar dan bata taba jin wannan kalmar daga bakinsa ba ALLAH yayi miki Albarka wani irin sanyi taji Zuciyarta nayi kalmar data dade tana sonji daga gareshi Kalmar da tasha ji take fatan tajita abakin Mahaifinta kalmar da takasance abun dakon san jinta kalma mafi dadin ji agareta.
  
  Da gaske Mafarkinta ne ya tabbata kallon sa tayi bakinta har rawa yake wajan fadin Affa mekace.
        😭😭Koni kaina saida nashare wani dan guntun hawaye na tausayi Lallai Affa yayi nadama ta gaskiya.
         Mrs Baba Bello Abubakar.
          .......✍️✍️✍️ 

                            WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
         PART TWO
Chapter 51

Sake maimaitawa yayi ALLAH yayi miki Albarka yarinya ta,wasu hawaye ne masu matu kar sanyi suka kama kwarara akan fuskar ta yau Affa ke sama ta albarka wace irin babbar rana ce wannan agare ta wane irin abun farin cikine ya same ta ayau kamar yadda take kuka haka Affa ke Kuka,tuni zuciyar Malam da Inna tasake karyewa ayau ji suke dukkan wani lefin da Affa yayi agare su sun yafe masa sunyi masa afuwa badan komai ba sai dan ganin farin ciki afuskar WA'AT jika mafi soyuwa agare su.

Ahankali sauran yayan sa sukazo suka zagaye shi daya bayan daya yake kallon su fuskokin su cike da damuwar halin da yake ciki dakyar ya bude bakin sa dukkan nin ku ALLAH yayi muku albarka nasan abaya na zalince ku,amma ina fatan ALLAH ya aramin rayuwa da lafiya tabbas zan gyara kura kauraina zakuji dadi fiye da yadda sauran yara sukaji awajan iyayan su zan goge dukkan wani tabo da wani kunci dana dasa acikin zuka tanku.
     Iname neman alfarma agare ku daku yafemin dukkan muzgunawar danai muku abaya bayi alkawarin bazaku sake shiga kunci asanadina ba kuyafemin 'Yayanah,hawaye kawai suke gogewa amma sun kasa tsayuwa yau dai Affa ke neman afuwar su dama zasuga wannan ranar musamman Nusaiba da Hafasah basu taba zatan wannan ranar zata zo agare su ba.

Ansha goran ta musu a Makaranta cikin kawayan su kudama baban ku baya sonku betaba kawo ku Makaranta ba sunsha yin Kuka akan haka,Hafsah ce ta dubesa Affa har Makarantar mu zakaje kawayammu suganka sudena fadin baka sonmu gyada mata kai yayi alamun zaije din washe bakitai tare da waiwayawa ta kalli Mama da takejin dukkan abunda yake faruwa.
    Kowa kallon sane ya koma bakin kofar datake tsaye sam taka sa shigowa dakin akwaita da rauni da matukar tausayi ayau taji zata iya yafewa Affa dukkan lefin sa agareta zatai masa afuwa tai masa uzuri zata karbeshi matsayin Mijinta akaro na biyu.
          
Affa kura mata ido yayi yana daga kwance kokarin tashi yake WA'AT tai saurin maida shi dan tagane in da yake nufin zuwa.A hankali tafara takawa hargaban Mama hannayanta ta ruko gaba daya duka biyun batai gaddama ko musu ba tabiyo ta har gaban gadon Affa ta kawota gefe tamatsa tana kallon iyayan nata data dade tana Mafarkin ganin su inuwa daya cikin so da mutunta juna.
    Kokarin bude baki yakeyi yayi magana saurin rufemai baki Mama tayi sa Hijab dinta tai ta goge fuskarta,basai kace komai ba Affa saida ya sake ware idanun sa akanta yaushe rabon dayaji wannan sunan abakun ta hakan yana nufin zata yafe masa laifinsa.
    Numfasawa tai taci gaba da fadin na dade da yafema tuntuni dama fatana naga ranar da zaka gane kuskuran da kake aikatawa kagane badai dai kake aikatawa ba kagane kamar kana jayayya da hukuncin ALLAH ne yabaka kyauta kace baka so saiya barka da iyawar ka dan ya jarrabeka saiya baka yaya Mazan hakan sai yasa kasake sakan kancewa tunda kasamu Mazan wadannan sun isheka sune zasu taimake ka.
    
    Kamanta yaya matan nawane suke taimakon iyayan su sukaji kan su alokacin da suka girma suka manyanta kana tunanin su matan basu da rana dukkan dawainiya da wahala aka haifamaka.
    Naji matukar dadi da ALLAH ya nuna maka gaskiya tunda rayuwarka mudai mun yafe maka dukkan kura kuran dakayi agaremu fatan da muke dashi ayanzu ALLAH ya baka lafiya.
    
    Hawayan farin ciki Affa yafara gogewa jiyake inama yana da damar tashi daya tashi ya rungume Mama yasata ajikin sa ya rarrasheta ya faranta mata yawanke mata zuciya dukkan bacin ran daya dasa mata ya gusar dashi yazaman to sai farin ciki kadai acikin zuciyarta,yayiwa kansa alkawari zaiji da ita zai kyautata mata bama itakadai ba har Danginta babu abunda zai saka mata dashi face bata lokacin sa data gaza samu abaya.
    ALLAH yayi miki albarka Aisha nadade ina alfahari dake acikin dukkan surukaina na tabbatar babu wanda zata Iya hakuri da juriya kamar yadda kikayi,dama ance me hakuri shike dafa dutse har yasha roman sa yanzu garanar hakuri kingani ALLAH ya ganar dashi gaskiya ALLAH ya albarkaci dukkan zuri'arku ameen suka amsa gaba dayan su.
    Hhh wani kallon kauna Affa ke jifan Mama dashi kunya ce gaba daya ta lullubeta da ido take masa nunin yadaina yi mata wannan kallon amma kamar begane meta ke nufi ba kememe yaki dainawa.
    
    Malam ne yafara juyawa Inna ta rufa masa baya dan ganin yadda Affa ya shagala ya manta da su gaba daya adakin, Wa'at ma bin bayan su tayi ganin abun nasu ya girmama daya bayan daya suka dinga fita kowa kaga fuskar sa kunshe take da murmushi gwanin birgewa.
    Suna fita ya riko hannun Mama akusa dashi ya zaunar da ita wasu kalaman kauna yake fada mata dani kaina baji nake ba,Mama sai zabga murmushi take wani zubin har rufe fuska takeyi kome yake gaya mata haka Oho.
    🤣🤣Ashe Affa haka ya iya soyayya dan danan saiga Mama tana tikar dariya kallon juna yan dubiya sukai kowa yana kunshe baki dan ganin wata sabuwar Soyayya data balle tsakanin iyayan nasu abundai sai san barka.
    Aranar aka sallamo Affa dan matsawa yayi sai an sallame shi ya warware saida Doctor ya tabbatar ya warware din da gaske sannan ya sallame su tas Mama ta gyaramai dakinsa tare da kunna masa turaran wuta saiga daki ya dawo hayya cinsa sai tashin kamshi kawai yakeyi.
    A ranar dai Affa tuburewa yayi dole sai ansamu mejinyar sa tsoro yakeji bazai kwana shi kadaiba nan jayayya ta kaure tsakanin Umma da Mama kowacce tana yar uwarta ce zata zauna Affa yana jin su amma Addu'a yake ALLAH yasa kar Umma ta yadda to addu'ar sa dai ta karbu dan akarshe dole Umma tai nasara akan Mama akan ita taci girma tabar mata.
    Sabon Amarci zatayi tadau alkawarin sai tayi sati daya tanai musu girki suna ci haka Umma tafita tana dariya cike da tsokana tabar Mama tare da Angonta.
    Sosai Affa ya zage ya sake rarrashin Mama da kalamai masu dadi da ratsa zuciya tuni Mama ta sallama dan itama tayi missng din Mijinnata dama ba kadan ba kawai dai tana daurewa ne amma yanzu tunda dama tazo bata dama kawai takarbe Mijinta hannu bibbiyu.
    💃💃💃Amarsu ta Ango kenan.
    Fans kuzo mucashe dan taya Affa da Mama sabon zaman su na amana da kaunar juna.
    Taku Mrs Baba Bello
    ........✍️✍️✍️
    
               WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
           PART TWO
    Chapter 52
    
    Wa'at kwana daya ta kara AA yazo daukar ta har ciki ya shigo dan duba Affa aiko yasha Godiya wajan Affa da Addu'a kala kala na abun alkhairin dayai masa haka Mama tayi masa godiya sosai da fatan Alkhairi shatara ta arziki ya sake yi musu Affa har kwallar farin ciki ya goge ikon Allah haihuwa me rana bai taba zatan samun wannan ni'ima daga wajan yaya matan daya guda ba.
    Ashe suma da ranar su koda suka zo tafiya wai Affa ne yau keamata nasihar zaman gidan miji oh rayuwa kenan suna tafiya yakira Hajara tare dayi mata nasiha itama takoma gidan mijinta samnan ta turo shi akan yana neman sa.
    Babu damuwar komai ta amsa da to dan dama tuni tasauko sun sasanta kansu yanzu tana san mijinta yana santa.
    Zaman lafiya agidan sai kara habaka yake abun gwanin ban sha'awa dama Namiji shiyake fara kawo baraka gidan sa aduk sanda ya jajirce bebawa wata kofa akan tafi yar uwarta matsayi awajansa ba to za asami zaman lafiya amma daga zarar kafifita wata akan wata dole akasa samun dai dai to da zaman lafiya.
    To yanzu dai ga Affa ya hade kan iyalinsa waje daya abun dai saidai ace Alhmdlh.
        Garin ABUJA
    
    Fuskar sacike da da damuwa yake sake taba jikinta daya dau zafi sai rawar sanyi takeyi amma saboda naci irin na Wa'at taki yadda sutafi asibiti dan kawai kar ayi mata allura.
    Haba wife yanzu baza ki yadda muje muga Doctor ba cikin tabara take fadin um um harda makale kafada akan bata zuwa ita kwafa yayi bakigani,tashiyayi daga bed din gaba daya wata atamfa ya dauko saida akasha dambe kan tayadda yasa mata kayan har dasu cizo bekula taba cak ya dauketa tana kukan sangarta.
    Suna fitowa Fareeda na fitowa daga nata part din wata ashar ta dura datasa AA tsayawa cak daga tafiyar da yakeyi harni za'ai wa karuwanci agida saboda kun maidani shara wannan gan samemiyar zaka dauko kaiko kunya bakaji ba.
    ALLAH ya isa duk hakkina da kake takewa wallahi bazan yafe maka ba aini baka taba daukata ka fita dani ba kallon up and down yake mata harzai tanka Wa'at tasa kukan shagwaba cike da kissa take sake barkewa ajinkinsa suna gota Fareeda Wa'at tayi mata gwalo.
    Kamar wata Mahaukaciya haka Fareeda ta rugo da gudu dan tacimmu su taji wane shege takewa gwalo amma abun takaicin kantazo sunfice harda bame kofa kukan takaici kawai ta fashe dashi baya dawo wllh koshi ko ita.
    
    Kowa kasa yayi da kansa hango Oga da madam akafada ko ajikinsa bemasan sunayi ba sit din gaba ya bude ya sakata dakansa yaja motar suka fice,acikin motarma gaba daya narke masa tayi ajiki nema take tasa yasaki kan motar tabara kawai take zuba masa yana biye mata.
    
    Da kyar suka karasa clinic din gaba daya tagama susuta bawan ALLAH office din Doctor suka wuce shiyayi masa bayanin Abunda yake damunta, okay yanzu za agwada fitsarinta dan atabbatar da abinda yake da munta badamuwa cewar AA wata nurse yakira ya hada su da Wa'at bata dade ba ta dawo sake langabewa tai ajikinsa shidai Doctor dole ya kautar da kansa dan abun yana neman finkarfin sa.
    
    Tuni AA yagama fitsarar da Wa'at batajin kunyar aganta makale da Mijinta result Nurse din takawo karba Doctor din yayi saidaya karanta tukunna yasaki Murmushi.
    
    AA sarkin fushi tuni ya kule cutar babyn tasa zai dinga yiwa Murmushi haka,bata fuska yayi sake sakin Murmushi Doctor din yayi tare da fadin Congratulations cikin rashin fahimta suke kallon sa AA daya sake kule cikin haushi yake fadin for what.
    
    Result din y mika masa akagauce yakarba yana karantawa sake duban Doctor yayi dan gasgata abunda idanun sa suke nuna masa,Jijjiga kai Doctor yayi alamar abinda yagani haka yake wani Madaukakin farin cikine ya kamashi idanunsa ya Lumshe wani sanyi ne yake ratsa dukkan Zuciyarsa Dady shine zaizama Dad.
    
    Cikin bccin daya fara daukarta taji amfara sakar mata wani zazzafan kiss mematukar gigita wanda akeyiwa shi atunaninta agida suke tuni tafara Maida masa martani,tsam Doctor ya mike tare da ficewa daga office din yau ALLAH ya hadashi da taka darai dan dole sun koreshi daga office dinsa saigashi 🤣🤣🤣ya koma dan gadin kofa dan bazai iya da wannan Lukutar masifa ba.
    Hmmm Masoya.
    Mrs Baba Bello Abubakar
          ......✍️✍️✍️
    
           WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
          PART TWO
    Chapter 53
    
    A kalla sunkai 30mnt kafin yaga fitowar su ba kunya suke kallon sa kowa fuska a washe da farin ciki shidai Doctor yaga ikon Allah please Inba damuwa zami magana cewar AA okay binsu yayi abaya har wajan parking ashe tuni AA yayi wayar akawo mai wata Motar key din Mota AA ya mika masa wadda sukazo acikinta sabuwa ce dal dan awannan satin ya fara hawanta.
    Baki sake Doctor yake kallon sa tukuicin albishir dinka mafi dadinji da sauraro agareni hannun matar sa yaja suka shiga motar da yasa akawo musu, Doctor sai zuba godiya suke sukaja sukai gaba ayyanawa yake aransa yau yashigo hospital da kafar dama ALLAH y kawo dubin ku.
    Tun amota ya kira Ammi yai mata Albishir aiko kamar ta taka rawa har doka tasamai ya lallaba mata Yarinya,Mami ma ba abarta abaya ba yakira ya fesa mata,ba kunya ya kira Umma ya gaya mata aiko Umma ta rangada guda suna tare da Mama suna hira lafiya kike wannan uwar guda haka kodai Amarya za akawo mana cikin Dariya Umma kefadin sabbi gal kuwa.
    Mijin Wa'at ya kirani tsabar rashin kunya wai atayasu da addu,a nakusa yin jika Mama kama baki tai gaba daya abun ma kunya ya bata yaran zamani ALLAH ya raba lafiya ameen oh ni Salamatu zamani me zamammiyar keya.
    Dariya Mama tayi ni bakiji bama nakasa mgana ALLAH y kyauta dai.
    Haka rayuwa taita garawa wannan ciki yanashan tattali tako ina ji akeyi dashi baga Uban ba baga kakannin ba kullum Ammi tana kan hanya zuwa dubata.
    
    Fareeda randa taga cikinnan mutuwa ne kawai batayi ba saboda tsananin bakin cikin data shiga duk yadda taso tatakali Wa'at fada tasamu damar dukan cikin bata kulata ba dan tuni tagano manufarta.Yau dai duk yadda taso boye bakin cikin ta akan cikin takasa saidata hango tahowar Wa'at da bata lura da itana sam jitai kawai an bangajeta tafiyatai zata fadi cikin zafin nama ya taro ta tsabar idanun Fareeda sun rufe bata lura da AA dayake bayanta ba.
    
    Zuciyarsa harwani bugawa take ganin tana neman kashe masa mata haka Wa'at bakaramin tsorata taiba kirjinta sai part part yakeyi saida yaga tasamu nutsuwa sannan ya zaunar da ita kan sofa,tana tsaye kyam babu alamar nadama a idanunta tabbas kashe tama zata iyayi.
    Cin kwalar rigarsa tayi tare da fashewa da kuwa tana zaginsa zagi na rashin mutunci inka cika kai dan halak ne ka sake ni mugu munafuki nime yasa bakamin cikin ba sai wannan yar iskar yarinyar nizakaci amana inkacika halima ta haifeka kasakeni kanta rufe baki ya yarfa mata wani shegen mari mematukar zafi da gigita wanda akayiwa.
    Bama ita da akaiwa ba hatta Wa'at saidata razana ta dafe kuncinta kije nasakeki saki biyu sai alakacin tasan naran batamar datayiwa kanta AA ya saketa sake rushewa tai da kuka nabaki 30mnt kihada kayanki kiyi waje hannun matarsa yaja suka koma dama tattaki zasiyi saboda kumburin kafarta.
    Fareeda saida tagama kuka da nadama mara amfani cike da sakejin tsanar Wa'at taja akwatinta tafuta dacin alwashin intadawo saita fitar da Wa'at daga gidan.
    Kunjifa karfin hali haryanzu batai nadama ba.
    Ammi dataji labarin abunda ya faru fada taimasa akan meyasa yayi saurin saki duk itama fareeda bata kyautaba amma karya sake saurin saki irin haka hakuri yabata tare da fadin bazai dawo da itaba bata matsa masa ba dan tasan mugun halin Fareeda.
    
    Watan haihuwar Wa'at takama Ammi ta matsamai lallai ya kawo ta gida ta haihu haka ya kawo ta badan yaso ba Ammi sosai take kulawa da ita shima gidan yadawo da zama dan gaba daya Gidan zafi yayi masa.
    Ranar wata Juma'a da yamma tatashi da nakuda tasha wuya sosai kafin ta sunkuto yayanta mata guda biyu masu kama da baban su bakin AA kamar zai yage saboda farin ciki komai lafiya sallama aka basu gidan Ammi suka sake komawa dan danan gida yafara cika da yan barka abunka da masu abun.
    A washe garin ranar Mama tazo ganin Jarirai Wa'at tayi farin cikin ganinta sai boye boye take ahijab ashe Mama ciki ne da ita aiko tasha tsiya awajan Ammi Wa'at sosai tayi farin ciki.
    Kwana daya tai tajuya a jirgi ana igobe suna su Umma akayo zuga sai ABUJA hadda Hajiya Uwaliya dan Zuwa ABUJA bazai taba wucetaba.
    Yara sunci sunan Aisha wato Mama da Sadiya me sunan Ammi ana kiran su da Ismah da Islah yara Ma sha ALLAH sunyi goshi katan barka tako ina sa da raguna Hudu AA ya yanka musu anci ansha atamfa me hoton Jarirai aka buga anyi rabon kaya kala kala babu wanda zaice be samu ba.
    Mejego da yaranta suna samun kulawa tako wane bangare sunayin araba'in suka tattara suka koma gidan su bayan sunyi yawan arba in.
          ......✍️✍️✍️✍️
    
          WA'AT
    By Kulsoom Ismail Idris
    Mrs Baba Bello Abubakar
    Oum Aneesat
         PART TWO
    Chapter 53
    
    Yau Mama tatashi da nakuda Affa ya kasa zaune ya kasa tsaye oh  rayuwa kenan Addu'a kawai yake yana jan carbi Allah ya sauki Mama lafiya.
    Kukan Jariri yaji ya karade dakin hamdala yayi yana godewa ALLAH gudar Umma kawai ya juyo cikin matukar Farin ciki suka yaran da sukai jugum tuni suka fara murna Mama ta haihu yaso shiga dakin Amma fur Umma tace bazai shigaba sai mejego ta kintsa haka ya hakura yaci gaba da Jira.
    Saida komai ya kammala tabarshi ya shiga wasu kyawawan yara ya hango jere akan gado su biyu sai tsotsar hannu sukeyi sake ware idanun sa yayi yana kallon Mama da take kallonsa tana murmushi kamar ba itace tagama gwawar maya ba yanzu cikin sauri ya dauki baby guda daya Namiji ne Allahu akbar abunda yafada kenan a Zuciyarsa dayan ya dauka shima Namiji ne.
    Sai yaji dama Matan ta kara Haihuwa taga yadda zai nuna musu soyy ah lallai su Affa anyi hankali Addu'a yayi masu yana ta jerawa Mama sannu idanunta ne ya ciko da hawaye tuna be taba yimata sannu danta haihu ba amma ayau shine zaune agaban ta babu bacin rai bakomai Alhmdlh abunda take nanatawa azuciyarta kenan.
    Dan danan saiga Inna ta garzayo yan barka ne sukai ta tururuwar zuwa barka Affa fa ya bude abkin aljihu sai shige da fice yake da ledoji ahannu kaji kuwa ai Mama harta gaji da cinsu kayan baby babu abunda be siya ba Umma itace akan komai hada hada kawai akeyi agidan saura kwana uku suna Wa'at ta duro tare da nata baby's din da Mijinta abin Alfaharinta sosai AA yayi bajinta shima.
    Mama kasa hada ido tai dashi saboda kunya yarta da yaya itama da yaya ai abunda kunya haka Wa'at tayi bajinta baka danba huduba Malam yayi musu da sunan sa dana baban Mama ana kiransu da Jawad da Amjad raguna uku Affa ya yan kawa Mama anyi suna na bajinta anci ansha anyi hani an kowa ya tafi da farin ciki awannan suna dai Dangin Mama sun yisha cikin kwanciyar hankali saidai suyiwa ALLAH Godiya.
    Haka rayuwa taci gaba da garawa Hajara ma ta haihu ta Haifi yarta mace akasa mata Hauwa'u sunan hajiyar Kamal suna kiranta da Arfat.
    Wannan Family dai saidai suce Alhmdlh yanzu nasu da wata damuwa Hankalin su ya kwanta AA yasa an ruguje gidan da suke ciki katafaran gida ya Gina musu aikin Hajji ya biyawa Mama da Affa harda Umma ranar Umma har kukan farin ciki saida tayi sanadin yayan kishiya zataje kasa me tsarki kunerun da aka taba bawa Wa'at ashe AA ne ya bada su batare da kowa ya sani ba Malam da Inna da Mahaifin Mama su Aka barwa kujerun Wa'at da kanta ta biyawa Mahaifiyar Mama suka dunguma harda su Ammi da Mami sai Saudiyya.
    Sosai suka zage sukai dawafi Affa kullum neman yafiya yakeyi akan Allah y yafe masa dukkan kura kiran sa satin su Hudu suka dawo Nigeria Wa'at da AA ba su biyo ba sun wuce Dubai zata saro kaya daganan su shakata Ismah da Islah Ammi tabarwa su suna can sunacin Duniyar su da tsinke.
    
    Akarshe dai andaurawa Ameer Aure da Zabba'u bayan ta haife yarta mace tazo babu rai yayi Nadama sosai sukai akai musu Aure dan Gudun sake fadawa barna.
    Umar ma yayi Aure wata yar layin su ya Aura Alhmdlh yasake nutsuwa shima yazama babban mutum dan Wa'at Jari me nauyi ta basu shada Ameer suka fara kasuwanci kuma Allah ya samu su albarka suna samu sosai.
    Anyi bikin su Zainab da Zubaida Jiddah da Safna rana daya aka hada su wannan Family guda biyu sun zama dangin Juna Malam da Inna tako ina jin dadi sukeyi Hankalin su akwance yake yanzu.
    Fareeda tayi nacin harta gaji AA ya maidata shi tunima ya manta da wata Fareeda dagashi sai hubbnsa babu wadda yake gani sai Wa'at yasha fadin ta ishesa yayi rayuwar sa da ita.
    Daga karshe Fareeda ta gano kb irin cin Amanar dayayi mata yanata amsha mata kudi yana zuba tawada aruwa yabata da sunan maganin mallaka ya gaya mata tatuna sandata mareshi daganan yayi Alkawarin saiya rama kuma babban burinsa AA ya sakota dama burin sa yacika ranar yasha tsinuwa da zagi tafiya yayi yabarta anan yanai mata Dariya harda su byeee byeee.
    Bayan shekaru Biyar.
    Yanzu yayan Wa'at Uku Ismah Islam sai Naufal shine karamin su.
    Wa' at tayi bul bul bazaka taba cewa ita bace sai Nera ta zauna mata tana taimakon na kasa da ita.
    Bata da wata matsala arayuwa Mijin ta yana sonta Surukar ta na sonta haka iyayanta na santa da Kaunarta ga yaranta na sonta ta godewa ALLAH ba abinda zatace sai dai Alhmdlh.
    
    Tammat bi hamdulillah
    ALHAMDULILLAH
    Anan nakawo karshan wannan Littafi Ina Godiya ga ALLAH daya bani ikon kammala Wannan Littafi lafiya.
    Allah ka yafemin dukkan kura Kuran dani acikin sa.
    
    In sha Allah nan gaba kadan zaku jini dauke da sabon Littafina me Suna asama.
    Bissalam Masoya na.
    
    Taku har kullum.
    Mrs Baba Bello Abubakar
          ALHAMDULILLAH
    
    
    
    
    

    
   

    
    
    
    
    
    
    
    
    
    
    
    
    
    

Post a Comment

0 Comments