SALAMAR ZUCIYA

      

    INUWAR GIGINYA (Na nesa kasha dado) By Kulsoom Ismail Idris Mrs Baba Bello Abubakar

5/9/2023
BISMILLAHIR RAHANIR RAHIM

Da sunan Allah me rahama mejin kai

    Labari na kirkirarre ne ban rubuta shi dan wani ko dan wata ba,in kaji labarin yazo dai dai da naka to akasi akasi samu ko sunan wani gari ko Unguwa.

Ban yadda wani ko wata ba yajuyamun shi tako wace siga.


Nafara rubuta wannan Littafi kamar haka.

          SALAMAR ZUCIYA 
     

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris


     *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "


https://www.facebook.com/profile.php?id=100063945240173




💦KULSOOM DATA SERVICE💦

Kuzo kusai Data me lasting me sauki da rahusa.

     😍😍Muna arha muna hana bashi.
Data A vailable all networks🔥

MTN                     AIRTEL      

500MB_150.          
1GB_260.        
2GB_500.          
3GB_750.      
5GB_1,400.     
10GB_2400.    


AIRTEL

1GB_260
2GB_500
3_750
5_1,400
10_2400

      Bismillahir Rahahanir Rahim.

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah.

Yauma gani dauke da sabin Littafi wanda nake fatan zai ilimantar daku,,ya wa'azantar daku,,ya nishadantar daku.

Page 1

Kano state

 Rijiyar zaki..

Rafin dan Nana

"Dadda d'ar iskar safiya ke kadawa"bishiyu nata rangaji gwanin ba sha'awa"awannan Lokacin wasu da yawa basu tashi ba"wani matsakaicin gida na shiga"da ganinsa dai gidan Malam Shehu ne.Tsakar Gidan kal yake ashare duk da ba siminti amma har daukar idanu yake saboda sharar daya yasha bata wasa bace"abunda ya ban Mamaki jin wani daddadan kamshin girki yana tashi"kamar ma kamshin farfesu nakeji"wata babbar macece ta futo akalla zatai 50years tana da haske"bata da jiki amma baza'a kirata da ramammiya ba."Kallo daya naiwa fuskarta na tabbatar da yadda take cikin madaukakin farin ciki"gaba daya fararan hakoranta sun gaza rufuwa"aiki take cikin karsashi da jindadi Acikin ranta.Mata shiyar budurwa ce ta fito daga dakin 'yar kimanin shekaru 18 kallon matar tai tare da kama haba kai Oum yanzu duk aikinnan kin kusan gama shi ke kadai?wai wane irin so kikewa Yayah Habib nagama bedamu dake ba,,harara Oum ta watsa mata,,karna sake jin kinfadi haka Zulaiha,,yayanku yana matukar kaunar mu"bana so koda wasa na karajin kince bedamu damu ba ranki ne zai baci"Allah ya huci zuciyarki Oum ta furta cikin sanyin murya.

"Wani matashi ne ya kara futowa daga dakinsa da alamar dakin kwanan sa a hanyar soro yake,,hayaniyar me nakeji haka,,nida kanwarka ne kasan kullum maganar ta daya yayanku baya sonku,,narasa meyasa ta dasa wanann tunanin azuciyarta,,shiru Saif yayi da alamar shima yana goyan bayan 'yar Uwar sa,,ko kaima bayanta kake bi,,girgiza kai yayi a'ah Oum kawai dai ina mamakin abunda yasa yatafi ya barmu tsahon shekaru masu yawa,,tunda bani da wayo yatafi ya barmu Oum.Shiru Oum din tayi batare data  amsa mai abunda yake son ji din ba"sakin maganar tai tana kallon sa,yawwa saif kankara nake so kaje ka samomin a can zoo road ina da tabbacin za'a samu"1k ta miko masa gashinan kai Kudin mashin ka siyo min" saura ka zauna harta gama narkewa a hanya,, murmushi kawai yayi yafice daga Gidan gaba daya,,shekarun sa bazasu fi 22year ba.

"Oum cigaba tai da ayyukan ta,,Zulaiha na gefe ta tsura mata idanu"uwa kenan duk yadda danta yake tana matukar kaunar sa"murmushi Zulaiha ta saki ganin yadda Oum take ta bata rai ita alallai fushi take da ita,,mikewa tai ta karasa gabanta,,borket da take kokarin dauka dan wanke toilet ta rike,,haba Oum taya ina zaune zaki dinga aiki ko bakisan na samu Albarka ne?harara Oum ta sake watsa mata kauce ni ki bani waje"kinsan ai abunda yasani fushin"tarar numfashin Oum tayi afuwan uwata takaina,, murmushi Oum din ta saki Zulaiha badai dadin baki ba.

"Sanda saif ya kawo mata kankarar ta bada aka kai mata markadan Aya,ta wanku tayi fari tas ana kawowa Zulaiha ta tace ta saka kankarar aciki,,dan tanajin sanda sukai waya da Yayah Habibullah akan ya kusa kara sowa.Komai ya kammala yayi nit bako kawai ake jira,,Oum wanka tai ta dana sabuwar atamfar ta sai kyawunta ya kara fitowa.Haka Zulaiha da saif sababbin kayansu suka saka zaman jiran bakon sukai dan awajan su bako ne.

"Karfe 10am suka farajin dirin motoci ankofar gidan su,,a tunanin su ba gidan su aka zoba sam basu damu da lekawa dan ganin ko suwanene ba"ganin wasu tika tikan mutane sun fara shigowa da kayan Abinci buhu buhu kamar wadanda zasu bude store ya sasu mikewa"bayin Allah batan kai kuka yo danna tabbatar ba nanne inda akace kuka wo wannan kayan ba,,daya daga cikin sune ya kalleta nanne Hajiya oga ya bamu Umarnin mu kawo nan din,,bude baki tai zata sake magana sukaji wani azababban kamshi ya kauraye gidan baki daya,,baki bude suke kallon wanda ya shigo din"Oum gaba daya tayi mutuwar tsaye tana binsa da kallo,,gaba daya ya canza kamar bashi ba,,ya zama wani babban mutum,,ya kara haske da kyau,,su Zulaiha kuwa tsayawa kawai sukai suna kallon sa,,koba komai sun gano tsantsar kamannin da sukeyi dashi,, Habibullah Oum ta furta cikin rawar murya,,dan Lumshe idanun sa yayi ya bude akanta,, ahankali tatako har gabansa,,tabashi tai danta tabbatar ba mafarkin da tasa ba yi bane.Rungume shi tai hawayan idanun ta na silalowa,dagaske kaidin nake gani agabana,,meyasa Habib meyasa zaka tafi ko sau daya kaka kasa waiwaiyar mu,,shin mantawa kai damu ko kana sane"shiru yayi batare daya furta komai ba,,wani dunkulallan bacin rai daya dade azuciyar sa yana tasowa zuwa makoshin sa,,shekaru 15 kenan ban sanyaka acikin idanuwa naba"ayau ina matukar farin ciki da Allah ya amsamin Addu'a ta ya dawo min dakai lafiya.

"Ko kadan babu fara'a da farin ciki akan fuskar sa,,((kodai beji dadin dawowa cikin ahalin sa ba oho))dan karamin murmushi ya saki yana san korar damuwar Fuskar sa,,koda yaushe kina nan dina Oum"saitin zuciyarsa ya nuna"kowane bugu da ke yake bugawa bazan taba iya mantawa da keba Oummuna.Shafa kansa tai nasan da hakan"dakin data gyara masa sai tashin kamshi yake nan taja shi"katifa ce karama aciki"sai ledar tsakar daki da aka malala a tsakar dakin"kayan Abincin data dafa masa yana jere angefe,,sàida yazo dai dai Inda su saif suke yadan tsaya,,kallon su yayi ku baku iya gaisuwa ba."An tashi lafiya suka hada baki wajan gaida shi,,bece musu Komai ba ya fada dakin da Oum ke cemai ya shigo"da kallo suka bishi,,dama Zulaiha bata sanshi ba,,Saif ne me tuna irin Rayuwa da sukai a baya shida yayansa,,yana matukar kaunar sa baya taba barin kowa ya dake shi awaje saiya rama masa,,amma yanzu meya canza shi haka lokaci guda"gaba daya ya juye ya dawo wani nadaban kamar ba Habibullah ma'abocin fara'a akowane Lokaci ba,,yanzu ya zama miskili na gasken gaske,,bashi da me bashi amsa shiyasa yayi shiru da bakin sa.

"Oum da kanta ta jawo kanukan data Zuba masa abincin"dambun kus kus tai masa yasha kifi sai kamshi yake yaji kayan hadi,,gashinan maza kaja kaci nasan halinka dama can baka san cin Abinci.Amma ka dawo kenan bazaka koma ba"gyada kai yayi na dawo kenan Oum bazan koma ba gaba daya kasuwanci na ya dawo nan"murmushin jindadi ta saki"yanzu saura Aure kenan"gaba daya annurin fuskarsa bacewa yayi bat kamar betaba sanin wani abu dariya ba.

    🙄🙄🙄Kodai Aurenne baya so.
        ......✍️✍️✍️✍️


          SALAMAR ZUCIYA

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "


https://www.facebook.com/profile.php?id=100063945240173



Short story

Page 2

"Kallonsa tayi tana nazarin sa"kamar zatai magana sai kuma tai shiru ta fada fadin abunda ke bakinta"duk yadda abincin ya farayi masa dadi saiya ji sam ya gundure sa"ture abincin yayi ya janyo cup din kunun Aya ya tsiyaya"sosai yasha kafin ya ajiye yana sauke numfashi,,bata kara ce masa kanzail ba tatashi ta fice daga dakin"jingina yayi da hango idanun sa alumshe da alamar Akwai abinda yake cin Zuciyar sa."Ya dade azaune batare dashi kansa yasan abunda yake azaune awajan ba,,sunan mutum daya ne ke kaikawo aransa,,yake mintsinar zuciyarsa,,yake hasala zuciyar sa,,yake gigita Duniyar sa,,tabbas Lokaci yayi dazai dauki fansar Abunda yayi masa,,dunkule hannunsa yayi ya kaiwa iska duka.

"Kwanan sa biyu da dawowa 'yan uwa da abokan arziki suka dinga zuwa taya Oum murnar da wowar sa,,ko yaushe gidan baya rabo da mutane 'yan alasanya Alkhairi"duk wanda yazo sai Oum ta auna masa shinkafa ta hada masa da Taliya"tuni sai tauraruwar Oum ta fara haksawa wadanda suka gujeta abaya sai gasu daya bayan daya suna rarrafowa dan su dangwali arziki."Wata sabuwar girmamawa 'yan unguwar ke mata Biki ko suna sai aka koma bata waje na musamman,,abun ba karamin daure mata kai yayi ba"wato dai yanzu kudinka mutuncin ka,,in kana dashi duk mugun halinka baza'a taba gudun ka ba,,ammafa da zarar baka dashi duk kirki da kyawun halinka babu meyi dakai.Allah yayi mana suttura madawwamiya.

"Watan sa daya da dawo babu inda yake zuwa"kowane Lokaci yana zaune yana aiki a laptop dinsa da lamaun wani aiki me muhimmanci yake yi"tsakanin sa da kananan sa baina baina,,yanzu baisan kowace irin damuwa abunda yasa gabansa shi kawai yake son cimmawa."Karfe 9am yayi wanka cikin wata dakakkiyar shadda gezna sai daukar idanu take,,ta matukar amsar fatar sa,,sai Zuba kamshi yakeyi tako ina."Wankakkiyar motarsa ya fada da yake ajiyeta a nan wani gareji dake cikin Unguwar su."Kai tsaye Kasuwar Kwari ya nufa"Sosai yake gudu burinsa kawai yaga ya isa cikin kasuwar"parking lot ya faka motarsa kafin ya fito daga motar,,Iska ya zuka ya fesar yana karewa kasuwar kallo yana ayyana tsayin shekarun da yayi be shigo ta ba,,a hankali yake takawa tafiya medan nisa yayi kafin ya karaso Inda shagon yake.

"Babbar plaza ce sai kyalkyali take bayarwa,,tundaga waje wajan shake yake da customer,,yaran Nasir dake ta sallamar customer ya tambaya ko yana nan,,tabbatar masa sukai yana nan,,wani hamshakin office suka nuna masa,,yana Cikin nan oga,,kallo daya sukai masa suka tabbatar yayiwa talauci rata me tarin yawa.Inda suka nuna masa nan ya nufa yadan jima yana kallon office din,,tunani barkatai sun cika masa zuciya.Murda handle din kofar tayi batare daya tsaya neman izini ba."Yana zaune akan kujerar sa gabansa zagaye yake da wani babban table sai takaddu dake kai birjik,,ga Laptop a gabansa,,alamar akwai aikin da yake ragewa"jin an shigo masa office yasa shi dagowa dan ganin wane hamshakinne ya shigo masa batare daya nemi izinin saba."Karaf idanun su ya hadu dana juna"kallon juna suke kamar wadanda suka warke daga makanta,,da sauri ya mike daga kan Kujerar sa yanai masa kallon mamaki,,Habib,,Nasir Habibullah ya furta yana kallon Nasir din,,da sassarfa Nasir ya fito daga inda yake zaune,, rungume Habib yayi yana sakin murmushin farin cikin ganin sa,,shima Habib din kara rungume shi yayi,,sosai yake jin Nasir a zuciyar sa tamkar dan uwan sa na jini,,jan hannun sa yayi suka zauna,,yanzu dama ka shigo garinnan amma baka neman ba Habibullah banji dadin daba kasanar dani zuwan kaba.

"Surprise naso naima Nasir shiyasa naki sanar dakai nashigo garin nan"dukan kafadar Habib Nasir yayi kafa shigo gari mutumin kaga yadda ka kara wani fresh yanzu abu daya ne ya rage maka"kallon karin bayani yayiwa Nasir,,dafa kafadar sa Nasir yayi kasan abunda nake nufi Habib meyasa bazakai Aure ba,,meyasa bazaka manta da baya ba,,Aure shine marufar asirinka inba haka ba mutane zasu fara yima wani kallo na daban."Tunda ya fara magana Habib ya tsura masa idanu yana kallon sa,,idanun sa da suka soma rikedewa zuwa jajaye ya Lumshe sam bayasan nuna fushinsa akan Nasir din,,sake bude idanun sa yayi akan Nasir wanda yasha jinin jikinsa"ganin yadda Lokaci daya kwayar idanun Habib din ta canza kala,,danne fushin dayake taso masa yayi kafin ya dafa kafadar Nasir din."Nasir meyasa kake son dinga da womin da maganar baya,,ayanzu Zuciyata a kulle take,,bazata kara kallon wata mace da sunan so ba har abada,,ka dauka Zuciyata ta dade da mutuwa akan soyayya,,matukar kana san zaman lafiya dani karka sake yimin magaan makamanciyar hakan,,in har kaki ji haka na nufin zamiiyi hannun riga dakai ne."Shiru Nasir yayi yana karanto zallar gskiayr dayake fada tundaga kasan zuciyarsa maganar ke fita,,kuma tabbas zai aikata abunda ya fada din.

"Cool down abokina ba haka nake nufi ba"kodan saboda Oum amma tunda ba kasan magana I'm finally,,daga kafada habib din yayi alamar shiyasa ni,, murmushi Nasir din ya saki kana nan baka canza ba,,bazan taba canzawa ba Nasir sai ranar da burina ya cika.Ina so kaimin Alkawari zaka tsaya miyi aiki tare harsai na cika burina akan Alhaji Sani."Zuciyata ba zata taba gamsuwa ba sai naga ya koma fakirin talaka,,sai ranar dana ganshi yana bara akan titi daga wanann rana kowane irin miki zai fita daga Zuciyata.Shiru Nasir yayi na wani Lokaci yana tunani aransa anya abunda abokin nasa zai aikata beyi tsanani ba kuwa,,ko bazaka taimakamin ba na nemi wani,,maganar Habibullah ce ta dawo dashi tunanin daya fada,,taya za'ai nace bazan taimake ka ba Habibullah kasan matukar ina da ikon yin Abu babu ta yadda za'ai naki yima kashi.Good yanzu kafin wannan din ya maganar ginin da akeyi an kammala,,kwarai masu zama acikinsa kadai ake jira an riga an gama komai,,ok nan da next week zamu koma cikin sa,,ka zauna cikin shiri Nasir ko yaushe zan iya neman ka.

"Mikewa yayi ya kara mika masa hannu,,amma bazaka zo muje kaci girkin madam ba,,dan yatsina face yayi ba kowane jagwalgwalo nake ciba,,'yar dariya Nasir ya saki shikenan kayiwa kanka,,har wajan da yayi parking ya rakashi,,sàida yaga tafiyarsa tukunna ya koma office din sa,, zuciyar sa cike da wasi wasin abunda Habib zai aikata,,ko yace zasu aikata tunda tare yake so suyi aikin."Habib bai koma Gida ba sai bayan La'asar,,Oum na tsakar gida tana mulmula tuwon shinka,,wanda yayi fari kal dashi abun birgewa,,dama Oum badai tsafta ba ga iya girki,,da sallama ya shiga Gidan amsawa sukai ita da Zulaiha,,sannu da zuwa Yayah face dinsa asake ya amsa,,me kikeyi bakije makaranta ba,,am yaya kaina ke ciwo,,harara ya wurga mata amma kuma kike zaune kike zuba kamar kanya,, murmushi Oum ta saki kaima kafada,,yanzu abunda na gama fada kenan,,amma dazu tawani langabe wai bata da lafiya,,kwafa yayi zaki kara cewa baki da lafiya kiki zuwa makaranta sai ranki ya baci,,shiru Zulaiha tai tana bata face ita fa batasan bada hadda ne shiyasa tai karyar bata da lafiya.

"Bayan sallar isha'i suna zaune suna hira a dankaramin tsakar Gidan su,,kallon Oum yayi,,nanda sati me zuwa zamu tashi daga wannan gidan Oum,,shiru sukai gaba dayansu kamar basuji daidai ba,,gyada musu kai yayi alamar tabbatar wa,,hawaye ne ya cika idanun Oum,,ashe sa rabon suma zasu fita daga kangin wahalar da suka shiga abaya,,idan ta tuna baya sanda Talauci yayi musu kamun kazar kuku, ta kalle su a yadda suke ayanzu wani sanyi ke kwarara azuciyar ta,,ashe dadin ba iya nan bane harwani gida na daban zasu koma,,mezataiwa Allah ita kuwa Inba godiya ba.

"Kallon sa tayi Cikin so da kauna irin na Uwa take duban sa,,Allah yayi maka Albarka Habib,,Allah ya rabaka da sharrin mahassada,Allah ya tsare gabanka da bayanka,,ayadda take furta Addu'ar ya tabbatar da yadda abun yayi mata dadi azuciyar ta,,farin cikinta ya kasa boyuwa sai share hawaye take da bakin zanin ta,,haka su saif bakinsu kamar zai yage dan murnar zasu koma sabon gida."Sosai yaji farin ciki yana shirgarsa ganin yadda Mahaifiyar sa da kananan sa ke farin ciki,, Lumshe idanun sa yayi yana sakin murmushi,,burinsa ya cika naganin dariya da annashuwa akan fuskar habibiyar sa mafi soyuwa agare shi wato Oum.

        Mrs Baba Bello Abubukar
           ........✍️✍️✍️✍️✍️



          SALAMAR ZUCIYA

Written and Narrated 

By Kulsoom Ismail Idris


*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Short story


Page 3

"Kamar yadda ya sanar da Oum sati na zagayowa suka tashi,,babu abunda ya bari suka dauka gaba daya kayan gidan kyautar dasu yayi,,'yan rakiyar sabon gida jingim haka suka dunguma dan rakiya,,Motoci aka kawo hadaddu masu matukar Numfashi,,dagani sun bawa miliyoyi baya,,Cikin su aka dinga kwasar mutane, AC ce take ratsasu tako ina.Katafaran gida Habib ya ginawa Oum din sa,,tako ina ma'aikata ke kaikawo"Liyafa ta musamman ya shirya duk adomin Oum dinsa da kannan sa.'Yan uwan su dangin Uba da dangin Oum gaba daya sun hallara,,gida ne iya ganin ka kamar dai ba a Nigeria kake ba inka shige sa.Bakin Oum ya kasa rufuwa ganin yadda Allah yayiwa danta arziki,,'yan rakiya 'yan uwa ansamu abinyi sai kashe selfie suke,,moto cine birjik sun cika parking lot din.

Shida Nasir suna ta shige da fice danganin duk wanda ya shigo Gidan be fita cikinsa ba komai ba,,saikaci Kayi kat,,nama har isar su yayi,,ga leda nan inkinga zakiyi guzuri kitafi dashi.Nan rijiyar zaki New sid anan ya dankara kataran Gidan.Gaba daya aikin Nasir ne shine ya tsaya tsayin daka wajan ganin Gidan ya tsaru yadda ake bukatar sa.Zulaiha bedroom dinta Habib ya nuna mata,,saidata kusa suman tsaye,,akalla data bude wardrobe din bataga karshan kayan ba,,wata dankareriyar wardrobe ce ajikin bango aka manne ta,,kayan shafe shafe kuwa ba'a maganar su.

"Dakin daya nunawa Saif sosai ya fifita shi part guda ya ware masa dan yayi rayuwarsa babu takura ba tsawwalawa,,sàida ya matse hawayan farin ciki ya rungume Habib yanai masa godiya.Basu suka sami hutu da Jama'a ba sai da magari ba tai,,haka mutane suka dinga tafiya badan ransu yaso ba.Part 6 ne agidan kowanne kayane dankare Acikin sa kayane kuma na alfarma.Bayan sunyi sallar isha'i suka hallara a maine parlo,,kallon kansu suke tamkar a mafarki,,wai sune a wanann kata faran Gidan Allah kenan meyadda so da bayin sa,me  azurta wanda yaso,ya talauta wanda yaso."Wata mata dattijuwa ta shigo cikin girmamawa tagaida Oum ta sanar dasu dinner is ready,,da fara'a Oum tai mata sannu da aiki.Matar taji dadin yadda basu wulakanta taba daga gani zataji dadin zama dasu.

Mikewa sukai kamar sokaye haka suka dan dosana sorket dinsu akan Kujerar,,yadda kasan za'a ce ket su zura da gudu.🤣🤣🤣to ba'a saba ba,,yadda shigo ya gansu ba karamar Dariya suka bashi ba,,sai zazzare idanu suke suna kalle kalle,,basu kadai ba hatta Oum abundai takeyi kenan,,jitake aranta kamar nanda anjima za'a iya zuwa ace suyi waje Gidan ba nasu bane.Jan kujera yayi ya zauna yana sakin Murmushi,,kayan shan Iska ne ajikin sa hakan saiya kara fito da kyawunsa.Sajansa yadan shafa kafin ya kalli Oum.

"Barka da dare Oum,, murmushi ta saki barka dai Habib,,ka gammu abundariya ko?jinake kamar za'a ce mufita ba namu bane,,nima wllh haka Yayah Zulaiha ta furta tana kallon sa,,jinake kamar za'a zo ace kui waje,,amma gaskiya bazanso fita daga wanann gidan ba,,kawayena masumin dariyar munfi kowa Talauci a Unguwar mu sai suci gaba dayimin yanzu."Shiru sukai na wani dan Lokaci,,ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta,,babu wanda zai kara yimiki wannan gorin Zulaiha,,a yanzu kin zama 'yar gata banajin duk cikin su akwai wanda yafiki jindadi a yanzu,,aiko babu Yayah gaba dayan su 'yan ala baku mu samu ne,,dariya suka saka ganin yadda tayi maganar,, Oum dai batace komai ba taci gaba dacin abincin ta.

"Bayan sun kammala kan sofa suka koma suna kallo da hira jefi jefi.Kallon agogon hannunsa yayi ganin time yana tafiya ya mike zanje na kwanta Allah ya tashe mu lafiya,, Ameen suka amsa gaba dayan su.Suma basu wani ja Lokaci ba suka mike kowa yayi hanyar dakin sa danya kwanta ya runtsa."Satin su daya agidan suka gane kansa,,abubuwan da basu iya amfani dashi ba,,gaba daya Habib ya koya musu,,dan danan saiga fatar su ta fara canzawa tana gogewa,,wahalar da suka sha abaya ta zama tarihi.

Tunda ta zauna ta zuba masa idanu tana tattauna maganar dake cin zuciyar ta tsahon shekaru."Habib ina so ka fadamin yanzu shekarun ka nawa,,shiru yayi yana kallon Oum,,amma meyasa Oum zatai masa wannan tambayar bayan tafi kowa sanin shekarun sa,,kana tunanin meyasa naimaka wannan tambayar ko?gyada kai yayi alamar eh,, murmushi ta dan saki"so nake na tabbatar da kana sane da shekarunka ko lissafi ya kwace maka ni saina kara tunatar dakai."Ina sane da shekaru na Oum 30years,, Numfashi ta sauke Alhmdlh tunda har kana sane,,kuma kasan shekarunka gaba suke ba baya ba."Babu abunda Allah beyi maka ba na tarin baiwa da daukaka,,in ana Auran mata dari a yanzu kana da kudin da zaka Aure su.Alfarmar da nake so kaimin kawai shine kayi Aure Habib shine Babban buri na.

"Shiru Habib yayi yana hadiye wani abu me daci,,da ace zai iya da babu abunda zai hana beyiwa Oum abinda take so ba,,saidai kash bazai iya din ba.Kiyi hakuri Oum har yanzu ina kan bakata na bazanyi Aure ba,,kinfi kowa sanin tabo da kaunar dake Zuciyata Oum karki tirsasani akan abunda zan cutu.Zuba masa ido tai tana karantar sa,,kana nifin kacemun har yanzu kana kan bakarka?saboda me bazaka manta baya ba,,meyasa kake son zama me butulcewa rahamar Ubangiji,,yanzu wannan baiwar da yayi maka baya sakar maka kunci da radadin daka fuskanta abaya bane?bana jayayya da maganar ki,,Oum kuma na yadda da abinda kika fada min,,amma har yanzu Zuciyata ta kasa barin abun Oum bazan taba hutawa ba sai nadauki fansar Abunda akai min.

"Sun kuyar da kansa yayi jin wata kwallah me zafi ta ziraro daga kwarmin idanun sa,,cikin matukar damuwa Oum ke kallon sa,,Kuka Habibullah,,rabon da taga kukansa harta manta tun shekarun da suka shude,,mikewa tai tsam ta fice daga part din baki daya,,dan kara dugunzuma zuciyar ta yake yi"shiyasa ta mike ta bar masa dakin."Binta yayi da kallo yana jin badadi a zuciyar sa,,shikansa zaiso yayi mata abunda take so amma hakan bazai samu a halain yanzu ba.Kiyi hakuri Oum jingina kansa yayi da jikin sofa yana ajiyar zuciya ahankali,,da furzar da huci mezafi.Sai sanda ya samu SALAMAR ZUCIYA tukunna zaiyi Aure da sauran Lokaci.

        Mrs Baba 🌹 Bello Abubakar
       .....✍️✍️✍️✍️


          SALAMAR ZUCIYA

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Short Story

Page 4

"Rai bace Oum ta karasa bedroom dinta,,zama tai ta dafe kanta dayake dan sara mata,,SALAMAR ZUCIYAR TA Habibullah yayi Aure,,in har yayi mata haka bata da wata sauran damuwa."Zulaiha ce ta shigo hango Oum cikin damuwa ya sata karasowa da sauri,,zama tai kusa da ita. Oum mezai sa ki zauna cikin damuwa,,bayan ayanzu lokacin farin ciki ne baki da wata sauran damuwa"ajiyar zuciya Oum ta sauke kayya dai Zulaiha ni ko nake da damuwa matukar Yayan ku beyi Aure ba bazan taba samun SALAMAR ZUCIYA ba.Kina zatan wannan jindadin zai cire min wannan damuwar,,ina da burin yayi Aure naga jikoki na,,kina ganin bamu da yawa,,kwata kwata ku uku na haifa,,ina so naga wataran Gidannan ya cika da yara.

"Ajiyar zuciya Zulaiha ta sauke,,karki manta Oum Aure Lokaci ne,,Indai Lokacin yayi ko yana so ko baya so saiya yi shi,,dan Allah ki cire wannan damuwar daga zuciyar ki.In sha Allah zaiyi Aure nan kuwa,, murmushi Oum tadan saki shikenan Zulaiha ina fatan haka,,Allah ya yi muku Albarka,,Ameen Oum.

"Nasir ya kafawa idanu tun zuwansa yaki furta masa ko wace kalma,,Habib nagaji da wannan kallon da kake min ya za'ai kace nazo sannan kuma ka sani agaba kana ta kallo na kamar wata sabuwar halitta,,cikin kuluwa Nasir din yake magana,, murmushi Habib ya saki yana kallon yadda Nasir yake ta tada jijiyar wuya.Gyara zaman sa yadanyi,,dadi na dakai gajan hakuri Nasir.Plan dimmu na farko akan company Alhaji Sani yake so nake ya dawo karkashin iko na,,shiru Nasir yayi ta wace Hanya zaka iya mallakar wannan company?"duk wata hanya da zanbi dan cikar burina zan bita Nasir,,ko nawa ne zan iya kashewa akan bukata ta tabiya,,kudi sune magana to da su zanyi amfani wajan kwatar wannan companyn."Abu na farko shine yanzu musan dukkan masu hannun jari a wanann company,,zan linka musu kudin da suka zuba,,idan sunki akwai wata hanyar duk wanda zan tunkara sainayi kwakwkwaran bincike akansa,,duk wani sirri daya boye baya son kowa ya sani zamu bankado shi,,kodai ka siyar da hannun jarinka ko kuma katsinci Abunda ka shuka a duniya.

"Murmushi Nasir ya saki,,kanka naja mutumina,,kaga dole uwar naki,,in mutum yana so ya tsira da mutuncin sa dole ya siyar da hannun jarin sa."Kwarai kuwa,,kin siyarwar na iya jawowa mutum babbar asara.Yanzu aikin yana hannun ka Nasir ka samo mun List din wadanda suka fi kowa zuba hannun jari a company ka kawon gaba na,,ni kuma.zanji da sauran aikin,,akwai yarana da zan baza sako da lungu na sirri kansu zai dawo tafin hannu na.Hannun Nasir ya mika masa suka tafa aikinka nakyau Habib,, Lumshe idanun sa yayi,,bazan taba gajiya ba harsai ranar dana tabbatar na samu SALAMAR ZUCIYA daga wanann ranar zan dawo rayuwa kamar kowa,,gyada kai Nasir yayi ba tare da yace komai ba.

"Kamar yadda ya nema cikin kwana biyu Nasir ya zube masa dukkan file din wadanda suka fi kowa hannun jari a company,,sosai ya duba yayi nazarin su mutum 30 cif aka kawo masa file din su,,jinjina yayi wa Nasir,,yanzu aikina zai soma abokina,,shima.Nasir martanin murmushi ya mayar masa.Phone dinsa ya dauka yayi dialling din wata number,,maganar 2minutes yayi ya ajiye,, office dinsa suka shigo su biyu ne da uniform ajikin su da alama ma'aikatansa ne,,cikin girmamawa suka gaida su,,nasir ne ya amsa Habib kuwa hannu ya daga musu,,files din gabansa ya tura musu,,cikin sati daya ina da bukatar ku binciko mun komai game da wadannan masu files ba,,bance kurage komai na daga abunda zaku samo akan suba."Angama yallabai daukar files din sukai suka fice.

"Nasir kallon Habib yayi,,yana mamakin irin tarin dukiyar da Allah ya bashi,,plaza plaza daya turo asiyamasa tunkan ya dawo Kano sunaki guda Goma,,bayan shaguna da Company daya ke dasu birjik,,ga companyn sàida motoci da yake dashi,,yana da tabbacin kodaga yau Habib yace ya saina neman kudi,,abunda yake dashi zai ishi iri irin zu'ar sa anan gaba,,da zaiji shawarar sa daya nemi ya yafewa Alhaji Sani laifin da yayi a gare shi,,amma yasan hakan bamai yiwuwa bane,,dole ne yaja bakin sa ya tsuke.

"Agajiye ya koma gida suit dinsa rataye a wuyansa ya fito daga motarsa fara tas,,hango Zulaiha yayi tana zance ya dan murmusa,,lalli yarinyar nan wai ita ma ta girma,,wucewa yayi batare da ya kara kallon su ba."Maine parlo ya shiga hango Oum a zaune tana kallo yasashi kara Sawa da fara'ar sa,,ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar dayake mata,,ganin yadda ya share shi sai sam haka beyi masa dadi ba,,muskutawa tai kafin ta kalle shi,,ina fatan kaga kanwarka awaje kafin kashigo?jinjina kai yayi alamar ya ganta,,to dama abunda nake so ka gani kenan,,kanwar bayanka gashinan ta kawo wanda take so sai kai gododo dakai ana fama dakai,,ina daf da daukar mataki akanka,,cikin jin haushin sa ta karasa Maganar,, murmushi kawai ya dan saki kiyi hakuri Oum.Siririn tsaki taja aikin kenan bani hakuri karike hakurin ka bazaiyi tasiri a tare dani ba.

"Ganin yadda ta harzuka sai yayi shiru yana kallon katuwar plasma din dake manne adakin,,azahiri dai idanun sa nakan TV din amma a badini ba ita yake kallo ba,,wani tunanin ya fada na daban,,ganin zaman bazai kaishi ko ina ba ya mike ya wuce part dinsa,,binsa da kallo tai tanai masa Addu'a a zuciyar ta.((Uwa kenan Allah ka karawa iyayammu Lafiya da nisan Kwana)).

"Kamar yadda Habib ya basu aiki kan satin ya zagayo sun samo masa dukkan bayanan su daya bayan daya,,sanda ya gama dubawa murmushin samun nasara ya saki,,jinjina yayi musu da hannun sa aikin ku yayi kyau,,durowa ya jawo dake manne ajikin table dinsa,rafar dubu dubu ya dakko guda biyu ya mika musu kowa daidai,,cikin farin ciki suka karba suna Godiya kamar zasu kwanta masa,,daga musu hannu yayi alamar babu damuwa zasu iya tafiya,,bakin su a washe suka fice bakaramin jindadin aiki suke da Oga ba saboda abun hannunsa be rufe masa idanu ba.Babu wanda suka nunawa suka sakaye kudin su a aljihu,,suna da tabbacin akwai wadanda zasuyi musu hassada yafi sauki suyi shiru da bakunan su.

Tattare dukkan bayanan yayi ya zuba su ahakar Laptop dinsa,,mikewa yayi ya dauki key din motar sa,,kai tsaye Plaza din Nasir ya nufa,,sanda ya shiga baya office din dan haka ya zauna ya jira shi,,yakai kusan 30mnt sanann Nasir ya shigo yana 'yar Dariya,,afuwan Oga nadan je wife ta bani abinci ne,,harara ya watsa masa shine kai wanann dadewar,,ko duniya zakaci ai sai haka,,dariya Nasir ya saki,,inma duniyar naci aiba laifi bane,,banza habib yayi masa ganin zai tafi wata maganar daban.Ganin yadda Fuskar Habib ta zaka serious shima saiya daidaita nutsuwar sa,,bayanan ya mika masa daya bayan daya ya dinga dubawa yana sakin Murmushi,,aikin yatafi yadda ake so,,yaushe zamu fara fita farautar su,,dan jim Habib yayi,,ranar Monday zamu fara binsu one by one,,ok hakan yayi Allah ya kaimu,,Habib ne ya amsa da Ameen.

"Wata hirar ta daban suka fada tsakanin su na aminan juna.
Kamar yadda suka tsara ranar Monday suka dira a office din Alhaji Usaini daya daga cikin masu kaso mafi tsoka na hannun jarin,,yana zaune yana aikinsa cikin Laptop sukai masa norking yes ya bada umar nin shiga.Dago kansa yayi dan ganin masu shigowar,,ganin zaratan samari ne ya sashi gyara zaman sa,,kallon su yayi duk babu na banza acikin su da alama customer din sane suka zo,,amma kuma ai besan suba,,yana wanann zancan zucin har suka zauna ba tare daya sani ba.Hannu suka miko masa sai Lokacin yayi firgigit ya dawo daga tunanin daya tafi,,mika musu nasu hannun yayi suka gaisa,,shiru ne ya ratsa na wani Lokaci.

"Kana daya daga cikin wadanda suke da kaso mafi tsoka a company Alhaji Sani,,gyada kai yayi kwarai kuwa,,dan muskutawa Habib yayi so nake ma siyar mun da hannun Jarin,,kallon baka da hankali Alhaji Usainin yake masa,,kasan nawa kuwa na zuba a wanann company"ban saniba saika fada,,cewar Habib daya tsareshi da mayatattun idanun sa masu matukar kaifi da kwarjini,,naira million 30 na zuba,,kallon juna sukai shida Nasir suka saki Murmushi"jin wai million 30 ya zuba shine har yake tada jijiyar wuya,,dan wannan ne abunda ka zuba?cewar NASIR da yake kallonsa dariya na cinsa,,bata fuska Alhaji Usaini yayi ganin sunan neman raina masa hankali,,dan furzar da hucin bakinsa Habib yayi,,na kara maka 30 million kaga zan baka 60 millions kenna.

Galala yake kallon su"kallon sama da kasa ya dinga yi musu,,shi zama aumayar mahaukaci,,banda bukatar kudin ku bazan sàida hannun Jarina ba.Daga kafada Habib yayi,,kana da zabi guda biyu kodai ka sàida a yadda muka bukata ko kuma kayi biyu babu babu kudi ba hannun jari,,afusace Alhaji Usaini ya mike,,kai bana son rainin wayo damme zaku dinga min wasa da hankali na,,bazan siyar ba kayi abunda zakai.Nasir miko mun file dinan,,babu musu Nasir ya mika masa file din,,turawa gaban Alhaji Usaini yayi,,kafara duba wannan saika yanke wa kanka hukunci,,kamar bazai zauna ba saidai ya zauna yana hura hanci,,Abunda yaci karo dashi a file din shiysa hankalin sa mummunan tashi,,gumi ya fara sharewa yana tunanin agidan ubanwa suka bankado wanann sirrin nasa,, case din da aka dade da shafe shi,wama yasan dashi,,case din fyade ne da dansa yayiwa wata yarinya ashekarun baya.Wani munafikin murmushi ganin yadda yake yarfe gumi,,to yanzu waka zaba Alhaji Sani ko danka?bakin sa na rawa ya furta dana nazaba,,dariya Habib ya fashe da ita wadda ya jima beyi irinta ba,,dukan kafadar Alhaji Usaini yayi kayiwa kanka gata mutumina.

"Ka tabbatar ba daka nazo na tinkare ka ba,,sài dana tabbatar na dana maka tarko,,dan ina da yakinin akwai wadanda arziki na binsu suna gudu,,a take awajan ya rubutawa Alhaji Usaini cak na kimanin 60 millions,,zugudi Alhaji yayi yana mamakin takadirancin wadannan matasa,,kudin ya kurawa ido yana san tabbatar wa kardai ko yahadu da 'yan damfara ne ba tare daya sani ba.

          Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
           ......✍️✍️✍️✍️


        SALAMAR ZUCIYA

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris



*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Short Story

Page 5

"Bin su yayi da kallo sanda suka mike suka fita,,haka suka dinga zaryar bin dukkan masu hannun jarin,,wasu lokaci daya suke yadda,,wasu kuma sai anfafata kafin su amince,,cikin wata daya Sàida komai ya kammala,,kaso mafi girma ya koma na Habib gaba daya wanann abunda ke faruwa Alhaji Sani besan abunda yake faruwa ba sam,,baya ma kasar gaba daya koda wasa be samu labarin ba.Akwai taron da yakeyi da masu hannun jarin sa duk karshan shekara,,sosai Habib ya tamawa wannan taron da za'ayi,,ya shirya tsaf shikadai yasan gadar zaran daya sakawa Alhaji Sani,,oho bema san yana yi ba,,saboda har yanzu besan dashi ba.

"Yau take Monday"Monday tushan Aiki,,ko nasara na tsoranki,,tsaf ya shirya cikin dakakkiyar shaddar sa meruwan makuba,,sosai tafito da ainihin kalarsa na black beauty,,yana da dara daran idanu,,Kamar sa daya da Oum sàida ta nuna masa haske,,pepas ya tattara ya saka awata 'yar karamar bag me kyau irin ta maza.Karfe 9 ya fito ya shiga wajan Oum tana zaune tana azkhar ta bishi da kallo,,sai ina kuma ta jefa mai tambayar tana kallon sa,, murmushi yadan saki,,zamu fita Oum asamana albarka,,yau akwai wani Aiki da mukai jima muna fatansa yau zai fara tabbata,,kallon sa ta danyi tana nazarin Maganar sa,,to Allah ya bada sa'a yasa a fara a sa'a"murmushi ya saki yana jindadin Addu'ar ta,,ameen Oum.Mikewa yayi yana daga mata hannu,,ajiyar zuciya ta sauke tana binsa da kallo.

"Gidan Nasir dake rumfar Shehu ya biya danya dauke shi,,yana gida befita ba,,hon yayi megadi ya wangale masa get din,,saidaya daidaita parking sannan ya fito,,wayar sa ya ciro ya dokawa Nasir kira,,kai dan Iska kafito kasan muna da aikinyi,amma kashiga gida ka makale,,ayau dole ka shigo kugaisa da madam nayi mata Alkawarin yau zaku gaisa,,dan jim yayi yana kallon wayar tasa,,ok ya furta yana maida wayar sa aljihu.Door bell ya danna Nasir da kansa ya tashi ya bude masa kofa,,Harara ya watsa masa,, murmushi kawai Nasir din ya saki wai Meyasa baka son zuwa gidannan,,kawai ya fada yana kallon wani barin daba,,kan sofa suka karasa Habib yanai yaba yadda aka tsara Gidan yayi kyau sosai.Sai kaxo miyi breakfast dama yanzu muke shirin yi,,a koshe nake,ai baka isa ba ya zama dole yau kaci abincin wife.

"Fitowa tai hannun ta dauke da flaks din tea da murmushi ta karaso,, lallai yau babban aboki ne yazo Gidan namu,,kema kya fada Habibty,,kara tamke face Habib yayi dan karma yarinya ta rainashi,,zama tai tana gaidashi kadaran kadaham ya dinga Amsawa,,kutaso na hada muku breakfast,mikewa Nasir yayi yana kallon Habib dan Allah ka taso kanai mana asarar time fa,,mikewa yayi badan yaso ba suka karasa dining din.Bawani abun kirki ya ciba ya mike ya koma kan sofa,,Nasir bece mai Komai ba dan yasan halin sa sarai,,yana gamawa ya mike ya dauki key din motar sa,,aibasai kafita da mota ba Alhaji zumudi a tawa zamuje.

"Dariya Nasir yadan saki yana girgiza kai,,sai akace kuma bazan dauki key ba sai zan shiga mota,,wai yaushe ka koyi korafi ne,,banza habib yayi masa yayi waje batare dayayi sallama da Nafisa ba wadda take kule acikin daki,,Nasir ne ya shigo wajan matar sa sukai sallama sannan yabi bayan Habib."Sharada suka nufa company robobi na Alhaji Sani anan sukai parking,,fitowa sukai ma'aikata sai shige da fice sukeyi.Ayau ne kuma yake taron masu hannun Jari a companyn sa ba guda daya ba dukkan masu hannun jarin yake tattarowa su zauna dan su tattauna.

Awani babban parlo akeyin taron kowa ya hallara,,akallah mutanan cikinsa sunkai mutum dari Biyu,,kujeru ne reras aka jera su sunyi matukar kyau da tsari."Alhaji sani ne a gaba sai masu take masa baya,,shigowa yayi face dinsa awashe yana kallon abokan kasuwancin nasa,,kujarar daya saba zama nan ya nufa ya samu ya zauna,,amma Abunda ya girgiza zuciyar sa,, manager daya matso yayi masa bayanin yanzu fa bashine da mafi kado me tsoka na hannun jarin ba saidai ya koma Inda kowa yake azaune,,sakare yayi yana kallon manager anya kunann sa yaji masa daidai.

"Bece komai ba ya mike ya koma inda sauran suke,,nanfa kallo ya koma sama,,wadanda sukasan da Maganar basi wani mamaki ba,,wadanda aikin Habib beje ta kansu ba sune suka fara cece kuce,,bangaran Alhaji Sani gaba daya kansa ya kulle besan wane tunani zaiba,,har yaushe wani ya siye hannun jari batare daya sani ba,,tagumi ya zabga yana kallon kowa d'ai d'ai,,inya kalla dai dai kamar dariya yaga wasu sunai masa dariya,,gyara zaman sa yayi dan ganin wanda yayi masa wannan aika aikar.

"Manager ne ya mike yana sanar da yanzu wadda yafi kowa hannun jari a wannan Company zai shigo dan ya gabatar muku da kansa.Tsit sukai masu 'yan kus kus aka daina.Shine a gaba Nasir yana yake masa baya,,face dinnan a dinke take tsaf babu alamun dariya a kan face dinsa,,kujerar Alhaji Sani ya d'ane yana kallon face din Alhajin sànin wani murmushi Habib din yake saki,,da gani kasan na tsokanane da neman fada."Tunda ya shigo Alhaji Sani yake binsa da kallo yana tunanin a ina yasan wannan fuskar,,kasa tunawa yayi ganin zai wahalar da kansa abanza.Mikewa Habib yayi ya gabatar musu da Kansa"Sunana Habibullah Aliyu"shiru ya danyi yana maida Numfashi,,kamar yadda suka sukai shiru suna kallon sa,,yadda suka ganshi matashi amma ya iya fidadda makudan kudade ya siye hannun jarin wasunsu da dama.

"Na shigo wanann company badan komai ba sai dan bincike akansa,,kallon kallo suka farayiwa junan su musamman Alhaji Sani daya ji maganar kamar saukar aradu,,tabbas abinda kukaji na fada to hakan kunnuwan ku yaji muku daidai.Tabbas wannan company an same shi da al-mundahana,,da sauran wasu munanan ayyuka da ake aiwafarwa a cikin sa,,saboda haka akwai yiwuwar rufe wannan company gaba dayansa.Zumbur Alhaji sani ya mike yana nuna Habib da hannun sa,,tsabar bacin rai ya kasa magana,,ganin wani karamin yaro yazo yanasan tarwatsa shi,,mekake nema agare ni da kake son tarwatsamin kasuwanci na? Ko Kasan ni wanene!!!? Cikin fushi Alhaji Sani ya karasa Maganar sa,,kafada Habib ya daga badakai zanba amma hukuma ce zata tabbatar min dakai wanene.

Bekara furta komai ba,,ya sauka daga step din da yake kai Nasir ya bishi abaya.......
   
Tofa!! Ana wata gawata.Wai menene tsakanin Habib da Alhaji Sani,,tabbas wannan dadaddiyar gaba ce,,nima sanin musababbin ta nake,,Kubiyo ni mu nutsa cikin labarin danjin yadda zata kaya.

     Taku har Kullum
      Kulsoom Ismail Idris
      Mrs Baba ikon Allah
     .......✍️✍️✍️✍️


        SALAMAR ZUCIYA

Written and Narrated 

By Kulsoom Ismail Idris

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Short Story

Page 6

"Zuciyar Habib fes suka fice daga Company,,babu me Magana acikin su,,sai Habib dake sakin murmushin samun nasara,,yau ya hango tashin hankali da damuwar da yayi shekaru yana fatan gani a fuskar Alhaji Sani,,yau zuciyar ta fara samun salama da aassauci akan baya,, Lumshe idanun sa yayi yana sakin ajiyar zuciya."Bantaba zatan akwai ranar da zanga razani da firgici akan fuskar Alhaji Sani ba Nasir,, murmushi Nasir ya saki babu abunda ya gagari Allah duk wanda ya zalinci dan uwansa tofa akwai ranar Sakamako,,zalinci duhu ne kuma Allah yana amsa Addu'ar wanda aka zalunta.

"Gyada kai Habib yayi ba tare da yace komai ba."Hankali tashe yake danna hon a tangamemen gidan da dake rijiyar zaki,,da sauri get man ya wangale masa kofa aguje ya shiga ko gama parking beyi ba ya balle murfin motar ya fito,,babbar rigar sa har neman tade shi take yana kara janta sama,,Sanda ya shiga maine parlo babu kowa sai karar AC da tv da take ta burari ita kadai,,zama yayi jagwaf ya cire hular kansa,,gaba daya kansa ya kulle,,mene alakarsa da wancan yaron,,wanene shi?meyake nema agare shi?waya aiko shi danyaga bayan sa?bashi dame bashi wannan amsar saidai shi kansa Habib din,,amma ta ina zai fara neman sa danjin wane laifi ya aikata masa haka.

"Hajiya Halima da sakkowarta kenan ta hango Alhaji Sani cikin tunani me tarin yawa da damuwa,,da sassarfa ta iso gare shi,,Alhaji lafiya kuwa kaga yadda kake gumi kamar wanda kunama take harba,,ajiyar zuciya ya saki kyaleni Halima da wanann masifar datake tumkaro ni na gwammata kunamar ta kwana tana cizo na.Innalillahi yanzu Alhaji me yayi zafi haka shiba wuta ba kasan zafin harbin kunama kuwa?ke kinsan zafin talauci kuwa?shima ya jefa mata tambaya,,tsuru tai tana kallon sa ganin yadda idanun sa sukai jajawur,,kayi hakuri Alhaji komai yayi zafi maganin sa Allah."Kasanar dani abunda yake faruwa,,gyara zaman sa yayi ya gaya mata abunda ya faru,,shiru tai tana nazarin kalaman sa,,kuma Alhaji babu wani abu daya taba hadaku,,tabbas kalamansa sunyi kama da name daukar fansa.Girgiza kansa yayi bantaba sanin saba Halima,,hasalima yau na soma ganin sa.

"Amma abunda mamaki amma Allah zai kare mu daga sharrin sa,,tunda har katabbatar babu wani abu daya taba hadaku dashi Allah zai karemu daga mugun mufinsa,,ina fatan hakan,,Alhaji Sani ya furta gwanin ban tausayi."Bangaran Habib be huta ba cikin sati biyu sàida ya shiga ya fita aka rufe companyn Alhaji Sani,,rufewa ta dindin.Ranar kamar Alhaji Sani zaiyi hauka besan Sanda ya fashe da Kuka ba kamar karamun yaro haka ya tasa Hajiya Halima yana Kuka shabe shabe,,ita ma kukan take tare da Addu'a Allah ya basu juriya da dangana.Yaran su guda uku ba wasu manya bane suma kukan sukeyi ganin yadda iyayansu ke cikin tsananin damuwa,,tabbas duk abinda ya sasu Kuka ba karamun abu bane.

"Habib farin ciki kamar zai ciki kunnan sa,,amma duk da haka bafa ya huce bane be hakura ba,,saiya tabbatar da kudurin sa,,saiya tabbatar da muradin sa,,aranar zai samu SALAMAR ZUCIYA.Haka Alhaji Sani ya dangana ya cigaba da kasuwan cinsa ya manta da Maganar rasa company dinsa.

"Yau Oum tun safe kanta ke matsanan cin ciwo damuwa tayi mata yawa,,ta rasa inda zata tsoma ranta,,Habib yaki yayi Aure ta rasa me yake nufi da rayuwar sa,,me yasa yake son mutane su fara wani tunani daban akansa.Kafin yamma jikin ta yayi tsanani sai suma take saboda zafin Zazzabi da yayi mata rufdugu,,babu shiri aka kwasheta sai hospitals,,sosai aka taru akanta dan shawo kan matsalar da take damunta,,gwajin farko aka tabbatar jininta ne ya hau dalilin damuwar data sanya aranta ya zama dole a magance abunda yake damun ta."Shiru Habib yayi yana kallon Doctor din jikinsa a sanyaye ya taso ya fita saboda gane abunda Oum din take bukata wato Auransa,,zuma mata idanu yayi yana kallonta.

"Dama har yakai damuwar haka na san ganin saiyayi Aure,,Meyasa takeson yayi Aure haka,,shekarunsa nawa da zata daga hankalin ta,,su Zulaiha na zaune sun zuba tagumi basu san musababbin cutarta ba."Sosai Habib ya shiga damuwa me tsanani yarasa Indai zai bullowa lamarin,,a yanxu dai an sallamo Oum kuma har yanxu bata daina tunani ba damuwa takasa barin ranta.

"Suna tafe amota shida Nasir,, tattaunawa suke akan matsalolin su,,sam basu lura da wani yaro daya taho da gudu zai tsallake titi,,da sauri Habibullah ya taka wani Uban burki,,sàida motar tai baya Kamar zasu kifa haka suka ji,,ajiyar zuciya suka sauke ganin basu taka Yaron ba,,wata matashiyar Budurwa ce ta taho da sauri.Abdul bakaji ciwo ba kamma hannunsa tayi tana talle masa keya,me shegiyar funtuna sai aita faman kiranka kana ji,,daya takaka ai shikenan,,kurawa yarinyar idanu sukai kafin su kalli juna shida Nasir,,ajiyar Zuciya suka sauke,,dan kallon Nasir ya karayi anemomin wacece ita.

"Sakare Nasir yayi yana kallon sa,,balle murfin motar yayi ya fice tare da kallon Nasir zan hau napep na koma gida ina son jin labari medadi,,gaba yayi NASIR ya bishi da kallo,,daga ganin 'yar mutane kace anemoma wacece ita,, murmushi yadan saki ba mamaki ya fada farkonta ne.Jan motar yayi ya bisu abaya dan ganin inda zasuje.

     Mrs Baba Bello Abubakar
        .......✍️✍️✍️✍️


    SALAMAR ZUCIYA
    
    Written and Narrated
    
    By Kulsoom Ismail Idris
    
    Short Story
    
    *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "



Page 7
    
    "Kamar yadda Habib ya nemi Nasir ya binciko masa wacece wannan yarinyar ya binciko Komai akan ta,,cikin Farin ciki ya koma gidansa,,sai bayan Sallar La'asar ya tafi gidan su Habib,,har part din Oum ya shiga yayi mata Sannu da jiki,,kafin ya karasa part din Habib dake kwance akan sofa,,dukan kafadarsa Nasir yayi tashi mitumina akwai daddadan story,,Mikewa Habib yayi yana sakin Murmushi,,bannasha.Gyara zama Nasir yayi,,sunan Yarinyar Aneesat Mahaifinta Umar ma'aikacin gwamnati ne basu da wani karfi,,suna dai da rufin asiri,,bata da yayye sai kanne ita ce babba agidan su.Amma meyasa kanemi sanin wani abu akan ta,,saboda ina son Auranta amma bawai dan ina santa ba zan Aure tane saboda hankalin Oum ya kwanta,,tadaina tunanin cewa nakiyin Aure.Murmushi Nasir ya saki,,zakai dan Oum kodan kanka malam kafito kafadi Abunda ke zuciyar ka na kasamu matar da kake so,,banza Habib yayi dashi kamar beji shiba.
    
    "A ranar ya samu Oum da daddare ya sanar da ita ya samu matar da zai Aura,, Oum kamar ta zuba ruwa akasa tasha dan farin ciki,,sai albarka take sa masa(tunkafin yaje neman Auran ya fara shelar ya samu matar Aure)ranar Oum baccin farin ciki tayi zuciyar ta fes,,zata samu SALAMAR ZUCIYA nayin Auren da zaiyi."Washe gari shida Nasir har gida suka iske mahaifin Aneesat,,duk da be sansu ba yayi musu tarba ta mutumci,,bayan gaishe gaishe suka fadi abunda ke tafe dasu,,bayan ya gama jin bayanin su shiru yayi yana nazarin Maganar su.Numfashi ya sauke kafin ya kalle su,,Hakika naji dadin Maganar da kuka zo da ita,,amma yanzu bazan ce komai ba sabo Akwai wanda yake zuwa wajanta yana gaf kuma da Kawo kudin auren sa.

"Tsit sukai suna sauraron sa"nawa kake bukata kafada daga kan naira million daya zuwa million dari"ni Auran ta kawaii nake bukata ko nawane zan iya kashewa akan Auran ta,,shiru mahaifin Aneesat yayi yana mamakin yadda yaron yake da hamasar cewa zai bashi wani abu,,million dari yake maimaitawa a Zuciyar sa,,kuje zanyi tunani akan hakan,,mikewa sukai sukai masa sallama ya bisu da kallo."Sanda ya shiga gidan Mahaifiyar Aneesat tana tsakar gida,,yadda taga mijin nata ya shigo ba walwala a face dinsa yasa tasan ba kalau ba.Dan karamin dakinsa ya shiga ta mike ta bishi,,a bakin katifa ta ganshi azaune ya rafka tagumi,,lafiya Abban Abdul,,ajiyar Zuciya ya sauke ina fa lafiya,,ina cikin rudani anzomun da wata magana wadda nake ta tunani akanta.

"Gyara zaman ta tayi wace magana ce wannan"sanar da ita yadda sukai da su Habib yayi,,shiru tai tana nazarin kalaman sa,,mekace dasu kaidin,,nace suje zanyi tunani,,Allah ya zaba abunda yafi zama Alkhairi,,ameen ya amsa jikinsa a sanyaye."Gaba daya abunda ake ciki Aneesat bata sani ba,, kyakykyawar yarinya ce black beauty tana da dara daran idanu kamar mejin bacci haka idanun ta suke,,tana da gashin gira da gashin kai,,komai nata ma sha Allah.

"Habib be fasa zuwa wajan Mahaifinta ba harsaidaya amince dan dole dan gaba da gabanta"Sanda Mahaifinta ya sanar da ita Kuka ta fashe Dashi akan ita bata sanshi,,barin ta yayi awajan ya fita daga gidan,, Mama ce ta kalle ta,,haba Aneesat yanzu dan Mahaifinki ya nemi wani abu daga gareki zaki zauna kina wanann kukan,,tunda aka haifeki yake dawainiya dake meyasa bazaki yi masa biyayya ba?ki daure kiyi masa abunda yake bukata Allah bazai taba bari ki toxarta ba matsawar kinwa iyayanki biyayya,,jikinta ne yayi sanyi saboda tunatarwar da Mama tai mata,,zanyi abunda kuke so mama,, murmushi Maman ta saki,,Allah yayi miki Albarka.Ameen ta amsa cikin sanyin murya.

"Ranar da Abbanta ya sanar da ita Habib zaizo kamar taita rusa ihu amma haka ta daure batai dinba,,karfe 5 na yamma yazo har kokaf gidan su,,yana cikin motar sa ta fito jikinta sanye da dogon hijab,,fuskar nan tata a cunkushe kamar bata taba dariya ba,,da sallama tashiga gaban motar gaba daya murafan motar a bude suke,,tunda ya amsa sallama da kyar be kara furta komai ba,,mamaki da takaici ya gama kamata,,ahaka zata Auri wanann mutumin kalli yadda yaba banza ajiyar ta,,tagama kuluwa iya kuluwa,,fitar mun daga mota zantafi,,galala ta tsaya tana kallon sa,,afusace ta fice daga motar ta bugo masa murfin motar,,Binta yayi da kallo yana jan tsaki,,badan Oum ba mezaisa yazo wajan wata mace mema zai ce mata.

"Sanda tashiga gida kuka tafashe Dashi"ni wllh Mama bazan iya Auran wannan mutumin ba"kina ganin tunda nafita ko kallona beyi ba,, murmushi Mama ta saki,,to banda abinki Aneesat ai kece zaki canza shi,,kefa macece mene Amfanin baiwar da Allah ya yi mana mu mata,,duk miskilancin Namiji mina iya sauya shi,,kiyi hakuri watarana zakice na gaya miki zaki juyashi kamar waina ba boka ba malam,, zumburo baki tai tana jin Maman amma fa baji a zuciyar ta waccan dan girman kan zai sanja ba.Haka Mama ta dinga rarrashin ta har zuciyar ta tadanyi sanyi.

"Sosai ake shirin Biki"kudi bana wasa ba ya bawa Oum a hado kayan lefe,,akwatuna 6 Oum aka cika da kayan Alfarma,,mahaifin Aneesat Kuwa,,makudan kudade ya bashi yaja jari ya hada da wata sana'ar,,Nasir ne akan harkar bikin dan Habibullah ya koma gefe ba karamin jin haushin Auran yakeyi ba,,'Yan uwa sukadai suke zumudin su,,tare da bikin Zulaiha za'a hada shiyasa abubuwa suka kacamewa Oum.Ankai kayan Lefe kuma iyayan Aneesat sun yaba sai ma sha Allah,,komai yayi sai san barka,,sati biyu aka saka wanda za'a biki.Nafeesa itama tazo gidan bikin matar Nasir da ita akeyin komai.

"Anfara Biki gidan Amarya da gidan Ango ko ina acike yake anata hada hada,,anci ansha kowa yasan yazo Biki,,ankawo Amarya,,ankaita wajan Oum tayi mata Nasiha kafin afita da ita amikata gidan ta,,Inda ya dankara nasa gidan yana jikin gidan Oum ba gida daya zasu zauna ba."Amarya Aneesat tun tana jiran Ango ya shigo hartai bacci sàida asuba ta farka taga ya ajiye mata ledar kaji gasassu sai drinks data gani birjik.Haushi kamar zai kasheta Lallai ma wannan dan rainin hankali ne,,bangaran sa babu abunda ya same shi dama dan Oum yayi Auren yanzu hankalinta ya kwanta.

"Tsakanin sa da Aneesat gaisuwa ce take hadasu,in yaga damar amsawa in bega dama ba ma bazai amsa dinba,,tun tana damuwa harta ware ta saba da halinsa,,saitaci gaba da rayuwarta ita ma ganin zata kashe kanta akan wanda bedamu da ita ba,,data gama ayyukanta take tafiya wajan Oum acan take wuni nanne yake debe mata kewa,,sosai Oum ke kaunarta tamkar diyar cikinta haka take janta,,sam bata ganin ta amatsayin surukar ta.

        Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
         .....✍️✍️✍️✍️✍️


      SALAMAR ZUCIYA

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris



  *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Short Story

Page 8

"A wanann Lokacinne ya koma kan Alhaji Sani dama bawai ya manta dashi bane"àah ya barshine ya sarara yanzu kuma hankalin sa ya dawo kansa gaba daya,,dukkan harkokin da Alhaji Sani keyi saidaya shiga ya fita ya tarwatsata,,saidata kai ta kawo babu wata kadara da Alhaji Sani zai kalla yace wanann kadarar sa ce,,rayuwa fa tafara yi masa zafi,,ga kananan yaransa da basu saba da rayuwar wahala ba,,dan danan suka fara ramewa suka,,haka matar sa Hajiya Halima sosai tashiga matsanan ciyar damuwa kamar zararru haka suka koma.

"Manager din Bank Habibullah ya samu akan yaje ya bawa Alhaji Sani bashin banki da nufin ya juya ya samu nasa aciki,, manager yaso yayi jayayya amma da Habib ya cillamasa 10million sai gashi yayi gum da bakinsa,,aguje ya bazama gidan Alhaji Sani dan aiwatar da Abunda Habib din yake so.Sanda ya samu Alhaji Sani Sani da maganar karbar bashi kin yadda yayi,,cewa yayi taya zai samu kudin dazai biya su,,cikin dadin baki yace ai bayanzu za'a karbi kudin ba kabada wanann gidan naka jingina,,da zarar kabiya kudin shikenan,,ganin Alhaji Sani baida wata madafa ya yadda ya karbi bashin banki maukadan kudade gidansa matsayin jingina inya biya kudi gida ya zama nasa.

"Cikin Nasara Alhaji Sani ya fara harkar kasuwan ci,,dandanan kasuwa ta fara bude masa,,ya fara samun kudade hankalinsa ya fara kwanciya dana itayalansa sun shiga rayuwar jindadi.Wata 6 da fara harkar Alhaji Sani Habib ya samu dukkan wasu customer da zazzafan gargadi su cire hannunsu daga bawa Alhaji Sani kaya,,haka suna ji suna gani suka daina harka dashi,,hankalin sa sosai ya tashi awanann time kuma manager yazo da bukatar a bawa bank bashin data bayar.Rasa Inda zai tsoma ransa yayi yaji dadi gaba daya jiyake duniya tana juya masa,,rayuwa tadaina yi masa dadi."Bashi da kudin biya dan haka Bank ya bashi nanda wata 3 har aka cinye wata 3 bebiya ba,, notice aka bashi na sati daya su tashi daga gidan,,satin na cika akazo da ma'aikata suka fidda musu kayansu waje suna Kuka suna komai suka fece daga gidan.

"Matar sa gidansu tatafi ga ita da 'yayan ta,,shi kuma baida wajan zuwa baida wajan kwana,,sai wani makwafcinsa ne yaji tausayin sa ya bashi wani kwango da ba'a gama ginawa ba yadinga kwana aciki"dandanan Alhaji Sani ya koma kamar mahaukaci yayi duku duku dashi,,sai mutane ke taimaka masa nacin abinci,,nan ma bata canza zani ba Habibullah ya aikowa masu shaguna kodai sudaina taimakonsa ko ya maida su kamar yadda ya mayar dashi ayanzu,,kowa yana son dukiyar sa sai suka daina bashi.

"Ranar wata Laraba sun fito shida NASIR suna tafiya kamar ance ya daga kansa ya hango Alhaji Sani yana bara akan titi,,da sauri ya taka burki ya zuge glass tabbas shine,,dariya ya fashe da ita,,kalli Nasir bara yakeyi,,wllh bara yake kamar tababbe haka habib ya koma sai tikar dariya yakeyi.Zuciyarsa fes kamar takadda,,jan motar Nasir yayi ganin yadda mutane suka fara kallon su.Motar data faka gaban Alhaji Sani ita tasa ya juyo yana kallon me motar,, Alhaji Shehu,,dama kuna Duniyar nan kalli yadda na koma,,abaya na taimaki mutane da dama amma a yanzu na rasa me taimakona.Ajiyar ZUCIYA Alhaji Shehu ya sauke karkaga Laifin kowa Alhaji Sani"abu daya zammaka na sanar dakai wanda ya maidaka haka,,kuma kamar yadda yasha alwashin duk wanda ya taimakeka abakin tasa dukiyar shiyasa muka janye jikimmu.Akwai wani yaro habib shine wanda ya maidaka haka,,tayiwu akwai wani abu atsakanin ku,,kayi gaggawar zuwa ka same shi ya yafe maka abunda kayi masa dan banajin ba wani mummunan laifi ka aikta masa ba.

"Alhaji Sani da yayi sakare yana sauraron sa"a ina zan same shi balle na nemi yafiyarsa duk da bansan abunda na aikata masa haka ba ya kashen rayuwata."kwatanta masa gidan Habib yayi godiya sosai Alhaji Sani yayi masa."Karfe 4 daidai Habib yana zaune a harabar Gidan sa,,Alhaji Sani ya shigo da kyar ya samu masu gadi suka barshi yashigo,,hango Alhaji Sani da habib yayi mikewa yayi afusace,,uban wanene ya shigomin da wannan Gida,,yadda yake masifa sàida masu gadin suka tsorata,, Aneesat data zo kawo musu ruwa shida NASIR sakare tai tana kallon sa.Alhaji Sani fashewa yayi da kuka tare da durkusawa akan guiwiwinsa,,wllh ni bakomai ne ya kawo niba saidan jin abunda na aikata maka kake bibiyar rayuwata haka,,na hadaka da girman Allah kayi hakuri ka yafe mini,,boll Habib yayi da table din gabansa,,cikin fusata ya kwallawa karensa kira tiger,,da gudu ya fito maza ka raka wannan mutumin,,ganin yadda karen yayo kansa yasa Alhaji Sani tashi ya juya da gudun gaske karen ya bishi a bays.

"Dariya Habib ya saka zama yayi yana babbaka dariya,,kafin kuma ya fashe da Kuka,,yau na samu SALAMAR ZUCIYA ayau Zuciyata ta 'yantu daga radadin da takeyi,,ina cikin farin ciki,,mikewa yayi Nasir zai bishi a baya ya dakatar dashi,,ina san kadaici a yau Nasir kaima kaje kai naka farin cikin,,fadawa yayi motar sa,,shikadai ya fita ba tare da kowa ba.Aneesat bayan ta koma parlo zagaye take tayi,,tana tunanin abunda Habib ya aikata menene dalilin sa,,dole tasan Abinda ke tsakanin mijinta da wannan mutumin,,mutum daya zata kira ya sanar da ita menene tsakanin su,,shine Nasir,,da sauri ta dakko wayarta takira NASIR akan dan Allah yazo.

"Ba jimawa ya karaso maine parlour,,da sauri tatareshi zatai magana,,nasan abunda zaku tambaya bai wuce abunda kikaga Mijinki yayi ba,,tom yau zan sanar dake abunda ke tsakanin su shin hukuncin da Mijinki ya dauka yayi dai dai ko beyi dai dai ba......

Ku biyo ni danjin wani Laifi Alhaji Sani ya aikata masa.

       Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
        ......✍️✍️✍️✍️✍️


     SALAMAR ZUCIYA

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris



*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Short Story 

Page 9

Zama Nasir yayi yana kallon Aneesat data matsu taji me zaifito daga bakin sa"numfashi yadan sauke nawani Lokaci."Banzaci zaki nemeni tun yanzu akan Wannan Maganar ba dan yayi wuri ace harkin kosa dan jin menene alakar Alhaji Sani da Habibullah"amma yanzu zan sanar dake wanene Habibullah,,menene kuma musababbabin abunda ya hada su har Mijinki ya dauki wanann matakin,shin yayi daidai abunda ya aikata ko ya zarce makadi da rawa.

     Waiwaye

"Malam Aliyu shine Mahaifi awajan Habib da kannasa guda biyu Saif da Zulaiha"Malam Aliyu ma'aikacin gwamnati ne bashi da wani karfi haka ake gurgura rayuwar"agidan haya suke da dadi daba dadi ake samun abunda za'a ci"Mahaifiyar su ita kadaice awajan Malam Aliyu wato Oum."Wata ranar Alhamis aka dawo da Malam Aliyu ranga ranga daga wajan aikin su bashi da lafiya,,abunka da talaka haka akadinga jelen zuwa asibiti,,magani aka dinga bashi wanda ba'a rasa ba,,hankalin Habibullah ba karamun tashi yayi."Bayan sati biyu Allah ya yiwa Malam Aliyu rasuwa.Sun shiga matukar tashin hankali sunyi Kuka kamar ba gobe,,haka suka hakura suka dangana,,abunka da zumuntar zamani kowa daga shi sai nasa yasa bawani taimako suke samu ba.

"Lokacin da Mahaifin Habib ya rasu muna Mungama Nd 1 zamu shiga Nd 2 a nan management."Buga bugar neman abinci wanda zai kaiwa kannan sa sai yazamana zuwa makarantar ya fara gagarar sa,,abunda yasa ya yanke shawarar daina zuwa makaranta babu kudin registration ta abunda za'a ci akeyi.Sanda ya sanar da Nasir zai daina zuwa makaranta nan shima Nasir yace zai daina zuwa bazai iya zuwa yabar Habib a gida ba,,da kyar Habibullah ya shawo kansa akan yaci gaba da karatun wata rana zai Musu amfani karatun,,badan Nasir ya soba yaci gaba da zuwa makaranta.

"Suna zaune a dan tsakar gidan su"duk da gidan hayane amma su kadai ne acikin Gidan,,sallama sukaji anayi a kofar Gida Habib ne ya fita dan ganin wanda yake yin sallamar,makwafcin su ya gani tsaye a kofar gidan cikin girmamawa Habib ya gaida shi dan zai kusa sa'an Mahaifin sa.Da fara'a ya amsawa Habib din da tambayar sa ya Umman sa da kananan sa yace suna lafiya.Dama in badamuwa ina son nai Magana daku ne kaida Umman ku,,babu komai bari ba kira ta,,shiga gidan yayi ya sanar da Oum makwafcin su nasan magana da ita,,mikewa tai dama da hijab ajikinta Allah yasa muji Alkhairi Ameen Habibullah ya amsa yana yin gaba."Habibullah ne ya leka akan ya shigo zaure ga Umman,,bayan ya shigo sun gaisa yake sanar da ita dama gani yayi da zaman da Habibullah yakeyi ba sana'a mezai hana tunda shi aikin gini yake in yasamu aiki yazo sudinga tafiya da Habibullah.Sosai Fuskar su ta cika da farin ciki,,Oum godiya ta dingayi masa haka Habibullah sinji dadin jin wanann maganar daga bakinsa,,yadda yaga suna farin ciki sai shima yaji dadin hakan,,sallama yayi musu har waje Habibullah ya rakashi yana sake yi masa godiya.

"Kamar yadda ya fada bayan kwana Biyu Malam Habu magini yazo dan sutafi da Habib,,ranar farko daya dawo da kyar yayi bacci saboda ciwan jiki,,tun yana ciwon jiki harya fara sabawa,duk da ba'a saboda wahala haka yadinga rarrafawa yana futa yana samo musu abunda zasu ci."Haka watanni suka dinga tafiya makaranta ta gagari Habib saidai Nasir yaje.Dan danan Habib yayi duhu yayi baki saboda wahala aikin gini ba karamar wahala bace kullum Oum tana tausaya masa sosai,,yana dawowa zata dora masa ruwan zafi yayi wanka kafin yaci Abinci,,bayan yaci Abinci ya shafa man zafi saboda yadda jikinsa ke masa ciwo sosai.

"Yakai kusan wata 7 yana aikin gini."Suna zaune shida Malam Habu ya kalli Habib,,Habib kaga aikin gini kararwa mutum karfi yake,mezai hana kadinga tara kudi koda kadan kadanne ka sami wata sana'ar,,shiru Habib yayi yana tunanin maganar sa,,Hakane Malam Habu kayi gaskiya,in sha Allah zandinga samun ko yaya ne ina dan tarawa.Koda yaje gida haka ya sanar da Oum tayi na'am sosai da shawarar sa,haka yadinga tara kudin sa da kadan kadan Nasir yake bawa yana ajiye mai,, ahankali suka dinga ta taruwa.Sanda kudin suka dan taru da yawa suka zauna shawara shida Nasir akan sana'ar da zai farayi."Nasir ne ya danyi jim yana tunani me zai hana ka fara yin takalma na fata,da gyaran takalma kaga dama can baya muntaba koyan irin wannan sana'ar."Murmushi ya saki yaba Nasir hannu suka taba,shiyasa nake sonka mutumina ka kawo shawara me kyau.

"Wani waje suka tambaya akan titi da Allah ya taimake su suna tambaya aka basu wajan da taimakon Nasir suka buga rumfa inda zai dinga zama yana yin takalman."Sàida suka sai komai da dan jarin dayake hannun su,,yafara cikin sa'a ya fara samun gyaran takalma,sai yafi samun gyaramma akan yin sabon."Dan danan Allah ya fara dafa masa abincin da zasu ci yadaina gagarar su"Habib bakin da yayi yadan fara washewa,, kullum Nasir in yadawo daga School wajan Habibullah yake tahowa da yake shima ya iya gyaran takalman sai yake taimaka masa.

"Misalin karfe 2 na rana yana zaune a rumfarsa,,aikinsa yake ka in da na'in,,sallama yaji ammasa wadda tasashi daga kai yaga me sallamar,,wata kyakykyawar budurwa yagani daga yanayin kayan dake jikinta kadan babu wahala tattare da ita.Amsa sallamar yayi yana kawar da kansa daga gare ta,,dinkin takalmi zakai min ta fada cikin sassanyar muryarta,,kawo ya mika hannu ya karba,, uniform ne ajikinta sosai ya amsheta matuka,,Sàida yaga dinkewa tana tsaye tana kallon sa,,mika mata yayi ta dudduba komai yayi,,nawane kudin,,dan murmushi yayi aah ki barshi kawai,, zaro idanu tai akamme zan barshi,,saboda ina girmama dukkan dalibin dayake cikin uniform,, àah gwara dai ka karbi hakkin ka neman kudi fa kafito yi,,fir Habib yaki karba ahakan tagaji ta kyale shi.

Bayan kwana biyu ta kara dawowa da takalmin againe ya dada tsinkewa,,jujjuya takalmin yayi kafin ya kara gyara mata lokacin Nasir yana zaune ta kawo,,bayan tatafi Nasir yake tambayar shi wacece wannan kuma,, tabe baki Habib yayi ina zan sani gyaran takalmi kawai take kawon,, murmushi Nasir yayi bece komai ba.Bayan kwana ki uku ta sake da wowa takalmin ya tsinke Nasir da ya kurawa takalmin ido girgiza kai kawai yayi shine ya karba ya din ke mata.A kalla takai sati bata kara dawowa ba sai rannnan gata da wannan takalmin ya sake tsinkewa,,bayan ya karba ya kalle ta,,mezai hana a canza miki saman takalminnan tunda naga yana wahalar dake,,kallon sa tai meya kamata ai kasa kenan,,zan canza miki samansa gaba daya zai saina baki matsala,,gyada kai tayi alamar ai hakan,,kwanaki ya bata akan taje ta dawo zai yimata sabon takalmi.

"Kwanankin daya debar mata ta dawo ranar su uku suka zo ita da kawayanta,,be kammala gyarawa ba yace su zauna sudan jira,,zama sukai akan benci suna hirar aikin da aka basu a makaranta sai musu suke kowacce tana nuna yadda aikin zai kasance,,ganin musun nasu yaki karewa Habib ya fara bayayyana musu amsar daya kata su saka,,da sauri suka dauko Litattafan su suka fara kwafewa,,suna gamawa sukaga amsar tayi daidai suka cika da farin ciki.

"Amma kayi makaranta muka ganka anan,,murmushi kawai yayi bace komai ba,Godiya sukai masa sanda ya gama dinke mata takalmin,,sanda sukaje class saida malamin su yasa ajinjina masu,sune wadanda suka fi kowa samun maki.Anatashi kuwa suka garzayi danyi masa Godiya."Sanda suka zo Nasir na zaune daya daga cikin su ce ta tambaye shi wai meyasa baka taba tambayar sunan kawar mu ba,,Dariya ya danyi daga ta kawon gyaran takalmi saina kama tambayar sunan ta,,to tunda baka tambaya ba bari mu mugaya maka sunan ta Habiba,ni kuma suna na Habibullah,,dan Allah kafada mama gskiyar sunan ka,,nan suka fara ja'inja yana sunan sa Habib suna ba sunan sa haka ba,,sàida Nasir yaji gaddamar taki karewa tukunna ya saka musu baki,,da gaske sunan sa Habib sàida sukaji daga bakin Nasir sannan suka yadda.Wadda aka kira da Habiba bata sa musu baki ba tana daga gefe tana jin su,, murmushi dauke akan fuskarta.

"Daga wannan rana sun kwana Biyu basu dawo ba,,rannan saiga kawar Habiba guda daya wadda suke zuwa tare ta zo Wajan Habib,,bayan sun gaisa ta kalle shi,wai meyasa baka taba tambayar Habiba komai nata ba,,shiru ya danyi meyasa zan tambayeta,,saboda naga ta dade tana zuwa mana,,bani da hurumi na tambayarta wacece ita,amma yana da kyau ai kasan dawa kake tare.Kaga Maganar gaskiya ranar farko da takalmin ta ya tsinke shine na gaskiya,,ranar motar tace ta samu matsala shiyasa tai Tafiyar kasa har takalminta ya tsinke kullum tana mota kaga babu ta yadda za'ai takalmin ta ya tsinke.

"Sauran ranakun kuma da kanta take cisge takalmin,,nasani Habibullah ya furta,,dan zaro idanu tai kasani fa kace,,gyada kansa yayi ai ta kalmin daya tsinke daban da wanda aka cisge da karfi,, murmushi ta dan saki,,kaga gidajan bayannan GRA dinnan anan gidan su yake,in munzo baka ganin wata mota acan gaba,ina ganinta,to motar gidan su ce,shiru Habibullah yayi Mikewa tai ni zantafi duk da kawata bata zoba amma tana miko gaisuwa,gyada kansa kawai yayi dan ya kasa magana."Sanda Nasir yazo babu abunda ya boye masa ya gaya masa komai shiru NASIR yayi,kallon Habib yayi kai me kayanke akan ahakan.Gskiya zan canza mata fuska kowa ya zauna a katsayinsa karnakai kaina inda Allah be kaini ba.Karna jawowa kaina matsala ina zaman zaman,,matsala kamar tame,naje na fada sonta,ko 'yan gidan su sudinga ganinta awajena kaga nashiga matsala babba kuwa,tunda ni ba sa'an Auranta bane kaida ganinta kasan 'yar manya ce,hakane banga Laifinka ba,,amma karka sanja mata aci gaba da gaisawar mutumci.....

       Mrs 🌹 Baba Bello Abubakar
            ........✍️✍️✍️✍️


          🌹🌹FATA NA 🌹🌹

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Short Story 

Page 10

"Kamar yadda Nasir ya bashi shawara yayi amfani da ita,,koda Habiba taci gaba da zuwa su gaisa me nuna mata komai ba,,zata zauna wani lokacin tatayashi hira,,ba dadewa take ba tana zama take tashi tai masa sallama,hakanan take jindadi aduk sanda ta zo Wajan sa.Abun sai ya zamar mata kamar wajibi in bata zo ta ganshiba batajin dadi.Haka suka dinga tafiya basu farga ba suka tsince kansu akan zazzafar soyayyar juna,Hankalin Habib ya tashi ganin da gaske zuciyar sa takeyi ta janyo masa masifa yana zaman zaman sa,ya tabbatarwa da kansa Habiba ba sa'ar soyayyar sa bace.

"Tunanin daya shiga saiya fara daure mata fuska inta zo dan dai yayi yaki da zuciyar sa amma abun yaci tura,canza mata Fuskar da yayi sai hakan yayi matukar damun ta,takan zauna tayi kuka Saboda sonsa daya yimata illah,anata bangaran gani take Habib sam bazai sota ba,bata taba kallon sa a matsayin ba ajinsu daya ba nacewar shi talaka ne,da zuciya daya take sonsa da kaunar sa,hatta Umminta tasan ta canza ko yaushe cikin tambayarta take me yake damunta amma amsa daya ce bakomai."Kawayan ta Zainab da Hauwa sune suke kara mata karfin guiwa da fadin taci gaba da jajircewa Habib zai zamo mallakin ta,saita sakankance da hakan tasawa Zuciyar ta zata samu habib.

"Haka bangaran Habib Oum ta lura da yadda ya sauya gaba daya,ada yana zama siyi hira da kanne sa amma yanzu daidai taga ya koma gefe ya shiga tunani,tun abun baya damunta har yafara damunta saidai yace mata babu komai."Yauma da yamma yana zaune yana gyaran takalman da suka fara tarar masa,ayanzu ko yaushe cikin samun aiki yake,wajan nasa sai kara bunkasa yakeyi.Takun tafiya da yaki ya sashi daga idanun sa dan ganin me tahowar,duk da kamshin turaranta ya sanar dashi ko wacece,amma idaniyar sa suna marmarin ganin ta."Itan ce kuwa kamar yadda zuciyar sa ta sar dashi,taci kwalliya cikin wani Less ash ta kashe dauri ba karamin kyau tayi ba,ba wani makeup tai ba amma hasken fuskarta saiya kara fitowa ras.

Murmushi take kashe shi dashi wanda yake kara dimauta zuciyarsa,yake karajin ya kara fadawa kogin kaunarta,yake sake dulmiya a tsantsar santa,shima martani ya mayar mata kamar sokaye haka suka koma anrasa wanda zaiyi magana."Shine yayi ta maxa ya dan kalle ta,sai ina haka wanann kwalliya kamar zakije gasar sarauniyar kyau, murmushi ta saki fararan hakwaranta suka bayyana,babu inda zanje wajan ka nazo dan natayaka hira, haba yadan rike nidin kuma,anya sarauniya ta cancanci tadinga bin bawanta,idanu tadan zaro tana kallon sa,wanneen bawan nawa?nuna kansa yayi alamar shine,dariya tasaka har tana tafa hannayan ta,amma kana da abun dariya kamar kai kace kaine bawana,aini kaine Uban gidana,ina fatan zan samu matsugunni a fadar ka,dariya ta bashi sosai saida ya dara,tabbas kedin kin kasance kamar zara ce acikin taurari,na tabbata duk Inda kika gifta sai an dangwali hasken ki.Face dinta dauke da murmushi take kallon sa kalamansa ratsa dukkan jiki da jijiyarta yake,,Habib ya gama sace zuciyarta baki daya.

"Amma kam mezai hana nima nadinga koyon gyaran takalmin nan dama ina neman sana'ar da zanyi,,uhm ai wannan aikin wahalar saimu dan daga ganin ki bakiyi kalar wahala ba,rike baki tai kaine ma Za'a ce bakai kalar wahala ba."Natambaye ka mana in ba damuwa"gyra zaman sa yayi ina jinki,wai dan Allah meyasa baka zuwa school kake zama anan koda yaushe,shiru yayi yana kallontà kafin saki ajiyar Zuciya,babu komai yanayin rayuwa ne kawai amma ina fatan na koma school wata rana."Zanyiwa Abbana magana ya samar maka school dan zaro idanu yayi yana girgiza kai, àah kam bana bukata,ni yanzu nan ce Makaranta ta,ina cikin farin ciki.To in bakason school zai nemo maka aiki, Murmushi ya sake yi ya girgiza mata kai alamar bai bukata,babu yadda Habiba batai dashi ba amma ya kafe akan ya gode baya bukatar hakane,daga karshe fushi tai tatafi.

"Sai data kwana biyu bata zoba,duk sai Habib yaji ya damu sasai harsai da NASIR ya gane halin dayake ciki,becemai komai ba dan yasan Zuciya tana jajibo ma abunda kai kanka zaka kasa control din kanka,amma azahiri yana matukar tsoron abunda zaije ya dawo agaba,ayadda ya lura ita ma Habiba tana mugun son Habib amma yana Addu'a koma me zaizo Allah yasa yazo da sauki.

"Gidan su Habiba dan kareren gida ne na gani na fada,'yar gata ce gaba da baya,iyayanta suna matukar kaunar ta da tattalin ta,amma duk da wannan son be hana siyi mata tarbiyya me kyauba,bata da wulakanci ko kadan,gata da taimako,komai 'yan aiki keyi Musu,basu da wata damuwa,tunda tataso batasan wahala ba ko kadan.....

Kuyi hakuri da wannnan

    Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
        ......✍️✍️✍️✍️


    SALAMAR ZUCIYA
    
    Written and Narrated
    
    By Kulsoom Ismail Idris
    
    *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Short Story 

Page 11
    
    "Soyayya suka ci gaba da sha tun Habib na dari dari har ya barwa Allah dukkan lamarin sa.Kamar yadda Nasir yasha sanar dashi indai Habiba matar sa ce,to saiya Aure ta,yadaina La'akari da cewar tafi karfinsa babu yadda Allah baya lamarin sa."Ya yadda kwarai da maganganun Nasir shiyasa ma yakara sakin jikin sa.Yana da tabbacin Nasir masoyinsa ne na hakika bashi da tamkar sa."Tunda ta tsaya take ta kame kame,,tsura mata idanu yayi yana kallonta yadai Habiba,, murmushi tadan kakaro,am dama Kawu wata magana nazo muyi,gyara zama kawun nata yayi yana kallon ta,ina jinki Habiba."Akwai wani da yake gyaran takalma anan bakin titi,gaskiya yana da hankali sosai kuma ayadda na fahimce shi yana son makaranta rashin kudi ne ya hana shi cigaba.

"Tun data fara magana kawun nata ke kallonta,tsaf yagane Abinda ke xuciyarta murmushi ya saki,,Habiba manya,taya harkikayi wannan sabon dashi har kikasam halayyarsa haka,?ai Kawu ina kai masa gyaran takalmi,,gyada kai Kawu yayi na fahimta,yanxu ya kike so ayi?yauwa dama sona ke kataimaka masa yakima Makaranta.Ok kituro shi naganshi tahakanne zan gane wane kalar taimako zammasa,Yawwa Kawu ngode.Ficewa tai daga gidan ya bita da kallo yana sakin murmushi.Kawu Aminu kawunta ne kanin mamanta uwar su daya Uban su daya,yana matukar son Habiba saboda yarinya ce me hankali,nutsuwa da tausayi,shiyasa kome take so yake tsayawa a dukkan Lamuranta.

"Kamar bakinta zai yage ta nufi wajan Habib,yana zaune a rumfarsa ta rangada sallama,amsawa yayi yana kallon ta,yadda yaga Farin ciki afuskarta,shima saiyaji zuciyarsa tayi fari tas.Um Habibty daga ganin wannan bakin naki akwai magana, murmushi ta saki tana zama akan bencin data saba zama in tazo wajan."Kamar kuwa kasani Habiby dariya ya danyi jin yadda ya ambace shi da wannan sunan"Shagwabe fuskatai tana kallon sa,ko sunan be maka dadi ba,,niko yayimin duk duniya bantaba jin suna medadin wanda kika ambace ni dashi ba, murmushin jindadin ta saki tana gyara zamanta.Albishirin ka,goro ya fada yana kallon ta,fari ko ja,takara jefamai tambaya fari tas ma kuwa.Kawuna yace kaje yana son magana dakai,idanu yadan zaro kawun ki?gyada masa kai tayi alamar tabbatarwa,ko bazaka amsa kira ba,nidin banza na batawa sarauniya ta rai,ainima Kawu nane, murmushi ta saki Yawwa kokaifa.

"Amma Habibty tsoron haduwa nake dashi gaskiya,saboda me?naga niba kalarki bane karnaje ma jamin kunne zaiyi akan ki, murmushi ta saki,waya fada ma,ni Kawu na ba haka yake ba,yana da kirki zakagani in kaje,to shikenan zanzo, yaushe yace naje,ko yanzu ma zaka iya tashi mutafi,'yar dariya ya saki,tunda nine me gamo da kasawa ba,daga kirana sai na zura takalmi natafi,to mene aciki,ah bakomai zanzo gobe in sha Allah.Amma saiki kwatantamin gidan, kwatanta masa tayi sàidata gane kafin tamai sallama tatafi.

"Kamar yadda yafada washe gari ya samu dan yadinsa mekyau Acikin kayansa ya saka,bakinsa dauke da Addu'a ya nufi gidan Kawu Aminu,ganin dan kareren gidan jiyayi kamar ya koma,amma haka ya dake ya kwankwasa get din,megadi ne ya leko,dama Kawu ya sanar dashi zaiyi bako wani matashin saurayi.Babu bata Lokaci megadi ya bude mai ya shiga.Jijjina kai yake yana Addu'a Allah ya basu arziki me amfani kudi sunyi.Iso get man yayi masa,dakin baki Kawu yasa aka kaishi,kan carpet ya zauna gani yake baikai matsayin hawa sofa ba.Da sallama Kawu ya shigo bayan yasa ankawo masa lemu da ruwa,tun yanayin dayaga Habib ya zauna yaji yaron ya matukar burge shi,cikin girmamawa ya gaida Kawu Aminu,da fara'a yake amsawa yana kara karantar sa.Ya zaka zauna akasa Malam Habib,nan dimma ya isa Kawu,babu yadda Kawu baidashi yahau kan Sofa ba amma yaki hawa gajiya yayi ya kyale shi.Tambayoyi yayi masa yadinga amsamai cikin hankali da tunani."Alhmdulillahi Malm Habib tabbas na yaba da Hankalin ka.In sha Allah zan mayar dakai Makaranta.Amma shawarar da zan baka karka rabu da sana'ar ka inka dawo daga school saika bude wajan sana'ar ka.

"Farin ciki ya cika zuciyar Habibullah har hawayan Farin ciki yayi,yanzu abunda nake so dakai zan baka jari kaje ka lissafo dukkan abunda kake bukata na sana'ar ka zan baka jari kasiyo komai, Godiya da Addu'a Kawu ya shata,baitaba zatan a masu kudi akwai wadda basa kyamar talaka ba,sai gashi ya gani akan Kawu.Har bakin get ya rako shi.Oum yaje ya sanarwa tayi matukar farin ciki,sannan ya sanar da Nasir,Nasir har rawa ya taka jin Habib zai koma school.Kamar yadda Kawu Aminu ya fada haka yayi yayo list din dukkan kayan sana'ar sa ya kawo masa.Take awajan Kawu Aminu ya zare kudin ya bashi batare dayaji komai ba.A wannan karan dama za'a data registration aiko ya biya masa ya koma school,hatta Malaman sunyi farin ciki da dawowar Habib saboda kwazonsa da hazakar sa."Dai dai nan Habiba ta gama secondary nan iyayanta sukace ta kawo wanda take so kafin ta dora karatu.Kanwarta Yasmin ta gayawa Labarin Habib akan shine zabin ta,babu bata time Yasmin ta fadawa Mom dinsu,ita kuma ta gayawa Mahaifin su.Kiran Habiba yayi ta Tabbatar shitake so tace eh.Bata Umarnin turo masa Habibullah yayi,aiko ba bata Lokaci ta sanar dashi.Washegarin ranar yazo Gidan tunda ya shiga harabar Gidan yake tunanin anya bekai kansa Inda Allah be kaishi ba.Ganin kerarran gida ga yan aiki birjik.Dan yadin jikinsa ya kalla da takalmi gaba daya kayan jikinsa da takalmi da hular daya saka basu wuce 5k ba,sai yaji shikansa yanajin kunyar kansa,yanajin kunya yashiga a matsayinsa name son 'yar masu gid.

"Harya yanke shawarar juyawa yaji wata mata abayan sa ance ka shigo,babu yadda zaiyi haka ya bita,dakin baki aka kaishi,beyi gangancin hawa Sofa ba,a carpet ya zauna kamar yadda yayi a gidan Kawu.Mahaifin Habiba Alhaji Abdussamad sanda ya shigo Habib kara sunkuyar da kansa yayi,bakaramin kwarjini Mahaifin Habiba yayi masa ba,cikin Ladabi ya gaida shi.Yayi masa tambayoyi sosai ya samu gamsuwa kuma yaron ya kwanta masa arai.Sallamar sa yayi bayan kwana biyu zai neme shi.Cikin farin ciki Habib yatafi gida ya sanar da Oum duk abunda ya faru,sosai tataya shi da Addu'a.Bincike sosai Mahaifinta yayi akansa be samu wani abu mara kyau daga gare shiba,duk inda ya tambaya halayan Habibullah ake sanar dashi Nagari.Aiko yaji dadi bayan kwana biyu ya kirashi ya tabbatar masa ya bashi damar zuwa wajan Habiba sannan kuma ya turo iyayansa.Ba bata Lokaci a satin ya turo su aka gama komai ambashi Habiba,ranar farin cikin da yayi bazai misaltuba,har wata yar walima yahadawa Oum da kananan sa da Nasir sumci sunsha abun su ma sha Allah.

"Habib fa yazama dan gida bashi da shamaki ko yaushe zai iya shigowa.Ga sana'ar sa sai bunkasa takeyi ALLAH ya sama sa Albarka acikin ta.Habiba da kawayanta ma sunyi matukar farin ciki da wannan al'amari.Soyayya suke me tsafta cike da so da kauna,tsakani da Allah suke son junan su badan wani abuba.A wannan Lokacinne kuma Alhaji Sani ya dawo daga Lagos can wani Company sa da yajima acan,ayanzu ya dawo gida dama kuma dan Kano ne,idanun sa be dira akan kowa ba sai akan Habiba Lokacin an aiketa......

  To ana wata ga wata,me zai faru haduwar Alhaji Sani da Habiba...

Habib zai samu Nasarar Auranta ko àah...
Kubiyo ni dan jin yadda zata kaya...

   Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
        ......✍️✍️✍️✍️✍️


   SALAMAR ZUCIYA

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

Page 12

"Idanun sa befada kan kowa ba sai Habiba,tafiyarta take hankali kwance, kyakykyawan murmushi ne a face dinta,ba komai take tunani ba face Habib dinta,tana lissafin sanda zai zama mallakin ta.Yaron sa ya kalla dayake tukin motar,Anas ina son bayani akan waccan yarinyai,kallo daya nai mata naji duk duniya babu wanda nake so kamarta,kuma kota halin kaka saina sameta.Kallon mamaki Anas yayi masa daga ganin yar mutane kace kota halin yaya saika sameta,bece wa Alhaji Sani komai ba.Kamar yadda yasa shi bincike akan ta yayi.Alhaji nayo bincike akanta amma sai dai wani abu guda daya shine ammata miji har ma ambada it's.

"Dakata Anas bani da matsala d bada ita,ko matar Aure ce ya zama dole mijinta ya sake ta nina Aure ta balle wata bayarwa,cikin kaduwa Anas yake kallon sa,amma Alhaji kana ganin hakan da kafada daidai ne,kasani nema cikin nema haramunne,amma sainaji kana ikirarin ko matar Aure ce saidai mijin ta ya sake ta ka Aura."Kwarai kamar yadda kaji na fadane zanbi ko wace hanya dan ganin na sameta.To gaskiya badani zakai wannan aikin ba,babu bi ga abun halitta wajan sabawa mahalicci, kai ko uwata ce tasani yin abunda Allah ya hana bazan yi ba,balle kai haduwar kan titi."Cikin fusata Alhaji Sani ya mike tare da kawowa Anas mari,da sauri ya rike hannun karka soma,ni dan yaune,ina tabbatar maka duka daya imnaima saika baje,bazan sake zama da azzalumi irin kaba,me matukar san zuciyar sa,me raba zuciyoyin da suka amunta da juna,kasani matukar ka raba wannan soyayyar Allah bazai barka ba.Yarfe hannun Alhaji Sani yayi tare da jefa masa key din motar sa,tsanar Alhaji Sani na mamaye dukkan zuciyar sa.

"Besan Habib ba amma haka kawai yakejin matukar tausayin sa,a bincike da yayi ya tabbatar suna matukar kaunar junan su.Rai bace Alhaji Sani ya shiga Gidan sa,Haj Halima dake zaune tana tambayar sa ko Lafiya ko kallo bats ishesa ba ya shige dakin s.Tagumi ta rafka ganin yadda Alhaji Sani gaba daya ya sauya kamar bashi ba,gaba daya ya daina shiga harkar ta,kamar ma haushinta take hangowa a idanun sa,tarasa me taimasa haka da zafi,duka tunanin da zatai tayi amma bata tuno me taimasa ba.Wani sabon yaron ya samo me suna Okasha shiya kara damkawa bincike akan Habiba,ananne ya gano tana da wata kaka anan 'yan kaba,aiko Alhaji Sani ya bazama yadinga kashe mata kudi kamar hauka,kunsan dai tsoho da son abashi tuni ya siye zuciyar Hajiya kaka.

"Yau dai Okasha ya sanar da Hajiya kaka jikarta Alhaji Sani ke so shiyasa,shiru Hajiya Kaka tai indai Habiba ce ya dauka ya samu,Abbah ta kira akan tayiwa Habiba Miji,abun bakaramin mamaki ya bashi ba jin abunda Hajiay kaka tace kodai bata cikin hayyacin tane.
   SALAMAR ZUCIYA
    
    Written and Narrated
    
    By Kulsoom Ismail Idris
    
    *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Short Story 

Page 11
    
    "Soyayya suka ci gaba da sha tun Habib na dari dari har ya barwa Allah dukkan lamarin sa.Kamar yadda Nasir yasha sanar dashi indai Habiba matar sa ce,to saiya Aure ta,yadaina La'akari da cewar tafi karfinsa babu yadda Allah baya lamarin sa."Ya yadda kwarai da maganganun Nasir shiyasa ma yakara sakin jikin sa.Yana da tabbacin Nasir masoyinsa ne na hakika bashi da tamkar sa."Tunda ta tsaya take ta kame kame,,tsura mata idanu yayi yana kallonta yadai Habiba,, murmushi tadan kakaro,am dama Kawu wata magana nazo muyi,gyara zama kawun nata yayi yana kallon ta,ina jinki Habiba."Akwai wani da yake gyaran takalma anan bakin titi,gaskiya yana da hankali sosai kuma ayadda na fahimce shi yana son makaranta rashin kudi ne ya hana shi cigaba.

"Tun data fara magana kawun nata ke kallonta,tsaf yagane Abinda ke xuciyarta murmushi ya saki,,Habiba manya,taya harkikayi wannan sabon dashi har kikasam halayyarsa haka,?ai Kawu ina kai masa gyaran takalmi,,gyada kai Kawu yayi na fahimta,yanxu ya kike so ayi?yauwa dama sona ke kataimaka masa yakima Makaranta.Ok kituro shi naganshi tahakanne zan gane wane kalar taimako zammasa,Yawwa Kawu ngode.Ficewa tai daga gidan ya bita da kallo yana sakin murmushi.Kawu Aminu kawunta ne kanin mamanta uwar su daya Uban su daya,yana matukar son Habiba saboda yarinya ce me hankali,nutsuwa da tausayi,shiyasa kome take so yake tsayawa a dukkan Lamuranta.

"Kamar bakinta zai yage ta nufi wajan Habib,yana zaune a rumfarsa ta rangada sallama,amsawa yayi yana kallon ta,yadda yaga Farin ciki afuskarta,shima saiyaji zuciyarsa tayi fari tas.Um Habibty daga ganin wannan bakin naki akwai magana, murmushi ta saki tana zama akan bencin data saba zama in tazo wajan."Kamar kuwa kasani Habiby dariya ya danyi jin yadda ya ambace shi da wannan sunan"Shagwabe fuskatai tana kallon sa,ko sunan be maka dadi ba,,niko yayimin duk duniya bantaba jin suna medadin wanda kika ambace ni dashi ba, murmushin jindadin ta saki tana gyara zamanta.Albishirin ka,goro ya fada yana kallon ta,fari ko ja,takara jefamai tambaya fari tas ma kuwa.Kawuna yace kaje yana son magana dakai,idanu yadan zaro kawun ki?gyada masa kai tayi alamar tabbatarwa,ko bazaka amsa kira ba,nidin banza na batawa sarauniya ta rai,ainima Kawu nane, murmushi ta saki Yawwa kokaifa.

"Amma Habibty tsoron haduwa nake dashi gaskiya,saboda me?naga niba kalarki bane karnaje ma jamin kunne zaiyi akan ki, murmushi ta saki,waya fada ma,ni Kawu na ba haka yake ba,yana da kirki zakagani in kaje,to shikenan zanzo, yaushe yace naje,ko yanzu ma zaka iya tashi mutafi,'yar dariya ya saki,tunda nine me gamo da kasawa ba,daga kirana sai na zura takalmi natafi,to mene aciki,ah bakomai zanzo gobe in sha Allah.Amma saiki kwatantamin gidan, kwatanta masa tayi sàidata gane kafin tamai sallama tatafi.

"Kamar yadda yafada washe gari ya samu dan yadinsa mekyau Acikin kayansa ya saka,bakinsa dauke da Addu'a ya nufi gidan Kawu Aminu,ganin dan kareren gidan jiyayi kamar ya koma,amma haka ya dake ya kwankwasa get din,megadi ne ya leko,dama Kawu ya sanar dashi zaiyi bako wani matashin saurayi.Babu bata Lokaci megadi ya bude mai ya shiga.Jijjina kai yake yana Addu'a Allah ya basu arziki me amfani kudi sunyi.Iso get man yayi masa,dakin baki Kawu yasa aka kaishi,kan carpet ya zauna gani yake baikai matsayin hawa sofa ba.Da sallama Kawu ya shigo bayan yasa ankawo masa lemu da ruwa,tun yanayin dayaga Habib ya zauna yaji yaron ya matukar burge shi,cikin girmamawa ya gaida Kawu Aminu,da fara'a yake amsawa yana kara karantar sa.Ya zaka zauna akasa Malam Habib,nan dimma ya isa Kawu,babu yadda Kawu baidashi yahau kan Sofa ba amma yaki hawa gajiya yayi ya kyale shi.Tambayoyi yayi masa yadinga amsamai cikin hankali da tunani."Alhmdulillahi Malm Habib tabbas na yaba da Hankalin ka.In sha Allah zan mayar dakai Makaranta.Amma shawarar da zan baka karka rabu da sana'ar ka inka dawo daga school saika bude wajan sana'ar ka.

"Farin ciki ya cika zuciyar Habibullah har hawayan Farin ciki yayi,yanzu abunda nake so dakai zan baka jari kaje ka lissafo dukkan abunda kake bukata na sana'ar ka zan baka jari kasiyo komai, Godiya da Addu'a Kawu ya shata,baitaba zatan a masu kudi akwai wadda basa kyamar talaka ba,sai gashi ya gani akan Kawu.Har bakin get ya rako shi.Oum yaje ya sanarwa tayi matukar farin ciki,sannan ya sanar da Nasir,Nasir har rawa ya taka jin Habib zai koma school.Kamar yadda Kawu Aminu ya fada haka yayi yayo list din dukkan kayan sana'ar sa ya kawo masa.Take awajan Kawu Aminu ya zare kudin ya bashi batare dayaji komai ba.A wannan karan dama za'a data registration aiko ya biya masa ya koma school,hatta Malaman sunyi farin ciki da dawowar Habib saboda kwazonsa da hazakar sa."Dai dai nan Habiba ta gama secondary nan iyayanta sukace ta kawo wanda take so kafin ta dora karatu.Kanwarta Yasmin ta gayawa Labarin Habib akan shine zabin ta,babu bata time Yasmin ta fadawa Mom dinsu,ita kuma ta gayawa Mahaifin su.Kiran Habiba yayi ta Tabbatar shitake so tace eh.Bata Umarnin turo masa Habibullah yayi,aiko ba bata Lokaci ta sanar dashi.Washegarin ranar yazo Gidan tunda ya shiga harabar Gidan yake tunanin anya bekai kansa Inda Allah be kaishi ba.Ganin kerarran gida ga yan aiki birjik.Dan yadin jikinsa ya kalla da takalmi gaba daya kayan jikinsa da takalmi da hular daya saka basu wuce 5k ba,sai yaji shikansa yanajin kunyar kansa,yanajin kunya yashiga a matsayinsa name son 'yar masu gid.

"Harya yanke shawarar juyawa yaji wata mata abayan sa ance ka shigo,babu yadda zaiyi haka ya bita,dakin baki aka kaishi,beyi gangancin hawa Sofa ba,a carpet ya zauna kamar yadda yayi a gidan Kawu.Mahaifin Habiba Alhaji Abdussamad sanda ya shigo Habib kara sunkuyar da kansa yayi,bakaramin kwarjini Mahaifin Habiba yayi masa ba,cikin Ladabi ya gaida shi.Yayi masa tambayoyi sosai ya samu gamsuwa kuma yaron ya kwanta masa arai.Sallamar sa yayi bayan kwana biyu zai neme shi.Cikin farin ciki Habib yatafi gida ya sanar da Oum duk abunda ya faru,sosai tataya shi da Addu'a.Bincike sosai Mahaifinta yayi akansa be samu wani abu mara kyau daga gare shiba,duk inda ya tambaya halayan Habibullah ake sanar dashi Nagari.Aiko yaji dadi bayan kwana biyu ya kirashi ya tabbatar masa ya bashi damar zuwa wajan Habiba sannan kuma ya turo iyayansa.Ba bata Lokaci a satin ya turo su aka gama komai ambashi Habiba,ranar farin cikin da yayi bazai misaltuba,har wata yar walima yahadawa Oum da kananan sa da Nasir sumci sunsha abun su ma sha Allah.

"Habib fa yazama dan gida bashi da shamaki ko yaushe zai iya shigowa.Ga sana'ar sa sai bunkasa takeyi ALLAH ya sama sa Albarka acikin ta.Habiba da kawayanta ma sunyi matukar farin ciki da wannan al'amari.Soyayya suke me tsafta cike da so da kauna,tsakani da Allah suke son junan su badan wani abuba.A wannan Lokacinne kuma Alhaji Sani ya dawo daga Lagos can wani Company sa da yajima acan,ayanzu ya dawo gida dama kuma dan Kano ne,idanun sa be dira akan kowa ba sai akan Habiba Lokacin an aiketa......

  To ana wata ga wata,me zai faru haduwar Alhaji Sani da Habiba...

Habib zai samu Nasarar Auranta ko àah...
Kubiyo ni dan jin yadda zata kaya...

   Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
        ......✍️✍️✍️✍️✍️


       SALAMAR ZUCIYA

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Short Story 

Page 11

Idanun sa ba akan kowa ya fada ba sai akan Habiba,jiyayi duk duniya babu wadda yake so sama da ita,Anas ya kalla akan yayi masa bincike akan ta,babu musu Anas yayi masa bincike,har gida ya same shi da maganar yayi bincike kuma.an sanar dashi ambada Habiba,cikin Masifa Alhaji Sani yake kallon Anas babu ruwa na da bada ita da akai,kai koda matar Aure ce sai inda karfina ya kare,saiya saketa na Aure ta,balle wani bada ita da akai be shafan ba.Mamaki ya kashe Anas a tsaye tsantsar mamaki ya hanashi magana,lallai Jahilci yayiwa Alhaji Sani katutu a kwakwalwar sa."Kana cikin hayyacin ka kuwa? Anas ya jefa masa tambaya mahaukaci ne ni cikin bacin rai Alhaji Sani ya bashi amsa.

"Mikewa Anas yayi to gaskiya badani zakai wannan jakantar ba,babu bi ga abin halitta wajan sabawa mahalicci,ko uwa tace bazan mata biyayya ba matukar abunda ta umar ceni sabon Allah ne,nema cikin nema haramunne,amma Abunda naji da kunne na kafurta yaban mamaki,kalmar daka fada nako matar Aure ce sai mijinta ya saketa ka Aura ya girgiza ni."Bazan sake zama akarkashin ka ba,kaje can Allah ya shirye ka,key dinsa ya cilla masa, baza'a hada kai dani acitar da masoya ba,masu san juan su saboda Allah."Kai ina tantama akan ka ba domin Allah kake sonta ba.Rai bace Anas yabar gidan Alhaji Sani cike dajin tsanar sa azuciyar sa.

"Rai bace Alhaji Sani ya fada gidan sa"Hajiya Halima dake zaune ta bishi da kallo tarasa meya canza mata miji,tunda ya dawo baya kallon kanta da gashi,kome tayi gwasaleta yakeyi yana kusheta da gaya mata magana mara dadi,tayi tunanin me tai masa amma bata tuno komai ba.Wani yaro ya canza me suna Okasha anan ya sake bashi aikin bincikar wacece Habiba,aiko ya binciko masa tana da wata Kaka a 'yan kaba,matukar ya kamata kamar ya Auri Habiba ne.Babu bata Lokaci ya dira gidan Hajiya Kaka ya dinga yi mata ruwan kudi abunka da tsoho kunsan shi da san kudi tuni ya siye zuciyar ta.

"Oka ne yake sanar da ita duk wanan abunda Alhaji Sani ke mata jikarta yake so,nan ta tabbatar masa kamar ya Auri Habiba ne.Wayarta ta dauka ta kira Abba akan tayiwa Habiba Miji, hankali tashe Abba ya dira gidan Mahaifiyar tasa da tunanin ko bata cikin hayyacinta,amma saiya sameta daran dakau,babu abunda ya sameta.Sosai suka tirza akan maganar Habiba,Hajiya nifa kika haifa baki da iko akan Habiba nine Ubanta,ni kuma.nice uwarka,zan iya tsinema akan maganar Aurannan,sosai ya kadu dajin abunda ta fada din,wai akan wa kike magana haryanzu bansan akan wa kike magana ba Hajiya,aizaka sanshi ne daka nemi kasan shi daka sani tuni.Tsanar Alhaji Sani ta dira a zuciyar Abbah ya tabbatar wanann ba mutumin arziki bane,ya sake tabbatar wa da Hajiya bazai bashi Auran yar saba dan ya riga da yayi wa yarsa Miji.Haka ya baro Hajiya tana rusar Kuka yaki jin maganar ta.

Hankalin fa Alhaji Sani ya fada tashi ganin yadda ake dauki ba dadi da Abba amma fir yaki yadda da maganar Auransa da Habiba.Oka ne ya tabbatar masa inhar beyi Wani abuba tofa zaiga samu yaga rashi dole ne a batawa Habib sunan ta hakane zai samu Habiba ta zama tashi.Hakan kuwa akayi wata rana Habib yana zaune yana sana'ar sa,sai ga wasu mutane guda uku sun shigo rumfar sa,sunan shiga yaji wani da yake tsakiya ya nuna shi shine wanann wllh shine,kan Habib yasan akan me suke magana sun rifeshi da duka tako ina,nan mutane suka taru suna tambayar me yayi musu haka,mu yan sanda ne,wanann da kuke gani barawo ne,in ya sato kayan mutane shi suke kawowa ya siya barawon zaune ne.Allah sarki Habib da jikinsa ke fidda jini ko ina ahakan yake cewa be sanshi ba,betaba ganin sa ba.

"Gaba daya mutanan wajan sun tabbatar da Habib yaran kirki ne,amma haka yan sandannan suka ja Habib akan titi suka dinga jansa har station,kawar Habiba ta gano Abunda yake faruwa da gudu ta ruga ta fadow Habiba,tana Kuka ta ruga gidan Kawu babu bata Lokaci Kawu Ya dauki lauya suka tafi police,ba karamar tirzawa akai ba kafin suba da Habib tsaf Lauyan ya bude musu aiki,basu da wata hujja sanin in na sama dasu sukaji sune aciki shiyasa suka bada belinsa.

"Sanda Alhaji Sani yazo suka sanar dashi abunda ya faru ransa ba karamin baci yayi ba,oka ya samu yayi masa bincike wanene yazo belin Habib,yako samo bayanai akan sa,ya sanar dashi kawun tane,aiko Alhaji Sani ya shirya ya tafi wajan Kawu Aminu,ya sanar dashi yana san Habiba ya shige masa gaba,nan Kawu ya sanar dashi ambawa Habib ita,kafadi daga kan million daya zuwa million dari zan baka, murmushi Kawu yayi bana bukatar komai daga gareka tunda ba atsiya ce la ganni ba,babu yadda beyi dashi ba fir Kawu yaki amsa.

"Washe gari da Kawu ya fita kasuwa duk Inda yake karbar kaya in yaje sai ace babu abun ya daure masa kai ganin babu wanda yake binsa bashi,amma ace an hanashi kaya,sosai abubuwa suka fara tsaya masa duk wani waje daya amsar kaya anki bashi,kai karshema gaba daya kudin account dinsa akace yan Yahoo sun kwashe,ya shiga tsanani sosai,wata ranar Alhamis Okasha yazo ya sanar dashi badai shi me taurin kaiba,ba kowa yayi masa hakan ba face Alhaji Sani.Abun ya matukar dukan sa,matukar baka fita daga harkar Habib ba ina me sanar dakai zaka koma fakirin talaka fiye dashi Habib din,babu yadda Kawu zaiyi ya zare hannun sa daga lamarin habib din.

"Yau yana dawowa daga makaranta abunda ya bashi mamaki sanda ya zo shagonsa an watsomai da kayansa waje an babballe masa rumfarsa,ransa yayi masifar baci,me wajan ya tambaya me yayi masa tunda biyan sa kudin haya yake,kuma ko tashin sa zaiyi.saiya bashi notice na wata 6 cayayi ganin damar sane,haka Habib ya kwashe kayan sa,duk wajan daya nema magana daya ake gaya masa suma zasuyi Amfani da wajan su.Abubuwa sun hadu sun jagule masa,sai abakin layin su yadan samu ya ajiye kayan nasa.Sai abubuwa sukai masa zafi,dan kudin da yake samu Yanzu babu abubuwa sun cakude masa.Gidan su ma Abinci ya fara gagarar su,ransa gaba daya ajagule yake.Be taba kawowa ransa wanine ya jefashi awannnan halin ba.

   Hankalin Habiba ma yayi matukar tashi da labarin data ji na rushe mai wajan sana'ar sa,,tayi Kuka ranar kamar zata mutu,, Zuciyar kamar zata babbake tsabar yadda tashiga tashin hankali,Umman tace ta dinga rarrashin ta,Abban tama yana wani hali Hajiya Kaka ta rikice kamar wadda Iska tahauwa ka,sai Kuka take zata tsine masa matukar yace Habiba bazata Auri Alhaji Sani ba, tsantsar tsanar Alhaji Sani ta mamaye ahalin wannan Gida,suna zaman zaman su yana neman tarwatsa musu farin cikin rayuwa....

 Mrs 🌹 Baba 🌹 Bello Abubakar
        ......✍️✍️✍️✍️


    SALAMAR ZUCIYA
    
    Written and Narrates
    
    By Kulsoom Ismail Idris
    
   *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Short Story  

Page 12
    
    Bayan ya koma bakin layin nasu duk da haka Alhaji Sani bai kyale shi ba,bayan kwana biyu,yana zaune yana hada takalman sa,saiga wasu garadan nan da ganin su kasan rikakkun 'yan daba ne,bawata magana suka fara sassara dan teburin da suka hada shida Nasir,mutane sun cika Sosai an rasa wanda zaiyi magana,dandaga ganin wadannan tantiran yan iska ne,haka Habib yana tsaye suka gama illata masa kayan sana'ar sa,babu abunda zuciyar sa keyi sai tafasa,idanun sa har tara ruwan hawaye sukai,ya rasa meya tsarewa wadannan Mutanan,me suke so agare shi.Nasir ne ya kalle shi,mezai hana kakoma wajan kawun Habiba kasanar dashi ko zayyi maka wani tai mako,kuma abu na gaba,dole mubar arear nan mukama wani wajan na daban,ko cikin kasuwa ne,ko Allah zaisa duk wadannan masifun siyi mana sauki, girgiza kai Habib yayi tabbas kakawo shawara Nasir.Kamar yadda sukai da Nasir washegari yayiwa gidan kawun Habiba tsinke,dukkan wani abu dayake faruwa ya sanar dashi,da irin Mutanan da da akadinga turo wa sunai masa taadi sunai masa ta'asa.
    
    "Sàida yagama bayani tsaf kasun Habiba yana akallon sa,Numfashi ya sauke gaskiya Habib naji halinda kake ciki,kuma nayi matukar tausaya maka,saidai bazan iya taimaka maka da komai ba,saidai zan tayaka da Addu'a Allah ya fitar dakai halin da kake ciki.Cikin tashin hankali Habib yake kallon sa,dukkan wani hope din sa yana kan Kawu Aminu gashi yanzu yace bazai iya taimaka masa ba.Cigaba Yayi da rokon sa,cikin tsananin tausayi Kawu ke kallon sa,tsanar Alhaji sani na yawo a zuciyar sa.Numfashi Kawu ya sauke,kayi hakuri Habib saboda yanzu inna taimakeka tabbas zan shiga cikin matsala,ina da mata da yara,abu daya zanyi maka na sanar dakai wanda yayi sana diyyar jefaka a cikin wannan halin.Tsuru Habib yayi yana kallon sa,Kwarai kuwa Kawu ya gyada masa kai,bakowane yayi silar fadawarka wannan halin ba,sai wani Alhaji daya kyalla ido yaga Habiba,yaji zai iya komai akan ta.
    
    "Halin da ake ciki ya tubure kota halin kaka saiya Aure ta,mahaifinta da ita kanta sun jajirce akan bazasu taba yadda da Alhaji Sani ba kaine zabin su.Sosai hankalin Habib ya kara tashi,bayan jin bayanin da Kawu yakeyi masa,idanun sa da suke matukar zugi yake duban kawun,yanzu a ina zan same shi.Fada masa sunan Companyn sa yayi dake Sharada,sosai yayiwa Kawu godiya kafin ya tafi,binsa yayi da kallo cikin tsananin tausayawa."Be sanar da kowa halin da ake ciki ba washe gari ya shirya ya tafi Company,sanda ya isa hanashi shiga akai.

Massinger Alhaji Sani ne ya shiga ya sanar dashi yayi bako,wanene ya tambaye shi,ban waye shiba yallabai, tambayo sunan sa,ficewa yayi ya karaso wajan Habib dake tsaye,wa za'a sanadar dashi yazo, Habibullah zakace masa.Kamar yadda ya sanar dashi haka yaje ya fada masa,wata dariya Alhaji Sani ya saki yana Buga kafarsa aka,ranar dana dade ina jira kenan.Shigowa Habib din yayi kallon Alhaji Sani yake kamar bazai iya abunda yake aikatawa ayanzu ba.Zauna Alhaji Sani ya ambata fuskarsa kamar gonar Auduga."batare da Habibullah ya zauna ya fara da fadin,zuwa nayi na rokeka kafita daga rayuwata,tunda bamsan ka ba,baka sanni ba,dariya Alhaji Sani ya sheke da ita,niko nasan ka,babu wanda yasanka sama dani,maganar kuma kace baka shiga gonata ba batama taso ba,kashiga gonata kadauke abunda nake matukar so da kauna,maslaha daya kabarmin abar sona,nikuma nayi alkawarin dawo ma da duk Abunda nasa kai asarar sa.

"Shiru Habib yayi yana dubansa,bazan taba iya bar maka Habiba ba,Saboda halaccin da iyayanta sukayi min da ita kanta,tsakani da Allah take sona da kaunata,bazan iya rushe wannàn yardar da sukai min ba,zan iya yin komai akanta,dukawa Habib yayi akan guiwinsa,na hadaka da girman Allah kafita daga dukkan shaani na,kadaina jawomin asara,ina da mahaifiya da kanne Biyu,ni nake ciyar dasu Kudin makarantar su gaba daya a wuya na yake,kataimake ni kadaina bibiya ta.Cikin zubar hawaye Habib ya gama wannnan maganar,ya mutsa Fuska Alhaji Sani yayi,kai ka yadda akan mace Mahaifiyar ka ta shiga gararin rayuwa da kananan ka,bazaka iya rabuwa da Habiba ba?ba rabuwane bazan iyayi da ita ba,ni dan halak ne nasan halacci bazan taba jiuya mata baya ba,duk runtsi ina tare da ita.

"Ni kuma bazan daina musguna maka ba tunda haka ka zaba,saina rabaka da dukkan wani farin cikin ka,kana ji kana ganin zan Aure ta,bayan na rabaka da komai naka,cikin bacin rai Habib yake kallon sa,ni kuma.zanci gaba da hadaka da Allah bani da ikon yin maganin ka,in har kafi karfina bakafi karfin Allah ba.In Allah ya yarda ko alahira bazaka taba Auran Habiba ba balle aduniya,yadda ka tozartani ubangiji ya tozarta ka,yadda ka kuntatamun Allah ya kuntata maka,ya dai dai taka,abunda kake takama dashi zan roki Allah ya bani shi,awannan Lokacin inna juyo kanka saina nunawa Duniya wanene kai,kai ka kasance azzalumi ne,me matukar son kansa,babu ruwanka da awane hali dan uwanka zai kasan ce.Mikewa yayi yana share hawayan sa,bazan sake rokon kaba kayi duk abinda kake ganin zaka iya,damar kace a yanzu,nima Allah zai bani dama ta,awannan Lokacin zanyi aiki da ita,zan shayar dakai ruwan Mamaki.Ran Alhaji Sani ba karamin baci yayi akan abunda habib yayi masa ba, tabbas zai shayar dashi ruwan Mamaki,zai gane kuransa.

"Ficewa Habib yayi tare da bugo masa kofar, Zuciyar sa ta gama bushewa kome Alhaji Sani zaiyi yaje yayi,amma yana tare da abar sonsa,abar kaunar sa.

 Ina masu ganin Laifin Habib har yanzu kuna kan bakar ku ko kun sauka?

     Mrs Baba Bello Abubakar
      ......✍️✍️✍️✍️


 SALAMAR ZUCIYA

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

 *KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Short Story  

Page 13


"Gida ya koma bai sanar da Oum komai game da Alhaji Sani ba,ya mikawa Allah dukkan lamuran sa,rukon Allah yake Allah ya karaeshi daga dukkan wani sharri na Alhaji Sani.Ya kuma tabbatar wa da kansa bazai taba iya rabuwa da Habiba ba,ita ce rayuwar sa baki daya,farin cikin sa,muradin sa."Yasanar da Nasir dukkan abunda ya faru tsakanin sa da Alhaji Sani,sosai abun ya dake shi ba kadan ba,yayi Allah wadai da Alhaji Sani,da dukkan masu hali irin nashi."Yauma yana zaune akan dan bencin da yasamu yana dan zama abakin layin nasu,suna zaune shida Nasir ba zato sukaga 'Yan Sanda tsaye akan su,kowa fuska a turbune alamar ba sassauci,babu wani bayani suka dakumi rigar Habib,jansa sukai suka watsashi a mota,da gudu Nasir ya taso yana tambayar su meyayi musu amma ko kallon sa basiyi ba,daga karshema gadan gadan sukayo kansa zasubi ta kansa,tsalle yayi ya koma gefe har yana fadawa wata katuwar kwata dake bayan sa.

"Sanda suka kai Habib police bayan kanta suka sakashi bayan sun masa jahilin duka,Habib ya daku tako ina fuskarsa ta kumbura,idanun sa ko iya bude su bayayi,sàida ya kwana ya wuni batare da yasan musababbabin kamo shi ba."Yau aka fito dashi wani office aka shiga dashi,sai layi yake kamar zai fadi,duk wanda ya ganshi a wannan halin dolene ya tausaya masa."Kasan dalilin dayasa muka.kawo ka nan,shiru Habib yayi kamar ba dashi suke ba,tsawa wani kurtu ya daka masa,badakai ake ba,sai Lokacin ya dago kansa da kyar yana kallon su,wani murmushi ya saki wanda yafi kuka ciwo,koda baku sanar dani ba ninasan wanene yasa aimun haka.Numfashi ya sauke yana Lumshe idanun sa da sukai azabar nauyi."Bazan taba yin abunda kuke so ba,matsawar kukaga na kyale masa Habiba to sai bayan fitar Numfashi na.

"Mari wani dan Sanda ya kawo masa,wannan yaron daga ganinsa bashi da rabon yin arziki a cikin wuya zai kare, Habibullah be sake tanka musu ba yayi shiru yana kallon su,daukar sa sukai suka fita dashi da alkawarin sai sun lika masa wani babban laifi,tayadda babu yadda za'ai ya iya tsallakewa.Haka suka dinga ganawa Habib azaba tsahon sati biyu,yayi baki ya rame kamar bashi ba,ya fita daga hayyacin sa sosai.Nasir ne yau ya kawo masa Abinci cikin tausayawa yake kallon sa,kallon sa Habib yayi ganin kamar da magana abakin sa,Nasir ka sanar dani abunda ke tafe dakai,shiru NASIR yayi yana tunanin maganar da zata fita daga bakin sa.Kayi hakuri Habib abunda zakaji daga gareni bame dadi bane,yanzu haka su Oum suna gidammu, Alhaji Sani yasa megidan da kuke haya yazo da rana yace Lallai sai Oum tafita saga gidan,ba notice ba komai,haka yadinga yimuku watsi da kayan ku,Oum na Kuka da kannan ka amma be kyale su ba.

"Shiyasa na kaisu gidammu na tabbatar babana bazai hana ba,tsaywa yayi dacin Abincin da yakeyi,hawaye ne ya fara zuba acikin idanun sa,yanzu abun haryakai a tozarta Mahaifiyar sa,tabbas yanzu ne yakarajin son Habiba ninkin baninkin din wanda yake ji abaya,da zuciya daya yake sonta da kaunar ta,daga kafadar sa Nasir yayi kayi hakuri Habib naima alkawarin zan kula dasu Oum kamar yadda zaka kula dasu.Hawayan idanun sa yake sharewa wasu na korar wasu,gyada kai yayi batare da yayi magana ba."Yau shara aka fito dashi yayi,gaba daya wani katon fili aka bashi tsintsiya ya share.Tafe suke tare da yayan ta dayake aiki a station din,tsaywa tai tana kallon Habib kamar tasan wannan Fuskar, Habibullah ta ambata cikin mamaki,cak ya tsaya da sharar da yakeyi yana kallon ta,meya kawo ka nan Habib,shiru yayi mata ba amsa sai dukawa dayayi yaci gaba da sharar sa.

"Kin sanshine,gyada kai tayi nasan shi yaya,amma me yakawo shi nan din,nan ya labarta mata komai,Kuka ta fashe dashi,yaya wllh babu abunda Habib yayi musu,ba akan kowa aka kamashi ba sai Habiba wannan kawar tawa,cikin mamaki yake kallon ta,dama Habiba ce Yarinyar da ake gana masa azaba akanta,gyada kai tayi alamar tabbatar wa."Yaron baida wani Laifi,tsabar ,zalinci yasa suka tsare shi,amma minyi magana dame gidammu,yace inhar ya dawo gaba daya saiya hukunta wadanda sukai wannan aikin,karki damu zai fito nan bada jimawa ba."Zainab kawar Habiba ce wadda suke zuwa wajan Habib tare,bata zarce ko ina ba sai gidan su Habiba,tana zaune da waya ahannu ta zabga uban tagumi,kiran Habib take amma bata shiga,duka Inda zata nemeshi taje babu wanda yasan inda yake.Kafadarta Zainab ta dafa, firgigit ta farka daga tunanin data tafi.Zainab yaushe kika zo,yanzu nazo Habiba,nazo miki da wani labari ne wanda nasan tabbas bazaiyi miki dadi ba,kiyi gaggawar sanar dani Zainab,Habib nagano ashe kamashi akai anacan ana gana masa azaba,cikin kaduwa Habiba ta mike,meyayi musu sike Zaluntar sa,wane police suka kaishi?hannunta Zainab ta ruko ki zauna miyi magana,bazan iya zama ba ki sanar dani kawai.

"Sanar da ita tayi da gudu ta fada room dinta ta dakko mayafi,Umma ce ta riketa me lafiya ina zakije,fadawa jikin Umma tai tana Kuka,Umma Habib akaina ake gana masa azaba,zanje nayo belinsa Umma,ko nawane zan kashe akan Habib.Kiyi shiru Yanzu In Abbankin ki ya dawo saiya kaiku,fir taki yadda banda Kuka ba abun da takeyi,to shikenan kije ki ganshi amma karki jima,da sauri ta saki Umma tai hanyar waje, Zainab data biyota abaya tana,yadda hankalinta or tashe yasa tana fitowa tahau kan titi,da yake gidan nasa akan titi yake,cikin tsautsayi wata mota data shararo aguje tai sama da ita,sàida Habiba tatashi sama kafin ta fado saman motar,Zainab hannu ta dora aka cikin tsabar kaduwa da tashin hankali aguje tai kanta tana jijjigata,da sauri memotar ya fito yana Jijjiga ta shima,babu alamar Numfashi atare da ita,sai kanta dake fidda jini,da gudu Zainab ta ruga tasanar da Umma,cikin fitar hayyaci Umma tai waje,Kuka tafashe dashi ganin halin da diyarta take ciki.Babu bata Lokaci akai Hospital da ita, emagency aka shiga da ita.

Adai dai sannan ne aka sako Habib,wannan mummunar Labarin ne ya fara riskarsa,asukwane yatafi asibitin da aka kaita.Iyayan ta na tsaye sunyi cirko cirko,hawaye yayi kaca kaca da fuskar su,babu alamun Habiba zata motsa,shigowar Habib yayi dai dai da dawowar Numfashin ta,da sauri ya karasa Inda take kwance,idanun ta tabude Ahankali tana dubansa,sunan sa take son kira amma hakan ya gagara,Ha ta furta kokarin ganin ta hada sunan sa,aman jini tafarayi ta baki da hanci,da sauri Doctor suka turata wani room danyi mata tiyata.Habib da yazama kamar robot atsaye,gaba daya baya gane komai waje daya yake kallo,babu jimawa suka fito kowanne face dinsa dauke da damuwa,saidai kuyi hakuri Allah yayiwa Yarinyar ku rasuwa.

"Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un gareka muke kuma gareka zamu koma,ayau gadai Habiba ta amsa kiran Ubangijinta,tabar 'yan uwa da Iyayanta cikin matsanancin tashin hankali,tabar masoyinta daya sadaukar da komai adomin ta,Allah daya basu ita yafi su sonta,ta tafi tana mecike da muradi,da fata na zamantowar ta mata ga Habib,Allah be kaddara hakan zata kasance acikin rayuwar ta ba.Duniya ba matabbata bace 'Yan uwa mufarka daga baccin daya rike idanun mu me matukar nauyi,bama tunanin Lahirar mu,me muka tanadar mata,ko yaushe muna Lissafin abunda zamu samu a wannan Duniyar ne,Duniyar gidan Aro ce.Allah yasa mucika da kyau da Imani,yasa mutuwa ta zamo hutu agaremu.

     "Ni kaina Kulsoom sàida na zubar da hawaye na tsanani tausayin Habib da Habiba.😭😭😭

"Tunda aka turo Habiba a gadon marasa lafiya Habib ya rike hannun ta,har aka sakata amota be saketa ba,har akaje Gida hannunta yana cikin nasa,bayajin komai baya ganin komai,baya sauraran kowa,Sanda aka zo yimata wanka babu Maganar da ba'ai masa ba kokadan be amsa ba,Oum dinsa tai masa magana ba amsa,kokarin banbare hannun sa akai daga hannun sa,sai awannan Lokacin ya saki wata kara mefirgitarwa,karar data karade kaf Unguwar babu wanda be jita ba.Kuka yake wanda be tabayin irin saba,koda mahaifinsa ya rasu beji rasuwar sa haka ba.Da kyar aka rirrike shi gaba daya baya hayyacin sa,har akai mata sallah kan gawarta ya durkusa yana kallon ta,Shikansa bazai tantance kallon meyake mata ba.

"Janye shi akai aka tafi da ita gidanta na gaskiya,sàida kowa ya tafi amma banda Habib da Nasir yana kan kabarin ta yana Kuka,Mahaifin Habiba da Nasir da kyar suka rarrashe shi,sannan ya tashi ya dawo gida,tunda ya dawo sàida yayi kwana uku yana halin rayuwa da mutuwa,da kyar aka samo rayuwar sa."Sanda ya dawo hayyacin sa yace bazai iya zama agarin nan ba,zai fita neman kudi yayi rantsuwa da Ubangijin daya Halicci sammai da kassai,saiya dandanwa Alhaji Sani kwatankwacin daci da ciwon daya dasa a zuciyar sa,saiyayi sandiyyar ahalin sa.Nasir ina son ka kulamin da mahaifiya ta da kanne na,zan turo ma kudi ka kama musu gidan haya,bazan taba dawowa ba saina cika alkawarina.Ajiyar zuciya Nasir ya sauke yana kallon Anisa da hawaye ya bata fuskarta,tsananin tausayin Habib da Habiba ya cika mata zuciya.

  😭😭Ni kaina tausayin su ya cikan zuciya,mutuwar Habiba ta daki Zuciyata,da rugurguza kuzari na.

Kufa Fans sainaji daga gare ku.
   
Mrs 🌹 Baba Bello Abubakar
    ......✍️✍️✍️✍️
     

     SALAMAR ZUCIYA

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(King and Queen Writers)*


 " *We Rule the World of Writing* "

Short Story  


    Last page 14


"Kinji dalilin daya sa Habib yake daukar fansa akan Abunda Alhaji Sani yayi masa,nikaina inna tuna rayuwar da Habib da Habiba sukai na kaunar juna,so sukeyiwa junan su na tsakani da Allah.Yanzu aiki ya rage gareki,kece zaki duk me yiwuwa wajan rarrashin sa da dawo dashi kan hanya,ya sani daukar fansa ba shine mafita ba,yana zaune Allah zai saka masa.Kin tuna sanda muka ganki muka rikice gaba daya,gyada kai tayi alamar ta gane Lokacin,yadda kikaga Habiba to haka kike,da ace Umman ta yan biyu ta haifa tabbas zamu ce kedin usainar ta ce,babu wani abu daya banbanta ku,wannàn shine yaja zuciyar Habib haryaji bazai tana iya barin ki ba saiya Aure ki.Da badan munsan ba'a taba dawowa ba in aka mutu to tabbas zamuce Habiba mutuwa tai ta dawo saidai kash ba'a dawowa in aka mutu.Share hawayan ta tayi,zanyi duk abunda nasan zai sakko dashi ya dawo kan hanya,gyada kai Nasir yayi yana mikewa,in kikai hakan kingama mana komai.Godiya tai masa na yadda ya cire ta daga cikin duhun daya mamaye ta,yanzu tasan abunda yake damun mijinta.

"Sai bayan magariba Habib ya dawo babu wata walwala a fuskarsa har wannàn Lokacin,Zuciyar sa a cunkushe take babu dadi sam,ya kasa mantawa da Habiba acikin rayuwar sa,zaka yayi tare da Lumshe idanun sa,zuba masa idanu Aneesa tai tana kallon sa cikin tausayawa.Nasan Abunda ya hada ka da Alhaji Sani,a hargitse ya dago yana kallon ta,taya akai kika sani,ta hanyar bincike saboda na damu da halin da kake ciki.Sakkowa tai ta zube agabansa cikin tsananin damuwa idanun ta tuni ya fara zubar da kwallah.Yakai Mijina kasani daukar Fansa sam ba abune me kyau ba,mezaisa bazaka yadda da kaddara ba,wannan abunda ya faru arubuce yake a Allon kudura,tunkan kuzo duniya Allah ya kaddara hakan a gare ku.Kana tunanin akwai wani dan Adam da zai iya cutar dakai,da ace duniya zasu taru dan su amfanar dakai,bazasu amfanar dakai da komai ba sai abunda Allah ya rubuta agare ka.Da ace duniya zata taru domin su cutar dakai da wani abu bazasu cutar da kaiba sai dai abunda Allah ya rubuta shi agare ka.Karka manta yana da yara yana da mata,hukuncin bashi kadai ya shafa ba har dasu,kana tunanin Allah bazai bimusu hakkin su akanka ba,matar sa batasan ya akaita hakane ba,haka yaran sa,yin hakan zai jawo kafada halaka me girma.

"Numfashi ya sauke na riga na gama daukar fansar da zan dauka akan sa, girgiza kai tayi wannan din ba daidai bane,shin asanda katafi yawon neman kudi kasan mutane nawa ne suka rasa rayuwar su adalilin ka,mutane nawane sukai Kuka akan ka,mutane nawane suka rasa farin cikin su akan ka,mutane nawa ne suka rasa dukiyoyin su akan,in har kayi masa afuwa kaima sai Allah ya dubeka ya yafe maka dukkan kura kuran ka.Sanda take maganar yadinga tariyo Lokacin daya tafi neman kudi irin gwagwarmayar daya sha,irin kakubalan daya fuskanta,tabbas yasan mutane da yawa sun shiga damuwa a dalilin sa.Cigaba tai dayi masa nasiha tana kara nusar dashi muhimmancin hakuri da yadda da kaddara,mekyau ko akasin haka."Zuciyar sa ce ta dinga sanyi dajin kalamanta,kallonta yake kamar Habiban sa,kamar Habiban nan data maida shi mutum,ta nuna masa shima mutum ne duk da yana talakan sa,tabashi sabuwar rayuwa,ta mantar dashi dukkan kuncin dake zuciyar sa.

"Mikewa yayi ya shige bedroom dinsa,key ya murza kafin ya durkusa akan guiwinsa Kuka ya fashe dashi wanda ya dade baiyi irin sa ba,tun Lokacin da Habiba ta mutu rabon da yayi irin wanann kukan,kiyi hakuri Habiba nagaza wajan daukar fansar ranki,nayi alkawarin zan dauki fansa kamar yadda yayi sanadin rasuwarki nima sainayi tashi,saidai kash na gaza Habiba ki gafarceni, Aneesat dake bakin kofa tana sauraran sa hawaye take sharewa,tausayin sa sake kwarara yake azuciyarta,sansa ya zagaye dukkan jini da jijiyar ta.A zaune bacci ya dauke shi ba tare daya sani ba.Yadda ya kwana a zaune haka Aneesa ta kwana abakin kofa,anan bacci ya kwasheta batare data sani ba.

"Washe gari da safe ya kira Nasir,sanar dashi yayi dukkan wata dukiya daya amsa a hannun Alhaji Sani a mayar masa da ita, company sa da Gidan sa,Nasir ba karamun Farin ciki yayi dajin wannan maganar ba,yayi Farin ciki sosai,Amma kasanar dashi bana son sake ganin fuskar sa har Abada.Yayi nesa dani ta yadda bazamu sake haduwa da juna,bana bukatar godiyar sa.Hakan yayi kamar yadda Habib yace yayi komai aka mayarwa Alhaji Sani.Yasha Mamakin yadda aka dawo masa da komai nasa, Alhaji Sani ya dinga bindiddigin wanene yayi masa haka.Wannan abokin nasa ya kara samu ya tambayeshi ya akai aka dawo mai da dukiyar sa,saidai kazo muje wajan Aminin sa,shine ya bada umarnin adawo ma da komai naka.

"Ba bata lokaci suka nufi office din Nasir,yana ganin su ya hade rai,meke tafe daku,nazo ne ka hadani da wanda ya dawon da dukiyata nai masa godiya,baya bukatar godiyar ka,kai gaba daya baya son yayi tozali da mummunar fuskar ka,in ko har ya ganka bansani me zai Iya aikata maka ba.Inda hali kayi nesa da garinnan kar asake jin duriyar ka.Nima dakaga ina Magana dakai akan dole ne amma natsani ganin fuskrka.Alhaji Sani da yayi zugudi yana kallon sa ya kuskuta,niko wane irin abu na aikata muku haka Kuka tsaneni a rayuwa,shiru NASIR yayi,sàida Alhaji Sani ya matsa kafin ya sanar dashi.Ka tuna da Habibullah da wanda zai Aura Habiba sàida kayi sanadin rabashi da ita,zabura Alhaji Sani yayi ya mike jikinsa na rawa,dama shine,kwarai kuwa shine ya zama haka,Wadda har kai sanadiyyar mutuwar matar da zai Aura.Dafe kirji Alhaji Sani yayi kafin suga ya tafi ya gadi ba numfashi, asibiti suka kwashe shi suka kai shi.

"Bayan Kwana Uku Habib yayi kiran Nasir,bayan yazo sunci Abinci ya kalli Habibullah,dama ina so na sanar dakai wani abu amma ba lallai yama dadi ba,aini Yanzu babu wata Magana da zata dagan hankali,Alhaji Sani ya rasu Sakamakon bugawa da zuciyar sa tai,daga kafada Habib yayi bani da matsala da mutuwarsa.Miyi Abunda yasa na kira ka,dama na biya mana Hajji ni da Oum da Aneesat dakai da matar ka,da iyayan Habiba,zamuje zan kara neman gafarar Allah na abubuwan danai abaya akan Allah ya yafe min,sosai Nasir yayi Farin ciki da jin haka,yayi masa godiya sosai.Ayanzu zaman sa da Aneesa sai san barka,ya dankarawa iyayan ta gida,ya samowa babanta aiki me tsoka,yadauke ta ya kaita Gidan su Habiba,sanda sukaga Aneesat ba karamun kaduwa sukai ba,kamar Yarinyar su suka gani,sunyi Kuka sosai suka roke shi ya dinga barinta tana zuwa amatsayin iyayanta.

"Yayi musu alkawarin zata dinga zuwa akai akai dan hankalin su ya kwanta,sunyi masa Matukar godiya,anan yayi musu albishir na tafiya aikin Hajji baki daya,sunyi masa godiya harda Kawu Aminu za'ai tafiyar sun samasa Albarka matuka.

"Bayan shekara daya na hange su jere a asibiti,iyayan Aneesat da iyayan Habiba da Nasir da Oum da Habib sai safa da marwa suke,Nurse ce ta fito tana murmushi,to Alhmdlh wadda Kuka kawo ta samu mace,hamdala sukaiwa Allah,me aka samu ta samu mace,zaku iya zuwa ku ganta,shiga sukai suna rige rigen daukar yarinyar, kyakykyawa me kama da mamanta.Aneesat ce tace ina neman alfarma,asawa yarinyar nan suna Habiba,sosai sukaji dadin abunda ta fada din,atake awajan Mahaifin Habiba yayiwa yarinyar huduba da suna Habiba.

"Ranar suna ansha shagali,an zubar da naira kamar ba asan zafin neman su ba, Little Habiba tasha gata tako ina sai san barka,abundai saidai ace Alhmdlh.

Nima Anan nace ALHMDLH
Abunda na fada dai dai Allah ya bani Ladansa kura kuran ciki Allah ya yafe mini.

Allah yasa mu amfana da darussan dake cikin labarin.

Godiya ga dunbin masoya da suke bibiyata ko yaushe.Wadanda nake Update a group din su ina mika godiya.

TAMMAT BI HAMDULILLAH

Post a Comment

0 Comments