UNCLE J BY KULSUM ISMA'IL IDRIS MRS BABA BELLO ABUBAKAR COMPLETE 1
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJIN KAI.
Ban yadda Wani ko wata ya juyamin labariba labarin kirki rarreni.
Na Sadaukar da Wannan Littafi zuwa ga Fans dina masu bibiyar Labarina akoda yaushe.
Na fara wannan Littafi Kamar haka.
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 1
Acikin jahar Jigawa karamar hukumar rimgim wani dan karamin kauye ne me suna tsoma.
"Wata yarinya na hango tana kyalla Uban gudu kamar fijo wata tsohuwa na biye da ita abaya tana sababi da tsine tsine amma tsabar tsokana tana gudun tana juyowa tanaiwa tsohuwar dariya da gwalo,abun da ya sake fusata tsohuwar kenan".
Wani Gida tafada matsakaici dan baza'a kirashi babba ba,babu sallama haka ta afka.
Tana zaune akan wata kujera yar tsuguno tankade takeyi acikin kwarya bum taji anyi gaba da garin sai ga garin ya tar watse akasa har Fuskarta saida tasa mu rabonta tai futu futu ko tsayawa batai ba ta afka daki.
Turo kofar gidan akai wannan tsohuwar ce ta shigo ina tsinanniyar yarinyar nan take wllh yau sai naga wanda zai kwaceta agarinnan sainayi mata tsinannan duka Inna da tai sakare tana kallan Iya me kayan yara tama kasan magana gaba daya bacin ranta akan garin da yake kasane itako Iya kumfar baki take bata fasaba wani kara Inna ta hango sun kuyawa tai tadauke shi dakin da taga tashiga nan tabita.
Tana kwance tai shame shame agado sai tikar dariya take tuna muguntar da suka yiwa Iya ita dasu Talatuwa jin saukar karan kawai tayi a kafafunta aiko kara ta kwalla tana wayyo na shiga Uku Inna zata kasheni Gwaggo zoki ceceni wayyo ni naga takaina.
Gwaggo dake bacci afirgice ta fado daga kan dan gadonta na karfe ko riga babu haka ta fado gidan dan katangar su daya kome za'ai tana jiyowa Inna ko ta zage iya karfinta take kirbarta da kyar gwaggo ta kwace ta duk kukan nan da take idanunta kamas babu alamun hawaye kawai kukan take da alama ma kukan iya shege takeyi.
"Haba Hauwa kasheta zakiyi tsabar takaici Inna kasa magana tayi ga Iya dake tsakar gida tana jiran tafito ta biyata barnar da tayi mata".
Yanzu Gwaggo bakiga barnar da yarinyar nan tayi mana ba dan garin da nake tankade wa zamiyi tuwo dashi gashi can ta tambadar akasa, Gwaggo ce tadau salati dan baccin daya kwasheta baccin yunwane ba karamar yunwa ce ta addabeta
Saurin ture Jalila tai daga jikinta yanzu saboda Allah dan abunda zamusa abakin salati shikika yasar akasa kyaci Ubanki kuwa zanga abunda zakici kema kuma fitinar da kikayo kece zaki kasheta da kanki tisa keyarta tai zuwa tsakar gidan da haryau Iya ke tsaye rike da kugu Jalila ce ta kalleta tare da murguda mata baki bam Inna ta buge bakin ina rabaki da rashin kunya kina cigaba waike wace irin yarinya ce da Allah ya yiki ba kyajin magana saiki biyata barnar da kikayo mata.
Ainaga bani kadai nayi mata ba har dasu Talatuwa to aikece shugabar su munafukar Yarinya me suffar ifiritai ni wallahi nafara tunanin anya ke mutum cema kuwa cewar Iya.
Miko mata hannu tayi bani kayana kememe taki bada kayan saida Inna ta daka mata tsawa sosai take jin tsoron Inna dan batai mata da wasa kwance bakin zaninta tayi dayayi cidin cidin da dauda su tsami gayene kantu gullisuwa garin bididis duk suka kwaso mata kamar jira take kuwa ta wafci kayanta gayyar tsiya da kinci kayannan kinciwa kanki masifa kuwa fuuuu tafita sukabita da kallo zuciyar Jalila cike da takaici amma takudurta aranta saitaci kayannan kota halin kaka.
Nuna mata garin data zubar akasa tayi bakiga barnan da kikaiba kenan sai Lokacin ma ta lura zare idanu tayi dan yunwa take ji bata tsaya wata wata ba kuka tafashe dashi baki bude su Inna ke kallonta ni wllh Inna yunwa nakeji nidai kibani abinci wayyo cikina abinci zanci banza sukai da ita dama Gwaggo ce take kulata in tana tabararta harta lallasheta itama yau tabata haushi dan jitake kamar ta rufeta da duka zata ja musu kwanan yunwa dan wannan garin shi suke dashi daka da waje.
Saidata gama kukanta mara dalili tatashi tawanke fuska da kafa jiki sai tashin tsami yake ahaka ta dauko mai ta mummulka jar hoda tadauko badani jaka ta ambula afuska aka dauki kwalli akaja jagira dige dige tas ta dige Fuskarta jam baki ja tadauko akuya ta dumbuli dusa shita shafa bakinnan jajawur hakora ta washe bayan takalli madubin hannunta bakaramin kyau taga tayi ba hakorannan kuwa har gansa kuka suke kai tabude za'ai daurin dan kwali ko tsagar kitson baka gani tsabar dadewar da yayi akitse Inna har dukan ta tayi akan ta tsaya atsefe amma taki yadda.
Kayanta tabude wata tsohuwar doguwar riga ta dauko aka saka dawani mayafinta daya fara tattarewa sukwal dinta datake bala,in ji dashi tadauko kwas kwas aka fara taku bata yaddaba ita budurwa kirjinnan ashafe kamar allon sha.
Inna ce tabita da kallo Jalila ina zaki da kika gambaza wannan hodar afuska fari tai da idanu aka jujjuya Inna baki ganni bane kinsanfa yau Lahadi gidan Maman Ladi zanje kallo yau za'ayi film din yan gayunnnan danake baki labari nima irin kwalliyar su nayi Inna dariya kawai tayi lallai ashe suma mahaukatane irinki shiyasa kika kulla abota dasu nidai nagaya miki karki kai magariba da anyi la'asar kidawo gida batace komai ba tafice taci dammara gidan Maman Ladi ta nufa ba sallama bako mai ta afka daki suna zaune ita da Mijinta suna kallo suna hira kamar dakin gyatumarta haka ta fada dakin saida suka zabura dan kamar ancillota haka suka ganta.
Cikin jin haushinta Baban Ladi yake fadin waike wace irin tinkiyar Yarinya ce da ba ayi miki tarbiyya agidan ku ba ko gidan arnane kyafado mana daki haka baki sallama ba ko ajikinta saima kara matsawa datai kusa da TV din kamar zata fada ciki Maman Ladi ce ta kunshe dariya dan tasan mutanan fa an hadu yanzu za a haura tashi yayi afusace fusgota yayi kamar kayan wanki haka ya watsota waje kamar Mayya haka ta sake zabura ko zafin faduwar batajiba tafara kiciniyar komawa dakin nanfa fada ya kaure atsakanin su tanason shiga ya hanata shiga shammatar sa tayi gaba daya kafafunsa takamo gata da shegen karfi rikica saiga baban Ladi akasa kanya tashi ta fada dakin tsabar karfin hali harda saka sakata tanajan tsaki.
Wallahi Maman Ladi wannan baban naki baida mutunci shi baza'aci arzikinsa ba to wallahi yama yiwa kansa kallon bazaiyi ba cikin dariya Maman Ladi tace hoo Jalila danja mutum da gidansa kice bazaiyi kallo ba na hanaki yiwa nagaba dake rashin kunya Jalila amma kinkiji yanzu kitashi kibude mai dakinnan yashigo kuma kibashi hakuri ko yanzu nakashe kallon.
Jin zata kashe yasa tai saurin mikewa ta bude kofar Baban Ladi ko kallonta beba danya fara zaton wannan yarinyar ba mutum bace kamarshi ace wannan ficiciyar yarinyar zata kayar kamar mutuniyar kirki harkasa ta tsugunna tana bashi hakuri banza yayi da ita yashige Uwar daka tabe baki tai kaika sani karma Allah yasa ka hakura.
Komawa tai taci gaba da yin kallonta yamma nayi Maman Ladi takashe kallo ta korota gida bagidan tanufa ba bala me tsire ta hango da buta ahannu zai zagaya dariya tai na angamu zakasan baka da wayo wallahi, sai kasan ni ka daka saidata tabbatar ya shiga kewayen kalle kalle tayi babu kowa awajan wani tsohon kwano ta hango cikin sauri ta karasa tadauka dam tacikashi da Kasa kan tsire da balangunsa tatafi da kasar hannunta.
Tas tabade naman nan da kasa zanga tayadda zaka siyar da naman yarda kwanon tai tasamu wajan buya hango Bala tayi da butarsa ahannu yana yan wake wakensa cije yatsa tai tana babbaka dariya kamar ance ya kalli Naman sa gaba daya kasa ta rufe kan naman cikin matukar kaduwa yake zabga salati yama rasa ina zai kama wayyo dadi kamar ya kashe Jalila.
Saidata tabbatar hankalinsa baya inda take tai wuff tafada gidan Maman Ladi sake gyara nutsuwarta tayi.
Kanta akasa tafito tana tafiya kamar ba ita ba jin Bala nata salati ta isa wajansa da sauri Bala me tsire meyafaru kare mata kallo yayi tabbas dagani ba ita bace dan da alama fitowarta kenan daga gida bansan wani dan asara ne yayi min hakaba koma wane In sha Allah kan dare zanyi masa kulla ciki saidai aga gawarsa kululu cikin Jalila ya murda haba Bala ba'a wasa da rayuwa koma wanene kai masa addu,ar shiriya amma banda maganar kisa to koma dai kece haba Bala aini kasan banajin tsoron ta mutu balle tai rai nicefa Jalila sa maza gudu kawai dai yau imanine ya sauka a zuciyata.
Yadda yayi da maganarta wani katon botiki ya dauko da ruwa haka yajuye Naman nan aciki yana wankewa Jalila na tayashi ba karamar asara yayi ba kamar yayi kuka saiko tsinewa wanda yayi masa haka yakeyi Jalila nata kunshe dariya tsire dai yatashi daga aiki ana tsomashi aruwa ya zagwanye roman balangu kuwa tuni ya zama kasa saida suka gama gyara wanda ze gyaru Jalila tace saiya sallame ta ba kanwa takasoba da zatai masa aiki abanza haka yabata tatafi ranta fes gida ta koma da Namanta aleda saidata leka ta tabbatar Inna na daki wuff ta fada dakinta saidata tabbatar ta cinye Namanta sannan ta futo buta tazara tai Alwala sannan ta leka dakin Inna da cikinta ke kugi.
Inna meyake da munki balla mata harara Inna tayi ban saniba tasan kwanan zancan dariya ta sheke da ita wallahi Inna daganinki cikin ki zulai zulai yake kira banza tayi da ita saidata gaji tabar kofar dakin.
Washe gari saida kyar Inna tayi dabara tadan dama musu kunu haka sukasha badan dadi ba gaba daya wannan Talauci yana damun Inna tunda malam yarasu yan Uwansa suka wawashe dan abunda ya bari saboda tsabar rashin imani wai ajiyewa Jalila gadonta zasuyi Alhalin ko biyar haryau babu wanda ya taba taimaka musu da ita ada suna da dabbobi amma yanzu ko kaza tafi karfin su kullum gari yana wayewa zata fara tunanin meza adafa wani abu zasuci musamman Jalila duk da tasan bata da kwadayi badai taje Gidan mutane abata abinci ba taci amma rashin bata abincin na damunta kar hakan yasa ta canja dabi,unta wani yayi amfani da wannan damar ya cutar mata da ita.
Ita kadai take da ita bayan sun shafe shekaru Allah bebasu haihuwaba kwatsam Allah ya karbi Addu,ar su tasamu cikin Jalila bayan haihuwarta bata kara ba Jalila tasha gata babu damar tai lefi Inna ta tsawatar mata Malam zai hau fada tatakura mata shiyasa tatashi fitinanniya ga tsokana Gwaggo makociyar suce tazama kamar Uwa agare su sosai take son Jalila itama matsayin kaka tadauki Gwaggo shekara biyu kenan da rasuwar malam sun shiga tashin hankali Jalila ma tasha kuka haka suka gaji suka hakura shekarun Jalila goma sha biyu kenan amma haryanzu batai hankali ba sai daukar magana dangin malam babu ruwan su da su tunda suka cinye dan gadon da malam ya bari suka dauke kafafunsu babu wanda ya karajin duriyar su.
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 2
Inna ce azaune ta zuba Uban tagumi gaba daya tayi zurfi acikin tunaninta gaba daya tunanin yadda Rayuwa ta juya musu takeyi ada inhar tai mafarkin zata wuni da yunwa saita karyata balle harta kwana da ita jitai hawaye sun taho mata tunawa da adalin Mijinta dabai taba gajiyawa da ciyar da suba harma ya taimakawa wasu Allah y jikanka Malam tare da share hawayan ta.
Assalamu Alaikum wata murya tayi sallama Wa,alaikumussalam Inna ta amsa lale maraba shigo yau kece agari wllh nice Inna kallon gidan tayi komai abushe kayau kayau kaida gani dai kasan ana cikin wani hali kujera ta dauko mata tazauna gaisawa sukayi tayi mata gaisuwar Malam cikin jimami Inna take amsawa.
Ina Jalila cewar matar uhm kema Indo kinsan tana can wajan neman maganar data saba yaushe kika shigo garin wallahi yau nazo shine nace aikuwa sai nazo mun gaisa nayi miki gaisuwa,aiko Nagode ALLAH yabar zumunci Ameen bakomai wallahi.
Dama nace Inna ko zaki bada Jalila saimu koma birni tare dan uwar dakina tacemin kawarta tana cigiyar yar Aiki kuma matar bata da matsala tana da kirki sosai bata da wulakanta talaka shiru Inna tayi dan gaskya batason ta rabu da yarta a halin yanzu gashi ta fara girma fatanta kawai tasamu Miji tayi mata Aure nanda shekara daya ko biyu.
Banki ta taki ba Indo amma kinsan rawar kan Jalila banaso taje ta jawo mana magana gata bata da hakuri duka wanda yayi mata sai ta rama.
Murmushi tayi haba Inna ai kowa yasan yarinta kuma zan jamata kunne ahankali zakiga ta sauya namiki Alkawarin zan rike miki amanarta dan ko basu fadaba ta hango babu atare dasu to zanyi shawara da Gwaggo yaushe zaku tafi gobe in ALLAH ya kaimu zan tafi to abunda muka yanke da Gwaggo zan gaya miki saiki shigo da safe in Allah y kaimu to Inna ba Damuwa.
Har waje tarakata sannan ta dawo gidan Gwaggo ta fada tana zaune itama cikinta na kiran curoma dan bata taba haihuwa ba danginta duka sun kare dama Malam ke taimaka mata gashi ALLAH ya dauke shi saidai su bishi da Addu,a.
Shigo mana amma yanaga fuskarki kamar da damuwa aidole kiganni haka Gwaggo nan ta zayyane mata komai shiru Gwaggo tai na wani Lokaci kindai san halin Jalila kartaje ta jawo mana abunda yafi karfinm mu kuma ance yan birni basa daukar irin hakan karsu koreta daga aikin kotayo barnar daza'a daure mu gaba daya.
Nima abunda nake tunani kenan Jalila ce ta shigo kafarnan tai bududu taci dammara daga sama harkasa suke kallanta yanzu wannan aka kaita birni aiba asan barnar da zataiba jin an anbaci birni kawai Gwaggo jitai ta fado kanta tana ihun murna za akaita birni itadai Gwaggo wahala ta isheta dama gashi cikinta be cikaba tazo ta dira akan cinyarta ke dalla dagata sokike ki karyata wazai kaiki birnin kina wannan haukan.
Kuka ta fashe dashi nidai Inna akaini birni wallahi nadaina duka wata fitina zannutsu nidai akaini Kuka take harda su birgima kallonta kawai suke da sukaga abun nata bana kare bane Gwaggo tafara rarrashinta dayi mata Alkawarin za'a kaita matukar tagyara halayanta.
Cikin Murna tatashi tana washe bakinta wani tunani Gwaggo tayi dan tana matukar so taga Jalila ta kintsu tazama kamar kowacce mace me aji da kamunkai amma shashancin da take yayi yawa gashi ba wanda yataba zuwa yace yana santa dan tasha fashe kawunan samarin da suka furta mata suna santa daganan duk suka rabu da ita dan tsira da lafiyarsu.
Za'a kaiki birnin amma da sharadi dole ki gyara halayanki kidaina kazanta da rashin kunya kidaina zagin nagaba dake duk abunda zaki bawa babba kiduka har kasa aikin da akace ke zakiyi shi to kisani kullum kar atuna miki kisan aikinki matukar kin yadda da hakan za akaiki sannan banda ramuwa akan duk abunda akai miki kice zaki rama ban yadda ba tabbas sai andawo dake gida ammiki Aure.
Kuka tasa dan tatsani ace za'ayi mata Aure nidai Gwaggo kidai maganar nan dan Allah ni banason amin Auren to naji yanzu kitaso atsefe kannan to nanfa ake yinta tuni ta bata rai dan ta tsani ace za'ai mata tsifa yanzu za'a samu matsala aidama me hali baya fasa halinsa kina gani Gwaggo wannan tafiya bazata yiwuba zanje atsefemin tafada badan ranta yaso ba Innace ta fara tsifar da kyar aka gama tana gunjin Kuka wankema ta shi tai tas sai Uwar dauda kuwa tana da gashi sosai sai muguwar kazanta batason ko yaya ataba kan.
Wankama Inna da kanta ta wanketa tas saigata takara haske dan ita kanta taji iska na ratsata bakinnan gawayi aka daka aka wanke mata shi shima sai gashi ya fara dawowa hayya cinsa,yan kayanta masu kyau Inna ta hadata mata awani buhu da sabon silifar dinta ranar Inna kasa bacci tayi dan sosai takejin rabuwa da yar tata kwaya daya tilo sosai tayi mata Addu,a sai da Asuba bacci ya kwasheta cikin banncin ta jiyo Sallamar Indo tashitai taleka tare da cemata ta shigo.
Dakin fes dan Inna akwai tsafta dakinta tas ashare zauna mana Indo tashin Jalila tafarayi wadda tun asuba ake tashinta tayi sallah taki tashi bazaki tashiba saita tafi tabarki zaram ta tashi kamar wata saliha har kasa ta duka tana gaida ita da fara'a ta amsa dan taji dadin yadda ta girmama ta dan Akallah zata haifeta.
Alwala taje tayi tazo tai sallah tana idarwa ta dauki jaka Innace ta dubeta babu abunda ya dameta itadai burinta atafi kawai.
Kya bari kiyi kalaci aiko a'ah Inna zamuyi amota zan siya mata dama inna tafadane kawai amma ko kwayar gero basu dashi itama Indo fahimtar hakan yasa tace tabarshi maganar Albashinta zan dunga turowa kanina sai ya dinga kawo miki In sha Allah.
Bakomai Nagode dan ÀLLAH ki kulamin da ita amanarta nabaki tuni Inna tafara share hawaye haka Jalila duk taurin Zuciyar ta batason rabuwa da Innarta rungume ta tayi suka fashe da Kuka jitake kamar tace tafasa bada yarta amma tariga ta amsa babu yadda zatai kuma batason mutum yayi nufin yimata Alheri ta nuna bataso zata bisu da Addu,a.
UNCLE J
Written and Narrated
By KULSOOM ISAMA'IL IDRIS
Page 3
Gidan Gwaggo suka shiga itama har Kuka tayi daga musu hannu sukai tayi har suka dena hango su tunda sukai nisa Jalila ta manta da wani kewar gida duk wanda tagani dagamai hannu takeyi tatafi Birni sai alaraka taki gona akeyi sai murna jama,ar gari keyi yau dai sun rabu da alakakai.
Ganin abun na Jalila bana kare bane Indo taja hannun ta tasha suka nufa suna zuwa mutum daya dama ake jira anata kaduna kaduna shiga sukai Indo tadora ta akan cinyarta dan danan direba yaja mota suka tafi tun Jalila na kalle kalle har bacci ya kwasheta.
11 dai dai suka sauka daga mota mashin ta tsare musu suna soma tafiya Uwar dakinta takirata akan ta wuce da Jalila gidan kawar tata,da yake tasan Gidan dan mashin din tafadawa inda zai kai su,wata hadaddiyar unguwa suka nufa shiru kamar ba mutam me numfashi a unguwar kowa na gidan sa.
Wani tan game man gida suka nufa tunkan kashige shi kasan an narka dukiya acikin sa,wasu fulawoyi ne masu gwanin birgewa suka zagaye katangar gidan tundaga waje.
Jalila dai kanta kamar zai tsinke sai mika wuya take tana kallon gidaje tsararru ba irin na kauyan su ba,kwankwasa get Indo tai wani buzu ne ya leko ta wata yar karamar kofa ganin ya santa karamar kofa ya bude musu suka shiga.makeken gida ne me girman gaske shuka ce kala kala kai zan iyacewa akayan fruit babu abunda babu.
Makwat Jalila tahadiyi miyau kai ashe zatasha gara ashe abirnima akwai bishiya bata sani ba,yan Aikin gidan gaba dayan su maza ne sai wata dattijuwa shine dalilin da yasa tanemi asamo mata yarinya mehankali wadda zata dinga taya Dattijuwar ayyuka,babban burin Jalila ta ganta akan bishiyar wani mangwaro data hango fes fes irin binta sugannan ne.
Kaida kaga Jalila basai angaya makaba kasan daga inda tafito,kofar parlon suka nufa itakanta kofar me azabar kyau ce da tsari.
Kinga Jalila muka shiga kikame kanki karki abunda zaija tace bakiyiba ajuya dake kauye,tab ni banda hankali zan shigo wannan gidan nafita ai nashigo kenan bafita karfin hali abunda Indo tace kenan to zako kiga ikon ALLAH karki nutsun in bata dauke kiba aidole kiyi waje.
Norking Indo tayi sunkai kusan mintuna biyu akazo akabude kofar wannan Dattijuwar ce da fara'a take kallon Indo danda akwai sanayya atsakanin su maraba kushigo mana cewar matar suna saka kafara su aparlon Jalila rai saurin da wowa baya danji tai wani suuuu wani abu me santsi taji tataka kamar zai kayadda ita
Taho mana Jalila so kike nafadi nakarye kina gani sun zuba mai adakin su salan haka kawai su cucan amaidani kauye nazo kenan harda su murguda baki aiko zan maidaki tunda baki da kunya.
Saida kyar tasamu Jalila tashigo makeken parlourn daya gaji da haduwa kamar me koyon tata haka Jalila tafara takawa daga karshe tsugunnawa tai takama rarrafe danji take kamar zata subale tafasa baki,cikin takaici Indo take kallonta ganin yadda take nema tabayar da ita tajawo Hajiyar ma tace tafasa,ita kanta Dattijuwar nan Dariya take sha ta tabbata wani babban comedy aka kawo musu.
Tsakiyar parlourn ta zauna tana zazzare ido gasanyin Ac yafara ratsa Jalila harwani lumshe ido take yi,ido hudu sukai da makekiyar plasma wayyo zokuga yadda Jalila tasa ihu saida suka razana gaba dayan su,adaidai lokacin wata hamshakiyar mata ta sauko kyakykya wace kamar balarabiya haka take fuskarta dauke da mirmushi akalla zatakai 50years amma jindadi ya boye shekarunta saika dauka batafi 40years ba.
Ganin su atsaye cirko cirko suna kallon ikon ALLAH dan Jalila fashewa tai da kuka baki bude suke kallon ta,ganin Hajiya ta sauko yasa Indo kama hannu Jalila datake gursheken kuka tazaunar da ita kan sofa Hajiya taiwa kanta matsaugunni.
Indo ta kalla kukan me takeyi haka Indo,wallahi Amma ban saniba kawai gani mukai ta fashe da kuka,kallon Jalila tayi ya akayine yammata saida Jalila aka fyace hanci tuni kwalliyar zuwa birni ta cakube fuska tai dama dama ga dauda ga uwar hoda data lancaba saita bada wata kala daban.
Wallahi Hajiya bakomai yasani kuka ba ashe kunanan cikin Aljannah muko mumacan cikin Jahannama to wallahi nazo kenan bazan koma ba ni ashe anjima ana cutata ban saniba ji wamcan katuwar TV ko rabi rabin tagidan Maman ladi batakai ba kai bama irinta bace kalli kan wani abu dakika zauna daganinsa zaiyi shegen laushi jiwani abu da kuka shimfede wannan uban wawakeken dakin.
Tunda nashigo banga kasaba muko munacan muna fama dajar kasa kema Hajiya dazakimin adalci nace zan koma kauye wallahi kyasa akaini gidan Mahaukata dan kinsan ba kalau nake ba.
Kalli fatarki subul subul inaga tunda aka haifeki a inji ake miki wanka.
Dariya suka fashe da ita har Hajiya jin shirman da Jalila takeyi to banda abinki waya gaya miki nance Aljannah aike Hajiya kingama shiga Aljannah tum tuni nice dai sai yanzu ALLAH ya kwatoni,àah Gwara dai nashiga ta gasken cewar Amma cikin zuciyar Jalila kuwa ayyana wa take amma wannan matar bata da godiyar ALLAH duk wannan dadin bemata ba wani take nema zata sake magana Indo ta rufe mata baki.
Waike Jalila wace irin yarinyace da bakin ki baya shiru wallahi matukar baki kama kanki ba zan maidakine ai miki Aure shiru tai dan Aduniya tatsani ayi mata zancan Aure badan taso ba tai shiru amma bawai dan tarasa abun fada bane.
Sai lokacin suka gaishe da Amma hakamma saida Indo ta kiftawa Jalila ido hankalinta yanacan wajan kallon plasma.Gatanan Amma inafatan tayi miki cikin murmushi take fadin tayimin sosaima kuwa gashi daga zuwanta tafara sani Nishadi kinga nasamu medebe min kewa tunda duk basa nan yaran.
Cikin jindadi Indo tace to Alhamdlh tafiya tayi kyau angode Hajiya Amma Dariya tayi babu komai Indo ina Hajiya Maimunan ai dawowata yanzu tace nafara kawo ta kunsake yin waya eh hakane kin kyauta ya sunan yar tawa Jalila kama baki tai kai suna medadi yanzu ki tashi kuhaura sama kinuna mata dakinta,koma dai barshi na kaita da kaina to Amma angode ALLAH ya saka miki da Alkhairi babu komai.
Bana tashi natafi kudi tadauko ajakarta gashi kyayi kudin mota ko amsa tai angod ALLAH ya kara arziki ameen,kallon Jalila tai bazaki rakani ko bakin Get ba kallon Indo tai lallai baki da hankali,um nagaji nibazan iya tashiba ma sarai Indo tagane manufarta karta futa kanta dawo arufe kor parlon dariya tai tana girgiza kai lallai jama'ar Gidan nan zasu sha fama sun hadu da daidai da su.
Dan tasan za asha gwagwar maya yi tafiyarki Indo tunda tace ta gaji sallama tai mata tare da sake jawa Jalila kunne akan ta kama kanta agidannan banda shiga abun da babu ruwanta to tace mata to wama zata takala fadan indai bada Hajiya zatai ba itadai bataga kowa ba sai Hajiyar zuwa bakin Get ma akwai tafiya medan nisa.
TAKU MRS BABA BELLO ABUBAKAR.
......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 4
Iya Iya Amma ta kwalawa wannan matar kira gani Amma yauwa dan ALLAH kawowa Jalila abinci dan da alama yunwa take ji, kallon Jalila tai cikin Dariya gaskiya da alama kuwa bana kawo mata minti 2 tafito da plate ahannun ta taf taciko shi agaban Jalila ta dire shi makwat Jalila tahadiye yawu kallon Iya tayi amma yanzu saboda ALLAH kirasa acikin abinda zaki samim abinci sai wannan dan mitsitsin farantin.
Baki bude suke kallonta azatan suma bazata iya cinye waba duba da yadda take yar firit da ita,keyanzu wannan abincin kadan yayi miki to aini wannan ko yayan hanjina bazai gama tasar suba zai kare,wannan din inji Iya cikin mamaki shidinfa cike dajin haushin Iya tana nema tai mata bakin ciki.
Kinga cinye sai akara miki cewar Amma data zuba ido taga yadda zatai da Abinçin tsam sukaga Jalila tatashi tafara kici kicin cire riga tofa abinda Iya kefadi azuciyarta haka Amma datake kallon ikon ALLAH atakaice dai saida Jalila tai tik daga ita sai wani bujan wando da Inna tasa aka dinka mata na atamfa komawa tai tazauna tare cire dankwali dan abincin yafi shiga sosai.
Batama san suna yiba cinyar kaza tadauka gam taruketa a hannunta fashewa tai da Dariya kai yau ALLAH ya hadamu wallahi saina yimiki cin rashin mutunci kamar yadda kika barar mun da abincina rannan wani cizo takaiwa cinyar waifa duk dan taiwa kazar mugunta ne🤣🤣🤣.
Tuni suka fara tunanin kodai tanada tabin hankali ne kafin mintuna uku tatashi da shinkafa da miyar kamar bata ci abuncin ba haka takeji lasar hannu take kamar zata cire yatsun hannunta, Hajiya ban koshiba kalli cikina tashitai tana jujjuyawa ko alamar tashi beba,uhm abunda Amma tace kenan lallai aiki ya same su.
Karo mata Iya karbar plate din tayi cike da jimamin dawa ALLAH ya hada su kara ciko mata shi tai tas takara hallakewa hakamma badan fa taji cikinta yakai geji ba maleji tayi dan kartai abun kunya abun kunya nanawa kuwa saidai kar akuma Jalila.
Tas tatashi tamaida kayanta Amma ce ta kalleta dauke da murmushi sannu da kokari shiru tai tana muzurai tashi muje nakaiki dakinki yan kullin kayanta tadauka tare da dorawa aka tabi bayan Amma ganin zasu hau bene taja tunga ta tsaya tana daga kanta tundaga farko zuwa karshe ina zasuje haka waiwayowa Amma tai tana kallonta taho mana Jalila
Hajiya nan kuma inane zaki kaini bene ko baki taba ganin saba a Tv din da kike kallo washe baki tai ina ganinsa yan gayu suna hawa Dariya tayi to aikema kinzama yar gayun ko da gaske ta kurawa Amma idanu cikin shakkun abunda take fada mata ehman amma sai kinfara wanka da kwalliya bata rai tai itafa indai saitayi wanka zata zama yar gayu saidai karta zama.
Ganin zata bata mata lokaci baya tadawo taruko hannun Jalila kamar gurguwa haka tadinga hawa benan akalla saida suka shafe kusan 10mnt dakyar Jalila takai karshe gani take kamar zata fado,ita kanta Amma tagajiyar da ita haka nan taji tana kaunar yarinyar shiyasa tashiryawa duk wani shirman ta amma tana tunanin zaman ta agidan dan tabbas mutanan gidan sukai arba da ita tofa bakaramin yaki za aiba dan sun tsani mutumin kauye.
Kunjifa wata sabuwa inji yan caca.
Wani daki dan madaidaici ta shigar da ita babu abunda babu adakin wani dan karamin bed ne ya matukar birgeta sai jujjuyawa takeyi adakin duk wannan nawane gyada mata kai tayi eh nakine amma bana son wasa kullum da safe zakidinga sauko wa kikama aikinki sharar parlourn da Moping shine aikin ki saiki shiga kiching kitaya Iya aiki kinjini ai gyada kai tayi.
Sannan banda tsokana da rashin Kunya kowa ki girmama shi karnaji karna gani sam ba sauraran Amma takeyi ba burinta kawai Amma ta futa tahau gadon can da take hange tayi tsalle akansa tamike tayi rawa akai shine burinta, toilat taja hannunta saidata koya mata duk yadda zatai amfani da kayan ciki sannan tafuta ta kyaleta.
Da gudu ko ta haura kan gadon tana birgima da ihun murna zata kwanta akan gado me laushi ba irin na Inna ba duk tauri tadade tana tsalle tsalle gaba daya ta hautsine dakin kamar bashiba duk abinda tagani saidata taba tai kaca kaca da dakin babu abunda ya dameta.
Da yake akwai Masjid a gidan ana kiran sallah taje tai Alwala duk fitinarta bata wasa da sallah ta inda taciri tuta kenan dan Inna saidata jajirce wajan ganin bata wasa da sallah.
Yau dai kwanan Jalila biyu agidan haryanzu bata fara aiki ba Amma tace sai tayi kwana uku zata fara bayan Iya tagama koya mata abubuwan da zatayi,har wannan kwanakin bataga motsin kowa ba da Amma tasha gargadin ta akan mutanan gidan tasha tunanin to ina mutanan da Amma take yawan jamata kunne akan su.
Yau Jalila zata fara aikin ta duk tsawon kwana kinnan batayi wanka ba kullum saidai tawanke fuska da ruwa talafka mai da hoda dan harda kayan kwalliyar ta tataho tun Amma namata magana har tagaji ta kyaleta.
Tana saukowa tadauko wani katon baho harabar gidan tafita takunna panpo taciko shi da ruwa da kyar takawo shi parlourn gaba daya tajike wajan mopar ta dauko kilin data gani a kiching ta dauko tsaf saidata juye leda guda abahon da hannu tafara dibar ruwan tana watsawa gaba daya sai data tabbatar wajan ya jiku yadda ya kamata yadda zaiyi dadin wanki dan sosai takejin haushin Iya akan bata iya aikiba yau kam babu wanda bazai tafa mata ba.
Zagewa tai ta dinga dirzar parlon baji ba gani aiko kumfa sai tashi take,tsayawa tai ta rike kugu tare da fadin wash alamar aiki yayi aiki itakanta nema take tasha kasa amma haka ta daure taci gaba da tsaiwa.
Megadi ne yaji ana zabga Hon da sauri ya tashi ya wangale kofar motoci biyune suka shigo kalu Innalillahi kawai yakeja kwana biyu da basanan bakaramin wata yawa sukai agidan ba,amma yau Masifa ta dawo shikan sa Direba beji dadin da wowar su ba kamar yace su koma haka yaji.
Wata hamshakiyar matace ta fito bayan Direba ya zagayo ya bude mata kofa dakyar ta fito tana baza hanci cimgom ne abakinta tamkar yarinya haka take taunar cimgom din.
Wasu yammata guda biyu ne suka fito suma cikin wasu matsatstsun kaya kamar ba yayan musulmai ba, wani uban hills ne akafar su me shegen tsini.
Sannu da zuwa Hajiya Get Man yakara so yana musu sannu amma ko kallo be ishe suba ko kusa ma basu nuna dasu yake ba daga uwar har yayan abun yayi masa zafi amma shanyewa yayi tunda babu yadda zaiyi sune masu gidan.
Taku har kullum
Mrs Baba Bello Abubakar
.........✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 5
Kai tsaye parlon suka nufa kamar baza su taka kasa ba Uwar ce agaba yayan nabiye da ita,cikin takama da tun kaho tashigo parlon gaba daya idanunta ya rufe sam bata lura yadda parlon yacika da ruwa da kumfa ba suuuuu tatafi jikake tim tamaku da kasa,kan su ankara da abunda yake faruwa sun sako kafafun su kusan tare suka kai kasa gaba daya jisukai kugun su yayi azabar amsawa kai anyama basiyi targade ba.
Faduwar yan matanne tajawo hankalin Jalila da aiki yayi aiki ganin mata yashe akasa sunyi tsamo tsamo kamar akuyar datasha ruwa fashewa tai da Dariyar mugunta tana nuna su hhhh kai amma wllh anyi girman banza yanzu wannan dan ruwanne yasaku faduwa kun tabbata ragwaye ne ku.
Kuluwa iya kuluwa sun yita wannan wace matsiyaciyar Mahaukaciya aka kawo musu Gida ko yar gidan Uban wacece sai jikinta ya gaya mata,wani ashar Hajiya Luba ta durowa Jalila dan lokaci daya sukaji tsanarta ta mamaye musu Zuciya wallahi muka tashi sai jikinki yagaya miki wace irin Mahaukaciya ce ke zaki zo kicikawa mutane parlo da ruwa.
Dan Uwarki ba Magana nake miki ba,karki sake zagin uwata wallahi dan ba sa arki bace yo wa yakawo ku tsabar Munafurci kushigowa mutane Gida da sassafe kusu Uban wane da bansan ku ba dan daganin ku maula kukazo.
Tashin hankali har su wata kucaka yar kauye zata tsaya tana gaya musu magana harda zagin Mom,kayan jikin su tatsaya tana karewa kallo fashewa tai da wata dariya tana nuna su ashema arnane nake bata wakaina lokaci karku damu in sha Allah bazan gaji dayi muku wa aziba saiku musulunta.
Wannan kowa ce shegiya ce Allah kadai zai raba su da ita,cigaba tai da aikin ta tabarwa banza ajiyar su tana rawa da raira waka irin wanda sukeyi adandali dakyar Mom ta daddafa tamike tsaye haka Rufaida da Salima kallo daya da sukaiwa Jalila sukaji tsanarta aran su balle kuma wannan lefi data sake yimusu komawa dabaya sukai cikin dabara suka fice daga part din gaba daya.
Da kyar suke tafiya kamar agwagi hardiga sukeyi sabida cikin ruwan da suka shiga part din su suka nufa da Jalila batasan dashiba tun zuwanta gidan,saida suka canza kaya tukunna suka samu bakin magana.
Yanzu Mom kina tunanin kyale wancan yar iskar yarinyar ne mukaga kinyi shiru,ai wllh Mom matukar baki dauki mataki ba muzamu dauka ba ataba dizgani irin yau ba ace wata kucaka yar kauye ita zatai mana wannan danyan aikin bazai yiwu ba Salima tafada cike da bacin rai wllh nayi alakawarin sai na yiwa yarinyar can dukan mutuwa saita manta sunan ta gaba daya.
Kwafa tayi itakadai take ayyana Abunda zatayiwa Jalila haka Rufaida take ayya nawa balle Mom da gaba daya bacin rai ya hanata magana intai magana ma aita bata bakin ta akan wata kucaka mewarin baki kwafa tai alamar zasu gauraya.
Iya ce tafuto daga dakinta suuu tatafi saura kadan tasha kasa fadi take kalu innnalillahi nashige su mezan gani nijikar furaira,dafe kirji tai tana kallon Jalila data zuba mata idanu tana kallonta haba Iya kamar wadda kikaga wata masifa kikejan wannan kalu haka ko gyaran nawane ya gigitaki yatafi da imanin ki dakuwa Iya tai mata ungo nakinan Jalila wane irin shirme kikeyi wannan dubafa kiga yadda gaba daya kika lalata parlon.
To bazan gyaraba aiduk acikin aikine eh naga alama kuwa,dai dai lokace Amma ke sauko cak tatsaya tana kallon aika aikar da Jalila tayi,sai washe baki takeyi ita alallai Amma tayabeta,yanzu haka kika maida wajannan Jalila kalli waje kin maidasa kamar wani kududdufi haka aka koya miki to matukar bazaki Iya aikinnan ba Gida za'a maidake.
Kamar wadda akasawa shorking haka tazabura tai baya saura kadan tasha kasa tsugunnawa tai ta dora hannu aka iyakar karfinta ta daddage tafasa kuka baki hangame Amma ke kallon ta,nidai dan ALLAH karki maidani aimini Aure tayama zanbar wannan dadin danake ci aka ciyar da arnema balle Musulmi.
Arne wane arnan bayanzu wasu gan sama gan saman arna suka fitaba tare da wata lutiyar mata dagani itakuma shugabar arnace,duk yadda Amma takai da shan kunu saida tayi dariya,su Hajiya sun dawo kenan fitina tadawo abunda tafada kenan aranta.
Kewaya cemiki arnane to itama matar gidannan ce kamar ni yadda zakimin aiki haka itama zata iya saki kiyi mata aiki kinjini ai,waro ido tai kema musulunta kikai daga baya kenan tanayi tana fata hanna yanta kin auna arziki Amma dayanzu ashe dagake se wannan bujan najikina zakina yawo,fashewa Amma tai da Dariya toko zata tafi tsirara aibaxa ta iyasa wannan bujan na Jalila ba daya hada uwar dauda kamar me.
Zata sake magana Amma ta daga mata hannu dan in zasu kwana suna muhawara bazata gajiba kimin shiru haka,Iya ta kalla temaka kitayata ku gyara parlon to kawai tace harara ta zabgawa Jalila haka kawai tabasu aiki da sassafen nan kai wannan yarinya bataji dadin halinta ba.
Sun shafe kusan awa biyu kafin parlo yadawo hayyacin sa gaba daya sun gaji anan kasa Jalila ta bingere takama baccin gajiya to wannan aiki aidole kisha bacci.
........✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 6
Amma zama tai kawai ta tsura mata ido anya yarinyar nan bata da aljanu haka take ayya nawa acikin zuciyar ta,Jalila kuwa saida takai kusan karfe 10 tatashi tana mitstsika idanu hango TV tayi akunne zumbur tamike abunnema fa ya samu,gaban plasma ta zura da gudu samun waje tayi ta tankwashe kafa kamar idanunta zai fado saboda yadda take zazzaro shi in anzo wajan Dariya tayi ihu da tafi sannan takoma ta zauna.
Babu kowa a parlon sai ita kadai Iya nacan tana aikinta dan bata tsayawa jiran Jalila talura ba aikin tazo ba kuma taga Amma tasa mata ido bata takura mata da tuna mata abunda ya kawo ta.
Alhmdlh abunda Salima tace kenan hango Mahaukaciyar da suke nema kallon juna sukai ita da Rufaida murmushin mugunta suka saki sket din jikin su da yayi matukar damesu suka tattare gaba daya tabada hankalin ta wajan film din da ake haskawa cak taji andaga ta dama aba banauyi ba tana shirin kurma ihu ruf Salima ta toshe mata baki da dankwalin hannun ta.
Basu direta a ko inaba sai gaban Mom,yauwa yaran albarka aini nasan dama bazaku bani kunya ba haba Mom taya wannan abar zata gagare mu ko Uwar ta basai mudauko ba balle ita,tsai Jalila tai tana kallon su da Mamakin mene dalilin dazaisa suje sudauko ta kamar wadda tai musu sata.
Mom ce tajuyo tana kallon Jalila wai wannan yarinyar ce ta kayar da ita rabonta da faduwa tun zamanin kuruciyar ta amma shine wannan village girl din zata sata faduwa,daga hannu tai kawai ta kwashe Jalila dawani azababban Mari duk taurin rai irin na Jalila wannan marin ya shigeta amma tsabar kafiya sam bata nuna ya shige taba,su kansu sunyi mamakin ganin ta dungurgur azaune kamar wadda aka sosawa kumatu.
Haduwa sukai su ukun suka dinga jibgarta kamar Allah ya aiko su bawai batajin zafin dukan bane a'ah tanaji kukan data fahimci suna so tayi shine bazasu gani ba amma sosai lugudan da takesha yake shigarta.
Sai da suka gaji dan kansu saigashi suna ta haki kallon su tayi daya bayan daya ta fashe da dariya ko banza taba su aiki kuma bashi suka ci ba ataba ta bama tayi balle kuma antakale ta.
Dama kwana biyu neman wanda zasu kara take sai gashi Allah ya kawo su har inda take,cikin mamaki suke kallon ta tome takeyiwa Dariya wace irin shedaniyar yarinya ce wannan,Salima ce takawo mata hanbari da kafa ke dan ubanki waye sa anki anan da zaki samu agaba kinai mana Dariya,wata dariyar kularwa tasake saki ta ya mutsa fuska ni dama kunji nace akwai sa'ana acikin nan aiku kunriga kuntashi daga aiki kunzama guzumayan mata gaku arna aikunga bana hada kaina da kuba.
Kuma kusani wllh bashi kukaci ni Jalila nice murucin kan dutse ban fito ba saidana shirya,nice kabewar kan kabari bakin cikin me taushe,ba aimin bama nayi balle kuma an takaleni kusa aranku saina wajiga rayuwar ku sai kunnemi hada kayan ku kunbar Gidannan.
Mom ce tasake kawo mata mari wani tsalle tai kamar birinya sai gata acan tsakiyar parlon haba dai inna zauna kuka sake duka na aiban cika Jalila ba wanda kuka daka yanzu ma kyale ku nai yadda innatashi ramawa Allah bazai kamani da laifin na zalince kuba bana manta ranar daukar fansa sai mun gauraya.
Ku sake kamomin aljanar yarinyar nan tara tara sukai dan su kamata amma saidata hargitsa musu parlour gaba daya su basu kamata ba ita kuma bata gudu ba wani glass cup ta hango dagani zaiyi tsada tana sane da suka biyota gadan gadan dama hanyar glass cup din tayi garam tai gaba dashi saidayayi sama sai gashi akasa tush ya tarwatse.
Hhhh kafin su ankara ta fyalla waje da mugun gudu tana dariyar mugunta Rufaida wadda idanunta ya rufe burinta kawai ta kamota cikin gudun da take sha tana daga kafar ta ta dora akan kwalba kara ta saki tuni jini ya fara tsar tuwa jabar tazauna ashe akwai wata akasan wata kara tasake kwallawa tare da fashewa da kukan azaba kwalbace ta shige mata bom bom.
🤣🤣🤣🤣Azaba kan azaba gata kafa gata bom bom kanta sukayo gaba daya suna tsinewa Jalila da danasanin dauko ta da sukai da kyar Rufaida ta mike kwalba tariga tanitse jini kawai ke shatata,cikin hanzari Mom ta dauki wayar ta doctor ta kira akan yayi sauri babu lafiya cikin 20mint ya karaso dan Rufaida babu dama ta zauna tana kwance ruf da ciki tana kukan azaba.
Da kyar yasamu ya zaro kwalbar ta kafarma ansha fama kan tafita saiga Rufaida da plaster a bom bom dan danan kuwa zazzabi ya ya rufeta cike da sakijin tsanar Jalila wadda ko sunanta bata sani ba amma tajawo mata wannan bala,in tana zaman zaman ta.
Haka Salima da Mom sai cin alwashin abunda zasiyiwa Jalila sukeyi dan baza su kyaleta tasha su abanza ba.
😁😁😁Haryau baku daddara ba muje zuwa.
Taku Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 7
Jalila kuwa saidata leka parlon babu kowa har yanzu Amma bacci ya dauke ta shiyasa bata san wainar da ake toyawa ba,dakinta ta shige sai lokacin taji yadda jikinta yake radadin azaba zama tai ta rafka tagumi su kuma waddan mutanan su wanene haka daga zuwan su zasu takurawa Rayuwarta.
Ko sune wanda Amma ke yawan yimata gargadi akan su inko haka ne tabbas bazata kyale suba koma wane matsayine dasu ita babu ruwan ta ko ciki daya kuka fito kaimata saita rama balle babu dangin iya babu na Baba,Murmushin mugunta tayi tuno abunda zatai musu sai sun sakan kance tukunna zata waiwaye su.
Babu wanda ta gayawa tai kus da bakin ta,haka taci gaba da warkajaminta da aikin ta dan yanzu Iya ta sake koya mata yadda yaka mata kuma Alhmdlh ta dauka bata da ganda ko kiwa Kichin ne bata damu da shigar saba al,adarta na cire kaya lokacin cin abinci babu abunda ta fasa kullum saitai sintir in zataci abinci.
Amma dakyar ta rabata da bujan nan datake ji dashi sababbin pants tasiyo mata guda 12 sai dinkunan ta kala uku takara akan kayanta kayan kwalliyar ta nakauye babu yadda basui da itaba awatsar asaya mata masu kyau amma fir taki yadda,maganar wanka mafa babu ita dan saitayi sati batai wanka ba data giftaka zakaji wani tsamin dauda ya daki hancinka,haka suke hakuri da ita ahankali wataran zata daina cewar Amma intai maganar tayi takiji saidai tace ALLAH ya shirye ki.
Yau watan Jalila daya agarin Kaduna har kawo wannan lokacin ko bakin Get bata taba zuwa ba tsoran ta daya karta fito daganan amaidata kauye,duk uban abincin datake loda bata kara komaiba to da tana wanka nema a tantance daga fatar ta babu daya saidai taci tai kwaskwarima abada hoda jambaki da gazar aja jagirar nan har kunne.
Harkawo wannan lokaci bata rama abunda su Rufaida sukai mata ba bafa waidan ta manta ba a'ah tana sane kome take sakawa aranta oho.
Yau haka kawai taji tana sha'war hawa bishiya dan andade ba ahaduba bayan tayi kwaskwarimar ta tagado data saba aka caba kwalliya riga da sket da Amma ta dinka mata tasaka sunyi kyau kayan amma da Jalila ta sasu ita daban kayan daban wani dankwali ta dauko acikin kayanta taci dammara dan arayuwarta inbatai dammara ba ai wankan be hauba.
Harabar gidan tafito babu kowa shiru sai sassanyar iska dake kadawa ta La'asar sakaliya,lambun gidan takarasa tsaye tayi tana canki cankar wadda zata fara hawa,idunan ta ne yafada kan wani apple daganin sa bakaramin zaki zaiyi ba,yauwa gawanda yakama ta nahau nagaji dashan mangwaro da gwaiba tun akauye gwara shima wannan na dandana shi kar ayi babu ni.
Daraf tahaye bishiyar ko tsoro bataji saidata daidai ta zamanta sannan ta fara tsinko guda daya takai bakinta lumshe idanu tai kai kambalastin dama akwai wannan abun medadi bantaba ciba kanta ta gaurawa mari amma nacuci kaina datun zuwana banzo wajannan ba,saidata cinye guda biyar tanaci tana sambatu dasawa wanda yadasa bishiyar nan Albarka.
Mota ta hango tana shigowa cikin gidan aguje har nema akeyi atake megadin tsayawa tai taga wane mara mutuncine zaifito daga motar nan.
Salima ce tafara fitowa sai wani wizzy da yasha az down kansa yasha wani aski narashin da'a kamar zasu shige cikin juna haka suka nufo lambun wasu kujeru ne da suke jere reras awajan kan guda daya suka hau duk ko da yadda ta matse su haka suka mamuki juna kamar zata hau cinyar sa.
Zaro idanu Jalila tayi kaga arnan banza har gida kuzo kuna iskanci aiko zanci ubanku daga kai har ita yanzu zakusan wacece Jalila,kiss taga sun fara yiwa juna kamar zasu cinye bakin juna hannu tadora aka dole nai muku jifan shedan yau dinnan.
Ahankali ta sauko daga kan bishiyar cikin sandar karsu juyota bishiyar mangwaro tahaye dakyar damma gwanar hawa bishiya ce da dole sai sunji motsinta,maida Numfashi tayi wani shirgegen mangwaro ta tsinko tsabar nemar rigima irin na Jalila rigar Jikinta tacire aciki ta tara mangwaro saidata tabbatar yayi yadda bazai bata matsala wajan aikin jihadin dazatai ba amma fa afadarta wai jihadi zatai 🤣🤣🤣.
Zuwa wannan lokacin su Hajiya Salima anshagala anata shedanci kamar mijinta tuni yayi fatali da breezeya da take jikinta daga ita sai sket tik haka Salima tai agabansa ba kunya ba tsoron ALLAH.
Sai data daidaici kirjin Salima da suka fara takalewa kamar silifas sai data wana hannunta yadda yaka mata ta saita daidai abun harinta jikake nik akirjin Salima wani ihu ta zunduma jin wata bakar azaba data ziyar ceta kanta tantace abunda ya sameta tafara jin ruwan jifa tako ina adari da sittin tatashi dan iskan saurayin nata tuni Jalila ta fasa masa kai dan saidata duba wani jibgege tukunna ta sakar masa aka.
Ihun Salima ne ya jawo hankalin ma aikatan gidan duk wanda ya rugo dan ganin meyake faruwa suna hango Salima na sabar sabar da kirji ba riga sai su dare kowa sai kaga yasha kwana aguje mazan su da matan su hatta Amma data fito dan ganin meke faruwa da gudu ta juya dan azaton su bakaken aljanu suka shiga jikin Salima hatta fara wurgi da kayan jikinta.
Mom da Rufaida fitowar su kenan suka hango abunda ke faruw amiliyan suka juya dan duk wanda zaiga Salima tabbas haka zaice ta haukace attachment din dake kanta tuni ya fadi sai wasu yan mitsi mitsin kalba da suke kanta ga Nono har kusan cibiya tana tafe tana zunduma ihu dakiran wayyo aljanu aljanu 🤣🤣🤣 basu tsaya ko inaba saida suka shiga daki suka sa sakata.
Muguwar kuwa tana kan bishiya tana tikar Dariya ko banza yau tarama fiye da abunda sukai mata ranta fes taci gaba da shan mangwaranta.
Sai data Tabbatar da sun bar wajan sannan ta sauko rigarta tasaka cikin farin ciki takoma part din su,tana shiga ta tarar da Iya da Amma anzuba uban tagumi cikin jimami kamar batasan komai ba haka ta waske Amma meyake faruwa naga kamar wadanda kukai gamo duk kun firgice,Uhm kedai bari Jalila ai gamon mukai gan samemiyar budurwa kamar wannan muganta sintir haihuwar tsohuwar ta ai ba lafiya gamon mukai.
Gumtse Dariyarta tayi haba Iya wace magana kike fadi haka wa kuka gani sintir cikin gulma dasan bada labari Iya ta gyara zamanta Amma dai ko kanzil bata ce musu ba,wa kuwa kika sani bayan wadan can kitika kitikan yan matan yayan kishiyar Hajiya,dafe kirji Jalila tai wace Hajiyar Amma mana wai dama wancan matar kishiyar Amma ce.
Au dake baki sani ba kishiyar tace mana da yayanta gansan gansan yau munga abu oh ni Habiba naga abunda ya isheni,wai nikam Iya kiyimin bayani amma sai kwana kwana kike kinkasa magana guda daya,to ai maganar ce bata fade ba shikenan nafasaji tunda abun jan raine eh naji bazakiji mutuwar sarki abakina ba nidai naga abunda nagani kawai.
Amma Iya wai dagaske Amma tana da kishiya af sai kuma kiyi dadina dake shegiyar tambaya,naga ke kika fara kawo zancan nan Iya amma shine zaki doramun lefi haka kawai,to naji gobe ma nasake ganin wani abu nazo nagaya miki tunda bakisan abun arziki ba.
Uhm bana tashi natafi jaje jame Iya ta tambayeta jaje tam jiki magayi ALLAH ya bada sa'a Ameen.
Mrs Baba Bello Abubakar
............✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 8
Kai tsaye part din su Rufaida ta nufa duk suna zaune aparlo sunyi jugum jugum Salima na kwance har Lokacin rike da kirji tana matsar kwallah damai da numfashin azaba.
Asslamu Alaikum ta rangada sallama kamar mutuniyar arziki haka ta sunkuyar dakai,ina wuni yame jiki ashe haka wannan abu ya faru to ALLAH ya kiyaye gaba kallon Salima tai sannu wai jikinne har yanzu kinga da akauye muke akwai masu kamun kirji aida ankaiki to Allah na tuba abune ma kamar jela taya za ai masa kamun fashewa tai da dariya.
Rufaida ce tamike afusa ce to dan ubanki komadai kece kika jajjefe su ba asani ba,wa ni karki dauramin jakar tsaba kaji su bini nida sai yanzu ma ake gayamin ga tsautsayin daya afkawa maman luku ke uban wace maman luku gatanan kuwa wannan aisedai akirata da maman luku na tabbatar wannan ta haifeni yasin nidaga yanzu ma Mama zan dinga ce muku.
Cikin fusata Rufaida ta biyo ta da gudu tai hanyar kofa tsayawa tai tana haki tana murguda musu duwawu tana musu gwalo harda su tafi tafara raira mata waka.
Maman luku me rababe rababe wacece me rababe rababe maman luku me rababe rababe,gaba daya mahaukata ta maida su, Mom kamar zata fashe tsabar tsanar da taiwa Jalila,saida Jalila tagama yi musu rashin kunya tsaf tukunna ta falfala da gudu ta koma part din su cikin nishadi da farin ciki.
Yau take Monday kuma ayau megidan zai duro kasa Nigeria kasarmu ta gado tare da babban dansa daya kammala karatun sa a America yau Gidan ba zama ko ina gyarashi akeyi girki kuwa kala kala haka aka shirya su.
Daga Amma har Mom kowa so take ta burge megidan nasu gyara akeyi tako ina yau Dad zai dawo su kansu su Iya ba abar su abaya ba dan sosai Dad yake musu alheri dole ne suyi farin ciki da dawowar sa.
Rufaida tarasa inda zata tsoma ranta yau sahibinta zai dawo agoge cen a mulke can wasu riga da wando ta saka wandon crazy ne sai riga body hop attached din kanta yasha gyara farata zako zako haka taje aka saka mata.
Mom sai kara gyare Rufaida takeyi dan dai kawaii yagani ya yaba takuma samu shiga duk wannan gyaran da sukeyi wanda akeyi bemasan da zaman suba sukadai suke haukan su.
Amma murna take kamar zata taka rawa sosai take mararin ganin tilon dan nata shi kadai ALLAH ya basu daga shi bata sake haihuwa ba.
Shiyasa Dad ba karamin ji yakeyi da shiba babu abunda zai nuna ya naso besa meshi ba matukar kudi yana siyan abun tofa zai narka ko nawane wajan siya masa.
Waini Iya suwane zasu dawo aketa wannan hada hada haka kamar wanda megari zaizo Dariya Iya tayi yo Allah natuba megari aikaramin alhakine keyanzu agarin ku inme gari yace zaizo gidan ku haka ake zama anata shiri,hmm tab to ai nagaya miki agarimmu ai saime matsayi megari zaije gidan sa har fadawa ne dashifa nasha yin lefi azo ace za'a tafi dani kafin azo nagudu.
Tab kice Jalila kin zuba fitina agarinku kibari kawai Iya kema karki mamakin kika shigo gonata na hukun taki nifa bana barin kota kwana har so nake atakale ni wllh jikina har kaikayi yake in nakwana biyu ba airigima dani ba,au harni ma bazaki kyale ba Jalila, kedai kawai kiyi Addu'a kar ALLAH yasa muyi arangama fada dani ba riba tasheke da Dariya tunawa da abunda taiwa Salima.
Dariyar me kike kuma uhm abardai kaza cikin gashinta kawai dan in aka figeta bazatai kyan gani ba,adai fige tan kowa ya ganta dan ubanta cewar Iya cike da san gulma dan arayuwar Iya akwaita dason tsogwami.Zan gaya miki amma bakin ki kisamai linzami inba haka ba zan dauki fansa akanki ato.
Cikin zakuwa Iya kefadin kinji nace zan fadawa wani kawai kifadamin kidaina jamin rai naimiki alkawarain babu wanda zan gayawa kima fada,saidata leka ta tabbatar Amma bata kusa sannan tajuyo yawwa ina rannan da wancan rindinar tai gamo da aljanu a wancan dajin, inane daji kuma inda wadan can bishiyun suke af lambu zaki ce to naji lambu to aini ce babbar aljanar zare idanu Iya tayi bangane ba yarnan ganar dani.
Karkace kai Jalila tai tafara bawa Iya labari tsuru Iya tai tana kallonta kai wannan yarinyar badai shedanci ba,yanzu dama kece kikai wannan aika aikar bayan tagama tikar Dariya amma kuma fa kin birgeni kinyi maganin yan iska bammu kashe Iya zamiyi tafiya tare dake a'ah Allah ya tsare ni da wannan iblishin naki zanci gaba da yamiki addu'ar fatan shiriya.
Koda daima ai dan megidannan tsaf zai dawo dake cikin hankalin ki imma ya gudu to zainemo miki shi wllh dan baya daukar wargi ko kadan kinga wadan can shirga shirgan su kan su tsoransa suke ji balle ke aba kamar abusheki kifadi,aini Iya wllh babu wanda nake jin tsoronsa da kowama zan iya karawa nan da kika ganni tokidai kama kanki wllh ina fada mikine karki jawo sanadiyyar da zaisa akaiki gadon asibiti.
Fashewa tai da Dariya ina tabbatar miki matsawar za akaini gadon Asibitin akan wani to kisa aranki tare za a kamu dan saidai muyi mutuwar kasko.
Hmmm wannan cin alwashi haka Kubiyo ni Fans dan jin yadda za afara wasan yanzuma aka fara muje zuwa.
Mrs Baba Bello ABUBAKAR
........✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 9
ALHAMDULILLAH komai ya kammala mata fiya ake jira kawai tuni an nufi airport dauko su karfe biyu dai dai na rana aka wangale musu makeken get ahankali motocin suka silalo cikin harabar Gidan.
Sannu da zuwa Alhaji Baba Megadi da Baba Direba suke sake maimaitawa murfin Motar suka bude masa fitowa yayi fuskar sa dauke da Fara'a yake amsa musu min sameku lafiya lafiya lau Alhaji.
Su Mom fitowa akai ana karairaya ita me Miji gaba daya bata ita yakeyi ba Amma kawai yake hange ina zai hangota,cikin takunta na nutsuwa tafito tasha lullubi cikin shigar kamala sabanin Mom da tafi to haka gandai gandai bataji kunyar mazan da suke wajan ba,tuni kwalliyar da Mom take ganin ta caba ta dusashe tunda Amma tafito washe baki yayi yana kallon ta sosai yake kaunar matar tasa.
Duk wani bacin rai ya hadu ya ruftowa Mom ita kanta tasani ko Amma batai kwalliya ba bazata taba hada kanta da itaba bare kuma tai kwalliya jibi tsabar tozarci itace tafara zuwa amma bemasan ALLAH yayi ajiyarta awajan ba shiyasa tasha alwashin saita tar watsawa Amma farin cikinta,kamar yadda take tar watsa mata nata ako yaushe.
Murmushi ta sakar mai itama cikin kaunar Mijin nata sannu da zuwa Dady haka take cemai kamar yadda dan su yake kiransa tun yana karami yauwwa Uwar Gida sarautar mata kum Mom tasake kumewa kamar ta rufeshi da kuka dakyar ta iya danne abunda yake zuciyar ta.
Cikin Kissa da kisisina take fadin nifa banga My Son din nawa ba Dariya Dad yayi kinsan halin miskilancin dan naki saiya gama shan kamshi tukunna zai fito,um ashe haryanzu halin be canba Mom ta fada cikin Dariyar yake saima abunda ya karu cewar Dad.
Amma da kanta ta karasa gaban Motar daya hakimce kamar wani sarki ja tai tabude kofar lumshe idanu yayi bakaramin missing din Amman tasa yayi ba sosai yake kaunarta jini da tsoka itace bugun numfashin sa akoda yaushe.
Kafafuwan sa ya fara zurowa kamar wanda baya taka kasa har wani jini jini kake ganin ya kwanta akafar luf ga gargasa data cikamai kafa tana kwance luf luf.
Jalila fa ana can ana caba kwalliya dan itama karfa arainata aimata kallon yar kauye yau har wanka tayi sabi biyu ahakan bakaramin kokari tayi ba aganinta dan dai kawai ta kashe kala itama.
Hhhh taba su runduna Mamaki kamar yadda ta saka musu suna zata tabbatar babu wanda bai gigice saboda ganin wankan data dauka ba tana gaban madubi an gambaza hoda ansha jam baki jagira akaja har kunne cunku tagano a Fuskar Rufaida tadau alwashin saita yita aiko tsaf tacike girar ta da uban baki.
Tsagun mage ta fara jerawa dan aruwarta tana son tsagun mage har tsakiyar kuncinta ta kaishi bayan dige digen da Fuskar tasha jujjuyawa tai komai yayi cikin jindadi ta zuge buhun kayanta doguwar rigar da Amma ta dinkamata tasaka wadda ta mayan cewa tsabar nacin satan da take yi harta fara tsofewa ta tattare.
Gwada irin tafiyar da zatai inta fita tai silifas dinta ta dauko ta dora shi akafar nan wow kai sai wanda yaga irin haduwar da Jalila tai abunma ai ba amagana.
🤣🤣🤣Fans naso kunga wannan wanka amma ku hasaso shi aranku tabbas har liki zaku manna mata.
Harabar gidan ta fito tana taku dai dai gawani Uban dauri data dan kwama akanta,dai dai lokacin daya fito daga mota adai dai lokacin sukai arba da juna wani ihu Jalila ta kwalla tare da zurawa a guje gadan gadan tayo kansa tana ihu da murnar ga dan Indiya ga dan India ALLAH y cikan burina naga dan India tuni aka dare kowa yayi ta kansa dan bakaramin firgita su Jalila tai ba yadda kasan damisa haka takoma.
🤣🤣🤣Tuni ya saki murfin Motar ya bawa hammata Iska amma ina Jalila tana biye dashi abaya tana cin gudun san takamo shi karya gudu batare data tambaye shi acikin film din da take kallo shikuma ya sunan sa,hhh shi gaba daya zuciyar sa tatafi a gamo yayi wannan ba mutum bace yarasa ma gane halittar macece ko Namiji.
Wani sufa Jalila tai saigata daraf ajikin Jalal jiyayi kamar numfashin sa zai dauke Jalila fa ta makale masa kamar kaska da kyar ya samu ya banbare ta kamar takadda haka yayi wulli da ita jikake kum ta bugu da kasa sai Lokacin ta dawo hayya cinta zumbur tamike kan Lokacin tuni ya samu wajan buya tsit kake ji babu kowa, kowa yayi takansa dan ma'aikatan gida babu wanda ya taba ganinta bare ya shaidata.
Cike da takaicin ya kufce mata tashiga parlour babu kowa sai karar AC dake tashi a parlour dakinta ta wuce tana cizon yatsa.
Amma ce take maida numfashi dafe da kirji Dad na kusa da ita da tunin me suka gani haka suke cin wannan uban gudu dan shi firgita ce tasashi gudu sam bega abunda akewa gudun ba dandai kar agudu abarshi ne bayadda zaiyi haka ya ware kafa ya dafe hularsa akai gudun tare dashi.
Waini gudumme kuka samu haka mekuka gani wanda ya baku tsoro,sauke numfashi Amma tayi haba Dady yanzu kai bakaga abunda muka gani ba wllh nidai damisa kawai nagani ta tunkaro mu shiyasa nai takaina tunkafin ta waiwayo ta ganni.
Cikin Mamaki yake kallonta damisa kuma agidannan kai gaskiya bakiga dai daiba Rukayya,au haka kace aida ALLAH ya nunama ita bazaka fadi haka ba, kingani ba wannan ba kizo ki sallameni yunwa nakeji to waima ina Jalal nifa banganshi ba.
Dafe kirji tai tashi tasahi muje mu nemoshi,mikewa Dad yayi tare suka fito suna karewa parlourn kallo babu kowa hatta Iya tasa sakata adakint tsit kake jinta.
🤣🤣🤣🤣Kubiyo ni danjin ina Jalal yaje ya buya.
Mrs Baba Bello Abubakar
.........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 10
Zagaye parlon suke tayi amma ba Jalal ba labarinsa daga karshe harabar gidan suka fice suna kwalla masa kira,Lambu suka shiga har zasu fito suka hango shi abayan wata bishiya cikin sauri suka karasa wajan sa fuskarsa tai hadu tayi jajir bakaramar tsorata yayi da ganin Jalila ba sak kura haka tadawo,son Dad yafada tare da tsugunnawa agabansa bawan Allah tuni zazzabi ya rufe shi gaba daya besaba da wahala ba.
Gaba daya Jalila tagoge mai hodar dake fuskarta da bakin kwallin data gambaza fararan kayansa sunyi cidin cidin hannunsa suka kamo da kyar ya mike yana tangadi,parlon suka shiga dakyar suka haura stairs dashi dakinsa suka bude suka shiga wani hadaddan dakine sai tashin kamshi yake komai blue ne acikin dakin ga wasu kwaikwaye da suke kawowa suna daukewa.
Bedroom suka wuce dashi cikin tsananin damuwa da halin da sukaga gudaliyar dan nasu kan bed suka kwantar dashi tare da jamasa blanket har kansa AC suka ragemai tukunna suka fice daga room din gaba daya,daidai lokacin Jalila ta bude kofar dakinta turus suka tsaya suna kallon kallo gaba daya Amma ta manta da wata Jalila daga sama har kasa take kallonta.
Dama itace tasa su wannnan Uban gudun Dad kuwa kallon Amma yake yana neman karin bayani,ina kika samo wannan yarinyar cike da takaici Amma ke kallon Jalila cikin hade fuska ta kalleta dazu kece kikafita harabar gidannan washe baki tai nice Amma bakiga yadda nacaba kwalliya ba harnaje na gano dan India amma ya gudu na rasa inda ya shiga.
Waro ido Dad yayi ya sake kallon Amma waini Rukayya ina kika samo wannan da alama tana da tabin hankali kika kawo mana ita gida,yar aikina ce Jalila maimaita sunan yayi aransa Jalila bece komai ba yayi gaba yabar Amma atsaye kamar ta maketa dan haushi,yanzu abunda kikai kin kyauta kenan Jalila kinsan sarai firgita Musulmi babban zunubine kinsan yadda kika firgita Al ummar gidannan kuwa.
Faritai da ido nimafa Amma wanka naci saboda bana so bakin da suka zo su rainani suyimin kallon yar kauye kankance idanu Amma tai to aigashi yanxu kallon Mahaukaciya ma sukai miki kifita daga idona Jalila kidaina firgita mutane yanxu ga Jalal can akwance babu Lafiya sanadiyyar arba da wannan mahaukaciyar kwalliyar da kikai.
Jalal wane ya satar mun suna haka wllh Amma yazama dole ma asiyo rago kodai ayankamin acanzan suna ko kuma shi ayanka masa acanza masa suna gaba Amma tai tabarta tsaye awajan dan ta lura intaci gaba da tsaiwa sai su zama daya.
Jalal be farka daga baccin wahala ba sai kusan karfe 4 na yamma ahankali ya bude idanun sa da sukai masa wani irin nauyi kansa har Lokacin sarawa yake Lumshe idanu yayi yasake budewa yadade azaune kafin ahankali ya sauko daga kan bed din kaynsa ya fara ragewa kafin ya fada toilet.
Bathtub yashiga tare da lushe idanun sa dumin ruwan yana ratsashi,Fuskar aljanar daya hadu dazu da ita kawai yake tunawa gaba daya tunin sa yakasa banbance mutum ce ko aljan jin yana neman bawa kwakwalwarsa wahala fara wankan sa yayi gaba daya jikinsa babu dadi.
Daure da bathroom ya fito yana yarfe gashin kansa tsayawa yayi gaban mirror applying cream yayi me matukar sanyin dadi kamar wani mace haka ya zauna yana shafe shefe jallabiya y saka tare da shimfida praying mat ya Kabbara sallah.
Ya jima azaune kafin y sake mikewa ahankali ya fara taking steps babu kowa a main parlo sai karar AC da plasma da take famanyi ita kadai kai tsaye dining y nufa kujera yaja ya zauna sam bakin sa babu dadi kamar wanda yadade yana cuta haka yakejin jikinsa.
Kwas kwas yafara jin karar tafiya alamar za ashigo parlon Rufaida ce sanye da wasu riga da sket sun bala,in matseta ajiyar Zuciya ta sauke hango shi datai shikadai sake gyara tafiyarta tai tana karairaya tare da yarfe hannuwa sarai yaga tahowarta amma yayi kamar be ganta ba,hade rai yayi kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa.
Hi yaya Jalal kamar ta ta watsa masa ruwan zafi haka yaji dan Aduniya ba wadanda ya tsana sama da Rufaida da Salima kai har Uwar suma ya tsane ta basu ba,karya wuyatai cike da kiss banai serving dinka daga mata hannu yayi am fine kamar zatai kuka haka takoma ta zauna wai meyasa yaya Jalal yakeyi mata haka gashi ita kuma aduniya babu wanda take so da kauna sama dashi dole ne saita same shi kota halin kaka.
Tsam yatashi ya barmata dining din kan sofa yaje ya lafe duk da yana jin yunwa ya gwammace ya hakura dacin abincin da dai Rufaida ta zuba mai.
Sosai ranta ya sake baci da wannan wulakanci na Jalal kwafa tai tana niyar tashi Jalila ta sauko da gudu kamar ankorota tana tsalle tsalle da wake wake hango Rufaida datayi yasata nufar wajan da sauri,Allah ya kamaki bayan iskanci kuma har sata kukeyi ko kunya ki shigowa mutane hargida kiyi musu sata wannan aiba adalci bane.
Fisabilillahi tunda dai Amma tana sammuku abincin basai ku hakura ba kuje can ku karata da iskancin ku dan Allah kitashi karkisa Amma ta gogi arnan cinku,kura mata idanu kawai Rufaida tayi cike da bacin rai wani wawan mari ta kawo mata jikake tas sosai marin yashigi Jalila amma bakinta be mutuba ni kika mara aiko wllh kin matar wa kanki masifa.
Sai data shammaci Rufaida abazata tai wata irin sun kuyawa takwa so gaba daya kafafun Rufaida sai gata akasa dim kanta ya daki dining table wata kara tasaka tare da fashewa da kukan azaba duk Abinda sukeyi Jalal yana kallon su tunanin sa wace aljanar yarinya ce wannan agidan su kwalliyar fuskarta ya kallah ras yaji gabansa ya fadi kardai itace ta razana shi dazu tabbas itace aiko zakici Ubanki.
Mrs Baba Bello ABUBAKAR
.......✍️✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 11
Tana tsaye tana tikar Dariya ganin Rufaida yashe akasa wani azababban mari ya tsinka mata saida Jalila tai wata katan tawa saigata dabar akasa gaba daya radadin har cikin kwakwalwarta take jinsa, Rufaida da farin ciki ya cikata atunanin ta ita yaramawa dukan harda sake fashewa da Kuka.
Kanta dawo daga hayyacinta ya rufeta da duka tako ina azabace ta ishi Jalila caraf ta kankame shi cizo daya kushi ta dinga kai masa sosai yakeji ajikinsa dan tuni fatarsa tafara fashewa Rufaida ce ta rusa ihu kufito za ai kisan kai zata kashe shi Amma Dad aguje suka fito har suna neman kayar da juna dakyar Amma da Dad suka banbaro Jalila daga jikinsa sai kuka take da tunanin metai masa yake jibgarta haka kamar jaka.
Cikin tsana yake kallon Jalila gaba daya ta yayyage masa fata sai azabar radadi yakeji daya san zaizo yasamu wannan yar daban dabe dawo ba kamar yadda yaji ya tsaneta itama haka taji ta tsaneshi kuma taci alwashin saita rama dukan da yayi mata bedaki banza ba.
Kala bece da kowa ba duk ko da tambayar da suke jera masa balle kuma Jalila dake rusar Kuka babu wanda yataba yimata wannan Uban dukun sai dan India kai ita ayanzu gaba daya yan Indian suma ta tsane su bama shiba.
Rufaida ce tafadi karya da gaskiya cikin jin zafinta Jalila tamike to almunafunfun saiki bari se antambaye ki kiyi karya medalili,Amma ta kalla wllh Amma saina dauki fansa akan abunda wancan dan Indian yaimin banmai komaiba zai mayar dani kamar wata jakar sa bashi ya dauka Fuuu tatafi daga wajan tana gursheken Kuka Dad Jijjiga kai kawai yayi kai ni nama rasa mezance wllh kome ya hadashi da wannan Yarinyar oho.
Amma data san halin Jalila inbaka tabata ba bata tabaka ta Tabbatar Jalal ne ya fara takalar ta itakuma bata barin kota kwana tamaida martani Allah ya kyauta.
Cikin tsananin bacin rai ya fada bedroom dinsa hargitsa gashin kansa yakeyi wace mara mutuncin yarinya aka kawo musu gida dole nema saita bar gidannan dan wllh saiya hanata sukuni matukar zaina ganin wannan halittar zai iya yimata mummunar illah.
Fatar sa yakalla da tasha ya kushi tako ina tayage masa fata kamar wata kura kwafa yayi zamu sake haduwa shikadai yasan abunda zaimata.
Kamar yadda ya kudurta aransa haka Jalila ta kudurta tana dakinta tana safa da marwa dukkan wata muguntarta saidata tattaro ta waje daya saita rama dukan dayayi mata atarihin rayuwar ta ba atabayi mata bata rama ba haka wannan shima bazata taba barin ya tashi abanza ba dolene tadau fansa babu ruwanta da wanene shi agidan koshi ne megidan saita rama balle ma bashi din bane.
Tofa Jalila tadau alwashi haka Jalal ya dauka wazaici nasara atsakanin su Kubiyo ni yanzu ma aka fara.
Amma ganin har magariba Jalal be fito ba dakanta ta hadamai abinci da sallama tashiga dakin nasa yana kishin gide har lokacin ransa amugun bace yake fuska ahade yake amsa sallamar murmushi kawai tayi indai Jalila ce kayi kagama dan kunta karawa kenan.
Son meyasa baka fito kaci Abinci ba cikin kara jin tsanar Jalila yake fadin banaci meyasa shiru yayi wai duk akan fadanka da Jalila kake wannan fushin Kanwar kace fa,da sauri ya dago yana kallon ta Jalila ransa ne ya sake baci ya zama dole acanza masa suna,hakan yake Ayyanawa a zuciyar sa.
Lallashin sa Amma ta somayi dan sosai take kaunar dannata da kyar ya sauku ya yadda zaici Abincin ganin yadda gaba daya ta damu da kincin abincin nasa dakanta tai feeding dinsa yana ci yana bata shagwaba ahaka ta samu yaci sosai sun dan taba hira lokacin sallar isha'i yayi tukunna ta fito daga dakin.
Taku har kullum.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 13
Washe gari Jalila tatashi fresh da ita kamar babu wani abu dayake damunta amma fa yana cikin zuciyarta ta basar ne kawai tasha kwalliyar ta yaudai hoda kawai ta bamgaza bata sa jambaki da gazar dinba,sotake ta gane a ina dakin dan rainin hankalin can yake saita gano hakan zatai tunani akan aika aikar da zatai masa.
Amma ce tafito daga dakin ta sam batama lura da Jalila ba ganin ta mike hanyar dakinta yasa tabita da kallo da tunanin ina Amma zataje wani hadaddan part da take yawan ganin sa akullum saitayi tunanin na wanene nan taga Amma tashige batafi 3mnt da shiga ba taji karar bude kofa kir idanunta nakan kofar Jalal ne agaba Amma na bayansa.
Wani shegen murmushi ta saki ganin tasamu abunda take nema Farin ciki ya mamaye zuciyar ta zaka gane Allah da girma yake ga mata nan bisa kanka saika gwammace da namiji dan uwanka zaku fatata danni Jalila fada dani ba riba abinda take Ayyanawa aranta kenan.
Taku daya yayi a stairs zuwa biyu yayi arba da ita tuni yaji ransa ya kara baci ganin wani shegen murmushi da take saki kamar kyanwa kallo daya yayi mata besake marmarin hakan ba kallon tama baya kaunar yi.
Amma ina kwana yaji muryarta ta doki kunnan sa kamar ba muryar ta ba haka ya ayyana azuciyar sa haukan da yake hangowa afuskarta bejishi acikin muryar taba.
Dan India ina kwana ya jiki kuma cike da tsokana take gaida shi in yayi mata magana to kasar wajan tayi mata murmushi Amma kawai tayi dan sarai yanzu tagane halayyar Jalila saidai tabaiwa wani labarin ta Amma ce ta harare ta tare da jamata kunne dining table suka nufa saida ya jawa Amma kujera ta zauna tukunna shima ya zauna.
Kamar wani mace haka yakecin abincin kamar baya so Dad ne ya sauko Jalila har kasa ta tsugunna tana gaidasa da Fara'a ya amsa sannu da aiki yawwa ALLAH ya yimiki Albarka Ameen Jalila ta amsa da alamar taji dadin addu'ar.
Wani bacin raine ya sake sauko wa Jalal ganin tun kafin Dad yayi masa magana yayi wa wannan snake din,kara tamke fuska yai.
Wani kishine yake kara shiga zuciyar sa arayuwar sa ya tsani yaga iyayansa sun hadashi da kowa saiga wata kucaka suna bude mata hakwara suna magana da ita, ko su Salima bakauna yake yaga Dad yana musu magana ba balle wannna yar kauyan.
Mom ce ta shigo yaranta na biye da ita har awannan lokacin Salima bata dawo daidai ba yawon club din da sukeyi sàidai taga Rufaida tafice yawonta amma ita ba dama dan haryanzu jifan da tasha bata gama warkewa ba,idanunta ne ya fada kan Jalila da ta kunshe baki wata dariya kecinta makamata harara tai tare da jan kwafa.
Sannu maman luku juyowa sukai gaba dayan su suna kallonta mazewa tai kamar ba ita tai maganar ba,Dad ne ya kallo Jalila data juya taci gaba da aikinta Jalila ya ambaci sunan ta tare zuciyoyin su suka buga Jalila wannan tsinanniyar dama sunan ta Jalila haka Jalal yakarajin tsanar sunan meyasa sunan su zaizo daya.
Kamar Mutuniyar Arziki haka ta tsugunna gani Alhaji murmushi Dad yayi aah Alhaji kamar wani tsoho kidinga cemin Dad kamar yadda yarana suke gayamin kema yata ce ai,washe baki Jalila tai tsabar dauda har wani gansa kuka hakwaran keyi nagode Dad Allah ya kara girma Ameen suka amsa shida Amma sauran kuwa ai sungama kulewa.
Wace maman luku cewar Dad dago idanu Jalila tai tare da gyara Fuskarta tadawo kalar tausayi Salima da Rufaida ta nuna gasu dan wadannan a kauyammu sun Aurar da yaya kai har jikoki zasu iyayi yanzu haka koda yake addinin mune ba daya ba shiyasa babu ruwan su kamar al amara Jalila ta barke da Kuka.
Baki bude suke kallonta to me akai mata Fyace hanci tai wllh duk inda naga arne tausaya masa nake sabida amakarantar allo yadda malam lawi yake mana wa'azin yadda walakiri zaita gididdibar yan wuta,to kunsan zuciyar musulci tausayi suke ban tundana gansu da su nake kwana nake tashi azuciyata amma nadauki alkawarin bazan gajiya ba harse sun musulunta.
Duk yadda Jalal yaso gimtse face dinsa saidaya murmusa ya tabbatar wannan yarinyar bata da hankali amma daya karkata yakalli su Rufaida bega lefin Jalila ba dan yadda kasan inyamurai haka suke shigar su ga su abubuwa ba fasaliba dirka dirka gasu da uban tumbi kai gaba daya dai basu da fasali.
Mom kuwa taje iya wuya cike da bacin rai ta kalli Amma waini Rukayya wannann tsintacciyar kin kawota Gidannan ne dan ta hana yarana sukuni ko kuma Alhajin kika kawowa ya Aura narasa wannan jaraba haka danna lura kece kike daure mata kugu amma zanyi maganinta bazan lamunta wata can tazo ta hana yan gida walwala ba da sake wllh kodai ki sallameta ko kuma ni nadauki mataki akanta.
Ai wllh inkinga nafita daga Gidannan da sunan komawa kauye saidai gawata amma nazo kenan ta Allah ba taki ba bazakimin bakin cikin jar miya ba haka kawai nakoma na kamacin miyar kuka baki isa ba.
To ALLAH na tuba ko Amma ce ai yanzu banga abinda zatamin da zanyi zuciya natafi ba inza afitar dani sau goma saina dawo sau goma.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 13
Rufaida ce ta kawo mata duka ke har kin isa yangida suna magana kidinga sa baki kina musu rashin kunya,Mtswww to ke kuma awa agola kawai kibar yayan gidan suyi magana bake ba danna tabbatar kudai bajinin Gidannan bane.Mom ce ta fashe da Kuka yanzu abun haryakai yar aiki ta dunga cin mutuncina wllh na tabbatar Rukayya kece kika gaya mata Allah ya isa tsakanina dake.
Dad ne ya dagawa Mom hannu kinga Saratu sarai kinsan wacece Rukayya bazata saka wannan yarinyar agaba tadinga yimata zancan ki ba karki sake zagarmin mata nagaya miki,au ni ba Matar kabace, ko da kike matata ban lamunta ki wulakanta min Rukayya ba ita kikazo kika samu dan haka karna sake jin haka daga gareki.
Jalila ya kalla karna sake jin kinfadi wata magana akan Saratu da yayanta itama kamar Amma take dole kiyi mata biyayya kinjini ai to kawai tace amma badan zatai abunda yake so ba dan bazata taba zama Mom da yaranta su maida ita jaka ba.
Mom kamar zuciyarta zata babbake tsabar yadda zuciyarta ke tafasa dole ne ma tadauki mataki akan Dady da Amma tana zaune baza ta taba yadda tazama boraba indai shigowar ta gidan bemata wahala ba to juya megidan ma bazai mata wahala ba,dole ne komai ya dawo karkashin ikonta tazama itace me fada aji da ita suke zancan.
Cikin Kissa Mom ta karkace kai aikomai ya wuce Dady kasan sharrin shedan za a kiyaye gaba,kuma itama dan yarinya ce shiyasa nan gaba kocewa akai tayi aibazata yiba Amma ta kalla yar uwata kiyi hakuri hakan bazata sake faruwa ba.
Kar Amma take kallon ta tadade dagane wacece Sarah wajan iya makirci da tuggu wannan abunda ta fadama ta tabbatar akwai wani abu datake kullawa aranta,murmushi tai babu komai Allah ya kara hada kammu ameen Mom tace amma a zuciyarta fadi take tare dawa Allah ya kiya sheni da hadakai da kishiya ai tsakanina da kishiya yaki ne babu ragayya ko kadan.
Amma afuskarta bazaka taba gane hakan ba.
Dad ta kalla am dama nace meze hana mudawo wannan part din kaga Zumuncin mu saiya sake kulluwa ba kamar ana nesa ba,tofa abinda Amma ta fada kenan a zuciyarta fadada fara'a Dad yayi hakane Sarah kin kawo shawara mekyau babban burina dama naga kun hade kanku waje daya.
Wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar Mom kamar ta tatashi tataka rawa intana nan aikinta zaifi tafiya yadda ya kamata,kallon Amma tai koba haka ba yar uwata sakin murmushi Amma tayi cike da basarwa hakan yayi kinyi tunani mekyau yawwa to Allah ya yi muku albarka ameen suka amsa.
Rufaida kamar ta zuba ruwa akasa tasha dan murna gata ga abun sonta haka Jalila take ayyanawa Alhmdlh ta kwana gidan sauki zako kuci ubanku saikin gwammace baki dawo dan ki takura mana ba munafukar mata,murmushin mugunta ta saki duk abinda takeyi Jalal na kallon ta ya tabbata yarinyar nan tana da aljanu zai fita daga harkarta gaba daya.
Tsam yatashi daga dining din yuuuu suka bishi da kallo Rufaida har hadiyar yawu take kamar mayyya sosai guy dinnan yake tafiya da imanin ta,haka Salima kejin wani abu akansa amma bazata taba nuna zalamar ta afili ba ita tasan ta wace hanya zatabi tasame shi cikin sauki bata da burin Auran sa amma ko yayane ta dan dani zumarsa koda saudaya ne wannan ya wadatar.
Haka suka bar dining din kowa da abunda ya kudurta a zuciyar sa.
Aranar Mom suka kwaso kayan sawar su komai akwai acikin part din part hudine a maine parlon na Amma saina Dad dana Jalal tunda Mom taga wannan part din taka zilamar sa tasawa zuciyarta saita shigo shi to yaudai burinta ya cika ta dawo kusa da Amma sosai tatsayawa Mom akahon zuciya da za'a bata dama babu Abinda zai hana takashe Amma murus kuwa har Lahira.
Kwana biyu da dawowar su part din wata haya niya bata taba tashi ba dan sosai Amma ke kawar da kanta akan dukkan abunda zata gani aiki fa yasake kacamewa Iya da Jalila data gama moping zasu bata kamar wasu yara ita kanta Amma ta dura da mugunta suke hakan kala batace musu ba.
Jalal da suke burin gani koda yaushe inya ga dama sai su kwana biyu ma basu ganshiba sai ya tabbatar da bakowa a parlon yake saukowa lambu shine wajan zaman sa dan fita sam bata dame shi ba yafi ganewa yayi zaman sa agida.
Mrs Baba Bello Abubakar
.........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 14
Yau Jalila ta ware ranar fara duty dinta 6 na safe tagama dukkan shirye shiryen da ta tanada kai tsaye dakin Jalal ta nufa cikin sa a taganshi a bude murmushi tayi sadaf sadaf ta shiga parlon sa baya ciki bedroom ta wuce kamar wani dakinta duk da dakin ya burgeta amma tatabe baki ina ruwanta ma da kyan wani daki.
Karar ruwa taji alamun wanka ake a toilet bakaramin jin dadin hakan taiba yarfe hannu tayi yanzu ta ina zata fara aikin ta wardrobe ta hango ahankali take takawa budewa tai kayansa ne a jejjere abun sha awa sai tashin kamshi sukeyi almakashin ta data boyo azani shita futo dashi saida ta zabi wasu shaddodi masu shegen kyau da tsada yanka na rashin mutunci takama yi musu baji ba gani saida tai musu lahanin da ta tabbatar bazai taba mora ba.
Futowar sa kenan kamar ance ya daga kansa ya hango aika aikar da take yi masa harde hannayansa kawai yayi ajikin kofa saidata gama aikinta tsaf dadi kamar ya kasheta tana dago kai tai abar dashi duk rashin tsoro na Jalila saidata firgita bacin ransa ne ya kasa boyuwa mene ribarta inta bata masa kaya kayan ya kalla tuno uban kudadan daya batar kafin ya dinka su.
Afusa ce yayo kanta gadan gadan dolene yayi mata dukan mutuwa yau da hannu daya ya cafkota a kokarinta na fyallawa da gudu kafin ya kara so inda take wasu tagwayan maruka ya kashe face dinta da su wani dummm taji kunnuwanta sunyi kafin ta farfado ya rufeta da azababban duka tsabar yadda dukan yake shigarta kukan ma kasayi tayi.
Saidaya tabbatar jikinta ya gayama ta tukunna ya kyaleta dan kwalin kanta daya dade da sabulewa ya dauka tam ya daure mata baki Allah sarki Jalila idanunta ma kasa budewa tai tsanar Jalal kuwa tasake samun matsugunni a zuciyarta hawaye kawai ke kwarara a face dinta keeee haka yaja ta kamar kayan wanki ya watsata a toilet kamar shara gum kanta ya daki bathtub saiga kan ya fashe tuni jini ya soma zuba daga goshinta.
Hankalin sa kwance yayi shirin sa cikin kananan kaya sosai sukai masa kyau kayandata gama kacaccalawa ya tattare wata katuwar leda ya dauka saida ya dura su tas ya barsu awajan makulli yasaka a kofar toilet din ta yadda babu wanda zai iya kawo mata agaji.
Ko tsayawa Breakfast beba yayi ficewar sa bayan get man ya wangale masa get da mugun gudu ya fita har Lokacin ransa a matukar bace yake da abunda Jalila tayi masa.
Karfe 8 Amma taji shiru ba Jalila ba labarin ta karfe 9 ta tabbatar kodai bata da lpyane dakinta ta bude yagama cakubewa tai kaca kaca dashi ga wani tsamin dauda dayake tashi adakin,Jalila Jalila shiru har toilet ta leka babu Jalila ba labarin ta saukowa tai tana tambayar Iya kotaga Jalila girgiza kai Iya tai aini Amma yau kome kama da Jalila ban gani ba ko aiki batayi ba yau.
Lambun gidan suka rankaya ita da Iya ba Jalila kai hankalin Amma fa ya tashi karfa yarinyar mutane ta bata tashiga uku,baba buzu ta tambaya yace shibema santa ba babu wanda yazo ya fita sai yallabai daya fita tun sassafe.
Part din su Mom ta tura Iya tagano ko tana can suka bada tabbacin basu ganta ba Iya tana futa suka sa shewa in sha Allah baza'a gantaba shegiyar yarin mayya alasa ansaceta akaita can imma yankata za ai a yanka basu da asara.
Amma zama tai tare da zabga Uban tagumi ina Jalila tashiga kodai guduwa tai tome zaisa ta gudu gaba daya batai tunanin duba dakin Jalal ba tana da tabbacin babu Abinda zataje yi dakin sa shidama akace yafita sassafe.
Dad ne ya sauko ganin Amma ta zuba Uban tagumi meyake faruwa ne gaba daya Amma ta kasa magana dan tana bude bakinta to kuka zata fashe dashi Iya ce tai masa bayanin abunda yake faruwa sosai abun ya daure masa kai to ina zata shiga dama tana fita ne àah Alhaji tunda tazo ko bakin Get banajin ta taba zuwa,dakan sa ya fita ya sake zazzaga gidan bega Jalila ba.
Allah sarki Amma ko ruwa kasa kurba tai saboda tashin hankali Jalal da yanacan wajan Abokin sa Jamal yama manta da wata Jalila sai karfe 2 ya nufo gida tunda yashigo parlon yasan ba Lafiya kusa da Amma ya zauna gaba daya ta firgice tai wujiga wujiga.
Taku har kullum.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 15
Iya ya kalla dan Amma takasa magana har zuwa wannan Lokacin,wllh yallabai Jalila ce tun safe ake nemanta haryau ba aganta ba babu inda ba aduba ba amma babu ita babu dalilinta,rasss yaji gabansa yafadi shi bamà ya manta da wata Jalila ba karfa yar mutane ta mutu,Allah y bayyana ta abunda yace kenan ya tashi da sassarfa yake taka matattakalar Ammah ce ta bishi da kallo cike da takaici 'yar mutane ta bata amma bazai tsaya asan yadda za'ai atafi nemanta ba zai tashi ya barsu awajan.
Da sassarfa ya karasa bedroom din key din toilat ya dauko tare da budewa tana ta kure waje daya tayi kuka harta gaji fuskarta ta bushe gaba daya babu alamun Numfashi tattare da ita tsugunnawa yayi cikin kyan kyami y fara tabata kara kunnan sa yayi daidai hancinta bayan ya kwance mata baki babu wani alamu daya ke nuna tana numfashi goshin sa ya dafe wannan yarinyar tana neman jawo masa matsala.
Kanta ya kalla ya kumbura yayi suntum buguwar datai adazu cak ya dagata ya fito da ita daga toilat din akan carpet ya shimfide ta dan bata isa tahau masa bed ba fridge yaje ya bude ruwa me shegen sanyi ya dauko murfin ya balle yana zuwa ya kwarara mata aka,sanyin ruwanne yayi matukar ratsa dukkan sassan jikinta Numfashi ta sauke cikin tsananin wahala da azabar ciwo.
Sam kasa motsawa tai dan ba karamar kirba Jalal yayi mata ba dukkan wasu kasusuwa dake jikinta be barsu ba saidaya tabbatar yayi musu mugun duka na gani kashe ni wasu zafafan hawaye ke kwaranya afuskarta gatsananin yunwar dake addabar yayan hanjinta.
Wannan azaune take saita dauki fansar abunda yayi mata saiya gwammace be taba sanin taba izayar daya gana mata saitayi masa fiye da abunda yayi mata,keeee tashi kibarmin daki kazama kawai me kwarkwata gobema kisa ke gigin shugomin daki saina kakkarya kasusuwanki saidai akwasheki amaidaki kauye kije can kikarata wannan somin tabi nai miki matukar bazaki fita daga harkata ba har lahira zan iya kaiki.
Tsawa ya sake daka mata zaki tashi ko saina sake ragar gazarki banza tayi masa dan ayanzu bata da lokacin sa ko yatsanta tanajin bazata iya motsawa ba balle tayi tunanin maida martani,amma matukar ita yar halak ce saita dauki fansa akan Jalal.
Kafarta ya kama feee yajata har kofar part din sa ya watsa ta waje kamar wata shara dan jiyake gaba daya dakin sa ya kauraye da tsamin dauda,yayi daidai da isowar Amma rass gabanta yayi mummunar faduwa ganin yadda Jalal ya watso Jalila waje cikin fitar hayyaci da alama bata cikin hayyacin ta hannun ta har rawa yake wajan tattaba jikin Jalila wanda tasake buguwa dif Numfashinta yasake daukewa.
Gaba daya Amma ta ciccibe ta tsabar kidima rasa inda zata nufa da Jalila tai bedroom dinta ta wuce da ita kan makeken bed dinta ta kwantar da ita gumi take sharewa tana mamakin meya hada Jalal da Jalila dama shine ya boyeta tome yayi mata,abinda take ayyanawa azuciyarta kenan,cikin sauri ta sunkuya tana sake kare mata kallo sket dinta taja kasa dole saita duba dan zuciyarta barazanar tsagewa take.
Pant din jikinta tai kasa dashi ajiyar zuciya ta sauke ganin ba abunda take zargi bane cikin tausayawa take kallon Jalila yadda gaba daya jikinta yayi rudu rudu kanta afashe haka bakinta afashe,to dama bakine arube ba brush yake samu ba dole duka daya ya fashe ya zama dole tadau mataki akan Jalal dan tabbas wataran kashe musu yarinya zaiyi.
Toilat ta fada saidata tara ruwa me dumi yadda tasan zaimata dadi sosai futowa tai ta dauketa bayan ta karasa cire kayan jikin ta towel ta dauramata kafin tawuce toilat din da ita a bathtub ta tsullama ta,zafin ruwan ne yafara ratsata wata ajiyar zuciya take saukewa ajejjere ajiyar zuciya Ammah ta sauke ganin Numfashinta ya dawo gangar jikinta.
Sosai Amma ta zage ta wanke Jalila fes saidatai mata sabi biyar sabin farko gaba daya ita kanta kumfar baka ta zama saboda tsabar daudar data dankare ajikin Jalila ba dole ba matar da bata wanka saitai sati biyu batai wanka ba ita kanta Ammah mamaki take wai wace irin kazama ce Jalila dama bata wanka haka take zama da datti shiyasa data gifta su sai sunji wani shegen wari da hamami na dukan hancin su.
Fes ta wanketa tasake nadota a towel kan bed ta kwantar da ita tuni tafara rawar sanyi hakoranta har haduwa suke da junan su,har awannan lokacin bata daina kwararar da hawaye ba najin zafin abunda Jalal yayi mata tea Ammah ta hada mata da kyar tasamu tadan sha kadan tana gama sha ta amayar dashi sosai Amma ta shiga damuwa ganin yadda jikin Jalila yake sake rikicewa rigar sanyi ta dauko ta jibga mata amma har Lokacin azabar sanyi take ji ga azababban ciwon kai daya rufto mata lokaci guda ga Kukan da takeyi kai abu dai goma da ashirin ya hadewa Amma.
Afusa ce ta fada dakin Jalal daya bararra je yana hutawa har bacci ya fara daukar sa wani mugun duka ta maka masa,a zabure ya mike ganin Amma tsaye akan sa tana huci kamar tarifeshi da duka haka takeji eh sannu Jalal nace sannu na gode da abunda kaimin ambani Amanar yarinya kasata adaki bansan uban da zakaci ajikinta ba in har sonta kake bazaka fada ba saika fara da sace ta.
Duk fa wani bacin rai Jalal jiyayi duniya har wani juya masa takeyi shine zai so wancan Abun mezaiyi da ita ya Aureta to yace ya Auri wa,badan Amma ce tai masa wannan furucin ba wllh ko wanene da saiya gane kuran sa,tashi muje ka duba yarinyar mutane tun kafin ta mutu kar ranka ya baci kaji dai abunda na gayama ka ,kamar zai fashe da kuka haka ya tashi wai Meyasa Amma takeyi masa haka box din sa ya dauka kamar zai hadiyi zuciya.
Yana gaba Amma na biye dashi kamar wadda take tsoron kar ya gudu oya maza kai mata taimakon gaggawa indai ba so kake kaga bacin raina ba,ajiye box din yayi harara yake makawa Jalila kamar idanun sa zasu fado oho ita batama san yanayi ba,tome akai kenan shine zaiyi jinyarta kome beci riba akanta ba kenan itace taci, wai tunanin me kake yi kayi abunda ya kawo ka mana,Allura ya fito da ita da srinji cike da mugunta ya tashi ya tsikara mata allurar duk da bata hayyacin ta saidata zabura dan aduniya ba abundata tsana sama da Allura yana zare allurar yafice Fuuu.
Jeka ala raka taki gona zama tai ta zabga tagumi da tunanin mezata ce da mutanan gidan aina taga Jalila adakin Jalal kai ina bazatai gangancin fadar hakan ba sarai tasan da Wadanda take tare zance dai toilet tashiga ta kasa budewa wannan kuwa akan wannan shawarar ta tsayar da zuciyarta.
Ahankali Zazzabin jikinta ya fara sauka saiga gumi ya fara karyo mata rigar sanyin ta cire mata wata vest ta dauko mata tatace data sakawa Jalila tazo iya cinyarta baccin wahala ne ya dauke Jalila cike da mafarkai marasa dadi.
Ajiyar zuciya Amma ta sauke tasamu nutsuwa sosai amma Mamakin ta me Jalila taje ta aikata masa haryayi mata irin wannan danyan hukuncin kwafatai zaka gane kuranka.
Mrs Baba Bello Abubakar
...........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 16
Kiran sallar magariba yasa Ammah tashi alwala ta daura bayan ta idar da sallah tajima tana addu'a kafinta shafa tafita daga bedroom din gaba daya,kasa ta sauka tuni su Mom anhallara gara sarakan ci tafada aranta da alama ko sallah basiyi ba amma sun rankayo cin abinci,cikin kisisina Mom ta rike haba ohni Saratu wai ina yarinyar nan tashiga ALLAH yasadai ba guduwa taiba dama tsiyar dan kauye kenan waya sanima ko sata tayi ta gudu.
Hmm kamar kin shiga zuciyata Mom nima abunda nake tunani kenan dama kina ganin idanun wannan yarinya ai kinsan barauniya ce,sam Amma bataji dadin abunda suke fada akan Jalila ba ai Jalila dai nariga naganta toilet dina tashiga ya kulle takasa fitowa sak sukai suna rarraba idanu gaba daya abun be musu dadiba sun so ace shegiya sace ta akai sa huta suma.
Rufaida ce tatabe baki kunji kauyancin ba taya zaka shiga toilet karufe kanka kakasa fitowa tur wllh jahilar banza kan yadade da dafewa da miyar kuka dariya suka saka tare da tafawa kamar wasu kawaye.
Banza Ammah tai musu danta lura so suke ta kula su ayi sa insa ita kuwa bata da lokacin su gaba daya,wai ina yaya Jalal yana sama Ammah ta bata amsa tsugul ta mike bari na hada masa Abinci nakai masa yawwa yar Albarka maza kikai cewai Mom data kiftawa Rufaida idanu,azuciyar Amma kuwa dariya takeyi gaki gashinan indai Jalal ne saikin gwammace bakije kai masa ba.
Saidata zuba masa komai dayake kan dining din tadauka tai sama har gyara tafiya ta sake ita alallai zataje wajan masoyin ta,tura kofar dakin tai wani sanyi ne da kamshi ya bugi face dinta lumshe idanu tai tana ayyana Jalal badai tsafta ba komai nashi fes fes.
Sallama tayi shiru da alama baya parlon abincin ta ajuye maimako ta fita tsabar naci kin fita tayi kai tsaye hanyar bedroom dinsa ta nufa kanta ta zura tare da lekawa.
Farka warsa kenan daga baccin daya kwashe shi yana niyar tashi yaji alamun anshigo masa room shiru yayi yana jiran yaga wanane ya shigo masa har uwar daki ya tabbatar ba Ammah bace da itace da yanzu tayi magana,gaba dayanta ta shigo dakin hangoshi datai akwan ce rabin jikin sane kawai arufe da blanket.
Gashin kirjinsa data hango a waje taji tana marmarin tabawa ahankali tafara sanda har bakin bed din ta isa zama tai dirim saida gadon yayi kasa a hankali tadauki hannun ta tare da dorawa akan kirjinsa kamar ta dora masa garwashin wuta haka yaji hannun nata ransa yayi masifar baci har shi zata zo tataba da wannan qazamin hannun nata.
Shiru yayi yaga iyakarta su Hajiya Rufaida fa tuni ta manta a inda take sunkoyo da face dinta tayi daidai tasa bakinta ta miko da nufin kissing dinsa dunkule hannu yayi saidaya daidaici ta kawo bakinta daidai nasa ya takarkare ya zabga mata wani uban naushi abaki tuni bakin ya fashe kanta dawo daga azabar da take fuskanta abakinta ya sake zabgama mata wani wawan mari.
Tare dasa dukkan kafafunsa ya harbota daga kan bed din kuka Rufaida ta fashe dashi gaba daya jikinta yayi mata wani uban nauyi lebanta kuwa ya haye kamar ganda da rarrafe take neman hanyar futa daga dakin amma gaba daya ta kasa gani tsabar gigi cewar da tayi hanyar toilet ta nufa tsawa ya daka mata karki kuskura kishigar min toilet da kazamin jikinnan naki.
Juyowa tai gaba daya taga ma gigicewa har wani dishi dishi take gani na azaba.
Da rarrafan tafita daga room din baki daya tuni ta mance da abunda ya kawo ta.
Da kyar ta samu ta tsaya da kafafunta daidaita nutsuwar ta tayi tare da jan vail din kanta ta rufe fuskarta dashi tun data fara taking steps suka zuba mata idanu musamman Mom dataji ta shiru har dadi ya mamaye zuciyarta suna can suna hirar soyayya🤣🤣🤣batasan wal mukalafatu take sha ba,Ammah kallo daya tai mata tagano halin da take ciki wata dariya ce take son kufce mata Allah ya kara take maimaitawa a zuciyarta ko barin da suke bata kalla ba tawuce part din su.
Gaban mirror ta tsaya tukunna ta bude fuskarta sai data runtse idanu ganin yadda tayi wani uban muni ga bakinta ya hadu yayi zungurere babu kyan gani ita kanta bata son kallon fuskarta bare kuma wani sai lokacin taji wasu hawaye na tsiyaya daga idanun ta menene laifinta dan ta so shi ta kauna ce shi duk wayewar ta ace akwai Namijin da zai dinga gudunta haka.
Yadda maza suke binta tanai musu wulakanci amma shi ya samuma tana binshi yake wofantar da ita, Mom ce tashigo danjin yadda suka kwashe da Jalal turus tayi ganin yadda fuskar Rufaida ta hadu takara wani uban muni kumatu yakara subu subu baki ya zama zungurere,wata ashar ta mulmulo wane dan iskanne yayi miki haka dakyar ta bude bakinta dayake azabar zafi Jalal eh lallai nayadda wannan dan iskan yaro ne.
Kamar ya samu jaka ya zauna yayi miki wannann mahan gurbar toke kina ubamme kika zauna ya dakeki daga abun Arziki kin kai masa Abinci samJalal badan arziki bane amma zanyi maganin sa ko zanyi yawo tsirara saikin Aure shi kinjuya shi kamar waina ni Saratu bantaba faduwa akan abunda nasa gaba ba.
Salima ce ta shigo jin hayagagar Mom tunga parlo karewa Rufaida kallo take tun daga sama har kasa fashewa tai da wata shegiyar dariya ke kinga yadda kika dawo kuwa kamar wata gwagwgwan biri waima garinya haka tafaru Jalal dinne yayi miki haka ko hatsari kikai a hanyar zuwa,harara ta maka mata Uban hatsarin nai ba hatsari ba dirshan Salima ta zauna tana tikar Dariya dan itafa wannan abu yayi mata dadi gwara su hadu su rasa gaba dayan su.
Ala baki hakuri daga tambaya dama ganinai abokin kuka shi ake gayawa mutuwa, Mom ce ta wurgamata harara wane irin rashin mutuncine zaisa kitisamu gaba kina tikar dariya kamar kina farin ciki da abunda ya faru aah Mom ni karki dauramin sharri aidama na lura kinfi son Rufaida akaina shiyasa kome kika samu saikin fara bata sannan kiban.
Banda abinki ba ita ce babba ba niba ruwana da girmanta wllh kowa ma babban kan sane,kinga Salima karkimin rashin kunya yanxu zan tashi mufidda rainin wllh,to mu fidda man daka musu tsawa Mom tai mene kuke haka ko sokuke magauta suyi mana dariya kushiga hankalin ku.
TAKU koda yaushe.
Mrs Baba Bello Abubakar
.........✍️✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 17
Tsaki taja tare da ficewa daga room din gaba daya zuciyar ta fes tasoma ace har hakwara ya cire mata kwashewa tai da dariya tuna yadda bakin Rufaida zai koma babu hakora.
Dafe kansa yayi cikin karajin tsanar duk wani ahali na Mom Sarah sosai yake jin tsanar ta kai bama ita ba har wadanda suka shafeta shiko mezaiyi da yayanta ko mata sun kare gwara ya gama rayuwar sa haka,sauka yayi daga kan bed din gaba daya alwala ya dauro ya fito parlo ko kallan abincin data kawo mai beba tsanar da yayi mata ya shafi abincin.
Ahankali tafara bude idanun ta da sukai mata nauyi har lokacin kanta sarawa yakeyi zuciyar ta cike da kunci da bacin rai dan tana farkawa kirbar da Jalal yayi mata adazu da safe dashi ta farka fashewa tai da kukan takai ci da bakin ciki arayuwarta ba ataba yimata duka makamancin haka ba koda amafarki ne bare agaske katon gardi dashi yazage yaita laftar ta ta tabbata so yayi ya kasheta da kwanan ta ya kare dayanzu tana can kabari cikin karkashin kasa akwance dan naman data samu tana ci kullum ya cuceta tabige da zama a karkashin kasa.
Kwafatai dan bazata taba yadda ba wllh alkawarine saita kaishi gadon asibiti kamar yadda yayi niyyar kasheta ita kadai tasan abunda zatayi masa babu duka ba zagi amma zaiji ajikin sa sai ya gwammace betaba taba.
Motsawa tai da nufin tashi taji bayanta yayi wata muguwar amsawa ga inda akai mata allurar wani shegen zafi yake mata mamakin ta wane yazo yayi mata allura,shinshina jikinta tayi dayake tashin qamshin turare data rasa a inama tataba jinsa zumburo baki tai koma nawane ina ruwana.
Ammah ce tashigo dakin dama ita tazo dubawa kota tashi,ma sha Allah Jalila kin tashi kasa magana tayi tana karewa dakin kallo ta tabbatar wannan ba dakinta bane kodai dakin Ammah ne hakane ma dakin Ammah ne sai tashin kamshi yake hakanan taji dakin ya birgeta tana bala'in son kamshi amma itafa bazata iya zama ta gyara dakinta haka ba.
Ruko hannayanta tayi ta zaunar da ita yajikin naki da sauki ta amsa cikin muryar marasa lafiya Allah y kara sauki tashi kije kiyi brush ki dauro alwala to kawai tace,ahankali take tafiya harta shige binta da kallo Ammah tai tana girgiza kanta gaba daya abun be mata dadi ba yadda lokaci daya Jalila tasake wani ramewa sai idanu awaje kamar kazar dataga wukar yanka.
Karewa toilet din kallo tai yayi matukar burgeta komai yana ajiye a mahallinsa tabe tabe tafara yi batai abunda yakaita ba shiru Ammah taji ta kwallah mata kira Jalila ko kwanciya kikai a toilet din sai lokacin ta farga da abinda yakaita toilet din sauri tai tayi brush ta daura alwala tafita sai rarraba idanu take.
Hijab ta miko mata ta zumbula ko ganin ta ba ayi acikin sa Kabbara sallah tai saidata rama duka sallolin da ake binta sannan ta zauna ta zabga tagumi,fita Amma tai ta zubo mata Abinci dama Jalila yunwa ta isheta gyara zama tai duk yawan abincin nan sai data hallakeshi itafa Jalila komin cuta bata taba kasa cin Abinci saita ci tayi kat tukunna zata sake kwanciya,sosai Ammah take kallon ta tana mamakin cinta amma ba agani ajikinta kamar kazar mayu.
Ruwa ta miko mata ta kwankwada saigashi tana maida numfashin wahala wata nutsuwa taji tana shigarta kai yunwa madai masifa ce kwarin jikinta ta sakeji har wani gumine yake yanko mata,saidata tabbatar ta samu nutsuwa Ammah ta kalleta Jalila inna tambayaeki zaki gayamin tsakani da Allah jijjiga kai tayi alamar eh gyara zama Ammah tai meyakai ki dakin Jalal.
Bata fuska tai jin an ambaci sunan makiyinta amma tsokanata yayi shine naje daukar fansa baki bude Ammah ke kallonta meyayi miki haka,rannan daya maran agaban sufadi wace sufadi ni Ammah namanta sunan ta yawwa fidah Ammah ce tayi dariya fida rufaida dai ko eh ita,wace irin fansa kika je dauka akan na tafi da almakashina na yanka shegun kayansa daba sufi dari biyar biyar agarimmu ba shine ya kamani yamin wannan dukan kamar wadda tai cikin shige.
Duk yadda Ammah taso gintsewa saida tai dariya kayan nasane dari biyar biyar meyasa ke bakya yafiya ne arayuwar ki Jalila ai mace da hakuri aka santa kunya da kamewa amma ke babu ko daya atare dake mezai kaiki dakin Namiji kinsan ba kyau mace da Namiji sudinga zaman waje daya ko,kallon Ammah tai to amma kema banaga kina shiga dakin Dady ba kidade acan aishima Namiji ne.
Ya salam wace irin Yarinya ce wannan toni ai babba ce kuma muna tattaunawa akan wani aikine daza mudinga samun kudi muna siyan Kazar da kikeci kullum,washe baki Jalila tai wllh Ammah kici gaba da zuwa dan bana son wannan dadin ya wuce kidinga kwana acan ma dan afi samun kudin sosai,kunshe dariya Ammah tayi eh inda yiwuwar kwanan ma zanyi sanda akaga kudin siyayyar yayi kasa dole na zauna atattauna sosai.
Amma kedai haramunne na sake ganinki adakin Jalal kebama shiba kowane Namiji babu ruwanki dashi,to abinda tace kenan amma bataji zata kyale Jalal yanzuma ta fara zuwa dakin sa sai ta tabbatar yayi laushi taci nasara akansa sannan zata barshi.
Amma nasiha taci gaba dayiwa Jalila tana wucewa ta bayan kunnanta dan abu kadan zatace tadauka aciki shine yin wanka ko bayan kwana biyu ne wannan ne zata iya daurewa tayi amma bayanshi bataga abunda zata iya bari ba kamar yadda Ammah take fatan hakan ya kasance.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 18
Ranar dai adakin Ammah Jalila ta kwana ta bararra je iska tako ina batsamin dauda babu hamamin da yake tashi daga jikinta ita kanta taji dadin jikinta amma wankanne fa gsky bazata taba jurar sa kullum ba,washe gari tana yin sallar asuba dakinta ta wuce kaya ta canza acikin yamu tsatstsun kayan ta yaudai bata shafa komai ba sosai taji dadin jikinta kamar batai wani ciwo ba.
Kasa ta sauko Iya naduke tana moping taga saukowar Jalila baki sake tabita da kallo ganin goshinta akumbure bata rai Jalila tayi wannan kallon fa iya kamar kinga sabuwar halitta,yo badole na kalleki ba jiya yarinyar nan kika tashi hankalin mutanan gidanan babu inda ba adubaba amma bake babu alamarki,kin bamu wahala wallahi.
Tabe baki tai kun sodai ku wahalar da kanku kunsan ko amafarki bazan gudu daga gidannan ba duk ranar da ku kaga haka koda amafarkine da kunfarka kuyi sadaka dan bani Jalila kuka ganiba saidai shafar aljanu,au damma mun miki abun arziki mun damu dake shine bamuyi miki gwananin ta ba aishikenan za akuma,babu abunda za akuma Iya kidaina min mugun fata dan bansan irin bakinki ba haka kawai kijamin salalar tsiya.
Naji bazan sake fada ba yanzu dai kifadamin meya faru kinsan nidake bata baci,murmushi Jalila ta saki gaskya Iya da agidan sarauta kike daba karamar munafuka za aiba kuma al gunguma hade rai Iya tayi nice zan zamo munafukar Jalila tabe baki tayi ke nifa ALLAH kawai nake jin tsoro da kika ganni ko innata tai lefi saina fada mata bare ke damukai haduwar kan titi.
Yau na tabbatar Jalila baki da mutunci ni kike gayawa haka,haba iyalliya ta wajena mene kuma abun hawa sama salan na kulaki miyi fada kiragemin zubin abinci tonidai bazaki fada daniba aminiyas,harara Iya ta galla mata da kika gama zagina yanzu ba aidole ki doje saboda tunawa da abinci,to kiyi hakuri tunda dai nabaki hakuri komai ya wuce subutal kalam nai dayake wani zubin kamar ba agasan baki ba haka nake saikinyi hakuri dani Iya.
To shikenan komai ya wuce yanzu dai kifadamin ina kika shiga jiya akaita nemanki,anya Iya ba mayya bace ta ayyana hakan azuciyar ta,hmmm kibari iya ainake fada miki jiyannan gamo nai da manya manyan ifiritai ba karamin artabu mukai dasu ba dayake nima kinsan badaga baya ba wajan jarumta,saboda kakana na bakwai yayi yaki da aljanu guda dubu 70 dafe kirji Iya tai kakan naki.
Kwarai kuwa cewar Jalila ganin yadda ta fara rufta Iya harta hau kan layi kuwa,to kinsan tsakanina dake akwai zama na amana ina saukowa naga wani shirgegen aljani ya durfafi dakinki waishi aljani dan kundale kuuuuu cikin Iya ya murda idanu awaje take kallon Jalila maganar gaskiya kike fadamin kota wasa,bata rai tayi kintaba ganin nayi miki karya girgiza kai tayi alamun aah jikin Iya sai karkarwa yakeyi saboda tsoro.
Tom shine fa nasha gabansa da tambayarsa mezaiyi adakinki Iya baiwar ALLAH da kullum kaganta da carbi ahannu,kada baki yayi tare da fadin kullum kinamai fitsari aka haka ankawo masa abinci merai da lafiya kinshiga toilet ba addu'a ba Bismillah kika fitsare mai abinci shine ya fusata yazo daukar fansa.
Tuna irin alkhirin da kikeyimin in kin bani abinci ban koshib haka bakya gajiya zaki karomin wani ga nama akai ga ruwa mesanyi bana manta Alkhairi ko kadan shiyasa nai kunar bakin wake natare shi muka dinga fafatawa, parlon nan yayi mana kadan har duniyar su na bishi mukai kaca kaca acan dakyar ya samu yagudu amma shine Iya duk baki ganiba akankifa nayi wannan kasadar na saida rayuwata saboda ke aiya kamata kijin jinamin tunda kinji dalilin dayasa kukaita nemana gwara ku iya nan kuka neme ni nikuma dana tafi Duniyar aljanu fa.
Fashewa Iya tai da kuka ashe Jalila haka kike kaunata agidannan ban saniba bani da wani masoyi bayan ke Jalila,aini yanzu ko sau goma zakici abinci nadaina jin haushin ki zoma ki zauna aidole kihuta nizanyi miki aiki yau taho taho kawar arziki,gintse dariyar dake cinta tayi wani munafukin hawaye ta kakalo Allahu akhbar kaji masu yi dan ALLAH kin cika yar Adam tagari in akaima alkhairi karka saka da sharri,aibazan taba saka miki da sharri ba nagode miki bazan taba iya biyanki ba.
Harkan sofa ta zaunar da ita tanai mata sannu feee Iya ta bude bridge wani sumamman drink ta dauko mata me shegen dadi makwat Jalila ta hadiye yawu,kai Iya na Dady ne fa ke toko Hajiya Ammah taji wannan aikin saida rai da kikayi abinda yafi wannan ma zata baki babu Abinda zata ce,kumafa hakane bana sha ko zanji sanyi araina.
🤣🤣🤣 Ina zuwa wani shegen zawo ne ya tasowa Iya gaba daya ta kasa sukuni tana barin wajan Jalila ta fashe da dariya saukowa tai daga kan sofa tai birgima harda hawayan mugunta gaskiya ta yadda Iya bata da wayo gaba daya zatayi amfani da ita taitacin dadi abinta sai inda manta ya tsaya yatsa ta ciza woni Jalilan Inna da Malam,tunda ya fito daga daki yake jiyo sautin driyar ta kobe ganta ba yasan wace mahaukaciyar ce ke wannan dariyar ilaikuwa itance tana kwance akasa tai shame shame cikinta harya kulle dan dariya.
Hade face dinsa yayi tsaf yana sane saidaya daidaici yan yatsun kafarta ya take su da takalmi dan mugunta harda murza kafar karar azaba ta saki gaba yayi kamar be aikata komai ba da sauri tatashi ta zauna tana kallon kafar tata dan yatsanta harya fara jini dan ba karamar mutstsuka yayi musu ba,idanun tane suka ciko da hawaye waime tayi masa hakane meta tsare masa kosan ganinta ne ba yayi agidan su kome zaiyi bazata fitaba tana nan daram saidai shi ya fita ya bar mata gidan amma itadai nan gani nan bari sadakin agalawa.
Da kyar tatashi ta komai dakinta ga azabar zugin da kafar ke mata ga takaicin drink dinta ya bare garin birgimar da tasha.
Mrs Baba Bello Abubakar
.........✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 19
Ammah ce tafito daga part dinta kai tsaye dakin Jalila ta nufa dan sake duba jikin nata,tura kofar tai hade da sallama tana zaune rike da kafa dan abun bana wasa bane kamar yadda ta daukeshi ji take kamar yatsanta zai cire hawayene wani na kurar wani aface dinta,da sauri Ammah ta karasa shigowa Subahanallahi meya sameki Jalila Cikin sheshshekar kuka take fadin kafata ke cewo.
Wa yayi miki hakan shuru tai tana sharar hawaye da dan kwalin hannunta shuru tai bata bata amsa ba ko faduwa kika gyada mata kai tayi alamar eh,haba Jalila Meyasa kina girma kina kara tabar barewa akalla fa zakika 13years ya kamata kisan kin zamo budurwa kikame kanki garin wasan ki kikaje kika bazge kafa,bata ce komai ba dan ita kadai tasan yadda zuciyar ta take tafasa akan abunda Jalal yayi mata.
Wayarta ta daga kiran Jalal tayi baya kusa bedaga ba Jamal takira ringing daya ya dauka gaisheta yayi cikin girmamawa da fara'a ta amsa abokinna kafa bama tare Ammah to dama yarinyar wajena zai dubawa kafa tadan samu rauni ne,bagani ba Ammah bana zo na dubata anan din bama sai kun zoba to shikenan Allah ya yayi Albarka Ameen Ammah.
Kallon Jalila tayi to kidaina kukan haka ga abokina Jalal nan zaizo ya duba miki kafar tsuke Fuskatai ai ita duk wani abu daya danganci Jalal ta tsane shi Ammah ce Kawai sai Dad suke suka fita zakkah sudai bataji ta tsane suba,sannu Ammah taci gaba dayi mata 20mnt ya karaso gidan kiran Ammah ya sakeyi akan gashi yazo to tace masa tare da bashi Umarnin shigowa maine parlo.
Hannun Jalila ta riko sauko muje ya dubaki kamar ta rafsa ihu haka takeji kafar wani azababban zafi takeyi mata duk dauriya irinta Jalila saigashi tana hawaye wani nabin wani,ahankali ta dinga saukowa saboda kafarta tunda suka fara taking steps yake kallon su da tunanin a ina Ammah ta samo wannan yarinyar da ganinta dai daga kauye aka kawota.
Kallo daya ya yimata yakaranci zatai rawar kai da kuma tsiwa face dinta ya kalla tahadeta tamau kamar wata babbar mace Abin Dariya ya bashi itakadai sai hura hanci takeyi agabansa Ammah ta zaunar da ita kara bata face tai dan karma yaga hakoranta ya raunata,gaida Ammah ya sakeyi tare da kallon kafar ta ta garin ya hakan ta faru,kabari Jamal garin kiriniyar ta taje ta bige kafarta.
Kallon kafar yayi sosai amma kamar taka mata kafar akayi ba bigewa bace wannan,da sauri ta kalleshi taya akai yagane hakan kenan abokin nasa ne ya fada mai harara ta galla masa Murmushi kawai ya saki na canka dai dai kenan wa kika tsokana yayi miki wannan hukuncin haka.
Kamar ta fashe dan tsabar yadda ya kular da ita,kayi abunda ya kawo ka kabar shiga abunda babu ruwanka abunda be shafeka ba shi wanda ya gayama shiya takanin kuje kaida shi nabarku da Allah akwai ranar kin dillanci ni Jalila kabewar kan kabari ce bakin cikin me taushe beci banza ba Ina nan bisa kan sa,tana wannan bayanin tana hararar Jamal danji take kamar ta tashi ta rufeshi da shegen duka.
Ammah ce ta auna kalaman ta ama aunin hankali tsaf ta gane abunda take nufi kallon Jamal tai sukayi murmushi dasu kadai suka san ma anarsa,nidai bani nakar zoman ba ratayar ma ba abani ba babu wanda ya gayamin takaki akai kawai nayi duba da yadda dan yatsannaki yayi ne amma zakiji sauki kanwata,ni bani da ya bani da kanwa bazan taba zaman kanwar kaba har mahadi ya bayyana.
Dariya ya saka dan ya kasa daurewa sosai ta bashi Nishadi kaga ka kyaleta kayi mata taimakon gaggawa kar kafar tata ta rube,bare baki Jalila tai ta barke da Kuka jin ance kafarta zata rube har sheshsheka takeyi tana tsinewa Jalal a zuciyarta,kinga kiyi shiru matukar kikai shiru akai miki abunda ya kamata babu abunda zai samu kafarki shiru tayi.
Ina box din Jalal tana dakinsa bana dauko maka,yi zamnki Ammah mene amfanina bari na dauko miki,tashi yayi ya haura sama kai tsaye bedroom dinsa ya nufa yasan tana ciki,yana shiga kuwa ya ganta a gefan bed dinsa harzai fito ya hango kayan daya dura awata bag dawowa yayi da baya ganin wasu sun leko a yayyage daga kayan yayi tare da zaro idanu kaya masu matukar tsada anya Jalal be fara sheye shaye ba mezaisa ya wulakanta kayansa haka kamar wani tababbe.
Aiko saiya tambayeshi yaji dalilin dayasa ya yiwa kayan haka in baya so yabawa mabukata mana,saiyaji duk ransa ya baci sarai yasan Jalal da zuciya zai iya yiwuwa wani abu ya bata masa rai ya huce akan kayan.
Asanyaye ya dawo ya zauna Ammah ta lura da yadda ya sauya amma batace komai ba, hydrogen yasaka ya wanke kafar duk wani taimako yayi mata magunguna ya ciro daga aljihunsa ya bata bewani jima ba yayiwa Ammah sallama ya fita,asibiti ya koma kai tsaye office din Jalal ya nufa shiga yayi tare da yin sallama akasan makoshi dan haushin Jalal ya cika masa zuciya.
Tana kishin gide ajikin kujerar sa kamar besan da shigowar sa Office din ba yatabbatar shine shikadai zai iya shigowa wajan sa batare da yabashi izini ba.
Jalal yaushe ka fara shaye shaye ban sani ba shan yayyun idanun sa ya bude masu cike da bacci da gajiya zuba masa su yayi,kawar da kansa yayi daga kallon sa shi kansa wani zubin Jalal yana yimasa matukar kwarjini shiyasa mata suka mato akansa kaf hospital dinnan matan su Dr Jalal Ma'aruf yayi wuff da su kai wasu ko magana cema ta hada su amma babu fuska kullum face dinsa adinke kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa.
Kamar besan abinda yake fade akan saba ganin bazai kulashi ba ya nisa meyahau kanka ka yayyanka kayanka kana da lafiya kuwa Jalal,ciwon hauka nake tsut ya tsuke bakinsa,in wannan maganar ta kawo ka zaka iya fitar mun daga office cikin barai yake nuna masa hanyar fita saboda duk wani bacin rai da Jalila ta kunsamai jinsa yayi ya dawo sabo kamar yanzune take yayyanka masa kayan.
Tuni idanun sa sun hadu sunyi jawur matukar be illata yarinyar nan ba bazai taba jindadi a rayuwar saba saiya hanata walwala dajindadi zai nemi kauyansu shida kansa zai dauketa ya maida ita ya yarda kwallan mangwaro ya huta da kuda.Yasan halin Jalal sarai inyayi fushi kabar shi kawai in ya sauko da kansa zai nemeka,bece komai ba ya tashi ya fita yana mamakin tomeya bata masa rai haka daga zancan kaya kodak bashine yayiwa kayan hakaba dage kadarsa yayi alamar shiya sani.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 20
Jiyayi ransa yana kara baci akan Jalila harshi wannan yarinyar zatayiwa wannan gagarumar asarar ita awa dazata shigar masa rayuwa abarda befi ya mutstsike taba yazama dole ya dauki mataki akanta tsaki yaja alamar Abun yana ci masa zuciya.
Wuni tayi akwance aparlo duk yadda su Rufaida suka so takalarta dan su daketa kin tankasu tayi kamar batasan da zamansu a parlon ba duk zata waiwayo kansu baridai taji sauki,abunda yake sake bata musu rai yadda Ammah takeji da ita kamar wata yar uwarta kamar ba aiki tazo yiba sai wani lelenta Ammah keyi abun yana kona musu Zuciya.
Biris Ammah tayi dasu sai harare harare sukeyi babu wanda ya kula su Allah sarki Iya wuni tai tana gudawa saboda firgitar da tai wuni daya tai zuru zuru Addu'a kuwa inzata shigar toilet saitai mintuna biyar tana jero ta gaba daya jikinta yayi Laushi Jalila tuni ta manta da wani labarin kanzon kurege data fadawa Iya itama tana can tana fama da kafarta wannan fa shine kowa da abunda ya dame shi makocin me akuya yasai kura.
Saida Jalila tai sati sannan kafar tata tasaki gaba daya ciwonma saura kadan ya warke,kullin kayanta ta dauko saidata nemi wajan zama akasa dirshan ta zauna ta bararraje kayan tafito da su kaf wasu bakaken leda tadauko kowanne da abu acikin su leda daya ta daka ta maida sauran ta zuge jakar tamayar da ita a mazaunin samun wajan ajiyeta tai.
Sassafe ta fito daga dakin ta kai tsaye part din Mom tafara nufa ajiyar zuciya ta sauke jin komar abude ahankali tafara ta kawa lekawa tai bakowa a aparlo dukan su suna daki suna sharar bacci tunani ta tsaya yi tana canki cankar takan wa zata fara takan uwar yaka mata ta fara sannan ta gangaro kan yayan,saidata lalleka ta tabbatar da bedroom din Mom tukunna ta tura kanta tashige.
Tana bararraje ta hangame baki tana sharar bacci sai jan mumshari take kamar rago, toilat ta nufa babu tsoron komai atare da ita bathtub ta duba babu komai aciki bakalledar hannun ta ta bude wani gari ta dauko harda guzurin spoon dinta debo garin tai ta barbade cikin bathtub din babu ta yadda mutum zai gane ansaka wani abu Murmushi ta saki sadaf sadaf ta fice daga part din gaba daya.
Har wannan lokacin babu motsin kowa part din Jalal ta sake nufa ahankali ta tura kofar bedroom din yana kwance yana sharar bacci yarfe hannu tai saboda wani dadi daya ziyar ceta ahankali ta wuce toilet dinsa yadda taiwa bathtub din Mom haka taiwa Jalal fitowa tai tana ajiyar zuciya,lallabawa tai ta isa har bakin bed din debo garin Maganin tai ta barbade daidai inda tasan da yayi juyi zai hau kan sa.
Tana fitowa daga room din ta sauke ajiyar zuciyah dakinta ta wuce ranta fes kamar ta kadda tsalle tai ta haye kan gadonta cikin tsananin munna da jindadi.
Baccin yau ba karamin dadi yayi masa wani mafarkin yake me matukar kayatarwa agare shi juyi yayi da nufin sake bararrajewa kamar an tsikareshi yafara jin kaikayi yana dan damun sa basarwa yayi kamar bejiba kai abunfa na gaske ne adari da sittin ya mike jin wani irin mahaukacin kai kayi daya ziyarci dukkan sassan jikin sa, toilet ya fada aguje famfo ya kunna tunkafin bathtub din ya gama cika ya afka ciki.
Jiyayi kamar ya fada cikin tafasashshen ruwan zafigigi cewa yayi ya rasa ina zaisa kansa yaji dadi susa ya farayi kamar mahaukaci jikin gini ya juya bayan sa yana susa yaji ina hakamma baiyi ba kaf jikin sa babu Inda besamu rabon saba tuni fatar jikinsa tai jajawur ta tashi tai rudu rudu dagashi sai boxer yafita asukwane dai dai lokacin Mom ta fito daga part dinsu aguje tana kai kayi kai kayi Wayyo Allah zammu tu na shiga uku ni Saratu ihuntane ya tada mutanan gidan gaba daya sukayo waje.
Mom daga ita sai sket iya guiwa ba riga ba dan kwali itama fatarta tayi burdun burdun har fuska,wai ina Jalal tuni Jalal ya fice daga maine parlo sam besan inda yake jefa kafafun saba tsananin tashin hankalin da yakeji adukkan sassan jikinsa tuni kansa ya fara juyawa Baba Direba ne ya soma hangoshi ya dirfafo kofa gaba daya baya hayyacinsa Subahanallahi meyake faruwa da yallabai kokarin fita yake daga gidan gaba daya baba megadi suka rukoshi yana fizgewa yana yi yana susa kamar mahaukaci sak haka ya koma.
Meyi musu wanki ne ya ruga cikin gidan da gudu Alhaji ga yallabai can ana kokawa dashi zaifita ba kaya ajikin sa,da gudu Amma tayo waje dan babu wanda yasan Halin da yake ciki kallo daya Ammah tai masa ta fashe da Kuka dan azatanta gamo yayi ko kuma aljanu aka turo masa sam baya gane kowa baya gane kowa kai hatta kwayar idanun sa masifar kaikayi sukeyi masa.
Dad ne ya rukoshi cikin tashin hankali meyasamu tilon dan nasa Ammah ce ta sake rugawa ta dauko masa jallabiya dakyar aka saka masa ita aka sashi amota tare da Mom da take ihu dkyar aka samata kaya itama aka rankaya dasu asibiti duk wanda yaga Jalal saiya tausaya masa amma banda Jalila zuciyarta wasai dama tai alkawarin saita kaishi gadon asibiti,allaurai akai musu sai wani magani d aka shafa musu na kashe kaikayi ankai kusan away daya dayi masa allurar kafin ta fara aiki ajikin sa allaurar bacci aka zarkada musu lokaci kan kani suka hau baccin wahala da azaba musamman Jalal yafi Mom jin jiki.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 21
Ammah zama tai akusa dashi ta rafka uban tagumi da tunanin meyasa meshi haka kamar me shafar aljanu hawayan fuskarta ta share ganin yadda lokaci daya ya hautsine kamar bashi ba duk ya kakkar ce fatar sa saboda susa yayi jajawur dashi.
Bude kofar akai aka shigo Jamal ne fuskarsa dauke da damuwar halin da abonkin nasa yake ciki,meyake da munsa ne Jamal me binciken ya bayar,Numfashi ya sauke gsky Ammah duk wani binciken da akai musu haryanzu ankasa gano musabbabin Abunda ya kawo musu kaikayin da suka fuskanta musamman na Jalal haryafi na Mom hatsari zai iya tabawa mutum kwakwalwa saboda yadda kaikayin yake zautar da mutum yarasa inda zaisa kansa.
Jinjina kai Ammah tai to muma munrasa wace masifa ce wannan ta kunno kai cikin gidan saboda abin shida Sarah kawai ya taba mugamu lafiyar mu kalau nafi tunanin ko a iska suka shaka,dan murmushi ya saki baza su shaka a iska ba saidai sunyi tarayya wajan amfani da abinda ajikinsa suka sami wannan cutar,gaskiya Jamal banajin akwai wani abu da Jalal zai yadda suyi tarayya dashi saboda ninasan wanene Jalal baya amfani da kayan kowa sai nasa.
Kuma sanda abin ya faru gaba dayammu muna daki bazamu tantance akan tata taya hakan ta faru ba amma yanzu alhmdlh tunda ansamo bakin zaran har sun sami bacci fatammu dai ALLAH ya kiyaye gaba za asanya ido ko za agano inda matsalar take,hakan yayi Allah ya kiyaye gaba Ameen cewar Ammah da haryanzu abun daure mata kai yakeyi.
Sake duba Jalal yayi ganin babu wata matsala yayiwa Ammah sallama ya fita.
Su Rufaida ma suna can suna tattauna yadda wannan lamarin ya kasan ce lokaci daya Mom ta birkice haka,anya Mom ba gamo tayi a toilet dinnan ba Salima tafadi haka tare da kallon Rufaida nima abinda nake tunani kenan tabbas aljanu ne suka shiga jikin Mom ba ita kadaiba har Jalal tunda bantaba ganin makamancin hakan koda wasa atare dasu ba,cigaba sukai da tattaunawa atsakanin su.
Jalal dai saida ya wuni a asibiti yasha allurai da karin ruwa kamar yadda Jalila tai alkawari saiya kaishi Gadon asibiti,bayan Magariba ya matsawa Ammah su dawo gida ya samu sauki babu yadda Dad beyi dashi ba akan ya bari ya sake kwana yace aah sutafi gida haka babu yadda suka iya haka suka taho gida Mom harwata rama tayi yini daya kawai sai idanu awaje har Lokacin afirgice take Jalal din ya fita karfin hali kansa har wannan lokaci azabar ciwo yakeyi.
Yana shiga part dinsa kan sofa ya lafe dan bayajin yau zai kwana akan bed din dan be manta akansa yafarajin wannan Mahaukacin kaikayin ba,ya zaka kwanta anan Jalal anan zan kwana Ammah kaida baka da lafiya kace anan zaka kwanta aikasan zaka Wahala ka koma kan bed din fir yaki yadda kuma yaki gaya mata dalilin da zaisa yaki kwana akai dakin yashiga ta dudduba bataga komai ma bedsheet din ta cire ta canza masa wani sannan ta fito.
To na canzama bedsheet jin hakan yasashi mikewa adarare yahau bed din jin babu Abinda yaji ya gyara kwanciyar sa sosai blanket Ammah ta jamasa ta jima adakin kafin taimasa Addu'a tafita duk yana jinta ya lumshe idanu ne kamar me bacci,shiru yayi ya zurfafa cikin tunanin Abunda ya sameshi ayau ta ina garin yaya wane ibtila'i ne ya fado musu haka towa zai aikata musu hakan.
Jalilah zuciyar sa tafada masa haka kawar da wannan tunanin yayi duba da yadda bashi kadai abun ya samu ba dashi kadai ne saiyace ita ce kuma aina ma zataje ta samo wannan abun me uban kaikayi bazama ta iya hakan ba haka ya karaci tunanin sa har bacci ya dauke shi.
Jalilah baccinta take kashirban ranta fes yau makiyinta ya hau gadon asibiti kai ita wace irin babbar rana ce agareta taga faduwar sa ko banza tafara huce haushin dukan da yayi mata ba wai tagama bane somin tabine wannan sainan gaba zata san abinda zata kara masa dashi dan ita bata yafiya ba kuma ta mantuwa.
Ita ce ta fara fitowa daga dakinta taci kwalliya riga da sket ne ajikinta yau shaawar kwalliya take ta zane fuskarta sosai da baki tasha jambaki da farin ciki tafito cikin Nishadi take aikinta.Mom ce agaba sai Rufaida abayanta kowaccen su ta dauki wanka ko ina zasuje da sassafen nan take ayyanawa aranta.
Ina kwana Mom ya jiki kuma ashe jiya hauka kikai gaskiya madai aljanun bada karfi suka shigeki ba tunda baki fara duka ba kuma gakinan ras kamar bake ba ina zakuje haka kukaci kwalliya gidan Ubanki zamuje ah daga tambaya zaki zagi ubana yana kabarin sa dannayi yakana saboda zaman tare naimiki ya jiki mene lefi anan.
Duka Mom ta kawo mata shegiyar Yarinya mekama da ifiritai ni kikewa rashin kunya zanyi maganin ki acikin gidannan nan kusa sai kin hada kayanki kin koma kauye badai agidannan ba banza taimata taci gaba da raira wakokinta abun ya sake kular da Mom zata sake magana Rufaida ta rikota ki kyaleta Mom ai ita bakomai bace kibari mugama da manyan tukunna wannan karamar alhaki ce koni zan gama da ita bama saikin sa min hannu ba.
Kwafa Mom tai aini shegiyar yarinyar ce haka kawai naji na tsaneta wallahi ko ganinta bana sonyi,aibaki fini tsanar taba da za aban wuka tsaf zan yankata wallahi,bangaje ta Rufaida tai saida Jalila takai kasa to dama abace kamar abushe ta tafadi shiyasa duka daya zata baje akasa babu karfi sai tsabar tsokana fita sukai daga parlon binsu tai da harara aikin banza kawai nidai ba yadda zakui dani.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 22
Saida tagama aikinta tsaf sannan taje ta ludi tea da 🍞 dinta tun bata iya sha harta saba sosai take zagewa tasha abunta,zaman jiran fitowar Jalal tai taga yadda ya koma amma harta karaci zamanta befito ba tana zaman jiran ta bingire ta hau bacci,bata farka ba sai kusan azahar tatashi tana zabga uwar hamma kamar batai baccin ba tashitai ta tafi dakinta alwala ta daura ta kabbara sallah.
Tana idarwa tacire dukun kunannan hijab dinta da yake tsamin dauda yau Lambu take sha'awar zuwa babu kowa aharabar gidan kai tsaye bishiyar goba ta haye har Lumshe idanunta take saboda yadda tayi mata mugun dadi,hon aka danna da mugun karfi da gudu baba megadi ya wangale get din aguje ta shigo da motar kamar gidan tsohonta.
Mom ce ta fara fitowa sannan Rufaida daga Ganin su sunsha matukar gajiya,yan iska sai yanzu suka dawo tun safe ko gantalin me suka tafiyi oho harkar gabanta taci gaba dayi tsawon mintuna 30 taga Mom ta sake fitowa kai tsaye Lambu ta nufo sai waige waige take alamun bata da gaskiya,kura mata idanu Jalila tayi to kodai cutar jiyace bata sake taba can cikin lambun taga Mom ta kutsa kai duk abinda takeyi tana kallon ta.
Sun kuyawa Mom tayi ta tona rami wasu layoyi ta dauko a gefan zanin ta ta binne bazaka taba cewa antona rami awajan ba,tashitai tafice daga lambun tana sakin murmushin nasara yanzu saidai ta zuba ido taga yadda aikinta zai fara wakana,makira metaje ta binne aiko komene saina gani wllh saidata tabbatar Mom tabar wajan sannan ta sauko daidai inda taga tayi hakar ta tsugunna saidata tone tsaf saiga layoyin data binne tab lallai wannan matar bazataga Annabi ba wata binnewa wannan layar dagani dai wani zata hadawa mugunta aiko zaki sani wllh.
Maida kasar tayi ta binne waje daya ta samu ta zauna saidata farke layar nan tas wasu rubutu ne ajiki data kasa gane menene tabe baki tai ita tasani dama fitsari takeji tsugunnawa tai ta tsula fitsari akan layoyin malamin su ya gaya musu fitsari yana karya asiri tana da tabbacin shine wannan watsar da takaddun tayi ta kama gaban ta,tana shiga parlon ta tarar da Mom an kame akan kujera an cokala dauri Fuskar nan tata awashe da fara'a.
Uhm sannu da zuwa Mom ashe kun dawo amma ina kukaje naga kundade tun safe kamar masu yawan maula kinsan sune zakigansu sassafe sun nufi kwararo kwararo lungu da sako,kuma ni danaga kumdawo kafafunku busu busu kamar wadanda kukai tafiyar kasa,to tambayau ina ruwanki da inda mukaje meshegen kilibibin tsiya ko aikemmu kikayi kinga kishiga taitayinki Jalila wllh inna waiwayeki bazakiji ta dadi ba.
Wace irin waiwaya zakiyimin Mom badai fiddani zaki daga Gidannan ba kimin komene amma banda barin gidannan inanan ba inda zani dole ne na zauna na taimaki wanda suka taimakeni muddin rai kuwa bazan bar mutum ya cika mummunar kudirin sa, Kamar yadda kikace karna bari ki waiwayeni toni yanzu zan waiwayeki bazaki taba cika burin kiba saidai ki mutu da bakin ciki hassada ce zata kashe ki atsaye batare da kin farga ba.
Zumbur Mom ta mike ke nikike gayawa haka koni sa'ar wasanki ce wllh hawainiyar ki ta kiyayi ramata amma zakiga abunda zai biyo baya Fuuu tai gaba inga Alkhairi babu abunda zan gani ni Zuciyata babu mugunta acikinta fes take aha barin wajan tayi tana dariyar mugunta dan tasan tagama yiwa Mom illah zata zuba ido taga abunda take nufi da binne layoyin datai.
Har akazo dinnar babu Jalal ba dalilinsa yana dakinsa har wannan time din befito ba Ammah ce takai masa da rana ga daren ma befito ba duk Ammah da Dad sun damu matuka,waini ina Jalal Allah sarki haryanzu jikin nasane nidai ALLAH ya temakeni na warware kamar baniba kai jiya naga masifa ganin idona babu wanda ya tanka mata kowa da abunda ya dame shi,Ammah ce ta hadamai Abinci awani dan basket mekyau Jalilah ta kwallawa kira.
Gani Ammah yawwa ungo kikaiwa Jalal ki aje aparlo saiki fito kina jina eh Ammah daganan zanje daki nakwanta bacci nake ji ok hakan yayi kinyi sallah eh nayi Ammah tom ALLAH ya tashemu lafiya Ameen,harta juya mom tai tsagal aida kinba yan Uwansa sun kai mai haka kawai kyatura yar aiki ina matsayinta yakai tashiga part din Jalal.
Karba tai tatafi idanun su Mom kamar zai fado dan harara ita ko ko ajikiñta batama san sunayi ba,kamar yadda Ammah tace ta ajiye aparlo anan ta aje amma tsabar neman tsokana bedroom dinsa ta shige ya zaune laptop dinsa na kan cinyar sa da alama wani aiki yake me Muhimmanci gaba daya ya tattara hankalin sa waje daya.
Yaji shigowar mutum amma besan wanene ba dan gaba daya baya so abinda yakeyi ya tsaya da yinsa,saidata zo har kusa dashi tukunna tatsaya tana muzurai tsamin daudar da takeyi ne ya isar masa da sakon ko wacece,afusace ya dago yana harararta Mahaukaciyar ina ce zaki shigomin har bedroom kina tsamin dauda ko kala bata ce masa ba tana tsaye kamar andasata tana kallon sa shekewa tai da wata muguwar Dariyar cikin Mamaki yake Kallonta metakewa dariya haka.
Mrs Baba Bello Abubakar
.........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 23
Kawaii ina dariya ne yadda naganka haka jiya sintir ashema kama da mata kakeyi ware idanun sa yayi akanta,eh kama da mata kake in kai ba mace bane meya hadaka da nono haba shiyasa kake abu irin na mata kana tafe kana yarfe hannu kamar wani dan daudu,kafarsa yasa ya tado ta Jalila saigata wanwar akasa jawota yayi har kusa da kafafunsa gaba daya kafafunsa ya dora akanta duk yadda taso janye kafafun sa takasa tuni azaba tasata fashewa da kuka ko kallanta beba yaci gaba da aikinsa zai tabbatar mata dashidin ba mace bane saita gane kuranta adakinnan tunda itace ta kawo kanta.
Tsabar mugunta irin ta Jalal hannayanta ya take yana sane har murza kafafun yakeyi akasa jitake kamar hannayanta zasu tsinke gashi da tafara kuka zai dalle mata baki da hannunsa azaba kan azaba tatsine masa yafi cikin kwando saida ya tabbatar da jikinta yayi Laushi sannan ya dagata gaba daya kasa tashi tai tsabar wahala sai matsar kwallah take lokacin ya gama aikinsa ya rufe laptop din.
Daka mata tsawa yayi batasan lokacin da tamike tsaye ba jikinta har rawa yake tsabar yadda ta tsorata hanyar kofa ya nuna mata har tuntube takeyi wajan fita tana gaba yana biye da ita harzata fita yagano Abincin data kawo masa keee!!! zonan da sauri ta dawo tana rarraba idanu zauna ki cinye wannan abunda kika kawo, murmushi ta saki cikin farin ciki dama cikinta ya fara kasa kamar zatai kuka take fadin na koshi.
Ko ki cinyeshi ko nazaneki yanzunnan wllh,harta zauna ta mike kallonta yayi alamun ina zataje dama wata doguwar rigace ajikinta dagata tai ta cire baki sake yake kallonta wannan yarinyar fa akwai damuwa a kwakwalwarta,daga ita sai pant ta zauna yayi cidin cidin da uwar dauda dankwalin kanta tacire tare da gyaran zama basket din ta janyo food flacks din ta bude Jallop ce aciki sai tashin kamshi takeyi Jalila har hadiyar yawu take.
Tunda tafara zabga wata uwar loma yake kallonta da tunanin zatace ta koshi amma ina shiru kake ji saidai Jalila ta cinye tas tea cup ta janyo saidata shanye ta bude ruwa ta kwankwada gaba daya kan Jalal ya daure aiyanzu shi kome za aimasa bazai iya cinye rabin abincinnan ba amman gashi wannan figaggiyar tacinye tas lallai,saidata gama tsaf tatashi tasa kayanta.
Kallon sa tai nagode dan India baka tabayimin abun arziki irin yauba tunda ka bani Abincin nan na cinye duk wasu lefuffukan ka sun goge saidai adora ana gaba amma na bayan nan dai babu su kaima ina so duk lefukan da naima ka yafemin kasan dai Mutuwa ake yi gwara ayafi juna,ni wllh yanzu har gyaran dakuma zandingayi maka dan India tsaninmu yanxu mutuncine da rukon amana.
Ko kallanta beba fitar min daga daki karna tashi na tattaka ki wllh,to sai anjima ni bana manta Alkhairi bana fita aini yau bazanyi fada dakai ba wllh tunda ka bani abunka nima nan gaba zan baka abuna,ke dallah fitarmin me kike dashi da zaki bani fitar min fita tai tana zabga mai Addu'a ALLAH ya saka a Aljannah dan India zanyima Addu'a kadawo namiji ba mace ba tashi yayi kamar zai biyo ta da gudu tafice zuciyarta fes dan India yabata abinci kuma harga Allah dagske ta yafemai har zuciyar ta.
Murmushine kawai ya subuce masa hakanan tasashi Nishadi,yadade azaune kafin ya tashi ya wuce bedroom sai da ya sake wanka sannan ya kwanta.
Washe gari tunda sassafe Jalila ta afka dakin Jalal da kayan shararta ahannu yanzu Jalila ta zama kwararriya wajan iya gyaran daki amma banda nata dakin zata Gyara na kowa banda nata, bedroom ta shige rike kugu tai lallaima bacci kake aiko zan janyoka kasa inna gyara na ciccibeka na mayar dakai,kodai bana barka ma karka tashi kamin jaraba, toilet dinsa ta shige saidata wanke shi tas.
Bedroom din ta fito ta gyara parlo ta wuce komai kal kal saidata goge har plasma ta goge komai sai walkiya yakeyi kayan ta fita dasu ta sauka kasa aikinta taci gaba dayi hankalinta kwance bata da wata sauran damuwa.
Tana gamawa ta koma dakinta hakanan taji tana so ta gyara nata dakin saidata dauke komai data hargitsa ta share ta shiga wanka Jalila dai yau tsafta ce tatashi,tana fitowa ta dauko kayanta cikas daya kayan duk sun kude dama basu da yawa haka dai ta samu tadan saka bata shafa komai a face dinta ba tai zamanta adaki.
Betashi ba sai wajan 11 yana kwance yana sharar bacci babu abinda ya dame shi,tunda ya tashi yaga alamun dakin ya canza ya kara fes fes toilet ya tashi ya shiga nan ma yasha mamaki komai qal tuninsa wanene ya shigo yamai wannan gyaran mekyau haka,saidaya gama duk abinda zaiyi ya fito parlo nan dimma ashare agoge zama yayi dan bayajin fita ko kadan plasma ya kunna ko kallon zai ragemai kadaici lumshe idanun sa yayi ya lula duniyar tunani kome yake tunanin oho.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 24
Dad dama wai nace mezai hana a hada rufaida da Jalal, zamansa ya gyara mekike nufi da fadin hakan Saratu, fari tai da idanu,nufina tunda gida be koshi ba ai ba akaiwa dawa ba tunda yaran nan ALHAMDULILLAH duk suna da hankali sun san abunda ya kamata zasu hada kansu shida yar uwar sa babu mejin kansu haka kawai Allah ya doramun kaunar Jalal kamar ni nahaifeshi haka nakeji shiyasa nake son hada zuri'a dashi.
Sai data gama tsaf Dad ya kalle ta kina nufin wai nahada dana Aure da yarinyar da tagama lalacewa ko angaya miki bana sane da dukkan abunda sukeyi agari anata zagina dafadin banyiwa yarana tarbiyya ba yawon club inane basa zuwa sai haka kawai nadauki tsarkakakken dana na aurawa wadda tagama yawon kwararo to tun wuri Saratu ki farka daga Mummunan baccin da kika fara ni Ma'aruf ba haka nake ba bana tilas tawa dana abunda baya ra ayinsa.
Kuma inamai jadda da miki ki jawa yaranki kunne na soke fitar dare ba agida naba indai zasu fita to saidai su hada kayan su su kona gidan uban su baza su gogan bakin fenti ba ke bama suba harke zaku iya tafiya tare karna sakejin makaman ciyar maganar nan a bakinki inba hakaba rankine zaiyi mummunan baci,bige babbar rigar sa yayi yabar Mom kamar an dasata.
Kambabakeran Uba harni zai kalli tsabar idanuna ya gayawa haka to boka yaudarata yayi ko maganinne be faracin Dad ba infa ran Mom yayi dubu toya baci dakyar take jan Numfashi yayan natane tambadaddu gantalallu zesan yayi da yar halak ita tasan mezatayi wllh saiya gane kuransa saiya gane bashi da wayo saita tabbatar ta dasa masa bakin cikin da zaikai shi kushewar sa badai da dan yake takama ba zatagani ai muzuba ni dakai shege ka fasa.
Rai bace Dad yabar part din gaba daya kai tsaye part din Ammah ya wuce har wani huci yakeyi saboda bacin rai dannasa guda daya tilo zai hada Auran sa da marasa tarbiyya ko ta dauka baida labarin inda ta samo yaran zai hada zuri'a da kazan taccen ahali shi.
saiyanzu ma yake godewa Allah dayasa be haihu tare da Sarah ba baya fatan hakan ko kadan Jalal ya ishesa fatansa Allah ya nuna masa Auran sa.
Ammah ce tashigo jiki asanyaye ganin yadda Dad din ya fito afusace ya razanata dan sam shi ba Mutum ne meson hayaniya ba kokadan kullum Fuskar sa dauke take da fara'a babban bacin rai kesa har agane akan fuskar sa.
Fridge tawuce ta dauko masa ruwa me sanyi glass cup ta dauko tsiyaya masa tai ta mika masa dan yaji sanyi aransa karba yayi dan yana bukatar hakan dama saida yasha sosai nutsuwa tazo masa dan Zuciyar sa ta lafa matuka gaya, Ammah ya kalla data zubamai ido cikin damuwa murmushi ya sakar mata Allah ya yimiki albarka ameen Dad.
Dan Allah Dady kadaina saka damuwa aranka duk da bansan abunda ya bata maka raiba ina mai baka hakuri mijina kai kadaine farin cikina inka shiga wani hali bansan yadda zanyi da kaina ba,kalaman kauna taci gaba dayiwa Dad kallon ta yake cikin tsananin kauna soyayyar ta na kara dulmiya a cikin Zuciyar sa yana matukar san Ammah macece tagari yana Alfahari da ita akoda yaushe.
Madallah da samunki matsayi matata Madallah da samunki mar'atussaliha Madallah da samunki ma'abociyar kwarjini da kamala Allah yayi miki albarka Uwar Gida sarautar mata, murmushi kawai take sake ita kanta tasan tayi sa'ar Miji me sonta da kaunar ta kokadan bata nemi sanin abinda akai masaba saboda daga part din kishiyar ta yafito ba hurumin ta bane shiga abinda babu ruwanta.
Hirar su suka ci gaba dayi cikin Nishadi da kaunar juna tuni ta mantar dashi bacin ran da Mom ta dasa masa.Da sallama ya shiga dakin Ammah dan murmushi ya saki akullum iyayan nasa basa tsufa koyaushe cikin nuna Kulawa suke wa junan su suna matukar birgeshi yana fatan suyi irin wannan rayuwar da matar sa to wacece ma matar oho ya ayyana aran sa tuna bashi da wadda yake so har kawo wannan lokacin.
Son harka tashi kaima dai Dady yanzunne haryau tashi 11:30 fa ko baka gani rana ta bude tarwai asararin subahana,to Ammah ai dannaki ne so nake naga yayi kiba amma sai tsawo yake kamar taliya dariya suka sa gaba daya.Zama yayi akasan kafafun Good Morning Ammah Morning Habiby shafa kansa tai hole kana lafiya daiko I'm fine Ammah cike da kauna Dad yake kallon su.
Kifada masa yariga ya girma ya kamata ya kawon suruka hakanan Ammah ce ta rike haba yanzu Jalal din har nawa yake 28years fa saiya kai 30 zan masa Aure au kece ma zakiyi masa ehman nida kaima zan zabo masa matar har nayi masa tanadinta jira nake kawai tagirma,gimtse face yayi Ammah kice jaririya ce kawai dariya kawai tayi zaka ganta gaba kadan kaidai kazuba idanu murmushi kawai yayi dan Ammah badai zolaya ba zama take taita tsokanar sa babu ruwanta da wani shidan farine bazata jashi ajiki ba jan abunta takeyi.
Sunjima suna hira,fitowar ta daga daki kenan ta rangada sallama adakin Ammah tana yan tsalle tsallenta ganin ba Ammah ce kadai adakin ba tajuya da sauri zata fita yanzaki koma Jalila tsayawa tai naga Ammah bake kadai bace kuma kince nadaina zama inda maza suke,tagefen ido ya kalleta ji munafuka kamar jiya bata je dakinsa ba.
Ahto kin kyauta amman wannan ai Dad dinkine wajan Jalal dama na hanaki zuwa.
Mrs Baba Bello Abubakar
.........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 36
Maza kizo ki gaida su da baya ta dawo harda su sun kuyar da kai ganin Dad awajan ina kwana mun tashi lafiya,da fara'a Dad ya amsa kin tashi lafiya lafiya kalau na tashi,dai dai kunnan Jalal ta matso da bakinta dan India ina biri ina akuya fatan katashi ba wuya tanayi tana murmushi saika dauka gaisuwar arziki take masa duka ya kawo mata tai saurin yin baya kingani ba Ammah ina gaida shi yana kokarin dukana bansan menai masa ba ya tsaneni.
Ammah ce ta harare shi wai meyasa bakasan abun arziki ba yanzu yarinya tana gaida kai baka amsa ba saika kawo mata duka harara yake wurga mata kamar idanun sa zasu fado,kwàfa yayi lamar zasu hadu awaje Dad bece komai ba kallon su kawai yake ya tabbatar Jalila ba abun arziki ta gayawa Jalal ba sai kunshe baki take tana Dariya Girgiza kai kawai yayi ganin wadda zatasa Jalal magana ko badan Allah ba.
Tashi kiyi tafiyar ki Jalila aike kingama aikinki tunda Allah yaga niyyarki ta alkhairi ce kin gaidashi shine be amsa ba kije wajan iya tabaki breakfast dinsa kikai masa dakin,zako kici ubanki haka ya ayyana aransa wayar sace ta fara ringing dama abinda yake so kenan yasamu hanyar fita Jalila kuwa tuni takai kasa da fatan Allah yasa yauma yace saita cinye itako da gaba takaita gobarar titi a jos.
Har Allah Allah take takai dakin nasa addu'a take alasa bedawo ba tabude ko yayane tadan ci tasan bazai iya cinyewa ba wata kilama yaga tasa hannu yace ya koshi ta cinye dariya tayi hakama zaice.Tana shiga ta ajiye basket din gaba daya bata lura da shi adakin ba yana lafe akan sofa yana kallonta yaga abunda zatayi ganin tana ta kokawa da basket lallai saita fito da kayan ciki,keee da sauri ta mike tana muzurai ashe dama barauniya ce ke bansani ba bayan rashin kunya harda sata.
Tuni ta hade fuskarta jin ya kirata da barauniya oya kneel down tsaye tayi tana kallon sa dan batagane meyake nufi Mtswww stupid girl ki tsugunna nace kidaga hannayan ki sama rike kugu tai tana kallon sa akan wane dalili menaima da zanyi hakan gaskiya ba wahala ta kawoni zaman duniya ba zaki da maiko nazo ci,ni kike cewa bazaki ba zumburo baki tai to da dawa nake.
"Juya masa keya tai gaba daya bataji lokacin daya taso ba kawai jin wani shegen rankwashi tayi aka,ash ta dafe kan bakaramar shigarta yayi ba tuni Hawaye ya fara tsere a face dinta kazama kawai,oya yi abunda nasaki durkusawa tai kamar yadda yasata akalla saidatakai 30mnt tuni idanunta sun raina fata tayi kuka harta gaji"
Mike da kyar tasamu ta mike guiwowinta jinsu take kamar ba nata ba sunyi matukar sanyi sai jamai Allah ya isa take azuciyarta dan babu halin furtawa yanzu jikinta zai karayin tsami,tafiya tafarayi da nufin fita adakin na sallameki ne dawowa tai kamar zata fashe da kyka tsallan kwado ware idanu tayi ni ban iya wani tsallan kwado ba to banazo na koya miki,da sauri ta tsugunna tafara tsallan kwado tanayi tana kuka face tayi jage jage da Hawaye amma tsabar taurin kai Irin na Jalila taki tabashi hakuri.
Hawan babur kai ranar Jalila babu kalar punishment din da Jalal be bata ba har tsotsar alawa saida yasata,daga karshe saida ta gagara tashi da kafafuwan ta tuni kanta ya fara tsananin ciwo ba ataba bata wahala irin yau kaf cikin rayuwar ta ba,zubewa tai a parlon tana numfarfashin wahala,shiko hamshakin yana zaune yana danne dannen waya saidai ya tabbatar ta dawo cikin hankalin ta,harshi zata cewa ina biri ina akuya aiko taga akuya ajikinta tashi ki ficemin adaki.
Da kyar tasamu tatashi zaune da rarrafe ta fara tafiya har takai dakinta bata hadu da kowa ba tana shiga dakinta ta baje Fashewa tai da kuka jin yadda gabobinta kamar an sassara mata su ko ina ciwo yake yimata zazzabi ne ya rufe ta sai rawar sanyi take haka ta wuni akwance sam Ammah bata san abinda ke faruwa ba,ta dauka tana can tana bacci dan yanzu Jalila ansamu hutu bata da aiki sai bacci.
Ga yunwa ta addabeta sai bayan la'asar ta samu da kyar tatashi tai alwala tai sallah,kamar me koyan tafiya haka ta fara taking steps tana saukowa ta tarar dasu Salima azaune an bararraje suna karta ita da Rufaida,kallon sutai da mamaki caca sukeyi wa Mutane agida danta san menene wannan tana gani a garin su anayi shima sai tantiran yan Iska sunayi suna busa hayaki lallai wadannan ba kananan marasa mutunci bane.
Ke dan Ubanki mu sa anninkine da zamuzo mu zauna kema kizo ki zauna kamar gidan Ubanki,dadinta ni daku duk daya muke kunga babu me yiwa wani gori babu sisin ubana aka gina gidan kuma babu sisin ubanku aka gina kunga kowa aimaganar ma tada jiniyar wuya bata tasoba.Gwarama ni nawa uban yana da Gida wayasani ko su o'o a gidan haya ake rayuwa.
Afusace Salima ta taso daga hannu tai zata dauketa da mari daidai lokacin Jalal ya sauko daga sama kallo daya yayi mata tagano mugun gargadi acikin idanun sa,sauke hannun tai sosai Jalal yake musu kwarjini barin inya hade rai kamar be taba Dariya ba,biyoni abunda yace kenan yayi gaba kallon kallo akafara to dawa yake wace zata biyo shi,harya kai bakin kofa ya juyo zubawa Jalila harara yayi sainazo na tattaka ki zaki taso.
Zumbura baki tai toni mezamma aina dauka da wadannan samudawan kake tashitai tabi bayan sa harlokacin jikinta ciwo yakeyi Rufaida da Salima har turereniya suke wajan lekawa ta window parking space suka ga ya nufa Jalila na biye dashi a baya kamar bindi,saimita take azuciyar ta ina zai kaita tuni zuciyarta ta bata kauye zai maida ita ai wllh babu inda zataje.
Durkushewa tai awajan tafashe da kuka juyowa yayi da sauri da tunanin ko wanine ya daketa ita kadai ya gane sai baba direba dame gadi da suke zaune sun zuba mata idanu suma da tunanin wacece wannan kamar wata me tabin hankali kinfito Lafiya amma haka kawai kizube kifara kuka kamar wata me iskokai.
Ubamme akai miki zakisa mutane agaba kidinga wannan kukan kamar wadda aka aikowa da sakon mutuwa,ai wllh gwara sakon mutuwa tunda ubana ya mutu uban kowama ya mutu bani da asara dadai wannan hukuncin da kake so ka yanke min namaidani kauye,ni dan India narasa mena tsarema acikin rayuwa ka takuramin duk wata hanyar jindadi na so kake ka toshemin ita kayiwa ALLAH kayi hakuri karka fitar dani daga Gidannan
Duk yadda yaso gimtse face dinsa saidai yayi murmushi sai shegen tsoro ga shegiyar tsokana,aiko yau dole kikwana akauye kije can kici gaba da cin tuwon masara da koriyar miya tundake baki da kunya,wllh wannan ma sharrin shedanne kasan shedan la'ananne shiyake kara zugani akowane lokaci amma daga yanzu naima alkawarin zanyi yaki dashi bazai sakecin galaba akaina ba wllh dagaske nake dan India kayimin rai.
Kuka ta sake fashewa dashi,su Rufaida dake hangen komai dadi kamar ya kashe su yau zasu rabu da kaya Jalal yayi musu daidai dazai fita da wannan tinkiyar suma sa wataya sukadai suyi abunda suke so babu me samu su idanu,baba me gadi sai tikar dariya suke ganin bilhakki Jalila take Kuka tana bashi hakuri kamar wadda yace zai maida ita gidan kurkuku.
Zaki taso kosai nazo dakai na dauko ki nidai kaimin rai karka maidani kauye Wayyo na shiga uku Ammah kizo ki ceceni kihanashi ya maidani kauye sake rushewa tai da kuka tayi jage jage da ita tattare hannun rigarsa yayi ganin ya nufita wuff ta mike da nufin guduwa taku biyu yayi yakamota cak ya dagata tana Kuka tana dukansa da yakushi saida ya danna ta amota ya rufe.
🤣🤣🤣Jalila har shidewa take tsabar yadda take gursheken Kuka aitanaganin sunfita daga gidan ta kwalla wata kara hannunta aka ta sake fashewa da Kuka ta tabbata tafita daga jindadi ita yanzu sam bazata iya rayuwar kauyeba wllh ina bazaima yiwuba,tsawa ya daka mata kokimin shiru kona wullaki ta glass dinnan motoci su take miki wuya kimutu kowa ma ya huta.
Shiru tai ina zata so ta mutu bata dauki fansa akansa ba wllh saiya san ya fitar da ita daga daula dajin dadi,fatarta ta kalla babu cizon sauro ko daya ajikinta yanzu zata koma kauye sauro ya samu nama,ranta ne ya sake baci gaskiya Jalal ya zalinceta har Lokacin matsar kwallah takeyi.
Jalal be tsaya ko ina ba sai wani katon super market manyan motoci ne kawai ke layin shiga kaida ganin wajan kasan na manyane in baka da yan canji bazaka doshi hanyar wajan baka tuni Jalila ta hadiye kukanta ganin wata aljannar Duniya daya kawo ta har sauke numfashi take tuni tamnta da batun wani kauye.
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 26
Sai da yakashe motar akallah yakai 5mnt kanya bude ya fito wow wasu yan mata dake fito suka fada kai amma guy dinnan ya hadu ya bala'in birgeni,hade ransa yakara yi dan yatsani kallo a rayuwar sa,budewa Jalila yayi ahankali ta fito sai zare idanu take sai Lokacin ya kalli kafarta ko takalmi babu harara ya maka mata kazama kawai wuce muje,to ina zanje bakaine kasan hanyar ba salan haka kawai naje na bata asace ni ganin zata mata mai lokaci yaja hannunta suka shiga.
Zo kuga Jalila kamar wata shashasha haka ta bude baki tana kalle kalle kamar sabon kamu haka ta koma Jalal ba karamin dana sanin zuwa da ita yayi ba duk Inda suka wuce kallon su akeyi ana dariyar kauyan cin Jalila itako ko ajikinta,kaya yake diba kamar besan zafin kudadan ba Jalila ke tura basket din daya bata saida ya cikashi taf da kaya suka je wajan biya,awasu manyan ledoji aka zubamai kayan har mota suka kai masa kayan.
Ganin Jalila batada niyyar shiga motar ya jata ya turata ciki,bata rai tayi amma wllh kaidai akwai marowa ci yanzu muje wajannan harmu fito amma baka siyamin ko dan tamatsitsin da nagani awata leda ba,banza yayi da ita yanajinta tanata mita,ko kimin shiru kona maidaki kauye yanzunnan shiru tai alabaka hakuri kwafa yayi kimaci gaba,kai tsaye wani salon ya wuce da ita.
Waya yadaga ya daddanna wasu Numbobi wata matace tafito babba ce da alama itace me wajan cikin girmamawa suka gaisa,kallon Jalila tai da murmushi a face dinta ma sha Allah ita ce kanwar taka dan murmuwasa kawai yayi,haka yace miki ni kanwar sace to karya yake babu abunda muka hada ni aiki nake agidan su haka kawai dan mugunta kaje kayo wata tsokanar azo ahuce akaina bazata yiwuba make mata baki yayi cikin takaicin yarfin da tai masa agaban madam Zarah.
Sosai taji Yarinyar ta birgeta,kina cewa karya yake ai yagirmeki bana son rashin kunya kuma dan yace ke kanwar sace ai girmamawa ce kobakisan in anji ke yar aikin Gidan su bace za adinga tsokanarki ko kin girma kinzama yammata anaganin kinci kwalliya za ace kun ganta yar kauye tasha ruwan binni ta waye,bata fuska tai toko yanzu aiba wanda zaice daga kauye nafito,injiwa ya fada miki matukar baki gyara bakinki ba kowa ma zai gane.
Madam ki kyaleta kawai zamu tafi tunda batasan mutunci ba ita zan maidake yadda na daukoki, a'ah Jalal ai baza ai hakaba tunda kayi nufin alkhairi karka juya baya,fito kekuma me shegen bakin rashin kunya,kama hannun ta tai suka shige hadaddan wajene na gyaran jiki gyaran gashi zaunar da ita tai akan kujera oya bude kan to Nanfa akeyin ta bata fuskatai ni banda gashi andade dayimin aski tun na askin jarirai da akaimin haryanxu be fito ba.
Uhm kawai Madam tace zare dan kwalin data dankwafa aka tai tun kafin ataba kan Jalila tafara Kuka banza tai mata tsabar dadewa tsagar kitson ma ta hade ba aganin ta takosha azaba madam kuma tasha zami ga wata kura data dinga tashi akan ankai awa 1:30 ana fama dakannan kafin ya fara dawowa hayyacinsa tsaf ta gyara matashi sai ga gashin Jalila ya sauko har wajan kafadarta ashe dama tanada gashi rashin gyara ne yasa gashin ya cukurkude ya dankare awaje daya.
Toilet ta jata tas tai mata wanka da brush anyiwa bakinnan kusan safi biyar kafin ya fara dan washewa danya dade da dafewa tun tuni,fita tai mintuna kadan ta dawo da kaya ahannun ta,wasu riga da wando ne masu azabar kyau help gawn ce iya cinya sai jins sai wata bandana da akasa acikin kayan tsaf ta sakawa Jalila kayan ita kanta madam ba karamin kyau Jalila tai mata ba Jalila kuwa sai jujjuyawa take farin ciki kamar tayi me sai kallon kanta takeyi kamar ba ita ba
Waya siyamin kayannan masu kyau wanda kika gama yiwa rashin kunya mana waro idanu tai wai kina nufin dan Indiya ne ya siyamin kayannan dariya tayi wane dan India ni Fatima wanda mukazo tare mana lallai kina da shirme to shine ya siya miki.
Marairai ce fuska tai Allah sarki ashe yanada kirki haka to daga yau yama babban abokina ba cuta ba cutar wa kome zaimin zan hakura tunda ya siyamin wadannan kayan dadai yafi miki,muje kayan da ta cire mata take kokarin dauka me zaki dasu gida zan tafi dasu ajiye zubda su zanyi kinyi gaba amma kina kokarin maida kanki baya,lallai ma wato matar nan sotake na barmata kayan ta samu takaiwa yarta.
Jan hannunta tai ganin ta gaddame saita dauki wadannan yamutsatstsun kayan,yana wajan duk wannan uwar dadewa da sukai sai jan tsaki yakeyi tunda suka fito ya zuba mata idanu anya Yarinyar nan ce kuwa tayi wani irin kyau saiyaga kamar ma ta kara haske kallonta yake daga sama har kasa dariya ce tazo masa ya kunshe abarsa tana tsaye kamar 1 suna tafe suna magana da Madam kome take gaya mata kuma oho.
Gaba ta bude ta sakata har zaiyi magana yayi shiru to Jalal angama sai Gani na biyu amma zaka kawon ita mudinga gaisawa ko watakila aah kadai dunga kawon ita nifa ita ai munzama kawaye bakiyi sa'ar kawaba kuwa,sallama sukai yaja motar Yayi gaba,kallon sa tai dan India ashe haka kake da mutunci daga yau mudena fada munzama kawaye hararar ta yayi ke ni macece to aikaima naga kama da matan kake yi nidakai babu wani ban banci.
Banza yayi da ita dan ya lura so take tamai dashi wani bican,Hon ya danna megadi ya wangale masa kofa kamar bakin Jalila zai yage dan farin ciki tadawo gidan jindadi kamar yadda ta samai suna, Ammah na tsaye tana kaikawo a parlo dan tuni su Rufaida sun fesa mata Jalal yatafi maida Jalila kauye takira shi wayar sa akshe shiyasa takasa zaune ta kasa tsaye sotake taji Inda yakai musu yarinya.
Ta widow ta leko Jalal ne ya fara fitowa daga motar saiwata kyakykyawar yarinya data ga tafito dafe kirji Amma tai tana jiran taga Jalila tafito amma shiru babu ita babu alamarta to ita waccan din dayaje ya kwakuso wacece tayi taf jira kawai take ya shigo ta sauke mai abunda yake damunta saiyaje ya dauko Jalila duk ma inda ya kaita.
Hartayi gaba ke nine dan dakonki dawo kidebe kayannan dawowa tai da baya dan yanxu tsakanin su fa biyayya ce injita dauka tayi sun mata nauyi kallon sa tayi kamar zatai Kuka dan India karufamin asiri kadauki daya nima na dauki daya,ganin da gaske bazata iya ba rankwashi ya zuba mata sannan ya dauka,shine agaba Jalila na bayansa.
Gidan ubanwa akace kadauki Jalila kakaita wllh tun kafin raina ya baci kako ma kadauko min yarinya ta nagaya ma,tsaywa yayi yana kallon Amma da idanunta ya rufe kawai fada take zazzagawa ganin yayi mata shiru abun ya sake kular da ita ba magana naje maka ba,jitai anrungumeta ta baya Ammah kin ganni fa da sauri Ammah ta juyo kara bude ido tai akan Jalilah kamar ba itaba kallonta take Daga sama har kasa jujjuyawa tai ya kika ganni Ammah.
Baki sake Ammah ke kallonta anya Jalila ce wannan kuwa gashinta ta kalla da yasha gyara harwani walwali yakeyi Jalilah kece kuwa nice mana Ammah kinga nazamo yar gayu ko dan India ne yasiyamin kayan nann na jikina har wanka fa akaimin Ammah bakiga gashina ba ya kara tsayi awani inji aka sakani.
Kallon Jalal tai tuni fuskar Ammah ta washe bakinta yaki rufuwa sake kallon Jalilah take kamar ba itaba Allah Yayi maka Albarka Jalal,dan Murmusawa yayi arayuwar sa yanaso yaga ya farantawa Ammah rai hakan yana matukar sanyashi nishadi part dinsa ya wuce danya watsa ruwa yayi alwalar magari ba.
Hannun ta Ammah takama kai Jalila kinga yadda kikayi yanzu ke bakiji dadin jikinki bama amma aita fama dake kiyi tsafta kikiyi yanzu dakikai tsaftar nan bakiga yadda kika zama budurwa ba,dariya tasa ALLAH Ammah sosai kuwa matukar kina wanka kullum to naman ki zai kara yawa kullum zakita cin nama babu yankewa amma fa in kina tsafta.
Zandingayi Ammah ai tunfarko kece bakimin zancan nama ba da babu yadda za'ai nabar wannan dadin ya wuce ni to koke fa,banaje nai sallah Ammah muje nima yi zanyi ledojin ta dauka sai nishi take to kawo na tayaki mana àah Ammah kayan amanane ba atabawa to aishikenan saikije ki karata kya hau dasu da wahala kuwa tunda bakisan abun arziki ba.
Dakinta ta shiga da kayan kara kallon kanta tai saitaga wannan kwalliyar bata dace da dakinba tayi kaca kaca dashi dole nema ta gyarashi ganin baai kiran sallah ba zagewa tai ta gyara dakin fes sai kullin kayanta da yake ajiye akasa,Alwala ta daura tana idar da sallah ta ciccibi kayan tayi dakin Jalal yana bedroom dinsa zaune akan daddumar daya idar da sallah.
Har gabansa ta ajiye tana ta uban nishi,zama tai kawata ga kayanka hararar ta yayi bazaki daina kirana mace ba ko,to me zan cema bakisan sunana ba kenan nasani mana ainaga sunan mu iri daya ne kaima ba mamaki macene shiyasa aka saka maka,ke ya isheni meya kawo ki kayanka na kawo ma kayan matan zan saka da kika kawon kallon sa take cikin rashin fahimta kayan kine kije kita sawa bani da hadi dasu.
Kuri tai ta zuba masa idanu nuna kanta tayi duk nawane nikadai gyada mata kai yayi dan gaba daya ta dameshi da surutu,gani yayi kawai Jalila ta fashe da Kuka abun ba karamin daure masa kai yayi ba,wllh bansan haka kake da imani da Tausayi ba sai yau dana san haka kake da tun farko ban takaleka fadaba ni yanzu kota kaina zaka dinga bi bazan ji haushi ba,dagaske fa Jalila Kuka take kashirban gaskiya wannan yarinyar tanada damuwa a kwakwalwarta.
Kinga ya isa haka kawai bazakizo kiisani agababa kinamin Kuka kamar wadda na doka, to ai kukan farin ciki nake kasan akwai kukan farin ciki dana bakin ciki yanzu da kukan bakin ciki nake da yanzu nafara ya kushinka da cizonka amma da yake kukan Farin ciki nake bagani azaune ba,sabida ke kura ce ko dole kihau cizo da ya kushi.
Mrs Baba Bello Abubakar
.........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 27
Aini ko kura haka taganni ta kyaleni dan baka sanni sanda nake kauye bane nakusa cirewa dije hanci sanda muka taba fada dakyar aka karbeta daga hannuna saboda inna fusata bani dakyau kullum amakarantar allo duk wanda ya tsokanan banayi masa ta dadi.
Nabar miki wannann kayan amma da shadi gyara zaman ta tayi sharadin me kafada ko menene yanzu zanyi maka ni wllh ko wankin kayan kane ma nadauki nauyin yinsa daka cire kayanka zan wanke,bana bukata kirike wankinki sharadina dole kidinga wanka kullum brush kullum gyaran daki karki yadda na leka dakinki naganshi kaca kaca hakan yana nufin nakwace duka kayana,Indai wannan ne me sauki ne indai zan dingasa kayan nan nazama yar gayu.
Kingama cika sharadi sai zuwa makarnata zan saki a school saboda na lura kanki ya gama dafewa da miyar kuka kamar ke wannan yar yarinyar ma za akawo ki aiki,ina ne garinku shiru tayi Allah ya kiyaye na fadama garimmu,am aini bamu da gari kaganni daga sama na fado nikaina bansan inane garimmu ba,nizaki rainawa hankali haba dan India kasan bazan yima karyaba har Zuciyata maganar nan take,hmm kawai yace dan yagane bazata fada bane dan karya mayar da ita.
Tashi kifatar min adakin to,mikewa tai ta debi kayanta hartakai bakin kofa kee juyowa tai sannan wannan tsummokaran kayan kisasu a shara karna sake ganinki dasu suna cikin sharadi suma,dan jim tayi kayan nawa danake wankan Juma'ar zan wullar wannan albazazzaranci ne,bazaki yar ba kenan aah nidin banza zanyar mana dama wai tunatar dakai nayi to kirike tunatar warki kezatayiwa amfani har mahaukatan kayan kwalliyar nan kiyi waje dasu.
Kamar kadangaruwa ta girgirza kai anya zata iya bin wadannan dokokin meyasa dan India zai gindaya mata wannan sharudan masu matukar wahala wanka kullum tab,dakin Ammah ta wuce bakinta kamar zai yake sai jan ledar take akasa Ammah zokiga kayana zan dinga daukar wanka dan India ya bani,amma dake kan dadduma ta zubawa ledar ido.
Kai Jalila dagaske kike duk nakine eh Ammah nawane bece harda ke ba Murmushi kawai Ammah tai Jalila danja.
To zomuga kayan zazzagewa tai kayan sunkai kala goma shabiyar kowannen su masu matukar tsadane inyeee Jalilan Amma ta shigo gari duk yan kantine babu kayan hausawa daga riga da wando sai riga da sket sai doguwar riga pants da vest sai kayan kwalliya da chocolate duk ya hado mata aifa Jalila dan dadi kamar zata ciji kunnan ta sai tsalle take tana murna Ammah nai mata dariya.
To aiba tsallan ba yanzu wanka ya zame miki wajibi kullum ba fashi,bama saikin fadan ba ninasan sauran in banyi ba bani basa kayannan haka ya fadamin Fuska amarairaice tafadi haka, Ammah ki taimaka kice yabarni ko kwana uku uku ne na dingayi meyasa ke baki fada masaba aini karyaga kamar na rainashi ne au nice marainiyar wayonki kenan da kike fadamin Allah ya baki hakuri Ammah ni banfada ba naraina babar dan India aida nacika butulu kinsan ni duk kankantar Alkhairi bana manta shi haka sharri shima bana mantawa saina mai da martani.
Allah ya shirye ki to ai matukar kina son cin ribar zaman duniya sai kin koyi hakuri,bana son ci Ammah matukar za aimin ban rama ba aidama ni ribar lahira nake so naci nashiga Aljannah nasha dadi na ganin bata da niyyar gajiya Ammah tace naji dauki kayan ki jera a wardrobe dinki kinkima tayi ta fice ranta fes,ko tinanin su Innah batayi hankalinta kwance take cin dadinta ita kadai amma wataran tana dan tunawa dasu kadan ga ciwon da jikinta ke mata narashin damban da batayi watanni masu yawa.
Tana shirya kayanta tana wakokin ta na kauye saida tagama tsaf samnan ta debi tsofaffin kayanta ta fita dasu tanaji tana gani ta zubar dasu har kuka sai datai to ya zatayi tunda tanasan sababbin kayan da dan India ya siyo mata dole ta hakura tabarsu ashara daki takoma anayin sallar isha'i ta bingire awajan tahau bacci.
Mrs Baba Bello Abubakar
.........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 28
Ammah wata shawara na yanke mezai hana akai yarinyar can makaranta hakan zai taimaki rayuwarta sosai zata rage wannan rashin jin da takeyi da giggiwa da rawar kai,numfasawa tai to banki ta taka ba Jalal amma kana ganin iyayanta zasu amince kuwa zasu amince Ammah aiba daina biyanta albashi za aiba za aci gaba da bata kamar yadda aka saba.
Ni zan dauki nauyin komai na karatun ta uhm Murmusawa Ammah tai Allah yayi Albarka zan kira Indo nasanar da ita shikenan Ammah,wata hirar suka shiga ta daban ta tsakanin su.
Wankafa yau ansha shi fes ta tsaya tài wanka babu algus aciki ba ha inci,zaman dirshan tai agaban kayan sai canki cankar wanda zata saka aciki take karshe dai wasu riga da sket ta dauko peach color sosai sukayi kyau data sasu das sukai mata tartare gashin kanta tai ta daure shi da ribom kallan kanta tai amadubi kamar ba ita ba palet shoe ta dauko tasaka acikin kayan daya siyo mata tun adaki take gwada irin tafiyar da zatai da zarar tafita.
Tafiya take kamar me tatata ahakan wai tafiyar gayu takeyi,step biyu tataka Mom da suke zaune a dining suka zubo mata idanu da tunanin wacece wannan tazo gidan basu sani ba,danta kala kular dasu taku ta sake canzawa saidata sauko sannan suka shedata wayyo ina wuta sujefa Jalilah har wani daci mom takeji amakoshinta kasayin shiru tayi.
Janyo rigarta tayi ke dan Uwarki a ina jika samo waddan kayan ko yawan kwaruwanci kika fara bamu sani ba inba hakaba wazai baki wadannan kayan da sai yayan wane da wanene ke sasu ko kifadan inda kika samo ko nai miki mummunan dukan da babu wanda zai iya shaidaki,cikamin riga karki shafan datti kumani ba karuwa bace wllh yayanki ne karuwai tunda rannan agabana naga Namiji yana tabata kuma ance duk wanda Namiji ya tabashi dan iskane kuma karuwa ce.
Rankwashi ta sakar mata aka sosai ya shigeta Iya ce tafito daga Kichin cikin al ajabi take kallon su tika tika dasu amma sun kama karamar yarinya suna zalintar ta,haba Hajiya metayi muku kuke dukanta haka ke dallah gafara can tsohuwar munafuka kema baki wuce mudake ki ba bama ita ba karki sake shiga abunda babu ruwanki kisaka ido kisha kallo,shiru Iya tayi cike da bacin rai amma babu yadda zatai barin wajan tai indai Jalila ce kutabata kuna sani wllh.
To matukar ba yawon karuwanci kika fara ba wannan kayan satoshi kikai,niba barauniya bace saidai kune barayi Salima ce ta durka mata duka abaya shegiya medogon baki sosai taji zafi abakinta dama wannan gabjejen hannun ba dole taji zafiba,tuni hawaye sun fara malala akuncinta,duka dai Jalilah ta shashi sosai take kuka ai Mom Abinda za'ai kayannan najikinta acire su dan basu dace da ita ba.
Kici kicin cirewa Jalilah kaya suka hauyi cizo da yakushi sun shashi amma saida sukai wa Jalila tik daga ita sai panta suka barta hatta vest din da ta saka saida suka cire,gashinta Mom taja shima wannan tsinannan gashin sai munyanke shi damu kike zancan saikin bar gidannan tunda bana ubanki bane,kuka kawai Jalilah ke risga cike da takaici da bacin ran abunda sukai mata wani cizo ta gantsarawa cizo babu shiri ta saketa tare da sakin karar azaba kansu farga tuni ta falla da gudu harta kusa kaiwa karshan benan.
Sun jawa kansu masifa dan wllh sai sun gwammace kida da karatu saita gana musu azabar da basu taba dan danar kamarta ba,kai tsaye dakin Jalal ta nufa tana kuka bil hakki,yana kwance ya bararra je yaji kuka asaman kansa yayi zatan mafarki yake jin kukan yaki ci yaki cinyewa ya bude idanun sa arba yayi da Jalilah sintir daga ita sai pant,da sauri ya tashi zaune yana kare mata kallo ganin kukan nata bana kare bane,wai me akai miki kike wannan kukan kuma ina kayanki kike yawo haka.
Kuka ta sake fashewa dashi hannunsa ta ruko tanaja nikazo muje ka ramamin dukan da wadan can azzaluman sukai min,cikani zauna gefansa ya nuna mata zama tai har Lokacin hawaye bedena zubaba babban takaicinta sababbin kayanta da suka kwace,inajinki suwa ne suka dakeki duk abinda ya faru saidata zayyane masa tsai yayi yana kallonta lallai iskancin su Mom harya kai sukama yar mutane siyi mata sintir ya tabbata da katuwar budurwa ce tsaf zasu iya yimata haka.
Rasa mezai cemata yayi shidai ba iya rarrashi yayi ba bare ya rarrasheta,oya kibar kukan haka zan siya miki wasu sai lokacin tai shiru tanajan ajiyar zuciya,sauka yayi daga kan bed din hannunta yaja suka fice daga dakin dakinta ya wuce betaba shiga dakinba koda wasa sai yau babu laifi tunda ta rage kazanta amma haryanzu dai sai ahankali, wardrobe dinta ya bude riga da wando ya dauko mata rigar Iya guiwa sai dogon wando.
Bata yayi maza saka kikwanta kiyi bacci banason fitina kinjini ai ban kumace ki kara sauka ba,fita yayi adakin zuciyar sa sam ba dadi ya rasa meyasa yanzu bayaso yaga damuwar yarinyar kodan yana tunanin tayi nisa da iyayanta akan talauci ne oho,haka nan yakejin tausayinta dan akwai shi da san yara dan ita tafara takalar sa da fadane amma da babu abunda zai saka ya daketa mezai dakama awanann jikin abu duk kashi.
Gaba daya Ammah batasan abunda ya faruba sai wajan 11 tafito ranar itace da Dady al adarta ce dama saita tsaya ta kula da mijinta kafin ta sauko,dakin Jalila ta fara lekawa tana takure awaje daya tana bacci tab lallai Jalila manya haryanzu bcci kike tayi,kasa ta sauka dama tun dazu bakin Iya kaikayi yakeyi tundazu take duban hanya Ammah ta sauko sai yanzu.
Iya ce ta zabga tagumi oh ni jikar isyaku ana zalinci agidannan wllh har Ammah ta gotata ta dawo da baya waya zalinceki Iya,anzo wajan abunda take jira kenan dama hmm wllh Ammah wani abune ya faru agidannan mara dadinji dazu da safe meyafaru haka nan Iya ta zayyanewa Ammah duk abinda ya faru,Jalilan sukaiwa haka eh Hajiyar Amma bakiga ba danai musu magana babu kunya haka suka zageni tas basu dubi girmana ba.
Shikenan Iya nagode,ran Ammah sosai ya baci to ina ruwan su da kayan jikinta da zasiyi mata wannan wulakancin zata dau kwakwkwaran mataki kuwa akansu dan bazata lamunta ba tunda ba zaman su takeyi ba itace ta kawo ta gidan bataga wanda zai takura mata ba.
Dakin Jalila tajuya ta sake shiga sai yanzu ta kare mata kallo da alama har tai baccin kuka takeyi Girgiza kai kawai tai takoma dakinta cike da takaicin halo irin na Sarah da Yayanta na rashin tarbiyya da wulakanta duk wanda beyi musu ba.
Sai bayan azahar Jalila tafuto har Lokacin ranta ahade yake tunanin Abunda zatayiwa su Mom kawai takeyi sakowa tai suna zaune aparlon suna tikar dariyar sunyi maganin Jalila gashi ta kasa futowa saita koma taci gaba dasa tsummokaranta,tsabar kidima tsaye suka mike ganin kayan da tasa ayanzu yaci uwar wanda suka cire mata dazu kallon kallo suke atsakanin su da tambayar kansa wa yake siya mata wannan kayan.
Ko kallon su bataiba ta wuce kiching wajan Iya taje tabata abinci,kare mata kallo Iya tai oh ni wai Jalila waya siyamiki wannan kayan dan India ta bata amsa saboda ALLAH fa zan miki karya ne,kinga yadda kikai kyau kamar bake ba amma wadan can azzaluman sun cuceki bayan duka harda cire miki sutturar jikinki sudai kayan summu su kadan bare nace sakawa zasi babu daya balle Kanwar biyu,kibarsu da Allah kawai Uhm kawai Jalila tace tafita daga kiching din.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 29
Suna tsaye har wannan lokacin cike da hassada da bakin ciki jira sukeyi kawai ta futo su sake yimata shegen duka su cire kayan jikinta,kamshin turaransa kadai ya isar musu da sakon saukowar sa daga kanta tai ta kalli saman hada idanu sukai kumbura fuska tai dan taji haushi da dazu yaki zuwa ya rama mata dukanta,kauda kansa yayi daga kallon ta.
Muzurai su Mom suka fara dan basu so saukowar saba kwafa Mom tai dayi musu alamun su zauna zama sukai sun zuba masa idanu kamar tsofaffun mayu kwarjini yake musu matuka aduk lokacin da Mom tasu yimasa tijara kwarjininsa kesata kasa aiwatar da komai saidai taita cika baki amma ingata gashi saidai tai kus takasa furta abunda yake kan harshan ta.
Biyo ni abunda ya cemata kenan kamar bashi yayi maganar ba kai tsaye dining ya nufa binsa tai abaya da plet din Abincinta ahannu set kikam tai masa kamar wata soja zauna sai Lokacin taji abunda yace zama tayi akan kujerun da suka zagaye dining din idanun su Mom kamar zai fado kasa su zauna wata yar kauye tazo ta zauna aiko bazata sabuba ba.
Yana sane dasu a parlon sosai yakejin idanun su akansa amma ya basar kamar besan da suba,kadan ya zuba abincin kallon Jalila yayi datai tsuru kamar ba ita ba yau bakin tsiwar ya mutu,ci abincin ki to ta amsa mikewa tai kallonta yayi da alamar tambaya daga rigatai tana kokarin cire wa dan sarar Jalila haryau tana nan inzataci abinci saitayi tik da ita.
Rike rigar yayi tare da zabga mata harara zauna zama tai kamar zatai kuka dan inda kaya ajikinta batajin abincin yana shiga yadda ya kamata.
Zama tai badan taso ba cikin kwanciyar hankali yake cin abincin sa haka Jalila ta zage tana zabga loma tama manta da Allah yayi ajiyar su Mom awajan, Rufaida kamar ta hadiyi zuciya ganin sahibinta yana cin abinci tare da wata kucaka ba ita ba sakejin tsanar Jalila tai acikin zuciyar ta dacin alwashi kala kala akanta.
Yana gamawa ya yagi tishu ya goge bakin sa tsam ya mike daga dining din,Jalila har nishi takeyi tsabar yadda cikinta ya cika hannunta yaja suka fice daga maine parlo hannu Rufaida ta dora aka tafashe da kuka Mom kuwa aiji take kamar zata amayo da zuciyarta,har turiri zuciyar ta take tsabar bacin rai da bakin ciki.
Shikenan na shige su wannan matsiyaciyar zai hada hannun sa da nata Mom na yadda bakya kaunata tuntuni kingaza samomin abunda nake so nake kauna alkawari nawa kikai min amma haryanzu kin kasa cikawa kuka take bilhakki wani azababban kishin Jalilah takeji da bata nasan me suke ba.
Suna fita ya cika mata hannu dama dan ya kunna su Rufaida ne ya bakanta musu rai yanxu ya tabbatar yagama kunna su babbakewa kadai ya rage suyi,lambu ya nufa dan sosai sassanyar Iska take kadawa me matukar dadi da sanya nishadi,daya daga cikin kujerun wajan yaje ya zauna Lumshe idanun sa yayi yanayin yanai masa matukar dadi kamar bacci ya dauke shi haka yakeji.
Swimming pool ne yayi matukar burge Jalila bata taba zuwa wajanba ahankali take takawa kamar tana tsoron kar ruwan ya jata,ta saba da wanka arafin garin su shiga takeyi babu ruwansa koda mazane aciki suna wanka to itama fa afkawa takeyi tayi abunda yakaita tafito taitafiyarta.zama tai agefan ruwan ta zura kafafunta sosai sanyin ruwan ke ratsata har Lumshe idanu take da hannu take dibar ruwan tana wasa dashi.
Ai wllh sainayi wanka taya za'ai ma nazo har wannan rafin me shegen kyau natashi banyi ninkaya aciki kinsa ba mikewa tsaye tai saidata daddage ta buga tsalle sai gata tinjim ta fada ciki,a yanda Jalila ta zata abin ba haka yake ba rafin garin su ba wani rafi bane wannan zurfinsa yafi na garin su facal facal tafara yi ga kayan jikinta sun taimaka wajan sakeyin kasa gaba daya ta gigice tuni tashide ruwa ta hanci ta baki ta kunne duk shiga yake.
Mrs Baba Bello Abubakar
.........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 30
Karar ruwan dayaji yasa yadan bude idanun sa harya basar ya kasa hakan dan bega sanda wani yaje wajan ba ahankali ya mike gaba daya yau bayajin dadin jikinsa kamar Zazzabi ke son kamashi,ruwan ya hango tunda ga nesa yana motsi alamar akwai Abinda ya fada cikin sa karasowa yayi idanunsa alumshe yanayin yayi matukar yi masa dadi musamman da yazo bakin ruwan.
Cikin ruwan ya kurawa idanu ras yaji gabansa ya fadi kara ware idanunsa yayi in yaga daidai mutum yake hange akasan ruwa,cikin azama yacire rigar jikinsa yayi wulli da ita ruwan ya fada saida yayi can kasa yadago ta gaba daya tayi wani irin nauyi babu inda ke motsawa ajikinta harlokacin begane wacece ba,futowa yayi dauke da ita akafada ganin Jalila yasa zuciyar sa wani irin harbawa yaushe tazo wajan meya kawo ta.
Akasa ya ajiyeta idanunta arufe danna cikinta yayi saiga ruwa yana fitowa ta hanci ta baki har wannan lokacin Numfashinta bedawo gaggar jikinta ba cak ya dauke ta suna zaune har wannan time din suna kulla yadda zasu bullowa Jalal da Jalilah kai harma da Ammah da Dad,binsa sukai da kallo ganin yadda ya shigo asukwa ne duk kwakwarka bazaka taba shaida akwai wata razana afuskrsa ba amma acikin zuciyarsa razana ce me matukar yawa da tashin hankali.
Kai tsaye bedroom dinsa ya wuce da ita dagashi har ita sai digar ruwa sukeyi rasa ta ina zaifara yayi,akan bed dinsa ya kwantar da ita hancinta ya toshe iskar bakinsa ya hura acikin bakin Jalila,ajiyar zuciya ta sauke kusan tare suka sauke ita da Jalal da yake cikin tsananin damuwa ga Ammah bata nan taje Unguwa rasa mezai taimaka mata dashi yayi kamar ba likita ba gaba daya kansa ya toshe.
Rawar sanyi tafara hakoranta har haduwa suke da junan su kayan jikinta ya cire mata danya lura sune suka saka mata rawar sanyin da takeyi wardrobe dinsa ya bude rigar sanyi ya dauko ya saka mata sai wani wandon sa three quarter harkasa yaje mata amma bata daina rawar sanyin ba.
Blanket ya lulluba mata gaba daya bata cikin hayya cikin ta box dinsa ya dauko ya hada allura yayi mata sannan ya fada toilet ruwa me dumi sosai yayi wanka dashi tukunna yaji dadin jikinsa, still rawar sanyi takeyi kamar zata shide masa dafe kansa yayi da sauri ya tashi ya fita ko Ammah ta dawo bata dawo ba har Lokacin toya zaiyi da Yarinyar nan.
Rigar sanyin ya cire mata da wandon daya sa mata towel yadaura mata, toilet ya wuce da ita ruwa me dumi ya tara a bathtub yasakata aciki ajiyar zuciya take sauke wa saidaya tabbatar ta gasu jikinta ya rake rawa sannan ya fito da ita bathroom ya saka mata,dauko ta yayi ya dawo da ita applying cream yayi mata me kamshi da sanyaya zuciya kayan daya cire mata ya mayar mata.
Blanket ya sake rufa mata gaba daya haki yake ya matukar gajiya be saba da wannan aikin wahalar ba ga Jalila da shegen nauyi cikin wasu mintuna bacci ya dauke ta gashin kanta yasha ruwa gaba daya ya mammanne a gefen fuskarta takara wani haske zuba mata idanu yayi yana kare cute face dinta kallo uhm sleeping beauty yafada a zuciyar sa,mikewa yayi ya koma parlo zama yayi har Lokacin zuciyarsa bata daina bugawa ba yayi zatan tuni Jalila ta jima da mutuwa me za ace da iyayanta in Yarinyar su ta mutu shine kadai abunda yake zuciyar sa.
Kiran sallar magariba ne yasashi tashi Alwala ya daura yana idar da sallah wayar sa tai kara peaking yayi ganin sunan wadda yake yawo akan screen din,Jalal ina Jalilah dan kallon ta yayi kadan tana dakin ta Ammah ok babu dai wani abu dake damunta uhm babu Ammah,dama zan gaya mane bazan dawo yau ba Zainab ce ta haihu kuma ni yakamata ace nazauna a asitin kakula da Jalilah dan Allah duk Abinda take so kabata.
Dan Lumshe idanun sa yayi da tunanin ya zaiyi da Jalila ita da bata da Lafiya shikenan Ammah saikin dawo Allah ya tashemu lafiya ameen sallama sukai ya sauke wayar daga kunnan sa,Numfashi ya furzar daga bakinsa goshinsa yake murzawa cikin tsananin damuwa ina zaikai Jalilah yana da tabbacin ya kaita wajan su Mom kafin safiya zasu kashe ta ko wajan Iya zai kaita no hakan ma be masa ba.
Kallonta ya sakeyi ahankali take sauke numfashi dagajin yadda take fitar dashi kasan ba dadi takeji ba tunani bar katai su suka cikamai kwanyar sa,yana zaune awajan har akai sallar isha'i yana idar da sallah Jalila ta farka,duk ilahirin jikinta jitake yayi mata nauyi kamar wadda akasa madoki aka doddoke guiwowinta haka take ji.
Dan motsawa tai hakan ya sanar dashi tashinta,ahankali ya taso kamar me jin tausayin kasa zama yayi kuda ita goshinta ya dafa babu wani zafi ya sauka kuri tai tana kallon sa babu bakin magana saidai idanunta da suka kara wani girma sunyi ja alamar bata da cikakkiyar lafiya,yaye blanket din yayi dagata yayi ya zaunar da ita amma Jalila kasa zama tai akan jikinta tafiyatai zata sake kwanciya yasake zaunar da ita amma fa zama ya faskara.
Gaba daya tayi laushi hatta dan yatsanta jinsa take takasa motsashi sai idanu kawai dake kallon sa,cikin damuwa yake kallon ta Yarinya lafiya kalau amma kalleta ta koma kamar wata zautacciya to kodai gamo tai acikin ruwan shidai betaba ganin dan mutum ya fada ruwa ya kasa zama sai akanta,daga karshe dai saidaya jinginata da jikinsa ta dan zauna.
So yake yaji magar ta koda tsiwar ce duk yadda yake tambayar ta metakeji takasa bude baki tamai bayani bawai dan batajin sa bane sarai tana jinsa amma bakinne yaki bata hadinkai ta budeshi tai masa magana,saiya kara shiga cikin damuwa da taraddadin ko tasami wata matsalar ne.
Yakici abinci gyada masa kai tayi alamun eh kwantar da ita yayi da kansa ya shigo Kichin wajan Iya tai mamakin ganin sa ita zata iya cewa ma bata taba ganin sa a Kichin ba, yallabai me kake bukata dan jim yayi abinci zaki hadomin sai tea to ta amsa dandanàn tahada mai gaba tai zata kai masa dining no kawo karba yayi yafi ce tabishi da kallo tunda zu zuba idon ganin Jalila takeyi amma shiru bata ganta ba.
Har bedroom din yakai Abincin dagota yayi ya nufi toilet da ita brush yayi mata sannan ya dauro mata Alwala bata da hijab haka shima baida wanda zai bata,dakin Ammah ya bude ya dauko nata key yayiwa dakin sannan ya fito tana kwance kan praying mat din da yadora ta hijab din yasa kamata atakaice dai Jalilah daga kwance tai sallah.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 31
Sai data idar yasake dagata tea yafara hada mata da kansa ya dinga bata saidata shanye tas,Lallai yarinyar nan badai ciba duk cutar da take kalli ta bude ciki tana dirkar abinci,abinci ya zuba mata dan kadan spoon ya dauka yana bata saiga Jalilah ta lamushe abinci wanda yadebo nashi da nata duk sai data hada ta cinye ya yadda ba ita kadai take cin Abincin nan ba harda aljanun ta.
Magani ya dauko zai bata nanfa Jalila tace batasan zan canba tuni ta fara Kuka,hade face yayi kodai kisha maganin nan wllh kona danneki na dura miki kememe kinsha tai gata da shegiyar kafiya da taurin kai bayadda beyi da ita tasha maganin fir taki,cup ya shiga Kichin dinsa ya dauko gaba daya maganin ya hade mata waje daya ya zuba ruwa a cup din saidaya tabbatar ya narke matsowa yayi kusa da ita babu damar tatashi tagudu matsa daya yayi mata ta kasa motsi yadda akewa yara dura haka ya dura mata tana kuka tana komai saida tasha.
Saidaya tabbatar yagama dira acikinta sannan ya saketa harara ya zabga mata kazama kawai yar kauye Kuka ta sake fashe dashi kamme zaice mata yar kauye Murmushi kawai yayi tunda bakya son sunan nan aiko na samu abinyi,malama yimin shiru ko yanzu nasake dura miki maganin shuru tai gaba daya bakinta ya kauraye da azabar daci ganin yadda take ta ya mutsa fuska durowar jikin gadon sa ya jawo saiga chocolate kala kala daukowa yayi ya bare ya samata abaki tuni Jalila tai shiru taji zaki sabanin dacin daya addabi rayuwar ta.
Ai tunda ka nunamin wajannan nasamu na zuwa nasha alawa saina shanye ta tas zakasan ka duramin magani mitar da takeyi kenan oho bemasan tanayi ba laptop dinsa ya dauko ya rage aiki sosai sai wajan 12 yagama kashe laptop din yayi sam ya manta da wata Jalilah adakin saidaya juyo ya ganta kwance a wajan datai sallah ta kudun dune a hijab din Ammah.
Hijab din ya cire mata ya kwantar da ita akan bed ya jamata blanket,parlo ya koma kan sofa ya kwanta yasan yau ba Lallai ya iya bacci ba
Besaba da kwanciya akan sofa ba to waccan magajiyar tazo ta gajemai shi kuma gaskya bazai iya kwana waje daya da ita ba duk da yarinya ce yana ganin hakan be dace ba.
Besan sanda bacci yayi awon gaba da shiba,kiran sallar farko a kunnan sa akayi shi mikewa yayi gaba daya jikinsa ciwo yake ga kwannan takura ga gajiyar da yayi ta dawainiya da Jalila kafadunsa wani shegen ciwo suke, toilet ya wuce yayo Alwala nafil fili yayi kafin yaji ana haramar tada sallah ya fita Masallaci,sai wajan 6am ya dawo har Lokacin Jalilah tana kwance tana sharar bacci.
Gsky Bazan iya sake kwanciya anan ba bedroom din ya wuce bed din ya hau can nesa da Jalila ya kwanta dan danan bacci yayi awon gaba dashi.
Ta dade da farkawa amma gaba daya gabobinta har wannan Lokacin ciwo sukeyi ahankali tatashi zaune ba laifi ba kamar jiya ba juyawa tai tana kalle kalle da tunanin a ina ta kwana hango Jalal tai yana baccin sa hankali kwance,waro idanu tai tab dama adakin dan India na kwana gadon ta kalla shikansa bed din abun kallo ne ga shege laushi kai ita dai tasha dadin ta.
Ashe haka yake da mutunci data sani da batai masa wannan muguntar ba kalli yadda har abinci ya dinga bata abaki,sauko wa tai kamar me koyan tafiya dakinta tatafi saidatai wanka sannan tai Alwala sai Lokacin tai sallar asuba,awajan ta sake kwanciya har Lokacin batajin dadin jikinta.
Salamu alaikum iya ta rangada sallama adakin Jalila sannu yar nema kinanan kina bacci kin barni inata faman aiki to wllh tashi zakiyi yanzun nan kafar ta tafara ja ke Jalila tashi kitashi kikama aikin ki,tashitai cike da jin haushin iya haba iya saboda Allah yanzu bazaki barni nayi bacci ba,jakar Ubanki bacci kikazo yi nifa nalura Jalila bakisan abunda ya kawo ki gidannan ba,kawai kifito fili kice kinfara yimin hassada da bakin ciki to inba hakaba ina ruwanki dani.
Au nice ma nake miki hassada da bakin cikin masu gidan sukace nata soki kifara aiki bazaki dinga ci kina kashi ba, to kije ki gaya musu nace bazan zo ba duk shegiyar data isa tazo ta daukeni inanan ina jiranta,dafe kirji Iya tai to badani ba sai dai kije kifada musu da kanki amma baza aji mutuwar sarki abakina ba keta shafa amma nidai kigaya musu sakona bazan zoba uwar su tazo ta daukeni.
Harta kwanta ta mike saboda ma kina bakin ciki da rayuwa ta da yanzu andade dayin jana izata shine bakimin ya jiki ba kinkama fadin nafito nai aiki nifa innaga dama zan Iya cewa nadaina aikinnan tunda nazama yar gayu gaskiya zan fadawa Ammah asamo wata ni na yaye kaina,ashe koma warki kauye yayi babu inda zani ina gidannan kuma bazanyi aikin ba kizuba ido kiga ikon Allah saidai na hangoki kina ta aikin wahala inai miki gwalo.
Zangani kuwa dan kika daina aiki nima denawa zanyi dariya Jalila tasa to kidaina mana Iya wai Meyasa kike son gasa dani kefa kin kusa mutuwa niko yanzu nake karama keko kin fara jiyo kamshin mutuwa,Kuka Iya ta fashe dashi dan arayuwar ta tsani ayi mata zancan mutuwa,Allah ya isa tsakanina dake Jalila na tabbatar bakya kaunata tunda kikemin fatan mutuwa.
Nifa ba fata nake miki ba kawai duba nai da yadda kika fara tsufa nan da kowane lokaci zaki iya arangama da mutuwa duka ta kawo mata ta goce tana dariya dayi mata gwalo,ganin inta biye mata ita zata bata ranta abanza,daga murya tai kice musu bazan zoba din suzo sujani,karaf akunnan Mom data hawo taga ubanda Jalila takeyi Acikin dakin.
Tofa kaka kara kaka ga Jalila ga Mom kubiyoni dan jin yadda zata kaya.
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 32
Wani ashar Mom ta lailayo ni kike fadawa haka cigaba tai da hawowa tanayi tana masifa saita zubarwa da Jalila hakwara inta shigo,karkashin gado Jalila ta leka tajawo bakar ledar data adana budewa tai aguje ta fada Toilat ruwa ta kam fato a cup ta zuba karkashin data dauko me uban yawa kofar dakinta ta kwara shi ta tura kofa ta yadda babu yadda za aita lura dashi.
Afusace Mom ta banko kofar ta fado dakin zuuuu tatafi santsin karkashin yajata ji kake kum ta buga kanta ajikin madubi sai jini tsananin azabar data ratsata tasata sakin kuka,dariya Jalila tasaka harda tafi wooni Jalila yanzu saiki tashi kidakenin ai gani anan indai zaki iya kitaso Mom,karar da mom tasaka itace ta tayar da Jalal daga bacci tsaki yaja wacece wannan zatazo tadinga yimusu ihu.
Futowa yayi rai bace bega kowa ba hango dakin Jalila da yayi abude yasashi nufar wajan Mom ya hango yashe akasa rike da kugu ga kafarta da takeji kamar ta karye,Jalila ya kalla wadda take tikar rawa gaba daya batasan da tsayuwar shiba girgiza kansa yayi ke yar kauye juyowa tai da sauri bata rai tayi,kallon Mom yayi data cika tai form kamar zata fashe tsabar takaici da bakin ciki.
Ko kallon ta bebe ya tsallaketa Jalila datai kalar tausayi matsawa baya take fuska amarairai ce kan yayi hakuri karya daketa,kunnanta ya kama ya jata dole tabiyo shi jin yana barazanar cizge mata kunne dan Allah dan India kacikamin kunne karkacire min ka tsaya nai maka bayani bani da hannu a faduwarta wayyo gwaggo zai cire min kunne tagaban Mom suka wuce anan suka barta sake da baki ta bisu da kallo.
Saida ya shiga part dinsa tukunna ya sakar mata kunne wash wllh kunnena kamar ya tsige rankwashi ya kaimata aka,meyasa kika kayar da ita ni babu ruwana tahowa tai zata daken akan banje nayi aiki ba shine Allah yasa kamin tunkafin takara so,karya kike wani abu kika samata ta fadi yanzu saikije kisan yadda zaki da ita,haba dan India nidakai fa bata baci bansan haka kake da mutunci ba sai jiya har abinci kadinga bani abaki.
Ashe dai kana sona harara ya wurga mata yimin shiru da bakinki awajan shiru tai dan yanzu kaf Gidannan tafi ganin mutuncin Jalal babu abunda zai sata bata aikata ba,tsaki yaja kansa harya fara ciwo saboda ya tashi baccin be gama sakin sa ba.
Kan sofa ya zauna TV ya kunna tuni Jalilah tai gaban plasma taiwa kanta matsugunni aduniya tana son kallo sai dariya ko take dama dan ita ya kunna kozata barshi ya huta.
Mom kuwa wani kululun bakin ciki yazo ya tokare mata a kahon zuciya har ita za aiwa wannan rashin mutuncin yakamata fa tafarka daga baccin daya fara daukarta itace fa Saratu wadda bata ragayya bata sanayya intasa kanta abu saita aiwatar kwafa tayi,Iya ta kwallawa kira da sauri Iya ta hauro harara ta wurga mata tsohuwar munafuka kema zan dawo kanki tare dake aka hada baki harna subale batare dana sani bako.
Wllh Hajiya banda masaniya ke dallah yimin shiru bakinki sai faman hamami yake wuce ni kikiramin su rufaida suzo su fitar dani daga dakinnan,juyawa tai cikin jin zafin abunda mom suke mata sanda taje part din suna bararraje a parlo kowacce daga ita sai vest da gajeran wando,Allah ya shirya Iya ta fada azuciyarta kuje Hajiya tana kiranku tafadi ta kasa tashi ne.
Kallon juna sukai tafadi kan sugama tan tancewa tayi juyawarta sunkai mintuna biyar kan Salima ta mike tanajan tsaki wai Mom meyasa zata dinga abu kamar yarinya bazata dinga kallon gabanta ba intana tafiya saita jawo mana wahala,nima abinda nagani kenan suna kumbura suna komai suka fita parlon kallon parlour sukai basu ga alamun wata Mom ba itako tana hango su kwala musu kira tai.
Kun ganni nan sai Lokacin suka hangota dabar azaune hawa sukai suna tunanin meyakaita dakin yar kauyan nan saura kadan Rufaida ta zame dakyar tasamu tarike kofa,haba Mom aisai kigaya mana Halin da dakin yake ciki ba kibarmu a duhu ba salan mufadi muzama daya mudake wannan dai ba rayuwa bace,ni sanda zan shigo dakin gayamun akai niba wani surutu ba kukamani ku saukar dani.
Me! mune zamu dauke ki tundaga sama har kasa gaskiya bazan iya ba bansani ba ko Salima zata iya wannan aikin,kema da kike yar gwal bakiba saini wllh bazan ba nima, wannan ai wahala ce ki sauko da rarrafe mana aizaki iya.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 33
Ni kuke yiwa wannan rashin mutuncin Kamar ba Uwar ku ba,to Mom dan kin haifemu kuma shikenan sai akace mu bayinki ne nidai Allah saidai ki kwana anan,Kuka mom tasa sai kuma kiyi gaba Salima tai tabar Rufaida a tsaye to nima bazan iya wannan jegon jakar ba aisaima ki karyani sai kin taho,itama sauka tai suka bar Mom jabe akasa kamar kayan wanki takaicin duniya ya gama cika mata zuciya.
Duk abinda sukai mata bataji wani abuba Jalila kawai ta dorawa alhakin haka kuma dole tagirbe abunda ta shuka mata,dajan jiki ta samu tafito daga dakin dakyar kamar yadda suka cedin da rarrafe ta fara tafiya tuni ta hada gumi tai sharkaf sai haki takeyi kamar zata shide dan azaba.
Jalila ce ta futo tana shan chocolate hango Mom tana rarrafe yasata rugowa da gudu shekewa tai da dariya wai wayaga gwangwarasa wllh Mom ko fasali bakiyi da rarrafan ba na tabbatar koda kina yarinya bakyau kikai ba sanda kina rarrafe,dariya ta sake fashewa da ita,muje na take miki baya kinga ba abarki kekadai ba karkije kizame kifasa baki.
Duka ta kawo mata afusace wllh duk ranar da kika shigo hannun na saikin gane baki da wayo matukar ni Saratu na haifu saina baki mamaki Duk iskancin ki na dameki dani kike xancan zakiga abinda zai biyo baya,ah nisaidai naga alkhairi duk wani shige da fican mutum akan idanuna kuke namiki alkawarin matukar ina Numfashi bazaki taba cin nasara akan Ammah da dan India ba nasan dai waccan me zubin samudawar kike so ki manna masa to kwalelen kare da hantar kura.
Buga cinya tai tai gaba tabar Mom sake da baki kirjinta na dukan tara tara aina shegiyar yarinyar nan tajiyo zancan nan,anya mutum ce ba aljana ba metake nufi da bazata taba bari aci galaba akan Ammah ba kodai tasan kudurinta,kai bata sani ba wama zai gaya mata bata da wayon da zatace ta karanci abunda mutum yake kullawa,sainaga bayanki Mom ta fada cike da cin alwashi.
Dakyar Allah ya taimaketa ta sauka guiwowinta kamar zasu cire bajewa tai aparlo tana shan iska kafarta ba karamin ciwo take mataba harta fara kumbura daga gani targade ta samu.
Jamal ne yayi sallama akofar parlon hango Mom abaje akasa tana numfarfashi yasashi shigowa da sauri subahanallahi Mom menene ya sameki haka,cikin bakin ciki take dubansa tunda shima abokin Jalal ne yana cikin makiyanta,nafadi ko aka kayar dani,wa yakayar dake Mom ina wata matsiyaciyar yarinya yar aikin da uwar Jalal ta kawo itace taimin wannan aika aikar,tana fadin haka ya gano watake nufi.
Ayyah abu beyi dadi ba gaskiya bata kyauta ba kaida kasan ya kamata kenan tsugunnawa yayi yana kallon kafar gaskiya dole sai angyara miki kafarnan to indai zan iya takawa a gyaramin, gyara zama Jamal yayi yadda inya damki kafar Mom bazai sakiba saiya gama aikin sa.
Yana rike kafar tunkan ya fara gyaran Mom tafara wash wash gaskya da zafi hmm zaki bayani nan gaba,fara gyarawa yayi tun Mom na daurewa saiga mom tafara kwarara ihu tana dukan sa ya cikata kememe Jamal yaki cika mata kafa tsananin azaba ta ishi Mom tuni tayi cilli da dan kwalinta.Jalilah dake wasa adaki jin kukan Mom yasata fitowa asukwane haka Jalal har gware suke wajan saukowa suga meke faruwa.
Tsaki yaja hango Jamal azaune yawani gwagwgwafe yanai mata gyaran targade juyawa yayi ya koma inda yafito,jalila rike ciki tai tana tikar dariya mom shabe shabe take kuka tai wujiga wujiga,tashi tai tana rawa da tsalle me kuka tana dariya ai mata dan kwadan daddawa,rufaida da salima ne suka shugo asukwane suma turus sukai ganin yadda Mom take gursheken Kuka ga Jalila agefe tana rawa da waka.
Jamal gumtse dariyar sa yayi shikansa dariya cinsa takeyi bilhakki take kuka babu algus ba ha'inci,samun waje sukai suka zauna zubawa Mom ido sukai abunma ba karamin haushi ya basu ba dan wannan gyaran takewa kwaroro to,ko sannu babu wacce tai mata acikin su kan agama ai tuni Mom ta tsula fitsari zirrrr saiga fitsari yana gudu.
Mom fitsari fa kikai cewar Salima ah lallai Mom nayadda da irin azabar da kike sha,gaskiya Mom ke bakaramar raguwa bace Kuka fa kikeyi ni wllh kinma badani kizauna agaban dan cikin ki kidinga wannan kukan kin barar mana da mutunci wllh,to dama mutuncinne daku da harza abarar muku kungama zubdashi tun atiti,dawa kike ah da wanda ya tsargu zakici Ubanki.
Biyota da gudu Rufaida tai dan taci alwashin saita ragar gajewa Jalilah baki duk yadda taso kama Jalila kasawa tai sai wahala data ke sha sai haki take,nifa bazan taba gajiya ba dama na kwana biyu banyi wasa ba ga abokiyar wasa hargida dan kanta tagaji ta kyaleta ta lura ba kamuwa zataiba walahar dakanta kawaii take.
Mrs Baba Bello Abubakar.
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 34
Mom ba karamar wahala tasha ba kan agama gyaran ta tainewa Jalilah yafi akirga,haka kuma Jalilah bata fasa yi mata dariya da waka ba,yana kammalawa ya sakar mata kafa tabishi da harara dan acewar ta da mugunta ya dinga matsa mata kafa,su Rufaida ta kallah da suka kunshe dariya duk wanda zaiga Mom awannan halin dole ya dara ko yaya ne kuwa.
Dukan kafadar Jalal yayi mutumina baka da dama kana gani mamarka tana ihu da neman dauki kaki zuwa ka rarrashe ta,harara ya wurga masa karka sake hadani da ita ko ahanya wllh in wannan ce tahaifeni ai banzo duniya a sa'a ba Murmushi kawai Jamal yayi to shikenan tunda haka kace dadai yafi maka gwara kayi abunda ya kawo ka.
Gyara zaman sa yayi aikasan meya kawoni wai Jalal meyasa kake da taurin kai karatun da zamu karo na 2years amma ka gaddame baza muje ba mekake tunani,iska ya furzar me zafi bana sha'awar sakeyin nesa da gida gaskiya matukar saina karo karatu za'a karan matsayi na hakura kayadda ka hakura daci gabanka mene aciki biyammu fa zaadinga yi muna karatu muna daukan salary,uhmm zan duba sarkin naci bazan can naci bane gaskiya ce.
Zanzo na sanar da Ammah da kaina tunda ni ancema bani da baki ko,ah ainaga kanaso kai mana sakiyar daba ruwa ne,kuma nasan Dad yana sane yayi biris ya kyaleka nan gaba fa kai zai dorawa Alhakin kula da Asibitin nan shiyasa yake so ka karo karatu amma narasa menene yahau kanka kodai kafara soyayya ne ban saniba, àah soyewa na farayi kyalkyalewa da dariya Jamal yayi gwara dai ka fadi gaskiya mutumina dan murmusawa kawai Jalal yayi besake cemai komai ba.
Harya tashi tafiya bega Jalila ba yana fita ya hangota a harabar gidan tana tsalle tsalle kai wannan yarinya bata rabo da wasa,sai lokacin ya kare mata kallo saiyaga kamar ba itaba takara girma ta kara haske kayan jikinta ya kallah yana da tabbacin Ammah ce ta siya mata.
Ganin yafito ta rugo da gudu tana haki tsayawa tai agabansa tana haki yadai Jalilah gudun me kikeyi haka kamar wadda za'a kama,canza fuska tai tana yamutsa ta abokin dan India dama tambayarka zanyi to inajinki kaima kana allura da bada magani kamar yadda dan India yakeyi,cikin Dariya yake fadin Inayi mana aikinga aminan junane na amana washe baki tai yawwa ta kwana gidan sauki.
Dama magani nake so kabani,name kenan akalla nakai wata guda banyi bayan gidaba shine nake so kabani maganin da zanta tsuga gudawa saina yi biyan bashin na baya dan bakaji yadda ya dankare min acikiba,ke Jalila bana son karya yaushe bayan gida ke makalewa mutum aciki,to tsayama meya hana kitambayi dan India saini bakar fata dan Nigeria,to aikaga garinmu daya kenan nidakai shikenan saika bani basai wani dan gari daban yaji sirrimmu ba.
Kallonta kawai yake waishi zataiwa wayo kuma kinyi magan mekyau yanxu yaushe kike so,katemaka kawon yau saboda bana iya bacci yadda naga rana haka nake ganin dare ok shikenan zan kawo miki nan da anjima,dama nasan kanada mutunci amma karka bari kowa ya gani meyasa,matse kwallah tai saboda kar hankalin su ya tashi shiyasa gwara ayi komai cikin sirri.
Ok saina zo anjimar,ngd zanjiraka anan harka dawo girgiza kai kawai yayi wannan yarinyar badai drama ba,tsalle ta daka cike da farin ciki ta koma parlo dadi kamar ya kasheta, Rufaida da Salima basa parlourn sai Mom da take baccin wahala bararrajewa tai babu abinda ya dameta ranta fes.
Ammah oyoyo tatashi da gudu ta rungumeta oh Jalila danja fatan dai ba wanda kika tsokana fada,dawa zanyi fada ai babu sa'a na a gidannan kuma kin sanni da hakuri ko ammin saidai na kauda kai naji nasihar da kikaimin ta hakuri kuma nadauka,kai Alhmdlh haka nake so kizama ainama zama Ammah tun tuni,hannunta ta kalla mekika kawon mezan kawo miki kuwa daga Asibiti nke fa.
Au wai baki da lafiya kalau nake haihuwa akai kece kika haihu kai Jalila wllh kincika tambaya kibarni na huta haka ko kinganni da ciki bare na haihu,aini Ammah Innata nikadai ta haifa bantaba ganin cikin taba na sani ko ciki ne dake kikaje kika haihu.To! bani bace kanwa tace zaki dani suna zanje dake zata sake magana Amma tarufe mata baki kiyiwa Allah ki kyaleni inaga aikin Jarida zaki karanta kowa ma ya huta.
Gaba tai tabar Jalila sam bata gaji ba in zasu wuni atsaye bazata taba gajiya ba,kallon Mom tayi datai rashe rashe tana bacci ke lafiya kuwa saratu take wannan baccin kalau take cinnaka ya shige mata riga shine taita kuka harda fitsari ke kauce nan ban yadda da wannan zan can naki ba na kanzon kurege.
Sama tahau tabar Jalilah anan kamar megadin Mom kar wani abu yazo ya dameta nan ko dariya takesha yadda Mom ta hangame baki tana sharar baccin wahala.
Mrs Baba Bello ABUBAKAR
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 35
Tun tana zaman jiran Jamal harta gaji harabar gidan takoma tazauna batafi 20mnt da zama ba taji andanna hon mikewa tai dan taga wanda zai shigo shidinne kuwa dadi kamar yayi mata me da gudu ta ruga tunkafin ya gama daidaita parking yana budewa zaifito da sauri tarike mufin motar haba abokin dan India aiba saika wahalar da kanka kafito ba kabani kawai la juya abunda za ayishi asirri kuma akaga ma dawo aise agane ma.
Au bazan ma huta ba,to wane hutu zakai dan Allah kabani kajuya,daban kawo miki bafa kinsan yanzuma zan iya juyawa da abuna,kai aina sanka da imani bazaka iya komawa dashi ba Murmushi kawai ya saki to naji cikamin murfin mota nafito nasha iska badan tasoba ta matsa ranta harya fara baci yaba ta abu amma sai faman bata mata lokaci yake.
Ungo hannun ta harrawa yake gashinan kina zuwa kisha yanxu guda daya da safe daya da rana daya da daddare hakama ya isheki basai kin kara shaba komai zai daidaita,washe baki tai amma allai maka albarka da gudu tajuya tabar shi anan binta yayi da kallo yana girgiza kai gaskiya suna aiki da suka iya zama da Jalilah.
Dakinta ta fada saidata adana maganin hankalinta ya kwanta,kwanciyatai tana wake waken ta ranta fes tasan abunda ta taka allah alla take kawai dare yayi ita tasan irin tsiyar da zata shuka yau acikin gidannan.
Mom sai bayan La'asar ta iya tashi dakyar tadan cangala tanufi part din su cike da sakejin tsanar Jalal da Jalilah itakadai tasan abunda take ayyanawa azuciyarta dole ne sushiga komar ta.Bayan sallar isha'i suka hallara dan cin abinci babu wadda taiwa Ammah magana acikin su balle suyi mata Allah ya raya itama bata kula suba.
Ke tsohuwa iya ce tafito daga daki tatsani irin wannan kiran da suke mata,kije ki dafo mana tea tunda bakisan aikin kiba komai sai angaya miki kina gab da barin gidannan Mtswww taja tsaki babu yadda iya zatai haka ta juya,wani mugun Murmushi Jalilah ta saki dama tasamu,bakar munafuka tashi kije kuyi tare kullum saidai ki kalmashe kafa kizauna babu aikin fari balle na baki,hmm aiko baku fadaba ma dama tashi zanyi kusha kurumin ku.
Mikewa tai tana sakin murmushin samun nasara dakinta tafara zuwa kai tsaye saida ta dauko ajiyarta,hajiya Iya kawo nadafa dan nasan ba karamar gajiya kikai ba kamar ko kinsani wllh nagaji harna fara bcci wa yancan marasa mutuncin suka taso ni,sai hakuri kije ki kwanta kawai aiko Allah yayi miki albarka bari naje na kwanta,kisha baccin ki hankali kwance Iyata to saida safe Allah ya kaimu.
Tana ganin Iya tafita ta dauko magninta akallah ta zuba kusan guda goma tuni magani yaji ruwan zafi ya narke tas citta da kamun fari ta zuga duk masifar su babu yadda za'ai su gane,tsaf tagama saida kowa tacika mai cup taf sannan ta dauka daya bayan daya takai musu Mom ce karsha kaiwa saidata zuba mata rankwashi aka shegiya ragowar yunwa kullum ci kike amma ba agani ajikin ki kin kusa hada kayanki akoma gidan Inna da baba aci gaba dacin gabza.
Ko kala bata ce musu ba komawa gefe tai tana kallon su,to koke mayyace bazakisha tea dinnan ba shiru tai itafa babban burinta taga sun fara sha,suna sha suna zafinta da tsine mata Albarka,dan dacifa sunajin daci a tea din kinga Mom tsabar muguntar yarinyar nan tatashi tacika citta da kanin fari shayin har daci yakeyi,nima naji tsabar Iskanci ne da samun waje dan mukasa shako dayake ba ubankine yake kawo kayanba to sai munsha saidai ki mutu.
To da mubata tasha ba Gwara mun zubdashi a rariya ba wllh kuwa,tas suka shanye tea saikizo kidebe cups din kuma kitanbatar kin wanke su shiru kake ji Jalila ko kanzil bata ceba abin fa ya basu mamaki yau yan rashin kunyar ne basa Kusa🤣🤣🤣basu san tsiyar data kulla musu ba,tana shiga Kichin din tai wulli da cups din biyu suka fadi suka tar watse rawa kawai tafara tika tsabar yadda farin ciki ya cika mata Zuciya.
Bata ankara ba kwalba ta shige mata kafa tsabar yadda take cikin farin ciki batasan ma cups din sun fashe ba kara ta kwalla tarike kafar ta tuni jini ya fara malala akwaita da tsoron taga jini kuka tafarayi tana yarfe hannu,wayyo ALLAH Ammah dan India kazo ka cecan jinina zai kare.
Dawowar sa kenan daga hospital ya bala'in gajiya tunda ya shigo yaga su Mom ya hade face kamar be taba Dariya ba harya taking steps yafara jin kamar kuka a kiching dan jim Yayi jin ana amtar dan India lokaci daya yagano ko wacece,hakiman suna zaune kuma sarai sunajin kukanta amma babu wadda ta nuna tajima koda wasa.
Da baya ya dawo hanyar kiching din yayi cikin sanyin jiki gaba daya yagaji da fitinar Jalila dole ne yasan yadda zaiyi da ita Bazata kashesa da ransa ba,tsayawa yai yana kallonta ganin yadda tai kaca kaca da kiching din ga glass din data tarwatsar akasa,kuka tasake fashewa dashi dan Allah takwarana kazo kasamin magani karjinina ya kare.
Ware idanun sa yayi akanta wai takwaranta lallai yarinyar nan tama raina shi,hade face yayi dawa yakawoki kiching din wllh tsautsayine nidai katemaken cike da takaici yake kallonta kafarsa daya yasa akiching din ya figota zaka karyan hannu dan India kasake ni banza yayi kamar be jita ba.
Saida yakaita har dakinta sannan ya dangwarar da ita bakaramin jin zafin yarda itan da yayi tajiba,kara tasaka Ammah dake shirin kwanciya a sukwane ta fito,ke meyake faruwa kike wannan karar ganin Jalal adakin yasa ta dakata tana kallon su Fuuu yazo ya wuce Ammah ko hutawa beba kansa yadau zafi tazo takara zafafa shi tsaki yake ja ajejjere.
Innalillahi Jalila garin ya kikaje kika taka wannan kwalbar,nima Amma a kiching na taka bansan wanda ya fasa ba dama ansane tunda ansan zan shiga naje na taka,dama kina shiga Kichin ne da har za'a ajiye kwalba saboda ke bana son karya kifadamin Abunda ya faru gaskiyar kenan Ammah,to aishikenan ni yanzu yaya zanyi dake saidai Jalal yazo ya cire miki.
Dakin Jalal Amma ta nufa yana tsaye gaban dressing mirror dinsa,Jalal kaifa nake jira ga Jalila can tana ta faman kuka kasan dai bazan iya cire mata ba kaine zakai wannan aikin wuce muje,rai bace yafita sai yayiwa Jalila mugun duka zata shiga hankalinta,har Lokacin kuka take tsugunnawa yayi agabanta ya rike kafar kwalbar tashiga sosai.
Da kyar ya samu ya zare ta zuwa lokacin hawayan Jalila sun kare sai ajiyar zuciya da takeyi wanke kafar yayi ya samata magani yana gamawa ya cika mata kafar yayi gaba,jarababbe tunda kayi mata aishikenan zama Ammah tai akusa da ita tanai mata sannu lamo tayi kamar me bacci wannan fa shine anyi ba aiba tunkafin abinda ta aiwatar ya fara aiki abu yana neman komawa kanta.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 36
10mnt wash cikina murdawa yake sai kun taho har gudu ta hada dashi kafin ALLAH y bata sa'ar afkawa toilet,ko gama daidaita batai acikiba Rufaida ta fara buga kofa dalla malama kiyi sauri kifito cikina murdawa yake,banza tai da ita kamar bataji ba aiko tasha zagi wajan Rufaida sai data gama tsaf sannan tafito,bangajeta tai ta afka toilet din itama kamar jira ake ta fito cikinta ta yasake wata azababbiyar kartawa durkushewa tai cikin tsananin azama.
Dakin Mom ta ruga asukwane ta afka toilat tana shiga Mom na fadowa dakin a hargitse sai uban gumi take hadawa ko ganin gabanta batayi burinta kawai taganta a toilat,amma me tana tura kofar tajita gam tashin hankali masifa Mom ta fara yayyafawa,wace yar iskar ce ta shigarmin toilet koma wace acikin ku tai gaggawar futowa tsit Salima tai.
Mom bugu take kamar mahaukaciya durkushewa tai jin yadda wata shegiyar gudawa ta matsota bata ankara ba taji tanabin kafafunta,Salima ce ta fito aguje Mom ta fada Toilat dakin ya dumame da wani shegen wari kamar mushe ya mutu hanci Salima ta toshe.
Gadon Mom tanufa da nufin ta huta ko gama zama batai ba cikinta yabada wani zuuuuuu kululu durowa tai da rarrafe takaraso kofar tafara bugawa da hada Mom da Allah akan ta fito kememe Mom taki fitowa,tsananin wahala tasa Salima fashewa da kuka jitake kamar ana hura mata wuta aciki,zuwa wannan lokaci ta dade da sakin abunta a wando sai dakin ya sake bada wani kafirin wari mara dadin shaka ko kadan.
Awannan dare tun suna iya kai kansu toilet saida suka kasa mikewa gabadaya kamar andadduke musu guiwowin su haka suke ji,suna daga kwance suke sakin abin su gaba daya sunyi zuru zuru,kafin gari ya waye gaba daya basu san inda kansu yake ba.
Karfe 7 Dad ya sauko daga bangaran sa yay sauri yake zai fita yana da meeting shiyasa yau zaiyi sammakon fita,har zai wuce part din su ya dawo da baya dan yana da tabbacin iyanzu dai basu tashiba.
Tunda ya doshi hanyar part wane shegen doyi ke masa welcome,to wannan doyin mene haka yana bude dakin Mom saida ya dawo da baya wani shegen wari ne ya bigi hancin sa toshe hanci yayi subahanallahi Sarah menene ya mutu acikin dakin nan jin shiru yasashe kundun bala ya shiga dakin,yadda ya hangisu ragaje ragaje kamar ma tattu ras yaji gabansa ya fadi da sauri ya karasa in ya kalla daidai kamar basa cikin hayyacin su.
Hannun Mom ya rike sai gashi koma,juyawa yayi ya fita da sauri dakin Jalal ya wuce kai tsaye,my son yana jamai kafara sa cikin bcci yaji kamar Dad din na kiransa farkawa yayi ganin Dad tsaye akansa yasan babu Lafiya mikewa yayi cikin alamun bcci be ishesa ba,maza ta so kaduba min su Sara gasu can akwance ita da su Salima kamar basa cikin hayya cin su.
Saukowa kawai yayi ya bishi abaya ba karamar dauriya yayi ba wajan shiga dakin sun jage jage da jikin su,to she hanci yayi Dad sunci wani abune da ya bata musu ciki abun yayi worst da yawa ko yaushe zasu iya rasa rayuwar su kwalara ta kama su ba da wasa ba,to kayi musu temakon gaggawa mana dage kafadar sa yayi wannan ba aiki na bane saidai akwashe su akai su hospital.
Kaine zakayi wai Jalal meyasa kakeyin haka badan yaso ba ya amsa da to dan Aduniya ba mutanan da ya tsana sama da su.daga waya Dad yai ya kira Ammah tana zaune tana lazimi cikin azama ta sauko dan jin wannann mummunan labari dakin Iya ta wuce sai data tasota suka taho tare su kansu sun girgiza da ganin yadda suka koma kamar basu ba,yanzu taya za'a dauke su agyara su kema Ammah banda abinki duk gidannan wazai Iya daukar wa yannan fafaromar ai saidai yallabai.
Wani kallo ya watsowa Iya tsit tai tana sunkui dakai ko zasu mutu babu wadda zai dauka acikin su saidai su shekara anan,allurai ya hada drip kowacce ya daura mata dan danan ya kare saidai kowaccen su tasha leda biyar sannan ya rage musu gudun ruwan ya daura musu ta shida kamar yayi bindiga dan takaici.
Waini son me sukaci haka ya sasu wannan kwalara da da tsautsayi fa sai dai azo aga gawar su kafada ya daga su suka sani koma me suka ci gobema sa kara,kowa dauriya yayi da ya tsaya adakin dan babu yadda zasi ne yana sa musu ta 7 yayi waje dan shi ya gama aikin sa kosu warke koma kar su warke ba shi da asara.
Rukayya ko zaki gyara musu jiki kin gan su cikin kazanta fa abundai ba dadi,Dad ta duba gaskiya bazan iya ba karya da ciwo mari da zafi in sun tashi sayi da kan su waje tai Iya ta bita abaya wannan dinma tayi ko kari ta tabbata da itace ko kallo bazata ishe su balle kuma suzo su jima adakinta alhalin tana cikin wannan yana yin.
Mrs Baba Bello Abubakar
.........✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 37
Parlo suka dawo kowa ya zabga ta gumi Iya dai ganin wannan zaman bana kare bane tashi tai tafara ayyukan ta.
Farka warta kenan daga bacci Ahankali ta sauko daga bed dinta kafarta ta kalla har Lokacin tanai mata zafi ya zama dole taje ta duba aikinta dan gaskiya matukar suna nan kalau dole ta rama abinda Jamal yayi mata dan akan murna taje ta taka kwalba wahalarta bazata tafi a banza ba.
Tana fitowa daga daki ta hango Ammah ta zuba tagumi cikin sanyin jiki tafara saukowa ahankali harta zauna Ammah bata san ta sauko ba, Ammah mene ya sameki sai Lokacin ta farga da sauko warta yadai Jalilah kafar tai sauki gyada kai tayi menene naga kin zabga tagumi kamar anyi mutuwa,uhm wllh su Saratu ne kwalara ta kama su abu kamar yaki suna can naga shiyan rai a hannun ALLAH.
Kamar ta taka rawa amma kawai sata kanne toh sukuma abinda ya same su kenan to ala Kyauta maganin masu shegen ciye ciye,au harke zakicewa wani me ciye ciye kidai yi ahankali kema karki jawo mana wahala muna zaman mu yanzu da kece ai Inaga sai qashi kawai zamu gani ajinki tsokar dai tagama karewa dariya ta saka ni Ammah ai ina da kiba eh gskiya fa naga alama sannu giwa.
Akallah su Mom basu suka farka ba sai kusan biyun rana Dad harya gaji dajira ya tafi meeting dinsa yayi muguwar makara,da kyar suka rarrafa suka shiga toilet kafafuwan suma bazasu iya daukar su ba.
Har daki Jalila tazo duba su sai kunshe Dariya takeyi bata tata suke ba yanzu shiyasa babu wadda ta amsa yajikin da take musu,ikon Allah waiku mena tsare muku agidannan baku da Lafiyar ma bazaku daina gaba dani ba gwarama ku sassautawa kanku nidai babu yadda zakui dani haka ta karaci neman tsokanar ta tafito ranta fes ganin kowaccen su sai Uban idanu awaje da goshi agaba.
Sunkai kusan 1 week kafin su dawo daidai ammafa ba karya sunji jiki awannan lokacin kuma Jalilah ta warke sarai tana ta warkajamin ta.
Gobe ne sunan kanwar Mom data haihu Jalilah sai murna take zasuje suna Ammah tace zataje da ita.
Jalilah koki tashi kishirya kona tafi asheke bacci ma kike tasha ban sani ba kafarta ta jawo azabure ta mike Ammah zanje karki tafi kibarni ke kika sani kuma nidai tafiya ta zanyi in har bakiyi sauri ba da gudu ta fada Toilat wanka ta burbura ta fito kayanta kawai ta dauka tasaka sababbine bata taba daka su sun mata kyau matuka,mayafinta ta dauka wanda Ammah ta siyo mata harda hijabai ta diddika mata.
Ammah na shirya to kin kyautawa kanki da kika shirya da wuri wane kayan zan saka ranar sunan basai kin dau kaya ba nayi miki anko rungume Ammah tai woo Ammata kina sona sosai kamar Innata murmushi kawai tayi naji dadi da dan India ba mace bane da yanzu harda shi zaki dinga siyawa,au ke kishi kike da dan Indian naki nikam eh bana so asiyamin abu asiyawa wani gaskiya wannan ma ai gasa ce bari ya jiki saiya daina siya miki kayan da kike sawa ainasan bazaki gayamai nafadi haka ba.
Muje ni kin tsaya shegen surutu dakin Jalal ta falla da gudu yana zaune yana danna laptop dinsa wani aiki yake ta sauri ya karasa ganinta kawai yayi kamar ancillota,sai haki take tana bude hanci,wash wallahi na gaji wai meyasa bakya abu na hankali kuma bana ce inkinzo kidinga tsayawa a parlo ba to dan India mene inna shigo dakinnan ban sani ba karki shiga hankalin ki zumburo baki tai ta juyamai keya.
Iyee ninake miki magana kike juyan keya to bakaine baka son ganina ba nibarama natafi,juyawa tai zata tafi cike dajin haushi ruko hannunta yayi ke baza ai miki fada ba sai kizo kinajin haushin mutum ko juyo da ita yayi hawaye ya gani shabe shabe a face dinta,me kuma akai miki bakai ne ba ok sorry me kikazo ki fadamin Unguwa zamu tafi da Ammah shine nazo yima sallama amma ka koreni,kallon ta yake komene abun Kuka anan oho.
To ya isa ina zakuje haka gidan suna kuma kwana zamiyi idanun sa ya waro kwana kuma har dake ehman bkaga na shirya ba,shine kika sha wannan kwalliyar banyi kwalliya ba,to ni kuma fa aina zaku barni kenan agida mana aikai kayi girma da zuwa Unguwa nidin eh kaifa uhm shikenan adawo lafiya.
Amma dan India bazaka rakamu ko bakin kofa ba tunda Saudiyya zaku tafi mezai hana ban raka kuba dariya tasaka yaushe zamuje Saudiyyar kefa babu mai akanki wllh fitani kin katsemun aikina,sai mun dawo zan kawoma tsara ba kaji to daga mata hannu yayi alamar byee,binta yayi da kallo harta fice dan murmusawa yayi yaci gaba da Aikin sa.
Kina can kina zuba kamar kanya ko,sallama naiwa dan India kin sanni Ammah duk me bani ina ganin mutuncin sa,af kenan ni bakya ganin mutunci na haba Iya aike ta daban ce keda kike bani abindadi ina zanki ganin mutun cinki,to yanzu naji magana har harabar gidan Iya ta taji su tanai musu adawo lafiya.
Baba direba ne zai kaisu har sun shiga mota ya fito face dinnan ahade baba kawai ya mikawa hannu alamun ya bashi key din bashi yayi,yana yi musu adawo lafiya Ammah ce take kallon sa baki bude kaida kace aiki zakai bazaka samu damar zuwa ba yanzu aikin ka gama kenan,um kawai yace dan India kaima kwana zakai banza yayi da ita zata sake magana Ammah ta maka mata harara komawa tai tazauna ta nutsu kamar ba ita ba.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 38
Tunda suka fara tafiya shiru sukai babu wanda yake magana bakin Jalilah dai kaikayi yakeyi tana son magana da sun hada ido da Ammah zata wurga mata harara don dole tai shiru badan taso ba,hayin Malam bello suka nufa hon yayi akofar gidan get man ya wangale masa kofa saidaya daidaira parking tukunna Ammah ta bude tafito Jalilah ta biyo bayanta.
Kallon Jalal tai da ya gyara kwanciyar sa bashi da niyyar fitowa,dan India kafito mana jagora zakimin kuje kawai jan hannunta Ammah tai suka wuce tunda suka doshi parlourn suka fara jiyo hayagagar wata tsohuwa,iyee nifa wllh nagaji haihuwa biri biri kamar mage yaushema Kuka yaye wannan Yaron kalle shifa amma harkin sake haihuwa sakan duk dukiyar dana takoma hannunki to wllh bazata yiwuba ni intashi atutar babu.
Sallama sukai a parlon amma wannan tsohuwar bata daina masifar da takeyi ba,yawwa me Rukayya shigo kisamu waje ki zauna zama Ammah tai tana kallon hajjah ina wuni hajja ba gaisuwarki nake bukata ba haihuwar ki nawa daya hajja to Alhmdlh akamme ita zata saki takashi taita haihuwa ke da yake kinsan abunda ya kamata aigashinan haihuwa daya kikai.
Shikadai na haifa amma Sure shekara 7 ta haifi yara bakwai wace irin masifa ce wannan ninasha gumin dana da wahalar da harya kawo haka haka Kawai kuma saitazo tacika mana gida da yara to bazan lamunta ba ehe.Ayi hakuri hajjah ai haihuwa nufin ALLAH ce ke yimin shiru kekiyi mana in haihuwar dadi ce dole taje asibiti Adam yadda zaai da ita haba wannan jaraba haka.
Kalli yara kamar Yayan kiyasai duk inda na juya yara nake gani duuu kamar kudaje.Anty Zainab ta kalla datake kukan bakin cikin wannan suruka da Allah y hadata da ita ai ba Kuka zakiyi ba kiyi abunda nasaki shine kawai zaman lafiyarki agidannan wallahi,Fuuu hajjah tatashi tai part dinta tana sababi da masifar za acinye dukiyar danta.
Kiyi hakuri Zainab komai me wucewa ne haka Allah ya yota saidai kiyi hakuri kawai.
wllh Ammah nagaji bakiga yadda a kullum take in mutunci na na na safe daban na rana daban yanzu da ban haihun bama haka fa zata dinga cin mutuncina kuma ko agaban wane bata ragamin kullum acikin kunci da bakin ciki nake haba dan ALLAH yaya ya ake so nayi.
Haka zaki daure kicinye jarrabawar da Allah yayi miki komai me wucewa ne hawayanta goge,sai Lokacin ta lura da Jalilah datai tsuru tana kallonta bataso taga mutum yana kuka fadi take amma wannan hajjar anyi shedaniyar mata, murmushi Anty Zainab ta sakar mata itace Jalilan taki murmusawa tai eh itace yaudai nace bana zo da ita banta ba zuwa unguwa da ita bag sai yau.
Ina wuni anwuni lafiya lafiya lau Jalila kai Ammah dama zaki barmin ita wah so kike hajja tacinna mata wuta jikokinta ma tana neman kai dasu bare ita bare,ai batayiwa bare tunda tasan tafiya zasi aa kafata kafarta babu wani dadin baki dazakiyi min,Uhm ai shikenan zo kidauki kanwar taki Jalila tasowa tai aka bata babyn kyakykyawa da ita Ammah mutafi da ita,rufan asiri inkaita ina aini yanzu na manta yadda ake raino danna na sameki nadan fara tunawa.
Kawota Jalilah maza kije wajan kannan ki kuyi wasa to ta mikawa Ammah babyn tashitai ta nufi inda yaga yaran zama tai akusa dasu,lah kema Agidan Ammah kike ya akai bamu sanki ba anan nake bakwa zuwa ne shiyasa baku sanni ba zamuzo in akai hutun school menene hakan toke bakisan schl ba daga kai tayi alamun eh to makaranta nake nufi.
Shiru tai dan batasan komai a harkar karatu ba waccan tsohuwar wacece,bata rai yarinyar tai kakar muce amma bata sanmu kai haba har kuma bataso na dauka babyn can cance kawai bata so harda mu,to ita kuma inane dakinta zo muje na rakaki to tashi tai suka rankaya gidan babbane sosai amma gidan Amma ya ninkasha a kyau da tsari har part din hajja ta rakata kinga part dinta zo mushiga mana make kafada tai nidai bazani ba duka na zatai,me kikai mata tace karmu sake matsawa inda take tunda mu yayan jarabane sai haifomu ake kamar qwari ita bata son yara shikenan bari ni na shiga mugaisa to anan zan tsaya
Dan madai daicin parlon take karewa kallo komai tsaf tsaf dan hajja badai tsafta ba,kai wanake ji anan nice kewa bakuwar da mukazo da Ammah to to aimata wadan can fitsararrun ne zauna ganinan fitowa zamatai akan sofa tana sake kallon ko ina,bayan mintuna uku hajja tafito hakora ta washe Allah sarki zauna yar nan.
Ina wuni ta gaida hajja lafiya lau yar nan kina lpy lafiya lau ina mamarki tana gida ku nawane agidanku nikadai aka haifa sake fadada fara'arta hajjo tai kaga irin albarka zauna sosai kinji tashi tai ta bude fridge damammiyar fura ta dauko mata sai tashin kamshi take ungo maza kisha aini akwaini da son yara amma kar su wuce daya zuwa biyu,makwat Jalila ta hadiye yawu.
Saukowa tai dirshan tafara shan furar me shegen dadi tana sha hajja na janta da hira sai data shanye tas sannan ta ajiye robar,duk dadinnan da kika ban bazai hana naci Ubanki anjima ba to bana tafi hajjah haba kekuwa jikata kiyi zaman ki mana ai karki damu zanzo na tayaki kwana anjima to! Aiko dakin kyauta zan gyara miki shimfida kuwa kiyi bacci ki more.
Zanzo kuwa karki damu tana fita taga yarinyar da suka zo tare zaune abaranda taso mutafi,naga kindade hajjan ce tace ki zauna ehman harta bani fura nasha ma me shegen dadi tab lallai kinyi sa'a tunda har hajja ta sakar miki fuska tabaki abunta uhm wai ya sunan ki Sajida sunana oh yayi dadi zo muje dakimmu.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 39
Wannan kayan na wanene nawa ne uniform din Islamiyya tane kuma da fararan kaya kuke zuwa eh,shikenan anan suka sha shance har kusan karfe 2 harabar gidan suka fito sudan zazzagaya motar da suka zo aciki ta hango da Mamaki take kallon motar tabbas acikinta suka zo da gudu ta ruga gidan gaba ta fara lekawa yana cike akwance kamar me bacci amma ba bacci yake ba shikadai yasan abunda yake tunani.
Dan India dama baka tafi ba tome kakeyi anan,ahankali ya bude idanun sa akanta daga ita sai vest harararta yayi ina kayanki suna gida zafi nakeji kuma wasa zamiyi Sajida ya kalla da take washe mai wawulanta ke kuma fa nima wasan zanyi ke bakiji kunya ba godai godai dake kirasa da wadda zaki wasa saida Sajida mene dannayi wasa da ita tazama kawata ai saikije kitayi kukoma gida kuyi wasan acan.
To kaima anan zaka kwana Jalila ki kyaleni karna fasa miki baki hannun Sajida ta kama sukai gaba cikin jin haushin Jalal yayi mata tsawa,futowa yayi daga motar ya nufi cikin gidan lallai idanunka kenan Jalal saiyau zaka zo min barka bana bukata Murmusawa kawai yayi ayi hakuri Anty Zee kinsan yanayin aikimmu,dama kana nan tun sanda mukazo mekakeyi to da baka tafiba.
Dariya Anty Zainab tai kema kinjiki Anty zamanne Inaga yayi masa dadi ko kuma akwai ajiyarsa atare damu babu wata ajiyarsa a hannuna kawai binbinine irin nashi kamar yaron goye, Ammah ya kalla kai Ammah meyasa wai kika rage ji dani sabida na samu mace mezan tsaya ina yi awajanka zauna yarona ka kyale yaya zama yayi tamiko masa babyn no Anty bana daukar baby iyee iyayi iya reto tom Idan matarka ta haifa zamuga yadda za ai sai kace bazaka dauka ba.
Iyayine kawai ba wani abuba zai dauka ne Allah ya nuna mana matar tasa ta haihu naga ya dauki dan da aka haifa,shidai yanajin su Murmusawa kawai yayi mikewa yayi Ammah zan wuce yaushe zanzo na daukeki sai gobe in angama suna sai darema zamu dawo,Allah ya kaimu ameen.
Ranar Jalila wuni tayi tare da yayan Anty Zainab suna wasa da tsalle tsalle Ammah har tayi magana ta gaji,bayan sallar isha'i suna zaune suna kallo hajja ta doka sallama saida gaban Anty Zainab ya fadi sannu hajja face ahade ta amsa yawwa kece da sannu ai ke za ayiwa ita shiru tayi dan tasan yanzu neman abunda zai hada su fada takeyi sabida danta ya kusa shigowa.
I lai kuwa tana zama yanayin sallama sai Lokacin ta saki fuskarta shigo dan Albarka kadawo eh hajja mun sameku lafiya lafiya lau hajja kusa da ita yazo ya zauna in dai yanasan zaman lafiya aiko hakan ba karamin dadi yayi mata ba kayan hannun sa ta karba tana budewa kayan Baby ne cikin wata katuwar leda ahaka dai zaka kare kullum kana yawo da kayan jarirai ahannu kullum matar ka biri biri ta haihu har nagaji da gayawa mutanan kauye naja bakina nayi shiru kai tir wllh.
Adaiyi hakuri hajja kyautar Allah ce bamu san wanda zasuji kammu ba kai tafican sauna sha sha sha ana nuna maka gabas kanayin yamma sai kaje can ka karata tunda ni bazaka taba goyon baya naba sai matar ka kardai ka manta nice na kawo ka duniya ahto.Shiru yayi yarasa wai hajja wace irin macece bata kaunar zaman lafiya ko kadan burinta kullum aita cece kuce akan magana guda daya.
Zo mutafi mukwanta yarinyar arziki kedai Uwarki ta iya farar haihuwa, Ammah Jalila ta kalla acan zaki kwana eh Ammah Jalilah shishshigi Amma ta ayyana hakan to tashi ki bita Allah y tashemu lafiya Ameen,tare suka fita har sunfara tafiya ta tsaya nayi mantuwa hajja kije kawai zan taho,to zadai kizo dinko eh zanzo to ina jiranki gaba tai tabar Jalila tsaye awajan.
Dakin su sajida ta nufa wasu kaya ta harhada aleda cikin hijab dinta ta boyo ledar tazo ta fice sanda ta shiga har hajja ta fara bacci samun waje tai ta ajiye ledar hannun ta tanemi waje ta kwanta.Karfe biyun dare ta farka saidata jima a zaune ledar data shigo da ita ta dauka kayan ciki ta zazzage fararan kayane aciki sai farar hoda da bkin kwalli.
Tsam tamike ta cire kayanta fararan kayan ta saka tasamu hodar nan ta babbur suna kanta dama atsefe yake ribom din ta cire ta barbaza gashin kwallin tasamu ta zazzane face dinta dashi saidata tabbatar komai yayi yadda take bukata, kiching din hajja ta nufa wata shegiyar wuka ta dauko me shegen kaifi da tsini duk shekara hajja ke amfani da ita saboda aikin sallah.
Dauko ta tayi tareke ahannu kafar hajja taxo ta faraja Atine!!! taji wata shegiyar murya tana kiran sunan ta afirgece tamike shekaru nawa rabon da taji wani ya ambaci sunanta,bayan gado tai aguje sabida abunda tai arba dashi bayan tafarka tacikin hasken farin watan daya haske dakin.
Wa innahu sulaimanu wa innahu Bismillah hasbunallahu lakadi ja'akum nashiga Uku ni hajja nayi gamo dan Allah dan Annabi kuyi hakuri kukyale marainiyar Allah,shiru!!! Aka daka mata tsawa tsit tai zaro mata idanu tai kin sannu wllh bansan kiba ko me kama dake ban taba gani ba zaro mata idanu tai wato ke muniyar banza ce kin takurawa surukarki akan tana haihuwa kin manta Allah ne ya bata kyautar Allah ba ta mutum ba,wllh na daina sharrin shedanne dama amma yanzu na gane gaskiya ban shirya mutuwa ba yanzu.
Wukar hannun ta taga kamar zata sara mata ki tabbata ni aljana hari ina sane dake duk iskancin da kike na kyaleki ne ina bibiyar ki,mema kika ce baza aiba gobe cikin rawar murya take fadin taron suna to ya zama wajibi ayi aci asha ayi wadaka daga rana me Irin tayau nasake ganin ko afuska kin nunawa jikokinki kiyayya ki tabbatar zakisha wannan wukar can Duniyar mu zaki koma sai kin dandana kudarki.
Nagode Allah ya saka da Alkhairi bazan kuma ba kiyimin rai ki rabu dani,sannan wani abu guda daya ina bakuwar da kikayi gatanan akwance to ya zama dole gobe suna kisamu katon kwano ki cika matashi da nama har saitaci ta barshi sannan kidamo mata fura me shegen sanyi wllh zan bata kuyi hakuri kindauki Alkawarin na dauka nadauka wayyo ni Atine!!! barkewa da Kuka hajja tayi.
Rufe idanun ki zamu tafi rufe idanu tai jikinta sai rawa yake tuni ta tsula fitsari yakai sau uku,da gudu Jalila ta ruga parlo kayan jikinta ta cire tamaida nata wukar data dauko ta mayar Inda ta ganta toilat ta wuce ta wanke Fuskarta da sabulu tas sannan tafito har Lokacin jikin hajja rawa yake idanu arufe.
Hajja lafiya kiketa hada gumi sai Lokacin tabude idanu fashewa hajja tai da kuka Allah natuba kayafin matsowatai kusa da ita wai lafiya,ina kuwa lafiya wllh gamo nayi yarnan gamo kuma acikin dakinnan ehman to wane irin gamo,aini bazakiji abakina ba tunda Allah yasa Mutuniyar arziki ce ta gafar ceni.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 40
Kunshe dariya Jalila keyi Allah sarki hajja daga gani kinsha wahala ba kdan ba,ai bazata kayyadu ba da rarrafe tafito daga bayan gadon jikinta har diga yakeyi saboda fitsari,hajja fitsari kikai ne shiru tayi ahaka takoma gadonta ta shige bargo bakinta cike da addu'a Kala kala.
Kwanciya Jalila tai ranta fes ko banza tayi maganin hajja ga kuma dadin da zata kwasa gobe aita komai zam zam.
Sam hajja kasa runtsawa tai gaba daya gani rai daran yayi mata tsayi kiran sallar farko akunnan ta tashitai cikin tsoro take dube dube ganin babu komai adakin sai Jalila dake sharar bacci hankalinta kwance, toilet ta fada saidatai wanka sannan ta dauro alwala ana idar da sallah tanufi part din Anty Zainab kwankwasa tai yar aikinta ce tazo ta bude ganin hajja yanzu tasan akwai Abunda ya kawo ta yanzu haka tijarar tatace ta motsa ta gaza hakuri har gari ya waye
Ina kwana hajja lafiya kalau cikin sanyin murya kamar wadda tai cutar shekara tayi zuru zuru samun waje tayi ta zauna tana jan cazbahar ta,zaman minti 5 tayi mijin Anty Zainab ya dawo daga masjid,ganin hajja saidai kirjinsa ya bada ras da sauri ya karaso gabanta har kasa ya duka yana gaisa ita antashi lpy lafiya lau amma hajja lafiya kuwa kika fito da asubar nan.
Kakalo murmushin dole tai lafiya lau dama. Maganar taron suna ce na janye magana ta kowa agayyato shi ai abun murnane da farin ciki jiyayi kamar beji daidai ba ai hajja maganar ce ban ganeta ba,ba matarka ta haihu ba kuma yau ne suna hakane hajja to shine nace agayyato yan uwa da abokan arziki ayi suna.
Kuma lafiyarki kalau hajja harara ta zabgamai aah ciwon hauka nakeyi ba haka nake nufi ba,karkacewa tai ta zaro kudi acikin sket dinta yawwa ga wannan sai ahada ayi hidimar suna,jujjuya kudin yake al,ajabi ya kamashi lallai Allah me iko addu'ar daya dade yanayi yau Allah y amsa masa hajja tagane gaskiya,tunda Matarsa take haihuwa haihuwar fari itace kawai tayi rawar gani daga wannan haihuwar bata sake nuna murnar taba.
Angode Allah ya kara girma Ameen ina Zainab din bari na kirawo miki ita to,minti biyu suka fito tare adarere tagaida hajja cikin sakin fuska take amsawa wai rabon dataga fara'ar hajja tun tana Amarya.Ina jaririyar wane suna aka saka mata Rukayya sunan yayar Zainab Allah sarki to Allah ya raya ameen suka amsa gaba dayansu.
Kowa da Abunda yake sakawa acikin zuciyar sa musamman Anty Zainab datake ganin abun kamar amafarki ikon ALLAH yafi ga haka,sai kuma maganar taron suna kigayyato duka yan uwanki ayi taro ai abun murnane nima yanzu zan kira yan kauye suzo ayi Dasu,lallai hajja ba ita kadai bace Mummunan gamo tayi kuma gata dai acikin hayyacinta to hajja Allah ya kara girma Ameen bari natashi natafi sai anjima.
Har bakin kofa suka raka hajja nanfa akafara kallon kallo wai anya ba mafarki nakeba abban sajida ido biyu kike Zainab ALLAH ne ya amshi addu'ar mu Allah ya ganar da hajja hanyar gaskiya Alhmdlh lallai wannan haihuwar tazo mana da Alkhairi me girman gaske.
Sosai kuwa ALLAH mun gode maka.
Daki hajja ta koma yan uwa da abokan arziki ta dinga kira runi yan kauye aka ciko mota dama tsoron hajja ke hana su gidan,gida ya cika dankam da bil adama kowa warkajimin sa yake Jalila taci nama haryayi mata yawa data tsaya daci hajja zatace yata kici iya cinki duk kwadayin Jalila ayaudai saidata kai ta kawo ko kamshin Nama bata sonji ansha shagalin suna kowa ya watse karfe 8 dai dai akofar gidan Anty Zainab taiwa Jalal jiyayi kamar sun shekara basa gidan ransa abace yake tunda suka tafi gidan bayayi masa dadi sam.
To mudai zamu tafi Allah y raya Ameen yaya Jalila sai yaushe kenan sai ankwana biyu zance dan India ya kawo ni wane kuma dan India ni abu dariya Ammah tai Jalal mana shine dan India dariya tai kai Jalila zan so agidannan kike wllh babu ruwana da bacin rai kullum cikin sani Nishadi zaki kasance dariya kawai tayi.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 41
Sanda suka shigo parlo su Mom suna baje suna shan iska har Lokacin idanun su bai dawo dai dai ba sannun ku da gida ya jiki kuma,naganku kowacce idanu awaje ko haryau zawon be tsaya ba zoki duba dan Ubanki nace zoki duba shegiyar Yarinya kai me kafirin surutu ina ruwanki da Lafiyar mu da zaki dinga shegiyar tambaya kamar makauniya.
Daga abun arziki tun baku son addu'ar Allah ya sake maimai tawa saidai kigani akan ki da uwar data daure miki kugu kike rashin mutunci,in sha Allah babu Abinda zamu gani dan mu bama hayam hayam kamar tinkiyoyi kullum baki abude, Ammah ce ta buge mata baki wuce muje bana son rashin kunya sama tahau tana juyowa suka hada idanu da Rufaida gwalo tayi mata ta karasa hayewa tana dariya.
Kiyi hakuri Saratu kinsan yarinya ce kinga Rukayya bana son wani gulma duk wa ya kitsa mata ta rainamu agidan Idan bake ba kiwuce kiyi Abunda yake gabanki kawai to alakara sauki inma baki fada ba zai bayar Mtswww suka ja tsaki,gaba tai cikin sanyin jiki bata son tashin hankali ko kadan a rayuwarta sukuma ta lura burin su kullum ayita hayagaga ana kumfar baki baza'ai wannan da itaba sam.
Dama ba yunwa suke jiba kowa neman waje yayi ya kwanta asuba tagari Jalil da Jalilah.
Haka rayuwa taci gaba da gangarawa ayi dadi ayi tsiya Jalila ta kara girma tarage fitina da tsokana zata iya sati ayanzu bata tsokani kowa ba ita da Jalal sosai ake dasawa.
Bording school ya samo mata daga primary two zata fara dan da aka kwankwasa kan Jalila babu wani labari in aka kaita js on za'a samu Babbar damuwa,ga Jalila tayi girma da primary akalla takai 14yers ayanzu haka wata malama ya samu a Makarantar yanemi alfarmar tadinga yimata lasson daya ke harka ce ta kudi da kauri ya biyata dan danan ta amince harda alkawarin zata kular masa da kanwar sa.
Tun daga kd ya sama mata makaranta mekyau da tsada amma suna da nisa sosai da gida gwara tai nisa da gida zatafi maida hankali akan abunda za'a koya mata.
Jalila ya kamata kije gida kiyi kwana biyu kafin kitafi makaranta to nan fa keyin ta saidai muje tare Ammah dawa zakije kauyan aini da zuwa garinku sai antashi auranki bata rai tayi ni bazanyi Aure ba bige mata baki Ammah tai kul karna sakejin kin fadi haka kuma kinsan ALLAH saikinje gida ko mutuwa zakiyi saboda Kuka.
Ni wllh Ammah wayo kawai kike so kiyi min amaida ni kauye shikenan bazan dawo ba haka na gaya miki bazaki dawo ba kitashi kihada kayanki indo zata zo kutafi nan da anjima sake rushewa tai da kuka Ammah da kanta ta hada mata kayanta.
Tunkan yayi parking ya hango Jalila azaune dirshan tana gurzar Kuka hmm matsala kome akai mata kuma oho,harya tsaya agabanta batasan yazo ba zata daina cin shinkafa da nama gaba daya hankalinta ya gama tashi,ke kukan me kikeyi sai lokacin tasan da tsayuwar kuka ta sake fashewa dashi Ammah ce tace sai nakoma gida kiyi me wai nayi kwana biyu.
Shine kike wannan kukan kamar wadda ake duka toko dai kiyi shiru kokuma inkin tafi kintafi kenan tundake baki da saiti garin nakune bazaki jeba,aini bana so naci tuwo murmusawa kawai yayi to aishikenan saiki kulle shinkafa kije kita dafawa acan inadai shikenan naman fa wannan kuma saidai ki rungumi sorry gaba yayi yabarta anan yana mamakin halin Jalila shegen kwadayi acikinta harda na siyarwa.
Sai lokacin taji dan dama dama wanke fuskarta tai da tagama cabewa da hawaye,kin gama kukan shiru tai Allah ya shiryeki Jalilah ni bansan sanda zakiyi hankali ba inaga saikinje makarantar zakiyi hankali dan can kikai rawar kai shegen duka zakisha babu ruwan su.
Saisu daken kamar wata jaka wllh koda aranar bazasuyi baccin dare lafiya ba mezaki musu uhmm bakomai Ammah zadai kawai suji ajikin su ni bana sanayya bana ragayya aiko zakici wahala wllh dalibai ma saki aiki zasu dingayi kuma dole kiyi.
Ammah kamar kin mance ni nikam ya za'ai na mance ki zandai biki da Addu'a kar adawon dake akakkarye shekewa tai da Dariya aiko da ban cika sunana Jalila kanwar dan India ba,Dariya Ammah tai kin yadda yanzu kanwar tasa ce ba yar aikin Gidan su ba,tuni Ammah aisu kansu yan makarantar nace musu yaya nane zakiga suna girmamani naga alama kuwa ko kuma su sakoki agaba ba.
Indo ce ta rangada sallama amsawa Ammah tai to kinga tazo dauko jakarki ki fito da ita to Ammah,maimakon tai Abunda aka sakata dakin Jalal ta nufa yana zaune yana rubutu ta shigo zumbura baki tai wai baka fara kewata ba,tsayawa yayi da aikin da yakeyi kewarmi tame aini dadi nakeji ma zan rabu da ciwan kai nice ciwan kan ehman aini kika tafi har kiba zanyi kafin kidawo shikenan tunda abun haka nema.
Mezaka bani to natafi dashi tunda nace kidauki shinkafa aina gama miki komai ko, to shinkafar gaya zan dinga ci.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 42
Kafadar sa ya dage alamun oho juyawa tayi zata futa Jalilah ya kira sunan ta yaune rana tafarko data farajin sunan ta abakin sa dama kasan sunana aah taya za'ai nasani ko kin manta abakin ki naji sunan mu iri daya ne,aini macece ni kuma mata maza mene mata maza nima ban sani ba,shiga bedroom dina zakiga leda akan bed kidauko to tafada juyowa tai wata katuwar leda ta hango jawo ta tayi har gaban sa kidauka tsarabar kice kikaiwa innar ki.
Kai amma dan India Nagode harda irin alawar nan da kake bani ikinje kyagani,aikuma bazan iya dauka ba au nine zan daukar miki kenan kijashi akasa ni ba bawanki bane,angode Allah yasa kafi haka kyau kan nadawo Dariya ya dan saki kekuma ki kara muni ba,zan kara kyau nima to asauka lafiya.
Jan ledar ta tai har kasa Indo ce ta kalleta oh ni Aisha haka kika sake girma Jalilah,bata fuska tai duk wane ya janyo min tafiya kauye kece kika ce zakije shikenan aka lakamin nima saina biki.Gidanne kike gudun zuwa wllh na yarda bakiyi hankali ba har yanzu da sauranki Jalila duk sanda naje innarki magana take akanki ammake kinanan ki mimmime kafafu kamar bakisan asalinki ba.
Kyale min yarinya haka Indo babu wanda baya san cigaba kiruciya ce wataran in ance tayi ma zata musanta haka,wannan kayan fa dan India ya bani nakaiwa Innata aikuwa kin gode mutuniyar dan India zamiyi missing dinki Jalila nikaina ba son tafiyar ki nake ba amma nasan ya kamata aitayi mana kawai cima kinfi shekara fa baki taba zuwa ta ganki ba.
Mikewa Indo tai to zamu tafi Hajiya Amma angode Allah ya kara arziki sai mun dawo kudi Ammah ta ciro daga pos dinta gashi kikaiwa Innarta wannan kuma kuyi kudin mota harda dawainiya haka angode har parking space tara kasu tare da Iya Jalila dai kamar zata fashe,baba direba ne zai kai su shiga sukai tana dagawa Ammah da iya hannu har suka fice.
Ajiyar zuciya ya sauke yana hangen fitar su girgiza kai yayi yadan zaiyi kewar hayaniyar ta da fitinarta betaba zatan zai jure hayaniya kamar haka ba dai gashi ya jure akan Jalilah,Uhm yar rigima yau sai kwanan kauye.
Tunda suka fara tafiya ta warware tana kalle kalle sai kuma taji dokin taje gidan taga Innarta da gwaggo sosai take son ganin su,basu sukaje ba sai sai La'asar tunda motar ta tsaya yan kauyan suke bin motar da kallo kamar idanun su zai fado Indo ce ta fara futowa sai Jalilah,sak sukai suna kallon ta saidaga baya suka shaidata ga Jalila ga Jalila yara suka fara tsalle da murnar dawowarta manyan kuwa a uziyya suke ja azukatan su annuba ta dawo.
Daga musu hannu ta dingayi cike da farin cikin ganin su da sauri ta fada gidan gwaggo da Inna suna soro jin ana cewa ga Jalila kamar wuyan su zai tsinke sabida leke abazata suka ganta rungume ta sukai cikin tsananin farin ciki,nayi kewar ku inna da gwaggo ke tafican babu wani kewarmu da kikai mudai mukai kewarki Jalila.
Hannun ta gwaggo ta kamo taho mushiga daga ciki,tare dawa Kuka zo Indo ce tataho dani Sallama tayi tashigo harara Jalilah tai shine kika tafi kika bar kayanki amota namanta ina murnar ganin su gwaggo abaki ba wannan murnar batakai zuci ba.Dariya sukai kamar kin shiga zuciya ta nima haka nace Inna kuwa ta kasa mgana sai bin Jalila take da kallo kamar ba itaba kai ta godewa Allah daya nuna mata nutsuwar Jalilah.
Angode Indo Allah ya saka miki da mafificin alheri nagode Allah ne kadai zai biyaki wannan temakon da kikai mana babu zamuce saidai miyi miki addu'ar gamawa lafiya, murmushi ta saki babu komai Inna ai Jalila nima kanwa tace jakarta ta zuge kudi ta dauko sunkai 50k gashi Uwar dakin Jalila tace akawo miki albashinta na watan nanne amma ta karo miki akan haka kyayi hidimar Gida.
Karba tayi tana zabga wa Ammah addu'a dubu goma ta zara ta kokawa Indo amma fir taki karba babu yadda basiyi da itaba tace bazata karbaba tashitai zan tafi Amma sati daya zami zanzo mutafi Jalilah to ko bazaki koma ba zan koma mana Dariya tayi nayi tunanin kin fasa makarnatar zanyi to shikenan sai nazo ko sallama sukai tatafi.
Ledar tsara ba ta jawo kwancewa tai atamfofine kala uku sai hijabai na manya guda uku takalma masu kyau kafa biyu sai kayan biskit da chocolate farin wadannan chocolate din bata wannan kayan take ba.Gashi Ammah dan India yace na kawo muku keda gwaggo atamfa daya da hijabi daya ta mikawa gwaggo gashi tunda ke kin kusa mutuwa,dundu tai mata zoki kasheni bayanzu zan mutu ba saina goya yayanki.
Dariya ta saka yayana lallai kin wahala gwaggo sauran ta mikawa Inna sai fara'a take bakinta har kunne aranar babu inda taje sai washe gari ta dinga zaga yan uwa da abokan arziki kowa yasan Jalilah ta canza babu wanda ta tsokana har wannan lokaci kwalliyar hauka tuni ta daina ta.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 43
Gidan Maman Ladi ya shiga da sallamar ta mijin ta na zaune adaki kuri yayi yana kallonta saidaga baya ya gano wacece hade face yayi jaraba kin dawo kennan to inma kallo kikazo yi ba akunna ba,harara ta maka mai tv dinka din banza ni yanzu wannan abar kamar kiyashi ma ai bazan iya kallo acikin ta nake birni naga yadda ake harkar arziki bata tsiya ba.
Ni ba kallo nazo yiba wajan Maman Ladi nazo to batanan saikiyi waje karyar banza babu wata tv datafi wannan duk Nigeria dariya ta sheke da ita hakane awajan ka ki haryanzu kanka abakar leda yake amma ni da naje na wataya abirni nasan Abun ba haka yake ba karike kwaranabbiyar TV dinka Jalila tafi karfinta.
Ficewa tai tana dariya wai TV dinsa kaf Nigeria babu kamarta,bala metsire ta hango tundaga nesa yake washe mata baki hade face tai Jalilah Jalila yan mata yatsina fuska tai ya akai Bala me tsire,washe hakwara ya sakeyi tunda na hango ki kindawo nake ta alla alla kifito na baki tsire.Allah sarki bala nagode kabar abunka yanzu ba da bace ni yanzu wannan naman naka da kudaje kebi bazan iya cinsa ba.
Zuru yayi yana kallon ta meyasa ai wannan tsiran naka yanzu kwayoyin cuta sun gama baibaye shi Iska ta gabas da yamma kudu da arewa duk ta hau kansa,da kuma da kike cifa to bakaji da kace ba kuma tana baya gaba tai ta barshi shanye da baki yana jimamin anya wannan Jalilah ce kuwa ba canjata akai ba.
Nan fa samarin kauye akaita layi akofar gidan su Jalilah gaba daya sun rikice ganin yadda tadawo fresh babu kazanta babu warin dake tashi daga jikinta ga suturar da take sawa Irin ta yan birni amasu zuwa neman Aure harda me gari yasha rawanin sa harda masu take masa baya.
Jikin Inna na rawa ta shimfida katuwar ta barma atsakar gida har cikin gida aka shigo dashi gwaggo ma sai yashe hakora take megari yau agidan su lallai sun duro Duniya a sa'a,cikin girmamawa suka gaida me gari gyaran murya yayi ya fara da Fadin.
Allah y jikan Malam mutumin kirki tun yana raye naso akulla wannan Abun alkairin amma yanzu duk da baya nan nasan zaiyi Alfahari da haka,wato abunda ke tafe dani shine Magana akan Jalila shekara kusan daya naso nazo da batun neman Auran ta saina samu labarin tatafi birni shiyasa na dan dakata tunda yanzu Allah y nufa ta dawo sai ayi komai agama tatare adakinta.
Gwaggo ce ta gaza hakuri Allah ya kara lpy bamu game inda kasa gaba ba,abunda megari yake nufi yaga iri yana so abashi Auran Jalila nan da sati biyu masu zuwa,shida kansa ko dansa nida kaina yafada yana gyara rawanin kansa.
Kallon kallo ake tsakanin gwaggo da Innah sake kallon sa sukai akalla yaba shekaru saba'in baya kodai ita kanta batajin zata Aure shi balle Jalila da take jikar jikar sa,burum Jalila ta fito daga daki duk tattaunawar da ake tana jin su karewa jama'ar kallo tai sannan ta dawo da kallonta kan gwaggo.
Wai gwaggo kasuwa kikai ne naji ana batun Auranki juyawa tai ta Kalli megari Allah yaja zamanin ka megari Indai gwaggo ce ambaka ita baka da wata matsala ina ce shikenan,gyaran murya megari yayi nkusa da shine ya ari bakin sa Allah ya temakeki ba gwaggo yake bidar Auranta ba ke yake bida saboda sanin kyawawan hayanki da nagar tarki.
Kujera ta jawo ta zauna ni kake nufi zaka Aura kare masa kallo takeyi daga sama har kasa to ngd da kauna Allah yasa ka da Alkhairi zaku Iya tashi sawunku a likkafa kufita Idan kuma kanaso na maimaita abunda naima abaya to kaci gaba da zama,makwat megari ya hadiye wani mugun yawu tuno tsiyar da Jalilah ta shuka mai.
🤣🤣🤣Akwai wani lokaci da Jalila tai lefi cak aka dauketa har gaban megari sai muzurai yake yana zare idanu,ke kina wasa da maganar muko zuwanki na 10 kenan gabana yau da kaina zan hukuntaki lawwali asamin ita adaki angama ranka ya dade daukarta aka sakeyi har dakin horo inda ake kai masu lefi a tsulale su.
Tashi yayi tsam daga wajan zaman sa saidaya tanadi zukekiyar dorinar sa ta dukan Jalila,tana rike da kugu ya daga bulalar ya zabga mata kirmi sisi tai kamar bataji dukan ba karka sake dukana ina ganin mutuncin ka sake daga bulalar yayi fit tashige babbbar rigarsa gasa mata mintsini ya kushi babu abunda bata yi masa jin azaba ta ishishe ya murde mata kunne jin yana barazanar tsige mata kunne caraf ta damke wandon megari.
Duk wasu ma'adar sirri dake kai kawo ajinkinsa saidata dena aiki tsabar Mugunta irin ta Jalila murdeta take kokarinyi tuni megari ya hada Uban gumi kiyi hakuri nagama ki da Allah ki kyaleni wannan itace rayuwa ta kimin rai wllh bazan sake shiga harkar kiba.
Katabbata kwarai kuwa sakar masa wandon tai har tuntube yakeyi wajan fita daga dakin yanayiwa Allah godiya daya rabashi daga ta addancin Jalilah.🤣🤣🤣katuna ko kwafa tai tashi kufita tashi yayi kamar kazar sa kwai ya fashewa aciki.
Fashewa tai tai da wata muguwar Dariya buga cinya tai saini Jalila me makaman yaki.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 44
Kowa mamaki yake yadda megari ya tashi ya fita salin alin sabida sannin halayyar sa matukar yace yana sanki to ko zaki mutu saiya Aure ki ta karfin tsiya kuma dole ki zauna babu yadda zakiyi daya gano wata zai sakeki ya aurota.Ajiyar zuciya suka sauke ganin yafice shida ta wagar sa kallon ta sukai da tunanin dariyar me take tabbas akwai abundata kulla.
Wai dariyar me kike haka babu komai Inna kawai na tuno da wani abune amma kinsan bazamu taba yadda ba babu ta yadda za'ai megari ya tashi ya futa daga gidan nan salin alin dole da wata akasa,tabe baki gwaggo tai kinga barta tunda Allah dai ya tsallakar damu daga sharrin sa ai shikenan.
Kai Allah y kiyaye mu da mugunji da mugun gani amen gwaggo sakin hirar sukai suka fada wata,sosai Jalila taji dadin zuwa kauye duk da tayi missing din abubuwa da dama amma yanayin garin yayi mata dadi sosai.Inna ta hada mata tsarabar su kuku kubewa daddawa zobo duk takaiwa Ammah haka gwaggo ma ba'abarta abaya ba ta hado tata tsarabar kaya rigijif suka hada mata sosai sukai mata nasiha da fada tayi abunda ya kaita.
Gidan su yanxu Alhmdlh ba rashin ci ba rashin sha komai saidai ma sha Allah suna cinna kansu daidai gwargwado.
Tun sassafe Indo ta doka Sallama motar safe take so subi bata so suyi rarnar tafiya tsaf Jalila ashirye take dama rungume su tai gaba dayan su kewar suce ta mamayeta fashewa tai da kukan rabuwa dasu kamar karta barsu haka take ji inna ma goge hawayan ta takeyi saboda kewar yar tata tana matukar son Jalila,dakyar suka rabu suna dagawa juna hannu tasha sabuwar atamfarta riga da zani wanda Innah ta dinka mata kala uku masu kyau.
Wannan karon babu dage dagen hannu da yiwa yan kauye bye bye anutse suke tafiya kamar ba Jalila samarin da suka nuna suna sannta sai cizon yatsa suke ganin zata koma basu samu shiga ba.
Kai tsaye tasha suka nufa basu wani jima ba Motar su tatashi saidai fatan sauka Lafiya.Lissafi yake tundaga Kwana daya har kwana ki bakwai ayau da zata dawo wani madaukakin Farin ciki yakeji yarasa meyasa ya damu da ita meyasa ma zai dunga tunanin ta ya wahala ba kadan ba tashin jinta surutunta duk yayi missing din su.
Jamal kansa yasan ya sauya tambayar duniyar nan yace masa babu komai baya jin dadine kawai dan dole yagaji ya kyalesa sake juyi yayi abed din karo na barkatai ko sun taho ko basu taho ba bashi da tabbaci murmushi yadan saki me kayatarwa tare da lumshe idanun sa.
Karfe 10:30 suka shugo gidan Ammah tundaga bakin get take gaggaisawa dasu baba direba yanxu sun saba sosai sai sannu da zuwa sukeyi mata,tundaga kofar parlour take zabgawa Ammah kira Mom ce agaba su rufaida abayanta,to! mayya saida kika dawo mutum kamar gidan tsohon sa bashi da ko gashi agidan amma saikin kara dawowa.
Salima ce tasaka dariya kokuwa yaushe za'a iya zama gidan inna da baba baki ya saba da dandanar Abin Arziki ku baku ga harta rame tayi duhu sai Yanzu na lura salima bakiyi karya ba anje anbigi mugun boss acan,mene kuma mugun boss dariya suka saka gaba dayan su af tuwo mana shi nake nufi,magana take sonyi Indo ta toshe mata baki muje karkice komai tamace wllh daga ke har ita zamu hada miyi muku shegen duka.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 45
Karki sake kikara sakoni cikin Jalhilcin ku aini bazan iya hada kashi da nakuba wllh innai hakan aimun zama daya kuma ajina yama zube karnuka suke haushi ako wane lokaci kuci gaba dayi dama in mutum yarasa aikinyi ai babu Abinda bazaiyi ba kuci gaba da haushi kunji.
Hannun Jalilah taja wadda bacin ran hanata magana ya tsaye mata amakoshi sai cizon yatsa takeyi amma in kere na yawo zabo na yawo watarana za'ahadu.Yana ganku kunyi cirko cirko aidole kigammu ahaka Ammah ashe har kiwon karnuka kuke agidan kullum kuna basu abinci suna kara habaka kaifin haushin su na sake tasiri,
Barin dasu Mom suke ta kalla sai huci suke kamar zasu babbake in basiwa Indo da Jalilah duka ba yau suba yan halak bane kai har Ammah yau saita gane kuranta dama haushinta suke ji yanzu zasu huce haushin su.
Rigar Indo Mom ta jawo tabaya ke awa har kun isa kishigo gidana kicemin jahila kaskantacciya yar aiki dake kinyi kadan wllh yanzu zamiyi miki tsinannan duka muga wanda zai tsaya miki,wai Saratu meyasa bakwa kaunar zaman lafiya mesukai muku daga zuwan su aidama haka zakice munafuka algunguma.
Duka takawowa Indo Ammah ta shiga tsakiya wata bangaza akaiwa Ammah saura kadan ta fadi saurin tarota Indo tai,saukewa Mom maruka tai har guda biyu kut Mom din kika mara kokawace ta harde Ammah ce merabo atsakiya Jalila ma ba'abarta abaya ba gashin Salima ta cafka duka take kawo mata amma taki sakinta azaba ta isheta.
Abinka da jikin kauye tuni indo ta zage taiwa Mom tsinannan duka sai numfarfashi datake ja na tsananin wahala zagi ko ta uwa ta uba takewa Indo ashe ke yar iskar karya ce kinsan bazaki iyaba kika takali fadan ni Aisha bana daukar wargi gobema kisake babbar banza kawai.
Jan hannunta Ammah tai dan Allah kubari kuzo muhau sama ni bazan iya wannan masifa ba,harara Mom ta gallawa Ammah wllh Rukayya ki tabbatar bashi kikaci dake da yan iskan dake daure miki kugu aizata tafi kuma tare za abarmu,ke kuma shegiya mekama da aljanu kema zaki shigo komata bani da kyau wllh.
Wooo andai ji jiki wllh Anty Indo kinmin daidai da kikaci uwar mara kunya nasoma kin dirje mata baki da kasa muga ta iskan ci,kwafa Salima tai inbanda radadi babu abunda kanta keyi itakadai tasan abunda ta tanadawar sa Jalila ko bajima ko badade zasu gauraya saita bata mamaki saita wullata agararin da bata taba tunani ba kowa dai da alwashin da yakeci azuciyar sa tsakanin Mom Rufaida da Salima ko alwashin me suka dauka oho.
Nan suka barsu suka hau sama dakin Jalilah suka shiga kowa yana maida Numfashi,kai Ammah wllh kina kokari ni wannan in kishiya tace aida yanzu mundade da kone gidannan,uhm indo kenan to mene Amfanin tashin hankali bashi da dadi ko kadan komai me wuce wane innai duba da wataran sai labari saina maida komai ba komai ba.
Lallai Allah ya kara miki hakuri Ameen.Oh Jalila lallai kauye ya karbe ki ai Ammah bawata karbata da yayi amma naji dadin zuwa sosai duka takawo mata da kuma inata fama dake akan kije kina kin zuwa harda su kuka,ai nadaina kukan yanzu kimaci gaba.
Inna tace tana gaisheki ga tsarabar ki karba tayi tana budewa Murmushi ta saki kai ma sha Allah aiko Nagode wllh Allah ya saka da Alkhairi,kai Ammah wannan din kikeyiwa godiya aida bazan kawo miki bama nazata bazaki karba ba niko mezai hanani karba Jalila aini ina son naga ankawo mun irin wadannan kayayyakin kice kince muci tuwo da hujja.
Nidai Ammah bazan ciba yako zame miki dole naje kauye naci tuwo ina murna zan dawo nan ma ace tuwo za ai Dan Allah Ammah ki canza shawara,Cikin dariya take fadin aidama bada wani nai shawara ba balle nacanza,kai gaskiya Ammah kina da kokari tambaya daga wannan sai wannan ba kwama babu fulsutof ai haka take harna ma saba da batanan bakiga yadda naji ba dadi ba na saba da bari Jalila tashi kiyi wanka bar tsalle tsalle data tafi bakina har tsami yake to ya saba da magana kwana biyu kuma ba'ai dashi ba.
Dariya suka saka gaba dayan su Ammah ina dan India aiko ko minti 10 beyi da fita ba kuka shigo kiran gaggawa akai masa daga asibiti,yana ta shirye shiryen tafiya shida Jamal,ina zasuje Ammah America zasu karo wani course da basu kara saba nima zan bishi Ammah kibishi inah aikema makaranta zaki tafi kinga duk bakwa gida nikadai zaku bari.
Ba saina fasa zuwa makarantar ba kibari inya dawo saiki gaya masa to Ammah,Indo tadan jima kafin tai musu sallama tatafi wannan karon harbakin get Jalila ta rakata tunda yanzu ta shaida ba mayar da ita kauye za'ai ba harta juyo zata dawo aka danna Hon tsayawa tai dan taga wanene zai shigo Jalal ne tundaga nesa ya hango ta saiyaga ta kara girma kamar ba ita ba yar kauye andawo kenan.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 46
Washe hakora take tana kallon sa ahankali ya tako har gabanta kare mata kallo yake yar kauye yaushe kika dawo canake ammiki Aure acan,bata fuskatai fatan da kakemin kenan aini bayanzu za'aimin Aure ba amma kaga su talatuwa kawaye na duk ammu su Aure.
Kema kina kan hanya kizuba idanu kigani muna zaune zamuji ana guda andaurawa Jalilah Aure Dariya ta kyalkyale da ita kuma kasan meyafaru danaje kauye,aah saikin fada inazan sani kina katsina ina daura.Hmm,kafa yadda samari suka dinga layi akofar gidammu wai suna suna harfa dame gari Dariya ce ta kwacewa Jalal kice kinyi kasuwa to yanzu ansa rana dame garin ko kinga babu ke ba zuwa makaranta.
Wane megarin ka ganshi kuwa yafi baba megadi tsufa fa gaskiya kinyi babban kamu Jalila ashe haka kike da farin jini muma nan gaba kadan za'afara dambe akofar gidannan,fari tai da idanu dagaske kake dan India mataba yimiki karya ne a'ah ni dai kadaiba min zan can Aure ni karama ce,amma kike cewa da wasu samudawa kema saikin zama kamar su kenan.
Lah wanene ya fada maka wannan sunan ai zancan duniya baya buya agari naji gidammu akwa samudawa guzumaye dariya tasa to ai ba karya nayi ba kasan kaima hakane ah ni babu ruwana karkisa suji su taru siyi min duka in kuma zaki shigar min to,mezai hana ban shigar maba ai bazan taba yadda su dake kaba uhm naga alama,hakanan yakejin Nishadi aduk lokacin da ya biye mata suna shirman tare.
Har parlon sa ta rakashi ina tsara bata kaima da zanta fi mekaban kin manta kenan alawarma daka bani yar micililiya ko makogwaro na bata jeba aiko kinyiwa kanki zaki sake zuwa gida ne babu abinda zan baki,yi hakuri dan India kai bakasan wasa bane ni wasa nake ma bara naje nakawo ma goruba ce da taura.Rike kayanki bantaba ciba bazan kuma taba ciba wannan ai wahalar da rayuwa ne shikenan takara auki dama wllh addu'a nakeyi karka karba murmushi yayi to addu'ar ki ta karbu lallai ke yar baiwa ce sosai ma.
Yawwa Ammah tace zakui tafiya kaida wannan abokinna ka zaka tafi dani,aike batafi dake wannan kasar tsaf zan iya kare rayuwata adaure dan bansan aika aikar dazakije kiyi ba,kamar wata bera wai meyasa kake cewa ina da fitina nidai nasan banda ita.Nan gaba Ammah tace zan zama yan mata in zama yar gayu babu wanda zai rainani hakan nake fata ai amma haryanzu da sauranki baki zama big girl ba mene haka kuma babbar yarinya mana aiko yanxu nagirma,baki da girma zaina jikinki amma hankali dai da sauki.
Kije Nagode zanne miki anjima tun ana abu na marmari saikinsa mutum ya kosa da magana fita tai tana kunkuni Jalal yace mata mesurutu,bin bayanta yayi da kallo Girgiza kansa kawai yayi mikewa yayi ya shiga bedroom dinsa.
Tafiya makarantar Jalila babu abunda ba agama ba gobe ne tafiyar Ammah da kanta ta wanke mata kai har wannan lokaci Jalila bata daina kukan kitsoba sosai gashinta yayi yawa tana kuka da burburwa aka gama kitson saida Jalal ya dauko belt ya zuga mata daya tukunna ta daina tirje tirjan da takeyi tana ji tana gani akai mata kitson.
Dungure ta Ammah tai kedai wllh kinji kunya Jalila bansan randa zaki hankali ba kina girma kina kara tabar barewa Allah ya shiryeki,haka zakije makarantar kina kazanta bazasu kyaleki ba dakan gumba zasiyi miki sai kindawo cikin nutsuwar ki,kala batace ba sai kukanta take hankali kwance kamar kara zugata akeyi.
Ke!!! yiwa mutane shiru karna tattakaki wllh me akai miki zaki kamayiwa mutane kuka tsit tai dan in Jalal ya hade rai kokai babba kwarjini yake maka.Tashi kazama kije ki wanke fuskarki tashi tai da sauri ta shige dakinta Ammah binta tai da kallo tana ayyana abubuwa da dama a zuciyar ta nufashi tadan sauke.
Karfe Nawa zaka kaita karfe 7 zamu fita kinsan jirgin karfe 2 zamubi dole naje nakaita da wuri to Allah ya nuna mana amma ina tunanin tafiya kubarni nikadai bazanji dadi ba sam,ga iya aidama da ita kika saba zama ada ba aini yanzu jinake duk randa Jalila zata koma garin su bansan yadda zanyi da rayuwata ba wllh haka kawai nake sonta kodan sunan ku kusan daya ne.
Dariya ya saka kin yadda da zancan Jalila datace sunan mu iri dayane yarinyar nan tacini wasa.eh aida gaskiyar ta dayanne ma,wata hirar suka fada cikin kauna irin ta da da Mahaifi.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 47
Tsaf Ammah ta hada mata akwatinta katifarta irin ta yan bording duk ansiya mata kayan tea babu Abunda Jalal be yi mata ba sai murna take ashema dadi zatadinga ci acan sai lokacin hankalinta ya kwanta.
Dad shima ya kawo tasa gudun mawar har bakin mota Ammah ta rakata kamar zatai kuka take kallon Jalila dan ALLAH Jalila in kinje ki kame kanki banda kawayen banza banda rashin kunya banda tsokana kigirmama malamanki kar asaki wani aiki kikiyi kina jina eh Ammah.
Allah ya yimiki Albarka kullum kidinga tunawa da abunda nake gaya miki to jitai itama jikinta yayi sanyi sai yaushe zan dawo Ammah sai kunyi hutu zamu dinga zuwa duk lokacin visiting mudinga ganinki maza kishiga kutafi.Shiga tai ta zauna tana dagawa Iya da Ammah hannu suna daga mata.
Mom da Rufaida dadi kamar ya kashe su atunanin su an sallameta ne daga aiki shiyasa za'a kaita tasha asata amota yanzu zasu sakata su wala suyi abunda suke so babu me samusu idanu balle ya hana su rawar gaban hantsi.
Saida suka fice daga harabar gidan su Amma suka koma,oh har amincin ya kare an tattarata an watsata kauye,banda abinki Mom dama tafiya ai azaune take tunda babu abunda ya hada aikatau ya kawo ta abunda tazo nema kenan dama dan kayan daki to gashinan anhada mata, dariya suka sheke da ita cas zamuje biki koba agayya cemu ba zamuyi kara.
Banza Ammah tayi musu kamar batasan da su awajan ba tai wucewar ta haka Iya dakinta tawuce cikin kewar Jalilah ita kanta tasan zai kewar Jalilah sosai tunda tazo gidan ta samu Nishadi da walwala to gashi tatafi sai wadannan marasa mutuncin da zasu sakota agaba da wulakanci kala kala.
Tafiyar awa daya da rabi sukai suka karaso makaran tar AMINA ROYAL Primary and Secondary school shine arbuce asaman Makarantar shiru kamar babu kowa acikin makarantar wangale masa get din akai ya danna hancin motar sa,babbar makaranta ce sosai iya ganin ka bangaren primary da ban secondary daban da alama daliban suna dakin kwanan su ko sun shiga class.
Jalila ya kalla datake ta kalle kalle tunanin ta to wannan jejen ina mutanan cikin sa ko kwaro bata hangaba sai masu gadi da suke zazzaune akan benci suna muzurai,saida yayi tafiya menisa sannan suka shigo cikin makarantar anan tafara ganin malamai suna kaikawo babu dalibi ko daya wayar sa ya dauka ya kira Anty Binta maganar minti biyu sukai ya ajiye wayar fito.
Ahankali ta sakko tana sake karewa makarantar kallo babu laifi tayi mata kyau harta ayyana Irin wasan da zata dingayi awajan shukokin wajan ta kalla masu abun sha'awa Shar shar.
Da fara'a ta fito sannun ku da zuwa dan Murmusawa yayi yawwa babbar macece akalla ta haura 40years muje ko gaba tai suka bita abaya.
Kai tsaye office dinta ta wuce bimillah ku zauna zama sukai yammata kece Jalila gyada kai tayi shekarunta nawa kallonta yayi yana kissima adadin shekarunta 14yers glass din fuskarta ta gyara gaskiya shekarunta sun haura ace primary za asakata da ace Namiji ce za aiya barinta ahakan amma tunda macece bata da wani dogon Lokaci.
Yanzu ya za'ai kenan numfashi ta sauke zanyi duk me yiwuwa akaita js 1 nikuma zan dage wajan koyadda ita har kwakwalwarta ta bude zanyi kokarin hakan,ok thanks ina uniform dinta kash kuma na tuna na primary aka dinka mata amma Akwai din kakku anan za abata ok abata kala uku shikenan ba damuwa taso muje.
Hannun Jalila tarike sai zare idanu take kamar mazarin tsire tasowa yayi ya biyo bayan su kajiramu anan tsayawa yayi gaban motar sa ya jingina yana bin su da kallo wani get daban ta nufa Jalila na rike ahannun ta sai waigen Jalal take kamar zatai kuka,kwankwasa get din tai tunda suka leko sukaga itace suka bude mata kofa da girmamawa suke gaisheta fuskarta dauke da fara'a take amsawa dayi musu sannu da aiki.
Wani class ta nufa akalla daliban ciki sunkai su 50 dukan su yammata ne manya Saudat Aliyu wata Budurwa ce tata so daganinta akwai hankali a tattare da ita naam maa yawwa Sauda ga kanwa na kawo miki kikula da ita kamar yadda zaki kula da kanwarki banason kowa ya takura mata kijawa yan class dinku kunne karnaji karna gani,za akiyaye ki muje kitayata kwaso kayanta.
Juyawa sukai Sauda tabisu abaya har bakin motar sukaje dan satar kallon Jalal tai wow cute face Jalila ta kallah sam basa kama kodai ba yayanta bane dauki mana Sauda kayan ta fara dauka Jalila na taya ta tas suka gama kwashe wa.
kwal kwal tai da ido tuni hawaye suka fara zarya a face dinta da gaske zatai kewar Jalal kai itafa tama fasa makarantar nan kuka ta fashe dashi.
Harya juya zai shiga mota da gudu ta rugo tabaya ta rungume shi nidai nafasa makarantar mukoma Gida kaji,saidaya daidaita face dinsa juyowa yayi yana kallon ta kukan fa banason kuka nima ina komawa Gida zan tafi makaranta so kema kitsaya kiyi karatun ki bana son wasa da zarar nadawo zanzo na dauke ki.
Hanky ya dauko ya goge mata hawayan face dinta oya maxa je kutafi zan siyo miki tsaraba in zan dawo ko bakya so,ina so, tom ayi karatu da yawa hannu ya daga mata alamar byee itama daga mai hannu tai.
Tanaji tana gani ya juya itama juyawa tai suka koma ita da Sauda.
......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 48
Har daki taraka ta gadaje hudune acikin dakin babu matsi babu takura kowa da jakarta akusa da gadonta sai lokar kayan Abincin ta wanda yake daga bakin taga shine babu kowa akai su uku ne acikin dakin,itace cikon ta hidun su akwatinta ta ajemata awajan sai lokar ta zuba mata kayan abincin ta,key din ta mika mata gashinan in kika yar babu ke babu cin abinci kikula dashi yadda ya kamata to ta amsa.
Ki zauna yanzu ankusa tashi in za'ai karatun Islamiyya saiki je kema ni zan koma class duk abinda kike so kine meni ina fatan kingane eh futa tai daga dakin tabar Jalilah tsuru azaune zafi harya fara damunta babu AC 🤣🤣lallai Jalila zakiyi medalilin.
Kusan zaman awa daya tayi kafin taga ana ta bullowa tawata hanya kamar kiyasai dan danan taga yammata da sa'anninta sun cika Makarantar ashe da akwai mutane da yawa ta ayyana hakan,su ukune kusan kansu daya dakin suka nufo suna tafiya suna hira gwanin ban sha'awa,wata Budurwa taga tasha gabansu babu wani bayani ta daga hannu takashe Fuskar daya daga cikin su da wani shegen mari saidata durkushe akan guiwowinta kafin ta saki wani marayan kuka.
Kyakykyawa ce Yarinyar dagani hutu da jindadi sun samu wajan zama ajikinta dafe kunci Jalila tai kan uba wace shegiyar ce wannan bala'i inni tamara aiyau saidai buzunta.
Dan uwarki harkin isa nasaki aiki kikiyi wai baki da lafiya Allah yasa suma kikeyi wllh daga yau wannan shine magana takarshe da zammiki bama keba duk wani mara kunya amakarantar nan zan gyara masa zama kuma anjima kifito kiyi noma tunda baki da mutunci kin shigo komata kenan sannan ruwan wankana na tsahon sati daya duk inda zakije kinemo ruwa nasameki a kokar toilet kina jirana inkunne yaji gangar jiki ta tsira.
Hankadeta tayi tai gaba kawayan nata ne suka sunkuya suka dago ta abunka da farar fata tuni fuskarta tai jajajir hawaye kawai ke shatata a kuncinta hannunta suka kamo basu ce komaiba face din su abace take dan babu yadda zasiyi ne dasai sun rama mata,dakin da Jalila take ciki suka shiga gaba daya basu lura da ita ba suna ta aikin rarrashi.
Dan Allah kiyi shiru Nasmah kibarta da Allah,yanzu Ablah menai mata ko zalinci ne kawai zata daken bansan me naiwa yan schl dinnan ba suka tsaneni haka kodan sunga bana ramawa nayi dana sanin zuwa Makarantar nan zance da Dadyna acire ni nakoma day,cikin zafin rai dayar dabatai magana tafara fadin itadin banza acikin kayan miya wane gwalagwajin ce da harzata hanamu sukuni babu inda zakije muna tare wllh.
Ismah bazaki taba ganewa ba ninasan zafin da nakeji acikin Zuciyata babu wanda yake dukana agidammu kowa sona yake da tattalina bazan zauna wata zindi kiya tadinga dukana ba.
Jalilah datai tsuru tana kallon su dan motsin datai ne ya sasu juyowa cikin mamaki suke kallonta sam basu san da za manta adakin ba.
Wow new student suka hada baki wajan fada tasowa sukai gaba dayan su suka zagaye Jalila datake binsu da kallo Nasmah ce ta miko mata hannu My Name is Nasmah Aliyu Sadauki,mika mata nata hannun tayi Jalilah Muhammad Uba dan sosai Jalil yai zaman koya mata full name dinta dukan su mika mata hannu sukai babu nuna kyama agare ta hakan yayi matukar yi mata dadi.
Fatan zamu zama kawayan juna murmushi ta sakar musu gyada musu kai kawai tayi,ko bakya magana um inayi mana ban saba daku bane aiko zaki saba damu yan ukune amma yanzu mun dawo yan hudu dariya sukai gaba dayan su sabanin Nasmah data dan mirmusa da alamun magana be wani dameta ba.
Nasmah take kallo da harlokacin fuskarta bata dawo daidai ba mekikai mata ta mare ki idanunta ne suka ciko da hawaye girgiza kai tayi alamar ba komai amma dai wllh muguwa ce kekuma zaman me kike dabaki rama ba,waro idanu sukai gaba daya akanta tarama fa kikace yau inta daki Anty Hauwa sai ankusa tsireta a tsakiyar Makarantar nan bakiga yadda malamai ke sonta ba saboda me saboda tana da kokari.
Mtswww ni ina ruwana wllh duk ranar data maran saina daga hannu na sama zan wanka mata mari dariya suka saka ammafa kina da cika baki Jalilah um kuna wasa dani ko kuzuba idanu duk zan kwato muku yan cinku sai andawo ana duka mana ahanya ana take mana baya,dariya suke sosai ko yanzu Jalila ta sasu farin ciki.
Ablah ce ta rungumeta munji dadin haduwa dake sister,hannu Nasmah ta miko alkawari dora hannayan su sukai akan nata munyi alkawari zamu zama kawaye na amana kawayan juna masu temakon juna bazamu taba juyawa juna baya ba zamu tsaya tsayin daka domin temakon junan mu, Jalilah dai kallon su take bazata iya jera wannan maganar ba suna sakin hannu taga sunnufi lokar abuncin su.
Roba kowa waccan su ta dauko kema kidauko taki ina zamuje abincin rana zamu karbo abincin da nazo dashi fa ai zamuci amma saimun karbo na namakaran ta inba haka ba kafin azo mana visiting mun tagayyara a school dinnan tab kamar wata almajira kuje ni ina nan ai yayana yace za akawon inya kare ba yadda basi da Jalilah ba taki haka suka tafi suka kyaleta zata dawo kan hanya ne.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 49
Har sukaje suka dawo tana zaune,kallon Abincin hannun su tai wani dan mitsitsi bamai ba kayan miyar arziki sai nama yanka biyu.
Ku yanzu wannan abincin koni aka hadewa shi ai saina cinye batare dana koshi ba,baki bude suke kallon ta wannan abincin zaki iya hadawa ki cinye tas ma kuwa wllh to mukuwa indai kincinye abincinnan zamu baki lambar yabo hade mata abincin sukai waje daya saukowa Jalila tai daga gadonta.
Dirshan ta zauna kankace me ta lakume abinci tsuru sukai suna kallonta anya Jalila ke mutum ce kuwa me kuka gani aini wllh inba wukar yanka nagani ba bazan iya cin rabin abincinnan ba to sai gashi ni babu abunda nagani kuma na cinya.
Amma kina da aljanu Dariya tasa nini kadaice aini aljanu ma basu isa sun rabo inda nake ba saboda masifata ku nifa bana barin ta kwana balle tai tsami.
Uhm kina wasa da bording kiyi Addu'a kawai Allah ya rabaki da mugayan makarantar nan dan wllh daukar Amarya za'a zo ayi miki kinaji kina gani za'ai miki shegen duka babu kuma yadda zakiyi,ai matukar wata shegiya ta daken amakaran tar nan ranar zataga tashin hankalin da tunda gyatumarta ta haifota bata taba gani ba wllh,to mudai duk randa kikayo tsokana bamu da karfin tare miki.
Harara ta galla musu mari ma kun kasa ramawa aidama ni bana son kowa yashigar min fada ni zan tare muku amma guguwar da zan tsokano bazaku iya tare taba saini dakai na zan tare kayata, gaskiya ina so naga wane irin kwarin guiwa kike dashi ko waje fa baki fitaba tunda kikazo kifita waje kiga manyan yammata wadanda zasu goyaki suzagaye schl dinnan basusan kina bayan suba,aini nasaba fada da irin su dama agidammu akwai samudawa kunga karo da wa 'yannan bazai min wahala ba dariya suka sa.
Kwarin guiwarki ya bala'in birgeni zamiyi tafiya tare Ablah ta miko mata hannu suka tafa dan daman tafi Nasmah da Ismah zafi da rawar kai jiki magayi cewar Nasmah kudai ku zuba ido kusha kallo dama namu idone inji Ismah,hirar su suka ci gaba dayi Lokacin Islamiyya nayi suka shirya kowacce tasa uniform dinta na Islamiyya blue din riga da wando sai fararan hijabai har guiwa muje.
Suna tafe Jalila tana ta kalle kalle kowacce zaka ganta da Alkur'anin ta ahannu da sauran litattafan da ake musu kai tsaye class din su suka nufa har amfara taruwa suna shiga akayo musu caaaa da idanu ganin su da sabuwar daliba,duk shan kunu sukai dan yaran badai jan aji ba tsaki Ablah tai nifa natsani kallo wllh kunyo mana har da idanu to li'ilafi kuraishin.
Babu wanda ya tanka mata dan sun san masifar Ablah su Nasmah basu ce komai ba waje suka samu suka zauna muraji'a suka farayi Jalila dai tayi zugudi iyakacin izu biyu ta iya,agida sai allonta ya fita daga hayyacinsa take wankewa asakeyi mata wani rubutun gaba daya tasa wasa a dukkan al-amuran ta akallah sun wuce ta da kusan izu goma sha uku tirkashi.
Gadai Alkur'anin a hannunta amma ta bude wajan da suke biyawa ma bata sani ba, Nasmah ce ta dubeta kibude mana Jalila Malama zai miki bulala inyazo yaga bakya karatu,zumbura baki tai ke nifa bantaba jin wajannan da kuke biyawa ba kallonta ta sakeyi sosai kamarya baki taba jiba kamar yadda kika ji,kina nufin mun wuceki akaratu eh to aiba damuwa zamu dinga koya miki to kawai tace karba tai ta bude mata inda ake biyawa haka ta kurawa rubutun ido saitaji babu dadi dama ace itama ta iya gwanin birgewa take kallon yan ajin sun hada baki sai raira karatu sukeyi gwanin sha'awa.
Kari Malam yayi gobe kuma za'a kawo masa hadda sai karfe 5:30 suka fito daga class din dakin kwanan su suka nufa,tundaga nesa ta hango yaya Hauwa ras gabanta ya fadi tuno abunda ta gaya mata dazu tuni idanunta suka ciko da hawaye agaban su taja tinga ta tsaya ke mena gaya miki dazu,yanzu zanje na debo makaranta mukaje Allah yasa dawafi kikaje wannan bedaman ba nabaki mintuna biyar na ganki da ruwan wankana,kallon su tayi daya bayan daya kowacce kanta asunkuye amma Jalila kir take kallon ta.
Ke ni sa'ar wasan kice dazaki tsaya kizuba min idanu kina kallon cikin idanuna ko kala batace ba still bata daina kallon nata ba,Jalila mekikeyi anan juyawa sukai suna kallon Sauda da zuwan ta kenan ga wadda ta tsayar damu nan.
Hauwa me sukai miki kika tare su ahanya shiru tai dan ba karamin shakkar Sauda takeji ba kutafi daki gaba sukai suna sauke ajiyar zuciya gaba tai tabar Hauwa da dacin zuciya kwafatai tarasa meyasa Sauda take shigar mata hanci da kudun dune.
Ita kadai tasan wacece ita amakarantar nan sirrinta atafin hannunta yake shiyasa bataso wata doguwar hira ta hada su gudun tonuwar asirinta kwafa tai yan kanzaginta suka take mata baya kana kallon idanun su kasan ba kananan fitsararru bane idanun su asoye yake da tantiranci da rashin kunya.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 50
Kowa Zuciya ba dadi suka koma daki,Jalilah ce ta dube ta kuma ke yanzu Nasmah ruwan zakije ki debo mata? gyada kai tayi tsabar takaici ma ta kasa magana tabe baki Jalilah tai to saikije kitayi kidinga yiwa wata banza bauta wllh dani tasa dataga yadda ake iya iskanci da daga yau bazata sake sa kowa yade bomata ruwan wanka ba.
Yanzumma bazan kyaleta ba zamu gauraya wataran,shiru sukai dan aganin su Jalilah cika baki kawai takeyi suma sun sha wannan alwashin abaya kafin su zubda makaman yakin su.
Uniform suka cire tare suka sake fita Ismah ce ta rike boket din,duk inda sukaje uban layine wanda kafin azo kansu magariba zata iya yi yammata ne kala kala manya da madai daita wasu da riga da zani wasu sket kai watama daga ita sai daurin kirji warkajamin su suke kamar agida suke ammafa inkema jan wuya ce inko baki kaiba saidai ki koma gefe.
Sun zagaye kaf makarantar basu samu ruwa ba tuni Nasmah tafara kuka kashirfan dan Allah kadai yasan irin dukan da yaya Hauwa zatai mata,kowaccen su face dinta dauke da damuwa suke rarrashin ta,wai babu rafi acikin makarantar nan akwai mana amma wa zaiyi wanka da ruwan rafi kinji sanyin sa kuwa.
Tabe baki Jalilah tai to ina ruwan mu da sanyin sa mudai ba mukai mata ruwa ba ita tasani kuzo muje,tsayawa sukai babu fa wanda yake zuwa wajan kuma ga nisa ni kubani sai naje mene abunni sa,bayadda zasiyi haka suka bita.
Dan danan sukaje wajan nanne me nisa kuban nashiga na debo mika mata sukai babu tsoro ba komai tashiga ruwan saidata cika shi taf da ruwa sannan ta fito ji take ma kamar tai wanka aciki,kallonta kawai suke koda kudi baza su iya shiga wannan ruwan ba muje bayan ta dora bokitin aka.
Har kofar toilet ta kaishi sannan ta sauke ko minti biyu ba'aiba yaya Hauwa tataho sai hura hanci take yi masu tsoronta tuni suka sunkuyar dakai.
Ruwan ta kalla fari tas tas dashi harara ta wurga musu Allah ya temakeki da kika kawo akan lokacin dana kayyade miki dana zo naijiranki awajan nan saidai buzunki ku ware ni kubani waje,da sauri suka bar wajan amma banda Jalilah data tsaya rike da kugu.
Nan fa hankalin daliban yayi kansu ke da kika tsayamin aka uwar me kike jira bokitimmu zaki bamu tunda badaga gidan tsohuwa kikazo dashiba,dif wuta ta dauke wa hauwa tana maimaita kalaman Jalilah idanun ta kamar zasu fado take nuna kanta jikinta har tsuma yake ni ni kike gayawa haka.
Jujjuyawa Jalilah tai au da dawa nake ko akwai wasu awajannan kedin din dai dake nake koki juye ko wllh na barar dashi akasa kowa ma yara sa,tuni wajan ya kaure da hayaniya masujin haushin Hauwa sai hamdala suke da Allah ya kawo merama musu,da masu ALLAH ya kara azuci saboda tsoron furtawa azo asamu matsala.
Daga hannu tai zata kashe fuskar Jalilah da mari caraf ta rike hannun karki fara wllh marin fuskar nan daidai yake da tsokanowa kanki bala'in duniya wanda bazaki iya tare shiba,yarfe hannun Hauwa tai tuni aka dauki sowa da tafi saiga Hauwa tayi tsamo tsamo kamar wadda aka tsoma aruwan zafi.
Akaf Rayuwar datai a makarantar babu wanda yataba daga mata murya balle hartace zata mareshi ya rike mata hannu ita Hauwa ta samu wadda zata kalu balance ta inah hakan bazai taba faruwa ba har abadah.
Hankadar da ruwan Jalilah tai kif kuwa ya sheke akasa daukar bokitin tai tai gaba,su Ablah kansu abun ya girgiza su ido bude suke kallon Jalilah mamaki ya hana su magana.
Har sukaje daki babu wadda ta iya magana acikin su sun zama kuraman karfi dayaji,banko kofar akai kamar za aballe musu kofar wata shirgegiyar matace ta shigo sai huci take tana hura hanci kare musu kallo take daya bayan daya tuni su Ismah sun dade da gurfana akasa jikin su na kakkar wa Jalilah kuwa ko motsawa batai daga inda take ba karewa matar kallo take da tunanin ita kuma wannan wacece.
Eh koda ban tambaya ba nasan kece kika aikata wannan mummunan lefin Hauwa dake gefanta tana huci gyada kai tayi kwarai ita ce,dan jim tayi na wani lokaci muje kamarya muje baki dauki mataki akanta ba,wani kallo matar ta wurgawa Hauwa kofa ta nuna mata dole tafita daga dakin zuciyar ta cike da sake saken meyasa takasa daukar mataki akanta kamar yadda ya saba.
Wani makirin murmushi ta saki tana karewa Jalilah kallo wanda ita kadai tasan ma'nar sa,juyawa tai tafi ta Jalilah tabita da kallo baki bude.
Numfashi suka dinga saki wanda ya tsaya amakoshin su sai yanxu suka samu damar fesar dashi.Kallon Jalilah suke kamar tibi wai wannan kallon na meye.
Ablah ce ta magantu dole mukalleki gaskiya ke yar baiwa ce tunda har Anty Zarifa ta kyaleki bata dauki mataki akanki ba.
Wacece ita Jalilah ta tambaye su.
To fans kubiyoni danjin wacece ita kamar yadda Jalilah take bukatar amsa haka nima nke bukata.
Kubiyo ni danjin yadda zata kaya.
Taku har Kullum.
Mrs Baba Bello ABUBAKAR
......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 51
Sake tambayar su tai akaro na Uku wacece ita?.
Nasmah ce ta bude baki da kyar wannan da kike ganin ta malama ce amakarantar nan ke hatta principal tana tsoron ta inta na sonki to zaki zauna lafiya a school dinnan matukar baki mata ba ko goya ta zaki dingayi kina yawo da ita abayanki bazata taba sonki ba,tana da magoya baya kama daga malamai zuwa dalibai matukar baki bita ba to zaki samu gagarumar matsala.
In kayiwa daya daga cikin wadanda takeji dasu amakarantar nan akwai wani dakin duhu da ake kai mutum saiyayi kwana biyu aciki bayan tayi masa dan banzan duka za'a watsoki waje kamar shara,shiyasa kowa shakkarta yake ji munyi matukar mamaki da kika taba yaya Hauwa yar gaban goshinta amma ta gaza daukar mataki akanki abun akwai daure kai.
Hakane Nasmah nima abun ya girgizani Anty Zarifa tashigo room dan kama me laifi tafita haka ban taba gani ba saiyau,tsaki Jalilah ta saki duk akan wannan ne kuke cewa ni yar baiwa ce kawai taga karo dani ba riba shiyasa sawunta alikafa tafita ni bana daukar wargi.
Kibar cika baki Jalilah bakisan wacece Anty Zarifa ba kedai tunda Allah ya tsallakar dake shikenan kiyiwa ALLAH Godiya,sai kuma kuyi banza tai musu tanaji suna ta maimaita maganar bata sake tanka musu ba dan bataga abin tada hankali ba.
Washe gari tun sassafe Anty Binta taturo aka tafi da Jalilah,da fara'a take kallon ta itama dan murmuwasa tai ina kwana lafiya lau Jalilah ya kwanan Makarantar lafiya lau,badai wata matsala ko babu to Alhmdlh leda ta miko mata ga uniform dinki yanzu kije kisa ka karki makara duk weekend zamu dinga karatu tare.To karba tayi ta fita daga office din.
Dif dif Zarifa tashigo office din ko kallonta Anty Binta batai ba ita tanemawa kanta mazauni,barka da safiya Binta dago kai Anty Binta tai tana karewa Zarifa kallo tarasa meyasa Zarifa ta rainata haka dannewa tai ta basar barkadai ,daga haka bata kara tofa mata ba, numfashi Zarifa ta sauke waccan yarinyar data fita menene alakarki da ita.
Tsam Anty Binta ta tsaya tana kallon ta meyasa kikai min wannan tambayar? saboda ina san kulawarta ta dawo karkashin iko na,uhm Anty Binta tadan murmusa baki da wannan hurumin kitsaya iya matsayin ki na malamar ta daga haka bana bukatar wata alaka tashiga tsakanin ku amana ce agareni,shiyasa nake so kibani naci gaba da kulawa da amanar kamar ahannuna zatafi samun kulawa irin wadda ta dace da ita gira ta dagawa Anty Binta datake binta da kallo.
Ita wannan Amanar tafi karfinki matukar kikaci gaba da bibiyar ta itace mabudin bankadar dukkan sirri kanki dan haka kitaka ahankali karki dauko abunda yafi karfinki,wannan yar shilar ba irin wanda kike lankwamewa bace ki zauna lafiya babban goro sai magogin karfe itadin kainuwa ce dashan Allah shawarar da zanbaki kihadiye kwadayin ki tayi miki nisa bazaki taba tadda ita bag,cikin bacinrai Anty Binta ta gama magana.
Cikin tsananin fusata Anty Zarifa take kallon ta binta kenan bakisan wacece Zarifa ba har ila yau banta ba neman abu narasa ba kisa aranki ni Zarifa matukar nacika sai wannan ajiyar ta dawo gareni ta zauna akar kashin umar nina da kulawa ta agaban idanun ki zan aikata abunda naga dama alkawari nane wannan.
Murmushi Anty Binta tasaki nikuma zan jira naga cikar alwashinki kamar yadda kikai alkawari nima nayi Alkawarin ni binta bazan taba bari kiyi nasara ba ke bama akanta ba akan kowa dake karkashin iko na bazan barki ba na kalu balance ki alkwarine sai kinfita daga makaran tar nan atsiya ce akaskan ce cikin nadamar da bazata yi miki amfani ba.
Hanyar kofa ta nuna mata bana bukatar masu halin dabbobi irin ki,wani mugun murmushi Zarifa ta saki tashitai ta fita batare da ta sake cemata komai ba.
Binta da kallo tai cike dajin tsanar Zarifa ta zame mata masifa acikin rayuwar ta itadin anno ba ce Allah kadai zaiyi musu maganin ta,sosai takejin tashin hankali akan furucinta tabbas zata aikata ko menene domin cikar burinta ya kamata tai wani abu akai lumshe idanun ta tayi cike da tsantsar damuwa.
Da murnarta ta karasa dakin su da kayanta ahannu sai washe baki take,inyee kema yau zaki fara zuwa class cewar Ablah wai Jalilah kodai baki taba zuwa schl bane irin wannan munna haka murmushi kawai tai bata ce komai ba shirya wa tai tsaf ash color ne kayan da farin hijab sosai sukayi mata kyau kowacce schl bag dinta ta goya suka fita su hudu rai ras abin birgewa duk kusan kansu daya.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 52
Duk inda suka wuce nuna Jalilah akeyi kunganta itace jan wuyan datai sa'insa da Yaya hauwa dayawa daga cikin su sunji tabirge su sun dade suna addu'ar Allah ya kawo wanda zai musu maganin iskancin ta da karfin izzarta dajin cewa ita watace aciki Makarantar.
Wajan zama suka samu daga gaba dama suke zama mutum bibbiyu ake zama Nasmah da Ismah sai Ablah da Jalilah.
Tun data tunkaro class din kowa yayi tsit babu wanda yake kaunar wani tsautsayi yasa ya aikata laifi,kamar wata giwa haka tashigo class din idanun ta be fada akan kowa ba sai akan Jalilah da gaba daya tamaida hankalinta akan wani zanen tsuntsye da yake bangon Littafin ta.
Good morning ma'am kowa ya mike dan girmama wa agareta daga musu hannu tai alamar ta amsa kowa zama yayi yana maida Numfashi, hankalin ta nakan Jalilah still nazari take ta wace hanya zata fara jawota jikin ta,basarwa tai tafara darasin daya kawo ta Home management take daukar su, Jalilah da gaba daya ba gane karatun ma take ba hankalinta sam baya class din tanacan wajan tunanin dan India iya da Ammah tasan yanzu suna can suna shan shiyi da wainar kwai.
Wani takaicine ya kamata da yanzu fa tanacan akwance amma yanzu kalle ta azaune anata surutun da ba gane kansa take ba,hatta karaci babatunta ta fice bata gane ko A acikin maganar taba haka akatashi ranar babu Abinda Jalila ta fahimta.
Wasa wasa kullum haka za'ai karatu Jalila bata gane komai ba ga dukan hadda da takesha kamar jaka harta saba da duka duk yadda su Ablah zasi da ita akan ta zauna su koya mata bata zama kayan Abincin ta tuni takusa tashin su daga aiki kullum saitaci tayi kat take hakura haryau bata fara zuwa karbo abinci ba saidai su Nasmah su karbo suci tare amma itafa bazata jeba har sun saba da halinta.
Satinta hudu a schl din amma babu wanda be santa ba bata barin kota kwana duk wanda yayi mata saita rama ga shegen dakikanci bata gane komai.
Anty Binta da kanta tazo har room din su da tambayar ba'asin abinda ya hanata zuwa wajanta daukar karatu shiru tayi ta sunkuyar dakai Jalilah matukar kinaso mushirya to lallai ne saikin jajirce wajan neman ilimi duk ranar weekend agida na zakidinga kwana babu ke ba bacci saikin haddace abunda na koya miki gyada kai kawai tayi to wait ita wannan wace irin takura ce ace lallai sai tayi karatu.
Badan taso ba ta fara zuwa Anty Binta tana shan fama har makogaranta ya fara ciwo Jalila dai kamar me kwakwalwar kifi bata ganewa tayi fadan harta gaji hakadai take dan jagwal gwalawa.
Jarrabar first time sukai Jalilah ce ta karshan aji amma ko agefen silafas dinta babu Abinda ya dame ta sai su Nasmah ne suka tayata jin takaici dan suna da kokari sosai data maida hankali da sunkoya mata abubuwa da dama.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 53
Hutun sati daya ne shiyasa babu wadda aka bari taje gida.
Yaune ranar visiting kowa kagani murna yake zaiga yan gidan su harda Jalila amasu murna da farin ciki tayi wanki tasa sabbin kayanta fes tafito kamar ba ita ba duk da wahalar Makaranta tasa tayi duhu ba kamar daba 12 daidai baba drieba ya daidaita parking acikin harabar makarantar tana tsaye daga can nesa hankalinta yana bakin get din dama.
Da gudu ta sheko tana oyoyo Ammah rungumeta Ammah tai bakaramin missing din Jalila take ba,juyawa tai taga iya sai faman washe mata wawulan bakinta take wayyo Iyata rungume ta tayi itama kai Jalila sakeni zaki kayar dani kefa dama baki da wani kwari haka kike,eh naji cewar Iya sakeni dai haka kawai bazaki cucan kifasamun baki a aikin banza ba.
Dariya ta fashe da ita ina bakin yake Iya bakinda babu hakora ma Ammah dai dariya kawai take musu harda ta barma suka taho samun waje sukai suka shimfida wasu kuloli masu kyau aka fito dasu daga motar wuyan Jalilah kamar zai tsinke sabida yadda take alla allah abude taga abinda yake ciki.
Wani kamshine ya bigi hancin ta farfesun kaji tahanga makwat ta hadiye wani mugun yawu,Ammah ni kika kawo wa dariya Ammah tai to da wazan kawowa inba keba jawo kular tai gabanta, Iya bafa ci zaki ba naga sai wani lekowa kikeyi af ke wannan yadama nida kullum sai naci nawa naci naki.
Bata fuskatai tana kallon Ammah wai haka Ammah meyasa bazaki dinga ajiyemin nawa ba,to baga shinan nahada nakawo miki ba dan wannan tunda kin raina kibawa Iya ta hada tacinye,tabdi cigaba sukai da hirar su gwanin birgewa kayan da suka zo mata dashi takira kawayanta suka gaisa da Ammah sannna suka tayata daukar kayan.
Ammah ina dan India yatafi unguwar da yace zashi tuni ma ai ranar daya kawo ki shima yatafi,yanzu dagake sai su samudawa dariya ta fashe dashi Ammah suna ina ko ammu su Aure, murmushi kawai Ammah tai sunanan suna gaishe ki,kodai Ammah ke kika fada nasan bazasu taba cewa kigaishe ni ba.
Kamar ko kin sani Iya tafada tana tabe baki cike dajin haushin su,aina gaya miki Jalila yanzu wani Iskanci da suka tsira kullum tara samari suke agidannan suita kide kide da raye raye oh ai muna ganin abu wllh kai ni wannan mata da yayanta basuji dadin halin su ba yanzu babu mu ba baccin rana yo ta ina zakai baccin rana Allah na tuba ankirawo jujal cikin gida an kafa uban kida.
Zaro idanu Jalila tai yanzu Iya abunda suke kenan sosai ma,ina Dad kuma ya kyale su, Ammah Iya ta kalla wadda hankalin ta ma baya kansu kasa kasa tai da murya ke aiyanzu Alhaji ya zama mijin kanta ce sai abunda wannan mekama da kafuran farko ta fadamai ai muna ganin tashin hankali ta kwace Alhaji sai abunda tace masa.
Bakiga Ammah duk ta rame ba,juyawa Jalila tai tana karewa Ammah kallo sai lokacin ta lura da yadda Ammah tarame tayi duhu kamar ba itace wannan yar gayun ba yar kwalisa,cikin damuwa take kallon Iya yanzu wani abu sukeyiwa Ammah uhm aikedai Jalilah in ana sallah ba'a magana saidai Hajiya Ammah ta hango Alhaji daga nesa.
Fyace hanci Iya tai tare da goge hawaye aikedai Jalilah wannan mata baza taga Annabi ba tunda burinta raba mata da Miji,kedai abunda nake so indai kika dawo hutu kihada daga ita har yayan kici mana uban su karki ragawa kowace shegiya acikin su saikin tabbatar jikin su yayi laushi kanki dawo Makaranta abunda zakiyi kenan ki burge ni wllh.
Ai iya sha kurumin ki harkin sa nafara kaguwa ma nadawo dan wllh ba mutun ci duk sai sunga abunda zai biyo baya tunda suka hade kai suna zalintar Ammah.
Juyowa Ammah tai tana kallon su sarai tasan gilamar Iya yanzu haka wani abun take fesawa Jalilah.Waini kus kus dimme kukeyi haka,babu komai dama muna hirar bayan rabuwa ne inji Iya datake rarraba idanu kaida gani bata da gaskiya,caraf Jalila tai hakane Ammah kinsan nida Iya bata baci atsakanin mu shiyasa muke kara gaisawa sosai.
Gyada kai kawai tayi dan yanzu sam batason doguwar magana saboda damuwar dake dan kare acikin Zuciyarta, murmushi ta kakalo kawai to hakan yayi kyau amma banda dai gulmar Jama'a sak Iya tai tasan da ita take fuskewa tai kamar batagane me Ammah take nufi ba.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 54
Waini ko Jalila kina karatu kuwa,shiru tai tana muzurai ina wadda Jalal ya damkaki ahannun ta tana gidanta inane gidan wasu gidaje ta nuna mata guda Uku da suke can nesa,ok tashi muje kirakani na tambayeta baki da baki,marairai cewa Jalilah tai Ammah bata nan fa da kuma kikace tanan tashi muje daga ganima baki da gaskiya.
Badan taso ba tatashi tai gaba suka bita abaya kwankwasa kofa tai bayan wasu mintuna tazo ta bude kofar a'ah Jalilah kece shigo mana.Sai lokacin ta lura ba ita kadai bace lale lale kushigo shiga sukai har parlo takai su ruwa ta kawo musu sannan ta zauna cikin mutuntawa suka gaisa da Anty Binta.
Jalila ta kalla Mamanki ce gyada kai tayi ma sha Allah sake gaisawa sukai sosai Ammah ta yaba da mutuncinta.Gyara zaman Ammah tai dama cewa nai ba muzo miyi miki godiya saboda dawainiya da kikeyi da Jalila Angode Allah ya kara girma Ameen ta amsa cikin jindadin Addu'ar ta.
Waiko tana maida hankali akan karatu,danjim tayi kafin ta sauke numfashi gaskiya Hajiya bazan boye miki ba Jalilah bata jin magana burinta tayi tsokana tayi wasa yanzu kaf makarantar nan babu wanda besan Jalila magen rashin kunya da dakikanci babu abunda ta sani taki tsayawa kuma akoya mata kullum fama nake da ita amma wllh kamar busa nake mata akunne.
Kinganta nan har angaji dayi mata dukan hadda tunda tazo ko sau daya bata taba bada hadda ba kullum cikin kawon kararta ake amma ina ta Addu'a ALLAH ya shiryeta.
Kallonta Ammah tai Jalilah dai an sunkuyar dakai,kallon Anty Binta tayi abunda takeyi kenan dama to kin kyauta angode Hajiya Allah ya saka da Alkhairi in sha Allah daga wannan lokacin zakiga canji zata maida hankali sosai akan karatunta,murmushi Anty ta saki haka nake fata zanyi matukar farin ciki naga Jalila ta nutsu kamar kowa tadinga gane karatu.
Zata gane kidai kara hakuri babu komai aida na kowane zuge jaka Ammah tai kudi taciro masu yawa gashi asai omo kai harda hidima haka babu komai to Angode Allah ya saka da Alkhairi Ameen har kofar gida tarako su.
Suna fitowa Anty Zarifa tana futowa daga gidan ta da Murmushi a face dinta ta karaso inda suke, Jalilah Mamanki ce wannan eh itace juyawa tai suka gaisa da Ammah wadda fuskarta ba yabo ba fallasa kallo daya tai mata taji matar batayi mata ba to zamu tafi sai Anjima gaba sukai sukabar Anty Zarifa atsaye.Kallon Binta tayi data galla mata harara ta rufe kofarta cike dajin tsanar Zarifa azuciyarta kwafa Anty Zarifa tai tabar wajan.
Yanzu dama Jalila abunda kikazo yi kenan wasa da tsokanar fada shiru tai,ni inacan ina cewa Jalilah ana nan anata karatu ashe abunda kike aikatawa kenan to matukar bazaki karatu ba kinsan ALLAH kauye zaki koma,fashewa da Kuka Jalila tai nidai wllh Ammah bazan koma kauye ba,to! Matukar bakiyi karatu ba can zaki koma.
Zammayi Ammah ai wannan lamari bekai asako xancan komawa kauye ba,aiko yafi hakama indai baki gyara halinki ba kikazo hutu bazaki dawo ba,kiyi hakuri Ammah Allah zandage karma ki dage sosai Ammah ta sakeyi mata nasiha ba laifi ta dauka zata dage tayi karatu,sai yamma lis suka tafi harda kukanta haka suka rabu.
Tadade ranar batayi bacci ba da tunanin ya kamata tafara abunda ya kawota daga wannan lokacin zata dage tukuru tayi karatu bazata ba dan India kunya ba tadade kan bacci ya dauke ta.
Tun daga wannnan lokacin ta dage ta zage tana zama su Nasmah su koya mata ga Anty Binta datake koya mata akowane lokaci.
Kafin wani visiting din tuni Jalilah tagama cinye kayanta tas tofa dan danan Jalila ta fara kashin wuya ta saba daci kamar gara yanzu kuma gashi babu abunda zatayiwa wannan ci haukan dan dole tadauki kwanon ta take zuwa karbo abinci,aiko tasha tsokana wajan su Ablah yar almajira takulu kuwa tayi fam kamar zata fashe.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 55
Yau sassafe wata azababbiyar yunwa tatashe ta daga abcci tashi tai ta zabga uban tagumi cikin sai kulululu yake babu kakkautawa rushewa da kuka Jalila tai dan bata tabajin yunwa irin wannan ba.Ismah ce tafara tashi da sauri ta taso har inda Jalila ke zaune ta zo dafa kafadar ta tai Jalilah me akai miki haka kamar wadda aka aiko babarki ta mutu.
To ba itance ta mutu ba ahalin yanzu gobara ake aciki na gaba daya yayan hanjina sun gama dafewa da azabar yunwa,wai dama saboda yunwa kike rusa wannan Uban kukan,ita yunwar ba abar ayiwa Kuka bane tafada cike da takaici,ah kinga baki nakar zoman ba ratayar ma ba abani ba kidora Inda kika tsaya saiki jira azo raba abincin safe tunda kin cinye naki abincin.
Komawa tai tai kwanciyarta tabar Jalila azaune bata da zabi dan dole ta kwanta itama,karfe 6:30 sun gama shirya wa idan akazo aka sameki akwance ba karamin duka kike ciba shiyasa suke tashi da wuri,cup kowacce ta dauka na zuba tea ko kunu yaudai ranar shayi ce,duk sammakon da sukai wani azababban layi suka tarar kam balastin aiko wllh bazan kira wannan uban layin ba.
Can gaba taje ta tsaya mikawa laraba cup dinta tai Mama azuba kin yunwa nakeji nan wajan ya kaure da hayaniyar damme bazata bi layi ba,babu wanda ta tankawa Mama Laraba maka mata harara tai wakikafi zane anan canake suma yunwar ce ta kawo su nan yadda sukabi layi dole kema kibi,sake kuyawa Jalila tai akalla kowanne layi sunkusa 150 ahakamma wasu basu fito ba.
Nidai kizuba min dan wllh bansaba da yunwa ba,baba laminde ce ta kalleta waike wace irin Yarinya ce dakinbi layin da yanzu kila ankusa zuwa kanki,ai layinne bazan iya boba gaskiya kuma dole abani ko banbi layin ba,to baza abaki ba kiyi abinda zakiyi Mama Laraba ta fada da hargowa ihu aka sawa Jalila kamar tafashe da kuka dan bakin ciki.
Tsit akai kamar mutuwa ta gifta Anty Zarifa ce tafe da magoya bayanta malamai da suke take mata baya kamar wata saraunyi me cikakken iko,kara sowa wajan tai cike da takama da dagawa kallon Jalila tai datake kallonta,meyake faruwane shiru sukai dan su kansu su Laraba suna matukar shakkat Anty Zarifa ba magana anke muku ba,watace acikin masu dafa abincin tai caraf ranki yadade akan wannan yarinyar ne tazo tanajin yunwa tace azuba mata yunwa take ji saboda bata da kunya ita fitsararriya ce.
Bata gama rufe bakinta ba Anty Zarifa ta kasheta da wani kyakykyawan mari,nanfa kallo yadawo sama Jalilah ba karamin razana taiba kallon Anty Zarifa take tana kallon matar da akalla zata haifi Anty Zarifa amma tadaga hannu ta tsinka mata mari.
Harku su wanene da zatace kubata abin break kuce dole saita bi layi to daga yau da tazo asallameta abata abunda ya kawo ta saboda munada danganta ka da ita.
A'ah wllh karya da ciwo mari da zafi babu abunda ya hadamu wllh can gasu gada zomo yaji kidan farauta danni kaf dangina babu me kama da Inya murai atoh Jama'a kushaida babu abunda ya hadani da ita,🤣🤣🤣🤣 tofa gaba daya wuta daukewa Anty Zarifa kowa kunshe baki yayi dariya nacinsa wannan fa shine ancusai shiga likkafanin aminiya.
Kunya da bakin ciki gaba daya suka baibaye Anty Zarifa ba ataba yarfata irin yau ba amma yarinyar nan ta shammace ta tagama da ita,cikin borin kunya tabar wajan buguzun buguzun saida aka tabbatar tayi nisa akasa shewa da ihu ahayye cas.
Wadda tasha mari ce ta mikowa Jalila hannu kekam yarinyar nan Allah ya yimiki Albarka kawo kofinki na zuba miki aini kingama min komai yadda kika kunyata matar nan tunda nazo makarantar nan bantaba farin ciki ba irin nayau,ah to baba Asabe aini ba ahada baki ayi karya dani haka kawai tawani ce muna da alaka alakar me to babu abunda ya hada biri da gada.
Bani kedai na zuba miki saidata cika mata kofi taf aidaga yau kindaina bin layi da kinzo ki kawo na zuba miki angama baba Asabe zami tafiya tare dake amma wani hanzari ba gudu ba akwai kawayena guda uku dole suma su shiga jam'iyyata takin bin layi,baba Laraba yazama dole suma kudinga zuba musu.
Ai fadan daya fi karfinka saika maida shi wasa kika karyata masu iko balle mu aidole miyi biyayya suna ina kawayan naki kwalla musu kira tai saigasu sun fito sunyi tsamo tsamo ba karamin shork suka shiga ba akan abunda Jalila tai wai anya kuwa Jalilah ita kadai ce.Karba akai aka cika musu cups din su sannan sukai gaba babu me magana acikin su.
Wai Jalilah meyasa kike da kwarin guiwa haka babu fa wanda kike ragawa a Makarantar nan ina mamakin yadda hakan take faruwa kuma sai muji shiru ba azo yimiki hukunci ba Ablah ke wannan babatun daga kafada tai su wannan ya dama nidai nasan bazan taba zama wani ya taka niba duk girman sa kuwa saina dauki mataki akan sa shiru sukai dan basu da tacewa.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 56
Ahankali sunan Jalila ya kara popular acikin school din tuni ta samu masu take mata baya kamar yadda tafadawa su Ablah sai anzo ana risina musu ahanya hakance ta kasan ce,har hayar Jalilah ake zuwa yi da anzalince ki tofa gunta zaki taho ita zata shige miki gaba babin ba'asi ba komai zata rufeki da duka duk girmanki kuwa,Js 1 take amma hatta yan SS 1 shakkarta suke ji kai har ss3 kikai mata abunda be gamsheta ba dan batuwa zakuyi kuraba raini.
Inkinfi karfinta ki kwaci kanki inta fi karfinki kuwa saitayi miki jinana babu ruwanta,babu kalar horon da ba'ai mata ba akan hakan amma abanza,akwai wani malamin su uncle bashir har hawan bango yasha sata asata noma wankin Toilat data gama oprition ya samu saita kaddamar koda kuwa yar wacece bazata raga miki ba.
Sun sake yin exam second time wannan karan Jalila tayi abun kai tazo ta 35 ta zubar da mutane 15 sai murna take sosai ko banza dai aita dance wani abu bakamar baya ba data zo ta takashin baya.
Yau zasu tafi hutu kowa kagani murna yake zashi gida su Nasmah anyi wanki hutun sati uku zasi su dawo Ablah aka fara zuwa dauka da take kano sai Ismah yar meduguri Nasmah yar Abuja gaba daya suka rungume juna suna kukan rabuwa dan sun bala'in sabawa da juna suna matukar san Jalila dan zuwanta ta kankaro musu mutunci da yanzu sunanan suna dakon ruwan wankan yan ss.
Sai kusan 12 baba direba ya kara so dama shi take jira da sauri kuwa tatare shi kai Baba ka dade baka zoba,wllh Jalila matsala aka samu shiyasa banzo da wurin nakai Hajiya unguwa Ammah uhm wace Ammah ai rabon Hajiya Ammah da hawa motar nan harna manta,hakimar gidan nakai unguwa ita da yayanta,kwafa tai ganinan bisa kanku.
Karfe daya da rabi suka isa Gidan gaba daya bakajin kunne wasu uban speakar ne manya manya aka kafasu a harabar gidan samari da yammata sai holewa ake da masu shaye shaye da masu bushe bushe wata ma akan cinyar saurayin ta take kai abundai sai kalu Innalillahi.
Kamar idanun Jalila zasu fado take binsu da kallo bantan Uba kace baba gidan karuwai aka zamar da gidan ai wani zubin haryafi haka yannan saidai Allah yayi mana maganin su wadannan anno bane wllh ALLAH dai ya shirya Ameen ta amsa jakar kayanta ta dauka ta gaban su tazo ta wuce.Kai baba kai kaga wata cika niban taba ganin ta agidan nan ba saiyau, nima dai cele bantaba arangama da ita ba saiyau.
Akwai irin wayyan mezami dasu Sali baby anriga angama rabawar atiti zan lallaba mu jone da wannan babyn, àah ba baba kar kaimin haka nina fara kamata saidai ka nemi wata aiko saidai kowa ya yagi rabon sa dan bazan taba barma wannan kyakykyawar ba.
Oho ita batama san sunayi ba tuni ta wuce gidan turus taja ta tsaya tana kallon abun Mamaki Dady ne azaune dirshan dagashi sai gajeran wando yana wankewa Mom kafa ta dora kafa daya kan daya,sosai tashigo parlourn tana kare mata kallo eh lallai yau taga abunda ya isheta Dad ta kurawa idanu duk yawani rame ya susuce kamar bashi ba gaba daya Mom bata lura da Jalila ba.
Hayewa sama tai kirjinta kamar zai babbake sabo da tsanar Mom da yayanta,dakin Ammah ta tura akan sallaya ta hango ta hannayan ta asama sosai take Kuka na tsabar takaici da bakin ciki sosai take Addu'a tana gayawa mahaliccin ta shikadai zai yaye mata damuwar ta,tarame tayi baki kamar ba ita ba hawaye Jalila taji yana zuba daga idanunta na tsananin tausayin Ammah.
Ahankali tataka hargaban ta sannan tsugunna tana kare mata kallo batasan da zuwanta ba saiji tai tana share mata hawaye kura mata idanu tai sanyi na kwarara acikin Zuciyarta tamkar taga Jalal haka taji sanyi aranta akalla zata samu me debe mata kewa tana matukar kaunar Jalilah tana yimata kallo ne na yarta jikinta,hawaye na shatata aface dinta ta sakarwa Ammah murmushi bayan Innarta da gwaggo aduniya wazata so itakuwa kamar Ammah tana son wannan halitta dake gabanta.
Ammah meyake faruwa meyasa meki haka wanene silar zubar hawayanki,hannun Ammah ta kama wllh Ammah namiki alkwarain saina hanasu sukuni acikin gidannan sai sun gwammace kida da karatu na tabbata ba haka tabar Dady ba karkiyi fushi dashi dan ALLAH.
Murmushi Ammah ke saki tana karajin kaunar Jalilah.
😭😭😭 Nikaina Ammah saida naji hawaye ya fara zuba a kuncina saboda tsananin tausayinki.
Taku har kullum
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 57
Naso zuwa da kaina na dauko ki amma bamsa mu damar hakan ba ayyuka sunsha kaina shiyasa,tashi kije kiyi wanka sai kizo kici Abinci to Ammah tashitai tafita Ammah ta bita da kallo,lumshe idanunta tayi taci gaba da laziminta.
Yana nan yadda tabarshi sai kura da yayi saidata share dakin tas kafin tayi wanka riga mara nauyi tasaka zuwa lokacin Jalila anfara zama yammata tafara kirgar dangi,dakin Ammah ta leka ganin bata dakin kasa ta sauka tunkan ta karasa saukowa ta hango Dad yana guga kananan kayan su Rufaida yake gogewa babu wata damuwa aface dinsa baki hangame Jalila ta cake tana kallon sa.
Dad ta ambaci sunan sa da sauri ya juyo dan ganin wayake kiransa tsaye ya ganta fuskarta dauke da Mamaki, murmushi ya saki Jalilah yaushe kika dawo um dan murmushin yake ta saki dazu na dawo amma ban lura da shigowar ki,eh ai sanda nashigo kana zaune kana wankewa mijin gidan kafa,kallon rashin fahimta yake mata wanene mijin bayanni tabe baki Jalilah tai a'ah Dad ai yanzu Mom itace Mijin kaine matar.
Shiru yayi abun yana matukar damunsa azuciya har gabansa tazo ta kwashe kayan da yake guga zabura yayi jikinsa har rawa yake dan Allah Jalilah kibani naci gaba karki jawomun masifa,ai wllh Dad bazakai gugar nan ba barima kaga part din Mom tai da kayan ahannu labulan dakin ta ban kada tashige kanta tsaye suna zaune sun baje soyayyun kaji ga drinks nan kala kala agaban su.
Dago kai sukai dan ganin wanene ya shigo musu daki ba izini ba komai,ido hudu sukai da Jalilah saida kirjin su ya buga alokaci guda tun daga sama har kasa suke kallon ta,tunkan suce komai ta watsa musu kayan afuska kazaman kayan wane wannan acikin ku da zaku mayar wa da mutane parlo ma tattarar ajiye tsummo karai to karna sake ganin haka.
Baki sake suke binta da kallo yawwa kuma wace la'ananniyar ce acikin ku tabawa Dad wannan matsiyatan kayan ya goge,kallonta suke kamar sun sami TV musamman Mom data tuno maganar boka matukar wannan yarinyar tana nan aikin ki zai iya lalacewa ako wane lokacin, firgigit ta kike ke wane dan iskanne agidannan yaje ya dawo dake wllh ko wanene sai ransa ya baci yau dinnan zaki bar gidannan basai gobe ba.
Parlo ta nufa afusace Ma'aruf Ma'aruf haka take kwallawa Dad kira sai huci take kamar wata kububuwa,abin tausayi sai gashi yataho da sauri gani Hajiya atsiya ce take kallon sa wanene acikin kai da Rukayya yaje ya dawo da wannan yar iskar yarinyar eh shuru yayi yana ta muzurai koba dakai nake ba,dama ai ba tafiya taiba daga makaranta ta dawo kace me makaranta.
Eh lallai kun samu sake ina cikin gidannan har akai yar aiki makaranta ba tare da sanina ba,kiyi hakuri banine na sata ba Jalal ne to aiko uban Jalal dinne ya sata yau saita bar gidannan wllh awa daya bazata karaba.
Amatsayin ki nawa zakice tabar gidannan Ammah tai magana cike da bacin rai shidai da kika shanye kin shanye ammani bazan shanyu ba yanzu Jalila ta fara zaman gidannan naga shegen da zai fitar da ita,ni kike gayawa wannan maganar Rukayya lallai kin samu kanki,Uhm Saratu kenan aishi Allah ba azzalumin bawan sa bane nadage wajan rokon ALLAH da yake bani da hakkin ki gashi cikin sauki ya dawo dani hayyacina.
Dad ta kalla zaka fitar da ita kosai nasa karti sun dauketa sun wulla waje,tofa Dad fa yana cikin tsaka me wuya saiya kalli Jalila ya kalli Ammah ya kalli Mom kowacce tana jiran jin amsar sa.
Salamu Alaikum waini ina mutan gidanne naketa zabga sallama amma ammin banza,ganin su atsaye sunyi curko curko yasa ta tsaya itama tana binsu da kallo wai meyake faruwa ne naga kun tsaitsaya kamar Wadanda kukaje coci harda masu gajerun wanduna nake gani ni Hadaza,sannu da zuwa inna Ammah tai mata sannu fuskarta dauke da fara'a yawwa Rukayya.
Sannu da zuwa Inna Dad ya ambata shima tundaga sama har kasa take kallon sa tabe baki tai yawwa aikai za'ai wa sannu kaida Allah ya hadaka da kaddara,dakyar Mom tace sannu yawwa Inna ta amsa atakai ce.
To! zaku zauna ko fadomin zakui aka fitsararru zama sukai Mom sai hura hanci take,ke Rukayya me yake faruwa agidannan gaba daya kun firgice kamar yan gudun hijira Kalli yadda kika dawo kin kwantsame kin rame kamar wadda ake dibarki ake miya, dad ta kalla har gwara ita akanka wai kodai cutar zamanin nan kaje ka kwaso ka goga mata bamu sani ba.
Bawani Abune yake faruwa ba Inna ina wannan yarinyar ta wajena dana ce ansamo min yarinya karama tana tayani ayyuka,eh naji anyi haka kuwa,to itace sai yaronnan yasata amakaranta shine yanzu tadawo hutu shine Saratu take ta masifar sai tafita daga gidan harda zatasa gardawa su dauke ta su wullar da ita awaje.
Gyara zama sosai Inna tayi saboda gidan na kanin Ubanta ne zatai dauki wata ta zubar awaje,to idan ita bata fita ke kya fita ai kallah yadda kika zowa da mutane yaya maka maka kamar dibar farko ni ban taba ganin Inda ka tasa yaya agaba garza garza katafi dasu gidan wani ba sai akanki su ba yara ba ba komai ba to ba nagaya miki matikar wannan yarinyar zata fita sàidai sufita tare da wadannan yayan naji masu ido atsakar ka.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 58
Cikin rawar murya Dad yafara fadin ai Inna dakin bari tatafin kar Saratu taga ba ayi mata dai dai,kaci ubanka kai da saratun ubanka nace harni zakacewa wai kartaji haushi intaji haushi tadau mayafinta ta fita daga gidan shine zan tabbatar da cewa taji haushin magana kafita daga idanuna na rufe wllh.
Nagama magana babu Inda yarinya zata kowa yata shi ya bani waje,tashi sukai sun kumbura sunyi suntum dagowa Jalilah tai suka hada ido da Mom gwalo tai mata tana kunshe dariya dan Aduniya yanzu faduwar Mom take da bukatar gani.
Zungui zungui Dad ya tashi zai bita kai ina zakaje cewar Inna dama ke kikace mutafi ai saina ce kuma inka tashi kabita yinan sama ta nuna masa kamar zaiyi Kuka haka ya juya yana tafiya yana kallon Mom da take makamai hararar.
Ke yaki yarinya yama sunan ki akace Jalilah oh ikon Allah kinji sunan ki daya da ja'irin can tashi ko dauko min ruwa nasha tun kan na huta dan jaraba ansani Inata babatu bagaira ba sabab kai tir wllh Allah ya rabamu da Airan irin jaraba Ameen Innah.
Safa da marwa Mom kawai keyi adaki innafa tana shigar mata al-amuranta yanzu gashi ta hana waccan yarinyar tafiya idan aikinta ya lalace fa gaskiya dole nema tasa idanu akanta tayi taka tsantsan akan duk Abunda zatai gobe gobennan zata koma wajan boka ayiwa tufkar hanci itama inna agyara mata zama baza yadda abata mata aiki ba.
Mtsww Rufaida taja tsaki gaskiya Mom kin fiye son kanki da yawa keda kin fara tsufa kiyi tatawa mana amma haryanzu magana ta Jalal babu wanda ya santa kifito kifada sai kunbiya kunbiya kikeyi gaskiya nagaji wllh,ke banda abinki Rufaida ai komai asannu ake binsa sonake sai Jalal din ya dawo zanyi maganar yadda ma za'ai abun cikin sauri amma inna fada da wuri itama uwarsa ta shiga malamai ta hanafa.
Kuma Hakane Mom ai bakiyi min wanna bayanin ba shiyasa ban game ba kinyi tunani mekyau muci gaba da shirin biki kawai inanan inayi ai meza' afasa ki kwantar da hankalinki kamar kin Auri Jalal kin gama wannan azaune take babu wanda ya isa ya hana Aure ya zama dole.
Inna wuni tai agidan sai Magariba aka maida ita gida mahifiyar Dad ce tana da fada bata daukar raini bakaramin shakkarta Mom keji ba duk wani iskanci da zatayi indai ranar Inna tazo bata yinsa tasan karan su ba dadi.
Ammah ina iya tunda nazo ban ganta ba ai iya tatafi ganin gida jikan tane ya rasu dama tadade bata jeba shine nace taje kawai tadan hutama kafin ta dawo,hutumme Ammah hutun masifar Gidannan mana ALLAH Ammah ke kika yarda da nice bazan taba yadda ba,girgiza kai Ammah kawai tayi Jalila kenan kedai Allah ya rabaki da makircin kishiya kawai,ni Ammah bazan yarda ba koka kadan.
Wayar Ammah ce tai kara miko min ita naga wake kirana daukowa tai screen din ta duba my son taga an rubuta,lallai su Jalila fa anshigo gari amfara gane abubuwa bani mana Jalila to Ammah ki tsaya mana nafara dagawa to kin san wake kiranne dagawa tai hello dan India,saida yaji wani yar Lumshe idanun sa yayi cikin tsananin kewar ta.
Gyara kwanciyar sa ya sakeyi wai bakaji nane Murmushi ya saki kamar tana gaban sa yadai yar kauye bata face tai kamar yana gabanta nidai ba yar kauye bace nazama yar birni,katse ta yayi mekika dawo yi ko wata kika cirewa hakori aka koro ki dariya ta kyalkyale da ita kamar wata yatta adda hutu mukai yaushe zaka dawo mezaki bani inna dawo kaidai kadawo kagani.
Shikenan na kusa dawowa ina Ammah gata mikawa Ammah tai tafita daga dakin.
Ammah ta Murmushi ta saki My Son ya karatun numfashi y sauke Lafiya lau Ammah meyake faruwa ne dan ALLAH kifadamin,shiru tai na wani sakanni mekagani kake cewa nafadama innakira Dad yadaina peaking gaba daya wataran kuma sàidai naji ankasha,ayyukane sukai masa yawa kuma bayajin dadi kataya shi da Addu'a bayan wannan bansan komai ba.
Jim yayi badan ya yarda ba yabar zancan gaba daya hankalinsa yadawo kan Ammah dan yasan ba adaidai take ba tabbas tana boye mai wani abu.
Karfe 7am aka saki wani shegen kida afirgice Jalila tata shi tana Salati saukowa tai daga bed daga ita sai vest da dogon wando ta sauko babu kowa aparlon fita tai ta hango an wangale get manyan motoci ne suke ta parking yayan masu dashi sai fitowa suke kowacce da shiga ta rashin mutunci duk wadda zata fito tana rike da hannun saurayin ta.
Gyada kai Jalila tai ah lallai wadannan kuncika tsinannu kowa yabaro gidan su da sassafen nan tafi yawon iskan ci kwafatai.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 59
Dakinta ta wuce so take ta koma bacci amma gaba daya ta kasayi wllh yadda kuka hanani bacci sai jikinku ya gaya muku naranste da ALLAH.Mikewa tai ta isa bakin madubinta mai tai dauko ta lan bata a face dinta hoda ta duba babu irin wadda take sawa ada saukowa tai ta nufi Kichin fulawa ta dumbulo takoma daki tas tagama bishine face dinta sannan ta dauki bakin kwalli ta zane fuskarta dashi jambaki ta dauka ta mulka alebanta.
Kanta ta warware ta barbaza shi buzu buzu kayan jikin tane bata sauya komai ba daga ita sai wannnan vest din ta sauka wata katuwar tabarya ta dauka Amfanin ta kadai in za'ai dakan sakwara duk nauyinta haka ta jure kafarta ba takami saidata tabbatar angama hallara baba megadi ya rufe get sannan ta fita kunsan dai Jalilah badai guduba.
Kamar filfilwa haka ta fita da mugun gudu gadan gadan kansu ta nufa watace daga cikin su ta ankara da Jalila ihu ta fasa tamike aguje mahaukaciya mahaukaciya tuni suka dare kowa yana neman wajan buya wadanda suka sa kayan dayayi matukar kamasu gudun ma sun kasa aiko ba tausayi Jalila ta dinga kirbarsu kamar Allah ya aiko ta hatta mazan bata kyale ba duk gudunka saita kure ka ta daidaici keyar ka take sakarma tabaryar.
Dataga sunyo hanyar get zata falfalo aguje sai kagansu riiiiii sun kara darewa ihu suke ba kakkautawa dan azatansu daga dawanau ta kunto,Baba megadi kememe yaki bude musu get sai sawa Jalilah Albarka yake yau datayi musu maganin yan iskan nan.
Glass din motocin su gaba daya saidata sauke su raga raga jina jina taiwa motocin,karar hon din da ake dannawa ita tasa dan dole baba yatashi ya bude get din har turereniya suke wajan fita Jalila na sakecin ubansu da duka har bakin get ta rakasu sai uban haki take tajike sharkaf da gumi zama tai dirshan tana maida numfashin wahala daga karshe bajewa tai awajan kamar zata shide zamar wuyar data sha saidata dan huta tukunna ta mike.
Ido hudu sukai da Jalal daya harde hannayan sa akirji yana kallon ta ware ido ta sakeyi akan sa yadda ta baryar hannun ta tai ta zura da gudu tana zuwa batai wata wata ba ta rungume shi oyoyo Yaya Jalal gaba daya tagama mulke masa bakin kwallin dake face dinta,rintse idanu yai dan runguma bata wasa tai masa ba,dagota yayi daga jikinsa yana bata face kowane Namiji ma zuwa kike kinayi masa wannan rungumar wai.
Bata fuskatai ancema ni yar iska ce kome dazan fita waje ina rungume maza,kaima dan mata mazane shiyasa duka ya kawo mata ta koma gefe tana dariya dayi masa gwalo,kyaleta yayi dan yanzu zata maida mahaukaci speakun dake tashi agidan ya kalla ganan yadda aka zuba kujeru ga wani katon cake aka table,dama yaji aransa akwai Abunda yake faruwa agidan su.
Wuce muje gaba tai ya bita abaya har zata shiga dakin Ammah ya ruko ta bayanzu yake son tasan da zuwan saba saida yashiga part dinsa ya saketa komai yananan fes fes dan lokaci zuwa lokaci Ammah tana gyara masa dakin.
Saidaya zauna sosai sannan ya juyo kan Jalilah datake tsaye tana zumbura baki yace tana rungumar maza,basar wa yayi kekuma soja kika fara ban sani ba kin tsayamin aka kamar zaki fadomin zama tai agaban sa face dinta ya kalla dan murmusawa yayi,suwane wadannan da kikai yiwa barin bakauniya,anzo wajan sai Lokacin tasaki ranta harda gyara zama dan tafijin dadin bashi story yadda ya kaimata.
Samarin wadan can samudawan ne,kallon rashin fahimta yayi mata nan ta karkace ta zayyane masa duk abubuwan da suke faruwa,in ransa yayi dubu to yabaci jijiyar kansa tafito rado rado shikadai yake huci tsananin tsanar Mom yasake dirga azuciyar ita da yayan ta,kuma dan India bakasan wani abuba Dad har guga yakeyiwa su rufaida guga ita yaketa maimai tawa azuciyar sa.
Lumshe idanun sa yayi tuni suka rine da bacin rai,daga mata hannu yayi alamar tafita ya sallame ta fita tai kai tsaye dakin ta tafada ranta fes ko banza taci uwar yan iska tasan gobe basu dawo ba,wankan tashiga tana fitowa ta zura doguwar rigarta saukowa tai tashiga kiching ta dauko wuka harabar Gidan ta fita duk wayoyin da aka juna speaker ta tsitstsinke sai gashi shru kida ya tsaya cak.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 60
Su Rufaida da basu kwana agida ba basu san abun da yake faruwa ba suna can,kirane ya shigo wayarta tana hotel tare da wani saurayinta sun gama watsewa daga dare har safe,tana dagawa muryar zuli ta doki dodon kunnan ta amma kedai rufy Allah ya tsine miki Albarka dama kinsan gidan ku akwai Mahaukaciya baki taba gaya mana ba saboda ke yar wahala ce kisa tazo tahau mu da duka gaba daya tajijji mana ciwo wllh saimun dauki mataki.
Kinga zuly da kata bangane me kike nufiba aidama bazaki gane ba yar tasha kawai kitt ta kashe wayarta tabar Rufaida sake da baki,cikin azama ta mike kayanta ta yayuba ta saka key din motar ta kawai tazara ta fice adari da sittin tataka kan motar kamar tai fiffike taganta Agida haka takeji.
Parlo Jalilah ta dawo ta zauna kafa daya kan daya tana jiran kota kwana dan tasan tabbas yau da bala'i agidannan duk ta shirya musu Allah ya kawo su,asukwane tashigo parlon ganin yadda akai musu kaca kaca da kaya,turus ta tsaya tana karewa Jalilah kallo wadda ta kurawa plasma idanu kamar batasan da zuwan taba kuma sarai taga sanda tashigo.
Eh babu mamki sai yanzu na tuna muna da mahaukaciya agidan ashe baki warke ba to yau saina cire miki aljanun da suke kanki wllh saina kakkarya ki yau agidannan,mikewa tsaye Jalilah tai wllh saidai mu kakkarya juna badai ki karya niba guzumar banza guzumar wofi wadda bata da girma saina jikin ta,afusa ce Rufaida ta kwashe Jalilah da wani mahaukacin mari ni sa'ar uwar kice dan ubanki wllh badai uwata ba kuma wannan marin bashi kikaci.
Daga hannu tai zata sake kai mata mari karki kuskura kazamin hannun ki yakara sauka akanta,cak tatsaya tana kallon sa da tunanin yaushe ma yazo gidan wannan ce rana tafarko kuma ta kare da zaki sake daga hannu ki mareta ina tabbatar miki da ranar saina zubar miki da hakura kazamar banza kazamar wofi ballagaza sha sha sha hannun Jalilah yaja da dadi yakashe ta atsaye dakin Ammah ya nufa tana gaban mirror tana shafa mai taji anshigo parlon nata.
Hannun Jalilah ya cika samun wake yayi ya zauna har Lokacin idanun sa basu dawo daidai ba, Jalilah shiga tai tare da Sallama shigo mana Jalilah shiga tai tana washe hakora lpy kuwa jalila keke wannan washare baki haka albishirin ki Ammah goro fari ko ja fari kalma kuwa darya tai to mezaki bani inna gaya miki ah aiba'a cikin kifi aruwa kifara fadamin tukunna sainasan mezan baki.
To dan India yana parlo hararar ta Ammah tai au yau kuma da abunda kika tashi kenan matsamin ni nasa kayana ALLAH Ammah dagaske nake kinsan bana karya saidai na fada ba daidai ba Dariya Ammah tai to ai ana jika,to zomuje kigani da idanun ki ruko hannun Ammah tai saida ta kawota har gabansa to ya kika gani,mamaki yaki barin face din Ammah Jalal meyasa kadawo yanzu murmushin yake kawai ya saki yana akallon Ammah data rame tai baki kamar ba itaba.
Hannunta ya ruko ya zaunar da ita kusa dashi yana kara kallonta tsananin sonta da tausayinta ke kwarara azuciyar sa idanun sa har tara kwallar bacin rai sukai, Jalilah kallon su kawai take sun bala'in bata tausayi kana kallon face din ko wannan su kasan suna cikin damuwa,ahankali tajuya tafice dga dakin gaba daya.
Ammah ya furta can kasan makoshi dan wani bakin cikine yazo mako garansa ya tokare har wani daci yakeji amakoshin sa,shafa kansa Ammah tai meyasa ka dawo son saboda ke Ammah na tabbatar kina cikin damuwa fadaminne bazaki yiba dan kar hankalina ya tashi,murmushi ta saki idanun ta cike da kwallah tabbas abubuwa da yawa suna damun ta.
Matukar ina jinkai awaya kuma ina tare da Jalilah bani da wata damuwa dawowarta jiya kadai nasamu saukin damuwar da nake ciki akullum ina godewa ALLAH daya azurtani da samun Jalilah Inaji araina mahaifiyar ta ni tahaifawa ina so ka kula da ita iyakar iyawarka dan Allah Jalal, kallonta kawai yake Jalilah na kara wani irin girma da matsayi azuciyar sa matsayin dashi kansa besan wane iri bane.
Murmushi Ammah ta saki idanun sa kawai ta kalla tagano asirin Zuciyarsa,shafa kansa yayi ganin kallon da Ammah take masa tashi yayi yafara tafiya cike da tsarguwar kallon da take masa, dariya tasaki tabishi da kallo cike da soyayyar dannata.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 61
Yana saukowa ya hango Dad zaune akusa da kafar Mom itako hakimar tana hakimce akan sofa,zuba masa idanu sukai kamar wasu mayu tsaf ya dinke face dinsa ko kallan barin da mom take beba samun waje yayi ya dora kafa daya kan daya, Ahankali Dad ya taso face dinsa shimfide da farin cikin ganin sa my son fuskarsa ya dan saki barka da safiya Dad,shafa kansa yayi barka dai saukar yaushe.
Dazu na shigo,satar kallon Mom Dad yayi sai huci take kamar kububuwa ga shakkar Jalal da take ji babu damar tai magana,cikin Kissa da kisisina my son saukar yaushe ba labari ko nunama yasan dashi take beba sarai ya jita ya share ta,rai bace take kallon sa wannan fa dan iskan yaro ne,um bakaji Mom dinka nai maka magana ba ai tana sama banga Mom dita anan ba kan Uba Mom ta dura zagi a zuciyar ta.
Ammah ce ta sauko tasha kwalliya kamar ba ita ba tayi alkawarin tadaina zama ba gyara saboda bakin cikin wata kishiya aiko Mom ta shaqa ganin yadda Ammah tai fes har walwali take da sheki ita kuwa sai faman narka kiba take tana sake rashin fasali kamar doya haka takoma.
Dad ne yabi Ammah da kallo kamar idanun sa zai fado,kwata Mom tai zakazo ka samanne wllh Jalilah Ammah ta kira sunan ta naam tashi tai tabi bayan Ammah zo muhada breakfast ke tunda zuciyar ki ta mutu bakya son girki kwata kwata kinga kikiyayan Jalila girki shine mace in baki iya Girki ba Mijinki koro ki zaiyi,toni Ammah dan ma ya koroni ai gaba takaini saina dawo muci gaba da zama tare,to aini ba Uwar banza bace koraki zanyi dariya tasa.
Yanzu me zakiyi mana yau Ammah? dan jim Ammah tai alalan dan kali zamiyi,ban taba ciba Ammah yaya akeyi.
Arish
Mai
Egg
Attaru hu da Albasa
Sai maggi da curry kadan
Leda
Arish zaki feraye in yayi kiyanka shi kanana kiwanke shi tas sannan kidauko tukunyarki kizauba aciki kidan sa gishiri kadan inkin taba ya nuna saiki sauke shi kitace ruwan kitsane shi akwando,
Kigyara attaruhu da albasa ki jajjaga kadan zakisa attaruhun ba aso yaji ya fito sosai,inkin tanadi wannan zaki dauko egg dinki kisamu bowl kifasa in kadan zakiyi akalla kifasa egg 7 inkin kadashi saiki zuba attaruhu da albasar kizuba aciki egg din da maggi da dan curry kadan.
Saiki samo leda farar leda dai wanda ake kulla alala arish din da kika aje a gefe zaki dauko kidiba kizuba aledar daidai misali kananu amma ba sosai ba saki debi wannan egg din da kika sawa kayan hadi kizuba acikin arish din da kika zuba aleda kidan mommotsa ko ina ya samu saiki kulle ki ajiye haka zaku ta kullawa harsai kinga again zaki sake zuba shi atukunya kimayar kan wuta.
Zak sake tanadar egg dinki kamar guda uku ko hudu albasa kawai zaki zuba aciki ba asaka magi shikadai ake bukata,bayan kin kadashi ki ajiye agefe kibude tukunyar ki inya dahu zakiga ya hade jikinsa ya cure awaje daya saiki sauke ki kwance shi daga leda,saiki dora man suyarki akan gas kisa albasa inya dauki zafi saiki dauki wannan dankalin da kika kwance kidinga tsumbulashi acikin kwana ki jujjuya sannan kidauko shi kisa acikin man nan da yadauki zafi zakiga egg ya baibayeshi tun acikin kaskon suyar ki.
Shikenan kina gama suya saici.
Tafi Jalila tai kai Amma daga gani zaiyi dadi wllh bari na gwada nagani ko ina da fasaha kamar yadda Ammah tafada haka tayi dan danan kamshi ya dinga tashi saitafi take tana jin dadi Ammah nayi mata dariya,su Mom dake parlo har amfara hadiyar yawu ba asan a girka ba amma sai shegen ci.
Zobo Ammah ta diba ta zuba amabarba aciki tatafasa tatace bayan tasa kayan kamshi sun dahu tare da zoban sugar ta zuba ta juye awani jog fridge ta dauka tasaka tasan kafin su gama aiki yayi sanyi sosai.
Kuma fans baza'a barku abaya ba kumatso kusa Albarka,dan harna hango su o'o ana hadiyar yawu lol🤪🤪
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 62
Saida suka gama komai tsaf suka gyaran kitchen din tare Jalila sai wash wash take girgiza kai Ammah tai zakiyi medalili daga nan harki koma makaranta tare zamu dinga Girki aikin girma babu abunda bazaki iya ba,kai Ammah kinganni fa wata yar karama dake.ai naga alama,kinga dauko kayan muje dauka tai suka jera har Lokacin su Mom suna zaune suna jira bayin su sugama girki suzo suci.
Jalal Ammah ta kalla bismillah kutaso tasowa sukai zaram Mom da tawagarta suka mike,Ammah cetai musu kallon sama da kasa ina zakuje da kuka mike badaku na girka abincina ba zaku iya wucewa part dinku kuje ku girka naku amma wllh babu shegiyar dazataci Abincin nan acikin ku,dadi kamar ya kashe Jalila sai sakin murmushi take su Mom gaba daya sun daskare a tsaye.
Harke wacece da zakice bazamu ci abincin nan ba to matukar bamuci ba saidai kowa ya rasa mudake buguzun buguzun tai hanyar dining din shan gabanta Jalal yayi yanayi mata wani mugun kallo dole taja birki ta tsaya ba karamar shakkar Jalal take jiba sai jijjiga take tana hura Hanci.
Dad ta kalla da yayi tsuru atsaye kai kana kallon danka yanamin rashin kunya bazaka dau mataki ba,shiru yayi ya sunkuyar da kanshi kasa kiyi hakuri tunda tace bazaku ciba kuje ku girka naku,sosai take kallon Dad karfa ace aikinta ya farayin sanyi ni kake cewa muje mugurka saika wuce muje kaine zaka girka mana,juyawa yayi zai bisu jiyayi anruko hannunsa cak ya tsaya.
Jalal ne yarike hannun nasa cike da bacin rai yake kallon sa gaba daya ya susu ce ya dawo kamar wani karamin yaro sai abunda aka cemasa shi zaiyi Ammah da take tsaye gaba daya ranta ya gama baci Mijin ta da yake gwarzon Namiji jajir tacce acikin gidan sa shine yau mace take juyashi kamar wani waina.
Har dining Jalal ya kaishi saida ya jamai kujera ya zaunar dashi sannan ya sake shi Ammah samun waje tai ta zauna itama Jalila gefe tako ma ta tsaya,kallon ta Ammah tai taho mana Jalilah tahowa tai ta zauna kujerar da take kusa da Jalal Ammah da kanta tai serving din kowa kafin tafara cinnata babu wanda yake magana acikin su tea mezafi yasha kayan kamshi sai tururi yake.
Har lokacin Mom suna tsaye kamar gumaka bakin ciki kamar su hadiyi zuciya su mutu gashi babu damar tada tarzoma boss yana nan,saida suka kammala tas sannan sukabar dining din ragowar da suka rage Jalila ta tarkata tai waje dashi danta rantse bazasu ciba binta sukai da kallo kamar idanun su zasu fado kowaccen su da abunda take sakawa aranta.
Baba megadi takaiwa shida Direba zama tai suna ci suna hira saida suka cinye ta karbo plat din ta dawo gida lokacin sunbar wajan kamar zasu tashi sama suna tainewa Jalilah da dukkan ahalinta.
Dan dole suka shiga Kichin babu abunda suka iya sai indomie sukadan bararraka dan Mom bakin cikin dake cinta bazai barta tayi girki ba tsanar Jalila kuwa ai ba amaganar ta,wata karamar yarinya ta hanata sakat ta hanata sukuni duk hanyar data samo saita rusheta zatai maganin fitsarar ta kwanan nan.
Fita Jalal yayi daga parlon wasu matasa ya samo suka zo sukai gaba da speakers dinnan ko banza gaba takai su tasko suka debe sunayi masa Godiya tundaga wannan rana abokan su rufaida basu sake dawowa gidan ba dan sosai sukaji jiki harda wadanda akaiwa plaster aka saboda walmukalafatu da suka sha ahannaun Jalila bata wasa bace🤣🤣🤣.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 63
Washe gari tun karfe 7 Ammah kejiran Jalila ta sakko shiru bata sakko ba gajiyatai da jiranta tanufi dakin nata tana mitar taje tayi zaman ta,akan gado ta hangota akudun dune tofa yau Jalila ce takai wannan time din tana bacci,ke Jalila tashi mushiga kiching ko bakiji nace daga yau tare zamuna girki ba.
Shiru Jalila bata motsaba janye blanket din data kudun dune Ammah tai wahaye tagani jage jage afuskar Jalila tai wujiga wujiga kamar wadda aka kwana ana duka, Subahanallahi Jalila kukan me kike janyo hannun ta tai Jalila ta fasa kara cikin azaba maida hannun ta tai kan cikinta wayyo Ammah cikina zammutu na bani na lalace wayyo Allah na.
Arazane Ammah ke kallonta ganin idanun Jalila har yafara kafewa yasa Ammah futa da gudu dakin Jalal tanufa yana kwance yana sharar bacci,daka masa duka Ammah tai Jalal taso muje kaduba min yarinyar ce gatacan bata Numfashi afirgice ya mike dagashi sai boxer yabi bayan Ammah gaba daya ya manta ma babu kaya ajikin sa.
Ammah baiwar Allah duk ta gigice duk sanyin AC bata jinsa tuni gumi ya fara yanko mata tsoran ta daya kar cikin dare wani ya farmaki yar mutane dataga ta kanta,jijjigata Jalal yayi Jalila ke Jalila shiru kake ji Ammah samo ruwa mesanyi da sauri takawo ruwan watsa mata yayi Numfashi ta sauke kafinta kankame hannun sa daya face dinta.
Ammah meya sameta haka cike da damuwa yake yiwa Ammah tambayar ina zan sani Jalal haka nazo na sameta nima,kukan data sake fashewa da shine yasa shi saurin juyowa ya kalleta tashi yayi da sauri ya fita sai Lokacin yaga ashe ko kaya babu ajikin sa ya fita,allura ya hada sannan ya dawo dakin da azama riketa yayi ya tsira mata allurar duk yadda takejin jiki saidata zabura.
Ahankali bacci ya fara daukarta sauke numfashi sukai kusan lokaci daya sundade adakin zugum kafin Ammah ta kike bari naje nadora break kaga intatashi tasamu taci tasha magani Allah ya kiyaye gaba amen ya amsa,shima tashiyayi ya fita daga dakin.
Baccin da Jalila tai befi na mintuna 30 ba tafar ka wani mugun fitsari ne ya tashe ta dakyar tamike tashiga toilet dan yin fitsarin tana tsugunnawa memakon tayi fitsari aah Jini taga yana zubowa arazane ta mike tana Kuka shikenan jinina zai kare yan yankan kai zasu shanyan Jini fita tai daga dakin kai tsaye dakin Ammah ta nufa afujajan bata dakin memakon takoma saita afka dakin Jalal.
Yana kan sofa akwance yana tunanin ko Jalila taji sauki yanzu baya tashi yaje ya dubota,jiyayi kawai ta fado masa aka hartana kuma masa kai,kanyayi wata Magana ta fashe da kuka yaya Jalal jini yan yankai zasu shanyan jinina wayyo katemaken,Kuka take tun karfinta tsabar takaicin Jalila ya hanashi Magana kallon jikin yayi yadda tai masa kaca kaca da farar jallabiyyar sa.
Abun bacin ransa ma yadda ta ruko pant ahannu tana dobamana masa afuska,dagani tunkafin nai miki tsinannan duka kalli yadda kikaimin da jiki a islamiyyar ku ba'ataba gaya miki haka ba,ganin Jalila bama jinsa take ba sai zuga kuka take kuma dan jaraba pant din na hannun ta,inya kalli jikinsa saiya kalleta yarasa ma mezaice dan takaici.
Hawowar Ammah kenan taleka dakin Jalila bata gantaba toilet ta duba taga gaba daya ta bata shi dafe kai tayi dama Jalila abunda zatai fara kenan to ina take karfa tatafi wajan Jalal tasan ba hankali ta cikaba,da sauri tafita dakin Jalal tashiga ta tarar da yadda tasashi agaba tana gursheken kuka yayi mata magani kallo daya taiwa Jalal wata dariya ta kusa kufce mata kallon yadda yai buzu buzu kamar mahaukaci.
Hannun Jalila kawai ta kamo suka fito yasan yadda zaiyi da dakin da jikin sa.
Mrs Baba Bello ABUBAKAR
........✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 64
Saidai Ammah ta gyara ta tas dakinta tashiga ta dauko mata pad sannan ta zaunar da ita,fuska ta hade tana kallon ta kemeyesa wai Jalila baki da siddi gaba dayan ki yanzu da kikaje kika gayawa Jalal shikenan gaba daya yasan sirrin ki niya kamata kifadawa ba Jalal ba,zumboro baki tai to Ammah naga shine Likita ke ma inbaki da lafiya bashi kike gayawa ba.
Gwabe bakinta Ammah tai ai wannan ba rashin lafiya bace girma ne yazo miki,girma kuma aini banji na kara girman ba a Makarantar ku bakiji ana jinin al'ada ba ko ba aimuku ba ammana to wannan shine,rufe idanu Jalila tai kai Ammah ni kunyarki nakeji tabe baki Ammah tai abanza ai tunda Jalal yasani menene kuma najin kunya ta.
Kina jina abunda nake son na gaya miki babu me babu wasa da namiji ko kusa dasu karnaga kinje Inba haka ba zaki haihu ne ko gefen hijab dinki kika yadda Namiji ya taba tofa za'a ganki da ciki,ware idanu Jalila tai har dan India ma harshi aishima Namiji ne.
Nan Ammah taitayi mata nasiha Jalala tai shiru tana sauraron Ammah sundade tare kafin su sauko kasa tayi garau kamar ba itaba, Jalal ne ya sauko kamar bashiba yayi fes hada ido sukai da Jalilah ya maka mata harara ko kallon dining din beba yayi waje dan yau Jalila ta gama dashi ta cuceshi dakyar zai iya kai wani abu bakin sa.
Binsa da kallo Ammah tai sarai tasan shegen kyankyamin sa za'ayi kwanaki yanzu kafin ya dawo daidai cigaba sukai da break dinsu hankali kwance Jalala dai ruwan tea kawai tasha gaba daya atakure take jitake kamar an daddaure ta.
Jalal bedawo ba sai yamma yana shigowa ya hango Jalila alambu yau ba kiriniya ta samu waje ta zauna waje daya ta kurawa idanu da alama tunanin wani abu takeyi haryazo kusa da ita bata sani ba,kanta yadan doka fir Jalila ta mike da gudu ta falla saidata je canne sa dashi tukunna ta tsaya,kafin ta zube kasa ta rushe da kuka baki hangame Jalal yake kallonta.
Cikin kuka ta fara fadin shikenan ka gama dani yanzu idan cikinnan da kaimin yafito ya zanyi da rayuwa ta,kara kallonta yake kamar andasa shi yake maimaita kalmar ciki wane ciki kike Magana akai wanda kayi min yanzu dazu Ammah ta gayamin matukar nayadda ka sake tabani shikenan ciki zan gani ajikina gashi ka tabani yanzu.
Murmushi kawai ya saki aidama ke babu mai akanki kinga tafiyata idan kin haifi dan zan karbi abuna ina sonsa kara fashewa tai da kuka tafiyar sa yayi ya barta har birgima take akasa.Allah ya shirye ki Jalilah danja harya shiga maine parlo yanajin kukan ta,dakinsa yashige besan sanda ta gama tumbotsan ta tadawo gida ba.
Mrs Baba Bello ABUBAKAR
.........✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 65
Satin Jalal daya ya juya saboda ya baro karatu sosai har air port Ammah da Dad sai Jalila suka rakashi tana daga gefe dan koyaushe tana tuna gargadin Ammah nakarta sake ganin taje kusa da Jalal sallama yayi da iyayansa kamar karsu rabu haryayi gaba ya dawo baya akusa da Jalila ya tsaya kici gaba dayimin rainon dana ina nan ina lissafi kinga yau cikina kwanan sa uku.
Tuni hawaye ya fara bin kuncinta murmushi yayi yawu ce kamar babu abunda ya fada mata,kakun me kike keda bakya rabo da kuka shiru Jalila tai Jiki asanyaye tashiga mota sai tunani take yanzu da gaske cikinne da ita wane Irin duka Ammah zatayi mata intaga cikinnan kai Jalal ya cuceta ya gama da ita,sake saken data dingayi aranta kenan.
Gidan Inna suka wuce babu nisa atsakanin su babban gida ne shima megadi wangale musu get yayi yana yiwa su dad sannu da zuwa,tana zaune aparlo tana cin tuwo miyar kubewa wanake gani haka kamar jalili bata fuska Jalila tai dariya Ammah tai inna Jalila sunan ta tabe baki tai to ai shekenan,dad ta kalla dayake ta faman sun kuyar dakai kece kika sakoshi agaba Rukayya badan haka ba aini ban isa yazo ya gaishe ni ba.
Ayi hakuri Inna kinsan da ba haka yake ba aike Rukayya bazaki gane ba komai yana haduwa da haline yana tafe salaf salaf kamar mace ba dole abubuwa suhau kansa ba,shiru Ammah tai tasan mitar inna katse maganar tai ina wuni inna lafiya lau kun wuni lafiya lafiya lau inna,ahankali Dad ya zauna kusa da ita ina wuni anwuni lafiya,lafiya abinda tace kenan taja bakinta ta tsuke.
Inna ina wuni Jalila ta gaishe da ita lafiya lau ke waini yarinyar nan bata da lafiya ne kingantafa duk tayi laushi kaamar ba ita ba kodai shawara ce take damunta,lafiyar ta kalau inna ta fara hankaline shiyasa kika ga tafara nutsuwa.
Hirar Duniya suka shiga Ammah tashitai ta komai dakin Inna dan taba su damar tattaunawa tsakanin su ance tsakanin da da Mahaifi dan danan saiga inna ta sakko harta na bashi shawarar daya dage da addu'a sai magariba suka koma Gida.
Mom tana parlo tacika tayi fam kamar zata fashe kallon Dad take daga sama har kasa daga ina kake gidan inna da izinin wa ka fita daga gidannan koko raini ne ya fara shiga tsakanin nidakai da har kasa kafa kafita bada izinina ba saboda kaga danka yazo shine kake take umar nina to aigashi yanzu ya tafi zaka gane nika dinga bakanta wa zuciya sai ka dan dana kudarka agidannan.
Wuce muje kamar soko haka yayi gaba tabishi abaya Ammah tana tsaye ita da jalilah kamar anda sasu suna mamakin wannan karfin hali na mom akwai ranar kin dillanci abinda Ammah ta fada kenan taja hannun Jalilah da tai sakare tana bin hanyar da Mom suka bi kallon Ammah tai sam babu wani damuwa a face dinta amma zuciyarta bugawa take kamar zata fado amma akwai Allah shine zai musu maganin dukkan matsalolin su.
Gaba daya gidan saiya koma babu dadi Jalilah ta daina walwala kwata kwata Ammah tayi tambya harta gaji ga bakin cikin da Mom take cusa mata har wani goyata Dad yake yana zagayawa parlo da ita gata da shegen nauyi amma haka yake daurewa saboda kartai masa fada ya zamo dai rakumi da akala sai yadda akai dashi.
Hutun Jalilah ya kare sosai Ammah tayi mata siyayya da kanta takaita kauyan su inna tayi farin cikin ganin ta wuni daya sukai suka juyo tunda awashe gari za'a mayar da ita.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 66
Ammah taso kaita da kanta aranar tatashi batajin dadi baba direba ne ya mayar da ita har kuka tai na rabuwa da Ammah tasan zata kwashi bakin ciki awannan Gida.
Sunyi farin cikin haduwa da kawayan ta Nasmah Ismah Ablah,karatu suka cigaba dayi ka in da na'in tun Jalilah na jiran ciki harta manta da zancan babu ciki babu alamun sa,tuni ta warware ta dora daga inda ta tsaya babu sani ba sabo inkai mata saita rama shiyasa suke zaune lafiya aschl ita da kawayanta babu inda basa shiga kuma su kwana lafiya.
2years ago
Wasu kyawawan yan mata na hango suna tafiya cikin nutsuwa kamar bazasu taka kasa ba saida suka matso sosai kusa dani sannan na gane su yan hudu ne wato Jalilah da tawagarta takara fari tayi kyau kamar ba ita ba ga wata nutsuwa data saukar mata duk wannan rawar kan babu ita yammatan ci ya gama ratsata,tazama miskila ta gaske bazaka taba cewa itace Jalilah tsidigu ba kamar yadda daliban makarantar suka sama ta.
Jalilah Muhammad Uba cak suka tsaya da tafiya kafin tajuyo fararan idanun ta ta dora akan me kiran sunan nata,ya akai Ablah ta jehowa matashiyar tambaya Anty Zarifa kekiranta tace tayi sauri,ya mutsa face Jalilah tai yanzu nagaji zata iya ganina anjima Inda yiwuwar haka byee tadagawa yarinyar hannu datai sakale tana kallon Jalilah.
Tsaki Ismah taja wai ita wannan Anty Zarifa mene hadinta dake da kullum saita aiko kiranki,kafada ta dage nothing haka kawaii naji na tsani matar nan gaba daya batayi min ba kina ganin idanun ta tabbas akwai wani sabon Allah da take aikatawa bayan haka alamunta tana shaye shaye,cewar Jalilah Nasmah ce tai caraf kamar kin shiga Zuciyata nima bataimin ba ni kama da mayuma naga tanayi dariya suka saka suka tafa.
Runtse idanun ta tayi da karfi lokacin da yarinyar ta sanar da ita abunda Jalilah tace wai meyasa yarinyar nan take son wahalar da Ita sam bata da burin cutar da ita tafiso tabata hadin kai ta nuna mata soyayya ita kuma daga naira daya zuwa million zata iya kashe mata ba tare data ji komai ba,yatsa tajiza dole ne tai wani abu akan ta bata taba sawa ranta samun wani abuba bata samu ba wannan ma saita sameshi.
Sai bayan La'asar Jalilah tayo hanyar office din Anty Zarifa,tundaga nesa ta kura mata idanu kai yarinyar nan badai kyan sura ba mikewa tai daga kujerar ta oyooyo my dota rungume ta take niyayyar yi Jalilah ta koma baya da sauri.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 67
Turus Anty Zarifa taja ta tsaya tsaf Jalilah ta hade face mene nawani tahowa kina min oyoyo kamar me tarbar Mijinki bana san wannan rungume rungumen,basarwa Anty Zarifa tai aini amatsayin yata nake ganin ki saboda Allah be taba bani haihuwa ba,yaushe kikai Auran da zaki haihu tsit Anty Zarifa tai kardai Jalilah tasan wani abu akanta basarwa Jalilah tai ba wannan ba kinsan bana shiga abinda be shafeni ba.
Kiramme kikemin waskewa tai to zauna mana samun waje Jalilah tai ta zauna,dama kiran da nake miki akan wajan kwana ne baki dace da kwana acikin makaranta ba ga sauro ga gado dan mitsitsi inkinyi duba da skin dinki gaba daya ba kalar wahala bane gashi ina so nadunga koya miki karatu mezai hana kidawo gidana da kwana.
Dan jim Jalilah tai tana sauraronta dama saboda wannan kika kirawo ni eh saboda shine Numfashi Jalilah ta sauke to Ngd amma duk bana bukatar hakan kikalleni daga sama har kasa kinsan bana bukatar temako ni awajan Allah nake neman taimako,nagode da kulawa bye Anty tana sakin murmushi idanu Anty Zarifa tabita dashi dole nasan abunyi zaki gane kuranki afusace tabar office din nata.
Shirye shiryen tafiya hutu suke suna dawowa zasu shiga ss 1,aiyanzu Jalilah sosai tazama haziqa acikin makarantar in batazo ta daya a class din su to zatazo tabiyu kota uku bata haura hakan.
Karfe 9pm suna zaune suna tilawa ita da su Ablah,sun kusan hade karatun su ahalin yanzu suna idar da karatun Ablah tai caraf tamike yau jalilah ko kinki ko kinso abed dinki zan kwana haka kawai zafi yaita damuna kekuwa kinanan kinashan iska to aiko baki isa kikwanar min agadoba ko kinhau saina jawo ki kasa tashi Ablah tai ta ruga kan gadon ta haye Jalilah binta tayi tana janta tana komawa su Ismah na musu dariya.
Rike kugu Jalilah tai wai bazaku zo kutani janta ba kunsan wannan lukutar nauyin bala'ine da ita,to karfinki ya cece ki mana inji Ismah kefa Nasmah mezakice nima dai bazan wahalar da kaina akan bukekiya ba kungama saida safe bacci nakeji kwanciya sukai sunaiwa Jalilah dariya,dani kuke xancan duk saina rama abunda kukaimin dungure wa Ablah kai tayi saiki kwanta ai natacciya.
Oho dai babu yadda zakiyi dani Dan kinsan nafi karfinkine shiyasa kika wayance,koma dai mezakice kifada Allah ya kaimu gobe baki isa ki kwanta ba cikin dariyar tsokana ke innaga dama fa nadawo gadon gaba daya kuma mutum figagge babu yadda zaiyi dani kinsan mu lukutaye ake yayi,hararar ta Jalilah tai aiko ba haka abin yake ba gamu tan daidai wayake yayin masu kiba mune cillani ka cafe oga.
Fashewa da dariya sukai gaba dayan su Ablah kuwa ta shaqa ganin zasu maidata mahaukaciya yasa tai musu banza kamar tayi bacci,tuni bacci yayi awon gaba dasu.
Iskace ta fara kadawa me matukar dadi Ablah sake bajewa tai tana sharar bacci sabanin Jalilah data kasa baccin kirki in bata saba da kwanan wajeba sam bata Iya bacci saidai taita juye juye.Ahankali aka zuro hannu ta window aka zare sakatar da suka sa daya ke suna kusa da juna tsakin kofa da window babu tazara kuma sakata daya suke sawa.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 68
Sadaf sadaf mutum uku suka shigo kaitsaye gadon Jalilah suka nufa wani hanky suka shaka mata ahanci baccin yakara nisa sosai,tun zare sakatar farko Jalilah ta bude idanu sosai gabanta ya fadi ganin wasu dirka dirka da bakaken kaya kafin ta tantance suwanene taga sunnufi bed dinta gaba daya gumine yake keto mata babu shakka ita akazo sacewa tsautsayi zai fada kan Ablah dole ne tatemake ta kota halin kaka.
Daukar Amarya sukaiwa Ablah da jikinta ya gama saki cikin taka tsantsan suka fice daga room din harda ja musu kofa,durowa Jalilah tai daga bed din kafar Nasmah taja daya ke bata da nauyin bacci dan danan ta farka arazane tatashi dan bata tantance wanda yatasheta ba harzata kwallah ihu Jalilah tatoshe mata baki ke nice saidata ji muryarta ta sauke ajiyar Zuciya.
Wajan Ismah ta nufa yin duniya taki tashi akwaita da shegen bacci,hannun Nasmah Jalilah taja suka fice daga room din atsorace Nasmah take kallon Jalilah jin makarantar tsit babu alamun akwai wata halitta datake yawo acikin schl din,wai ina zamuje ne banza Jalilah tai mata tana cigaba da jan hannun ta tsayawa tai ahankali takejin sautin tafiya hanyar datakejin tafiyar nan sukabi.
Basu da wata tazara meyawa Jalilah ta hangosu wata hanya taga sunnufa da ita kanta bata taba sani da ita ba,cak masu tafiyar suka tsaya alamun sunajin wani sauti saurin sunkuyawa sukai suka buya gudun karsu hangosu Nasmah sarkin tsoro hawaye sai rige rigen zuba yake a face dinta,sunyi tsayuwa kusan minti daya sannan sukaci gaba da tafiya.
Wata shawara Jalilah ta yanke matukar ta barsu sukaci gaba da tafiya batasan inda zasukai Ablah ba karmadai ace ficewa zasi da ita daga schl din,ganitai sun tsaya awani waje sundire Ablah daya aciki taga ya dauko waya alamun akwai wanda zai kira dabaya suka koma daki daki Jalilah tafingabi tana tsahin kowa barayi sun shigo satar dalibai zumbur zakaga kowacce tamike za'a iya cewa cinikin Ablah aka zauna yi.
Suncika su Hudu da alamar tattauna wa akeyi,bazato ba tsammani sukaji ruwan dutsuna kota ina suna jifansu suna barayi barayi kankace me malaman su kowa yafito hankali tashe koyaya kai magana Makarantar amsa kuwwa take,kafa menaci ban bakiba tarwatsewa sukai suka bar Ablah awajan haka dalibai suka tisasu yuya guda babu tsoro bakomai akafara kasa tsere harda malaman su a kokarin su na kamo masu lefin.
Da kyar suka kamo mutum biyu biyun kuwa sunyi batan dabo duka aka rufe su shi na tashin hankali dan danan akai musu jina jina fata fata akai musu sannan aka kaisu dakin horo katon makulli aka saka aka kulle kofar.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 69
Clinic aka kai Ablah har gari ya waye bata farfado ba karfe 8am aka je fito da masu lefi za'a bude face dinsu kowama ya gansu kaf student suna tsaitsaye da jiran abude musu yan isakan mutanan nan su gansu suna da tabbacin mazane ayadda sukai shiri bazaka tana tantance macene ko Namiji ba.
Tsit filin makarantar yayi Uncle Bashir shine agaba wajan bude face din ta farko aka fara budewa,abunda yabawa kowa Mamaki yaya hauwa aka gani tai tsamo tsamo tasha shegen duka fuska akumbure nan hayaniya ta kaure harda masu son sake zuwa su sake laftar ta,da kyar Anty Binta ta tsawatar ta biyun aka budewa face abunda yafi girgiza su shine ganin Anty Zarifa kunyar duniya da bakin ciki yagama lullubeta.
Wata daliba ce take karewa Anty Zarifa kallo tabbas itace sai yanzu kwakwalwace ta tunatar da ita abunda ta manta abaya kamar anshafe mata tunanin sa sai ayanzu ta tuna da komai fashewa tai da matsanan cin kuka har abusa kaho bazata taba yafewa Zarifa abunda tai mata ba ta cuceta ta cuci rayuwar ta.
Abunda ya daurewa malaman kai ganin kusan fiye da kwatansu Kuka suke na bakin ciki da takaici tundaga kasan zuciyar su kukan ke fitowa tabbas duk abunda aka aikata musu bame dadi bane agare su,wata acikinsu data kasa danne zuciyar ta na nannagegen dutsan wuta ta dauka sai aface din Zarifa tuni goshinta ya fashe jini ya fara zuba,kowa da abunda yake sakawa azuciyar sa menene dalilin su na shiga har room su sato daliba.
Anty Binta ce tafara jawabi kamar haka.
Asslm Alaikum hakika muna godiya ga ÀLLAH daya nuna mana abunda ya jima yana faruwa acikin wannnan makaranta babu wanda ya farga babu wanda ya iya daukar mataki,tayiwu akwai wanda ya farga tuntuni amma wasu dalilai suka hana ya bayyana hakan ga kowa cikin kudurar ubangiji yau ga rana tazo dazamu tankade murairaye bara gurbi daga cikinmu.
Tayiwu masu laifi suna da hujjar kare kansu Matukar basu da wata kwakwkwaran hujjah zamu dam kasu a hannun hukuma dansu girbi abunda suka shuka.
Zarifa me zakice game da shiga hardakin kwanan dalibai asato miki yarinya matukar wani laifi ta aikata miki meya hana kijira gari yawaye sannan ki hukuntata,shiru tai ta kara sunkuyar da kanta bawai nadama take ba a'ah bakin cikin bata cika muradin zuciyar taba shine yafi komai bata mata rai akaro na farko ta fadi atarihin rayuwar ta wannan ne faduwar ta tafarko akan wata ficiciyar yarinya ta wargaza mata komai.
Muna sauraron ki,aibata da abin fada Anty cewar wannnan dalibar datake kallon Zarifa cike da tsana nizanyi bayanin dalilin satar dalilabai da takeyi dan jim Anty Binta tai hannayanta tahade alamar roko har wannan time din hawaye bebar zuba a idaniyar ta ba, Numfashi Anty Binta ta sauke ambaki dama Hajar fitowa tai gaban dalibai sun zubo mata ido kowa yana jiran yaji me zatace.
Kamar yadda kuka sani sunana hajar misbahu atarihin zamana awannan school bana shiga harkar kowa magana ma bata dameni ba amma wannan azzalumar matar ta cuceni ta gama da rayuwa ta,akwai wata ranar Laraba da bazan taba mantawa da ita ba ta aikeni gidanta nayi mata wanki banyi musu ba saboda ganin Malama tace tana da ikon sani kowane irin aiki.
Nafara yimata wanki cikin karsashi Inayi ina yan wakokina dawowarta ke dawuya naga tanayi min wani shegen kallo dani ban gane ma'anar saba sai nai tunanin kodai wankinne befitaba takemin kallon gargadi hakan yasa nasake dagewa na wanke kayan tas,na shanya nagama Anty na sanar da ita ok abunda tace min kenan babu sannu babu nagode kamar jakar gidan su.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 70
Wani tea tamikon sai tururi yake gashinan zauna kisha nasan kingaji kamar yadda ta fada hakanne dama dan abu medumi nake bukata na zauna nasha tundaga wannan rana banta ba fashin zuwa gidan taba atakai cedai wannnan makirar da kuke ganin ta cikakkiyar yar lazbian ce suna da wata kungiya haka take rarraba yayan mutane ansha fita da yara batare da kowa ya sani ba.
Matukar suka baki wannan tea kikasha to shikenan saidai ÀLLAH ya kwato ki daga kaidin su tamayar damu hajarta muke nemo mata kudi makudan kudade take samu ajikimmu bantaba tuna abunda wannan matar ta dorani akai barna bace sai yanzu dana dawo hayyacina nagane tai min babbar illah wadda bazan taba yafe mata abunda tai minba koda zai rage saura nikadai zan yafe mata tashiga Aljanna wllh bazan yafe mata ba takara sa fadar hakan cikin Kuka da tsabar bakin ciki.
Anty Binta kanta saidata goge hawaye tabbas ta yarda ba haka tabar suba sautari tana gani ake fita da yara daga makarantar amma bata taba yunkurin hanawa ba duk da tana son hana hakan amma hakanan takeji anyi mata dabai bayi.
Yaya hauwa ma kuka take sai ayanzu tadawo hayyacinta matukar cuta Zarifa ta cuce ta dan bazata iya tuna kudadan data samowa Zarifa ba kuma ko sisi babata takeba saidai ta kalmashe tasa ajakarta ruwa tasha har abada bazata yafe mata ba,dan ahalin da ake ciki ita kanta batasan cutar data kwaso ba Kullum kwana take tana susa prvt pant dinta harjini ke fita inta sosashi tarasa wanda zata gayawa matsalarta.
Dama tuni Zarifa tadaina yayinta tunda taga ta kwaso cuta tadaina kiranta koda wasa,duk bayanan da akeyi su Jalilah na tsaye tana tasbihi ga Ubangiji daya tseratar dasu daga sharrinta tana da tabbacin ita taturo asace sauyin wajan kwanciya yasa aka saci Ablah ba tare da sun tantance ba.
Hayaniya dalibai suka tayar abarsu su kashe Zarifa shine zasu huce daga bakin cikin data dasa musu azukatan su wasu da yawa sun fara dana sanin zuwa bording schl.
Tsawatar musu Anty Maimuna tayi daya daga cikin Malaman su.
Babbace sosai danta girmi dukkan malamai Matan dake schl din,cikin rawar murya tafara magana sosai abun ya daki zuciyarta.
Karku yi dana sani ko kadan da zuwa bording domin yanzu wannan masifa tagame ko ina wani bala'i ne daya game sako da lungu sai wanda Allah ya tsare ko yaushe muna tare da su muna ma'amala dasu agidane amakaranta ne ahanya ne maganar guda daya ce Addu'a da taka tsan tsan da wadda zakiyi mu'amala shiyasa ayanzu yadda tayi karanci matukar kikaga yar uawarki mace tanai miki mu'amalar da baki gane mataba ya zama wajibi kiyi gaggawar kauracewa daga gareta.
A day ansha samun wannan cases din tsakanin daliba da daliba babu a inda ba'a samun bata gari,haka social media sunan suna yada alfahasha kullum burinsu ya za'ai asamu sabuwar member ta shiga wannnan kungiya ina horar ku da taka tsan tsan koda ba anan ba acikin gida janku da sauran wajan harko kinku wannan babbar bata ce.
Ina me rokon Allah akan ya shirya dukkan zuri'ar musulmi ya tsaremu daga fadawa mummunar halaka ya shiryi masu yada mummunan alfasadi sosai tayi musu Nasiha meratsa zuciya dabyawansu sun zubar da hawaye dajin kara tsoron Ubangiji imani yasake shiga zuka tansu sunyi Alkawarin bazasu sake aikata wani abu makamancin haka ba suna rokon Allah yafiya akan abunda suka aikata abaya.
Yaya Hauwa tafi kowa shiga tashin hankali da nadamar abubuwan data aikata abaya,oganniyar kuwa kodar bataji azuciyar taba saboda zuciyar ta gama bushewa da rashin imani tunanin yadda zata dau fansa akan Jalilah take dan duk asanadin sonta asirinta dake lullube ya tonu.
Yan sanda ne sukazo sukai gaba da Zarifa ba ahada da yaya Hauwa ba itama bayin kanta bane ko yanzu taga ishara tunda gashi tasamu tsarabar cutar data kwaso wadda batasan kalar taba itakadai tasan masifar da take ciki ga gabanta dayake tashin wani mugun wari ko kusa da ita kaje saikaji hakan.
Allah ka karemu da fadawa halaka.
Ya Ubangiji ka kare mana dukkan zuri'ar mu kanann mu da yayyemu yayan mu da dukkan yan uwa musulmi Allah ka shiryar damu abisa tafarkin daidai tafarkin addinin Musulunci😭😭😭 Ameen
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 71
Haka yan sanda suka tasa keyarta awulakance aka fice da ita,dan danan abinda ya faru a school din yakarade ko ina akarasa wanda ya dora abin a social media saiga iyayan yara asukwane suna ta tururuwar daukar Yayan su duk yadda Malaman suka so fahimtar dasu kin Fahimta sukai burinsu ayau basai gobeba yaransu su kwana ahannun su.
Babu yadda zasiyi haka suka barsu sukadinga daukar yayan sa dayake makaranta ce tamasu rufin asiri motoci ne ke layi wannan tana wane wannan waccan tana wane waccan,acikin wanda akazo dauka harda Ablah da Ismah wadda Mahaifiyar ta da kanta tawanko kafa tazo har Makarantar rungume yarta tayi tana kuka, Murmushi Ablah ta saki Momma kidaina kuka haka ALLAH ya tseratar dani bisa kudurar sa da kuma taimakon kawata agareni.
Sakin Ablah tai ta rungume Jalila Allah ya yimiki Albarka yarinya Allah ya kiyaye ki daga dukkan wani sharri nagode da taimakon da kikaiwa diyata bazan taba iya biyanki ba saidai ALLAH ya biyaki.
Murmushi Jalilah ta saki babu komai Mama aimun zama daya zan iyayin kowace irin sadaukar wa akan kawaye na kuma yan uwana,to Allah Yayi muku Albarka baki dayanku Ameen suka amsa atare,sallama sukai cikin jimamin rabuwa da juna da tunanin zasu sake zama amakarantar ko bazasu sake zama ba.
Duk yadda yake gudu gani yake kamar ana maida shi baya,yana zuwa ya danna hancin motar sa saboda yau babu Maganar rufe get abude yake saboda shige da fican da aketayi parking ya daidaita kafin yafito daga motar.
Saidana danyi tunani na wasu sakanni sannan na gane wanene mammallakin wannnan motar ya kara girma ya kara kyau wani kwarjini da haiba sun kara lullube shi durkwar sa kenan yasamu labarin abunda ke faruwa bazai taba samun sukuni ba saiya zo ya dauko Jalila yar rigimar sa.
Anty Binta dake tsaye tana tsinewa Zarifa Albarka kwando kwando ta hangoshi ya jingina da motar sa yana rarraba idon aina zai ganta,asanyaye ta karaso inda yake sallama taimasa ya amsa da Murmushi a face dinsa,kazo daukar ajiyarka kenan Murmushi kawai ya saki hakane tana ina kaima bazaka barta ba daukarta zakai barin Jalila makarantar nan zamiyi babban rashi.
In harda yiwuwar ta dawo zan dawo da ita madam kuma ALLAH yasa to,gaba tai ina zuwa har Inda suke tsaitsaye taje ta sameta Jalila yayanki yana jiranki abakin get jitai gabanta ya fadi yayanta Jalal take nufi tabbas shine ma tsahon shekaru biyu kenan rabon data ganshi.Nasmah ta kalla da tuni idanun ta suka ciko da hawaye ganin zasu tafi subarta ita kadai.
Dafa kafadarta tai kiyi hakuri Nasmah ina da tabbacin kema za'azo adauke ki bamu rabuba munzama yan uwan juna zumuncin mu bazai taba yanke wa ba,gyada mata kai Nasmah tai tare da rugume ta zanyi kewarki Jalila nima haka tafada idanun ta na cikowa da hawaye tayata daukar kayanta tayi Ahankali suke ta kawai kamar bazasu taka kasa ba.
Tundaga nesa ya kura mata idanu duk tsayin shekaru bazai manta da Jalila ba takara kyau ta kara girma da alama hankali ya fara ratsata,ajikinta taji kallonta akeyi dan jitai idanuwa na yawo akanta dagowa tai suka hada ido saida gabanta ya fadi ganin yadda Jalal ya canza yasake zama handsome ga wani kwarjini dayayi mata wanda ada bata ganin wannan.
Cikin rada Nasmah ta matso kusa da ita shine Uncle j din da kike ta bamu lbr amma ya hadu sosai, Murmushi kawai tayi shine mana ko yayi kasuwa ne dariya Nasmah tasa wani tab aini ba yanzu za'ai min Aure ba sainayi karatu mezurfi inji Abbana,kawai dai kice be miki ba um nifa ban fada ba Jalilah.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 72
Agabansa ta tsaya amma sam taki yadda su hada idanu kwarjinin sa yafi karfin tatsaya ta tsira masa ido kamar yadda ta saba abaya,tundaga sama har kasa yake kallonta Murmushin gefan baki ya saki kafin ya juya wajan Nasmah dayake gaishe shi,amsawa yayi kadaran kada han dakansa ya karbi akwatinta ya saka abut kafin ya shiga ya zauna.
Sallama suka karayi da Nasmah kafinta bude back sit tana kokarin zama,ashe zamu kwana awajannan tasan abunda yake nufi Ahankali tafito ta koma gaba harsai da suka fita suka daina dagawa juna hannu ita da Nasmah.
Numfashi Jalila ta sauke sàida Jalal yadan kalleta wai itama ta zama yammata ko dan mursawa yayi.
Uncle j tafada cikin wata siririyar muryar ta sàida yaji wani yar sunan data kirashi yake maimaitawa sosai sunan yamai dadi,um abinda yace kenan bude idanun tai da suke lumshe ta dora akansa baki iya gaisuwa ba, zumburo baki tai gaba to ba gaidakai din zan ba da can aibaki gaidani ba.
Yaushe kadawo ta cillo masa tambaya dazu waro idanunta tai dazu gira ya daga mata kuma kataho daukata meyasa,bankai nazo daukarki ba kenan Madam Jalila dariya tasaka nidai ba madam bace kamar wata yar lukuta,hm itace mana koda haka kike haka nake ah karya kike ba ahaka nasanki ba shiru tai tana kallon sa mekake nufi kafada ya dage nothing bata sake magana ba haka shima har sukaje gida.
Gaba daya gidan yayi wani iri babu walwala su kansu masu gadi sun rage hira da nishadi atsakanin su laifi kadan Gimbiyar gidan zata saka akore ka,shine agaba tana bayansa tana jan akwatinta akofar parlon suka cake Mom ce zaune kafa daya kan daya tana taunar cimgom kas kas takara kiba sai muninta ya kara fitowa,daga can gefe Dad ne arakube akasa kamar wani almajirin dake aike aiken gida.
Kallon kallo akeyi tsakanin su ganin su kadai sàida zuciyar Mom ta harba ganin yadda suka kara girma da kyau uwa Uba wata muguwar da cewa data hango sunyi,mikewa tsaye tai tana sakin wani munafukin murmushi my son jiyayi kamar yaje ya kutufi bakinta tsabar yadda yaji ransa ya baci data kirashi da danta Allah ya tsare ni dazama danki.
Ko kallanta beba yashigo parlon kai tsaye wajan Dad ya nufa da yayi tsuru yana kallon sa mikar dashi yayi yaja hannun sa ko waiwayowa beba dan gudun kar Mom ta hanashi hawa rabinda yahau sama yafi shekara sabida karyaje wajan Ammah Mom takasa tatsare babu Inda zai matsa harkokin kasuwancin sa dayawa sun dawo hannun ta ga asitin sa yana karkashin ikon ta.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 73
Kallo tabisu dashi kamar zuciyarta zata fito kwafatai ta dawo da kallonta kan Jalila data nemi waje tazauna akan sofa kafa daya kan daya,wani matsiyacin kallo Mom keyi mata ke sauko nahau kihau matsayimmu daya dake kenan to sauka tunda badaga gidan Ubanki kikazo da ita ba.
Murmushi Jalilah ta saki ah Mom duniya Mom katafila sarkin aiki ashe haryanzu aikin nakan tudu be warware ba gaskya fa kin shana kin kuma shakata kin murza kambunki yadda kike so nawani dan lokaci shiyasa gakinan him kamar ana huraki kawai tsabar cin dadine da kwanciyar hankali jinjina rigiji gabji.
Mom data daskare atsaye tana nanata sunan nakan tudu,kinga Mom basai kinyi wani tunani ba kimanta kawai bana son ko yaya wannnan kibar taki tasamu tangarda gwara kitaci gaba da hawa yadda inkinje can walakiri yadakike yadda ya kamata,am amma bana barki haka karna cika ki da surutu tsaraba ce nabaki dama kinga ai banayi tafiya nadawo haka ba dole asan Jalilah tsidigu ta dawo.
Bye nace ba dan Allah kimikamin gaisuwa ta wajan su dindimari kafin miyi gaba da gaba kisanar dasu Jalilah ta dawo su shirya tsaf adora daga inda aka tsaya ba gudu ba ja da baya inanan ba inda zani ahuta Lafiyar.
Wani kululun bakin cikine ya tsaya mata awuya wai meyasa Jalilah tarainata haka wani abune yataba hadasu ko yayane kafin su san juna da har wannnan rainin yashiga tsakanin su,dole ne tadauki mataki yanzu ne lokacin daya kamata ta tilasta Dad yasa Jalal ya Auri Rufaida shine irin mijin da take son yarta ta Aura mijin nunawa sa'a wanda kawayanta bazasu taba kushe shiba.
Dakin Ammah tashiga da sallama Amsawa sukai ita da Dad da yau Allah ya kwato shi daga hannun Mom,fadada fara'arta Ammah tai Jalilah sannu da hanya murmushi ta saki har kusa da Ammah taje ta zauna akusa da kafafunta,dad anwuni lafiya face sake ya amsa lafiya lau Jalilah yammakaranta har kingama Makarantar ne Girgiza kai tayi akwai saura dad to Allah ya taimaka,mikewa yayi banaje dakina nadanyi bacci.
To afito lafiya Ammah ta fada tana kallon sa cike da tausayi,fita yayi dawo da kallonta tayi kan Jalilah kare mata kallo takeyi harsai da Jalilah tagaji wai Ammah na canjane ina kallon kine ko wani abu ya sameki yau bakiga yadda nashiga tashin hankali ba harna dauki matafina zan taho daukarki saiga Jalal yace na zauna zai dauko ki amma wannan mata bataji dadin halin ta ba.
Allah ya kara kiyaye gaba nidai tunda kindawo lafiya Alhmdlh bazaki sake komawa ba,shikenan Ammah bazan karasa karatuna ba to sai akace imani sai acan zaki karasa ga day nan sai asaki hankali na saiya fi kwanciya dama can iyayin Jalal ne wai shi bording sai kinfi karatu sosai,aikuwa inayi sosai kome zakice bazaki koma ba to Ammah.
Tashi kije kiyi wanka saiki sakko kuci abinci keda yayan ki shima beci ba to tashi tai tafita Ammah ta bita da kallo.Tsaf dakin yake saboda Ammah da kanta ta gyara mata dazu Iya dai haryanzu shiru daga tafiya ganin gida danta ya riketa wai tagama aiki shine haryau shiru bata dawo ba.
Tana fitowa ta zura doguwar riga mara nauyi tana fitowa Jalal na fitowa three quarter ne ajikin sai single kannan yasha gyara kamar gashin larabawa akwance luf luf kallon sa Jalila tai uncle j wai me kake ci haka dan kallonta yayi a kaikai ce menake ci name naga fatarka ta kara kyau ka kara fari kamar ba kaiba,um ke kuma fa muni kike kakara hancinki kamar na boto rami.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 74
Bata face tai tana kallonsu kamar zatai kuka nidin ke dinfa gaba yayi yana murmushi biyo bayansa tai Fuska turbine harya zauna a dining din yana kiciniyar hada tea karba tai ta hada musu sannan ta zauna,harzata kai tea din baki ya rike mata hannu kallon sa tai da tambayar lafiya,ai baki gama shiryawa ba nagama tuna dai akwai saura name kin manta baki cire riga ba.
Saurin kallon sa tai da sauri tamike zatabar wajan idanun ta arufe ba karamar kunya ya bata ba,caraf ya rike hannun ta yana dariya ya zaki tashi daga nasamu ladanki na tuna miki abinda kika manta,bubbuga kafa tafarayi akasa nini kacika ni tunda abunma hakane saurin kauda kansa yayi daga kallonta ya kadai yasan abunda ya ganowa kansa,cikin dauriya yace to shikenan nadaina zauna namanta fa yarinyar tatashi daga kwaila.
Sake kwabe face tai kakuma ko,bakinsa ya bige kai bakaji ko ka kiyayi gingimari Jalila dariya suka saka ashe yanajiyo su dramar su ta dazu ita da Mom.
Shigowar su kenan daga gantalin su sukaja suka cake suna kallon yadda suke break cikin Nishadi da farin ciki kamar wasu masoya,wani kishine ya turnike su duka su biyun ahaukan Rufaida ita Salima take tayawa kishi,kallon su suke kanar tv sukan su sun hango yadda sukai masifar da cewa fuuuu suka wuce su ko nuna sunsan da tsayuwar suma basiba.
Cigaba sukai da break din su yana yimata tambayoyi akan karatun ta tana bashi amsa suna gamawa suka mike daki Jalilah ta koma shikuma ya fice.
Wai Mom meyasa bazakiyi wani abu akai ba kina ganin waccan yar iskar yarinyar tadawo kinga yadda ta kara kyau ta kara wayewa mujikinta ya murje kamar bada kauye tazo ba,kwantar da hankalinki Rufaida badai ya gama karatun ba ya dawo to dole za ai auranku bari uban nasa yagama rabe raben yadawo Auri ba gudu ba ja da baya kamar anyi angama,ah to yanzu naji magana gwaradai kisan abunda ya kamace ki shigewa tai daki tabar Mom tana babatu kamar zautacciya.
Ma'aruf na'am Amarya bakya laifi kona kashe dan masu gida ba,ba wannan ba wata magana zami dakai me muhimmanci ina so kirike wannan akwanyar kanka ba zancan wasan yara zamiyi ba,ai maganar ki abar ji ce hajiya yawwa.
Dama zancan Rufaida da Jalal na hada Auran su da mukai acan kwanakin baya to ai wannan duka yayanki ne kina da ikon zartar da kowane hukunci akan su kamar kin shiga Zuciyata abunda nake so nagaya miki kenan tun rannan sai maganar ta kwanta mun, Murmushin samun nasara Mom ta saki to yanzu sai mufara tsara yadda biki zai kasan ce ai yanzu ma kuwa.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 75
Kai tsaye daga dakin Mom dakin Jalal Dad ya wuce yana zaune yana aiki a laptop ganin Dad yasa shi ajiyewa yana mamakin meya kawo shi dakinsa,samun waje Dad yayi ya zauna barka da hutawa Dad barka aiki kake ne eh aiki nakeyi,to Allah ya taimaka Ameen shiri ne ya biyo baya kafin Dad ya gyara face dinsa babu alamun wasa kamar yadda Mom tayi masa gargadin karya yadda yafito daga dakin Jalal ba tare da kwakwkwarar magana ba.
Magana zami dakai Jalal kuma kai tsaye umar nice ba shawara zan baka ba,cikin mamaki Jalal ya dago kai yana kallon Dad wace magana ce haka gyada kansa yayi alamar yana sairaron sa.
Magana ce akan yar uwar ka dan zumuncin ku ya kara karfi na yanke hukuncin hadaka Aure da ita,wacece yar uwa ta rufaida yar wajan Saratu jin maganar yayi kamar saukar aradu Rufaida wacece ma Rufaida sai lokacin kwakwalwar sa ta gayamasa wadda yake nufi ya tabbatar lallai Dad baya cikin hayyacinsa,dama wannan itace maganar dan haka kafara shirin biki kuma ka sami yarinya kudaidaita.
Tashi Dad yai yafice yabar Jalal da binsa da kallo tuni idanun sa ya rine da bacin rai ko kaf itakadai ce tarage mace aduniya bayajin zai iya zaman minti daya da ita balle harya Aure ta kome zai faru saidai ya faru amma bazai taba Auran yayan Saratu ba.
Ammah data fito daga part dinta tahangi Dad yana ta zuba sauri zaije ya gayawa Sarauniya sako ya isa inda aka turashi,dakin Jalal din ta nufa halin data ganshi ya masifar tayar mata da hankali har wannan lokacin yana durkushe hakoransa har haduwa suke tsabar fusatar da yayi huci kawaii yake fitarwa sarai tasan Jalal matukar wani abu ya fusata shi baya iya control din zuciyarsa.
Fridge ta nufa ruwa ta dauko mai tai tsiyaya acup tabashi kadan yasha yana sauke numfashi a kejjere kusa dashi ta zauna tana shafa kansa ahankali da buga bayan sa, ahankali nutsuwa ta fara sauka azuciyar sa saidata tabbatar yasamu nutsuwa sannan ta tambaye shi,abinda Dad ya sanar masa shi yagaya mata tsai tayi na wani lokaci tadade da hasashan abunda ke zuciyar Saratu.
Murmushi ta saki kan wannan zaka kashe kanka abanza Jalal kabarni da ita intasan wata ai batasan wata ba bazan taba yadda na hada zuri'a da Saratu ba ninasan wacece ita ka kwantar da hankalinka my son shiri yayi ya sake lafewa ajikin ta cigaba tayi da masa nasiha harya warware suka shiga hirar su.
Tana shiga dakinta takira inna bayan sun gaisa ta labar ta mata abinda ke faruwa,uhm lallai Saratu to in atafe ta wuni mu atafe muka kwana ko afuska karki nuna baki amince ba kibarsu suci gaba da shirye shiryen biki,shikenan Inna Allah ya kara girma Ameen,aje wayartai tabbas abinda inna tace haka za'ai.
Tun Mom nakasa kunnan taji Ammah tatubure bata yadda ba jin shiru yasa tayadda tabbas aikin boka yayi kyau tunda dama yace zai daurewa kowa baki babu wanda zaiyi jayayya da wannan Auran kowa harkar gaban sa ya kama haka Jalal koda wasa benuna ma yasan da zaman Maganar ba yaci gaba da harkokin sa.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 76
Karfe 9pm Jalilah na zaune a parlo su Mom aka shigo da kaya rikici rikici anlodo siyayya kamar wanda zasu bude shago,me musu wanki ne ya dinga shigowa da kayan sàida yagama tas ba sannu ba ngd awulakance ma suke kallon sa,wash Mom gaskiya na gaji badan siyayyar Aure na bace aida bazan yi wannan wahalar ba duk dama order akai amsowa ce tamu.
To banda abinki Rufaida ai wannan ba wata wahala bace keda kinkusa kizama amarya yan aikatau dayake ba farin jini har yau shiru kakeji sai mugun bakin jini gwarama akoma kauye ko asamu me karba da hakuri,kwashewa sukai da dariya sarai Jalilah ta gane da ita suke karkace kai tayi tana kallon su face dinta dauke da Murmushi.
Ah ma sha Allah ashe su dindimari ansamu shiga da kyar da malamai da bokaye da yan tsubbu da yar me ganye nasan babu wadda ba atsugunna agaban ta ba,dan bata face tai amma ko wanene wannan angon na tausaya masa zai kwashi ragowar karatan banza to Allah na tuba inhar ba uwar sace tacemai jeka kagani ba mezaiyi da wadannna da babu wanda besan iskancin su agarinnan ba.
Koda kai kuyi hakurifa ashema zancan be shafeni ba dama wai duk acikin taya murnane dan bazan samu damar zuwa bikin yayan gata ba dan babu shakka Matukar naje bikinki kisa aranki mijin nizai Aura yaga yar camas mas taya zai dauki kayan nauyi,zabura Rufaida tai ta kawo mata duka dan Ubanki in Jalal din yazo Aurena ki hana.
Sunan Jalil ne kawai ya dira acikin kunnan ta batasan meyasa taji zuciyarta na lugudan daka ba basarwa tayi bata kara ranka musu ba tai gaba wani abu takeji data rasa menene ya tsaye mata akahon zuciya gaba daya kasa tafiya yayi daga makoshinta,azafafe tatashi dakin Jalal tanufa idanun ta arufe tsabar masifar da take cinta harta wuceshi aparlo bata ganshi ba.
Binta yayi da kallo da mamakin meya fito da ita haka ko dan kwali babu akanta sai kalbar da akai mata har kafada,bata ganshi a bedroom din ba amma har kan bed din tahau ta laluba kodai itace bata ganshi ba jin baya kai ta sauko burinta kawai tayi ido biyu da Uncle j tambaye shi sannan ne zuciyarta zata huta.
Sake futowa tai sai lokacin ta hangoshi kamar tababbiya haka tai kansa bawani ba yani tarufeshi da duka da yakushi ganin zata yayyagemai fata ya riketa gam sai lokacin ta fashe da kukan da ita kanta batasan kona menene ba yana jinta saidatayi kuka me isarta sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya.
Hanky yasa yana goge mata face bige masa hannun tayi da rinannun idanun ta take kallon sa,murya acunkushe ta jehomai tambayar wane Jalal din Rufaida zata Aura sakare yayi yana kallon ta waidama duk akan haka yasha wannan jibgar abanza.Murmushi ya saki danya sake kular da ita Jalal nawane agidannan nine wanda zata Aura dafe goshin sa yayi kash wai dama baki da Labari kina matsayin babbar kawar Ango.
Kallon sa kawai take ranta na dada baci,kuma acikin hayyacinka kake hada kanka da Rufaida duk yammatan garinnan karasa wadda zaka zaba sai ita ko bakasan yar iska bace,tabe baki yayi ina ruwana dawani iskancinta aishi so ba ruwansa da wannan tabbas matukar ka Auri Rufaida Ammah ce taima baki batare danasan lokacin ba.
Gimtse dariyar sa yayi wane irin baki ta tsine maka mana shiyasa gashinan zakabi duniya bantaba zatan haka kake ba seyau to matukar ka Auri Rufaida babu ni bakai ko ahanya bamu hada alaka ba.
Tashitai afusace zatabar dakin caraf ya ruko hannun ta haba kawar amana yanzu kawai dan zanyi Aure shine ba zaki tayani murna ba nina dauka duk abinda abokinki keso kema zaki so,harara ta dalla masa ALLAH ya kiyaye kaidai kaje kaita sonta amma bandani Jalilah nika cikani karka shafan tsinuwar da akai maka,sake barkewa tai da kuka kamar wadda ake duka.
Ganin bazai saketa ba sunkusa tai ta gantsara masa cizo ba arziki ya sake ta yana yarfe hannu ficewa tai gaba daya daga part din ko ganin gabanta batayi afadarta Ammah zata taya wannnan yakin,bin hanyar data fita yayi da kallo kafin ya saki murmushi yasamu amsar dayake son sani cikin sauki shafa kansa yayi yana sakin wani munafukin murmushi.
Mrs Baba Bello ABUBAKAR
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 77
A Wannan dare gaba daya Jalilah bata rintsa ba aiko kan safiya Zazzabi da ciwon kai sun rufeta jin shiru yayi yawa Ammah ta leko dakin tayi wujiga wujiga da ita har lokacin Kuka take idanun ta sunyi suntum.
Da sauri Ammah takarasa harkan bed din gaba daya tasata ajikinta jikin Yayi zafi rau Jalila meyasa meki haka dama baki da lafiya amma baki fada ba shru taiwa Ammah idanun ta arufe ita yanzu Ammah bata san Jalila haushinta take jiba damme zatayiwa uncle j dinta baki yaje yabige da Aurar rufaida,juyin duniya Jalila kinyin magana tai Ammah saitayi zatan duk rashin lafiyar ce ta hanata yin magana.
Phone tadaga Ring biyu Jalal ya daga kai fito ka dubamin yarinya bata da lafiya,ajiye wayar tai mintuna 2 yakara saigashi ya shigo har bakin bed din yazo yana kallonta meyasa meta Ammah,ina zansani nima yanzu nashigo naganta ahaka yin duniya taki tai magana kasan dai kafiyar Jalila taurin kaine da ita kamar ganda.
Dan Murmusawa yayi taba wuyanta yayi jin zafin yayi yawa,towel ya dauka ya shiga toilet wani karamin baho ya dauko ya zubo ruwa acikin sa zama yayi abakin bed kusa da Ammah sai anrage mata zafin jikinta.Ammah data tsuramai ido tana kallon sa batace komai ba kokarin jawo Jalila yake bige hannun sa Ammah tai au ko jikinma kai zaka danna mata.
Eh Ammah eh lallai na yadda baka da hankali tunda agarin mahaukata ake meze hana banbaka ita ba ka danna mata jiki,to Ammah haryau fa Jalila yarinya ce aah motsin gado ce,ko yanzu naimata Aure wata tara saita haifomin jika tashini kafice kaban waje jin inda Ammah ta dosa tsam ya mike shi aganin sa Jalila ma nawa take saunawa yana yimata wanka shine yanzu za'ace bazai tai maka mata ba.
Ammah binsa tai da harara tanajan tsaki tayadda Jalal dan farine beida hankali yarinya nono ritsi ritsi akirji zaice mata wai ai bata girma ba daba tanan haka zaizo yayi wannnan aika aikar kwafa tayi zamu gauraya dakai.
Dakyar Jalila ta tsaya tana kare karen kirji sàida amma ta daka mata duka zaki tsaya ko saina kira Jalal din shiyayi miki uwaki zangani dazaki dinga tirje tirje koba vest ce ajikin kiba matukar baki tsaya ba itama yanzu zan tsigeta,shiru Jalila tai Kunyar Ammah tagama lullubeta saidata tabbatar jikin ya sassauta sannan ta mayar mata da kayanta daukar phone tai saidata kusa tsinkewa ya dauka inkaga dama kazo ka duba ta.
Kit ta yanke kiran face akumbure ya tashi box ya dauko saicin magani yake shi alallai fushi yakeyi,banza Ammah tai masa magunguna ya bata intaci Abinci tasha tashi Ammah tai bari na hado mata tea saitasha maganin fita tai daga room din.
Kadan Jalila tadan bude idanun ta jin shirun yayi yawa yana tsaye akanta kamar wani megadi hada idanu sukai ta zabgamai harara bude idanun sa yayi nikike harara murguda masa baki tai ta juya mai keya,tab lallaima yarinyar nan kin rainani kan bed din ya hawo yaurde mata baki kuka ta faahe dashi amma Jalal besake taba sàida yaji tahowar Ammah ya cikata yakoma gefe kamar babu abunda ya aikata.
Kukan me takeyi kowani abu kai mata? ni babu abunda nai mata haka kawai take kuka bansan abunda take tunowa ba da alama akwai wani abu da yake damunta akahon zuciyarta yakama ta kitambaye ta,jiwani dan raining hankali Jalila ta ayyana a zuciyarta.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 78
Ammah batace mai komai ba tatashi Jalilah zaune dakyar ta iya zama wata hajijiya takeji tana katan tanwa da ita sàida takaita toilet taima bruh sannan suka dawo kadan tasha tea din wajan shan magani seda akasha daga da ita tana kuka tana komai tasha maganin sannan ta kwanta saidata fara bacci suka bar dakin.
Kasa Ammah ta sauka Mom da iyalanta ana zaune sai Dad da yake zaune akan sofa gaba daya hirar yadda biki zai kasance sukeyi.
Inna ce ta rangada sallama amsawa sukai gaba dayan su sàida gaban Mom ya fadi tasan zuwan inna ba Alkhairi ne agare ta ba,cikin yake take fadin sannu da zuwa inna yawwa zaka tai tana wash kai nagaji zaman mota mafa wahala ce oh nasara babu Abinda be kera ba amma dan kan uba babu shi ba halittar dan Adam dan jakar Uba.
Dariya suka sa jin inda Inna ta dosa har kasa Dad ya duka yana gaisheta amsawa take kadaran kadaham saidata sha ruwa ta huta sannan tajuyo tana kallon Rufaida da Salima oh to wacece Amaryar acikin ku cikin jindadi Mom ta nuna Rufaida munafuka harwani sunkuyar dakai take wai ita taji kunya,annamimiya Inna ta fada azuciyarta jita kamar ta ÀLLAH nanko tanacan tana tsula tsiyarta.
To!! Allah dai ya sanya Alkhairi yazabawa kowa daidai da abunda ya dace dashi ameen suka amsa babu wanda yagane me inna take nufi sai Ammah data san magana cikin magana ta yaba musu,toke saratu haka ake lamarin duniya Aidole aje dangin uban yarinya anemi Auranta acan in sun bamu shikenan.
Tuni gumi ya fara yankowa Mom yaken dole ta kakalo aidama inna naga komai na gidane dadinsu ma ai ya isa ya wakilceta awajan daurin Aure,aina kikaga anyi haka agarin mahaukata ko aiko zai wakilceta sai anga dangin Ubanta awajan ai duk wani da nagari da Uba yake ado ba rigar aro ba.
Wannnan matar tanaso ta jikamin aiki wai meyasa inna tafiye shigarmun rayuwa ne,kallon juna sukai inna da Ammah suka saki Murmushi tsagal dad yafara fadin ai Inna gaskiyar Sarah ne tunda yarannan awajena suke aini ya kamata nazama waliyinta,agidan ubanka zaka zama waliyin nata kakiyaye ni dannan kafita daga idona na rufe saboda hauka akeyi kaida za'a Auri danka babu bincike ba komai sai kawai ka kwakwasawa danka yarinya.
To ba haka nake ba nina san ya kamata ba hauka nake ba tsufana bekai na manta abunda ya dace nayi ba,ke kuma ina jiranki kiyimin kwatance yanzu basai anjima ba ina komawa gida nasa yan uwansa sutafi nemar masa Aure gurin dangin Ubanta.Duk iskar dake fifita Mom bata jinta tuni ta jike sharkaf da gumi sai rarraba idanu take to inna kinsan dangina ba anan suke ba suna can ikara to Allah na tuba ko a fatakot suke ai zuwa za'ayi balle ikara.
Mom tanaji tana gani sàida tabawa inna address din gidan su azuciyarta ta tsinewa inna babu adadi to kokefa yanzu hakan baya fiba gwara adingayi ana sanin juna.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 79
Innalillahi kai dannan da kata sanda zaka auto saratu kana nufin bakai bincike ba ko yaya ai Inna kekikace basai anyi wani bincike ba karkamin karya ni nafada wllh Inna kece to Lokacin bana hayyacina to wllh yanzu hannun agogo ya dawo baya bincike biyu zaayomin na Uwa da ya kasani daga wannan rana Auran ka da ita yana tangal tangal matsawar naji abunda beminba waje zasiyi daga ita har yayanta.
Kuka Mom ta Fashe dashi wai inna meyasa bakya kaunata,ke karki dauramin jakar tsaba kaji sibini bantaba cewa bana kaunar ki matukar halinka bemin ba shine zamu dinga samun sabani,yanzu Rukayya data san ya kamata kinji muna haka da ita aini ba amunafurci dani abunda yake raina shi nake fada ah to.
Tashi Mom tai fuuu tanufi part dinta binta abaya sukai cike da tsanar inna ko ina ruwanta da danginsu oho Aure dai ba fashi haka Rufaida take Ayyanawa Salima kuwa tikar dariya take azuciyarta Allah yasa Auran ya wargaje kowama ya rasa amma aface dinta bazaka taba gane hakan ba tayi kicin kicin da face kamar bata taba dariya ba.
Zama sukai kusa da Mom data shiga zuzzurfan tunani yanxu in akaje bincikennan aishikenan ta shiga uku ina zatasa kanta,ya mutsa face Salima tai wai Mom menene Abun tada hankali daga maganar danginki dana Ubammu nima nadade ina son sanin su wllh in sukazo biki ai kinga duk zamusan juna banza Mom tai mata wai Mom bakije menake cewa ba.
Banjiba sainaji duka tukunna ah daga tambaya alabaki hakuri bana tashi dama wannan damuwar bata shafanba tunda bani zaa Aura ba,wainikam Salima kodai bakin cikin Auran nan kike min inji Rufaida data tsurawa Salima ido Murmushi ta saki bakin cikin me zan miki ana zaune kalau raina fes yake ba hawan jini ba ulcer ba bakin cikin da namiji kedai da bakin cikin ke damunki kije kiji da Abunda ya dameki.
Fita tai tana sakin murmushi ranta kal kamar takadda waka ta kunna ta fara cashewa babu Abinda ya dameta.
Muskutawa inna tai ke nikam ina Yarinyar nan tatafi naga banganta ba,ayya Jalila ai tana daki bata da lafiya oh ÀLLAH sarki yarinya me hankali taso ta nai mata sannu to inna sanda Ammah tashiga tana zaune ba laifi tadanji dadin jikinta amma har Lokacin face dinta aturbune take,ah ma sha Allah jiki yayi kyau kita so inna tana kiranki zaku gaisa to Ammah.
Ahankali ta mike tabi bayan ta suna fitowa Jalal yana fitowa daga part din sa kallon juna sukai ido daya ya kanne mata da daga mata gira kauda face tai tarasa wane kalar iskanci Jalal ya koyo haka zai dinga kashe mata ido kamar wata yar iska kwafatai,yadai Jelly baby jinsa tai kawai akusa da ita cikin kuluwa take kallon sa àah kamanta ba jela ba Dariya ce ta kufce masa sàida Ammah ta juyo ta kalle su.
Gaba tai ta kyalesu kyalkyale wa yayi da dariya kumafa kinma yi kama da jelar tunda kaje ka dauko jinin samudawa mezai hana bakaga nai kama da jela ba,to waike mene hadinki da Aurena gaba daya kika tashi hankalin ki,Allah ya sauwake akan Auranka na tashi hankalina babu Abinda ya dameni Zuciyata fes take Ammah kadai nake jiwa haushi za akwace mata danta.
Kedai Malama kifadi gaskia kishi kike kinga zukeken saurayi wata zatai wuff dashi,kishin wa zanji kaikasan wani kishima ni bansan shiba zumbura baki tai tayi gaba cigaba yayi da tsokanarta har suka sauko Inna ce ta zuba musu idanu kawar da kanta tai daga kansu.
Har kasa Jalila ta duka tagaida inna Amsawa take bakinta a washe ance bakiji dadi ba sannu kinji yawwa inna Allah ya kara sauki.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 80
Allah ya kara sauki kinji Ameen,yar tsohuwa yaushe kika durgo na durgo daga gidan wa saikace wata aljana kace min na durgo ko kuma yar fashi murmushi Jalal ya saki ai baku da banbanci keda su nifa innakalle ki da daddare ma firgitani kike tsabar yadda farinki yayi yawa saura kadan kizama zabiya to tunda ban zaman ba aida sauki.
Gaisawa sukai cikin bar kwamci Jalila ta kalla da taketa hura hanci wai nikam jalili na tambayeki mana Dariya Jalal ya fashe da ita jalili kumafa name din yahau harara Jalilah ta watsamai kafin ta kauda kanta to Inna inane garinku kuwa murmushi tadan saki jigawa kai aikuwa ina da yan Uwa ajigawa sosai wace unguwa tsoma,duk yadda Jalal yaso rike Dariyar sa kasawa yayi wai tsoma.
Tashi kabar wajannan yazaka samu agaba kanai mana Dariya kamar wasu mahaukata Ammah ce ke magana tana makamai harara tashi yayi yana dariya har time din,kyaleshi Jalilah na kore shi ai Innah ce ta kalli Jalila aiko nasan wannan kauyan sosai ma kuwa lah ai inna Inagama kinsan gidammu ba mamaki kinsan dan karamin garine hakane Innah.
Aikina cewa gidan Malam Muhammad Uba za anuna miki gidan mu Allahu akbar tabbas natabajin sunan nan gyara zama Jalilah tai cikin jindadi ansan babanta ai inna ya jima da rasuwa dafe kirji inna tai Allahu akbar kabiran Malam mahammadu ya rasu oh rayuwa kenan mutumin arziki Allah ya jikansa yasa ya huta ameen Jalila ta amsa cikin sanyin jiki tunowa da mahaifinta da irin gatan daya nuna mata.
Tuni idanun ta ta ciko da hawaye kallonta sukai cike da tausayawa tashi kije abinki kinji addu'a zaki dinga yimasa ba kuka ba gyada kai tayi tatashi harabar gidan ta fita kaitsaye lambu ta nufa ko zuciyarta zatai sanyi,harta zauna bata kula da shiba hawayan face dinta take sharewa wani nabin wani.
Tsam ya taso daga wajan zamansa kusa da ita ya zauna yana tunanin me kuma akai mata haka me yasa kike kuka dama neman wanda zai kula ta takeyi Kuka ta fashe dashi kamar wadda ake duka yana zaune yana kallonta dan ya rasa mezai ce mata gaba daya saidata gama kukan ya goge mata hawaye tas.
Me akai miki haka Jalila kodan na toskane ki dazu girgiza kai tayi babana na tuna to zankaiki kiganshi hawayene ya sake zubo mata ai yarasu kallonta yake cike da tausayawa dama mahaifinki ya rasu daga masa kai tayi alamar eh saiya ji sam be kyauta ba meyasa betaba tambayarta ahalinta ba bayan ita ko yaushe burinta ta kyautatawa iyayan sa taga farin ciki aface dinsu.
Ansha fada da ita ackin gidan adalilin saita kwatar musu yancin su kwanciyatai a cinyar sa jin kanta yana barazanar tsagewa sosai yake mata ciwo,Allah ya jikansa da Rahama ameen ta amsa da kyar jijjigata ya farayi kamar wata baby dandanan bacci ya dauke ta jingina bayansa yayi ajikin kujerar ya lumshi idanun sa.
Tana da wani babban matsayi matsayi mafi kololowa megirman gaske kowace da kika kaunarta ragargaza zuciyar sa take taya zata fuskance shi aganin sama Jalilah tai masa kankanta yasan kansa yasan wanene shi bazata iya dawainiya da dashiba duk da tana da wayo amma shekarunta sunyi kadan.
Kallon ta yake so happy aduk sanda take kusa dashi yana samun kansa cikin farin ciki da nishadi dukkan damuwar sa yayewa takeyi,harya karaso inda suke besan yazo ba dukan kafadarsa Jamal yayi shegen kaya ka dauki yar mutane kadorata acinya ga Amaryar ka can ita ya kamata ka dauka ai.
Harara ya watsa masa dariya Jamal ya saka wannan kallon fa koba gaskiya na fada ba,nidama nadade dagani san Yarinyar nan kake to katsaya kallon ruwa kwado yaima kafa waikai ai yarinya ce aiga babbar can ambaka saika kyale karamar,kaifa dan iskane wllh ya daga zuwa zaka faramin ihu aka to bata da lafiya shiyasa nake jinyar ta.
Allah sarki suma take kana yayyafa mata ruwa karshan cuta kenan inzaka farka kafarka malam kodai ka Aure su su biyun ko kuma kakyale waccan dumbarun ka dauki wannan dariya suka sa suka tafa.
Mrs Baba Bello Abubakar
.........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 81
Yayi daidai da lokacin da Rufaida tafito daga gida ta rataya uwar jaka kamar me tallan magani wannna dariyar da sukai saitaga kamar da ita suke sukuwa basu sanma da fitowar taba, cikin jin haushi buguzun buguzun tanufo inda suke zaune tana zuwa idanunta ya fada kan Jalila da tai rashe rashe akan cinyar Mijinta.
Kan ubancan abunda kukeyi kenan saboda cin amana kadauketa ma dorata acinya ni inacan cikin gida bansan abunda ake ba,kanya ankara ta fusgo Jalila wurgi tai da ita kamar ta dauki takadda babu zato tajita tim akasa afirgice tamike ba karamar buguwa taiba sàida hannunta ya amsa.
Cikin bacin rai Jalal ya wanke face dinta da mari har guda Uku wace irin dabbace ke da zakizo kawaii kidauki yar mutane kiyi wulli da ita Mahaukaciyar inace ke tsaki yaja yabar ta awajan shikansa jamal bakaramin haushi Rufaida ta bashi ba,wajan Jalila ya nufa data dafe hannun ta cikin azaba gaba daya hawaye ya jike mata face.
Riko hannun yayi tasa kara saboda tsananin zafin daya ziyar ceta,anya bata jimata targade ahannun ba Jamal ya fada yana kallon Jalal nima abinda nake tunani kenan ya za'ayi yanxu gyara mata zakai riko hannun ta yayi suka bar Rufaida tsaye kamar andasa ta.
Parlo suka koma inna da Ammah suna zaune sukaga anshigo da Jalila ranga ranga mikewa sukai suna tambayar meyasa meta,sam Jalal kasa magana yayi saboda bacinrai Jamal ne yayi musu bayani,tana ina dan gyatumar ta ko baiwar tace zata nemi ta karya yar mutane tunkafin a Aure ta hartafara ta addanci kajimu da ja'ira mara kunya Inna ce keta wanna sababin.
Ammah ce takamo ta jikinta sannu Jalila zaunar da ita tayi tana kallon hannun daya kasa tsayawa waje daya ni anya Jalal bama karyewa taiba bari na duba,kuka Jalila ta fashe dashi Ammah karya taban hannu zafi nakeji kuka take harda majina kiyi hakuri in baagyara miki ba akwai matsala kinji gyada kai kawaii tayi ita kadai tasan yadda hannun yake mata azaba.
Kurikemin ita riketa Ammah tayi sosai Jalal ya fara gira mata targadan sosai Jalilah take zanbarwa tana kuka kamar ranta zai fita babu wanda be tausaya mata ba Jalila harda fitsari awando.
Inna ko sai masifa take Allah ya saka miki Allah ya hadata dame karairayata ayawon gantalin data tafi yitake bakinta kamar zai cire,yanki aka samo ya daure mata hannun kai wannan rana Jalila taga ta kanta ga Zazzabin ga targade abun saiya sake hade mata.
Duk abunnan da ake mom sunaji amma koda wasa basu fito ba suna part dinsu suna tikar dariya da Allah shikara, Rufaida kuwa tuni tatafi yawon ta ko ajikinta babu Abinda ya dameta taci gaba da harko kinta.
Tsanar Rufaida sake shiga zukatan su tayi da alkawarin bazasu taba yadda Jalal ya Aure ta ba aniyarsu zata koma musu kansu.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 82
A kallah Jalilah sàida tafi sati kafin ta warware hannun yayi sauki sosai Jalal shine dan jinya ko yaushe yana tare da ita tuni ta warware tamanta da labarin wani auran Jalal har office take taya shi in yana gida zataga dariyar sa amma da sunfita zataga ya koma kamar bashi ba bazaka taba ganin hakoransa awaje ba.
Yau wajan indo tatashi da burin zuwa tun jiya tasanar da Ammah zataje tace Allah ya kaimu sai baba direba ya kaiki,karfe 11 tagama shirinta tsaf less maroon tasaka sai farin mayafi data yafa face dinta fiyau babu abunda ta shafa sai turare data dan fesa kadan,hand bag ta dauka har wannnan time din bata da waya.
Ammah na shirya to Jalila leda tamiko mata gashi inkinje kibawa Hajiya memuna kice ina gaisheta to Ammah parking space ta nufa,àah Jalala ikon Allah amfito kenan dariya tai eh nafito baba taho kutafi to angama uwar masu gida,ni baba karufan asiri ai asirinki arufe yake shalelen Hajiya yana da barkwanci har sukaje gidan Hajiya Maimuna yana bata dariya.
Fitowa tai to baba saikazo daukata to sai anjimar sallama sukai ta juya kusan cin karo sukai da wani saurayi da yake fitowa daga parlo ah sorry,rike kugu Jalilah tai ta zabgamai harara asoron gidanku nake kwana haryayi gaba ya dawo baya.
Murmushi ya saki yammata ai abun bana fada bane Allah ya huci ranki gimbiyar mata,zumbura baki tai da ya zamemata jiki aimun afuwa in Sarauniyar mata batamin afuwa ba ai dole nasha dauri dariya yabata tadan mirmusa shikenan na hakura inbaki hakura bama zan iya dukawa harkasa ai girmanki ne fari tai da ido hakamma ya isa.
Gaba tayi yabita da kallo dama matar Aure yake nema gashi kuma Allah ya kawo masa ita hargida ko wacece wajanwa tazo haka yatafi yana ta tunane tunane.
Oyoyo Jalilah yau kece agidan namu anty Indo ce tazo ta rungumeta bata face Jalilah tai aini anty nayi fushi nida bakya nemana dan kiran nawa da kikeyi kindaina,to aikece Jalila baki da waya shiya haryau surukina bekara so ba balle ya kawo wayar rufe fuska Jalila tai kai Anty to aigaskiya nafada Allah dai ya kawo shi akusa murmushi kawaii tayi tabi bayanta.
Hardakin Hajiya Maimuna takaita Hajiya ga babbar bakuwa minyi agidan rike naki Hajiya tai lallai kuwa idanki kenan Jalila ma sha Allah haka kika girma,rufe ido tai alamun sun bata kunya zo kizauna nasan dai ba wajena kika zoba wajan Antyn ki kikazo dariya tayi ni wajan ki nazo Ummi to Allah yasa dagaske kike.
Zama tai suka gaisa sannan tamika mata ledar hannun ta gashi inji Ammah oh Rukayya bata gajiya duk sanda zaazo abun alheri yana tafe to angode ALLAH yabar zumunci Ameen,zama tai suka dan taba hira to tashi kije wajan Antyn taki to mikewa tai tatafi dakin anty indo.
Da sallama tashiga dakin wa'alaikumussalam shigo shiga tai tazauna kai Anty kinaji da gayu duk wannan dakin kine kajimu da yarinya ke dakinki bayafi ma wannan ba ai Jalal ya tsaya miki dariya tasa to aini yarinya ce mikima gyatuma ba tare suka saka dariya.
Wai yaushe zanje gida ke zan tambaya ai in zakije ai Ammah zatasa akaiki aiko kwanannan zanje ina son ganin Innata itama tana kewarki tana ta jira kidawo bala me tsire tanacan yanata jiranki kumbura fuskatai wane balan.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 83
Bala me tsire wanda kika sani yakasa ya tsare yakiyin Aure yanacan yana jiranki dariya ta fashe da ita to wllh tun wuri yakama Matarsa amma bani ba,um aishikenan itaku keda shi taso muje kitayani aiki to tashi tai suka fita tare sukai aiki ranar tana sake kokkoya mata wasu abubuwan.
Saurayin dazune ya kara shigowa hango Jalila dayai a parlo ya kara so wajan ta face dinsa dauke da murmushi zama yayi yana facing dinta Sarauniya ashe kinanan ina ta sauri na dawo karnai asarar kyakykyawar mata,kallon sa kawai tayi wacece Matar taka kemana aini naga mata tunda naganki naji kin kwantamin azuciya dama Matar Aure nake nema.
Uhm kawai tace ganin ya cikata da surutu ta mike dakin Indo ta koma tagaji da jarabar surutun sa ko sunan sa bata sani ba yazo ya sata agaba,ba laifi shima hadaddene amma bekai uncle j ba itafa duk maza bata ganin kyansu saishi kadai,tsaki taja tuna bulkutar dazai Aura amma dai anyi asara wllh,indo ce ta kalleta wanene yayi asarar tabe baki tai.
Uncle Jalal mana ya rasa wadda zai aura sai gingimari,wa kenan Rufaida haba anty ta kama toke imma katafila ce meyayi ruwanki ai wllh Anty dole ne raina ya baci duk yammatan garinnan yarasa wadda zai kwasa sai ita ta ina suka dace da juna sakare anty indo tai tana kallon ta Murmushi kawai tai ta Girgiza kai to Allah ya kyauta nidai ranar biki karki manta dani,wani kululun bakin cikine ya tokarewa Jalila shiru tai bata sake tankawa indo ba.
Sai yamma lis tafito zata tafi tajira baba direba har kusan Magariba be zoba har bakin get Hajiya Maimuna suka rako ta,yawwa kinga ga mus'ab can ma saiya kaiki wannan saurayin taga ya taho sai zuba murmushi yake gani Ummi yawwa mus'ab dama Jalila zaka mayar gidan Hajiya Rukayya to Ummi dama abinda yake jira kenan dan shi yatsara hakan baba direba har bakin get yazo dan daukarta amma yace yayi tafiyarsa shizai kawo ta.
Harararsa take ta gefan ido wannan ya cika rawar kai wuce kuje Jalila Allah ya tsare hanya ameen gaba tashiga fuskarta babu wata walwala,datake yadan gidan bewani tambayeta inane hanya ba yana tafe yana zuba shi alallai yana son ya kafa gwamnatinsa tun tana share shi hardai tafara kulashi saigashi yana sata dariya.
Hon ya dannan get man sàida ya leko hango Jalila ta kame agaban mota ya zuge get din daidai sanda Jalal ya fito dan zuwa dauko ta yana dawowa ya tambayi Ammah tana ina tace bata dawo ba shine yataho zai dauko ta.
Ganinta amotar wani gardi sàida kirjinsa yayi masifar faduwa tun idanun sa suka kada jawur zuciyar sa tafasa kawai take kamar zai amayar da ita,ko gama daidaita parking mus'ab beba ya bude sit din azafafe ya figo ta saidata kwalla kara dan bakaramin ruko yayi mata ba,janta yake kamar wani kayan wanki kusa da Ammah dake azkar ya cillata saidata tsorata.
Kai Jalal lafiya kuwa haka kawai zaka damkota kamar wadda tai maka sata ki tambayeta abunda tai Ammah bakisan meta aikata ba,kallon Jalila tai data fara matsar hawaye sosai ta tsorata da Jalal anya bashi da aljanu abunda take ayyanawa kenan.
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 84
Kallon Jalila Ammah tai mekika aikata yake wannan ihun kamar wadda kukai kisan kai.Wllh Ammah nima bansan menai masa ba mangara yakawo mata Ammah tatare kai banason shashanci kaki fadar abunda tai maka kuma nema kake kadaketa haka ake lamarin duniya cikin numfarfashi yake fadin yanzu Ammah wannan yarinyar kawai saita hau motar wani kato ya kawo ta gidannan.
Hangame baki Ammah tai wanene ya kawo ki nima Ammah Ummi ce tace ya kawo ni kallonta tamayar kansa akan wannan kake hayagaga kamar zaka tada Iska to tsayama Auranta kayi kokuma sadakinta kabiya da haka kawai kaganta da wani zaka fara fuffuka kana hakilo,yanzu Ammah wannan yarinyar har nawa take da zata fara kula samari yaushe tai wannan girman.
Bansani ba ubana sainaji ajikina tukunna zan amsa maka barkaina tun kafin raina yafadi kabari in kaga Rufaida da wani sekai wannan haukan,fuuuu yahau sama kamar kububuwa tsaki Ammah taja kekuma kukan me kikeyi bakomai Ammah banaje nabashi hakuri hartamike Ammah ta dangwarar da ita koma kizauna wadda bata da zuciya mekikai masa da zaki bashi hakuri.
Kuka ta fashe dashi to Ammah bakiga yayi fushi dani ba budewa baki Ammah tai tana binta da kallo au saboda na hanaki zuwa shine kike wannan kukan to tashi kije mugani wadda bata iya jan ajiba ke dan jan ajinnan ma na mata baki iya shiba kai Allah ya sauwake.
Tashine kitafi wajan bakonki kikai masa ruwa nifa ba bako na bane to danwa yazo koni yadauko acikin motar tashi tunkan na hambare ki,mikewa tai face aturbune tafita babu shi babu alamarsa tuni yaja motar sa tun sanda yaga Jalal ya figo ta daga cikin mota ya juya yayi tunanin inya fito kansa zai dawo yana tunanin kodai tayi masa laifine zaidawo koba yanzu ba.
Sam kasa cin Abinci tai da daddare saboda Jalal ransa na bace akanta sai juya cokalin take acikin abinci, Ammah tana kallonta tai mata banza tasan sarai duk akan Jalal take wannan abun tana gama cin abincin ta tatashi tabarta awajan,tana ganin Ammah tatashi tamike itama saidata leka dakin Ammah ta hangota azaune tana ninki ahankali ta fito taja mata kofa.
Sarai Ammah ta ganta amma saita basar kamar bata ganta ba part din Jalal ta nufa ahankali tashiga har bedroom dinsa bata ganshi ba parlon ta dawo sai time din ta hangoshi yana kwance yana girgiza kafa tun sanda ya shigo ya ganta amma yayi kamar be ganta ba.
Akusa dashi tazauna Uncle shiru yayi kara kiran sunan sa tai akufule yatashi mezan miki aikin san dani kikaje kika hau motar wani kato karki sake kiran sunana, Allah bansan shiba Ummi tace ya kawo ni gida kayi hakuri bazan sake ba,harara ya watsa mata har shekarar ki nawa dazaki fara kula samari kuka take kashirban,sassauta murya yayi matukar kina so mudaidai ta babu ke babu wani saurayi.
Gyada kai tai alamun taji saikin gama makaranta sannan zan duba naga wanda ya dace dake amma ba yanzu ba,to ta amsa goge hawayanki gogewa tai uncle to bakaci abinci ba banaci na dauko mana muci tare dan jim yayi sannan ya gyada mata kai alamar eh da murnarta tatashi tafice binta da kallo yayi yanajin bacin ransa na raguwa ahankali lumshe idanunsa yayi jin wani abu na tsirga masa.
Dawowa tai da Abinçin ahannun ta ajiyeta tai sauko muci ahankali ya sauka ta zuba musu faten doya da wakene yasha nama sai tashin kamshi yakeyi, ahankali suka fara ci har suka gama babu wanda yayi magana acikin su tashi tai takwashe kayan sàida safe kamar bazai amsa ba ya yamusta fuska Allah ya kaimu.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 85
Ido hudu sukai da Ammah da take kofar dakinta atsaye tsayawa tai tana zare idanu kamar mazarin tsire kwafa tai tajuya daki asanyaye ta juya ta kai kayan kiching kafin ta dawo tashige dakinta.
Washe gari kin yadda tai su hadu da Ammah wasan buya suka dingayi sarai Ammah tasan akan maganar jiyane take wannan wasan buyar,sai wajan azahar sannan ta ware kayan da hajiya Maimuna ta bata tadauko ta nunawa Ammah kingode kuwa daga haka bata kara cemata komai ba,gaba daya saitaji bataji dadi ba kiyi hakuri Ammah da kikai min me.
Shiru tai ta sunkuyar dakai babu Abinda kikai min tashi kije kiyi harkar ki mikewa tai ta koma dakinta kwanciya tai tana tunanin meyasa Ammah batason taje wajan Uncle to aitaga yagirmeta menene dan tabashi hakuri,haka taita tunani barkatai har bacci ya dauketa batare data saniba.Fitowar sa kenan daga daki harzai gota dakinta ya koma da baya akofar dakin ya cake yana kare mata kallo sleeping beauty yadan jima kafin yabar wajan.
Hada idanu sukai da Ammah harara ta wurgamai ta Kaida kanta shafa kansa yayi yana sakin Murmushi tuba nake Hajiya Ammah,tabe baki Ammah tai sekuma kayi da wata mekaimin da zaka ban hakuri tsabar rashin adalci kakama yar mutane da fada kamar ubanta to zanga duk ranar data sake yin saurayi ka korar matashi sai ranka ya baci.
Shiru yayi yanajin Ammah tana ta mita kamar zata ari baki shidai betanka ba intana zancan saurayin nan kamar wuta take watsa masa aiko zaiga wanda zai sake cewa yana sonta saiya gurje masa baki ajikin gini,tashi yayi afusace ya fita yama fasa breakfast din asauka lafiya kafi jirgin sama tashi.
Sai kusan azahar Jalila tatashi ko breakfast bataiba damuwa ce fal azuciyarta sam batajin dasu,tana saukowa ta hangi Inna face dinta tadan saki tunda tafara saukowa Inna ta zuba mata idanu kafinta kawar da kanta tana tabe baki,me kuma dama kina daki kamar wata daddawa kinshiga daka sai kace mejego.
Dariya tadanyi kai Inna mejego ke zaman daka kwarai kuwa damma jegon yanzu ya zama na zamani sai mace ta haihu kawai kazo kasameta tayyare atsakar gida mu zamanin mu ai bahaka akaiba shiyasa mukafi kwaliti.
Lallai Inna kunsha wahala saidai asaku adaki bazaku fito ba,wahala ko gata aimu gata akai mana ba wahala ba shiyasa gamunan ras damu babu abunda bazan iya yiba ke tukunya lamba 50 zan iya tuketa nikadai, dariya ta saka kai kina da karfi naban mamaki inna af bana fada miki ba kina wasane yarinya,nan tazauna suka sha hira da inna.
Ke tashi kikirawo mun Saratu to mikewa Jalila tai har part din Mom tashiga da sallamar ta babu wadda ta amsa acikin su ke lafiya zakiwani dauko tsummar kafarki kishigowa mutane sai zarnin fitsari kike da tsamin dauda, Murmushi kawai ta saki yau banda lokacin ku amma next karki bari kushiga gona ta.
Haka kawai bazan shigo wannan kazamin part dinba da mala'ikun Rahama basa sauka acikin sa saidole to yanzumma dole tasani shigosa uwarku Saratu ake kira intaga dama taje in bataga dama ba tazauna,harya juya Mom tafito daga daki wani shegen ne yake kirana Inna data biyo bayan Jalilah jinta shiru yasa tabiyo bayan ta nice shegiyar danake kiranki.
Sak sukai gaba dayansu Mom sai rarraba idanu take eh lallai Saratu na yadda rashin mutuncin ki yakai intaha sanin kanki dai karamin yaro bazai aiko yace kije ba sai babba to tunda kika zageni dama maganar Auran yarki ya kawoni bana juya.
Da sauri Rufaida tasha gaban inna dan Allah inna kiyi hakuri sharrin shedanne yasata fadin haka kiyi hakuri ki zauna,hakane inna cewar Mom danasan kece ta ina zan zageki kimin afuwa inna dan jim inna tai shikenan tasamu waje ta zauna tare suka sauke ajiyar zuciya.
Mrs Baba Bello ABUBAKAR
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 86
Maganar bincike danace za aje to Alhmdulillahi komai yazo da sauki anyi bincike ansamu abunda ake so!!! komai yatafi yadda aka tsara shi dan haka aci gaba da shirin biki yarki dai za'adaura mata Aure tabbas awannan ranar bikin,washe hakora sukai kamar sokaye Rufaida jitake kamar tatashi tataka rawa haka takeji.
Sabanin Salima da ranta ya baci damme Rufaida zatai Aure tabarta ita kuma tana zaune, Jalila da take zaune jitai gaba daya dunyar tai mata zafi da gaske dai uncle dinta wannan botoramar zai aura tashitai tsam tafice binta sukai da kallo.
Mikewa inna tai to nidai na isar da sakona to inna Allah ya saka da Alkhairi ya kara girma ameen har bakin kofa suka rakota tana fita Mom da Rufaida suka sa ihun murna suna rungume juna cikin farin ciki,yanzu Mom shiri zai dada kan kama yanzu kuwa.
Waya Rufaida ta dauka ke zuly akwai labari fa yau akwai casu ahada min gagarumin fati ki gayyato kowa da kowa ihu zuly tasa kice yau akwai shanawa ina yinki rufy tabbas za'arakashe kedai kiyi abunda nasaki angama kashe wayar tai tana kallon Mom ai yau mom dole mucashe nida kawayena wannan babbar ranace agare ni hakan yayi daidai cewar mom da babu wani abu daya dameta.
Jalila dakyar takai kanta daki tsabar yadda kirjinta yake suya tarasa meke damunta haka meruwanta da auransa amma sam zuciyarta gaya mata take tana da ruwa mana dan Ammah ne fa kuma ta tabbatar itama bason Aurannan take ba,kasa zaman dakin tai tafita lambu anan ta karasa wuninta hardare bata da walwala ko kadan.
Da sallama tashiga dakin Ammah yadai Jalilah na ganki acikin damuwa shiru tadanyi nawani lokaci Ammah wai kinsan yaya Jalal zai Auri Rufaida? babu wata damuwa a face din Ammah eh mana nasani yanzu shirye shiryen biki zamu fara kamar zata fashe da Kuka take kallon Ammah har farin cikin Auran kike to bazanyi farin ciki ba Jalila shikadai na haifafa.
Hawaye kawai taji ya cika mata idanu kawar da kanta tayi kema kifara shirin biki har gyara na musamman zan miki amatsayinki na kanwar Ango sonake kifi amaryar kyau awannan rana.Jinta kawai Jalila take tacika tayi fam kamar zata fashe Ammah tana kallon ta tabasar kamar bata gani ba cigaba dayi mata hirar bikin tai tsam ta mike sàida safe.
Binta da kallo Ammah tai tana dakin Murmushi.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 87
Jalal Ammah ta kira sunan sa na'am dama nakira kane akan maganar Auranka to Alhmdulillahi Inna dai sunyi bincike kamar yadda ta fada kuma komai yayi daidai dan haka kaje kafara shirin biki nan da sati uku za'ai komai agama,kallon rashin fahimta yake mata aure na dawa Ammah.
Auran da mahaifinka ya fada maka rannan ko harka manta tuni duk wani annurin fuskarsa ya dauke kamar an aiko masa da sakon mutuwa yake kallon Ammah ya kake kallo na haka ko bayanin da naima haryanzu baka gane ba Auranka da rufaida nanda sati uku kaje kafara shiri.
Inkuma kana da wadda kake so kazo ka sanar dani tin kafin lokaci ya kure maka fita tai tabarshi kamar an dasa shi,tuni kansa ya fara sarawa jingina yayi da jikin kujera kirjinta yana lugudan faduwa,kayi shirin Auran Rufaida jiyayi ransa yana sake baci sake sake yayi tayi har kusan asuba be rintsa ba.
Washe gari kowa face dinsa aturbune tsakanin shi da Jalilah babu me fara'a Ammah suna zaune aparlo ita da Hajiya Maimuna suna tsara yadda biki zai kasance tafito daga dakin ta,gaskiya Hajiya rukayya dole wannan bikin atsarashi yadda zai kawatar da kowa auran Jalal fa kinsan abun ba karamun abu bane dole abude bakin aljihu maganar kayan lefe kibarta ahannuna dama kayana sun kusa isowa babu abunda babu na kayan lefe aciki.
To hakamma yayi Hajiya ALLAH yabarmu tare ameen dai,ah jalilah kin tashi kenan eh Ammah tafada asanyaye dagaske dai bikinnan yinsa za'ai,ina kwana Ummi lafiya lau Jalilah yanzu nagama baza idanun naganki ashe kina daki eh Ummi to ma sha Allah ya shirye shiryen biki zumbura baki tai kamar zata fashe da Kuka kallon juna sukai suka saki Murmushi
Yadai Jalilah kike zumburo baki daga tambaya ni Ummi ba dake nakeba wane shirin biki zanyi ai wannan ba Aure zaiba ni da ita da kato duk daya nake kallon su,kunshe dariya su Ammah sukai wane irin kato kuma Jalilah kina ganin Yarinya yar duma duma ma sha Allah sankowa kin wanda be samu ba kuma kice wai kama take da namiji.
Kama haba Jalilah tai kema Ummi ko bakya cikin hayyacinki saboda na tabbatar Ammah Akwai abinda aka bata taci shiyasa ta yadda da wannan auran,cikin Dariya Hajiya Maimuna tace to ni kuma da bana Gidan taya aka bani abun naci kalau muke kinsan dai yayanki ya isa Aure gwara ayi masa awuce wajan,kuma Ummi duk matan garinnan sai ita cike da bacin rai take fadin haka.
Ammah ta kalla ah kuma fa gaskiyar Jalilah akwai yammata zuka zuka ga misali ma akan Jalilah kodai yar gida zamiyi,waro idanu Jalilah tai hadda dafe kirji wah aini yayana ne sedai na zabo masa matar da kaina akwai kawayena kyawawa babu me duwawu kamar murhu,duk yadda Ammah taso rike dariyar ta kasawa tai saidata saki dariya.
Hajiya Maimuna ma rike dariyarta take tundazu jin karfin hali irin na Jalilah gaba daya kishi ya rufe mata ido amma haryanzu takasa gano abunda yake cikin zuciyarta,to shikenan gaskiya Rukayya maganar Jalilah abun dubawa ce kar aje ayi baya ba zani adai tsaya akara tankade da rairaya,washe baki tai yawwa Ummi aikinga ke dayake lafiyar ki kalau kin fahimceni Sosai kuwa niko na fahimce ki yadda ya kamata.
Tuni Jalilah ta saki ranta tafara fara'a kamar ba ita ba,yauwa dama zuwa nai natafi dake can gidana mezanyo acan Ummi dama gyaran biki za'a fara yimiki tunda yar gatan Ammah ce ke baza'a barki bayaba yadda amarya zata fito kema haka zakifito amma wannan bayanin da kikayimin yanzu yasa nima naji auran yafita daga raina amma duk da haka nayi niyyar alkhairi gyarannan dai zanyi miki shi kifito fes ko baza'ai bikin ba.
Numfashi ta sauke ai Ummi bama za'ai Aurannan ba to aishikenan yanzu dai kidauko kayanki ko kala biyarne saiki zo mutafi to taamsa tare da mikewa,binta sukai da kallo harta bacewa ganin su.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 88
Da sallama Mom tashigo parlor tunda aka fara maganar biki tasaki ranta kamar ba ita ba amsawa sukai Fuskar su sake ah Hajiya Maimuna ce wllh kuwa nice kinsan abu yazo dole nazo adinga shawar wari,fadada fara'ar ta tayi hakane abu yazo muma kin gammu nan babu zama ko yaushe muma muna kan hanyar siyayya jibi ma nake son shiga dubai dan karasa siyayyar da ayi ba.
Hakan yayi kyau gwara a shishsirya kar Lokaci ya kure wani abu yazo ya hana faruwar shirin atsanake hakane Hajiya shiyasa kikaga bana samun zama, Ammah tana jinsu ko kala bata ceba iyakacin tadan murmusa mikewa Mom tayi to bana tashi zanje naci gaba da ayyuka kigaida gida Hajiya gida yaji.
Jalilah ce ta sauko tagama shirinta tsaf kai Jalilah kodai dama kin gaji da zama danine daga cewa kitaho zaku tafi zaraf harkin mike kin hada kaya dariya tasa kai Ammah ta nina isa aitace gyaran jiki zataimin kuma dama sonake naga nasake zama yar gayu dariya suka sa gaba daya kefa Jalilah bakya girma haryanzu yarinta na damunki ai ahakamma ke yar gayu ce inji haj Maimuna ai Inaso nakara kyan Ummi to zaki kara kuwa sosai.
Har bakin Motar ta Ammah ta rako su to Jalilah saikin dawo sati daya zakiyi kina dawowa zaki tafi gida kigano innarki to Ammah daga mata hannu tai tayi harsuka fice daga Gidan.
Ummi ce ta kalle ta wainikam Jalilah baki da saurayi ne zaro idanu tai kai Ummi ai Uncle j yacemin ni yarinya ce karya sake gani na da wani saurayi saina gama karatu zai zabomin da kansa,gyadakai tayi eh gasky kam dama ina kika girma yayi gaskiya daga haka bata sake Magana ba harsuka je,dakin indo aka sauketa Indo zatai magana Ummi ta kifta mata idanu.
Basarwa tai Jalilah ashe tare dake za'a taho amma Hajiya baki fadan ba eh dama shirin bikin yayanta zammata kin kyauta Ummi gwara kanwar tawa tafito tai ras itama tazama yar gayu kamar yadda take son zama koba hakaba Jalilah hakane anty.
Jalal sam besan Jalilah bata nan ba saida safe ya leka dakinta beganta ba duk inda yasan zai ganta be ganta dakin Ammah ya shiga ina Jalilah Ammah tatafi gyaran jiki kallon rashin fahimta yake mata gyaran jikimme wanda akewa amare yadda zakai Aure itama Aure zaai mata agarin su besan sanda ya mike zumbur ba haba Ammah wane irin kuma Aure za aimata akauye imma Auranne arasa wanda za a aura mata sai dan kauye.
Haka akaga yadace kuma Aure ba fashi shiza'ai mata kaima kaje kamaida hankalinka akan naka auran daga yanzu ma ba sake ganin Jalilah zakai ba sàidai intazo da ziyara,jiyayi hajijiya na dibarsa kamar zai kifa haka yafita daga dakin binsa da kallo Ammah tai tana tabe baki.
Kan sofa ya fada yana maida Numfashi tuni kirjinsa yadau zafi kamar ana soya masa zuciya haka yake ji tsabar abunda yazo ya tokare masa makoshi juya kai kawai yake abun tausayi lokaci daya ya fita daga hayyacin sa kamar zai rasa ransa,yanajin wayar sa na ringing amma yakasa dauka yanayin da yake ciki bame dadi bane.
Jamal ne yake zanga masa kira jin bedaga ba yataso yabiyo shi hargida sanda ya karaso part dinsa tuni Jalal ya dade da fadowa daga kan kujera,sallamar da yayi niyyar yice ta makale da sauri ya karaso inda yake Jijjiga sa yake Jalal yana dukan fuskar sa baya hayyacin sa sam kirjinsa sama da kasa kawai yake.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 89
Jin yadda yake kiran sunan Jalal yasa Ammah futowa asukwane hartana cin tuntube gabanta ne ya fadi ganin yadda jikinsa ya saki kamar baya motsi da gudu takarasa shiga tana tambayar Jamal meya sameshi nima yanzu na shigo Ammah bari nadauke shi mutafi asibiti.
Kinkimarsa yayi dama da hijab ajikin Ammah bin bayansu tayi da sauri baba dreba ya taso yana meyasa meshi babu wanda yasamu damar amsa masa shine yaja motar gaba daya sun rude,tunkan ya karasa yakira afito da gado dr Jalal baida lafiya kusan ma'aikata asibitin gaba daya fitowa sukai dan daukar sa suna gama parking suka baibaye motar da kan su suka dauko shi aka dorashi akan gadon.
Taimakon gaggawa suka farayi masa dakyar aka samo numfashin sa da yayi nisan kiwo yarfe gumi kawai suke musamman Jamal dayafi kowa shiga damuwa.
Ammah ya kalla datake sharar hawaye Numfashi ya sauke Ammah meyasamu Jalal haka jinin sa yayi mugun hawa kara sharce hawayanta tayi ta labar ta masa abunda ya faru, murmushi yadan saki meyasa kika gaya masa haka nadade da sanin yana sonta yabude baki yafada ne bazai iya ba shi tayi masa kankanta.
Nasan da haka Jamal amma nafiso yafurta da bakinsa yana sonta amma shi dan taurin kai yaki fada,hakuri zakiyi Ammah haka tashi soyayyar take zai fadane wata rana.
Tsahon awa Uku tana zaune batare data gajiya ba Allah yasakawa iyayammu da mafificin Alkhairi Ameen.
Ahankali ya fara bude idanu yana sambatu Ammah ina santa itace rayuwata Ammah bazan iya rayuwa ba sàida Jalilah I love you Jalilah I love you too the extreme I love you fashewa yayi da kuka kashirban kamar karamin yaro.
Jamal da Ammah kallon juna suke dariya kamar ta kashe su yau ina miskilanci da jiji dakan yake,basu ankaraba suka ga yaduro daga kan gadon ya tsige ruwan da aka daura masa da sauri suka tare shi ina zaka Jalal Ammah kina ganin za'ai mata aure karki bari itace rayuwata ina sonta wllh Zuciyata zata fashe to naji dawo ka zauna dakyar ya dawo ya zauna.
Dagaske Ammah karki aura mata wani aje dakkon matata,kaida kace bata isa Aure ba ai rainonta zanyi Ammah wllh babu Abinda zan mata ganin yana neman sakin layi ta toshemai baki naji tunda harka furta kana sonta zan shiga nafita naga amfasa wancan Auran na aura ma ita kayadda da hakan gyada kansa yayi kamar yaron goye to koma ka kwanta komawa yayi ya kwanta.
Jamal kallon Jalal kawai yake lallai ashe haka Jalal yakeson Jalilah amma zaiwa kansa sakiyar daba ruwa,dan danan ya koma bacci dama baccin ba isarsa yayi ba yatashi yake wannan dramar.Yanzu Ammah ina Jalilah take tana gidan Hajiya Maimuna dauko ta za'ai yazo ya ganta babu Inda zata zo sa hadu agarin su zaima tashine yagama bige bigen ya mike.
Dariya Jamal yayi adai sassautawa abokina Ammah ya kamu da yawa fa son yarki yayi masa dabai bayi asassuta mana,ai maganin sa kenan waishi jan aji itama ja'ira sai hauka take akan zaiyi Aure batasan san shi take ba Murmushi kawai yayi tasu soyayyar ta yan gayu ce Ammah,saji dashi shida ita.
Sai kusan magariba ya farka saicin magani yake kamar bashine ya gama rusar kukan soyayya ba dazu,mutafi gida Ammah au harka watstsake daga cutar soyayyar kallon Ammah yayi eh ka kalleni ai tunda dazu kagama barka Kuka kan so da kaunar Jalilah.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 90
Hade face ya karayi jin yadda Ammah take tsokanar sa,Jamal ne ya kalle sa yana dariya shafar aljanune Ammah kinsan bazai ce yana son Jaririya ba Ammah kibarshi dai da yar duma dumarsa zasufi daidaitawa harara Jalal ya watsa masa koba gaskiya na fadaba danma ina tare maka shine zaka dinga harara ta.
Har sukaje gida Jamal bai daina tsokanar sa ba suna shiga su Mom akataso asukwane yanzu muke cewa bara muzo mutafi dubiya ashe Jalal ne basi da lafiya,eh shine dazu kamar bayayi ba inji Jamal meyake damunsa ai yariga ya warke Mom abunda yadade azuciyarsa daya fitar dashi sai gashi ya samu afuwa,wace irin cutace wannan azuciya ai Mom cutar maganin ta daya ne kuma ya samu yanzu sai kutaya shi da Addu'a ALLAH ya tabbatar.
Ameen aiko zamu tayashi wannan ciwo dazai kai mutum gadon asibiti ai bakadan bane,hakane shiyasa nace kutaya shi da Addu'a kamar da kasa inji me fadar auransa mom tafada harda dukan cinya.
Ammah data zauna tanajin shakiyancin da Jamal ke musu Rufaida ce cikin kwarkwasa ta matso Sannu yaya Jalal muje na hadama ruwan wanka nasan kagaji ko kallanta be dago yayi ba balle tasa ran zai amince da abunda ta nema,dako kin kyauta dama wankan ya kamace shi zaram ta mike ALLAH Jamal haka za'ai banaje na hada mai to maza yar Albarka ai gwara tun yanzu kisaba da kulawa da mijinki.
Sosai Ammah tai kokari wajan gumtse dariyar dake cinta haka Jamal cikinsa kamar zai fashe tun dazu yake rike dariya tsam yatashi yafita ko gama fita daga maine parlourn beba ya fashe da dariya saidaya kwanta akasa yayi dariya kamar cikinsa zai kulle kawai hango yadda face din Jalal tai sanda Rufaida ta nufi part dinsa dan hada mai ruwan wanka.
Saidaya daidaita nutsuwar sa sannan ya koma yana shigowa Rufaida na saukowa Amarya Amarya harkins gama hadawa angon naki ruwan kamata yayi kikamashi kikaishi daki kinsan jikin ba kwari, Rufaida ba hankali gadan gadan tayo kan Jalal dayake jin duk iya shegen da Jalal yake mai itako Mom dadi kamar ya kashe ta yarta tayi sa'ar miji taji dadin yadda taje ta hada masa ruwan wanka bece komai ba akwai alamar nasara yafara sonta da kaunarta inda dane bazai taba yadda ba.
My sweet katashi muje kai wankan bari na kamaka kokarin rukoshi take yayi saurin bude idanu wata harara ya watsa mata saidata koma baya kafin yaja siririn tsaki mikewa yayi ahankali ya haura dakin sa kamar Rufaida zatai kuka haka tabishi da kallo.
Shiru ne ya ratsa parlourn Ammah mikewa tai banaje na watsa ruwa nima nayi alwala shima Jamal mikewa yayi yafita akan zaije masallaci,dan dole suma su Mom suka mike kowa ya kama kansa.
Yana shiga kai tsaye toilet ya nufa tako taramai ruwa ya cika taf sàida ya zubar dashi tsaf sannan yatara wani, bathtub ya shiga ya Lumshe ido face din Jalilah kawai yake gani daya rufe ido soyayyar ta kara habaka take da ruruwa acikin Zuciyarsa yayi missing dinta bakasan ba burunsa yanzu kawai yaganta tayi masa tabarar nan tata data saba.
Daure da bathroom yafito tsaf yagama shirin sa cikin wani danyan boyal ash sosai yayi masa kyau daura hula yayi ya feshe jikinsa da turarurruka masu dadin kamshi da sanyi,dakin Ammah ya nufa danya roketa tagaya mai inda Jalilah take harzai shiga ya dakata jinda wadda suke waya kuma ta ambaci sunan Jalilah ya gane tana gidanta juyawa kawai yayi tafice.
Motarsa ya nufa tasha wanki sai kyalli takeyi tana daukar idanu bata wuta yayi su baba nayi masa ALLAH ya kiyaye hanya,sàida ya tsaya yayi shopping kayan kwadayi ya daukarwa Jalilah ya santa badai kwadayi ba hon ya danna get man ya wangale masa kofa saidaya daidaita parking dinsa yayi mintuna befito daga motar ba.
Ahankali ya fito yana tunanin wazai kirawo masa Jalilah Anty Indo ce tafito daga gidan zata ba masu gadi abinci hangoshi datai tayi Mamakin zuwan sa amma tunawa datai Jalilah tana gidan sai batai mamaki ba ahankali ya karasa har Inda take cikin mutuntawa yagaisheta amsawa tai yau Jalal ne agidanna mu dan murmusawa yayi to shigo tsayawa yayi yana sosa keya dama zuwa nai na duba Jalilah dan Murmushi ta saki kuma daganan zaka tsaya bari to na turo ma ita.
Harta kwanta Indo tatasheta kije kinyi bako awaje kwalalo idanu tai bako kuma ni Anty da bansan kowa ba ba wajena akazo ba to zammiki karya kenan tashi kije inyaso inkinga ko wanene saiki dawo in bazaki tsaya kiji me yakawo shiba tashitai tana kumbura face tafigi mayafinta yafita,rai abace tafito tun daga nesa ya hango ta baki acune ita alallai taji haushin wanda yazo wajanta.
Kamshin turaran daya daki hancinta shiya sanar da ita wanene agabanta da sauri ta dago kai ido biyu sukai da Jalal daya zuba mata idanu kamar zai cinye ta washe fuska tai tana kallon sa uncle dama kaine Murmushi ya dan saki yana hararar ta ban sani ba meyasa kika taho wani waje harda kwana baki gayamin ba,ainima cewa akai nazo mutafi.
Me akace za'ai miki gyaran jiki irin na amare oh ke amarya ce da za'ai miki ko taya Rufaida gyaran zaki,turbune face tai ai Ummi tace wannan Aure ma fasashi za'ai kuma bakwa cikin hayyacin ku dariya yadan saki mudin to aimana magani mana zamu dawo hayyacimmu kwana kusa.
Saidai atayaku da Addu'a ALLAH ya kwato ku daga mugun hannu.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 91
Kallon sa tai mekazo yi gidannan da daddaren nan bakajin tsoro daga zance nake shine nace bana biyo naga abunda kike aikatawa kikai shiru agidan mutane,mezan aikata kuwa ni babu abunda nake aikatawa naji amma badan na yadda ba,me Ummin ke baki naga kinkara kyau kamar bake ba dan murmushi ta saki sirri ne ba kowa zaiji ba kar Allah yasa kifadamin nima ina da abuna ai ci naka naci nawa aiba laifi bane.
Mota ya bude zama yai asit din gaba ya zaro Ledar dayazo da ita ice cream ya dauko ya bude ya fara shan kayan sa makwat Jalilah ta hadiyi yawu dan matsowa tai to nifa keme jinake kema dadinki kike ci baki ragen ba rau rau tai da idanu ni babu Abinda nkeci na hanaka kabani ko 1 spoon ne nayi.
Sai kuma kiyi bafa zaki shaba yarinya fakar idanun sa tayi ta wafce biyo ta yayi yana son kwacewa amma taki tsayawa tana gudu tana sha gajiya yayi ya kyaleta bazai iya irin gudun da takeyi ba,haki yadawo yanayi dama tsokanar ta yake dan ita ya siyo ba damunsa yayi ba saidata shanye tas ta wullar da robar sannan ta dawo.
Kallon ta Kawai yake duk wata damuwa dayake cikinta ta yaye bayajin komai sai tsananin shaukin ganin ta jiyake kamar yajawo ta ya rungume su dawwama ahaka har karshan rayuwar su,anan ya shashance be ankara dare yayi ba sai kusan 11 da sauri ya zaro idanu sam besan dare yaja haka ba,kinsa nayi dare yanzu idan wani abu ya kamani ahanya fa kizo kawai mutafi kirakani har gida.
Kallon sa tai cikin damuwa gaskiya Uncle bazan so wani abu ya kamaka ba shiga muje dariya ya saki ke koma gida haka kawai ace nazo har gida na saceki so kike Ammah ta gasani yau kamar tsire dariya ta saka kasan me natuna girgiza kansa yayi alamar àah,tunawa nai da bala metsire dayake kofar gidammu ance yana can yana jirana nadawo miyi Aure.
Dif annurin fuskarsa ya dauke rai bace yake kallonta jinin kinta tasha mene to na bata rai daga tabashi labari fuu ya fada mota aguje yaja motar saura kadan yabi ta kanta tai tsalle ta koma gefe hannun ta akan kirji sosai ta razana Ledar hannun tama saidatakai kasa,asanyaye ta sunkuya ta dauka kanta ya kulle me zai sashi fusata haka.
Allah ne kadai ya kaishi gida Lafiya sabida mahaukacin gudun da ya dingayi akan kwalta kamar shikadai aka shimfidawa titin kamar wanda yasha kwaya haka yake taka steps yana rangaji da kyar ya karasa dakin sa ya zube yana matukar jin kishin ta baya so kokadan yaga wani ya rabeta kwana yayi be runtsaba cuta ta dawo sabuwa fil Zazzabi ne me zafi ya rufeshi har asuba dakyar ya mike yayi sallar asuba yana idarwa ya sake kwanciya.
Dad ne yashigo wajan 9 dan yaga yadda jikin nasa yayi sauke yana kudin dune cikin bargo sai rawar sanyi yake kusa dashi Dad ya zauna cikin damuwa taba kansa yayi zafi rau harhuci jikin keyi toilet ya nufa towel ya dauka karami ya jiko shi goge masa jiki ya dingayi ahankali zafin ya fara ragewa bacci me nauyi ya dauke shi Numfashi ya saki ya tsurawa dan nasa idanu mafi soyuwa agare shi.
Yajima adakin kafin yatashi yafita,sàida Jalal ya kwashe 1 week yana jinya kafin ya samu sauki saura sati biyu biki amma babu shirin da yakeyi komai Jamal ne akan sa sai abokan su sune suketa aiwatar da duk wani abu daya kamata.
Jalilah taci gyara harta gaji sosai ta kara kyau naban mamaki duk inda ta gifta kamshi ke dukan hancin wanda ta gifta ta Kusa dashi kamshi ya samu wajan zama ajikin ta,yaune kuma zata tafi gida dan gano innar ta tare zasu tafi da Ammah sai murna take Ammah zataje gidan su tsaf suka gama shiri sai washe garin da zasu tafi ta sanar da Jalal ya shirya zasiyi tafiya to kawai yace mata danshi yanzu gaba daya duniya tayi masa zafi Ammah ta hanashi zuwa wajan Jalilah.
Yarasa wannan wane irin kaddararran gyara akeyi mata kamar wata Amarya shifa abun nan yafara bashi haushi imma gyaran biki ake mata to shifa bazai taba Auran Rufaida ba kome za'ayi kuwa.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 92
Da wuri suka gama shiri harda Indo zaatafi itace zatayi jagora karfe 9 daidai akofar gidan Hajiya Maimuna tai Musu Ammah tasha shiga ta alfarma haka Jalal yasha manyan kayan sa amma face dinnan ahade babu walwala ko kadan,suna gama daidaita parking Ammah tafita shiga gidan tai bata wani jimaba suka fito tundaga nesa ya tsura mata ido kirjinsane ya buga da karfin gaske ganin yadda tayi matukar kyau kamar ba itaba ta kara dawowa kamar baby.
Dago kai tayi suka hada idanu washe fuskatai da kara sauri ta isa gare sa caraf Ammah ta rike hannun ta harara ta watsa mata da sauri ta sunkuyar da kai ganin kallon da Ammah ke mata na gargadin takama kanta nutsuwa tai duk abinda Ammah tai yana kallon ta basarwa yayi kamar be gani ba.
Gaisawa sukai da Hajiya Maimuna da Indo to Jalilah saimunzo munanan tafe yar dariya tayi Ummi kema zakizo garimmu sosai ma inbanzo wazaizo kedai kizuba idanu kisharemin hanya tas zaki ganni nan kusa tana murmushi take fadin Allah ya kawo ki Ummi Ameen bankwana sukai kafin su dunguma sushiga mota.
Gidan gaba Ammah tasa Jalilah sukuma suka zauna abaya gaba daya kamshin Jalilah ya cika motar lumshe idanun sa yayi tuni kamshin ya haifar masa da kasala,waskewa yayi yana satar kallonta ta gefen ido kamar yadda itama take satar kallon sa,gudun kar Ammah ta hangota tana kallon sa shiyasa take kallon sa akaikai ce kallon juna akai Ammah da Indo murmushi kawai suka saki suka ci gaba da hirar su kamar basuga irin satar kallon junan da suke ba.
Sàida suka tsaya sukai sallah ahanya sukaci abinci sannan sukayi gaba basu sukaje ba sai kusan Magariba tunda suka shiga kauyan yara kebin Motar da gudu suna ga yan birni ga yan birni adaidai kofar gidan su jalilah Jalal ya faka motar duuu manya da yara suka zagaye motar.
Matan Aure hatta katanga suke leke bala metsire yana zaune da tsiran sa agaba ya zuba idanu yana jiran yaga wanda zai fito daga motar, su Ammah ne suka fara fitowa agajiye sai jalilah da data fito zuba mata idanu akai kamar sunga wata sabuwar halitta,bala ne yayi zumbur ya mike huhuhu ga jalilah tadawo wllh Jalilah ce ta dawo baturiya.
Nan yara akasa sowa ga Jalilah ga Jalilah Jalal da yake mota kare musu kallo yake sanda bala yayi magana ya juyo yana kare masa kallo tunawa yayi da abunda Jalilah tagayamai na yana jiran tadawo adaura musu Aure besan sanda ya fashe da dariya ba dama akan wannan ya zauna yake bata ransa abanza.
Wata cukui kuyayyiyar riga ce ajikin sa tayi cidin cidin ya dankwara wata muguwar hula kamar dan dako hakorannan kamar jarkasa sun dafe jawur babu kyan gani sai washe baki yake budurwar sa ta dawo,cikin gida suka dunguma banda Jalal da har wannan time din be fito ba cikin farin ciki inna suka tare su manyan tabarmi aka shimfida musu atsakar gida.
Gidan yasha filasta alailayeshi da siminti Jalilah sai kallon gidan take kamar ba gidan suba inna takalla tayi fes tasha atamfarta da sabon mayafi data yafa bakaramin dadi hakan yayi mata ba,kallon gwaggo tai datayi ras itama tsufan daya fara bayyana ajikin ta yanzu ba kamar daba zama sukai suna sauke numfashi.
Kai Inna wannan gari naku badai nisa ba tafiya yankin azaba dariya inna tayi kai Hajiya aibaku saba zaman mota ba shiyasa Kukaga nisan sa yanzu dai bari na baku ruwan Alwala in kukai sallah saiku zauna gaba daya haka za'ai Alwala sukai shima Jalal aka kai masa nasa ruwan alwalar Masallaci ya tafi kamar ba Masallaci ba wasu yan tabarmi akadan jejjera sun gama tsofewa.
Jiyayi bazai iya sallah a masjid din ba dawowa yayi aka karbomai dadduma asoron gidan yayi sallar sa,jeki shigo da Jalal din inji Indo tashi tayi tazo tasame shi ance kashigo ok mikewa yayi yabi bayanta ganin gidan fes yasa hankalinsa ya kwanta dan ya tsani kazanta arayuwar sa,sàida ya zauna cikin girmamawa yake gaishe dasu inna fuska sake suka amsa.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 93
Sosai sukaji dadin yadda ya girmama su tuwon dawa aka tuka yayi danko mulmul dashi miyar kubewa bushashshiya aka kada tasha naman kaji musamman suka yanka kaji biyar dan zuwan baki yajin daddawa suka miko musu ga man shanu,tunanin Jalal taya zai iyacin wannan bakin tuwon kamar bazai ciba ganin yadda Ammah take kallon sa yasashi jawo kwanon gabansa wani daki aka kaisu angyarashi fes ga katifa adakin yasha ledar tsakar daki.
Basu waje sukai dagashi sai Ammah da Jalilah loma daya yafarayi wani mugun dadine ya ziyarci kunnan sa sàida ya lumshe idanu tunda yafara cin ruwannan be tsayaba sàida yafara laluban tuwon yaji babu Ammah da Jalilah dake kallon sa fashewa sukai da dariya ganin shirgegen tuwon daya share batare daya sani ba.
Shafa kansa yadanyi yana Murmusawa eh lallai to daga yanzu kadinga cin abincin hausawa ko zakai kiba gafa yadda ka bude tumbi kashare wannan uban tuwon harda shanye miya duk batare daka sani ba,cikin dariya Jalila kefadin Ammah bakiga yadda cikin sa ya zama kato ba kamar me haihuwa fa hararar ta yayi ke zan haifa amma dariya sukai dukan su.
Ita ma Ammah taji dadin tuwon ba kadan ba magana ce kawai bataiba seda sukai kat sukasha ruwa sannan nutsuwa ta saukar musu, Jalila ce tafita da kwanukan sosai taji dadin yadda sukaci Abincin Innarta dama tasan badaga baya ba wajan Iya girki inna karshe ce.
Tsakar gida suka fito aka dasa sabuwar hira sai can Indo tai musu sallama zata wuce gidan su sosai inna sukai mata Godiya akan temakon datai agare su,kwana Ammah zasiyi sai gobe zasu juya inna dakinta takai Ammah Jalal shi kuma wannan dakin da sukaci abinci nan aka gyaramasa aka daura masa net tunanin sa taya zai iya bacci awannan dakin ba fanka ba AC yanaji yana gani haka ya kwana adakin be iya wani baccin kirkiba saboda zafi.
Kunu aka dama da safe aka soya kosai shima sunji dadinsa haka Jalal ya zage yasha kunun da kosan yaji dadin su matuka,fes Jalila ta gyara gidan tai wanke wanke Ammah da inna sun shiga gidan gwaggo wai zasu kara gaisawa daga ita sai Jalal agidan gabadaya badadi yake jinsa saboda rashin wanka bazai iya shiga toilet dinsuba ahankale gani yake duka daya kofar zata balle.
Kujerar daya gani kusa da ita ita ya janyo ya zauna ke yar kauye garinku badadi,seda kagama bude baki hadda su yawun bacci zakace ba dadi haba yarinya aini bana yawun bacci sedai ke aiko bazaka taba ganin yadda nake bacci ba dariya yadanyi zan gani mana saura kadan ki zuba idanu shikenan zan gani ai.
Yaushe zaka maidani makaranta kafadarsa ya dage sanda na bishi Iska inkuma na manta karatun baya fa ke kikasani se amaidaki js 1 tab taya zan koma baya gashinan kince zaki manta karatu nifa wasa nake ma.
Marairai ce fuska tai dan ALLAH Uncle j ka aramin wayarka nakira kawayena ke har wasu kawaye ne dake gyada masa kai tayi kaban nakira su please Uncle ke karki sake cemin wani uncle duk suna yannan to yaya Jalal shima banaso tome zan cama kallonta yayi nawasu sakanni.
My Choice zaki dinga cemin mene maanarsa to basai kinjiba haka nake so kidinga kirana ko aina ne kuwa shikenan my choice murmushi yasaki aikin ki yana kyau ta wajena miko mata hannu yayi suka kashe,to my choice bani aiyanzu kuwa mika mata wayar yayi tarike number din da suka bata.
Nasmah tafara kira Maman ta ce tadaga gaisheta Jalila tai amma bangane me magana ba yata dariya Jalila tai kawar Nasmah ce Jalilah kaikai kice babbar kawace Nasmah kizo ga kawarki Jalila aguje Nasmah tazo ta karbi wayar tarasa inda zata zauna tai wayar Maminta sai dariya take mata kullum maganarta daya Jalila yaushe zataga Jalilah.
Jalilah kece nice Nasmah nayi missing din matuka baki kaini ba har kukafa nakewa mamina ta nemo minke mina inaiwa Ammah ta Kuka fa cikin farin ciki sukai hira number wanene wannan ta yayana ce Idan kika kirashi zai kawo min sallama sukai bakinta kamar zai yage yana zaune yana kallon ta saiya jishi shima acikin Farin ciki.
Ablah ta kira itama Umman ta tadauka sanda taji an ambaci Jalila tun kan Umman ta bata ta wafta tana ihun murna sàida Jalilah tacire wayar daga kunnan ta tana dariya ke karki kashan dodon kunne sunsha hira ita daga karshe takira Ismah babu wadda batai murna da jinta ba ita ma hakan take tayi farin ciki matuka.
Wayar tamika masa Thanks My Choice dariya ya saki ya tabbatar Jalilah bata da wayo.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 94
Tsaf tagama gyaran gidan sunjima agidan gwaggo kafin su dawo,suna shigowa yimike dama yagaji Ammah kawai yake jira tafito yarasa wannan wace irin gaisuwa ce anshafe awa kusan daya da rabi,sallama sukaiwa su inna harbakin mota Jalila tarako su.
To Jalila muzamu tafi nanda sati biyu zanturo adauke ki daganan kinkoma can gaba daya saidai da ziyara zakizo wajan inna dan murmushi tasaki aidama acan nake Ammah ina jimawa banzo naga innata ba,yar dariya Ammah tai kuma hakane fa dama tuni inna tadade da barmana ke kallonta jalal yayi kamar yace yafasa tafiya amma gaskya bazai iya zaman kauyannan ba.
Saida tadena hangen su takoma Gida bala sai dago mata hannu yake tana sane ta nuna kamar bata ganshi ba ta lura baida hankali yarasa wadda zaice yana so kaf kauyannan sai ita yama raina mata hankali matuka harara ta watsamai tashige Gida.Har sun tafi eh inna kai gasky mutanan badai kirki ba Allah ya saka musu da Alkhairi ameen inna.
Kedai abinda nake so dake karki bani kunya kar kiki zama da kowa lafiya kinga bada yin Allah ba wannan yaron sedai ki hange shi ahanya amma daya ke Allah ya tsara hakan saiya nufeki da zuwa gidan su sunyi mana karamci matuka baxamu iya biyan su saidai muyi musu addu'a.
Kallon rashin Fahimta takewa Inna datake ta kwararo mata bayani nifa inna bangane Abunda kike nufi ba,zaki gane gaba kadan daganan tabar hirar suka fada wata gwaggo ce tashigo aka dora hirar da ita daka gansu suna cikin Nishadi babu wani abu dayake damunsu hankalin su kwance.
Bikifa ya fara kankama Hajiya Maimuna takawo kaya nagani nafada akwatuna guda goma haka ajere su reras sai daukar idanu suke kana ganin su kasan ankashe kudi kafin siyan su, Mom takasa zaune ta kasa tsaye lefen ya ya iso amma Abunda ya basu Mamaki har aka kwana aka wuni ba adauko lefan ankawo musu ba tun suna xuba idanu har mom tagaji ta magantu.
Suna zazzaune aparlo harda Inna datazo ganin kaya Mom tafito da fara'a a face dinta tagaisu suma rai asake suka amsa,Inna ce tai caraf dama yanzu nke shirin aikawa kizo kaga lefen dan naki murmushi ta saki ai inna kodaga ido ma nasan dan nawa yayi kokari dama ganinai tunda mu za'a kawowa ai bama saina tsaya gani Anan ba Idan aka kawo nagani atsanake.
Idan aka kai ina cewar Inna data tsareta da idanu part dimmu mana,tabe baki Inna tai to anfada miki nan za'a kawo can inda akaje neman Aure ai can za'a kai daga bayane za'a dawowa da Amarya kaganta,dan jim Mom tai bataso hakaba gaskiya aida senaga hakan kamar wahala ne saboda nisa babu zancan wahala badai mu mukaga zamu iya ba to abar mu mu aiwatar da Abunda mukai niyya.
To shikenan Allah y kaimu lokacin yanzu yaushe za aje kai kayan gobe gabannan aiba abori da sanyin jiki sassafe za'a tafi kai kaya, murmushi ta saki to Allah ya kaimu goban ameen mikewa tai bana shiga daga ciki binta sukai da kallo inna ce taja tsaki shashasha kawai sauna sudai su Ammah basuce komai ba.
Tunjiya Jalilah tarasa gyaramme inna suke tayi haka anshare agoge nan ga yan uwan babanta da yan uwan inna da suka zazzo,yau kuma sassafe aka aikata gidan gwaggo ramatu kanwar inna wai acan zata zauna saidare zata dawo haka tatafi da tunanin me za'ai agidan su da alama wata hidimar akeyi wadda ba'a sanar da ita ba tabe baki tai inagadai bata shafan ba.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 95
Inna ta aikawa makota za'a kawo lefen Jalila gida kam yacika kamar masu taron Biki,kusan azahar yan kawo kaya suka bayyana su Hajiya Maimuna kamar yadda tayiwa Jalila alkawari yaudai gata akauyan su mota daya sukayo saboda nisa yan uwan Dad guda biyu sai yan uwan Amma biyu sai Hajiya Maimuna baba dreba ne ya kawo su dama yasan hanya.
Ammu su tarba ta mutunci kuma sunya ba da karamci irin na mutanan Jigawa sun gabatar da kaya ana san barka kowa face din sa da farin ciki su maman Ladi sune yan gaba wajan karbar kaya sai washe hakora take zataje birni tagano tv da Jalila tace tayi goman tagidanta🤣🤣🤣wannan fa shine kowa da Abunda ya dameshi makocin me akuya ya sai kura.
Guda kawai ake saki kunsan dai mutanan mu na karkara badai iya guda ba dangin Jalal da Ammah sunji dadin yadda aka tarbe su babu wata kyama tattare da su shiyasa yan uwan inna da makwafta suka sake sakin jiki suka ci gaba da murnar su,basu jimaba bayan sunyi sallah sunci hadaddan dambu da akai musu suka juya da tukuici kala kala suma yan garin ba abar su abaya ba tsara ba suka dinga kawowa basi kasa aguiwaba suka dinga karba cikin Godiya da nuna farin cikin su.
Har kofar gida suka fito sunai musu Godiya da fatan sauka lafiya sàida suka ga kulewar su suka dawo gida nan zance ya zagaye kauyan Jalila Zata Auri dan birni yara da manya tururuwar zuwa ganin kayan suke.
Sai datayi sallar magariba tataho gida tana tafe ana daga mata hannu amarya Jalila har abun ya fara bata haushi kowa yace musu ita amarya ce oho,yau bala me tsire fuskarsa a hade take dan dazu agabansa aka dinga shiga da akwatuna tundaga nan yasan Jalilah tayi masa nisa,cikin sanyin jiki yataso ya tsaya agabanta Jalila ayau nasan kinyimin nisa ke kalar matar manya ce ba irina talaka ba inayi miki fatan alkhairi a rayuwar Auranki.
Anya bala baka fara shaye shaye ba waya cema Aure za'ai min kallon kimma rainamin hankali yake mata kinga Jalila ya zaki rainan hankali bayan dazu naga zahiri da idona gaba tai tabarshi tsaye ta lura akwai kwayar daya sha to Allah ya shirye ka tafada afili tana shigewa gida.
Gidan shiru kamar ba dazu aka dinga hada hada ba dakin inna tabude bakinta dauke da sallama kasa karasa sallamar tai ganin yadda wasu hadaddun akwatuna sukai mata welcome har kashe mata idanu suke tundaga kasa take kallon kayan yadda akajere su gwanin sha'awa set biyar biyar aka jera sai suka bada wani style na daban.
A hanzarce ta shigo dakin inna tana zaune akan dadduma tana lazimi jabar ta zauna agaban ta cikin mamakin take kallon Inna,inna dama Aure zakiyi batasan lokacin da dariya ta kufce mata ba kafin ta tsagaita da kyar yanxu ke Jalila banda abinki kamata tsofai tsofai dani wazai kawon wadannan iyayan kayan.
To kayan wanene indai ba nakiba inna gyara zama inna tai kayanki ne Jalila kwalalo idanu tai waje kayana Inna akamme za'a kawon wannan kayan akan munda aurenki ga wanda yake miki so na hakika babu algus kedin dai ke yake so bawani abu naki ba bamu da Abinda zai soki danshi yayi mana zarra tako ina.
Kallonta Jalila take kamar sokowa anya inna tana cikin hayyacinta kuwa inna kinamin zancan gaskiya ne kona wasa,harara inna ta watsa mata dama ina miki karya ne Girgiza kai tayi to kibude kunnuwanki da kyau kijini Aure za'ai miki nan da sati daya babu fashi kamar da kasa inji me fadar auransa.
Inna gani kawai tai Jalilah ta rushe da Kuka harda majina nidai wllh inna ko wanene yace zai aureni saiya sani aini bance ina san kowa ba kuma uncle dina yace ban isa Aure ba shida kansa zai zabo min mijin da zan aura,wanene uncle kuma yaya Jalal mana na gidan Ammah murmushi Inna ta saki yaro yaro ne haka ya gaya miki gyada mata kai tayi.
To aiyanzumma shiya ya zabo miki mijin kuma da yardar sa za'a daura aurannan nan da sati daya,dif ta tsaya da kukan da take haka ya gaya miki inna shiya turo wanda zai Aure ni kwarai kuwa shiya fadamin da bakin sa,zan can auransa kuma fa af ai har wannan sakon ya sanar dani nafada miki ya fasa Auran Rufaida take kowa da sauri ta dago tana kallon Inna washe hakora tai yanxu inna kina nufin ya fasa Auranta gyada mata kai inna tayi.
Tuni Jalila ta share hawayan ta tunda harshine ya zaban mijin kuma yafasa Auran Rufaida na aminin ce da wannan Auran Inna gaban akwatunan tatafi tana shafawa amma fa inna sunyi kyau kizo kibudemin naga kayan haba kawai inna ta rike tana kallon yarinta irin ta Jalilah tana son mutum amma kiriri takasa fahimtar hakan.
Yanxu ke Jalila sai azo aga kin tasa kayan Auranki agaba kina kallo salan kisa azagemu to bazaki gani ba ki bari semun kulle koda da daddare kyagani marairai cewa tayi dan Allah inna kibarni nagani bari na kulle kofar tashitai harda hadawa da gudu ta kulle kofar.
Inna tana kallon ta tana sauke kaya saidatayi musu filla filla ihu taji tasaka sàida inna ta razana ta mike tsaye kirjinta na dukkan tara tara idanu waje take kallon Jalila da abu ahannu ashe wai ihun murna take.Inna zokiga waya aciki wayyo dadi kici kicin bude wayar tahau yi akashe take dayake dama ta saba da daukar wayar Ammah babu abunda bata iya awaya ba kunnawa tai saigata acike full akwai sim guda daya aciki.
Kamar jira ake ta kunna tafara ringing tsurawa sunan dayake yawo akan screen din tai My Choice taga anrubuta tana ganin hakan ta gane wanda yake kira da sauri ta daga my choice ta ambata ciki happy Lumshe idanun sa yayi tanajin saukar numfashinsa akunannan ta.
Shagwabe face takarayi gaba daya ta manta da inna data daskare atsaye tana kallon ikon ALLAH kayan datai kaca kaca dasu takalla tasake kallon Jalila da batajin me take mafada taga dai sai rangwada kai take kamar kadanga ruwa.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 96
Kara gyara kwanciyar sa yayi tare dajan filow ya kankame jiyake kamar yajawo ta tacikin wayar shagwabar nan datake gaba daya ta su su tashi.
My Choice waida gaske ka fasa Auran Rufaida saidaya dan saki murmushi wa yasanar dake hakan cike da yarinta take fadin Inna yanzu tafadamin shiyasa na yadda da Auran da akace kaine ka zabon mijin,yar Dariya ya saki kin yadda kenan kitafi gidan wani ni kuma nazauna agida gyada kai tayi kamar yana gabanta eh gwara kazauna agida kawai,meyasa saboda bana so ka Auri Rufaida.
To acikin kawayanki wa zaki bani bata fuska tai gwara dai kazauna kaikadai daga kai sai Ammah saini,gidan Mijin naki fa aini babu inda zani muna tare tunda kai kasamo mijin sai yadawo wajan Ammah shima,dariya Jalal yake sosai farin ciki na sake mamaye shi matukar yana tare da Jalila bashi da wata sauran damuwa.
Tun inna najiranta tagama wayar ta gyara kayan data wargaza harta gaji dakanta ta zauna ta gyara tana mitar shirman Jalila yayi yawa haka za'ai mata Auran yarinya ba hankali koda yake kunfi kusa kuje can kedashi kukarata.
Sai kusan goma suka rabu kamar bazasuyi sallama ba dakyar dai suka rabu kowa ya kwanta itakadai take sakin murmushi duk farin cikinta baya rasa nasaba da cewar yafasa Auran Rufaida kuma bazai Auri kowa ba bayan bikinta amma sakaryar babu Abinda ta gane ranta fes tahana Auran Jalal da Rufaida.
Acan gidan Ammah shiri ake tako ina Dad babu zama sako da lungu gayyata yake na Auran dan sa haka Ammah anbugo IV amma abun mamaki babu sunan amarya saina Ango Jalal Ma'aruf Muhammad &Yar Aljannah abinda aka rubuta kenan hakan be damu mom ba aganin ta wannan duk acikin sone sai fankama take tana hura hanci.
Har wannan lokacin Rufaida bata denabin maza ba kamar karya Mom ta zage sai gyarata take tana fita mazan banza irinta suke kwashe gyaran sarai Jalal yasan abunda take aikatawa amma tunda bashi da hurumi da ita ko ajikin sa ya kauda kansa daga sha'anin su
Shi dai tunda Allah ya tsallakar dashi daga kaidin su ya godewa ALLAH.
Duk wanda yaga katin saiya dinga mamakin lallai Jalal ba karamin son rufaida yake ba,biki bidiri burede gidan kansa gyara na Musamman akai masa babu inda besha gyara ba takanas Ammah tasa aka kira mata dan iya akan ya kawo iya ko bayan bikine saita dawo aiko ya kawota har kd yayi murna ganin inda Mahaifiyar sa tai rayuwa kuma angirmamata.
Can kauye Jalilah tanashan gyara Inna gyara irin nasu na gargajiya take mata mata dan danan takara wani sihir taccen kyau babu wata damuwa a zuciyarta hankalinta kwance zabin My Choice dinta zata aura kullum basu da aiki suna makale awaya wata shakuwa ce ta musamman takara shiga tsakanin su.
Sosai ya kara dasa mata sansa azuciyarta tako susuce bata da aiki sai tunanin Jalal haka shima abangaransa gani yake kamar lokacin baya tafiya kullum acikin lissafi yake din kuna kala kala haka yayi su yawancin duk wata kala daya sawa Jalilah shima yana da kalar su burunsa komai sudinga sa kala daya.
Takanas Ammah ta aiko dame tsantsarawa amarya kunshi tako zanu Ja da baki haka aka tsara natashi dan danan ta kara fitowa Amaryar ta sak dangin inna dana babanta sun cika gida sai hada hada ake wasu dika dikan tukwane aka girke matan kauyan suna da hadin kai kowaccen su fitowa tai takama aiki abundai sai san barka.
Gobe ne daurin Aure gidajan biyu fa sun kacame kota ina shiri akeyi Jamal shima babu zama shine akan komai ankon farar shadda sukai Jalal shima babu zama gidan sa da Dad ya mallaka masa bawani nisa ne daga gidan Ammah ba komai ya zubawa Jalilah hatta da spoon Amma ta siya mata ita Jalilah yar tace halak malak.
Hakan ta fadawa inna itace Uwar amarya bata bukatar komai daga gare ta ranar Inna tai Kukan farin ciki amma duk da haka taroki Ammah tabarta itama ta bada gudummawar ta.
Mrs Baba Bello ABUBAKAR
.......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 97
Ranar asabar karfe 11 dai dai dubban al,Umma suka shida daurin Auran Jalal Ma'aruf Muhammad da Amaryar sa Jalilah Muhammad Uba akan sadaki naira duba dari biyar,maroki sai shela yake yana kara nana tawa gaba daya kauyan ya dinke da mutane Jalal yasha dokakkiyar shadda da bababr riga dark blue ba karamin kyau tayi masa ba sai baza babbar riga yake fara'a kuwa ba azancanta.
Shima Dad yasha farar shadda bakinsa har kunne Allah ya nuna masa Auran dan sa babu abunda zaiwa Allah sai Godiya da wannan babbar ni'ima da yayi masa,gaida iyayan Amarya suka dunguma cikin gida sai nuna jaka akeyi ana ga angon sai sunkuyar dakai yake zuciyar Inna kamar takadda saboda farin ciki yarta tatako duniya a sa'a.
Jalilah ko tana daki tayi lamo tunda kace andaura mata Aure taji jikinta yayi sanyi duk rawar kafar da takeyi tai lakwas tunanin ta wa Uncle ya zaba mata shiyasa duk tashiga damuwa.Shima be nemeta ba yasan rigimarta sarai sa hadu agida yau zasu juya har da ita acan za'a sha shagalin biki shiyasa suka taho da dangin babansa mata su biyu sune yan daukar Amarya.
Ko awa daya ba ai da daura Aure ba suka bukaci abasu amarya su juya da ita karasa Jalilah tai wanka akai aka canza mata kaya babban mayafi aka lulluba mata haushi duk yacikata na wannan lullube lulluben da akeyi mata kamar matar liman wajan Inna aka kaita tai mata fada sosai tai mata nasiha har kuka sàida Inna tai amma Jalilah idanunta kamas ita bataga abun kuka anan ba tadaiji badadi saboda rabuwa da Innarta.
Motoci guda goma suka zo dasu yanayin tafiyar nesa befi mutum 10 aka dibaba ciki harda gwaggo da maman Ladi,haka sukai jerin gwano reras suka dau hanya harda Ango acikin tawagar amma babu wanda zai dauka akwai shi aciki yayi luf acikin mota,sai yamma lis suka isa tun daga layin gidan kasan bikin manya ake motocine reras masu numfashi.
Get baba ya wangale musu gaba daya suka duru aciki manyan matane suke zazzaune akan wasu fararan kujeru da aka kawata harabar gidan da su kowacce ta kashe dauri ganin zuwan amarya suka mike dan tarar ta,cikin wadanda suke zaune awajan harda kawayan Mom jin ana ga amarya suka fara kallon kallao da tunanin ko mutum biyu akeyiwa Aure Agidan.
Tashi sukai dan subawa idanun su hakkin sa ganin amfito da figaggiyar yarinya abun ya daure musu kai sunsan rufaida ba kadan bace balle suce ramewa tai inko har itace tatadawo haka to tabbas sai HIV ta kwaso amma tunanin su wacece wannnan da aka lullubo ake sakin guda ayarin yan rakiyar amarya suka bi dan su bawa idanun su hakkin sa.
Yan uwan Mom maza sune suka ciko wata katuwar mota suka taho daurin Aure kai tsaye masallacin gidan aka dunguma harda Dad shine agaba sai wadansu dattijai guda biyu da wani atsugunne agaban su wanda bansan wanene ba.
Jinai kawai ana fatiha andaura Auran Rufaida Saminu da angonta Kasimu akan sadaki dubu 50 wani maroki ne me jarabar surutu yaketa nanatawa,kowa kasa kunne yayi danjin wani sabon al'amari daya afku babu wanda yasan taya hakan ta kasance.
Mom tana tsakiyar kawayanta ana shewa afujajan wata kawarta hajiya turai tashigo kamar zata tashi sama hannun Mom kawai taja suka koma gefe bakinta har rawa yake wajan tambayar ta ya sunan angon da Rufaida zata Aura,dariya Mom tayi Allah natuba kemadai hajiya Turai kamar wata me magagin bacci Jalal dinne baki sani ba dan me gidannan hajiya Turai zatai magana Mom tabar wajan saboda kiranta dataji anayi.
Binta da Kallo kawai Hajiyar tayi tana jijjiga kai lallai yau zasu sha kallo ba taja bakinta ta tsuke intai wari kowa zaiji.
Can dakin Ammah Jalilah tana kwance ajikinta tana zuba mata tambayoyi kamar yar jarida Ammah ina My Choice kallon ta sosai Ammah tai wa kenan Uncle ni tunda nazo banganshi ba yazo ya nunan wanda yace ya auramun dan murmusawa kawai Ammah tai haka ya gaya miki eh to saiki jirashi yazo ya fada miki daga nini karki karya ni.
Tashi Ammah tai tafice wajan bakinta tabar Jalilah adakin tana kwance bacci ya fara daukarta taji anturo kofa,hawowarsa kenan da kyar ya kufto abokan wasan sa sun sashi agaba sai tsokanar sa sukeyi ya taho neman Ammah.
Ajiyar zuciya ya sauke hangota da yayi akwance ana kiran sallar magariba ita tana kwance jin shiru ba'ai magana ba yasata dagowa dan taga wanene ido biyu sukai ita da Jalal,kwabe face tai kamar zatai kuka dariya yadan yi yana kallonta ahankali tataso tazo tatsaya agabansa.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 98
My Choice sàida yaji wani yarrr ajikin sa jininsa yahau yamutsawa tundaga saman kansa harkafar sa yakejin tsigar jikinsa na tashi ganin yayi shiru ya zuba mata ido kamar wani soko taruko hannun sa,tare gaban su ya fadi jitai kamar shorking yajata da sauri ta cikamai hannu shima kallon hannun nasa yayi abunda taji shima yaji shi,diddira kafafu tafarayi akasa kauda kansa yayi da sauri bayason idanun sa yakai Inda zata karasa kassarashi gaba daya.
Meyasa bakazo wajan bikinnawa ba um kin gayyace ni ware idanun tayi saina gayyaceka ma zakazo gyra ya daga mata alamun eh zai sake magana akabide kofa Ammah ce ta shigo take kare musu kallo sosa keya yayi ganin irin kallon da Ammah kemasa sunkuyar da kansa kasa yayi yafice sum sum dashi dawo da kallonta tayi kan Jalilah dabishi da kallo.
Wuce kije kiyi wanka ina zamuje Ammah Dinner mana maza kiyi sauri me kwalliya ta karaso to kawaii tace tajuya tafada toilet din Ammah da yake tashin kamshi.
Can gidan Inna ma cike yake da dangin Dad suma suna can sunata shirin tafiya Dinner haka bangaren Mom har amfara cancada mata kwalliya ita uwar amarya da kawayanta babu danginta ko mutum daya danginta maza da sukazo har wannan Lokacin batasan da zuwan suba waje na musamman Dad ya killace su.
Rufaida tana tsakiyar kawayanta suna shakiyanci zantukan da suke saidai ace Allah ya shirya amma magana suke mara lissafi dagajin lafuzan bakin su kasan tarbiyya babu ita atattare dasu,itama kwalliyar ake sheka mata salima tana gefe azaune bakin Cikin duniya ya taru yayi mata yawa zuciyarta sai tafasa takeyi dagaske dai Rufaida tayi nasarar Auran Jalal.
Kafin karfe 9 gidan ya sake dinkewa da jama'a kamar rana ko ina haske ne tarwai sai dibar mutane abokan Ango sukeyi, Jalilah tayi kyau harta gaji da haduwa wata doguwar rigace dana rasa dame aka dinkata kamar angwadata dunkin yayi das ajikin ta,jitai anrufe mata idanu ana dariya Ahankali aka bude mata idan suna jere agabanta duka su ukun kowaccen su tasha kwalliya kayansu iri daya.
Cikin rawar murya take nuna su gani take kamar amafarki Nasmah Ablah Ismah dagaske ku nake gani a idanuna cikin Dariya suke gyada mata kai mikewa tai daya bayan daya ta rungume su kamar bakinta zai yafe tsabar farin ciki bata taba zatan zata gansu awannan Lokacin ba.
Wanene yafada muku,harara suka watsa mata tunda ke baki gaya manaba ance kowama irin kine yayanki ne ya gaya mana kuma shine yayi mana wannan kayan na jikimmmu yace mune kawayan amarya sake kallon su take baki bude my choice dinne ya dinka muku kallon juna suke suna maimaita abunda sukaji tafada ihu suka sa suka tafa ah cass.
Soyayya ruwan zuma kunji fa yan uwa Ablah ta kalli su Nasmah da suke dariya kallon tashin fahimta Jalilah take musu dariyar me kukemin ah bakomai ashe ana diga lobayya ah su Jalilah angirma,banza tai musu ganin yadda suke son juya mata Maganar ta.
Sai aka gama dibar kowa sannan aka fito da Amarya adaidai Lokacin aka fito da Rufaida,kakakara kaka ga Jalilah fa Rufaida kallon kallo akeyi da mamakin kwalliyar da aka caccadawa Jalilah kamar itace amaryar sai gaba daya Rufaida taji ta raina kanta motoci biyu ne awajan Hajiya Maimuna data ruko hannun Jalilah motar da take gabansu ta bude ta saka ta.
Sai kawayan ta Nasmah aka saka agaba Ablah da Ismah tace su biyota tatafi dasu,tsaye akabar Rufaida da kawayan ta daya motar da sukaji ana danna hon nan suka nufa Rufaida da kawayan ta suka shiga tunanin ta to ina Jalal din dama batare zasu tafi ba ko acan zasu hadu.
Saidata daidaita zaman ta tukunna ta kalli gefanta jin kamshin turaransa ya cika motar shidinne kuwa ya hakinmce ba karamun kyau yayi mata ba kallonsa take kamar tasamu TV duk abunda take yana kallonta kamar me bacci amma fes yake kallonta bakaramin tafiya tai dashi ba,gudun karya bada kansa yaki tashi daga kishingidan da yake yasan matukar yazauna to akwai damuwa tabbas bazai iya control din kansa ba.
Ganin kamar bacci yake yi saita koma wajan Nasmah da dariya take cinta ganin irin kallon da Jalilah tamewa angon nata ba kunya ba kara haka Jamal dayake tuki dariya duk ta cikama sa ciki Lallai Jalal dan iskan duniya ne sai gara yar mutane yake yafito ya gayamata shine angon amma yaki waikar yarinya ta rainashi zaiga karshan raini kuwa.
Tunda Nasmah tashigo Jamal yake satar kallon ta yarinyar ta matukar tafiya da imanin sa ya fada da yawa bazai bar wannan damar ta wuce saba kafin su tafi zai kafa gwamnatin sa.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 99
Parking sukai awani kawataccen event Iman Event Center tungaga farkon get za'a farayi maka welcome kusan Lokacin daya suka iso da su Rufaida kikicin bude kofar Jalilah keyi taji anrike mata hannu yana ayadda yake ko motsawa beba Ahankali ya tashi zaune saurin kauda idanunta tai daga kansa ganin yadda idanun sa suka rikida kamar ba nasa ba.
Murmushi ya saki yasake murza hannun danta kalleshi amma taki kallonsa,sàida ya tabbatar su Rufaida sun gama shigewa sannan yafito ya zagaya ya bude mata da kansa fitowa tai Ahankali kanta akasa gaba daya kanta ya kulle wai ina Mijin nata me yaya Jalal keyi anan kaynsu iri daya kanta ya toshe gaba daya.
Abokan Jalal da Jalilah atsakiya suka saka su tundaga waje mc ya saki kidan tarar Ango da Amarya sannu amarya wakar da take tashi kenan kallo fa ya koma sama sanda Rufaida tashigo babu wanda ya kalli barin datake kawayan tane suka rakata Inda amarya da Ango ke zama itakadai tsuru ranta abace yake da wulakancin da Jalal yayi mata nakin zuwa da wuri.
Jin ana amarya da ando zasu shigo kallo ya koma sama Innah data hakimce kawai sakin murmushi take tana kallon face din mom data mike tsaye danjin wani bakin labari kodai nasu kadai zasu gudanar da Dinner din ba akwai wata amaryar,atsare ajere suka shigo hasken 📷 ne ketashi yaki ina ganin Jalal da Jalilah yasa wasu da dama mikewa sai akallo Rufaida sai akalli Jalal da Jalilah.
Nan fa hayaniya ta kaure dakyar aka samu kura ta lafa waje na musamman Jalal da Jalilah suka zauna zuciyoyin mom da Rufaida harbawa kawai suke na tsanin kaduwa da tashin hankali dama su biyu ya aura be gaya musu ba amma ya cucesu ya ha ince su sunci alwashin kota halin kaka sai sunfitar da Jalilah daga gidan za'ai tashin hankali.🤣🤣🤣🤣
Suna can suna tunanin zuci sukaji ana neman ango Jalal da Amaryar sa Jalilah gaba daya Jalilah ta zama hoto jin ana hadata da Jalal matsayin shine mijinta kallonsa takeyi amma yaki yadda su hada ido yana tsoron abunda zai karanto acikin kwayar idanun ta inhar Jalilah ta gujeshi besan inda zaisa kansa ba.
Mikewa sukai ba karamin dacewa sukai da juna ba Ammah bakin aljihu ta bude tako ina zazzaga musu nera take tana shiga akasa mata wakar wayyo Allah mamana wayyo Allah mamana meshare hawayena mamana mamana zuciya fa ta raurawa batasan sanda hawaye yafara tsiyaya daga fece dinta ba gaba daya ta hada su ta rungume kafin ta fashe da kuka Mutane da dama ta karya musu zuciya.
Jalal shima idanun sa cike da hawaye Jalilah kuwa kuka take shabe shabe har wannan lokacin still wakar ce ke tashi sàida hajiya Maimuna tazo tajanye Ammah ta bata baki sannan tai shiru nan biki yaci gaba da gudana kara iya kara anayinta awannan waje.
Wai ina yan tim din Jalal da Jalilah kubude bakin aljihu fans dan wannan bikin nakune.
Bakin ciki da bacin rai yasaka Mom barin wajan ita da tawagarta rufaida rusar Kuka take kamar zata shide ai Salima kamar ammata Albashir da aljannah ranta fari kar kamar takadda sai tikar dariya takeyi ta tsananin farin ciki burinta yana dab da cika tana da tabbacin ba kaunar rufaida yake ba ako wane lokaci zai iya sallamar ta.
Abokan Rufaida su baba da cele sanda suka ga Jalilah matsayin matar Jalal hankalin su ya tashi dan sun kwallafa rai akanta rai bace suka bar wajan babu wanda ya kula dan uwan sa shida babaa da gaske yake sonta kuma a shirye yake daya aure ta tun sanda ya ganta har wannan lokacin Zuciyar sa bata huta ba.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 💯
Sai kusan 11 suka dawo daga wajan Dinner kowa burinsa ya nemi waje ya kwanta amma me suna shigowa sukatar Mom tatada masifa agidan tana tsaye taci uwar damara Ammah ce akan gaba wajan shigowa tana shigowa taji anshaki wuyanta nan fa fada ya kaure Dad dayake dakinsa yaji hayani tayi yawa yafito.
Yana fitowa tasaki wuyan Ammah datashi shaka ta shako wuyan Dad dura masa zagi takeyi tako ina ba girma babu mutunci ransa abace ya sharara mata mari saidaka walkiya sannan tai zaman yan bori sosai taji wannan marin dafe kunci tai tana kallon sa cikin tashin hankali mari Lallai kwabarta tayi ruwa tunda har ya iya daga hannun sa sama ya zabga mata mari.
Duk da haka bata daddara ba ta sake mikewa taci gaba da tijara babu wanda ya kulata kowa tafiyar sa yayi yabarta awajan dan kanta tagaji da hayagaga takoma part din su afusace har wannan time din Rufaida kuka takeyi tsabar bakin cikin abunda akai mata ankunya tata acikin kawayanta.
Jalal sune na karshan shigowa shiyasa basu san abunda ya faru ba dakinta tawuce tana shiga su Nasmah suka sa mata ihu Amaryar Jalal kallon kawai tayi gaba daya jikinta yayi sanyi dagaske Uncle din ta aura kodai kunnan tane beji mata daidai ba amma meyasa to baagaya mata shine wanda ta aura ba.
Sedatai wanka tai shirin bacci harta kwanta tamike baki azumbure setaje tatambaye shi yayi mata bayanin da zata gane dan bazata zauna kanta aduhu ba,daga ita se rigar bacci iya guiwa sai hijab data saka azummar ai yanzu zataje ta dawo bata tsaya aparlo ba ta kutsa kanta cikin daki daidai lokacin da Jalal ya fito daga wanka babu abunda ya daura ajikinsa da tunanin shikadai ne adakin ai karaf Jalilah tai mummunan gani jin karar ta kawai yayi tabaje akasa tatafi dogon suma na tashin hankalin abunda ta ganowa idanun ta.
Asukwane ya tsagunna agabanta yana girgizata ai Jalilah tayi nisan zango sai Lokacin ya lura da yadda ya fito da sauri ya dauko boxer ya saka sannan ya ciccibe ta gaba daya ya dora ta akan bed kafin ya dauko sassanyan ruwa ya shafa mata afuska hijab jikinta ya cire duk yadda yaso kauda idanun sa daga kanta kasawa yayi makwat ya hadiyi wani mugun yawu.
Jalilah data farfado yanzu ganin irin kallon da Jalal yake mata asukwane ta mike dan yanzu ba karamin tsoransa takeji ba caraf ya damkota ya maida ita ya kwantar nauyinsa ya sakar mata gaba daya yana kallon face dinta idanunta kamar zasu fado.
Sai nishi take saboda nauyinsa daya jibga mata waya kawoki dakina adarannan bakomai dan Allah uncle ka dagani wllh kana da nauyi bazan dagaki ba sai kingayamin abunda ya kawo ki tukunna zuwanai na tambayeka dagaske kaine mijina wllh abunda ya kawoni kenan karya kikeyi waya sato ki kalleni rufe idanun tai da sauri ni babu abunda nagani amma kika suma sekingayan abunda kika gani fashewa tai da kuka ganin irin iskancin da Jalal ke mata ni babu abunda nagani kaina ne yake ciwo shiyasa na suma.
Har dariya yasaki kin tabbata da sauri ta daga masa kai alamar eh to shikenan kin fanshi kanki amma tambayar da kika zo da ita yanzu zan baki amsarta, girgiza kai tayi Allah na hakura basai ka fadamin ba zan tambayi Ammah aini yakamata dama ki tambaya nine nake da amsar baki to ana dole ne nidai na fasaji nikuma saina tabbatar miki zata kara magana ya rufe bakinsa da nata.
Duk yadda Jalilah taso ya cikata ki yayi saidaya tabbatar ya kashe bakinta dakyar ya iya control din kansa karyayi Abun kunya tana ganin ya saketa da gudu tamike da hijab dinta ahannu gyaran gashin da akai mata gaba daya ya tarwatsa shi afujajan ta fada daki idon su Ablah biyu tundaga sama harkasa suke kallon ta kafin su fashe da wata muguwar Dariya suka tafa da alama ya baki kyakykyawar amsa.
Banza tai musu tafada toilet ta dade aciki kafin tafuto fuska ahade sàida suka sake taokanarta kafin bacci ya dauke su.
Jalal kuwa kasa bacci yayi saboda tsanin shaukin Jalilah likin daya dade yana lallabawa ya ballowa kansa sàida aka kusa assalatu da kyar bacci ya dauke sa cike da mafarkan habibiyar sa abar sonsa da kaunar sa.
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 101
Da asuba ma da kyar ya tashi saboda tsabar baccin daya cika masa idanu dan yayi baccin ya gudo yabar abokansa acan hotel gashi ya dawo Jalilah ta hargitsamai lissafi,ruwa me dumi ya sakarwa kansa yana fidda numfashi me zafi ya dade a toilet din kafin ya fito daure da bathroom yana tsane kansa da towel, jallabiyya ya zura jin za'a tayar da sallah yafita da sauri karya rasa jam'i.
A masjid suka hadu da Dad sai zabga Murmushi yake burinsa ya cika Allah ya nuna masa bikin Jalal tare suka fito hannun su rike da juna kamar abokai hira suke hankalin su kwance,rabuwa sukai kowa yayi hanyar part dinsa kamar ya leka yagano Jalila kawai ya basar yayi gaba baya son yaran can su rainashi.
Sai kusan 9 suka farka daga bcci ganin yadda rana ta kwalle yasata mikewa da sauri toilet ta fada tai wanka tana fitowa Ammah tashigo yawwa tin dazu nke zuwa duba ku ko kuntashi amma sai naganku abaje kuna bacci oya kowacce taje tai wanka kufito mi break amsa mata sukai da to,a gurguje sukai wanka suka shirya Jalila ce tai musu jagora har dinning table din sun hallara sukadai ake ji.
Hada ido sukai da Jalal dayake binta da wani shegen kallo saurin sunkuyar da kanta tayi tare da runtse idanu sosai takejin tsoron sa ayanzu da kuma kunyar da,jan kujera sukai suka zauna bayan sun saiga da Ammah Dad da Jalal kan Jalila na kasa tana facing din Jalal takasan ido yake kallontà taki barin ko yaya su hada ido Ablah da Ismah sai kunshe dariya sukeyi ganin yadda Jalal ya mance agaban iyayan sa yake ta kasani table din ya zuro kafarsa yana taka kafarta basarwa tai kamar bata jishi ba.
Duk Abinda yakeyi Ammah na kallon sa mikewa tai ganin wannan rashin kunya ta Jalal bame karewa bace Dad tashi yayi yabi bayan Ammah yana jinjina rashin kunyar Jalal break dinma ya kasayi hankalinsa yana kan matarsa oh zamani Allah ya kyauta.
Su Ablah kememe kin tashi sukai Jalal ne ya kalle su ku kuma zaman me kuke ransa hade yake kallon su,ai bamu gama break dinba kaga ko ina zamuje harara ya watsa mata saurin sunkuyar dakai tayi sukaci gaba da break din su hankali kwance.Innace ta rangada sallama gaba daya hankalin su kanta ya dawo yayyan Dad da kanin sa suna biye da ita abaya oh ni jikar mutum hudu mezan gani.
Rasa kunya dakazo kasata agaba kahanata tai karin kumallon mene ribarka yaro bata ido kasata agaba kabari akaina ita mana kai dai Jalal baka da kunya,tashi kekuma kina zaune yana kare miki kallo aike yanzu tsadane dake be kamata ma ya ganki awannan lokacin ba kamar ya make inna dan haushi haka kawai tazo zata katse masa jindadi.
To ke Inna ina ruwanki badai matata na kalla ba ko matar wani kikaga nake ina kallo halal dina nake kallo fa lailahaillallahu ni kake fadawa haka to wllh kamin rashin kunya baza akaita yau ba sai wani satin sainaga yadda zakai ja'iri mara kunya tashi kiwuce daki kekuma sakarya sai zazzare idanu kike kamar mazarin tsire.
Iya da futowarta kenan daga daki ta samu abinyi nimadai Inna yanzu na fada daki ganin abun yafi karfin ganin idona yaran yanzu bata ido ganemin hanya yar uwa,tashi Jalal yayi fuuuu yafice daga Gidan gaba daya Ammah ce ta sauko tanai musu sannu da zuwa shima Dad fitowa yayi yagaida yan uwansa da inna data gama sababi yanzu.
Kai jeka kira min saratu mikewa Dad yayi har part din su ya shiga rai bace yake binsu da kallo rufaida idanu sun luhu luhu tasha Kuka ba ita kadai aka aura ba harda makiyiyarta Mom tana zaune kamar zata fashe saboda tsabar takaici da bakin ciki saiku fito keda yayanki ko tsaywa jin amsarta beba yafice,kamar baza su zoba can kuma sai gasu sunfito Cikin harara inna ke fadin aina dauka bazaku zoba tabatattu marasa mutunci.
Kaf nan babu sa'anku da zaku shanya mu kamar marasa aikin yi to kodai jiran zaman haihuwa muke aiyaci ace ta haihu mun kama gabammu,babu wadda ta tanka mata har suka zauna cikin bacinrai Mom take kallon Inna yanzu inna duk rashin adalcin da akai mana ba'a gani ba maimakon ararrashe mu sekuma abimu da masifa.
Cikin bacinrai Dad ya daka mata tsawa mahaifiyar tawa keyi miki masifa saratu zan baki mamaki wllh mamaki nanawa kuwa tunda aka ha'ince ni akaiwa yata kishiya,zai sake magana inna ta daga masa hannu kyaleta haka komawa yayi ya zauna zuciyar cike da tsanar Mom da ahalinta gaba dayansu ba ita kadai ba.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Isma'il Idris
Page 102
Kallonta tamayar kan Mom rashin adalcin me akai miki saratu ai rufaida kadai Jalal zai aura amma tsabar Munafurci irin na uwarsa saidata shiga tafita aka hada da waccan yar kauyan yata tafi karfin tayi zaman kishi da ita,dan Murmusawa inna tayi ALLAH sarki kallon rufaida tayi toke zaki zauna da kishiya ko bazaki zauna da ita ba cikin hura hanci tace babu zamana da.kishiya a tsarin rayuwata hasalima ko sunan ta na tsani ji.
Madallah Dad ta kalla ina wadanann bakin jeka shigo dasu mikewa yayi minti biyu yayi yashigo da sallama kusan mutum biyar ne suka biyo bayan sa ko kallan su wanene mom batai ba lale ku zauna inna ta yimusu maraba gaisawa suka farayi muryar da Mom taji yasata dagowa da sauri batasan lokacin data mike tsaye ba jikinta na karkarwa kallonta shima yake kallon tsana da kyama da bakin ciki.
Kauda kansa dattijon yayi kamar zai amayo da zuciyarsa yadda takeyi masa matukar daci da radadi,saiki zauna ai inkin gama rawar jikin inji inna zama tai kanta akasa wanda idanun ta ya sake sauka akansa tuni tashin hankalin ta ya sake hauhawa.
Ina fatan kingane su inna dake kallonta tafada kyaleta hajiya ko alahira bana fatan mu hadu da wannan marar mutuncin,ashsha adaiyi hakuri malam adanne zuciya sai an hada da hakuri kowa da tasa jarrabawar.
Shiru kawai yayi dan ganin girman Inna amma jiyake kamar ya tashi ya rufeta da shegen dukan da saiya kakkarya mata kasusuwanta sannan zai barta,gyara zamansa yayi tare da gyaran murya Hajiya wannan bazata taba sanar dake my suwanene agare ta ba dan mun taba hanya tunkafin tayi rikar haka.
Kamar yadda kika sani ni mahaifinta ne mahaifiyarta tabada gudummawa me karfi wajan tabarbarewar rayuwarta ta sangartata kome take so shitake yi mata babu kwaba babu fada kome tayi daidai ne awajanta tatara kawayan banza yau itace anan gobe itace acan harkwana tashayi awaje amma bani da katabus inzanyi magana mahaifirya kamar zata hau kaina da duka.
Ganin irin lalacewar datai mahaifina ya bani umarnin hadata da dan uwanta ayi musu aure ko zata nutsu dakyar akai wannan aure dayake Allah ya tsara sai anyi Auran dan dole najata nakaita har gidan mijin ta wulakancin yau daban na gobe daban haka tatisa mijin agaba zagi nacin mutunci bata raga masa kokadan Gashi ALLAH yayi shi da hakuri.
Karfa kice tadaina yawo àah tananan tanayi saitaga itafa bazata zauna cikin talauci ba ta girmi wannan rayuwar ko wata biyar bata rufa ba ta dawo gida da sunan yaji nan nai tsalle na dire nace bazata zauna min agidaba saidai ta koma gidan mijin ta tanunan ban isa ba haka mahaifiyar ta,zaman datai agida gantalinta taci gaba dayi dakyar aka samu takoma gidan Mijinta.
Bayan shekara daya da wani abu tasamu ciki wannan cikin shiyasa ta dan nutsu yawon ma tarage yinsa shima mijin ta saiya samu kwanciyar hankali saboda laulayi take me zafi bayan wata tara tahaifi yarta aka samata suna Rufaida batai wata biyu da haihuwa ba wata ranar alhamis fada ya hadata da mijin ta tafashashshan ruwa yana kan murhu ta daukeshi gaba daya ta juye masa aka dataga aika aikar datai ta dauki yarta ta gudu.
Yasha wahala matuka kamar bazai rayuba haka yadinga jiyya mahaifina harya rasu yana dana sanin wannan Auran Mahaifiyar ta cewa tai sharri akaiwa yarta bata aikata hakanba shidai yasan yadda akai ya kone.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 103
Kallon kallo akeyi tsakanin Innah da Mom Salima da Rufaida gaba daya Mom suka zubawa idanu jin cewar Rufaida ita kadai ta haifa kan tabar gida saliman fa,ke Saratu ita kuma wannan agidan ubanwa kika samota shiri Mom tayi tana kuka kashirban ashe akwai ranar da zatayi nadamar irin rayuwar datai abaya.
Tsawa babanta ya daka mata zakiyi Magana kosai jikinki ya gaya miki cikin kuka take fadin nima bansan wanene Ubanta ba kamar saukar aradu haka Salima taji saukar maganar a kunnanta muryar Mom ce take zagayawa acikin kanta bansan wanene Ubanta ba shegiya ce ita kenan.
Kukan kura Salima tai tadira akan Mom wata shegiyar shaka takai mata gaba daya Jama'ar parlour mikewa sukai dan kwatar Mom amma shakar da Salima taimata ba tawasa bace tuni tafarajin kamshin Mutuwa dakyar aka banbaro ta daga jikin Salima wadda take kuka cikin fitar hayyaci wllh Saratu kin cuceni kingama da rayuwata kina nufin ni shegiya ke bazan taba yafe miki ba har Duniya tanada sake zaburatai zata cafko Mom da gudu mom ta mike suka fara kasa yar tsire.
Tarara tara Mutanan parlourn sukai dakyar aka kamo Salima data gama zaucewa kamar wadda kanta yasamu matsala haka ta koma Saboda shork din data shiga lallai Mom ta zalinceta Yanzu wa zata nuna tace shine Ubanta,kowa haki yake nacin gudun da suka saka su babu wanda be tausayawa Salima halin da take ciki ba Rufaida ma kuka take jin kaddarar data fadawa yar uwarta ashe shedancin da sukai ba abanza ba anono suka tsotsa.
Cikin takaici mahaifinta ya kalleta bakisan wane Ubanta ba gyada kai tayi Lokacin dana baro gida bansan Inda zan nufa ba akwai wata kawata itace ta sauke ni agidanta haka alhazai suke mana layi dan neman abun Duniya nadunga basu hadin kai kwatsam naga ciki ajikina hankalina ya tashi babu irin maganin da ban shaba dan cikin yafita amma bai fita ba sàida na haifo ta batare da nasan wanene Ubanta ba
Daga wannan garinne na dawo Kaduna nayi shekara da shekaru agarinnan har yayana suka zama yammata haka suka taso alalace Saboda irin tarbiyyar da mahaifiyata taimin irinta nayi musu,awannan halinne na hadu da Ma'aruf tunda na ganshi naki duk Duniya shikadai nake so saidana shiga na fita harya Auran batare da yasan wacece ni ba.
Tsit parloun yayi sai kukan Salima dake tashi to kunji wacece Saratu kuma Inaso ki bude kunnan ki da kyau Jalal bashine ya Auri Rufaida ba mahaifinta da kansa ya bada auranta ga yaron sa dayake tayashi ayyuka gashinan azaune sadaki Babanta ta ciro daga aljihunsa ya wulla mata ga sadakin yar ki nan dagowa sukai suna kallon wanda akace wai shine mijinta.
Wata kodaddiyar shadda ce ajikinsa ya dankwara wata uwar hula kamar me tallan mandako Fuskar nan sai shining takeyi sai muzurai yake Kuka Rufaida ta fashe dashi ni wllh bana son wannan bazan zauna dashi ba saiya sakeni, Mom ma kallonsa kawai takeyi yanzu ace yarta ce ta Auri wannan.
Nidai baba duk da haka ba'aimin adalci ba taya za'ai yata ta Auri wannan abun ko baka ganshi bane har yanzu jikinki beyi laushi ba kenan.
To wai wane munafukinne ya canza auran aka mayar dashi kan waccan aljanar yarinyar,nice munafukar dana canza inna ta fada tana kallonta kwarai kalleni da kyau tun Lokacin da Ma'aruf ya dage akan wannan auran na tabbatar baya cikin hayyacin sa shiyasa nai amfani dashi wajan sashi agaba har garinku tunda Lokacin da kaikayin bakinki yajaki kika sanar dashi garinku baki sani ba.
Sarai nasan address din da kikaban ba daidai bane shiyasa ban nuna miki komai ba muka tafi akan Aure nakan yarki koda mukaje garinku bamu sha wahalar gane gidan ba saboda bakin fentin da kika shafa masa mahaifinki yayi farin cikin ganin mu kuma shiya hadamu da tsohon Mijinki acan muka tsara komai har kawo yanzu.
Kuka mom ta sake fashewa dashi shikenan tata takare kallon mahaifin Rufaida tayi sanadin ruwan zafin data zuba masa ya dawo kamar wani dodo gaba daya ya salube abun tausayi kautar da kanta tayi daga kallon sa jin Zuciyarta natashi.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 104
Saratu kije nasakeki saki biyu inkin samu miji kiyi Aure babu wanda yasan dad zai yanke wannan hukuncin ba ahaka tunda ta tuba ka mayar da ita sunkuyar dakai yayi kiyi hakuri inna amma bazan iya cigaba da zama da ita ba nasha tunanin ya akai ma na Aure ashe akwai abunda ta aikata harsaidana Aure ta bazan iya zama da ita ba.
Karki damu Hajiya duk wanda ya zauna da Saratu tabbas ba karamin kokari yayi ba wannan da kike ganin ta har kisa zata iya yi,cikin Kuka mom take bawa dad hakuri ya amayar da ita ko kallanta beyiba Ammah da take gefe sam abun be mata dadi ba musamman Salima ta matukar tausaya mata,tsawa babanta ya daka mata tashi kije ki hado kayanki kiwuce mutafi garin dai da kika gida shi zaki koma tanaji tana gani tamike Rufaida ta rufa mata baya cike da jin tsanar Mom a Zuciyarta.
Abunda zasu iya dauka suka dauka suna ta Kuka gwanin tausayi har harabar gidan suka rako su Dad kudi me kauri ya basu tare dasa Direba yakai su har gida Salima dai babu abunda takeyi sai kallon mutane sàida aka kamata akasata amotar suna yiwa gidan kallon karshe suka fice daga cikin sa sake rushewa sukai da kuka sunfita daga rayuwar jindadi ko wace irin rayuwa zasi acan Oho.
Cikin gida suka dawo kowa face dinsa cikin jimami saboda girman gidan yan biki babu wanda yasan abunda ya faru part din Mom nada Anan aka sauke su shiyasa basu san wainar da ake toyawa ba haka Jalilah da suke daki suna shan hira da kawayanta bata san me yake faruwa ba.
Shiyasa ake so ka aikata alkhairi a rayuwar ka yanzu wa gari ya waya ribar me taci gashi ta lalata tarbiyyar yayanta da kanta ni babu ma wadda na tausayawa irin wannan salimar wllh kamar nai mata Kuka cewar Innah,sauke numfashi Ammah tai nikaina Inna na tausaya mata wllh gaba daya jikina yayi sanyi wannan rayuwar abar tsoro ce ALLAH yasa mudace Ameen suka amsa gaba dayan su.
Kan kace me gida ya sake cika da Jama'a yan biki yau Ammah take wunin ta Amarya tasha kwalliya kawayan Mom dama babu wadda ta dawo tun abunda sukaga ya faru awajan dinner sukasan akwai matsala babba Acikin gidan suka sa kida tako ina duka yake wasu na zazzaune wasu na tsakiyar fili.
Maman Ladi ma ba abarta abaya ba ta girgiza babu kama hannun yaro kuma sunwa Amarya kara tasha liki Ammah sai shiga take tana futa kamar itace Amaryar bayan Magariba aka fara shirye shiryan kai Amarya tun wanna time din Jalilah ta fara kuka ita dai wllh tsoron Jalal ya shiga Zuciyarta har bata so su hadu koda ahanya ne.
Sàida Ammah ta sata tai wanka aka fesheta da turaruka masu kamshin gaske mayafi me girma ta dauko mata akayan ta data dinka mata na musamman motocine reras na tafiya kai Amarya harda Ammah za'aje mota daya suka shiga Ammah da Jalilah da gwaggo sai yar uwar babanta tana jikin Ammah ta rungumeta tana kuka itama Ammah jitake kamar zatai Kuka.
Gidan babbane ba canba amma ya tsaru kamar ba akasar nan ba yayi matukar kyau da tsaruwa kowa san barka yake gida fa yayi ma sha Allah,har daki Ammah ta kaita ta zaunar da ita nasiha ta sake yimata gyada mata kai kawai take sàida Ammah bta share hawayen ta itama goggo ma tayi mata nasiha tashi sukai zasu tafi nan Jalilah tace batasan zancan ba ta kankame Ammah.
Dan Allah Ammah karki tafi kibarni mu zauna tare dan murmushi tayi kin manta keda yayanki zaki zauna kullum fa kuna tare kin riga kin saba dashi mene abun Kuka haba Jalilah ya zaki bani kunya nida nake cewa Murna zakiyi ko Aurenne bakya so gyada mata kai tayi alamar eh to shikenan inyazo saikice ya dawo dake gida sai kin kara girma kya dawo to ta amsa dakyar Jalilah ta sake ta.
Har kawayanta Ammah tasa keyar su tai suka tafi tare akabarta ita kadai tsuru kamar mayya kara takurewa tai tana zazzare idanu basu jima da tafiya ba taji anturo kofar dakin da take dagowa tai da sauri sukai ido hudu da Jalil daya sha wata dokakkiyar shadda sai zuba kamshi yakeyi fuskarnan wasai sai kyalli takeyi.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 105
Bata face tai ta kawar da kanta gefe murmushi ya saki ahankali ya tako har inda take zaune ledojin hannun sa ya aje kafin ya zauna cak ya dauke ta ya dorata akan cinya mutsu mutsu takamayi akan ya saketa,wana kama dazu ni kike harara saboda na kalle ki kawar dakai tayi ni ban harare ka ba kuma katashi kamayar dani gida ni bana son nan.
Ware idanu yayi yana kallon ta ina zan maidaki wajan Ammah tace nace kamaidani inna girma saina dawo yar dariya ya saki yanzu baki girma ba kenan eh tagyada masa kai saimu hadu mukoma tare koni Anan zan zauna kai zamanka anan saiya fiyima dadi um kawai yace sauke ta yayi daga cinyarsa yaja hannun ta suka fita waje.
Su ukune azaune aparlo dan iska ya zaka shanya mu anan kamar wasu maroka to waya sani ko rokon kuke,Jamal ne ya kalle su ya fashe da dariya yadai yar raino Kuka kikayi dan zaki zo hannun me rainonki hararar sa Jalal yayi kaifa baka da mutumci ba zancan rashin Mutunci abunda nasani fa nafada.
Zaunar da ita yayi akusa dashi gaishe su tai tana wasa da yatsun hannun ta hirar su suka cigaba dayi irin ta abokai agogon hannun sa ya kalla oya atashi atafi haka lokacin baccin babyna yayi kunsan ta kwashi gajiya dole nabata kulawa dariya sukasa gaba daya kunji munafuki kai kutashi mutafi karya goge mana hadda mikewa sukai gaba daya suna dariya ita dai Jalilah tana gefe atakure.
Har parking space ya raka su sàida yaga fitarsu ya dawo ciki rurrufe kofofin yayi tana Inda ya barta zama yayi akusa da ita yadai kallon sa tayi nidai Uncle yunwa nake ji to acici tashi muje mikewatai yaja hannun ta suka koma bedroom kayan daya shigo dasu ya dauko ya aje agaban ta jan ledar tai wani kamshine ya daki hancinta saidata Lumshe idanu yadda yayi mata dadi yawunta harya tsinke tunakafin kazar takai bakin ta.
Tashi tai tsam tashige kiching plat ta dauko da knife dawo wa tai ta zauna ta jawo ledar tafuto da kazar sai kici kicin yan kawa take yana kallonta yana jinjina kwadayin Jalilah saidata debi wadda zataci ta juya masa baya tafara harrakawa,dariyar sa ya kunshe karfin hali harda wani juyawa jawota yayi daga ita har palat din ai baki isaba nima sai naci zumbura baki tai ta dauki plat din tadagashi sama.
Aiko bazaka ciba kaima kaci taka mana wannan ai tawace kokawa suka fara yana son kwacewa taki yarda ya karba kawai ya kyaleta ne amma da tuni ya kwace,sàida kyar ta ajiye da sharadin sai an hada anci har tasa yace yayadda sannan ta aje sukaci tare duk rabi da kwata Jalilah ce ta cinye kamar kura haka take da nama.
Sàida tankinta ya cika kat sannan ta kwashe wadanda nasu tababa takai fridge toilet ta shige tai brush tana fitowa ta haye gado inka fita ka turomin kofa jan bargo tai ta gyara kwanciyar ta yadda zataji dadin bacci yana zaune inda tabarshi yayi mintuna kafin ya mike toilet din ya nifa sàida yayi wanka ya dauro alwala nafila yayi ya jima yana addu'a kafin ya shafa ya mike.
Wadrob ya bude kayansa ne reras aciki dana Jalilah waje daya ya hada musu tsarinsa ne wannan kayan bacci ya dauko masu taushi yasaka dauko mata kayan bacci yayi yasan bazata iya kwana da wannan kayan ba sai juye juye takeyi jira take ya fita amma yaki fita kan gadon ya hawo yaja blanket din data rufa mikewa tai ta zauna tana kallon sa dare fa yayi katafi dakinka.
Ai nanne dakin nawa kinga ko anan zan kwana kallon sa takeyi gaskiya ni ban yadda ba ai kowa naga da dakinsa acan anan ma kowa yatafi dakin sa saikuma kiyi.
Kayan baccin ya miko mata tashi kisa kizo ki kwanta juya mata baya yayi ya kwanta ganin ba kallon ta yake ba tatashi sa kayan tai ahankali tahawo kan bed din dan karya jita tana kwanciya ya mirgino har inda take jawo ta yayi ya rungume kayarsa zatai magana ya dora yatsansa abakinta alamun tai shiru baccine yake cin idanun sa.
Rungume kayarsa yayi dandanàn bacci ya sace su asuba tagari ango da Amarya.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 106
Tsabar gajiyar da sukai da asuba da kyar yatashi ya tashi Jalila fir taki tashi tai sallah daukarta yayi gaba dayan ta ya tsumbula ta a bathtub azabure ta farka daga baccin da take kallon kanta take yadda ya jiketa jagaf da ruwa mikewa tai kamar zatai kuka tana kallon sa dariya yadan saki bake me bacci ba nayi maganin ki ai.
Ruwa ta diba ahannunta ya watsa masa karewa yayi yana dariya yar watse watsen ruwa suka dingayi saidata jikeshi jagaf har aka idar da sallah suna toilet suna wasan ruwa sàida suka gaji dan kansu bathtub din ya fada yana sauke numfashi kokarin fita daga ciki Jalila tai ya rikota gaba daya kansa ta fado taitai ya cikata yaki idanun sa alumshe kamar me bacci.
Kacika ni uncle bakaji sallah akeyi ba dakyar ya bude idanun sa da suka rine sukai jajawur anya zai iya kuwa kare mata Kallo yayi wata yar firit da ita agaban sa kasa jurewa yayi rigar jikinta ya kama sadaya tsargeta tundaga sama har kasa da sauri ta fada jikin sa dan kare jikin ta batasan kara kunna shi taiba tuni ya mance dawa yake tare Jalila tai Kuka harta gaji.
Wanka yayi mata tas ya nadota a towel bayan ya daura mata Alwala har Lokacin takiyadda su hada idanu dashi idanun ta arufe tana jinjina abunda yayi mata azuciya ashe dama haka Uncle j yake yana wani sussunkuyar dakai kamar na Allah azuciyarta take mita yaudai ba damar surutu tai mukus kamar ba ita ba.
Hijab har kasa ya zura mata suna idarwa ko azkar kasawa yayi ya sunkuci abarsa bazai iya wannan rainon ba kansa zai cuta haka kawai gwara tai hakuri ta girma a hannun sa,ganin lamarin ba wanda zan dauko muku rahoto bane jawo musu kofa nai nadawo parlo na zabga ta gumi zuciyata cike da tausayin Jalila.
Jalilah fa iya gurzuwa ta gurzu ko idanunta kasa budewa tai yana zaune yana tuhumar kansa aika aikar da yayi mata meyasa be hakura har wani Lokaci ba bazai iya hakan ba so da kaunarta bazasu barshi yayi hakan ba.
Tana jikinsa yana aikin lallashi amma fir takiyin shiru sai kuka take masa tana saiya maida ita wajan Ammah lallashin ta yake yi kamar zaiyi Kuka,daukar ta yayi bayan ya cika bathtub da ruwan dumi tsumbulata yayi acikin zaburatai zata mike ya maida ita kankameshi tai tana Kuka kamar zata shide kamar yayi Kukan shima haka yakeji sàida yagama yimata duk wani taimakan da zai mata ya nadota kamar baby.
Kwantar da ita yayi kaya masu kauri ya dakko mata wajan sa kayan sàida takai Zuciyarsa nesa yana matukar jin tausayin ta yasan zatasha fama kanta saba.
Kiching ya shiga tea ya tafasa mata me zafi tashinta yayi amma ta kasa zama har Lokacin bata daina Kuka ba kadan tasha ya bata magani ta koma ta kwanta dandanan bacci ya dauke ta sakata yayi agaba kamar TV yake kallon ta sonta da kaunarta na sake huda Zuciyar sa yana matukar son Jalila shikansa besan adadin son dayake mata ba.
Tun ranar daya fara ganin ta Allah ya dora masa santa da kaunarta duk wani hukunci dazai mata danta gyaru yake mata hukunci badan baya sonta ba,aikin gida tsaf shine yayi shi shara da kade wajan da yayi kura tas ya gyara gidan yayi musu breakfast wanka ya shiga yana fitowa ya dauki wani lallausan yadi ya saka Ango sak face dinsa sai annuri take fitarwa.
Motsawa ta farayi ahankali kamar jiratake yayi magana ta fashe mata da Kuka dafe kai yayi yaufa ya taba dan gwalolo zaman yayi yajawota jikinsa Zazzabin ya sauka sai rashin jindadin jiki kayan da yadauko mata atamfa ce riga da sket ya saka mata agaban mirror ya ajiyeta tsaf ya gyara mata gashi ribom ya saka mata harda yar hoda da lipstick ya shafa mata.
Daurin dan kwali akazoyi nan dai babu labari wani uban dauri yayi mata kamar takifa gammo aka kallon kanta tayi amadubi dariya ta kyalkyale da ita ganin daurin daya dankwafa mata Nishadi ne ya sauka azuciyarsa ganin dariyar ta,gyara ya dage mata yadai kinga haduwar da kikai ko cuno baki tayi wannan wane irin daurine kamar malafa.
Yar dariya ya saki ainayi kokari princess dan kallonsa tai ta kauda kai habarsa ya dora akan kafadarta wai wane lefi nayi da baza'a kalleni ba,tacikin madubi takalleshi rufe idanu tai aikasani kaima cike da shagwaba sake narkewa yayi afagen kaunarta.
Kallonsa tayi to kabani kyautar dakace zaka bani kallonta yayi na rashin fahimta,gyara tadagamai kamar yadda yake yimata cikin sakalci take fadin bakace kabarmin gidannan ba hartakardun zaka ban da safe bani yanzu na adana,fashewa yayi da dariya yana kallonta yaushe nafadi hakan rufe face dinta tai da tafukan hannayanta dazu kafada fa,wani abu ya rada mata akunne saurin dukar da kanta tayi tana yar dariya.
Wardrobe dinsa ya bude wani dan akwati ya dauko me matukar kyau budeta yayi sarka da dankunne da awarwaro da zobe na gold sai kyalli da kyalkyali sukeyi sakar ya dauka yasa mata ba karamun kyau tayi ba haka awarwaro da dankunne duk shine ya makala mata fuska awashe take kallon sarkar my choice kuma duk nawane gyada mata kai yayi.
Tukaicin abunda nakarba medaraja daga wajan matata tashitai da sauri tafita parlo yabita abaya yana dariya.
Mrs Baba Bello Abubakar
.......✍️✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 107
Zama akeyi naso da kaunar juna kusan kullum sai sunje wajan Ammah fada take musu sosai akan kafar yawo saitace Ammah tsoro fa nakeji nikadai gidan yamin girma hartagaji ta kyale su hankalinta ya kwanta daga ita sai Mijinta da yayanta.
Kauye suka tafi wajan Inna tayi murna da ganin su matuka tarasa Inda zata sakasu ganin yadda yarta tai fresh tayi bulbul da ita daki guda inna tawarewa Jalal Abincin su irin na gargajiya ta dafa musu sosai suka kwashi girki.
Ta zazzaga gidan yan uwa da abokan arziki bala metsire dai ya dangana haryayi auran sa har tsire ya aikowa Jalila besan yanzu inba wuka tagani ba bazata iya cin wannan naman ba,karfe 9 harta kwanta inna tashigo aa yana ganki anan kallon Inna tai eh Inna kwanciya zanyi Mijin naki fa keni bana son shashanci tashi kije wajan sa.
Cikin jin kunya Jalila ta mike tana shiga ta hangoshi ya zabga tagumi yana tunanin tayadda zaiyi bacci babu Jalila akusa dashi ajiyar zuciyah ya sauke ganin shigowarta bude mata hannu yayi da sassarfa ta isa wajan sa ya rungume kayar sa tare suka sauke ajiyar zuciyah cikin jikinsa yasata dan danan bacci ya kwashe su.
Washe gari Jalila tataya Inna aikin gida sàida suka gama tas sukai break suka fara shirin tafya,har daki ya samu Inna akan yaushe zata zo kanta asunkuye tace ba yanzu ba dakyar ya shawo kan inna ta yadda nanda wata zata zo taga dakin Jalilah,ko Jalila be fadawa ba surprise yake so yayi mata shiyasan abunda ya shirya.
Tsaraba niki niki haka suka tafara da Ammah tayi matukar murna,tunda suka koma Jalilah take zazzabi taki yadda Jalal yasani dan kar tasha magani.Yau da zai fita rigima tasa saiya tafi da ita bayadda be rarrasheta ba ta tubure saije haka ya hakura ya tafi da ita takawa suke gwanin burgewa duk wanda ya kalle su yasan kwanciyar hankali dajin dadi ya zauna ajikin su.
Office dinsa suka shiga kan kujerarsa tahau ta zauna my noor kallon ta yayi ya akai Gimbiya bcc nakeji kallonta yayi yana wani nazari tacika bacci yan kwana kinnan.Jamal ne ya kwankwasa kofa yes come in shigowa yayi aah yauda Gimbiya aka taho kallonsa tayi tana yar dariya bugun kafadar Jalal yayi kai mutumina kana wutafa tafawa sukai suka shige wani room acikin office din.
Dan iskan karya raino yayi kyau tunda har madam ta samo mana baby kallonsa yayi zakacemin baka sani ba gyada masa kai yayi to kazauna wasa kana zaune zakaji inya inya dariya sukadaie kai dallah saikace wani sauna har matata cikinta ya isa haihuwa banganiba kamar wani makaho to aiko makahonne gashi ka nuna hakan.
Ihu sukeji tunda suka shigo hospital din kukamme nakeji haka um wata mata aka kawo baka ganta ba abar tausayi sai ihu take anrasa yadda za'ai da ita dama kai akejira bazaka rasa abinda zaka yimata ba numfashi yadan sauke muje,mikewa Jalila tai zani nima zaki iya da sauri ta daga kai babu kunya ya kama hannun matarsa suka fita duk inda suka wuce sai ankalle su matan da suke sonsa kishi ya turnike su.
Dakin da aka kwantar da mara lafiar suka shiga nurse ne tsaye akanta da yan uwanta da andaura mata zani take yaye shi sai sambatu take wasu tsutsotsi ke fita daga gabanta sai tsagar gashin kanta take tana cusawa agabanta saurin kauda kansu sukai jan yo hannun Jalilah yai data razana ta rungume shi ta baya are you ok Jalilah gyada masa kai tayi.
Jin an ambaci sunan Jalilah matar ta zabura zata mike kara daddanne ta akai saina kashe ki Jalilah bantaba neman abu narasa ba sai akanki sena kasheki,ras gaban Jalilah ya fadi kodaga bacci ta farka tasan wacece kallo ne ya koma sama fashe da kuka Jalila tai kan Jalal ya daure mene hadinta da wannan matar,wata dattijuwar ce daga cikin wadanda suke tsaye ahankali ta karaso Inda Jalila take.
Kece Jalilah gyada kai tayi alamun eh murmushi matar ta saki nagodewa Allah daya tsallakar dake daga kaidinta wannan abunda kikaga ya sameta duk akan hanyar nasai ta mallakeki kota halin kaka gidan wani boka tatafi dayake yafita hatsabibanci da rashin imani dodannin sa yabawa ita badare barana kwanciya suke da ita sàida suka tabbatar wajan ya rube yasa yaransa suka zubar da ita abola ita da mushe duk daya.
Nasha jin tana cin alwashi akanki bansanki ba amma ko yaushe ina Addu'a ALLAH ya kiyaye ki daga sharrin ta nagodewa Allah dataga karshan ta tun agidan duniya daga haka matar taja bakinta tai shiru.
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
UNCLE J
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 148
Last page
Masu karatu ko bangaya muku ba kunsan wacece bakowa bace face Anty Zarifa,jan hannunta Jalal yayi suka shiga office dinsa gadon dake dakin ya kwantar da ita saidata samu nutsuwa ya tambayeta nan tai masa bayanin Abunda ya hadata da Zarifa ya jinjina lamarin matuka cigaba yayi da rarrashin ta hartai bacci.
Mutuwar wulakanci Zarifa tayi ta tana ihu da bige bige naman gaban ta duk ta kwasheshi ta ciccizge gashin kanta haka ta koma ga mahaliccin ta tana kiran tashiga uku ta lalace Allah kayi mana kyakykyawan karshe.
Haka rayuwa taita tafiya Jalila dai cikin ne da ita ko yaushe Ammah tana hanyar dubata haka Dad sosai suke murna da wannan ciki gogan kuwa ai ba'a magana,Inna dai tadawo birni ita da gwaggo tunda ya tura adauko su ya rike su dama ya shiyawa hakan.
Soyayya tsakani Nasmah da Jamal tayi karfe har ankusa shan bikinsu Ablah da Ismah duk kusan lokaci daya za'ai Auran su.
Wata tara daidai Jalila ta sunkota yarta mace me tsananin kama da Ammah ranar suna taci sunan Ammah Rukayya suna kiranta Amnah ansha shagali agidan Ammah akai suna taci gaba da kulawa da su Inna yar kalloce babu abunda zatacewa Ammah sai fatan cikawa da Duniya Lafiya.
Duk sanda Dad yake gida ahannun sa take wuni sosai yake kaunar yarinyar Jalila takara wani kyau kamar ba itaba tanayin araba'in tako ma gidanta zaman lafiya yaci gaba da wanxuwa atsakanin su sai sabanin da baza'a rasa ba tsakanin harshe da hakori ma ana sabawa.
Yamaida ita makaranta tana cigaba da karatunta bazaka taba cewa ammata Aure ba harda yarta,sunsha bikin Jamal itama Nasmah nan Kaduna aka kawo ta Ablah da Ismah akano sukai Aure kowaccen su ta samu hankali agidan mijin ta.
Innah ma tayi Aure wani bazawari yafito dakyar da ta yadda shima yanada rufin asirinsa Matarsa ce tarasu daran su biyar inna taci gaba da kulawa dasu kamar yayanta.
Waiya labarin su Mom sanda suka isa garin su babu wanda be shaida Mom ba kowa ala wadarai yakeyi gashi dai taje ta dawo tagama yawon Duniyar,koda tashiga cikin gida Mahaifiyar ta ta rame ta kanjame kamar aljana tana girbe abunda ta shuka tana ganin Mom takama Kuka ko kallon ta Mom bataiba duk wani abu daya sameta ita ce sila.
Aranar baban Mom ya tasa keyar Rufaida har gidan mijinta tasha Kuka haka ta zauna bayadda zatai.Mom tana gama iddah aka daura mata Aure da tsohon mijinta daya koma abun tsoro saboda yadda halittar sa ta sauya tanaji tana gani haka ta zauna toya zatayi tare da Salima ta tafi har kawo wannan lokacin babu wanda yazo ya taya.
Jalilah tacika alkawari taje wajan Anty Binta da shatara ta arziki taji dadin yadda Jalilah bata manta da ita ba.
Misalin karfe 9pm suna parlo suna kallo Amnah datakiyin bacci sai fitina takeyi da rigima sai anyimata doki aiko bazan miki ba sedai Abbanki yayi miki sake kwanciya yayi nima nagaji da za'ai min so nakeyi driya Jalila tai zo nai miki Amnah da gudu tataho suka cafe ta tare kallon juna sukai tare da sakin lallausan murmushi.
Nima anan nasaki lallausan murmushi gareku fans.
Ina Godiya ga ALLAH daya nunamin karshan wannan Littafi lafiya.Allah ya karawa Annabi Daraja Ya Ubangiji ka daukaka Musulunci da Musulmai Allah kai mana kyakykyawan karshe.Marasa lafiyarmu nagida dana asibi Allah ka basu lafiya muda muke da Lafiya Allah kasa muribaceta ta hanyar aikata Alkhairi.
Abunda nafada ba daidai ba Allah ka yafemini kabani ikon rubuta daidai.
ALHMDULILLAHI
0 Comments