ππππ»♀️A SANADIN TIKTOK ππ»♀️ππ
Story and writing
KHAIRIYYAAHH BAKARRYY (PINKIE)
*King and Queen Writing Chamber*
Gajeren labari
Gargadiπ€π» ban yarda wani/wata yayi amfani da littafina ko wani 6angare daga cikinshi ba tare da izinina ba ‘yan satar fasaha kuma gareku banyarda ayimin copy dinshi ba svd mallaki nane ni kadae duk wanda yayimin ban yafe ba.
Bismillahirrahman Raheem
π
Ώ️1-10✍π»
Sunyi abun yasha musu kai chasss... wai ya hakane wanka yabi jiki chasss..... itace wakar da take tashi a cikin dakin sae tikar rawa take kamar wadda akasa
Wata matashiyace wacce bazata gaza shekara 20-21 ba gajerace tanada jiki masha Allah tasha wasu Atamfah riga da shket kayan ya kamata sosae
Ta tsaya a gaban camera sae video take a tiktok tana gamawa tayi posting acikin minki 10 ta samu like sama da 1m viewers kuwa baa magana
Hafsa!!! Baki ta zun6ura tana gunguni kawae sae mutum yana abun shi aeta wani kiranshi kamar ana binshi bashiπ
Hafsa wae bakya jinane umma gani nan ina zuwa saeda tayi tsaki kafin ta fita
Dan iskanci hafsa kina ganin rana tayi bazakiyi wanke wanken nan ba iye koni kike jira nayi miki umma nipa bacewa nayi basanyi ba abupa nakeyi shi abinda kikeyi din yafi kiran nawa kenn ko yayi miki kyau hafsa Allah dae ya shiryeki Ameen ta amsa ta wuce tana zun6ura baki.
Adams nipa inaga kawai ka nunawa Mommyy hoton hafsy hmmm Nasir kenn bazaka gane ba akwae matsala babba Ina fada maka idan taga hoton hafsy komae zae iya faruwa gara idan akayi bikin kawae ta ganta to shikenn Allah ya nuna mana lokacin Ameen duk suka amsa dashi.
ππππππ
Zuby ce tazo gidansu, Hafsy kinsan nayi wani sabon friend waishi nafsoon kinga gay din handsome gay dashi kinga pics din shi wow so cuteπ
Kibani account dinshi zanyi fallowing dinshi bata tayi a take tayi mishi mgn suna fara hira kamar sun dade da sanin juna kallanta zuby tayi hadeta yi mata wani murmushi wanda ita kadai tasan maanar shi, hafsy tafia zanyi kinsan baba ya kusa dawowa tohm shikenn zuby sae munyi waya ki gaeda mama kwanciya tayi tacigaba da chatting dinta hankali kwance
Bayan futarta saeda tadanyi nisa kadan sannan ta fara magana hmmm hafsy kenn har yanzu bakisan wacece niba bana barin a zalinci wani sae nasa kinyi kukan abinda zaki aikata ta inda baki ta6a zataba muje zuwa yanzu ne zaa fara wasannn...........
ππππππ
Mommy na fada miki su a gidan su bazaa barta taje gidan su saurayi ba kiyi hakuri dan Allah mommy hmmm Son kenn ni bada wata manufar nace taxo ba dama kawae so nakeyi na ganta amma tunda kace haka shikenn Allah ya kaemu lokacin bikin rungumeta yayi yana yar daria hade da cewa Ameen ya fice tana sosa qeya.
πππππ
Hi beba inaso mu hadu yau pa ki zo fizza hot akwae abinda zan nuna miki beba inasonki byeeee......
Hmmm akwae magana pa ku biyoni
Comments and share pls
Taku harkullum KHAIRIYYAAHH BAKARRYY (PINKIE)
+2347088392884
ππππ»♀️A SANADIN TIKTOK ππ»♀️ππ
Story and writing
KHAIRIYYAAHH BAKARRYY(PINKIE)
*King and Queen Writing Chamber*
Gajeran labari
Gargadiπ€π»banyarda wani/wata yayi amfani da littafina ko wani 6angare daga cikinshi ba tare da izinina ba ‘yan satar fasaha kuma gareku baryarda ayimin copy dinshi ba svd mallaki nane ni kadae duk wanda yayimin ban yafe ba.
Bismillahirrahman Raheem
π
Ώ️11-20✍π»
Zuby ta kira nipa inajin tsoro kinsan samarin nan na yanzu sae a hankali kuma dama bae dade da turamin 5000k ba sae naga kamar kudinshi yakeson fanshewa ta fada da duk gaskiyarta kirkije kawae ki share shi idan ya kiraki karkiyi picking karpa ki dauka tohm shikenn kawata ngd
Shiru tayi tana tunani tashi tayi da saura tunawa da tayi yau wata kawarta ‘yar tiktok zatazo ficewarta tayi batare da tambayar ummanta ba kasan layinsu ta nufa ta danyi tafia me dan nisa kafin ta karasa gidan yanada dan kyau ba laifi noking tayi aka bude mata parlor ta shiga wow gaskia parlor din ya hadu over ashe ta wajene baayi masa kwalliya ba gaida matar gidan tayi shiru ne yadan biyo baya chan tace uhmm maman nana dama kinga wata kawata ce zatazo dan Allah zan kawota kamar yanda aka saba idan bazaki futa ba badamuwa sae kunzo ngd sosae tayi mata sallama ta futa maman nana tana mamakin irin rayuwar da hafsa tasa kanta ta karya tafi karfin ta nunawa kawaye gidan su kenn Allah ya kyauta, tana barin gidan ta wuce kasuwa kaji ta siyo da lemuka kala kala harda snacks ta siyo a gidan su tayi girkin ta gama sannn ta dauka ta kae gidan maman nana ya dawo ta shirya tayi kyau amma ga matar aure zan babu wani sura na jikinta wanda zae fitoba Atamfah ce akayi mata dinkin fitet gown tayi pitting dinta sosae fuskar nan tasha makeup hill tasa duk kuwa da itadin doguwace wani dan mayafi da ta daura a kafadarta daya wanda garama ta cireshi asan haka ta futa ba komae tsakar gida ta futa tana kallan kanta a madubi ni na futa kallon ta umma tayi sosae yanzu ke hafsa a haka zaki futa ko sayan kisa ayita zagina a anguwa wae me yasa bakyajin magana ne iye, ni gaskia umma kina takuramin shikenn ni bazan wataya ba haba gaskia nagaji da abinda kikemin a gidan nan nipa nama kusa bar miki gidan ki huta nima na huta kawae kiyita taku ramin ba dalilin komae ni bazan iya ba ahto mtwsssss tayi tsayi ta futa tana maganganu kasa kasa kuka umma tasa dan ita kam tasan bakin cikinta ne zai kasheta.
Sosae sukayi hira da kawarta dan ba ita tayi gidan su ba sae wajen 11:35 wani saurayinta yazo ya dauke ta sallama sukayi itama ta hada komatsanta tayi nasu gidan kodata shigo a zaune taga umma amma batayi ko sallama ba sae tsaki da tayi ta wuce dakinta kae kawae umma ta girgiza tashiga dakinta wanka taje tayi sannn tazo taci abincin data ajiye tun kafin ta tafi wayarta ta dauka tafara chatt bata ajiye wayar ta kawanta ba sae wajen 3:40 sannn ta kwanta.
πππππ
Zaune yake shida wata kyakkyawar budurwa zaune a gefenshi yaya magana pa nake maka zakiji me nace miki ba kenn ita wadda akayi engagement dinmu da ita me zance mata da kinsan kina sona me yasa baki fadamin ba sae dana kae kudin wata na fadawa Mommyy pa tacemin ba matsala kawae sae naji ka kae kudin aure to sae kiyi hakuri Allah ya baki wanda ya fini komae hmmm ni dae banaso wannn zancen ya shafi zumuncin mu kaji yayana in sha Allah kanwass sukayi daria a tare tashi kije kiyi sallah Nima bari naje masjid sallama sukayi ya tafi masjid itama ta tafiyin sallah.
πππππ
Yau sati daya kenn batayiwa umma magana ko aikin gidan ma datayi yanzu ya daina Dan a cewarta itaba baiwarta bace tunda duk abinda take mata bata gani tana kwance tana chatt kiran jabeer beb Ina waje pa ki fito da sauri ta miqe waje kuma wajen ina gidan ku zuby ta bani address din ki tunda kinki daga wayata gani nan jiki a mace tasa mayafi tayi waje yana jikin mota sae yamutsa fuska yake yana ganinta ya gyara fuskar shi dan karta gane sannu da fitowa gimbiyar mata tauraruwa a cikin taurari yar daria tayi kawae ki shiga mota dan banaso rana ya ringa ta6amin ke da kanshi ya bude mata ta shiga ba musu zagayawa yayi ya shiga yana shiga yayiwa motar key da mugun gudu sosae yake sharara gudu amma ta kasa yimasa magana kamar an rufe mata baki sae daya fara shiga daji daji sannn ya shiga wata hanya mara kyau tsorone ya kamata kardae Dan secret ne dammm gabanta ya fadi bata kara karaya ba saeda Taga katan gidan da suka shiga shikenn ta faru ta qare ya tabbata dan secret ne kuka ta fara tana hadashi Allah Annabi amma ya shareta tsaida motar yayi ya fito da ita janta kawae yakeyi wani daki me shegen duhu ya turata sannn ya rufe kofar ya bar gidan.
Topa su hafsy an shiga wani hali kome dalilin kawota gidan nan ohoπ€ ku dae kuciga da kasancewa tare dani danjin yanda zata kasance
Mu hadu a next page danjin ya zata kaya
Comments and share pls
Taku harkullum KHAIRIYYAAHH BAKARRYY (PINKIE)
+2347088392884
ππππ»♀️A SANADIN TIKTOK ππ»♀️ππ
Story and writing
KHAIRIYYAAHH BAKARRYY (PINKIE)
*King and Queen Writing Chamber*
Gajeran labari
Gargadiπ€π» ban yarda wani/wata yayi amfani da littafina ko wani 6angare daga cikinshi ba tare da izinina ba ‘yan satar fasaha kuma gareku banyarda ayimin copy dinshi ba svd mallaki nane ni kadae duk wanda yayimin ban yafe ba.
Bismillahirrahman Raheem
π
Ώ️21-30✍π»
Tunda ya tafi yake dariyar mugunta direct gidan su zuby ya wuce a dakinta ya zauna sae ta suka sha suka bugu amma ph ita sae tari takeyi svd bata sababa sae da tayi sallah sae masifa yake mata shiryawa sukayi a gaggauce suka futa daga gidan inda ya kae hafsy suka nufa saeda suka rufe komae na gidan sannn ya dauko wata igiya me kauri ya daureta yanda bazata iya ko wani motsi da kyau ba reaping dinta yayi tana kuka tana tsine masa albarka da nadamar saninshi da tayi ta dade tana kuka daga baya tashiga toilet tayi wanka tana fitowa ta ganshi zaune a bakin gado ya tsareta da ido sae lasar lips dinshi yake kamar wani saban maye dauke ido tayi daga kanshi dan wani muni taga yayi mata zo kisa kayan ya daga mata wata yaloluwar riga harara ta watsa masa tareda dauke kae hmm yarinya kenn tome zaki 6oyemin kuma hhhhhh ya fice yana dariyar rainin hankali kuka ne ya kuma kubce mata saeda tayi me isarta
Kullum sae yayi amfani da ita ya mayarda ita kamar matar shi sannn ya bata maganin daya gusar mata da hankali yanzu ba saeya daureta ba Dan wani time dinma itake kiranshi
Abinda batasani ba duk lokacin ta suke aikata masha’arsu anayi musu video kuma ana posting dinshi a tiktok amma baa nuna fuskar shi
Watanta 4 a haka tun tana tunanin gida harta hakura ta sallama
πππππππ
Tunda ta 6ata umma ta shiga mawuyacin hali dukda rashin kunyar da takeyi mata amma dake soyyayar uwa daban take haka taketa fafutukar Allah ya nuna mata ita.
πππππ
Ba karamar damuwa ya shiga ba yayi neman dunia harya gaji amma bako labarinta har ‘yar rama yayi
πππππ
Watanta 3 da 6ata umma ta rasu zuciyar tace ta buga sakamakon videon da aka nuna mata lokacin suna aikata alfasharsu shine yasa zuciyarta bugawa anyi jana’izarta kamar yanda addinin musulunci ya koyar sae dae muce Allah yajikin ki ummaπ₯Ί
πππππ
Wae har yanzu bazaka cire son yarinyar ba har yanzu pa baasan inda takeba
Hmm mommy wlh ina sonta kicigaba da tayani addu’ah in sha Allah zata dawo gashi ma umma ta rasu idan ta dawo bansan inane zataje ba tohm shikenn Allah ya bayyanata Ameen sallama yayi mata sannn ya futa sae da je yayi sallah sannn ya wuce dakinshi kodaya shiga dakinshi kwance yaga Nasir a kan bed dinshi yana kallon videon da aka tura masa saurin cirewa yayi Dan bayaso yagani murmushi kawae yayi tsokananshi yakeyi saurayin 6attaciya shiru yayi masa kamar badashi yake ba har suka futa.
ππππππ
posting din videon da tayi musu yau comment section ta shiga banda tsinuwa da aibantawa babu abinda akewa hafsy kowa da irin tsinuwar da yake mata hakan ba karamin dadi yayi mata ba kashewa tayi ta tashi wani daki ta shiga tayi kwanciyarta sallah tayi sannn ta kwanta tare da mafarkae ma banbanta.
πππππ
Watanni sunata ja har yau shekarar ta daya a gidan tama daena tunanin gida yanzu kwata kwata babbar damuwanta yanzu tanada ciki 7 months kuma tayi tayi dashi kan a zubar yace idan ta kuskura ta kashe mata danshi itama saeya kasheta
Wata ranar laraba cikinta yanada wata tara taji ana tafia a hankali ga wani irin kakari a tsorace ta tashi abinda tagani shine ya furgitata harta fara nakudar dole.
Hmmmm kome abinda tagani hakaπ€
Kudae kucigaba da kasancewa dani
Comments and share pls
Taku harkullum KHAIRIYYAAHH BAKARRYY (PINKIE)
+7088392884
ππππ»♀️A SANADIN TIKTOK ππ»♀️ππ
Story and writing
KHAIRIYYAAHH BAKARRYY (PINKIE)
*King and Queen Writing Chamber*
Gajeran labari
Garigadiπ€π» bayarda wani/wata yayi amfani da littafina ko wani 6angare daga cikinshi ba tare da izinina ba ‘yan satar fasaha kuma gareku banyarda ayimin copy dinshi ba svd mallaki nane ni kadae duk wanda yayimin ban yafe ba.
Bismillahirrahman Raheem
π
Ώ️31-40✍π»
Dole kayi aure dan bazan bari kaci gaba da da zama a haka ba sae kace wanda akayiwa asiri ina dalili nagaji da wannn abun zan hadaka da daddyn ka ni tunda ka rainani
Mommy kiyi hakuri dan Allah ni wlh yanzu ba maganar hafsa ce ta hanani aure ba inaso nayi amma tsoron yammatan nake bansan da wadda zan hadu ba Ina tsoran na auri wadda zata rainaki dan bazan lamunta dan naga yammatan zamanin nan majoritin su basu da kunya shiyasa
Dadi mommy taji Allah ya sani har zuciyar ta Tana so ya auri Aysha amma tafi so ya fada da bakinshi dan bataso yaga kamar tallarta tayi masa
Mama aysha nace ko anyi mata miji ne ya fada yana sosa qeya wani dadine ya ziyarci mommy har saeda ya gane hakan shima
Aa baayi mata ba inaga dama ita kake so kenn ko shiru yayi yana sosa kae daga karshema guduwa yayi dan yanaso yaje wajenta
Aysha kanwar wannn budurwarda ta ta6a zuwa wajenshi ce wato zarah ‘yayan kanwar daddy ne wato mahaifinshi akwae fahimtar juna sosae a tsakanin mommy da mami wato maman su Aysha kasancewar dama chan kawayene kuma sae Allah yasa mommy ya auri yayanta zarah tayi aure harta haifi danta namiji ta aure wani lawyer suna zaman su lapia
Sauri sauri ya shirya mommy yayiwa sallama harta bashi sako ya kaeka mami
Sharada police station layi na 2 a gaban wani tsantsareren get yayi parking getman ya wangale mishi ya chilla motar ciki yana fitowa ya shiga parlor din da sallama a bakinshi mami ce zaune tana yiwa aysha tsifa sae kuka take kamar wata yarinya wae zafi
gaeda mami yayi itama ta gaedashi sannn yabawa mami sakonda akabashi ya kawo mata tunda ya shiga idonshi a kanta ko qiftawa bayayi farace sol da ita tanada kyau masha Allah doguwace amma ba chan ba batada qiba akwae diri
ya shagala da kallon ta baesan mami ta gama yi mata harta futa ba yaya ga ruwan e e eh au aysha Ina mamin ta shiga ciki tana maka magana bakaji bama ae
Hira suka danki amma baece mata yana sonta ba kodaya koma gida gizo ta dinga mishi tabbas da ace ba kanwar shibace da yace aljanace ita kiranta yayi a waya sun dade suna waya yace ta tura masa pics dinta sukayi sallama saeda yayi sallah raka’a biyu sannn ya kwanta
Wasa wasa shakuwa ta shiga sosae a tsakaninsu amma har yanzu baece mata yana sonta ba kuma itama haka dan mugun sonshi takeyi kishin juna sukeyi kamar me dan akawae wani causing brother dinta dan kanin Abban su me suna fahad yazo gidan suna hirar bikinshi yake ce mata matar suwace ko hausa taba iyaba sae take cemishi itama ta iya ba haka akeyi baππ»
Naksmksowksnsosmsosn kowkndowk olwpmsjso
ae Nima na iya sosae abin ya bashi daria itama dariyar tayi harda riqe ciki dae dae lokacin ya karaso wajen babu zato kawae ya rufe shida duka jina jina yayi masa da kyar aka 6am6are shi a jikinshi.
Haka itama yazo gidansu wata ‘yar kawar mami tazo shi yana tsaye a jikin window ita kuma tana offside dinshi a zahiri kamar ita yace kallon amma a badini tunani yake baisan ma da zaman ya a wajen ba haushi ne ya kama aysha ta dauko miya ta taho saedata dae daeci face nata ta watsa mata daria abin ya bashi danya gane da gangan tayi mata hakan.
πππππ
Sunqi furtawa juna har yanzu Mommyy ce suke magana da mami
Nipa har yanzu na kasa gane inda yaran nan suka sa gaba so suke su maedamu kananan yara kome Mommyy ce ke magana
Numfasawa mami tayi tace nina rasa abin cewa ma amma zo kiji shawarar dana yanke rada tayi mata a kunne daria sukayi harda tafawa
Mommy tace kinsan ban ta6a tunanin hakan ba zasuga tsiya ae hirarsu sukaci gaba dayi
πππππ
Zuby tanagani yana janta kamar ba mutum ba a nan ta haihu ko inda take bae zoba jinjirin ya dauka ya fice baece mata komae ba a hankali taja jikinta taje wajenta tayata tayi ta gyara jikinta
Kukan munafurci ta fara kinga yanda rayuwa tayi damu ko ni bansan me wannn mutumin ke nufi damu ba kina nufin kema yana miki abinda yakemin kenn
Eh mana jibi kiga yanda nazama kamar wata tsohuwa ya cuceni yaci amanar kauna kuka take sosae kamar gaske tausaya mata tayi kiyi hakuri kawata zamu futa daga cikin wannn wajen nan bada dadewa ba dazu na fara fasa wani waje tana nan zamubi mu gudu
Da sauri ta kalleta inane wajen da zuciya daya ta nuna mata wajen
Kuka tasa tace ni chanzamin daki ma zayyi nasan ba lallae mu sake haduwa ba idan kin futa ki gaedamin mamana ta juwa da jan jiki ta futa daga dakin, hamdala hafsy tayi wato ita a aljanna tace tunda tana iya tafia da kafarta sosae ta tsaya mata a rai har dare
Washe gari da wuri tayi wanka tabi ta wannn hanyar data bude saeda tayi nisa sosae har tana ganin titi taji an rufe mata fuska ihu tafayi wata allura ya dauko a aljihunshi yayi mata suma tayi daukarta yayi yasa a mota yanausa dajin da ita.
πππππ
Assalam alaykum mami gani ance kina kirana shigo ciki daughter a gefen kafarta ta zauna daughter kinsan wannn kawar tawa hajia batula ko eh mami nasanta kinsan Khaleed ae wannn dan nata daya dawo daga wannn America eh nasanshi yauwa dama shine ya ganki yana sonki so zaezo kuga juna banaso kiyi abinda raena zae 6aci kinsan yanda muke da mahaifiyarshi dae daskarewa tayi a wajen ko motsi ta kasayi kasa kasa mami take mata daria danta fahimci halinda ta shiga tashi kije dama itace maganar shiru kamar ita daya ce a dakin
Ina wlh bazae yiwuba akanme bazan ta6a son wani ba indae ba ya Adam ba kuma wlh bazanso wani Khaleed yake koma waye oho
Aysha kina tare dani kuwa??
naam mami magana kike nace kije nagama ko tashi tayi jiki a mace
Daria mami tayi sosae kiran Mommyy tayi nanta labarta mata yanda sukayi da aysha yarinyar nan kinga yanda tayi kuwa kamar nace mata Abban su ya mutu sosae Mommyy tayi daria sukayi sallama
πππππ
Wlh gabana faduwa yakeyi ji nake kamar yanzu ma zan rasata wlh mutuwa zanyi, idan na rasata ko rantsuwa nayi maka babu kaffara tana sonka sosae nasan tana sona amma ji nake kamar zaa rabamu da ita ka kwantar da hankalinka in sha Allah zakuyi aure harta haifa maka yara masu kama da ita har ranshi yaji dadi
Kamar ph kiranka akeyi ni banmaji ba picking yayi yanzu ok to gani nan zuwa rabuwa sukayi kowa ya shiga motarshi ya tafi
Mommy wace magana kikeyine haka kina nufin wata zan aura ba aysha wlh Mommyy kiyi hakuri zan iya miki biyyaya akan komae amma banda wannn maganar dan bazan ta6a iya aurar watan aysha ba indae kikaga na auri wata sae dae da gawata ni na aysha ne kadae maganganu yakeyi yama manta dawa yake magana da farko abin daria ya bada amma yanzu tausayinshi take dan ta fahimci ba karamin so yake mata ba
Kayi kagama aurenka da Fatima babu fashi tashi yayi zai fita
timmmmm ya yanke jiki ya fadi ihu Mommyy tasa tayi kanshi sae jijjigashi take tana kuka waya ta dauka takira daddynshi ta fada masa halinda yake ciki dama ya kusa gidan karasowa yayi daukanshi yayi suka wuce asbiti taimakon gaggawa aka bashi watanshi daya amma har yanzu bae farfado ba daddy ya fara tunanin kaishi India dan a dubashi a chan
πππππ
Tunda taji labarin halin da yake ciki hankalinta ya tashi ta rasa yaya zatayi daga karshe ta yanke shawara sallah tayi ta dade tana addu’ah a sujjada bayan ta idar ma tayi addu’ah sosae tayi karatun qur’ani bayan ta gama dakin mami ta nufa kae tsaye
Mami tasamu a daki bayan ta gaedata mami dan Allah inaso naje gidan yaya zarah na dan huta kinga yanzu ni kadae kike bari idan kin tafi asbitin kuma gidan babu dadi kinji mami dan Allah karkice aa kamar zatayi kuka
Shikenn amma yanajin sauki zaki dawo eh mami na yarda wlh ngd ta futa tana tsallen murna da kuma nasara dama ta hada kayanta tare suka futa da mami ta sauketa ita kuma tayi asbiti
Kingana shiryawa nayiwa Dr magana komae yazama ready rungumeta tayi ngd sosae ‘yar uwata Allah ya bamu nasara Ameen
Kayan jikinta tacire tasa black abaya sannn ta daura jalbab a kae asbitin suka wuce office din Dr suka wuce wani uniform ya bata ta shiga wani dakin a office din tasa sunyi mata kyau sosae duka blue black ne riga da wandon hijab da face mask din kuma fari sak ta fito da ita babu wanda zaece ba ma’aikaciyar bace a haka ta futa taje dakin ta yake duk su Mommyy suna ciki futa sukayi suka barta a dakin saeta tayi kwalla ganin yanda ya koma cikin karamin lokaci
Satinta daya tana zuwa amma batayi abinda zaa ganeta ba ko kadan
Ranar da zaa tafi dashi dole zaa tafi da ma’aikacin asbitin mutum daya itace wadda zaayi tafiyar da ita sun shirya tsaff su Mommyy sae addu’ah suke musu daddy yace idan anyi nasara kafin su dawo zasu zo addu’ar samun nasara sukayi musu wannn sukayi sallama saeda suka shiga ta zauna a kusa dashi wayartace tayi kara dauka tayi ta duba text ne abinda ta gani shine yasa tayi mutuwar zaune sae zare ido takeyi.π€
Toph akwae magana ph a bakina amma muje zuwaππ
Nasan kunaso kusan suwaye Adam Aysha Hafsa da kuma Zuby ku cigaba da kasancewa dani zakuji komae dalla dalla
Comments and share pls
Taku harkullum KHAIRIYYAAHH BAKARRYY (PINKIE)
+2347088392884
ππππ»♀️A SANADIN TIKTOK ππ»♀️ππ
Story and writing
KHAIRIYYAAHH BAKARRYY (PINKIE)
*King and Queen Writing Chamber*
Gajeran labari
Gargadiπ€π»ban yarda wani/wata yayi amfani da littafina ko wani 6angare daga cikinshi ba tare da izinina ba ‘yan satar fasaha kuma gareku ban yarda ayimin copy dinshi ba svd mallaki nane ni kadae duk wanda yayimin ban yafeba
Bismillahirrahman Raheem
π
Ώ️41-50✍π»
Idan kingama 6oye fuskar saeki tsaya ki kula da mijinki yanda ya kamata aysha kuma ki kiyaye duk abinda zae 6ata masa rae Allah ya kaeku lapia yasa ayi nasarar abinda akaje nema
kunya ce ta kamata ashe mami tasan itace to amma taya yazama mijinta itakam kanta ya kulle announcement aka farayi kowa ya kashe waya kashewa tayi tasa a handbag dinta taredayin addu’ah safe travel Romeo and Juliet.
πππππ
Bayan wata qatuwar bishiya ce akwae wata rijiya me zurfin gaske tinjin kakeji ya jefata a ciki wata qara tasaki dan azaba nayi kuka sosae kamar randa zayyi kuka gashi babu abinci rijiyar dama tshohuwa ce babu ruwa a cikin ta
Saeda tayi kwana 10 a haka babu ci babu sha tagama gala baeta ta futa daga cikin hayyacinta
Kamar daga sama taji ana magana zan taimaka miki amma sae kinyi rantsuwa zaki fadawa dunia dalilin dayasa kikeson aurenshi zan fada wlh zan fada ka taimakamin ta fada a qagauce
Igiya me kwari aka sako mata daga saka ki dauka a jikinki daurawar tayi jiki na rawa sama akayi da ita a wata bakar mota aka sata me blacktink gudu sosae sukeyi har suka bar dajin dadine ya kamata ganin tabar wannn uqubar
Murnar tace ta koma ciki ganin sunyi wata hanya me karancin mutane shikenn mutuwartace tazo daga wannn sae wannn wani daki aka kaeta babu komae a cikinshi
Ga toilet nan kiyi wanka kiyi sallah sae kizo kici abinci da to ta amsa ya futa ya barta a dakin
Sallah nikam yaushe rabona dayin sallah chab din umma ma tayi ta gama Nikam wanka zanyi naci abinci nayi kwanciyata
Hakan kuwa tayi dan tana gama cin abinci sae bacci
πππππ
Sunje lapia sun samu tarba me kyau a asbitin PC room aka bashi svd haka tare suke kwana saeda sukayi kwana 3 da zuwa sannn aka fara yi masa aeki
Angama aiki lapia amma bazae farka ba sae nanda 2 day’s kuma ta tabbatar tasamar mishi abinda yafiso idan ya tashi
Sallah tayi tanayi masa addu’ar Allah ya tashi kafadanshi har bacci ya dauketa a kan sallayar
After 2 days idar da sallarta kenn kamar daga sama taji ana qiran sunanta
Ayush Ayush Ayush naaa naam ya Adam kece a kusadani ko kunnena ne yakeji nice Ayush dinka bude idonka kaganni rungumeta yayi yasa kuka kamar wani karamin yaro My babyy karki bari a rabamu bazan iya rayuwa ba tareda keba Ina qaunarki farin cikina
Nima ina qaunar ka mijina kuma nidin yanzu mallakinkace lavari ta bashi dadine ya kamata bacci ne sosae a idonta
Da kanshi yayi mata dabara yanata janta da hira har bacci ya dauke ta a jikinshi kwantar da ita yayi shima ya kwanta farin ciki fall ranshi a haka bacci yayi gaba dashi
πππππ
Ke tashi kiyi magana ba bacci na kawoki kiyi ba ya fada yana takata da kafa
Furgigit ta miqe tana zare ido harara ya watsa mata aeda sauri ta miqe tsaye zan zanyi yanzu wlh amma dan Allah ka daina kallona tsoro nakeji fara taji yace a dakile waya ya dauko ya fara mata video
Da farko dae sunana Hafsa Idris Magaji mahaifina dan asalin jihar kano ne a wani kauye da ake kirada dan tamashe mahaifiyata kuma babu wanda yasan asalinta svd mallam magaji wato kakana shine ya tsinceta wata rana ya dawo daga gona tanata kuka yayi mata tambayar dunia amma ta kasa magana hakan yasa shi zuwa wajen me gari ya fada masa amma sae yarinya taqi yarda da kowa sae kakana me garine ya bashi shawarar daukarta tunda kowa yasan mallam magaji mutumin kirkine koda yakae yarinyar gidan shi matar sa tayi murna sosae dan tanason yarinya mace amma danta daya ne idris wato babana mallam magaji shine ya riqeta harta girma yasa mata sunan maman shi khadija amma suna kiranta da ummi
Soyyy ce mae karfi ta kullu tsakanin idris da Ummi fahimtar hakan da mallam magaji yayi ya hada su aure bayan auren sune kasuwanci yasa idris barin kauyen su saeda sukayi shekara 10 da aure basu haehuba harma sun cire rae Allah yasa tasamu ciki tayi laulayi ba kadan ba haka ma wajen haihuwar har jijjiga tayi ta haifi yarta tubar kalla masha Allah mallam ne da kanshi yasa mata suna wato hafsa ni kadae Allah ya bashi tun tasowarta babu abinda ta tsani ace tayi kamar sallah sam bataso da farko sun dauka na yarintane sa daga baya suka fahimci abin babba ne babu irin dukan da baayi mata amma a banza dan qememe taqiyin sallah
Tayi primary da secondary a wata government school kullum cikin Jin haushin iyayenta take svd basu nemi kudi kun gina musu katan gida ba
Tun daga lokacin ta tsani mahaifinta dan bashida kudi bae kuma siya musu katan gida ba lokacin da take secondary tayi wata kawa me suna zakiya itace ta kara lalata mata tarbiya kullum saita ganta da babbar waya dasu chocolate’s da ah tunanin ta a gidan su ake bata saeda ta fada mata saurayinta ke kawo mata ranar data fada mata kwana tayi tana tunanin yanda zata samu saurayi bata waya babba washe gari har gidan su taje akan maganar
Hmmm zan hadaki da saurayi amma kinsan bazae baki a banza ba zo kiji rada tayi mata a kunne eh wlh zakiya na yarda indae zae bani babbar waya zanyi koma menene a lokacin ta kirawo wani musa ta fada masa komae ba 6ata lokaci yazo ya dauke su shopping ya farayi musu sannn ya wuce dasu gidan shi a nan ya cinma burinshi a kanta sannn ya bata iPhone 12 da kudi me yawa wae tasa data murna kamar tayi me dan dadi har kofar gidan su zakiya ya maedasu kayan daya suyo ya bata sannn ya tafi shiga gidan sukayi saeda ta kowa mata komae da yanda zatayi amfani dashi a wayar sannn ta tafi gida tun daga wannn ranar ta farayin tiktok da farko harda hijab mayi takeyi amma daga ko kallabi daena sawa tayi
Haduwar su da Adam wata rana sunje shopping itada zakiya jalbab tasaka tayi kyau sosae shima sunje shida Nasir tunda ya ganta yaji duk dunia ba macen daya keso sae ita a haka yayita bibiyarta tana mishi wulakanci danba soyyaya ce a gabanta ba
Wata ranar laraba ta tashi da matsanancin zazza6i zakiya ta kirawo ta rakata asbiti gwajin farko aka tabbar mata tanada cuta me karya garkuwar jiki HIV hankalinta ya tashi sosae amma zakiya ta dinga tausarta a wannn lokacin ne ta quduri niyar sawa Adam ita danta huce abinda namiji yayi mata amma data fahimci shiba me neman mata bane saeta yarda da auren shi har akasa rana tayi burin tana saka mishi zata gudu ta barshi a lokacin ne kuma zakiya tayi aure aka kaita kwara state da farko suna waya daga baya kota kirata bata shiga hakura tayi taci gaba da rayuwar ta ita amma kuma har yanzu bata sallah
A lokacin ne zuby ta shigo rayuwarta following nata tayi itama tayi unfollowing nata a haka suka fara chatt har zuby tazo gidan su
duk video din da zatayi zuby bata ta6a yarda sunyi tare ba sae dae kowa yayi nashi ta dauki zuby tamkar yar uwanta da suka fito ciki daya ana haka wani abayan layinsu ya fadawa mallam idris tanada HIV a ranar ya mutu svd bakin ciki ita kam har party ta hada wae a tayata murna ta yarda kwallan mangwaro ta huta da quda a cewarta tun daga lokaci ummana bata kuma lapia ba harna baro gida yau ciwo gobe lapia amma hakan bae ta6a damuna ba burina kawae naga na cutarda wanda baejiba kuma bae gani ba.
Kofa aka bude da sauri ta kalli wurin wazata gani..........
Hmmm kowaye wanda taganiπ€Mu hadu a next page bye
Comments and share pls
Taku harkullum KHAIRIYYAAHH BAKARRYY (PINKIE )
+2347088392884
ππππ»♀️A SANADIN TIKTOK ππ»♀️ππ
Story and writing
KHAIRIYYAAHH BAKARRYY (PINKIE)
*King and Queen Writing Chamber*
Gajeran labari
Gargadiπ€π» ban yarda wani/wata yayi amfani da littafina ko wani 6angare daga cikinshi ba tare da izinina ba ‘yan satar fasaha kuma gareku ban yarda ayimin copy dinshi ba svd mallaki nane ni kadae duk wanda yayi ban yafeba
Bismillahirrahman Raheem
π
Ώ️51-60✍π»
Zuby tagani tasha kaya na alfarma da sauri ta mike tsaye bakinta har rawa yakeyi zu zub zuby kece a nan meya fawoshi kuma taya kikasan ina nan hmmm zakiji duk amsoshinku kawata kenn
Ni dae sunana Nafisa ba zuby ba kamar yanda kika sani kuma nashigo rayuwar kine dan naga na lalata duk wani shiri naki akan bawan Allahn da baeji bae gani ba kuma duk wannn abun mune muka shirya nida wannn ta fada tareda nuna namijin bakisan shiba ko sunanshi Nasir abokin Adam ne kuma wanda zan aura tun ranar daya fara ganin hotonki yaji hankalinshi bae kwanta dake ba shine yazomin da maganar ki yanaso na shiga jikinki dan na sami dalilin ki na yarda da auren abokin shi da kikayi kuma na samu
Kinci amanata zuby Allah ya isa pant of correction Nafisa nake
Aikin mu ya kare babyy inaga kawae mu barta iya haka ma abinda zataje ta gani ma ya isheta futa sukayi suka barta ita kadae sae kuka takeyi daga karshe ta tashi tabar dakin tafiya takeyi a cikin daji fatanta kawae ta ganta a titi tun tana saka rai harta hakura saedata kwana 2 da yini 3 kafin tazo titi ba karamar gala baita tayi ba a gefen wani me shayi ta zauna dan wata bakar yunwa takeji har jiri jiri takeji duk wanda taga yana cin abinci sae tazuba masa ido ko Allah zaisa yaji tausayinta ya bata
Yunwa kikeji ko zan baki abinci amma saekinzo dakina da sauri ta miqe zanje indae zaka bani abinci gaba yayi tana biye dashi sun danyi tafia me dan nisa kafin suzo wajen wani sago budewa yayi saeda yagama leke leken shi tunna yace tayi saurin shiga dan kar a ganta tana shiga shima ya bita ya rufe kofar saeda yayi abinda yake bukata da ita sannn ya bata abincin taci kamar yar yunwa hannu baka hannu kwarya tas ta cinye
Saeda tayi sati a wajen wannn mutumin ranar kwananta na 8 tace masa zataje gida tadan ga ummanta kudin mota ya bata ta shirya ta tafi tunda me napep ya sauketa a layinsu taga anata nunata kamar tayi kisan kae ko hanya daya sukayo da mutum yana ganinta zae chanza hanya basarwa tayi koda taje kofar gidan su kusan suman tsaye tayi dan gida aka gina na alfarma sae kace ba kwara66a6an gidan su ba noking tayi me gadi ya bude mata amma ya hanata shiga
Ina umma wace kuma haka ke dalla wa kike nema to yau ba ranar sadaka bace almajira kawae nice almajirar kaga nayi maka kama da almajirai ne
Wlh idan baki bar wajen nan ba sae nayi kasa kasa dake sae wani warima kikeyi inagama shaye shaye kikayi zakizo kinawani yiwa mutane tin6ele garam ya rufe kofa , kuka ta zauna tanayi yara ne suka zagayeta waega hafsy yar tiktok data gama karuwancinta ta dawo bata ankara ba taji an riqe hannunta ku sata a mota maza mutane ne suka taru sosae sae kallonta akeyi masu zaginta nayi masu la’antarta nayi masuyi mata addu’ah nayi kowada abinda zaice
Wayyoo Allah nani hafsa me nayi muku ku kyeleni dan Allah kuce karsu tafi dani shi take nanatawa amma babu wanda yayi yinkurin hanawa har suka tafi
πππππ
No gaskia ni bazan koma 9ja yanzu ba sae munje honeymoon
Allah ka cika rigima jaan shikenn ae ya zanyi dakae tunda kace haka amma babu ruwana idan Mommyy tana fada gaskia zan fada mata
E naji din nida matata har sae anfadamin abinda yakamata nayi mata
E mana because sun fika sanin me dunia take ciki
Au haba lallae ma yarinya
π‘ wace yarinyar? Ke manaπ
Pillow ta jefa masa shima ya rama tashi tayi zata dakeshi ya arce a million yana gudu tana binshi tana dan kukan shagawa6a ita dole saeya tsaya ta dakeshi tunda yace mata yarinya
Dan buga kafarta tayi a jikin kujera yanda bazataji zafi ba wayyoo kafata shikenn na karye wayyoo mami Mommyy kizo ki taimakeni yaya zarah shikenn kafata ta karyeπππ
A gigice ya dawo honey meya samu kafar kuma saekiyita jiwa kanki ciwo kamar wata yarinya ko saedata bari ya sakan kance ta rufeshi da duka kuma narama Nima wooo ya ruga tana mishi gwaloπ€ͺπ€ͺ
Ba karamin daria yayiba binta yayi shima bae yardaba saeya rama harda yar shagwa6aπππ wae nida garzali
πππππ
Hisba ne suka kamata because tana yada badala a page dinta na tiktok kotu aka kaeta anyanke mata hukuncin zaman gidan kaso na shekara 1 ko za6in tara dubu hamsun sannn kuma an sake yanke mata hukuncin zama na wata 9 babu za6in tara a taqaece zatayi wata 21 a gidan yari tunda batada kudin kuma babu wanda zae biya mata
Gidan yari aka wuce da ita su 18 ne a dakin akwae wata babba a dakin duk yan dakin tsoronta sukeji dan ita kisa baya mata wahala sosae hafsy take tsoronta kuma take mata biyyayar dole
πππππ
Wato ni ban isa na fada maka magana ta shiga kunnenka ba ko shikenn yayi maka kyau ka kawomin diyata kaki amma kasani duk abinda ya samu diyata ko jikana saena 6ata maka rai Mommyy wl qittt ta kashe wayarr
πππππ
Hlo yaya muna airport ne kizi ki daukemu amma karki fadawa kowa pls surprise mukeso muyi musu ok ganinan kanwata after 50 minute you’re highly welcome ππ» mutan turai aa su aysha masu ciki wae kece zaki haihu au yaya kema hardake ko tsokanata kema zakiyiπ«π« nina isa shalelen mami karkisa ta daena amsa gaesuwana baki ta tura mata daria sukayi mata suka shiga mota sae gidan Mommyy
Murna wajen Mommyy da Mami abin baa cewa komae kamar zasu goyata dan gata haka sukeji a gidan Mommyy ta zauna dan tace bazata bada diyarta ba mami bata damu ba dan tasan zata samu kulawa fiyeda yanda zata mata satin su biyu da zuwa aka mata CS danta kyakkyawa dashi sak babanshi ranar suna yaro yaci sunan Daddy wato Muhammad anace mishi Abiey
Sunayin 40days mami tazo ta tasa qeyarta har gidan mikinta bayan ya dawo daga aiki yana dakinshi yana chatt da Nasir inda yake fada mishi bikinsu saura 2weeks Allah ya sanya alkhairy yayi masa
Kamar daga sama naji ance my boo your food is ready da sauri ya dago dagata sama yayi dan murna ji yake kamar yayita tsalle nayi missing dinki sosae my love nima haka mijina kazo muje kaci abinci ta fata tareda jan hannunshi binta yayi kamar wani raqumi da akala wae tsayama Ina Abiey bacci yake ta fada a ta kaece
Saeda sukaci suka koshi sannn suka yada zango a π ban ankaraba naji anyi ball dani garam ya rufe kofar ta window ya leko saenaga ta ina zaki shigo mana daki ae yayimin gwaloπ«π€ͺ jiki a mace na tattara yan komatsaena nayi waje.
πππππ
Gidan yari kam ya zamarwa hafsy ishara dan taga rayuwa iri iri bayan ta zauna dame kisan kae din nan an chanza mata daki inda aka kaeta wani dakin shi kuma nayan less ne daga nan aka kaeta dakin yan secret taga rayuwa ba kadan ba dan har farautar ranta suka dingayi da sukaga bazasuyi nasara ba suke dukanta kullum babu ranar banza ta shiga hankalinta kuma tayi nadama mara amfani yanzu babban burinta shine ta futa ta koma kauyen su dan tagaji da wannn rayuwar kuma yanzu aure takeso tayi amma duk sanda ta tuna da cutar dake jikinta sae tayi kuka kamar ranta zae futa saura wata 5 ta futa daga gidan yari Allah Allah take watan ya cika taje taga kakanta.
πππππ
Sosae take kuka svd ba kaene kakeshan wahalar ba dole kace haka nikam gaskia saina zubar da cikin nan duka!! Watan Abiey 5 pa kuma ace inada wani cikin yanzu ni kam bazan iyaba futa yayi daga gidan ya gyaleta gidan zarah yaje ya fada mata har gida tazo tayi mata nasiha sannn ta dauki yayen Abiey svd harya fara ramewa yaron
Watan cikin 9 aka kumayi mata CS shima namiji ne me kamada babanshi sunan Abba akasa mishi Mahmoud ana kiranshi da Abis anyi mata planing din 7 years gashi yaran sae girma suke masha Allah
Shekarar Abiey Daya da wata 4 shikuma Abis Shekarar shi daya amma kamar duka shekarunsu daya because Abis nada garin jiki
Anyi bikin Nasir da Nafisa harta haihu diyarta mace kyakkyawa da ita masha Allah sunan Aysha akasa mata amma Alisha akece mata sosae yarinyar tasaba dasu dan bata yarda da iyayenta indae tana wajensu hakan yasa suka barmusu ita Nafisa nada wani cikin tsoho haihuwa ko yau ko gobe
Alisha ta shiga ran Abiey sosae dan baya bari kowa ya ta6ata indae yana nan shikam Abis yace Ammi Nafisa kenn zata haifa mishi matarsa
Ranar wata lahadi Nafisa ta santalo yarta masha Allah Fatima Ahlam suna cikin farin ciki da son junan su Allah dae yaqara hada kanku yarana abin Abbu suka fada a tare
Hannunta ya kama yana shafa cikinta ya kamata a sama mana new babyy ture hannunshi tayi tana daria har yanzu an girma baasan an girma ba nipa babyy ne kin manta babyy pa kike cemin kinga kuwa da saurana ya fada yana kashe mata ido dayaπ
Abbu Ummu kuzo kuga abinda Abis yakeyiwa Ahlam har rige rige suke me zasu ganiii............
Wasshhhh Allah na idona kae Allah ka yayemin wannn ciwan idon dama duk masu fama da wani ciwan Ameen
Bari na huta haka mu hadu a last page bye
Comments and share plsππ»
Taku harkullum KHAIRIYYAAHH BAKARRYY
(PINKIE)
+2347088392884
ππππ»♀️A SANADIN TIKTOK ππ»♀️ππ
Story and writing
KHAIRIYYAAHH BAKARRYY (PINKIE)
*King and Queen Writing Chamber*
Gajeran labari
Gargadiπ€π» banyarda wani/wata yayi amfani da littafina ko wani 6angare daga cikin shi ba tareda izinina ba ‘yan satar fasaha kuma gareku banyarda ayimin copy dinshi ba dan mallaki nane ni kadae duk wanda yayi ban yafeba
Bismillahirrahman Raheem
Last page
π
Ώ️61-70✍π»
Ta fito amma abinda ya bata mamaki shine ganin mallam da tayi wato kakanta sosae taji son tsohon ya kamata tayita kuka a ranar lallashinta mallam yayi suka samu mota sukayi kauye
Sosae mallam yake kulawa da ita har sallah ya koya mata karatu kam batada abinyi sae shi kullum cikin kuka take da dana sanin abinda ta aikata a bayan sosae mallam yayi mata nasiha akan tubanta Allah yanason mae tuba kuma godiya ya kamata tayi masa dan wasu da da dama suna cikin aikata sa6on suke mutuwa ita Allah yanasonta da rahma tunda harya nuna mata hanyar gaskia
Kullum cikin yiwa iyayenta addu’ah take da sadaka dan ladan ya isa kabarinsu
Mallam ne yayi mata maganar aure da sauri ta kalle shi hmm hafsatu nasan tunanin da kikeyi shima yanada irin cutarki ne abaya shima yayi rayuwa irin wadda kikayi amma yanzu shima ya tuba dalibi nane sunanshi musa zaezo anjima ku zanta tashi ki shiga ciki Allah yayi miki albarka Ameen mallam ta amsa tana shiga cikin gidan
Hmm rayuwa kenn wato koka tuba sae Allah ya taimakeka kake samun me nutsuwa hmm Allah ya bamu zaman lapia. Nace Ameen
Anyi daurin aure kamar yanda addini ya tanadar sae dae muyi fatan Allah ya basu zaman lapia
πππππ
Abis ne ya daura Ahlam akan TB wae Abiey ya kare mata bata gani sosae daria sukayi me isarsu Ummu harda kwanciya
Wae dariyarme akeyi a gidan nan munata sallama amma baajimu ba ya fada yana kallon kowa Abiey ne ya basu lavarin abinda ya faru daria sukayi sosae suma aka lokacin sallah yayi mazan suka wuce masjid matan kuma sukayi tasu bayan sun dawo a dining suka yada zango sukayi dinner π₯ bayan zungama ne aka shiga hirar yaushe gamo.
After 25 years
Kuka takeyi sosae kamar zata shide Allah ummu idan yarinyar nan ta sake kula wani saena mata dukan tsiya dan ma ta rainamin hankali zanyi maganinta Abiey ne yaketa bala’i dan yaga Alisha dawani baesan ya rufe ido sae fada yakeyi iya karfinshi daria yaji ankwashe da ita da sauri ya bude ido suwa zae gani Mommyy Mami Abba Daddy Abbu Ammi Affa Abis da kuma Ahlam sosae suke masa daria dan sunkama ganeshi chaff kishi ne yakeyi kunya ce ta kamashi Mommyy ce ta kamashi zonan me gidan yanzu kae akan wannn abar kakeyin kishi kaeda kake dani shagwa6e fuska yayi kepa kin tsufa yanzu ita ake yayi kowa sae daya dara
Abba ne yayi gyaran murya alhamdulillerh Allah mungode maka daka nuna mana wannn rana Allah yayiwa wannn families Allah duk suka amsa da Ameen
Sannn babban maka sudin taron shine akan yaran nan inaso kobayan raena a hadasu aure Abiey da Alisha Abis da Ahlam sannn kuma daga yanzu banaso in sake ganin sun tsaya da kowa
In sha Allah Abba Daddy ne ya rufe da addu’ah.
πππππ
Hafsa kina ina gani me gida sannu da zuwa tabarma ta shimfida masa tadebo masa ruwa a randa me sanyi dumamen tuwo ta kawo masa saedaya gamaci sannn yace ina yaran nan sukene banji motsin suba sunjie gidan mallam ae wae achan zasu kwana to ae shikenn tashi yayi ya tafi masjid lokacin sallah yayi itama alwala tayi ta tada sallah.
Tammat bi hamdullah
Inaso na danyi tsokaci akan wannn littafin magana ta farko
Akan sallah sallah itace babbar ibadah acikin musulunci shine ban bancin musulumi da kafiri ko ranar lahira itace abu na farko da zaa fara dubawa acikin littafin mu idan tayi kyau sauran aikin namu ma yayi kyau mu tsaida sallah sannn kuma akwae wanda basayin sallah akan lokaci idan sunayin wani abun sukaji anyi kiran sallah basa iya ajiyewa suje ga kiran da ubangiji yake musu ba sae sun gama abinda yake gabansu hakan ba dae dae bane dan babu azuri akan hakan Allah yasa mufi karfin zukatanmu.
Iyaye ba abun wasa bane bae kamata ace yarinya ko yaro yana raina ko musu da iyayenshi ba musamman uwa itace tayi dawainiya damu tun muna ciki ta haifemu bata huta ba idan munyi kuka ta shiga damuwa idan bamuda lapia saeta fimu shiga wani halin amma mun girma bamuda abokin gaba ko wanda muka raina sae wannn baewar Allah din wadda ta sadaukar da farin cikinta domin mu Allah ya bamu ikon kyautatawa iyayenmu Ameen.
Sae zalinci Allah baya zalinci kuma baya barin azzalumi mu tsarkake zukatanmu karmu nufi kowa da sharri sae Allah ya karemu daga azzalumae da masu neman mu da sharri Allah yasa mu dace Ameen
Anan na kawo karshen wannn littafin A Sanadin TikTok Allah ya bamu ikon amfani da darasin dake ciki Allah yasa mufi karfin zuciyar mu Ameen saemun hadu a next book dina me suna BAK’AR RANA in sha Allah
Comments and share pls
Taku harkullum KHAIRIYYAAHH BAKARRYY(PINKIE)
+2347088392884
Subhanakallahumma wabi hamdikah nashhadu Allah ilahah illah anta nastagfiruka wanatubu ilaikaππ»
0 Comments