WA'AT
By kulsoom Isma'il
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Bismillahir Rahamanir Rahim
Labarina kirki rarran labarine ban yadda Wani ko wata ya juya munshi ta kowa ce suga.
Na sadaukar da Wannan Littafi ga kannena da yayyena Allah ya kara hada kawunan mu ya dawwa mar damu cikin kaunar juna
Na fara rubuta Wannan Littafi kamar haka.
WA'AT
By kulsoom Isma'il
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 1
Cikin tsakiyar dare yayin da kowa yake kwance yana bacci cikin salama da aminci,amma ita tana zaune tana kai ku kanta wajan meduka sarkin da babu kamarsa mekomai me kowa me yaye damuwar bayin sa shika daine wanda ze yaye mata damuwar ta.
"Roko take cikin tsananin kaskantar dakai Allah ya dawo mata da mahaifinta kan hanya tagari kan hanya madai dai ciya.Allah ya sauya mai zuciyar sa ya gane suma 'ya'ya mata suna da rana ababan kauna ne da tausayi, saida taji amfara kiran sallar asubahi tai sallah ta kwanta
Wa'at wa'at tajiyo mahaifinta yana zabga mata kira tamkar zai tashi sama kamar mako garan sa ze tsage kirjinta ne ya bada ras addu'a tafara karan tawa sannan tafita tsugunnawa tai gani Affa wani ban zan kallo ya yai mata da kuka shige daki keda uwarki ubanwa zaizo ya dora mana abun kari.
" Saurin jijjiga kai tayi kayi hakuri dama yanzu zan fito nadora saboda Mama batajin dadin jikinta,wata mangara ya kawo mata ubanwa yake jin dadi yanzu da zakice batajin dadi amma in angirka ai zata iya jin dadin ciko tashini kibani waje kidora mana abun kari"
**********
Kiching din tashiga tana sharar hawaye shin menene laifinta dan an haifota a mace ita aganinta ai mace rahama ce kuma ni'ima ce amma mahaifinta yake jayayya akan lamarin ubangiji yake jayayya da hakan.
Ita har yanzu bataga wahalar da suka dora masaba shidai kudin makaranta ma ba biya musu yake ba mamar su ke biya musu sai dai ya biyawa 'yan uwansu maza acwarsa su ze amfanesu nan gaba zasu tai maka masa,sukam sai dai yaita wahalta musu abanza duk ya manta kiwo Allah ya bashi yasa kafa ya shure hakan.
Gama girkinta keda wuya umma ta banko labule ta futo tana mika ba salati ba komai haka take gan tsarewa da alama ko sallar asuba batayi ba fuskar nan duk yawun bacci, ya mutsa fuska tai ke mara amfani kin gama yimana abin karin ko yaya ba karamin jin zafin maganar taiba amma ta shanye ta dake eh nagama umma.
WA'AT
By kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 2
"Buguzun buguzun ta nufo kiching din ta dauko wani bokiti sai data cikashi da kunu dumaman tuwanma sai da takusa kwashewa tukunna ta bar musu dan kadan duk wa'at na tsaye na kallonta.
Bayan ta futa ta sun kuya ta kwashe sauran fuskarta cike da damuwa dan tasan ba isar su zaiba"
Da sallama ta shiga dakinnasu tana kakalo murmushin karfin hali maman suce ta kalleta cike da tausayawa dan duk abunda ya faru tanaji itama murmushin ta mayar mata tana fadin sannu kedai Allah yai miki albarka ameen Mama.
Ya jikinnaki Mama, da sauki to Allah ya kara sauki Mama ameen ameen, kici gaba da hakuri watarana sai labari idanunta ne ya cicciko da hawaye kallan Mama ta sakeyi wai Mama kodai Auran dole akai muku keda Affa.
Murmushi Mama tayi mekika gani da kika fadi haka, naga Mama baya sammu musamman mu 'yayanki a gidan nan barinma nidake naga baya kaunar ganinmu murmushi Mama tai wanda yafi Kuka ciwo tare da kallon 'yartata.
"A'ah ba haka bane kawai dai mahaifinku ya dorawa kansa wata akidane takin 'yaya Mata acewar sa wahalane, sune in kazo auransu saika kashe inta haihu nanma ace ka kawo kayan barka kai gaba daya haka zaka kare rayuwarka kana wahalta mata batare dakai kasamu komai daga gareta ba.
Wannan tunanin nasa sam ba daidai bane da yawan maza suna irin wannan gurba taccen tunanin sun manta duka Allah ne ya basu kuma ba susan wanda zasu moraba, akullum ina addu'ar Allah ya nuna mun ranar da mahaifinku zai gane hanyar gskiya ranar da zanga yayi alfahari daku na kasan cewarku 'ya'ya mata"
Taku ako yaushe Kulsoom Isma'il
Yawan comment dinku yawan jin dadin labarin da kuka karanta..........✍️✍️✍️✍️
WA'AT
By kulsoom Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 3
A salinsu yan garin zariya ne iyaye da kakan ninsu hakama mamansu itama yar zariya ce, sunan mahaifinsu kabir ya taso agidan yawa dan mahaifiyar sa tana da abokiyar zama sun kai kusan su ashirin agidan su.Mahaifinsu malam sama'ila mutumin kirkine kuma malamine ana matukar ganin gir mansa agarin,kabir shine na biyu a dakinsu kuma dama tunda ya taso akwai rashin ji sauran yan uwansa duk sun fishi nutsuwa.
Ko yaushe malam yanai masa misali da yan uwansa ya nutsu yayi koyi dasu yayi koyi da halayansu amma shifa abunnan yana matukar bata masa rai barin yadda ake cewa ko matan sun fishi hankali da sanin ciwon kan su abun da ya kara rura wutar gabarsa da mata kenan.Kamai mahaifinsu ya siyo sai yace na kannan sune mata shiyasa ya dinga dukansu kenan ba damar ya hadu dasu awaje saiya dakesu shiyasa suke matukar tsoransa.
Koda a kazo sakasu amakaranta malam yace matan zai sanya aboko mazan kuma sai sun fara zuwa makarantar allo wayyo kabir jiyayi ranar kamar ya hadiyi zuciya ya mutu bare yadda yaga abokan sa nayi masa dariya zai tafi bara har tsokanar sa suka din gayi sai sulabe abayansa suna iya allazi wahidi Iya ko gayane ba miya abun ya sake kular dashi haka ya tafi gida yana kuka shidai kar akaishi bara malam kuwa yace be isaba zuwa ba fashi.
Har zazzabi saida yayi kannan sa suka dinga yi masa dariya sunai masa gwalo duka kuwa sun shashi kafin akaisu makarantar matan sun fara zuwa boko zuwa yake hanyar makarantar ya labe suna zuwa kusa dashi sai dai suji duka tako ina har akwata yasha jefasu saboda takai cin aishi ba asashi ba saida malam ya kamashi yai masa dan karan duka ya daure shi amari tun daga sannan yaci alwashin matukar aka haifo masa 'ya mace agidan sa zataga bala,i da masifa kuwa shi yanzu duka matan ma ya tsane su.
Bayan wasu kwanaki aka kwashe su sai makaranta koda aka kaisu makarantar babu wani karatu da yakeyi ya wonsa yake tafiya daga nan ya fada nan malamin su yayi fadan yamai nasihar ya da keshi amma abanza baji yake yiba malamin da yaga haka kar yaje dan mutane ya lalace ahannun sa da kansa ya tattaro kayansa yadawo dashi har gida.Ba karamin bacin rai malm sama,ila yayi ba saboda ganin yadda dan nasa ako yaushe yake kun samai takaici duk cikin 'ya'yan sa bame sashi magana sai shi.
************
Haka yaci gaba da binsa da addu,ar Allah ya shiryeshi kasuwa ya kaishi dayake yana da shago acan nasaida robobi nan fa likafa ta bude masa ya dinga kashe kasheni kudi yana dinka sittiru kullum zai dau guga ya fita yana kwanbo shiga saurayi alokacin yayi shekaru 18 kullum malam cikin nasiha yake masa wata makarantar boko ya sakashi to balaifi yadan zauna anan din Inya taso sai ya tafi kasuwa da yake yasa abun aransa bedena zuwa ba amma yana fashi ba kullum yake zuwa ba.
.............✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 4
Da kyar aka samu ya gama scondry lokacin yana shekaru 25 a san nanne ya hadu da wata budurwa da take kawo musu abinci suna siya daga haka suka kulla soyayya har soyyar tai karfi yaje ya fada agida ga wadda yake so ya aura bincike sosai malam yayi aiko ya gano yarinyar bata da kamunkai nan yace sam bai yadda da wannan auran ba anan kabir ya daka tsalle shifa inba salamatu ba baze iya auran kowa ba.
Haka mahaifiyar salamatu azababbiyar matace ba tada mutunci kai kaf danginsu ma anshaida ba a tabasu azauna lafiya dan in kataba daya acikin danginsu to taran dangi zasuyi maka har gida zasuje su lakadama duka kuma babu abunda aka isa ayi musu.Bayadda baai da kabir ba yace shifa sai salamatu malam yace abarshi jiki magayi amma ya sani komene ya faru ba ruwansu kamar ma ya tunka resu yace yaji haka innar sa babu kalar fadan da batai masa ba yakiji har tagaji ta zuramai ido.
Haka malam ya wakil ta wanda zasuje nemo auran haka sukaje suka kai kudin auran kadaran kada han babu wata walwala atare dasu akasa rana wata uku,wai ranar salamatu kamar ta zuba ruwa akasa tasha haka babarta uwa liya shirye shire aka farayi babu kama kafar yaro akwai wani gidan malam shiya bashi yace su zauna agidan dan danan lokacin biki yataho kayan lefema ba wanda ya kalleshi balle ya bashi tasa gudummawar dan kowa basan auran yake ba.
Sai da ya gama hadawa balaifi yayi kokari akwati uku ya hada aka kai musu kayan akai kayannan ma seda aka kisa dan batuwa da wata qanwar inna dan cewa sukai kaya yayi kadan nan akafara cacar baki suka taru zasu yiwa yan kawo kaya duka sai da kyar aka raba wannan fada haka aka rabu baran baran koda suka koma gida suka labarta abunda ya faru kabir sai cewa yai sharri aka kulla musu ba yadda zaai hakan ta faru.
Malm cewa yayi su rabu dashi kar wanda ya sake tayar da maganar haka sukai shiru badan ransu ya soba dandai ya hanasu magana ne.Biki yayi biki inna dai batayi wata gayya ba sai inna lamice abokiyar zamanta tai gayya akasha biki kowa ya watse ankai amarya gidanta dake gyallesu gidan babbane dan akwai dakunan da baa karasa ba anyi mata jere ba laifi dakin ya fito fes saidai muce alabada zaman lafiya.
An sha amarci kamar ba gobe sai da akai sati tukunna ya fara fita kasuwa duk tsawon kwana ba kwannan dangin salamatu agidan suke wuni agirka abinci aci asha ai wadaka dashi tun kabir ba ganin nan da kwana biyu zasu dena zuwa har akai sati abu yaki ci yaki cin yewa dan abincin daya ajiye gaba daya an Kusa cinye shi tamkar shanu haka suke wajan ci kuma ko yana gidan haka Zasu afko daki babu ruwansu saidai ya fita ya bar musu gidan sosai abun yafara da munsa gashi ya rasa wanda zai gayawa.
WA'AT
By Khulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Chapter 5
Ango in yana cikin kwan ciyar hankali zaaga ya murmure amma shifa ba wannan sai uban kashin wuya daya farayi inna da malam ba wanda ya tanka masa sukai biris dashi kamar basu gane halin da yake cikiba shima da yake yasan abunda yayi da aka hanashi auran ta sai ya kasa fadar halin dayake ciki."Tofa acikin sati na biyu gaba daya kabir ya gane halayan salamatu yan zune da abu ya hadasu zataci kwalarsa tanai masa zagin tsamar nama.
Sosai suke shan dambe Wani zubin sai makota sun shigo sun rabasu ba tajin kunyar ko agaban wanene ta zageshi tsaf haka in sukai fada zataje tagayowa uwarta uwaliya tabishi har kasuwa tai masa tijara,abun fa ya fara ga garar sa duk abun nan dake faruwa Iyayansa sun sani amma ko afuska basu nuna masa ba akwai wata rigima da sukai akan sai dai yayi mata wanki Ita agidan suma bayi take ba yace sam bazaiyi ba saidai ta fasa sa kayan garin cacar baki ya falla mata mari.
Aikuwa ta debi jiki sai gida tana rusar Kuka Kamar wadda ake yan kawai uwaliya tadauko gyale tare da yayyan ta da kannan ta dagame gariyo a hannu sai masu dau ko dorina suka nufo gidan afusace.Yana kwance lokacin yana tunanin hanyar da zebi ya gyarawa salamatu halayyar ta ba zato ba tsammani yaji an rufeshi da masifaffan duka tako ina kiiii suka jawo shi waje suka ci gaba da suka tsabar wahala kukan ma ya kasa yinsa.
Wata uwar tabarya uwaliya ta maka masa a hannu jikake kas amma saboda rashin imani irin nasu basu kyaleshiba sai sukai masa jina jina suka tsallake suka barshi anan har matar tasa babu abunda ya shafeta tabi uwarta gida.Shidai kabir betashi farkawa ba sai agadon asibiti idanu sun shige ciki saboda tsabar yadda yasha kutufo afuska da baki hannunsa ya motsa yaji Wani azababban zafi ya ziyara ceshi.
Inna lami itace awajan sanda ya farka da innarsa catai bazata zoba tsun tsun dayaja ruwa shi ruwa ke doka da ganan tai masa addu,ar samun lafiya,sannu inna ta farayi masa cikin tausayawa sosai yake bata tausayi ya hadu da jarrabawa a kananun shekarun sa har yau shema yayi auran daya fara fuskan tar wannan bala,i haka kayi hakuri kabiru taka jarrabawar kenan sai dai muyi maka fatan ka cinye ta Allah yasa kaffara ce.
Bai iya cewa komai ba dan gaba daya zuciyar sa zafi takeyi Kamar zata babbake amma duk da haka abin da yake bashi mamaki san salamatu bai fita daga zuciyar sa ba yara sa waca irin lukutar masifa ce.
*********
Sosai yasha wahala kafin ya warke dan kashi sane ya tsage ba karamar azaba ya shaba malam ma yazo ya dubba shi haka sauran yan gidan su ba wanda be zoba duk wannan abun da ake salamatu bata zoba ba ita ba dan ginta suna can suna cin duniyar su da tsinke hankalinsu kwance dama mahaifinta ya jima da mutuwa shima mutane suna rade radin bakin cikin sune ya kashe shi.
WA'AT
By Khulsoom Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Chapter 6
Gaba daya malam kin bashi damar su tattuna maganar yayi dan har yanzu jikinsa bai gama gaya masa ba haka innarsa bata bashi fuskar hakan ba dan dole ya hadiye dukkan wata da muwarsa saida yayi sati da da wowa daga asibiti sannan salamatu ta dawo ko sannu bata hada suba shima be tanka mata ba ya bita da ido.Haka akaci gaba da zaka da dadi ba dadi ana gan garawa zuwa wannan lokacin salame tana da ciki.
Samun wannan cikine yasa ale kwana biyu baai fada ba sosai yake tattalin cikinnan dan ba yason wani abu ya samu cikin kullum zan can sa daya dan sa ya kusa zuwa duniya siyayya sosai akeyi ta haihuwa kullum salame ta tsarsa take kamar bank haka ta mayar dashi awo in zataje sai ya bata dubu biyar sai tace ai magani zata siya bayan ta dawo tace likita yace tadaina cin Abinci ba nama ko kifi haka ya dinga wannan jigilar ai dan danan saiga salame an hada naman wuya shiko sai ramewa yakeyi kamar kudin guzuri.
To yau dai salamatu aka tashi da nakuda kuka take shabe shabe da hawa yanta mako tansa ya roka suka kaita asibiti tun salamatu na kuka har hawayan ma ya gagara fitowa azaba tai azaba sai kururuwa take tana tsinewa kabir albarka kai tun daga kan kakansa na hamsin ta hada tazago da alwashin tana haihuwa sai yaga Abinda zatai masa masu dariya nayi masu tausaya mata nayi masu ganin bata kyauta ba nayi tun karfe tara na safe take nakuda amma sai la'asar ta haifo danta san kacece namiji.
Koda akazo aka sanar wa kabir shifa tame aka haifa yake sai da ya tabbatar da namijine tukunna fuskar sa ta fadada da farin ciki kamar ya taka rawa burinsa ya cika an haifo masa magaji dan danan ya bazama ya tafi gidansu ya sanar hakama gidansu salamatu aiko yasha tsinuwa wajan uwaliya yar ta na nakuda amma dan bakin hali yaki yazo yasanar da ita da wuri shidai hakuri yake bata kamar ko idanunta zai fado dan harara.
Sai data gama hararar sa sannan ta tambayeshi meta haifa washe baki yayi ai inna namiji akasamu ran gada guda tayi zuciyar ta fes ko yanzu kabir ya mutu gida ya zama nasu dan danan tadauki wani dukun kunannan mayafinta ya goyata amashin dinsa suka tafi asibiti
WA'AT
By Kulsoom Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 7
Sai da ta kwana a asibitin aka sallamo ta balaifi yan gidan su kabir din suma sunnu na farin cikin su haka suka hado kayan barka suka kawo amma araine haka suka karba suna ya mutsa fuska a dole su kayan baiyi musu ba.Ranar suna yaro yaci sunan mahaifin salamatu sa,id suna kiran sa da ameer raguna biyu haka kabir ya yanka masa dika dika zuwa lokacin yana samu akasuwa ba laifi.
Amma da aka gama suyar naman nan wasu yan kasusuwa aka tattara aka ware na dangin kabir gaba daya suka taru suka handime naman sosai ran inna ya baci awannan karan tace dole ta magantu malam yace ba ruwanta ta samu ido dan dole ta hakura ta rabu dasu amma abun ya bata mata rai kunyar mutane ya kamata dan su in har danka ya haihu sai kayi rabon nama koda na mijine kuwa sai hakuri ta babbawa mutane.
Sosai kabir yake kula
da Ameer amma Salame babu ruwanta da gyarashi haka zata barshi gaja gaja ba gyara ita kanta ba gyara Jikinta take ba bata gyara gida sai dai taci inda taci abinci nan take barin kwanu kan daidai in ya dawo ya tattare gidan ya kama dansa yayi masa wanka ya sauya masa kaya kai hatta wanki shiyake masa shiyasa yaron tafi sabawa dashi.Sosai ya fara wayo yafara kiran babansa da appa wai ga shegen Rashin ji tun yana dan karamin sa akwai fitina yana sheru uku daya fita waje zaiyo tsokana adakesa.
Ranar wuni zatai tana tsine tsine alayi in baaci saa ba zataje har gidan su wanda ya dokar mata da tarama masa in akayi rashin saa itama wancan kalar tace saidai abige da dambe watarana sai dai kaga ta dawo da fasashshen baki in anfi kar finta in kuma Ita tafi karfi Itama ta daka kan ta fito daga gidan.
Bayan Ameer ta sake haihuwar Umar sosai nan ma y nuna farin cikinsa suka ci gaba da rayuwa ahaka suna kiran baban su appa ita kuma Umma.
Ana haka ya hadu da yar abokin malam wato Aysha yarinya ce mai hankali da nutsuwa tarbiyya uwa uba ilimi tana zuwa gidansu in an aiko ta samun malam yayi da maganar yana santa da aure jim malam yayi kabiru da gaske kake wannan maganar koda wasa dan bana son ka cutar da yarinyar mutane kaida matar ka in sha Allah malam hakan ma bazata faruba to Allah y sanya alkhairi sai kaje Inta amince shikenan.
A ranar da daddare ya sha wan kansa ya nufi gidansu aysha dayake duk basu da nisa yaro ya aika yakira masa ita sake aiko yaron akai ya tambaya wanene yace kabir ne na gidan malam sama'ila a Lokacin aysha na zaune tana cin Abinci amma jin wanda aka ambata gaba daya sai taji takasa cin abincin mamaki ne ya kasheta azaune to mene alakar su da zaizo yace yana sallama da ita innarta ce ta kalleta aisha ko bakiji ana kiranki ba naji inna haka ta fada cikin sanyin jiki tashi tai ta dauki hijab dinta tasaka tafita.
A tsaye ta same shi tsabar ta kaicinsa da kyar tai sallama da fara,arsa ya amsa sallamar tata shiru sukai nawani lokaci ya rasa ta Inda zai fara da kyar dai yai kun dun bala ya furta abunda yake zuciyar sa tsai tai tana jinsa harya gama suru tansa sukai sallama kodata shiga gida ba wanda tacewa uffan amma inna na lura da ita sam fuskarta babu fara'a.Sai da safe take sanar da inna abun da ya kawo kabir ita kanta inna wannan maganar bata kwanta mata ba dan sarai tasan halin matar sa amma bata nuna ba Allah ya tabbatar da Alkhairi shine abunda ta fada taja ba kinta ta tsuke.
Karamar Magana fa tazama babba malam da kansa yaiwa abokin sa maganar sosai ya nuna jin dadin sa da wannan lamari take anan yace ya basu aysha asa ranar biki kawai
Ai ko da Aysha taji wannan magana kwanatai tana kuka dan ita sam kabir be mata ba ga bala,in matar sa da take tsoro amma saboda tsananin biyayya takasa furtawa mahaifinta bata san kabir haka ta hakura ta mikawa Allah dukkan lamuran ta.
WA'AT
By Kulsoom Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 8
Gadan gadan aka fara tada sabbin dakuna gidan kabir salamatu batasan wainar da ake toyawa ba tayi tunanin dakuna Zaa kara mata saboda yaranta sai fasalin yadda zata sake jere asauran dakunan take saida aka gama gini tsaf daki yasha fulasta da fenti haka dakunan datake ciki da tsakar gida.A ranar kabir yai kun dun bala ya gaya mata aure zai kara sai datai suma na wucin gadi danji tai kamar kunnuwan ta ba daidai suke ba ita zaaiwa kishiya Ita salame yar gidan uwaliya uwarta ma bata zauna da kishiya ba sai Ita.
Tab ai adaran nan kabir yaga tashin hankali yaga tijara gaba daya bata barsu sun koda rufe idanu da sunan bacci ba daga karshe ma wuka tadauko sai dai ta kasheshi inyaso sai amaryar ta auri gawar sa saiga kabir yana cin gudun neman wajan buya da kyar yasamu ya shiga daki ya kulle yana maida numfashi.Sai da aka fara kiran sallar asuba yadaina jin zage zagenta ya bude yaje yai alwala ya tafi masallaci daga can bedawo gidan ba ya nufi gidan su acan ya karya.
Yanzu innar sa tana sakar mai fuska tunda yace zai kara aure suka dai daita dan tana san aysha sosai ita kanta shirin bikin tkeyi,haka salamatu tagama haukanta aure ba fashi ansha shagalin biki aka kai amarya gidan ta tasha jere.
Ranar ma salamatu bata barsu sunyi bacci ba kwanatai tana fashe fashe sukan su yayan nata sun sha bugu haka tazo kofar dakin aysha ta dinga duka kamar zata ballata.
Aiko kan safiya tai wujiga wujiga kamar sabuwar kamu koda yake basu da ban banci da mahau kaciya inka kalleta awannan lokacin ko abun kari ba wanda ta kalla dashi sai gida yaje ya karbo awajan inna ita dai
Aysha tasha Kuka awannan dare sosai auran kabir yasake bata tsoro dan ta tabbatar matar sa mahaukaciya ce babu abunda bazata iya yi mata ba.To duk fa Wani aikin gida sai ya dawo kanta dama matar gidan kazama ce alokacin tana da Wani cikin.
WA'AT
By Kulsoom Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 9
Itace shara wanke wanke kamar dai me aiki aka dauko haka ta koma shima megidan bashi dawata katabus sai abunda salamatu tace shi akeyi su ameer ita ce take musu wanka ta canja musu Kaya amma duk wannan besa umma ta sauko ta sassauta mata ba wata tara umma ta sullubo yarta mace sosai sukai rikici akan wannan haihuwar dayaga tafi karfinsa dole ya hakura dolansa haka yayi hidima nan ma akasha suna yarinya taci suna hajara.
Sosai yake takaicin ganin hajara dan dai bayadda zaiyi ne har gida uwaliya tazo tajamai mummunan gargadi akan bata yadda ya ware mata jika ba itama dole ya sota duk abunnan da ake aysha bata saniba sai dai tajiyo hayaniyar su amma batabi takai tunda be dameta ba dan Ita komai na gidan ba dadinsa take jiba ana yaye hajara aysha tana da ciki lokacin appa sai rawar kafa yake zaakara haifo masa namiji duk wasu kayan haihuwa na maza ya siya.
Ita dai aysha ta zuba masa ido taga yadda zaai Inta haifo mace dan Ita gaba dayama bata dauki zan cannasa wani abuba tayi tunanin fada kawai yakeyi haka taci gaba da rainon cikinta har ya isa haihuwa ranar wata jumaa tatashi da nakuda anyi saa alokacin saiga innar su tazo gidan dan danan kuwa aka samo mota aka kaita asibiti.Tasha matukar wahala kafinta san kato sanka ceciyar yarta tubar kallah ma sha Allah kyakykawa kamarta daya sak da mahaifiyar ta gashin kanta luf luf gwanin burgewa.
Da aka dubata aka tabbatar da lafiyar su ita yarta komai kalau aka sallamesu suka dawo gida suna shiga daki
Umma tajiyo kukan jariri afujajan tafuto daga dakinta ta fada dakin aysha dan taga me aka haifa aiko wata gagarumar ajiyar zuciya tai ta farin ciki sai da inna ta dago ta kalleta dan jin yadda take ajiyar zuciya kamar wadda tai gudun tsere.Kamar ta taka rawa haka take ji bakinta a washe take fadin inna ashe mun samu karuwa to Allah ya raya ameen inna tace dan ta lura farin cikin nan badan Allah take yinsa ba akwai wata akasa.
"Aiko da rawar jiki tafita ta hura wuta awata katuwar tukunya ta dora ruwan wankan me jego da yarta ana cikin haka appa ya shigo sai fara'a yake yana washe baki dan labari yaje masa matar sa ta haihu umma rike hanci tai ta rangada wata uwar guda fadi take angon karni ango kasha kamshi mijin aysha da salame be kulata ba har tun tube yake wajan karasawa dakin aysha"
Juyowa yayi me akasamu dafe kirji tai aah ni jikar isuhu aiba aji mutuwar sarki abakina ba gani ya koriji gwara kaje ka ganewa idanun ka jiyayi jikinsa ya fara sanyi dan sarai yasan halin umma baka ganin fara'arta sai wani abun tsiya ya faru hakadai ya daure yaje kofar dakin da sallama ya shiga dakin ras yaji gabansa ya fadi jiyai duk wani tashin hankali ya hadu ya rufto masa aka meyake ganine kamar fa mace yake gani shida zaiga namiji aiko bazata sabuba wai bin diga a ruwa.
Dukkan wata annurin fuskarsa daukewa tai dif ya dinke fuskar sa kamar hadari,inna ce ta kallesa tsaf takaran cesa dan tadade da sanin kudirinsa matso mana kazo kadauki yarka jiyayi kamar ta watsa masa bar kono ajiki zuciyar sa har suya takeyi ya santa sarai yanzu zataci mutun cinsa cike da takaici ya matso tabashi yarinyar ko kallanta ya kiyi dan takaici.
Allah sarki aysha tana zaune tana ganin ikon Allah tarasa gane abunda yake faruwa yarce bayaso ko yaya dan taga yadda fuskarsa ta nuna tsantsar bacin rai sai Lokacin kalamansa ya dawo mata dayake cewa shibaya san mace karta sake ta haifo masa Ita tadauka abunnasa wasa ne ashe da gaske yake gaya mata.Kallan sa takarayi kamar wanda ya dauki kashi haka yake yunkurin kayar mata da 'ya inna ce ta banka masa harara riketa inka sake kayadda ita ranka saiya baci wallahi.
Maza kayi mata addu,a kuma kayi mata huduba da sunana zaka samata Fadimatu Zaa dinga kiranta da WA'AT alkawari kenan maza kayi mata huduba haka yayi mata huduba badan yaso ba hararar yarinyar yake kamar wata babba abanza dan batasan yana yiba yana gamawa ya direta acinyar inna fuuu ya fuce daga cikin dakin.
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 10
Duk yadda aysha taso rike kukanta kasawa tai saboda abun yanacin Zuciyarta kuma yadaki zuciyarta bata zaci akwai Masu halayya irin ta kabir ba tayi tunanin tun azamanin jahiliyya akwai irin Wannan banda yanzu sai gashi agaban ta tanaji kuma tana gani tasamu kyautar 'ya sukutun guda amma ya nuna shiba ita yake soba.Kasa cewa komai inna tai dan Yau dai kabir yagama zubda mata da mutunci agaban surukar tata rasa mezatace tayi dan gaba daya wata irin kunya ce ta lullubeta gaba daya ranta ya gama baci da Wannan tsan tsar jahilci irinna dan nata.
Rarrashinta tasoma yi dayi mata nasiha da karbar kaddara me kyau ko marar kyau da kalamai masu kwantar da zuciya sosai kuwa zuciyar tata tai sanyi tana matukar alfahari da inna matsayin surukarta sosai take jin kaunar ta acikin zuciyarta tana nuna mata kauna fiye da yadda take nunawa dan nata sosai ta warware kamar ba itaba suka hau hira.
'Yan barka ne suka fara sintirin zuwa ganin baby duk wanda ya dauke ya kamar karya ya aje saboda kyawun da Allah ya bata Wani irin sihirtaccen kyaune da ita jama,a da dama fadi suke dama 'yar suce tana da matukar shigarai duk da jaririya ce ba tasan meyake wakana ba.
Washe garin haihuwa umma wuni tai taware redio tana tikar rawa tsabar farin cikin da take ciki na haihuwar mace da makiyiyarta tayi zuciyarta fes dan jiya kabir kwana yayi beyi bacci ba saboda tsananin takaici yakoci alwashin daga ita har uwarta zasu dan dana kudarsu dan shibazai taba san 'yaya mata ba.Duk wata hanya da yasan zaibi dan yaci mutuncin aysha da yarta babu ita dan mutanene cike da gidan tako ina yarasa hanyar dazaibi wajan cimma manufarsa yasha tunanin yaje ya murde kan yarinyar kowama ya huta sai wata zuciyar ta kwabeshi.
Ga mummunan gargadin dayasha wajan inna da malam dan inna har Allah ya isa tayi masa matukar yaje ya sake tada wata magana to bata yafe masaba dan bazai je ya zubar musu da mutunci ba a idon duniya aiko abun nan yakara bata masa rai akan wata banza har mahaifiyarsa zatai masa Allah ya isa aidai bakin zasu tafi subar su tare a sannan zaiga wanda ya isa ya hanashi abunda yake son aiwatarwa.
Ranar suna kememe yaki ya Kawo komai ba rago babu kayan girki ba kayan baby duk su inna suna sane dashi karfe tara kowa yai jugum jugum saiga babban yayan su kabir din da tika tikan raguna guda biyu kayan miya kayan baby buhun hi shin kafa taliya mai haka ya ciko mota dashi saiga kaya anata shigowa dashi dan danan yan suna ko wacce taji nutsuwarta ta dawo dan su atunanin su kabir dinne ya kawo.Umma jitai kamar aradu ta fado mata aka itada tana daki tana murna da farin ciki babu Wani abu dazaai asunan nan saidai aga bakin ciki da takaici amma wai taga anata shigowa da kaya raguna har biyu kabir ya munafur ceta ai wallahi kuwa zaisan yayi mata haka fuuu tai daki afusace.
WA'AT
By Khulsoom Ismail
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 11
Sukam Suna sukai cikin walwala da farin ciki taro ya tashi lafiya akabar umma da ciwon rai ranar kuwa sun shawota da appa dan sosai sukai bala,i da ita Ita data haifi namiji bai yan kamata raguna biyu ba amma ga wadda ta haifi mace ya yanka mata duk yadda yake son fahimtar da ita bafa shine ya yanka ba taki ganewa daka karshe saida ya gaggura mata mari tukunna suka dai daita tarabu dashi yaji da bakin cikin daya dameshi dan acewar sa annuna mai amfison diya mace akan mazan daya haifa ya kullaci iyayansa.
Saida kai kwana uku da suna yan uwa kowa ya watse akabar me jego dameyi mata wanka acikin kwana kinnan appa ko kallon kofar dakin aysha beba yaga lafiyar ta kota jaririyar ta ita kanta me mata wankan Abun ya isheta har so take lokacin tafiyarta yayai dan aysha bakaramin tausayi take bata ba ganin yadda miji ya wofantar da ita Allah Yayi masa BABBAR kyauta ya nuna baya so baya bukata yayiwa Allah butulci.
Adaddafe tai sati uku ta hada kayanta bayan taiwa aysha nasiha ne ratsa zuciya haka tabarta tana rizgar Kuka da nadamar auran kabir fal cikin zuciyarta.Tun daga wannan lokaci tashiga cikin matsala dan babu dama ta aje yarta atsakar gida saita samu me dukanta lokacin da tafara rarrafe in har appa ya dawo Zata rarrafa tatafi wajansa har boll yashayi da ita kanta daina matsowa Kusa dashi yaro ba hankali hakan bazai hana gobema ta kara ba daidai in mamarta tana kusa sai ta dauke yarta intaga ya dawo.
Babu abunda yake musu Abun cimma ba wanda zasuci su koshi ake basu ba sai wanda akaga dama ko dan pant betaba kawowa da sunan tasawa yarta ba komai itace take mata dga gidansu appa ansha akawo mata abinci dan inna tamai nasihar taimasa amma abanza kamar susa takemai akunne babu Wani abu da yake dauka acikin nasihar tata.Haka rayuwar taci gaba da garawa bayan Wa'at ta kara haifar nusaiba da hafsah sai namiji data haifa ya koma dama bezo da raiba nan
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 12
Umma ta kara zuga appa dagan gan mama tabari dansa ya mutu aiko yakara tsanar mama dan asharri irin na umma wai taga sanda ta danne kansa da fulo dan bakin cikin karta haifomai abinda yake so.
........
Wannan magana ta sake tunzura Appa sosai suke cikin tsanani dan danan mama tafara tsofewa duk kyan nan yafara guduwa wahala tana neman takashe su ita da yaranta babu sabulun wanka ba omo abincimma ba kullum suke samu abasu ba sai randa gimbiyar gidan taga dama tadan sammusu koda Kuwa mama ce tai girkin tofa umma ce mai rabawa kudin cefanan yana hannun umma itadai mama takoma tamkar yar aiki yar aikinma da bata da galihu baa dauketa amatsayin komai ba to haka take sunan wai Itama matar gidan ce.
Umma bayan hajara tahaifi zainaba da zubaida sosai 'yaya matan nan ke batawa Appa rai amma ba yadda zaiyi dan Zuwa wannan lokacin va maganar wadda yakeji sama data umma ko malam inya gaya masa magana tofa saiya gayawa umma inta amince da zancan shima zai amince in bata amince ba to shimafa zai shafawa idanunsa toka ya nunawa malam bai amince ba haka malam ya gaji ya zuba mai ido yana binsa da addu,a dan ita kadai yafi bukata ya hadu da shaidaniyar mace sai dai Allah ya fiddashi.
Wahala ce tasa mama kama sanaa har wankau take karba na mutane dan ta rufawa kanta asiri bayan kayan miya da take siyarwa dan danan sai gashi sun fara dawowa hayya cinsu in basu sami abinci ba acikin sana'ar take tsakura tasiya musu abinci.Makaranta sanda Wa'at ta isa sawa mama da kanta takaita dan tasan Appa ko kudine suke binsa bazai sata ba wata islamiyya tafara kaita Itkanu Ulumil Kur,an dan danan tafara karatunta cikin kwazo da hazaka sosai take da Matukar kokari malaman makarantar kansu suna Alfahari da ita.
Bayan ita tasaka Nusaiba da Hafsa suma suna da hazaka sosai batun umma Kuwa ba ruwanta da wani karatu dan tace yaranta ba 'yan wahala bane bazata kaisuba saida Appa ya dage saiya kaisu ta hakura amma kokawa Kuwa anshata da umma dan duk malamin daya dakar mata yaya rufe kanta take taje har makarantar in macece sai andam batu inna mijine zaisha zagi kowa yasan halinta na jahilci da rashin tarbiyya yaran nata ita Suka gada babu nazaba acikin su musamman hajara.
.....✍️✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 13
Akwai wata rana da wata malama tadaki hajara aiko ta dawo gida tagayawa umma ba bin sa,asi ba komai umma akadau mayafi aka tafi makarantar nan taje ta samu malamar azaune a cikin aji ba zato ba tsammani malamar kawai taji saukar mari a kuncinta sosai ta razana sai da tadago kanta taga umma ce tsaye akanta tana huci tana hura hanci jiki sai rashin tsami yake kaida gaji kasan andade ba ahadu da ruwa ba sosai Abun ya batawa malamar rai.Tana tashi Itama batai wata wata ba ta shararawa umma Wani zazzafan mari hagu da dama dama gata lukuta saiga umma tana taga taga zata fadi sosai yan ajin sukasa ihu da shewa suna tafawa malamar su yadda ta rama marinta.
Dabar umma tai akasa saiga hanci yana jini wasu daga cikin dalibai ne yan manyan aji Suka shigo jin hayaniya na tashi da malamai dan danan ajin ya cika ana kallon umma datake zage zagen saita doki malamar abunka da masu tashan balaga wasu daga cikin yammatanne suka zagaye umma suka fara jibgarta baji ba gani dama ba karamin haushinta suke jiba yadda take zuwa take zagin malamansu saida suka fanshe haushinsu saida kyar malaman suka kwaci umma wadda zuwa lokacin ancire mata hakora biyu nagaba tasha naushi fuskar nan tahaye.
Babu wanda beyi dariya ba da yaga yadda umma takoma tamkar sabon kamu haka ta koma kannan yayi dikin dikin daalama ya dade akitse dama kai ba gashiba keyar nan duk ta cukur kude haka tatashi tafito daga ajin tsabar yadda
taji jiki har Wani duhu take gani agabanta bata damu da yafa mayafinba haka taje gida aiko duk wanda ya ganta ahanya sai ya tuntsire da dariyar taje ta tsokano inda akafita rashin mutunci sosai abun ya sake bata mata rai.
Sanda ta shiga gidan mama tana zaune tana wanki kallo daya tai mata ta fashe da dariya Appa yana cikin dakin umma dam bema san sanda tafita ba abunda ya bashi mamaki jin dariyar mama yai abunda ya dade baijiba kenan lekowa yayi dan yaga meyafaru yana lekowa ya hango umma tamkar mahaukaciya wata dariya ce tazo masa dan babu wanda zai ganta bedauka da motsi akanta ba futowa yayi daga dakin ya kare mata kallo bakinta ya kalla ganin ba hakora besan sanda ya sake fashewa da dariya ba rana fa zafi inuwa kuna dariyar da suke mata yakara tunzurata.
Umar ne ya shigo da rakensa ahannu dan shima bai damu da zuwa makarantar ba jan birki yai ganin wata mahaukaciya acikin gidansu saidaya kare mata kallo tas tukunna ya shaida mahaifiyarsa ce cilli yai da raken ya hada hannayensa biyu yana sara mata cau cau umma Allah dai ya biya nadade ina jiran Wannan ranar da zanga wanda yai Wannan aikin danayi masa kyauta aidama gaba da gabanta inkafi karfin Wani Wani yafi karfinka hajiya umma ikon Allah fashewa da dariya yayi yana kallon mama.
Mama sha kuru minki Allah ya fara sakamiki abunda Wannan tsofaffin ke miki Allah ya kara na gaba wucewar sa yayi yabar umma kamar an dasa ta wai dan tane yake murnar an daketa yau ta tabbatar umar baida mutunci dan daman baya raga mata ko kadan.
..........✍️✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 14
Tun daga Wannan Lokacin Umma bata kara zuwa makarantar da sunan yin fada ba amma bakidai yananan yazama wawulo aduk sanda ta kalli bakinta taga yakoma haka bakaramin bakin ciki take jiba ita wadda tatafi dan taramawa ita kanta dariya take mata duk sanda iskancinta ya motsa dan ba girmanta suke ganiba matsayinta na mahaifiyarsu.
Haka shima Appa bajin maganar sa suke yiba in yayi musu magana umma cewa take haka kawai bazai ta kurawa yaranta ba yayan mama dai sune ya maidasu kamar jakai kusan kullum saiya dakesu ita kanta maman da dahali dukannata zaiyi wannan ne ta nuna bazata dauka ba bazata taba yadda tazauna ya daketa ba yayansa dai bazata hanashi dukan suba amma banda Ita.
Daga Wannan lokacin ba wanda ta kara haihuwa mama nada yaya uku duk mata umma nada yaya biyar akoda yaushe alfaharinta gida ya zama nata tunda Itace me yaya maza bata taba hangowa kanta mutuwa ba akowane lokaci Appa take hangowa mutuwa kamar ita jiran duniya zaa bar mata cin karanta take babu babbaka lafiyar Allah miji yazama nata sai yadda tai dashi yawo kuwa kullum kafarta na waje daga Wannan kasuwa tafada wannan kasuwa gidan biki kuwa ko baa gayyaceta ba saitaje dan mutane har Suna suka sama gayyar sodi amma babu Abinda ya dameta saifa taje.
Haka rayuwar taci gaba da garawa da dadi ba dadi zuwa lokacin WA'AT tafara zama budurwa nutsuwarta dabkyanta kara fitowa yake hakama Nusaiba da Hafsa suma ba baya bane wajan kyau da kokari amakaranta gasu da tarbiyya duk Inda suka hadu dana gaba dasu zasu girmamaka sabanin su hajara zainab da zubaida in zaku bangaji juna dasu bazasu taba nuna sun sanka ba ballatana sugaisheka ko baki akayi agidan basa gaisuwa ko innace tazo bazasu gaisheta ba dan umma tagama gaya musu inna ba kaunarsu take ba tafi son su Wa'at shine abunda yasa suka kara kullatarta nacewar bata kaunar su matsayin jikokinta.
Wanna kenan
Mama ce ta sauke Numfashi saboda tunano bayan da tayi idanunta yayi jajir tanada matukar hakuri amma inka kureta bakaji da dadi gyara kwanciyarta tai dan har lokacin batajin dadi ta danganta hakan da irin bakin cikin da Appa yake cusa mata dan ita bata dauki Umma a matsayin matsalarta ba bata gabanta batakai tazauna tai bacin rai akanta ba da muwarta yadda Mijinta baya ganin ta da kima da mutumci bata taba daga hannu taroki Allah daya saka mata abunda yake mataba saidai tayi masa fatan shiriya dan ta tabbatar takai kararsa wajan Sarki mai duka zai saka mata to ribar metaci kenan tun in ya shiga masifa har ita abun zai shafa.
Yake yar uwa kisani kada mijinki dan yana zaluntarki kidinga yimasa mummunar addu,a to kara fan darewa zaiyi akoda yaushe kidinga nema masa shiriya awajan Allah daya shiryar miki dashi yadawo miki dashi kan hanya madai dai ciya.Kada kidinga rokon Allah da ya saka miki inya tashi saka miki kema abun zai shafeki in kikaimai addu,ar shiriya sanda Allah ya shiryeshi ke zakici riba yar uwa
WA'AT
By kulsoom Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Kim Aneesat
Chapter 15
Ci gaban Labari
Karfe 2:00 dai dai suka gama shirin islamiyya kamar yadda suka saba kayan su a wanke agoge tsaf tsaf dasu dan badai tsaftaba duk Inda zasuje zaka gansu fes babu wani alamun dauda a tattare dasu babu wani abu da mama batai musu sosai Allah yasa mata nasibi a cikin kasuwancinta datakeyi agida zobo bakalar wanda bata iyaba musamman aka siya mata frig daga gidansu yako taimaka musu sosai kunun aya dinja zobo dage duk tanayi sosai take ciniki anta abayar abayar in har basujiyo sanda ake cewa abada abuba to kana shigowa Umma take rarakarsu musannan yara.
Manyan kuwa basa koruwa tsayawa suke aita hararar juna dan kowa yagane halinta na hassada dan sosai take bakin cikin wannan sana,ar da Mama takeyi.Mama mun tafi kiyi mana addu,a cewar Hafsa murmushi Mama tayi to yaran Albarka Allah ya kiyaye hanya Allah yakade duk wata fitina Allah ya karemun ku aduk Inda kuke suna murmushi suka amsa Ameen Mamammu fitowa sukai daga dakin gwanin sha,awa.
Mtswwww sukaji anja tsaki aikin banza kullum azum bula hijabi sunan antafi makaranta nanko munsan komai yawun iskanci ake tafiya.Duk da WA'AT tagane da ita take batace komaiba
Nusaibace tajuyo ta ballawa Hajara harara tare da murguda mata baki aiduk meyin abu shiyake zatan wanima haka yake tomu dai munyi muku nisa saidai bakin ciki yakashe ku ehe zaro idanu Hajara tai ke dani kike to da dawa nake kedin dake ake medogon baki.
Biyota tayi da gudu zata kamata aiko Nusaiba ta falla da gudu tana dariya dayi mata gwalo dan tayi alkawarin tadaina zama suna cusa musu haushi da bakin ciki ko Mama zata daketa daga baya saita rama. Hafsa ce cikin jin dadi tabi bayan Nusy da gudu itama dan tadade tajin haushin Yaya Hajaran nan tafi kowa takura musu ita da Umma yau ko Zuciyarta fes Nusaiba ta rama musu,iya dai Wa'at batace komai ba tai wuce warta tabar Hajara nacin alwashin Irin dukan da zatai wa Nusaiba inta dawo.
Wallahi Anty Nusaiba kin burgeni gwara dakika ramo mana ita Anty Wa'at matsoraciya ce tana kallo zaaita zagimmu amma babu abunda take cewa danice nakai kamarta bazan yadda ba tsaki tai aiku baku da hankali shiyasa ninasan abunda nake bazan zauna kamar karya kullum naita fada ba duk abinda sukai mana ai Allah yana ganinsu cike da gabunta take maganar. Haushine yacika Nusaiba tarasa wace irice Anty Wa'at komai saita nuna ita yar farice ji yadda take magana, tura baki Nusaiba tai eh naji amma ai Allah yace tashi na taimakeka ramawa zan dingayi tunda ke bazaki rama ba ni zan rama.
Tun daga nesa suka hango malam Sadam na dukan makara tuni idanuna Wa'at yacika da hawaye dan sosai take tsoron bulala muguwar matsoraciyace ko Hafsa bata nuna alamun razana ba sai ita hada ido sukai suka sheke da dariya Suna kallon Wa'at data kyararrabe fuska kamar me shirin fashewa da kuka sam bata kulasuba ita batasu takeyi ba yanzu na dukan datake hangowa anayi dan jitake kamar takoma.
.......✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 16
Shi kansa tun daga nesa daya hangosu yasake gimtse fuska dariya na cinsa dan yadade da sanin tatsani suka bakaramar matso raciya bace,suna zuwa Nusaiba ce tafara bada hannu bulala biyar yayi Mata masu shiga jiki sannan akaiwa Hafsa bulala uku akazo kan megayya me Aiki tuni fuska tai shabe shabe da hawaye abun sosai ya bashi dariya amma dan karta Kawo masa wasa daure fuska yayi kizo kina batan Lokaci dan Allah malam kayi hakuri su Nusaiba ne suka makarar damu daga kafadar sa yayi ni wannan bedaman ba kodai kikawo konakira yan ajinku sudaga minke dan yasan abunda tatsana kenan yace zai kira yan ajinsu sudagata.
Jiki narawa tamiko hannunta dkyar dai akagama bulalar haka tashiga makaranta tana matsar kwalla saidata goge fuskarta tas tukunna tashiga ajin bata yadda ta kalli kowa ba kawarta Jidda Itace ta nuna Mata kusa da ita zama tayi sosai Jidda me kallonta dariya nacinta dan da ganinta tasan yauma tayi halin.Kasa tai da muryar matuniyar daalama yauma kinsha tsabga harara Wa'at ta zabga mata ban saniba saiki tashi kine kitambaya ai dariya Jidda tayi tsabar salon tsokanar sai tafara yaye mata hijab wai Zata sosa mata dukan hannunta tayi cikin fushi tace zan tashi daga kusa dake tunda Abun naki wulakancine.
Allah ya huci Zuciyarki Mutuniyar haka dai suka shirya sukaci gaba da karatunsu,karfe biyar da rabi akatashi daga makaranta cikin nutsuwa suke tafiya dayake duk kusan unguwa daya suke da Jidda suna tafe suna hirarsu sama sama alayin su Jidda sukai Sallama sukai gaba itama tashiga gidansu.
Karfe 8 Wani yaro yashigo Asslamu Alaikum wai ana Sallama da WA'AT Umma dake daki zaraf tafito kai mekace kodai Hajara akace aah kai jeka tambayo dai haka yaron yafita ya sake dawowa wai yace Wa,at yake kira ba Hajara ba kamar Umma ta watsamai mari afuska haka taji tsaki tayi ta fada daki tana mita.Mama kuwa duk tanajin abunda yake faruwa Kallon Hafsa tai leka kice tana zuwa.
WA'AT takalla dako motsi batayi ba bakyajin ana Sallama dake awaje kamar zatai Kuka ni wllh Mama bansañ ko wanene ba aje acemasa bananan Murmushi kawai Mama tayi ke banason shashanci maza kirashi keje Nusaiba tarakaki jin ba itakadai zatajeba Yasa tatashi hijab kawai tasaka suka fato,Umma nazaune sun dasa kujera awaje kamar zasu fashe da wata uwar harara suka bisu tare da jan tsaki.
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 17
Cikin nutsuwa suka karasa Inda suka hangoshi atsaye jingine jikin motarsa Sallama sukai masa ya amsa fuskarsa cike da fara,a gaidashi sukai bayan ya amsa sukai shiru dan basu da abun fada ganin hakane yasa ya magantu.Nasan baki sanni ba ina yawan ganinki ahanya in zakije makaranta nutsuwarki da tarbiyyarki yasa naji kin kwantamin a zuciyata nadade ina so nakawo kokon barata amma sai naga kamar bazaki karbeni ba murmushi kawai tayi tana wasa da yan yatsunta, nisawa yayi yaci gaba da fadin ni sunana Kamal anan tudun jukum gidan iyayena yake Mahaifina Alhaji Muttaka nidai bamai Kudi bane amma Inada rufin asiri ina fatan zanji kyakykyawar amsa daga gareki.
Kallon Juna sukai ita da Nusaiba kifta Mata ido tayi akan tace Wani abu itama numfashi tadan sauke naji duk kan bayanan ka amma inaso kabani lokaci nayi tunani bakaramin kokari tayi da fadar hakan ba dan muryarta rawa takeyi kamar meshirin yin kuka abunka daba a sa baba Jinta take gaba daya atakure dan wai da Nusaiba suka taho aida bazata iya zuwa inda yake bama balle hartai masa wata magana.
Dan jim yayi dan baya fatan ace ya rasata shikenan kamar nan da kwana nawa zan baki nan da wata daya tafada da iyakar gaskiyarta dan ita ko kofar zuciyarta bekarasoba balle ya shiga, zare idanunsa yayi tare da dafe kirji abinda yaba Nusaiba dariya kenan dan sai taga kamar wani mace dariya tayi kema kanwata kinji wani ban bara kwai ko adai a gazamin ina laifin sati daya hakamma nayi matukar kokari
Bata saba musu ba dan hakan ba dabi,ar su bace ako yaushe itadin me karbar umar nice tasaba dayi bawai da kinyi dinba dan ta horu iyakar horuwa Agidan su.
Ga Mama da Akullum take kara nusar dasu akan yiwa nagaba dakai gardama matukar ba sabawa Allah yace kayi ba to Kayi masa biyayya, shikenan Allah ya kaimu satin Ameen har kinsa naji dadi sallama yayi musu dan ya lura gaba daya bajin dadin tsayuwar sukeba duk atakure suke.Motarsa ya bude wata katuwar leda ya jawo da Suna radau ajikinta SAHAD STORE kaida ganin kayan ciki kasan iyayan kudi aka kashe kan adauko su, toga wannan bayawa kememe sukaki karba Duk yadda yayi dasu kin karba sukai haka suka shiga gida suka barshi da leda ahannu.
Duk wannan tsaiwar da sukai ashe su Umma ana labe asoro ana zuro dakai kamar maguna suna ganin tahowarsu sukai sauri suka juya cike da takaici hassada fal Zukatansu musamman Hajara jitake kamar ta shakosu dan tsabar takaici ledar can kawai take hange jitake kamar tafita ta karbo ta kwafa tayi.Da Sallama suka shiga gidan amma kamar kafurai babu wadda ta amsa sai binsu suke da harara kamar idanunsu zai fado in dai yawan karuwancine ayi mugani muna zaune za,afito adinga amaye amaye cikin daga murya Hajara tace gaya musu dai dan wallahi har gidan redio sai mun kaisu gaba da nan ma cewar Zubaida.
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 18
Suna shiga daki ko zama basiba yaro yayi sallama da leda ahannunsa wai gashi ance naba wayanda suka shigo yanzu inji Kamal Kamal Hajara ta maimaita duk da Acikin duhu ta hangoshi Sosai yayi mata dan daganinsa handsome ne gakuwa yayan banki dolene ma tayi Wani abu akai dan bazata zuba idoba makiyiyarta tai Aure tabarta Agidan ba Impossible.Nusaibace tafito daga dakin kawo nan tace da yaron kodan ta cusa musu haushi takarba bude ledar tai Allah sarki Yaya Kamal kace mungode Allah ya kara budi taciccibi ledar tai dakinsu da ita aiko tashaka musu haushin Hajara ce takalli Umma cikin rashin kunya take wai yanzu Umma kina kallo kin zuba ido waccan maikama da aljanar zatai Aure tabarni gaskiya nifa in bazaki nemomin mafitaba ki kyaleni na nema dakaina nadade dagane baki damu da al,amurana ba.
Cikin rashin damuwa datake fadin kefa dadina dake banza ce ance miki zama zanyi na zuba ido tatafi tabarki ashema nidin ba diyar Uwaliya bece nikaina ina tsoron kaina saboda iya hada tuggu yawwa yanzu naji zance kedai kizuba ido kisha kallo wata dariya suka sheke da ita suka tafa.
Nusaiba wayace kukarbo wannan kayan kinga kikiyayeni nasan wannan aikin nana Kowa bane sai naki kai Mamammu kina jifa damukai karba yasake biyo mu dashi hargida kinsan kuma bkyau maida Alkhairi, dakuwa Mama tai mata nizakiyiwa wa,azi dariya tayi a,ah Mama nifa tuna miki kawai nai girgiza kai kawai tayi dan Inta biyewa Nusy sata magana zatai tayi Allah ya shiryeki to saiki aje kayan ban kuma ce ki buda ba ki ajesu kawai to Mama.
Wa'at tana jinsu batace komai ba cigaba da karatunsu sukayi dama shi sukeyi aka kirata tatashi suka Tafi bayan sun gama sukayi Addu,a suka kwanta.
Karfe 7 suka jiyo hayaniyar Appa atsakar gida dakinsu ya nufo yana kumfar baki buga kofar yake kamar zai karyata kafa yasa ya doki kofar saiga sakatar dasuka saka tacire kamar zautacce haka ya afko dakin yana haya gaga, Mama ya zabgawa harara ke ina ledar da akace jiya anshigo da ita munafuka koko kin budeta kuncinye keda yayanki saida taji Wani dum wai 'ya'yanta dagaske yabar matasu kenan ya tsame kansa daga jibantar lamuransu Wani abune ya tsaya mata amakoshinta me matukar zafi.
Da hannu ta nunamai ledar ya figeta yafice ko waiwaye beba gaba daya yaran suka bishi da kallo Sosai tsanarsa tasamu matsuguni azuciyarsu dan babu yadda zasiyine da Mama zata yadda da suntafi sun bar masa gidansa amma saboda yanayin tarbiyyar dasuka samu nasu taba mayar masa da magana ba saidai siyi ciwon ran su gama.Umma ana tsakar gida Zuciyarta fes dan tasha alwashin dama bazasu amfana da kayan ledar ba saidai su suyi ita da 'yayanta aiko duk Suna tsakar gidan suna jiran afito da ledar.
Dan tsabar munafurci Irin na Umma harda yimasa shimfida abinda yadade da rabon daya ga ammai shimfida ya dade saidai yayi da kansa.Zama yayi ya juye kayan ciki gaba daya kayane Sosai da kayan ciye ciye kayan sawane Wasu dogayan rigunane masu matukar tsada guda biyu sai sai su shampoo sabulai mayuka na gyaran jiki Chocolate biskit da sauran kayayyaki kayan kwalliya babu abinda babu.
..............✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 19
Hajara tana zaune dafi,an agabansa Zaram tasa hannu tadebe dogayan rigunan yana kallonta bece komai ba kayan kwalliya turarurruka duk itace ta kwashe kayan su chocolate maya mayai duk tadebe takoma gefe fuskarta awashe ko banza tasamu nayin wanka Kowa bashi nasa yayi rai fes suke shan kayansu Umma kuwa kamar kura sai wawake wawulanta takeyi abin dariya tana shan chocolate.
Duk abunnan da akeyi Umar yana daki yana jinsu murmushin mugunta yayi shikadai yasan abinda yashirya musu acikin Zuciyarsa kwafa yayi Irin zamu gauraya daku. Appane yadauki dan abinda ya rage yana zuwa ya watsawa Mama ajiki ga rabon kunan in kuma bakwasha muhada mushanye ko uffan batace masaba haryaga tijarar sa yafita girgiza kai kawai tayi dataga abinda ke cikin ledar chocolate ne guda uku sai biskit guda daya basu tayi amma gaba dayansu sukace basasha tasansu sarai sunada matukar zuciya.
Itama bata matsa musuba kuma ko afuska bata nuna Musu taji haushin abinda Mahaufinsu yayiba ta hadiye bacin ranta tsaf kari sukai zuciya ba dadi dan tun kafin su karya Appa yazo yayi musu wannan tijarar.A dakin Umma kuwa baki washe suke bude kayayyakin dasuka dauka Wani Mega Umma tadauko ya matukar burgeta kare masa kallo tayi daalamun wannan sabulun tsarki ne haka ta ayyana aranta abunda ba azauna a class jiki narawa aka zari buta sai toilet kamar mintuna biyar akajiyo ihun Umma a toilat.
Da gudu su Hajara akafito daga daki haka su Mama dan ihu take kamar wadda ake zarewa rai cirko cirko sukai abakin toilet din ana tambayar ta lafiya Amma ba amsa kawai kukanta akeji tana tashiga uku naman jikinta ya kwakwakwabe dakyar akasamu Umma ta fito da zani ahannu fuskar nan tai wijiga wujiga da majina da yawu sai bude wawulannan takeyi abun dariya ashe Umma da akashiga toilet tsabar dan wajan yafi wankuwa laftawa tai yayi mintuna yadda zata dawo yar budurwa.
Dan danan taji azaba tafara ziyartarta kamar ana tsatstsaga mata wajan haka taji banda kauyanci irin na Umma abunda ake Sawa aka itataje tasa a HQ dinta aiko waje yafara kwalayewa dan rashin azanci duk ihunnan da takeyi bata wanke ba kallo daya sukai mata suka fashe da dariya wata tafiya da takeyi kamar wadda akaiwa shayi idanu yayi jajawur Mama ma saidata dara dan tuni tafahimci aika aikar da Umma taje taiwa kanta.
Zainab ce cikin dariyar mugunta take kallon Umma Allah sarki su Umma anji jiki abinka daba sabanba ba asaba gani babu a house gidan Mijin ma baa samu ba Shiyasa baa san yadda zaai amfani da abuba Allah ya kara mugunta fitsarin fako ni wllh da wajan ma yafado da kin huta shekewa da dariya tayi yabarsu awajan dan duk da basu saki tarbiyyaba sosai takejin haushin yadda Uwar tata takewa Mama itadai bata shiga har karsu amma baza,a taba hadakai da ita a cutar dasuba.
Cikin dariya Nusaiba take fadin to Allah dama ai Arrahimu ne tun aduniya yake sakayya basai ammutu ba Mama ce tabiyota zata bige mata baki da gudu tashige daki tana dariya kowa tafiyarsa yayi yabar Umma atsaye Hajara da Zubaida ma tabe baki sukai irin keta shafa suka barta agun.
WA'AT
By Kulsoom Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 20
Cikin takaicin a bunda sukai mata tace tsinannun yara harni zaku tafi kubari inda ku masifar tafadawa aibazan iya tafiya na barku ba yan iskan yara kawai,dakyar ta kai kanta daki jagwaf tafada kan gado dakin kaca kaca kamar na mahaukaciya yai dukun dukun kulli kullin kayan wanki kamar me wankau dakin sai tashi yake da wari amma basaji ahaka suke zaune babu wadda zatasa tsintsiya yayi shara sai dai ita intaga dama ta tattare dakinta shiyasa yan uwan Appa babu wanda yake iya zama adakinta iya karsu da ita bakin kofa zasu gaisa suyi wajan Mama dan ita a kullum dakinta tashin kamshi yake haka Jikinta da na yayanta Komai nata das.
Ranar Umma taga masifa son zuciyarta ya jamata babu wanda ya karabi takanta bare yayi mata sannu Appa daya dawo tabashi labarin abunda ya faru da kyar ya iya rike dariyarsa dan karta sauke mai bala,in akansa ammafa yana fita sai daya dara yau ya sake tabbatar da Jahilcin Salame ko A bata sani ba ba arabi ba boko.Suratul Fatiha wannan sai da kame kame zata iya kaita hakamma sai ansha fama shiyasa sallar ma ba kowane lokaci takeyiba in zatayinma saidai ta duddun gura tatashi.
A kalla tafi sati kafin Wajan yafara yimata sauki su kansu su Wa'at kwana biyu sun sami saukin masifarta sosai suka wataya dan ko kiching din bata iya zuwa balle tahana ruwa gudu ci sukeyi su koshi dan Nusaiba da Hafsah har addu,a sukeyi Allah yasa karta warke ta zauna ahaka ko saji dadi Acikin gidan su wataya su huta.
Shi kansa Appa ya rage masifa wani abun duk itace take kara tun zurashi ashe kwana biyun da bata da bakin magana be muzguna musu sosai ba in sun gaidashi yana amsawa duk da fuskar nan ahade take hakamma sunji dadi dan da in sun gaidashi yaki amsawa in basu gaida shiba yace sun rainashi komai sukai masa basu tsira ba babu wani abu da zasuyi mai ya nuna yaji dadi sai dai hantara da kyara tsakaninsu babu wannan jin kan tsakanin 'ya'ya da iyayansu sautari suna rayawa aransu dama ya mutu suhuta da gasu sai Mamarsu.
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Kim Aneesat
Chapter 21
GARIN ABUJA
A can Unguwar A Sokoro katafariyar Unguwa data hada jiga jigan masu kudi da suka amsa sunan su ba yan kuci ku bamu ba shiru take Unguwar ba ruwan wani da wani manyan gine gine ne wani tanga meman Gida na gano ko ina zagaye yake da Scurity Kaida Gani kasan gidan wani hamshakinne saida nasan yadda na kutsa domin dauko muku rahoto.
Ma aikatane birjik suke ta kaikawo duk da dare ne amma tamkar rana haka gidan yake tarwai da haske tako ina kowanne sanye da Uniform riga da wando Iya mazane ke shawagi a harabar gidan Scurity sukuma da kayan Sojoji kowannan su da katuwar bindiga A hannunsa zazzare idanu kawai suke suga wani kuskure su farwa mutum dan wannan Zakunan suka rufu a kanka ko namanka baza agani ba sai sunyi fata fata dakai.
Wani kayataccen falo na hango na kutsakai cikinsa sai da alkalamina ya kusa faduwa ban taba cin karo da falon daya dauki hankalina Kamar sa ba Wasu Azababbun Cushing ne masu matukar kyau komai na dakin pink and white ne sai ya hadu ya bada wata kala ta musamman sai tashin kamshi yakeyi Kaida gani kasan mamallakiyar Falon tana da matukar tsafta da kuma san gayu.
Wata hamshakiyar Mata na hango azaune da alamar tayi Zurfi acikin tunanin da takeyi fuskarta dauke take da tsantsar damuwa mamaki ne ya kamani itako me ya dameta haka duk wannan daular datake ciki, sai kuma nai tunanin duk mulkinka da izzarka dukiyarka dan Adam kowa da Kalar Jarrabawar da Allah yayi masa tabbas zaasamu wani abu daka gagara samunsa kudin da kake dashi yakasa yimaka maganinsa.
Tafara manyanta akalla zatakai shekaru 55 duk AC din sake falon behana jikewa da zufa ba koni dana shigo nake kwasar arziki tuni na bushe wani sanyi medadi yana ratsani sainaji matukar tausayinta ya kamani dan da ganinta kamilalliyar dattijuwa ce fara ce tas a zamanin yam matancinta na tabbata bakaramin gwara kan yan Maza tayi ba.
Taku Naji alamun zaa sauko daga sama wata yar budurwar ce kyakykawar gaske take saukowa da alamun bacci a idanunta idanunta kafe akan wannan matar dake zaune Kusa da ita taje ta zauna akan sofa harta zauna kusa da ita bata sani ba.Ammi sunan da matashiyar takirata dashi kenan firgigit ta juyo tare da kakalo murmushin dole dan bataso tazo taganta a wannan halinba cikin damuwa take kallonta haba Ammi so kike murasaki kinsan yadda tunani yake yiwa dan Adam illa Kuwa meyasa bazakiyi tawakkaliba kici gaba da Addu,a na tabbata Addu,ar Uwa bata faduwa kasa banza Allah zai karba miki Addu,arki.
Numfaahi ta sauke hakane Marwa amma abunne yana cin Zuciyata haka zaki daure Ammi Dan Allah cike da shagwaba take fadin hakan shafa kanta tai to shikenan Marwa zan rage aah kidena gaba daya to zan daina Murmushi tai ta rungimota jikin ta tashi sukai suka haura sama kowa tanufi dakinta.Koda Ammi tashiga dakin Alwala ta dauro ta shimfida sallaya ta tada Sallah tadade tana Addu,o,i sannan ta shafa.Kata faran gadonta tahau duk da tasan balallai baccin ya dauke taba amma tana fatan hakan ko Zuciyarta zata samu hutu,Allah Alhakim saiko ga baccin Ya dauketa batare data ankare da hakanba.
A suba tagari
........✍️✍️✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 22
Rikitattun idanunsa ya zuba mata yana kallonta cikin tsananin konar rai da tafasaf zuciya yama rasa mezai cemata shikadai yasan Irin masifar datake ratsa dukkan sassan jikinsa gaba daya jijiyoyin kansa sunyi rada rada abunka da farar fata zazzafan huci ya furzar daga bakinsa dun kule hannu yayi tare da kaiwa bango naushi metake so ta maidashine neman mata take so yafara ko kuwa tunda sukai Aure yake fuskantar kalu bale daga gareta ina soyayyar datayi masa abaya dama badan Allah ya makale masaba harsaida ya Aureta hankalinta yakwanta.
Nifa kana batan Lokaci kasan inada abunyi Matukar bazaka bani 2millions din dana nema daga gareka ba wllh nima bazan baka abunda kake soba haka kawai dik zakabi ka tsofar dani da jarabarka nifa nagaji da kuruciyata kamayar dani gyatuma abunda bazai taba yiwuwa bane kudinka biyan buka tarka in baka dasu kabani hanya na wuce, da Lumsassun idanunsa da sukai bala,in sauyawa yake dubanta da ace yaso da zai iya kwatar hakkinsa takarfi har nawa take dazata tsaya tana jamasa rai amma yarasa meyasa yakejin shakkarta yake tsoron tsallake Umar ninta wai anya shine kuwa shine AA kodai ansauya shine shida maza sukejin shakkarsa bare mace macemma Fareeda wadda ba kowan kowaba amatan da suka soshi kafarsu bata kama akyau da diri da komai da komai ba.
Kamar zaiyi Kuka muryarsa har rawa take yake rokonta tabashi hakkinsa kodan guje mata fushin Ubangiji da tsinuwar Mala,iku Cikin daga murya take fadin Wallahi AA ko suma kake Matukar baka biya kudinnan ba bazan baka jikina ba narasa wannan jaraba waya sanima har kannanka kanabi wannna jaraba dame taikama.Kura mata ido yayi jin Wani bacin rai yana taso masa sakamakon mummunar kalmar data jefeshi dashi kannansa shine abunda yake Amsa kuwwa akunnansa.
Take yaji duk Wani abu dayake bukata daga gareta yafice masa arai tashi yayi gaba daya yabar dakin dan Inya zauna babu shakka saiya kakkarya mata kasusuwa bayason yayi Wani abu dazaija Hankalin yaransa dake harabar Gidan da masu aikinsa da suke Matukar ganin mutuncinsa.Dakinsa ya nufa ko ganin gabansa bayayi saboda tsananin tafasar da Zuciyarsa keyi kaitsaye toilet ya nufa gaba daya ya warewa kansa shower batare daya cire kayan jikinsa ba cije lips dinsa yake kamar zai rabasu da bakinsa ajiyar zuciya yake saukewa ajajjere yadade a haka kafin yaji Zuciyarsa ta fara san yaya ahankali futowa yayi bayan ya dauro towel ajikinsa dakin ya kalla yaushe rabonsa da gyara dan ya hana yan Aiki shigomai daki yace inhar bazatai gyaramai da kanta ba tota barshi.
Tsaki yayi dan gaba daya Fareeda tagama fitar masa daga Zuciya amma yarasa maiyasa ya kasa daukar mataki akanta kayan bacci ya zura kawai ya kwanta kansa ba karamar darawa yakeba kamar zai cire dan dole ya sake tashi drowar dake jikin gadonsa ya janyo magani ya balla yajefa abaki ko zaiji saukin abunda yakeji sake kwanciya yayi yaja bed shit yarage hasken dakin Zuciyarsa fal tunani.
By Kulsoom Ismail
Kuji gaba da biyoni dan jin wanene AA.
Comments dinku na karan karfin guiwa
.........✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 23
Karfe 7 Masu Aiki sunata kai kawo fes suka gyara falon hakimar tana daki ko sallah batai ba tana can tana bacci tunkan ya sauko kamshinsa ya sanar da yan aikin Megidan ne dan tararansa na da banne Ma sha Allah cikin kakinsa na Soja yake kafadarsa rataye da jakarsa ta laptop fuskar nan ahale saye da glass a idanunsa dan har Lokacin idanunsa basu washe ba ko Kallon sashin da take baiyi ba gaba yayi yana dagawa yan aikin hannu gaisuwar da suke masa kowacce kanta akasa yake dan ba karamin kwarjini yake yi Musu ba.
Harabar Gidan yafita da sauri yaransa suka rugo atare suka kame suka saramai hannu kawai ya daga Musu hakan ya tabbatar Musu dayau ran Ogan nasu abace yake sun tabbatar baya rasa nasaba da matar Gidan dan kosu sun gane halayyarta bamasu kyau bane budemai mota sukai shiga yayi har Lokacin bece dasu uffan ba kobe fadaba sun san abinda yake nufi maiduri suka nufa dan baifiya son hawa jirgiba yafison yadinga ganin da zazzuka hakan yana bashi nishadi matuka.
Hanyar gidansu ya kurawa ido Tamkar ana fizgarsa dakin bin hanyar haka yakeji danko san Kallon hanyar bayayi sukansu yaransa sun rasa meyahau kan Oga daya daina Zuwa gidan nasu ada koda wane Lokaci yana tare da Mahaifiyarsa da kannan sa amma yanzu ya canza ko Kallon hanyar baya sonyi shiru sukai dan basu da hurumin shiga abunda bai shafesu ba.
Lumshe idanun sa yayi Wani abu na danne Zuciyarsa da son ganin Ammin tasa basarwa yayi suka dau hanya Maiduguri.
*********
Ba ita tafarka ba sai kusan 11 wanka tashiga tayi sai alokacin tayi Sallah ba kunya ba komai haka ta bubbuga tana idarwa ta cillar da mayafin dan kaf dakinta babu hijab wayarta ce tayi kara kamar bazata dagaba saita daga Kb abunda tace kenan ya zaki fito din kuwa ko wanda karfan yananan tabe baki tayi ko bayanan yau banajin fita ina son na hutane kai babbar yarinya ya kike hakane nifa bana son harkar yawa
Tsaki tai nifa dadi na dakai Kb akwai naci bazan samu fitowa ba to ya maganar kudadannan kinsan fa shagalinnan saida Money basu samuba kai beb gasky baki haduba ina da barar taki da wayon naki kikai sake baki karba ba tun ajiyan kabari kawai Kb jiya nayi wata wautane nan tabashi labarin dukkan abunda ya faru gasky Man dinnan yana sonki da yawa aiko nine saina babballaki amma beyi hakanba ya barki har kike Numfashi cikin salama.
Batarai tai kamar yana ganinta kaga Kb bana son wulakanci kit ta yanke wayar acan kyalkyalewa yayi da dariya yar wahala kawai muje zuwa ya buga kafarsa akasa cike da alwashi azuciyarsa Kome ya kudurta oho.
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 24
Da sallama aba kunan su suka shigo gidan Amma babu wanda ya dago kai ya kallesu yi sukai kamar basu jisu ba Zubaida ce ta dago fuska a tatsine take dubansu kunga kun ishemu da sallama kamar sababbin tuba, Nusaiba ce ta galla mata harara towa yasani ko sababbin tubanne mutum dai ya fara kashe wutar gabansa kafin ya hango wutar Wani dan munsan komai wasu sun dade da ridda.Fau taji andauke ta da mari kara daga hannu zatai Wa'at tarike hannun Hajara ce tsaye take huci tana hura hanci ke kuma dallah malama sakarmin hannuna karki shafan datti.
Karewa Hajarar kallo tai sai taga ai itacema zata shafa mata daudar sakin hannun tai batare data matsa daga gabanta ba kiyi hakuri dan Allah Yaya Hajara bangaje ta tayi aiyau ko Uwar kice taimin wannan rashin kunyar saina rama balle wannan karamar halittar sai naga gatanta a garin nan.Duk abinda zamiyi karki kuskura kisake sa Uwata aciki dan ba Ita tayi miki laifinba kuma ba Itace ta saka tai miki ba au lallai kam ke harkece kika samu bakin magana hannu takawo da nufin marinta rike hannun tayi hannunki bazai taba sauka a fuskata ba yar far da hannun tayi taja hannun kannan ta sukai gaba Hajara kamar zata amayar da kayan cikinta haka take masifa sai sun Ita sukayiwa haka bari Appa ya dawo.
Dan Allah kibishi kasuwa tun yanzu inya dawo karya barku darai daki suka shige suka barta anan duk wannan dan barwar da akasha Umma batanan tanacan yawonta.
Mama Kallon su tayi kunji dadi kuci gaba da jawomin magana aina gaya muku kome zasu muku kuyi hakuri my kyalesu dan kunsan karshe ku zakusha wuya awajan mahaifinku dan kun tabbatar inya dawo bazai barku ba sai hukunci ya biyo baya shiru sukai Inma basu rama ba duk hukuncinne gwarama su rama susan sun rama zafin baya hadar musu biyu ba.
Mama Meyasa bakya son mudinga ramawa kina ganin ita Aunty Wa,at tazama Wata solobiyo tana tsaye sai kanwarta ta gaggaya Mata magana sudinga zagimmu nidai bakina bazai taba shiru ba matukar basu daina zaginki ba.Shiru Mama tayi dan bata fatan ace yaran sun rike mahaifinsu aransu shiyasa kullum take nusar dasu Wataran zai sosu ya kaunace su a matsayinsu na Mata.Hade rai tayi koma dai menene ban yadda ku dinga zama kuna cece kuce dasu ba kiyi hakuri Mamammu.
Appa yana dawowa tun kan ya zauna Hajara aka fito daga daki ana matsar kwalla kallonta yayi ke kuma mene kikazo kika sani agaba kina Wani matsar idanu kabari Appa ai wallahi dole nai Kuka irin zagin tsamar naman dasu Wa'at sukai maka dazu harda cewa su basuga amfaninka ba dan babu abunda kake tsinana musu dan abincimma dakake basu daga yau inkai dan halak ne kadena.Tuni jikin Appa ya fara rawa harshi wasu yara zasuyiwa haka aiko yau duk sai yaci Ubansu ganin ya juya ya shiga dakinsa ta daka tsallan farin ciki tashige daki Umma taje takira sufito suyi kallo.
Aiko Umma har neman yadda zani take tsabar farin ciki da doki aka dasa kujera wata katuwar doruna ya dauko daga dakin nasa Suna zaune Suna cin Abinci Kamar wanda ya diro daga sama haka suka ganshi laftarsu ya farayi Kamar Allah ya aiko shi ko kisan kai sukayi ai iyakar abunda zai musu kenan keeee Kamar kayan wanki haka ya wullosu tsakar gidan daya bayan daya Mama tana zaune kala bata ceba Amma inka shiga Zuciyarta ita kadai tasan yadda takejin zafin saukar dukan Kamar ajikinta yake sauka haka taji.
Saidai ya faffasa musu jiki gaba daya sun gala baita daga bulalar yayi da nufin sake zuba musu ita ajiki jiyayi anrike bulalar a fusace ya juyo dan yaga Wani me tsautsayinne.
Taku har kullum
Mrs Baba Bello Abubakar
......✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 25
Umar ne ya rike bulalar fuskar sa dauke da bacin rai yake kallon Appa kai Umar sakar min bulalar nan yau inban kashe yarannan ba Bazan taba hucewa ba taran tsin tsinya ba shara banga amfanin haihuwar suba in banda asara da suka jawomin da zan lissafa Abincin da suka cemin da yanzu nazama me kudi 'yaya Mata nibanga Amfanin Suba bayan wahala to Wallahi daga yau Abincina ya haramta agaresu sai dai su mutu saboda yunwa.
Yanzu Hajara tagama zayyana mun dibar Albarkar da sukamin dazu suka gama zageni tas suda Munafukar Uwar su me fuska biyu.
Cikin takaici Umar ya Kalli Hajara dama akan wannan makirar kake musu wannan dukan nima yau zanga Ubanda ya isa ya hanani nai Mata kirbar sakwara a gidannan sai Lokacin Umma ta mike Wallahi ahir dinka ka dokarmun yarinya ba hawainiyarka ta kiyayi ramata.Ko kallanta beba bulalar hannun Appa ya fisga gadan gadan yayi kanta Umma tsakiya ta shiga dan kar ya daki Hajara Wata janyowa yayi Umma Saida takai karshan bango jikake kum ta buga goshinta ajikin gini dabar tai zaman yan buri dan Jinta tayi tana sama tana kasa.
Duk yadda su Nusaiba suka zanu saida abun ya basu dariya,dukan tsiya yayiwa Hajara dan saidai Itama ya rugur guzamata fata yai Mata biji biji tun tana Kuka saida hawayanta suka kafe Appa na gefe dan bakaramin shakkar Umar yake jiba daya taho zai ceceta Wani mugun kallo da yayi masa ya sashi dole ya koma gefe saidai yayi Mata lilis tukunna ya yarda bulalar tunda ke annamimiyace gobema ki kara.
Hannunsu Wa'at din ya kama hardaki ya kaisu bece da Mama Uffan ba duk da basa magana da juna amma tasan shidin me kaunar yayanta ne Nagode abunda tace masa kanzil bece ba yafita adakin gaba dayama ficewa yai daga gidan dan ransa abace yake.
Hhhhh Zainab ta sheke da dariya dadina da gobe saurin zuwa in zaka gina ramin mugunta ka ginashi dai dai dakai kan Hajara tazo ta tsaya da baki yayi sun tum Kamar ganda Allah ya kara ya dada azaba ni Wllh bema burge niba dabe karyaki ba an hutama da kafar yawo.Bam taji an bige Mata baki Umma ce sai huci take dan ji take Kamar ta tsinewa Umar yau Irin bata Mata ran da yayi akan makiyanta yayiwa shalelenta wannan dukan. Umma dan na fadi gskya zaki dakar min baki na dakeki to Allah ya isana Wallahi danba yafe miki naiba kuma in sha Allah gobema Kuka kulla makirci saiya koma kanku.
Ko ajikinta Allah ya isan da tai Mata dan Itama haka tayi zamaninta matukar Uwaliya zata daketa sai tayi Mata Allah ya isa,bata dauki hakan awani abuba kama hannun Hajara tai suka shige daki sai zage zage take shiko Mijin hajiya tuni ya shige daki.
Tundaga Wannan rana Rayuwa tasake yi Musu tsanani dan dagske an daina basu Abinci sai dai Mama tasan da barar da zatai Musu sudan samu abun kaiwa bakinsu murna wajan su Umma kuwa ai baa magana suna kallo zasu dafa Abinci suzauna su cinye ciyarwa ba wasa bace dan danan jarin Mama yayi kasa sosai sai dai azo aita abayar abayar amma babu babu jari kanta saro kayan sun cinye kudin ga kudin makaranta da yake a wuyanta dan danan suka fara wata irin rama sai idanu awaje yanayin kokarinsu A Makaranta ya farayin kasa to ciki baya samu shiyasa kwakwalwar ta cin kushe da tsananin tunanin makomarsu da damuwa yadda zasu tsinci kansu agaba.
Kamal bayan wannan zuwan ya dawo har sun fara sabo da juna sosai yake yi musu siyayya saidai su boyota su shigo da ita dan muddin Umma zata kyalla ido taga ni toba rabonsu bane.Dan dole Mama take karbar kayan dan tayi Alkawarin ba zata taba kai Appa karaba zataci gaba da rokon Allah ya yaye musu dukkan kincin da suke ciki.
........✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 26
Bayan Sallar Magariba Suna zaune akofar dakinsu karatu sukeyi yaro ne yayi Sallama wai ana kiran Hajara a waje kamar Umma zatai tuntube tafito kai jekace injiwa yaron komawa yayi wai inji Kamal cikin sauri suka dago Suna kallon yaron Nusaiba Kallon Wa'at take da neman karin bayanin wane Kamal din ake magana akai itama Wa'at din ita take kallo.
Cikin washe baki Umma tace yawwa dan Albarka maza kaje kace gatanan zuwa harda bawa yaron naira 50 yafita kuwa yana murna,cikin kwarkwasa Hajara akafito ansha wanka tayafa wani dan mitsistin mayafi dashi da babu duk daya tabaza wani uban turare gaba daya baida dadin shaka kamar zakai amai haka turaran yake har soro Umma tarakata tanai mata kirari.
Tana fita ta canja taku kamar wahainiya haka ake taku dai dai sai kas kaka kas take da cimgom abakinta bakin yasha pin lips tik sai shaining yake ba Sallama ba komai haka tabe tayi tsaye shiko kamar gaula sai faman washe baki yakeyi dan tunda ya kara shakar wannan turaran ya kara susu cewa akan Hajara babu wadda yake san gani sai ita.
Malam ina fatan lafiya daka aika akirawoni dan wajan kanwata kake zuwa baniba cikin rawar jiki yake fadin tuba nake gimbiyar mata wane Ita ta hada kanta sake ada dimma rashin sanin akwaiki shiyasa harnai kuskuran fara zuwa wajanta danni a yanzu kosan jin sunanta banayi balle naganta.Wani makirin Murmushi tayi anzo wajan fuska tasaki to yanzu naji magana katabbatar maganar nan har Zuciyarka take sosaima kuwa yanzu akaf duniyar nan ko Uwata bana Jinta araina saike wani Murmushin tasake yi Uwar takama zanyi maganinta kazama nawa ni kadai tafada a Zauciyarta.
Sai wajan 11 tadawo gida a hakamma da kyar yatafi kamar zaiyi Kuka dan wata soyayyr Hajara yakeji Kamar zaiyi hauka,leda ya miko mata shake da kayan alatu tuni fuskarta ta kara washewa abunda take Jira kenan dama ba nagodi bare nagode tai Zaram takarba sallamar da yake mata baji taiba hankalinta yana kan laidar hannunta. A tsakar gida ta tarar da Kowa dan lokacin zafine ana shan Iska Umar yana zaune akofar dakinsa dan sarai yaga sanda take zance awaje daya karemai kallo yagane Saurayin Wa'at ne yayi mamaki va kadam ba amma daya tuna Wacece Mahaifiyarsa a wajan tuggu da makirci ya batta shima Yashiga komarsu ne sai yadda Allah yayi dashi.
Hannu kawai ya miko mata batare da yayi magana ba tana matukar jin tsoransa haka ta mika masa kamar zata fashe da Kuka Umma tana zaune takaici ya kamata tarasa meyasa Umar yake shigar mata hanci da ace ba ita ta haifeshiba da yanzu ta dade da maganinsa kwafa tayi hakamma bazata kyaleshi ba ya dinga yimata iskancin da yaga dama ba.
Kayan ciki ya dinga futowa dasu wasu manyan kajine ga sassu sai tashin kamshi suke makwat Hajara ta hadiye yawu kamar tsohuwar Mayya🤣🤣haka Umma take mika wuya kamar wuyan zai karye kamshi ya cika mata ciki itama Appa da yake gefe abunda ke Zuciyarsa kenan yana shiwa duk wanda ya kawo kazar nan Albarka.
Fresh Milk kusan guda biyar sai Drinks kaya ne dai makare acikin ledar.
Saidai yaga tsaf ya bude wannan Kazar cinya ya dauka ya kare mata kallo abakinsa ya sata ya gutsira sai da ya lumshe idanunsa sai da ya cinyeta tas suna kallansa anrasa kuma wanda zaiyi magana a cikinsu kasata hudu yayi ya hade kashi biyu awaje daya kashi dai dai daban daban.Nusaiba ya kira Wannan kashi biyun ya mika mata da fresh Uku drinks Uku kayan kwalliyar kuwa tas ya batasu da su Chocolate nuni yayi mata da zata Iya tafiya.
Kuka kawai Hajara ta fashe dashi dan bakin ciki wannan shine kura dashan bugu gardi da kwace kudi.Wannan kaso dayan ya basu da fresh guda daya dayan kason kuma ya jashi gabansa yanaci yana korawa da drink ko kallonsu bai karayi ba.Haka dole suka ja nasu suka rarraba Zuciya cike da takaici.
Bangaran Mama bude namansu sukai sukaci suka kora da Ruwa Zuciyarsu ko dar babu dan yanzu basa tsoron duk Wani abu dazai biyu baya saiga cikinsu kuwa yayi dam dama abunka da masujin yunwa dan danan Wani bcci mai dadi ya dauke su.
🤣🤣🤣Anya Mama baku ciwa kanku ba kuwa karfa kumanta da Umma buhun Kaya zata barku ko kuma zata dau fansa.
Kuniyoni Fans
..........✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Kim Aneesat
Chapter 27
Kafin Umar ya fita saida yayi musu gargadin karyaji karya Gani duk wanda ya tada maganar nama shiyasan mezai musu tsit kakeji Kamar Ruwa ya cinye su babu wanda ya tanka tamkar dai shiya haifesu basu suka haifeshiba.
Washe gari karfe 7 na safe sukaji ana bugu kamar Zaa balla kofa cikin bacin rai Appa ya fito dan yaga wane mara mutuncinne meneman balle masa kofa haka Umma tafito tana zage zagen wane dan asara ne wannan yazo ya tashesu daga bacci.Zare sakatar yai gararam kakeji abanko kofar sai a fuskar Appa bakaramar azaba yaji ba tuni bakinsa da goshinsa suka samu rabonsu kafin ya farfado yaji an angajeshi ana neman wucewa afusace ya dago dan yaga wanene wannan mekarfin halin fasamai baki.
Ameer yayi to zali dashi yana tsaye yana tangadi kaida Gani yasha ya maku kannan yasha aski Irin na manyan kwari gawata Uwar sarka awuya Wandon jikinsa ko guiwa bekaiba sai singlet ajikin tamkar gumaka haka suka kame cikin al ajabi.Cikin muryar maye yake magana ah Papa ya naga kawani tsamure kugu kamar an daurawa biri igiya fashewa yayi da dariya gaskiya dagus kana karbar kida.
Umma ya kalla aah momcy nayi missing din masifarki bakinta yakalla dariya yakamayi ashema kin tsufa dana sani natsaya nayanko likkafani a hanyar lagos dan har partyn mutuwarki zan hada aci asha acashe.Umma ce tafashe da kuka tare da dora hannu aka nashiga Uku ni Salamatu Wallahi wannan sharrin makiyane sukaiwa dana asiri koma waye Bazan barshiba sabida tsabar bakin ciki anga dana Allah zai dau kakashi yatafi neman Kudi za amaida munshi haka.
Hannunsa tariko ya fizge haba haba momcy yazaki shafamin dauda kebakiga jikinki ba hannunki tana tsami bakya wanka gyarani nawuce taga taga ya taho zaibi ta kanta saurin matsawa tai tabashi hanya baki bude suka bishi da kallo.Tuni bakin Appa ya haye him rufamai baya sukai a kofar dakin Mama yaja birki buga mata kofa ya farayi tasowa tai ta bude saida kirjinta ya bada ras saidata karemai kallo tukunna ta ganeshi kokarin kutsa kai yake ciki dakin cikin sauri tatare hanya ina zakaje haka Ameer.
Haba ya kike yawane kamar baki ganeni ba kyakykwata nazo nagani fa dan kullum sai nayi tunaninta dan nasan dagus yananan yana dukanta zan duba ta Duk Wani tabu dana Gani naranshe da sarkin dake busan numfashi da wukata zan kashi na tsatstsaga mai jikinsa shima wata sharbebebiyar wuka yadauko akugunsa tuni Mama ta hadiyi Wani yawu dakyar Umma kuwa ai da gudu taruga daki tana haki.
Karkiji zancan wasa wllh sainayi masa bille naimasa balli balli,ai Tun da katafi babu Wani abu daya samu kanwarka tana nan kalau kin tabbata danni na tsani aimun karya na tabbata cije baki yayi ya jijjiga kai dakinsu yaje ya fada akan katifarsa ya fara bacci.Binsa da kallo Mama tai cike da tausayawa tanai masa fatan shiriya daki takoma dan tuni suma sunyi ta kansu Appa yana can tana jinyar kansa dan tuni zazzabi ya rufeshi dole yatashi ya balli panadol ya kwanta yana rawar sanyi.
🤣🤣Niko Nace kadamma kafara Gani yafara baka tukuici tun yanzu.
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 28
Hisnul Muslim ne a hannunta ta dade tana azkhar sai data kammala addu,o,inta ta shafa sosai tayiwa danta Addu,ar Allah ya kare matashi Aduk Inda yake.Wayar dake Kusa da Itace tadauki kara ok Allah ya kawoki lafiya abinda tace kenan gallary tashiga pics din sune gaba dayansu kurawa hotunan idanu tai cikin tsananin kewar dan nata da muradin ganinsa sosai tati nisa akan kallon hutunan hartai Sallama tashiga ta zauna kusa da ita batare data saniba Ammi girgizata tai tare da kiran sunanta da sauri ta juyo fuskarta cike da damuwa.
Yanzu Ammi tunanin ne har yanzu kin kasa dainawa Numfashi ta sauke ya zanyi Safa taya zaai nadaina tunanin yayanki kina tunanin abu mai sauki ne Uwa ta Iya mantawa da danta bazan iyaba tinaninsa nake dare da rana kullum addu,a bake binsa da ita ban kuma yi fushi dashi ba nayi masa uzuri bayin kansa bane.
Cike da tsanar Fareeda a zuciyar Safa tai kwafa Wallahi Ammi ni dama tunda naga wannan me kugun kamar Akuya tamike tsaye naji batai minba kwata kwata amma Yaya ya nace sai ita wagari ya waya yanzu tara bashi da kowa ita kadai yake Gani a idanunsa zamuci gaba da Addu,a Ammi bazamu taba gajiyawa ba.Amma ga shawara Ammi mezai hana bazaki kara masa Aure ba ko batare daya sani bane.
Girgiza kanta kawai tayi yarwa kike tunanin zanje nadauko batare da sunsan Mijin da yarsu zata Aura ba banaso nasa yar kowa acikin matsala dan akan waccan matar tashi zai Iya nakasa yar mutane ko Auranne ba yanzu sai naga hankalinsa ya fara dawowa jikinsa tukunna shikenan Amma.
Ina Noor din nabarta agida Ammi kannansa ne suka zo saina bar musu ita au bakima kikai shine kika fito kika barsu aah Ammi aiba baki bane yan gidane ai shekenan Hirarsu sukaci gaba dayi tsakanin 'Ya da Uwa.
"Kwas kwas karar takalmanta yacika falon da sauri Harira takara sun kuyar da kanta dan yanzu zata Iya cewa tayi laifi ta kura mata idanu,wasu shegun kayane ajikinta wando pencil sai riga ko cibiyarta bata rufeba kannan yasha atach ga farce da aka samata zako zako kamar ba yar Musulmaiba barka da saukowa Hajiya ko kallanta batai ba kai tsaye dining table tanufa da sauri Samira dake tsaye awajan ta jamata kujera ta zauna bubbude Abuncin tayi tazabi wanda take so ayatsine take kallon abincin babu wanda Yayi mata aciki tea kawai tace fara hada mata tai tana cikin hadawa tadan dunguri Cup din yafara zubewa akan table din tass kake ji ta wanka mata mari ke wace irin mahaukaciya ce zaki konani in ban dake dakikiya ce taya bazaki dinga lura da aikinki ba.
Cikin kunar Zuciya Samira take bata hakuri saidata zageta tas tukunna tabar dining din kai tsaye waje tanufa da wannan kayan ajikinta dasu da babu duk daya.
Share hawayanta tayi sosai takejin tsanar Fareeda acikin zuciyarta saboda batasan mutuncin dan adam ba bata dauki talaka abakin komai ba tana rokon Allah daya kawowa Ogansu sauyi da mace tagari shidai nagarine amma Allah ya jarafceshi da matar da batasan mutuncin kanta ba balle tasan nawani.
Dafa kafadarta Harira tayi kiyi hakuri Samira wataran sai labari Murmushi kawai tayi bakomai komai lokacine tayi yayinta ta gama Allah zai tonamata asiri koma metake aikatawa,hakane Allah ya shirya mana Zuri,a Ameen.
Tunda tafito yaransa suka sunkuyar da kansu direba malam Idi kuwa kwashe mata Albarka yake a Zuciyarsa betaba ganin ballagaza Irin wannan matar ba aiko Wata arniyar bazatai Irin wannan shigar tafita ba balle ita yar Musulmai sai taunar cimgom take kas kas kamar tinkiya.
Idi Yazo shiga mota ta dagamai hannu alamar bata bukata motar tashiga taiwa key aguje ta debeta shikansa megadi saura kadan ta kwashemai kafafu Allah ya taimakesa yayi tsalle ya koma gefe.hhhh dayake ba yajin hausa sosai fafi wooo na wawoo wannan sinannan yaro ne ala sinema Albarka zayayi shut shut dani me sauran zasi banda dariya.
..........✍️✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 29
Mom mom take kwalla kiran mahaifiyarta Mom ce tafito daga Wani daki taci uban sauri ture kaga tsaya fuskarnan tasha bilicin kaida ganinta kasan tsohuwar yar duniya ce Hajiya luba kenan Mahaifiya ga Fareeda zuwatai ta rungumeta tana bubbuga kafa haba Mom kinaji Inata kwallamiki kira Amma kika shareni.Haba shalele yaya zanji kinzo Nakasa futowa diyar Alkhairi aini haihuwarki tayimin rana fari tayi da ido Allah ko Mom sosaima kedai zomu zauna.
To yanzu ya akeciki shida waccan matsiya ciyar Uwar tasa ina fatan aiki yananan yana cigaba sudin banza aituni ya manta da shafinsu amma saidai matsala daya yafara yimin musu da gardama inna fadi abinda zaai shikuma saiya fadi raayinsa kuma sharuddan boka yace banda sa insa aikin zai iya warwarewa gaskiya Mom asake sabon aiki karkiji komai konawa zan kashe ainasan banyi asaraba tunda zan ninka gomansu kinji yar gari shiyasa kike birgeni Mom shewa suka sa suka tafa daga nan cigaba sukai da kulle kullensu yadda zasu kwace kaf dukiyar AA Inda dama su shiga har dukiyar Ammi Itama tazama tasu(ooh anya zaku Iya kuwa mujedai zuwa)
Dagana wajan KB tanufa tundaga nesa suka hangota daya daga cikin abokan sane ya tabosa ya kai baba gafa yar walarcan tafe mekama da tsohuwar Inya mura fashewa sukai da dariya kakyale matsiyaciya tana tatsowa muna karbewa Akwai time kudai kuzaba ido guys tafawa suka sakeyi.
Tana daga cikin motar ta daga Musu hannu KB ne yatashi yana Wata Irin shegiyar tafiya sit din gaba yazauna beb kinafa kasheni da wanka kin bala,in haduwa cikin jindadi take fadin shiyasa nake tafiya dakai saboda kana cikin masoyana sosai ma kuwa toya ake ciki kinsandai harkar nan ta kudice akwai Wani sabon malami aikinsa kamar yankan wukane ana bukar Kudi akalla dubu dari biyar bkm Indai aiki mekyaune Kudi ba matsala bane Jakarta ta zuge tafito da rafar Kudi guda biyar ta doramai acinya jiyai kamar ya taka rawa acikin motar amma ya kanne tsuke fuska yayi tomene kuma ladan aikina ban ganiba kaidai wllh mayan kudine kafiye san Kudi duk san kudina ban kama kafarkiba inkin manta bari na tuna miki.
Bata rai tayi bana hukatar ji KB wai Meyasa kakeson kadinga yimin hakane alabaki hakuri kudi taciro ajaka rafa biyu ga ladan aikinka nan dauka yayi yafice daga motar ko banza yafigi rabonsa kafin AA ya sakota Murmushin Mugunta ya saki.
Ba ita ta dawo gidaba sai bayan magariba ba Sallah ba komai tafada kan gado tahau sharar bcci sai kusan 9 tafarka duba maajiyarta tayi Inda take ajiye magungunanta magani daya ta balla tasha kona meye oho tasake maida kai ta kwanta.
A Meduguri kuwa Sallar isha,i ya idar sosai kansa yake azababban ciwo kirjinsa na matukar bugawa lumshe idanunsa Yayi da yakemai wani irin ciwo dan danan zazzabi me zafin gaske ya lullubeshi dakyar yaja jiki yahau bed babu babu magani a Kusa balle yasha shikansa gadon da yahau har Jijjiga yakeyi bakinsa yarufe bam addu,ar ma ya kasa.
"A hankali yaji zafin jikin na raguwa kannasa na rage zafin da yakeji ya dauka kirjinsane yai wata irin dokawa duk yadda yakejin jikinsa saiya nemi ciwon ya rasa Ammi abunda Zuciyarsa take nana tamai sosai yaushe rabon da yaganta Meyasa meshi meya shiga kansa Ammin tasa Rayuwarsa ce abar kaunarsa ce habibiyarsa ce anya yacika dan halak kuwa daya iya mantawa da ita Wasu zafafan Hawayene suka sulmiyo daga idanunsa"
Kubiyo ni dan jin yadda zata kaya Fareeda zataci nasara kuwa tunkan aje ko ina aiki ya baci
Taku Akoda yaushe
Mrs Baba Bello Abubakar
WA'AT
By Kulsoom Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 30
A daidai wannan lokacin hannayan Ammi sama suke tana mai zubar da hawaye akan Allah ya karkato mata da hankalin danta zuwa gareta yakare mata shi daga dukkan sharri yarabashi da sharrin makiya da mahassada da suke san shiga tsakanin ta da danta.
Shidin katan gartane akoda yaushe tana Alfahari da zaman towa Uwa agaresa tana rokon Ubangiji daya dawo dashi gareta kafin Numfashinka ya fita daga gangar Jikinta tayi shafa Addu,ar tai Tamkar wanda ake jira ta shafa taga phone dinta na kawo haske kamar bazata dubaba wata zuciyar ta Umar ceta data duba.Gudun Zuciyarta ne ya karu kara murza idanunta tayi tabbas My Son shitagani radau akan wayar Kasa takai goshinta tai Sujjada Shukuriyya Tana mai godiya da Allah da tsarkakeshi da sunayan sa guda 99 dayiwa Annabinsa Salati da ahalin gidan ANNABI MUHAMMAD S A W💝💝💝.
Kafin ta dago kiran ya yanke sake kira akai tana dagowa ta dauka tare suka sauke ajiyar zuciya daga can bangaran ya goge hawayan fuskarsa.
I'm really Missing you First Love shiru tai wani sanyi yana ratsa mata zuciya Ammi please Help me.
Tamkar zai sake fashe mata da Kuka haka yai maganar Al Ameen takira sunan sa akaro na farko zai iya Cewa tun da ya girma betabajin sunan abakin Ammi ba lallai ya kureta kiyi hakuri Ammi tuba nake kiyafemin bani da laifi kici gaba dayimin Addu,a dan Allah.
Tausayinsa ne ya tsirga mata azuciya tasani tadade da sanin bayin kannasa bane amma dole ta hukunta shi dole ta nunamai bacin ranta akan abinda ya aikata musu muryarta adake laifin wane laifina nane kenan daban bika gidanka na goyoka ba katabbatar mun da cewar kasamu wadanda suka fini tunda har kazabesu akaina na tabbata nidin ba kowa bace awajanka Abie sosai hankalinsa ya sake tashi zaiyi magana kenan ta yanke kiran daga kar shema kashe wayar tai gaba daya.
Tarasa wane Irin Farin ciki zatayi lallai Allah maji rokon ba wansane daya kwato mata danta daga hannu miyagu su Hajiya luba sosai tasan Wacece ita Baban Fareeda yananan shine ya zama Matar itace Mijin zata dage dayiwa danta Addu,a shima dole ta tir sasashi ya dage da azkhar hakan makamine agareshi.Kwanciya tayi cikin madaukakin farin ciki bacci tayi Irin wanda tadade batayi ba.
Asuba Tagari Ammi
....✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 31
Karfe 7 Ammi ta sauko duk wani kayan da yake fridge taba yan Aiki Umarnin kwashewa su raba atsakaninsu STORE tasa aka bude duk wani kayan Abinci da Yayi wata 6 tace su kwashe sosai suke godiya su kansu ayau sun san Uwar dakinna su tana cikin matukar farin ciki List tasake basu na dukkan abunda zasu siyo a kasuwa kayan girki babu Abinda bata bada List a kawo ba lemuka kalar wanda tasan Abie nasha suta yi waya takanas tundaga campany aka dauko mota aka kawosu ayau dai wata yar kwarkwayar liyafa Ammi ta hada.
Babu yadda Safa batai ba akan tafada mata mene ya sata farin ciki haka With time kawai tace mata kafin 9 gidan sai tashin kamshi yake yasha gyara kyalli ne tako ina.Girki kawai tasa anyi Yayi kala 7 kowa tace yafebi duk abinda yakeso Dining Table daga far konsa har karshan sa tsare yake Manyan Woms masu matukar kyau da tsada komai Yayi fes fes Saura bako ake jiran ya diro kowa agidan yana mamakin wannan wane bakone haka megirma da mukami a wajan Ammi 9:30 Jiniya ta karade Unguwar saida kowa ya shaida lallai magajin gidan ya dawo ayau shida ya ransane akalla kusan mutum 10 wanda suka yomai rakiya sosai suke taya Ogan nasu murna dan su kansu sunga canji duk da yana Cikin fargabar wane irin tarba Ammi zatai masa.
Get Man da Gudu ya wangale makeken get din gidan saida motocin suka gama shiga aka rufe gidan akalla yake mintuna 10 yana tunanin yadda Ammi zata karbeshi anya zata yafe masa Kuwa kwarin guiwa ya bawa kansa ahankali ya zuro kafafunsa waje kafini ya fito gaba dayansa.Wata shadda ce ajikinsa me azabar kyau Maroon wadda ta haske farar fatarsa Kaida gani kasan kudi yayi kuka asiyanta.
Kamshinsane Kawai ya sanar da ita ya tunkaro falon idanunta akan kofar yake tana tsumayan ta ina zai bullo Safnah da Marwanah Suna zaune suma Fuskarsu washe da tsananin Farin ciki tare suka Mike ganin tsayuwarsa abakin kofar Lumshe idanunsa yayi tare da budewa akansu sosai yayi kewarsu hannuwansa ya bude Musu alamun su taho gareshi kamar Jira suke suka kwasa da Gudu suka fada jikinsa suna matukar kaunar Yayansu irin son da bashi da adadi duk da baya sakar musu fuska a hakan suka shaku dashi Idanunsa nakan Ammi data daidaita Fuskarta tsuketa tai tas babu alamun fara,a kamar ba Itace ta gama Farin ciki a dazunba.
Sakinsu yayi tare da ruko hannayansu suka shigo Cikin Falon gaban ya duka Cikin tsananin biyayya da jin kaunarta da san ganin Farin First Love saida taji Wani tsam Yaushe rabon dataji Wannan Muryar kafafunta ya rike Cikin Muryar tausayi yake fadin Hakika Nasan ni melaifine amma gani abanki Ammi kiyimin dukkan hukuncin da kikaga ya dace dani amma banda yin fushi dani.
Please Ammi cewa Safnah Hakama Marwanah take kallonta alamun ban hakuri bazata iya fushi dashi ba dama tasani hannunsa takamo Kusa da ita ta zaunar dashi dariya sukai gaba dayansu Safnah ce take fadin nidama Ammi nasan Alwashin da kikaci akan Yaya Abie bazaki iyaba Murmushi kawaii tayi tana kallonsa tabbas baacikin dadi yake ba dan yayi rama sosai kamar mesan karanto Wani abu take kallonsa,baka da lafiya Uhm lafiyata kalau Ammi jiyake kamar ya gayamata damuwarsa amma bazai iyaba yana jin nauyinta matuka Kuwa.
Ina Fareeda cewar Ammi gaba daya annurin Fuskarsa daukewa yayi gaba daya shiyama manta da Wata Fareeda fahimtar hakan Yasa takama hannunsa batare datace komai ba suka nifi yin Lunch zama zukai Safnah ce tai serving dinsu shida Ammi a plate daya sukaci abinci Cikin tsananin Farin ciki sukai suka gama Farin Cikin da suka dade basiyi ba.
........,.✍️✍️✍️✍️
WA'AT
By kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Kim Aneesat
Chapter 32
Betafi gidansa ba sai bayan Sallar Isha,i cikin matukar Nishadi yake tafiya sannu ahankali yau shike driving din da kansa betafi da kowa ba Hon yadanna megadi saida yaleko da sauri ya wangale get din Ganin Ogane da kansa yake tuki yau cikin girmama wa suke gaisheshi Fuskarsa dauke da fara,a yake amsawa kai tsaye cikin gidan ya nufa yana shiga yai arba da hakimar azaune afalo ta dora kafa daya kan daya ita kanta tayi mamakin Ganin sa amma saita basar gaba daya jiyayi ransa ya baci ganinta kawaii da yayi sai yanzu yake tambayar kansa wai ya akaima ya kwaso wannan guzumar Inbata girmeshi ba akalla zasiyi saannin Juna ahalin yanzu yana da shekaru 38years gaba daya fuskar tata tafara ya mushewa tashafa man har yabemi yimata illah bakinta ya kalla yadda kasan na dumbaru cikin karai raya tatashi tare da nufoshi yadda kasan silinda haka take ba gaba ba baya.
Tana dososhi yaji Wani mugun karni na tashi daga Jikinta tasamu gashin doki ta jibga aka aiko sai tashi take jiyayi zuciyar sa na hautsinawa cikin sauri ya daga Mata hannu alamun karma ta karaso kallan Juna suke cikin ido sosai Gabanta yake faduwa yaushe rabon da AA ya tsaya yana kallonta ido cikin ido haka tunkafin suyi Aure dan sosai yake tsoron hada ido da ita Wani Irin kwarjini take masa amma ayau babu abunda yake Gani tattare da ita sai tsabar muninta dayake hangowa dajin danasani a Zuciyarsa na yadda ya kwaso wannan abar Tamkar ya makance.
Cikin kakkausar Murya yace bana hanaki sa wannan gashin dokinba ko bakiji yadda kike karni bane kamar rubabban kwai gaba daya daakarewa tayi awajan Itace take karni yau ita AA yake kallo yake gaya mata haka lallai,cikin tsabar jin haushin abunda ya gayamata take fadin yanzu nice nake warin nake karni to matukar ina karni da wari haka gyatumarka daya muke da ita bata kai ga karasawa ba taji saukar Wani zafafan maruka hagu da dama sai dataga taurarin azaba wanwar tafadi akasa kai bama zata tan tance suma tayi ko ido bude take.
Jikinsa har rawa yake Saboda ba cinrai matukar dukanta zeyi to saidai azo adauki gawarta barin wajan Yayi gaba daya Dajin tsanarta acikin a Zuciyarsa Fareeda takai mintuna 30 kafin ta dawo hayya cinta kuncinta ta taba tuni ya kumbura fashewa tayi da kuka meke shirin faruwa da ita yau AA ne ya daga hannu sama ya zabga mata wannan Uban marin da tunda Uwarta ta haifeta baataba yimata shiba dakyar ta rarrafa ta shige dakinta su Samira dake labe akofar dakinsu suka sheke da dariya ransu fes shegiya me fuskar gwaggon biri kadamma kika Gani In sha Allah nan gaba da belt zai zaneki zannira ce ta bigeta abaya Wallahi kedai Akwai ki da mugunta kina Ganin babbar yarinya tabaje akasa mari biyu kacal gsky Oga ya bala,in birgeni yau cewar Zannira ya birgeki ko ya birgeni wllh so nake ayowa wancan tunkiyar kishiya naga yadda zatayi dariya sukasa gaskiya zamuga drama.
Daki suka shige ransu fes kamar takarda.Ko da Yashiga dakin bebari bacin ranta ya hanashi sukuni ba danya lura sotake tamaidashi mahaukaci Laptop dinsa ya kunna yafara rage ayyukan da suke gabansa sai kisan karfe 12 yagama saida yayi azkhar kamar yadda Ammi ta Jadda da masa yagama addu,o,in da zaiyi ya kwanta.Hhhh Fareeda dai kwanan bakin ciki tayi kafin Safiya fuska ta haye kamar fanke ko idanunta da kyar take budewa kin saukowa tayi sai kusan azahar tana saukowa afalon Dasu Zannira taci karo kunshe baki sukayi dan dariya ce take matukar cinsu Tamkar wanda ta cusa bread abakinta haka kumatunta ya koma sai bakin ya kara tsini kai babu wanda zai ganta be dara ba.Barka da fitowa hajiya cewar Samira ko Kallon su batayi ba tasamu gu ta zauna tana jiransa ya fito dan Wallahi saiya san ya mareta bazata taba yadda ba ita ba abun kunya ne awajanta ba tafita harwaje suyi kokawa.
Hmmm Lallai Fareeda kin hada kanki da wahala marin da kika shane begama shigar kiba🤣🤣🤣🤣.
Mrs Baba Bello Abubakar
.........✍️✍️✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 42
Gigar gigar kake ji ana wasa wuka Tamkar a mahauta haka tsakar gidan ya dauki wannan sautin cikin muryar maye yake fadin Kabiru Salame Wllhi saina yankaku dole wukata yau tasha jiniku tundaku bakwajin magana sena yankaku yau naba kar nuka su cinye ku luf kake ji babu wanda Yayi tari Suna daki sunyi cirko cirko gaba daya cikinsu ya gama durar Ruwa ai Umma tayi fitsari yafi a kirga amma gaba daya batasan tanayi ba kuka take shabe shabe harda majina su Hajarako Suna kuryar gado sun sami wajan buya dan Umma ba yadda batayi ba su matsamata itama tashiga fir sukaki matsawa acewar Hajara Wallahi keda kika haifeshi kekadai bala,in zai shafa.
Dole ta hakura ammafa gaba daya jikinta rawa yakeyi bangaran Appa ya a dakinsa shima gaba daya hankalinsa atashe yake gani yake kamar zai iya balle kofar ya shigo ya kasheshi gaba daya yarasa tunanin ma da Zaiyi lallai ya yadda da zancan Salame cewar makiyane sukai masa Sihiri ya koma haka ya tabbata dansa ba haka take ba koma wanene zai ganoshi.A can Dakin mama gaba daya sun mamuketa sboda Tsananin razana danko da baa ambato sunan suba sun tabbata suma bayan yagama yanka su tofa kansu zai dawo WA'AT datafi Kowa tsoro tuni har zazzabi ya rufeta sai rawar sanyi takeyi.
Kofar Dakin Umma ya Nufa da Wukarsa ahannu sai sheki take ga shegen kaifi bum bum ya fara buga kofar Dakin bata kibude tunda wuri kafin na shigo nai miki yankan rago saina fede ki zanba karnuka na su cinye ki jikake fatata fat bur bubur bur Umma nasakin zawo atsaye tare da sake fashewa da Kuka kai Yau itadai taga bala,i Ameer ya zame mata masifa yanzu Ita yake yunkurin kashewa tana matsayin Mahaifiyarsa kara dukan kofar da yayi yasata zabura dagudu tanufi sif dinta da babu gyara tacika da tsummo karai kayan wanke da wankakku Duk awaje daya agwamutse
Kayan ciki tadunga watsowa waje tasamu tashige tare da turo kofa to nanfa ake yinta gaba daya zafi ya hanata sukuni babu Iska ko kadan dan kanta ta bude data farajin kamshin mutuwa sai gab da asuba suka dainajin bugun kofar sa.
Ashe bacci ne ya kwashe shi awannan rana babu wanda yayi Sallar asuba suna makale adaki karfe 6 Mama tai shahadar bude koda ahankali akofar dakin Umma ta hangoshi yana ta sharar bacci kamar matacce ajiyar Zuciya ta sauke ahankali tafito butiki tadauka daya da ruwa daya ba ruwa sai buta data diba sadaf sadaf ta koma ajiyar Zuciya Tayi bayan ta Tabbatar tamaida sakatar dakinta suma su Nusaiba sai lokacin hankalinsu ya kwanta dan suna tsaye abakin kofa ita da Hafsa sunai mata gadi WA'AT kuwa tana kudun dune agado tashimma ta kasayi idanu yayi jajir Saboda tsabar Kuka tuni harta hango Jamaa na zaman makokinsu Ita da yan Uwanta da Mama.
Alwala suka daura sukai sallah sai lokacin Nutsuwa tazo musu Karatun Alkur,ani sukayi duk Wani tsoro da sukeji sai sukaji Allah ya kawo musu saukinsa.Su Umma kuwa aibama me tunanin Sallah acikin su shi kansa Appa adaki yayi alwala yayi sallah har kusan karfe goma babu wanda ya futo gaciki yanata kugin Yunwa su Mama babu abunda ya damesu dama sun saba da Yunwa shiyasa basuji Komai ba su Zubaida kuwa anacan anrike cike ana kukan Yunwa ga dakin ya dume da warin zawayin da Umma ta barka da daddare Ita kanta Jikinta ya dameta amma bayadda zatayi tanason Rayuwar ta daga karshe Appa ne yayi ta maza ya bude kofar sa ya futo kamar Jira yake yafuto Ameer ya farka daga bacci da yake jikake zuuuuu cikin Appa ya bada wata kara kamar ya juya dakin da Gudu haka yaji amma ba dama.
Tashi yai yana kade ajikinsa kai wane dan Abu takazanne ya kawoni kasa ina kan katifata akwance ya kawoni tsakar gida Saboda ni bolane kowa na daki ni ambarni na kwana awaje banza Appa yayi masa dan bashi da abun fade nan ya gama tajararsa ya fada daki buta ya dauko kamar bashiba yayi alwala yatada Sallah.Sai alokacin su Umma suka bude kofa da gudu kuwa suka fito Zainab bakin rariya tawuce Saboda yadda zuciyarta ke hautsinwa Wani surum kakeji har tsakar gidan dumamewa yayi Appa ne yayi saurin toshe hanci kai wane mushenne ya mutu adakinku dariya ce takamasu Appa mushe to Umma ce tai kashin wando sakare yayi atsaye yana nanata maganar acikin Zuciyarsa.
.........🤣🤣🤣✍️✍️✍️✍️
WA'AT
By kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 34.
Tana futowa yuuuu kudaje suka bita abaya gawani Uban wari dayake tashi gaba daya tsakar gidan ya turnuke da wari idanu sun kumbura tsabar Kuka ko kallan Dakin Ameer batai ba ta fada bayan gida saida tai wanka tukunna tafara jin Iska tana shigarta tana fitowa Zainab ta fashe da dariya kai Maza maza anga maza wuya ba dadi haihuwa merana Allah y kara maimaita muku dan bansani wllh wata harara ta banka mata tarasa Zainab wace irin Yarinya ce dabata kishinta kokadan har jira take Wani bala,i ya afka mata tasata agaba taitayi mata dariya kwafa tayi ta wuce daki afusace.
Babu wanda ya gyara mata Dakin Itace ta gyara abunta cikin sif din Yayi dama dama da zawon da tayi dolenta ta kada kumfa tawanke cikin sif din tafito da kayan da suka baci saiga Dakin ya dawo hayya cinsa dan rashin imani irin nasu babu wadda ta tayata itakadai tagama jibagar aikinnan ga yunwa na sasakarta tanayi tana kallon dakin Ameer dan karya fito ya ganta awaje ya samu damar yankata.
Appa kuwa tuni ya kama gabansa yacikawa bujansa Iska saida yaje kasauwa hankalinsa ya kwanta anan yasamu ya karya yana tunanin sama sa hannu akai dansa ya lalace dan wannan dagaji jinnune ajikinsa dole ne ayimasa rukiyya sufita.Yana tashi daga kasuwa gurin Malm ya nufa fuskarsa cike da damuwa bayan sungaisa yake yiwa malam bayani jinnu sun shiga jikin Ameer ashsha Subahannallahi garinya haka tafaru ina Ameer din aiyana gida Malam yananan ba yadda yake dan jiya wuka ya dauka cikin dare saiya yankamu.
Komawa malam yayi ya zauna danjin zancen kuma yafita daga namasu hankali bangane ya dauki wuka zai yanka kuba eh malam kamar yadda kaji na fada nan ya zayyanawa malam komai shiru malam yayi sannan ya saki murmushi irin nasu na manya.Hmmm ya sauke ajiyar zuciya dadina da gobe saurin Zuwa ai wannan bakomai bane bayan jiran dakayi shekarun baya kuma gashi yanzu Allah ya amsama Addu,arka kasamu magaji nibanga abun duwa ba akan Duk Abinda zai janyoma zaka Iya shanyewa karka manta da namijine fa abun so da kauna abun Alfahari.
Shiru yayi dan yarasa ina maganganun malam suka nufa kamar dai gugar zana yake mai,babu Wasu aljanu da suka kamashi face kune manyan aljanu kaida Mahaifiyarsa da tun yana yaro baku Iya tankwarashi ba mudai namu miyi Addu,ar fatan shiriya Allah y shiryeshi.Tsuru Appa yayi yana tattauna maganar malam nan ya tashi ya barshi jiki bakwari yadade azaune shiru daga karshe yatashi ya tafi danko gidanma nayajin zai Iya shiga saboda yadda gaba daya guiwarsa ta sage.
Uwaliya ce ta rafka sallama fatakal fatakal dawani sidaddan ailifas dinta wai ina mutan gidanne gida kamar wanda akai mutuwa kowa ya shige daka yayi shiru Mama ce ta futo da fara'arta sannu da Zuwa baba tabe baki tayi yawwa kilibabba yau kuma baba nakoma Hajiyar ce bazaki Iya cemin ba kona haifeki dazaki cemin wata baba in bazakicemin hajiya ba to kiyi shiru da bakinki.Umar ne ya leko daga daki Hajiyar mahaukata ba gaba daya dariya ce takama Mama amma ta gimtse yanzu ke Uwaliya saboda Allah inkina da kunyama kyace ace miki hajiya nifa inada yakinin ko saudiyya kikaje bazakiga Ka,ababa dora hannu tai aka ta rafsa uban ihu wayyo ni Uwaliya naga takaina.
Salamatu Salamatu fito fito Wllh ammana farraku da yaranann harni zai dinga jifa da wannan miyagun kalmomin marasa da dinji.
Wai Uwaliya meyafaru gaba daya kincika tsakar gidannan da hayaniya kibarni Salame taya wannan Yaron zemin dibar Albarka akan wannan kudaddiyar kishiyar taki Kallo Mama tai datake tsaye take Kallon ikon Allah abun arziki ya zama tsiya.
..........✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 35
Banka mata hara tayi aikadan kika Gani Uwaliya Indai akan wancan Munafukarce mefarar kafa babu Abinda bazai gaya miki ba bankado labulan dakinsa yayi tare da fitowa yana jin tsaki waini wace yar wahalar ce tazo take haya gaga tatasheni daga bacci tsit kake ji babu wanda ya tanka nice yar walahar yanzu ni kukewa wannan Wulakancin au waidama Uwaliya kece nayi zatan wata Mahaukaciya ce ta bayan layi dayara ke binta saina ganku sak Idanu Uwaliya ta ware Kaima kace min Mahaukaciya share hawaye tayi takalli Umma yanzu kina ji Suna zagina bazaki dauki mata kiba kiyi hakuri kawai Uwaliya ki kyalesu.
To Wallahi Bazan hakura ba dolene na hukuntasu Tunda jikokinane bana Wani ba nizaki hukunta bari kiga Wani katako yadauko yabiyota dashi saigashi ana yar tsere kafin tafada daki tuni su Umma sun sako sakata haka Mama tayi ta kanta hanyar soro tanufa da Gudu gudunda tuntana Yarinya rabon da tayisa gam sukai karo da Appa ingijeshi tayi tafice da mugun Gudu cikin rufewar ido ya daddage ya ranfawa Appa azatansa Uwaliya ce Jikake kararas kashin hannunsa ya Amsa ihun azaba ya saki sai asannan Ameer ya lura ba Uwaliya bace.
Haba dagus wai taya ina Operation zaka biyo takan hanyata aiga irinta nan hukuncina ya sauka akanka koda yake bakomai Ai Uwar matarka Uwar kace kafansheta bansha wahalar Banzaba tsallakesa yayi yai ficewarsa ko waiwayansa beba.Umar da yake cikin daki jin kamar karar mutum ya fito ya dauka Uwaliyar ya bazar yana zuwa yaga Appa yashe akasa jiyake kamar hannun ba ajikinsa yake ba tsananin radadin azaba yake masa, Appa lafiya kowa kokai yasamu aiba babakin magana gaba daya bakinsa ya kulle kamashi yayi yakaishi tsakar gida ya zaunar dashi futa yayi ba dadewa megayara ya shigo ihun Appa ne yasasu bude kofa sai alokacin sukasan meyake faruwa.
Kuka yake harda hawaye dan a wancan hannun da Uwaliya suka taba targadashi ahannun kashin ya kara gocewa kowa yayi cirko cirko dan jin baasin Abinda ya faru saidai aka gama gyara tukunna Umar yabasu Labarina yadda ya faru tsaki Umma tayi Tunda akan Ubansa abun ya kare bakan Uwata ba aishikenan suje can sukarata.
Sudai su Mama sannu sukai masa amma ko kallonsu beba shifa Duk wannan wahalar daya fara karba haryanzu beji yanasan yaya mata ba tunaninsa yafi karkata asiri akaiwa yaran nasa Maza saboda anga sun taso zasu taimaka masa su Mama daki sukai komawarsu tare da dakko tabarma subaza atsakar gida suka zauna Suna harkar gabansu su Hajara kuwa ai babu wadda tayi masa sannu sai kallo da suke binsa dashi Suna dariya kasa kasa.
Yana ankare dasu Amma ya nuna kamar begansu ba shiyanzu tunanin yadda zaai karya sihiri yakeyi.
Hhhhh har yan zufa jikin Appa beyi sanyi ba bekuma sauka daga kan kudurinsa ba.
Muje Zuwa Fans yawan comment dinku yawan Jin dadin Labarin dakuke karantawa.
Taku Mrs BABA BELLO ABUBAKAR ........✍️✍️✍️
WA'AT
By kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 36
A kalla Appa yayi sati biyu beje ko ina ba sai azabar fada dasuke suke sha babu damar suyi Wani motsi zai fara fada sun takura masa yaya mata matsalane dama zai ta fadan bakaken magan ganu sai Umma tafito tana masifar yaji da abinda ya dameshi in zeji to asannan nefa zaiyi shiri wanda Yayi masa aika aikar ko Sannu bece masa ba washe gari yayi ware warsa Lagos shine fa hankalin jama,ar gidan ya kwanta basu da fargabar komai matsalarsu ya tafi hatta Umma saida tayi Sam barka da tafiyarsa Uwaliya kuwa cewatai har abada Ita dashi matsawar taji yazo gari babu ita babu zuwa Inda yake.
Yan Unguwa da sukasan abunda ya faru dan gulma tururuwar zuwa yimasa Sannu sukeyi tare da yiwa Umma jaje ALLAH ya kiyaye gaba dan Cikin daren nan babu wanda beji wasa wukar Ameer ba kowa bakinsa kunshe da dariya yake futa abunfa yana yiwa Umma zafi dan tagane ba domin ALLAH suke zuwa yin Sannu da jikinba akwai wata akasa saita dauki gaba da Mama acewarta tasan babu wanda zaije yafada sai ita.
Mama bata kulata ba dan Ita yanzu wallahi bata da Lokacin Umma abunda yake gabanta ma ya dameta.Yan zuwa dubiya har Dasu malam da Inna tare suka zo da Inna Lami kishiyar Inna kallonsa suke kamar wanda Yayi shekara yana ciwo duk ya Wani rarrame sai idanu awaje shikadai yasan wahalar da yake sha dan har kafafuwansa ma sun bugu Shiyasa baya futa ko ina.
Sannu da jiki ALLAH ya kara afuwa cewar malam Inna tabe baki tayi tana kallonsa gaskiya sai yanzu na yadda da maganarka Kabiru dole wannan Aikin Aljanune dole atashi tsaye cewar Malam Washe baki Appa yayi ashe kaima ka gano hakan Malam Shiyasa Naje rannan dan ayiwa tufkar hanci aida ban yadda ba sai yanzu na yadda dana gani da idona sarai Inna tagane Abunda malam yake nufi uhm kawai tace nan sukaci gaba da hira duk akan yadda zaai akarya sihirin Jikin su Ameer.
Da Sallama suka shigo gidan ganin su Malam yasa da fara'arsu suka karasa tundaga nesa suka hango yadda Appa ke dalla musu harara yi sukai kamar basu gani ba har kasa suka Duka Suna gaishe su amsawa sukai cikin sakin fuska sosai suke kaunar yaran saboda Tarbiyyarsu,duk abunda yake Inna da Malam na lura dashi lallai mehali baya fasa halinsa haryanzu beyi laushiba Allah ya nuna musu Lokacin da zaigane babban kuskuran daya tafka a Rayuwarsa tashi sukai dama su WA'AT suka Jiran ganin da wowarsu gashi kuma sundawo babu kuma Wani sauran abunda zasiyi agidan.
Har Soro mama tarakasu tana sugai da gida cikin mutuntawa suka rabu Umma kuwa na daga daki tace sugaida gida.
WA'AT
By Kulsoom Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 37
Haka Rayuwar taita garawa ranar da WA'AT tagano Kamal yaci amanarta ya koma wajan yayarta sosai tayi kuka dan yafara shiga ranta su Umma kuwa rai fes kusan kullum zaisa Hajara agaban Mota tadawo da leda niki niki su shege daki suna murna ansamu banza aiko akasake rikeshi gam shiko sai barin kudi yakeyi musu duk fa abunnan harda Appa akecin duk abinda aka Kawo duk da bakomai ake bashiba amma shima yana dan lasawa balaifi shiyasa baya wata magana akan daukarta da yake da sunan antafi shopping.
Malam Sadam malaminsu na Islamiyya shine ya fito yanasan WA'AT duk bemata ba amma bata musa ba takarbeshi hannu bibbiyu magana ta fara nisa dan harya fara zancan turo iyayansa ko Appa ne yazo wucewa har kasa yake dukawa ya gaidashi amma da kyar yake amsawa fuska adaure tunda baya mikowa nera biyar bata taba hadasu ba shine abinda yake batawa Appa rai dan acewarsa yacika mammako tunda Kamal Matukar zasu gaisa saiya dunkulo ya bashi amma wannan kuwa tsit kake ji babu bayani.
Nanma saida Umma tashiga tafita ta hana wannan Aure gaba daya Malam Sadam ya dena zuwa bata Wani damu ba dama ba sonsa take ba dan acewar Umma bata isa tayi Aure yarta na gida ba.Kamal ya turo iyayansa ankawo kudin Aure Naira dubu Dari su Umma sai fankama ake ana hura hanci ankawo kudin shalele yar gaban goshinta.Ana haka tabawa Appa shawarar mezai hana ahada WA'AT da kaninta Wani rikakken dan shaye shayene tsabar mugunta take kokarin hadasu Aure dan bakin hali irin nata da yake shima Appan yagaji da ganin su dan acewarsa duk sanda ya kallesu ransa baci yake sun jibgemai agida Alhalin ko WA'AT 18years take bakunya ya shiga dakin Mama yake fada mata yayi wa yarta miji.
Ko kala bata cemasa ba saida taji karshan zan can tace wannan ne be isaba Kaima bakaji abinda kace ba 'Yata toni nake da hakkin zaba mata miji ba kaiba daga hannu yayi zai wanka mata mari rike hannun tayi zan lamunci Komai amma banda duka wannan ne bazan taba yadda dashi ba kuma maganar Yata dakace kaje kagayawa wadda ta aikoka wannan karan bata isa ba kai irin zuri,ar suma yata Bazata aura ba balle dan gidansu kaninta wanda Uwa daya ta haifeso yarfar da hannun tayi tabar Appa da baki asake dama Aisha haka take be saniba sosai yaji wata shakkarta ta kamashi dan Duk abinda yake mata bata taba ramawa ba sai Ayau din nan ya fita yana kumfar baki.
Sosai rigima ta barke akan lallai sai an Auri kaninta tunda shiya Gani yace yana so rigima har gaban malam har gida inna tazo tayi musu wankin babban bargo dagashi har Umma aiko Umma akasa kuka wai dama ta lura Inna bata kaunarta tunda aka Auro ta take nuna ban banci yanzu gashi tana sonsu da Alkhairi amma tace basa so.Rike alkhairin ki Matukar daga gareki ne Aisha bata bukata ai Akwai yaya adanginku awanke daya abashi.
Juyowa kan Appa tayi Kabiru yace Naam sau Uku tana kiran sunan sa yana Amsawa mene tsakaninka da yayan Aisha shiru yayi ba magana nake maka ba Yayanta ne Alhmdlh dama abinda nakeson ji kenan to baka da hurumi acikin lamarinsu Matukar ka kara shiga abinda be shafeka ba Zanyi Mummunan saba ma Kasan bani da kyau kuma kasan halina bakai basu yara ne taji tayadda natane to naka Ido bana son kasake shiga abinda babu ruwanka.
Kema kuma nagaya miki Nayi mata iyaka da kaninki babu abinda suka hada Aure ne babushi atsakaninsu har abusa kaho ban yadda Wani Jinana ya debo danginki ba kema dakika shigo zuri,ata kin Isa Allah ya bada lada basai ankara yawa ba ina fatan kin gane cikin konar zuciya Umma ta amsa da to dan tana shakkar Inna akwai Lokacin da tazo gidan zatai mata Rashin kunya kannan Appa sukai mata shegen duka tundaga sannan takama bakinta da yimata Rashin kunya ta shiga hankalinta.
Ranar dai Umma Kwanan bakin ciki tayi danta shirya yadda Zata wulakantan rayuwar Wa'at gashi wannan tsohuwar ta rusa Komai sosai takejin tsanar Inna azuciyarta dan Wallahi tana shigar mata hanci da kudun dune amma zatayi maganinta itacefa Jinin Uwaliya kwafa tayi ta gyara kwanciyarta.
..........✍️✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 38
Tun daga wannan Lokacin babu wanda yasake tada zan can kanin Umma dan Malam ma saida yayiwa Appa fata fata akan ba ruwansa da shiga harkar su ya rike yaya maza suma surike Yaya mata ko kunya babu haka haka yayiwa Malam godiya dan jiyayi anrabashi da alakakai tunda Malam yace yadau nauyin Komai nasu kama daga kudin magani Abinci suttura duka zaina musu Zuciyarsa wasai yaci gaba da harkar sa.
Bikin Hajara nata kara karatowa dama wata biyu aka saka su Umma ba zama yau tana nan gobe tana can zaai bikin 'Ya saiko shan gyara takeyi ansiyo mai sai mulkawa akeyi dan dole Appa ya dinga fito da Kudi dan catai Wallahi dole ya fitar da ita kunya Auran yarta guda akasa ganin abun arziki haka yana dacin rai tana Komai yadinga bata kudin da gaske dai yaya mata sun zame masa matsala sai asarar kudinsa yakeyi abanza acewarsa fa amma.Anko kansa kala Uku aka fitar akwari guda Kamal ya dinkawa Umma wai tayi fitar biki aiko Umma ranar Kamar ta zuba ruwa akasa tasha tsakar gida tafuto tana rafka guda haihuwa merana ta iya haihuwa ta godewa ÀLLAH da yarta tayi farin jini tayi goshi habaici dai ranar su Mama sun shashi.
Yi sukai kamar basu jitaba dan ita Kaya yadama su baya gabansu.Yau take Laraba kuma yau zaa kawo Lefan Hajara ansha soye soye Kaji kuwa Umma har gida taje takamo kajin Uwaliya da take kiwa tawa aiko tasha tsinuwa Wajan Uwaliya tazo zata karyata tadebe mata Kaji bako sisi mirsisi Umma taki ajiye Kaji kuma bata bada ko kwandalaba haka ta debo Kaji tayo gaba dasu sai data zo gida aka yankasu sukasha suya.
Tun safe aka tashi aka share gida kal abinda basayi kenan shara sai dai bayinsu suyi amma dayake abun nasune da wuri aka share gidan saiga yan uwanta anata tururuwar zuwa Umma kuwa sai hura hanci take yarta zata Auri mekudi Mijin nunawa sa,a 'Yarta ta tako arziki makwadaita sai fadanci akeyi mata.Karfe 4:00pm suka karaso akwatuna aka fara shigowa dasu akwatina 8 ne sai dasu buhun shinka gero da dai sauransu.
Tun daga soro suke ya mutsa fuska ganin gidan matsiyatan dayaje ya kwaso yar talakawa sunyi zatan zasuga Get na Alfarma daza abude musu sushige da Motocinsu sai Gashi sun bige da ajiyewa awaje dan wasu aciki har sunfara kananun maganganu dama Suna da labarin yar talakawa ce amma basu zata tsiyar takai hakaba Wani kallan hadarin Kaji sukewa Jama,ar tsakar gidan da aka shimfida wata katuwar tabarma suko da kwadayi ya rufewa ido bama su lura da kallon da ake musu ba sai washe baki suke sunai musu sannu da Zuwa.
Kannan Appa dake gefe ne Kawai suka lura gyara zama sukai Suna kallon Ikon ALLAH Anty Asmi ce ta tabo Anty Safiya kina Kallon abinda nake gani kuwa Uhm tokema inba makahoba wane bazai fuskanta ba sai shawaragi hmm to ALLAH ya kyauta sun dauko Wadanda suka fisu rashin Mutunci danke daga kallon Idanuwa wadannan Matan kinsan ba mutunci dariya sukai suka tafa ayidai mugani.
Da kyar suka zauna atabar mar kamar sun hau kan kashi sai yamutsa fuska suke kojira abude kayan basiyi ba suka mike aah yazaku tashi baku gabatar da kaya ba cewar kanwar Uwaliya kaya tunda sun shigo gidanku aiba sai ance muku gasu ba ruwan kune kubuda ruwan kune kubarsu kuki budawa daya daga cikin masu kawo kaya ta fada kowa tsit yayi ana kallon Kallo dansu dai basu taba ganin kawo kaya irin wannan ba ba bayani ba komai a ajiye muku kaya ajuya.
Watace a cikinsu takara jan tsaki to aini wannan gidan na dade a cikin sama dole naje naga Doctor babu Iska ko ina acin kushe tir tashitai tafita waje Suna sauran mikewa sukai zamu wuce dan kunsan mun bar kayan kudi awaje duk wannan abun kwadayayyun ciki har yanzu basu karaya ba,kayan da aka tana dar musu kanwar Umma ta kinkimo toga shi ko wannan aikwa karba Wani banzan kallo suka bita dashi to aiko ruwan gidannan bazamu Iya shaba balle abinda kuka sarrafa ya fito daga hannunku kubar kayanku zai muku amfani dan naga akwai mabukata da yawa a Wajan tafiyarsu sukayi suka barsu da binsu da kallo.
Umma ce ta tabe baki to ALLAH natuba aimu gaba takaimu dabasu karbaba dama rabon danaci naman kaza ankwana biyu aikuna ganinsu kunsan basi kalar matsiyataba dama ba abinda zasiyi da wannan abun kowa dai shiru yayi Saboda in antashi rabo kar ahanashi inya tofa tashi ammafa akwai masu dariya a Zukatansu dan tabbas sun gano akwai gagarumar Matsala amma gwara su Sawa bakinsu sakata dan Gudun rasa dan abunda zaa yayyaga abasu.Umma ce agaba wajan bude kaya kowace a kwati cike take da kaya masu tsada amma ba canba tas saida suka gama kallon kaya anata rangada guda ana yarwa da Mama habaici data fito karbar kayan Itama sarai tasan da ita suke amma ko afuska bata nuna tasan Suna yiba.
........✍️✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 39
Kuma har Zuciyarta ta tayasu murna da fatan ALLAH ya bada zaman Lafiya.Uwaliya ce ta rangada sallama tare da rangada guda hango kayan jika an baje shi ana ta kallo Umma takasa ta tsare dan kar Wani Yayi musu sata tana Gudun kar ayi mata abunda takewa mutane dan tabbas taje Ganin kayan Lefe sai tasan ta yadda akai ta sakayo Wani shine take gudun karfa Itama aimata haka.
"Hango kayan Soye Soyen da akai yasa Uwaliya da katawa dan farantai Uku aka cika tare da nannadesu da leda mekyalli sai walwali sukeyi wajan farantan tanufa kai tsaye wannan kayan fa Salamatu Uwaliya aimu Allah ya hutar damu sunce sun bar mana.Alhamdulillah abunda Uwaliya tace kenan faranti daya ta dauka dama ai duk rabin kayannan da kudina akayishi tunda basu karbaba ainaci nima namaida miyauna Umma ce tamike da sauri aah fa Uwaliya taya zaki samu kamar wannan gaskiya ajiyewa zakiyi In aka raba kyaci naki kason bafa zan ajiyeba dan Wallahi bazaa shani basilla ba dole in dauka tunda hakkinane ba kyautama aka bani ba"
Nan fa cacar baki ta barke anata ja inja da faranti saiga ledar ta barke kayan ciki sun fara zubowa Kasa hhh to dama kowa ya wunsa tsinkewa yake yan karbar kaya aka dasa wawaso har sauran farantan tas suka lebe kayan ciki sunyi dama dama da wajan dan wanwar aka yarda Umma Uwaliya ko takaici Kamar ya kasheta ko cinya daya bata samu ba kayan lefanma so akai ahada dasu kannan Appa ne suka hana faruwar hakan kaj hatta faran tan ansamu masu sashi dan danan ya karbar kaya kowacce takama hanyar Waje da dangin Umman da Makota wadanda basu samu ganima ba sune atsaye suna cizon yatsa.
Ai Umma gaba daya kwankwasonta rikewa yayi dan Wannan wawaso takanta akadinga bi ana mutstsikewa sai numfar fashi takeyi duk Masifa irinta Umma bakinta ya mutu to Masifarma bazata Iya ba dan bakinta shikansa ya samu nasa rabon harya fashe.
Mama dai na tsaye tana jimamin Wannan dibar Albarka Mata Kamar shanu dan danan kun wawashe kaya Allah ya Kyauta tace takoma gefe,Uwaliya dai cike da bacin rai tabar Gidan dan Akallah ta doshi kusan shekara rabon dataci naman Kaza amma ita da hakkinta ancinye ko kashi bata tsotsaba🤣🤣🤣.
Saida kyar Umma tagama numfar fashinta tatashi dan su Anty Safiyya ba wanda ya kalleta balle tasa ran zasu dagata dakyar ta mike tsaye mehali baya fasa halinsa banka musu harara tai tare da jan tsaki feee tafara Jan akwatunan tana kaiwa daki duk yadda takejin Jikinta bata hakuraba saida takai kayan gaba daya Hankalinta ya kwanta tabe baki sukai basu kulata ba dan basa son wata hayaniya takara hadasu dakin Mama suka shige suka kama hirar su sukaba banza ajiyarta dadai taga bame kulata saita koma daki rai bace Amma kuma data kalli akwatunan saitaji Duk Wani Damuwar ta ta yaye.
......✍️✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 40
Sai can Yamma su Hajara suka dawo haka su Wa'at Makarantar su suka tafi dan sun san zaman ba amfani zayyi muba ga shirye shiryen Saukar da akeyi sun Kusa hade karatunsu dan WA'AT a Hafiza zata fito tana da matukar kwakwalwa Shiyasa Malaman Suke matukar kaunarta Itace Ameera kullum zaka ganta fes fes cikin Wanki da guga.
Hajara ba kunya ta zauna aka bude kaya Itace kan gaba wajan baje kayan fan kaf kayan saidata fito Dasu ta kare musu kallo asan Zuciya Irin na Hajara kayan datai zaton Zaa Kawo yafi haka.Gaskiya Umma ni wannan kayan begama yimin ba wai kinga gidansu Kamal kuwa amma ace ko Sarkar Gold babu sannan banga wata kyauta ta musamman acikin kayan ba ninayi tunanin har mukullin Mota zai sako min,nima abunda yake cizon Zuciyata kenan tun dazu amma na lura yan uwannan nasa Suna so sukawo mana Matsala nan ta zayyane musu Duk abunda ya faru aiko Hajara ta fara kumfar bakin Duk seta gyara musu zama 🙄🙄Kujifa karfin hali irinnata.
Shima kuma Kamal din zaizo ya saman Idan shi yasa yan Uwansa suzo suyi musu wulakanci tsaki tai Gaskiya Umma nifa banason harkar talauci dole gidannan asan yadda zaai a gyarashi gashi tun yanzu amfara jawomin raini nima abunda nake tunani kenan dole Kabiru ya gyara gidannan Wallahi to yadai fi.
Mama ce ta kallesu bazakuje kuga kayan Lefan yayar taku ba Nusaiba ce tai Caraf gaskya Mama kinsan yanzu muna zuwa zasi mana mana wulakanci nikuma kinsan Mama zan Iya ramawa kuma kice zaki daken wullo mata mificin hannunta tayi aike wannan yarinya bakinki baya shiru tashi tai tana dariya kuzo muje muga ko Sabon Gari aka Kawo Mata dariya kawai sukai Nusy Badai surutu ba.
Assalamu Alaikum Munzo ganin Kaya Inji Nusaiba To aiga kayannan sai kindinga zabgawa mutane Sallama kamar sabuwar marokiya to Allah na tuba Inda Zaa baka ainan kake roko ninan banga abinda zaai roko akansa ba mena sama yaci balle na kasa, dawa kike wannan maganar mara kunya a ah Hajiya Umma nidai ban kama Suna ba Ita dai WA'AT batace komai ba bubbude kayan sukai sukaga abunda zasu Gani.
Tabe baki Hafsa da Nusaiba sukai to waini ya banga Gold da Gold yana tashiba sai wasu sarkoki danake Gani ke Hafsy ba sune mukaga ana kada Musu kararrawa ba aiko sune nisaida kika fadama kaina ya Kawo wuta fashewa sukai da dariya ashema ba kudin bane Duk bugene ko kuma matsayinne bekaiba waya sani.
Wa'at ce ta balla musu harara dan Hajara kamar hancita zai cire tsabar yadda take huroshi harara kuwa kamar idanunsu zai fado,gaskiya ni ban zaci zanga haka ba wai a mota suka zo ko a jirgi dannaga kamar tayoyin mota nake gani a kofar gida nima dai abunda nagani kenan.Umma ce tamike afusace zata dan kosu suka fice Suna dariya Wa'at suka bari atsaye ta kif kifta ido Jikinta harya fara rawa dan sosai takejin tsoron su ke kuma munafuka dakikaiwa mutane tsaye aka saiki wuce kitafi Kamal nedai yafi karfinki sai dai kikare adan garuwa kome faskare.
Cikin Sanyin Jiki tafita daga dakin abunda basu saniba ita tuni tadade da goge Kamal acikin Rayuwar ta tunda tagane ya koma wajan yarta tai Alkawarin tabarshi kenan ko shine Autan Maza kuwa.
........✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 41
Tana zaune afalo gaba daya abun Duniya Yayi Mata zafi har ita AA zai dagawa murya mekenan aikin datai ya karye ko kuwa Wata matsalar aka samu tabdi aiko da sake Wallahi gashi jiya Wani Mafarki datai meban tsoro AA yayo Mata Kishiya abunda ta tsana arayuwarta bata kaunar Kishiya ko kadan,girgiza kai tayi ai hakamma bazai faruba dan yasha gaya Mata bashi da raayin Mata biyu watsar da zancan tayi ta dauko wayarta takira Kb ringing biyu tayi yadaga kamar jira yake dama.
Kb yamagar malamin nan an kammala aikin kamar kinsan Yanzu nke shirin kiranki Aiki ya kammala yawwa shiyasa nake sonka saboda baka wasa da lamarina nina isa ai dole nasan yadda zanyi nataimaka miki akowane lokaci karki damu ana Mugun tare bayan sun gama maganarsu ta ajiye phone fuskarta Dauke da farin ciki zatai maganin AA kenan dole yasake dawowa tafin hannunta.
Shewa Suka sa da ihu shege mutumina kana wutafa kai to ance muku nidin na wasane Wani yaro ne ya dawo da abu aleda gashi ya mikawa Kb karba Yayi ya bude ledar saidana sake lekawa tawadace kullin naira 20 gawasu galan guda biyu a gefe sabbi fil ihu suka sake Sawa baka da kyau kb ko shedan yana Gudun sharrinka,ruwa yajawo abokiti yadaga tawadar nan ya juye aciki saiko ga ruwa ya koma baki kamar rubutu ya dura awannan galan din nakusa dashi saidata cika taf ya daure yana wata dariyar shakiyanci Fareeda me maganin mallaka zako ki mallakeshi yadda ya kamata,wani garin magani ya dauko wanda bansan Indai ya samoshi ba kulli biyu ya hada da rubutun awata katuwar leda ya daure har kallah ta fada suka tafa shida abokansa.
Cikin sauri tatashi tafada daki tafara shiryawa dan tun yau zata fara amfani da wannan Maganin Kicking taleka su Samira na tsaye suna aikinsu galla musu harara Tayi yau kar wacce ta daura abinci da AA inna dawo zandorawa Mijina abinci dakaina dan nagaji da bashi jagwal gwalonku yana ci,kallan Juna sukai baki kunshe da dariya tab lallai yau Oga zaici dadi ashe shikenan Hajiya adawo lafiya ko Amsawa bataiba taigaba fashewa sukai da dariya lallai yau zasu sha kallo marar dako tea inta dafa baya Iya sha sboda tsabar rashin dadinsa shine zatai girki yau.
Allah yasa yauma ya zabgawa wannan shegiyar fuskar tata mari naga ta tsiya kinji Wani salon makirci wai ita zataiwa Oga girki yau me Wallahi kin cika daukar dumi mace da Mijinta kibarsu sunfi kusa Kuka sanima ko haryaje ya rarrashi abarsa ta huce daga mahangurbar datasha kara tafawa sukai Suka cigaba da aikinsu suba gulmar Fareeda.Daga nesa tatsaya takira Kb dauko ledar yayi yana tafe yana dariya a zuciyar sa ko Yanzu kasuwa ta watse dan koli yaci riba dan hargida ya sayawa Iyayansa a kudin da yake tatsa awajan Fareeda yau bata tsaya Wani surutu ba yayi mata bayanin yadda zatai Amfani da magani cikin gaggawa sukai sallama ana sauri aje aiwa me House Girki🤣🤣🤣
......✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 42
Tana dawowa ta adana rubutun ta tadebi wanda zatayi girkin Dashi da garin maganin da zata barbada a kan abincin.Kiching tashiga tana kare masa kallo komai akwai abunda zata bukata matsalar daya bata san ta ina zata fara ba kuma girman kai bazai barta ta tambayi su Samira ba dasuke falo Suna aiki doya ta hango ga kwai nan ko create nawa takeso zata bare bara nai doya dakwai doyar ta kinkimo tafara yankawa saidata yankata tas duk girmanta.
Daddatsata tai tazuba Acikin ruwa ta wanke ta aje agefe mai tai tittila ta dora a kan gas kwai kusan Create tafashe aka dan barbada magi da gishiri wannan doyar data gama ferewa ta dauko ta dunga tsumbulawa akwai tana zubawa a kaskon da take kan gas tana soyuwa akwashe ta haka tai tayi harta gama kamshi da karni sai tashi suke dan ko Albasa bata yanka ba abudai raba jan jan gaba daya tahada gumi.
Kayan Miya ta diba Acikin fridge tare da kaza tukunya ta dauka tasa Kazar ta wanke wannan kayan miyan ta dora agas saidata leka ta tabbatar da bakowa ta dauko rubutun malam ta juye acikin Kazar nan da kayan miya ta Jujjuya garin maganin ta dauko shima ta barbada Farfesu naci gaba da bararraka lumtsun acikin romo Magi da gishiri kawai tazuba ta tsiyaya mai tai rufe tana yarfe gumi akallai yakai awa biyu akan Gas sannan tabude aiko yagaba ragar gajewa ga romo Yayi bakikkrin yasha rubutu tsam tayi tana Kallon Naman Ita kanta be burgeta ba bare AA tasan halinsa sarai Amma zata lallabashi yaci.
Juyewa tayi ta dora shinkafa tacika tukunya da ruwa Kamar me dahuwar gidan biki tana dorawa ta zuba shinkafa ba wanki ba komai aganinta ai daga buhu tafito kuma bata da wani datti to shinkafar dai bata cakude ba har aka gama dahuwarta Ita da kanta tajere abincin tana sakin Murmushi tasan yau ba karamin birge AA zatai ba.
Tafiya tai taje ta fesa wanka akasha atamfa dan yasha gaya Mata yana matukar yaga tasa atamfa shine yau dan tasamu yaci Abincin ta saka tana Cikin fesa turare taji darar motocinsa da sauri ta sauko aka kame a falo Fuskar nan sai washe baki take tunkan ya karasa shigowa tatashi tatare sa Jakar Laptop dinsa ta karba tare damai Sannu da zuwa.
Abun kuwa ya matukar bashi Mamaki yaushe rabon da Fareeda taimasa Sannu da zuwa ko adawo Lafiya in be mantaba tin washe garin da aka kawota mazewa Yayi tare da Amsawa kina Lafiya ya gidan Lafiya lau.Har Bedroom ta bishi aka shiga Toilet ta hada masa ruwan wanka shidai yana zaune yana ganin Ikon Allah.
Cikin Fari da ido tana Wani karya kwankwaso kamar igiyar shanya My Love Inka kammala Food is ready bece Mata Komaiba ya shige ya barta awajan sauka tai Itama taja kujera tana Jiran Fitowarsa ya kwashi Gara.
🤣🤣🤣To nima banaja gefe naga yadda zata kaya Fans kubiyo ni.
..........✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 43
Kamshin turaransa ne kawai ya isar Mata da sakon fitowar sa dakanta taja masa kujera ya zauna tunda ta bude Farfesun nan ya daki hancinsa yaji Zuciyarsa ta fara tashi gashi bakikkirin kamar ta kirba gawayi ta zuba komai ta zuba masa ta turamai gabansa sai kashe shi take da Murmushi gabadaya abincin yake karewa Kallo jiyayi bazai iya kai komai bakinsa ba dan tabbas amai ne zai biyo baya.
Doyar ce dai yakejin zai daure yaci Itama dan kartace beci bane Fuskarsa kadaran kada ham wata karama ya hango ya dauketa batunanin komai ya sata abaki cak ya tsaya da fara taunatan da yake kokarin yi dan jin Wani mugun karni gashi da Ita da danya babu Wani ban bancin dan dole ya furzar da ita daga bakinsa turamata gabanta Yayi mene Wannan cikin rashin fahimta tace doyace mana ci kiji dayake tasan doyar bata sa Mata komai ba dauka tai tasa abaki tuni tafara zare ido jitai ina doyar bazata samu shiga ba ta furzar da Ita daga bakinta.
Tsam ya Mike yabar Wajan kai tsaye Toilet yanufa saidai Yayi brush kusan sau biyar Amma har Lokacin wannan karnin yakeji yana hawar masa ka zama yayi abakin bed yana maida Numfashi Abun takaici gani yai kawai tashigo da kayan abincin har dakinsa wata Uwar tsawa ya buga Mata dahar saidai kayan hannunta ya tarwatse gaba daya hannu ta dora aka ta fashe da Kuka dan babban bacin ranta dabeci Abincin ba ko yayane.
Ransane ya sake baci yadda tai masa kaca kaca da daki tsugunna ki kwashe wannan kayan kazantar da kika kawon daki haka ya tisata agaba saidata gyara masa dakin tas sannan yace tafice mai adaki haka ta futa tana rizgar Kuka Kamar wata karamar yarinya saidai tai Kuka me isarta sannan tai shiru har bcc ya kwashe ta yanzu duk wahalar datasha tatashi abmza kennan tazauna ta shirya girki amma ace ko kadan beci ba.
Su Harira tsabar gulma suka fito akahau tattare kwanuka Suna kaiwa Kiching saida suka gyara ko ina sannan suka koma kan abincin Madam Fareeda budewa sukai da sauri suka rufe jin wani mugun karni ya daki hancinsu ga farfesun abun ma ba kyawun Gani kallon Juna suke Duk rashin iya girki na Fareeda basu san yakai hakaba dan kaf gidannan sunsan babu wanda zai iyacin abincin nan sai wanda bashi da hankali kulleshi sukai aleda gaba daya abincin Get Man suka roka daya fiddashi waje haka ya karba dan yagane abincine ya lalace amma kuma yayi mamaki dan ya dade bega abinci ya lalace har anfito dashi waje zaa yadda ba.
AA yana kwance Tamkar me bacci Amma ba baccin yake ba be Tabbatar Fareeda bata da hankali ba saiyau tarasa abinda zata bashi sai wannnan Abun tsaki yaja Phone dinsa ya jawo yakira Amminsa suka sha hira kozai rage bacin ran dayake ciki Allah Sarki Uwa medadi tuni ya manta da duk wata damuwarsa.
........✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 44
Kwanci tashi ba wuya awajan Allah biki yana ta matsowa shirye shirye Umma kawai takeyi anshiga anfita har bashin mutane taje ta karbo Duk dan ta kankarowa yarta mutunci Fenti akayiwa gidan gaba daya amma tsabar bakin ciki aka zagaye kofar dakin Mama banda Ita a fentin ko daya babu abunda ya dameta dama harkar biki baasaka da suba dan haka ko Anko batayiwa yayanta ba sudai sun zama yan Kallo komai saidai su juyo shi daga nesa Party kala hudu aka shirya zaai Mamar Kamal tai tsalle ta dire bataga Jama,ar dazata ta Tara awannan bikin ba saidai abata kunya Party taje Tayi akofar layinsu.
Da kyar dai aka samu ta sakko zaai guda daya dan ba karamin jin haushin Auren nan take jiba dannata guda daya datayi shirin bajinta abikinsa yarasa wadda zai debo sai yar talakawa wannan abu na batawa Dangin Kamal rai Duk wannan badakala da akeyi besa jikin Umma yayi sanyi ba babban burinta ayi Auran saisu kamashi ahannu dagashi har Danginnasa sai yadda sukai dasu shiyasa hankalinsu kwance suketa shirin bikinsu.
Yau ne Zaa fita Party tun safe Amarya Hajara aka tafi wajan gyaran Jiki daganan aka tsantsaro mata kwalliya Tayi kyau sosai Nan event suka kama jigari jigari Anan zaai Party daga motar dazata dauki Amarya basu karo kowace mota ba casukai kowacce ta hawo napep dama Dashi aka saba kai abundai ba arziki komai kayau kayau tsabar Rashin mutuncin da sukai musu shinkafa ce fara damai da yaji agefe Ita aka dinga kawo musu wai saboda kar cikinsu ya lalace gwara abasu abinda suka saba ci.
Sosai abun ya kular da yan Uwan Umma Ananne fa suka fara maida martani dan harda masu guzurin leda in bazasu Iya cinyewa ba su juye🤣🤣 Amma tsabar wulakanci arasa me Zaa Kawo sai garau garau da zobo dan kulli kai ba karamin wulaqanci suka tata musu ba iya danginsa akadinga fitowa da Abinci kala kala kaji zuku zuku akan abincin Suna kallo saidai hadiyar yawu babu damar ci.
Lemuka haka suka dinga hangosu babu damar sha Amarya da Angone suka iso wajan party tunda suka fito daga mota yan Uwansa ke masa liki amma basu Hada da Hajaraba saima wata muguwar harara da suke auna mata Inda aka tanada dan zaman Ango da Amarya suka zauna nan biki yaci gaba da gudana awajan dangin Ango dan gaba daya Dangin Amarya ransu abace yake na Wannan Wulakanci da ake yimusu,a Wannan karan sunyi matukar kokari da basu raba hali awajanba.
Haka aka tashi daga Wajan Party rai bace,suna dira Gida kuwa saka balle da hirar yadda abun ya kasan ce sosai ran Umma ya back dole ne ta mike tsaye danta lura abun nasu babu mutunci.Ranar Lahadi Dubban Al, Umma suka shaida Auran Hajara Kabir Da Kamal akan sadaki naira Dubu Hamsin
Acikin gida kuwa Umma na jiran taji sadakin yar gaban goshinta Makullin Mota ko Wani kudi masu nauyi kawai taji Ana fadin dubu Hamsin kamar bakinta zai yage saboda Masifa saida kyar wata kanwar Uwaliya ta tausheta akan tayi shiru Duk Dangin su Itace Zakka babu ruwanta da duk Wani shashanci na Dangin su ko yaushe Ita ke Musu Nasiha da subi Duniya a sannu shiya baa shiri da ita ko kadan.
Appa ana ta yawo da babbar riga kamar gaske fuskarsa babu alamun Wani abun Farin ciki ya sameshi yau yarsa zatai Aure Alasanya Alkhairin ma da kyar yake Amsawa kamarshi ace zai Aurar da ya har nawama yake sai dazu dayaga abokansa sunzo da yayansu maza Kowa ras dashi babu me wata damuwa kuma kaf cikinsu beji wanda Yayi zancen yana diya mace ba balle har azo ga zancan Auranta sai shi yanzu jikoki zasuzo su bai bayeshi.
Dan haushi gidamma gaba daya ya bari da ace da lashine ma da da sauki Amma daga Gani Dangin Kamal dinnan matsiya tane babu Wani katabus da sukayi sun kankame komai bazasu bayarba balle shima yasa ran zai dinga samun Wani abu kai shidai gaba daya jiya ke Duniyar ma na juya masa gashi Duk sanda yayi tunanin Ameer fa koyaushe zai iya dawowa sai yaji kirjinsa ya bada ras.
Umar ne kawai awajan Daurin Auran da shashashan abokansa irinsa da bashi da fus shima ko naira biyar betemako da Ita ba kuma yana dashi bayarwa ne bazai ba tsaki Appa yaja yabar unguwar gaba daya.
.........✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 45
Acan cikin Gida kuwa 'yan kidan kwarya Umma ta dauko tana tsakiya tana tikar rawa ita da Amarya ba kunya haka Amarya ta zage tadinga rawa yan Uwa nai nata liki inzaka lura da wakar dame kidan kwaryar takeyi gaba daya habaici ne kuma Umma tafadi yadda kidan zai kasan ce Mama ko ajikinta bata nuna Musu taji haushi ba har liki tafito taiwa Amarya dan ita bata taba rikarsu a Zuciyar taba da zuciya daya take zaune dasu anci ansha Motar kai Amarya karfe 6 tatsaya akofar gidan ana jiran aga jerin motoci babu wata mota sai wannan.
Ga mutane jingim ana jiran atafi kai Amarya shiru kake ji daga mota sai Direba babu Dangin Ango da suke zuwa Tafiya da Amarya babu abokan Ango Abunda ya kara fusata Umma kenan da cewar bazata basu yar taba matukar basu aiko masu daukarta ba.Nan Appa yai tsalle kan cewar dole tabada ita dan anriga Andaura tafita daga hannunsa haka kawai bazai zauna yana ci da Matar Wani ba rikici sosai sukayi ita dai Mama na gefe dama tare ta gansu Uffan bata ceba dan Wannan sulhun ba nata bane.
Saida Inna taga zasu raba hali acikin taron Jama,a takashe takaddama hannun Hajara kawai takama tai waje da ita sai rusar Kuka take na bakin ciki dan tasha gayawa kawayanta Irin jerin motoci na Alfarma da zasu Gani sunzo daukar ta Amma sai taga sabanin haka ko wata bazawarar aitafi karfin haka balle ita Budurwa dalleliya da Ita,aiko Wallahi Sai Kamal ya gane kuskuransa itakadai tasan abunda zatai masa.
Daga Inna sai Mama da Uwaliya Akatafi kai Amarya yan gulmar son ganin kwakwaf sai cizon yatsa amma tsabar naci ahakan wasu saida Suka dinga tarar napep Suna Tafiya.Gida kam yayi Ma sha Allah ashe dama agidan Surukanta zata zauna Wani bangare aka ware musu da zummar Inya gama gininsa zasu koma abunda basu saniba yanada dan kareren gidansa Amma Ummansa tace bazai zauna aciki ba anan gidan zasu zauna dan wacce ya dauko batakai matsayin ta zauna agidan ba.
Dan dole ya hakura badan yaso ba dan gaba daya baya son zaman gidan yasan kannansa takura wa Matar sa zasuyi,koda Suka je har wajan Uwar Mijin aka kaita ganin kwarjinin su Inna ya hana tai musu rashin mutunci amma aizasu tafi subar yar tasu kadaran kada han ta karbesu aka gaisa tare da bada amanar ta itadai batace takar baba bakuma tace bata karba ba,haka Suka taso jiki asanyaye Suka kaita sashinta Indai zasu zauna waje kam Ma sha Allah komai Yaji dakinta yayi kyau sosai dakuna ukune sai kiching da Toilet da tsakar gida ginine mekyau da tsari.
Sun Mata Nasiha sosai gaba daya jikina Uwaliya yayi Sanyi da wannan Aure saikace Wadanda akaiwa dole sai sun Auro musu yar dama Ita bata san tayadda akayi wannan Aure ba ance matadai Hajara tasami miji Mai kudi Amma wannan Aure kamar bana Siyayya ba.Itako Hajara Duk ba wannan ne ya da metaba Allah Allah take sutafi tatashi ta zagaya gidan taga yadda yake.
Suna Tafiya kuwa tatashi tana zagayawa cikin Farin Ciki Duk da ba haka taso ba taso ace Ita kadai ce amma tunda ya Kusa kammala ginin sa ai zasu tashi,komawa tai ta zauna tana zuba idon ta ina Ango zai shigo dan A Lokacin anyi Sallar Magari ba ko Sallah batai ba ta dauko Powder takara shafawa aka faffesa turare aka zauna zaman Jiran Ango.
......✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 46
Haka akai biki aka watse akabar Amarya da Ango, a lokacinne kuma Appa ya kara sako su Mama a gaba motsi kadan yace ya gaji da zama dasu suba wata tsiya suke tabuka masa ba da ace dakin haya ya saka da tabbas yasan iyanzu ya samu abunda ya samu amma ba sidi ba sadada sun cike mai waje in yana wannan fadan sai dai suyi shiru adaki Suna mamakin Irin kiyayyar da Mahaifinsu ke Nuna musu kamar sukadai ne yaya mata agidan Alhalin ga Zubaida da Zainab su be tsan gwamesu kamar suba kodan yasan Umma ba kyalesa zatai ba oho.
A Wannan Lokacin cinne ciwo ya sako Mama a gaba koda sukaje Asibiti Jininta yayi Mugun hawa saboda bakin cikin da ake cunkusa mata ako yaushe Magunguna aka rubuta mata babu kudin da zasu se Maganin,haka suka sai wanda zasu iya haka sukai ta lallaba Rayuwar da dadi ba dadi ga saukar WA'AT tana tahowa basu dako sisi a Rayuwar su basu Iya Cewa ayi musu ba shiyasa ko Malam ta Kasa fadawa gashi har ankusa rufe karbar kudin Saukar.
Inna ce taji Labarin an Kusa rufewa abakin wata yar makotansu ajinsu daya da Wa'at sai a lokacin suka san meyake faruwa sosai Malam ya nuna bacin ransa akan kin gaya masa da sukai damme bazasu fada masa Lokacin yazo ba aishi yace ya dauki komai nasu.Dan danan yasa Kanin Appa yaje ya biya musu shirye shiryen Sauka ake tayi Amma Appa baida labari Inya sani ma mezeyi katin Gayyata babu wanda Malam bai bawa ba shima Appa har gida Malam da kansa ba sako ba ya kawo masa nasa katin atunaninsa Wani biki zaayi saida ya karanta ya sake maimai tawa tabbas sunan sane har yaushe duk wannan din ya faru bai sani ba.
Amma Malam ya akai bansan da zan canba Suna cikin gidana ace zatai sauka ni baa gayamin ba,Malam ne yayi masa Wani Kallo agayama awane Matsayi Iya matsayinka Gayyata kuma gashi na gayyace ka inkuma zuwa ne bazakai ba fakat kagayamin tun yanzu shikenan tunda ni baa daukeni abakin komaiba kaje kayi Kabiru Duniya ce ta ishi kowa riga da wando ko Sallama Malam bai masa ba ya juya ya tafi cikin gida ya shiga yana ban bamin fada baa daukeshi abakin komai ba zaai sauka agidansa Zaaci azzikinsa amma shine shi bazaa gaya masa ba.
Cin arziki zamiyi to Matukar dan anyi sauka agidanka shine munci arziki gwara ko makota ne muje muyi balle kasan kaf dangina babu Gidan wanda bazanje nayi taro na acan ba Gidanka ne An barma bazamu kawo Jama,a cikinsa ba ai Ita Duniya tanada fadi.Wallahi Kabiru baka da abun da zanci arzikinsa awajanka ban ganshi ba Mama ce take fadin hakan cikin kunar rai da tafasar Zuciya gaba daya idanunta sun ciko da hawayen bakin ciki bazatace bataga Amfanin Auranta ba Tunda Allah ya bata kyautar 'Yaya mata har uku kuma ako yaushe tana gode masa abisa Kyautar da yayi mata.
Hawayan Fuskarta ta goge tatashi tsam tabar Wajan Umma kuwa ranta fes kamar ta taka rawa itafa aduniya babu Abinda takeso sama dataga bacin ran Mama babban burinta akoda yaushe Appa ya dinga ci mata mutunci atsakar gida to ai Ita wannan rana yagamai mata komai.Tashi sukai suka bi bayanta tana kwance Tamkar me bacci amma ALLAH kadai yasan Irin Damuwar sake dan kare acikin Zuciyarta.
Duk zama sukai sukai tagumi gaba daya Duniyar Juya musu takeyi Suna Matukar son Mahaifiyarsu Babban muradinsu ALLAH ya kaisu Lokacin da zasu taimaka Mata Itama taji dadi kamar kowa tayi dariya da farin ciki.
Gaskiya Umma ki rage son Zuciya Wallahi waike babu abunda kika iya sai mugunta nina rasa me su Mama suka tare miki matar da babu ruwanta amma Duk kin addabi Rayuwar su Abincima andaina basu kuma naga suma gidan na Uban sune,iye lallai nikike gayawa haka Zainab wai anyama ke yata ce Kuwa nasarasa wace irin ya na haifa memun hassada da bakin ciki bakyaso ko yaya kiga Dariyata agidan nan to Wallahi zansa kafar wando daya dake nadai gaya miki.
Saikije kiyi tayi kuma Allah saiya saka musu Wallhi ta fada daki cikin jin haushin Umman ita bataso taga ana zaluntar yan uwanta Duk da bata shiga sabgarsu amma tana sonsu ahakan.
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 47
Ammi ranar yaushe zamu tafi saukar ne Wallahi na matsu naje Zariya kinga na dade banje ba cewar Safna ance mikima dake zanje Saukar dakike bayanin yaushe za a tafi ba Inda zakije yarinya kai Ammi Dan ALLAH kitafi dani kinga nadade banga Anty Juwaira ba Murmushi kawai Ammi tayi to kisha kurumin ki ranar Friday zamu tafi tunda ranar Saturday ne Saukar Tsalle tai ta fada kan ciyar Ammi wayyo kin karya ni Safna zaki karasa min kafa Dariya kawai Safna take dan Murna ta hana ta Magana gaba daya.
Wai Ammi Harda Yaya Abie zaaje wajan saukar aah nikam bazan daurawa kaina ba kinsan bashi da Lokaci innace yajema zai iya bani Uzuri tunda shine agogo sarkin Aiki dagani saike zamu tafi ko Marwana ba lallai taje ba nidai Ammi tunda zakai dani ai komai Yayi Kyau.
Ranar Friday kuwa suka Dira a Zariya Gidan Anty Juwaira Itama harda yarta a masu saukar kanwa Ammie ce Uwarsu daya Ubansu daya sosai tai Farin cikin ganin su tarasa Inda zata sakasu dan Murna Jiddah da Safna rungume Juna sukai sabida sun dade basu hadu ba dakin Jidda suka wuce anan suka yada zango.Karfe 4 ta dauki Safna tai mata rakiya gidansu kawarta kuma Aminiyarta Lokacin da suka shiga gidan Umma ce atsakar gida tana tatar kunu dakyar ta amsa Sallamar tana harararsu dan itafa bata kaunar taga kowa ya rabi Inda su Wa'at suke musamman wannan da tasan gidansu akwai ba daga karamin gida ta fito ba.
Tabe baki Jidda tayi dan tasan bakin hali irinna Umma tun tuni dakin Mama suka shiga Mama kawai suka samu dan ta aikesu gidan Malam da Murmushi take Kallonsu Aah Jiddodo bakuwa kukayi ne dayake Wani Lokacin tana tsokanarta da haka dariya tayi ai Mama Safna ce danake yawan baku labarin ta yar yayar Ummu na ta ABUJA Mama ce ta rike baki Au kice manyan bakine to sannu da Zuwa kazauna mana ta nuna musu kujera.
Zama sukai zobo me sanyi ta Kawo musu da kunun Aya sosai ya yiwa Safna dadi kai Amma Wallahi yayi dadi sosai da Ammi tana Kusa aida tashi ALLAH Sarki tare kukazo da Mamanta ki eh tare Mukazo to bakomai inzaku tafi sai nabada kikai mata kai Mama ALLAH ki barshi kai ni Banason Gulma Safna Itama Mamar muce fa babu wata kunya atsakanin mu Mama tana jinsu kawai Murmushi tai sosai yarinyar ta burgeta ganin bata da Wulakanci dagani tasamu Tarbiyyar me kyau.
To wai Mama ina aminiyar ni bamgansu ba tab to aikin baro su abaya Suna Gidan Malam hannu ya dora aka kai Amma Wallahi banji dadi ba yanzu ma ashe Suna layimmu na zabaro kafa nataho har nan ALLAH bata kyauta minba aida saita tura Hafsa tace tana gidan Malam na sameta acan kuma fa Mama na gaya mata zanzo,to ai kunfi Kusa itaku ni mene nawa aciki inkun hadu kyayi mata mitar Dariya Safna tayi aini Mama naji dadima da mukazo bagashi nasha abun dadi ba kuma naga gari to aikuwa ke gaba takaiki gobarar titi A Jos.
Cigaba sukai hira da Mama kamar yayanta haka ta dauke su dan dama tasaba da Jidda sosai tana yawan zuwa in ta samu lokaci hatta Maman ta tana matukar kokari wajan taga ta taimaka musu dan Jidda tana bata labarin halin da suke ciki.Mekewa sukai zamu tafi Mama saimu hadu dasu agidan Malam din dama kunshi zamuje da gyaran gashi to ALLAH yasa baayi mata ba dama kunshin suka tafi ai tab aiko ALLAH Mama dasai nayi fushi da Ita aina gayama ta akwai Inda na kama mana zamuje ai mana sosai ta iya kunshi Matar.
To aishikenan ALLAH yasa karkuyi sabani kuwa leda ta dakko ta zuba musu zobo da kunan Aya kusan na 500 ta zuba musu Mam akwai hannun kyauta Duk da bata dashi in harkazo gidan bayan kasha inka tashi tafiya saita zubama aleda katafi dashi tana da matukar karamci da girmama bakonta Godiya sukai sosai suka fito har tsakar gida Mama ta rakasu Umma ta bisu da harara kwadayayya kawai🤣🤣tadauka kowama haka yake kamar Ita.
......✍️✍️✍️
WA'AT
By Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Oum Aneesat
Chapter 48
Suna fita safna ta Kalli Jidda kai Amma Matar nan tana da mutunci, aidamma baki zauna da ita ba tana da kirki sosai gata da Kyauta babu ruwanta Wallahi itace babar Aminiyata danake baki Labrinta.Aini har na matsu ma naga kawar taki danna san itama zatayi kyau Kamar Mamanta Dariya Jidda tayi ke ai hartafi Maman nata ma kyau kedai in ana Sallah ba,a Magana koni tana birgeni balle me hula Dariya sukai suka tafa kuma fa har kinsa tunanina ya tafi Wani waje haba wane tunani kikai a,ah bazan fada miki yanzu ba saina ganta Nasan Wani Ma,auni zan Aunata duka Jidda ta kaiwa Safna nifa dadi dake jan aji kar ALLAH yasa kifadamin din ta murguda mata baki.
Suna shiga Gidan Malam me lalle zata Fara yiwa Wa'at cikin sauri Jidda take fadin baiwar ALLAH tsaya banda ita tana hararar Wa'at Dariya kawaii tayi dan tasan Laifinta dan tagaya mata zasuje wajan kunshi ita bataso tadinga kai kanta Inda ALLAH be kaita ba kiyi hakuri kawas kinsan dai Mantawa nai bawani Mantawa da dai bansan halinki bane Malama kawaii ki taso aidaga gidanku nake yanzu Mama tabani Umarnin nazo natafi dake Dariya tayi au kimazo kitafi dani Kamar wata mai Lefi to ai Lefin kikai ashe kinanan aida saiki Aika su Hafsa sugayamin kina Kusa da gida.Dago kanta tayi sukai ido biyu da Safna datake ta binta da kallo tunda Suka shigo sai yanzu ta Lura da ita,Murmushi sukaiwa juna bakuwa kuka Aminiyas aibaki da Kirki to Safna ce danake baki Labarinta kai kai kice nakusa nai Laifi Sannu da zuwa take mata cikin Fara,a.
Bata rai tayi ashe dama ni bama kisanni ba da Nasan hakane da bazan shigo gidannan ba yanzu Duk pic dina dayake wayarki ko saudaya kikasa nuna mata ni,to kiyi hakuri tayi Laifi karma ta hakura cewa Jidda Wa'at ce ta jawo mata kujera kizauna nabarki atsaye ko bawani maganar ta zauna tashi zakiyi mutafi kina ganin yamma tanaso taimana.
Inna dake Juyosu daga daki sai Lokacin ta leko mutanan anhadu babu zaman Lafiya ko yaushe kuna haurawa to ai Inna jikar takice take bani haushi haryau takasa yadda mun zama daya Gani take Kamar nafita kumani Wallahi abunnan yana batan rai Inna cewar Jidda Kamar zatai Kuka to ai ni Wannan sulhu bazan Iya shiba dan ina da aikinyi zuwa anjima zaku bani kunya najiyoku kuna Dariya adaka.
Safna ce cikin Dariya take fadin hakane kuwa Inna koni dana gansu yau na yadda da maganar ki to kinjifa yar Albarka ganemin Hanya Sallama sukaiwa Inna suka fita cikin Nishadi da walwala a Fusko kinsu.Kai tsaye wajan me Lalle suka fara zuwa dama tasan da zuwansu Shiyasa bata karbi masu zuwa Lalle ba da yawa Jidda aka farayiwa Ja sai Safna Wa'at ce karshe sosai sukayi kyau suna cire Ja aka zana musu baki ba karamin kyau sukai ba.
Jidda ce ta biyata kudinta daganan gyaran gashi suka wuce basu suka dawo ba sai bayan Magariba gida Wa'at ta wuce bayadda basi da itaba tazo tazo suje gidansu zasu rakata har Gida taki yadda dole suka hakura suka kyaleta tashiga tadauko su Nusaiba da suke jiranta tana zuwa ko zama batai ba suka tafi gida sai santin kunshinta sukeyi tumma kafin sugama Ganinsa sosai ga kanta da yasha gyara abun burgewa Kamar wata Amarya haka takoma.
ALHAMDULILLAH
Anan nakwo karage Littafin WA'AT part One.
Ina Godiya Ga ALLAH Madaukakin Sarki daya bani ikon kammala Wannan Littafi Kashi Na Daya.
Ina matukar Godiya ga dinbin Masoya Da suke Bibiyar Wannan Littafi Har kawo Iyanzu.
ALLAH ya bar Zumunci Jinjina gareku Mara yankewa.
Kubiyoni Cikin Littafin WA'AT PART TWO dan jin Yadda zata kaya.
Shin Appa zai sadu da yagane Daraja da Martabar Yaya mata In zai dawo Hanya sai yaushe kenan.
Ya Hajara zata kaya Agidan Mijinta Kamal Auran Cin Amana Da son Zuciya.
Fareeda Zataci Gaba da cin Nasara Akan AA ko Bazata ciba.
Wani Plan KB yake hadawa Fareeda.
Duk Kuniyoni Alittafin WA'AT PART TWO.
Taku Har Kullum.
Kulsoom Isma'il Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
........✍️✍️✍️
0 Comments