zahrazu

                                                                              GIMBIYA   ZAHRA ZU
                                                                                     by
                                                  Abdul King Article & Abdul Alhaji Musa 10K
                                                                                Episode 1
                                                                            Labarin Ƙabar
In the memory of Kamal No Love
Dedicated to Amina Idris & Meenat A Yandoma
Page 1
Masarautar Ƙabru sunada wata al ada ta hana baƙi shiga garin a cikin dare, kuma wannan ya samo asali ne tun zamanin sarki Barhan dan Jandan, a wannan lokaci an taba kawo wani hari na sumame a cikin dare, wasu mata ne su huɗu da ba a san ko su waye ba, ko wacce ta rufe fuskarta da baƙin ƙyalle, a lokacin da waɗannan matan suka tunkari wannan masarauta a saman dawakai, dakarun dake gadin ƙofar birnin basu wani tsananta bincike akan su ba sabida ganin cewa mata ne, to bayan sun shiga garin ne sai suka rabu wato kowace ta kama gabanta, bayan sun yi tafiya mai nisa a rarrabe sai kowacensu ta tsaya, daya a bangon gabas ɗaya a bangon yamma, ɗaya a bangon kudu ɗaya kuwa a bangon arewa, wani Ƙundi kowacensu ta fito dashi ta jefar, ai kuwa yin hakan keda wuya sai ga wani hayaƙi yana fitowa a cikin kowane  Ƙundi, a haka hayaƙin ya fara tiriri a sama yana zagaye birnin gabaki daya, daga nan sai hayaƙin ya fara shiga cikin mutane, to abun mamaki shine duk wanda ya shaƙi hayaƙin sai ya faɗi sumamme ba tare da sanin inda yake ba, a haka wannan hayaƙi yaci gaba da ratsa mutane, kuma a duk inda ya ratsa sai mutane su faɗi sumammu, cikin daƙiƙu kaɗan sai ga mutanen masauratar  Ƙabru sun kasance a yanayin suma, wannan damar waɗannan  matan  su huɗu sukayi amfani da ita suka sace dukiya mai yawa a masarautar Ƙabru kuma daga karshe sukayi garkuwa da sarki Barhan dan Jandan
Wayewar gari ya mutukar kasance babbar razana ga mutane masarautar Ƙabru da suka wayi gari cikin jimamin rashin adalin sarkinsu, babbar matsalar itace ba a san ko su waye sukayi wannan aika aika ba kuma ba a san meye dalilin yin haka ba, shi kuma sarki Barhan da sukayi garkuwa dashi ko wane abune suke nema a wurinsa? Ba a tsaya ɓata lokaci ba aka naɗa Yarima Mahir a matsayin sarkin da zai ci gaba da gudanar da al amurran yau da kullum, tun daga wannan lokaci masautar Ƙabru ta ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki na hana baƙi shiga garin a cikin dare domin kada abunda ya faru a baya ya maimaita kansa.
Page 2 
kasancewar masarautar Ƙabru babbar masarauta, wannan abu daya faru da kuma wannan hukunci da suke yanke na hana baƙi shiga cikin dare yayi tasiri sosai ga manyan biranen dake ji da kansu, amma abun mamaki shine ko kaɗan wannan hukunci da masarautar Ƙabru ta yanke bai girgiza wani saurayi dake tafe a saman ingarman dokinsa ba yana sharara wani namijin gudu, gudu yake gadan gadan a saman dokinsa da zimmar cimma wannan masarauta ta Ƙabru daya nufa, to abun tambaya shi wannan saurayi waye kuma meya kawosa a wannan masarauta ta Ƙabru? kuma da gaskene wai bayada masaniya cewa an hana baƙi zuwan dare? A haka wannan saurayi yaci gaba da sharara gudunsa har ya iso babbar ƙofar birnin, a nan dokinsa yayi haniniya tare da yin turjiya ganin ƙofar a kulle, rawanin dake kansa ya gyra daga nan ya ƙara daidaita baƙin ƙyallen daya rufe masa fuska, a nan ya ja dokinsa baya, dokin tafiya ya farayi baya da baya sai da yayi kamar taku talatin, daga nan sai saurayin ya kaɗa linzamin dokin, a nan dokin yayi haniniya daga nan ya tunkari wannan ƙofar gadan gadan a cikin wani matsanancin gudu, saida ya rage saura taku biyar ya cimma kofar kawai sai saurayin yaja linzamin dokin, yin hakan keda wuya sai dokin yayi wani tsalle tamkar tsuntsu shi kuwa saurayin wata alkafira yayi yana cillawa a sama  da matsanancin gudun tsiya, cikin sauri ya fiddo wata doguwar kaca mai ɓota a can ƙarshenta, da sauri ya jefa kacar, ai kuwa cikin sa a ɓotar kacar ta rike ƙofar garin kaf, a haka saurayin ya fara hawan kacar yana ƙoƙarin isa can saman kofar garin, shi kuwa doki tsaye yayi yana kallon abunda uban gidansa ke shirin aikatawa, bayan saurayin ya isa saman ƙofar garin, sai yayi wata busa da bakinsa, shi kuwa doki yanajin haka sai ya fara tafiya da baya da baya sai da yayi kamar taku talatin, daga nan sai ya sheƙo da wani matsanancin gudu ya tunkari ƙofar wannan gari, sai da ya rage saura taku biyar ya cimma ƙofar sai yayi wani uban tsalle, da karfin tsiya dokin ya riƙe kacar dake rataye a ƙofar garin, shi kuwa saurayin na ganin haka sai ya ƙara yin busa da bakinsa, dokin najin haka sai ya fara takawa zuwa saman ƙofar bayan ya riƙe kacar gam kamar yadda yaga uban gidansa yayi, a haka dokin yaci gaba da takawa yana hawan saman kacar har sai da yakai can ƙolukuwa inda uban gidansa yake, daga nan sai saurayin yayi murmushin jin daɗi ganin cewa dokin nasa yayi abunda yake buƙata, cikin sauri saurayin ya haye dokin daga nan ya saki linzami.
Page 3
shi kuwa dokin na ganin haka sai yayi wata haniniya mai mutukar ƙarfi daban tsoro daga nan sai yayi wani uban tsalle tun daga saman ƙofar garin har ƙasa, dokin na dirowa sai yayi tsaye cak, a nan saurayin ya fara kallon birnin dake tattare da gine gine masu ban sha awa, a wannan lokaci birnin tsit yake baa jin motsin kome in banda iskan dake kaɗawa, da sauri ya sakar ma dokinsa linzami shi kuwa dokin anan ya fizga da gudu yana shiga lungu lungu dake birnin, a haka wannan saurayi yaci gaba da mazga namijin gudu a saman dokinsa, cikin dakiku kaɗan ya iso masarautar birnin, koda yazo ƙofar a bude take sanadiyar dakarun dake gadi bacci ya daukesu, yana shiga masarautar sai ya kara yiwa wurin kallo, bako shakka masarautar ta ginu, saukowa yayi saman dokinsa daga nan sai yayi wata yar busa da bakinsa, ai kuwa dokin najin haka sai yayi gaba da gudu, shi kuwa saurayin tsundumawa yayi a cikin masarautar, babbar sa ar daya samu itace duk kofar daya murda sai ta bude. A haka yayita shiga lungu lungu na masarautar yana binciken wani abu, yana cikin haka ne sai ya shigo wani kayataccen daki, narkeken gado ne na sarauta a tsakiyar dakin, yarinya ce kyakkyawa matashiya ke kwance sai sharara bacci take, da sauri ya dauko wata fatar damisa, a cikin fatar damisar an zana taswirar wannan yarinyar dake bacci, saurayin na ganin haka sai yayi dariya kamar da alama ita yake nema! To amma idan ita yake nema to me zaiyi da ita? cikin sauri ya nufota gadan gadan, ai kuwa kafin ya iyar da nufinsa ne sai kawai yaga wata kaca kamar daga sama ta makalkalesa da karfin tsiya, ba yadda bai yi ya kubce ba amma ya kasa.
      A haka yayita kokuwa da wannan kaca domin ya kubce amma ya kasa har daga karshe ya fadi kasa, faduwarsa keda wuya sai kawai wani saurayi a cikin sulke na yaki ya fito a wani lungu na dakin. Saurayin na fitowa sai ya kura masa ido kamar bazai kyafta ba, sai da ya gama kallonsa tsaf kafin ya fara magana.
      " Yarima Amran, kamar yadda aka fadamin kai kyakkyawa ne, ashe kuwa haka abun yake!" Haka ya fada cikin murmushi. Shi kuwa Amran din da yake kwance makalkale a cikin kaca mamaki ne ya rufe sa jin an ambaci sunansa, shi wannan saurayi ko waye? Meye kawosa a wannan masarautar, kuma yama akayi yasan sunansa? Kai bama wannan ba kada ace abu daya suke nema, to idan hakan ta kasance wato abu daya suke nema to wa zai samu wai zai rasa?
Page 4
" Kai waye, kuma... Me ya kawoka a wannan masarautar?" Haka Amran ya fada cikin fushi.
 " Kada ka damu kaji ko! Zaka iya kirana da Gazman." Haka ya fada yana murmushi daga nan sai ya nufi wani lungu inda ya dauko wata yar karamar jaka ta fata. Tunanin da Amran ya farayi shine mahaifinsa ya taba basa labarin wani azzalumin sarki da ake cewa Afran, shi Afran sabida tsabar zaluncinsa a cikin birninsa duk wanda yayi sabuwar amarya, to shine zai fara kwanciya da ita kafin angon, kuma duk wanda ya karya wannan doka tasa to yanzu kansa zai riga rana faduwa, bisa wannan dalili ne mutanen birnin Maliya wato birnin da sarki Afran ke mulki suke taka tsantsan dashi, a bisa wannan doka tasa ana gama shagalin biki dole ne ango ya kai amaryarsa ga sarki, haka kuma manyan dakarunsa ya basu umarni suyita yawo a cikin birni duk inda sukaga ana shagalin biki to su gaggauta fada masa. Sarki Afran yanada da kwaya daya da yake mutukar so kuma shi wannan da ya samesa ne ta hanyar wata mace da ake kira Azmana, Azmana mijinta manomi ne kuma dan asalin birnin Maliya, sabida zalunci irin na sarki Afran sai ya kashe mijin nata ita kuma ya aureta da karfin tsiya, to a cikin wannan aure ne ya samu dan sa mai suna Gazman,mako daya da haihuwar Gazman Azmana ta cika, shi kuwa sarki Afran tun daga wannan lokaci ya dauki wannan dabi ar ta kwantawa da amare kafin angwayensu. 
 Anan tunanin Amran ya tsaya, tofa kada ace wannan saurayi daya dabge sa da kaca shine Gazman dan sarki Afran, domin indai shine Gazman dan sarki Afran to bako shakka shima azzalumi ne tunda ance kyaun da ya gaji mahaifi, shi kuwa idan ya gado mahaifisa Afran to bako shakka baza ayi mai kyau ba domin mahaifin nasa yayi ƙaurin suna a fannin zalunci.
" Kace sunanka Gazman, ko kana nufin dan sarki Afran?" Haka Amran ya fada yana dubansa. Shi kuwa Gazman dubansa yayi yana mamaki kafin ya fara magana.
" Ka tsinka dai dai, amma ya akayi kasan koni waye?" Inji Gazman.
" Ai wannan ba wani abu bane duba da irin nasabar mahaifinka!" Inji Amran.
" Haka fa, na gane." Haka Gazman ya fada yana girgiza kai kamar mai nazarin wani abu, daga nan sai ya dauko wata yar karamar akwati ta karfe ya nufin wurin wannan yarinyar dake bacci abunta.
Page 5
    " Menene kake shirin aikatawa kuma?" Amran ya tambaya a tsawace.
    " Nazone na aikata abunda ya kawoni a wannan masarautar!" Inji Gazman.
    " To fadamin menene ya kawoka a wannan masarautar?" Amran ya tambaya. Gazman shiru yayi da alama baya son bashi amsa sabida haka sai ya tunkari wannan yarinyar da nufin iyar da nufinsa, to kafin ya karasa ne sai Amran ya kara tsokanarsa domin yaji abunda zaice.
    " Hala kanajin tsoron bani amsa ne domin kada na hanaka cikar burinka?" Inji Amran. Da karfi Gazman ya juyo yana dubansa da alama maganar ta masa zafi.
    " Ko kadan ba haka domin nasan bazaka iya yin komai akai ba!" Haka Gazman ya fada daga nan sai ya tunkari wannan yarinyar.
    " Idan kana tsammanin bazan iya komai akai ba me zai hana ka kwance wannan kacar daka daureni da ita!" Inji Amran. A nan Gazman ya tsaya yana nazarin maganar ba tare daya juyo ya kalli Amran ba, can kuma sai yaci gaba da tafiyarsa da nufin cimma yarinyar.
     " Ashe kai raggon namiji ne." Inji Amran. Da karfi Gazman ya juyo da alama maganar ta masa zafi, wurin juyowar tasa akwatin na karfe ya fadi. " Idan kai ba raggon namiji bane mezai hana ka kwance wannan kacar daka daure ni da ita, hala kana tsoron ganin abunda zan aikata ne? Kuma idan kai ba matsoraci bane me zai hana ka fadamin abunda kake shirin aikatawa  da wannan yarinyar!"  Anan aka fara kallon kallo tsakanin Amran da Gazman domin kowanesu a hasale yake, can sai Gazman yayi murmushi daga nan sai ya fara magana.
     " Nazo wannan masarautar ne domin gimbiya Zahra Zu!" Haka ya fada yana nunata da yatsa.
      " To idan ka sameta me zakayi da ita?" Amran ya tambaya.
      " Wannan kuma ba abunda ya shafeka bane." Inji Gazman, " Kuma bama wannan ba, kaima ya kamata ka fadamin meya kawoka a wannan masarautar?"
     " Nima nazone domin gimbiya Zahra Zu!" Inji Amran.
     " To idan ka sameta me zakayi da ita?"Inji Gazman.
     " Kuma wannan ba abunda ya shafeka bane!" Inji Amran. Anan Gazman yayi murmushi yana duban Amran.
Page 6
    " Kuma ga wata shawara, tunda tsakaninmu ni da kai muna neman abu daya wato gimbiya Zahra Zu to me zai hana muyi gasa idan yaso duk wanda ya samu nasara shi kenan ta zama tasa." Inji Amran, anan Gazman yayi dogon murmushi hadda zama saman wata kujera mai laushi a kusa dashi, da alama yaji dadin kalamin na Amran.
   " Yanzu sai ka fadamin ya kake ganin ya kamata muyi wannan gasa?" Inji Gazman. Anan Amran yayi murmushin jin dadin ganin cewa ya fara shawo kan Yarima Gazman.
   " Wannan yafi kome sauki," Inji Amran, " Wannan masarauta ta ƙabru sunada wata al ada tasu tun kaka da kakanni, ita wannna al ada tasu asalinta shine:
   A zamanin baya tun kafin wanzuwar masarautar Ƙabru, an yi wani mahalbi mai suna Ƙabar, shi wannan mahalbi yana zaune ne a wani ƙaramin sansani nasu a cikin daji, sana ar mutanen wannan sansani shine halbi, to wata rana sai aka wayi gari wasu arnan daji sun kawowa sansanin mutanen Ƙabar hari. Cikin rashin tausayi wadannan mutane suka yita kone gidajensu da kuma kwashe musu dukiya, wannan hari da aka kawo yayi sanadiyar mutanen  Ƙabar gaba daya sun mutu da yake sansanin nasu ba yawa, dakyar Ƙabar ya tsira yana gudu yana gurmanta har ya samu maboya a cikin wani kogo,a wannan kogon yayi ta zama yana jinyar rauninsa kuma yana cin ya yan itatuwa domin sune abincinsa, su kuwa ruwa basa masa wuyar nema domin kasar wurin mai albarka ce, da yayi gina kadan sai ruwa su fito, bayan ya warke sarai daga rauninsa sai yaci   gaba da tafiya abunsa da zimmar cimma gari, a haka yayita tafiya ba dare ba rana har ya cimma wani wuri gwanin ban sha awa, ga itatuwa ga furanni ga kuma korama na gudana, a lokacin daya iso wannan wuri a cikin dare ne kuma ga gajiya data addabesa, sabida haka bai tsaya wata wata ba sai ya samu wurin domin kwanciya da zimmar cewa gobe zai duba ingancin wurin, ai kuwa kwanciyarsa keda wuya sai ya fara jin ihu da kururuwa na mace kamar daga can nesa, firgigit ya farka yana tunanin ashe da rabon yaga wani mutum domin rabonsa da ganin mutum tun baya kona masa sansani da akayi, anan ya fara bin inda sautin ke fitowa, haka yayita tafiya yana jin muryar na matso sa, saura kiris ya cimma wurin da yakejin kukan kuma sai yaji tsit anyi shiru, anan Ƙabar yayita dube dube amma baiga kowa ba, anan yacigaba da tafiya ko zai dace amma hoho bai ga kowa ba.
Page 7
   Ƙabar tsaye yayi a wurin yana dube dube ko zai kara jin muryar amma bai ji kome ba, sabida wannan dalili ya koma makwancinsa da nufin cewa gobe zai kara dubawa, bayan safiya ta waye, yana kammala kalaci sai ya shiga dube dube ko zai ga mai kukan jiya amma bai ga kome ba, da farko yayi niyar tafiyarsa amma sai yaga bari ya kara tsayawa wata kila ya kara jin muryar a cikin dare, ai kuwa dare nayi bayan bacci ya fara daukarsa, sai ya kara jin muryar, da sauri ya tashi, cikin kuzari ya nufi inda yakejin sautin na fitowa, sai da yayi tafiya mai nisa kuma sai yaji sautin ya tsaya, Ƙabar yayi bakin ciki sosai na jin cewa sautin ya tsaya domin yasan da cewa bazai iya gano ko waye ba. Anan ya koma makwancinsa amma kafin gari ya waye sai ya samu dubara.
   Tun da kulu kulun safiya Ƙabar ya fara gyara kwarinsa, wasu itace ya saro daga nan ya hada wasu kibau masu tsini, bayan ya kammala sai ya ajiye yana jiran duhu ya gabato, abun ba wuya cikin rashin tsammani sai ga duhu ya karaso, a wannan lokaci Ƙabar ko bacci bayaji jira kawai yake ya fara jin ihun, ai kuwa sai da angaje ya fara dibarsa kafin daga bisani ya fara jin kukan, yana tashi bai tsaya wata wata ba kwarinsa kawai ya dauko, anan ya dauko kibiya ya aza, daga nan ya saita dai dai inda yakejin kukan na fitowa, anan yaja ya saki iya karfinsa, ai kuwa yana saki sai zabga da gudu domin a lokacin kukan ya canza salo ne zuwa sheshsheka, a haka Ƙabar yayita bin wannan sauti  har ya cimma wata yarinya, ai kuwa yana zuwa wurinta tausayinta ne ya kamashi domin halbin da yayi ya sameta, dama abunda yasa yayi halbin shine idan ya samu mai kukan, to mai kukan zaici gaba da ihu sabida radadin halbin, shi kuwa sautin kukan yakeso domin da sautin kukan kawai ne zai iya gano ko waye ke kukan, cikin sauri ya cicciɓi wannan yarinyar ya kaita makwancinsa, a nan ya shimfideta daga nan ya dingi yi mata magani da ya'yan itatuwa ba dare ba rana har yarinyar ta murmure, bayan ta murmure ne sai ya bata hakuri akan halbin daya mata kuma ya fada mata dalilin halbin har daga karshe ya nemi sanin labarinta, anan ta basa labari cewa a yanzu haka batada kowa a duniya domin arnan daji sun fatattaki sansaninta, wannan dalili yasa take kuka a kowane dare idan ta tuno da yan uwanta, kuma abunda yasa takeyin shiru a lokacin da yake kokarin ganinta shine tana tsammanin cewa arnan daji ne. Wannan dalili yasa take yin shiru idan taji motsinsa, anan Ƙabar ya lallasheta kuma shima ya bata labarinsa, wasa wasa dai sai soyayya mai karfi ta shiga tsakanin Ƙabar da wannan yarinya mai suna Malliya.
Page 8
Amma kuma Malliya bata aminta da auren Ƙabar ba har sai ya biya sadaki darhami dubu, ba karamin tashin hankali ne ya samesa ba domin yasan da cewa samun irin wadannan makudan kudi haka sai ya yan sarakuna, amma sabida zuciya irin tasa yace ya aminta, anan yayi shirin shiga duniya domin neman wadannan kudi, kwanci tashi har ya isa wani gari, bai sha mugun wahala ba domin sana ar mutanen garin shine " Su " Wato kamun kifi, shi kuma ya kware a wannan harkar. Anan ya samu uban gida mai kudi, Ƙabar yana masa aiki shi kuwa yana biyansa, kwanci tashi har ya tara darhami dubu, anan ya dauki hutun komawa gida anan uban gidansa ya aminta bayan ya masa goma ta arziki. Malliya tayi mamaki sosai ganin cewa Ƙabar ya dawo domin ta debe rai da ganinsa, daganan sai Malliya ta aminta da auren shi kuma yayi alkawarin riketa dai dai gwargwado. A nan Ƙabar da Malliya suka gina gida na itatuwa, daga nan kuma suka auri junansu cikin yarjejeniya cewa zasuyi rayuwa cikin so da kauna, da sanyin safiyar wata rana bayan Ƙabar ya mike domin ya fita farauta, yana tafiya cikin sanɗa sai ya fara jin ihu da kururuwa, abunda ya fado masa arai shine arnan daji ne domin a lokacin da suka kawo musu hari irin wannan ihu suke, takobinsa ya zare daga nan ya gyara kwarinsa da bakansa, ai kuwa cikin abunda baifi dakika ba sai gasu sun nufosa a guje da matsanancin gudu, abunda ya basa mamaki shine wadannan arnan daji sune suka kawo ma sansaninsa hari to amma kuma idan sune to ya akayi suka san inda yake zaune ko kuwa dai hanya ce ta fito dasu a wurin? A haka Ƙabar ya shiga cikinsu yana kunji cikin wani salo da kwarewa, sabida tsananin kwarewa a harkar halbi tun kafin ya riskesu yake rage musu yawa da ruwan kibau, a lokaci guda yakan saki kibiya goma sai dai kaga mazaje na zuba, a haka yayi ta ragargazarsu da kibiya da kuma takobin dake hannunsa. Cikin kankanin lokaci ya gama dasu, daya kawai ya tsira kuma shima da gan gan ne Ƙabar bai hallakasa ba domin yanaso ya bisa domin yaga sansaninsu, haka Ƙabar yayi ta bin wannan mutum mai tafiya yana gurmanta sabida raunin dake jikinsa, sai da sukayi tafiya mai nisa sannan suka iso wani dan karamin sansani, a nan Ƙabar ya labe cikin itatuwa yana kallon yadda mutanen wannan sansani ke gabatar da al amurran rayuwarsu, bayan ya gama kallonsu ne sai ya koma da zimmar cewa zai dawo a cikin dare domin ya dau fansar abunda suka yiwa mutanensa, bayan ya koma sai ya labartawa Malliya abunda ya faru, ita kuma ba karamin dadi ne ya rufe taba jin cewa zai dau fansa akansu domin tanada yakini cewa sune suka hallaka  mutanen sansanin ta.
Page 9
 A cikin dare bayan Ƙabar ya koma a sansanin wadannan arnan daji domin ya dau fansar kisan gillar da suka yiwa mutanensa, abunda ya isko ba karamin basa mamaki yayi ba domin an kone gidajen wannan sansanin gaba daya kuma ga gawawwaki a koina birjik, ko waye ya musu wannan aika aika? A haka Ƙabar yata zagayawa a cikin konannun gidajen ya gani ko akwai abun dauka, anan ya hango wani gida da mai gama konewa ba, da gudu ya shiga domin yaga abunda ke ciki,ai kuwa yana shiga yaci karo da dan karamin akwatin karfe, yana daukarsa sai ya fito waje da sauri domin a lokacin gidan ya fara zubewa  ƙasa sabida zafin wuta, a nan ya kama hanyar tafiya gida, bayan yayi nisa cikin daji ne sai ya fara jin hargowar gudun wasu dabbobi, da sauri ya janyo kwarinsa,yana duba bakarsa sai yaga ya manta da ita a wancan gidan daya tsinci akwatin karfe domin baka ɗaya kawaice yazo da ita.Hakama takobinsa ya manta dashi a gidan, cikin sauri ya aza kibiyarsa daya a saman kwarinsa yana zaman jiran abunda ke karasowa, cikin rashin tsammani sai yaga wasu manyan manyan barewa masu tsananin yawan da bai taba gani ba domin girman nasu ya wuce tunanin mai tunani, abunda ya basa mamaki shine barewa dabba ce mai tsoron dam adam, amma su wadannan barewa ɗin ba haka suke ba, tsaye sukayi suna kallon kallo dashi, to anan ne yasan ba lafiya ba domin idanunsu sun rine jajir, wani karaji sukayi daga nan sukayo kansa, shi kuwa yana ganin haka bai tsaya wata wata ba iyaka wani uban tsalle daya buga, cikin sauri ya haye itace daga nan ya sakoma wata barewa mai shirin biyo bayansa kibiya, yana ganin barewar ta fadi sai ya sabko da gudu ya cire kibiyar ya kara halba ma wata barewa itama ta fadi, a haka yayita gudu yana hawan itace yana halbin wadannan barewowin da kibiya, abun burgewa a wannan yaki shine da kibiya ɗaya yake halbinsu, iyaka idan ya halbi wannan barewa sai ya cire kibiyar daga jikinta ya kara halbin wata, a haka yayi tayi yana gudu yana hawan itace kuma yana halbinsu har sai da ya gama dasu gaba daya, daga nan sai ya dauki akwatinsa na karfe daya ajiye a gefe, daga nan kuma sai ya dauki  barewa ɗaya ya aza a saman kafada ya nufi gida da ita.
   Tun daga nesa Malliya ta hango sa, da gudu ta sheko ta rungumesa daga nan ta kama masa suka ajiye barewar, ita kanta tayi mamakin ganin girman barewar, sabida tsananin gajiya bai iya cewa da ita komai ba, ita ya bari tayi gyran barewar sai da safe sannan ya zayyana mata abunda ya faru, a nan ya dauko akwatin karfe ya buda a gabanta, ba abunda suka gani in banda darhamai, Ƙabar yayi mamaki ganin wadannan kudade haka domin yawan nasu ya bace, a haka dai Ƙabar da Malliya suka cigaba da rayuwa har zuwa wata rana daya fuskanceta da zimmar yin magana
Page 10
  " Inaso kiyimin wani alkawari!" Inji Ƙabar.
  " Fadi kome kake so ya sanyin zuciyata." Inji Malliya.
  " Inaso kiyimin alkawarin cewa wannan gida namu wata rana zai kasance babbar masarautar da babu kamarta a duk fadin duniya."
  " Ka dauka cewa an gama, bayan shi kuma akwai wani?" Malliya ta tambaya.
  " Kuma inaso kiyimin alkawari bayan wanzuwar wannan masarautar to za ayima ta lakabi da sunana."
 " Ka dauka cewa an gama kuma bayan shi akwai wani?" 
  " Kuma inaso kiyimin alkawarin cewa bayan masarautar ta wanzu, duk shekara zasu dinga yin gasa, ita wannan gasa tanada matakai uku, mataki na farko shine sai mutum ya biya darhami dubu, mataki na biyu kuma sai mutum yaci galaba akan sadaukai dubu, matakin karshe kuma za nemo barewar daji kala kala har kwara dubu, a dauresu a cikin keji, kuma za a daga kejin a can kololuwar sama. Daga nan sai a baiwa mutum kwari da kibiya daya. Anaso mutum yayiwa kowace barewa halbin da jini zai fito amma kada ta mutu, kuma da kibiya daya, ma ana idan mutum ya halbi wannan barewa to zai sheka da gudu ya fito da kibiyar daya halbeta daga jikinta ya kara halbin wata barewar da kibiyar, kuma anaso mutum yayi taka tsan tsan don kada kibiyar ta karye domin data karye to mutum ya fadi, da zaran mutum ya kammala wannan mataki to yaci gasa!" Inji Ƙabar.
   " To amma meye dalilinka na sanya wannan gasa?" Inji Malliya.
   " Dalilina shine inaso a tuna dani domin nayi bajintar daba kowane namiji zai iya ba, kada fa ki manta kafin na aureki sai da na biya darhami dubu, kuma kada ki manta nayi yaki da sadaukai dubu na samu galaba akansu, kuma kada ki manta nayi yaki da barewa har dubu kuma na hallakasu, kinga kuwa wannan abun dubawa ne."
   Anan Malliya ta tuntsire da dariya tana kallonsa, "Na yarda kayi bajinta daka biya darhami dubu, kuma na yadda kayi bajinta daka samu galaba akan sadaukai dubu amma fa kada ka manta ita barewa bai kamata ka lissafo ta a cikin aiki na bajinta ba."

Page 11
   " Dama ace zakuna ne kayi faɗa dasu ko kuma kuraye da sai ka samu jinjina amma wai barewa fa." Anan ta kara tuntsirewa da dariya tana kallonsa.
   " Ke saurara kiji," Haka Ƙabar ya fada a fusace. " Zan miki wata tambaya kuma inaso kiban amsa."
   " To ina saurare." Inji Malliya.
   " Yanzu idan zaki halbi barewa uku kibiya nawa zakiyi amfani da ita?"
   " Kibiya uku mana." Inji Malliya.
   " To idan zaki halbi barewa goma kibiya nawa ya kamata kiyi amfani da ita?"
   " Kibiya goma mana." Inji Malliya.
   " To amma kin san wani abu?" Ƙabar ya tambaya.
   " A a sai ka fada!" Inji Malliya.
   " Ni a lokacin danayi yaƙi da barewa dubu ban yi amfani da kibiya dubu ba, nayi amfani da kibiya ɗaya, idan na halbi waccan na halbi wannan kuma haka na hallakasu gaba ɗaya ba tare da kibiyar ta karye ba." Anan Malliya tayi shiru tana jinjina maganar domin ko a mafarki bata taba jin wanda yayi irin wannan ba balantana ace wai a zahiri abun ya faru. Wai kuwa da gaskene ko kuwa dai yana sharara mata ƙaryane domin ta kara sonsa?
    " A cikin gasar kace kanaso ne mutum ya halbi kowace barewa  jini ya fito ba tare da sun mutu ba, hala ka manta kai kanka bakayi haka ba tunda kashe barewowin kayi?" Inji Malliya.
    " Wannan ba wani abu bane a wurina domin da ace naso da zan yi hakan!" Ƙabar ya bata amsa.
    " To amma meya hanaka yin hakan?" Malliya tambaya.
    " Sabida barewa din danayi fada dasu basu cikin hayyancinsu, da alama akwai abunda ke damunsu, kada fa ki manta barewa dabba ce mai tsoron mutum amma wadannan tsaye sukayi suna kallona har daga karshe suka kawo min farmaki. Kinga kuwa dole na hallaka su!" Inji Ƙabar.
    " To amma a tunaninka waye zai iya yin irin wannan jarumtar da kayi?" Malliya ta tambaya.
    " Komi na duniya sanya kai ne tunda ni ya akayi nayi!" Inji  Ƙabar, anan malliya tayi shiru da alama bata san amsar da zata bashi ba, can sai ta nisa tace.
     
Page 12
  " To amma duk wanda ya samu nasarar wannan gasa wace kyauta ce kake gani ya kamata a basa?" Inji Malliya. Anan  Ƙabar ya dauko kwarinsa da baka ya mika mata.
  " Na gaji wannan kwari daga mahaifina kuma shima ya gaje shi daga mahaifinsa. Kuma hasalima kafin mahaifina ya gaji wannan kwarin sai da  aka naɗashi sarkin mahalba na sansanin mu gabaki daya, haka nima kafin ya bani wannan kwarin sai da na samu wannan sarautar ta sarkin halbi, sabida haka duk wanda yaci wannan gasa dana zartar, to ya cancanci mallakar wannan kwari nawa da baka masu kundin tarihi da nasaba." Anan malliya ta kalli wannan kwari da baka, in banda sheki ba abunda yake.
      " Zanyi kokari wurin ganin cewa wannan buri naka ya cika." Inji Malliya.
Cikin jin dadi Ƙabar ya rungumeta yana shaukin abunda ta fada masa. A haka Ƙabar da Malliya suka hayayyafa, zuri' ar su ta bunkasa har wurin ya koma birni. Kuma wannan birni shine masarautar Ƙabru, kuma an saka sunan ne sabida wannan jarumin mahalbin wato Ƙabar,  Ƙabar shine mutum na farko daya assasa garin kuma ya wanzar dashi. Tun bayan wanzuwar wannan masarauta ta Ƙabru ake gabatar da wannan gasa a kowace shekara, shekaru daruruwa da suka wuce amma har yanzu ba a taba samun gwarzon da ya samu nasarar wannan gasa ba, mafi yawa a mataki na biyu suke faduwa, kalilan ne ke kaiwa a mataki na uku kuma suma a can ake watsar dasu.
    " To kaji tarihin wannan gasa." Inji Amran bayan ya kammala baiwa Gazman labarin gasar. " Kuma gobe ne za a yi wannan gasa domin gobe ne karshen shekara sabida haka idan ka aminta sai mu shiga tare idan yaso duk wanda ya samu nasara shi kenan gimbiya Zahra Zu zata kasance tasa."  Inji Amran din.
    " Na aminta, kuma zan shiga." Haka Gazman ya fada yana murmushi. Anan Gazman ya mike da nufin daukar akwatinsa na karfe.
    " Wai menene a cikin akwatin?" Amran ya tambaya
    " Meye ruwanka  a ciki, idan lokaci yayi zaka sani." Haka Gazman ya fada ba tare daya juyo ba daga nan ya dauki akwatinsa.
   " To me zai hana ka kwance min wannan kacar tunda mun yi sulhu." Inji Amran. Anan Gazman ya juyo yana masa murmushin raini.
   " Kai a tunaninka zan yarda da kai ne cikin sauki?" Inji Gazman.
   " To idan aka kawo mana hari ya za a yi na kare kaina?" Amran ya tambaya.
   " Zan kareka!" Inji Gazman.
   " Idan ka gaza fa?" Amran ya tambayesa. Anan Gazman yayi murmushi yana kallonsa.
   " Inason kasancewa  dakai ko sabida nishadin da kake sanya min." Inji Gazman.
Page 13
   " Amma ka sani a tarihina ban taba faduwa gasa ba kome tsananinta kome wuyarta kuma a tarihina ban taba faduwa a yaki ba kome tsananinsa kome wuyarsa. Sabida haka zan kwance ka." Anan Gazman ya dauko wani tsinke a cikin akwatinsa na karfe ya sokawa Amran shi a kirji, sai da Amran yayi yar karamar kara. " Wannan tsinke da kake gani guba ne, kuma zaka yita jin kasala har zuwa gobe, gobe kuma zan baka magani ka warke."
  " To meye amfanin sanya min guba a jikina?" Amran ya tambaya.
  " Sabida kada ka tsere, yadda ko ka gudu to bazaka iya tafka komi ba domin jikinka ba karfi,sabida haka ka taimaki kanka kada ka tsere idan yaso zuwa gobe zan baka magani sai ka warke." Anan Gazman ya zaro wani bakin gatari, sara daya yayiwa kacar ta zube gaba daya. Anan Amran ya mike tsaye, ai kuwa yana mikewa  sai yayi caa zai fadi sai da Gazman ya rikosa, anan yaji kasala da rashin kuzari sun rufe sa wato da alama gubar ta fara aiki a jikinsa.
   " Anan zamu bar gimbiya Zahra Zu, zamu shiga wani daki muyi bacci ni da kai idan yaso zuwa gobe zan baka magani ka warke daga nan sai mu gabatar da abunda ke gabanmu, ina fatan ka fahimta!" Inji Gazman.
    " E na fahimta!" Amran ya amsa. Anan gazman ya taimaka masa suka fita dakin a sanda domin kada motsinsu ya tayar da dakaru, wani daki suke shige sukayi baccinsu da zimmar cewa gobe zasuyi abunda ya kawosu.
     SHIN WAI TSAKANIN YARIMA AMRAN DA YARIMA GAZMAN WAYE ZAI CI WANNAN GASA?
KUMA A CIKINSU WAYE ZAI MALLAKI GIMBIYA ZAHRA ZU?"
       IDAN YARIMA AMRAN YA MALLAKI GIMBIYA ZAHRA ZU TO WANE ABU NE ZAI YI DA ITA?
       KUMA IDAN YARIMA GAZMAN YA MALLAKI GIMBIYA ZAHRA ZU WANE ABU NE ZAI YI DA ITA?"
MU HASU A SASHE NA BIYU DOMIN JIN CIGABAN WANNAN LABARI.
To be continue in episode two........


                                                                        GIMBIYA   ZAHRA ZU
                                                                                     by
                                                  Abdul King Article & Abdul Alhaji Musa 10K
                                                                                Episode 2
                                                                          Labarin Zahra Zu
First class admin of King Article Novels Naxeer Hr
Page 14
Tunda kulu kulun safiya Amran ya tada Gazman domin ya basa maganin wannan guba dake jikinsa, anan Gazman ya dauko akwatinsa na karfe, a ciki ya dauko wani tsinke ya soki Amran a kirji, yin hakan keda wuya sai Amran yaji wani bacci mai karfi, a nan ya kishingida kafin kaceme bacci yayi awon gaba dashi, haka shima Gazman juyawa yayi yaci gaba da baccinsa, suna cikin bacci ne sai suka fara jin hayaniyar mutane, da farko basu dauki abun da tsauri ba amma duba da irin yadda abun ya tsananta, dole suka fara shirye shirye domin a tunaninsu gasar ce za a fara, Amran sanya rawaninsa yayi daga nan ya rufe fuskarsa da bakin kyalle, shi kuwa Gazman shigarsa ta sulken yaki ya kara gyarawa daga nan suka fita tare, suna fita suka tarar dakaru sun cika masarautar gabaki daya, ganin haka ba karamin tsorata sukayi ba domin sun san cewa ba lafiya ba. Anan wasu dakaru suka basu umarni da cewa suje can kasan masarautar a cikin wani fili da alama akwai taro da za a yi a cikin filin, Anan Amran da Gazman suka nufi wannan fili, a wannan lokaci Amran garau yakeji domin gubar ta sakesa tunda Gazman ya basa magani, bayan sun isa filin ne sai suka tarar da mutanen gari sun cika filin  makil. Can sai wani mutum ya fito cikin kaya na alfarma a can saman benen gini inda kowa zai gansa, fitowarsa keda wuya sai fili yayi tsit da alama akwai maganar da zai gabatar. Anan mutane suka daga kai suna kallonsa domin jin abunda zai ce.
    " Tun wanzuwar wannan birni namu ba a taba yin shekarar da ba a gabatar da wannan gasa da muka gada kaka da kakanni ba, amma yau anyi wayi gari wata masifa ta fado muna, kuma a sanadin wannan masifa bazamu iya gudunar da wannan gasa ba, yau munyi wayi gari cikin rashin gimbiyar mu Zahra Zu, kuma muna kyautata zaton cewa an yi garkuwa da ita ne kamar yadda aka yiwa kakanta wato tsohon sarkinmu Barhan, babbar matsalar itace ba a san ko su waye sukayi wannan aika aika ba kuma ba a san meye dalilin yin hakan ba, sabida haka mun bada umarni cewa ba shiga ba fita a wannan birni har na tsawon wasu kwanaki, kuma a cikin wadannan kwanaki zamu yi bincike mai tsanani kuma muna bukatar hadin kanku."
Page 15
Mutumin yana kawowa a nan sai ya juya ya tafiyarsa su kuwa dakaru suka rufa masa baya, anan Amran da Gazman suka fara mamakin abun domin sufa jiya jiya sun ganta amma ace kafin wayewar gari wai anyi garkuwa da ita, anan mutane kowa ya kama gabansa su kuwa su Amran juyawa sukayi suka nufi dakin Zahra Zu dake can saman bene domin su tabbatar da maganar, ai kuwa haka akayi, suna shiga suka tarar wayam ba kowa, anan sukayi tsaye tsuru tsuru cike da mamaki domin a daren jiya din basuji wani motsi ba balantana suce ga wanda ya shigo.
  " To yanzu meye abunyi?" Inji Amran.
  " Mu fita waje domin muga abunda ke faruwa." Gazman ya bashi amsa. Anan suka fito waje a tsakiyar filin masarautar suna dube dube. Suna cikin hakane sai suka fara jin kururuwa daga nesa, cikin sauri suka zuba da gudu basu damu da mutane na kallonsu ba, a lokacin da suke gudun sauran mutane hankalinsu ya dawo ga kururuwar, a haka su Amran suka yita gudu har suka cimma kofar garin, anan ne suka tarar cewa dakaru ne ke kokarin kulle kofar garin sabida hango wasu miyagun barewowi a cikin  matsanancin gudu suna kokarin shigowa garin, duk kokarin da dakaru sukayi na kulle kofar yaci tura domin sai da wasu yan kazagi a cikin barewowin suka shigo, su wadannan barewowin ba kamar saura suke ba domin manya manya ne kuma abun tsoro, ga wasu manyan hakora da suke fama dasu masu tsananin tsini, idanuwansu sun rine jawur kai da gani kasan ba lafiya ba, daga shigowarsa cikin garin suka hau mutane da masifaffen yaki, idan suka bugi mutum haka zaiyi majaujawa kamar an cilla shi, yana fadowa zai ragargaje, haka kuma idan sun bugi mutum zasu iya binsa da matsanancin gudu, kafin ya fado kasa sai su caɓe sa su ɗebe masa kai sai dai gangar jiki ta faɗo, anan hankalin mutane ya tashi, kafin kaceme an fara guju guje su kuma dakaru na ganin haka dole sukayi caa da wadannan barewowin anan azababben yaki ya barke. Cikin wannan gumurzu da ake Amran da Gazman sun lura da wannan mutumin da yayi musu jawabin cewa anyi garkuwa da gimbiya Zahra Zu, tsaye yake a can gefe cikin shigarsa ta sarauta, dakaru sun zagayesa domin basa tsaro shi kuwa sai kallon wannan gumurzu yake, hankalinsa a tashe yake irin yadda yaga wadannan barewowin suna yiwa dakaru kisan walakanci, cikin kankanin lokaci wadannan barewowin suka sheƙe dukkan dakarun daga nan sukayo kan wannan mutum mai shiga ta sarauta.
Page 16
Anan dakarun dake gadin wannan mutum sukayi kukan kura, daga nan suka fadama wadannan barewowin, anan masifaffen yaki ya kaceme, tunda aka fara wannan gumurzu jikin wannan mutumi ke karkarwa sabida tsananin tsorata domin wadannan Barewowin in banda kisan gilla ba abunda sukewa dakarunsa, cikin kankanin lokaci suka gama da dakarun daga nan sukayo kansa suna gurnani, anan ya fara ja da baya yana karkarwa, su kuwa su Amran na ganin haka kallon juna kawai sukayi daga nan sukayo wani uban tsalle a tare sai gasu a tsakiyar wadannan barewowin, anan barewowin suka fara kallonsu shi kuwa wannan mutumi a wannan lokaci ya samu wurin ɓuya rakuɓe ga wani gini, wani gurnani wadannan barewowin sukayi a tare mai hauhawa kafin suyo kan su Amran, su kuwa jaruman guda biyu wato Amran da Gazman fito da makamansu sukayi, Amran ya fito da kwarinsa sai bakarsa, shi kuwa Gazman wani bakin gatari ne ya fito sai wata yar karamar takobi.
   Anan wannan mutumi ya bude baki yana kallon yadda wadannan jarumai guda biyu  suke fafatawa da wadannan barewowin, Amran kan saki kibiya goma a lokaci daya cikin salo da gwaninta, shi kuwa Gazman cikin kwarewar yaki yake sarrafa gatarinsa da takobinsa, a haka wannan mutumi yayi ta kallon wannan gumurzu yana murmushi tare da tunani, da alama wannan yaki yana tunatar dashi wani abu daya faru a baya amma kuma wannan abu ko menene? Bayan su Amran su sheƙe wadannan barewowin sai mutumin ya sheƙo da gudu wurinsu cike da murmushi da sakin fuska.
   " Ban san irin yadda zan gode muku ba, domin kun yi abunda manyan dakaru na wannan birni suka kasa, sabida haka idan bazaku damu ba zan so ku bini a gidana domin na gabatar da kaina a wurinku." Yana fadar haka sai ga wasu dakaru a saman dawakai a guje sun nufosa, a nan ya hau wani doki daga nan ya nunawa su Amran dawakan da zasu hawa.
   " Kada ka damu zamu hau namu dawakan." Inji Gazman. Anan yayi wata busa mai karfi da bakinsa sai ga dokinsa ya sheko da gudu, haka shima Amran yanayin busar sai ga dokinsa yazo wurinsa, anan wannan mutum ya cika da mamakin wannan al amari na wadannan baki nasa. Bayan su Amran sun hau dawakansu  sai sai suka gane cewa ashe mutanen gari suna kalle da abunda ke faruwa. Ai kuwa suna wucewa sai mutane suka hau su da kirari  da  jin jin musu.
Page 17
Anan gari ya dauka gaba daya cewa anyi wasu jaruman baki masu fadi aji, bayan su Amran sun isa gidan wannan mutum, anan suka gane cewa lallai mai arziki ne domin girman gidan kadai ya isa ya tabbatar musu da hakan, tunda aka bude musu babbar kofar gidan ba abunda suke gani in banda barori da dakaru sai harkar gabansu suke, fili ne makeke suke ta wucewa, sai da sukayi tafiya mai nisa kafin su iso ga wani narkeken gida, iya tsaruwa ya tsaru domin su kansu su Amran sai da suka tsaya kallon gidan duk da kasancewarsu ƴa ƴan sarakuna, anan yayi musu iso a cikin babbar fadarsa, bayan sun zauna ne sai barori suka gabato musu da kayan ciye ciye. Anan wannan mutumi ya zauna tsakiyar babbar kujera domin ya gabatar da kansa.
  " Ina kara yi muku godiya akan wannan gudummuwa da kuka baiwa wannan birni namu, zaku iya kirana da Hamim, nine wazirin wannan masarauta ta Ƙabru kuma da alama ku baki ne sabida haka zanso naji sunayenku da kuma abunda ya shigo daku a wannan birni namu."  Anan su Amran suka fara tunanin irin ƙaryar da zasu shaƙa masa domin bazasu iya fada masa cewa sun shigo ne sabida gimbiya Zahra Zu ba, can sai Gazman ya nisa daga nan sai ya fara magana.
   " Ni sunana Gazman shi kuma wannan abokina ne Amran, kuma mun shigo wannan birni naku da zimmar yin kasuwanci!"
   " Kasuwanci kuma! To idan ku yan kasuwane ta ina kuka koyi yaki da sarrafa makamai?" Haka Hamim ya fada cikin alamar zargi. Anan Gazman ya gano cewa yayi kuskure daya fadi haka, dole yayi shiru domin bai san amsar da zai bayar ba. Shi kuwa Amran da yaga asirinsu na shirin tonuwa sai yayi sauri ya amshe maganar.
   " E da yake mu asalinmu dakaru ne a karkashin sarki Jalil na birnin Kistab, amma kuma muna taba kasuwanci ba sosai ba, to sabida kasancewarmu dakaru shi yasa muka samu horo mai tsanani a fannin yaki da kuma sarrafa makamai."
    " Na fahimta," Haka waziri Hamim ya fada cikin amincewa da maganar Amran. " Ku dan jirani zan dawo." Anan ya tashi ya shiga wani lungu na gidan. Su kuwa su Amran ajiyar zuciya suka farayi domin saura kiris da asirinsu ya tonu.
    " Kayi hakuri abokina, nasan nayi kuskure akan abunda na fada!" Haka Gazman ya fada cikin takaici.
    " Kada ka samu damuwa ai kowa na kuskure!" Inji Amran.
Page 18
  " Gashi na fada masa sunayenmu na gaskiya to idan ya gano asalinmu ya kenan?" Gazman ya tambaya.
  " Bazai iya gano kome ba sabida ai bani kadai ne Amran ba,  za a iya samun wani, haka kuma ba kai kadaine Gazman ba za a iya samun wani, abun dubawa anan shine za a iya samun wasu masu irin sunayenmu kaga kuwa tunda hakan zata iya kasancewa bazai iya gano kome ba." Inji Amran.
   " Ka fadi gaskiya abokina." Inji Gazman. Can sai ga Hamim ya fito, zaunawa yayi kafin ya fara magana.
   " Na yanke shawarar cewa zaku cigaba da zama a gidana har zuwa lokacin da aka kammala bincike, idan yaso daga nan zaku iya tafiya duk inda kukeso." A haka Amran da Gazman suka yita zama a gidan waziri Hamim, basuda matsala da masaukinsu domin an tanadar musu duk wani abu na more rayuwa. Abunda ke basu mamaki shine waziri Hamim ya kasance kullum a cikin bakin ciki yake, sukan yi mamaki idan suka gansa a cikin wannan hali domin a ganinsu mutum mai arziki irinsa bai kamata ace yana rayuwar bakin ciki ba, sau da yawa sukan gansa zaune shi kadai rike da fatar damisa biyu, yakan kura musu ido yana zubar da hawaye, da alama akwai abunda yake kallo a cikin fatar amma wannan abu ko menene? Da farko su Amran sun so su kyale maganar amma da sukaga yin hakan zai sakasu cikin tunani sai suka yanke shawarar tuntunbarsa. 
   Hamim ne zaune a saman kujera kusa ga itace a cikin babban filin gidansa yana kallon dakaru na daukar horo sai kuma barori dake kai komo a cikin gidan, tebur ne a gabansa cike da kayan marmari amma ko kadan hankalinsa baya wurinsu,fatar damisa guda biyu dake gabansa  yake kallo yana zub da hawaye, a wannan lokaci rana ta fadi sai iska ke kadawa abun gwanin ban sha awa, yana cikin wannan hali ne sai ga Amran da Gazman sun fado a gabansa, kujerun dake kusa dashi guda biyu suka janyo suka zauna, daga nan sai Amran ya fara magana kamar haka:
   " Ba abunda na tsana irin naga mutum cikin halin ƙaƙa nikayi, a duk lokacin da naga mutum cikin wannan hali nakanyi kokarin cewa na tambayesa matsalarsa domin na gani idan zan iya taimaka masa, na dade da sanin cewa baka cikin nishadi sabida haka me zai hana ka bamu labarin abunda ke damunka wato kila zamu iya yin wani abu akai."
Page 19
Anan waziri Hamim ya dago kai yana kallonsu daya bayan daya, daga nan sai ya mika musu wadannan fatocin nasa, anan Amran ya rike dayar shima Gazman ya rike daya, ita fatar da Amran ya rike an zana taswirar wasu yara mata biyu wadanda kamaninsu ya bace, ita kuma fatar da Gazman ya rike an zana taswirar daya yarinyar ta cikin fatar da Amran ya rike da kuma wani yaro kyakkyawa. Daga nan sai waziri Hamim ya fara magana kamar haka.
   " Nasan bazaku iya share min hawaye ba, amma zan baku labarin abunda kuke bukata kodan ku samu natsuwa, wannan taswirar ta yan mata biyu da kuke gani Zahra Zu ce tare da yar uwarta wadda suke uwa daya uba daya wato Zuhru Zu, ita kuma daya taswirar Zahra Zu ce tare da masoyinta wato Zabir wanda yake ɗana ne na cikina, ni da kaina na zana wannan taswirar a lokacin sunada shekara goma goma. Sabida haka sai ku kasa kunnuwanku kuji domin yanzu zan fada muku abunda ya faru shekaru da dama da suka gabata:
    Tun bayan da aka naɗa  yarima Mahir a matsayin sarkin da zai cigaba da gudanar da al amurran masarautar Ƙabru abubuwa suka samu cigaba sosai duk da cewa yana cikin jimamin rashin mahaifinsa sarki Barhan da akayi garkuwa dashi, a wannan lokaci babban aminin Mahir shine Hamim, shi kuma Hamim dan wazirin garin ne wato Nashab, sabida kunci da damuwa da Mahir yake ciki, sai amininsa Hamim ya nemi umarni a wurin mahaifinsa Nashab cewa yanaso ya basa karagar mulkinsa wato wazirintaka domin a hakane kawai zai iya taimakon abokinsa ya kuma shawo kansa a kan matsalar da yake ciki, kamar yadda ya zayyana wa Nashab cewa Mahir ya kasance a cikin damuwa sabida rashin mahaifinsa da akayi garkuwa dashi, kuma babbar matsalar itace ba a san abunda yan garkuwar din suke bukata ba domin har yanzu basu aiko sako ba.
   " Sabida haka idan na zamo wazirinsa zan taimakesa dai dai gwargwado har sai inda karfina ya kare." Inji Hamim. Anan waziri Nashab ya cire rawaninsa ya naɗawa Hamim.
   " Ka dauka cewa kaine wazirin masarautar Ƙabru , rantsar da kai kawai ne ya rage kuma zuwa gobe zan sa ayi haka." Inji waziri Nashab. Anan Hamim ya rungumesa mahaifinsa cikin jin dadi da annashuwa.
   " Ina godiya mahaifina." Inji Hamim.
Page 20
  " Kada ka damu ɗana zan iya yima fiye da haka." Inji waziri Nashab. Tun da sanyin safiya aka fara shirye shiryen rantsar da Hamim, a wannan lokaci masarautar Ƙabru ta cika sosai domin duk wani mai fadi aji sai da ya halarto, anyi taro cikin lafiya kuma an kare cikin lafiya daga nan aka naɗa Hamim a matsayin wazirin Sarki Mahir wato babban amininsa, Mahir da kansa yajin dadin wannan naɗi domin abokantakar dake tsakaninsu sai dai a kirata da yan uwantaka. Kasancewar Hamim mai baki da kuma salo na magana, yayi amfani da wannan hikima tasa ya kwantarwa abokinsa Mahir hankali, a haka har Mahir din ya fara shagaltuwa da mulkin dake gabansa. Kwanci tashi sai ga gasar shekara ta faɗo, anan aka fara shirye shiryen domin sarki Mahir yana cikin gwarazan da za a tafka dasu domin tun kafin ya zama sarki duk shekara dashi ake tafkawa, kuma a kowace shekara sai ya taka rawar gani kafin a watsar dashi, wannan gasa ta wannan shekarar an samu gwarazza dari cif cif da suka samu damar biyan darhami dubu, duk jarumin daya biya kudin akan basa wata karamar fata mai wani zanen wani tambari, shi wannan tambari shi ke nuni da cewa mutum ya biya, kuma dole ne mutum ya gabatar da fatar kafin dakaru su yadda ya shiga filin gasa, ga dokar wannan gasa duk wanda ya biya kudi za a karba kuma babu adadin mutanen da ake bukata domin ko mutun nawa sukazo za a karbesu indai sunada kudin biya. Iyaka a cikin gasar za a hadasu fada da juna ne, duk wanda bayansa ya gogi kasa toya fadi daga nan sai dakaru su caɓesa suyi waje dashi, kuma duk wanda ya faɗi ba za amayar masa da kudinsa ba, a haka za a yita hadasu fada da juna har sai ya zama gwarzo daya ya rage, to shi wannan gwarzo shine zai fuskanci sadaukai dubu, idan yayi nasara akansu sai ya hau mataki na karshe wato halbin barewa. A cikin mutum ɗari da suka biya kudin wannan gasa akwai mace huɗu, kasancewar mata a cikin wannan gasa ba karamin mamaki mutane suka yiba sabida  ba a taba samun mata a cikin wannan gasa ba, wannan dalili yasa mutane daga birane daban daban suka samu damar halartar wannan gasa domin ganin abunda zai faru, masarautar Ƙabru ba karamar daukaka ta samu akan wannan gasa ba domin mafi yawan birane akan wannan gasar suka san dasu, haka kuma masarautar Ƙabru ta tara dukiya mai tarin yawa a dalilin wannan gasa domin duk dan kallon da zai shiga filin gasar to sai ya biya darhami goma, kuma idan ya biya za a bashi shaidar da zai nunawa dakaru domin su bari ya shiga filin gasar.
Page 21
Shi kansa Mahir yana ji a jikinsa cewa gasar wannan shekara ta banbanta data saura, domin a can da yana yarima sabida haka ko ya fadi ba matsala, amma yanzu a matsayinsa na sarki idan ya fadi tofa akwai kunya,  a lokacin da yana yarimansa kafin ayi garkuwa da mahaifinsa, mafi yawan lokutta tun farkon fada da junansu ake masa wawan kaye, anan dakaru zasu caɓesa suyi waje dashi ba ruwansu da matsayinsa na yarima, wannan abu kan bakanta masa rai irin yadda dakaru ke ingiza keyarsa waje idan ya fadi, iyaka dai doka ce ba yadda ya iya. To yanzu da yake sarki idan ya fadi dakaru suka ingiza keyarsa waje ai kuwa zai ji kunya, a bisa wannan dalili ne ya kira abokinsa Hamim domin ya basa shawara.
   " Gaskiya na fasa shiga wannan gasar." Inji Mahir a tsorace.
   " Wai kai wane irin mutum ne hala? fasawarka shiga wannan gasa zai sa mutane su tabbatar da abunda suke tunani!" Inji Hamim.
    " Hala menene mutane ke tunani?" Mahir ya tambaya.
    " Suna tunanin cewa kai raggon namiji ne kuma yaro wanda bai cancanci karagar mulki ba, kaga kuwa ya kamata ka shiga wannan gasar kodan ka nuna musu cewa kai jarumin namiji ne wanda ya cancanci karagar mulki." Inji Hamim cikin kakkausar murya, " Kuma ka sani cewa manyan sarakuna na duniya sun shigo wannan birni naka domin su kalli wannan gasar, amma ka sani ba wai gasar sukeson kallo ba, aa, suna so kawai suga irin jarumtakar ka da kuma jumriyar ka sabida haka idan kayi wasa zamuji kunya gabaki daya!" Inji Hamim.
  " To amma ya akayi kasan da cewa manyan sarakuna sun shigo kallo wannan gasa?"Mahir ya tambaya.
  " Kada ka manta nine wazirin garin nan, kuma yana daga ciki aikina na tabbatar da tsaro da kuma sanin masu shige da fice a wannan birni namu, sabida haka ka yarda dani cewa manyan sarakuna sun shigo wannan birni domin kallon wannan gasa.
  " To yanzu wace shawara zakaban?" Hamim ya tambaya.
  " Shawarata a gareka shine ka nemi sarkin yaki Baidu domin ya baka horo mai tsanani kafin zuwan wannan rana ta gasa." Inji Hamim.
   " Tun tuni inada horo a fannin yaki, kaga kuwa bana bukatar wani horon." Inji Mahir.
   
Page 22
   " Inaso ka sani cewa Baidu yana daya daga cikin sadaukan da suka baka horo mai tsanani a kasancewarsa na sarkin yaki na wannan birni kuma gwani a wurin sarrafa makamai da dabarun yaki, Baidu yayi zamani da mahaifinka wato Barhan kafin ayi garkuwa dashi, kaga kuwa kodan dadewarsa a wannan fanni ya kamata ka girmamasa domin bazaka taba hada gwanintarka da tasa ba." Inji Hamim. Anan Mahir yayi tunani na dan lokaci kafin ya fara magana.
   " Na aminta da wannan shawara taka amma inaso muyi wannan horo a cikin sirri, sabida haka a kullum zamuyi fitar sirri mu iskosa har gidansa domin ya bani horon, kuma wannan zai kasance ne a cikin dare!" Inji Mahir. Haka Mahir ya fara zuwa gidan Baidu kullum a cikin dare domin daukar horon yaki tare da rakiyar abokinsa kuma wazirinsa Hamim, kasancewar gidan Baidu babban gida ne kuma yanada makeken filin da yake horar da dakaru, ana nan ana nan sai ga ranar gasar shekara ta fado, a daren wannan rana sarki Mahir ba karamin horo ya samu a wurin sarkin yaki Baidu ba, domin yana dawowa gida ya fara bacci shine bai farka ba sai da yaji an fara  buga wasu mazajen ganguna masu nuni da cewa ana gab da afara gasa, a wannan lokaci kidi ya  zarce sai wasanni ake gudanarwa a filin gasar kafin sadaukan su fara halartowa, cikin sauri Mahir ya kimtsa daga nan yayi waje abunsa, ko karin kumallo bai tsaya yiba sabida gaggawa, ai kuwa yana fita sai yaci karo da abokinsa Hamim.
   " Me kake yiwa sauri haka? Kada ka manta irin wannan safiyar ba kowa zai yi saurin tashi ba sabida haka ka sanya wani abu a cikinka kafin ka fita!" Inji Hamim. Anan Mahir yayi murmushi cikin kwarin gwuiwa, tare suka zauna a saman kujeru sai tebur a tsakiya. Abinci ne kala kala irin na sarauta, anan suka fara ci suna hira har sai da ya ishesu, daga nan suka fita tare, suna fita dama dakaru suna jiransu, dawakai aka gabato musu, suna hawa suka saki linzami su kuwa dakaru suka rufa musu baya suma a saman nasu dawakan, sai da sukayi tafiya mai nisa kafin su cimma wani gini kayattace, babbar kofar ginin aka bude, suna shiga aka fara taɓi da ihu domin a lokacin dukkan sadaukan gasar sun halarta sarki Mahir ne kawai ake jira, makeken fili ne abun gwanin ban sha awa, an zagaye filin da kujeru kala kala wadanda yan kallo zasu zauna domin su kalli gasar, a can saman benen ginin kuwa alkalin gasar ne tare da masu fadi aji. Hamim da sauran dakaru fita sukayi a filin suka bar sarki Mahir ya jeru da sauran sadaukan.
Page 23
Tunda Mahir ya jeru da sauran sadaukai wadannan matan su hudu ke masa wani kallo wanda bai san abunda suke nufi ba, gashi kowace ta rufe fuskarta da bakin kyalle balantana ya fassara abunda suke nufi. Anan alkalin gasar ya tashi tsaye domin gabatarwa wanda hakan yasa filin yayi tsit.
   " Kamar yadda kuka sani nine naku wato Faris ɗan Haris, kuma nine alkalin wannan gasar, kuma a tare dani akwai mukarabaina wadanda zasu tayani yanke hukunci dai dai gwargwado ba tare da tawaya ba, sabida haka ba tare da bata lokaci ba munaso jaruman gasa su bada hadin kai domin ayi bincike akansu idan basu shigo da wani makami ba," Yana fadar haka sai ya zauna. Su kuwa jaruman gasa su dari tsaye sukayi tare da daga hannuwansu sama, anan dakaru suka dubasu tsaf sai da suka tabbatar da cewa ba wanda ya shigo da ko allura, daga nan sai alkalin gasa ya tashi domin cigaba da bayani.
   " Kamar yadda muka sani wannan gasar tanada mataki uku, na farko shine biyan darhami dubu, kuma dukkan sadaukan wannan gasar sun biya, mataki na biyu shine fuskantar sadaukai dubu, sai mataki na uku shine halbin barewa. To tunda dukkan sadaukai sun biya darhami dubu ba zai yiwu  muce kowanensu zai fuskanci sadaukai dubu ba, sabida haka mun shigo da wata doka wadda zata taimaka mana karancen wahalar wannan gasar, kuma wannan dokar itace zamu hada sadaukan wannan gasa yakar junansu, zasu yaki junansu har sai ya zamo cewa mutum daya ya rage a cikinsu, to mutum dayan daya rage shine zai shiga matakin gasa na biyu wato fuskantar sadaukai dubu, idan yayi nasara akansu sai ya shiga mataki na karshe wato halbin barewa. Sabida haka sadaukan gasa zasuyi fada na hannu da junansu, duk wanda aka kayar to ya fadi, kuma duk wanda ya fadi baza a mayar masa da kudinsa ba." Anan alkalin gasa ya zauna, sai da aka buga ganguna na yan dakiku kafin alkali ya basu umarin farawa. Anan sadaukan gasa suka fara zagayar fili suna kallon kallo kowa na neman gwaninsa, a wannan lokaci Hamim na tare da sarkin yaki Baidu, kowanensu hankalinsa ya koma ga sarki Mahir. Kukan kura sadaukan sukayi daga nan suka fadawa junansu, anan ƴan kallo suka ɓarke da ihu dama abunda suke so kenan, duk wanda aka yiwa kaye sai dakaru su caɓesa suyi waje dashi, anan aka yita zubar da maza har sai da sadaukan suka dawo arba in cif cif.
Page 24
Abunda ya daurewa Mahir kai shine har yanzu a cikin wadannan matan hudu ba wadda akayiwa kaye, daga nan sadaukan suka fara kallon juna kowa na neman gwaninsa, suna cikin hakane sai suka jiyo wani karaji mai amo da hauhawa a can gefensu, cikin tsananin tsorata suka duba domin ganin ko meye, juyawar da sukayi ba abunda suka gani in banda barewowin da aka daure a cikin keji suna fitowa. Kowace girmanta ya wuce misali, abunda ya daure musu kai shine a lokacin da aka sanya barewowin a cikin keji basu kai girman haka ba, amma yanzu halittarsu ta juya zuwa naban tsoro har sun samu karfin ɓalle kejin da aka tsaresu dashi. To wai me yake faruwane ga wadannan barewowin kuma menene sanadin sauya musu halitta? Anan dakarun gasa suka fara ja da baya ganin wadannan barewowin sun zagayesu suna shirin afka musu, kowace sai bude hakora take tana gurnani mai ban tsoro ga idanuwansu jawur ba kyan gani. Haka suma yan kallo ja da baya suke cikin tsoro domin abun ya daure musu kai yadda akayi barewar da aka daure a cikin keji ta ɓalle shi ta fito. Anan wadannan barewowin suka afka wa sadaukan gasa, duk wanda suka mazga sai aga yayi tsalle sama koda zai fadowa sai  ya ragargaje, wani lokaci kuma idan suka mazgi mutum sai da aga kai ya guntule ko kuwa hannuwa, haka suka dingi yiwa wadannan sadaukai kisan gilla kasancewar sadaukan ba wanda ya shigo da wani makami, yan kallo kuwa duk sun rude domin sun san ba lafiya ba, yadda akayi wadannan barewowi suka samu irin wannan karfi haka! Shi kuwa Sarki Mahir tsundumawa yayi a duniyar tunani. Zai iya tuno lokacin da yana yaro, a wannan lokaci baida jarumtaka ko kadan ga kuma tsoron tsiya.  kullum idan mahaifiyarsa tana masa nasiha takan ce:
   " Zonan yarimana." Anan zai zo ya zauna saman cinyoyinta, ita kuma sai ta fara yi masa kirari tana cewa. " Ɗaya tamkar dubu jarumi uban jarumai wanda bai gaji tsoro ba balantana yasan tsoro." A duk lokacin data masa wannan kirari yakan ji kuzari  kuma tsoronsa kan gushe, babban abunda ke bata masa rai shine wata rana mahaifiyarsa sarauniya Lubaiya zata kaiwa kanwarta ziyara wadda suke uwa daya uba daya  a wani sansani mai nisa. A wannan lokaci mafaifinsa wato sarki Barhan bai biyo suba. To akan hanyarsu ne sukayi gamo da yan fashin dare, a can saman itatuwa yan fashin suka labe sai ruwan kibau sukewa dakarun sarauniya Lubaiya, cikin kankanin lokaci suka gama dasu daga nan suka  sabko saman itatuwa rufe da bakin kyalle a fuskarsu, a gaban idonsa suka danne mahaifiyarsa suna kokarin yi mata fyade,ita kuwa in banda kokuwa dasu ba abunda take.
Page 25
To a cikin wannan fada datake yi dasu ne suka hasala suka yi mata wani yanka da takobi a ciki, a nan ta fadi jini na zuba, shi kuwa Mahir da gudu ya sheka ya rungume mahaifiyarsa yana kuka, gashi yaro karami balantana yace yayi fada dasu, ga shi kuma ba jarumi bane balantana yace ya gwada afka musu, a gabansa suka dauki mahaifiyarsa suka jefa a wata korama daga nan suka wawashe duk wata dukiya dake saman dawakan sarauniya. A nan sukabar Mahir cikin bakin ciki ba yadda ya iya, da taimakon wasu matafiya ya samu damar dawowa garinsa inda ya labartawa mahaifinsa abunda ya faru, tun daga wannan rana Mahir ya fara koyon dabarun yaki a makarantar Baidu tare da sauran yara kamarsa, kuma a wannan makaranta ne ya hadu da Hamim wanda ya zama babban abokinsa. Shi kuwa mahaifinsa sarki Barhan alwashi yasha cewa sai ya gano ko su waye sukayi wannan aika aika kuma sai ya hukunta su.
   Koda sarki Mahir yazo nan a tunaninsa sai hawaye ya fara zubo masa, ya manta da cewa a gaban mutanensa yake, zuciyarsa ce ta kara cika a lokacin da yaga wadannan barewowin na yiwa abokan gasarsa kisan gilla, su kuwa sadaukan gasa in banda guje guje ba abunda suke domin a cikinsu ba wanda ke rike dako allura domin an hanasu shigowa da makami a cikin gasar.
   Wani uban ihu Mahir ya saki wanda ya janyo hankalin mutane dawowa kansa, daga nan yayi wani namijin tsalle ya diro tsakiyar wadannan barewowin, su kuwa suna ganin haka sai suka zagayesa suna gurnani, barewar farko data durfafo sa, tsaye yayi yana kallonta, sai da ya bari ta iso sannan ya dunkule hannu ya mata wani sadaukin naushi, iskan dake tattare da karfin naushin ne yayi waliliya da wannan barewar koda ta fado kasa sai akaga cikinta ya bare ana ganin hanji na yawo, a haka Mahir yayita kashe wadannan barewowin cikin sadaukanta da bajinta da naushi ɗaya ɗaya, su kuwa yan kallon wannan gasa wangale baki sukayi cike da mamaki, su kuma sauran yan gasa komawa gefe sukayi suna kallon wannan gumurzu, a haka Mahir yayita kashe wadannan barewowin har sai da ya gama dasu gaba daya. A wannan lokaci sadaukan gasar da suka rage goma ne cif cif hadda Mahir din, sauran sadaukan duk sun mutu wasu kuma sun samu rauni mai tsanani, mata hudun da suka shigo gasar biyu sun mutu biyu sun rayu, kuma su biyun da suka rayu sun samu rauni sosai, a nan yan kallo suka fara ihu suna yiwa Mahir  jin jina bisa wannan namijin aiki daya aikata.
Page 26
  " Mahir, Mahir, Mahir." Haka yan kallo ke fadin sunansa cikin jin jina da kasaita, su kuwa sauran sarakunan duniya da suka shigo kallon wannan gasa in banda bakin ciki ba abunda suke, duk wadanda suka mutu a wannan gasar sai da masarautar Ƙabru taba yan uwansu dukiya mai tarin yawa da kuma basu hakuri akan wannan danyen aiki daya faru, su kuma wadanda suka samu rauni zasu dawo karkarshin kulawar masarautar Ƙabru har sai sun warke sarai, wannan namijin kokari da Sarki Mahir ya aiwatar ya kara masa farin jini da daukaka ga mutanensa da kuma sauran sarakuna na duniya domin ba karamar jarumtaka ya nuna a wannan gasa ba. Shi kuwa sarkin yaki Baidu kamar ya zuba ruwa a kasa ya shanye sabida tsabar farin ciki domin ba abunda ke burgesa irin ya koyar da mutum dubarun yaki kuma mutum ya fito fili ya nunawa duniya cewa shi cikakken jarumi ne kamar yadda sarki Mahir ya aiwatar. Abun burgewa a wannan gasar shine sarki Mahir ya yaki barewa dubu da hannu ba tare da yayi amfani da makami ba kuma ya hallaka su da naushi ɗaya ɗaya. Haka ayita nanata maganar har saida duniya ta shaida cewa sarki Mahir cikaken jarumi ne.
    Duk wanda ya warke daga rauninsa akan basa kyauta mai tsoka daga nan sai ya kama gabansa, a haka ayita yi musu har sai da aka sallami kowa in banda wadannan matan biyu, gashi sun  warke sarai domin ba rauni a jikinsu amma kuma a kullum cikin jimami suke, bisa wannan dalili ne yasa sarki Mahir ya bada umarni cewa a dawo da su cikin masarautar wata kila su samu sauki. Ai kuwa yin hakan keda wuya sai suka saki jikinsu, anan ne dayar ta labartawa Mahir cewa sauran matan da suka mutu yan uwanta ne uwa daya uba daya, kuma sabida rashin sune yasa ta kasa sakewa da kowa ita da kanwarta. Kamar yadda ta labarta masa sunanta Zulaiya, ita kuwa kanwarta sunanta Zulaira, sun fito daga sansanin Kudu dake cikin daji, wannan sansani ana masa lakabi da sansanin budayya, gidajen dake cikin wannan daji basuda yawa sosai amma kuma mutanen sansanin sun yi kaurin suna a fannin sata da kuma garkuwa da mutane. A lokacin data fada masa wannan labari yayi bakin ciki sosai domin yana zargin cewa mutanen wannan sansani sune sukayi garkuwa da mahaifinsa, amma kuma sabida rashin shaida yabar maganar, balantana ba a taruwa a zama daya. A hankali a hankali sai soyayya mai karfi ta shiga tsakanin sarki Mahir da Zulaiya, shi kuwa waziri Hamim a wannan lokaci yana soyewa da Zulaira wato kanwar Zulaiya.
Page 27
Wannan soyayya itace ta kaisu ga yin aure, sarki Mahir da zulaiya shi kuwa waziri Hamim da Zulaira, abu kamar sihiri domin sarki Mahir da waziri Hamim basu tsaya bincike akan wadannan mata ba kuma basu tsaya binciken yan uwansu ba. Bayan shekaru uku ne Zulaiya ta haifi tawayen mata, ɗayar aka sa mata Zahra Zu ɗayar kuwa Zuhru Zu, murna a wurin sarki Mahir bata misaltuwa, haka shima waziri Hamim matarsa ta haifi santalelen saurayi da aka yiwa lakabi da Zabir, a rana daya Zulaiya da Zulaira suka haifu kuma a lokaci daya. An yi shagali sosai kama hannun yaro, Zahra Zu da Zuhru Zu sun taso tare, gasu yan uwan juna kuma abokan juna, a makarantar koyan dubarun yaki suka hadu da Zabir wato dan waziri Hamim, shi kuwa Zabir ko kadan bai damu dasu ba domin a wannan lokaci ba abunda ke burgesa irin ace yayi wani abu na jarumtaka, akwai yan mata da yawa a makarantar da keyin Zabir amma ko kadan bai damu dasu ba, sai dai yanada wani aboki da ake kira Kalim, kalim dan sarkin fada ne kuma yaro ne mai son nishadi a rayuwarsa, tun a ranar daya kyalla ido yaga Zahra Zu yaji ta kwanta masa a rai amma kuma bazai iya fada mata ba domin yasan a duk ranar da gigi ya kaisa yi mata magana tofa kashinsa ya bushe domin Zahra Zu ta tsani raggon namiji shi kuma raggo ne ko kadan bayada jarumtaka, a wannan dalili yasa yake abota da Zabir domin ya karesa daga harin masu son raina masa wayo, Zabir shine jarumi wanda yan mata keso amma shi kuma a cikin ransa ya tsani mata.
    A wannan lokaci dukkansu suna ƴan shekara goma goma, a kullum Kalim kan yini ya tashi da soyayyar Zahra Zu, ba yadda bai yiba domin ya cire sonta amma ya kasa, wata rana sai Kalim ya yanke shawara zuwa gidan kakanninsa domin ya tattauna maganar dasu, ai kuwa yana shiga ciki suka hausa da tsiya, shiru yayi sai da suka gama sannan ya fara magana.
   " Kaka kasan abunda ke damuna?"
   " A a sai ka fada." Inji kakan.
   " Kasan fa ina daukar darasi ne a makarantar koyon yaki, wai ko kasan hanyar da ake bi a samu jarumtaka?"
    " Sosai kuwa, zan iya fadama yadda ake samun jarumtaka amma meye tukwicina tukuna." Inji kaka, anan kaka mace ta dubesu cikin murmushi da alama hirar tasu na burgeta.
Page 28
  " Ka fada kawai ko nawane zan biya." Inji Kalim, anan kaka yayi murmushi kafin ya fara basa labari kamar haka:
A lokacin da ina yaro kamarka, mahaifina ya taba bani labari cewa anyi wani lokaci da wata  kububuwar macijiya ta addabi mutanen wannan birni, ita wannan macijiya tanada kawuna ɗai ɗai har kwara dari, girmanta da karfinta ya wuce tunanin mai tunani domin a wannan lokaci sadaukai da yawa sun yi kokarin ganin bayanta amma ba wanda ya kai labari, a cikin dare take fitowa kuma duk wanda taci arba dashi to zata wuce dashi a matsayin abincinta,a sati sau daya take fitowa a cikin gari ta tafi da mutum daya, a cikin wani bakin kogo dake bayan gari take zama, ita wannan macijiya a duk sati idan taci mutum takan haifi kwai biyu, wato farin ƙwai da kuma bakin ƙwai, shi farin kwai idan mutum ya fashe sa yasha ruwan dake ciki zai zamo farin jarumi, shi kuma bakin kwai idan mutum ya fashe sa yasha ruwan dake ciki to zai kasance bakin jarumi."
    " Menene farin jarumi kuma menene bakin jarumi?" Kalim ya tambaya.
    " Abunda ake nufi da farin jarumi shine mutum zai samu jarumtaka, kuma zai yi amfani da wannan jarumataka ya taimaki mutane, shi kuma bakin jarumi anan nufin mutum zai samu jarumtaka, kuma zai yi amfani da wannan jarumtakar yana azabtar da mutane da kuma muzguna musu." Inji kaka.
   " To menene ban ban cin farin kwai da bakin kwai?" Kalim ya tambaya.
   " Banban cinsu shine a kalar su, zakaga guda fari ne guda kuma baki ne," Kaka ya bashi amsa.
   " To ita wannan macijiya me ya faru da ita, me yasa yanzu bata shigowa a cikin gari?" Kalim ya tambaya.
  " Sabida ta tsufa, yanzu batada karfin daukar mutane, sabida wannan dalili yasa tayi zamanta cikin kogo tana jiran lokacinta." Kaka ya bashi amsa.
   " To amma idan hakane me take ci a matsayin abincinta?" Kalim ya tambaya.
   " Wasu kance macijiyar ta sauya daga halittarta zuwa wata halitta ta daban, kuma wannan sauyawa da tayi shi yasa bata cin mutane." Inji kaka.
   " Me hakan ke nufi?" Kalim ya tambaya.
   " Hakan yana nufin akwai wani abu daya shiga jikin wannan macijiyar kuma wannan abu shine yasa bata cin mutane kuma bata iya shigowa a cikin gari." Inji kaka.
Page 29
   " To amma menene ya shiga jikin macijiyar?" Kalim ya tambaya.
   " Nima ban sani ba." Kaka ya bashi amsa. Anan Kalim yayi shiru yana tunanin wannan labari. Daga nan yayi ban kwana da kakanninsa ya tafiyarsa gida. Washe gari yaje ya baiwa abokinsa Zabir wannan labari kuma yace yanaso ya rakesa su gano kogon macijiyar amma Zabir ya kekasa kasa yaki domin a tunaninsa wannan labari ba gaskiya bane. Anan Kalim ya dauki zimmar cewa zai gano inda macijiyar take komi tsanani. A sirrance Kalim ya fara fita wajen gari yana binciken koguna barkatai, ba dare ba rana a kullum cikin wannan aiki yake har wata rana ya samu kansa a cikin wani kogo, shigarsa keda wuya ya fadi yana huci sabida tsananin gajiya, anan bacci yayi awon gaba dashi, koda ya farka ganinsa yayi kusa ga ƙatanyar macijiya tana kallonsa da alama tana jiran tashinsa ne, ihu ya saki mai firgici daga nan ya fadi sumamme, shine bai farka ba sai da akayi yan dakiku, yana farkawa ya ganta, anan ya kara faduwa sumamme, anan macijiyar ta gane cewa idan sau goma zai ganta to sau goma sai ya suma, sabida haka sai ta daukesa ta ajesa a can nesa da ita, daga nan ta koma gefe tana jiran tashinsa, ai kuwa yana tashi kidimewa yayi domin a ganinsa zata cinyesa ne, da gudu ya juya da nufin tserewa kawai sai yaji kamar an kira sunansa da muryar mace.
   " Kalim." Haka aka fada, cikin mamaki ya tsaya, juyowa yayi a hankali domin yaga waye ke kiransa kawai sai yaga macijiyar ta durfafosa, anan ya fara matsawa da baya cikin tsoro.
    " Kada kaji tsoro bazan cutar dakai ba." Muryar mace yakeji tana fitowa a jikin macijiyar amma abun mamaki bakin macijiyar baya motsawa.
   " Zaka iya kirana da Lauziya." Maganar a jikin macijiyar take fitowa amma kuma bakinta baya motsawa. " Ni ba mutun bace kamar kai da sauran mutanenku, kuma na shiga jikin wannan macijiya ne domin na ceto mutanen wannan birni daga kisan gillar da take musu, kuma sabida ni yasa wannan macijiyar bata shiga cikin gari balantana taci mutane." Haka ta fada bayan ta matso daf da Kalim. " Amma kuma yanzu lokayi yayi da zan fita jikin wannan macijiyar na koma ga yan uwana. Bisa wannan dalili yasa nakeso kayimin alkawarin ganin bayan wannan macijiyar bayan na fita daga jikinta."
   " Ta yaya zan yi haka tunda ni ba jarumi bane." Inji Kalim.
Page 30
   " Kada ka damu yanzu zaka zama jarumi." Haka macijiyar ta fada daga nan sai ta nuna masa wani wuri a can gefen kogon, ai kuwa yana zuwa wurin sai yaga kwai  kala kala ga farare ga bakake.
    " Ka dauki fari ka fasa kasha ruwan." Ai kuwa haka Kalim yayi, yana shanye ruwan sai jikinsa ya fara karkarwa, daga nan ya fadi bai san inda yake ba. Sai da akayi yan dakiku kafin ya farfado, ai kuwa yana farkawa sai yaji kamar ba jikinsa ba, wani sadaukin karfi ne yakeji wanda bai taba ji ba, anan macijiyar ta dauko wani takobi ta mika masa.
   " Wannan kyauta  ce na baka kuma yanzu zan fita a jikin wannan macijiyar." Ai kuwa tana fadin haka sai yaga macijiyar ta fadi, wani hayaki ne ya fara fitowa a bakin macijiyar, shi wannan hayaki ya fito ne da siffar yarinya kyakkyawa wadda ta kasance girmanta ɗaya da Kalim, murmushi ta masa daga nan sai tayi tsaye  saman iska  da zimmar yi masa magana.
   " Shawara ta a gareka itace ka nisanci soyayya da gimbiya Zahra Zu, domin itace ajalinka da kaida abokinka Zabir," Tana fadar haka sai ta juya zuwa hayaki daga nan ta ɓace ɓat. Kalim bai ji dadin tafiyarta ba domin yaso ya tambayeta me take da nufi da wannan maganar kuma ya akayi tasan da hakan, kai bama wannan ba fadin sunansa dana abokinsa da tayi abun mamaki ne, kuma da tace ita ba mutum bace, to idan ba mutum bace  wacece? Anan Kalim ya juya da nufin tafiyarsa amma wani bakin gurnani daya jiyo a bayansa yasa ya kasa motsawa, a hankali ya fara juyowa domin yaga ko menene, ai kuwa yana jiyowa yaci karo da wannan macijiyar ta kanannade, kawunan nata dari cif take budawa iya karfinta da alama ta hango abinci,da karfin tsiya ta nufosa tana wani ruri mai hauhawa, anan Kalim yayi alkafira sama yana kaucewa bugunta, shi kansa abun mamaki yake basa domin bai san inda ya koyi tashi sama ba! A haka wannan macijiya taci gaba da kaiwa Kalim wani sadaukin hari shi kuwa in banda gudu da tsalle tsalle ba abunda yake, suna cikin hakane ya zare takobinsa da Lauziya ta basa, cikin mamaya ya kai mata wani bahagon sara a kai, cikin sa a ya guntule kan, anan tayi ruri mai hauhawa tana matsawa baya, shi kuwa alkafira yayi sama yana datse kawunan nata, a haka Kalim yayi ta datse wannan macijiyar cikin rashin mutunci har sai da ya hallakata, a nan ya sauko kasa yana huci, da jikin macijiyar ya shafe jinin dake diga a takobinsa daga nan yayi tafiyarsa.
 Page 31
Kalim bai fadawa kowa wannan labari ba iyaka dai mutane sun ga banbanci ga lamurransa, Kalim da aka sani da cewa raggon namiji ne amma sai gashi ya zama jarumin maza, a haka ya samu daukaka har sai da aka basa kambu na cewa shine dalibin da yafi kowa kwazo a wannan makaranta ta daukar dabarun yaki, su kuwa kakanninsa da sukaji wannan labari na cewa jikansu ya zama jarumi murmushi kawai sukayi domin sun san da cewa Kalim yasha farin kwai ne na macijiya, shugaban wannan makaranta ta koyon dubarun yaki wato  sarkin yaki Baidu yayi mutukar mamakin ganin wannan canji daga Kalim, babban abunda ke basa mamaki shine hamshakin takobin da Kalim ke fama dashi, amma sabida yasan da cewa mahaifin Kalim din sarkin fada yanada dukiyar da zai iya sayawa dansa irin wannan takobi to bai tsaya binciken inda Kalim ya samo takobin ba, sabida wannan jarumtaka ta Kalim sai Zahra Zu taji yana burgeta shi kuwa a wannan lokaci ta fara fita ransa sabida abunda  Lauziya ta fada masa na cewa itace ajalinsa shida abokinsa Zabir. 
   Ita kuwa gimbiya Zahra Zu lakewa Kalim tayi ba dare ba rana, a kullum maganarta shine ya fada mata yadda akayi ya zama jarumi, a haka tayita damunsa har ta ciyo kansa kasancewarta mace kyakkyawa wadda ta kware a sanin lafazin magana, a dalilin haka ne Kalim ya manta da maganar Lauziya, akan dole ya amshi soyayyar Zahra Zu kuma ya bayyana mata sirrin zama jarumi, kasancewar gimbiya Zahra Zu yar damuwa, ta takurawa Kalim ala dole sai ya rakata a kogon macijiya domin itama tasha ruwa kwai ta zama jaruma, shi kuwa Kalim cikin sauki ya aminta da zimmar cewa idan dare ya raba zasu fita tare, a cikin dare ta iskosa har gidansu, anan suka durfafi kofar fita gari da kafafuwansu, bayan sun fita ne suka nufi kogon macijiya, a lokacin da suka shiga kogon Kalim ya manta ya fada mata cewa farin kwai ake fasawa asha ba baki ba, ita kuwa gimbiya Zahra Zu tana zuwa bakin kwai ta dauka, anan ta fashe sa ta shanye ruwan, ai kuwa yin hakan keda wuya sai jikinta ya fara karkarwa, a nan ta fadi ba tare da sanin inda take ba, cikin yan dakiku ta farka, ai kuwa tana farkawa sai tayi arba da Kalim a gabanta, a wannan lokaci ba cikin hayyacinta take ba domin idanuwanta sunyi jawur, dunkule hannu tayi, daga nan ta gwabza masa wani uban naushi, karfin naushin yayi hajijiya dashi a sama koda ya fado kasa ya dade da zama matacce, daga nan sai ta fadi kasa ba tare da sanin inda take ba.
Page 32
A cikin gari kuwa sai neman gimbiya Zahra Zu ake amma ba a ganta ba, sabida wannan dalili yasa aka baza dakaru su fita nemanta wajen gari, a cikin dakarun da aka turo ne wasu suka samu gawar Kalim tare da gimbiya Zahra Zu a gefensa. Daga nan suka dungumesu suka nufi cikin gari dasu, shi kuwa sarkin fada wato mahaifin Kalim, da aka fada masa abunda ya faru cewa yayi sai ya kashe Zahra Zu domin a tunaninsa itace sanadiyar kashe dansa, sai da dakaru suka yita rike sa daga karshe kuma yasha alwashin hallakar da ita. Anan labari ya gewaye gari cewa Kalim ya mutu, bakin ciki gun Zabir baya misaltuwa domin Kalim shine babban abokinsa. Abun bakin ciki a mutuwar shine har yanzu ba a tabbatar da wanda yayi kisan ba amma da yawa mutane suna zargin gimbiya Zahra Zu, washe gari bayan gimbiya Zahra Zu ta farfado, anan aka fada mata abunda ya faru kuma aka bukaci ta fadi abunda ta sani, kome bata fada ba in banda kuka data cigaba da rerawa. Daga wannan rana sai Zahra Zu ta mayar da akalar soyayyarta ga Zabir, ba yadda Zabir bai yiba domin ya kubce amma abu ya faskara har sai da ta shawo kansa da karfin tsiya, anan suka kulla soyayya mai karfi kamar bazasu daina ba, abunda ke baiwa Zabir mamaki shine gaba daya Zahra Zu ta canza, Zahra Zu daya sani yarinya mai mutunci amma yanzu  sai dai rashin mutunci, ga tsananin kishin tsiya da saurin fushi, kuma idan tayi fushi zata fita hayyacin tane, data fita hayyacinta to duk wanda ta samu zata yi masa naushi daya ne, kuma duk wanda ta nausa tofa sai dai wani ba shi ba.
   Bisa wannan dalili mutane suka kyamaci Zahra Zu suna tunanin cewa ta dauko maita ne domin bazai yiwu ace data bugi mutum sai ya mutu ba, Zabir ne kawai ke iya hankurin zama da ita shi kansa sabida yana cikakken jarumi ne, kai hatta yar uwarta Zuhru Zu tsoronta take domin a gabanta wata rana da tayi fushi ta fara naushin dakaru abun ba kyan gani. A hakane wata rana ta hango Zabir na magana da wata yarinya a cikin filin makaranta, kishinta ne ya motsa cikin rashin sanin cewa yar uwarsa ce, koda ta durfafosu a cikin fushi take, tana isowa gun tayiwa Zabir wani namijin naushi, a nan yayi hajijiya sama ya fado kasa matacce, ita kuwa yar uwar tasa ihu ta saki daga nan tayi ta kanta haka suma yaran makaranta duk suka watse, anan dakaru sukayo kanta domin kamata amma abu ya faskara, duk wanda ya taso kanta sai ta hallaka sa, a haka tayita kisan mutane har sai da abun ya saketa sannan ta fadi sumammiya. 
Page 33
Lauziya ta fadi gaskiya, kamar yadda ta fada cewa Zahra Zu itace ajalin Kalim da Zabir haka kuwa abun ya kasance domin itace ajalinsu, mutuwar Zabir ba karamin tashin hankali ya saki ga mutane ba domin wannan ya tabbatar musu da cewa gimbiya Zahra Zu mayya ce, su kuwa kakannin Kalim da sukaji wannan labari, girgiza kai kawai sukayi domin sun san da cewa gimbiya Zahra Zu tasha bakin kwai ne na macijiya wanda yayi sanadiyar mayar da ita Bakar Jaruma. Zulaiya tayi bakin ciki sosai ace wai yarta ta cikinta itace da wannan hali har tayi sanadiyar kashe dan yar uwarta Zulaira wato Zabir. A bisa wannan dalili ne yasa sarauniya Zulaiya ta kaima waziri Hamim wato mijin kanwarta Zulaira ziyara a cikin dare domin su tattauna wata magana mai muhimmanci. A lokacin data shiga turakarsa ta samesa ne zaune saman kujerarsa shi kadai yana hawaye, wasu fatoci guda biyi ne a gabansa sai kallonsu yake yana hawaye, fata ta farko an zana taswirar Zabir da Zahra Zu, fata ta biyi kuwa an zana taswirar Zahra Zu da Zuhru Zu.
   " Ina bada hakuri bisa ga abunda ya faru, kuma inaso na tabbatar maka da cewa na dauki zimmar fita duniya domin nemowa gimbiya Zahra Zu magani." Inji Zulaiya. Anan waziri Hamim ya dago yana kallonta. " Zan tafi da Zuhru Zu, ita kuwa Zahra Zu zan barta a nan, kuma zan tafi da yar uwata Zulaira kuma inaso ta dauki diyarta Lamiyo." 
   " Meye amfanin zuwa da Zulaira da kuma diyarta?" Waziri Hamim ya tambaya.
   " Sabida barin su a nan zai iya sanya su a cikin hatsari."Inji Zulaiya.
   " Wane irin hatsara kuma?" Waziri Hamim ya tambaya. Ita kuwa Zulaiya anan ta fara basa labari kamar haka:
Sarauniya Lubaiya wato mahaifiyar sarki Mahir ta kasance tanada wata yar uwa da ake kira Munaihat, Munaihat tana auren hamshakin manomi kuma dan kasuwa da ake kira Budda a can wani sansani mai nisa da ake kira sansanin Budaiya, to wata rana sai sarauniya Lubaiya ta shirya kaiwa yar uwarta ziyara wato Munaihat, a wannan lokaci yarima Mahir yana dan shekara goma sabida wannan dalili yasa tace dashi zata tafi. Sarki Barhan bai biyosu ba domin sha anin mulkinsa ya masa yawa, sabida haka sai ya shirya dakaru wadanda zasu rakata, to akan hanyarsu na zuwa wannan sansani ne suka hadu da yan fashin dare, anan yan fashin suka kashe sarauniya Lubaiya ita da dakarunta, daga nan suka wawashe duk wata dukiya dake saman dawakan sarauniya, yarima Mahir kawai ne ya tsira daga sharrin su.
Page 34
Da taimakon wasu matafiya yarima Mahir ya dawo gida ya bayyanawa sarki Barhan abunda ya faru, shi kuwa Barhan alwashi yasha cewa sai ya gano ko su waye sukayi wannan aika aika kuma sai ya hukunta su. Anan ya tsananta bincike game da wannan al amari kuma a cikin bincikensa ne ya gano cewa wannan sansani da sarauniya taso kaiwa ziyara sunada tantiran yan fashi a ciki, kuma a cikin bincikensa ne ya gano cewa Budda mijin Munaihat wato kanwar sarauniya Lubaiya dan fashi ne, kuma shine ya kashe sarauniya Lubaiya ya wawashe dukiyarta. Kuma abunda yasa aka tabbatar da hakan shine an gansa da dukiyar sarauniya Lubaiya, mutane da yawa sun shaida wannan zance, anan sarki Barhan yayi fitar sirri shi kadai ya nufi wannan sansani domin neman Budda, Sarki Barhan baisha wahala wurin gano gidan Budda ba kasancewarsa sananne, anan ya dauki zimmar cewa ko kazar gidan bazai bari da rai ba, a cikin dare ya shiga gidan amma cikin rashin sa a Budda baya nan, ita kuwa matar Budda Munaihat batada lafiya, diyanta mata su hudu da bazasu wuce shekera goma goma ba sun zagayeta sai kuka suke, su wadannan mata sun hada da Zulaiya, Zulaira, Zulaisa, da Zulaima. Ganin tsananin rashin lafiyar Munaihat sai tausayinta dana diyanta ya kama sarki Barhan, anan yayi watsi da nufin daya dauka sabida haka sai ya tafiyarsa, fitarsa keda wuya Munaihat na cikawa, kuma a dai dai wannan lokaci ne Budda ya dawo, a nan Zulaiya ta fada masa cewa sarki Barhan yazo nemansa da yake itace babba a cikin yaran kuma tayiwa sarki Barhan farin sani domin mahaifiyarsu Munaihat tana yawan tafiya dasu wurin yar uwarta sarauniya Lubaiya. Anan ran Budda ya bace domin a tunaninsa sarki Barhan yazo daukar fansa ne kuma daya tarar baya nan sai ya kashe matarsa a madadinsa. Daga wannan rana Budda ya fara koyawa yaransa dubarun yaki da rashin imani har suka girma, bayan sun girma ne sai ya aika su a masarautar Ƙabru domin suyi garkuwa da sarki Barhan, wani Ƙundin sihiri ya baiwa yaransa, kowace da kundi daya, anan ya umarcesu da cewa Zulaiya zata tsaya bangon gabas na masarautar Ƙabru ita kuwa Zulaira zata tsaya bangon yamma, ita kuwa Zulaisa zata tsaya bangon kudu, ita kuwa Zulaima zata tsaya bangon arewa, kamar yadda ya fada musu suna tsayawa a bangon to kowace ta saki Ƙundinta da sun saki Ƙundin to wani hayaki zai fito cikin Ƙundin yayi tiriri sama.
Page 35
 Kuma duk wanda ya shaki wannan hayaki to zai fadi sumamme, sabida haka sai suyi amfani da wannan damar suyi garkuwa da sarki Barhan kuma su wawashe dukiya mai tarin yawa.
   " Kaji abunda ya faru!" Inji Zulaiya cikin hawaye " Mune mukayi garkuwa da mahaifin sarki Mahir wato Barhan kuma ko wannan gasar da muka shiga mahaifinmu ne ya turomu domin mu kashe sarki Mahir amma bamu samu nasara ba, nayi dana sanin bin zuciyata da nayi da kuma bin bakar shawarar mahaifina Budda, sabida haka inaso kayimin alkawari cewa bazaka fadama sarki Mahir wannan labari ba, idan lokaci yayi zai sani da kansa." Anan Zulaiya ta fita dakin daga nan ta nufi dakin yar uwarta Zulaira, a wannan lokaci Zulaira na kwance ita kadai saman gadonta na alfarma, tana ganin shigowar Zulaiya sai ta sheko da gudu suka rungume juna cikin kuka, sai da suka jima a kankame kafin su saki juna su fara shirye shirye, bayan sun aza kayayyakinsu saman dawakai kowace rike da diyarta, wato sarauniya Zulaiya rike da Zuhru Zu ita kuwa Zulaira rike da Lamiyo.
   " Inaso ku fadamin inda kuka boye mahaifin sarki Mahir wato Barhan." Waziri Hamim ya tambayesu. Anan sukayi tsit ba tare da magana ba sai hawayen dake kwarara saman idanuwansu. " Kuma ni a tunanina wannan tafiya taku batada amfani tunda har yanzu sarki Mahir baida masaniyar cewa kune kukayi garkuwa da mahaifinsa." Inji waziri Hamim.
   " Inaso ka sani cewa makasudin wannan tafiyar da zamuyi shine mu nemowa Zahra Zu maganin wannan maita dake jikinta, kuma ka sani cewa sarki Mahir yana gab daya gano sirrinmu domin a kullum cikin bincike yake kuma saninka ne daya ganomu kashinmu ya bushe domin hukuncinmu shine kisa, wannan tafiya itace rufin asirinmu kuma idan da rabon ganawa to zamu sake haduwa." Inji sarauniya Zulaiya, anan ta kada linzamin dokinta ita kuwa kanwarta Zulaira ta biyota a baya, a haka suka fara gwabza wani namijin gudu da nufin cimma kofar garin domin fita a sirrance kowace rike da diyarta, tun waziri Hamim na ganin dushi dushin dawakansu har suka bace masa da gani. Anan ya koma gidansa cikin shaukin matarsa Zulaira da kuma diyarsa Lamiyo, anan ya dauko fatocin da yake zana taswirar mutane yana dubawa, anan ya gano yayi kuskure.
Page 36
Domin duk kwarewarsa a wurin zane bai taba zana taswirar matarsa Zulaira ba da kuma diyarsa Lamiyo ba, Zabir kawai ne ya taba zanawa shima tare da Zahra Zu a lokacin suna tashen soyayyarsu kafin mai rabawa ta rabasu, sai kuma Zahra Zu da Zuhru Zu, suma ya zana taswirar su a cikin fata, wadannan taswirori daya zana sune yakan dauko yana dubawa domin sukan tuno masa wannan rayuwa da yayi tare da matarsa da diyansa, a duk lokacin daya kurawa wannan zane ido tofa sai idonsa ya ciko da kwalla har yakan yi kuka mai isarsa. Washe gari da sarki Hamir ya farka baiga matarsa Zulaiya ba da kuma diyarsa Zuhru Zu ba, bai tsaya wani bincike ba domin a tunaninsa anyi garkuwa dasune kamar yadda aka yiwa mahaifinsa Barhan Shi kuwa waziri Hamim kamar yadda yayi alkawari bai taba kuskuren fadama sarki Mahir abunda ya faru ba. Haka suka cigaba da rayuwa har zuwa wannan rana da akayi garkuwa da gimbiya Zahra Zu.
   " To kunji abunda ya faru." Inji waziri Hamim. " Wannan dalili yasa a duk lokacin dana kurawa wadannan fatocin idanu nake zubar da hawaye domin ina tuno rayuwata ta baya." Injisa.
     " Kada ka damu ya kai waziri Hamim." Inji Amran, " Kamar yadda ka bamu wannan  labari to mu kuwa zamu taimake ka. Amma zamuso ka fada mana wane hali mahaifin kalim yake ciki a yanzu?"
      " Mahaifin Kalim wato sarkin fada yanzu haka yana gidan kaso, domin sarki Mahir yana zarginsa da sace gimbiya Zahra Zu, domin idan zaku tuno a shekarun baya lokacin da Zahra Zu ta kashe dansa Kalim yasha alwashin cewa sai ya hallakar da ita, wannan dalili yasa aka tsaresa a gidan kaso kafin a gama bincike." Inji waziri Hamim.
   " Zamu yi iya kokarinmu domin muga mun dawo da gimbiya Zahra Zu a duk inda take kuma zamu binciko maka matarka Zulaira da kuma diyarka Lamiyo." Inji Amran.
    " Idan har ka aminta gobe zamu fara wannan tafiya." Inji Gazman.
   " Wannan ba kome bane amma inaga kamar abunda kuke fada bazai yiwu ba domin babbar matsalar itace ba a san inda za a neme suba." Inji waziri Hamim.
  " Kada ka damu da wannan, ka bamu goyon baya kawai!" Inji Gazman.
  " Ba matsala, zuwa gobe zan tanadar muku duk abunda kuke bukatada idan yaso sai ku gwada sa arku ku gani!" Inji Waziri Hamim. 
Page 37
Anan yayi musu bankwana kasancewar duhu ya fara gabatowa, haka suma su Amran shiga masaukinsu sukayi domin samun bacci mai nauyi.
   " To amma idan muka gano gimbiya Zahra Zu to a cikinmu waye zai mallaketa?" Inji Amran.
  " Idan muka ganota a tare sai muyi Yaƙin Mutuwa, idan na kasheka shi kenan zan mallaketa, kuma idan ka kasheni shi kenan sai ka mallaketa." Inji Gazman.
  "  Ba matsala na aminta." Inji Amran.
  " To amma me zai hana mu fadawa juna abunda muke bukata a wurinta inaga haka yafi." Inji Gazman.
  " Nima abunda nakeso na fada maka kenan, amma yanzu tunda dare yayi mu bari sai gobe idan mun bar birnin gabaki daya sai mu tattauna maganar." Inji Amran. Anan Amran da Gazman suka kishingida saman gadonsu domin samun bacci da zimmar cewa gobe idan sun fita neman Zahra Zu kowanensu zai bayyanawa dan uwansa manufarsa akan gimbiya Zahra Zu.
  MEYE MANUFAR AMRAN AKAN GIMBIYA ZAHRA ZU?
  MEYE MANUFAR GAZMAN AKAN GIMBIYA ZAHRA ZU?"
  SHIN ZASU IYA GANO GIMBIYA ZAHRA ZU KUWA?
  IDAN SUN GANOTA TARE TO WAYE ZAI SAMU NASARA AKAN WANNAN YAKI NA MUTUWA DA ZASU KADDAMAR AKANSU?
 YA LABARIN BUDDA?
  YA LABARIN MAHAIFIN MAHIR WATO BARHAN?
  WANE HALI BARHAN YAKE CIKI, YANA NAN DA RANSA KO KUWA YA MUTU?
  WANE HALI ZULAIYA DA ZULAIRA SUKE CIKI?
  WANE HALI ZUHRU ZU DA LAMIYO SUKE CIKI?
  WAYE YAYI GARKUWA DA GIMBIYA ZAHRA ZU KUMA MEYE MUNAFARSA AKANTA?
  Mu hadu a sashe na uku domin jin cigaban wannan labari...
 To be continue in episode three........
  


                                                                          GIMBIYA ZAHRA ZU
                                                                                     by
                                                  Abdul King Article & Abdul Alhaji Musa 10K
                                                                                Episode 3
                                                                            Labarin Amran
To you Queen Teei, based on the novel by " Alaƙar Jinnu "
Page 38
Tun da sanyin safiya waziri Hamim ya gabatar da duk wani abun bukata gasu Amran, anan sukayi godiya suka saki linzamin dawakansu, tun daga nesa dakarun dake tsaron kofar garin suka hango su, da yake waziri Hamim ya bayyana musu kome sabida haka basuyi jinkiri wurin bude kofar ba. Da matsanancin gudu su Amran suka fita garin, anan suka nausa cikin tsananin gudu. Haka suka yita kutsa daji sai da rana ta fadi likis sannan suka tsaya hutawa, daure dawakansu sukayi daga nan suka zauna kusa ga itace suna hutawa, kowanensu dauko guzurinsa yayi yana ci cikin nishadi da shaukin wurin da suke zaune.
    " Nifa ban san inda muka dosa ba domin tunda muka fara wannan tafiyar biye kawai nake dakai." Inji Gazman.
   " Zamu tafi sansanin Budaiya ne mana, kada ka manta a can ne muke tsammanin ganin Zulaiya da Zulaira tunda sun kasance yan asalin sansanin!" Inji Amran.
   " To amma meye amfanin ganin Zulaiya da  Zulaira, kada fa ka manta muna neman Zahra Zu ne!" Haka Gazman ya fada yana kallonsa.
   " To ai idan mukaga Zulaiya da Zulaira kamar mun ga Zahra Zu domin inaji cewa sunada  hannu wurin garkuwa da Zahra Zu din." Inji Amran.
   " To amma idan hakane me zaisa suyi garkuwa da ita?" Gazman ya tambaya.
   " Kada ka manta bamu tabbatar da wannan maganar ba, sai idan mun gansu wato Zulaiya da Zulaira idan yaso sai mu tabbatar da hakan bayan mun tambayesu." Inji Amran. Anan Gazman ya aje battar ruwansa da sauri, shi kuwa Amran yana ganin haka sai ya dubesa da sauri.
    " Lafiya kuwa!" Inji Amran.
    " Saurara kaji." Haka Gazman ya fada yana daga masa hannu.
    " Ku taimake ni, zasu kasheni, ku taimakeni." Muryar mace suka jiyo acan nesa, ai kuwa suna jin haka suka zuba a guje inda suka jiyo muryar na fitowa.
Page 39
Sai da sukayi tafiya mai nisa kafin su cimma wani dan karamin gida, cikin sauri suka tsunduma suna dube dube, suna cikin dube dube ne sai sukaga wata mace a can gefe ta hada kai da gwuiwa tana kuka, tafiya suka farayi a hankali da nufin cimmata, ai kuwa suna cikin tafiyar ne sai kafafuwansu ya taka wani boyayyen tarko, wata kaca ce ta fado da karfin tsiya ta musu mugun dauri, anan kacar ta daga su, kafafuwansu a sama kansu a kasa. Gani sukayi matar ta tashi tsaye tana dubansu, taba hannuwa tayi sai uku sai ga wasu samudawa sun fito a cikin shigar yaki.
   " Kin yi aiki mai kyau Zuhru Zu." Haka wani basamude ya fada yana kallonta, anan Amran da Gazman suka kalli juna cikin mamaki, dama tarko ne aka hada musu da mace domin a kamasu? Bama wannan ba Zuhru Zu fa yace, to yana nufin Zuhru Zu kanwar Zahra Zu ko kuwa wata Zuhru Zun ce ta daban? Kuma idan itace Zuhru Zu to ina Zahra Zu? Kuma me ya faru da Zulaiya  da Zulaira, ko ana nufin suma sun zama yan fashi kenan? Anan Amran da Gazman suka yita kokarin kubcewa kodan suga wannan yarinya amma ko matsawa bazasu iyaba, gashi kansu a kasa yake balantana suce su dago su dubeta. Anan basamuden ya dauko wata yar karamar jaka ya jefawa Zuhru Zu din. " Ki dauki wannan ki tafi gida, zamu nemeki idan lokaci yayi." Anan wannan yariyar ta dauki jakar ta fita, su Amran suna jiyo haniniyar dokinta kafin ta saki linzami ta fara gudu, babban bakin ciki a wurin su Amran shine basu san inda zasu kara ganinta ba, kuma da basamuden yace ta tafi gida to wane gida zata tafi, gidansu na sansanin Budaiya ko kuwa boyayyen gidansu na yan fashi? Kuma idan gidansu na yan fashi zata tafi to wane wuri gidan yake? Kuma jakar daya bata to meye a ciki? Anan wadannan samudawan suka yanke kacar dake dauri dasu Amran, suna fadowa sai aka sanya musu wata kaca wadda ta daure musu hannuwa da kafafuwa, daga nan aka gyara kacar yadda suna iya tafiya. Anan aka ingiza keyarsu waje, suna fita sai suka tarar da mutane maza da mata an daure musu hannaye da kafafuwa kuma sun jero sahu, anan aka tilasta su Amran don dole sukabi sahun wadannan mutane. Daga nan aka ingizasu zuwa wani narkeken teku, wani jirgin ruwa suka gani mai mutukar girma a nan gefe, daga nan sai aka sanya su a ciki bayan an zaunar dasu an kulle hannuwansu da karfen jirgin. Cikin sa a kuwa sai aka ajiye Amran da Gazman a wuri daya, anan jirgi ya fara tafiya su kuwa wadannan samudawan tsaye sukayi suna gadin wadannan mutane da suka kamo.
Page 40
A wannan lokaci dare ya gabato, bakajin kome sai iskan dake kadawa, cikin mutanen da aka kamo wasu sun fara bacci wasu kuwa sai hirarsu suke abunsu. Anan ne Gazman ya dubi Amran da zimmar yin magana.
   " Wai wadannan mutane da suka kama mu su waye kuma a tunaninka ina zasu kaimu?" Inji Gazman.
   " Ban san ko su waye ba kuma ban san inda zasu kaimu ba amma inada yakini cewa azzalumai ne." Inji Amran.
    " To amma me muka yi musu!" Haka Gazman ya fada cikin mamaki.
    " Kada ka manta shi azzalumi ba sai ka masa laifi ba yake cutarka, a duk lokacin daya tashi zai iya cutarka." Inji Amran.
    " To yanzu meye mafita kenan?" Gazman ya tambaya.
    " Mafita itace muga inda zasu kaimu, idan mun isa wurin zamusan meye abunyi!" Inji Amran.
    " To tunda hakane me zai hana ka bani labarinka, ma ana ka fadamin manufarka akan gimbiya Zahra Zu idan yaso daga baya ni kuma sai na fadama nawa labarin." Inji Gazman. Anan Amran yayi murmushi kafin ya fara  labarin sa kamar haka:
       Birnin Tabul yana daya daga cikin manyan biranen da sukayi kaurin suna a duk fadin duniya, sarkin wannan birni wato Habir dan mas'ud yanada tarin dukiya da wadata wadda shi kansa bai san irin yawanta ba, babbar matsalarsa daya ce, kuma wannan matsala ta fito ne daga diyansa na cikinsa wato Amran da Zamran, Amran shine karami Zamran babba, su wadannan ya'ya na sarki Habir sun kasance basu ga maciji da juna sabida suna son mace daya, wata yarinya da ake cewa Nalisha diyar sarkin kasuwa Razdu, wata rana Zamran ya shiga kasuwa dakaru na take masa baya, a wannan lokaci ya shiga kasuwar ne da zimmar sayen takubba cikin sa a kuma sai ya tsaya daya daga cikin shagunan Razdu wanda shi wannan shago ba abunda ake sayarwa inba kayan yaki ba,kuma a wannan lokaci diyarsa Nalisha na tare dashi domin ta tayasa aiki, to anan Zamran yaji ta kwanta masa a rai, sabida haka sai ya nufota da nufin bayyana mata abunda ke ransa, to a wannan lokaci da Zamran ya nufo Nalisha da nufin furta mata, ashe shima Amran ya shiga kasuwar da nufin sayen takubba kuma ya tsaya wannan shago na Razdu, kuma anan yaga Nalisha yaji ta kwanta masa a rai.
Page 41
Daga nan shima Amran sai ya nufota da nufin furta mata, ai kuwa sai ga Amran da Zamran sun iso wurin Nalisha tare, anan suka  fara kallon kallo domin kar tasan kar.
   " Kai me ya kawoka anan ne?" Haka Zamran ya fada cikin hasala.
   " Meye ruwanka da abunda nazo yi ne? To nazone na furta ma wannan yarinyar abunda ke raina ko zaka hana ne?" Haka Amran ya fada cikin zafi.
   " Nima abunda ya kawoni kenan, kuma kada ka manta nine gaba da kai sabida haka ka bacemin da ganni." Inji Zamran.
   " Kai har ka isa, idan a rigaye ne na rigaka sabida haka kaga hanya." Anan Amran ya nuna masa hanya. Daga nan sai cacar baki ta sarke su, ita kuwa Nalisha dake tsaye a tsakiyarsu tana kallonsu abun dariya ya bada yadda taga kowanensu ya takarkare ala dole shine da ita.
   " Ku dakata." Anan ta dakatar dasu, jin tayi magana sai sukayi tsit suna sauraren abunda zata fada.
   " Kunaso kuce dani duk kuna sona ne?" Inji Nalisha.
   " Sosai kuwa!" Haka Amran da Zamran suka fada tare.
   " To ai wannan yafi kome sauki, saninku ne cewa namiji biyu bazasu auri mace daya ba, sabida haka yanzu zamu iya duba can canta idan yaso sai muyi sulhu akai." Inji Nalisha cikin murmushi.
   " Idan can canta ne to nine na can canta sabida na fisa kome." Haka Zamran ya fada cikin hasala daga nan sai cacar baki ta kara shiga tsakaninsu, shi kuwa sarkin kasuwa Razdu dayaji hayaniyar ba mai karewa bace sai ya fito daga shago domin ya shiga tsakani.
   " Wai me yake faruwane?" Haka Razdu ya fada bayan ya iso daf dasu. Anan Nalisha ta labarta masa abunda ke faruwa. Shi kuwa daga jin haka murmushin farin ciki yayi domin a garesa ba karamin girma bane a wurinsa ace ya'yan sarki Habir suyi soyayya da yarsa.
" Abunda za a yi shine ku tafi zuwa jibi ku sameni a gidana cikin dare idan yaso sai mu tattauna maganar." Inji Razdu. Anan Amran da Zamran suka kama gabansu kowanensu ya nufin wurin dakarunsa. Shi kuwa Razdu da diyarsa bayan sun isa gida ne sai suka kadaita.
Page 42
   " Wannan al amari yanada rudani sosai amma ke a tunaninki me ya kamata muyi idan sun dawo jibi?" Razdu ya tambayi diyarsa Nalisha.
   " Ni inaga kawai zamu basu aiki mai wahala muce duk wanda yayi shine da mata." Inji Nalisha.
   " Wannan shawara ce mai kyau amma a ganinki wane aiki ya kamata mu basu?" Inji Razdu.
   " Kasan da cewa akwai gasar kamun kifi da ake gudanarwa a wannan gari duk shekara, abunda akeso ga wannan gasa shine mutum ya kama kifin da babu irinsa a wurin girma, duk wanda yayi hakan to masarautar wannan birni takan bada kyauta mai tsoka, kuma kaga jibi ne za a gudanar da gasar, kaga kenan muna da damar cewa Amram da Zamran su shiga wannan gasar kuma duk wanda yayi nasara to shine da mata." Inji Nalisha. Anan Razdu ya karbi wannan shawara ta diyarsa. Jibi bayan su Amran sun dawo sai ya bayyana musu kudurinsa na cewa su shiga wannan gasa, anan suka aminta, to abun mamaki bayan an fito daga gasar ne sai aka tarar da Amran da Zamran kifinsu yafi na kowa girma, kuma kifayen da suka kamo sun kasance girmansu daya kuma komi nasu daya kamar yan tagwaye, anan Razdu da diyarsa Nalisha suka kara kidimewa domin bazasu ce ga wanda ya samu nasarar wannan gasa ba.
   " Nifa wannan abu naban tsoro to yanzu meye abunyi?" Inji Razdu.
   " Kada ka manta nan da kwana biyu za a gadunar da gasar farauta, kuma abunda ake so ga wannan gasar shine mutum ya kama dabbar da ba wanda ke iya kama irinta, kaga kenan zamu iya cewa su shiga wannan gasar."Inji Nalisha. Anan Razdu ya kara daukar shawar yarsa, bayan su Amran sun dawo ya musu bayanin abunda ake bukata dasu kuma a nan suka aminta, to abun mamakin daya kara faruwa shine Amran da Zamran sun kamo zakuna masu mutukar girma wadanda suka kasance girmasu daya kuma komi nasu daya kamar yan tagwaye. Anan Razdu da diyarsa Nalisha suka kara kidimewa domin bazasu ce ga wanda yaci gasa ba, a haka suka yita baiwa Amran da Zamran aiki mai wahala amma sai suyi tare daya bai fi daya ba har daga karshe Razdu yace suyi hakuri shi bazai iyaba. Tun daga wannan lokaci Amran da Zamran suka zama basu ga maciji, ba yadda mahaifinsu sarki Habir bai yiba domin ya shawo kansu amma abu yaci tura.
Page 43
Zamran ne a saman gadonsa yana sharara bacci sa wani ihu mai hargowa ya tayar dashi, anan ya tashi yana tafiya a hankali domin ganin ko waye, yana cikin tafiyar ne sai ya shigo wani lungu, acan karshen lungun mace ce a durkushe sai rusa kuka take. Anan ya nufota domin yaji dalilil wannan kukan da take, yana isowa daf da ita sai ta dago kai ta kallesa, anan ya mata kallon tsaf kafin ya fara magana.
  " Wacece ke kuma meye dalilin wannan kuka da kike?" Maimakon ta bashi amsar tambayar daya mata sai tayi magana kamar haka.
  " Ina kuke ne sabida hatsarin dake shirin afka min,"
  " Wane irin hatsari?" Zamran ya tambayeta. Anan tayi shiru ba tare da amsa ba, sai daga bisani  tace.
  " Ka fada masa ya taimakeni, ka fada masa ya taimakeni."
  " Waye zai taimakeki?"
  " Jininka, jininka." Inji matar.
  " Jini na fa kikace, ta ya za ayi jini na ya taimake ki?"Inji Zamran.
  " Idan nace jininka ba ina nufin jinin dake yawo a jikinka ba kuma ba ina nufin kai ba, inaso kayi tunanin abunda nake nufi kuma ka fada masa ya taimakeni." Inji matar, anan tacigaba da rusa kuka bai man tsoro da firgici har sai da Zamran yaji kamar kansa zai tsage.......
     Firgigit Zamran ya farka yana nishi dai bayan dai, wai ashe mafarkine yake, abunda ya basa mamaki shine ita wannan mata daya gani bai san ko wacece ba kuma bai san dalilin da yasa take kuka ba, babban tashin hankali a wurinsa da tace ya fadama jininsa ya taimake ta, to abun tambaya anan shine waye jininsa? Anan Zamran ya dauko wani ƙoƙon karfe dake cike da tawadda tare da alkalamin karfe, fatar damisa ya dauko daga nan sai ya yanka yar tsito, yana yankawa sai ya fara zana surar wannan yarinyar daya gani a mafarki tana kuka, yana kammala zanen sai ya tashi ya nufi turakar Amran, a wannan lokaci da sanyin safiya ne domin masarautar tsit take bakajin motsin kome in banda dakarun dake kai komo domin su tabbatar da tsaro. Koda ya shiga turakar mai dauke da wani wangamemem daki dayasha kayan alatu, shi wannan daki an tanadesa ne kawai domin hutawa, kamar daga can nesa sai ya fara jin karar takobi kamar da alama Amran na ciki, da sauri ya shiga wani lungu wanda ya kawosa a wani daki kayattace.
Page 44
 A nan ya isko Amran yana baiwa kansa horo rike da takobinsa, shi kuwa Amran yanajin motsi sai ya juyo domin ganin ko waye, juyowa da zaiyi sai ya tarar da Zamran a tsaye.
   " Meya shigo dakai a turakata?" Amran ya tambayesa, shi kuwa Zamran bai basa amsa ba, miko masa fatar damisar daya zana wannan yarinyar yayi, shi kuwa Amran yana amsar fatar sai ya kura ma zanen ido kamar bazai daina ba, abunda Amran ya fara tunani shine yana yawan mafarkin wannan yarinyar cikin zumamin cewa ya taimaketa.
   " Lafiya kuwa?" Zamran ya tambayi Amran.
   " Ka miko zanen ba tare daka fadamin me kake nufi ba!" Inji Amran. 
   " Kada ka damu yanzu zan maka bayani." Anan Zamran ya bayyanawa Amran mafarkin da yayi. " Kuma ni a nawa tunani kaine jini na da take fada kaga kuwa kaine ya kamata ace ka taimake ta." Inji Zamran.
   " Kada ka manta mafarki ne kayi, kuma ba kowane mafarki ne yake zama gaskiya ba, to idan wannan mafarki da kayi ya kasance karya fa?"Inji Amran.
   " Mafi yawan mafarkan da nake sukan zamo gaskiya, kuma inaji a jikina wannan mafarki gaskiyane." Inji Zamran, anan Amran yayi shiru yana tunani domin shima a mafarkinsa duk abunda Zamran ya gani haka ya gani, kuma ba sau daya yayi mafarkin ba, kuma kamar yadda Zamran ya fada masa shima ba wannan ne karo na farko  da yayi mafarkin ba, tun tuni Amran nada niyar fita neman wannan yarinya domin shima mafi yawan mafarkan da yake sukan kasance gaskiya kuma yanaji a jikinsa wannan mafarki da yake gaskiyane kuma  sai gashi yanzu Zamran yazo masa da maganar.
   " Ya za ayi na taimake ta bayan ban san ko wacece ba kuma ban san kowane gari take ba balantana na nemeta a can."Inji Amran.
   " Wannan shine amfanin zanenta dana baka, dashi zakayi amfani ka tambayi mutane har ka dace, kuma idan ka nemota ka mata irin taimakon da take bukata na maka alkawari zan bar maka Nalisha har abada." Inji Zamran. Anan Amran yayi shiru domin yasan fa wannan aiki ne ja.
   " Na aminta amma me zaka fadama iyayenmu sarki da sarauniya bayan tafiyata?"Amran ya tambaya.
  " Kabar kome a hannuna, zan musu bayani yadda zasu fahimta, kuma idan da hali zan so ka fara wannan tafiya yanzu." Inji Zamran.
Page 45
  " Na aminta."Inji Amran. Cikin sauri Amran ya kintsa kayansa, daga nan yayi bankwana da Zamran ya nufi kofar fita gari saman dokinsa, bayan ya fita garin ne yaci gaba da gwabza gudu baji ba gani, a haka yayi ta gudu bai gamu da kowa ba balantana ya tambayesa har dare ya riskesa likis, anan ya yadda zango da nufin hutawa idan yaso zuwa gobe sai ya cigaba da tafiyar, kwantawarsa keda wuya sai yaji kamar daga sama wasu mutane na dirowa a saman itace, kafin ya ankara an zagayeshi, kallo daya ya musu ya gano cewa yan fashin dare ne domin kowanensu ya rufe fuskarsa da bakin kyalle, sai wasu muggan makamai da suke fama dasu, anan aka fara kallon kallo tsakanin Amran da wadannan yan fashi kafin daga bisani su afka masa, Amran yayi iya kokarinsa na ganin cewa ya kare kansa amma abu yaci tura sabida sunada yawa sosai, a cikin wannan gumurzu ne suka mamayesa suka kwace jakarsa ta fata wadda ke dauke da guzurinsa da kuma taswirar da Zamran ya basa. Suna kwace jakar sai suka zuba a guje cikin matsanancin gudu, gudu suke suna hawan itatuwa suna saukowa kamar walkiya. Cikin dakiku kadan suka bace, haka suka bar Amran cikin bakin ciki ba tare da sanin abun yiba. Dakyar ya iya bacci zuwan gari ya waye, ai kuwa safiya na wayewa ya hau dokinsa ya mika a guje, gudu yake ba tare da sanin inda zashi ba har ya cimma wani babban birni, tunda ya shiga birnin mutane ke kallonsa domin shigar da yayi ta sarauta ce, a haka yayita tafiya saman dokinsa har ya iso kasuwar birnin, a cikin kasuwar ne ya samu kansa a cikin wani shago na sayar da abinci, tunda ya shiga ya zauna mutane sai kallonsa suke. Zamansa keda wuya sai wata yarinya ta nufo wurinsa.
   " Barka dai dan saurayi ko zan ce me za a kawo maka?" Haka ta fada cikin sakin fuska. Anan Amran yayi shiru domin yunwa yakeji amma kuma bai san irin abincin da yake so ba.
    " Ki zubo kawai zan biya ko nawane." Inji Amran. Anan yarinyar ta kalli suturar jikinsa kafin ta kada kai ta tafiyarta, cikin dakiku sai gata dauke da babban akushi, tana zuwa wurinsa ta girke akushin a gabansa.
      " Kudinka darhami uku." Inji yarinyar. Anan Amran ya dauko darhami uku ya bata daga nan ta tafiyarta, cikin sauri ya bude rufin akushin, ba abunda ya isko in ba nama ba, abunda ya basa mamaki shine bai san kowane irin nama bane iyaka dai ci ya farayi sabida tsananin yunwar dake addabarsa.
  Page 46
Yana kammala cin abincin sai ya fita waje inda ya tarar da dokinsa, anan ya hau ya nufi kofar fita garin, koda ya fita garin sai ya mika cikin matsanancin gudu ba tare da sanin inda zai tafi ba, sai da rana ta fadi likis sannan ya iso wani sansani, tunda ya shiga wannan sansani mutane ke kallon suturar dake jikinsa, shi ko a jikinsa domin bai damu ba, tafiya kawai yake yana dube dube kamar mai binciken wani abu, yana cikin hakane sai yaji an jawosa da karfin tsiya a baya, ba yadda bai yiba ya kare kansa amma ina sai da ya fado saman dokin. Yana tashi sai yaga irin wadannan mutanen da suka yi masa fashi sun zagayesa dauke da muggan makamai. Sai da aka fara kallon kallo tsakanin shi dasu kafin su afka masa, ai kuwa a wannan karon Amran ya basu mamaki domin sai ya zame musu alaƙaƙai, ba abunda yake in banda kare kansa da kuma mayar musu da martani kasancewarsa gwani a wurin halbin kibiya da fadan takobi, a cikin wannan gumurzu ne Amran ya kaiwa wani daga cikin wadannan yan fashin wawan sara, shi kuwa wanda aka kaiwa saran da yaga kansa na shirin faduwa idan bai dau matakin gaggawa ba sai yayi sauri ya dauko wata jaka ya kara, a dai dai lokacin daya kara jakar a lokacin saran Amran ya kawo. Nan take jakar ta rabe biyu, anan Amran ya gane cewa jakarsa ce domin ga komi nasa lafiya lau ba tare da an taba ba, cikin hasala ya cafko dan fashin a lokacin shi kadai ya rage domin sauran yan uwansa duk sun baje ga kasa.
   " Fadamin kai waye?" Inji Amran.
   " Kada ka hallakani, duk abunda kake da bukata zan yi maka." Inji dan fashin cikin magiya, Anan Amran ya nuna masa taswirar da Zamran ya basa.
   " Kasan ko wacece wannan yarinyar?"Amran ya tambaya.
   " Ban sani ba, amma zan iya hadaka da mai gidana Budda, inada yakini cewa zai iya fada maka ko wacece domin ina yawan ganinsa da irin wadannan taswirorin." Inji dan fashin. 
   " Kafin nan zaka rakani na saye sabuwar sutura ta sanyawa domin na gane cewa mutane suna kallona ne sabida suna min daukar attajiri kuma wannan dalili yasa ire irenku barayi kuke bibiyata." Inji Amran. Anan dan fashin ya rakasa babban shagon saida sutura, anan Amran ya zabi irin wadanda yakeso daga nan suka fito.
  " Zan baka ajiyar wadannan kayan nawa na sarauta, idan na kammala abunda nake zan dawo na karba amma inaso kayimin alkawarin cewa bazaka nuna ma kowa wannan sutura tawa ba."
   " Na aminta." Inji dan fashin, anan dan fashin yakai Amran har gidansa domin ya canza sutura, kuma anan ne Amran ya baiwa dan fashin kayansa na sarauta.
Page 47
   " Meye sunanka?" Amran ya tambayesa.
   " Haladu, zaka iya kirana da Haladu."Inji dan fashin.
   " Idan muka tafi wurin mai gidanka inaso ka nuna masa cewa ni abokinka ne domin a hakane kawai zai aminta dani."Inji Amran.
   " Na aminta amma kuma..." Haladu na fadar haka sai ya dubi hannunsa dake zubar jini sanadiyar yankan da Amran ya masa da takobi a lokacin da suna gumurzu. " Idan ya tambayeni game da wannan ciwo nawa me zan fada masa?" Haladu ya tambaya. Anan Amran ya kalli hannun nasa, daga nan sai ya yanko wani kyalle ya daure ciwon.
   " Idan munje ya tambayeka zaka iya fada masa cewa ka samu rauni ne a wurin horo, kuma ina fada maka wannan shine matsalar zama dan fashi, kaga da ace kana neman naka da hakan bata faru ba, kuma idan kaci gaba da wannan hali wataran wuyanka ne zai samu irin wannan raunin. " Inji Amran.
   " Kada ka damu aboki, wannan shine na farko kuma shine na karshe." Inji Haladu. Daga nan sai Haladu ya jagoranci Amran har zuwa gidan Budda wanda shine mai gidansa. Bayan sun gaisa da Budda ne sai Amran ya nuna masa taswirar kuma ya fada masa bukatarsa, daga nan sai Budda ya amshi fatar da aka zana taswirar kafin ya fara magana kamar haka:
   " Wannan yarinya sunanta Zahra Zu diyar sarki Mahir na masarautar Ƙabru, kuma inada yakinin cewa itace sabida nayi mata farin sani, kuma abunda yasa na mata farin sani shine mahaifiyar Zahra Zu din ta kasance yar uwar matata." Anan Budda ya tsaya ya kalli zanen kafin ya cigaba da magana. " Amma kai me kake nema a wurinta?"
   " Kada ka damu idan lokaci yayi zaka sani! ko zaka iya fadamin inda masarautar  Ƙabru take?" Amran ya tambaya. 
   " Zan fada maka amma inaso kayimin alkawari daya!" Inji Budda
   " Wane alkawari?" Amran ya tambaya.
   " Inaso idan kayi tozali da Zahra Zu, to ka sace ta ka kawo min ita ni kuwa zan maka kyauta wadda baka tsammani."Inji Budda.
   " To amma me yasa kake son aiwatar da wannan danyen aiki a kanta, akwai wani laifi data yima ne?" Amran ya tambaya.
   " Ba itace tamin laifi ba Kakanta ne  Barhan yamin laifi." Inji Budda
   " Wane laifi ya maka?" Amran ya tambaya.
   " Wato ka sani mahaifin gimbiya Zahra Zu sarki Mahir yanada mahaifi da ake kira Barhan, to shi Barhan din shine sanadiyar rabani da matata Munaihat wadda take kwance a cikin kasa.
Page 48
  " Kuma akan wannan dalili yasa nakeson daukar fansa ga jikanyarsa Zahra Zu!" Inji Budda.
  " To amma meye hujjarka na cewa Barhan  shine ya kashe matarka Munaihat?"Amran ya tambayesa.
   " Wannan labari ne mai tsawo wanda bazan iya fada maka shi a yanzu ba, amma idan ka sato Zahra Zu kazo min da ita to ni kuma zan baka kyauta mai tsoka daga nan kuma sai na fada maka wannan labari da kake bukata wanda a cikinsa ne zakaji hujjar dake baiyana  cewa Barhan shine ya kashe min mata Munaihat," Inji Budda. Anan Budda yawa Amran kwatancen masarautar Ƙabru daga nan Amran ya hau dokinsa bayan ya musu ban kwana, anan ya kama hanyar zuwa wannan masarauta ta Ƙabru.......
   " To kaji labarina, nazone da nufin kare gimbiya Zahra Zu ba wai da nufin na saceta ba kamar yadda Budda yake bukata ba, kuma nazone da nufin kareta daga hatsarin  dake shirin afka mata duk da har yanzu ban san kowane irin hatsari bane!" Inji Amran. " Sabida haka yanzu sai kaban naka labari da kuma abunda yasa kake neman gimbiya Zahra Zu!" Anan Gazman yayi murmushi yana kallon ruwan teku.
    " Bazan iya baka labarina a yanzu ba domin dare yayi, amma idan mun isa wurin da wadannan miyagu zasu kaimu bayan mun samu hanyar kubuta to zan iya baka nawa labarin." Inji Gazman.
   " Ba matsala dama nima bacci nakeji." Inji Amran. Anan suka kishingida suna angaje sabida baccin daya addabesu, haka suma sauran fursunoni da yawansu sunyi bacci, wadannan samudawan  mutanen ne kawai a tsaye cikin shigar yaki ko motsawa basuyi suna kallon kowa domin su tabbatar da tsaro, shi kuwa narkeken jirgin ruwan sai gudu yake yana ambaliyar ruwa idan iska ya kada da karfi.
   WADANNAN SAMUDAWAN MUTANE DA SUKA KAMA AMRAN DA GAZMAN TARE DA SAURAN MUTANEN DA BASUJI BASU GANI BA, SHIN ME HAKAN YAKE NUFI?KUMA WANE WURI NE ZASU KAISU?
   MENENE LABARIN GAZMAN?
   SHIN AMRAN DA GAZMAN ZASU KUBUTA DAGA SHARRIN WADANNAN MUTANE KUWA?
   SHIN AMRAN DA GAZMAN ZASU GANO GIMBIYA ZAHRA ZU KUWA?
   MU HADU A SASHE NA HUDU DOMIN JIN CIGABAN WANNAN LABARI
  to be continue in episode four
                                                                                 
                                                                                     
                                                                              
                                                                                GIMBIYA   ZAHRA ZU
                                                                                     by
                                                  Abdul King Article & Abdul Alhaji Musa 10K
                                                                                Episode 4
                                                                            Labarin Gazman
To my confrere Halima Bala Wakili and Yareema Shahid
Page 49
Hargowar mutane shine yayi sanadin tashin Amran da Gazman, anan suka mike tsaye suna kallon wadannan samudawan mutane dake ta faman tayar da sauran fursusonin dake daure da kaca, a wannan lokaci narkeken jirgin ruwan ya iso bakin gaɓa, da karfin tsiya wadannan samudawa suka fito dasu Amran a cikin jirgin daga nan suka ingiza keyarsu a cikin wani kasurgumin daji dake kusa ga ruwan, tafiya su Amran keyi ba tare da sanin inda za a kaisu ba, su kuwa samudawan zagaye suke dasu wasu a gabansu wasu a bayansu, wasu kuma gefensu na hagu dana dama. A haka su Amran suka cigaba da tafiya cikin tsaro da tursasawar wadannan samudawan.
   " Wayyo, bazan iya tafiya ba." Haka wata mace ta fada daga nan sai ta fadi kasa tana nishi dai dai, anan sauran fursononi maza da mata sukayi tsaye suna kallonta, daga nan sai wani basamude ya zare takobinsa, taku ya farayi daya bayan daya har ya iso wurinta, daga nan sai yasa takobi ya yanke kacar da aka daureta dashi.
   " Zaki iya tafiya ko bazaki iyaba?" Haka ya fada cikin muryarsa mai ban tsoro.
   " Bazan iyaba, ka taimakeni." Haka matar ta fada cikin siririyar muryarta. Basamuden najin haka sai ya daga takobi, sai da ya saita da kirjinta daga nan ya karaso wurinta da nufin soka mata shi, shi kuwa Amran na ganin haka sai ya daka masa tsawa da wata murya mai ban tsoro.
   " Kai." Anan basamuden ya juyo yana kallon Amran. " Kai wane irin mutum ne, idan bazata iya tafiya me zai hana ku bata ruwa tasha." Anan basamuden ya kara kallon Amran da kyau domin ya tabbatar da cewa shine ke masa magana ko kuwa dai. Murmushin rainin wayo basamuden yayi wa Amran daga nan sai ya nufi matar.Da karfin tsiya ya soka mata takobin a kirji, abunda yaba mutane mamaki shine duk da tsananin zogin da matar keji amma batayi ihu ba, sai murmushin da take tana kallon Amran. Daga nan basamuden bai kara komawa ta kanta ba.
Page 50
A haka aka ingiza keyarsu su Amran cikin rashin sanin cewa matar ta mutu ko kuma tana da rai! Haka suka cigaba da tafiya har suko iso wani irin tangamemen gida mai doguwar gina, kofar gidan ma abun kallo ce, daga isowarsu wani basamude ya kwankwasa kofar, anan mai tsaron kofar ya leko cikin wata yar karamar huduwa domin yaga ko su waye, bayan ya tabbatar dasu sai ya bude kofar, anan su Amran suka shiga suna mai dube dube, makeken fili ne sai wasu samudawa dake ta faman daukar horo, sai mutane maza da mata yan fursuna sai aikace aikace suke, wasu suna fashin duwatsu wasu kuma suna baiwa dawakai abinci, a can karshen filin wani gida ne ya tsaru iya tsaruwa, Haka aka tursasa su Amran har sai da suka iso gab da gidan, daga nan sai aka tsayar dasu, ba a fi dakika goma ba sai ga wani mutum ya fito  a cikin gidan, kai da ganinsa kasan yana hutawa domin sanye yake da sutura ta alfarma, tafiya yake wasu samudawa a cikin shigar yaki suna take masa baya, tsaye mutumin yayi saman matattakalar gidan daga nan sai ya tsura musu idanu a cikin murmushi kafin ya fara magana.
     " Ina muku barka da zuwa fadar Jalani, mashahuri a fagen kasuwancin bayi da kuma yan tasu, ina muku bushara da cewa dukkan wanda ya zo wannan wuri to ba shida wani suna wanda yafi bawa, sabida haka dukkaninku kun dawo karkashin kulawar shugabanmu Jalani, sai yadda yaga dama zai yi daku," Mutumin na fadar haka sai ya juya zuwa cikin gidan su kuma samudawan dake bayansa suka rufa masa baya, daga nan aka tura su Amran makwancinsu, daga shigarsu makwancin sai sukaga ashe makeken daki ne sai wasu kananan gadaje a ciki, anan aka kwance musu kacar dake daure dasu daga nan aka basu umarni duk wanda keso zai iya hutawa, anan kowa ya kama gadonsa maza da mata ba ruwan kowa da kowa, Amran da Gazman sun samu gado a waje daya, a kusa ga Amran wani mutum ne mai tsananin surutu, tunda su Amram sukazo yake damunsu dasu fada masa labarinsu yadda yaga suna abubuwa tare. 
 " Me yasa kake son sanin labarinmu?" Amran ya tambayesa.
   " Sabida naga kuna kome tare da alama akwai wani sirri a tare daku!" Inji mutumin.
   " Wane sirri kaka magana akai?" Gazman ya tambayesa.
   " Da farko dai sunana Ragib." Inji mutumin.
  Page 51
   " Kuma abunda yasa nakeson sanin labarinku shine tun a lokacin da aka shigo daku a wannan wuri naga cewa baku damu ba ko kadan amma sauran mutane kowane sai mazurai yake cikin tsoro." Inji Ragib. Anan Amran da Gazman suka kalli juna, can sai Amran ya nisa kafin ya fara magana kamar haka:
     " To ai haka kaima, ko kadan baka damu ba, kuma idan da hali zan so naji abunda yasa baka damu da zamanka a wannan gida ba." 
    " Ni abunda yasa ban damu ba sabida sabon danayi ne, domin a kalla yanzu na shekara biyar a wannan gida ina bauta." Inji Ragib.
    " Shekara biyar fa kace, kuma baka gudu ba?" Amran ya tambayesa cikin mamaki! Ragib murmushi yayi kafin ya bashi amsa.
   " Da ace akwai hanyar gudu a tunanin zan cigaba da zama a nan ne?" Inji Ragib.
   " To ka fada muna a cikin shekarun da kayi a wannan gida shin ko akwai wani sirri da ka sani kuwa!" Gazman ya tambayesa.
   " Gaskiya ba abunda na sani akai sabida suna gudanar da  abubuwansu a sirrance ba tare da kowa ya sani ba, haka kuma sun dauki kwakkwaran mataki game da duk wanda ya shigo a wannan gida yadda bazai iya fita ba komi gwanintarsa, kuma abun mamaki shine duk tsawon shekarun da nayi ban taba hada ido da shugaba Jalani ba domin baya fitowa, kuma inada tabbacin cewa idan zaka tambayi mafi yawan yan fursunan da aka kama to bazasu iya fada maka kammaninsa ba domin ba wanda ya taba ganinsa, iyaka idan yanada sako sai da ya aiko dan aikensa wato Tajir wanda ya muku hudubar shigowa idan zaku iya tunosa."
    " To amma a tunaninka me yasa shugaba Jalani  baya fitowa?" Inji Amran.
    " Nima ban sani ba! amma nasan da cewa duk sati shugaba Jalani yakan aiko mayakansa suzo nan su zabar masa namiji daya, kuma a cikin wadanda ake zabar masa har yanzu ba wanda ya taba dawowa kuma banada masaniya akan abunda yake aikatawa da mazan da ake kai masa." Inji Ragib.
   " To amma ya akayi kasan da cewa shugaba Jalani ake kaiwa mazan ba wani ba?" Inji Gazman.
   

Page 52
   " Sabida shi kadaine a cikin gidan, kuma a duk lokacin da za a yi zaben to Tajir ne ke jagorantar mayakan, kuma a cikin maganganunsa yakan nuna cewa shugaba Jalani shine keda bukata da a zabar masa namiji daya." Inji Ragib. 
     " Ka taba tambayar Tajir abunda shugaba Jalani yake aikatawa ta mazan da ake kai masa?" Inji Amran.
     " Aa, ban taba tambayarsa ba domin hukunci zai iya hawa kaina!" Inji Ragib.
     " To amma kai ya akayi ka shigo wannan gida?" Amran ya kara tambayarsa. Anan Ragib yayi shiru kadan kafin ya fara basu labari kamar haka:
Ni mutumin Karaba ne, Karaba wani dan karamin sansani ne a kusa ga ruwan teku, mafi yawan mutanen wannan sansani sana arsu itace Su, amma ni bana Su, sai dai inada narkeken jirgin ruwa da nake daukar fasinjoji daga gari zuwa gari, da wannan jirgi nake daukar nauyin iyalina domin na kasance inada mata daya da ake kira Harita, wata rana a cikin dare bayan na dawo daga aiki na ajiye jirgin a gabar teku, juyowar da zanyi haka sai naji ihun mace, anan na ranta a guje domin bada agajin gaggawa, haka nayi gudu har na iso wata bukka inda nakejin ihun yana fitowa a ciki, ai kuwa ina shiga sai naga mace a durkushe ta lullube fuskarta yadda mutum bazai iya ganin kome ba. Anan na fara tafiya da nufin zuwa inda take ai kuwa kafin na isa wurinta sai kafata ta tsunduma a cikin wani boyayyen tarko, wata kaca naga ta fado kamar daga sama, a nan wannan kaca tamin mugun dauri yadda ko nishi dakyar nakeyi, kafafuwana a sama kaina a kasa. Matar na ganin haka sai ta mike tsaye, tabi tayi sau uku sai naga wasu samudawa sun shigo cikin shigar yaki. 
  " Kinyi aiki mai kyau Zuhru Zu, yanzu ki tafi gida sai mun nemeki!" Haka wani basamude ya fada daga nan sai ya jefa mata wata karamar jaka, anan ta dauki jakar ta fita, tun inajin haniniyar dokinta har na daina. Anan ne na gane cewa wadannan samudawa sun hadamin tarko ne da mace, daga nan suka kamani suka zo dani a nan gidan, mafi yawan wadanda na tambaya zakaga duk kusan abu daya ne ya faru damu wato suma an hada musu tarko ne da mace, yanzu shekaru biyar kenan danabar matata Harita ba tare da sanin halin da take ciki ba, na barota da ciki yanzu ban sani ba kota haihu ko kuwa dai.....

Page 53
  Anan Amran da Gazman suka kalli juna bayan Ragib ya kammala labarinsa, wato kenan wadannan samudawa sun dade suna hadawa mutane tarko da mace.
   " Inaso ka fadamin wane irin namiji shugaba Jalani yakeso akai masa?" Amran ya tambayi Ragib.
   " Bayada zabi, domin duk bayan sati Tajir kan hada ƙuria, ita ƙuriar yadda ake yinta shine za a samu karamar fata ta dabba a yankata iya adadin mazan dake wannan gida, kowace fata za a yi mata zanen takobi amma sai a zabi daya wadda za a yiwa zanen maciji, sai ace kowa ya zaba, bayan an gama zaba sai a biyo layi daga nan Tajir zai dinga bi yana dubawa, duk wanda fatarsa ta kasance dauke da taswirar maciji to shine za a kaiwa shugaba Jalani." Inji Ragib.
   " Shekarunka biyar a wannan gida amma ƙuria bata taba fadawa kanka ba hala me yasa?" Inji Gazman.
   " Nima abunda ban sani ba kenan har yanzu." Inji Ragib.
   " Yaushe ne za a gudanar da wannan gasar ta ƙuria?" Inji Amran.
   " Gobe ne, domin gobe ne cikar kwanakin mako." Inji Ragib, ba a fi dakika goma sai sukaji ana buga musu ƙararrawa mai nuni da cewa lokacin cin abinci yayi. Anan suka fita waje bayan Ragib ya musu bayani, layi sukabi daga nan sai suka fara tafiya daya bayan daya kowa na karbar nasa akushi da moɗar ruwa har kowa ya samu daga nan kowa ya kama gabansa. A cikin dare kuwa su Amran sun yi fira sosai kafin bacci yayi awon gaba dasu.
   Tun da sanyin safiya dakarun shugaba Jalani sukazo tayar dasu Amran, da karfin tsiya aka fito dasu daga nan aka tursasa su bin layi. Shi kuwa Tajir tafiya yakeyi daya bayan daya yana kallonsu kafin ya fara bayani.
    " Ba sai nayi dogon bayani ba domin nasan da cewa kun san abunda yasa muka fito daku, sabida haka ba tare da bata lokaci ba yanzu zamu fara gasar ƙuria." Amran najin haka sai ya baro layinsa ya dawo dai dai inda Tajir zai gansa.Daga nan sai ya fara magana kamar haka.
   " Ni zan sadaukar da kaina a matsayin wanda za a kaiwa shugaba Jalani, sabida haka gasar ƙuria ta wannan mako ba sai an gudanar da ita ba."
Page 54
 Anan mutane suka tsurawa Amran ido suna mamaki domin ba a taba samun wanda ya taba yin irin wannan kasada ba duba da cewa duk wadanda ake kaiwa shugaba Jalani ba wanda ya dawo kuma har yanzu ba a san abunda ke faruwa dasu ba. Shi kansa Tajir sai da abun ya basa mamaki domin kallon Amran yake ko kyaftawa baya yi. Shi kuwa Gazman yanajin haka sai ya sheko da gudu ya rikewa Amran hannu.
   " Kai wane irin mutum ne, kafi kowa sanin cewa duk wanda aka kaiwa shugaba Jalani ya tafi kenan bazai dawo ba, amma kai sabida zamanka mutum baka damu ba." 
   " Kada ka damu abokina." Haka Amran ya fada cikin murmushi. " Ka zuba ido ka gani yadda na tafi haka zan dawo." Amran na fadar haka sai samudawan dakaru suka cabesa. Anan suka ingiza keyarsa zuwa gidan shugaba Jalani, shi kuwa Gazman da Ragib kallonsa sukayi tayi har ya bace musu da gani.
    Bayan an shigo da Amran a cikin mashahurin gidan shugaba Jalani sai ya gane cewa gidan ya tsaru iya tsaruwa, cikin sauri aka jefashi bayi domin ya wanke jikinsa, bayan ya kammala ne sai aka dauko wata sutura ta alfarma aka danka masa, daga nan sai aka nufo dashi wurin wani kilisi mai tsananin laushi, abincuccuka ne kala kala na alfarma, a nan Amran yaci yasha har sai da yacika cikinsa. Yana kamallawa sai dakaru suka jagoranceshi har zuwa wani daki, daga shigarsa dakin wani narkeken gado ya isko, kwanciyarsa yayi ba tare da bata lokaci ba bacci yayi awon gaba dashi. Haka Amran yayita sharar bacci shine bai farka ba sai tsakiyar dare bayan da yaji dakaru sun shigo dakin da yake, da karfin tsiya suka dankesa daga nan suka shiga wani lungu dashi, haka suka cigaba da shiga lungu lungu sako sako har sai da Amran yayi zaton gidan baida iyakar girma, cikin wani daki mai ban tsoro suka jefashi daga nan suka kulle kofar, anan Amran yayi tsaye yana dube dube domin baya gani sosai sabida fitilar dake dakin yar karama ce, shi dai dakin ya kasance katon gaske mai dauke da lunguna lunguna kuma da alama kayan dake ciki babu yawa, wani dan karamin sauti marar ma ana ya faraji a can gefen dakin daga nan sai yaga wani duhu ya hade wuri daya. 
     " Amran dan Habir." Haka Amran yaji wata karamar murya mai ban tsoro ta fadi sunansa.
    " Waye?" Amran ya fada da karfi.
 Page 55
   " Inajin kamshin dan sarki Afran," Haka muryar ta kara fada, shi kuwa Amran idan ya duba inda yakejin muryar ba abunda yake gani in banda duhu daya cure wuri daya. Anan Amran ya fara tunani ko shugaba Jalani ne ke masa magana kuwa? To amma idan shine ya akayi yasan sunansa. Kuma yace yanajin kamshin dan sarki Afran, kuma dan sarki Afran shine Gazman! To ya akayi yasan da Gazman?
   " Dama ka sanni ne?" Amran ya tambaya.
   " Dama nasan da zuwanka," Haka muryar ta fada, " Naso ace dan sarki Afran ne!" Inji muryar.
   " Da ace shine me zaka yi masa?" Amran ya tambaya. Anan Amran yaji wani dan karamin sauti marar ma ana yana tashi.
   " Afran ya yaudareni!" Haka muryar ta fada a hasale cikin sauti mai amo daban tsoro," Ya yaudareni." Haka aka kara maimaitawa, shi kuwa Amran kallo yake inda yakejin sautin na fitowa amma baya ganin kome in bakin duhu daya cure wuri daya. 
     " Meye nufinka a kaina?" Amran ya tambaya.
     " Meye nufina a gareka!" Haka muryar ta fada daga nan sai Amran yaji sautin bugegeniya ta hakora, sauti yakeji ana buga hokara da matsananci karfi kamar baza a daina ba. Daga nan sai yaga duhun ya taso gadan gadan ya nufosa, anan Amran ya fara ja da baya domin yasan haduwarsu bazatayi kyau ba. Amran na cikin ja da baya sai yaga duhun ya bace baya ganin kome, anan yaci gaba da kalle kalle, yana cikin haka sai yaji wani abu da bazai iya bayyanawa ba ya dagasa sama, haka kawai yaji an yi sama dashi ana juyashi da karfin tsiya, daga nan sai aka fara mulmula shi a can gefen dakin inda duhun yake, anan Amran yaga duhun ya kara dabaibaye koina, ba yadda Amran bai yiba domin ya rike kansa amma abu yaci tura sai kara janyosa ake da karfin tsiya, cikin wannan hali ne Amran ya janyo yar karamar fitilar dakin, yana haskawa sai yaji an sakosa da karfin tsiya, anan yayi mugunyar faduwa ba tare daya samu damar ganin abun ba, amma a can gefen dakin inda duhun yake sai wani sauti yakeji mai ban tsoro wanda ke nuni da cewa abun ya samu rauni, cikin tsoro Amran ya mike ya nufi kofar dakin, a wannan lokaci kuwa duhun ya durfafo sa da matsanancin sauri, cikin jarumta Amran ya fara bugun kofar dakin har sai dai ya balle ta, yana fita dakin duhun na karasowa, cikin sauri ya kulle kofar yana mai ja da baya.
Page 56
Har yanzu yanajin sauti mai amo daban tsoro  yana fitowa a cikin dakin, daga nan sai Amran ya mika a guje yana shiga lungu lungu na gidan domin neman hanyar fita, har yanzu tunani yake wai kuwa wannan abu daya gani shine shugaba Jalani kuwa? idan shine to me yasa yake zama a cikin duhu? kuma idan shine me yasa bayason haske? Haka Amran yaci gaba da gudu har ya fara jiyo motsin dakaru, a nan ya labe a wani lungu domin yayi tunanin hanyar da zai bullo musu. Yana cikin laben ne sai yaji saukar naushi a fuskarsa, juyawar da zaiyi haka sai yaga wani badakare ne ya gansa shine ya kawo masa farmaki, a nan wannan badakare ya fara kaiwa Amran sara da suka da takobinsa da garkuwa, shi kuwa Amran sai kaucewa yake gashi bayada makami balantana ya mayar da martani, suna cikin wannan artabu ne Amran ya mamayesa ya masa kwaf daya, anan badakaren ya zube kasa sumamme, anan Amran yayi sauri ya cire kayansa ya aje gefe daga nan sai ya sanya na badakaren yadda idan an gani sai ayi tsammanin shima badakare ne, Anan ya dauki makaman badakaren ya rike daga nan ya cigaba da tafiyarsa cikin natsuwa cikin rashin sanin cewa wasu dakaru biyar sun hangosa tun lokacin da yayiwa dan uwansu kwaf daya. Anan sukayi kukan kura sukayo kansa, shi kuwa ya wanzu yana mai kare kansa da mayar da martani, cikin kankanin lokaci ya gama dasu daga nan ya dauki makamansu ya boye a cikin jikinsa. Cikin sauri Amran yaci gaba da tafiya yana mai bin lungu lungu na gidan har ya samu damar fitowa ba tare da an ganesa ba, daga nan sai ya nufi makwancinsu, koda ya shiga su Gazman sunyi bacci, da sauri ya tayar dasu tare da dukkanin yan fursunan da aka kama maza da mata. Anan ya fada musu cewa idan har zasu basa hadin kai to shi zai jagorance su  domin su samu damar fita a cikin gidan yanzun nan. Cikin amincewa suka yarda, anan ya rarraba musu makaman daya amshe na dakaru daga nan suka lallaba zuwa kofar gidan, suna zuwa suka yiwa masu gadin kofar kwaf daya, daga nan suka fara kokarin bude kofar gidan, to a cikin wannan kokari na bude kofar ne wasu dakarun suka hangosu, anan suka nufosu suna mai sako musu kibiyoyi. Cikin gaggawa su Amran suka bude kofar daga nan suka fara gudu, su kuwa dakaru sai binsu suke suna halbi baji ba gani, da yawan mutane sun tsira wasu kuma an halbe su, Amran, Gazman da Ragib suna cikin wadanda suka tsira, bayan fitarsu gidan ne sai suka nausa daji suna gudu iya karfinsu kamar ransu zai fita.
Page 57
  Sun dade suna gudu dakaru na binsu saman dawakai suna halbinsu da kibau kafin su samu maɓoya a cikin wani kogo, daga shigarsu kogon sai suka hango wuta naci a can nesa, cikin sauri suka isa wurin, anan sukaga mace a zaune tanashan wuta, Amram da Gazman sun gane matar domin itace wadda ta fadi a lokacin da za a kawosu gidan shugaba Jalani ta nuna cewa bazata iya tafiya ba wanda sabida haka wani basamude ya soka mata takobi a kirji, har aka kawosu gidan shugaba Jalani basuda masaniya cewa ta mutu ko kuwa tanada rai. Ragib na ganinta sai ya sheko da gudu wurinta, itama sai ta mike tsaye, anan suka rungume juna cikin farin ciki. Sai da suka dade kankane kafin su saki juna.
   " Wannan itace kanwata Sumairat." Inji Ragib.
   " Yanzu bamuda isashshen lokaci sabida haka mu fita mu nemi wurin domin ako yaushe zasu iya riskarmu a nan." Inji Amran.
   " Kafin nan inaso ki fadamini meya kawoki wannan wuri?" Inji Ragib.
   " Tun bayan daka ɓata abubuwa suka fara ja da baya sabida haka naga ya kamata na fita nemanka, to a cikin wannan tafiya ne na hadu da wadannan miyagun mutane, anan suka kamani suka mayar dani baiwa." Inji Sumairat. Anan ta nuna masa tambon sukar takobin da akayi mata a kirji, su a tsammaninsu ta mutu ashe bata mutu ba, a cikin wannan kogo ta samu mafaka kuma taci gaba da jinyar ciwonta tana ciyar da kanta da ya yan itatuwa, bayan Sumaira ta kammala labarinta sai dukkansu suka fita cikin kogon, anan suka nufi gabar ruwa da gudunsu domin gani ko zasu samu jirgi, haka suka yita gudu har suka fara ganin dishi dishin ruwan teku, a can gabar ruwan wani katon jirgi ne sai mutane maza da mata keta shiga ciki, anan suka kara kaimin gudunsu domin a wannan lokaci sunajin sukuwar dawakai a bayansu da alama dakarun shugabana Jalani ne suka biyosu, anan aka fara halbo musu kibiyoyi, su kuwa gudun suke iya karfinsu domin su cimma ruwan, gashi jirgin ya tashi sai zuba gudu yake, bayan sun iso gabar ruwan ne sai sukaga jirgin yayi nesa dasu amma kuma cikin sa a an bar musu igiyoyi wadanda zasu rikewa sai mutanen jirgin su janyo su, haka kuwa akayi, da sauri suka rike igiyoyin su kuwa mutanen jirgin sai faman janyosu suke, a wannan lokaci dakarun shugaba Jalani sun iso gabar ruwan amma ba abunda zasu iya domin su Amran sunyi nesa dasu, dawakansu haniniya sukayi suna ja da baya cikin tsoro.
Page 58
Tajir wanda shine ke jagorantar dakarun ba karamin bakin ciki ne ya rufe saba ganin cewa dukkan yan fursunan gidan sun tsere ba wanda suka kama in banda yan kalilan da suka halbe har lahira, bayan an janyo su Amran a cikin jirgin sai suka gane cewa mafi yawan mutanen da suke cikin jirgin yan fursuna ne abokansu na gidan shugaba Jalani, bayan sun karaso ne sai mutane suka fara musu jin jina akan wannan kokari da sukayi, shi kuwa Ragib tun da ya shigo jirgin sai ya fara kalle kalle domin ji yake kamar yasan jirgin, yana cikin dube duben ne sai yaji an kwala masa kira, juyawar da zaiyi haka sai yaga matarsa ce Harita, anan ta sheko da gudu suka rungume juna cikin farin ciki, a nan ta labarta masa cewa wannan jirgin sane kuma dashi take sana ar kai fasinjoji gari zuwa gari, yanzu ma ta ajiye wasu fasinjoji ne sai ta hadu da yan fursunan da suka tsero a gidan shugaba Jalani, anan suka bukaci taimakonta bayan sun fada mata labarinsu daga nan ta aminta zata taimakesu cikin rashin sanin cewa mijinta na cikinsu, kuma a tare da ita akwai yara biyu namiji da mace.
   " Wadannan diyanka ne, Talim da Talima, bayan ɓatarka ne na haifesu." Anan Ragib ya rungumesu cikin farin ciki sake saduwa da iyalansa. Daganan sai Sumaira tazo suka gaisa, daga nan suka kebanta a can gefe suna hira, Amran da Gazman dake tsaye suna kallon abunda ke faruwa suma sai suka koma gefe a nan suka samu wuri suka gincira suna kallon yadda ruwan teku ke ambaliya da karfi idan iska ya kada. Daganan sai mai aikatan Harita suka fara rabawa mutane akushin abinci, haka suka yita rabawa har sai da suka tabbatar kowa ya samu, wani katon kwatarne suka girke cike da ruwa, a cikin kwatarnen akwai moɗa yadda mutum zai iya shan ruwa cikin sauki. 
     " Inaso ka fadamin waye shugaba Jalani?" Amran ya tambayi Gazman bayan ya kai loma a bakinsa.
     " Ya za a yi nasan koshi waye!" Haka Gazman ya fada daga nan sai ya tashi tsaye da alama ya koshi da abincin,  anan ya  nufi kwatarne, moɗa ya janyo ya wanke hannunsa daga nan ya cika cikinsa da ruwa, shi kuwa Amran kallonsa kawai yake yana jiran dawowarsa, bayan Gazman ya zauna ne sai Amran ya basa labarin abunda ya faru bayan dakaru sun kaisa gidan shugaba Jalani da yadda akayi ya fito.
   " Amma akwai ban mamaki sosai." Inji Gazman, shi kuwa Amran murmushi yayi daga nan shima sai ya mike tsaye domin ya koshi da abincin.
Page 59
Anan Amran ya nufi kwatarne, moɗa ya janyo ya wanke hannunsa daga nan ya cika cikinsa da ruwa, bayan ya zauna ne sai ya fuskanci Gazman.
   " Yanzu lokaci ne daya kamata ka fadamin labarinka da kuma manufarka akan gimbiya Zahra Zu!" Inji Amran. Gazman najin haka sai yayi murmushi daga nan sai ya fara labarinsa kamar haka:
   A birnin Maliya an yi wani maƙeri da ake kira Jadir, Jadir yanada ɗa ƙwaya daya da ake kira Afran, Afran ya taso yaro mai tsananin son dukiya da kuma son abun duniya domin a duniya ba wanda ya tsana irin talaka, duk da cewa mahaifinsa Jadir ba mai arziƙi bane amma yanada ruhin assiri, shi kuwa Afran  duk da wannan ruhin assiri na mahaifisa ji yake gaba daya duniyar ta masa zafi, ba abunda yakeso in banda ya samu wata dama ta samun arziƙi ko yaya ne, Afran yanada wani aboki Jalani, shima Jalani irin zuciyar Afran ne dashi domin ya tsani talauci, gashi mahaifinsa ba wani mai arziƙi bane domin maƙeri ne ana ce ma mahaifin nasa Galandu, kamar yadda Afran da Jalani suke abokai haka Jadir da Galandu suke abokai, Jadir da Galandu basuda mata domin matansu sun mutu ne a wurin haihuwa, kamar yadda Afran yake shi kadai ne a wurin mahaifinsa haka shima Jalani shi kadaine a wurin mahaifinsa. Afran da Jalani ba kananan tantirai bane domin basu damu da taimakon iyayensu ba. Mafi yawan lokutta sukan raba dare a dandali kafin su dawo gida, ba yadda iyayensu basu yiba domin ganin cewa sun daina wannan hali nasu amma abu yaci tura sabida haka suka zura musu idanu, to wata rana Afran da Jalani sun dawo daga dandali kamar yadda suka saba suna tafiya suna angaje domin bacci ya musu yawa, cikin wannan tafiya da suke ne sai Jalani ya fadi domin baccin yafi karfinsa, ba yadda Afran bai yiba domin ya tayar dashi amma ya kasa, sabida haka sai ya janyosa gefe ya aje daga nan ya nufi wani gulbi dake kusa domin ya debo ruwa ya zuba masa ya gani ko zai tashi, tun da ya nufi wannan gulbi gabansa ke faduwa ba tare dayasan dalili ba, hakama jikinsa sai karkarwa yake kamar mai jin sanyi, bayan ya iso gab da gulbin sai yaji busar sarewa na tashi, anan yayi tsaye cikin mamaki domin bai san inda busar ke fitowa ba, bayan dakiku kadan da yaga tsayin bazai amfane shiba sai ya cigaba da tafiya har ya iso gaɓar gulbin, bayan ya iso gaɓar ruwan gulbin ne sai ya gane cewa busar sarewar a cikin gulbin take fitowa, anan yayi tsaye yana dubawa iya ganinsa amma ba abunda yake gani in banda duhun dare daya dabaibaye koina.
Page 60
   A can cikin ruwan gulbi nesa dashi sai ya hango wani dan karamin jirgin ruwa kwale kwale, a saman jirgin yana iya hango dishi dishin wani abu kamar mace amma kuma bayada tabbacin cewa mace ce iyaka dai yana ganin wani abu a saman jirgin kamar inuwa, haka jirgin yaci gaba da karasowa inda yake har yakai cewa tsakaninsa da jirgin bai wuce taku talatin ba amma kuma duk da hakan baya iya ganin ko waye a saman jirgin, bayan jirgin ya tsaya ne sai busar sarewa ta tsaya tsit. A wannan lokaci tsoro ya cikawa Afran ciki amma kuma duk da hakan bazai iya gudu ba, tsaye yayi yana kallon kallon wannan abu na cikin jirgi da har yanzu bai san ko menene ba.
    " Ka fadamin bukatarka yanzu kai kuwa zakaga aiki da cikawa!" Murya yaji tana fitowa daga cikin jirgin kamar mace kamar ba mace ba, yanaji a jikinsa yaji anyi magana amma bazai iya fadin ko wace irin murya ce yaji ba. Anan Afran ya fara tunani to shi yanzu wane abu yakeda bukata in ba dukiya ba.
   " Dukiya itace bukata ta." Haka ya fada a gaggauce kuma cikin tsoro.
   " Ka dauka cewa an gama, yanzu ka tafi gida zakaga abunda kake bukata." Haka yaji an fada daganan sai yaga jirgin ya koma da baya ta inda ya fito, daganan Afran bai kara sanin inda yake ba, sai tashi yayi yaga abokinsa Jalani na jijjiga shi.
    " Me kakeyi anan inda gaɓar ruwa?" Jalani ya tambayeshi, Anan Afran ya mike da sauri yana tunanin abunda ya faru jiya gashi yanzu safiya ce sumul.
    " Ba kome." Haka ya fada daganan ya kama hanyarsa ta zuwa gida shima Jalani ya nufi nasa gidan. Haka Afran yaci gaba da tunanin wannan  abu daya faru har ya shiga dakinsa, to a mamakinsa shine dan karamin akwatin karfen daya isko a gefe, cikin sauri ya bude akwatin domin yaga ko meye a ciki, anan yaga darhami dubu, ba karamin farin ciki ne ya rufe sa ba domin wannan shike nuni da cewa abunda ya faru jiya dashi gaskiya ne ba wai mafarki ne yayi ba, a hankali a hankali Afran ya boye akwatinsa yanacin kudinsa ba tare da kowa ya sani ba, babban abunda ke bashi mamaki shine kudin basu karewa, idan ya debi darhami goma yanzu to kafin a jima sai yaga wasu darhamai goma sun kara dawowa cikin akwatin, baa fi shekara ba sai ga Afran ya kayata gidansu kuma ya buda manya shaguna a kasuwanni daban daban, mutane sai mamaki suke ganin irin wannan dukiya amma kuma basuda masaniya akan sana ar da yake yi.

Page 61
  Afran bai manta da abokinsa Jalani ba, domin ya basa dukiya mai tarin yawa domin yaja jari amma kuma yaki fada masa ainahin inda yake samun kudi, haka shima Jadir mahaifin Afran ba yadda bai yiba domin Afran ya fada masa yadda akayi yake samun kudi amma Afran yaki. Wata rana sai aka wayi gari sarki ya mutu, kuma gashi sarkin bayada magaji, sabida haka sai aka sanya gasa da zimmar cewa duk wanda yaci gasar shine zai kasance sarkin garin, ita gasar yadda ake yinta shine mutum zai kayar da wargajejen itace da sara goma. Tunda aka sanya wannan gasar ba wanda yace zai iya shi kuwa Afran da yaji hukuncin gasar sai ya dauki aniyar shiga, sai da ya bari dare ya raba sai ya sudada ya tafi gulbi, yana isowa bakin gaɓar ruwan sai yaga jirgin ruwa irin na wancan lokaci ya durfafo inda yake, ba karamin jin dadi yayi ba domin abunda yake bukata kenan, jirgin na tafiya sai busar sarewa ke tashi, idan ya duba bazai iya gane ko waye a saman jirgin ba amma a nasa tunanin yana kyautata zaton cewa mace ce iyaka dai baida takamammen sani akan hakan. Sai da jirgin ya tsaya sannam busar sarewar ta tsaya. Anan Afran ya duba amma bazai iya ganin ko waye a cikin jirgin ba domin ba abunda yake gani in banda tsananin duhu mai hade da wata inuwa.
   " Meye bukatarka?" Haka muryar ta fada kamar mace kamar ba mace ba. Anan Afran ya zayyana bukatarsa nason cin wannan gasa kuma daga karshe aka amsa masa, wani takobi aka jefo masa a gabansa daganan aka umarcesa daya dauka.
   " Duk abunda ka sara da wannan takobi zai tarwatse ko menene." Haka muryar ta fada daga nan sai yaga jirgin ya juya zuwa inda ya fito, haka Afran yayita kallon jirgin har ya bace masa da gani daganan sai ya juya zuwa gida. Da sanyin safiya bayan an gudanar da gasa, Afran ne ya samu nasara da yake shi kadaine yace zai iya, ba tare da bata lokaci ba aka nada Afran a matsayin sarkin Maliya. Murna a wurin Jadir bata boyuwa wai yau tantirin dansa ne ya zama sarki, hakama Jalani da mahaifinsa Galandu sun tayasa murna sosai, daga wannan lokaci rayuwa ta dawowa Afran sabuwa dashi da abokinsa, gari ya zama nasu sai yadda sukeso, Afran ya nada Jalani a matsayin wazirinsa, shi kuwa mahaifinsa Jadir yanzu yafi karfin yayi  ƙira sai dai yasa ayi tunda dansa ne sarki, haka shima Galandu baya  ƙira sai dai yasa ayi tunda dansa ne wazirin sarki. 
Page 61
Shi kuwa Afran sai yaci gaba da mu amala da wannan abu da yake ganin cewa mace ce cikin rashin sanin ko menene, mutum ce ba mutum bace bai sani ba, a duk lokacin da yakeda bukata iyaka ya tafi bakin gulbi, kuma a duk lokacin daya tafi to cikin jirgin ruwa zata iskosa, kuma a duk lokacin da jirgin ya tsaya to duk yadda ya hanga bazai iya fadin siffar jikin abun ba, namiji ne ko mace bai sani ba, amma yafi ganin cewa mace ce, hakama muryar, bazai iya tantance ainahin muryar ba amma yafi ganin cewa ta mace ce, to abun tambaya shin wai shi wannan abu da Afran yake mua mala dashi menene? Wata rana sai Afran yaje da bukata a wurin wannan abu marar siffa, bayan ya isa bakin gulbi sai ya fadi bukatarsa nason zama sarkin da yafi kowane sarki karfin mulki, kuma ya zamana cewa dukkan sarakunan dake makwabtaka dashi su zamo tamkar bayinsa, wato shike juyasu yadda yakeso, anan wannan abu mai siffar mace ya fada masa cewa, idan har yanaso wannan bukata tasa ta biya to dole sai ya auri wata mace mai suna Azmana, ita wannan mace itace zata haifa masa yaron da zai janyo masa wannan matsayi da yake bukata, anan Afran ya koma gida da zimmar cewa gobe gobe zai auri wannan mace tunda har an masa kwatancen siffarta, kuma abun burgewa shine a cikin birninsa take, tun da sanyin safiya Afran ya jagoranci dakaru suka nausa bayan gari inda aka fada masa, a nan ya tarar da dan karamin gida sai gona a gefe, a nan ne Afran ya gano cewa Azmana tanada miji kuma mijinta manomi ne,  kishi da son zuciya irin nasa ne ya harzuka sa har ya kashe wannan manomi, ita kuwa Azmana da karfin tsiya ya aureta ba don tana soba, ba a fi shekara ba sai ga Azmana da ciki, kwanci tashi sai ga Azmana ta haihu, a nan aka radawa yaro suna Gazman, mako daya da haihuwar Gazman sai Azmana ta cika, sarki Afran yayi bakin ciki  sosai da rasa matarsa amma ba yadda ya iya. Gazman tun yana yaro ya kasance cikakken sadauki, wannan sadaukantaka ta Gazman na mutukar burge Afran domin hakan yakeso dan cikinsa ya kasance. Bayan Gazman ya zamanto saurayi sai sarki Afran ya koma gun wannan abu na cikin ruwa mai siffar mace, anan Afran ya tunatar da abun cewa dan cikinsa ya girma amma har yanzu baiga biyan bukata ba. Daganan sai abun ya fada masa cewa:
   " Mun dade muna sadaukar maka da abubuwan da kake bukata, sabida haka kaima yanzu zaka sadaukar mana da abunda muke bukata."  
   " Menene kuke bukata?" Afran ya tambaya.
Page 62
 " Muna bukatar jininka." Inji abun.
 " Jinina fa, meye ma anar hakan?" inji Afran.
 " Ma anar hakan shine zaka sadaukar da jinin wani mutum mafi kusanci a gareka." Inji abun. Anan Afran ya kidime domin mutane uku ne sukafi kusanci a garesa, daga dansa Gazman, sai mahaifinsa Jadir, sai kuma abokinsa Jalani! to idan hakane kenan a cikin wadannan mutane uku ne zai sadaukar da daya, to amma kuma idan hakane a cikinsu wa zai sadaukar? 
    " Wannan sadaukarwa ta zama dole a gareka, zamu baka kwana uku kayi tunani, idan kuma baka zartar ba to zamu dauki daya daga cikin jininka." Daganan sai yaji busar sarewa na tashi a cikin jirgin ruwan, daga nan sai jirgin ya juya ya nufi inda ya fito, haka Afran yayita kallon jirgin har ya bace masa da gani. Koda Afran ya isa masarautarsa kasa bacci yayi sabida zullumi da fargaba, a wannan lokaci Afran sai da yayi dana sanin yadda da wannan abu da yayi, ashe dama haka duniya take, duk abunda wani ya baka to yayi hakan ne domin kaima ka basa wani abu. Matsayar da Afran ya yanke shine zai sadaukar da abokinsa Jalani, a cikin wannan dare Afran ya koma bakin gulbi inda ya zayyanawa wannan abu mai kamar inuwar mace hukuncin daya yanke, bayan afran ya gama magana sai ya saurara domin yaji abunda za a  fada masa, sai da akayi daƙiƙu kadan kafin abun ya motsa, cikin rashin tsammani sai Afran yaga wani  katon kasko mai tsananin kyau ya fito a gabansa cike da ruwa. daga nan kuma sai yaga wani marfi yazo ya rufe kaskon. Afran kallon kaskon yakeyi baya ko kyaftawa sabida tsananin kyaunsa, shi dai wannan kasko bazai misaltu ba domin Afran bazai iya fadin ko dame aka ƙerasa ba, zinari ne, ƙarfe ne, oho shi dai bai sani ba iyaka dai yasan da cewa kasko ne.
   " Wannan fa?" Afran ya tambaya.
   " Daga yau bazaka kara ganawa dani ba, wannan kasko dana baka shine abun ganawar ka, duk abunda kake bukata shine zai fada maka." Daganan sai jirgin ya juya ya nufi inda ya fito busar sarewa na tashi, cikin sauri Afran ya kinkimi kaskonsa ya nufi masarautarsa, tafiya yake yana boye boye dayake ya batar da kama domin kada a ganesa. Bayan ya isa masarautar ne sai ya samu daki ya ajiye kaskon, kulle dakin yayi yadda shi kadai zai iya budewa don gudun kada wani yayi masa lahani.  

Page 63
Tun da sanyin safiya dakarun dake tsaron waziri Jalani suka fadawa sarki Afran cewa Jalani ya bace tun jiya suke nemansa basu samu ba, shi kuwa Afran ko a jikinsa domin yasan abunda ya faru, umarni ya basu cewa suka cigaba da nemansa. Tun daga wannan rana Afran ya zama azzalumin sarki, baya tausayawa mutanensa ko kadan, sai kuma wata bakar ɗabi a daya azawa kansa ta lalata da amare, duk angon da yayi aure to kafin ya kwanta da amaryarsa dole sai ya kaiwa sarki Afran ita, Afran ne zai fara kwanciya da ita amaryar kafin shi angon, kuma duk wanda ya taka wannan doka tasa to yanzu kansa zai riga rana faduwa, dakaru ya baza cikin gari domin su maida ido ga duk inda sukaga ana shagalin biki to su fada masa, ba yadda Gazman bai yiba domin ya hana mahaifinsa wannan ɗabi a amma abu yaci tura. Lokaci sai shudewa yake amma halin sarki Afran sai abunda ya karu sabida haka Gazman yasa masa idanu duk da cewa ya tsanesa sosai. Wata rana da sanyin safiya sai tsohon burin Afran ya dawo masa nason zama sarkin da yafi kowane sarki karfin mulki kuma ya zamo cewa sauran sarakunan dake makwabtaka dashi suna kasansa wato shine ke juyasu yadda yakeso. Cikin sauri ya tashi ya nufi dakinsa na sirri domin ya gana da kaskonsa. A hankali ya bude marfin kaskon ya aje gefe daganan sai ya zubawa ruwan dake ciki idanu kafin ya fara magana.
   " kasko kasko, inaso ka nunamin hanyar dazan mallaki sarakunan duniya gaba daya ya zamana cewa nike juyasu yadda nakeso." Ruwan dake cikin kaskon kumburi suka farayi suna kadawa da karfi suna canza kala har sai da Afran yaja baya kadan, can sai yaga taswirar wata yarinya ta fito a cikin ruwan, yarinya ce kyakkyawa budurwa mai jini a jika, cikin sauri Afran ya dauko alkalami da tawadda, sai wata yar karamar fatar damisa, anan ya zana taswirar wannan yarinya da yake gani ga fatar damisar domin yasan da cewa itace idan ya mallaketa to bukatarsa zata biya, amma kuma abu tambaya ita wannan yarinya wacece kuma ina zai sameta? bayan Afran ya gama zanen sai ya kara tambayar kaskonsa.
   " Kasko kasko, inaso ka fadamin ita wannan yarinya wacece kuma ina zan nemeta!"  Anan yaga ruwan kaskon suna kadawa suna canza kala, can sai ruwan suka koma baki kirin, anan Afran ya dafe kai domin yasan da cewa kasko bayada amsar wannan tambaya daya masa.

Page 64
Bayan wani dan lokaci sai Afran ya kara tambayar kaskon. " Kasko kasko, inaso ka nunamin wanda zai taimaka min domin na mallaki wannan yarinya!" Anan ruwan kaskon suka fara kadawa suna canza kala, bayan dakiku kadan sai taswirar Gazman ta fito a cikin ruwan, anan sarki Afran yayi murmushi domin yanzu ya gane cewa Gazman shine wanda zai iya nemo masa wannan yarinya. Da sauri ya rufe kaskon daga nan ya fita dakin, cikin gaggawa ya nufi dakin Gazman, ai kuwa daga shigarsa sai ya iskosa rike da takobi yana baiwa kansa horo, Gazman najin wani a bayansa sai ya juyo, anan yayi arba da mahaifinsa Afran, shi kuwa Afran kusantosa  yayi daga nan sai ya mika masa fatar damisar daya zana wannan yarinyar da kasko ya nuna masa.
   " Banida masaniya game da wannan yarinya, amma inada masaniyar cewa kai kadaine zaka iya nemota, sabida haka ina baka umarni ka tafi duk inda take ka nemo min ita kuma ka kawomin ita da ranta, zan shirya maka duk abunda kake bukata domin a yau nakeso kabar garin nan." Gazman bai nuna ya damu ba, cikin saukin kai ya aminta amma a cikin ransa yanada zimmar cewa idan ya nemo wannan yarinya bazai kawo ta ga mahaifinsa  sarki Afran ba domin yasan da cewa ba alheri ne zai aikata da ita, kuma ya dauki niya na kareta iya karfinsa. Gazman bai tsaya tambayar mahaifinsa kome game da wannan zance ba domin ya dade da sanin cewa akwai wani boyayyen sirri game da mahaifin nasa. Kamar yadda sarki Afran ya bukata a wannan rana Gazman ya bar garin bayan ya kimtsa a cikin shigarsa ta yaki, tun daga nesa dakarun dake kofar garin suka bude masa kofa, cikin matsanancin gudu yake zaburar dokinsa cikin kwarewa, haka Afran yaci gaba da tafiya kwanci tashi har ya iso wani gari, koda ya iso wannan gari dare yayi. A cikin kasuwar garin ya samu kansa yana tafiya yana kallon mutane sai wasanni ake, a haka yayita tafiya har ya tsinci kansa a wani babban shago na sayar da abinci. Daure dokinsa yayi a waje, Daga shigarsa shagon sai ya samu kujera ya zauna, yana zaunawa sai wata yarinya ta nufosa dauke da murmushi 
   " Ranka shi dade me za a kawo?" Inji yarinyar. Anan Gazman yayi shiru, can sai yaji a cikin ransa yafison kifi to amma kafin ya furta sai yaji magana  a gefensa.
  " Ki kawo masa kifi kawai." Wannan magana da Gazman yaji yasa dole ya duba domin ganin ko waye, abunda yaba Gazman mamaki shine yadda akayi mutumin ya fadi irin abunda yakeso yace a kawo masa.
Page 65
 Anan mutumin ya samu kujera kusa ga Gazman ya zauna. " Amma ka tsinka dai dai domin ni kaina kifin nakeso nace a kawomin." Inji Gazman. Anan mutumin yayi murmushi kafin yayi magana.
    " Gazman kenan, kai a tunaninka tsinka nayi ko?" Inji mutumin, Anan gazman ya kara rudewa jin wannan mutumi ya ambaci sunansa, ita kuwa yarinyar tana ganin hira ta barke tsakaninsu sai ta juya domin ta kawo kifi kamar yadda aka umarceta.
   " Kai! Ya akayi kasan sunana?" Inji Gazman.
   " Ai ba sunanka ba, har sunan wadda kake nema zan iya fada maka." Inji mutumin.
   " Wadda nake nema?" Gazman ya fada cikin mamaki. " Wai kai waye kuma ya akayi kasan da cewa akwai wadda nake nema?" Inji Gazman, a wannan lokaci yarinyar ta dauko akushi cike da kifi, tana zuwa sai ta girke sa a saman tebur.
   " Kudinka darhami uku." Inji yarinyar. Anan Gazman ya dauko ya mika mata ita kuwa tana amsa ta tafiyarta.
   " Inaso ka bani amsar tambayar dana yi maka!" Inji Gazman.
   " Da farko dai  ....." Inji mutumin
   " Saurara!" Gazman ya tsayar dashi, " inaso ka fadamin yadda akayi kasan sunana da kuma yadda akayi kasan ina neman wata!" Inji Gazman, anan mutumin yayi murmushi kafin ya fara magana.
   " Kafin na baka amsa nima zan tambayeka!"
   " Ina saurare!" Inji Gazman.
   " Inaso ka fadamin wace baiwa ce kake da ita?" Inji mutumin.
   " Inada baiwa na iya yaki da kuma sarrafa makami a fagen yaki." Inji Gazman.
   " To haka nima inada baiwa," Inji mutumin. " kuma baiwar na dake da ita itace ta ganin abunda zai faru, da kuma ganin abunda mutum ke tunani, kuma inada baiwa na ganin abunda mutum keso koda bai fadamin ba da kuma abunda mutum zai aikata ko kuma ya aikata, kuma inada baiwa na ganin alheri ko akasin haka ga aikin mutum, kuma wannan baiwa tawa da ita nayi amfani nasan sunanka da kuma wadda kake nema kai harma da labarinka gabaki daya. " Inji mutumin.  Anan Gazman yayi shiru yana tunanin wannan magana domin tun da yake bai taba jin mai irin wannan baiwar ba. Gazman na cikin tunaninsa sai wata mace ta gifta kusa da inda suke zaune rike da jakar fata.
Page 66
Anan Gazman ya kalleta kafin ya maido da kallonsa zuwa ga mutumin. " Tunda kanada irin wannan baiwa to inaso ka fadamin waccan matar data wuce ina zata tafi kuma me zatayi a wurin da zata tafi, kuma menene a cikin jakarta!" Anan mutumin yayi murmushi daganan sai ya kalli matar na yan dakiku kafin ya juyo kan Gazman.
   " Duk da baka tambayi sunanta ba amma ni zan fada maka sunanta," Inji mutumin,  " Da farko dai sunanta Hairata, sunan mijinta Kamim, tana da ya'ya guda biyu mace da namiji, namijin ana ce masa Yahir, macen kuma ana ce mata Subaida, mijinta ne Kamim bayada lafiya to sabida jinyarsa da take shine bata samu damar dafa musu abinci ba, a bisa wannan dalili yasa tazo wannan shago domin ta siya musu dankali da kifi, yanzu idan zaka duba jakarta ba abunda zaka gani in banda dankali da kifi, kuma in takaice maka labari yanzu tana kan hanyarta ne na zuwa gida, kuma zan so kabi bayanta kaga inda zata tafi domin ka tabbatar da abunda nake fada maka." Cikin sauri Gazman ya mike baiyi takan abincinsa ba domin tunda ya fara hira da wannan mutumi yaji ya daina jin yunwa, anan Gazman yabi bayan wannan mata tana tafiya yana tafiya har suka iso wani karamin gida, sai da ya bari ta shiga sannan shima ya shiga, wani dan lungu yaga tabi wanda ya kaita zuwa wani daki, anan Gazman ya labe bayan kyaure domin ganin abunda ke faruwa, a cikin dakin zai iya hango mutum kwance marar lafiya sai yara biyu mace da namiji a kusa dashi, anan mamaki ya kashe Gazman wato kenan abunda wannan mutumin ya fada masa gaskiya ne, matar na shiga dakin sai yaran biyu mace da namiji suka rugo suka rungumeta.
   " Sannu ku dai yarana Yahir da Subaida." Haka ta fada bayan ta rungumesu, shi kuwa Gazman najin ta ambaci sunan wadannan yara kamar yadda wannan mutumi ya fada masa sai ya kara rudewa, 
   " Abun begena Hairata, menene kika siyo mana." Haka marar lafiya ya fada cikin rashin kuzari. Anan Hairata ta kallesa cikin tausayawa kafin ta bashi amsa.
  " Kada ka damu masoyina Kamim, kifi ne da dankali na siyo mana, bari ka gani." Anan Gazman ya zura ido ga jakar domin yaga abunda zata fito dashi, akushi yaga tana fitowa dashi tanaba kowa nasa, kowane akushi cike da kifi da dankali. Anan Gazman ya saki baki domin wannan mamaki yafi karfin tunanin mai tunani

Page 67
Cikin sauri Gazman ya fita gidan ya nufi wannan shago daya baro wannan mutumi, koda ya shiga shagon abun mamaki mutumin ya bace kasa da sama babu shi, anan Gazman ya dafe kai yana tunanin ina  ace ya kara ganin wannan mutum domin akwai tambayoyi da dama da yakeso ya tambayesa, daga nan sai Gazman ya fito shagon ya nufi inda ya daure dokinsa, yana zuwa wurin dokin sai yaga mutumin tsaye kamar yana jiransa.
   " Duk abunda ka fada gaskiyane, ba abunda ka rage." Haka Gazman ya fada yana kallon kyakkyawar fuskar mutumin, dan guntun murmushi mutumin yayi wanda yasa kyawonsa ya kara fitowa. " Akwai wani mutum a garinmu daya bata shekaru da dama har yanzu ba labarinsa, wannan mutumi shine wazirin mahaifina kuma ana ce masa shugaba Jalani, zan so kaban labarin sa da kuma abunda ya batar tashi, kai inda hali har inda yake zanso naji!" Inji Gazman. Anan mutumin yayi shiru na yan dakiku kafin ya dago kai ya kalli Gazman, daganan sai ya fara bayani kamar haka:
   " wato ka sani cewa mahaifinka sarki Afran shine ya sadaukar da wazirinsa Jalani ga wata yar ruwa, ita wannan yar ruwa ba mutum bace, kuma itace ta batar da Jalani daganan kuma ta mallake rabin jinkinsa, a yanzu haka ta nakkasar dashi ta yadda baya iya zama wuri mai haske dole sai cikin duhu, kuma yadda wannan yar ruwar ke amfani da mutum a matsayin sinadarin rayuwarta haka shima Jalani ya yazamana cewa mutane yake amfani dasu a matsayin sinadarin da zai basa karfin rayuwarsa, bisa wannan dalili yasa Jalani ya samarwa kansa wani makasudin gida a cikin wani daji mai duhu a cikin dukiyar da wannan yar ruwa ta basa, daganan ya samu wasu samudawan dakaru da zasu dinga yi masa hidima, su wadannan dakaru sun kasance masu nada tarko domin kama mutane, duk mutumin da suka kama to ya zamo bawa, kuma a duk sati dole sai an sadaukar da mutum daya ga Jalani domin ya samu karfin rayuwarsa. Kuma yanzu haka shugaba Jalani yana gab da daukar fansar abunda sarki Afran ya masa. inji mutumin.
   " Ita kuma wannan yarinyar da nake nema, wato wadda mahaifina yaban taswirarta yace na nemota, inaso ka fadamin ita wacece kuma ina zan nemeta, kai inda hali harda abunda yasa mahaifina ke nemanta!" Inji Gazman. Anan mutumin ya kara yin shiru na yan dakiku kafin ya dago kai ya kalli Gazman.
   " Wannan yarinya da kake nema sunanta gimbiya Zahra Zu diyar sarki Mahir na birnin Ƙabru, ita wannan yarinya ta kasance tana dauke da wani sinadari a jikinta."
Page 68
   " To wannan sinadarin mahaifinka yakeda bukata domin idan ya samesa zai mayar da sarakunan duniya su zamo tamkar bayinsa." Inji mutumen.
   " Sai kuma mutumin da naje gidansa wato Kamim, zai warke daga wannan cuta kuwa?" Gazman ya tambaya.
   " Zai warke sarai nan da mako daya kamar ba shi ba."Inji mutumin.
   " Gaskiya ina godiya sosai da wannan, gashi zamu rabu amma har yanzu ban san ko kai waye ba."Inji Gazman.
   " Sanin koni waye bayada amfani a wurinka domin daga wannan rana bazamu kara haduwa ba har abada." Inji mutumin.
   " To amma me yasa bazamu kara haduwa ba?" Gazman ya tambaya.
   " Kasan kowane mutum da yadda aka tsara masa rayuwarsa, to kamar yadda aka tsara mana rayuwarmu shine bazamu kara haduwa ba har abada." Inji mutumin, daga nan sai ya dauko wata fatar damisa mai dauke da zanen wani saurayi ya mikawa Gazman, "  Wannan saurayi sunansa Amran dan sarki Habir na birnin Tabul, Amran kyakkyawa ne sosai, Amran shine mutum na farko da zaka fara haduwa dashi idan ka tafi masarautar Ƙabru." Anan mutumin ya kwatantawa Gazman inda masarautar take daga nan yayi masa fatan samun nasara bayan ya basa dan karamin akwatin karfe, " A cikin wannan akwati akwai allura ta guba da kuma maganinta." Anan mutumin ya nunawa Gazman, " Kuma akwai wasu abubuwa masu muhimmanci a ciki wadanda sai nan gaba zaka gano hakan."  Daganan sai mutumin ya kama hanyarsa, haka Gazman ya kura masa ido har ya bace masa da gani, daganan sai Gazman ya hau dokinsa ya nufi masarautar Ƙabru ba tare da shayin dare ba da kuma zimmar cewa idan ya gano gimbiya Zahra Zu bazai kaita ga mahaifinsa ba, zai kareta har sai inda karfinsa ya kare......
   " To kaji labarina." Inji Gazman, " Nazone da nufin kare gimbiya Zahra Zu ba wai in saceta na kaiwa mahaifina ba." Anan Amran yayi murmushi yana kallonsa. 
  "  Kaga kenan dani dakai duk hanyarmu daya tunda dukkanmu munzo ne domin mu kareta daga hatsabiban dake shirin afka mata." Inji Amran. " To amma ya akayi tun tuni baka fadamin labarin shugaba Jalani ba?" Amran ya tambaya.
  " Kayi hakuri abokina ban yi tsammanin Jalani dana sani bane, sai yanzu abun ya fadomin. " Inji Gazman.
Page 69
Anan Amran da Gazman sukayi shiru na yan dakiku suna kallon ruwan tekun daketa faman ambaliya, shi kuwa narkeken jirgin ruwan sai faman gudu yake, sauran mutanen cikin jirgin kuwa sai hirarsu suke suna wasanni. Cikin rashin tsammani sai sukaga Ragib ya tunkarasu, bayan ya iso sai ya zauna kusa dasu. 
   " Kamar yadda na fada muku ni mutumin Karaba ne, to yanzu haka a can muka nufa, kuma zanso ku bani hadin kai mu tafi tare domin ku huta kwana biyu kafin kuci gaba da tafiyarku, amma su sauran abokanmu yan fursuna da mun isa garin zan fada musu kowanensu zai iya kama gabansa. Amma ya kuka gani?" Inji Ragib.
   " Hakan yayi kuma mun aminta zamu bika domin mu huta kwana biyu."Inji Amran. Daganan sai suka cigaba da hira cikin nishadi suna kallon ruwan tekun duk da a cikin dare ne, shi kuwa narkeken jirgin ruwan sai faman gudu yake domin isa wannan gari na Karaba......
      SHIN AMRAN DA GAZMAN ZASU GANO GIMBIYA ZAHRA ZU KUWA?
     SHIN KO SHUGABA JALANI ZAI DAU FANSAR ABUNDA SARKI AFRAN YA MASA KUWA?
YA LABARIN ZULAIYA DA ZULAIRA?
     WANE HALI MAHAIFIN SARKI MAHIR WATO BAHRAN YAKE CIKI?
    WANE HALI GIMBIYA ZAHRA ZU TAKE CIKI?
Mu hadu a sashe na biyar domin jin cigaban wannan labari
To be continue in episode 5
This page of the book Gimbiya Zahra Zu written by Abdul King Article and Abdul Alhaji Musa 10k was dedicated to King and Queen writing chamber and Mayaƙiya Authors Forum with the appreciation to the founding fathers of the two institution Abdul King Article and Mansur Usman Sufi, your efforts and commitment might change humanity as our ambition is to see our future generation prosper with dignity and integrity, lastly may you live long, the kings, may you becomed united for the fulfilment of our magnificient dream... Amin
Arewa Online Writers and Bloggers (Male Chamber 2022)
Abdul King Article
Abdul Alhaji Musa 10 K
Abdulaziz Yareema Shaheed
Abubakar Saleh Alquyrameey
Abba Abdullahi Garba
Kingboy Isah
Kamal Muhammad Lawal
Mansur Usman Sufi
Malik El ashtar
Muhammad Abba Gana Kolo
Mujittafa D Muhammad
Shurai Usman
Imam Bandirawo
 










                                                                    GIMBIYA  ZAHRA ZU
                                                                                     by
                                                  Abdul King Article & Abdul Alhaji Musa 10K
                                                                                Episode 5
                                                                                  Annoba
                                                                                  
Page 70
Gimbiya Zahra Zu Episode five Summary:



Episode five zai kasance akan isowar su Amran a cikin sansanin Karaba, kamar yadda muka faɗa sansanin Karaba a kusa ga ruwa yake kuma sabida wannan dalili yasa mutanen garin keyin Su a matsayin sana a, bayan su Amran sun iso garin Ragib zai basu kulawa sosai tare da matarsa Harita a cikin gidansa, ana nan ana nan sai wata anoba ta shigo garin, anobar itace duk wanda ya sayi kifi yaci to cikin ƙanƙanin lokaci sai bakinsa ya rufe ya kasance baya iya magana, sannu sannu sai mutane su gano hakan kuma daga nan sai mutanen dake sayen kifi a sansanin suka daina. Yunwa ce ta yiwa mutane yawa har takai an fara mutuwa, ta wannan dalili ne su Amran zasu fara bincike akan anobar, kuma a cikin wannan bincike ne zasu gano cewa  akwai wani baƙon mutum a cikin sansanin da ake kira Makil, Makil shine dasa hannu ga wannan anoba, burin Makil shine ya zama sarkin sansanin sabida wannan dalili sai ya sanya wata gubar sirri a cikin ruwan garin, kuma wannan gubar itace ta janyo wannan anoba, abunda yasa Makil yayi hakan shine domin ya nunawa mutanen sansanin cewa sarkinsu wato Zahir shine keda rawanin tsiya kuma shine ya janyo wannan anoba, amma kuma shi yanada maganinta kuma idan suka basa sarautar garin to zai basu maganin wannan anoba dake addabarsu. Amran da Zamran zasu gano wannan makirci da Makil ya ƙulla daga nan kuma su tona masa assiri a gaban mutanen garin, hakan zai ƙara musu girma da farin jini ga mutanen garin daganan sai akori Makil a garin bayan yasha alwashin ɗaukar fansa gasu Amran, su kuwa su Amran basu damu ba iyaka daga ƙarshe zasuyi bankwana da Ragib da sauran masoyansu na garin daga nan sai su kama hanyar fita domin cigaba da neman gimbiya Zahra Zu.









       

Post a Comment

0 Comments