"YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
Assalamu alaikum warahmatullah
Ina fatan kuna cikin koshin lafiya, a yauma nadawo dauke da sabon littafi da zai ilimantar da ku, ya fadakardaku ya kuma nishadantar da ku.
Labarin ya kunshi:
Tausayi
Juriya
da ma wasu abubuwa da dama da bakina bazai iya fada ba ku biyo ni, domin jin yadda zata kasance...
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
Wannan littafin 'kir'kirarren labarine kada wani yay zaton gaskene...
GARGA'DI
_Ban yadda wani ko wata ba su canjamun labarina ba indai bada izinina ba_
29/February/2024
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Da sunan allah mai rahama mai jin kai
SADAUKARWA ga
MAIMUNATU IBRAHIM MUHAMMAD
RABI'ATUL ADAWIYYA SUNUSI
RUKAYYA SUNUSI
HAFSAT AND AMINA
Ina matukar alfahari daku 'YAN UWANa allah ya kara hada kanmu ameen.
1_2
KANO STATE (Unguwar Tudun Yola)
Unguwa ce wadda ta tara mutane daban daban masu addinai daban daban,dai dai wani gida na tsaya, kai da ganin gidan zakasan irin gidan mu ne na talakawa, shiga gidan nai saboda hayaniyar da naji tana tasowa, anan na tarar da wata mata a tsaye sai zazzaga masifa take,
Yanzu idan ba tsabar rashin mutunci ba ni Mufida zatayi wa haka a matsayina na uwarta,wadda aka kira da mufida ce ta kalleta tai sororo tabbb allah ya kiyaye ki zama uwata ni uwata tana daki,rike haba matar tayi tana kwala kiran eyeh lallae mufida,fitowar wata mace daga bandaki ce ta katse hakan da gani ta girmi dayar dan da alama ita ce mahaifiyar mufida,kallonta tayi take mufida tasha jinin jikinta ta wuce daki,eaa dole ai kya shige mana juyowa tayi tace wallahi sadiya idan baki dau mataki akan wannan yaran naki ba sai na ci mutuncin su gaba daya yara basa ganina da gashi,abinda suka so shi suke min,kowace magana ta fito daga bakinsu fada min suke,sadiya ce ta nisa tace ai kema karima da lefinki ki daina biyo musu yara ne fa, aa lalle ne sannu sadiya nace sannu sadiya wato wadan nan ganda ganda yan mata kike cewa yara ko,ai yanzu ko shukura ba a kira ta da yarinya ba bare kuma ace mufida ki sake tinani dai,wani dattijo ne ya shigo yana tofa ai garin ya waye, safiyar tayi ba dole ai ku fara,me ya hadaku karima ce ta fashe da kuka tace yanzu ace malam kamar mufida ni zata ringa zagi har na dubi sadiya ina fadamata amma kuma tace wai bata zageni ba yanzu malam anyi dai dai kenan, wani kallon banza ya jefawa sadiya da take rike da buta, sannan ya fara kiran mufida mufida da dan gudu ta fito ta tsugunna dik da tana jin dramer da ake bugawa,kallon ta yayi tare da zuba mata carbi a baya,kuka ta saka tace wallah baba haka bata faru ba,kara mata yayi ya kalli karima yace yanzu ya kikeso ayi mata,kallon ko in kula tai mata tace ai malam mufida bataji bata ganin uban kowa da gashi idan ka cire uwarta,amma nasan dalilin dan jikinta bai gaya mata bane,wuce wa yayi ita k baiwar allah sadiya tana tsaye tana kallon Ikon allah,wata katuwar dorina ya dauko mai baki biyu,tinda mufida ta hango dorinar tasan fa to kashinta ya bushe,sadiya ce tai saurin matsawa kusa da shi tana kiran haba malam yanzu wannan bulalar da ita zaka daki yarinyar nan,kallon banza ya watsa mata tare da fadin wallahi sadiya idan baki matsa ba yanzun nan zan sakeki,kije can ki karata,saurin matsawa tayi tace malam amma ai katseta yayi ,karima ce tace dama zaka saketa din da na samu yaran nan naci uwarsu,ihun mufida ne yasata dawowa duniyar mutane,kallon yadda yake jibgarta ne yasa ta yin murmushi tare da shigewa dakinta ta varsu a tsaye,sadiya wani bakin ciki ne yasata barin wajen,ba ji ba gani yake daga bulalar yana zabga mata kamar an aiko sa yayin da ita kuma take ta zabga ihu sai da ya zageta tas yadda ko hannunta bazata iya dagawa ba,jikin ta dik burdi na duka,wani wajen har jini yake zubarwa,tsabar wahala kasa kukan tayi ta kwanta anan.
Sallamar su ce yasa ta bude idanunta da gudu wasu yammata nagani sun zube,suna kiran aunty mufee lafiya,daya ce ta kalli daya sai kuma tace kingani aunty khary yauma tasaka an daki aunty shisa nace mata mu shirya mu tafi makarantar amma ina tace bazata ba kasancewar ummi bata jin dadi kalli yadda ya faru da ita,da kyar suka dagata suka fara shiga dakin da ita,a zaune suka tarar da mahaifiyar su,saurin tashi tayi tana kama hannun mufida tare da kwantar da ita akan gadon dakin da yake shi kadai sai sif daya a dakin,iya sif da gadon ne suka cika dakin sai kuma wata 'yar karamar kujera 1seeter a gefe ita tasha jiki ta kwararrabe,amma dakin kall yake ko tsinke bazaka gani ba shukura ce ta kalli Ummieh tace yauma ummin su Jafar ce ko ummi daga kai sadiya tayi,tashi tayi tare da zuwa ta dakko musu barbaden abincin ta mika musu,yayin da mufida jikinta ya kara zafi,kasancewa garin ana mugun zafi,sadiya ce ta fice daga dakin zuwa wani makewayi, ruwan zafi ta hada ta kai bandaki kama mufida tayi ta kaita tace ta gasa jikinta,da kyar ta iya gasawa ta fito,fitowarta yayi dai dai da shigowar wani saurayi ya fito tsawo sannan zai dan fita jiki ma,tsayawa yayi yana kallonta yana dan lashe baki, a zuciyar sa ke furta allah ya kai damo ga harawa yarinya zan nuna miki ni namiji ne, da sauri mufida ta shige zuwa dakinsu tana shiga wata shaloluwar riga ta saka, ta koma ta kwanta tana rawar dari,khairy ce ta kalli shukura tace wallahi so nake na samu ranar da zan koyawa karima hankali,rike baki shukura tayi tace to amma sai dai idan karki bari baba ya sani.
To mutanen gida salamu alaikum,nace salamu alaikum khairy ce ta kalleta tai banza da ita tana ci gaba da wanke wankenta rike haba tayi tace iyee wato ummalkhairy ni kikewa wannan gani gani ko ba laifin ki bane laifin uwarki ce mai bakin hali,karima ce ta fito tana aa yau hajiya ce a gidan namu maraba maraba ki shigo mana, shiga tayi aka shimfida mata katuwar tabarma a waje,zama tayi baba ne ya fito daga dakin karima yana kallonta cike da farin ciki yana cewa sannu da zuwa hajiya,kinzo lafiya amsawa tayi da lafiya,karima ce ta ajiye mata ruwa a cup,ta juya ta kawo mata abinci tana cewa sannu da zuwa hajiya,sai da suka gaisa sannan ta fara ina wannan mai bakin halin take gayyar yaya mata mara sa amfani,sadiya na jinta ta tashi ta fito ta tsugunna tana gaishe da ita,katseta tayi tace wato da ban tambayeki ba da bazaki fito ba ko,shiru sadiya tayi,kallonsa tayi tace sani wai yanzu ya kai da wannan Matar ta nuna sadiya,sallamar shukura ce yasata zuwa da tsugunnawa tana gaishe da hajiya, tsaki taja tare da fadin ke kuma tambadaddiya daga ina kike,sadiya ce ta saurin kallon ta, ke kuma fa ko da wani abu kinzo kin haifa mana jaraba wallahi sadiya wataran sai na shake ki kin mutu, khairy iya kufula ta kufula, da haka ta gama wanke wankenta ta shige daki.salamar wasu samari biyu ne yasata sakin fara'a tare da fadin aa kaga yan biyu kyautar allah alhassan daga ina kuke,hussain ne yace daga inda kika aikemu mana,murmushi tayi tace aa gaskia hassan ne yace yanzu dai hajjah ba wannan ba bamu abinda ya samu mu tashi domin akwai inda zamuje,kunce zaninta tayi ta fito da Yan dubu dubu ta mika musu 3 tace gashi nan ku raba allah ya tsareku daga idon makiya.
Sadiya tana shiga daki ta fadi da sauri khairy da shukura suka kamata tare da mikar da ita tsaye suka dorata kan kujera,rike hannuwansu tayi kawai tana kallon su tana murmushi,koda kowa zai guje ku,ni son ku nake domin nasan yara mata rahama ne kuma sai allah ya dubeka yake baka su,ni nagode allah daya bani ku,dan haka ko mai wani zai fada akan ku kada kuji haushi kunji yara na,dik mun tsanani yana tare da sauki dan haka ku rike allah da manzon sa, khairy ta share hawayen fuskarta tace ummi jikin aunty mufida yayi zafi,kallonta tayi tace ni kuma bani da ko sisi bare na siya mata magani,t ashi khairy tayi ta fito a zaune ta tarar da malam sani shi da karima suna ta hira,suna ganinta suka chanja fuska,tsugunnawa tayi tace baba dan allah idan kana da dari ka bani,kallon baki da hankali ya mata yace gidan uwarki zan nemo dari na baki,to bani da ita tashi ki bani waje,shashashar banza kawai.
"YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
3_4
Shukura ce ta tashi ta dakko wata fatattakakiyar jaka da gani taji jiki,lalube take hannu ta zaro ta fito da kullin leda aunty khaity rabu da baba kinji kinga a bata wannan kawai shima paracetamol ne,sadiya ce ta kalleta tace ke shukura a ina kika samo wannan maganin, shiru tayi cikin dagawar murya sadiya tace wai shukura ba da ke nake ba ne, shukura ce tace ummieh a makaranta da kaina yana ciwo shine naje staff room na karbo maganin to har na taho kuma sai aunty jamila ta kirani tace idan banci abinci ba kar na sha, to ummieh da na dawo gida kuma na ci abincin sai naji na daina jin ciwon kan,shikenan shukura khairi ku bi duniya a sannu,idan yau mune gobe ba mu bane, dan haka ku zauna lafiya kinji, gaba dayan su toh suka ce,shukura mikomin ruwa cewar mufida,yayin da ummieh tai kwance tana tinani, daga ta sukai suka bata maganin tasha ta kwanta.
KADUNA (Unguwar Sunusi)
Wani katafaren gida na tsaya ina kallon gini gidan me cike da kyau da kasaita,gidan da gani kudi ya zauna,cikin gidan na shiga anan na tarar da katon fili wajen harabar motoci, sai kuma wani katon garden me cike da kayan marmari, wata hanya siririya nabi anan na tara da wani falo,kato ne dauke yake da kujerun na alfarma,light purple shima center table din ya kasance sai kuma katuwar plazma, jin motsi nayi daga wani dan siririn lungu,wata yarinya na hango dauke take da doguwar riga iya gwiwa sai wandon ta dik da ya matseta sosai, ga wani gashin rubber attachments da ta zuba,sai karamar jaka handbag,kafar nan wani uban takalmi ne mai shegen tsawo,ficewa tazo yi wata dattijuwa ce ta fito tace ke Hanan ina zaki, juyowa tayi tace mom zan dan je cikin gari ne kina nufin kuma a haka zaki fita,eaa mom hade rai take tace wai hanan wane irin abu ne ya hau kanki ne wallahi zan matukar bata miki rai tinda naga alamun kwana 2 kanki rawa yake,zaki huce kije ki chanja shiga ko sai na bata miki rai,tsaki ta danja ta wuce ta nufi hanyar data sakko,zauna wa hajiyar tayi tace ya allah ka taimakeni ina iya kokarina wajen bawa hanan tarbiyya allah ka taimakeni.
Dakin ta bude masha allah karamin daki ne mai dauke da kujeru 2 kalar pink sai kushin da karamar plazma gefe gefen kujerun kuma teddy ne sai dan karamin kofa, wucewa tayi ta kara bude wata kofar anan kuma karamin bed ne gefe kuma computer ce ta saurin books sai karamar jaka da takalma,cire takalmin tayi ta saka a jaka,tare da cire kayan ta cusa su a jaka,wata doguwar riga ta saka gown sai karamin hijabi,a falo ta zauna ta fara turo baki ni a kyaleni nayi rayuwata mana anzo an takuramin da haka ta tashi ta fito,a falo ta tarar da ita murmushi hajiyar tayi tace ko ke fah hanan jeki saikin dawo.
Tana fitowa mota ta dauka taja ta fice daga gidan dai dai wani hotel ta tsaya shiga tayi reception ta dan tsaya sai kuma tajuya tayi wani dakin,dai dai daki mai 120 ta tsaya anan ta tsaya tana knocking bata dau lokaci ba aka bude,shiga tayi wasu maza ne su 3 sai mata biyu tana shiga wani saurayi ne ya taso tare da rungumota yana fadin ai na dauka baza ki zo ba dariya tayi tace badai har kun shirya ba, aa suka bata amsa toilet ta shige sai gata da shigarta wani ihu suka saka tare da furta allah dai ya biya hanan shisa kike birgeni maganar wadda ya rungume ta,matsowa yayi kusa da ita ya dan shafata yace amma yau tare zamu kwana ko, dariya kawai tayi tace yadda kace nidai kawai inji dimisss da haka suka fice ana ihu.
ASALIN LABARIN
Sadiya ta kasance ya ce ga alhaji Salisu mutum mai dukiya amma tin tana kara ma allah yayiwa mahaifiyar ta rasuwa,alhaji salisu ya tsani sadiya kasancewar ta a mace,haka take zaune har lokacin da ta girma alhaji salisu ya bayar da aurenta ga sani wanda yaronsa ne a da,sadiya batason sani amma ganin tsangwamar da ake mata ne yasa ta auresa, a haka akai auren.
Hajjah ta kasance mahaifiya ce ga sani ta kasance sai da ta haifi yara 5 dikansu maza, sani shi ne na farko,sai Hamisu,Dauda,Sadiku,Garba,hajjah ta na son yaranta ko lefinsu bata gani, bayan ya auri sadiya ne sai bayan shekara 2 da àuren sai allah ya bata ciki ta haifi mace,h ajjah iya bakin ciki tayi bakin ciki,a haka ne yasa shi ta auri karima 'yar kawarta ita kuma da auren ne allah ya bata ciki har ta haifi yaranta 2 sune alhassa da alhussain,sai kuma Mudassir amma daya ke shi yana da girman jiki sai ya zamana kamar shine babba, sai ja'afar,ita kuma sadiya sai ummulkhairi da shukurah,sadiya ta taso cikin tsangwa ma dik da cewar dama can tana fuskantar tsangwamar,saboda da ta haifi yaya mata amma ita son abinta take,kuma tana kulawa dasu, tinda yaran suka taso ma ita ta kaisu makarantar primary wadda yanzu ya kasance mufida tana aji 4 ita kuma khairy 2 sai shukura da ta kasance 1 makarantar ma ita ta saka su, komai na su da kudinta ake,tin da suke da malam sani bai taba yiwa su mufida dinki ba,tsakaninsu da mahaifinsu sai tsangwama da kyara,
Zuwa yamma jikin mufida yayi dan sauki tinda har ta fito tsakar gidan,shigowar mudassir ne ya kalleta tare da yin dariya, yace da alama wata yau tasha duka a hannun tsoho,mufidah ko kallonsa bata yi ba taci gaba da abinda take,ummieh ce ta fito ta kallesa kawai ta kau da kanta,shukura zo nan kije gidan auntyn Zee ki ce ta bani sakon kinji,to kawai tace ta fice daga gidan dawowarta ne sukai kicibis da mudassir kallonta yayi sai kuma yace ai kwananan sai nayi abinda nayi niyya akanku,shukura sam bata gane zancen ba shisa ma ta wuce da 'yar ledarta a hannunta,a tsakar gida ta tarar da malam sani wani kallo ya watsa mata tareda fadin daga gidan uwarwa kike shiru tayi batai magana ba,khairy ta fito ta ja ledar hannunta ta wuce,kallon khairy yayi yace ke sai kuma yayi shiru yana kallon yarinyar tasa domin dik cikinsu khairy ce kadai yake dan daga mata kafa akan al'amuran yau da kullin, kasancewar dik cikinsu tafi kowa zafi...
"YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
5_6
Cikin duhun daren sadiya ce kwance yayin da take numfashi sama sama kokarin taba mufida take nan kuwa ta farka,tashi tayi ganin mahaifiyar ta su a wannan halin ne yasa ta fara tashin sauran, a hankali suka tashi suna kiran ummieh,kallonsu tayi tace kusani dama na gaya muku idan yau mune gobe bamu bane,ku bi rayuwa a sannu ku rike mutuncin ku mufida,ki kula da kannenki kinji,ki kasance mai yawan hakuri dik da nasan dan na barku a gidan nan ba wani abun azo a gani bane kasan cewar yanzu kunsan mahaifinku baya sonku,amma kuma na barku a wajen allah madaukakin sarki,mufida ummulkhairi shukura kuyiwa mahaifinku biyayya muddin ba cutar daku zai ba,wani tari ne ya tirneke ta dik maganar da take kuka suke,cikin tarin ne take furta ku bani ruwa,cikin hanzari shukura ta mike ta debo ruwan,cikin dasasshiyar murya take furta la'ilaha illalahu muhammadur rasulillah difff ta daina motsi wani kuka mufida khairy suka saki, shukura ce ta kallesu tace kai aunty mufy ku daina kuka mana ummieh fa bacci takeyi khairy ce ta rungume ta tana kuka,shukura kuka ta fara ganin da gasken gaske mahaifiyarsu ta rasu kuma gatansu,khairy ce ta fito ta fara dukan kofar dakin karima tana mai furta sai ku fito burinku ya cika ta mutu, dama haka kukeso kun kashe ta kun huta,karima ki fito na tabbata bakin cikin kune ya kashe ta,mufida ce ta fito da gudu ta rungume ta tana rufe mata baki,malam sani ne ya fito da touch light yace wannan wane irin iskanci ne kuma da tsohon daren nan zaku tashe mu,fizgewa khairy tayi tace dama ai dole kace wane irin rashin mutunci ne baba, to ta mutu kun huta,kallon mufida yayi hakan ya tabbatar da cewa eaah da gaske fa take da sauri ya shige dakin,a kwance ya tarar da ita kamar mai bacci,ba abinda ya furta sai sadiya shukura ce tace masa baba ai ta mutu,kuma wanda ya mutu bazai taba dawowa ba,wata surender yayi ba shi kadai ba daidai da karima taji mutuwar a haka suka zauna yayin da mufida shukura ummulkhairi suke ta kuka har gari ya waye,mutane da Dama sun halarci janaizar sadiya domin mutane da yawa sun mata shaida,ko da akazo za a tafi da ita mufida ce da kannenta akan gawar suna mata addua suna zubar da hawaye,ganin da gaske tafiya zasuyi da ita yasa su kokarin riketa da kyar suka banbare su daga jikinta aka tafi kowa na tausayin yaran,(allah yaji kan magabatan mu ameen)A haka ta kasance dik wani dan unguwar idan ya shigo musu gaisuwa suna dakin da mahaifiyarsu anan wasu su basu sadaka,wasu kuma kawai su tashi,karima ta kagu ayi sadakar 7 kowa ya huta.
Hanan ce ta shigo gidan ba kowa a falo hakan yasa ta yi hanyar dakinta, tana shiga ta zauna akan kujera tana mai yin dariya tare da furta amma yau fa nayi nishadi sosai,shigowa mom ce ya katseta mikewa tayi tana raba ido,kallonta tayi tace yanzu hanan kin kyauta kenan tin yaushe kika fita amma sai yanzu zaki dawo,kallonta hanan tayi tace kiyi hakuri mom bazan kara ba shikenan ki fito muyi lunch, to kawai ta amsa mom tana fita taja tsaki,aikin banza nifa wallahi na fara gajiya da wannan halin matar kawai shawara samu zanyi na tattara yana wa yanawa na fece domin naje naji dadi na batare da damuwar ko wa da haka ta fito ta nufi hadadden dinning din a zaune na hangi wani dattijon mutum tana zuwa tace dad ina wuni,lafiya lou hanan ya gidan alhamdulillah kawai tace ta zauna suka fara lunch.
Alhaji Auwal ya kasance mutum ne mai yawan dukiya yana auren matarsa mai suna khadija,tin bayan aurensu suke neman haihuwa amma basu samu ba sunje kowane asibiti akan wannan matsalar daga karshe likitan yace ba ma zasu haihu ba har abada,khadija da auwal sun hakura hakanne yasa suka nufi gidan marayu,anan ne suka dakko hanan tin tana shekara 6 hajiya khadija tayi matukar kokari akan hanan amma Hanan sam ita ba wannan ne a gabanta ba,kasancewar ta hadu da kawayen banza da kuma rashin sanin ciwon wahala yasata shiga hanyar banza,a haka ne ta dore amma dik wannan abin da take khadija bata taba sani ba kuma batason ta sani,Hanan a yanzu tana da shekara 17 amma idan ka ganta sai kace tafi dan haka ne ma wannan shekarar alhaji awwal ya biya mata waec da neco tayi.
Bayan sadakar 7 suna zaune a dakinsu kowannensu yayi shiru yana ta tinani,karima ce ta leko ta kallesu tace ai sai ku tashi kufara aikace aikacen ku domin naga uwarta ku ba dawowa zatayi ba,tsaki khairy taja tace wallahi nidai a daina zagarmin uwa saboda uwa uwa ce,karima banza tayi da ita a zuciyar ta tana tinanin irin wahalar da zata dinga gana musu,fito wa sukai gaba daya wankin kayanta ta jibgowa mufida, mufida da bazata wanke ba sai ta tina da wasiyar mahaifiyar ta dan haka tana wankin tana kuka,khairy ce a zaune shigowar malam sani ne yasata kallonsa tana kiran baba kallon ta yayi yace to to gayyar masifa me ya faru,me kuma zan baki,wani tukukin bakin ciki ne ya cika zuciyar khairy yasata fasa magana,shukura ce ke wanke wanke,mudassir ne ya shigo tare da kallon yammatan yace yanzu haka bani da matsala,matsalata daya wannan tsohon amma bari zan saka masa maganin bacci sai yayi tayi ni kuma na kashe boss,dariya yayi ya wuce,khairy kamar tasan me yake aikatawa take ta fara karabto addua,yamma liss yasa su fitowa sanye da uniform din su uku,karima ce ta kallesu tace kai ku tsaya gidan uban wa zaku,shukura ce tace mata makaranta mana aunty,bakusan ancireku ba ta fadi haka da gadara,dariya khairy tayi tace waye kuma ya cire mu,tsaki taja tace ubanku mana ko kuna da wanda zai cireku idan ba shi ba,sallamar sa ce yasa su tsayawa suna kallonsa ku je ku cire uniform din nan dan nidai bazan iya biya muku wadan nan uban kudin ba, bani da su daga yau ba ku ba kara zuwa makaranta daga ta yahudawan harta islamiyyar,khairy ce tace to amma baba ba..katseta yayi watau ina magana kema kinayi ko khairy,shikenan ku tashi kubar wajen nan kin tashi sukayi dai dai nan mudassir ya shigo yana kallonsu,malam sani ne ya ciro bulalarsa ganin mudassir ne yasa shi mika masa ka zanemin su yanzun nan, mudassir yana murmushi yace to tunkaro su yayi zai dakesu da gudu suka fada daki dan shukura tin kafin bulalar ta sauka a jikinta take kuka,biyosu yayi yana daga bulalar shiga yayi ya zanesu dan malam sani har daga waje yana jin ihunsu amma dan muganci yaki yace a daina dukansu sai da mudassir ya gaji ya fito.Karima ce ta kalli malam sani tace dama ni inason na fada maka zan fara dora musu talla,ba komai ai sai ki dora musu dan banga amfaninsu ba idan ba tallar ba,dan haka hakan yayi.
Haka rayuwa taci gaba daga wajen su mufida wataran dadi wataran akasin hakan domin dik 'YAN kudadden da masu zuwa sadaka suka dan babbasu yanzu babuma dik sun cinye su,amma wahala kam kullun suna cikin ta dik da mufida ta rike kannenta kullun tana ja musu warning tana tina musu wasiyyar mahaifiyar su,mudassir har yanzu bai chanja kudurinsa ba akan su mufida.
"YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
7_8
Shigowa shukura tayi tana goge hawaye,kallonta mufida tayi ta taho tana cewa shukura me ya faru kuma,goge hawayen ta fara yi tana nuna mata bokitin taka yaga din hannunta,rufe mata baki yayi yace kin san me za ayi dai dai nan karima ta fito tare sakin wata uwar ashar,rike baki tayi ta furta wai shukura kar dai kice min abinda kikai kenan,to wallahi ko ki biya ko kuma na jibgi kudina,mufyda ce tace dan allah aunty karima kiyi hakuri kinji,nasan bata na sane ta barar ba karima ce ta matso tare da shararawa mufyda mari da ke nake, kunen shukura ta murde ta jawota kallon raini tayi mata,tare da janyo dorinar da ke sakale ta fara lantaya mata a jiki,wani ihu shukura ta zumbuda tana kiran aunty mufyda,matsawa tayi da niyyar ta kwace ta amma ta kasa sakamakon irin rikon da karima tayi mata,sai da ta zane ta tsaff sannan ta wulla ta gefe kanta mufida tayi sai a lokacin mufida ta lura da jini da yake zuba a hannunta,taba shukura take amma taki motsawa kuka take bil hakki da gaskiya,sauri tayi ta dakko ruwa ta watsa mata sai gata ta dawo,cikin murya kasa kasa take kiran aunty mufy dan allah mubar gidan nan kinji wallahi ummieh jafar kashemu zatayi,rufe mata baki tayi kallon jikinta tayi,ganin burdin da, da bai gama warkewa ba amma ga wani, kuka ta fashe da shi,h ajjah ke kwada sallama tare da cewa na bayanta shigo mana naga kana tsayawa,biyota yayi da kaya niki niki akansa,mufyda kokarin daukar shukura tayi suka wuce dakinsu,hajjah ce tai parking dai dai kofar dakin karima ta kalli yaron tace debo min sauran kayana na waje gaba daya bance kabar komai ba,to yace mata ya huce,karima ce ta fito tana cewa sannu da hajjah yawwa ganin kaya ne yasa ta yin turus tare da cewa hajjah wannan kayan fa dan murmushi wadda aka kira da hajjah tayi tace ai nan zan dawo,karima ce tai shiru a fili sai cewa tayi amma kuma wane dakin kenan nuna mata dakin mariganyi ya tayi,tace anan mana karima,shigowar khairy yasa su yin shiru ajiye katon farantin tayi tare da zubewa a kasa tana gaishe da hajjah wata harara ta zabga mata,shegiya mayya kawai ni kike gaidawa ko mai,khairy wani bakin ciki ne ya cikata ta kasa magana,kudin ta mikawa karima ta tashi ta shige dakin nasu,tana shiga tai turus ganin mufyda rungume da shukura,mataccen gadon khairy ta hayo tana fadin aunty mufy meye ya faru, kallon hannunta tayi ganin jini yasata ciro dan kwalin kanta tana goge kulle mata wajen,mufyda ce ta kwashe labarin abinda ya faru ta gaya mata shiru tayi itama tare da rungumar 'yar kanwarsu suka hade kai suna kuka.
Kwala kira hajja take tana fadin mufida tashi mufida da khairy sukayi suka fito hajjah ce ta kallesu tace ku tattara abinda kukeso ku fito dan shara za ayi mun,mufida cikin rashin fahimta tace to hajjah shara za ai mana ne,wata harara ta zabga mata aa uban shara, mufida tashi zakuyi daga nan dakin,khairy ta cabe da cewa to ina zamu koma hajjah dakin da yake soro,kusa da na su mudassir,mufida ce tace dan allah hajjah ki barmu anan kinji,wani mari ta wankawa mufida tare da fadin ke kin isa in bar muku kuyi uban me da shi ai idan baku sani ba ku sani can shine yafi dacewa da ku,khairy ce taja hannun mufida suka shige dakin, a zaune suka tarar da shukura tana kuka saurin goge hawayen face din ta mufida tayi tana murmushi tare da fadin shukura har kin tashi,kama hannunta shukura tayi tace aunty mufy ya dace kenan abinda ake mana,kamar ba yaya mata ba, basu son wasu nema suke ba amma allah bai basu ba,su sun samu shine suke wulakanta mu,aunty khairy nagaji da wannan halin na karima da hajjah kawai mutafi aikatau mu huta,saurin rufe mata baki khairy tayi tace aa ki daina fadar haka kinji 'yar kanwata,dik min tsanani yana tare da sauki,jin muryar hajjah sukai tana kiran to wai uban me kuke da bazaku fito ba,ai masifa take zabgawa sai gasu da kunshin kayan su kowanne da nasa,kallonsu tayi tace to ku huce ku koma can,khairy ce tace amma hajjah ko tabarma fa babu a dakin, tsaki taja tace to anan dakin me kuka bari,me uwarku ta bari ma har kike fadar haka,shikenan je ki dakko waccen tabarmar ku shinfida,mufida ce ta dauka zata wuce karima ta kallesu tare da furta wallahi kadan ma kuka gani,yan iskan yara kawai masu bakin jini da haka suka wuce.
BAYAN KWANA BIYU
Karima ta dorawa khairy da shukura tallah sai kuma mufida da take wanke wanke,sallamar mudassir ne ya kalleta yasa shi komawa dakinsu wani uban tilin wanki ya kwaso ya jibge, sai wani dan karamin sabulu da klin kallonta yayi yace ki tabbata kin wanke min ko jikinkibya gaya miki,kallonsa tayibtace haba mudassir karka manta nidin fa yayarka ce kuma kasani dik gidan nan ni ce babba kuma ni zaka sa wanki,hajjah ce ta fito eyee sannu mufida ina girman yake ke ba namiji ba yanzu wadan nan sune manya a gidan nan kuma ki tabbatar da cewa sai kin wanke wadan nan kayan ina zaune ina kallonki kaga dan albarka je ka kawai zata wanke ma su,kallonta yayi ya ce hajjah ai ba fita zan ba sai dai nazo na tayaki hira,to taho mana dan nan ta ambaci hakan,sallamar khairy ce yasaka shi kallonta ajiye katon farantin tallar abincin tayi kawai ta shige dakin karima,can kuma ta fito ta gifta ta gaban su hajjah,mudassir ne yace mata ke saurin juyowa tayi baki iya gaida mutane ba da kike kokarin zuwa can din me zaki dakko wajen auntyn zanje na tayata wankin wani kallo hajjah tayi mata,mudassir ne yace ai kin iya knelldown ko cikin dan tsoro tace ea wuce ranar can kiyi knelldown din,dan tsaya tayi ganin zai biyo ta ne yasaka ta wucewa da sauri tare da yin knelldown din,ita kuma mufida tsabar bacin rai kuka take kawai...a haka nan kuma shukura ta shigo tsugunnawa tayi ta gaishe da su amsawa sukai mudassir ne ya kirata yace zo nan shukura zama tayi kallonta yayi cike da manufa yace to cire hijabin mana ki huta,kallonsa tayi tace aa aunty mufy ta hana mu,cire hijabin kawai yayi ita kuma hajjah ta saki baki sai kallon tsakar gidan take,yayin da mudassir ya fara shafa shukura da dayan hannusa,khairy ce idanunta suka kai wajen alama take wa shukura amma ina taki ganewa ganin haka yasa ta sakin kuka,kallonta su dika sukayi anan ta samu taiwa shukura alamar tashi,tashi shukura tayi kallonta mudassir yayi yace ina zaki amsa ta bashi da abinci na zan dakko da haka ta wuce dakin soro,sai da ta tafi da 'YAN mintuna mudassir ya tashi tare da cewa hajjah bara na fita amma yanzu zan dawo,ficewa yayi a lokacin khairy na nan tana knelldown dakin su mufida ya nufa kai tsaye,yana shiga ya tarar da shukura tana cin abincin tana ganinsa tace yaya mudan dama yanzu zan fito,kallonta yayi yace ai ba sai ma kinzo ba ni nazo ko,a tsorace take kallonsa tana zazzare idanu ganin ya yo kanta ne yasata zillewa ta fita da gudu,cikin gidan ta koma kawai tana numfashi lokacin hajjah ta tashi,kallinta suke nan ta kwashe komai ta fada musu,wani kuka ne ya kwace musu khairy ce tace dan allah aunty mufida mubar gidan nan idan ba haka ba kashemu za ai wallahi,mudassir tin da ya fice bai kara dawowa ba amma ya tamawa dare."YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
9_10
Sai da ta gama wankin nan tsaf sannan suka tafi dakinsu tare,zama sukai suna cin abinci jin kiran sallar magariba ne yasa su mikewa tare da gabatar da alwala suka ta da sallah, sannan sukai sallar magariba,addua suke sosai iya bakin kokarinsu iya wadda suka iya akan kai din mudassir domin shukura da khairy sun wa mufy bayani,mufyda kuka take tana addua tana tina alkawarin da tai wa mahaifiyar su akan cewa zata kula da kannenta,bayan sun idar suka zauna sukai shiru, khairy ce ta katse Shirin da cewa yanzu ace ko arzikin fitila bazamu samu ba kalli,ji yadda sauro yake bin mu,aunty mufy wai meye laifin mu dan mun kasan ce 'YAYA MATA shikenan ba wata kukawa a wajen mu,ba wajen wanda zamuje mu fake kenan,ina mutanen da suke cewa yaya . mata sun kasance abin so abin riritawa,aunty mufy ina riritarwa dik wannan maganar cikin kuka take,kalli shukura dika dika shekarunta 12 amma tasan wahala,kalli yadda ta koma aunty mufy kalleni dika da nawa nake amma jibi yadda mukai wani dukun dukun,bamu maraba da almajirai,kwara ma almajirai su suna koshi da abinci mu fa,dakin da aka bamu ko arzikin wutar nefa babu, turema ta wannan yanzu haka a hatsari muke fa saboda me mudassir mun fahimci abinda yakeson aikatawa aunty mufy,mahaifinmu baya san mu ga dakin daya bamu duka daya zakaiwa kyauran nan ya karye,aunty mufy nidai bazan iya zama a cikin gidan nan ba nagaji aunty,shukura ce ta amshe da fadin nima wallahi na gaji da rayuwa a cikin wannan gidan kawai mu gudu,wani wawan kallo mufida ta watsa musu tare da furta ai baku da hankali kunsan irin bala'in daya ke wajen idan mun tafi,idan mun tafi ina zamu, kun san bamu da kowa ko haka suka ci gaba da tattauna wa har aka kwala kiran sallar isha'i sai da sukai nafila sannan sukai sallah isha'i,zama sukai suna cin abincin da gani ba isarsu zai ba,ba laifi suna iya ganin kyallin wata daga soronsu.
Mudassir ne ya shigo cike da sanda kamar munafiki,dakin nasu ya fara lekawa ganin suna ciki ne yasa shi wucewa cikin gida,ya dade a ciki dan a kalla sai da ya kai 10 sannan ya fito dakin nasu ya dawo a lokacin mufida ce idanunta 2 amma ta kwanta sai sauran da suke ta baccin gajiya,ganin mutum tayi ya shigo dakin nasu saurin in shiru tayi tana kallon sa,tattabawa yake sai da ya taba khairy sannan yace kai wanann bazan moreba ina yayar take a haka yayi ta binsu,mufida ganin yayo kanta ne yasata zira hannu ta janyo kwananan kusa da ita yana karasowa ji yayi dikkk akansa,abinda ya tada khairy da shukura kenan kokawa suke da shi,khairy ganin haka yasata shiga fadan tana amma ina karfin mace dana miji ba daya ba da kyar shukura ta kara daukar kwanan ta sakar masa shi a kafa, wata irin kara yayi kara dagawa tayi ta kara sakar masa a ka,take ya fadi,mufida ce ta kalleta tace shukura me kika aikata haka,kasa magana tayi kawai tana kuka,aunty khairy tabashi sukai sukaji shiru,mufyda ce ta jiyo motsi ana kiran mudassir muryar baba ce domin gaba daya ya fi dashi a yayansa,saurin rufe baki sukai,jin ya wuce ne yasasu zama,suna jin motsin dawowar sa ne yasa su kwanciya kamar masu jin bacci,yana wucewa khairy ta fashe da kuka tare da dukunkuno 'YAN kayanta ta kallesu tace wallahi muka bari baba yasan mun kashe mudassir,walalhi muma sai ya kashe mu aunty mufy ku tashi tattaro kayan su sukayi,suka fito da dan gudu dama ga su ga kofa dan haka abin bai musu wuyar sillewa ba.gudu suke sosai har sun fito daga laying su suna gudu,dai dai wata bakar motar ta faka,wasu ne suka janyo hannuwan khairy da shukura kasancewar su sune a gaba,mufida kam bin motar tayi tana ihu tare da neman taimako amma shiru kakeji ba kowa a layin hakan yasa bata daina gudun ba amma tini motar ta wuce ta bar wajen,komawa tayi ta debe kayansu da suka zubar,tana tafe tana kuka,zama tayi tana mai furta ko na koma gida,kina koma wa kashinki ya bushe wata zuciyar ta bata wannan amsar,tinanin wahalar da ta sha a baya take ga hawaye,cikin kukan ta furta kara na tafi dik abinda zai faru ya faru,domin bazan dawo ba sai da 'YAN uwana da wannan shawarar tayi amfani ta tashi taci gaba da tafiya.
A bangaren su khairy kuwa ganin yara sukai su 3 a motar sai su wata kara suka saka tare da kiran aunty mufida ganinzasu tona musu asiri ne yasa su saurin shaka musu maganin bacci,drivern ne ya kallesa yace amma dauda baka da mutunci kana ganin yaran 3 ne amma ka kamo 2 tsaki yaja yace ina laifi da naja biyu,ni da daya ma zan dakko.da haka suka bar zancen suka ci gaba da bada wuta a motar.
Hanan ce take waya ba matsala kawai zan zo karka damu,kamar ya hanan ya bata amsa,kai dai jirani,dik da sanye take da sleeping dress mayafi kawai ta dauka ta fice daga gidan,ta kofar baya ta fice daga gidan,tana fito wa wata ash color mota na hango tana daukar ido kasancewar wajen da haske matuka,shiga motar tayi kawai jan motar yayi sai da suka tsaya bakin wani club kallonta yayi sai kuma suka fara dariya,kallon kayan jikinta yayi yace gaskia hanan iskancinki kullun karuwa yake duba fa kiga yadda kika fito,gaba dayanki dariya tayi tace kawai malam muje,shiga sukai ana hangosu aka fara ihu,ana kiran hanan,waka aka saki tin a lokacin ta shige tana dirkar rawa,sai da ta gaji dan kanta sannan ta fice tabi bayan Atif suna shiga dakin yayi masa lock..
YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
11_12
Mudassir tin cikin daren daya farka ya duba yaga dakin shiru kuma ya laluba amma bai ga kowa ba hakan ne yasa shi tashi,amma me kafar ta rike gam kasa tafiya yayi jan kafar yayi da kyar ya bar dakin,dakinsu ya nufa turawa yayi yaga su alhassan na bacci,shiga yayi tare da hawa katifarsa,ya kwanta yana jinya.
Washe gari gidan su mufyda ne naga karima ta shiga ganin wayam yasata fadin ji Yan iskan yara gidan uwarsu suka tafi kenan,fitowa tayi ta shige dakinta a kwance ta tarar da malam sani,zama tayi tare da fadin ni ko malam kaga giccin yaran nan,aa ya bata amsa ina suka tafi oho musu nima bansani ba,ke rabu da su allah yasa ma sun tafi kenan,tsaki ta ja kawai ta fice daga dakin,hajjah ce ta fito daga bandaki tana fadin me take cewa jinai kina cewa kamar an nemi su mufida an rasa,allah yasa ma su tafi har abada kar au dawo,wai karima me ake da yaya mata, ai ni alhamdulillah indai suka tafi kuma allah kar yadawo da su,karima tabe baki tayi ta shige dakin ta.
Mufuda ce ta farka anan ta ganta cikin jar kasa,kayan su khairy taja tare da fada wa duniyar tinani,shin ina su khairy suke yanzu,sunci abinci ma kuwa,to wa zai basu ma abincin,jin an dafata ne yasa ta firgigit ta zabura ta juyo,take fuskarta tayi tozali da wata mata katuwa kai da ganibkasan 'yar duniya ce saboda irin kwailin din da tasha wato bleaching,kallonta mufyda tayi tace lafiya dai ko,murmushi matar tayi tace ea lafiya lau amma naga kamar ke bakuwa ce ko,daga kai tayi,daga ina kike ta jefo mata wannan tambayar,shiru mufida tayi ba amsa taso muje, ina zamu mufyda ta tambaya,zaki gani ta bata amsa,mufyda har bazata tashi ba sai kuma tai wani tinani kawai ta tashi ta bita.gida biyu suka wuce sai wani gida mai dauke da gate milk,shiga sukayi dik inda suka wuce sai kiga ana zubewa ana gaida babbar matar nan,dik masu gaida ta mata ne sai wasu tsirarin maza a cikinsu,ita dai mufida da 'YAN kayanta a hannu tana kallon mamaki a gidan.
Khairy ce ta fara farkawa take abinda ya faru ya dawo mata sabo,inalillahi wa inna ilaihi rajiun aunty mufy tashi tayi anan taganta tare da wasu maza dik yara ne,cikinsu ita ce babba sai wasu yara kanana suma,kallonsu take dan gaba daya hankalinta na kansu,a ina nake ta furta wani dan yaro ne ya matso yace mu ma haka aka kawo mu bamusan ina ne nan ba,tashi zaune tayi tana mai kallon yaron gaba daya tausayin yaran sun kamata tashi tayi tana kokarin bude kofar,yaron ne a gain ya kara cewa ai kofar bazata buduba,kanwata shukura bansan inda take ba,inaga tana dayan dakin ya furta,kuka take sosai amma sun tsaya suna kallonta,yaron ne ya taso yace mata ai nan gidan gaba daya gidan ajiye yara ne wadan da aka sato,bamusan inane nan ba amma dik wanda ya shiga gidan nan baya fitowa da rai,zaro ido khairy tayi take ta tina da shukura da aunty mufy,a lokacin ta tina batayi alwala ba tambayar sa bandaki tayi nuna mata yayi,shiga tayi amma ko taga babu sai ac data ke gudu,gaba daya wajen sanyi sharrr.
Shukura tin lokacin data farka take rusa kuka,tare da tuno irin rayuwar da suka sha a baya yanzu kuma ga wata,akan dan kwalinta take tana kuka tana addua,gaba daya dakin nasu hankalinsu na kanta,sai da ta shafa ta juyo ta kallesu ba laifi wadan nan suna da dan girma dan zasuyi sa'anin mufida,wata budurwa ce ta matso kusa da ita tace baiwar allah ya sunanki shukura ta bata amsa,allah sarki irin sunan kanwata,shiru shukura tayi ji sukai ana kokarin bude kofar gaba dayansu shiru sukayi,ba wanda suka gani sai plate din abincin da aka jero akan table ya shigo dakin,tashi sukai suna rububin dauka yayin da shukura ta tsaya kallin ikon allah,sai gani nayi table din na komawa,wannan budurwar ce ta kalli shukura tace kukkun haka ake yi idan za a bada abinci,wanda ya samu ya samu wanda bai samu ba shikenan,yanzu karbi wannan kici, kallon ta shukura tayi tace aa ki barshi kinji,to me zaki ci ke ta tambaye ta,shikenan to yanzu ki sa muci kawai ko,daga kai tayi tace to nagode aunty dariya tayi tace ba aunty ba jiddah.
Mudassir dik neme nemen da akeyi na su mufida yana daki kafarsa taki takuwa ga wani dan masifan ciwon kai dayake fama dashi,hussain ne ya shigo ya kallesa yace mudassir lafiya kake kuwa,am bani da lafiya inaga naji targade a wannan kafar tawa,shikenan kaje a gyara maka mana,to kawai ya bashi amsa ya juya baya yana tinanin yadda zai bullowa alamarin su mufida,domin tabbas sai ya rama abinda sukayi masa,dan sai sun gane sun tabasa.hajjah ce ke karyawa cike da farin ciki malam sani ne ya fito ya kalleta zama yayi suka gaisa,ai ni sani naji dadin yadda yaran nan suka bar gidan nan,dan tsuke fuska yayi yace to hajjah bakya ganin cewa mutane zasu zageni akan na barsu sun gudu,tsaki gaja kajika to ubanwa yasan sun gudu idan har ba kai ka fada musu ba, kai sani kai fa yanzu kaji dadinka domin ni fatan da nake allah yasa su gamu da ajalinsu a wannan guduwar,karim ce ta amsa da ameen shi kuwa malam sani shiru yayi tare da tashi ya bar wajen.
Hajiya ce ta shiga dakin hanan a bararraje ta ganta tana bacci,tashinta take kallonta hanan tayi tare da tashi zaune hajiyarce ta kalleta tace ke kinyi sallah daga kai tayi tace to kuma jiya da daddare na shigo naji kina bandaki me yafaru na jiki a bandaki haka kuma kin dade,mom bani da lafiya gudawa nake amma yanzu ma ai da sauki shikenan to,idan kin shirya breakfast is ready,juyawa tayi ta fita tsaki hanan ta ja ta kalleta allah ya kyauta wallahi,ni na gaji fa so nake na fita yawon duniya.
YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
13_14
Mufida gani tayi sun hau kan upstairs gaba daya ta koma 'yar kauye domin kallon kanta take kamar wata gailuwa,cikin wani katon falo taga anshiga anan taga wata mata katuwa dan tafi wadda suke tare,zama tayi tare da cewa mufida zauna,ita dai baiwar allah sai raba ido take,dayar ce ta kalleta tace hajiya zeenatu wannan ita ce mufida,na kawota wajenki kin dai san sauran,d ariya wadda aka kira da zeenatu tayi ta kalli mufida tace haba hajiya Saro wannan ai saidai kaduna,domin kina kallonta kinsan ba kalar kano bace,ita dai mufida jin su kawai take,tana jin tsoro amma kuma idan ta tina da kannenta tasa a ranta sai ta nemo su,waya zeenatu ta dauka tana kira nan da nan sai ga wata dauke da rigar apron,tana kallon mufida ta kauda kai,zeenatu ce ta ce yawwa ki dauke ta zuwa nan da gobe da asuba zasu tafi kaduna,ki bata dakin ta ita kadai to kawai tace tare da kiran mufida,mufida tattare kayanta tayi ta tashi ta bi ta,w ani daki dan karami aka bude mata mai katifa da bandaki,matar ce ta ce zauna,kin zama tayi tace amma baiwar allah ina ne nan kallonta tayi tace ke bakisan ina kikazo bane,eaa kawai ta bata amsa,to waccen matar na ganku tare fa wallahi bansanta ba nima cewa tayi nazo zata taimaka min,zama matar mai apron tayi tace kinsan nan ina ne,nan gidan bariki ne,wato gidan da maza da mata ake haduwa domin aikata aikin sabon ubangiji,kuma waccen matar da kika gani zeenatu ita ce mai wannan gida,dik yarinyar da take wannan gidan tana biyan kudin haya,a haka ake lalata rayuwar yaran mu masu tasowa,mufida kallinta tayi tare da furta nashiga uku,tashi matar tayi ta fice mufida tashi tashi tayi ta kara hade kayan ta.
Malam sani tin bayan batan su mufida tin yana saka abin aransa har ya daina,akan bench na gansa shi da wani abokanan sa dayan ne ya kalle sa yace wai nikam malam sani ina su shukura ne kwana 2 banji duriyarsu ba,waro ido yayi yace ea dama dayake sun tafi kauye wajen kakanina da haka ya tashi kawai yayi musu sallama sukam suka bisa da kallon tuhuma.
Mudassir ne ya dangyaso ya taho,kallonsa hajjah tayi tace yawwa dan albarka dama yanzun nan nakeso nazo na aika a kira saboda kasan cikk ta tsaya ganin yadda yake dangyasa kafa,rike haba tayi tana furta mudassir lafiya mai ya sameka,kai jafar maza debomin ruwa a kofi,tashi jafar yayi shi kuma Mudassir ya zauna,duba kafar tayi taga ashe ma targade ne,garin yaya kaji wannan ciwon,shiru yayi bai iya bata amsa ba.
Khairy ce take cin abincin da sauran yaran,sai da tagama ta zauna tare da zabga tagumi,wani yaro ne ya kalleta yace lafiya kike dagowa tayi kawai tace a ina ne nan,yaron dazu ne da yake ya fisu wayo yace mu ma bamu sani ba amma kuma nasan dai nan ba kano bane,wani kuka ta saki tace nashiga uku,nashiga uku,aunty mufyda,kuka take sosai,jin motsi tayi hakan yasa su kwanciya kowa yayi shiru,shigowa akai khairy kallon mutumin tayi sanye yake da fuska,idanun nan jawur kamar gauta,kallon gefen sa tayi taga keys dayawa,gani tayi ya sunkuci yaro daya,yayi waje yaja kofar, yana futa suka mike,khairy share hawaye tayi a take ta tino da shukura, saurin kallon kofar tayi tana bubbuga kofa tana kiran sunan shukura,sukam sauran shiru suke dan da sabo ai sun saba,dawowa tayi ta zauna kawai a zuciyar ta take furta nasan ma shukura yanzu ai batanan yazama dole nabi su ki nima kawai su kasheni ko na hutu da wannan azabar,saurin rije baki tayi tana furta allah na tuba ka yafemin,alhamdulillah da haka ta kwanta saboda dik yawancin Yan dakin sunyi bacci.
Firgigit ta farka tana tina mai tagani kuka ne ya kubce mata tana furta ummieh na kiyi hakuri,dole zan bar gidan nan,kuma bazan koma ba sai na nemo sauran 'YAN uwana,jin gidan shiru yasata tashi da mikewa tsaye ta taga ta leka taga wayam dik wannan mutanen babu su data gani a baya,k allon inda ta ajiye kayanta tayi ta gansu daukowa tayi ta fito daga dakin gidan shiru kamar ba mutane,sakkowa take daga kan upstairs sai da ta sakko sai tajiyo motsi saurin shigewa karkashin upstairs din tayi ta buya,gicci ta gani sai kuma taji magana irin da 'YAN kwaya yana kiran washhhhhh allah garin nan yayi min dadi,wani zazzafan hawaye ne suka biyo kuncinta tana allah wadarai da wannan rayuwar da suke,sai da ta tabbatar sun wuce sannan ta fito,cikin sa'a kuwa ba kowa a kofar gate din da gudu ta fito dai dai nan aka haske ta da wata katuwar torchlight,w ani wawan gudu ta saka amma riketa yayi mai torchlight din ganin fa ba sakinta zai ba yasata ta takarkare da gabza masa cizo a hannun take ya saketa,ita kuma kafa mai naci banbaki ba sai gudu,gudu take mutumin nan na binta amma ina ta masa nisa,ganin ba zai iya kamota bane yasa shi dawowa yana furta shegiya ashe tana da gudu haka,tinani ya fara to yanzu kuma ni me zan cewa hajiya, shiru yayi yace ba sai ma idan ta sani ba wallahi nunawa zan bansan anayi ba.
Hajjah ce tayi wani irin zabura tare da sakin ihu, tashi tayi take dik wani gumi ya shiga tsattsafo mata tana zare ido,kallin dakin tayi tana kece sanadi,kece sila,ko mr ya faru kece dan haka ba abinda zamuyi miki amma ki sani ko kisa a nemo mu ko kuma mu barki da hakki,musan dai kinyi karatun allo ko kin san ubangiji,da kike cewa baki son mata ke ba mace bace,hajjah dik ba wannan ba ki tabbatar kin nemo mu idan ba haka ba. ,,
Mufyda tin tana gudu har ta tsaya dai dai wani bakin kango,shigewa tayi kawai ta zauna,tana huci tana furzar da wata nauyayyiyar ajiyar zuciya,take bacci ya kwasheta,cikin baccin ne ta ji motsi,lekawa tayi daga kangon ganin wasu mutane tayi sun ajiye wata yarinya sun huce sunyi tafiyarsu,sai da ta tabbatar da sun tafi sannan ta fito tare da juyo da yarinyar, kara kunnenta tayi a kan kirjinta taji bugun zuciyarta take hawaye suka fara zarya,kallonta ta kara yi bata fi sa'ar shukura ba amma kuma,kanta ya fashe jini na zuba sai sawun dukan da yake jikinta,wani irin kuka ne ya kwace mata tare da rungume ta tana tina dukan da ake musu a gida,ganin jinin yaki tsayawa ne yasata rungumar ta ta tashi ta shigar da ita kangon ta kwantar da ita,dan kwali ta ciro daga kayan ta,ta kulle mata kanta ta kwantar da ita anan itama ta kwanta.
YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
15_16
Nifah wannan abu murtala yana bani mamaki, duba fa kaga yadda malam sani ya samu yara masu tarbiyya amma kalli wai sun tafi kauye,shi allah ya basa yaranma amma yi yake kamar bayaso,ni neman haihuwar yarinya mace nake amma allah bai bani ba shi ya samu shine yake wasa da damarsa,wanda aka kira da murtala ne ya kallesa yace ai yanzu sai dai mu ce allah ya ji kan sadiya,dikansu suka amsa da ameen.
Hajjah dai gata zaune tin dare har gari ya waye kowa ya fito amma itakam tana nan cikinta ya gama durar ruwa,kamar kace mata kyattt da ruga,karima ce ta leko a zaune ta ganta shigowa tayi tana fadin hajjah lafiya ko,shiru ne ya biyo baya karima ganin abin bana karewa bane yasa ta dafata firgigit ta fara waige waige,hajjah ce tace nashiga 3 karime,anya kuwa yaran sadiya ba mayu bane,zaro ido karima tayi tace allah hajjah me ya faru ke bazaki gane ba,jiya da daddare ne fa suka zo min sukai ta tsoratani da wasu 'yan iskan surutai na ba gaira ba dalili,karima ce tace me suka ce miki,hajjah ce tai fuska tace basai kinji ba shegiya kema,kallonta karime tayi tace tabb wallahi badai ni ce shegiya rike haba hajjah tayi tana fadan to kina nufin ni ce shegiyar tashi karime tayi ta karkade jikinta tace ohoo kuma dik yadda kika dauka to hakane.
Shukura suna zaune kamar kullin yauma table din aka sako ai kuwa nan da nan kowa ya fara dauka,sai da suka gama dauka sannan aka dauke, ba afi 1minute ba sai ga wani mai fuska ya bude dakin ya shigo,kowa nutsuwa yayi yana kallon kasa,take idanunsa suka sauka akan shukura,rike haba yayi hade da murmushi sai kuma ya fita su kuma nan suka fara lodawa cikin su abinci,domin kallo daya zaka musu kasan da yunwa a cikinsu.
Mudassir ya rasa me yake masa dadi dan ma ya samu kunburin kafar tasa ya sabe kuma ga shi har ya fara take kafar,amma kullun tinaninsa daya ne,shin ina su mufyda suka tafi,kamar kullun yauma yana zaune a daki,yana tina abinda ya faru a iya sanina su khairy basu da wasu 'yan uwa,to amma ina zasuje,naga baba shi ko a jikinsa ma da batan su bare kuma umma ita ba abinda ya shalleta,hajjah ma ita naga murna take,to wai me yasa aka tsanesu a gidan nan ne,ni narasa dalili fa,amma ko me zai faru sai na nemo su dan tabbas na tabbatar da suna raye,kuma ko ma menene ai laifi na ne da nai,kishingida yayi ya kwanta yana kallon ceiling din dakin.
Shukura ce ta kalli jiddah tace aunty jiddah yaushe zamu bar nan wajen,amsa mata tayi zamu bari insha allah kinji 'yar kanwata kici gaba da addua,ai inayi ta bata amsa,amma kuma kin tabbatar min aunty khairy tana cikin gidan nan,shiru tayi kara kallonta tayi tace aunty jiddah magana nake miki fa,haba shukura bani da wata amsa da zan baki wallahi saboda kullin daya ake dauka dan haka gaskia ban sani ba,kuka kawai ta saki tana faman kiran mufyda da khairy.
Zeenatu ce ta saki wata ashar a yayin da ta shiga dakin taga wayam,take ta fara lallema ni saro zata cuta wato ta kawo yarinya kuma tazo ta dauke ta,fitowa tayi tana kiran gateman a bakin aikinsa yaje yaji kira,da dan gudu ya taho yana fadin hajiya gani kaga wannan bakuwar budurwa ta jiya,saurin girgiza kai yayi kai da gani kasan ma bashi da gaskia amma dayake a rude take bata gane hakan ba,komawa tayi gaba daya gidan anfito ana kallonta,waya ta ciro tare da dialling number saro,tayi sa'a ta daga,ke dallah saurara har ni hajiya zeenatu zaki damfara,kinsan da cewa yarinyar nan guduwa zatayi amma shine kika amsar min kudi,ya isheki saro na baki nan da sati 2 ki nemo min yarinyar nan dan nasa ta a budget di na dan haka ke kikasan abinyi,kittt ta katse dafa kai saro tayi tace nashiga 3 dama ance tsintacciyar mage bata mage,ni saro yanzu ina zan nemo ta,ga hajiya zeenatu bata jira fa.
Zaune take tare da kurawa yarinyar idanunta,tana kallonta dik da kyakkyawa ce kallon jikinta tayi taga sawun bulala a hankali ta furta allah sarki,ashe ko ina ana dukan Ya'ya mata,kyakkyawa ce gata da dogon gashi baki sidik,mai sheki da santsi amma daudar wajen ce yasashi rinewa da yin ja,sanye take da riga da wando a jikinta,mufyda ganin bata fara motsi ba yasata fara tabata,amma shiru,mufyda yunwa takeji amma batasan inda zataje ta samo abinci ba,dan haka al dole ta zauna tare da bazo da kayan su,kamar daga sama hoton sadiya ya fito kallonta mufyda tayi tana shafa fuskarta,ummieh na miki alkawarin cewa tabbas zan nemo shukura da khairy kinji ummieh na,jin an taba ta ne yasata saurin matsawa baya,ganin yarinyar ne yasata dan murmushi yarinyar ko kallonta batayi ba,tashi tayi zata gudu,rikota mufida tayi tace ina zaki ki zauna anan kinji yarinya harara kawai ta zabga mata,tana fadin allah ya kiyaye,sai ji kake luuuu ta fadi a cikin kasa,mufida da saurinta ta fice daga kangon yana neman ruwa amma babu,kan kwana ta tafi nemo ruwan amma babu da kyar ta samu wasu ledoji da ruwa a ciki da dan sauri ta dawo,yanda take haka ta ganta,da sauri ta zuba mata ruwan anan ta fara dan numfashi,rungumota tayi tafara hura mata iskan bakinta,da kyar ta bude idanunta tana kallon wajen,sai da ta kalle wajen sai ta kalli mufyda tace wacece ni,saurin zabura mufuda tayi tace ya allah inalillahi wa inna ilaihi rajiun ke bakisan wacece ba,kamo hannunta mufyda tayi tare da dafe wajen ciwon,ta zaunar da ita dik da cikinta na kiran yunwa amma haka ta daure,har zuwa la'asar.
YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
17_18
Mudassir ne zaune shi da hajjah sai karima,kallon su yake kamar wani mara lafiya,hajjah ce tace wai kai dan gidanku mudassir lafiyarka kuwa sai wani bi na kake da kallo,dan tsaki yaja kawai yace hajja dan allah da gaske su mufida sun gudu,tsaki hajjah ta ja tace da akan wannan yan iskan yaran ka tsareni da ido,to bani zan baka amsar wannan tambayar ba uwarka ce gata nan a gefenka,mudassir kam shiru yayi yana tinani hade da mamaki,ban taba tinanin haka aka tsani su khairy ba da tabbas sai na jawo su a jiki,amma hakan ma lokaci ai bai kureba,zan je na nemosu na dawo da su kuma cikin gidan nan,karima cikin karaji tace wai mudassir ba magana nake maka bane,me yasa kwana 2 nan dik ka chanja ka zama wani iri,kallonta yayi yace umma dan allah kawai ki kyaleni ni zan tafi ma na bar garin nan,ina zakaje kenan,ta tambayesa tashi kawai yayi ya bar wajen,yana tinani,karima mamakin sauyawar mudassir take,tana tambayar kanta shin me yasa ya chanja,yayin da hajjah kuma tayi shiru tana tinanin mafarkin da tayi haka.
Mudassir dakinsu ya shige tarad dasu alhassan yayi suna zaune dan da alama wani abun suke sha,alhassan ne yace kai mudassir zo kasha wannan kaji wani irin shegen dadi ne da shi,tsaki mudassir yaja yace sai dai ku kusha amma ni na tuba da irin wannan halayar da nake, kuma insha allah bana fatan na koma,saboda bansan ranar da zan mutuba, a ina, a wane hali kawai dai nasan allah yana madakata yana jirana,kuma kamar yadda su shukura sukabar gidan nan wallahi sai naje na nemo su wannan alkawari na ne,ficesu yayi sukuma suka saki dariya,alhussain ne yace anjima fa zamuje ko sai kuma sukai wa junansu signals suka fashe da dariya.
Yarinyar ce can gefe daya yayin da mufyda take sallah ita kuma tana ta raba ido tana kallonta,sai da ta idar tai addua sai ta juyo ta hade kayanta tace mutafi,tsaki yarinyar ta ja tace nifa ba inda zani sai kin fadamin wacece ke,saboda ni nasan abinda ya faru dani,mufyda ce ta ajiye kayan tare da zama kusa da ita anan ta bata labarin yadda akai komai ya faru da kuma abinda ta gani,yarinyar ce tace kenan nan ina ne,kano mufyda ta bata amsa,yarinyar ce ta fashe da kuka sai kuma ta kalli mufida tace dan allah inaso mu tafi abuja,zaro ido mufida tayi tana mamakin wannan 'yar mitsilar yarinyar amma kuma sai daukowa mutane aiki,mufida ce tace aa baiwar allah ina muka ga kudin mota kinsan kuwa nisan da yake tsakanin kano da abuja,gyada mata kai tayi tace aa bansani ba amma inason naje saboda na baro yayana a can din bansan kuma,shiru tayi tana goge hawayen face din ta,mufida ce ta rungume ta tace shikenan naji amma ki fara fadamin ke wacece,kallon mufyda tayi tace yanzu dai ba wannan ba yunwa nakeji fa,mufida ce tace nima yunwar nakeji amma narasa inda zan samu abincin da zanci,yarinyar naga tana lalube a jikinta,sai ga wata tsohuwar 500 da ta yakune,kallon kudin tayi tace tabbas kafadi gaskia sunyi mini amfani yayana ina fatan kadawo a lokacin kuma dad ya samu lafiya,kallonta kawai mufida take sai ta mika mata,mufida ce tace kizo muje kawai mu siyo abincin tare,kar na barki anan bakisan gari ba,to tace mufyda har tayi gaba sai kuma tayi saurin dawowa,ta debe kayan yarinyar ce tace kawo na rike miki kayan naki kinji 'yar uwa,dariya tayi tace sunana mufyda kinji,ni kuma hibbah dariya tayi tace to shikenan kama hannunta tayi suka fito daga kangon,unguwar shiru kakeji ba kowa saurin rufe fuskarta tare da kama hannun hibbah.
Hajiya saro ta shayo kwanar da su mufyda suke tafiya amma dayake allah yasa idanun mufida a kasa suke bata ganeta ba har tayi ni sai ta tsayar da mota,sai da tsaya tayi nazari sai kuma ta ja motar ta fice,yayin da mufida ita ko kallonta ma batayi ba,gidan hajiya zeenatu tayi parking ta bide ta shige ciki,a falon ta tsaya tana taunar chewing gum,tare da kallon zeenatu da nuna ta da hannu ke zeena wallahi kinyi kadan ki cimin mutunci,kuma yarinyar da ta gudu ai kece da laifi da ke da wancen shashashan gateman din can,aikin banza zeenatu ce ta mike tana fadin ni kike fadawa hakan saro,lalle zakiyi dana sani dan tabbas sai na batarda ke,take tai tabi da hannunta,wasu kattin maza ne naga sun zagaye saro,yayin da saro gumi ne ke keto mata ta fuska,kanta da kowace gaba ta jikinta,kushigar da ita inda ba a fitowa,take suka bace batt zeenatu ce ta babbake da dariya tana furta sanin da kikayimin saro.
Abinci da suka siya,suka ci mufida ce ta kalleta tace hibbah na fito neman Yan uwana ne kuma zan taimaka miki ki koma gida amma ki bani labarinki da dalilin dayasa har aka daukoki daga abuja aka kawoki nan,hibbah ce tace mufyda dan allah mu fara samun wajen da zamu kwana,bamu da kowa anan,kinsani zan baki labarina anjima da idan har mun samu wajen kwana,tabbas rayuwarmu abin dubawa ce mufida kasancewar mu mata masu rauni,tashi tayi mufida binta tayi tana mamakin wannan yarinyar da take da shegen wayo amma kuma sai kankanta.
Dakin ya shigo tare da dauko shukura ya fito da ita,shukura kuka take domin an rabata da aunty jiddah,sai a lokacin take kallon gidan ganin dakuna tayi sunfi 10 sai kuma aka shigo wani karamin falo anan taga wani saurayi a zaune,kallonta sukayi sai dikansu sukayi murmushi,wanda ya dakkota ne yace oga yau zamu kaita be,girgiza kai yayi yace aa ni zan kaita da kaina ni da Silva ku yanzu ku kula da sauran yaran idan ansamu matsala kamar yadda aka saba,zan maka alama,silva ne yace ai bama fatan matsala sir,shukura tirjewa tayi tana fadin ni wallahi bazani ba,jin yatsu 5 ne yasata hadiye dik wani zance,silva ne yaja hannunta suka bar gidan,mota suka hau suja fice daga gidan tana kuka tana kiran khairy,tafiya suje dai dai bakin saman titi suka hangi police silva ne zai chanja hanya amma sun ganosu,suna chanjawa za a iya samun matsala,ogan ne ya shakawa shukura wani abu take ta sume, a hankali ya bude kofar motar ya wullota sannan suka mai da kofar suka rufe suka matsa,shukura batasan a duniyar da take ba,amma sai dai bayanta tsakiyar wasu ciyayi ne,su suka kareta yasa ma ba a hangota ba.
Hanan ce dauke da katuwar trolly bag ta janyo a falo ba ta tarar da kowa ba dan haka zagayawa tayi ta fuce ta kifar baya tana yi tana kallon gidan,tana murmushin samun nasara.
YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
19_20
Narantse da girman allah ko ki fito min da hibbah ko yanzu nai maganin ki a cikin gidan nan,wani kyakkyawan saurayi kai dagani kasan yayan hibbah ne,sai wata mata katuwa da take gefensa,shikenan idan ka fasa kaji,yi maganin nawa kuma kasani hibba bazan taba fito da ita ba,domin na tabbatar da cewa yanzu ta dade da barin duniya sai dai muce ma hade a lahira,zaro ido yayi gaba daya kansa ya dau chaji ya rasa me yake masa dadi,k allonta yayi tare da murmushi yace zanyi maganin ki har dai na amsa sunana na Aliyu Haidar,tabe baki tayi tace kuma dai sai kaje ka nemota,da kai da wannan shashashan uban naka mara kangado,kai ma ina dab da batarda kai wallahi da haka ta shige daki.dakin ya tsaya budewa yayi masha allah tsayawa yayi yana kallon dakin kai da gani kasan dakin na yara ne,ganin hotunan hibbah ne yasa nasan da cewa tabbas dakinta ne,gasunan sunfi guda 10 wani suna tare su 4,da mahaifinsu,sai mamansu,ali da hibbah,wani kuma ita kadai tana dariya,shiga yayi anan dakin na hango shi gaba daya pink ne da fari akai kwalliya,zama yayi akan dan karamin gadon tare da fashewa da kuka,tabbas munyi rashi,mama kin tafi kin barmu da kewarki,kin bani amanar hibbah,amma na gagara rike miki amana,kin cucemu kin zalunce mu,kin kashe min hibbah,kuma kisani nima bazan taba rabuwa da ke ba sai na dau fansa a gareki jummai da haka ya kwanta yana kuka da idanunsa.
.
Hibba ce ta dafe kanta ta kalli mufida tace nagaji mufida ga kaina yana min ciwo kamar zai fita daga jikina,saurin kamata mufida tayi tace ya salam na manta ni da ciwon amma bara mu karasa waccen pharmacy din sai na siya miki paracetamol ko,kallonta hibba tayi tace wallahi banasha ko a gidanmu,hakuri zakiyi hibba nan din ai ba gida bane ko kallonta hibba take taba mamakin tausayi irin na mufyda.pharmacyn suka shiga sauran chanjin 100 da ta rage ta mika masa tare da nunawa masa ciwon da yake kan hibbah,kallinta yayi yace wannan ai sai 500 amma 100 ba abinda zatayi,mufida ce tai rau rau da ido tace dan allah ka taimaka min sauran chanjin mu kenan kuma gashi bamu da kudi,shikenan zan miki saboda allah kamo hannun hibbah yayi tare da fara yi mata dressing a ciwon nata,ita kuwa baiwar allah sai godiya take zabga masa,kallo daya dr ya karayi musu yasan suna cikin tashi hankali,1000 ya dauko tare da mikawa su mufida,kin karba mufida tayi sai da yace mata ai badan kin rokeni ba yarinya,kawai na baki sadaka ne,kuma ki lura kinji dan unguwar nan akwai mutane daban daban,m murmushi tayi tace to nagode sosai hibba ma tsugunnawa tayi tace mungode kawu allah ya saka da haka suka fice yayin da dr ya ke matukar tausayin su yana furta,to yanzu da aka sake su ina zasuje wadan nan a haka ya bar zancen.
Yaya Haidar ka taimaka mini zan mutu,dan allah zumbur ya mike yana me shafe gumin dayake tsattsafo masa dik da sanyin AC amma hakan bai hanashi gumin ba,cikin rashin sanin me zeyi ne yasa shi furta hibbah kina raye,kina raye ashe tabbas zanje na nemoki hibbah na farinciki na,tabbas hibbah bata mutu ba karya jummai take masa.karar wayar ne ya katsesa kallonta yayi ganin an saka Doctor yasa shi saurin mikewa,yana fito wa ya tarar da doctor a falo,gaisawa sukai tare da yin musabaha,Haidar ne yace muje to ko,shikenan wani sashe naga sun nufa a yayin da komai na wajen ya kasance dark green ne,wani daki naga sun nufa shiga sukayi,dakin dai dai gashi a gyare kan bed nai dubana anan ne naga wani mutum,gashi dai kamar matacce amma idanunsa a bude suke,sanye yake da shadda dinkin jamfa,Haidar ne ya kallesa yace barka da hutawa dad jiyowa yayi ya kallesa,sai kuma ya juya fuska,Haidar hawayen fuskarsa ya boye yana tina halin da mahaifin su yake nuna musu,gashi dai ba lafiya amma kuma baya kulasu kwata kwata,fitowa yayi tare da barin doctor da dad nasu.
Tare su police din sukayi nan suka fara tambayar su,ganin kamar basu da gaskia ne yasa ogan fadin daukesu ka ajiyesu gefe,silva ne zaiyi magana oga ya dakatar dashi koma wa sukai suka zauna,oga ne ya danna wayarsa yayin da dauda da abokin zamansa suka ga haka sun gane me yake nufi,tini suka tashi suka fara firfito da yaran gidan,sai da suka fito da kowa,khairy sai raba ido ko zataga shukura amma me bata gani hakan ya tabbatar mata da zarginta take a wajen ta zube tana rusa kuka,ido ne gaba daya ya dawo kanta,dauda ne ya dagota ya jata ta bayan gidan suka fice suka nausa dajin dayake bayan gida suna tafiya,khairy ta rasa ina za a kaisu gashi taki yiwa kowa magana,kowa ka kalli fuskarsa kasan ba farin ciki,khairy tinani tafara ba aunty mufy ba shukura ya ilahi,wata shawara ce ta fado mata amma sai tayi shiru tana dan tinani tana tafiya,dai dai wata sarkakiya ce kowa yana wucewa khairy sai ta buya sai da kowa ya wuce amma ba wanda ya ganta shiru tayi a wajen,sai da ta bari sunyi matukar nisa sannan ta fito ta fara gudu amma kasancewar wajen yayi duhu yasata fara lalube.
Mufida ni 'yar garin abuja ce,mahaifina ya kasance mutum ne mai ilimin addini dana zamani ya kasance babban dan kasuwa sannan yana da mata daya sunanta khadija,mahaifiyata kenan suna zaune cikin zamansu lafuya da kaunar juna,a haka har allah ya bata ciki ta haifi ya haidar,ya haidar ya taso cikin kulawa Sannan mahaifina yana matukar kaunarsa,bayan wadansu shekaru da suka wuce a lokacin mahaifiyata tana da cikina,a lokacin dad ne yace zai karo aure to mama ko damuwa batayi ba amma har dad ya karo aure,bayan auren da wata 1 ne aka haifeni ni kuma,dik da cewa da farko jummai da mamana suna zamansu lafiya,sai daga baya kuma jummai ta fara fito da wata halayya wadda mamana batasan ta da ita ba,a haka da dadi ba dadi kuma har aka dau shekaru dik da cewa jummai yanzu ta tsani mamana,watarana na tashi daga bacci da safe na fito falon ne anan na tarar da falon komai a kusan fashe yake,a gefe daya kuma ya haidar ne shida dad a zaune,ya haidar ne naga yana hawaye,tafiya nayi ina tambayar sa,kallona kawai yayi tafiya nake ina kiran sunan mamana amma kuma shiru,ya haidar ne ya biyo ni ya rikoni ta baya tare da juyo dani dan murmushi yayi yace karki damu 'yar kanwata,mama bata nan amma zata dawo nan bada jimawa ba,a haka dai muka ci gaba da rayuwa dik da cewa jummai batason mu amma yaya haidar yana min komai,bayan kamar wata 2 da faruwar wannan al'amari da safe na fito sanye da shirin tafiya makaranta anan naga doctor gidan mu shida ya haidar karasawa nayi na gaishesu,tambayar ya haidar nake me ya faru ba abinda yace min sai dai wai dad ne bashi da lafiya,kallona yayi ni kuma nayi shiru,kinyi break hibba amsar daya sakarmin daga kaina nayi kawai,mufida na kasance tin ina shekara 7 na iya girki kasancewar jummai bata bani abinci yasa ya haidar yayi min dan karamin kitchen a dakina komai akwai na buqata,idan zanyi sati daya ban fito ba abinda yayi wa jummai zafi bare ta duba ko lafiya,Mufida ce ta kalleta tace tabbas hali daya da karima amma baki fadamin meyasa har taso halaka ki ba,zan fada miki,watarana ne nafita bayan gida wasa a lokacin naji tana waya,abinda naji ne yayi matukar bani mamaki dik da a lokacin kinganni karama amma ina da tsantsan wayo da kuma hangen nesa takardu take magana,ina jin wayar ta nikuma kawai sai na koma na juya dakin dad na shiga yana bacci a lokacin na fara binciken takardun,cikin sa'a kuwa na gansu cikin wardrobe din dakin,ni na daukesu tare da tafiya dakin ya haidar domin na kai masa,sai da mai baya nan,haka na shiga nai ta zagaye har narasa inda zan ajiye daga karshe ne na taka kujerar dakin,na dauko wani frame na hoton maman mu dama akwai jaka daga baya,na zuba a ciki na maida na gyara dakin na fito kamar banyi komai ba,to jummai ta tafi neman takardu amma abin ya bata mamaki ganin bata gansu ba,ba abin ta tambayi dad ba ni dai ina kallonta tana nema nikam ina ta dariya kasa kasa,ina saurin gayawa ya haidar me nayi amma kuma shi a ranar bai dawo ba saboda ya tafi lagos wani aiki da dad ya turasa.
YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
21_22
To ni bansan me yafaru ba sai farkawa nayi na gammu tare da ke,mufida ce ta kalleta tace allah sarki lallae rayuwarku tana cikin wani hali amma zan maida ki gida kinji,hibba ce tace amma kuma mufida ke meye ya raboki da gida,dan murmushi tayi kawai tace zan fada miki hibba amma ba yanzu ba,yanzu dai hibba ba kya jin yunwa ko,gyada kai tayi mufida ce tai murmushi tare da yi mata shimfida ita kuma sauran purewater da hibba ta sha magani ne yasata daura alwala da shi tazo ta fara sallah yayin da hibba ta kura mata ido.
Silva ganin yan sandan nan sun dadar dasu ne yasa oga yace wa silva tada motar nan ka kureta kawai mu wuce mu barsu anan yanda ya fada haka ce ta faru police din ne suka bisu amma ko me kurar su kawai suka gani a wajen,babban cikinsu ne yace ba matsala ai zan gansu kuma zan ganesu,dayan ne yace ok,silva ne yace oga yanzu ya zamuyi da yarinyar da muka wullar oga ne yace kai rabu da ita ta sha kawai wannan,muka ce zamu koma wajen nan ai kasan daganan sai prison,da haka silva ya kure motar yaci gaba da bada wuta,dajin suka shiga anan oga ya bada umarnin ya dura yaran a mota sai da aka gama zuba su sannan aka tada motar suka bi ta cikin dajin suka kara nausawa.
Tin a lokacin da sanyin asuba ya fara bugar shukura ta farka,ganin ta tayi a inda batayi tsammani ba tinani take shin ina ne nan din ganin ba kowa gata kusa da titi ne yasata fashewa da kuka,tashi tayi tana kuka ta hayo kan titin tana tafiya ba kowa a hanyar kasancewar safiya ce sai Yan motoci jefi jefi da suke wucewa,tafiya take tin tana yin ta marmari har ta gaji rana ta take ga yunwa ga kishirwa gashi ba gida gabas ba gida yamma,haka taci gaba da tafiya har karfe 12 tana ciki tafiya sai ji kake shaff shukura a kasa tana faman haki domin kallo daya ya isa ka tabbatar a galabaice take,ta dade a wannan yanayi wasu jerin motoci ne suka taho su 5 babbar cikinsu ita ce a tsakiya,kirar bmw black ce,gani nai sunyi parking,wata mata ce naga ta fito daga cikin motar bayan sauran bodyguard din sun bayyana suma sanye take da tsadadden material mai matukar daukar ido,gaban shukura ta karasa ganin yarinya a yashe ne yasata saurin dafata,dagota tayi taga idanunta na lumshewa,alama tayi da akawo min ruwa,miko mata akayi budewa tayi ta kara mata a baki take ta fara sha kamar wadda ta shekara bata sha ba,sai tana gama shan ruwan ta rike cikinta dayake ta faman kullewa,matar ce tai musu alamar da su daukota su sakata a mota,saka ta sukai sannan suka ci gaba da tafiya a cikin motar kuwa,nayi mamakin ganin yadda shukura take a jikin wannan hamshakiyar matar shin dama tasan ta ne ko me, tafiya take jin karar waya ne yasata daga wa tana furta sorry,kallon driver tayi tace ina tinanin mu fasa bin flight saboda wannan yarinyar kawai muje a motar insha allah dai nan wajen 11 nasan zamuje da haka driver yace ok suka ci gaba da gudu.
Jummai zaune akan dining waya take tana furta wallahi hajiya abin nan yana dauremun kai amma kinsa me za a yi yanzu akan maganar da mukai dake nasan indai har wannan aikin ya kasance to tabbas zai samu tabin kwakwalwa,kinga bani da matsala dika na gama da su,dariya tayi tace kedai kawai kije saboda yanzu idan na fita zai zama abin zargi kasancewar jikin alhaji yana tashi,kashewa tayi ta ajiye ta fara cin abincinta,d ik abinda takeyi akan kunnen haidar shi ya rasa ma yazaiyi da ita,amma shi dai ya dogara ga allah yasan allah shine zai bashi mafita akan dik abinda yake faruwa,kuma yasan tabbas watarana mahaifiyar su zata dawo garesa dan yasan dole tana raye,kawai tayi nisa da su ne akan wani dalili na daban.
Hajiya ce ta shigo dakin hanan amma shiru rike kanta tayi tana furta ya ilahi tabbas hanan ta girma,har zata fi ce sai kuma taga wata takarda akan table dauka tayi,abinda ke cikin takardar ne ya mutukar girgizata sakin wani marayan kuka tayi tana kiran shikenan hanan,ta tafi wallahi fitowa tayi tana hawaye alhaji ne ya karbi takardar ya karanta ajiye ta kawai yayi,ya kalleta tare da rungumo matarsa yana me ce mata haba hajiya kiyi hakuri mana nasan dama tabbas hanan guduwa zatayi,dik da kin shaku da ita amma nasan dik dadewa tabbas zata dawo gareki kinji Zainab,share hawayen fuskarta tayi kawai,tashi tayi da dan gudu ta haye upstairs bata dade ba ta fito da mayafi a kanta,alhaji ne yayi kokarin riketa amma ta zille,fitowa tayi da dan gudu² tana share hawaye tana furta kiran sunan hanan kafin alhaji ya fito har ta shanye wannan lungun dai dai bakin titi ta tsaya idanunta basa ganin gabanta bare tasan a inda take,kan titin ta hau take alhaji ya fara yi mata magana tare da ihu amma ina sai jin kara nayi.
Hajjah wai mudassir ne zai tafi neman su khairy,sakin kwanon hannunta tayi tare da kallon mudassir din tace kai baka da hankali,muna samu mun rabu da ala kake shine zakaje ka dauko mana su to wallahi mudan ahirrr dinka,kaji min dan iskan yaro karima,karima fito kiji abinda danki yake kokarin aikatawa,da dan sauri karima ta fito tana kallon mudassir,cikin rashin sanin abinyi yasa ta fadin wallahi har indai kafita da shirin nemo su khairy wallahi sai na tsine maka,mudassir nadamar fada musu yayi kawai,malam sani ne yaja hannunsa sukai waje zama sukai akan iccen kofar gidan,malam sani ne ya kallesa yace tabbas nayi dana sanin abinda ya faru kamar yadda kaima nasan kayi dana sani,a yanzu bamusan inda zamuje nemansu ba mudassir,abinda ya dace mu bisu da addua kawai dan shine babban gatan da zamu iya yi musu,mudassir ka kyauta kuma kanuna kana kaunar 'YAN uwanka,dikda inason yara na haka nake dannewa saboda mahaifiyata,tin bayan mutuwar sadiya naso daukesu daganan amma hajjah tace idan nayi hakan sai ta tsine mini,dan haka Mudassir karkaje saboda mahaifiyar ka ita matayi wannan furucin kawai mu bari insha allah zasu dawo idan muna da rabon ganin juna,tashi kawai sani yayi ya bar mudassir yana goge kwallar idanunsa.
Zaune take cikin wani daki dik jar kasa shigowar zeenatu yasa ta mikewa tana kuka tana fadin dan allah hajiy ki yafemin tabbas nayi kuskure amma bazan kara ... dakatar da ita tayi tace saurara saro ko da zan yafe miki wallahi sai kin mallakamin dik abinda kika mallaka idan ba haka ba ki kwana a lahira,murya na rawa tace na mallaki miki nidai ki kyaleni na tafi kawai,dariya kawai tayi tace ai bazaki tafi haka ba,cikin daga murya tace akawomin wuka,zaro ido saro tayi sai ga wuka fill tana sheki da daukar ido,bata fargaba sai jin yanka tayi keet a gefen fuskarta take jini yayi tsartuwa,kallon guard tayi tace ai mata magani a sallameta a kawo min dik abinda ta mallaka,to kawai yace ya fito da ita yana ja kamar kayan wanki.
Daga alkalamin AUNTYNMU CEH✍️✍️✍️
Jannat
Kawancen mu
Ramadan kitchen
A sanadin Kishiyar uwa
And Ya'ya mata (meye laifin mu)
YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
23_24 🌻
Wayyo allah mufida yunwa nakeji wallahi dafata mufida tayi tace to hibba ya zamuyi kinga sauran 1000 kuma masu abinci basu fara siyarwa ba amma muje nasiya miki bread da tea ko,hibba ce ta share hawayen fuskarta a zuciyar ta tana tina a lokacin da takeyin breakfast a gida sam batacin bread amma yanzu gashi zataci,mufida ce ta juyo tare da rungume ta tashare mata hawaye tana fadin haba hibba kiyi hakuri kinji,insha allah zan maidaki gida,dama yau zan sami aiki anan kinga kudin dana samu sai na kaiki gida ko,da fara'a ta dago ta kalleta tana murmushi tace nagode mufida amma kinki fadamin tarihinki fa,zan fadamiki kama hannunta tayi taja zuwa wajen mai shayin.
Auwal bansan ya zanyi ba hibba ta bata kuma wallahi jummai ce sanadin komai,ga mahaifinmi ya daina kulawa da mu sam baya bukatar kallonmu,kuma inason hibba ta dawo ne dannaji ya akai abin ya kasance,auwal ne ya dafasa yace kayi hakuri haidar kaji amma yanzu abinda yafi muhimmanci shine mu nemo wadan da suka dauki hibba domin jin ina suka ajiyeta,dan tinda harkai mafarkinta to tabbas tana raye,hakane auwal yanzu ta ina zamu fara,auwal ne kawai ya ce nasan yadda zanyi kai dai kawai ka bini yadda nace haka za ai.
Alhaji da dan gudu ya karaso yana kallon hajiya da tana a mike tsaye,sai kuma wata yarinya da a lokaci daya jini ke zuba daga jikinta,kyakkyawan saurayi ne ya fito yana duba yarinyar ba abinda ya furta sai inalillahi wa inna ilaihi rajiun,daukarta yayi ya sakata a bayan mota kallon sa hajiya tayi tace tsaya na shiga alhaji ka biyomu a baya,haka kuwa akayi cikin 4mint suka isa asbitin direct emergency suka nufa,shigar da ita akayi wata nurse ce ta fito tana fadin wannan case din dole sai da police,murmushi saurayin yayi ya fito da id card dinsa ya bata,wata takarda ta mika masa yasaka hannu,hajiya da alhaji kuwa tinani suke wacece ita especially hajiya domin tabbas tasan kowacece wannan ta taimaki rayuwar ta,dawowa saurayin yayi ya zauna a kusa da su,ba'a dau wasu mintuna ba sai ga doctor ya fito,kallonsu yayi yace ku biyoni office,saurayin dik a tinaninsa yarsu ce,zama sukayi doctor ne ya kallesu yace abu na farko ya sunan majinyaciyar,shiru sukayi hajiya ce tai karfin halin fadin Deeena rubuta wa yayi sannan ya dago yana mai kiran tana cikin matsala,saboda dik da ta kasance yarinya amma tana dauke da citar ulcer kuma a gaskia ta kamata da yawa,sai kuma naga dik da tana yarinya jininta yana kokarin hawa,hajiya kam share kwallah take tana jin bayanin doctor,bayan haka kuma ta samu karaya a hannu da kafa,saurayin ne ya furta inna lillahi wa inna ilaihi rajiun,rike kansa yayi,sai kuma ciwon kanta yayi zurfi da yawa sai an dage da bata magunguna,card ya basu sannan suka fita,zuwa ppharmacy saurayin ne siyo magungunan mika mata yayi dai dai lokacin wayarsa tai kara,dagawa yayi yana fadin mommah gani nan yanzun nan,hajiya ce tace kaje kawai kaji dan nan mungude,alhaji ne ya kallesa yace to yaro nagode ko sai anjima.wucewa yayi hajiya zama tayi tana sharar kuka,alhaji ne ya zauna yana fadin to hajiya ina amfanin hakan hanan ta gaji da zama damu ta tafi to bashi kenan kallonsa tayi tace allah sarki yarinya abin tausayi dan ta taimakeni kawai ta shige gaban motar da tini yanzu ni ce a wannan halin,ko ya sunanta bansani ba,amma ta taimakeni tabbas kuma zan mata sakayya ko.
Dai dai wani tangamemen gida akai parking ni kaina bazan iya cewa ga girman gidan ba amma fa babbane,gate ma 3 ne a cikin gidan,(na barku kawai ku kiyasta da kanku fans)fitowar hajiyar tayi umarni tayi tace ku daukomin yarinyar nan,dauko ta sukayi suka nufo falon masha allah falo har falo kayan alatu kuwa ba karya anzuba su,parlourn ta shiga anan nai kicibis da wasu samari su 3 suna hira shigowar ta ne yasa su mikewa suna hugging dinta daya bayan daya,guard sin taiwa alama daya sauke ta akan kujera ya fita,ajiyeta yayi a lokacin shukura kam bacci takeyi sosai,samarin ne suka kalleta sai kuma suka kalli hajiyar dayan ne yace ammi wannan fa kallonsu tayi tace sudais ka duba ta kafin na fito domin ana jirana da to ya amsa kawai ya shige dakinsa domin dauko kayan aikinsa,yana fita, Sha'aban ne yace kai Mus'af kalli wata kyakkywar yarinya kallonsa Mus'af yayi yace ea kuma gata karama wallahi,kalli kayan jikinta sha'aban allah sarki,sudais ne ya fito dauke da kayansa ya fara kokarin dubata yana gamawa hajiya ta fito kallonsa tayi tace yawwa sudais ka kyauta da ka sa mata drip yanzu zanje office ana jirana,ku kula da ita plz idan ta tashi kubata abinci idan nadawo zamuyi magana da to suka bita suna kallon yarinyar,sudais ne ya kara kallonta sai ya wuce dakinsa,mus'af ma wucewa yayi yayin da sha'aban yace shi ba inda zashi sai ta tashi yana zaune anan dai yana kallo.
Mufida ce tsaye a gaban wata mata mai sai da abinci,tsugunnawa tayi ta gaisheta amsa wa tayi fuska a sake,mufida ce tce dama hajiya so nake dan allah ko zan iya yimiki aiki kina biyana,shiru hajiyar tayi sai kuma tace aa gaskiya kiyi hakuri amma ina da masu aiki,mufida ce tace to hajiya nagode,wucewa tayi har zata tafi sai hajiyar ta kirata tace yarinya na yaba da hankalinki,karbi wannan katin kije wannan address din suna damai bukatar wanke² da murna ta karba tana ta fadin nagode sosai hajiya,wucewa tayi suka dau hanya,ba su wani dadeba suka isa wajen,a lokacin ba kowa sai wani ma'aikaci,katin ta mika masa karba yayi sai kuma ya shige ciki,bai dade ba ya dawo yace kizo inji hajiya kama hannun hibbah tayi,kallonta yayi ke kadai fa tace,hibba ce tace mufida sakarni kawai kinji ni zan jiraki anan,ke dai kawai kije,shiga tayi bata dade ba tafito tana fadin ta daukeni hibbah,kullun kuma zatana bani 1000 daga safe zuwa dare,murmusgi ta saki tana furta na kusa komawa gida mufida,da farin ciki suka bar wajen,suna tafe suna hira,mufida ce ta kallet tace yanzu abincin safe kadai zamu rinka ci ko hibba sauran kuma a wajenta,da haka dai suka tafi.
Saro ce a yashe a kasa tana ta zare ido ga hasken rana,tashi tayi ta taba gefen fuskarta taga sawun dinki a wajen,da kyar ta lallaba ta wuce zuwa gidan wata kawarta,tana shiga sa sallama ta ganta akan katifa zuwa tayi ta zauna itama,kallonta matar tayi tace saro daga ina,saro zaro ido tayi tace bazaki ganeba zulai amma zan miki bayani,bayani tayi mata dariya ta babbake da ita tana fadin Allah ya kara wanda baiji bari ba yaji hoho,kuma wallahi saro kin bani mamaki ina su boka,malam,yan tsubbu har kika zauna kina tsoran wannan matar,saro ce tace ba tsoranta nakeba zulai amma wallahi nayi alkawarin ko zanyi yawo ba kaya sai na rama abinda tayi min kuma ita na ta hukuncin m sai yafi wannan muni,zulai ce ta ce ahayye nanaye anayi inajin dadi yanzu naji zance kawata,amma da kin tsaya kina hura hanci bara na kawo miki ruwa da dan abin tabawa.
Cikin muryar baccu take fadin aunty mufyda kizo,ina nan fa banyi nisa ba,nurse ta fito da gudu tana fadin doctor deenah ta farka,da dan sauri suka nufo dakin idanunta a bude amma ta kasa tashi,kallon kanta tayi tace ni kuma tawa kaddarar kenan,doctor ne ya kalleta yana fadin deenah shiru tayi ko dagowa batayi ba,hajiyar ta gani a tsaye a gabanta,khairy ce ta kalleta tace hajiya kina lafiya ko,daga kai tayi ta kalleta tace inafatan kina lafiya ko,kauda kai tayi,doctorn ne ya kalleta yace ya sunanki khairy sani ta bashi amsa,shekarunki nawa sha 14 ta fada tana kallonsa,ya jikin naki da sauki,yanzu ba inda kikejin yana miki ciwo,kallinsa tayi tace kaina yana min ciwo fa sai kuma ta nuna sai tin kirjinta,doctor ne ya kallesu yace ku samo mata abinci da zata ci domin yunwa ce,daga haka ya mata allah sawwake ya fice daga dakin,yn fita hajiya ce ta kalleta tace khairy ko meyasa kika taimakeni dauke kanta khairy tyi hakan nan kawai bai kamata kina babba ba kuma ace mota bigeki da yanzu kece da wannan karayar har 2 amma yanzu tinda na taimakeki ni zan samu lada,ko ba komai ni yarinya ce ke kuma hajiya kalleki babba.
YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
25_26🌹
Office din yake tare da doctor magana yakr yana fadin kace sunanta deenah bayan kuma ni khairy ta cemin,alhaji ne yace ea khairy ai ummulkhairi kenan mu kuma da deena muka santa,doctorn ne yace yanzu ya kakeson ayi,alhajin ne yace so nake idan da dama a maidata gida acigaba da jinyarta,kallonsa doctor yayi yace a gaskia bazan iya ba abinda zan iya yimaka daya shine kawai sai dai a chanja mata asibiti wannan shine,alhajin ne yayi jim sai kuma yace shikenan kawai doctor nagode amma zuwa yaushe za a sallameta, doctorn ne yace nan da wata 1 inshaah da haka ya fice ya bar office din,tafe yake yana yiwa allah godiya tin daga waje ya hango hajiya zaune akan kujera karasawa yayi yace hajiya lafiya,rintse idanu tayi tace lafiya lao kawai inajin kaina yana min ciwo ne shisa,alhaji ne yace yarinyar nan bata farka ba,ta farka ta bashi amsa,kuma gashi ba abinci amma bara naje restaurant na siyo mata,hajiya na siyo miki ne girgiza kai tayi shikuma ya wuce,hajiya ce ta tashi ta koma dakin a zaune take har yanzu amma kuma kuka take sosai domin fuskanta dik ya baci da ruwan hawaye,zama tayi kusa da ita tana goge mata hawayen kallonta take,kallon tsanaki tana fadin meya faru da ke ko wani ne ya miki wani abu,kallonta khairy tayi tace aa hajiya ba komai fah,hajiya ce ta kalleta tace amma ke daga ina kike,kuma meyasa kika taimakeni,shiru khairy tayi da farko ganin shirun bashi da wani amfani ne yasata fara fadin.
Auwal ne tsaye yana kallon haidar yana fadin my man wadan nan sune suka sace hibbah,zaro ido haidar yayi yana fadin to kai taya akai kasani auwala bayanni ko sani banba,dariya auwal yayi yace ai kajika,ban karbi number jummai ba da wani statement na wayarta,daga kai haidar yayi yace eaa ka karba,kamanta wanene ni ko haidar to na datsi bayanan wayanta anan naji komai da suke tattaunawa sai kuma suma nasamu na datsi nasu har na kamo su,haidar ne ya tafi tare da rungumar abokin nasa,yana fadin tabbas auwal nagode sosai wallahi,kallonsu haidar yayi yaga kuwa ba laifi sun sha duka,auwal ne ya kamo hannunsa yana fadin,hajiya ce ta saka su kuma sun tabbatarmun da cewa hibba ta dauki wani abu mai muhimmanci da hajiya take hari,shine yasa jummai ta saka suka sace ta da farko a kaduna suka tsaya suka kwana,bayan sun dirka mata maganin bacci sai suka dauki hanyar kano a kano dai anan suka wullar da ita kuma sun tabbatar da cewa zasu iya kaimu wajen,cikin fushi haidar ya kwace hannunsa kansu yayi ya shako wuyan daya,yayin da auwal yana kokarin kwace wa amma sam aliyu bai bashi dama ba,sai da kyar suka bambare dayan daga hannunsa,take launin idanunsa suka juye daga fari zuwa jawur,jijiyiyin hannunsa suka tashi,auwal ne ya jashi ya zaunar da shi yana fadin haba aliyu calm down plz idan ka kashe su wazai dawo da hibba,shiru yayi sai kuma kawai ya fashe da kuka,auwal ne ya matsa yana lallashinsa dan tabbas ya cancanci hakan a wajensa.
Bude idanunta tayi ganin ta tayi a wani waje mai kyau a zuciyar ta take furta to kodai mutuwa nayi bayan nasha ruwan nan,kokatin mikewa takeyi sha'aban ne ya karaso yana kallonta,saurin mikewa tayi tana kwala kara sai dai mai ganin drip tayi kokarin fizgewa takeyi,shaaban ne yace zo na ciremiki,aa ta furta da karfi tana layi sha'aban ne ya tashi daga wajen ita kuma har lokacin tana tsaye tana zaro idanu dan iltinda take bata taba zaton zuwa irin wannan gida ba haka,fitowa sudais yayi ya kalleta tare da hade rai kamar hadari yana fadin ke sit down amma fur taki zama ke wai ba magana nake miki ba,kodan na manta ashe bakyajin English sai hausa shikenan zauna,musaf be ya jiyo hayaniyar da take wakana ya fito da saurin sa,yana fadin meya faru,shukura duba hannunta tayi ganin jini yana zuba yasata fara kuka tana fadin ni dai dan allah ku kasheni kawai nagaji da wannan rayuwar da ku lalatamin rayuwa kara kawai kun kasheni zan fi jin dadin hakan,wani wawan mari sudais ya zafga mata take ta fadi kasa,kallon kallo suka shiga tsakaninsu Mus'af ne yace ai ga irin ta nan mutum sai bakar zuciyar masifa,idan ta mutu ai ta rataya a wuyanka kuma kasan ammi,jin karar mota ne yasa su saurin dagata suka maidata kan kujerar,shaaban kam warewa yayi yana tafe yana wai waye,sudais ne ya gyara mata hannun,yana gamawa wani saurayi nagani ya shigo sanye da bakaken kaya na lawyer,kallon sudais yayi yace meye haka ina aka samo wannan cikin hade rai,sudais jiki na bari yace am dama ammi ce tazo da ita kuma ta fita tace nakula da ita har ta dawo,ka kyauta yace sai kuma kawai ya wuce yana dan sakin fuska.
Mudassir ne zaune a gaban malam yana masa bayani kallonsa yayi yace bakomai hakan ma amma kabi umarnin mahaifiyar ka saboda bakin uwa yana matukar tasiri akan yayanta,sannan tinda daga karshe kace kanason ka cigaba da zuwa daukar karatu ba komai,kazo sai mudinga yi tare da sauran dalibai,tabbas mudassir ka shiryu allah ya kara shiryaka,kuma na tabbata batan su mufida ne,sannan malam dan allah karka fadawa kowa wannan maganar,murmushi yayi na manya yace karka damu ba wanda zan fadawa kaji dan nan,d aga haka mudassir ya tashi ya tafi.
Zaune suke a bakin wani titi karkashin inuwa wajen,wani mutum suka ga yayi parking ya fito ya raba su ya wuce,kallonsa hibbah tayi tace mufida kamar nasan wannan mutumin fa,mufida yi tayi kamar batasan tana yi ba,bai jima ba ya fito kallon yaran yayi sai kuma kawai ya tsinci kansa da mika musu kudi,mufida ce ta ce aa kabar abinka yallabai,kallota yayi yace wannan ba komai bane nima akwai wanda zan bawa kuma baizo ba dan haka ku karba rabonku ne,hibbah ce ta karba tana fadin angode yayin da mufida take kallonta,yana wucewa hibba ce tace tabbas shi ne ga maganarsa nan mika mata kudin tayi mufida a tsorace tace ni bazan iya kirga wannan kudin ba gaskia,hibba ce tai dariya ta fara kirgawa dubu 20 ne cif zaro ido mufida tayi tana fadin kuma ya bamu kyauta hibba,dariya hibba tayi kawai,mufida ce tace yanzu wannan ai zasu mai daki gida ko hibba eaa ta bata amsa,shikenan hibba muje to narakaki ki hau mota ko,tashi sukayi suka fara tafiya.
Hawayen fuskanta ta share tana fadin bai kamata kuma ki.kashe kanki ba khairy tabbas rayuwarki tana cikin wahala dik da cewa gaki yarinya amma kinsa abinda ya kamata,khairy ce ta kalleta kawai ta kauda kai domin matar kwarjini take mata,suna zaune alhaji ne ya shigo hajiya ce ta tashi ta karbi ledar ya jiki yayiwa khairy ta amsa da sauki,bude abincin ne ya daki hancin khairy taje dik wata yunwa data dade a cikinta ta ta tashi,kallon abincin take fried rice ce sai naman kaza da lemo,khairy dai kallonsu take kawai,hajiya ce ta mika mata plate daya,ba musu ta karba a hannun da ba mai karaya ba,ajiyesa tayi akan gadon ta fara aikawa cikinta shi tana yi tana raba ido kai da gani kasan tabbas an dade ba a hadu ba.
Shigowa tayi ganin falon shiru sai karar ac yasata fito da wayarta tana dialling fitowa Mus'af ne yayi dai dai da cewa ammi sannu da zuwa,yawwa tace masa,kiramin sudais da sha'aban da to ya amsa ya nufi daku nan su bai dade ba suka fito tare,kallonsu tayi tana mai fadin kun kyauta,nace ku kula da ita amma duba tsabar rainin hankali da rashin sanin darajar dan adam shine yasa kuka barta kowa yaje ya dauki waya ko,dan nasan dai waya ce ta maidaku daki,to wallahi ahirr dinku mutanen banza kawai,shiru dikansu sukayi suka sunkuyar da kai dan suna matukar tsoranta,fitowar sa ce yasa ta fadin au yanzu ashe ma'id har da kai a gidan shikenan kun kyauta,kun san wacece ita baku sani ba,nima bansani ba,ko banza ai sai ku kula da ita,to ku sani ita din yarinya ce karama duba da yadda na tsince ta gefen titi tana mukusisin mutuwa amma na kawota nan shi ne har kuka kyaleta kun kyauta kunji kuma kunyi dai dai hakan ma,kokarin daukarta ta farayi ganin shatin mari ne yasa ta ajiyewa tare da juyowa,wato harda mari ko,waye ya mareta shiru sukayi,wai ba tambayar ku nake ba take sha'aban yace sudais ne,wani wawan kallo ya aika masa.
YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
27_28🍂
Saurin riketa ma'eed yayi yana fadin aa ammi ya hakuri,wani wawan kallo ta bishi dashi take ya saketa,tana karasawa kenan ta jiyo muryar shukura tana kwala kiran kuyi hakuri nadaina,saurin juyowa tayi tana kallon yarinyar,karasawa tayi tana dafata shujura kallon wajen take,idanunta ne suka sarkafe da na sudais marin dazu ta tina ta kau da kai,hajiyarce tace waya mareki a cikinsu murmushi shukura tayi tace ai ba wanda ya mareni,saurin dagowa sudais yayi yana kallonta cike da mamaki,hajiya ce tace banason karya fa ea hajiya allah ba wanda ya mareni,to wannan sawun yatsun fa, kawai dai naki tsayawa yayi min allura shine naki tsayawa bai sani ba ya mareni amma ba komai,cike da mamaki suke kallonta,ma'id murmushi yayi yace a zuciyar yarinya karama amma mai hankali,hajiya ce ta kalli sha'aban tace kawo mata abinci,tafiya yayi bai dade da dawowa ba dauke da plate a hannunsa mika mata yayi,ita kuma ta fara aikawa,hajiya ce tace ina Arfan sha'aban ne yace ammi bai dawo amma inaga yana hanya,yana rufe bakinsa suka ji shigowarsa,sanye yake da suit sai coat a sama da wando,kana ganinsa kaga ma'id,zagayowa yayi ya rungume ammi,yana kallon shukura da take ta dura abinci,ga su sha'aban a tsattsaye,zama yayi a kujerar da shukura tayi sai kuma shukura tayi saurin sauka tana sannu da zuwa,da mamaki suka bita,shaaban murmushi yayi,arfan ne yace yawwa yarinya,kallon hajiya yayi yace ammi daga ina kika samota,zan muku bayanin komai yanzu dai kowa yaje zuwa dare zamu tattauna,nasan dai ba wanda zai fita yau ko,tashi tayi ta kalli shukura tace muje na kiwanka ko,kallon hajiyar tayi ta kalli plate din tace ina zan ajiye wannan,ajiye anan ta bata amsa,sannan ta tashi ta bita,gani tayi sun shiga wani abu wato lifter,basu dade ba ta bude sai ga su a wani rantsattsen falo na gani na fada,wata yar karama upstair suka hau mai matattakala 5 bakin dakin hajiya ta bude,sai ga daki mai kyau dauke da bed kadai sai bandaki hajiya ce ta shiga ta nuna mata komai,sai kuma ta fito da riga guda daya tace idan kin gama ki saka zan dawo yanzun nan,to kawai tace mata tafice,yayin da shukura kuma take bin wajen da kallo,tana zama akan gadon tinaninta ya dawo akansu khairy da mufyda,hawayen fuskarta ta goge,aunty khairy ina cikin koshin lafiya,ina fatan kema kina ciki da haka kawai ta tashi ta shige toil.
Har ta shiga motar sai ta fito tana mai kuka da fadin mufuda indai ba dake ba bazani ba wallahi bazan koma ba,mufida ce tace kinga na fito neman Yan uwana ne amma da na tabbata zan biki,hibba ce tace kinsa inda suke yanzu ne ai baki sani kema nemansu kike ko dan allah mufida kika sani ma ko ki gansu a can din mufida,shiru tayi sai kuma ta fara nazari tabbas,taga wannan motar number jikinta ta abuja ce,amma kuma kar ta je taga bata gansu,mufida ce ta kalleta tace amma kuma kin yadda idan na nemesu ban gansu to ki sani tahowa ta zanyi,cike da hawaye ta furta na yadda walahi mufida,bazan taba iya rabuwa da ke ba,na riga da na saba da ke,mufida ce ta kalleta tace amma kuma hibba baki canja kaya ba a haka zaki tafi,rike hannunta tayi tana fadin to ni nasan ma zanje ne,idan na koma gida yanzu to wallahi sai dai wata amma kuma,katseta tayi tace kuma yau bakisha maganin ba,ki kyalesa mufida dan allah,zamu hada plan kedai kinji,to kawai ta ce mata sannan suka mufida tana ta faman tinanin rayuwar kannenta,wadda ta tabbatar da yanzu suna raye.
Haidar ne ke jan motar da wani matsiyacin gudu,sai dai cikin motar sautin karatun alkur'ani ne ke tashi,auwal ne ya kallesa yace haidar kayi hakuri ka rage gudun nan mana haba,ko kallonsa baiyi ba yaci gaba da gudu,haka yaketa faman gudu har suka zo zaria,amma bai rage gudunba sai da ya tabbatar da cewa yakusa kano sannan ya rage gudun.
Hajjah ce take ta zare ido domin ganin yamma nayi ga wannan addababben mafarkin da takeyi da su mufida,dan karamin tsaki taja tana fadin aikin banza,shigiwar mal sani ne ya sashi daga kai yana kallonta,sannu yayi mata,har zai shige kuma ta kirasa,zama yayi yana mai kallonta,kai sani wai lafiyarka kuwa,ahiru yayi wai ba kai nake tambaya ba,to hajjah ya kikeso nayi a ta dalilinmu kinsa yaran nan sunbi duniya,kowaye yanzu ni zai zarga da batansu,kinji yadda magana take tashi akan na kori yara na na cikina,haba hajjah wai meye laifinsu ne,tin tasowar su inason yara na amma saboda in miki biyayya na faranta miki ne yasa nake musu dik wani nau'in wulakanci,amma hajjah hakan ma kenan bai miki dadi ba,hajjah dan girman allah ki barni da abinda yake damuna dan allah,tashi yayi yana mai rintse idanunsa ya samu ya wuce dakin karima,yayin da hajjah ta tabe baki tana mai kiran me ake da yaya mata aikin banza kawai,(ta manta da cewa ita ma macece fa).
Fitowa yayi yana mai nuna wajen da cewa nan ne,jiki dik ciwo suke fadin ea wallahi yallabai dubawa yayi yana mai fadin to tana ina,nace tana ina,dukansu yake,auwal ne ya leka kangon wajen,fitowa yayi dauke da karamin veils yana fadin kodai wannan nata ne,kallon veil din haidar yayi yana mai fincika wallahi nata ne wannan,auwal sun batar min da hibba,sun batar da ita inalillahi wa inna ilaihi rajiun,zama yayi dirshen a wajen yana mai rusa kuka kamar an aikosa,auwal ne ya dafasa bige hannun yayi yana fadin ina ruwanka da ni wai,ka kyaleni wallahi.
Saro ce kwance yayin da gefen fuskarta ya wani kumbura,zulai dan allah taimakamin da ruwa kallonta zulai tayi tace zan taimaka miki amma kuma gaskia nima,dame kikeso na taimake ki,murmushi zulai tayi zan fada miki yanzu dai taso muje chemist tinda kin amsa da bakinki.
Alhaji ne ya tsaya yana kallonta ya rasa ta ina zai fara ga dare yanayi,hajiya to wai ya za ayi da khairy kuma,kallinsa tayi tace ni zan kwana da ita tinda a ta dalilina ta samu karaya,dafata yayi yace ko dai mubarwa nurse ita,mikewa tayi tace a a alhaji ko da na koma tabbas sai na tina da hanan kara nan din ko banza idan ina ganinta bazan tina da hanan ba wadda ta guje mu,shikenan to ni dai na tafi,sai da safe ameen tace tare da juyawa tana kallon khairy da take bacci.
Tafiya tayi tafiya a bangaren su mufyda,dai dai lokacin da zasu shiga garin abuja,wata mota ta tare gabansu,kowa na motar ba abinda yake furtawa sai inalillahi wa inna ilaihi rajiun,fitowa sukayi tare da gyara tsayuwarsu,motar suka nufo tare da umarnin kowa ya fito,fitowa suka yi,hibba da mufida sai zare ido ake, idanunsu suka dora akan hibba,dayan ne ya tabosa ya nuna masa,zaro ido yayi tare da jan hannunta,kara ta kwallah mufida ce ta riketa tana bashi hakuri,hankadeta yayi ya janye ta ya saka ta a mota, mufida ce ta mike amma kafin takai motar ta bule ta da kura amma dik da haka ta bita da gudu tana kuka,har sai dai motar ta kule,sannan ta juyo ta rasa ma me zatayi kawai zama tayi tana kuka.
Tsakar dare yayin da dik wata halitta mai rai take fatan samun hutu ta kwanta, a wannan lokacin ne na tsinci mufida a tsugunne gaban wani gida tana kallon yanayin unguwar da take shiru ba mutane,fitowar wata tsohuwa ce yasa ta firgita,ita kuwa tsohuwar ko a jikinta,kama hannun mufida tayi suka shige cikin wannan gidan tare da karowa kafff (ban samu damar shiga ba take na koma garin kano).
Hajjah ce zaune akan katifarta gefe daya kuma fitilar lagwami ce ta ke ci irin ta tsofaffi ta zabga uban tagumi,kai da ganin idanunta kasan a tsorace take,ba abinda take sai raba ido,nisawa tayi tare da sakin ni shi uhuuuummm wannan yara suna cuta ta sun hanani bacci,amma yau dik abinda zai faru sai ya faru dan sai na ci uwarsu idan suka kara zuwar min mafarki shashashun banza,anya ni fa yaran nan zato na kuwa ba mayu bane,ko dai tattara wa zanyi na koma gidan sani,idan kuma naje wannan figigiyar matar ta isheni kai ni yau na shiga 9 ba uku ba.
To hajjah ke dai kika sani
Alkalamin Auntynmu Ceh❤️💖💕
YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
29_30🍂
Koda suka je chemist,likitan ne a zaune yana duba wasu Patience zaman jira sukayi,saro wani azababben radadi takeji,duniyar tinani ta tafi lalle yarinyar nan dole na nemota amma kafin nan sai na fara gamawa da hajiya dan wallahi bata ci banza ba,zata san da ni take zancen,zulai ce ta ta bata taso muje,karasawa sukai,dr ne ya kalli ciwon yace sorry wannan sai dai ai mata dinki,zulai ce ta ce to likita ayi mata mana,dan jimm yayi saro ce tai saurin fadin indai kudi ne baka da matsala,murmushi dr yayi yace to ba matsala,take ya fara duba mata ciwon.
Tin washe garin ranar mudassir ne ya fito dauke da jaka a bayansa,a kan tabarma ya ga mutanen gidan zama shima yayi bayan ya gaishe da su,karima ce ta kallesa tace kai kuma ina zaka,dan sosa kai yayi yace umma dama zan tafi neman kudi ne,hajjah ce ta tsomo baki yauwa mudan ko kai fa kara ma ka tafi ka nemo mana mu samu mu warwasa,wani wawan kallo ya jefa mata da ba wanda ya kula sai jafar,malam sani ne ya kallesa yace to yanzu mudassir ina zakaje,baba zan bar gari ne zan je nema ne ina neman adduarku,alhassan ne ya kallesa yace to yanzu ace dik girman garin kano ace sai ka bar gari neman kudi,kallonsa kawai yayi bai tanka ba,karima ce tace to mudassir tinda haka ka zaba ka je sai ka dawo allah ya tsare,amma wallahi naga aike idan ba haka ba wallahi kasanni tsafff,kallonta yayi kawai ya kau da kai babban farincikin sa ya bar gidan nan ko zaiji sanyi,tashi yayi malam sani ne yabi bayansa,a waje suka tsaya bayan ya gama yi masa addua sannan da nasihohi,mudassir ne ya kallesa yace ba komai baba kuma kai kasan makasudin shirya wannan tafiyar,baba kai min addua insha allah nasan zan samesu dan inaji a jikina suna raye,murmushi yayi sannan sukai sallama mudassir ya tafi,malam sani kuma ya juya ya koma yana mai masa addua.
Shukura nagani zaune akan kujerar falon wata yar dattijuwar mata ce nagani ta shigo falon shukura ce ta gaisheta dattijuwar ce ta kalleta tace aa yarinya daga ina,shiru shukura tayi kawai sai kuma ta bi bayanta ganin ta shiga kitchen,juyowa tsohuwar tayi tace au biyoni kikai kenan,shukura ce ta bata amsa da cewa ea dama ai inaso naga yadda akeyin girkin nima na iya,dariya tsohuwar tayi tace to taho mu fara,tsohuwar ce ta kalleta tace yau yaushe,amsa ta bata da Asabar murmushi tsohuwar tayi tace to dik ranar asabar mutanen gidan nan sai karfe 11:00 suke tasho daga bacci,zaro ido shukura tayi sunayi suna hirarsu,dan tsohuwar nan ita ma ba dai surutu ba,a haka karfe 9 sun gama sun jera komai a dining daga nan tsohuwar tai mata sallama,shukura kuma ta koma dakin da aka sauketa kasan cewar jiya da daddare an mai dota kasa,saboda wani dalili da ban sani ba.
Mufida na hango kofar gidan nan da tsohuwar nan a tsaye kallon ta tsohuwar ta karayi tace to dama munyi da ke ko,dan haka kiyi umarnin da dik aka baki a cikin gidan nan matukar kinason ki zauna Lafiya,dalilin da yasaka ma nace zan kaiki saboda da dama can ta kwatanta min irin yarinyar da take so akai mata dan haka mufida ki kula,ita dai mufida kallonta tayi kawai a zuciyar ta tana furta,inalillahi wa inna ilaihi rajiun tana mai furta addua a bakinta,dai dai bakin titi suka tsaya basu dade ba sai ga mai taxi shiga sukayi tsohuwa ta fada musu unguwar da za a kaisu unguwar sun dan yi tafiya mai nisa sannan suka tsaya a kofar gidan wani katon gida mai matukar kyau, kwankwasawa tsohuwar take,wani dan tsamurmurin tsoho ne ya leko tare da fadin wace,dariya yayi yana fadin aa sannunki yau kece tafe,yake hakoranta itama tayi tana mai fadin eaa ni ce wallhi gani sai yau,bude mata yayi ta shiga ita dai mufida sai zare idanu take,falo suka tsaya zama sukayi,suna zaune yayin da mufida sai kalle kalle takeyi domin haka kawai takeji gidan bai mata ba,da saurinsa ya fito daga dakin yana kallon agogo da ke daure a hannunsa fuskar nan tam ba alamun fara'a a tattare da shi,gaba daya mufida ido ta zuba masa tabbas taso ta tagane sa amma ta rasa a ina ta sanshi,shigewa yazo yi sai kuma ya dago da kansa tare da kallonsu,tsohuwarce ta baje hakora tana fadin aa yallabai haidar kallonta yayi kawai yace ina kwana bai jira amsawarta ba ya haye upstairs da take kallon wajen,bai dade da hawa ba sai ga hamshakiya wato hajiya jummai sanye da wani tsadadden lace black sai ratsin golden a jiki ta fito tana taunar chewing,mufida ce ta mai da hankalinta kan matar domin ita mufida gani tayi matar ko kyau bata da shi,fuska dik bleaching,harta karaso sannan ta zauna tare da duban tsohuwar tana me fadin yauwa iyah wannan ce yarinyar kenan,eaa iyar ta fada ita ce,kallonta jummai tayi tsaff tin daga sama har kasa sannan ta furta tayi ya sunanki,mufida ta fada a hankali murmushi jummai tayi tare da bude jakar data shigo da ita ta zaro kudi ta mikawa iyah amma tayi tana yake hakoran da dik sun dafe wasu ma babu,kirgawa ta farayi taga dubu 20 ciff,jummai ce ta mike hade da fadin ina zuwa,tana fita iya ta juyo to mufida ga dubu ashirin yanzu nan zan baki dubu 5 gaskia sauran kuma zan ajiye miki suma dubu biyar din idan kinga wani abu kya siya tinda ba rashin ci ba na sha,mufida karba tayi tana ayyana wannan hali na tsohuwa,bayan shigowar jummai ne iya tai mata sallama sannan ta wuce,mufida tana zaune inda take bayan fitarta ne jummai ta kalleta tare da furta ke kalleni nan ki sani dik wani aikin gidan nan kece na iya ciki ba ruwanki da waje kece wanke wanke,shara goge² ke harda ma girki nasan ai kin iya ko daga kai tayi alamar ea,yayi kyau yanzu tashi ki wuce wannan dakin,tashi tayi tare da hucewa dakin data nuna mata,mufida shiga tayi tare da zube kayanta kallon dakin tayi ba laifi dik tiles ne sai karamar katifa bayan haka kuma ba komai aciki sai wata kofa,mufida ce ta furta hakan inaga ban daki ne nan,budewa tayi nan kuwa taga bandakin ne,sai da ta dauro alwala ta dawo ta tada sallah,sai da ta idar sannan ta rafka uban tagumi tana zuba tinani,kar dai ace nan gidan su hibbah ne,tabbas waccen yayan nata yana kama da hibba kuma gashi sunansa haidar yadda ta fada min,idan kuwa nan ne gidan su hibba ya zama dole na taimakesu daga sharrin wannan makirar matar uban nasu,sai ga hawaye allah sarki hibba ko ina kike yanzu,tana cikin wannan yanayin ne ta jiyo kiran jummai tashi tayi da saurinta ta fita,a zaune ta ganta kallonta tayi ta hade rai tare da kamo kunnenta ke dan ubanki daga yanzu idan na kuma kiranki kikai banza da ni wallahi sai na ci uwarki,shegiya mara mutuncin wato ga 'yar iska kin ajiye ko dole ki barni ina ihuu,tashi ki wuce kije ki min wanke wanke shashashar banza,wannan hanyar zaki bi kuma soson da sauran kayan amfanin suna wajen da kin duba drawer kusa da wajen,to mufida ta ce tare da tashi tabi hanyar da aka nuna mata.
Khairy ce zaune ta lumshe idanu kasancewar ba kowa a dakin shigowar hajiya amma tai luff kamar tana bacci domin gaba daya batasan magana tinani take ta yaya zataga aunty mufy da kanwarta shukura bayan ita ga ta a karye take,hawaye ne ya gangaro mata,dai dai nan hajiya ta dafata tana fadin haba Khairy kiyi hakuri mana insha allah zaki ga 'YAN uwanki kuma zaku koma gida tare kinji yata murmushi tayi tace sannu da zuwa hajiya,yawwa kawai ta amsa tare da mika mata plate din hadaddiyar jellop din talia karba tayi tana ci,tana kallon hajiya da take dawainiya da ita a ranta tana godewa allah daya hadata da wannan mata,sallama da akayi ce yasa khairy saurin dagowa,sai kuma ta mai da kanta kasa saurayin daya bigeta ne ya shigo yana kallonta zama yayi tare da gaishe da hajiya,khairy ya kalla yana mata ya jiki da sauki ta bashi amsa,cikin tsokana yake fadin ai kam da sauji tinda gashi har abinci akeci,khairy dai shiru tayi,bai dade ba ya tashi tare da ajiyewa khairy tsaraba mai yawa,sannan yayi sallama ya wuce.
YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
31_32♨️
Gaba daya suna kan dining sudais ma'ed Sha'aban arfan sai hajiya da take tsakiyarsu,kallonsu tayi tsaff tace ina kuma Zunnur da baba karami sha'aban ne yace mom zunnur yana wajen momyn rayyan shi kuma baba karami bansaniba,arfan ne yace yana daki dan a can na barosa kansa yana ciwo,ba yanzu zaiyi break,ok ta furta tare da kallon sudais kiramin shukura,tashi yayi a zuciyar sa yana fadin wannan shegiyar shukurar mai idon mage ta dameni wallahi,dakin ya shiga a zaune ya ganta tana kallon tom and jerry sai dariya take,kallonta ya tsaya yi sai kuma ya hade rai ya daka mata tsawa keh da sauri ta dago tana kallonsa kizo inji mom tashi tayi itama tare da kallonsa yana wucewa a ranta tana fadin kai wannan anyi miskili,a zaune ta gansu cike da ladabi ta tsugunna har kasa ta gaishe su mom ce ta kalleta tana aa shukura manya yaushe kika tashi,tin 8 mana, murmushi hajiya tayi tace gaskia tohm yanzu muyi break,Sai da kowa yayi wanka sannan dik suka fito banda hajiya da shukura,sudais ne ya kalli maed yace yanzu fa dole sai munje family meeting kaki zuwa ace ka raina mutane,arfan kam tabe baki yayi batare da yace kala ba,a lokacin wani hamshakin saurayi ya fito sanye yake da bakin yadi cikin dinkin jamfa yadin yayi matukar amsar jikinsa,kallonsu yayi take kowa yayi shiru yana kallonsa,wucewa yayi sai kuma ya juyo yana dan yake wa kuke jira anan arfan ne yace mom ce bata fito ba,ok ya furta ya wuce kan kujera bai dade da zama ba hajiya ta fito hannunta rike da na shukura ba laifi tayi kyau sanye take da doguwar riga Maroon color tayi kyau,da fara'a ya kalli hajiya yana gaisheta amsawa tayi tare da yi masa ya jikin amsawa yayi da sauki mom,kallonsu tayi tace ai sai ku huce mutafi ko zunnur dama yana can,to suka amsa tare da barin falon sai da kowa ya fice sannan baba karami ya biyo su a baya,shujura dai kallon ikon allah take domin gani tayi anshiga wani part daban take taga wani tangamemen gida kamar an dasa sa,wata kofa suka shiga dai dai nan suka sauka a katon falo mai matukar girma amma dik girman sa haka aka cika shi da kujeru masu kyau,mutanen da suke dakin zasuyi 40 manya da yara,dattijai da samari,yammata,sai kuma iyayen yaran,hajiya da fara'a ta karasa ta zauna tare da fadin mu ake jira kenan,wata mata ce tai murmushi aa ai baffan ma bai fito,hajiya ce tace auhh gaisawa suka fara yi,sannan falon kuma kowa ya gaisa da dan uwansa.
Baffa ne ya fito da katuwar malun malun ita dai shukura yar kauye sakkk,zama yayi a kujerar da aka tana dar masa sannan kowa yaje ya gaisgeshi,amsawa yayi hade da gyara zama ya fara jawabi dalilin wannan zama namu na daya munyi nasarar samun yarinyar khadija wadda jummai ta so a kasheta yanzu haka tana cikin gidan nan kowa kallonsa yake yana murmushi tare da son barka,jawabi yayi sosai sannan ya kalli shukura yace yarinya ya sunanki shukura ta bashi amsa,ke yar ina ce shiru tayi kawai tana kallonsa sai kuma ya katse shirun da cewa shijenan hakan ma badamuwa amma yarinyar nan taso taimin kama da sai kuma yayi shiru tare da mikewa,fita yayi anan kowa suka kama hirarsu,hibba na gani ta shigo falon kalon mutanen falon tayi sai kuma ta nufi wajen maman rayyan tana mai fashewa da kuka,dafata tayi tana fadin to kiyi shiru mana hibba dik ba gamu ba,kallonsu tayi tace dama ashe dik kuna nan amma taso ta kasheni kenan ma bakwaso na,kowa na dakin dariya yayi banda baba karami daya ja uban tsaki,w asu samari ne su biyu naga sun kallesa sun sa dariya,hajiya ce ta kama hannun shukura ta kalli mom rayyan tace muhe wajen baffan ko to ta amsa tare da mikewa ta kama hannun hibba,a zaune suka tarad dashi yana jan carbi zama sukayi suna masa sannu da murmushi ya kallesu yace yawwa Madina ya akai,hajiya ce ta kallesa dama a game da maganar shukura ne baffa,dan nisawa yayi yace ai madina ba wani abu da na kowa ne baki da matsala ta zauna anan din kingama gata sa'ar hibba sai su zauna tare,hibba ko bazaki zauna ba,da dariya ta kallesa tace aa baffa zan zauna mana amma a kiramin ya haidar plz,shikenan zuwa anjima zan kirasa sai muyi masa surprise ko,tashi sukayi hajiya cije da jin dadi da jin tabbacin baffa ya amsa ta zauna sai kuma alhaji idan ya dawo sai muyi maganar da haka suka tashi suka fito a lokacin dakin ya karade da surutu da ihu wasu na zaune akan kujera,wasu kuma katon dining din daya ke dakin,wasu yammata na hango su hudu zaune ba laifi kyawawane daya ce ta kwala kira shukura kallonta shukura tayi sai kuma takalli hajiya,murmushi tayi mata suka karasa wajen,kinga shukura wannan din yayyenki ne kinji wannan sunanta Anisa,Suhaima,Baby,sai kuma Arifah,murmushi shukura tayi tare da gaishe su,cike da kulawa suka amsa suna dariya zauna mana shukura,zama tayi tana kalkansu tsaff take ganinsu kamar yayyenta,arifah ce ta mike kinga bari na kawo miki abinci ko wucewa tayi batare da taji me zata ce ba,tana wucewa hibba tana tahowa da plate 2 a hannunta zama tayi tare da cewa aunty anisa kinga na zubowa shukura nata a haka dai har yamma tayi kowa ya watse cike da kaunar juna,shukura mamaki take na kulawar da suke bata dik da ita din ba yar cikin gidan bace.
BAYAN SATI BIYU
Saro ce kwance ba laifi suna zuwa asibitin ciwon nata da sauki,k amar kullun yauma suna zaune akan tabarma saro ta kalleta tace zulai akwai inda nakeso muje yau idan zakije toh,kallonta zulai tayi tace ina ne kuma haka murmushi saro tayi tare da kallon zulai kinsan bazan taba mantawa da abinda zeenatu tayi min ba,dan haka na tama a yanzu haka zanje wajen malam ne in fara gani koda sa'a,zulai tana jin haka ta mike nima kuwa har kyamin aikina dama ance kyan alkawari ai cikawa,mikewa sukai suja fito tare da jan gidan da saka kwado,tafiya suke sai da suka fito bakin titi sannan suka tsayar da mai napep suka shiga.
Haidar ne ya fito daga dakinsa kallon inda mufida take yayi sai kuma yace keh wuce kije ki gyaramin bedroom di na,kallonsa tayi domin dik lokacin data gansa to tamkar taga hibba da murmushi tace to shikuma ya wuce sakamakon kiran da auwal yayi masa,cigaba tayi da goge gogen nata shigowar hajiya jummai ce yasata saurin durkusawa tare da fadin ina kwana,a yakune ta amsa kamar an mata dole tare da kallonta ke mai haidar yace miki,kallonta tayi ido cikin ido tace haka yace na gyara masa dakinsa,wani murmushi ne ya subucewa jummai jakar hannunta ta bude tare da dakko wani kunshin magani karbi nan ki tabbatar kin saka shi a karkashin gadonsa tare da wannan layar kinajina ko,mufida zaro ido tayi tare da fadin inajinki aunty kuma wallahi kika sake naji a bakin wani sai na kasheki kowa ya huta,kuma kinsan na kasheki na kashe banza ko,da sauri ta daga kai,ki tabbatar kinyi abinda nace ni yanzu zan fita sai na dawo wucewa tayi tabar mufida a tsaye tana zullumi tafi minti 10 a tsaye tana tinani can kuma kamar wadda aka mintsina ta mike maimakon tayi hanyar dakin haidar sai tayi hanyar dakin jummai,tana tafe tana waiwaye dakin ta shiga tare da kallon gadon,hangota nayi ta daga katifa ta saka wannan maganin da layar tare da turasu can ciki,fitowa tayi tana murmushi tare da fadin an gaya miki zanci amanar hibba ne ai sai na taimaketa wallahi,fitowa tayi har zata wuce hankalinta yakai wani daki,kawai gani tayi tanason shiga dakin,budewa tayi tare da shiga komai na dakin neat sai ka rantse da mutum a ciki,take kwatancen da hibba tayi mata ya dawo mata tabbas wannan dakin hibba ne,ta dade a dakin sai kuma ta fito tare da komawa dakin haidar ta fara shara,tana kallon hotunan hibba,kallon wani hoto tayi sai kuma ta leka bayan hoton murmushi be ya subuce mata tare da furta hibba badai wayo ba,gyara tayi tsaf sannan ta fito ta re da komawa dakinta.dakinta,sallah la'asar ta gabatar tare da kwararo addua ga kannenta kamar yadda ta saba kullun.
Khairy ce zaune a cikin mota dik da a takure take amma bata nuna hakan ba,kallon hanya kawai take tana tinanin rayuwa,dafata akayi da sauri ta juyo.YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
33&34🌫
Dai dai lokacin da aka bude gate din gidan alhaji auwal khairy sakin baki tayi tana kallon aljannar duniya,ana parking dr daya rakosu ne ya fara kokarin fito da khairy,anan ta kara karewa gidan kallo tabbas wannan gidan allah ya zuba masa kyau ta ko ina ya isa a saka shi layin masu kyau,allah sarki aunty mufy naso ace shukura ce ko aunty mufy suka samu wannan gidan amma ina allah bai amsa ba kowa yana da kaddararsa ina fatan a dik inda kuke kuna cikin farinciki,ina fatan watarana zamu hadu da ku,domin tabbas nasan watarana zamu koma gidan mu allah ka shiga lamarinsu,tabata da khadija tayi yasata wurrr ta juyo tare da dan kakaro murmushi,shiga sukayi a falo ya ajiye ta bayan ya turota a kujera kallonta yayi yace shikenan kullun zan dinga zuwa dan ganin lafiyar jikin nata,alhaji awwal ne yace ba komai ai mungode sosai dr allah ya saka da haka suka fita suka bar khadija da khairy zaune suna hura jefi jefi.
Auwal ne ya kalli haidar yace yau kuma baffa ne yake nemanka lafiya kuwa,haidar ne yace nima bansani ba wallahi,amma dai nasan dai wannan babban al amari ne ttinda har baffa yasa waya ya kirani,kodai yasan da batan hibbah ne,girgiza kai auwal yayi yace anya kuwa yasan da hakan amma yanzu dai muje,ta da motar yayi tare da yi mata key suka bar wajen,daidai kofar gidan baffan suka fara horn budewa gate man din yayi yana daga masa hannu,wucewa sukayi tare da yin parking fitowa sukayi suka dau hanyar shiga gidan,haidar mamaki yake yana kallon yanayin gidan a zuciyar sa yana fadin to ina mutanen gidan suke haka naji gidan shiru,kai tsaye turakar baffa suka shiga bakinsu dauke da sallama,jin shiru ne yasa su suka zauna basu dade da zama ba baffa ya fito cike da farinciki ya kallesu yana musu sannu da zuwa,zama yayi yace aa haidar yaushe akazo kenan,dan sunkuyawa yayi yace ai dama yanzu muka shigo baffa,shikenan ai bari nasa a kawo muku wani abun,tashi yayi ya fita.
Hibbah ce da shukura sai sauran yammatan da suke zaune a falon hajiya suna hira fitowar baba karami ne yasasu yin shiru suna kallonsa dan karamin tsaki yaja kallon deejah yayi yace ke jeki ki dauko min jaka ta a falo na ki tabbatar kuma kin cire takalmi dan banason kazanta,hibba ce ta kalli shukura sai dariya,cike da bacin rai ya kallesu yace ku kuma uban wa kuke wa dariya,hibba ce ta kifta mata ido kansu yayo da gudu suka fita suna dariya,harda ihu anisa ce ta sukuyar da kai tana dariya,part din baffa suka shiga jin shiru yasa hibba taja hannunta tare da fadin zo muje wajen baffa musha hira kawai,shukura ce ta ce dama kuma yace zai bamu labarin dan zaki ko ai da sauri suka nufi falon nasa,sallama suka fara shiru ba a amsa ba,haidar ne yace amma dai nifa jin murya nake kamar ta hibbah,auwal ne yace kai anya kuwa hibba ce shigowar baffa ce yasa su shiru,shukura ce ta leko ta tsagar kyaure tana kiran hibba baki yayi mu koma,hibba ce tace suwaye suka zo,shukura ce tace ke kizo ki gani mana to yanzu ya zamuyi ne kuma gashi baba karami fa zai iya shigowa,kafin su rufe baki sukaji motsi,ai da gudu suka fada dakin baffan suna kokarin huce falon karaff idanun hibba suka sauka akan na haidar tarr.
Mudassir ne zaune a kan tabarma gabansa dauke da litattafai fitowar wani dattijo ne yasa shi mikewa yana mikewa sai wasu sauran samari suka karaso tare da zama bayan malamin ya zauna,abin mamaki mudassir naga yana daukar darasi a kalla dai xasuyi awa 1 sai kuma aka fara kokarin kiraye kirayen sallar magariba sannan suka watse,wata siririyar hanya na hango mudassir yana tafe yana jan casbi,a dai dai wani kofar gida ya tsaya tare da ciro mukulli daga cikin aljihunsa ya bude shagon,shiga yayi bai dade ba na hangesa ya fito tare da nufar masallaci.
A wani zabure ta mike tana furta inalillahi wa inna ilaihi rajiun shisa aka hana mu baccin yamma wannan wane irin bala'i ne allah na rokeka allah yasa mudassir ba mutuwa yayi ba,allah kaga bamu da niyyar kashesa allah yasa bai mutu ba,ummieh na dube dube ta fara ganin wuta tare a dakin ya tabbatar mata da cewa tabbas magariba tayi tashi tayi ta shige toilet tare da dauro alwala sallar ta gabatar tare da kwararo addua,sai da ta gama tsaf tai azkar din ta da kullun takeyi sanann ta fito falon ganin ba kowa ne yasata zama akan kujerar ta fara kallon talabijin din da takeyi dikda a haka zakace kallo takeyi amma kuma hankalinta baya wajen tana duniyar tinani shigowar haidar da fara'a ya kalleta yace mufida amma shiru mamaki yake kawai sai ya huce zuwa dakinsa yana murmushi,gaba daya komai na gidan yau dadinsa yakeji ko ba komai yaga 'yar uwarsa yau wadda jummai ta batar da ita,d ai dai lokacin jummai ta shigo rai a bace haidar ya kalleta sannan ya wuce murmushi tayi tace zanyi maganinka mara mutunci kawai,mufida ce ta furta sannu da zuwa aunty yawwa ta bata amsa,sannan ta wuce sai kuma ta dawo kinyi abinda nasaka ki,kallon ta mufida tayi tace aunty wani abun hade rai jummai tayi ke sai kuma ta furta eaa aunty na saka kamar yadda kika umarce ni wucewa tayi tana murmushi samun nasara.
Magariba liss a wani daji da bashi da wani kyan gani saro da zulai suka tsaya,kallon dajin saro tayi sai kuma taci gaba da tafiya wani karamin dakin kasa ne shi kadai kwall a cikin dajin direct shiga tayi zulai ta bita,gaba daya dakin bashi da wani fasali domin dik wani nau'in kayan bokanci akwai a dakin dariyar da akayi ce ta saka ni kula da wani mutum zaune gefe daya gaba daya jikinshi ya shafe da farar kasa yayi furtutu ku zauna ya ambata cikin wata murya mara dadin saurara,sai kuma ya mike tare da dauko wata tukunyar kasa da ruwa a ciki ajiyewa yayi sai ya fara wasu surutai take wannan tukunyar ta tarwatse dakin ya fara girgiza lokaci daya bokan ya hada gumi idanunsa sunyi jawur kamar garwashi,kallon saro yayi tare da furta tashi ki fita bazan iya wannan aikin ba,nace ki tashi saro ko na mai daki kadagaruwa,cikin rawar kafa suka mike suna tsuma da gudu suka fito daga dakin fitowar su yayi dai dai da kama da wuta da dakin yayi,ai da gudu suka kwasa,a bakin titi na tsinto su a zaune yayin da saro ta zabga tagumi tana tinanin mafita akan wannan lamarin daya faru zulai ce ta kalleta tare da nisawa tace to wai zeenatu wane irin boka takebi ne har wannan bokan ya kasa cin nasara a kanta daga karshe ta kone sa,murmushi saro tayi ban karaya ba zulai daga nan har birnin sin idan zeenatu zata wulakantu to wallahi sai naje dan haka idan kema kinaso buqatar ki ta biya to ki biyo ni idan kuma bakya so zauna anan.
Hajjah ce ta fito da buta a hannu tare da tsugguna wa zata fara alwala shigowar jafar ne da fasasshen goshi ne yasa ta sakin butar kai jafaru meye me ya faru kuka yaje wiwi hajjah dukana sukayi,uban waye suka dake ka hajjah wasu ne a waje yanzu haka sun ce sai sun tafi dani ofishin yan sanda me? Jafaru wallahi ba wanda ya isa ya tafi dakai idan kuma akwai to wallahi ban gansa ba,karima ce ta fito jafar me naji kana cewa to wallahi naga dan iskan daya isa yazo ya tafi da kai haba dai dai lokacin suka jiyo sallama daga waje,su dika biyun sukayi waje banda jafar dayake ta zare ido kamar mujiya,dandazon mutane ne sun cika kofar gidan mal sani tabb yara da manya,suna kallon yadfa motar yan sanda ta faka wani police ne yace ku fito mana da yaron daya shigo hajjah ce tai karaf kamar ya na fito maka da shi to wallahi ba inda zaizo,tsaki yaja tare da cewa wallahi idan baki matsa ba sai na tureki na shiga naga abinda zaki iya,iyeeeh hajjah ta fada to na matse hanya ya zakayi da ni,karima ce ta kallesa wai yallabai me yayi akeso a tafi da shi bansani ba idan munje can kwaji abinda yayi dan haka wuce kije ki fito min da shi ganin sunkiya bada hanya ne yasa wata budurwa bangajesu da shiga ta kamo hannunsa karima ce ke kokarin kwatarsa amma ta kasa a haka har ta kawosa wajen dan sandan sannan kuma ta juya tare da hawa mota suka tafi karima binsu tayi tana kiransu amma ina,mutanen wajen ne suka fara hayaniya.YA"YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
35_36🌌
Ai wallahi allah ya kara sun fara gani kenan waya gaya musu zasu iya korr marayu ai hakan ma bazai taba yiwuwa ba wallahi sun kore su daga garin sai kazo kana tambaya su wani ce maka ai sunyi tafiya allah ya kara,allah sarki su mufida allah yaji kanki sadiya,wallahi dik gidan nan sadiya tafi kowa mutunci allah yasada ki da rahamar sa,dik wannan maganar akan kunnen mal sani wucewa yayi gidan ba wanda ya kula daga nan mutane suka fara watsewa,a zaune ya tarar da hajjah sai karima da take ta safa da marwa,kallonsa tayi tace wallahi mal bazai yuwu ba ni za a rainawa hankali to wallahi bazaiyuwa tin wuri ka tashi mutafi ofoshin yan sanda idan ba haka ba,yana jinta amma yayi iskar karen mahaukaciya da ita ya wuce wata uwar ashar ta saki tana girgize girgize,hajjah ce ta kallesa wai sani ni bangane ba kana nufin wai bazaka je ofishin ba,kallonta yayi yace eaana to hajjah ni nace yaje ya dakko maganar ai bani na saka shi ba ko,ahirr dinka sani wallahi ko ka wuce mutafi ko kuma yanzu na maka baki,murmushi yayi yace dama nasan hajja haka zako ce gasu nan wadamda kika nunawa so ga inda suka kare wanda kikayi silar korarsu kuma wayasan a halon da suke,hajja ce ta rike haba iyee sani kai komai zaka fada ka fada wuce mutafi,ko yanzu ranka yayi mugun baci,bai tanka ba ya fito binsa sukayi da gudu suka fito tare da nufar titi.
Suna isa suka tsaya ganin yadda akasa jafar a bayan kanta,wata uwar ashar karima ta saki malam sani ne ya daga mata hannu kinga karima banason shashancin banza da na wofi akan me zaki dinga yi musu ashar a office wa billahillazi suka kulleki ke da su,diff tai shiru tana sakin ajiyar zuciya,matsawa yayi kusa da wadanda suke yin duty ya fara magana da su bai dade ba ya dawo ya kallesu to sai mu tafi bazamu samu damar ganinsa ba sai gobe idan dpo yazo,karima ce ta saki kuka tana kwallara kara wallahi bazaiyuwa ba hajjah ce ta kallesa sororo wai sani kana nufin tsabar rashin mutunci jafarun zasu rufe sai gobe,kallonta yayi yace hajjah ba rashin mutunci bane shi ya jawa kansa dik abinda ma suka masa dan haka ni bazan iya jiraba sai kun taho fitowa yayi tare da shan wani lungu ya bace musu,yana tafe yana tinani kamar wani mara kan gado.
Khairy ce zaune ta lunshe idanu akan kujera gaba daya tinani take a ranta allah sarki aunty mufy da shukura allah ya bayyana min ku allah ya bani ikon ganinku,khadija ce ta shigo zama tayi dik bata sani ba dafata tayi saurin bude ido tayi ta kalleta tana murmushi Alh auwal ne ya fito sanye da shadda sai kuma wata jaka a hannunsa,kallon khadija yayi yace ni to zamu tafi sai nan da sati daya insha allah,murmushi tayi kawai to badole ba nayi nayi kizo mutafi kinki ai ke kin samu yarinya ko,ita dai batai magana ba tasowa tayi kawai suka fice,khairy a fili ta furta allah ya baki kema aunty khadija allah ya baki gudan jininki,allah ya biyaku da gidan aljannah,kallon dakin ta farayi komai na dakin burgeta yake kallon kanta tayi sai kuma ta share hawaye,jin motsi ne yasa ta saurin gogewa,khadija ce ta shigo tare da dora khairy a kujera ta turata dakin da yake kasa anan khairy ta kara zama 'yar kauye,domin komai na dakin burgeta yake,katon gado ne daya a dakin sai bandaki,gyarata khadija tayi tare da dorata akan gadon,zaki ci abinci girgiza kai tayi alamun aa shikenan ina zuwa bata dade ba ta dawo tare da kwanciya itama,khairy idan zaki shiga bandaki ki min magana kinji dama ai naga kinyi sallah ko ea ta bata amsa kashe fitilar dakin tayi sai kuma da safe.
Hibbah ce ta fito da sassafe a hankali ta fice daga part din,part din su sha'aban ta shigo ba kowa a falo dakin shukura ta shiga amma wayam ba kowa a ranta ta furta yau kuma a sama ta kwana kenan a hankali ta haye lifter ta haye sama,kofar dakin shukura ta tsaya ganin ba kowa ne yasata shigewa a zaune ta tarar da shukura tana ganinta tace dama yanzu nakeso naje ashe ma kinzo,ea mana lallabowa nayi nasan dai yanzu ai kin tashi,shukura kinsan me dan kiji Egypt zamu tafi kallonta tayi tace egypt kuma hibbah ea mana ni da maman Sudais zamuje shukura ce takalleta tace dan allah,kwana nawa zakuyi nima bansani ba amma dai nasan bazai fi sati 1 ba yauma zamuje ai mun passport allah da haka suka chanja akalar hirar da wata,daga kaeshe kuma suka fara kallo,har wajen 11 kowa yana dining amma banda shukura,mom ce ta mike tare da hayewa sama sai dai mai tana shiga ta tarar da hibba da shukura suna ta wasa tsayawa tayi tana kallonsu,sai kuma sukai saurin mikewa,cike da mamaki mom tace hibba yaushe kika shigo nasan dai ba anan ki kwana ba ko,ea mom da suba nazo wajen shukura sai ku fito muyi breakfast ai allah yasa basu nemeki ba,ai nan ma gidanmu ne,mom ce ta murmushi ke dai hibba ba a kadake a zance ko,fitowa sukayi sai da suka gaishe da kowa a falon sannan suka zauna suka fara breakfast,shigowar baby ce yasata sakin gwauron numfashi wallahi baki da mutunci hibba Mami tana can tana nemanki amma kina nan ko to kin kyauta sai kizo,kallon da baba karami yayi mata ne yasata saurin juyawa har tana tuntube.
Mom ce ta kallesa wallahi baba Karami banason iskanci taya zaka koreta,to dan allah mom saurara min kaci abincinka,kara kallon su hibbah yayi sai kuma ya tina da abinda sukayi masa jiya kara kuluwa yayi domin tabbas sai sunji a jikinsu,sai da suka gama mom ta kallesu hibba kuje ku shirya maza zamu fita cike da murna dan ita tasan inda za a shukura ce ta tsaya kallon ta,mom ce tace ke shukura tashi mana har dake fa nake ko dole ta mike ta fice itama.
Abincin gabansa ta kalla tare da dauke kai ta fice,yayin dashi kuma sai danna waya yake dai dai lokacin da zata shigo ta hangosa a dining yana shirin gara cin abincin da sauri ta karasa tare da kwace cokalin ta dauke faratin cikin hade fuska ya kalleta wai mufida wannan wane kalan rashin mutunci ne ko nayi miki kama da sa'an ki dubeki fa ke kin isa inacikin abinci har ki kwace daga hannunsa,saurin yin alama ta masa yayi shiru tana kallon hanya ganin haka ne yasa ya tsaya yana kallonta shima kaga haidar wannan abincin an riga da an badesa da magani a gaban idona hajiya jummai ta zuba wani magani a cikin abincin,sai naga tayi murmushi tare da fadin da kyau haidar yau kashinka ya bushe wallahi haka tace tsayawa yayi yana mamakin meyasa take son kashesa,daga baya kuma sai ya dan Murmusa,shafa kansa yayi tare da fadin nagode mufida mika masa abincin tayi tace kasan yadda zakayi dashi sabods kar ta gane baka ci ba,akwai abubuwan mamaki a gidan nan fa dole sai ka kula tana kaiwa nan ta fice daga wajen tare da shigewa dakinta taja farantin gabanta ta fara cin abincin ta tana mamakin wannan matar.
Ke zulai wallahi bazan hakura taya ma lalle kalli fa wani katon shatin yankan wuka ita ce fa sanadi kawai saboda haka dai dai lokacin suka shiga wani lungu da ba kowa sai mutane jefi jefi dai dai wani gida suka tsaya sallamar mai nafef sukai tare da shiga cikin gidan wata shirgegiyar mata na gani tayi gwajab a zaune tana da hauka ita kadai wato surutai,zama sukai yawwa sannu da zuwa tin kafin kuzo dama an sanar da ni cewa zakuzo,nasan me yake tafe da ke akan zeenatu,zan miki maganinta amma zaki biya naira dubu 500 sai ki kawo marayan jaki,da kwakwalwar kifi,hhhhh to yanzu inaso nasiya a wajen ki nawa zan biya,zaki biya nai dubu 700 hhh shikenan zan biya,ke kuma zulai kije buqatarki zata biya amma kuma zaki biya dubu 300 nasan buqatarki kawai ku biya kuga aiki hhhh a nan take suka ajiye mata dubu 500 tare da fada mata cewa zasu dawo gobe,fitowa sukayi zulai sai murna take tana fadin wai ke saro a ina kika nemo wannan matar mai aiki da cikawa gaskia ne shisa fa nake mugun sonki domin gaskia akwai ki da basira indai wajen hada makirci ne,dariya kawai tayi tace lalle kam kina wasa dani zulai yanzu dai ki samu a samu wanda zamu mai da kudinmu.
"YA"'YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
37_38🏖️
Again mal sani na hango a office din dpo gefe karima ce da hajjah sai jafar dayake tsaye,dpo ne ya fara magana akan me zai je ya tabawa mutane kaya har cikin gidan su,to wannan wace irin tarbiyyce,hajja ce tai caf ta karbe haba yallabai ayi hakuri kasan yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi halinsu ba amma dan allah kayi hakuri insha allah hakan bazata sake faruwa ba,katseta yayi yace kinga kaka ni ba abinda nace fa kenan saurin taryar sa mal sani yayi yace dan allah kayi hakuri zamu biya kayan,dpo ne yace yanzu naji magana,segeant Bukar wani dan siriri ne ya shigo kallon dpo yayi tare da sara masa shigo min da ayuba,shigowa sukayi tare suna karima ce ta bashi waje ya zauna magana aka fara da kyar aka samu sulhu akai belin jafar suka taho gida.
Lafiya ummulkhairikhairy me ya faru khadija take tambayar khairy cikin sunkuyar da kai tace ba komai aunty kawai so nake na warke naje na nemo aunty mufida da shukura dafata tayi tare da fadin haba Khairy kiyi hakuri mana dik inda suke nasan suna cikin kwanciyar hankali ba'a rasa na allah ai khairy ki cire damuwar nan kinji karki jawa kanki wani ciwon,murmushi tayi tace shikenan aunty,yauwa yar albarka yanzu fadamin me kikeso ki zama idan kin girma kallonta tayi tace aunty so nake na zama 'yar jarida abinda nakeson zama kenan wallahi,karki damu khairy zaki cika burinki indai kina tare da mu kinji,murmushi tayi kawai.
Auwal abinda nake fada maka kenan,kenan kuma ita mufida ce ta cece rayuwarka,e aa ita dai yar aikin jummai itace fa,auwal ne ya furta cewa ya kamata muje mu nemi yarinyar nan dan nasan tabbas ta sanka,tayaya zakace ta sanni kawai dai inaga bazata iya kaga plz haidar ko ka yarda jo karka yadda mufida ta sanka tayaya zata ceci rayuwarka bayan kashedin da jummai tai maka harda cewa kasan yadda zakai ka nuna kaci abincin data zuba maka tin wuri haidar ka farka wallahi ta sanka shiru yayi kiran wayar ne ya katsesa,shikenan aunty gani nan zuwa yanzun nan ok shikenan muhadu a can din ba matsala,kallon auwal yayi yace zan wani shago idan zakaje to muje ko,shikenan muje.
Hajjah ce tsaye kan jafar kenan kana ganin kayi daidai ko jafar dayake kai baka da mutunci har kaje ka tabawa mutane kaya to wai meka rasa ma nace maka mai karasa dan iska kawai,karima ce ta furta dakata hajja tayaya zakizo kina zagin dana salon ya kara lalacewa to wallahi bazan yadda ba ehee dan ni yarana bana zagi bane,rike baki hajjah tayi tana fadin yanzu karima ni kike fadawa haka anfadamiki hajjah me zaki iya ai doke na taka miki birki saboda kwata kwata naga so kike ki wulaqanta min da sallamar mal sani ce ta katse hirar da cewa ya isa haka ke yanzu karima hajjah kike fadawa haka saboda baki gaji mutunci ba,ea nafada nace na fada malam sani daga hannu yayi da niyyar marinta,hajjah ce ta furta kull sani ka barta kawai taje duniya ce,ahayye ayirir hajjah har kinada bakin da zaki ce naje duniya ce nan kika samu marayun allah kika koresu saboda bakin hali irin naki wallahi hajja ke za a cewa kije duniya ce kuma zaki gani,wani wawan mari sani ya kaimata rike kuncinta tayi tare da fadin wallahi sani zaka sani idan na cika karima jan jafar tayi ta shige daki.
Aunty ya naganki da wannan wata yarinyar kuma,to haidar ya kaganta ko tamaka ne na baka ita,dan tsaki yaja yace haba aunty wannan sa'ar hibba zan so kenan na zama mijin yarinya ko,duka ta kai masa ya goce,waiter ya kira ya fada masa abinda zai kawo musu kallon aunty yayi yace aunty dama inaso zamuyi magana,akan jummai ne ko alhaji aa aunty akan 'yar aikin da jummai ta dakko ne,me yafaru nan tiryan tiryan ya fada mata komai,aunty ce ta kallesa tace hakan ma yana da nasaba da adduar da mukeyi shikenan haidar yanzu zamuje wajen malamin amma ka shirya tafiya kaima eaa aunty zanje amma 1week zanyi,to ai muma 1week din zamuyi auwal ne ya shigo bayan ya gaishe da aunty ya zauna,kallon shukura yayi da kyau tsamm ya hango kamarsu da mufida amma gani da yayi kamar idan sa ne ya saka shi yin shiru,to yanzu aunty binki zanyi na karbo rubutun kenan,ea haidar ko kuma nasanka da mantuwa kazo min da yarinyar dan itace zatayi aikin idan na fadamata dokokin rubutun bazatayi wasa ba,shikenan aunty yadda kikace,cigaba aukayi da hira.
Shukura kasa kasa da murya ta kalli hibba tace wai shi wannan yayan naki ya sunansa ke ma kijiki yayanmu dai,sai kuma tayi shiru tabata shukura tayi amma shiru taki magana sai da ta jijjigata sosai har sai da haidar da sauran mutanen suka kuka da su firgigit ta dawo,aunty ce ta kalleta tace ke hibba lafiya meyafaru,hawayene ya gangaro mata,sai ta rungume aunty shikenan hibba za a ganta kinji kiyi hakuri nasan dik inda take tana garin abuja tinda dai kince tare ku ka zo abuja kinji yar albarka ta,shukura ce ta dafata itama,haidar ne ya ce aunty meya faru ne zan maka bayani haidar ba matsala kaji,insha allah yanzu dai ba wannan ba mutashi ko kaga yamma nayi.
Gida ya shigo tin daga nesa ya hango mufida zaune ta zabga uban tagumi har haudar yayi parking ya fito ya tsaya akanta amma batasan ma yanayi ba,gaba daya ta lula duniyar tinani,magana yake amma shiru allah sarki yarinya karama amma tana wannan tinanin tabata yayi dagowa tayi tana murmushi tare da fadin sannu da zuwa ya haidar yawwa amma mai kike tinani am bakomai ina jummai batanan ta bashi amsa,shikenan taho muje nasan dai bazata dawo ba sai wajen 10 amma ina zamuje,yawo ya bata amsa a takaice,kallon kanta tayi dai dai bakin motar ta tsaya shigo mana mufida cikin raba ido tace ai karna bata ma mota ko nace ki shigo ko,ba yadda ta iya shiga tayi tana mai addua a bakinta,fita ya karayi saboda kawai so yake ta sake ta daina wannan tinanin da take,yawo sukai sosai,dan kuwa mufida ta sake sai hira suke katon mall suka tsaya bai mata magana ba yace ina zuwa kawai,fita yayi bai jima ba ya dawo ya juya akalar motar suka tafi,gida suka koma kallon ta yake yadda gaba daya ta saki jikinta kamar ba ita ce dazu take wannan tinaninba,parking yayi suka fito kallonsa tayi tace ya haidar nagode sosai,tafiya zatayi amma sai ya kirata,juyawa tayi ya mika mata leda katuwa,aa ya haidar ka barshi hade rai yayi yace banaso nabawa mutum abu yace min aa dan haka ki karba kawai,dole ta karba ta juya,da sauri tana shiga dakin ta ta shiga tare da bude leda abinda ta gani ne yasata yin tsalle ba komai bane illa dogayen riguna 3 sai hijabi 2 har da su pants da bra ko da ta kallesu kawai sai ta sunkuyar da kai amma ko ba komai ya taimaka mata saboda tana son siya,sai wata karamar leda da take da takeaway daya turesa tayi gefe tana kara kallon kayan kowacce riga kuma da mayafinta cike da murna ta shige bandaki domin ta yo alwala,haidar ma dakinsa ya shige domin ya gabatar da sallah.
Ina labarin 'YAN biyun hajjah wato hassan da Hussaini,can na hango tsakiyar daji suna zaune kai da gani kasan a chake suke domin gaba daya basa hayyacinsu,gefe kuma wata mace ce tana ta rausaya sukuma suna ta shewa da tafi hussain ne ya kalleta yace ke wai kullun style daya ki chanja mini mana kinji baby.
A falo ya tarar da mufida yace ki shirya mufida gobe zaki rakani unguwa da to ta amsa,ina abincin daddy ai ba'ai girki ba ya haidar sai dai ko idan na dafa masa,aa mufida zaki iya kuwa abincinsa fa yana da wahala ea mana me za a dafa ba alkubus bane ko funkasau,ko tuwo shikenan mufida kindai dage muje to na tayaki ko miya ce tinda dama tuwo za ai masa yafi cinsa akan komai,da murmushi tace aa ya haidar ka bar... Kallin da yayi mata ne yasata yin tsit tare da tashi tabi bayansa shima,a kitchen ta gansa har ya kunna gas cikin kasa da murya tace ya haidar naga kaya nagode ubangiji allah ya kara arziki mai amfani,cike da farin cijin jin adduar da tayi masa ne yasashi yake kallonta,tinda yake ba wanda ya taba yi masa addua bayan mahaifiyar sa,murmushi yayi yace ameen mufida nagode.
Auntynmu Ceh💕💘💝
"YA"'YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
39_40🎇
Zulai ke ya kuka gani ji yadda wannan mai kudin ya like miki kai gaskia naga aikinki ya fara ci nikuma naji labarin zeenatu shiru yanzu dai ki tashi mu shirya mu tafi domin muje muji a wacce ake kema ki karbi hadin da zai sa kifi haka zulai ce ta kalketa tace dallah ni dadina dake kenan kinsan dai bazamu san halin da zeenatu take ciki ba sai munje gidan ko lumshe idanu tayi tace ea hakane amma gaskia ba yanzu ba mubari sai dare yayi saboda kinga nan yankan ban manta dashi ba wallahi dariya zulai tayi tace allah saro.
Hajjah ce zaune gaba daya ta rike kai abin duniya ya dameta ta rasa ta ina zata fara ji tayi kamar ba ita ba,dik masifarta amma wai yau karima ce take gaya mata maganar da taga dama tabbas sadiya ta kasance yar kirki yar albarka yanzu sadiya ko tsire ta zanyi bazata zageni ba amma wai karima wacce nafiso nafi sin yayanta ita ce take fadamin haka cabb lalle nayi babban kuskure allah yaji kanki sadiya allah sarki,kishingidawa tayi ta kwanta ranta fall tinani.
Kusan mutanen gidan dik an hadu a falon baffa ana hira idan ka cire baba karami da sudais da basanan deejah ce taja hannun shukura da hibba kuzo muje na nuna muku wani abu da fara'a suka bita suna fadin ina zamuje deejah,binta sukayi gaba daya sai da suka zagaye gidan nan tsaf dai dai wani katon hoto shukura ta tsaya tana kallonsa,da alama hoton ya daddadene shine akai masa frame kallo take amma ta manta waye na ciki gani take tasan mutumin dayake jikin hoton amma ta manta waye shi,kiran deejah ne yasaka ta koma da gudu tana waiwaye.
Washegari tin karfe 11 jummai ta fice daga gidan sashen alhaji mufida ta shiga ganin dakin tayi dukun dukun kamar ba mutum bane yake kwance a cikin dakin,fitowa tayi kofar dakin haidar ta tsaya tana knocking bai dade ba ya bude yana sanye da jallabiya,kallonsa tayi tace dama inaso ka kama min wani abu ne idsn ba abinda kake,shikenan muje ko ya furta hakan,tafiya sukayi ganin sunayin dakin dad ne yasa abin ya bashi mamaki,shiga sukayi shi kanshi sai a lokacin yaga daudar da dakin yayi kuma gashi shi dad baya iya motsa jikinsa,mufida ya kalla zai magana ta katsesa da cewa bani aron wayarka idan kana da karatun alkur'ani a ciki,mika mata yayi connecting tayi da Bluetooth ta ajiye,kallon haidar tayi tace ya haidar ko zaka iya fitar da shi falon waje,haba mufyda taya zan iya kinsan dai upstairs ce a wajen fa,shiru tayi sai kuma ta ce ina zuwa bata dade ba ta dawo da kujera ta marasa lafiya,ya haidar dorashi mu fitar da shi.
Dakin suka dawo shara suka fara basu dade ba haidar ya fara kicibis da layu da wasu kulkinkan magani ajiyewa yayi da niyyar ya dauka saurin dakatar dashi mufida tayi tace aa karka taba ya haidar kallonta yayi yace meyasa aa ya haidar fasawa yayi daga katifa sukayi nan idanunsu sukayi kicibis da abinda basu taba tinani ba,haidar ne ya janyo wayarsa ya fara video domin ya zama masa sheda,gamawa yayi ya ajiye ya kalli mufida yace yanzu ya zamuyi mufida wannan matar wallahi ta cucemu matuka gaya,murmushi tayi tace nasan me za ai amma yanzu mu share dakin sai da suka gama tsaff suka debe komai suka fita zuwa bayan gidan suka juyesu a kasa,kallon kallo aka fara mufyda ce ta fara karanto ayatul kursiyyu,tare da daukar ashana ta kyasta ta babbakesu,haidar ne ya kalleta tare da fadin nagode mufida,ba wannan ba ya haidar wannan tsubbu ne kuma abinda nakeso ka sani shine ya zama dole mu tattara mu bar gidan nan idan ba haka ba wallahi ya haidar za a sami matsala indai jummai ta shigo gidan nan,malamin mu na islamiyya ya fada mana a dik lokacin da aka karya wani sammu ka kalli wannan ya hauiar ya fi sammu domin gaba daya ta maidashi ba komai ba,to yanzu me kike jira mubar gidan nan kawai da dad idan ba haka ba wallahi sai ta kara mai dashi halin da takeso ya kasance juyawa sukayi amma me wani azababben ihu sukaji yana tashi tare da shewa da kara addua suka tsaya tofawa sannan ta lafa,kai tsaye cikin gidan suka shiga,dad haidar ya dauko ya sakashi a mota,mufida kuma tana hade kaya,dakin jummai haidar ya shiga ya fara bincike
Fitowa yayi tare da sallamar mai gadin ya kuma umarcesa daya bar gidan kafin jummai ta dawo,tafiya suke mai matukar nisa,waya ya zaro yayi dialling number auwal kaje office please tafiya ce ta taso min kaje ka gabatar da abinda yafi dacewa idan mun hadu zan maka bayani kaji,tafiya suke shararawa,mufida ce ta kasa hakura tace ya haidar wai ina zamuje,ina zamuje ne so nake mubar garin nan mufida amma ya haidar meyasa dik inda mukaje sai ta nemo mu wallahi,murmushi yayi yace bazaki gane ba,dai dai wani filin jirgi suka tsaya da bansan ya sunansa ba,mufida ce ta kallesa abin ya daure mata kai tace ya haidar ina zakuje kuma kinga mufida banason tambaya kizo mu tafi jan hannunta yayi tare da wucewa,komai lafiya aka gama yayin da mufida mamaki take tasan dai idan mutum zai bar kasa dole sai da passport da visa amma ita bata dashi amma kuma gata har a cikin jirgi,wani hawaye ne ya zubo mata saurin kallonta haidar yayi yace mufida me ya faru kuma menene,bakomai goge hawayen tayi tana kallon dad sai kuma ta kalli haidar tace dad fa baici abinci ba ya haidar.
Malam sani ya shigo yana mai kiran sunan karima karima fitowa tayi tare da rike kugu tana fadin me kum akai sani yayin da hajja tana tsaye tana kallo,wai karima wannan wane irin iskanci ne yau kwanan su hassan nawa amma basa nan washa rabon da na gansu a idanu na na kusa sati 2 girgiza kugu tayi tace yadda baka gansu ba nima ai ba ganinsu nayi ba aikin banza dama ka ajiye ni ne domin na rinka yi maka gadi to wallahi ni ba yar gadi bace dan haka jeka ka nemosu da kanka ficeqatayi tana kallon hajjah tare da shigewa bandaki.
Wasa suke tayi fitowar khadijah ce yasaka ta fadin shukura hibba kuzo mu tafi da gudu suka karaso suna dariya,shiga motar sukayi suka fice daga gidan suka dauki hanyar titi.
Khairy ce rike da television kallo take gefe kuma tana cin cheese gaba daya hankalinta na kan kallo bataji sallama ba sai ji tayi kawai an rufe mata idanu kara ta kwalla wadda sai da khadija ta fito a tsorace amma tana fitowa ta fuskarta tai tozali data alhaji awwal da farinciki ta rungume sa tana masa sannu da zuwa,khairy ce ta kallesa dikda taji kunya wallahi sannu da zuwa kawu murmushi yayi yace to matsoraciya kawai ke yanzu daga rufe miki idanu shine zaki fasamin kunne da kara,dariya kawai tayi dai dai lokacin gatemn ya shigo da akwatin alhaji yana mai yiwa hajiya sannu da gida amsawa tayi shi kuma ya fice,khairy sai kallon su take itakam komai yana birgeta a gidan nan wallahi.
Shigowar jummai yasata tai tayi horn amma shiru ba a bude ba hakan yasaka ta mikewa tare da fadin ko dan yasan lokacin dawowa ta bai ba,wani ta kira tare da ya taimaka ya bude mata bai mata musu ba ya bude mata ita kuma ta kutsa kai cikin gidan komai na gidan tsaff falo ta shigo tana murmushi ajiye jakarta tayi tare da dauko wata laya ta shiga dakin haidar sakale ta tayi bayan hotonsa,sai kuma ta fito ta shiga dakin alhaji abinda yayi matukar daga mata hankali ganin dakin yayi fes ba kowa a ciki cike da hanzari ya daga katifar amma bakomai wata kara ta kwalla tana fadin shikenan kashina ya bushe wallahi nashiga uku na mutu na lallace wannan wane irin bala'i ne haka,da gudu ta fito ta shigo dakinta abinda ta gani yayi matukar daga mata hankali.
Auntynmu Ceh💨💨💨
"YA"'YA MATA
(Shin meye laifin mu ne)
Written and Narrated
Waleeda Muhammad (Auntynmu ce)
KING AND QUEEN WRITERS ASSOCIATION
We rule the world of writing
41_42🎀🎀
Zeenatu ki tashi tsaye matuka akan lamarin nan domin komai yana nema ya lalace,tin wuri ki nemi abinda na zayyana miki a baya idan ba haka ba kika bari wannan abin ya lalace to wallahi kisani kashinki ya bushe domin komai da kika rufe sai ya budu,domin ni nasan da cewa wannan bokanya ta fimu karfi dan haka zabi yana gareki kuma ki tashi ki bani waje.
Dakata anan jummai komai ya lalace ina mai tabbatar miki da cewa idan har bakije kin nemo yaran nan da suka ruguza miki aiki ba to kisani wallahi aikin kanki zai koma kuma kinfi kowa sanin yadda aikin nan yake yanzu haka kinada da wata 2 kacal idan ba haka ba to kisani sai dai kawai kiyi hakuri,kuma ki sani da cewa kullun rana tana wucewa dik wani nau'in aiki da kikayi na hawa jikinji idan kika bari wannan watan ya zama saura kwana 5 ya kare to ki tabbatar da cewa sunanki gawa kuma ba wanda ya isa ya iya karya wannan aikin hhh dama ance ramin karya kurarrene kuma ramin mugunta idan zaka gina shi ginashi gajere,jummai kifita ki bani waje domin kin lalata komai,cikin dan kasa da murya tace amma boka su waye wadan nan da suka min wannan aikin,dariya yayi yace da bazan fada miki ba amma ki sani haidar ne da ga wanda kika aura da niyyar cinye dukiyarsa,jummai karki sake dawo min nan saikin nemoshi dan haka ki fice daganan tin kafin nasan boka dan tsoto yayimin waje dake.
Shukura zo nan nace miki ko tafiya tayi sai da taje saitinta tace aunty gani zo ki soyamin wannan filling din ina hibba,tana falo tana kallo kwala mata kira tayi sai gata ta shigo,ke yanzu hibba ina aiki sai nace kuzo ku tayani ko,ko dan bakomai bane yarinta ce kawai a kanku,hibba ce ta kasa jurewa tace wai aunty tin dazu sai girki kike waye zai zo ne,dan murmushi tayi tace abbih ne zai dawo yau nasan ma yanzu nan zaki jisu,kuma zai dawo yau ke bazakije a dakkosu ba aunty,aiki ta cigaba da yi tai banza da ita,itama share zancen tayi sunayi suna hira da shukura.
Karar horn din motors ne ya cika gidan da kara gateman ne ya fara wangale gate wasu arnan motoci ne suka fara shigowa kamar ana turosu, parking akayi a parking space wani babban muyum ne ya fito sanye da babbar riga kai dagani kasan hutu ya samu dagani kasan mai ilimi ne domin komai nasa a nitse yake tafiya yake sai kuma ya tsaya ya kalli daya mota ganin me ciki bai da niyyar fitowa ne yasaka shi shigewa harabar gida gaba daya harabar gidan a cike take da mutane ana ta murna da dawowarsu.
Shukura da hibba da suke ta leke ta taga ne yasa hibba fadin cabb shukura anayi bamu wallahi kiduba kija abbih can wallahi nidai sai naje taho muje,aa hibba nidai gaskia ba ruwana aunty fa aiki ta saka mu amma shine zaki tafi,ke sai ki zauna amma ni kinga tafiya ta,tafiyarta tayi tana cewa yarinya natafi,tin fitarta shukura take aikin soya filling ganin sun soyu ne yasata kashe gas din ta nemi waje ta zauna ta kurawa tagar dakin ido hakan nan kawai taji tanason ganin aunty mufy da khairy,aunty ce ta shigo da niyyar daukar ruwa kallonta tayi shekeke ke shukura me kike anan tin dazu har za a faru lunch ba ke,shiru taji a hankali ta matsa ta dafata firgigit ta mike am dama aunty nagama soya miki,shukura dama kina kitchen din nan me kike anan tin dazu,shukura me ya faru hawaye ne ya zubo mata daga idanunta tace aunty inason nagansu,inaso nagansu da idanuna aunty, rungume ta aunty tayi tana ya hakuri shukura insha allah za a gansu kinji 'yata to taya za a gansu aunty bani da hoto bare a dubaminsu,hoton yana wajen aunty mufy ya zanyi aunty durkushewa tayi ta fara rera kuka kamar an aikota,tsugunna wa aunty tayi tace karki damu na miki alkawarin zan nemo miki su kinji shukura,taso muje falo gyara fuskarki kinji shukura ta,ba yadda taso dole ta mike ta tattara nutsuwarta suka tafi.
AUSTRALIA
SYDNEY INTERNATIONAL AIRPORT
anan jirgin su haidar ya sauka,gaba daya mufida ta cika da mamaki jirgi su kadai kawai amma an dakko su har nan fitowa tayi gaba daya ta rasa me ke mata dadi ko a mafarki bata taba ganin kasa mai kyan wannan ba,ko a mafarki batai tinanin zuwa wannan kasa ba,haidar ne ya kalleta yace mufida muje ko fitowa sukayi suka fito bayan angama dik wani tantance tantance,wasu arnan motoci ne guda 5 suka faka dik iri daya ne wani bodyguard ne ya zagayo ya bude motar tare da sarawa haidar gaba daya mufida ta zama yar kallo kamar wata gaula,tafiya sukayi dik da basuyi wata mai nisa ba,wani katafaren gida na turai suka sauka kai da gani kasan dole a kirasa mai kyau,ga wasu korayen shuke shuke masu ban sha'awa da daukar hankali.
Bayan mintuna 40 haidar ne zaune akan daya da kujerun falon ya dora kansa a bayan kujerar mufida ce ta fito ta zauna ya haidar dagowa yayi yana murmushi na'am mufyda ya akai meyasa ka kawoni wannan kasar,kodan bakasan labari na ba me yasa ka raboni da kasata,ina kokarin fara nemo yan uwana amma ka dakko ni munzo nan bayan bamusan kowa ba haba ya haidar,dakata mufida please nasan ban kyauta miki ba amma idan na tafi na kyaleki tabbas na sanyaki a bala'in da bazaki iya fita ba shisa muka taho nan kuma zuwa nan da wani satin zamu bar kasar nan,nasan da cewa jummai tana can tana neman mu saboda mun karya dik wani aikinta mufida ki taiamaka kiyi hakuri sannan inaso ki bani labarinki da kike cewa bansani ba idan har kika bani ni zan nemo miki yan uwanki wannan alqawari ne mufida.
Me kike nufi Zee ea ai kin gane mai nake nufi wallahi ina fadamiki bokan nan karya ce kawai yake fadamiki,amma kuma zee shi fa yayi aikin kuma yace idan banyi abinda nayi na nemosu ba nan da wata 2 zan samu matsala babba,ke wallahi karya ne tin wuri ki wuce ki tafi wajen na kan tudu shi zai san me zai miki akan lamarin nan dan allah zee kina nufin ba wata matsala,ba wata matsala jummai kedai kawai ina fada miki,shikenan zee muje in sauke ki a gida ko tafiya sukayi ta sauke zee a gida ita kuma ta juya tana ta tinanin mafita,dole ta dauki shawarar zee ta juya zuwa wajen na kan tudu.
A zaune take a gabansa jummai ba sai kin fadamin komai ba nariga da nasan komai kuma zan taimaka miki kasa ya taba ya buga ya fara wasu surutai can sai ga su mufida a zaune a falo tana bada labari kamar yadda tace,kallon bokan tayi tace suna ina yanzu haka,suna kasar waje kasar Australia tin wuri kije domin ki dawo dasu nan gidan cike da farinciki ta dumbuzo kudin ta zube masa ta fuce da sauri,wani mahaukacin gudu take burinta ta isa gida a dai dai wannan lokacin ne taga kamar motar tayi sama lekawa tayi ta taga ganin yadda ake lulata a cikin gajimare ne yasata fara ihu da neman taimako amma ina a banza a haka har ta kule.
Wai ke karima meyasa baki da mutunci ne eye ki duba kiga abinda kika min tinda baki wanke min ba ai bazan wanke ki lalatamin ba,kallon sama da kasa ta bita da shi cab di sannu uwata nace sannu uwata ai wallahi yadda ban wankewa uwata ba to bazan wankewa wata katuwa ba,me kike nufi karima ni ce katuwa ni fa uwar mijinki ce,ahayye ai sai dai ta tsaya iya uwar mijin amma ba dai uwata ba dan uwata ba kalarki bace aikin banza aikin wofi,da gudu ya shigo yana fadin umma wani yaro ne ya biyo sa da gudu.
Masha allah ai jikin nata ma yanayin sauki sosai nayi mamaki ko dan bata da kan jiki ne shisa nan da wani dan lokaci zami fara mikar da ita sannu khairy yawwa likita nagode,amma kamar akwai abinda yake damunki ko,b akomai kawai inaso ne nima na mike karki damu zaki mike kinji ki dawo kamarni harma ki fini,d ariya tayi tana fadin anya kuwa dr zan fika karfi hira sukayi sosai daga bisani kuma sukai sallama ya tafi khadija mirna take ganin yadda jikin khairy ke samun sauki.
0 Comments